An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels CANJIN RAYUWA Halima /k Mashi Creat:- Shuraih Usman Littafi na daya 1 Domin dauko wasu hausa ebooks din ko wasu kayatattun littatafan hausa a matsayin hausa ebooks, sai ku ziyarci shafinmu na internet akan wannan Adireshin zaku samu http://shuraih.waphall.com CANJIN RAYUWA (1) Hajiya saudat tana zaune kan sallayarta ta idar da sallar azahar tana istigfari, 'yar kimanin shekaru arba'in da bakwai zuwa da takwas,amma ba ta yi kama da shekarunta ba saboda kyan jikinta da kuma hutu.in an ce ka fadi shekarunta za ka iya cewa talatin da doriya,kyakyawa ce mai cikar mutunci. wayarta da ke gefe samfurin nokia tayi ruri, cikin natsuwa ta kai hannu ta dauka tare da kallon fuskar wayar. kamar yadda ta za ta, maigidan ne domin duk yinin yau ba ta samu kiransa ba.sallama ya yi,ta amsa cikin ladabi, sunanta ya kira ya ce,hajiya ki karbi bakuncin mu anjima. cikin taushin murya tace,shine ba ka fada mini ba tun safe? cikin lallashi ya ce,na yi ta neman layin ki bai samu ba, ta ce,da ka nemi ta su usaina,kila network ne domin waya ta kunne ta ke,ya dan murmusa,ba mamaki zan iso da yunwa fa,don haka a tarbe ni,ta yi 'yar dariya,wace irin yunwa?shi ma yayi 'yar dariyarsu ta manya,duk wata yunwa ta,da ita zan zo,ta ce, kar ka damu allah ya kawo ka lafiya,ya ce,amin. ki sa a yi wa uwata farfesun kifi tare za mu zo,take ta hade fuska, tamkar yana kallon ta,ta ce alhaji don allah kar ka zo min da mimi.ya ce,saboda me?ta ce,ka san komai, alhaji MIMI in ta zo gidan ba,ba maaikatan gidan ba.ta sani,na fada mata kar in sake ganinta a gidana matsawar ba ta canza halin ta ba,ba na bukatar ta.yayi shiru domin ranshi ya baci,kusan minti daya duk sun yi shiru. sannan ya ce,sauda, ba zan gaji da fada miki cewa ban jin dadin abinda kike yi wa MIMI ba gaskiya, zai fi kyau ki fito fili ki zage ni sai ya fi min sauki maimakon aibanta MIMI. allah! in ji hajiya saudatu,ta sake tausasa muryarta,ban san lokacin da za ka fahimce ni ba alhaji,amma kayi hakuri.in dai don mu zaka zo,to ka zo kai daya zan fi so haka.cikin dan zafi ya ce,sauda muna hanya kar ki manta da abincin ta na yau da kullum,ki fada ma duk 'yan gidan wanda bai son ganin ta zai iya barin gida har sai ta tafi, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (2) sannan ya kashe wayarsa. ta dan ciji lebe tare da lumshe ido cikin takaici,ba ta da zabin da ya wuce yin abinda mijin ta ke so.a fili ta ce ni kan bana son zaman MIMI garin nan,na tsani halin ta,a ce yarinya karama a bar ta tana yin yadda ta ke so.ta mike tana nunke sallaya. Abdulkarim ya yi sallama, ta amsa fuskar ta daure,sannan ta yi tsaki, abdulkarim ya ce,lafiya hajiya?alhaji ne ya kira ni wai suna tafe shi da MIMI. abdulkarim ya ja tsaki,don jin ambaci sunan MIMI, sannan yace,ashe yanzu zan juya a kan sawuna mu gaisa kawai hajiya in sabi jaka ta,ai a wannan sati bani da darasi kamar yau,sai na sake dawo wa. hajiya sauda ta yi yar dariya tare da fadin haba abdul,ka taho tun daga zariya har katsina sannan ka ce mu gaisa kawai ka wuce saboda MIMI?ta ci gaba da fadin ba zai yiwu ba.dauki jakarka kawai ka wuce sashin ku,ka watsa ruwa.barin in sa mutuniyarka tabawa ta kawo maka abinci na san yanzu sun gama na rana.ya ce,ai ni bana son rainin wayonta ne hajiya,a ce yarinya karama kanwar bayanka ta zo tana kawo maka rainin wayo,ba dama ka yi magana.ni kuma kin sanni da zuciya sai in doke ta. hajiya tace,aa kar ka soma,ka san halin alhaji.ina fatan baka manta da yadda yayanka abbas suka kwashe ba,in ka tuna zungure mata kai kurum yayi,amma ta inda alhaji yake shiga bata nan yake fita ba.tsawon wata shida yaki ams gaisuwar abbas.sai da biki shi sannan alhaji ya sauko,shima sai da abokan abbas suka taro abokan alhajin aka hadu ana taba shi baki, sannan ya hakura da kyar da dokoki a kan 'yarsa. Abdulkarim yayi ajiyar zuciya cikin takaici,sannan ya ce,ban manta ba.hajiya shi yasa nace, zan koma,tace ka hakura da harkanta.yace, gaskiya alhaji ba yayi mana adalci,a ce cikin 'ya'yansa mu ishirin da biyu,amma ya zabi daya rak yace,ita ce star don kawai tana da sunan mahaifiyarsa.allah hajiya abin yana damu na, kanwarmu ce fa,amma ko shawara da ita sai abinda ta ce a family. hajiya sauda ta ce,ku yi ta hakuri, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (3) Dadin abin ita dai ta mace ce,duk abinta ai dole ta yi aure ko? abdulkarim ya ce, tabdi, wannan 'yar jin kan?ya zauna a kujera, sannan ya ce,allah ya sa ta saurari wani.hajiya ta ce, ayya abdulkarim dole tayi aure. ba dai mace ba ce?shi kanshi zai so a bar masa ita a gabansa?abdul' ya yi 'yar dariya,sannan yace,kila ya ce mijin ya dinga biyo ta nan gidansa.hajiya ta ce, oho mishi su dai suka sani, suka yi 'yar dariya,ta ce ba su lokaci kawai.ni dai ina ta fada ma allah,ku da ma na haifa ciki daya kuna jin takaici da haushinta,bare wadanda ba ni ce na haife su ba.abdul ya mike tare da saba jakarsa,bari ni kan na isa dakinmu,hajiya ta ce, to ni ma bari in je babban kicin. hajiya sauda ta tafi gefen babban kicin,ka san cewar gidan babban gida ne mai tsari,tun daga waje za ka san cewa mamallakin gidan ya tara abin duniya ba kadan ba.ta isa babban kicin din,mata uku ta samu a ciki suna ta aiki,suka maido da hankalinsu gurinta tare da yin mata sannu da shigowa,ta amsa da sannunku da aiki cikin girmamawa,ta kalli tsohuwar cikinsu ta ce,baba tabawa me aka yi da rana?tsohuwar tace,taliya ce ke kan layi da rana,da dare kuma zamu yi tuwon masara da miyar danye kubewa,ga taliyar nan ma yanzu na sauke. hajiya tace to,a canza na dare a yi mana dan waken gari dawa sannan ayi shi da wuri.baba tabawa tace,maigida yana nan shigowa kenan?hajiya tace eh,suna tafe,suka hada baki guri cewa,allah ya kawo su lafiya.hajiya tace amin.sannan ta kalli jummai muna da kifin ruwa ko?jummai ta ce eh,hajiya ta ce yawwa ki dafa kadan kar ki cika yaji kuma kar ki sa tafannuwa. sannan ki kula kar ya dagargaje na MIMI ne. dukkan su suka hada baki gurin tambayar har da MIMI ne za a zo?jummai ta ce, allah ya fishe ni yin kuskure. hajiya tace kar ki damu, sannan abinda kawai zan fada maku in tazo,ku kawar da kai duk abinda za tayi kun ji ko?cikin karyayyar murya suka ce to shikenan,tabawa ta kalli jummai kar ki sa mata tafannuwa, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (4) Wancan zuwan da ta yi maman sani daga sa tafannuwa shikenan ya zama sanadin korarta. jummai tace,zan kula insha allah. hajiya ta kalli ramma tace,da safe me muke da shi?ramma ta ce, shayi ne,hajiya tace,to a canza zuwa kosai da kunun gyada,ta ce to hajiya. tabawa tace akwai kafar safa ko wannan karon ba zaayi ma alhaji ba?hajiya tace,a dora zan dinga zuwa ina dubawa,na zata babu ne,tabawa mutumin ki fa yazo abdul,a kai masa abinci,ina magajiya?tabawa ta ce allah sarki abdul ne yazo zan kai masa ma da kaina maigida sukutum.hajiya ta juya tana dariya tare da fadin kowa ya duba abinda babu sai yazo ya fada min. Da kanta ta nufi wajen me wankinsu yana ta gugar kayan yara,ta ce masa ka je ka fadawa mai gadi da mai kula da fulawa cewa MIMI za tazo anjima,sannan yau direba ya same ni a falo.ta sake cewa,danladi na fada maku ne don ku kiyaye bana son ana korar min ku,danladi yace,zan fada masu.ya nufi gurin mai gadi,ya turo mata direba ya sanar da su zuwan MIMI nan suka dinga tattauna rashin mutuncin MIMI,ya same ta tana duba nono a cikin firiji.domin tasan aladan shi ta sha furan dare. Direba yayi sallama cikin girmamawa,hajiya ta amsa,ya gaida ta sannan yace,ga ni tace,malam yau da ma ina son sanar da kai ne,yau MIMI zata zo na san ba ka santa ba.amma ka samu labarinta?cikin in'ina yace eh naji gurin su danladi.tace to ka tafi filin jirgi tun misalin hudu da rabi,gara ka jira su,domin da jiran da suka yine wancan direban namu shine sanadiyyar korar shi da MIMI ta sa alhaji yayi.ya ce zan kiyaye insha allah. Tun hudu yau ya nufi filin jirgin,jiran zai fi masa sauki da haduwa da fushin MIMI. biyar da minti talatin suka iso,Alhaji bashir aliyu masari ya fito daga cikin jirgi,MIMI tana biye da shi, sanye cikin riga da wando masu kalar pink sun dame ta tsam.sai after diress baka mai sheki,sannan ta gaba an ratsa pink hakanan rigar ba ta kai kasa ba.don haka ana ganin wandonta, dan siririn mayafinta ba shi da girma, [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (5) Shima pink bai rufe dogon gashinta ba. Kafarta sanye cikin takalmi shima pink dinne,da ratsin baki marar tudu mai igiyoyi,purse din hannunta da wayoyin ta kirar nakia duk kalar pink ne.can sama goshinta zaka iya kallon wani katon gilashi irin wanda wayayyun 'yan mata masu jin kansu suke sakawa.da gudu yau ya nufe su domin duk da bai san MIMI ba ya san maigida na su.cikin ladabi ya yi masu sannu da zuwa,ya amshi jakar hannun alhaji, alhaji ne kawai ya amsa, MIMI kan ko kallon shi ba ta yi ba. ya bude kofofin motar sannan ya sa jakar alhaji a kujerar gaba,bayan sun fito daga filin yana hawa titi zai raraka da gudu,alhaji ya ce tafi a natsuwa MIMI bata son gudu,yau yace,to ranka ya dade. shi kanshi mai gadi a waje ya tsaya yana jiran zuwan su,yana hangosu da gudu ya nufi ciki ya wangale get din,kamar yanda MIMI ke so,don bata son jira.ko da direba ya tsaya ya bude masu sannan ya cire jakar ya bi bayan su MIMI ta kalli gidan sannan tace,Dad gidan nan yana son fenti yayi datti,ya yi 'yan kalle-kalle,yace,na lura da haka za a sabun ta shi da fenti.direban ya ajiye jakar a kujera sannan ya kalli alhaji Alhaji, na barku lafiya ya fita.Alhaji yaso ma kiran hajiyata-hajiyata,ta fito,dankwali a hannun ta,domin lokacin ta gama saka kayan,ta yi adonta cikin super kalar blue da ratsin yellow sai kamshin turare take yi. Ta kalli mijinta, sannu da zuwa alhaji,ya ce,yawwa sauda ta dubi MIMI wadda tunda suka shigo falo ta natsu saboda duk iya-shegenta tana tsoron uwarta,ta san hajiya sam bata daukar reni.ta dago ido cikin fargaba ta kalli mahaifiyarta sauda tace, sannu hajiya,ta amsa yawwa,ya mominku nafisa da kuma sauran kannenku?ta ce kowa lafiya,hajiya ta ce,masha allah,ta dauki hular alhaji da jakarsa da kuma malun-malun dinsa ta nufi dakinsa tana fadin za a hada ruwan wanka ko? aa rabona da abinci tun safe shima ba wani abinci na ci mai nauyi ba coffee ne,ta karasa dakin ta aje kayan hannunta ta fito tana fadin mu je Dining. [01/10 12:45 pm] Abdul: STEP (6) Hajiya ce ta janyo masa kujera ya zauna,ya kalli MIMI zauna mana uwata.ya mayar da kallon shi ga hajiya sauda, an yi mata farfesun kifin? hajiya ta kalli MIMI cikin daurewan fuska,sannan ta ce,an yi,MIMI ta turo baki tare da hada rai. hajiya tana zuba masu dan waken cikin plate tare da colslow,ta janyo wani plate din tana zuba masa farfesun kafar sa,ta tura gabansa tana fadin alhaji ba ka tambayi yaran gidan ba?ya kalle ta cikin 'yar zolaya yace,duk ganin ki ne ya mantar dani.ko da dai na san zuwa yanzu suna lslamiyya ko?ta ce eh,yau kam ma da murna suka fita,don na gaya masu cewa kana tafe,ya ce ga shi ban riko masu tsaraba ba.amma bari in sa direba ya sayo masu,ta ce aa zai fi kyau ka fita dasu don yaran nan basa samun kulawarka,kamar fa sam basu shaku da kai ba. Ya kalli MIMI wacce ta jibga tagumi,ya ce zan gani ko da lokacin,kin san fako a can ba samu zama nake yi ba.shiru tayi don ta san kome za tace ba fahimtar ta zai yi ba,ta jima tana yi mishi nacin cewa,ya dinga baiwa yaran ko da awa daya ne a cikin lokacinsa, amma sam ya ki.ko su da suke matansa basa ganin shi a kan lokaci,sai yayi wata ko sati uku in kuma yazo kwana biyu yake yi, nan guri ta ya kwana daya ya je malumfashi wajen hajiya binta ya kwana daya tunaninta ya katse lokacin da ta ji yana tambayar MIMI menene uwata?na ga duk kin bata ranki?ki ci kifinki mamana. ya kalli hajiya sauda ina kifinta?hajiya ta nuna kular da cokali,ga kular kifin nan gabanta?ta dauka mana ko a baki zan bata?MIMI ta sake tura baki tare da kallon mahaifiyarta,ni na koshi,hajiya sauda ta ce, karyarki dubu wallahi kin yi kadan ki ce a dafa miki abin, yanzu ki ce baza ki ci ba,saboda bakin raini ai na lura da ke tunda ku ka shigo gidan nan na san baki so zuwa ba, ko katsinar ce baki so zuwa ba oho miki, amma bakin ranki ya kare miki can. Sauda!alhaji ya katse ta tare da daga hannu, gaskiya ni bana son abinda ki keyi,a ce ke da 'yarki ta cikinki amma ba ki kaunarta?.... [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (7) Hajiya tace, ba kaunarta bane bana yi, halinta ne bana so.kuma in har ta ga mun zauna inuwa daya da ita to ta tabbatar ta canza halinta,in ko ba ta canza ba to sai dai ta nemi wata uwar ko da yake tana da ita ma. ya tausasa murya ai ba maganar fada bane, amma gaskiya ba zan iya kallo kina mata irin kalaman ba, kullum tana yi mini korafin ba ki sonta,ita in fada mata gaskiya ko dai bake ce ki ka haife ta ba?ya aje cokalin hannunshi,na rasa me take miki,ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba.sai ta zo hutu irin haka,amma sam ba kya ko yin kewar ta. hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba,wanda ta hada masa,a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce,halin ta kawai zata canza,in dai tana son soyayyata.yanzu baka kalli shigar da tayi ba? tun daga abuja ka sako ta gaba har katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje,kayar jikinta duk sun dame ta,wai ita dole ta waye. ya kalli MIMI sannan ya kalli sauda, da dan murmushi,ina laifin kwalliyarta,ni ban ga aibun ta ba,haka 'yan mata matasa irin ta ke yi.ya kalli MIMI,ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?tsaki hajiya ta yi ta nufi dakinta.sai lokacin MIMI ta samu damar yin mita,kaga ko dad,sai da nace ka barni can in gama hutu na,ka ce aa sai na zo, ni daman na san hajiya ba za ta taba so na ba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta,shiga tafa, mene ne aibunta?ya kalle ta cikin sigar lallashi yace, ban ga laifi ba.ita hajiya wai sai tace,sai na saka hijabi da atamfa,ni kuma ba zan iya sa iri wannan kayan zafin ba.na yi karatu na waye ni ba irin su usaina ba ce kauyawa.yayi murmushi,shgwabarta tana burge shi.kallon ta ya ke yi tamkar 'yar shekara biyu. ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta,kar ki damu uwata.mamanki tana sonki,na san ta ga nafi damuwa da kene cikin 'ya'ya na,kin san don ita ce ta haife ki,shi ya sa fa.in da a ce kamar hajiya binta ce ko nafisa da tuni na sallame su,kin manta na taba kora hajiya binta saboda ke?ta ce na tuna Dad, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (8)Ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da bata haifamin ke ba, bare ta haife ki. kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare?ta ce ba zan so ba dad.amma ka yi mata magana ta daina matsa min,ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kaya sawarki,ki rinka saka irin wadanda take so.ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so,ya ce za ta barki mana kin ji,ki dai na kuka.ya yi ta lallashinta har ta daina kuka. suna cikin cin abinci hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga lslamiyya da sallama suka shigo, ita ce ta amsa sallamar,husna da hasina ne a gaba,suka ce sannu da gida hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na.ina sauran? kafin suba ta amsa sai ga su suna ta yin sallama,da hannu ta nuna masu gurin dining,ga dadin ku,suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya.ya dafa kan husna da hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu.MIMI ta hada rai ita ba ta son hayaniya. dady ya ce,ba ku gaida sista MIMI ba.suka kalle ta don suna tsoron ta,sannu yaya MIMI,cikin daure fuska ta ce,yawwa,na amsa duka ne ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba.hasana da usaina sune 'yan matan da suke bi MIMI a haihuwa.dad ya kale su ku shirya da kannen ku, yau yazo ya kai ku super market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya zabo abinda ranshi ke so. Yara suka shiga murna hasana da hussaina suka ce dad,mu kam ba zamu je ba.ya ce,saboda me?suka ce,muna da karatun hadda gobe,malamin mu zai zo, bin abdulrahaman.hajiya ta ce,tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba zaku sha dukan tsiya gurin shi.duka kuma?in ji dad dinsu,hajiya tace sun wuce duka kenan?karatu sai da zare ido.abdulkarim ya yi sallam, ya shigo falo suka amsa,ya iso gurin dadin shima ya gaida alhajin.MIMI tana ta chatin dinta ba ta dago kai ba,shima bai ko kalle ta ba. ya dubi su hasana ya ce, kun dawo?suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun hajiya ta fada mana zuwan ka. mun je dakin ku kana wanka, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (9) Kuma lokacin lslamiyya ya yi dole muka tafi.ya ce,na ji shigowar ai, ya ya zauna,usaina na fadin,lslamiyya lafiya,munyi murajaa ne yanzun. ya ce, kun kusa fara jarabawa kenan suka ce eh! hasana ta ce,yawwa yaya don allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida bin abdulrahaman.abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci,ku ce gobe zanyi kallon duka. usaina ta ce agaji yaya abdul, bulalarshi akwai zafi,suka sa dariya tare.ya ce,bari mu yi sallah sai in karbar maku,suka ce,yawwa yayanmu mun gode. MIMI daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su,sai ta soma mita,ni na san duk 'yan gidan nan ba sa so na,dole kawai suke gani na,kalli yaya abdul,ko kallo na bai yi ba.alhaji yace,kai! abdulkrim,ya ce naam,ya zo ga ni dad.ya ce baka ga MIMI ba ne?ran abdulkarim ya baci,nan a take fuskarsa ta nuna,cikin wata murya marar dadi ya ce,na ganta mana dadi.shine ba za ka yi mata magana ba? Kafin ya yi magana hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba?shine ya kamata ya gaida ta,ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. alhaji ya ce,amma ita bakuwa ce.bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta?a kalla ya nu na kewarsa gare ta ko?kan abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.hajiya ta ce,bai gaishe ta din ba.tafi abinka abdulkarim,cikin sauri ya wuce.su hasana ma suka yi dakinsu ita ma hajiya ta juya zuwa dakinta,MIMI ta kalli dad,kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu,ya dafa ta karki damu ina zuwa. baki gado hajiya sauda ta zauna ta zabga tagumi,wannan abin ya ci mata rai,a ce mutum kamar alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro.kirikiri yana gani garkiya sai ya runtse ido saboda son zuciya,bai san cewa haka zai sa kan 'ya'yansa ya rabu ba ne?sallamar shi ce ta katse ta,ta dago ta dube shi,shima ya iso ya zauna bakin gadon.haba hajiya ki sakarwa 'yarki fuska mana?ke ba abin faharin ki bane a ce nafi son 'yarki,duk cikin 'ya'ya na? [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (10) Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce,haba sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonki ne fa ya shafe ta ko baki lura ba?ta daga ido ta kalle shi,ban musa ba,na san kana so na,amma ni burin na shine ka yi adalci tsakanin yaranka alhaji, ko don gudu rarrabuwar kansu. ya ce,menene na yi mata wanda ban yi masu ba?ta kalli cikin idon shi,ai ba za su kirgu ba,banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasa wajen karatu bayan ita?to indan wannan ne,karatun na su na gida ya fina ta cin kudi sauda. umm, haka dai za ka ce,tunda kana son kare kanka,ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi.ta kalle shi,ta rasa me zata ce masa,sai kurum ta ce to. don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta,na gode,ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta,ina son a kyuatata shimfida ta anjima. don na iso da muradin hakan. Ta sake murmushi tare da kallon shi,wai alhaji yaushe zaa girma ne?ta yi tambayar cikin sigar wasa. ya janyo ta jikin shi,wa ya ce miki ana girma da lada? sai dai in mutuwa ce ta dauka.suka sa dariya tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar.suka mike, ta ce lokacin sallah yayi bari in fita 'yan mazan nan sai nayi fama sannan su wuce masallaci.tare suka fita ya nufi dakin shi,har lokacin MIMI tana zaune a falo.sai dai lokacin ta koma kan kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin. alhaji ya nufe ta yana cewa,mamana kina hutawa ne?ba tare data dago ba,ta ce eh dady.ya ce da kyau.ya wuce dakinsa. hajiya sauda ta dube ta,ki tashi kiyi sallah,ta dago ta kalli hajiyar ta ga fuskarta a daure,ta zabga mata harara na ce,ki tashi ki yi sallah.tsam ta mike ta nufi dakin su usaina inda nan ne take sauka in ta zo,kayan tama cikin suke.sai dai ita bata sm hakan saboda a abuja sasanta dabam, amma a nan hajiya ta hana a yi mata dakinta dabam.ta sami su hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta.ga al'ada alhaji in ya fita sallah, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (11) Yakan kai sha biyu bai shigo gida ba zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa 'yanuwa suka ji cewa ya shigo gari.don haka ita ma hajiya bata fito ba sai bayan sallah isha,ta shiga daki alhaji don sake kalailai ce shi,tare da kunna turarukan kamshim daki,ta fitar ma da alhaji kayan barci,ta dama masa fura,ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya.daki maza ta fara shiga, umar da aminu suna ta yin home work, abdullahi yana kwance kan gado, sadik yana buga game a tv. ta ce,sarkin game kai ka yi home work dinka? ya ce, eh nayi hajiya ta kalli abdullahi,kai fa bawan allah yau da wuri zaka yi barci kenan? ya tashi zaune kaina ke ciwo hajiya shi yasa ki kaji na ce dad ya bari sai gobe mu je super maket din.don ba zan iya kula da su ba. ta ce,ba sai kun yi haka ba,ya ce,kin shiga daki lokacin ta ce,to ka sha magani?ya ce eh!ta ce to allah ya sawwake,ya ce ameen.ta ce,sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe,suka ce,to ta ce,kar fa ku manta da yin addua lokacin barci,suka ce to.ta nufi dakin su husna da hasana da kuma zainab yar gidan hajiya binta, wace ta ki komawa wajen uwarta,tun lokacin da alhaji ya saki hajiya binta,ya kwaso yaran ya kawo su nan.hajiya sauda tace sam ba zai yiwu ba,lallai ya mayar da ita,ta rike kayanta. domin ita kanta ba zata sa araba ta da 'ya'yanta ba.shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da zainab,don kuwa ta kekashe ba9a ta bi su ba. lta ta fi son zama a nan, hajiya sauda ta rike ta,ta hada da 'ya'yanta guda goma sha biyu da ta haifa suka zama sha uku.su kam sun fara barci.don haka ta shigo ta yi masu addua tare da kulle masu kofar dakinsu. hasana suna zaune suna kara ma juna haddar alkur'ani mai girma, ita kuwa 'yar gwal,wato MIMI tana kishigide kan gado.tana ta chatin,kai tsaye gurinta hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri MIMI ta dubi wayar cikin bacin rai.tana ganin hajiya sai ta yi kasa da kai kamar munafuka,kin yi sallar ne? cikin tsawa ta ji maganar MIMI, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (12)MIMI ta yi shiru, ta ce,ba ki ji niba ne?ta girgiza kai tare da fadin banyi ba. hajiya ta rufe ta da fada bangane ba kiyi ba? Anya ma kina yin sallar na kuwa? ta kalli hajiya cikin sauri tare da fadin ina yi mana,hajiya tace,karya ne kalli agogonki karfe nawa ne yanzu?da har zuwa yanzu baki yi ko sallar magariba ba bare lsha.in na lura musulunci ba ya birge ki,lslamiyya kin daina,duk wani abu da lslam yazo da shi,komi na addini kin mayar da shi kauyanci,ke ga 'yar boko ko?MIMI dai bata dago kai ba,hajiya ta ce,na san ko zaa kashe ki yanzu da kyar in zaki iya kawo mini fatiha cikakkiya. kin zauna kina ta danne-dannen waya,in ba ki sani ba ne gara ki sani,kina cutar kanki ne.rayuwar daki ka daukar wa kanki ba mai dorewa ba ce,don haka ba ta dace da ke ba.ki ta shi ki yi sallar yanzun nan, sakarya marar hankali. simi-simi MIMI ta tashi ta nufi bandaki,hajiya ta ce,tunda abin naki ya soma nisa haka,wayewar taki har ta kai ki da gudu salla,to nan gida za ki kare hutunki.ki dau karatu gurin malamin yaran nan,ki koyi salla tun da bani da tabbacin kin na yi.bari baban naku ya shigo,ta juya ta fita da wayar a hannunta.MIMI daga cikin bandaki,kuka wiwi ta dinga yi,ita kam baza ta iya zam har ta gama hutu cikin takurar ba. a silent hajiya ta saka wayar MIMI ta ja durowa ta jefa.MIMI tana kuka ta yi sallar,su hussaina suna kallonta,ta idar ta fada kan gado ta ci gaba da kuka.don ita amshe mata wayar da hajiya ta yi,ya fi bata mata rai fiye da fadan,don jin ta take tamkar an raba ta da ranta, sam bata nisa da wayarta. misalin shabiyu saura alhaji ya shigo,tuntuni yake ta neman layin 'yar lelanshi,amma sai tayi ta ruri har ta yanke ba a daga ba. hajiya ta shiga ta same shi tana cikin shirin barci,ya kalle ta da wayansa a hannu,MIMI fa?ta kalle shi,in kira maka ita ne?ya lura cikin gatse ta yi masa maganar,don haka sai ya ce,aa dama in ji ko ta yi barci ne,saboda ina ta kiran wayarta bata dauka ba.cikin jin haushi hajiya ta ce oho.. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (13)Na zata ita ma nan zamu kwana tare don kar wani abu ya cinye ta. ya mike tare da kama hannunta,sauda kin canza sani na ba haka kike ba.yanzu kin zama mai saurin fushi.ta kalli fuskarsa,kai da 'yarka kuka canza ni.ya ja hannunta,to zo mu zauna in ji mai zan samu.ya basar da wancan zancen.ita ma sai ta biye masa da cewa,duk abinda kake so.ya tallabe fuskarta kin san mene ne sauda?ta girgiza kai kullum na kalli fuskarki.rana mai tarihi a guri na.hajiya sauda ta ce, ikon allah ni kan da a ce kalmar karatu ce,da sai in ce,tuni na haddace ta,tun muna da kananan shekaru. ya yi 'yar dariya ina jin dadin tuna baya,wani lokacin sai in ji tamkar in mai do lokaci.ta lumshe ido, ai alhaji kuruciya cike ta ke da shirme,in ta wuce sai ayi ta kewarta, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (14)Ni kaina ina son tuna baya,rayuwa tana da sauri,duk da haka in muna tare,sai in rika jin kaina tamkar 'yar kasa da shekara ashirin.yayi dariya,a haka ni ke kallon ki sauda,kullum na kan ce, lokacin na sauri.ta kwantar da kanta a kafadarsa.allah ya kara mana tsaw rai da rayuwa mai amfani.a kunne ya rada mata amin.da ma an ce soyaya bata tsufa, sai dai masoya su tsufa, allah ka yi mana mai kyau. karfe bakwai alhaji bashir yana ta shiri cikin sauri,hajiya tana taimaka masa gurin saka kaya, rokonsa take yi ya dan sa wani abinci a bakinsa,ta ce don kai nasa a yi kunun gyada da kosai,saboda na san kana so.ya kalle ta,ta na saka masa liks a hannun riga ya ce,ki yi hakuri mata ta,ba komai,na yi alkawarin zan gana da wani mutum ne,wanda na fi wata guda ina neman damar ganinsa. ta ce,duk da haka ka karya zai fi.ya ce sai na dawo,domin in na samu damar da nike nema a gare shi,kasuwanci na zai ninka,in ko haka ta samu yaya kika gani?ta ce, umm! kai dai da ma kullum saurin ka bai wuce kasuwanci,a kasuwanci ina ne ba a sanka ba,duk fadin afirka ina ne sunanka bai kai ba! wane irin kudi ne baka mallaka ba kullum cikin samun riba ka ke. ta mika masa hularsa,me ya kamata ka nema kuma alhaji?yanzu baya ga aljanna? murmushi ya yi,ba tare da yaba ta amsar duk tambayoyin da ta jero masa ba.ta ci gaba, ni dai ba zan gaji da baka shawarar cewa,kamata yayi zuwa yanzu kayi murabus ka bar abba da mukhtar su jagoranci kasuwancinka.ya ce,ni kuma fa ta ce,ka zo mu zauna mu huta,mu karasa rayuwarmu,'yan kananan yaranmu su shaku da kai.ya saki dariya tare da cewa,sauda kenan.in ki ka fadi wata magana sai ki tuna mimi tadinmu na farko da ke.ta ce au!kana nufi maganar ma dana fada shirme ce?ya ce,kusan haka,kina cewa in bar ma su abba ragamar kasuwanci,ki na tsammanin za su yi jarumtar kasuwanci kamar ni? bai jira amsa ba,ya ci gaba da cewa,da ma MIMI ce babba,ko da tana mace na san za ta iya.amma su abba shirme kenan,shi yasa kika, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (15)Ga ko shawara ce na fi son yi da ita koyaushe ta na bani shawara ta musamman yadda ake fadada kasuwanci a duniya ta cikin yanar gizo.su kuwa su abba bakin ku daya.kullum in takaita kasuwanci a iya gida nijeriya,ni kuma na wuce nan tuni. ta ce,ka fahimce ni ba muna cewa kar kayi kasuwanci da waje ba ne aa,ai bunkasar ka ta isa ka yi kasuwanci da waje.harkar shigo da magunguna ne muka ce ka daina,tunda ana yawan zargin kana shigo da haramtattun magunguna da kuma miyagun kwayoyi.ya gyara zaman hularsa,ya sa hannu ya shafi kumatun ta, ki ci gaba da yi min addua sauda,ke ce kurum ki ke fada min son ranki in ji ban ji haushi ba.ya cire takalminsa tana fesa masa turare ya ce,ban sani ba ko zamu gama tattaunawa da wuri ko ba zamu gama ba, amma ko yaya ne dai daga can zan wuce malumfashi. in duba su binta da yara sannan in kewayo gona ta, na jima ban leka ta ba.inda lokaci zan shiga masari can ma na jima ban je ba.kin ga sai na kwana kenan,gobe zan dawo in dauki uwata mu koma inda muka fi wayo.ta ce,allah ya tsare sai ka dawo din amma batun tafiya da MIMI ne nake tunani a kai.ya kalle ta, kamar yaya?ta ce,sai ka dawo dai allah ya tsare,ya dan tabe baki amin.suna fitowa falo yara suka nufo suna yi masu sannu da fitowa tare da gaishe shi,ya amsa da daidai,ya kalli usaina,MIMI fa?ta ce tana kwance dady,ya ce,shikenan zamu yi waya.hajiya ta raka shi har mota,ba sabon abu bane,haka ta saba tun suna da kuruciya.falo ya kacame,yaran suna ta karin kumallo,sai hayaniyarsu da karar kofuna.MIMI ta fito sanye ciki riga da wando masu dan kauri na barci. sauri ta ke yi,tare da fatan allah ya sa dad dinta bai fita ba,don ba za ta taba bari ya fita ya bar ta ba.ta iso gurin hajiya,fuskar ta babu annuri ta ce,ina kwana hajiya?ba tare da ta dube ta bata ce,lafiya lau.MIMI tayi tsaye shiru,tana son yin magana amma tana tsoro.hajiya ta dago ta dube ta,ga kayan shayi can a kan dining,na san ba kya shan kunu,ta ce tam!ehemm!da ma zan gaida dady ne,yana ciki ne? hajiya ta ce a'a. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (16)Ya tafi malumfashi sai gobe zai dawo.MIMI ta zaro idanu yaya dady zai min haka ya tafi ya bar ni,ta kalli hajiya wanda ta soma watsa mata harara ta ce,hajiya don allah ina waya ta?hajiya ta ce,sai za ku tafi zan baki,don ni ba za kiyi mani chatin din naki ba a nan,ki karya ki je ki yi wanka,in malamin su hussai ya zo zaki bisu,ki je daukar karatu a gurinsa.ina sa ran ma alhaji ba zai tafi da ke ba,nan zai bar ki sai kin san addininki za ki tafi,ko da zaki cinye hutun ki a nan. cikin sauri MIMI ta koma daki cikin kuka sai da tayi me isarta ta shiga wanka,a fili kuwa fili kuwa fadi ta ke, allah ba zan zauna ba, shi ya sa na tsani zuwa katsinan nan.dolenta ta saka atamfa riga da siket,a cikin durowarta ta ciro don tana da kaya a nan gida, duk lokacin da aka yi wasu usaina sai an yi mata.ta shirya tsaf ta koma kan gado ta kwanta tana tunanin yadda za ta yi.amma ko ta halin kaka baza ta zauna cikin irin takurar ba.can ta hango wayar hasana kan durowar ta.cikin sauri ta tashi ta dauko,layin dad ta kira wanda ta san in ta kira zai dauka da sauri,cikin kuka ta soma magana,bayan ya daga dad kaga hajiya ta dauke min waya ta,kuma wai ba zan tafi ba,ni dai dad wallahi bazan zauna ba.ya ce,ya shiru uwata kar ki damu ba zan barki ba ni ma,yanzu me kike so?ta ce,phone di na,ya ce,shikenan zan ce ta ba ki,kin ci abinci?ta ce,aa ya ce,to kije ki ci zan sata baki wayarki kin ji? ta na zaune a kan dining ta hada shayi tana sha da cokali cikin hankali don ita sam bata da hanzari,tana kallo lokacin da hussaina ta kawo ma hajiya waya ta ce,dady ya kira,ta daga.ta na jin lokacin da hajiyar take cewa,tsaya kaji alhaji, sai kuma tayi shiru,da alama ya katse ta ne,ya hana ta magana,don taga hajiya tayi shiru,amma ranta a bace yake.sai kuma tace to alhaji naji zan bata, amma bana son chatin din nan data keyi.MIMI ta yi murna,a ranta tace dady na kenan,ta nufi daki da murna,alhaji ya ce,kar ki damu sauda,'yarki mai kamu kai ce.ita da kowa ya shaida ko saurayi ba. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (17)Shi yasa nike dubawa don in samo mata miji wanda zai kimanta min ita,ya bata kulawa fiye da wanda take samu a guri na. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (18)Hajiya ta ce umm!allah ya taimaka,ai ni dana zaci ma baza ka iya auradda ita ba(cikin gatse tayi maganar)ya ce,kash kin ji ki da wata magana kuma sauda,in ban aurar da ita ba ai kuma na cuce ta.ina maki kaga an taba haka?ke dai kiyi mana addua,ta ce,allah ya taimaka,kun gama ganawar ne?ya ce,eh,yanzu haka muna hanyar malumfashi sai na dawo ta ce,allah ya tsare,ka dawo lafiya,ya ce, amin,ga dai uwata nan amana naba ki,katse wayar yayi ba tare da ya jira jin amsa daga bakinta ba.ga zaton MIMI tana aje wayar alhaji zata zo taba ta tata,amma sai taji shiru. ta sake fitowa falo nufin ta kila hajiya ta ganta ta tuna,idan ta manta ne, amma sai taga hajiya ta ci gaba da lamuranta.yaran duk suka yi wanka suka fito,husna da hasina suka shiga falo da gudu suna cewa,ga malam nan yazo.ga mamakin MIMI sai ta ga duk yara sun rude, wasu sun dauko alkur'anin su suna karantawa da sauran littafai da yake masu.a ranta ta ce ni ko bari in ga wanene malamin ,kai har naji na tsane shi tun kafin in ganshi.a zaton ta nan zai shigo sai ta ga abdullahi da umar da aminu da sadik sun soma fitowa bayan dawowansu sai zainab da hasana da hussaina suka fita. hasina da husna kuma sun dukufa suna ta karbarma juna hadda,kafin a zo kansu.MIMI ta tabe baki tare da cewa,wahalar da kai,basu dade ba suka dawo.su hasana sun mike kenan hajiya ta fito daga daki ta ce,ke ma tashi kije, ta nuna MIMI ta hada rai,sai dai bata da damar yin musu,don babu alhajin da zai tare mata.hasana ta ce. yaya MIMI sai kin sako hijabi fa,ta banka harara,ban dauko ba,ina wasa da ke ne?in ki ka kara yi min magana sai na mare ki. suka yi shiru suka wuce,ta warware dan kwalin kayanta ta yafa,tana biye da su har falo baki,kafin su shiga sai da suka kara gyara hijabansu suka yi sallama suka shiga,ta tsaya tana mamaki wai malami ne suke yi ma bare-baren, malamin ma wai na lslamiyya,ita malami ko na boko bata dauke shi wani abu ba,face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da ba zata iya, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (20)Saboda ba son karatun ta ke yi ba.ka soma mata daga fatiha don ba na zaton ta iya,don allah malam lsmail kar kayi mata da sauki.lsmail ya ce, ba komai hajiya.amma ta saka hijabi ta ce,to ba komai bari in sasu hasana su kawo mata,in ta ki yi ka dake ta ko ka kira ni. hajiya ta fita shi kuma ya kai duban shi gare ta, MIMI ta cika tayi tam.ya na zama hasana tana shigowa da sallama,shine ya amsa,ta ce,yaya ga shi, harara ta watso mata,ta ki amsa,hasana ta aje a hannun kujeraq da take zaune ta fita. ya kalle ta,malama ki saka hijabinki mana,cikin sauri ta dago kai ta dube shi duban tsana mai tsanani,domin ba a taba ci mata mutunci kamar yau ba a gaban kaskantacce irin wannan.ba a taba rena mata wayo ba kamar yadda shi din ya yi mata,ya ganta sarai,amma ya ce,bai ganta ba.abin yayi mata ciwo fiye da abinda hajiya tayi mata.ta harare shi sama da kasa sannan taja tsaki, malam baya daukar reni,sabi da haka sai ya hada rai tare da rufe alkuranin shi. ta ce kai waye suna da ake kiranka? ina son ka sani na wuce ka rena min wayo kuma kai baka isa ka koya min karatu ba.ya daga hannu tare da katse ta da cewa ke.ba ki da ladabi ne? gaskiya ba tarbiyyar nan gidan ba ce,domin yaran gidan nan mazansu da matansu nayi shedar su guri ladabi game da sanin darajar mutane,ke ma ina yi maki nasiha ki canza.kuma ina son ki sani karatun nan in kin yi kin ma kanki ne bani ba,don haka ka da allah yasa ki yi,ya mike ya fita abinsa. yana jiyo tsakinta gami da cewa, talakan banza kana ci a karkashin mahaifi na ka nuna ni da yatsa,to bari ka gani lokacin barin ka aiki yayi.har ya tafi ya dawo ke ma dukiyar daki ke takama ba taki ba ce,ta mahaifin ki ce,ina son ki sani ba keki ka dauke ni aiki ba bare ki sallame ni.ba kuma maula nake zuwa yi a gidanku ba,ina son ki san wannan.kafin ta sake yin wata magana ya wuce ya barta cikin takaici,lallai sai nayi maganin sa,shine mutum na farko a tun tasowar ta da ya taba fada mata abinda ya ke so, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (19)Face bawan ta mai ci a karkashin su.bare da baza ta iya bambamce shi da maigadi ko mai sharan gidansu,kosawa ma ta yi ta shiga ta gani wane gaja ne? ta jingina da kofar,sannan ta kai kallonta gurin shi,yana zaune kan kujeran zaman mutum daya sanye yake da jallabiya mai ruwan madara mai dogon hannu da maballi a hannu,tare da kwala a wuyarta.ga wani dan ado da zare mai ruwan kasa da aka yi a wuyar da hannun rigar,bata kai can kasa ba,irin dai shiga ta sunna,hular kanshi baka ce irin wanda ake kira minista. ya na rike da alkurani yana bude inda suke.su kuma su hussaina suna zaune a kasa kan kafet a gabanshi duk suna rike da alkuraninsu,MIMI ta tabe baki tare da harde hannuwanta a kirjinta,tana kare masu kallo.a ranta ta ce,tabdi,ai ba a yi mutumin da zai zo gidan ubanta ta zauna a kasa yana kan kujera ba.malam lsmail ya dago ya kalli bakin kofa da kyawawan idanunsa,duhun mutum ya gani,ya sa shi kallon gurin ya kalli MIMI da ke tsaye ta watso masa wani kallo da ba zai iya fassarashi ba.ya mayar da kanshi ga abinda yake yi.su hussaina suka ci gaba da kawo masa hadda yana yi masu 'yan gyare-gyare, suka kamalla,sannan suka soma sauran littafai. ta shiga ta zauna tare da daukan rimote ta kunna tv, ya dago ya dube ta, tamkar zai yi magana,amma sai ya fasa. ya san da gadara tazo, bayan su hussaina sun kamalla,sai hussaina tace, yaya kizo mun gama,ta kalle su cikin harara,ku fita mana, suka fita suka je suka sanar da hajiya ko mai.ita kam suna fita ta mike tana tafiyar nan tata, ta isa kan kujerar gefen shi ta zauna. ya dago ya dube ta,ya mike tare da tattara littafansa,ya nufi fita,a bakin kofa suka ci karo da hajiya zata shigo,ya dakata ta kara so suka gaisa,ta ce, har ka mata karatun?ya ce, wace kenan?ta ce, MIMI, bangan ta ba ai,hajiya ta ce aa ta shigo ciki falon, ta ce gata nan fa,ya dawo cikin falo,ok!wannan ce? na ganta amma ban zaci karatu za ayi mata ba.ita kuma bata fada min ba. hajiya ta ce,ai ba zata fada maka, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (21)Kuma tana son ya zama na karshe, takaicinta ma talaka ne shi, ba wani isashshe ba. daf da zai fita daga cikin gidan,abdulkarim ya yi masa sallama,ya tsaya suka gaisa ta hanyar yin musabaha.ya ce,ai ina ta sallama baka ji ba,ya ce, na ga fuskar ka ba walwala ko yaran ne suka hada maka zafi?malam lsmail ya ce,ko kusa ai yaran gidan nan basu da matsala sam, sai dai wata bakuwa da hajiya ta ce a koya mata karatu,amma ba yar ta bace ko?abdulkarim ya sake matsowa kusa da shi,ya ce,ba dai MIMI ba? lsmil ya ce,kamar haka naji an kira ta,gaskiya saboda ita zan iya daina zuwa gidan nan in har zata dinga zuwa karatu.abdulkarim ya ce,kai mata nuna maka halinta kenan,don allah kayi hakuri zan fada ma hajiya, kuma ina zaton ma gobe zata tafi,lsmail ya ce, shikenan ba damuwa. suka yi sallama ya fita, abdulkarim ya nufi ciki kai tsaye zuwa falon hajiya, duk suna falon,MIMI kuma tana kujerar dining,ranta cinkushe,ya kalli hajiya,ke ki ka tura MIMI tayi karatu gurin lsmail,ta ce tayi masa rashin kunya ko? abdulkarim ya ce,ta yi masa kenan tunda ya ce, matsawar zata dinga zuwa gurinsa daukar karatu to kuwa zai daina koyar da yaran gidan nan. hajiya cikin fushi mai tsanani ta rufe MIMI da fada,ta ce,in kika sake na samu labarin kin yi sanadiyar koran malamin nan sai kin sha mamakin abinda zan yi miki,sai kin yi zaton ban sanki bama,sam bare ki tuna cewa nice na haife ki.don malamin nan ya fi min ke amfani,MIMI ta sa kuka,hajiya ta ci gaba,tunda na lura karatun ne baki so,to sai kin yishi,bari alhaji ya dawo nan zai barki sai nayi maganin abinda ke damun ki a cikin kanki. MIMI ta fada daki tana kuka. hajiya ta kira layin malam tana bashi hakuri a kan abinda MIMI tayi masa,yace babu komai ai yarinya ce. washegari misalin shadaya da rabi alhaji ya dawo.ya iso cike tam,ya ce,a ba MIMI wayanta, amma ba a bata ba.sai dai yadda ya samu hajiya rai bace kamar ma har kuka tayi,sai kuma ya juya da tambayar shi kanta yana son jin abinda ya same ta ciki, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (22)Damuwa mai tsanani irin wanda bai taba gani a fuskarta ba,ta ce,ko kaji bazaka magance mun abinda ke damuna baya tausasa murya haba sauda yaya zaki ce haka?daga lokacin da muka zama maaurata shekara talatin da bakwai zuwa yanzu kin taba samun kanki cikin matsala ban taimaka miki ba?ta dube shi,karon na san bazaka...ya daga mata hannu dole ta dakata ya ce.amsa min kawai. ta ce,ban ce baka taimakamin ba alhaji,amma karon na san zai yi wuya, ya kama hannunta. matsalar kudi ce?ta ce,aa ni da yar gwal dinka ce MIMI,ta kalli fuskarsa yayi dan murmushi,ki ce abun me sauki ne,me ya faru?ta ce,ina son dai ka bar ta a nan saboda sam bata san komai kan addininta na musulunci ba. sallah har da kuka tayi,saboda allah a ce kamar MIMI shekararta nawa?amma bata yin sallah,malamin yaran nan lsmalil don ance taje ya koya mata karatu kurum, ta je tayi masa rashin mutumci. sannan ta toge tana jiran ka dawo ta ce ka kore shi.to bazan yarda ba,ita kanta ma dole ta zauna ya koya mata karatu,don baza ta koma bata yi tazama cikin jahilci, yayi shiru yana nazari.ya san dai komai za a yi bazai bar MIMI a gidan nan ba. ta ce,ai dama na san zai yi wuya ka bar MIMI nan,to ina son tunatar da kai iyaye abin tambaya ne game da kiwon da aka ba suna 'ya'ya a ranar gobe kiyama, ta mike ta fita abinta. ya fito falo.hussaina tana yin home work ya ce,ke ce da MIMI ta same ni a daki na.itama cikin kuka wiwi ta cewa dady,don allah ka kori malamin nan wallahi na tsane shi.tunda nake ba a taba yi mini abinda yayi min ba.ina son in nuna mi shi talaka ba komai bane a guri na.alhaji ya ce,uwata yi shiru ki daina kuka.zauna,ta zauna a kan kujera shi kuma yana bakin gado ya ce,MIMI ina son kibar batun koran yaron nan,domin mahaifiyarki mata zo min da zancen.ta bukaci in barki a nan ki kare hutun ki,domin ta lura baki cika son ibada c,kuma nima tunda baki son yin sallah bazan amince ba, domin abin yayi yawa kenan MIMI.don gaskiya mahaifiyarki tana da hujjar cewa in barki, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (23)MIMI ta rude,dad don allah kar ka bar ni,ka san fa ba sa so na. ya ce,suna sonki na sani MIMI,in kin dan zauna zaku shaku ni ma ba a son raina zan barki ba.ta soma kuka wiwi tana fadin dady kawai ka ce ka daina so na,please dady kar ka barni ba zan zauna ba.ya dafa ta,shikenan naji ki yi shiru zan tafi dake,amma kin san dole sai ta bata rai ko?ta ce,dad in mun tafi zata huce,ya ce aa dole mu sunkuyar da kai mu tafi da yardar ta.ta yi shiru tana tunani,ya katse tada cewa, dole mu samu wani malami wanda zai dinga koya miki karatu,don ni maba zan so a ce 'ya ta mai kyau kamarki,bata san komai a cikin addininta ba take wata dabara ta fado wa MIMI ta ce,dady me zai sa bazaka daukar min wannan malamin ba? ya kalle ta,ke kika ce kin tsane shi zaki ce a daukar miki shi?ta kirkiro murmushi,dady naga yanda hajiya ke son karatun shi ne.sai naga in shine zata fi saurin yarda in tafi.yayi 'yar dariya me wayo kawai,to zan shawarce ta,amma zaki yi karatun ko?don na sanki duk abinda kika ce kin tsana,tabbas kina nufin abinda kika fada,ta ce,zan yi dady.ya girgiza kafadarta cikin jinjinawa 'ya ta.kira min mahaifiyarkin in lallaba ta ta amince ina so ki bata hakuri a bisa laifukan da take tuhumarki, ta ce,to dady zan bata,sannan ta fita. ta sami hajiya tana jera kayanta na sawa a cikin wadirof.bayan sallamar da ta yi hajiya ta amsa ta kasa cewa komai,ita kuwa hajiya dama bata waiwayoba kuma bata fasa abinda take yiba.ta dai san MIMI ce,bayan shudewar mintunan da basu kai uku ba,sai MIMI ta soma magana cikin in'ina ta ce,emm,da mazan ce ne hajiya don allah kiyi hakuri in sha allahu ba zan sake ba.kuma zan rika yin sallah ta a kan lokaci.hajiya ta ajiye kayan dake hannunta ta dauko zata saka a cikin durowar ta zauna a bakin gado.da hannu ta kira MIMI alamun tazo,ta ce,zauna kusa dani,MIMI ta zauna. hajiya ta tausasa murya ta kalli MIMI ta ce,ina son ki sani ba ina nuna miki kuskuren ki don wani abu bane,face don rayuwarki, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (24)Tayi kyau,ba ina cewa ki yi sallah don ni ba ne,aa don kanki ne kiyi don allah.malamai suna fada mana cewa sallah ita ce abu ta farko da za a fara binciken aikin bawa in ya mutu.in tayi kyau ana sa ran sauran ayyukan sa zasu yi kyau.sallah ita ce abinda ta raba tsakanin musulmi da kafiri. lta ce ta raba mutum da dadda,sallah ba abin wasa ba ce,ki kiyaye.ki zubar da duk dabiun banza nan da kikeyi na yahudawa da nasara,wanda kike zaton na wayewa ne,to ina son ki sani ba wayewa ba ce,duk wata wayewa ta duniya da lahira addininmu na musulunci yazo da shi wancan kuwa da kika ka dauka bata ne,mu hausawa da mu ke da alada mai kyau wadda bata ci karo da addini ba.ina me yi miki nasiha da ki daina irin shigar ta kafirai,ki kama suturar ki ta aladarki da addininki,ki dauka ke da kowa duk daya ne,ba don allah yafi sonki ba ne ya sa ki ka fito a guri mahaifinki mai tarin arziki,ki muamakanci kowa kamar yadda addininki ya zana. kan MIMI kasa,kwarai ta kosa ta gama wadannan zantukan da ita sam bata ma fahimtar hajiyar.yaya ma allah yaba ta ubanta, hajiya ta ce,kar ta yi gadara?tayi dai murmushi a ranta ta ce,tab wannan ma kuskure ne,ta daga ta kalli hajiyar,dad ya ce,ki je. hajiya ta mike tsaye tare da dafa kafadar MIMI naji dadi da kika gane kuskurenki.kuma in kin canza zan nuna miki kauna irin ta 'ya da mahaifiya, murmushi MIMI tayi,wanda ita kadai ta san maanar shi, hajiyar ta fita tare da cewa karasa jera min kayan nan cikin word durop tana fita MIMI tayi dariya irin wadda ta fi yi idan taga mugunta,a fili ta ce,ka ji hajiya wai da talaka da mai kudi wai duk daya ne,ta ina suka hadu?ai bambamcin ma a bayyane yake.ai talaka wahalalle ne bayin mu ne,ita hajiya dai kawai bata waye ba ne,take irin maganar. shi kuma wawa sakaran malamin allah yasa ya yarda ya bini zuwa abuja, sai na taka shi,na ja shi,na tozarta shi,sai ya gane ya taba MIMI.lta kuwa hajiya da dadin rai ta fita dakin,na ta a zaton ta 'yarta ta soma hawa hanya, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (25)Tunda har ta soma ba da hakuri,abinda bata taba yi ba a tsawon rayuwarta.watau tayi laifi ta bayar da hakur,gani ta ke yi ta kaskanta. da sallama hajiya ta shiga dakin yana zaune kan kujera,yana duba jaridar leadership.ta zauna a hannun kujerar ga ni alhaji. ya kalle ta,kin san dai tafiya zan yiki ka koma dakin kika share ni ko?ya ci gaba,ni gaskiya wannan zuwa ba samu wa maraba sosai ba kamar baya.ta yi yar dariya,sai dana ce,kar kazo da MIMI,ai amma ka ki,duk ita ce ta yi ta dama min lissafi.ya ce,to naji shikenan,ai tunda nima nayi mata fada wasa da sallah,ta daina in sha allahu, don haka ma nike so ki taimaka kiba mu aron malamin nan na yaranki tunda naji kina yabon shi gurin kwazo da jaruntar koyar da yara,in ya so sai ki samo masu wani. hajiya ta ce,tabdi,ai ba zai yiwu ba,sai dai in a samo maku wani,ya ce.saboda me?bafa da koyarwan gidan nan kadai ya dogara ba.malami ne a makarantaru,ina zaton akwai gidajen da yake koyarwa.ka bar ta kawai ta karasa hutu a nan,na san kafin ta koma nan da wata biyu ta samu abinda ta samu.ya kama hannunta ina son ki kira shi fiye da abinda yake samu.ta ce,in har ya amince kana ganin zata yi karatun a can? ya dan matse hannunta, kar ki damu sauda zata yi,ta ce,shikenan zan kira shi,sai dai ban so ba zai bar yara na,ni dai suna karatu sosai a gurin shi. hajiya sauda ta kira malam lsmail ta ce masa don allah in yana da lokaci yazo maigida yana son ganin shi.ko yarinyar nan ce ta kai karar shi,kuma yasan halin masu kudin nan da jarabar son yaran tsiya. ta katse mishi tunani da cewa,kar ka damu alheri ne,bari ma dai in fada maka,a takaice so yake ya dauke ka zuwa abuja saboda yarinyar nan,ka dinga koya mata karatu da kannen ta na can.don allah zan roke ka kar ka ce aa, saboda nasan zai biya ka da kyau.kuma nima zaka taimake ni.ya ce,hajiya gaskiya yarinyar nan da kyar in zata bayar da hadin kai a kan karatu,ga ayyuka na a nan.ta ce,ka dai zo din a yi magana a zaune ko? [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (26)Ya ce,to shikenan in na yi wanka yanzu zan taho. sai da ya bita gidan su mahamuda abokin shi,ya isa yayi sallama mahamud ya amsa tare da cewa,dan halak!sauri nake in zo gidanku yanzu,ashe kana tafe,ya ce,lafiya dai zaka zo?mahamuda ya ce,lafiya lau,takardun nan ne na manta,wanda headmaster ya baka kayi makin na dalibai. ya ce,shaf! na manta,ko dana zo gida fa ban tuna ba.suka fito tare ya ce,in bazaka fita ba mahamud mashin dinka zan ara,zan je gidan bashir masari.mahamud ya ce,to ka sauke ni bakin kasuwa?ya ce,to ka san me zai kaini?ya ce,aa lsmail ya ce,hajiya ce ta kira ni, wai tana son in koma abuja in koyar da wannan mara kunyar da nake baka labari jiya.wai tasan zan sami kudi.mahamud ya ce, kawai kaje,kar ka manta da tarin bukatun ka wadanda kudi kawai suke so.lsmail ya ce,ina sane, matsalar kawai bana jin zan dauki rainin yarinyar ko da suna taka kudi.mahamud ya ce,ka dai je kaji in abin zai yiwu,amma dari bisa dari na baka goyon baya. A falon baki abdulkarim yayi wa lsmail jagora,ya shiga ya sanar da hajiya cewa ga malamin yaran nan tare da alhaji.suka jera zuwa falon bakin ya gaida su cikin mutumci da sanin ya kamata,hajiya ce ta gabatar ma malam lsmail bukatar,yayi shiru.alhaji ya ce,kar ka damu nasa kana koyarwa a gurare dabam-dabam ba da gidan na kadai ka dogara ba.ina son ka hada abinda kake samu a kowane wata ka fada min.in har zaka amince ni kuma zan ninka maka kudi abu daya dai da zan roke ka shine ka tabbatar yarinyar nan ta iya karatu. hajiya ta ce,ka dinga yi mata nasiha ka tsoratar da ita.alhaji ya daga mata hannu,wata irin tsoratarwa kuma?karatu dai ta ce, shikenan karatu ai ya hada komai.lsmail dai yan jinsu kanshi a sunkuye lissafi yake tsakanin amincewa ko akasinta,can alhaji ya katse mishi tunani da cewa, me ka ce?ya dago ya dube shi da nufin cewa aa,sai mutuncin hajiya da kwarji ninsu ya hana shi fadin haka,sai ya bige da cewa,a bani lokaci domin sai na sanar da gidajen dani ke koyar da 'yayansu. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (27)Na rubuta takardan barin aiki a lslamiyyar dani ke koyarwa. alhaji ya ce,yanzu dai a takaice ka yarda kenan?lsmail ya ce,na yarda,sai dai in fara watan gobe.alhaji ya ce, shikenan,nawa kake samu duk wata?hajiya ta ce,ai sai ya je yayi lissafi ko malam lsmail?ya ce,eh! haka ne.alhaji ya ce,kana da mata ne?ya girgiza kai tare da cewa aa,ina dai nema.alhaji ya ce,to shikenan,hajiya gaki nan,za ji komai gare ki.amma kafin haka zan so in san wanene lsmail?ya dago ya kalli alhaji,hajiya ta ce,wannan kaidar shi ce in dai zai dauki mutum aiki a karkashin sa,sai ya san wani abu daga tarihinsa,ko da kadan ne. lsmail ya ce,haka ne. lsmail bin abdulrahaman shine suna da aka fi kira na.mahaifina malam abdulrahaman ya rasu tun ina jss2,haifaffen nan katsina ne,dan kauyen 'yargoje.amma shi yayi gidansa a nan kofar soro.hakanan mahaifiyata ta rasu wata shida bayan rasuwar mahaifina,mu biyu ne 'ya'yanta.kasancewar tana da ciwon sikila tana shan wahala a guri haihuwa ta hakura tun daga kaina,sai aka tsaida mata,ciwon shine yayi sanadiyyar mutuwarta. kafin haka dama bata jin dadin zama da abokiyar zamanta lnna,wacce ita ce uwargida.lrin mata nan ne masu kishin tsiya,yaranta goma sha daya,kuma duk su ne manya damu,bakwai duk maza ne,sai mata hudu,kuma duk suna raye,daga cikin yaran nata, manya guda uku suna zaune a gidan yanzu haka da matansu da 'ya'yansu. dama an raba mana gado, ni na samu daki a soro,ita kuma yata dake aure a kofar soro sai aka bata wani dan fili karami dake jikin dakina ta kofar gida. lsmail ya dago ya kalli su hajiya,ku yi hakuri ina fada maku ba.nima ban san dalilin da zuciyata amince in sanar daku abinda bana son ina tunawa bama.hajiya ta ce,kar ka damu ci gaba.tunda na rasa iyayena haka na taso bana jin dadin kowa a gidamu,tun daga yayyina har ya zuwa mahaifiyarsu, babu mai biya min kudin makaranta.yaya amina kuwa,ita ma ba mai karfi take aure ba.ga yara tana dasu har biyar.don tsakani na da ita akwai tazara ta, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (28)Don tsakani na da ita akwai tazara ta gurin haihuwa,mijinta ne ya kai ni wajen koyon gyaran TV,da yake ina son karatu sosai,sai na mayar da hankali har na iya,da dan abinda nake samu na biya kudin makaranta. lslamiyya kuwa akwai mahaifin abokina malam aminu shine malaminmu na lslamiyya,shi ya dauki nauyi karatu na lslamiyyata.da ya lura ina son karatu lokacin dana kammala sakandire di nada saukar alkur'ani.haka kuma mahaifin mahamud shi ya tsaya min na samu shiga mutawassid wato js1 na lslamiyya tare da dansa mahamud.koda yake ya ce min makarantar tana da tsada,ta yaran masu hali ce,ya roki mai makarantar ya rage masa biyu bisa biyar na kudin. amma fa akwai karatu,malaman kwararu ne,makarantar reshen ta yana madina.sukan bayar da tallafi ga dalibai guda uku da suka zama zakaru a matakin difloma,don yin karatun digiri a jamiar madina.wannan yasa na zage dantsen karatu bana wasa ba.duk da karancin shekaru na malam aminu shine ya sake yimin hanyar koyarwa a wani gida,saboda in dinga samun na siyan littatafai.hakanan ina koyarwa a lslamiyyar shi wanda muka yi sauka. da wannan ne nake tallafe da rayuwata.har na kammala shekaru shida na sanawiyya,lokacin ne na samu koyarwa a nan gidan, wanda malam lsa mai makarantar mu yayi min tayi,ya ce min yaran a makarantar sa suke karatu, 'ya'yan bashir masari ne,in zan koyar dasu.ban yin gardama ba,don ina son ci gaba da difilomata a nan makarantaarmu eh-mukhtar,yau wata biyu da kammala difiloma,ta kuma nayi nasarar zuwa na uku a ajinmu,sai dai kash makarantar daza muje a madina mutum biyu ta bukata,don haka bana ciki.sai dai ko wani lokaci zasu iya neman na uku,ina burin in karanta larabci ko kuma tafsir. amma a yanzu ina da haddar sittin,ina da haddar hadisai da dama.na san tauhidi da fikihu daidai gwargwado. malamai da dama suna jinjina ma kwakwalwata. malam aminu mahaifin mahamuda yana yin tafsiri da azumi a babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (29)Malam aminu mahaifin mahamud yana yin tafsiri da azumi a babban masallacin unguwarmu,sau da yawa nine nake ja masa baki. kuma zuwa yanzu shekara ta ashirin da bakwai. ya kalli su hajiya wadanda suka yi shiru suma saurare.ya ce,shine tarihin lsmail bin abdulrahaman.alhaji ya ce, shikenan zaka iya tafiya duk yadda kuka yi zanji gurin hajiya.kuwa tausayin lsmail ya cika ta,ta ce,zan iya tambayarka?ya ce,eh zaki iya.ta ce a fannin boko fa,daga sakandire ka tsaya?ya ce,eh,amma yanzu na zana jamb domin karanta zama ban samu wancan damar ba.hajiya ta ce,ALLAH ya taimaka ya bayar da saa,zan baka 'yar shawara ka dinga ziyartan malamai don neman karin ilimi,ya ce,ina zuwa hajiya, duk asubahi ina daukar karatu.ta ce,ALLAH ya taimaka alhaji ya ciro kudi daga aljuhunsa ya mika masa,ga shi ka hau mota.ya ce,ba komai alhaji da mashin nazo ka barshi,hajiya ta ce,ka amsa sai ka sha mai. sai na ganka,ka sanar dasu. ya amsa tare da yin godiya suka yi sallam.lsmail ya buga mashin kai tsaye gidan su mahamud ya nufa don ya kai masa mashin dinsa.kuma ya gana da mahaifin mahamud,su kuma sake tataunawa a kan batun tafiyarsa abuja.cikin saa yana tsayawa mahamud yana fitowa cikin faraa,suka nufi juna lsmail ya ce,sai ka ce dama kana jiran isowa ta?mahamud ya ce,wai inna ke son alayyahu,duk ga yaran sun tafi islamiyya,suka yi musabaha tare da gaisawa,lsmail ya ce,to hau muje a mashin mana muje mu amso mata,sai da suka je suka dawo suka zauna a dakalin kofar gidan. lsmail ya kalli mahamud,ka san cewa na kasa samun natsuwa da batun zuwa abujan nan?ga shi naje da nufin ince aa ba zanyi ba, amma ban san kadarar data sana amsa ba.duk sai suka yi min kwarjini na kasa kin amincewa. mahamud ya ce,in ka ce haka ka ban mamaki,kai dana sani dakakke mara tsoro,naga ko a nan a lslamiyya da muke koyarwa duk yaran masu da shi din ne,amma shakkar ka sauke yi lsmail ya ce,baza ka gane ba,ita fa yarinyar ina zaton irin, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (30)Tabararrun nan ne ko da ban sani ba dai,amma na ga alamar kamar uban bai so a takura mata,ga ta da alamun ta tsani talaka bata dauke shi wani abu ba,ni kuma duk sun san hali na,bana son raini.shi yasa bana raina mutane,dalili kenan dana keta tunanin ya ya koyarwar tamu zata kasance?mahamud ya ce, shawarata a nan kawai ka aje duk wani waswasi kai dai ka amshi kudinka ka cika burinka. ka tuna da karatun da muke son yi,kai ko yau jamiar madina suka kira kaza ka bukaci kudi.ga yarinyar nan daka dauki son duniya ka dora mata, zainaba,kar ka manta da abinda mahaifiyarta ta ce,sadakin 'yarta dubu dari, akwatin 'yarta me shida ne,lsmail ya ce,da na tuna abubuwan nike jin cewa ya kamata in jajirce in je,yanzu dai malam nake son gani in nemi shawararsa. da ya amince zan kara samun kwarin gwiwa.haka kuwa yana unguwar har aka yi lshai, lokacin ne lsmail ya samu magana da malam,yayi masa bayanin komai,malam ya bashi goyon baya tare da karfafa masa gwiwa, cikin farin ciki ya nufi gidasu dakinsa da ke soro ya bude ya shiga ya kunna wuta haske ya gauraye dakin,ya zauna bakin katifarsa ya cire hularsa da agogo tare kuma da wayarsa ya dora a teburin da ke gefen katifar mai dauke da tarin littafai,ya ciro kudin da alhaji ya ba shi,da ma ya ba mahamud dari biyar daga ciki.ya dauko wani littafi wanda a cikinsa ya ke ajiyar kudi ya dora su a kan kudin da yake ciki,ya mayar da su ya rufe,ya mayar dashi a mazauninsa.ya dan kwanta rigin-gine gurin zainaba yake son zuwa don zuciyarsa ta matsu da son ganinta,amma yana jin jikinsa ya gaji.wayarsa ta soma ruri,yana daukowa ya ga hajiya ce. ya daga tare da sallama ta amsa ya gaida ta.ta ce, ka yi hakuri na kira ka cikin dare.ya ce,ba komai hajiya. ni mana so in kira ki,sai naga bari dai in bari sai da safe.ta ce daman na kira kane in sanar da kai cewa alhaji sun tafi dazun da mimi,ina son don mu karkare maganar ina son in sanar da shi.ka fada min albashinka,yaushe kuma za a kai, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (31)Yaushe kuma za a kai ka abujan?saboda ku soma karatun da wuri.lsmail ya gyara zama,hajiya batun albashi dai ni ba zan iya cewa ga shi ba,ta ce yauwa ni ma bana son ka ce ma shi kaza ne. don alhaji in mutum yana son ya ce moriyar shi to ya biyo shi ta haka,zan fada mishi cewa ka ce duk abinda ya ga yayi,na san zai nemi shawarata.ni kuma na san abinda zan ce masa.labarinka daka bamu a jiya na tausaya maka, kuma na tabbatar kana bukatar taimako,yanzu ka yi magana da malamin naku?ya ce,eh?gobe zan je gidajen da nake koyarwa in sanar da su.ko zuwa jibi sai mu tafi abuja din.ta ce shikenan lsmail sai ka zo jibin,ya ce to na gode, hajiya ta ce ba komai. sun yi sallama hajiya tana ji a zuciyarta lsmail tamkar danta.washegari kamar yadda ya alkawarta ya sanar da duk wanda ya kamata cewa,gobe zai yi tafiya zuwa abuja,ya sanar dasu zainaba kadai ta rage masa ya je su yi sallama. da yamma laasar ya shirya zuwa gurin mahamud don ya raka shi zuwa gurin abar son sa,su yi sallama.yana isa lslamiyyar da suke koyarwa ya samu mahamud ya fito daga ajin da yake.bayan sun gaisa lsmail ya ce mu je ka raka ni gidan su zainab in duba ta da jiki,daga nan in yi sallama da ita.ko ta zo lslamiyya?mahamud ya bata fuska,gaskiya lsmail ka je kawai.ka ga ba a ma ta shi ba.ya ce amma ka fito ajin ai,wai me yasa ne ko yaushe idan na ce muje gidan su zainab sai ka be min aa?yau dai dolenka mu je,kuma gurin ka zanbar amanar ta. mahamud ya ce,mu je dai, amma ba ruwa na da wata batun amana.suka jera a hanya ya kalli mahamud,ban san me yasa kuke jin haushin yarinyar nan ba.haka yaya amina kullun sai ta yi min korafi. mahamud ya ce,ai ban boye maka dalilin ba.yarinyar tana da karancin tarbiya,sannan 'yar mace ce.ga shi uwar ta dora dogon buri a kanta. lsmail ya ce in fadi maka ni ba wata matsala ba ce a guri na.ni dai ina sonta don allah ita ma tana so na. ln ta zo hannu na ba sai yadda na yi da ita ba? mahamud ya ce,haka kake fada. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (32)Mahamud ya ce, haka kake fada.suna isa kofar gidan suka aiki wani yaro ya kira ta.ya fito ya ce an aike ta,lsmail ya ce jikin yayi sauki kenan,ya kalli yaron,je ka ce nesa ne ta je,ko kusa ne mu jira ta?yaron ya koma,lsmail ya kalli mahamud,in nesa ne sai mu tafi mu dawo da daddare.mahamud ya ce ka dawo dai ni kan bazan zo ba.yaro ya iso tare da cewa da nisa,suna juyawa da niyyar tafiya. sai ga ta dauke da tire goro,ta tsaya cikin daburcewa irin ta marasa gaskiya.sam ba ta tsammaci zuwan su ba.don bai cika zuwa da yamma ba.ran mahamud ya yi matukar baci.duk da irin yarjejeniyar da muka yi?da ma karya ne lafiyarki lau,ki ka dain zuwa lslamiyya? zainab cikin in-ina ta ce,dama gidan wata tsohuwa kadai na kai, amma bana zuwa talla.ya ce,karya kike yi,in mutum daya zaki kaima wa,ya ya baki sa a leda ba?sai ki dora tire a kai,bayan kuma na fada miki babu abinda nafi tsana irin in ganki da wannan tiren a kai. kuma na fada na sake fada,bana son talla.kun dora min dari uku kullum, na yarda,kuma ina baku,shine zaki munafunce ni?ta sassauta murya ta ce,ka yi hakuri,ya ce,ke malama ba wani hakuri jeki yi min sallama da innarki,don bazan tafi in bar baya da kura ba.ta nufi ciki tsaki mahamud yayi,ya ce kalli irin gidan daza ka nemi aure. a ce uwar daza tayi wa yayanka tarbiya?wai kyan take birge ka ko me? lsmail ya ce,don ALLAH mahamud ka bar ni in ji da abu daya.kalli wulakancin, sama da wata takwas duk sati biyu sai naba su dubu biyu da dari daya ko dari uku.ko da ba zan ci ba, ba zan sha ba,sai na basu kudin nan.don kawai ta daina talla,ashe suna nan suna yaudara ta ne. mahamud ya be duk kai ka so,yaran mata gasu nan a fadin garin katsina masu tarbiyya da ilimi,ka kau da kai a gurin su,na san dai ka san cewa,in ba nema wa 'ya'ya uwa ta gari.lsmail ya ce,baza ka gane ba,ina yiwa yarinyar wani mugun so ne,ba zan iya rabuwa da ita ba.mahamud ya daga kafadunsa guda biyu tare da fadin ruwan ka. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (32)Daidai lokacin zainab ta sake fitowa ta ce, shigo daga soro,nan suka tsugunguna.lta ma innar ta tsuguna.suka gaishe ta,lsmail ya soma magana cikin fushi,inna nazo ne nayi wa zainab sallam zan tafi abuja.sai kuma na ganta da tiren goro,bayan na san mun jima da wuce maganar talla.eh.nina ce ta zaga da goro tunda tun shekaranjiya ya kamata ka aiko da kudin amma shiru. lsmail ya sake shakar takaici,ciki sauri ya ce,amma inna ko na sati biyu na tara ina badawa ko? ya ci gaba gaskiya bai kamata a saba mun kaida ba.inna in na bar gari sai yaya kenan,bai da be fa a saba mun alkawari ba. lnna ta dago ta dube shi, aikin gwamnati ka samu a can abujan?ya dube ta,ya sunkuyar da kai ya ce,aa koyarwa ce.ta ja tsaki ta ce,ana nan dai.ta mike ya ce,inna zan bata kudin ta kawo,ni dai roko na kada ta dinga daukar tallar nan. ina hijaban dana dinka mata ne,yau na ganta da gyale?ta daga masa hannu,dakata kai lsmail,ba fa ka bada sadakin zainab bane daza kayi ta sa mani dokoki iri-iri a kan 'yata,kuma bazan gaji da fada maka cewa ba zan bayar da 'yata inda zata sha wuya ba,kamar yadda ni na sha wahalar talaucin ubansu.'yata tana da kyau, baza maida ta baya ba. lsmail ya mike shi dama mahamud tuni ya kai waje. ranshi ful takaici,zuciyarsa tana tafasa. zainab dake cikin gida kusa da soro ta leko cikin damuwa ta ce,innarmu don ALLAH ki daina wannan zancen,wai ke kullum in zaki yi magana sai kin sako babanmu?lsmail yasa hannu cikin aljihu,zainab zo in baki sako,innar ta koma cikin gida.zainab ta kalle shi,malama don allah kayi hakuri,ya ce,zainab ni dai rokon da zan miki,don ALLAH ki rike min amana. ya sake yin kasa da murya,kin dai san ina sonki ko?ta kalle shi da manyan idanunta na sani malam.to ki kula min da kanki,yasa hannu cikin aljihu ya ciro dubu uku,ki cire kudin sati, sai ki rike saura.in na dawo zan saya miki waya saboda mu rinka gaisawa, zan turo iyayena.ta ce,to nima zan fi son ka turo din,don allah kayi kokari ka dan yi kudi ko. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (33)Da ba masu yawa bane,saboda innarmu ta daina yi maka haka. ya ce,kar ki damu shi arziki na allah ne yana bayar da shi ga wanda ya so kuma a lokacin da ya so.muna rokon shi ya bamu na halas,ta ce amin.yawwa a gidanku wace ce fatu?ya ce,me ya faru?ya tattara hankalinsa gurinta,sun hadu ne a gidan wani biki can kofar marusa,shine take cewa innarmu wai kar ta yadda ka aure ni,wai wuya zan sha baka da komai,sai dan daki daya daka gada a zaure.baka da aiki,sai kalallahu,kala rasulu.lsmail ya lunshe ido na dan lokaci, ya bude tare da furzar da huci mai zafi.ya ce,zainab don ALLAH ki toshe kunnuwanki,wadannan abubuwan duk kafin in mallake ki ne.da zarar kin zama mata ta,dole kowa ya zura mana ido.ta ce to shikenan amma wace ce fatu din?ya ce,matar wa na ce,kar ya dame ki,ni zan tafi ta ce to shikenan. sai yaushe?ya ce,sai dai na zo, don sai naje naga yanayin gurin,har ya kai bakin kofa ta ce,malam don allah kar ka manta ka samo kudin. bai iya cewa komai ba.ta shiga cikin gida shi kuma ya je ya samu mahamud suka wuce.mahamud ya kasa yin shiru,suna tafe ya ce, lsmail don ALLAH dubi irin wulakancin,don ALLAH ka yi zuciya ka bar mata yarinyar ta.lsmail ya ce,hmm ka san na sha yunkurin yin haka,amma sai in samu kaina cikin tashin hankali,ban san lokacin da na soma son ta ba.ka yi hakuri mahamud ban ki batunka ba,abin ya wuce duk yanda kake tunani.kai dai ka gode ma ALLAH tun da baka da matsala da iyayen rabia. mahamud ya ce,ko da ina da matsala da su bazan dauki haka ba,sai in bar su da yarsu.kaima ina mamakin duk zuciyar da kake da ita,ya dafa mahamud kar kaji komai,ka sa ni cikin adduarka. mahamud ya ce,ka binciki asalinsu?lsmail ya ce,yaya amina ce ta binciko,ranar take gayamin wai ubansu bakano ne.dan wani kauye wai shi kurje keya.ita kuma uwar 'yar ruma ce,can wajen safana.ya auro ta lokacin yana da abin hannunsa.'ya'yansu shida maza uku mata uku,maza ne manya mata kuwa zainb ce babba,tunda arzikinsa ya karye sai buga-buga sai ta raina shi. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (34)Sai ta raina shi, 'ya'yan ma suka raina shi,sai abinda ta ce.ta dauki dogon buri ta dora a zainab,don kuwa ta ga yarinyar tana da kyau,ita sam ba za ta ba talaka ba. sannan yaran babu tarbiya babu karatu sai talla.maza kuwa daga kwandasto sai kwasan bola,sai karamin su mai sayar da rake.ka ji bayanin da yaya amina ta yi min. mahamud ya ce,tabdijan kuma ka ji ka gani?lsmail ya ce,to yaya zan yi?ba ni da zabin da ya wuce aurenta.buri na shine in ta zama tawa zan tsaya mata ta yi karatu duka biyu.mahamud ya ce,ALLAH ya taimake ka. bayan sallar lsha suka yi sallama da mahamud kan cewa sai gobe in sun hadu, kafin lsmail din ya tafi gida, gidan yaya amina ya nufa, a tsakar gida ya same su ita da yara suna cin abinci. nan yaran suka shiga yi masa sannu da zuwa.ya ciro naira dari ya ba sadam babban,je ka sayo maku biskit,ya ruga da gudu yana murna,yaya amina ta ce,ba ka gajiya ne?haba dai.ta ce aisha dauko ma kawunku tabarma.bayan sun gaisa sai yake sanar da ita batun tafiyarsa abuja.ta ce, gaskiya na yi murna.ALLAH ya sa alheri ne ya kira ka abujan.lsmail ya ce,amin yaya ina son in na dawo in tura gidan su zainab.yaya ta ce,umm!kai dai kana son wannan zainb din yayi dan murmushi,ku taya ni da addua ALLAH ya sa haka shine mafi alhari.ta ce.umm to amin,sun jima suna hira sannan suka yi bankwana ya tafi.yana shiga gida ya kunna wayarsa ya shiga soro su ya ciro makulli dakin ya bude.ya dubi makunnin wutar ya kunna haske ya wadace dakin ya shiga.ya dauki buta ya fita zuwa cikin gida don zagawa ban daki.a tsakiyar gidan matan yayyin sa ne da 'ya'yansu suke ta hira,ya yi sallama suka amsa yayi masu sannunku ya wuce.don shi dama tsakaninsu bai wuce haka ba,sai da ya fito bandakin sannan ya nufi dakin inna,ya yi sallama tana ta gyangyadi.sallamar shi ce ta tashe ta,ya shiga ya gaida ta,ta amsa tare da cewa kananan?ya ce eh na shigo da safe ki na bandaki. ta ce,haka dai ka ce,indai nina haife ka ai don ina bandaki ka jira ni.yayi dan murmushi, [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (35)Zuwa yanzun ya saba da halin inna.ya daina jin haushin maganganun da take fada masa marasa dadi.dama zan sanar da ke ne gobe in ALLAH ya kaimu zan tafi abuja.ta ce habuja?kai ko me zaka yi a habuja?ya ce,koyarwa na samu a wani gida zan dinga koyar da yaran gidan ta tashi tsaye,can kuma ka kutsa,lallai ba shakka,ya mike,ya jima da sanin inna zai yi wuya tayi masa adduar ALLAH ya sa alheri. ya fito yasa takalmi tare da daukar butarsa.tun kafin ya bar tsakar gida yana jinta tana cewa kunji mutan gidan nan,samail ya samu koyarwa a habuja,ya fadawa mazajenku?fatu ce ta soma magana,lallai ba shakka,ya fadawa mazajenmu su a su wa?ke ma don kar a ce dai bai fada bane,kala bai ce ba ya wuce dakinsa. Da safe sai da ya shirya tsaf,sannan yayi wa yayyansa maza sallama,su kam sun yi masa ALLAH ya sa a dace.gidan su mahamud ya nufa.yayi sallama da malam aminu mahaifin mahamud sannan suka nufi gidan hajiya sauda.mahamud ya goya shi a mashin,kuma sun yi shawara a kan mahamud zai ci gaba da koyar da su hussaina. A waya ya kira hajiya ya fadi mata ya iso,ta sa ya shigo,kar ya damu ai shima tamkar shi dan gida ne.suka shigo falon baki nan ta same su,ya gabatar mata da mahamud,bayan sun gaisa ta kuma kara rokonsa a kan ya tsaya mata sosai a kan MIMI,duk lokacin data yi yunkuri ko barazanar koran shi,to ya kira ta.ta ce nasan aiki ne na baka mai wahala,amma kamar jihadi ne,ya ce,na yi miki alkawarin zan tsaya a kanta kamar kanwa ta,zan jure saboda ALLAH da kuma halaccin da ki kai mun.ya'u direba ne zai kai shi,sai da motar ta tashi sannan mahamud ya buga mashin cikin kewa.suna tafe suna labari shi da ya'u cewa yayi,gaskiya ina yi maka jajena kan wannan aiki,gara in yi aikin kwasar kashi don na tsani wulakanci,lsmail ya ce,hmm ni fa gani nake kamar wata kaddar tasa zan je koyar da yarinyar nan. wata zuciya kuma tana fada mini ALLAH zai taimake ka.ina tunawa ni NAMIJI ne,sai inga to wai meye ne abin tsoro. [01/10 12:46 pm] Abdul: STEP (36)Ya'u ya ce,ba za ka gane ba,ai ubanta zata sa ya tozarta ka.ga zagin wulakanci,lsmail ya ce, ALLAH ta zage ni sai na mare ta.ya'u don dariya sai da motar tayi kamar zata sullube masa.ya ce gaskiya kar kayi wannan kuskuren, lsmail ya ce,nanne kaduna? ya'u ya ce,eh amma ba garin kaduna ba ce zariya ce,nan dama baka taba zuwa ba?kai ni ina zaton sokoto kawai muka taba zuwa yin gasar karatu lokacin ina SS1.ya'u ya ce gaskiya ni ban zata ba,in na kalle ka sai ka ce ka taba fita kasashen duniya. lsmail ya ce,ni kifin rijiya ne ban san ko in ba.in mun zo kaduna ka nuna min ina jin labarin garin ina son zuwa. ya'u ya ce,shike nan za nuna maka,tun daga na yake nuna masa garuruwa har suka isa kaduna.ya ce, bari in bi da kai ta cikin garin maimakon by pass tunda kana son ganin garin. shikenan lsmail sai kalle-kalle ya ke yi.ya ce,garin ya birge ni.amma duk a zato na ya fi haka,yadda sunan kaduna ya cika ko ina.ya'u ya ce,zaman garin yana da dadi saboda ba su shiga harkan abinda bai shafe su ba.lsmail ya ce,wani ya taba bani labarin garin 'yan karya ne ko?ya'u ya ce eh, to ni ma dai haka na ji ana cewa,to muna da 'yan'uwa. suna zuwa katsina gurin innarmu,mu ma mukan zo,ba wasu masu karfi ba ne,amma komai za su yi sai inga suna son yin wanda yafi karfinsu,ni ma sai na amince 'yan karya ne.amma daga baya lokacin ina yin tuki a nan kaduna a wata unguwa wai ita unguwa rimi sai na gane ba wai karyace da su ba,yin hakan a jinin 'yan kaduna ne yake.ka gane malam lsmail? su mutane ne masu son yin komai me kyau,kuma basu da kyashin sayan duk abinda ransu ke so,ko da kudinsu kenan idan za a aje maka dan kaduna mai dubu dari biyar,da dan wani gari mai milyan biyar,za ka ce dan kadunan ne mai milyan biyar,wancan mai dubu dari biyar.lsmail ya ce na gane,in ko haka ne sun burgeni.saboda ni mai irin raayi na kenan,arziki na ALLAH ne,in na samu zanyi abinda nake so da halas di na.haka suka yi ta labarin 'yan kaduna har suka kai abuja garin manya. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Shi kam a ranshi 'yan kaduna sun yi mashi, yana son mutane masu test,wadanda ba komai ne ya yi masu ba. Tafkeken gida ne na gani na fada,tunda suka doshi gidan lsmail ke mamaki sai ka ce fadar shugaban kasa,duk yadda yake kisima gidan a rashi ya wuce nan,tun kafin su shiga ma kenan.su na shiga sai ya ga ma kamar wata sabuwar duniya ce,wannan mutumin wane irin kudi ya mallaka?lsmail ke tambayar kanshi. dama tun kafin su kara so ya kira hajiya ya fada mata cewa sun iso unguwar,ita kuma ta kira momi nafisa ta sanar da ita.lsmail ya na jingine jikin mota,wani matashi ya iso wurinsa ya ce,wai wanene malam lsmail?ya ce,ni ne. ya ce,to zo mu je,ya kalli ya'u direba zo muje, ya ce,a'a,ni dama aiki na shine na kawo ka,kuma na kawo ka,yanzu zan juya.lsmail ya bashi hannu suka yi sallama bayan gidan suka nufa inda suka nufa gefen yara, suka je ya bude wani daki, an ce ka shiga nan.lsmail ya kalle shi,ba mu gaisa ba?ya mika masa hannu suka gaisa.ya ce,suna na lsmail,kai fa?ya ce hamisu, kuma nine direban yaran gidan nan.ga daki na nan kusa da na ka,mu biyu ne a cikin dakin,ni da me share-share,game da kula da fulawoyi.lsmail ya ce, ALLAH ya sa mu amfani juna,hamisu ya ce,amin. lsmail ya shiga yana kallon dakin tamkar ba dakin masu aiki ba,hamisu ya ce,ai kurar dakin ba ta yi yawa ba,don kanin momi bai yi sati da tafiya ba,da cikin dakin yake.lsmail ya ce,kurar ba tada yawa ma kenan,amma duk da haka bari in dan kakkabe,ya shiga ciki sosai,hamisu ya ce,in zaka yi sallah ga bandaki nan.lsmail ya ce,tunda muka taso,duk inda sallah ta same mu,sai mu tsaya muyi ta.ya ce, shikenan baka da wani nauyi a kan ka.lsmail ya gyara daki mai dauke da katifa katuwa,sai duruwar ajiye kaya,sai kuma dan teburi a gefan katifar. hamisu ya ce,bari in sa a sanar da momi cewa ka iso,kuma naba ka masauki, yanzu saura abinci. kusan minti ta latin da fitar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (37)Kusan minti ta latin da fatar hamisu,sai ga wani kuma dauke da plate a rufe da cokali da kuma ruwa.suka gaisa,sannan ya ce,ga abincin ka.shi ma nan haka lsmail din ya sake gabatar masa da kansa, suna na lsmail kai fa?ya ce, suna na jabiru,kuma nine mai dafa abincin rana da dare,lsmail ya bashi hannu suka gaisa.bayan fitan sa ne ya bude plate din abincin, dafa dukan shinkafa ne,ta ji kifi da alayyahu,ya ci ya koshi,ya sha ruwa ya koshi.daga nan barci ya sace shi, saboda gajiya bai taba yin doguwar tafiya kamar haka ba daga katsina zuwa abuja. can da ya farka ya kalli agogo,sai ya ga lokacin sallah ya karato,nan da nan ya tashi yayi alwala,ya fito waje bakin gate don ya ga karamin masallaci a gurin. hamisu yana zaune kusa da maigadi suna hira,yayi masu sallama,suka amsa. ya ce,hamisu ina ladani ya kira mana sallah lokaci yayi, hamisu ya ce,ba a fa kiran sallah a masallacin nan,sai dai kawai kowa yayi alwalarsa ya shiga yayi sallah.lsmail ya ce,saboda me?hamisu ya ce,ni dai haka na tarar suna yi,to ai duka-duka mu uku ne ke yin sallar,ni da maigadi da mai shara.ko maigidan ba kullun yake sallah a cikin masallacin ba,ya fi yi a cikin gida.yaron sa namiji daya. ya kai shekara shabiyu, amma ko shi ba a turo shi. lsmail ya ce,ko ku uku za ku iya jam'i,don haka ni kam zan kira sallah. lsmail ya shiga ya ga da abin magana da komai,yana kwada kiran sallah daidai lokacin motar alhaji bashir tana kunno kai ko da direban ya tsaya bai fito ba,sai da ya ji karshen kiran sallah,muryar tamkar balaraben saudiyya. maimakon ya shiga gida sai ya samu kansa da nufar masallaci,gurin da aka tanada don alwalla,nan ya je ya tattara hannu rigarsa ya soma alwalla.su hamisu suka tsaya suna kallonsa, nan dai lsmail yaja su sallah,hamisu yayi masu ladanci,sai dai alhaji shi kadai ya tsaya a sahunsa. suna idarwa suka fito, lsmail ya gaida alhaji,ya nuna masa jin dadinsa da sallar da ya kira har suka yi jam'i.lsmail ya ce. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (38)Ismail ya ce,alhaji zan yi wata magana,amma in na bata maka rai ka yi hakuri,amma hakki ne a kaina in sanar da kai.bai kamata ka tsaya ba a sahu ba,duk da cewa mu din masu nema a karkashin ka ne,amma gurin allah ba bu bambamci,musamman gurin sallah.sahu dole ne,na san alhaji ya sani.tuni kawai na yi masa,alhaji ya ce.na gode ba komai,sannan ya nufi cikin gida. sai karfe tara na dare, kuku ya sake kawo masu abinci,da ya karba sai ya fito,ya samu hamisu shi ma yana cin nasa,ya aje ya ce, me zai hana mu rinka ci tare?hamisu ya ce,ba damuwa bisimillah.suna ci hamisu ya ce,na ji mamaki da na ga kana magana da maigidan nan,wai me ka ce masa ne?lsmail ya ce,wata magana wanda bai dace in fito na fada ba,a takaice kuskure ne nayi masa tuni, hamisu ya ce tabdi,gaskiya ka yi saa,ai maigidan na mu mafadaci ne na gaske. wanda bai son a shiga huruminsa,kuma yana da wata yarinya mara mutunci,wanda kowa ke tsoron ta,hatta matan gida. sai dai gaskiya yana biyan kudi da tsoka,shi ya saka ga na jure,ni ne direban yaran gidan,don haka na fi kowa wulakanta. lsmail ya ce,na san ta,kuma ni malaminta ne,na zo in koya mata karatun addini. hamisu ya dago ya kalle shi,yayi dan murmushi, lallai ina mai baka shawara,ka nemo duk wani hakuri da kau da kai,ka kara a kan wanda kake da shi.lsmail ya yi 'yar dariya,ya ce,ta taba yi maka?ya ce,to da wanda ta raina ma iri na? ban san iya sau nawa ta zuba min miyau a fuska ba.banda kalaman cin mutunci.lsmail ya ce,kai kuma sai ka tsaya kana kallonta?hamisu ya ce,ya ya zan yi,tunda ina so,dubu talatin yake biya na a wata,ba ko'ina zan samu haka ba.lsmail ya ce,sannu da kokari,amma ni kam ba zan dauki wulakancin nan ba.sun jima yana ba shi labara,kafin suka yi sallama. haka da asubahi ya kwada kiran sallar farko, MIMI wacce lokacin ta yi sallama da kalil dinta wanda suke chatin tun misalin taran dare,ta bude idanunta tana jin sabon lamari a gidansu.ta tashi ta sauko daga kan gado,ta kunna wutar dakin na ta, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (39)Sannan ta nufi windo,ta yaye labule tana kallon masallacin,wanda dama saitin windon nata yake.tabbas masallacin nan ne,to wane ne wannan da karfi hali?lta tunda ta ta so bata taba jin an kira sallah a masallacin nan ba.ta koma ta kwanta ta saki tsaki.za ta ga mai wannan kokarin na hana mutane barci.ta fara barci ta ji an sake kiran sallar,aka shiga masallaci aka yi sallah,ba ita ta samu barci ba sai da aka idar da sallah. don haka bata farka ba sai shabiyu,ta yi mika tare da hamma,ta silalo kafarta kasa kan lallausar kafet. tamkar sarauniya ta ke jan taku har zuwa bandakinta, wanda aka tsara shi da kalar pink,kalar da take bala'in so,bandakin da yafi na kowa tsaruwa a gidan, hatta mahaifinta.ta shiga bahonta,bayan ta cika shi da ruwan dumi,sama da awa daya ta dauka a wanka,ta fito.gurin shafarta daya ne da kayan sawanta, bata cika yin kyale-kyale a fuska ba, hoda kadai sai jambaki bayan mai,amma tsadarsu ta ishi talaka jari. ta saka wando baki irin mai kama jikin nan,da riga ja,ta ja dogon gashinta ta kama shi da bakin ribbon. ta soma wanka da turaruka.ta nufi gadonta ta dauki wayarta tana dubawa,miss call kusan goma dadin ta,da na dear khalil,dana hajiya guda biyu. bakin gadonta zaune tana kiran layin dadinta,ya daga tare da cewa uwata ya ya aka yi?cikin shagwaba da muryarta din nan wanda ke fid da sauti a hankali cikin salo ta ce, dad na ga miss call din ka ne fa?ya ce,uwata har na fita baki tashi ba,lafiyarki kalau ko?ta ce,eh dad,emm yawwa dad wane ne jiya cikin dare ya hana ni barci da kiran sallah?ya ce, malaminki ne,gabanta ya yi bala'in faduwa ta ce,dad shine da zuwansa zai canza mana tsarin gidanmu?mene ne nufinsa da haka?ya ce,babu komai MIMI,kin san malamai da son masallaci,yau ni mana samu yin sallar asuba a kan lokaci,sannan makwabtanmu sun shigo mun yi sallar tare da su.ta ce kash dad,yanzu gidanmu gurin tara mutane kenan? ya ce,kar ki damu musuluncin kenan,ina fata za ki sauko domin daukar karatu. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (40)Gurin malamin na ki.kuyi amfani da falon baki, ko falo na ki ke so?ta ce,aa dad ya tsaya can falon baki,ba falon ka ba,da wannan bakauyiyar kafar tashi.ya ce,shikenan tunda naima tana gida ita mata soma karatun,in su ahmad sun dawo da yamma sai yayi masu,ta ce,shikenan dad,bari in kira hajiya naga ta kirani.ya ce,ok nima yanzu muka gama waya,ki ce ina gaida ta.cikin fargaba ta kira mahaifiyarta,hajiya ta daga cikin lallausar murya ta yi sallama,MIMI ta amsa tare da cewa,ina ki ka bar waya?ta ce,ina barci yanzu nayi wanka sai naga miss cal dinki.hajiya ta ce,na zaci kin fita gurin karatu ne?ta ce,hajiya ban san ma ya zo ba sai yanzu dad ke fada. ln na yi break zan yi yanzu,hajiya ta ce,ki maida hankali saboda ki san abinda zaki bauta ma ALLAH mahaliccin ki.suna yin sallama kiran kalil ya shigo sai da yayi daf da tsinkewa ta daga,wannan wani raayinta ne.ta ce, hello dear ya aka yi?ya ce,ba komai ina son in ji muryar ki ne?yanzu ki ka tashi?ta ce, fh,yaya hutu?ya ce,ga shi muna yi,don ALLAH ina son in zo gidanku wannan karon,ina jin tsoro kamar zan rasa ki,kar ka damu dear na fada maka don juna aka yi mu,ina jin haka a jiki na. ya ce, lovely har yanzu ban yi mafarkin haka ba ina ganin sai zancen ya je gurin manyanmu.ta yi 'yar dariya, ka san fa dad naka ba zai yarda ka yi aure yanzu ba, ni kuma in dad dina ya ganka guri na kila ya ce,zai min aure,ka ga sai matsala ta samu. ya ce,na fahimce ki,ba na son na sha wahala a aurenki kamar yadda na sha kafin na samu amincewar soyayarki na garu.ta yi 'yar dariya cikin salon maganarta ta ce,dear ka manta da haka,bari na karya,ya ce,to shikenan sai in mun hadu online ta ce,tam.cikin tafiyarta tamkar mai tausayin kasa take saukowa daga benenta,wanda ita kadai ce a sama ta ke mallakin kato falo da dakuna uku.daya dakin barcinta daya kayan karatun ta,tun daga computer zuwa kasa, dayan kuwa rufe yake duk da cewa shima da komai a cikinsa. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (41)Momi nafisa tana zaune tana kallon fim a cikin tafkeken tv dake manne a bangon falon.ta waiwayo,kin fito MIMI?ta kalle ta,na fito momi an tashi lafiya?ta ce,lafiya lau, dadinku yayi ta kiran ki baki fitoba,ta yatsi na fuska,mai kiran sallar cikin dare nan ne ya hana ni barci.momi ta ce,ai malaminki ne,na ga dad dinki ya yaba da hakan.ta ce,na lura da haka a wayar da muka yi dazun. ta isa gurin karin ta hada shayi tana sha,ta dubi mahaifiyar tasu naima fa?ta ce,tana dakinta,ta dauki wayarta dake kusa da ita,ta soma kiran layin na'ima,tana dagawa MIMI ta ce,sis zo mana,naima ta fito cikin riga mai gajeran hannu da wandon jins damamme,kanta ita ma babu dankwali,ta kama gashinta da ribbo blue. ta ce,sis gani,MIMI ta daga fararen idanuwanta ta kalli na'ima cikin harshen turanci suka fi yin magana.ta ce,ki je gurin folina a kicin ki gani ko ta gasa kifin,ta ce,sis mu je snacks store mana mu ci, MIMI ta harare ta,ki yi abinda nasa ki mana,ta daga hannu,alamun ban hakuri ta rinka fadin sorry. folina ta zo,ta shirya wa MIMI gasashen kifi tare da gasashen biredi,tana gamawa ta kalli naima ina son a kira mini malamin da yazo jiya,amma ban san yaya zan yi ba,don ba za kije ba,amma ki duba in kin ga direban ku,ko wani dai ya kira shi,ta ce tam sis. lokacin da hamisu ya sanar da lsmail cewa ya je ciki ana neman sa,sai ya ce,sai mun yi sallah tukuna. don yanzu zan kira.bayan sun idar sannan ya ce,ma hamisu ya yi masa jagora zuwa cikin gidan. barandar kofar falon,nan suka danna 'yar wata danja,jim kadan aka bude. naima ce ta kalle su irin kallon da wasu 'ya'yan masu da shi suke yi wa masu yi masu hidima.ta ce, wane ne malamin?hamisu ya nuna lsmail wanda ke tsaye sanye cikin yadi mara nauyi,hularsa ta dace da yadin wandonsa a dage irin na ahalil sunna. ta kalle shi sama da kasa, ta ce,ina zuwa.kamar minti biyu ta dawo ta ce,sis ta ce,ka shigo,ya shiga dankareren falo wanda tsarin saya wuce duk tananin lsmail ga sanyi AC [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (42)AC ko ta ina.ta waiwayo ta ganshi tsaye, ka bi ni mana,ya ci gaba da binta cikin zuciyar shi yana addu'ar ALLAH ya tsare shi daga sharrin da ke cikin gidan,alherin dake ciki ALLAH ya sada shi da shi. wata kofa suka shigo inda suka iske wani falon madaidaici,shima ya tsaru ta ce,ka jira ta a nan. kusan minti biyar,sannan MIMI ta shigo falon ba tare da sallama ba,rashin sallama yana kona ran lsmail,don haka bai ko kalle ta ba.ta zauna tana kallon fuskar wayarta,ta fi minti biyar chatin ta ke yi da kalil dinta,labarin karfin halin malamin take ba kalil.ta ce, ni da zai ci a gurin ubana, amma ni yake jira in ji da shi,kalil ya ce,kin san talaka da girman kai.ta dago ido ta kalli lsmail wanda ya bude ALKUR'ANI yana karantawa a zuciyarsa.ta ce,hamm mai neman taimako baya girman kai. ya dago ya kalle ta,kafin in ce komai zan soma yi miki nasiha,da saka hijabi don suturta jikin ki. ki koyi sallama yayin da ki ka zo gurin mutane,abu na uku,ba neman taimako na zo ba,ke nazo in taimaka ma wa,don haka yanzu sai ki dauko littafi mu fara daga huruful ija'iyya.ta ce,ba ka isa ka ce za ka taimake ni ba,don baka da komai,kuma ba zanyi sallamar ba,ba zan rufe jikin ba.ln baka sani ba,barin in fada maka,na sa a kawo ka nan gidan ne saboda in tozarta ka,in nuna maka kai kaskantacce ne.ya ce,don na miki wane laifi?ta ce,kai ne mutum na farko dana taba yin sa-in-sa da shi.wanda ya taba kallon cikin ido na ya fada min magana,kuma ina son ka zama na karshe,wannan shine laifin ka.lsmail ya ce, yanzu dai za ki yi karatun ko a'a?ta ce,na ce ba zanyi ba,ya mike tare da kwashe takardunsa.ta ce,ban sallame ka ba,yayi tafiyarsa ya bar ta zaune. MIMI ta bi shi da kallo cikin mamaki,shi wannan dame yake takama,har da baya jin shakka ta,kamar yadda sauran jamaa suke ji?ya san wace ce ni kuwa?ya san wane ne ubana? Ba wani ba ne uban MIMI fa ce alhaji bashir,dan asalin masari ne,karamar hukumar kafur jihar katsina. mahaifiyarsa 'yar dabai ce,su shabiyu ta haifa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (43)Amma yanzu saura su biyar,bakwai sun rasu,mahaifiyarsu ta rasu lokacin ya kammala sakandire,yayyin shi. mata uku ne,sai namiji daya dake bin shi,rakiya da basira a malumfashi suke aure, saratu kuma tana cikin kafur,malam aliyu mahaifinsu ya sake yin aure. inda matar ta kasance mai son kanta game da son zuciyarta.wannan yasa ya bar masari,ya soma shiga cikin garin katsina don neman abin kanshi, maimakon noma da suke taya mahaifinsu,shi da shafi'u kaninsa. ya yi sana'o'i kala-kala, tun daga kan kwandastan mota har zuwa dako,daga bisani ya soma bin wasu abokansa guda biyu da suka kama shago daya su uku,da lsa mani da kabiru naalla suna harkan dabbobi. tun yana karba yana saidawa ya cire ribarsa,har ya zo ya samu jarin kansa. sannu a hankali suka yi zangonsu na dabbobi, lokaci bayan lokaci yana zuwa masari ziyartar danginsa da mahaifinsa kuma yana yi masu alheri. kaninsa shafiu har yayi aure matarsa ta haihu,don haka mahaifinsa da yayyansa kullun burinsu yayi aure.wani zuwa da yayi har mahaifinsa yana cewa,ga 'ya'yan 'yan'uwansa ya zo ya auri daya daga cikinsu,sai bishir din ya ce,yayi hakuri,shi ba ya shaawar auren zumunta,amma duk lokacin da ya ga wanda ta yi masa,to zai yi aure,amma a yanzu neman kudinsa ya sa a gaba. ranar wata jumaa lsa mani ya tare shi yana sauri za shi masallaci ya ce masa,bashir ga wadansu shanu can zaa saida su a rugar fulani nan mashi.bashir ya ce,har mashi?gaskiya da kyar zan je,lsa mani ya ce,za ka samu alheri mutumi na,don jiya na dawo tafiya,ka sani da na saye su,amma ka daure mu je in ka dawo masallaci.hardon gar ne ke son zuwa aikin hajji,shine zai cikon kudi.bashir ya ce,ni dai masallaci na nufa ga shi ina jinjina zuwa mashin nan,lsa ya ce,mu je dai masallacin nan tare ma kawai,da zanje na karfe biyu ne,in ya so daga can sai mu wuce.a masallaci suka hadu da kabiru na'allah,inda suka nufi mashi dukkan su. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (44)Sun je rugar fulani,inda suka shiga garke shanu don duba shanu.ya nuna masu,aka shiga ciniki, an daidaita kuma bashir yayi alwashin kawo kudi gobe,saboda kudi suna banki.suna cikin sallama ne idon bashir suka kai kan wasu 'yan kwailoli guda biyu,sun dawo daga tallar nono,dayar ya kure da ido, 'yar similmila ta yi masa kyau,sai da ta bace ma idanunsa,ya bar kallonta.har lsa mani ya gane,bayan sun bar gurin ya ce,bashir kana ta kallon 'yar mutane saboda me?kar dai ka ce min son wata kake yi daga cikinsu?bashir ya ce laifi ne yin hakan?lsa ya ce,aa ban ce ba,sai dai ka bani dariya kawai,duk 'yan matan da ke cikin garin katsina? ka rasa wanda za ka zaba sai wadanan 'yan ruga mitsi-mitsi da su?kabiru na'allah ya ce,in dai fulanin nan nema,ba su son baiwa bare 'ya'yaansu.bashir ya ce,ku yi min addua in rabo na ce za su bani,don gaskiya na ga wacce nake so.suka sa mishi dariya. Abin ya wuce da tunanin bashir,domin ranar da tunanin 'yar fulani ya kwana,ya kosa ya je su kai kudin shanu,don haka tun tara ya shirya ya nufi banki ya ciro kudi,daga nan suka nufi mashi. ko da suka isa burinsa ya ga yarinyar da ta hana rayuwarsa sakat, har suka bayar da kudin shanun suna kokarin zuba su a mota,amma bai ga giccin wani da ba.ya kama mota zai hau sai ya hango ta tana kada nono cikin dan kuttunsu da suke cire mai,da sauri ya fasa shiga motar ya nufi gurinta. sallama yayi mata ta dago a firgice ta ji abin kamar daga sama,ganin mutum sai ta amsa cikin dariya. ya ce,'yan mata ya ya sunanki? ta kalle shi ta ce, suna na?ta kau da kai,ta ci gaba da abinda ta keyi.lsa ya kwada masa kira daga nesa,bashir ka zo mu tafi mana,bashir gani ya ke idan fa ya tafi ya bar damarsa,ya ma rasa ta kenan,shi damuwa.don haka da ya ga abinda zai dame shi,nan da nan zai yi maganin abin,in har zai iya, musamman in na kudi ne, tunda yanzu ba laifi yana samu. sake komawa yayi ya sa aka yi masa sallama da ardo,wanda ya tafi don ya adana kudinsa.kabir yazo gurinsa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (45)Zo mu je in ya so mu sake dawo wa,bashir ya ce,ba a haka da ni,ka san ni in ina son abu,zan yi duk abinda zan iya in kuna sauri kuyi gaba zan zo.kabiru ya gane fusata ta sa bashir fadin haka,sai yayi dariya,ya yafito lsa mani da hannu, suka zosu ukun suna jiran fitowar ardo. ya ce,da muna daki daya da ku,duk ku kayi aure ku ka barni,dole ku yi min dariya.duk yadda suka dauki lamarin da zafi gurin ardo,maana ba sauki sai suka ga akasin haka.ardo yana da ilimin addini,ya fahimce su,kuma yayi masu bayanin cewa lallai sun yi dace,domin har an bayar da ita,sai wanda aka baiwa din ALLAH yayi masa rasuwa wata biyu kenan. ya kara da cewa,in yana son ta ta amince ya nemi soyayyarta,in ta amince gurin shi babu wata matsala.kwana biyu tsakani bashir ya sake yi wa rugar fulanin tsinke,cikin ado aljihu dam da kudi.lsa mani yasa shi yin tsarabar sarka da 'yan kunne,wai mutanan ruga suna son abin ado mai kyalkyali.bai samu ardo a gida ba sai babban dansa jabiru.sun gaisa inda yayi masa bayanin cewa,ardo ya je cikin gari maganar tafiyarsa aikin hajji.sai dai yayi wa jabiru alheri,ya ce, masa yana son ganin bengel,kamar yadda ya ji ardo ya ambata rannan. sai jabiru ya ce,oh!sauda? ai saudatu sunanta,ardo kadai ke fada mata bengel, na gode bari in turo ta,domin yanzu zasu fita tallar nono.yana tsugune sauda ta isko shi,tana sanye da koriyar atamfa da kuma farin mayafi mai kyalli.duk da fuskarta babu walwala farin ciki gurin bashir ba ya misaltuwa.ta tsuguna can nesa da shi,ta gaishe shi,ba tare da wata kwana-kwana ba ya ce, saudatu kina so na?rufe fuska ta yi da gefen mayafinta ta ce,ardo ba za ya bada ni ga wanda ba bafulatani ba.ta yi magana cikin hausar da bata goge ba.ya ce,kar ki damu ardo ya san da zuwa na,ya amince in nemi soyayarki. saudatu yarinya ce ba za ta wuce sha uku-sha hudu ba,sai kyau tamkar balarabiya.ta ce,in na amince me zai faru?ya ce, aure ne zai faru,ya fada cikin kwaikwayon muryarta, ya lura akwai kuruciya, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (46)Gurin yarinyar.ta ce,kamar ya ya?yanzu da na amince sai a kama aure? ya yi dariya,to me za a jira?zan turo iyaye na su gana da naki,zan bayar da sadaki da duk abinda kuke yi na al'ada,sai a daura mana aure.ta sake kallon shi,sai me daga nan?ya ce, a kai ki gida na,ta ce,ina?ya ce,cikin gari,ta ce daga nan sai me?kuma me zanyi a gidanka?ko kaima kana da shanun ne da zan dinga tatsar nono ina kaiwa kasuwarku.ya ce,aa abinci kawai za ki dafa min,sai in kin haifa min yara ki kula min da su.ta rufe fuska,zan tafi ya ce,haba da sauri haka muna hira mai dadi? ya ce,saada ce ke jira na za mu je talla.ya ce,wace ce saade?ta ce,'yar'uwa ta ce, kanmu daya,ya ce,tare zaayi maku aure?ta ce,ni kan zan tafi ta fada tare da rufe fuskarta.ya ce, ba na son tallar nan,ta ce,ni kan ina son zuwa talla,don naga kasuwa,kai kam,me ya sa baka so?ya ce,ina tsoron kar wani ya kwace min ke.ya ciro tsarabar sarka cikin gidanta ya ce,ga wannan,ta amsa da murna. tana godiya.ya sake fiddo da sabbin kudi 'yan naira goma-goma ta yi ta godiya ya ce,mata zai dawo jummaa ta ce,sai ka zo,cikin abinda bai fi wata daya ba ya mallaki zuciyar 'yar fullo.lyaye sun shiga, inda aka tsayar da rana,sai ardo ya dawo daga aikin hajji.su biyu aka hada bikinsu da saade,ita an kai ta wata rugar fulani da ke kusa da su.lta kuma saudatu can masari aka yi da ita,inda mahaifinsu ya ba su daki. satinsa guda ya koma katsina,a nan tudun wada ya nemi daki,ya koma ya dauko ta,ya saka ta lslamiyya saboda ya lura tana da karancin ilimin addini.ta kasa fahimtar cewa shi din fa mijinta ne,fa di take,yadikko,ta ce, ka da ta bari namiji ya taba ta,balle ma jikinta,ita kan ba 'yar iska ba ce. sai da ya lura ta saka hankalinta a karatu,kuma tana fahimta,sai ya samu malamin ya sanar da shi matsalarsu,nan malamin ya cire minti biyar kullum yana yin nasiha ga dukkan dalibansa don akwai me irin matsalar addini bai rufe komai ba,don haka bayani filla-filla ya dinga yi masu ya yin. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (47)Nasihar.sauda ta fahimci komai,kuma ta mika wuya ga mijinta game da neman gafarar sa,lokacin watannin su goma da aure, shi kam yayi ta ji da ita tare da kara son ta tamkar ya ba ta kamshi. sunyi shekara uku,kafin ta samu cikin farko,ta sauka lafiya danta namiji, ya ce,sunan mahaifinsa aliyu,suna kiran sa abba, kullum kara son saude ya ke yi,saboda biyayyanta da ladabi.a wannan lokacin mahaifinta ardo ajalinsa ya sauka,sun shiga tashin hankali,domin damuwarta ta tayar da hankalinsu sosai.tana nan a rugarsu har ta yi sati biyu da kyar ya lallabe ta suka dawo. Bayan iyayensu sun fita takaba,sai aka yi masu rabon gado,sauda ta samu shanu tara da raguna, saboda su biyu ne a gurin ardo,bashir ya ce,ta ba shi aronsu ya saida,zai fadada kasuwancinsa,in komai ya daidaita zai maido mata da shannunta ko kuma kudinsu. amma ta je ta yi shawara da yadikkonta,yadikko ta ce,ki ba shi,in kin san zai ba ki.sauda ta ce zai ba ni,ta ce,to ki ba shi,sauda ta tattara komai da ta mallaka ta damka ma mijinta. ALLAH ya sama abin albarka,inda kasuwanci ya bunkasa ya fadada ta hanyar bude manyan shagunan kayan masarufi, kayan abinci,shaddoji da zannuwa,ba a fi shekara ba ya soma fita irin su kwatano,togo da dai sauransu.kafin shekara biyu ya fara shiga china da dubai.ln ya sayo kaya sai ya raba ma 'yan kasuwa. daidai lokacin ne ta sake haihuwar danta na biyu,inda aka rada masa muktar.bayan ta yaye,shine suka je aikin hajji,shine ya biya masu ita da shi,da wata shekara ta zagayo kuma ya biya wa mahaifinsa. shekara daya ya bude kamfanin kansa da ake sarrafa robobi da katifu. shekarar ne ta sake haihuwar danta na uku,aka sa ma shi suna abdulkarim. lokacine ya soma nuna mata maitarsa ta son 'ya mace.ya ce,sauda ban taba fada miki ba tun cikin abba na ke son 'ya mace.ln kina da ciki koyaushe ina cikin addua,ta ce,mu ci gaba da adduar ALLAH ya bamu 'ya mace amin.sai in sa mata suna khadija,suna mahaifiya ta ce, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (48)ALLAH ya bamu masu albarka.abdulkarim ya shiga shekaru uku,amma ba ta samu wani ciki ba,lokacin ne alhaji bashir ya hadu da hajiya binta a saudiyya, bazawara ce,mijinta ya mutu,ya bar mata dukiya, amma bata taba haihuwa ba.a girme zata girme sauda,a boye suka yi ta soyayya,don ya rasa yadda zai yi ya fada ma sauda,sam baya son bacin ranta.wani dare bayan sun gama muamalarsu ta ma'aurata,sai ya rike hannunta yana me sake jaddada mata cewa sonta daban yake a cikin zuciyarsa.matuka take jin dadi a duk lokacin da ya yi irin wadannan kalaman,ta ce,ai tuni ta san haka,kuma ta yarda da wannan.ta kuma fada masa cewa,ba fa sama da shi a rayuwarta,amma in an cire yadikkota.ya yi murmushi sannan ya ce,kin san aure mukaddari ne ga kowane bawa ko?ba tare data fahimta ba ta ce hakane. ya ce,zan kara aure,da farko ta dauka wasa ne, amma jin yadda ya kuke yana ta zayyana mata inda suka hadu,da inda maganar ta tsaya a halin yanzu,sai ta mike cikin fushi ta nufi dakinta.kishi kenan,kumallon mata,rigima sosai suka yi har ta bukaci kudinta.ba da bata lokaci ba ya maido mata,sannan ta dauki matakin kaurace masa,ya yi ta lallabarta amma ta ki.ta kai kudinta gidansu,inda za a sai mata filaye da shanu.wannan ne karo na farko da ya taba kai karanta gurin kannin mahaifinta.har gida baffa ya zo yayi mata fada da nasiha,ta ci kukanta ta hakura doke. An yi biki inda aka kawo amarya sabon gida daya gina masu a sabuwar unguwa.katon gida mai tsari,sai da zama ya soma yin nisa,a nan saudatu ta gane lallai mijinta ya fi son ta.don haka ta saki ranta ta zauna da su zuciya daya. cikin wannan zaman ne ta samu cikin MIMI,haihuwar MIMI ta zo masa cikin nasarori,randa aka haife ta, rannan ya bude kamfaninsa na fulawa a kano.da ya dawo ya ga 'ya mace kyakyawa,mai kama da abar son shi wato mahaifiyarta,yayi murna tamkar ya hadiye 'yar. Yayi walima gagaruma, inda aka rinka sanarwa a jarida,gidan rediyo da talabijin,sabon abu,saudatu ta ga sabon abu kamar na fari. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (49)Wani abinda ya fi bata al'ajabi,tuni ya amshi renon jaririyar tamkar ba zai fita ba.ya na burge ta har ta soma jin haushi, domin baya kula da ita yanzu kamar da koyaushe uwarsa MIMI,wai shi sam baya son jin kukanta,duk lokacin da yaji kukanta,ya dinga fada kenan,ita kuma ga shegen kuka.sannu-sannu MIMI ta soma girma, sai ta shiga yi ma kowa kuya sai dady,lokacin zama take yi.amma in dady yana gida ko hajiya sauda bata amincewa ta dauke ta.hakanan zai iya barin kowa da komai ya lallasheta,in har tana kukan rigima.haka ta taso cikin mugun gata da rigima ga shagwaba,abin da ta ce,shi zaayi,su abba har suka soma jin haushinta, yayyanta kenan.domin kirikiri zata yi laifin da ya kamata a zane ta,amma sai a ce ko kallon banza ba zaayi mata ba.da aka tashi sanya ta a makaranta,sai aka sanya ta a wadda tafi ta kowane yaro tsada a gidan,makarantar da duk wani mai ji da kansa a katsina nan yake kai 'ya'yansa.sai wani babban abin takaici a gurin hajiya sauda yadda kirkir MIMI ta ki lslamiyya. Da ta dage sai an sa MIMI,hakan ya hakura aka sa ta,in ta je bata komai sai kuka da birgima,rannan wani malami ya dan dake ta,saboda ta ki yin shiru kuma ta ki zama ta kage a tsaye,ai ko ya gane kurensa,domin 'yan sanda alhaji bashir ya kirawo wa malamin.lokacin da MIMI ta sanar da shi cewa malaminsu ya duke ta,'yan sanda suka rufe shi,ya ce a rama wa 'yarsa dukan da yayi mata,domin shine mutum na farko daya soma dukn ta.hajiya sauda ta yi bakin ciki matuka,haka nan ita ce taje ta yi belin malamin tare daba shi hakuri.tun daga lokacin ta kawo idanu ta zuba wa mijinta da 'yarsa,ya ce ta daina zuwa lslamiyya,wai sauda ta dinga koya mata a gida,ai ita da ilimi. sauda ta ce,ai ba zai yiwu ba,a ce baza tayi lslamiyya ba,yaushe za ta san kanta bare addinita.sai ya ce,ai ita mace ce,in ta iya na sallah tunda ba waazi za tayi ba,ba limanci zata yi ba ya ishe ta.sauda ta ce,ai kuwa a dai rayu cikin jahilci. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (50)Tun daga lokacin MIMI bata kara lslamiyya ba, hajiya sauda sai ta dauki matakin tsare ta da bulala tana koya mata,in ta kiya sai ta zane ta.a kan haka suka yi rikici,wai bata son MIMI,shi ko sai ya dauki matakin tafiya da ita duk inda za shi.ta zama tamkar jaka,shi ke kai ta boko ya kuma dauko ta,ko da yana ofishinsa ne,lokacin tashi yayi zai bar komai ya je ya dauko ta.ta na gurinsa,sai zai bar ofis sannan sun koma gida tare.ln ko za shi wata kasa ko wata jihar,to fa zai kashe mata makaranta,tan gefen damansa. hajiya binta tana matukar bakin cikin abinda MIMI ke yi,tamkar ta kashe yarinyar ta ke ji.cikin haka sauda ta haifi 'yan biyu duk mata,hasana da husaina,ta yi murna sosai,tana zaton tunda ga wasu yara mata 'yan biyu ma abin shaawa,to lallai mijin na ta zai rage son MIMI,za su ture mata gwamnati ko ta samu ta yi mata tarbiyyar da ta dace,amma me?sai yana cewa,MIMI fa dabam take,da duk wasu 'ya'ya da ya haifa baya da kuma wanda zai haifa nan gaba. haka hajiya sauda ta kawo ido ta zuba masu, wai sai data kai MIMI ba ta maimaita kayan sawa,sai in ta yi raayi,ci-banza-ci-wofi shine abincinta.amma ba wai abincin kirki ba,wanda aka dafa ba,haka hajiya sauda ta yi ta haihuwarta a kai-a-kai,ta yi abdullahi sai ameen,sannan umar da sadik,a jere ta yi ta haihuwarsu,amma har lokacin MIMI ita ce ta gaba goshi.lokacin da hajiya sauda ta samu cikin husna, lokacin ne ita ma hajiya binta ta samu nata rabon. sauda tayi mata murna sosai ita mata yi farin ciki matuka.kasan cewar wannan ne farko da zata ga kwanta aduniya,lokacin data haihu an samu mace aka sa mata zainab,kishin MIMI yasa suke yawan rigima da mijin,ita wai dole sai yaji da 'yarta kamar yadda ya keji da MIMI. A wannan lokacin ne ya gina wani katafaren gidan gona a malumfashi,kuma ya gina wani gida a cikin garin malumfashi don haka sai sauda ta bashi shawarar ya maida daya daga cikinsu can tsakanin ita da hajiya binta,don ita kan bata son rigima ta gaji da takalarta fada da binta ke yi kan, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (51)MIM.ya yarda kuma ya dauki hajiya binta ya maida ta malumfashi, bayan husna,sai cikin hasina shima bata yaye husna bata same shi.wani sabon al'amari,wata jumaa sauda tana daki kwance guraren shadaya na rana,sai jummai mai yi mata aiki ta yi sallama ta ce, hajiya kin yi bakuwa.ta fito taga mace wayayya kuma gogaggiyar 'yar boko,daga ganinta kuma 'yar masu hali ce,ko kuma mijinta mai hali ne.sauda ta ba ta mazauni, ta sa aka kawo masu abin sha.suka gaisa,sauda ta ce, sai dai bangane ki ba fa? bakuwar ta ce,suna na nafisa kuma daga abuja na zo nan,na san cewa ba ki sanni ba.amma ni sai ta dan yi shiru,sauda dai ta ji gabanta yana ta faduwa. cikin zakuwa,ta ce,ina jinki?bakuwar ta ce,za kiyi mamaki idan na ce miki ni matar mijinki ce?gaban sauda ya fadi cikin daga murya ta ce,me ki ka ce? bakuwa ta ce,ni matar alhaji bashir ce maigidan nan.jikin sauda ya soma bari ta ce,karya ki ke yi, mijina ba zai yi aure ba tare dana sani ba wallahi. Nafisa ta daga mata hannu tare da cewa kar ki rantse,domin mun yi aure da shi shekaru bakwai kenan.ta nuna babba daga cikin yaranta ita ce na'ima kuma ita ce 'yarmu ta fari.sai wannan sunan ta suhaila,sai kuma wannan karamin ahmad.na'ima sa'ar abdullahi ce danki,kuma inda MIMI 'yarki tana nan zata shaida miki,domin ita kadai kawai ta sanni,ta san yara na a duk lokacin da alhaji ya je abuja MIMI tana zama a hannu na ne. Na dade ina son ya kawo ni in ganku iyalinshi,ku sanni amma yaki sai ya ce, zai kawo ni,sannan wai baya son ki tada hankalinki, ni kuma naga cewa akwai mutuwa.shi yasa tunda ya sanar dani zai tafi china ni kuma na dauri aniyar zuwa mu gana daku saboda halin rayuwa.hajiya sauda jinta kawai take yi tamkar a cikin mafarki.sai da ta lallashi zuciyarta sannan ta ce,shikenan ba komi.ku jira shi a nan in ya dawo sai ku tafi,nafisa ta ce,ni ma haka ne kudurina,ina son a nuna muga dangi,sauda ta ce, babu damuwa.kwanan su biyu,ALLAH yayi wa mahaifin alhaji bashir rasuwa a masari, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (54)Kwana su biyu, ALLAH yayi wa mahaifin alhaji bashir rasuwa a masari,da ma bashi da lafiya har misira an fita da shi,amma da yake jikin tsufa sai a hankali.nan suka tattara suka nufi masari, shima dole ya bar komai ya nufo gida,shi da 'yar lelensa MIMI,bayan an natsu hajiya sauda ta gabatar da nafisa ga dangin mijin na su.nan suka yita surutu bai kyauta ba,bai kyauta ba, wasu kuma suce giyar kudi ce.lta kam sauda cewa ta yi,ni haushi na daya,mene ne na kin fada mani,wa zai hana shi aure?kuma da ya ki kawo ta,inda ta ALLAH ta kasance a kanshi ta zo da yara ta ce ita matarsa ce za a yarda cikin sauki? lta kuwa hajiya binta zagewa tayi tana ta tsula rashin mutumci duk da cewa gidan mutuwa ne, karara ta nu na kishinta. Shima duk da yana cikin ciwon mutuwa,ya girgiza da samu nafisa a gidan, sam bai so ba.dole ya hakura ya jure masifar da hajiya binta ta dinga yi masa son ranta,ta fada ma shi maganganu.lta kuma sauda bata ce komai ba,sai rashin yin maganarta yafi daga mashi hankali fiye da masifar da hajiya binta ta keyi.sai da aka yi bakwai sannan kowa ya watse suka koma gidajensu. Daga nan yasa aka maida nafisa abuja,shi ma ya nufi katsina. Har cikin daki ya samu sauda tana shirya yaranta zasu tafi lslamiyya,sai da suka tafi sannan ya zauna kusa da ita ya ce,sauda na san nayi miki laifi,don ALLAH ina son ki yafe min, dama kullum cikin tunanin zuwa wannan ranar nake yi.ta kalle shi laifin me?ya kasa bata amsa,ta tabe baki baka yi min laifin komai ba.ya ce,ai nina san nayi laifi,ki fahimce ni,sam banyi da nufi ba. Tunanin halin da zaki shiga ne ya hana nina fada miki,saboda naga yadda muka yita samun matsala a lokacin auren hajiya binta,ni kuma bana son bacin ranki sam.ta ce,umm!ni yanzu lamuranka babu ruwa na da su,ya ce,don me kika ce haka?ta ce,na zata ni da kai duk daya ne,ko mutuwa zanyi don kishi ai ka fada min in ya so in mutu.kuma bayan kayi ma,ai sai ka fada min.ya ce,to nayi kuskure, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (55)Ai lokacin auren ne yazo babu shiri don ALLAH bari in fada miki yadda abin ya faru. Lokacin ina son sayan wasu filaye a cikin garin abuja,saboda ina son fara harkan gine-gine ina saidawa,to mahaifinta shine shugaba a maaikatar filaye, da safiyo,ni da lauya na muka je gidansa don ganawa ta musamman kamar yadda ya bukata, shine na ganta,amma har ga ALLAH ba sonta nake yi ba.don in samu saukin wannan harkan shi yasa na nuna ina sonta,kuma alhamdulillahi sai ya bani ita. su alhaji lsa mani ne suka amsar min aurenta, ban zaci zamu dade a cikin auren ba,domin nayi ne na wani lokaci,amma sai mutuncin mahaifinta,da yanda ya sakar min nake samun alherin filaye,shi yasa na hakura.abinda yasa ta kara shiga raina shine yadda take son MIMI sosai har ma wani lokaci ina cewa a ce ita ce mahaifiyar MIMI,domin bata takura mata.hajiya sauda ta ce,wato ita MIMI har da ita a munafunta ta,yayi mata kyau.ya ce,kar ki ga laifin ta,ta ce,kaima ba cewa nayi kayi laifi ba cewa,na yi don me ka boye min?ai aure ba laifi bane,na isa in hana ka yi? ya ce,ba zan kara ba,ta ce, nan gaba in zaka cike ta hudu na roke ka,ka sanar damu.ya ce,ai na gama sauda.ta ce,uhum,haka dai ka ce,ni yanzu na daina yarda da kai.ya shiga lallashinta da fada mata maganganu,tsakanin mata da miji sai ALLAH,nan dai suka sasanta tamkar basu taba samun matsala ba,har ranta tabar abin a kaddara. Tun da ya samu sauda da sauran danginsa suka san da nafisa,sai yaga bashi da matsala,tuni yake son ajiye MIMI a gurin nafisa amma babu hali saboda ina zai ce ya kaita? amma yanzu ga dama ta samu,tuni ya tattara ta ya maida ta,MIMI mata yi murna da hakan,don ta san momy nafisa na sonta. lokacin da za su tafi kalma daya ta fada mishi,alhaji tunda kana ganin zaman MIMI a can yafi guri na,to babu matsala,amma ina son kasan cewa,duk iyayen da basu sa dansu kuka ba, to wata rana sai dan ya sasu kuka ya ce,wannan kuma irin naki tunanin kenan,ni dai zan maida 'yata inda za ta samu 'yanci ta kuma huta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (56)Lallai MIMI 'yargatace,domin a dankararren gidan da ya gina a abuja maitama,an tsara gidan sama ne hawa daya,amma saman na MIMI ne kowa yana kasa,dakin baccin ta komai pink don shine kalar data fiso.dayan dakin kayan karatun ta ne a ciki,shi kuma dayan an gyara shi an rufe.lokacin shekaranta goma kacal, momy nafisa tana yin iya yinta don ganin ta danne zuciyarta ta kauda kanta ga abinda alhaji ke yi ma MIMI,ba don komai ba,sai don ta samu shiga da kuma abin duniya da yake sakar mata.amma a badini bata son MIMI,bata kamar tana sonta,kullum burinta yanda zata shiga tsakanin su,don ko makaranta da zai sata wanda 'ya'yan jiga-jiga abuja ke zuwa yasata wata rana za shi katsina shi da MIMI ya ce bari su fara zuwa malumfashi don ya gasu hajiya binta,ya kuma ga gonarsa su wuce, tunda binta ta ganshi da MIMI ta hade rai,lokacin wayoyin hannu basu yi yawa ba,sai ta ga MIMI da dankareriyar waya mafi tsada a wannan lokacin.sai binta ta bata rai ta shiga jero zantuka marasa dadin ji,tana fadin ma alhaji cewa ya cika son kai,ba shi da hakki ya bambanta MIMI da 'ya'yansa nan fa ranshi ya baci an tabo rabin zuciyarsa ya ce,duk abin da zata yi,ta yi mishi don shine ya auro ta,amma ta cire sunan MIMI a bakinta, nan fa suka yi kaca-kaca abin har ya kai su da yi mata saki daya,ya tattara yaranta guda uku suka wuce katsina. Ran sauda ya baci matuka,ta duddungure MIMI a gabansa,ya dai daure fuska amma bai yi magana ba,ta matsa mishi lallai sai ya dawo da hajiya binta,ta ta sashi gaba suka je biko, bayan binta ta dawo ne ta zo kwasar 'ya'yanta amma sai zainab taki binta,saboda suna yin wasa dasu husna,ta yi-ta yi,yarinyar ta ki dole ta hakura ta barta. bayan husna hajiya sauda ta sake haihuwar hasina wadda ta zame mata auta, don ta sha wahala a haihuwar tamkar bazata tashi ba,sai da aka yi maka aiki,alhaji ya firgita sosai don haka ya ce da likita ayi masa taimako a tsaida haihuwar.hajiya binta ta kara biyu najaatu da fadila su biyar kenan. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (57)Momy nafisa ita ma ta kara biyu mas'ud da aisha.bayan MIMI ta kammala secondary ta ce da alhaji bishir mahaifinta, daddy ni fa nafi son in fita waje america ko england ko spain.ya ce ba matsala ta zabi duk wadda take so, ya sayi hannun jari da sunanta,banda kamfanin da ya bude duk wata ribar tana shiga asusunta,sai da ya gama komai sannan ya samu sauda da batun har yana kara fada mata cewa zata fita karatu waje,hajiya sauda ta ce duk bata yarda ba,sun yi rigima sosai dole ta kyale shi. Shi kuma jin ta kushe kasashen turawa,sai ya ba MIMI shawara ya ce ta tafi dubai,tunda can garin larabawa ne,da kyar MIMI ta yarda ta tafi don yin karatun law,zabin ta shine ta zama lauya,amma in a son mahaifinta ne tayi karatu a kan kasuwanci, don ya dora ta a kan alamuransa.abba ya gama digree dinsa a kan mass com,ya samu aiki a banki,ya na kaduna,kuma ya auri samira wadda suka hadu a a ABU zariya, mahaifinta shine ambasadan najeriya a Egypt.su na da yaro daya, wanda suka sa mishi sunan alhajin suna kiran shi ta karshe,don karatun shi mai tsawo ne,likita ne fannin magunguna.shima abdulkarim shekarar shi ta karshe yake,engineering ya ke karantawa.lta kuma MIMI ta cinye shekarar farko ne ta zo hutu,za ta shiga ta biyu,wannan shine asalin su MIMI. Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula yazo ba,don haka baya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa,mahmud yana tsokanarsa,da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce,gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula.mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara,to yaya kuka yi da yarinyar nan?lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada.sannan ga mahaifiyar ta, ko don ita ya kamata ka jure.lsmail ya ce shikenan, amma fa sai dai mu zuba. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (58)Tunda lsmail ya koma dakinsa yake mamakin MIMI,har me ta dauki kanta da take wani ji da kanta haka?shi kam ba maula ya zo ba,don haka ba ya zaton zai kaskantar da kanshi,ya kira layin mahmud suka gaisa, mahmud yana tsokanarsa, da cewa mutanan abuja garin daula,lsmail ya ce, gaskiya duk da ban fita cikin garin ba a gidan da nike kadai na tabbatar cewa akwai daula. mahmood ya ce,ai mutumin nan ya shahara to ya ya kuka yi da yarinyar nan? lsmail ya ce,kai dai bari,nan ya sanar da shi duk yanda suka yi,mahmud ya ce kar ka ce zaka yi zuciya,ka natsu ka danne zuciyar ka in ta shiryu zaka samu lada sannan ga mahaifiyar ta,ko don ita ya kamata ka jure. lsmail ya ce shikenan,amma fa sai dai mu zuba. lta kuwa gimbiyar,wato MIMI,sintiri ta dinga yi a falon tana nazarin wannan mutumin wane irin hukuncin ya kamata ta yanke masa?wata zuciyar ta ce, don kin kore shi,ai ba ki rama ba,kin shirya me zaki ce ma hajiya?kar ki manta dai data gargade ki sosai sannan aka turo min ki shi.a fili ta ce,to me zan mi shi in huce?ta kalli wayarta, yawwa bari in kira mina dakingari. Bakin gadonta ta shiga, bedroom ta zauna,mina ta daga tare da fadin khadija masari ya?MIMI ta ce,lafiya dakingari,kin san mene ne? (ta ci gaba)mom di ta ce in fada miki ta dage sai wani malami ya koya min karatun islamiyya.mina ta ce,mene ne laifi?MIMI ta ce, dan rainin wayo ne,kinga yanda yake son nuna min iyaka ta?nan ta kwashe komai ta fada mata,mina ta ce,kin san me zaki yi masa? MIMI ta ce,aa,mina ta ce,in dad din ki ya dawo ki sa a kira shi,sai ki ce kina son a ware lokacin karatun ku minti talatin ko awa daya,yanda dai kika zaba, kinga ba zai taba tashi daga gurin karatun ba sai lokaci ya cika,MIMI ta ce, yawwa kin kawo shawara, kin ga sai in yi masa duk cin mutumcin da naso na tsawon lokacin,kuma dolen shi ya tsaya ya saurare ni, mina ta ce,in kin ga zai wuce gona da iri,ki mari fuskarsa,suka sa dariya ta ce,kin san ba na son taba jikin talakawa, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (59)Amma zan tsirta mishi yawu,mina ta ce,haka yayi. yaya khalil dinki? oshshh!kin tabo rabin rayuwata,yana lafiya,ya ya faisal dinki?mina ta ce,sun gama hutunsu ya koma jiya, ta ci gaba da cewa,ina mamakin irin son da kike yi wa khalil dinki,kamar ba ki tsane shi ba,MIMI ta ce,kin san me mina?can dama ina son khalil tun lokacin da na soma ganin shi,na ja aji na ne kawai.mina ta ce,don ALLAH da gaske?MIMI ta ce,ALLAH kuwa,mina ta ce,kin iya jan aji kuwa to, shikenan in kunyi waya ki ce,ina gaida shi,MIMI ta ce, zai ji.bayan sun yi sallam ta shiga nazarin mau'du'in wulakancin da ya kamata ta dinga yiwa malami. Tara daidai lokacin cin abincin su na dare kenan,ta sauko da 'yar jar doguwar rigarta da kadan ta wuce gwiwarta,kamar kullum ta yi ado da gashin kanta,kowa ya hau kan teburin,tuni yara sun soma ci ma,sai da ta isa kusa da mahaifinta ta gaida shi, sannan ta dawo gurin zamanta ta kalli momi nafisa,mommy kin dawo?ta ce,ai ban dade ba MIMI,alhajin ya ce,ina kika je?ta ce,gidan hajiya adama na je,in duba masu takalma,ta dawo daga lngila.MIMI ta ce,kin samo mana?ta ce,duk kina da shigen su,ke kuma na san baki son duk wani abin ki ya zama gama gari.amma ta ce,wasu kayan na zuwa. MIMI ta ce,mommy ki bar shi ma kawai.takalma sun min yawa,akwai wadanda har yau ban sa su ba.na'ima ta ce,sis ina wadanda ki ka ce za ki ba ni?MIMI ta ce,ki tuna min da safe,ALLAH ya sa suyi miki,ke da katon kafar nan na ki,duka suka sa dariya. Alhaji ya ce,MIMI ke komai na ki daidai aka yi maki,kuma mai kyau,kalmar ta soki zuciyar momy nafisa ta ce,duk dai dan adam tara yake bai cika goma ba,ya ce,me ki ke nufi?ta maida abin wasa. ahaji na gani ne koyaushe sai ka wasa mamarka cikin dariya tayi maganar,shima cikin dariya ya ce,kin ga laifina kenan. Ya kalli MIMI,uwata ci abinci mana,ta zuba farfesun kaza ta soma ci tana yi,tana chating,bayan sun gama ne,alhajin ke ce ma MIMI zai yi bako ranar lahadi,ina so ayi masa tarba ta musamman, [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (60)Nan zamu yi diner da shi,inda zai zo da iyalansa,sai na fi yin murna. mommy nafisa ta ce wane ne?ya ce alhaji akilu bala, ministan man fetur,MIMI ta kalli mahaifinta,dad,ka samu ganawa da shi kenan,ya ce,uwata ai yanzu mun zama abokai tamkar tare muka taso.shi yasa na gayyace shi don ya ga iyalaina,MIMI ta ce dad insha ALLAH za mu tarbe su.kiran hajiya sauda ya katse shi,ya daga bayan sun gaisa ta ce,ya binciki MIMI ko ta yi karatun,ya ce,ki daina damun kanki sauda,za ta yi,suka ci gaba da maganarsu,jin haka ne bayan ya gama wayar ya mike daga kujerar ya nufi dakin shi,MIMI ta ce.amma dad dama ina so muyi magana a kan malamin nan.lna son a tsaida lokacin da zan dauka,don koya min karatu,ya ce kamar ya ya?ta ce,dad yau karatun minti hudu ya yi min,ya ce, ok na gane,da safe zan neme shi mu yi magana.ta ce,ok dad ni ma zan fito da wuri don a yi komai a gaba na ya ce,to bari in shiga ciki,ta ce tam,dad ni ma zan koma sama ne sai da safe ya ce,ALLAH ya kaimu. lsmail yana tsaye bakin kofar falon,tunda ya danna baa bude ba,kusan minti biyu,ya sake dannawa sai lokacin aka bude,daga ganinta 'yar aiki ce,kuma ba musulma ba ce,ta ce kaine malam?ya ce eh,ni ne,ta ce, ka shigo,a nan cikin falo ya same su dukkan su,ya kalli alhaji cikin girmamawa ya gaida shi,sannan ya gaida mommy nafisa,ya ce gani alhaji,malam hamisu ya ce,kana nema na. Alhaji ya nuna masa kujera zaka iya zama a kan kujera,MIMI ta kalle shi da gefen ido,aa dad kar ka bashi damar zama a kan kujera,ya kalle ta,saboda me?ta ce,dad bai kai matsayin ba,shi mabukaci ne a gurin mu,ta kalle shi, zauna a kan kafet,ya danne zuciyarsa,babu damuwa in maganar ba mai tsawo ba ce zan iya tsayawa alhaji,alhajin ya ce,kar ka damu zauna a kan kafet din abin ya bawa lsmail mamaki,amma sai ya zauna saboda alhajin ne ya bukaci hakan.ransa ya ce, lallai dama an ce karshen zamani baiwa zata haifi uwar gijiyarta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (61)Muryar alhajin ta katse shi,malam wanene ma sunanka?ya ce lsmail, alhaji ya amshe da cewa, yawwa lsmail,MIMI ce ta bukaci ka sa lokacin da za ku dinga yin karatu,da kuma tsawo lokacin da za ka dauka gurin yin karatun. lsmail ya ce hakan yana da kyau,wane lokaci ne ta tsaida?alhajin ya kalle ta, uwata wane lokacin ki kafi so ya koyar da ke?ta dan yatsina baki sannan ta kalli damfareren agogonsu a jikin bango kirar dubai,ta ce, kamar sha daya sai ya dinga zuwa don kada ya ce sai an aika a kira shi,ni bana son jira,nafi son a jira ni.lsmail ya yi dan murmushi a ransa ya ce,son kai, amma a fili sai ya ce,to mu tashi nawa?ta kalle shi sama da kasa.tsawon awa daya za mu yi gurin karatun.lsmail ya kalli alhaji, ba damuwa kullum zan zauna karfe shadaya mu tashi sha biyu kenan.ba lallai hakan ba ta katse shi. zaka iya zuwa misalin sha daya ya zama ban sauko ba,kai dai in ka zo shadaya daga lokacin dana sauko, daga saman na zo gurin karatu shine zaa dauki awa daya,lsmail yayi murmushin takaici,babu laifi matsawar lokacin sallar azahar ba zai shigo ba,alhaji ya ce,sai batun albashi,hajiya ta ce min ka ce duk abinda aka baka,lsmail ya ce haka ne. alhaji ya ce,aa zai fi kyau ka fada,lsmail ya ce,alhaji me karantarwa ladan shi yana gurin ALLAH,abinda zaa ba mu kyautatawa ce,alhaji ya ce,to da kana samu dubu hamsin a wata?lsmail ya ce,aa gaskiya basu kai ba,ya ce,to zan dinga baka dari. da sauri lsmail ya kalle shi, sai MIMI ta fashe da dariya kudin sayan kayan kwalliya na kenan fa,ta kalli na'ima, dubi yanda ya rude,ashe ni ma zan iya biyan shi da kaina,alhaji ya ce,ka iya tafiya,sai lokacin ya yi.lsmail ya ce to,tare da mikewa, ransa bace ya fita,lallai yarinyar nan 'yar wulakanci ce,anya kuwa zai jure?. Alhaji ya kalli MIMI,uwata ki daina irin wannan a gaban mutum.ta kalle shi,dad wallahi duk duniya ba wanda na tsana kamar shi,na'ima ta ce,shine to zai dinga yi miki karatu?ta ce, eh,amma na tsane shi,ta ce to mu fa karatun mu yaushe ne sis? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (62)MIMI ta ce,ku kan sai karshen sati.alhajin ya mike cikin murmushi bari na fita,mommy nafisa wadda kallo ya daukar mata hankali,ta mike don yi masa rakiya,ya shafi kumatun MIMI ki yi min addua uwata, ta ce,sai ka dawo dad ALLAH ya baka saa,na'ima ta ce,sai ka dawo dad,ya ce,yawwa na'ima. mommy nafisa ta zauna a kan kujerar madubi tana kallon na'ima wadda ta fada kan gado ta yi ruf da ciki,ta ce,na'ima taso ki ji,ki taso mana na'imata,ta dago fuskarta da jurwayen hawaye,ta ce,mommy dad ba ya so na,komai sis MIMI, ni kam na gaji.nafisa ta ce. amma me nike fada miki kullum?ba ke kadai ba ce yake yima haka,ku duka ne, amma nayi miki alkawarin sai ya so ki fiye da MIMI. na'ima ta soma kuka,na gaji da jin haka mommy,sai yaushe ne haka zata faru?mommy nafisa ta tashi ta koma bakin gado ta zauna,ta janyo na'ima zuwa jikinta,kar ki damu,mu bi a hankali da sannu za ki zama 'yar gaban goshi. akwai shirin da na jima ina shiryawa,na'ima ta kalle ta da gaske?mommy nafisa ta ce,kar ki yi shakka.ta share hawayanta,shikenan zan so in yi kamar abinda take yi,ko kuma fiye suka sa dariya. Shadaya daidai lsmaik ya shiga cikin falon,bayan me aikin ta zo ta bude,na'ima ce kadai a falo tana kallon fim din india,ya ce,ki fada mata nazo,ta yi mishi kallon banza,ba ta ce, in kazo ka jira ta bane?ga falon da kuka zauna can a jiya,zaka iya jiranta a ciki.ya nufi falon ransa bace,anya rayuwar gidan nan zata yiwun masa?mintinsa goma shabiyu,sannan ya soma da jin kamshin turaren ta,gabansa ya fadi,ta ja kofar wadda ta kasance ta gilashi,kallo daya ta yi masa yana sanye da jallabiyya fara sal,ya yi kyau matuka,ta tabe baki,ta zauna shima ya kalle ta kamar koyaushe shigarta babu tsari,ya kauda kai,ya ce,ta ina za mu fara?ta daga wayarta ta sa a kunne,hello dear ka tashi lafiya?ta dai yi jim,ok zamu yi waya anjima,yanzu ina tare da talakan nan ne,sai kuma tasa dariya,khalil kenan sai anjima din.ta kalli lsmail me ka ke fada?ya ce,ta ina zamu fara? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (63)Yanda ya kafa mata ido hadi da hade ranshi,sai ta ji yayi mata kwarjini,ba za ta iya kallon shi ba,yayi da zata yi masa rashin mutunci,ta kauda idanunta gefe,ko ta ina ka fara mana,ka tsare ni da idanunka,yayi dan murmushin takaici,ya ce,to zamu fara daga huruful hija'iyya,alifun kenan.ta dube shi da sauri tun ina 'yar nursery na yi wannan, yanzun kam university nike, don haka sai ka koya min karatun da yayi daidai da ajina,lsmail ya ce,zan so in baki shawara,dul me neman ilimi ko bana addini ba zai fi kyau ya zama me biyayya da saukar da kai, girman kai ba ya kai mutum ga gaci. ta daga mishi hannu,baa dauke ka don ka bani shawara ba,an kawo ka ne kurum ka koya min karatu. ya ce,to bari mu fara daga fatiha sai mu shiga bakara zuwa kasa ko?ta tabe baki,ina jin ka,ya ce,zan karanta miki kamar sau uku,sai ke ma kiyi.tunda ya soma karatun danna wayarta ma take yi,ya gama ya dube ta,yanzu sai ki karanto fatihar in ji ke ma daga nan sai in dora miki daga bakara aya biyar-biyar zamu dinga yi duk kwana biyu sau biyu a sati sauran kwanakin kuma sai mu saka fikihu,hadisi da tauhidi.ta ce,me kake fada ne?ni fa duk ban jika ba,ya ce,karatun na ce kiyi,ta harare shi,yanzu fa ka ce, sai ka fara sannan zanyi ya daga murya,kina nufin baki ji karatun da nayi ba?ta ce,shine gaskiya,da kayi ai da naji,ya rufe kur'anin cikin takaici,ya zuba ma kafet din kasan idanu, shi kam ya gaji.ta katse mashi tunani,a banza zaa ba ka dubu dari?ya ce,in na fasa koyarwar fa?ta ce,ka rasa,zan fin son ma ka ce ka fasa,don ni dole idanu na suke kallon fuskar ka,kuma bana son in kore ka saboda hajiya zata yi min fada,amma in ka tafi da kan ka shikenan. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (64)Ya ce,yanzun zan kira hajiyar in fada mata komai,gabanta ya fadi,ta yi shiru cikin fargaba. ya ce,zan fada mata komai don kar ta zarge ni,ta ce,bari in riga ka fada mata,ga mamakinsa sai ya ga ta saka wayarta a handsfree ta kuma kira layin hajiyar,ba ta jima tana ringing ba ta daga.sun gaisa ta ce,ya ya kuwa karatun ki na yi?ta ce eh! hajiya yanzu haka ina kan yin karatun,na kira ne nayi miki godiya,ki yi wa malamin godiya in kun yi waya,don ina fahimtar karatunsa,ta ce,ai lsmail yana da himma ALLAH ya taimaka,ta ce amin,suka yi sallama. ta kalle shi,ka gane nufi na?na san yanzun dai za ka ji nauyin ce mata bana karatu,tunda na ce ina fahimtarka,ka ga kenan sai ka nemi dalilin ka na kin koyar da ni da zaka yi,yayi banza da ita ya ci gaba da kallo agogo minti goma da suka rage sun yi mishi nisa,sai da ya ga saura minti biyu,ya kalle ta, tana ta chatin,ya ce,ki yi amfani da lokacin ki tun kina da kuruciyarki,ki nemi sanin addininki sannan ki bauta ma ubangijinki kafin lokaci ya kure miki.ta ce,kai har ka samu sake da yawa irin haka ne?ganin ka ka kai ka dinga fada min magana son ranka ne?ya yi murmushi,in kin gaji da kallon kyakyawar fuskata zan tafi,don lokaci ya cika, kin san lokaci baya jira. Ta mike tsaye,shima ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,har wani kyau ne da kai? [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (65)Dube ka,ya ce, sosai kuwa,don na san nafi ki nesa ba kusa ba.ta ce, karya kake yi,na sha jin mutane suna gulmar kyau na,ban da wadanda suke fada a gabana.ya yi 'yar dariya,da son ya cusa mata takaici,sanna ya ce,ina zaton suna tsoron ki ne,ko jin nauyin ki,ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau su fada maki tsakani da ALLAH.ya kalli agogo,kash har na kara minti biyu,ya face,kafin ta kai ga cewa wani abu, ranshi kar,ya san cewa ya guma mata.don ya san mata ko basu da kyau,sun tsani a fada,shi kuma yayi ne kawai don shakar da ita,bai yi nisa ba,ya ji ta saka kuka,sauri ya kara ya fice daga gefen na su. Mommy nafisa ta fito da sauri jin kukan MIMI, abinda ta dade bata ji ba, ta ce, mene ne?MIMI ta ce, mommy kalle ni sosai da gaske bani da kyau? mommy ta ce,in ji wane makahon?MIMI cikin shagwaba ta ce,wancan talakan malamin mana, mommy nafisa ta ce,barshi kawai karya yake,MIMI ta ce,bari dad ya dawo dole ne malamin nan yayi kwanan cell,mommy ta ce,ki share shi ne kawai, hajiya sauda ba za ta ji dadi ba,in har ki ka kai shi gurin 'yan sanda. MIMI ta yi samanta cikin matsananciyar damuwa,kai tsaye dakin ta ta wuce,sai gaban madubin ta na jikin sif dinta,don shine zai nuna mata siffarta tun daga sama har kasa,ta dinga juya kowane gefen ta tana kallo,zantukan malamin suna yi mata yawo a cikin kai.ki je ki roki masu fada maki cewa kina da kyau,su fada maki tsakani da ALLAH,wadannan kalaman sun sa ta a cikin rudani,ta dauki wayarta,ta kira layin na'ima,bayan ta daga ta ce, ki je ki ce ma hamisu direba zamu fita,na'ima ta ce to sis,ni ma zan bi ki,cikin tsawa ta ta ce,aa ki je aike na kawai. gidan su amina dakingari ta nufa,mina ta yi mamakin ganin MIMI ba ko sanarwa,bayan sun shiga daki,MIMI cikin kuka ta ce, mina don ALLAH ki fada mun gaskiya tsakani da ALLAH.mina ta dafe kirji,me ya faru MIMI?MIMI ta ce,ni dai ki fada min,ina da kyau?,mina ta ce,ko makaho ya shafa,MIMI ya san kina da kyau sosai ma. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (66)Wai duk me ya kawo wannan tambayar? MIMI ta ce,hum!wannan malamin ne talakan banza nan dai,MIMI ta sanar da ita yanda suka yi.mina ta yi tsaki,na zata ma wani na kirki ne ya ce miki haka,ya fada ne kawai don ya baki haushi.ke to me zai dame ki tunda ba khalil ba ne ya ce baki da kyau!ln duniya za a taru a ce baki da kyau, na tabbata khalil ba zai ce ba. MIMI ta sauke ajiyar zuciya,ta isa gaban madubin mina tana kallon kanta,ta ce,mina cewa fa yayi kawai ana dai jin tsoro na ne ake cewa ina da kyau,mina ta zo ta dafata, kar ki ruda kanki MIMI,dube ki fa doguwa fara sal ga gashi har baya,idanuwanki masu haske.MIMI hatta hakoranki abin birgewa ne, so kar ki damu kanki.MIMI ta dauko wayarta ta soma kiran layin khalil,ta zauna daidai lokacin da ya daga ta ce,zan tambayeka wani abu,ka fada min gaskiya.ya ce,ina jin ki,ta ce,kana so na?ya tausasa murya,haba khadija wannan tambayar ai kin dade da sanin amsarta,amma in kina son in sake maimaita mi ke ne, sai in ce ina sonki,ina sonki sosai fiye da yanda ni ke son kaina,ta ce,saboda me kake so na khalil?ya ce, abubuwa da dama khadija, amma daga ciki akwai halinki da kuma kyawunki, MIMI ta ce,hali na kuma? khalil ko dai gaskiya ne mutane basa son fada min gaskiya?ban taba jin wanda ya yabi hali na ba, daga daddy na sai mommy nafisa,sai kai yanzun,ta kashe wayar,hawaye na zuba mata. Mina ta ce,MIMI kin cika son sama kanki damuwa, wani banza talala ya rikitaki duk ki damu kanki,ki dawo hankalinki mana? wayarta ta soma ringing ta duba ta ga khalil ne ta jefar da wayar.mina ta ce,shi kuma me ya shafe shi? MIMI ta ce,tsakanin da ALLAH mina kin taba jin wanda ya ce,ina da hali mai kyau?hatta mahaifiyata kullum fada take yi min in gyara hali na. ke ma in na yi wani abu,kina ce min irin hakin nan ba shi da kyau,amma yanzu khalik yana min wai yana sona don hali na. maganar malamin nan ta zama gaskiya,kenan masu cewa ina da kyau basu fada min gaskiya. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (67)Mina ta ce,oh my god,don ALLAH ki daga wayar khalil,in kowa zai ce halinki ba kyau,khalil ba zai gani ba,don so yana hana ganin laifi,ka da ki dama ma kanki lissafi,shawara ta ki kori malamin nan ki huta mana.MIMI ta ce,kina nufin khalil iyaka gaskiyar shi ya fada min?mina ta ce kina dai karatun englis novel na soyayya dama baki fahimtar komai?MIMI ta yi shiru tana nazari,can ta yi ajiyar zuciya,ta dauko wayarta daidai lokacin khalil ya sake kira.wanda ba ta san ko kira nawa kenan ba.ta daga muryarta tana rawa ya ce,khadija fada min gaskiya nayi miki wani laifi ne?ta ce,aa na i ka ce kana so na don hali na,ni kuma kullum kowa ce min yake ba ni da hali,fada min gaskiya.ya ce,ni halayen ki sun mini,ko da ba su yi ma kowa a duniya ba,zan iya yin komai a kan sonki,ki yi min izini in zo abuja mu yi magana a cikin tsanaki.ta ce,na fada maka dad dina bazai so ya ga ina hira da saurayi bai san lokacin da muka hadu ba,ka bari na bashi labarin ka,sai ka zo ku gana.ya ce,ko wani guri daban sai mu je, in na zo sai mu yi maganar kin ji?don ALLAH dama ina son ganin ki,ta yi shiru.can ta ce shikenan,gobe ka zo, amma zan turo maka address din gidan su mina sai mu hadu a can,ya ce, shikenan sai kin turo,ki kwantar da hankalin ki kin ji?ta ce,babu komai. mina ta riko mata hannu, kar ki damu da sauraran shi,ki kore shi kawai.MIMI ta ce,bani da damar yin haka, don dazun na kara daure kaina na fada ma hajiya cewa ina jin dadin karatunsa ina fahimta,in na ce a kore shi bisa ga wane dalili?mina ta ce,kin hadu da alakakai,ta tashi,bari in je gida,duk da haka zan nemi shawarar mommy nafisa a kan shi.lokacin da ta iso gidan mommy nafisa, mommy nafisa suna dakin na'ima suna tattaunawa a kan matsalarsu,wato MIMI, mommy ta ce,na'ima ai na ji dadin zuwan malamin nan,saboda na jima ina son in ga ran yarinyar a bace,sai dai ni bani da damar in bata mata.na'ima ta ce,don ALLAH mommy kar ki bari ta kore shi,ai ni ya birgeni da yake mata abinda take yi wa mutane. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (68)Kira da take yi wa mommymomy shine ya sa ta yin sauri ta fito daga daki,ta ce,ya ya ne MIMI,kin dawo?ta ce,eh,ni mommy kina ganin ba zaifi kyau in kori malamin nan ba? mommy ta ce,a'a bana son hajiya sauda ta zarge ni,don haka kiyi hakuri 'ya ta, bari in sa folina ta kira shi,in gargadeshi,don kada ya ci gaba da fada miki magana,ta ce,shikenan, amma ina son a yi mashi fadan a gabana don ya san ni ba sa'ar shi ba ce. Haka kuwa folina 'yar aiki ta kira lsmail,a gaban MIMI tayi mi shi gargadin kar ya kara cewa ba ta da kyau.ya ce,lnsha ALLAHU, ko ba komai dai lsmail ya ji dadin bata mata ran da yayi. A katsina kuma kwana biyu da tafiyar lsmail zainabu ta soma yin tallar ta,kuma a ranar ne ta hadu da wani alhaji,babban mutum ne a shekaru haka kuma a aljihu.direban shi ya tura ya tsaida ita,ya tambayi sunanta da kuma gidansu,ba ta boye ba don mahaifiyarta ta shirya mata cewa,ta saurari duk wanda ya zo,tunda lsmail ba ya gari,a nan ma za su samu kudin siyan mata kayan kicin.zainabu tana son lsmail sosai,don haka ta yarda tana son ta ji ana yin zancan auran su.alhajin ya zo da dare kuma ya tura uwar da kanta ta dinga gyarawa zainabu kwalliya har zaure ta rako ta, tamkar ta bi ta wajen a yi hirar da ita,tunda 'yar ta ba ta labari,ta ji a jikinta cewa irin wanda ta ke so ne ya zo.alhajin yaji dadin fitowar zainabu,don yarinyar ta yi masa,ya ce mata auranta zai yi,shi sunansa alhaji lawal,ta ce,ta yarda,da zai tafi nan ya cika su da kudi masu dama,wanda suka sa mahaifiyar rawa,ta kuma yarda cewa 'yarta ta samu miji. washegari da safe lsmail ya kira mahmud ya roke shi don ALLAH ya kaima zainabu wayarsa, don yana son su gaisa yaji muryarta,mahmud ya ce,shi fa ba ya son yaje ne a raina mishi wayo.lsmail yayi ta rokon shi,da kyar ya yarda,ya ce,zai je da yamma.suna gama waya ya mike ya debi takardu don zuwa cikin gida koyar da 'yar mulki,sunan da ya fi kiran ta kenan in zai yi maganar ta da hamisu direba. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (69)Ta fi minti talatin sannan ta fito,tunda ya ga hakan ya san yau akwai matsalar da ta fi ta kullum. ALKUR'ANI da ma yake karantawa tun kafin ta zo, ta kalli inda yake,ta ja tsaki ta zauna,ya kai aya sannan ya dube ta barka da shigowa fatan kina lafiya? ta zaro ido,ba ruwanka da lafiya ta,ko kai likita ne? bai ce komai ba,amma idanunsa suna kallon ta,ta ja tsaki tare da fadin aikin banza shishigi kawai.ya ce, ki na ji na ko?yau ba neman fada nike yi ba,don ALLAH ki tsaya mu yi karatun nan shine ya kawo ni garin nan,ni na roke ki kin ji?ta ce bazan yi ba,ya ce, to zan kira mahaifiyarki in fada mata gaskiyar komai, sannan ni kuma in tafi abina,na soma gajiya da zama haka.ta ce,zan so haka,na fi kowa son ka tafi don na tsani kallon fuskar ka,amma bai kamata in barka ka tafi haka nan ba,ya kamata ni ma in yi maka abinda ba zaka mance ba.kamar yanda kaine mutum na farko da ka soma cusa min bakin cikin da bazan manta da shi ba.ba a taba bata min rai ba tunda ni ke sai kai,ya yi shiru,don shi ya gaji da wannan wasan kwaikwayon,ya ce,to in na baki hakuri fa?ta ce,ka rike kar ka bani don bazan karba ba,ka barni in rama. ya ce,ba laifi,daga nan yayi banza da ita,sai kuma ya mike tare da kwasar littafansa,ta ce,na sallame ka ne?lokacin ka bai cika ba,ya ce,ba amfanin zaman,tunda ba karatun zaayi ba ya ta fi abinsa. yana zuwa dakin shi ya kira hajiya sauda da nufin ya fada mata komai,suna gaisuwa sai ta soma yi masa godiya har ya kasa fada mata,suka yi sallama, ya kwanta yana tunanin abin yi.haka suka yi ta yi har ranar lahadi,wacce ta kasance ranar da alhaji bishir zai amshi bakuncin sabon abokinsa,ministan man fetur.karfe takwas zai zo,amma tun shida an hana kowa sakat a gidan.girki an yi shi yafi kala goma,ban da nau'in kayan sha na kanti,ga busassu tun daga kan goro dabino,kayan marmari ma gasu na kala-kala.takwas zai iso gidan, don haja zuwa lokacin kowa na ta shiri.ya kira alhaji bishir ya ce,alhajin ALLAH zan zo fa da nawa iyalan ne. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (70)Alhaji bishir ya ce,na yi murna sosai,ina yi maku maraba. Ya fito daga dakinsa yana kiran nafisa,ta fito cikin sauri tana cewa,sun iso ne?ya ce,aa da iyalansa zai zo,ta ce,ALLAH ya kawo su lafiya.cikin azama ta shiga dakin na'ima ta same ta tana yin kwalliya, sai ta ce,yawwa na'ima ki yi gayu sosai,da iyalansa zai zo,inda namiji kiyi kokari ki ja raayin shi,ta haka ne za ki samu shiga gurin dadinku.zai so ki fiye da MIMI,na'ima ta ce,ya fada ne?mommy nafisa ta ce,aa ba ya fada bane,kin san yana son zama kut-da-kut shi da minista,in surukanta ta shiga tsakanin su yaya kike gani?na'ima cikin murna ta ce,zan yi kokari, amma in shi kanshi ne mommy ai yayi tsufa. ALLAH ya sa yana da yara maza mommy,nafisa ta ce,ina ruwanki da tsufansa?daura shi zaki yi a wuya?kudin muke bukata, ballantana a ce kin haihu,randa duk ba shi mu sha gado,ga gata gurin dadinku,na'ima ta ce,lnsha ALLAH za ta yi hakan. MIMI tana daki tana shirin ta,ita ba gwanar shafa abubuwa rakwacan ba ce,amma man ta da hodar ta zuwa turare tsadarsu ta isa.jambaki kurum ta shafa pink ta saka riga da wando damammu bakake a sama ta dora pink din shimin kayan ta zo mata gwiwa,ta tattare gashin kanta zuwa gefe ta kama shi da pink din ribom kasa-kasa,ta fesa turaranta na yau da kullum,don ta fi son turarukan arabia,takalmin ta flat baki mai ratsin pink. ta dauki wayarta daidai lokacin da wayar ta soma ringin,ta daga dad ya ce, uwata sauko sun iso,ta ce to daddy.lokacin da ta sauko falon kasan babu kowa,sun tafi tarbo bakin, bata bisu ba,sai ta samu kujera ta kame.suka shigo da sallama,ta tashi ta nufe su,matar minista ce suka shigo tare da mommy nafisa,sannan su alhaji bishir din,sai wani saurayi sannan na'ima da wata budurwa saar MIMI,sannan kananan suka shigo tare da su ahmad.kan kujerun fakon alhaji suka zauna,sun gaisa inda suka gabatar da junansu,ko in ce alhaji akilu ya gabatar da iyalansa.ya nuna uwar,ga madam dina hajiya bilkisu,sai yaro na na farko abbas. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (71)Ga shi nan ina ta fama ya yi aure yaki.ya gama karatunsa,yanzun yana aiki da central bank ne,alhaji bishir ya ce,ya kamata kam a yi aure.abba zai shekara talatin ko?alhaji akilu ya ce,talatin din ce kuwa,alhaji bishir ya ce,saan abba kenan dana na fari.shi kam yayi aure har sun yi min takwara, alhaji akilu ya ce,ka gani ko abinda ni ke buri kenan in ga 'ya'yan.alhaji bishir ya ce,ka kokarta ka ji dana? abba cikin murumushi ya ce,lnsha ALLAHU. ya nuna ta mace,waccen kuma aisha ce tana shekarar ta ta farko a jami'a ta kasar ghana,sai samira da azima da jamil duk 'yan primary ne da j.s.s. alhaji bishir ya ce,masha ALLAH,ALLAH yayi masu albarka.kai ba su da yawa ni yara na ishirin da biyu, mata na uku,alhaji akilu yayi 'yar dariya,ku manya ne, amma hakan yayi kyau, dama ka yi kokari ka cike, suka dariya,alhaji bishir ya ce,mu yi tare,kai ta biyu sai a yi rana daya.suka kalli matan wadanda suma dariyar suke har suna hada baki gurin fadin ku yi ta yi mana,ga dai yaranku nan,sun girma.bayan sun gama gabatar da iyalansu sun dan yi wasa da dariya, sai kuma mommy nafisa ta ce,ya kamata mu je dining, nan fa aka hau kan teburin cin abincin. MIMI ta kalli na'ima cikin maganar nan ta ta a hankali ta ce,ki lura tun daga kan aisha zuwa kasa ni zan ji da su daddies, mommies da brother abbas.yanda tayi maganar, iyayen suka sa dariya,haka ta yi ta zuba masu sai da kowa ya ce,yayi,ita ma na'ima ta kula da na ta gefen.bayan an kammala aka koma kan kujeru, MIMI da ba son hayaniya take yi ba,sai ta kama hannun aisha zo mu je sama na.haka yayi wa mommy nafisa dadi,har ma ta dauki wayarta ta tura ma na'ima messege,inda ta ce,ga dama nan ta samu,ki lura da abbas kuma ki ja hankalinsa.a sama,aisha sai santin falon MIMI take yi, MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce,gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina ki ke karatu?MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji da ni fiye da zaton ki,duk abinda ni ke son. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (72)A sama,aisha sai santin falon MIMI ta kai ta ko'ina a saman ta,ta ce, gaskiya MIMI kin ji dadi,ke kam 'yar gata ce,duk nan ke daya?a ina kike karatu? MIMI ta ce,dubai,ai in fada maki aisha dad yana ji dani fiye da zaton ki,duk abinda ni ke so yana yi min.can kasa kuwa mommy nafisa ta ja hajiya bilkisu zuwa dakinta,alhazan su ma tasu hirar suke yi,kananan kuma sun bar falon alhajin sun nufi na su,suna gaban damfareriyar talabijin din falon suna buga game, Na'ima ta koma kusa da abbas wanda ke ta latsa wayar shi ta ce bros ya kokari,ya kalle ta, alhamdulillah,ya makaranta? ta ce,ai yanzu ina gida ne ban fara zuwa makaranta ba,ina son in je wajen ni ma,amma dadinmu ya ce, ko abuja ba zan bari ba.ya ce,kila kina rawar kai ne,ta ce,aa raayinsa ne haka,sai kuma ta canza maganar da cewa in ga phone din ka bros,ya mika mata ga shi. ta yi ta shiga nan fita nan ta dinga kallon hotunan shi lokacin yana karatu a waje, ya birge ta sosai.ta ce,ka hade fa bros,ya ce,na gode,ta saka lambar wayarta ta ce.ga lamba ta nan,in maka saving din ta, ya ce,eh,ta ce,kana da me irin suna na?ya ce,aa ta saka sunan,ta yi saving din ta shi.kamar daga sama sai taji ya ce,sa min ta sister din ki,mene ne sunanta na gaskiya?ta ce,khadija,ya ce,ok sa min lambarta,da ta tashi,sai ta canza lamba daya ta mi shi saving ta ce,in kun tafi sai yaushe?ya ce,ku ya kamata ku kawo mana ziyara ai,ta ce,haka ne,za mu zo,muryar alhaji akilu bala ta katse su. Goma tayi ku tashi mu tafi,alhaji bishir ya ce,tun yanzu?to sai mun zo muma, alhaji akilu ya ce,abinda zance kenan muna jiran zuwan ku,amma da rana za ku zo mana ko?alhaji bishir ya ce,in ka samu lokaci ka sanar da ni sai muzo,ya kalli na'ima,je gurin mominku ki ce su fito, alhaji akilu ya ce,ka san mata da kus-kus.sun fito inda mommy nafisa ta cika hajiya bilkisu da kayan mata,alhaji bishir ya cika yaran da kudi,na'ima kuwa abbas tayi wa kyautar turaruka masu kamshi,ita kuma MIMI kawarta aisha ta yi ma kyautar irin kaya jikinta. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (73)Da takalmi da kuma turare,sannan suka yi canjen number,alhaji bishir ne ya kira MIMI ya ce,su sauko,abbas ya kosa ya sake ganin MIMI don komai na ta yayi masa,kuma ita ce yake ganin zai zaba ta zama matarsa,tunda suka fito yake sake kallonta zuciyarsa tana kara kuranta ta.sun raka su har bakin mota katuwa jeep, direba yana ciki yana jiransu,aisha ta rungume MIMI sis sai naji ki,MIMI ta ce,yawwa sis aisha sai kin ji ni. Tunda suka koma gida, abbas ke kiran layin da na'ima ta sa mi shi na MIMI, wani ke dagawa,duk ya damu sai kai kawo yake yi a gefen nasa,ji yake yi tamkar ya nufi gidan su MIMI ya fada mata ya na sonta. a gidan alhaji bishir kuwa bayan sun yi bankwana da juna kowa ya shiga makwancinsa, dad da momi sun shiga nasu makwancin,sai take ce masa,alhaji na ga kamar na'ima da abbas sun aminta da juna,ya ajiye rigarsa da ya dauka da niyyar sawa ta bacci ya ce,haba!!ta ce,(cikin dariya) da gaske kuwa,har canjin number ta ce min sunyi.ya kamo hannunta nafisa ALLAH yasa haka ta tabbata da sai nafi kowa murna.da na'ima ta ga aure gata,ina son mu hada surukanta sosai,ta haka zan zama na gaba a cikin masu yin dillancin man fetur,buri na in zama na daya mommy nafisa ta ce,kar ka damu,zan kula maka da wannan alakar tasu,lnsha ALLAHU har a kai ga yin auran,ya rungume ta,ke kanki kyautar ki daban ce,suka sa dariya. Abbas ya samu aisha a cikin falon su,ya sami waje kusa da ita ya zauna ya ce.sis don ALLAH ba,ta ce ina jin ka,ya ce lamba za ki bani,ta kalle shi,ta wa?ya ce kawarki,ta sa dariya, wacce kenan?ya ce.ta gidan da muka kai ziyara mana,na ga kun kulle.aisha ta ce,ok,MIMI ko lallai ka samu 'yar gaye,ka ga gefenta kuwa?ta shiga ba shi labari.yana sauraronta zuciyarsa tana kara fari.ta bashi number ya koma sasan shi.sai dai abin takaici ya kira ta kusa so biyar amma ba ta daga ba. abinda bai sani ba.MIMI bata daga number din da bata sani ba,don haka tana kallon wayar tana yi tana katsewa. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (74)Sake komawa ya yi hankali tashe gurin aisha yana tuhumarta cewa bata bashi lamba daidai ba.ta ce,bari in kira ta da layi na,a ringin na hudu ta daga ta ce,hello sis aisha ya ya aka yi?lafiya lau in ji ta,bros ne yayi ta kira baki daga ba,shine ya zo ya tare ni wai na bashi number ba daidai ba.ta ce ok dama shine?ayya ban sani ba tsari na shine bana daga bakuwar number, amma zan yi saving dinta yanzun nan,ta ce to zai kira ki,MIMI ta ce babu damuwa ya kira kawai. Sasan shi ya sake komawa,sanna ya kira ta,sun gaisa bai tsaya bata lokaci ba ya ce,MIMI kin tafi da dukkan tunani na,tun da na ganki naji gaba daya na birkice,ke ce matar dasu dad su ka ce in nemo, lokacin da suke min maganar aure,ke kawai nike kallo a amaryar.MIMI ta yi shiru tana jinsa,sai da ya kai aya sannan ta ce kayi hakuri da abinda zan ce yaya abbas.gaskiya ina da wanda ni ke so sosai,ban san adadin son da muke yi wa juna ba.don ALLAH kayi hakuri saboda gudun faruwar haka na bar falon don na lura da yawa satar kallon da ka ke min,amma ina me yi maka adduar samun wadda tafi ni.sannan zan baka shawara ga kanwata na'ima,bata tare da kowa, kuma tana da hankali,ya katse ta,ki bani lokaci in zo muyi maganar daga zaune. ta ce kowane lokaci ina gida,ya ce,in zo yanzun?ta ce a!haba dai mu barshi gobe.sannan sharadi kar ka zo da batun so na kazo da batun kanwata,yayi 'yar dariya,sai dai in na zo din,ta ce shikenan. Misalin shadaya lsmail ya nufi gurin karatunsa kamar kullum,ya jira sannan ta fito,haka nan ya bude kur'ani yana karantawa kamar yadda ya tsara.ya gama ya kalle ta,gaskiya ya kamata yau ki karanto in ji,ko kina rikewa tunda kin ga mun kammala shafi biyu na suratul bakara,sai ji amma a ce kullum ni zanyi karatu,ke kina danna waya don ban sa ran cewa kina ji ba.ta ce,in fahimta,ko kar in fahimta ya shafi albashinka?don haka kayi kawai ina jin ka dama aya biyar yake yi kullum,don haka ya karanto mata ko daya gama ya dago ya kale ta daidai lokacin.. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (75)Wayarta ta yi ringing,ta daga tare da cewa,brother abbas,ya na'am gani nazo fa,ta ce,ok ka shiga mana,na'ima tana nan a falo ka ce ta kawo ka falon baki na ciki.ya ce, ok to,lsmail ya kalli agogo abin haushi yanzun shadaya da rabi saura minti talatin. Bako yayi sallama lsmail ne ya amsa da ya shigo,sai ya mika wa lsmail hannu.shi ma ya miko masa kenan za su gaisa MIMI ta ce,aa yaya abbas,kar ka hada hannu da shi,abbas ya dakata sannan ya kalle ta lafiya?ta nuna ma shi gurin zaman,zauna kawai,lsmail ya bude kur'anin shi ya ci gaba da karantawa a zuciya,sai dai kunnansa yana gurinsu.ta ce,dan aiki na ne,kana dan minista zaka hada hannu da talaka? ni da zai koya min karatu ma na ki ya ji karatu na don bai kai matsayin ba, sai kai ka hada hannu da shi,kodayake mu bar zancan shi,ka iso lafiya?ya ce,lafiya lau,da farko ai na zaci shine na musamman din naki,ta ce,shishshhh haba mana abbas ka cuce ni,daka hada khalil da wannan,don ALLAH ka bani hakuri don ka cuce ni.abbas ya ce,to shikenan yi hakuri,amma so ba shi da haka,kuma wannan din ban ga laifinsa ba,ta ce zan hau sama in kana irin wannan zancen,ka yi abinda ya kawo ka. Abbas ya ce,ok na san jan ajin ku ne na mata shi ya sa kika ce min kina da wani,kar ki damu da jan aji don kina da ajinkin MIMI.tun ranar da muka zo ban kara sukuni ba don ALLAH ki duba ni.ta ce,yaya abbas don ALLAH ka bar zancen nan,ni da khalil mun fi shekara daya muna tare, shi yasa tun jiya na ce kar ka zo da batun nan,ka zo in ba ka kanwata na'ima.ba laifi in ka ce mu zama abokai,mu dinga ba juna shawara,ya ce,MIMI ni dai ke ni ke so,ta sa yatsan ta a kan lebenta ta ce shhhh, don ALLAH bar zancan,ka amince da batuna, bari ka ga na'ima,tana da kyau kuma ga hankali. Kafin ya ce komai ta danna kiran layin na'ima,ba ri ka ganta da kyau,na'ima daidai lokacin tana dakin momi cikin damuwa tun zuwan abbas da ta nuna mashi falon baki kamar yadda MIMI ta umurce ta. dakin momy nafisa... [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (76)Momy ta ce dama na san zai zo,na'ima ta ce,ai gurin sis MIMI yazo. gaban momy ya fadi ta maimaita cewa,gurin MIMI? na'ima ta ce,suna ma falon baki,momy ta yi shiru tana tunani,can ta ce,ni wai yaya zanyi da wannan shegiyar MIMI?wayar MIMI ce ta katse su ta dubi momy,ga MIMI tana kira na,momy ta ce,daga muji,MIMI ta ce,sis na'ima ki kawo ma bros abbas abin sha ta ce,ok gani nan.ta kalli momy,wai in kai masa abin sha,ta ce maza je ki kai masa,har ta fita,ta kwalo mata kira,zo na'ima ta ciro wani turare a jerin turarukanta ta fesa mata sosai,ta ce,je ki ko babanku na fesa turaran nan yana sa shi nishadi.a falo ta ajiye dan kwalin kanta,a ranta tana fadin in gashi ne ni ma akwai. Da sallama ta shiga falon,nan ma lsmail ne ya amsa,wanda ke zaune yana jin komai,ta shiga ta aje,sannan ta sake gaida shi,MIMI ta ce,zuba masa a kofi na'ima ta zuba,sannan ta ba shi a hannu ya amsa yana ta kallonta,sai da ta tafi sannan ya ce,MIMI kuna da bambamci da yawa, kyau kuma ba irin daya bane,ina son ki don ALLAH. MIMI ta ce,in baka amince da na'ima ba to ka tafi ka nemi wata,na yi haka ne don na san iyayanmu za su yi murna.ya ce,ni da ke zasu yi murna,ta ce,to abinda ya yi ni,shi yayi na'ima,ya mike,ke da ita akwai bambamci,zan tafi amma fa ban hakura ba. Ismail dariya yayi ta yi a daki tare da tausaya ma abbas,don ya san menene so,in ya tuna zainabun shi, kila ma in ya ci wata daya sai ya je katsina ya ganta, ya sai mata waya don ya dinga jin muryarta kowane lokaci. MIMI tana cikin damuwa,sam ba za ta so zancan nan ya kai gurin dady ba,domin zai so hakan. tun bayan tafiyar abbas MIMI take sake-sake. momy ta hau sama ta sami MIMI tana ta tunani ta ce, na'ima ta ce min abbas ya zo gurinki,MIMI ta bata rai,ya zo ne ya dama min lissafi momy,wai sona yake yi.gaban momy ya fadi,ta dan zaro ido,sai kuma ta wayance,mene ne,to ki amince kawai.MIMI ta ce, gaskiya momy ina da wanda ni ke so,momy ta ce,haba da gaske?ta ce, ALLAH,sunan shi khalil.. [01/10 12:47 pm] Abdul: STEP (77)Khalil,su 'yan kaduna ne,baban shine dan takarar da aka tsayar a jihar kaduna zai yi takarar gwamna.sunan mahaifisa usman kaura,haifaffan zariya ne.momy ta ce,to shawarar da zan ba ki ki yi saurin sanar da dadinku kafin shi ya sanar da na shi mahaifin. MIMI ta rike hannun momy,don ALLAH momy ki taimake ni ki fada min yanda zan fada masa. momy ta ce,kar ki damu in ya dawo ki same shi ki fada masa,inda hali ma ki ce da yaron ya zo ya gaida shi.MIMI ta ce,ai tsoro na kar dad ya ce masa ya turo iyayansa,to shi kuma karatu yake yi,gidansu ba za a yi masa aure yanzu ba,sai ya fara aiki.momy ta ce,ba damuwa don wannan kin san dadinku bai son damuwarki,ba zai takuraki ba.MIMI ta dan ji sanyi a ranta,ta kuma yarda duk abinda take so, shi mahaifin ta ke so. Abbas ya zauna kusa da mahaifinsa alhaji akilu bala ya ce,daddy na ga irin matar da ni ke so.ya tattaro hankalinsa ga dan nasa,'yar gidan waye? abbas ya sunkuyar da kai, gidan da muka je ziyara, gidan alhaji bishir masari. alhaji akilu ya dafa kafar danshi,yaro kayi abinda nake so,ka san buri na?mu zama surukai da shi,abbas ya ce,saboda me daddy? ya ce,saboda siyasa ta abbas,duk dan siyasa yana son hulda ya mutum mai jamaa.alhaji bishir babban dan kasuwa ne yana da mutane fiye da zato ka, lokacin da ya bukaci hulda da ni sai da na bincika,ka taimaka ka samo min soyayyar 'yarsa mu zama surukai.yana tare da mutanan da in suka goya min baya zai yi wuya ban dare kujerar shuganbancin kasar nan ba.abbas ya ce, na yi mata magana ta ce tana da wanda take so, amma ina zaton jan aji ne, don ALLAH kayi wa mahaifin ta magana. babbar na ke so,alhaji akilu ya ce,kar ka damu yanzu zan kira shi. Sun gaisa da alhaji bishir ya ce,ka samu hutu kenan mu kawo ziyaran,alhaji akilu ya ce,danka ne nan ya fiti ne ni wai tun da mun ce yayi aure,shi 'yar uwarsa yake so MIMI,tunda muka kawo ziyarar nan ya kasa sukuni.alhaji bishir cikin matukar murna ya ce,masha ALLAH....... [01/10 12:47 pm] Abdul: (78) ka fada masa kar ya damu, mimi ta zama ta shi don na bashi. nan Alh akilu ya hau godiya cikin murna, Abbas cikin murna ya rungume mahaifin sa. Alh bashir ya kosa ya iso gida don yayi Albishir ga mimi da momi nafisa, lallai burin shi zai cika. Alh lawal ya kalle direban shi, yarin yar nan ba zata bamu hadin kai ba, dan haka kayi min sallama da maman ta. haka kuwa ya rangada sallama, kaninta ya leko ya ce, yauwa ka ce Alh yana sallama da maman ku, yaron yace inannar mu...? ya ce, eh, ka ce inji Alh lawal. ba da jimawa ba, innar su zainabu ta fito, tamkar marokiya, haka take tayiwa Alh barka da zuwan ka ka iso lafiya, sannu sannu. ya fito ta durkusa bari a yi shin fida a zaure, ta mike ta koma cikin gida da gudu. daga gani Alh wanan yar raka yarima ce a sha kida, suka yi dariya tamkar ba direba da uban gida ba. to direba za a kirashi ko kawali, tunda shi ne me kawo ma Alh mata. suna zaune a kan tabarma a zaure, Alh ya ce, inna na zone akan maganar aure, zainabu taki bani hadinkai in turo manya ns, sai fada min take tana da wanda zata aura. inna ta cefke zancen da cewa, karya ne bata da shi, ka turo kawai, ya ce, to na gode. ya ajeye daurin yan dari biyar-biyar, inna ga wanan kyaci goro, kuma zan turo manya na gobe, bana son bikin ya wuce sati uku. ta ce, ai kuma lokacin bamu shirya ba, Alh kasan sai min nemi na gado. ya ce, ina da ko mai inna, mata na ce ina so, kuma ita za a bani ba tarkacen kaya ba. ta ce, to shike nan, in gobe kake so a daura bare nan da sati uku. tirkashi!!! ku biyuni a kashi na biyu don jin yadda zata kaya. taku halima k/mashi. ina sauraran ku,08081165107 dan shawara ko kuma korafi na gode...."" CANJIN RAYUWA Halima /k Mashi Creat:- Shuraih Usman Littafi na biyu 2 Domin dauko wasu hausa ebooks din ko wasu kayatattun littatafan hausa a matsayin hausa ebooks, sai ku ziyarci shafinmu na internet akan wannan Adireshin zaku samu http://shuraih.waphall.com (1)Ahaji bishir ya kosa ya isa gidansa don kai wannan albishir.haka nan MIMI ta kosa matuka dad din nata ya dawo don ta sanar da shi labarin masoyinta khalil.momy nafisa kuwa tana cikin damuwa,tana ta tufka da warwara a kan yadda zata hada fitina tsakanin MIMI da mahaifinta. A haka alhajin ya iso gidan,cikin doki.tun daga shigowarsa falon yake zuga kiran nafisa!nafisa ta fito cikin sauri tana cewa, "Alhaji ga ni.lafiya kake ta kira na?"ya ce,"Lafiya lau. sai alheri." Ta amshi jakar hannusa da hularsa da malum-malum. "Mu je ciki ki ji albishir!"Gabanta ya fadi. wani sabon kasuwancin ne? ya ce,"wannan duk ya wuce nan.sai da suka zauna,sannan ya ce,"Abbas, ashe MIMI yake so?"Gaban momy ya fadi. ya ci gaba da cewa, "gaskiya na yi murna sosai.burina zai cika."ta yi dan yake,ta ce,gaskiya kam, da abin zai yiwu,zaa yi murna."Ya ce,"me zai hana shi yiwuwa?daina fadin haka. Nafisa ta ce,dazun take sanar da ni cewa saurayinta zai zo daga kaduna gaishe mu. ya zaro ido yana kallon ta.ya ce, wane ne shi?wannan ba gaskiya ba ne.lnda MIMI tana da wani saurayi,nine mutum na farko da zan fara sani,domin kin san babu wani abu da take boye min.ba ta da aboki ko kawar da ta fi ni. Nafisa ta ce,haka ne, amma jiya tayi min zancen. da alamu kuma tana son sa sosai.ya daga hannun, alamun dakatarwa.sannan ya sa kai ya fita daga dakin.kai tsaye saman MIMI ya nufa.tana kwance a kan kujerarta,catin suke yi da khalil,tana ba shi labarin halin da take cikin na damuwa.shi ma duk hankalinsa ya tashi.a sama ta ji muryar dad yana cewa, uwata tashi zaune da sauri!tana fadin dad ka dawo ne?ban sani ba,ai da na sauko. Ya zauna kusa da ita.yau ina cikin farin ciki ne MIMI.burina zai cika.ya kama hannunta,kin san na dade ina addu'ar ALLAH ya kawo miki mijin da zai kula da ke ko?gabanta ya fadi,ta ce,"eh dad."ya ce,"to ga abbas dan gidan minista. mahaifinsa yake sanar da ni tsananin son da abbas din ke miki..... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (2)Wannan lamarin ya zo a daidai da burina na hada surukunta da minista. zai kawo ci gaban kasuwancina,musamman ta fannin man fetur." Ta ce,"Dad akwai matsala.shi abbas din ai mun gama magana da shi."Ya ce,"Wace irin matsala kuma?"Ta ce,"Dad,ya zo ya ce yana so na.na fada masa ina da wanda nake so.lokaci mai tsawo muna tare da shi. dad ya kama in bar shi in koma wa abbas?"kallon ta kawai alhaji ke yi.bai fara jin haushinta ba don yana sa ran zai shawo kanta.ya ce,"Za ki iya barin sa,tunda bai nemi aurenki ba.sannan ban zaci zaki boye min komai ba.wai kina tare da saurayi tsawon lokaci ban sani ba.to ina son ki ajiye batun wani saurayi.ki natsu kin ji mamana?" Ta yi shiru,ranta bace, lndanunta sun soma kawo kwalla.ya daga fuskarta, "mene ne abin kuka?murna za ki yi.ALLAH yayi miki zabi na gari."Ta ce,cikin kuka,"Dad ba na son sa ne. ai ni khalil nake so.zai zo yau ka gan shi.lrin mijin da zuciyata take so kenan." Ya daga murya,"MIMI zo lokacin da zan ce ina son abu,ke kuma ba kya so?mun fara jayayya kenan?"Yanzu kam kuka sosai take yi"Dad ba haka bane,amma bai dace a tsananta min in so shi ba.kar ka damu zan kira abbas din in sake tuna masa cewa ba na son sa." Saukar mari ta ji fau! a fuskarta.ya ce,"ba ki isa ba!" A fusace ya nufi fita.ta rike kumatu tana kuka sosai.momy da ke labe ta sauka da gudu,jin alamun zai taho.cikin dakinta ta shiga.lallai tana cikin farin ciki.bari ta je ta kara wa wutar kananzir. Ta fito ta nufi dakin alhajin,tamkar bata san komai ba.ta yi sallama, alhajin ya amsa a ciki,yana ta zirga-zirga a cikin dakin nasa.cikin alaye ta nufe shi,"Lafiya alhaji?Me ya faru?"Ya kalle ta,"MIMI wai take nema ta tona min asiri.bakina da na uban dan nan na ce,na basu yarinyar nan,amma in zo mata da batun,ta ce,bata san zancen ba?"Nafisa ta zaro ido,tare da dafa kirji,"in ji MIMIN?"Momy nafisa ta ce,"aa wasa take yi,kana ji ko alhaji?kiyayyar mace bata wani tasiri,sai dai in ba a yi auren ba. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (3)Ku tsai da rana. kafin ta kammala makaranta ku daura musu aure.bikin kwa yi in ta gama karatun."Ya ce,"Kina ganin hakan zai yiwu?"ta ce, sosai kuwa.ldan ta san cewa da akwai igiyar wani a kanta,dole ta rabu da kowa.ya ce,"Ke ma kin kawo shawara.amma zan so ki je ki dan kara bata shawara. ko don gatan da na nuna mata,ya kamata ta yi min biyayya."momy ta ce bari in je.amma kafin in tafi, za a hada maka ruwan wankan ne,ko abincin za ka fara ci?"Ya ce bana bukatar ko daya.ya zauna bakin gado,"bari in kira sauda,ko zan samu natsuwa."ranta ya dan sosu,amma ta danne. bari to in je gurin MIMI din.ka ce da ita ina gai da ta." Kuka sosai ta samu MIMI tana yi.don haka ta shiga lallashinta da cewa ta yi shiru,su yi magana.ta zo ne don sama mata mafita. bayan MIMI ta share hawayenta ne,momy nafisa ta ce,ki ce masa ya turo iyayensa,shi khalil din. kila in alhaji ya ga magabatansa sun zo ya hakura. cikin disasshiyar murya ta ce,momy bana fada miki ba karatu yake yi?lyayensa,yanzu baza su saurare shi da batun aure ba.da ma mun bar shi a kan sai mun gama karatu ne.momy nafisa ta yi shiru tana tunanin mafita.MIMI ta kama mata hannun,don ALLAH momy ki fada min yaya zan yi? Ta rungumo ta,kwantar da hankalin ki MIMI.wannan karamin abu ne,kuma kin san dad dinki yana son duk abin da kike so.shawarar da zan baki ita ce,ki tsaya a kan raayinki na cewa khalil ki ke so.zai hakura. amma in kika bi raayinsa,ba za ki ji dadin zaman auren wanda ba ki so ba. MIMI ta ce,to ni bana son dad ya ce ban ji maganarsa ba.ta ce,kar ki damu da haka.yanzun nan daga dakinsa nake.ya ce in ya ga kin dage zai hakura. MIMI ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta ce, shi kenan zan tsaya a kan raayina.momy nafisa ta ce,duk runtsi ki ce baki son abbas.MIMI ta ce, "shi kenan." Alhaji kam, hajiya sauda ya kira yana labarta mata komai daya faru,tun daga burinsa har zuwa yanzu.ya ce,ina son ki kira ta ki yi mata fada,ta bar batun wani yaro....... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (4)Ta tsaya ga wanda ni na zaba mata. hajiya sauda ta ce,alhaji ba zan shiga zancenku ba,kai da lelenka.abu daya kawai nake ganin zan iya.shi ne zan kira ta in bata shawara. ya ce ban gane ba zaki shiga zancenmu ba. ta ce alhaji ke nan.yanzu ne da ta kwabe muku ka san da ni?lna uwarta mai son ta wadda aka canza mata da ni,saboda ni ina takura mata ta yi abin da ya kamata?shawara kawai zan ba ta ta yi maka biyayya,amma ba wai in takura mata ba.ldan ta ki yarda,sai ka yi mata abin da take so,kamar yadda ka sabar mata tun tana karama.shiru ya yi,ya kasa magana.sai kuma ya kashe wayar. momy nafisa ta same shi cikin damuwa, yana ta tattauna maganganun hajiya sauda a cikin zuciyarsa.ta zauna kusa da shi.alhaji nayi maga da MIMI.ya kalle ta cikin sauri,ta amince? "MIMI ta ki sam alhaji.kuka take ta yi.da na tsananta mata da lallashi,da nuna mata cewa ta yi maka biyayya, sai ta ce min don na ga bani na haife ta ba.ln dani na haife ta ba zan so a yi mata auren dole ba.ya ce haka ta fada?kenan tana da daurin gindin mahaifiyar tata?domin da na kira ta a kan ta yi mata fada,ce min ta yi ita shawara zata iya ba ta, ba fada ba. Momy nafisa,cikin jin dadi ta ce,amma hajiya sauda ba ta kyauta ma kanta ba.ta yaya za ta hana 'yarka ta yi maka biyayya?"ya ce,shi ne abin mamakin amma zan gwada musu su duka cewa ba su isa ba."ta ce, "abin da ya kamata kenan da ma ku zauna kai da minista ku sa lokacin auren sati uku ko hudu,ku daura kawai,ka wuce gurin kamar yadda na fada maka.ya ce, gobe za mu tattauna da shi.amma MIMI ba ta isa ta ja min asara ba.ta lelo ta koma min kenan. lta kuwa hajiya sauda, wadda ba ta san komai ba, sai da alhaji ya fada mata, amma ita ma yanzun laifin ya shafe ta,ta kira MIMI. can kasa-kasa ta ji muryar MIMI ta amsa sallamar hajiyar.hajiya ta ce"ba ki da lafiya ne?"MIMI ta soma kuka,dad ne wai sai na auri dan minista,kuma ni bana son sa."Hajiya sauda ta ce,ni dai in na isa in fada miki ki ji,to ki bi zancen mahaifinki, [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (5)Ki auri wanda yake so.yanzu ke wannan ba abin kunyarki bane,saura 'yan uwanki su ji kina takaddama da ubanku? mutumin da ya nuna miki gata,ya yi miki duk abin da ki ke so,ya nesanta ki da duk wani abu da zai bata miki rai.MIMI na zaci ko wuta babanki ya hura ya ce,ki shiga,za ki shiga ba tare da kin tsaya dogon nazari ba.ashe ba kya yi masa son da yake yi miki. ki yi tunani sosai,kuma ki yi abin da ya dace.shawarata kenan."Ba tare da ta ji uzurin MIMIN ba ta kashe wayar. Alhaji lawal ya kawo sadakin zainabu dubu dari kamar yadda lnnarta ta fada musu.kuma an kawo akwatuna,an kuma sa ranar bikin sati biyu.zainabu na ta kuka kuma har gidan su mahmood ta je ta fada masa,ta kuma bukaci ya bata wayar don ALLAH,ta kira lsmail.ya ce mata ai kawai taje tabi maganar iyayenta.lsmail ba abinda zai iya tunda an rigaya an yi mata miji.shi ba ya so ma lsmail din yaji zance ma haka ta tafi ba tare da ta cika burinta ba.lsmail kuma duk kwanakin sai yayi ta fama da muggan mafarkai marasa kai.ln ya kira mahmud,sai ya ce masa kowa lafiya.tun kwanaki da yayi waya da zainabu, mahmud bai sake hada su ba.ln ya ce masa don ALLAH ya je gun ta za su yi waya,sai ya ce masa ba lokaci.daga karshe har ya ji haushi,ya ce,na daina cewa ka kai mata wayarka.da na dawo zan sai mata in huta. mahmud ya ce,ka taimake ni,don ba a son raina nake zuwa ba.lsmail ya kashe wayarsa cikin takaici. kusan kwanaki uku,in lsmail ya shiga gidan don koyar da MIMI,har lokaci ya cika bata fitowa,don haka sai ya kuduri niyyar yau in alhaji ya dawo zai sanar da shi. haka kuwa bayan sun yi sallar isha.sai ya sanar da alhajin.alhaji ya ce zai yi mata magana.ln ma bata fito ba kar ka damu.ka ci gaba da koyar da kannenta. lsmail ya ce shi ke nan.alhaji ya ce in ta fito kuma,to don ALLAH ka dinga yi mata nasiha.ka ji ko?lsmail ya ce,insha ALLAH. momy nafisa ita da naima sun kulle kansu a dakin momy tana sanar da na'imar yaddaa tsarin da ta yi yake tafiya yadda take so. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (6)Ta ce an kusa zuwa gurin kar ki damu. na'ima yanzu fa har hajiya sauda,alhaji haushin ta yake ji.ya zaci ita ce ke zuga MIMI.shekaran jiya MIMIN ke fada min wai hajiyar saudar ta ce lallai ta bi zabin alhaji.na ce mata MIMI kin san dai sai dai mahaifiyarki ta gwada min ta haife ki,amma ba ta kai ni son ki ba ko?MIMI ta ce eh.na ce to ki yi duk abin da na ce,lta kin ga bata yi boko ba,ba lallai ta san 'yancin kanta ba,bare naki. MIMI ta ce haka ne.nan da nan na zuge ta.sai da na goge dan tunanin da ta soma yi na danganar da uwar ta sa ta yi."Na'ima ta ce momy ai na ji dadi.yanzu dad ya fi kula mu a kanta.momi ta ce shegiya ba,ni ma na dan ji tsai,a yi nan dad dina,a yi can dad dina,ta kwaikwayi muryar MIMIN,suka kwashe da dariya.na'ima ta ce,to ba ki ganin dad zai iya daura musu auren,ni kuma fa? tunda kin ce masa kawai su sa rana.momy ta ce,ina so ne a yi mai yiwuwa ne a gama.shi ya sa nake son a sa rana.ke dai duk abin da na ce ki yi,to ki yi kokari ki aikata.na'ima ta ce,"an gama." Alhaji akilu da alhaji bishir suna zaune cikin ofishin alhaji bishir din,su zabi haduwa a nan ne don su tattauna batun auren yaransu.alhaji bishir ya ce,ka san ja'irar yarinyar nan wai ina fada mata sai take neman yi min gardama."haba dai?!"in ji alhaji akilu.alhaji bishir ya ce,"ALLAH kuwa.amma na san duk iyayi ne na yaran nan."alhaji akilu ya ce,ka san mata ba mamaki tana zaton mu ne muka hada su,ba shi ne ya gan ta ya ce yana so ba.ka bar ta kawai.da zaran an yi kiyayyar mace bata dorewa.sai dai in ba ta samu kula ba. Cikin jin dadi,alhaji bishir ya ce na gode daka fahimci hakan.yanzu wane lokaci kake ganin za musa? alhaji akilu ya ce kar mu ja abin;mu yi mu wuce gurin. ni ma haja na gani,in ji alhaji bishir.mafi sauki mu saka sati uku ko hudu.alhaji akilu ya ce,mu bar shi hudun.don naji mata suna cewa za a fita dubai ko chaina hado kayan auren.shi kuma angon ya soma gyaran gidan nan nawa na asokoro. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (7)Alhaji bishir ya ce, ka fasa sai da shi ke nan? ya ce,ba dole in fasa ba, tunda abbas ya dage gidan yake so?gidan yayi masa girma,amma shi wai tsarin gidan yayi masa.alhaji bishir ya ce,to a bar masa. ALLAH ya sa hakan ya fi alheri.alhaji akilu ya ce. amina.zan turo waliyyan nasa,kanina da alhaji sa'idu abokina za su zo.alhaji bishir ya ce,babu matsala. ni ma zan yi wa nawa kanin da kuma alhaji kabiru magana.yaushe ne za su zo?alhaji akilu ya ce cikin satin nan.za dai muyi waya. bayan sun gama tsarinsu ne suka koma batun kasuwancinsu. Abu kamar wasa,zance ya soma nuna,don an kawo sadaki.kuma momy nafisa da wata kawarta sun shaki kudi gurin alhaji sun nufi dubai siyayyar kayan kicin, ta zage kuma tana ta zabar masu kyau da tsada,domin tana fatan su rikide su zama na na'ima. Tafiyarsu da kwana biyu,sai ga khalil da mahaifiyarsa har gidan su MIMI.yadda abin ya faru kuwa,hajiya amina ta ga danta ya shiga damuwa da tashin hankali ta rasa gane kansa,sai ta tsare shi a daki don ya fada mata damuwarsa.ta yi ta lallashin sa da nuna masa cewa,ita ce ta fi dacewa da ta san matsalasa,kuma ta magance masa,in har za ta iya.jin haka ya sa shi koro mata komai.ba ta yi kasa a guiwa ba ta sanar da mahaifansa wanda hankalinsa yake kan siyasa. nunawa yayi wannan ba damuwarsa ba ce damuwarsa kawai khalil ya yi karatu ba tare da zabin da ya wuce bai wa dan nata hakuri,gami da shawarar tsayawa kan karatunsa.amma cikin kwanakin sai ga yaro kwance warwas,ba ci ba sha,duk ya fita hayyacinsa. ba arziki ta taso shi zuwa abujan don rokon a bar masoyan su ci gaba da soyayyarsu har zuwa lokacin da za su hattama karatunsu,sai a daura musu aure. na'ima da ke falo ita ce ta amshi bakuncin nasu. suka gaisa.ta ce,kun zo gurin momy ce?ga shi ba ta nan.hajiya amina ta ce, mahaifinku fa?na'ima ta ce, yanzun nan ya fita.khalil ya ce MIMI fa?na'ima ta ce tana samanta;in kira ta ne? hajiya amina ta ce,eh.kudundune take cikin bargo.yau tun safe zazzabi ke jikinta. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (8)Na'ima ta yi sallama,ta shiga ta sami MIMI.baki aka yi.sun ce in kira ki.ta ce daga ina?ki ce su hawo,ba zan iya sauka ba.na'ima ta raka su har falon MIMI,ta ce,sis ga su nan.MIMI ta yunkura za ta tashi,ta kasa.ta ce,tambaye su na'ima,daga ina?ba zan iya tashi ba.na'ima ta tambaye su.sai ko hajiya amina ta mike mu je kawai,in yi mata bayani. Ta zauna bakin gado,ta kamo hannun MIMI,yata ni ce mahaifiyar khalil.da sauri, MIMI ta tashi zaune.sannu da zuwa momy.wa ya nuna miki gidan nan?ta ce, ga shi nan a falo,tare muke. da sauri MIMI ta sauko daga gadon don tabbatar wa idanunta khalil dinta ne kuwa?sabbin hawaye suka soma zubo mata.ta je ta zauna a kujerar da ke kusa da shi.cikin damuwa ya ce, dubi yadda kika rame,don ALLAH MIMI ki yi hakuri.ga momy na nan na kawo ta za ta yi magana da momy dinku ko dad. MIMI cikin kuka ta ce,ba zai saurare ku ba.don sun yi nisa da shirin aura min abbas.hajiya amina ta dafa bayan MIMI.bayan ta zauna a hannun kujerar da take,sai ta ce,kar ki damu 'yata.yaya za a yi in gan shi?MIMI ta ce bari in gwada kiran sa ko zai daga,don yanzu bai damu da daga kirana ba, Sai a kira na biyu,sannan ya daga me ya faru MIMI? abin da ya soma tambayar ta ke nan,bayan ya daga wayar.ta soma kame-kame am,am da ma wannan ne, baki ne suke son ganin ka. Hajiya amina ta amshi wayar,sannu da kokari alhaji.ya ce,yawwa,wace ce?ta ce,sunana hajiya amina daga kaduna.kuma ni ce mahaifiyar khalil saurayi MIMI,wanda take so. Haushi ya kama alhaji bishir,amma sai ya danne, ya ce,to lafiya?ta ce,na zo ne ina son ganin ka don mu yi magana a kan yaran nan. ya ce,babu bukatar wata magana domin na riga na ba da ta.yanzun haka nan da sati uku ne bikin.don ALLAH ki bawa dan naki hakuri.ta ce,amma alhaji kana sane cewa ba ta so ko?ya ce,ba damuwata ba ne,kuma ke ma ba damuwarki ba ce.ln kin zo nemawa danki aure ne, tuni ya kamata ki yi haka ba yanzu ba.yanzu kam kun makara.na gode.sai an jima.ya kashe wayar. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (9)Ta yi shiru,ta rasa me zata ce wa yaran,ga shi sun tsare ta da idanu.ta ce,ku hakura kawai.tashi khalil mu tafi.MIMI ki bi zabin iyayenki.sai kawai ta ga sun soma kuka su duka biyu.MIMI ta riko hannunta, don ALLAH momy ku gudu da ni.ba zan iya rayuwa babu khalil ba.zan mutu,don ALLAH.momy ta ce,ba zai yiwu ba 'yar nan rufa min asiri. shi ma ya ce,momy don ALLAH mu tafi da ita. uwar ta kalle shi,lallai ba ka da hankali.ta dafa kafadar MIMI,ki yi hakuri 'yata.mu yi addua ALLAH yayi mana zabi na gari.har kasa MIMI ta biyo su da kuka,har gurin motarsu.maaikatan gidan wadanda ba su san me yake faruwa ba,sai kallon MIMI suke yi.sun fi zaton mutuwa ce aka yi gagaruma.fatansu allah ya sa ba maigidan ba ne domin gudun tarwatsewar aikinsu. Na'ima ce ta kama ta suka nufi cikin falon kasa.ta zauna ta ci gaba da kuka, na'ima tana bata hakuri. daidai lokacin lsmail ya shigo falon,don lokacin karatun sa ne da yara.ganin MIMI cikin halin da take ciki, har zai koma sai ya tambayi na'ima,lafiya dai ko?banza ta yi da shi cikin salon wulakanci.ya dan yi jim,can ya ce,baiwar ALLAH kuka bai taba zama mafita ga bawan da musiba ta auka masa ba. ldan kina da bukata zan ba ki maganin damuwa da yaye bakin ciki.kila ma ki cimma burinki.duk ba su tanka shi ba har ya fice. MIMI ta fi saa guda tana kuka har kanta ya soma ciwo.na'ima ta yi lallashi ta gaji,don haka ta kira momy nafisa ta fada mata abin da yake faruwa.momy ta yi ta kiran MIMI bata dauka ba,da yake tana kasa, wayar kuma na sama.sai da ta soma jin jiri.ta mike ta nufi saman.ta jima a kwance kafin ta ji rurinta. cikin sauri ta dauka. tunaninta khalil ne,ashe momy ce.ta dauka, muryarta can kasa,ta ce, momy'momy ta ce,na'ima ta fada min komai.lna so ki kwantar da hankalinki.na fada miki baza ki auri abbas ba.ta soma kuka,kin yi min alkawari momy?ta ce,ko rantsuwa nayi miki,ba zan yi kaffara ba.don haka nayi miki alkawari.lna dai sake fada miki,ki tsaya a kan raayinki.ta ce,shi ke nan momy. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (10)MIMI tana tsaye a windonta na falo,wanda yake kallon boys quaters da kuma lambun gidan. fararen tantabarunta take kallo masu yawa,wadanda dad ya sai mata tun shekaru da dama da ta ce tana so.hamsin ya sai mata, amma yanzu sun fi guda dubu,duk da cin su da suke yi.ta tuna ta yi kwanki rabonta da zuba musu abincinsu.sai masu aiki ke ba su.duk da kayan barci ke jikin ta,haka ta sauka. na'ima tana cewa ina zaki? ta ce,zan duba tantabaruna ne.tunda aka soma matsalolin nan ban je gurin su ba.ta kicin ta bi zuwa barandar baya,inda nan abincinsu yake.ta diba ta watsa musu.duk da ba safiya bace,yanzun lokacin da ta saba watsa musu,sai ta ga suna nan da yawa. har ta yi mamakin hakan, domin da rana suna fita. Kamar an ce waiga,sai ta hango malam lsmail yana shanya a gefensu.da alama ya wanke kananan kayansa na ciki ne.take zantukansa suka fado mata. in kina bukata zan baki maganin yaye damuwa da bakin ciki.kila ma har ki cimma burinki.lna ya san tana da wani buri? kodayake shi malami ne, kuma ta ji ana fadin malamai suna yin magani.ta tuna mina kawarta ta taba ba ta labarin cewa kishiyar mamansu ta yi wa babansu magani,sai abin da ta ce.a fili ta ce,zan nemi taimakon malamin nan, amma ta yaya zan yi masa magana? Da wannan tunanin ta hau samanta.ta jima kafin ta yanke shawarar kiran na'ima.bayan ta daga ne,ta ce,ina son ki je ki amso min lambar malam din nan mai koya mana karatu.na'ima ta dan yatsina,ba ki san ba na son zuwa boys quaters ba sam.bari in tura polina.MIMI ta ce,aa ki sa malam hamisu kawai ya amso miki ki kawo min.ta ce,ok. Na'ima ta amshi wayar MIMI da ke hannunta ta saka mata lambar lsmail,ta yi mata saving da malam.ta mika mata.MIMI ta ce,aje kawai.har na'ima za ta fita, sai kuma ta dawo.sis wai me zaki yi da lambarsa? MIMI ta kalle ta,ki je kawai. kar ki damu sai kin san dalili.tun fitar na'ima,MIMI take tufka da warwara a kan kiran malam lsmail.ln ta kira shi me zata ce masa?kuma yaya ma zai dauki zancen nata. [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (11)Kuma yaya ma zai dauki zancen nata? wanan tunanin shi ne ya dauke ta har zuwa karfe takwas din dare,wanda har lokacin ba ta tsai da matsaya ba. Sallamar mahaifinta ne ya zaburar da ita cewa an bude kofar.ta waiwayo,ta dube shi.kwanaki kusan hudu ba ta sa shi a ido ba, domin yana fushi da ita. cikin in-ina ta amsa sallamar, ta dinga kallon sa cike da kewa.ya zauna kusa da ita.cikin sigar lallashi ya ce,uwata ta kaina.ta dube shi,dad na yi kewarka.don ALLAH ka yi hakuri a kan abin da na yi. ya ce,kar ki damu.kina ji na MIMI,ki tashi ki je ga abbas can ya zo don ku tsara irin shagalin bikin da kuke so lokacin bikinku,ku zabi kasashen da za ku tafi shakatawa. MIMI ta yi shiru tana tunani,kamar ta amince,sai kuma ta tuno zance momy nafisa da ta ce duk runtsi ta tsaya a kan raayinta.don haka sai ta ce,dad don ALLAH ka taimake ni. wallahi dad ba na son shi. ya ce,"what?! lna cewa mun gama wannan maganar.ya rike kansa yana tunanin yadda zai bullo mata.can ya saki ya dube ta cikin lalama.MIMI ki yi nazari da kyau.tunda kika fito cikin mahaifiyarki nake dawainiya da ke.na fifita ki cikin 'ya'yana.na yi miki dukkan gata.MIMI zan tambaye ki,na taba neman wani abu gurinki? ta ce,dad,ni ba ni da komai da za ka nema.ni ma da kai nake takama. ya ce,to yau ina neman alfarmarki,ki taimake ni ki min biyayya,ki auri abbas.ta ga kamar zai sauko ya runsuna mata.sai ta yi sauri ta ce,na amince dad.ta soma kuka wi-wi.ya rungume ta.na gode 'yata. ni da ma na san irin son da kike mini ba za ki ba ni kunya ba.daina kuka.ki share hawayenki.ki je ku yi magana.ln kun gama,ni ma ina son mu yi magana da ke.za mu je store din wani abokina ki zabi kalolin gadon da kike so.gidanki dakunan barci shida ne; gaba dayansu zan zuba miki gadaje na alfarma 'yan dubai da chaina da lndiya. zan nuna miki wata mota da na yiwo miki oda.ba ta karaso ba.amma hotonta yana cikin laptop dina don ki yi yawon amarci in kun dawo.... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (12)Shakatawa tashi maza ki je kin ji MIMI. MIMI ta mike cikin kasala ta nufi dakinta.mayafi kawai ta dauko,suka jera da mahaifinta har kofar falon baki ya raka ta.sai da ta shiga sannan ya dawo. Ta zauna kujeri biyu tsakaninta da abbas.ya mike ya dawo wadda suke daf da juna ya zauna. sabon kuka ta soma.abbas ya ce,haba MIMI,wai ta ina ALLAH ya rage ni ne da kike ta ki na har haka?ta dago ta dube shi,"Ya rage ka ta soyayyata.abbas don ALLAH ka taimaka min ka rabu da ni.khalil kadai nake so.ya tausasa murya,MIMI ki ba ni dama ni ma in nuna miki kalar tawa soyayyar. na yi miki alkawarin zan koya miki sona har sai kin manta cewa an taba halittar wani da namiji a doran duniya in ba ni ba. Ta ci gaba da kukanta.ya ci gaba da fadin,gobe karfe goma zan zo mu fita.ki fada ma kawarki amina, zan zo da abokaina don mu duba guraren da za mu yi shagalinmu.me da me kike son mu yi?ni dai ina son dinner. Ta ja tsaki,don ALLAH ka bar ni,ka shiga tsakani na da mahaifina.ya ce,kin kasa yi masa biyayya ne MIMI?me zai sa ba zaki yi wa mahaifinki sakayyar son da yayi miki ba?ta mike,zan je in kwanta,kaina ciwo yake.ya ce,ba ki ba ni amsa ba.MIMI ta ce,ba ni da amsar da zan ba ka.amma ka sani in ka matsa cewa sai ka aure ni,nadama da dana sani sune karshen lamarin. shi ma ya mike, ban damu da su ba MIMI, saboda ban taba sanin su ba.kada ki manta gobe karfe goma za mu zo. fatana za mu same ki da kawarki.suka fito a jere.ta ce,ban taba ganin mutum mai son kai irin ka ba.ya ce, ban taba ganin mara tausayi irin ki ba.ko barci fa bana yi.amma ban damu sosai ba,da kin zama a gefena,zan rama duk barcin da na ci bashi.tsaki ta ja,har yanzu ban taba hasashen hakan ba.ko cikin mafarki aurenmu ba zai kasance ba,na yi ma kaina alkawari.daidai lokacin suka iso babba falon,ya runsuna ya yi wa dad bankwana tare da sanar da shi cewa gobe za su fita don duba guraren da ya dace su yi bikinsu.dad ya ce ba damuwa,sai ka zo.ya kalli MIMI wadda ke shirin... [01/10 9:45 pm] Abdul: STEP (13)Ya kalli MIMI wadda ke shirin yin samanta ya ce,ki taka masa mana zuwa gurin mota.ba ta yi gardama ba, suka fita. Ya dube ta, nawa kika sa in auren ya kasance?ta ce,in har auren nan ya kasance,na yi maka alkawarin halaka kaina.ya waigo ya dube ta,ni kuma nayi miki alkawarin hana hakan faruwa.sannan zan yi kokarin ganin mun samu 'yan biyu a haihuwarmu ta farko.rasa me za ta ce ta yi,sai ta ja tsaki,ta koma ciki tana jin shi yana cewa,mu kwana lafiya. Dad ya ce,zo uwata zo ki ji.ya bude laptop dinsa ya dinga nuna mata kalolin kayan kicin din da momy nafisa ta siya ta turo masa ya gani.ya ce,suna da kyau, sun yi miki?cikin kosawa ta ce,eh.ya nuna mata motarta.motar ta ja hankalinta don ta shekara mai zuwa ce,amma ga shi an sai mata cikin wannan shekarar.ya ce,bari ki ga fa irin gadaje da abokina ya turo min.su ma sai kin zaba. Ta kalle su,ta kalli dad, sun yi yawa.ya ce kar ki damu uwata.zan yi miki duk abin da kike so.zan kashe ko nawa ne gurin auren nan ba tare da jin cewa na yi asara ba.ribar mai daya in aka bani kwangilarsa,zan ribanya dukkan kudin da na kashe. MIMI ta mike.zan sha magani dad,zan kwanta ne. ya ce,to je ki kwanta.ya fada miki za ku fita karfe goma ko?ta ce,eh.ya ce,to sai ku je har da na'ima.ta ce,to.A sama MIMI ke ta nazarin abubuwa.zuciyarta ta fi aminta cewa ta bi umurnin mahaifinta.dubi duk daular da yake shirya mata. gaskiya bai kamata ta bari a ji su ba.ita da mahaifinta.hakuri shi ne kurum mafitarta.za ta huce haushinta a kan abbas ne kurum,wanda ya dage cewa sai ya aure ta. Har ta kwanta da nufin barci,sai agogonta ya buga sha daya.kallon agogon ya zo daidai da ringin din wayarta.khalil ne.gabanta ya fadi.shi da take tunanin shafe babinsa,amma ba ta iya share shi,don haka ta daga.cikin sanyin murya ta ce,dear,ina ka shiga na kasa samun ka a waya?ya ce,na yi kokarin na hakura da ke ne,shi ya sa na kashe wayata,sai na ga ashe ba zan iya ba.zan mutu MIMI.don ALLAH ki fada min yaya za mu yi." [01/10 9:45 pm] Abdul: ya soma kuka. itama kukan ta soma yi. sai kuma ta tuna da batun malam Isma'il. da sauri ta CE, yauwa Khalil zanyi wa malam din nan magana, ko zai bamu magani. ya ce AI ba irin shine masu yin maga ni ba. ta ce bari kaji abin da ya CE min... nan ta fada masa yadda sukayi. ya CE, OK, ki kirashi yanzu. sai dai ina so ki Sani ba mu da ishashen lokaci, sabo da kullum kwanakin aurenki kara matsowa yake. ta CE, to bari in kira shi. zan fada maka duk yadda m kayi. ba tare da wani dogon nazari ba, mm ta soma kiran Layin Isma'il. ya gama shafa'i da wururi kenan, yana kwance kan doguwar dar dumar, duk hankalin shi ya koma katsina, gani yake kamar akwai abin da mahamud yake boye masa. yana ganin cikin satin nan zai koma gida...karshen wata yayi mashi nisa, duk da saura kwanaki takwas watan ya kare... Ringing din wayar Sa ne ya katse masa tunani. cikin sauri ya duba, bai San lambar ba, amma yadda yaga numbobin ya San cewa na musan man ne. ya daga tare da sallama, yar siririyar murya CE, ta amsa da helo! ya sake yin sallama, ta CE, ni ce mm. ya CE, baki amsa sallamata ba..." [01/10 9:45 pm] Abdul: Wanda ya kasance ba ya qmsa sallama wajibi ne a cikin addini. cikin kosawa ta amsa, sanan Tace, kasan dalilin kiranka..? ya CE, a a...Tace, ka CE, zaka bani maganin bakin ciki da, yaye damuwa. sanan kace, zan iya cimma buri na. Isma'il yayi dan murmushi, amkar yana gaban ta, sanan ya CE, kwarai kuwa...ta CE, to don Allah ka tai maka min ina cikin damuwa, mahaifi nane .yace, dakata! ba sai naji damuwar ki ba, ko abin da kike ciki ba, sanan zan taimaka maki. ta ce , nasani malam. INA so be kawai in fada maka, kila zaka tausaya min cikin gaggawa.. ya CE, Allah ne me taimako. tun da kin zabi ki fada min, INA sauraron ki.." ta CE, dady nane zai yi Mun auren dole...INA kuma da Wanda nake so. wlh mlm ni dashi Muna cikin wani hali. shine muke son mafita. Isma'il yace, mafita dai ita CE komawa ga Allah. Zaki: ya tashi cikin dare..?...ta CE, zan iya ko mai mlm don in cin ma buri na. ya CE ki tashi karfe ukun dare kiyi alwala, kiyi sallah raka'a biyu ko sama da haka. [01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki. in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki. sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma. ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka. Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki. ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba... ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi. ta CE, to, amma ka bari zan kiraka. Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.." [01/10 9:45 pm] Abdul: ki fada wa Allah da muwarki. in sha Allahu Allah zai yaye maki halin da kike ciki. sanan ki yawaita zikirin Allah da karatun Alkur'ani mai girma. ba wai sai can cincikin Alkur'ani ba, ko kanan surorine kiyi ta karanta su, Zaki sami waraka. Mimi dai shiru, tayi, yana magana ita tana kuwa tana tunanin ta daban...to, shi wanan malamin da yake cewa tayi sallah, baya ganin cewa da ba ta damu da yin sallah ba, yanzu da matsala ya sameta, sai kuma ta wai wayi sallar...?...tam kar ya shiga zuciyar, ta, ya CE, kar ki dubi yawan zunubin ki, matsawar kika t ba, Allah zai yafe maki kurakuran ki sanan, yana da kyau kiyi adu'ar istihara, wato Neman zabin Allah kafin kikyi zabin mahaifin ki. ta CE, to malam AI ni ban iya ba...duk abin da ka CE min inyi din nan bansan ta inda zan fara ba... ya CE, in kin amince sai in koya maki yadda zakiyi. ta CE, to, amma ka bari zan kiraka. Khalil, ta kira, ta fada masa ko mai.." [01/10 9:45 pm] Abdul: Shi ya sa kike son shi,to ki ba abbas dama ki ga irin tasa.MIMI ta ce,ke yanzu za ki so a raba ki da faisal?ta ce,aa. amma in ta kama zan iya sadaukarwa.ina nufin dad dinki ya cancanci sadaukar da soyayyarki don ki faranta masa rai. MIMI ta ce,na yi yunkurin haka,amma na kasadon haka yanzu mu tsai da shawara ta karshe,ni da khalil.kuma ita ce mafita. mina ta ce,me kuka yanke? MIMI ta ce,kar ki damu,ba sai kin ji ba.suna yin zantukan nan ne a inda suka kebe kansu lokacin da abbas da abokansa suka je gurin manajan hall din da su mina suka ce yayi musu. Duk komai mina da na'ima suka zaba,MIMI ko kallon su ba ta yi.sai kusan daya saura suka nufi gidan da za su zauna.ba su da nisa da gidan iyayen mina. sai murna take yi,wai za ta dinga zuwa a kai,a kai,ga shi gidan ya burge ta.ko MIMI ta yaba gidan a zuciyarta,amma ba ta nuna ba. abbas ya zo kusa da ita,dear ya kika ga gidan naki?saman nan naki ne ke daya,falulluka uku,duk naki ne.da na lura kina son zama a sama,shi ya sa kike abar so kamar tsuntsaye.MIMI ta kau da kai,ina jin yunwa,don haka zan je gida.ya ce,bari mu je gurin cin abinci,mu ci mana. ta ce,aa ba na cin abincin ko'ina,ba komai nake ci ba. ya ce,shi ke nan bari mu fara kai mina ko?ba ta kanka ba ta nufi fita. sun fara sauke mina wadda take ta yaba wa abbas,har MIMI ta soma jin haushinta,ya sauke abokansa gidan cin abinci, ya ce bari ya kai ta gida ya dawo,zai same su a nan.duk zantukan da yake mata tun sad da suka taho ba ta tanka shi ba,har suka zo gidan,yana yi mata magana,ba ta tanka shi ba. ta sauka ta nufi ciki. ko da ya koma,abokansa korafi suka yi masa a kanta.munir ya ce,don tana da kyau sai ta hada da iskanci?don wannan ya wuce jan aji,tana kallon mu sai ka ce ta ga kashi.ya ce,ku yi hakuri abokaina.tana cikin fushi ne,amma lokaci kadan za ku ce tafi kowa kirki a nan gaba.dariya suka yi masa,don sun gane yayi nisa a soyayya. [01/10 9:45 pm] Abdul: Isma'il yana murna zai soma cusa tauhidi a zuciyar MIMI,ya tanaji abubuwan da zai fada mata don kara cusa mata ALLAH a cikin lamurranta.ya yi ta jiran kiranta,amma shiru.bayan laasar sun fita shi da direban yara,hamisu ke nan, don in an aike shi ko zai kai yara wani gurin,lsma'il kan bi shi don ganin gari.ya kosa su dawo don ya kira ta.haka kuwa aka yi.suna dawowa ya shiga daki,sai da ya zauna tsakiyar katifa ya nemi layinta ya kira.gab da za ta tsinke,ta daga.ya yi sallama.a kagare ta amsa.ya ce,ya ranki ya dade na ji shiru ne?ta ce,malam ka bar shi kawai.mun canza dabara. khalil ya ce naka zai ci lokaci.lsma'il cikin sauri ya ce,amma nawa shi ne mai tabbas,ln kin yi sabanin abin da na fada miki,karshe ki yi nadama.ba lalle ba ne adduarki ta dauki lokaci, domin ALLAH mai jin kan bayinsa ne.ba ki da wata dabara sabanin yi masa biyayya.ta yi jim,ta ce,don ALLAH ka bar shi kawai malam.sai ta yi tsaki.ta kuma kashe wayarta. Ta ko'ina abubuwa sun dauki zafi,domin ko can katsina tuni an daura auren zainab da alhaji lawal.an kuma kai ta gidan.matansa uku ga yara nan kwatsam. gidan bene ne hawa daya. dakinsa ne a saman,sai matarsa ta ukun,sai kuma dakin zainabu.a kasa matansa biyu ne da 'ya'yansu da kuma 'ya'yan wasu matan da suka fita. tunda aka kai zainabu take cikin kuka.bayan kowa ya kama gabansa,ta tashi ta datse dakin alhaji lawal ya taho misalin karfe sha daya da tsarabar kazarsa da abin sha.ya murda kofar amarya,ya ji ta gam.ya yi ta bugawa tamkar zai balla kofar ta ki budewa.ba zainabu ba,ina zaton duk matan gidan suna jin irin zagin da yake surfa wa amaryar tasa.fadi yake,ni zaki kawo wa rainin wayo don ubanki?yar matsiyata, ba za ki bude ba?ln kika bari na balla kofar nan na shigo,sai na karairaya ki,ko in sa a daure iyayenki har sai su biya ni abin da na kashe.lta dai zainabu jikinta sai bari yake yi,tana ta kuka.alhaji cikin takaici ya nufi dakin matarsa ta ukun ya sauke mata wahalar da ya debo ta magungunan da ya dankara. [01/10 9:45 pm] Abdul: Zainabu har goman safe ba ta bude kofa ba.sai da ya bar gidan,uwargidan ta zo ta buga,ta ce,bude yarinya ni ce,shi ya fita. matar ta shiga dakin,tana kallon zainabu cikin tausayi,ta ce,ALLAH sarki, ashe yarinya ce karama.ke ko me ya kai ki auren alhaji?cikin kuka,zainabu ta ce dole aka yi min.kudi ya nuna wa iyayenalna da wanda nake so,yake so na.ta ce,amma iyayenki ba su bincika ba ne?ta ce ni fa ban san komai a kan auren nan ba.ta ce,kai iyaye da yawa suna yin kuskure.da zara sun ga kudi,sai su tura 'ya'yayensu kawai,babu bincike. zainabu cikin tsoro, ta ce don allah hajiya me yake yi?ta ce,ba komai,kar ki damu.shawarar da zan ba ki,kar ki sake rufe masa kofa.duk abin da ya ce,ki yi,kar ki ke yi masa gardama hakan zai fi miki alheri,ke da iyayenki.ln kuma kin ki,to zai tozarta ku gaba dayanku. zainabu cikin kuka ta ce,na shiga uku!hajiya to ke 'yar uwarsa ce?aa,ni ce matarsa ta farko.ya aure ni tun bashi da ko kwabo. 'yayana goma da shi. zainab ta zaro ido,dama yaransa goma ya boye min?ta ce,nawa ke nan kadai 'ya'yansa ashirin da biyar,banda masu ciki uku. zainab ta ce ban gane ba. matar alhaji ta ce,matan da ya saka goma cif.ta karshen tana da ciki.sai sauran matansa biyu,duk suna da ciki.zainabu ta sake rushewa da kuka,tare da cewa,ita dai za ta gudu. matar ta ce kar ki fara!zai sa a kama iyayenki,kuma ba zai sake su ba sai ran da ya ji an ce an ganki,kin dawo dakinsa, ta mike, bari in sa a kawo miki abin kari. zainabu ba ta ce aa ba,dm tana jin yunwa,rabonta da abinci tun jiya da safe.koko ne da kosai,duk sun huce,yarinyar da ta kawo za ta kusan saarta.zainabu dai haka ta tuttura. da rana lnna yalwa ta zo, aminiyar lnnarsu ce.zainbu cikin kuka ta fada mata komai.lnna yalwa,ta ce,da allah can, duk karya ta fada miki,kika kama.kishiya ce har za ta ce miki ga laifin miji,ki hau kai?zainabu ta ce,lnna yalwa gaske ne.ga shi nan jiya sai zagi na yake yi dana rufe masa kofar.jiya fa na zo gidan.ln da mutunci bai dace yayi hakan ba. [01/10 9:45 pm] Abdul: Laifinki ne.yaya zaki rufe masa kofa?lna kika taba jin haka? bayan tafiyar lnna yalwa,ba jimawa yaran gidan suka cika mata daki, wanda gado ne kurum wanda alhaji ya sa mai kyau ne,amma da gani ba sabo ba ne.wadda ya aura nan dakin yake kawo ta.ln za ta tafi kuma ta bar masa gadonsa. ya shigo tana sallar magariba.ya zauna bakin gado,yana ta huci,sai ka ce kumurcin maciji.tsoro da fargaba suka hana ta idar da sallar.sai yi take tana sallamewa.ta sallame ta sake mikewa.ya finciko ta, ni za ki zo mawa da salon salla?magariba dai rakaa uku ce.kuma nafilar da na sani bayan magariba rakaa biyu ce,amma ke da na shigo kike ta zabga salla ko?cikin tsoro da kuka ta ce,aa baba ba haka ba ne. baba?ya tambaye ta,cikin fushi.kuka ta ci gaba da yi. ya kashe ta da mari,nine babanki?to,bari in nuna miki cewa ni mijinki ne,ba ubanki ba! da karfinsa ya yi amfani,ya raba ta da tufafinta,ya jefa ta kan gadon.duk 'yan gida da yara suna jin ihunta.da ma ya yi mata nata shiri na musamman.don kansa ya bar ta,ba don rokon da take masa ba,ko don wahalar da ta sha.ya bar ta yashe ba kulawa bare tausayawa,ya nufi dakinsa. haka ta kwanta babu barci sai kuka take yi.ya fita da wuri,don haka hajiya lndo ce uwargidansa ta zo ta duba ta,ta dafa ruwan zafi ta taimaka mata,ta ba ta abin kari.tsawon sati guda da yayi a dakinta bai raga mata ko sassauta mata ba.haike mata kurum yake yi.don haka ta sha azaba.tsoronsa da tsanarsa sun dasu cikin zuciyarta. khalil ya yi nasarar goge dan imanin MIMI da dan tauhidin da lsma'il ya soma cusa mata.ya zuwa 'yan kwanakin da suka biyo baya,sun yi nisa cikin tsarin yadda za su gudu.ko yanzu da suke yin waya fada mata yake yi,ta nuna cewa ta amince sai daf da auren sai su gudu.suna da bukatar kudi kafin ranar.ya ce,zan dauki sarkar mamana in kai kasuwa in sai da,sbd dad dinmu ba shi da kudi a gida sbd siyasarsa din nan.MIMI ta ce,kai baka da naka kudin ne?ya ce,account dina babu kudi,bai fi dubu ashirin ba.dad baya zuba mana kudi. [01/10 9:45 pm] Abdul: (2)Dad baya zuba mana kudi sosai yanzu saboda siyasa.ta ce,ka bar shi,ina da kudi a cikin karamin account dina.kamar nawa za mu rike?ya ce,muna bukatar kudi sosai,sbd za mu kama guri mai kyau ne a wani state din wanda ba za su yi tunanin za mu je ba.MIMI ta ce,ok,ka samo,ni ma zan samo,sai mu hada.ya ce,shi ke nan sai mun yi waya. bayan sun yi bankwana ta soma tunanin yadda za ta kwashe duk wani abu nata mai amfani.matsalarta daya.kudinta masu yawa suna cikin babban account dinta.ln kuma ta taba dole ne mahaifinta ya ji alat. Momy nafisa an dawo daga dubai,'yan gidansu abbas sun kawo kayan lefe.ran hajiya sauda ya baci da yadda alhaji ya nuna mata.matsayinta na wadda ta haifi MIMI ya kyautu a bata hakkinta ko da na shawara ne,amma alhai yayi mata dif,tunda ta ce baza ta shiga lamarinsa da MIMI ba,ita 'yar ba da shawara ce.bata fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma alhaji kurensa,amma ya dauka da zafi,don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je,domin auren abba a nan katsina aka yi shi,na MIMI in baza a kawo nan ba,to su je can su yi kayansu. biki saura kwana goma MIMI ta yi wanka,ciki sauri ta zura doguwar rigarta atamfa,sai dan bakin karamin mayafi. takalmi mara tudu ta saka,ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki,ta zuba su cikin jakarta da takan je saloom,ta ra aya takar.ta kwashi wayoyinta.tana sauka kasa,momy zata hawo saman ta ce,aa sai ina haka MIMI? ta ce,za ta je saloon.na'ima ta ce yayi wuri sis.saura kwana goma biki fa?MIMI ta tabe baki,ke kika san da wani biki,ni kam ban san da shi ba. momy nafisa ta ce,ki zo ga tela,zai gan ki sbd dinkunan kayan biki,kin ki zuwa ki ga kayan ki.MIMI ta ce.momy har da ke a wannan maganar bayan kin san komai?ni fa ba son shi nake yi ba.momy ta sassauta murya,yanzun dai ki bi ni kawai.ln lokacin da za ki ce wa alhaji baki son abbas yayi,zan sanar da ke ki tubure kawai.a ran MIMI ta ce,ke ma baki san namu shirin ba.a fili ta ce, [01/10 9:45 pm] Abdul: (3)A fili ta ce,shi ke nan momy.tela ya gwada MIMI sosai.kafin ta fice,makullin motar momy ta dauka ta fita.lta ta ja motar zuwa bankinta na karamin asusunta,inda ta kwashe kudinta kaf.ta nufi babban asusun da ke wani bankin daban,ta dibi dubu dari biyu.za ta kara sai kiran dad ya shigo.ta daga ya ce,MIMI kina ina ne?ta ce, ina banki ne.dad ya ce,yaya kika taba wannan account din MIMI?ta ce,dad ba ni da kudi ne,kuma zan yi gyaran jikina ne.ya kalli alhaji akilu,ya ce,shi ke nan ya isa,ki bari zan ba ki kudi. kar ki kuma cira daga wannan account din,ina son yi miki wani tsari ne da kudin.za ki yi kasuwanci kina daga gida,kuma na manyan kudi kin gane?MIMI ta ce,eh dad ba zan kara cirewa ba.ya ce,shi ke nan. alhaji bishir cikin dariya ya ce,ka ji 'yar kwal uba? wai tana fadin bata so,amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.suka sa dariya.alhaji akilu ya ce,me na fada maka?kiyayyar mata ba ta zuwa ko'ina.amma shi ma abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin. alhaji bishir ya ce,ai ita da shi duk daya ne.ka rabu da shi,zan ba ta.alhaji akilu ya kira layin abbas.bayan ya dauka,ya ce abbas ya baka bai wa amaryarka kudin gyaran jiki ba?abbas ya ce,dad ta ki ba ni damar in san abin da take bukata ne.amma zan ba ta anjima. ya ce,shi ke nan ka je ka ba ta.ka lallabe ta,ka san yarinya ce.abbas ya ce, insha allah dad. MIMI gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su,amma banda kaya. lsma'il ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da alhaji bishir ya yi musu albashi.duk da kin karatun da MIMI ta yi,bai sa alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba.lsma'il yayi ta juya kudin a cikin dakinsa,yana farin ciki.sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa.lalle goben nan sai katsina,ya je ya biya kudin gaisuwa,ya hada kayan sa rana,ya sai ma zainabu waya,yayi alheri,yayi sabbin dinkuna,yana ta baje burinsa.nan ya kira mahmud ya sanar da shi cewa gobe yana tafe. [01/10 9:45 pm] Abdul: (4)Tun dare yake ta shirin sa,washegari ya kira hajiya sauda ya fada mata cewa yau yana son zuwa gida ya ga 'yan uwa.ta ce ba laifi,sai ka iso.ln ka zo kuma don allah ina neman ka.ya ce babu matsala.sai dai ina son don allah ki sanar da alhaji sbd ban san lokacin da zai fito ba.ta ce,ya ba ka albashi dai ko?ya ce, wallahi ya ba ni.ki yi min godiya.ta ce,to zan sanar da shi yanzun nan. ba a yi minti talatin ba, sai ga hamisu direba ya ce lsma'il ya je in ji alhaji.a falo ya same shi.ya zauna,ya gai da alhajin cikin girmamawa.alhaji ya ce, sauda ta kira ni,ta sanar da ni cewa zaka je gida yau. haka ne?ya ce,eh alhaji.lna son in je in ga 'yan uwa ne. alhaji ya ce,da fatan ba mu takura maka ba ko?ina nufin ka ji dadin zama da mu?lsma'il ya ce,na ji dadi sosai.alhaji ya ce,to ina fatan za ka dawo.lsma'il ya ce,eh to,na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure,shi ne ban sani ba ko hakan yana nufin ni ma na gama aikina ke nan?alhaji yayi murmushi,ai in na lura ita din bata yin karatun,amma kannenta suna yin karatun. kana yi mana salla.ga yaran nan suna yin karatu sosai,suna yin salla a kan lokaci.wannan ya fi min komai.yanzun ma da ka ce zaka je gida din,na kira ka ne in ji ko kwana nawa za ka yi?lsma'il ya ce,to ina ganin dai zan yi kamar sati daya.alhaji ya ce,har sati daya?na zaci baza ka wuce kwana uku ko biyu ba.har me zaka yi haka?lsma'il ya ce,eh to ina so dai za a sa ranar aurena ne tukuna.alhaji yayi 'yar dariya,oho haka ne?to ba damuwa.allah yasa alheri.ya laluba aljihunsa,dubu biyar ya kara masa.ga wannan kayi kudin mota.ka amshi lambata gurin sauda.ln ya so in ka tashi kira na.sai ka kira ni kai tsaye,ba sai ka bita gurin hajiya sauda ba.lsma'il ya ce,to na gode sosai. bayanan fitarsa ne momy nafisa ta ce,na lura yaron nan yayi maka ko?alhaji ya ce yana da hankali sosai.lna son mutum haka.har gareji, hamisu direba ya kai lsma'il,bayan yayi sallama da dukkan maaikata gidan. [01/10 9:45 pm] Abdul: (5)Kowa yayi kewarsa, damuwarsu kar ya dade ko ya ma ki dawowa. shida na yamma daidai ya isa gida.matasan da suke zama a gindin bishiyar da ke kofar gidansu suna nan zaune kamar yadda suka saba.hirar ta kwallo ce sai ta siyasa.dukkansu sun juyo suna yi wa lsma'il sannu da isowa,bayan dayansu ya sanar da su cewa ga lsma'il nan ya dawo.ya isa gurinsu ya babba su hannu suka gaisa.suna ta yi masa murna da samu aiki a abuja. wasunsu har suna cewa.ustaz ka ga yadda ka yi kyau kuwa?gaskiya abuja ta amshe ka! shi dai godiya yayi musu,ya shige gida.kai tsaye cikin gidan ya shige.matan gidan suna ta haramar sauke girki, sallamarsa suka ji.fatu ce ta soma ganin sa.cikin irin faraar da bata taba yi masa ba ta ce,ga yan abuja,ga yan abuja!nan dai aka yi ta masa sannu da zuwa.ya amsa cikin jin dadi da mamakin fatu.a wata zuciyar ya ce,kila don dai ta daina ganin sa ne. dakin lnna ya shiga ya gaishe ta,sanan ya mika mata tsarabarsu.ya tashi ya koma dakinsa ya bude,yayi kakkabe-kakkabe a gurguje,sbd lokacin salla ya kusa.ya shimfida katifarsa,ya dauki bokitin ruwa wankansa ya kulle kofar da makulli,ya nufi cikin don yin wanka.da ya dawo,yayi alwala ya zura jallabiyarsa ya sake kulle kofa ya nufi masallacin kusa da su. bayan idar da sallar ya dawo ya zauna ya kasafta kudinsa,ya adana sauran ya canza kaya tare da fesa turarurruka masu kamshi.ya yi kyau matuka cikin shadda mai ruwan toka,ya murza hula.ya kosa ya ga zainabu,ga shi tunda ya shigo garin katsina yake ta neman layin mahmud. cikin nishadi yake takawa,duk da lokaci bayan lokaci gabansa yana faduwa.sam ba ya ganin nisan gidan su zainabu daga nasu gidan.a kafarsa ya taka.har ya je kofar gidan,sai kuma ya tuna bai zo mata da tsaraba ba.don haka ya juya,ya tare dan acaba ya hau,sai wani shago ya je inda ya siyo mata waya ta naira dubu biyar.ya sake komawa kofar gidan.kamar an turo shi,sai ga kanin zainabu.kafin lsma'il yayi masa magana har ya juya da gudu ya koma ciki.a ran lsma'il ya ce, [01/10 9:45 pm] Abdul: (6)Yawwa kira ta,kai ma ka zo ka dan ja wani abu.kwarai idanunsa suka kosa su ga fitowarta.cikin duhun zauren ya ga alamun fitowar mutum.a zatonsa zainabunsa ce,har da gyara tsayuwa. muryar mahaifiyarta ya ji daga sama tana cewa,sannu malam lsma'il da zuwa.cikin faraa ya ce,yawwa lnna. cikin girmamawa ya gai da ta.ta amsa.ta ci gaba da cewa,sai ka samu labarin zainabu ta yi aure ko?ledar wayar da ke hannunsa ta subuce,ta fadi a kasa.cikin in-ina ya ce,mene kika ce lnna?ta ce,zainabu ta yi aure.allah ya sa ba rabonka ba ce.kodayake laifinka ne. tunda baka kawo ko da sallama ba.lsma'il ya ce, inna don allah kar kiyi min haka.da shirina na zo.sai an sa bikinmu zan koma.ta ce assha!ai ka bar shiri tun rani yaro.tana gidan alhaji lawan.ba tare da jiran sake ji daga gare shi ba ta koma ciki. lsma'il ya tsuguna,ya dauki wayarsa jiki babu karfi,zuciyar na tafarfasa,ya nufi gidan yaya amina.da kyar ya kai. sai ganin mutum ta yi babu ko sallama.kan tabarmar da ya gani a shimfide ya zube zaune tare da dora kansa a guiwowinsa.cikin fargaba ta ce,lsma'il lafiya?ta tambaye shi fiye da sau biyar,ya dago kai da kyar ya ce,lafiya lau.ta ce ina fa lafiya,dube ka fa?me ke maka ciwo?ya girgiza kai, babu. ya sake dosa kansa a kan hannuwansa wadanda suke sarkafe a guiwowinsa.ya ce,yaya ashe zainabu ta yi aure?ta ce,au da ma damuwar ke nan?ta sake tausasa murya,ka yi hakuri.allah ya rubuta cewa zainabu ba matarka ba ce.nan ta shaida masa abin da ta ji game da auren. ya ce,mahmud bai kyauta min ba.me zai sa muna waya,amma yaki sanar da ni?ni na san da a ce ina nan ba yadda za a yi a raba ni da ita.sam mahmud bai cika alkawari ba,kuma bai rike min amana ba.yaya amina ta ce kar ka ga laifinsa,domin a boye duk aka yi komai.sai daurin aure aka ji.lsma'il ya sauke ajiyar zuciya,wasu zafafan hawaye suka zubo kan kumatunsa.ta ce,haba don allah lsma'il,sai ka ce ba namiji ba?kamar baka da ilimi.ka fa san komai mukaddari ne.ka yi hakuri,zainabu ba rabonka ba ce. [01/10 9:45 pm] Abdul: (7)Allah zai baka wadda ta fi ta komai.lsma'il ya ce,shi ke nan yaya na gode.ya ciro dubu uku daga aljihunsa, ga wannan yaya.ta amsa tana fadin, har da kudi haka.ya ce,ba yawa.lna ganin gobe ma zan juya kawai,da ma da kyar alhajin ya bari na taho. ta ce,haba dai ka dan kwana biyu mana?ya ce,aa ba zan iya zama a garin nan ba,ina tuna zainabu.lna bukatar cire ta daga raina. ya mike a kasalance,ya dauki ledar wayarsa ya ce,to ni sai na dawo.ta ce, ba zaka biyo ba gobe ke nan?ya ce sammako zan yi. da kyar ya isa gida.tunda ya bude kofarsa ya fada kan katifa,bayan rufe kofar ya soma kuka.shi kansa bai san yana tsananin son zainabu haka ba sai da ya rasa ta.ya yi kuka sosai,ya dangana,ya fita cikin dare yayi alwala.gurin allah ya yi ta kai kukansa.bukatarsa allah ya cire masa son zainabu,ya ba shi dangana ya sada shi da mafi alheri. daga bisani ya dauki alkurani,yana karantawa. Kafin wani lokaci,salama ta sauka a zuciyarsa.sai da yayi sallar asubahi,ya soma jin barci. yana dawowa daga masallaci ya kwanta.ba shi ya farka ba sai goma saura. shi ma kwankwasa kofarsa aka yi ya farka.ya tashi da kyar ya zare sakatar.mahmud ne,don haka ya dawo ya zauna. mahmud ya shigo,shi ma ya zauna. lsma'il ya ba shi hannu suka gaisa.ya ce,na yi ta kiran wayarka a kashe. mahmud ya gyara zama.ina sane na kashe,domin bana so ka rike ni a ranka.na san dai zuwa yanzu kaji komai.lsma'il ya tsura ma bakin kofa ido,kamar mai kallon wani abu a gurin. mahmud ya ce,ka yi hakuri allah ya kaddara ba matarka ba ce.lsma'il ya ce,duk da haka mahmud,kai ma na ga laifinka.me zai sa ba ka kira ni ka fada min ba?na tabbata zainabu dole aka yi mata,don tana so na.mahmud ya ce,fada maka ba zai kare ka da komai ba.a lokacin da na samu labarin kwana kadan suka rage a daura aure. amma ka yi min afuwa.lsma'il ya ce,ni yanzu zan shirya in koma abuja.malam yana nan kuwa?mahmud ya ce,yana nan.na dai bar shi a gida. haba dai ka ce yau za ka koma?ya ce.tun jiya katsina ta fita daga raina. [01/10 9:45 pm] Abdul: (8)Mahmud ya ce,allah yasa hakan shine mafi alheri.amma ya kamata ka dan yi kwana biyu.lsma'il ya ce,in na zauna babu abin da zan yi.da a ce na san da wannan matsalar.lallai da ba zan zo ba.mahmud ya ce,shi ke nan allah ya kai ka lafiya.ko wanka lsmail bai yi ba,ya hada nasa-ya-nasa ya shiga cikin gida yin sallama.fatu ta ce, lsma'il sai ka ji batun auren zainabu.bai san lokacin da murmushi ya sauka a fuskarsa ba.ya ce,zainabu ta yi aure.fatana allah ya bata zaman lafiya.fatu ta yi 'yar dariya,ka dangana ke nan?bai tanka ta ba,ya wuce abinsa dakin lnna.ya shiga ya sanar mata cewa zai koma,ya kawo dubu biyu ya bata.ta amsa tana godiya.ta ce ko ka hadu da yan uwanka?ya ce mun gaisa da asuba a masallaci,amma ga wannan ki basu.ya mika mata dubu uku.ta ce,an gode.allah ya saka da alkhairan.sai kuma kaji wannan yarinyar da kake nema ta yi aure ko?ya ce eh na ji lnna.allah bai yi dani ba.ta ce,duk da haka ma sun so yaudararka ne.ka je ka amshi duk abin da ka san cewa naka ne,lna nufin wanda ka bata.ka kuma lssafa kudin da ka bata, tallar nan duk a amso su,ya ce,lnna a bar wannan maganar kawai.ban bata don in karba ba.ya mike,ya fito,ta ce,to shi kenan allah ya tsare hanya.nan su ma matan gidan ya basu dubu daya,ya dauki jakarsa. Bayan ya ba mahmud dubu biyu,mahmud ya ce, kudin mene ne?ya ce,kudin albashina mana.dana yi niyyar gabatar da abubuwan aurena har zuwa a sa rana.amma tunda babu zancen,gara in yi alheri in samu lada. mahmud ya ce,na gode sosai.gidan su mahmud suka je,inda ya ba malam dubu uku.ya goya shi a mashin dinsa.har za su wuce tasha,ya ce,kodayake ka kai ni gidan alhaji bishir in gaisa da hajiya sauda.sai da suka je kofar gidan,ya kira layin hajiyar ya ce mata ga shi a waje,ta turo abdullahi suka shiga tare.lsmail bai boye mata komai ba game da MIMI na kin karatu ba.ya sanar da ita halin da yake ciki.ta ce,ba komai kar ya damu da batun MIMI tunda aure za ta yi.yanzu ya koma ya ci gaba da abin da yake yi,a kan zainabu kuma tace kar ya damu, [01/10 9:45 pm] Abdul: (9)Kila ita din ba alheri ba ce a gare shi.ta ce,in da zai yarda ma da ya koma makaranta don zurfafa iliminsa gaba daya a fannin bokon da kuma lslamiyyar ya ce,shi ma tunaninsa ke nan a yanzu suka yi bankwana,bayan ta ba shi wani turare mai kamshi.ya fito mahmud ya kai shi tasha.bai samu motar abuja kai tsaye ba,don haka sai ya hau ta kaduna. suka miki hanya,zuciyarsa da rauni,bai san lokacin da zai warke ba. hajiyar mardiyya,matar alhaji lsa mani,abokin alhaji bishir ita ce ke kwada sallama a falon hajiya sauda.hasina ce ta fito daga dakinsu ta ce,sannu da zuwa maman su nabila.ta ce,yawwa hasina,hajiya fa?ta ce,bari in duba ta.nan hajiyar mardiyya ta zauna kan kajera.hasina ta fito ta ce, tana wanka ne.hajiya mardiyya ta mike,bari in shiga cikin dakin.kawaye ne sosai,har yanzu ba su yada juna ba,don sun fi mazan nasu zumunci,har da matar alhaji kabiru,hajiya ramatu, abokansa na tun ana talakawa. kan gado ta zauna tana 'yan dube-dube. ke kullum aka zo dakinki kal,sai ka ce amarya.daidai lokacin ta fito tana cewa, me kika ce?hajiya mardiyya ta maimaita.sauda ta yi dariya,to ni ke gyra dakina da kaina.ku ko kun fi son na 'yan aiki.ta ce,to meye aikinsu in ba shara da wanke-wanke ba?sauda ta ce,ku dinga duba masu. kullum ina fada muku,suna yi kuna dubawa,kuma gyara musu. hajiya mardiyya ta ce,ke ni zuwa na yi in ji dalili ko kuma laifin da nai miki baki fada min biki ba,sai dai in ji a gurin alhaji.hajiya sauda ta yi tsaki,kin san allah,ban san komai a kan bikin nan ba.ke in takaice miki,yanzu alhaji fushi yake yi da ni.hajiya mardiyya ta ce,a kan me?ta ce,kin san bata son auren,shi ke so.ya kira ni wai in tursasa mata ta yi abin da yake so.sai na nuna masa cewa ba ruwana, yanzu ne aka san da ni?to ni shawara zan ba ta,tursasawa ba.kar ki dada,kar ki raga.daga wannan shine laifina.wai ni ce ke zuga ta.har yau bai sake ce min kala a kan bikin ba.na'ima take fada wa su hasana ta waya wai nafisa ta je dubai siyan kaya.an kawo lefe,an yi kaza,an yi kaza. [01/10 9:45 pm] Abdul: (10)Hajiyar mardiyya ta ce, amma alhaji bai kyauta ba. ko da keke zuga ta.ai kamata yayi ya baki hakkinki na haihuwa.sauda ta ce,ni ma dai shi na gani. don haka nasa musu ido.ya maki zuwa garin nan sam. ko kira waya yayi.sai ya yi ta wani dake-dake yana magana a cije. hajiya mardiyya ta ce, amma da kin yi masa magana da kanki,ki yi masa bayanin nufinki don ki amshi ragamar auren 'yarki. sauda ta ce,kin san allah ba zan kula auren nan ba.kuma ba zan taba yi masa magana a kan wai ya fahimci ban zuga MIMI ba.mu je a na zuga tan.ita ma ba halin kirki gare ta ba.so nake su gane kurensu,dukkansu shi da ita.mardiyya ta ce,shi ke nan,allah ya kai mu.mu dai za muje biki.ln abuja din ne,in nan ne ma dai duk da mu za a yi,allah ya taimaka, in ji hajiya sauda. Ana saura sati daya bikin ne,alhaji bishir ya zo katsina.bai ko sanar da zuwansa ba.barcin rana take yi lokacin da ya iso. yaran suka yi masa sannu da zuwa.kai tsaye ya nufi dakinsa,ya bude ya shiga.ya zuba jakar hannunsa da hularsa zuwa wayarsa a kan kujera. shi kuma ya zauna a bakin gado.hasna ce ta shiga dakin hajiya sauda ta tashe ta,tana sanar mata zuwan dady.ta sha mamaki sosai, domin sai ya sanar kafin ya isa.ta kalli husna,shi ne ya ce ki kira ni?husna ta ce,aa ya shiga dakinsa ne kawai.sauda ta ce,to je ki ina zuwa.har ta mai da kanta ta kwanta,a zuciyarta ta ce tunda da abin da ya zo gidan ke nan ba za ta kula shi ba.amma sai wata zuciyar ta ce, mijinki ne kina kasansa ki je. ta same shi yana cire safar kafarsa.ta yi sallama, ta shiga.daga bakin kofa ta tsaya tana fadin,sannu da zuwa.alhaji a ciki ya amsa da cewa yawwa.ta zauna a hannun kujera,na ji mamaki,ba ka ce min kana zuwa ba,kamar yadda ka saba.ya dago ya dube ta laifi ne?ta lumshe ido,cikin takaici ta ce,aa babu laifi.ta mike tsaye,me kake bukata?ina nufin abin da zaka ci ko sha?ya mike, alhamdulillah ba na bukatar ko daya.ta ce,har wanka?ya dan yi tsaki,kin ga na yi datti ne?ta kautar da kai gefe. [01/10 10:34 pm] Abdul: (12)Ameen.me kuke bukata a cikin bikin ke da yaranki? ta ce,ba ma bukatar komai bikin da ba a nan za a yi shi ba.mu ma fa yan gayyata ne.ya ce,ba na son kina fadin haka.ba za kuyi ashoben ba?ta ce,aa ba za mu yi ba.ya ce,don me?ta ce,ba za mu samu dinki ba kar ka damu.ya ce,shi ke nan.ya kwana,washegari ya wuce malumfashi.ya koma abuja saura kwana biyar biki.kuma ranar ne aka yi jeren amarya a gidan angonta. lsma'il ya isa abuja yammacin magariba. maigadi da ya soma ganin sa ya sha mamaki.ya ce, malam kai ne ka dawo?ya ce,ni ne daga kiran sallar lsha'i ne,alhaji ya bukaci ganin lsmail a kebe.bayan sun gaisa ne alhaji ke tambayar lsma'il lafiya ya dawo da wuri?lsmil bai boye masa komai ba.ya fada masa abin da aka yi masa,ya ji ya tsanin garin katsina.alhaji ya ce, kar ka damu.allah yasa haka ne mafi alheri a gare ka.lsmail ya ce,amin na gode [01/10 10:34 pm] Abdul: (11)Ta yi dan huci,ta mike. har ta kai bakin kofa,ta kasa jurewa,ta dawo,alhaji wai laifin me na yi maka da duk ka canza min.ya kalle ta,baki san kin yi laifin ba ko?ta ce,wallahi ban sani ba.ka sanar da ni mana.ba sai in baka hakuri ba.ya ce, ban zaci zan ce ki yi abu ba,amma ki ce min ba za kiyi ba.ni ne na ce kiyi wa MIMI fada kan ta bi zabin da nayi,amma kika ce min ba za kiyi ba,karshe ma sai kika zuga ta ta katse shi,na zuga ta kuma?ln ji ta ne ta ce na zuga ta?shawara na ce zan bata,kuma na bata. ka tambaye ta wace irin shawara na bata?zan yi mamaki sosai in ka ce ka mance halina.a tunanina mun kai matsayin da zaka san abin da zan iya da kuma wanda ba zan iya ba.don ni yanzun zan iya rubuta kundi a kan halayyarka.haka kuma in an fadi wanda ba za ka iya ba,zan ce sam baza ka iya yin haka ba.kansa yana kasa,yayi shiru,domin ya san cewa gaskiya ta fada.can ya dago kai,me kika ce mata?ta mike ta koma kusa da shi.bayan ta dauki wayarsa ta soma latso lambobin ta kai kan lambar MIMI ta dannan kira,ta latsa handsfree sai da ta soma ringing ta mika masa,ina son ka tambaye ta,mu ji.kafin ya ce,aa,har MIMI ta daga,muryarta ta ratso,inda ta ce,hello dad.ya ce,MIMI,in tambaye ki?ta ce, eh dad.ya ce,me mamarki ta fada miki game da auren abbas?ta ce,wace maman,momy nafisa?ya ce, mahaifiyarki.ta tura baki,dad cewa fa tayi wai in hakura in bi abin da kake so,ko don irin kaunar daka nuna min.wai shawara ta bani.ya ce,shi ke nan. yana kashe wayar sauda ta mike.ya kamo hannunta, kar ki yi fushi matata,ki yi hakuri,na fahimce ki.bai-bai ta dan yi jim,ta ce,shi ke nan ya wuce.ya ce,to zauna muyi maganar auren MIMI.ta ce bani da ta cewa game da auren MIMI,face allah ya bada zaman lafiya. yanzu ka hakura zaka ci abincin?ya girgiza kai,aa sai in kin zauna.ta lumshe ido, ta zauna.ya ce,ni ma na yi miki laifi ban fada miki komai ba.yau saura kwana bakwai.kuma za a yi bikin ne a can abuja.sauda ta ce,babu damuwa. allah ya sa a yi lafiya.ya ce ameen. [01/10 10:34 pm] Abdul: (13)Washe gari saura kwana hudu biki,amarya ta sha gyara jiki,ita da na'ima.duk abin da aka yi mata,an yi wa na'ima.mai gyara ta musammam momy nafisa ta dauko.an zuba musu zanen lalle har ba za ka iya bambance amarya ba.kawayen MIMI su mina suna ta kai koma don ganin shirye-shiryensu sun kayatar.yammacin laraba za su yi family night. na'ima tayi zaton zuwan 'yan katsina,amma shiru. MIMI bata damu ba,don ta san ita ba zama za tayi ba. rashin zuwansu ma zai fi mata.a ranar alhamis kuwa za su yi 'mothers day, wanda momy nafisa ta shirya.kuma a ranar ne MIMI suka shirya guduwa,ita da khalil dinta.amma momy nafisa a nata tsarin sai daren jumaa,in an dawo daga kumbo,an yi kamu ke nan sai ta sa MIMI ta tubure.daga nan sai ta tura na'ima ta ce wa dad din su ita ta yarda a daura da ita. An yi mothers day lafiya an tashi ana ta daukar hotuna,MIMI ta daga wayarta ta kira khalil ta ce su zo,shi da wani abokinsa kamar za ta yi magana da wani ta fita wajen hall din ta nufe su.da mota suke,don haka ta shige.kai tsaye gidan su MIMI suka koma.babu kowa,duk ana gurin biki,amma dad yana nan.da ta dauko jakarta za ta sauko sai ta ji shi yana waya.tana fitowa ta ji ashe a falonsa yake,amma daf da babban falon nasu. sai ta yi sanda ta fice.da gudu ta ja mota suka tafi. Ta dubi khalil,yanzu ina muka nufa?ya ce,kaduna. don in muka ce za mu kwana a abuja,da safe za a kama mu.haka cikin dare nan suk dauko hanyar kaduna,gudu suke yi sosai. ga shi lokacin sanyi.ga MIMI ba ta son sanyi,kuma kayan jikinta irin na amare ne,ba na dumi ba.ta kudundune duk da cewa khalil ya cire t-shirt din sa ya bata ta dora a kan kayan jikinta.shi kuma ya zauna da singileti.zuciyar MIMI ta kasa natsuwa,wani gefen yana fada mata cewa ba ta kyauta ba,za ta yi nadama,ta kunyata mahaifinta.wata zuciyar kuma tana zuga ta da cewa ke ki tafi kina kan daidai.alamarin dai ga shi nan. [01/10 10:34 pm] Abdul: (15)Amma da yaje daki na musamman suka kama,sam ba ya fitowa ko kofar daki.duk abin da suke so sadau ke zuwa ya sai musu.su kuwa su momy nafisa ba su ankare ba,suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. a zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu sai lokacin da na'ima ta zo tana cewa momy ina sis MIMI?ga abbas sun zo da abokansa.nan fa aka shiga neman amarya,ba ta babu dalilinta.hankula suka tashi. nan dai biki ya kare.momy nafisa kuka wi-wi.nan ta kira alhaji bishir tana fada masa cewa MIMI ta zo gida?ya ce babu wanda ya zo gidan nan.shi ma zuwansa ke nan.daidai lokacin da suke yin wayar da a ce ya waiwayo da zai ga MIMI,tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa. Ta ce masa,to MIMI dai an neme ta an rasa ta,ko kasa ko sama.har zuwa sha biyun dare ana ci gaba da neman ta lungu da sako, banda wayoyi da ake ta yi don ji gurin abokanen arziki. matuka hankalin alhaji ya tashi sosai.alhaji akilu ya kira shi yana jajanta masa. ya ce,amma alhaji bishir da ma yarinyar nan ba ta hakura ba?alhaji bishir ya ce,ta hakura mana.ga shi ana ta biki.sai yau a ce ta gudu?alhaji akilu ya ce,baka ganin ko yaron da suke yin soyayyar ne ya zo ya sace ta?alhaji bishir ya ce, komai zai iya faruwa.amma bari mu gani zuwa da safe.alhaji akilu ya ce,in ko ya tabbata yaron nan sace ta yayi,lallai babu abin da zai hana shi zaman gidan yari.ka ga halin da abbas yake ciki kuwa?ya ce,ko ni ma ba zan kyale iyayansa ba bare shi,tunda daga gani ba da yardarta ya sace ta ba, domin bata bar wani sako ba,ba ta dauki komai na sawarta ba.alhaji akilu ya ce,kun kira lambarta?ya ce tana ta ringing ba ta daga ba.kusan karfe dayan dare alhaji bishir ya kira hajiya sauda tana barci,ta dauka, tana fadin,alhaji lafiya?ya ce ina fa lafiya,an sace MIMI.ta diro daga kan gado.an sace MIMI kuma?ya bata labarin komai hajiya sauda ta ce,ko dai guduwa suka yi tare da saurayin nata?ya ce, bana tunanin haka,ta nuna min ta hakura.kuma sun shirya komai da mijinta, har kudi ta cire a account din ta don gyaran jiki. [01/10 10:34 pm] Abdul: (14)Dayan dare suka shigo garin kaduna.sadau abokinsa shi ne ya kawo shawarar su shiga cikin wata unguwa su nemi otal,kar su kama na bakin hanya.ta titin kagoro suka shiga,inda suka sami wani otal suka kama.MIMI ta ce su kama mata dakinta daban khalil ya ce,dear za ki iya kwana ke kadai?ta ce,eh mana kar ka damu.ta yae,shi ke nan. daki biyu suka kama a sama.khalil ya kalli sadau bayan sun kwanta,abokina ina kake ganin ya dace mu je?sadau ya ce,gobe ku shiga motar sakkwato ko zamfara.ba za a yi tunanin za ku je can ba.khalil ya ce,ni da lagos na so mu tafi,mu boye kamar na sati daya.sadau ya ce,kai banza ne.wane sati daya.ai in ni kai sai na dinke yarinyar za mu fito. yadda dole za a aura min ita.khalil ya tashi zaune,ban gane ba.sadau ya ce,ina nufin,yayi kwatance da hannunsa da cikinsa.khalil ya ce allah ya sawwake.ba ni da niyyar in cutar da MIMI zan barin mu yi halastaccen aure da ita. sadau ya ce,ka ji matsalarka.a shawarwarin da na baka,wacce ce aka samu matsala?na ce ka sai da gwal din mom dinka,mun sai da na ce ka dauke ta ku gudu.ba ga shi ka yi nasara ba?khalil ya ce,ban dauke ta da niyyar aikata wani abu ba,sai don in fid da ta daga auren wani na.kai dai naka da safe ka kai mu garejin mota mu tafi.kai kuma koma gidanku mun gode. MIMI kuwa ta kasa barci, sai juyi take yi.wayarta tana,silent,amma tana kallon kira.da wani ya yanke,wani zai shigo da farko ta ki dubawa,amma daga baya sai ta duba.kiran dad dinta ne da momy nafisa har da su na'ima. kuka take ta tayi tare da tausayin mahaifinta.ji take kamar ta daga ta ce su zo su dauke ta,kuma ta amince za ta auri wanda suke so.amma sai shaidaniyar zuciyarta ta kangare,ta kuma hana ta aiwatar da hakan.da zazzabi ta farka tare da ciwon kai mai tsanani,don haka sai batun tafiya ya fasu.sun fita suka sayo mata doguwar riga da hijabi ta saka,suka dauke ta zuwa asibitin biba.gado likita ya bata,don tana cikin damuwa.hankalin khalil ya kara tashi, tsoron sa kar wanda ya san shi ya gan shi burinsa su bar kaduna, [01/10 10:34 pm] Abdul: (16)Ba ta dauki komai ba. hajiya sauda ta ce,allah ya kyauta.amma a zuciyarta tafi yarda cewa MIMI kudi ta diba suka gudu.ta ce to yanzu wane mataki ka dauka?ya ce,mun sanar da yan sanda,gobe za mu je kaduna gidan iyayensa. hajiya sauda ta ce,to ku kuwa hada da addua. bayan sun yi sallama da kansa ya taka gefen masu masu aiki ya kwankwasa kofar dakin lsma'il ya yi sallama ya amsa,don lokacin yana ta juyi cikin damuwar rashin masoyiyarsa zainabu.jin muryar alhaji ya bude kofar cikin fargaba.ya ce.alhaji lafiya?ya ce baka ji abin da yake faruwa bane?lsma'il ya ce,ban ji ba alhaji.a zatosa ma barayi ne suka shigo gidan.alhaji ya ce mu shiga daga ciki.a tsakiyar dakin suka yi cirko-cirko. alhaji ya ce,malam lsmail a gurin shagalin biki aka sace MIMI.aka sace MIMI?lsma'il ya maimaita.alhaji abbas ya ce,na zo gurin ka ne ina son a taya mu da addua kafin gobe in samu malamina saboda ya duba min inda suka boye ta.lsmail ya ce,allah ya kyauta,ya kuma bayyana ta sai dai alhaji baka tunanin ko sun gudu ne? alhji ya ce,bana tsammani, tunda bata bar wata alama da za ta nuna hakan ba.ba ta dauki kaya ba.lsmail ya ce haka ne.shi ke nan insha allah zan taya da addua. ikon allah a gabana suka hau mota alhaji da zasu tafi. to ni dama muna yin isha'i,na yi shafa'i nake shiga in kwanta da wuri saboda ina tashi cikin dare. alhaji ya ce,to bari mu je mu yi sauraro.lsma'il ya ce allah ya jishe mu alheri. bayan fitar alhaji,lsmail yayi ta mamakin MIMI.tabbas sun gudu ne,tunda ta fada masa cewa sun samu mafita,ya kira layinta,yayi ta ringing har ya tsinke.haka yayi ta kira har ya gaji.alhji kam yana tafe yana tunanin maganar lsmail haka sauda ta ce ko sun gudu ne.shi ma gashi ya ce hakan.momy nafisa ya samu ta zabga ta tagumi bakin gadonsa.ya dafa ta,kar ki damu nafisa za a gan ta.ni damuwata ma da sauda ta ce ko dai guduwa suka yi haka ma malaminta ya fada min yanzu.sai dai ina shakku don na san MIMI baza ta guje ni ba ta bi wani sakarai. [01/10 10:34 pm] Abdul: (17)Momy nafisa ta ce,haba ba za ta gudu ba.don ta tabbatar da ya zai yi in gudun ta yi,sai ta ce,ko ta gudu ma,ai dole ta dawo.ya ce,me kika?ya mike cikin tashin hankali,ya ce kuskure mafi girma da MIMI za tayi shi ne ta guje ni.kin ji na rantse miki,in MIMI guduwa ta yi ta kunyata ni,to ni kuma sai na yi mata abin da ba za ta manta da ni ba wannan alkawarina ne. tunda asubahi momy nafisa ta shiga dakin na'ima ta ce,tashi ki ji,ga fa dama ta samu.na'ima ta gyagije daga barci.ta ce wannan gudun na MIMI yayi matukar zuwa mana a daidai.yanzun abu daya ya rage mana.shi ne dad dinku ya san cewa tana sane ta bar gida.na'ima ta ce,in ya sani mene ne?nan momy ta sanar da ita alwashin da ya ci,ta ce,kuma tabbas MIMI ba sace ta aka yi ba. ga shi na yi ta kiran ta bata daga ba.amma zan ci gaba da kira.ln ta daga zan sa ta fada wa alhaji cewa ta gudu ne.safiyar ranar lsmail yana masallaci zaune,alhaji ya fito zai fita.ya nufe shi ya gai da shi cikin girmamawa.ya dada jajanta masa.alhaji yayi godiya.lsmail ya ce,sai dai jiya na yi mantuwa.sai bayan ka tafi na tuna.alhaji ya ce,ta me?ya ce,alhaji duba haramun ne a musulunci.akwai inda yake zama shirka ma.wato mutum ya fita daga musuluci.alhaji ya ce, istihara ce ai za a yi malam lsma'l ya ce,alhji ai istihara kai ne zaka yi da kanka,ba wani ne zai yi maka ba, kamar yadda wasu malaman suke cewa don su ci kudinku.alhaji ya ce, shi ke nan.ana jira na.ln na dawo zamu yi maganar. bayan ya koma daki ne ya ga kiran hajiya sauda. nan take ya kira ta.cikin girmamawa.ya gaishe ta,ya jajanta mata abin da ya faru.ta ce,lsma'il na kira ne ina son a taya ni da adduar allah ya tsare yarinyar nan, don ina zaton guduwa ta yi tare da yaro nan.lsmil ya ce,ina yi hajiya ni mana fi zaton sun gudu ne.ta ce,ina amfanin gatan da ya nuna mata.ai da ma kuskure ne mutum ya gina dansa a kan cewa duk abin da yake so sai ya samu.gara ka nuna wa yaro cewa akwai kuma kaddara.amma sam ita ba ta san wannan ba.duk abin da take so zai mata. [01/10 10:34 pm] Abdul: (18)To yaya yanzu ba za ta turbure ya bata wanda take so ba?lsmail ya ce, haka ne.a ransa ya ce da ma hausawa sun ce,ka sa danka kuka kafin yasa ka a fili ya ce,allah zai saukaka mana lamarin da yardarsa. hajiya sauda ta ce,allah ya sa.abbas kuwa shi ma cikin tashin hankali yake.a nasa zaton an sace ta ne,tunda ya ga gab da bikin ta saki jiki.da alamu ta yarda za ta aure shi.cikin mutunci ta amshi kudin gyara jikin da ya kai mata.ranar da aka yi family night sun yi ta hotuna tare.a ce an sace ta.ko dai masu yin garkuwa da dan adam ne?alhaji akilu ya ce kar ka damu.ln ma sune zamu ba da ko nawa ne don su sake ta. Alhaji bishir ya sanar da duk masu kofofin sadarwa don neman ta,ko in ce cigiyarta.da kamfanin layin MTN aka gane cewa tana kaduna,don haka can suka dosa.kwamishinan yan sanda na kaduna shi ne ya kira mahaifin khalil ya sanar da shi cewa ga iyayen yarinyar da dansa ya gudu da ita sun zo.bai yi kasa a guiwa ba ya iso gidan kwamishinan,sun tattauna da mahaifin khalil,ya ba su hakuri,tare da tabbatar musu cewa dansa khalil ya gudu tare da yarsu.ya fada wa kwamishina cewa in ya zo a kama shi kamun barawo don ya dauke sarkar mahaifiyarsa. Daidai lokacin MIMI ta daga wayar momy nafisa, bayan momy ta tura mata message cewa ta daga su yi magana,ta san dai tana tare da ita a kan komai, bayan khalil ya karanta,sai ya ce,MIMI momy nafisa ce, ki daga wayarta.na san za ta taimaka mana.ta tashi zaune ana yi mata karin ruwa.ta daga.cikin sauri momy nafisa ta ce, MIMI kuna ina ne yanzu?ta ce momy yaya dad?wane hali yake ciki?ta ce,dad dinki yana cikin matsananciyar damuwa.yana tunanin ko an kashe ki ne,ko an sace ki.kuma sun ce za su daura aurenki gobe,ko gawarki aka gani dai abbas ne mijinki.don haka ki rubuto masa text cewa kin gudu ne,don ba ki son abbas.ke ba za ki dawo ba har sai ya amice zai baki khalil.kin ji ko,ki yi haka yanzu.na san zai ce ki dawo.cikin kuka MIMI ta ce,ni fa na soma yin nadama momy.zan hakura ne kawai in auri abbas. [01/10 10:34 pm] Abdul: (19)Wallahi ina jin tausayin dad dina.momy nafisa ta ce,aa ki yi abin da nace. 'yan gidan su abbas din ma da suke ta zagin ki,wai kin bi namiji.wa ya san abin da za kuje ku yi?MIMI tana kuka tace shi ke nan zan yi momy.ta ce,yanzu nan za ki yi,MIMI tana kuka tace to Suna cikin yin musabaha don yin sallama message din MIMI ya shiga wayar dad dinsu.bai yi kasa a guiwa ba,ya bude ya soma karantawa kamar haka: Ka yafe ni dad in na bata maka.na yi kokari in yi maka biyayya,amma na kasa.ba na jin zan iya zama da abbas a matsayin mijina.zan dawo gida,in ka amince zaka bani wanda nake so.ya dago ya kalli alhaji lsa,wanda dashi suka zo kaduna,ya ce,ka gani ko? karbi ka karanta.ka gani guduwa suka yi ba sace ta yayi ba.ni kuma zan nuna mata cewa ta yi mummunan kuskure. Da kyar alhaji bishir ya kai cikin gida saboda ciwon kai.amma kafin ya kai tsakiyar falo,tuni ya zube kasa.sabon alamari ke nan wanda yata da hankalin mutan gidan.nan da nan aka yi asibiti da shi.ya farfado,inda aka tabbatar masa jininsa ya hau sosai. an gano yana da ciwon sugar.cikin abin da bai fi minti talatin ba,dukkan iyalansa sun samu labari kuka sosai hajiya sauda ta yi domin ta san MIMI ce silar komai. karfe sha daya momy nafisa ta kira na'ima ta ce,ga lokacinki fa yayi daga yanzu zuwa da safe.na'ima ta ce,shi kenan momy ya farka ne?ta ce,eh in ya farka yana tambaya ta wai ga shi gobe daurin aure.bai san yadda zai yi ba.na dai lallaba shi.ki shirya zan fita in sa hamisu direba ya dauko ki,don shi ya kawo su kawunku da suka zo biki.tana fitowa ta leka ta ce ma hamisu ya je ya dauko na'ima.alhaji lsa ya ce ta yi me da daren nan? momy nafisa ta ce,kuka take yi sosai.kuma ta ce tana da magana da shi,cikin kuka na'ima ta shigo dakin momy ta rungume ta,yi shiru mana.ai jikin da sauki. kalle shi har ya farka. Ta isa gurin sa,dad ta kama hannunsa.dad kar ka damu ni na amince in har abbas yana so na.gobe a daura auren da ni.wallahi dad bana son in rasa ka.ya yunkura zai tashi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (20)Momy ta rike shi.ya jingina,ya kama hannuwan na'ima,da gaske kina son abbas?ta ce,ni ban san so ba dad.amma zan koye shi a gidan abbas.zan so shi in ya zama miji gare ni.alhaji bishir ya rumgume ta.na gode yata.allah yayi miki albarka.ya kalli momy ta ce,na ji.allah yayi miki albarka.kar ka damu,ka kira alhaji akilu din.bai san ma akwai matsalar bai san kana asibiti ba.ln ya zo sai ku tattauna.ya ce,haka ne. ke ma din allah yai miki albarka.momy nafisa ta ce, amin.ya ce,leka ki kira min alhaji lsa. nan suka shigo,ya sanar da su abin da naima ta ce,suka yi ta sa mata albarka alhaji ya ce,to kowa ya koma gida,insha allah,biki babu fashi.momy ta ce,alhamdulillahi ga shi da ma yan biki sun cika gidan,yan masari da yan malumfashi.hajiya binta da ma bata taho ba,tana shirin zuwa ta ji labarin batar amaryar,don haka ta dakata.yanzu kuma sai ga labarin ciwon alhajin don haka dole gobe sai abuja. A daren,alhaji bishir ya sanar da alhaji akilu komai. da yake kowannensu ba damuwar 'ya'yan bane,su dai hada surukuntar ne kawai don cimma burinsu.ba tare da neman shawarar abbas ba,ya amince da auren na'ima sai da asubahi bayan sun dawo sallah yake sanar da abbas din canjin da aka samu.nan take abbas ya ce, shi sam bai so na'ima alhaji akilu ya ce,ba damuwata ka so ta ba.ln aure ya dauru burina ya cika.ka aure ta in ya so daga baya ka auri wadda kake so.abbas ya ce,MIMI nake so.ln kuma ina auren kanwarta yaya zan yi in aure ta?ya kawo iyaka wuya,cikin fada yake cewa,kai ma za ka yi min irin abin da 'yar alhaji bishir ta yi masa ne?to bari ka ji. ba zan dauki rainin wayo ba.kawai kayi abin da nace. dukkan su ai mata ne.abin da waccan ke dashi,ma tana dashi.yanzu an daina auren soyayya,sai auren me zan samu.ka gane?na fada maka nasarar da zan samu ta hulda da alhaji bishir so kake sai ka ja min asara ne?abbas ya ce,shi ke nan dady,na yarda har da hawaye ya bar gurin.a dakinsa kuwa yaci kuka sosai domin ya kallafa rai a kan MIMI. [01/10 10:34 pm] Abdul: (22)Ba ki zo bada 'yata ta bata,amma da jin an ce mijinki babu lafiya,kin debo yara kun taho.sauda ta ce, shi ne dole na,yarki,ai ba dole na ba ce.suka gaisa ta ce,ina muktar?hajiya sauda ta ce,mun yi ta jiran sa bai karaso ba.na ce mu tafi,ya zo.sauda ta isa gurin mijinta ta zauna daf da shi.ya kama hannunta.har kin zo? ta ce,jiya ban yi barci sosai ba,amma yadda na ga jikin naka,alhamdulillah.ya ce, ashe ina da ciwon sugar ne.kwanaki kina ce min duk na rame.sugar?sauda ta tambaye shi.ya ce,tabbas har ya soma yi min yawa. yanzu dai likita ya dora ni kan magani da dokoki da kuma abincikan da zan kiyaye.hawaye suka zubo a idon sauda.ya dafa ta,aa kar ki yi kuka sauda,insha allah zan warware,ta ce, allah ya baka lafiya.ya ce, amin.ya kalli abba,ina takwarana?abba ya ce, suna gida.za su zo da mamansa.alhji ya ce,madallah,allah yayi maku albarka.kun ji abin da MIMI ta yi min ko?ya dinga kallon su da dai-dai,ya dan sunkuyar da kai.na san har da hakkinku.lna mai baku hakuri.abba ya ce,haba dady babu komai.allah ya ba ka lafiya.sauda ta ce,to yanzu ya ake ciki?ya ce, na me fa?ta ce na bikin ya ce,na'ima za a daura da ita.ya kalli abdulkarim ya nuna masa wayarsa.miko min wayar can.ya miko masa.ya bata,bude ki ga sakon da yarinyar nan ta turo min.hajiya sauda ta kammala karantawa cikin kuka.ta ce,alhaji ba zan gaji da fada maka,laifinka ne kai da nafisa ba.kun gina ta a kan yi mata duk abin da take so.ya kamo hannuwanta,na yarda laifina ne.nafisa ta biye min ne don ganin haka nake so. abba ya ce,to dady ka ce ta dawo mana.ln yaso ka bata shi wanda take so din,tunda na'ima zata auri wanda ba ta so din. ya kalli abba,ba canji ke nan.zan ci gaba da yi mata abin da take so ke nan?ai yadda ba ta yi min abin da nake so ba,haka nan ba zan taba yi mata wanda take so ba ai ta yar da wannan gatan da kanta.lta ma zan mata abin da ba za ta manta ba,kamar yadda ni ma ba zan manta da abin da ta yi min ba. hajiya sauda ta ce,yanzu a ina take?oho!in ji alhaji. [01/10 10:34 pm] Abdul: (21)Suna idar da sallar asubahi lsmail ya ce wa hamisu direban yara,don allah kai mu asibiti mu duba alhaji.har da kanin alhaji da 'ya'yansa mata suka tafi tare.sun samu alhaji yana salla.don haka suka zauna momy nafisa ce ta kwana a gurinsa.lta ma tana sallar ne.bayan sun idar ta leka ta ce.ku shigo mana.suka shiga suka gai da shi.ya ce. na samu sauki.nan da karfe bakwai zan koma gida.a ci gaba da biki kun ji na'ima ta share min hawaye ko? lsmail da bai san kan maganar ba,sai ya kalli alhaji daidai lokacin da kanin alhajin ke cewa,mun ji zata auri shi yaron da waccan ja'irar ta gudu domin sa.yanzu ai sai ta dawo.alhaji ya ce,ta dawo ina?ai ko ta dawo,ita ma sai nayi mata abin da ta yi min.suka ce hakuri dai za a yi.lsmail yayi wa alhaji addua.suka ce za su koma. alhaji ya ce,malam lsmail na gode.sai na zo. suna komawa gida lsmail ya kira layin hajiya sauda.har sau biyu bata daga ba.don haka ya bari. yana gugar kayansa,sai ga kiran ta.ya daga suka gaisa. ya ce,kin samu labarin ciwon alhaji?ta ce tun jiya.yanzu maga mu nan ni da yara za mu biyo jirgin karfe takwas.yaya jikin nasa?ya ce,da sauki.ta ce,an ji labarin MIMI?ya ce, eh to,na ji dai an ce tunda ta yi masa text ne cewa ba za ta dawo ba sai in zai yi mata abin da take so,shi ne ya fadi.amma yanzu na'ima ta yarda za ta auri wanda MIMI ba ta so. hajiya sauda ta ce,oh ni saude!allah ya shirya wannan yarinyar.shi ke nan sai mun iso. bakwai da rabi alhaji ya iso gidansa,jamaa sai shigowa suke.yayi wanka,ya karya.ya sha magani,ya dan kwanta kafin tara.daurin auren sai karfe biyu,in an idar da salla a babban masallacin abuja.tara saura hajiya sauda da abba da abdulkarim da su hasana da usaina suka shigo.na'ima ta rungume su hasanan,ta gai da hajiya ta ce,lna momy taku?ta ce,tana dakin dad.dukkan su suka shiga.ya tashi barci suna magana da nafisa momy nafisa ta ce,oyoyo, sannun ku da zuwa.nan yaran suka gai da ta,suka nufi gurin dadynsu.lta kuma ta ci gaba da yi wa hajiya sauda mita. [01/10 10:34 pm] Abdul: (23)Jiya dai an ce suna kaduna.hajiya sauda ta ce, allah ya kauta.daidai lokacin wayarsa ta yi ringing,momy nafisa ta shigo tana cewa, alhaji kana da baki. Duk tare suka fito.hajiya sauda da su hasana saman MIMI suka nufa saboda gidan da mutane.har an soma cin abinci dangin momy nafisa sun fi yawa. usaina ta kalli hajiya sauda bayan sun zauna,hajiya ki kira ta mana a waya,ki ce ta dawo.ni na ga na'ima kamar tana murna da hakan.ta ja mu tana nuna mana lefen sis MIMI,wai nata ne.ga mota can a gare ji,an zuba dukiya a gidanta. abdulkarim ya ce,ai ni na yi murna da faruwar hakan.shi dad din yanzu yayi nadama ai.abba ya ce,ni zan zo ma in ma koma ne fa hajiya.don ba zan kwana abuja ba. gaskiya tunda ya samu sauki,ga shi ma sai bikinsu suke yi.sai ga masu aiki da kulolin abinci,wai a kawo musu.hasana ta tashi ta shige dakin barcin MIMI. usaina ta biyo ta.hasana ta kalli usaina,gaskiya sis MIMI bata duba wa kanta ba. kalli fa dakinta.dubi duk nan bangaren ta ne,ya fi ko'ina kyau a gidan nan,amma ta kasa yi wa dad biyayya. allah ta ban kunya.usai ta ce,ai ga shi nan na'ima ta yi abin da ita ta kasa.na san ko moy nafisa za ta iya sa ta ko don su birge dad. Hasana ta ciro wayarta, mu gwada kira mu gani ko za ta daga.nan suka soma kiran layinta.yana ta ruri yana tsinkewa,ba ta daga ba.daidai lokacin MIMI tana gado asibiti kwance. damuwa ce ta sa take jin ta babu wani sauki.duk wanda ya kira,tana kallon kisansa.yanzu haka tana kallon lambar usaina, hawaye suka soma zubo mata.yaran da bata damu da su ba,ashe suna son ta.lta yanzu tana jira ne ta ji kira momy nafisa don ta san matsayin da take.ln dad dinta ya yarda,kai ko bai yarda ba,yadda take jin zuciyarta za ta koma gida ne kawai.khalil ya dauki wayar bayan ya ji shigowar sako.ya ce,sako ne dear.ki duba ko momy din ce ko?cikin sauri ta amshi wayar.usaina ta gani.har ta ajiye wayar sai kuma ta bude.ga abin da usaina ta ce: [01/10 10:34 pm] Abdul: (24)SIS MIMI DON ALLAH KI DAWO DAD BA LAFIYA YA FADI SABODA JIN CEWA KIN GUDU NE,BA SACE KI AKA YI BA.ANJIMA ZA A DAURA AUREN NA'IMA DA ABBAS. Ihun da MIMI ta yi ne yasa khalil mikewa. tambayar ta yake yi,me ya faru?cikin kuka take fadin, dad ba shi da lafiya.ni zan koma gida ne kawai.khalil hankalinsa ya tashi.ya shiga lallashin ta.ki yi hakuri mana dear.za mu koma ai.amma bari su neme mu.ta ce,ba ni wayata.bari in kira dad din.ya ce,aa kar ki kira shi tsaya ki ji.MIMI ta tsaya tana kallon sa ya ce,ki kira su usaina din kiji komai daga bakinsu.nan suka kira layin.hasana ce ta daga wayar:MIMI cikin kuka ta ce, usaina!hasana ta ce,ni ce ba usaina ba ce,ta ce,yanzu wane hali dad yake ciki?hasana ta ce ya ji sauki,babu laifi,amma ya kwana a asibiti ne.ya ji zafin sakon da kika turo masa cewa kin tafi saboda wani.usaina ta amshi wayar tana cewa,sis MIMI ki dawo kawai zai fi miki. dad ya ce,ba zai damu daki dawo ko kar ki dawo ba, don na'ima ta gama fitar da shi kunya,ta amince anjima za a daura aurenta da abbas.MIMI ta kasa magana kuka kurum take yi.suka nufi hajiya da wayar usaina ta ce.ga sis MIMI tana jin lokacin da hajiya take fadi me za a yi mata don ga ta a waya?abin da ya kamata ta yi ta kasa.don haka bani da lokacin sauraron ta.ubanta ma da ya nuna mata so,ta yi masa butulci, bare wani.da allah kashe wayarki!hasana ta katse wayar.kuka sosai MIMI dinga yi tun khalil yana bata hakuri,har yayi shiru ya tsaya yana kallon ta.sai da ta gaji don kanta,ta kalli khalil ni zan koma gida.ta sauka ta soma duba jakarta.zan koma gida khalil in yi wa dad dina biyayya. amma har abada ka sani ina son ka a cikin zuciyata. ya ce,ki tsaya ki ji sauki mana.ba a sallame mu ba.ta ce,ba na bukatar sai na samu sauki zan tafi.ka zo ka kai ni gurin da zan hau mota.tana daukar jakarta,ya nufi ofishin likitan,ya sanar da shi cewa wai tana son ta tafi.lokacin da likitan ya fito,ta kai harabar asibitin.suka sha gabanta, [01/10 10:34 pm] Abdul: (25)Khalil ya ce,MIMI ki saurari likitan mana.ta ce, likita ka yi min afuwa, awanni suka rage a daura min aure.ka san cewa guduwa nayi?babana ya fadi sbd na gudu.likita ya ce,na ji zaki koma,amma ki bari ki gama karbar allura. MIMI ta ce,bari in tafi.na yi nadama sosai da na bijire wa mahaifina.zan koma in ba da hakuri,in nemi ya yafe min.ya aurar da ni ga ko waye yake so. Dole likitan ya ce,ka bar ta ta tafi kawai.ba shi da zabi,dole ya koma ya dauko tasa jakar suka je titin bypas don samun motar zuwa abuja.suna cikin motar ne ta sake kiran usaina,karfe nawa za a daura auren?ta ce,bayan azahar ne a babban masallaci.mu ma hajiya ta ce,da an gama daure aure za mu koma gida.ta ce,shi ke nan sai na iso.ta kalli khalil,ina za ka tsaya?ya ce zan je har gaba mahaifinki, yayi yadda ya ga dama da ni.amma na gama hango mutuwata,in har na rasa ki. ta kalli agogo,yanzu sha biyu da wani abu,kana ganin har za mu je abuja ba a daura da na'ima ba?ya ce zan fi kowa so in hakan ta kasance.ki yi adduar allah ya sa ni ne mijinki.daya saura alhaji ya shigo gidan don shirin zuwa masallaci ko kuma in ce gurin daurin aure.daidai lokacin ne kuma hajiya binta ta shigo,ita da yaranta. mamakinta da tunaninta alhaji ya rasu ne?ko an ga amaryar ana ci gaba da biki,shi yana asibiti?ta ga harabar gida an zuba kujeri da rumfuna,ga mutane da yara.suka shiga falo.nan ma duk jamaa.dakin nafisa hajiya bintar ta nufa.cike da manyan kawayenta,tana zaune a gaban madubi,ta yo wanka ana yi mata kwalliya.hajiya binta ta ce,nafisa wai biki ake yi ne?ta mike da sauri,sannun ku da zuwa kun iso?eh,kin san tafiyar mota,tun bakwai muka fito.ban gane ba,wai bikin ake yi ne?eh bikin na'ima.cikin mamaki, hajiya binta ta ce,na'ima kuma?momy nafisa ta karaso gurin ta cikin murmushi,eh,kin san MIMI ta gudu.shi ne na'ima ta zabi ta fitar da mahaifinta kunya. hajiya binta ta ce,to shi alhajin wane asibiti yake?ta ce,ya shigo yana gefensa,zai yi wanka. [01/10 10:34 pm] Abdul: (26)Tun jiya aka sallamo shi.yana jin na'ima ta yi wannan furucin,sai ya gyare.wata daga cikin matan da ke zaune a kan gadon ta ce,yarinya ai ta share wa ubanta hawaye. wata ta ce,ai ko ta yi saa jiya maigidana ke ba ni labarin irin gudummawar da abokan kasuwancin alhaji suka yi ta ba amarya. babban dan kasuwan nan wanda yafi kowa shahara a afrika an ce zunzurutun kudi miliyan ashiri ya ba da, banda motoci.hajiya binta dai ta ce,bari in duba alhaji. momy nafisa ta ce,to ki duba shi.yawwa hajiya sauda ma suna saman MIMI to kawai hajiya binta ta ce, ta nufi sasan alhajin,cikin al'ajabi.gani take yi momy nafisa murna take yi da aure ya juye a kan 'yarta. Ta kalli yaranta ku hau saman sis MIMI,hajiya sauda tana nan.da farko har za su noke,don suna tsoron MIMI,tunda bata kula su.amma jin cewa sauda tana nan,sai suka nufi saman cikin murna.suna son hajiya don in sun zo hutu ba sa son tafiya.ta iya tafiyar da yara sosai. Ta samu alhaji ya fito wanka,ya ce,aa ku ma kun iso?ta ce,eh,alhamdulillah sam ban zaci zan samu jikinka haka ba.na ji an ce sugar,mene ne mene ne.ya ce,da sauki.da ma karin damuwar kunyar da MIMI ta so ta ba ni ce,sai kuma na'ima ta zo ta tare matsalar.yanzu dai burina a daura auren nan.zan koma asibiti,likita ya duba ni yadda ya kamata.ta ce allah ya sawwake.to,yanzu mene ne labarin MIMI? ya kalle ta.bayan ya gama saka wando,yana tura singiletinsa,ba ni da labarinta, kuma bana bukatar in sani.hajiya sauda sun zo da su abba.lna zaton suna saman.hajiya binta ta ce,to bari in ji gurinsu.ta samu su abba za su fito.nan suka tsaya suka gaisa.suka ce bari su fita su yi salla.ln an daura aure za su wuce.hajiya binta ta ce,wai ni hajiya yaya lamarin ya zama haka?ba kya tunanin cewa nafisa ta san komai a kan gudun MIMI ko bijirewarta?ba na tunani,in ji hajiya sauda.ba na zargi a kan abin da ban ji ban gani ba.abin da na sani kawai alhaji shi ne silar komai.haka nan kullum ina cikin adduar allah ya shirya MIMI.ya bata miji na gari. [01/10 10:34 pm] Abdul: (27)Ban yi fushi ba ko da aurenta bai kasance da dan gidan minista ba.kila ba alherinta.hajiya binta ta ce, haka ne allah zai amshi adduarki,domin bakin mahaifiya yana da karfi a kan yara.hajiya sauda ta kalli usaina wadda ke dube-dube a kan kwamfutar MIMI,ta ce,ku sa wa yaran nan abinci ga shi nan.hasana ta sa wa hajiya binta.hajiya binta ta ce,ni duk damuwata ta a ba na jin yunwa.sauda ta ce,damuwar me,bayan ga jikin mijinmu da sauki? hajiya binta ta ce,batan MIMI ai abin tunani ne.ko kusa,in ji hajiya sauda,guduwa ta yi,ba bata ta yi ba.kin ga kwanukan da su abba da abdulkarim suka ci?cewa suka yi tunda jikin dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci.ni ce ma ban riga na ci ba.na fi son abu mai ruwa da safe,mai kuma dumi kamar shayi.hajiya binta ta ce,ya fi dadi ai hasana sa min wainar allah ya rufa asiri.suka ce amin. Duk da gudun da motar da su MIMI suka shiga take yi,gani take yi kamar ba gudu ba.ba ta taba shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau.bugu da kari bata taba shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta.shiru da ta yi daga zaune abubuwan da take lissafawa ke nan.duk da tsananin son da take yi wa khalil ba ta jin za ta sake barin gida,ba tare da yardar mahaifinta ba.abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba.cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati,wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi lmani da shi.ta zaro idanu,lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya, sosai ta firgita,ta soma fadin wayyo allah!daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak.wai ashe taya ce ta fashe,tana duniyar tunani,bata ji kara ba.babu wanda ya zaci motar nan za ta tsaya.motoci suka tsaya ana ta yi musu allah ya kyauta.hankalin MIMI ya sake tashi.har aka canza taya jikinta bai daina bari ba.haka nan duk lallashin da khalil ke yi mata bata daina kuka ba.shi kansa yayi dana sani sosai na tahowa da ita.da kyar ma ta yarda ta sake shiga motar suka nufi hanya.karfe biyu daidai aka daura auren. [01/10 10:34 pm] Abdul: (28)Karfe biyu daidai,aka daura auren na'ima da abbas.daurin auren mai dimbin tarihi irin manyan mutanen da suka halarci gurin.babbar matsalar angon yaki halartar daurin auren,yana gida kwance,lta kuwa na'ima suna can gidan yayar mommy nafisa suna cashewa da makadan da suka dauko.sun koma can ne wai kar a ce suna murna da auren ya koma kan na'ima.wani karin abin aushin ma na'ima ita da abbas din ba su taba yin magana ko da ta waya ba. kuma daga momy har na'ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala mai zaman kanta ba ce.uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar layinsu.kasancewar layin baya fita,sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin,ga mutane ta ce,me ke faruwa?ba dai dady ya mutu ba?dan tasi din ya ce,gaskiya ina zaton ba mutuwa ba ce,sai dai biki.ta ga nisan su karasa har kofar gidan,don haka ta ce,tsaya ina zuwa.yana tsayawa ta dauki jakarta,ta zura da gudu.kofar gidansu duk jamaa.gate dinsu a bude.tana shiga da malam lsma'il ta soma yin ido hudu. mutane ba su gane ta sosai ba,saboda ita ba maabociyar saka hijabi ba ce.lsma'il ya ce,daga ina kike?ta ce,me ake yi a nan gidan?ya ce,auren na'ima ta zaro ido,an daura da na'ima?ya ce,tabbas!sai ta juya,yana cewa ke!za ta fita ke nan su abba da abdulkarim za su shigo don yin sallama da hajiya sauda don basu so su kai wannan lokacin ba a abuja.dad ne ya tsare su,wai sai an gama daurin aure.yana ta nuna su ga abokansa, wadanda a da MIMI suka sani,basu san ma yana da wasu yaran ba.sai abokansa na tun farko irin su alhaji lsa.abdulkarim ne ya gane ta,don abba ne a gaba,amma bai kalli fuskarta ba,kuma hijabin da ta sa ya kara boye ta.da karfi abdulkarim ya rike hijabinta,har ta dan gota shi.ya jawo ta ya falla mata mari.sai da ta ga wani haske,ya ce,gidan uban wa za ki koma?ta tsala ihu,wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan.lsmail ya iso gurin yana cewa a yi mata hakuri.abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. suka iza keyarta tana kuka, suna rankwashin ta,gami da zagi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (29)Momy nafisa ta fito da gudu,domin wata kawarta ce zata tafi gida,sun yi sallama.amma tana fitowa ta ga MIMI a hannun su abba.sai ta koma da gudu ta sanarwa momy nafisa cewa ga fa MIMI.da farko momy nafisa idanu ta zaro,tana cewa,na shiga uku!me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?sai yarta ta ce,kar ki damu tayi ta dawowa.an riga an daura aure.momy nafisa ta ce, kuma fa haka ne.bari in fita in ga yadda wannan fim din zai kare.suka sa dariya gami da shewa,ita da kawayenta.ta kalli wata hajiya nana,ba ni wayata!ga ta nan kusa da ke in sanar da ubanta.ln ya zo fim din zai fi dadi kallo. shine nan ta fito da gudu.a daf da hawa sama ne ta iso ta rungume MIMI ta fashe da kukan karya.lna kika shiga ne yata?me ya sa kika yi haka?abdulkarim ya ce,momy sake ta mu je sama.sake komawa za ta yi.abba cikin fushi ya ce,ki wuce mu je mana!don shi yana jin haushin momy nafisa ta taimaka gurin lalacewar MIMI.momy nafisa ta sake ta suka iza keyarta zuwa sama. abdulkarim yana rike da jakarta.momy nafisa cikin kukan ta kira alhajin ya ce? tana sheshekar karya ta ce,ka zo gida,ga MIMI nan ta dawo su abba suna ta dukan ta ya ce,haka shi ne daidai.na gode musu.ya kashe wayarsa. hajiya sauda tana inda take zaune ba ta tashi ba tunda ta yi sallar azahar sai ko ga MIMI ta shigo da gudu.a gaban hajiya sauda suka yi mata duka.dama kowannensu yana da haushinta.hajiya binta ce ta kwace ta.ko kallo bata ishi hajiya sauda ba,bare ta yi magana.hasana da usaina sun yi jungum-jungum cikin tausaya mata ta rakube gefen kujera tana ta kuka. abba ya ce,wawiya mara hankali kin bata sunanki a duniya.kin zubar da mutuncin kaki.abdulkarim ya ce,sosai kuwa,duk yarinyar da ta gudu ta bar gidan iyayenta,ai sunanta yar lska.hajiya binta ta ce, gaskiya baki kyauta ma kanki ba MIMI.ba ki yi wa mahaifinki adalci ba lrin son da alhaji ya nuna miki,ln kina da hankali,ko wuta ya hura ya ce MIMI shiga,ba za ki yi tsalle ki shiga ba,bare aure? [01/10 10:34 pm] Abdul: (30)Sai lokacin hajiya sauda ta yi magana,ta ce. ai shi yasa haihuwa ma da yawa take da dadi.ln wani ya saka kuka wani sai ya share maka hawaye.na'ima ta kai yar albarka.allah ya bata zama lafiya a gidana,ke kuma sai ki zauna mu gani,wanda kika bijire mawa din kika watsa masa kasa a ido,kika so ki kunyata shi zai ci gaba da jiyar dake dadi,gami da nuna miki kauna kamar da. Daidai lokacin alhaji ya shigo yana cewa,ba ta da mazauni a gidana.ta zo ta fita ta ko inda ta fito.na sallamawa duniya ita!hajiya binta ta ce,haba alhaji wannan ma ai ba mai yiwuwa ba ne.ka yi mata afuwa,ta yi kuskure.alhaji ya isa gabanta,ke khadija!na ce ki zo ki bar gidana!sunan uwata kika ci,ni uwata ta dade da mutuwa.don haka yadda kika yi min abin da ba zan manta ba.haka nan ke ma zan yi miki abin da ba za ki manta ba.MIMI ta mike ta zo gabansa tana kuka a tsugune,dad don allah ka yafe min.wallahi dad na yarda na dawo,zan auri duk wanda kake so.dad ya ce,me abbas zai yi da ke a halin yanzun?kin je kin kwana da wani ki zo ki ce kin yarda!cikin tashin hankali MIMI ta ce,wallahi ban kwana da wani ba.na rantse maka dad! hajiya sauda duk dauriyarta ba ta san lokacin da ta soma zubar da hawaye ba.su usaina suka je jikinta suna bata hakuri. abba ya ce,daddy to kawai ka daura mata aure da shi wanda ta bi din mana.dad ya sake daga murya,har abada wallahi!ba zata aure shi ba.yadda bata yi min abin da nake so ba,ita ma har abada ba zan taba yi mata wanda take so ba. momy nafisa ta shigo tana kuka,tana ba alhaji hakuri. ya ce,na yi rantsuwa,yau dole yarinyar nan ta bar gidana,ko da ita kadai na haifa.yarana ashiri da biyu. don na rasa ita kadai bana jin cewa nayi asara. Hajiya binta ta ce shi ke nan za mu wuce da ita gidana can malumfashi.ya ce,gidanki ko gidana?can ma gidana ne,don haka ba ta ba shi.ta gama cin arzikina,don ko gidan mahaifiyarta na yi mata tsakani da shi.abba ya lumshe ido,yana tunanin dad ya tsaurara da yawa.don haka ya ce, [01/10 10:34 pm] Abdul: (31)Dad shi ke nan bari mu wuce da ita,in tafi da ita gidana.alhaji bishir ya girgiza kai,ban lamunta ba.ln kuma ka yi hakan ba zan yafe maka ba.ka sa min idanu kaga irin hukucin da zan yi mata.hajiya binta ta ce,don allah alhaji ni dai kar ka ce zaka kore ta a gidanka,ka ji?momy nafisa ta shigo cikin kuka tana cewa,don allah alhaji kayi hakuri,ka yafe mata,tunda na'ima ta riga ta auri abbas din sai a bar zancen.MIMI ta zo tayi shirin komawa makaranta.cikin zafin rai,ya waiwayo,wace makarantar?nafisa za ki sa in tafka miki ashariya!ya nuna MIMI,wannan yarinya don ubanta ta gama boko a gidana,ta je tayi zaman aure.yau din nan zan aurar da ita ko ma ga uban wane ne.bana son kowa ya ce,min uffan.a kalle ni da hukuncin da zan yanke duk inda na bada ta da sunan aure.na gindaya allah ya isa ga duk wani ahalina da ya je,ko na sani ko ban sani ba.sai lokacin hajiya sauda ta daga ido ta kalle shi,duk da halin MIMI,amma da da mahaifi sai allah.ta ce,alhaji kana ganim wannan hukuncin bai yi tsauri ba?a fusace ya kalle ta,bana bukatar ki sa bakinki a cikin lamari,kamar yadda tun farko kika ce ba ruwanki ke yar shawara ce.to don allah ina son shawarar ma ki bar ta.kina da kima sosai a idona bana son mu fara abin da bamu yi a da ba.za ta yi magana.abdulkarim yayi mata alama da hannu wai ta yi shiru.don haka sai ta kulle bakinta.shi kuma alhajin ya fita yana fadin zata gane ba ta da wayo. Hajiya sauda ta kalli MIMI maganinki ke nan!hajiya binta ta ce,ni fa ina zargin cewa MIMI shigo-shigo ba zurfi aka yi mata. momy nafisa ta ce,me kike nufi?ke nan ni na sata bijirewa mahaifinta?hajiya binta ta ce,komai zai iya faruwa.yaran da suka tashi a karkashin tarbiyyarki me zai sa na'ima ta lankwasu, amma MIMI ta kasa lankwasuwa?hajiya sauda ta ce,ku bar zance nan.laifi dai duk na MIMI ne.ban ji haushin alhaji ba,duk hukuncin da ya yanke mata.da ta tsaya a kan bata so,sai ya fi mata a kan gudun da tayi.wa ya san abin da ya faru a gudun da ta yi?MIMI ta ce,hajiya ku yarda da abin da zan ce [01/10 10:34 pm] Abdul: (32)Na rantse muku babu wani abu da ya faru da ni.ni kadai na kwana a dakin da na sauka.abba ya ce,kin dai cuci kanki da kika sa kafa kika bar gidan mahaifinki,kika bi wani kato. kuma duk sunan da aka kira ki da shi dole ki amsa. abdulkarim ya ce.alhakinmu ne yasa ta yi wa alhajin haka.don haka ni duk mai zai mata ba zan ji haushi ba.usaina bata ce,yaya ni kuma a nawa ganin tunda wannan ne karo na farko da sis MIMI ta soma saba masa da ya yafe mata,sai in ta kara.momy nafisa ta ce,yawwa usaina,abin da ni ma nake so ke nan. shi kuwa alhaji ya fita ne da niyyar ba ta duk wanda ya ci karo da shi.babu abin da ta fi tsana a duniya kamar talaka,don haka za ta dandana rayuwar talauci.har zai fita gate,sai idanunsa suka hango lsmail yana alawala,tamkar an tsai da shi ne,ya tsaya cak, yana kallon lsmail.sai ya tuna ta taba furta masa cewa ta tsani lsmail. murmushin takaici ya yi,ya ce,malam lsmail yana kan wanke kafafu,ya dago da azama ya karasa,ya mike cikin girmamawa yake cewa,alhaji barka da arziki.na ga MIMI ta dawo.alhaji yayi yake,tare da cewa,barka ka dai.wato malam lsmail kamar kai ne kake fada min an aurawa budurwarka wani ko?lsmail sam baya ko son tuna lamarin don haka sai ya ce,ni ne alhaji,amma na dangana.haka allah ya hukunta.alhaji ya ce,wane ne wakilinka wanda zai amsar maka aure?gaban lsmail ya fadi,cikin in-ina ya ce,alhaji ban gane ba.ka ce mene ne?ya ce,kar ka damu,in mu i sallar laasar ka samu ko baba maigadi ne ka wakita shi ya amsar maka aure.kar ka ji mamaki hausawa suna cewa wani hani ga allah baiwa ne.sai kawai alhaji ya wuce ya bar lsmail tsaye,zuciyarsa cike da tambayoyi,amma bai san wa zai amsa su ba. Maigadi da hamisu suka nufo lsmail suna cewa, malam lokaci fa,baka yi kiran salla ba.maigadi ya ce,kodayake alhaji ne ya tsai da shi ko?lsmail ya ce,ku ji alhaji wai in samu wanda zan wakilta ya amsar min aure,wai ko kai. su ma suka cika da mamaki.hamisu ya ce,ko cikin yan aikin gidan ne tunda ya san kayi rashin budurwarka? [01/10 10:34 pm] Abdul: (33)Isma'il ya ce,ni don na riga nayi fushi da soyayya, don ma kar in ce na daina yin ta ne,a ce na dauka da zafi.hamisu ya ce,tunda ya zabe ka zai yi maka alkhairi kar ka ce aa,ka yi shiru.lsmail ya ce,ba zan iya musu da shi ba,dana yi tun tuni.ku taya ni adduar allah yasa in ci jarabawar don ina cikin gwaji.suka ce,amin allah ya sa ka ci. bayan sun idar da salla,alhaji ma ba a nan yayi sallar ba.kamar minti goma,sai ga alhaji da abokansa hudu da kuma kaninsa kawu shafiu wanda daki lsmail yake kwana tunda suka zo bikin.nan alhaji ya ciro naira dubu talatin,ya mika wa maigadi.sadakin malam lsmail ne.ga wanda zai ba da auren nan,ya nuna kaninsa cikin masallaci suka koma,inda aka daura auren KHADIJA DA ISMA'iI duk ba su yi saurin dago wace ce khadija ba,saboda sunan MIMI ya boye.sun fito suna tambayar juna,alhaji kuma da kaninsa suka shiga gida. daki lsmail ya shiga yana kai-komo a fili ya ce,kaddara ta kawo ni abuja.ya dauko wayarsa yana ta zufa,ya kira mahmud ya sanar da shi komai.cikin murna ya ce, allah ya sanya alherh.lsmail ya ce,ba na son wulakanci jaje ya kamata ka yi min ba murna ba.mahmud ya ce bari in sanar da malam, in kuma je gida yaya amina in fada mata.lsmail ya ce,ni damuwata ko daki ban kama haya ba ban san ma yaya zan yi ba.amma komai ake ciki zamu yi waya.alhaji kam da ya shiga ciki,shi da dan uwansa kai tsaye suka wuce saman MIMI,inda su hajiya sauda suke.alhaji ya ce,mika wa binta sadakin, duk suka zura ido,hajiya sauda salla take yi,amma sai da ta ji kamar ta fadi.momy nafisa da ke biye da su alhajin don tana falon kasa da baki suka shigo,ta ce,wane ne mijin alhaji?ya ce,zai shigo ai lna take MIMI?hasana ta ce,ta shiga cikin tana wanka.ya ce,to in ta gama ku fada mata ta shirya maza-maza alhajin ya sake sauka ya bar su nan cirko-cirko shi ma dan uwan ya basu kudin,ya fice. [01/10 10:34 pm] Abdul: (34)MIMI tana fitowa wanka,hasana tana shiga dakin ta ce,in ji dad ya ce ki shirya.MIMI ta zaro idanu, zuwa ina?hasana dai ta ce,haka dai ya ce,amma ban sani ba.riga doguwa ta zura ta zauna bakin gado tare da yin tagumi.hajiya sauda ta idar da salla ta zabga tagumi,tana hawaye,lalle alhaji.jim kadan ya sake hawowa, wai ina su abba ne?usaina ce ta iya cewa,sun tafi tun dazun.sun ce za su je suyi salla su wuce.ya sake sauka ya fita.hamisu ya samu a bakin gate,ya ce, malam hamisu ga shi ka je ka cika tankin motarka.don allah ka zo ka kai amaryar katsina.lna shi lsmail din yake ne?hamisu ya ce,yana dakinsa.ya ce,to ka je ka ce masa na ce ya shirya kayansa,ya zo ina nemansa.yan kayansa da ma basu da yawa,ya tattara su,ya zuba a jaka,ya fito ya tsaya a wajen su maigadi,shi kuma hamisu ya tafi siyan mai. Alhaji ya sake fitowa ya yafito lsma'il da hannu. lsmail ya nufi alhaji cikin faduwar gaba yana cewa,kaddara da ta same ni,allah ka duba min.ya isa gurin alhajin.ya ce,biyo ni. suka ratsa falon.har yanzu da mutane,amma sun ragu ba kamar dazun ba. matakala alhaji ya soma takawa,shi ma ya bi shi.ya waiwayo ya yi masa alama da kai. suna shiga alhaji ya kalli usaina, kira min MIMI.hajiya binta ta ce,alhaji wai me kake nufi ne?momy nafisa ta ce,kana nufin wannan ne mijin? usaina ta shiga ta same su da hasana ta ce,sis MIMI dad yana kira.da sauri ta mike,kanta babu dan kwali,ta fito a firgice.duk zatonta zai ce ta koma gidan mamanta ko gidan hajiya binta.tana fito ta kalle shi,ga ni dad.ya ce,ki shirya ga mijinki nan za ku wuce.ta zaro ido,tare da fadin dad me ka ce?na shiga uku!dan da nan sai kururuwa,ta zube kasa.su hajiya binta suka nufe ta, suka daga ta suna salati. Momy nafisa tana fadin sam alhaji ba zai yiwu ba. tsaki ya ja,kar ki bata min rai nafisa.ku yayyafa mata ruwa ta farfado da wuri.ku hada mata komai nata, katsina ba nan ba ce.ya kalli lsmail,wanda tsabar firgici ya hana shi magana, ya ce,kai kuma daga yau na sallame ka daga aiki. [01/10 10:34 pm] Abdul: (36)Kuka MIMI ta saka. momy nafisa ta shiga cewa, ai ni kuma na shiga uku,watan kuma nawa ne tunda na'ima ta auri abbas, amma ia na ga dai ita MIMIN ba son shi take yi ba. ta ja tsaki,ta fice fuu.su hasana ne suka shiga shirya wa MIMI kayanta na sawa da irin abin da ya danganci na karatu.tana ta kuka alhajin ya sake sawowa lokacin hamisu ya dawo.ya shiga har dakin MIMI ya ce,ta ba shi katinan ATM duka.ta ba shi tana kuka tana rokon sa.ya amshi duk wani abu da ya danganci dukiya. gwalagwalanta kuma hajiya sauda ta amsa. hasan suka ce hajiya da kin bar mata.ta ce,duk ku rufe min baki.suturun MIMI ma ba duka suka dibu ba.an dai cika duk akwatunanta. takalma da kayan shafa duk an diba.sai lokacin ta tuna da wayarta.jakarta kuma da kudi,ta kalli hasan, ina jakata?hasana ta fita falo ta dauko mata.sai ta tura ta cikin wata jakar bayan ta cire wayarta wada take a silent.miss call din khalil ya fi hamsin.kuka ta soma.a zuciyarta ta raya yanzun kam babu makawa za su gudu. Haha aka yi ta fita da kayan MIMI ana zubawa a bayan mota da kuma bayan boot.lta kuwa banda kuka,babu abin da take yi. hajiya binta ta yafa mata mayafi.dad da kansa ya tasa ta har mota.duk 'yan bikin sun fito sun yi cirko-cirko suna kallo.ya ce,ko da sunan wasa ba na bukatar sake ganin ki a gidana har sai in ni na bukaci ganin ki.ya dubi lsmail,kai ma ina kara ja maka kunne ka kula,don na san sai ta ce za ta gudu.ya ce,insha allahu alhaji,har motar za ta tashi,sai ga hajiya binta da gudu da kudin sadakin ta damka wa MIMI,ga shi an manta ne.MIMI ta amsa don ta san tana bukatar kudin. motar babba ce,cikin ta da boot dinta duk kaya ne,sai gurin da mutum biyu za su zauna,MIMI ta zauna,lsmail yana gaba tamkar zai saka ihu bakin ciki.alhajin ya sake zuwa kusa da shi,na ga duk ka damu.yanzun mene ne babbar matsalarka? lsmail ya dube shi da sauri,babbar matsalata ita ce inda zan ajiye ta.ya ce, ba kuna da gida ba?ya ce, muna da shi,amma dakina a soro yake.alhaji ya ce,kar ka damu,ka ajiye ta a nan....! [01/10 10:34 pm] Abdul: (37)Ya ce,shi ke nan alhaji na gode.tunda suka taso MIMI kuka take yi har suka yi nisa.lsmail sai dai ya waiwaya ya kalle ta,ya kasa yi mata magana. tsakani da allah shi tsoron ta ma yake yi yanzun. hamisu direba ya ce,ka bata magana mana.ai sai ka lallashe ta.lsmail ya ce bar ta kawai ta yi ni kaina ji nake tamkar in saka kuka wallahi.hamisu ya saki dariya,ya ce wane irin kuka kuma?kai ko yau da wanda ya kai ka farin ciki? tsaki ya saki,ya ce,yau sai dai in daidaita ta da ranar da mahaifiyata ta mutu. hankalin MIMI ba ya tare da su don haka ba ta san me suke fadi ba.ta ciro wayarta,ta cire ta a silent. layin khalil ta soma kira.a ringing na biyu ya daga cikin sauri ya ce,MIMI kina ina?ta ce ka san wani abu ne?ya ce,aa ta ce yanzu muna hanyar katsina.ka shigo motar katsina ka biyo mu,zan ta yi maka kwatance.za mu bar garin nan.ya ce,shi ke nan.ln ban samu ta katsina ba,za hau motar kaduna.ln na sauka komai dare zan hau ta kaduna.ln ban samu ba,zan je gidanmu,ko a boye ne in dauki mota.ta ce,kar ka je gida a gan ka.ba zan so su tsare ka ba.abubuwa da yawa sun faru zuwa na gida.na yi danasani matuka, amma in mun hadu za kaji.don allah ka yi alkawarin za ka zo?ya ce,in biye da ke,kar ki damu.ta ki fada masa cewa an daura mata aure ne.kar ta kashe masa guiwar zuwa gurinta. Su kuwa su hajiya sauda nan take suka soma shirin tafiya su ma.hasana da usaina suka zazzabi kaya cikin kayan MIMI,suka fito.sam hajiya sauda bata bi ta kan alhaji ba,ta ce, su tafi kawai ko a motar haya ne.momy nafisa dai ta biyo su tana don allah su kwana. hajiya binta dama ko sallama ba ta yi wa nafisa ba.sauda ce ta tsaya yin sallama.nan take ta dauki waya ta soma kiran alhaji.ya daga ta ce masa,ga fa su hajiya sauda nan za su wai tafi gareji su hau mota.nan da nan ya kira hajiya sauda wai su jira karfe shida zai yi musu booking din jirgi.ta ce, wa hajiya binta,ba komai mu jira.ai shi mijinmu ne.dole mu ji maganarsa.hajiya binta ta ce,shi ke nan. [01/10 10:34 pm] Abdul: [7/27, 11:10] A~PROF: (38)Shida daidai suka nufi katsina a jirgi.su kuwa su na'ima daidai lokaci suka dawo gida don za a kai ta gidan miji.nan fa aka turo motoci don daukar amarya. an dauke ta zuwa gidanta da ke asokoro.jamaa sun yaba gidan.ga motocinta guda biyu,daya na lefe,daya ta gurin dad dinsu. kawayenta da yan uwa sai murna suke yi mata.karfe tara daidai abokan ango suka rako shi zuwa dakin amarya.ango abbas wanda yake jin yau tamkar ranar mutuwarsa ba ranar aure ba,ya zauna a falon yana kallon su usman suna yi da kawayen na'ima.shi haushi ma suke ba shi kwarai.ya kosa su gama shirmensu su tafi don ya gaji,barci yake ji. suna tafiya,ya nufi sama inda nan ne dakinsa da komansa yake yayi kwanciyarsa,ya bar amarya tana ta jira sa.duk da azabar daurin dankwalin kanta ke yi mata,shiru da ta ji yayi yawa,shi ne ya sa ta tashi tana lekawa har sha biyu.sai lokacin ta kira momy nafisa.lta ma lokacin tana dakin dad,wanda ke kwance jiki babu dadi.ta daga wayar ta ce,na'ima yaya ne?na'ima ta ce,momy ban gan shi ya shigo ba.tunda ya tafi raka abokai.ta ce ki duba dakinsa mana.na'ima ta ce,ai ban san ina ne dakin nasa ba.ta ce,ki duba mana,ke da gidanki.ni ina nan gurin dad dinku ne, jikinsa babu dadi sam. na'ima ta ce to a gai da shi. Daga nan ta soma neman dakin maigidan. ta binciko dakin mijin,sai dai yana kulle.ta kwankwasa sau uku,yayi magana cikin dakewar murya,waye a nan?ta ce,ni ce.ya ce,ke ce wa?ta ce,na'ima.ya ja dogon tsaki,don allah bar nan gurin.waye ya neme ki da za ki zo ki ta da ni daga barci?ta yi tsuru cikin fargaba.ta ce,yi hakuri,ina jin tsoron dakin ne.ya ce,ina ruwana da tsoronki.da ma abin da kike sone kara taba min kofa.dole ta juya,ta sauka ta koma dakin cikin firgici ta kulle,ta sake kiran wayar momy a kashe.sai ta hakura ta kwanta. Zainabu tana kasa inda kicin dinsu yake, tana ta kici-kicin dora katuwar tukunyar da suke dafa abinci.mudu takwas suke dafawa in shinkafa ce suna yin tazarce ne daga rana har dare.ln tuwo ne, [7/27, 11:11] A~PROF: (39)Suna tuke mudu hudu ko hudu da rabi.tana hada ice,alhajin ya shigo.sallamar sa kawai ta ji,gabanta ya fadi take ta soma kuka,don ta san abin da ya maido shi gida,ci gaba ta yi da aikint uwargida wadda suke ce mata maman bishira ta ce,zainabu ki je mana ga alhaji can ya dawo.ta kalle ta cikin raunanniyar murya ta ce,wallahi na gaji.lnnar su bishira don allah ki bashi hakuri.ta katse zancen, sakamakon kira da ya kwala mata.ke zainabu,ni saanki ne,kina kallo na shigo kin tsaya?mama bishira ta ce,je ki zan sa miki hannu.laure da ke wanki wadda ita ce ta biyu ta ce,kwadayi mabudin wahala.zainabu ta shiga dakin tana ja baya,tana fadin sannu da zuwa.ya ce,rike sannunki,ba na so.sai da na kira ki,za ki zo?ta ce, ina sanwa ne,da ma zan zo.ya ce,to mu je!ai kin san abin da ya kawo ni ko?ba ta da zabi face mika wuya. shi sam bai san wani wasanni ba.auka wa iyalinsa kurum yake yi.ln ya cimma burinsa sai ya kakkabe jikinsa ya tashi. Rayuwar zainabu a gidan alhaji lawal,abin tausayi ne.ga girka babbar tukunya,abin da bata saba ba,ga fama da wannan miji,uwa uba ga su laure. suke dame ta da nuna kishinsu a kanta.don haka in ba girkinta ba ne, ba ta saukowa,sai in su laure ba sa nan.wani lokacin kuma in yarasu sun shiga dakinta su yi ta wasa ta biye musu. amma duk wanda ya san ta kallo daya zai yi mata ya san cewa ta rame.ta yi baki,kyawunta da cikar budurcin da ta soma,duk komai yayi lakwasa. cikin haka ne wata rana kannanta suka zo.ganin ta suka yi cikin yanayin suka je suka sanar da lnnarsu. washgari sai ga ta salati ta zabga tare da fadin na shiga uku ni.yasu zainabu kin yi ciwo ne?ta ce,aa ta soma kuka,wallahi innarmu na gaji da zaman gidan nan.mutumin nan bashi da imani,don allah ki tafi da ni.kullum sai ya zazzage ni.ga matansa biyu kullum sai su yi ta min habai ci tun ban gane da ni suke yi ba, har na gane.lnna ta ce,duk wadda ta yi miki ki rama ai zamansa suke yi,ke ma haka.to ki fada masa mana. sallamar maman bishira ce,ta katse su.ta shigo suka gaisa [01/10 10:34 pm] Abdul: (40)Zainabu ta ce,lnna wannan ce uwargidansa,ita dai tana taimaka min sosai. lnna ta ce,na gode baiwar allah,amma su sauran ta ce,suna yi mata habaici.na ce to ba zan lamunci wannan ba.sai in zo in same su har nan don ba ni da hakuri.maman bishira ta ce,ita zainabu yarinta ke damun ta.lnda tana da wayo,za ta ke masa faran-faran,ta daina jin tsoronsa. to da su kansu ba za su soma yi mata haka ba.tsoro za suji kar ta fada masa.kafin wani lokaci za ta dan samu abin da ta samu.amma ita sai raki da tsoro.nan suka yi ta shirya mata yadda wai a ta yi masa.jinsu kawai take yi, ba ta jin za ta iya kallon alhaji da wata kauna ko birgewa.lta dai kullum zuciyarta tana gurin dan kyakkyawan farin saurayinta lsma'il. Ismail shi da hamisu direba suna jin MIMI duk wayar da take yi,don tana yin maganarta kai tsaye ne,ba tare da wani noke-noke ba.a nata ganin wannan malam lsmail din shi ne wa har da za ta ji shakkar sa.ya san dai ita ba saar aurensa ba ce.ln ma ya ce zai kalle ta a matsayin mata zai bata wa kansa lokaci ne.shi kuwa lokacin fargaba ne ya sake dabaibaye zuciyarsa.tabbas shi rin guduwa take yi,ba ta zo zama ba.tambayar da yake yi wa kansa,yaya ke nan?yaya zai yi,ta nina zai bullo wa lamarin?a filin ya ce,allah da kai na dogara. ya ciro waya ya sake neman mahmud.bayan a dauka ya amsa sallamar, sai ya soma zolayar sa,ango,ango!ya ce don allah ka bar fada min kalmar.da ma zan sanar da kai ne cewa muna hanya. yanzu haka mun kusa kaduna.za dai mu iso dare yayi ne.don allah ina son ka dan tsaya a dakina,mu same ka a nan.ya ce ba damuwa.sai ma in dan share kafin ku iso.cikin zolaya mahmud yayi zancan.tsaki isma'il ya ja,ya canza harshe zuwa larabci, inda yake fada wa mahmud cewa MIMI din nan aka bashi fa tare da sanar da shi halin damuwar da yake ciki da duk yadda abin ya faru a takaice.sai dai bai ja sunan MIMIN ba.ya yi masa misali ne yadda zai gane.bayan sun yi sallama ne hamisu ya ce,ka san allah malam in kana larabanci kyau kake kara yi mi kamar. [01/10 10:34 pm] Abdul: (41)Balaraben da ma amma ku fulani ne ko?yayi murmushi tare da fadin ta wurin uwa ba.da yake lsama'il saurayi ne kyakkyawa sosai,sak ya debo mahaifiyarsu wadda ta kasance fulanin daura.ga shi da tsafta sosai,ga ilimin addini.na zamanin ma yana kan nema,don duk biyun yake da burin ya hada.yana da tsare gida sosai.amma akwai farin jinin jamaa.duk inda ya shiga mutane suna son sa.kodayake halayyar shi ta janyo don yana da son jamaa da son yi wa jamaa nasiha.ba ya ganin kuskure yayi shiru.ko ina ya shiga da wuya ya bar gurin bai samu wanda ya amshi lambarsa ba ya ce za mu dinga gaisuwa.tare da haka sam ba ya son raini ko cin mutunci ko wulakanci.yam mata da dama suna son sa,musamman dalibai.sai dai ba ya bada fuska, kasancewar ba abin da yake kai shi makaranta ke nan ba.zainabu ya soma so amma ga yadda rayuwa take canzawa,abu ya juye,ya je abuja neman kudin aure,ya dawo da mata.takwas daidai suka shigo kaduna.lsmail ya ce lallai su tsaya su yi salla. hamisu ya rada masa cewa kar mu fita ta gudu. lsmail ya ce,ka rufe motar mana,ka je ka yi.ln ka idar ni ma sai in je in yi.daga nan suka dauki hanyar katsina.jefi-jeri lsmail yana jin MIMI tana tambayar khalil sun kusa kaduna. sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida, mahaifinsa ya yi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyarsu don ya san za ta hakura ba,sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha. ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saar ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar.maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai.yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce ya bi ta. [01/10 10:34 pm] Abdul: (42)Sha biyu da minti goma suka shiga katsina,lokacin khalil ya kira MIMI wai bai sami motar katsina ba.sai dai ya sauka a kaduna. kuma ya je gida,mahaifinsa yayi tafiya,don haka kai tsaye ya wuce gurin hajiyasu don ya san za ta tausaya masa.ya ba ta hakuri,ta ce baza ta hakura ba.sai ya bata gold dinta.ya ce da safe zai kaita gurin wanda ya saida mawa.da haka ta yi ta yi masa fada da nasiha.ba ta san shi ba abin da ya dawo da shi gida ke nan ba.ya dawo ne don ya dauki mota.ya san ta da barcin safe.don haka sai da ya karya ya fita ya duba lafiyar motar,ya koma dakinta ya ci saa ganin makullin motar tata a kan madubi.ya fita ya dauki motar maigadi ya ce,ina za ka?ya ce,hajiya ce ta aike ni in sha mata mai.sai bayan ya zo zariya ya tsaya ya sha mai yayi tambayar ina zai bi in za shi katsina?aka nuna masa wata mota aka ce yabi ta.lokacin ne kuma ya kira MIMI ya fada mata ya taso daga zariya.su kuwa yadda suka yi jiya,suna isa katsina hamisu ya ce,to yanzu kai ne zaka yi ta mana kwatance har gidanku.haka kuwa aka yi. unguwar shiru.kowa ya rufe gidansa,tunda lokacin sha biyu ta wuce,ga kuma yanayin sanyi.lsmail ne ya fita ya je ya turra kofar gidansu,don ya san bata rufuwa da sakata.mahmud ya bude kofar dakin lsmail ya fito.kana ciki ke nan? mahmud ya mika masa hannu tare da fadin gaskiya kun sha hanya. lsmail ya ce,to bari mu kwaso mata kayanta.suka fito.tare da wayarsa yayi amfani ya haska,ya bude murfin gefen da MIMI take zaune ya ce,ki fito.ba ta yi musu ba.ta sauko.sai dai tana saukowa ta toshe hanci,ya haska mata har ta shiga zuren gidan.ya nuna mata dakin.ki shiga nan.a fili ta ce,tafdi!ta shiga tana kallo ko'ina na dakin ta ce,na yarda dad ba ya kauna ta sam.ko tantabaruna dakinsu yafi wannan.lsmail dai ya juya. jiki a sanyaye ya nufi waje.suka soma shigo da kayanta.can ta rakube da bango a kan katifar,tana sake kallon ko'ina a yatsine, hawaye na ta zuba daga idanunta,tana kara karfafa wa kanta cewa lallai gudu shi ne abin da ya halasta ta yi. [01/10 10:34 pm] Abdul: (43)A wannan gidan,a wannan dakin za ta yi rayuwar aure?suka gama shigo da tulin jakunkunanta da kayan takalmanta,suka loda su a gefe.lsma'il ya ce. mahmud kuje da hamisu ya kwana gurinka.da safe zai dauki hanya.mahmud ya ce,ba damuwa.mahmud ya kalle ta,to amarya,an iso lafiya?da sauri ta dago idanunta ta balla masa harara,tare da jan dogo tsaki,ta ci gaba da latsa wayarta.haka suka fice.lsmail ya raka su mota, suka shiga suka tafi.shi kuma ya dawo ya dauki buta ya fita waje yayi alwala ya shigo ya ra sakata.duk da yana ta addua,gaban sa bai daina faduwa ba.yayi shafa'i,ya daga tsohuwar akwatinsa ya dauko bargo ya kalle ta,ga abin rufa.ta yi masa hararar sama da kasa,ta ce,tunda dai ka ji ban ce maka komai ba.to ka gode wa allah.amma kar ka sake ka kara yi min magana.ka ga na yi kama da tsumman bargonka ne?lsmail ba ya daukar raini sam don haka ya ce,za ki iya ce masa tsumma,amma naki sabon ina yake?kar ki cuci kanki,ki amsa ki rufa don ana sanyi sosai.ta yi masa wata harara irin ta sama da kasa,ta ce,kar ka zata wai an daura maka aure dani, shi ke yake ba da damar in zama matarka.ya ce,na nawa kuma?sai dai in kar a kara,amma aikin gama ya gama.ta ce,ai ba bisa yardata aka yi ba,don haka babu aure.yayi yar dariya,yadda kika ce ba.amma aure daram, musulunci ya kulla shi.kuma nine kadai zan iya warware shi ta hanyar saki.ta ce,to maza ka warware shi.don ni da gari ya waye zan kama gabana.ya ce,da hakan za ta yiwu tun daga abuja zan yi hakan.sai dai kash na riga da na yiwa mahaifiyarki alkawari.ta daga murya,kai ni yanzu ba ni da wata mahaifiya,ban da iyaye,ban da kowa. mahaifiyar da tana zaune aka gama cin zarafina.ban ji haushinta sosai ba,dama can na san ba wai tana so na bane.don haka zan fi son in tafi inda babu wanda zai ji labarina. ya sake mika mata bargon,ki rufa,sanyi yayi yawa.ta ce,ka bar shi in ya so sanyin ya zama ajalina.lsmail ya ce,ni ma dana huta da tunanin nan. [01/10 10:35 pm] Abdul: (44)Ta kalle shi sannan ta ja dogon tsaki.tabarma ya shimfida.bata bude sosai ba, don dama gurin da ya rage bai fi gurin salla ba.ya dauko wani zanin gado ya shimfida,ya dauki filo daya ya saka.tunaninsa daya,duk tsananin sanyi,shi ba maabocin yin barci da kaya ba ne,sai dai ya rufa.har ya kamanta haka,dole ya tashi ya cire riga,ya kwanta da dogon wando.lta dai tana inda take rakube,iyaka dai kau da kanta tare da tabe baki.sama-sama yake yin barcin saboda ba ya kwanciyar kasa har ya zuwa lokacin da ya saba tashi don yin nafilfili.ya yi mika,ya saka rigarsa ya waiwaya ya kalle ta,ta takure,kanta yana cinyarta, wayar ta fadi can gefe.da alamu sanyi sosai take ji.ya daga akwatinsa ya ciro malumalun dinsa a goge,tana ta kamshin turaren da yake sawa a kayansa,ya lallaba,ya rufa mata.ya fita don yo alwala. ko da ya dawo ta zame ta kwanta,ta kankame filo,ko fuskar ta ba a gani.yayi sallarsa,ya gabatar da adduoinsa ga mahalicci.abin da yafi alheri kawai yake ta roka tsakanin sa da MIMI.ya sake kwanciya yana fuskantar inda take kwance.bai iya ci gaba da barci ba,sai hasashen me zai faru gobe da jibi?lna zai samu kudin da zai ci da ita irin cimar da take ci?lna zai samu kudin irin tufaein take sawa zuwa kayan shafanta wanda a gabansa ta ce dubu dari albashinsa shine kudin kayan safanta.a haka har asubhi tayi.ya kulle dakin ta baya,ya tafi masallaci.a can suka hadu da yan uwansa,wato yayyinsa maza,suka gaisa. suka yi masa murna mahmud ya zo ya fada musu cewa maigidansa ya ba shi yarinya.ya ce haka ne.babba ya ce.amma ai mu ne ya kamata mu zama wakikanka duk lalacewarmu.lsmail ya gano sun dauki zafi ne,don haka ya fada musu yadda abin ya taso amma duk da haka cewa kurum suka yi,allah yasa alheri ba don sun yarda ba.daga nan gidan yaya amina ya wuce.idar da sallarta ke nan yayi sallama,ta amsa,suka gaisa. cikin murna ta ce,sai ga labari mai dadi.ya ce,uhum yaya ke nan.ta ce,mene ne uhum,kun zo da amaryar ne?ya ce,eh,tana dakina.amma matsalar ba ta so na. [01/10 10:35 pm] Abdul: (45)Ni ma sam bana son ta ko da wasa.nan dai ya fada mata komai.ta ce.to allah dai ya daidaita ku.ka tashi ka je kar ta farka.yanzu to me zaka bata na kari?ya ce,sai dai na je na ji daga bakinta,don ban san da me za ta karya ba.nan suka yi sallama ya nufi gida.kai tsaye cikin gida ya wuce,fatu tana kicin ya ce mata ina kwana?ta dago ta dube shi,aa yan abuja ne?sai muka ji aure.na ce kila dai don mu bamu da zanin zuwa abuja ne.yayi dan murmushi ya wuce.saura suka fito su ma dai ya gaishe su,amma sai sakin magana suke yi.dakin lnna ya shiga tana kwance,ga rushi a gabanta,ya zauna ya gai da ta.ta ce,sai kuma mamuda abokinka ya zo mana da labarin aure.ya ce,eh.abin allah ya kawo shi kafin a yi shiri.ya ce,to allah ya ba da zaman lafiya.mu da har muna cewa kila ka canza dangi ne.ya ce ba haka ba ne.ni ma abin ya zo min ne ba shiri.tana ciki ai tana barci.ta ce,to kuma a nan dakin za ku zauna?ya ce,eh,to sai dai yau zuwa gobe za mu fara neman daki.ya mike,bari in gani ko ta farka. ya sa makulli ya bude dakin.har lokacin bata tashi ba.ya kira mahmud yana tambayar sa ko hamisu ya tashi?ya ce tunda suka yi salla ya koma.ya bar shine ya dan warware gajiya tunda hanya zai kara bi. sai karfe goma da kwata,lokacin tuni lsamail yayi wanka,yayi shirinsa cikin shada mai ruwa siminti.yayi kyau yana ta kamshi.ta farka,mika tayi ta yi tsaki.ya ce,ai kamata yayi ki yi adduar tashi daga barci,ba tsaki ba.yanzu da kin bude ido kin gan ki a kabari fa?ta tashi zaune,da sai na fi murna fiye da in gan ni a dakin nan.da sauri ta shiga neman wayarta.ta dauka ta soma kiran layin khalil,ya katse.ya kira ta, lokacin ne yake fada mata ya taso daga zariya.ta ce, shi ke nan zamu yi ta waya har ka iso.ya ce,shi ke nan,sai na iso din. lsmail ya ce,wai da wa kike ta yin waya ne?ta harare shi,na ce ka daina yin min magana ko?ya ce,to ki tashi ki yi salla.ta harare shi,ta ja tsaki,ba zan yi ba.ya ce kina fashin salla ne?ta mike tsaye cikin mamakin wuce gona da irin. [01/10 10:35 pm] Abdul: (46)Na mutum,ta ce,cikin daga murya,zo ka matse ni ka duba ka ji ko?ta zare idanu a karshen maganarta. ya mike,mai da wukar.me za ki ci?ta sake hararar sa,kai har ka mallaki abin da za ka iya ciyar da ni?ta sauka daga kan katifar ta nufi jakarta wadda ta sa jakarta mai kudi a ciki.ta ciro ta zo zata zauna,sai ta ga malum-malum dinsa,ta sa kafa ta ture.ya ce,oho dai ta yi miki amfani. ba ta kula shi ba ta kwance kudin sadakin da aka bata a gefen gyalenta,ta zuba a cikin jakar,ta dauko karamin akwaiti cikin jerin akwatunanta,ta bude akwatunan tana zabar kayan da za ta sa.yawanci kananan kaya ta diba.ta bude wata jakar ta dauki kayan ciki da na shafa,sai takalmi daya ta saka jakarta mai kudi,ta rufe.ta sauka daga kan katifar.ya ce,wai ke ko fitsari ba ki ji ne,duk sanyin nan da ake yi?ta ja tsaki,ban ga gurin da zan iya tsugunawa ba.ya ce,mu shiga cikin gidan.daga nan sai ki gai da lnnata.tunda ya ambaci fitsari,sai ta ji ya matse ta har kamar zai zuba.shiru ta yi,sai ya dauko buta,mu je in raka ki.ta dauki mayafinta ta dan yafa.suka fito zaure a share fes.don tun kafin ya shiga wanka ya share.suna shiga tsakar gida,matan gidan suna ta aikace-aikacensu.ta sa gefen mayafinta ta rufe hancinta.ya ce,ki gai da su mana.ta zabga masa harara,ta ce,nuna min toilet ni kam.ya nuna mata,ta shiga da kyar ta yi yin fitsari saboda zarni da kuma rashi inda zata tsugunna.ba ta taba ganin irin wannan ban dakin ba,don ko na kauyen su dad da ta tsani shiga yafi wannan kyau.ta fito duk ta bata kafafunta.sai da ta fito ne take ta wanke kafarta,tana zubar da miyau.cikin sauri ta bar tsakar gidan.sai da ta je soro ta sauke numfashi ta soma kuka.matan gida suka yi ta kallon kallo.fatu ta ce,salo da yayi,wai kaza ta ji shikar dare.lsmail ya ce,ku yi hakuri ba laifinta ba ne,ba ta saba da ganin haka ba.suka sa dariya,gami da shewa,to a kai ta inda ta saba,ln ji fatu. shi dai fita yayi ya bar su suna ta habaici da kananan zagi. [01/10 10:35 pm] Abdul: (47)Ta shiga cikindakin ta dauki wayarta ta soma kiran khalil.ya ce,mun kusa ki ba ni minti talatin.gudu nake yi sosai,kin ji dear ta ce,to inda nake ne ko dakin karen gidanmu ya fi shi.ran lsmail a bace,ya ce karya kike yi.lna sake fada miki karya kike yi.ta ce,dakin karenmu akwai tayils,na fa? ya ce,dakina akwai alkurani da littattafan addini.ke nan dakina yafi naki ma,duk kyawunsa.ta sake bin dakin da kallo,tana tabe baki.ta ce,tsayawa yin musu da kai bata lokaci ne. ta sake mikewa ta zage wani zif din akwati ta ciro muhimman takardunuta,ta zage jakar da za ta tafi da ita ta zuba.ta zauna ta yi tagumi,jifa-jifa tana duba agogo,shi kuma ya kasa ya tsare ya ga inda za ta. Na'ima amarya kuwa an yi barci sama-sama a gidan abbas sai takwas ta farka ta zauna zugum a bakin gado.ta dauki wayarta ta soma kiran layin momy.momy tana dagawa ta ce,na'ima an tashi lafiya?bata jira amsa ba,ta ci gaba da cewa,da dinku jikinsa fa ya tashi kamar yadda na ce miki jiya.yanzun haka mun koma asibiti.ki fada wa maigidanki.na'ima ta ce to kawai don ta san babu damar ta yi korafi a cikin wannan halin.wanka ta shiga,ta yo alwala.ta dan fi MIMI tunda ita takan yi sallah ko da dai ba kullum ba.ta zo ta yi kwallaiya,ta bude wardrobe dinta ta ciro sabuwar jallabiya mai shegen kyau ta saka,ta yafa mayafinta irin yadda MIMI ke yi,ta fesa turarruka,ta saka lallausan silifas na zaman gida,ta nufi sama abbas.ta jima a tsaye bakin kafar tana tunanin bugawa.can dai ta daure ta murda kofar,sai ta ji ta a kulle.daga ciki ta ji an ce waye?ta dan yi shiru tare da zaro ido.a sanyaye ta ce,ni ce.a lokacin ya riga ya zo zai bude kofar ya ga ko wane ne.duk da haka bai fasa ba,sai ya bude.ganin ta sai ya bar kofar a bude.ta shiga da alama wanka ya fito don ga rigar wankan a jikinsa. a hannunsa akwai karamin tawul,yana goge kansa.ta tsuguna har kasa,ina kwana?ya bata rai ya kau da kai lafiya.ta ce,da ma momu ce ta yi min waya wai dad dina ba shi da lafiya.an mai da shi asibiti. [01/10 10:35 pm] Abdul: (48)Ya waiwayo ya kalle ta,irin kallon kashi din nan,to me zan yi masa?ln za ki je.ga ki ga hanya,amma ni bani da lokaci.kin gane?ta mike a sanyaye.har ta kai bakin kofa sai kuma ta waiwayowa,am na ce me zan dafa?ya sake waiwayowa,bana bukata. ranta ya dan sosu.ta mike ta nufi dakinta tana kuka. Bakin gado ta zauna, lallai za ta shiga matsala babba.da ma abbas bai amshe ta ba?shi ne ya amince ya aure ta don kawai yayi mata wulakanci?haka ta yi ta kuka.ko kayarwa bata yi ba har kusan karfe biyu,sai ga kannen momy,su anty rukayya.suka ce lafiya ke kuma kike kuka?anty jamila ta ce,wawiya mana,yanzu an daina wannan abin dan.kin yi daren farko a gidan miji,kiyi ta wani kuka.ta ce,ba haka bane.ta fada musu komai ta ce,ya san bai yarda ba tun farko ba sai ya ce,aa ba.sai yanzu ne zai fara yi min wulakanci?anty rukayya ta ce,ke dai sakarya ce.don wannan za ki yi kuka.ki saurare mu kiji.tunda daga ke sai shi a gidan,abu ne mai sauki ki ja raayinsa.anty jamila ta ce,ina kananan kayan nan da momy dinku ta siyo miki daga dubai?ta ce,suna cikin akwatunan da kuka zo da su.ta nuno shi,ga su can. suka je suka bude.suka ce yawwa ki gwada mu gani.ta yi ta gwadawa suna tafa mata,tare da koya mata kalolin sanya su yadda za ta ja raayinsa.ba su bar gidan ba sai da suka tabbatar da haddace duk abin da suka koya mata.ba su jima da fita ba,sai ga dangin abbas da masu aiki an kawo mata.da dattijiya da mana yarinyar dai yarinyar gwari ce,sannan ta kuko namiji.karfe tara na dare na'ima ta yi wanka sosai,ta yi gayu kamar yadda suka ce maties din ta suka ce.ta saka rigar da suka zuba mata wadda ita ce ta dace da ita a wannan dace.hannu din rigar gare ta.shi ma kulle shi aka yi kirjinta a waje.tsawo rigar bai kai guiwa ba.ta kama gashinta a tsakiyar kanta,ta yi wanka da turarurruka masu daukar hankali.ta soma rihasal din yadda za ta shiga dakin da yadda za ta tunkare shi da duk abin da suka ce ta yi.sai da ta tabbatar zata iya ta nufi saman abbas, duk da tana fargabar kar ya gwasale ta. [01/10 10:35 pm] Abdul: (49)Ita kuwa MIMI kamar karfe shabiyu sai ga kiran khalil.ta daga ya ce,kina ji na?ta ce eh.ya ce,na iso.ta mike ta bude jaka lsmail suna tsane da mahmud a kofar gida suna tattaunawa a kan inda zai nemi dakin yanzun nan hamisu direba ya wuce bayan ya kawo mahmud sun yi sallama ya lsmail ya ce masa godiya,mahmud yana cewa,mu je mu samu malam.mahaifina kayi mai bayani,lna zaton akwai daki a gidansa na kofar guga amma can bayan gari ne,ba mutane sosai a gurin.gidan dai mutane biyu ne,amma daki uku ne ciki da falo.lsmail ya ce,to da ma ina da kudin nan.mahmud ya ce,ka san ma ba zai amshi kudinka ba. fatanmu allah yasa bai riga ya ba wai ba.rufe bakin mahmud ke nan,lsmail ya ce,amin...bai karasa ba,sai ga MIMI ta fito sanye da riga da wando damammu,sai dan mayafi da ta rataya shi kamar yadda take yi tana janye da dan akwatinta.da sauri ya nufo ta,ina za ki je?ta kalle shi sama da kasa,ta ja tsaki,ta tsallaka kwata.ya kalli gurin zaman yan majalisar kofar gidansu ba su fito ba rana.mahmud ya ce,bar ta mu bita a baya. haka kuwa tana tafe suna bin ta.sai ta tare dan acaba ta hau.su ma suka hau suna hangenta tana waya har zuwa garejin mota.tana tsayawa suka tsaya ta ciro kudi ta ba dan acaba,su ma haka.ta nufi wata mota.kafin su tsallaka su isa ga motar har sun tashe ta.lsmail ya shiga tashin hankali sosai.ya ce, mahmud barin ta za mu yi ta tafi?na yiwa mahaifiyarta alkawari. mahmud ya ce,zo mu dauki mai gulf din can ya bisu.sun nufi gurin sai suka ga hamisu direba ana sa masa fasinjan abuja.lsmail ya ce,aa me kuma ka tsaya yi?ya ce,lodin abuja zan yi,in dan kara na mai,ln samu na batarwa.lsmail ya ce,sauke sumu bi su MIMI,ta gudu ga su can sun dauki hanyar kaduna. [01/10 10:35 pm] Abdul: (50)Nan da nan hamisu ya sauke su,lsmail ya shiga gaba,mahmud ya shiga baya.duk da halin da lsmail yake ciki bai hana shi ya yi wa hamisu direba nasiha ba.ya ce,hamisu tsakani da allah ban zaci kana cikin direbobi masu cin amanar iyayengidansu ba.sam bai dace ka yi lodi ba tare da izinin maigidanka ba.haramun ka ci.ai gara ka ce min in kara maka na mai.amma wannan cin amana ne.ya baka amana ne fa.ko ya san kana yi?hamisu ya ce,wai!ln alhaji ya ji ai na shiga uku. lsmail ya ce,ka gani ko?yana biyan ka hakkinka.hamisu ya ce, lnsha allah na daina.daga yanzun ba zan kara ba. Da yake hamisu gudu yake yi,sun hango su,har sun kusa zuwa daf da jun. MIMI ce ta gane motar gidansu.ta ce,ana bin mu. waccan motar gidanmu ce. nan suka kara gudu.gudun nasu yayi yawa.allah dai ya tsare...karan da suka ji shi ne ya tabbatar musu da cewa taya ce ta fashe ta su MIMI. daga inda suke suna hangen yadda motar take tuntsira gudi-gudi a kan titi.gaba dayansu suka hau salati.hamisu na cewa taya ta fashe shi. kuma ya taka burki.hankalin lsmail ya yi mugun tashi.suna isa gurin,motar tana tsayawa bayan ta tokari bishiya.suka fito suka nufi gurin.motoci suka tsaitsaya ana ta kokarin ciro su.duk jikin lsmail bari yake yi.wasu na cewa tun dana ga tukin da yaron nan yake yi na san zai yi wuya basu fadi ba. Nan zan dan huta.sai mun hadu a kashi na uku don jin shin su MIMI za su rayu?ln sun rayu,yaya zamansu zai kasance?wai na'ima ta ci nasara da ta hau saman abbas?mene ne labarin zainabu? Taku Halimarku K Mashi. sai na ji ku a 08081165107. lna jiran shawara ko korafi. CANJIN RAYUWA 3 Halima K mashi Littafi na Uku Hausaebooks Shuraih 99% Daga:- http://keffiansonline.cf Hankalin isma’il yayi mutukar tashi lokacin da aka juyada motar domin gaba daya khalil yadagargaje har kwanyarsa tanzuba juyawa yayi yana salati kmar yadda sauran sukeyi bai iya sake kallon grinba har aka faito da mimi sai da aka zuba su amota sannan mahmud yazoya kama kafadun isma’il yana cewa karka damu isma’il mutafi asibiti sun nufi motar kenan mahmud ya hango wani daga cikin masu kawo daukin ya kunkuci dan akwatin mimi dajakar khalil ya gane akwatin mimi ne sbd a gabansa tafito lkacin dazata tafi dasauri mahmud yanufishi yana cewa kaiba ni kayan nan konakane? Yace ammm dama inace za aje gurin yansadane mahmud yace nanne hanyarguri yansandana,a gurin sojoji zaaje ba yan sandaba irinku ne masu yin sada in anyi hadariko? Mutumin ya miko akwatin tare da cewa bani kadi bane yanuna wani gawanda yadauki waya chan! mahmud ya kwada masa kira, kai zonan bani wayar hannunka shi ma babu kunya yamiko ta muhmud yace kuji tsoro allah batare da ya jira jin ta bakinsu yajuya ya nufi motar hamisu ya zuba kayan sannan ya shiga yana cewa “muje hamisu!” kuwwar motar yansanda itace ta tsaidasu,suka iso. Sannan suka nufi asibitin tare. Cikin sauri aka amshi su aka yi emergency dasu, musamman dayake angansu da yan sanda.isma’il yana tsaye cikin matsanancin hali.addu’o’in da isma’il yake yine sukasa jikinsa ya daina bari saidai kallo daya zakayi masa ka san cewa yana cikintashin hankali.daya daga cikin yansandan ya nufosu.ya kalli mahmud waiyaya abin yafarune? Mahmud yakalli dan sandan gudu yakeyi sosai,dan sandan yace naji lokacin da mukazo gurin,wani yana cewa,koyasha wani abune? Sai wani ne acikin motar yace,irin yaran masu kudin nan ne suke dauko mota suzo sunamugun godu atiti.mahmud yce, yarinyar da suke tare matar wannance, yanuna isma’il.jiya aka daura musu aure shne yazo ya dauketa zasu gudu, shine fawannan hadarin yafaru.dan sandan yakalli isma’il batason kane? Lsma’il yace, babanta ne yahada nida ita ranka yadade baxan iya saniba.kafin dan sandan yasakecewa wani abu,sai ga likitan da sauri.ya ce, kune yan uwan masu hadarin nanko? dasuri mahmud ya taso,mune likita.likitan yace kun san cewa namijin yarasu ko? duk da cewa dama suna tunanin cewa ya mutu,saida suka dauki kabbara. Sannan suka ce, allh yajikansa da gafara.isma’il yakama hannun likitan yana fadin”doctoh itafa? “yace,kar kadamu,munayin iyak kokarinmu.ta samu karaya guda biyu a kafarta, da kuma guda daya a hannu.sannan munaso ne ta farfado don mu sani ko ta samu wata matsala awani guri daga cikin kanta, saboda ta zubar da jini sosai.yaba shi wata takarda, kaje gurin sai da magani,gashi can zasu baka wadannan,yanxun kakawo mana. Isma’il yace to,sannan ya kalli mahmud,gashi kudin suna gida.mahmud yace,to muje kadauko mana. Daga nan sai mutan gadan su san halinda ake ciki.kafin su wuce saida suka dauko jakar khalil da wayarsa suka ba wa yan sandan.don tasa aka gani ba agata mimi ba. hamisu yajasu, kai tsaye gidan suka koma, inda isma’il ya aje jakar mimi,sannan ya dauko kudinsa duka na aikinsa da alhaji ya bashi. Ya kulle dakin ,sannan yashiga cikin gdan yasanar da su inna abin daya faru.bai tsaya amsa tambayoyin dasu innar sukeyi masa akan wai yaya akayi haka,ko unguwa suka fita?ya fita suka koma asibiti suka sai magungunan. lokacin ne ma dansandan yake fada musu cewa,yakira iyayan khalil.sunyi amfani da wayar khalil din ne. yakuma sanar dasu cewa,dansu yayi hatsari, kuma ya rasu.suzo su dauki gawarsa.isma’il ya girgiza kai don jinjina yadda mahaifan khalil zasuji wannan lamari.alhaji yakira hamisu don yaji ko ya kosa kaduna. Zai sa shiya amsar masa sako gurin wani abokinsa na maganin diabetes ne na hausa da abokin nasa yace xaiba shi,don shima yaji dadinsa. Hamisu yace,matsala aka samu alhaji,ko katsina ban baroba har yanxun.alhaji ya ce, meya faru kuma? Hamisu ya sanar da shi komai. ran alhaji ya bace mutuka dajin cewa mimi tasake yankurin guduwa.cikin bacin rai yace ma hamisu,”kataho kawai!”yace,alhaji yarinyar nan tana cikin mawuyacin hali sosai,don duk akakkarye taka.alhaji yace,hamisu kabarsu kawar. Babu abin da zan iya yi mata, kaima bbu abin daxaka iyayi mata,don haka kayi abin da nace kawai.yace, shikenan,alhaji zan taho yanxun.”yace,” to, kana kusa dashi malam isma’il din ne? Yace, “eh ina kusa dashi.yace,toka bashi!”ya mikama isma’il wayar.sun gaisa,alhji yace,”ashe abinda yafaru kenan?”isma’il yace kwarai kuwa alhji.yace Allh yakyauta.”cikin tashin hankali isma’il y2e,alhji kayi mata duk abinda takeso,zata iya rasa ranta,domin shi khalil din ya rasuma.”duk da alhajin ya jinjina batun mutuwar khalil a ransa,amma afili sai yace,”karka damu malam isma’il,tunda yanxun ta karye ai bazata sake yankurin guduwa ba.ka ba hamisu wayar.”isma’il yace alhji kuzo ku taimaka mata.”alhji yace,isma’il inayi maka jajen abin da yafaru da iyalinka,amma kayi hakuri ba zan iya taimaka mata ba.kaba hamisu wayar!”cikin rawar hannu,isma’il ya mika ma hamisu wayar. (Za mu ci gaba)…. (Tare da Halima K Mashi) Canjin rayuwa A sanyaye ya koma ya jingina da bango. Sai lokacinne ma ya tuna ya kamata ya sanar da hajiya sauda. Ya kalli mahmud, “ya kamata in sanar da mahaifiyar yarinyarnan ko? ” Mahmud yace, “tabbas ya kamata ka sanar da ita” kan benci ya zauna, sannan ya soma kiran layinta. Bata jima ba ta daga. A sanyaye ya gaishe ta. Ita kam yanayin muryarsa tasa ta faduwar gaba. Tace, Ismail ta sake guduwa ne? Yace Eh hajiya, amma sunyi hatsari akan hanyar su ta guduwa. Yanxu haka muna asibiti. Tace, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Da sauqi dai ko? Yayi ajiyar zuciya, to da sauqin dai za’ace amma shi ya rasu… Ya rasu?? Ta katse shi. Yace tabbas, ita dai sunce suna jira ta farfado. In har ta farka a cikin hayyacinta, to suna ganin karayar data samu ce guda biyu a kafarta daya kuma a hannunta sune kawai matsalar, cikin kuka hajiya tace, wane asibitin kuke? Yace babbab asibiti, tace shikenan bari in Kira alhaji zanzo ynxu,. Kafin ya amsa da cewa Alhaji ya kirashi, har ta kashe wayar. Hajiya ta soma kuka. Su hasana suka fito da sauri suna tambayar ta lafiya? Tace musu mimi ce sukayi hadari. Nan suma suka shiga damuwa. Tace bari in kira Alhaji Muje mu ganta. Ta shiga kiran layin Alhajin, tana soma ringing ya daga, Tace cikin kuka Alhaji kaji abinda ya faru? Yace naji. Ko ba hadarin su mimi ba? Tace ashe ka sani. To dama zamu tafi da yara ne. Ga mamakin ta sai taji yace, ban amince ba, yaci gaba da cewa, ki Fadama duk sauran ‘ya’yanki banyi wa kowa izinin zuwa duba ta ba, matsawar na isa. Mamaki ya cika hajiya sauda, tace sbd me Alhaji? Yace cikin fushi, ban isa ince ga abinda nakeso ba saina fadi dalilina kenan ko? Tace kayi haquri. Yace to na saka Allah ya isa! Daga kanki har sauran da suke qarqashi na matsawar kuka taka gurinta! Ya kashe wayarsa. Shi kansa Alhajin cikin damuwa yake, amma ya tsara ma kansa cewa, dole ya haqura don wani dalili nasa, sannan yasan cewa, abin Ya ta6a zuciyar hajiya sauda, sbd hk ya yanke Shawarar sake kiranta. Ta daga, har lokacin kuka take, a nata ganin bai dace abar mimi cikin wannan halin ba. Yace amma hajiya don Allah kiyi haquri, akwai dalilin da yasa dole sai nayi hakan. Zan yi miki bayani daga baya. Sannan ina mai jaddada miki ban haquri na, ki taimaka kuyimin wannan. Nasan zaki iya saka ‘ya’yanki su dangana da zuwa gurin mimi. Kuma daga baya zaki daina jin zafi na in kinji dalilina. Kin fahimceni ? Tayi ajiyar zuciya, shikenan zanyi duk yadda kk so. Shima ya sauke tasa ajiyar zuciyar. Na gode, Allah yayi miki albarka, ya saka miki da aljannah. Sai nazo. Tace to Allah ya kawo ka lfy. Ta kalli su usaina tace, inaso kubar maganar nan anan, ko su yayanku abba, bana son su sani. Hasana tace sbd me hajiya? Tace sbd hk dadynku ya buqata. Kuma banison ku damu da cewa sai kun san dalili. Zamu dinga jinya lafiyarta daga bakin mijinta. Suka kalli juna da ido, suka mamakin zancen mahaifiyar su, sannan suka miqe suka shiga dakinsu. Ita kuma sai ta daga waya ta kira layin Ismail. Cikin sauri tare da yin sallama, ya amsa a sanyaye, yace kun iso ne? Tace a’a ba zan samu zuwa ba, in dai ta tashi kace ina gaisheta. Yace hajiya kema baki samun damar zuwa kenan? Ta soma shesshekar kuka, mahaifinta yayi mana iyaka da zuwa gurin ta, cikin sauri yace sbd me? Don Allah ku yafe mata, sbd tana cikin wani hali, wanda ba dole bane ta tashi. Hajiya tace na yafe ma ta duk abinda tayi min, wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma nima bansan dalilin sa nayin hkn ba, amma idn ya fadamun zan sanar dakai. Sannan kuma malam Ismail zan sake baka amanar mimi, ka qadd ara batada kowa, sai kai kadai mijinta. Lokaci zuwa lokaci zan dinga jin yadda jiki nta yake, amma ta waya daga bakinka. Ismail yace shikenan nayi miki alkawarin zanyi iyakar iyawata, sai Anjima. Ya kalli Mahmud, bayan ya kashe wayar, wannan wace irin qaddara ce ta hau kaina? Alhaji ya hana su zuwa ma. Mahmoud yace wanna n abin da Mamaki, amma tunda kai iyalinka ce, nauyinta ya rataya ne a wuyan ka. Kai ya cancanta kaci gaba da kula da lfyr ta har zuwa lokaci n da zasu huce. Nawa zaton sunji zafin guduwar data sake yi ne. Amma in sun huce zasu zo. Ismail yace Allah ya sani, tunani na dama banida qarfin dazan iya kula da lafiyarta. Mahmud yace, kar ka damu Allah zai duba maka. A sanyaye Ismail yace Allah ya duba mana, suka hada baki gurin cewa Ameen! Saida lokacin sallah yayi sannan suka miqe suka nufi masallaci. Daga masallaci ne Mahmud ya nufi gd don sanar wa malam Aminu. Ismail yace kabi ta gdn yaya Amina ka fada mata don bata sani ba, Mahmud yace zanbi insha Allahu. Kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai, tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani da Addu’a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya shige mana gaba. Yace Ameen. Bayan la’asar su malam suka zo tare da wasu malamai suka yi masa jaje, tare da addu’ar cewa, Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci. Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a’a yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda hakan, yace a’a ki riqesu a hannunki, sbd kema kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku abincin da wuri. Yace a’a kai ki yo abincinnan yau tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso suka shiga s Canjin rayuwa Canjin rayuwa sun kai kusan minti goma, sannan wata nurse ta leqo, ta kalli Ismail, tace masa wanene khalil? Yace mata shine wanda sukai hadari tare ya mutu. Ta juya da sauri, Ismail dai yanata kai komo. Ya kai kusan rabi sa’a sannan likitan ya fito, ya kalli Ismail yace masa, zo muje! Ya bishi zuwa offishinsa, inda suka zauna, ya kalli Ismail, kai wanene dinta? Ismail yadan yi jim kadan don yana jinjina kalmar, duk lokacin da zai furta ta. Tsakanin jiya zuwa yau, ya lumshe ido, “ni mijinta ne” likitan yace ok to zamu kaita dakin jinya, domin ynxun ta farka, amma yanxu munyi mata allurar varci sakamakon tana ta kiran sunan marigayin. Ya ajiye biron daya dauka, sannan ya kalli Ismail yace, wazai zauna da ita? Ismail yace nine, likitan ya girgiza kai, babu dama ka zauna da ita, sbd kai namiji ne, kuma dakin akwai matan mutane, sai dai in zaka biya daki na musamm an, sannan za’a buqaci kudi sbd likitan da zai mata dorin zaizo ne da ga kano, kuma gashi dorin har guri uku ne, Ismail yace to likita kamar nawa ake nema? Yace kasan shi likita ne mai zaman kansa, dauko shi akeyi, qila yakai gurin dubu sittin, banda magani. Ismail yace insha Allahu za’a san yadda za’ayi, Amma likita bata samu matsalar da ake tunanin ta samu ba ko? Ya girgiza kai, bana zaton ta samu wata matsala, Ismail yace Allah yasa dai, zan biya kudin daki na musamman din. Likitan yayi masa kwatancen inda zai biy a kudin dakin. Har ya miqe sai likitan ya sake kallon sa, ba tada iyaye ne a garinnan? Eh, kawai yace, to ko cikin dangin ka ba wanda zai iya zama da ita? Cikin qosawa yace nima yayata ce guda daya, kuma tana da qananan yara. Baya son doguwar magana, shiyasa ya amsa a qagare, shikenan ka iya tfy, inji likitan, an kaita daki na musamman akan kudi naira dubu ashirin a sati biyu. Dakin akwai TV da dan fridge, sai na’urar sanyaya daki. Ismail yana tsaye yana kallon mimi, an manna mata bandeji a gurin da taji ciwo. Addu’o’i kawai yake yi mata, har lokacin da yaje yayi sallar magrib a bata farka ba. Yana shigowa yaci karo dasu yaya Amina, suna neman dakin da aka kaisu. Ya amshi kular hannunta sannan suka nufi dakin, suka gaisa da abbab saddam, yayi masa jaje. Basu jima ba suka ce zasu wuce. Yabi su don yadan taka musu, anan ne take tambayarsa ko ‘yan gdansu sunzo? Yace kinsan dai koda zuwan ne, sai dai in mazan, amma matan ban sa rai ba, mazan ma daqyar in sunji, tunda lokacin da naje gdn basa nan, tace to ba komai Allah ya bata lfy, yace Ameen, tace tuwo ne fa akular da muka zo da ita, naga kana son tuwo, yace nifa yau ko karyawa banyi ba, dama zan samu ruwan zafi, tace vari to inje in dafa maka, sai abban su saddam ya kawo maka, tunda ga mashi n ahannunsa. Ismail yace to na gode. Suna fita, wayar Ismail ta soma ringing, ya daga ashe Mahmud ne ya kawo innarsu zata duba ta, suna cikin gaisawa da innar sai ga kiran hajiya sauda. Bayan sun gaisa take tambayarsa jikin mimi, yace da sauqi, amma tana varci, bata farka ba, tace to zata kira zuwa gobe, sannan ya turo mata account number dinsa, yace to insha Allahu, sannan yayi mata godiya. Kusan qarfe goman dare, mimi ta farka, lokacin Ismail yana zaune kan sallaya, ya idar da sallar shafa’i da wutiri. Sai yaji tana cewa, “daddy na, daddy na!” cikin wani irin sauti mai ban tausayi. Da sauri ya miqe ya nufi gadon da take, ya kama hannunta yana “khadija, sannu kinji. Kin tashi ne? Bari in kira likita” ya miqe ya nufi qasa da sauri domin kiran likita. Ta soma kuka, ni fa taimako nayi sbd kar aji kunya, yace aikuwa zakiyi da kin sanin wannan taimakon. Inaso kisan wani abu, ni mutum ne wanda in naga abu inaso, to so ne na gske, kuma ba zanyi wasa da son ba. Haka nan kuma qi, don bana yin qi da wasa, mimi na gani nace inaso, tunda tace bata yi ai sai abarni inji da ciwon rashin ta, ba wai akwaso min ke ba, baqi qirin! Ni farar mace itace ra’ayina, kin gane? Na’ima ta soma kuka wiwi, tana cewa, toni ynxun ka fatamin matsayi na, ya miqe tare da nufar dakin varcin sa. Gashi na fada miki kuwa, banda wannan matsayin wanne kk son ji? Don Allah tashi ki fita a daki na, Na’ima ta miqe jiki babu qwari, ta nufi dakinta cikin kunya da kuka, ta kira momy nafisa a waya, momy tace lfy da wannan daren? Na’ima cikin kuka tace “momy Abbas baya so na, ya fadamun ” momy tace sakarya! Baki dai iya kissa ba kawai zaki ce. Har akawai namijin d zai raina mace? Bare ke da kyanki da komai, amma dai ki vari zamuyi magana dake zuwa da safe, na fada miki jikin dadynku ne ya motsa, gashi ma anyi masa waya mimi tayi hadari. Duk da ya nuna abin bai dameshi ba, amma jikin nasa ya qara rikicewa, ynxun dai ya samu varci, bayan likita ya gama dubashi. Na’ima cikin sauri tace “sis mimi din ce tayi hadari momy? ” tace eh itace, sake guduwa wai tayi, ita d wanda takeso din, sunyi mummunan hatsari, shi wanda take so din ya mutu. Na’ima tace innalillahi wa inna ilaihi raji’un! To ynxun tana ina? Amma da sauqi ko? Momy tace, dalla can, duk kin wani rude, ni ina zan sani? Dadyn ku ya hana zuwa. Hamisu direban yara yace, tana jin jiki. Na’ima tace Allah sarki sis mimi! To shi daddy ya haqura mana, momy tace karma ya haqura, su qarata can, kedai ki samu kija ra’ayin mijinki, yadda zaki samu hanklin mahifinku ya dawo kanki. Ni araina ma cewa nayi dama itace ta mutu, Na’ima tace a’a momy kar ta mutu, tunda dai mun samu ta barmin abbas din ba shikenan ba. Ki tayani in shawo kansa, baki ga irin wulaqancin da yayi min ba, tace shikenan zanzo da safe. Na’ima tace Yauwa gara ma kizo kiyi masa magana, tace to shikenan sai nazo din, sukayi saida safe. Zainabu tana kwance akan gadonta, sai juyi takeyi, cikinta banda hautsinawa babu abinda yake yi, amai kawai take ji, amma ta kasa yi, ga zazza6i data kwana dashi. Da qyar tayi sallah. Budo qofarta da akayi ne yasa ta tashi a firgice, tasan Alhaji ne, kullum sai ya shigo dakinta daidai wannan lokacin, yayi buqatarsa da ita, kuma babu ruwansa ko da dakin wa yake cikinsu, ya cire rigarsa ya rataye, tace don Allah kayi haquri yau banida lfy, yace ruwa na da ciwonki? Nima yau sauri nake yi, ba ddewa zanyi ba. Ya fado kan gadon. Ji tayi aman da takeson yi tun jiya ya taho. Nan kuwa tayi ta sheqo masa shi a jiki har kan gadon, ji tayi turarensa dada hankado mata aman, da sauri ya tashi ya wanka mata wani wawan mari. Yana ta surfa mata ashariya. Ita dai amai take ta wankawa, har saida ta amayar da duk abinda taci, sannan ta kwanta tana maida numfashi. Shi kam da zage-zage ya fita har xuwa dakinsa, ya wanke ya fito ya nufi gurin wacce zainabu take bi mata don kai buqatarsa can tace, sai yau kasan dani? Tunda kayi amarya ka daina shigowa da safe, yace ai tsiyarki kenan mita. Ita wancan har mace ce da har zaki damu kanki? Yarinyar da kullum saina dake ta ko na zage ta sannan zan samu buqatata. Wai ahakan ne ta kama amaye amaye, in dai ciki ne zanci mutuncinta, sbd ban mori kudina ba. To bata sonka kai kuma ka nace, in bata sona ai tanason kudina ko? Ba sai a faranta min na kudina ba, sisina bazai yi ciwo ba.in ba zata zauna ta faranta min rai ba, to zasu bani ‘yan kudina. Uwar ta ga roqon tsiya, ko jiya saida ta aiko wai in bata dubu goma. Kuma kabata? Ta katseshi. Yace dan iska ne ni, dari biyar na bada aka kai mata. Wane farin ciki nake samu gurin ‘yarta da har zan dinga bata kudi? Tace inace ka bata ne,nima ince akai wa uwata. Yace ke har kinyi magana? Ko wata uku ba’ayi ba, tsohonki ya dage saida na sai masa mashin, tace eh amma kayimin gori yafi sau dari akan mashin dinnan, kai matsalar ka kenan gori duk wanda kaba abinka to ya tabbata zaisha gori, yace eh amma su kuma iyayen naku rokonsu yayi yawa. Ni muje kinji, sauri nake zan fita. Alhaji lawal kenan, sam bai damu dayin al’amuransa bisa tsarin addinnin musulunci ba bare bin doka. Rayuwar gdansa yana tafiyar da ita bisa son zuciya, shi ganinsa, kudi za suyi masa maganin komai, bai qara bi takan zainabu ba ya fito. Shirun da uwar gd maman bushira taji, yasa ta leqa dakin tana cewa, amai kkyi haka? Kai ta daga, alamun eh, maman bushira tace anxo gurin kenan. Ta kama ta, tashi in taimaka miki, ban daki takai ta tace ta wanke jikinta. Ita kuma ta koma tana kwashe kayan gadon, saida ta gyara ta, sannan tasa aka kawo mata abin kari. Da qyar ma tadan kur6i ruwan kunu. Ta kalli uwar gdn, maman bushira me yasa kk ce anzo gurin? Uwar gd tace alamu sun nuna cewa kinada ciki ko? Zainabu ta zaro ido, nima ban sani ba. Uwar gd tace gsky ina zaton ciki gareki. Yaushe rabonki da al’ada? Zainabu ta sunkuyar da kai, fashin sallah kuma? Eh, inji maman bushira. Tun ana saura kwana biyar bikina. Maman bushira tace tabbas ciki ne dake, abinda yasa nace haka, sbd Alhaji baya son haihuwa. Zaki fuskanci wulaqanci sosai. Zainabu tace, banda wannan wulaqancin, har akwai wani kala da zai min? Maman bushira tace sosai ma kuwa! Amma Shawarar dazan baki, in ya tambayeki cewa kina da ciki ne? Kice masa a’a shawara ke damunki, Zainabu tace sbd me to? Tacesbd zai baki maganin zubar da ciki. Zainabu tace zaifi murna, in har cikin ya zube, maman bushira tace ai ba wannan ne matsalar ba. Matsalar zaije ya kawo miki magani, kuma ba wai zai kaiki asibiti bane. Akwai wata yarinya daya ta6a aure, haka akayi qarshe Yarinyar rasuwa tayi, sbd jini ne ya 6alle mata. Tace to in na 6oye masa, kuma yasa aka kaini asibiti aka gano cewa inada ciki fa? Maman bushira tace bazai gane ba. Don ba zai kaiki asibiti ba, don kuwa baya daga cikin mazajen da suka damu da lafiyar iyalinsu, don ko panadol sai dai ki saya. Zainabu ta soma kuka tana fadin dole zai sani, tunda cikin zaiyi girma, maman bushira tace kafin cikin naki yayi girma, da ace zaki iya sakin jiki dashi kema ki sauko, ki tarairaye shi, to da kin yagi na xuwa asibiti, dana kayan jariri. Zainabu tace, nayi ta qoqarin in kwatanta tun kwanaki da kk fadamun, amma na kasa sakin jiki dashi, don inada wanda nake so, kuma yake sona. Tace shikenan zako kiyi zaman wulaqanci, duk ranar daya gano akwai wannan cikin, sabulun wanka sai kin rasa. Zainabu tace zan kwatanta in gani ko zan iya. Maman bushira tace da dai yafi miki. Ranar Zainabu wuni tayi sheqa amai da kuka. Ta galabaita sosai, da magriba ya shigo ya ganta kwance. Ya dube ta a wulaqance, ke kuma kukan me kkyi? Tace shawara ce, dama ko a gd inayi, yace oho’ to kina shan wani magani ne in ya tashi? Tace eh, amma banida kudi ban sayi na asibiti ba, sannan ina kuma shan na hausa. Yace to ina kumazaki samu kudin na siyen maganin, tunda ni dazan baki kin mai dani kamar wani dodo? Ta kalleshi, ai na bari, yace da gske? Ta sunkuyar da kai, sannan tace eh. Yace kinyi alqawari? Ta daga kai, alamun eh. Cikin yace to shikenan vari inzo in nemo miki magani. Ko ke fa? Ynxun zaki san kinyi aure. Amma zan vari yau ki huta tunda baki jin dadi, amma gobe da safe zanzo ko? Tace eh, yana fita ta nufi ban daki ta dinga kakarin amai, don gsky shi kansa wari kawai yake yi mata. Washe gari yana shigowa, haka tayi qoqarin yi masa duk abinda yake so, tare da maida masa martanin duk abinda yayi mata. Tasha wahala matuqa, amma haka ta jure ta nuna masa tana tare dashi, yaji dadi matuq a. Dazai fita ya kawo dubu biyar ya bata. Ya ce ki jirani da daddare, gabanta ya fadi, tace a ranta na shiga uku, a fili tace ai yau ba’a dakina kk ba, yace ina ruwana da wani inda nake, karki damu, abinda kawai na sani dukkanku matana ne, kuma zan shiga gurin duk wacce raina ya biyamin ko kina da ja? Cikin sauri tace, A’a haka ya fita ya barta tana mamaki, tare da tambayar kanta wai daman haka auren yake, ayi ta abu sai kace cin tuwo, kuma ba gajiya? Ita kam ta gaji wlh. Ta dinga juya kudin a hannunta, sannan ta bude akwati nta ta saka, tana yin wanka, sai kuma zazza6i ya rufe ta, ta qudundu ne akan gado cikin bargo. Bata san tsawon lokacin data dauka ba akan gadon nata. Can kamar daga sama sai taji muryar su innarta suna salalla ma. Da sauri ta tashi suka shigo, itace da aminiyarta inna yelwa. Suka iso bakin gadon suka zauna. Inna tace lafiya na ganki cikin bargo haka? Zainabu tace banida lfy ne inna, tace me kuma ke damunki? Ta sunkuyar dakai, tace wai uwar gdnsa ce tace ciki ne dani, shi kuma gashi baya son haihuwa, inna tace to ynxun daya ji kina da cikin me yace? Zainabu tace, bai sani ba. Uwar gdn tace, kar in fada masa, shine nace masa shawara ce ke damuna kawai, kuma tun ina gd take damuna, shine ya siyo min magani. Inna yalwa ta ce, anya kuwa gsky wannan matar ta fada miki? Ance kar ki sake ki saurari maganar kishiya. Har wata soyayya ce zaki samu a gurin kishiya? Zainabu tace Allah kam tana sona da gske. Don tana fadamin gsky, kuma in tabani shawara in nabi ina ganin daidanta. Jiya ma saida ta matsa kan cewa in na saki jiki dashi zan samu kudi, wai anan ne zan samu nayi siyayyar kayan Jariri. Shine nadan daure na saki jiki dashi, shine ma har ya bani dubu biyar. Kuma dama ko yaushe tana fadamin cewa inyi hakan, don dai naqi yi ne. Inna tace kedai akwai sakarya, dama qin sakin jiki kkyi dashi don ubanki? Shiyasa ni kaina ya rage bani abinda yake bani, don jiya na aiko ya bani dubu goma, amma sai ga dari biyar, yadda kk san in yaga ta don haushi, amma na fasa, to tashi ki dauko min dubu biyar din, Zainabu ta turo baki, to zan tara ne fa inna, don fa an fadamun har in ya gano cikinnan, bazai bani komai ba, kuma kayan Jariri ma fa nice zan nema. Inna yalwa tace, jaririn banza, ke kk ta Jariri, waya ce miki za’a barshi? Yanxun nan zamu je a hado maganin da zaibi makwarara, ko yaya kk gani Aminiyata? Ta kai qarshen zancen da kallon innar Zainabu. Inna tace tace, yadda kk ce dinnan haka za’ayi. Zainabu ta soma kuka, don Allah inna kar ku bani maganin zabar da ciki, ance fa wata matarsa ta rasu sakamakon shan maganin zubar da ciki. Inna yalwa tace to shikenan don ta mutu sai aka fada miki cewa kema .mutuwar zakiyi ko? Inna taja tsaki, bar sakarya! Duk abinki cikinnan baza’a barshi ba. Inna yalwa tace, saurara kiji Zainabu. In an zabar da cikin, sai kinfi jin dadin kar6ar kudin a gurinsa. Duk lokacin daya zo gurinki, ki tarairaye shi. Zainabu tace shifa ko wane lokaci, sai yace zai shigo dakina, koda ba anan yake ba, inna yalwa tace saurare ni dakyau, in kullum zaizo gurinki, karki sake kice masa NO, inji ku ‘yan boko, kuma kar ki nuna kin gajiya. Sannan zamuje a hado miki kayan da’a a gurin ‘yar jibiya sbd aqara samun kansa. Kinga ya qara sakin miki baki n aljihu. Inna tace shikenan sai a shigar mata zubin adashi, ai kya san abinda kk tara ko? Ta kalli inna yalwa. Tace qwarai kuwa. Inna tace to yaya batun zuwa gdn malaminnan yalwa? Inna yalwa tace, abar batun zuwa gidan malamin nan, tunda shi ga inda yasa gaba, sai mubishi tana gurin. Tayi ta dirkar maganin da’a masu qarfi. Inna tace shikenan hakan yayi, inna ta miqe, ynxun dai tashi muje yalwa, zamu dawo zuwa Anjima. Zainabu ranta 6ace tace anjima kuma? Nidai zaku fa sa ace iyaye na suna ta sintiri a gidannan, ayi min gori. suka ce a daura miki goruba! Anjiman nan zamu zo. Ai da zafi-zafi akan bugi qarfe. Don haushi ko sallama bata yi musu ba, ta sake qudundunewa akan gado tana ta kuka. Ismail kusan kusan tare suka shigo da likitan, har lokacin daddyn ta take kira cikin sarqarqiyar murya wadda take a galabaice. Likitan ya isa gaban gadon ya dafa goshinta, sannu khadija ? Bude idanun ki in gani. Ta soma yunqurin budewa, dishi-dishi take gani. Yace kin sanni? Ta sake lumshe idanu. Ya waiwaya ya kalli Ismai l sannan ya yafito shi da hannu, Ismail ya matso. Likitan yace yi mata magana. Ismail yace bude idanunki ki ganni. Yakai hannu ya dafa goshinta. A wahalce ta bude idon ta numfashin ta sama sama, tace malam ina khalil di na? Yace yana nan yana varci acan dakin maza. Bai mutu ba? Yana samun sauqi, sannu kinji. Ta daga idanunta a wahalce, ta kalleshi, malam ka kaini gurin daddy na zan mutu ne kaji? Zan mutu. Hankalin Ismail yayi mugun tashi. Ya kama hannun likitan. Don Allah ka bata magani. Wlh Yarinyar nan amana ce a gurina likita. Likitan ya kama hannun Ismail zuwa bakin qofa, yace karka damu, tambaya daya zan maka, Ismail yace to. Sunan data ambata wanene? Ismail yace daddy mahaifinta ne, shi kuma khalil .shine wanda yasu, ina nufin wanda sukayi hadari tare. Likitan yace Alhmdlh. Ynxun ina ganin matsalarmu wannan karayar ce. Sai dai kafin zamu qara mata jini, don ta zubar da jini sosai, daga nan sai mu dora ta. Ismail yace babu matsalar jini, a gwada nawa, in zan iya bata, sai asa mata. Likita yace babu matsala, da safe zamu gwada jinin naka. In zaiyi sai mu ta ce asa mata. Sannan maganar dori, nayi maka batun mai dori, ban nemi shawararka ba, ko kuna son na gd, Ismail yace to ni dai likita, wanne kaga yafi? Domin wannan Yarinyar amana ce a gurina. Likitan ya dafa kafadarsa, kar ka samu damuwa. Mu dai a gurin mu wannan likitan, kamar yadda na fada maka zaizo ne daga kano, kuma yana yin dori sosai anan asibitin, kuma bamu ta6a ganin wata matsala ba. Amma kayi shawara da ‘yan uwanka. Yace to shikenan zuwa da safe duk yadda muka yi zaka ji. Likitan yace, babu komai. Ni zan tafi dama na jira ne sbd inga farkawarta. Ismail yace, to yanxu ba zan iya bata wani abu ba ko da tea ne? Likitan yace kai ka damu, zaka dai iya bata ruwa ne in ta buqata. Nurse zasu zo su saka mata ruwa tare da yi mata allurai, domin ta samu varci da kuma sauqin radadin. Ismail yace, nagode likita, saida safe. Ya girgiza kafadar Ismail, kar ka damu. Insha Allahu zata samu sauqi, ‘yar amanarka. Akwai likitan dare ma, wanda ina zaton ma yazo. Inda wata matsala sai ka fadawa nurses, zasuje su kira likitan. Ismail yace nagode sosai likita. Bayan fitar likitan ne Ismael ya sake dawowa ya tsaya akan mimi. Yana matu qar tausaya mata. Ji yake kamar ya kar6ar mata ciwon. Nunfashin ta dai-dai yake fita. Yasoma karanta addu’oi don nema mat a sauqi daga mahaliccinta. Bada jimawa ba Nurses guda biyu suka shigo suka sa mata ruwa tare da yi mata allurai. Suka ce, ka lura ko da cikin dare, kar ka bari ya goce. Yace musu, to suna fita ya zauna yana riqe da tattausan hannunta, wanda shine mai lafiyar, yana ta kallon fuskarta tare da tuno yadda abubuwan suke ta faruwa tamkar cikin mafarki. Alamun tayi varci yasa shi ajiye mata hannun a gurin da ba zata gotar ba. Sannan ya tashi ya koma kan dayan gadon ya kwanta yana fuskantar ta, har ynxun yana ci gaba da kallon abubuwan kamar almara ko kuma mafarki. Ina mabya farka ya ganshi a dakinsa na zauren su, ace ma shi baisan wata mimi ba. Amma da ya dan ciji yatsansa, sai ya tabbatar cewa ba mafarki yake yi ba, domin yaji zafi. Amma ya tattara komai ya barma Allah, da haka varci 6arawo yake ta fisgarsa sama-sama. Cikin dare ne yaji shigowar nurses din, sunzo ne su sake duba ta, yayi musu sannunsu da aiki, suka amsa suka tambaye shi ko kwai wata matsala? Yace musu babu komai suka ce to. Suna fita ya shiga bandaki yayo alwala yazo ya soma yin sallah, yana fada ma Allah matsalolinsa. Washe gari misalin qarfe bakwai na safe yana zaune kan sallaya yana tilawar qur’ani, sai aka turo qofar tare da yin sallama, Mahmud ne dauke da flask din shayi a hannunsa. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jiki, Ismail yace, da sauqi, gata nan bata ma farka ba, tun jiya data farka suka yi mata allura, Mahmud yace, ta farka babu wata matsala ko? Ismail yace, babu matsala, don ta gane ni, tana ta kuma kiran daddyn ta da kuma khalil dinta. Ban san yaya zanyi mata ba. Da nace mata yaron yana raye. Kasan ni na tsani inyi qarya, amma hakanan na fada mata sbd kar ta qara tada hankalinta, Mahmud yace, to yaya za’ayi dama ka fada mata gsky? Gara dai in ta samu sauqi, sai a fada mata. Ismail yace, tunani na kenan. Sannan kuma likita ya tambaye ni wai anan za’ayi mata dori, ko kuma a gida,wai inyi shawara, shine nace bari dai kazo inji yadda za muyi. Mahmud yace gara dai ayi mata anan asibitin, kasan dalili? Ismail yace a’a, Mahmud yace, kasan masu kudinnan aje ayi mata na gida, Allah ya kyauta ba’a fata, a samu matsala suce an barta a gd babu kula. Ismail yace hakane, duk nayi wannan tunanin. Sannan ga matsalar gurin zama. Ina zan kaita in an dora ta? Ni mai daki daya a zaure, Mahmud yace, hakane koma dai yaya ne, mu roqi Allah yasa ayi a sa’a. Baki suka hada gurin cewa Ameen. Ismail ya kalli flask din yace, harda ruwan zafi kazo min? yace eh, inna ce tace in taho maka dashi, ynxun ma zanje in siyo maka bread, sbd lokacin dana fito duk masu shagunan basu fito ba. Ismail yace, ka bari sai kamar qarfe takwas, don ynxun zaiyi wuya ka same su. Mahmud yace, to shikenan dama kai nake tunani, qila ma jiya ba kaci komai ba. Ismail yace saida yaya Amina suka zo, sannan da suka zo da abinci nace nafi son, ruwan zafi, shine mijinta ya kawo min bayan sun koma. Mahmud zai sake magana kenan, sai yaga kamar mimi tana motsi. Da sauri yace Ismail kamar tana motsi. Cikin azama suka isa gaban gadon, Ismail yace mimi kin tashi? Ta lumshe idanunta, sannan ta sake budesu ta kallesu. Alamu sun nuna yau jikin da sauqi, Numfashinta ya daidaita. Hawaye suka soma zuba daga idanunta, Mahmud yace sannu ya jiki? Bata amsa ba, sai dai hawayen ne ka bin gefen kumatunta. Ismail ya dora hannunsa akan nata, cikin damuwa yace sannu kinji? Zaki sha ruwa? Taja wani numfashi, cikin muryar marasa lfy tace, ni daddy na zaka kai ni, ban son wannan asibitin. Mahmud ya daga ma Ismail kai alamun yace mata eh, zai kai ta, Ismail yace eh zan kai ki, amma sai kin samu sauqi, sbd kinsan ba za’a iya tafiya dake a haka ba ko? Ta lumshe ido, ina.. Ina hajiya ta? Da momy na? Yace duk zasu zo. Sunce inyi miki sannu. Tace malam kace suzo su tafi damu, ni da khalil, kirasu ynxun malam. Yace zan kira su, zaki sha ruwa? Ta sake juyar da kai, dai dai lokacin ne wayar Ismail ta soma ringing. Ya ciro ta daga aljihunsa, sannan ya kalli fuskar wayar, hajiya sauda ce, don haka sai ya fita waje, ya daga tare da sallama, suka gaisa. Tace masa, Ismail yaya mai jikin? Yace da sauqi, tace ta farka ne? Yace eh ta farka kuma Alhmdlh jikin da sauqi sosai. Tace to mungode ma Allah, kar ka manta ka turomin account number dinka. Yace insha Allahu. Tace nagode sosai. Bayan ya kashe wayar, zai juya kenan sai ya hango likitan ya nufo dakinsu don haka sai ya jira shi, likitan ya qaraso. Sun gaisa ta hanyar yin musabaha, sannan ya tambayi yadda ta kwana da jikin? Ismail yace jikin da sauqi yau, don ta daina wannan nishin. Likitan yayo ciki, Ismail ya biyo shi yana masa qorafin har ynxun bata ci wani abu ba. Daidai sunje kanta ne, likitan yake bashi amsa da cewa, kar ka damu da wannan, sbd ruwan da muka sa mata jiya da daddare yana dauke da sinadaran abinci, so, ko bata ci ba, ba zai zama matsala ba. Ynxun muje a debi jininka a gwada mu gani, in yayi sai muyi qoqarin saka mata a yau. In mun tabbatar da samun sauqin ta, sai mu saka ranar da za’a yi mata aiki, ina nufin dori. Ismail yace, na zaci yau za’ayi mata sbd kar qafar tayi tsami. Likitan yayi murmushi, kar ka damu zata samu sauqi, ba tare da wata matsala ba. Haka kuma babu abinda zai faru ko da takai sati daya ba’a dora ta ba. Ismail yace, shikenan Allah ya bata lfy. Ameen, inji likitan, tare da dafa kafadar Ismail ya jinjina. Sannan ya kalli mimi, sannu khadija. Ta dago, ta kalli likitan, ya kama hannunta mai lafiyar, inane yake yi miki ciwo ynxun? Tace duk jikina, amma qafafu na sunfi yimin ciwo da hannuna. Likitan yace, bayan nan fa? Ta soma kuka, nidai gidanmu nake son a kaini, can zanje gurin daddy na. Likitan yace, za’a kai ki da zaran kin samu sauqi, kinji ko? Tace ina khalil? Likitan yace, yana nan yana samun sauqi kinji? Cikin sigar lallashi yayi maganar. Kar ki damu kisha tea kinji ko? Tace ni banajin yunwa. Ina son in wanke baki na. Likitan yace, karki damu k8nji ko? Ya kalli Ismail, ka bini muje ko? Ismail ya dubi Mahmud, ina zuwa ynxun. Mahmud ya koma bakin daya gadon ya zauna tare da cewa to. Ismail yabi bayan likitan, suna fitowa, sai gasu yaya Amina, yace su shiga bari ya dawo Yanxun. Likita ne ya nuna masa har sashen masu dibar jinin, sannan ya kalleshi, in sun gama, ka sameni a office dina, kar ka damu ko kaga mutane ga shigo kawai, Ismail yace to nagode. Bayan an diba ne, sai suka ce ya tafi zasu kaima likitan sakamakon in sun fitar. Yace to, nan ya nufi office din likitan, kamar yadda likitan ya fada masa haka yayi, ya shiga duk da wadanda ya samu suna ganin likitan. Ya samu yana ganin wani a ciki, har zai fita, sai likitan yace, dan jira mu kadan, ynxun zan sallameshi, yana fita, ya nuna ma Ismail kujera, zauna nan. Ya dora hannuwansa saman babban teburin dake gabansa, sannan ya kalli Ismail wace, shawara kuka yanke? Game da daurin dorin matarka. Ko baku riga kun yanke shawara ba? Ismail yace mun yanke, kawai ayi mata anan. Likitan yace, shikenan za’a kawo maka takardar biyan kudi, sai kaje ka biya, sannan su baka takardar shedar biyan kudi, Ismail yace to, na gode. Likita yace, amma shi wanda ya mutu yaya suke da ita? Ismail yace, shi take so, likitan ya aje biron dake hannunsa, ya tattara hankalinsa a gurin Ismail, kamar yaya shi take so, gaka mijinta? Ismail saida ya danyi shiru, don ya tsani bada labarin, sannan yaba likitan labarin aurensu a taqaice. Likitan ya danyi jim, sannan yace, kayi haquri, ka kuma riqeta, wata rana zakaji dadin haqurinka. Ya miqe tare da cewa na gode likita, kar ka damu zan taimaka iyakar iyawa ta, inji likitan, Ismail ya sake cewa nagode, yace ba komai kaje, in sun kawo sakamakon kazo. Lokacin daya dawo, ya samu mimi tana ta kuka, yaya Amina tana ta bata haquri, ya isa gurinsu, yaje cikin damuwa, daidai kunnenta ya rusuna yana cewa, yi haquri mimi, ki fadamin me kk so? Tace ni gurin daddy zanje, ka bani wayata in kira daddy na. Yasa dan yatsansa yana share mata Hawaye, wayarki ta 6ace a gurin da kukayi hadari, amma ki bari zan siya miki wata. In kinji sauqi, zan kaiki gurin daddyn ki. Sabon kuka ta saka, tana fizge-fizge, ya miqe ya koma kusa da Mahmud yace, nifa gsky zan kira mata shi suyi magana, Mahmud yace ka kira shi kawai don kada ta zarge ka. A handsfree ya saka wayarsa, sannan ya kira layin daddyn nata, tayi ta katsewa ba’a daga ba. Ya sake kira, gab da zata katse aka daga, tare da cewa hello! Ta gane muryar daddy, don haka cikin kuka tace, daddy kazo ka tafi dani. Zan mutu anan. Daddyn cikin zafin rai, a fusace yace kar ki sake kiran layina. Ni ba mahaifinki bane, baki daga cikin ‘ya’ya na, da farko nayi niyyar in huce sbd kinyi min biyayya a karo na biyu, kinbi wanda na baki, ashe ke kina kan bakanki, to inaso ki sani, ko mahaifiyarki na samu labarin inda kk, sai na kada ta ta barmin gidana, bare wata nafisa da kk kira tazo, kisa a ranki bakida kowa sai wannan mijin naki. In kinga dama ki zauna. In kuma sake tafiyar za kiyi, duk ba damuwa ta bace. Nidai gargadina kar ki sake kirana, ko ke ko mijinki! Yakai qarshen zancen tare da kashe wayar sa. Ihu mimi ta saka, tare da fizge ruwan da aka sa mata a hannunta mai lafiyar. Saboda tsananin kukan da takeyi, ya hana Ismail lallashinta, don bai san ta ina zai fara ba. Tayi kuka har muryarta ta dushe, babban takaicin ta, ba zata iya tashi ba, don da tuni ta fita titi, mota ta taka ta ta huta. Ganin abin bana qarewa bane, yasa Ismail kiran likitan. Yayi fada sosai, ganin halin da mimin ke ciki, yace bai dace mara lfy irin haka a sata cikin damuwa ba. Ya kalleta, khadija kiyi haquri dadyn ki zai huce insha Allahu, kinji ko? Tace ya daina so na, tunda ya iya hadani aure da talaka, nasan ya daina so na, kuma da gske yake yi, abinda yz fadamin, ya cire ni daga cikin ‘ya’yan sa. Likita ka taimake ni, kayi min allurar guba in mutu, likita yaja kujera ya zauna, bai kamata ki nemi mutuwa ba bayan Allah ya raya ki, kun yi mugun hadari fa, da Allah ya ga dama, sai ya dauki ranki a lokacin. Ki natsu koda daddyn ki ya qi ki, ba ga mijinki ba? Tace bana sonshi! Malami ne fa? Ismail ya lumshe ido cikin takaici, kar ki damu, ki bari ki qara samun sauqi, muga yadda za’ayi, kinji? Ta dago ido ta dubeshi, zaka barni mu tafi tare da khalil? Ynxun bani da kowa sai shi, yace zaku tafi, da qyar suka lallashe ta tayi shiru Kwadayi madudin wahala na’im da mom Nafisa bakuga komaibama ai, Ismail yace, ga ruwan da ta cire nan a maida mata. Likitan yace, babu damuwa, tunda ta dawo hayyacinta, zata iya cin komai ba sai an maida ba. Sannan jininka za’a iya ba kowa, don haka za’a zo a diba ynxu. Ismail yace, zanje can ne? A’a ba sai kaje can ba, inji likitan. Anan ma za’a zo a diba. Da qyar Mahmud ya matsa ma Ismael yasha ruwan tea. Shi kansa duk ya rame sbd tashin hankali. Tara da kusan rabi, Sai ga wata nurse ta shigo da wasu mata guda biyu, lokacin yaya Amina tana cewa bari ta tafi, shi kuma Ismail yana cewa Mahmud, ya kamata kaima ka tafi. Shi kuma yana cewa, bari dai in an dibi jininka din sai na wuce. Sallamar wasu matan ne, yasa su yin shiru daga zancen da suke yi don jin ko su waye. Dai dai lokacin mimi ta dangana daga kukan da takeyi har ma ta yanke hukuncin yadda zatayi. Nata ganin, abin da zai fissheta, in sun samu sauqi ita da khalil, zata bishi gidansut tunda shi hajiyarsa tana sonsu tare, sai ta zauna a gidansu, in ya kammala karatu sai ayi musu aure, Amma ta daukar ma kanta alqawarin yadda daddy yace ya barta, ita ma har abada ba zata sake nemansu ba. Dama hajiya bata sonta, shikenan zata yi Rayuwar ta da khalil, ta amince bata da kowa sai shi din. Sallamar matan ne ta katse mata tunani. Ta daga ido ta kalle su. Ko cikin mata dubu ba zata kasa sheda fuskar mahaifiyar khalil ba. Ba wai don kamar da sukayi dashi ba, domin tun kafin suje gidansu a kwanan baya ita da khalil din, ta mallaki hotunan mahaifiyar tasa masu dinbin yawan gske a wayar ta wadanda khalil din ke turo mata. A ranta tace shikenan ma tazo tafiya damu. Nasan khalil ya riga ya fada mata komai. Sai taji wani farin ciki ya darsu acikin zuciyar ta. Kukan da mahaifiyar khalil din ta fashe dashi ne ya katse tunaninta, tare da tattaro dukkan hankalinta zuwa gurin ta. Ji tayi tana fadin. Alahu Akhbar! Yarinyar nan babu rabon kuyi aure da khalil, ajalinsa ya jawo miki wahala. Ni dama nayi tunanin wannan zazzafar s soyayyar da khalil ya kamu da ita, da qyar in zai rayu, yaron nan bai ta6a min sata ba tunda ya taso, sai dalilin wannan soyayya. In da mahaifinsa ya bada hadin kai, kila da ynxun khalil yana raye. Allah ya baki lfy. Mimi ta zaro idanu tana kallonsu. Qwaqwalwarta ta kasa saita zantukansu. Wai suna nufin khalil ya mutu ne? Ismail kuwa ya rikice, yana ta yi wa nurse din alama da yatsansa a baki wai suyi shiru, amma sam basu lura ba. Saima fadi da nurse din take yi, wai iyayen wanda ya mutu dinne suka zo daukar gawarsa, shine suka ce a rakosu su duba ta. Daya matar kuwa wadda suka zo tare, fadi takeyi, kiyi haquri aunty Amina, Addu’a kawai zaki yi masa, kinyi dauriya a gida, baki masa kuka ba, sai anan? Cikin kuka mai tsanani mahaifiyar take cewa, ban gaskata mutuwarsa ba saida nazo naga gawar khalil. Ihun da mimi keyi ne ya katse mahaifiyar khalil. Wani yunquri da mimin tayi shine ya saka su nufar gadonta. Sai dai Ismail ya rigasu isa. Duk da haka kafin yakai ta riga ta kai qasa a sume. Ya dauke ta yana fadin, inata alamta muku cewa kuyi shiru. Sbd batasan komai game da mutuwarsa ba, amma sam baku kula ba, gashi kunsa itama za’a rasa ta. Ya dora ta akan gadon yana cewa, ku taimaka ku kiramin likita! Mahaifiyar khalil fadi take, Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Ai ban san bata sani ba, nurse kuwa tuni tayi qasa da gudu don kiran likita. Qarfe sha daya da mintina momy Nafisa ta shiga gidan ‘yarta Na’ima. Aljannar duniya. Ha ta furta lokacin data iso cikin falon farko, Ta kalli ‘yar tata, wadda tazo ta bude mata qofa. Na’ima kina cikin irin wannan gdn kk daga hankalinki? Na’ima ta turo baki, momy ni wannan gdn yayi mintg girma, abin haushi kuma ni hadai ke yini a cikin sa. Momy tace, a’a ina masu aikin da akace an kawo miki? Tace, suna gefensu. To ai su ba abokan hirana bane momy. Suje su raina ni? Momy tace, ba nufi na kenan ba, ba wai kuyi hira ba, ina nufin a qalla kina jin motsin wasu a cikin gdn. Na’ima ta turo baki, to momy shifa bashi da lokaci na. Momy tace, matsalarki dai mijinki ko? Na’ima tace eh. Momy nafisa tace, kije kice masa inason ganinsa, ko har ya fita? Na’ima tace, yananan banji fitar sa ba. Ta miqe ta nufi sama cikin zumudi. Tana bude qofar ta jiyo shi yana waya, yana zaune a kujerar computer. Daidai abinda kunnenta ya jiyo yana cewa, “tsaya mana kiji Jennifer. Kar kisa ma kanki damuwa, na fada miki ba wadda nakeso din na aura ba, ko da ita dince ma kinsan cewa ke ta musamman ce, kina tsammanin rayuwa ta zata tafi sak ne in babu ke? Cikin turanci yake magana. Yayi jim, alamun yana sauraron abinda take fada. Sannan yayi ‘yar dariya, tare da cewa, na san dai zaki iya bada sheda ta kan fadar gsky komai dacinta. Ya sake yin jim, sannan yace, to zan tabbatar miki da cewa kinfi wadda aka kawomin a matsayin mata. Zan tabbatar miki yadda ke da kanki zaki gamsu da batun, ya sake saurawa. Sannan yace, fadamin me zan miki ki yarda tunda naga kina tantama, kamar kin manta ni waye. Dariya taji ya saki, tare da fadin, ai wannan mai sauqi ne, in dai kwana da nine, ina me yi miki albishir cewa, ni da ke yau a gida na zamu kwana. In nayi miki haka, zaki gamsu cewa ni dake mutu-ka-raba? Maganar ta maqale, bai qarasa ba, sakamakon jin muryar Na’ima da yayi cikin kuka tana cewa, dama mata kk nema? Ya saki murmushi, sannan ya maida wayarsa kunnensa. Baby zan kira ki zuwa Anjima. Ya kashe wayarsa, sannan ya juyo da kujerarsa gaba daya, don irin mai jujjuyawarnan ce, cikin fara’a yace, baki sani ba dama? Ta tsaya tana Numfashi, tare da mamaki, gami da zaro idanu. Yayi murmushi mai sauti, kina nufin dama bakuyi bincike ba? Ya girgiza kai ayya. Ni qasurgumin manemin mata ne. Sannan ina shan wiwi da giya kadan, akwai wata matsala ne? Ta rasa me zata ce, sai kuka. Cikin kuka take cewa, ba zan iya zama dakai ba. Mutumin da baya iya 6oye laifinsa. Yace, oho, dama kinzo kin la6e min ne? Kada ki zauna dani din mana, dama ni na kawoki? Ko na riqe ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e baki, wacece kuma momy? Tace, don wulaqanci, mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren agogon bangon falon, me kuma tazo yi da wannan safiyar? Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani, aiki nakeyi, in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo wani lokacin, in abinda tazo dashi ya dame ta. Na’ima tace, wadda ta haifeni ce fa? Yayi mata wani kallon banza, cike da izgili yace, don ta haifeki, ni ta haifa? Kuka ta fasa, sannan ta juya ta tafi ranta a 6ace, hankalinta kuma a tashe. Cikin kuka ta sami momy nafisa zaune a falo, tana zaune tana jiranta. Momy kinji abinda na sameshi yanayi? “me? ” inji momy. Na’ima ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don nayi masa magana, kai tsaye yace min waishi yana neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi. Momy nafisa ta zaro idanu, cikin faduwar gaba tace, da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake. Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole zaiji shakka. Ki barshi bari yazo. Na’ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy ta yi shiru tana ta kallon Na’ima cikin matuqar mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara mutunci kawai. Na’ima ta kalleta. Da kin barshi kawai momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara in taka masa birki. Ta tasa Na’ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai, yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace, bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida momy Nafisa ta zauna, sannan tace “lfy” shine wato Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to zaka iya bani ‘yan mintuna muyi magana? Ya hada tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to zuwa nayi inji laifin da Na’ima tayi maka da har zaka soma wulaqanta ta daga kawo ta. Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin. Ya kalli Na’ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta? Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason matsala. Tayi harkarta inyi tawa. Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye yana kallon momy tare da cewa, “au dama baku sani ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso. Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa, damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk nufi? Ya kalleta, ban gane ba. Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna Na’ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, inji masu magana. A gabana kk fadin bakason ‘yata? Yayi guntun murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane, saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba’a masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na farar mace nake so. Kinsan kowa da ra’ayinsa. Qila da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni, kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son takura. Ta kalli Na’ima, tashi muje. Na’ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai momy, ta dube shi a qufule. Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu, sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama irinki ce, tafi son ‘ya’yanta akan na kowa. Ni dai kunji ra’ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin Na’ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na’ima tana ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa, sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace yakeso ba? Na’ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da zaki ja ra’ayinsa. Na’ima ta dan ta6e baki tallafe kanta sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba, ma’ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata bilicin din ba. Momy ta dafa Na’ima, cikin sigar lallashi, karki damu Na’ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana, domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke saka fari. Na’ima tace, to kafin ta wuce saida ta tabbatar hankalin ‘yar tata ya kwanta, ta nuna mata cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana sai abin da tace masa zaiyi. Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na’ima cikin damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke. Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za’ayi da wannan dankalin? ‘Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi. Na’ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan yazo yai magana. Na’ima tace, ni bance sai kinyi min lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na’ima kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar, Na’ima ta kasa sukuni. Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa. Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi suke mata a wuya. Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta, don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa. Tana fadin, na yarda honey. Cikin matsanancin kuka, Na’ima ta kira layin momy, wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy. Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na’ima ba nace zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa?? Momy ta tambayi Na’ima. Ta rantse, sannan ta ci gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na’ima ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar auren Abbas. Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki, Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai? Zainabu ta sunkuyar da kai. Ni wallahi da baku dawo ba, za’a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa kawai kuka yi. Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura miki goruba, mu dai in burinmu ya cika ina ruwan mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din, basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta ciro wata gora mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna kisha shi maza-maza. Zainabu ta soma kuka tana shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye Anjima sai ki shaki shanye sauran. Karki sake baki shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can muna qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki shanye. Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata zage-zage, wai shi za’a kawo wa raini da rashin mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma kudinsa. Duka-Duka yaushe ne akayi auren ma? Ko wata daya ba’a yi ba za’a ce har tanada wani ciki? Uwar gidan tace, haba Alhaji yaya kake irin wannan maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke kallonka. In jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba. Zanje in fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da kuma kudin sun, tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan al’amarin. Cikin tsawa yace, in zakije gida, kizo muje! In ba zakije ba, in tafi. Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta wata takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga wasu nurses, anan ne zaku biya kudin gadon, sannan zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai shigo ya rubuta magungunan daya kamata tasha. Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da takarda bayan tafiyar nurse. Gashi ba tada ko sisi tunda fitar bana shiri bane. Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada, gidan su Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira direbansa, dan korensa. Bayan ya daga, sannan yace, iroro kana ina ne ynxun? Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da amarya ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar gidan, ya hangi iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya nufo Alhaji yana cewa, sannu da qarasowa Alhaji. Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke jira? Iroro yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a, sannan ya zuba sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, “lafiya dai kazo nan? Alhaji yace, zuwa nayi in sanar da iyayen Yarinyar nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti. Kaji ma wai har tanada ciki, Duka-Duka yaushe akayi bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori kudinka ba ai da sakinta kayi kawai, ka kawo wata. To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun dirka mata maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata. Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun daga ynxun. Alhaji yace, shiyasa nake matuqar sonka iroro. Sau da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da ace ta kwana biyu, zuwan nan da nayi, yadda take asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma su gama jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba, kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace 6era. Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, “kai kanaso ne sai zuciyar ta ta buga tukunna? Me zaisa ku fada mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason ganin kowa anan sam. Bai saurari kowa ba, bare yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi waje,, Ismail yana cewa, kun gani ko? Nasan dama laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar khalil take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane, Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai, shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi, Allah ya bata lfy. Ameen ya rabbi, ina fata ‘yan sandan sun baku jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda tare da mahaifinsa muka zo, qila sun bashi, Mahmud yace, ‘yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace bari zanyi musu magana in munje. Mahmoud yabi su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam tamkar zuciyar sa ta buga don damuwa. Ya qosa likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan rabin sa’a tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa bai zauna ba, kuma bai musu izinin su zauna ba. Sai ma fada da ya hau yi musu, tare da cewa, kasan meye? Kaje ka samo wacce zatayi jinyar ta, domin kaikam baza ka iya ba. Ismail yace, doctor ba laifina bane, nan ya sanar dashi komai, likitan yace, shikenan, daga yau zuwa gobe bamason ganin koea gurin ta. Ina nufin ‘yan dubiya. Likitan ya sassauta murya, ka nutsu sosai, ka lallasheta, sbd kasan dole ne ta zamo ta farka cikin damuwa da tashin hankali. “Ismail yace, Insha Allah. Na gode likita. Ynxun ta farfado ne? Mun kuma yi mata allurar varci, bamu fito ba saida varcin ya dauke ta. Don haka saiku kula sosai. Tashi kuje, za’a zo a dabi jinin naka ynxun. Ismail yace, to nagode likita. Suna fitowa suka dawo gurin su Mahmud, yace vari ya wuce, sai zuwa anjima. Ismail yace, Allah ya kaimu. Bayan tafiyar su, Ismail, a hankali ya tura dakin ya shiga. Ya jima tsaye a kanta, yana kallon ta tana varci, ya juya ya koma kan kujera, zamansa keda wuya, sai aka turo qofar dakin. Ya dago ya kalli mai shigowar, Namiji ne da riga fara, irin wadda likita ke sawa, sai wasu kayan aiki dake hannunsa. Yace. Kaine Ismail bin Abdurrahaman? Ismael yace, Na’am, Mutumin yace, nazo ne in debi jininka. Ismail yace, to bismillah. Bayan an dauki jininsa ne, sai wata nurse ta kawo masa wani dan tea a kofi da wasu ‘yan qwayoyin magani, yasha ya dan kishingida, kafin lokacin sallah. Bayan la’sar, sai ga babban wan su Ismail yazo, lokacin Ismail yana dawowa daga masallaci, suka shiga ya duba ta. Har lokacin bata farka ba, bayan sun fito yace masa, ance zata gudu ne tayi hadari. Ismail Yace, eh, yayan yace, in bata sonka dolene? In ta warke ka maida musu ‘yarsu, Ismail bayason doguwar magana, don haka yace wa, to, sai ya sake cewa, ka fadama iyayen ta? Yace eh, da haka suka kai qofar asibitin, inda yayan ya hau mashin, shi kuma ya koma ciki. Duk fargaban Ismail, in ta farka baisan dame zata tashi ba, bai san wane qalubale zai fuskanta ba. Kuma shi gaba daya ma zaman asibitin ya gundure shi, sam ya qosa ya barshi. kiran hajiya sauda yake shigowa, sai lokacin ya tuna da zancen account number da tace ya tura mata. Suka gaisa, bayan ya daga, tace masa. Baka turo ba, gashi har yamma tayi. Yace, kiyi haquri hajiya, kaina ne yadau zafi. Ban tuna ba, kuma banida account nawa na kaina, sai namu na makaranta. Insha Allahu dana sanar da malam Aminu zan turo. Tace, zancen dorin fa? Yace, sai gobe. Ynxun dai jini za’a qara mata. Tace, an samu jinin ne? Yace, eh, nawa ne za’a sa mata. Tace, Allah ya bata lfy, sai naga number, yace, insha Allahu. Ismael ya shanyo kwanar da zata kaishi matakalar da zai koma dakinsu, sai kurum ya hango innarsu Zainabu, ita da aminiyarta hannunta riqe da wata takarda. Ya jira har saida suka iso gurinsa, sai dai da alamu innar bata lura dashi ba. Yaji tana cewa, wannan maganin shi kadai dubu daya da dari bakwai, su kuma sauran kudinsu ya zama nawa? Qawar tace dama nice ke, tunda ta samu dan qwarin jiki daukarta zanyi mu gudu, mu bar asibitin. Baiji mai innar tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya hau sama yana tunanin, to wa suka kawo asibiti? Sai dai babu mai bashi amsa. Ya samu har an sawa mimi jinin, har lokacin tana varci. Likitan ya tambayeshi inda yaje? Yace ya raka wansa ne. Ya tambayi likitan ko babu matsala a irin wannan varcin da takeyi? Likitan yace, babu komai karka damu. Fitar likitan da nurse dinnesai ya kira malam Aminu suka gaisa. Malam ya tambayi mai jikin, Ismail yace, da sauqi, sannan yace, dama mahaifiyar tace take son in tura mata account number na, nace mata banida shi, amma zan turo mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai, Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi sallama. A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa hajiya Account number din, bada jimawa ba ta kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi sallar magriba, yanason sai yayi isha’i zai dawo don haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar isha’i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci. Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har zuwa shigowar wannan matsalar. Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace, nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take? Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa kacemin Mahmud? Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba, sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi. Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita? Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba. Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu’a, ki roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan. Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi. Ismail Yace, Mahmud yadda kasan in fasa kuka haka nakeji. Yarinya sai kace wata jaririya, bata jin lallashi. Nifa in ta qure ni, sai in tafi in barta. Domin yadda bata sona, nima bafa yimin tayi ba. Gashi sai wani uban kuka takeyi, ban san yaya zanyi mata ba. Mahmud ya dafa shi, kar ka damu Abokina, kayi haquri. Ka jure, ka jajirce, in ka tafi to ka barta da wa? Kada ka manta matarka ce, wadda take a matsayin ba tada kowa, sai kai. Kayi iyakar yinka, ka hada da Addu’a. Zamu taya ka, wata rana sai labari, ka jure, karka sare, Ismail ya sauke ajiyar zuciya, tare da cewa, abin ne ya fara isata. Mahmud yadan girgiza kafadarsa kadan, alamun lallashi, kar ka damu akwai Allah. Ya sake sauke ajiyar zuciya. Allah ya taimake mu. Mahmud yace, Ameen, sannan ya miqe, bari in tafi, gidansu rabi’a zanje. Insha Allahu gobe zamu zo da ita. Ismail ya kalle shi da dan murmushi, kace ina gaishe ta. Sai kunzo. Ya miqe ya taka masa zuwa gurin matattakalar benen. Har ya juya zai tafi, Mahmud yace, Ismail kaga na manta ko? Ismail ya waiwayo. Yaya akayi? Mahmud yace, na zo ne in fada maka anyi admission fa. Haba? Inji Ismail. Mahmud yace, sosai ma kuwa. Ya kamata muje mu duba. Ismail yace, bari mu gani ko zuwa gobe ne, in wannan rigimammiyar ta dangana, sai yaya Amina ta zauna da ita muje, Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu goben.! Yadda mimi taga rana haka taga dare, kuka kawai take, babu qaqqautawa har mutyarta ta dishe. Tun Ismail yana lallashin ta, har ya gaji ya fice yayi alwala don yin shafa’i da wutirinsa tare da da addu’o’insa daya saba. Haka suka kwana har asuba tayi ya tafi sallah. Gurin qarfe taran safe aka shigo aka soma yi mata shirin yin aiki, wato dori. Goma saura aka shiga da ita. Lokacin ne malam Aminu ya kira Ismail yana sanar dashi cewa, yaga alert. Ya duba yaga an turo kudi naira dubu dari(100,000). Kuma yaga sunan saudatu bashir. Ismail yace, eh, saqon da mahaifiyar ta ta turo din ne. Ynxun haka ma an shiga da ita gurin dori. Zan fito Anjima sai in amshi katin ATM din in yana gurin Mahmud. Dama kudin hannuna sun qare kaf. Yace, kar ka damu, ko nine sai inje in ciro maka tunda akwai mashin a gurina. Allah dai ya bata lfy. Ameen, inji Ismail. Sannan sukayi sallama. Ismail ya saukar da ajiyar zuciya, har ya danji dadi sbd samun wannan kudin, domin hannunsa babu kudi. Tagumi yayi yana tuna irin kukan da mimi tayi ta rerawa jiya. Ko sallolinsa yayi ne dai kawai, amma gunjin kukanta yana daukar hankalinsa. Cikin wannan tunanin ya hango yaya Amina. Yaji dadin zuwanta sosai, domin zamansa shiru ya isheshi. Ya tare ta, tare da amsar kular hannunta da kuma ledar ruwan pure water, suka shiga cikin dakin, tace ina mara lafiyar? Yace, an shiga da ita dakin da za’a yi mata dori. Ya bude kular, dame kk zo? Tace, alala ce don nasan kanaso. Yayi dan murmushi, a fili yace, naka sai naka. Yaya Amina nagode da hidima. Tace, haba Ismail wa gareni banda kai? Kaima kuma bakada wadda ta fini. In ban maka ba in ma wa? Donma Allah yasa ni ba mai hali bace. Yayi dariya, hakane yaya. Allah ya qara mana zumunci. Tace Ameen, yaci alalar sosai, yana ci suna hira, har take bashi labarin cewa, su inna dasu fatu sunce sunanan zuwa anjima. Yace, Allah ya kawosu qila ma ke zasu samu yaya. Sbd jiya Mahmud yace min anyi admission, zamuje mu gani ko Allah zaisa mu samu. Don kinsan qasarmu sai Allah. Qiri-qiri zaka ci jamb amma saika rasa admission. Sai ace baka ci post UTME ba. Mu dai munce zamuje mu gani. Sannan mahaifiyar mimi ta turo kudi a account din makaranta zanje in cire. In kuma malam ya ciro shikenan, don yace koshi sai yaje ya ciro tunda da mashin a gunsa. Sha daya saura aka fito da mimi daga dakin da aka yi mata dori, tamkar wadda akayi wa operation. Nurses suka kwantar da ita akan gadonta tare da maqale qafafunta da gadon. Bayan sun gama kintsa ta ne likitan shima ya shigo, tare da ainihin doctor salis, likitan dayake kula da ita. Sunyi ma Ismael bayanin babu matsala, insha Allahu zata samu lfy, cikin zolaya doctor salis yace ma Ismael, “yar amanarka zata warware. ” Ismail yace, Allah yasa. Sannan suka rubuta magunguna suka ce ya siyo kafin ta farka. Yace musu zata iya cin abinci? Suka ce eh, zata ci komai in ta farka. Wannan varcin ma da takeyi anyi mata allura ne sbd ta wahala. Sai azahar Mahmud yazo, don haka nan yabar yaya Amina suka tafi. Sai dai iyakacinsu banki don bazai yiwu suje zariya yau ba, sai gobe, Daga nan yaje ya sai magungunan da likitan ya rubuta masa wadanda bai samu acikin asibiti ba. Sannan ya koma gida yayi wanka, ya shanza kayansa zuwa farar jallabiya qal da hula ‘yar fakistan. Ya fesa turaruka, sannan ya fito. Ya rufe qofar zai fita saiga su inna zasu shigo. Ya tsaya suka gaisa, sannan yace, daga unguwa kuke ne? Suka ce, daga asibiti muke. Ai mun samu Amina. Yace to mun gode, Allah ya saka. Sukace Ameen. Fatu tace, umm. Wannan abu yaban mamaki Inna. Me ya janyo wannan hadarin? Inna ta kalleshi, “ina zan san abin da ya janyo. Kai sama’ila yaya abin ya faru ne? Yace, tsautsayi ne kurum. Fatu tayi murmushi. Zancen dake yawo a gari haka ne kenan. Guduwa zatayi sbd bata sonshi. Ta kalleshi, kaima kayi wauta Ismail. Dubi wannan Yarinyar, kallo daya zaka san ta saba da hutu, amma ka cusa kanka. Da ido kawai Ismail yake binsu. Kuma bai shirya ce musu komai ba. Yasa kai ya fita. Tsaki Inna taja “Mtsss” sannan tace, aishi tsiyar sa kenan. Qarya ne kaji cikinsa. Shidai ya sani. Inji rashida, daya matar wan nasa. Matar musa ce kurum bata ce, komai ba don bata cika shiga shirginsu ba. Sai da ya fita titi, sannan ya kira Mahmud yake fada masa cewa, gashi zai koma asibiti. Mahmud yace, to sai sun shigo Anjima shi da rabi’a. Ya tare dan acha6a zuwa asibiti. Suna cikin tafiya ne yana kalle-kallen sa, idanun sa suka sauka akan wani super market. Yace ma dan acha6an don Allah dan dakata in duba nan. Dan acha6an yace, amma ba dadewa zakayi ba ko? Daidai lokacin da ya tsaya, A’a insha Allahu bazan jima ba, Ismail ya bashi amsa bayan ya sauka daga mashin din. Ya shiga tafkeken super market din tunaninsa kawai ya sayi abinda mimi zata iya ci ko sha. Da makilin ya soma cin karo, gasu nan kala kala, ko wanne da kudinsa manne a jiki. Sai ya dauki mai tsadar ciki, ya sai brush da sabulun dettol na wanka. Sannan ya koma gurin kayan sha. Ya rasa wanne irin drink take sha. A qarshe sai ya dauki maltina a nasa tunanin kowa yanasha. Ya sai katan din ruwan gora guda biyu, sai kayan tea na manyan gwangwani. Suga na kwali. Ya sai flask din ruwan zafi. Daya fito wajen gurin ne kuma ya isa gurin masu saida kayan marmari, ya sayi Apple, lemon zaqi, sai kankana da abarba. Dan acha6a yace, gsky malam za fa kaimin qarin kudi. Ismail yace, babu komai, Allah dai ya kaimu lfy. Da kaya niqi-niqi ya hau samansu, gabansa har faduwa yake yi daya tunkaro asibiti. Haka dai ya nufi dakinsu, tunaninsa a wane hali zai samu mimin aciki? Don yasan zaiyi wuya in bata farka ba. Ya tura qofar cikin sallama, k idanunsa suna kan gadon. Yaya Amina ta amsa Sallamar tana kishingide a dayan gadon. Yace sannu yaya na barki ko? Ta sauko tana tana fadin, banyi zatonka a wannan lokacin ba, ko har kunje zariyan? Ya nufi gadon mimi yana cewa, mun bari sai gobe, sbd yau yamma tayi. Bata farka bane? Yaya Amina ta iso gaba gadon. Tace, ta farka, ko ido bata bude ba, kuka kawai take yi. Don nima nishin kukan ta yasa nasan ta farka. Tsaki yaja cikin damuwa yace, nidai Allah ya sani wannan kukan yana damuna. Yasa yatsansa ya debe mata gashin kanta daya watso kusa da idonta, ya maida mata shi bayan kunnenta. Ya tsura ma fuskarta ido, wadda tayi jajur don kuka. Idanunta kuwa sun kumbura sunyi luhu-luhu. Ya dora tafin hannunsa akan goshinta. A fusace ta bude idanunta, qwayoyin idon sunyi jajur. Ta zuba masa harara, sannan ta girgiza kanta, alamun ya cire mata hannunsa daga goshinta. Yace bakisan in dafa miki goshi ne? To na cire. Amma ynxun ki tashi kici wani abu. Ya rusuna ya soma ciro abubuwan daya siyo daga cikin ledar. Yaya Amina tace, Yauwa yanada kyau ta wanke baki kuwa, ga makilin da brush. Amma ka manta baka siyo roba ‘yar mai fadi ba, da FO sbd fitsari, don kaga tana varcin nan duk ta fitsare kayan jikinta da na kwanciyr. Gashi Kaje gida amma baka dauko mata kayan sawa ba. Ismail yace, fitsari kuma? Ya dago ya kalli mimi, fitsarin lfy? Sabon kuka mimi ta saka. Domin farkawar da tayi taji ta sharkaf cikin fitsari ya tada mata hankali. Wai ita mimi ce haka? Mimin daddy mai shanawa. Sam bata son ta bude ido ta kalli asibitin bare malam Ismail, wanda ta tsana fiye da kowa. Ta tuna lokacin da tayi wani zazza6in mura, waje suka fita, can England aka duba lafiyarta. Tunda ta taso, duk bayan wata uku dad yake kaita a duba lafiyarta a qasar Misra. Amma yau gata a wani qazamin asibiti kwance cikin fitsari. Ina ma dai mutuwa tazo ta dauke ta. Da ma da sukayi hadarinnan itama ta mutu da yafi mata wannan Rayuwar. Ismail yace, ba zaki yi magana a saki ba mimi? Yaya Amina tace, haba Ismail, Kalli yadda take mana qafafu a sagale taya za’a sata tayi fitsari? Yace hakane. To ynxun sai dai ta dinga yi a kwance? Yaya Amina tace, dole a samu robar fitsari, amma mu nemi Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma ynxun ya kk ganin za’ayi gurin cire mata kayan? Ko inje in fara dauko mata wasu in dawo? Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida sbd abincin dare. Insha Allahu yanxun zan dawo. Duk akwatunanta ya chaje su tsaf, babu riga da zani, mafi yawa daga cikin kayanta ‘yan kanti ne, riga da wando, sai dogayen riguna. Na atamfan ma daga doguwar riga sai riga da siket. Tsaki yayi, cikin haushi ya bude qaramar Jakarta, wadda ta dauko zata gudu da ita. A ciki yaga Jakarta wadda ta zuba kudadenta data debo sbd guduwar su. Ya ciro jakar yaje ya daga can qasan katifarsa ya sata cikin tsohuwar malum-malum. Ya daga ledar tsakar daki, ta qasan katifar ya saka, sannan ya maida katifar. Yayi hakane sbd tsoron 6arayi, tunda shi ba wai yana kwana a gidan bane, kar a zo a bude dakin. Ya dawo ya bude akwatin da yaga kayanta na ciki. Aciki ya ciro siket da dan kanfenta, sai best. Baisan meyasa ya zuba ma rigar mamanta ido ba, qila kyau tayi masa, amma duk da haka bai dauka ba. Qamshin turarenta kayan sukeyi, sai ya dauki ‘yan shirt guda uku, tunda babu zannuwa. Yace zaibi ta bakin kasuwa ya sai turmin zani ya tsaga su gida uku. Ya dauki bargon rufarsa da zanin gado, sannan ya nufi kasuwa, daga can ya wuce asibitin. Yauma ya hangi innar su Zainabu acan baya gurin wanki. Yauma haka ya hau sama yana tambayar kansa wai wa take jinya? Ya samu yaya Amina da taimakon nurse din dake aiki a wannan lokacin suna cire mata kaya. Ido hudu sukayi da ita, lokacin daya shiga an cire mata riga. Cak ya tsaya, domin idanunsa sun kalli abinda bai ta6a gani a fili ba Runtse idanunsa da yayi, sunzo daidai da ihun data yi. Yaya Amina tace, “mun yi miki fami ko? ” Malam Ismail ku rufemin jikina. Tun farfadowarta, sai ynxun tayi magana. Ismail ya ajiye kayan hannunsa a gurin. Idanunsa a Runtse ya juya. Sannan ya bude idanun. Abin daya gani suna yi masa gizo. Ya fita kan benci, ya zauna tare da tura hular kansa baya. Sannan yasa hannunsa ya shafe fuskarsa. Wani yanayi ya samu kansa a ciki, wanda ba zai iya tantance shi ba. Wata zuciyar tace, ba fa haramun ka gani ba, duk ka rude haka, matar kace. A cikin dakin kuwa, yaya Amina ce ta zo ta dauki kayan da uwanta ya ajiye taje kan daya gadon ta zazzage su tana dubawa tare da cewa, shikenan tunda ya fita sai kiyi haquri. Nurse tace, wane haquri, ba kunce mijinta bane? Yayan tace ai bata ta re bane shiyasa. Nurse tace, to kuwa kina da aiki. Mimi dai sai kukanta takeyi, saboda baqin cikin qirjinta da malam Ismail ya gani, har suka gama kintsa ta bata daina kuka ba, sunce zasu sa mata robar fitsari, tace ita dai bata so, Nurse din ce taba yaya Amina Shawarar su sai mata pampers na manya. Shi sai dai kawai a cire a yar, ayi mata tsaki, yaya Amina tayi mata brush, taqi cin komai, sai ruwan data sha kusan rabin gora. Baiji fitowar nurse din ba, sai dai muryarta yaji tana cewa, kana zaune anan ne? Ya kalleta, kun gama? Tace eh, ya ce na gode. Tace ba komai, sai kaje kayi lallashi, don shagwa6ar matarnan taka tayi yawa. Hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da yin guntun murmushi. Ta wuce gurin aamansu shi kam ya kasa shiga dakin.\Yaya Amina ta fito, cikin jin nauyi ya kalleta. “tafiya zakiyi? “Tace, eh, kaga yamma tayi, ga girki. Ummi ba girki ta iyaba. Nasan dai zata share min gd tsaf, har ma ta hana su Saddam yimin wasa a cikin daki. In ba ayi sa’a ba sai yayi ta dukanta. Ismail yace, ai rigimar sako da sako na gurin saddam da Ummi, kamar masu ganin hanjin juna. Tayi dariya. Haka suke, amma in daya baiga daya ba, ayi ta damuna, mama ina take, ko ina yake? Ismail yace, haka suke fa. Cikin zaulaya yace to kisa abbansu saddam ya qaro aure mana. Kin ga kin huta, baki da tunanin yin wani girki. Tace oho, sakamakona kenan nayi maka jinyar mata? Cikin dariya yace, yaya laifi ne? Tace, ban sani ba, ni kaga tafiya ta, sai anjima. Yace yaya ki vari sai gobe mana. Tunda ma da kayan tea, sai in sha ruwan zafi. Tace shikenan sai goben. Yace, zaki zo da wuri ne, sbd inason zamuje zariyar nan. Tace, zanzo dai kamar qarfe goma. Yace, Allah ya kaimu. Har gurin matattakalar ya rakata sannan ya dawo. Tsaye yayi a bakin qofa yana tunanin yadda zai shiga dakin. Daga bisani yayi ta maza, ya tura qofar tare da yin sallama. Tana zaune akan gadon, an cire mata qafafun daga sagalewar da akayi musu. Sannan an dago gadonta, gurin kwanciyr, ta yadda zata iya kishingida. Ya kasa kallon fuskarta. Yace, meyasa bakici komai ba? Ya isa gurin fridge ya bude, ya ciro gwangwanin maltina. Kisha maltina mana? Tsakin da ta ja shine yasa shi kallon fuskarta. Harara take ta zabga masa da jajayen idanunta. Ya sauke idanunsa, yasan kan abin da ya kalla dazu ne. Sannan ya sake kallon fuskarta. “kiyi haquri, dazun bansan ana shiryaki bane. Kuma ni banga komai ba ma. Bata dai tanka shi ba. Yace, kisha maltina ko kadan ne kinji? Tace, ni bana sha. Yace to fadamin kk so kici? Ta soma kuka. Yace, kinga matsalarki. An ce miki kuka yana maganin matsala ne? Wannan kukan sai dai ya qara miki ciwon. Tace, ni da zan mutu sai nafi murna. Rayuwata ba tada amfani. Yace sbd me? Tace, khalil ya mutu. Shine kawai ya ragemin a duniya. Ismail yayi murmushin takaici. Ko zaki bishi ne? Ta Kalli Ismael a fusace, ai da ace inada izinin tashi, to da tuni na fada ta wannan windon. Ismail yace, in kuma Allah baiga dama ba, kk karye, kuma yaqi daukan ranki, kizo kiyi ta jinya ba. Wai shin ma in tambayeki, da kk ta burin mutuwa, me kk tanada na ibada ko na alheri, wanda zaki kare kanki, ko kuma ince wanda zaki amsa tambayoyi a gaban Allah? Mimi ta sunkuyar da kai. Yace, inaso kisan wani abu, fushin iyaye ba qaramin bala’i bane. Dakin mutu a hadarinnan, kin tafi da fushin iyaye a gudun da kk yi, kinsan illar dake cikin guduwar ‘ya mace kuwa? Koda yake kece zaki bada labari tunda gaki a gadon asibiti. Sannan gudunki na farko ma nasan kin hadu da wani qalubalen, sai dai in ba zaki fada ba. Ta daga masa hannunta mai lafiyar, ni bance maka kaimin wa’azi ba. Da zama da kai a matsayin miji, gara min mutuwa. Yace sbd me? Tace ni ban son ka, na tsane ka. Ismail baya varin bashin magana. Don haka yace, ashe duk daya muke. Nima mimi bana sonki. Sam bakya cikin tsarin macen da nake so. A ra’ayina inason mace mai kyau, mai son addini, kuma maijin maganar mahaifanta. Kalamansa sunyi wa mimi zafi. Har ta kasa cewa komai, sai kai data sunkuyar ta soma kuka. yasa hannu ya daga fuskarta. Karki damu in kin samu sauqi, zamu san yaya za’ayi ,ta goce kanta da qarfi, kar hannunka ya sake ta6a ni. Yace, nifa damuwa ta kici wani abu, tace bazan ci ba, ni ka barni, ya koma bakin dayan gadon ya zauna. Ya soma shan maltina tare da cewa. Na barki. Har bayan isha’i tana kukan maganganun da Ismail ya danqara mata, lokacin kuma likita yazo. Bayan sun gaisa, ya tambayi jikin nata. Ismail yace, jikin da sauqi, amma taqi taci komai. Likitan ya kalleta, khadija! Ta dago ta dubeshi. Yace me zakici? Cikin wata murya mai ban tausayi tace, ba komai. Ismail ya ta6e baki, barta likita, cikinta ne zai fada mata. Sai kuma maganar pampers, dazun wata nurse ta ba yayata Shawarar mu sa mata pampers sbd fitsari, tunda taqi a sa mata roba. Likitan ya kalleta, ki bari mana a sa miki robar fitsari? Tace doctor bana so. Ta sunkuyar da kai tana tuna zuwansu katsina, ita da hajiya. Ta matsa wai sai an kai ziyara asibiti da gdn marayu. Daddy baiso zuwa ba yace zai bada abinda za’a kai, amma hajiya ta cije tace dashi za’aje. Aka tafi harda ita, a wani asibiti ne taga marasa lfy an daura musu ledar fitsari. Ta tambaya menene wannan? Aka ce mata ledar fitsari ce, saida tayi rashin lfy sanadin ganin marasa lafiyan. Sannan ace za’a sa mata. Shikenan ka sai mata pampers din, amma amma dai zaku sha kudi, in kuma zaka dinga sata a toilet din da kanka, da sai yafi muku. Da sauri mimi ta daga kai, Allah ya tsareni, ko hannuna karka sake ta6a min. Ba mijinki bane? Ko pampers din waye zaisa miki in ba shi ba? Duk wahalar da yake miki, yana kashe kudi akanki shine zaki dinga yi masa haka? Mimi tasoma kuka,”Ni bana son yasake tabani,na tsaneshi”. Kuma ai kudina ya dauka yakemin magani.Ai bashida kudin dazai kashemin. “Likita kar ka damu da ita,nima inayi mata ne don Allah,da Lima tausayin halin da take ciki,amma rashin mutunci halintane ko tayi min bazae dameni back.Ita ikirarinta bata sona,nima kuma bnga abinso a gurinta ba”. Likitan yayi murmushi ,don ya fahimci Isma’il yana maganar ne don son cusa haushi ga marar lafiyar. Yace “khadija wae bakya son shi?” Tace “eh”. Saboda me? Tanuna isma’il da yatsanta,”saboda abubuwa da yawa. Ina zargin sa da shiga cikin rayuwata. Kuma ya taemaka gurin shigata wannan halin. Isma’il yazaro ido yana kallonta,a zuciarsa yace”sharri zatayi min?” Likitan yaja kujera, yazauna tare da tattara hankalinsa gareta. Sanar dani hujjoinki,kila inada taemakon dazanyi miki. Tasoma kula “Ranar wata asabar nasoma jin lavarinsa a wurin kannaina. Sunaji dashi a matsayin malaminsu. Ranar farko Dana dora idanuana a Kansa,ranar ya raena min wayau,tare dafada min maganganu na wulaqanci. Abinda baa taba yi min ba a rayuwa ta. Sannan shi ne mutum na farko da banyi nasarar rama abinda yaemin ba, duk da cewa yayi min abin da baa taba yimin ba. Sannan shine mutum na farko dana taba kae qaran shi wurin daddyna bae amshi korafina ba. Tundaga ranar asabar din daya dira gidanmu Abuja,van qara samun kwanciar hankali ba.A qarshe shine daddy ya daura min aure dashi a ranar asabar kuma. Kalli wannan abin doctor,ta yaya zan yafemasa wannan zunubin? Salis yayi qoqarin danne dariyar da ke qoqarin kufce masa,sannan cikin zolaya yacee “gaskia yayi babban zunubi”. Ismail kam dariyarsa yayi harda qwalla.sannan yace, “Mimi kenan ,kiyi haquri,don nifa haka nake, duk inda nashiga sae nayi nasara akan duk mae ja dani, saboda na dogara ga Allah.kinsan duk Wanda ya mika lamuransa ga Allah,to fa Allah ya Isar masa.kinci sa’a ma wannan guntun labarin naki agaban likita kika fada,ba agaban alqali ba, da sae ya daureki.Domin babu abinda ya hada labarin nan da halin dakike ciki.ni na hanaki bin umurnin mahaefinki? Ni nace miki ki gudu? To, in baki sani ba kisani,bijirewa mahaifinki da kuma gudun dakikayi kika bar iyayenki sune silar shigarki wannan Hamlin. Likita have, wai-wai-wai kin gudu ne dama? Ta sunkuyar da kai, hawaye ne kawai ke zuba. Lallai kinyi babban laifi. Ko dani ba alqali bane. Kamar yadda Ismael yace, amma na yarda gudunki ne ya jawo miki wannan halin da kk tsinci kanki a ciki. Ta soma tuna yadda suka auna arziki a gudun farko. Ashe gargadi ne suka tsallake. Na biyu kuwa shine masoyinta ya mutu, ita kuma gashi ta kakkarye, Burinta in ta warke ta sake guduwa inda iyayenta da danginta ba zasu ta6a jin labarinta ba. To kenan mezai faru in ta sake guduwa? Duk zatonta a zuciya takai qarshen maganarta. Ashe a fili ne. Sai kurum taji yace, in kk sake guduwa na uku, qila qafafunki da hannayenki su gutsire, ki koma gundulmi, kinga kenan sai bara. “Bara? ” ta zaro ido. Likita cikin son firgita ta yace, “bara kuwa” sabon kuka ta dora, tare da cewa, ” Allah ya dauki raina in huta. ” Ismail yace kinata burin mutuwa, an fada miki sauqi zaki samu in kin mutu a haka? Na tambayeki guzurin da kkyi na zuwa lahira, amma baki ban amsa ba. Kk yarda kk mutu a haka, ai kwanciyr kabari ma kawai ya isheki. Ta Runtse ido cikin tsoro, tana tunanin kalmar likita. Wai tayi bara, Nan ta tuna wani English novel data karanta yadda Yarinyar cikin labarin ‘yar sarauta, sakamakon son zuciya, ta qare da gutsurarrun qafafu kuma a gidan yari. A firgice ta dago ta Kalli likitan, sai taga ya yagi kwalin magani ya ciro biro a gaban aljihunsa ya soma rubutu. Ya gama, sannan ya miqa ma Ismael tare da cewa, duba ka gani, kasan wannan magani? Ismail ya kar6a tare da cewa to, Ya soma karantawa kamar haka. “Ismail inason ka sauke duk abinda ke ranka game da Yarinyar nan. Ynxun na san bata san tunanin da zatayi ba. Amma ni da kai in mun hadu zamu saita mata tunanin ta. Ismail ya dago kai, ya kalli likitan sannan ya kada kai, na san shi. Likita yace, to kasai mata shi a hada cikin magungunan. Ba damuwa, inji Ismail. Likitan ya sake kusantar gadon mimin, “yanxun, menene tunanin ki a gaba, ko ince burinki? Inason in taimakeki ne matuqa. Mimi cikin kuka tace, banda wani sauran tunani, tunda malam ya dage wai mutuwa ma ba hutu bace a gareni. Da farko na daura aniyar dana warke zan gudu, in nesanta kaina da mahaifana, yadda baza su sake samun labari na ba. Inason su manta sun haifi ‘ya irina. Kai in mutu ma yadda zan nesanta dasu gaba daya. Amma ynxun kunce haka. Likita kai ka taimakeni ka nesanta ni dasu mana. Doctor salis yace, “yi shiru daina kuka, in miki abinda kk so, ta tsagaita saidai ajiyar zuciya da takeyi. Yace, na tabbata in kin kwantar da hankalinki, Ismail dinnan zai nesanta ki dasu, kamar yadda kk so domin shi mijink… “Ta katse likitan da cewa, bana buqatar yaci gaba da zama mijina. Doctor salis yace, dukda haka zai iya, zaka iya ko? Ya kalli Ismail. Yace zan iya matsawar zatayi min alqawari guda daya, sannan zata kwantar da hankalinta tare da bani hadin kai, to zan nesanta ta da mahaifanta, sannan ba aanci gaba da zama mijin nata ba, in ta buqaci hakan. Tace, menene tabbacin, zaka bar gari dani ko qasar? Ya ce, kina cikin garin katsina amma ba dole ku hadu ba, ko susan inda kk. Ta danyi shiru, sannan tace, fadi alqawarin inji. Yace, zaki dauki alqawarin cewa, ba zaki gudu ba, duk wuya, duk runtsi. In kinyi haka, ni kuwa zan 6oyeki, tare da yi miki duk abinda kk so, iyakar iyawa ta. Haka kuma in bakya buqatar inci gaba da zama mijinki, sai in koma wanki. Likita yace, bakida wani za6i sama da wannan. Kuma asirinki rufe. Tace, in kuma hajiya ta kirashi fa ko Alhaji don jin inda nake? Yace daga yau zan kwafe duk numbers din dake wayata banda nasu, sai in baki sim din ki karya, ki zubar. Tace, to in akazo gidanku fa? Ai kafin mubar asibiti zan nemi haya a wata unguwa daban, kuma ko ‘yan gidanmu ba zasu sani ba. Dama basu san gidanmu ba. Dama Hamisu direba ne kawai ya sani. Tayi shiru, domin qaramar kwanyarta ta yarda da abinda akace. Ta kalli Ismail, kenan daga ynxun kai ba mijina bane? Ismail yace, a’a wannan shine zai zama a qarshe, ko yaya kace likita? Likitan yace, wannan hakane. Ta girgiza kai, tare da dan yatsina fuska, sbd dan radadin da ciwonta keyi mata. Tace ban fahimta ba. Likita yace, kinsan za’a bi abin daki-daki ne. Farko dai zamu fara ta lafiyarki. Zanso ki bada hadin kai gurin ganin anyi jinyar ki cikin sauqi. Ki dinga cin abincinki, kina shan magani har a sallameki. Kinga wannan ne farko. Sai mu koma kan abu na biyu, bayan an. Sallameki ki zauna dashi tamkar ‘yar uwa, kiyi haquri da duk abinda ya samo ya baki na abinci, ko na sutura, ki kuma nutsu, babu batun guduwa, don kamar yadda yace, zai zamar miki wa. Ko ince kun riga da kun zama daya ma, domin jininsa ne aka zuba miki yake hade da naki. Ta dago ido ta Kalli Ismael, sannan ta Kalli hannunta mai lafiyar. Ta runtse tafin hannunta tana kallon tsintsiyar hannunta, kamar mai kallon jinin yana haduwa. Likitan shiru yayi, daya ga tayi hakan, don yasan zantukan nasa sun shigeta sosai. Ta katsewa likitan tunani da cewa, Doctor in nayi haka fa? Ina nufin sai menene a gaba? Yace, sai batun raba auren ku dashi. Ismail yace, kuma in kin samu wanda kk so, ba zai hana muyi miki aure dashi ba. Da sauri ta Kalli Ismael. “Ni bazan qara soyayya ba. Nayi ta na gama, don na haqa rami na binne ta. Zan rayu ne ni kadai. Ismail yace, duk wannan babu matsala, matsawar zaki cika alqawarinki na qin guduwa ko ina. Ni kuma zanyi miki duk abin da kk so. Ta soma qoqarin zamewa don ta kwanta. Sai dai amma ta kasa. Likitan yace, yayanki ya taimaka miki? Tace a’a likita, bana so ya dinga kai hannunsa jikina. Likita yace, wannan babu matsala. Ya miqe ya nufi waje, nurse ya kira yace tazo ta taimaka mata. Sannan ya kira Ismail, zo mana, mu danyi wata magana. Sun jera tamkar abokai. Likitan yace, Ismail banaso ka damu da duk abinda Yarinyar nan zatayi. Ka ceci Rayuwar ta ta hanyar kyautata mata don kar tace zata sake guduwa. Kabi da ita ta hanyar da muka sata akai. Sannan kayi mata qoqarin nesanta ta da mahaifanta na wani lokaci, sbd a samu ta nutsu, ta kuma saba daku. Ismail yace, Allah yasa ta iya. Domin in kaji labarin gatan da take ciki zaka sha mamaki. Allah dai ya shige mana gaba. Doctor salis yace, Ameen. Sannan inason duk lokacin da kk buqatar taimakona a game da wannan matsalar taku, ka kira number ta, sannan ya ciro katinsa ya miqa ma Ismael, “akwai numbers dina a jiki, ko da bana nan a asibiti. Ismail yace, nagode sosai Doctor. Na’ima kuwa, yadda taga rana, haka taga dare, sbd mijinta yana samanshi tare da wata mace, wadda ba halalinsa ba. Tayi kuka ta gaji, idanunta sun kukkumbura sunyi jajur. Maimakon Na’ima ta tashi cikin darennan ta miqa kukanta ga Allah, madadin kukan da takeyi. Saidai kash ba zata iya yi ba. Tasan ma anayin hakan. Allah ka ganar damu, Ameen. Bata qara tsurewa ba saida gari ya waye kusan goma da wani abu tayi wanka ta fito. A tunaninta sun bar Gidan. Ta nufi kicin ne don tasa masu yi mata aiki su hada mata abin kari. Cak ta tsaya sakamakon ganin karuwar tare da angon nata suna hada abin da zasu karya. Batasan sadda zuciya ta kwashe ta ba, ta qarasa kicin din cikin fushi ta daqumi wuyan ‘yar best din da Jennifer ta saka, tana kuka tana cewa, “zo ki fita a gidana, shegiyar karuwa. Saukar marin da taji ne ya sata sakin Jennifer cikin sauri, ta tallabe kumatunta. Ta kalli Abbas, wanda yake cewa, kinsan dawa kk son yin fada? In baki sani ba, to tsaya in sanar dake. Sunanta Jennifer kuma itace ta musamman dina. Ko da ace mimin da nakeso ce na aura, dole ta barni da ta musamman dina, bare ke wadda baki cikin ra’ayina! Karki sake ki sake kai wannan baqin hannun naki jikinta. Sannan ya juya gurin Jennifer, wadda ta koma gefe, ta 6ata rai matuqa, ya janyo ta jikinsa. Kar ki damu da wannan ‘yar wahalar kinji ko? Banida lokacinta. Na’ima tace, cikin kukan takaici, Akan wannan zaka mareni? Yace kadan na miki na gargadi. In kin sake kuma, zaki bada bayani. Sannan ki fita anan, in mun gama, mun fita kina iya shigowa kiyi abinda zakiyi, haka Na’ima ta fita, ta koma daki, cikin nadamar auren Abbas. Bakin gado ta zauna, tare da daukar waya ta soma kiran layin momi, tare da fadin cewa, ko momy bata zo ta tafi dani ba, yau na gama Rayuwar gidannan. Momy tana dagawa, kafin Na’ima tayi magana, ta katse ta da cewa “ga daddyn ku kiyi masa sannu da jiki, kafin mu gaisa sbd Jikinsa yayi zafi yau. Na’ima ta fahimci tayi hakane sbd ta sanar da ita tana tare da daddy. Sbd batason daddy yaji wannan matsalar. Muryar daddyn ce ta katseta da cewa, “Na’imatu. Tace, Na’am daddy ina kwana? Yace lafiya lau Na’imatu, yaya kuke da maigidan naki? Tace, lfy daddy yaya jikinka? To da sauqi kenan za’ace tunda ina gd. Amma sugar din yaqi sauka sam. Tace to Allah ya sauwaqe daddy, sai nazo duba ka. Yace a’a Na’imatu karki soma fitowa da wuri haka, in dai ba mijinki bane yace kuzo tare. Tace to daddy, Allah ya qara maka lfy. Yace Ameen. ga Momyn taku. Ta amshi wayar, sannan ta nufi fita. Alhajin yace, kizo ki bani maganin. Tace to Alhaji ina zuwa. Alhaji bashir ya kwanta shiru, yana tunanin yadda sukayi da likitansa daya fita ynxun. Bayan likitan ya auna shi ne yace, “Alhaji meyasa sugar dinka bata sauka? Alhaji yace kuma ina qoqari gurin shan magani da kuma kiyaye duk abinda aka hanani. Doctor yace, to kuwa kana tare da wata damuwa. Saboda shima sugar haka yake, kamar hawan jini 6acin rai yana tayar dashi. Alhaji yace, ni bana tare da 6acin ran komai likita. Likitan yace, to ynxu zanyi maka allurar da zata saukar da sugar din inqha Allah. Sannan kasha wannan maganin. Ya dago daya daga cikin magungunan ya nuna masa. Sannan yace, Allah ya qara sauqi. Kuma yana da kyau kadan qara samun varci. Momy Nafisa ce ta katse masa tunani da cewa, “Alhaji ga ruwan kasha maganin. Ta dauki kwalin maganin ta bude masa tare da cewa, likita fa yace, ka rage wannan tunanin. Wai tunanin me kkyi ne Alhaji? Saida ya afa sannan yace, ko na fada bakida maganinsa. Amma ni burina ynxun in dan samu sauqi inje katsina. Inason ganin sauda sosai, don tana buqatar lallashina. Na tabbata ban kyauta mata ba. Nafisa ta ta6e baki, ka 6ata mata rai, ko mimi ta 6ata mata rai? Shawarata dai a gareka Alhaji. Ka kauda kanka ga komai din lafiyar jikinka ta samu. A tunanina tunda Na’ima ta share maka Hawaye, bai dace ka tsaya tuna wata damuwa ba, wadda zata hana ciwonka sauka, “hannu ya daga mata, alamun tai shiru. Sannan yayi mata alamun cewa ta fita daga dakinsa kurum. Rigingine yayi, tare da dora qafafunsa wadanda sukeyi masa zafi tamkar ana hura musu wuta akan filon, ya kalli qafafun nasa wadanda ciwon sugar din yasa suke masa radadi, ya mai da kansa gefe, yana tuna sai zuwa yaushe kenan zai rabu da wannan ciwon? Domin kuwa damuwa agurinsa ta zama dole. Bai ta6a tunanin cewa, don ya yi wa mimi abin da yayi mata zai dameshi ba. Duk da qoqarin da yakeyi na tanqwasa kansa don fada da zuciyar sa. Mimi ce dai, har ynxun sonta a zuciyar sa bai canza ba. Harma wani sashen na zuciyar sa yana fada masa cewa, bai yi wa ‘yar tashi adalci ba, domin yasan har ynxun mahaifiyar ta kawai yake yiwa tsantsar SO. Sai yaji tamkar ya daga waya ya kirata, ko kuma ya tashi yaje gurinta. Amma in ya tuna qudirinsa, sai ya fasa, ya lallashi zuciyar sa da cewa, lokaci baiyi ba da zan nemeta. A fili yace, ynxun sauda ce babbar damuwa ta. Yakama in je inyi mata bayani, yadda zata fahimci dalilina. Ya karkata kansa, ya kalli wayoyinsa dake saman durowar gefen gadon. Cikin qarfin hali irin nasa, ya kai hannu, ya dauko qaramar ciki, wadda itace ya tanada don iyalinsa kawai, mata da yara. Ya shiga Numbers, sannan ya danna, kai tsaye yayi qasa, ya latsa masoyiyata sauda. Sunan da duk cikin matansa ba wadda bata nuna kishinta tsantsa akanshi ba. Domin su ya rubuta musu matata wance dukkansu. Yayi guntun murmushi sbd tuna hakan, sannan ya latsa kira. A ringing na uku, ta daga tare da yin sallama. Yayi shiru na kamar qiftawar ido, sannan ya amsa. Sakamakon duk lokacin da yaji muryarta, sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Yace “sauda.” tace Na’am Alhaji. Mun tashi lfy, ya kuma jikinka? Yace da sauqi sauda, amma fa ciwo yananan. Koda yaushe likita ya gwadani sai yace sugar yana qara sama. Kila ma ciwon bana tashi bane. Ji tayi wani abu ta tokare mata qirji, sbd fargaba. Tace Alhaji bakaje asibiti bane? Yace na gaji da zaman asibiti. Kinsan bayan taron nan, na kai kaina asibiti an bani gado. Tace ynxun a gd kk a kwance? Yace eh. Likita yana zuwa dubani. Kar kijini shiru sauda, kina raina. Da naji ‘yar dama zanzo in wanke kaina a gurinki Zugum tayi tunda suka gama wayar da Alhaji. Kalmarsa ta qila ciwon ba na tashi bane ta tsaya mata arai. Ta san cewa, mutuwa dole ce, amma gsky batason rabuwa da Alhajin ta. Bata san yaya zatayi ba, in har hakan ta kasance. Kurum sai taji Hawaye na zuba daga idanun ta. Hasina ce ta katse ta da cewa, menene hajiya? Cikin sauri ta share hawayen, tare da cewa, babu komai hasina. Ta zauna kusa da ita, shine kk kuka? Ba kuka nakeyi ba Hasina, tunanin rayuwa nakeyi mai cike da canje-canje. Yau fari, gobe tsumma. Hasina bata fahimci hausar ba, don haka sai tace, sis mimi ce? Eh, kawai hajiya tace, don kawai Hasina ta rabu da ita. Miqewa tayi ta nufi gefen masu aiki, sbd aiken da zatayi ayo mata niqan dan waken da muktar ko Abba zai tafi dashi Abuja Anjima. Momy nafisa kuma, lokacin da taje dakinta ta saurari koken Na’ima sai tace, ta jira, bari ta bawa dadyn su magani. Bayan yace, ta fita ne ta koma dakinta ta soma kiran Na’iman. Cikin sauri Na’ima ta daga har lokacin kuka takeyi. Na’ima wai kkce Abbas ya mareki? Tace eh momy marina yayi akan karuwar daya kawo suka kwana tare. Gsky momy zan dawo gida bazan jure ma wannan cin kashin ba Allah. Momy tace, kai wannan abu ya isheni. Aure ko sati daya baiyi ba, amma matsalarsa tafi ta shekara daya. Amma ba komai, ki qara haquri. Zan turo Aminiyata anjima, zatazo da mayukan da kuma qwayar da zakiyi amfani da ita. Munyi waya tun jiya. Ni kinga dadynku ba zai barni in fita ba sbd baijin dadi, amma kome kenan ki fadawa hajiya nana din kinji? Na’ima tace to. Suna gama wayar, ta budo grp chat dinsu na wtsapp. Qawayen ta suna ganinta tayi musu hello, shikenan suka shiga shewa. Ga Amarya! Ina ango? Amarci ya 6oye ki. A turo mana sababbin hotunan da aka dauka cikin amarci. Kowa da kalar tambayar da yake mata. Kasa cewa uffan tayi a group din sbd hawayen da suke zubo mata. A fili tace, da ace kun halin da nake ciki, haqiqa da baku tambayi Amarci ba. Tana kashe data dinta ta jiyo qwanqwasa qofa. Tayi kamar ba taji ba, sbd tana zaton ko sune da suka fita suka dawo. Kusan minti uku ana buga qofar, sannan ta tashi ta nufi qofar da zummar taga ko waye. Tana budewa, sukayi ido hudu da surikarta Hajiya Bilkisu da qawayen ta. Ta hau raba ido tana kallon su. Sannan tace musu, “sannunku da zuwa. Ku yi haquri. Wlh bansan ku bane. Hajiya Bilkisu ta harareta, cikin 6acin rai tace, “au dama in kinji a ta6a qofar bazaki bude ba, sai kin san ko wanene? Hum kuzo mu shiga hajiya ladi. Suka shiga Na’ima ta zauna a gabansu tana cewa, kuyi haquri momy. Sannan ta miqe ta nufi kicin don kawo musu abin sha. Zuciyar ta cike da nadamar rashin bude qofar akan kari. Hajiya ladi ta kalli hajiya Bilkisu, Yarinyar nan tanada tarbiyya kuwa? Hajiya zuwaira tace, banga alama ba. Hajiya Bilkisu tace, ai kuwa ba zan dauki rashin tarbiyya ba. Kusan minti uku muna buga qofa kina ciki kina yauqi, sai kace gidanki. Har Na’ima ta kawo musu abin sha da cincin, su diblan, da alkaki, irin wanda amare ke ba ma baqinsu, amma basu daina maganar ba. Kai kurum Na’ima ta sunkuyar, suka yi mata tatass. Har kuka saida tayi tana bashi haquri, amma basu daina ba. Sunyi kusan minti talatin, sannan suka ce zasu tafi. Har gurin mota ta rakasu, sannan ta dawo cikin damuwa da takaici mara misaltuwa. Alamu sun nuna sam ba zata ji dadin dangin mijinnan nata ba. Tun kafin motarsu tabar harabar gdn, hajiya ladi tace, hajiya Bilkisu gsky bakiyi sa’ar sarakuwa ba, alamu sun nuna zatayi rowa. Kin tuna lokacin da muka raka hajiya mairo gdn danta mansur? Wace irin kyauta tayi mata harda mu? Hajiya Bilkisu tayi tsaki. Abinda ke raina kenan ladi. Mu kanmu surukar hajiya mairo ta bamu turaruka masu tsada, ita kuwa lesuka ta bata da atamfa. Hajiya zuwaira tace, ko qannensa da sukaje yini, sai da ta hado su da kayan shafa. Gsky hajiya Bilkisu ki taka birki tunda wuri. Domin in kk bari wannan rowar da rashin son jama’ar nata yayi nisa, to kuwa nan gaba shi kansa dan naki, kina ji kina gani, zai tsani danginsa, ya kuma qanqame abin hannunsa. Ran hajiya Bilkisu ya qara sosuwa, ta ce, ina zai yiwu! Gobe zan turo su Aisha da samira, har Azima da jamil, in gani suma rowar zatayi musu. Hajiya ladi ta saka dariya, kinji hajiya Bilkisu, kema tayi miki rowa ballantana wasu yaranki? Kawai danki zaki tasa a gaba ki nuna masa cewa, yayi mata tarbiyyar kyuta da son jama’a tunda an kasa yi mata gidansu. Hajiya zuwaira tace, zancen kenan. Tafdijam! Wannan shine gaba kura baya damisa. Na’imar da bata samu kwanciyr hankali daga Abbas ba, ta yaya zata san yadda zatayi abida ya kamata? Muje dai zuwa. Haka kuwa washe gari sai Na’ima ta sake jin bugun qofa, guraren qarfe dayan rana. Bata yi qasa a gwiwa ba, ta tashi ta nufi budewa don kar ayi irin na jiya. Su Aisha ne da samira da kuma Azima harda auta jamil. Cikin ‘yar fara’a mai kama da yaqe tayi musu sannu da zuwa. Suma suka amsa cikin isa, musamman samira da Azima. Sun zauna, ita kuma ta nufi kicin don kawo musu abin sha da dan na ta6awa sannan ta sanar da masu aiki cewa, ga baqi a dora musu abinci. Taje ta kawo musu hotunan biki. Sannan ta zauna. Jin basu gaisheta ba tace musu, ina yininku? Suka ce lfy. Aisha tace, ina bros Abbas fa? Na’ima tace, ya fita tun safe, don tana daki taji fitarsa. Samira tace, sis Aisha kin manta jiya bros daya zo yace, zai koma aiki? Aisha tace, haka ne, Na’ima tace, eh ya koma aiki yau. Ta fadi hakane kurum, sbd kar su fahimci irin zaman da sukeyi. Sun wuni cur, amma bataji dadinsu ba. Komai cikin isa da nuna mata iyakar ta sukeyi. Sannan Abbas ya shigo kusan shida na yamma. Tana dag cikin daki tana jiyosu yana ce musu, kunci kunsha duk abinda kk so, ko kuma anyi muku rowar? Samira, wadda tafi kowa rashin kunya, tace, an ma isa? Bros muzo gidanka ayi mana rowa? Za ma mu jira kenan. Kowa abida take so, shi tasa masu aiki suka dafa mata. Yace, kunyi daidai. Bari inyi wanka inzo in kaiku gida. Aisha ce ta shigo tana ce mata. Bros fa ya dawo. Tace to, sannan ta taso daga kan gadon, ta nufi samanshi, cikin fargaba, sbd kar qannensa su fahimci wani abu. Ta tura qofar falon ta bude. Na’ima ta shiga cikin fargaba. Yana zaune kan kujera yana ciro wasu takardu daga cikin jakarsa. Tace sannu da zuwa. Baiji shigowar ta ba, sai magana kawai yaji. Ya dago a fusace, “lafiya? ” A tsorace kuma cikin faduwar gaba tace, dama Aisha ce tace min ka dawo, kuma su baqi ne dai, kada su gane cewa akwai wata matsala Tsakanin mu. Ya watso mata harara. Don Allah fitan min anan! An dade ba’a gane cewa, Tsakanin mu akwai matsala ba. Waton ma jiya da Momyn mu suka zo shine kkyi musu wulaqanci ko? Na’ima ta riqe kanta sbd wani sarawa da yakeyi. Tace, ai dai na basu haquri ban zaci sune suka zo ba. Na zaci wannan matar ce data biyo ka. Yace, in itace sai kiqi bude qofa tunda gidan babanki ne? To bari in sanar dake, in baki sani ba, ta fiki matsayi. Ke har iko ta fiki a gidannan. Sbd haka kibi a sannu. Sannan duk lokacin da ‘yan uwana suka zo wani yayi kuka dake, na rantse miki sai na zane ki. Fita! Wawiya kawai! Na’ima ta dubeshi rai 6ace, kai bakasan darajar dan adam ba. Ka sake ni kawai, don ba zan iya da wannan wulaqancin ba. Yace, fita nace kiyi. Da kuka ta fito, sbd 6acin rai har ta manta da baqin da suke gidan. Gadonta ta fada tana kuka. Samira, suka kalli juna da Aisha, lokacin da ta wuce su a falo. Har suka shiga dakin, sallar magriba tana kwance tana kuka. Aisha ce ta tambaye ta ko lafiya? Sam Na’ima bata tanka ba har zuwa lokacin da suka gama shirinsu suka ce, mun wuce, Na’ima bata daina kuka ba bare ta amsa. Sun isa gida cike da dokin labarin kaiwa mahaifiyar su. Aisha tana jinsu tana kallon su, samira Tana sanar da mahaifiyar su cewa, Bros Abbas yasa Na’imar kuka. Qila ma dukanta yayi. Azima kuma tace, sannan munyi abinda muka ga dama a gdn. Aisha tace, ku dai bakuda hankali, ina ruwan ku da kukan ta?shiyajiya Bilkisu tace, yayi min daidai! Ai shiyasa jiya daya zo na fada masa abinda tayi, sbd ya kwa6a mata. Samira tace, mu ma da zamu taho ba tace mana komai ba. Aisha tace, ku dai kuna da matsala wlh, ba kuga tana ta kuka bane? Tayi tsaki, ta miqe ta nufi dakinta. Ita dai ko a cikin ranta, bata so Bros Abbas yaci zarafin matarsa ba. Domin ta ba ta tausayi lokacin da take ta kukan. Na’ima kuwa kiran layin momy nafisa tayi, amma bata daga ba. Don haka sai ta tura mata saqon waya kan cewa, ita fa ba zata iya wannan auren ba. Domin mimi ba qaramar sa’a tayi ba, da bata kasance matar Abbas ba. Don Allah ki ceci rayuwa ta. Sam ynxun na haqura da son Abbas. Saqon yaje sama da minti goma sannan kiran momy nafisa ya shigo. Na’ima ta tashi zaune, ta tallafe kanta mai matuqar sarawa, sannan ta daga wayar, momy tace, Na’ima yaya ne? Na’ima ta soma kuka. Momy tace kashh! Ke kullum Sallamar ki kenan kuka? Sake dukanki yayi? Na’ima ta sanar da momy zuwan mahaifiyar sa da qannensa. Momy tace, tirqashi! Abin harda danginsa? Na’ima tace, momy kizo ki daukeni don Allah. Momy tace gobe zamuzo da hajiya nana. Na’ima tace, don Allah mommy kuzo. Tace karki damu zamuzo. Kwanan Zainabu biyu a asibiti, amma babu labarin alhaji. Innar ta kuwa taci bashi yafi na dubu goma. Sawunta hudu a gidan Alhajin, amma bata samunsa. Don haka sukayi shawara da aminiyarta yalwa cewa, in an sallami Zainabu su wuce da ita gida kai tsaye, in yazo ya biya kudin saita koma. Baban su Zainabu kuwa yaje ya duba ta sau daya, bai kuma komawa ba. Zainabu kuwa kuka takeyi akan ba zata koma ba, domin kwanakin nan da bata gidan, duk da cewa a asibiti take yafi mata zaman gidansa. Hankalinta bai sake tashi ba, saida ‘yan gidan su Ismail suka zo duba ta, taji wannan fatu din tana cewa innar su wai sunzo duba matar Ismail ne tayi hatsari. Innar su Zainabu tace, ai yayi aure ne? Nan su fatu da sauran matan gidan suka soma ba innar su Zainabu labari. Ai maigidansa ne ya bashi ‘yarsa, ita kuma bataso, ta gudu shine tayi hatsari. Daga nan Zainabu bata iya ci gaba da saurarensu ba, ta shiga rera kuka. Daren ranar bata runtsa ba, kenan Ismail yananan asibitin yana jinyar matarsa. Ita dai zata so ta sake ganinsa a rayuwar ta ko da daga nesa ne. Ta san lallai ta rasa Ismail tunda har yayi aure. Ta yi ta tuno kalaman da yake fada mata na irin tsantsar son da yake mata. Washe gari da safe innar ta taje famfo inda zata wanko ‘yan kayan Zainabun, ita kuma zainabu ta sauko a hankali, ta dauki zani guda daya daga cikin zannuwanta ta yafa ta nufi fita. Matar kusa da gadonsu tace, ina zakije Zainabu, ko bandaki zaki shiga? Tace a’a zan dann tattaka ne, sbd jikina duk ciwo yake sbd zaman guri daya. Ta fito tana tunanin ina zata nufa. Tafe take sannu sannu tana ‘yan waige-waige. Daga baya ta yanke shawarar tambayar dakin ‘yan hadari. Dan haka sai ta tun kari wata nurse. Tayi mata sannu, ta amsa. Sannan tace, don Allah inane dakin ‘yan hadari? Nurse din tace, mata ko maza? Zainabun tace “mata.” Nurse din ta nuna mata. Zainabu ta nufi gurin a cikin zullumi kala-kala. Shin zata gashi ko ba zata ganshi ba? Matar tashi ta fi ta ko bata kaita ba? Ta shiga, dogon falo ne kamar nasu, kwakkwance da marasa lfy gado-gado. Tabi tana yi musu sannu, tare da tambayar matar Ismail, amma har ta gama dubawa bata ganota ba. Ta fito ta tafi tana waigen dakin. Yinin ranar cikin damuwa tayi shi, don ko ‘yar shinkafa da waken da innarta kan siyo mata taci, yau kam kasa ci tayi. Da magriba, innarta ta nufi dan lungun da sukan shinfida tabarma suyi sallah. Ita kuma zainabu ta fito ta sake zuwa dakinnan na ‘yan hadari. Bata shiga ta qofa ba, window qarshe ta nufa, ta dafa windon tana leqen mara lafiyar dake kwance a gadon. Zuciyarta ce ke zargin cewa, lallai wadda ke kwance a Gadon nan ita ce matar masoyinta. Bisa dalilinta na ganin cewa, kaf dakin itace yarinya qarama. Sannan da safe da tazo babu mai jinyar ta a gurin gadon su, sannan da tace mata kece matar malam Ismail? Kai kurum ta girgiza alamun a’a. Ita kuma sai take qara dogara da cewa, batason sa shiyasa shine dalilin da yasa tace a’a. Fatanta ace Ismael yana gurin ta samu ta dan ganshi ko zataji sanyi. Sai dai tana leqawa taga wata gyatuma zaune kusa da Yarinyar. Tayi ta leqe-leqe kusan minti biyar. Ko mai kama da Ismail bata gani ba. Taja silifas dinta zata tafi dakin. Daidai kwanar da zata kaita babban daki, inda suke kwance, sai ta hango Mahmud shida rabi’a, budurwarsa, don ta san ta, itama ‘yar islamiyyarsu ce, sai dai ita, ‘yar babban aji ce, ajin da Ismail ke koyarwa. Da sauri ta shiga kwanarsu ta juya baya, sam su basu ganta ba suka wuce. Ta fito ta bisu da kallo, yana riqe d kula ita kuma da leda mai dauke da lemu da ayaba. Wata zuciyar tace, ki bisu mana, kinsan dai babu gurin wanda zasu, sai gurin masoyinki. Da sauri tabi bayansu, sai taga sun nufi wata matattakala. Itama sai ta bisu har suka hau saman. Wata qofa suka shiga, dan tsayawa tayi kamar mai tsoron binsu don batasan yaya cikin qofar da suka shiga take ba. Sai kuma taga ashe dogon guri ne mai dauke da dakuna. Can ta hango su sun kusa kai qarshen dakunan. Don haka ta shiga itama cikin azama. A tsorace take tafiya har takai gurin da Nurses masu kula da wannan sashen suke zama. Yadda take tafe tana waige-waige ne yasa wata nurse tace, ke ina zakije? Nan Zainabu ta daburce, ta soma inda-inda, “am zan..zanje can ne. Yin me? Nurse din ta katse ta. Duba mara lafiya zanyi. “ya sunan wadda zaki duba? Zainabu ta sake rudewa, ni ban..bansan sunanta ba. Nurse din tace, daga ina kk? ynxun bama yarda da mutane, sbd rashin gsky yayi yawa, don ko jiya an saci Jariri a dakin ‘yan tiyata. Zainabu ta firgita. Nima nan nake, can dakin ‘yan 6ari aka bani gado. Dan uwana ne matarsa take nan tayi hadari. Shi sunansa Ismail. Nurse tace, ok na gane shi, wani ustaz haka ko? Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke ajiyar zuciya. Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta, dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi’a kuma ta zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado. Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail data gani, hawaye suka soma sharara akan kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi’a ta tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin dake gurin. Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi mata, sai suce, “Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo asibiti ko sau daya bai leqo ba. Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona ma kanki asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun farko da kk qi nuna masa so. Zainabu tace, to ni bana sonshi, kuma bazan koma gidansa ba. Inna tace, sai kiyi tayi. Ga faten doya nan da mai wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace, bana ci. Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi da tuwon da wannan ta kusa damu din ta bani Zainabu ta zame ta kwanta, idanunta na qara hasko mata Ismail dinta ke baiwa matarsa abinci a baki. Ta tabbatar da irin son da Ismail yake yi mata, da ace ita ce, qila ma sai ya tauna a bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun rasa mai kawo musu, sai dai maqotansu na kwanciya su sam musu. Da wannan takaici Zainabu tayi varci mai cike da mafarkan masoyinta Ismail. Mahmoud ya kalli rabi’a kinyi qoqari domin mara lafiyar nan bata ci komai ba tunda tazo asibitinnan sai yau da kika kawo mata. Azaton Mahmud Ismail baijishi ba yanayin jinjina ne ga masoyiyarsa. Sai kurum yaji Ismail ya cafe da cewa, ni kaina na jinjina miki rabi’a domin a tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai abinda basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce, kuma farfesunshi rabi’a tayo da alayyahu. Haka nan ta dai yo ne don batasan me zata yi ta kawo ba. Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana saida ma masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam mata zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai data qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha sannan tace zata kwanta. Tun lokacin da likitan ya taimaka masa suka shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada masa cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan ruwa, kuma sun saka mata pampers ita da wata nurse. Harma mimin tace, su sake canza mata rigarta. Yaji dadin sannan ya dawo da murna sun samu admission islamic ya nema. Mahmud kuma sai suka bashi English baiso ba amma hakanan ya haqura. Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka fito, Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma wadannan Nurses din na gefensu da zai wuce, sai dayar take tambayarsa dazun wata ‘yaruwarka ta gane gurin ku ko? Ismail yace, da yau she kenan? Tace dazun nan kuma nice nayi mata kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru kodai rabi’a ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina dinnan ko? Nurse tace, a’a ita daya ce tace, tana nan asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai. Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace, naga lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton tana tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya sake dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take nema? Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira. Yace to gsky bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu dama munga har kwatancenka anyi mata tace kaine. Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi wata baquwa? Tace A’a sai dai ina neman wata alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta.”ina saauraronki” yadan rusuna sbd Mimi bayayin magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu. Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd suna ne mai dadi da ma’ana. Allah yasa halayenki su rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta farko data soma kar6ar musulunci a tarihi. Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci. Sa’annan itace ta haifawa ma’aiki ‘ya’ya guda shida. Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta. Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba musulmi ba yasan mai tsira da Aminci. Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za’a yi hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane. Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce masa qala ba. Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi. Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba. Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa. Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan ya nufi gadon mimi yayi mata addu’o’i ya shafa mata, sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado masa, to ko wacece? Ko kuma cikin ‘yan uwanta ne? Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane. Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba. Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo, kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo. Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau. Mimi tace, yaya don Allah za’a iya yimin wanka? Yaya Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, “yaya ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami. Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta sunsuna. Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija, don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta. Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? “Don Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai domin wani ciwon zai shigar ki. No related posts. POST COMMENT 22 Let God take the burden off your shoulders. Connect now. GodLife OPEN 22 Ismail ya miqe “yaya ni dai bari in barki da ‘yar rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi, zan koma gida da wuri. Ismail yace, zan dawo da wuri insha Allah. Ya kalli mimi, khadija bari inje in dawo, ko kina son wani abu inzo miki dashi? Ta girgiza kai alamun a’a. Taci taci gaba da kukanta. Yace, shikenan sai na dawo. Yasa kai ya fice mimi ta qara sautin kuka. “yaya malam ya saba da ganin kukana, ya daina lallashi na ynxun. Yaya tace a’a bayason kukan ne, shiyasa. Kuma gashi inya lallasheki bakyayin shiru. Ai khadija a rayuwa in akace maka kayi haquri, to kayishi. Karka ce wai kai zakayi tayi, mai lallashinka sai ya gundira. Mimi tayi shiru. Can tace, Yaya wai kuma baku da ‘yan uwa ne? Tace me kk gani? Tace naga ku kadai ne kuke zuwa. Yaya Amina tace, muna dasu khadija, amma dai basu damu damu ba. Ni da Ismail ne muke uwa daya. Nan ta ba ta labarinsu. Bata 6oye mata komai ba game dasu. Mamaki ya cik mimi, tace dama ana samun haka? Ni kam kishiyar mama na har tafi mamana sona. Ynxun haka nasan tanaa cikin damuwa. Yaya Aminu tace, bana zaton akwai wanda zaifi uwa son ‘yarta. Khadija duk inda mahaifiyar ki take a ynxun tafi kowa tashin hankali, sai dai in qila ita mai kawaici ce. Soyayyar uwa da ‘ya na daban ne kinji. Amma zaki gane haka nan gaba. Mimi tace, ko qawayena sunsha fadamun haka, amma har yau ban gamsu ba. Yaya Amina tace, to ke dame kk dogara wanda har yasa kk ganin mahaifiyar ki bata sonki? Mimi tace, zan baki labari, saina qara jin sauqi, amma ina da hujjoji masu yawa. Shi kam Ismail har ya Sauka samansu, ya dauki hanyar fita, sai ya fasa, ya dawo ya nufi gurin saida magani domin ya amshi canjinsa. Tun kafin ya qarasa dan windon da zai amshi canjin nasa, sai ya jiyo muryar innar Zainabu tana cewa, ni kudina sun qare banida sauran ko na mota. Wani yace, ina ruwanmu da qarewar kudinku. Kuma bamu damu ku sai mata magani ba. Mu dai ku bamu kudinmu, ynxun da wannan abokin aikin nawa bai ganku ba, da ynxun kun gudu. Ismail ya qarasa gurin su daidai lokacin da innar su Zainabu take cewa, nima ba laifi na bane, Alhaji ne baizo ba. Dayan yace, ku kirashi a waya mana babu inda zakuje. Ismail ya miqa wa Mutumin hannu tare dayi masa sallama suka gaisa, sannan ya kalli Inna wadda tunda ta ganshi taji kunya matuqa, kamar tace, qasa bude in shige. Yace, inna lfy kuwa? Tace lfy qalau. Dayan yace, kawai inna ki fada masa gsky. Kanaji ko malam. Wannan matar tun ranar da suka kawo ‘yarsu aka bata gado, bata biya kudin gadon ba, sannan akwai cikon kudin magani, wanda zata bada ciko, amma taqi, kullum sai tace, sai alhaji yazo. Yau likita ya ba sallama kurum, sai dai wannan abokin aikin nawa ya ganta a bakin Gate zasu hau tasi. Kaga mu taja mana kenan, ace mu muka cinye kudin. Ismail yace, nawa ne kudin? Inna cikin kunya tace, umm ai da ma ka barshi kawai, Alhajin dama yayi tafiya ne shiyasa. Mutumin yace, inna ki bari kurum a biya muku. Ba wani Alhaji, kullum kina zaizo, amma shiru. Ya kalli Ismail, dubu biyar. In kuma za’a basu ragowar maganinsu, dubu shida da dari uku da saba’in. Ismail ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro ‘yan dubu dubu ya miqa musu dubu shida. Sannan ya ce, jiya canji na nawa na bari anan? Dayan yace dari bakwai da hamsin. Ismail yace, ku cire cikon ku bani sauran canjin. Kanta a qasa tace, an gode Ismail. Ta juya zata tafi, suka ce, ki tsaya mana ki amshi sauran magungunan da kuma takardar shedar biya. Ismail ya amshi canjin sa, sannan ya kalli innar Zainabu, “Allah ya qara sauqi” bai jira amsarta ba, ya wuce. Ita kuwa dama kunya ta hana ta amsawa. Zainabu ta nufo gurin, sbd itama tasa baki, ko zasu yarda za’a kawo musu daga baya. Sam basuga juna ba, saida suka zo daf. Itace ta soma ganinsa. Tsayuwar da tayi ne yasa shi ganinta. Tayi sauri ta juya baya. Ismail ya runtse ido ya bude. Gabansa yaci gaba da faduwa. Shima yayi saurin dauke idanunsa daga kallon bayanta. Da qyar yace, “yaya jikinki? Tace, da sauqi, cikin rawar murya dake dauke da kuka tayi magana. Yaya taka mai jikin? Ya dubi inda take, a ransa yace, ashe taji. A fili yace ta samu sauqi. Yaja qafafunsa wadanda sukayi masa nauyi yace, sai anjima. Ta bishi da kallo bayan ya wuce. Sam ta kasa ko motsi, sai kuka har innarta ta iso tana tambayarta lafiya? Zainabu tace, an cuce ni. Dajin haka innar tasan Zainabu taga Ismail. Cikin borin kunya tace, “kina ta an cuce ki. Matar mutum ai kabarinsa ko? Ki barshi a qaddara. Zaizo ya sameni shi kuma Alhajin. Ya sanni, ni walki ce ina daidai da qugun kowa. Zainabu dai bata tanka ba, sai ta fita abinta. Tunda suka koma gida ko yaushe Zainabu tana cikin qunci da kuka. Musamman da innarta ta fada mata cewa, Ismail dinne ya biya kudin gado. Innarta tanason Alhajin yazo ya biya kudin da suka kashe, indai yanason zama da Zainabu. Ita kuwa Zainabu ba haka nata tunanin yake ba. Jiran Alhajin takeyi. Ko nawa zai kashe, batajin cewa, zata koma gidan Alhajin. Ismail ya jima zaune akan katifarsa kafin ya tashi ya dauki bokitinsa ya nufi cikin gidan, suna ta nasu harkoki. Yayi sallama suka amsa sannan ya gaidasu, ya nufi dakin Inna, tana ta gyangyadi, ya gaida ta. Ta tambayi mai jiki, yace, da sauqi, tace kai dama ashe Yarinyar nan ba sonka takeyi ba? Ismail yayi murmushi, tare da cewa ai wannan ya wuce Inna. Ya miqe ya nufi bandaki. Tace, haka dai kk kullum ba’ajin cikinka. Jeka can ka qarata. Bayan ya fito ne yaga wata yayarsu tazo ya gaida ita, zai wuce, fatu tace, kin masa jaje kuwa? Yaya shafa tace, meya faru dashi? Fatu ta tuntsire da dariya. “huce haushi akayi masa da mace. Ashe bata sonsa ta gudu, sai kuma tayi hadari a hanya. Shafa ta kalli Ismail wanda shi yana daf da zaure tace, to ashe haka akayi Ismail? To Allah ya kyauta. Yace, Ameen tare da shigewa zauren. Ya gama shirinsa tsaf cikin yadi mai kalar sararin samaniya marar nauyi. Ya saka hula sannan ya feshe jikinsa da turarukansa na musamman da yake hadawa a gurin masu saida turaruka sannan ya fita ya nufi gidansu Mahmud don amsa kiran malam Aminu. Da Mahmud ya soma haduwa, sai dai irin fara’ar da ya gani a fuskar Mahmud din ta bashi mamaki. Yace, malam ko anyi maka baiko da rabi’atu ne? Mahmud yace, qila da hakan ne zaiyi wuya ka gane a fuskata. Gara ma inda ranar daurin auren ce. Ismail ya dafashi, to sanar dani mana game da farin cikinnan naka? Mahmud ya kama hannun Ismail. “Zomuje kaji daga bakin malam. Tunda na iya jure daren jiya dana samu labarin, na jure safiyar yau, to kuwa zan jure ynxun muje kaji da kanka. Na yafe goron albishir din. Cike da fara’a suka gaisa da malam yace, malam Ismail yaya mai jiki? Jiki da sauqi Alhmdlh. Malam yace, masha Allahu. Ka samu labari daga bakin dan uwanka ko? Cikin zaquwa yace, bai fadamun ba malam. Yace, inji daga gareka. “malam ya fadada fara’arsa, sannan ya kalli Mahmud dake zaune gefe, yana murmushi, ya maido da kallonsa ga Ismail, “Scholarship dinku ya samu. Shekaran jiya malam mukktar yazo ya sameni da batun. Don haka sai ku soma shirye-shirye, nan da wata daya Matsalarmu kudin da zakuyi amfani dashi. Ismail yayi mutuwar zaune, jinsa yake tamkar a mafarki. Wai malam madina yake nufi ko zariya? Da darsuwar wannan zargin, sai ya kalli malam. “Malam wai madina dinne? Malam yayi dariya, ka samu nutsuwa Ismail, madina ce zaku tafi, kaida dan uwanka. Saiku soma shiri, tare kuma da neman kudin da zakuyi ‘yan abubuwan daya kamata. Sam Ismael baisan lokacin daya rungume malam ba. Sunyi murna sosai harda sujjada don nuna godia ga ubangiji. Ismail ya soma tunanin wa zai soma fada mawa? Duk lokacin da wani abin farin ciki ko baqin ciki ya sameshi, sai ya tuna mahaifinsa, ‘yar qwalla ta taru a cikin idanunsa, amma sai ya daure ya cije. Yace musu bari yaje ya fadawa yaya Amina da mutan gidansu. Mahmud yace, to sai ya shigo anjima, a gaida ‘yar amana. Ismail yayi murmushi, “zata ji.” Sam ya manta da Damuwar Zainabu daya baro asibiti da ita. Saida ya idar da sallar azahar sannan ya nufi cikin asibitin, zuciyar sa fal da murna. Yana shiga yaya Amina tana nunke sallaya, ta idar da sallah. Ismail yana shigowa sai ya rungume ta, ta tsorata sbd bata ta6a ganin haka ba. Ya sake ta yana dariya, “naga kin tsorata?” Tace ai dole Ismail ban ta6a ganin haka ba. Yace, zamu tafi karatu madina, nida Mahmud. Yaya Amina ta sake rungume shi, cikin tsananin murna tace, Allah da uwana? Allah mun gode maka. Sai kuma ga hawaye suna zubar mata. Ya ciro hankici yana share mata hawayen. Ba ason kuka a cikin murna yaya, cewa zakiyi “Alhmdlhi llazi bini’imatihi tatimmussalihat. Ta maimaita abinda ya fada, sannan sukayi murmushi. Ta kalli mimi. Wadda take kallonsu, kinji ko khadija? Mimi tace, Allah yasa alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan suka zazzauna yaya tace, to ya batun karatunka na nan? Yace yaya ai kuma ba wannan zancen. Tunanina ina zamu samu kudi sbd tafiyata da kuma sauran hidimomi. Yaya tadan yi shiru, can tace “to ko daura zamuje wajen su kawu a saida gonarmu ta gurin mamarmu? Ismail a’a yaya gonar fa ba ta ni kadai bace, gaki kuma kema mai buqata ce. Yaya tace, ko ni na siya da kudina bazan sadaukar maka da ita ba, balle gadonta mukayi. Haba dan uwana abin duniya fa na duniya ne. Ya kama hannunta “nagode yaya, Allah ya kaini lokacin da zanga nayi miki fiye da abinda kikai min. Tace Ameen Ismail, in jikin khadija ya qara sauqi sai muje dauran ko? Yace to hakan za’a yi. Dama basu san komai game da auren nan nawa ba. Sai kuma sai kuma ya kalli mimi, tunda ba wai lallai auren ya dore ba, mubarsu kawai. Yaya ta gane yana fadin hakane don kar mimi taci gaba da rikicinta. Kafin kwana goma labarin tafiyar su Ismail ya zaga dukkan ‘yan uwa da abokan arziki, sai murna akeyi wa Ismail da Mahmud. Mimi kuwa jiki ya soma sauqi, gashi tanacin abinci amma fa rabin abincinta kifi ne. Hajiya sauda ta shiga damuwa sakamakon rashin samun Ismail a wayarsa. Ynxun ma da take zaune saida ta dauko wayarta da zummar ta sake gwadawa, kamar wasa sai layin ya shiga. Cikin Jindadi tace, Alhmdlh. Lokacin Ismail yana zaune yana 6are wa mimi lemun zaqi, ya daga ne ya kalli mimi, wadda ta qosa tasha lemun. Yace, ina zuwa. Ya fita cikin sauri. Suka gaisa, sannan yace, hajiya kwana biyu? Tace layin ka baya shiga. Yaya mai jiki? Yace da sauqi sosai hajiya. Ina tsammanin matsalar ntwk ne, amma wayata a kunne take, kuma akwai charge. Tace sauqi na samuwa sosai ko? Ismail yace, tunda tana dai kar6ar abinci. Hajiya sauda tace, to mun gode Allah, sannan ina qara jaddada maka amanata, sannan ina qara baka haquri. Na sani zakaga abubuwa gurin mimi. Ismael yace, don wannan karki damu hajiya. Sannan ina godia kan kudin da aka turo. Tace, karka damu wannan ba wani abu bane. Zan sake turo ma wasu insha Allahu. Daganan sukayi sallama. Ya dawo ciki yaci gaba da 6are lemunsa. Sai da ya gama ne, ya kalli mimi tare da cewa,, qanwatah ga lemun. Fuskarta daure tace, bana sha. Sbd me? Ya tambayeta cikin sauri. Tace, saida ka gama yin wayar, sannan zaka 6are min, alhalin tun tuni nace zansha lemu. “cikin irin shagwa6arta data zame mata jiki tayi maganar. Sannan qasa qasa don ita mimi ko yaushe maganarta qasa-qasa ce. Ya matsa kusa da ita haba qanwatah waya nayi. Ta harareshi, bana son ana hada uzuri na dana wasu. Inka gama nawa sai kayi na kowa. Yayi ‘yar dariya sbd yadda ya lura itafa iyakar gskyrta take magana. Yace, shikenan ranki ya dade. Ko wane lokaci uzurinki zansa a gaba. Tashi kisha lemun to. Tace ya fita raina. Barci nakeso inyi ynxun. Ya kalli lemun na hannunsa, sannan ya ajiye ya gyara mata kwanciya, tare da cewa, ayi bacci lfy. Ismail shida yaya Amina sun tafi Daura sbd maganar saida filin mahaifiyar su na gado. Hannun Ramatu Nurse Ismael ya bar mimi. Domin yace, komai dare aranar zai dawo ba zai kwana ba. Mimi kam ko amsa shi batayi ba, lokacin da yake yi mata saiya dawo. Ya gama karantar halin mimi tsaf, dan zaman da sukayi tare, shirunta na nuna taji haushin tafiyarsa. Bai damu ba, nasa ganin tafiyar itace zata kawo masa qarshen tunanin, ina zai samu kudin tafiya jami’atul madina. Sun samu tarbar mutunci da qauna, kamar yadda aka san dangin uwa. Sannan sunyi murna dajin batun tafiyar Ismail qasa mai tsarki don yin karatu. Haka nan sun jajanta masa batun hadarin matarsa da suka basu labari. Sannan sunsha alwashin zuwa su dubata. Kawunsu yace, shikenan nan ma in za’a zo sai a taho da kudin tunda yau za’a sata a kasuwa. Qarfe takwas da rabi Ismail ya iso katsina, yabar yaya Amina a can zatayi kwana biyu. Ya nufi gida kai tsaye, yayi wanka yasa jallabiya mai ruwan siminti, sannan ya nufi asibiti. Sai da yayi mata tsarabar kifi, sannan ya qarasa asibitin. Kuka sosai ya sameta tanayi idanunta jajur. A rude yake tambayarta abinda ya sameta. Bata tanka ba. Yace, to ga gasasshen kifi na siyo miki, nasan zaki ci. Ya duba cikin kular da yaya ta dafo mata abinci kafin su wuce, ashe faten wake ne da kifi, amma bata ci ba. Ya dawo ya zauna bakin gadon. “Kar dai duk yau bakici abinci ba? Ta kalleshi idanunta jajur, “yau na yarda banida kowa, muryarta tana rawa irin na wanda ya gaji da kuka. Yace me akayi miki khadija da bana nan? Fadamin. Kuma karki sake cewa, bakida kowa. Gaki da ni, ga yaya Amina, muma da mu biyu ne, amma ynxun kinga mun qara mun zama mu uku. Mun tafi da tunanin ki. Ya warwaro tissue ya soma share mata hawayen. Sannan ya dauko kifin ya soma bata a baki sala-sala tare da jajjagaggen kayan miya. Taci sosai, sannan ya debo ruwa ya kawo mata, ya taimaka mata ta wanke hannu da kuma baki. Sannan yace khadija tunda ynxu kina iya zama zaki iya yin sallah. Ta 6ata rai. Yace wai meyasa duk lokacin da nayi miki zancen sallah, sai ki 6ata rai? Tace to yaya zan iyayin sallah a haka? Yace, zaki iya mana. Shi addinin musulunci sauqi ne dashi, ya nuna mana yadda zakayi ibada matsawar kana cikin hankalinka. Ita kuwa sallah sbd muhimmancinta, ko a filin yaqi anayin ta. Tace, ni ynxun dai ka barni barci zanyi. Ya ce, kinada yaqinin daga varcinnan zaki farka? Tayi shiru, yace bakida yaqinin cewa, zaki farka, kuma zaki iya farkawa ki ganki a kabari. Tace, oh Allah na, don Allah kabar zantukannan. Yace assha! Assha! Ina tsoron kar zuciyarki ta kamu da mugun ciwo, wanda batason ko kadan taji an ambaci Allah ko manzonsa, ko wani abu na addini. In hakane kuwa lallai kin daura qawance da shaidan, kuma yaci galaba akanki. “Don Allah ka barni mana! Ga mamakinsa, sai yaga ta soma kuka, shiru yayi, ransa 6ace. Lallai akwai matsala babba, akan zancen addini mimi ke kuka. A fili yace “akwai aiki!. Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za’a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za’a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. “kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na’ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na’imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, “ke da Allah natsu! Na’ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki. Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar ‘yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba’in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na’ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. “Na’ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. ‘yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na’ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na’ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za’a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za’a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. “kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na’ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na’imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, “ke da Allah natsu! Na’ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar ‘yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba’in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na’ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. “Na’ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. ‘yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na’ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na’ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Na’ima tayi kuka, iya kuka cikin daren kafin varci yayi gaba da ita. Qarfe takwas ya farka. Halin daya ganshi ciki ya sashi kallon gefensa. Na’ima ya gani kwance cikin irin yanayin daya samu kansa. Ya soma tunanin da yaushe har tazo masa daki akai hakan? Ya dai iya tuno jiya sun samu matsala da Jennifer. Yarinyar daya kawo ta Abuja da kansa ya kama mata gida tana zamansa, ynxun kuma sai ta dinga munafuntarsa. Jiya yaje mata zuwan bazata sai ya sameta ta kawo wani gidan. Yayi mata magana tana fada masa cewa, itafa ba matarsa bace bare ya dinga yi mata dokoki. Yayi mata duka kafin ya baro gurin ta ya nufi club dinsu inda suke hadewa da abokansa suna shayeshayensu. Ya fada musu halin da yake ciki, nan suka bashi shawarar cewa, yasha mayensa ya manta da ita, ya daina zuwa ta gani in akwai wanda zai mata kwatankwacin abinda yake mata. Sha yayi sosai, don bai ta6a sha irin haka ba. Ko iyayensa basu san yana sha ba, domin baya sha da yawa. Ya kasa komai don haka suka kawoshi gida. Tuna hakan yasa shi gane cewa, maye ne ya suranta masa Na’ima a matsayin Mimi. Tsaki yaja sannan yasa hannu ya daddaka mata duka. Firgigit ta farka tana kallonsa, fuskarsa daure. Yace, tashi ki fita! Tace dama kai ka kawoni bani nazo ba. Ta soma kuka, yace ban tambayeki wani dogon zance ba. Nace dai ki fita. Na’ima ta saka rigar varcinta ta fita da kuka. Ya jima shiru yana takaicin faruwar hakan Tsakanin su, don bai tsara zaiyi hakan da ita ba. Amma sai ya miqe ya nufi bandakinsa. Na’ima ma bayan tayi wanka da sallah, ta koma ta zauna tanata tunanin yadda mijinta yake mutuwar son mimi. Kai ita da ta sani, da bata kawo kanta gurin son maso wani ba. Can ta miqe ta nufi kicin, yauma da kanta ta girka abinda zataci kifi ta gasa, irin gashin da Mimi kansa ayi mata. Na’ima ta dan iya girki, domin ko a gidansu tana shiga kicin gurin masu yi musu girki jefi-jefi. Ta gasa bread dinta, zata fito shi kuma zai shigo kicin din, ya kalli tiren hannunta, “bani kiyi wani! Bata musa ba, ta miqa masa don tanason su riqa ‘yar hulda ko yaya. Ta koma ta hado wani abin karin. Bayan ta karya ne ta shiga turare gidan da turarukan da aka kawo mata. “Yayi qamshi. Ya fada, duk da ba cikin walwala yayi maganar ba. Taji dadi, kuma taji mamaki. Don haka bayan fitarsa, sai ta dauko sauran abubuwan ta kama amfani dasu. A waya Abbas ya kira Usman, yana bashi labarin abinda ya faru a jiya. Usman yace, kai sakarai me nace maka? Ai na fada maka kawai ka more quruciyar Yarinyar kace a’a, to ynxun don ja nuna ma Jennifer kurenta kawai, ka share ta kaci amarcinka. Abbas yace, banason Yarinyar tayi tunanin cewa, ina sonta ne. Usman yace, ai ba wai zaka sakar mata fuska bane sosai. Ka gane? Abbas yace, shikenan zan kwatanta. Tun daga ranar Na’ima tadan samu sauqin mijinta. Zai sata ta dafa masa abinci, kuma zai kirata shimfidarsa. Amma ba wata soyayya, ko kulawa, ko hira ko sakin fuska. Abin da ta lura amfaninta kenan tayi masa girki, sannan yayi buqatarsa. Wani dare ya kirata a waya taje samansa. Ta sameshi a falo tace gani. Yace ki shiga mana. Kin tsayamin akai, sai kace wani sa’anki. Ranta ya sosu, tace, wai kai kana bani mamaki. Kana nema a gurina amma kayi ta dauremin fuska, kana fadamin abinda kk so. Yace kar ki kawomin raini. Ki wuce muje. Tace, ni varci nakeji, ta juya. Nan take ya kamota, saida ya mammareta, sannan yayi abinda yake so anan falon, ya kuma koreta zuwa dakinta. Zahiri baya sonta, amma abubuwan da take sha, da wanda take qamsasa jikinta suke fizgarsa gareta. Irin Rayuwar da Na’ima ke ciki kenan. Gashi danginsa sun tsane ta, musamman uwarsa wadda tace, Na’ima ta bada ita a gaban Qawayen ta. Zainabu kuwa tana can gidansu, saiga Alhaji ya diro da la’asar sakaliya. Yayi sallama dz innar su Zainabu. Yau kam fuska daure ta fita, da nufin bala’i tare da ita. Sai dai shima tana kallon sa tasan cewa da hakan yazo, kuma in ba sa’a bama shi ya dama ta ya shanye. Kafin tayi magana ya riga ta. Nazo daukar Zainabu ne. Ta lailayo ashar ta maka, sannan tace, Zainabu ba zata koma ba, sai ya sauke dubu ashirin da hudu na asibiti. Yace, tunda dai banyi muku qorafin cikina da kuka zubar ba, to ku bani matata kawai mu tafi. Inna tace, au tanan ka biyo? To ai inason ka sani, tuni muka samu labarin baka son haihuwa, bare kayi wata barazanar banza. Ba zata koma ko ina ba, sai ka canke kudin mutane. Yace, haka kk ce? To kuwa ku shirya cin wani bashin don zaku amsa sammaci, kotu zamu shiga. Ya ciro wayarsa, iroro dake gefe yace, Alhaji ai sai ka kira lauyannan naka tukun, domin duk wanda baisan mutunci ba, gara ayi masa abinda yafi sani. Wato rashin mutuncin ba. Inna tace, ku kira alqali, ba lauya ba. Kai kuma dan kanzagi makwadaici kabi a sannu. Kaje ka nemi sana’a ba maula ba. Iroro yace, ai indai wannan ne sunanmu daya dake, wato ‘yan maula. Kwadayinki kuwa ya ninka nawa. Tunda kk miqa ‘yarki ga wanda bashi ta za6a ba. Alhaji yace, ko ba haka bama Iroro, ai baka kaita roqo ba, kullum dan aike yana hanya. Tace, kodai me zaku fada, ku fada. Lokacin ne layin ya shiga wanda yake nema. Alhaji yace, yauwa Barista audu kaji ko? Daga can suka ji murya tace, eh ina jinka Alhaji lawal. Iroro yace, Yauwa Alhaji ai gara kasashi a speaker taji. Alhaji game da zancen da mukayi ne na matata. Ynxun haka ina gidan uwarta ta hanani matata, don haka zanzo mu shigar da qara. Daga can sukaji muryar barista yace, qarar kisan kai zamu shigar, tunda basu da mutunci. Ina ga ko dan gidan da suka mallaka, sai sun daida ba tare da kuma sun kare kansu ba. Don haka kar ka damu. Alhaji yace, shikenan nagode. Ya kalli inna yayi murmushin mugunta, sai mun hadu a kotu. Iroro ya sheqe da dariya. Dana sani tanata bibiyarki. Har sun juya tace, Alhaji ya tsaya. Sannan ya waiwayo. Lafiya? Tace, bari in turo ta ku tafi. Kudin mutane dana aro kuma idan nayi maka Allah ya isa fa? Tare suka sheqe da dariya, Iroro da Alhaji. Iroro yace, shegiya wuya! Alhaji yace, inna ai dama Allah ishasshe ne. Cikin jin haushi, inna tace, ni ba innarka bace don na tabbata ni kaina ka girmeni. Ta juya cikin takaici, suna tayi mata dariya. Zainabu tana kuka, tana komai, ta fito tabi Alhaji, tabar innarta cikin takaici. Wani qarin abin haushi a lokacin suna isa gida, saida yayi buqatarsa ya fita, ya barta tana kuka. Kishiyoyin suka shigo sunayi mata sannu tare da bata haqurin rashin zuwansu. Ko kawo mata abinci sunce Alhaji ne ya hana. Haka Zainabu taci gaba da Rayuwar gidan Alhaji mai cike da matsi da takura, gami da wahala, duk ta qara kodewa, ta fige ta lalace. Kuma ya hana innarta zuwa, kamar yadda itama yace ta daina zuwa gidansu. Innar Zainabu tasha kuka tare da takaici da kuma da na sanin hada Zainabu da Alhaji lawal. Alhaji bashir ya dauki wayarsa ya soma neman layin Abba. A ringing na biyu Abba ya dauka, ya kara a kunne yana fadin dad ina kwana? Bayan sun gaisa Alhajin yace, inason kazo yau ka tafi dani katsina. Abba yace, amma lfy dai ko dad? Alhaji yace, lfy lau, inason ganin mahaifiyarku ne, gashi har ynxun bana jin dadin jikina. Abba yace, shikenan daddy, sai nazo. Qarfe biyu Abba ya sauka garin Abuja. Tuni daddy ya turo direba yana jiransa. Suka nufi maitama. Momy Nafisa batasan da batun ba, saidai taga Abba. Ya gaisheta tare da tambayar jikin daddyn, tace da sauqi. Lokacin data shiga don sanarda Alhajin zuwan Abba, sai yace ta hada masa wasu kayansa na ciki da kuma wasu takardunsa. Tace, ina zaka Alhaji? Yace katsina, nine nace wa Abba yazo ya tafi dani. Tace, ba zaka bari kadan qara samun sauqi ba? Yace, karki damu, can ma zanci gaba da ganin likita. Shida daidai suka sauka a filin jirgin sama. Sun samu direba na jiransu, domin kafin su taso daga Abuja, Alhaji yasa Abba ya kira direban hajiya sauda, batasan da zuwan Alhajin ba tana zaune a falo tana ba Zainab magani, don yau kwananta uku babu lfy, kullum suna hanyar asibiti. Sai kurum taji Sallamar su. Bata zaci Alhaji bane, don muryar Abba irin ta Alhajin ce. Saida taji yaran suna Oyoyo daddy. Da sauri dago tace, sannu da zuwa Alhaji. Ta miqe cikin sauri bayan ta kwantar da Zainab, tace, Alhaji baka sanar dani cewa kana tafe ba. Yace karki damu tu tunda mun iso lfy. Sun gaisa da Abba sannan ya nufi gidansa. Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki. Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti. Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan sha. Tace, a’a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa. Ya tsura mata ido, “sauda nayi miki laifi ko? Ta kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi. Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai ta6a son wani cikin ‘ya’yansa kamarta ba. Amma dole ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa. Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share hawayen sa, saida tace “na shiga ukuna! Alhaji kukan me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani babban al’amari. Ta kama hannunsa. “Na roqeka karka 6oyemin komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa hannunta, “sauda karki tada hankalinki ba wani abu bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan cewa, na sa6a miki da yawa. “qara firgita tayi, gani takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, “sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani. Tunda munyi sallar isha’i, sai inje in sallami yara na inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin plate, tasa a gabansa. “in baka a baki?” yadan karkatar da kai, “bana tuna shekaru na matsawar ina gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka. Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam. Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano maganar Mimi ce damuwarsa. Batun ‘yan uwanta ta dauko masa na auren ‘ya’yan sa’ade ‘yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu. Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai. “sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai yarda ba shiyasa na haqura. Ya qura mata ido na ‘yan kakwanni. Ta shafi kumatunsa, “wai wannan kallon fa? Yace, karki tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. “wlh tsoron kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya. “sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a’a sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin ‘ya’yanki su samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin samun tarbiyyarki. Ma’anar in na mutu kuyi farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane. Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki. Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti. Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan sha. Tace, a’a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa. Ya tsura mata ido, “sauda nayi miki laifi ko? Ta kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi. Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai ta6a son wani cikin ‘ya’yansa kamarta ba. Amma dole ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa. Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share hawayen sa, saida tace “na shiga ukuna! Alhaji kukan me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani babban al’amari. Ta kama hannunsa. “Na roqeka karka 6oyemin komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa hannunta, “sauda karki tada hankalinki ba wani abu bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan cewa, na sa6a miki da yawa. “qara firgita tayi, gani takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, “sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani. Tunda munyi sallar isha’i, sai inje in sallami yara na inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin plate, tasa a gabansa. “in baka a baki?” yadan karkatar da kai, “bana tuna shekaru na matsawar ina gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka. Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam. Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano maganar Mimi ce damuwarsa. Batun ‘yan uwanta ta dauko masa na auren ‘ya’yan sa’ade ‘yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu. Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai. “sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai yarda ba shiyasa na haqura. Ya qura mata ido na ‘yan kakwanni. Ta shafi kumatunsa, “wai wannan kallon fa? Yace, karki tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. “wlh tsoron kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya. “sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a’a sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin ‘ya’yanki su samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin samun tarbiyyarki. Ma’anar in na mutu kuyi farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane. Hajiya sauda, cikin mamaki tace, kana da wani hali ne na daban? Domin in da za’a tambayeni halinka, zan bada shedar cewa, kai mutum ne na gari. Yace, “sauda kowane dan Adam ajizi ne, in dai ba ma’asumi bane. Harkoki na sunsa bana samun yin sallah akan lokacin ta. Harkokina sunsa ‘ya’ya na basu samu soyayyata ba. Harkokina sunsa ‘yan uwa maqota ban basu nasu haqqinba. Shawararki da nayi ta guje mawa ynxun na gano itace mafita. Zan aje tunani na na kullum, wato maida Naira ta zama Dala, ko ko taro ya zama sisi. Ta kamashi, tashi ka koma kan gado, bari in kwashe kwanukannan, in kuma tabbatar da yarana suna cikin makwancinsu. Ya miqe tare da komawa kan gadon. To karki jima maman yara. “Bayan fitowar ta ne ta tsaya bakin qofar, sannan ta daga hannunta sama, “Alhmdlh, ya Allah ka qara sa mijina akan hanya madaidaiciya. Kamar kullum daga dakin su Abdullahi ta soma har zuwa dakin su Zainab dasu Hasina. Nan ta dan 6ata lokaci don sai da taba Zainabu magani sannan ta fito. Zata shiga dakin su usaina saiga su sun fito. Tace, ina zakuje? Suka ce munason mu sake yiwa daddy sannu da zuwa, sannan muga jikinsa ne. Tace, to kuje yana ciki, ina zuwa nima. Dakinta ta shige don ta dan sake kintsawa cikin kayan varci. Su Hasana suka shiga dakin daddyn su bayan sunyi sallama, ya kuma basu izini. A hannun kujera suka zauna suka gaida gaida shi tare da sake tambayar jikin sa. Ya tashi zaune daga kishingidar da yayi. “kuzo nan yarana! Suka kalli juna cikin mamaki, sannan suka nufeshi. Ya ce, ku zauna bakin gado kyawawan ‘yan biyu na. Suka zauna. Ya dora hannunsa akan kafadar ko waccensu. ‘Yan biyu kuma fa kun girma, masha Allahu. Hajiyarku tace min zakuyi jamb da Waec ko? Suka sake kallon juna, sannan sukace “eh daddy mun kusa mu fara. Yace, to Allah ya baku sa’a. Suka ce Ameen. Ya sake cewa, me kuke karantawa ne? Ina nufin Art ko science? Usaina ta kalleshi “‘Hassana ce take science class, ni Art nike. Yace, Hassana zamu doctor kenan? Ta kalleshi cikin Jindadi tace, eh daddy inason in zama medical doctor. Yace, Usaina fa? Tace, daddy nikam ‘yar jarida nakeso in zama, ina sha’awar haka, shiyasa mass com zan karanta. Cikin farin ciki yace, nagode ma Allah. Allah ya cika muku burinku yara na. Daidai lokacin Hajiya sauda ta turo ta shigo da sallama. Ta kallesu da fara’a ” ‘yan biyu azo aje ayi varci ko? Suka miqe, sannan suka sake cewa, daddy Allah ya baka lfy. Yace, Ameen nagode. Suka ce, Hajiya saida safe. Tace, mu kwana lfy karku manta da Addu’a. Suka ce, to. Ta zauna tana kallon fuskarsa, “sun dameka da surutunsu ko? Yace, inason su saki jikinsu dani. Tace, ya kamata kam. Yace, “ynxun wace shawara zaki bani? Ta kalleshi “tame? Maganar da nayi miki dazun, ta damqa harkoki na ahannun yara, kamar yadda kike ta bani shawara tuntuni. Tace, ynxun kwanta kasha magani fa, in ka samu varci, gobe idan Allah ya kaimu, sai muyi maganar ko? Ya kwanta tare da cewa, Allah ya kaimu. Itama ta kwanto masa, tare da kashe fitilar dakin. Alhaji Bashir ya jima bai samu varci kamar na yau ba. Yaji dadin jikinsa daya farka, har masallaci yaje. Sannan da gari ya dan yi haske, sai yace, ki fitomin da kayan motsa jikina, zan dan fita. Likita yace, in dinga motsa jiki sosai, zufar da zan fitar tana fita da cutar. Hajiya sauda tace, tunda yarannan suna hutu, to ka fita dasu Abdullahi mana da Sadiq da Ameen da Umar. Take ya yarda sbd ynxun kam burinsa bai dara kusantar duk ‘ya’yan nasa ba. Suka fito cikin kayan motsa jiki. Yaran sun sa gajeran wando da riga mai gajeran hannu, yayin da uban yasa mai dogon hannu da kuma dogon wando. Yaran cikin murna, domin suna son fita motsa jiki sosai, Hajiya ce take hanasu, wai tace, batasan da wadanne irin abokai zasu hadu ba in sun tafi can gurin motsa jikin. Alhaji ya dube ta, “sai mun dawo.” Cikin salon tsokana tace, “to Alhajina. “Ta kalli Abdullahi, “Yarana masu albarka, ku lura min da mijina. Gaba daya suka sa dariya. Tace, da gske nakeyi Abdullahi, kar yayi gudu, tafiya kawai zakuyi. Suka ce “To” suka jera suka fita, biyu nan, biyu nan, suka sa mahaifinsu a tsakiya. Kafin ya dawo tuni ta dama masa kunun alkama da qosai. Qarfe takwas suka dawo, duk yayi zufa, yaran suka nufi dakinsu don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka masa tayi tayi, yayi wanka don nuna kulawa. Bayan yaci abinci, yasha magani, sai yace, ki shirya zamu fita. Tsaf tayi kwalliya cikin koriyar super da hijabinta wanda kyansa ya nuna tsadarsa. Qamshi take yi, ta bar sallahun komai gurin masu aiki tare da sauran yaran, sannan suka fita. Direban shi ya taso, Alhaji yace, je ka huta. Nine zanja motar. Saida ta zauna a gidan gaba, sannan ta kalleshi da murmushi. “kai da baka da lfy? Yace, sauda kowane lokaci in muna tare bana son mu samu na uku. Sai inga tamkar mu kadai ne a duniyarmu. “Tasa dariya, daidai lokacin daya tada motar. Tace, to kaba ni in tuqa mu. Kaifa jiya kazo. Yace, baki lura ina ganinki na samu sauqi ba. Ynxun ma kinsan ina zamuje? Tace, a’a. Sai da ya hau titi sosai, sannan yace, gidan saukar baqina. Inason muyi hirar da muka dade bamu yi irin ta ba. Sannan mu tattauna muhimman zantuka. Murmushi tayi batace qala ba. Kwance suke a tsakiyar gadon na dakin baqin, suna fuskantar juna, yace sauda na buqaci muzo nan ne musamman don in baki haquri, sannan in fada miki dalilaina. Sauda nasan cewa, na sa6a miki lokacin dana rabaki da ‘yarki na kaita ga wata, wanda harga Allah lokacin soyayyar Mimi ta rufemin ido har na aikata haka. Amma kika yi haquri. Sannan na biyu kece kadai zanyi wa ‘yarki abinda nayi mata, wato aurar da ita ga talaka ba tare da kin dagamin hankali ba. Da wata ce, cikin sauran matan, na tabbata da ranar aurenmu da ita zai mutu. Sai na qarshe kece kadai ‘yarki zata samu hadari, in hanata zuwa, kuma ta hanu. Sauda duk inda ake neman mace ta gari, kin kai. Ina roqon Allah yasa ki zama shugabar matana a gidan Aljannah. Cikin murmushin jin dadi tace, Ameen Alhaji. Ya tashi zaune. “sauda dalilina na aurar da Mimi ga malam Ismail, tare kuma da yanke duk wata alaqa da ita tare da cire ta cikin ahalina shi ne. Kashhh! Mu hadu cikin littafi na hudu, kuma na qarshe. K. Mashinku ce, sai na jiku a 08081165107 Chanjin rayuwa book 4 1⃣Saboda ta samu canjin rayuwa, daga jahilci zuwa ilimi, daga rashin tarbiyya zuwa tarbiyya, daga mara mutunci zuwa mai mutunci. Sauda, da farko nayi wa Mimi wannan auren ne don in quntata mata, in qona mata rai, kamar yadda ta qona min. Amma daga baya tunani ya shige ni, nayi nazarin dalilin wannan auren zata iya samun canjin rayuwa. Ismail zai iya bata ilimi na addini wanda ta rasa daga gareni. Sannan, ilimi zaisa ta zama mai tarbiyya ko dan yaya, tunda anbar shiri tun rani. Dalilin da yasa nace kar kuje gurinta, nima nace kar su sake nemana, sbd idn bata tare damu, zata fi samun tarbiyya. Shi ba zaiji shakkar mu ba, ko tsoron mu in tayi abin hukunci. Kuma yanda na lura dashi, bashi da shakka, kinga kenan ba zaiji tsoron duk wata barazanar ta ba. Haka kuma ba zamu taimaka musu da kudi ba, sbd shi kansa banason mu kashe masa zuciya, ya kasa neman na kansa, ko yaushe yana jiranmu. Haka kuma ita kanta rashin taimaka musun zaisa ta saba da Rayuwar babu, wadda bata sani ba ada. Yanke alaqa dasu shine zaisa ita da shi suyi abinda ya kamata. Hajiya sauda ta sauke ajiyar zuciya, "Na fahimceka sosai Alhaji, saidai nayi wani kuskure daya. "ya kalleta, na tura musu dubu dari. "karki damu, saidai karki sake tura musu kudi. Da zaki iya ma ko wayarsu karki sake kira. Ta danyi shiru tana nazari. Ya katseta, kar kisa ma kanki damuwa, nayi miki alqawarin bibiyar miki labarin duk halin da suke ciki. Ta tsura masa ido, a cikin qwayar idanunsa ta tabbatar da abin da yake fada. Tace, shikenan Alhaji. Allah yasa mu dace. Yace, "Ameen matar qwarai". Ya kama hannunta, "nasan ranki ya nutsu da yaron, kuma nima na fahimci cewa, yaron mai hankali ne. "Sukayi dariya. Yace, kinsan menene sauda? Tace a'a. yace, "Ni kaina ina cikin matsanancin kewar Mimi. Na sani sarai tunaninta ne ya hana ciwwonnan sauka. Tace, nasan za'ayi haka, amma tunda kanada wannan qudurin, wajibinka ne ka daure, ka jure, ka kuma kauda kai, sannan mu hada da Addu'a, Allah ya taya mu. Yace, Ameen ya rabbi. Ynxun kuma na samu natsuwa tunda Allah yasa kin fahimceni. Ranar nan suka yini suna qoqarin kyautata ma juna. 2⃣Haka itama Mimi tayi ta jinya, yaya Amina da Ismail suna matuqar kula da ita. 'yan uwan mamansu na Daura sunzo, sun duna jikin Mimi, sannan sun kawo musu kudin gonarsu da aka saida. Don haka shirye-shiryen tafiyar Ismail ya kankama. Haka nan 6angaren Mimi, zuwa ynxun Ismail yayi nasarar saka Mimi ta fara sallah dole, ba don ta so ba. Yawan nasiha da nacinsa ya sata sauraronsa. Ya nuna mata yadda zatayi sallah, kuma ya dauki nauyin yi mata akwalla. Ranar daya fara tsananta mata tayi sallah da kuka tayi sallar. Da farko ma bata yi ba, sai da yace shikam ba za yayi jinyarta ba, matsawar ba zata yi sallah ba. Ya nuna mata shifa tafiyarsa zaiyi. Yaya Amina ita ma cikin son ta tsorata ta tace, in ko ka tafi, nima zaman me zanyi? Kinga kenan saiki zauna babu mai jinya, ba mai kula dake. Tana kukan nata tace, yayi mata alwalla. Tun daga ranar, duk lokacin sallah in yayi, sai ta yita. Wani abin da yaba Mimi al'ajabi shine tunda ta soma sallah, sai ta samu kanta cikin wata natsuwa, ta kuma qara imanin cewa sallah tana kusanta bawa ga ubangijinsa. Haka kuma lokacin da yace zai dinga koya mata gajerun surori, bata qi ba sbd sallah. Kwanci tashi har taci wata daya da sati daya a asibiti. Lokacin ne kuma da Doctor din dabyayi mata dori ya dibar mata zaizo ya duba in dori yayi kyau, sai ya kwance. Ranar litinin da misalin qarfe goma na safe, likitan suka shigo shida doctor salis. Kallon qafafun nata kawai yayi, yace inasa ran cewa dorin yayi kyau. Zan kwance shi ynxun sai ku kaita ayi mata hoto, sai ku kawo mu gani. Ismail cikin murna yace, Alhamdulillahi, dama na gaji da zaman asisibitin nan, har ita ma khadijan ta gaji ko?. Ya fada tare da kallonta. Mimi ta kalli likitan, kenan in hoton ya nuna cewa, dorin yayi za'a sallameni ne? Likita yace, eh, to ku daiyi hoton mu gani. Bayan an kwance tana ta shagwa6a, ta qanqame yaya Amina. Likitan yace, a kaita hoto ynxu. Ismail ke tura ta a kujerar tura marasa lfy suka nufi gefen hoto. Yaya tana jere da shi suna magana. Yace, "Yaya Allah yasa hoton babu tsada sbd Kinsan fa babu sauran kudi, gashi kudin dakinmu dana sake biya ya qare. "Wai saura nawa ne ma kudinnan da aka ajiye sbd tafiya? Yace "ta6" ai baifi saura dubu goma ba acikin dubu hamsin din dana ba Mahmud don kar in kashe, amma duk sun qare. Tace, ai dama zara bata barin dami. Barkanmu da sallah sis 🙌 [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣A qofar gidansu yakeyin wankin, amma yanajin nauyin shanya kayan Mimi a igiyar waje, sbd duk qananan kaya ne matsattsu. Sannan har pant din ta yake wankewa, don haka sai ya daura igiya acikin zauren kusa da qofar dakinsa yana shanya kayanta a gurin. Wani lokacin ma sai ya jira sun dan sha kadan ya kwashe, sbd yaran Gidan marasa ji, wani sa'in suna zubo da kayan qasa. Yau ma daya gama wanka, yayi shirinsa zai fita, sai ya kwashe panties din da vests yaje ya shanya su kan akwatunanta, ya kunna musu fanka, sannan ya kulle qofar ya nufi gidansu Mahmud. Hirarsu kullum bata wuce ta tafiya. Mahmud yace, Ismail kasan Rabi'a ta daga hankalinta akan batun tafiyarnan? "saboda me to?" Inji Ismail. Mahmud yayi 'yar dariya, wai tana tsoron kar in hadu da wata acan in manta da ita. Nace ta daina wannan tunani, tana damun kanta bayan anyi mana baiko. Sai tace, to yaushe zan dawo? Nace mata ban san lokacin ba. Shine take fushi dani. Ismail yace, mata kenan 'yan rigima. Ni baga wannan shagwa6a66iyar Yarinyar ba. Lokacin da zan fito fa kuka takeyi, wai bazan fito ba. Mahmud yasa dariya, to ba yaya Amina tananan ba? Yace bata nan, tana gidansu. Tazo dai da safe, amma ta koma sbd batajin dadin jikinta. Kasan Allah, Mahmud na gaji da zaman asibitin nan, ita kuma gata da shegen son jikin tsiya. An ce, ta dan dinga dan takawa, amma taqi. Shiyasa na barta ita kadai don tayi zuciya ta motsa. Mahmud yace, Ismail saidai fa kayi ta haquri, domin yarinyarnan cikin shagwa6a ta taso, hakan ya zama jinin jikinta. Ai ma kaci nasara tunda tana cin duk abin da aka dafa aka bata, sannan ta amince zata zauna daku. Ismail yace, ni damuwa ta ynxun, inda zan barta in zamu tafi. Mahmud yace, inda lafiyar ta lau ne, da sai mu tafi tare da ita. Ismail yace, kasan Allah, ko lafiyarta lau bazan iya tafiya da ita ba, haka kawai taje ta dameni. Tunanina in barta gurin yaya Amina da mijinta, tunda suna da dakin yara, da kuma dakin da mahaifiyarsa da take ciki kafin ta rasu. 6⃣Mahmud yace, hakane, kai ai yaya Amina tanada zumunci. Nasan ma ba zata qi ba. Ismail yace, ba zata qi ba insha Allah. Yaya Amina, aita zamar min uwa saidai ince Allah ya bani ikon yi mata biyayya. Mahmud yace, Ameen, ai tafiyar tamu ma tazo. Naji yana cewa nan da qarshen wata, sati uku dai a taqaice. Ismail yace, tabbas tafiya tazo, Allah dai yasa a sallamemu kafin ranar. Kai ni gobe ma zan samu likitan ince masa sallama kurum nakeso. Mahmud yace, kafin su sallameku, ya kamata itama ta dan taka su gani. Matsa mata ai zakayi. Sai daf da magriba sannan suka rabu. Gida ya koma ya kwashe kayan shanyarsa, sannan ya daukar mata wasu kayan ya nufi asibitin. Yana sauka ana tada sallah. Don haka sai ya bada ajiyar ledarsa cikin wani shago, ya shiga sallah. Har zai bari sai yayi isha'i, sai kuma ya tuna itama tana buqatar yin sallar. Zaune ya same ta akan gadonta, taci kuka ta gode ma Allah. Tausayinta ya kamashi, amma sai ya dake tamkar baiga fuskarta ba. "Muje kiyi alwalla! " Tayi banza dashi. Yazo zai dauke ta zuwa bandaki, tace, ka barni, ka tafi abinka. Dama nasan dole ka gaji dani, iyayen da suka haifeni ma sun gaji dani, sun gujeni bare kai da suka jona maka ni? Banga laifin ka ba. Amma meyasa kasa nayi maka alqawarin zama tare da ku bisa sharadin cewa zaka kula dani, sai gashi tun kafin mubar asibitin ka gaji? Nasan kaida 'yar uwarka kuna dawainiya dani, amma yadda ka nuna nima 'yar uwarka ce, na zata za'a dan jima kafin in gundureku. Ismail yadan tausasa murya, cikin sigar lallashi yace, wai waya fada miki cewa, mun gundira dake ne? Ni kin bani haushi ne yadda kk qi kidan taka ko sau daya ne. Kuma khadija wanki naje nayi miki, ya sake matsowa kusa da ita daf, yasa hannu ya dago fuskarta, cikin wani salo ya kira sunanta, khadija! Ta dago jajayen idanunta ta kalleshi. Yace, "Wlh baki gundiremu ba, kuma bamu gaji dake ba, kuma ke 'yar uwarmu ce. Tace, nidai nafiso ka bani saki na, ka tafi abinka. "Ya dora yatsansa akan la66anta, "shhhh, ki daina cewa haka mana qanwatah. Kiyi haquri! In kaiki kiyi alwalla ko? Taqi magana. Da qyar ya lallasheta, sannan ya kaita alwalla. Bayan isha'i ne tana cin cake da fanta, yace, kinji tafiyarmu zuwa qarshen wata ko? Tayi takwa-takwa da fuska "to ni kuma ina zaka barni? Ya kwaikwayi muryarta, shine nakeson muyi shawara dake. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwan 3⃣Mimi, wadda ake turawa tana jinsu, duk qarma-qarmar da yakeyi tana jinsu, kuma ta sani. A zaton ta ma da kudinta akeyi mata komai, har suka qare ya shiiga nasa. Tace, to yaya Amina su sallamemu mana tunda dai babu kudi. Yaya ta kalli Ismail, "Nima nawa tunanin kenan, ko ya ka gani? Ismail yace, bari dai ayi hoton mu gani. Allah yasa dai kudin babu yawa. Ynxun ma tunanina ko zan barku anan inje in amso ragowar na hannun Mahmud. Yaya tace, muje dai, in kaji kudin, sai ka tafi. Dubu shida da dari shida ne kudin hoton, don haka dole ne ya tafi ya amso ragowar kudin, kafin ya isa, saida ya kira layin Mahmud din, don haka mai acha6ar da ya kaishi, shine ya dawo dashi. Don haka suka biya akayi musu, sannan suka amshi sakamako suka koma. Sai sha biyu sannan likitan ya dawo ya duba, yace Alhmdlh, kuma tana da jiki mai kyau. Don haka zata iya soma koyon tafiya. Ismail ya kalli doctor. Ismail ya kalli Doctor salis yace, za'a iya Sallamar mu? Sbd gsky duk abinda muke dashi ya qare. Doctor salis yace, karka damu malam Ismail, kayi qoqari sosai. Ba duka namiji za'a samu ya tsaya kan matarsa haka ba. Mimi ta dago, ta kalli Ismail, idanun ta da alamun tambaya. Sai yayi murmushi, ya kalli likitan, ai yaya baya kasa dawainiya da qanwarsa. "Take likitan ya kalli Mimi, sai ya tuna 6aran6aramar da yayi, don haka yace, "oh na manta hakane, yaya ne ashe. " Yammacin ranar, Ismail babu yadda baiyi ba da Mimi ta dan soma takawa, amma taqi, sai kuka takeyi wai ba zata iya ba. A qarshe haushi ne ya cika Ismail ya fita waje ya zauna akan benci. Tunanunnuka ne kashi-kashi suka addabeshi, yana mamakin yadda yaketa neman layin Hajiya sauda, amma baya samu itama kuma ta daina kiranshi. Sannan yau sati uku kenan da ita hajiyar ta sallami Mahmud daga koyar dasu hasana. Ko yaushe in Ismael yayi ma Mahmud wannan qorafin, sai yace, karka damu ni dama ko basu sallameni ba, dole in barsu tunda kaga karatu zamu tafi. Game da rashin waiwayar 'yarsu kuwa ka qara haquri. 4⃣Gashi yana tunanin ina zai samu kudi, ko ba don ciwonta ba, ko don sbd tafiyarsa. Sannan in an sallamesu, ina zai ajeta? Domin gsky bai kyautu ba yasa ta dakin zaure.Duk bama wannan ba, gurin wa zai barta? Yana jiyo ta daga ciki tana magana cikin shagwa6a, "to kazo mana, ka kamani zan kwanta ne fa kaji! Shiru yayi mata, sai dai zuciyar sa tana tambayarsa meyasa ynxun Mimi bata kiran sunansa? Bata cewa, Ismail, bata cewa, malam. Nauyinsa take ji, ko menene? Oho! Tayi, har ta gaji tayi shiru. Saida yaji kiran sallar la'asar, sannan ya shiga dakin. Har lokacin idanunta da hawaye. Ya kalleta, sai kuma ta bashi tausayi, yace, khadija! Taqi kallonsa. Ya gane alamun tayi fushi kenan. Yace, zan yi miki alwalla ne, nima zan tafi masallaci. Ta kumburo baki, to ka kiramin nurse Ramatu. Inaso inyi fitsari ne. Yace, ba zan kira wata ba. Muje in taimaka miki. Nurse dinnan fa da kkga tana kulaki, ina bata wani abu. Kwanakin nan da bani dashi, ban bata ba, kinga tana shigowa? Mimi tace, to fa, kai namiji ne, shine zaka taimaka min? Banida lokacin 6atawa khadija, sallah zanje. Menene zaki 6oyemin wanda ban gani ba? Kuma tunda ni matsayin wanki nake, ai ba wani damuwa. Ta zaro idanu, me ka gani? Bayan yaya Amina ce takemin komai. Da zaka ce... "kafin ta kai qarshen maganar, har ya dauketa cak ya sakata a toilet din. Ya zaunar da ita a kan kujerar da yaya Amina kan zaunar da ita in zatayi mata wanka. "sai kuma me zan taimaka miki dashi? " ka fita nidai kawai! Zaki iya yin komai harda fitowa? Tace, nidai ka fita! Murmushi yayi sannan ya fice, "to karki dade, kusan mintina hudu tace, "to kazo ka fito dani! Tayi maganar, ranta a 6ace. Ya shiga, inyi miki alwalla? Ta turo baki, "ni nayi abina. "A qasa yayi mata shinfidar sallah, yace, kiyi a qasa, tunda an kwance maki. Yasa mata hijabin sannan ya fita. Bayan ya dawo ya soma hada kayan da yaya Amina ta cire mata da safe. Yace, zanje gida inyi wankinmu, ya dan taru, sai kuma inyi wanka. Ta 6ata rai, cikin shagwa6ar ta tace, ni kuma ka barni da wa? Yace, da Allah mana! Dama shine mai tsarewa. Kinga kuma kinji sauqi babu laifi ko? Ya qarasa cikin sigar lallashi. Ta matse kafada cike da shagwa6a, idanunta suka soma zubo da hawaye, nidai bazan zauna ba. Ya ce, (cikin takaici ) karki zauna, inkin gaji da zaman Asibitin kidan taka mana, ki yarda kidan taka ko a sallamemu, amma kinqi. Ya dauketa cak ya dora ta akan Gado. Sai na dawo. Bata dai ce komai ba, shi kuma yayi tafiyarsa. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣Ta aje cake din hannunta akan gado, "Nidai ka tafi dani mana." yace kwantar da hankalinki, wannan ba abin damuwa bane, ga yaya Amina, sai ku tare, inkin sauqi sosai, in nazo sai mu tafi. Tace, to ka fadawa yaya Amina dinne? Yace, ban fada mata ba, amma nasan cewa ita babu matsala. Tace, shikenan yaya jikinta fa? Yace, da sauqi, dukda banbi ta gidanta ba. "Ya ciro wayarsa, bari in kira Abban su saddam ya bata mu gaida ta. "sun gaisa da abban su saddam, sai ya tambayi mai jiki. Abbansu saddam yace, gatanan tanata rawar sanyi, ta qudundune, ta dai sha magani. Ismail yace, to ka gaisheta. Khadija ma tanayi mata sannu. Abbansu saddam yace, zataji. Ya kalli Mimi, kinji har ynxun jikin ko? Tace, Allah warki yaya! Allah ya bata lfy. Washe gari yaya bata samu zuwa ba, sbd jikin nata. Ismail yace, to yau yaya zamuyi da wanka? Ko in miki? Ta zaro idanu, tana kallonsa, a ranta tace, shi wannan nufinsa dole sai yaga tsiraici na ne? A fili tace, na haqura sai taji sauqi. In tazo zatamin, harda gashina zata wankemin, yayi datti, duk ya dameni. Yace, wai meyasa baki yarda dani ba, sai kace zanyi miki wani abu. Ki tsaya ko gashin ba sai in wanke miki ba? Naga yadda tayi miki ranar nan mana. Tace a'a karka samin ruwa a kunne. Ni saloon nakeson zuwa. Yace to yau kidan taka ne mana khadija. Kinga basu so mu tafi da wata matsala ne. Da sunga kindan taka zasu sallamemu, sai in kaiki duk inda kk so. Ranar dai da qyar ya samu ta dan taka, daya biyu yana sagale da ita, sai ko ta fada jikinsa. Wani iri yaji, tsigar jikinsa ta motsa. Yayi mamaki, bai ta6a jin haka ba aduk irin daukanta da yakeyi mata a cikin wannan jinyar. Cikin sauri ya dagota daga jikinsa, muryarsa a sarqe ya dago ta, "kin cika ragwanta, to zauna kidan huta. 8⃣Cikin sati daya, mimi tana dan fita tare da taimakon yaya Amina don taji dan sauqi ta dawo, da kuma taimakon uban gayya, Ismail. Burinsu lokacin a sallamesu, domin basuda kudi a hannunsu. Ranar litinin kuwa Doctor salis da lukman, likitan da yayi mata dori suka tabbatar ma da mimi sallama. Ismail yayi murna tamkar dan kurkuku a ranar daya fito. Duk sunyi murna sosai. Yace, ma yaya Amina ta shirya kayansu, shi kuma zaije ya dan karkade dakinsa. Yaya tace, ina zata? Gidanmu zamu wuce tunda mun riga mun sanar da Abbansu saddam. Yace da inason indan gyara mata dakin na Gidanku, tare da dan sa mata abin kwanciya kafin dai mu wuce. Tace, hakane. Tare da Mahmud suka share ko ina na dakin sannan suka dauki shatar tasi zuwa asibiti. Likitoci da Nurses sunyi masu murna da barin asibitin, nan ne ma Doctor salis ya basu tabbacin cewa, duk lokacin da wata bukatar taimako ta taso, to qofa a bude take su tunkareshi. Yaba Ismail katinsa mai dauke da lambobinsa a jiki. Ismail ma bai qwauron baki ba ya fada masa cewa, shi zai tafi karatu ne a madina, amma duk abinda ya taso ga yaya Amina nan. Doctor salis yayi masa fatan alheri, tare da samun nasara. Zainabu tana zaune a bakin gadonta da 'yar rediyo a hannunta, tana sauraro. Ta babansu ce ta dauko lokacin da zata dawo gdn Alhajin bayan barowarta daga asibiti, sosai rediyon ke debe mata kewa, da shirye-shiryensu, musamman wanda suke karanta littafin hausa. Da ta qagara taji wani littafi da ake karantawa, sai ta samu bushira tana ce mata ina zata samu littafai? Bushira tace mata, sai dai na haya. Wannan ne mafarin karance-karancen ta. Kuma suna debe mata kewa don tana cin karo da matsalolin da suka zarta nata. Kuma tana qaruwa sosai. Don haka sai tayi haquri ta dangana, ta kuma ci gaba da kai ma Allah kukanta. Shi kuma Alhaji lawal bai canza ba, saima abinda yayi gaba. Hakanan wani abin dake damunta shine tunda ta dawo gidan batayi al'ada ba. Saidai bataji wani canji a jikinta ba. Tsoronta daya, kar dai wani cikin ne ta sake samu, domin gsky ba tada burin hada zuri'a da Alhaji lawal, sai dai masoyinta Ismail. Kullum cikin sa take, duk da wata zuciyar tana fada mata cewa, Ismail yayi mata nisa. Amma bata debe tsammani ba tunda tana Addu'a. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣Haka rayuwa take, dama idn kace tukunyar wani bazata tafasa ba, taka ko dumi ta bar yi. Na fadi haka ne sakamakon gani halin da Na'ima take ciki, Ga ta kwance cikin halin laulayin ciki, amma shi ko a jikinsa. Gashi irin crikinnan ne mai aman tsiya. A qarshe ma da yaga ba zata yi masa wani amfani ba, sai ya yaye zaman gdn. In ya fita tun safe sai dare. Bata sanin shigowarsa, sannu bata hada su. Ganin abin yana qara gaba, ta daga waya ta kira momy tace mata, "ki fada masa zanzo in maido ki nan gida gurina, tunda daddyn ku yana katsina ba zaisan kina gidan ba. Washe gari da sassafe kafin ya fita, Na'ima da bin bango takai saman Abbas, ya fito cikin shirin fita ya ganta sharkaf a kwance a falo, cikin tsawa yace, ke! Ki fita a falona banason qazanta, karki sake kiyimin amai anan. Cikin numfarfashi tace, don Allah ka kaini Gida, su kaini asibiti. Yace, ba zaki haumin mota ba, saidai in ki kira su, suzo da tasu, su daukeki, su 'yan gidan naku. "yace ke sauka muje zan rufe gefena. Tace, to don Allah ka kiramin su. Yace, banida lambar kowa a Gidanku. Qiri-qiri yaqi kiran su sam, sannan ya tasa qeyarta har dakinta ya fice abinsa. Ita ce ta sake kiran momy ta fada mata komai. Momy tace, gatanan zuwa. Gidan aminiyarta Nana ta soma zuwa, ta karanto mata komai. Nana ta sa6i mayafinta tace, muje Gidan uwarsa domin lallai sai tasan halin da ake ciki, in yaso ta jawa danta kunne. Momy Nafisa tace, shiyasa na biyo ta gurinki, don nasan dole zaki kawo shawara mai amfani. Cikin motar Momy Nafisa suka dunguma zuwa gdn minister. Saida masu Gadi sukayi waya cikin gdn bayan sun fadi ko su suwaye, sannan aka basu izinin shiga ciki. A falo aka dauke su. Sunfi qarfin minti sha biyar sannan masu aiki suka kawo musu abinsha. Cikin isa da cin magani, Hajiya Bilkisu ta sauko gurinsu, dai-dai take kallonsu. Hakan yasa su momy Nafisa yin dari-dari. 1⃣0⃣Hajiya Nana ce tayi qarfin halin cewa, Hajiya dama abinda ya kawomu, qara muka kawo miki, qaran Abbas. Sai sukaga tayi wani murmushi, wanda ba zasu iya fassara shi ba. Hajiya Nana taci gaba da cewa, tunda muka kai yarinyarnan banda wulaqanci da cin mutunci babu abinda take fuskanta daga gareshi. Gashi ynxun tana fama da laulayin ciki amma yaqi ya kaita ko asibiti. Momy Nafisa tace, kuma banda diban matan banza babu abinda ya... "Hannuwan da Hajiya Bilkisu ta daga shine ya dakatar da Momy Nafisa. Cikin matsanancin 6acin rai, Hajiya Bilkisu tace, ina zaton kun manta alaqar dake tsakanina dashi ne, kuka zo kuna aibanta shi a gabana. To bari in tuna muku, shine dana na farko, nasan dukkanku kunsan zaqin soyayyar dan fari ko? Ta miqe tsaye, wato ku ga masu 'ya ko? To ni kunsan abinda 'yar taku tayiman da qawayena? Taje daf dasu ta zauna akan hannun kujera, in baku sani ba, inason kuje ku tambayeta. Hajiya Nana tace, tayi mana bayani, kunzo kun buga qofa bata san cewa ku bane, tayi zaton ko Abbas ne da matan da yake kawowa, tunda yana zuwa dasu harsu kwana. Ranb Hajiya Bilkisu ya sake 6aci, ta nuna Hajiya Nana, "kece lauyar Na'ima? Watau in shine sai taqi bude masa gidan, don tana taqama gidanta ne ko me? Momy Nafisa ta tausasa murya, ba tana nufin wai don Gidanta bane, kinsan dai kishinmu na mata, ko ke da girmanki ba zakiso mijinki ya shigo miki da matar banza cikin gidan aurenki ba ko? Hajiya Bilkisu cikin tsawa tace, don Allah ku saurara min, ya kawo mata dubu ciki gidan, ba Gidansa bane? Ko da kudinta yake bin mata? Ba Kuma sammata zunubin za'a yi ba. In bata iyawa ga hanya nan ta fita. Yarinyar da bakuyi mata tarbiyyar arziki ba sai rowar tsiya. Naje nida qawayena tayi mana rowa. Haka yara da suka je ko dan turare ta gagara basu. Sbd haka shi kansa bakusan abida take masa ba. Don haka ya kamata ya nema, lokacinsa ne. Ku fita a Gidana! Kuje kukai 'yarku asibiti, ko nawa aka caza zamu bada albarkacin danmu da take dauke dashi. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣1⃣Momy Nafisa tace, kin bani mamaki, da sunan wasa ban zace ki ahaka ba. Hajiya Bilkisu tace, nafi nan, in dai akan yarana ne. Haka kema ban zaci 'yarki bata samu tarbiyya ba. Hajiya Nana tace, zo muje! Kuskure dai anyi shi tunda aka basu aure. Hajiya Bilkisu tace, Eh kuje, bazan takura ma dana ba, ya mori quruciyar sa da lafiyarsa. Haka dai aka rabu ana fadawa juna magana. Gidan Na'ima suka dire, inda suka dauke ta zuwa asibiti. Kai tsaye Gado aka bata sbd halin da take ciki. Momy Nafisa ta kira Alhaji bashir ta fada masa cewa, an kwantar da Na'ima a asibiti, kuma an tabbatar musu da cewa, tana dauke da juna biyu. Daganan bata fada masa komai ba. Lokacin data yo wayar, Alhaji suna zaune a babban falo, shi da saudar shi da kuma yara. Nan suka shiga murna kamar ance ta haihu. Yace, abata wayar. Momy tace, tana varci. Yace, ko inzo in duba jikinta? Tace, a'a kayi zamanka Alhaji. Jikinta da sauqi. Kasan dama shi ciki, in an dauka, sai an sauke kafin a samu lafiya gar-gar. Yace, haka ne. To, zamu kira in ta farka. Sauda tace, bani mu gaisa, suka gaisa. Tayi mata murna, tare da fatan samun sauqi. Bayan sunyi sallama ne, sauda tace, al'amarin Allah kenan, mai rayuwa cike da canji, da kuma launi kala-kala. Dama rabon a gurin Na'ima yake, shiyasa Mimi ta bijire. Yace, hakane. Allah ya nuna mana daidai ya bamu ikon bi. Yace, Ameen. Ta danyi jim, ita kuma Mimi ko menene labarin ta? Oho. Alhaji yadan runtse ido, sannan yace, tana samun sauqi insha Allah. Allah yasa, inji Hajiya sauda. Kwanan Na'ima uku a asibiti sannan aka sallameta, suka wuce Gida. Abbas dai baizo ba, amma Hajiya Bilkisu tazo ta kuma biya kudin komai. Shi ko minister baisan komai ba, saida Alhaji bashir ya kira shi yace, kai zanyi wa murna ko juna za ayi wa murna? Minister yace, tame? Na'ima tana dauke da jikanmu. Ba ka samu labari bane? Cikin murna minister yace, bani da labari. Kasan yau kwana na uku bana qasa. Ynxun haka durowa ta kenan, ina filin jirgi. Kaine mutum na farko da na amsa wayarka. Nayi murna sosai, kuma naji dadi qwarai. Amsarka kuma ni za'a yiwa jika. Domin kai ka dauki dan Gidan Abba. Suka sa dariya, sannan sukayi sallama. Cikin murna minister ya isa Gida, sai dai baiji kowa yayi masa batun jikan da zai samu ba. Hajiya Bilkisu tana rawar jikin tarbar sa ta hanyar abinci da sauran kyautatawa. 1⃣2⃣Ya Kalli abicin sannan ya kalleta, "Wai ni banji kunamin batun jikan da zan samu ba. Wani abinda kuka bani haushi, wanda ya kamata ace nina bashi labarin qaruwar, sai shine yake bani" Da sauri ta soma neman yadda zata wanke kanta, sbd tasan shi akwai maida qaramar magana babba. Tace "wai dama Alhaji ban fada maka ba?" kaina bisa wuya. Ya dauki cokali, "ta yaya kk zaton zan manta da wannan babban labarin in har kin fadamin? Ta dora hannunta akan nasa, kayi haquri nayi tsammanin cewa, na fada maka sbd hankalinmu yana tashe, ita Na'imar ce babu lfy. Yace, banji haushi ba Bilkisu. Na dai yi miki takaicin rasa goron albishir daga gareni. Yace, Abbas din fa? Shima bai fadamin ba, kodai wani abu ya faru ne, ko kuma yana shirin faruwa? Tace, babu wani abu, ina zaton dai bai wuce, jikin matarsa ba, kuma ga yanayin aiki. yace tana gida ne ko asibiti? Ta soma in-ina, "eh, a'a tana asibiti, amma munyi shawara in an sallameta su wuce gida, sbd ta dan qara samun qwarin jiki. ya aje cokalin dake hannunsa, "ban amince da wannan Shawarar taku ba! Wai keda wa kuka shawarta? Tace, da Abbas ne da kuma mahaifiyarta. Yace, to nan Gidan ya kamata ta dawo, sbd jikana ya saba da gidansu tun kafin ya iso Duniya. "A ranta tace tirqashi! Wannan wace irin qaunar jika ne haka? Amma a fili sai tace, ai sai a canza shawara, duk ba laifi bane. Yace, shi kuma Abbas yazo, shima jikana a bude masa account din, kamar yadda nake yiwa 'ya'ya na. Sannan jikana na fari, in ya kasance namiji, zanyi masa kyauta mai tsoka. Yayi 'yar dariya, meya kamata in ba jikana? Hajiya Bilkisu, wadda abubuwa uku suka tarun mata a lokaci daya, qaryar da tayi masa, takaicin dawowar Na'ima Gidansu, ga kuma kudin da ta lura za'a 6arnatar ma cikin. Cikin yaqe tace, sai mu jira mu gani me zamu samu? Yayi 'yar dariya, kuma fa Gskyrki ne, qila ma 'yan biyu ne. Ta lumshe ido sbd takaici, sannan ta bude, Allah yasa haka. Yace, Ameen. Yana shiga wanka, ta nufi dakinta. Cikin sauri ta kira Abbas a waya, ta karanto masa duk yadda sukayi. Tace, ynxun yaya kkga za'ayi? Domin dadynku ya zurfafa da qaunar abinda ke cikin matarka. Abbas yace, karki damu, zanje gidan kuma dole ta dawo. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣3⃣Na'ima tana zaune a dakin momy tana cin tuwon semo, suhaila ta shigo, tana cewa "sis Na'ima ga Abbas nan yazo da abokansa. Na'ima ta ture tuwon dake gabanta gefe, tare da jan tsaki, tace, ni bazan fito ba harma naji na qoshi. Suhaila tace, suna tare da momy ai. Na'ima ta fito falonta, ta tsaya inda ba zasu ganta ba. Tana iya jiyo muryar Abbas yana cewa, "Ayyuka ne suka sa ni banzo asibitin ba, amma ai momy tazo. Tace, Momyn taka me tazo tayi in ba wulaqanci ba? Don haka inason in fada maka babu inda Na'ima zataje. A Gidanka ma bataji dadi ba bare a gidan iyayenka? Usman yace, ayi haquri dai momy. Nan da can duk daya ne. Momy tace, ba zataje ba. Abbas yace, shikenan zan kira daddyn nan gidan. In ba zata koma ba, saidai mu rabu. Momy tayi shiru, ta kasa magana. Domin tasan Alhaji baisan komai ba a kan matsalar. Da qyar tace, ka fada masa mana! Zai matsa mata dole ne? Abbas ya miqe, ku tashi muje su usman! Zan bada mamaki Gidannan. Suna fita Na'ima ta fito tana kuka tace, Momy ni bazan koma Gidansa ba, bare Gidan iyayensa. Ni tsoron mamansa ma nakeji. Momy tace, qyaleshi yayi ta fadama daddynku din. Ynxun ne suka san ki koma can? Da suna so ki koma da basu kaiki asibiti ba? Na'ima dai sai kuka, ita kuma momy tana lallashi. Shi kuwa Abbas ya gama tsara ribar da zaici gurin mahaifinsa da wannan cikin. Ynxun burinsa a samu namiji kamar yadda mahaifinsa ke matuqar so. Haka kuma shi da mahaifiyar sa suna ruwan ido akan abinda ya kamata su za6a a matsayin kyautar da kakan zai bawa jikansa. Shi dai yana sha'awar gidan saida motocin Alhajin nasu, yayin da Hajiya Bilkisu ke sha'awar wani kamfanin Alhajin. Ranar asabar, Alhaji Bashir yana zaune a bayan mota tare da 'yan samarin sa guda hudu, malumfashi suka nufa gurin Hajiya Binta. In sun kwana biyu su wuce masari don ganawa da dangi, wato su ziyarce su. Wayarsa ta buga, Ameen ya miqo masa, yana kallo yaga lambar Abbas. Bai ta6a kiransa ba. A fili yace dan nemabbaka ta6a kirana ba, sai yau da aka samu qaruwa. Ya daga suka gaisa, sannan yace, daddy dama inason in fada maka ne an sallami Na'ima daga asibiti, amma momy tace, ba zata dawo gida ba saidai ta zauna Gida gurinta. To kuma daddyn mu daya dawo yace ta koma can gidanmu gurin Hajiyarmu. Da naje don mu taho, sai kuma momy ta hana. Ran Alhaji Bashir ya 6aci matuqa, cikin zafin rai yace, karka damu zansa akawo ta har gurin Hajiyar taku. Abbas yace, nagode daddy. Alhaji yace, babu komai. Suna yin sallama ya kira layin momy Nafisa, tana dagawa, ko amsa Sallamar ta baiyi ba ya soma ruwan bala'i. Nafisa kina hauka ne zaki rabo yarinya da Gidanta? Sbd me? Ba zan amince ki zubarmin da mutunci ba, in har ke baki damu da naki mutuncin ba.1⃣4⃣Tace, tsaya kaji Alhaji! Ba zanji komai ba. Ya katse ta. Zan kira Hamisu ynxun nan yaje ya kai yarinyarnan Gidan minister, kamar yadda suka buqata. Sannan zan gargadeki, kar ki bari inji wata matsala ta fito da sunanki a ciki, ko wani tseguminku na mata. Aure zaki kashe mata ko me? Tace, kasan da Yarin..."ya sake katseta, ba nace kiyimin shiru ba ne? Kinsan Allah kikayi sanadin kashewa yarinyarnan aurenta, ko kuma kika zama silar matsala tsakanina da Abokina, wlh saina baki mamaki, zan yi miki abinda baki zata ba bare tsammani. Ke baki da hankali ne? Baki ganin halin da nake ciki na rashin Mimi da kuma ciwon dake damunap. Shiyasa har in koma ga Allah ba zan daina son Sauda ba da ganin qimarta da girmanta. Kizo katsina ki ganni, kiga yadda na samu lfy da kwanciyr hankali, sbd ina tare da mace ta gari mai tattali. To na fada miki, ki fita idona in rufe. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayarsa Momy Nafisa, tayi shiru da waya a hannunta, bata ta6a ganin ranar da Alhaji yayi dogon sababi ba kamar na yau. Bata da wani za6i face, yin abin da yace, amma dukda haka saida ta kira layin Hajiya Nana, ta fada mata cewa, Alhaji yace, lallai sai Na'ima ta koma Gidan surukanta. Hajiya Nana tace, ki barta ta koma zamu san yadda zamuyi mu samu mafita. Tana aje wayar, Hamisu yana shigowa. Ya gaida momy, ta amsa rai 6ace. Yace, maigida yace... Ta katseshi, karka cikani da surutunka! Jeka naji, zata zo inta shirya. Ta shiga dakinta inda Na'imar take kwance kan gado, ta zauna a bakin gadon. Na'ima taso kiji! Tace, menene? Bayan ta taso, momy tace, ki tashi ki koma can gidan su Hajiya Bilkisun. Na'ima ta soma kuka, ni ba zanje ba momy. Gsky, na haqura da auren Abbas. Baya sona ko kadan. Momy Nafisa ta riqe kai, cikin damuwa tace, kai ni dai wannan abu ya isheni dai, wannan abu ya isheni. Duk nice na jawoshi. Inda nasan ma haka halin Abbas din yake, wlh da nabar Mimin ta auri Abbas din. Na'ima tace, inda itan ce na tabbata ba zai mata haka ba, don yana mugun sonta. Momy tace, yi mata zaiyi dan bariki, dan bariki ne. Da an gama soyayyar, za'a shiga tsiyar. Ke dai ynxun ki tashi muje can din mu gani. Na'ima tana kuka, tana komai ta kwashi nata ya nata aka nufi Gidan minister da ita. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣5⃣Mimi tana zaune a tsakiyar katifar dakin Ismail na zaure, da idanu take ta bin dakin da kallo tamkar bata ta6a shiga cikinsa ba. Ismail dake qoqarin kunna mata 'yar tsohuwar fankarsa, ya kalleta, "me kk kallo a dakin? Shine dai, ba'a qara komai ba, kuma ba'a rage komai ba. Mimi batasan ma yayi ba, tunaninta yana can gurin sashinta na Abuja, amma dubi inda take ayau. Gsky bata ta6a tsammanin ko a cikin mafarkinta abinda ya faru dinnan zai faru da ita ba. Kuma kowane lokaci tayi dogon tunani don ta gano menene laifinta a cikin duk wadannan abubuwan da suka faru, amma bata gano ba. Kowane lokaci tunaninta yana tsayawa ne akan laifin na mahaifanta ne. Tafi dogara akan cewa, basa sonta ne, ko kuma tace, daddy ya daina sonta, don dama can Hajiya ba wai tana sonta bane. Da wannan ta dogara, takeson nesanta kanta dasu iyayen nata yadda ba zasu sake jin labarinta ba. Ismail dai tsaye yayi yana kallon yadda hawaye ke kwaranya daga idanunta. Dukda cewa ya saba da ganin kukan mimi, amma daga ganin wannan na musamman ne. Da haka ya nufi gurinta, ya zauna a gefen katifar, cikin sanyin murya ya kira sunanta, "khadija! Kina jina khadija? Kina jina? A firgice ta kalleshi, yace me kk yima kuka? Cikin shasshekar kuka tace, babu komai. Yace, khadija, Kalle ni! Ta dago ta kalli cikin manyan idanunsa. "zuwa ynxun na fahimci halayenki a dan zaman da mukayi, fahimta ta sosai. Inda ni marubuci ne, tsaf zan rubuta halayenki. Duk kalar kukan da zakiyi, ina iya fahimtarsa. Nasan kukanki na shagwa6a, nasan kukan ki na rigima, sannan nasan na takaici da kuma na zallar baqin ciki. Wannan kukan naki na tsantsan baqin ciki ne, hade da takaici. Don Allah ki fadamin menene silar wannan kukan naki?" Ta sunkuyar da kai. Yace, karki manta kin dauki alqawari a asibiti cewa, zaki riqeni tamkar dan uwanki. To, in baki fadamin damuwarki ba, wa zaki fada mawa? Kuma nima ynxun dole ne in inada wata damuwa kece zaki fara sani, kafin kowa tunda kece muke daki daya. Ki kalli cikar Gidanmu, amma babu wanda zan iya kaima kukana cikinsu. Daga yaya Amina, sai Mahmud, sune abokan shawarata. Fadamin abin da yasa ki kuka. 1⃣6⃣Tace (cikin shessheka) Na tuna yadda mahaifana suka watsar dani. Dubi inda na dawo. Ni ko cikin novels din da nake karantawa na turanci, labarai irin na turawa masu yin wata irin rayuwa da tasha bambam ta tamu, amma ban ta6a cin karo da labarin masu hali irin na iyaye na ba. Ismail yace, khadija inkin duba tsaf, zakiga cewa, kema fa baki kyauta musu ba. Yadda na samu labarin gatan da mahaifinki yayi miki, bai dace ki watsa musu qasa a ido ba. Amma shikenan duk abinda zai faru ya riga da ya faru. Bari in miki wani alqawari, na sani cewa arziki na Allah ne, amma inya bani, zan miki duk abinda kkso. In ya kai arzikina kamar na mahaifinki, zanyi miki fiye da abinda mahaifinki yayi miki. Inason ki rubuta wannan ki ajiye ko don sheda. Amma ynxun inason ki daina kukan nan, ki kuma yi haquri da yadda kk sameni. Ta runtse idanunta. Ina matuqar da na sanin dawowa ta hutu daga Dubai, na rantse da na san cewa duk wadannan abubuwa zasu faru dani, da na zauna can nayi hutuna. Daddy ya matsamin wai in dawo, ya kuma sake matsamin inje katsina. Ashe yamin hakane sbd ya daina sona. Ismail ya sake yin qasa da murya, "ki daina fadin haka khadija. Ki sani bawa baya iya gujema qaddararsa. Sannan bana zaton akwai iyayen da zasu daina son dansu. Kuma na tabbata inda iyayenki suke, ynxun suna tare da takaicin rabuwa dake. Hankalinsu yana kanki. Tace a'a ban yarda da batunka ba. Hankalinsu yana kaina ne zasu watsar dani bayan sun samu labarin halin da nake ciki? A dan qaramin tunani na kome nayi musu bai dace su banzatar dani ba acikin halin ciwo. Shiyasa nima nakeso ka nesantani dasu kamar yadda kayi min alqawari. Ta soma wani irin kuka mai shiga rai. Baisan lokacin da ya rungume taba ajikinsa. Kiyi shiru. Zanyi miki duk yadda kk so khadija. Saidai ina sake neman hadin kanki. Yadda kk sameni talaka, ki qara haquri. Kinji khadija? Kimin alqawarin zama na har abada. Ko na tafi makaranta ki zauna da yaya kinji. Haka dai Ismail yayi ta lallashin Mimi da kalamai. Kasancewarsa mai hikimar magana, har tayi shiru, ta kuma amince, tare da alqawarin ko baya nan kar ya damu babu inda zataje. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣7⃣Ismail ne ya girka musu abinci, taliya ce yayi dafa duka, ya zabga kifi. Kuma Mimi taci sosai. Matsalarsa ban daki, amma tunda ga 'FO' din daya siyo mata, sai yace, tayi amfani dashi, zai dinga zubarwa. Cikin kwana ukun da sukayi, Mimi har nauyin Ismail takeji, domin ko cikin dare ta farka fitsari ko ba haya zaisa ta a 'FO' in ta gama, ta wanke sai yazo ya zubar, kuma ta lura yanada matuqar tsafta sosai sbd yadda yake gyaran dakin, ya wanke komai na girki, sannan yayi musu wanki. Wanka ne dai matsalarta ynxun, don acikin kwanaki ukun nan batayi wanka ba, sannan yana sata su danyi tattaki a cikin layin ya sagale ta a kafadarsa don tadan taka qafarsa. Sai dai damuwarta yana matsa mata sai ta saka hijabi, ita kuma bata saba da yawo dashi ba. Da ma shi ya sai mata sbd sallah. Yakan lallasheta da cewa, kinga duk kayanki matsattsu ne, khadija ki saka, in mun dawo daki, sai ki cire. A ranar ne Ismail ya daga katifa yayi share-share, har ya ciro ma Mimi Jakarta. Daya gama share-sharensa, sai ya taimakawa Mimi, ta koma kan katifar dama cikin zaure ya zaunar da ita. Sannan ya dauko Jakarta ya ajiye a gabanta. Har ta dauki littafin daya bata na tarihin Annabi Muhammad (SAW) ta bude tana cewa, ina page na ashirin da uku. Sai yace ga jakarki. Tace jefa ta can kan akwatunan can. "yace da kudinki a ciki fa." Ta dago ta dubeshi, sannan ta kalli jakar, "kudi?" yace duba mana. Ta ajiye littafin, sannan ta dauki jakar, ta zazzago kudin. Cikin mamaki ta kalleshi, "dama ba dasu ka biyamin kudin asibiti ba? Yace a'a. Tayi shiru tana kallonsa, ta sake cewa kodai bakasan dasu bane? Yace na gansu. Sai taga ya qara qima a idonta. Sai tace, nagode sosai, amma ka amshi wannan kudin kayi duk abinda kkso dasu, na baka. Yace, kudin da yawa khadija, ki riqe abinki. Tace babu abinda zanyi dasu. Amfanin dana debo kudin don inyi dasu basu min ba. Komai ya zama tarihi. In ma bakada buqatarsu, to zaka iya ba wasu masu buqata. Kuka ya kufce mata. Ismail yace, shikenan kiyi shiru, na amsa kuma nagode. Ya tattara kudin guri daya, yana tunanin me zaiyi dasu? Cikin baqar leda ya zuba su. A zuciyarsa yana Jindadi, domin ko babu komai, zai samu tarin buqatun dake gabansa. 1⃣8⃣Waje ya fita ya kira Mahmud cikin waya ya sanar dashi komai, Mahmud yace, Ismail ka gode ma Allah. Duk lokacin da wata matsala ta taso maka, sai kuma Allah ya kawo maka mafita. Kaga kana cikin matsalar abinda zaka bar musu in zamu tafi da wanda kai kanka zaka riqe don amfaninka, sai kuma ga wadannan kudin. Ismail yace, Allah shine abin godiya. Ni kaina nayi tunanin sassauci ne Allah ya turomin. Kuma fa kasan harda darajar aure ko? Inji Ismail. Mahmud yace, tabbas! Kasan aure daraja gareshi. Albarkacinsa sai kaga budi ko ta ina. Shiyasa ko yaushe nake baka haquri, ina tausarka a kanta. Kuma duk runtsi kar kace, zaka saketa. Ismail yace, insha Allahu zan kula. Amma fa karka manta ba sona takeyi ba, kuma nima harga Allah banajin sonta a zuciyata, tausayinta kurum nakeyi. Mahmud yace, "Allah yayi mana za6i mafi alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan sukayi sallama. Ummin yaya Amina ce tazo ta kawoma Mimi faten wake hade da kifi. Sai Ismail yace, ummi zauna da aunty khadija inje gurin mamanki in dawo. Tace, to kawu. Amma ka fada mata inanan. Yace zan fada mata. Ya kalli Mimi, sai na dawo. Kai kurum ta daga masa. Sun tattauna da yaya Amina, inda sukayi shawarar a gyara ma Mimi dakin kakarsu saddam. Babansu saddam da ma ya Amince ta dawo nan. Yace, ai Ismail dansu ne tunda ance babbar ya uwa. Yaya Amina tace, ka ba Salisu aikin,, qanin babansu saddam. An kira Salisu yaga dakin, kuma Ismail ya fada masa yanason asa masa tayals a qasa, sannan a saka silin na zamani na roba, kuma a yi masu fenti duka Gidan, ya canke kudin da Salisu ya fada ya bashi harda na aiki. Sannan ban dakinsu yasa shima a duba, aka duba, yace abin tsugunno na zamani asa tayals a qasa ayi fenti asa wuta. Dama tsakar gidansu mulmule yake da siminti. Sannan ya ware wasu kudi ya ba baban su saddam yace, su siyo kayan abinci sbd halin yau da gobe. Bayan fitarsa itama yaya Amina ya bata 'yan wasu kudin ahannunta, sbd yasan Mimi ba zata amshi kudi daga wannan kudinba. Yace ta riqe do zuwa asibiti ko wata buqatar. Bayan ya koma ya tarar Mimi tana varci, ummi kuma tana zaune a tsakiyar dakin tana wasa. Yace, a'a varci tayi antin taki? Ummi tace, eh tana cikin karanta littafi, sai naga tayi varci. Ya kalli littafin, sai yaga littafin tarihin nan ne daya bata. Ya dauka ya duba yayi mata alama a inda ta tsaya ta hanyar ldan linke gefen littafin sannan ya ajiye. Ya kalli Ummi, to tashi kije gida ko mamana. Tace, to kawu, sai Anjima. Ta tashi ta fita. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣9⃣Daga tsaye yake yana kallon Mimi. Duk runtsi saidai yace, bayason Mimi, amma ba dai yace, ba tada kyau ba, don ma fatarta ta rage haske sakamakon canjin rayuwar data samu. Ga ta da gashi, abinda yake matuqar so ga mace. Ya koma gefen teburin daya dora littafin akai ya zauna yana kallon Mimi sosai. Yaga abubuwa da yawa a tare da ita wadanda suke sawa mace ta amsa sunanta mace. Harma ya jishi cikin wani irin yanayi daya tilasta masa lumshe ido. Muryar Mimi yake tunowa irinta matan da suka amsa sunansu na mata. Domin duk macen data amsa sunanta mace, bata yin magana da qarfi. Mimi ko masifa takeyi ba zakaji muryarta a sama ba. Hakanan in tana waya, qarya ne don kana kusa da ita kaji me take fadi, in dai ba ka saurara sosai ba. Haka zalika in tana magana da kai tamkar bata so. Wadannan dabi'un da kuma shagwa6arta tana matuqar burge Ismail, kuma yana sonta ga matar da zai aura. Qarar wayarsa ya dawo dashi tunaninsa. Ya daga, Mahmud ne yace, ka fito ina waje. Ismail yace, ganinan. Yayi masa bayanin Yadda sukayi da yaya Amina. Mahmud yace, yayi hakan. Ismail ya ciro dubu biyar yaba Mahmud yace, kaima kadan qara. Mahmud yace, babu matsala ka barsu don Allah. Ismail yace, a'a ka amsa kudinfa sunada dan yawa, dukda ban qirga ba. Ni tunani ma in na cire abinda zanyi amfani dasu, sauran sai in buda account in zuba, ko don buqatar su khadija. Mahmud yace, wannan ma tunani ne mai kyau. Sun jima suna tattaunawa sannan sukayi sallama. Daren ranar, gurin misalin sha daya Mimi ta farka daga varci, sakamakon hasken wutar lantarki da aka kawo, dana rashin wankanta na kusan kwana hudu, ya sata sai juyi takeyi. Ta tashi zaune tana kallon Ismail, wanda babu riga, ta lura sam shi ba mutum bane Maison varci da tufafi. Amma yanason rufa sosai. Ynxun haka rabin jikinsa, ko ince daga qafa zuwa qirjinsa a rufe yake. Sannan fuskarsa tamkar yana murmushi. Ta dauke idanunta tare da lumshe su. Sannan ta sauke ajiyar zuciya. Wannan duk don idanunta sun kalli sumar dake kwance a tsakiyar qirjinsa ne. Hasken wuta ne yasa shi bude ido, yayi miqa tare da salati, yace NEPA sun kawo wuta kenan. Yana tashi zaune yaga Mimi a zaune. "kema hasken wutar ne ya farkar dake? Na manta ban kashe ba. 2⃣0⃣Ta 6ata fuska, cikin shagwa6a tace, jikina yana yimin qaiqayi. Yace khadija kinqi yin wanka dole kiji haka a jikinki. Tace yaya zanyi ynxun to? Yace, bari in kaiki ciki, ki daure kiyi mana. Tace amma zaka tsareni a waje? Yace eh. Riga ya saka, sannan ya nufi cikin Gidan. Saida ya wanke bayin, sannan ya kai mata ruwan wankan. Yace, babu dai na zafi, kuma kinga har ynxu da dan sauran sanyi. Tace, zanyi hakanan. Kujera yasa mata ta zauna sannan ya fita. Data gama saida tasa kayanta data dauko na varci masu dan kauri sannan tace, na gama. Yazo ya kamota suna tafe a hankali. Sunzo daidai qofar dakin fatu, sai ta turo qofa ta fito. Ta kallesu, "ikon Allah, don jaraba ba'a bari a warke ba? Su dai basu tanka ta ba. Sai da Mimi ta zauna akan katifa sannan tace, wai me matarnan take nufi da abinda ta fada? Ismail dukda ya fuskanci inda fatu ta dosa, sai yace, nima ban gane nufinta ba. Daya koma kwaso kayan wankanma, saida tace, ya dai kamata a bari a warke. Ismail yace, ai da ciwon ma ba haramun bane. Tace, eh lallai ka riqa. Shidai ya fice a zuciyarsa yana cewa, sa ido sana'ar banza! Cikin kwanaki uku zuwa hudu an kammala gyara tsaf. Lallai komai yanason gyara, inji abban su saddam, lokacin daya gama kallon Gidan. Sannan ya juya ya kalli Ismail, qanina muna godia fa. Ismail yace, Ameen. Ismail shida Mahmud sukaje kasuwa, inda suka siyowa Mimi Gado waya goma na kwanciyar mutum daya, saitinsa harda sif. Sai fanka, dan TV dinta madaidaici. Mahmud yace, ga wata shawara, me zai hana kudin da kace kaba yaya Amina, ka amshe su ka cika ka sai musu firji ko dan qarami ne. Kaga ko da ruwan sanyi suke saidawa zasu samu dan na rufin asiri. Ismail yace, haka ne, amma bari mubar musu wancan kudin tunda ga wasu nan, sai mu sai musu dashi. Dogon fridge suka siya, sannan suka nemi shatar a kori-kura suka loda kayan, suka nufi Gidan yaya Amina. Maqota sai leqe sukeyi. Wasu suce 'yan haya suka sa a gida, wasu kuma suce kodai aure abbansu saddam ya sake yi. Suka shiga da kaya suka shirya komai tsaf, firjin kuma suka sashi a dakin yaya Amina. Su Ummi kam murna babu dama. Tana fita wata maqociyarsu, Bakaraba tana ta leqe, dama tanason taga giccin wani dan gidan ta kirashi. Tana hango Ummi, ta kwada mata kira. Ummi tazo, tace kunyi baqi ne a gdn naku, ko ko abbanku ne yayi aure? Ummi tace a'a kawunmu ne zai tafi madina, shine matarsa ta dawo Gidanmu. Tace ohoo, wadda ke asibiti? Ummi tace eh. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣1⃣Daga nan fa duk wanda yazo jin meya faru, sai tace, qanin mamansu Ummi ne zaije karatu, ya dawo da matarsa Gida. Dama ita balaraba gun nan duniya ce. Ga duk maison jin wani tsegumi a Unguwar, gurinta yake zuwa don ta shahara. Tunda taga anayin fenti a gidan take shige da fice don jin dalili. Bata samu cikakken bayani ba, sai a bakin Ummi. Saida komai yayi tsaf, sannan suka tafi. Bayan sunyi sallama da Mahmud ya shiga gida, ya zauna. "khadija na barki ke daya ko? Don Allah kiyi haquri. Ta dube shi, sannan ta kwantar da kanta gefe, babu komai, karka damu dani na saba da zama ni kadai. Yace, an gama gyaran dakin naki, na gidan su yaya Amina, yaushe zaki koma? Cikin sauri ta tashi, "ynxun zan koma. Yayi murmushi, meyasa kk gaggawar rabuwa dani? Kin gaji da zama dani ko, bana kula dake yadda ya kamata. Cikin sauri tace, a'a Nayi kewar yaya Amina ne, kuma nan din ina takura maka sosai. Qasa fa kk kwana, amma kana kula dani sosai. Yace nikam inata kewar rabuwa dake, tsawon lokaci muna kwana daki daya, zamu rabu. Ta sunkuyar da kai, "ba zaka rinqa zuwa Gidan ba? Yace, zan dinga zuwa kullum kafin in tafi. Ya kamata in sai miki waya ko? Sai mu dinga gaisawa ko? Tace, ka barni kawai tunda banida wanda zan kira. Yace, ba gani ba? Tace, a'a ka saimin novels na dan dinga karatu. Yace, wadanne iri? Tace, na turanci. Yace zan hada miki dana addini, tarihin Annabawa, da kuma wadanda zasu koyar dake, kisan yadda zaki ibadarki. Suma akwai masu fassarar turanci, akwai na hausa. Tace, to ka saimin. Yace kuma sai gobe zako koma gidan yaya din, sbd yau da dare nida Mahmud mu kwashe kayankin nin, ya nuna akwatunanta da yatsansa. Tace, "to Allah ya kaimu. Ya shiga cikin Gida ya sanar dasu inna cewa, matarsa zata koma gidansu yaya Amina, sbd zasu tafi makaranta. Tace, "sbd nan din ba za'a kula da ita ba? Yayi murmushi, don dama ya zaci zata fadi haka. Yace a'a saboda bata gama samun sauqi ba. Tace, Allah ya taimaka. Yace, Ameen. Haka kuma da dare ya samu 'yan uwansa mazan ya fada masu. Suma sai suka ce, hakan yanada kyau. A daren suka kwashe kayansa da Mahmud tsaf. Sannan washe gari ya kama ta Suka shiga cikin gidan tayi musu sallama, dukda dai ba kulata suke ba, sai wanda yayi biyya yake leqawa dakin yayi musu sannu. Tayi mamakin ganin dakin haka don gsky bata zaci dakin yayi kyau haka ba. Ta kalli Ismail, nagode da kulawa. Sannan tace ma yaya Amina taba ta Ummi su dinga kwana. Yaya tace gatanan. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣2⃣Shi kuwa Ismail daya koma ya kwanta a dakinsa kan katifarsa, sai yakejin dakin yayi masa girma. Zuciyarsa ta cika da kewar Mimi. Itama a nata 6angaren haka ce ta kasance, juyi kurum takeyi tana kallon Ummi wadda keta sheqa varci. Gizo Ismail yakeyi mata, sai taga kamar gashi yana sallah. Koda ta tabbata ba wai tanason Ismail bane, amma yana da dabi'un da take matuqar so, suke kuma burge ta. Yanada tausayi, ga gsky da Amana. Shine mutum na farko wanda ya kasance mai addini kuma yake birgeta. A da in taga ustaz kamarsa, sai ta dinga yi musu kallon 'yan kauye wadanda basu waye ba. Haka kuma yana burgeta Kasancewarsa tsayayyen namiji, wanda baya daukar raini, gwarzo mai tsayawa da safafunsa. Don duk lokacin da ta tuno da yadda suka yita takun saqa dashi, tana jinjina masa, domin ko a gabanta bai ta6a shakkarta ko nuna Tsoronta ba, kamar yadda sauran mazaje da yawa sukayi a baya. Ta tuna irin yadda tayi ta wulaqanta samari 'ya'yan manyan mutane, wadanda suka nuna cewa suna sonta. Kai ko khalil dinta ya wulaqantu kafin ta soma sonshi, kuma har zuwa lokacin da ya rasu, bai daina shakkarta da tsoronta ba. Tasan cewa da ya kasance mijinta, babu shakka za suyi zama ne na sai yadda tayi. Domin ba zai iya juya ta ba. Da wadannan tunanukan varci yayi awon gaba da ita. Shikam Ismail bayan ya dawo daga masallaci sallar asubahi, saiya nufi gurin malaman da suke daukar karatu. Daga gurin karatun ne ya nufi gidan yaya Amina. Lokacin abbansBBCu saddam shima zai shiga Gida. Suka gaisa, cikin salon tsokana abban saddam yace, kazo duba ajiyarka ne? Ismail cikin dariya yace, kuma fa kamar hakane. Tashin Mimi kenan daga varci, tana tunanin da suna tare da Ismail da ynxun ya kaita ban daki, sai taji Sallamar sa. Da sauri ta koma ta kwanta don taga me zaiyi. Yaya Amina tana kicin tana dora ma yara ruwan wanka, suka gaisa. Yace, 'yar amanata ta tashi kuwa? Yaya Amina tace, leqawata biyu bata farka ba. Yace, kinsanta sarkin varci ce dama, ko gajiya batayi. Yace, bari in tasheta tayi sallah. Yaya tace, "to" amma tasan cewa mimin tana fashin sallah, domin jiya da dare bayan tafiyar Ismail ta tambayi yaya audugar mata. Yaya kuwa da kanta ta fita zuwa shagon Bello ta siyo mata. [17/09 1:18 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣3⃣Ya jima tsaye yana kallonta, sannan ya dauko kujerar gaban madubi, yazo bakin gado ya zauna. Babban yatsan safarta ya kama ya dan ja. Dole tayi motsi, domin taji dan zafin qafar. Yace, ki tashi kin makara, kiyi sallah. Ga Ummi har ta tashi tayi nata. Tace, cikin salonta na shagwa6a "nifa ba zanyi ba yau. Ta sake sunne kanta cikin filo don kunya. Ya gane batunta, cikin sigar tsokana yace, wai, wai, wai, shine baki fadamin ba in sai miki biredinku na mata? Koda yake naga ba kiyi ba muna asibiti, sai na zata baki fara bane. Ta dago, tayi masa wani kallo, meke daukeni ne? Ya kashe ido daya, "Baby mana. Ta tashi zaune, me kace? Kada ka manta fa naje jami'a. Yace, haka fa, kinje jami'a, na manta sam, shekarunki nawa ne ma? Ta gano so yake yaji shekarunta, don haka tace, ba zan fada maka shekaruna ba, sai dai ranar zagayowar haihuwata. Tace daya ga watan daya. Yace tabdi! Gsky ke ta musamman ce, to bari in kalleki in fadi 'yan shekarun naki, don basuda yawa. Tace, fadi muji. Yace sha takwas, sha tara, ashirin, in na cika miki kenan. Ta dan zaro ido, alamun aciki ya fadi daidai, amma sai ta wayance da cewa, sam ba haka bane, baka canka ba. Yaya Amina ta katsesu da sallama suka amsa, tace, khadija ga ruwan wanka can muje in kaiki ko? Ismail ya miqe "to nima bari in tafi dama nazo ne mu gaisa. Yaya Amina tace, kardai ka manta da sandar da za'a sai mata ta tafiya, tunda sunce zai taimaka mata sosai gurin tafiya da sauri. Ismail yace, ai kuwa nagode, shaf na manta. Anjima zamuje asibiti da Mahmud. Haka kuwa sun sai mata sandar. Kwanci tashi, babu wuya har anzo jajibirin tafiyarsu Ismail. Kafin ranar tafiyar dama ya zaga duk 'yan uwansa mata, yayi musu ban kwana, domin shi harga Allah yanason 'yan uwansa mata, yayi musu ban kwana, domin shi harga Allah yanason 'yan uwansa. Kuma yana sha'awar suyi zumunci. Wadanda basuje asibiti duba su ba, sai 'yan kame-kame gami da ban haquri yace, babu damuwa Allah ya bada ladan niyya. Haka nan yaje Daura, yayi bankwana da dangin mahaifiyar sa. Ta kano zasu tashi, don haka tun ranar jajibirin zasu tafi kano din tare da Malam Aminu. Sai yaga tashinsu sannan zai dawo. 2⃣4⃣Sun gama shirinsu tsaf, Ismail ya shiga don yin bankwana da matarsa da kuma yaya Amina. Ya dauko wayarnanda ya ta6a saima Zainabu yazo ya samu tayi aure, ya bawa yaya Amina, yace, ya dinga kira don jin lafiyarsu ba sai ya dami abbansu saddam ba. Mimi tana kwance akan gado Rigingine, ta tasa tulin littafin daya sai mata, sai dai duk na addini ne, bai sai mata novels dinba, waishi baisan ina ake saidawa ba. Yace, ta karanta wadannan don tafi buqatarsu ynxun, kuma kinga duk na turanci ne, tunda kince hausa tana baki wahala. A sanyaye yace khadija! Ta kalleshi, yace munfa shirya zamu wuce. Malam da abokinsa da kuma Mahmud zasu biyo tanan ynxun mu wuce. Ta dubeshi, "tam shikenan sai kun dawo, kamar zuwa yaushe kenan zaku dawo? Yace, sai dai munje muji lokacin da suke samun hutu. Ai zan dinga kiranku muna gaisawa. Tace, am nayi zaton kafin ka wuce zaka sakeni? Gaban Ismail yayi wata muguwar faduwa, har taso ta gane. Amma sai ya wayance tare da yin dan yaqe, "kinada gurin da zakije ne kafin in dawo? Ta kalleshi "a'a" yace to kada kiyi gaggawa, wannan kibar zancen, sai in nazo hutu, sai muga yaya za'ayi ko? Tace shikenan, Allah ya taimaka, ya kaiku lfy. Ta koma ta kwanta. Ya dube ta, "babu rakiya? Tace ka manta banida qafa? Yace, shikenan kiyimin Addu'a sai munyi waya. Su yaya Amina ce da yaranta suka rakashi lokacin da su Mahmud suka iso. Suna tsaye har saida motar ta 6ace, sannan suka koma Gida. Suna idar da sallar asubahi, jirginsu Ismail ya daga, su Malam suka dawo cike da kewarsu. Zainabu ta gama girki ta raba taba kowa, kusan kwano ashirin da uku. Matuqa ta qosa ta fita a madafin sbd hayaqi da kuma zafi. Ta dauki nata da kuma na mai gidan, duk da baci yake ba, amma qa'ida ce kullum sai an zuba masa. Habu da adamu suna jira ace su dauka, tace, ku dauka, sai ku fadama sauran cewa suzo su dauki nasu. Habu ya dauka tare da fadin, ke kullum abincinki baya dahuwa. Adamu yace, eh mana ke baki iya girki ba. Tace, ku bakuda kunya. Ni sa'arku ce? Maman su Habu ta fito, dama kamar tana jira, "karki takura min yara. Ai ba qarya sukayi ba. Duk ranar girkinki, saidai a zubar ko ko aci da haquri. Jikin zainabu ya soma 6ari don tsoron fada gareta. Tace, ni bazan takura musu ba kuyi haquri, ta nufi samansu. [17/09 8:49 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣5⃣Daidai lokacin kuma Alhaji ya shigo, yana jiyo hayaniya, yace, Hama lfy kuke min hayaniya da farar magriba? Tace, Zainabu ce zatayi min rashin kunya, don yara sunce ba zasu iya cin abincinta ba. Alhaji yace, sbd me? Tace, to abincin bai ciyo don bata iyaba. Alhaji mutum ne wanda komai qanqantar magana, sai ya ririta ta. Don haka sai yace, yanason duk 'yan gidan su hallara. Ya tara su har zainabun. Yace, su fada masa da gske ne girkin Zainabu babu dadi? Maman bushira tace, injiwa? To kai da zaka tambayemu baka ta6a ci bane? Yace, to iya magana, jikar zance, ban dake, don na kula kinfi son yarinyarnan da iyalina. Ya dinga bin yaran da sauran matan yana tambayarsu ko ta iya? Suka dinga cewa babu dadi. Sai 'ya'yan Maman bushira ne kurum Sukace sudai suna ci. Alhaji yace, ban ta6a cin abincinta ba amma yau zanci, in har baiyi dadi ba, kamar yadda kuka ce, to zan dauki mataki. Don bazan dinga fita da sassafe neman abinci ba, sannan kizo kina girka shi son ranki, a kasa ci ana zubar dashi. Zainabu dai shiru tayi, sbd ba tada ta cewa, amma fatanta shine Allah yasa ya yanke mata hukuncin saki. Shi Alhaji ba mutum bane maicin abincin gidansa, yafi zuwa Gidan abinci shagunan masu indomie koko gurin masu tsire. Dakinsa ya kira Zainabu yace, ta bude abincin ya gani. Jikinta sai 6ari yake, ta bude, qauri ya cika dakin. Yace, eh lallai dole yara su kasa cin abinci, tun kafin in kaishi baka ne wannan qaurin yake tashi? Ta kalleshi cikin tsananin tsoro, yace, uwarki bata koya miki girki bane? Tace, ni ban iya yin girki da babbar tukunya ba, kuma gashi a murhu. Yace, da Allah rufe min baki! Nine zaki fadawa baki iya girki a murhu ba. Ubanki baya iya ci da gidanku. Ni nake riqe da gidanku, da har zakice min baki iya girki da murhu ba. Wa zaki gaya ma kokai dan uban waye. Da dai kince sakaryar uwarki bata koya miki ba, sai yawon talla da nafi yarda. Ran Zainabu yakai maqura gurin 6aci, tace nidai gsky duk abinda za'ayi, ayi, amma a daina zagin iyayena. Kuma ai duk yaushe muka hadu da zaka ce kai ne kake ci da gidanmu? Ashe Zainabu ta tafka kuskure daya fada ta fada. Domin ba'a fadi yana fadi. Nan take ya tashi a fusace, ya hau kilarta. Maman bushira tana zaune Zugum tana jiyo ihun Zainabu, baqin ciki fal a zuciyarta, domin tana tsoron kar wannan halin da mijinta keyi ya juye kan 'ya'yanta, sbd in ka cutar da dan wani, sai an cutar da naka don kaima kaji. Haka yayi ta kilarta har ya gaji, yabarta don ba zuwa ceto. 2⃣6⃣Tun Zainabu tana kuka har ta kasa. Yace, tashi ki fitarmin a daki! Kasa tashi tayi, domin data yunqura, sai ta koma ta zube. Sai kuma ga jini ya soma zuba. Idanu ya zaro yana kallonta. Sai kuma ya soma kiran Maman bushira. Ta shigo ranta 6ace, yace, kamata zuwa daki, naga jini yana zuba, ko dai al'ada takeyi? Maman bushira tace, wace al'ada kuma? Yarinyarnan ciki gareta, saidai inka sake doko cikin. Yace, ni ban doketa a ciki ba. Maman bushira ta dago ta tana kiran sunanta "Zainabu! Zainabu! Cikin tsoro tace, Alhaji yarinyarnan tana da rai kuwa? Da sauri yasa takalmi yace dauke ta zuwa dakinta, bari in kira danladi Mai chemist. Tace, ka dauketa dai, ni ai bazan iyaba. Cikin tsawa yace, kama ta muje mana. Kan gadonta suka dora ta, duk jini ya 6ata hanyar da kuma dakinsa da nata. Ya fita da sauri. Maman bushira tace, maganinka kenan! Allah yasa ya zamar maka ishara. Zainabu dai tanaji, ba suma tayi ba, amma tana cikin mawuyacin hali. Sake yin lamo tayi tare da sakin jiki sbd jin rudewar da Alhaji yayi. Ko da danladi mai chemist yazo, dauke Numfashinta tayi. Dama shi ba wai ilimin gareshi ba, ya ta6a yin shara ne a asibitin Gwamnati, shine yazo ya bude chemist mutane suke ta tururuwa. Danladi yana ta6a ta, sai yace wai, wai, Alhaji! Gsky kuje asibiti, don gsky ba zan iya ba. Dubi jinin fa kamar an yanka qaramar dabba. Alhaji ya zaro ido cikin fargaba, to ni yanxu wane asibiti zamuje? Banason zuwa wannan asibitin Gwamnatin. baba yace bari in kwatanta maka wani na kudi ka kaita bakinka alaikum. Sun kaita, an amsheta, amma yayi kashin kudi masu yawa, sannan kuma cikin yananan bai fita ba. Bayan tafiyarsa Gida, gurin qarfe sha daya Nurse din da ta taya likitan aiki lokacin da ake qoqarin tsaida jinin, ta samu maman bushira a zaune kan kujerar dake kusa da gadon da Zainabu take kai kwance, tace, sannu mama. Maman bushira tace, yauwa 'yan mata sannu da aiki. Mun gode fa. Tace, yauwa dan Allah mama, wannan 'yarki ce? Maman bushira tace, a'a kishiya ta ce. Nurse din ta zaro ido. "Kishiyarki kuma? Kina nufin wancan daya fita mijinku ne?" tace, eh. [17/09 9:56 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣7⃣Nurse tayi shiru tana matuqar mamakin lamarin. Can tace, to wai wanene yayi mata dukan jikinta? Tace, shine ya duke ta. Wlh haka yakeyi. Yayita auro 'ya'yan mutane yanacin zalinsu. Nurse din tace, kinga ko Mama da ace Allah zan hadaki da ainihin babbar likitar dake da wannan asibitin. Kiyi mata bayani, wlh zata gyara masa zama. Maman bushira tace, rufamin asiri. In ya sani ai na shiga uku, domin dama inacin darajar manyan 'ya'ya na ne, sai kuma irin wannan ranar in yayi ta'asarsa yazo ya matsamin in tayashi. Nurse tace, inda zaki iya da na hadaki da ita. Allah zatayi muku maganinsa, sai ya daina. Kuma ko daya sunanki ba zai fito ba. Tace, to shikenan ki hadamu don zan mata bayani, amma don Allah kamar yadda kkce, kar sunana ya fito. Tace, ba damuwa. Gobe ai kina nan ko? Tace, eh nizan kwana, amma na san shima zaizo da safe. Alhaji lawal, tunda yaje Gida ya tara sauran matan yasa su suka gyara gurin jinin. Shi dai tunda ya shige dakinsa ya zauna ya zabga Tagumi, ya rasa bakin magana. Da na sani ce cankas a zuciyarsa. Tsoronsa daya kar 'yar mutane ta mutu. Ranar dai bai runtsa ba, sai juyi yake. Washegari tun takwas ya nufi asibitin. Lokacin Zainabu tana varci don ta farka cikin dare har Maman bushira ke bata labarin yadda sukayi da Nurse. Zainabu tayi ta roqon ta akan cewa, ta taimaka mata don Allah don Allah ta fadawa mai asibitin. Ya kalli Maman bushira yace, ya jikin nata? Tace, da sauqi. Yace, ta farka? Cikin son qara tsorata shi, tace eh ta farka, amma bata cikin hayyacinta. Domin bata ganeni ba ma. Alhajin ya sake rudewa. To likitan bai sake dubata bane? Ance asibitin kudi, kuma na bada duk abinda akace, amma ba zasu duba ta yadda ya kamata ba? Zai fara sababinsa tace, Alhaji gara fa kabi ahankali sbd likitan ya fara tambayoyi akan shedar dukan dake jikinta. Sannan zuwan su biyu nemanka. Yace, to ni dai bari ma inzo in tafi kawai. Ya ciro kudi ya qirga dubu goma ya bata, "ga wannan ki riqe a gurinki. In sun tambaye ni kice nayi tafiya. Sannan karki sake aji daga bakinki cewa, ni na duketa." Tace, to shedar dukan fa data fito a jikinta? Yace, kice musu bulala ce ta fito mata. Ba awai ciwon bulala ba? Tamkar Maman bushira ta saki dariya, sbd ganin yadda Alhajin ya birkice. Bayan tafiyarsa tace, ai zaka gane kuranka. Nurse dai tazo kamar yadda tace, kuma ta raka ta har gurin mai Asibitin a cikin ofishinta. Da ma takan zo qarfe goma ta tashi sha biyu. Bayan Maman bushira ta gaisheta ne, sai Nurse din tace, gata nan momy. Doctor din ta kalleta, malama kiyimin bayanin dana samu daga wannan Nurse din. Maman bushira tayi mata bayanin yadda abin ya faru har ya kaiga dukanta. Sannan tace, tashi muje in ganta. Sun samu Zainabu ta farka. Tana ganin likitar ta soma kuka tana cewa, don Allah ta taimake ta. Likitar tace, karki damu, hadin kanki nake buqata. Tayi ma Zainabu tambayoyi, ta amsa. Sannan tace, to babu damuwa qarfe nawa zaizo? Maman bushira tace, ai yazo har ya tafi. Kuma zaiyi wuya ya qara zuwa don a tsorace yake. Likitar tace, qarfe nawa za'a saleshi a Gida? Tace takwas na safe ko tara na dare. Likitar tace, babu komai. 2⃣8⃣Doctor Asma'u Adamu mace ce mai kamar maza. Tana da taimako sosai, musamman akan abinda ya Shafi mata. Duk lokacin data samu matsala makamanciyar wannan, ko ba'a Asibitinta ba ne, takan nemar wa mai haqqi haqqinta. Har ta kai ga kafa qungiya mai qwato wa mata 'yanci. Suna da lauyoyi da mai qwato wa mata 'yanci. Suna da lauyoyi da 'yan sanda da malamai da kuma alqalai a cikin qungiyarsu. Bada 6ata lokaci ba suka rubuta takarda suka aikawa 'yan sanda, inda suka gayyaci Alhaji lawal zuwa ofishinsu. Da yaso yayi gardama, sai suka tura masa 'yan sanda. Dole ya zo suka tasa shi har asibiti. Lokacin Zainabu tana zaune tana shan tea. A cikin kudin daya ba Maman bushira ta fita ta siyo kayan tea din. Sun duba jikinta kuma sunyi mata tambayoyi ta basu bayanin duk avinda kenan tun daga tun daga tursasa mata auren sa da akayi har zuwa yau dinnan. Sun tasashi har Gidansu Zainabu inda aka taso qeyar innar Zainabu. Likita Asma'u ta rufe innarsu Zainabu da fada. Tace, aje a rufesu, sai gobe za'a shiga dasu kotu. Nan fa hankalin Alhaji yayi matuqar tashi. Ya shiga bada baki, tare da roqon don Allah ayi masa afuwa tunda bata sonshi, yaji kuma ya haqura, zai sake ta. Likita tace, ai dama wannan dole ne, sannan kai zaka kula da ita har ta warke, sannan ka dauki nauyin cikinta, har ta haihu ta yaye. Yace, duk na yarda. Ita kuwa inna, saida aka rubuta takarda dasa hannu kan cewa ba zata sake tursasa ta ba. Cikin su duk wanda ya sake, sai yayi zaman jarum. Bayan gargadi mai tsanani aka sallamesu, bayan Alhaji ya rubuta takardar sakin Zainabu, yayin da maman bushira ta shirya yanata-yanata, ta dauki kudin da Alhajin ya bata, taba Zainabu. Zainabu taba ta dubu uku daga ciki. Har taqi kar6a, Zainabu tace, lallai saita kar6a. Ta qara da cewa, taimakon da kk yi min, Allah ne kawai zai biyaki. Murna gurin Zainabu tamkar sallah, wannan sakin da akayi mata, matsalarta daya, wannan cikin dake jikinta. Kwana uku ta qara aka sallameta. Suka je ta kwashe nata-yanata suka nufi Gida. Kafin su wuce, dama likita ta tabbatar ma da Zainabu duk wata, gurinsu zata dinga zuwa ta amshi duk abinda aka yanke dashi. Shi kuma sun tabbatar masa cewa, sun saka ido akansa, in ya sake yiwa 'yar wasu haka, to ba shakka zai qare rayuwarsa a Gidan kaso. [18/09 3:31 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 2⃣9⃣Rayuwar Na'ima a Gidan minister dai sai a hankali, don in yana gari ne zaka ga suna kula ta, amma da yayi tafiya ko ya fita, banza ma ta fita. Abbas kuwa ko yazo gidan bata isheshi kallo ba. Haka qannensa batajin dadinsu, har gara Aisha ma data dawo hutu, takan dan kulata. Saima ta gwammace zaman gidan Abbas dana iyayensa. Don haka wata safiyar talata ta samu Hajiya Bilkisu, bayan ta gaisheta, ta amsa cikin jin kai. Na'ima tace mata, momy na samu sauqi inaso in koma gidana. Hajiya Bilkisu tace, ai gara kam ki koma don nima kin takuramin. Ta kira Abbas tace masa, "ka kira daddynku ka fada masa cewa, zaku koma gida. Ko da Abbas ya kira shi, saida ya kira Na'ima ya tambayeta cewa, ko itace ta buqaci komawa gidanta? Tace, eh itace. Ya tambayeta ko akwai wani abu da take buqata? Tace, a'a babu komai. Yace to likitan dake dubata yayi mata? Tace eh yayi yace, to zaici gaba da zuwa duba ta a gidanta. Haka ta tattara ta koma Gidanta wanda bata iya bambantashi da gidan yari, ko da dai bata san gidan yarin ba. Shi kam Abbas dalilin cikinnan ya samu abubuwa da dama a gurin mahaifinsa. Sannan, yasha gargadi cewa, ya lura da jikansa, tare da ba uwar duk abinda take so, don jikansa ya fito duniya da girma.kusan duk sati biyu, sai anyi hoton cikin don tabbatar da lafiyar sa. Namiji ne kamar yadda sukeso. Sai dai fa, har ynxun Abbas bai daina kawo mata gidanba, mata kala-kala wataran a ita yake sawa tayi musu girki, kuma dolenta tayishi tana kuka, tana komai ga ciki. Hakanan kuma duk randa yaji cewa, yana ra'ayinta dolenta ta miqa kanta, sannan kuma ya gargadeta cewa, har dai in ta bari dadynsa yaji wata magana daga gareta, to kuwa nata daddyn sai abinda yafi haka. Babu ranar banza da Na'ima ba zatayi kuka ba, gami da dana sani, ga dinbin nadama data cika zuciya da ga6o6inta. Gani take ko mimi ynxun ta fita kwanciyar hankali. Abin takaicin gashi babu dama ta koma gida sbd in daddy yaji allura ce zata tono garma. Ita kanta Momy Nafisa komai ya kwance mata. A ynxun bata qi ace auren Na'ima ya mutu ba, cikin ma ya 6are. Rayuwa kenan mai canji. 3⃣0⃣Kwancitashi har an cinye wata daya da tafiyar su Ismail. A farkon tafiyarsu, Mimi bata da wata matsala domin yaya Amina tana yi mata komai, sannan ko girki zatayi, saita tambayi Mimi me zata ci, a dafa. Mimi bata komai, sai kwanciya sai sallah, sannan takan dan taka da sandarta a tsakar Gida da cikin daki. Zuwa ynxun ma takan dan taka ba sanda, amma ba sosai ba, din Mimi tana da tsoro. Haka nan Ismail kan kira su a waya yana jin lafiyar su a duk lokacin daya samu sukuni. Sai dai kamar yadda hausawa suke cewa, zara bata barin dami haka yake. Domin kudinda Ismail yabar ma yaya Amina sun qare, sannan abincin ma ya qare, sai dai awo sukeyi in abban saddam ya dan samo. Haka ruwan sanyi in sun saka na saidawa a fridge, sai a yini bai fisu yi Naira hamsin ba, ko kuma maqota su amsa bashi. In kuma da kudi zasu saya su tafi shago. Hakan yasa suka shiga halin matsi, musamman ga Mimi wadda bata saba da irin wannan rayuwar ba. Kafin akai wanu lokaci, Mimi ta qara lalacewa, tayi baqi, ta kode. Ga wasu qurarraji da suka fito mata a fuska. Wata safiya Mimi tana zaune akan tabarma a tsakar dakinta, ruwan Lipton ne a gabanta da yankan biredi. Hawaye suka zubo mata da ta tuna abinda takeyin kari dashi a gidansu. Ta kalli fatar jikinta, a fili tace, dubi yadda fata na mai daukar hankali ta dawo. Ta shafa sassan wuyanta, ga rama wadda ta sani yin muni. Ta kalli dakinta, dole jikina ya zama haka, babu cima mai kyau, ba AC, ba makwanci mai kyau, ga hayaniya. Sai dai duk da haka babu abinda zance ma wadannan mutanen. Saboda sunyi matuqar qoqari daidai qarfinsu kenan. Duk abinda takeci a gurinsu bata saba da cinsu ba koma tace, bata ta6a ci ba. Amman batada za6i, dole taci, domin yunwa ba tada hankali, kamar yadda taji wani almajiri yana fadi in yazo bara. Haka nan ta tsantsoma taci ta tashi. Su kuwa mutan madina suna can karatu yana tafiya yadda ya kamata, musamman dayake sun samu wadansu 'yan Nigeria acan suna gabansu a karatu. Don haka basu sama wata matsala ba, domin har abinci sukan samu gurin 'yan uwa mazauna can wadanda suka je da matansu. Hazaqa da nacin karatu, da nacin halattar majalisin da malaman sukeyi sune suka sa Ismail kar6uwaba gurin malamansu da dama. [18/09 10:20 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣1⃣Wata rana suna zaune da Ismail da Mahmud, sai Ismail yace, ko yaushe tunanina in mun gama karatunnan mun koma Gida, wace sana'a mutum zai kama don ya kare mutuncin kansa. Mahmud yace kamar yaya? Ismail yace, banaso in zama daya daga cikin malaman da gwamnati take juyawa ko 'yan siyasa. Inaso in riqe kaina ta hanyar sana'a ta, yadda zanji dadin fadawa mutane gsky. In kirasu zuwa ga addinin Allah, ba tare da na canza maganar Allah da manzonsa zuwa son zuciyata ba. Kwadayin abin hannun mutane shike sa wasu malaman kasa fada masu gsky. Ya dafa Mahmud, ka san Allah, sai ynxun ne ma na dana zo nan na qara sanin darajar ilimi. Na fahimci cewa, babu wani mai kudin daya kamata abi shi Gidansa don koyama 'y'ayansa karatu. Ilimin addinin musulunci ya girmi haka. Kamata yayi duk mai buqata yabishi zuwa makaranta. Mahmud yace, hakane batunka Ismail. Amma in mun yi digiri dinmu, ba koyarwa zamu nema a jami'a ba? Ismail yace, zamu nema, ba don dokar makarantarnan ta hana dalibi yin sana'a ko aiki ba, da munyi aiki ko sana'a. Mahmud yace, da ko littattafai muke siya da irin su jallabiyu muna turasu can Gida. Ismail yace, ko ta gurin Malam ne, da an samu alheri. Amma tunda qa'idarsu ce, sai mu haqura mu bisu yadda sukeso. Mahmud yace, karka damu, zamu yi wannan tunanin in mun kusa hada karatunmu. Ismail yace, inason in gina makaranta, babbar makaranta, amma lamarin babu sauqi. Mahmud yace, inda anan qasar ne, zaka samu masu taimakawa, amma mu masu kudin qasarmu, gsky taimakonsu da sauqi. Masu taimakon basuda yawa, wasu ma in zasu taimaka sai sun debi 'yan jarida. Sukayi dariya, sannan suka tafa. 3⃣2⃣A batun kyau, Ismail yayi kyau. Sun yi kyau na ban mamaki, musamman Ismail, wanda ya kasance fari. Jajir yayi sbd AC, ga cima mai kyau. Yayi 'yar qiba, farinsa yayi tas-tas, gashin kansa da sajen sa zuwa gashin bakinsa, sunyi shar tamkar an shuka su. Idanunsa sunyi tas-tas le6unansa sunyi jajir. Kallo daya daka masa, zaka san ya canza. Kai ko shi da kansa ya kalli kansa yana gode ma Allah daya halitta shi. Ko Mahmud dayake baqi yayi kyau, yayi sumul. Kwanci tashi rayuwa tana tafiya, har azumi ya kawo kai. Su Ismail sukan dan yo aike daga dan abinda sukayi ta ragewa daga dan abinda suke samu na tallafi daga makaranta. Wani dan uwansu dalibi shine ya hadasu da wanda zasu dinga turawa saqon, sai Malam ya amsa sannan ya kira abbansu saddam yaje ya amsa. Farkon azumi sai yaya Amina ta samu ciki, ta kama laulayi, sai aikin gidan ya koma hannun Ummi da saddam. Rashin lafiya yaya Amina takeyi sosai. Hakan shi ya tilasta Mimi fitowa don kamawa su Ummi aiki. Tana taimaka mata da girki, shara da wanke-wanke. Sbd lokacin ta warke sarai, sai dan dingishin da takeyi wanda ba dolene a gane in ba kayi mata kyakkyawan sani ba. Shima dingishin da takeyi saida sukaje asibiti, Doctor salis ya fada musu lokacin da likitan da yai mata aikin zaizo. Ko da lokacin yayi sunje kuma sunyi masa bayani, yace karta damu zata koma rass dinta. Tsoro taji lokacin da zata soma tafiya. Amma tunda batajin ciwo agurin, babu wata matsala. Haka kuwa kafin sallah, tayi sumul a fannin lfy. Saidai fa ga wanda yasan Mimi zaiyi wahala in ya ganta ya ganeta. Hakanan tunda tazo gidan bata ta6a fita ba, ko kanta saidai a wanke a gida. In ya isheta, tasa yaya ta kama mata kalba, domin ko a da bata damu dayin kitso ba. Amma lokacin sallah a ranar idi ta saka Ummi ta rakata saloon ta wanko kanta. CANJI DAI NA RAYUWA gashi nan qarara a gurin Mimi. [19/09 9:35 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣3⃣Alhaji bashir ya kalli Hajiya sauda, sannan ya 6alli karas din data wanke masa yakeci, sbd likitansa yace, lallai yana da kyau ya dinga cin karas sbd yana qarawa masu ciwon suga qarfin ido. Yace, "kina dai korata ko?" ba haka bane, ta yaya zan gaji dakai? Yace to kince in tafi Abuja. Tace kawai naga ka dade bakaje bane, kusan tunda ka sallamawa yaran nan kasuwancinka, sau daya kaje. Gashi har anyi azumi, an gama, yau kuma sallah. Yace, shikenan zance Nafisa ta tattaro yarannan gaba dayansu, suzo katsina suyi sallah anan katsina. Sam bana jin dadin yin sallah ko ina inba gida ba. Kinsan wannan. Tace, shikenan suzo nan din. Yace, banda Na'ima tanada tsohon ciki, da sun zo da ita nan itama cikin danginta. Sauda tace, zaiyi wuya minister yabarta, yadda naji kana fadin yanaji da jikansa. Yace, hakane kam. Sai kuma Mimi ta fado mata a rai. Ko ynxun ina Mimi take? Ko tana cikin wane hali? Anya kuwa ba zata bi shawarar Hajiya mardiyya bane? A wani zuwa da tayi ne, suna zancen Mimi, tace ynxun ke Hajiya sauda kin biyema zancen mazannan, kinbar 'yarki ba tare da kinsan halin da take ciki ba? Kiyi tunani fa, su maza ba kamar mu bane, zai iya jure rashin ta, kuma koda wane irin hali take ciki. Hajiya sauda tace, ni banason yace, banji maganarsa ba. Tace, a 6oye zakisa a bincika miki inda take, sai kije ki ganta. Sauda ta danyi shiru tana nazari, can tace, yayi min bayani kuma na gamsu, harma nayi masa alqawari. Hajiya mardiyya tace, shikenan tunda kince haka. Alhajin ne ya katse mata tunani da cewa, kina tunanin Mimi ne ko? Ta kalleshi. Yace, sauda nima tana raina. Hawayen data jima tana tarawa suka zubo mata. Ya zaro idanu, cikin matuqar mamaki. "Sauda keda kk bani haquri, kuma yau kece da hawaye? Lallai haqurinki ya soma gazawa. Tace, Alhaji inason Mimi kamar yadda kowace uwa takeson danta. Kaga kuwa dole in damu da lamarinta. Da ace mutuwa tayi, na tabbata da ynxun na dangana. Amma tunda tana raye dole in zama cikin tunaninta. Kila ma ynxun ta rasu. 3⃣4⃣Ya matsa hannunta, ba ta mutu ba, ta samu sauqi tun watannin baya, an sallameta daga Asibiti, kuma tana zama gidan 'yar uwar mijinta wadda sukayi zaman jinyarta tare, ko da bata fita, ina zaton zuwa ynxu ta saba da irin rayuwarsu. Ta kalleshi da mamaki, "duk ina ka samu wannan labarin? Yayi murmushi, ke kinsan son da nake yiwa Mimi bazan iya yin da nake tayin iqirari ba. Sbd haka nayi bincike akanta. Tun daga kan likitan daya amshesu har zuwa can Unguwar tasu. Kuma an tabbatarmin yaron yana kula dasu sosai. Haka nan tunda ta shiga gidan 'yar uwar tasa bata ta6a fita ba. In ma ta fita, to mai bani labarin yace, shi bai ta6a ganinta ba. Hajiya sauda tace, lokaci yayi daya kamata mu nemeta, tunda ta horu. Yace, a'a lokaci baiyi ba. Ki sake yin haquri kadan, sbd ynxun haka batun da nake miki mijin nata bayanan, yana madina yana karatu. Sannan akwai wata yarjejeniya tsakanin Mimi da mijinta. Likitan ke bani bayani. Bai fadamin yarjejeniyar da sukayi ba, amma ya bani shawara akan kar mu nemeta da wuri, domin akwai yiwuwar ta sake guduwa. Ya tabbatar min cewa zai nememu da kansa in lokaci yayi, don ya kawo mana ita da kansa, a wata fira da sukayi. Don haka inason ki qara haquri. Ta sauke ajiyar zuciya. Shikenan Allah yasa munada rabon ganawa, ya sada mu da alkhairi. Yace, insha Allahu zamu gana da ita. Tace, to Allah yasa. Mutuwa ce gatanan da take ci kamar rana. Ynxun kuna tare da mutum, Anjima ace maka ya mutu. Yace, hakane, Allah dai ya bamu cikawa da imani. Dubi maqocin nan namu mutuwarsa ta kada ni sosai. Tare fa mukayi sallar isha'i, lafiya mukayi sallama dashi. Amma sai muka wayi gari ya zama gawa. Sauda tace, ikon Allah kenan. Allah yasa mu cika da imani, in tamu tazo. Ameen, inji Alhaji. Sannan ya miqe yana fadin bari indan fita. Itama tashi tayi donyi masa rakiya. Bayan dawowarta ne ta nufi dakin su hasana don tabasu labarin data samu game da Mimi. Domin kullum suma cikin zancenta suke. [19/09 6:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣5⃣Kwanci tashi mai cinye kwanakin bawa. Yau gashi mun wayi gari su Na'ima anayin naquda. Da qyar ta kira wayar momy Nafisa ta fada lata, sbd azaba. Tace, Momy kizo marata tana yimin wani irin ciwo wanda ban ta6a ji ba, ina zaton ma dai mutuwa zanyi. Momy tace, ganinan haihuwa ce. Saida tabi ta gidan Hajiya Nana ta dauketa suka nufi asibiti. Hajiya Nana tace mata ki kira mara mutuncin ki fada masa mana. Ta kira Abbas har sau biyu bai dauka ba. Don haka sai ta kira uwarsa ta fada musu. Ba'ayi minti talatin ba sai gasu a asibitin. An gaisa sama-sama, sannan suma suka nemi wani mazaunin suka yada nasu zangon. Momy Nafisa tana fatan 'yarta ta sauka lfy, yayin da Hajiya Bilkisu ke fatan jikanta ya iso lfy. Kusan awa biyu a haka sannan wata Nurse ta fito tanayi musu albishir da haihuwar 'yarsu, kuma ta samu da namiji kamar yadda hoto ya nuna. Nan aka kaure da murna. Su Hajiya Bilkisu kam tasu murnar tayi yawa. Nan suka shiga kiraye-kirayen 'yan uwa suna fadawa dangi tare da daukan yaron hotuna kala-kala. Qa'idar asibitin, ko lafiyarki lau kk haihu, sai kinyi kwana biyu kafin a sallameki sbd su tabbatar da babu wata matsala. Hakan ta kasance ga Na'ima. Amma randa aka sallameta, rannan tsiya taso ta kaure a Tsakanin su. Domin Hajiya Bilkisu tace, gidanta za'a je, yayin da mai jego tace, itafa ba zataje can ba, Gidansu zataje. Momy Nafisa tace, tunda bataso abarta. Hajiya Bilkisu tace, sam. Nanma Abbas dinne ya kira Alhaji wanda ke umra, ya fada masa halin da ake ciki. Ransa ne yayi matuqar 6aci, ya kira Momy Nafisa yayi mata tatas. Yace kula ta bar masa mata yayi yadda yakeso da abarsa. Kuma yana mai sake sheda mata kar ta bari tayi sanadiyyar auren yarinyarnan. Ba tada yadda zatayi, cikin takaici ta bari suka tafi. 3⃣6⃣Ranar suna yaron yaci sunan mahaifin Abbas, wato Aqilu. Sam Na'ima bataso wannan sunan ba, domin itama taso ne tasa sunan nata mahaifin. Amma yace, ba tada ikon za6a ma dansa suna. Tace, kai kayimin naqudar yaron? Yace ai ba ruwa kk sha kk samu cikin ba. Haka dai take ganin qarfin hali iri-iri akan san da ta haifa. Sai kace wanine cikinsu yayi mata wahalar cikin. Hajiya sauda da Hajiya Binta, duk sun halarci sunan, amma Gidan Momy Nafisa suka yada Zango. Sai dai 'ya'yansu ne sukaje can gidan sunan, domin harda su usaina akaje. Sai yamma sannan su Hajiya sauda sukaje gidan mai jego. Sai dai Hajiya sauda tayi matuqar mamakin ganin yadda Na'ima take a kode, a rame, Na'ima mai garin jiki, amma harda qashin wuya. Hajiya sauda ta kasa dannewa tace, Na'ima kinyi ciwo ne kafin ki haihu? Kai ta sunkuyar, "nayi ciwo sosai Hajiya. Hajiya Binta kuwa baki ta ta6e, tare da cewa, Ai dama hangen dala ba shiga birni ba. Alhaji Bashir kuwa, ta Abuja ya sauka don yaga sabon jikan nasa tare da 'yar tasa. Duk da yana namiji, yayi matuqar mamakin ganin lalacewar Na'ima. Amma sai yayi shiru sbd ya san cewa haihuwa tayi, kuma baisan irin wuyar da tasha ba. [19/09 6:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣7⃣Ismail da Mahmud suna zaune a farfajiyar makarantarsu, inda sukan hadu da abokansu don qarama junansu sani, da qaruwa da basirar juna. Yau kam su biyu ne saura basu riga sunzo ba. Mahmud yake cewa, Ismail kasan me nake tunani? Ismail ya dago kansa daga littafin dake hannunsa, yana dubawa yace, sai ka fada. Mahmud yace, wannan hutun da zamu samu tunda na qarshen shekara ne, yanada tsawo, zamuje gida. Ina tunanin da matata zan taho. "wace matar?" Mahmud yace, Rabi'a mana. Aure zansa a daura mana. Dariya sosai Ismail yayi, sannan yace, ba kace ka fasa ba? Mahmud yace, kai malam haqurina ya qare. Kullum cikin mafarkai, gara kai gwanin azumi ne. Ismail yace, in kaga zaka takura kuwa yin hakan shine mafita. To amma ya batun aikin hajinmu? Don gsky koda hutuna zai qare banje gida ba, nayi wa kaina alqawarin aikin hajji. In na samu yadda nakeso la duk shekara sai nayi har in gama karatu. Mahmud yace, munada lokaci ma, tunda sai an yi fiye da sati biyu da gama aikin hajji za'a koma hutu. Ka ga kuwa har zamuje mu dawo. Ismail yace, Allah ya kaimu lokacin, ai hutun ma ya qarato. Su Ismail sun dan tara kudi sakamakon wani aiki da sukayi tare da amincewar hukumar makarantarsu. Wadanasu masu hannu da shuni ne suka nemi makarantar ta taimaka musu da dalibai wadanda zasuyi musu rabon abincin sabil, da yake can qasar kowa so yake yi yaga an cinye nasa. Shine makarantar ta nemi dakiban ta tuntu6e su ko akwai wanda keson yi. Ismail da Mahmud suka shiga cikin sahun wadanda suke son yi. To anan ne suka samu kudi. Kamar yadda suka tsara hakan ce ta kasance, domin sunyi aikin hajji lfy sun gama lfy. sannan suka koma makaranta sukayi shirye-shiryensu suka nufi gida Nigeria. Abuja aka sauke su. Zukatansu fal da farin ciki mara misaltuwa. Ismail yace, gsky Gida daban ne, duk da cewa Abuja ba katsina bace, sai naji wani irin dadi, duk da cewa qasar dana baro tafi tawa komai, amma farin cikin na daban ne. "Ai Gida yayi." inji Mahmud. [20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 3⃣8⃣A kaduna sukayi azahar, sannan suka dauki hanyar katsina cikin qosawa. Mahmud yayi murmushi don Jindadi, don cewa zaiga iyaye da kuma Rabi'a. Ya kalli Ismail, na qosa matuqa mukai Gida. Ismail yayi dariya, "wai kai wa kk zumudin gani ne haka?" Mahmud yace, su inna dasu Malam, sai kuma rabi'a. Ismail yayi murmushi. "Gara dai ka fadi gsky. Mahmud yace, gskyr kenan, kai wa ka qosa ka gani? Ismail yace, yaya Amina mana da 'yan yaranta, tunda ni ba uwa gareni ba bare uba. Sai dai 'yan Gidanmu da yayuna, duk da cewa, su ba lallai bane suyi murna da ganina. Amma harga Allah nidai ina sonsu, kuma nayi kewarsu. Haka ina kewar Malam sosai. Mahmud yace, kayi tuya ka mance da albasa, matarka fa khadija? Ismail yayi murmushi, "kasan harga Allah na manta da ita." Mahmud yace, sbd me? Ismail yace, sbd ko waya na kira, ba ko yaushe take amsa ba. Ba ta damu dani ba, shiyasa. Amma duk sadda zan sayi Tsaraba bana mantawa da ita. Mahmud yace, kenan bakayi kewarta ba? Ismail yace, ba sosai ba. Don nasan itama bata damu da ganina ba. Mahmud yace, kamata yayi kawai ka taho da ita in zamu dawo. Ismail yace, banajin hakan a jikina, ni kwanakinnan ma mafarkin Zainabu ke damu na, da kuma yawan tunaninta. Mahmud cikin jin haushi yace, wacece kuma zainabu? Nayi tsammanin ma ka dade da shafe babinta? Gidan wani fa take. Ismail yace, na dade da shafe babinta Allah kuwa. Tunda tayi aure, ka ta6a jin nayi maganarta? Mahmud ya girgiza kai. Ismail yace, ni kaina bansan dalilin dayada ta dawo cikin rayuwata ynxun ba. Mahmud yace, sharrin shaidan da mugayen mafarkai. 3⃣9⃣La'asar sakaliya, guraren qarfe biyar suka sauka garin katsina. Shatar mota sukayi zuwa gida, za'a fara sauke Ismail gidansu yaya Amina, domin suna kan hanya, sannan a wuce da Mahmud. Ta kan layinsu Zainabu zasu wuce, sbd Gidansu yana bakin titi. Tun kafin su qaraso yaketa leqen gidan. Daf da zasu gota gidanne, kamar cikin mafarki, idanunsa suka qyallo masa Zainabu ta fito daga maqotansu dauke da bokiti a hannunta. Da alamu ruwa ta debo. Ismail cikin sauri yace, Kalli Zainabu, Mahmud. Mahmud ya waiwaya ya hangeta. Yace, tabbas itace. Qila tazo ganin gida ne. Ismail dai yana can yanata waiwayen Zainabu har ta shige gidansu. Ya lumshe ido gabansa yana wata irin faduwa. Gida Zainabu tazo kamar yadda Mahmud yace, ko kuwa aurenta ne ya mutu? Mahmud ya lura da yanayin da Ismael ya shiga. Don haka sai ya harareshi, cikin salon son kushe Zainabu yace, duk ma ta tsufa, qila ma ynxun ta haifi yara uku. Da sauri Ismail ya kalleshi, "haba dai Mahmud! Sai kace, akuya, duka yaushe akayi mata auren? Mahmud yayi dariya, tsufan ne naga yayi yawa. Ismail dai bai tanka ba illa dai yanason sanin labarinta. Sadam yana fitowa an aikeshi sai kurum yaga mota ta tsaya. Shima tsayawa yayi, domin ganin ko su kawun nasa ne. Sororo ya tsaya yana kallon kawun nasa tamkar wani sabo fil. Da gudu ya juya cikin gida yana fadin mamanmu! Kizo ga kawunmu nan ya iso! Mimi ta rasa dalilin dayasa taji gabanta yayi wata irin faduwa. Tana daga cikin dakinta, ta sake jiyo saddam yana fadin, kinga kawunmu sai kace wani balarabe. Da sauri su yaya Amina suka fita, ga tsohon ciki, Ummi kam da gudu ta isa ta qanqameshi. Cikin murna suka gaisa da Mahmud, sannan aka kwashe kayan Ismail zuwa cikin gidan, sannan ya rako Mahmud zuwa gurin motar, sukayi musabaha, yace, ka gaidamin Malam. Sai na shigo zuwa dare. Ya koma cikin Gida, ya samu su yaya sunata yi masa shirye-shiryen inda zaici abinci. Ya Kalli yaya, dama ciki ne dake? Shine muna waya baki ta6a fadamin ba, da nayi miki tsarabar kayan jarirai da kuma pampers. Suna arha acan. Ina gani gurin abokan karatunmu masu iyali. Tayi murmushi, cikin kunyar qanin nata. Tace kurum sai ince maka inada ciki? Kafin ya sake magana tace, mu shiga ciki mana ga abinci. [20/09 12:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣0⃣Ta kalli Ummi, "kira auntynku mana, ko tana varci ne, sarkin varci." Ya kalli dakin, "dama tana ciki ne? Yaya tace, eh, sai dai ynxun haka varci takeyi. Yaya ta soma gabatar masa da abinci dana sha mai sanyi harda kaza aka soya masa. Yace da baku wahalar da kanku ba gurin soya min kaza, ko acan na jima banci ba, sbd ta hau min kai. Yaya tace, ai kuwa gashinan ka zama tamkar balarabe. Ka ganka kuwa? Ismail yayi murmushi, bari inci Alalata dai yaya. Yana ci suna hira. Ummi ta shigo tace, mamanmu aunty khadija tana varci. Tace ki tasheta kawai. Yace a'a ki varta kawai. Bayan ya gama, suka fito, yace, su saddam su kwashe kayansu sukai masa dakin khadija. Tana kwance tamkar mai varci, amma idanunta biyu. Gabanta ke faduwa tanajin jin qamshinsa, lokacin daya shigo dakin, bata ta6a jin irin qamshin ba. Yana tsaye yana kallon ta. Yaya ta shigo tasa hannu ta girgiza ta, "khadija ki tashi mana, magriba tabkawo jiki, ke varci baya yi miki wahala." Miqa tayi sannan tace, yaya kk ce mene? Tace, ki tashi Malam Ismail sun iso dazu. Shikam yana jingine da bango ya harde hannuwansa. Mamakin ramarta yakeyi, ga shi tayi baqi, ga qurarraji a fuskarta. Da ma ita ba qiba ba, sai tyi tamkar wata baby. Mimi kasa dago ido tayi ta kalleshi. Kanta a qasa tace, sannu da zuwa kawun su Ummi. Sunan data kirashi dashi yasa shi murmushi. Yace, yauwa sannunki malama khadija. Muryarsa da taji ta canza ne yasata dago kai. Jin muryar tayi tamkar ta balaraben da ya koyi hausa, ko ko bafillatanin da hausa bata isheshi ba. Mamakin kyawun surarsa ta bayyana a fuskarta, ta kafa masa ido, batasan lokacin da bakinta ya furta cewa, kai! Amma kayi kyau da yawa. Qasar ta canza ka, ta amshe ka. Yayi murmushi, a zuciyarsa yace, ina girman kan? Ya dubeta, nayi kyau? Khadija dama can ni mai kyau ne. Tadan ta6e bakinta tare da yin dana sanin fadar hakan a ranta, ta lumshe ido. Maza sunada kyaune? Kawai dai ka samu hutu. Yayi dariya, ko ma dai yaya ne kin yaba, kuma nagode. Taso kidan taka in gani, tafiyarki ta koma daidai? Yaya dake zaune bakin gado tana jinsu, sai ta tashi, "bari in kira abbansu saddam in fada masa ka iso, ta fice. [20/09 8:59 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣1⃣Mimi tace, in kayi haquri, ai zaka gani, ba sai kasa ni yin wata tafiya ba. Yace, amma kin daina dingishin? Harynxu tana tare da jin haushin maganarsa ta dazun, tace, "Qila." ya matso ya zauna a bakin gadon, ya rage muryarsa, "kinyi baqi, kin rame. Amma muryarki dinnan mai sauti can qasa da miskilancinki suna nan." Ta zuro qafafunta ta dayan gefen ta sauka. Sannan tace, bai kamata kaji mamakin ganin na canza ba, domin kafi kowa sanin komai. Ina Mahmud? Shi ma ya miqe, yana gida. Anjima ki shirya muje mu gaida malam. Ta girgiza kai, "ban fita kayi haquri." yayi dan murmushi, hakane, tam bari na dan yi wanka kafin a kira magriba. Ta nufi gurin madubinta tana fadin yanada kyau. Ummi ce tasa ruwan wanka takai masa. Ya bude jakarsa ya dauki kayan wankansa cikin wata jaka ta leda, wadda aka yita don saka kayan wanka. Sannan ya ciro jallabiyarsa, wata mai shegen kyau ruwan hanta, tana da zif daga qirjinta har wuya, sai kuma tsintsiyar hannu da ma6alli. Sai hula mai kalar zaren da akayi dinkin. Mimi tana kallonsa da gefen ido, ya dora kayan saman gadonta, sannan ya fita. Da kallo tabi bayansa. Kyawunsa yana bata mamaki. Bayan ya fito, sai daya shirya tsaf, Mimi tana ta satar kallonsa. In ta ga alamun zaya waiwayo saita sauke kanta. Ya feshe jikinsa da turarukan larabawa, qamshinsa ya gauraye ko'ina, sannan ya kalleta, nayi kyau? Cikin zolaya yayi tambayar. Ta ta6a baki, tare da cewa, ina wani kyau anan? Yace son ranki kk fada. Bari inje gidanmu. Daga can in wuce in gaida malam. Tace ka gaida su. Ya dauki qaramar jaka daga cikin jakunkunan da yazo dasu. Tabi bayansa da kallo har ya saki labulan. Ta jingina da sif dinta tana mamakin yadda ya rikita ta har haka. Yaya tana zaune zatayi alwalla, ya ajiye jakar a gabanta, tsarabar 'yan gidanmu ce, su yaya jallabiyu, matan kuma dabino ne da zam-zam. Inna kuma harda darduma da wata doguwar riga. Yaya tace, yayi, Allah ya bada lada. Yace Ameen. Ya dauka ya fita.4⃣2⃣Duk wanda suka gaisa da Ismail, sai yace, Masha Allahu kayi kyau. Yana shiga gidansu ana kiran magriba, ya Kalli dakinsa yayi murmushi, sannan ya shiga cikin gidan, babu zato suka ganshi. Don haka suka shiga kallon kallo. Sai kuma aka shiga yi masa sannu da zuwa. Yayi musu qwarjini sosai, don haka da 6are-6aren jiki sukayi ta amsa gaisuwarshi. Ya shiga dakin inna sai yaga ta qara masa tsufa. Ya gaida ta sannan ya kawo tsarabarsu ya bata tare da yi mata bayani a gurguje ita kanta duk sai yaga tayi sanyi. Ya nufi masallaci. Bayan sun idar da sallah nan sukayi ta gaisawa da mutane suna tayi masa sannu da zuwa. Yana tare da jama'a har zuwa bayan isha'i, sannan ya nufi Unguwar su Mahmud. Ya shiga cikin gidan suka gaisa da mutan gidan, sannan ya fito ya zauna gaban Malam inda suka gaisa tare da ci gaba da hira. Malam yayi murna da zuwansu, sannan ya saka musu albarka. Sun jima suna hira suna ta bashi labarin makarantar. Daga bisani suka nufi gidansu Rabi'a, shida Mahmud. Yaro ya samu ya tura cewa, ana kiran Rabi'a. Bayan tafiyar yaron ne yace, bari mu gani tana fita da bananan. Ismail yace, kar kayi zargi. Rabi'a ba zata yi maka haka ba. Dan aiken ne ya katse su da cewa, wai ance tayi aure. "Aure?!" Mahmud ya tambaya cikin faduwar gaba. Ismail yace, ba kunyi waya ba? Mahmud cikin tashin hankali yace, ko jiya munyi waya, bazata kawai naso inyi mata, shiyasa bance mata muna hanya ba. Ismail yace kai yaro je kace inji Mahmud. Tare da dan aiken suka fito tayi murna sosai da ganin masoyinta. Tace ina zuwa. Duk da cewa dare ne, saida ta qara hoda a fuskarta sannan ta fesa turare mai madaidaicin qamshi, sannan ta dauki tabarma ta fito. Shikam Ismail, suna gaisawa daya lura masoyan suna dokin juna, sai yaga ya dace ya basu guri. Don haka sai yace, to ni zan tafi. Suka yi musabaha da juna. Ismail yana cewa, sai na shigo da safe. Zan shigo in kawo ma Malam tsarabarsa. Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu. Gidan yaya Amina zaka kwana? Ismail yace, a'a Gidanmu zanje in gyara dakina ynxunnan. sukayi bankwana ya wuce. 4⃣3⃣Gidansu ya koma, inda ya bude dakinsa, duk qura da yanar gizo-gizo. Ya kai qarfe goma sha biyu Tsakanin share-share da kuma goge-goge, sannan ya shiga gida yayi wanka. Sai daya kwanta sannan ya tuna cewa yayi masu yaya alqawarin cewa, zai koma. Ya kalli agogon wayarsa, a fili yace dare yayi. Washegari tunda ya dawo daga masallaci ya sake kwanciya bai farka ba sai qarfe takwas. Ya shiga cikin gida suka gaisa da mutan gidan. Sai dai yayi Mamakin ganin yadda suka sakar masa fuska. Amma sai ya tuna cewa fa yayin dawafin sa a dakin ka'aba, yayi ta roqon Allah cewa, Allah yasa shida 'yan uwansa da suke uba daya sun fahimci juna. A fili yace, Allah ya amshi addu'ar sa. Bayan yayo wanka ne, sannan ya ciro jakar kayansa tada, ya cire ma abbansu saddam kala biyu, sannan ya dauki sauran zuwa cikin gida yaba yayyinsa, sannan ya nufi gidan yaya Amina. Mimi ce amsa sallamarsa lokacin da ya isa gidan. Tana zaune akan qaramar kujera, tana wanke-wanke a bakin rijiya. CiKin Mamaki ya kalleta, tare da tausayi, yace, Mimi kece kk wanke-wanke? Ina Ummin? Ta dago ta kalleshi, "sunana khadija ne, ba Mimi ba. Ummi sunje makaranta, yaya kuma taje ganin likita. Ko dama tana nan ka san tana buqatar taimako. Ya tsugunna kusa da ita, qamshinsa ya daki hancinta, gabanta kuma ya shiga wata irin faduwa. Maganarsa tamkar rada yace, in taimaka miki ko? Ta dago ta dubeshi, wata irin kunyarsa ce ta ji ta kamata, sbd cikin idonsa ta kalla, ta sunne kanta cikin cinyarta. Tace, ka barshi kawai, "yaya ma za'ayi kayi aikin mata? Cikin kwaikwayon muryarta yace, ai nima na matanne, kinga kenan babu laifi don nayi aikinsu ko? Yadda yayi din, sai taji ya birgeta sosai. Tace, nikam ka barshi kawai. Ya miqe tare da fadin shikenan tunda bakison taimako. Ya koma kan galan din ruwa ya zauna. "ki gama muyi magana dake. Tace, to. Kallonta kawai yakeyi cikin tausayi da birgewa. Ta gama ta kife, ta kai kwandon mazauninsa, Sannan tasa ruwa ta wanke gurin. Tana sanye ne da doguwar riga, tun irin kayanta ne data zo dasu. A ransa yace, kaya masu tsada sunada qwari, dubi yadda har ynxun kayanta suke da kyansu. Zasu jima basu lalace ba. Ta dubeshi, sannan ta nufi dakinta. [20/09 9:57 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣4⃣Da kallo ya bita, yana tuno asalin Mimi 'yar gata, 'yar jin kai, yarinyar da batason talauci balle hulda da talaka. Matuqar tausayinta yakeyi ynxun. Sannan ya jinjina mata sosai, domin bai ta6a zaton zata sauko haka cikin sauri ba. Hakanan ya fahimci cewa halinta ne yin abinda tace zatayi. A fili yace, wannan ya zama dole in cika mata dukkan alqawuran dana daukar mata. Wata zuciyar tace, harda saki? Gabansa ya fadi, amma sai ya miqe ya nufi dakin. Tana kakka6e gado, ya shigo ciki. Yace, ina zan zauna? Ta nuna masa bakin gado, bayan ta gama gyarawa, ka zauna anan. Ya zauna, yana kallonta tare da ci gaba da tuno da gatan ta har ta gama. Aikin dai babu sauri, amma tsaf-tsaf. Ta kalleshi, in nace zanyi wanka zan 6ata maka lokaci ko? Yace, yi wankanki. Ta dauki hijabi ta saka sannan ta fita. Ta dauki ruwan wankanta da Ummi ta zuba mata, sbd bata iya jan ruwa a rijiya, tsoron rijiya gareta. Bayan fitarta ne yaga wani littafi akan Allon gadonta. Ya dauka ya Kalli bangon, INDA RAI, DA RABO. Haka yaga an rubuta ajikin littafin, sunan littafin shine yaja hankalinsa zuwa ga bude shafukan littafin yana dubawa jefi-jefi har ta fito. Lura da tayi baya kallonta, sai ta shafa manta a cikin hijabin, da tazo saka kaya ne ta kalleshi, a tunaninta hankalinsa yana kan littafin ne, sai ta faki idonsa ta saka kayan. Murmushi yayi, a ransa yace, khadija ke nan, domin tunda ta fito hankalinsa yana gurinta. Bayan ta gama tazo ta zauna a daya gefen gadon. Ya dubi littafin, menene ma'anar inda rai, da rabo? Ta danyi murmushi, bansan yaya zance maka ba, sbd ka san bansan kan hausa sosai ba. Kawai dai naji su yaya suna sauraron littafin ne a rediyo, shine nace, a siyomin. "wa ya siyo maki? Tace ban sani ba yaya ce tasa aka siyo. Yace, kin karanta? Ta daga kai, alamun eh. Kin qaru da wani abu? Tace, sosai ma, duk da cewa labarin soyayya ne. Yace, shikenan zaki bani labarin wani lokaci. [21/09 3:17 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣5⃣Ya aje littafin ya fuskance ta sosai, "ki bani hankalinki muyi magana mai muhimmanci. Ta sunkuyar da kai, "ina sauraronka" bata iya kallonshi, don sai taga yayi mata wani qwarjini, ya cika dakin, "zan fara da son sanin matsalarki, in kina da wata matsala. "tana wasa da hannunta, tace, ni banida wata matsala, domin duk abinda akaci, shi za'a babi daidai qarfinsu, kuma zuwa ynxun na iya cin komai. Kuma ba'a takura min, komai nakeso nayi, zanyi ba wulaqanci. In babu zan haqura kamar yadda kowa ya haqura, shine kawai. Yace, na fahimta, to kina son siyan wani abu, ko burin yin wani abu, ina nufin na kudi? Ta saci kallonsa, banison komai na kudi, don duk abinda nakeso na kudi, bakada qarfin saimin. Don haka kar ka damu, khadija ba mimin daka sani bace, Nayi haquri da iyayena ma bare wani abin duniya. Babu komai a raina. Babu abinda yake birgeni cikin duniya ynxun. Yace, har nayi zaton zaki koma makaranta, don ki kammala digiri dinki? Tace, baka zaton in na fita iyayena su samu labarina. Yace, har ynxun baki huce da fushi dasu ba? Tace, na huce tun bayan da bakanan yaya Amina tayi ta karantomin kurakuraina ta hanyar nasiha, har na fahimci irin sa6awar da nayiwa iyayena. Ynxun kam ina nesanta kaina dasu ne, sbd ganina kusa dasu zaita sakasu cikin 6acin rai, zasu dinga tuno abinda nayi musu. Shiyasa bana fita. Banida wani buri daya wuce cikawa da imani inje in tarar da khalil. Gaban Ismail yayi matuqar faduwa, domin bai zaci jin haka daga bakinta ba. Baisan lokacin daya ce, dama har ynxun baki manta da khalil ba? Da sauri ta kalleshi, ta yaya kk zaton zan manta da wanda yake matuqar sona? Wanda ke fadamin kalamai masu sani cikin farin ciki, da nishadi. Wanda ke kwadaita min wata irin rayuwa, amma kafin mukai gareta, sai mutuwa ta katse hakan. Ya barni cikin qunci da takaici! Kuka ya kufce mata. 4⃣6⃣Shiru yayi tamkar ruwa ya cinyeshi, nazarin zantukanta yakeyi. ya dan qara matsowa kusa da ita, ya tausasa muryarsa qwarai. "Yi haquri khadija, inda zaki bani labarin soyayyarku da khalil, zanso ji. Ta dubeshi, fuska cike da hawaye, ba zan iya ba. Banason in tuna da komai game da labarin. Abinda kawai ba zan manta ba shine tsananin son da khalil yayi min. Haka kuma ba zan manta da yadda nayi ta wulaqantashi ba. Salon son da khalil yake nunamin ta hanyar chatting dina a facebook, wtsapp, da sauran irin wadannan kafofin, tun bana bashi amsa, har dadin kalamansa suka sa na soma bashi amsa, duk da ni ba amsa mai dadi nake bashi ba. Ranar dana soma son khalil, yawun bakina na watsa masa fa a cikin mutane. Amma kasan me yayi? Ismail yace, a'a tace,, ga mamakina sai naga kurum yasa harshensa ya lashe yawuna daya sauka kan kafadarsa, sannan yayi murmushi, "komai naki inason sa. In na bari yawunki ya sauka a qasa nan, nayi muguwar asara. Ta soma sabon kuka, wannan kadan ne daga irin son da khalil yayi min. Ismail yace, shikenan kiyi haquri. Allah ya yafe masa tace Ameen. Yayi shiru. Yasan ynxun yaya Amina ta rage mashi hanya da tayi wannan jihadin, na yiwa mimi nasiha harta fahimci cewa tayiwa iyayenta laifi, ba zai wahalar shawo kanta don zuwa basu haquri ba. Amman wannan ba ynxun ba. Ya dubeta, har ynxun tana share hawaye. Nace kiyi haquri. Kuma zaki iya samun wanda yafi khalil sonki, kema kuma ki soshi fiye da son da kk yiwa khalil din. Ya girgiza kai, Da wuya hakan ta kasance, nina kulle babin so, koda na samu mai sona, ni kam na tabbata ba zan soshi ba. Ismail yayi murmushin yaqe, to yaya batun islamiyya fa? Mimi tace ina daukan karatuna a gurin yaya Amina. yayi dariya, shikenan Allah ya biyata da aljannarsa. [21/09 7:46 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣7⃣Ya miqe ya dauko jakar tsarabarsu, ya dawo ya zauna bakin gado, "zo ki za6i abinda kk so cikin tsarabata. Ta matso. Ya dauko jakar ya dora ta saman Gadon. Ya soma ciro jallabiya, pink mai ratsin baqi, sai jarta, itama mai ratsin baqi, sai takalma da riga da wando kala biyu, duk ire-iren wadanda take sawa. Ta tsaya tana kallonshi, sbd ta san tsadar kayan. Kafin tace wani abu, sai kurum taga ya ciro wani gwangwani a can qarshen jakar, ya miqo mata. Da sauri ta kar6a sbd irin turarenta ne. Ta soma karanta rubutun jiki a fili tace, "tabbas shine" ta dago ta dubeshi, "siyan turarennan kayi? Yace eh, siya miki nayi. Tace ina ka samu kudi haka? Na ga kai din dalibi ne, kuma duk kayan nan suna da tsada, musamman wannan turaren? Yayi murmushi, "munyi aikin raba abinci ne ga mabuqata aka biyamu. Ta soma hawaye, ban ta6a tunanin zan qara amfani da wannan turaren ba. Nagode sosai. Ya tausasa murya don jin dadin sake burgeta. Karki damu khadija, nayi miki alqawarin in Allah ya buda min, zanyi miki gatan da yafi wanda kk ta6a shiga a fannin jin dadi. Ta sa idanunta cikin nasa, "nasan zaka iya, domin duk abinda kayimin alqawari, ka cika. Ina ganin kimar ka sosai, ynxun saura abu daya ya rage. Ya zaro mata manyan idanunsa, me? Tayi shiru, gabanta yana faduwa. Yace karki damu ki fadamin, qila na manta ne. Ta sunkuyar da kai, "maganar rabuwarmu." Gabansa yayi wani mugun faduwa. Dakin yayi tsit na wasu daqiqai kamar hudu. Maimakon yaci gaba da zancen, sai kawai yace, yau yau dale kuka karya ne a gidan nan? Yunwa nakeji. Tace, ruwan Lipton ne da biredi. In zaka ci ina zaton akwai a flask. Yace zansha shayin, kinsan mu shine ma abin shanmu kowane lokaci. Ta miqe ta nufi kicin ya bita da kallo, tafiyarta ta dawo tamkar da, cikin nutsuwa da kamewa. Ta dauko filas din ta hado da kofi da cokali da kuma suga. Sai ledar bread din. Zuciyarta kuwa tambayar kanta takeyi menene dalilinsa na share zancen rabuwarsu? Yace, ba zanci bread ba. Na saba dana can da mukeci bashi da suga. [9/21, 16:54] A~PROF: 4⃣8⃣Ya miqe ya janyo jakarsa, ya zuba wani ganyen tea, ya zauna yana sha. Duk sukayi shiru, kowa da kalar tunaninsa. Shi ba wai ba zai iya sakinta bane, amma tsoron sa kar ya saketa, ta sake guduwa. Ta katse masa tunani, "Wai meyasa ka share batun da kawo? Ya kalleta, "ba sharewa nayi ba. Khadija muna buqatar qarin lokaci ne. Kiyi haquri har in kammala karatu na." Tace, zuwa yaushe? Ya dubeta da sauri, "kin samu wanda kk so ne? Itama cikin sauri ta kalleshi, "Allah ya kiyaye min, ni kam banason kowa. Nauyin ne nikeson a sauke min. Yayi murmushi baice komaiba. Sati biyun da Ismail sukayi a Nigeria sunyisu ne a cikin hidimar bikin Mahmud. Babu yadda baiyi da Mimi ba akan taje gurin walimar bikin, amma taqi, dolensa ya haqura ya barta. Bayan kwana biyu da kammala bikin, suka soma shirin komawa madina. Ango da Amarya cikin dokin juna a ranar tafiyar, ko cikin jirgi tamkar su hadiye juna suna ta birge Ismail, wanda ya lumshe ido yana tuno hawayen Mimi da suke zuba lokacin da sukeyin sallama. Ya tuna tambayar da yayi mata. Khadija wannan kukan kuma na menene? Ta girgiza kai, "nila ban san ko na menene ba. Ya ciro kyakkyawan hankici daga aljihunsa, sai qamshi yakeyi. "share hawayenki da wannan, sai in munyi waya kenan ko? Ya sauke ajiyar zuciya, tare da furzar da wani huci mai zafi. Yana kewar rabuwa da yarinyar. Yayi ta tuna huldarsuda kuma irin CANJIN RAYUWAR da Allah ya saukar mata. Allah yasa ya zama sanadin shiriyarta kenan. Labarin data bashi na tsohon saurayinta, abinda ya fahimta da Mimi, ita mutum ce maison aso ta, aji da ita, a nuna mata tsantsan so a fili, sannan a fada mata kalaman tada hankali. A fili ya furta cewa ban iya wannan ba. Sai kuma Zainabu ta fado masa, ya tuna da zancan su da yaya Amina bisa ganin da yayi mata. Yaya tace, masa tana gidan mijinta, qila dai tazo duba su ne. Haka yayi ta tunane-tunane har Allah ya kaisu lfy. [9/21, 17:35] A~PROF: Satin su Ismail daya da tafiya, yaya Amina ta haifi 'yarta mace, aka sa mata Aishatu. Yaya tasha mamakin ganin 'yan uwanta mata yadda suka zo mata barka harda suna, sa6anin da ba kowa ke zuwa mata barka ba bare suna. Inna kuwa zuwanta uku. Mimi kam ta takura sosai ranar suna, domin sam batason jama'a, kamar ta bar gidan amma ba yadda zatayi, dole ta haqura. [22/09 11:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 4⃣9⃣Lokaci yana qhudewa kwanaki quna qarewa, yau gashi su Na'ima anyi arba'in. Ta matsu qwarai tabar gidan minister, domin ko abincin da zataci sai taje kicin da kanta ta kar6a. Hatta 'yan aikin gidan sunsan batada wata kima, tunda a gabansu za'a zage ta tass. Don haka ko aiki tasa su basa yi mata. Sannan ga gadara da yaron, kullum akayi masa wankan safe, za'a tafi dashi gefen kakarsa, sai yamma ko in ya buqaci Nono. Da ma mai wanka da shirya shi musamman aka dauko. Shi kuwa Abbas sai dai ta jiyo muryarsa daga can sasan. Bata damu ba don ita ynxun ya gama sire mata. Kwana arba'in da bakwai suka maida ta gidanta bayan an kafa mata dokoki da sharudda akan yaron, sai kace ba itace ta haifeshi ba. Lokacin ne ma ta samu zuwa gidansu yini. Kuka momy Nafisa ta tasa Na'ima tayi tayi, sbd baqi data qara akan nata, gashi duk tayi zuru-zuru, idanu sun shige. Lokacin Alhaji bayanan Abuja, tace, bari dai yau dadynku ya dawo zan fada masa komai game da halin da kk ciki. Na gaji, gara komai zai faru, ya faru. Na'ima tace, yauwa momy don Allah ki taimaka min. In ba haka ba, wata rana zakije ki dauko gawata a gidan Abbas. Har dare Na'ima tananan tana jiran dawowarsa. Sun zauna sun karanto masa komai game da halinda Na'ima take ciki. Yace sam qarya ne, domin ta jima tanason kashema Na'imar aurenta. Su tashi su bashi guri. Ya kalli Na'ima, "karki daka ta mahaifiyarki, ki zauna dakinki shine cikar mutuncinki. Na'ima tace, Allah dady duk abinda kaji dinnan shine yake faruwa, yace kije zan bincika. Fitarta keda wuya, Alhaji Bashir ya kira layin Abbas. A tunanin Alhaji Bashir, Abbas da Na'ima duk daya ne agurinsa. Bayan sun gaisa, sai Alhaji Bashir yace, zantuka nakeji marasa dadi abakin Na'ima, tana fadamin wai bakwa zaman lfy tunda taje gidan. Shine na kira ka inji menene gskyr zancen? Abbas yace e.. to kusan akwai hakan daddy. Alhaji Bashir yace, to menene dalilin hakan Abbas? Abbas babu kunya ko shayi, yace, gsky daddy ina matuqar qoqari gurin zama da Na'ima, sbd gsky ni na wai ina sonta bane sam, Mimi nake so. "kalaman sukazo ma Alhaji Bashir a bazata, ya kuma fassarasu da cin fuska. 5⃣0⃣Amma sai ya danne, yace, in banda abin Abbas abinda yayi Mimi aishi yayi Na'ima, dukkansu 'ya'yana ne. Abbas yace, daddy Mimi fara ce mai aji. Na'ima baqa ce mai naci, amma aka dauki dauki Mimi aka ba wanda baisan darajata ba... "Dakata Abbas! Alhaji ya katseshi, cikin zafin zuciya. Yaya inayi maka magana kanayi min wani shirme? Zancen Mimi ba naka bane, qanwarta ce matarka, kuma a kanta muke yin magana. Bakason ta shine baka fada ba tuntuni, sai ynxun da kuka soma samun qaruwa? Ynxun dai abinda nakeso dakai, in tana yi maka wani laifi ne to sanar dani, sai in tsawata mata ta daina. Abbas yace, nidai son da banayi mata shine kawai matsalarmu. Alhaji Bashir yayi shiru, cikin Mamaki ya rasa me zaice, sai kawai yace, shikenan in ka samu lokaci kazo ina nemanka. Mamakin Abbas ne ya cika Alhajin, yadda yake magana cike da rashin ladabi. Kar dai ace yaronnan bashida tarbiyya. Sai kuma ya canza kiran wayarsa zuwa ga minista. Bayan sun gaisa, sai yace, ashe dama yaran nan zaman rashin jituwa sukeyi tun tuni? Minister yace, kamar yaya? Nan Alhaji ya kwashe komai ya fadawa minister har yadda suka yi ynxunnan. Sai kawai yaji minister yasa dariya, tare da fadin, karka shiga zancen yarannan. Baya sonta, yaya akayi ta haihu? Ya kamata da kayi masa wannan tambayar, lokacin daya ke fada maka cewa baya sonta. Alhaji Bashir yace, neman mata da tace yanayi shine matsalar ai. Minister yasa wata dariyar. "kar ta damu da wannan, in dai ya sauke mata nata haqqin. Kasan yarannan ba'a rabasu da son nishadi. Su kuwa mata, ai sune nishadin rayuwa. Kan Alhaji Bashir ya kulle, kenan ya daure ma dansa gindi yayi duk abinda yakeso, kuma bazai iya hanashi sa6ama Allah ba kenan? Minister ya katseshi da cewa, nayi zaton zakayi min magana akan hauhawar farashin man fetur ne? Alhaji Bashir yace, a'a ba wannan bane. Shi kenen saida safe mayi maganar kasuwanci, in Allah ya tashemu lfy, minister yace, Allah ya kaimu. Kada kasa kanka a damuwa game da batun wadannan yaran. [22/09 11:55 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣1⃣Kwana Alhaji Bashir yayi da abin a ransa. Washegari ya nufi katsina. Tun saukarsa hajiya sauda ta karanci damuwa can qasa tare dashi. Amma data tuntu6eshi, sai yace, wai babu komai. Ta takura masa da tambaya don ta fada masa cewa, saidai inba zai fada mata ba, to ba zata takura masa ba. Amma batun matsala tabas tasan yana ciki. Sannan ya fede mata komai. Yace, ni damuwata ban san ta ina zan 6ullo ma lamarin ba. Hajiya sauda cikin damuwa tace, dama Alhaji baku binciki halinsa ba? Yace, ni ina na wani bincika. A zatona yayi tarbiyyar 'ya'yansa, nayi hasashen sunada lfy tamkar nawa. Ashe nayi kuskure. Shi kansa ministan, sai ynxun nake sanin nasa halayen, sbd haduwarmu babu dadewa muka qulla wannan auren. Hajiya sauda tace, duk abinda ya faru, da kuma wanda zai faru nan gaba, duk laifinka ne, kai kawai ka duba abinda zaka samu ne kawai, ka dauki 'yarka ka bada. Yace, sauda abinda ya faru, ya riga da ya faru, sai dai a kori gaba. Ni ynxun roqo na a gurinki, ki bani shawara, domin kaina ya riga ya kulle. Hajiya sauda tayi shiru, tana tunanin me zatace. Gashi dai lokacin da za'a qulla abin ba'a nemi shawararta ba, sai ynxun da za'a kwance shi. Tanason ganin mijinta cikin kwanciyar hankali, musamman shida ke fama da ciwon suga. Don haka ba tare da ta tuno masa wani abu da yayi mata abaya ba tace, shawara dai daya ce, tunda shi uban yaqi kuyi batun, ka samu shi abbas din kuyi magana. In har baya sonta, da zaman uquba gara su rabu kawai, Allah ya hada kowa da rabonsa. Yace hakane kawai mafita, ai nayi da na sani babu adadi, har ina tozarta Mimi, ina cin zarafinta, ashe ba dan mutunci bane, kuma bai fito daga cikin mutunci ba. Hajiya sauda tace, kuskure ne dai ya riga ya faru, sai dai muce, Allah ya tsare gaba. Kwanansa uku ya koma Abuja sbd kawai ya gana da Abbas. Da safe Abbas ya sameshi a Gida. Bayan sun gaisa, yace, na kiraka ne don muyi magana ta fahimta, ni da kai. In har kana ganin bakason Na'ima to kawai ku rabu. Allah ya raya muku danku. Abbas yace, daddy ka samu daddy na kuyi magana, kamar yadda kukayi lokacin da zaku qulla auren, in ba haka ba zaice nine na saketa sbd banajin maganarsa. Alhaji yace ni zan masa bayani, abinda nawai nakeso shine ka fadamin abinda ke ranka Abbas yace, daddy nima inason a rabamu. Alhaji u, shikenan jeka zanyi magana da Dadyn naku. 5⃣2⃣Sai dai duk yadda Alhaji Bashir yaso suyi maganar da minister sam yaqi. Ransa ya 6aci sosai. Don haka ya taka har gidan Abbas ya samu Na'ima, ya tambaye ta ko akwai wani canji tsakaninta da mijinta? Tace, babu wani canji, domin ynxu ko wace irin mace kawowa yakeyi, kuma dole inyi musu girki, sannan ya daukarmin yaro ya kai musu shi, kowace jaruwa tayi ra daqunarsa. Yace, dauko mayafinki da kayanki kizo muje gida. Wannan shine mafarin tsiyar data 6arke Tsakanin Alhaji Bashir da minister. Qiriqiri minister yace, shifa bai yadda da wannan hukuncin ba, saidai inta koma can Gidansa da zama har zuwa lokacin da zata yaye jikan nasa, tabashi abinsa. Alhaji Bashir yace, wannan kuma wani abu ne da ba zai yiwu ba ko a cikin mafarki. Buqatarsa kawai Abbas yaba 'yarsa takarda, in ta yaye dansu, suzo su dauka. Wannan rigima itace ta datse kasuwancin da suka qulla suke aiwatarwa. Ikon Allah kenan. Shiyasa akace, komai mutum zaiyi, tofa yayishi don Allah. Masu son Zainabu sunata fitowa tun daga lokacin da ta haifi danta saurayi, amma kowa fada masa takeyi tanada wanda takeso, duk da cewa ba tada tabbaci akan samun wanda takeson, ko inda yake bata samu labari ba, bare tasan ko zata samu shiga. Amma begensa yananan cikin Zuciyarta, dashi take kwana, tana tashi. Bugu da qari, dole inna ta zuba mata ido, sbd tsoron hukuma, duk da irin son kudinta. Ita fatanta Zainabu tunda ta haufi danta lfy, ta samu miji ta qara gaba, ko bata yaye danta ba. Su kuwa mutan madina suna can suna ta karatu, babu ji babu gani. Ismail ya qware sosai a fannin tafsiri, yana da haddar litattafai da dama a cikin kansa. Malamansu suna jinjina ma Qwaqwalwarsa sosai. Sun sake samun wani hutun, lokacin Rabi'a matar Mahmud tanada tsohon ciki. Wannan hutun sun sameshi daf da azumin watan Ramadan. Sunso tsayawa, amma sai Malam Aminu yace, su dawo sbd shine sukeson ya gabatar da tafsir a sabon masallacin da aka gina nan Unguwar su. Masallacin Juma'a ne katafare. Kuma lokacin azumi za'a budeshi. Don haka suka nufo gida cike da doki, sbd shi Ismail mutum ne maison ganin yana daukaka kalmar Allah, kuma jama'a su qaru da iliminsa. [22/09 4:38 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣3⃣Wannan karon sun sauka cikin shirye-shirye sbd karatun azumin da zasuyi. Sam bai zauna dasu Mimi ba. Tun ranar da suka iso suka gaisa, ko kan kayansa bai dawo ta kansu ba, sai dai suyi waya da yaya. Sai ana sauran kwana biyu Azumi, sannan ya samu zuwa gidan yaya Amina, ya kwance kayansa ya basu tsarabarsu. Ranar ma dai bai zauna ba, sbd yana shigowa, Mahmud ya kirashi ya sanar dashi cewa, Rabi'a tana kan gwiwa. Da sauri ya fita ya samu Mahmud din a qofar gidansu Rabi'a. Fada ya rufe Mahmud din dashi kan cewa a fito da ita akaita asibiti. Zasu tafi nemo mota kenan, saiga wan rabi'a ya fito daga cikin gidan, cikin murna ya fada masu cewa, ta sauka, kuma an samu da Namiji. Murna gurin Ismail tamkar tashi matar ce ta haihu. Da dare ya shigo Gidan su yaya Amina, Aishatu ce kadai a tsakar gidan tana ta wasan ruwa, yasa hannu ya dauketa cak. Yayi sallama a qofar dakin yaya, tana sallar isha'i, yace Ummi yaya kk barta ita kadai a tsakar gida tana ta wasan ruwa duk ta jiqa jikinta. Tace, nima ina sallah ne kawu. Ynxun na ida. Ya miqa ta ,amsheta kisa mata kaya. Auntynki tana ciki? Tace, tana cikin tana sallah itama. Mimin batasan dalilin dayasa ta damu da Ismail ba wannan zuwan nasa. Duk da cewa, shi sam bai damu da ita ba wannan karon, tanason yin abinda zai birgeshi. Haka wannan karon yafi wancan zuwan wayewa, da gogewar ilimi, sannan kyawunsa yafi na wancan zuwan. Ko itace ke ganin haka? Oho. Lokacin da ta jiyo muryarsa, saita samu kanta da fesa turare a jikinta da kuma dakinta, ta zauna a bakin gado. Sai Zuciyarta ke tambayarta wai sbd me tayi hakan? Kafin ta lalubo amsa, har yayi sallama, ta amsa. Yace, in shigo? Tace ka shigo mana. 5⃣4⃣Ya shigo, cikin salon zolaya yake cewa, bayi zaton bake daya bace. Tadan ware idanu, da alamun Mamaki, "nida wa kk zaton samu? Yace, qawarki mana. Ta dafa hannunta da saman gadonta, tare da karkata kanta, ta dora kan kafadarta. "Nikam banida qawar data wuce Ummi, sai ko Aishatu. Yace, kardai kicemin har ynxun baki fita? Tace to ina zani kawun su Ummi? Wa na sani? Yayi dariya sbd sunan da ta kirashi dashi. Sunan nan da kk fadamin yana bani dariya khadija. Me zaisa ba zaki kirani da sunana ba Ismail? Tayi murmushi, "to ni bana iya fada ne. Na fa girmama ka ne. Ta fada da sigar shagwa6arta. Nidai gsky a daina fadamin wani kawun su Ummi, a kirani da wani abu kawai. Ta dubeshi, to Malam? Yace a'a ni dalibi ne, koyon karatu nakeyi. Kice min Ismail bin Abdurrahaman, ko kice, Abu Rumaisat. Tace ban gane Abu Rumaisat ba? Yace sunan yarinya ta kenan ta farko in Allah ya so. Rumaisat ko kice ummu suleim, duk sunanta ne. Ba kayi aure ba, amma kana fadin Yarinyar da zaka haifa? To in Maman taqi yarda fa? Maman babyn. Ya rasa dalili, sai yaji gabansa ya fadi, da take Cewa baiyi aure ba. Yace, nasan zata yarda, domin duk matar da zan aura, ba taqi yimin biyayya akan hakaba. Zataso abinda nakeso. Game da batun aure kuwa, zanyi shi da zarar na kammala karatuna. Kafin lokacin na samu mai sona. Mimi ta samu kanta da damuwa, sakamakon amsar daya bata. Tayi shiru. Ya katse ta, bayan ya Kalli agogon hannunsa. Lokaci yana tafiya. Nazo ne muje kiyi ma Rabi'a barka. Karki cemin a'a, duk abinki yaukam sai kinje. Mimi ta 6ata rai. Yace tashi tashi kawai. Ta miqe tana fadin nidai banason fita ne. Yace, kuma saikin fita ba, gashi da nisa kuma a qafa zamuje, dare ne bare kice kar wanda yasanki ya ganki. Tace kai baka gane nufina ba. Ni fa banason inyi hulda da kowa ne, ballantana in saba da kowa. Yaya Amina da kai da yaranta kun isheni. Yace, amma ai kinsan cewa mutum rahama ne ko? Shikenan muje, ba sai kunyi hira ba, bare ku saba. In kinyi mata varka, kiyi shiru. 5⃣5⃣Ta dauki qaramin mayafinta ta yafa. Ya kalleta, kisa hijabi mana khadija. Tace duk fa hijaban da ka kawomin qasa suke ja. Ni ban saba dasu ba, ina yin sallah dasu ne. Yace karki damu kome suke ja, in dai baki sani ba zakiyi sallah da abinki. Bata sake cewa komai ba, ta bude durowar ta ta ciro ta saka, suka leqa tayiwa yaya sai sun dawo, shi kuma tsaya suka gaisa, ya fada mata inda zasu je. A hankali suke tafe iskar damina tana kadasu, zukatansu sun cika da nishadi. Ismail yace, ki tunamin in zamu dawo akwai wani gurin saida kifi, sai mu biya in sai miki. Cikin doki tace, tam, dama nayi kwana biyu banci kifi ba. Nagode. Yayi 'yar dariya, "menene na godiya? Tace, gurinka na koya. Koni ka saima abu in na amsa, sai kace min wai ka gode. Ta dubeshi, kai baka damu da cin kifi ba ko? Yace, aikam bai dameni ba. Amma ynxun na koya a gurinki. Tasa dariya, shikenan mun koya ma juna abu kenan. Yace ai dole kiyi abinda nakeyi. Tace, sbd me? Cikin zolaya yace, kin manta da jinina dake yawo a jikinki, ya gauraye da naki? Tace, daman hakane? To kai ba'a sa maka jinina ba, amma ya ka fara cin kifi? Yayi dariya, sbd ganin yadda ta shiga, ta yarda da abinda ya fada mata. Yace ni ai kara nayi miki. Yadda naga kinata son kifi dinne, shine nima naji ina sonshi. Tayi dariya, "kuna siya a madina ko? Nasan sunada shi, lokacin da mukaje umra da daddy naci sosai, sai dai nasu ba maggi sosai, yace, inaci mana, musamman innaji kewarki, sai in sayi kifi inci. Wani dadi taji a Zuciyarta, Ashe yana tunata. Tace kasan me? Ya dubeta, "a'a. Ban zaci kana tunani ba. Yace, sbd ke ba kya tuna ni, shine kk zaton nima bana tunaki? Ya ce, hakane don yaji ta bakinta. Wa ya fada maka ba na tuna ka? Yace, To in kinyi kewa ta me kkyi? Ta dago ido ta Kalli sararin samaniya babu taurari, sai alamun hadarin dake gudu. Sannan ta dubeshi, "qila zaka manta da wani hankacif daka ta6a bani, in ka tuna, to shine nakan dauko in kalla, wani lokacin ma har in shaqi qamshin turarenka. Dadi yaji matuqa, sannan yace, ashe na kai har haka a gurinki? Kafin tayi magana, yace, gashi har mun iso gidan, sai naga babu nisa ko? Ya fada tare da kallonta. Tace, nima dake fadin nisa, sai naga munyi sauri. Yace, to shiga kimin iso, zan kira angon qarnin ynxun a waya. [22/09 9:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣6⃣Tana shiga Mahmud din yana fitowa, yace, ga dakinnan, ki shiga. Bari mu shigo, ynxun ya kirani. Ta shiga da sallama dakin mai jego. Tana zama suna shigowa. Suka gaisa, Ismail ya miqa ma mimi yaron, ta amsheshi tare da kallon Ismail, "banfa iya daukar jarirai ba, karka sakemin shi." Hannuwansu suka hadu, dukkansu sun samu kansu cikin wani yanayi sakamakon hakan. Ta kalleshi. "me me ake cewa? Yace, hausawa suna cewa, Allah ya raya ko Allah ya amfanashi da dai sauransu. Ta kalli mai jego, "to Allah ya raya shi, yayi masa albarka. Ta sake kallonshi, haka yayi? Suka sa mata dariya. Mahmud yace, yayi. Nan kuma sai su Ismail suka canza harshe zuwa larabci. Ismail ke tambayar Mahmud "da wa yaron ke kama?" Mahmud yace, da ni mana. Ismail yace, a'a yafi ka kyau. Ismail ya miqa ma Mahmud yaron, tare da qifta masa ido, alamun zai tsokani Mimi, "khadija to in kin haifi naki yaron wa zai daukar miki? Ta harari Ismail, "ni ba zan haifi ko wane yaro ba. Don ko Aishatu ban ta6a daukarta ba saida tayi girma. Rabi'a tace, ba zaki haifi yaro ba. Sai yarinya? Mimi ta zaro ido, ni dai ba ruwana. Suka sa mata dariya sbd yanayin yadda tayi maganar Ya tsugunna kusa da ita, "yaya kk ga yaron? Cikin harshen turanci tace, yanada kyau sosai. Domingo mimi tafi iya harshen turanci fiye da harshen uwa. Duk lokacin da zatayi magana mai kalma goma, to turanci zai zama guda bakwai. Don haka saddam da Ummi suke qaruwa da ita. Tana taimaka musu da homework. Sun jima a Gidan har goman dare ta gota, sune dai sukeyin Hirarsu, ita dai Mimi jinsu kawai takeyi. Hammar daya lura tanayi ne yasa shi miqewa, "to bari dai mu tafi, yau dai mun hana 'yan barka sakewa. To duk wadda tazo saidai mamansu Rabi'a ta leqo a miqo mata yaron." Mahmud ya miqe shima, "nima wucewa zanyi" sukayi musabaha tare dayin sallama. Mimi ma sukayi sallama da Rabi'a. 5⃣7⃣Suna fitowa shagwa6a66iya Mimi tace, Ni kam na gaji kawun su Ummi, bazan iya tafiya da qafa ba. Yace, ba don kince min kawun su Ummi ba, da na goya ki hai gida. Cikin hamma hade da shagwa6a, ta ce, don Allah kawun su Ummi, ka mu hau abi hawa. Kaga inajin varci kaji? Yace kin cika langa6ewa khadija. Tace ni ba kaga qoqarina ba, don Allah ban ta6a yin tafiya kamar ta yau ba fa. Nayi qoqari mana. Yace, ba zamu samu mota ynxun ba, kuma ko da mun hau mota, inda za'a sauke mu da nisa, tafiya sosai kafin aje gidanku, sai dai in aca6a. Tace eh naji mu hau aca6a din. Yace, ni banason mata suna hawa aca6a. To ka siya mana mota mana. Yace lokaci ne, insha Allah. Mahmud ya fito, "har ynxun baku tafi ba? Ismail yace, tana nan tana shagwa6ar ta, ba za ta iya zuwa gida a qafa ba. Mahmud ya miqo ma Ismael makullin mashin dinsa, tare da cewa, kuyi amfani da mashin dina tunda ban kaiku nisa ba. Kuma ga hadari yana haduwa. Ismail yace, to kar ruwa ya sameka fa. Mahmud yace, ko ya sameni kaga ni daya ne. Ismail ya amsa, tare da fadin shikenan muje ko? Tace, yaya zan hau? Ka san fa sau daya na ta6a hawa mashin, lokacin zanje in samu khalil a gareji. Saboda sauri ban san ta yaya na hau aca6ar ba, na dai ganni akai. Ina tsoron mashin da yawa. Yace ki dafa ni ki hau. Ta dafa shi ta hau suka soma tafiya. Don ya tsorata ta, sai ya taka birki, a tsorace ta qanqame Ismail, tana salati. Ya sa dariya. "Ya kamata ki rage tsoro. Ita kam batasan ma yana yi ba. Illa hannuwanta da tasa ta zagaye cikinsa ta riqe gam. Sannan ta kwantar da kanta a Gadon bayansa. Wani irin nishadi Ismail ya tsinci kansa aciki mara misaltuwa. Don haka maimakon ya nufi Gida kai tsaye, sai ya dinga shawagi ta layuka, sannan ya sassauta gudu, iga iskar hadarin tana ta kadawa, sai Ismail ke ganin kamar su kadai ne a garin katsina da kewayenta. Ita kuwa Mimi wani daddadan varci ne taji yana fizgarta, iskar tana ratsa ta ko ta ina. Ga kuma qamshin turaren Ismail dake saka Zuciyarta shiga cikin wani yanayi mai wuyar fassara. [23/09 5:32 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 5⃣8⃣Can yace, zamuje siyen kifin ne, ko muje gida? Ji tayi tamkar suyi ta yawon su a haka har abada. Don batason abinda zai tashe ta daga yadda suke. Amma kifi fa? Sai tace zanci kifi mana. Ya karkata kan mashin zuwa Gidan suya. Gurin ya burge Mimi musamman tunda taji qamshi yana dukan hancinta. Ya kalleta, zamu ci anan ne? Tace, amma zamu yi ma su yaya Amina tsaraba in munci bamu ko? Yace, yadda kika so, tace, in ba mutane muci, sai mu sai musu nasu. Babba daya ya sai musu, sai tataccen 'ya'yan itace mai sanyi, wanda za'a taceshi a juye maka cikin kofi a gabanka. Sunaci, Ismail yana kallon Mimi, wadda ke ta yin hannu baka, hannu qwarya. Yayi murmushi, "ci sannu Dija! In bai usheki ba zan qara miki." Ya shiga salo mata tsokar kifin sala-sala, yana ajiye mata a gabanta. Ta lumshe ido, "kar kaga laifina, inason abin nan. Ta salo tsokar ita ma ta aje a gabansa, "In baka ci, nima sai ya ginsheni. Ya dauka ya saka a bakinsa. Haka sukayi ta salo ma juna tsokar kifin, suna turawa a gaban juna, har suka cinye. Suka sha abin shansu. Yace, zaki qara? Ta girgiza kai, "cikin yayi dam. Dama banci abincin dare na ba." Yace, kunyi tuwo kenan? Tayi 'yar dariya, "shine kam. Na kasa sabawa da tuwo. Shi kadai ne har ynxun bai min ba, duk a abincin mu na Hausawa. Yace yaya ta fadamin, kin kasa sabo da tuwo. Amma kikanci kadan. Kafin tayi magana, sai sukaji iska mai qarfi alamun tasowar hadarin. A tare suka miqe, da sauri, ya biya sannan suka dauki nasu yaya Amina suka dane mashin. Fatansa tayi irin zaman dazun wanda itama hakane muradinta. Tana lafe a bayansa suna keta gudu, sai ko ga ruwa mai qarfi ya sauka. Sake qanqameshi tayi. Yayin da shi kuma ya rage gudun sbd ya Kalli gaban shi da kyau. Sha biyu da wasu abubuwa suka tsaya a qofar Gidan su yaya, sun jiqe sharkaf. Ya sauka ya buga gidan sosai, kafin suka ji takun Abban su saddam. Sai da ya tambaya wanene? Ismail yace, mune. Sannan ya bude. Mimi ta kalleshi, "kazo ciki mana ruwa yayi sauqi! Yace karki damu, gara in tafi sbd dare zai qara yi. Abban saddam yace, to ka kwana mana anan? Yace, a'a duk na jiqe kayana suna gidanmu. Saida safenku. Ta daga masa hannu tare da fadin bye! Sai da yaga abban saddam ya rufo qofa, sannan ya wuce. Ita kuma tana shiga taba abban saddam ledar tsarabarsu. Yace, bari in taso miki Ummi, don irinki ce, sarkin tsoro taqi varci a dakinku, wai ita kadai. 5⃣9⃣Bayan ta kunna tocila, sannan ta rufe qifar, ta cire kayanta ta maida na varci. Tayi lamo akan Gado, sam varcin yaqi zuwa mara. Sai tuno yadda suka kasance da Malam takeyi. Bata ta6a jin a kafatanin rayuwarta irin na yau ba, domin batasan ya zata fasalta yadda taji ba har a fahimce ta. Saidai a can qasan Zuciyarta tana tambayar kanta shin yadda ta ta6a jikin Malam ya dace, su da zasu rabu? Ta sake yin juyi akan gadon tare da maqale filo, sbd sanyin da taji yana ratsata. A fili tace, kai gsky bayansa yafi katifar nan dadin varci. Wata zuciyar tace, ba wani laifi domin har ynxun mijinki ne, tunda baku rabu ba ai. Haka tayi ta tunani tare da surutai barkatai har varci gwanin iya sata yayi gaba da ita. Washegari yaya tayi ta ma Mimi tsiya, tana cewa, mun zaci ko kun kama daki ne, mu biyo ku da kayanku? Mimi tace, munje siyan kifi ne ruwa ya tare mu. Tace, muma munci kifi, gsky sun iya gashi. Dariya kurum Mimi tayi. Tun kwanakin baya Mimi tana yawan tuno mahaifanta, haka kuma har abada ba zata manta da gatan da dadynta yayi mata ba. Kewar ganinsu takeyi. Sau da dama takan zauna daki taci kukanta ma'ishi, ta share hawaye, saidai tanajin kunyar tunkarar mahaifinta sbd ta kasa yi masa abinda ya dace, a lokacin daya dace. Duk da cewa ya nuna wa momy Nafisa cewa zai haqura in taqi yarda kamar yadda Momyn tace mata. Amma ita ta yarda cewa tafi kowa laifi don me yasa ba tabi abinda yace ba tun farko? Don haka ta tattara duk wasu laifuka ta dora a kanta. Sannan zata jira lokacin da Allah zai sake hadasu don ta roqesu gafara. Kwanaki biyu da fara azumi, Mimi tana zaune a saman gadonta tana karatun littafin tahzib mai fassara da hausa, duk lokacin da take karanta littafin dashi da Al'adab, sai ta dinga tunanin cewa gsky rayuwar da tayi ada, rayuwa ce irin ta dabbobi, tunda batasan komai game da addininta ba. Abinda ya kamata ace ta sani tun tana ajin rauda shine take karantawa ynxun. Bokon da dauka a matsayin wayewa, ashe qauyanci ce ga wanda baida ilimin addini. Duk ilimin Bokon da take taqama dashi, wani lokacin Ummi ke cinta gyara a fannin addini. Kai ta fahimci ko maganar fatar baki ta mai ilimin addini ta bambanta da ta mai taqama da boko. [23/09 5:37 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣0⃣Ummi ta katse mata tunani da cewa, kunna TV dinki kiga kawunmu yana yin tafsir. Sai tsalle Ummi keyi. Ita kanta Mimi batasan meyasa ta sauri ba don ganin ta kunna TV. Dirshan ta zauna a gaban TV din tana kallon Ismail cikin qaton masallaci, mai cike da jama'a sunyi tsit suna sauraron daddadar muryarsa. Ta qaro sautin TV din ta koma saman gado tana kallonsa. Tsawon awa daya daya dauka yana yin wa'azin, haqiqa ya ratsata. Bata ta6a zama ta saurari wa'azi ba kamar yau tunda take. Yaya ta shigo tana cewa, kinfa kawunsu Ummi ko? Mimi tace, gsky yanada basira sosai, ya iya tafsir. Yaya tayi dariya, ji tayi tana alfahari dashi. Mimi kuwa, qosawa ma tayi ta ganshi. Inda ya sake burgeta, yadda ya yita amsa tambayoyin mutane da sukayi ta rubutowa bayan an gama wa'azin. Haka ya yita basu amsa cikin ilimi da hikima tare da kawo hujjoji cikin Qur'ani da Hadisai, ko kuma ittifaqin malamai. Mimi dai Ismail ya burgeta har qarshe. Don haka yau da sukayi qosai da kunun gyada, da kanta ta debi nasa ta shirya masa, ta shinfida darduma tana jiran zuwansa. Amma har kusan tara baizo ba. Bata ta6a damuwa don Ismail baizo ba irin yau. Jiya ma da yazo Ummi ce ta kawo masa abin buda baki, amma yau wata kimarsa ce ta qaru a idon Mimi. Tayi ta kai kawo a cikin daki, ta qosa sosai ta ganshi. Agogon dakin ya buga qarfe tara da kwata, ta miqe da nufin ta tambayi yaya, wai yau Kawunsu Ummi ba zaizo ba? Sai kawai taji muryarsa yayi sallama ya shigo gidan. Ta koma baya ta zauna a bakin Gado. Qosawa tayi su gama gaisawa da yaya Amina ko ya shigo, amma ya jima can kafin ya shigo. Da farko ta tsara zata tareshi cikin murna, amma yana shigowa sai taji wani jinkai ya taso mata, ta kishingida tare da fadin sannu da zuwa. Ya zauna bakin gado, sannunki da hutawa. Tace, kaine da sannu. Yau kam bakazo shan ruwa ba? Yace, eh wani bawan Allah ne ya gayyace mu shan ruwa. Can mukaje. Tace ok. 6⃣1⃣Sun danyi shiru na wasu 'yan daqiqoqi, kafin Mimi ta kori Shirun da cewa, mun kalli tafsir dinka, yau kayi qoqari. Yace, to nagode. Wayarsa ta soma ringing. Ya dauka tare da sallama. Ta amsa, macece. Yana qoqarin tambayar wacece, sai ta katseshi da cewa Malam mun yini lfy? Yace lfy Qlw. Tace dama Malam ba kira ne in gaisheka. Wani haushi ne ya tirniqe shi a zuciya. "Amma don Allah kaiki sake kirana." ya kashe ba tare da ya jira jin amsarta ba. Mimi ta kalleshi, "wacece?" shima ya dubeta, "Nima bansan ko wacece ba. Tace, ina ta samu number dinka? Yace ina zan sani? Kinsan Allah, khadija abinnan yana bani haushi da Mamaki. Wai mata masu daraja da aka sansu da kima shine suke tallar kansu ga mazaje. Kafin tace wani abu, sai daya wayar ta soma ruri. Tamkar kada ya dauka, amma saibya daga, kamar yadda yayi zato itama macece. Kamar ya kashe, saidai ya fasa, ya amsa gaisuwar da takeyi masa a qagare. Tace, din Allah Malam zanyi talbaya ne akan bashin azumi da nasha, gashi har wani azumin yazo. Jin cewa ita neman fatawa takeyi, sai ya saurareta, yayi mata kuma cikakken bayani yadda zata gamsu. Mimi dai tana kallon Ismail cike da birgewa. Duk abinda yayi sai taga yayi masa kyau. Ya kalleta. Bari inzo in tafi. Tace da wuri haka? Yace dama nazo ne in duba ku. Akwai wasu litattafai da zanyi nazari, sannan zan qara karatu a gurin Malam, duk a daren nan. Tace ok. Yace, babu wani abu ko? Ta girgiza kai, tare da fadin babu jolai. Yace shikenan in tafi sai gobe kenan? Ta daga kai. Ismail ya soma karatun nan da qafar dama inji hausawa. Domin kafin azumi ya raba, saida labarin basirarsa da hikimar wa'azinsa ya watsu cikin birni da qauyukan katsina. Faya-fayan karatunsa da kasina naji dana gani, sun fantsama a kasuwa. Su kuwa wasu shaidanun matan, labarin kyawunsa sukeyi, da yadda yake shigarsa ta manyan kaya da kuma jallabiyu 'yan gske. Wasu kuma yadda yake fitar da larabci da turanci tamkar yarensa shi ke burgesu. Kai ko hausa Ismail keyi zakaji hausarsa mai burgewa. Wasu kuma suce, iyayi da salo. [25/09 9:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣2⃣Masallacinsu kam yana cika tantsam har ta harabar makarantar. Ganin haka sai Ismail ya kawo ma manyan malamai dasu Malam Aminu shawarar cewa, me zai hana su kafa asusun marayu don taimakon marayun dake unguwarsu da maqotan Unguwar. Suka amince. Shida Mahmud suka soma bada tasu gudunmuwar har yace ga ta yayarsa da kuma matarsa. Shi kuwa Mahmud harda ta dansa mus'ab ya saka. Daganan sai Ismail yace yanason kowa ya saka tashi sadakar a ranar na duk abinda Allah ya hore masa. Ranar dai yayi wa'azi ne akan falalar dake cikin taimakon marayu da tsabar ladar da hakan ke dashi. Kafin wani lokaci mutane sukayi ta zuba kudi, wadanda kuwa basuda shi sukayi alwashin kawowa gobe. Kafin sati daya saida takaisu ga bude asusu a Banki. Sbd, wadanda suke kallon wa'azin a TV kuma suna son su bada tasu sadakar. Wannan al'amari ya haskaka Ismail, amma dukda haka bai kasance daga cikin malaman da in daukaka tazo musu, zakaga sunayin girman kai ba. Yana bin duk malamin daya san zai samu qaruwa dashi, ko da kuwa ya girmi malamin. Hakanan ko qaramin yaro ya nuna masa kurensa a harkar karatu yana kar6a. Sannan ko yau yayi tafsir, bayan ya tashi wani yace masa, jiya fa kaza ba daidai bane, in ya dawo gobe zaiyi bayani cewa jiya nace kaza, ba daidai bane, wani dan uwa yayi min gyara. Haka nan shi yayi imani cewa, daukaka ta Allah ce, ba wai iliminsa ne ya kaishi ba. Daukaka daban, ilimi da hikimar wa'azi daban. Ismail ya zama cikin uzurin da sai yayi kwanaki baije gidansu Mimi ba. Ita kuwa Mimi sai take zargin ko don yaga ya soma zama wani abu shine zaija baya dasu. Yau kwana uku tanason ganinsa don taji wacece matarsa din daya bada sadaka harda ita. Amma baizo ba, saidai su ganshi a TV in yana tafsir ko lacca, wadda aketa faman gayyatarsa. Yana yiwa maza ko mata, wata lacca da aka nuna yayi wa mata mai taken Ramadan lacca. Tasha mamakin yadda yake fadawa mata su riqe mazajensu, da hanyoyin kula da miji. Ya kuma kwadaita musu irin romon ladan da zasu samu a gurin mahaliccinsu. Sai taga duk ta zama wata sokuwa, domin ita kanta da take macen bata san abubuwan dashi ya sani ba, na game da yadda ita kanta mace zata kula da kanta. Ta jima tana Mamaki, kuma ta sake yarda Ismail ya dara kallon da takeyi masa.6⃣3⃣Shikam Ismail yakan kira yaya Amina su gaisa, yaji lafiyar Mimi a gurinta, kuma tana sanar da Mimin, domin bashida lokacin kansa. Ba su suka ga Ismail ba, sai azumi yana ashirin, misalin qarfe uku, lokacin Ummi tana daga citta zata kai niqan geron kunun tsamiya, ta gai dashi. Ya amsa tare da cewa, ina mamanki? Mimi qin dago kai tayi. Ummi tace, tana ciki. Yaya ce ta fito tana fadin dan gyangyadi ne ya soma dauka ta, sai kuma naji muryarka sama-sama. Yace, nine kun ganni sai yau. Ya saci kallon Mimi, cikin zolaya yace, 'yar amanata ma na lura fushi takeyi dani. Ko kallo ban isheta ba. Mimi ta dago ta dubeshi, ya dan rame, hakan sai ya qara masa kyau. Shaddar jikinsa mai tsada ce sosai, mai ruwan siminti, hular kansa ta dace sosai. Ta maida kanta taci gaba da firar dankalin da dama shi takeyi tun kafin ya shigo. Ta kammala ta kwashe 6awon sannan ta kai kicin ta wanke hannunta, duk yana kallonta, suna 'yar hira da yaya. Ta zo ta shige dakinta. Ya bita tare da cema yaya, bari inyi lallashi. Can saman Gadonta ta harde qafafun ta. Ya shigo da sallama,a ciki ta amsa. Ya tsaya a gaban gadon, "yau fushi kkyi dani? To, kiyi haquri. Ya ranqwafo tare da sa hannuwansa duka biyu ya dafa gadon. Kinji. Sam ta kasa fada masa cewa, rashin ganinsa ne ya bata haushi. Sai ta kauda kai. Yace, kullum ina fada ma yaya ta gaisheki, sannan ina fada mata uzururruka na, ko bata fada miki? Ta turo baki, ni fa rashin zuwanka bai dameni ba. Cewa din dakai ni matarka ce. Ya zauna, na fada a ina? Cikin salon shagwa6arta ta nuna TV, "anan mana, daka bada sadaka, harma kace, da na yaya. Yayi murmushi, yana son salon shagwa6arta. Yace amma nace matata khadija? Ni fa nufina wadda zan aura. Ta ware idanunta ta kalleshi, zakayi aure ne? Yace eh mana insha Allah. Ta ta6a baki tare da cewa, Hu'um! Zuciyarta fal da takaici. Ta dubeshi, "to ni yaushe zamu rabu? Tayi tambayar cikin daurewar fuska yace, kinsan dai ko ba lokacin azumi ba, laifi ne mace ta nemi a sake ta, babban laifi ne ko!? Ta sake turo baki, ai shi ma alqawari cikashi abu ne mai kyau ko? Yayi murmushi, "haka ne, amma banda haramtaccen alqawari. Ina nufin kayi alqawarin laifi. Misali mutum ne yayi alqawarin aikata wani laifi da Allah baya so, to ba'ason ya cika. Tace, jiya fa naji kana cewa saki halasne, a cikin tafsirinka. Yace, sai kuma nace me? Allah baya sonshi, dukda halas ne. Na lura in kinyi ilimi nan gaba za'ayi fama dake kema.6⃣4⃣Yasa hannu cikin aljihu ya ciro kudi 'yan dari biyar-biyar. Yace zan sallameku sbd batun sallah dake gabatowa. Tace, ai yaya zaka bawa kudi. Ni ina zuwa kasuwa? Yace, nima bance kije kasuwa ba ai. Tace, to naga zaka bani kudi ne. Yace na fasa baki ki shirya gobe muje tare. Tace, kana son sole sai wanda ya sanni ya ganni kai kam. To shikenan, ki rubuta min abinda kk so. Ya miqe ya shiga dakin yaya ya qirga dubu goma ya bata, yace ta saima yara kayan sallah. Tayi godiya tare da cewa, kaima da kk fama da kanka. Kaima fa dalibi ne har ynxu. Yace wani bawan Allah ne ya sameni nayi masa bayanin yadda zai fidda zakkarsa, shine da ya cire ya bani. Yaya tace, Allah ya taimaka. Ai ranar da kayi wa'azin zakkarnan, dole zukatan mutane su raunana, indai da sauran imani, su fito da zakkar su ba da. Yace kinsan kudi shiga zuci ne dasu. Sai su dinga ganin kamar in sun bada zakka kudin zai qare. Ba su san in sun cire haqqin Allah daga cikin dukiyarsu ba, Allah zaisa musu albarka, qila ma tafi ta da. Tace, rannan ma munji ka bada sadaka harda mu. Allah ya saka da alheri. Yace, Amin. Tare da miqewa. Ya koma dakin Mimi, "bani in kin rubuta. Ta miqa masa 'yar guntuwar takarda. Ya amsa, ya bude. Sai yaga ta rubuta cewa, duk abinda ya sauwaqa. Ya kalleta, zuciyarsa dajin dadin hakan da tayi. Yace nasan ba zan iya sai miki abinda kk so ba, amma zanyi iyakacin qoqarina. Ya juya ya fita. Kwana uku bayan nan, Ismail yazo Gidan da safe, misalin qarfe takwas, Mimi tana varcin safe. Ya gaisa da yaya sannan ya shiga dakinta. Bai mata dogon kallo ba, ya aje ledar hannunsa ya duba durowar gefen gadonta ya dauko takarda da biro ya rubuta cewa, ga kayan nan, in kin farka ya ke mai yin kyau a varci. Ya dora takardar a tafin hannunta. Sannan ya fice, yayi sallama da yaya ya wuce. [25/09 9:28 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣5⃣Mimi kuwa tana farkawa taji da abu a hannunta, sai ta duba, taga abinda ya rubuta. Sai tayi murmushi tace, waton in idanuna biyu banida kyau, amma a varci inada kyau. Ta dauki ledar ta bude, wani tsadadden leshi ne mai kalar 6awon dorawa, sai Atamfa 'yar England sai takalma masu kyau da tsada. Ba anan tasha mamaki ba, saida taga irin man shafawarta da hodarta, sai kuma jan bakin da take shafawa. A fili tace, "ina Ismail yasan wadannan? Lallai zan tambaye shi inji. Ta ciro hijabai dogaye guda uku, sai niqabi guda daya. Tace, wai harda wannan yakeson in sa, ta6! Na dai saka hijabin in zanyi sallah. Ta kaima yaya ta gani. Suka tayata murna. Tace, in yazo anjima sai ince yakai dinki ko? Yaya tace, eh kam ya kai don inda na kai nasu Ummi macece, kuma ba wani qwarewa tayi ba. Dama su Ismail sun kafa kwamiti qarqashin jagorancin Mahmud inda za'a dauki sunayen marayun Unguwar, da na kusa dasu. Don haka sai suka sai kayan abinci dana sallah na yara, maza da mata. Sannan sukaje suka kai ziyara gidan yari, inda yayi musu wa'azi tare da basu taimako. Ana saura kwana biyu sallah, ya kawo masu Mimi cefane jibgi guda, da kuma kaji, sannan Washegari ranar jajibiri masu hali sukayi ta aiko masa da nama cikin manyan ledoji. Yaba Malam Aminu, harda Mahmud, sannan ya miqa cikin gidansu. Irin wadannan abubuwan suna burge Mimi.6⃣6⃣Hasana da usaina suna zaune suna kallon rufe tafsir din Ismail, Hasana tace, kai Malam yayi wlh! Na qosa daddy yayi mana izinin zuwa muga sis Mimi. Itama nasan ynxun ta hadu. Usaina tace, ai na dauki number din da ya bada wadda yace mutane suyi message kawai banda kira in sunada tambaya, so muyi masa text cewa, mune. Sainya fada mana gidansu, sai muje muga sis Mimi. Muryar Hajiya sauda ta katsesu da cewa, Allah yasa in samu labari. Wai ba ku nace ma tana lfy bane. Kuma fa na fada muku cewa, akwai matsala in munyi yunqurin zuwa gurinta zata sake guduwa. Karku damu tunda muna samun labarinta. Muyi ta Addu'a komai zai wuce. Hasana tace, Hajiya shi Malam a matsayinsa na Malami ba sai ya nemi lambarki ba kiji komai daga bakinsa? Usaina tace, ya fa san nan gidan meyasa ma ba zaizo ba? Hajiya sauda tace, Nice da laifi, don na tura masa saqo cewa, naji dalilan mahaifin Mimi, kuma na gamsu dashi. Don haka nima zaka jini shiru. Kaima kayi haquri karka sake nemana ko a waya. Ina mai sake baka amanarta. Lokaci yana zuwa da zamu nemeka da kanmu. Kunji tun daga lokacin ban sake nemanshi ba, shima bai sake ji daga gareni ba. Hasana tace, to sai zuwa yaushe ne sannan za'aje gurinta? Usaina tace, ke kam kamar bada hausa Hajiya tayi magana ba? Hajiya sauda tace, zaku soma musunku ko? To ni nayi nan! Ta nufi kicin. Ranar sallah, Ismail ya matsawa Mimi wai ta shirya suje masallaci. Da ma tun ranar jajibiri yake fada mata lokacin da yazo ya kawo mata dinkinta. Tace, ba zataje ba, qila 'yan gidansu zasuje. Yace, ba ga niqabinki ba, sai ki 6oye fuskarki, dama amfaninsa kenan. Zama haka ba ya yiwuwa Mimi, dole sai da dan fita ana dan motsa jiki. Balle sallar idi wadda daga shekara sai shekara. Ba tada za6i dole ta shirya cikin leshinta, yayi mata kyau matuqa, tayi alwalla, sannan ta shafa hodarta da jan baki, ta saka hijabin da niqabi. Suka fito tace, yiwa yaya sallama. Ummi ma da take ta rabon abinci gidajen maqota tayi kyau cikin kayan sallarta. Su kuwa su saddam dama sun tafi da abbansu a mashin.6⃣7⃣Ismail yayi kyau cikin wani tsadadden yadi, mai ruwan madara, malum-malum ce ta dauki aiki. Hularsa da takalminsa sun dace da kayansa. Yayi kyau matuqa. Ita kanta Mimi lokacin da ya shigo Gidan, sai da Zuciyarta ta buga. Daga lokacin da Ismail ya soma tafsir zuwa ranar sallah, yayi abokai kala-kala, kowa yanason ace suna hulda, masu da kuma talakawa. Daga cikinsu ne wani yazo har gida ya daukeshi, shine yace, su biyo ya dauki matarsa. Mutane sukanyi mamakin ganin Ismail a wani guri daban. Duk wanda ya tambayeshi yakan ce masa, shi ba lazauni bane. Matarsa kuma ba tada isasshiyar lfy, shiyasa ya barta gidan yayarsa. Bayan sun dawo sallah ne Ismail yaci abinci anan gidan, sannan ya miqe zai fita. Sai Mimi taji sam batason ya fita. Amma ba tada ikon hanashi, wani sonshi ne taji a cikin Zuciyarta. Tana kallonshi ya fice. Bayan sallah da kwana tara Ismail suka shirya nasu-yanasu sai makaranta. A ranar ne Mimi taji inama itace, Rabi'a. Ranar ce, tayi kuka sosai, wanda batasan ko na menene ba. Ismail yayi zaton ko tana yi ne don bai saketa ba. Sai yace, karki damu khadija, shekara kamar kwana ce, in na dawo komai zaizo qarshe, kinji? Bayan tafiyarsu tayi ta dana sanin qin yarda da tayi ya sai mata waya. Amma tace, bataso. A fili tace, kashh! Menene ma zai sa ince ban son waya? Tsaki taja, tare dayin tagumi. Ynxun kam ta gama fahimtar cewa, Zuciyarta tana matuqar son Ismail, sai dai tsoronta daya shine, shi baya sonta. In ba zata manta ba ya sha fadin cewa, shi mace mai kyau yakeso ya aura. Tuna hakan sai taji jikinta ya mutu. Ta kalli kudin daya bata kafin ya tafi. A fili tace, dole ne in nemi wanda zai siyomin waya ko don in hada hulda dashi. Tsaki taja, a ranta tace, ta yarda jama'a rahama ne, inda tana hulda dasu da ynxun ta samu mai siyo mata. Dakin yaya Amina taje, tace yaya inason a siyomin waya ne. Yaya Amina tasha mamaki, "ke kuwa meya hanaki yarda Ismail ya siya miki? Don nasan babba zai sai miki. Tace, lokacin banason wayarne, amma inasonta ko don inji Rediyo. Amma fa karki fadama kawun su Ummi. Tace, shikenan ki kawo sai qanin abban su saddam ya siyo miki. Ta dauko dubu bakwai, cikin dubu ashirin din da Ismail ya bata kafin ya tafi. [25/09 9:30 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 6⃣8⃣Zainabu kuwa tunda taga Ismail a TV, hankalinta yayi matuqar tashi. A fili tace, Ismail yafi qarfi na ynxun. Ta saka kukan takaici, tayi har ta gode ma Allah. Innarta cikin tsantan nadama tace, zainabu kiyi haquri, qila zaku hadu ne ko anan gaba. Tunda yana sonki, na san ma zai dawo gareki. Zainabu dai bata tanka ba. Innar ce da kanta ta fita neman labarin Ismail, har gidan mahaifinsa gurin su fatu. Anan ne fatu take fada mata cewa, Ismail yana madina garin manzo, dama zuwa yayi don can yake karatu. Ta qara da cewa, Ismail fa ya wuce da tunaninki, mu kanmu mun dangana bare ke. Dole mu dangana ko don alherin da yakeyi mana. Azumin nan shine geron kununmu, shine waken qosanmu. Da sallah tazo kuwa, zo kiyi kallon hidimar, dinkunanmu da yara, ke har cefanen sallah. Innar zainabu tace nima ai nadamar ta kawoni, ban san yaya zanyi da zainabu ba, taqi sauraron kowa. Fatu tace, dama ta saurari kowa, sbd Ismail da ya yafe tunaninta. jiki babu qarfi ta koma Gida.6⃣9⃣Ya zuwa wannan lokacin, rikicin su Na'ima ya kai su ga zuwa kotu, inda shi Abbas ke qarar Na'ima, akan ta bashi dansa. Ita kuma Na'ima tace, ba zata bada shi ba. Duka 6angaren guda biyu sun dauki lauyoyi. Inda ake fafatawa tare da dage zaman sauraron shari'ar. Nadama kuwa, Momy Nafisa tayi akan auren nan yafi cikin buhu. Ita kuwa Na'ima nata ganin alhakin Mimi ne. Duk lokacin da tace haka, sai momy Nafisa tace, ki daina wannan maganar, ai komai muqaddari ne. Na'ima tace, qaddarar da mutum yake qadddara ma kansa ba. Da mun bar Mimi ta aure shi, na tabbata hakan ba zai faru ba. Haka Allah yake ikonsa, sau da yawa sai mutum yayi ha'inci, sai kuma kaga ya dawo yana nadama. Kukan Na'ima da yawa, ita ba a karatunba, ita ba ga auren ba. Ynxun ne take burin in ya saketa, ta koma makaranta. Shi kuma yace, tana bashi dansa zai sake ta. Lauyoyinta suna ta zuba hujjojinsu kan cewa, dole ne ya saketa tare kuma da bar mata danta don itace tafi dacewa ta kula dashi. Su ma nasa lauyoyin hujjojinsu suke bajewa akan cewa shine yafi dacewa ya riqe dansa a matsayin sa na uba. Nidai nace, ku kuka sani, mu dai 'yan kallo ne. Lokacin da aka kawo wa Mimi wayarta, ta hada ta tasa aka sai mata layi ta saka aciki. Number Ismail kawai ta dauka a cikin wayar yaya Amina. Wtsapp Mimi ta bude, cikin sa'a kuwa da lambar yakeyi, hotonsa ne ma yasa a D.P dinsa,yana sanye da farar jallabiya. A saudiyya ya dauki hoton daga gani. Wannan lokacin ma yana online. Mimi tayi murmushi sannan tayi masa sallama. Sam bai kula sallamarta ba, duk da tayi ta kusan sau goma. Tace, nasan yaya zanyi. Ta sauka daga kan wtsapp din ta tura masa message, da cewa. Dama haka malaman suke basa son sauraron al'ummarsu, balle su basu fatawa akan matsalolinsu? To, ka sani bin Abdurrahaman, in har na mutu ban samu mafita a matsalar da nake ciki ba, to ka sani har da kai zunubin, domin na kira baka daga ba. Kuma nayi maka magana ta wtsapp baka kula ni ba. To ynxun ga message dina nan. Tana turawa tayi murmushi, sai ta kashe wayar ta aje.7⃣0⃣Bata sake kunnawa ba sai bayan kwana uku. Tana kunnawa saqonni guda uku suka shigo, data duba daya na MTN, biyu na Ismail dama da Malam tayi saving. Murmushi tayi, sannan ta bude saqon. Gajerrn saqo ne, kawai cewa yayi, ki fadi matsalarki. 'yar dariya tayi don ganin cewa zatayi wasa da hankalinsa. Ta hau wtsapp nan ma saqon iri daya ne. Ta soma tunanin me zata rubuta masa, wanda zaija hankalinsa, ya saurareta? Sai ta soma rubuta cewa, Malam Allah ya sani tunda nake ban ta6a ji ko ganin matsala irin tawa ba, ko da a film ko kuma labarin qirqira. Sai ta tura masa. Daga nan sai ta kashe wayar. Washegari data hau wtsapp sai taga yace, ki fadi matsalarki kai tsaye ba tare da kin gutsutsura batun ba. Ke nake sauraro. Dariya tayi, sosai sannan ta tura masa cewa, roqo na da kai, shine in kaji wannan matsalar tawa ka taimakamin, kuma ko da kisan kai ne ya kasance hukunci na to zan dauka. Ta tura masa. Haka tayi ta tura masa wadannan saqonni na wasa da hankali, tun yana nuna mata yanason jin ko wace matsala ce, ta daina jin tsoronsa ta fada masa, har ya gaji yayi banza da ita. Tare da haka, in ya kira yaya Amina yakance, a bashi Mimi su gaisa. Cikin ja masa ajin data saba yi take amsa su gaisa. Inya tambayi matsala, sai tace babu. Kwancitashi su Ismail sun kammala karatu na digiri, tare da sakamako mai kyau. Hukumar qasar ta tuntu6i daliban da aka yaye a wannan shekarar, ko akwai wanda yakeson yin aiki tare da su bisa ga albashi mai tsoka? Su Ismail kam cewa sukayi sunfi son suzo su amfanar da ilimin da suka samo ga al'ummar qasarsu. Sannan Ismail yanason samun nasa iyalin, ya gaji haka. Mimi bata ta6a yin murnar dawowar Ismail ba kamar wannan karon. Domin gsky tayi kewarsa, tanason ganinsa, sosai matuqa. Wani abu da ya sake burge ta shine tasha gwada Ismail da sim kala-kala, don taga ko yana hulda da mata, amma sai ta sameshi a natsattse wanda bashi da lokacin shashanci. Sun iso gida cike da murna da doki. saidai Ismail ya baro madina cike da burin komawa don samun digirinsa na biyu, in komai ya tafi masa daidai. Dakinsa ya sauka, wannan karon zai kama masauki amma sai ya saita lamuransa.7⃣1⃣Shi mahmud bashi da wannan matsalar ta gurin zama, domin suna da mazauninsu, daya daga cikin gidajen mahaifinsa. Sunyi isowar dare ne wannan dawowar. Kusan qarfe biyun dare suka shigo katsina. Kai tsaye gidansu ya wuce, ya sauna da kayansa. Su kuma su Mahmud da Rabi'a da dansu mus'ab yayi wayo sosai, suka wuce nasu gidan. Ismail ya buga gidan. Yayyinsa maza guda biyu sukazo sun a tambayar ko wanene? Ismail yace nine Ismail. Da sukazo suka buds mass, suna yi masa sannu da zuwa. Sun yi sallama Sai da safe, suka nufi ciki. Shikam bai kwanta back Sai daya share dakin. Want Abu daya bawa Ismail mamaki, bayan yay sallar asubahi ya dawo, ya kwanta don ya huta, bai yi niyyar fita ba don yana tsammanin babu Wanda yasan ya dawo, gurin qarfe goma yaji sallama a qofarsa. Barcin nasa sama-sama ne. Don haka Sai ya tashi ya suka jallabiyarsa ya fito, ya baqon nasa, Sam bai sanshi ba, amma ya miqa masa hannu, suka gaisa. Mutumin ya Ciro wasu takardu ya miqa masa, game saqo daga wani bawan Allah, yace in Baka tun kusan wata uku da suka wuce. Ismail ya kalleshi cikin rashin fahimta, saqon menene? Yace mai gidana be, inayi masa aikin sama. Ni kafintan same ne. Duk wani aikin gidajensa ni keyi masa daya shafi Sana. To shine ya tambayeni ko ma sanka? Nace unguwarmu daya. Ta yiwu Baka sanni ba, ina can bayan mayo be, gidan malam kadi. Ismail ya kalleshi. Gidan su hashimu? Baqon yace, yauwa, to ni wansu hashimu be. Zakkar gida be, ko ince kyautar gida yace in Baka. Wadannan takardun gidan be. A can unguwar GRA be gidan take. in ka shirya Sai mine in Nina mama. [25/09 3:10 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣2⃣Cikin mamaki, Ismael yace a ina wannan mai gidan naka yake, kuma yaya sunansa? Baqo yace nidai sunana Nasiru amma shi mai gidana ya hana ni in fadi sunansa ko unguwarsa. Yace, shi yayi ne don Allah, kuma malam ya sakashi a cikin addu'ar Allah ya biya masa buqatunsa na alheri. Ismail yace jirani ina zuwa. Ya koma daki ya canza kaya, ya fito yace, zo muje gurin malam. Sun samu malam Aminu, inda dan aike yayi masa bayanin kimai. Bada 6ata lokaci ba, suka nufi gidan, harda mahmud, wanda ismail yayi masa waya, shima yazo ya samesu. Sun samu mai gadin gidan ya bude musu suka shiga. Mai gadi yazo ya gaishesu tare da tambayar su ko wanene mai gidan cikinsu? Mahmud yace, wa yasa ka gadin gidan? Yace 'yalla6ai ne. Yace min duk randa wanda yaba gidan yazo, shi aikinsa ya qare. Mahmud yace, to ya sunan shi 'yalla6ai din? Tsoho maigadi yace, ya hanani in fadi sunansa. Sun zaga gidan qato ne sosai. Ginin na gefe hawa daya. Mai gadin ne yabasu makullan ciki tare da nuna musu ko ina na gidan. Shikam ismail filin gidan ne yafi burgeshi, domin har ya hango yadda zaiyi makaranta a gurin, harda masallaci. Take ya sanar da su malam Aminu sha'awarsa da gurin, suka ce tabbas bakan yayi. Sun yi bankwana da maigadi bayan ismail ya bashi dan abinda ke hannunsa tare da bashi baquri kan cewa bai fito da kudi ba. Suka fito suka kulle gidan suka tafi da makulli. Babu abinda gidan ke buqata saidai kayan da za'a zuba na amfani. Sun koma gida, inda Ismail ya kawo dubu biyar tare da sabbin jallabiyu a cikin kayansa yaba dan aike tare da bashi haquri, kan cewa dawowarsa kenan daga karatu bashida kudi. shi kuwa dan aike godia yayi, tare da cewa, ni ai babu abinda yafi faranta mun rai kamar sada ka da saqonka da nayi. Domin tun shekaran jiya yake cemin cikin satinnan zaku dawo. Ismail yace, wato harma ya san lokacin da zan dawo. Dan aike yace gsky ya sanin kenan. Sukayi bankwana, ismail ya rakashi tare da yi masa godiya mai yawa. Ko daya dawo daki, yayi iyakacin qoqarinsa don ya gane ko wanene. Amma hakan yaci tura. Sai kurum yayi masa addu'ar Allah ya cika masa burinsa, duniya da lahira. 7⃣3⃣Mimi suna da labarin dawowar ismail amma basu ganshi ba. Mimi bataji dadin hakan ba, domin sai taga kamar bai damu da ita ba. Sai washe gari bayan la'asar, yinin ranar Mimi tayishi ne cikin qunci da rashin walwala. Har yaya ta nemi dalili, amma sai Mimi tace, kanta keyi mata ciwo. Tana zaune a tsakar dakinta tana yanke qumba, kanta babu dankwali ta kama gashinta a tsakiya, kamar yadda ta saba tun tana 'yar gayunta, muryarsa ta jiyo yayi sallama, sai sowar yara ta jiyo suna yi masa sannu da zuwa. kamar ta tashi ta fita sai kuma ta fasa, ta kalli jikinta, riga da wando ne wadanda shine ya sai mata su. Taje madubi ta kalli fuskarta. Sai ta samu kanta da zazzaga hoda a tafin hannunta ta hure, sannan ta shafa ta hau tsakiyar gadonta ta zauna, ta kunna TV. Catoon sukeyi. Kusan minti ashirin da tara, sannan ya kalli dakinta, ita wannan bata nan ne? Yaya tace, tananan. Dazun dai tayi fama da ciwon kai, amma yayi sauqi. Da sallama ya shigo. Ta dago tamkar lokacin taji shigowarsa. Qwarjinin dake kan fuskarsa ya doketa, tayi saurin sunkuyar da kai, sannu da zuwa. Yace, sannunki, in zauna bakin gado? Ta dago ta dubeshi, yaune zaka nemi izinina? Yayi murmushi, ai na qara wayau ne ynxun. Da kinsan yaro ne. Tayi dariya, to ka zauna. Ya tsura mata ido, "kinci naman hawainiya ne? Yayi tambayar cikin tsokana. Ta zaro ido, meka gani? Duk lokacin da na tafi na dawo, sai inga kin canza kala. Gabanta ga fadi, tsoronta kar ya kusheta, ta kalleshi, duk nayi muni ko? Yayi dan murmushi, nidai ban fada ba. Tace to fadamin me nayi? Da ya fahimci tanason jin ta bakinsa game da yabon da yayi niyyar yi mata, sai ya canza da cewa, wai don Allah meyasa in na dawo baki doki na? Tayi masa kallon gefen ido, injiwa? Yace injini mana. In ana dokin mutum ai anayi masa tarba ta musamman da girke-girke. Ta ta6a baki, ai muma bakayi dokin ganinmu ba. Sai fa da kayi kwanaki, mutane suka gama ganinka, sannan kake zuwa mana nan. Yayi murmushi, amma zuwana na farko nan na fara sauka. Mimi tace, wannan ne kawai. Ta sake maido da wancan zancen. Baka fa bani a msa ba. Tame? Ya fada tare da kanne mata idonsa daya. Canzawar daka ce inayi. Shine nace muni na qara ko? Yayi 'yar dariya nidai bance ba. Ki kawomin ruwa mai sanyi insha, ya sake kauda zancen. 7⃣4⃣Ta sauka sannan ta dauki qaramin hijabi tasa. Yasan sbd kayan jikinta ne don sun kama fa tsam, duk motsin da tayi jikinta yana rawa. A zuciyarsa yace, lallai! Yau Mimi ce da rufe tsiraici? A fili yace Albmdlh. Ta kawo masa ruwa da kofi, ya kalli goran ruwan, lallai 'yan gayu, swan kuke sha? Tayi masa hararar wasa, wa zai bamu ruwan swan? Na fanfo ne muke sawa yayi sanyi. Ya tsiyaya ya sha. Cikin son jin me yayi niyyar cewa yaqi fada, tace ai kaima ka canza. Ya dubeta don ya riga ya dago ta. Yace, eh nima nasan na canza, na qara kyau sosai haka? Ta harareshi, ka cika son kanka da yawa. Yace inba gaky na fada ba sanar dani kawai. Tayi shiru. Yace shiru yana nufin eh ne. Ni nasan inada kyau. Ta 6ata rai, kai kyau ya dama. Ni ynxu nafison kyan hali. da ne nake kallon kyau wata tsiya. Yayi dariya shima inada shi, don naji mutane suna fada. Ranta ya sake 6aci. Da gske batasan shi zolayarta yake ba tace, ka cika wasa kanka. Kuma ance duk wanda yace shine, to ba shi bane. Yace nidai nine ismail bin Abdurrahaman. A ranta tace, karma yaga cewa na wani damu dashi ne ma, bari in masa zancen rabuwarmu. Tace gashi dai karatu ya qare, yaushe zamu warware maganarmu? Gabansa ya fadi. Nasa zaton ta dangana da wannan maganar. Maimakon yabata amsa, sai yace, ni na manta ma munyi gida fa. Ya miqe bari in sanar da yaya Amina. Itama ta miqe ta biyoshi. Nan ya labarta musu komai. Suka yi murna sosai. Yaya tace, kuma takardun da sunanka da komai? Yace cikakken sunana kuwa. Tace ko wanene wannan, Allah ya saka masa da alheri. Yace Ameen, gurina da akwai wasu kudi, zan gani ko zasu sai mana kayan gado dana girki. Ba sune dai akafi buqata ba? Yaya tace sune mana. In ma na gado ko katifa ce zatayi muku. Kayan kicin shine yafi zama dole. Yace hakane mu shirya gobe zanzo in kaiku gidan. Haka kuwa washegari yazo ya kwashesu. Gidan ya burgesu sosai. Mimi ta shiga fargaba, tana tambayar kanta wa zaisa a gidan? Bata san lokacin da tace to kawunsu ummi yaushe zaka dawo nan gidan? Ya kalli cikin idonta, ya karanci wani abu. Don haka sai yace, bari mu koma gida, zaki bani shawara ko? Ta daga gira, alamun eh. Yayi murmushi. [26/09 8:41 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣5⃣Ismail tunda ya dawo bai zauna ba, abubuwa zunyi masa yawa. Sun raba takardun neman aiki a jami'o'i kamar su A.B.U da B.U.K, har Abuja. Sannan qungiyarsu ta da'awa, suna ta gudanar da aikace-aikace, musamman na gidan marayun da suke ginawa. Sannan ga gayyata da yake samu gidajen rediyo, da talabijin da gabatar da filaye na addini irinsu tambayoyin addinin musulunci, Filin fatawa, da dai sauransu. Haka sauran jihohi irinsu kaduna, kano, sakoto, suna gayyatarsa don yin majalisi dashi. Hakan yasa ismail ya zama kullum yi nan, yi can. Ga shi har ynxun bai daina zama gaban malamai ba don neman qarin ilimi. Daukaka ta Allah, lokaci qanqani sunansa ya karade jihohin Arewa. Wannan yasa mahmud ya matsa masa. Wai ya tare a gidansa. Yaso su tare da mahmud din tunda sama ne da qasa, amma sai mahmud yace, in har ya sake ya tare a gidan ismail din, ba zai maida hankali a nasa ginin ba, wanda yayi nisa da farawa. Ranar wata lahadi misalin qarfe takwas da wani abu na dare, ismail ya shigo gurin su mimi, lokacin babu wutar NEPA ta kwanta a tsakar daki akan tabarma, tana dannan wayarta. Sallamarsa ta jiyo yasa ta kashe tocilar wayar, sannan ta kashe ta gaba daya, ta tura a qasan gado. Lokacin daya iso dakin da sallama, ta amsa. Yace farko dana shigo, sai naga kamar dakinnan da haske. Tace, idonka ne yaga haka. Ya ciro qaramar wayarsa daga aljihu, ya haska dakin. Kafin ya zauna yace, me kuke dashi na ci? Tace shinkafa mukayi da wake, sai mai da yaji. Jiya ne yaya tace, muyi alala, qila kozo, tunda ka kwana biyu baka zo ba. Amma sai kaqi zuwa. Yace ba zaki gane bane khadija. In a lissafa maki lamurran dake gabana, zaki sha mamaki. Karku damu da yin abinci dani. In nazo kamar haka in na samu zanci. Ban cika son cin yaji ba, shirya ki rakani muci abinci. Ko kuma ke kici kifinki. Tace kana son jana yawo, ni kuma banason fita. Yace shikenan ba zan matsa miki ba. Tace to bari in shirya muje. Ya ciro wayoyinsa banda wadda ya haska. Kamar ana jira sai ga kira, tamkar kar ya daga, sai kuma ya daga don ya lura da lambar anata kiransa da ita bai ta6a dagawa ba. 7⃣6⃣Kamar yadda ya zata kuwa mace ce, ya amsa suka gaisa. Yanason tuna inda yasan mai muryar.Ta katse masa tunani da cewa, baka ganeni ba ko? Yace cikin qosawa eh. Tace zainabu ce. Sai kuwa Mimi taga ya miqe da sauri tare da fadin zainabu?! Tace eh nice, malam. Zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri. Yayi ta maza , yaya gida da mai gida da kuma yara? Tayi 'yar dariya, gida dai lfy mai gida kuwa bama tare. Munfi shekara biyu da rabuwa. Da kuwa qwara daya ne, ya dauki kayansa. Yace, subhanallahi, to Allah yayi miki za6i na alheri. Tace Ameen nagode, na gaisheka. Wannan kuma number ta ce. In ba laifi adan ajeta, don nayi ga kira baka daga ba, qila don bakasan lambar bane. Ban sani ba ko zan kira neman fatawa. Cikin wani shirinka na samu number lokacin daka bada. Yayi 'yar dariya, karki damu zanyi saving dinta, nagode. Kasa kashe wayar yayi, sai itace, ta kashe. Ya zauna bakin gado tare da cewa, auren zainabu ya mutu tun shekara biyu? Kenan ma tun ganin da nayi mata. Yaya tace min tanada aurenta, ashe ba tada shi. Sam ya manta da wata Mimi tana dakin. Ita kam tana zaune hankalinta tashe. Tambayar kanta kawai takeyi wacece kuma Zainabu? Batasan tambayar ta fito fili ba, saida taga ya tsaya cak, daga rawar jikin saving din lambar Zainabu wanda yakeyi. Shi sam ya manta a ina yake ma. Yace, am.. Wata yarinya ce. Ya miqe, ba zaki santa ba. Ya kalleta, ni bari in tafi. Tace zuwa gurin cin abincin fa? Yace mu barshi sai zuwa wani lokaci, zan sha tea in naje gida. Hankalin Mimi yayi qololuwar tashi, tace, ynxun fa kazo amma har zaka tafi? Yace inada wani uzuri ne, karki damu zan dawo da safe. Bata iya amsa shi ba ya fice. Kai kawo ta dinga yi a dakin. Ta gama yarda cewa tanayi ma ismail wani mugun so, shi yanason wata kenan. Ta fita zuwa dakin yaya Amina ta zauna. Yaya tace yau naga malam ya fita da wuri. Mimi tace, yaya in tambayeki mana? Yaya tace ina jinki. Mimi ta tsura ma yaya ido, wai wacece Zainabu? Yaya tace Zainabu? Kinsan tane? Mimi ta sake tambaya. Tace umm, wata yarinya ce da ismail yayi mata wani mahaukacin So, shine iyayenta suka yaudareshi, suka bada ta ga wani mai kudi. Zufa ta karyo wa Mimi, ta miqe. Yaya tace, yayi miki zancenta ne? Mimi tace kawunsu ummi ne naji suna waya, ta fada masa aurenta ya mutu shine fa ya fita jiki yana 6ari. 7⃣7⃣Yaya Amina ta miqe tsaye tabdi! Ai ko duk nacinsa ba zai aureta ba! Shegiya, ko wa ya bata lambarsa? Tuni nasan aurenta ga mutu, amma na share ban fada masa ba. Saboda kar ya koma mata. Mimi cikin fargaba ta miqe tare da fadin saida safe. Yadda yaya taga hankalin Mimi ya tashi ne ya bata mamaki. Har ta miqe da nufin zuwa ta bawa Mimi shawara, sai kuma ta fasa, tace bari in barta ta fara yin shawara da kanta tukunna. Yarinya kinada miji tun tsawon lokaci, amma me kin dage sai an rabu dake. Daga ganin ta kasan kishi ne can qasan ranga. Ta koma ta zauna. Mimi kuwa tana shiga dakinta ana kawo wuta. Sam bata damu da wutarba, duk da cewa fankar data soma kadawa tana kai mata iska. Sitiri kawai takeyi tsakar daki. Ta rasa wane irin tunani zatayi, ta rasa wa zai bata shawara. Ta zauna bakin gado. Na shiga uku na, ni khadija wa zai bani shawara ynxun? Kalaman yaya Amina ke mata yawo cikin kai, "wata yarinya ce da ismail yayi wa mahaukacin so. Ta maimaita sunan wai Zainabu. Ta tuna yadda ya miqe zumbur lokacin da ta ambaci sunanta. Ta tuna yadda ya manta da ita a dakin sbd zainabu. A fili tace, lallai za'ayi tan kuwa. Wani tuquqi ne ke taso mata daga qirji, tace, qila ma suna can tare. Ranar dai su Mimi ba'a runtsa ba, sannan bata qulla ma kanta mafita ba. Barci sama-sama tayi shi har asubahi. Sai da tayi sallah sannan varci ya dauketa. Ta kai kusan tara na safe sannan ta farka. Ta fito da nufin gaida yaya, sannan tayi wanka, sai kuma taga yayar sanye da hijabi zata fita. Tace ina kuma zakije yaya? Tace nan maqota zan shiga aikin biki, wannan gidan da sukace muje muga lefe. Kinsan yau ne daurin auren. Mimi tace, wai dole ne jn mutum yananan garin sai ya shiga aiki kenan? Ban saba ganin haka ba. Mu in zamuyi biki, ko suna sai akai gurin yin abincj ayi a kawo. Yaya tace, sha'anin masu kudi kenan. Mu nan in baka zuwa, wa zaizo maka? Bakiga sunan Aishatu ba, gidannan cika yayi? Kinsan dai in bana zuwa ba za'a zomin don tsorona ba. Mimi tace, sai kin dawo. Ni dai bana ra'ayin haka. Tayi 'yar dariya. Aishatu tananan tana varci a uwar daki. Mimi tace to. Ta dauki ruwan wankanta wanda ummi ta zuba mata, kamar kullum tunda bata iya jan ruwa. 7⃣8⃣Tana wanka taji shigowar ismail, yana ta sallama ba a amsa. Tana jinshi yana cewa, inma dai yaya Amina batanan, yasan babu inda Mimi zataje, qila tana bandaki. Saida Mimi ta gama ta fito, sannan ta dauki Hijabin Ummi dake kan igiya ta saka. Ta shiga dakin. Yi tayi tamkar bata ganshi ba. Ta wuce, kan madubi ta zauna tana shafa mai. Ta zame hijabin, ya sauka a wuyanta, dogon gashinta ya bayyana. Ta dauki mataji tana tajeshi. Baqi sidik. Ta lakuto manta na gashi tana kallon gashin cikin madubi. A ranta tana cewa, inda nagode ma Allah, duk lalacewar da nayi gashina bai zube ba. Ta kalli fuskarta a madubin, tace wai wane irin kyau mutuminnan yake buqata wanda yafi nawa? Sai dai ko in balarabiya yake son ya aura. A fili tace, zan so ni kuwa inga zainabun nan wace iri ce ita? Kyanta yaya yake? Yace me kk ce? Cikin sauri ta waiwaya, ta dubesbi. Yace yau 'yan miskilancin ne ko? Kin shigo kinyi kamar baki ganni ba. Shiru tayi, sam ta manta yana dakin, tayi zancen zucinta a fili, fatanta Allah yasa baiji taba. Tace kaji abinda nace ne? Yace a'a me kk ce? Ta sauke ajiyar zuciya, sannan ta maida hankali gurin abinda takeyi. Yace, ki fada min me kk ce mana? Sai naji kamar dai kin ambaci zainabu. Ta danyi dim, sannan tace, wai kai ka damu da wata zainabu, tunda ta kiraka jiya, ka fita hankalinka, harma takai ynxun kunnenka yanayi maka gizo ko? Magana mutane sukayi, sai ka zata sunce zainabu ko? Yace ni bance ba ranki ya dade. Ta zauna tana shafa hoda. Ta gama, taja durowar madubi, ta ciro abin daure gashin ta kamashi a tsakiya. Ta fesa turare sanna ta ciro daguwar rigarta leshi ta saka. Ba tare da ta daura dankwali ba ta nufi kicin. Shi dai yana binta da kallo. Tayi masa kyau a idanunsa. Ta dauko biredinta da ruwan shayi mara madara ta zauna, amma sai damuwa ta hanata cin biredin, sai ruwan shayin take kur6a. Yace nima zansha. Ta miqa masa na hannunta, kar6a. Yace, ki hadamin wani mana. Ta kalleshi, munin nawa har ya kai cikin kofin shayin ne, shiyasa ba zaka iya sha ba? Yace bance ba naga kamar baki qoshi bane, tunda ko biredin bakici ba. Ta daure fuska, nina qoshi. Yace shikenan bani. Ta miqa masa. Kan gado ta koma ta kwanta, fuskarta tana kallon gefe, tana tunanin nafita. Ya kalleta, baisan me take yiwa fushi ba. Sai ya samu kansa da shiga damuwa. [26/09 9:16 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 7⃣9⃣Yace ki tashi khadija, magana zamuyi, duk da naga yau kina fushi dani.Ta tashi amma taqi kallonsa, kanta yana qasa, tana wasa da yatsun hannunta, fuskarta a daure tam. Yace, to inason zan tare a gidana. Kina ganin ya kamata mu koma tare ne ko kuwa zaki zauna anan? Mimi tayi shiru cikin nazari, sai taga ya kamata ta gwadashi. Tace, kai me ka gani yafi? Ni ko ina daya ne a gurina. Ya dago yana kallonta cikin ido, sannan yace, banason in takura miki ne, kamar yadda nayi fa fada miki a tun baya. Abin da kikeso shi zan miki. Ta tura baki cikin jin haushi tace ni banida za6i. Ranshi ya sosu, cikin fushi ya miqe, shikenan, ni zan tafi. Duk lokacin da kk za6a, saiki fada min. Ni dai zan tare, kuma zanyi aure. Batasan lokacin da ta miqe tsaye a tsakiyar gadonba. Me kk fada? Yace nasan kinji. Tace ka auri dubu, amma kafin nan ka warware nawa auren dake kanka. Yace, nufina kenan don nasan bakida burin daya wuce wannan. Amma sai kina ta shirmenki. A sanyaye tace, dama kazo ka sakeni ne? Kafin ya amsa, qaramar wayarsa ta soma ruri. Ya daga ya fita a dakin yana amsawa. Mimi ta zauna tasa kanta cikin gwiwarta tana kuka. Batasan dalilin kukan ba bare asalinsa. Wata zuciyar ta ingizo ta tare da rada mata cewa, tayi tafiyarta. Ta sauka ta dauko akwatunanta, ta dauki daya, ta soma kwaso kayanta tana zubawa a ciki. Shikuwa yana gama waya ya dawo, da bango ya jingina yana kallonta. Bai hanata ba kuma bai tambayeta dalili ba, har ta gama ta dauki mayafinta tasa takalmi, sannan taja jakar, dariya ce taso ta su6uce masa, amma sai ya fasa. Ya tare qofar dakin. Tace, ka bani hanya zan wuce! Yace zuwa ina? Tace ina ruwanka dani? In tafi ko ina ma, mun hada zuri'a ne? Kawai ynxun ka bani saki na. Kai ko baka sakeni ba ma tafiya zanyi. Ya girgiza kai, bamu bada zuri'a ba, sai dai bansan gaba ba. Amma ynxun kafin ki tafi tsaya mu gama magana, in yasa sai ki tafi, ba zan hanaki ba. Ya nuna mata bakin gado, ki zauna anan! Fuskarta a daure ta zauna. Shima ya zauna. [26/09 4:09 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣0⃣Fadamin mecece damuwarki wadda tasa har zaki tafi ki barmu? Shiru tayi, domin ta rasa me zata ce. In zata fadi gsky, to kishi ne kawai ke cinye ta a zuciya. Amma sai tace, na gaji da kushe ni da kkyi. Duk lokacin da ka tashi, sai kace min mummuna. Sannan kaqi ka cika min alqawari na. Yayi murmushi, ni ban ta6a ce miki mummuna ba. Ta kalleshi, ba girmanka bane yin qarya. Domin kune masu fadin illarta. Jiyan nan kace min ko yaushe ina canzawa. Yace, canzawa nace ko muni nace? Tayi shiru. yace, banda jiya sai kuma yaushe nace miki? Cikin qarfin gwiwa tace, da muke asibiti, lokacin da nace, bana sonka me kacemin? Inka manta in tuna maka. Cewa fa kayi kaima kafison mace mai kyau. Ya sake yin wani murmushin, tabbas nace haka, amma nace bakida kyau? Tace kusan haka ne? Yace ba dai hakan bane tunda kusan ne. To naji wannan sai kuma batun alqawari, duk alqawurran dana daukar miki a gaban Doctor salis wanne ne ban cika ba? Tayi shiru, tabbas yace zai nesanta ta da iyayenta kuma yayi. Yace zai kula da ita daidai qarfinsa, kuma yayi, in zata duba tsawon lokacin da ta dauka tana jinya, sun yi ta dawainiya da ita. Ta dubeshi, sai na rabuwa, shine baka cika ba. Yace banda shi na cika sauran? Ta daga kai, alamun eh. Yace to bari in tuna miki. Kinsan na jima ina yi miki alqawarin cewa zan yi miki fiye da kk taso anayi miki na gata ko? Tayi shiru tana kallonsa. Ya tausasa murya, inason ki jira ni in cika wannan alqawarin, ko zamu rabu, ki bari in gama yi miki gatan dana tsara ma kaina, inji dake wani irin dadin da baki sanshi ba. In yasa nan, sai inyi miki abinda kk so. Tayi wani dan tunani. Sannan tace, zan yarda ne kawai in kaima ka yarda da abinda zan fada ynxun. Yace inajinki. tace zaka daura aure ne lokacin da ka warware nawa auren. Yace ban fahimta ba? Tace, ina nufin ba zaka ki aure ba, sai lokacin daka warware nawa auren. Yayi shiru don shi tun jiya ya gama tsarinsa. Ya tsara zai auri zainabu don ya gaji da zama haka, ita kuma lokacin data gama shirmenta sai su shirya don babu saki acikin zuciyarsa a ynxun. Daga nan sai ya kaita gaban iyayenta ta nemi gafararsu, duk da Hajiya tace zasu nemeshi in lokaci yayi. Amma dubi yadda ita kuma ta 6ullo masa da wata magana. 8⃣1⃣Ta katse masa tunani da cewa, kayi shiru? Yace, kina ganin zamana babu aure ba ragewar mutunci na bane a matsayina na mai fadakarwa? Ta miqe tsaye, tayi dan taku daya zuwa uku, sannan ta kalleshi, ni da kaine kawai muka san cewa ba kada mata, amma Duniya ta jima da sanin cewa kanada aure. Yace naji saidai karki manta ni fa mutum ne, kuma ba yaro ba, wanda yakai. Kinsan dole ina buqatar abokiyar halittata. Kinsan shekaruna nawa ynxun? Tace ban sani ba, qila zaka gota talatin. Yace yauwa, to in na rantse miki ba zanyi kaffara ba, a takure nake, sannan inason yara. Ynzun dubi mahmud, matarsa tanada ciki na biyu. Ya numfasa, khadija saka idonki cikin nawa, ta kalleshi. Yace ina buqatar abokiyar rayuwa. Ta sunkuyar da kai, wannan ai zancenka ne da kuma wadda zaka aura. Kukan Aishatu ta jiyo, ta miqe da sauri, har tana tuntu6e da qafarsa zata fadi. Ya sa hannuwansa ya tare ta. Sai tsintar kanta tayi a jikinsa.Duk zun jisu cikin wani yanayi. Shine yayi ta maza. Yace ina zakije haka? Kike sauri zaki fadi kije ki karye, dama gaki nan kamar 'yar tsinke. Ta tashi da sauri, bakaji kukan Aishatu ba? Da sauri ta nufi gurin Aishatu. Ta shigo riqe da hannunta, sai lallashinta takeyi. "Yarinya tana kuka kin firgice, ranar da kk haifi naki, sai yaya? Ta harareshi cikin wasa, me zai hadani da haihuwa? Yayi qasa da murya, "wai ba kyajin komai game dani? Tace Aishatu dai tana kallonka. Ya miqe, bari dai in gafi tunda kin fasa yajin. In yaya ta dawo ki fada mata cewa nazo, kuma batun tarewa ya kawoni. Ynxu zance in samu mahmud ne muje kasuwa mj sayi abinda ya sauwaqa, mu zuba a gidan, to shikenan. 8⃣2⃣A zaure zuka hadu da yaya. Nan suka gaisa yayi mata bayanin dalilin zuwansa har yadda sukayi da mimi. Dariya yaya tayi, domin ta gama gano mimi tsabar son mijinta takeyi, amma sai bata nuna ma Ismail din ba. Tace khadija kenan 'yar daru, 'yar shagwa6a. Zamuyi magana da ita. Amma ni shawarata karka tsaya bata wani za6in ko nan ko can. Kawai kace mata ku koma, ko don sbd kauda hankalin mazu zaton bakada aure. Yace nima haka nekeso, amma kinsan rigimarta. Gashi zai da'awar in saketa takeyi. Ni kuma gsky sai inga in nayi haka ban kyauta wa mahaifiyarta ba. Yaya tace wannan ma bata taso ba. Kudai koma din, qila ma ku sasanta. Ismail yace, Allah yayi mana jagora. Yaya tace Ameen. Sukayj sallama tayi ciki shi kuma yayi waje. Kafin sati daya, ismail ya sayi abinda ya sauwaqa, sun kai sjn shisshirya. Sannan sun shirya walima, inda su yaya da maqotanta sukayi musu girki, shinkafa ce da waina, sai kaji. Girkin yayi kyau sosai, ga kuma abin sha. Bayan sun tashi daga walimar ne, sannan sukazo suka kwashe kayan sawar mimi, shi da mahmud. Kayan Gado dai tabarma su Ummi. Duk da haka basu koma ba, sbd ismail zasuje kaduna da kuma Abuja, don gabatar da wasu muhadarori, da kuma lakcoci. Haka kuma suna durowa katsina, ya tarar da takardar gayyata daga gwamnatin jihar katsina. A hannun Malam Aminu ya samu saqon. Yace wannan taro ne na manyan malamai, to ni meya kaini gurin? Malam yace daukaka ce daga Allah, ismail. Shawarar da zan baka kayi taka tsan tsan, domin Malamai ma wasu basa tsoron Allab, musamman in sunga Allah ya baka nasibi. Sannan kar kayi sanyi gurin fadar gsky, komai dacinta. Ismail yace shikenan zan kula insha Allah, nagode. Gidasa ya wuce, sai da yayi wanka ya huta, sannan ya fita zuwa gidan yaya Amina. Yayi matuqar qosawa Mimi ta dawo, ko don Abinci. Gashi a gida mai kyau, amma abinci sai ya siya. Can yaci abinci, sannan yace, yaushe zaku raka mimi can gidan? Tace sai jibi. [26/09 10:32 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa Washegari ya samu halartar gayyatar da akai masu. Maqasudin zaman dai, sbd tafsir ne na Azumin dake gabatowa. An yi musu jan hankalin hadin kai, su daina zagin juna, da kafirta juna. Sannan kowa yayi wa'azinsa ba tare da izgilanci ba, ko cin mutunci. Ka abinda Allah da manzan sa sukace, a tsage gsky komai dacinta. Malamai sunyi bayani, inda shima ismail yayi nasa bayanin, wanda ya gamsar da dukkan mahalarta taron. Sbd ismail, Allah ya hore masa hikimar iya magana. Shi mutum ne wanda zaiyi wahala yayi maka bayani baka gamsu ba. Bayan an fito ne, ismail ya miqa hanya da nufin neman dan aca6an da zai kaishi gida, sa6anin sauran malaman da suka zo da motocinsu. Wannan dalilin shine ya kawo inda aka bincika cikin malaman da suka halarci taro, aka fidda guda hudu wadanda basuda abin hawa. Washegari saiga mota sabuwa dal, babu ko lamba an kawowa ismail. Lokacin da Malam Aminu ya kirashi yazo, shiru yayi ya kasa magana, lokacin daya gabatar masa da motar. Bai san da wace kalma zai fara magana ba, duk wani alheri da zaizo masa ta gurin Malam Aminu yake tahowa. Yace Malam, Allah ya saka maka da aljanna. Sunyi ta murna. Ya kira mahmud. Dama mahmud ya iya mota. Nan suka shiga suka zagaya gari, tare da zuwa gurin abokan arziki. Sunje gidansu, inda 'yan gidan suka fito suka ga mota sunata murna. Ta fito wanka , tana shafa, ummi ta shigo da gudu. "Aunty zo kiga motar kawunmu, sabuwa dal, baqa kuma qatuwa. Mimi tayi dariya sbd yadda Ummi ta jero maganar, tare da cewa, Allah yasa alheri. Sai gashi da kansa, khadija kizo ki gani mana, munyi mota. Mimi ta miqe taje taga mota, kuma tayi murna. Yace ki shiga mana ko kin manta da yadda akeyin tuqi? Murmushi tayi, sannan ta amshi makulli, su Ummi suka shiga, ta tashi motar ta tuqa zuwa cikin layi, suka dawo. Ummi sai mamaki takeyi, tana cewa, anty yaushe kk koyi tuqa mota? Ismail ma cewa yayi ashe baki manta tuqin ba. Tace in manta tuqi? Ashe zan manta da yadda zanyi tafiya da qafata. Suka sa dariya. 8⃣3⃣Washegari Ismail da mahmud suka soma fita don koyo ma ismail tuqi. A yammacin ranar ismail, ya kira yaya Amina yace, su shirya zasuyi tasu walimar a gidansa. Bayan la'asar suka zo kwashi su yaya Amina, suka biya suka dauko Rabi'a da innarsu mahmud. Bayan sun kaisu ne, sai suka koma suka dauko su inna, dasu fatu. Dukda ba wani alatu. Ismail ya zuba a gidanba, gidan yayi kyau sosai. Katifu ne a dakunan da sabbin zannuwan gado da fuloli, sai labulaye masu tsada. Sai falon ne ma ya gyarashi sosai, don tsadaddun kujeru ya zuba da kafet din tsakiyar, shi ma mai tsada ne, TV da sauran kayan kallon zamani. Sai dai falon saman bai saka komai ba. Yace sai ahankali zai saka komai. Mimi taga qorarinsa sosai, tunda tasan shi talaka ne. Sun je sun kawo musu abin sha na gora. Daf da magriba suka koma kai su innarsa, sannan su yaya Amina. Mimi harda kuka wai abar mata Ummi. Yaya tace a'a za dai tazo miki hutu, kuma kinsan zata tayani aiki, ga makaranta. Mimi tace yaya baga saddam ba. Kuma indai makaranta ce ai zan kaita tunda ga mota a hannun kawunsu. Tace kiyi haquri har suyi hutu. Ismail dake kallonta burgeshi takeyi, don yanason shagwa6arnan tata. Shiyasa ma yaqi sa musu baki, don yanason kallonta a haka. Ita kuwa yaya Amina, taqi barin Ummi ne don zamansu, su biyun wata hikima ce, tana sa ran su shirya kansu. Sun barta da Rabi'a in sun dawo kaisu yaya, sai mahmud ya tafi da matarsa. Bayan tafiyar su ne, sai kuma suka shiga kicin don ganinsa. Freezer ce, sai tukwane da kuloli, plates da cokula, amma babu risho ko wani gas. Rabi'a tayi dariya, tace to da me zakuyi girki? Mimi tace oho masa. Suka koma sama sukayi sallah, sannan suka dawo qasa suna 'yar hira. 8⃣4⃣Ranar Mimi harta dan saki jiki da Rabi'a, don ta lura Rabi'ar ta san me takeyi. Rabi'a tace, niko da ace zaki yarda da na baki shawara. Mimi tace, me zai hana? Rabi'a tace kar kibar wata mace ta shigo gidannan a matsayin matar malam ismail. Mimi ta tattaro hankalinta gurin Rabi'a. Ta yaya zanyi hakan? Nasan dai kinsan komai dake tsakaninmu da malam din, tunda Aminin mijinki ne. Bafa son juna mukeyi ba. Rabi'a tace ni kuwa sai ina kallon so acan cikin qwayar idanunku. Na farko da baya sonki, da tuni ya sakeki. Rashin sakin jikinki shine ya hanashi nuna miki. Mimi tayi murmushi, ya fada miki ne? Rabi'a tace a'a nice nayi hasashen hakan. Mimi tace bana zaton zai soni, sbd na samu labarin yadda yakeson wata Zainabu. Rabi'a tace, tabbas yanason zainabu, amma da kinso, da tuni kin mantar dashi ita. Kiyi tunani. Mimi ta sauke ajiyar zuciya, ni damuwa ta ma ko auren namu yananan daram ko ya lalace? Oho. Kafin Rabi'a tayi magana, sai gasu sunyi sallama. Don haka, sai suka rufe bakin hirar. Tare suka tafi dukkansu, aka kulle gidan. Mahmud ne ya jasu zuwa gidansu. Sun danyi hira, sannan Mimi ta jawosu zuwa gida. Ismail yaji dadin yadda Mimi ta saki jiki da Rabi'a. Bayan tayi wanka tayi isha'i, ta saka kayan varci, ya buga qofarta, taja hijabi ta saka, sannan tace, shigo mana. Bakin katifa ya zauna, sannan yace kinga dan kayan dake kicin din ko? Sai a hankali zamu qara abinda bamuda shi. Tace maimakon kabar wani abin ka siyo gas ko risho, to dame zamuyi girkin? Ya zaro idanu, alamun sam ya manta da Risho. Sannan yayi dariya, lallai yau akeyinta. Sam na manta fa. Kinsan abubuwan da yawa, gashi ba wai inada kudin bane. Amma karki damu zuwa gobe ko risho dinne, sai in samo. Gas daga baya zamu samu. Ina son ma ki zauna ki rubuta abinda muka fi buqata, sai muyi ta siya a hankali. Ki fara da wanda muka fi buqata. Tace mu bari saida safe. Yace rubuta dai ynxun. Ta dauko takarda da biro, shi kenan dame zamu fara? Yace kayan gado, sai falon sama, abubuwan cikin ban daki, sai me? Tayi dariya sannan ta soma tuno wasu tana fada, suna rubutawa. Sun kai kusan sha daya, kafin yace mata bari ya tafi saida safe. [27/09 7:59 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣5⃣Ya jima kafin yayi varci, sbd gsky haqurinsa zai gaza. Ko da bayason Mimi, to yasan yana muradinta a gefensa. Ballantana yana da tabbacin cewa wani sashe na zuciyarsa yanason Mimi. Duk lokacinda yazo da niyyar sanar da ita hakan, sauta 6ullo masa da zancen saki, sai dai wasu abubuwan da takeyi, sai yana zargin cewa tana sonshi. Washegari da safe, yana zaune a falon qasa, yana duba wani littafi, ta sauko tayi wanka tasa daguwar riga ruwan qasa, mara nauyi, bata daura dankwali ba, ta kama gashin kanta a gefe. Tunda ta nufo shi ya kasa daina kallonta har tazo ta zauna akan kafet kusa dashi. Tace ina kwana? Yayi murmushi, "lafiya lau" kefa kina lfy? Tayi dan fari da ido " qalau" ta gyara zama tace ynxun yaya zamuyi, tunda bamuda abinda zamu hura wuta? Yayi murmushi. Fita zanyi in siyo mana abinda zamuci. Tace a'a kawai muje gdn yaya Amina muci. Yace kinsan yau dai ba zasuyi damu ba, amma bana siyo butar dafa ruwan zafi ba? Tace haba? Ni banganta ba. Ta miqe zamu dafa ruwan tea. Yace muje in gani, amma tabbas na siyo Butar ruwan zafi. Sun dafa ruwan zafinsu, suna sha, suna labari kadan-kadan. Daga bisani yayi wanka ya fita. [27/09 3:47 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣6⃣Ranar da suka cika kwana uku, Ismail yaji haqurinsa zai kasa. Don haka yaga babu abinda yafi illa ya ziyarci zainabu. Koda ya shawarci mahmud sai yace masa kar ya soma, ya dai yi qoqari ya sasanta da matarsa. Sam ismail zancen bai shigeshi ba, domin yasan tun filazal ba sonshi da Zainabun sukeyi ba. Don haka ya yanke shawarar kiranta a waya don ya fada mata cewa zai kawo mata ziyara. Misalin qarfe hudu bayan sun fito la'asar ya ciro wayarsa ya soma neman lambar zainabu. Koda yazo kan lambar saida yadan jima yana tunani kafin ya danna kira ya tafi, lokacin zainabu tana kwance a qofar dakin innarta tana buga game din maciji, sai kawai taga kira ya shigo. Ganin sunan dake rawa akan fuskar wayar, saita zaro ido tare da murza idon, sannan ta dauka cikin sauri tare dayin sallama. Sun gaisa sannan yana ganin saqonta na gaisuwar juma'a kuma yana godia, tace ashe kana gani, nayi zaton ma baka gani tunda kuna hulda da jama'a sosai. Yace ina gani, ko zan sameki anjima? Cikin sauri tace, inanan Malam. Yace, qila in shigo anjima. Tace to Malam, Allah ya kawoka. Duk mahmud yana jinshi.Misalin takwas da mintuna mimi tana daki tana danna wayarta, so take ta tsokani ismail tana kiranshi amma yaqi dagawa, sai kawai Mimi taga ya fito cikin shadda wagambari sai maiqo takeyi. Mai kalar blue, haka hularsa. Ta wundo ta hangoshi. Cikin sauri ta 6oye wayar sannan ta fito, ina kuma zakaje da darennan? Yace wata 'yar unguwa zanje bazan jima ba. Tace inzo in raka ka? Ta fadi haka ne don ranta ya raya mata ko gurin wata zashi. Yace a'a ki barshi ba ni kadai bane nida mahmud ne. Tace kasan dai inajin tsoro, don Allah karka zauna. Yace ynxun zan dawo. Tace amma bada mota zakaje ba? Yace da ita zanje mana. Nifa na tuqo motar daga unguwar su mahmud dazu, bare ynxun da babu cunkoso. Ta windon su na sama take leqensa ya fita da motar, sannan ya dawo ya rufe gidan, ta saki labule, ta koma ta zauna tana ta karanta wasiqar jaki. Yana isa gidansu zainabu, ya kira ta cikin waya ya fada mata ya iso. Cikin soron gidansu suka zauna. Sun gaisa sannan ismail yace, gani nazo a karo na biyu, banda zuciya ko? Cikin sauri tace, malam kayi haquri, ko da ba laifina bane. Wlh ina sonka, shine ma dalilin da ban iya zama gidan Alhaji ba. Yayi murmushi, to ina fatan ba zan sake samun matsala ba, don wannan karon banason aja lokaci. Tace ni ko gobe ka turo, don dama zaman jiranka nikeyi. 'yar dariya yayi, sannan yace shikenan ko ban sake zuwa akan lokaci ba zamu dinga waya. 8⃣7⃣Wasegari ya samu gayyata daga abuja, jami'ar da ya nemi koyarwa. Yaje kuma sun daukeshi, yayi murna sosai. Haka ma dangi sunyi murna, illa mimi kadai da take ganin cewa za suyi nisa da juna. Yayi mata tayin ziuwa abuja tace, ko sha'awar zuwa bataso. Yace, nasan ba zaki iya zama ke daya ba, yaya kk son ayi? Tace zan koma gidan su yaya Amina, in ka dawo sai in dawo. Da kanta tace, ya sakata islamiyya a unguwar su yaya. Sam in kaga Mimi ba zakace ita bace. Sbd dogon hijabi da niqabi. Lecturing daya soma sai ya dauke hankalinsa daga kan batun auren daya so yi cikin gaggawa. Amma dai suna waya da zainabu. Duk sati yake zuwa, wani lokacin sati biyu. Shi mahmud ABU zaria ya samu. Ismai ya kira masu aiki sun duba filin dake gidansa sun tabbatar masa zai iya yin makaranta harda madaidaicin masallaci. Bayan sun bashi tsarin ginin, sai ya soma tunanin yadda zai samu kudin ginin don kudin da aka qiyasta makarantar zataci ba qanana bane. Harkoki sun bude ma ismail, ga alherai da yake ta samu daga jama'a, domin ranar da akayi wata hira dashi a gidan TV na Africa, lokacin gidan TVn yana sabon budewa, har ya sako bayani akan makarantar da yakeson ginawa, ko sati ba'ayi ba, saiga shi mutane sun fara kiransa don son bashi gudunmuwa. Kafin wani lokaci tuni an soma gini. Babban qalubalenshi mata. Ko a makaranta, mata ne keta kawo mashi hari. To don yana malami, shi kam ba waliyyi bane, da yawa ana jarabtar Malamai da son mata da kuma kudi, in bakayi taka tsantsan ba, sai ka fada halaka. Shi yasa ya gama yanke hukunci. Yana samun hutun qarshen zango yazo, to kuwa aure zaiyi, ko ma da wacece. Wata asabar ya dauki takardar da Mimi ta rubuta duk abinda suke buqata, ya shiga kasuwa, sai da yayi rabi, tun daga kan gado zuwa saurensu. Dakin mimi kuwa saida ya tsara mata shi fiye da nasa, sannan yayi mata sayayyar kayan sawa, sannan ga sabuwar waya da kuma layi, tsohon nasa ne ma ya bata. Don har ynxun baisan tanada waya ba.zainabu ma yayi mata 'yar sayayya. Bayan sunyi hutu, dukda cewa sati biyu ne hutun nasu, amma cikin sati biyun zai yaye ma kansa damuwa. Shiyasa ma washegari da safe yana zaune falon qasa yanashan tea, saida yaga itama tazo ta zauna , sai ya dauki wayarshi yana kiran layin zainabu, da farko hankalinta baya kansa, saida taji yace zainabu, cak ta tsaya ta kada hadiye tea din data kur6a. Yaci gaba ina gari zan shigo anjima yaudai zamu gama magana. Inason kafin hutunnan ya qare zaki zama a gidana. Cikin murna take fadin sai kazo. Yana kashe waya mimi ta maida tea din dake bakinta cikin kofin, sannan cikin wata irin murya tace magana zaku gama? Ya dubeta fuska daure, "khadija aure zanyi" ji tayi tamkar ya soki zuciyarta da qaho. A hankali ta jingina da kujera, sannan ta lumshe ido, ta rasa me ma zatace. Sai kawai ta tashi ta nufi dakinta. Bakin gado ta zauna, rashin wanda zai baka shawara matsalane. Tasan tunda yace mata aure zaiyi, to kuwa yana nufin rabuwarsu tazo kenan. Wata zuciyar tace, lokaci yayi da zaki koma gidan iyayenki. A fili tace, kai da saura. Haka zan koma musu bayan shekara uku, babu wani ci gaba, ba kuma auren da suka daura min, bayan tsohon laifina na baya? Ta girgiza kai, lokaci baiyi ba. Mafita ya kamata in nema. Ya turo qofarta ya shigo. Jikin sif dinta ya jingina. Khadija ban zaci zakiyi fushi ba, Nafi zaton zakiyi murna, don lokaci yayi da zan warware aurenmu. [27/09 3:48 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 8⃣8⃣Ta daga masa hannu. Don Allah ka fita! Inason inyi tunani. Yace inace kin gama tunani daga yau? Ta miqe, ta ra6a ta gefensa ta fita, qasa ta koma ta kwanta kan doguwar kujera. Murmushi yayi, sannan ya shiga dakinsa. Wayarshi ta gani da sauri ta dauka ta shiga kicin. Bata sha wahala gurin ganin sunan zainabu ba. Ta dauki lambarta. Sannan ta dawo da wayr inda ta dauka. Bayan ta shiga dakinta ma harda shiga bandaki. Layin zainabu ta kira, bayan ta daga mimi ta soma magana da kakkausar murya, "kece zainabu?" tace eh nice. Dama na kiraki ne in fada miki cewa ki fita harkar mijina, in har kinason zaman lfy. Zainabu tace wai waye mijin naki? Mimi taja tsaki, "kinsanshi tunda har kina shirin aurensa. Zainabu tace, oh wai kina nufin malam? In shine sai ince kinyi kuskure. Domin aurensa shine abinda nake buri koda zaki zama ajalina. Ki sani kafin ya soki, ni ya soma so. Kuma ina sonshi, aure babu fashi! Mimi tace, mu zuba! Ni dake zanga wanda keda nasara! Ta kashe wayar, sannan ta fito daga ban dakin, ta jefa wayarta akan gado. Ta shiga yin kai kawo a tsakar dakin. A fili take fadin, wai meyasa ni bana burgeshi ne? Dame zainabu ta fini ne? Ta janyo hijabinta da niqabi ta saka, sannan taja durowa ta dauki kudi ta nufi qasa. Bata zaci yana qasan ba. Saida taji yace, ina zaki? Ba tare da ta tsaya ba, tace gidan yana Amina. Ya daga murya. Ba zaki je ba. Ga waiwaya ta dubeshi, fuskarsa murtuk, sama ta koma fuuuu. A zuciyarta da qudirin cewa shima kuwa sai tayi masa abinda ba zai fita anjima ba. Haka suka yini kowanne zuciya babu dadi. Da dare tanata fakonsa , ya shiga dakinsa yana tashi, sai kuwa ta sauka qasa , ta dauke masa makullin mota, ga jefa qasan kujera. Sannan ta kulle qofar falon ta saka makullin cikin rigar mamanta, sannan ta koma dakinta. Tana kwance, rigingine kusan minti shabiyar, sai kurum taji turo qofarsa. Tashin da tayi da sauri shine ya kawo har yaji qaran makullin. Yace bani makullin mota dana qofar fita. Tace ajiya ka bani? Inama zakaje? Ni gsky tsoro nakeji, ba zaka fita ba. Yace, tadi zanje ki bani, karki 6atamin lokaci. Cikin 6acin rai tace, nifa bazan zauna ni daya ba. Yace to kizo muje tare. Da qarfi tace, Allah ya tsare ni. 8⃣9⃣Har inda take ya tako, daf da ita ya tsaya, ya sa hannu ya dafa kafadarta, girgiza ta yayi don yaji daga ina yaji qaran makullin. Amma sai baiji qaranba, sbd sun samu mazauni mai kyau a tsakiyar qirjinta, makari guda biyu sun taresu. Sai ya soma yi mata wani irin lalube tun daga qugunta yake shafawa da hannuwa guda biyu gaba da baya. Hakan ya kashe mata jiki, har ya tilasta mata lumshe ido, daga ita harshi. Haka nan yanajin makullin, sai ya zura hannunsa ta saman rigarta don ciro makullin. Ya ciro, amma yanayinsa gaba daya ya raunana, kamar yadda itama ta sukurkuce. Ta bude idanu ta kalleshi, shima fuskarta yake kallo. Cikin ido suka kalli juna, sannan a hankali yace, saina dawo. Ta fahimci muryarsa ta canza. Kan gado ta fada ta soma kuka. Kusan minti biyar ta tashi ta rufe qofarta. Shi kansa baisan meya hanashi yin wani zance mai muhimmanci ba, aun daiyi 'yar hira yace, zai dawo kan batun aurensu, yana sauri ne don matarsa ba tada lfy. Ta so ta fada masa kiran da matar tasa tayi mata, sai kuma ta fasa. Lokacin da ya dawo, ya hau sama, kai tsaye qofar Mimi ya murda, amma sai ya jita gam. Don haka sai ya wuce zuwa nasa dakin, bayan yayi duk abubuwan da yakanyi kafin ya kwanta, sai ya kwanta. Juyi kurum yakeyi tare da tuno yadda ya caje matar tasa. Ya gama yarda itama ko bata sonshi, to kuwa tana buqatarsa, don ya lura da halin data shiga a lokacin. Yanke shawara yayi ya tuntu6eta da batun, amma sai ta huce daga wanna fushin da tayi. Da asubahi, kamar kullum saida ya qwanqwasa mata qofa kafin ya wuce masallaci. Ita kam tuni idanunta biyu, domin dai yau duk satar varci, saida yayi mata haquri. Ta amince, baya sonta tunda har ta zubarda kimarta ta 6oye makulli, amma saida ya dauka kuma ya tafi. Zucigarta dai tanata bata shawara akan ta fito fili ta fada masa abinda ke ranta. Sai dai ita tsoronta kar sai yaji sirrin zuciyarta, sannan yace, ba irinta yakeso ba, kamar yadda yayi ta fadi a baya. Takaici ne ya hanata fitowa daga daki. Koda gari ya waye, shi kuwa shareta yayi, har ya gama komai ya fita, sai dai alamu sun nuna bata bude qofar ba, har ynxun qarfe hudun yamma. Yaje ya daga labulen windonta, tana kwance akan sallaya, da alamu tayi la'asar ne. Yace khadija, ki tashi ki bude qofa mana! Tana jinsa tayi shiru, daman so takeyi ya lallasheta, amma ko zata bude ba ynxu ba. Yace kinci wani abu ne? Bata tanka ba. Ya sauka qasa. Baisan me yarinyarnan keso dashi ba. Yau duk ta hana rayuwarsa sukuni, don koda ya fita, hankalinsa yana gida. Baisan mimi da gske takeyi ba saida yaga anyi sallar isha'i ya dawo bata fito ba. Da ya leqa ya ganta kwance rub da ciki akan gado. [27/09 9:54 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣0⃣Yace kadija ki dubi girman Allah ki bude, muyi magana. Nifa bansan dalilinki ba. Hava khadija ya kk so inyi da rayuwa ta. Ganin bata tanka shi ba, sai ya yanke shawarar kiran mahmud. Kafin isowar mahmud din, ismail yaci gaba da lallashinta, amma ko motsi batayi ba. Bataji takun shigowar mahmud ba, sai dai muryarsa taji yana cewa, don Allah khadija ki bude qofar nan, muyi magana. Don Allah zaki bude ba don ni ba. Kuma ina bayanki akan kowane dalili ne yasa kika rufe qofar. Sunfi minti biyar kafin ta taso ta bude, tana layi. Cikin hanzari ismail ya shiga ya kama hannunta. Dukda qaton hijabin sallar data saka ya hada, ya dauke ta zuwa falon qasa. Yunwa da damuwa sun hadu sun ramar da ita. Ya zaunar da ita akan kujera. Yace haba khadija kowane irin laifi nayi miki, ya dace ki yanke ma kanki irin wannan hukuncin? Cikin raunanniyar murya tace, ku barni don Allah. Mahmud yace, ka kawo mata ruwan zafi, tunda bataci komai ba, hanjinta zai warware. Ya nufi kicin ya hado mata ruwan zafi. Saida yayi ta lallashinta, sannan ta amsa tanasha. Kafin tayi rabin kofi, zufa ta rufe ta. Sannan taji qarfi a jikinta. Ta kama gefen hijabinta tana sharewa. Mahmud ya dubeta khadija bai dace kiyi irin wannan ba. Horon kanki da yunwa, wannan ba dabi'ar musulmi na gari bane. Ismail yace mema akayi mata ne? Taqi bani dama in nuna mata muhimmancinta. Kullum zancenta daya ne in saketa. Nace mata in nayi aure zanyi mata abinda takeso, kuma ynxu na soma neman aure. Sai tazo tanayin irin wannan? Sai kawai sukaji muryarta tace, duk wadda zaka aura, ka aura amma banda zainabu. Cikin sauri ya miqe, sbd me zakice haka? To ai wannan ba huruminki bane. Wadda zan aura sai kin za6a min, sai kace uwata? Ok, na gane nufinki, wato tunda baki sona kar wadda ta soni ko? To na gaji da wannan mulkin naki. Kuka ta soma, tare da fadin dole ka barta, kamar yadda dole tasa na haqura da khalil. Yace in ba haka ba fa? Tace za kayi da ka sani. Mahmud dake kallonsj, bai katsesu ba, sai yayi murmushi. "Da ace zaku fito da abinda ke zukatanku, wlh da kun huta. Sukayi shiru. Yace shikenan zainabu an bar maganarta. Zai canza wata. Haka yayi miki? Tace eh. 9⃣1⃣Ismail zaiyi wata magana mahmud ya daga masa hannu, tare da fadin an wuce wannan. Ka samu Malam, akwai wani sanata faruk da ya samu malam da maganar 'yarsa. Banji dai kan zancen ba, amma tabbas naji malam yace mutumin ya baka 'yarsa. Ismail yace, Hanan umar faruk kenan. Nasan yarinyar daliba ta ce a Abuja. Tanan kuma ta biyo? Mahmud yace bakamin zancenta ba. ismail yace banida ra'ayin auren yaran masu kudinnan, amma tana da hankali. To in anyi haka ya zanyi da zainabu? Banyi mata adalci ba. Duk zantukan da zukeyi, mimi mutuwar zaune tayi. Sai alokacin ta gane ba wai zainabu kawai take kishi ba. Duk matan duniya takeyin kishi dasu akan mijinta. Saidai ba tada ikon cewa komai akan wannan. Sun juya harshensu zuwa larabci, inda ismail ke qorafin ba'ayi ma zainabu adalci ba. Mahmud yace kafin kayi masu, sune suka fara yi maka. Sannan yarinyarnan tana matuqar sonka. Ina mamaki da kullum kuna tare, amma ni na gane hakan, kai ka kasa. Ismail yace nima inaso in fahimci hakan, sai tayi ta maganar saki, saki. Shiyasa naga kawai in haqura. Yace to ka gwada mana, zaka iya ganewa ta hanyar ta6a jikinta. Mahmud kaqi yarda cewa kana sonta. Alhalin shine dalilin daya hana ka daketa. In kaqi yarda dani ynxun, zaka yarda dani a gaba. Mahmud ya miqe, tare da cewa, bari inje gida nima, kar Rabi'a ta kullemin qofa. Ismail ya kalli mimi, ya tausasa murya, ina makullin motar in saukeshi a gida? Ta kalli kujerar da suke kai, tana qasan nan. Suka ciro suna dariya. Ismail yace babu irin leqen qasan kujerar nan da banyi ba, ashe yana ciki. Sai daya miqe mahmud yace, dama saboda ta nuna makullin nayi shiru, amma da mashin nazo. [27/09 9:55 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣2⃣Bayan ya rakashi ya tafi, shi kuma ya kulle gida, ya kulle qofa. Har lokacin mimi tana zaune anan, amma ta zurfafa a tunani. Wacece Hanan? Ya zauna kusa da ita, "khadija hakan yayi miki ko? Ta kalleshi firgigit, batasan ma yazo kusa da ita ba, ta sauke ajiyar zuciya, "wai itama Hanan din kana sonta? Yace ban sani ba, sai naje na ganta sosai. Ya kalli cikin idanunta data tsareshi dasu. Kishi ya gani qarara a ciki. Tace, itafa tana sknka? Yace gsky tana sona, domin ta nuna min alamu. Tace, dama kana iya gane alamun mace, tana sonka? Yace, sosai kuwa. A ranta tace, to baka qware a wannan fannin ba, tunda ka kasa gane irin wanda nakeyi maka. A fili sai tace, tanada irin kyawun da kake so kenan? Yace banyi mata kallon qurilla ba. Ya rufe wannan da cewa, yau kin tsorata ni. Don Allah karki sake yi min haka kinji? Kallonsa kawai Mimi keyi, amma ita tamaicinta yafi tunaninsa. Ta miqe, bari inje in kwanta. Yace duk yinin da kikayi a gado a kwance baki gaji ba? Tace, karka damu bana gajiya da varci kai ka sani. Ya bita da kallo, damuwarta tana matuqar damunsa. Ya miqe shima yabi bayanta. Tana fitowa ban daki ta ganshi zaune a bakin gadonta. "Lafiya?" ta jefo masa tambaya. Yace, babu inda yake miki ciwo? Ta girgiza kai, a'a yace naga kina cikin damuwa ne har ynxun. In dai maganar zainabu ne ki dauka ya zama tarihi. Tace kaje ka kwanta kawai, ya wuce nima. Ya miqe ya nufi fita, sai kuma idanunsa suka hango wayarta dake kan madubi. Yace waccan wayarfa? Tare suka isa gurin, ya rigata dauka. Cikin sa'a ta amshe, tare da cewa, wayata ce bani. Yace shine baki ta6a kirana ba? Tace, ni bana kira da ita, sai dai inajin rediyo. Yace shikena saida safe. 9⃣3⃣Ya jima yana kai-kawo a dakinsa, zai tattara alamomin so da mimi take nuna masa, to me zai hana ta fada masa? Kuma meya kawo ta dinga batun saki? Wata zuciyar tace kaima ya kamata ka tantance kanka, shin kana sonta ne? Ko tausayinta kk ji? Ko ko sbaquwa ce? Can qasan zjciyarsa sai yaji an amsa da cewa duka ka hada. A fili yace, khadija! Babu batun saki. Ko da baki sona, balle zan gwada ki in gani. Washegari da safe, tana kicin tana hada masu abin karyawa, ya shigo cikin rashin walwala, ta kalleshi, "barka da safiya? Yace barkanmu. Ya kusanto ta, "bar ynxun baki huce ba Dija? Ko itama Hanan din baki sonta ne? Ta kalleshi, sannan ta ta6a baki. "in kai kana sonta, me ya shafi khadija? Yace Allah in bata miki ba, sai in fasa. Ta zaro ido, ni asuwa dan wake a hotel? Yace da gske nakeyi, amma in zaki yarda da wani sharadi guda daya. Tayi 'yar dariya, "inji sharadin. Yace zan turo miki a message. Sai ki bani amsa. Tace, sbikenan ina jira. Ta dauki tiren da abicin karin su, muje mu karya. Ya lura da yadda ta saki ranta daga yin wannan 'yar maganar. Suna karyawa, kowa da tunaninsa. Bayan sun gama ya miqe bari in fita. Tace Allah ya tsare. In ka shigo anjima zanje na wanke gashi na. Yace ki bari na kaiki da dare. Da mimi taji alamun shigar saqo a wayarta, sai ta duba, sai taga MTN ne. Kusan biyar na yamma ya dawo. Tayi kwalliya cikin riga da siket na atamfa. Ta yi masa sannu da zuwa. Ledojin daya shigo dasu ta amsa ta nufi kicin. Ya biyo ta a baya, kin jini shiru ban dawo ba? Tace nasanka da uzuri ai. Daidai lokacin ta bude ledar, kaji ne guda hudu, sai dayar kuma danyen kifi. Ta soma zubawa a freezer, tana cewa farfesun kifi zamu sha anjima kenan? Yace naje sai miki kifin, sai ga wani bawan Allah. Sai kawai ya biya, Kuma yasa asa min kaji. Shiyasa kk ga bana son yin siyayya a unguwar da aka sanni. Sai kawai wani yace zai biya. Tace, arziki ne hakan ma. [28/09 3:34 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣4⃣Yace bari inje inyi wanka, zamu fita da ismail. Gabanta ya fadi. Ina kuma zaku je malam? Ya dubeta, gidansu Hanan. Ta rufe freezer, sannan ta biyoshi, to ba ka fadi sharadinka ba. Ko dama kana yi min wasa ne? Yace oh na manta. Ina zuwa. Ya shiga dakinsa, bakin gado ya zauna. Ya rubuta cewa, "in kin yarda in sumbaci bakinki sau daya kullum, to zan haqura da Hanan. Idanu ta zaro, tana qara maimaita abin da ta karanta. Sai taji tanajin kunyar bashi amsa, amma tunda ya ta6a bata amsa da cewa shiru alamu ne, to tayi shiru. Baiga amsa ba. Don haka yayi shirinsa na fita. Ba wani gidansu Hanan zasu ba, don dai ya gwada tane. Rashin ganin amsarta, sai ya zata ko batayi na'am ba, don haka, sai ya shareta. Ita kuwa tanajin fitarsa, amma kunya ta hanata fitowa. Har washegari ba suyi batun ba, duk da sunci abincin dare tare, daren ranar qananan kaya yasa, abinda bata ta6a ganinsa da su ba. Ta kasa daina kallonsa don burgeta da yayi. Sam baiyi niyyar fita ba, kuma dama ya siyo qananan kaya ne don ya burgeta. Amma sai yayi nufin gwada ta. Ya dauki makullin mota zai fita, da sauri tace, ina zaka? Yace, khadija ya kamata ki daina tambayata in zan fita kamar wannan lokacin tunda kinsan komai. Ya kusa kai bakin qofa ta rasa me zatayi, sai kawai ta riqe ciki, "wash Allah na cikin! Ya waiwayo da sauri, yasan cewa qarya tayi, amma sai ya biye mata. Ya riqeta, ya kwantar da ita a cinyarsa, yaja rigarta sama kadan, ya soma yi mata addu'a yana shafa mata a cikin. Lamo tayi cike da burin dama su kwana a haka. Can yace, kinji sauqi? Tace eh, amma kar ka fita. Yace shikenan na bari sai gobe. Tuni Hajiya taba Alhaji shawara akan su miqa ma minista jikansa, sbd dalilinta data fada masa cewa, mutuncinka zai zube a idon jama'a, in kayi la'akari da cewa Abbas shine ubansa. Gashi 'yan jarida sunata bin shari'ar, ana ta yada ku a media. Yace shikenan. Da kansa yaje Abuja, ya kira Abbas yace ya zo ya dauki dansa. Sai dai sati biyu da daukar yaron ya farka da ciwan kunne. Sun kaishi Asibiti sun dubashi, sun basu gado. Kafin yamma ashe ciwon ajali ne, sai kuwa yace ga garinku nan. Hankalin ko wane 6angare ya tasbi. Na'ima kuwa kamar zatayi hauka. Amma dole suka dangana. Allah ya raba musu gardama. Abbas ya tura ma Na'ima saqon sakinta. Bayan watanni kuma sai ta nemi jami'a anan Abuja ta samu ta shiga, amma duk ta rame. Yanxun burinta taga mimi ta nemi gafara. Momy Nafisa kuwa tafi Na'ima da na sani. Hasana da Husaina sun sama mazaje, suna shekararsu ta biyu a jami'ar 'yar adua. Usaina, Abokin yaya mukhtar, kaduna yake. Ita kuma Hasana, Lecturer ne na makarantarsu, amma dan Gusau ne. An basu, amma sai sun qare karatu sannan za'ayi bikin. Shi yasa suka matsawa Hajiya sauda kan don Allah suna son abarsu suje gurin Sis mimi tunda an fada musu unguwar da take. Sun san Gidan ma. Hajiya sauda tace, susa ransu a inuwa daddyn sh ma yace, in ya dawo daga ganin likita a England zamuje gidan gaba dayanmu. Suka dauki murna. Burinsu dai ynxun daddy ya dawo. 9⃣5⃣Mimi kuwa tunda malam ya fita da safe take tunanin wane irin lambon da zatayi in dare yayi don kar ismail ya fita zuwa gidansu Hanan. Wanka tayi, taci kwalliya sosai, da riga da wando masu dame jiki. Ya shigo bayan la'asar. Tana kallonsa yayi ta satar kallonta, lokacin da yakecin abinci. Bayan ya dawo sallar isha'i, yayi kwalliya da qananan kaya, jeans ne baqi sai farar T-shirt mai gajeran hannu. Gaban rigar an rubuta, da harshen turanci cewa ina Alfahari kasancewa ta musulmi. Lokacin itama ta canza kayanta zuwa doguwar riga irin mai rawa dinnan ta kama gashin kanta a tsakiya. Da makullinsa a hannu ya fito, ta dubeshi, "sai ina kuma yau? Jiya ban samu zuwa gurin hanan ba, kuma na fada mata, kinga ai ya dace yau inje ko? Tayi shiru tana kallonshi. Yace sai na dawo, har ya fita daga falon, sai ta bishi, "Malam! Ya tsaya. Sannan ya waiwayo, menene kuma? Tace kalli garinnan hadari ne, kasan kuma ana fara ruwa Nefa zasu dauke wu, kuma inajin tsoro. Ya kalli sararin samaniya, tabbas hadari ne. Yace, zan dawo kafin ruwa ya sakko, wadannan qananan kayan na siyosu ne don ita. Biyu ne kacal, jiya nasa daya, yau ma gashi nasa dayan. In na bari sai gobe me zan sa? Kuma in banje ba, na zama qaramin mutum. Jiya nace, ganinan banzo ba, yauma haka? Ko zamu tare? Shiru tayi masa. Har ya kai gurin motar, guguwar hadarin ta taso. Da sassarfa ta nufeshi, "kazo ka koyamin karatu mana, wai ba ka bani sharadi ba, kuma na Amince? Ya lumshe ido don dadi. Ya juyo, "amma baki fadamin ba, kuma baki turamin message ba. Tace, to ba kace min shiru alamun eh bane? Ya kai hannu ya kamo tafin hannunta, ni kuma sai nayi zaton baki harda bane. Ya fizgo ta da qarfi ta fado qirjinsa, a kunne ya rada mata, tunda kin amince, bari in fara ynxu. Dumin sautin muryarsa a kunnenta, yasa tsigar jikinta tashi. Tafin hannunsa guda biyu yasa, ya lalubo fuskarta. Ya sa bakinsa ya sumbaci le6unanta. Ta zata shi kenan, sai kawai taga ya saka harshensa ya bude mata le6e. Wata kalar sumba yake mata. Kafin minti biyu, ta rasa duk wani kuzarinta. Jin cewa zata zube ne, sai ya jingina ta jikin motar. Saukar ruwan saman bai sashi barinta ba, sai da tace, Ma..lam ru..wa! Cak ya dauketa zuwa cikin falonsu, duk sun jiqe. 9⃣6⃣Kan kujera ya shinfide ta. Sannan yaje ya rufe falon. Har lokacin tananan lamo babu kuzari. Ya dubeta, muryarsa a dushe, "tashi muje ki kwanta. Sai kuma na gobe ko? Ya lura ba zata iya hanzari ba. Don haka ya riqe mata hannu, har bakin qofa ya kaita yace, saida safe. "Lamo tayi akan gado tare da maqale filo, idanunta rufe tana tuna abinda ya faru. Ta kasa tashi ta cire rigarta data soma jiqewa. Shi kansa Malam din juyi kurum yakeyi akan gado. Qarshe dai ya gano mafitarsa daya ce, ya watsa ruwa. Yafi minti biyar ruwan sanyi yana sauka daga tsakiyar kansa zuwa tafin kafarsa. Tsigar jikinsa data tashi ce yasa yasan cewa da akwai matsala. Ya fito kafin yayi wani yunquri har zazza6i ya rufeshi. Singileti da gajeran wando ya saka, sannan ya qudundune da zanin gado. Haka ya kwana. Lura da Mimi tayi yau Malam bai buga mata qofa ba shine yasa data idar da sallah ta nufi dakinsa. Tana turawa ta sameshi yana kakkarwa. Cikin sauri tace, malam lfy? Ta zauna a bakin gadon. Tanason takai hannu ta ta6a wuyansa kuma ta kasa. "In kawo maka magani? Bai iya amsawa ba. Da sauri ta sauka ta dauko panadol da ruwa. Da qyar ya tashi zaune, ya amsa ya sha, sannan yace, "rufamin bargo." ta janyo bargo ta rufa masa, sannan ta zabga tagumi tana yi masa sannu. Kusan minti shabiyar sannan ya ture bargon, zufa ta soma zubo masa. Tace mura ce ko? In dafo maka ruwan zafi? Tea yace eh, bari inyi sallah. Ya shiga bandaki ita kuma ta sauka kicin. Kan sallaya ta sameshi, ta zauna itama ta aje tiren a gabansa, sannan ta tambayeshi, tun yaushe ne bashida lfy? Ya kalli cikin idonta, kece kika zama silar ciwo na. Ta zaro ido, cikin shagwa6a tace, da nayi me? Ya kusanto kunnenta sosai yayi mata rada. Ni dai banji me yace ba, naga dai ta sunne kai a cinya, tare da fadin "kai Malam!" shi kuma yasa dariya. Murmushi nayi don salon soyayyarsu yayi matuqar burgeni. Ranar haka ya yini bai fita ba, wai yana jinya. Ko sallah shine yayi ta musu jam'i. Yayin da mimi tayi ta JI dashi. [29/09 7:22 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 9⃣7⃣Bayan sallar isha'i ne ta leqo don yi masa sai da safe, "yau baki amshi karatun ba" Tace wane karatu? Yace, kin manta ne? Jiya fa kk ce in dinga koya miki karatu. Tace ai jiya ne kawai nace. Yace, naga alamun kin manta da karatun da nike nufi. Zokiji, ta zauna a gabansa yana kan sallaya. Jallabiya ce, a jikinsa mai ruwan qasa, kuma mai gajeran hannu. Ta lura yayi wanka ne bayan fitarta. Ya matso da bakinsa kunnenta, abinda ta zata shine ya fada mata. Ta zata ya manta, domin tana sane ita, kuma tana ra'ayi. Don haka zama ta gyara. Ya tallafe fuskarta suka kalli juna a cikin ido. A hankali yake magana. "INA SONKI KHADIJA..." Wani dadi taji ya rufeta. Har ma ta lumshe ido, lokacin ne ya saukar da la66ansa akan nata. Sai da ta koma tamkar ba tada rai sannan ya barta, don in yace, zai wuce gona da iri ma ya lura ba zata hana ba. Amma yanason koya mata komai daki-daki. Don sai ya raina wayewar da take iqirarin tayi. Domin ya lura batasan komai ba a wannan karatun. Rana ta uku ne ta soma biya karatun daya koya mata. Don haka a dare na hudu, sai yace, suyi wata sallah raka'a biyu. Bayan sun idar ne, ya dubeta, "kin san sallar nan da mukayi ta mecece?" ta girgiza kai, yace ta ma'aurata ce. Yau karatunmu zai canza salo. Kije kisa turare a duk ga6o6in jikinki kizo. Sam bata iya yi masa gardama ynxun, ko menene dalili? Oho! Tabbas yau sabon darasi ne, sai da karatun yayi nisa, sannan ya rada mata a kunne, "in barki haka ko? Tace, da wuya? Yace ba zan bari kisha wuya ba, sbd naga ke budurwa ce har ynxu. Idanuna ba zasu iya kallonsu ba. Don haka na tura qofa a hankali na fita don barin ma'aurata da sirrinsu. Saidai daga bakin qofa nake jiyo ismail yana karanta addu'ar da mazaje na qwarai sukeyi lokacin kusantar iyalinsu. A fili nace, "an kashe Boss kenan." ban koma dakin ba saida na kusan awa biyu. Lokacin dana leqa ban gansu ba . A raina nace, suna bandaki. Ina nan la6e suka fito. Ya kwantar da ita, shi kuma ya shimfida sallaya. Nace su mimi Amaren asali, kin kai masa mutunci. Shi kuwa sallar godia ce ga Allah yayi. Da asubahi mimi batayi ragwanta ba, tashi tayi ta nufi dakinta don yin sallah. Bayan ta idar, ta kwanta a gadonta, tana tuna abinda ya faru jiya. Gsky Malam ya wuce da tunaninta. Mamakin sa kawai takeyi, dama zata iya tambayarsa, da tace, ina ya koyi salon sa mace ta manta da duniyar da take? Sai dai kashh, tanajin kunyarsa. Barci yayi gaba da ita. 9⃣8⃣Ismail daga masallaci dakinta ya nufa ya kwanta bayanta ya rufesu. Barci sukeyi tamkar wasu taurari. Naso in musu hoto. Sai tara saura ya tashi. Shine ya hada musu abin kari. Lokacin daya dawo saman tana wanka. Ya tsaya jikin bayin, "inzo in taya ki? Tace na gama. Ta fito ta kasa kallonsa. Yana zaune ta gama shiri, harda taya ta gyara gashin kanta. Suka nufi qasa don yin karin kumallo. Cikin sati dai ismail baya nisa, launukan karatun da yake koya ma amaryar tashi kam babu dama. Itama batason yayi nisa, shiyasa ma ta yanke a ranta in zai koma Abuja ba zai barta ba. Haka kuwa hutunsa yana qarewa, tace, Malami na zaka dani? Yace dama izininki zan nema. In kinji zuwa daya kenan. Da ma kema ki soma karatunki. Tace amma zan canza layi. Islamic zan karanta, don sai ynxu na fahimci Musulunci yazo da komai na wayewa. Sam ismail ya manta da wata zainabu, khadija ce a gabansa, wadda yake kira my Dija. Kafin wani lokaci, mimi tayi kyau, ta goge. Da kanta tace, ismail ashe na jima ina cutarmu. Kuma ka san na dade ina sonka? Yace, na gano haka tun ranar dana saci wayarki na bincika sai naga ashe kece matar dake ta damuna a wtsapp. Tayi dariya, shine baka fadamin ba? Yace gashi ynxun na fada. Yaya Amina kuwa tunda taga Mimi, tasan an kashe boss, domin ta ciko masha Allahu. Sam Na'ima basu ta6a haduwa da mimi ba, ko don ba department daya suke ba, oho. Lokacin da Alhaji ya dawo daga ingila, sai ya samu labarin Mimi suna Abuja kuma tana karatu. Yaji dadin haka, kuma ya jinjina wa malam ismail. Shima ismail ynxun abu daya ya rage masa, shine ya sada Mimi da iyayenta. Amma ya bari sai sunje katsina. Cikin haka, Mimi ta soma laulayi. Ta ga gata ganin idonta. Har da kanta ta darsa a ranta cewa data bar ismail, da ta tafka asarar da ba zata iya maida ta ba. Kullum tayi sallah, sai ta godewa Allah, ta kuma godewa mahaifinta daya za6a mata ismail, ta samu CANJIN RAYUWA. 9⃣9⃣Cikinta wata bakwai sukazo katsina, domin za'a bude makarantarsa, kuma zaya kai Mimi gidansu. Bayan an gama kai kawon bude makaranta, da sati daya, tuni ma an soma karantarwa. Ya danqa komai gurin wani bawan Allah dake nan unguwarsu malam Aminu. Shine ma ya kawo shi, yace tunda Ismail baya zama. Sai ismail ya amince, don yasan malam ba zai kawo musu bara gurbi ba. Kuma ya zuba qwararrun malamai a makarantar. Safiyar juma'a, Mimi tana kwance kan cinyar ismail, yace muje in taimaka miki kiyi wanka , zamu fita. Tace zuwa ina malamina? Yace inda muka kwana biyu bamuje ba. Kinsan falalar zumunci. Gashi ke nake jira ki haihu, zamu tafi Madina don neman digiri dina na biyu. Bayan ta fito tana zaune, ya shafa mata mai, sannan yace, wane kaya zamu sa? Tace ka san dai yau juma'a, kuma kamar yadda muka tsara ma kanmu rana ce ta saka kayanmu na al'ada. Dubamin shadda ko atamfa. Sabbin riga da zani ya fito mata dasu na super mai kalar popple, sai ratsin baqi, har da sarqa da dan kunne masu kyau yasa mata. Shima ya shirya tsaf, cikin shadda sabuwa. Tasha hijabi da niqabi, suka shiga sabuwar motar da yayi kakara, ya canza. Saida sukayi tsarabar kayan sha, dana zaqi, sannan ya tuqa su zuwa unguwar. Sam Mimi bata fahimci inda suka dosa ba, sakamakon an samu canje-canjen gine-gine. Wani gurin ma babu gini da. Ko gidansu, saida suka shiga ta ganeshi, sakamakon an canza gaban. Ta kalli ismail, "yaya zaka yi min haka? Gsky mu juya, tunda ba wanda ya ganmu. Yace ni ba wannan ya dameni ba. Baki lura da yawan motocin da ke harabar gidannan ba? Sannan ga mutane can ansa rumfa. Da alamun anayin wani abu agidannan. Kai tsaye tace, Allah dai yasa ba daddynh bane ya rasu. Sai kuma ta bude qofar da sauri, ta fito. Shima ya fito, ya riqeta. Yi sannu My Dija. Babu abinda ya faru, sai alheri. Alhajin ne suka fito daga falonsa tare da qaninsa kawu shafi'u da kuma su Alh kabiru, da Alh isah. [29/09 8:26 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣0⃣Ismail yace, to ga Alhajin nan ma. Da sauri ta nufesu tana fadin daddynah! Cak ya tsaya domin ko cikin mjrya dubu zai fidda ta Miminsa, ko da zai shekara dubu bai ganta ba. Cikin sauri yaje ya daga niqaabinta. Kamar yadda ya zata Miminsa ce. Yace, uwata. Idanunta suka kawo hawaye, na'am daddy. Sai ya rungume ta, idanunsa suna masu kawo hawayen farin ciki. Ya kalli Alhaji kabiru. "yanxun fa mukeyin maganarta. Ance min kunzo gari. Ina jira a gama hayaniyar biki, muje gidan. Tace daddy wa ke aure? Yace 'yan biyu, sai mukhtar. Tace nazo a sa'a. Ta kalli mijinta wanda ke kallonsu cikin tausayi, tace Malam baka gaida su daddy ba. Ya qaraso tare da cewa, na jira ne ku numfasa. Nan suka gaisa suka nufi ciki. Shi dai Alhaji nan ya juya shima yabar abokansa da qaninsa. Falonsa ya yace ismail ya shiga. Ita kuma ta rufe niqabinta. Alhajin ya tasa ta suka nufi ciki. Hajiya sauda tana gaisawa da wasu baqi da suka shigo, Alhajin ga shigo yana kwada mata kira, tace Alhajina ho! Yau dai gidanmu da jama'a... Ya katseta, baquwa kikayi. Ta kalli Mimi fuska rufe, tace to ta shigo daga ina? Mimi taje ta rungume mahaiyarta. Sannan ta daga niqabi. Da sauri tace, Mimi ce! Nan dai akayi ta murnar ganin Mimi. Amare suna gidan mai musu gyaran jiki. Da yake sai washegari Asabar ne za'a daura auren. Hajiya da kanta ta kirasu ta fada musu, sai gasu. Murna tamkar zu cinye ta. An kawo mata wannan da wancan duk an jibge mata, sai dai hankalinta yana can gurin mijinta. Hajiya sauda tasa ta gaba, tana cewa, in bakison wannan me zakici? Saboda kowa yaga tsohon cikinta. Ta kalli Hasana, "wai ina Malam ne, ko suna gare da daddy? Hajiya sauda tayi murmushi, yana tare dasu daddynku, harda sy yayanku. Sannan Mimi ta soma tsakurar abincin don batajin yunwa, kuma ta saba ci da Mijinta. 1⃣0⃣1⃣Su Hajiya Binta suka iso da yaranta. Ita ma rungume Mimi tayi don murna. Kowa sai mamakin ganinta yakeyi. 'yan uwan hajiya sauda da dama basu san Mimi ba , sunanta sukeji, yau sai gata gasu. Hatta kakarta saida aka nuna mata. Yau dai ta gane 'yan uwa dadi garesu. Ashe ita 'yar dangi ce, gaba da baya haka? Daddy ma sai kiranta yakeyi yana tambayarta ana bata duk abinda takeso ko? Dariya takeyi, sannan tace, ana bani daddy. Suna dakin daddy ita da Amaren, sbd ko ina mutane sun cika. Ta ce ku tashi muje gurin gyaran jikin, nima za ayi min. Ta ciro waya, "bari in fadama Malam zamu fita.Ta kira wayarsa, dai dai lokacin da ya daga Hajiya sauda ta shigo, tace, musu su koma gurin gyaran jikin. Sai taji mimi tace, Malamina, na zata zanga Miss call dinka? Ka shareni ko? Cikin sigar shagwa6a ta fada. Yace kinsan dai ko a mafarki My Dija ba zan shareki ba. Na barki ne ku walwala da 'gan uwanki. Tace kana inane ynxun? Yace inason zan tafi masallaci, amma sai na koma gida na dauki takardar budubar dana rubuta. In zan dawo zan biya in dauko yaya Amina. Tace da ka kyauta min. Ta zo dasu Ummi, kaji My Malam? Yace zan fada mata. Kina son wani abu ne daga gida? Tace, illa mai da hoda na, sai turare. Yace shikenan. Tace zamu fita da Amare. Yace zuwa ina? Tace inda za'a yi musu kwalliya. Take yaji bari ya gwada ta. Sai yace, a'a ki zauna ki huta abinki. Bata zata ba. Don haka ta danyi dim, sannan tace, shikenan Malam, sai kunzo din. Sosai ta burgeshi, ya san ko ina zatayi masa biyayya. Sai yace, Dijana kuje kawai, sai kun dawo. Tace Allah Malam in baka so, ba zanje ba. Yace, na tsokane ki ne kawai. Basu Hasana ba, hatta mahaifiyarta saida Mimi ta burgeta. Lallai Malam ismail ya ciri tuta. Hajiya sauda ta dauko zanin anko, da wasu sufofi guda uku, da lesuka masu tsada, ta kira telan su, ta bashi tare da cewa gobe takeson su, amma anko yau za'a dinka. Tela yace, an gama! Don yasan Hajiya akwai sauke kudin dinki. Haka bayan sun dawo gyaran jikin ne Hajiya sauda ta zube Hijabai kan gado sabbi sun kai kala goma, tace, Mimi ta za6a in ma tana sonsu duka ta kwashe, ga takalma da jakarsu. Mimi tace, Hajiya kin siyane dama kin ajiye? Tace a'a saida sj mukeyi. Su Hasana suke kaiwa makaranta. Daga baya kuma sai muka kama shago. Odarsu ma mukeyi yanxun daga dubai da china. Mimi ta za6a, ta kuma za6arma yaya Amina, itama harda jaka da takalmi. 1⃣0⃣2⃣Qarfe uku akayi kamun Amare, lokacin ne kuma za'a saka anko. Mimi tayi kyau matuqa, duk da cikinta yasa tayi qiba. Kwalliyarta tasa ta saje da amare, duk da itama har ynxun da 6ur6ushin amarci, tunda bata dade da fara amarcin ba. Jeren kumbo ne akayi. Wannan karon ne na farko da Mimi taga irin bikin nan, kuma yayi matuqar burgeta. Yaya Amina sun iso da yaranta sunga tarba gurin Hajiya da ita kanta Hajiyar. Sunci, sunsha, sannan aka kwashe su a mota zuwa gidansu yaya Abba inda acan ake kamu din. Sai dare sannan Ismail ya kira Mimi yace, su yaya Amina su fito ya maida su gida. Tace abar Ummi, tunda zasu dawo gobe, sbd gobe ne daurin aure. Hajiya ta had musu kayan biki. Mimi ce ta raka su har gurin mijinta. Sun shiga mota, shi kuma ya fito, suka ke6e da Mimi. Yace, ke kam nasan sai an gama biki ko? Tace, sai yadda kace. In kuma kafison na koma, sai mu tafi, ka kawoni da safe. Ya kai hannu ya kama nata, ki zauna kuyi bikinku. Daddy ma dazu yace min, wai inyi haquri sai an gama biki, in barki. Tace ai yadda kasan yana tsoron kar in gudu, ba ayin awa daga bai kira layina ba. Ismail yayi dariya, gurina ya amshi lambar. Ya murza hannunta, yau zanyi kewarku, da dana. Tace mu ma haka. Har ya kai mota zai shiga, ta ce Malam! Ya dawo, tayi qasa da murya saitin kunnensa, "don Allah kar kayi tunanin kowa sai nawa. Ya shafi kumatunta. Yace ai kinyi kane-kane a zuciyar nan. Baki bar gurin da zata tuna wata ba. Zan kiraki an jima, in bakiyi barci ba. Ta shafi kumatunsa, zan jira ka. Saida motarsa ta fice, sannan Mimi ta juya zata koma cikin gida. Ashe duk daddy yana kallonsu daga inda yake zaune. Sai ya fito ya kira Mimi, Uwata! Da sauri ta nufeshi tace, ina ka 6oye daddynh, tun dazu banganka ba, sai dai waya. Yace muna ta fama da jama'a Uwata. Naga mijinki ya tafi. Tace yayarsa ce da yaranta. Yace naji dadin ganin yadda kuke da mijinki, kina sonshi, kuma naji dadin ganin yadda kk samu canjin rayuwa. Tace daddy kullum ina saka cikin addu'a Allahvya saka maka da Aljannarsa, sbd kalar mijin daka za6amin. Yana sona sosai daddy. Kuma shine ya nuna min hanyar wuta data aljanna. Daddy ka yafemin laifukan dan yi mak. [29/09 2:42 pm] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣3⃣Yace, Mimi ba kiyi laifi ba, daidai kk yi da kk gudu. Kinga momynki a bikin nan? Mimi tace, Inason in tambaya, amma sai abin ya shigemin. Ya bata labarin komai. Yace, ynxun haka Na'ima tananan gida. Momyn ku suna bikin qaninta shiyasa bata zo ba, amma Na'ima kunyar fita takeyi. Ko makaranta sai dai tasa hijabi. Mimi tayi ta mamakin Abbas, tace ban zaci zaiyi haka ba daddy. Shima yace, nima ban zaci basuda tarbiyya ba, har na takura rayuwarki. Ai nine silan komai. Kije ki kwanta. Zamuyi magana, sai an watse biki. Gado daya suka kwanta da Hajiya sauda. Mimi tasha labarinsu Na'ima. Hajiya sauda tace, ai gara wahalar da kk sha, da ace ke kk auri Abbas. Daddynku fa har cewa yai gara da Allah yada kk bijire masa. Mimi tace, ni ko inacan ina dana sanin bijire masa. Kuma lokacin don dai Nomy Nafisa tace min duk abinda Za'ayi kar in yarda, wai daddy yace in naqi yarda zaya haqura. Sai daga baya na gane kamar da makirci. Nan dai Mimi taba Hajiya sauda labarin komai. Hajiya tace, saida Hajiya Binta tayi zancen nan, amma nace kar a zargeta, dama 'yarta take son takai gidan. To ai in baka da haqqin mutum, gashinan yadda suka kwashe. Sun raba dare, suna hira kafin sukayi varci. Washe gari daurin aure, ansha sha'ani. Tela ya kawo dinkunan Mimi, sai shiga takeyi tana fita. Yaya Amina sunzo harda Rabi'a. Mahmud ya kawota don shima yayi mota. Sun ga kula, kuma sun kwashi kayan walima. Shi dai Ismail sai kallon Mimi yake, sbd kyawun data qara. Ta jashi ciki, wai ya gaida su kakarta, da kuma dangin mamanta. Inna sa'ade tace wannan Malamin nan bane shaikh Ismail bin Abdurrahman? Mimi tace, shine. "Dama shine mai gidanki? Mimi cike da alfahari tace shine. Sukayi ta sa masa albarka. Suna fadin shirye-shiryensa da suke kallo, da kuma irin qaruwar da sukeyi. 1⃣0⃣4⃣Haka da suka ratso ta falon mata, sai gaida shi akeyi irin gaisjwar ban girma, wadda mazoya suke yiwa wanda suke so. Haka biki ya tashi, sbd Amare sunada nisa. Mimi taso zuwa kai Amare. Daddy yace, ki bari ki sauka lfy, sai kije ma kowa. Tace to shikenan, ba don ranta yaso ba. Ta haqura don dan zaman nan ta san dadin 'yan uwa. Washegari duk mutane 'yan biki suna ta tafiya, don haka Mimi sake kwana tayi. Hajiya Binta da zasu wuce tace ma Mimi, sai kin haihu kuma zamu zo. Har mota mimi ta rakasu. Yau dai Alhaji da Hajiya da kuma Mimi sun zauna sun sha labari, inda Mimi ta basu labarin bayan rabuwa, suma suka bata. Kuma taji mamakin yadda Alhaji yabi diddigin inda suke. Ashe shine ma ya ba ismail gidannan. Kuma sai yau Alhaji ya gano Nafisa ta hada komai, don mimi ta fada masa har yadda tasa ta ta turo masa text. Ransa ya 6aci, kuma yace, sai yaci mata mutunci. Hajiya sauda tace, a'a karka yi mata komai. Banqi ka fada mata ba, don tasan ka sani. Amma ai Allah ya gama nuna mata sakamakon maci amana. Mimi tace, hakane daddy. Take ta kira ismail, ta fada masa yazo, shima yasha labari. Kuma sai ranar yaji dalilin daddy na sharesu, kuma ya gamsu. Domin in har Mimi tana cikin gatanta ba zata juyu agareshi ba. Sun bar gidan goman dare. Bayan motar su shaqe da abubuwan biki. Suna kwance sunyi kewar juna tace, Malamina yaushe zamu koma Abuja? Yace sauran kwana uku, kin manta ko? Tace na manta sosai kuwa. Ai naji dadin zuwa gida lokacin bakinnan . Naga 'yan uwa, sun ganni. Ta rungumo shi, Allah barni da kai har abada. Yace, Amin tace, kayimin alqawarin cewa ba zakayi min kishiya ba. Yace, Dija banida ra'ayi, amma bansan qaddarata ba. Ina son kema kimin alqawari, in qara aure yana cikin qaddarata ba zaki juyamin baya ba. Ta qanqameshi, "nayi maka, amma zan shiga wani mawuyacin hali, sbd ina tsananin sonka. [30/09 6:43 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣5⃣Washegari sunyi girke-girke sbd ziyarar dasu daddy zasu kawo musu, da su yaya Abba da sauran qannenta. Yaya Amina da Rabi'a sune suka taya su. Gidan tamkar biki, haka ya cika. Daddy yaba Mimi kyaututtuka sannan kuma ya fada musu yaba sauran 'ya'yansa irinsu, sakamakon wa'azin da yaji a wani kaset daya kalla na Ismail, mai taken yin adalci ga iyali. Sannan yayi wa ismail kyautar qaton fili, yace ya gina irin makarantar da yakeso. Take ya yanke shawarar zai gina jami'a ta musulunci, duk da ya san ba abune mai sauqi ba, amma zaiyi hakan. Su Malam Aminu sun samu kyaututtuka. Shi kujerar makka, mahmud gida. Sunkai har dare a gidan, sannan suka tafi. Ranar da zasu koma Abuja, sunzo sallama daddy yaba su makullin wani gidansa dake Asokoro, yace su zauna har sai ranar da suka gaji suka tashi don kansu. Ranar wata talata, Mimi ta tashi da naquda, ismail bai fadama kowa ba, saida ta haihu. Kuma abin da ya burge malaman asibitin mai zaman kansa, yadda ismail ya shiga har cikin dakin haihuwar yana shafa kan matarsa tare da lallashi da addu'o'i har ta haifi santalelen yaron su mai kama da su. Hajiya sauda ya soma fadawa, sai daddy da kuma su yaya Amina. Duk da sun yanke cewa gida zata dawo, saida su Hajiya sauda sukaje Asibitin da take a Abuja. Shi kansa Alhajin saida yazo. Momy Nafisa tazo asibitin, sai kunyar Mimi takeji, sbd Alhaji yazo ya warwareta, kuma ya fada mata cewa taci darajar sauda, sbd itace tace, in barki da ishararki. Ranar ta kira sauda tana bata haquri. To yau kam ta yarda cewa, duk wanda yace, tukunyar wani ba zata tafasa ba, tashi ko dumi tabar yi. Yadda taga Mimi, Mijinta yana ji da ita, ga daukaka, ga kuma soyayyar da take yiwa mahaifinta ta dawo sabuwa. A katsina gidan suna ya cika. Dan yaci suna Aminullah, sunan Malam Aminu, Ismail yasa, domin ya nuna masa qauna. Hasana da Usaina sunzo. Abin sha'awa suke ta kula da 'yan suna. Gurin bada abin tsaraba in mutane zasu tafi, sun samu alheri. Malam Aminu kuwa yaji dadi sosai, wannan kara da ismail yayi masa. 'yan gidan su ma sunzo. Zo kaga idanu gurin fatu, sun ga abin duniya, abinci kuwa sunci sun diba a leda, duk da Mimi tasa anyi musu kyaututtuka na musamman matsayin dangin masoyin mijinta. 1⃣0⃣6⃣Kwanaki arba'in sukayi, duk sati Malam ke zuwa duba su. Abin da yaba Mimi mamaki ta kuma qara miqa masa wuya, yadda shine ya kawo mata abubuwan da zata yi amfani dasu don gyaran jikinta, sannan ya fada mata abubuwan da zata yawaita ci. Yaso sunayin arba'in su dawo, amma tace yayi haquri sudan zaga suga 'yan uwa. Da gusau suka soma (har naji kamar in bisu inje gurin tawa Baida'u Gada) sannan kaduna, duk kwana dai-dai sukayi, sannan suka dawo, sukaje Dangin Hajiya sauda. Sun zaga acan kwanansu biyu. Duk da ba masu kudi bane , taga soyayya irin na dangin uwa. Sannan sukaje masari suka kwana daya, daga nan sai Malumfashi gurin Hajiya Binta. Bayan sun dawo ne kuma suka soma shirin komawa gida Abuja. Har da Hajiya sauda da yaya Amina a 'yan rakiya. Qannenta kuwa su Hasina dasu husna, harda kuka don sun saba da Al'amin. Shi kansa Alhaji yayi keawar dan jikan nasa. Ranar 'yan rakiya suka dawo suka barsu da kayan arzikin da suka rakasu da shi. Qarfe taran dare, Mimi cikin kayan varci, tana ta lila Al'amin a gadonsa ya soma varci, sai taji qamshin turaren masoyinta, kafin ta waigo sai taji hannuwansa a jafadarta. Cikin murmushi ta juyo, "Malamina ka shigo tun yaushe? Yace baki ganni cikin shirin varci ba? Tun lokacin da kk wanka, na san ni ake yiwa wankan. Don haka nace, kema bari inje in miki. Suka sa dariya. Ya tsugunna ya sumbaci goshin dan nasu, sannan yayi masa addu'a. "Muje ki amshi darasin da kk tara ma kanki." Cikin shagwa6a tace, Malam mu bar karatunnan sai gobe. Ya dora yatsansa akan le6unanta, tare da fadin "shhhhh, wannan ba halinki bane. Na shaide ki baki cikin mata masu juya baya. Ya kai bakinsa kunnenta yayi mata rada, suka tallafe juna zuwa gadon aurensu. Na juya zugum-zugum don in anyi radan nan inajin haushi banjin me suke fadi. [01/10 8:04 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣7⃣Watan Al'amin uku, yaro mai cike da kuzari da lfy. Sukazo katsina suka sallami dangi suka wuce Madina don yin digiri dinsa na biyu. Yaso Mahmud ya taho, amma shi yace sai nan gaba. Don haka komai na game da makarantarsa ya barma Mahmud. Watansu uku da zuwa, Azumi gazo, don haka suka dawo gida sukayi Azumi, sbd tafsir din da ismail keyi. Bayan sallah suka koma. Lokacin aikin Hajji sukayi shiri da dansu don yin aikin Hajji. Mimi ta zazzo umura, amma bata ta6a aikin Hajji ba. Koda yake umura dinma, lokacin zuwa kawai take, amma batasan me zatayi ba sai siyayya. Rayuwarsu irin ta larabawa suke kwaikwayo gurin soyayya. Don haka ko yaushe suna nane da juna. A makka ne sun fito harami zasu je masaukinsu, Ismail dauke da Al'amin a kafada sanye cikin jallabiyya fara sol, Mimi cikin baqar doguwar riga ta rufe fuskarta da niqabi tana rataye da jakar tarkacen Al'amin, tana kuma maqale da hannun mijinta suna tafe kamar taurari. Sai kawai ta hango Na'ima. Tace, Malam ga Na'ima suka tsaya a gabanta. Zata kauce, Mimi ta daga niqabinta, tace Na'ima. Wata kunya ce ta rufeta, sai kuma ta rungume Mimi. Mimi tace keda wa kuka zo? Tace nida Momy. Masaukinmu zan koma wancan Hotel din. Mimi tace, muma nan muka sauka. Ta kalli Malam ta gaida shi, sannan suka wuce zuwa masaukin. Momy Nafisa taji kunyar ganinsu, nan suka gaisa ta dauki Al'amin tana fadin yaro yayi girma. Na'ima bata tsaya 6ata lokaci ba ta shiga neman gafarar Mimi cikin kuka. Itama Momy sai tayi narai-narai tana roqon gafara. Mimi ta rungume Na'ima, tace babu komai, komai ya wuce, nima ku ya feni. Ismail yayi musu nasiha tare da nuna musu illar hakan. Sukayi godiya. Anan ne ma Na'ima tace, ai Malam ina ganinka a makarantarmu, 6oyewa nakeyi. Bayan ya dauki Al'amin ne yace bari suyi gaba kafin ta shigo. Na'ima tace, sis Mimi sai kin qara riqe wuta, sbd 'yan Makarantarmu suna bala'in son Mijinki, don dai dai ne yarinyar da bata labarinsa. Mimi tace, sunyi au gama. Momy tace ke Na'ima karki tada mata hankali, gashi kun saje da larabawa. Mimi tace hakane momy, gsky ta fada, kiran wayarshi da mata keyi ma kadai in nace zan damu, sai jini na ya hau. Sauqi na basa gabansa. Ta jima sannan ta koma dakinsu. 1⃣0⃣8⃣Duk lokacin da suka samu wani dan hutu ko na sati daya ne sai sunje Nigeria. Hakanan daddy yakan nuqo gari yazo ya gansu. Bayan sun shiga shekara ta biyu, lokacin Al'amin yana da wata takwas yana gudunsa ko ina, sunzo. Da zasu koma, Ismail yace, Dija ina ganin ya kamata mubar Al'amin gurin su Hajiya, don mu samo Rumaisarmu ko? Ta kalli dan nata dake varci tace Allah sarki Aminullah, har ya bani tausayi. Zanyi kewarsa. Yace ko yaya kk gani? Tace duk yadda kace babban Malami. Alhaji Bashir tamkar ya goya su Mimi don murna sun bar masa jikan daya shiga ransa. Saidai bai nuna ba don tsoron kar yayi masa irin na Uwarsa. Shekara kwana ce inda rayuwa, domin su Mimi sun dawo gida bayan Ismail ya samu shaidarsa mai kyau, ta samun digirinsa na biyu. Ya iso cike da burika, musamman gina jami'ar Musulunci a katsina. Sun gyara gidansu sosai. Da yake Mimi ma bata zauna ba, a Nadina taci gaba da neman ilimin addini, sai Makarantar nan tasu ta koma qarqashin kulawarta. Zumunci kuwa ita da Rabi'a, tamkar 'yan uwa. Ta sa Ismail ya gyarawa su yaya Amina gida. Ita kuma ta bata jari. Suna yin taimako sosai, duk na kusa da maqota sun shaida haka. Rashin samun cikinta yana damunta, da tace suje Asibiti yace a'a su sake jira, tunda wancan babu inda sukaje. Kwana biyu da yin haka ta soma mura. Yace shikenan gashinan Allah ya bamu. Tace ba ciki bane. Yace na Al'amin daga irin murannan ne. Haka kuwa da suka je asibiti sati shida. Wata Alhamis mimi ta gama hada masa kayan buda baki, sai ta nufi dakinta tace kaci zan dan watsa ruwa Malam, banason ina kusa da kai bana qamshi. Yace sai kin dawo dalibar Malam. Tana barin gurin message na shigowa, kamar yadda ya zata zainabu ce. Ya bude ya karanta. Tunda suka dawo, kullum sai samun saqonta tana fada masa halin da take ciki na sonshi. Kuma in zata mutu babu aure, to kuwa zata jirashi. Yayi shiru yana tunani. Shi gsky ynxu babu ko 6ur6ushin son Zainabu a ransa. Sai dai tausayinta. A fili yace bari dai mai ni din tazo muji ko zata lallasu. [01/10 8:05 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣0⃣9⃣Bai munafunceta ba ya nuna mata komai. Shiru tayi ta rasa me zata ce. Yace, me kk gani? Ta ban tausayi ne. Sai kurum Mimi ta miqe zata wuce, ya janyo ta jikinsa. "Wlh ba sonta nakeyi ba kinsan dai baki bina bashin rantsuwa. Tace shikenan duk wadda ta baka tausayi sai ka aureta har mu zama mu hudu? Yace shikenan batun ya wuce. Sun zanta da Mahmud akan batun zainabu, Mahmud yace, inda hali a duba yarinyarnan. Tazo gurina yafi sau talatin. Ismail yace to nidai kasan mijin tace ne, sbd banason damuwar matata, kamar yadda batason tawa. Mahmud yace nidai naga wata nan kusa dasu yaya Amina. Kuma dama inason fada maka ne, sai in yiwa su Malam magana suje su nemo min izini. Ai kaima Ismail kayi kuskure yaya zaka nemi shawarar mace, akan zakayi mata kishiya? Ai bari zakayi sai zance yayi nisa sannan ka fada mata. Shiyasa dana fada ma Rabi'a naga wadda nakeso, tayi fushinta ta gama. Ismail ya samu yaya Amina da batun, tace duk da batason ayiwa Mimi kishiya , tana tausayin zainabu. Wani dare ya yanke shawarar ziyartar Zainabu don bata shawarar ta nemi miji tayi aure. Sai dai ya kasa fada mata hakan lokacin da ta fito ta ganshi ta kuma saki kuka. Duk ta rame, tace Malam na sani ko yaushe Allah zai turomin kai. Domin a bakinka naji addu'ar daya kamata bawa yayi in yana neman buqata gurin Allah, litinin da Alhamis in nakai azumi, kafin nasha ruwa, ina fada ma Allah kaine nakeson Allah ya bani. Duk tsawon shekarunnan ban cirema raina ba. Ismail ya kasa magana, sai dai sun rabu da alqawarin zai dawo, don jikinsa ya mutu da kalaman zainabu. Shawarar mahmud itace abinyi. Ya koma gida ya kasa sukuni. Mimi kuma ta tsareshi don son jin dalili. Yace in kinji ma bashida amfani, don haushi zakiji. Ta nace, shi kuma ya fada mata komai. Ranar ce ta farko da suka raba daki tunda suka hada, saidai in daya baya gidan. Cijewa Ismail yayi baije lallashi ba don yasan ba zata saurareshi ba. Ita kam hakan ya sata zaton ko ismail ya daina yayinta. Kwana tayi kuka, sannan tunda duku-duku taja motarta ta nufi gidan Ubanta. Yaji fitarta daya duba sai yaga tabar Al'amin. Shine yayi masa shirin makaranta, ya kaishi. Daga can ya samu malam Aminu suka zanta akan batun zainabu, shima Malam ya amince da Ismail ya auri zainabu, sbd ubanta yazo gurinsa kusan sau biyar. Yace, suje aji sadaki, ya bada, a daura kawai ta tare. Daganan sai ya wuce gidansu gimbiyar sa. 1⃣1⃣0⃣Sun gaisa da Alhaji bayn sun shiga falon baqi. Alhaji yace, saiga mutuniyar fuska kumbure kuma har ynxun sai kuka taqi cewa komai. Ismail ya koro ma Alhaji komai. Alhaji yayi murmushi, "Ni dama nasan tatsuniyar gizo bata wuce ta qoqi. Mata sun tsani kishiya, kuma bayan da biyu ma akace mu fara, sannan uku ko hudu. Ita dama tana auren Malami zata ce ita daya zata zauna? Ismail yace nida banida ra'ayin sake aurema daddy, amma in yana cikin qaddara ta dole nayi. Yace karka damu, kaidai kayi qoqarin adalci, Mahaifiyarta tanada abin ce mata, kuma zata dawo anjima. Ko da Alhaji ya fadama Hajiya sauda maqasudin zuwan Mimi gida, a gaban Mimin Hajiya sauda tace haka ne? Mimi tace hakane. Ran Hajiya sauda ya 6aci, tace dama kina zaton mijinki ya zauna dake daya ne har abada? Ta dago ido ta kalli Hajiyar, "ya fa yi alqawarin ba zaimin kishiya ba, Hajiya sauda tace ga mahaifinki nan zaune, ni ma yayi min alqawarin ba zai min kishiya ba, amma yau kishiyoyi nawa gareni? Mimi tayi shiru. Hajiya ta sake cewa, inace harda ke kun hada baki aka auro miki Momynki Nafisa? Kin manta duk da wannan? To inaso ki sani, mata da yawa suna hana mazajensu aure, a qarshe sai mazajen suje suna bin matan banza. Sannan wasu suna hana mazan su aure a qarshe sai kuma su mutu ayi auren. Banda ma wannan qannai nawa gareki mata? Ce miki akayi ko wacce an bugo mata mijinta ne? In kin hana a auri qanwar wasu waccan ta hana a auri qanwarki, shikenan sai su tabbata babu aure? Inaso ki koma gidanki, ki nutsu ki ba mijinki qwarin gwiwa yayi muku adalci. Karki canza daga son da kk masa. Ki qara gurin kyautata masa. Ki riqe amanarsa, ki zama mai haquri da kuma ki hada da addu'a. In dai ni na haifeki, to karki kuma zuwa gidannan da sunan yaji. Ku kashe, ku rufe keda mijinki. Alhaji ya dubeta, "Mahaifiyarki ta gama fada miki komai. Ni dai zan qara miki da cewa kiyi haquri. Haka mimi ta koma gidanta cikin damuwa, sai dai zantukan mahaifiyarta sun isheta tunani. Ko da ya dawo lallashin ta yayi, tare da nuna mata cewa ba don bai sonta bane. Har zuwa ranar asabar din da aka daura auren, sama-sama suke, sai dai Mimi tace ya nemi gurin da zai saka matarsa, ba zata zauna tare da ita ba. Baiji komai ba, dama ya kama gida, unguwarsu Mahmud, can ya sata. Ranar farkonsu ya tausaya ma Zainabu sbd irin son da take masa. Ita kuwa Mimi kwana tayi kuka, ta san cewa ynxu sun zama su biyu masu shi. Daga masallanci, gidan ya wuto. Tana varci shima ya kwanta kusa da ita. Data farka ta ganshi, sai kawai ta fita ta koma kicin tana hada abin kari. Sai da ta gama soya dankali, da qwai da sauransu, sai taga ya dauki kwando ya jera, yace kiyi wani, wannan zan tafi dashi. Ta daga murya sbd me? Yace sbd Allah da kuma cewa kin isa. Ya debo dankali, muyi in tayaki. Banason ki zubar da kanki gurin zainabu, don a komai bata kaiki ba. Inason kiyi zama da ita na adalci, ki nuna mata girma. Kar kiyi wasa da muqaminki na Uwar gida. [01/10 8:09 am] Inna👬👫: Canjin rayuwa 1⃣1⃣1⃣Zantukansa ta hada dana Mahaifiyarta data sake kiranta a waya ta nana ta mata. Dole ta haqura, kuma ta yarda cewa, mijinta fa ba laifi yayi ba don ya qara aure. Sunna ya raya. Ba taji haushin kanta ba, sai ranar daya kawo mata zainabu, gaba daya sai taji ba taga abin kishi ba. Ita kuwa Zainabu sai taji tana shakkar Mimi. Ga wani qwarjini da Mimin tayi mata, har ita kanta Mimin ta lurabda haka. Don haka sai ita Mimin tace, kar fa kiji komai, nan gidan mijinki ne. Zainabu ta yarda Allah ne kawai ya bata Malam, domin mai kamar Mimi ba zai kalleta ba. Mimi ta sauka, wannan ma Namiji ne, sai yaci sunan Alhaji. An sha suna, sannan itama zainabu ta kama nata laulayin. Lokacin Ismail baya qasa. Sun tafi Africa ta kudu. Shine ya kira Mimi ya fada mata cewa Zainabu babu lafiya, don Allah ta dubata. Mimi ta tausaya mata halin da ta sameta. Ita ce takai ta Asibiti. Bayan gwaje-gwaje an gano ciki wata biyu. Mimi ta wuce da ita Gidanta kafin mijin ya dawo. Dakin su Al'amin ta sauketa. Da yake ynxu tanada masu aiki, yarinya da tsohuwa, sannan sunada Mai gadi. Mimi tsakani da Allah take kula da Zainabu, kwana biyar ya dawo, samun Zainabu danyayi gurin Mimi tana samun kula, sai ya sake daga darajar Mimi. Harma ya fada mata cewa, My Dija, na jima da yarda cewa ko dabba na daure zaki kula da ita, bare Mutum. Hakan ya qara mata qaimi gurin zama zama da kishiyarta lfy. Zainabu ta haihu ta samu 'ya mace. Ga mamakin Mimi sai Zainabu tace ya sama 'yar sunan Mimi wato Khadija. 'ya kuwa taga kaya gurin Mimi. 1⃣1⃣2⃣Mimi cikin motarta tare da yaranta, a Abuja sunje bikin Na'ima ne ta auri wani maqwafcinsu da matarsa ta rasu gurin haihuwar danta na biyu. Bayan biki ya watse da ranar da zata tafi tace, bata barin Abuja, saita nemo mina qawarta. Gidan iyayen mina taje neman labarin. Har gidanta qanin mina ya raka Mimi anan cikin Abuja. Sun rungume juna sunata murna, kafin suka 6arke da labari. Mina tasha mamakin jin cewa, sheikh Ismail Abdurrahman shine Malaminta da mahaifinta ya bata. Tace, ta san shi domin yana daya daga cikin malaman da take nutsuwa da wa'azin su. Sai mallon mimi takeyi tana Mamakin ta. Tace dubeki kamar matar shugaban qasa, wai matar Malami. Mimi tayi dariya, tace kinsan Allah duk wadda mijinta ba Malami bane, ina mai jajanta mata, domin ta rasa abubuwa da dama. Me zanyi da wani shugaban qasa da ba zai samu lokacina ba sai na mutan qasa? Barni da mijina mai kasheni da kalolin soyayyarsa. Mina tace, qwarai na yarda dake, domin wata lakcarsa da naji yana yiwa mata da maza, saida nace, Allah yasa haka yakewa iyalinsa. Mimi tana dariya, tace yana min. Suna cikin haka saiga wayarsa. Mina kallon mimi takeyi tanata zuba shagwa6a a waya. Wai gobe zata dawo, shi kuma yace idanunsa aun qosa su ganta. Ta bashi mina sun gaisa, suka yi bankwana tare da amsar lambar juna. Rayuwar su mimi abin koyi ce ga mutane na qwarai. Bayan shekara uku Ginin Ismail yayi nisa, na jami'a, lokacin Mimi tana goyon Abdurrahman sunan mahaifin ismail. Sannan sun tare a sabon gidan su dake nan layin, ita kuma Zainabu ya gyara mata inda suka tashi. Kwanciyar hankali da qaruwar arziki kullum suna cikinta. Yaran ta uku duk maza, Hajiya sauda tace, qila irin tawa zakiyi, sai na hudu ki samu mace. Ta dauko Ummi tana zama gurinta, kuma ta saka ta makaranta mai kyau. Ita ma kuma ta koma makaranta don ta samu digiri dinta ko ba za tayi aiki ba, ta aje kwalinta don wata rana. Mimi ta fito wanka tana zaune a gaban madubi tana ta shafe-shafen jiki da turarruka masu qamshi. Yau Malaminta ya dawo daga tafiyar da sukayi ta sati biyu qasashe biyar, suka zagaya shi da manyan Malamai don yin da'awa. Dakinsa ta nufa don daukar darasi. Fatanta Allah yasa ta samu rumaisa a yau. Yana cikin bandaki, sai ta shige. Ni kuma sai na dawo baya tare da fadin Allah ya qara danqon soyayya. QARSHE....... Mu hadu a sabbin littafai na, SANADIN FURUCI...da RUDI KO BURI....Taku a kullum Halimarku K/Mashi. Sai na jiku a 08081165107 don jin ta bakinku. Nima Abdu pro mlf (Abdurrahman) da na rubuta muku, ina yima kowa fatan alkhairi, da fatan Allah ya amfanar damu darussan dake cikin labarin Ameen. Ma'assalam👏🏼👏🏼👏🏼 sai inna Habiba wace take muku post a whatsapp nace mu Ma'assalam👏🏼👏🏼👏🏼 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels