Showing 1 words to 3000 words out of 21966 words

Chapter 1 - RASHIN SANI

16 Oct 2024

2506

RASHIN SANI

by



oum yasmeen



Da sunan Allah me rahama me jin ƙai

ban yi da nufin cin zafarin wata ko wani ba wannan labarin ƙirkirarrene duk wanda yaga yayi daidai da rayuwar sa to ya ɗauka arashi ne


Marubuciyar


Afif

Yaɗin gamae

Mu zuba mu gani

Binta yar jagali

Kin cuce ni

Destiny love


Chapter 1-5




Tun daga ne sa in ka kalli building din makarantar kasan makaranta ce ta ya'yan manya ce iya tsaruwa ta tsaru tamkar ba a ƙasar nan kake ba gaskiya mai makarantar nan ba ƙaramin attajirine


S.D.giwa midwifery and nursing da ke kano da sauri ko wanne dalibi yake fitowa daga hostel saboda ƙarfe 7:30 kowa ya shiga aji



cikin hostel ɗin na shiga aikuwa naga duniya domin tundaga reception

nasan cewa an kashe dukiya wasu irin kujerune na gabion akajere su a waje ga wasu irin bishiyu masu kyau da yake lokacin sanyine iska sai kaɗawa su take shiga cikin reception ɗin nayi wasu ma aikatane suna zaune sai danne danne suke a computer ga wata web camera sai aiki take gawata ƙatuwar tv sai nuna abin da ake awaje da shige da fican dalibai

kusan hawa biyar ne awajan duk hostel ne hostel A,B,C har D duk wanda yaje da ya kusan fita daga makarantar na maza daban na mata daban hawa na ɗaya nayi inda na shiga room three

wata yarinya nagani tana kwance talilluɓa da wani blanket mai uban taushi

duk ta rufe jikin ta da sauri wata budurwa bazata huce shekara goma sha taraba tana sanyi da farin hijab iya kirjin ta hakama rigar ta fara wandon ta blue kayanta sunci guga ga school bag pink color kusa da gadon

" ta tsaya tayi fara tashin wacce take kwance fanna fanna fanna 7:30 fa kinsan muna da lecture fa da huri muke shiga aji amma kin sami gu kin kwanta ,

da sauri ta tashi tana sanye da kayan sanyi masu kauri gashin ta duk ya har gitsai har gadon baya fara ce tas yawa ka taɓaa jini ya fito ta na da madedecin baki lips ɗin mai dan tudu kadan bakinta dan ƙarami gwanin ban sha'awa

ga wasu manyan idanuwa dara dara girar ta har haɗewa take

gashin ta baƙi siɗik hancin ta yana da tsayi daidai misali wanda ya ƙawata duguwar fusƙar bazata huce shekara goma sha takwas ba

duk wanda ya kalle ta ba zai so ya ɗauke idon sa ba akan ta domin ta dauko kyahun barebari na usul baggara dafe kirji tayi da hausar wacce bata fita tace

"na shiga uku kar sir yusif birnin kudu ya shiga ƙinsa aƙwai baƙin hali duk da abokin sa ya fisa ,


Cikin faɗa lailah tace


"kinga fanna ki yi sauri ki shirya mu tafi bana son surutu ,


Cikin tsiwa fanna tace

"kinga inƙin ga zan ta kuraki ki tafi ai daman dan family ɗin kune dole kiyi kishin sa .. daga taɓa dr giwa kin fara kunfar baki ,

tana gama faɗar haka ta shiga toilet


Kama ƙugu lailah tayi tace



"lalle yarinyarnan kinji hausa ni kike faɗawa haka kinci sa'a ammy da abbie a hannu na suka ɗamƙaki da yau na tafi na barki,

har ta shiga ta leƙo tace


"Owo dai,


kujerar dake gefe ta jawo ta zauna ta fito da wayar ta iphone 14 tana dannawa tayi banza da ita dan ta lura yau yan faɗan ne a kan fannah


daure da towel ta fito da sauri ta dauki hair dryer domin busar da gashin ta

ɗa gowa lailah tayi tace

"u yanzu sai kin tsaya busar da gashi.. fanna we me isa kikeso idanuwan dr giwa ya fara kaiwa kanmu...?,

"kinsan fa wallahi ba yason makara yana tsaye akan mu da malaman da suke koyar damu,

kama ƙugu fanna tayi tace

"Laila yanzu so kike in tafi gashina na zubda ruwa haba laila a dinga yin na Allah mana ta faɗa cikin tsokana,

Ajiyar zuciya ta saki ta zuba mata ido tace

"fanna yanzu da abunnan na hanci zaki fita kinsan fa an hanamu sa abun ado,

fari tayi da idanuwanta ta dafe kanta tace

"Wayyo lailah giwa yanzu ɓulal hancin da tun da aka haifani akai min sai kice sai na cire barima ta tab wallahi yayi abin da ya gadama yawa ba prevent school ba fi'ilin sa yayi yawa we dan Allah in tambaye ki... ?,

Wayar ta ta ajiye a cinyar ta yace

"da hallacan ki sauri ,



Hmm tace mata da


sauri ta sa irin kayan da ke jikin laila sai de ita jakarta sky blue ce ta sayan ya madedecin glass mai kyau da alama medical ne sai ya ƙawata fusƙar ta wayar ta ta ciro dake chaji tace

"muje lailah giwa ...,

ta shi tayi ta zura wayar ta a jaka ta rataya ta ta saki ɗaya hannu jaƙarta yana ɗan yawo rufe ɗakin su lailah tayi tafiya suke suna hira har suka fito farfajiyar makarantar..........

wata ash color mota ce ta tawo aguje da alama mai motar sauri yake yayin da ya tada ƙura...

har ta sauka akan fararan kayan fanna


Zuciyar ta ce ta tun zura cikin faɗa tace


"wanne shegenne ya baɗamin ƙurah ai bata ƙarasa ba taga wanda ya fito zaro dara daran idanun ta tayi yayin da futsari ya kusan zubuwa lailah domin ta tabbata ya jita Allah yayi masa jiii……………✍🏼




RASHIN SANI



story
and

writing

Oum yasmeen



Chapter 6-10




"Na shiga ukku fannah shikkenan baƙin ki yau ya jamana kin san waye acikin motar nan kuwa ?,

cikin tsiwa ta murguda baki tace

ko ma waye ba ya ganin gaban sa ya baɗa mini kura jibi fa kayana yarda sukayi...?nasan wannan alhuda hudar ne mai baƙar zuciya ,

Dafe girji lailah tayi domin ta rasa wacce irin tsana fanna buƙar gana take wa dr giwa ko ba komai ai dr giwa yayanta ne domin da baban shi da baban ta uwa daya uba daya fanna tana girmama kowa na dangin giwa ban da dr giwa


abu ɗaya tasani fanna bata son makarantar kwana sai gashi an kawota in tayi mata fada sai tace da be buɗe makarantar shi ba da ba a kawo ta da ƙyar ta i ya buɗe baki tace

"dan girman Allah fanna kiyi shiru ...kinga fa yana ƙoƙarin fitowa ,


ai kuwa bata rufe baki ba sai gashi ya fito kallo daya nayi mai ban so in dauke ido akansa ba chocolate color ne irin black american ko kuma ka ce ethopian color shi ba fari ba shi kuma ba baƙi ba

irin farine da shi idanuwanshi suna sanye da baƙin glass ga wata iriyar ƙasumba ta sha gyarah sai sheƙitake yana sanye da suit baƙa inda ya samata fa'ar shirt yana sanye da wando baki yayi kyau yawa ƙar kadena kallosa a kuma tunsa na dama yana da wata tawadar allah wacce ta ƙarawa fusƙarsa kyau


hannunsa ruƙe da lab coat da wasu files ahannusa yayi da sir yusif birnin kudu ya roƙemai jaka da alama magana suke mai mahimmanci


Laila tace

"Fanna zu mubar gunnnan ,


Gyara jakar ta tayi tace

"naƙi wallahi ko ba yau ba sai na rahama dan rainin hankali mai ido yawa na mujiya ...,

hmmm fanna ai keda shi baku da maraba yana da ido kina dashi wallahi wani zubin ganin ki nake kina kama da family ɗin giwa

Harara ta zab ga wa lailah tace

"Allah ya kiyaye inyi kama da shi jibe shifa tsoho dashi yo ba dole yayi baƙar zuciya ba antsufa ba aure dole abubuwa su dame shi ,

rufe mata baki tayi karaf a idon sir birnin kudu yace lailah giwa ku zo lafiya kike janta yawa wasu yara

wata uwar harara fanna ta yiwa lailah kamar idonta zai waɗo ƙasa sum sum suka fara tafiya duk da fanna ji take...


Kamar ta koma hostel ta canzo kaya gawata yunwa da take ji daman bata karyaba suka fito sai anjima

Sai sudawo suyi girki su ci

haka lailah ta take mata baya har suka isa gunsu


tsugunawa sukai da ƙƴar suka haɗa baki wajan cewa

Good morning sir daga haka su ja bakim su sukai shiru....

yayin da dr giwa ko arzukin kallo basu samu ba yan mata da yawa na makarantar sun mutu akan son sa

sir birnin kudune ya amsa yace

"lailah lafiya kuke faɗa kida aminiyar ki ?"

Cikin tashin hankali har tana rarrabe magana alamun ba gaskiya tace

Sir ba-komai ke fannan tashi mutane fi aji

aa ai ban sallame kuba ke yar barno ya akai ake janki kike turjewa da alama de jinin secondry yana jikin ku ya kafe ta da ido

Wani baƙin cikine ya tokare zuciyar fanna ga wani rainin hankali shiru tayi tana wasa da yan yatsunta zara zara

cikin deep husky voice ɗinsa kamar ko yaushe yace

"ke ciro abin da ke hancin ki ,

Da sauri ta dago ta kalleshi wato shide wannan tsohon duk inda aka haɗa hanya da shi matsalane yanzu duk irin dukiyar da yake da ita sai ya karɓi gold ɗin da befi na dubu dari biyar ba yanzu inta koma gida ta cewa ammi me...?,

inta tambayeta tana ina domin da za akawo ta sai da ta ƙarba ta ajiye a gunta saboda sun karanta roles ɗin makarantar sunga ba ado ba sa abin hannu balle sarka ba yin kunshi to sai tayi da bara ta je ta dauko abarta cikin sassanyar muryar ta kamar sarewa yaɗi da shagwaɓa wacce ta zame mata jiki tace

"sorry dr ,

Tsawa ya daga kamata aikuwa tuni hawaye ya fara zarya afusƙarta da sauri ta tashi ta rungumai lailah ta fara kuka

Lailah ciro min abin da ke fusƙarta

"TO, to yaya giwa

da sauri ta dago fusƙar ta ta fara cirewa

kash...barimar irin me ƙawanyar nan ce kunsan da huya sata da cire ta abin ka da farar fata tuni hancinta yayi ja ana cirewa ta ja da baya ta kifa ƙanta amotar sa ta saki kuka mai cin rai

ungo

okay ya sa hannu ya amsa motar sa ya shiga ya ajiye ta sannan ya dubi sir birnin kudu yace

ni zan shiga office nan da anjima zani giwa hospital

dayake bani sa da makarantar taci kima ana iya shiga

"okay afito lafiya,

tafiya ya fara tamƙar mai tasauyayin ƙasa da nutsuwa tambas kamiline kuma muskili mai kafiyar zuciya ba macan da zata same shi amatsayin miji ta kusheshi

yanzu yar barno kiyi haƙuri zan yimai magana insha Allah zai baki kinji

cikin kuka tace

"ɗazu ya baɗamin kura yanzu kuma ya kwacemin abuna ,


Sir Birnin kudu yace


"dokar makaranta ce haka yar barno kiyi hakuri ba mukula ba muna saurine..,

tashi tayi daga kifa kan datayi idanunta sunyi ja saboda kuka tace laila zo mutafi

cikin tsokana yace lailah kama hannun babyn ki naga alama yar rigima ce daga magana sai kuka

dan Allah fanna kiyii haƙuri insha Allah dr giwa zai baki

kinga lailah bara in je hostel inshirya kinga naɓaci da gudu ta bar gun tanufi hostel yayin da laila ta mara mata baya



wannan kenan

yana shiga office ɗinsa ya tararda aiki da yawa zama yayi ya fara duba abin da ke gaban sa cikin rashin sani ya kai hannusa daidai hanci sa wani dogun tsaki ya ja we wannan rigimammiyar yarinyar tun ɗazu yake zuwa toilet yana wanke hannunsa amma oud ɗin datayi amfani dashi yaƙi barin hannun sa shifa yanzu yafara tunanin anya kuwa mutumce wannan wanne irin turarene yayi tsaki yafi cikin kwando

lafiya dr naga kana tunanin ?"

Firgigit ya dawo hayyacin sa ya mazewa yayi dayake yana da zurfin ciki da huya kagano meke damunsa yace

"lafiya qalau yanzu so nake inje giwa inga ya aikin nasu yake tafiya...tashi yayi yafara neman mukullinsa da wayar sa ,

hmmm dr giwa dan Allah ina nemarwa fanna afuwa kaga sabowace bata san yarda...

be ƙarasa ba ya da katar dashi yayi yace

"pls birnin kudu bana son jin maganar nan ai duk wata doka ta makarantar nan sai da na faɗa kuma ranar da suka fara lecture an tara su an ƙara sanar da su,


Sir birnin kudu yace

"baka daukan abu da zafi amma ayannzu ka zafafa dan wannan kuskuran da fanna tayi ...,

ban za yayi mai ya fita ya bugumai kofa mota ya shiga zuciyarsa na ɗaci yarasa dalili shima

besan da lilin dayasa yayi haka ba tunda yana yiwa sababbi afuwa
……………✍🏼





RASHIN SANI

Story and writing

Oum yasmeen


Chapter 11-15





Amma me isa ita naƙi in mata uzuri toni wata zuciyar ta ce mai saboda ta nuna maka sangarta ta ya'yan gata shiya,

tsaki yaja ganinn tunani zai zautar da shi ya damu kansa gani yake kamar be kyauta mata ba tsaki yaja


gaban wani tamfatsaitsan asibiti ya tsa inda yayi horn gate man ya najin horn ya taso ya buɗe mai cikin girmamawa yace

"Barka da zuwa oga ,

Yauwa yace ya ja motar sa yayi gaba parking space ya nufa inda ya faka motar sa ya fito kai tsaye yanufa office ɗinsa ya nufa

aikuwa ya tarar da mutane da yawa yau yasan ba zai bar Asibitin nan ba sai dare saboda ya tara aiki da yawa

da sauri wata budurwa ta sha gaban sa tana sanye da fitted gown ta matsaita sosai inda ta rataye mayafi chantili a kafadar ta sai taunar chin gum take ta ci make up bakin nan ya sha jan janbaki takalmine mai tsaye a kafarta cikin salon jan hankali tace

" your well come my dr tayi wani far da ido ita ala dole saita burgeshi,

banza yayi mata ya sa wani kati aikuwa nan da nan kofar ta buɗe ya shiga iya haduwa office ya hadu

ga kayan more rayuwa biyoshi tayi har tana tuntuɓe kamar zata waɗi saboda saurin da take ga kuma rigar ta matsaita sai uwar tsaga har cinya cikin muryar kuka da yake cin ta tace

"haba dr tun safe nake jiran ka amma kaxo kayi banza dani honey kasan irin son da nake maka kuwa....?,

Mayafin ta ta ruƙe a hannu tace

" wallahi ba zan iya rayuwa bakai ba ka tausayamin ka aure ni wallahi in kaina kakeso in baka zan baka ?"

File ɗin hannunsa ya ajiye yace

"pls dan girman Allah rumaisa ki fita ina da patient da yawa kuma na san kin gani kin san asati sau biyu nake zuwa asibitin nan. ki tafi gida zan neme ki ,

Wallahi ba inda zani sau nawa kake cemin in tafi bacin faɗi kake baka nemana dan girman Allah ka temaka min wallahi sonka zai hallaka ni


Ta haɗe hannuwan ta alamar bada hakuri...

daya daga cikin kujerun da aka tanadar domin zaman marasa lafiya ta ja ta zauna ta kifa kanta tana kuka mai ban tausayi

Zuba mata idanuwanshi yayi sunyi ja tamkar garwashi domin ya cire glass ɗin sa....

ransa inyayi dubu ya ɓaci me isa rumaisa ba xata gane ba tana ɓata wa kanta lokaci me isa takasa fahimtar bata ɗaya daga cikin jerun matar da zai iya aura numfashi ya fesar mai huci yace

"Pls rumaisa ki fita ina da aiki da yawa tun da nace miki zan ne meki ki yarda ,

dagowa tayi duk make up ɗinta ta ɓaci ta saki ajiyar zuciya tace

" rely?"

yes i promise to you

farin ciki ne ya mamaye zuciyarta ta saki dariyar jin daɗi ta ɗauki jaƙarta ta tsaya tana kallon sa

da tana da iko zata iya mai da dr giwa zuciyar ta ba macan da ta isa ta kalle shi tana mai wani irin so....

wanda ita kanta batasan iya kacin saba a hankali ta sunkuya har yana iya jiyu numfashin sa tace

"My honey ina sonka ina jinka ajinin jiki na pls ka tausayawa rayuwata karayu dani har abadah ƙar ka bar wata ƙofa da wata macan da zata zo cikin rayuwar mu wallahi ba dan dukiyar ka nake son ka ba ina yi maka true love wacce ba sirkin cuta a cikin ta kai min alkawari zaka rayu dani har abada love can never lie,

Rintsai idonsa yayi ya nuna mata hanya da hannun sa

Cikin sauri tace

"Okay bakomai na gode da ka tsaya ka saurareni ta juya zata fita ta murɗa handle ɗin kofa ,

yace

kice wanda yake kan lahi ya shigo

"To, my dr ,


Flash back



aguje ta waɗa kan gadon ta tasaki kuka domin yau dr ya ɓata mata rai taci alwashi kala kala akansa domin sai ta rama

Haba fanna yanzu ki canza kaya kizo mutafi kin tsaya wani kuka

yanzu a gaban ki dan uwanki ya cimin mutunci baki dakatar da shi ba shine kike cewa inzo mutafi ba zani ba

"Hmmm fanna kece ki kaja wowa kan ki tun farko sai da nace miki ki cire kika ƙi kiyi haƙuri,

Cikin tsiwa tace


"wallahi sai na rama dan rainin hankali tsoho kawe ,

uhm uhmm fanna ba asan inda rana zata faɗiba

Allah ya kiyaye ko zata waɗi saide awani gun mai zanyi da tsoho

hmmm kina ban mamaki inkin ce da dr giwa tsoho shekarar sa arba'in fa matashi ne fa

Wallahi an cucu matashi ni nayi mamaki ma dabe fara furfura ba

hmmm wallahi fanna kinyi nisa

tashi tayi ta canza kaya suka fito kai tsaye aji suka nufa har sir birnin kudu ya shiga sosai suka maida hankali kan karatunsu

Wannan kenan

Da gudu ta faɗa jikin mahaifiyar ta cikin muryar kuka tace

"wallahi hajja in ban sami ya sa'eed

Join Our Groups

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login