Showing 1 words to 3000 words out of 4355 words

Chapter 1 - KUNDIN TSATSUBA

30 Nov 2024

1251

KUNDIN TSATSUBA
Rubuta Labari
Abdul’aziz Sani Madakin Gini
Shekarar Rubutu
2008
Ɗaukar Nauyi
Mansur Usman Sufi
08137237071




Shekara goma sha, ba don siffar gafobin jikina ha. Yana da baiwa ta rashın gashi, da yanayin tsufa. Kuma har yanzu ya kasance ƙaƙƙarfa, ga ƙoshin lafiya. A tarihin rayuwarsa, bai taɓa rashin laliya ba ko da kuwa ciwon kai
Wata rana da sassafe Gimbiya Sima ta aika aka kirawo ƙaddaru, Da yake ba a yi masa iso gareta, sai kawai ya wuce izuwa cikin ƙuryar turakarta, inda ya iske ta a cikin bahon wanka mai cike da kumfar sabulu, kayangi na cuɗa ta
Ko da ya ganta a cikin wannan hali, sai ya sunkuiya da kansa kas cikin sauri ya ce "Kaicona da cin amanar gidan nan, lallai ba zan iya kallon tsiraiciinki ba. Ranki ya daɗe ki gafarce ni, ban san zan riske ki a wannan hali ba na shigo."
Ko da jin haka, sai Sima tayi murmushi ga Ƙaddaru ta ce “ka yi sani cewa, ban kirawo ka nan ba sai domin idanunka su ga kyakkyawar surar jikina guda daya. Don haka ina umartar ka ɗaga kai ka ƙare mini kallo daga sama har ƙasa, sannan daga bisani zan yi maka wata tambaya.
Na rantse da kabarin mahaifina, idan ka ƙi bin umarni na zan kashe kaina, kuma na ɗora alhakin raina akanka. Ka yi sani cewa tuni na gama shirya komai, tare da wadannan kuyangi
Sima na gama faɗın haka suka, sai Kaddaru ya ga kuyangi su goma sha ɗaya sun firfito daga inda aka ɓuya sun rufe ƙofofin fita daga wannan taraka sun bar guda ɗaya jal. Cikin tsananin razana, Ƙaddaru ya ɗago kai dubi Gimbiya Sima jikinsa na karkarwa.
A wanan lokacin ta mike tsaye daga cikin bahon wanka, kumfar sabulu na manne a jikinta. Take wata kuyanga tasa wani kyakkyawan farin kyalle ta goge surar jikin Sima ta bayyana ƙarar tumbur babu wani hijabi.
Gashin kanta bakl sidik mai ƙyalli-ƙyalli ya zuba har Kasan mararta, Cikinta a shafe yake kamar ba ta taɓa cin komai ba. Ƙugunta kuwa a tsuke yake, daga baya ya fashe yai doro kamar a ɗora kofin lemo akai ya zauna. Fatar jikinta ja ce subul-sumul, ko digon kwarzane guda babu a ko ina. Tana da siriri wuya kamar na barewa. Sima doguwa ce mai kaurin jiki. Tana da manyan cinyoyi, da zara- Zaran yan yatsun hannu da ƙafa. Batun ido, hanci, da baki kuwa, kamar kwararren mai zane ne ya zana su bisa takarda dai-dai yadda take bukata. Idan tayi murmushi, mutum na iya jin kamar an zare masa cutar ajali wadda aka sha fama shekara da shekaru.
Ya yin da waziri Ƙaddaru yayi arba da wannan kyakkyawar sura, sai ya ja dogon gwauron numfashi ya ce "Ranki ya dade, na rantse da girman abin bautarmu, ban taɓa ganin wani abu mai kyau ba a doron ƙasa tamkar ki ba. Inda na san haka kike, da tuni na mutu wajen neman kyakkyawan mijin da ya dace da ke, domin sai ne a kawo miki wanda babu mai kyawunsa a duniya."
Ko da jin wannan lafazi, sai Sima ta kyalkyale da dariya ta ce "Ka fara hawa kan turbar da nake so. Ya Ƙaddaru kayi sani cewa, a rayuwata ta duniya babu abin da nake so face tafiye-tafiye, don ganin abubuwan al'ajabi cikin duniya. Ka sani cewa ina da kyau, mulki
babu abin da na nema na rasa, face abokin rayuwa da ya dace da ni.
To ka sanı, ni Sima na rantse da darajar tsafin da na gada a wajen iyaye da kakanni, ba zan auri wani da namiji ba face wanda ya fi ni kyau, mulki da dukiya. Na yi bincike a cikin madubin tsafina na gano cewa akwai wani littafi da ake kira KUNDIN TSATSUBA, shi wannan littafi ya Kunshi manyan abubuwan al’ajabi guda dubu. Lallai idan na mallake shi, na sami ikon karanta shi, zan yi ɗaukakar da babu wani mahaluki da ya taba yi, walau yanzu, ko da, ko nan gaba. Na yi iya ƙoƙarina akan na gano inda wannan littafi yake na kasa. Ya kai Ƙaddaru ka yi sani cewa, bincike na ya nuna mini cewa ba zan taɓa haduwa da namijin da zai dace da ni ba, har sai na karanta wani shafi daga cikin shafukan Kundin Tsatsuba. Yanzu ina neman shawara gareka?"
Lokacin da Gimbiya Sima ta zo nan a zancenta, sat hankalin Ƙaddaru ya dugunzuma ya kasa cewa komai, ya yi shiru yana tunani. Wata kuyanga ta zo da wani babban shuɗin mayafi ta lulluɓawa Sima. Sima ta matsa kusa da Kaddaru ta hai bannu don dafa kafaɗunsa, sai yai sauri ya matsa baya.
Cikin firgici ta dube shi ta ce "Lafiya, me ya faru gareka
Kaddaru ya numfasa ya ce "Ranki ya daɗe, ai ina ishi ne a ce wannan hannun naki ya taɓa jikin wani da mijin da bai dace da ke ba. Na rantse da darajar gidan nan. a sani na tun daga ranar da mahaifiyarki ta haife ki kawo i yanzu namiji bai taɓa taɓa ki ba, har shi kansa mahaifinki kuwa. Kuma shi ne da kansa ya kafa dokar, duk namijın da ya taɓa jikinki a sare kansa, ba don komai ya sa wannan doka ba, sai don gain tsananin kyawunki.
Har yau wannan doka na aiki. kuma muna kiyayewa da ita."
Sima tayı murmushi ta ce "To na ji batunka, zauna ka saurari nawa.
Kaddaru ya zauna nesa kadan da ita, ya sunkui da kai kas, yana mai sauraro cikin biyayya.
"Abin da nake so da kai shi ne, ka kai ni wajen bokan da ya fi kowa ne boka isa a kasar nan, domin ya bincika mini inda Kundin Tsatsuba ya ke, kuma ya taimaka mini na isa wajen, har na mallake shi."
Yayin da Kaddaru ya ji haka, sai ya kara yin shira sawon yan dakiku kadan, sannan ya dago kai ya dubi Sima ya ce "Ranki ya dade, ai kaf kasar nan babu wanda zai iya wannan arki face Boka Sulbaini Ibn Barzuk. Ki yi saní cewa, a halin yanzu yana can jejin Falwas ya shiga kogon Ruhim don yin doguwar halwar tsafi ta kwana arba in da daya, saboda wata muhimmiyar bukata tasa. Ina jin tsoron mu je mu katse masa aiki, fushinsa ya tabbata a kaina."
Yayin da Gimbiya Sima ta ji haka, sai ta dakawa Kaddaru tsawa ta ce "Kai waziri! Ai sawun giwa ya take na rakumi. Bukatarsa ce a saman ta mu, ko kuwa ta mu ee a saman tasa? A she ba ni ke mulkin kasar Laharim ba? Duk mahalukin da ke zaune a wannan kasa yana Karkashin iko na ne Lallai Boka Sulbaini bawan mu ne, ubansa ma yayi baute a gıdan nan, dole ne ya bi umarninmu
"Haka ya ke ranki ya dade, zancenki dutse ne yafe ni."
Da jin haka, sai Gimbiya Sima tayi murmushi tace "Ya kai Kaddaru na umarce ka da ka hanzarta komawa gida don ka yi sallama da iyalanka, ka dawo nan bayan magariba. Yau din nan zamu tafi jejin Falwas don mu sadu da Boka Sulbaini."
Cikin biyayya Kaddaru yai sujjada ga Sima, ya ce "An gama, ranki ya dade."
Nan da nan ya fice daga wannan turaka, zuciyarsa cike da damuwa, domin bai san abin da ka iya faruwa ba ga rayuwarsa. Tabbas ya san cewa gimbiya ta tsokano al'amarin da ba zai taba yiwuwa ba, domin ya taba jin labarin Kundin Tsatsuba a wajen Boka Sulbaini, kuma ya gaya masa cewa babu wanda ya san inda ya ke bare a san wanda ke da mallakinsa.

*** ****
A can birnin Sin kuwa, cikin sulusainin dare Ruziyal na kwance cikin dakinsa yana barci, kawai sai ya farka a firgice sakamakon wata irin kara da ya ji mai kama da saukar aradu. Nan take ya mike zumbur ya ruga izuwa ga tagar dakin ya budeta da sauri. Tartsatsin hasken tsawa ne ya bugi fuskarsa, ya ja da baya a tsorace. Cikin karfin halli ya kara lekawa waje. Wannan karon bai ga tsawar ba, sai a can nesa kadan ya ke hango kyallinta. Ruziyal ya dubi sararin samaniya da kyau, ya ga babu ko alamar hadari, sai kirjinsa ya fara dakan uku-uku, don ya tabbatar ba lafiya ba. Take zuciyarsa ta fara wasuwasin shin an ya kuwa ba aljanin nan ba ne ya sake dawowa? Tabbas daga bangaren rijiyar nan mai dauke da Kundin Tsatsuba ya ke hango kyallin walkiyar.
Ba tare da bata lokaci ba Ruziyal ya dauki rigarsa ya sa, sannan ya bude kofa ya nufi tsakar gida gadan-gadan. Da zuwansa bakin rijiyar sai ya iske, an dauke wannan katon murin nata an ajiye shi a gefe guda. Cikin tsananin tsoro, Rumyal ya leka cikin rijiyar. Yin haka ke da wuya, ya ji wani abu yai fitar burgu ya doki kansa, sai ga Ruziyal yayi tsalle sama ya fado kasa tini! Ko da ya dago kai sama, sai yai arba da shi. Ba wani ba ne face dansa Jafar bisa wani aljani mai siffar tsuntsu, hannayensa biyu na rungume da littafin KUNDIN TSATSUBA a kirji.
Ko da suka yi arba, sai Jafar yai murmushi ga Ruziyal ya ce "Ya kai abbana, ai dama na gaya maka cewa sai na dauko wannan littafin, to ga shi kuwa lailai rana ba ta karya."
Cikin tsoro da matukar mamaki da damuwa, Ruziyal ya mike tsaye ya ce "Ya kai dana, ka rufa mini asiri, ka rufawa kanka, ka mayar da wannan littafi inda yake. Idan kuwa ka ki zaka tsokano masifar da ajali ya fita dadi.
Ko da jin haka, sai Jafar ya bushe da dariya yа се "Haba abbana, ka manta ko ni waye? Ni ne fa hatsabibi uban hatsabibai. Ni ne likitan kasada, mai binciko bala'i. Ni ne guguwar fitina, mai tada duniya tsaye. Ban so a zauna lafiya, kuma bana son a mutu. Ni da tsoro mun raba gari. Da a ba ni labari, gwara ni na bayar. Abba ka yi hakuri, ni kam na yi gaba, sai wata rana. Idan da rabon mu sake saduwa zan dawo gida, idan kuma babu shi kenan, wannan ga ni ya zamo na Karshe a tsakaninmu."
Jafar na gama fadın haka, ya zunguri cikin aljanin da kafafunsa, kawai sai aljanin ya kara yin sama ya luluka cikin gajimare. Shi kuwa Ruziyal sai ya daga kai sama yana mai kallonsa cikin tsananin fargaba da damuwa. Hawayen takaici ya zubo masa, ya ce a ransa "Duk da dai Jafar ne dana kadai a duniya, da shi da gwara babu, domin ga shi yanzu ya janyo mini masifar da babu wanda ya isa ya kare ni."
Tafiyar dakika sittin suka yi a sararin samaniya, suka iso wani jeji da ke bayan gari. Aljanin ya sauko kasa gaban wani kogon dutse. Saukarsu ke da wuya, Yelisa ta fito daga cikin kogon, ko da ta ga Kundin Tsatsuba a hannun Jafar, sai fuskarta ta cika da annuri, ta dubi wannan aljani da ya kawo Jafar ta ce "An gaisheka ya Gulzum, yau ka yi aiki mai girma."
Cikin fara'a ta karbi Kundin Tsatsuba ta dube shi da kyau duba na nutsuwa, sannan ta gyada kai ta ce "Barkanmu da samun wannan litttafi, yanzu sai ku biyo ni zuwa cikin kogon nan, don mu zauna mu yi binciken hanyar da za mu bi mu samo kubar da zata bude shi."
Tana gama fadin haka, ta juya ta nufi cikin kogon. Jafar da Gulzum suka bi ta a baya. Bayan 'yar gajeriyar tafiya ne a cikin kogon, suka iso wani fili mai fadin gaske wanda aka kawata shi da ginin lu'u lu'u. Wajen a haskake yake da wani irin haske, wanda ido bai isa ya ga ta inda ya samu ba. Wajen ya kasance wata 'yar karamar fada ce, amma babu komai a wajen face tarkacen kayan tsatsuba iri- iri. Babban abin da ya baiwa Jafar mamaki shi ne, farko sa'adda za su shiga cikin wannan kogo, yana ta lullube wajen kai ka ce fiye da shekaru arba in baya wata halitta ba ta shiga wajen ba. Ko da suka tunkari wajen, sai yanar ta yaye da kanta kamar labule, ta ba su wuri suka wuce, suna wucewa sai ta dawo ta rufe hanyar. Kai tsaye Yelisa ta wuce izawa gaban wani dogon tebur kuma faffada, na bakin karfe man dauke da kayan tarkacen tsafi iri-iri. Da zuwa sai Yelisa ta ajiye Kundin Tsatsuba bisa wannan tebur.
Jafar da Gulzum suka tsaya a bayan Yelisa, suna kallon abin da zai faru. Yelisa ta rufe idanunta, ta fora hannayenta biyu bisa wani dutsen tsafi ta fara surutai irin na tsafi. Bayan kamar dakika dari uku da ashirin, sai ga wata karamar guguwa ta bayyana akan wannan tebur tana katantanwa, jim kadan sai guguwar ta rikide ta zama wani siririn aljani wanda kaurin jikinsa bai wuce na silin kara ba, dogo ne zankalele kamar igiya, domin kansa na tabo dutsen saman kogon.
Yelisa ta dube shi ta ce "Ya kai Lubumaz, me ka sani dangane da wannan littafin? Ta yaya zamu iya samo kubar Muftahul Zarbil mu bude shi?"
Ko da jin wannan tambaya, sai Lubumaz ya kwalla ihu, yai tsalle ya runtuma da kasa, sannan ya dago kai cikin damuwa ya dubi Yelisa ya ce "Kaicona ya shugabata, ki yi sani cewa yau kin yi mini tambayar da nake tsoron amsawa. Ki yi sani cewa, duk duniya babu wata kuba da za ta iya bude Kundin Tsatsuba face Muftahul Zarbil. Ita kuwa Muftahul Zarbil kuba ce da aka gina daga sassa uku, ko wane sashi guda an tafi da shi izuwa bangon karshen duniya, bangaren gabas, kudu da arewa, yau saura kwana arba in cif sashin karshe ya isa bangon arewa. Ya shugabana ki yi sani cewa, babu wani mahaluki daga cikin aljanu ko bil'adama da ya isa ya je wadannan wurare a cikin lokaci kadan, face wani aljani guda daya da ake kira Murkahul Sabus.
Yanzu haka shi wannan aljani na can a tsare a eikin fadar sarki Lu'umanu na birnin Teheren, a cikin wani kurkuku da ke Karkashin
Kasa, a ɗaɗɗaure da sarkar tsafi a cikin wata battar Ƙarfe, ita kuma battar an sa ta a cikin akwatin bakin karfe, akwatin bakin karfen kuma an kulle shi da katon kwado, wanda ba shi da mabudi sai dai a sare shi da wata takobi da ake kira Sarjis. Ya shugabata, ita kuwa takobin Sarjis mallakar wani tsohon muridi ne da ke cikin karshen jejin Kalkim, jejın da saboda tsananin masifar wannan maridi da akewa lakabi da Magulus. Masana tarihi sun kiyasta shekarun Magulus da cewa a kalla za su kai dari uku da talatin da uku, duk shekara yana haihuwar 'ya'ya dubu uku. A halin yanzu jejin Kalkim a cike yake da iyalansa, ko ina su ne babu masaka tsinke. Duk duniya babu wanda ya san yadda za a yi a kiyaye dokokin shiga wannan jeji a fita lafiya, face mahaitinki Boka Jinshan. Saboda haka ina mai shawartarku da ki kai wannan bukata ga mahaifinki, shi kadai ne zai iya taimakawa ku mallaki aljani Markahul
Ko da Lubumaz ya zo nan a zancensa, sai Yelisa da Jafar suka kawo gwauron numtashi suka ajiye. Yelisa ta kara duban sa ta ce "Ya kai Lubamaz, ina son ka gaya mini dalilin da ya sa aka kulle aljani Markahul Sabus a cikin akwatin Karfe?"
Ko da jin wannan tambaya, sai Lubumaz ya nisa ya ce "Ya shugabata, kin yi mini tambayar labari mai tsawo, to amma zan yi kokari na gajaree miki labarin a cikin ko da sa'a biyar ne. Sai ku saurara don ku ji wani labari mai cike da al'ajabi.
"Fiye da shekaru goma sha biyar baya, sarkı Lu'umanu na birnin Teheren na da wata zabgegıyar
kyakkyawar mace da ake kira Fatisa, saboda tsananin kyanta ake zaton cewa ba mutum ba ce zalla. Wasu sun ce ruwa biyu ce, ana zaton ubanta mutum ne, uwarta aljana. Wasu kuma sun ce a'a, ubanta ne aljani, uwarta mutum. Har yau dai babu wanda ya tabbatar da gaskiyar al'amarin. Bayan sarki Lu'umanu ya auri Fatisa tsawon shekara hudu ba su sami haihuwa ba, sai al'amarin duniya suke cabe masa, domin ba shi da burin da ya fi na samun magaji. Yayın da tunani da bakin ciki su kai masa yawa, sai ya tara dukkanín bokayensa ya sanar da su halin da ya ke ciki, kuma ya nemi da su share masa hawaye. Gaba daya bokayen aka rasa wanda zai ce wani abu a wajen tsawon dan lokaci.

1
2
Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login