Showing 1 words to 3000 words out of 39152 words
*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha.
*Wannan shafin nakine 'Yar uwata Hafsat Elham, Allah yabar mana zumuncinmu, Yakuma albarkaci rayuwarki Ameen*
01
Hafsat!! Malamin nasu ya daka mata tsawa,d'aukacin yaran class d'in sun tsorata da wannan tsawar amma Hafsat ko'a jikinta a zahiri ma ko d'ago kanta batayi ta Kalli malamin ba, zuwa yayi cikin azama ya daki teburin da take Kai yace cikin fusata "How dare you! Are u stupid? " a hankali ta miqe daga zaman datake sannan cikin ko inkula tace "No sir I'm not" cikin qaraji yace "what!! Repeat what u just said now" cikeda kwanciyar hankali ba alamun tsoro tattare da ita tace " I just say I'm not sir" murmushin mugunta yayi dama yana jiranta a cike yake da ita fam
"Hafsat look into my eyes and repeat after me OK? "batayi magana ba ya kuma cewa
"oya say that you,you are stupid " wani shu'umin murmushi tayi sannan tace "You! You are stupid!!!! " zaro idonshi yayi sabida ba haka yake tsammanin zatace ba yace
" How dare you, are u in ur senses? " ita d'inma cikeda raini tace tana Zare ido Kamar yanda yayi tace " How dare you? Are you in ur senses?? " cikin azama ya sanya qaton hannunshi irinna yarbawa ya zabga mata lafiyayyan Mari seda taga jiri dafe wurin tayi ta saka kuka aikam malamin se wani cicika yakeyi irin ya hasala, hanyar fita waje tayi Kai tsaye office na principal nasu ta nufa Tanata uban kuka irinna shagwab'abb'un yarannan marasa ta ido, PC na ganinta ya miqe tsaye ya sani idan ba'ayi sa'a ba lokacin korar wani malamin ne yazo
"Hafsat lapiya me kikewa kuka haka? Meya sameki?" tana kukan ta kwashe qarya da gaskiya ta sanar masa, a haka aka tarar wa malamin sanda ya bata haquri sannan tace ta yadda bazata fad'awa daddyn tab'a, domin kuwa mahaifin nata shine mamallakin makarantar kuma itadin yar gatace gaba da baya ba Wanda ya isa ya taba Hafsat Poojah ya zauna lapiya mahaifinta be had'a kowa da itaba kasancewar ita k'adaice 'ya d'aya tilo da Allah ya bashi se kuwa yayan ta shammaz......
Class dinsu ta koma,dashigarta mazan class d'in suka dauki ihu,pooja!pooja!pooja!....wani Yaro dan masu ji da naira nalura yana dai daga cikin taqadarun students d'in makarantar yace,
Poojah babe ina fatan kinsa an lallasa wannan malamin?,
Abokinsa Wanda duk halinsu d'aya yace, Ni bama Sonai takaishi Kara ba,
Sonayi itama ta kifa masa Mari ya za'ayi tana yar me makaranta ya Mareta?,
Haushi taji yadda yanuna rashin gamsuwarsa da abinda tayi, wato ma bata burgeshi ba harara ta kwadamai kafin tace,
Banga damar ramawa bane,kaima kasan inkifa masa Marin yana dai daga cikin kananun ayyukana kamar yadda Kaima baka wuce in zabga MA Marin ba mtswww,
Baki asake yake kallonta se Abokinsa wizkid Yasoma ihun kiran sunanta,poojah!poojah!kina burgeni wallahi,
Cikin halinta na basarwa tace,
Dalla kuyi mana shiru ninagaji da wannan banzan hayaniyar naku,
Sum sum mata da mazan dake a tsaye suka Nemi mazaunin su batareda sunyi magana ba,
Wannan shine kadai aikin hafsat a makaranta taga damar submitting plane sheet lokacin exam kuma duk teacher Dinda yai failing dinta ze rasaa aikinsa ne bakuma Dan wai batasan mezata rubutaba sedan kawai ta nuna isa da tantagaryar shagwab ganin makarantar ta mahaifinta ne kuma baya ganin laifin ta aduk shirmen dazatayi,
1:50pm aka Tashe su tun daga sama ta leqo bata hango motar driver dinta ba, tafiya take bata kallon gabanta hartagama saukowa daga stairs d'in be k'araso ba,tafiya take Tana tunanin hukuncin dazatayi wa Ayuba yau,tana isa gate segashi yazo dasauri yazo ya Karbijakarta ya sa bayan motar itama yabude mata tashiga Se cin magani take,
Wallahi tallahi tayarce tayi faci dan Allah kiyi hakuri karkisa narasa hanyar cin abinci na,ayuba yasoma bata hakuri bayan yashiga motar,
Wannan shine babban kuskuren daka tafka banaso kadamu kunnuwana dawannan kalmar tahakuri Dan bawai zan yibane,
Gumi yake ta ko'ina,shine gatan kannen sa da mahaifiyarsu,wannan aikin dayake ciyarda su dashi,
Dagudu ta k'arasa wurin daddy ta tana kuka,
Lafiya dai Hafsat waye yataba min ke?,
Daddy wannan ayuban ne yabarni har Nazo gate dakafa,
Subhuhanalillahi, Ayuba dama Kai ya akayi haka?,
Wallahi ranka yadade tayarce tayi faci kuyi hakuri,
Sautin kukanta Takara,
Tsaya Hafsat me kikeso ayi yanzu?
Daddy ni akoreshi banasonshi,
Kudubi girman Allah kiyi hakuri insha Allah wannan shine nakarshe bazan kuma irin hakaba wannan aikin shine hanyar abincina,
Furr taki saurarensa daddy yace to za akawo miki sabo kaikuma Ayuba zaka ringa fita da hajiya dakumawanke motocin gidan, godiya yayi yajuya yana godewa uban giji daya sanya dukda kasancewar hafsat batada m mahaifanta nagartattun mutanene dasuka san girman dan adam matuka....
A tsakiyar parlor ta fara wurgi da jakarta da sannan tacire takalminta a hanyar dazata sadata da matattakalar benen gidan komai a inda ta samu take wurgi dashi gata da tsafta amma bata farin cikin ganin masu aikin gidan suna hutawa,mero me aiki ce ta sameta a daki tace bayan ta saka kayanta da tabi ta tsinto akasa cikin laundry basket ta ajiye school ba da sandal a ma'ajiyarsu " kulelen daddy yau me kike sha'awar ci??" ko kallonta batayi hakan ya tabbatar wa mero bawai kulatan zatayi ba sabida indai da sabo toko ta saba da rashin kunyar Hafsat,wannan ya sanya ta juya kawai taje ta hado mata snacks da apple and avocado smoothie ta kawo mata a saman table na coffee chairs dake a parlor dinta ta ajiye mata sannan ta kalleta tana zaune tana danna remote domin canja channel tace da ita " Hafsat ga favorite dinki nan na hado miki" a wulaknce ta kalli kayan tace
"Grill fish and chips,plus sugarcaine and apple juice nakeso ni kenan kullum fulawa so kikeyi na zama bom bom adena yayi na" shiru mero tayi se can tace " ki daure ki dan rage yunwa da wannan sena hado miki wancan din" harara ta wurga mata "nace baran ciba ana dolene?" kwashe kayan mero tayi ta juya tana girgiza kai a hakan ma wai meron kadai ke shiri da ita acikin yan aikin,kuma itace abokiyar hiranta sabida tana mata gatana, itadin ta kasance abokiyar wasan mahaifiyanta ta wurin uwa auren wuri aka mata a qauye Allah yawa mjjin rasuwa itadin bazata wuce shekaru ashirin ba aduniya sedai akwai kaifin hankali,kusan shekararta goma agidan tun hafsat na yar shekaru hudu,sun shaqu sosai da ita.
Koda ta dawo daga school mamakin mutanen data gani birjik a kofar gidan tasomayi mafiya hawa daga cikinsu 'yan gidena ma'ana y'an uwansune,bata wani kawo komai arantaba tazo zata wuce su,abba haris ta gani da gudu ta ruga ta fad'a jikinsa tace cikeda shagwab'a
"Abba haris zanbika gun ummi" murmushi yayi yace "kulele ai bakui hutu ba,ina saura kwana bakwai kuyi hutu? Bazan ma turo driver ba da kaina zanzo na d'aukeki" murmushin itama tayi sannan tace
"To abba zaka sauya mun waya? Anfa dena yayin tawa?"
"Lele ai dole na sauya miki yanzu blackberry bold 4 zan siya miki,an dena yayi curve dinnan" tsalle ta kuma ta fada jikinnshi sannan tayi ciki aguje,tab'e baki shammaz dake tsaye yayi wanda akanshi akayi wannan taron murnar dawowanshi dayayi shekaru kusan 8 baya kasar yace aranshi "kaddai har yanzu su daddy basu dena shagwab'a hafsat ba,inko hakane da matsala a tarbiyar yarinyar,ko yanzu ya fahimci ba wanda ta gayar a duk yawan mutanen dake wurin.....A parlor ma ba wanda tawa magana se Aunty surayyah wacce ita kadaice take masifar tsoro indai har tana wuri tofa iskancin hafsat qasa qasa yakeyi,kallon ta surayya tayi tace
" ke Hafsat ni kadai kika gani anan sauran fa? ,d'an turo baki tayi sannan ta juya ta kalli jama'ar parlor din a wahalce tamkar wacce zatayi kuka tace "Ina wuninku" amsawa sukayi daganan suma saka mata dariya ganin irin shirmen datakeyi mafiya akasarinsu kuwa sun dauki hakan datayi amatsayin kuruciya,wasunsu kuwa sunsani sarai iskancine sundai kama bakinsu ne sabida suna samun alkhairi a wurin uwarta Haj Nasara wacce bata had'a kowa da ita ba,tana sharar k'wallah tayi sama a hanya ta hadu da mairo kalllanta tayi tace "Kulele momy ya akai?? Waye ya tabamun babbar 'yata" wurgi tayi da jakar ta tace
"Bayan Aunty surayyane tace wai dole sena gayar da mutane bayan kuma arayuwa ni natsani gayar da kowa ma wlhy" rungu mota tayi jikinta "Haba babyn dady kiyi hakuri kinji ba wanda ze kuma tilastaki gayar da mutane amma fa ki sani ita gaisuwar wajibice idan ba hakaba yanzu zakiji ana cewa bakida kirki" wucewa kurin tayi bayan ga qwace jikinta ba tare da tayi magana ba,bayan like an hour se gatanan tafito sanye da vest da gajeren wando iya gwiwa tana tsotsa alawar lollipop,mutane sund'an ragu se yan uwa na dole batare data kalli kowa ba tayi dining serving warmers tagani tuma tuma awurin tsayawa tayi daga inda take ta kwallah ihun kiran mero
"mero!!" wanda ya mayarda hankalin akasarin mutanen dake parlor akanta,da sauri mero tazo tace "Lele ya akai?" zumburo baki tayi tace "Dayake kinfison mutanen nan dani shine kika barni da yunwa tun dawona nake jiran abincina,ni ki zubamun to" kallon ta mero tayi tace "Dady ne ya sakani aiki kiyi hakuri mezan saka miki?" duk abinnan dasuke a gaban idon shammaz ne, ko kallonta batayi ba ta saka alawar datakesha a baki ta hau tsotsa sannan ta hard'e hannayenta gu daya,ganin haka mero ta gano rigima takeji yasanya ta dauki plate ta saka mata snacks da papaer chicken ta juyo ta miqa mata, karb'a tayi sannan ta kifar da abincin a wurin cikeda raini da shagwaba tace "ni wannan nace dake ina so? Shreded chicken zanci" batayi auneba taji saukar lapiyayyen mari wanda ya kusan zautar da ita,dafe wurin tayi ta saka kuka kowa a parlor din ya taso ana baiwa Shammaz haquri ita kuwa mero tazo da sauri ta riqe hafsat tana rarrashinta,wani kallo shammaz ya wurgawa mero, cikin fada ya furta " Maryam zan mareki wlhy kema,maza ki saketa ta clearing wannan mess datayi" jikinta har rawa yakeyi ta duqa ta soma tattare wurin tana sharar k'wallah tana gamawa yace " se kinci wannan din yar rainin hankali da zaki wani zo tana tambayarki kina iya shege sannan yanzu an zuba miki ki kifar an gaya miki a qasa ake haqowa" juyawa tayi zata haura sama da plate a hannu tana kuka yace cikin daga murya
"Maza zo nan zaki zauna ki cinyeshi a gabana" dawowa tayi ta janyo kujerar dining daya tana kuka tanaci harta cinye tatas,momy dai batace komai ba amma harga Allah bataji dadin abinda shammaz yayiwa Hafsat ba agaban mutane,kumama tsabar rashin tunani daga dawowarshi duk wanda yaga yayiwa qanwarshi wannan abin aiseyaga tamkar baya san tane..........
Mom Nuaiym ce
[7:07PM, 2/10/2018] +234 808 677 7945: *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin. wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*
02
Hawa saman tayi bayan ta kammalawa cinyewa taje rufe kofar d'akinta tasaka wani uban kuka tanata faman shura qafa,duk abinda ta samu seta fasa ita adole zuciya,su momy sunzo juyin duniya sunyi akan ta bude kofar d'akin amma fir taqi se dad'a sautin kukanta takeyi Aunty surayya ma datazo tayita fadan amma yau ko gezau,surayyace takira Yaa shammaz yazo bakin k'ofar yace cikin daga murya
"Hafsat Allah idan har kika kuskura na sameki a d'akin batare da kin budeshiba ranki ne zeyi matukar b'aci anan" cikeda fargaba ta bude kofar d'akin ta qura masa ido jan hannunta yayi sukayi waje sannan yakaita b'angarensa,zaunar da ita yayi suna fuskantar juna yace
"ke har yanzu Hafsat girma da hankali basu wadace kiba? Mero sa'an kice sannan yanzu wannan uban borin dakikeyi a daki ke kadai wa kikewa shi? Sarai kinsan halina tsaf zan zaneki karkiga kamar yanzu na dawo zaneki zanyi sosai,kuma idan na kuma ganin kina wannan kukan ko hawaye daya na gani a idonki sena zaneki yanzumma kece da kanki zaki gyara barnar dakikayi a dakinki,sakaryar yarinya kawa,kuma daga yau duk bayan kwana biyu kece zaki riqa zuwa kina gyaramun wannan bangaren nawa,ki share ki goge da komai kina jina?" da sauri ta daga masa kai a ranta tace "Ina kammala exam zan gudu gidan Abba wlhy bazan zauna wannan mugun ya kashe niba" a fili kuma godiya ta masa sannan ta fita daga dakin.....
*Washe gari*
Yaa shaam na zaune a a daya daga cikin gujerun da aka qawata ht dake farfajiyan gidan dasu yana karatun news paper hannunsa daya na riqe da cup na hot meantleaf coffee yana kurba a hankali,ganin Hafsat ta fito ya sanya da sauri kuma cikeda mamaki ya mayarda dubanshi zuwaga wrist warch dake hannunshi,dagowa ya kumayi yaga driver yazo ya bude mata tashiga gidan baya ta zauna,driver din ya kwallawa kira yazo ya da sauri ya durqusa yana jiran cewar sa,kamar baya sanyin magana yace
" Ina zakujene k'arfe tara da rabi na safe?" kanshi a qasa yace "Yallab'ai Haj qarama zankai makaranta?" Haj k'arama ya nanata a ransa sannan a sarari yace
"yaushe yakamata ace kana fitowa kaita makaranta?"
"yallab'ai dama da safene kullum k'arfe bakwai anan gidan yakemun,hajiyar ne bata fitowa se sanda taga dama" cikin mamaki yace "Ita hafsat ne setaga daman zuwa skul zataje? Maza jekamun kiranta" koda friver ya sanar mata tana fitowa mota kuka ta saka ta kwasa ciki aguje,miqewa shima yayi a fusace yabi bayanta,daddy da mommy na zaune a dining taruga ta fada jikin dady,kan wani cikinsu yayi magana sega yaa shaam ya shigo a fusace,momy ce tayi saurin magana
"shaam lapiyanka kuwa meya sameka kaida qanwarka haka taketa kuka" daddy ya kalla yace "Amma daddy sabida Allah kuna kallo se yanzu hafsat zataje makaranta qarfe goma saura fa?? Wannan wane irin tarbiya aka mata ba kwab'a ba komai ace yarinya se sanda taga dama zataje skul wannan ai ba soyayya aciki" shiru daddy yayi saboda yasan gaskia shaam ya fada momy ce tace cikin quluwa "Kaga shammaz nafa kula tun dawowarka jiyannan ka takura yarinyarnan,hafsat baccin safe ne da ita kamar me ya kakeso muyi? " kallon momy yayi rai a b'ace yace "wannan ai rashin sone idan naga zatayi rashin hankali na barta,wannan ba takura aciki tsantsar soyayya ce nake mata,kuma ita jakar inace bata ma tsoron duka irin wannan mugun lattin ai dole setasha duka kullum"
"makarantar mahaifinku take zuwa,se abinda taga dama takeyi ba wanda yake takura ta wlhy" tsaki yaja yace "wlhy ba wanda ya isa ya b'atamun qanwa ina numfashi haba mana daddy ni haka kayimun? Ni bansan wannan wane irinn qata kuke nunawa hafsat ba sekace a kanta kuka fara ganin 'ya'ya wlhy ni idan suka gama wannan jlce din sauya mata skul zanyi" momy zatayi magana daddy ya hanata "duk yanda kayi daidai ne shammaz na tsame hannuna a lamuran hafsat tunda magajinta yazo haj kema naki idone lallai idan kina taka masa birki zakija masa raini a gunta kuma kinsan ya isa da ita sannan kuma ke karan kanki nasha sanar miki zaki ruguza rayuwar hafsat ne idan kina biye mata,yarinyar nan tanada kokari sosai zama mu iya cewa gifted idan bakya nuna mata muhimmancin karatun watsarwa zatayi" shiru momy tayi badan ranta yaso hakan ba daganan daddy ya daga hafsat ya bar gidan gaba daya,a gaba shaam ya saka hafsat har wurin mota yayi kiran driver din yace
"Daga yau ita zata riqa bude mota da kanta tashiga sannan karna kuma jin kace mata wata hajiya karama,kuma ita zata riqa gayar dakai ba wai ka gaidata ba,yarinya sa'ar y'arka zaka zauna kana wa biyayyah kuma kullum idan tawuce 7/30 batazo kun wuce skul d'in ba kazo ka sanarmu" tana kuka tawuce suka je.......
*Bayan wata daya*
Tun bayan da yaa shaam ya dawo gaba daya rayuwar poojah ta sauya ko a makaranta sun fahimci hakan,sabida tazamo so quiet a rayuwarta ta tsani yaa shaam kuma masifar tsoransa takeji matuqa,zuwa yanzu duk wani abu dazesa yamata fad'a tofa gudunsa takeyi kuma idan tana parlor d'n k'asa ya shigo yanzu zata gudu shi kanshi ya kula da hakan kuma harga Allah baya san rashin walwalarta a kusa dashi danya kula momy ma ta sauya masa ba kamar daba gani takeyi tamkar yana cutar mata da yarinya......yauma kamar kullum hafsat na zaune a parlor tana kallon wani catoon series na barbie yaa shaam ya shigo ko kallonta beyiba ya zauna tana ganin haka ta miqe zata gudu yace yana danna wayar hannunshi " Hafsat zo" kawai seta soma hawaye dawowa tayi ta tsuguna a gabanshi tana sharar k'wallah,kan yayi magana phone nashi ya soma ringing d'agawa yayi ya kurawa hafsat data sadda kanta ido,mamaki yakeyi me aka mata take wannan hawayen ,cikin sanyin murya yace
"Haleema na ya akayi?" a d'aya bangaren seji yayi tana kukan shagwab'a "Haba mana boo me kwana biyu kana cikin garinnan amma sam bakazo ka ganni ba Allah yau idan har bakazoba ni gobe da sassafe zan wuce wana sokoto kuma Allah bazan dawoba sekaje da kanka" k'arayin kasa da murya yayi
"Haba leemah dear,zanzo yau dinnan inshaa Allah kuma ma yaune alqawarin new phone nakifa nama isa naqi zuwa,u expect me anything 7:pm inshaa Allah" daga nan sukayi sallama akan se yazo kallon hafsat yakumayi yace
"Lele zoki zauna kusa dani" da mamaki ta d'ago ta kalleshi amma bata taso d'inba sanda yakuma cewa "zomana ki zauna anan,magana zamuyi" yafada yana nuna kusa dashi d'in, jiki a mace tazo ta zauna kusa dashi ya kalleta yace " haba lelen dady kukan kuma na menene eye? Ba abinda zan miki,nifa yayan kine uwa daya uba daya,me zaisa kina tsoro na har haka daga yauma mun zama best friends kinji" murmushi tayi tace "To na gode" a sanyaye
"Dama zancen school ne,zakice premier kuma interview din gobe ne,ss1 zakiyi interview nasu" girgiza masa kai kurun tayi sannan tace "Zanje nayi