Showing 1 words to 3000 words out of 28630 words
ο»ΏCompiled by Princess Aysha Muhammad
[10/7, 17:10] βͺ+234 706 738 2588β¬: βπ·π·π·π·π·π·π·
'YAR AIKI.
0β£1β£
NA
ALAWIYYA ADO
π·π·π·π·π·π·π·π·.
Khalid ne jingine jikin kofar da zata sadashi da falon mahaifinsa, Alhaji Abbas, yakai kusan mintuna biyar yana buga kofar falon cikin nutsuwa, ganin ba Γ bude kofar ba yasa shi jingina da jikin kofar.
Aunty salma ce ta fito ta bude kofar falon, ganin khalid Γ tsaye jikin kofa shine yasata sakin fuska, cikin fara Γ ta bude masa kofar sosai yasa kai ya shiga.
"yarona sannu da zuwa yau kaine da wuri Haka ?
Ina kabar min surukata ?
Cikin fara Γ take masa wadan nan tambayoyin.
" ko zama banyi ba Aunty kike tsareni da tambayar ina surukarki, surukarki na gida, KO tashi batayi ba ma na fito ".
Tab ! Kace ko sallama ba kayi mata ba ka fito ?
Inafatan dai lfy ?
" lafiya lau Aunty sammako nayo muku Alhaji nakesan gani kafin ya fita shiyasa nayo sammako dan ko gun Hajiya ban Shiga ba "
Ai kuwa ka daki gurbi dan wallahi Alaji yayi sammako sunje gidan Alhaji Bukar, jiya cikin dare akayo masa waya yana gida ciwan ciki ya murdeshi cikin dare, toh Sun kaishi asibiti cikin daren Amma basu kwana ba suka koma gida, shine yayi sammako yaje yaga jikin nasa ".
Ya Salam !
Aikuwa bari intashi inbisu inga jikin nasa.
bari in leka mu gaisa da Hajiya sai in wuce daga nan.
Aunty Natafi, cikin sauri ya tashi ya fice daga falon .
kai tsaye bangaren mahaifiyarsa y dosa Hajiya jiddah, Γ gurguje suka gaisa ya fito ya doshi gidan Aminin mahaifinsa Alhaji Bukar dake unguwar farawa.
Karfe goma Sha daya na safe agogon dake manne Γ babban dakin ya buga, bugawarsa yayi daidai da farkawar SUHAIMA daga baccin da ta kwanta tun jiya, idanuwanta ta daga takai dubanta kan agogo ganin da tayi lokaci ya ja, shine ta tashi cikin sauri ta fada bandakin dake makale Γ cikin dakin barcin maigidan ta.
Wanka tayi, sannan ta sanya doguwar riga ta gabatar da sallar asubahi ,bata tsaya yin doguwar addua ba tafada dakin girki dan samun Abinda zata Sanyawa cikinta, sabida azababbiyar yunwar da takeji.
Ruwan shayi ta tafasa ta sanya cikin fulas, ta soya wainar kwai ta debo kayan shayi ta nufi falonta dan ta karya kumallo.
Kusan karfe d'aya na rana taji ana kwankwasa kofar falonta, Dan kwalli tayafa akanta, ta je
domin ta bude kofar, tana budewa idanuwanta suka sauka kan aminiyarta, wata wawar runguma tayi mata suka shigo falon suna dariya.
"kai kawata baki da kirki kiri kiri kinki zuwa gidana sai da Γ waya ko muyi chart " ?
cikin dariya Nabila tace "Amma dai kya barni in zauna kafin ki fara yin mitar" yauma sa a kikaci nazo miki kema Ai ba kirkin gareki ba daga ke har khalid din.
Wallahi kawata KO jiya mun dade muna hirarki.
Hmm !
Ku kuka sani dai.
Tashi ki samo min abinci yunwa nakeji.
yunwa ?
Aikuwa sai dai kisha shayi nima daxu shi na gama sha ,ko kuma ki shiga madafin ki dafa Ai kema nan gidanki ne kawata.
Nabila kuwa kasake tayi tana kallanta, cikin mamaki, toh yanzu daga zuwa na gidan mutane ina bakuwa sai Γ tura ni kichin yin girki, wato Suhaima kiwar nan taki har yanzu baki daina ba duk fadan da akai miki bakiji ba ko !!
"yanzu mijin nakima ruwan shayin kika bashi yasha da zai fita ?
kinji ki ko da wani zance, idan baisha ruwan tea ba me zan bashi ?
ni yauma ina bacci ya fita, Ban saniba ko ya karya ko bai karya ba ya fita.
wani wawan kallo Nabila ta jefa mata, Amma kedai kin zama shashasha wallahi ace mijinka shine zai fita kana kwance kana baccin asara, ki tunafa ke amarya ce ko wata guda baku rufe ba,, baxaki tsaya ki kula da rayuwar mijinki ba, sai ki zama shasha cikin gidan Aurenki.
nikam kin bani mamaki wallahi karatunki ya zama na banza da wofi ma.
ke ke ke dakata !
Suhaima ta daga mata hannu cikin bacin rai take magana ai gara muyi dama mun dade bamu kwafsa ba, dan nayi Aure kuma shikenan baxan huta ba menene amfanin auren Ai Nayi Aure ne dan muji dadi mu huta amma Sam bazan iya yin aikin gida ba kin san ko mumy ba sani takeyi ba.
Nabila dai, takaici ya cikata ko magana taki yi, mayafinta ta cire ta shiga kichin din, tana shiga tafara cin karo da kayan wanke wanke jibgi guda, kichin din yayi gaja gaja, omo ta dauka tayi wanke wanken ta gyara ko ina Γ kichin din yayi fes.
sannan ta dora musu abincin da zasuci.
Bayan tagama girkin ta zubo musu suka zauna sukaci suna hirarsu ta sun dade basu hadu ba, sai kusan karfe biyar na yamma sannan Nabila ta tafi gida.
wannan kenan
[10/7, 17:11] βͺ+234 706 738 2588β¬: βπ·π·π·π·π·π·
'YAR AIKI
0β£2β£
Na
ALAWIYYA ADO
π·π·π·π·π·π·π·π·
Bayan tafiyar Nabila, suhaima komawa tayi tayi kwanciyarta, bayan wani lokaci bacci yayi gaba da ita.
Khalid kuwa yana fita ya dauki hanyar farawa gidan Aminin mahaifinsa, Alhaji Bukar, da yake ya saba da masu gadin gidan yana zuwa suka bude masa tangamemen gate din shiga gidan ya sanya hancin motarsa ciki, kai tsaye cikin gidan ya shiga dan dan gidan ba bakunsa ba Ne bayan yaje Sun gaisa da mumy, bangaren Alhajin ya nufa ,Γ zaune ya samesu shida mahaifin nasa, Bayan ya shiga ya sami guri ya zauna har kasa yaje ya gaida mahaifinsa sannan aminin mahaifin nasa yayi masa sannu da jiki.
"sannu yaran kirki wanene ya sanar maka bani da lfy ne ?
Alhaji Bukar ya tambaya.
Abba naje gida ne gun Alhaji shine Aunty take fadamin baka da lfy, Alhajin ma yana nan gidan" Shine na taho dan inga jikin naka.
Ka kyauta kuwa, Nagode maka ai naji sauki aussi, jiya ban zaci zan kwana a duniya ba sabida azabar ciwo.
Ayya sannu Abba, Ai jiki yayi kyau.
Allah ya kara afuwa.
Amen y Allah yarona.
Shikam Alhaji yana zaune yana jinsu, sai da suka gama sannan yakai dubansa ga Khalid yace .
"ince ko lafiya na ganka da wuri haka ?
lafiya lau, Alhaji dama gaisheka naxoyi.
Γ Γ babban mutum ban sanka da karya ba lallai akwai magana Γ bakinka, cewar mahaifin khalid.
shikam dariya yayi yace Alhaji ,da gaske babu komai, tafiya ma zanyi tunda naga jikin Abban yy sauki.
Ai jiki yayi sauki sosai nima tafiya nake sanyi, tunda ya warware.
Karfe Bakwai na dare, khalid ya dawo gidansa, gimbiyar tasa tana kwance kan doguwar kujerar dake kewaye da falon,, Jin bude gate din gidan shine yasata tashi da sauri dan tasan maigidan Ne ya dawo, kafin ya shigo taje dakinta ta kara gyara fuskarta da powder, ta feshe jiki da turare.
sallamarsa ce tasa ta fitowa da sauri daga cikin dakin, da dan gudunta tazo ta rungumeshi, tanai masa sannu da zuwa, shi kam kamshin turarenta da yabugeshi shine ya cenza masa komai.
Baby na yau fa nayi fushi da kai, ta dan tureshi daga jikinta tana turo masa baki na shagwaba.
Haba matata laifin me kuma nayi miki akai fushi dani ?
Bacin kaine tunda ka fita tun safe baka dawo ba sai yanxu kuma ko ka kirani a waya kaji yaya ma nake.
tasake turo baki tana shagwaba.
Yi Hakuri matata, yau aiki ne yayi min yawa amma bazan karaba, ya kama kunnensa Alamar yanaja kamar wani yaro, Hakan da yayi kuwa abin dariya ya Bata.
toh, Baby na hakura.
Yauwa matata, ya fada cikin dariya.
wanka yaje yayi a bandakinsa, daga baya ya dawo ya sameta zaune Γ kan kujera tana ta chart, kusa da ita yazo ya zauna ya karbe wayar dake hannunta ya ajiyeta gefe, wato ke dai bakya gajiya da chart kullum ?
tashi tayi ta zauna daf da shi har takan jiyo bugun ziciyarshi, toh Baby na yaya zanyi, kullum ina zaune ni kadai daga kallo saΓ― chart sune abokan hirar tawa.
kada kansa yayi to shikenan, me kika dafa min yunwa nakeji.
ta ware idanuwanta dara dara, wai gashi banyi girki ba, dazu ma Nabila ce tazo shine ta dafa mana Amman akwai ragowa ko in debo maka zakaci ?
gyada kansa yayi kawai, yace to jeki ki kawo min.
mekewa tayi taje kichin din ta dakko filet taje ta bude tukunya ta zubo masa, ganin taliyar bata da yawa kamar bazata ishe shiba har kanzo kanzon ta kwasu masa.
yana zaune yana kallo ta shigo ta ajiye masa akan dan karamin teburin dake gabansa.
Gefen sa ta dawo ta zauna, lomar farko yakai bakinsa yaji kanzo Γ bakinsa da sauri y furzar da ragowar dake cikin bakinsa.
lafiya baby na ?
kai kawai ya daga mata alamar ehhh lafiya nake.
kawo min ruwa shine abin da yace mata.
na urar sanyaya ruwa ta bude ta dakko masa ruwa roba daya, ko kufi Bata dora akai ba haka ya balle murfin ya kwankwadi ruwan, saΓ― da ya kusa shanye ruwan sannan ya ajiye sauran.
SUHAIMA, ya kira sunan ta, ita kanta ji tayi banbara kwai sabida bai saba fadar sunanta kai tsaye ba.
cikin sanyin jiki ta dago da kanta takai dubanta gareshi.
kina jina ko ?
ya kuma magana a karo na biyu.
"ehhh, ina jinka.
ta fada jikinta a sanyaye.
[10/7, 17:12] βͺ+234 706 738 2588β¬: βπ·π·π·π·π·π·π·
'YAR AIKI π
Page 0β£3β£
NA
ALAWIYYA ADO
SUHAIMA, kina ganin haka ya dace ace muna gudanar da rayuwar Auren mΓ» ?
Ki sanar dani menene matsalarki Γ gun girki da gyaran gidan nan ?
Baki iya ba ne ?
Inje in kirawa maryam kanwata ta koya miki.
Suhaima tunda mukayi Aure yau kusan sati uku kenan, bakya girkan abinci, sai dai muje gidan cin abinci na siyo mana, ko inje gida inci acen, kina ganin haka kowanne magidanci yakeyi Γ gidansa ?
Idan akwai matsala kiyi kokarin sanar dani matata, ya fada muryarsa cikin rauni.
Tunda ya fara maganar nan, ita kam hawaye ne yake sassarfa zuba akan kumatunta, bata da Katar Da shi ba sai da ya gama maganarsa.
Cikin kuka ta fara da cewa.
"Haba Baby na, kasan inayin aikin gidan nan dai dai kokarina, kasan kuma abubuwan sai a hankali tunda ba sabawa nayi da yi ba bayan haka kuma ga wasu hidin dimun sun kara hawa kaina wadan da ban saba da su ba.
Kaga dazu ma da kyar na iya tashi nayi sallar asubah sabida gajiyar da nayi duk jikina ciwo yake, ta karashe maganar cikin shagwaba, hmm toh yaya kakiso inyi ?
Shiru yayi, yana jinjina magan ganunta, ya kuma gasgata abun data fada masa, musamman ganin hawaye akan kyakykyar fuskar tata.
kamo hannunta yayi Ya sanya cikin nasa, ya tallafota yana rarrashinta, nan da nan ta sake ranta suka fada cikin nishadi.
Karfe goma, na safe, khalid Ne rike da bakar jakarsa, wadda yake tafiya kasuwa da ita, gefansa kuwa suhaima ce ta rakoshi bakin motarsa.
Baby na, cikin wata sigar Jan hankali ta kirashi, cikin kasalalliyar murya ya amsa mata.
yaya akayi ne madam ?
"Dama cewa nayi ko inzo mutafi tare ka sauke ni agun mumy na, kaga tunda makayi Aure bata zo gidan nan ba, nima kuma banje ba "
Tabb !
Ai ke da ki fara fita sai bayan wata shida.
Ya fada yana dariya.
itama dariyar takeyi.
Haba dai dan Allah ka barni inje.
toh ki bari idan Allah ya kaimu gobΓ© idan zan fita saΓ― mutafi tarΓ© in saukeki agidan naku.
Murna tayi sossi har da rungumarsa, motarsa ya bude ya shiga,mai gadi ya bude masa gate din ya fita.
Suhaima kuwa ciki ta koma da tsananin murnarta, wayarta ta dauka tayiwa mumy Albishir din zuwanta Γ gobe, itama mumy taji dadin ziyarar ta 'yar tata zata kawo mata.
Tunda Ta kwanta Γ kan doguwar kujerar falon, data ta bude ta fara sana ar tata ta chart, sallah ce kawai take tashinta ita ma ba akan lokaci ake yinta ba.
washe gari tun da sassafe suhaima ta tashi ta shirya sabida murnar zuwa gida, karfe goma da rabi, ya sauketa a kofar gidan su, tare da bata sakon ta isar masa da gaisuwarsa Γ gun mumy, kafin yazo da daddre.
da gudu ta tusa kanta cikin dakin mumy din ta tana kwance taji suhaima a kanta tana ihun murna.
tashi tayi ta zauna tana fadin ohhh, suhaima ko yaushe zakiyi hankali ?
Ki dubi yadda kika fadomin aka ko sallama babu, Dan Allah ki dinga nutsuwa.
yi hakuri mumy murnar ganinki ce ta mantar dani komai.
Gefen kujerar da take taje ta zauna ,mumy dady kuwa yana nan ?
Sabida inganshi nayi sammakon nan.
" Aikuwa kinyi sa a yana kusa bai fita ba"
Da gudu ta tashi zata tafi gun dady, ke dakata cewar mumy ai baya gidan dan gidan mlm mude ne ya rasu sunje gun jana iza amma zai dawo dan ko karyawa baiyi ba"
Jiki Γ sanyaye suhaima ta dawo ta zauna, mumy wanne daga cikin yaran gidan ?
Wannan mara lafiyar kwakwslwar ne ya rasu.
Allah sarki Allah ya jikansa ai ya hutama wallahi.
Ke yaya maigidan naki, ince ko kuna zaune lafiya babu wata matsala ko ?
Mumy bubu wata matsala,, sai dai gidan ne yayimin girma bana jurΓ© shareshi gaba daya, mumy ga wanke wanke ga girki, sune kawai suke bani wahala mumy.
Shine matsalata kawai.
Ai shiyasa nake fada miki ki koyi aikin Gida sabida duk macen data iya komai kafin tayi aure ta huta komai zaizo mata da sauki.
Ni wallahi mumy bazan iya ba.
kawai ki bani mu ifa in tafi da ita ta dinga tayani aikin.
kema kin san wasane wannan, ta yaya zan dauki 'yar data ragemin in baki ita, Ai ko dadynku bazai yarda ba, shi khalid din ba yanada kanne ba abaki guda daya mana a cikinsu, sai ta dinga taimaka miki.
Ni wallahi mumy bana san kannensa suzo gidan nan koda da yini ne bare su dawo gidan da zama.
" ke SUHAIMa kada fa kizama irin matan nan da basa son dangin mijinsu su rabesu, kiyi kokari ki dinga jan 'yan uwansa Γ jikinki hakan zai kara bashi dama akan ya kara kyautata miki "
Zumburo baki tayi Tom mumy zanyi tunda kince ayi din.
ranar dai yini sukayi suna hira da mumy da kannenta, har dady shima ya jima ana hirar da shi daga bisani kuma ya shirya ya fice kasuwa.
Kusan karfe takwas, saura Khalid ya shigo gidan, dukkansu Γ falo ya samesu, har da dady din.
Bayan ya tsuguna ya gaida surukan nasa, ya jiyo kan kannen matar tasa, Suhail da Na ifa, manyan gari sannunku.
Suhail ne ya fara gaida Shi sannan Na ifa, gaisuwa sosai sukayi da wasa da dariya.
mukullin motarsa khalil, ya mikawa Suhail.
"jeka cikin mota ka dakko muku alawa Γ bayan mota "
Cikin girmamawa ya karba ya tafi aiken da mijin yayar tasa yayi masa.
Suhaima na kwance jikin mumynta koda khalili ya shigo hakan baisata ta Mike ba daga kwancen tayi masa sannu da zuwa.
Suhail ne ya shigo da mayan ledoji guda biyu kowacce shake da kayan kwalama yaje gaban mumy ya dire mata .
cikin murna mumy tayiwa surukin nata godiya, da fatan samun zaman lafiya cikin Auren nasu.
shikam dady fada yayi akan kashe kudin da khalil yayi gun siye siyen da Yayo.
sannan yakara da yimusu nasiha, akan wasu nauyin da Allah ya dora musu akan junan su.
sai kusan karfe goma na dare sannan suka koma gida cikin farin ciki bama kamar Suhaila dataje taga mumy da kannenta.
wannan kenan
[10/7, 17:12] βͺ+234 706 738 2588β¬: βπ·π·π·π·π·π·π·
'YAR AIKI.
Page 0β£4β£
NA
ALAWIYYA ADO.
π·π·π·π·π·π·π·π·
πHAJOWππ
π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§π©βπ§βπ§ HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS βπΎ
Rayuwa tana ta tafiya a tsakanin, Khalil da Suhaima a yanzu haka suna cikin watanni hudu da Auren su sai dai babu abinda ya cenza, sai ma karuwa da wasu abubuwan sukai.
Suhaima ta samu yadda takeso a gun khalil, kudi bata da matsalarsu, kuma da yake ta kasance bamai rowa ba ce, takan yawan yin baki daga bangaren 'yan uwanta da kawayenta, 'yan uwan khalili kuwa basa zuwa sabida basu samu fuska agun matar gidan ba.
WACECE SUHAIMA ?
Alhaji Salisu sharif, shine cikakken sunan mahaifinta, Wanda yake zaune Γ unguwar NA ibawa, Alhaji salisu, dan kasuwa ne cikin kasuwar kwari, Yana sai da atamfofi cikin shagonsa, rufin asiri dai dai gwargwado Allah yayi masa, Asalinsa dan garin katsina ne cikin wani gari da ake kira da KAYAWA, kasuwanci ne ya kawoshi garin kano har Allah yasa, zamansa Γ kanon yake.
Bayan ya dawo kano da zama Allah ya hadashi da safiyya, kanwar Abokinsa ce Rabiu, tun ana soyayya Γ boye har da kowa yaji manya suka shiga maganar har Allah yasa safiyya rabansa ce akayi Aure akasha biki.
gida madaidaici ya kama musu haya Γ unguwar tarauni, zaman lafiya suke sosai Γ tsakanin su.
tunda sukayi Aure Allah ya budawa salisu harkokinsa, kasuwa ta bude masa, cikin ikon Allah yasiyi fili a unguwar Na ibawa sannu a hankakali yake ginin filin har Allah yasa ya gama.
Γ wannan lokacin kusan shekarsu uku da Aure Amma ko bari safiyya bata taba yiba.
ita kam Abin yana damunta, anma kullum mijinnata rarrashinta yake akan tayi hakuri, in Allah yaso zata samu rabonta itama.
Kwanci tashi babu wuya a gun Allah ,safiyya ta samu ciki, bayan dogon laulayi da tasha, watan cikin tara wata ranar lahadi nakuda ta kamata, hankallin Alhaji salisu ya tashi sosai, cikin hanzari yaje gidansu ya fada .
Tare suka taho da inna Rabi kishiyar mahaifiyarta, Asibiti suka tafi Cikin ikon Allah basu jima da zuwa ba ta sallubo jaririyarta, cikin koshin lafiya.
Kar kaso kaga murna agun Alhaji salisu da danginta, ita kam safiya ji take tamkar ta hadiye jaririyar sabida murna.
Ganin lafiyarta kalau, ita da jaririyar aka basu sallama.
Kai tsaye gidan mijinta aka wuce da maijego.
Dangi