An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku An dauko wannan littafi daga shafin https://gistrog.com.ng ku ziyarci shafin na https://gistrog.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348141702912 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://gistrog.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348141702912 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://gistrog.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.gistrog.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/SuleimanUsmanKurya Twitter : https://twitter.com/Kuryaloaded_Ng Telegram : https://t.me/+Um7CIRmWSIU2NTg8 *GURBIN IDO* _Ba ido bane_ *Mallakar* *Safiyya Abdullahi huguma* *Arewabooks username* *HUGUMA* ©️®️ *ZAFAFABIYAR* *ƊANƊANO* *Page 01* Faffada kuma yalwataccen daji ne iya ganinka,wanda ya wadatu da korayen tsirrai da kuma shukoki nau'i daban daban,masu tsaho da kuma gajeru,ciyawa tafasa da sauran tsirrai da ubangiji ya huwace musu su wanzu a wajen,wanda wasu ma dan adam bai san meye ba,wasunsu kuma magani ne da garkuwa ga jikkunan dan adam. Yadda sararin yayi kore shar da nau'in tsirran da kuma yawaitarsu kadai xai bayyana maka cewa muna lokacine na yawaitar saukar ruwan sama wato lokaci na damina,duk da da cewa gurin waje ne mai cike da ni'ima da kuma albarka,albarka data sanya mawuyacine ka samu wajen a bushe ko kuma a qafe.....wannan dalili ya kawo wanzuwar fulani wajen a muhallin,suka kafa bukkokinsu suka kuma tashi gagarumar ruga a wajen....saboda waje ne daya dace da muradinsu da kuma buqatar dabbobinsu,wanda buqatar dabbobin nasu sama take da tasu buqatar. Yammaci ne lis,wanda daqiqu kadanne ne zasu ratsa magariba ta shiga,lokacine da kowanne makiyayi yake qoqarin kada kan dabbobinsu zuwa gida inda zai turkesu saboda gabatowar dare,daga cikin wannan dajin mabanbantan tawagar shanu wani lokaci harda raguna da akuyoyi ke kutsowa cikin ainihin wajen da suke kira da gari a wajensu,kowanne tawaga na tafe ne da masu kula da ita,mutum biyu uku hudu har zuwa biyar idan sunyi yawa,yawancinsu maza ne,matan dake ciki daidaiku ne. Da sannu sannu wadan nan dabbobi ke wucewa zuwa guraben da muhallinsu yake,kamar sun gama wucewa.....saiga wani garken na daban na bullowa a hankali. Kyawawan shanu ne tunkiyoyi raguna da kuma awaki masu tarin yawa da daukar hankali,ba komaine ya kawo haka ba sai yanayin qoshi da kuma tsaft da garken keda yashi,kusan duk dabbar dake ciki fara ce.....sai wasu daga ciki dake da ratsin ruwan qasa......duka ba wannan ne abun mamakin ba,abu mafi daukar hankali shine Kyakkyawar matashiyar dake kara kaina daga hagu tsakiya xuwa daman dabbobin tana saita su,da fari zaka zaci ba ita daya ke wannan aikin ba,amma idan ka tsawaita dubanka a kanta zaka fahimci ita kadai dince,dauke da sanda guda daya tak. Kyakkyawa kyau na musamman kuma na asali koda cikin fulanin,irin kyan da zaka tsammaci half case ce,maimunatu nada wani irin kyau na daban wanda ke sanya duk wanda yake baqon gani a gareta ke bata lokacinsa wajen binta da kallo,saidai kuma.....duk da wannan kyau nata babu mutum daya daya aboceta wajen tahowa gida,kusan kowa ya kado dabbobinsa ya barta,babu koda mutum daya ma cikin wadanda sukayi gaba dake waiwayota ko duba halin da take ciki bare yayi niyyar tayata ta samu ta iso gida da wuri. Kusan itama hakan bai dameta ba,duk da tanashan wahala,amma ya zamar mata jiki,ta kuma saba da yanayin......sanye take da baqin saqi maimakon farin saqi da akasan mafi akasarin fulani na tu'ammali dashi,zaka iya hangen yadda kayan suka dangale mata sosai fiye da dangalewa ta al'ada da aka saba gani tattare da fulanin,don kuwa koda rigar maimunatu tayi dagewar da banda baqar rigar yadi data saka daga ciki,babu abinda zai hana mutum ya hango albarkatun qirjinta da suka fara tasawa,sai kuma yalolon baqin mayafin data sake rufe qirjin nata dashi,duk kuwa da cewa ba wani kauri ne dashi ba,bashi da maraba da abun tace koko,hakanan bashi da tsaho,don ko mazaunanta baikai ba,tun abun yana da girma da kuma kaurinsa take amfani dashi,amma har kwanan gobe ta kasa rabuwa dashi,saboda dumbin tarihin da mayanin yake dashi a gareta da kuma rayuwarta gaba daya. Zanin jikinta shima a dage yake sasai,kanta na sanye da Hular kaba irin wadda fulani ke yawaita amfani da ita da suke kira da(malafare)sakamakon yawaitar zafin rana ko kuma tunanin saukar ruwan sama,wadda ta baiwa doguwar jelar gashin tsohon kitson dake kanta bayyana sosai,kitson DOKA inji hausawa,su kuma suce dashi(BIƊEJI)(mai tudu daga tsakiya)shine a kanta,don haka jelar ga sauko dama da hagu na fuskarta da kuma bayanta,abinda ya qarawa kyakkyawar fuskarta kyau da kuma bayyana asalin yarenta. Kunnenta babu dan kunne,saboda bata dashi,bata ma ta'ammali dashi,amma hannayenta cike suke cankas da duwatsu kalar kore shar da kuma ja,irin shirin duwatsun da akasan fulani dashi,hagu da damanta gaba daya,masu yawan gaske,wasu daga ciki ma sun girme mata,amma dai wasu abubuwane da bata iya rabo dasu,tana jinsu ne tamkar fitar numfashinta. Daga qugunta salkar ruwa ce ta duma da aka fafe daure tam,abu guda daya da take da damar tafiya dashi zuwa wajen kiwo,qafafunta kuwa wasu takalman roba ne rufaffu wanda baka rasa bafulatani dashi saboda yanayin shiga daji qayoyi da sauransu,shi kadaine fari a jikinta,duk da tsufar da yayi amma fes yake,da alama ya samu kulawa. Cikin matuqar juriya da kuma jajircewa take wulga sandar tata tana maida dabbobin hanya,duk kuwa da cewa numfashinta baya sauka zuwa cikin cikinta saboda uwar yunwar dake sakadar hanjinta kamar zata tsinka mata su,cikin matuqar kulawa take kada sandar,saboda ko kadan batasan ta samu kowacce dabba a cikinsu,wannan kusan al'adarta ne,bata dukansu,saidai duk umarnin da zata basu suna ji suna kuma biye da ita,hakan ya haifar da shaquwa mai ban mamaki tsakaninsu,idan tana magana dasu wani lokaci,kai kace tana magana ne da mutane 'ya uwanta. Har mantawa take cewa ba bil'adama bane kamarta,sau tari takanji sunfi mata mutanen dake kewaye da ita take kuma rayuwa a cikinsu,idan tana tare dasu,tana jin kamar bata da wata sauran damuwa,tana daukansu ne kamar wasu 'yan uwanta. Sannu a hankali take ci gaba da kadasu cikin juriya da qarfin hali zuwa hayar da zata sadasu da gida. Tafiya me matsakaicin nisa suka bayyana a rugar ummaru,faffadan riga mai dauke da bukkoki masu yawa,ga wadanda suka zaunu kuma sun fara gini na jar qasa da kara wanda suka tasheshi a matsayin katanga. Ta bayan dakunan da suke mallakin wasu suka keta,jimawa kadan sai gasu a haggo(wajen daure dabbobi),ta waiwaya a hankali tana duban sararin gidan,babu matar daya zame mata wajibi duk sanda fa dawo ta shaida mata dawowarta,wannan qa'ida ce,wadda tsallaketa ko saba mata dai dai yake da saima kanta tashin hankali da rashin nutsuwa tsahon wasu kwanaki,idan ma batayi sa'a ba,cikin duka kwanakin da zasu biyo.....za'a yita kiranta da sunan da duk duniya babu sunan data tsana sama dashi "Miwarti inna!" Ta bude dukka kaifi muryar da Allah ya bata tana qwalawa innar kira tare da shaida mata ta dawo,saidai yanayin zaqin da muryarta ke dashi,sam bata da amsa amo ko kuwwar da kiran xai isa inda takeso "Inna miwarti!" Ta sake fadi,saidai da alama ko kusa da inda innar take basu jita ba. Waiwaya tayi gefe guda,yarone dan kimanin shekara takwas,zaune yana wasa abinsa,yayi fututu,kai zaka ce daga sansanin gudun hijira aka tsamoshi,kai ta jinjina,tanason tace dashi wani abu amma tana tsoro kada cibi ya zama qari,bata da zabi illa ta aikeshi ya kira innar "Laulo,yanoddanan inna" daga kai yayi ya dubeta yana yamutse fuskarsa dake harmutse da qasa "Owalad'o(bata nan)" ya amsa mata a tsiwace yana maida kansa ga wasansa. Kanta ta daga sama tana kallon sararin samaniya,hadari ne yake hadowa wanda bisa dukkan alamu ba zai dadeba zai bada ruwa daga yanzu zuwa kowanne lokaci,bata qaunar yanayi irin wannan,lokacin da take dawowa daga kiwo.....cike da gajiya qishi da yunwa,take fara ta turke dabbobin a muhallinsu....ta sanar da inna ta kuma shaida dawowar tata,ta wuce zuwa cikin gida,duk da cewa koda ta wuce din bata da tabbacin samun hutun da dukka jiki irin nata daya wuni yana kara kaina tsakanin jeji da jeji a tsakiyar dabbobi,ba shakka da biyu inna ke aikata hakan a gareta,sai taja da baya kadan ta jingina da wani turke tana ci gaba da duban sama,zuciyarta cike da addu'ar dawowar inna a wannan lokacin. Cikin matuqar d'ar d'ar take a wajen,duk da ba karatu ne da ita ba mai yawa....amma ta sani xama a wannan lokacin cikin turakun dabbobi abune mai hatsari,bugu da qari ma,a al'adarsu tasan yadda suke taka tsantsan da wajen a lokaci irin wannan. Sosai ta lula cikin duniyar tunani a dan zaman da tayi a waje,wanda har batasan laulo yabar wajen ba,hakanan batasan hadarin ya gama hade jikinsa ba waje guda,ya kuma fara busa iska dake hade da qura,saida qurar ta gifta ta gaban idanunta,daidai sanda ruwa ya fara sauka.....dai dai kuma lokacin da idanunta suka kai mata ga dabbobin da suka tarwatse a wajen. Da sauri ta miqe cike da fargaba guda biyu,na farko ruwan saman da zai taba jikinta duk yadda taketa qoqarin kauce masa,na biyu kuma warwatsewar dabbobin data tabbatar da cewa saita sake wani aikin kan ta hade kansu. Tana miqewa dai dai bullowar wata mata,doguwa ce sambal,farar bafulatana ta usul,sanye da fararen kayan saqi,ta yane kanta da babban mayafi kore shar da shi,a gurguje matar take,da alama itama tana gudun tabatan da ruwan saman zaiyi "Maimunatu!"ta qwala mata kira bayan taja birki tana hangota tsakiyar dabbobin cikin dan ragowar hasken da duhun hadari dana dare ya fara hadiyeshi "Na'am inna" "Muguwa!......saboda bana nan ne shine kika barmana dabbobi su wulaqanta......seto me wanna nima ɓerde(sai na bata miki rai),ki kamasu ki kallaceminsu" daga haka ta sanya kai zuwa shiyyar da dakunansu suke ganin ruwan na sake qarfi. Abinda ya daga hankalin maimunatu kenan,ta riga data saddaqar yau din mawuyacine ta samu barci matuqar ruwan yaci gaba da taba jikinta,wani irin jiki Allah yayi mata da baya qaunar ruwan sama,indai zai tabata to lallai zata kwana da zazzafan zazzabi,amma sai gashi innar ta wuce abinta ko a jikinta,nata burin dai kawai ta tattala mata dukiyarta. Duk da yadda ruwan yake dukanta hakata dinga kamasu tana killacewa,ta daure wata saniya tana laluben danta da aka haifa wancan satin,santsin tabon dake wajen ya debeta,ta tafi suuuuu idanunta a rufe tana jiran ta jita a qasa,amma sai taji wani abu ya cake gaban qafafunta,abinda ya hanata faduwa kenan,ya kuma sanyata bude idanunta d asauri wanda tun kan ta bude din haske ya cika idanun nata. Tarwai ta bude manyan idanun nata da ruwa ya jiqe gashin idanun nata,kamar yadda ya jiqe na girarta da kanta yasa suka hade gaba daya,fuskarta ta sake haske ta kumayi tarwai da wani irin kyau. Idan har idanunta dai dai suka nuna mata mutum ne tsaye a gabanta,matashin saurayi dauke da lema da kuma fitilar torch light mai tsananin haske. Da sauri taja da baya cike da tsananin tsoro,saboda tunda take kaf kafin rugarsu bata taba sanin wannan fuskar ba,abune kuma mawuyaci indai kaidin haifaffen rugarne ka tashi bakasan dan wani gidan ba"tsaya mana" ya fadi da dan qarfin murya amma a tausashe,abinda ya dan bata nutsuwar tsaiwar,yadda take dubansa ya tabbatar masa data gamsu dashi ba,don haka yace "Me kike a ruwa a daidai wanna lokacin a haggo?" Qas tayi da kanta saboda wadatuwar hasken da walqiya ta bayar a lokacin ya haska mata fuskarshi sosai,ta kuma so ta ganeshi "Ina daure dabbobi ne" kamar xaiyi magana sai kuma taji baice komai ba,ya ajjiye lemar kansa gefe,ha saqale fitilar a jikinsa,ya fara kama mata dabbobin yana tayata dauresu. Tsai tayi tana dubansa,sai kuma ta taka a hankali itama ta fara kama wadanda zaa daure din tana tayashi sunayi tare,lokaci lokaci tana satar kallonsa,kamar yadda shima yake satar kallon nata lokaci bayan lokaci,ta gaza gasgata idanunta,wani yau a rugar yasa hannunsa yana taimakonta?,abinda ba zata iya tuna lokaci na qarshe da hakan ya faru ba,rashin sabo da ganin hakan ya sanyata dari dari dashi,har zuwa sanda suka gama tas,ya qarasa wajen lemar ya dauketa yana rufeta,saboda bata da wani sauran amfani a wajensa,saboda abinda zatayi masa rigakafi dashi ya riga daya faru. *ZAFAFA BIYAR* *_Kundi kuma dausayin zaqaqa kuma da d'ad'an litattafan hausa masu cike da nishadi soyayya darasin rayuwa dana zamantakewa,tsantsar ilimantarwa da kuma fadakarwa_* *Wannan karon ma gasu tafe da wasu taskirar tsararrun litattafan guda biyar* SANADIN LABARINA Hafsat rano BABU SO Billyn abdul GURBIN IDO Huguma FARHATUL K'ALB Miss Xoxo INAYAH Mamuhghee Dukka guda biyar din akan 1k Guda hudu:::700 Guda uku:::500 Guda biyu:::400 Guda daya:::300 *_Garzaya ki biya naki a fara a kan idanunki ta wannan account din_* Hafsat Kabir Umar 2270637070 Zenith bank *Saiki tura shaidar biyanki* 07040727902 *MASU KATIN WAYA ZASU TURAWA WANNAN NUMBER TARE DA SHAIDAR BIYA* 09134848107 *_KARKU MANTA.....HAR KULLUM,SIYAN NA GARI MAIDA KUDI GIDA NE_* *GURBIN IDO*👀👀👀 *Free page 02* "Migodake" ta fada a hankali tana sharce ruwan fuskarta,dubanta yayi,ya sakar mata murmushi,wani abu me suna nutsuwa da sanyin halin daya karanta tattare da ita na dan qaramin lokaci yana burgeshi "Karki damu,ba komai" kai ta jinjina,saita juya tana nufar cikin gidan tana qudundune jikinta waje daya saboda yadda sanyi ya fara ratsata,da alama akwai damuwa kenan,yayin da shi kuma ya juya ya dauki torch dinsa ya fara gangrawa yana barin wajen,saidai sau kusan uku yana waiwayarta kafin ta qule masa yabar ganinta,ya sauke ajiyar zuciya yana maida hankalinsa sosai ga hanya,zuciyarsa na qissima masa ita,tsahon wanzuwarsa a rugar bau taba kula da ita ba,hakanan bai taba ganin macen da Allah ya zubawa kyau me sanyi da tsari irinta ba,ko wacece ita?,da wannan tunanin ya isa kofar wani gida,wanda shi dayane kaf kafin wajen dake dauke da ginin qasa da bulo. Babban tsakar gidane daya kasance wayam babu kowa saboda ruwan daketa sauka,yakai dubansa ga dakunan dake jere a tsakar gidan,har ya nufi wani daki daga ciki,sai kuma ya dakata ya juya akalarsa zuwa wani daki dake daura dashi,muqullin ya taba,a rufe dakin yake dole dai ya karbo muqullin,abinda yasa ya juya da dan sassarfa ya nufi daya dakin,yasa hannu ya dage asabarin da aka saukema qofar dakin saboda kaucema shigar ruwa. Dumine ya fara dukan fuskarsa kafin hasken fitilar aci bal bal dake dakin ya cika masa idanu,matasan mata ne guda biyu da yaro namiji guda daya zagaye da fitilar,kowannensu d kwanon tuwo a gabansa yana ci,sai babbar mace guda daya da alamu suka nuna mahaifiyarsu ce zaune gefe daya tana dubansu,jikinta nannade da mayafi me kauri,da alama sanyi takeji "noi saare daada" "Jam....alhamdulillahi,ina ka tsaya?,inata taraddadi ruwan nan sai daya dakeka" murmushi ya saki "Zan canza kaya daada,a bani maqulli" hannu ta miqa wata qwarya dake kusa da ita da alama a nan take ajjiye ajjiyenta ta dauko,ta miqawa daya daga cikin yaran "Nabugol(karbi)" ta fadi,sai yasa hannu ya karba din,sannan ya miqe zuwa inda yayan nasa ke tsaye Cikin girmama ya miqa masa muqullin yana cewa "Hamma....." Dakatar dashi yayi "Micanjato kayaa sadam,ina zuwa" "To" ya amsa yana murmushi,saboda ya qagu ya bashi labarin dake bakinsa,a nutse ya juya ya fice daga dakin ya sake nufar dakin da yayi nufin shiga dazu. Batayi wani hanzari ba wajen isa dakinsu,saboda ta riga data jiqe,kuma koda ta isa dinma tasan bata da wani wajen zama daya wuce bakin qofa,dakinsu ne su biyu,amma kuma ya zama gaba daya kamar mallakin mutum guda,wato 'yar uwarta gaaje. Cikin kula da takatsantsan ta dage assabarin dakin,hasken fitilar dake dakin ya bayyana,motsin shigowarta ya sanya matashiyar dake amsa sunan gaje din daga kanta tana dubanta,gabanta akushi ne madaidaici cike da dambu tana ci,wanda shine yawa yawan cimarsu,tuwo ko dambu,ba kasafai zaka gansu da shinkafa ba Wani kallo ta watsa mata kamar wadda taga qullin kashi "Dirdutu malama(matsa malama)" tasan neman bala'i ne kawai irin na gaje,amma inda take tsaye ma sam bashi da alaqa da wajen da gajen ke zaune,sai ta matsa gefan don kawai a zauna lpy,ta miqa hannunta zuwa ga wata tsohuwar baqar jakar bacco dake saqale jikin bango,darajarta wajen maimunatu dai dai yake da akwati a wajen kowa,duk kuwa da cewa duba daya zaka yimata kasan cewa ta sha duniya ta kuma ji jiki,a nan din take ajjiyar duk wani abu nata,duk da dewa ba komai ta mallaka ba face kayan saqinta kala daya da take boyansa saboda sallah ko wani sha'ani idan ya tashi,duk da cewar ita din ba shiga jama'a take ba,rayuwarta na maqale da wani tabo da ya hanata duk wani 'yanci da walwala da kowanne dan adam kan samu,laifin da bata da masaniya a kansa,bata kuma san sanda aka aikatashi ba. Kayan jikinta ta zame ta matsesu da kyau daga bakin bukkar tasu,sannan ta dawo ta daura wani fallen zani guda daya da take rufa dashi,ta tara hannu a ruwa bunun dake sauka ta dora alwala,sannan ta dawo ciki ta tada sallah. Sallar magrib ce kawai a kanta,saboda koda wajen kiwo bata wasa da sallarta sam,duk da ba ilimin addini gareta ba mai wani zurfi,amma tun kafin takai haka,zamanin da take rayuwa da mahaifiyarta ta koyar da ita yin salla da zarar lokacinta yayi,abu guda daya da ba zata manta da shi ba,ta kuma riqeshi har yau da kyau,kasancewarta mutum da bata da yawan mantuwa da kuma qwaqwalwa mai yawan riqe abu. Da kyar takai sallar da takeyi din saboda tsananin yunwa,takai dubanta ga kwanon da gaje ke cin abinci,tuni ta hallakeshi,dan abinda yayi saura a ciki bazai wuce loma biyu ba,ya tabbata bata da abincin dare kenan duk da dan karen yunwan da take ji?,ta rasa wanne irin azanci ne wannan....tare inna ke hada musu abinci ita da gaje,bayan bambancinsu da gajen kwatankwacin bambacin sama da qasa ne,saboda gaje irin mutanen nan ne masu shegen cin abinci,kamar ci suka kawo duniya,duk yawan abinci sai sun tasheshi....yayin da maimunatu ta kasance wata irin mace,duk yawan yunwar da takeji dan abinda zata ci maka bai taka kara ya karya ba,har wani lokacin ma idan kawai nono tafi ganewa tasha shi ko ajiyayyar madara idan tana da sauranta,kusan duk sanda aka hada musu abinci da gaje sai gaje ta kusan cinyewa ko ta cinye ma sannan take tunawa da ita,duk da cewa a yawancin lokuta bar mata take yi,amma duk lokacin data ratso da tsautsayi irin haka tana jin yunwa tofa saidai ta lashi walqiya ko ta nemi ma duk abinda zata ci din,gajen duka duka sa'anni suke da maimunatu,har maimunatun ma ta bata tazarar kwanaki masu dan dama a duniyar. "Gaje ya baki ragemin ba?" "Idan kina da wani ma ki qaro min" ta bata amsa tana sude hannu tare da ture kwanon da qafa ta gicciye anan wajen tana sakin gyatsa. Fararen idanunta masu sheqi ta dauke daga kan gajen,dan qaramin bakinta mai dauke da jajayen labba yana motsawa kamar zata ce wani abun,saidai ba komai zata fada din ba,zallar bacin rai ne qasan ranta,wanda bata isa ta furta ba,bata jun a daren zata iya runtsawa matuqat bata sanyawa cikinta wani abun ba,ga gajiya da takeji tana nuqurqusar qashinta tare da qaramin zazzabi da taji ya fara lasarta,wanda dama tana tsammanin zuwan nasa. Tsam ta miqe tana leqen waje ta qaramin window din cikin ginin bukkar,ruwan yadan sassauta,amma yana sauka kadan kadan da dan qarfinsa,saita dage qofar ta sanyo kai zuwa waje. Gabanta na faduwa amma ta daure ta qarasa qofar dakin inna,sallama tayi,shuru ba'a amsa ta ba,ta sake sallama,a sannan aka amsa daga ciki a tsawace "Wai waye!?" "N.....nice inna?" Kamar ba za'a fito ba sai kuma ta jiyo motsinta,ta dage labulen ta fito tana mata wani duba daga sama zuwa qasa "Menene kuma?" Sunkui da kanta maimunatu tayi "Yunwa nakeji inna" "Shine kika zo ki cinyeni?" Amsar data sanya maimunatu daga kanta da sauri tana duban innar hadi da girgiza mata kai "A'ah inna" "To meye?,bayan kinsan na hada muku abinci da gaje?" "Ta cinye inna" "Kina kallonta ta cinye?,to babu wani sauran abinci cikin gidan,saiki kwanta haka,kyaci gobe" "A'ah,ba za'ayi haka ba" sukaji an fada daga bayansu,rabewa maimunatu tayi gefe daya,ko bata juya ba tasan waye,mutumin da shi kadai yayi saura wanda yake dubanta da idanun rahama,ya qaraso garesu yana sanye da rigar ruwa,da alama dawowarsa gidan kenan. Da sauri maimunatu ta karbi kayan hannunsa tana tayashi saukewa hade dayi masa sannu da zuwa,inna na daga tsaye tana zabga mata harara amma bata kulaa da lamarinta,don ba zata iya ganinsa da kayan bata karba masa ba "Yaya mutum zai kwana da yunwa......ki debar mata cikin nawa mana" tuni ta cika dama tayi fam da yadda yake nuna kulawarsa akan maimunatun,uwa uba kuma ya buda ledar hannunsa ya bata bread cikin tsarabar da yayo "Wallahi ba zata ci ba....koda abincinka ne kuwa" "Ka barshi bappa,zanci wannan" maimunatu ta katsesu da sauri,saboda tasan muddin jayayyar taci gaba to la shakka a kanta abun zai qare,inna zata yi mata hukunci ne wanda ba zataji dadinsa ba,sannan babu abinda zai sanya innar ta sauya rantsuwarta,saboda ba wai tsoro ko shakkar bappan take ba,duk da tasanshi farin sani,yana sakar mata ne,saboda kasancewar maimunatu daga tsatsonta ta fito,shi yasa yake dage mata qafa,baya zaqewa cikin al'amarinsu da yawa "Shikenan,balejam(mu kwana lpy)" "jam" ta amsa tana juyawa da dan hanzarinta tabar wajen zuwa nasu dakin. "Kiji tsoron Allah fulera,kiji tsoron randa Allah zai kamaki da haqqin marainiya" daga haka ya dauka ledarsa ya rab'eta ya wuce ciki,ta bishi da harara,sannan ta sauke idanunta tabi hanyar maimunatun ta wuce da hararar itama har zuwa qofar dakin nasu,sannan taja qwafa tana sakin labulen "Tsoronka da zanji,rashin godiyar Allah ne yasa baka ganin qoqarina ai,banda ni ma waye zai riqeta?" Taci gaba da mita abinta,saidai ko daga kai bappa jauro baiyi ba bare ya kalleta,idan da sabo ya riga ya saba da halayyarta. Saman shimfidarta ta koma ta zauna sannan ta bude ledar biredin,a hankali ta dinga yaga tana turawa,cikin ranta tana godewa Allah da ya turo bappa jauro,da haka zata kwana da tsohuwar yunwarta. Yadda biredin ya fara mata go slow a wuya ya sanyaya bisa dole ta miqe cikin raunin da jikinta ya fara yi ta lalubi wani tsohon kofi nata ta tsiyaya ruwa a jallonsu dake dakin,ta sake komawa ta zauna,tana ci tana korawa da ruwan,kafin sannan tuni bacci yayi gaba da gaje,wadda maimunatu bata da tabbacin tayi sallar magariba bare isha'i. Jahilci ya sanya gaje da wata ire irensu sam basu baiwa ibadarsu muhimmanci,duk da cewa akwai makarantar islamiyya guda daya tal,wadda anan ake koyarwa da kowa da kowa cikin rugar tasu,maza da mata yara da manya,cikin hobbansa da malaman ahlussunnah sukayi suka kawo musu malami bafulatani irinsu yake zaune dasu.yana koyar dasu,saidai ba kowa bane ya fahimci alfanun hakan ba bare har yace zaije,da yawa wani kallo sukewa makarantar,dai daikunsu ke zuwa. Tana da.matuqar buri da kuma sha'awar kasancewarta daliba a makarantar,saidai inama taga lokacin da zai zama rara(saura) a gareta tsahon wuni guda,wanda bata bautar komai,da gar zatayi.amfani dashi ta ziyarci makarantar da sunan daukan karatu,kullum aiki take,babu dare ba rana,ba asabar babu lahadi,kamar yadda babu alhamis babu kuma juma'a,koda makara tar bokonsu dake da dan karen nisa,koda yuashe maimunatu mafarkin zuwanta take,bare wannan dake kurkusa dasu,gaje nada dama mai yawa da zata iya zuwa makarantar,saidai sam ita ba wannan bane a gabanta ba,bata taba ma kwatanta zuwa din ba. Dai dai lokacin da gari ya sake daukan shuru bayan daukewar mamakon ruwan saman.....dai dai lokacin da wata iska me sanyi ke kadawa,a wannan lokacin zazzabi ya fara saukar mata,yana murqushe duk wata gaba dake da sauram qwari a jikinta,takurewa tayi sosai waje guda,tana jin yadda zazzabin ke ratsawa ta qashi da tsokar jikinta,a hankali yana saukar mata da sanyi da wani irin radadi,saita cure waje daya,numfashinta na fita da qyar tana kokawa dashi. Duk da cewa wannan din ba baqon yanayi bane tare da ita,amma shi ciwo ba'a taba sabo dashi,ta jima cikin wannan yanayin tana kokawa da numfashinta,tana hangen kanta tsakanin rayuwa da mutuwa kafin ubangiji cikin tausayinsa rahamarsa da kuma jin qansa ta fara samun sassauci,numfashinta ya fara komawa dai dai,saidai qirjinta dake riqe da kuma ciwon dake ratsawa cikin jikinta yana sandarta a hankali,har wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita. *********** "Maimunatu!.....maimunatu....." Can tsakiyar baccinta....sannan cikin tsakiyar kwanyarta taji ana ambatar sunanta,shurin da aka kaima gefan cikinta shi ya qarasa tabbatar mata da cewa ba cikin duniyar mafarki take ba,abinda ya sanyata zumbur ta miqe daga kwanciyarta,sai kuma ta sanya hannayenta guda biyu ta dafe kanta tana furta "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" saboda wani nauyi da taji kan nata yayi mata,baya ga dan karen ciwon da yake mata "Ke yafi kamata a jawa innalillahi,akalluɗo(muguwa)" inna dake tsaye bisa kanta ta fada cikin fushi,bata ko motsa ba bare tace wani abu,kanta na qas tana jin yadda zuciyarta ke suya,jikinta ke tsami da kuma ciwo saboda ciwon dake jikinta "Ananata haala maimunatu?(bakyajin magana maimunatu ko)da kika zo kika kwanta kina barshi,waye zai miki tatsar nonon,waye zai fita da dabbobin?,ko uwarki ce zatazo tayimin?" Idanunta ta runtse,tana jin xafi cikin zuciyarta fiye da kowanne irin zafi,koda wasa bata qaunar inna ta dinga sanyo mahaifiyarta cikin kowanne irin sha'ani ko laifi da zata aikata mata,ta kuma tabbatar ci gaba da shurunta xai bawa innar dama taci gaba da zagin nata ne,don haka cikin murya mai cike da rauni tace "Minyauɗo inna(bani da lafiya inna)" idanu innar ta qanqance tana dubanta "Wannan keta shafa,yahudillo durgul,wurtawa(zo ki tafi kiwo,fito)" ta fada a tsawace kamar zata finciko maimunatun. Bata da sauran zabin da ya wuce ta miqe din kamar yadda inna fa buqata,duk kuwa da yadda takejin jikinta,ta dafa a hankali ta miqe tsaye,a sanda innar ke mata wani kallo "Nikam kin zamemin alaqaqai masifa" saita juya ta fita zuwa waje tana zazzaga masifarta,idan lokacin ka shigo gidan zaka tsammaci wani mummunan abu maimuntun ta aikatawa innar. Kayanta data saqale.jiya ta miqa hannu cikin juriya ta cirosu,hawaye me dumi ya subuce mata,ta zame zanin jikinta,ta fara shirya kanta a cikinsu,babu batun wanka bare akai ga abinci,dama bata lafiyarta take ba "Wurtawa fa maimaunatu" ta tsinkayo muryar innar tana fada cikin salo na azalzala "Mihosh shawai filkul(dan kwali zan dauko)" maimunatun ta fada tana duqawa a hankali ta dauki dan yalolon dan kwalinta ta dora kan sassalkan gashinta dake cure waje daya cikin kitson doka(bijaɗe a fulatance),sannan ta matsa zuwa bakin kofa tana laluben wuffajen ta(asalin rufaffen takalmin da fulani ke amfani dashi wajen kiwo. Ba zata iya duqawa ta sakasu yadda ta saba ba,dole sai datakai qasa ta zauna dirshan sannan ta samu damar sanyasu ga qafafuwanta,ta miqe tana riqe da sandarta tana takowa zuwa tsakar gidan nasu iska na kadata. Kamar kullum babu kowa a tsakar gidan,daga inna dake can rumfar da suke girki,sai gaje dake zaune tana cin tuwo,tuwon da take da tabbacin da safen akayishi,amma bata da darajar da za'a bata ta sanyawa cikinta,ko don darajar bautar da zata fita yi musu. Ganin tuwon ya tuna mata da guntun biredinta na jiya,ta sanya hannu ta dafe qaramar jakar da take daureta a qugunta taji tudunsa tabbacin yana nan,sanna ya fara takawa zuwa ma'adanar dabbobin,muggan kalaman inna sunayi mata rakiya,har zuwa sanda ta kammala kunce na kuncewa,ta kuma fara kadasu suka dauki hanya. ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* 😄😄😄😄😄😄😄 *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 *_GURBIN IDO_* *Huguma* *Free page 03* Duk wani taku da takeyi tana yinsa ne da taimakon sandar dake riqe a hannunta,a yau madadin sandar ta zame mata ta saita dabbobin da take jan ragamarsu,sai ta zame mata mataimakiya wajen sanya diga diganta zuwa qasa. A yau din da baki ta.dinga saitasu tana basu umarni,duk da yadda magana ke mata wuya ainun,duk kalma daya idan xata fitar sai taji kamar kanta zai tsage,sun dan dauki lokaci kafin su isa inda suke qyale dabbobin,kowacce ta ni'imtu ta kums amfana daga rahamar ubangijinmu. Tana isa kamar koda yaushe,mabanbantan makiyaya dake wajen kowa ya fara qoqarin tattare dabbobinsa don gudun afkawa ko cakuduwa da nata dabbobin,ba yaune farau ba,nan da anjima kadan ma tana iya ganin wajen babu kowa sai ita daya da nata dabbobin,abune data saba da ganinsa,canfi ne da suka riga suka dasawa ransu,wanda batasan ranar da zai goge ba,hakanan babu me cire musu shi sai mahaliccinmu. A yau dinma bata damu ba kamar kowanne lokaci,bayan ta tabbatar da sun iso inda ya dace,saita fara zame jikinta daga cikinsu,tana wara manya kuma fararen idanunta da kalarsu ta jirkita saboda zafin ciwo dana zazzabi,tana neman inuwar da zata dace da ita. Babbar bishiyar mangwaro ce,mai yawam sanyi da kuma inuwa,wadda bata da wani tsaho.mai.yawa amma sai yawan 'ya'ya,daga nan inda bishiyar take basu da nisa da inda zata hangi dabbobinta,hakanan ba nisa da inda zata gangara dasu susha ruwa da zarar lokacin hakan yayi. A hankali ta zame malafare(hular kaba da suke amfani da ita" ta ajjiye a wajen,duk da hular ba nauyi gareta ba,amma sai takejin kamar ta dora wani dutse saman kanta,ta zare jakar dake qugunta itama ta ajjiyeta,da zata iya kwanciya zatayi,amma tana jin nauyin sallar da batayi ba takai mata ko ina,don haka ta juya zuwa sashen da ruwa ke gudana,ta daura alwala ta dawo ta tada salla saman dankwalin kanta data cire ga yane kanta da mayafin da akoda yaushe bata rabo da yafashi,duk kuwa da cewa baqon abune cikin al'adarsu,zata iya cewa ma kaf fadin rugar ita daya ce cikin matasan yara masu shakaru irin nata dake amfani dashi. "Maimunatu!.....maimunatu" da sauri ta daga kanta daga durquson da tayi masa,tana ware idanunta cikin matuqar kaduwa da razana,murya mafi muni da razanarwa a wajenta.....muryar da mamallakin muryar abubuwane da tunda take a rayuwarta bata taba jin abinda ta tsana cikin duniyarta sama dasu ba "Yaushe ya dawo?" Ta jefawa kanta tambayar tana wurga idanunta don tantance daga wanne bangare yake dosota. Daga can nesa ta hangeshi,tsabar kauri da qarfin muryarne ya sanya ta dinga jinta kusa da ita kamar yana gab da ya cimmata,qasa tayi sosai don kada ya hangota,sannan ta miqe a hankali,ta tattare dankwali hula da jakarta waje daya ga wurga saman bishiyar da take zaune qasanta,karo na farko da tayi ala wadai da rashin iya koyan hawa bishiya irin nata,saita saita mayafinta ta lullube jikinta da kyau,sannan ta zagaya ta bayan bishiyar ta lafe sosai a jikinta,ta yadda zata iya hangoshi,zuciyarta na wani buguwa ɗik ɗik,tana cike da fata da kuma addu'ar rashin samun sa'ar ganinta. Dube dube da waige waige ya shiga yi,yana kuma sake qwala mata kira iya qarfinsa,fuskarsa a firgice da alama ya zaqu da son ganin nata,bai kuma tsammaci rashin samunta a wajen ba,dube dube yaci gaba dayi,yana sake kiran sunan nata dai,har zuwa sanda ya sare,jikinsa da zuciyarsa kuma suka gaya masa bata a kusa "Kayyasa" ya fada da kaushin murya,yana kaiwa bishiyar dake kusa dashi karta da wani kakkaifan abu dake hannunsa,da sauri ta zame kadan saboda gudun samuwar ciwo a jikinta,saura kadan kartawar da yayi ta hada da tsintsiyar hannunta,ta dauke numfashinta cak sanda yake sake takowa da baya,sai kuma ya dura wata ashariya,yasa giyaa zuwa gaba ya taka ya fara barin wajen. Bin bayansa tayi da kallo farincikin boye masan da tayi yana saukar mata,kwata kwata kuma ko sau daya bata taba yiwa buderi kallon mutum mai hankali ba,hasalima tsoro yake bata ainun,buderi kenan,baqin bafulatani na usul,wanda ke ciie da wasu irin baudaddun halaye na wauta jahilci da hauka,irin nau'in haukan da jahilcin ne ke haifar dashi,zuciyarta cike take da mamakin me yasa shi din baya gudunta kamar yadda sauran samarin qauyen ke gaza rabarta bare su furta mata kalmar so?,me yasa shi bai gujeta ba?,ta jima tana yiwa kanta wadan nan tambayoyin. Sai data tabbatar da cewa ya yiwa wajen nisa sannan ta fito,zuwa sannan zazzabin jikinta yayi wata irin saukar da babu shiri,sai sauran dumi,ciwon kai mai tsanani saboda razana da bayyanar buderi da kuma ciwon jikin da har yanzu tana jinsa shima,ta tako a hankali ta dawo ainihin wajen da ta fara zama da farko,tana tattare jikinta waje daya. A nutse yake takowa yana kuma sake nazarin rigar tasu,yanayin yadda ko yaushe take bunqasa da tarin dabbobi da albarkar kiwo kusan ya zarce na kowacce ruga dake maqwabtaka dasu,ni'imar dake wajen ta banbamta daya sauran yankuna,hakan shi ya sanya yanayin wajen da rayuwarsu t bambanta data sauran sassa. Tun daga qasan ruhinsa zuwa saman fuskarsa cike take da wani irin nishadi,tun daga daren jiya da yayi gamo da ita.....har kawo warhaka da yake takowa cikin rugar tasu daga doguwar tafiyar da yayi zuwa cikin ainihin garinsu,tunaninta,siffa da kuma kamanninta basu bace daga idanunsa ba,duk sanda siffarta zata wulqa cikin idanu da tunaninsa sai ya samu kansa da subucewar murmushi,wani lokaci hatta da haqoransa sukan bayyana,nuni da girman nishadin da zuciyar tasa take ciki. Goye yake da baqar jaka,yana sanye da baqin wandon jeans,sai asalin rigar fulani dake jikinsa mai gajeran hannu,daga ciki kuma t.shirt ya sanya mai dogon hannu saboda hana bayyanuwar dantsen hannunsa,saman kansa ma hular fulanince,sai qafarsa dake sanye da wani rufaffen baqin takalmi na danqo. Ba qaramin qara masa kyau da haiba kayan sukayi ba,sun kima fidda ainihin salsalarsa na bafullacen usul,duk da kana dubansa zakasan cewa ya dan banbamta da sauran matasan fulani irinsa dake rayuwa cikin rugar,akwai wani banbanci na daban da kuma haske tattare dashi. Hakanan kawai zuciyarshi ta bashi yabi ta gefan ruwan,yana da tabbacin hakan zai qara masa nishadi,bayi wata wata ba yabi shawarar zuciyarsa,yana tafe yana kallon yadda dabbobin dake baibaye da gefannin kogin keta kaima cikinsu ruwan. Da kallo yaci gaba da.binsu yana sake takawa izuwa gaba,babban abinda ke sake hanashi sakewa da garin kenan,had'akar ruwan sha a gurbi guda tsakanin dabbobi da kuma al'ummar yankin,daya daga cikin burin da yake dashi idan har Allah ya cika masa burinsa,banbance ruwan shan dabbobi dana mutanensa. Dauke idanunsa yaso yi,saidai daga gefe guda dab da rafin wani abu ya dauki hankalinsa,ya rage sassarfar da yake a tafiya,ya sake qura mata idanu saboda tabbatar da hasashensa,shin itace koba ita bace,bashi da sauran zabi.bayan ya tabbatar da ita dince illa bin umarnin zuciyarsa dake azalzalarsa yakai gareta,ko zai rabauta da daddadan sautin nan da take magana dashi a koda yaushe. "Assalamu alaikum" ta tsinkayi sallama daga gefanta,bata tsorata ba duk da bataji takun tafiya ba darajar sallamar da aka gabatar mata,sai ta cira kanta dake boye tsakanin qafafuwanta. Fes ta zubesu a kansa,tadan tsura masa idanu na wasun gajartattun mintuna,qwaqwalwarta da zuciyarta nason tuna mata fuskar,ba tare da daukan dogon lokaci ba ta harbo mata wayeshi,mutumin da ya fara taimakonta tsahon xamanta a rugar ummaru,bai kyautu ba ace ta manta fuskarsa haka da wurwiri ba. Dukkan jarumta da juriyarta ta tattaro,ta sake masa murmushi wanda yayi fidda wani boyayyen kyau dake kwance saman fuskarta "Yallijam(ina yini)" ta furta da sassanyar muryarta tana sauke qafafunta dake takure cikin jikinta kai tsaye sukayi masauki cikin ruwan dake gabanta,sai daya maida mata da murtanin murmushinta,yana jin wani.abu na narka zuciyarsa sannan ya amsa mata "Jam....alhamdlh" ya amsa mata idanunsa bisa kanta,tana wasa da qafafunta cikin ruwan "Nobaluɗa ke`yen(ya kika kwana jiya)" "Lafiya alhmadlh" ta amsa masa tana masa kallo daya,saita maida idanunta ga ruwan ganin ita yake kallo "miyatti fa,na gode sosai da alkhairinka na jiya" Karamin murmushi mai sauti ya sake sannan yace "ko'en waɗi ken yen?(me akayi jiyan?" Dubansa ta danyi cikin mamaki,sai kuma ta kawar da kai ganin kallonta yake,shuru ne yadan ratsa a tsakaninsu,kafin ya buda bakinsa a hankali cikin nutsuwa yace da ita "Anaunaaki nke'yan?(bakiji ciwo ba jiya?)" Hannayenta ta kalla a hankali,tana jin yadda jikinta yake mata babu dadi "Eh" ta amsashi a hankali,sai shuru ya sake wanzuwa a tsakaninsu,jifa jiya yake satar kallonta,yana son sake mata magana ne,akwai abubuwan da yakeson sani game da ita,bazai yiwa kansa qauron baki ko ya cuci kansa ba,kansa tsaye zai iya fadima kowa cewa daga jiya zuwa yau din ta sace zuciyarsa,ta kuma tafi da hankalinsa,dan zaman nan kuma da sukayi na wasu gajerun mintuna ta sake burgeshi qwarai da yanayin tsarin dabi'arta,yawan shuru shuru da kuma alamun cikakkiyar nutsuwa,dukka sun nuna kansu tattare da ita "No'indema surbajo(ya sunanki ne 'yammata?)" Ya fada yana kallonta,fuskarsa qunshe da murmushi,yanayin yadda ya furta maganar tasa maimunatu jin wani banbarakwai "Inde'an maimunatu,daada ta tana cemin diyam" ta fadi maganar wani abu yana motsa zuciyarta,don har sai da hakan ya nuna a saman fuskarta,kai ya jinjina "endema eweli (Sunanki nada dadi....ni baki tambayi nawa sunan ba" satar kallonshi kadan tayi,bataga amfanin tambayar nashi ba,saidai tana duba da alkhairinsa gareta,don haka tace "No'indema" murmushi ya saka kadan sannan yace "Ibrahim.....anfi kira na da himu" kai ta jinjina kawai ba tare data ce komai ba,dukkansu idanunsu kan ruwan dake wucewa ta gabansu "Deko tata nwulo?(yaushe zaki tafi gida?)" "joni(yanzu)" ta samu kanta da fada,duk da ainihin abinda yake cikin zuciyarta kenan,saidai tana tunanin komawar,bataso taje ta tadda bud'eri cikin gari yana jiranta,tanajin kamar taci gaba da zamanta cikin jejin,saidai kuma dole ta koma gida,ko don yadda takejin yanayin jikinta a yanzu. "Amma kamar lokacin komawa bai qarasa yi ba ko?" Himu ya fada bayan ya gama qarewa sama kallo,wadda keda sauran rana tarwai,kai ta gyada,sai taji bata sha'awar fada masa qarya,yar kulawa daya nuna mata daga jiya zuwa yau takejin girmanta har ranta,tunda abune da bata saba ganinsa ba "Minyauɗo(bani da lafiya)" tayi maganar kanta a qas,zuciyarta na karyewa "Subhanallah" ya fada cikin rudewa kadan yana dubanta "Tun yaushe?" "Jiya" ta amsa masa a taqaice "amma hanjun foɗi gurtoyiɗa durgul?ginɗimu?(Amma shine kika fito kiwo,me yasa?" Shuru tayi ba tare data furta komai ba,shi kuma yayi tsaye yana jiran amsarta,amsar da bata da ita,tunda batasan me zata gaya masa da zai fahimta ba. Ganin bata da niyyar cewa komai,da alama shuru shuru da rashin sonyin magana cikin jininta da halayyarta suke,sai ya miqe yana ajjiye jakar dake goye a bayansa yana cewa "kowanna tama?(me yake damunki?" "Zazzabi ne" "qila inpab ɓoje(wataqil malaria ce)" shuru tayi masa,duk da tasan cewa ba malaria din bace,har zuwa sanda ya yiwa jakar ma'ajiya "imi wara(Ina zuwa" ya fada yana takawa zuwa wata hanya da zata fiddaka daga wajen kiwon gaba daya. Binsa tayi da kallo,ko waye shi?,me yasa yake rabarta?,baisan wace ita ba?,maganganun 'yan rugar tasu dangane da ita bai iskeshi ba?,saita maida idanunta ta lumshe ta sake budesu kan jakarsa daya ajjiye gefanta,ta kalli jakar me kyau da ita,kuma fes take,da alama tsafta ta wadaceta,tun ganin farko data masa zuwa yanzu ta tabbatar ga banbanta da dukka sauran mazan qauyen,ta kwantar da kanta saman cinyarta tana tariyo magangun da sukayi dashi daga jiya zuwa yau. *Arewabooks username* *HUGUMA* ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* 😄😄😄😄😄😄😄 *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 *_GURBIN IDO_* *Arewabooks::HUGUMA* Free page 04 Sallamarsa ta yanke mata dan qaramin bacci mai dadi data fara yi,ta daga kanta tana amsa masa,da murmushi ya bita,hannunsa dauke da baqar leda qananu guda biyu,inda ya tashi dazun ya koma ya zauna,sannan ya bude ledan yana cewa "Ga magani kisha" idanunta ta lumshe gami da budesu lokaci guda cike da.mamaki,yau ita ake cewa ga magani?,anya kuwa ita dince......maimunatu?,bata sauka daga wannan mamakin ba ta sake jin muryarsa yana sake miko mata wata ledar "Amma ki fara cin wani abun tukunna,na sani idan baku da lafiya bason cin abinci kuke ba,haka innata ke fama dasu zubaida idan basu da lafiya" ya qarashe maganar yana miqewa "Bari na baki waje,amma idan bakisha maganin ba zan dawo" saiya juya yayi nesa da ita,yayin da ta rakashi da kallo har sai data daina hangoshi,sannan ta janye manyan idanunta ta mayar kan ledojin,ta sanya hannu ta jawosu tana budewa. Ledar farko magunguna ne,qwayoyi tablet sosai,sai leda fa biyu dake dauke da gurasa mai kyau,wani yawu ta hadiya,duk da yanayi na lalurar rashin lafiya da take amma sai da tsohuwar yunwa ta taso mata,batayi qasa a gwiwa ba ta dauka ta fara ci,tana ci tana lumshe idanunta tsananin azabar yunwar data tarawa cikinta,dama don bata da lafiya ne,amma duk sanda inna ta gwada mata irin wannan rashin imanin......a nan gurin kiwo take samun daya daga cikin naggen ta tatsi nono mai dumi tasha,duk da ta sani,yawanci da safe shine lokacin tatsar,amma dole tasa wasu lokutan take hakan,idan kuma ta samu ta faki idon innar sanda take tatsar da sassafen ta ɗaɗɗaki wani,shine zata wuni nata damu ba,yunwa kuma bata addabeta ba kamar yanzun,har shan nonon ya zame mata jiki,ya koma kamar shine abincin nata,abinda yasa ko kadan bata da wani jiki kwata kwata,duk sirantaka irin ta bafullace tata ramar ta fita daban. Bawai don ta qoshi ba ta janye hannunta,a'a,tayi hakanne saboda kunya kara da alkunya,kada yazo ya taras ta tashi da ita,ta bude ledar maganin wanda ya sanya ledar ruwan pure water guda daya,ta daga pure water din ta jujjuya shi a hannunta,ba zata iya tuna sanda tasha ruwan leda ba a rayuwarta,saita koma kan magungunan,ta balli kowanne kamar yadda taga anja sandunan layi ajiki ta kora da ruwan. Idanunta ta mayar tana sake lumshesu,tana jin yadda numfashinta yadan fara daidaita albarkacin gurasar data ci tun kafin magani ya soma mata aiki,a hankali take zuqan iskan wajen tana kuma sauraren koke koken dabbobi dake kai kaw a wajen,jikinta yana mutuwa murus kamar wadda aka yiwa dukan tsiya. Tun daga nesa ya kafeta da ido,idanunta dake lumshe sai suka sake qarawa fuskarta kyau,yana ganin baqonnin yanayi tattare da ita,yana son sanin wace ita sani na haqiqa,da kuma dalilin da yasa take kebance kanta take nesa da jama'a haka. Sallamarsa ta sanyata bude idanunta "A henyi?(Kin gama?)" Kai ta gyada masa tana kallon qasa,kunya tana cikata,tanajin yadda tayi abun kunya,na yadda zata zauna taci abinda ya futo daga hannun saurayi "hokkoyon dunni sauro(miko min sandar can)" ya fada yana nuna sandarta dae gefe,sai data kalli sandar sannan ta maida dubanta kanshi,ya fahimci me take nufi,don haka murmushi kawai ya sakar mata,ya taka da kansa zuwa gefanta ya dauki sandar,ga bishi da kallo mamaki fal zuciyarta "waye shi?" Tambayar da taketa nanatawa kanta kenan. Daga nan inda take tana iya hangen yadda yake tattare mata kan dabbobin nata cike da hikima da kuma qwarewa wadda ta lunka tata,da alamu shima din gwanine wajen iya kiwo,bai dauki wasu lokuta masu dama ba ya dawo gareta,yana sabe da sandar kan kafadarsa "indillo(Muje ko?)" Yace da ita,dubansa tayi sanna ta janye idanunta gefe daya,sam maganar batayi mata ba,ta yaya zata jera dashi har cikin gari?,akwai idanun mutane masu yawa a kanta,sannan tana da kunyar da ba zata iya aikata hakan ba "ummadillen(Tashi mu tafi),ko ba zaki iya tashi ba?"ya sake maimaitawa a tausashe,a hankali ta girgiza masa kai "Kaje kawai,na gode,zan qarasa kaisu gida da kaina,na gode qwarai" idanu yadan zuba mata kadan,sai ya sauke ajiyar zuciya yana sauke sandar daga kafadarsa,ya fahimci me take nufi,tabbas ga cika bafulatanar gaske. "Shikenan,zan kora miki su,tumudilli tokkirawaya gaɗa taajan banna wala kyettaiɗo ingwandi(idan na tafi ki biyo bayana,karki damu,ba wanda zai gane tare muke)" duk da hakan yayi mata,amma kuma batason dora masa wani nauyin kuma ko dawainiyarta,saidai kafin ta sake cewa komai yayi gaba,dole ta miqe,ta dauki malfajenta ta mayar saman kanta,ta dauki jakarta ta daura tabi bayansa. Bata sani ba ko shima ya kula,sharewa kawai yayi,ko kuma bai kula din ba.....da gaske ita daya ta lura,yadda mutane keta binsa da kallo a sanda aka ganshi yana kora shanun da ita ke da hakkin kula dasu,yayin da ita kums ke biye dasu a baya,kasan samun nutsuwa tayi kwata kwata,jinta take a daure,har sai da suka isa gida,ya miqa mata sandanta idanuwansa akanta,fuskarsa dauke da murmushi "Sai jaaango?" Ya fada yana sake nazartar kyakkyawan fuskarta "Miyatti" ta amsa masa a gajarce,sai ya jinjina kansa "Alla ɗaudane jamu(Allah ya qara lafiya)kisha magungunanki da kyau" "to Allah jaɓe" ta fada tana jin nauyin mixanin kyautatawarsa a gareta. Ko sanda himu yake nufar gida tunaninta ne fal cikin ransa,kamar yadda murmushi yaqi barin fuska da bakinsa su huta,sosai yake ji cewa yayi gamo da Matar aure,ta kuma zo dai dai lokacin da ya kamata ace tazo din,bayajin zaiyi nauyin baki ko jinkirin shaidawa innarsa,duk da cewa babansu baya nan,amma dai yana da kyau innar ta sani,ta kuma shaidawa baban da zarar ya dawo. Da sallama ya shiga faffadan tsakar gidan nasu,kishiyar mahaifiyarsu wadda asalin sunanta shine rahama....amma sauran dangi da 'yan rigarsu na kiranta da ramatu,su kuma yaran gidan suna kiranta da yuuma,tana duqe gaban murhu,ta kammala kwashe tuwon dare tana wanke muciyar cikin tukunyar tuwon himu ya shigo. Fuskarta dauke da fara'a take amsa sallamar tasa,macace mai matuqar kirki haquri hagen nesa da kuma sanin ya kamata,duk da kasancewarta wadda Allah bai azurtata da haihuwar yaro ko daya ba,amma sam bata kasance mai baqin hali gabyaran mikin nata ba,mutum ce mai sauqin kai,wadda take kallonsu ibrahim tamkar ita ta haifesu,tana kulawa da kowanne daya daga cikinsu,duk da zamantowar safara'u mahaifiyar ibrahim mace mara haquri da biyema zuciyarta a wadansu lokuta,amma yuuma ta danne,suna zaman lafiyar daya sanya jama'a da dama cikin karkarar ke sha'awar zaman nasu,ba tare da sunsan cewa fiye da kashi tamanin cikin dari na zaman nasu haqurin yuuma ne ya qawatashi. Barka da gida yayi mata ta amsa tana masa sannu da zuwa "Inna walaɗon(inna bata nan ne?)" "o'o immoder,one ɓayi e'ummakiɗo(A'ah tana ciki,don bata jima da tashi daga nan ba),kila barci ne ya saceta,don tacemin bata danjin dadin jikinta sosai" kai ya gyada sannan ya sake tambaya "Yaran nan fa?,su safiya?" "inna'onliliɓe,amma ɓeɓadake wartuki(Innar ce ta aikesu,amma suna gab da dawowa)" har ya taka zaiyi gaba sai ya sake tambayarta "Yaushe baaba yace zai dawo ne?" Murmushi ta sake "Yau kuma 'yan tambayar ne a kusa himu?,rana wata yau in sha Allah" kai ya gyada yana murmushi,yaji dadin jin cewa bazai jima ba zai dawo gidan,ya tafi ikko ne da wasu shanunsa zai saidasu,wanda dama.yawanci can yake kaisu,shi kansa ibarahim din yafi zama a can,mafi yawan rayuwarsa ta can ce wajen wani dan uwan baaban nasa,yanzu ma gajiya yayi da zaman can din ya dawo gida yadan huta sannan ya koma,uwa uba kuma sun samu hutun semester,don acan din bai zauna ba yana karatunsa. Ya daga labulen dakin ya samu barcinne kuwa ya dauketa,sai ya sauke ya wuce dakinsa,yayi abinda zaiyi a ciki sannan ya fito ya fara daura alwalar magriba,bai kammala ba innar ta fito tana daura dankwalinta "denattoi ɗa himu(yaushe ka shigo himu?)" Ta fada tana dubansa,ita din duk da bafullatsna ce amma sam ba ruwanta da wannan kunyar da kaara tadan fari "Ban jima ba,na leqo na samu kina bacci,ya jikin naki?" "Alhamdlh,nasha ragowar maganin nan daka taba kawomin kwanaki kafin na kwanta,kaga kuwa har ya fara sakina" "To alhmdlh,hammiyami jula miwarta(bari nayi sallah na dawo)" ya fada yana warware hannun rigarsa,a bakin kofar shigowa gidan sukayi kacibus da qannensa,yammata masu tasowa su biyu,yace maza su shige gida an fara kiran sallah,suka amsa masa amma suna binsa da.kallo,saboda labarin da suka samu a kansa tun a hanyarsu ta isowa gida. Bayan sallar isha'i ya shigo gidan,babu kowa tsakar gidan sai yuuma dake zaune daga bakin kofar dakinta ita daya,gabanta fitilar aci balbal ce,sai qaramar redio da bata rabo da ita saboda jin labarai,sannu da gida yayi mata,ta amsa masa tare da shaida masa abincinsa na wajen innarsa,ya amsa mata yana wucewa kai tsaye zuwa dakin innar,bayajin dadin yadda wasu lokuta safiya da zubaida ke barin yuuma ita kadai,duk da lokaci lokaci zaka samesu wajenta,yana matuqar jin tausayinta,saboda rashin haihuwa abune mai ciwo da kuma sanya mutum cikin kewa da kadaici. Da sallama ya shiga dakin,ya taras dasu sunata hira abinsu dukkansu,safiya zubida da sadam qaramin qaninsu,sannu da xuwa sukayi masa,ya samu waje yana zama "Ra nyam kima,hokkumoki sadam(ga abincinka,sadam mika masa)" inna ta fada,sai sadam din ya mika masa,yaja kwanon ya bude ya fara ci bayan yayi bismillah,ba qaramin son tuwon yuuma yake ba,bama shi kadai ba,hatta da jama'ar gidan,saboda yadda ta iya girki,duk da innar tasa ma ba baya bace. A hankali yake cin abincin yana kuma jefa baki a hirar tasu,saidai fiye da rabin hankalinsa nakan ta yadda zai gayawa inna maganar dake bakinsa,a qa'ida da yuuma zaiyi zancan,amma ya sani idan yayi hakan ransa ne xai baci wajen innar,saboda batason hakan,tafiso kowace magana suke da ita su sameta kai tsaye su shaida mata,itama yuuman tunda ta fuskanci haka,da sunzo sun gaya mata zata ce "Kun gayawa innarku?" Idan sukace a'ah,takan ce "Ku sameta ku fara shaida mata muji abinda xata ce". Sai da ya gama cin tuwon tas ya wanke hannu sanna ya gyara xamansa cikin jin nauyi da kunya yace "iwodi haala kaginmi gaɗen Inna....(akwai maganar da nakeso muyi inna)" "Shine tun daxu kaketa wani mutsu mutsu ka kasa gayamin?,tawi'aayanka,mojetta bi'owaka(idan baka gayamin ba wa zaka gayawa duk duniya?)" Ta qarashe da sigar tambaya tana kafeshi da idanu,yasan me take nufi,sai kawai yayi murmushi yana cewa "Babu" "iminamma(ina saurarenka)" dan jim yayi kadan sannan yace "Inna.....na samu yarinyar da nakeso fa". Zuba masa idanu tayi saboda yadda maganar tazo mata a bazata,bata tsammaci jin maganar ba a wannan lokacin,saboda tuntuni tana da tsari da kuma muradi a kansa,amma duk da haka saita danne wannan a ranta,tace dashi "Emi namma,immoi 'onni?(ina jinka,wacece?)" Kansa yadan shafa kadan sannan yace "Sunanta maimunatu" "Maimunatu ta gidansu laulo" muryar zubaida ta ratsa hirar tasu,da hanzari inna ta juya tana duban zubaida saboda yadda maganar zubaidan ta dauki hankalinta,yayin da himu shima ya juya yana kallon zubaidan saboda baisan waye laulo din ba,saidai idan ita dince yaji dadin yin maganar da zubaidan tayi,saboda baisan ta yadda zai kwatantawa innar ita ba yadda zata fahimta "Da gaske ita kake nufi himu?" "Gidansu na kusa da hanyar fegin maraba" mummunar faduwa gaban inna yayi,tabbas maimainunatun ya hango,take hankalinta yayi mummunan tashi,maimunatu 'yar uwa ga gaje?,gaje dai 'yar inna furaira "Yuuma.....yuuma.....warnano wakka haala kawela(zo kiji wani mummunan labari)" ta fara qwalawa yuuma dake xaune qofar dakinta kiran,abinda ya sanya himu zubawa innar idanu cike da mamakin meye ya gigita innar tasa haka?,har take irin wannan kiran?. "Ku tashi ku fita" innar ta fada tana waiwayawa gasu safiya dake zaune tun dazu suna kallon kallon a tsakaninsu,tsam suka miqe suna masu ficewa kowacce bakinga fal da magana,dai dai sanda yuuma ta shigo dakin a rude "Lafiya kuwa?" Ta tambayi inna tana laluben wajen zama hankalinta a tashe,sai da inna taja wani dogon numfashi mai nauyi ta furzar da iska sannan tace "Yaron nan ne yakeson dauko mana jaraba rana tsaka" sake tashi hankalin yuuma yayi tana duba inna tace "Subhanallahi,jaraba wacce iri?" Kai inna ta gyada cike da jin xafi tace "Wai yarinyar nan maimunatu ya gani yakeso?" "Maimunatu?....maimunatu?" Yuuma ta maimaita sunan tana son tuna aka wace ake magana "Diyam ta gidansu laulo" take yuuma ta fahimta,sunan kuma ya fado mata a rai,saboda ita daya keda sunan kaf rugar,hakanan kuma mahaifiyarta kadai ke kiranta da sunan,sai ta sauke ajiyar zuciya,alamun tashin hakalin da ya taso tun daga zuciya zuwa fuskarta ya fara zagwanyewa "Hankalina ya tashi sosai innar sadam,na dauka wani abun tashin hankalinne" "Yo akwai tashin hankalin da yafi wannan yuuma?""ai abinda yasa nace haka innar laulo.....kaf fadin rugarnan anyi ittifaqi babu yarinyar dake da nutsuwa da kuma kamun kai da tarbiyya irin maimunatu....." "Amma kinfi kowa sanin ainihin wacece ita ko?" "Wannan duk camfi ne ko ince hasashe....duk cikin masu hasashen babu wanda yake da tabbas kan abinda yake fada koda kuwa a gaban Allah ne,dukka abinda al'umar rugar nan keyi ba komai bane illa jahilci zalla da kima gurguwar fahimta gami da mummunan zato,koda ba zato bane hakanne,babu wanda ya taba kama maimunatu da wani mummunan aibu da za'a qita,a karan kanta maimunatu bata da wata matsala ko illa....." Idanu inna ta zubawa yuuma,a hankali a kuma sanyaye tace "Yuuma...kodai don bake kika haifi himu ba kike qoqarin wanke maimunatu gami da kore kowanne aibu daga gareta?" Ba yuuma kawai ba,hatta da ibrahim sai da maganar ta tabashi,qas yayi da kanshi yana jin babu dadi a ransa,yayin da yuuma ta rintse idanu,maganar tana sauka saman zuciyarta da wani irin dafi mai zafi,dai dai maganar take da saukar mashi saman zuciyar tata,duk yadda take zaman kawaici da innar laulon....bata taba gwaba mata magana me zafi akan yaranta ba irin wannan "Kaico!....kaico!" Yuuma ta fada tana girgiza kanta "Inama ace Allah ya bani d'a na cikina wanda yakai shekarun ibrahim....kai koda ace bai qarasashi ba,matuqar ya isa a daura aurensa,da ba shakka na tabbatar miki da cewa magana nake Miki da zuciya daya.....Allah ya kyauta,kiyi haquri bisa shishshigin da nayi miki" yuuma ta fada bayan ta yunqura ta miqe,zuciyarta na wani irin tafasa,wanda tana fita qofar dakin hawaye ya silalo mata. Shuru ne ya ratsa dakin na wucin gadi,cikin ranta innar laulo tana jin kamar bata kyauta ba,wata zuciyar kuma na gaya mata daidai ne abinda tayin,zallar mugunta ce kawai tasa yuuman bada wannan shawarar a gaban himun,bayan tasan kowa gudu da qyamar yarinyar yakeyi,ko ita bata sake ganinta tana hulda da yarinyar ba "Amma inna abinda kika yiwa....." "Kaga dakatamin" inna ta tsaida ibrahim dake Shirin nuna mata rashin dacewar abinda tayin "Kada kace min komai,maganar maimunatu kada na sake jinta a bakinka,domin kuwa ba kai ba,koda wanda na isa na gaya masa yaji ne bazan bari ya aureta ba,bare kai dan cikina,bama maimunatu ba,banason ka sake kawomin maganar kowacce yarinya,na riga na zabar maka matar aure tun shekarun baya.....kaje gidansu maimunatun ka nemi gaje ku dai daita". Tsaf kwanyarsa fa birkice,ta yaya zaizo da maganar maimunatu inna ta umarceshi da auren gaje?,gaje dai da ya sani?,ya akayi suka zama 'yan gida daya ita da maimunatun?,babu kama ta siffa ko dabi'a ko qanqani a tsakaninsu,wanne aibu ne ma wai da innar ke magana a kai da har zai zama hujjar raba sabuwar tarayyar da yanzu aka fara kiwonta tsakaninsa da maimunatu?. *FREE PAGES ZASU KARE NE ZUWA GOBE IN SHA ALLAH,ZAKI IYA BIYAN KUDINKI TA WADAN NAN HANYOYIN* Hafsat umar kabir 2270637070 Zenith bank *Saiki tura shaidar biya ta nan* 07040727902 *Idan katin mtn ne kuma zaki tura ta nan tare sa shaidar biya* 09134848107 *Thanks for choosing zafafa biyar* *_GURBIN IDO_* *LAST FREE PAGE 05* *AREWA BOOKS::HUGUMA* Cikin kwanakin da suka biyo baya gaba daya kusan rabi da rabi na dawowar maimuntu daga kiwon ibrahim ne,wasu lokutan yakanyi gaba wani lokaci kuma tana biye dashi a baya,har sukai gida,ya tayata daure na daurewa ko sharar wajen idan bata samu tayi ba,sudan taba hira sannan ya wuce zuwa gida. Duk da cewa fiye da rabin hirar shi kadai yake abarsa,na maimunatun baya wuce eh ko a'ah. Haka kawai fa tsinci kanta da jin dadin tarayyarsu ita dashi,sai takejin wani canji na zuwa ma zuciya da rayuwarta,gaba daya wannan kadaicin babu shi,tana jin kamar ta samu wani bango da zata raba ko ta jingina dashi ko yaya yake,sabanin daa da bata da wanda zai magana da ita,magana da ake kirame dadi,idan taji magana daga bakin wani to fada ne,idan taji hira akanta to ta tsangwama ce,wani lokaci takan jima kwance duk sanda taje bacci,tana tuno irin hirarrkinsu da ibrahim,wani abun takan saki murmushi ne ta kuma juya ta gyara kwanciyarta. Ta bangaren ibrahim din wani matsayi na musamman yakeji maimunatu na sake damu cikin ruhi da zuciyarsa,a dan zamansu ya fahimci abubuwa masu tarin yawa tattare da ita,ta banbanta qwarai da duka yaran rugar tasu,tana da wata irin nutsuwa da fasahar magana wadda ya jima baiga irinta jikin wata 'ya mace ba,komai nata na hankali ne da sanin ya kamata,yakan zauna yana kallon yadd take iya controlling dabbobinta da baki kawai ta hanyar basu umarni,lokaci dai daiku ne takanyi amfani da sandarta wanda xaiyi wuya ma kaga hakan. Yadda take tausayin dabbobin kamar 'yan adam,bayan dukka alamu sun nuna sun fita samun gata da kulawa,duk da har yanzu bata taba bude baki tayi masa wata magana data shafi gidansu ba,yadda take communicating dasu kawai abun burgewa ne,duk da shima cikakken bafullace ne amma ba kasafai yake ganin hakan ba,lokuta da dama idan ya tsokanetan saidai tayi murmushi kawai,wanda kusan wannan din dabi'arta ne. Ko sau daya himu baiyi nufin zuwa ga gaje ba kamar yadda daada ta buqata,wani lokaci ma sai ya rako maimunatu yake tunawa da batun,saidai yana ganin ba abu bane mai yiwuwa,yana da tabbacin komai zai daidaita da zarar bappansa ya dawo,wanda ya qara kwanaki kan wadanda yace zai dawo,saboda jiran haduwar kudadensa dake hannun mutane. **************Yammacine lis,wanda yake busa wata ni'imtacciyar iska me dadi,yanayi ne da ya yiwa halittu da dama dadi,bawai ga dan adam kawai ba,hatta da sauran tsirrai da kuma dabbobin daketa kai kawo suna kiwo a farfajiyar wajen da ya zame musu wajen yini. Daga can qasan bishiyar idan kakai kallonka wajen,bafullatana maimunatu ce cikin baqin saqinta,zaune saman koren hiramin da himu ya shimfida mata,shi kuma yana zaune daga gefanta saman wani dan mulmulallen dutse da bai cika girma ba. Murmushine ke fita daga saman fuskarta,murmushin da kana kallonsa kasan kunyace cike dashi,ko a iya zamanta idan ka.kalla da kyau kasan a takure take,hannayenta sarqafe cikin juna tana kallonsu,yayin da shi kuma ibrahim ya zuba mata dukka idanunsa yana jiran amsar tambayar daya jefa mata. Wani irin nauyi ibrahim din ke aza mata duk lokacin da ya zaunar da ita irin haka yana karanta mata kalaman soyayya......daga qarshe kuma a yau din ya tirketa kan lallai sai ta furta masa da bakinta tana sonshi,saboda bai taba jin hakan daga bakinta ba. Wani abune kuma ita din da bata jin zata iya gaya masan,kalma ce data ji ta girmi kanta matuqa,koda baya kallonta ba zata iya fada ba,bare yadda yake zaune yana kallonta. ,sirara kuma jajayen labbanta ta motsa a hankali "midelli...yamma tayi" dauke idanunsa yayi daga kanta yana murmushi,duk da yasan yau din sun gota lokacin komawarsun,amma tayi hakanne don ta kaucewa tambayarsa,yana mamakin kunya irin tata kawaici da kuma kamewa,sai ya miqe kawai ya dauki sandarta da a yanzun shike amfani da ita idan zasu koma gida. Kamar ko yaushe ya tayata suka kammala komai,yayi tsaye daga jikin wata rusashiyar bukka dake daura da wajen yana dubanta cikin murmushi "Shikenan,tunda ba zaki bani amsa ba maimunatu zan tafi,sai jaaango?" A kunyace tayi murmushi tana kauda kanta gefe daya,ya sauke qafarsa da ya harde waje daya ya fara takawa a hankali yana barin wajen "Ka gaida gida" ta fada cikin siririyar muryarta da ba kasafai ya fiya jinta ba,sai daya waiwayo cikin jin dadi ya kalleta yana jinjina kai sannan yaci gaba da takawa,hakanan taji kunya ta kamata,abinda yasa ta juya da sauri da nufin shigewa zuwa shiyyar da dakunansu suke. Saidai kuma cak ta tsaya,saboda ganin inna tsaye daura da ita,da alama taji komai ta kuma ga komai. Kallon da innar kawai ta tsareta dashi ya sanyaya mata gwiwa ya kuma sanya mata fargaba me tarin yawa,gabanta ya fara faduwa da wani mugun qarfi,duk da haka ta ari dakiya taci gaba da nufar inda innar ke tsaye tana ci gaba da kallonta "Immoi'onni?(waye wancan?)"innar ta fada a tsawace cike da tuhuma da kuma zargi,yanayin yadda tayi mata maganar ya jefa tsoro a zuciyar maimunatun,ta qanqame jikinta waje guda,tana jiran jin saukae duka daga wajen innar,don wannan din ba sabon abu bane a wajenta "Tambayarki nakeyi waye wancan din?" "Sunansa ibrahim.....ya tayani qaraso da dabbobi gida ne" "Meye hadinki dashi?" Inna ta sake tsareta da tambaya,saboda zargin da ya shiga ranta,taso taha fuskarsa amma kuma haqarta bata cimma ruwa ba,saidai batajin wanda take tunani dinne,don bata da shakka akan alqawari da yarjejeniyar dake tsakaninsu "Babu komai" ta amsawa innar kanta a qasa,tana matse hannayenta waje guda,tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa fat fat "Yauwa.....gwara ki rufawa kanki asiri,ke ta buɗeri ce,shi daya zai iya rufa miki asiri ya aureki,don haka kada ma ki batawa kanki lokaci ki yaudari kanki kice zaki saurari wani,kaf fadin karkarar nan bana jin akwai wanda zai iya daukarki idan bashi ba,koda an samu to yayi miki qarya,saboda haka ki kiyaye" daga haka tayi gaba zuwa garken dabbobin,tabi tana dubasu daya bayan daya tana kuma irgasu kamar yadda ta saba duk sanda maimunatun ta dawo,kai zaka zaci tana duba kaya data bawa qasurgumin barawo ajiya ne. "Wuwuɗandu(ki share wajen)" ta bata umarni tana fita daga garken tayi gaba abinta,duk yadda takai ga gajiya hakanan dole babu yadda zatayi haka ta laluba kayan sharar ta fara gyaran wajen,duk da cewa a dazun kafin su tafi ta gyara wajen,batasan me ya bata wajen hakan ba,duk da tasan ko ba yaro idan innar taso bata wahala,zata qirqiro mata aikin ko kuma wanda yayi kama dashi,duk dai don kada ta huta,bata qaunar ganinta a zaune ko da na minti daya ne. °°°°°°°°°°°°°° A nutse yayi sallama cikin rumfar innar yana yafe da koren hiraminsa,dawowarsa kenan daga sallah sadam yace masa innar tana kiransa. Abinda ya bashi mamaki shine ganinta da yayi a tsaye tana kai kawo daga wancan bangon zuwa wannan,idanunta dake cike da fushi ta daga ta dubeshi,ba tare data amsa sallamarsa ba kai tsaye tace dashi "Joɗa(zauna)" kasa zaman yayi,sai ya duqa daga gefe kawai yana kallonta,ta tako gabansa a hankali tana dubansa "Inaso naji bayan ni wace mahaifiyar kake da ita?" Sosai tambayar ta bashi mamaki,har ya tada kai yana dubanta sosai kafin ya kauda kansa ganin itama shi take kallo,yaro ne shi mai tsananin biyaya,don haka bazai iya hada idanu da daadan ba "Babu daada....amma wani abune ya faru?" Sake baci ranta yayi "Ni kake tambaya wani abune ya faru himu?,ashe ni ba uwarka bace?,ashe ban isa na gaya maka magana kaji ba?,tun a waccar ranar ban rabaka da maimunatu ba?,ban gaya maka babu kai babu ita ba?,shine kasa qafarka kayi wancankali da maganata akan diya mace saboda bani da wani muhimmanci a wajenka?" "Ba haka bane inna..." "To yaya ne?" Shuru ya gifta wanda bai gaza qasa da second hudu ba ".......ko kuwa maganar yuuma ce ta shiga kunnenka fiye da tawa ni mahaifiyarka?" Girgiza kansa yayi da sauri "Ko kadan.....kada ki saka sunan yuuma don Allah daada,ba ruwanta,batasan me akeyi ba tun wancan ranar data fita a dakinki" "Ibrahim!" Ta kirayi cikakken sunansa,abunda ya sake tabbatar masa zata yanke tsatstsauran hukunci ne,kuma kowanne irin hukunci ne hakan zata fadeshi ne ba da wasa ba "Daga yau.....idan ka sake ka sake zuwa inda maimunatu take Allah ya isa ban yafe maka ba,sannan koda bayan raina ka sake ka aureta ban yafe maka ba" qarasa zama dirshan yayi a qasa maimakon tsugunon da yayi,ba qaramin kaduwa da hukuncin nata yayi ba "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" ya dinga maimaitawa kansa a qasa,bai taba zato ko tsammanin hukuncin innar zaiyi tsaurin haka ba "Don Allah inna ki sassauta kiyi haquri,maimunatu bata taba yi miki komai ba,banda......." Tsawa ta dakeshi tana katseshi "Banason na sake jin komai daga gareka,wannan shine hukuncina na qarshe,tashi ka fita!" Ta fada a zafafe tana nuna masa qofa,sai da ya dafa qasa sannan ya miqe "Himu" ta kirashi sanda yakai qofa "Na baka kwana hudu kacal,ka shirya fara zuwa wajen gaje kamar yadda na gaya maka,umarnine nake baka" bayajin xai iya cewa da ita komai,don haka kansa da yayi masa nauyi kamar ya dauki kaya ya gyada mata sannan ya fice daga dakin yana jin jikinsa kamar zazzabi na shirin rufeshi. **********Sake juya rufaffen takalmin danqon hannunta tayi don ta tabbatar dabarar data yi masa zata kaita gida,ita kanta batasan adadin liqin data yi masa ba,wani gurin da garwashin wuta da leda,wani gurin kuma tana samun zaren lilo ta zarge inda yake shirin rabewa dashi. A hankali ta duqa ta ajjiye takalmin a qasa ta zura qafafunta,tadan motsa qafar ta tabbatar yayi,sai ta sauke ajiyar zuciya,tana godewa Allah da ya sake fiddata a yau dinma dai still,takalmin bai mata tutsu ba,batasan ya zata kasance mata duk randa hakan ta faru,itadai shi daya ta sani a matsayin takalmin da take dashi,wanda ita kanta batasan adadin kwanakin ko shekarunsa ba a duniya bare ta iya tantancewa. Sake waiwayawa tayi hagunta da damanta,har yanzu bata debe tsammani da ganin himu ya bullo ba,duk da cewa lokacin zuwan nashi ya gota sosai,tana da tabbacin babban abune ya tsaidashi,saidai tana fatan koma meye ya kasance yana lafiya qalau. Waiwaya tayi sashen wata saniya ke zaune,gefanta jaririn san data haifa ne a dazu jimawa kadan bayan isowarsu wajen,ta tabbatar inna batasan cikin ya isa haihuwa ba,da ba zata bar mata ita zuwa wajen kiwo ba,dole idan lokaci yayi himun baizo ba,haka zata hada da kula da sauran dabbobin,da ita wannan sabuwar haihuwar su wuce gida,yau din tana jin gajiya sosai a jikinta,ita kadai cikin wajen,cikin tsoro da fargaba saniyar tahaihu a wajenta,wanda ita kanta tasan babbar kasada tayi,saboda samuwar matsala ta mutuwar uwar ko abinda aka haifa,dai dai yake da samuwar matsala cikin tata rayuwar,ko daya innar batasan wata aba wai ita asara ba bare haquri da ita idan ta sameta,haka ta dinga kai kawo har haihuwar ta kammala. Saman dan dutsen da himun ke zama ko yaushe idan yazo ta koma ta zauna,idanunta nakan abun hannunta na shirin duwatsu green da jaa,tasa yatsanta guda daya tana wasa dasu,ta warasu wani lokacin ta hadesu,tana tuna lokacin da innarta ta zura mata su,har yanzu lokacin yaqi bacewa cikin idanunta. Ta jima zaune a nan,tana jin wata kewa da kadaici suna shigarta,lokaci lokaci tana daga kai ta dubi yanayin yadda dabbobin ke kai kawo sannan ta sake maida kanta. Karo na qarshe data daga kanta ta tabbatar lokaci yayi da ya dace su koma gida,ta sauka daga kan dutsen a hankali,ta gyara zaman hularta sannan ta dauki sandanta ta fara ratsawa ta tsakaninsu tana hada kansu. A gaba take sanyasu mafi yawancin lokuta,idan taga zasu canza hanya ko zasuyi wani abu ba dai dai ba takan tsawatar musu,suna ji kuma suna fahimta yawancin lokuta,yau dinma haka ne,hannunta na dauke da sabuwar haihuwar da daya daga cikin shanun tayi. A hankali baqaqen lafiyayyun motocin guda biyu ke kutsowa cikin rugar,tana haura duk wani tudu da kwari da kuma kwazazzabo dake kan hanyar ba tare da mutanen dake ciki sunji komai wata jijjiga ko wahala ba da ire iren wadan nan hanyoyin ke dashi a duk sanda mota zata ratsasu ba,hakan ya faru ne sanadiyyar kyau da lafiyar motar,wanda hakan yake da nasaba da irin tsadar da kowacce mota guda daya ke da ita. Motar farko mutum hudu ne a ciki,driver salmanu,sai wani zaune a gefansa hayatu,daga seat din baya kuwa dattijuwar macace,hakimce cikin shiga ta alfarma,kyakkyawar lallausar blueblack din atamfa ce wadda tayi matuqar haska farar fatarta,duk da akwai tsufa tattare da ita,amma yanayin da take ciki na hutu da kuma jin dadi ya hana bayyanuwar tarin shakarunta,daga shekara sittin da takwas,ya maidata zuwa 'yar shekara hamsin,idan ka cika qwaqwafi kuma ka qara mata da uku,hankalinta na ga window din motar,tana duban hanyoyin da suke wucewa,wanda sukanyi gamo da mutane jifa jifa,duk mutumin da suka gifta sai ya bisu da kallo,saboda abune baqo a wajensu,zasu iya irga sau nawa suka samu labari ko sukaga shigowar mota rugar tasu,wasu sukan cika da fargabar su waye suka shigo musu?,wasu kuma kyau da motar ke dashi ne yake daukar hankalinsu har sai tayi nisa ta bacewa ganinsu. Daga gefan dattijuwar kuwa kyakkyawar matashiyar budurwa ce wadda duka duka ba zata haura shekara ashirin ba a duniya,shigarta kadai zai gaya maka cewa ta fito daga gidan ilimi wayewa da kuma wadata,kacokam ta tattara hankalinta ga wani littafi dake da shafuka masu dan dama,da alama nazari takeyi. "Salmanu........saukemin gilashin nan.....naga alama wannan baqin abun da kuka lafta masa bazai bar idanuwa suyi kallo yadda ya kamata ba" ta fadi tana hade gira. Karaf matashiyar ta daga kanta daga kan littafin "Haba anni....me kuma za'a sauke miki kiji?,an kunna ac ne fa,ta yaya za'a sauke glass,kuma ta hakan ma ai ana ganin komai,tunda ba dare bane" harara ta juyo ta watsa mata "Ke....kiyi ta kanki,ni ba dake nake ba,toke da wanne mataccen idon ma kike iya gani daga nan din?,idon da komai za'ayi saida gilashi?,salmau zaka saukemin ko kuwa?" "Za'a sauke anni" yayi maganar yana sauke mata da hanzari kamar yadda ta buqata. Sai da aka sauke mata gilasan tas sannan ta sake matsawa jikin window din tana fara'a "Yawwa,yanzu naji batu,amma daa an qunshe mu kamar 'yan kidnapping,ni ba baqin hali gareni ba da kullum xan fita zance a rufeni cikin gilasai" sarai matashiyar ta fahimci da ita take,kuma idan da sabo ta saba ko kuma tace sun saba da halin anni,duk wanda ke zaune da itama ya riga da yasan halinta sarai,don haka sai ta maida mayafin da yake kafadarta zuwa saman kanta,ta kuma rufe littafin saboda hasken ya mata yawa,karatun bazai mata dadi ba ta maida jakarta,ta ciro wayarta a maimakon littafin ta soma qoqarin kunna data,saidai yanayin rashin network mai kyau ya hana wayar tata amfani,dole ta maidata itama jakar. "Ma sha Allah,kai ma sha Allah,lallai na jima rabona da adamawa,wai" anni keta fadi,fuskarta na nuna alamun jin dadin tafiyar sosai. A dan rude maimunatu ta maida hankalinta ga marabar hanyar da shanunta ke tsallakawa saboda jin wani sauti,hango motocin suna tahowa yayi matuqar daga mata hankali,na farko yadda zata tsaida dabbobin da sukayi nisa da tsallakawa ta bawa motocin dama su wuce,na biyu kuma motocin sunyi matuqar sanya mata fargaba da tsoro kamar yadda suka sanyawa mutanen da suka baro a baya,su waye a ciki?,me sukazo yi cikin rugar tasu?,wadanne irin motocine wadan nan da sam bata taba ganin koda me shigen kamarsu ba?. Yadda suke sake kusanto inda suke ya sanyata yunqurawa da hanzarinta ta fara bawa dabbobin nata umarni da dukka salon da tasan suna iya karbar umarni da hani daga gareta,tanayi tana kutsawa ta cikinsu tare da dan daga muryarta. "Kai salmanu......dakata" anni ta fada da sauri,idanuwanta suna sauka akan maimunatu,sosai ta zuba mata idanu cike da mamakin yadda take iya bawa dabbobin umarni da baki take kuma iya sarrafasu ba tare da takai duka ma ko daya daga cikinsu ba,idanun anni ya sauka ga dan qaramin dabbar dake hannunta,fari qal dashi sabuwar haihuwa,abinda yaja hankalinta kenan zuwa ga garken dabbobin,ta dinga binsu da kallo daya bayan daya "Ma sha Allah,wadan nan dabbobin gaskiya na qwarai ne,sun samu kiwo da kulawar data kamata" "Abinda nake fada a raina kenam hajiya yanxu hajiya,babban abun mamakin yadda qaramar yarinya kamar wannan take iya kula dasu gaba dayansu" cewar hayatu shima idanunsa akan maimunatu "Bari hayatu,kaga inda ake mata,ba irin 'ya'yanmu ba cima zaune da komai suna zaune ake musu" anni tayi maganar tana tabe baki. Dariya ce taso qwacewa matashiyar amma ta danneta,sai murmushi da ya fita a fuskarta,yayin da hayatu da kuma salmanu suka dan dara kadan,saboda sunsan da wadda take,a tsakaninsu suka dinga tattaunawa,har zuwa sanda maimunatu ta ratsa ta gaban motocin suka wuce da dukka dabbobin,tana dan duba da kuma waiwayen motar tana mamakin yadda suka dakata mata suka bata dama ta wuce. Ajiyar zuciya ta sauke me qarfi bayan data tabbatar sun tsallake lafiya,abinda ya taba faruwa da ita shekarun baya bai sake maimaita kansa ba,wanda ita daya tasan bala'i da masifar daga fuskanta a sannan,har yanzu tana iya tuna sanda motar ta taho a guje,bata kuma damu data tsaya ba ganin dabbobi suna qetarawa,tana hango sanda motar ta banke dan dalonta da take matuqar ji dashi,ya zube a qasa jini na fita ta hanci da bakinsa,ta bishi da gudu ta tsugunna a gabansa tana kuma saboda ta tabbatar bazai tashi ba,taji mugun cin birkin da motar tayi,da fadan da wata murya ke mata tsaye a saman kanta,fadan da yafi kama da a dakeka a hanaka kuka saboda cikin xafi da fadar maganganu marasa dadi ake yinsa,abinda ya sanyata daga kanta ta dubi.mai maganar. Kalmomin da zata gaya masa masu zafi take nema amma ta rasa,saboda ita din ba gwanar rashin kunya bace,bata ma iyata ba sam,to dawa zatayi bayan dabbobin sune qawayenta?,abu na qarshe da take ganin xata iya shine watsa masa harara gami da tsaki mai nauyi,kafin ta sauke kuwa aka sauke mata wani zazzafan mari da ya sanya wuta ta dauke mata gaba daya,ta daina gane komai,bata tashi dawowa hayyacinta ba sai bayan wani lokaci. Ko a yanzun data tuna sai data runtse idaunta,tana tuna zafin marin saman fuskarta,abinda ya biyo baya kuwa ta gefan inna azaba ce ta cita mai yawa,bata damu da yadda fuskarta ta tasa ba saboda marin data samu akan abinda ita ke da gaskiya,ta tattara laifin gaba daya a kanta,tare d adora alhakin mutuwar dan maraqin saniyar a wuyanta. Ajiyar zuciya ta sauke sanda suka iso gida,kamar kowanne lokaci ta daga murya ta sanarwa innar ta dawo,bata ajjiye dan jaririn a hannunta ba sai data qaraso ta miqa mata shi,bakinta har kunne,kai kace jika aka haifa mata na dan mutum "Dama kinsan ta kusa sauka amma baki garzayo kin kirani ba?" Innar ta fadi haka cikin tuhuma,bata amsa mata da komai ba,itadai tana duqe tana daure wasu akuyoyi,banda abu irin na dan adam,ta samu uwa da dan lafiya,bata damu da yi mata sannu na wahalar datayi da naggen ba har ta sauka lafiya,ta buge fa tuhumarta,wanda tayi imani cewa inda ta barta a can ta taho kiranta wani abu mummuna ya faru,lallai ba zata daga mata qafa ba. Tunda taji maimunatun tayi shuru tasan ba zata tanka mata ba,ita kanta ta santa da wannan halin,a wasu lokutan idan tayi mata irin hakan,yaxo akan gabar da take cikin fushi ko takejin haushinta,kamata take ta nada yadda ranta yayi mata suga. *Daga yau free pages sun qare,paid pages zasu biyo baya in sha Allah,hanzarta biyan naki kudin koki bibiyemu ta shafukanmu dake arewabooks* ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* 😄😄😄😄😄😄😄 *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 *06* "Alhmdlh" anni ta furta sanda motocin suka faka a qofar ginin gidan bappa labaran,mahaifi ga ibrahim,qafafunta ta zuro qasa tana fadin "Hasbiyallahu la'ilaha illa huwa alaihi tawakkaltu wa huwa rabbul arshil azim" kana tayi bismilla ta yunqura,gaba daya qafafuwanta sun riqe,jikin tsufa ga kuma zaman mota "Salmanu ku jirani,idan mun gama gaisawa inajin tare daku zamu fita can cikin gari na duba masauki" cewar matashiyar,dakatawa da tafiyar da anni keyi ta waiwayo tana yamutsa fuska "Laila....me naji kina fada?,au dama ba rakiyar Allah da ma'aiki kika yimin ba?" Shaf ta manta da annin tana jinta,fuska tadan kwabe "Kuma me nayi anni?,duk wannan dawainiyar?,ina cewa flight zamu bi kikace kefa sai mota,amma ban fasa rakoki ba" "Yo rakiyar banza da wofi?,tunda ba zaki iya kwana a gidan ramatu ba" hannayenta laila ta hade waje daya "Shikenan,zan kwana abar maganar" don sarai ta sani mitar annin ba abu bane me kyau ko dadi ba,duk da hakan taci gaba da takawa zuwa cikin gidan tana ci gaba da mitar,ta dauke kanta tana sake ajiyar zuciya,idanunta na sauka ga yaran da suka fara baibayesu suna kallonsu,sannan ta dubi su salmanu "Kuyi tafiyarku kawai,amma ina buqatar ruwan sha" "Akwai ai za'a samu" yahaya ya amsa mata,sai ta juya tana bin bayan anni zuwa cikin gidan. Dai dai lokacin da yuuma ke qoqarin daura alwalar sallar magariba,wadd ta saba duk lokacin da tayi girki ta kammala,tana hadawa da alwalarta sanna ta wuce daki. Cikin mamaki ta ajjiye butar data gama zubawa ruwa ta waiwayo da hanzari jin muryar annin "Yafendo?,yafendo yau kuma ni kika tuna?" Yuuma ta fada cikin madaukakin farincikin da ya kasa boyuwa a fuskarta,kana ta kasa jiran qarasowa anni,ta taka da kanta ta cimmata a tsakiyar gidan "Nice rahama,yau dai Allah ya qaddara ganawarmu,kimin aikin gafara" anni ta fada tana kama hannun yuuma,murmushi ya kuncewa yuuman,ta shiga marabtarsu,dai dai sanda aka fara shigowa da kayan amfani na abinci,wanda ya zamewa anni kamar ibada duk sanda zata ziyarcesu,takan sauke musu kayan abincin da sai su kusa shekara basu qare ba,mota biyu takeyi,daya ta kayan abinci,daya kuma wadda zata taho a cikinta. Hajiya maryama wadda ake kira da anni,tamkar uwa take a wajen yuuma,saboda da ita da mahaifiyar yuuman 'yan mata zarr suke,'ya'yan yaya ne(namiji) da 'ya'yan qanwa,kakanninsu daya,a turance ake cewa(cousins),tun zamanin yammatanci akwai shaquwa sosai tsakanin anni da mahaifiyar yuuma,uwa uba sunansu daya,maryam da maryam,kakan yuuma asali dama bafullacene,mazaunun ruga,koda ya tashi aurar da diyarsa maryam saita auri jinsinsu,mahaifiyar yuuma a ruga tayi aurenta kamar yadda ta taso a nan,yayin da daya maryam din anni tayi aure cikin gari itama kamar yadda ta rayu a nan,saidai duk da hakan zumuncinsu bai yanke ba,duk sanda dama ta samu suna ziyartar juna su da 'ya'yansu,har zuwa sanda suka fara tara zuri'a,rayuwar mahaifiyar yuuma batayi tsaho ba Allah ya karbi abarsa,a sannan duka duka yuuma din bata wuce shekara sha biyar ba a duniya,sosai anni taso ta riqe yuuma ta kuma aurawa danta na fari,saidai kuma mahaifin yuuma yaqi bada ita,saboda ita daya ce 'ya mace a wajensa,dole ta haqura,taci gaba da kulawa da ramatu(yuuma) da kai mata ziyara har zuwa sanda aka aurar da ita ga bappa labaran,ita ta yiwa yuuma komai kamar diyar cikinta,saboda ita dinma Allah bai bata diya mace ba,sai maza da take dasu guda hudu. Tun daga sannan takan ziyarci yuuma akai akai,ramatu yuuma ta zama 'yar gata,batayi kukan rashin mahaifiya ba ko kadan,saboda anni ta tsare mata komai,bata da matsala ta kowanne fanni na rayuwa,tun daga sutura zuwa cima,ko yaushe anni naka hanya wajen yo mata aike koda bata zo ba. Sanda shekaru suka fara tafiya yuuma bata haihu ba hankalin anni ya tashi,ta kashe kudi sosai akayita duba yuuma,saidai ba wata damuwa data nuna wadda zata hanata haihuwa bare a maganceta,daga qarshe anni taso fita da ita waje,don tana cikin sukunin rayuwa sosai annin,dukka yaranta ba wanda bai zama wani ba cikin garinsu na gombe amma yuuma tace ta barwa Allah,kome za'ayi idan haka Allah yaso ganinta ba wanda ya isa ya canza mata qaddararta,hakanan dole anni ta haqura,da kanta yuuma ta baiwa bappa labaran shawaran qaro aure,da farko yaqi amma ta matsa ganin cewa shi ba abinda ya nuna bazai iya haihuwa ba,bai kamata ta rageshi ba,daga bisani ya haqura,ya laluba ya zabo karimatu mahaifiyar himu,sanda tazo gidan itama sai data shekara biyu sannan ta samu cikin Ibrahim,bayan ta haifeshin ma sai daya kusa shekara bakwai ta haifa safiya sannan xubaida,sai auta sadam. Ramatu macace mai tsananin haquri da hangen nesa,ita kanta fureran tasan da haka,shi yasa itama take qoqarin kiyaye wasu abubuwan kada ta shiga haqqinta da yawa,saidai kuma Allah ya jarabceta da son 'ya'ya,sam bata iya yiwa kowa kara a kansu,tun daga sanda bappa yace zai dauki ibrahim ko safiya ya baiwa yuuma daadar himu ta runtse ido ta dunga diga rashin mutunci sai yuuma ta sake kiyayewa,kyautatawa da nuna kulawa da duk uwa zata yiwa danta idan ya ratso tsakaninta dasu tana musu,ta daukesu kamar yaranta,amma ta kiyaye duk wani abu da tasan zai bata ranta ko yaja musu cece kuce da furera,abunda yasa xaman nasu ya sake dadi kenan,zaman lafiya kuma ya wanzu tsakaninsu,duk da wani lokacin daadan himu kan dan taba,amma hausawa sukace idan kace wargi waje yake samu,kuma sai bango ya tsage qadangare ke samun qofar shiga,dole itama wasu abubuwan fureran ke kiyayewa. Fadin irin murnar da yuuman a yau ta tsinci kanta ma bata bakine,saboda anni tadan kwan biyu batazo mata ba,ba kasafai yuuma ke zuwa wajen anni ba,saboda bappan mutum ne mai kulle sosai,itama anni bata zafafawa saboda tasan ya tsarewa diyarta komai,yayi mata riqo na amana bai barta ta wulaqanta ba,sannan ita annin a yanzu babu nauyin kowa a kanta,sakamakon mijinta ya kwan biyu da rasuwa,don haka kafin ma yuuma taje ita taje mata. Yuuma bata dubi dare daya fara yi ba,haka ta tashi takanas ta yiwa anni sabon girki,cikin cimarsu ta fulani da tasan annin tafi so,a ranar kusan raba dare sukayi suna hira,sai gab da zasu kwanta anni tace da ita "Wajen fa labaran nazo....." "Lafiya yapendo?" "Lafiya qalau ramatu,shanu nake da buqata zan qara cikin gidan gona ta,wancan yaron hamdan naso aikowa,naga zai batan lokaci nace gwara nayi tattaki nazo da kaina" murmushi yuuma tayi,tasan dramer din anni da jikokinta sarai,takan gani idan taje musu,annin irin matan nan ne da basa daukan raini,bata da haquri akan abinda tasan kan gaskiyarta take,amma tana da matuqar kirki da kuma tausayi "Aiko dai bappansu gaba daya dabbobinsa na garin yayi kudu dasu,kwana goma yace zaiyi ya dawo kinga muna ta zuba idanu shuru,amma naji suna waya da himu yace nan da jibi ko gata zai dawo,saidai ko ki tsimayeshi,cikin rugar nan nasan zai duba miki irin wadanda kikeso din" "Kash.....kuma sai da nayi wannan tunanin,amma bari mu gani,Allah yasa ya dawo kafin na wuce,don kwana uku zanyi,ranar litinin zan koma ga likitan qafata abuja" "Har abuja anni?" Yuuma ta fada tana kama baki,baki anni ta tabe "Ina zaman zamana rigimammen yaron nan ya hadani da zirga zirga,duk kusan qarshen wata sai yasa an sakani a jirgi ba gaira ba dalili na tafi ganinsa,nace ya canzamin ya kafe,wai duk nigeri shine lamba daya.....kijimin qarya ramatu" anni ta qarashe fada tana yatsina fuska da tabe baki. Murmushi yuuma ta sake tana kada kai,tana matuqar sha'awar yadda suke kula da anni,tana jin cewa dama ace itama tana da arziqin da zata ramawa anni koda dan kadanne cikin irin alkhairanta gareta "Tunda ya fada ai hakanne anni" kashingida tayi kan lallausan katifa da bargo da yuuma tayi mata shimfida da ita "Ke rabu da shi ramatu,bokon tasu ma ta wannan qarnin tafi qarfin hankalinka,ke bakya ce sunyi muhammadiyya ba" anni ta fada tana fadawa wani tunani can,wanda har sai da yuuma ta ankara "Yanzu anni har yau baki bar sana'a ba?" Idanunta ta bude sosai tana kallon yuuma "Ramatu,kome arziqin mijinki jikoki da 'ya'ya kada ki kuskura kice zaki rabu da sana'a,duk tsiya naka naka ne,koda ba'a rageka da komai ba,amma naka yana da dadi" kai yuuma ta jinjina tana gamsuwa da zancan anni,tun tale tale anni bata saba da zaman banza ba,har kawo yau da babu abinda ta nema ta rasa,ko rai tace tana so idan ana siyar dashi za'a siya mata,amma bata daina nema ba,tana da makeken gidan gona,wanda tafi ji dashi fiye da komai nata. Tun suna hira sama sama har bacci yayi awon gaba da anni,sai a sannan yuuma ta gyara nata wajen ta kwanta itama. *_WASHEGARI_* K'arfe takwas na safe yuuma ke dosar dakin daada dauke da turamen atamfa gudu hudu a hannunta da shadda ta maza yadi goma,sai takalmi na maza me kyau wanda ta tabbatar zaiwa ibrahim. Da sallama ta daga labulen dakin daadar,safiya dake zaune tana shan kunu ta amsa mata tana gaidata,dai dai lokacin daada ta fito daga uwar dakinta tana daura zani,kafadarta saqale da hijabi. Gaisawa suka fara yi da yuuma sannan ta'ajjiye mata kayan "Gashi inji anni" "Too.....anni bata gajiya,to Allah ya amfana ya qara arziqi" daadan ta fada cikin farinciki,mutum ce dake matuqar son ka yiwa 'ya'yanta alkhairi,safiya dake shan kunu tataso itama tana daga atamfofin tare da fadin "Bara na zaba tawa kafin zubaidata iso ta dauke wadda tafi kyau......gaskiya anni nada kirki,bata gajiya" murmushi yuuma tayi ta miqe,har takusa da qofa ta juyo "Af.....niko daada nace ba,ko ibrahim ya gaya miki inda yaje ne?,tun jiya anni keta tambayarsa,kuma kamar banga shigowarsa gidan nan ba tun shekaran jiya,abincinsa ma sai da safen nan na hada a dumame" tana shirin saka hijabinta ta amsa mata "Eh.....na turashi gidan sukaina" "Sukaina?" Yuuma ta maimaita a ranta cike da mamaki,saidai ba kasafai take magana akan wasu abubuwan da daada ke yankewa kan yaranta ba "Ayyah...to Allah yasa zasu hadu,don jibi annin zata koma" "Ba lallai gaskiya,inajin sati zaiyi acan kafin ya dawo" "To ba laifi" yuuma ta fada tana ficewa,kanta ya daure tamau,sukainan yayar furera ce,bata da kirki ko kadan,masifaffiya ce ta bugawa a jarida,tana aure ne a wani qauye dake maqotaka da rugarsu,ta yaya za'a tura saurayi kamar himu gidan yayi kusan sati?,duk da itama tana da samarin yara kamarshi,amma kuma tafiyar ai ba ta radin kansa bane,kamar wani qaramin yaro?,da wannan tunanin yuuma ta koma dakinta,inda tabar anni da kuma laila wadda ke jira a kawo mata qosai da yuuma ta bayar a siyo mata,tace shi take sha'awa,tunda suka tashi da safen take jiyo qamshinsa. Suna tsaka da hira daada ta shigo a shiryenta tsaf,suka gaisa da anni sannan tayi mata godiya daga bisani tace "Zanje na dawo yuuma,ba dadewa zanyi ba" kallonta yuuma tayi cike da mamaki,ina zata da safen nan,uwa uba kuma ma kusan dokar bappa ce,basa fita unguwa a gidan matuqar ya tafi kudu irin haka sai ya dawo,kamar anni tasan tunanin da yuuman take sai tace "Labaran ya sassauta tsaurin nasa kenan?" Tayi maganar tana dariya. Kai daada ta kada fuskarta na nuna zallar damuwa "Ko daya anni,dole ta kama na fita ne,zanje na yiwa wata yarinya data nacewa himu gargadi,waye zaiso hada iri da irin tsiya irin jaraba",laila dake dan sauraron voice note na watsapp ta earpiece din dake kunnenta sai ta zareshi,ta miqe ta zauna sosai tana kallon daada,saboda yadda taji maganar banbarakwai,ita kanta anni dake rayuwa cikin tsakiyar birni,cikin ahali da muhallin da wayewa da kuma boko suka yiwa katutu sai data ji maganar bawai "Tooo....ikon Allah,to....abi a sannu dai,Allah ya maganta mana" "Ameen ameen,sai na dawo" "Allah ya kiyaye" yuuma ta amsa mata. Shuru yuuma tayi tana juya batun cikin ranta,me yasa daada take haka?,akan yaranta gaba daya idanunta suje rufewa?,yanzu Allah ne kadai yasan idan taje me zasu aiwatarwa da yarinyar,tunda ta riga data sani,innar laulo qawace kuma aminiya a wajenta,ita kanta banda ubangiji ya riga da ya qaddara tafi qarfinsu,da ba qaramar wuya zata bata ba ta hannun daadan. "Wai....nace ba" laila ta fada tana duban yuuma,sai ta maida hankalinta ga laila "Wai daada kuwa cikakkiyar bafulatana ce yuuma?" Murmushi yuuma tayi,tasan me lailan ke rayawa cikin ranta "Gaba da baya,har gwara ni innata itama ruwa biyu ce,amma ita babu sirki" Tun gabanin lokacin tafiyarta kiwo yayi yau din ta shirya,da wurwuri tayi wanka don kada innar laulo ta farga ta hanata yi,ta gyara jikinta sosai,ta kama jelar gashinta ta nannadesu tayi musu wata lanqwasa me qawanya me kyau,hatta da duwatsun kwalliya na kanta da hannunta sai data qara wasu,ta sake fita bufalatana zam. Can qasan ranta takejin cewa tana yin wannan kwalliyar ne duka saboda ibrahimu,tana ji a jikinta zaiyi wuya ace yau din baizo inda take ba,saboda yaune kwanaki uku suka cika bata ganshi ba,bata saurari wani abincin safe ba,tunda ba ita zatayi ba yau,ta cika gorarta da nono wanda ta tatsa ta barwa innar laulo xatayi aikinsa za'a fiddashi kasuwar qauyen dake maqotansu wadda take ci yau. Tun kafin innar ta tashi ta kada dabbobin kiwo,yau fes takejin zuciyarta,da wani nishadi na daban,ba kuma lallai ka fahimci haka ba,amma idan ka kalli fuskarta da kyau xakaga akwai banbancin yanayi a tattare da ita. Wajen daya zame musu gurin zama ita da ibrahim din ta koma ta zauna bayan ta gama duk abinda ya kamata tayin,lokaci bayan lokaci tana daga kanta zuwa sama,ta wurga kallonta hagu da dama,tana ji kamar ibrahim din yana hanya,kamar yana tahowa inda take. "Kin fara son ibrahim ne?,me yasa zuciyarki ke canzawa?" Ta yiwa kanta wannan tambayar karo kusan na uku kenan,sai ta girgiza kanta a hankali,har yanzu batace ga dalili ba,amma rashin zuwan ibrahim din a kwana uku rak sai takejin kamar tans komawa izuwa wata duhuwa ne data fita ta bari. Duk da yadda lokaci ke qara jaa amma bata saare ba,bata rasa qwarin gwiwarta ba,taci gaba da dube dube,har daga bisani ta miqe daga wajen,ta fara kewaye cikin dabbobin,wai ko hakan zai sanya lokaci yayi gudu,ya kusantata da zuwansa wajen. "Maimunatu na!" Kakkaurar muryar mai cike da kaushi ta doki kunnenta,ta kuma zama musaya ko ince madadi ga muryar ibrahim da take ta dako da fatan ji. Buɗeri ne,ba shakka shine,saboda shi daya yake mata wannan kiran mafarautan,kiran dake sanya zuciyarta luguden bugu,ta sauke sandarta a hankali tana nufin juyawa zuwa gareshi,saidai kafin ta waiwaya din har ya iskota ya sha gabanta,taja baya da sauri saboda yadda kusancin dake tsakaninsu yayi qanqanta da yawa. Fuska ya hade yana kallonta "Meye na ja da bayan?,kin manta ke din tawa ce?" Ya fada yana nunata da yatsa,kau da kanta tayi,idanunta suka sauka ga qafarsa dake cikin huffaje,saidai shi kansa huffajen yayi daqal daqal dashi,kamar yadda sutturar jikinsa take cidin cidin,sau tari tana mamakin uban tulin qazanta irin naa buderi,abune me matuqar wuya ka sameshi fes cikin tsafta "Amma kinyi kyau maimunatuna......ina fata babu wanda ya kallemin ke" yayi maganar yana washe baki,kanta ta daga a hankali tana duban gefe da gefanta,tana fatan kada Allah ya kawo Ibrahim a yanzu har sai buderi ya wuce,tasha jin alwashi daga bakin buderin na cewa,duk randa yaga wani ya rabi maimunatunsa,wala shakka sai ya sha jininss,tana kyautata zaton wannan na daya daga cikin dalilan daya sanya babu wanda yake mu'amala da ita "Me kike nema kuma?" Ya fada yana hade rai,kai ta girgixa "Babu komai" amsarta tasa ya saki fuska "Na sani,kinfi kowa hankali cikin 'yammatan rugar nan,nasan babu wanda zaki kula,ungo wannan" yayi maganar yana miqa mata wata leda. Babu batun ma tace ba zata karba ba,don kuwa bata baki ne,don haka ta saka hannu ta karba tana cewa "Na gode" "Yauwa,medillu,dan men waratam?(zan tafi,yaushe zanzo?" Mummunan faduwa gabanta yayi,kada dai xancan da innar laulo ke gaya mata ya tabbata,buderi..... Buderi ne zai fara zuwa tadi wajenta? "Ban sani ba" sandarsa ya wulwula sama ya caketa a qasa "Shikenan,ni xan saka rana da kaina" sai ya juya abinsa ya fara tafiya,dama can shi din ba mutum ne da ya iya yin sallama ba,da ya gama abinda ya kawoshi xai saka kai ya wuce abinsa,har ya dan bata rata sai taga ya dawo da tsaya a gabanta "Baki taba cewa kina so ba maimunatu,ate ayyam?,ayid'iyam?(zaki aureni?,kina sona?)" Banbarakwai taji maganar tasa,ta kuma rasa amsar da zata bashi,tana matuqar tsiron buderi,batajin xai kasa maketa a wajen idan tace bata sonshi,amma kuma idan tace tana sonsa din tayi masa qarya,sannan yaudara ta shigo ciki. Dariya ya bangare da ita "Ja'ira,kunyar gayamin kikeji kenan.....shikenan,idan nazo saiki gayamin tunda zuwan dare ne,bana ganinki sosai" daga haka ya juya abinsa yana waqar tauri.irin ta matasan fulani yana cilla sandarsa. Baya taja a hankali ta jingina bayanta da bishiyar dake wajen,ta sauke nannauyar ajiyar zuciya tana lumshe idanunt,sannan ta saki ledar hannunta a hankali ta sulale zuwa qasa. A matakin rayuwarta gaba daya ba zata iya dorar da komai ba,ba zata iya fadin meye ainihin rayuwa ba,kamar yadda ba zata iya fadin me rayuwa ta qunsa ba,meye manufar tata rayuwar?,me ta cimma?,me takeso ta cimma?,tabbas a karan kanta tasan cewa akwai abubuwa da dama da takeso ta cimma,tana da mafarkai da burika masu yawa irin na kowanne dan adam,saidai ita kanta batasan wadanne ne burikanta ba,me takeso ta cimma din,dukka bata sani ba,rayuwata qwaqwalwarta dama komai nata na tattare ne a waje daya,a yanzun kumma innar laulo ta dauko hanyar da zara qara ruguzata zuwa pieces gaba dayanta,aure da buderi?,me hakan yake nufi?,wanne buri ne a ran innar da takeso ta cimma?. Ta jima a haka kafin ta iya bude idanuwanta,dukka wani fata da take dashi na ganin ibrahim ya fara zagwanyewa daga zuciyarta gaba daya,ganin yadda lokacin da ya dace tabar wajen zuwa gida ya gabato,jiki a mace ta miqe daga jikin bishiyar,saidai tana taku biyu takalminta ya katse "Innalillahi" ta fada gabanta yana faduwa,ta duqa a hankali da zummar daukoshi,sai tayi arba da ledar da buderi ya kawo mata wadda ta jima da faduwa a wajen,ta sanya hannunta a nutse ta budeta,sai tayi arba da gasashen naman daji,cikin tashin zuciya ta dauki ledar gaba daya tayi wurgi da ita can cikin daji,sannan ta dauki takalminta ta duba da kyau,ya gama moruwa,bataga laifinsa ba,saboda yayi mata iyakar qoqari,bata da wata sauran dabara data rage mata,abu dayane a yanzu yayi mata saura shine ta cire dayan ta dauresu a qugunta,sannan taci gaba da tafiya da zallar tafin qafarta tana fara hade kan dabbobin,tanayi tana takatsantsan kada ta taka qaya. 07 Tun batayi nisa ba gaba daya qafafunta taji sun daddaure saboda tsakuyiyin da take takawa,wani gurin harda cabalbalin daya cakude da ruwa da qasa,tuni ta jima da sanin cewa ba qaramar rahama bane takalman a gareta,rashinsu a yan mintuna kadan yasa fa fara dandana kudarta,bata kuma san sanda zata sake mallakar wasu ba. A hankali motarsu daada ke kutsawa rubibbiyar hanyar mai yawan gargada,kamar yadda sukazo a yanzunma su hudune,saidai yanzun akwai qarin saddam da zai musu rakiya,a hanyarsu ta zuwa ziyara qauyen dake kusa da rugar ummarun. Cikin motar tattaunawa suke kan yadda gwamnati tayi banza da nuna halin ko in kula da jama'ar dake rayuwa a irin wadan nan muhallan,babu ruwa ba wuta babu hanya me kya bare azo ga maganar tsaro "Subhanallah" salmanu driver ya fada yana taka burki sanda shanun suka fara keto burtalin xasu wuce,salmanu ya kalli agogon hannunsa yana cewa "Aqalla sai sun kusa minti biyar ko takwas suna wucewa,shi yasa tun dazun nake sauri mu wuce kafin su iso" "Wai daman kuna iya kula da dabbobi babu duka?" Laila ta fada cikin mamaki,idanunta nakan maimunatu dake koro shanun daga can baya "Qalilan ne gaskiya,kiwo yana da wuya fa adda laila" maganar data ja hankalin daada,ta daga kanta zuwa ga sashen da maimunatu take. Ido ta zuba mata sosai cike da mamaki da kuma burgewa,gaskiya sadam ya fada ba kowane ke iyawa ba,kula da dabba koda guda daya ne abune mai matuqar wahala,sai mutum me haqurin gaske da kuma tausayi,bare wadan nan da sun haura talatin,banda akuyoyi,yarinya qarama irin wannan me qananun shekaru,ita daya babu mataimaki,zata iya cewa bata taba ganin wannan ba,koda akwai din sai jarumar mace mai kamar maza,wadda taga jiya ta kuma ga yau. Idanun maimunatu nakan motar sanda ya rage ita daya ce zata haura hanyar,idanunta cike fal da fargaba da tsoro,karo na biyu kenan da taga motar,amma sai take ga kamar abinda ya faru da ita shekarun baya zai sake faruwa da ita,sassanyar ajiyar zuciya ta saki sanda taga ta tsallaka,dai dai lokacin da anni ta sauke idanunta ga qafafuwan maimunatu,mamaki ya cikata ganin yadda take ratsa wajen da zallan qafarta ba takalmi. Ta buda baki xatayi magana ta jiyo sautin maimaunatun "Wayyo Allah" tayi maganar a matuqar jigace tana duqawa zuwa qasa tana duban tafin qafafunta "Tsaya salmanu.....dubamin me ya samu yarinyar can" anni ta tsaida salmanu dake shirin tada motar,wajen suka kalla su duka,laila tayi kamar zatayi magana amma sai ta fasa kada qilu ta jawo bau,seat belt din jikinsa ya zare ya bude murfin motar ya fita,bai wuce minti daya ba ya dawo "Kaya ce ta shige mata qafa,ta huda wajen sosai,amma naga ta zareta ma" "Garin yaya?" Wajen da take salmanun yakalla "Qafarta ce ba takalmi,dana tambayeta yana ina sai tace ya tsinke ne" "Ina silifa din nan da nace a sakaminsu a mota?,daukomin daya a ciki" ta fadawa laila,daukowa laila tayi ta miqowa annin "Bawa salmanu yakai mata ta saka" hannu salmanun ya saka ya karba ya juya yakoma indatake,zuwa sannan ta miqe tsaye bayan ta yagi wani ganye dake gefanta ta manna a wajen. Daga kai tayi ta dubi salmanun sanda yake bata takalmin,sai taja baya kadan gami da girgiza kai alamun ba zata karba ba,abinda ya sanya salmanu dawowa inda anni ke zaune tana kallonsu "Anni taqi karba fa,kamar bata yarda bane damu" "Budeni" anni ta bashi umarni,sai ya zagayo ya bude mata qofar "Anni,karkice zakiyi magana da ita,kaf fadin rugarmu babu wanda yake kulata" sadam ya fada,a mamakance anni ta kalleshi "Saboda me?" "Ban sani ba nima,amma tsoron mata magana akeyi" shuru anni tayi na wasu sakanni sannan ta zura qafafunta waje ba tare data sake bi ta batun saddam ba Har maimunatun tayi taku daya biyu taji muryar anni "Yarinya" cak ta tsaya,a tsorace ta waiwayo idanunta akan anni,tsoro ya sake kamata,don sam annin batayi zubin mutanensu ba. "Yallijam" maimunatu ta fada a hankali ganin idanun annin har yanzu yana kanta "Jam" anni ta maida mata tana kallonta tare da karantar yanayinta "ya kike tafiya haka ba takalmi?" Qafarta ta kalla sannan ta kalla annin "Sun tsinke ne daada" yadda ta kirata da girmamawa sai yasa anni ta saki murmushi "Salmanu bata wadan nan ta saka,da hatsari wajen taka gurin nan haka" da fari kai maimunatu ta sake girgizawa kamar yadda ta yiwa salmanu,don batasan me zatacewa inna ba idan ta ganta da takalmin "Na gode daada,zan qarasa a haka" haka kawai taji ta burgeta,akwai alamun tarbiyya da kamun kai me yawa tattare da ita "Karki damu ki saka,idan ma kina tsoron fada ne a gida kice baquwa ce daga gidan bappa labaran ta baki" daga kai tayi sosai tana duban anni,idan ta canka dai dai fa kenam gidansu himu take nufi,ita a wa sa zata ambaci sunan gidan tace wani abu daga hannunsu ya fito zuwa gareta,a sanyaye ta karba takalman ta sakawa qafarta. Cif da cif kuwa kamar an aunata,wasu irin slipper ne na danqo amma me garai garai dake nuna hoton flowers daga dukka jikin takalmin kaman tangaran,kallon qafar tata tayi ta sake kalla,sai ta daga kai a hankali tace "Na gode sosai daada" duk kuwa da tana da yaqinin wannan takalmin idanunsa idanun inna ba rabonta bane,murmushi anni tayi "Ba komai" sai ta juya maimunatun tana qara hanzari don ta taddo dabbobinta da sukayi gaba,tana kuma kiransu da wani irin salo da yasa anni ta bita da kallo. "Anni....anni kenan,qaqale qaqalen mutane,tayiya jajibo jama'a ana zaune qalau" laila tayi 'ya qaramar mita ciki ciki,abinda yaja hankalin anni dake maida qafafunta cikin motar salmanu yana shirin rufe mata "Me kike cewa ke kuma?" "Bance komai ba" "Oho miki,idan ma zagina kikayi kin zagi marwanu da Aishatu" idanu laila ta lumshe tana dafe goshinta,kafin tace wani abu wayarta dake kan cinyarta ta dauki sautin kida me dadi,saita daga wayar tana dubawa "Ga marwanun nan" lailan ta fada tana hade rai tare da miqawa anni wayar "Kin fada dai dai ai,sunan ubanki kenan" ta amsata tana warce wayar daketa harbawa da sunan super dad,ta shafa ta kara a kunnenta. "Sai da salma ta gargadeni kan tafiyar nan,ashe ni zan karba gashin" bata daddara ba dai ta sake yin qorafin murya can cikin maqoshi,saidai babu yadda za'ayi anni taji,saboda tayi nisa a waya da shalelen dan nata. Sai da tayi duk wani abu daya zame mata al'ada idan ta dawo da dabbobin daga kiwo sannan ta kira sunan innar,saidai babu ita ba motsinta,dole ta fara takawa zuwa cikin gidan,qirjinta yanata dukan uku uku,don batasan me zai biyo baya game da takalmin qafarta ba. Daga qofar dakin innar ta tsaya "Miwarti ɗilaulake inna(na dawo daga kiwo inna)" shuru taji,hakan yasa ta sake maimaitawa "Dalla malama matsa ki bamu waje,kinxo kinata yiwa mutane hayaniya aka" muryar gaje ta fito daga cikin dakin,da alama itace kwance a dakin,wanda dama kusan aikinta kenan ko da yaushe,taci ta sha ta kwanta. A sanyaye ta juya don barin wajen,dai dai sanda innar ta fito daga makewaye dauke da buta,sam bata lura da yanayin da fuskarta ke ciki ba "Miwar......." Ragowar kalmar ta tsaya mata a maqoshi,sakamakon wani zazzafan mari daya sauka a kuncinta hagu da dama,a take ta gigice,ta dafe dukka kuncin nata da tafukan hannayenta tana kallon inna,wadda ta taka gefan wani qaramin rumbu dake daura da ita,take tashin hankali ya bayyana muraran saman fuskar maimunatu,tunda taga ta doshi wajen tasan me zata dauko. Tsumammiyar bulala ce,wadda ta debi shekaru ana azabtar da ita da bulalar,yadda ta tsani mutuwar ta haka tabtsani bulala,wannan ne dalilin da yasanya take dukka iya bakin qoqarinta taga bata aikata wani laifi da bulalar zata taba lafiyarta ba,zata iya cewa tabon da bulalar ta bar mata a gadon bayanta ba zaya lissafu ba. Kusan daukewa numfashinta yayi sanda innar ta ware dukka qarfinta ta zuba mata ita,kafin daga bisani qarfin dukan ya sanyata ta sulale ta duqe a wajen,tun tana iya roqarta tare da bata haquri har bakinta ya mutu,duk da batasan me ta aikatawa innar ba,sai data gamsu don kanta da yawan dukan data yi mata sannan ta tsaya tana maida numfashi "Gaje....gaje zo nan" ta qwalawa gaje dake daki abinta kira,gajen da duk yawan dukan da akewa maimunatun,duk magiyar da takewa innar bai sanyata ta koda leqo ba,hatta da sassan dake maqotaka dasu dukka kowacce ta leqo tana tsaye tana kallo,wasunsu suna qus qus a junansu tare da tir da dabi'a da halayen inna,wasu kuma suna fadin "Allah ne kadai yasan me tayi mata,kila ko yau ta dana halin uwarta ne" saidai babu ko mutum daya a cikinsu da ya isa ya tukari innar da sunan ceton maimunatu,kowanne irin hukunci ko horo kuwa zatayi mata. A gadarance gajen ta fito daga dakin,tsaf da ita cikin kwalliyar kayan saqi,wanda kusan ko da yaushe cikin canza mata su innar take,idanun gajen sun kumbura sunyi jazur,abinda.ya bayyana har saman fuskarta,da alama kuka tasha ta qoshi. Tsaye tayi saman kan maimunatu tana hura hanci tare da harare harare "Daga kanki ki kalleta.....tayi kama da sa'arki?" Inna ta fada cikin hargagi,koda ciwon mutuwa maimunatun takeji a jikinta ya zame mata dole ta kalli gaje kamar yadda inna ta buqata,idan kuwa ta saba hakan wani sabon tashin hankalin ne,da qyar ta daga kanta ta dubi gaje,suna hada idanu gajen ta sanya qafa ta haureta cike da baqinciki da kuma jin haushin maimunatun,tasa hannu ta dafe wajen saboda radadi da zafin da ya ziyarceta "Shegiya munafuka,ni zaki ha'inta,ashe yaron dana ganki dashi rannan ibrahimu ne?,to idan bakisan waye ibrahimu ba bari na gaya miki,shi din alqawarin gaje ne,bashi da matar aure sai gaje kiji na gaya miki,kusantar inda yake kuma shine babban kuskure da zaki aikatawa rayuwarki,wallahi wallahi kinjin na rantse miki,kome kike taqama dashi baki isa ki shiga tsakanin tsohon alqawari ba.....kukan da kika saka gaje yau sai kinyi mafiyinsa,ki bata haquri!" Inna ta fada tana kai mata harbi da qafa,ta sameta kuwa a gwiwarta wadda ta bugu sosai,tana dafe da wajen,cikin tsananin azaba tana dafe da gwiwarta ta fara baiwa gaje haquri,wadda keta qunci,tana jin babu abinda maimunatu zatayi mata ta huce haushin kula mata Ibrahim da tayi,tsahon wanne lokaci sukayi suna tare da ibrahim din?,tunda hatta da mutanen gari sun san da haka,baya ga haka kuma ace har sai da daadarsa tazo da kanta don yiwa tufkar hanci sannan sukasan da batun,lallai maimunatun ta cika cikakkiyar makira kuma macijin sari ka noqe kamar yadda innarta tasha fada mata. "A'ah,lafiya?,me yake faruwa?" Muryar jauro ta ratsa kunnensu,abinda ya sanyasu waiwayowa gaba dayansu,duk da cewa innar bata so dawowarsa yanzu ba amma sai ta dake "Meye hakane?,me ya faru?" Ya sake tambaya yana kallon gaje kafin ya maida dubansa ga maimunatu dake zube a qasa,hakan ya baiwa gaje damar sulalewa zuwa dakonsu,tasan halin jauro tabbas yau cikin gidan ba za'a qarke lafiya ba "Gata nan ka tambayeta maciyar amana" inna ta fada tana huci. Gabanta ya duqa yana kiran sunanta,ta daga kanta wande ta sokeshi tsakanin qafafuwanta tana duban ardo din,yanayin yadda yaga maimunatun ya tabbatar masa lallai ta daku,hatta da bakinta a kumbure yake,gefan fuskarta yayi kwanciyar jini da shacin bulala "Wanne irin rashin imani ne wannan furera?" Jauro ya fada a mugun fusace yana miqewa tsaye "Ita ya kamata ka yiwa wannan fadan bani ba,qanwar bayan gaje har ta iya hilatar maza tana binsu?,saboda rashin kintsi ta rasa wa zata bi sai ibrahimu?" "Shine kikayi mata irin wannan dukan?,inda kuma kin nakastata fa?" "Shikenan da kowa ya huta da ganin shegiyar fuskar dake daukan hankalin maza" cacar baki ce taso barkewa a tsakaninsu,ran jauro yayi mutuqar baci "Waike wacce iriyar macace furera?,maimunatun zaki yiwa irin wannan dukan?,kowanne irin laifi ma tayi miki?,don kinga ina dauke kai ina barinki saboda kina nuna min kunfi kusa ko?" "To dama meye naka a ciki?" Kai ya gyada cikin bacin rai,iskar data fara kadawa wadda ke tafe da dan yayyafi yasa jauro ya maida hankalinsa ga maimunatu "Tashi ki shiga dakinku,Allah zai saka miki,a kusa ko a nesa,baya yafe zalunci" kasa miqewa tayi,ya tabbatar ba zata iya tashi ba,cikin muryar fushi ya qwalawa gaje kira. A tsorace ta qaraso tana raba ido hadi da matse hawaye,tsawa ya daka mata "A'ah ya haka?,ka bita a sannu,rai aka bata mata fisabilillahi sannan ka bita da irin wanna tsawar?" Kallon banza ya watsa mata,yana ganin zallar son rai da son kai irin na innar "Munafuka,kamata ki kaita daki" ya fadi yana zabga mata harara,da sauri ta zabura ta matso ta kama maimunatun,irin riqon tsaurin da tayi mata na mugunta yasa maimunatun cewa "Wash hannuna" "Sassauta mata riqon kafin nayo kanki na maimaita miki irin dukan da uwarki tayi mata" "Dalili dame?,ke bi masharranciya a sannu ku rabu lafiya kada ta shafa miki jarfa ba gaira ba dalili" inna ta fada saboda tasan tsaf jauro zai aikata daga yadda ranshi yayi mummunan baci. Sakin maimunatu tayi sanda suka isa dakin,abinda ya sanyata ta buge gefan kanta,qauuuuu taji wani abu na yawo cikin kwanyarta,ya dafe wajen tana kiran sunan Allah,gaje na tsaye a kanta tana zuba mata harara "Shegiya mayya,wallahi kikayi gangancin sake rabar ibrahim sai mun kasheki a gidan nan nida inna mun binneki,kuma mun kashe banza,tunda babu wanda zai tuhumemu" daga haka ga tsallaketa kamar zata takata,ta haure kan katifarta. Ta jima tana jinta a wata duniya ta daban,kowacce gaba ta jikinta ta zame mata kamar wani gyambo,da qyar take iya motsawa. Kiran sunanta da jauro yayi ya sanyata bude idanunta da qyar "Tashi zan shigo" ya fada yana tsaye daga bakin qofar dakin,duk da yayyafin dake sauka har yanzu,jikinta taja ta miqe ta zauna sosai tana jingina da bango,ya dage labulen bayan ya shigo ya maqale shi sannan ya tsugunna daga gefe yana turo mata kwanon abincinsa "Dauki kici maza diyam" sunan da ya kirata dashi yayi matuqar karya mata zuciya,ya tuna mata da tata daadarta,itace wadda ke kiranta da sunan,suna mafi soyuwa a gareta,fararen manyan idanunta suka cika da qwalla,tasa hannu a kasalance ta jawo kwanon gabanta ta fara ci. Wasa wasa sai gashi ta kusa tashi da abincin duk yawansa,ta riga ta saba ba kullum take samun abinci ba,idan ma ta samun to sau daya ne a rana,tana ci yana mata nasiha tare da kwantar mata da hankali,gaje na kwance tamkar mai barci,ranta ya baci sosai,shi babanta wai baya kishinta?,me yasa yafi nuna kulawarsa ga maimunatu fiye da ita diyar cikinsa?. "Miyatti bappa" maimunatun ta fada a tausashe kanta a qasa cikin nuna jin dadin kulawar da ya bata "Ba komai,kema diyata ce kamar yadda gaje take" kai ta jinjina,tana kin sauqi cikin ranta,ko babu komai yau din ba zata kwana da yunwar dake da take matuqar wahal da ita ba a duk dare. Har jauro ya juya ya fita maimunatu tana binsa da kallo,sai daya sauke labulen ya qarasa ficewa sannan ta sauke nannauyar aiiyar zuciya tana janye idanunta daga wajen,dai dai lokacin da gajee tayi caraf ta miqe zaune "Munafuka algunguma,kamar a idanun inna akayi wallahi,Allah ya kaimu safiya" tsoro ne ya cika zuciyar maimunatu,saboda tasan tunda gajen ta fada sai ta aiwatar,idanunta fal da qwalla ta shiga roqon gajeen tayi haquri,maimakon ta amsa mata sai ta lullube kanta da mayafi tayi kwanciyarta gami da juyawa maimunatun baya. Sai da dukka yawun bakinta ya dauke kan roqon gajee tayi haquri,daga qarshe dole ta haqura da roqon,ta rufe idanunta,hawayen da suka taru suka gangaro mata. Wani wahalallen barci tayi mara dadi,saboda ko ina na jikinta ciwo yake mata,ko da tayi sallar asuba ma zaune tayi a wajen,saboda ciwon da jikin yake mata,inda ace shimfida ce mai laushi irin ta gaje wala'alla ta iya rabawa takwanta,amma shinfida irin tata da bata da maraba da tattauran dutse babu ta inda zata iya kwanciya taji dadi. "Maimunatu!!!,ke maimunatu!!"kiran mafarautan da ya ratsa tsakiyar baccinta ya sanyata farkawa firgigit,inna ce tsaye a kanta,hannunta riqe da robar da yawancin lokuta suke tatsar nono a cikinta,duban maimunatun take kamar zata afka mata "Yahudillo dirgul.....(zoki tafi kiwo)......" "A ina?" Maganar jauro ta katse hargagin da inna ta fara yi mata,ratsowa yayi sanye da riga 'yar shara da malfare a kansa,hannunsa riqe da baqar leda,bisa dukkan alamu fita zaiyi "Daga yau.....har zuwa ranar da maimunatu zata warke babu ita babu zuwa kiwo,wallahi wallahi wallahi sau nawa kenan?" "Tati(uku)" innar ta amsa masa tana riqe da qugunta tana kallonsa "Idan naga akasin hakan zakisan waye ainihin jauro wanda ada can baki sanshi ba,wannan shine hukuncinki na irin dukan da kikayi mata" "Wai dakata,wai me kake nufi ne?,ko kana yimin baqinciki ne da dukiyar dabbobin da Allah ya bani ne?,wanda dama an jima ana fada,ganin muna zaune shekara da shekaru tare yasa ban gasgata ba,amma ayanzu na fara ganin alamu ganin idona kuwa" dubanta yayi "Ki bari sai zuwa sanda kika tara taki dukiyar ta halastacciyar hanya saiki gayamin haka" sosai maganar daya fada tayi mata ciwo,tana ganin jauro shi daya ne mutumin da yasan sirrinta yake kuma shirin xamar mata tarnaqi a rayuwa,wannan amsar da ya bata ta hautsinata,ta dinga jifansa da kalamai,wanda kalmarta ta qarshe ita ta sanya ya tsaya cak yana dubanta "Ban sani ba ko son maimunatu ma dai kake yi a taqaice,idan sonta kake ai gwara ka fito ka gayamin,saika hadamu mu duka ka aure" "Idan ke mahaukaciya ce ni da hankalina" sai ya qara gaba kawai ya fice yabar mata gidan,ya tabbata idan ya tsaya yaci gaba da biye mata zasu raba abun fada ne gaban 'ya'yansu,wannan ba komai bane a wajen furera. 08 Fitar jauro daga gidan sai dukkan bala'i da masifar suka dawo kan maimunatun,inna nayi gajee nayi "Tunda ya daure miki gindi ko?,to wallahi baki isa ki kwanta kiyimin saqe saqe kamar gawar sababi ba,bayan jiya ya shirga miki abinci kin cinye,to kin ciyoma kanki,kinci abincinki na jiya dana yau,waryo wan en jungul!,(zoki dora mana abinci)" ta fada a tsawace,har maimunatun tana jin kanta kamar zai cire. Tuwo ne na masara miyar danyar kubewa,gaba daya kayan aikin innar ta tura mata,ta baza tabarma tayi zamanta qasan bishiyar dake basu iska. Zata iya cewa batasan ta yadda akayi take aikin ba,don komai tana yinsa ne a wahalce,cikinsu kuma babu wanda ya taimaka mata koda da firfita wuta ne,yadda bata da lafiya haka aikin yaja lokaci yaqiyin sauri,saboda rashin kazar kazar da kuma qwarin jiki,abinda ya qara iza wutar masifa da bala'in inna,ya kuma sanya maimunatun taji inama ace kiwon ta tafi a haka,tabbas ya fiye mata wannan wahalar girkin. Tana zaune tana niqan kayan miyan da zata dora miya saman dutsen markade taji sallama,ta daga kanta a wahalce tana amsawa,matashiyar da aqalla zatayi sa'a da ita ce(zubaida),sai kuma yaron dake gefanta(sadam),kasa dauke idonta maimunatu tayi daga kan fuskar yaron,saboda kamarsa muraran da ibrahimunta. Shima yaron ita yake kalla,kafin daga bisani ya dauke kansa,abinda ya bata mamaki hararan da zubaidan ta wurga mata kafin su miqa zuwa inda inna ke zaune tana kada nono,maimunatun kuma ta maida kanta ga aikin da takeyi cikin mamaki,iyaka saninta da zubaida saidai kallo daga nesa,ba abinda ya taba hadata dasu,koda gaisuwa kuwa,takan jima bata gansu ba,kamar yadda suma suke jimawa basu ganta ba,domin su din zuwansu kiwo na lokaci bayan lokaci ne bawai koda yaushe ba,koda ma koda yaushe ne,tana daukar watanni kafin magana ta hadata da wani a wajen kowo har taje ta dawo,saidai idan baqin makiyaya da ba 'yan asalin rigarsu ba sun ratso ta dajin da suke kiwo. "Maraba da zubaida da saddam" innar laulo ta fada cikin wani irin kirki da kuma fara'a,wanda ya sanya har sai da maimunatu ta tasa kanta dake mugun sarawa ta saci kallonta. Daga gefan tabarmar da take kai suka zauna,gaisheta yaron ya farayi sannan zubaidan "Dama daada ce ta ailo na gaya miki,akwai baqi da sukazo daga gombe,naggen bappa suka saba siya,to wannan karon babu,bappan ya fita dasu gaba daya,shine tace nazo na gaya miki,tasan cikin naki akwai irin wadanda sukeso,gobe zasu zo da safe kafin a fita dasu su gani" madaukakin farinciki ya kama inna furera,cikin ranta ta sake jin duk duniya bata da masoyi sama da daada din,dama ta jima tana shawarin saida wasu daga ciki,ko don ta saku ta sake badda dukka wata alama da zata iya zama shaidar rashin zamowarta mallakin dabbobin,to amma kuma batason saidawa anan kusa,tafison waje me nisa inda zasu siya da daraja "Miyatti Allah,miyatti daada,amma naji dadi wallahi,Allah ya kawosu" "Ameen,sannan tace na gaya miki,anjima yaaya himu zaizo wajen gaaje,su sake ganin juna" kamar inna furera zafa taka rawa haka tayi,takai ta kawo ta rasa wanne tukuci zata bawa zubaida,qarshe dai har suka bae gidan bakinta yaqi rufawa. Saukar zancan a kunnuwan maimunatu sai ta kasa tantance cikin wanne yanayi take ciki "Ibrahimu zaizo yaga gaaje" wannan shine dalilin da yasa ta daina ganinsa kenan?,me hakan yake nufi?. Tunanin ya sanya aikin nata ya sake yin slow fiye da dazu,tun inna na mita da baki har sai data fara kai mata duka da hannu "Me shegen baqin halin tsiya,bakyason aikinne,a haka kuma zakiyi shi". Takanas innar ta taso gaje,ta hada mata madarar shanu da lalle ta murje mata jikinta,zaka tsammaci kamu za'ayi mata irin na amare,duka a wannan lokacin ta sanyata ta tsefe kanta mai yalwar gashi,wanda datti ya dakushe tsahonsa ta wanke mata shi fes,ta raba mata gida biyu ta zubo mata da jelarsa hagu da dama. Tun yammaci aketa shiri gamida da gwada yadda zata tarbi ibrahim din,duk don saboda ta burgeshi,mudukaje(kayan saqin fulani) na can qasan kayanta ta ciro ta ajjiye,dukka abin nan da ake na maimunatu idanu ne,saidai gefe daya zuciyarta ta gaza hutawa da tunanin abinda zaije yazo. Dai dai sanda maimunatun ke saman dan mayafin da take shimfidawa tayi sallah....dai dai sannan gaje keta faman fecewa fuskarta kwalliya,ta kalli madubi yafi sau shurin masaki,ta juya ta sake juyawa har sau babu adadi,burinta shine taga komai yayi,sannan ta burge ibarahim matuqa,maimunatu tana zaune a wajen,bata motsa ba bare ta waiwaya taga abinda gajen keyi,saidai kuma kunnuwanta na samun aiken saqonnin waqe waqen da gajen keyi cikin harshen fullanci,tana yi tana juyi,abinda zai nuna maka cikin zallar farinciki take a yau din. Laulo ne ya shigo dakin,yaron da za'a iya cewa yafi gaje hankali,don wasu abubuwan da shi din yakeyi yana yinsu ne da yarinyata,da kuma rashin samun isashshiyar tarbiyya da kyau "Himu yazo,inna tace akai masa taburma" sai yaron ya juya ya fita yana tsalle tsalle abinsa. Juya idanunta gajee tayi cikin farinciki,ta jima tana qaunar himu tun ba yanzu ba,tun daga sanda inna ta gaya mata cewa shine mijin da suka zaba mata ta riqe hakan a ranta,bata taba mancewa ba,hakanan bata yarda ta kula kowa ba saboda ibrahim,duk da tarin masoyan da take dasu a rugar,don dai dai gwargwado tana da irin nata kyan. "Ki dauko tabarma ki kawomin zagaye" ta bawa maimunatu umarni kai tsaye tana ajjiye madubin hannunta,har takai bakin qofa ta tsaya ta juyo tana duban maimunatun jin bata ce komai ba "Ko ba zaki kawo bane?" "Yanzu zan tashi" ta amsa mata murya a raunace,qwafa gajee taja sannan ta sanya kai ta fice. Babu yadda zata kaucewa umarnin gajen,ya zame mata dole,hakanan ta miqe dauke da tabarmar ta nufi inda gaje ta umarceta. Salon tafiya na daban ta canza kamar yadda suka wuni suna gwadawa ita da inna furera,ibrahim din na tsaye,jingine da wani kutturen ice,qafarsa harde da juna yana duban gajen sanda take tahowa,cikin salo na nuna jin kunya ta dan sunne kai sanda ta fuskanci kallonta yake,farinciki ya cika zuciyarta,tana hangen ba wani faɗi tashi me yawa zatayi ba zata samu kan ibrahim din. Wani tattauran yawu me daci ibrahim din ya hadiye,ya rufe idanunsa yana sake tursasawa kansa da zuciyarsa daurewa da kuma bin umarnin daada,yana jin kamar zuciyarsa zata fashe saboda takaici,meye ne daada ta hango masa tattare da gaje,me yasa idanunta suka rufe ta kasa gano abubuwa masu tarin yawa da yake gani tattare da maimunatu?. Yana bude idanunsa ya hangi maimunatun biye da gaje,gaba daya sai ta wafce kallonsa,ya tattaru gaba daya a kanta,hasken wutar kara da mazauna wajen suka kunna daga can gurin zuwa can ya haske wajen sosai da har yake samun damar ganin kowacce a cikinsu "Sannu da zuwa" gajee ta fada tana dan russunawa hadi da rausayar da idanu "Sannunki" ya amsa mata murya a ciki,yana dauke dubansa daga maimunatu wadda ta qaraso wajen riqe da tabarmar "Ki shimfida masa mana kin bar mutane a tsaye,sai wani abu kike kamar mara laka a jiki.....mayya...." Hannu ibrahim ya daga mata da sauri,saboda zafi da zuciyarsa ta fara yi masa,bazai iya daukan hakan ba,a nutse ya dubi gaje "Wannan din ba bil'adama bace kamarki?,bakisan Allah ya karrama dan adam ya kuma mutuntashi ba?,matuqar wannan itace dabi'arki,to kin dauko hanyar da ba zaki sake ganina a nan ba" sosai maganar ta bata mata rai,ta kuma sake saka mata kishin maimunatu a ranta me yawa,amma a yanzun nema take,dole ta jure,don haka ta sadda kai "Kayi haquri" bai amsa mata ba,sai ya miqawa maimunatu hannu ya karbi tabarmar,ya sani sarai anyi hakanne don a tozarta maimunatun,a sake kuma nuna masa ita din ba kowa bace,tunda daadansa bata boye masa komai ba,ta gaya masa duk irin matakin da suka dauka,tayi ne da nufin jan kunne,ta kuma gaya masa zaman lafiyar maimunatu shine ya rabu da ita,abinda basu sani ba shine,wannan abun da sukayin shi ya sake zubda darajar gajee harma da inna furera a ransa,ya kuma sake sanya masa tausayi da qaunar maimunatu. Batasan cewa himu ya fara taka wani matsayi a zuciyarta,batasan cewa ya fara bude wata rufaffiyar qofar da bata tsammaci budewarta ba sai data koma daki,gaba daya ta gaza sukuni,ta kuma kasa kwanciya kamar yadda taso ta kwanta din,saboda yadda jikinta yake wani irin radadi da kuma zugi sakamakon aikin da tasha,ga kuma tabbai na duka wani wajen har ya fara rurucewa,abinda ya hade mata kenan,ya kuma saukar mata da zazzabin da ya tilasta mata kwanciyar da a daxu ta kasa yinta. A hankali ta bude idanunta sakamakon muryar gaje data jiyo cikin muryar kuka "Ke....mene....meye?" Inna furera data fito daga daki zaninta a hannu ta fada,hankali tashe tana duban gaje "Inna,kai tsaye himu fa yake gayamin wai bani bace a zuciyarsa,zuciyarsa tuni wata ta karbeta,kuma wallahi nasan ba kowa yake nufi ba sai waccar mayyar,tunda na daka mata tsawa har ya tafi banga faraga a fuskarsa ba,ki taimakeni inna,wallahi inason himu" wani dogon tsaki innar ta saki tamkar zata tsige harshenta "Ahaf.....aikin banza kenan,yo yayita fadi baya sonki.mana,qarewa ya samu amsa kuwwa ya daura,yayita bi rugage yana fadin hakan,ai yayi aikin banza,maganar nan babu me tashinsa,shi ya san wace uwarshi,tunda ta fada babu me tashin maganar,shi yasa ya biyo ta hakan don kice bakiyi,wadda kuma yake qulafucin haihata haihata shi da ita,qwalelen kare da hantar kura,yadda naci alwashi in sha maka Allahu....matuqar ina raye saikin aurin namijin da kaf rugar nan babu irinsa,ibrahimu ne,kuma shine naki,muje na karanta miki karatun zaman duniya" inna ta fada tana kama hannun gajee sukayi dakin innar. Maida idanunta maimunatu tayi ta rufe,tana fitar da numfashi me azabar dumi saboda zafin zazzabin daya ratsa kowanne sashe na jikinta,kadaici gami da kewar mahaifiya ya cikata,koda zata mutu a saman wannan shimfidar babu lallai a ankara,koda za'a lura din wala'alla sai ta kumbura ta fara fidda wari,ko kuma sanda suka nufaci tashinta don ta biya musu buqatunsu "Innalillahi wa inna ilahi raji'un" ta samu kanta da fada tana rushewa da kuka mara sauti,addu'a ce da take yawan jin mahaifiyarta tana yi,rashin uwa wani babban gibi ne a cikin rayuwa,wanda babu wani abu da ya isa ya cike maka wannan gurbin. Duk yadda take jin jikinta bayan ta idar da sallar asuba amma hakan baisa ta koma barci ba,tasan koda ta koma din ma wani tashin hankali da kuma firgici zata kirawa kanta,don haka taci gaba da zama,har zuwa lokacin daya dace ta fara aiki yayi,ta miqe a hankali ta yaye labulen zanin atamfa dake qofar dakin nasu tayo waje. Duk da yadda suke da sammako da kuma tashin wuri amma wajen tsit yake,kowa yana ta sashensa,babu komai sai kukan dabbobi dake turke a muhallensu. Sannu sannu tana aikin gari na dada yin haske,mutane na sake fitowa daga muhallansu kowa na kama sabgar gabansa. Inna furera ce ta fara fitowa daga nasu gefan,ta saki wanke wanken da takeyi ta qarasa inda take tsaye tana gaidata,bata bi takan gaisuwar tata ba tace "Ki saki wanke wanken,kije ki gyara wajen dabbobin can,nasan masu sayen suna hanya,tunda da wuri zasu zo,sannan inaso ki nutsu da kyau,na tabbatar sai an kiraki lokacin cinikin,saboda ke kike kiwonsu,kinfi kowa sanin wadanda sukafi kowanne lafiya da nada nono da kyau,to bance ki tsaya nune nune ba,ki barsu su zaba da kansu,ki kula....bazan lamunci ki jawomin asara ba" kanta a qasa take amsawa innar,bata miqe ba sai data bata umarni,ta taka zuwa inda take adana kayan sharar wajen ta debesu da qyar ta zagaya zuwa makwantar dabbobin. Sanda suka ganta sai da dukkaninsu suka motsa,ta saki murmushi itama tana isa gabansu,kwanaki biyun da bata gansu ba sai takejin tayi kewarsu ba kadan ba,suma kuma tasan hakanne,don dai kawai basu da baki bare su bata labari. Duk da jikinta babu qwari,cikin boyeyyen ciwo dake cin naman jikinta take amma cikin qawa zuci take aikin,tana yi yana musu magana kai kace da dan adam take,sai data bi kowacce dabba data saba dubawa ta dubata sannan ta fara aikin. A hankali suke takowa da qafa,tun daga gidan bappa labaran din,anni da kanta ta zabi su tako da qafan "Ku barni da qarfen nasaran nan,gwara mu taka da qafa tunda ba nisa ke da gidan ba" tace da daada,wadda da kanta tayi mata rakiya ita da safiya da kuma laila. Tahowar da sukayi din ya bawa lailan dama daada damar kallon rugar sosai,bambancin rayuwa qarara na zahiri da suke gani,wanda yayi dai dai da karin maganar nan ta bahaushe da hake cewa Allah daya gari banban,suna tafe laila na tambayar sadam wasu abubuwan,tafiyar ta zama wani mabudi na ilimi a gareta. "Maraba,lale,sannunku da zuwa" shine abinda inna furera ke faman fadi,tana kai kawo tare da qoqarin shimfida musu tabarma gaban dakinta,yayin da gajee ke zaune abinta saman kujerar tsuguno. *Don samun ci gaban sabbin galla gallan pages,ziyarci page dina a AREWABOOKS da sunan HUGUMA* 09 Tarba cike da fara'a da nuna matuqar kirki inna furera ta yiwa su anni "Ina kwana daada" gajee ta fada tana dan zamowa kadan daga saman kujerar da take zaune a kai hannunta riqe da mudubi tana ta faman kallon fuskarta da kuma kankare duk wani dan tabo ko ciwo da ta gani akan fuskar tata,so take lallai ta hango dame maimunatu ta fita ne,da har jiya himu zai iya duban fuskarta yace mata baya sonta?. "Lafiya lau gajeje,ya akaji da baqi kuma jiya?" Murmushi tayi ta noqe tana komawa saman kujerar,ita ala dole kunya,saidai hakan bai sanya tabar wajen ba,hakanan kuma batayi yunqurin gaida anni ba,duk da cewa ta girmi duk wanda yake wajen. Kallo daya itama annin ta yiwa sashen da take ta maida dubanta ga inna fureran,tana matuqar mamaki idan akace mata wadan nan din fulani ne,saidai kuma duk da ita da zafinta,amma mutum ce da ba kasafai zaka ga ta shiga abinda babu ruwanta ba,saidai idan ta kama. Gaisawa suka fara yi,sannan innar ta fara yi mata bayanin yawan dabbobin da kuma farashin da ta yankewa kowanne "Farashi ba tsada bane,indai sunyimin shikenan.......laila,leqa ki kirayi salihu ya shigo" tace da laila,salihu shine kusan manager din gidan gonarta,a yawancin lokuta shike bi rugage ya qaro mata dabbobi a duk sanda ta buqaci hakan. Ba jimawa suka dawo tare,innar tayi musu jagora zuwa makwantar dabbobin,suna tafe tana qara yi musu bayani,burinta ta gamsar dasu,su siye ta caski kudinta. Tun daga nesa idanun anni suka sauka akan maimunatun,gefanta kayan share wajen ne a zube,tana tsugunne a cikinsu,hannunta riqe da qafar wata akuya tana dubawa,idan ka kalleta da kyau zaka fahimci magana takeyi saboda yadda bakinta ke motsawa,tana kuma shafa bayan akuyar da hannunta daya cikin nuna tausayawa da tausasawa. Suna sake riskarta annin na ci gaba da kallonta,tana kallon tarin baiwar da yarinyar ke da shi,yadda take nuna kulawa da tausayawa ga dabbobin yana burge anni,tana mamakin yadda take magana dasu tare da isar musu da saqo da bakinta,tayi imani akwai wani abu tattare da yarinyar na musamman wanda ba lallai wadanda ke kewaye da ita sun fahimci haka ba. Sosai ran inna furera ya baci,ta kuma tunzura sanda ta fahimci maimunatu bata share wajen ba,ta cika tayi fam,tanason jawo mata asara ne?,ta yaya zata kawo baqi irin wannan wanda duba daya zaka yi musu kasan duniyar da suke rayuwa ya banbamta da tasu amma tabar wajen a haka?,yanzu idan suka ce sun fasa fa?.….….tunanin da ya sanyata ta kwatsawa maimunatun da batasan da tahowarsu wajen ba tsawa "Ke maimunatu!!!" Kiran yayi matuqar razanata,saboda bata tsammaceshi ba,abinda yasa tayi wata miqewa cikin matuqar hanzarin daya rage kadan ta kifa,sai data dai daita tsaiwarta sannan ta dawo da dubanta zuwa sashen da kiran ya fito,ta sauke manyan idanunta da suka rusuna saboda tsoro a kansu. Yadda take dubansu haka anni itama ke dubanta,wani abu yana taba ran anni haka kawai,matsowarsu kusa da ita da yasa ta sake kallon maimunatun sosai,akwai wani yanayi tattare da ita "Uwarki kike tun dazu baki gyara wajen nan ba?,ban gaya miki baqi zasu zo ba?,lallai dai sai kin nunawa duniya zallar baqinciki da adawar da kikeyi dani ko?,to ni nafi qarfinki,nafi qarfin kiyi takun saqa dani......" Tayi maganar yana zarar wani sanda dake jingine wajen ta durfafi maimunatun a fusace. Gam ta runtse idanunta tana jiran jin ta wanne sashe dukan zai fara sauka a jikinta?,tana wassafa radadi da azabar da zata fuskanta lokacin da dukan zai sauka kan mikin wancan dukan da yake jikinta?,ashe kiwon da take tafiya ta wuni acan wani bangaren rahama ne a gareta?. "A'ah dakata 'yar nan" muryar anni ta katse inna daga yunqurin dukan da take shirin kaiwa maimunatu,sai dukka hankula suka koma kan anni "Banda abinki.....mu ai dabbobi muka zo gani ba wajen kwanciyarsu ba,muyi abinda ya kawo mu kawai" "Allah hajiya da kin barni na bubbugeta,tsinanniyar yarinya babu abinda ta sani sai mugun hali da baqar zuciya,ka bata ci ka bata sha ka bata suttura....." "Ba haka akewa yaro ba,haquri akeyi dashi ana nuna masa dai dai da ba dai dai ba,sannan ma yarinyar nan inacewa ba itace ke fita da dukka dabbobin nan kiwo ba?" Anni tayi tambayar tana duban fuskar inna "Eh itace,haqqun" "To a ganina ai ba cancanci a daketa ba,don ko dabbobin da take kiwon idanuna bai taba gani ita din ta dakesu ba,don me ita ta cancanci duka da irin wannan sandar?" Jikin innar ne ya mutu,bawai don tana jin ta aikata kuskure ba,a'ah.....don sai tana tsoron kada tayi abinda zata jawo ma kanta asarar cinikin da za'ayi mata,don haka ta jingine sandar tana cewa "Haka yake......Allah ya shirya muna" "Ameen" anni ta fada tana maida dubanta ga maimunatu dake tsaye,wadda har yanzu bata iya bude idanuwanta ba "Muje ki nunna mana su maimunatu" anni ta kira sunanta a tausashe,abinda ya sanyata bude idanun a hankali cikin mamakin daga inda kiran ya fito,ta tsammaci dama baquwar fuska ce,hakanne kuwa,akan fuskar anni idanun nata sauka sauka,idanunsu cikin na juna,saita sadda kanta qas kana cikin girmamawa tace "Sannu da zuwa,ina kwana?" Murmushi ya wadaci fuskar anni,cikin kulawa ta amsa mata "Lafiya lau 'yar fillo,ya hidima da kai kawo?" "Alhamdulillahi" ta amsa.mata wani sanyi yana sauka cikin rai da zuciyarta,zata iya cewa tsahon lokacin da ta dauka tana bauta,bata taba jin wanda ya buda baki ya tambayeta irin haka ba. Waiwayawa tayi ta gaida daada,ganin idanun anni yasa ta amsa mata babu yabo ba fallasa,saita juya ta gaida laila,lailan ta amsa mata cikin kulawa,tana binta da kallo,kyakkyawar yarinya data tasamma zama budurwa.irin wannan,me tsananin kyau da sura,inda a birni take rayuwa.wanne irin rububi za'ayi a kanta,sai taji maimunatun ta kwanta mata a rai,yanayin nutsuwarta da sanyin halinta baiyi koda.kama dana 'yaruwarta da suka baro a bakin dakunan can ba. Cikin nutsuwa take nuna musu kowanne a ciki,yanayin yadda take musu bayani tare da zabosu kawai ya isa ya gaya maka tayi musu sani na haqiqa ba qaramin sani ba,sosai anni ta yaba da dabbobin,kamar yadda salihu yace,akwai alamun cikakkiyar lafiya tattare dasu,zasu bada nono da iri me kyau yadda ake buqata. "Waccar sanuwar fa?" Anni ta tambaya tana nuni da ita "Wancan naggen basu fiya bada irin abinda akeso da kyau ba,ba kowa keson irinsu ba,irin ne da wasu ke kasheshi don kada a sake samunsa" maimunatu ta fada tana duban saniyar. Kallon maimunatun anni tayi cike da birgewa da wani qaunar yarinyar da ya shiga zuciyarta,karo na uku kenan da tayi musu bayani makamancin haka,ta lura gaba daya cikin harkarta babu ha'inci babu rufa rufa,kayansu za'a siya,maimakon ta lullube aibunsa sai ta fidda musu da komai babu rufa rufa,gaba daya shekarunta basu taka kara sun karya ba,amma kuma dabi'u da halayenta irin na manya ne,hali na girma da muma dattako "Ma sha Allahu,kinyi sa'ar yarinya qwarai furera,samun yaro mai irin dabi'a da halayenta abu ne me wahala" anni ta fada tana gyada kai cike da burgewa "Gaskiya dai..." Salihu ya fada shima yana murmushi cikin mamakin halayyar maimunatun,saboda yasan halim mutane da dama kan cinikayya irin wannan,kowa kazo kana son siyan abunsa qoqari yake ya linke aibun abun ya baka shi ta fuskar da zaka gamsu da ingancinsa. Maganar ta sanya inna furera dauke idanunta daga hararar da take danqarawa maimunatu zuwa kan anni,bayan ta wadatar fuskarta da murmushin yaqe "Haka ai take,kuma har 'yar uwarta da muka baro a can ta fita" ta fadi tanason fidda gajenta kunya gaban surukarta da kuma baqin idanun da suke wajen "To ma sha Allah,Allah ya dorar dasu akan hakan" "Uhmmm...meen ameen"inna furera ta fada tana son nuna jin dadinta. Yadda inna furera ta fada haka anni tasa salihu ya irga kudinta cas aka tafe mata,harda qaramar rawarta saboda farincikin ganin irin kudin data karba sama ta ka,lallai a duniya bata da masoyi kamar daadar himu,wadda ita tayi mata silar wannan ciniki mai gwaggwabar riba. Har sun juya zasu wuce anni ta waiwayo tana duban maimunatu "Jikata kema ai ya kamata ace an baki wani abu ko,saboda qoqarin nuna mana zabin qwarai da kikayi" qaramin murmushi mai cike da kunya da kuma kawaici ta sake,tayi qas da kanta ba tare da tace komai ba,kamar ma kuma taga hararar da inna furera ta fara auna mata "Basai kin ban komai ba kaaka,haqqina ne nayi hakan don fita haqqin Allah a kaina" tabbas badon idanun da suke wajen ba ba abinda zai hana inna furera kai mata mangari,qiri qiri yarinyar nason jaza musu asara?,don batasan yawan kyautar da matar tayi nufin yi mata ba "Gaskiya ne" anni ta fada,saita karba jakarta a hannun laila wadda duk wannan abun da ake hankalinta nakan daukar hotuna cikin wayarta kusa da dabbobin,don ta samun abun adanawa ya zame mata tarihi,kuma ta bada labarin xuwanta rugar,don kuwa da wayonta ba zata iya tuna yaushe tazo rugar na qarshe ba. Sabbin kudi ta fitar ta irgasu a miqe ta miqa maimunatu "Naji dadin riqe gaskiyarki,wannan kyauta ce bisa hakan" dan noqewa kadan tayi kamar ba zata karba ba,har sai da salihu ya sanya baki,sai data saci kallon inna furera taga yadda take watsa mata harara sannan tasa hannu biyu ta karba tana fadin "Allah ya saka da alkhairi,ya maida ninkinsu" "Ameennn" anni ta fada cikin jin dadin addu'ar maimunatun. Bata tsammanin ko sassan nasu su anni sun bari inna furera ta miqa mata hannu,ko batayi.magana ba tasan me take nufi,shi yasa gaba daya batayi nufin amsar kudin ba,saboda tasan cewa zata raba matar da kudinta ne,ita kuma da tayi niyyar bawa ba zata mori komai a cikinsu ba,duka ta dunqule kudin hannun nata ta miqawa inna fureran,sannan ta tsugunna ta debi kayan aikinta ta fara gyara wajen bata ko waiwayeta ba. Babu kunya babu kuma tsoron Allah ko daya a tattare da ita ta hade dukka kudaden ta irge abunta cas ta soke su tayi gaba abinta tana rera waqa,yau itakam ranta fes,mutuwa batayi mata komai ba sai rana data yi mata,banda silar mutuwar ina ita wannan dukiyar?,ina ita ina mallakar wadan nan kudade?,kudi kam sunzo mata a dai dai,tanadin bikin gajenta zata farayi tun yanzu,saboda bikin gata takeso tayi mata. >>>>>>>>>>"sannu anni.....an gama komai ko?" Yuuma ta fada sanda take shigowa rumfarta dauke da kwanon sha da ta cikashi da damammiyar fura da nono wadda babu surkin sugar ko kadan a cikinsa "Mun gama komai ramatu..dabbobi lafiyayyu,har sunso sufi na labaran din ma" "Ai sunfi ma anni,sun hadu da makiyayiya mai hazaqa da iya kiwo,irin kiwon da babu ha'inci a ciki" yuuma ta fadi tana zama sosai gaban anni tana murmushi "Ai naga alama,ko ba wata yarinya maimunatu ba?" "Itafa,baiwar Allah" yuuma ta fada fuskarta na dan canza yanayi "Ai tunda na shigo Allah yake hadamu,naketa ganin abubuwan mamaki daga wajen yarinyar,na jima banga me kiwo irinta ba,sannan abinda zai sake baki mamaki da ita.....wajen cinikin nan,kowacce dabba da muka nuna manaso sai datayi mana bayanin lafiyarta da sauransu,babu ha'inci" cikin gamsuwa yuuma take gyada kai "Bata tsinta a qasa ba ai,gado ne me kyau daga wajen mahaifiyarta,Allah ya jiqan ruma" "Allah sarki,kice marainiya ce?" Anni ta fada tana jan kwanon furar gabanta tana qoqarin budewa "Marainiya ce,wadda aka kasa yi mata riqo na tsakani da Allah.....kinsan mahaifiyarta anni,kin tuna matar da kikaga wata balama me juna biyu a wajenta kikai sha'awarta shekarun baya can da suka shude,ta qara miki da kyautar wata akuya,akuyar da kikace ta miki albarka fiye da kowacce dabba a kiwonki?" "Af.....af ina zan manta da wannan baiwar Allar,dama itace mahaifiyarta?" "Itace anni" yuuma ta amsa mata tana dauko wani kwanon da ta shaqewa anni shi da dambu me dumi tana aje mata "Allahu akhbar......." Maganar annin ta tsaya sakamakon shigowar laila tana qananun mita. Daga kai anni tayi ta dubeta,daure take da zani daurin qirji da kuma qaramin hijab fari,sai jakar kayan wankanta dake riqe a hannunta,daya hannun nata kuma wayarta ce "Wanne irin sakarci ne haka zaki fadowa mutane ba sallama?,banason tsiyatakun banza da wofi fa?" Cuno bakinta tayi gaba tana sauke wayar daga fuskarta tana kallon anni "Don girman Allah anni ki karba wayar da abbi ya baki ko zamu huta da ire iren takurar su ya jabir" gyara zamanta tayi tana kallonta sosai "To...idan kuma naqi sai yaya kenan uwata?" Hannu laila ta yarfe,bataso annin ta hutsance mata,lallabata takeson yi ta karba a wuce wajen "Anni.....yanzu fa wanka zan shiga,ashe muna hanya daxun ya kirani banga miscal dinsa ba sai yanzu,ina daga wayar ko tsayawa amsa sallamata baiyi ba ya hauni da balbalin masifa,Ni bansan sanda ya koma haka ba wall....." Maganar tata ta katse saboda shigowar wani kiran,saita duba sannan tace "Gashinan ma" gaba data tattar wayar harda earpiece din jiki ta miqawa anni ta juyawa tana shirin ficewa "Wannan zaren na jiki da kika hadani dashi shi zan qaqabawa kunnena?,bada ni ba gada a maqabarta,zoki tsige abinki ki karbi naji da gayan wayar ma" dole ta dawo ta cire matan yadda ta buqata da sauri don kada kiran ya katse ta sake jazawa kanta wani sabon mita da qorafin. *Arewabooks:Huguma* *10* "Assalamu alaikum" ta furta kamar yadda yake a al'adarta duk sanda zata amsa waya,daga daya sashen muryarsa ta bayyana,cikin sanyi daya sanya annin ta shanshano wani abu daga gareshi tun kafin yace wani abu "Barka da dare" "Dare?,a garinku kenan" daga can sashen da yake sai daya dafe goshinsa,ba zata taba yarda ta karba yadda ya bata ba sai tayi challenging dinsa "To barka da safiya shikenan?" "Yanzu naji magana.....barkanmu kadai" dorawa yayi da "Kun tashi lafiya,ya jama'ar gidan?" "Alhamdulillah,lafiya qalau,jama'ar gida mun barsu a gida,mu mun danyo balaguro nan cikin adamawa" "da wannan qafar anni?" Ya fada murya a kwance cikin nuna kulawa "Eh,to ya za'ayi,duk inda Allah ya tsaga sai ka taka saika taka din kafin lokacin da takun naka zai qare" "Hakane....." Ya fada a taqaice "Banji duriyar jafar ba" ta fada cikin zaquwa da son jin muryarsa,ajiyar zuciyar da taji jabir din ya sake sai da gabanta ya fadi "Maganarshi na kira nayi miki anni" ya fada a sanyaye "Menene kuma?" Ta tambayeshi gabanta yana faduwa "Anni har yanzu dai.....har yanzun babu wani ci gaba anni,sai abubuwan sunyi kamar zasu gyaru sai su sake rikicewa" "Kuma dai?" Ta fadi cikin tsantsar damuwa,kamar tana gabansa ya gyada kai "Wallahi anni,yanzu haka tun jiya banga fuskarsa ba,nayi iya bakin qoqarina ma naga ya fito ko ruwan zafi ne ya sha idan ma bazaici abinci ba amma ko motsi yaqiyi bare ya bani alamar da zata gayamin yana raye lafiya lau" "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" kalmar da taja hankalin yuuma,ta koma ta zauna daga shirin tashin da takeyi din,ta kuma kamawa daada sukakai salatin tare. Sosai fuskar anni ta nuna alamun tashin hankali da kuma damuwa,wannan wata matsala ce data zama kusan jarrabawa cikin tata rayuwar,saidai a yadda Allah yayi mata komai a rayuwa,ya albarkaci zuri'arta,to ta dora hakan a matsayin jarrabawar da ubangiji kan yiwa kowanne bawa don ya gwada imaninsa "Ka kira wayarsa?" "Ya rufeta anni,yaqi bude wayar.....amma ki kwantar da hankalinki,koda bazaice komai zan sanar dashi daga bakin qofa,awa uku suka rage ya cika awa ashirin da hudu a dakin,idan har bai bude ba ya fito zan sanarma jami'an tsaro na qasar su shigo su balle qofar su dubamin shi,duk da jikina yana bani lafiya qalau yake,tunda fitilar dakinsa naga a kunne take tun jiyan kawo yau" "Jabir.....duk yadda zakayi ka tabbata kayi ya fito haka a dakin nan,na gaji da zamanku a wannan qasar jabir,bana jin zan barku kuci gaba da zama kamar yadda kukeso" "Kada ki damu anni" "Ka kula dashi don Allah,duk abinda ake ciki ka shaidamin,kada ka yarda da maganar babanku kan kada a gayamin komai,ni hakan shine kwanciyar hankali na" "In sha Allah,i will do my best anni" Jikinta a matuqar sanyaye ta sauke wayar daga kunnenta ta ajjiyeta a gefanta,sai ta hade hannayenta waje guda "Ya Allah.....mun tuba Allah,Allah ka kawo mana qarshen wannan matsalar,wannan damuwa Allah ka yanke mana ita gaba daya,ubangiji ka aiko mana da HASKE" "Ameen......lafiya kuwa anni?" Yuuma ta tambayi annin cikin matuqar kulawa da kuma damuwa,saboda ta fuskanci koma wacce irin matsala ce lallai ba qarama bace a wajen annin "Jafar ramatu,har yanzu jafar ya kasa komawa kamar kowanne irin mutum,jafar ba jahili bane....amma bansan me yasa ya kasa yarda da qaddararsa ba,gaba daya rayuwar jafar ba ita bace a yanzu,wani jafar ne na daban da dukka muke kallon an sauya mana shi,tsahon shekara uku amma komai ya kasa wucewa?" "Jafar dai anni?" Yuuma ta tambaya tana dubanta,kai ta jinjina "Shi.....tun daga shaheeda da amra suka rasu,bamu sake gane kan ja'afar ba,babu irin roqon Allahn da ba'ayi masa ba,ana kan yi masa ma,ba irin nasiha jan hankali da ban bakin da jafar bai samu ba,ba za'ace babu sauqi ba sam,saidai tashi danganar data zo sai tazo wani iri,duk da cewa dama miskili ne mara son magana me kuma bau dadden hali.....amma hakan baisa rayuwa ta naqasa tako ina ba,yana rayuwarsa kamar kowa,yana kuma yin dukkan wani abu daya dace da mutum kamarsa zaiyi,amma tun bayan nan jafar gaba daya ba shine tare damu ba,sai abun yayi kamar zai dai daita,sai ya sake dilmiya cikin damuwa me zurfi,na dauka zaman gidansa ke sake dagula masa lissafi......sai nasa ya tattaro ya dawo cikin gida,duk da haka babu wani canji,sai na sake tunanin kodai zaman kadaici ne?,tunda a baya shi din me aure ne?,na shiga nema masa yarinyar da zata dace dashi,ta kuma kula dashi......amma abun takaicin,wallahi ramatu yadda kikasan nayi busa a iska,baisan ma anayi ba,wannan yasa duka yaran suke kasa daurewa,saboda kowacce tana tsammanin samun kulawa da soyayya daga gareshi,to duka babu ko daya da suke samu,abinda yake sanyasu sarewa kenan,su kuma ce sun haqura......ba tare da sun duba cewa a yanzun shi din tamkar mara lafiya yake ba,zuciya da qwaqwalwarsa na buqatar magani ta hanyar mu'amalantarsa da dawowa dashi ya dawo ja'afar na asali......sannan koma meye sai ya biyo baya.....karo hudu kenan,amma dukkaninsu sun gaza daurewa zama dashi.......abinda ya bani mamaki da tsoro,yasa kuma na saare shine,wadda na nema masa a karo na shida 'yar uwarsa ce,a yadda abun ya dauko naji dadi.matuqa,saboda ina hangen haske da kuma waraka,don yadda yarinyar ta jajirce,ashe akwai mummunar manufa a ranta,dukiyarsa take hange,Allah ya toni asirinta,na gano na kuma watsa tafiyar,tunda dama shi wanda ake dominsa baima san inayi ba" shuru anni tayi tana maida numfashi,abun yana matuqar damunta da zuciya,a yanzu duk duniya zata iya cewa bata da matsala sama da wannan. "Iyaka nazari da hangena,babu wata hanya da zamu samu yadda mukeso sai ja'afar ya haqura yayi aure,saboda jabir bazai taba dawwama tare dashi ba,shima mutum ne,aure zaiyi,don maganar da ake yanzun,watanni kadan suka rage akai masa kudi da sa rana,yau idan jabir ya tafi,shikenan haka zamu zuba idanu muna kallon rayuwar jafar ta dulmiya ta nutse a gaban idanuwanmu?" Kai yuuma ke girgizawa,tsahon wasu mintuna shuru ya baqunci dakin,kafin yuuma ta saki ajiyar zuciya "Maganarki gaskiya ce anni,hanya daya ce tak ta fitar da ja'afar daga yanayin da yake ciki,hanyar kuwa itace,a sama masa mace mai tsananin sonsa,so fisabillahi saboda Allah,jajirtacciya da zata iya kasancewa koda yaushe tare dashi,mai juriya da zata iya daukan dawainiyarsa.....komai nisan zangon da zasu samu dashi kafin a cimma gaci...." "Wannan shine abunda muka kasa samu har yanzu" anni ta katsi numfashin yuuma,gyara zama yuuman tayi "A nawa tunanin kaf cikin matan da kuke nema masan,kuna sama masa ne irin matan can wajejenku,wadanda idanunsu ke a bude,suke ganin cewa 'yantattun mata ne su,wadanda zasu shiga gidan aure ne da dukka iko da isa irin wadda d'a namiji ke da ita,ba bautar aure zasuyi ba,zama ne na 'yanci da cin gashin kai" shuru ne ya sake ratsa dakin,sai hayaniya daga jama'ar dake karakainarsu daga waje jifa jifa tana ratsasu. Sosai maganar yuuma ta ratsa anni,ta kuma sanyata zama ta dinga wareta daya bayan daya tana nazarinta,lallai yuuman tayi wani dogon nazari da kuma tsinkaye,wanda ita kanta bata yishi ba tsahon lokacin da aka dauka matsalolin suna faruwa. Kusan rarrabuwa hankalin anni yayi kashi kashi,tana sauraren kira daga khalid,tana kuma ci gaba da nazarin maganar yuuma,tare da tunanin inda zata kamo bakin zaren,ta damu da ja'afar matuqa,tana kuma shiga damuwa ainun game da lamarinsa. Sam hankalin anni bai kwanta ba har sai data samu tabbacin lafiya lau daga bakin jabir "Ka bani shi jabir zamuyi magana" kai jabir din ya girgiza yana duban bakin qofar dakin da yake zaune a yanzu daura da ita,kamar wanda aka bawa gadin wajen "Bai fito ba har yanzu anni,duk da munyi magana,amma ina da tabbacin nan da dan wani lokaci koda baiyi kiran kowa ba zaiyi kiranki" ya fada with full confidence,saboda yasan tsakaninsa da annin "Shikenan,ka sake kula don Allah jabir" "In sha Allah anni" ya fada shima zuciyarsa na karyewa,bayason wannan ja'afar din na yanzu,yafi qaunar ja'afar dinsa na asali,duk da dama tun asali azama da ja'afar din sai shi,duk da yadda mutane suke daukansa suke kuma kallonsa....amma zai iya cewa bai taba rayuwa da wani mutum me dadin zama irin ja'afar din ba,wasu abubuwa ne game tattare dashi da idan ka fahimcesu shikenan. Wunin ranar gaba daya anni ta qarar dashi kan tunanin maganganun yuuma,ita kanta yuuma ta fuskanci yau din annin akwai damuwa fal tattare da zuciyarta,don ko abincin rana data kawo mata bata cishi ba sai kusan gefin la'asar,ta jima sosai tana waya da daya daga cikin yayanta. Sanda rana ta kammala faduwa,wanda ya zamana lokaci ne na sallar magariba,annin na daya daga cikin mutanen da basa wasa da ibada,wannan ya sanya ubangiji ya bata kyakkyawan tsufa da kuna qwarin jiki,banda ciwon qafa babu abinda yake damunta,zaka zaci shekarunta basu kai yadda take fada ba. Tana saman abun sallah tana lazumi,hannunta riqe da carbinta,ta tsakankanin labulen dakin tana hangen wulgawar mutanen gidan kowa na sabgar gabansa. Waiwayawa tayi ga laila dake kwance tana latse latsen waya abinta sakamakon bata sallah ta watsa mata harara,ta shafa addu'arta tana shirin mata magana akayi sallama daga tsakar gidan. Tsam anni tayi da ranta,saboda sautin muryar kamar tasan me ita,hakanan sai taji kamar ta saba jin muryar dama. Yuuma dake alwala tana wanke qafafuwanta ta waiwayo,sosai mamaki ya cikata,karon farko bayan wasu shekaru da suka shude rabon da taga maimunatu cikin gidan,don haka ta miqe cikin kulawa "Lafiya maimunatu?" Tafukan hannuwanta dake a dunqule ta budewa yuuma,kyakkyawar sarqar wuya ta ainihin dutsen wuri da kuma murjani na asali ta bayyana "Kun yada wannan ne a gidanmu dazu" zubawa sarqar idanu yuuma tayi,don tasan bata da ita,dutsene maj tsada wanda su kansu fulani sunsan dajarsa "Anya kuwa?.....amma....qarasa rumfata ko anni ce,don nasan da laila ba zata saka wannan ba" kai ta gyada tana sakin siririn murmushi,sannan ta fara takawa zuwa rumfar yuuman,gabanta yana dukan uku uku,batason ta hadu daada mahaifiyar ibrahim,bare shi ibrahim din kansa,ita daya tasan irin jan kunne da kums gargadi da tasha daga wajen inna furera,ba shakka banda akwai qudurin da innar keson cimmawa ma,babu abinda zai sanyata ta kawo musu sarqar. "Wa'alaikumussalam,shigo mana" anni ta fada tana zubawa maimunatun idanu sanda take sanyo kai cikin dakin,idanunta ya sauka ga gefe wuya da kuma kunne zuwa kuncin maimunatu karo na barkatai a yau din,ita din bata jiya bace ba kuma ta yau bace,wannan tabon tun dazu data kalleshi ta tabbatar da cewa na duka ne,to amma me yarinya kamar maimunatu tayi da za'ayi mata irin wannan dukan?,me aka saka akayi mata wannan dukan dashi?,sai taji ranta yana baci abinda.bai faru ba a yanzu. Ita din wata irin macace da bata qaunar zalunci ko kadan,ko kai waye,ko yaya kake da ita,matuqar ta fuskanci kana da dabi'a ta zalunci yanzu zaku raba hanya. Gaban annin ga durqusa,tasa hannu biyu tana miqa mata sarqar,anni ta miqa hannu ta karba "Hukumullahi...ni nayar da ita,tabbas,to kinga basan ma ta fadin ba banda Allah ya tsananta rabo yanzun kin ganta kin kawomin,da haka zan yita bulayin nemanta" anni ta fada tana sakarwa maimunatu murmushi,zuciyarta da ruhinta cike da soyayya da kuma kaunar maimunatun,halayenta mabanbanta ne da halayen sauran al'umma,abar yabo ce ta gaske kuma a zahiri,godiya ta yiwa maimunatun sosai,tans juya abun a ranta ta tayar da sallah. "Anni.....gaba daya yau tunani ya sanyamin ke agaba,komai yayi zafi maganinsa Allah anni,aci gaba dai da addu'a,wataran komai zai warware in sha Allahu" yuuma dake ajewa anni kwanon tuwo ta fada,don idan annin tazo har ta koma babu ruwanta,irin tasu cimar takeci,takan ce ko a gida rashin samun me tsaya mata da irin cimar ne yadda takeso,amma ita bata da kamar irin abincinsu. Ajiyar zuciya annin ta sake tana miqe daya qafar tata data jima a lanqwashe ta fara yi mata tsami "Ramatu,inajin wani abu a jikina tattare da yarinyar nan" "Wa fa?" Yuuma ta tambayi anni tana tattara hankalinta gareta "Maimunatu" "Ohhh.....maimunatu?" "Ita.....tun dazu da mukayi magana dake ramatu nake juya zancan cikin raina,da magaribar nan bayan yarinyar tazo ta kawomin sarqa ta,sai gaba daya tunani ya damfaru a kanta,na lura da irin dabi'un da nake buqata tattare da yarinyar,ta hada juriya haquri da kuma amanar da zata iya zama da ja'afar,dabi'u da kuma halayen da tabbas zata iya dawo da ja'afar yadda yake ja'afar dinsa" "What!" Laila dane kwance ta fada cikin rata,har maganar tata taso ta fito fili "Me anni ke fada ne?,ta manta waye ya ja'afar?,ta manta waye yaa J?,the classic and unique guy?,ya ja'afar fa ake magana da wata bafulatanar ruga?,saura kadan ta miqe ta zauna,amma sai taci gaba da kwanciya,tanason jin yadda maganar zata kaya. Dukka idanunta yuuma ta fidda tana duban anni "Anya kuwa anni?,bakiyi ragon tunani ba?ja'afar fa?" "Me yasa kika ce haka ramatu?,ko hasashe na bai hasaso dai dai kan dukka nagartarta ba?" Kai yuuma ta girgiza a hankali tana juya abun a ranta,bai kamata tayi shuru ba wani abu ya kasance daga baya kuma ta zama abar zargi ba daga kowanne bangare,abu me muhimmanci ta fara gayawa anni wace ainihin maimunatu tukunna "Dukkan abinda kika hasaso akan halayen maimunatu haka suke,yarinyar har tafi haka ma,dukka rugar nan sunsan da wannan,saidai wani baqar al'ada da jahlici gami son rai sun rufe musu idanu basa ganin wannan,bari na gaya miki wace maimunatu tun daga tushe,wanda ba kowane cikin rugar nan ya sani ba,domin kuwa,ni din,nice qawa qwaya daya tilo da mahaifiyarta keda ita a rugar nan,wadda bata da kamata,wani rikici da ya faru tsakanin gidan da gidan nan yasa bappa ya yanke huldata dasu saboda wanzar da zaman lafiya,abinda ya rabamu kenan da shatu,har zuwa sanda ta koma ga mahaliccinta" kai anni ta gyada tana bada hankalinta zuwa ga yuuma,yayin da itama yuuma ta nutsu sosai ta fara yima anni magana "Furera mahaifiyar gaje,waddda kukayi ciniki a hannunta,mata ce ga jauro,wadda keda yara biyu dashi,macace mara mutunci ta gasken gaske,wadda ba kasafai ake tabota ta qyale ba,me son abun duniya ce da kuma masifar son 'ya'ya,asalinta bafulatanae gembu ce,jauro ne dan wannan rugar,muna zaune tare da ita tsahon shekaru,kwatsam tayi baquwa,wadda ta shigo rugar nan tare da furera da taje ganin gida,matar itace shatu,wadda tazo da diyarta maimunatu......sun shigo tare da tarin dabbobi wadda dukka dabbobin nan mallakin shatu da diyarta maimunatu ne,amma kuma a idanun kowa dabbobi na furera ne,don a haka ta gayawa kowa wannan labarin,ta shaidawa mutane cewa gadonsu dama taje gida karbowa ta taho dasu,ta kuma hado da wadda zafa dinga mata kiwo tana biyanta wato shatu,abinda zai baki mamaki,shatu ba kowace bace a wajen furera face 'yar uwarta da suke uba daya,bata da ikon musawa ko qi,saboda a sannan shatun na cikin wani yanayi na tashin hankalin rayuwa,tana neman mafaka,mahaifin maimunatu baqo ne,irin baqin dake shigowa garin na gembu saboda huldar kasuwanci da kuma yawon buda idanu,a nan yaga shatu ya kuma tsaya kai da fata sai daya aureta,a nan garin ya barta saboda ta nuna tafison zama cikin danginta,yana zuwa yana ganinta yayi mata kwanaki ya koma,mutum ne mai arziqi,don haka gida na alfarma ya ginawa shatu,ya zuba mata dukka kayan alatu da more rayuwa,ta yadda gidan shatu shi ya zama abu kwatance da kuma burin kowa cikin garin nasu,wannan ya haifar da hassada daga zuciyar 'yan uwanta da suke 'yan uba,saboda ita shatu su biyu mahaifiyarsu ta haifa a gidan,ita da 'yar uwarta sa'ade,kusan jinin dakinsu ne haka,sannan kuma da baiwar zallar kyau da Allah yayi musu fiye da sauran 'yan uwansu,itama sa'ade nata mijin me hali ne sosai,hakan ya sake haifar da zallar 'yan ubanci a tsakaninsu,saidai sunata dannewa saboda suna rabarta suna kuma samun akhairai da abun duniya daga wajenta,kasancewarta ba mai rowa ba,a haka ta haifa maimunatu,dukka alhaji na zuwa wajenta ne yayi mata satittika ya tafi,bayan ta.haifi maimunatu yake maganar zai kaita taga danginsa,saidai kuma wata tafiyace ta taso masa,wanda ya dauki tsahon watanni kafin ya dawo,koda ya dawo din kuma shima yana da niyyar kaita,har sun shirya sun saka rana,yace zai taho takanas daga kano ya dauketa. Shiri sosai shatu tayi domin zuwa ganin surukanta,ta shirya maimunatu da kyau wadda ke samun gata kamar babu gobe,itama haka,saidai haka ta yita jiran alhaji amma shuru babu shi babu dalilinsa,nata da wayar hannu bare ta nemeshi,haka tayita zaman jiransa har dare yayi ta fidda tsammani,ta sanyawa ranta qila wani abune ya tareshi,ta barwa gobe. To washegarin ma dai haka ta yita jiransa shuru babu shi babu labarinsa,haka wata washegarin,wasa wasa sai ga kwanaki nata tafiya shatu bata sake ganin gilmawar alhaji ba,abun ya daga hankalinta qwarai da gaske,tafi tafi watanni suka fara shudawa shuru babu shi babu dalilinsa,ga ciki da ya bayyana a jikinta,ita dai ta yarda da alhaj dari bisa dari,saboda iya tsahon zamata dashi tsakaninsu ita dashi babu komai sai son barka,mutum ne mai son addini da kuma kiyaye dokokin Allah,kusan a wajensa shatu tayi karatun addini mai dan dama wanda ta dinga koyawa maimunatu,duk da a sannan ta sanyata makarantar islamiyya da boko,amma kamar tasan yadda rayuwa zata juya musu,sai take zama duk bayan sallar magariba take mata nata karatun,ganin cewa yarinyar tana da budaddiyar kwanya dake saurin kwashe karatu,don tun bata isa sakawa a makaranta ba ta sanyata,tace tayi wayon acan,hakan yasa adan lokacin ta samu karatu me yawa,tana cika shekara tara zata shiga ta goma ta gama primary,mahaifinta nada niyyar yi mata shirin shiga makarantar gaba wannan abun ya faru" *Follow my arewabooks account for more new pages* HUGUMA *11* "Yau da gobe bata bar komai ba,hakanan zara bata qyale dami ba,dukka kayan abincin da shatu ke dasu wanda alhj ke jibge mata suka faru suka qare,ta fara kame kame,a sannan yan uwanta suka fahimta,sukayi mata caa,yar uwarta saade tace kada ta kulasu,ita ta dinga taimaka mata har zuwa wani lokaci,wanda kishiyar mahaifiyarsu wadda wajenta suka rayu sanadiyyar rasuwar mahaifiyarsu tun suna qananu ta tayar da borin qarya,ta tara manyan gari,ta fada musu qabli da ba'adi kan rashin dacewar zaman shatu ita daya cikin gidan,tace saidai lallai ta dawo gabanta da zama,saade yayar shatun bata qalubalanci hakan ba,hakan yayi,duk da tasan badon Allah inne tayi hakan baAmma kuma bayan giya akwai wata caca,maza maza tayi ta sanya aka saida gidan da shatu ke ciki,tunda mallakin alhj ne,ya ginawa shatun,ta tattara kudin ta siyawa shatun dabbobi ta damqa mata,saboda gudun abinda kaje yazo,babu jimawa shatu ta tattara ta koma gida ita da maimunatu,gidan da suka fara sabuwar rayuwa me cike da qunci da kuma takura,wahalhalu iri daban daban,zuciyar shatu na cike da qauna da kuma begen mijinta,jiki da zuciyarta sinqi yarda da zancan daketa yawo a garin kan cewa,mijinta guduwa yayi ya barta,tafi kowa sanin halinsa,tayi imani bazai aikata mata haka ba. Zama ya sake tsanani a wajenta sanda inne ta fahimci cikine da ita,tayi tsalle ta dire kan ba za'a haifa mata dan da bashi da uba ba,maganar data tsayewa shatu da saade a rai,ta kuma kusan haifar mata da ciwo,a lokacin saade bata kusa da ita,kasuwanci ya shillata ita da mijinta zuwa benin republic,wanda tayi matuqar baqincikin hakan,saboda sanin halin da 'yar uwarta take ciki,amma babu yadda zatayi dole tabi mijinta. Ana tsaka da wannan fa shine inna furera taje garin,ita tunda ta qyalla idanu taga dabbobin da shatu ke dasu tayi mata romon bakin ta biyota rugarsu tayi xamanta,ta kula da dabbobinta ta haihu a can babu takura. A zaton shatu ta samu mafaka a wajen yayartata,saidai tun basu kai ga shigowa rugar ba ta fara yanka mata sharuda tare da shaida mata dokokin da rugar ke dasu,suka kuma yi yarjejeniyar dabbobinta zasu shiga a mazaunin na ita fureran,idan ba haka ba zaayita kawo musu farmaki ana kashesu tunda ita baquwa ce. Ko a sannan shatu shekarunta basu fi ashirin da hudu ba,saboda auren wuri akayi mata kamar yadda aka saba. Shatu ta shigo baquwa a rugar nan,wadda hatta da kyanta ya banbanta da irin namu,babu tausayi ko tsoron Allah furera ta maida shatu da maimunatu tamkar bayi da basu da 'yanci,shatu bauta maimunatu bauta,Allah ya zubawa shatun wani irin haquri juriya da kuma kau da kai wanda cikin irin nata ta sanwa maimunatu,don babu lallai tayi yakai irin nata,a haka dai suke rayuwar. Abinda ya faru ya kuma janyo shatu da maimunatu suka zama abun qyama shine......a al'darmu ta fulani,baka ganin nagge ko sauran dabbobi ka nuna su tankasu,komai kyau da burgewar da suka baka,cikin irin haka,cikin rashin sani shatu taga wasu nagge na bappa labaran,yana gab da fita dasu kudu,ranar an fiddasu kiwo ta nuna wata babbar nagge a cikinsu tace a haka kamar lafiyayya me kyau da ita,amma kuma bata da lpy,suka yita fada dame kiwon,aka mata ca,ta bada haquri,saboda mantawa da tayi ta aikata hakan,kuma tace tana musu tsoron asara ne,magani ya koma a maidata gida a bata,koda suka dawo gida baice bata da lafiya ba yadda shatu ta fada,ba'a wayi gari da naggen ba ta rasu,rigima sosai daada taso a tayar,amma bapp ya hana,abinda basu sani ba ni da kaina bayan asuba na fita zan dora sanwar safe,na lura da naggen bata da kuxari yadda ya kamata,ni da kaina nasan tabbas bata da lpy,to amma dana fada qaryatani daada tayi,tace kawai dai don tana zuwa wajena ne yasa nakeson kareta,anyi wannan rigimar ta mutu,shatu da tsohon cikinta taje diban ruwa matan gidan barau daya daga cikinsu ta takaleta da fada yadda suka saba mata,tunda muke da shatu bata taba gayamin ko kawomin qarar kowa ba,amma inajin labarin yadda wasu cikin rugar suka matsanta mata,a ranar taso dauke kai amma yau da gobe,ga yanayin tsohon ciki haihuwa ko yau ko gobe,talatu bata duba wannan ba ta dinga ja mata riga shatu na gocewa,daga qarshe dai da talatu taga ba zata kulata ba sai ta tureta,wanda sauran kadan ta afka cikin rafin,Allah ne kawai yayi ruwan ba shine ajalinta ba,sosai ran shatu ya baci bayan tasha da qyar,cikin bacin rai idanuwanta cike da hawaye ta kalleta "Na dauka ko banci darajar komai a wajenki ba zanci darajar cikin dake jikina,tunda kema macace,idan kinyi hakane don ki tozarta ni kije,Allah yana gani,kuma ina fatan kiga sakayya da gaggawa anan kusa" daga haka shatu bata qara ba bata rage ba,ta dauki ruwanta ta wuce,suka taru suka yita maida magana,tare da maido maganar nagge,a nan suka fara qulla wataqil mayya ce ita din,kwana biyu tsakani kuwa talatu taje diban ruwa ruwan yayi ciki da ita,ya kuma zama ajalinta,aka fara lugwigwita magana tare da fara yada jita jitar shatun mayyace,kafin kace me?,magana ta fantsama a gari,dangin talatu da sauran mutane 'yan bani na iya suka dauki sanduna sukayi gidan furera kan sai an fiddo shatu sun kasheta,ya tabbata mayyace ita,da qyar da sudin goshi qurar ta lafa,baiwar Allah shatu,ashe sanadin wannan tashin hankalin naquda ta tasammata,furera haushin abinda ya faru tayi banza da ita,daga ita sai maimunatu ne suka yita fama,daga qarshe tace maimunatun ta lallaba ta kirawo mata ni,har maimunatu takai bakin qofa ta qwala mata kira,saita tsaya,ta yafitota da hannu ta koma gaban shatun ta duqa "Daada,akwai wani abun da kike so ne?" Murmushi ta sakar mata,ta daga hannayenta ta cirw dukka duwatsun jiki da maimunatu ta dade tana qulafucin tabar mata ta zura mata su,saidai yarinyar a sannan sam bataji farincikin da take ayyanawa zataji ba duk sanda daadar tata tabar mata dutsunan "Daada kin barmin ne wai?" Kai ta gyada "Na bar miki maimunatu......kiyi haquri kiyi haquri.....kiyi haquri kinji,ki fuskanci rayuwa duk yadda tazo miki,ki zama mai gaskiya da amana,karki yadda a kamaki kinci amanar wani,idan kinga saade,kice ina mata fatan alkhairi" sanda yarinyar ke gayan abinda uwar tace nayi mamakin yadda ta iya riqewa,hankalin maimunatu a sannan ya tashi sosai duk da qarancin shekarunta,ba kowa zai gane hakan ba sai wanda irin haka ya sameshi,cikin rudewa tace "Daada" hannu ta daga mata "Barci nake ji,yi sauri ki kiramin yuuma" maganar data sanya maimunatu tashi ta fita a dakin da gudu,fitar da ta zama silar rabuwarta da mahaifiyarta kenan rabuwa ta har abada,don koni sanda na shiga wajen shatu rai yayi halinsa,haka akayi mata sutura bata ko haife abinda yake cikinta ba,sanda na koma gida da daddare randa shatu ya rasu,tunda na tsaya na taya maimunatu da bata dame rarrashinta zama,mahaifiyarta ta rasu ta barta babu ko mutum daya da zata jingina dashi tayi kuka taji sauqi cikin ranta,Bappa da kansa ha sameni,ya shaida min ya yanke hulda da wata alaqata da duk abinda ya shafi shatu matuqar shike aure na,duk randa na kuskurewa hakan kuwa,zai dauki tsatstsauran mataki a kaina,bansan me aka gayawa bappan ba bayan fitata wajen shatu,amma dai na sani cewa akwai qullin daadar himu da kuma furera a ciki da suka sake tunzura komai,don kuwa bappan mutum ne mai sanin ya kamata,sannan ta yaya zaa rabani da maimunatu kuma abar mu'amalar dake tsakanin furera da daadar himu?,bayan duka gida daya ne,abu daya ne?,duk da furera ta cikasu da labaran qarya na cewa babu abinda ya hadata da shatun illa aikin bauta data dauketa,mutuwar shatu sai furera ta sake sakankancewa,ta mallake dukka dabbobin shatu da maimunatu suka zama nata,maimunatu bata tashi a komai ba illa me aikin bauta,ta riqeta wani irin riqo na qunci da kuma wahala,dole inaji ina gani na dauke idanuna daga kan maimunatun,nayi kamar bansan tana raye ba,saidai ban fasa mata addu'a ba da nema mata sasauci" "Yanzu 'yan wadan nan abubuwan sune suka zama hujja da kuma dalilin da ake qyamatar yarinyar bayan cikin abun babu wani abu guda daya data aikata?" "Sune anni" kada kai kawai anni keyi,wani abu ya tsaye mata a zuciyarta me taba rai,tana kwatanta yuuma da maimunatu,inda an samu sakaci ko wani abu makamancin hakan haka zai iya faruwa da yuuma kenan sanda tana qarama,duk da ita tana gaban mahaifinta ne cikin soyayya da kulawa a sannan?. "Wannan duka ba hujja bace,zallar jahilci ne da kuma son zuciya,kuma tabbas sai Allah ya yiwa yarinyar sakayya,zan dauke maimunatu daga wannan garin don bata cancanci zama a nan ba,maraya?,maraya wasa ne?,daka taba maraya hawayensa guda daya tak ya diga a qasa saboda kai,gwara ka rasa dukkan abinda ka mallaka ciki harda lafiyarka,kukan maraya masifa ne bare a sakashi a damuwa" yalwataccen murmushi ne ya bayyana fuskar yuuma "Da nafi kowa jin dadin hakan anni,tabbas zanfi kowa murna" "Kafin na wuce zan karba maimunatu zan wuce da ita,in sha Allah qarshen kukanta yazo,lallai mahaifiyarta macace mai nagarta,nagartar da nake jin yaqini da tabbcin akwaita tattare da maimunatu,tunda dukkan alamu sun bayyana" "Amma anni wani hanzari ba gudu ba.....anya kinyi duba da tarin banbanci da tazarar dake tsakanin ja'afar da maimunatu kuwa?,shirinki me yuwuwa ne?" Tambayar dake rai da zuciyar laila kenan,labarin ya dauki hankalinta cike da mamaki da kuma al'ajabi,zuciyarta kuma ta narke matuqa da tausayin maimunatu "Nasan ta inda zan bullowa lamarin,ki tayani da addu'a,kiyimin fatan dacewa" ajiyar zuciya mai qarfi yuuma ta sauke "Allah to yasa a dace,yasa ta silarki marainiya maimunatu zata samu salaama a rayuwarta" "Ameen ya hayyu ya qayyumu" anni ta fada tana lanqwasa yatsunta,tare da tunanin ta inda zata fara. *_Arewabooks::huguma_* ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* 😄😄😄😄😄😄😄 *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 12 Ajiyar zuciya ta sauke sanda ta tabbatar ta maida sarqar wa anni,ta godewa Allah da ya hani inna furera sanya son zuciyarta a gaba ta hana a maidawa anni sarqar,ta tabbata da ta aikata haka ba zata taba samun nutsuwar zuciya ba,haka zuciyarta take,bata qaunar haqqi koda qanqani a kanta,dalilin da yasa ta guji kiwon dabbobinta da bugu kenan,ta zabi horar dasu da magana. Sosai hankalinta yayi nisa cikin zuzzurfan tunani,abinda ya sanya kwata kwata bata ankara da tahowarsa ba,sai da taji ta bugi wani abu sannan ta tsaya cak,ta kuma ja da baya da sauri tana kai dubanta gabanta. Himu ne,sanye da kayan fulani,ya fito a bafullataninsa sak,kayan sun matuqar karbarsa sun kuma haskashi matuqa,saidai babu fara'a ko walwala kwata kwata saman fuskarsa. Gabanta ne yayi mummunar bugawa sanda ta tuna da gargadi da kuma izayar da tasha hannun inna furera duka akan himu,abinda ya sanyata yin gaba da sauri ta rabeshi zata wuce,saidai cikin hanzarin shima ya matsa ya tare mata hanyar,da azama ta koma daya hannun nan ma ya bita ya tare,ya kare ko ina,bata da zabi illa ta roqeshi "Don girman Allah ka bani hanya na wuce" "Saboda me maimunatu?,me yasa kike guduna?" Tsoro ne ya sake kamata,sam bazai fahimci halin da take ciki ba,wannan tsaiwar da yayi a gabanta sai takejin kamar ana tsigar ranta "Magana nakeso muyi dake maimunatu" wace magana?,a yanzun akwai.maganar kuwa da ita din zata fahimta? "Kayi haquri,bazai yiwuba,ka barni na wuce" "Dole ki tsaya ki saurareni maimunatu,don me yasa zaki saurin bada kai akan soyyayarmu?,kodai dama bakya sona?ni daya nake kidina da rawata?" Tuni hawaye ya balle mata,himu so yake kawai ya janyo mata bala'i,baisan yanayin da take ciki ba,da bai tsaya haka a gabanta ya tilasta mata sai sunyi magana ba,bayan ita bafahimta take ba,ta juya baya a matuqar razane sanda taji takun tafiya,take qafafunta suka fara rawa,sai shima ya waiwaya yana duban hanyar. Kaf jinin jikinta sai daya daskare sanda taga inuwar mutum kuma macace a wajen,abinda ta baiwa ranta shine daada ce ko zubaida ko safiya,ta saddaqar ta gama yawo,kashinta kuma ya bushe,tun daga fuskarta zuwa tafin qafarta sukayi sanyi qalau "Kuyi haquri,na katse muku jin dadin ku ko?,zan dan wuce ne?" Laila ta fada tana dan sakin fuskarta,ta fuskanci akwai wani abu me kama da soyayya a tsakaninsu,to amma anni tasan da haka kuwa?. Jin baquwar murya da sautin da ba na fulani ba ya taimaka wajen dawowarta hayyacinta,matsawa laila himu yayi ta fara wucewa,abinda ya baiwa maimunatu damar yin wuf tabi bayan lailan "Maimunatu" ya kirayi sunanta,saita qara hanzari da kyau ta fara shawarar bi ta duhuwa don kada ma ya biyota ya jawo mata jarfa "Ina sonki.maimunatu,kuma wallahi bazan fasa sonki ba koda ke baki sona,zanci gaba da sonki har sai na sameki a matsayin matata" kalamai na qarshe kenan dataji daga bakin himu,ta qara hanzari,tana jin cewa inama itadin tana cikin nau'in mata masu hanzari wajen tafiya,lallai da tayi amfani da wannan don ganin ta sake yin nesa da ibrahim. "Haba 'yammata,saurin me kike haka?" Muryar laila dake biye da ita ta ratsa kunnuwanta,yadda ta juyo kawai zai gaya maka har yanzu a tsorace take "ya kike gudun wanda yake sonki?" Laila ta fada a tausashe bayan ta iso gaban maimunatu ta tsaya,ta kuma dora hannunta saman kafadar maimunatun zuciyarta na narkewa a tausayinta. Daddadan qamshin dake tashi jikin laila maimunatu ta zuqa zuwa hancinta,laushin turaren ya sanya zuciyarta karyewa,yadda lailan ta tambayeta cikin taushi da nuna kulawa yasa rauninta ya ninku,take hawaye ya cika idanunta,a wannan lokacin gaza tareshi tayi,sai kuka ya qwace mata. Kasa hanata laila tayi,duba na tausayi takewa maimunatu,tana kwatanta kanta a matsayinta,tana kwatanta inda itace ta yaya zata rayu babu abbi babu momma?,ya rayuwarta zata kasance?,maimunatun jaruma ce qwarai kuma abar tausayi ce ga dukka wani me tausayi. Dole ce zata sanyata ta guji himu ba din ya cancanci a gujeshi ba,bata da yadda zatayi matuqar tana son tsira da lafiyarta da kuma rayuwarta,goge hawayen fuskarta ta fara da tafin hannunta bayan taji zuciyarta ta fara mata sanyi daga radadi da suyar da take mata. "Kiyi haqurk,komai mai wucewa ne,watarana sai labari" daga kai tayi ta bi laila da kallo jin abinda ta fada,tasan wace ita ne?,tana tantama,inda tasan wace ita tatabbatar ba zata tsaya tana magana da ita ba,amma duk da haka a sanyaye sai tace "Miyatti" murmushi laila ta sake "Me kenan?" Murmushin da bata shirya masa bane ya qwacewa maimunatu,ta manta ba da daya daga cikinsu take magana ba "Nace na gode" murmushi lailan ta sakeyi "Babu komai" daga haka maimunatu ta juya tayi gaba,sai kuma a sannan fargabar kada inna taga dadewarta ta qara cikata,don haka saita qara sauri. Bin maimunatu da kallo laila tayi har sai data bace mata,ta sauke ajiyar zuciya me nauyi,a yanzun tana jin zuciyarta ta gamsu dari bisa dari da daukar maimunatu da anni zatayi,saboda hakan tamkar wani babban jihadi ne a wajensu gaba daya,to amma kuma dai dai da qwayar zarra zuciyarta bata gamsu ko kuma kwanciya da qudurin annin na biyu ba,yaa ja'afar fa?,ya ja'afar take magana,ba khalid ba,ba kamal ba,bare jabir,ja'afar take cewa,saita girgiza kai kawai tana komawa hanyar gida,don dama neman network ta fito yi,cikin gidan gaba daya network ya dauke. A ranar maimunatu tayi kuka tayi kuka qwarai da gaske,tana jin cewa farin cikin rayuwa yana sake yin nesa da ita,tana jin cewa tana sake rasa komai nata,sai ta samu kanta da addu'a a karon farko "Ya ubangijina,ka kulaa dani,ka kula da lamarina" saita juya gefe daya tana sake curewa waje guda,hawaye masu zafi na tsiyaya har zuw cikin kunnenta. **********Da fari sanda inna furera taga yuuma a gidanta tadan hade rai,amma kuma data tuna cewa dukka arziqin da tayi kwanaki biyu da suka wuce ta silar 'yaruwarta ce sai ta sakar mata fuska,harda sanya laulo ya dauko mata tabarma,ta kuma qwalawa maimunatu dake baya tana ta faman wankau na kayansu,wanda har yau ma jauro ya hana zuwanta kiwo "Wadi diyam(kawo ruwa)" a nutse ta qaraso ta tsugunna gaban yuuma tana ajjiye ruwan sannan ta gaidata,yuuma ta bita da kallo zuciyarta na tsinkewa tana amsa mata,kullum kwanan duniya maimunatun sake fita daga hayyacinta da kuma kamanninta take,amma a yanzun tayi imanin inda maimunatu zata,zaya kasance mata tamkar tana hannu mahaifiyarta,koma sama da haka. Bayan gaisuwa data biyo baya tsakaninta da inna furaira,wanda ta manta yaushe rabon irin haka ya shiga tsakaninsu,sai yuuman ta gyara zama tana lanqwashe qafafunta "Wajenki nazo furaira" "Allah yasa alkhairi?" Ta fada tana tattara hankalinta ga yuuma "Alkhairin ne,don kullum mu shike tare damu" "To ina jinki" "Ina tunanin baki manta dattijuwar da kukayi cinikayyar nagge da ita ba kwana uku da suka wuce ko?" Fadin haka kawai ya yalwata fara'a a fuskar furaira "Har nabar duniya ai bazan manta da wannan baquwar alkhairin ba" "Ashe kinsan wataran zaki bar duniya furaira" yuuma ta fada cikin ranta,amma a fili saita gyada kai "Ita din tamkar mahaifiya take a wajena...." "Allahu akhbar....." Inna furaira tayi hanzarin fada tana duban yuuma "Amma kike zaune cikin wannan rugar tare damu?" Murmushin da yafi kama dana yaqe yuuma tayi,saboda ita sam ba qaunar wata doguwar magana take ba tsakaninta da furaira "Aure ya gaji haka,yakai diya mace duk inda yaso" "Shakka babu" ta amsa tana qarewa yuuman kallo,ba banza ba ta zama macen da duk fadin rugarsu babu me sutura irin tata,hakanan yanayin hutu da jin dadi daya bayyana qarara tare da ita,hakanan cimar gidan bappa labaran ba inda labarinta bai karade ba,dama daadan ta taba bata labari kan wadda take kawowar "Itace ta aikoni,wato kinsan jikin girma,tana fama da ciwon qafa lokaci lokaci,kuma tana da buqatar mataimaki dai a kusa wanda zai dinga mata wasu ayyukan,to taga maimunatu ta kuma yaba da amanarta,shine tace nazo na tambayar mata ko zaki bata ita,zata dauketa a matsayin ma'aikaciya da zata dinga biya da albashi me tsoka,hasalima tace ki yanka dukka albashin da kikeso a dinga biyanki duk wata,sannan kuma dabbobinki da take kiwo,ki dauki.masu kiwo suma su fadi abinda za'a dinga biyansu,ita zata dinga biya shima" shuru furera tayi,fuskarta na rage kaifin fara'ar dake kanta a dazu,ga qoshi ga kwanan yunwa,haqiqa ko shakka babu wannan albishir albishir ne me dadi a gareta,arziqi kuma har cikin gidanta,saidai kuma ta yaya za'a zabi maimunatu bayan ga gaje?,saboda.matar kana kallonta kasan tana cikin sukunin rayuwa da jin dadi,ita kuwa duk duniya babu wanda takeso ya rayu cikin walwala irin gajenta,gaskiya bata jin zata iya bada maimunatu,wadda take sanya ran tana aurar da gaje ba jimawa ta aurar da ita,ta kuma dora da kiwon da take mata koda tana gidan buderi,sunyi yarjejeniya ya kuma amince,dalilin da yasa.ma ta alqawarta masa auren maimunatu kenan. "Me kika ce?" Yuuma ta fadi ganin furera ta shiga zuzzurfan tunani "nakega me zai hana na baku gaaje?,babu abinda maimunatu zatayi wanda ba zata iya yinshi ba" murmushin takaici ne ga qwacewa yuuma,tana da wannan masaniyar amma ta tattarawa maimunatu dukkan wata wahalar aiki "To ni kinga 'yar aike ce,kuma taga gaaje ta kuma ga maimunatu amma ta zabi maimunatun,ina ganin idan maimunatun ba zata samu ba,zanje na shaida mata kawai,saimu laluba cikin yaran dake rugar" yuuma ta fada tana miqewa,abinda yadan kadan hankalin furaira "Aah,ba za'ayi haka ba,amma inason a bani lokaci kadan zanyi shawara,zan gayawa kuma jauro ma" kada kai yuuma tayi,tasan ba wani jauro da zata gayawa,amma sai ta bita a hakan,sukayi sallama ta tafi. Yuuman na fita ta aiki laulo a sirrance yayi mata kiran daada,bata bata lokaci ba kuwa tazo,ta kuma rattaba mata dukan bayani,kishi ne sosai ya kama daadan,me yasa bata nema safiya ko zubaida ba?,indai ko haka ne bata ga dalilin da zata aika gaje ba su da sukafi kusa da daadan suna zaune,gwara maimunatun taje,ko da zata samu kudi daga gareta ai dai ba zata samu jin dadi da daular dake gidan anni ba "Ya zakiyi ragon azanci irin haka furera?" "Kaman yaya innar himu?" "Ta yaya zaki tura gaaje?,tafiyar maimunatu ai shine dai dai,zata je fa samowa gaje kudin aurenta da wanda zaki mata kayan daki da sauransu,don na tabbatar miki himu gini yake na kere sa'a,kinga kina buqatar kudin da zaki mata duk wata hidima,na tabbar jauro zaiyi iya abinda yaga zai iya ne,abu na biyu idan maimunatu ta tafi dole ne himu ya sake haqura da ita,ya kuma tattara hankalinsa ga gaje,saboda maimunatu tayi masa nisan da yasan bazai ganta ko ya sameta ba,kinga komai zai tafi mana dai dai babu wata matsala,sannan ke kanki yarinyar nan alaqaqai ce a wuyanki,har mamaki nake yadda kika ci gaba da riqon diyar mai miki kiwo,kinga yanzun kuwa salamun salamun" sosai inna furera ta gamsu da shawarar daada,tabbas ita din masoyiya ce,kuma maganganunta na bisa hanya,maimunatu zata zame mata tamkar wani jari,hankalinta kwance zata zama wata me arziqi tana daga kwance,da wannan gamsuwar ta taka da kanta har gidan bappa labaran,ta kuma tabbatarwa da anni cewa ta amince. "Nawa ne kudin da za'a dinga biyanki na aikinta?" Anni ta tambayi furaira da kanta tana kallonta,tsanarta na shiga ran annin,murmusawa tayi sannan tace "Ina ganin a duk wata ki bada dubu biyar" inna furera ta fada tana fatan anni ta amince da kudin data yanka din. "Na ninka miki sau hudu,zan dinga aiko miki da dubu ashirin da kuma ladan kiwo" mamaki ne ya cika furera qwarai,har ma ta rasa abinda zata fada,bata taba tsammatar samun haka daga anni ba,ashe maimunatu alkhairi ce tare da ita,ashe ita shatu ta haifawa. Cikin tsananin murna da farinciki ta koma gida,ta samu maimunatu ta gama da wanki ta kuma dora sanwar abinci,bayanta kamar zai karye saboda duqen da tasha,sanda fureran ta kirata ta shiga fargaba da tsoro "Zauna nan,ki kuma saurara da kyau kiji abinda zan gaya miki" qas tayi da kanta,zuciyarta na tsananta bugu,tana ayyano masifu kala kala a ranta,ko waccece ta sameta a yau din?. "Dattijuwar da tazo gidan nan kwana uku da suka wuce,ta ganki kuma tayi sha'awar tafiya dake domin ki taimaketa da aikace aikace,na kuma amsa mata,don haka ki zama cikin shiri,daga gobe zuwa kowanne lokaci zata daukeki ta tafi dake can garinsu" da fari maganar ta razanata,ta kuma rude sosai,ta lumshe idanunta tana kiran "Ya Allahu,ya Allahu" a hankali sai taji zuciyarta ta fara dai daita data tuna daga inda matar ta fito,daga bangaren yuuma,yummar da zata iya cewa kaf fadin rugar ita kadai ce masoyiyarta,ta tabbatar yuuma ba zata bari abunda zai cuceta ya rabeta. Ta sake maida tunaninta ga matar,akwai cikakkiyar suffar kamala dattijantaka tattare da ita,ta tuna yadda take dubanta fuskarta dauke da fara'a da kuma tarin kulawa,tabbas akwai kyakkyawan zato a kanta. "Bakiji bane!" Kakkausar muryar inna furera ta saukar mata cikin kunnuwa,sai ta bude idanunta tana gyada kanta "Kina jina ko?,wallahi wallahi kikaje kika aikata wani mugun hali,ko kikaje kika gwada musu halin maitarki kikayi sanadin da kika dawo gidan nan,na rantse da sarkin da raina yake hannunsa saikin gwammace mutuwa da rayuwa,duk da bansan matar ba a zahiri,amma na tabbatar gida ne na wadata,basu damu da abun duniya ba,duk wani abu me amfani da kikaga sunyi wasarere dashi ki dauka ki adana min,ni ina da buqatarsa,kome zakici maimunatu idan zai ajjiyu baki ajjiyemin ba Allah ya isa" maganganun data dinga yi sun yiwa maimunatun nauyi qwarai,sai tayi qas da kanta tana saurarenta har sai data gama ta sallameta. Yini tayi cikin taraddadi da kuma fargaba,duk da tana samun relief duk sanda zuciyarta ta gaya mata cewa yuuma ce,masoyiya guda daya da take da,ta bangarenta ne wannan lamarin,sai tayi qoqarin saisaita qwaqwalwarta tare da addu'ar kome meye ya zame mata sauqine na rayuwarta. *13* Tunda gari ya waye take zaune tangaram tana duban qofa zuwa window,tana lissafa wucewar mintuna da awanni da yatsun hannunta,wucewar kowacce daqiqa bugun zuciyarta ne ke daduwa,ta kalli qullin kayanta da ba komai bane a ciki illa fararen kayan saqinta,wadanda su daya ne abinda ta mallaka take kuma ji dasu,Sallamar da taji da baqin murya ya tabbatar mata ranar barinta rugar yayi,karon farko da zata fita daga rugar tun sanda suka shigo ita da mahaifiyarta. Laulo ne ya leqo yayi kiranta,sai ta miqe riqe da qullinta tabiyo bayansa,saboda tasan cewa abinne yazo wai inji mai tsoron wanka. Laila da yuuma ne tsaye a tsakar gidan,lailan cikin ado take dake nuni da zallar ilimi dukiya da kuma wayewa,ta qaraso a hankali ta gaida yuuma dama lailan,dukka suka amsa mata da sakakkiyar murya. Sosai inna furera ta kama kunnuwanta,har data dafe gefen fuskarta saboda tsananin zafi "Banda dauke dauke,banda mugun hali,iya abinda aka kaiki shi zakiyi,kada ki yarda a kawomin qararki,idan haka ta kasance kuwa kashinki ya bushe" kai take gyadawa da sauri don ta samu ta saketa,duka yuuma da laila sai da zuciyarsu ta motsu,saidai kowannensu da sauqi,saboda sunsan taqi kadan ya rage ta rabu da wannan rayuwar . Sanda suka qaraso gaban motar tsaye tayi kawai tana qarewa motar kallo,tana qissima yadda zata tsinci kanta a ciki,wai yau itace zata shiga wannan abar?. "Ki shiga maimunatu,anni na jiranmu" laila ta daga kai daga danna wayar da take ta yiwa maimunatu magana,ajiyar zuciya ta sauke sanda ta shiga motar,saidai gaba daya a takure take saboda rashin sabo,sai da suka koma ta gidan yuuma suka dauko anni sannan suka juya suka nufi hanyar barin rugar gaba daya. Duk inda suka gifta sai maimunatu tabi wajen da idanu,tana jin wata kewa tana ratsata tun yanzu,tana jin wani yanayi mara dadi cikin zuciyarta,tana qissima yaushe zata dawo?,yau ko gobe?,ko kuma ta tafi kenan tafiya ta har abada?. "Ki saki jikinki maimunatu,ki sanya a ranki zaki je kiyi rayuwa ne irin ta kowanne yaro dake gaban mahaifiyarsa" anni ta fada bayan ta karanci damuwa da tunani daya cika kwanya da zuciyar maimunatu,qas tayi da kanta tana jinjinashi,sannan tasa hannu a fakaice ta goge qwallar dake shirin sauko mata,babu abinda yake dawo mata sai wani lokaci can baya da suka baro garinsu na gembu ita da daadarta shatu zuwa wannan rugar,a zahiri rayuwar sam mara dadi ce,to a yanzun gata ra cira daga nan din zuwa wani wajen,an mata bushara da kyautatuwar rayuwarta,to amma kuma sanin haqiqanin yadda zata kaya din sai ubangiji,sanin gaibu sai Allah,ko wacce irin qaddara ce cikin wannan tafiyar kuma?. _ku biyo alqalamin 'yar mutan huguma_ Sosai maimunatu ta bude idanunta tana kallon hanya,a wancan lokacin da suka shigo garin akwai qarancin shekaru,shekarunta basu kai haka ba,don haka ta dinga kallon hanya abinta,tun daga cikin rugarsu har suka fito suka dauki hanya dodar. Bayan 'yan hirarraki motar ta dauki shiru,bacci yayi gaba da anni,haka ma yahaya,sai ita sai driver,sai laila data nutsu ta tattara hankalinta kan waya,ta karanci yadda laila ke son waya,daga dan qaramin sanin data yi mata,ta saci kallonta kadan sai kuma ta sake maida hankalinta ga titi,tana kallon yadda ubangiji ya shimfida qasarsa. Wani sashe na ranta kuma cike yake da mamaki,gashi dai tafiya suke,amma kamar a tsaye suke a waje daya,banda tana ganin yadda suke wuce dazuka da bishiyu tabbas da zata ce ba tafiya suke ba. Awa biyu cur sukayi suna tafiya kafin anni ta farka,ta sanya drivern ya shiga dasu cikin wani gari,sukayi sallah,kafin su idar kuma saiga yahaya nan ya shigo musu da takeaway,wanda suka wuce dashi mota,suka dora tafiyarsu. Tunda ta karba ledar abincin take hannunta a riqe ba tare da ta ci ba,abinci ne data jima rabonta da irinsa,tama manta lokacin,tun a zamanin da suke muhallinsu ita da mahaifiyarta,cikin ranta take tantamar anya abincinta ne?,bata sake budawa ba saida laila wadda ta gama cin nata ta kalleta "Ki buda mana maimunatu kici?,ko bakison irinsa?" Dan qaramin murmushi ta saki ta girgiza kai,sai ta buda ledar a hankali,laila ta bita da kallo,wani irin kyau fuskarta ke fitarwa fiye da wanda take dashi duk sa'ad da tayi murmushi,janye idanunta tayi,tana gyara zamanta yadda zataji dadin ci gaba da danne dannenta,zuwa lokacin maimunatu ta fara kaiwa cikinta abincin. Yawan wanda yaci sai yasa ta dinga jin kunyar suga ledar,ita kanta tayi mamaki qwarai,amma kuma daga bisani da taga laila sabgarta take a tab dinta,anni kuma ta koma baccinta sai ta sake itama. Duk yadda taci burin ganin hanya tun daga adamawa zuwa gombe amma sai da bacci yayi mata tsiya,tana gama cin abincin jikinta ya mutu murus,tsohuwar yunwar data jima a jikinta ta kwanta,tsohuwar gajiya kuma ta shekara da shekaru,basussuka baccin da batasan adadin yawansu ba suka taso mata haiqan,bata shirya ba baccin yayi awon gaba da ita. *GOMBE STATE* *_G R A GOMBE_* _DR SULAIMAN KUMO ROAD_ _Dr marwan khalid akko residence_ Katafaren gida ne wanda ya amsa sunansa ta kowacce fuska,irin ginin da aka yishi ba don alfahari fariya ko taqama gami da almubazzaranci ba,gini ne na ma'ana da sanin rayuwa da kuma abinda duniya ke ciki,duba daya zaka yiwa gidan kasan cewa daga zubi da tsarinsa ginin ya zaunu matuqar zaunuwa,hakanan yakan dauki hankalin mafiya yawan jama'a,tun baka ma shiga cikinsa ba. Gidane dake dauke da sassa guda hudu,biyu na matan gidan,daya kuma mallakin me gidan,yayin da daya bangaren ya zama mallaki ga mahaifiyar me gidan wato haj maryam Farooq kumo. Gaba daya gidan mallakin dr marwan khalid akko ne,babban limamin gombe gaba daya,shararre kuma sanannen dan kasuwa,wanda Allah ya yiwa baiwar arziqi dama dukiya gaba daya,gami da tarin ilimin addinin islama wanda shi ya kaishi ga zama cikakken dr,hakanan ta fannin boko din ma ba'a barshi a baya ba. Wani irin mutum ne da Allah ya yiwa baiwar kwarjini da kuma farinjini,mutum ne me amfani da ilimin addininsa ainun,mai yawan taimako sadaka da kuma kyauta ma gaba daya,dukka sirrin nasararsa ya ta'allaqa ne ga mahaifiyarsa,jajirtacciyar uwa da bata daukan raini ko kuma wargi komai qanqani,tsayayya akan 'ya'ya da kuma jikokinta. Marwan shine babban d'a a wajen haj maryam anni,hakan ya sanya yayi mata matsuguni cikin gidansa tun bayan rasuwar mahaifinsu,kuma dama shi din mutum ne mai matuqar qaunar mahaifiyarsa da kuma qawa zuci,hakan ya sanya itama haj maryam anni ko cikin yaranta tafi ji dashi,duk da cewa dan fari ne ba auta ba,autansu alhj sagir yaso daukarta ganin kamar shi yafi dacewa,amma gaba daya ya hanasu hakan,yace shi yafi cancanta tunda shine babba. Matan Dr marwan akko biyu,akwai haj Aishatu,wadda take da yara bakwai dashi,diyarta ta farko macace mai sunan anni wato maryam suna ce mata maama,sai ja'afar d'a na biyu a wajenta,wanda ya zamto halitta mafi soyuwa a wajensu,duka sauran mata ne,salma,hafsa,nadiya,safina,sai autansu namiji khadim,daya dakin kuwa dakin amarya umamatu tana da yara hudu ne,suma din mata ne,fa'iza ce babba,sai khadija,zahra'u,sai mai sunan yuuma rahama suna ce mata baby. Tsakanin aishatu da suke kira da amma da kuma umamatu da suke kira da ammy zama ne na fahimtar juna da kuma zaman lafiya dai dai gwargwado,yadda Allah ya dorawa kowa son ja'afar haka ammy ke qaunarsa,shi din dan gidanta ne tun farkon zuwanta gidan,amma kuma ta tattara ta miqa mata shi,shima kuma ya dauketa kamar uwa a gareta. *_Ja'afar marwan khalid akko_* matashin saurayi kuma matuqin jirgin sama,mai jini a jika,wanda Allah ya yiwa baiwar qira ta jiki,bashi sahun dogaye ko kuma gajerun maza, moderate ne,yana da murjajjen jiki mai siffar qarfi dake nuna shi din ma'abocin gym ne,kalar fatarsa ruwan tarwada ce,wadda ta samu kulawa ta gasken gaske take bada wani irin launi mai daukan hankali matuqa,baya tara suma kamar yadda shi din ba ma'abocin yin aski bane,saidai yadda yake barin sumar kansa zuwa habarsa da kuncinsa abun yana da matuqar qayatarwa da kuma daukar hankali,Allah ya zuba masa wani irin mugun kwarjini wanda yake qara masa kyau haiba da kuma cikar kamala,yana da wani irin farinjini na musamman,bawai a wajen mata kawai ba,a'ah.....hatta a wajen al'ummar gari gaba daya. Dan gayu ne na gasken gaske,gayu wanda ake kira gayu bawai muna gayu ba,mai tsananin tsafta ne daya tsani qazanta dama qazami,yana da tsari da kuma dokoki da ya sanya ba kowa ke iya mu'amala dashi ba,kamar yadda shima bada kowa yake iya mu'amala ba. Miskili ne ajin farko,irin miskilancin da zakayi tunani bebe ne ko kuma kurma,magana ko hira bata daga cikin abubuwan dake burgeshi,abu ne mai wuya ka zauna dashi kaji wata doguwar magana a bakinsa,sau tari yafi ganewa amfani da body language,kamar wani me ciwon baki ko kuma mara lafiya,yana da tsananin kamewa da kuma tsare gida,akwai jinin sarauta sosai cikin jikinsa,hakan ya sanya yake da izza da kuma rashin daukan raini,bai yarda da qasqanci ba,yana da neman na kansa sosai,mahaifiyarsa diya ce ga turakin akko,yana da matuqar girmama na gaba dashi,komai qanqantar shekarun daka bashi,duk da mutane da yawa sun masa shaidar wulaqanci da kuma girman kai. Mutum ne mai tsanani ta fannin so ko qi,bai iya so ba,hakanan bai iya qiyayya ba,idan jininku bai hadu ba ka fita a hanyarsa kawai shi yafi maka alkhairi,yana tsananin son mahaifiyarsa fiye da kowacce halitta a duniya,mahaifinsa da kuma anninsa suke da gurbi na biyu,don yakan kasa tantance cikinsu wa yafi so?,sannan gwaggwo sadiya qanwa ga anni,akwai mutanen da yake ganin kima sosai cikin rayuwarsa da zamantakewarsa. Jabir shine qawa kuma amini ga ja'afar,d'a ne ga qanin mahaifin ja'afar,mahaifiyarsa ta rasu ta barshi sanda ta haifeshi ko juyawa taga abinda ta haifa bata yi ba,akwai aminci sosai tsakaninta da mahaifiyar jaafar,kuma rana daya aka haifesu,don haka ta dauka jabir ta hada jaafar ta riqesu gaba daya,duk da taso qwarai ta shayar dashi kamar yadda ta shayar da jaafar amma anni ta hana,tace tayi haquri,yasha madara,saboda gudun samun matsala anan gaba,idan hakan ta faru zata haramta masa duk wata 'ya da ita din zata haifa jaafar yace yanaso,ko kuma wata daga cikin 'ya'yan 'yan uwanta,ba'asan kuma me Allah zaiyi ba,dukkansu sun gamsu sun kuma fahimta,taci gaba da bashi madarar,madarar kuma ta amsheshi sosai,ya tashi tubarkall,dashi da jaafar me shan nono babu bambamci,sun tashi tamkar 'yan biyu,don haka ma ake ce musu,akwai matuqar shaquwa da fahimtar juna a tsakaninsu,kowannensu bashi da kamar dan uwansa,dashi yake shawara,shi yake gayawa sirrinsa. Farinjinin ja'afar ya sanya yake da tarin 'yammata dake hauka a kanshi,saidai ko sau daya bai taba sha'awar bata lokacinsa akan kowacce yarinya ba,a haka kwarjininsa ya sanya mata da yawa sun hadiye kwadayinsu,don basa iya tunkararsa da zancan soyayya kansu tsaye,masu tsaurin idanu ke biyo ta hannun jabir,to shima jabir din yasan waye ja'afar,kuma dabi'un nasu suna dan kamanceceniya,duk da jabir bashi da miskilanci,saidai yana ararsa a duk sanda yaso,hakan yasa sau tari wasunsu baya ko gayawa ja'afar ma yake barin batun yabi iska. A sannan babban burin ja'afar a duniya shine ya zama pilot,dukka hankali nutsuwa da kuma rayuwarsa ya tattarata ne kan karatunsa gaba daya,sanda yake gab da zama pilot,a lokacin da suke komawa gida hutu daga qasar da yake karatu,a filin jirgin sama shaheeda ta fara ganinsa,d'iya ga shugaban malamai na qasa gaba daya,kuma babban limamin masallacin shugaban qasa dake abuja,yarinyar data bala'in mato masa,saidai tasirin tarbiyya data samu ya hanata bayyana masa,tana da kunya da kuma tsananin kamun kai,amma duk da haka ta kasa kanta sakat,sai data gano waye ja'afar din. Ta shiga tsananin tashin hankali sanda aka gama karanto mata waye ja'afar?,ta yaya zata shawo kansa?,da wannan tunanin ta dinga rayuwa,haka ta dinga ramewa. Kwanaki qalilan da ya rage musu su koma gida daga hutunsu suka giwa dr marwan rakiya abuja shi da jabir zuwa taron musabaqa na kasa da ake gudanarwa acan,a ture yaje bawai don yana so ba,don bai shirya zuwan ba. Cikin hall din kansa yana qasa yanata danne danne a wayarsa,yana jin jabir sunata hira da wasu matasa biyu da suka hadu a can,har zuwa sanda aka fara gabatar da musabaqar,bai daga kansa ko sau daya ba,saidai duk wanda yahau zaiyi karatu har ya sauka yana bibiyarsa a zuciyarsa,yana taya alqalan cin gyaransu,don shima Allah ya bashi haddar qur'ani izifi arba'in cif,sauran kuma biye ne da qur'ani. Kiran sunan wata daliba da akayi yaji daya daga cikin abokan hirar jabir din yace "Alhamdlh......ga sister dita din" baiyi niyyar dago da kansa ba,amma jin ana sake maimaita kiran sunanta ganin bata fito ba,sabanin sauran dalibai da kowa ake kiransa sau daya.....shi ya sanyashi daga kansa sanda yaji me kiran sunan ya ajjiye abun maganar alamun ta taso. Daga rukunin kujerin dake opposite dinsu ta taso,sanye cikin yalwataccen dogon hijabi har qasa,qafarta da hannunta duka safar hannu ne,baka ganin komai nata sai kyakkyawar fuskarta wanda nutsuwa ke kwance samanta. Kansa ya dauke ya maida ga wayarsa,amma sai ya samu kansa da dakon jin nata karatun,ta daidaita zamanta aka tambayeta wacce qira'a take amfani da ita,ta fada,mai jan karatun ya janyo mata sannan aka bata damar ci gaba. Gaba daya hall din sai daya dauki shuru sanda tayi bismillah,zazzaqar muryarta ta karade hall din cikin kyakkyawan sauti da qira'a,wanda tunda aka fara ba'ayi mata gyara har ta dire,kabarbarin mutane da yawa data burge suka dinga fitowa daga bakunan jama'a 14 Sanda aka gama musabaqar suna tsaye a jikin motar dr marwan(abbi) suna jiransa yayi kiransu,ya hadasu da mahaifin shaheeda da ita kanta shahidar suka gaisa,irin dadin da shaheeda taji ba qarami bane ganin cewa akwai sanayya tsakanin mahaifinta da nashi,ko meye zai dan zo mata da sauqi,ba kamar ace babu komai tsakaninsu ba,kwata kwata bata nuna wannan farincikin a fili ba saboda kamun kai da kuma tsira da mutunci. Babu jimawa shaheeda ta ziyarci gidan dr marwan,nan da nan ta saba da mafi yawa na jama'ar gidan,tayi amfani da hikima da kuma hankalinta da wayo ta shiga jikin anni da amma mahaifiyar ja'afar sosai,a lokacin jaafar tuni sun koma hutunsu,bata damu ba tasan tana da target a kansa komai dadewa,baka isa kace son ja'afar take ba,don ko zancansa bata taba yi ba bare ka kawo hakan cikin ranka,saidai a hikimace ta gama karantar dabi'unsa daga hirarsa dake bakin 'yan uwansa,da kuma yawan ambatonsa da anni takeyi,ta gama gane abinda yakeso da wanda bayaso,ta haddacesu tsaf bisa kanta. Sanda suka dawo hutu sun samu shaheeda a gidan,don tuni ta maida gidan wajen zuwanta,sun kuma saba sosai ta zama kamar 'yar gida,da yawa suna cewa saboda gidansu duka maza ne shi yasa tafison gidan baba dr kamar yadda take kiransa,don nata 'yan uwan duka maza ne,ita daya ce mace. Eh tabbas,zamanta a gidan na mata dadi,saboda tana da abokan hira sosai ba kamar gidansu ba,saidai nata plan din ja'afar ne,boyayyen sirrinta da babu wanda ya sani,tayi qoqari matuqa wajen ganin ta janyo hankalinsa kanta cikin hikima da basira,ba tare da shi kansa ta bari ya fahimci komai ba,komai na ja'afar din dabanne,ita ke kula da wasu abubuwa nasa. Da farko bai farga ba,saboda sam hankalinsa bashi a wajen,mma daga bisani ya soma fahimtarta,ya kira qanwarsa nadiya,ita yake nema idan yana buqatar wani abu da anni ko su amma basu iya ba ko ba zasu iya ba,wadda tasu tafi zuwa daya saboda kamanceceniyar da kuma nutsuwarta,ya yanka mata warning akan ta cire shaheeda akan duka sabgarsa sai idan shine ya buqata. Farko nadiya ta kasa gayawa shaheeda,sai ita da kanta ta fahimta,ta kuma yiwa nadiya maganar,bata boye mata ba ta gaya mata,tun daga ranar shaheeda ta fita a sabgarsa gaba daya,duk wani abu da ya shafeshi ta fita a ciki,koda zaune take a wajen yazo zata tattara tabar wajen,hakanan abu idan ya dangaceshi komai yadda ta iya babu ita a ciki,abun yana cinta a rai,tana jin ciwo amma ta danne zuciyar tata,mutum ce mai yawan addu'a,maimakon damuwa ta rinjayeta,saita rinjayar da addu'a,takan hana idanunta barci ta tashi cikin dare ta gayawa Allah damuwarta. Sannu a hankali shima ya fara noticing canzawarta,sai ya fara jin damuwa a kanta cikin zuciyarsa,shi da kansa ya dinga mamakin kansa,damuwa for what?,akan wata mace?,sannu sannu Allah ya fara matsa zuciyarsa,sai ga ja'afar da kansa ya fara nema shaheeda tayi masa wasu abubuwan,kamar kalolin girke girken da take masa a baya,amma fur sai ta murje idonta taqiyi,duk da yadda zuciyarta kan buga,taji babu dadi amma haka take mazewa. Rana ta uku daya aika tace ace bata da lpy taqiyi zuciya tazo masa iya wuya,yana zaune a sannan yana duba saqonnin da yake samu daga companies na jiragen sama dakeson yin aiki tare dashi,zare laptop din yayi daga saman qafarsa ya ajjiyeta gefe ya miqe ya fice. A dakinsu nadeeya ya samesu zaune an kafa majalisar hira,tana ta dariya tana dariya harda riqe ciki,Har kowa yayi shuru bata ankara ba,sai da taga hankalin kowa ya karkata ga qofa,sun kuma saka nutsuwa a jikinsu sannan ta ankara,tayi hanzarin jawo dankwalinta ta rufe lallausar sumarta ta fulani,gabanta na wani irin faduwa saboda zallar kwarjinin da yayi mata,tana jin kamar zaman ma ba zata iya ba. Bata ji yace musu komai ba amma sai taga kowace ta fara miqewa tana fita a dakin,ganin sunata ficewa ba tare da tasan dalili ba sai itama ta miqe tayi joining dinsu. Nadeeya ce qarshe sai ita,nadiya na fita ya matsa yayi blocking qofar gaba daya da jikinsa yana kallonta da idanunsa da suke fasa mata zuciya,tayi baya kadan ta kuma sauke kanta qas,don ba zata iya jurewa kallonsa ba,ta fara lanqwasa yatsunta,tana son tace ya matsa mata itama ta fita amma kuma tasan cewa tayi kadan ta iya fadin hakan. "Baki da kunya ko?" Ya fada a taqaice kamar me ciwon baki,abinda yasa babu shiri ta daga kanta ta kalleshi,sai kuma ta sake saukarwa saboda idonsa yana kanta "Ni sa'anki ne da zan dinga aikowa kiyimin abu kina rejecting,bakisan ba kowa nake sawa yayi mun abu ba?" Sosai maganar tasa tayi mata dadi,wani abu ya tsarga mata,gefe daya kuma rauni ya kama zuciyarta har ya sanya qwalla silalowa daga idanun nata tare da kalmar "Kayi haquri" shuru na sakanni yayi kafin ya sauke hannayensa ya juya ya fara ficewa daga dakin,sai ta bishi da kallo har yabar wajen. Kwata kwata ji tayi bataji dadi ba,cikin ranta kuma tana tsoron kada fa ta barar da damarta,a sukwane tayi kitchen ta fara hada masa abinda ya buqata a daxun,tana tsaka da aikin su safina suka shigo "Me yayi miki?,me ya faru?" Tambayar da suka dinga mata kenan "Ba abinda yayimin" ta amsa musu hankalinta na ga girkinta "To wannan abincin fa?,naga bamu jima da gama cin abinci ba" safina ta fada tana bude tukunyar "Na yaa ja'afar ne" amsar daya sanyasu kallon kallo a junansu,suka fara kuma tsegumin anya kuwa?,bata bi ta kansu ba,itadai burinta ta gama ta kai masa. Sanda khadim yakai masa dawowa dashi akayi,yace bayaso,abinda yasa hankalinta ya tashi sosai,ta kuma boye ta dinga kuka,washegari ta hada kayanta tace zataje,duk da kwanakin da takeyi basu cika ba. Kwana biyu rak a tsakani ya karanci bata gidan,yayi kaman ya share amma sai yaji ya kasa,ya kira nadeeya ta tambayeta,bata boye masa ba ta gaya masa duk abinda ta sani,ya sallameta,sannan yayi shuru shi daya yana tunani,rashin cin abinda ta aiko masa ne ya kawo faruwar hakan?,washegari sai ya tsinci kansa da shiryawa ya tafi gidan daukota,babu ko rakiyar jabir. Suman zaune tayi sanda akace mata ja'afar ne na gidan baaba dr,bai shigo ba ya dai aiko da gaisuwa wajen ummanta,sannan yace a gaya mata ta fito su tafi,saqon da ya bata mamaki,haka ta shirya kayanta ta biyoshi. Cikin motar kamar bashi ba,har ta fara cire hope,saboda ko uffan bata hadasu ba,sai da suka kusa gida sannan ya magantu "Idan kika sake wannan kuskurem sai na hukuntaki" ta fahimci da qaramar magana yake isar da saqo me yawa,maganarsa guda daya idan ka fassarata taka dauki.ma'anoni.masu yawa "Kayi haquri" tace dashi,yaji dadi cikin ransa na yadda take da sauqin kai,saidai ko ka fuskarsa haka bai nuna ba. Wasa wasa sai shaheeda ta karbe komai nasa cikin gidan,nan da nan kowa ya fara daukan haske,duk da cewa shi gogan yana jin dadin hidimarta sosai saboda ya yadda da tsaftar ta da qwarewarta wajen girki,sannan yana jinta a ransa wanda yafi ta'allaqa hakan da sabo,amma babu wata maganar soyayya data taba gittawa tsakaninsu. Tsarin gidansu shaheeda daga candy mahaifinta bashi da ra'ayi barin diyarsa mace ta qara gaba,sai kuma gashi guda daya ce macen da Allah ya bashi,a lokacin shaheeda tayi candy,mahaifinta ya tasamma aurar da ita,dr marwan na samun labari ya nemawa ja'afar bisa shawarar anni,saboda qoqarin da taga shaheeda nayi a kansa,da kuma yadda ta karabceshi tsaf,tamkar ita ta haifeshi. Kowa yayi tunanin za'a samu matsala sanda ja'afar yaji an nema masa auren shaheeda,sai gashi bai wani damu ba,hasalima kusancin dake tsakaninsu ne ya sake daduwa,hakanan itama ta sake qara qaimi wajen kula dashi,abinda yake matuqar yi masa dadi a rai,duk da dan uban miskilancinsa. Wata iriyar zazzafar soyayya yake mata silently,mutum ne shi da bai iya so ko qi ba,shi daya yasan girma da kimarta cikin ransa,ta kula da komai nasa,dai dai da lokacin sallah ta dauki wayarsa ta saita masa,hakanan duk sanda ta tashi sallar dare dai tasan yadda tayi ta tasheshi,ko.ta tura masa tex ko tayi masa flash call,duk sanda tayin kuwa sai ya gani,kasancewarsa mutum da baya bacci da wuri,ita ta koya masa sallar dare,ta kuma koya masa abubuwa da yawa wadanda daa basa cikin habit dinsa,ta samu gurabe sosai cikin rayuwarsa,wanda hakan ya qara soyayyarta da qaunarta cikin ransa ba tare da ya ankara ba. Sanda sukayi aure da shaheeda lokacin ya zaba kamfanin da zaiyi aiki,saidai ba anan nigeria yake ba,anni ta dinga fada,akanme zai zaba kamfani a wata qasar bayan yanzun yana da iyali,Allah sarki shaheeda ba haka taso ba,amma ita ta haqiqancw kan cewa babu komai,saboda fa fahimci burinsa kenan,yana matuqar qaunar piloting,tana bala'in girmama buqatarsa da burinsa saman nata,tayi kwance kwance ta dinga bawa anni haquri gami da kareshi. Suna kan hanyarsu ta komawa sashensu ya kama hannunta ya saka cikin nasa "Me yasa kike bani kariya?,bayan kema nasan ba haka kikeso ba?" Murmushi tayi sannan ta dora kanta a jikin kafadarsa "Bani da wani zabi bayan naka,bani da wani abu da zanso sama da abinda kai kake sonshi,bazan taba son wani abu sama da wanda ka zaba ba,dukka zabina dama rayuwata ta narke cikin taka,taka ce" wani abu ne ya dunga tsarga masa,baisan wanne irin so shaheeda ke masa haka ba,kasa magana yayi,sai kawai yasa hannu ya dauketa cak yaci gaba da takawa da ita zuwa sashensu,abinda tafiso daga wajensa kenan fiye da komai,tayi luf a qirjinsa tana murmushi tare da shaqar daddadan qamshin da bata taba jin makamancinsa ako ina ba sai a wajensa. Mutum ne tsayayye dan gaske,wanda komai zaiyi baya daukarsa da wasa matuqar ya sa kansa,don haka sanda ya fara aikinsa ya bashi muhimmanci qwarai da gaske,abinda ya jawowa shaheeda samun qarancin kulawa,tana jin babu dadi amma ta danne,taci gaba da haquri dashi da kuma dukka abinda zai taso,a yawancin lokuta shi da kansa yasan tana buqatar kulawarsa,amma babu lokaci,hakan ya sanya shima yaqi dauketa daga cikin gidan nasu,saboda zamanta tare dasu anni xai rage mata kewa da zaman kadaici. A haka shaheeda ta samu cikin twins,a lokacin laulayinta tasamu zama dashi sosai saboda hutun qarshen shekara daya fara yi,ya kuma dan dade. Wata takwas da sati biyu ta haifa masa kyawawan 'yan biyu dukkaninsu mata,ikon Allah dayar shi tayo,dayar kuma babanta sakkk,ya kashe kudi bakin iyawarsa,ya kuma gatanta,ta samu gift masu yawa daga gareshi. Yaran yarane masu shiga rai kamar mahaifinsu,hatta da baban nasu wata iriyar soyayya yake musu ta musamman,a haka yara suka fara wayo,ya kuma koma bakin aikinsa. Sannu a hankali yara suka fara girma,sunata wayo abinsu,har zuwa sanda sukayi shekara biyu,ya dauki hutu yazo dai dai randa su nadeeya suka hada musu birthday,akayi komai dashi,ya kuma cikasu da gifts ya koma aikinsa. Kamar dai baya haka ya koma aikinsa ka'in da na'in,a wannan karon shaheeda kanyi qorafi lokaci xuwa lokaci "Muna buqatarka,muna buqatar kulawarka,ba don ni ba ko don yaran nan" shi a kansa yasan da haka,don haka ya fara tsara musu yadda zasu xama kusa dashi ba tare da ya gaya mata ba,shi kansa yana kewarsu sosai. *_MUTUWA rigar kowa_* Tunda watan ya kama take masa complain din tana yawan jin ciwon kai,murmushi yakeyi yana tsokanarta,saboda yasan wani lokaci idan tana buqatarsa ko buqatar ganinsa da hakan take fakewa,har sai yabar dukka abinda yakeyi yazo ya gansu. Wannan karon sai yake basarwa,saboda so yake zuwa qarshen watan yayi musu suprise ya debosu suzo suyi hutu tare dashi. Sati kusan uku suna a haka,ranar wata alhamis.......... A ranar akwai jirgin da zai tuqa,awa daya saura su tashi sai ga kiran shahidan,tana shaida masa gata a qasar,da fari ya dauka wasa take masa,don last week sunyi hirar taji duka schedules dinsa na satin,amma daya duba number ya tabbatar ta qasar ce sai ya yarda da hakan,mamaki ya cikashi,da alama ta gaji da kewarsa ne ta biyoshi kenan,waya ya dauka yayi musu booking masauki sannan ya kirata yace su biyo cave ta kawosu nan,a marairaice tace "Yanxu ko sau daya?,ko sau daya ba zaka iya qarasowa na ganka ba kafin ka wuce?" Agogon dake daure a hannunsa ya kalla,lokaci ya qurace sosai,bashi da zabi illa ya bata haquri,cikin karyayyar murya ta amsa masa da "Shikenan......ga amna" murmushi ne ya wadata a fuskarsa,ya karba wayar sukayi magana sosai da yarinyar,don bakinsu dukka ya bude,abinda ya jawo ma kenan wayar ta katse sanda 'yar uwarta amra ke shirin karba,yaso suyi magana da ita,don tunda suka fara waya da amnah take cewa ta bata daddy,zata bashi wani labari. A sannan lokacin fara aiki yayi,ya kalli wayar yanason kira a bashi yarinyar amma ba hali,sai ya yanke bari suje sukai passengers,lallai a ranar zai dawo in sha Allah,cikin ransa ya dinga jin excitement na haduwarsu,ashe samun nasu da bazaiyi ba kenan saidai ya taras da gawar matarsa da kuma gawar diyarsa guda daya amra. Lamarin yayi matuqar bugarsa da kuma gigitar dashi,don saura kadan ya zauce a sannan,bai taba kawo irin hakan a ransa ba,tun daga wannan lokacin komai ya tabarbare masa,ya tashi daga ja'afar akko ya koma wani mutum na daban,musamman lokacin da yaci karo da diary na shaheeda cikin kayanta,yadda take kewarsa da yawa da tarin qaunar da take masa, movement na yaransa a lokacin da baya kusa dasu. Sosai depression ya sameshi,ya tattara komai nasa ya ajjiye,ciki harda aikin nasa da yake matuqar so,yace shine sila na faruwar komai,dukka qoqari anyishi kan jaafar don ya koma dai dai,amma inaa abubuwan sai a hankali,sai da aka tsaya da addu'a da roqon Allah sannan aka fara samun sauqi,amma sam ya canza totally,hakanan duk sanda abun ya motsa masa birkicewa yake gaba daya. Sosai jabir ya taka rawar gani,saboda tsayawa da yayi akan jaafar din,da qyar aka sha kansa ya koma kan harkokinsa,amma piloting dai ya ajjiyeshi,ya zama wani mutum me zafin rai,miskilancinsa ya sake daduwa qwarai da gaske,babu abinda yake burgeshi a rayuwa,ya sake zama wani very careless akan sha'anin kowa,yafi ganewa kadaici,wanda kadaicin kuma illa ne tattare dashi,saboda shike tuna masa da shaheeda. Wata irin soyayya yakewa diyarsa guda daya data rage wato amnah,wani irin gata yake mata,soyayyar mahaifiyarta da 'yar uwarta duka sun dawo kanta,amma fir yaqi zaman nigeria duk da babban kamfaninsa anan yake kano gombe da lagos,dole don kada su matsa masa suka barshi,suke ci gaba da binsa da addu'a da kuma fatan Allah ya kawo qarshen komai. 15 *Dawowa cikin labari* Tafiyar awanni biyu suka qara suka shigo garin gombe,a lokacin anata sallar la'asar,wasu masallatan ma sun idar. Slow da motar ta fara yi sanda suka qaraso unguwar suka fara gangarowa faffadan layin gidan dr marwan din ya sanya maimunatu farkawa,ta zauna sosai tana murza idanunta tare da kallon sabuwar duniyar da rayuwa ta kawota,murmushi anni tayi "Lallai kinsha barci maimunatu,harma kin fini jimawa" murmushi tayi cikin jin kunya ta sadda kanta,itama anni murmushin tayi tana maida dubanta ga qofar gidan da suka fara harin tsaiwa "Marwan dinma yana nan ashe" ta fada tana leqe fa window "Eh ga motarsa nan,harda baqin motoci ma" hayatu ya amsa mata "Marwanu marwanu na jama'a,hutun qarshen satin ma shi ba samu yake ba" "Wallahi haj anni,ai aljanna kawai ta ragewa alhj,amma yana samun yabo da shaida me kyau" kanta ta jinjina cikin jin dadi,ita kanta ta sani,matuqar dai aljanna qasan qafar uwa take,to babu abinda zai hanata dagewa marwanu ya shige. Kakaf hankalin maimunatu yana ga hanya sanda motarsu take shigewa cikin tangamemen gidan,ba laifi tana da dan sanin rayuwar dadi 'yar mitsitsiya,amma komawarta rugar ummaru ya sake maidata baqauya sosai,don haka ta dinga bin gidan da kallo cikin mamaki su anni,ya akayi su dake rayuwa a guri irin wannan suka iya zuwa rugarsu har sukayi sati guda?,lallai su din nagartattu ne wadanda basu maida duniya a bakin komai ba. Kafin hayatu ya budewa anni qofa ta fito wajen ya fara cika da mutane,mafi akasarinsu ma'aikatan gidan ne maza da mata,kowa na mata sannu da zuwa tare da qoqarin nuna kulawarsa a gareta,abinda zai nuna maka irin girma matsayi da kuma muhimmancin da take dashi. Waiwayawa tayi ga maimunatu wadda ke rabe bayan murfin motar da suka fito a ciki,cikin tsoro,kamar xaka ce mata ket ta zura da gudu,sannan ta dubi daya daga cikin ma'aikatan,babba ce aqalla zatayi shekara arba'in da takwas,kuma da alama ita din ta hannun daman anni ce nesa ba kusa ba "Tabawa riqo min baquwar nan ki shiga min da ita ta qofar baya" ta fadawa tabawan qasa qasa,gyada kanta tayi sannan ta juya inda anni tayi mata ishara,tunda tayi mata magana ta haka tasan cewa wala'alla abune na sirri bataso kowa da kowa ya sani. Murmushi tabawa ta sake mata sannan ta kama hannunta,ko ba komai maimunatun taji ta sake da tabawa farat daya,saboda yadda ta kama hannunta babu kyama ko alamun kyara ko kuma tsangawa,tana biye da ita har sanda duka bulla wani tangamemen falo,falo ne daya wadata da dukkan nau'in kayan alatu na rayuwa,rukunin kujeru biyu ne a cikinsa saboda girmansa,kowanne color dinsu daban,akwai qofofi a ciki dake nuna alamun dakunan bacci ne,sai wata gajerar siririyar hanya wadda kitchen yake a ciki. Kitchen ta wuce da ita,wanda maimunatu ga bishi da kallo cike da mamaki,farat daya ta gane kitchen ne,duk da na ainihin gidansu na gembu bai kama koda qafar wannan ba "Tsaya ina zuwa" tabawa ta fada sannan ta juya ta fita,bata yi koda minti daya cikakke ba ta dawo,tana murmushi ta dubi maimunatu "Kiyi haquri ko,na barki a tsaye,muje na nuna miki dakinki" kai ta gyada kawai tana maida mata martanin murmushinta,a salube kuma tabi bayanta. Dakin yafi kusa da kitchen din gidan,don shi daya ne area din,babban dakine da aka shimfideshi da tiles marbles baqaqe masu dishi dishin light blue a jikinsa,yana dauke da babban gado madubu da wardrobe ta jikin bango,gurin ajjiye takalma,da manya bedside guda biyu masu dauke da bedside lamp,tun daga curtains zuwa dan qaramin carpet din dake malale a gaban gadon duka light blue ne,abinda ya qarawa dakin haske da kuma kyau. "Anni tace nan ne dakinki,ki zauna ki huta sosai,sannan ki fadi abinda kikeso kici,ga bandaki can koda wata buqata zata kamaki,tace zata kiraki idan ta gama" kai maimunatu ta gyada,jikinta a sanyaye,tana ganin kamar taxo inda bai cancanci tayi rayuwa dasu ba,tako ina mutanen nan sunfi qarfinta sun kuma wuce tunaninta,yanzu wannan dakin shi za'a bata a matsayin dakin kwananta?,ita a wa?. "Me zakici?" Tabawa ta sake maimaitawa idanunta akan maimunatu tana nazarinta,da sassanyar muryarta tace "Ba komai,banajin yunwa,bamu dade da cin abinci ba" gaskiyarta kuma ta fada,cikinta ya riga da ya zama mara space sosai da bazai iya daukan wani abincin ba bayan awanni biyu,yunwa ta zamar mata jiki "Shikenan,amma idan kinji kina da buqata,ga waya can ki daga ki kira kitchen,za'a kawo miki duk abinda kike buqata" kai kawai ta sake gyadawa bawai don ta fahimci yadda zatayi kiran ba,sai taga tabawan ta qarasa wajen da qullin kayanta suke tana niyyar dauka "Kaya na ne" daga kai tayi ta dubeta,murmushi tayi mata sannan tace "Anni ce ta bada umarnin a daukesu,za'a kawo miki wasu kayan da xakiyi amfani dasu" bata son rabuwa da kayan,kayan suna d matuqar amfani da kuma tarihi a wajenta "Don Allah ki cewa anni tabarmin su,ina so" fasa dukan tayi,sai ta amsa mata da to,ta juya ta fita a dakin sannan taja mata qofar ta rufe A nutse ta gama qarewa dakin kallo kusfa kusfa,daga nan inda take zaune tana iya jiyo maganganun mutane sama sama,saidai kuma bata iya rabewa da abinda suke fada. Daga can bangaren anni kuwa sannu da zuwa jikokinta suke ta shigowa sunayi mata,duk da cewa ba kasafai take wannan wasan dasu ba,amma kuma su din basu qyaleta ba,duk da zafin da take dashi. Fitowar annin kenan daga wanka bayan ta fito tana zaune a qasa,ta miqe qafafunta da sukayi mata nauyi da kuma tsami saboda zaman mota,man zafi take qoqarin shafawa tabawa ta shigo dakin,dauke da wani qaramin flask din silver da cup guda daya,gefe ta zauna anni ta daga kai ta dubeta "Sannu tabawa" "Yauwa hajiya anni" ta amsa mata tana murmushi tare da qoqarin bude flask din ta zuba mata abinda yake ciki,dan yamutsa fuska tayi "Dakata mana tabawa,yaa daga dawowata zaku hau duramin magani?,ba wani abu me galmi galmi sai magani kamar bugagga?" Dan danne dariyarta tabawa tayi,ita din ba baquwar hutsun anni bace,ta riga data saba da hakan tsahon shekara goma sha "Ammi ce tace shi xa'a fada baki" "Ta rasa abun arziqin da zata yimin sai wannan?" "Abu me galmi galmin yana hanya ai anni,ita da kanta ta karba girkin abinda zakici idan zaki dawo,yanzu haka a kitchen na barta" sai a sannan annin ta saki fuska "Allah sarkiAishatu,badai qoqari ba....ba daga nan ba" ta fadi tana miqa hannu tare da karbar maganin da tabawa ta zuba matan tana kurba a hankali,ita kanta tana son maganin,saboda yana saurin warware mata gajiya daga jikinta. Kurba uku tayi aka turo qofar dakin hadi da sallama,matashiya ce sanye da rigar material da aka yiwa budadden dinki,kanta yane da mayafi plain daya dace sosai da kayan jikin nata,tabawa ce ta amsa sallamar tata tana dubanta "Ina kika shiga tun dazu ga aikinki can an dade da gamashi?" Sai data zauna gefan gadon annin ta yage mayafin kanta sannan tace "Bari kawai baba tabawa,ai na baje zanci dadi kawai aka kirani daga makaranta nazo ga lecturernmu da yace bazai samu shigo ba ya shigo,mugu ne mutumin nan na qarshe,shi yasa ba shiri na tashi na tafi" Murmushi tayi "Ai gashi can a ajjiye" "Yauwa baaba tabawa.....godiya nake" waiwayawa tayi zuwa ga anni tana murmushi "Anninmu ta mutunci......barka da sauka,kun dawo lafiya?" "Lafiya garas na dawo,gashi ma kin ganewa idonki?" Dariyar dake cin salma ta danne,don tasan anni na ciki da ita,domin kuwa ita ya khalid(shine babban jika a wajen anni ta danta na biyu me bin dr marwan)yace ta shirya ta rakata amma ta kawo nata uzurin bata je ba "Amma nafi kowa jin dadi a gidan nan,Allah da bakya nan duka gidan babu dadi,ai bansan yau zaku dawo ba don munafurci laila bata gayamin ba,da na saka an siyo miki nama a wani suya sport nan bayanmu me shegen dadin tsiya......" "Ke.....kiyi ta kanki,wato ga kuriya ko?,to ta Allah ba taki ba,bana so" fuska tadanyi qoqarin canzawa,duk a qoqarinta nason gamsar da anni duk da dariyar daketa taso mata,saboda tana da buqata wajen yayansu ja'afar,kuma ta tabbatar da zarar annin ta saka baki anyi an gama "Allah anni da gaske nake,kar kiso kiji yadda duk naji......" "Ki rabawa aishatu da marwanu biyar biyar....."annin ta fada tana danqara mata daquwa,wanda babu shiri salma ta miqe ta zari jakarta tana cewa "Allah ya baki haquri ya huci zuciyarki tsohuwa me ran qarfe" tayi waje,annin bata barta ba ta dora mata "Sannan kada uban wanda ya sake saka tabawa aiki cikin gidan nan na gaya muku,ba me aikin kowa bace ehe......" Murmushi tabawan tayi bayan ficwwar salman "Ba wani abu bane hajiya anni,koda aikin gidan nan duka zai dawo kaina indai zan iya zan yishi,keda iyalinki ai kunfi qarfin komai a wajena" kofin maganin ta ajjiye gefe "Na sani,amma ace duk ma'aikatan dake gidan basu ishesu ba?,ubansu ya lalata su ya dauko masu aiki ya zube musu kamar ba diya mata ba da gobensu a gidan aure zata samesu?,kiga yarinya batasan ta zagi jikinta tayi aiki gidan aurenta ba?,shi yasa suke wayar gari qazamai,ko cikakken tuwo basu iya yiwa miji da zaici kamar ya cire yatsunsa ba......haka yaranmu na karkara suke?" Kai tabawa ta kada tana murmushi "Sha wuya ne ai wadan nan" furucin na tabawa ya tuna mata da maimunatu "Kwarai da gaske kuwa,kin tunamin ma,akwai maganar da nakeso muyi dake tabawa" anni ta fada tana gyara zama,tabawa bame aiki anni ke kallonta ba,yar uwa take kallonta kuma abokiyar shawara,bama ita daya ba,kusan duk wanda ya girma ya tashi a gidan kallon kaka yakewa tabawa,mutum ce ita me tsananin mutunci da kuma dattako,bata aikin komai ma cikin gidan,saidai idan anni na buqatar wani abun da sun riga sun saba tabawan kadai keyi,duk da akwai masu aiki sosai cikin gidan "Kinga yarinyar dana sanya ki kaita ciki ai ko?" "Qwarai kuwa haj anni" tabawa ta fada tana bawa anni dukka hankalinta "Yarinyar kyakkyawa sosai,saidai akwai alamunrashin sukuni a tattare da ita da kuma wahala" kai anni ta gyada "Bama alamu bane,akwaisu" a nutse ta bawa tabawa labarin maimunatu,tare da qudurinta a kanta,labarin da yayi matuqar sanyaya jikin tabawan,tare da saka mata tausayin maimunatu me yawa cikin ranta "Kiyi nufin alkhairi sosai hajiya anni,kuma dama halinki wannan,Allah ya baki nasara akan hakan,yasan kuma iya bakin matsalar ce,yasa ta zamto masa haske cikin rayuwarsa" "Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu"anni ta fada tana jin dadin yadda tabawa ta fuskanceta "Amma kuma wani hanzari ba gudu ba.….." "Uhmmm,ina jinki tabawa" "Kinsan akwai matuqar banbanci da tazara me yawa tsakanin manya(sunan da takan kira ja'afar dashi,saboda sunan babban malamin da yaci,kuma wasu sukan kirashi da sunan) da ita yarinyar?,kinsan kuma hali da dabi'ar yaran zamani,musamman shi daya keta qasashe da dama,yaga kuma mata iri iri,inajin kamar idan akace za'a bashi yarinyar nan a haka zai zama da matsala" murmushi anni tayi "A hakan zaa bashi ita ba kuma a hakan za'a bashi ba" cikin rashin fahimta tabawa ta kalli anni don bata gane hausar ba "Abinda nake nufi shine,inaso ki kulamin da duk abinda zata ci ta kuma sha,nasan ba lallai a yanzu ta farat daya ta dauki cimarmu ta iya sakin jiki taci yadda ya kamata ba,sannan ki kulamin da tsaftarta ki jata a jiki a kiyi mata duk abinda ya kamata,sauran abubuwan zanyi magana da salamatu,abinda ya samu zuwa sanda zai zo gida shikenan,zan bashi ita a haka,shi nakeso ya qarasa rainonta,kinsan hikimar yin hakan?" Kai tabawa ta girgiza tana duban anni "Inaso ne yasan ciwonta,yasan dadi da kuma wuyarta,yadda bazai riqeta sakwa sakwa ba,sa'annan inason ya ginata kan tsari da dabi'ar da yakeso,ya dabi'anceta a yadda yakeson matarsa ta kasance,hakan shi zai bada damar da zata shiga zuciyarsa fiye da marigaiya shahida,don shahida tazo da tarbiyyar ta da kuma dabi'unta ne daga gida,ita kuma wannan shi zai saitata a yadda yakeso,zata kasance ne kan tsarin da duk yaso" sosai tunani da hangen anni ya yiwa tabawa dai dai,kuma hikimarta tayi mata,ta sha alwashin lallai zata yiwa annin duk abinda ta buqata,don tana cikin mutane na gaba gaba da takejin ciwo da zafin yadda har yanzu suka kasa shawo kan matsalar manya,tana jinsa kamar danta,don tun yana qarami take a gidan,da ita akayi rainonsa. "Dubamin ita tabawa,ki duba ma'ajiyar kayan nan da aka dinka wancan watan ki ciccire mata wadanda zasu yi mata dai dai,inason ta fito muci abinci da ita anjima kadan" "To an gama haj anni" tabawa ta fada tana miqewa. Tana shirin fita a dakin sallamarsa cikin muryar dake cike da tarin nutsuwa da kuma haske na ilimi da dattako ta ratsa falon,dr marwan ne,sanye yake da lafiyayyar shadda ruwan qasa dinkin babbar riga 'yar ciki da wandonta,kansa kuwa hula ce da ba'a iya hangota saboda fari qal din rawanin dake nade a kansa,idanunsa sanye yake da farin gilashi dake qara masa qarfin gani,akwai cikakken gemu a fuskarsa wanda furfura ta fara yiwa ado ta gauraya da baqin dake jiki. A girmame tayi maaa sannu da shigowa sannan ta juya ta fita a dakin,shi kuma ya sanya kai dakin mahaifiyar tasa,bakinsa dauke da sallama. Fuska a sake ta amsa sallamar tata,sannan ta janye qafafunta don ya samu wajen zama saman lallausan carpet din da take kai,don qasa ne wajen zamansa duk sanda yazo gaidata. "Kun sha hanya anni" ya furta bayan sun gama gaisawa da tambayar mutanen data baro. "Wlh marwanu,amma alhmdlh,gamu a gida" "Mun godewa Allah" ya fada yana murmushi "inata zuba idanu na zaci baku qaraso ba,har ina shirin kiran jibril" "Mun iso marwanu,kana tare da baqi lokacin.....na iso da baquwar yarinya ma" "Eh tabbas,muna tare da ministern ilimi ne,batun da nakeso mu tattauna kenan dake akai" kai ta jinjina "Nima akwai batun da xamu tattauna din,amma kamar lokaci bazai bamu dama ba,naga an kusa sallar magariba,inaga idan aka idar da sallar isha'i sai mu zauna" "Eh hakan yayi anni,Allah ya nuna mana" "Ameen.....amma kunyi waya da jabiru ne?" Dan dubanta yayi "Sai da ya sanar miki kenan?" "Kana da wadda ta fini ne marwanu?" Qas yayi da kansa "Babu anni,amma banason tashin hankalinki ne ko kadan" "Ja'afaru rayuwata ne,Allah ne ya doramin qaunarsa cikin dukka jikokina,idan har an aka fara boyen matsalar ja'afar saboda kada na shiga damuwa to kuwa ba'a kyautamin ba,zanyi dukkanin me yiwuwa ne don naga rayuwar jaafar ta daidaita kamar yadda take a baya" "In sha Allah ba zata sake faruwa ba,kuma maganar da nakeso muyi din tana da alaqa da jaafar din" "Allah yasa alkhairi" "Khairan in sha Allah" ya amsa mata 16 Da sallama tabawa ta tura dakin,ta ajjiye ledar kayan hannunta fuskarta dauke da murmushi tana duban maimunatu "Ki shiga kiyi wanka,ki canza kayan jikinki maimunatu ko?" Kai ta gyada mata,saidai ta maida dubanta ga jikinta,bata ga wani datti da zai sakata yin wanka ba,don yau din da safe Allah ya 'yantata,ta samu tayi wanka kafin su baro gida,kuma bataga wani aiki da tayi wanda ya bata mata jikinta ba,hasalima ta jima bata samu cikakken hutu da yanayi me kyau irin na yau ba "Muje ko na nuna miki bayan gidan" abinda tabawa ta fada kenan bayan ta ajiiye wasu maya mayai saman madubi,sai kawai ta miqe tabi bayanta. Komai na cikin bandakin ta nuna mata tare da yi mata bayani,maimunatu na biye tabawan har ta gama nuna mata komai sannan tace "Idan kin gama kin fito ki dannan nan ina daga falo,zan shigo na gyara miki kanki" kai kawai ta gyadamata,har ta fice tana tsaye tana bin toilet din da kallo. Yadda ta nuna mata komai haka tayi amfani dashi,sai gashi ta dauki lokaci me tsaho tana wanke jikinta lungu da saqo,irin wankan da daadanta ta koya mata ta dinga yi a sanda take da gatanta. Ajiyar zuciya ta sauke mai nauyi tana shaqar qamshin sabulun da tayi wanka dashi,ga wata iska tana ratsata tako ina,bata buda ledar da tabawa ta shigo da ita ba,sai ta zauna qasan tiles din tana qanqame da jikinta waje daya,saboda har wani sanyi sanyi takeji,ta kuma danna inda tace matan,a haka ta share wasu mintuna tana zaune. Gajiya da zaman jira tabawa tayi,gashi anata kiraye kirayen sallar magariba,don haka ta dawo dakin,ta samu maimunatu zaune "Ya kike zaune haka?baki kirani ba baki kuma saka kayan naki ba?" Qas tayi da kanta,tabawa ta karanci akwai baqunta sosai da kuma takura kai ga maimunatu,wataqila rayuwarta ta baya ce tayi tasiri sosai a kanta. Kayan ta fidda mata harda half vest tace ta koma bandakin ta sanya tazo suyi gyaran kan. Ta jima tana jujjuya kayan a hannunta,tamfar ba zata iya sanyasu ba,sai kuma ta tuna jiranta akeyi,abinda yasa ta budasu ta saka sannan ta daure kanta da dankwalin tayo waje,daf da zata fita ta hangi kanta ta wani dogon madubi da akayi cikin bandakin,harta gota ta dawo tana duba kanta. Farat daya ta fara canzawa daga maimunatun bafulatanar riga,babu mudukajenta(kayan saqi) babu wuffije,babu komai na fulani tattare da ita sai duwatsun hannunta da na kunnenta,hakanan fatarta haskenta ya qaru koda ba'a gaya mata ba idanuwanta sun gaya mata hakan,sai ta soma takawa a hankali tana saqe saqe masu yawa cikin ranta. "Babu ma wani datti me yawa akan naki ai" tabawa ta fada sanda maimunatu ta bude mata yalwatacciyar sumar kanta,tabbas babu datti,amma kuma tana da buqatar qyara,ita da kanta idan ta samu sarari take guzurin toka duk sanda taji kan nata ya dameta,ta tsaya daga bakin rafinsu sanda shanunta ke shan ruwa ta badeshi da toka ta wankeshi,saidai tana shan wahala qwarai,saboda wata irin suma Allah ya bata ga tsaho ga cika,babu mataimaki,a baya daadarta ke gyare mata shi fes,ta xauna duk tsahonsa ta bata lokaci ta zuba mata kitson fulani a bishi da wasu irin duwatsu nasu masu kyan gaske,duk randa zatayi mata irin wannan aikin wuni guda suke kashewa kafin a gama,amma fa duk wanda ya kalla kan sai ya kalla ya sake kalla ya kuma tanka,daadarta kadai ke iya mata wannan aikin,ita kanta duk randa ta wareshi ta wanke saidai ta cukuikuyeshi cikin dankwali ta maidashi yadda yake taci gaba da rayuwa dashi a haka,babu cikakkiyar taza bare ta samu kitson arziqi. Tabawa batayi tsammanin aikin zai daukesu lokaci mai tsaho ba,sai gashi kafin ta gama wanke mata shi ta busar a hand Drayer sun dauki kusan awa biyu,har anni ta aiko laila. Tsaye laila tayi tana fiddo idanu sanda ta shigo dakin "La la laaaaa......maimunatu,dama haka kike da suma?,ma sha Allah,kice mu fulani kawai muka rako duniya,ga inda ainihin fulanin suke" murmushi kawai maimunatun tayi,kasancewarta bame yawan son magana ba,zama laila tayi tace tare zasu tafi,tana ta qarewa maimunatun kallo,cikin zuciyarta tana tadinta,yadda cikin awanni kadan kamanninta da kyawunta sun fara fita tun ba'aje ko ina ba. Duka su ukun da sallama suka shiga falon anni,a lokacin ta nutsu tana amsa wayar jabir,sun fahimci waya take mai muhimmanci harda maimunatu dake baquwar gidan,sai suka samu waje kowa ya zauna,laila ce ta qarasa gaban tv ta dauka remote kafin takai ga zama ta canza channel sannan ta dawo itama ta sama waje ta zauna kamar su. "Shikenan......amma ka zama cikin shirin kai jabiru,ba lallai sai ka sanar masa ba,ka rabu dashi kawai kaci gaba da sabgarka.....toh....Allah ya bamu alkhairi" shine maganar qarshe da annin tayi tana sauke wayar daga kunnenta tare da bin wayar da kallo,kana ta dauke idanunta tana maidowa kansu. "Sannu tabawa,kun gama kenan?" Ta fadi tana murmushin jin dadin yadda taga maimunatun fuskarta ta sake fitowa fayau,sannan kuma tayi tarwai "Eh hajiya anni,aikinma bamai yawa bane" "Kedai sannunki da qoqari" anni ta fada tana sake kallon maimunatu "Me zakici maimunatu?" Kanta a qasa ta girgiza kai,don har yanzu cikinta a cushe yake,tana jin daga nan har gobe da hantsi zata iya zama babu komai a cikin nata "Bana jin yunwa anni" "Badai a gidan nan ba,ke lailaa,shiga madafi,ki cewa lami ta zubo tuwon nan da aishatu ta kawo,cin mutum biyu ta kawo mana" ambatar sunan da anni tayi sai taji ya tsarga mata har cikin ranta,a duk sanda aka kirayi me irin sunan,babu abinda yake tuna mata face mahaifiyarta. Sanda laila ta kawo tuwon zama tayi zataci,amma anni tace batasan wannan zance ba,ta koma can wajen uwarta taci "Wallahi anni ke kadai ta yiwa tuwon nan duk gidan nan,ko abbi babu shi a ciki" "A nan kuka fi kauri,wajen bada gudunmawar ci,da wani cikinku nace yayimin babu me katabus" ita dai laila bata damu ba,ta saka hannu a kwanon maimunatu ta fara cin abincinta tana sakowa maimunatu hira,abinda yasa anni fa sake qyale lailan kenan,saboda hakan da tayi tasan zai bawa maimunatu damar sakewa. Ta kuwa dan sake din,tana tsakurar abincin,iyakarta da hirar laila uhmm ko um um,sai kuma murmushi wani lokacin,duka anni tana ankare da ita,tausayin maimunatu take ji sosai cikin ranta,gefe guda kuma tana sake shiga ranta,komai nata mai sanyi ne,cike kuma da nutsuwa a cikinsa. A hankali a hankali 'yan mata matan gidan suka fara shigowa da daya da daya kamar yadda suke yawancin darare,suna shigowa anni su kuma dade wajenta,don ma fadanta yakan sanya wani lokaci suqi zama,amma idan suka sameta akan laushinta har kwana sukanyi. Duk wadda ta shigo sai tabi maimunatu da kallo,wasu suce "Ma sha Allah,anni baquwa mukayi?,ina kika samu balarabiya?" "Yar uwarku ce" amsar da take basu kenan taci gaba da harkar gabanta,cikin girmamawa maimunatun take gaida duk wanda ga shigo,har suka dan cika a falon,sunata hirarrakinsu tana jinsu,koda sun sakota saidai tayi musu murmushi kawai,abinda ta lura dashi,su din mutane ne masu mutunci da girmama dan adam,hakanan suna da sauqin kai,duk da adan taqin zaman nasu ta fuskanci wani yafi wani sauqin kai a cikinsu,dama haka halittarmu take,kowa da dabi'a da kuma yanayin da Allah yayi masa. Ranan kusan a nan duka suka sukaci abincin dare,maimunatu nata kallon banbancin rayuwa da kuma gaskiyar karin maganar nan ta bahaushe da yake cewa 'Allah daya gari bam bam' kowa yakanje ya diba zabinsa ne da abinda yakeson ci,ya kuma buda ma'ajiyar abunsha ya dauka kalar lemo da ruwan da yakeso,wasunsu kuma su sanya ma'aikatan gidan su kawo musu,babu kyara babu tsangwama,akwai alamun hadin kai da zaman lafiya bakin gwargwado tsakaninsu. Tabawa anni data jima da tashi a falon ta aiko kan maimunatu ta tafi ta kwanta,kusan dama ta gaji da zaman,don bata saba hira da mutane ba,duk sai zaman ya gundureta,amma ta rasa ta yadda zata tashi ta wuce dakin,don haka tabawa na idar da saqon ta miqe "Balenjam" ta fada da tattausar muryarta,sai kuma ta danyi sak ganin yadda suka zubo mata idanu "Sai da safenku" ta fada da harshen hausa,laila ce ta saki murmushi "Allah ya tashemu lafiya fillo" murmushin tayi itama sannan ta juya zuwa ciki,tana mamakin yadda suna fulani amma basu damu da yin yaren a tsakaninsu ba,don tunda tazo da hausa taji suna hira har yanzun data tashi,wala'alla shi yasa suka bita da kallo sanda ta yaara musu. "Gaskiya yarinyar nan kyakkyawa ce,tana da hankali da alama" salma data miqe dauke da.plate din data gama shan farfesun kayan ciki ta fada,dubanta laila tayi "Sosai,tana da nutsuwa sosai,tana burgeni" "Ni kaina haka" fa'iza ta amsa musu,daga haka laila bata ce musu komai ba,don tasan cewa ba wanda yasan komai kan zuwan maimunatu gidan,bai kuma kamata ita din ta fara cewa komai ba. Sanda ta shiga dakin idanunta sun fara mata nauyi saboda bacci,qullin kayanta data hana tabawa dauka daxu ta janyo ta tasa kanta dasu,bayan tayi kwanciyarta qasan tiles ba tare da tayi gigin hawa gadon ba,babu jimawa wani nannauyan bacci mai dadi yayi awon gaba da ita. *********Kyakkyawar macace wadda shekarunta na haihuwa suka kusa arba'in da bakwai,kana mata kallon farko zakasan cewa sanda take da qananun shekaru ba qaramin kasa maza dr marwan yayi a kanta ba,tana da siffa me kyau ko a yanzun ma,fara ce sosai kamar yadda akasan asalin farin bafullace,hakanan bata da tsaho can can,kamar yadda ba zaka kirata gajeriya ba,saidai alamun tsafta da qamshi da suka samu wajen zama a tattare da ita sun nuna kansu muraran. Cikin nutsuwa kamewa da kuma sanin kimar kai take shigowa bangaren surukar tata,sanye cikin atamfa england me ruwan ganye,dinkin riga da plain zani,bayanta masu aikin gidan ne wadanda ke qarqashin bangarenta masu kula da bangaren kitchen dauke da trays,sai kuma salma dake riqe da wani warmer me kyau guda daya a hannunta,a shirye take tsaf da alama wani wajen zata wuce,tana daga gefan mahaifiyarta(Aishatu amma) suna magana ita da salma din. Dakatawa masu aikin sukayi har zuwa sanda amma da salma sukayi sallama cikin qawataccen falon annin,wanda sam baiyi kama da falon tsohuwa ba,dai dai lokacin da DR marwan ke zaune gaban mahaifiyar tasa yana gaisheta,shima sanye da wata dakakkiyar shadda fara qal,kamar kusan ko yaushe kansa nannade da tattausan farin rawani na zallar auduga,da alama shima din fita zaiyi. Jinin sarauta ce ita amma sam ba zaka dauka haka ba,saboda sauqin kai da take dashi da kuma sanyin hali,Gefan anni amma ta qarasa tana zama a qasa kamar yadda ta samu me gidanta,wannan din wata dabi'a ce tasu ita da dr marwan tun suna da jajayen sahunsu,dabi'ar data maida aishatu tauraruwa a zuciyar anni cikin kafatanin surukanta,ya sanya kuma wasu daga cikinsu suke kishin hakan,duk kuwa da cewa anni tana matuqar qoqarin boye hakan,saidai ko daga yadda ja'afar keda matsayi a wajen annin kadai ya isa ya fallasa maka wace aishatu a zuciyarta. Sai data fara gaida anni sannan ta waiwaya ga me gidanta shima ta gaidashi,duk da cewa sun gaisa a ciki kafin ya fito,ya amsa mata cikin kulawa kamar ko yaushe,salma ta matsa kadan ta gaida dr sannan ta maida dubanta ga anni,murya qasa qasa tace "Ranki ya dade hajjaju anni" wani kallo ta jefi salman dashi,tasan duk me salman take wa "Allah ya baki haquri anni ina kwana" "Lafiya sumul natashi 'yar nema,duk take takeki kar nake kallonki,gwara kiyi ta kanki 'yar nan" wuri wuri salma tayi,da alama tonin silili anni keson yi mata a gaban wadanda take gudun yin maganar a gabansu,bata gama tunanin ba kuwa maganar annin tayi mata saukar aradu "Wai marwanu.....ita wannan kazar mayun har yanzu bata isa ayi maganar aurenta bane?" Ji salma tayi kamar qasa ta tsage ta shige,maganar da tayin tana nuna kuma yasa dr maida idanunsa kan salma "Me ya faru anni?" Gyara zamanta tayi "Yo ni na gaji da hada kafada dasu idan ku baku gaji ba,ina buqatar ganin wasu 'yan dagwai dagwai din,ko ka aurar dasu ko ka auro,zuri'a nake da buqatar gani me tarin yawa......yawwa......duk gidan nan billhillazi babu yaron da bai isa aure ba,ramatu ce kawai za'a iya dagawa qafa,amma ace babu me aure?,baga mazan ba baga matan ba?,to idan baqinjini garesu zan buga gangar bada sadakarsu mazansu da matansu" kafin ta diga aya salma ta kwashi takalmanta a hannu tayi waje,don taga alama yau annin me manya manya take barota. "Ayi haquri anni" abinda dr yake fada kenan,don yasan da biyu take wannan fadan,tana tunanin kamar shike qin bada auren yaran nasa,bayan kuma yaran da kansu suke sha'awar karatu shi yasa ya qyale kowacce da zabinsa,uwa uba ma duka duka salma hafsat da laila ne a makarantun gaba da secondary,samma hafsa nadiya fa'iza da khadija sune 'yan candyn bana,zahra'u na ss one,sai rahama dake j.s,mazan kuwa dukkansu ba wanda ya gama jami'a banda ja'afar da haisam,sai Mahmoud dake ajin qarshe "Yanzu fisabillahi....salma zaman me take?,shi karatun da take cewa akayi bashi yuwuwa ta qarasashi cikin dakinta?" "Ta fiddo wanda takeso anni,ai baza'a qi aurar da ita ba" "To ta fitar kuma shi take ta raragefan gaya maka kai da uwar tata" qas amma tayi da kanta,wal'alla ta gayawa anni sunyi zancan da ita kenan "To ba damuwa anni,zanyi magana da umar(qaninsa kenan me bi masa),saita turashi can yaje ya gaidasu" "To ba laifi" annin ta fada tana sassautan fadan,dai dai sanda salma tayi dake labe daga waje tayi tsallen dadi,anni tasu,anni ta wajensu,ayi tsiya ayi dadi,ga tsiya ga aiki,lallai yau dole ta yiwa annin wani tagomashi,saita juya cikin jin dadi zuwa ma'ajiyar motocin gidan,inda driver yake jiranta,ranta fari qal. Daga can falo kuwa duban dr anni ta sakeyi "Shi kuma jabiru da ja'afar fa?,da aka barsu suke zaune a wata uwa duniya,ga wancan qaton tuzurun haisam?" Miqewa amma tayi saboda kara da yakana irin tata,tana ganin ya kamata ta basu waje suyi maganrsu sosai "Ina kuma zuwa?" Anni ta fada tana binta da kallo "Zan duba meye baku dashi a kitchen" "Idan kin shiga,kiyi waya can gidansu marigayiya,ya kamata a dawo da amna,jimawar da tayi a can wannan karon tayi yawa" "To anni" ta amsa mata cikin girmamawa tayi ciki,dawo da dubanta tayi ga dr marwan tana tattara hankalinta sosai a kansa sanda ya fara mata bayani "Maganar da nakeso muyi kenan.....a jiya da kika sameni da baqi kamar yadda na gaya miki ministern ilimi ne na qasa ya kawomin ziyara,bayan mun gama tattaunawa kan batutuwa irin namu,sai kuma ya jefomin maganar diyarsa unaisa,ya yimin tayin aurenta da ja'afar kamar sanda ya taba yimin a baya ban karba ba,lokacin ja'afar din yana aviation school,magana kuma tayi nisa tsakaninsa da marigayiya,to a yanzun inajin nauyi na sake qin karba din,kada yaga kamar banason hada zuri'a ne dashi ko kuma wani abu makamancin haka,na amsa masa ne duba da cewa gaba dayanmu dama muna laluben masa abokiyar zaman da zata iya zama dashi bisa juriya da kuma haquri kan sauyin hali da dabi'arsa,na kuma tabbatar kema idan kikaji hakan zaki farinciki,tunda burinmu kenan gaba daya" Shuru anni tayi tana duban dr marwan,bawai don yayi kuskure ko kuma maganganunsa ba'a kan hanya suke ba,a'a......saidai tana tunanin wace unaisa?,akwai yiwuwar samun dacewar zama tsakaninta da ja'afar din?,uwa uba kuma ga batun maimunatu da take tafe dashi,sai takega kamar akwai matsala. _To masu karatu,muje zuwa,shin al'amarin zai yiwu?,duk da bamusan wacece unaisa ba,abbi baisan wace maimunatu ba,kamar yadda wanda aketa abun a kansa baisan wainar da ake toyawa bama_ *17* "Ni ai tuni na samarwa ja'afar matar aure"anni ta fada kanta tsaye,ba tare data jira komai ba ta dora "Ire irensu unaisa ba daya ba ba biyu ba......amma sun kasa jumuri da juriya da kuma samar mana da abinda mukeso" anni ta fada cikin cikakkiyar nutsuwa da bawa zancan muhimmanci,har yanzu ita dr marwan yake kalla,ganin haka ya sanyata ta dora "Eh,hakan yasa na sauya shawara bisa hasashen ramatu" nan ta ware masa komai kan hasashen yuuma,da yadda ta gamsu da maganarta,da kuma yadda ya zamana tashin farko maimunatu ce ta fara zuwa mata zuciya da ranta,mizani da ma'aunai masu yawa da maimunatun ta hau taga kuma tabbas ta dave da matsayin matar ja'afar. Cikin nuna gamsuwa dr marwan yake gyada kai,dukka hasashen annin dama abinda ta aikata yayi dai dai da nasa ra'ayin "Saidai duk wanda keson naka yakeson hada jini da kai ba qaramin masoyinki bane,sa'an nan wannan ba shine karon farko da ya nuna sha'awarsa kan hakan ba,to bai kamata mu watsa masa qasa a ido ba,kuma namiji mijin mace hudu ne ai,fatanmu shine Allah yasa a dace,yasa qarshen matsalar kenan" kai abbi ya gyada "Gaskiya ne anni,Allah ya saka da alkhairi,ya qara girma" "Banga abun godiya ba marwan,wajibi na nayi,babu abinda bazanyi ba saboda rayuwar ahalina matuqar bai sabawa shari'a ba,yanzu abu daya ya rage,ja'afar ya dawo cikinmu,koda zai koma sai komai ya dai daita,don ban gamsu mu bashi yaran mutane ya tafi dasu har wata uwa duniya ba" "Gaskiya ne anni,hakan yayi" "Shikenan,zan sa a kiramin jabirun ko zuwa anjima ne". Dai dai lokacin maimunatu ke fitowa daga dakinta zuwa falon,tayi wankanta ta shirya tsaf bayan baba tabawa ta leqa da safen sun gaisa,ta kuma umarceta da yin wankan,mamaki ne yaketa kasheta,duka duka yaushe tayi wankan jiya?awa nawa ne a tsakani?,duk da hakan bata musa ba tayi kamar yadda baba tabawa ta umarceta,ta kuma shirya kamar jiya,saidai yau din haskenta ya sake fitowa fiye da jiya. Da murmushi anni ke kallonta sanda take isowa wajen,daga nesa dasu ta zube har qasa tana gaidasu,abbi baisan wace ba,amma ya amsa mata cikin kulawa kafin ya maida kansa ga labaran qasa da ake gabatarwa a tashar NTA da ya dauki hankalinsa. Cikin kulawa anni itama ta amsa "Ya kwanan baqunta?" Ta tambayeta cikin salon jan mutum a jiki da kuma son ya sake,murmushi kawai tayi mata tana sad da kanta qasa "Kinsan kitchen ai,leqa kice aishatu tazo,ta taho da qarin plates" "Toh" maimunatun ta amsa tana miqewa a nutse tayi kitchen din. Kafin ta qarasa tadan dinga jiyo hirarraki da alama akwai mutane a kitchen din,ta saka kanta a hankali bakinta dauke da sallama,abinda yaja hankalin amma dake tsaye suna magana da baaba tabawa,hannunta dauke da wata roba tana duba rubutun jiki. Waiwayowa tayi,sai suka hada idanu da maimunatu,dan zubawa maimunatun idanu tayi,tana mamakin jin irin muryar data sani daga gareta,amma kuma batasan fuskar ba,bata taba ganinta ba. Gaisuwar da take mata ta amsa cikin kulawa,sannan ta maida dubanta ga robar hannun nata,saidai kuma hankalinta naga muryar tata sanda take gayawa baaba tabawa anni ce ta aikota ta kira wata,kasa fadar sunan tayi kai tsaye,saboda suna ne dake da girma da kima a idanunta "Yanzun bansan wa anni ke nema cikin madafa ba,kin kuma kasa fadi,hala sunan yana da nauyi a wajenki maimunatu" murmushi tayi a takure gami da jin nauyinsu su duka,musamman amma da hakanan taji tayi mata kwarjini. Murmushi amma tayi "Falon zan koma,muje naji wanda ake kira....tabawa qarasa aikinki,idan kin gama ki sameni keda bara'atu a sassana,zaku yimin gyaran wardrobe" "To in sha Allah" haka suka jero,amma tana gaba maimunatu tana binta a baya,har suka qaraso falon "Baquwar taki ta kasa faden wanda kk nema anni" amma ta fada tana zama daura da dr cikin shirin serving dinsu abincin data kawo musun,murmushi anni tayi "Ke na aika ta kiramin,hala kasa fadin sunan tayi" gyada kai amma tayi "Eh wallahi,anni ina kika samo mana bafullatar usul" "Daga garinsu ramatu,gata nan don Allah aishatu,inaso a kulamin da ita da kyau,so nake ta zama 'yar gida tamkar su salma" "In sha Allah"amma ta fada tana dan sake kallon maimunatu kadan,wadda kanta yake qasa har lokacin,sai kuma ta miqe,don a takure take,ba zata iya zama cikinsu ba. Anni na shirin tsaidata don taci abinci a cikinsu tabawa ta fito ta kirayeta zuwa kitchen,abinda yasa anni ta qyalesu,ta maida kanta ga surukuwarta da danta. Cikin yanayi na shaquwa da kuma fahimtar juna suke cin abincin,suna kuma tattaunawa kan lamuran rayuwa wanda suka shafesu,amma na gefe ba tare data sanya musu baki ba,wannan daha daga cikin halayyarta kenan. Gab da zasu gama akayi sallama cikin falon,kyakkyawan matashine,yana da white skin hakanan giant ne shi sosai,kamanninsa na zahiri shi da dr Marwan sun bayyana. Yayi dressing very neat cike da tsafta kamun kai nutsuwa gami da zallar ilimi,hannunsa daya riqe da lab coat dake bayyana cewa shi din tabbas likita ne,a nutsensa sannan cikin girmamawa ya tube takalman qafarsa ya qaraso falon,ya duqa ya fara gaida anni sannan dr sai amma. Kansa yadan shafa kadan da yasha saisaye me kyau "Anni,zan samu sauran abinci kuwa?" Kai tsaye anni ta kalla amma "Bakuyi girki ba yau aishatu?" "Munyi anni,sanda zan fito ma na leqasu suna gab da gamawa,zuwa yanzu nasan sun gama" qaramin tsaki taja "Shine wannan qaton gardin zaizo ya sani gaba da tambayar abinci?....kaga idan zaka wuce gwara ka wuce,kuci a waje kamar yadda kuka saba,tunda haka kuka zabarwa kanku" dama yasan za'a rina,tsautsayi yasa yayi mata maganar,tun kafin ta tafi adamawa dama taketa rikici dasu,aure kawai takeso wai kowannensu yayi,wani lokaci sai yaji gwara ma dasu JJ suka basa nan,sun huta da ciwon bakinta. Idanun dr marwan dake a wajen ya sanyashi miqewa yana sake shafa qeyarsa hadi da cewa "Allah ya baki haquri" "O'o'o'o,na kusa yiwa tufkar hanci ai" "Fitarmin da briefcase din nan,ka cewa muslimu ya tada motar gani nan fitowa" cewar dr marwan,sai haisam ya qarasa ya dauka jakar ya musu sallama ya fice,amma tana masa addu'ar Allah ya tsare. Kusan idan da sabo amma ta saba raka dr koda a gaban anni ne,idan ma bata je ba zata ce ita ta tashi taje,don haka yanzun ma ta tako masa har zuwa farfajiyar dake sassan annin "Da gaske wannan karon anni ta tada wannan rigimar kan yaran nan,gaba dayansu so take a kauda su" rausayar da aki amma tayi "Eh banga laifinta ba,tunda abinda ya kamata kenan dama ayi,kowannensu ya kamata zuwa yanxu ace bashi kadai bane" "Musamman ja'afar da yake da buqatuwa ta kowanne bangare" dr ya fada don yasan daya daga cikin abubuwan da amma ke kwana dashi ta tashi dashi ne a cikin ranta,amma kuma yakana da kara ya sanya bata nunawa ko a fuska,amma shi din sau tari yasha jinta cikin tsakiyar dare tana kaiwa Allah kukanta akan matsalar yaron nasu,ya sani dole abun zai tabata sosai ya kuma dameta kamar kowacce irin uwa. Kamar yadda ya zata din kuwa fuskarta ta dan sauya daga yadda take a daxun,hakan yasa cikin kulawa ya bata dukka hankalinsa "A wannan lokaci muna saka rai da fatan samun warwarewar komai,bake daya ba bani kadai ba,kusan duk wanda ke cikin gidan nan ya damu da lamarin,amma kuma addu'ar bawa mumini bata faduwa qasa banza" kai amma ta gyada cike da gamsuwa,koda yaushe shi din mutun ne da yake da qoqarin ganin ya kwantar mata da hankali kan dukkan wani lamari,bawai iya na ja'afar kadai bama "Idan na dawo akwai maganar da xamu tattauna,duk da ban sani ba wala'alla anni ta shaida miki kafin na dawo din" "Allah ya tsare hanya,a adawo lafiya" "Ameen een,zan samu dambun nan kuwa?" Ya fada yana murmushi,cikin nata murmushin ta amsa masa "Ka cika cikakken bafulatani kai din,zaka samu in sha Allah" da haka yana dariya ya juya ya fice,ita kuma ta koma ciki tana murmushin itama,wani sashen na zuciyarta kuma ya lula ga tunanin dan nata,wanda ta kwashe wasu kwanaki bataji muryarsa ba,abinda a shekarun baya bata saba da hakan daga gareshi ba,komai cunkushewar aiki baya iya tsallake wuni guda baiyi kiranta ba,qaddarar data afkawa rayuwarsa tasa komai ya canza. **************** Cikin sati guda rak maimunatu ta gama fahimtar abubuwa masu dama tattare da family din anni kuma familyn dr marwan khalid akko,ba shakka duk tubalin iyalin da nagartaccen uba ma'abocin ilimin addini da kuma aiki dashi ya samar dashi zaka sameshi ya banbamta da sauran ahali ta fuskoki da dama,kowanne mutum cikin gidan yana rayuwa bisa kyakkyawar tarbiyya da suka samu daga mahaifansu,mutane ne masu fahimta gami da sauqin kai da daukar kansu ba komai ba,duk da tarin dukiya da kuma arziqi da Allah ya yiwa mahaifinsu,akwai haduwar jini tsakanin maimunatu da 'yammatan,babu wanda ke nuna mata qyamata ko wani mummunan hali da zai sanya taji babu dadi cikin ranta. Gida ne da baya rabo da baqi 'yan uwa family kuma jinin marigayi khalid akko mahaifi gasu dr marwan,mutanen gidan suna da son baqi da son ganin wani baquwar fuska yazo musu,abinda yasa suka kasance masu son jama'a. Kusan dukka jama'ar gidan ba mazauna bane,idan ka cire matan gidan da anni,kusan zamansu a gidan kadanne ne idan ba weekends ba,hakan yasa ta fara sabawa da anni sosai da kuma amma,duk da cewa har yanzun bata sake sosai dasu ba,musamman amma da hakanan take jin nauyinta,tafi sakewa dasu laila. Bisa shawarar tabawa anni ta daga qafa,ta kuma fasa kiran ja'afar kamar yadda ta tsara,abinda ya karkatar da hankalin annin tasa aka maida maimunatu islamiyya cikin satin,tabawa kuma ta qara da cewa "Ina ganin haj anni,me zai hana a maidata boko ma?,tunda rannan naji suna hira da laila,da alama meson karatu ce,kuma hakan shine dai dai,ta yadda babu yadda za'ayi babban mutum ya raina zabinki" murmushi anni tayi "Haka maganarki take,amma kuma tabawa,inaso ne yayi mata hidima da kansa,ya raineta da kansa,ya kuma san ciwonta,ta yadda kome zaije yazo bazaiyi wasarere da ita ba,banqi shawararki ba,amma zan samar mata wanda zai dinga zuwa gida yana dora mata karatun bokon,har zuwa lokacin da zan fara aiwatar da abubuwan dana tsara,idan yaso shi da kansa ya samar mata duk makarantar da yaga dama,ya kuma cire kudinsa ya biya,hakan nakega sai yafi" kai tabawa ya gyada,lallai ta hangi dabaru masu yawa kan wannan shirin na anni,fatansu dai shine Allah ya tabbatar da alkhairi,ya shige gaba akan dukka lamarin. Cikin satin maimunatu ta zama cikakkiyar daliba ta kuma saje da iyalan gidan dr marwan,islamiyya dake layi na biyu dake bayan gidansu,ranar da zata fara zuwa din laila natsaye falon anni hanunta dauke da qur'aninta tana tisa haddar da zata bayar a yau din,maimunatun ta fito sanye da Egyptian hijab dinta har qasa dinkin kalar blue black. "Wow....ma sha Allah" laila ta fada tana murmushi,idanunta bisa fuskar bafulatana maimunatu,fuskar da zuwa yanzu ta sake washewa,ta fara fresh da ita saboda samun canjin weather da kuma zama waje daya gami da sauyin cima dama makwanci "Kinga yadda kayan sukayi matuqar karbarki kuwa maimunatu?,kamar don ke aka zaba kalar?" Murmushin nan nata me sanyi ta sakarwa laila,wanda kusan shi ta fiyi yi fiye data yi magana. Sai data leqa anni dake dakinta tayi mata sallama,sannan suka fito suka rankaya ita da hafsa da laila din da nadiya,fa'iza da rahama sun rigasu yin gaba,don dama ba kasafai suke jerawa dasu ba. Abinda ke bata mamaki yadda duk sanda zasu islamiyyan da qafa suke takawa,duk da cewa idan da sunso jikinsu zasu iya bin motar gidan ya qarasa dasu,amma sam basu damu ba tafiyarsu suke,babu wani girman kai ko jin cewa ubansu wani ne,ko kuma sun fito ne daga babban gida. ************* Zaune take cikin qawataccen falon anni,wanda ya wadata da tsafta da kuma qamshi ta ko ina,falon da a yanzu yake qarqashin kulawar maimunatu da bata bari koda tsinke ya sauka a kansa,ita daya ce qwal a falon,sanye take da wani milk high waist skirt na material mai santsi,sai rigarsa ta chiffon material milk color mai torches na brown,fatarta ta sake wani irin haske da kyau,ta kuma yi luwai luwai,duba daya zaka yi mata kasan cews tabbas ta samu nutsuwar zuciya da kuma ruhi a watanni ukun data shafe cikin gidan,saman kanta baby hijab ne da bata rabo dashi ruwan madara kalar skert din jikinta,wanda ya zame daga gaban kanta,ya bayyana lallausar sumar dake kwance daga gaba,kai baka ce akanta akwai manya kalba data roqi laila tayi mata ba,wansa lailan taso taqi matan,saboda sunyi sunyi ta bisu suje saloon da suka tsara zuwa a ranar saboda shirye shiryen bikin da suke a dangin ammi amaryar dr marwan kenan amma maimunatun ta qiya,ba kasafai take zarmewa da kuma zaqewa cikin lamuransu ba,don har yanzu bata saki jiki dasu yadda suke so ba,bawai don tans musu mummunar fahimta ko kuma zato ba,a'ah.....saidai ita din a koda yaushe tafi ganewa tsaiwa iya matsayinta,kada rayuwar ta rudeta ta kuma sanyata mantawa wacece ita. Komai dake tattare da maimunatu ya sauya,saidai har yanzun bata bar wasu dabi'u nata ba,saboda gudun manta asali da tushe,kamar yadda bata zubda ko cire duwatsun hannunta ba,hakanan kayan saqinta suna nan,tayi musu kyakkyawar ajiya,kamar yadda lokaci zuwa lokaci idan taji kewar gida ko dabbobinta,take sanyasu a jikinta ta wuni da abinta,su laila suyita tsokanarta,saidai ta bisu da murmushi kawai,kasancewar shine fiye da rabin amsar maganarta. Yau din gidan babu yawaitar jama'a sosai,kusan dukka kowa ya fita sha'aninsa,'yan mata matan sun fita wankin kai,anni kuma yau tana daki a kwance,don kwanaki biyu kenan bata da dan jin dadi tana fama da mura,masu aikin dake sassanta kuwa suna kitchen,wasu kuma suna bangarensu suna hutawa,ammi ta fita unguwa itama,sunata shirye shirye da hidimar biki,acan sassan nasu sai amma kawai. Yankam farce takeyi abinta da nail cutter,ta bada hankalinta sosai ga yankan,yayin da wani sashe na zuciyarta yayi nisa cikin zurfin tunani,yadda rayuwa ke gara mata,babu mahaifiya bakuma tasan inda mahaifinta yake ba,takan kalli su laila a matsayin 'yan gata gaba da baya,bawai gata na dukiya da daular da suke ciki ba,a'ah,gata na kasantuwarsu suna rayuwa gaban mahaifi mahaifiya kaka harma sa danginsu,sukan burgeta a yawancin lokuta,takanji inama ace tana da wannan gatan. Takun tafiya da sauri da asauri da kuma sautin kukan qaramar yarinya cike da rigima ya sanyata daga kanta daga abinda takeyi,ta kuma maida dubanta ga qofar shigowa falon duk da labulayen alfarmar da suka kangeshi daga ganin wanda ke tahowa daga waje,jim kadan me kukan ta bayyana,ta bankada labulen tana shigowa da sauri kamar yadda ta taho. Kyakkyawar yarinya ce ta gaske,wankan tarwada,kalar da dukka gidan mutum daya taga yana da ita,sanye da wata irin short sleeve gown mai azabar kyau,qafarta sanye da rufaffen takalmi na mata daya dace da kayan jikinta,kanta mai cike da suma me santsi da laushi kuma an masa wani irin gyara mai kyau da daukar hankali,an qawata shi da ribbons,hannunta daya dauke da wata qatuwar teddy da suka kusa yin kai daya,kai tsaye taci gaba da takowa cikin falon tana kuma kukanta,tare da rarraba idanu da alama akwai wanda take nema. Da idanu maimunatu ta bita,kuka take yarinyar da gaske,hawaye shabe shabe kan fuskarta,hakanan kawai tausayinta ya tsirga mata,duk da batasan wacece ba,batasab me akayi mata ba,saita miqa hannu a tausashe ta riqo hannun yarinyar,abinda ya ankarar da ita kenan da wani a falon,ta waiwaya a hankali tana duban maimunatu. Murmushi ta sakarwa yarinyar,duk da yadda taji idanun yarinyar har tsakiyar kanta,wasu irin idanu ne da uta masu kyau da daukan idanu,a hankali ta buda bakinta "yaki,zoki gayamin wane ne?,me akayi miki" ta fadi da taushi cikin sigar lallashi,kai tsaye kuwa yarinyar ta soma takowa zuwa wajen maimuntun,batayi qasa a gwiwa ba ta dorata saman cinyarta kana ta jinginata da jikinta,take yarinyar ta narke jikin nata. Dumin jikin yarinyar yasa maimunatun taba wuyata,da alama zazzabi kenan take,saita zagayo da kanta gefan fuskarta "Waye ya tabaki?,waye ya sakaki kuka?" Ta sake tambayarta kanta tsaye,salon tambayar da alama ya taba zuciyar yarinyar,sai ta saki kuka sosai cikin sheshsheqa tana cewa "Uncle hisham ne......." "Ya isa,yi shuru,indai shine sai mun hukuntashi,ki daina kukan haka,kinji akwai dumi a jikinki kada ya sake qaruwa" maimunatu ta fada tana jin tausayinta ba tare da tasan dalilin hakan ba. Qanqameta yarinyar tayi "Ba za'a yimin allura ba?" Ta tambayi maimunatu tana duban idanunta,murmushi ta sakar mata tana shafa tattausan gashinta "Babu wanda zai miki allura kinji" ta qarashe maganar tana jan yarinyar cikin jikinta sosai ta rungumeta,sai ta narke itama tana sassauta kukan gami da sakin ajiyar zuciya me qarfi,da alama abinda take buqata dama kenan,tunanin maimunatu yadan cilla wani waje jin yadda yarinyar tayi luf a jikinta tana sauke ajiyar zuciya,kamar tasan fuskar yarinyar a wayoyin al'ummar gidan,kamar tana ganin fuskarta a wajensu. Tsakiyar tunanin da take aka daga labulen akayi sallama wadda ke cakude da sauti na dariya a tausashe,ta daga kanta a hakali tana amsa sallamar,idanunsu suka sarqe waje guda dame sallamar. 18 Karo na uku kenan da ta taba ganinsa cikin gidan tun zuwanta,ba zata iya cewa ga ainihin sunansa ba,don babu abinda ya taba hadata dashi da ya wuce gaisuwa,daga nan take barin waje,tana da dabi'ar barin guri a duk sanda taga iyalin gidan sun hadu waje guda,har sai idan sun buqaci tayi zamanta. Cikin tsarguwa ta janye idanunta daga cikin nasa tana sake gyara zamanta gami da jan skert dinta zuwa qasa sosai,duk da dama ya sauka din,shima nasa idanun ya dauke yana shigowa cikin gami da sassauta dariyarsa "Ina yini" ta gaidashi idanunta nakan teddy din yarinyar data yar "Lafiya lau.....anni na ciki ne?" "Eh ta amsa masa a taqaice" "Yimin kiranta idan ba damuwa" da to ta amsa masa tana yunqurin tashi tare da qoqarin ajjiye yarinyar,saidai fir taqi ta qanqame maimunatu da kyau,idanunta nakan hisham. Qaramar dariya ya sake yana kallonta "Duk ki gama guje gujen naki tsaf kuma azo ayi allurar,wannan zazzabin jikin naki ta yaya za'a barki dashi" kafada ta noqe tana sake tale baki da alama zata sake sakin wani sabon kukan ne "Miqomin ita ki kiramin annin" gam ta sake riqe maimunatu tana cukuikuye dan qaramin hijab din jikinta,har sai da maimunatun tadan jashi kadan saboda jikinta daya dame "Qyaleta,bari na kira maka ita a hakan" ta fada tana saba ta a kafada,sannan ta fara takawa a hankali zuwa gefan anni. Da.kallo yadan bisu har suka bacewa ganinss,sai ya dauke idanunsa yana sakin boyayyar ajiyar zuciya,wannan shine karo na hudu daya ganta a gidan,baisan wacece ba,baisan kuma relation dinsu da ita ba,saidai akwai wani abu me fusgar hankali tattare da ita,bama kamar yanzun da sukayi kusa da juna ba kamar kwanakin da yake hangota daga nesa ba. Saman lallausar dardumar dake dakin ta samu anni,tanata danne danne a wayar da ala dole ta karbeta,saboda ciwo baki na jikokinta,bata daga kanta ba,tadai amsa mata sallamar cikin kulawa saboda hankalinta na ga wayar,har sai da maimunatun da zuwa yanzu ta maida yarinyar bayanta ta shigo dakin gaba daya "Wa nake gani a bayanki kamar amna?" Leqowa yarinyar tayi da kanta don anni ta tabbatar "Ja'ira,sai yau Allah yayi suka dawo mana dake kenan?" Anni tafada tana dariya,koda bata sake cewa komai ba maimunatu ta gane wacece,yarinyar da kullum rana ba zata fito ta fadi cikin gidan wani bai ambaceta ba,taji yadda akasha gwagwagwa da kakanninta na wajen uwa kafin su yarda su dawo da ita,saboda ita kadai ce jikarsu,jikarma kuma ta wajen diyarsu mace qwaya daya tal da suka mallaka,taji kuma ance mamanta ta rasu,take tausayi da qaunar yarinyar ya sake saukar mata fiye da dazu,qaramarta da ita tasan dacin maraicin uwa?,ko ita dake da girmanta yaya takeji a ranta bare wannan,hukuncin Allah ne,ba yadda baya tsarawa,haka bawa zai karba a duk yadda yazo masa. Kememe amna taqi sauka daga bayan maimunatu,duk yadda anni taso tazo gareta "Yar nema,zamu hadu ne,wannan din kin santa ne?,daga zuwanki zaki dafewa diyar mutane?" Annin ta fada tana dungure mata kai,abinda yasa amnan ta sunne kai a bayan maimunatu ba tare data ce komai ba,maimunatu na jinsu tana tayasu da murmushi "Yaa hisham ne yace nayi masa kiranki" ta fadi sunansa kamar yadda taji yaran gidan na fade "Ya shigo mana,baisan dakin nawa bane da zai tattago ni ina fama da kaina?" Goye da amna ta fita a dakin don gaya masa saqon annin. Waya yake dannawa,amma jin takunta yasa ya tsaya ta daga kansa yana dubanta,ta shaida masa abinda anni tace,har ya miqe kira ya shigo wayar tasa,sai yace "Ina zuwa" yana duban fuskar wayar ya fice daga falon,dai dai lokacin da daya daga cikin ma'aikatan gidan me suna sha'awa ta shigo falon tana shaidawa maimunatu malaminta yazo "To ina zuwa" ta amsa tana komawa wajen anni ta gaya mata abinda hisham din yace,taso aje mata amna amma yarinyar taqi,haka ta juya zuwa kitchen don kaita wajen tabawa,wadda dama ita ke rainonta amma sam wajen tabawan ma taqi zaman "Haba uwar gijiyata,wannan zazzabin na jikinki da kin haqura kin zauna,bakya fita gurin shukokin can ba iska ta sake kadaki" fir taqi,saboda tana tsoron kada hisham din ya biyota nan yayi mata allurar da ya ambata din,haka maimunatu ta fita da ita inda ake mata karatun tana goye da ita,hannunta kuma riqe da litattafanta. Tana cikin jikinta suna karatun,tana bala'in qaunar karatun nata,saboda.malamin ba qaramin qwarewa yayi ba da kuma sanin makamar koyarwa,cikin watanni uku kacal ta fara gogewa fiye da tsammaninta,duk da dama dai ta samu foundation me dan kyau ba laifi daga makarantar primary din da tayi a gembu. Gab da magariba suka gama karatun kamar kullum,tana goye da amna da barci ke dibanta suka shiga cikin gidan,ta taras dasu laila duk sun dawo,sun sha qunshi da gyaran kai tubarkalla,kowacce cikinsu tana da suma dai dai gwargwado irin na fulani. Duk yadda suke daukin amna tazo gurinsu taqi kowa,kowa da kalar wayon da zaiyi mata amma ta qiya,murmushi maimunatu ta sake,har fararen haqoranta suna fitowa "Saiku haqura,yau dai kam ni ta zaba" sunata yiwa yarinyar tsiya ta wuce da ita dakinta ta kwantar da ita saman gadonta,zuwa lokacin bacci yayi awon gaba da ita. Washegari amnan tana barci maimunatu ta wuce islamiyya,sanda ta farka bata ganta ba ta saka rigima,rarrashin duniya kowa yayi mata amma ta qiya,hatta da anni da amman da suke dasawa yau taqi,saboda sun bari hisham kafin ya fita aiki ya nata allura,basu samu lafiya ba sai da maimunatu ta dawo,da gudu ta taryeta kuwa tun daga bakin qofa,maimunatu ta dagata tana taba jikinta,ta samu zazzabin ya sauka,baki ta tura gaba cikin murya irin ta yaran da suka samu gata "Ba uncle hisham bane yayimin allura" "Ya salam,sannu kinji,kiyi haquri" maimunatu ta fada tana shafa bayanta,saita kwanta luf a jikinta tana bata labarai har suka qarasa cikin gidan. Cikin kwanakin wata irin shaquwa ce sosai ta shiga tsakanin amna da maimunatu,ta maisheta tamkar uwarta,duk gidan a yanzu babu wanda take dafewa kamarta,kowa yasan hakan cikin gidan,gaba daya ma ta dawo da kwananta dakin maimunatu,hakan yayiwa maimunatu dadi sosai,saboda tafi sakewa da amnan akan kowa cikin gidan,zasuyi zamansu a daki suyita hira da amnan kai ka dauka da wata babba take magana,sosai amnan ke jin maganarta,da gaske yarinyar qaunarta take,amna yarinya ce me wayo da surutu,haka zata zauna ta yita baiwa maimunatu labarin mommynta da twin sister dinta da ta rasu,takan ce "Ummu(mamam shaheeda)amma/anni sunce sunje maka,zasu dawo,zasu siyomin tsaraba me yawa ko?" Sai maimunatu ta gyada mata kai cike da tausayinta "Amma me yasa ni mommy bata tafi dani ba?,kuma ta tafi da amra ta barni?" Ire iren maganganun dake karya zuciyar maimunatu kenan akan yarinyar,yake qara mata sonta da kuma tausayinta,sau tari takan faki idanun yarinyar ta share hawayenta,saboda ita da yarinyar dukkaninsu suna cikin jarabawar maraici,har gwara amna,tana da gata gaba da baya,saboda tsabar gata ma kowa so yake a bashi ita ya riqeta,ita kuma fa?. Idan ta gama wannan kuma sai ta koma zancan mahaifinta,wanda maimunatu batasan wayeshi ba,saidai da alama yarinyar tana kewar mahaifin nata kewa me tarin yawa,a zuciyarta take jin tunda yana raye bai kamata ya nisanci yarinyar haka ba,tana da buqatarsa a kusa da ita,duk randa ko ta samu yin waya dashi,ranar gaba daya labaranta nasa ne,maimunatun takan bata lokacinta ta biye mata suyita yi,abinda ya qara sabonsu da shaquwarsu kenan da ita. Yammaci ne sosai,wanda yake dauke da lullumi sosai da zakayi tsammani damina ce zata fara,saidai maimakon daminar ana dakon zuwan zafi ne kafin gabatowarta. A irin wannan lokacin gidan yakan kasance shuru,rana ce da babu makaranta both islamiyya da boko,yawanci a wannan lokacin 'yammatan gidan sunfi kwanciya suyi barci idan basu da abinda zasuyi,idan kuma suna dashi kowa yakan kama aikin gabansa,zuwa dare kuma su hadu zaman hira,ma'aikata kuwa na kitchen na sassan biyu,sassan dr marwan ko na hajiya anni. Maimunatu ce ta dage dan qaramin falon da anni kan zauna ta huta lokaci zuwa lokaci,hannunta dauke da zobo data dafawa annin tsurarsa,babu suger bare kayan hadi sai citta da kanunfari kawai,tun zuwanta gidan takan dafawa anni shi akai akai,saboda qarin jimi da kuma gyara zuciya da sauran cututtukan hawan jini,sosai anni takejin dadinsa,don tana ganin amfaninsa a jikinta. Tashi xaune anni tayi tana amsa sallamar cikin sakin fuska,idanunta nakan maimunatu,a duk sanda ta kalleta tana jin dadin sauyin da ake samu tattare da ita,zuciyarta kuma a kullum tana gaya mata kamar lokaci yayi da zata bayyanawa maimunatu qudurinta. "Sannu da hutawa anni" "Yauwa maimunatu,ke zaa yiwa sannu" murmushi tayi ta zauna ta fara zuba mata zobon,annin ta karba tana godiya ta fara kurba,jifa jifa suna hira. "Maimunatu......qarasa jikin soket ki ciromin wayar can da Allah" amsawa tayi ta ciro kamar yadda ta umarceta "Yauwa laluba ki kamomin ja'afar" maida dubanta tayi ga numbers din dake kan wayar,ta fara laluba sunayen,har takai ga sunan da annin ta nema "Gashi anni" "Yauwa kiramin shi" ta fada tana ci gaba da kurbar zobon,zuciyarta na ayyana mata tunani kala daban daban. A nutse la latsa icon na kira,kiran kuwa ya tafi kai tsaye,take daga qasan sunan number wayar qasar waje ya bayyana,kuma sunan TURKEY ya fito daga gaban number kadan *TURKEY* *TURKEY CAPITAL* _ANKARA yanimahalle_ _Green forest mahalle_ Cikin babban ginin me dauke da apartments apartments,hawa na biyu,madaidaicin falo ne da ba zaka kirashi tangamene ba,kamar yadda ya wuce ya amsa sunan qarami,me dauke rantsatsun kujeru irin na asalin qasar turkey din,lafiyayyen carpet da curtains ash color light and dark dukka na qirar qasar,sai rantsatsiyar wallpaper kalar kayan dake falon,qananun sideel table da babbansu daga tsakiya,dining space da aka maqalawa fridge dukkansu kalolin kayan falon ne. Daga gefan fridge din lafiyayyen matashin saurayi ne jingine da fridge din,hannunsa riqe da cup daya cika da tataccen ruwan kayan marmari kala daban daban da aka markada aka kuma tacesu a mazubi guda,dogo ne me murjajjen jiki,yana sanye da shirt mai dogon hannu da kuma trouser,yayi crossing qafafunsa hannunsa daya soke a aljihun wandon nasa,daya hannun kuma yana riqe da cup din da yake kaiwa bakin nasa lokaci bayan lokaci. Kana kallonsa zakasan yayi nisa a tunani da kuma nazarin inda idanuwansa suke kallo,gaba kadan dashi inda aka tsara rukunin kujerun dake falon. Mutum biyu dake zaune cikin falon,daya farar fata ne,bature sosai,mr denis evoy dan asalin qasar Belarus,yayin da dayan ya kasance baqar fata ne,wanda ya mallaki wata sassalkar fata me kyan gani da kuma burgewa ko cikin jinsin masu baqar fatar da ake kira da chocolate color,CAPTAIN JA'AFAR MARWAN KHALID AKKO qwararren kuma sanannen matuqin jirgin sama wanda ya ajjiye aikinsa,ya kuma yi switching kansa ya zuwa babban dan kasuwa,mamallakin kamfanoni dake samar da manyan gine gine na manyan ma'aikatu jami'o'i da manyan kamfanoni tituna dama gidaje,manyan gine gine masu ban sha'awa da qayatarwa. Kyakkyawa ajin farko,irin kyan nan da a hankali yake bayyana kansa,wankan tarwada ne,a very husky man built like a football player,dukka qirar jikinsa na nuna alamun qarfi dake bayyana cikar mazantaka,yana da tsaho da kuma kauri dai dai misali wanda ya taimaka wajen sake boye ainihin tsahonsa,wasu irin shanyayyun idanu masu matuqar daukan hankali da kuma tafiya da imanin diya mace ko wacece ita,lafiyayyen qasumba ne dashi wansa bata rabo da saisaye da kuma gyara,gyaran da yake dacewa da kyawawan labbansa hancinsa me tsaho da tudu da kuma cikakkiyar girarsa,akwai wata suma ta musamman saman kansa mai sulbi da kuma sheqi ta asalin bafullace,wadda batayi yawa ba hakanan ba kadan bace. Iya lafiyayyar fatarsa da kuma zara zaran yatsun qafarsa da na hannu kadai idan ka kalla zakasan cewa a huce yake cikin cikakkiyar wadata da kuma hutu,sau tari qannensa na sha'awar yanayin qafarsa dake luwai luwai kamar ta mace,saboda yadda ta samu hutu da kuma gyara,tako ina ja'afar ya cika cikakken namiji,wanda ya samu kusan cikar komai na rayuwa......saidai abu biyu daya rageshi,na farko mutum ne shi miskili na gasken gaske,irin miskilancin dake baiwa mutane da dama mamaki,ake kuma tunanin lokaci zaizo da zai sauya,saidai har zuwa lokacin da aka tsammaci zai sauya din yazo bai sauya ba,lokacin kuma ya sake zuwa ya hade masa da baqar qaddarar rasa matarsa da kuma diyarsa mafi soyuwa a wajensa,abinda ya sake canzashi kenan,ya kuma sake cillashi duniyar miskilanci. Sosai yayi relaxing bayansa da jikin kujerar da yake zaune,very calmly yake kallon Mr Denis,sai kayi tsammanin duk duniya bashi da wata matsala a rayuwarsa dake barazana ga farinciki da kuma ci gabansa. 19 *Arewabooks:Huguma* https://arewabooks.com/chapter?id=6351005edace9b957e575eaf Saidai shi din haka yake,komai nasa a nutse yake cike da tsari da kuma nutsuwar,yana duban mr denis ne jabir dake jingine da fridge shima yana nazarinsa,cikin kwanakin nan gaba daya aikin ja'afar din kenan,ya dawo da dukka hankalinsa akan kamfaninsa,ganawa yake tayi da mutane daban daban duka akan kamfanin,wani irin huge change yake gani tatare dashi a dare daya,sau tari yakanyi sha'awar inama ace ja'afar din ya tabbata a haka?,wasu lokutan a baya sai yayi kamar zaici gaba da rayuwarsa kamar kowa,sai kuma abun ya sake tabarbarewa,but surely a wannan karon yana ganin yanayin kamar ya banbamta da na baya,ko wannan din zai dore?. Murmushi jabir ya saki,yana dora cup din saman fridge din sanda yaji mr denis na complain kan cewa "Sir, you didn't say anything since we start the negotiation" a ransa yake cewa da alama mr denis ja'afar din baqo ne a wajensa,sai ya fara takawa zuwa inda suke zaunen,gab kuma da zai qarasa wayar ja'afar din ta dauki ruri kiran anni ya shigo. Da idanu kawai ya kalla wayar,sai da yaga sunan me kiran sannan ya miqa hannu a nutse ya dauka,ya kalli mr denis "Excuse me" ya fada da wata deep and husky voice,saidai kuma akwai taushi da laushi daya cika muryar. Shi ya fara yiwa annin sallama cikin ginshira da nutsuwa gami da wani irin kamun kai kamar mace,daga can sashen anni ta amsa tana sauke ajiyar zuciya "Anya?,anya babban mutum?" Anni ta fada tana nuni da yatsanta kamar yana gabanta "Barka da warhaka anni" yayi fatali da zancanta ya maye gurbinsa da gaisuwa "Barka kadai,kuna lafiya?" "Alhamdulillahi,fatan kowa yana lafiya" "Lafiyar dai da sauqi" anni ta fada zuciyarta fal kewa da kuma rashin dadi kan sauyawarsa "Subhanallah,wani abu ya faru ne?" Ya tambayeta yana gyara zamansa kadan gami da yamutsa fuskarsa,abinda yasa girarsa dake cike da gashi ta kusan hadewa waje daya "Mene ma bai faru ba ja'afar?,fisabilillahi.....yanzu ace haka rayuwa zata ci gaba da tafiya" qaramar ajiyar zuciya ya sauke,shi kansa yana damuwa,yana damuwa kan yadda ya kasa moving forward yadda ya kamata,yana damuwa kan damuwar da mutanen nan masu muhimmanci a rayuwarsa ke shiga damuwa saboda shi,yana damuwa da yadda kowa hankalinsa yake kansa,to amma ya zaiyi?,shaheeda ta daban ce,tayi masa wani mummunan tasiri me matuqar qarfi da kaifi a rayuwarsa "Aci gaba da tayamu da addu'a, everything will be okay in sha Allah" nannauyar ajiyar zuciya ta sauke "Addu'a kam ita aketa yi babu fashi,babu kuma kama hannun yaro.....sai yaushe ka shirya dawowa qasarka?" Ta jefa masa tambayar da shi kansa baisan amsarta ba,gani yake kamar bashi da wani sauran zama da zaiyi a qasar "Ban shiryama hakan ba anni,har yanzu da sauran lokaci" fuska tadan hade kadan "Kamar yaya ja'afar?,bakasan har yanzu zamanka a nan bashi da wani amfani ba?,idan kuma akwai ka gayamin"ta masa tambyar da salon titsiye,maimakon ya amsa mata sai ya sanya hannu saman kansa yana shafa lallausar sumarsa "Ina amna?" Kamar tace masa sai yanzu zai tuna da ita?,sai kuma ta bari,don a yanzun babu abinda take da buqata irin dawowarsa "Dazun maimunatu ta kaita wajen Aishatu" "okay.......aci gaba da yimin addu'a,ita nafi buqata,am little busy,zan kiraki anni" "Ja'afar!" Ta kirayeshi da kakkausar murya "Naam" "Ina jiran kiranka,akwai magana me muhimmanci da nakeso muyi dakai,ka tabbatar kome kakeyi ka kirani bayan ka kammalashi" kai ya jinjina,domin annin mutun ce me kima a idanunsa,ba kasafai yake mata kallon kaka ba,yafi mata kallon uwa "In sha Allah" daga haka suka yanke wayar,yana dan tunani cikin ransa wacce magana zasuyi da annin?,duk da jikinsa ya bashi tatsuniyar gizo dai ba zata wuce ta qoqi ba. Sanda yake qoqarin kiran ammansa yaji annin ta kirayi jabir,baisan me take ce masa ba,saidai jabir din ya tashi daga wajen ya fita yana amsa wayar annin. Saida amma ta sauke ajiyar zuciya sanda taga kiranja'afar din nata,abune me matuqar wuya ta daga waya ta kirayeshi,saboda zallar kara da yakana irin tata,zamantowarsa dan fari a wajenta,ta ajjiye rigar amna da take ninkewa wadda yarinyar ta cire yanzun ta dauki wayar. Kamar ko yaushe cikin girmamawa da qanqan da kai ya gaidata,ta amsa masa cikin nuna kulawa tare da tambayarsa jikinsa,wanda daga nan bata iya qara cewa komai ba,sai shine ya tambayi amna "Yanzun nan maimunatu tazo ta dauketa suka fita" "Okay amma" yayi mata sallama yana ajjiye wayar "Maimunatu,maimunatu dai?,wacece haka?" sai yaji ransa yadan sosu,don yaso jin muryar yarinyar,yayi matuqar kewarta har baisan iyaka ba,yanason yazo ko don ita,amma duk sanda ya ganta tana karya masa gwiwa ne,don tana tuna masa da mahaifiyarsa da kuma 'yar uwar tagwaitakarta. Last time da ya kira haka akace tana wajen maimunatu,har kusan sau uku yana kira amma ana sake gaya masa tana wajenta,abinda ba al'adarsa bace maimaita kiran waya,wacece ita din ma?,amsar da baisan ta ba,haka kawai yaji kansa ya dauki zafi,sai ya dubi mr denis "I heard everything you said,i need a time to think about what we discuss,i will contact you " kai mr denis ya kada masa,sannan ya bashi hannu sukayi musabaha,me denis ya tattare takardunsa ya masa sallama ya fice zuwa qofar gidan,inda PA dinsa ke zaune cikin mota yana jiransa. Zazzafar iska ya furzar daga bakinsa wadda ta fito hade da sassanyan qamshin alawa me taste din mint da baya rabo da ita,hannunsa a saman goshinsa yana murzawa a hankali,ya daga shanyayyun kyawawan idanunsa ya aza kan agogon dake manne a falon,wanda yake nuna lokaci daga qasa kuma kwanan wata. Duk rana irin ta yau rana ce da yake tafiya Istanbul ya kwana,washegari ya shiga ziyartar guraren tarihi da suka shafi annabawa da sahabbai,da wahala yayi missing ranar ba tare da yaje ba,abune me muhimmanci cikin rayuwarsa,yana daya daga cikin ababen tarihin da shaheeda ta barwa rayuwarsa,ita ta koya masa hakan,ita ta sanar dashi wanzuwar wajen,sai ya miqe da hanzarinsa dake nuna zallar lafiya da kuma cikar kuzari,ya dauki wayarsa da kuma agogon hannunsa dake saman table ya nufi dakinsa,dai dai lokaci jabir ya dawo falon,yabi hanyar da kallo,sai kawai ya rufa masa baya. Goye yarinyar take a bayan maimunatu,suna takowa. Ahankali daga sassan amma zuwa wajen anni,tun sanda ta fuskanci anni waya zatayi ta zame daga dakin,ta kuma fake da dauko amna,hakan tafi nutsuwa da hakan,ko babu komai annin zata sake tayi wayarta yadda ya kamata,tun annin tana qorafi harta saba,indai wannan ne halin maimunatu ne. Dariya yarinyar keta yi abinta,hankali kwancw tana jin dadin labarin da maimunatu ke bata. Kusan minti goma kenan da dawowarsa cikin gidan,amma bai shiga ciki ba,ya tsaya daga bakin motarsa yana amsa waya,hannunsa dauke da briefcase dinsa da kuma lab coat,harda qarin baqar leda. Siririyar muryarta dake cike da wani irin taushi ce ta ratso ta inda yake tsaye,abinda yaja hankalinsa kenan,ya daga kansa a hankali yana dubansu daga inda suke takowa. Sanye take da skert high waisted wanda ya kama qugunta ya kuma baje sosai daga qasa,sai wadatacciyar rigarsa me hannu wanda ya tsaya mata iya gwiwar hannunta,kanta lullube yake da mini hijab wanda shima ya taimaka wajen suturce jikinta,saidai kuma yayi matuqar haskata kasancewarsa peach color. Samun kansa yayi da binta da kallo,dan qaramin bakinta me siraran tausasan labba suna motsawa,tana da wani irin kyau me sanyi da fusgar hankali,tun ranar da ya fara ganinta ya tantance hakan,ta dauki hankalinsa ta kuma burge shi qwarai,duk da kasancewarsa mutum da ba kasafai mata ke burgeshi ba,bama shi kadai ba,kusan duk haka mazan gidansu suke,dalili da ya sanya ake musu kallon masu jin kai kenan "La la la,kika yarda kike goyata a bayanki saita karya miki baya?" Maganar haisam ya ratsa kunnenta sanda take shirin giftashi ba tare data kula da tsaiwarsa a wajen ba,hada idanu sukayi,ya bita da murmushi,sai tayi maza ta janye idanunta tana sakin wani qaramin murmushin ba tare da tace komai ba. Gyara tsaiwarsa yayi,yana maida wayarsa gaban aljihun rigarsa tare da sake cewa "Baki gani ta kusa kamoki a qiba?,amna bakisan yanzun kin girma ba,saura kadan ki cika 4years fa" kafada ta noqe tana buya bayan maimunatu sanda yake shirin karbarta,a dole ya haqura da amsar nata,maimunatu ta wuce da ita bayan ta gaidashi,ya amsa yana binta da kallo har sanda ta bacewa ganinsa. Cikin jikinta takejin wani iri a duk sanda haisam yake mata irin wannan kallon,batasan ma:anarsa ba,ba kuma tasan dalilinsa ba,ya mata shige da kallon da himunta yake mata,amma dai tana jin nauyi da kunya sosai. A dining area suka tadda khadim,shi ya karba amna daga wajenta,ta bashi ba don ta gaji ba,sai don khadim din shima mutumin amna ne na gaske,saidai tun bata isa dakin anni ba sai ga amnan ta sake biyota,ta kama hannuwanta tana dariyar meya hadota da khadim din taga ta bata rai,bata amsa mata ba suka wuce. A hankali anni ta ajjiye wayar gefanta tana fidda ajiyar zuciya,dai dai lokacin maimunatu ta shigo dakin,goye da amna a bayanta,kusan wannan al'adarta ce,mtuqar zasu tattaka zuwa wane waje kamar haka sai ta dauketa ta aza a bayanta,dukkaninsu fuskokinsu dauke suke da dariya,da alama wani labarin suke baiwa junansu. Idanun anni a kansu,wani abu ya darsu a ranta,kusan tafi kowa jin dadin qulluwar wannan kyakkyawar mu'amalar tsakanin amna da maimunatu,taci gaba da kallonsu a fakaice,farinciki ne shimfide saman fuskarsu,wanda abune da ba kasafai ake ganinsa akan fuskar amna ba,tun daga sanda ta rasa mahaifiyar da 'yar uwarta da suka kwanta ciki daya. Kwarin gwiwa gami da yaqini taji yana shigarta,zuciyarta na bata shawarar tunkarar maimunatu,gwara tun yanzun tasan da maganar,tana ganin kamar hakan zaifi dacewa,akan ta samu zanca lokaci daya,amma kuma idan ta aikata hakan maimunatu zata ci gaba da walwalarta da sakewa dasu yadda take a da?,babu gamsashen tabbaci akan hakan,abinda yasa hankalinta yafi karkata da barin maganar a cikinta,har zuwa sanda zata gama magana da ja'afar kan ainihin lokacin da zai dawo cikin ahalinsa. Ta baya jabir ke kallon ja'afar kadan kadan,cikin ransa yana juya maganar da suka fara yi da anni a kansa. Yana tsaye ne yana shirya kansa cikin wasu lafiyayyun suit saqar qasar Italy kamfanin kiton k-50 wine color masu dan haske kadan,agogon hannunsa gold color ne na companyn lange and sohne mai asalin tsada da kyau. Bayan ya feshe jikinsa da mayen tattausan turaren bad boy,ya zauna baya a hankali yana saka socks dinsa,sai a sannan jabir yayi magana,ganin cewa tunda ya shigo shi din bai ce masa komai ba "Ina zaka ne haka a wannan lokacin?" Sai daya daga kai ya dubeshi sannan ya sauke yana ci gaba da sanya safar "Ka manta yau wacce rana ce?" Dan tunani kadan jabir yayi sannan ya amsashi "Oh,yeah,amma kamata yayi ka jirani mu fita tare" "I finished bazan iya jiranka ba,saidai ka sameni a mint garden" "Alright,ba case" ya fada yana miqewa ya nufi toilet,shi daya ne keda wannan alfarmar a wajen ja'afar din,banda shi din yasan bazai tsaya jiransa ba. Kamar yadda yace din kuwa,ya cimmashi a mint garden cafe and bistro,saman table din shi daya ne,yana kurbar coffee din me zafi a hankali yana duban wani sashe na daban, joining dinsa jabir yin yayi,idanunsa kan fuskar ja'afar din kafin ya sauke cup din yana dubansa. "lokaci yayi fa,daya kamata ace ka sake ajjiye wasu family din da zasu zame maka makwafin wadanda ka rasa" tsaf ja'afar ya daga kai ya kalli jabir,tsahon wasu sakanni kamar bazai amsa ba kafin yace "Kai ka taba ganin inda GURBIN IDO ya zama idanu?" Tambayar data sanya jabir zuba masa idanu,yana hasashen irin dagar da za'a diba nan gaba kadan,shi da kansa ya qarashe amsar tambayar bayan ya miqe tsaye ya zuba hannayensa a aljihun wandonsa "Banajin har kawo yau an haifi macen da zata mayemin gurbin shaheeda,ita kadai ce,kuma ta tafi da dukkan abinda zai burgeni daga diya mace" daga haka ya fara takawa sannu a hankali. Tabbas jabir ya sani,ba abune mai sauqi ja'afar yaso wata diya mace ba,koda a nesa ne balle nan kusa,ko kafin shigowar shaheeda rayuwarsa,shi din ba irin mutanen nan ne da ake samun soyayyarsu da sauqi ba,bare kuma wannan babban al'amari yazo ya yiwa rayuwarsa karan tsaye. A wajen jiran jirgin qasa me tafiya da lantarki ya sameshi,tsaye yana kallon gefensa guda,hannunsa cikin aljihun wandon nasa,duk da yaji takunsa amma bai waiwayo ba,matsawa gaba kadan yayi ya daidaita tsahonsa da nashi,kusan kansu daya,amma ja'afar din ya darashi "Dole dole ja'afar ka dai daita rayuwarka zuwa yadda take a baya,koda komai bai dawo ba,shekaru uku ba wasa bane,kana tunanin shaheeda zataji dadin wannan halin da ka sanya kanka?,wanda ya mutu ya riga da ya mutu,bazai taba dawowa ba,indai bakayi qoqarin saita kanka ba tabbas nan da lokaci qalilan zaka ji sanarwa daura maka aure,confirm" wani kallo ya juyo ya watsawa jabir,daidai lokacin da jirgin ya tsaya,sai ya taka zuwa gaba sannan yace "Mafaashi" qaramin murmushi jabir din yayi,sannan yabi bayansa a hankali shima yana amsa masa "Zaka gani kuwa" 20 Sannu a hankali rayuwa ke juyawa,cikin wani yanayi me dadi ga maimunatu,dukkan wani ci gaba a hankali yake samunta,ta zama cikakkiyar diya ga Dr marwan,bai taba bari an banbantata cikin duka hidimar da zaiwa iyalinsa ba,bata da matsala da kowa kasancewarta yarinya me haquri kawaici da kuma sanyin hali,zallar biyayya da kuma girmama kowa koda na qasanta ne,wannan ya siya mata soyayya sosai daga wajen iyalin gidan dr marwan,saidai a rayuwa ba kowane zai soka ba,hakanan bazaiyiwu ace kowa gudunka yake ba,cikin surukai da kuna sauran jikokin anni ba za'a rasa wadanda suke mata wani kallo na daban ba,duk da babu wanda yasan daga ina fa fito,ko kuma ita din wacece. Babu abinda yafi mata dadi irin ilimin da take samu,batasan cewa a baya rayuwar da take rayuwa ce dake cike da zallar duhu ba sai yanzu,batasan haka ilimi yake da dadi ba sai yanzu,duk cikin abinda anni tayi mata babu abinda take jin ya mata dadi fiye da kima irin karatun da take,qoqarinta kan karatun ya ninka adadin karatun da ake mata,wannan ya sanya ake qara mata karatun da yawa,yake kuma mugun gudu,hakanan ta fannin boko,shi kansa malamin yakanyi mamaki idan yaga wasu guraren da yawa ta iyasu kafin suxo wajen,dole hakan kuma ta kasance,don kuwa duk sanda ta koma gida bita take sosai,tare da duba duk wani karatun da ya shafi wanda aka qara matan,koda yaushe baka rabata da dan qaramin dakin karatu dake gidan,wanda dr ya qirqireshi saboda yaran,su din kuma ba wani damuwa sukayi dashi ba,ba kasafai suke shiga,zuwan maimunatu da yawan shigarta wajen sai wajen ya soma rayuwa,a kullum zata tsaftaceshi,ta kuma bata lokaci a can tana nazari,daga fannin bokon har na addini. Zuwa lokacin maimunatun ta goge sosai,a hakan ma don ba ita din ba me yawan buri ko son qyale qyale bace,sau tari idan zasu shopping ko wani abu makamancin haka bata binsu,suyita mata tsiya da kazar gida,saidai ta bisu da murmushi,ta gwammace ta zauna da amna suyita labarai,tatsuniya da sauransu,ko ta tsefe kanta ta gyara mata tayi mata kitso ko kalba,ita kanta yarinyar tunda maimunatu ta fara kula mata da kanta ta daina yarda a kaita saloon,har yanzu tana nan a bufulatanarta,bata bari ta jirkita komai nata ba baya ga suturar jiki da kuma tsaftarta data qaru. ************K'arfe uku na azahar anni ta sanyata ta shirya don rakata gidan uncle abbas qani ga dr marwan,zata duba diyarsa da bata da lafiya ita da yaron da amaryarsa ke goyo,magana tayi da maimunatu kan ta shirya tayi mata rakiya ita da tabawa,babu musu ta shirya din,karo na biyu kenan da zata fita tun zuwanta gidan,fitar farko ma hisham ne ya debesu ya kaisu wani eatery sukaci abinci saboda qarin girma da ya samu a asibitinsu,shima tun suna shirin take kallonsu,duk da sun mata tayi amma tace a'ah,zata zauna da anni,kada a barta ita kadai. Har sun fita suka dawo sukace yaa hisham din yace ta fito suje "Kuje kawai ku dawo ina jiranku" "A'ah,tashi ki shirya kuje" anni tace da ita,a dole ta sauya kaya ta bisu. Kusan daga tafiyar har dawowar a takure take,saboda yadda yace ta zauna gaban mota,suna tafe kuma yana janta da hira da 'yar tsokana,abinda ya aza mata nauyi sosai,yasa ta dinga jin kunya ta kuma gagara sakewa har suka dawo. Bala'in nauyin hisham din takeji,saboda yadda yake mu'amalantarta ya banbanta da yadda sauran mutan gidan suke mu'amala da ita,yana da kirki sosai,yawan barkwanci musamman idan a cikin gida yake cikin family dinsa. Tsaf ta shirya cikin doguwar rigar atamfa,sabuwa ce,cikin dinkunan da anni tasa akayi mata,ta yane kanta da madaidaicin mayafi,dankwalin yana riqe a hannuta saboda rashin sabo da daurashi "Ma sha Allah"anni ta samu kanta da furtawa,saboda wani irin kyau da maimunatun tayi mata,tana ji a ranta ko a yanzu ja'afar ya dawo bai isa ya kushe maimunatu ba,don ta goge qwarai,ta tabbata ko a rugarsu yanzun sai sunyi mamaki idan suka ganta. Daga ita sai annin sai amna suka tafi,drivern gidan shike tuqa su,jifa jifa suna hira da anni,hankalinta kuma na sama hanya,tana sake ganin ainihin garin na gombe,tafiyar duka duka bata wuce minti talatin ba suka isa unguwar,unguwa ce itama me kyau dake dauke da gidan masu wadata. Maimunatu na dauke da amna suka fara takawa zuwa cikin gidan,jikokin annin uku suna biye da ita suna ta tsokanarta,saidai taqi kulasu,da alama a qule take dasu,saida sukazo qofar falon daya daga cikinsu tace "Anni,bari na cire miki takalman"ta fada tana dariya gami da duqawa "Ke arcan,kiyi ta kanki,ni ba take nake ba,gwandamar banza,wallahi ina tafe cikin gidan nan,duk saina bada sadakarku" ihu yammatan suka saki,namijin na musu dariya harda dafe ciki "Eh,ba zaku saka min 'ya'ya a gaba kuna cinye tattalin arziqinsu ba,kowa ya kama gabansa mazanku da matanku" tasa kai cikin falon abinta tana sakin sallama,yayin data barsu suna ihu da dariya na tsiyar data lafta musu. Karbar girma amaryar uncle abbas tayi musu,ta dinga nan nan da annin,da alama yar gaban goshinta ce,saida suka gama shafe wasu mintuna sannan dayar ta shigo,haj munubiya,uwar gidan uncle abbas. Da kallo anni ta bita kafin ta dauke kai tana amsa sallamarta,ta samu waje cikin jin izza ta soma gaida anni,saidai cikin girmamawa ne,sanin cewa annin bata daukar raini sam,daga nan ta zauna ana taba hira da ita lokaci lokaci. Karo na kusan biyar idanunta suka sake kaiwa kan maimunatu dake wasa da hannayen amna "Anni a ina aka samo mana bafulatana haka?" Waiwaya tayi ta dubi maimunatu sannan ta dawo da dubanta ga munubiya "Surukarku ce" "Matar wa kenan?" Dan qaramin murmushi annin ta sake "Ina fatima.....ke fadima" ta qwalawa daya daga cikin 'yammatan gidan kira ,dubanta tayi sanda ta qaraso "Dauketa ki kaita dakinku,daga nan ki duban idan hafsatun ta farka" "To anni" ta amsa da girmamawa,da alamu dukka cikin yaran ta fisu nutsuwa da hankali,waiwayawa tayi fuskarta dauke da murmushi ta cewa maimunatu ta taso. Tana gaba tana biye da ita,har zuwa sanda suka isa isa qofar wani daki,ta tura ta saka kai da sallama a bakinta maimunatun na biye da ita. Wata matashiya ce zaune saman gadon,ta jingina bayanta da fuskar gadon,sanye da wata doguwar riga cotton me yankakken hannu,kanta hula ce baqa da ta dan jata baya kadan,fuskarta babu alamun annuri,da alama itace mara lafiyan da annin taxo dubawa. "Ya hafsa,anni tazo dubaki,tace na duba naga idan kin tashi" fuska ta yatsine,murya kuma can qasa tace "Banga amfanin zuwa duba nin data yi ba,tunda ba zata iya maganta min komai ba" maganganun da maimunatu ta jisu wasu iri a kunnuwanta,har sai daa dan saci kallonta,wadda take qoqarin sake shigewa cikin bargo ta kuma kwanciya abinta "Ayyah yaa hafsa,wai me yasa kike irin wadan nan maganganun ne?" "Kinfi kowa sanin dalilin,ja'afar ne,ja'afar shine dalili" dubanta fatima tayi,sannan ta matso gefanta kadan ta zauna "Me yasa ba zaki haqura da yaa ja'afar ba yaa hafsa?" Idanu ta zubawa fatiman,tana kuma qanqanceshi,tsahon wasu sakanni sannan ta amsa mata da "Ashe baki da hankali fatima,hala bakisan meye ainihin haqiqanin ma'anar so ba ko?,ta yaya zan bar ja'afar?,kinsan yadda nake sonshi kuwa?,wait.....waye ma ya gaya miki ja'afar irin mutanen da ake iya haqura da soyayyarsu ne?" Kai fatima ta rausayar "Amma dai yaa hafsa,bake kadai cikin family kike da irin wannan qudurin ba,kuna da yawa,ke surayya hannah da walida,ga madina dama sauran wadanda basu bayyana ba,kunfi kowa sanin waye yaa ja'afar tun sanda yake lafiyarshi lau ma bare yanxu da kura tayi hauka,ke kinsan wayeshi,duk cikinku bana jin akwai wadda zata iya dashi idan aka barku,wannan dakatarwar da anni tayi muku ma kamar taimakonku tayi,ta kuma tsare muku mutunci da martabarku" "Ta barmu din yafimin,yafimin wannan kisan mummuqen......" "Don Allah ina bandaki?" Maimunatu ta katse musayar maganganun da suke a tsakaninsu,sai a sannan fatima ta waiwayo "Yi haquri don Allah,na barki a tsaye,gashi can" ta fada tana mata nuni da wata qofa dake kulle,takawa tayi a hankali ta nufi bandakin,saidai zuciyarta cike fal da mamakin maganganun hafsah,har yanzu dama akwai irin wannan soyayyar?,waye ne shi wanda takewa irin wannan soyayyar?,wannan tunanin ya tuna mata da himunta da kuma buderi,ko a wanne yanayi kowannensu yake ciki?,ta tabbatar himu yana can yana dakonta,yana kuma nege da shauqin ganinta,wanda kusan ita dinma tana jin hakan a ranta a kansa. Fitsari tayi sannan ta daura alwala,ta fito daga bandakin tana gyara rolling din mayafinta "Ba zaki gane ba fatima....na jima inason yaa ja'afar,ba zaki gane me nakeji ba a kansa" kalaman hafsa da suka sake shiga kunnuwanta kenan,ta dan kauda kanta tana jin kunya da mamakin yadda budurwar keta haqilo akan namiji,ta tayar da sallah abinta. Kafin ta idar sun gama maganar,wanda fatima ce ta sakar mata ganin ba zata fahimci abinda takeson nuna mata ba,a nan suka zauna suna taba hira ita da fatima,wanda dukka kusan akan islamiyya ce,da alama itama mayyar islamiyyar ce kamar yadda maimunatu take,kusan bata taba ganin fatima a gidansu ba,saboda yawanci tana islamiyya,ko a makarantar boko bangaren islamic take,abinda ya bawa maimunatu sha'awa sosai,har taji itama islamic take sha'awar yi inda zata samu dama,saidai ba zata iya buda baki ta yiwa anni ko dr maganar ba. Daya daga cikin yaran gidan ne ya leqo bayan sallar magariba,yace maimunatun tazo inji anni taci abinci zasu wuce gida,da hanzarinta ta tashi,abinda yasa fatima zolayarta "Dama kin gaji da gidan namu,da alama so kike dama a tafi" murmushi maimunatun ta sakar mata ba tare da tace komai ba "Allah yasa ki iya zuwa mana ma da bikin anty amira ki kwana" "Allah ya kaimu" ta amsa mata tana murmushi,sai fatiman ta taka mata zuwa falon da annin ke zaune. Tun kafin ta qaraso muryar mai kauri da zurfi take ratso inda suke,matashi ne mai cikar haiba da kamala zaune sosai gaban annin suna magan,da alama akwai sabo sosai a tsakaninsu,farin bafullatani sak,wanda yake diban kama ta sosai da haj munira. "Dole cikin satin nan kije,ko fatima saita rakaki,tunda kina jin dadin maganin bai kamata a fara fashi ba,zan kirashi na gaya masa sati daya zakuyi" ya qarashe maganar yana daga kansa,dai dai sanda idanuwansa suka sauka kan fuskar maimunatu dake takowa a hankali jere da fatima. Tamkar haduwar mayen qarfe da maganadisu haka yaji wani abu mai qarfi ya fusgeshi,duk yadda yaso ya dauke idanunsa daga kanta hakan ya gagara,harta qaraso ta soma gaidashi a darare tana lafewa daga gefan anni. Da mamaki fatima ke satar kallon yaa khalid din,shi da baya yiwa mace kallo uku amma yau gashi ya kafe idanunsa akan maimunatu?,sai daya fuskanci fatiman na kallonsa sannan yajanye idanun nasa ya kuma bata rai yana komawa ga batunsu shida annin,saidai lokaci lokaci yana satar kallon ta. Iya tafiya ta tafi dashi,duk da bata qarasa kalar macen da yakeson aure ba,amma fa hada komai da komai,special care kawai zata samu ta wasu bangarori ta yiwa mata fintikau. "Nidai bansan me kakeson maidani ba khalid,wannan jewar fa ta isheni,nidai a barni,ciwo ai ba mutuwa ba,idan lokaci kuma yayi dole na tafi" anni tayi statement din qarshe tana miqewa tsaye da zummar tafiya,bayan maimunatu taqi cin abincin da aka kawo mata,sam ba zata iya ba,tana jinta ne duk a daure saboda kallon data fuskanci saurayin yana ritsata dashi,wai shin kam haka samarin family dinsu suke ko kuwa su din su biyun daga garesu ne?. Shi ya musu tattaki har zuwa bakin motar da sunan yiwa anni rakiya,fiye da rabin hankalinsa yana kan maimunatun,duk da yana yine yana basarwa har motarsu ta daga. Yayi tunanin da sun yafi shikenan,saidai kuma kasa nutsuwa zuciyarsa tayi,har sai da yakai kansa gida dr marwan,ya kuma sakeyin ido biyu da.maimunatu,tun daga sannan abun ya zame masa kamar wani jarrabi,duk bayan kwana biyu daga office yake zartowa nan din,baya barin gidan sai bayan sallar isha'i. *********Karfe shida suka dawo daga islamiyya,tana sanye da babban hijabinta da ya saukar mata har qasan qafafunta,kalar blue black,abinda yasa yayi matuqar haskata tare da yi mata kyau,tana rungume da qur'aninta a qirji,laila na gefanta tana amsa waya. Suna sallama a falon sukayi idanu biyu dashi,qirjinta yayi mugun faduwa,taja da baya kamar zata koma sai kuma ta kasa,ganin ya ganta sarai,cikin zuciyarta bata son haduwarta dashi,saboda kallon da yake tsareta dashi da kuma sanyata cikin lamuransa da yawa,har fiye dasu laila da suke jininsa. A hankali ta biyo bayan laila kamar me tsoron wani abu zai iya kamata,tana jin laila na masa sannu da zuwa sai itama tabi sahunta,ta kuma sulale da niyyar wucewa dakinta,saidai ya tsayar da ita da tambayoyi kan karatunta,abinda ya bawa laila damar wucewa ta barsu su daya a wajen. Sallamar hisham daga bakin qofa ya ja hankalinsu duka,suka hada idanu da dukka su biyun,take fara'ar dake saman fuskarsa ta bace bat,ya fara shigowa falon cikin rashin walwala yana faman shan qamshi. Kowa a cikinsu cikakken matashi ne mai jin kansa,wanda ya hada komai da komai,musabaha sukayi da juna kowa yana dauke wuta,ba kamar yadda suka saba ba,har zuwa sannan kan maimunatu yana qasa,ta yiwa hisham sannu da zuwa,maimakon ya amsa,sai ya koma da baya ya zauna cikin daya daga cikin kujerun falon yana cewa "Je kitchen ki kawomin ruwa" a hankali ta tashi tana jin wani nauyi na raguwa daga cikin zuciyarta,zamanta a wajen tana jinta ne kamar cikin wani matsatstsen keji ne da babu sakewa. Shuru ne ya biyo baya a falon,hisham na danne danne a wayarsa,khalid kuma yana kallon news,kowanne da tunanin da yake a ransa game da dan uwansa,ba tun yau ba duka sun tsargu da juna,sun kuma fahimci mawuyaci ne idan basiu tarayya akan wani abu guda ba. Ruwan ta kawo masa hade da cup,ya dauki gorar ruwan yana cewa "Ba daga islamiyya kike ba?" Kai ta gyada masa "Bita ce ta kamaceki ba ki zauna kina surutun banza ba...wuce daki ki ajjiye qur'anin hannunki" cikin jin kai da isa khalid ya gyara zamansa sosai yana kuma dubansa kai tsaye "Dakata mana hisham?,wanne irin nonsense ne zaka same mu tare sannan kace ta wuce ciki?.... please kada ka shiga hurumin da ba naka ba" wani kallo hisham ya watsawa khalid sannan ya saki murmushi "Nonsense?......hmmmm,dani da kai za'a samu wanda ya dace a gayawa hakan,wuce maimunatu tun raina bai fara baci ba" "Ba zata wuce ba!" Khalid ya fada a tsawace,dai dai sanda anni ke qarasowa falon,ta bisu da kallo cikin mamakin yanayin data taras dasu. _To fa masu karatu,khalid dinne ko hisham?,ko kuma ja'afar?,waye zaiyi wining?,muje zuwa yanzu aka fara wasan_ 21 "Kai.....kai,meye hakan?" Anni ta dakatar dasu cikin tsawa,ganin zasu fara sa'insa a tsakaninsu "Ya zaizo ya samemu zaune,sannan kawai yace sai ta tashi ta shiga daki anni?,wannan wanne irin raini ne?" Khalid ya fada cikin jin ciwon abinda hisham yayi masa,yana jin ya disgashi abinda ba'a taba yi masa ba "Anni,dawowarta kenan daga makaranta,da alama ko ke bakisan ta dawo ba,don nace ta shiga ta ajjiye qur'aninta sai ya zama laifi?" Shuru ne ya biyo baya,anni tana nazartar kowannensu cikin sakannin da basu wuce biyar ba,sai taji hankalinta ya dan tashi,zata iya cewa bata taba ganin irin wannan sabanin ba a tsakanin jikokinta,wannan shine karon farko da hakan fa faru,duk da tasan dama tsakanin khalid da hisham ba jituwa bace can can,amma kuma basa cecekuce,tabbas ya kamata ta yuwa tufkar hanci da wurwuri "Wuce ciki maimunatu" anni ta bawa maimunatu dake daskare a wajen umarni,da hanzarinta kuwa qafafunta na rawa tayi ciki,kamar ta tashi sama haka takeji,har ta samu ta isa ga dakinta,ta tura qofar ta shige,ta zame a hankali a qasa ta zauna qafafunta suna rawa saboda tsabar tsoro,me ya kaisu fada a kanta?,shin wai basu duba kamanninsu da darajarsu ba da zasu tsaya suna fada a kanta?,kamar ita maimunatu?,wadda bata da komai?,bata kuma mallaki komai ba?,me yasa?,abinda ta dinga tambayar kanta kenan cikin mamaki da kuma tsoron abinda ya farun yanzu. "Ku zauna" anni ta fada musu itama tana lalubar wajen zaman "Ka zauna mana nace!" Anni ta fadawa khalid tsaye cikin matuqar bacin rai a tsawace. Sun kusa minti biyu shuru kowanne anni tana karantar fuskarsa,kafin daga bisani ta kirayi sunan kowa a cikinsu "Me idanuna suke gani?" Ta jefa musu tambayar da ba wanda ya shirya amsa mata,sai cin d'aci da kowannensu yakeyi "Tun ina raye hakan zata fara faruwa ina ga ace qasa ta lullube idanuna?......to in sha Allahu wannan abun ba dai cikin ahalina da zuria'ta ba,haihata haihata,bazan lamunta ba kuji da kyau,na meye zaku dinga sa'insa akan maimunatu?,to dukkaninku ku dauketa a matsayin qanwarku,banason kowa ya sanya wani abu a ransa bayan wannan.......kuma inaso a yanzu yanzu ku baiwa junanku haquri" "In sha Allah" kowa ya fada a cikinsu saidai murya ciki ciki,hisham ne ya fara bawa khalid din haquri,tunda ya girme masa da watanni kusan shida,shima khalid din ya maida masa,sannan khalid din ya miqe hannayensa zube a aljihunsa yana shaidawa anni zai tafi "Aiba yanzu k saba tafiya ba,ko don na muku fada?" Kai ya girgiza yana duban agogonsa "A'ah,dama da wuri naso na koma yau din,ina da abinda zanyi" tabe baki anni tayi "Oho maka.....a sauka lafiya" qaramin murmushi ya sake ya juya yana ficewa daga falon,qasan ransa yana juya maganar anni da tace su dauketa matsayin qanwa kawai,shikam.dai Allah ya sani ya gani yana so,zai kuma yi duk iyakar bakin qoqarinsa,zai kuma fafata da kowa don ganin ya samu maimunatu,bawai ya haqura bane. Sun fita sun bar anni ne da dogon nazari da tunani,tana tsoron kada abubuwa suzo su kwabe ba kamar yadda take shiryawa ba,tana hangen al'amura masu nauyi a idanun kowannensu tsakanin hisham din da khalid,wannan tunanin ya sanyata daga waya ta laluba number dr marwan,ta shaida masa idan ya shigo gida da wuri a yau tana son ganinsa,idan kuma bai shigo akan kari ba gobe da sassafe ya nemeta kafin ya fita ya amsa mata da to,saita maida akalar kiran nata zuwa number jabir. "Me kuke har yanzu a qasar nan ne jabiru?" Ta tambayeshi kai tsaye ba tare data tsaya bi takan tambayarsa,sumarsa yaci gaba da tsanewa da towel "For now dai ni na gama duk schedule din da nake nasu a turkey,matsalar tana ga mutuminki,sam bashi da sha'awa ko nufin tahowa" gyara zamanta anni tayi sosai "Nan da yaushe kake ganin harshi xai iya dawowa gida?" "Karshen watan nan nan da 2weeks kenan komai nasa zai kammala" "To ka shaida mana,lalai dakai da shi din ina da buqatar dawowarku qasarku zuwa farkin sabon wata......kai kaga ma,hadani dashi a waya" "Okay, hold on karki kashe" yayi maganar yana maqale da wayar,gami da ajjiye wandon hannunsa da yake da niyyar sanyawa ya fita a dakin. Kofar dakinsa da sassanyar qamshin turarukansa suka kamashi ya tura,luf luf dakin yake,saidai bashi a nan,ya kalli a gogo,lokacin da yake shiga gym ne,tabbas yana can,don haka ya juya da 'yar sassarfa yayi can. Sanye yake da farin wando qal me ratsin green daga gefe da gefansa,iyakar wandon wasan gwiwarsa,hakan ya sanya sambala sambalan qafafunsa dake cike da gargasa suka bayyana,sai rigar kayan armless shirt,yana tsaye daga bakin window,hannunsa riqe da qaramin towel yana goge zufar jikinsa,idanunsa kuma na ga waje. Duk da yaji sautin bude qofar amma bai juyo ba,haka ya sanya jabir din takowa ya iskeshi a wajen da yake tsayen "Anni na magana" ya fadi masa a taqaice,kamar bazai motsa ba,sai kuma ya cilla towel din gefe yana juyowa duk da har yanzu idanuwansa naga wajen "Duk randa mutanen can suka shiga gonata zasu gane shayi ruwa ne" ya fada fuskarsa na nuna alamu na bacin rai,wajen jabir yakai idanunsa,wasu 'yan asalin turkey dinne,baisan me yasa mutanen suke da jin kansu da alfaharin su turkawa bane,ba yau ba sun saba wulaqanta baqar fata kamar yadda yanzun sukewa wasu,duk da laifinsu ne,yawanci suke zubar da kansu "Kar ka fara,ka rufa mana asiri,a qasarsu kake fa?" "And so what" ya fada cikin nuna halin ko inkula,kana ya miqa hannu ya zame wayar daga kunnen jabir ya maidata kunnensa,yana qara taku zuwa gaba gami da gaida anni. Waje ya samu ya zauna bayan ya gama jin dukka bayananta,yatsunsa ya nutsa cikin lallausan gashin kansa,baisan me zai gayawa anni ta fahimta ba,kamar yadda ya rasa gane taqamaimen dalilinta na birkice masa,tare da bashi umarnin tahowa gida next month,bayan kuma shi bai shirya hakan ba,banda amna ma,baya tunanin xai koma nan kusa "Zan duba,zanyi qoqarin zuwa" wannan itace amsar daya bata. Sanda anni ta ajjiye wayar saita qwalawa tabawa kira "Ina maimunatu ne?" "Tana dakin karatu,kinsan lokacin karatunta ne yanzu,kin santa kuma da himma" murmushi anni tayi,ita kanta tasan yarinyar daban take cikin dukka yara data sani,ba sawa ba fitarwa ba,babu hayaniya hakanan babu hargowa,uwa uba bata dauki rayuwarta da zafi ba,har cikin ranta kullum kwanan duniya tana jin nutsuwa da kuma gamsuwar hadin da take shirin yi da yarinyar "Kiramin ita tabawa,wannan maganar ce ta taso,inajin lokaci yayi da zata san da zaman maganar,saboda ta sama zuciyarta tun kafin qarasowarsa,bawai sai daga bisani taji maganar sama taka ba,uwa uba ina hango wutar rikici dakeson ruruwa,gwara na yima tufkar hanci" kai tabawa ta gyada "Gaskiya ne wannan haj anni,ubangiji ya tabbatar mana da alkhairi,yasa komai yazo mana cikin nasara da sa'a,ya kuma sanya qarshen abun ne yazo" cikin jin dadin addu'o'in tabawa anni ta amsa "Ameen,ameen ya hayyu ya qayyumu tabawa" daga haka tabawan ta juya ta fice. Sosai yau din takejin dadin karatun,hakanan Allah ya sallada mata qaunar hadith,dalilin da yasa zaiyi wuya ayi musu qarin hadith bata haddace su ba,kamar yau din,saura guda biyu ta gama haddar qarin da akayi musu jiya juma'a tabawa ta turo qofar tare da sallama ta shigo. Qaramin murmushi ya wanzu saman fuska da siraran labban maimunatun,ta rufe hadith din tana duban tabawa "Yau ban shigo kitchen ba ko?,karatu ne ya tsaidani amma na kusa kammalawa" murmushi itama tabawan ta maida mata,maimunatu nada saurin shiga rai saboda sauqi da dadin mu'amalarta "A'ah muna,bansan me yasa kike takura kanki ba wajen zuwa kitchen kullum" "Bana takura baaba tabawa,inajin dadin zuwan sosai,na qaru da kalolin girke girken da bansan ana yinsu ba,ina kan qaruwa ma,hakan yana min dadi" "Gaskiya ne" tabawa ta amsata tana murmushi,don ita shaida ce,tuquru maimunatun ke maida hankali tana koyar duk wani girki da tazo ta samu zasuyi,daga inda taga anyi sau daya a gabanta to tabbas ta haddaceshi kenan,idan ta maimaita irinsan kuwa zakayi mamakin yadda ya bada ma'ana,kamar wadda ta jima tanayi. "Yanzun ma anni ce take kiranki" "Tom,gani nan zuwa" tace da baba tabawan tana qoqarin ajjiye Hadith dinta a take,ta kuma miqe tabi bayan baba tabawa,suna dan zancan islamiyyarsu,har zuwa sanda suka isa qofar dakin annin "Tana ciki,zan koma kitchen mu qarasa hada abinci,don yau anan Alhj Dr(haka tun da baba tabawa take kiran dr marwan) zaici abincin dare" "Idan na fito zan sameki a can saimu qarasa in sha Allah" ta fada saboda gwada kyautatawarta akansu itama komai qanqantarsa "To ba laifi" ta amsa mata tana komawa zuwa hanyar kitchen,ita kuma ta tura dakin anni ta shiga,bakinta dauke da sallama. ,kamar ko yaushe,cikin nuna matuqar kulawa ta amsa mata tana gyara zamanta "Kinga miqon wancar jakar kafin ki zauna" anni tace da ita tana mata nuni da wata jaka dake gefan gadon,miqa matan tayi sannan ta zauna tana fuskantar annin. Zuge jakar anni tayi,ta fiddo wani abu,sannan ta daga kai tana duban maimunatu tana sakin qaramin murmushi "Yau hira zamuyi dake" murmushin nan nata dake nuni da nutsuwarta gami da kamun kai ta sakewa anni "So nake naji samari nawa kika taba yi maimunatu,sannan a cikinsu wa kikafi so?,inaso kuma naji har yanzu kina sonsa?" Sosai maganar anni tayi mata nauyi fiye da zaton ita annin,taji kamar qasa fa tsage ta shige ciki,ta yaya zata fara irin wannan hirar da anni?,bayan ko dasu laila ba zata iya wannan maganar ba?. "Uhmmm,ina jinki,ki bude baki ki gayan" sake daureta kunyar annin tayi,sai kawai ta hau kada kai a hankali,dan bata fuska tayi "Kina nufin ba kowa?" Da sauri ta daga kai alamun eh,sai annin ta motsa tana ajewa maimunatu hoto a gabanta "To ga jikana,zaki iya aurensa?" Kasa daga kanta tayi bare ta kalli hoton,tanajin kamar ta kulle idonta ta bude taga bata a gaban anni,kayan kunyar yayi yawa "Da gaske nake miki maimunatu,zaki auri ja'afar?" Wannan karon sautin muryar annin ya fito da wani irin amo dake nuna babu wasa cikin maganganunta,abinda ya sanya maimunatu cira kai,a maimakon ta kalli hoton sai ta kalli anni,suna hada ido ta jinjina mata kai "Inaso ki taimaki rayuwar ja'afar,ki aureshi,inajin qamshin alkhairi a tattare dake,bansan me yasa zuciyata take gayamin ke zaki fitar dashi ba" a nutse ta zayyanawa maimunatu waye ja'afar,ta koma dora da "Kiyimin wannan alfarmar maimunatu,bansan me Allah yake nufi ba da yasa nakejin ke zaki iya....." "Kiyi duk abinda ya dace dani anni,don Allah basai kince neman alfarma kike daga gareni ba" maimunatu ta fada,dukka jiki da muryarta suna rawa. Kai anni ta girgiza tana kallonta a nutse "Aiba baiwa bace ce,'ya ce ke kamar kowa,don haka ya zama dole a nema daga wajenki cikin baki cikakken 'yancin yin zabin eh ko a'ah,kije kiyi tunani maimunatu,na baki dama,idan har kikaji baki gamsu ba,ko ba zaki iya wannan alfarmar ba,kada kiji komai,ki gayamin kanki tsaye,ni kuma nayi miki alqawari har tsakanina da ubangiji na,zamu ci gaba da riqonki ba tare da komai ya sauya ba.....tashi kije" kasa cewa komai tayi,ta miqe cikin wani irin yanayi data gaza fassarashi,kamar anbi kowacce gaba ta jikinta an zare sinadarin dake bata kuzari,komai na jikinta yayi sanyi qalau,maimakon ta wuce study room ko kitchen kamar yadda ta tsara yi,saita wuce dakinta kawai,ta tura qofa ta kuma haye gado. Inda batasan wace anni ba da sai tace wasa take mata,ja'afar dai da takejin sunansa a bakunan al'umar gidan nan?,koda batasan fuskarsa ba amma mutum ne da kowa ke ganin girma da kimarsa,kamar ita?maimunatu?,bafullatanar ruga 'yar qauye?,ta yaya zatayi kan kan kan da mutumin da take da tabbacin a yanzu ma baya qasar nijeria?,ta yaya zata iya wanke wannan babban tabon daya nannade rayuwarsa?,kai tana ganin a rayuwar gida irin ta dr marwan,koda drivern gidansu darajane dashi,koda drivern gidan ya fita daban da sauran drebobi,koda shi aka ce ya aureta tana ganin kamar ya zarce mata,bare ace dan gida,dan gidan ma irin ja'afar dan gata ta kowacce fuska,anya kuwa zata iya?,idan ba zata iya din ba kuma zata iya kallon anni tace mata A'AH?,.....kalmar tayi nauyi da kuma muni da yawa,anni mutum ce guda har da rabi,wadda 'yantata ta kuma maidata cikakkiyar mutum. Ire iren wadan nan tunanukan su sukaci gaba da kassara maimunatu,suka kuma cika mata kwanya taf,ta rasa yadda zata sarrafasu su dace da hange da kuma fikirarta. Ajiyar zuciya anni ta sauke bayan fitar maimunatu,fatanta daya komai ya daidaita,komai yazo da sauqi,don muddin maimunatu ta amince,to fa babu daga qafar da zata yiwa ja'afar har sai ta tabbatar komai ya kammala,wannan shine buri da kuma fatarta. Wannan magana da sukayi da anni sai ta zamewa maimunatu kamar wani dabaibayi,dukka kuzari karsashi da walwalarta suka yi qaura sosai,duk da dama ita din miskila ce,wadda bata damu da hira ko hayaniya ba,tafi ganewa karatu,to shima karatun a dan tsukin nema yake ya gagareta,idan ta buda littafin sai ta tafi duniyar tunani,sai ta kasa qulla komai har ta gama zamanta ta tashi. A wani yammaci ne,tana dakin karatun dauke da qur'aninta tana tilawa,saidai can tsakiyar karatun nata tunanin da ya zame mata jiki ya kutso mata kai,sai taci gaba da riqon qur'anin kawai ba tare data iya ci gaba da karatun ba. A wannan lokacin baba tabawa ta shigo dakin,hannunta dauke da cup data cikashi da kunun gyada fari sol sai maiqo da qamshi gyada da yakeyi,daya daga cikin cimar da maimunatun keso kenan,tayi firgigit tana amsa sallamar baaba tabawa.gami da gyara riqon alqur'aninta,sai baba tabawan ta sakar mata murmushi tana miqa mata cup din,sannan ta zauna saman kujerar dake fuskantar maimunatu "Na lura kwana biyu kin zama wata aba,don wannan kunun qilan saidao a zubda ba tare da kinzo kin dauka ba" dan murmushi tayi tana juya spoon din dake cikin kunun,cikin ranta tana ayyana yadda mutanen birni ke kashewa ciki kudi,suci wannan suci wancan "Shawara nazo baki muna,don banaso kiyi asara har irin wannan a rayuwarki" daga kai maimunatu tayi ta dubeta cikin rashin fahimta,idanun baba tabawa cikin nata ta gyada kai tana tabbatar mata da duk abinda zata ji "Maimunatu,tun zuwanki gidan nan naji kin kwantain,ina kuma qaunarki,maimunatu,naji na kuma san abinda ya sanyaki kika canza gaba daya,ba zancan ja'afar ba?" Tayi zancan da sigar tambaya,saita sad dakai,wato kowa ya sani kenan?,ya kuma fahimta?. "Duk yadda zakiyi kada ki bari ja'afar ya subuce miki,duk yadda zakiyi kada ki soma wauta ko gangancin cewa baki sonshi,ja'afar yana cikin dai daikun mazan dake da wuyar samu duk da wahalar sha'aninsu,samunsa kuma sai mace mai matuqar sa'a kuma 'yar baiwa,bawai don yana da kyau da kudi ba,a'ah.....yana da wata irin nagarta da kuma kebantattun kyawawan halayen da ba kowa bane ya sansu,ba shakka kowacce mace da tasan abinda takeyi zata yiwa wadda take so ko qauna fatan kasancewa da shi a mazaunin miji.....maimunatu,a shawarce.....ki aminta da maganar hajiya anni,ina mai baki tabbacin ja'afar gaba yake da nagartaccen miji idan ma akwai" shuru maimunatu tayi tana jujjuya maganganun tabawa cikin zuciyarta,tana ganin matsayinta baikai inda anni keson kaita ba sam "Akwai abinda kike tsoro ne?" Tabawa ta tambayeta kai tsaye,a wannan karon batayi nauyin baki ba "Bansan waye ubana ba,bafullatanar ruga nake,har na isa na hada kafada da zuri'ar anni?" Murmushi tabawa tayi "Zallar karamci irin na hajiya anni babu abinda ba zaki gani ba,sa'annan ke din halastacciyar 'ya ce,babu abinda ya nuna baki da.uba ne,ke koda haka ne,ina me tabbatar miki tunda hajiya anni tayu niyyar aiwatar da hakan,babu abinda zai dakatar da ita,ba kowanne mutum ke ganin baiwar da Allah yayi masa ba,kamar ke din,kina da wasu kebantatattun halaye da siffofi dani kaina nake saka ran akwai alkhairi me yawa a tare dake" shuru maimunatu ta sakeyi,tambayar qarshe kuma wadda take ta cin ranta "Shi ya santa ne?,yana kuma sonta" maganar data fito sarari,sai murmushi kawai taga tabawa tayi "Muna.....ke din ta musamman ce,hakazalika kina da tarin baiwar da namiji bai isa ya kalleki yace baiso ba,saidai idan wani abun daban kuma ba wannan ba" tabawa tayi matuqar sanyata cikin nazari,tana jin kokwanto tana kuma jin qwarin gwiwa,wanne zata rinjayar?. "Anni ta damu qwarai,kin amince a shaida mata ko zata samu nutsuwa" 22 Bata da wani sauran zabi,sai ta samu kanta da gyadawa tabawa kai. Unexpected wata guda ta ratsa kunnuwa zuwa kwanyar maimunatu,ta rintse idanunta tana jin wani abu na mata yawo,wanda yake cakude da zallar fargaba da kuma kokwanto. "Alhmdlh alhmdlh alhmdlh" shine abinda anni ta dinga maimatawa fuskarta kamar wata dam daren sha hudu,bakinta yagaza rufuwa,hakanan Allah ya sanya mata qaunar maimunatu da kuma tausayinta a ranta. A haka maimunatu taci gaba da rayuwa,cikin kunya nauyi da kuma fargabar al'amarin dake tunkararta,saidai kuma ta sake maida hankalinta ga karatunta,wanda a yanzu ta sake maida hankalinta dari bisa dari a kai,ranta da zuciyarta na gaya mata idan tayi aure shikenan,ta rabu da karatunta,tunda abinda ta taso kenan ta gani,matan aure kowacce tana gidanta a zaune,zuwa makaranta na 'yammata ne. Saidai a kullum tana tambayar kanta ta yaya lamarin yazo kamar mafarki?,yaya kuma zaici gaba da kasancewa?. **********Duk yadda yaso ya taushi zuciyarsa ya taho nigeria abun ya faskara,haka kawai yakejin baison zuwa din ko kadan,akwao memories masu tarin yawa da ya binne wanda baison tunosu,ko sau daya zuciyarsa bata sassauta daga tunani da kuma kewar shaheeda ba,wanda cikin jikinsa yakejin da wannan ciwon zai qarasa rayuwarsa ya kuma mutu shima,mutuwar da inda zabi take bayarwa shi zaice ta dauka ba shaheeda ba,koda kuwa ta dauketa zai zabi ya bita shima. Duk wata hanya da jabiru yake jin zaibi ya shawo kan ja'afar abun ya faskara,hakanan itama annin tabi duk hanyar da ya kamata ta lallashi amma abinda take son bai samu ba,ranta ya fara baci,don haka a wani dare ta nema ganin dr marwan *_08:pm Dr marwan khalid akko residence_* Dr marwan ne zaune gaban anni,sanye da wata jallabiyya ta matsa ruwan hanta saqar qasar oman mai budadden hannu,an qawata gabanta da adon zare ruwan madara mai turuwa kadan,fuskarsa na dauke da wani annuri na zallar nutsuwa ilimi gami da samun cikakken hutu da kwanciyar hankali,yana da cikar haiba kwarjini da kuma kamala sosai a fuskar tasa da wani bangare nata ya fara samar da furfura. Ya miqa hankalinsa matuqa zuwa ga mahaifiyarsa "Kaji duka irin abubuwan dake faruwa,banyi tsammanin abun na ja'afar yakai har can ba,ina ganin ya kusa fin qarfinmu dai" da hanzari dr marwan ya girgixa kai "Kiyi haquri ki daina fadin haka,bai isa ba wallahi,koda bana raye koda aishatu bata raye,bare gaba dayanmu da ranmu.....bai isa ba don ubansa,banda wancan matsalar ma harda iya shege na fuskanta ciki lamarin nasa,ai mu muka haifeshi bashi ne ya haifemu ba,ya zubda komai da kowa nasa saboda mutuwar matarsa da diyarsa kawai?,zan nuna masa mu muka haifeshi kam tabbas,karki sake bi ta kansa anni don Allah,abinda za'ayi shine.....ki shirya ki kuma saka lokaci zuwa adamawa gurin magabatan maimunatu cikin satin nan,ni kuma zanyi magana da honorable commissioner ya tsaida randa za'a kai kudin auren tasa diyar" hakan ya yiwa anni dadi qwarai da gaske,ta dinga sanyawa dr marwan albarka,yana da tsananin biyayya,abinda yasa a kullum yake sake shiga ranta. Shiri ta fara yi gadan gadan na tafiyarsu adamawa,sanda ta shaidawa maimunatu wani dadi taji ya tsarga mata,amma kuma wani sashe na zuciyarta sai taji tana tsoro da fargabar wacce tarba zata samu daga wajen innar laulo dama gaaje?,dama kuma bata da wata fargaba akan jauro,duk inda mutumin kirki yakai yakai nan. Saura kwanaki biyu su wuce da wani yammaci anni ta kirata,tace taje aishatu tace a turota ta kama mata aiki,haqiqa tana matuqar jin kunya da nauyin matar,tunda tasan itace mahaifiyar ja'afar,duk da cewa wata magana data shafeshi bata taba hadasu ba. Atamfa ce a jikinta doguwar riga,sai ta zura hijab din da bata jima da cireshi daga jikinta ba saboda sallar data idar,ta zura wasu slippers dinta ta nufi sashen amma,tana tafiya a hankali tana shaqar iskar yammacin,duk bata jin dadin gidan saboda dauke amna da dangin mamanta sukayi,sun roqi alfarmar a basu ita akwai bikin da ya taso zasuyi can dangin mahaifiyar shahidan,dr yace a basu. Gab da zata shiga sassan ta gamu da ammi,kishiyar amma tana fitowa ita da khadim,bisa dukkan alamu unguwa zata je Cikin girmamawa ta gaidata,tadan tsokani khadim kadan sannan tayi musu a dawo lafiya ta wuce ciki. Masu aikinta biyu ta samu a falon suna kai kawo,kowa da abinda yakeyi,ta gaidasu kamad yadda ta saba,daya daga cikinsu tace "Tana kitchen" saita miqe zuwa hanyar da zata sadata da kitchen din. Kamar kowanne lokaci,a duk sanda maimunatun tayi magana ko tayi sallama sai taji kamar tasan muryar,yau ma da sauri ta juyo,sai taga maimunatun ce,ta sakar mata murmushi tana fadin "Shigo ciki" kanta a qasa take takowa,tana mamakin yadda amma ga daukaki gayu,da wahala ka sameta ba cikin kwalliya ba,wannan ya zame mata jiki,kamar yanzun da take sanye da atamfa dark blue da yarfin baqi da kuma fari a jiki,jikinta yana fidda ni'imataccen qamshi,gashinta yananan da tsahonsa da kyansa,duk da girma daya fara nunawa. "Matso ki tayani hada wannan dambun,babanku keso,sai daya taho hanya kuma yayi magana" amma ta fada tana murmushi,saita amsa da to,ta janye hannayen hijabin nata zuwa baya sosai sannan ta ja zogalen dake cike da kwando ta fara gyarawa. Da fari shuru kitchen din yayi,sai qarar kayan amfani,amman ce ta katse shirun da cewa "Inafata baki takura ba ko da maganar auren ja'afar?" Amma ta fada a tausashe,tana son ta bincika ta dabara ta tabbatar babu wata matsala,kunya ce ta bijirowa maimunatu,ta duqar da kanta hannunta ya fara dan rawa saboda hakan,amma ta fuskanci haka,ranta ya sake fari,don dama halaye da dabi'un maimunatu ba baqinta bane,tanason yin maganar daga ita sai maimunatun tun a wancan lokacin da dr ya shaida mata komai,to sai yau ta samu wannan damar,ta umarci masu aikinta duka su fice,don tana kunyar su jita tana maganar da maimunatun,kamar yadda tayi imanin itama yarinyar ba zata sake ba "Sai kinyi haquri da ja'afar,zuciyarsa nada tsananin so,tun yana qaraminsa,idan yaso abu yana masa wahala sanda zai barshi,saboda ba qaramin so yake masa ba,hakanan idan yaqi jinin abu,akwai mata da yawa da muka saka rai a kansu kan zasu kawo canji ga rayuwarsa,saidai babu wanda mukaci nasara,ko a yanzunma zuciyata da jikina duka sunfi bani hope a kanki maimunatu,don Allah kiyi haqurin zama da ja'afar,don Allah,kada rayuwarsa ta tabarbare a rasa kuma sauran me zama dashi" sosai wani tausayin amma ya kamata,ashe itama abun yana damunta har haka,amma kunya da kawaici suka sanya bata nunawa?,a sanyaye a kuma kunyace ta gyadawa amman kai. Tare suka dinga aikin,amma.tana qoqarin sanyata sakewa da ita,cikin hikima ta dinga nuna mata itama kamar mahaifiya take a wajenta,ta dauketa kamar hakan. Sanda suka gama aikin gift amma ta bawa maimunatu na set din kayan wanka,cream,shower gel, perfume,body spray,hair mist da sponge a ciki,kallo daya tayi musu ta tabbatar masu shegen tsada ne,don qamshin da suke fitarwa ma na daban ne,don haka ta ajjiyesu,batason fara amfani dasu bare zuciyarta ta zarme. Sanda ta isa qofar sassan anni taji hayaniyar mutane,taji muryoyin wasu daga cikin yaranta maza,tabbas sune,don dazu da safe taji suna magana da umar kan zuwansu gidan commissioner,don haka taja da baya ta koma can bayan gidan tayi zamanta,don yau gidan duka basanan,sun tafi gidan babbar 'yar amma,wadda taci sunan anni,saboda yau din suke dawowa daga tafiyar da sukayi ita da mijin nata har na tsahon shekara uku,sai yau suka dawo,yau dinma babu yadda basuyi ta bisu ba tace aah,zataje watarana,haka suka tafi suka barta. **********K'arfe uku da wasu mintuna akai suka sauka a adamawa,motarsu kuma ta kutsa kai cikin rugar ummaru a hankali tana keta burtali da kuma hanyoyin da mazauna rugar ke amfani dasu. Watannin da suke shude sun zamarwa maimunatu wasu sababbin shafukan rayuwa ne a gareta,cuke da tarin sauyi wanda yayi wancakali da qalubale wahala bauta da kuma azabtarwa data fuskanta a baya na tsahon wasu shekaru,ware idanu maimunatu tayi,tana kallon duk wani bigire daya zame wajen kiwo ko wucewa a wajenta,kewa sosai ta cikata,ta dinga tuno mummuna rayuwar mai cike da jahilci da kuma wahala,a yanzun da take ganin muhallan da hakan ya faru da ita,sai take ganin kamar mafarki. Duk inda motarsu ta keta sai ta kwashi idanu,saboda abu ne da ba kasafai suke ganinsa cikin rugar tasu ba,basu tsaya ko ina ba sai qofar gidan yuuma ramatu. Fa'iza da khadim wannan karon sune 'yan rakiyar,kusan sunfi kowa son tafiya muhallin daba nasu ba ba kuma su sanshi ba,sune a gaba janye da akwatin kayansu,maimunatu na biye dasu anni a bayansu. Cikin wani hanzari yuuma ramatu ta fito daga dakinta bayan bankade labule data yi,wani irin farinciki mara misaltuwa ne ya saukar mata,a wannan karon maimunatu ta fara rungumewa cikin matuqar farinciki tana cewa "Miyatti Allah,miyatti annabi,maimunatu?,kece haka?" Murmushi maimunatun ta sake cike da kunya,yuuma kuwa baki ta saka cike da mamaki tana kallonta "Kinga ta canza miki kenan ramatu" anni ta fada tana 'yar dariya "Ba kadan ba kuwa yafendo" yuuma ta amsawa anni tana maida dubanta kanta,sai a sannan ta marabcesu gami da yi musu jangora zuwa dakinta,bakinta har kunne,ta rasa inda zata sakasu. Bata zauna ba tahau dora musu abinci na musamman kamar yadda ta saba,duk yadda yuuma taso maimunatu tayi zamanta amma ta qiya,tare suka dinga shirya komai,suna aikin suna hira,yuuma tana tambayarta labarin rayuwa a can,bata boyewa yuuma komai ba,ta yabi anni ainun kan irin tarin karamcinta da yadda ta sauya mata rayuwa "Indai yafendo ce,bakiga komai ba,a jininta yake,dabi'arta ce" jinjina kai maimunatu tayi,tana sake gasgata zancan yuuma. Tunda suka fara aikin take satar kallon qofar dakin daada dake a rufe,bata ji motsinta ba bata kuma ganta ba daga ita har yaran,cikin ranta take tunanin inda suke,daga bisani taji yuuma na gayawa anni suna ta tafi maqotan rugarsu,qanwarta Ayaana ce ta haihu,sun tafi duka ita da yaran,cikin ranta take tambayar shi kuma ibrahim fa?,ba zata iya tambayar yuuma ba,abun ma baiyi tsari ba,tunda tasan ainihin dalilin ma daya kawosu garin,wanda tabbatuwarsa zai sake nisantan tsakaninta da ibrahim din har abada. Gefin magriba suka gama komai,maimunatu na saman abun sallah,ta idar kenan saiga sallamar daadan ita da iyalinta,cikin murna da zumudi ta zarto dakin yuuma,don ta sani tabbas zuwan anni alheri ne,bata zuwa haka hannu babu komai. A girmame ta gaidata,fa'iza da khadim da sukayi zaman cin tuwo suma suka gaidata,sai maimunatu ta waiwaya kadan itama ta soma gaidata. Dan jim tayi na sakanni saboda ji da tayi kamar tasan muryar,amma canzawa maimunatu da kuma rashin wadatar haske a dakin ya sanya bata gane wacece ba,har sai da zubaida ta ankarar da ita "Daada fa kamar maimunatu na gani a tare dasu" harara ta balla mata "Maimunatun da aka kai aikatau ce zata koma haka,ke arcan" "Wallahi tallahi daada" shuruu tayi tana nazari,ita kanta kuma taji muryar kamar tatan "Toooo,anzo wajen,Allah yasa ba wata tsiyar ta shuka suka dawo da ita ba,in kuwa hakane nita cuta,saboda kayan dana buqata na aurensu da himu ko rabinsa ba'a gama siya ba.....maza tashi safiya kije ki shaidawa fulera zuwansu,don na tabbatar batasan tazo ba,tunda dazu da zamu gitta ta shiyyarsu mun hangi juna mun gaisa amma bata yimin maganar ba" rai safiya ta bata tana duban daada "Haba daada,daga zuwan ta,kawai saiki fassara zuwan da mugun tunani,don Allah ki daina haka,irin wannan abubuwan su suka saka ya himu fa kullum bashi da cikakkiyar lafiya" da murfin tukunya ta jefeta,ta kuma balbaleta da masifa,a dole safiya ta miqe tana qunaqunai ta wuce gidan inna furera. Sanda labarin ya isketa saita kasa zaune ta kuma kasa tsaye,fargaba ta cikata,ita ba abun ta tafi gidan yanzu taji meye ba'asi ba,haka dai ta daure,ta cewa safiya tace musu tana musu sannu da zuwa. Bayan sun gama cin abincin daren anni ta sanya khadim da fa'iza suje su raka maimunatu ta gaisa da inna furera,a sannan ta samu sararin yin magana da yuuma,ta shaida mata abinda ya kawosu. "Alhamdulillahi,alhamdulillahi,lallai wani hanin ga Allah baiwa ne,Allah ya tabbatar da duka alkhairi,Allah ya baki ladan wannan jihadi da zakiyi yafendo,ubangiji yasa alkhairi ya kuma hade mana kansu fiye da yadda muke zato da tsammani" "Ameen ramatu,ameen" "Kinci sa'a kuwa kawunsu yana nan,nan da bayan isha'i zai shigo gidan" "To alhmdlh" anni ta fada tana jin zuciyarta wasai. Zau biyu maimunatu tana yin sallama inna furera bata amsa ba,sai idanu data bita dashi bayan fa dgaa fitila ta hasketa da kyau,sai datazo gab da ita sannan ta zabga salati,zuciyarta cike fal da qunci da rudanin ganin maimunatun tamkar an sauya mata halitta,maimunatun kamar wadda aka yiwa wankan inji,duk da cewa tana nan itama lalitarta suna cika duk qarshen wata da kudin aikin maimunatun "Ke yarinya,ina fatan ba wata muguwar aika aikar kika tamfatsa ba aka maidoki ba,don wallahi ban gama hada kudin auren gaje ba,kika sake kuwa haka ta faru dake na rantse miki da Allah na lahira sai ya fiki jin dadi" takaici da mamaki suka cakude suka hadewa maimunatu,wai ita din yayar mahaifiyarta ce,sannan ita din a yau baquwa take ga inna furera,amma irin tarbar da zata samu kenan daga wajenta "Babu abinda ya faru inna,kawai zuwa mukayi gaisheku" ta amsa mata tana nemawa kanta wajen zama bayan ta nunawa su khadim inda zasu tsuguna suma. A gaba ta sanya maimunatu da tambaye tambaye,tambaya maras ma'ana tabin qwaqwafi,har maimunatun ta fara jin kunyar idanunsu fa'iza,saboda tambayar tayi yawa. Zuwa jimawa kadan saiga laulo ya ashigo shi da gaje,yaja ya tsaya turus a gabanta ya zuba mata idanu,sai kuma ya washe baki yana kiran sunanta,abinda yasa gaban gaje faduwa,ta kuma waiwayo tana duban tsaleliyar matar da ake kira da maimunatu. "Turqashi" ta fada qasan ranta,qarara baqinciki da kuma hassadarta ta bayyana,don takawa tayi gabanta ta kuma duka taba kiran sunanta don tabbatarwa ita dince,maimunatun kuwa ta amsa da kyakkyawar zuciya,ta kuma bi gaje da murmushi,murmushin da gaje ta dinga jin cewa da biyu tayi mata shi,kawai saita miqe tayi daki fuuu. Ganin zaman da suke bana wani abu bane sai na banza ya sanya maimunatun tace da.inna furera "Inna zamu wuce,sai da safe" "A'ah,ki wuce ina?,ai kuma kinzo kenan,ke da tafiya sai zaku koma,wala'alla ma gajee ta ta fansheki,taje itama ta dandana ta dawo" maimunatu naji na gani inna fureta tace mata nan kwana fa,ko raka su khadim zuwa hanya don ba zasu gane ba ta hanata,sai laulo ta sanya ya rakasu,ita kuma taci gaba da zama a nan tana amsa tambayoyin innar,don yanzu ta samu guri sosai ganin yaran sun tafi. Shuru innar tayi,wani abu yazo ya tsaya mata a wuya,tana tsoron kada fa maimunatu a nan gaba ta zama wata,ta kuma fisu a komai,anya ba fitittike musu zata yi ba?,tayi kwance kwance ta zayyano musu aibubbukan data dade da laqabawa maimunatu ta bata ta a wajensu ta basugaje itama taje ta dandali wannan arziqin?. *Arewabooks:Huguma* ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* 😄😄😄😄😄😄😄 *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 23 Sallamar jauro ita ta kubutar damaimunatu daga tulin tambayoyin inna furera,shikam karon farko ya gane maimunatun,yayin data miqe kamar yadda ta saba a baya tana masa sannu da zuwa gami da karbar ledar hannunsa. Yana shirin xama ta duqa har qas ta gaidashi,ya amsa cikin nuna kulawa,tamkar diyarsa gaje "Baki tafi gida kin kwanta ba?" Wani kallo inna furera ta jefeshi dashi a fakaice "Akwai inda yafi nan ne?,naga dai nan dinne gidan" "Qwarai kuwa" "Tun daxun ma nake tsimayin shigowarka..." "Eh nadan tsaya ne muna magana da labaran,ashe bidar alkhairi ne ya kawosu garin ma" sosai inna furera ta bada hankalinta ga jauro "Kamar yaya kenan?" Huffijen qafarsa ya cire,ya zauna sosai yana tanqwashe qafafunsa "Wato Allah ne kadai yasan alkhairi dake tattare da yarinyar nan,uwar dakinta hajiya anni,ita tazo ta shaida mana cewa,suna so mu basu dama zasu turo a nemawa jikanta auren maimunatu" Kamar ya dauko qaton qarfe ya doka mata a tsakiyar kai haka inna furera taji,sai taji gaba daya ta daina ganewa,kwanyarta ta dode "Ban gane abinda kake magana akai ba jauro,kace me?" "Nace gidan da taje aiki,uwar dakinta tazo nemawa jikanta izinin turo magabatansa neman auren maimunatu" zumbur kamar wadda kunawa ta harba haka nan ta miqe,take ta hada zufa da kuma gumi,zallar tashin hankali yana nuna kansa saman fuskarta "Wallahi wallahi ba zata sabu ba,aini ba haka mukayi da ita ba,ba kuma abinda na turata yi kenan ba,ni arziqi na turata nema mana bawai aure ba,hasalima ni ban shirya aurar da ita yanzu ba....."saita waiwaya bangaren da maimunatun take "Don uwarki don ubanki dama karuwanci kika je yi?,aure nace kije ki samo ba kudi ba?,shegiya mayya,kinje da idanunkin nan kin lashe kurwar dan mutane?" Inna furera ta fada cikin hargowa da fada matuqa "Ah.....kinga dakata furera,me kikeson kice ne?,.....ke maimunatu,tashi ki wuce daki wajen 'yaruwarki ki kwanta" ya baiwa maimunatu data cure waje guda saboda tsoro umarni,ta manta da irin wannan rayuwar sam,ta manta rabon da wani ya daga murya a kanta sai yau,sai ta miqe da hanzari ta durfafi dakin gaje,duk da shima batasan me zata taras ba. "Zauna furera" jauro ya bata umarni kai tsaye yana dubanta "Na zauna nayi me?,aini na gama magana,babu uban da ya isa yasa maimunatu tayi aure yanzu ehe" cikin matuqar mamaki yake kallonta "Awala hankali furera?,wanne irin batu ne na wai maimunatu ba zatayi aure ba?,ina cewa nan tanadin auren gaje kike yi?,sai kuma yanzu zaki ce ita maimunatu ba zatayi aure ba?,.....to......to,na gama fahimtar inda kika saka gaba,tsaf na karanceki,to bari kiji,idan kin saba watangaririya da rayuwar yarinya,idan kin saba saka rayuwar yarinya a gaba kiyi duk yadda kikaso ina zuba miki idanu,to wannan karon tayi qaura,kuma baki isa ba,yadda suka zo neman izinin auren maimunatu zasu sameshi kuwa da yardar Allah,muddin bake kadai kika rage a doron qasa jinin shatu da maimunatu ba" ya miqe cikin tsananin fushin data jima bataga yayi ba,sai tabi bayansa da kallo tana cewa "Me kake nufi jauro?" Ko tankata baiyi ba,yasa kansa abinda ya wuce dakinsa. Komawa tayi jabar ta zauna a wajen tana fidda zazzafar iska daga bakinta,kwanyarta ta cika taf da tunani,mutanen nan koda bataje ta ganewa idanunta ba tabbas tasan masu tarin arziqi da wadata ne,ta yaya maimunatu zata shiga cikin irin wannan ahalin alhalin gaje na zaune a qauye?,duk da babbar sa'a tayi na samun himu cikin qauyen?,shawara ta qarshe da zuciyarta ta bata shine,ta tunkari jauro kai tsaye,ta fayyace masa abinda yake zuciyarta,ai shima gaje diyarsa ce,kuma bazaizo ci gaban maimunatu fiye da diyarsa ta cikinsa ba. Wani kallo ya dago ya watsa ma furera sansa ta kammala bayananta "yanzu na fahimci bayan ciwon mugunta da hassada dake damunki,harda ciwon hauka kadan a kwanyarki,toki sani.....ni ba qaramin mutum bane,yadda suka furta maimunatu babu abinda zai sauya wannan in sha Allah saidai idan sauyin daga wajensu ne" maganar ta sake harzuqa inna furera matuqa,ta miqe cikin masifa "Nidai bansan ko dakai.akayi cikin maimunatu ba,banda haka,ta yaya ga jininka zaka ajjiyeta kafifita wata bare akanta?" "Duk yadda rai da zuciyarki ya baki haka ne" abinda jauro yace da ita kenan,don ya fuskanci tayi nisa bata jin kira,ba zata fuskanci duk wani bayani sai abinda zuciyarta da shaidan suka qawata mata. Yadda maimunatu batayi cikakken bacci ba a daren saboda maganganun da gaje ta dinga gasa mata har zuwa sanda bacci ya dauketa......haka itama inna furera bata runtsa ba,Kuka irin wanda maimunatu ta jima bata yishi ba tun barinta gidan a yau ta yishi,tana cike da tantamar anya inna furera yayar daadarta ce da gaske kuwa?,sam ko daya cewar da tayi ba zata auri jika ga anni ba shine damuwarta ba,a'ah.....yadda a kullum ta bude baki mugunyar kalma ce ke fita daga bakinta a kanta,bata taba ambatar alheri a kansu,daga ita har marigayiyar mahaifiyarta,ta duba ta kuma dubo amma ta gaza gano laifi guda daya tak da suka yiwa inna furera wanda suka cacanci wannan abun daga gareta,bata damu da zantukan gaje ba dama ta saba dasu,amma qiyayyar inna furera tana mugun taba mata ruhi. Ita kuwa inna furera kaf a daren tunaninta ya tafi ga yarda zata turgude maganar auren maimunatu ne,idan da hali ma ta maida akalar zanca ya koma kan gaje,bata damu da koma wanne irin kallo daadar himun zata yi mata,indai suka haye wannan bigiren shikenan komai yazo qarshe a wajenta. Shawarar qarshe data yanke da ita ta kwanta,ta kuma miqe tun kiran assalatun farko ta buga sallarta,ta zauna tana dakon kira na biyu ta fice a gidan. Sanda ta fita din kuwa ko sallamewa daga sallar ba'ayi ba adan masallacin dake tsukin rugar tasu,sai a hanya dab da isarta gidan bappa labaran aka idar,ta kutsa kai gidan babu cikakkiyar sallama saboda bataso daadar tasan tazo,ta nufaci dakin yuuma kanta tsaye. Dai dai lokacin da yuuma ke tsaye tana shirin zare hijabinta daga jikinta bayan ta idar da salla,yayin da anni ke saman abun salla tana lazumi itama. Tsorata yuuma tayi da ganin furera a irin wannan lokacin,ta matsa da baya tana amsa sallamarta sanda ta shigo ta yiwa kanta mazauni,tsaf anni ta gane matar,don haka bata katse lazuminta ba sai data cika dari cif sannan ta sauke carbin bayan ta shafa,inna furera ta fara gaidata cikin tsantsar ladabi,anni ta amsa tana dubanta a kaikaice,don tana da tabbacin kome meye ya futo da ita da asussubar fari to ba alkhairi bane. Rai rai ta fara jerowa anni maganganun da tun a jiyan ta gama shiryawa kanta game da maimunatu,da dukkan wata siga da zatayi baqi a idanunta,anni na kallon ta,bata ce da ita komai ba hakanan bata dakatar da ita ba,har sai data dasa aya "Kin gama?" Anni ta tambayeta "Eh....to shine naga gwara na shaida miki,tunda dai kinga amana ce ta hadamu,bai kamata na rufeki ba kada ubangiji ya tuhumeni,ni kaina yarinyar kaffa kaffa nake da ita da kuma neman maganin tsari daga maita,shine fa kikaga mun kawo har warhaka lafiya lau bata taba kowa a cikinmu ba" Sosai yuuma dake zaune daga gefe ta cika tayi famm,fata take annin ta bata dama ta wanke furera mara tsoron Allah data iya kaikaicewa ta yankarowa jininta mummunar qazafi da qarya har haka saboda kawai zallar hassada da baqar zuciya "Yanzu me kikeso ayi kenan?" Anni ta tambayeta cike da gatse,wanda ita furera bata fahinta ba,sai murna data saukar mata,ta kuma karkace ta gabatar mata da gajenta,bayan ta gama kodata "Kinga dakata baiwar Allah,kiyi ta kanki kinji,banason wannan soki burutsun,banda ma baki da hankali........idan maimunatu mayya ce ku zaku kubuta ne?,ko ce miki akayi ba wanda yasan alaqarku da ita?" Gumin tashin hankali ne ya yankowa furera,ya akayi wata halitta tasan da wannan?dama kowa kallonta yake kenan?. "Ai....to,ai dama ita din.....maitarta ta can jikin kakarta ne.....bawai daga ubanmu bane,daga kakarta ne......sai....sai ta tsotsa daga nonon uwarta itama" "Ke!......ki kiyayeni fa?,wallahi tallahi ina sake jadda miki kiyi ta kanki,yo banda tambadewa irin taki,ina ake irin haka?,to bari kiji na gaya miki,ki kama.kanki,idan ba haka ba in na tashi tafiya billahuwallazi kaf garken maimunatu da uwarta da kika danne kike qafafa dasu sai nasa anyi awon gaba dasu,gwara ki.saita kanki aci gaba da tafiya ahaka,wata shari'ar sai a lahira" sosai jikin inna furere ya dauki bari jin ana shirin yi mata bankada. Ta tambayi kanta Wanne tsinannen ne yake fitar mata da sirri haka?,anya ba daadar himu bace?,babu shiri ta kwashi takalmanta a hannu ta fice don anni ta fara daga mata murya. Abinda ya sake kada mata hanji kuma shine kallon banzan da daadar himu ta watsa mata sanda sukayi kacibus a tsakar gidan,saita qarasa daburcewa,ko taji abinda yake tafe da ita ne?,don haka ta hadiye gaisuwarta tayi waje,don ta soma zargin daadar cikin ranta,saboda tasan kaf fadin karkarar ita kadai tasan da wannan maganganun. Tunda ta idar da sallar asuba tana zaune bata koma ba,lokaci lokaci idanunta suna kan gaje daketa sharbar bacci abinta,babu shiri ko niyyar tashi tare da ita bare ta sauke farali,har yanzu halindai ashe yana nan ta raya hakan cikin ranta. Haka kawai tayi sha'awar tashi tayi irin ayyukan data saba yi a baya,don haka ta miqe a hankali,ta zura hannunta inda ta cusa takalmanta watannin baya sanda zata bar gidan,cikin sa'a ta samesu,murmushi ta sake,duk da sun ratattake,suna tuna mata da abubuwa masu yawan gaske da suka gabata,saita miqe dogayen qafafunta da a yanzun suka qara haske suka kuma yi luwai luwai ta zura su,sannan tayo waje. Tana fitowa jauro na dawowa daga salla,ta gaidashi cikin girmamawa ya amsa mata cikin kulawa yana tsokanarta kan yau ta tuna kwanan ruga,tana murmushi ta soma aikin gidan,sai gashi ya fito yana tambayarta inda fureran taje "Ban sani ba kawu,yanzu nima na futo" sai ya jinjina kai,har yayi gaba ya dawo yace mata ta aje aikin ta koma ta kwanta "Ba komai kawu,hakan yana min dadi" kansa ya jinjina cikin tausayi da qaunar yarinyar,ya shige dakinsa,babu jimawa ya fito da koren hirami na maza jikinsa daya yafa,ya wuce dakinsu,tana jinsa yana rafkar gaje kan ta tashi tayi sallah,kana yayo waje yana ce mata zaije ya dawo,tayi masa a dawo lafiya tana ci gaba da ayyukanta,saidai har ta gams gaje bata futo ba. Ganin ta gama saita wuce kanta tsaye zuwa haggo,tun daga nesa take kallon dabbobin cikin kewa da shauqi,tayi matuqar kewarsu ba kadan ba,amma abinda yadan taba ranta ya kuma bata mamaki,yadda yawansu kyau da tsaftarsu suka ragu sosai,taga sabbin fuskoki dake nuna an hayayyafa,to amma indai hakane me ya hana su qara yawa?. A nutse taje ta kwance wadanda suke daure,ta zari sandar data gani a jingine a wajen,ta kuma soma korasu cikin nutsuwa da tsohuwar qwarewa zuwa makiyaya. Kusan za'a iya cewa kallo ne ya koma sama,duk inda ta wuce dai ta kwashi fiye da rabin hankalin mutanen wajen,wasu da yawa basu ganeta ba,suna mata kallon baquwar fuska,don atamfa ce a jikinta dinkin doguwar riga,ba kayan saqi ba. Dukka wajen data saba ta'ammali dashi a wancan lokacin sai data tsaya a wajen tana tuna komai daya wuce,daga qarshe ta dangana da qasan bishiyarta,wadda a yanzun ta qara yawa da rassa,tana shirin zama taji sallama da muryar da ta kasance sananniya a wajenta. A nutse ta daga kai tana amsa sallamar,bafullatanin saurayin nan daya taimaki rayuwarta a shekarun baya,himu,shine yau tsaye a gabanta bayan shudewar wasu watannu masu tsaho,yana nan a yadda ta sanshi,saidai kuma yayi rama ba kamar a baya ba da yake da cikar jiki.....Ya tsinke sosai ya qara tsaho,har yanzu wannan murmushin nasa yana nan saman fuskarsa,sai ya tako daura da inda take zaune,ya zauna saman dutsen daya saba zama shima "Maimunatu....'yammatan birni" maganar data sanya siririn murmushi kubuce mata,ta kuma soma gaidashi,ya amsa mata cikin matuqar kulawa "Tafiya haka katsam babu bankwana maimunatu?,saidai na laluba naji wayam babu ke?" Har yanzu himu nada wata kima da daraja a ranta,yana kuma cikin jerin mutane masu muhimmanci a rayuwarta "Kayi haquri,haka tafiyar nima tazomin,kuma a sannan bansan inda zan ganka ba" kai ya gyada,shima yasan da wannan "Hakane,to yaya bayan rabuwa?,duk da alamu sun nuna komai yana tafiyar miki yadda ya kamata" ya fada kansa tsaye yana hango canji qarara daga wajenta,canjin da yasa ya saare,ya sake kuma sallamawa bayan kunnuwansa sunji ana zancan aurenta da wani. Mintuna kadan ya miqe bayan zaman shuru da sukayi shi da ita "Sallama nazo muyi,saboda nasan ba lallai bane na sake samun dama irin wannan,ban taba kawowa a raina zan rasaki ba,sai gashi qaddara ta wanzar mana da hakan,duk da zuciyata ta soki matuqar so,bazanyi jayayya ba,saboda bansan me Allah ke nufi da hakan ba,kin cancanci samun kyakkyawar rayuwa fiye da wadda nake miki tanadi,ina miki fatan alkhairi a dukka rayuwarki maimunatu" daga haka ya juya ya soma barin wajen. "Na gode sosai" abinda ta iya gaya masa kenan tana bin bayansa da kallo,tausayinsa da kuma wani irin yanayi na cika mata zuciya,har ya bacewa ganinta. Ko awaguda bata rufa ba inna furera ta aiko kan ta tattaro mata dabbobinta ta dawo mata dasu,tayi hakanne saboda tsoron daya cika zuciyarta kan kada ta rasa dabbobin data qwallafa rai a kansu,fitar da maimunatun tayi dasu sai take ganin kamar wani shiri ne. *Follow my arewabooks account for more latest pages* *Arewabooks:HUGUMA* ❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥 *_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_* *_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_* *_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_* 😄😄😄😄😄😄😄 *YA KUKAJI SALON MASU KARATU?* *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 24 Kai tsaye jauro ya damqawa anni rubutaccen kwatance har zuwa gembu mahaifarsu maimunatu tushensu asalinsu,inda yake da tabbacin zasu samu qannen kakan maimunatu da sauran danginta na wajen uwa da zasu iya aurar da ita. Koda inna furera ta samu wannan labarin hankalinta yadan kwanta kadan,saboda tasan babu wadda zasu fara samu sai babarta inno,ta kuma san cewa duk kanwat jaa ce,inno ba zafa taba amincewa ba matuqar taga irin wannan ci gabanne zai samu jinin shatu. Saidai cikin rashin sa'a ga inna furera,sa'a gasu anni,sai suka samu qanin kakan maimunatu,wanda ya karbesu hannu bibbiyu,ya kuma laluba bangaren mahaifan shatu ya sanar musu da abinda ke faruwa,sukayi murna qwarai,suka kuma amshi su uncle umar wanda dr marwan ya wakilta nemo auren maimunatun,karba ta girma karamci da kyautatawa irin na fulani. Sun karba kudin auren maimunatu,sun kuma amince da satittikan da aka yanke na daurin auren maimunatu,an rabu cikin mutunci da mutuntaka,zuciyar dangin maimunatu fes,a yanzun duk wata shakka da suke da ita kan rayuwar da maimunatu ke ciki ta kau,hankulansu suka sake kwanciya. Sosai hankalin annin ya sake kwanciya,ta kuma sake nutsuwa,hukuncin kuma da suka yanke na wanzarwa da ja'afar komai ba tare da sun sake bi ta kansa ba taji bai dameta ba,tunda anyi me wuyar,sauran kuma zata sanar masa da kanta idan suka koma gida suka huta suka kuma nutsu. Sati daya kacal sukayi a adamawa suka tattaro sukayo gombe,anni cike da farinciki da murnar yadda aka basu maimunatun,kamar yadda honorable ya basu auren diyarsa shima,aka sanya rana kuma dai dai da wadda aka saka ta maimunatu,a yanzun abinda ke gaban anni shine shirin auren. Yammacin wata asabar,cikin daya daga cikin falukan annin wanda aka qawata da tattausan carpet,tana zaune ta miqe qafafunta sosai,daga gefanta surukarta ce,matar uncle usman,mahaifiya ga hafsat,shigowarta kenan gidanma gaba daya. Suna tsaka da gaisawa maimunatu ta shigo falon,sanye da brown din chiffon skert,sai rigarsa me dogon hannu,ta yane sassalkan gashinta da mayafin kayan light brown,fuskarta ta fito fayau tayi kyau sosai,duk da kasancewarta ba ma'abociyar son kwalliya ba,saika tsammaci ta fito ne daga yankin larabawa. Sai data isa gaban annin,ta ajjiye hadin fruit salad data yi,wanda duk cikin girke girken da take koya ne hannun tabawa tana murmushi ba tare data ce da annin komai ba "Da kyau,sannu da qoqari muna" ta ambaceta da sunan da baba tabawa ke kiranta wasu lokutan,sai ta juya sashen da momy kamar yadda suke kiranta take ta soma gaidata. Sama sama ta amsa mata,maimunatun bata wani lura ba ta miqe abinta ta fice,duk da annin taga abinda ya farun,amma sai tayi kamar bata gani ba,ta jawo fruit salad dinta ta fara ci,dai dai lokacin da momy ta motsa kadan,ga duk wanda ya qare mata kallo yasan maganganu ne fal harshenta "Su ja'afar kuma ashe ankai kudi,saiga daddynsu ya shigo da zancan" "Eh,anyi haka" anni ta fada ba tare data dubeta ba "Diyar commissioner ko?,samiha,sai kuma wata agwai,wannan yarinyar data shigo" cak anni ta dakata da shan fruit salad din da take,ta sanya hannu ta zare gilashin fuskarta da takanyo amfani dashi wasu lokuta "Inaji yanzu kikaji na kirayi sunanta ko?,to ba agwai sunanta ba,kada na sake jin wannan sunan daga bakinki,maimunatu take" "Ayi haquri,bada gangan na fada ba,sunanta ne ga kwantan" "Ato,gwara kiyi ta kanki" ta amsata tana maida gilashinta,maganar data tsayawa haj munubiya Momy a rai,wanne irin so annin ke gwadawa yarinyar ne?,duk yadda su shaffa'u ke gaya mata bata yarda ba sai yanzu da dukka alamu suka nuna,tanaso tayi shuru hakanan amma kuma maganganun bakinta basu qare ba,don haka fa sake motsawa "Amma yanzu anni,fisabilillahi ba za'a duba halin da yarinyar nan hafsat ke ciki ba?,gida bai qoshi ba za'a kaiwa dawa?" Sake dubanta tayi wannan karon kallon tsakiyar idanu,tafi kowa sanin wacece munubiya,kaf surukanta babu wadda take fama da ita kamarta "Shi sagirun da yazo da zancan,bai gaya miki anihin abinda nace dashi bane?" Kai ta gyada tana jinjina taurin kai irin na annin "Ya gaya min" "To du Allah du annabi munubiya,banason maida hannun agogo baya kinji ko" sai ta gyada kai kawai,zuciyarta fal takaici,taso ace diyarta ta samu ja'afar,ba tun yanzu ba,tun aurensa na fari,a sannan hafsat din bata wani nuna da yawa ba,take gani shine silar data gaza jan hankalinsa har ya auri shaheeda,a yanzun kuma da take ganin komai yakai anni tayi ruwa tayi tsaki ta hana wannan damar. Miqewa tayi tana rataya jakarta,annin ta dubeta "Zan wuce anni,Alla ya sanya alheri" "Ameen,ki gaida gida,a gaida yaran" har tayi gaba ta sake cewa da ita "Yauwa,ji mana" tsaiwa haj munubiya tayi "Ki turon khalid,na gaza samunsa a waya,kice ina nemansa" dole hakanan ta amsa mata da to,sannan ta taka ta fice. A hanya ita kadai kamar ta taune zuciyarta saboda baqinciki,haka ta fitoma daga gidan babu wanda ta yiwa sallama,duk irin bautar da khalid din kewa annin har yau bata jin tana masa rabin son da takewa ja'afar,a bakinsu shaffa'u takejin kamar ya soma son yarinyar amma annin ta hanashi ta bawa ja'afar,duk da bata taba jin qaunar yarinyar ba amma taji zafin hakan,hakanan ta hana hafsat ja'afar ta bawa wasu baare daban,wannan babu abinda yake nunawa illa zallar qin da take mata,qwafa taja gami da dogon tsaki,zata gamu da khalid dinne. "Allah ya sawwaqe,ya yaye miki munubiya" anni ta fada tana jan wayarta "Shima zan gamu dashi,shegiyar kafiya da riqon abu a rai,wannan wanne irin SO BAYAN RAI ne?,tana nan tana yaqi a kansa bai sani ba,tana ta baqin jini wajen jama'a. Tana ta bulayin nemansa khadim ya shigo "Kiramin jafaru da wayarka" "Allah yasa ya daga,na canza sabon layi" ya fada yana laluben wayar a aljihunsa,sannan ya zauna daga gefan annin yana tambayarta me zaya samu cikin dakin nata "Ban sani ba,zaka kamomin shi ko sai ka cinye kurwata tukunna" ta fada tana harararsa,don tace khadim din ya cuka kwadayin tsiya,yana qunshe dariyarsa ya dannan kiran ja'afar din,saidai har tayi ta tsinke bai daga ba,sai da ya maimaita kiran ana uku ya dace ya daga,kai tsaye ya miqawa anni wayar ya koma corner falon yayi zamansa yana daukar wayar annin. Dan madaidaicin waje ne dake bayan gine ginen gidajen nasu,wanda ke shimfide da korran ciyayi,kujerun qarfe ne masu kyau guda uku da table dinsu a tsakiya,saman table din akwai glass cup daya cika da lemo yana kurba time to time,tsaye yake ya baiwa table din baya,hannuwansa riqe da wasu fararen takardu kusan guda shida,wanda ya bada hankali sosai a kansu,da alama akwai muhimmin abu da yake dubawa a ciki,sanye yake cikin shirt da trouser masu taushi duka na kamfanin Louis Vuitton,iskar wajen ta gauraya da daddadan turaren jikinsa tana bada wani yanayi me dadi,wasu slippers ne masu kyau na fata sanye a qafarsa,hannayensa goye a bayansa,lokaci lokaci yakan cire hannun ya shafi tausasan labbansa. Karamin tsaki yaja sanda wayarsa ta sake qara,karo na kusan uku kenan,sauke takardun yayi daga fuskarsa a hankali,kyakkyawar fuskarsa dake fidda wani irin kwarjini da kuma calmness irin nashi ta bayyana,taku biyu yayi baya ya isa gab da table din inda wayar tasa take,har yanzun wani busar sarewa take me dadin sauraro. Sai daya kalla screen din some few seconds sannan ya shafa wayar ya karata a kunne "Assalamu alaikum" ya fadi with husky voice,daga can bangaren anni ta amsa,saiya dan sauke numfashi kadan jin anni ce,ya maqale wayar a kafadarsa yana gyara takardun bayan ya soma da gaisheta "Lafiya alhmdlh,manya,me yasa kake mancewa da gida?" "Taya zan mance daku anni?,akwai abubuwa ne da har yanzu bayi settling dinsu ba" haushi ya cikata,koda yaushe maganarsa kenan,to itakam koma meye dai ai ta kawo qarshen abun,don haka cikin kaushi tace dashi "Kullum maganar dai kenan,tamkar kaine kafi kowa sabga a duniya,to koma dai meye wannan matsalarka ne,mukam ba zamu zauna mu zuba idanu rayuwarka taci gaba da tangal tangal a haka ba,bayan ko talatarka bakaci ba balle laraba,ban sani ba ko dan uwanka ya labarta maka" ta sauke maganar tana jiran amsarsa,dai dai sanda ya gama gyaran takardun ya duqa yana niyyar ajjiyesu saman table din "Me kenan?" "Kai kudin aurenka wa 'yammata biyu,nan da sati hudu kuma in sha Allahu kowacce zata shigo gidanka a matsayin matarka,saboda haka ka maida hankalinka,ka tattaro kayo gida,koma meye daga baya zaka qarasashi" "What a funny story anni" ya fada cike da tantama yanayin fuskarsa na sauyawa zuwa ga yanayi na son yin murmushi,saisai murmushin bai fita ba,saboda yadda yaji labarin yafi masa kama da tatsuniya "Anni,zancan aure fa kike da mata har biyu" ya fada sounding like dariya zata kubce masa,yanayin da anni tagama karantoshi tsaf,saita hade muryarta itama "Kafi kowa sanin wacece maryama farouq akko ko?" Yes,yasan anni fiye da kowa a gidan dama family dinsu,tuna hakan ya sanya duk wani shakku dake ransa wankewa,uwa uba yadda ta kirayi sunanta in full ya sake tabbatar masa she's serious "Seriously?" Yayi tambayar da wani irin tune,tambayar da baisan dawa yake ba,da anni yake koda kansa? "Inadai gaya maka,sati hudu kacal suka rage" "Ya salam ya Allah,anni why?, Me yasa?,mu nawa ke zaune a gidan,amma why me?" Ya fada yana jin wani irin zafi na taso masa har saman fuskarsa "Bakai kadai ba,wannan karon duk wanda yakai munzali sai ya bar gidan nan ya tafi nasa,abun ya isa hakanan" "Okay okay fine.....zan dawo zanyi packing komai nawa zan bar gidan,but..... please anni,kada kiyi punishing nawa ta wannan hanyar,bazan iya zama da kowacce mace ba anni please" ya fada cikin kwantar da murya,tare da fatan zai shawo kan annin. Baki ta tabe daga can,dama tasan za'a rina,tasan halin ja'afar sarai,tasan komai zai iya faruwa,kuma dama bata tarki abun ba sai data shirya masa "Kaga babu fa wannan zancan,an riga an gama magana da magabantansu,ba zaka maidamu qananan yara ba,kuma ba gidan mukeso ka bari ba,zaman aure mukeso kayi" zaman aure kamar wani mace?, Ya qiyasta hakan cikin ransa "Anni,ki fahimceni mana,ta yaya za'a auramin mata har biyu bayan babu fahimtar juna a tsakanina da kowaccensu bare azo maganar soyayya wadda already nayi banning dinta" "Zaku fahimci kawunanku a dakunanku ai" ya zuwa yanzu ranshi ya sake baci fiye da dazun "Anni!" Ya kirayeta da murya mai kaushi kadan,wanda shi kansa baisan yayi hakan ba "it will not be possible,ta yaya hakan zai yiwu?" "Ahap gashinan kuwa?" Da gaske take ba zata fahimceshi ba,saidai ma idan bai wasa ba ta sake tunzurashi,don haka sai kawai ya yanke wayar da sauri,sannan cikin wani irin zafin nama yaja kujera guda daya gabansa ya zauna a kai bayan ya jefa wayar saman table din,baya ko tsoron ta fashe. Dukka hannayensa ya cusa cikin gashinsa yana yamutsawa tare da fadin "No...no,it can't.....it can't.....am not ready.....am not ready to face it this challenge" ya fada cikin zafi,sai kuma ya sake miqewa,yana buqatar yayi magana da wani,sai ya janyo wayar yana furzar da zazzafar iska daga bakinsa ya soma laluben number ammansa,gab da zata shiga ya sauya shawara ya kashe,sai ya maida kiran kan jabir "Where are you?" Ya tambayesa kai tsaye,tsabar bacin rai yama manta inda yace masa zaije,tunda jabir din yaji muryarsa yasan cewa akwai matsala,cikin ransa yake fatan Allah yasa ba depression mode dinsa ne ya motsa ba "Am on my way,is there a problem?" "Zaka dauki mintuna nawa?" "Few" ya amsa masa a taqaice "Okay,am waiting for you, please don't stay long" bai jira amsarsa ba ya katse wayar ya sake jefata inda ya dauko,dukka hannayensa ya zura cikin aljihun wandonsa,yahau kai kawo tsakanin wannan bangaren zuwa wancan,wanne irin hukuncine wannan da zasuyi masa?,wannan auren aiko mace a wannan zamanin ba za'ayi mata shi ba,wadanne irin mata ne su kansu da suka dauki kasadar aurensa ba tare da sun gana dashi ba?,kawai sun amince da auren mutumin da bashi ya nema yardarsu ba?,anni tana tunanin akwai macen da zata cike masa GURBIN shaheeda ne?,babu?,sam babu,yanajin cewa daga kanta an gama haifar diya mace a duniyarsa,wadan nan matan data debo GURBIN IDO ne kawai,fanko ne,ba zasu taba zamtowa IDO ba wato shaheedansa,yayi imani da hakan har cikin zuciyarsa. Kafin jabir yakai ga isowa ya duba agogo sau babu adadi,a gaban idanunsa cave ta saukeshi,ya fito dauke da niqi niqin siyayya a manyan ledoji,sai a sannan yayi noticing wani abu,kwana biyun jabir fita yake siyayya kusan koda yaushe,kamar wanda ke shirin komawa gida. Sai daya shiga gida ya aje kayan sannan ya sake fitowa,kafadarsa ya dafa daga baya "Meye haka ne man?" Waiwayowa yayi ya dubi jabir,idanunsa a sannan har sun kada sun sauya kala saboda zallar bacin rai,wanda ta nan ake iya gane qurewar bacin ransa "Yanzu kamar ni?,kamar ni anni zatayi forcing dina akan aure?" Tuntuni ya shanshano komai,don yasan da komai din,ya samu labari,saidai baiyi gangancin shaidawa ja'afar din ba,ya zuba idanu yaga ya caftar zata kaya. Dubansa sosai jabir yayi "That's right...." Sosai maganar ta baiwa ja'afar mamaki,ta kuma sake qular dashi "Like how? what are you trying to say jabir?" Ajiyar zuciya ya sauke,shima ya maida hannayensa aljihunsa "Ja'afar,ka gaza nutsuwa ka karbi qaddarar rayuwarka kayi moving forward yadda ya dace....." "Yanzu qoqarin me nake?" Ya fada da zafinsa "Yes,naga canji,kanata qoqarin maida harkokinka yadda ya dace,amma bata iya wannan fannin kawai ya kamata ka maida kai ba wajen gyarawa,ya kamata ka sake building a new family da zasu debe maka kewa,su sake maidaka cikakken mutum,abinda kai ka gaza yi anni ta tayaka ginashi,so bai kamata ka zargeta ko kaji haushi ba,a shawarce ka tsaya ka nutsu,ka yiwa abun kallo na fahimta,don't upset please" "Okay na gane,kaima kana goyon bayan abinda tayiminkenan?, wait.....waima wa yace musu a yanzun ina sa buqatar wata mace cikin rayuwata?,dolen sai na rayu da wata,a barni nayi rayuwata a haka mana,me na ragu dashi" jabir zai sake cewa wani abu ja'afar din yaja tsaki ya daukin wayarsa a fusace ya wuce cikin gida da sassarfarsa. 25 Kamar jabir din ya shareshi,sai kuma ya kasa,ko babu komai yana buqatar kwantar da hankalinsa kada kuma ya birkice musu a koma 'yar gidan jiya,bayan abubuwan suna danyi kyau ba kamar can baya ba,don haka sai ya kwasa shima ya bishi. Cikin rashin sa'a ya sameshi ya kulle kansa a dakinsa,yayi ta bugu ya bude masa amma yayi kunnen uwar shegu dashi,ya sani ya qulu sosai,kuma cikin bacin rai yake,haka dole ya haqura,saidai yana fatan kada ya jima a kulle a dakin temper tayi masa yawa. Komawa yayi ya zauna saman kujerun falon,kam kujerar dake fuskantar dakin,lokaci lokaci yana danna wayarsa yana kuma duban qofar dakin tare da fatan ya bude,saidai har kusan awa guda da rabi ba motsinsa ko alamar budewa,abun da yadan saka jabir yaji shakka a ransa,sai ya sauka daga game din da yakeyi don dama ta fara isarsa,ya kirayi layin anni. Gaisawa suka fara yi sannan ya gaya mata abinda yake faruwa,duk da taji fargaba itama cikin ranta amma saita dake "Rabu dashi,zaiyi ne ma ya gama,kayi sabgarka,idan ya gaji ya fito" ta fada cikin dakiya,murmushi jabir yayi,don shi kansa yasan dakiya kawai annin tayi. Suna gama wayar ya isa ga makunnin kayan kallonsu ya kunna tv din,sannan ya maida channel din dake kai zuwa saudi qur'an da madaidaicin sauti,ya ajjiye remote ya wuce dakinsa ya sauya kayan jikinsa daga shi sai farar singlet da boxer,ya fidda siyayyar da yayo,yakai daki sa,saura kuma ya wuce kitchen dasu. Abinci ya fara shirya musu,yana aikin amma hankalinsa yana falo,yana yi yana leqawa ki ja'afar din ya fito,saidai har ya gaji da leqan baiga ya fito ba,tilas ya haqura har ya gama abincin. Yana fitowa daga kitchen din yana qoqarin fidda afron din jikinsa jaafar din na fitowa a dakin,sosai jabir din yaji dadin hakan,ganin fushin baiyi tsaho ba,a yanzun ma ya sake wanka ne don kayan jikinsa na dazun ba sune yanzu ba. "Ina zuwa?" Jabir ya tambayeshi yana fidda ruwa daga fridge "Zamu fita da mr mickey,akwai meeting da zamuyi,so if i stay long kada ka jirani" "Abincin fa?" "Ka cinye kayanka" dariya ce ta qwacewa jabir,ya sani fushi yake dashi,yaji haushin that's right da ya fada,da kuma goyon bayan anni da yayi,fushinsa ne ya shafi abincinsa "Cikinka ba nawa ba" ya bashi amsa sanda yake takawa zai fita daga falon,saidai bai waiwayo ba ya fice abinsa,kamar ma baiji abinda jabir din ya fada ba. Diban iya wanda zai isheshi yayi ya sanya masa sauran a fridge,yasan idan ya dawo zai nema abincin da kansa,don duk abin nan nasa baya wasa da cikinsa ko kadan. Shirye shirye ake gadan gadan daga gidan dr marwan akko na aurar da ja'afar din,wanda tun ranar da sukayi waya da anni bai sake neman kowa ba,kamar yadda itama annin ta watsar dashi,hakanan daga ita har dr babu wanda ya sake nemansa,shima hakan yayi masa,don kuwa ya riga ya gama shiryama ransa komai,baiga ta yadda yana namiji me cikakken hankali,ba auren fari ba za'ayi masa irin wannan karan tsayen,ya tuhumi kansa da kansa kan ceqa ya bawa anni dama ne da yawa cikin rayuwarsa shi yasa tayi wannan tunanin,bama su da suke nigeria ba,hatta da jabir baibi ta kansa,ya shiryama ransa zai koma nigeria ne a duk sanda ya gama uzurorinsa a nutse. Ta bangaren jabir kuwa duk da ya damu,yana kuma ankare da abinda ke faruwa amma bai nuna ba,shima shirin tafiya gida yake,saboda a yanzun aurensu su biyu za'ayi,sbi da ja'afar din,anni taso a hada harda su salma amma sai aka samu tsaiko,hisham bai fidda gwanarsa ba,hakanan salma tana kan qadamin kammala nata karatun ita da hafsat da kuma laila,don haka annin tace a barshi zuwa sanda zasu gama din watanni shida nan gaba masu zuwa. ********Dai dai lokacin da suke shigowa farfajiyar gidan sanye da hijabansu na makaranta suna taba hira,motar dake fake a parking lot na gidan ta tsaya,mamallakiyar motar ta budeta ta fito. Zabgegeyar farar bafulatana,fara tas,wadda kamanninta da haj aishatu ta nuna qwarai,sanye take da wani danyan lace daya kwanta a fatarta,komai na jikinta matching ne,jikinta ba abinda yake sai fidda wani tatausan qamshi,tana rungume da baby boy wanda duka duka bazai wuce shekara daya da watanni biyar ba. "Auty maama" 'yammatan suka kusa hada baki wajen kiran sunanta,tana rufe motan da key ta waiwayo tana dubansu,fuskarta ta wadatu da fara'a sosai,macace m'abociyar fara'a da kuma kirki,bata debo a qasa ba,ta debo kyawawan halayen mahaifiyarta haj aishatu umar sanda da kuma dr marwan akko "Yammatan gidan baaba dr" ta fada sanda suka qaraso gaba dayansu,murmushinsuka sako,don dukkansu sunji dadin zuwan nata,saboda akwai shirye shiryen da suke akan bikin gidan,wanda sun tabbatar bazaiyi armashi yadda suka tsara ba saita ce wani abu,a matsayinta na babbar yayarsu,wasu na shirin amsar yaron hannunta,yayin da khadija ta amshi hand bag dinta,suka soma rankayawa ciki bayan sun gaisheta hira ta balle. "Ina kuka baro maimunatun kuma yau?" Anty maama ta tambaya sanda suke gab da shiga ainihin ginin gidan,inda zao sadaka da qofar kowanne sashe dake cikin gidan,sai a sannan suka laluba suka ga ba maimunatun,da alama guduwa tayi saboda anty maaman "Tare muke guduwa tayi halan,kinsan halinta,halim fulani ne har yanzu a jikinta,bada kowa yanzu take iya haduwa cikin gidan nan ba,hatta amma wasan buya sukeyi" murmushi ya kufcema anty maama,kunyar yarinyar da kamun kanta yana matuqar burgeta,duk da a cikinsu take amma bata yada dabi'ar kunya ba,har yanzu yarinyar batasan hanyar gidanta ba,da hirar maimunatun suka rakata ta gaida ammi sannan ta isa sassan mahaifiyarta amma,bayan ta aikawa anni da saqon gaisuwa gami da sanarwar ta iso zata shigo. "Ina duka yaran?" Amma ta tambayi anty maama "Suna islamiyya,amma for now nasan ma sun taso,nace ma iliyasu driver ya wuce dasu wajen haj,idan na dawo zan biya na debosu" "Yayi kyau,Allah ya taimaka" amma ta fada,don ba wani dogon hira suke da ita can can ba,kasancewarta diyar fari a wajenta "Wai maimunatu nita gani ta gudu amma?" Anty maama ta fada tana dariya,sai amman tayi murmushi "Kyagaji da gani indai maimunatu ce,yanzu ko sassan nan bata zuwa" kai anty maama ta gyada,kamar ba zata ce wani abu ba sai kuma ta magantu "Allah dai ya tabbatar da alkhairinsa,ubangiji yasa ta zame ma rayuwar ja'afar haske,nafi sanya hope a kanta amma akan samiha gsky,duk da ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare,Allah yasa dai manya ya riqesu da kyau" ajiyar zuciya amma ta sake,don abinda taketa tsoro da fargaba kenan,musamman da yadda kwanaki suketa matsowa,amma bataji.batun dawowarsa ba,koda kuma sunyi waya baya ce mata komai kan dawowar tasa ita kuma bata taba tambaya ba saboda.kara da kuma alkunya,amma dai duk sanda tayi sujjada tana gayawa Allah,wannnan shike bata nutsuwa. Bata jima sosai ba tace bari taje wajen anni ta fita a sashen. Bayan gama gaisuwa da 'yar tsokana da wani lokacin take kwasan annin da ita,sai anni ta kirayi sunanta "Inaso kiyimin total na kayan jere dana kitchen,babanku ya buqata,zai siyawa maimunatu" "A ina anni" "Oho,wani kamfani ne yace anan da suke kawo kaya daga turkey,da so yayi aje can direct,to kuma lokacin ya qurace,danginta daga can gembu sun nema ya barsu suyi kayan,yace ai diyarsa ce,duk da haka saida suka aiko da kudin kayan,to nace gwara a siya wani abun me daraja da kudin a bata,tunda shi yayi niyyar yin kayan" "Ma sha Allah,abbi ya kyauta,kuma hakan yayi,ko gold ne sai a siya mata,ba matsala anni" ta amsa mata tana fiddo wayarta daga jaka "Yauwa,sannan kuma,bashi nakeso ki bani" kai ta daga tana duban anni tana 'yar qaramar dariya "Me zakiyi da bashi kuma tsohuwa,bayan duka lalitar familyn farouq kumo na hannunki" "Ke banson iya shege,kiyi ta kanki,magana nake miki ta gaske,aron kudi zaki bayar,amma ni ba kawomin zakiyi ba,lefe nakeso ki hada na maimunatu dana samiha,banason sanya kudina nazo na kasa tambayar jafar,idan nakine sai nafi maida kai ya maida miki kudinki akan kari,so nake komai yayi da kudinsa saboda sai yafi jin auren a jikinsa" dariya anni ta bawa anty maama,ta wani fannin kuma jikin anty maaman yayi sanyi "Wai har yanzu baice komai ba?,baya cewa komai?" Kai anni ta jin jina "Eh,amma ki barni dashi,idan yasan wata ai baisan wata ba,kallonsa kawai nakeyi,zai shigo hannuna ne,baisan wace maryam kumo ba har yanzu" ajiyar zuciya anty maama ta saki "To Allah ya kyauta,ya kuma shiga lamarin" "Ameen ya hayyu ya qayyumu,jabiru ya turo nasa kudin ta hannun hisham,duk da naji yace akwai wasu kayayyakin daya siya musu shida jafar din,daso yayi ya biya harda na jaafar din na hanashi" "Eh gwara da bai biya din ba,gaskiyarki anni,gatan sai yayi masa yawa ya gaza riqe abun da muhimmanci" "Shina gani ai" anni ta fada da qwarin gwiwa,shi yasa takeson anty maama din,saboda tana da matuqar hankali da nutsuwa "Ba damuwa,naga wasu akwatuna sabbin design masu goma goma,zan siyawa jabir a matsayin gudu mawata,shi kuma zan siya masa set daya,set daya kuma zan saka cikin lissafinsa" "Yayi dai dai,Allah ha saka miki da alkhairinsa kema,ya qara muku zumunci,Allah ya qara hadamin kanku" anni ta fada cikin jin dadi "Ameen summa ameen" daga nan suka shiga tsara yadda komai zai kasance daga kan kayan lefen zuwa sauran hidimomi na bikin,harda yadda za'a gyara maimunatu duka anni ta dora saman wuyan anty maama. Bayan ta gama da anni kuma ta koma bangaren qannenta,a sannan su salma sun shigo,nan suka zauna suka tsara komai bisa tsari da kuma burgewa,saidai har suka ci suka cinye hirarsu babu giccin maimunatu. Can cikin garden na gidan ta boye kanta,batajin komai a kan auren tunda batasan meye gundarin abinda ya qunsa ba,bata gama wayewa da sanin meye shi ba,bata saba da zabin abubuwa a rayuwarta ba bare tace wannan zabin bai mata ba,kota damu,kawai dai tana jin kunya da kuma nauyin mutan gidan,tunda tasan meye surukuta,ta gefe guda kuma wani lokacin zuciyarta nayin rawa da kuma d'ar d'ar,tunda ta sani cewa kowacce mace tana auren namijin daya ganta yace yana sonta,itama ta maida masa martanin tana sonshi,amma ita nata angon batasan wanne kala bane,daga wacce duniya zaizo?,yaya kuma zai karbeta?,wadan nan sune kawai abubuwan sa takan nanatawa kanta lokaci zuwa lokaci,saidai yadda taga kowa ya daukaki abun a gidan yana bata mamaki,sannan yadda su laila ke sanyata a gaba,suyita gaya mata abubuwa game da angon nata sai ta yita mamaki,don ita bataga alfanun hakan ba,kiyi kaza kiyi kaza,kullum maganarsu kenan,sun canza mata abubuwa masu yawa,kama daga manta turarenta sa sauransu,itakam duka bataga wannan takurar da tsare tsaren na meye ba,badai a daura aure bane kawai a kaita can gidan ba shikenan dai?,amma magana daya biyu sai suce kina da kishiya,saikinyi kaza kinyi kaza,itakam bataga wani abun damuwa da damun kai ba. ********Cikin tsari ilimi da kuma gogewa anty maama ta hada lefe na alfarma,kowacce amarya ta rabauta da akwati goma goma,rana daya aka kai na samiha dana amaryar jabir Aaliya,said kuma kumbo da ammi abokiyar zaman amma ta qarawa kowacce amarya guda hurhudu,shima kowanne shaqe yake da kayan al'adun aure dana zamani,abun dai ya qayatar ya kuma bada sha'awa sosai. Tarbar girma suka samu daga kowanne bangare na gidajen amaren,suka dawo gida suna yabon tarbar da suka samu,suna kuma tattauna yadda suka fuskanci dangin hajiya Aayah dama ita kanta haj aayah din keji da samiha,kasancewarta diyar fari a wajenta da zata fara aurarwa,su uku kuma kacal Allah ya bata. Gembu aka yanke za'a kai lefan maimunatu,za'a kuma tafi ne har da ita,daa sunce abar kayan basai an kawo ba saboda gudun wahala da kuma zirga zirga,amma anni tace sam,aure za'ayi mata na gata da kuma 'yanci cikin danginta kamar kowacce diya,za'a kai mata kayan kamar yadda aka kaiwa kowa,kuma za'a daukota daga gaban danginta a kawo musu ita. Wannan abun da anni tayi yayi matuqar qara mata kima da daraja a idanun dangin maimunatu,ya kuma qara musu qaimin fidda maimunatu kunya,tare da nuna ita din jininsu ce,duba da abunda bare tayi mata?,ina ga su da suke jininta?. Kamar yadda annin ta tsara kuwa haka akayi,bikin saura sati biyu suka daga gembu da maimunatu da kayan aurenta. Gidan kawu sule suka sauka,qani ne ga mahaifin shatu mahaifiyar maimunatu,mutum ne mai zumunci ba laifi,qaddarar abubuwan da suka farun zasu faru yasa ya barwa fulera riqon shatu dama maimunatu,uwa uba kuma da yadda ta nuna tsananin tausayawar tata ga 'yar uwarta,abinda yaja kawu sule kenan,ya dinga tunanin ko wannan abun ya kawo jituwa da gyaruwar alaqa tsakanin su shatun da yaran inno,yayi tunanin ya barta ko Allah zai sake dai daita al'amarin,kuma har yanzun nan baisan rayuwar da shatu da diyarta maimunatu suka fuskanta ba,yayita yabawa fuleran ma,ya tsammaci aiki tayi da hankali tace a kawo auren nan wajensu sabida girmamawa,baisan ko labari bata dashi ba,sai bayan da yuuma ta tabbatar sun sauka a gembu sannan ta aikaqa fulera da saqon ankai kayan,abinda ya dugunzumata,ya kuma bata mata rai,kamar yadda suke da maimunatu amma ace sai daga wajen baare zata samu labarin aurenta?,ta kuwa ci alwashin tafiya gembu cikin satin ko satin gaba,lallai sai ran kowa ya baci,idan sunsan wata ai basusan wata ba. 😊😊😊😊😊 *_SHIN KINA YIWA KANKI DA JIKINKI TANADIN SABULAN WANKA MASU KYAU MAI DA TSOHUWA YARINYA KO KEMA HAR YANZU DANGWALI YABA KIKE SAWA JIKINKI?_* *_SABULUN DAKE GYARA JIKI DA FUSKA YA MAIDA FATA TAMKAR TA JARIRI SABUWAR HAIHUWA?_* *_SABULUN DA DUK INDA KIKA SHIGA FATARKI ZAKI FITA DABAN DATA SAURAN MATA?,YA MAIDAKI TAMKAR WATA DAN DAREN SHA HUDU?_* *NASAN ZAKIYI TUNANIN A INA ZAKI SAMU WANNAN INGANTACCEN SABULUN?AMSAR ITACE_* *_J-SKIN CARE PRODUCTS (JANNAT SKIN CARE PRODUCTS)_* _SUKE SAMAR DA KALOLIN SABULAI NA KECE RAINI KAMAR HAKA_ Black soap Kiddies Black soap Sugar body scrub Body butter Kojic acid soap Turmeric soap Goat milk soap Honey soap Carrot soap Face and body cream Hair growth oil *_dukka wadan nan kalolin sabulai J-SKIN CARE PRODUCTS sun samar muku dasu bisa farashi dai dai da aljihun kowa_* *_Baya ga haka kuma,wani abun qayatarwar,suna karbar kwangilar yin sabulun cold process ga masu yin biki ko suna_* *Zaku iya dubasu a shafukansu na sada zumunta* *Instgram*:J-skincare products *Tiktok*:jannatskincare *Ko ki tuntubesu kai tsaye ta wannan number wayar* 0813 801 1240 *J-skin care products,DUNIYAR SABULAI MAI DA TSOHUWA YARINYA* 26 Kulawa me kyau maimunatu ta dinga samu daga wajen yadikko matar kawu suleman,itace matarsa ta biyu,kuma tafi daada saratu quruciya,don haka ta zage da bawa maimunatu duk wasu kaye kaye irin nasu daya kamata ace amarya tayi amfani dashi,sannan ta zage ta dinga karantar da maimunatun mene ne aure?,waye miji da sauransu,abubuwan da suka sake fadada tunanin maimunatu,ta wani fannin kuma suka sake haifar mata da wani tunanin na daban "Wannan shine aure?,irin zaman da zanyi kenan da mutumin da bansan waye shi ba?,shima baisan wacece ni ba?" Abinda ta yita juyawa kenan cikin ranta. ***********Zaune yake gaban laptop dinsa,ya baje takardu yanata shigar da wasu bayanai cikin system din,gaba daya hankalinsa kacokam yana kan aikin,wanda ya share kwanaki uku yana yinsa,burinsa ya kammale komai waje daya ya kuma gama da wannan aikin. Wuninn ranar ko abincin kirki baici ba,sai uban coffee da yaketa danqara,lokaci lokaci kuma ya hada da cake,ko a yanzunma mug din daya sake tsiyaya coffee din na gefansa,ya dauka a hankali yakai bakinsa ya kurba ya maida ya ajjiye,dai dai sanda jabir ke qarasowa wajen,hankalinsa akan ja'afar,hannunsa kuma riqe da wasu rantstsun invitation cards,mamaki fal randa da zuciyarsa na yadda baiji ja'afar din yace komai ba kan yadda IV din nasu keta trending yana yawo tsakanin family and friends,duk da ya lura aiki yakeyi wurjanjan a kwanaki ukun nan. Yaji isowarsa amma bai juya ba sakamakon shigowar wasu emails har kusan hudu a jejjere,sai yayi minimizing abinda yakeyi ya tafi kai tsaye ga email din,don dama yana jiran wasu bayanai daga secretary dinsa,yace masa a daren ya kammla su ya turo masa. Maimakon secretary dinsa sai yaga saqon daga wajen hamza BBY yake,daya daga cikin abokansu tun na makaranta ake kuma tare har yanzu,budewa yayi gajeran rubutune da kuma hoto daga qasa sa bai budu ba _Allah ya sanya alkhairi manya,da ba'a gaya mana ba JB ya gaya mana,Allah ya nuna mana lokacin big boos,i salute you🫡,biyu ka b'aro ashe_ Danna hoton yayi, within seconds ya bude, invitation ne dake dauke da sunansa,da sunan samiha da maimunatu,mutuwan zaune yayi,wani bacin rai yana ratsashi,ya dunqule hannunsa waje daya yana furzar da wata iska daga bakinsa,da gaske suke kenan,ba zasu fasa ba?. Dai dai lokacin da jabir ya zagayo gabansa,yaja wata kujerar ya zauna yana zube masa IVs din a gabansa "Ga hard copies" wani kallo ya watsama jabir din,wanda banda ya saba da irinsa ba shakka sai ya razana "Are you in your sense?, what did you do?,su suna nasu kenan kai kana naka?,to sai kasan ya zakayi da mutanen daka gayyato da labarin qanzon kuregenka,don banga abinda zai kaini nigeria a yanzu ba bare na fuskanci abinda yake shirin faruwa" sai ya miqe ya fara tattara abubuwansa masu muhimmanci,huci kawai yake kamar wani maciji "Da kaje da kada kaje babu abinda zai canza,so gwara ma ka nutsu ka karba abun hannu biyu,ka kuma fuskanci abinda ke gabanka dude" baiko daga kai ba bare ya bashi amsa,ya gama kwashewa ya wuce yabar masa wajen. Dariya jabir ya saki yana kada kai,duk duniya su qalilan ne suka iya zama da ja'afar,cikinsu shi da shaheeda sun shiga ciki,shi yasa kowa yake jinjina mata har yau da bata raye,yana da murdadden hali da kuma wuyar sha'ani qwarai. Sanda ya shiga dakin kasa ci gaba da aikin yayi,ji yake kamar yaci kansa,wani irin bacin rai ya dinga taso masa,yakai ya kawo yana jin wani huci na fita saman fuskarsa,idanunsa suka kai kan dan qaramin frame dake dauke da hoton shaheeda,sai ya qarasa wajen ya duqa "Why did you go and leave me?" Ya furta a hankali yana kai hannunsa saman fuskarta dake qunshe da faffadan murmushin nan nata me sanyi,sai ya miqe da sauri da nufin yiwa zuciya da harshensa linzami,ya kuma ja da baya yana fadin "Astagfirullah wa'atubu ilaika" yaqi yake da kansa ba tare da sanin kowa ba,bayason maida hannun agogo baya,bayason wannan mode din da yake zama out of sense,yanaso yayi nisa dashi,sai kawai ya fidda wayarsa ya duba cave mafi kusa dasu ya kirasu suzo su fiddashi,kayan jikinsa ya fidda ya sauya wasu ya jefa wayarsa a aljihu ya fito,jabir na zaune anan yana ta duba tarin saqonnin mutanensu,baice masa komai ba yadai bishi da kallo gami da tabe baki har ya fita. Cikin mota kwanyarsa ta cake sosai,neman dukka hanyoyin da zai kaucema wannan auren yake,ana tsaka da wannan kiran wayar dr marwan abbi ya shigo wayarsa. Sai daya sauke gauron numfashi sannan ya daga wayar,sallamarsa kawai dr ya amsa ya hau balbaleshi da fada,ta inda yake shiga ba ta na yake fita ba,maganarsa ta qarshe itace "Duk abinda kakeyi ka barshi,kada ka sake jabiru ya baro turkey ba tare da kai ba,ka biyoshi ku dawo gida" daga haka dr ya kashe wayar. Hannunsa guda daya ya sanya yana yamutsa sumar sa gami da kallon yadda suke wuce titi bayan ya sulalar da wayar gefansa,jin abun yake kamar mafarki,duk inda bacin rai yake ransa yakai nan wajen baci,zuciyarsa ta gaya masa jabir ne ya shaidawa abbi abinda yace "I will deal with you jabir,definitely" ya fada cikin huci kamar jabir din yana kusa dashi. ********Kwanansa uku cur bai dawo gidan ba tun ranar daya fita,jabir yayi kiran yayi kiran har ya gaji,gashi dai kiran yana shiga,amma sai ja'afar din yayi rejecting,daga bisani jabir ya daina baiwa kansa wahala ya dakata da kiran nasa,don yasan tabbas a yanzun bazai daga ba,bazai kuma saurareshi ba. A rana ta hudu ya iso gidan,tunda yayi knocking sau uku ya tabbatar jabir din baya nan,sai ya sanya key dinsa samfurin katin cirar kudi na atm ya bude qofar ya shiga. Sai daya kunna qwai haske ya gauraye falon sannan ya wuce dakin baccinsa,yana tura qofar idanunsa suka sauka kan hoton shaheeda,sai yaji kamar ya jima bai kalli hoton nata ba,don haka ya qarasa a hankali,ya zauna gefan gadon nasa,sannan ya dauki frame din hoton. Yadan dauki wasu sakanni yana kallon fuskarta,kafin ya ajjiye frame din bayan yayi kissing hoton,ya kuma karanta mata addu'a cikin ranta kamar yadda ya saba. System dinsa ya dauko hade da charger dinta ya fito daga dakin,don dama kusan itace ummul'aba'isin dawowarsa gidan,sai kuma ya koma da baya,saboda tunawa da yayi da maganar da sukayi da abbi,ya buda wardrobe dinsa ya ciro passport dinsa ya sanya a aljihunsa ya dawo falon,ya jona caji a system din ya kunnata sannan ya wuce kitchen, fridge ya bude yana laluben abun sha,duk ya gama bulayin sa daga sama zuwa qasan fridge din amma baiga drink din da yayi masa ba. Wani mix fruit ya dauka,saidai yana gama karanta rubutun jiki yaja tsaki ya maidashi,a qa'ida shan abun sha na kwalba gwangwani ko roba basu dameshi ba,yafison abun sha irin namu da gargajiya da za'a hada a gida,kamar kunun aya zobo da sauransu,daga qarshe ya dauki wani matstsen ruwan lemon zaqi hade da cup ya dawo falon. Bai jima da fara aikin ba jabir ya iso,daga sallamar sa daya amsa bai sake bi ta kansa ba,shima jabirun sai ya shareshi,saboda ha fuskanci abun sai 'yar tursasawa kadan ta shigo ciki,dole sai an ma ja'afar haka idan anaso rayuwarsa ta dai daita nan kusa,don haka shima sai ya wuce daki abinsa. Sai da yayo wanka ya canza kaya sannan ya dawo falon,saman hannun kujerar dake daura da ja'afar din ya zauna yana fadin "Ka gama yajin kenan kayo bikon kanka da kanka" maimakon ya amsa masa,sai kawai ya ciro passport dinsa ya cillawa jabir din. Bin passport din yayi da kallo,kafin ya sanya hannu ya dauka ya soma budewa yana dubawa. Idanu jabir ya fidda waje sannan ya dorasu saman ja'afar din "Over stay?" Kamar bazai amsa shi ba,sai kuma yace "Yes" a daqile yana ci gaba da concentrating kan aikinsa,ajiyar zuciya jabir ya fitar yana daga passport din daga fuskarsa "Ya Allah,why ja'afar?,kasan visa dinka ya qare amma kaci gaba da zama musu a qasa baka biya anyi expanding maka ita ba?ka sani turkey ba kamar kowacce irin qasa bace, you know how people suffer before they get the visa....shine ka samu suna baka whenever you need zakayi wasa da damarka?" "I don't like noises please,idan zakayi abinda ya dace kayi,if not ka ajjiyemin passport dina ka qara gaba ka barni naci gaba da zama,dama ban shirya tafiyar ba" gimtse dariyarsa jabir yayi,ya gano shi sarai,neman duk hanyar da zaya kubucewa komawa yakeyi "Alright,sai kamin transfer abinda za'a kashe ta account dina,kasa dole sai na nema baaba ambassador" ya fada yana bata rai shima hadi da miqewa "Bani dako sisi" ya fada kansa tsaye "Kut!" Jabir ya fada yana fito da ido waje,dariya kuma na masa yawo can qasan ransa,lallai ja'afar din mugun dan rainin wayo ne,recently yaga amount din dake qaramin account dinsa ma,wanda shine baya ajiya kudi mai yawa a ciki,the amount is very huge,kamar yasan me yake tunani,sai ya daga kyawawan idanun nan nashi dake dauke da wani irin sinadari mi qarfi ya zubewa jabir su "I mean bani dako sisin da zan batar don komawata gida,bcoz ban shirya ba" dole dariya ta subucewa jabir,cikin ransa yace "Kayi ka gama,komawa gida dole,mu lafiyarka da hankalinka mukeso,tafi mana kuma komai" "Okay,.....duk naji,but bani zan maka komai ba,you know,dole kaje da kanka,tunda kai mai laifi ne a wajensu yanzu" kamar bazai amsa ba kafin yace "Naji" ciki ciki,kada kai jabir din kawai yayi yana nufar kitchen,cikin ransa yana fadin "Allah ya shirya ja'afar,mai zama dashi sai ya shirya,zuma ga zaqi ga harbi ga kuma ba tsoro" . Abinci ya shiryo musu,ya kuma kawo har nan inda ja'afar din yake,yanata wani ciccijewa da basarwa amma jabir yayi kamar bai gane me yake nufi ba,ya gama daagiyar duka ya sauko suka fara cin abincin. Yadda jabir din yaga yana ci ya tabbatar masa a kwanakin da ya qauracewa gidan bai cin wani abincin kirki,dama can shi din irin mutanen nan ne da ba abincin kowa suke iya ci ba,sau tari sun gwammace su haqura da abincin,sai yaji tausayinsa ya darsar masa a rai,yaji har cikin zuciyarsa yana fatan wannan auren ya zame ma rayuwar ja'afar din wani babban sauyi da kuma ci gaba,suna gamawa kiran amaryarsa ya shigo,don haka ya miqe yabar wajen,jaafar ya bishi da tsaki da kuma harara,ganin yadda yaketa zumudin amsa kiran nata. 😊😊😊😊😊 *_SHIN KINA YIWA KANKI DA JIKINKI TANADIN SABULAN WANKA MASU KYAU MAI DA TSOHUWA YARINYA KO KEMA HAR YANZU DANGWALI YABA KIKE SAWA JIKINKI?_* *_SABULUN DAKE GYARA JIKI DA FUSKA YA MAIDA FATA TAMKAR TA JARIRI SABUWAR HAIHUWA?_* *_SABULUN DA DUK INDA KIKA SHIGA FATARKI ZAKI FITA DABAN DATA SAURAN MATA?,YA MAIDAKI TAMKAR WATA DAN DAREN SHA HUDU?_* *NASAN ZAKIYI TUNANIN A INA ZAKI SAMU WANNAN INGANTACCEN SABULUN?AMSAR ITACE_* *_J-SKIN CARE PRODUCTS (JANNAT SKIN CARE PRODUCTS)_* _SUKE SAMAR DA KALOLIN SABULAI NA KECE RAINI KAMAR HAKA_ Black soap Kiddies Black soap Sugar body scrub Body butter Kojic acid soap Turmeric soap Goat milk soap Honey soap Carrot soap Face and body cream Hair growth oil *_dukka wadan nan kalolin sabulai J-SKIN CARE PRODUCTS sun samar muku dasu bisa farashi dai dai da aljihun kowa_* *_Baya ga haka kuma,wani abun qayatarwar,suna karbar kwangilar yin sabulun cold process ga masu yin biki ko suna_* *Zaku iya dubasu a shafukansu na sada zumunta* *Instgram*:J-skincare products *Tiktok*:jannatskincare *Ko ki tuntubesu kai tsaye ta wannan number wayar* 0813 801 1240 *J-skin care products,DUNIYAR SABULAI MAI DA TSOHUWA YARINYA* 27 *********Sosai maimunatu takejin dadin zama gidan bappa sule,saboda tana samun kulawa qwarai da gaske,ga kuma 'yammatan 'ya'yansa da suke kusan sa'anni da ita,hanne da hauwa,sun fita wayo da kuma gogewa,don inda suke din ba za'a kirashi da karkara ba,maraya ce,jininsu ya hadu sosai saboda kirkinsu da yadda suke nuna mata qauna da janta a jiki,nan da nan shaquwa ta shiga tsakaninsu,abun na yiwa maimunatu dadi,ashe dangi dadi garesu,koda ace batasan dangin mahaifinta ba,amma a qalla samun wadan nan a kusa na dauke mata kewa da fargabar rasa dangin mahaifi da kaso hamsin cikin dari. A lokacin maimunatu ta sake tabbatarwa kanta lallai inna furera shigo shigo babu zurfi tayi musu,a duk sanda tazo gembu ashe nuna musu take komai lafiya lau,sannan maimunatu najin dadin can shi yasa taqi biyota nan ganin dangi,abunda yayi matuqar baiwa maimunatu mamaki,kasancewarta miskila ba kasafai takan buda baki tacewa inna furera zata bita b,saidai ita kanta takan karanci tsantsar yadda maimunatun ke son biyotan,don tasha gwaba mata baqar magana kan cewa duk ta gama nacin da qwallafa ran,wataqila ita da gembu sai idan taje yawon arba'in idan ta haihu gidan buderi,wani lokacin saidai ta sakaye taci kukanta,wani lokacin kuma har hanya take bin inna furera cike da fata da kuma burin zataji tausayinta ta tafi da ita,saidai ko sau daya bata taba sauyawa ba,daga bisani data qara wayo sai ta tattara ta qyale,ta sanyawa ranta dangana da haquri. A sannan maimunatu taga kara ta dangin mahaifiyarta da zumunci,kowa da abinda zai kawo bisa al'adar auren fulani,basu duba cewa DR yace abar komai zai mata ba,cikin qaramin lokaci aka tara mata kayan amfanin kitchen irin nasu kala kala,wanda ba lallai a sameshi a can ba. **********Biki ya rage saura sati guda kacal,tun a lokacin hidima ta balle daga kowanne bangare,gidan dr da kuma gidan minister harda gidansu amarya ga jabir wato fatima,saidai hidimar da ake gidan minister zata baka mamaki,kai kace bikin yara shida za'ayi ba yarinya daya ba,tun a kwanaki bakwai din da sukayi saura gidan ya fara karbar baki. *********Katafaren beauty parlor ne,wanda aka tanadeshi musamman saboda gyaran jiki,turara jiki,fidda duk wata dauda,tada komada da maida tsohuwa yarinya a zamanance,waje ne na wane da wane,waje ne na idan ka isa ka shiga. Daga cikin wajen fira ce ke tashi,da alama mata an hadu,kuma an samu abunda ake buqata,qawayen amarya samha ne,kowacce da abinda ake mata a wajen,wasu gyaran manicure and pedicure,wasu gyaran gashi,wasu kuma lalle ake zana musu,yayin da wasu kuma ake musu gyaran fuskarsu don su sake kyan gani a wajen bikin. Gefe guda amarya unaisa ce cikin wata irin riga data lullube jikinta da ita,sai kanta kawai ake gani,hayaqi dake cike da qamshi ne yake futowa daga wuyanta,magana suke qasa qasa ita da wata matashiya kamarta dake gefanta,wanda hayaniyar da sauran keyi yasa ba zaka iya jin me suke fada din sosai ba saika matsa kusa dasu "Na samu information.....jibi zai dawo nigeria" "Na rasa wanne irin so kike masa samiha,ta ya zaki auri mutumin dako zance bai taba zuwa wajenki ba bare ayi maganar so?" Murmushi ta saki tana girgiza kai "Ba zaki gane ba husna,ja'afar na daban ne,irinsa ba'a jiran sai sunzo zance kafin su cancanta a auresu,na musamman ne shi,sabodashi naqi aure har sai da na samu cikar burina ta hanyar daddy,na nace duk da yayi aure,har Allah ya qaddara rabona ne,matarsa da yake matuqar so ta rasu,saboda shi naqi auren unais naqi auren ahmad naqi auren hanif ke da duk wanda kika sani" kai husna ta jinjina "Amma wanne qwarin gwiwa kk dashi na cewa zai soki?,da har zaki auri mijin matacciya wanda yake cikin halin SO BAYAN RAI?" Murmushi ta sake saki "Karkiji komai,duk abinda kk so baka gajiya dashi,soyayyar da nake masa ita zata ja mana ragama,i will do all my best naga ya soni,kada ki manta,ni ba qaramar mace bace,na hada komai da kowanne namiji zaiyi sha'awa ya kuma burgeshi" "But kin manta kina da kishiya kenan" murmushin dake nuna hankalinta a kwance yake ta saki "Kusan hakan gaskiya,yarinya ce qarama wadda ta fito daga ruga,kinga yaushe zata tsoratani?,beside ma kuma itama hadi ne,rigima ce irin ta kakanni kawai,abun ma dariya yake ban idan na tuna,namiji irin ja'afar da wannan a matsayin mata idan banda rigimar tsofaffi?very classy guy,har na fara imagining yadda zai fatattaketa wlh a kurkusa duk sanda suka fara haduwa da ita" ta qarashe fada tana sakin dariya,don ta tabbata abinda zai biyo baya kenan,wannan shine yaqini bisa hasashenta. Ita kanta husna data hasaso ja'afar din,ta kuma san wayeshi da yadda yake,sai taji hasashen unaisan haka yake,'yar ruga?,ba shakka kam bazai iya zama da ita ba,kamar yadda tayi amanna ba zata iya goga kishi da kyakkyawa kuma me aji irin qawarta unaisa diyar minister ba. _ba'asan maci tuwo ba sai miya ta qare,muje zuwa_ **********Ƙarfe hudu na rana agogon turkey,biyu na rana agogon nigeria jirgin Turkish airline ya sauka a filin sauka da tashin jirage na malam aminu kano,dauke da tarin passengers,ciki harda jabir usma khalid akko da ja'afar marwan khalid akko. Dukkansu sanye suke da wasu lafiyayyun Italian suit,kalolin da suka dace da gayu aji da kuma kyansu,duk wanda ya kallesu sai ya maida kansa ya dada kallonsu,zaratan fulanin samari guda biyu,wadanda ilimi hutu da kuma kudi ya ratsa kowannensu,jikoki kuma jinin khalidu akko. Zaman jiran jirgin da zai tashi zuwa gombe sukayi,wanda duka duka bai wuce awa guda ba suka daga zuwa gomben. Ta gefan idanu jabir yaketa karantar ja'afar tunda suka sauka a qasar,fuskarsa kadaran kadaham take,babu walwala hakanan ba wata fara'a bace saman fuskar tasa ba,hannunaa guda daya yana soke a aljihunsa,har zuwa sanda suke nufar motar da tazo daga gidan Dr marwan domin kaisu gida. Muslimu driver din abbi shine yazo daukansu,cikin wata baqar range Rover,ko ba'a gaya maka kasan cewa sabuwa ce,sai qyalli take da daukan idanu,jabir yayi tsammanin samun masu tarbarsu bayan muslimun da zai tuqa su,saidai babu kowa saishi din,sai ya alaqanta hakan da shakkar ja'afar da sukeyi,don ba kasafai ko a baya zasuyi tafiya tare a samu masu tarbarsu ba. Cikin matuqar girmamawa da jin dadin dawowarsu muslimu ya gaidasu,sannan ya sanya jakankunansu a mota,ya shiga ya tada motar suka dauki hanya. Tunda suka hau hanyar idanunsa na bisa titunansu,yana qiyasta watanni da ya share bashi qasarsa,watanni ne masu dan dama,dashi kansa baisan gudun da suke ba sai yanzu. Tazarar dake tsakanin gidan dr marwan akko da airport din ba mai yawa bace,dalilin da yasa basu dauki wani lokaci mai tsaho ba suka isa gidan. Bin ginin gidan nasu yake da kallo kamar wanda a yau yafara arba dashi,ba komai yake kallo ba sai sabon fenti da yaga anbi gidan dashi duk da girma da fadinsa,cikin qanqanin lokaci yaji zuciyarsa na masa qunci,da gaske shirin bikin suke kenan,sai ya dauke kansa daga inda yake kallo din,ya sanya hannu ya bude murfin motar ya fito ya biyo bayan jabir. Tun a harabar gidan tarin ma'aikata dake aiki a qarqashin gidan suka fara musu maraba,kusan da jabir ya barsu,dama shike da wannan juriyar,ya sanya kansa zuwa cikin gidan,a yau din da yake a cikin gidan,sai yaji wani irin kewa da zumudi mai yawan gaske nason ganin mahaifiyarsa ita da gudan jininsa amna,baisan yayi kewarsu kamar hauka ba sai yanzu da yake a kusa dasu. Da tattausar muryarsa mai zurfin nan yayi sallama cikin falon nasa,haj aishatu dake nutse saman kujerun alfarma da aka yiwa falon nata qawanya dasu ta daga kanta daga duban farar takardar dake dauke da rubutu a hannunta tana amsa sallamar tasa,idanunsu suka gauraya da juna,ta saki boyayyar ajiyar zuciya mai nauyi "Alhmadlh ya rabb" ta fada can qasan zuciyarta,sai ta dubi matar da suke tare "Ki shiga ciki kice ina samra?,ta baki waje kici abinci,zan kiraki mintuna kadan" miqewa tayi tana godiya,sannan tabi hanyar da zata sadata da farfajiyar sassan haj aishatun da take kamae qaramin tsakar gida mai siffar garden da aka wadata da wasu fararen duwatsu na wuta. Ci gaba yayi da takowa cikin falon,yayin da amma wannan karon tayi qoqarin ajjiye kunyar dake tsakaninsu "Maraba lale,ashe kuna gab da isowa?" Wani dan qaramin miskilin murmushi ya subuce masa,ya qaraso gabanta ya zube ya soma gaisheta,tana amsa masa itama cikin kulawa tare da karantar yanayinsa. Baiyi wata qiba ba sam,saidai jikinsa a murje yake kadan,sai kuma fatarsa data sakw fresh da kuma haske,alamin weather din qasar data karbeshi,akwai maganganu masu tarin yawa dake ran amma,saidai a yanzun kamar yayi wuri tace komai,don haka ta barwa lokaci na gaba idan suka gama warwarewa daga gajiyar tafiya. Yadda ja'afar ya zube mata haka jabir,don marabarsa da ja'afar din daukan cikinsa ne na tsahon wata tara ne kawai batayi ba. Kusan shi ya fara fita yabar jabiru da amma,wanda dama koda a baya abun kusan haka yake,hirarsu da amman bata qarewa,zaka sauka jabir ya haifa ba ja'afar ba. Yana fitowa sukayi kacibus da ammi,kana kallonta kasan an fara shiga hidima,daga boys quarters na gidan take,taje ta duba yadda aka gyara gami da tsara wajen saboda saukar baqi 'yan biki. "Oyoyo,saukar yaushe?,ina ta ciki ban jiku ba?" Murmushin gefan baki yayi,ya gaidata itama a girmame kamar yadda suka saba "Me zakuci?,don gidan gaba daya a hargitse yake,banjin zaku samu kalar abincin da kuke so" "Ki turo mana hisham kawai ammi" muryar jabir dake tahowa daga baya ta bata amsa,don yasan halim ja'afar din sarai,tsaf zai iya cewa "We are okay" bayan shi magana ta gaskiya yunwa yakeji "Banajin zaku samu hisham cikin gidan nan jabir,gidan yau kusan babu kowa sai baqi,yana can hidimar saukar nasu baqin" "Ba damuwa zan kirashi" jabir ya fada suka soma gaisawa sannan shima yabi bayan ja'afar wanda ya wuce sassan anni,ammi tayi gaba tana tunanin abinda zata sa a samar musu me dan sauqi da zasu iya ci. Sanda ya sanya kai falon har yayi kamar zai koma saboda muryoyin baqi da yaji sai kuma yaci gaba da cusa kai,sai daya shiga din sannan ya fuskanci su waye a falon,anty maama ce,sai ummi badi'a matar uncle abbas. Qaramin tsaki yaja qasan ransa,su kadai amma sun cika falon da hayaniya kamar mutum dubu,dukkansu maraba suke masa banda anni da taja bakinta ta tsuke,ya qaraso ya zauna saman hannun kujera yana amsa marabarsu,kafin dukansu su biyun su miqe anty maama tana cewa "Anni bari muje,nan da awa biyu idan bamu dawo ba don Allah hayatu ko muslimu suje su debomin yaran nan" "Zan gaya musu,amma kada kuje ku zauna kuma" "Muna samo abinda mukeso zamu dawo" "Allah ya tsare" suka amsa suna ficewa,sai falon ya rage saura shi da annin. "Barka da warhaka" ya fada cikin rusunawa "Barkan ka" ta bashi amsa a taqaice tana bata fuska,saidai a yau din baiji bata fuskarta ya dameshi ba kamar yadda suke da ita a baya,yana jin a wannan bigiren shi yafi cancanta ya bata fuska akan kowa "Ina wuni?" "Daban wuni ba zaka ganni?,ai da zamanka kayi a sassanka,ni yafi cancanta nazo na gaisheka ai,tunda yanzu ka zama uban kowa,sai abinda kakeso ka tsara zamu dinga bi,tunda kaika haifi kanka" kyawawan idanunsa ya lumshe kana ya budesu,ita tsohuwar batasan abinda yakeji bane?,batasan irin qunci da ciwon data haddasa masa ba haka siddan yana zaman zamansa yana lallaba rayuwarsa? Muryoyin sallamarsu ta katse anni daga ruwan tijarar data debo ta shirya sauke masa su tas yau a kansa,duka 'yammatan gidan ne suka shigo,wansa dawowarsu kenan daga gyaran gashi. Da hayaniya suka shigo saboda yadda sabgogin bikin suka fara musu dadi,amma suna hada idanu kowacce sai tayi turus,ta kuma saita bakinta,kudin goro ya yiwa gaisuwarsu ya amsa su gaba daya,babu wadda tayi gigin zama dukka suka juya suna barin sashen,daidai lokacin da amna wadda aka yiwa kanta gyara na musamman take rugowa cikin falon riqe da leda a hannunta cike da kayan qwalam tana qwalawa anni kira gami da cewa tazo suci. Cak ta tsaya sanda tayi idanu hudu da mahaifin nata,sai kuma ta watsar da ledar hannun nata,ta take da gudu tayo wajensa tana kiran "Dadddyyyyy...." Qasa ya sauko ya tanqwashe qafafunsa,ya kuma bude mata hannayensa gaba daya,yana jin wata irin qauna da qarfin jini dake tsakanin uba da diyarsa yana fusgarsa,ta kuwa iso ta fada jikinsa,ya sanya hannayensa gaba daya ya rungumeta cikin jikinsa yana sauke ajiyar zuciyaSosai ta qanqameshi itama kamar zata koma jikinsa "Daddy" ta sake kira tana sauke ajiyar zuciya bayan shuru da tayi na wasu sakanni,dukka gaba dayansu shida annin sai tausayinta ya lullubesu,ya dagata sosai ya sake tallafarta yana dubanta "Amnee" ya kirata da sunan da shaheeda kadai take kiranta da shi "Daddy....kaima shine ka tafi ka barni?,mommy ta tafi,amra ta tafi,kaima haka?" Kai ya girgiza yana shafa sumarta da tasha gyara tana ta qyalli "Am sorry my little angel......daddy yana neman afuwa,bazai sake tafiya ya barki ba" fuskarta ta washe sosai,da alama taji dadin maganarsa,sai kuma ta sake cune fuska "Adda maimoon ma ta tafi,har yanzu bata dawo ba,daddy zaka je ka dauko min ita?" Anni ya kalla da alama yana da buqatar qarin bayanin sanin wacece ita,kamar kuma ya jijji sunan a bakin annin da ammansa,ganin anni bata bashi wani hint da zai gane wacece ba sai ya gyada kai kawai "Zan dauko miki ita lil princess" qanqameshi tayi tana murna "I love you daddy" "Love you more amne na" sai ta shige jikinsa tana sauke ajiyar zuciya dake nuni da samun cikakkiyar nutsuwa. Karamin tsaki anni ta sake "Kalli.....wannan daukar hakkin har ina?,Allah ya kyauta wannan banzar zuciyar taka data kasa daukan kalar tata qaddarar" bai tankawa annin ba,don yasan jiqaqqiya ce tsakaninsa da annin,kuma ba zata qyaleshi ba tabbas sai ta maida masa kai tsaye ko kuma a fakaice. Koda ya tashi tafiya qin yarda amna tayi ta sauka daga jikinsa,tana maqale dashi,da ita yatafi sassansa,ya samu.jabir har ya fito a wanka,yanata fama da wayoyin al'umma. *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 28 Wani kallo ja'afar ya watsa masa,da alama gayyar al'umma yayo musu,wanda shi baisan da hakan ba,bai kuma shiryama tarbar kowa ba,dakinsa ya wuce ya sauke amna saman gadonsa,tana ta faman zuba masa surutu,labarai iri iri,a lokacin idan kaganshi kai baka ce miskilin ja'afar din nan bane,mai yawan dakiya tsare gida da kuma shan qamshi,duk yabi ya cika fuskarsa da fara'a,hakanan duk tambayar da amna tayi masa sai ya bata amsa,saidai da yake halin a jininsa yake,ba jimawa yaji kansa ya fara cakewa da surutun amnan "Amnee.....pls be quiet for a while,ki huta kada maqogoronki yayi ciwo,zanyi wanka,idan na fito then sai muci gaba" kai ta gyada masa,sai dai tun bai gama fidda kayan jikinsa ba taci gaba daga inda ta tsaya. Yana daga toilet din ma yana saurarenta,murmushi kawai ya saki ya girgiza kai "Surutun waye tayi haka?,shaheeda?,nooo....shaheeda nada hira,amma bata da surutu me yawa,salma?,laila?,hafsah?,maybe ya amsawa kansa da kansa yana tabe baki. Sanda ya fito ya taddata da jabir,da yake shi din sarkin yara ne ya biye mata sosai sunata sabgarsu,sai ya juya ya buda walking wardrobe dinsa ya shiga yana duba kayan da zai saka,kafin ya futo sun fita,sai ya fasa shirin fitar da yayi niyya,ya saka boxer dinsa kawai ba tare daya nema ko singlet ba,turarukansa ya fesa,sannan ya shafe lallausan baqin gashin dake cike aqirjinsa wani irin azababben oil perfume,yabi lafiyar gadonsa ya kwanta,bayan ya ragewa dakin haske ta hanyar sauke duka labulayen dakin,ya kuma kashe duka fitilun dakin. Bacci yayi sosai mai wani irin nauyi da dadi wanda ya jima baiyi irinsa ba,knocking da ya dinga ji sama sama cikin barcinsa ya sanyashi bude kyawawan idanunsa da suka qara girma saboda bacci,yadan mutstsukasu kadan,sannan ya ture lallausan duvet din daya rufe jikinsa dashi,ya zuro qafafunsa qasa yana miqewa,ya isa qofar ya bude. Jabir ne dauke da amna,kwalliyar jikinsa ta bambanta data dazun "Wanne irin bacci kake?,ko a masallaci ban ganka ba" "What?" Ya fada calmly,ya aza idanunsa ga agogo,sai yaga har bakwai tayi,a hanzarce ya saki handle din qofar ya shige toilet don ya daura alwala. "Na shirya zan fita mukaci karo da abbi yana dawowa,yace na gaya maka yanason ganinmu after isha prayer" kai kawai ya gyada masa,yana budewa amna hannunsa,ta taho da hanzari tana ci gaba da zuba masa surutunta,tare da bashi labarin inda sukaje dazun,sai jabir ya miqe ya fita ya basu waje. Yana shirin fita sallar isha din hisham ya shigo,cikin girmamawa ya gaidashi,ya amsa masa yana sanya qaramar hular tashi ka fiya naci saman sumarsa "Ina kaje duka yau?" Kansa yadan shafa "Ina da patient ne yau a asibiti da yawa da zan gani,so bayan kuma na gama dasu na wuce wajen gidan yaa jabir,na sallami companyn da suka zuba home decor na gidan" kansa ya gyada kawai,hisham din ya daukar masa abun sallah suka fito zuwa masallacin suna taba hira kadan kadan. Sai daya sake komawa ya duba ammansa,sannan ya wuce sassan anni,ya nema abinci wajen baba tabawa,wadda dama tun da can gurinta ko wajen ammansa yake cin abinci duk gidan,to sassan amman nasa yaga ya soma cinkoso,bazai iya tsayawa karbar komai na sassan ba,don bashi da tabbacin amman itace ta girka duk abinda za'a bashin. Yana ankare da yadda annin keta faman cin magani,sai shima ya basar kamar bai gani ba,ya zauna sosai hankali kwance yana cin abincinsa,cokali daya bakinsa,cokali daya bakin amna hira,duk tabi ta cikashi da zancen adda maimoon,kome yayi mata sai tace 'haka adda maimoon takemin'. Yana gamawa cikin sa'a yaji shigowa abbi,don haka ya miqe yana dauke da amna "Kaje ka dawo,kazo muyi lissafin kudin kayan lefen da maama ta ranta maka ka zube mata abunta" "lefe?,lefen wa?" "Au da tattabaru kayi zaton za'a aura maka?,ko kuma babyn roba na wasan yara?,'ya'ya ne kamar kowa masu gata,ehe" anni ta maida masa amsa sannan ta fuske,sai kawai ya juya baice da ita komai ba ya fice,yana jin haushi yana sake cika masa zuciya. Da sallama ya shiga katafaren falon dr marwan khalid akko,can ya hangesu saman dining shi da jabiru,da alama zamansu kenan,yayi masa izinin ya qaraso,yana jawo kujerar sake daura dashi hadi da nuna amna yace ta zauna,tayi daraf kuwa fa haye ta fara masa surutun nata,har sai da ja'afar yace cikin lallausan muryarsa,very calm "Amnee,pls....keep quiet" narai narai tayi da idanunta,don bata gama bawa daddy dr kamar yadda take kiran abbi ba labarin da take bashi,to amma ita kanta duba daya uban nata yake mata take laushi,dole tayi shuru,ta fara saka yatsanta tana dangwalan romon pepper soup din kifi da aka yiwa abbi. A sannan ya samu suka gaisa da abbi din,ya musu maraba,sannan ya tura masa warmers din yace ya diba abinci yaci "Am full abbi,yanzu na gama ci wajen anni" "Yayi kyau" yace yana ci gaba da cin abincinsa,sai dinning din yayi shuru,kasancewar dabi'ar abbi din,ba kasafai yake cin abinci kuma yana magana ba,har sai ya kammala,shurun da ya sanya ja'afar ciro wayarsa,yanajin abbin da jabir suna magana jefi jefi,wanda kusan duka kan tsare tsaren bikinsu ne. "Bismillahi" abbi ya fada yana zama saman kujerun falon,yayin da jabir da kuma ja'afar kowanne yayi matsugunni a qasa "Kai jabir alhmdlh,mun gama duka maganar da zamuyi dakai.....am ja'afar,abinda yasa na kiraka" abbi ya fadi yana gyara zamansa sosai,gami da cire hularsa ya aje gefe "Inason in tambayeka......wacece ta haifeni?" Girma maganar ta yiwa ja'afar sosai,har sai daya dago suka hada ido da abbi,kana ya maida idanunsa qasa "Anni ce abbi" "Ma sha Allah,to ban sani ba,ko ka manta ne,dani da umar da sagir da abbas da usman.....dukkaninmu anni ce ta haifemu,kuma qarqashin ikonta muke damu da dukka abinda muka mallaka,ba zanyi magana me tsaho ba,saboda nasan kasan matsayinta a wajenmu,hatta da mahaifiyarka zabin anni ce idan baki sani ba,shi yasa ta zamto ta musamman a wajena,na kuma yi dacen da maza dubu basuyi ba,dukka hukuncin da anni ta yanke a kanka yatabbata,kuma ba komai bane ya janyo hakan ba ina da.imanin qauna ce da kuma damuwa da halin da kake ciki,Allah yayi maka wata iriyar zuciya data banbamta data kowa,amma ka sani,jajircewa da karbar al'amura a yadda sukazo suna iya kawo sauyi,hakanan lokaci yana iya warkar da kowanne irin ciwo komai girmansa,duk wani abu da zakayi a yanzu akan aurenka shizai nuna dai dai matsayin anni a wajeka,idan ka wulaqantata ko ka watsa mata qasa a idanu to ni ubanka marwan ka yiwa haka,idan ka karba abun da kima da mutunci,ka kuma riqeshi da daraja to ni ubanka marwanu ka mutunta,saboda haka zabi ya rage naka,dan halak dai shike rama halacci,anni kuwa halacci tayi maka ba butulci ba,zanga dame zaka sakawa mahaifiyata". Maganganu ne gajeru marasa dogon zango,saidai nauyinsu yafi qarfin wani ma'auni ya iya gwadasu,shigen shigen magana irin wannan bata taba hadashi da mahaifinsa ba sai a wannan karon,nauyin maganganun da har dr ta sallamesu basu bar dukan sassan jikinsa ba,har sun kusa fita ya sake kiransa "Ka shirya daga yau zuwa gobe,kaje gidan minister ka gana da unaisa" "Unisa?" Ya fada cikin ransa,yana jin he knew the owner of the name UNAISA,to amma a ina?, somewhere..... somewhere,for sure,indai gidan minister ne,bu he may not remember ainihin inda yasan ta din. Dukka wannan shi da zuciyarsa yake wannan tadin,wanda tuni ya riga yace da abbi "To" yabi kuma bayan jabir sun fice. "Ya?,yau din zamu wuce?,don inason naje naga fatima gaskiya,i missed her badly" yana jin iya maganarsa ta yau ta qare,so saboda haka bashi da abinda zai cewa jabir din,saidai ya masa wani kallo,yana shirin yi gaba jabir din yasha gabanshi "Shawara guda daya J.pls and pls,kayi qoqarin bin maganar abbi,indai har kai din masoyin shaheeda ne da gaske,na tabbatar da tana raye itace mutum ta farko da zata fara tursasaka kabi abinda dukka magabatanka suke so,for the first and last time may be da sukeso kayi musu wani abu cikin rayuwarka,we will see if you can do it" jabir yakai qarshen maganar yana duba yanayin ja'afar,duk da cewa ya bashi baya,kamar yadda ya zata din,baice masa komai ba sai gaba da yayi ya barshi a wajen. Sassansu ya yanke ya koma kawai,saboda kansa gaba daya ya gama daukan zafi,tako.ina abbi ya gama daureshi,tun jabir baice komai ba dama ya riga daya yankema ransa dole ya tsaya ya fuskanci komai,zaiyi duk yadda abbi da anni keso for the sake of them. Ya jima a haka kafin yayi qoqarin dai daita nutsuwarsa,ya daga waya ya turama hisham tex kan ya kawo masa amna,ba jimawa sai gashi da ita,ya dire masa ita ya juya. Jaka guda ta kayan wasan daya jima yana siya ya tura mata,duk sanda ya fita yaga wani abun wasa saiya tuna da ita,sai kuma ya siya ya ajjiye,murna ta ishi amna,ta dauki wancan ta ajjiye,ta dauko wannan ta ajjiye,komai sai data nuna masa,kamar ba shi ya siyo ba. A gaba ya sanyata yana kallo kawai,iya wannan farincikin nasa ya sauke kaso mai yawa daga cikin nashi bacin ran,abu na qarshe da yarinyar ta fada shi ya tashi zaman nasu,ya kuma dawo da mutuwar shaheeda da twin sister dinta amra danya a ransu duka su biyun,kewa da maraicin shaheedan ya kamasu "Daddy.....mommy taqi dawowa,taqi kawomin amra muyi wasa,daddy yaushe zasu dawo?,zanyi fushi fa daddy" cikin jikinsa ya rungumeta,yana shafan gadon bayanta "Kada kiyi fushi,kita musu addu'a kinji?,zamu hadu dasu in sha Allah sooner or later"ya fada yana qoqarin hadiye wani abu mai tauri daya tsaya masa a wuya. Ta jima a haka kwance a jikinsa,yana jin yanayin saukar numfashinta da yadda ta qara nauyi a jikinsa ya tabbatar tayi bacci,sai ya miqe sabe da ita,daya hannun nasa kuma yana riqe da jakar kayan wasanta yayi sassan ammansa da ita. Yana shiga tana shigowa itama falon daga ainihin qofar baya na sassan nata da zata sadaka da masaukin baqi na gidan,ita da masu aikinta su biyu,lili da laraba,suna dauke da jibga jibgan duvet da ana fiddosu yawanci a lokacin taro irin wannan musamman saboda baqin. Jikinta sanye da Egyptian hijab daya saukar mata har qasa,duk da dare ne amma akwai eye glasses tare da ita,wanda takanyi amfani dashi lokaci lokaci idan taji bata jin dadin idanuwanta. "Karbeta lili,ki kaimin ita dakina,idan kin shiga ki rage qarfin acn nan,don naji kaman mura nason kamata" a ladabce ta amsa,ta dauki amna da ja'afar ya shimfide mata saman kujera ta wuce ciki "Manya" ta kirayeshi da sunan da takan kirashi dashi don ba kasafai zakaji ta kirayi sunan nasa kai tsaye ba "Zauna muyi magana" kamar yadda ta umarceshi haka yayi,ya koma ya zauna din yana bata hankalinsa "Kayimin wata alfarma man" sosai yake duban amman tasa,abinda yasa ta fahimci tambaya yakeson yi kan alfarmar data ambata "Don Allah na roqeka,ka daure ka karba qaddararka a duk yadda tazo maka,kada kayi wani abu da kasan cewa ba dai dai bane,ka riqe amanar da aka baka bisa gaskiya da na sanka da ita,don Allah" "Ku daina roqata hakanan amma,kunfi qarfin haka a wajena" ya amsa mata yana bata assurance din haka ta cikin qwayar idanunsa,ta san yana da qoqarin bin umarnin na sama dashi daman,saidai sanin halinsa yasanya mata shakku kadan,amma a yanzun hankalinta ya gama kwanciya gaba daya "Allah yayi ma rayuwarku albarka,shikenan sai da safe" A daren gaba daya ya gama lissafa yadda zai tafi da komai,yadda zaibi umarnin mahaifansa ta gefe guda ba tare da rayukansu sun baci ba,hakanan ba tare kuma da matan da aketa qoqarin liqa masa sun dameshi ba,don haka a washegari bayan ya shirya ya fito,ya nema ma'aikata daga cikin kamfaninsa,ya tsara musu abinda yakeso. Cikin gidaje hudu da yake dasu ya zaba daya,wanda yake dan nesa kadan da nasu gidan,yasa aka hau aikinsa baji babu gani,don dama gidan kusan an gama komai nasa,fenti da saka qwayaye da sauran kayan qawata gidanne kadai ya rage,abinda yasa yayi saurin yin hakan,don bayason abbi ko anni wani yace su zauna a ainihin gidansa dakegovernment house road,don yafi kusa da nan gidan nasu,gidane iya gida,wanda ya amsa sunansa,kuma ya ginashi ne musamman a sannan saboda shaheeda,a sanda ta haifa masa twins,ya zuba musu komai da komai,sanda zasu tashi zuwa gidan suturar jikinsu kawai suka dauka,kuma ko bayan rasuwar shaheedan babu abinda ya bari aka taba cikin gidan,hatta da suturarta,da anyi maganan kwasan wani abun sai a rasa kansa,sai aka yanke shawarar a jinkirta ko yana kan tsinin zafin mutuwar ne,saidai har kwanan gobe komai yana nan a muhallinsa,a baya cikin gidan yake rayuwarsa,saidai yadda yake dada komawa yasa anni ta yanke shawarar ya tattaro ya dawo gida cikin jama'a,a kulle wancan gidan ko za'a samu sauqin wasu al'amuran,an dan samu din,saidai babu abinda ya canza shaheeda daga zuciyarsa har kwanan gobe ita da amransa *SO BAYAN RAI* Gidan daya zaba din gida ne sama dake da babbar haraba da zata iya daukan motoci goma,akwai balcony da zaka shiga wanda yake dauke da babban falo,hagu da dama na bangon falon qofofi ne guda biyu,kowacce qofa akwai babban falo hade da bedroom a cikinsa, kitchen daya ne wanda yake falon,saidai babba ne,babu wanda zai takura wani,hakanan side biyu gareshi,a falon akwai stairs da aka qawata da wasu irin makarai masu kyau,marbles ne zube har zuwa saman,inda zai sadaka shima da falo babba ne dakuna guda uku ne a saman kowanne manne da toilets dinsa,sai wani balcony din daga sama wanda zai baka daman ganin ainihin harabar gidan fetal,a qasan akwai spare din daki guda daya,sai dakunan baqi maza da na me gadi daga can wajen gidan. Gidan yana da girma,don kowanne daki da falo babbane qwarai,hakanan yadda aka tsara ginin ya bada sha:awa ainun,saidai jabir da ya gani yaga gazawar ja:afar din,a matsayin da Allah ya bashi,duba da gidan da zai dauko unaisa "Idan gidan bai mata ba saita fasa dani ta zaba wani fine,iya abinda zan iya kenan" ya gayawa jabir,kamar shine unaisan. Duka kudin anty maama na lefe ya tura mata abinta ba tare daya sake wani musu ba,hakanan dukka wata zirga zirga ta samarwa da baqinsu masauki tare dashi aka yita,saidai sau tari har suje su dawo ba zakaji yace kanzil ba,lokutta mafi yawa wayarsa na a hannunsa ne,cikin abokansu guda biyun da suketa zirga zirgan tare babu wanda ya kawo komai ransa,saboda sunsan wayeshi,captain j din haka nan dabi'arsa take sun sani tun ba yau ba,magana ko surutu shine assignment mai wahalar cinyewa da zaka hadashi dashi. Sai daya qara kwana biyu sannan ya samu ya sukunin saka time na zuwanshi gidansu unaisa kamar yadda abbi yayi masa umarni,ganin yadda yake shiga cikin sabgogin yasa abbi bai tanka masa,don yana ganin sauyi muraran da kuma qoqarin bin umarni daga wajen ja'afar din. A ranar yayi zamanshi a sassansu kamar bashi da plan na zuwa ko ina,tab ce saman cinyarsa yana duba wasu abubuwa,sanaye yake da bawin boxer wanda ya fidda ainihin qirar tsayayyun qafafunsa dake cike da tarin gargasa,jabir ya turo qofar dakin ya shigo,a shirye tsaf cikin shadda,sai yaja turus ya tsaya "Me zan gani?,J baka duba agogo ne?" "What happened?" Ya tambayeshi a nutse abinsa,kamar ma baisan meke faruwa ba "You are very stubborn manya,me yasa kakeso ayita maimaita magana daya?,just simple instruction amma ka kasa bi" idanu ya watsa masa bayan ya kashe tab din "Yaushe na gaya maka fasa zuwa na?" "Ai banga alama ba" "Kamar?" Ya tambayeshi yana shafa dan qaramin gemun dake manne a habarshi,ya kuma hade da zagayayyen gashin dake kumatunsa zuws qasan hancinsa "Gashi nan kuwa ina gani,you are sitting properly,dafa'an kamar babu inda zaka?" Yatsansa ya sanya yana bin tsahon karan hancinsa daga sama zuwa qasa,ya lumshe idanunsa kana ya budesu yana furzar da iska,sai daya sauke qafafunsa qasa daga samam glass table din da take kai sannan yace "Okay,so kake kazo ka sameni ina ihu guri guri ina announcing ma mutane zanje naga hurul'een ko?" Idanunsa ya lumshe yana sake girgiza kai alamun a'ah "You should remember.....ita din ba kowa bace a wajena face GURBIN IDANUN da ba zasu taba zamowa idanu ba,koda zasu shekara miliyan anan din" daga haka ya miqe a nutse yana ajjiye kayan hannunsa ya nufi toilet "Oho dai,no matter how dolenka kaje,na baka minti ashirin ka taddani falo,idan kuma ka wuce hakan....,basai na qarasa ba" Kusan sai da jabir yayi dana sanin fadin wannan maganar,saboda sai da ja'afar ya ninka ashirin sau uku,don sai daya dauki awa daya cif sannan ya fito,saidai ya dauki kyau iya kyau yadda ya kamata,sanye yake da wani lallausan farin yadi na maza dake da shara shara,takalmin qafarsa baqi ne dan qasar Italy,hular dake kansa tun daga nesa take qyalli kamar farin tangaran,sosai kwalliyar tabi jikinsa,ta kuma dace da yammacin,hatta jabiru sai daya yaba da adon,amma sai ya fake da qorafin dadewa da yayi,bai kulashi ba,saima seat mai zaman banza da yayi zamansa,ya fidda wayarsa yana aikawa wani client dinsu saqonni,ya kuma turawa saubam secretary dinsa saqon ya sameshi a wani eatery goben yanason su tattauna. Cikin wata farar Rolls-Royce ghost v12 mallakin ja'afar din suka fita,suna cillawa saman kwalta jabir ya qarawa motar gudu sosai,bayan ya cikasu da ac kamar yadda suka saba amfani da ita,basa ko ji ga jikinsu. 29 _ZAFAFA BIYAR💯💕_ _ZAFAFAN LITTATTAFAI GUDA BIYAR🤌_ _YAN BIYAR MASU BIYAR DIN:_ _1-DARUSSAN RAYUWA_ _2-FADAKARWA,_ _3-WA'AZANTARWA, 4-NISHADANTARWA_ _5-TSAFTATACCIYAR KAUNA MARAR GAURAYE_ _KADA KU MANTA, YAN BIYAR DIN NA TAFE NE CIKIN TAFIYA TA KARO NA 7, SABON SALON TAFIYAR DATA FI KOWACCE INGANCI DA DIMBIN DARUSSA NA RAYUWAR YAU DA KULLUM_ _KU SHIGO A DAMA DA KU DON JIN ME KE FARUWA ACIKIN LITTAFIN *SANADIN LABARI NA*: NA *HAFSAT RANO*, LALLE AKWAI BABBAN SANADIN DA ZAI WAKANA ACIKIN ZUKATAN BIYU... DON SANIN SU WAYE SAI KU GARZAYO A DAMA DAKU._ _SHIN *BABU SO!!! (MIYA KAWO KISHI?)* NA *BILYN ABDULL* LALLE LAMARIN FA AKWAI GUMURZU. DOMIN TSAFTACEN *SO* SHI KE JANYO ZAZZAFAN KISHI A TSAKANKANIN MASOYA BIYU. KU ZO A CIGABA DA TAFIYA DA KU._ _*NAYAH....(RIBA BIYU)* NA *MAMUH GEE* RAYUWAR AYSHA INAYA NA DAUKE DA WASU SINADARAI NA TACACCIYAR KAUNA. AMMAN WANENE GWARZON DA ZAI SAMU NASARAR CAFKE WANNAN RIBA BIYU? TA KAUNAR INAYAH DA INAYAH DIN KANTA. KU TAHO MU TAFI DA KU A TAFIYAR MU_ _*FARHATAL QALB (FARIN CIKIN ZUCIYA) NA MSS XOXO* FARIN CIKIN ZUCIYA MAGANI NE NA ZUKATAN DA KE CIKIN DAMUWA. LALLE AKWAI NASARAR FARHATAL QALB GA DUK ZUKATAN BIYU DA SUKA TSINCI KAN SU CIKIN BEGEN JUNA . KU ZO MU KARASA WANNAN TAFIYAR DA KU_ _*GURBIN IDO (BA IDO BA NE) NA SAFIYYAH HUGUMA* ... SO BAYAN RAI..... KAUNA CE MARAR YANKEWA DAGA ALLAH. SU WAYE ZASU SAMU NASARAR CIKE GURBIN DA KE IDO? ZUKATA BIYU NE..KU BIYO MU DON GANEWA IDANUN KU CIKEWAR GURBI_ _DUKA WADANNAN LITTAFAI GUDA BIYAR. NA MARUBUTAN ZAFAFA NE WANDA KE YIN SU A YANZU._ _WANNAN TAFIYAR ZAFAFA MA TAZO MUKU DA TSARIN TALLACE TALLACE WADANDA ZAMU KAI MANHAJOJIN MU NA:_ _*FACEBOOK, INSTAGRAM, YOUTUBE, WHATSAPP GROUPS DA STATUSES, TELEGRAM DA MA WATTPAD... MUNADA DIMBIN MASOYA DA KE BIBIYAR MANHAJOJIN SHAFUKAN MU. SU KE KUMA KOKARIN SIYAN DUKKANIN KAYAYYAKIN DA MU KA TALLATA._ _MUNA TALLATA HAJOJIN KU CIKIN FARASHI MAI RAHUSA._ Tafiyar mintuna ita ta sadasu da unguwar cikin gidan minister,sun samu tarba me kyau bayan haj Aaya ta samu sanarwar zuwansu,waje na musamman cikin gidan tasa aka kaisu,sannan tasa aka taso mata unaisa dake barci a sannan,ta fara shiryata da kanta bayan ta sanyata ta sake wanka,cikin wani material na alfarma mai dan banzan kyau da tsada. Karo na biyu ja'afar ya sake duban agogon hannunsa,yayin da yake biye da maganar da jabir din ke masa kan dakunan da aka kamawa baqinsu sunyi kadan,za'a qara wasu da kuma yadda suka tsara event din da za'a gudanar "Komai yayi,amma banda ni a taronku,saboda babu abinda zanje a ciki,walima ce kawai ta zama sunnah,ita dince ma nake tunanin zanje,anma fa babu tabbas itama,kada ka zura jiki da yawa" yayi dukka wannan maganar yana kallon lafiyayyen agogon dake kwance a fatar hannunsa "Time up" yafada yana miqewa tsaye cak,sai jabiru ya bishi da kallo "What do you mean?" Sai daya zuba hannayensa duka cikin aljihun rigarsa yana duban jabir "Mintuna takwas nayi niyyar ware mata a yau din,kuma ta cinyesu wajen jira, you know.....i don't wait for anyone,amma dai na cika maganar abbi tunda nazo" dubansa jabir yake cike da mamakinsa,ja'afar.....ja'afar?. "Amma dai abbi ba cewa yayi ka shigo gidan ka fita ba ko?,cewa yayi kuga juna,ka ganta ne J?" "Na meye sai na ganta?,no need" ya amsa masa yana dage kafadarsa,sai ya juya da zummar takawa yabar wajen,dai dai sanda ta iso,cikin matuqar ado,mutum uku cikin masu aikin gidan na biye da ita da.manyan trays da aka jerawa kayan ciye ciye da shaye shaye. Idanunta a kansa,kamar yadda fuskarta ke baibaye da murmushi "Hello" ta fada tana waving hannayenta,murmushin fuskarta na sake fadada "Welcome our bride" amsar jabir kena data qara ninka farincikin dake zuciyarta "Thank you " ta amsa masa kafin ta sake maida dubanta ga ja'afar wanda har yanxun yake tsaye "am sorry,i keep you waiting ko?" Ta fada tana murmushi,sai ya motsa kafadarsa "Don't mind,ina cika umarni ne" gatsal jabir yaji maganar tayi masa,bai murmure daga wannan ba yaji unaisan na cewa "Have a set please?,kaman maganan zaune tafi ta tsaye" "It's too late......lokacin zamana ya cika,i have a lot to do,see you later" ya fada yana qetareta zai wuce abinsa. Wani abu ne ya tsayawa unaisa a wuya,duka wannan lokacin data bata amma ko na minti uku cikakke bai kasance da ita ba zaice tafiya zaiyi?,uwa uba ma sau daya tak taga ya kalleta ya dauke kai?,tana da tarin.abubuwa masu yawa da takeson su tattauna dashi,don haka batayi qasa a gwiwa ba tabi bayansa tana tsaidashi Cak ya tsayan,sai taji abun ya mata nauyi kasancewarta maje mai bala'in jin kai,sai itama fa tsaya tana duban ingarman bayansa take tsaye sosai tsakanin mayalwatan kafadu dake cike da siffar qarfi da cikakkiyar tsaiwa ta cikakken namiji,a hankali taga ya waiwayo,ya kuma tako zuwa gabanta ya tsaya,tsaiwar da taji ta har tsakiyar kanta,saboda tazarar dake tsakaninsu bata da yawa,uwa kuma wani shegen kwarjini yayi mata,wanda ya mamayeta kota ina,qamshin lallausan turarensa ya ziyarci hancinta,sa'annan kuma hucin fitar numfashinsa data rasa me yasa yake fita da nauyi haka?,bata gane amsar tambayar tata ba sai daya fara magana,ta fuskanci cikin fushi yake,ransa ne ya baci,abinda ya bata tsoro kenan,duk da cewa fuskarsa a murtuke take cike da rashin fara'ar da dama can kowa da ita ya sanshi,to amma wannan bacin ran dake kwance saman fuskarsa bai jima da samoshi ba "Ki kula,ki kuma yi a hankali,banason matsi ko takura,zaifi kyau ki kasance me nisantata akan yunqurin kusantata da kikeyi,stay away from me.....na gaya miki wata gaskiya guda daya wadda babu lallai a samu wanda ya gaya miki ita?" Yayi maganar yana dage girarsa dukka biyun,bata amsa masa ba saboda wani yanayi daya shigeta,shima bai damu ta amsa din ba ya dora mata "Bana buqatar rayuwar kowacce mace da sunan matata a cikin tawa rayuwar,already na rufe wannan babin,idan kin shirya ma kuma kutsa kanki ciki...... it's okay for me" ya qarasa fada yana dage kafadunsa,sai ya juya cikin takun nan nasa mai cike da ginshira yana barin wajen. Ko sau daya batayi yunqurin tsaidashi ba kamar dazun,sai kallo data bishi dashi qirjinta yana dukan uku uku har ya bacewa ganinta,kafin muryar jabir ta katse mata dukka hanzarinta "Are you okay?" Ya tambayeta yanason karantar yanayinta,don baisan me ja'afar yace da itaba,kasancewar akwai tazara tsakaninsu,amma yafi kowa sanin halinsa,tabbas something bad happened,akwai abinda ya gaya mata,saboda yadda fuskarta ta sauya gaba daya ta kuma birkice. Abirkicen ta girgiza kai "Akwai damuwa tabbas" batayi qasa a gwiwa ba ta gaya masa maganganun da sukayi,sosai jabir yaji babu dadi,amma a zahiri sai ya kawar da hakan daga saman fuskarsa "Karki damu,nasan J,a yanzun rashin sabo ne ya kawo yake gaya miki haka, with time zaku saba,zakiga kuma kaman bashi ba" sosai yayi qoqarin gaya mata maganganu masu kwantar da hankali,har sai daya fuskanci ta nutsu sannan ya taka mata gaban main entrance na gidan,sannan ya wuce zuwa inda suka ajjiye motarsu. Hannu yasa ya bude murfin motar idanunsa na sauka kan fuskar ja'afar,wanda ya kwantar da seat din motar ya kuma miqar da bayansa sosai a kai,jin bude motar baisa ya motsa ba,har sai da jabir ya shigo,sannan ya bude kyawawan idanunsa da suka sauya kala a hankali ya watsasu kan fuskar jabir "Kaci sa'a kaine,da saidai kazo ka samu empty din wajen" "Yanzun ma me ya hanaka tafiya?,tunda kazo kayi abinda ranka yakeso?" Ya amsa masa yana dan nuna masa bacin ransa,duk da yasan ja'afar din dole abishi a sannu,saboda wata irin zuciya da yake da ita da bata iya qaramin so ko qi ba,hakanan ba qaramin riqo shaheeda ta yiwa rayuwarsa ba adan tsukin lokacin na zaman da sukayi. Bai sake cewa jabir komai ba,sai dan qaramin tsaki da yaja yana tada seat din ya zauna sosai,tun basuyi nisa ba suna isa wani guri yace jabir din ya saukeshi qofar wani gini,kamar ya tambayeshi me zaiyi sai yaja baki ya qyaleshin,ya saukeshin ya kuma wuce da motar. ***********Dukkan tafukan hannayenta ta buda tans kallon tsakiyarsu,batasan me zata tuna ba,saidai ta samu kwanyarta fayau babu komai tun daga sanda taji ana hargowa sa hayaniyar zuwan al'ummar gombawa,ta dai tsinci kanta da matuqar sanyi da kuma faduwar gaba,wanda tunda aka fara bikin kwana hudu kenan yau cikon na biyat bataji irinsa ba sai yau,tasa ran ganin anni da amnanta cikin matan da suka iso,saidai babu daya cikinsu,kusan dukka baqin fuska ne idan ka cire anty maama wadda ita ta jagoranci tafiyar. Ko ba'a gaya mata ba tasan cewa ayau qaramar hukumar ta gembu ta karbi baquncin manyan mutane irin wanda bata taba karba ba,jiniya da qarar ababen hawa kala kala ke tashi,hayaniyar da hatta cikin dakin da take zaune bai tsira ba,dakin dake cike da 'yammatan fulanin da suke danginta ne,duk kuma cikinsu bataga gaje ko gilmawar inna furera ba,tun ranar da za'ayi mata kamu inna fureran ta iso,da tarin sharrikanta wanda ya zame mata tonuwar asiri saboda zuwan yuuma garin,wadda da ita ake gudanar da komai,batasan inda inna fureran tayi ba tun ranar da aka silleta,umarni dai na qarshe da aka bata maimunatu tayi yaqinin shine abu mafi tsauri a wajenta da zai iya sanyata batan dabo "Ki tattaro duk wata dukiyar dabbobi ta shatu da maimunatu dake hannunki ki kawo mana ita" bammmm!!!!. "Alhamdlh,aure ya dauru" muryar maroqin mai babban maqogaro ta kwararo cikin gidan,ta kuma isar da saqon nasa inda yakeson ya isa,lungu da saqo na gidan,sai kuwa mata suka dauki guda,gudar data zagwanyar da duk wani qwarin gwiwa na maimunatu,ta nannade kanta da kyau cikin mudukajenta(kayan saqi na zallar lallausar auduga na musamman da matan bappa sama'ila suka tanadar mata harda na yafawa saboda wannan ranar),take taji kamar zazzabi keson kamata saboda sanyi daya fara ratsa qashinta wanda batasan dalilinsa ba,tana jin 'yammatan na waqe waqensu na fulani suna kuma tsokanarta amma ko motsawa batai ba. Tana ji daga tsakar gida wata qanwa ga kakarsu ta wajen mahaifi tana fadin tare za'a wuce da ita da 'yan daurin aure zuwa can gombe,sunce nan da awa daya a shiryata" gabanta yayi mummunar faduwa,tana jin fargaba sosai,tana jin kamar su annin baqinta ne,duk da zuciyarta na gaya mata,bawai dasu anni zata zauna ba,zataje ne tayi rayuwa da wasu mutane na daban da batasansu ba,batasan halaye da dabi'unsu ba,bakuma tasan yadda zata fusakanci zama dasu ba. Tana jin sanda aka gama tiri tirin hada kayayyakinta tsaf,yuuma na tsaye akai,tamkar ba daga dangin ango ta fito ba,domin tace ita din a yanzun uwace ga maimunatu bawai suruka ba,ita ta riqeta ta rakata zuwa gaban baffaninta da wadanda ke a mazaunin uwayenta a yanzu,sunyi mata dukkan nasihar da akewa kowacce diya mace a al'ada sanda ta tashi tafiya gidan miji,dukkan wannan abubuwan maimunatu ganinsu take kamar a majigin film bawai a gaske ba,kamar raqumi da akala haka take biye dasu sanda suke riqe da ita zuwa jerin gwanon motocin dake jiran fitowarta,su kuma tashi dasu zuwa gombe. Shi daya ne cikin motar sai driver kamar yadda jabir ya tsara hakan ba tare dashi ya sani ba,zaman da yayi cikin motar ya yishi ne yana jiran fitowar jabir da yace yayi mantuwa a inda suka zauna,duba daya zakayi masa kasan cewa ango ne shidin zammm,yayi wani irin kyau na musamman cikin wata arniyar shadda ruwan sararin samaniya,wadda ta lashe maqudan kudade tun daga wajen siyota har ya zuwa dinkin da aka yi mata,aikin hannu me matuqar kyau tsari da kuma tsada,takalmin sauciki kalar dark blue sosai daketa daukar idanu saboda sabunta kyau da kuma tsafta yana aje gefe,qafafunsa babu komai sai sock,gefensa ya fidda babbar rigar ya ajjye,a samanta ya cire hularsa kalar dark dark blue da ratsin light mai wani irin walqiya da daukar idanu ya ajjiyr hade da babbar rigar,hatta da links din hannun rigar gold color ya cireshi,ya nade hannun rigar zuwa gwiwar hannunsa,gargasarsa dame kwance luf ta bayyana sosai. Wata magazine data wallafa sunayen fitattu kuma manyan kamfanunuwan gine gine a satin yake dubawa,kamfaninsu shine yazo a jeri na biyu,duba bayanan yake,amma can tsakiyar qirjinsa wani irin nauyi ne dake cunkushe a cikinsa,ranar ta yau gaba daya tazo masa ne kamar cikin mafarkai,tunda ya auri shaheeda kuma mutuwa ta rabasu bai taba tsammanin akwai rana irin wannan da zata zo ba,dukka wannan abun yanata qoqarin yaqi da abinda yakeji cikin zuciyarsa ne,amma a yau din,babu wadda ke ziyartar zuciya da kuma tunaninsa sai shadeedan,yana tuna rana irin ta yau cikin rayuwarsu data kafa masa tarihin da bazai gogu ba har abada. Haske ne kadan ya bayyana a motar bayan an bude murfin motar,yana shirin daga kansa ga zatonsa jabir ne,sai yaji muryar mata suna fadin "Shiga da bismillah,Allah yasa kin tafi a sa'a" wani abu ya tsaya masa a wuya sanda take shigowa motar a hankali,tana gama zama kuma aka maida murfin motar aka rufe,sai yaji driver yaja ya soma tafiya. Shuru ne ha ziyarci motar,babu wani motsi ko kadan a cikinta illa motsin injina dake aikinsu can qasa,cikin jikinta take jin sauyin waje da yanayi tabbas ya fara daga wannan lokacin,duk da bata iya ganin komai clearly amma tasan tabbas ba ita kadai bace cikin motar. Hannunsa ya zura a aljihun rigarsa ya fiddo wayarsa yanata qoqarin hadiye bacin ransa,shi jabirun zai rainama wayo?,yana nufin shi da ita zasuyi tafiya har ta wadannan awannin a mota guda don ya rainama kansa hankali?, numbers dinsa ya nema ya kuma kirashi,bugu biyu ya daga "Jabir" ya ambata da wani irin sound dake nuna zallar bacin rai,saidai kuma ba wani da qarfi yayi maganar ba Lumshe idanun ta maimunatu dake qudundune cikin yalwataccen mayafin da aka rufa mata har ka tayi,bugun zuciyarta dake qara bugu take qoqarin saitawa,sautin muryar ya doki kwanyarta,tamkar a cikin kunnuwanta aka furta sautin kalmar jabir din,saita hade jikinta waje daya sosai,tana jin takalminta ya zame daga qafarta,amma babu damar ta motsa bare ta maidashi,hakanan kawai takejin wani irin tsoro yana ratsata,tabbas wannan shine mutumin daya zama mijinta a yau. "Kada kace komai,don muna tare dasu abbi,ga motarmu nan tasowa,wataqil zamu tsaya a hanya mu kwana saboda nisan tafiyar,please i beg you, don't misbehave,ka dorar da farincikin dasu abbi suka samu a yau din" magiyar jabir ta yau ta tabashi,don haka baice komai ba,amma hakan bai hanashi jan tsaki ba bayan ya kashe wayar "Stop the car solomon" ya fada da tattausar husky voice dinsa "Okay sir" ya amsa masa cikin girmamawa,sannan ya gangara gefan hanya ya tsaya. Rigarsa da hularsa ya dauka ya bude murfin motar ya fice ya koma zuwa seat din gaba,sannan ya bashi umarnin ci gaba da tafiya bayan ya gyara zaman kujerar yadda zaiji dadin jingina ya zama comfortable sosai. 30 ASSALAM ALAIKUM DEARIES BARKAN KU DA KOKARI…. KAMAR KODA YAUSHE. WANNAN KARON MA MUNA BARAR ROKON KU WAJEN TEMAKAWA CHANNEL DIN SUDEIS DAKE MANHAJAR YOUTUBE YARO NE DAYA TASHI DA SON KARATUN ALQURANI ME GIRMA. YA KE KUMA KWADAYIN GADON ME SUNAN SA SHEIKH SUDEIS. DAN ALLAH A TEMAKA A DANNA MASA SUBSCRIBE. A KUMA YI VIEWING DA LIKING. A TEMAKA DA SHARING MA... JAZAKUM ALLAH KHAIRAN AS YOU DO... " Assalamualaikum dear sisters and brothers. Welcome to ummu sudais YouTube channels? A channel where the Holv Quran is been recited from different Angles. Click on this link and listen to the Beautiful recitation that will melt your heart https://youtu.be/Lafgc749sK8 Your subscription to our channel is of Great important. Please help us grow our channel by subscribing and likitoci 30 Ko sau daya bacci ko gyangyadi basuyi nasarar fusgarta ba,hakanan ko qwaqwaran motsi batayi tsahon a wannin da suka dauka suna tafiya,hakazalika motar haka ta kasance shuru,ba zata ce ga ainihin abinda yake faruwa cikin motar ba,sai daga bisani ne tadan janye mayafin dake kanta kadan saboda ta samu damar kallon gefan hanyoyin da suke wucewa da mugun gudu. Taraba suka wuce kai tsaye saboda su raba tsahon tafiyar,uwa uba kuma yammaci tayi lis,babu security ace sunyi tafiyar dare,don haka suka yanke sauka a wani hotel dake kan babbar hanyar da zata sadasu da gombe,kafin su iso ma tuni jabir yayi booking dakuna,don haka suna isa kowa key na dakinsu aka bashi. Itakam tana zaune cikin motar,har zuwa sanda anty maama ta qaraso ta fiddota,ran anty maaman cike da haushin ja'afar din,ta yaya sunsha wannan doguwar tafiyar xai fita yabar diyar mutane cikin mota?. Yana tsaye a tsakiyar dakin yana amsa waya sanda anty maama tayi knocking,ya qarasa bakin qofar ya murza handle din ya bude mata ba tare da ya tsaya tambayar waye ba,kana yaja da baya yana ci gaba da amsa wayar. Bakin madaidaicin gadon dake shimfide da farin lallausan bedsheet,tadan duqa kadan dai dai kunnuwan maimunatun,ta yadda ita kadai zataji abinda take gaya mata "Ki saki jikinki da mijinki,ki samu kiyi wanka da brush kafin ki kwanta,zan ciro miki wasu kayayyaki cikin akwatinki za'a miqo miki,ki saki jiki kinji ko?" A hankali maimunatu da kanta yake a duqe ta gyada kan nata,tana jin zuciyarta na wani irin bugawa,a tsahon shekarunta na goma sha shida tunda take bata taba kebewa da wani d'a namiji ba a daki daya kamar haka,balle har ta kaisu da kwana kamar haka,yau gashi za'a fita a barta da wani,wanda yake amsa sunan miji a gareta. Juyawa anty maama tayi ga ja'afar wanda har yanzu bai gama wayar ba,sai ta kada kanta ta fice a dakin,qarar rufe qofar dakin ya sanyashi waiwayowa,don bai lura dawa suka shigo ba,ya zaci tazo wajenshi ne zasuyi wata maganar,kuma sai yaji ta fice ba tare da tace komai ba,abinda ya sanyashi juyowa kenan. Cikin mamaki idanuwansa suka sauka ga maimunatun,kawo masa ita sukayi kenan?,lallai dai sai sun qure haqurinsa da juriyar da yaketa azawa ransa?,sai ya dauke idanunsa yana sallama da wanda suke wayar dashi,ya yanke kiran yana neman number jabir. Bugu daya ya daga,muryarsa cike da wani irin nauyi yace "Baku da wani extra dakin?" "For who?" Ya tambayeshi kai tsaye,don dama yasan dole ko yaya sai ya nuna turjiya "Ban sani ba,am asking you ne,it's simple question,just answer me bawai ka tsaya tuhuma na ba" "Oh...oh sorry, let me ask abbi first,but dakin kadan ya muku ne?" Ya tambaya cikin zolaya izgili da neman fada,haushi da takaici ya sanya ja'afar jan dogon tsaki kana ya tsinke kiran,wai dole sai jabir ya sanyashi dogon magana ne?,baisan abinda yakeji bane?. Sai ya cilla wayar saman madubu,sannan ya jawo kujerar gaban mudubi ya zauna a kai. A hankali ya duqa yana zare takalmin qafarsa,idanunsa suka kan farar qafarta dake dauke da dogayen yatsu da suka sha jan lalle wanda ya sake qawata qafan,ya kuma zame mata ado sosai,sai ya janye idanuwansa,qafafun are tiny,abinda yake alamta masa tana da qarancin shekaru kenan?,haka kawai sai yaji zuciyarsa na darsa masa son ganinta da tantance wacece ita?,ta yaya zasu dubi kamarsa suce zasu aura masa yarinya kamar haka?,sakanni qalilan zuciyarsa ta kacame da wasuwasin yarinyar ce ko kuma hasashe ne irin nasa?. Miqewa yayi yana sake jan tsaki duk a qoqarinsa nason mantawa da wannan wasuwasin da yake azalzalarsa a rai,ya taka zuwa qofar bandaki bayan ya kalli agogo yaga lokacin sallar magrib yadan gota kadan,ya daura alwala,ya sake fitowa yana sauke hannun rigarsa daya nannade kafin fara alwalar,yana son ce mata taje tayi alwala suyi sallah amma kuma ya rasa ta yadda zai gaya mata,bawai kuma baisan yadda zaice mata bane,a'ah,kawai qyashin maganar yakeji,har ya fidda abun sallah ya shinfida tana zaune,sai daya sake jan tsakin nan nasa dai,wanda ya kuma sanya maimunatu faduwar gaba ta kuma rintse idanunta kamar kowanne lokaci idan yayi tsakin,don tana jin tsakin ne har tsakiyar kwanyarta,faduwar gabanta kuma nada nasaba da muryar dake mata kama da wata firgitacciyar murya data taba ji shekarun baya da suka wuce "Kiyi alwala kizo" ya fadi mata yana jona qaraman kettle dake a gefansa. A hankali ta miqe,ta kuma dan ja mayafin nata baya kadan,sannan ta wuce zuwa bandakin. Gaban madubi ta tsaya bayan ta yaye lullubin kanta gaba daya,tana sakin wata ajiyar zuciya me nauyi gami da kallon fuskarta,wadda lallausan gashinta me azabar santsi da yasha gyara daga wajen yakumbo saratu ya fito kadan ta gaban dankwalin nata,saita debe ruwan dake zuba daga famfo ta fara alwalar,tana yi tana kallon fuskarta a madubi,zuciyarta nata mata saqa abubuwa masu yawa harta gama,ta maida dankwalinta da mayafinta ta fito,ta kuma tsaya a inda ya mata nuni suka tada sallar. Yadda yake sallar cike da nutsuwa yayi matuqar burgeta,ko banza alamune dake nuni da sanin addininsa. A hankali ya sallame,idanunsa suka sake sauka akan dogayen hannayenta suma da suka jiqu da jan lallae cikin ado me ban sha'awa,hakanan ya samu kansa da juyowa gaba daya yana fuskantarta,idanunsa suka sauka gaba daya a kanta,ta tanqwashe qafafunta sosai tana zaune,sai ya ganta 'yar qarama a gabansa,tazarar dake tsakaninsu ba mai yawa bace Shuru ne ya baquncin dakin,numfashin kowannensu yana fita tare sa tulin tunanin dake zuciyar kowannensu,yaci gaba da zama a haka yana fuskantarta tare da wassafa me zayace da ita?,duk sanda yadan dubi sashen da take zaune sai yaji wani abu ya tokare masa wuya,yanzun haka bayan ita akwai wata daban dake gombe tana jiransa?,for god sake anni zatayi masa haka ne wai?. Kamar wadanda aka umarta daga shi har ita kowanne ya daga kanshi zuwa ga dan uwansa,take fuskarsu ta hade waje daya kamar yadda idanuwansu suka cudanya da juna,fari qal din idanuwan nan nata da baqaqen qwayar idanunta masu digon zaiba jiki,kyakkyawan idanunwansa dake da wani irin shape,tare da wani irin maganadisu dake cike da zallar kwarjini. Kusan lokaci daya wani abu ya daki zuciyar kowannensu,wanda ta bangaren maimunatu ba komai bane face wani irin tsoro razani da kuma firgici da ya kusa tafiya da numfashinta,cak ta tsaya da zuqar iska zuwa huhunta na wucin gadi,hatta da ja'afar din ya karanci hakan,yayin da shi kuma zallar mamakin qananun shekarun da take dashi hadi da kamanni da tayi masa da wata suka ratsashi. Cikin jarumta ta zuqi wani dogon numfashi ta kaiwa hunhunta cikin wasu sakanni masu mugun sauri,abinda ya tallafa mata numfashinta ya dawo da aiki,saita lumshe idanunta da kyau tana shaqar numfashin da qyar,tana kuma jin yadda zuciyarta ke mugun bugawa da sauri kamar zata tsinke daga inda take ta fito. "Hey" ya fadi cikin mamakin yadda take wasu abubuwa kamar wadda taga giftawar mutuwarta a gabanta,maimakon maganar tasa ta taimaka wajen bude idanuwanta ko samun nutsuwarta......a'ah,sai ta sake razana,saboda muryar ta sake tabbatar mata da shi dinne dai,shine dai wannan mutumin,take jikinta ya dauki rawa,zuciyarta taci gaba da kadawa a tsakanin qirjinta,sai tayi wuf zata tashi jikinta na kakkarwa kamar wadda azababben zazzabi ya rufe. Caraf ya damqi tsintsiyar hannunsa cike da haushinta da mamakin firgitar da tayi,riqon da yayi mata ya sanyata sakin kuka babu shiri tana dubansa,mamaki ya cikashi qwarai,sai ya janyota ta koma ta zauna a inda ta tashi. Sosai hankalinta ya kuma tashi,ta hade jikinta waje daya hawaye naci gaba da bin kuncinta,ta yaya zata manta da wannan fuskar?,yaya zata manta dashi,mutumin da ya kusan sanadin cirewar qwayar idanunta saboda marin da ya zabga mata duka akan dabbobinta?,mutumin da ya mata barazana da kakkausar murya,wanda tun daga ranar bata sake ganinsa ba,saidai duk sanda taga mota,ko taga wani abu da yayi kama da mari saita tunda da abinda yayi mata,sau tari takan shafa kuncinta idan ta tuna da wancan lokacin,mutumin da razanata matuqa,ta tsani taba,ta kuma tsani me shanta,sai gashi ya fesar da hayaqinta saman fuskarta,abinda ya kusan haddasa mata daukewar numfashi,wanda ya aikata mata wannan duka shine zaune yanzu a gabanta,shine kuma mijinta?. Samun kansa yayi da zuba mata idanu,abinda ba al'adarsa bace,yana dubanta tare da son tuna inda ya santa,tsahon wasu daqiqu kwanyarsa ta dauko masa komai,bafullatanar yarinyar nan,daya jima yana tunawa bayan marin da ya dauke fuskarta dashi,ya jima yana murza hannunsa a lokacin cikin fushi da jin haushinta na yadda ta qarasa tunzura fusatacciyar zuciyarsa ya aikata mata abinda ba halayyarsa bane,fuskar da yakan tunata lokaci bayan lokaci saboda qarfin halinta da kuma yadda ta bashi haushi a sannan. Ga mamakinsa sai yaji duk wani temper na zuciyarsa ya sauka daga kaso casa'in cikin dari,zuwa kaso arba'in ciki dari,ta yaya zai zauna da wannan yarinyar?,wadda gaba dayanta baifi ya haifeta ba inda ace auren qauye akayi masa?,ta yaya zai zauna da wannan bafulatanar rugar?,wadda ya tabbatar babu abinda ta sani,babu kuma abinda ta iya?,ya aureta yace ya auri me?,ta yaya ma duniya zata kalleta a matsayin matarsa?,wanne irin rigima ce wannan ta anni?, take kwanyaraa ta hasaso masa unaisa,yayi comparing nata da wannan,sam babu hadi,ko ita unaisar bata cika mizani da ma'auni ba,tayi masa girma da yawa,don shaheeda bata kai wadan nan shekarun ba har ta rasu,barema tun halittarsa shi mace bata taba burgeshi ba,shaheeda ce mace qwaya daya tallin tal da ya taba daga kai ya dubeta da wata ma'ana ta daban,itace macen data fara bude rayuwarsa,kuma sanda ta tashi tafiya.....yanajin ta hada da muqullin komai nashi tayi gaba dashi. Cikin rai da zuciyarsa ya dinga jin yanzu zaiyi solving daya daga cikin matsalolin kamar yadda yake kallon maimuntu da unaisa a natsayin MATSALA kuma GURBIN IDANU ne kawai,wadanda baijin zasuyi ko suna da amfani ko wata rana ga mamallakinsu,wanda dasu da babu duk daya "Relax" ya fada idanunsa a lumshe,yana zagaya lips dinsa da yatsun hannayensa "Yamin shuru!" Ya sake fada a karo na biyu,ganin taci gaba da rera kukanta kamar ma bataji abinda yace ba,yadda ya buqata kuwa a wannan karon....sai ta fara hadiye kukan sannu sannu har ta samu nasarar tsaidashi. Shuru ya sake ratsa dakin,tamkar bazaiyi magana ba,kafin daga bisani ya bude dukkanin idanunsa ya watsasu a kanta "Kinsan menene aure?" Yayi tambayar with husky voice,wani irin abu ya ratsa mata tun daga saman kanta zuwa tafin qafafuwan maimunatu,saboda girma da nauyin da tambayar tayi mata,me zata ce masa? "Kinsan me aure yake nufi?" Ba tare da tayi dogon nazari ba ta gyada kanta alamun eh,kasancewar ba mutum ce ita wadda ta iya qarya ba. Wani miskilin qaramin murmushi ya sake "Okay......yayi kyau,tell me menene aure?" Ya fada yana yin qasa da muyarsa,hadi da tsareta da idanunsa nasu nauyin kallo,duk da bashi take kallo ba amma sai da taji gaba daya ta rude ta kuma daburce "Ehhnnnnn" ya fada da madaukakin sauti,sai ta shiga girgiza kai alamun a'ah,bata sani ba "Qarya kike kenan da farko..... okay let me show you the real definition of marriage" ya fada with confidence,zuciyarsa na gaya masa that's the only way da zai cimna gaci na abinda yakeson aiwatarwa,ba tare da yasan maimunatun was simple and peace maker ba,sai ya miqa hannu ya janyota cikin zafin nama daya sake tsoratata zuciyarsa na ingizashi,ya sanyata tsakiyar qirjinsa duk da yadda zuciyarsa ke qin hakan. Fara yamutsata yayi,abinda yayi matuqar dukan hankalin maimunatu ya kuma kadata sosai,abinda tunda take makamancinsa bai taba faruwa da ita ba,mugun gigicewa tayi cikin tsoro da razani,ta sake sakin kuka tana riqe masa hannayensa da yakeson fara yawo dasu cikin sassan jikinta,sai ya tsaya cak numfashinsa na wani irin gudu,yana duban yadda ta riqe dukka hannayensa biyu cikin siraran tafin hannunta,jikinta na wani irin rawa kamar an kada mata gangi "Bai kamata ba,baka kyauta ba" yaji can tsakiyar kansa zuciyarsa na gaya masa,bai musa ba,take zuciyarsa ta gamsu da cewa bai kyauta din ba,saidai kuma wannan ce hanya guda daya da zaiwa tufkar hanci,tunda baisan irinta ba yarinyar,abu daya ya sani game da ita,tsiwarsa da har ta iya buda baki tace masa Allah ya isar mata a wancan lokacin,yana jin this the only way out da zai dorata kan duk abinda ya tsarama zuciyarsa. Saidai kash,yana shirin sakinta anty maama ta turo qofar riqe da jakar kayanta,abinda ta gani ya sanyata fadin "Subhanallah" da sauri tana komawa da baya,abinda yaja hankalinsa,yayi hanzarin sakinta ya kuma miqe a nutse,ya isa bakin qofar dakin ya sake bude mata ita sosai,sannan ya juya zuwa bandaki bacin rai yana cinsa kan yadda ta gansu,yayi yaqinin abinda zaizo ranta daban,abinda zata rayama ranta yasha banban da abinda yake faruwa,ya tura qofar toilet din ya shige. Gaban madubi ya tsaya yana duban fuskarsa,hannunsa yasa yana yamutsa sumarsa zuwa bayan kansa,yadan riqeta da qarfi yana jin haushin kansa da kansa,ta yaya zai riqe yarinyar cikin jikinsa har kamar haka?,sai yaja wani irin tsaki kamar zai cire harshensa,yana jin tsantsamin jikinsa dama hannayensa,duk da cewa babu abinda ke fita a jikinta sai lallausan qamshin turaren firdaus. Wayarsa ya ciro ya turawa jabir tex kan ya shigo masa da kayan sawarsa,sannan ya ajjiye wayar,ya soma fidda kayan jikinsa yana jefarwa,ya daidaita ruwa me dumi sosai daga shower ya shiga ciki yana sabe jikinsa kamar zai cire fatar wajen. Da wani irin nutsuwa dakiya da kuma tsare gida ya dawo dakin,bayan ya shirya cikin wata lallausar jallabiyya da aka yiwa aiki d wani gold zare mai kauri,idanunsa suka sauka a kanta,tana lafe a wani lungu dake daura da gadon,sai ya sake jan tsaki can qasan ransa,yana jin takaici na sake kamashi,baisan me anni ma ta dauki aure totally ba data hadashi da wannan. Bai tsawaita magana da ita ba,cikin taqaitattun mintuna ya gama tsara mata dukkan wasu qa'idoji da dokoki da yakeso tabi da kuma zauna akai,ya riga daya sani a yanzun bai isa yace ya rabu da daya daga cikinsu ba ko ta yaya kuwa sukazo masa indai bada wani qwaqwaran dalili ba,sai ya sauke boyayyar ajiyar zuciya,yana jin yayi maganin rabin matsalarsa,ya tabbatar a yanzun bashi da wani sauran case da ita wannan yarinyar,saura dayar,ya fuskanci itakam waccar kanta yana rawa sosai,zai kuma shata mata layi tsakaninta da rayuwarsa. Fita yayi ya barta a dakin,bai dawo ba sai da bacci suka kama idanunsa,duvet din ya yayima ya koma saman kujera yayi kwanciyarsa,bayan ya kashe hasken dakin,bai wani jima sosai ba bacci ya daukeshi,don tunani da damuwar dake kansa a yanzun ta ragu sosai. Kasa sakewa tayi cikin dakin,motsi kadan saita tuna abinda yayi mata dazun,abinda ke sake bata tsoro kenan,duk da maganganun da yayi mata dazun sun sake nuni da girman tazarar dake tsakaninsu,wanda zuciyarta tafi raya mata cewa gargadine ya sanya ya aikata mata hakan,bawai don ta isa ko tana da wani abu ba,babban shinge da layin daya gindaya tsakaninsu kawai ya sake tabbatar mata da cewa da gasken gangancin aka aikata na hadata aure dashi kamar yadda ya gaya matan,ita kanta daga dazu zuwa yanzu da kuma sanin data yi masa a baya ta sake tabbatarwa kanta tako ina yafi qarfinta,ya kuma yi mata fintikau,tun tana takure har gajiya tasa gabbanta suka saki,ta kuma zame da jikinta a nan qasa daura gadon,bacci mai nauyi ya fara fusgarta,zuciyarta cike fal da tsoronsa daya dasa mata a wannan rana. 31 Ya samu nasarar dasa tsoronsa sosai cikin zuciyar maimunatu har ma fiye da yadda yakeso,washegari da suka fito tafiya kasa hada idanu tayi da anty maama,wani irin kunya da nauyinta ta dinga ji,cikin motar kuwa tana cure waje daya,kamar xaka ce ket! Ta zura da gudu,wannan karon a bayan ya zauna,ya kame owners corner abinsa,duk wani motsinsa tana ankare dashi,saidai da kunnuwanta don tuni ta saye idanuwanta cikin mayafi. Duk tsahon awannin da suka diba suna tafiya aiki yake da na'ura,daga system zuwa wayar hannunsa,tsahon wadan nan awannin ko daya baiji tayi wani qwaqqwaran motsi ba,abinda ya sanyashi daga kai suna dab da shiga garin gombe ya dubeta. Ko ta cikin yalwatacce mayafin data lulluba har saman kanta yana iya hangen zallar quruciua da kuma qanqantar data yi masa,wani takaici na sake kamashi kan anni,sam ita babu ruwanta da duba da cancanta ne ko kuma dacewa?,gwara unaisa ta cika shekarun da zai kirata da mace,saidai ko ita din ma bata burgeshi ba ballantana wannan rabin macen,ta yaya ma idanuwansa zasuji wata diya mace ta burgeshi?,baya zaton zuwan wannan ranar,wannan duka shaheeda ta tafi dashi,tabar masa fankon zuciyar,ta yaya fankon zuciya kuwa zata san dai dai daba dai dai ba?,sai yaja dan qaramin tsaki acan ciki,yana maida dubansa ga allon computer,yana karanta saqon rubutun da ya mamayr fuskarta. Katafaren wuni ake cikin gidan dr marwan,don sanda duka isa gidan a cike yake maqil,abinda ya sanya ammi ta bada maqullin wani kebantaccen waje dake gidan aka sauki maimunatu da danginta,aka kuma cikasu da cimaka kala kala,kafin yammaci inda suka hau shirya maimunatun bisa jagorancin anty maama,don Allah ya sanya mata matuqar qaunar maimunatu,tana burgeta ainun. Sanda suka kammala sunso su kaita cikin gidan wajensu anni da amma,amma sai annin tace a wuce da ita gidanta kawai,maimunatu tasu ce,babu wani abu sabo da zasu gaya mata,don haka direct aka fito da ita zuwa jerin gwanon motocin da aka aje domin miqata gidan captain ja'afar marwan khalid akko. Duk abin nan da ake tana jin komai ne tamkar a mafarki,wasu hawaye masu dumi suka zubo mata sanda taji.motocin sun fara motsawa zasu bar gidan dr marwan,babu abinda ya fado mata a sannan sai "Allah ya nunan ranar aurenki,ya baki miji na gari" sai gata yau a bigiren zuwa gidan mijin da batasan yadda zasu rayu dashi ba,a lokacin da qasa ta jima da rufe idanun mahaifiyar tata "Allah ya jiqanki daada"ta fada cikin ranta,wannan din addu'a ce da kullum rana batasan sau nawa take yinta a ranta da kuma sarari ba. Tana jin sanda 'yan uwanta da sauran 'yan rakiya ke yaba kyau da kuma tsarin gidan,kowanne bakinsa na furta addu'o'i a kanta,abinda ita ta rasa gane kansa har yanxu,Allah ya zaunar da ita yakuma dawwamar da ita a gidan mutumin nan?. A hankali yake takawa zuwa sassan ammansa,sanye da wani irin sassalkan yadi ruwan hanta,wani irin dinki aka masa me kyau wanda yake nuni da zallar zamani da kuma wayewa,takalmin fata ne a qafarsa budadde wanda ya dace da kayan jikinsa,kamar yadda saman kansa yake sanye da hular da itama ta dace da kalar takalmin qafarsa. Wata irin tafiya yake,sam jikinsa babu kuzari hakanan Babu karsashi a tattare dashi,ya tura qofar falon amman,akwai sauran baqi da suka rage cikin gidan,umma ce qanwa ga ammansa ita da wasu mutum uku,su suka gaya masa amman tana bedroom dinta,sai ya wuce kansa tsaye. Sai da yayi knocking ta bashi izini sannan ya tura ya shiga bakinsa dauke da sallama,luf luf dakin yake a tsaftace gana fidda wani irin qamshi me dadi,kai baka ce ba biki akeyi cikin gidan ba,tana saman gado tana gyarawa amna kwanciya,sai ya matsa ya rusuna gabanta yana gaidata,ta amsa kana shuru na sakanni ya biyo baya,ta gama gyarawa amnan ta saka mata pillow sannan ta waiwayo ga ja'afar "Zaku wuce kenan?" Kai ya jinjina mata,yana zare hular dake kansa,can qasan zuciyarsa kuwa wata nannauyan ajiyar zuciya ya sauke,yana jin komai har yanzu kamar a mafarki "Ma sha Allah,Allah ya tsare,ubangiji yasa a shiga a sa'a,Allah ya kauda dukkana abunqi,ya albarkaci tarayyarku,kayi qoqari ka riqe amanar yaran mutane,ka kuma ji tsoron Allah a zamantakewarku,ka sauke nauyin da duka Allah ya dora a kanka,na horeka ka zama adali,ka kiyaye haqqin kowacce akan 'yar uwarta,karka yi zalunci,kada kuma ka bari a zalunci kowa,Allah ya shige muku gaba" "Ameen ya rahman,na gode amma" ya fadi yana jin jikinsa yana yin sanyi,wannan daren yana tuna masa da daren aurensa na fari ne da shaheeda,wanda akwai tarin bambance bambance masu yawa. Matsawa yayi gaban gadon ya dora hannunsa saman kan amna ya shafa,sannan ya duqa yayi kissing kuncinta,ya maida mata abun rufar ya miqe tsaye yana zuba hannayensa cikin aljihunsa "Sai da safe" yace da amma yana takawa zai fice "Allah ya bamu alkhairi" ta fada tana bin.bayansa da kallo,duk yadda yake qoqarin boye damuwar dake saman fuskarsa ita ta karanci hakan,saita rakashi da addu'a "Wannan hadin ubangiji kasa ya zama silar waraka a rayuwarka". Motarsa ya wuce kai tsaye kamar yadda ya zaba tafiya shi kadai babu dan rakiya ko daya,don zuwa yanzun ma yasan abokansu sun tsufa gidan jabir koma suna shirin juyowa,yace baya buqata,shi din ai ba auren fari xaiyi ba. Yana shirin bude motar yaji sallamar khadim a bayansa,sai ya waiwaya yana amsawa,cikin girmamawa ya miqa masa wasu ledoji dake hannunsa "Gashi inji ammi" jim yayi na sakanni yana bin ledar da kallo,sai kuma ya bude masa back seat bau tare da yace komai ba,khadim din ya fahimta abinda yake nufi,don haka ya qarasa ya saka musu su a baya,har ya juya zai tafi yace masa "Kace mata na gode" yayi maganar ne sanda yake shigewa cikin motar,ya maida.murfin ya rufe ba tare daya jira cewar khadim ba. A hankali yake tuqin kamar wanda baison isa gidan,tafiyar data daukeshi mintuna masu tsaho fiye da mintunan da zasu isheshi a al'adance,horn daya mai gadin gidan ga dage masa gate din,sai a sannan yadan ja motar da gudu ya shige da ita farfajiyar gidan,sannan ya faka ta a parking lot idanunsa na sauka kan wata qaramar sabuwar mota ruwan zuma,ya dauke kansa yana kashe tasa motar. Har ya fito ya tuna da ledojin da ya bari cikin motar,sai ya koma ya debosu,tun kafin ya bude ma ya fuskanci meye a ciki,sai ya riqesu a hanauyensa,dai dai sanda me gadin gidan ya iso cikin rusunawa ya fara gaidashi,amsa masa yayi cikin kulawa,saboda yana daga cikin dabi'arsa girmama duk wanda yake aiki a qasansa,barshi dai da zafinsa miskilanci rashin daukan raini da rashin son wasa da aiki,hannunsa ya sanya cikin aljihunsa ya fiddo 'yan dari biyar biyar sababbi guda shida ya miqa masa,hannu biyu ya sanya ya karba yana ta zabga godiya,yayin da shi kuma yayi gaba abinsa ba tare da yace tak ba. Sai da yayi addu'ar shiga gida sannan ya kutsa kai cikin babban falo,shuru yake babu alamun motsin me rai cikin gidan,cikin nutsuwa ya fara takawa zuwa stairs,sai kuma ya tsaya cak saboda maganar da abbi da kuma amma suka gaya masa a daren jiya da yau,ledojin hannunsa ya kalla,a hankali sai yayo baya,ya kuma nufi qofar dake hannun dama na falon. A hankali ya tura qofar,falo ya bayyana,wanda aka qawata da kalolin kujeru da curtains masu azabar kyau,royal blue da golden,komai na falon,a tsaftace yake cikin qamshi da sanyi daya gauraye da sabunta,ci gaba yayi da tafiya har ya isa qofar bedroom din,itama ya turata ya shige. Dai dai lokacin da take zaune saman abun sallah,saboda ganin yadda lokaci yaketa tafiya,an doshi sha biyu na dare,kuma ana binta sallar isha'i da kuma shafa'i da wuturin da batayi ba. Can qasan maqoshinsa yayi sallama idanuwansa suna sauka a kanta,gabanta ya buga fat,don bata tsammaci shogowarsa din ba,saboda dukkan wata magana daya gaya mata a jalingo ta haddacesu tsaf a kanta, janye kansa daga wajen da take yayi,ya isa gaban madubi ya ajjiye ledar a kai,sai ya tsaya yana goye da hannayensa a qirjinsa. Raka'ar qarshe take amma kawai sai ta miqe taci gaba da kawo wasu raka'o'in,abinda ya sanyashi sakin hannayensa kenan,ya kuma juya a hankali ya fice a dakin bayan yaja qofar kamar yadda ya ganta. Sallamewar sallarta ta fito ne hade da ajiyar zuciya,ta danyi shuru tana karanta la'ilaha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin,tana kuma jin yadda zuciyarta take bugawa,lumshe idanunta ta sakeyi,ba shakka tana tsananin tsoronsa,tana tsoronsa bilhaqqi da gaske,hoton sanda ya zuba mata lafiyayyen marin nan ya gilma a idanunta,sai kuma sanda yake zuqar hayaqin taba yana bulbular da ita daga bakinsa zuwa hancinsa,sai ta girgiza kai,tana jin wani bala'in haushinsa yana ratsata. Yaya akayi ya kasance mashayin taba?,bayan shi din ya fito ne daga gidan tarbiyya kamar haka?,mutane masu karamci dattako da sanin darajar dan adam?,bata tunanin akwai wanda yasan yana sha din cikin gidan,don ko da wasa bata tabs jin anyi magana makamanciyar wannan ba. Tunanin ta ture gefe,ta fara karanto azkar dinta da bata samu tayi ba a yau din,gefe na zuciyarta kuma cike taf da kewar amna,tana jin cewa zaiyi wuya bata nemi su anni su bata yarinyar ba,don ko a yau ma sai da akayi wayon janyeta sannan suka tahi,wanda ita bata kawo hakan ba,ta tsammaci zasu taho ne da ita,amma sai taga akasin hakan,to me zata zauna ne tayi a gidan?,gwara gwara ma ace da amnan,zata taimaka mata wajen debe kewa. Kamar yadda ya shiga sasssan maimunatu haka ya shiga na unaisa,saidai ita ya sameta tsaye ne a gaban mudubi tana kallon kanta bayan ta gama sake feshe jikinta da turare tana gyara zaman rigar jikinta. Sallamarsa hade da turo qofar ya sanyata saurin maida mayafinta saman kanta, ta rufe ruf,saidai tana iya hangensa ta cikin mudubin,wani sassanyan abu ya ratsa zuciyarta ya kuma haifar mata da yalwataccen murmushi akan fuskarta,a fakaice taci gaba da binsa da kallo,tana jin wani farinciki yana ratsata,burinta ne na tsahon wasu shekaru Allah ya cika mata shi,duk da cewa ranta ya baci a dazun da ganin irin gidan daya zaba a jjiyeta kuma tare da wata,saidai anty talatu ta kwantar mata da hankali "Kinsan baso yake ba,ta yiwu yayi hakanne don ya baki haushin dama harkiyi wani abu da zai janyo a fasa gaba daya,dole fa saikin anjiye rashin haqurin nan,kin janyo hankalinsa a hankali a hankali,sanda zai canza miki gida ko ya rabaki da qasar ma gaba daya bai sani ba" qwarai ta gamsu da maganganunta,don haka ta ajjiye komai gefe a ranta. Cikin salo ta amsa sallamar tasa cikakkiyar amsawa,bai sake cewa komai ba itama ya ajjiye mata ledar,ga zatonta zai qaraso koda gefanta ne yace wani abu da ita,saidai gani tayi yana shirin ficewa,muryarsa can qasa ya furta "Gudnyt" ya tursasa zuciyarsa ta fada,duk don son ganin yayi abinda ya dace bakin gwargwado. Gabanta ne ya fadi sanda yake gab da fita,ta daga kai tana dubansa ta madubin,zuciyarta tana bata shawarar tsaidashi,yayin da wata zuciyar ke hanata,tana gaya mata girman wannan rana a wajenta,ita yafi kamata ace an tsaida,an kuma nema kasancewarta cikin dakin,tana wannan shawarar da tattaunawar da zuciyarta har ya fice. Kasa zaune tayi,ranta ya baci sosai,ta dinga kai kawo tana tunani a ranta,shin sassansa ya tafi ko kuwa na maimunatu?,sai taji zuciyarta taqi aminta da hasashen daketa mata yawo,don bai kamata ace sassan maimunatun ya fara sauka ba,tunda a qa'ida itace babba,ta girmewa maimunatu,ita ya kamata ta fara karbar baquncinsa,tafi maimunatu sanin rayuwa dama komai da komai da za'a tarairayi mutumin da ya jima babu mata a gefansa kamarsa,don haka ta gyara rufin mayafinta,ta kuma bude qofar ta fito. Bata ma isa sassan maimunatun ba taji motsinsa daga sama,don haka taja birki,ta kuma koma nata sassan,girman kai yana sauko mata,tana jin ba zata iya nemansa a yau ba itama. Yana shiga dakin ya sauke ajiyr zuciya mai qarfi kamar zai tofar harda qirjinsa,ya soma bin dakin da kallo,an qawata masa shi yadda yakeso ya kasance,idanunsa daya bayan daya suna sauka kan hotunan shaheeda da amna da amra wanda aka musu tare yasa aka gyarasu aka shiryasu a falon gwanin burgewa,kai kace idan ka kirayesu zasu amsa,zakayi tsammanin har yanzu sune ke rayuwa cikin gidan,addu'ar da baya gajiya dayi musu yayi wani abu na motsa ransa,ya wuce zuwa bedroom dinsa. Sai daya gama duba komai daya ce a sanya masa a dakin,wanda yake buqatar ya canza masa waje ya canza masan ya ajjiyeshi inda yakeso,sannan ya fidda kayan jikinsa ya zubasu a laundry basket,sai ya wuce toilet kai tsaye,ya daura alwala sannan ya fito ya kuma bude walking wardrobe dake manne da bedroom dinsa ya shiga ya duba wasu navy silk pyjamas Natalya's company,ya shirya kansa wadata jikinsa da turaren da yake amfani dashi duk dare,sannan ya feshe kansa da BB hair spray. Abun sallarsa ya shimfida sannan ya tattara dukkan hankalinsa da nutsuwarsa ga alqibla. Unaisa kuwa kusan raba dare sukayi suna waya da anty talatu qanwa ga mahaifiyarta haj Aayah,tana gaya mata abinda yafaru,ita kuma tana shirya mata yadda zata aiwatar da komai,sun jima sosai suna tattaunawa kafin suyi sallama "Amma dai lafiya ko?" Haj Aayah da suke kwance daki daya da qanwarta wadda bata kai ga komawa gida ba ta tambayeta "Eh to,lafiya amma ba lau ba" abinda ya farun ta gaya mata,sai ta sauke ajiyar zuciya "Yaron nan fa ba lafiyar kwanya ya cika ba,idan anyi magana sai kuce depression ne ya kamashi bawai ciwon hauka ba,ni tsorona ma kada ya kama min diya ya jibga,don banjin zanyi kawaici,babu yadda banyi da unaisa ta haqura dashi ba amma ta kasa haqura" murmushi talatu tayi "Banda abinki yaaya,ta yaya yana da ciwon hauka zan goya ma unaisa baya ta aureshi,an gaya miki ciwon damuwa ne,kuma a yanzunma komai yana wucewa tunda gashi ya amshi mata har biyu,mudai burinmu kawai diyarmu tayi zarra ta zama star dinsa,don kishi da bafulatana sai an kula,shegen surkulle garesu" haka suka yita tattauna maganar a tsakaninsu a daren. Itako maimunatu wani nutsuwa ta sauko mata bayan ta gama dukka addu'o'inta ta isa ga gadonta ta kwanta,gadon data dinga ji kamar ba nata ba,dakinma kansa jinsa take kamar an bata aronsa ne,kewa da kadaici suka dinga damunta,sosai ta dinga ji cikin ranta inama ace an bata amna,sannu a hankali idanuwanta suka dinga nauyi,bacci kuma me qarfi ya fusgeta. *Follow my arewabooks account for more latest pages* *Arewabooks:HUGUMA* ______________________________ *YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA* INAYA(riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 32 *WASHEGARI* Tun sanda ta idar da sallar asuba bata koma bacci ba kamar yadda ta saba,tana ta azkar dinta,yayin da rabi da rabi na hankalinta ke kan tunanin yadda rayuwa zata kaya mata cikin gidan. A hankali taji idanunta suna mata nauyi,gajiyar zaman mota daga gembu zuwa gombe ya sanya bata kai ga qarasawa ba bacci yayi awon gaba da ita,ba kuma ta farka ba sai wajen qarfe tara saura na safe. "Hasbunallahu wani'imal wakil" fa fada s sauri hamma na qwace mata,ta miqe tana linke abun sallar data tashi akai,daga nan kuma fa zarce sa bubbuge bubbugen qura duk da dakin babu abinda yayi,ta kauda abinda yake zaune ba'a kan tsari ba,daga nan ta wuce toilet kai tsaye,ta hada ruwa tayi wanka. Sanda ta fito hudubar anty maama da yadikko matar kawu sulaiman akan tsafta da kula da kanta,duk da cewa kwatakwata qazanta ba dabi'ar ta bace. Cikin mayukan dake jere saman madubinta ta bude wasu ta shafa,sannan ta duba makekiyar wardrobe dinta ta jikin bango. Tsaiwa kawai tayi tana kallon tarin uban suturun da a yanzu suke mallakinta,sai takejin kamar ta zurawa rayuwa jikinta da yawa,banda haka ina ita ina wadan nan kayan da batasan ranar da zata gama sanyasu ba?,haka ta dinga dubawa har zuwa lokacin da hannunta yakai kan wata atamfa,kalarta ce ta dauki idanun maimunatu,data gwada sanyawa kuwa saita amsheta,tayi mata kyau matuqa da gaske,batayi amfani da dankwalinta ba,a maimakon hakan sai ta nema qaramin hijab ta maqala a kanta. Bakin gado ta koma ta zauna,ta rasa abinda zatayi,sai kuma ta fada tunane tunane,abubuwan da suka faru a rayuwarta,suke ma kan faruwar,tsakiyar haka taji kamar qararrawar falon nata neman dauki,hade da knocking,tayi kamar kada ta fita,amma jin baa fasa knocking din ba ya sanyata miqewa. Cikin nutsuwa ta fita,qafafunta suna nutsewa cikin lallausan carpet dake malale a wajen har ta iso falon ta doshi qofa,dai dai sanda yake saukowa daga samansa,sanye da wata jallabiya saqar qasar morocco,ruwan a qasa da aka yiwa ado da wani zare mai dan kauri ruwan madara,yankakken hannu gareta,don haka dukka singalalinsa dake lullube da gargasa waje yake,sumarsa tadan hargitse kadan,haka nan fuskarsa na nuna alamu na jin bacci. Idanunsa a kanta sanda ta bude qofar yana step na qarshe,ta gane fuskar matashin saurayin dake miqo mata kwanduna dauke da fulasai masu azabar kyau "Daga gidan dr,amma ce tace a kawo muku" sosai taji dadin karamcin amman har cikin ranta,tasa hannu ta karba tana cewa "Kayi mata godiya,Allah ya saka da alkhairi" sai ta maida qofar ta tura ta yadda take,ta kuma waiwayo don komawa ciki ta sama musu mazauni. Karaf idanunta ya sauka a kansa sanda yake isa gaban babban freezer dake falon tamkar ma bai ganta ba,budeta yayi ya ciro babbar gorar ruwa guda daya,gabanta ke wani irin faduwa,tsoronsa dake shaqe a zuciyarta ya motsa "Ina kwana" ta fada bakinta yana dan rawa kadan,tana jin kamar zai mata wani mummunan abu ne,banda alamun sauti da taji da sai tace bai amsa gaisuwar tata ba,kunnuwanta na biye da takunsa sanda yake shirin komawa saman,sai tayi ta maza tace "Ga abinci amma ta aiko dashi" shuru na wasu sakanni suka ratsa yana ci gaba da tafiyarsa,kamar bazai ce komai ba sannan tayi yace "Madalla,an gode" yaci gaba da hayewa saman,kunnuwanta dai na biye da sautin takunsa,takun da ake yinsa cikin wani irin salo da kuma tafiya wadda jinin sarauta ke yawo a cikinta. Sai data daina jin motsinsa sannan ta daga kanta tana duban kwandon hannunta tare dason gane me madalla da yace take nufi?,ita yanzu ya zatayi da wannan abincin?,sai ta maida dubanta ga sassan unaisa dake a rufe,zuwa zatayi ta mata magana ko kuwa ta qyaleta?,kai ta girgixa,zuciyarta tafi karkata da ta qyalesu gaba daya,don haka tayi kitchen da abincin,ta ajjiye acan,bayan ta bude ta diba iya abinda cikinta zai iya dauka,wanda duka duka cikin plate daya ta xuba komai. Tunda ta koma daki bata sake jin motsin kowa ba,don ko data gama cin abincin sake kwanciya tayi,ita ba gwanar kallo bace bare ta dawo falonta tayi,sai bayan kusan awa biyu taji tashin mota daga farfajiyar gidan,wadda batasan ta waye ba,saidai tana kyautata zaton tame gidan ce. Qarfe daya da ashirin na rana tana fitowa daga alwalar sallar azahar taji knocking da 'yar hayaniya,sake fitowa tayi falon,har yanzun kamar dazun dai babu kowa ba kuma motsin kowa. Murmushi ya subuce mata sanda ta bude qofar,laila ce ita dasu hanne da hauwa,sai fa'iza da safina harda khadija,kusan dukkaninsu mutanenta ne,akwai sabo tsakaninsu sosai,abinda yasa ta sake jikinta ta kuma ji dadin zuwan nasu "Ina fatan dai yaa ja'afar bai nan?" Fa'iza ta fada tana dan fidda idanu gami da watsa idanunta a babban falon gidan hadi da kallon stairs din,qaramin murmushi maimunatu tayi tana kada kai "Ya fita" ta amsa musu kai tsaye,don motsin fitar motar dazun ranta yana gaya mata shine "Na baroshi wajen amma ma fa sanda muke fitowa" safina ta fada tana zare mayafinta daga kanta "Au to,dama wai don mufi sakewa ne" ta fadi tana dariya,ita dai maimunatu jagora ta musu zuwa sassansu,suna tafe suna gaya mata ba dadewa zasuyi ba,amma tace au dawo da wuri,kuma su hauwa da qyar idan ba anjima zasu wuce ba,zasu biya ta jalingo ne,akwai gaisuwar mutuwa da akayi da zasu fara zuwa sannan su wuce gembu. Awa biyu kawai sukayi,amma sai taji kamar sunyi awa biyar,saboda yadda hirarsu ta dinga debe mata kewa,kowacce na qoqarin koya mata yadda zata zaun a gidan,ta kuma kama hankalin mijinta sannan ta tserewa kishiyarta,kasancewar dukansu sun girme mata,ita dai jinsu kawai take da kunne,hausawa sukace me daki shi yasan inda yake masa yoyo. Da suka tashi tafiya sukace zasu leqa wajen unaisan su gaisa,cogewa maimunatu tayi har suka shiga suka fito,sannan tayi musu tattaki zuwa farfajiyar gidan,karon farko kenan da taga yadda harabar gidan yake,salmanu drivern abbi ne ya kawosu,tana tsaye tana binsu da kallo har suka fice daga gidan,sai ta sauke ajiyar zuciya tana jin tamkar ta bisu,cikin matuqar sanyin jiki ta dawo cikin gidan. Tunda ta koma din bata sake jin motsin kowa ba,gaba daya gidan sai take jinsa wani iri,babu armashi babu kuma dadi,tana jin inama za'a maidata gidan abbi?,inama zaa maidata wajen anni,rayuwar can tafi mata dadi dari bisa dari. UNAISA tun bayan tafiyar 'yan uwanta da sukazo mata bayan sallar magrib ta shiga toilet dinta ta sheqa wanka,sunyi maganganu masu tarin yawa da anty talatu,wanda ta dinga qoqarin ganin tabi kowacce shawara da umarni da anty talatun ta dorata akai. Cikin wasu azababbun English wears ta shirya kanta, straight leg jeans da rigarsa wadda tsahonta iyakarta cinya,ta zuba turare sosai a jikinta,ta kuma wadata fuskarta da powder da lip gloss da ya qarawa lips dinta sheqi,nails polish remover ta saka ta cire tsohon nail polish din,ta sabunta da wani da yaketa glittering. Sai data tabbatar komai yayi,ta juya gaba da baya sannan ta dauki wayarta,already tana da number dinsa,saidai bata taba gigin kira ba,ta zauna gaban dressing mirror dinta ta kara wayar a kunne sanda take ringing,tana kuma kallan fuskarta,gabanta yana dukan uku uku,don batasan da wacce fuska zai tarbi kiran nata ba. Dai dai lokacin da yake kashingide bayan motarsa suna magana da mr husain daya daga cikin manyan ma'aikatansa,kallo daya ya yiwa wayar ya dauke kansa ya maida ga maganar da sukeyi dashi cikin ma'ajiyar motoci ta kamfanin nasa,wanda ya budewa wuta yakeson ya dawo dashi.hayyacinsa,ya kuma ci gaba da aiki fiye da yadda yakeyi a yanzu. Al'adarsa ce haka,ba kasafai yake daga baquwar number ba,don haka da ring din ya isheshi saiya maidata silent yaci gaba da uzurin gabansa. Da matuqar sarewa ta sauke wayar daga kunnenta,kira uku kenan bai dauka ba,sai ta yanke ta tura masa gajeran saqo kawai,don haka ta batayi qasa a gwiwa ba ta senda masa _hello hottie,it's your wife calling you,i missed you so much today,please come back as early as possible,akwai abubuwa masu dadi dana tanadar maka....am waiting for you,urs.....unaisa_ Sanda saqon ya shigo wayar tana hannunsa yana duba wani verification code da wani company suka turo masa,zai bawa mr hussain,tsaki yaja wanda sai daya fito a fili,har sai da mr hussain ya daga kai ya kalleshi,saidai bai tambayeshi ba,shi sam yama mance dasu,tunda yasa qafa ya fice yau din duka aiki ya riqeshi,gaba daya hidimar company dinsa ne a gabansa,ko gidama da yaje amma kawai ya samu ya gaisar ya wuce,bai samu ganin abbi ba bare anni,saboda akwai sauran baqi,shi kuma bayason wannan wasan banzan da akema mutum da sunan abokan wasa. Sai daya bawa mr hussain duk abinda zai bashin sukayi sallama sannan ya yiwa driver dinsa sign da ya shigo su tafi,sai daya tada motar suka fice a company din sannan ya tambayeshi "where are we going sir?" "Take me to the nearest restaurant" ya bashi amsa yana kara wayarsa a kunne,jabir ya kira,don tun dazun yaga miscalls dinsa,a sannan yayi calling urgent meeting da ma'aikatansa,daya fito kuma ya manta sai yanzu ya tuna. Sai data kusa tsinkewa ya daga,cikin wata irin raunanniyar murya me cike da sanyi jabir din ya masa sallama,muryar data sanya ja'afar din tuno abubuwa masu yawa a shekarun baya wadanda suka shude masa,kamar shi a irin wannan lokacin da jabir din ya kirashi,da qyar ya samu ya daga,a sanda yake rayuwa da muradin zuciyarsa shaheeda. Yayi kamar zai katse kiran,sai kuma ya dake,suka gaisa ya gaya masa uzurin da yasa ya kirashin "Am sorry J,amma if possible please kayi postponing schedule din zuwa upper month mana,saboda ina tunanin tafiya honey moon ni da my fa'eem" wani dogon tsaki ja'afar ya sake a kunnen jabir,yana jin kamar ya raina masa wayau ne "What nonsense are you talking about?,ina maka magana ne akan abinda ya shafi company kana min maganar honeymoon,if u r not ready to accept your vacancy shikenan fine,i can I can manage the company" daga haka ya katsr kiran cikin fusata,tamkar wani gagarumin abu jabir din ya gaya masa,yana furzar da wata zazzafar iska daga bakinsa. Ko da yaje eatery din da drivern ya kaishi,ya kuma zaba abinda zaa kawo masan sai ya kasa ci,daga qarshe haka ya miqe ya biya abinda aka cajeshi duk da tsadar abinci a wajen ba tare daya ci wani abun kirki ba,yace su wuce gida kawai. 33 A hankali yake takawa zuwa cikin gidan,duka hannayensa cikin aljihun rigarsa,duk da yadda ya gaji amma sai daya daure ya biya ta store din gidan,ya duba kayayyakin amfanin da yace a zuba a ciki,ya tabbatar a saka komai da komai na amfanin gida na yau da kullum,sannan ya rufe,ya bulla ta qofar kitchen. Dai dai lokacin da maimunatu ke cikin kitchen din,tana tunanin yadda za'ayi da abinciccikan da aka kawo na safe rana dana dare,tunda bai cinyu ba,daga qarshe kamar yadda taga acan gidan sunayi,saita kwashesu ta zuba a freezer. Hannunta take daurayewa a bakin famfon dake cikin kitchen din,tana gamawa ta kashe ta juyo tana yarfe ruwan dake jiki,dai dai sanda yake fitowa daga store din,idanunsa suka sauka a kanta,cikin lausasan kayan bacci,doguwar riga baby pink da baby hijab light blue,kalar datayi masifar haskata,ta kuma fidda gewayayyar fuskarta dake nuna qarancin shekarunta,sam bata lura dashi ba,saboda idanunta yana kan hannayenta,har sai data zo gab sannan ta ankara da inuwarsa,taja baya kuwa da sauri gabanta yana faduwa,idanuwanta suka fada cikin nashi,zallar tsoron dake zuciyarta ya bayyana qarara cikin idanuwa da fuskarta. Wani kallo yayi mata fuskar nan a dinke babu ko digon annuri,jinta tayi tamkar nutumin da zaki ya ritsa a tsakiyar jeji babu gurin kubuta,sai ta rasa me ya kamata tayi,cikin juriya da qarfin hali jajayen lips dinta suka motsa "Sannu.....da zuwa" ta fadi a rarrabe,dauke idonsa yayi daga kan labban nata yana jan qaramin tsaki qasan ransa,yadda tayi maganar ma kawai zai gaya maka shes very young,ta yaya wai ma anni zata ce ya ajjiye kamar wannan a matsayin matar aure koda ya tashi yin auren?,wannan ba saidai a dauki buzunta ba duk sanda yace zai kaara jikinsa a nata?. "Ungo nan" taji ya fada a maimakon amsa sannu da zuwan data yi masa,daga kai tayi a hankali tana duban abinda yake miqo matan,kafin ta saka hannu ta dauka a saman fridge din dake daura dasu,inda anan ya aje mata kafin takai ga karbar,sababbin kudi ne a daure a kyauro masu yawa,don ko da batasan adadinsu ba amma tasan cewa suna da yawa qwarai "Idan kina da buqatar wani abu kiyi amfani dasu,banason ki nemeni,don banason damuwa da takura,take care" gyada kai tayi a hankali,sannan tace dashi sanda yake fita a kitchen din "Allah ya saka da alkhairi" bata iya jin ya amsa ko bai amsa ba,itadai tabi bayansa itama ta fita bayan ta tabbatar yayi nesa da wajen,kudin na rungume a hannunta,saidai tana tsananin jin qyamar kudin har cikin ranta,itafa...daga randa ta ganshi yana zuqat taba shikenan kuma,bata masa kallon komai sai dan iska,mugu kuma azzalumi,biyo bayan abinda yayi mata,zuciyarta cike fal da tunanin mema zatayi da kudade haka?,me zafa buqata dasu?,da wannan tunanin ta fada dakinta ta kulle,ta isa gefan gadonta ta jawo side drawer ta jefa kudin ta mayar ta rufe. Tunda taji motsi a sama ta tabbatar shine ya dawo,don haka ta sake duba kanta da kyau,sannan ta bude freezer dinta ta dauki sassanyan ruwa da lemo ta aza saman wani set din tray me hade da cups,ta yane kanta da wani dan yalolon mayafi,sannan ta fito. Wani abu ya mintsini mai kama da kishi sanda idanunta suka sauka a sassan maimunatu,basu taba haduwa da yarinyar ba,basu taba gamuwa ba,ko yaya take?,tana ina yanzu oho?,taja wata qwafa kamar zata cire harshenta sanda zuciyata ta raya mata ace dai taje ta sameta tare dashi. Har tsakiyar zuciyarta falon nasa ya tafi da ita,akwai wani yanayi na musamma tattare dashi,taci gaba da takawa a hankali ta nufi bedroom dinsa kai tsaye,saidai kuma kamar yasan wani zaya shigo masa,yana shiga kafin ya shiga wanka ya murza key,tana taba handle din ta gane hakan,dole ta koma saman kujerun alfarma dake falon,ta zauna ta dora qafa daya saman daya bayan ta kunna tafkekiyar tv dake falon,takuma canza tasha zuwa mbc Bollywood,ta samu kuwa suna wani film me kyau,saita maida hankalinta a kai,yayin da wani sashe na zuciyarta kuma yaketa wassafa mata yadda zai tarbeta,duk da tasa a ranta ba zata samu tarba me kyau dari bisa dari ba. Cikin jallabiyya Morocco's male abaya me ruwan gold mai gajera hannu ya shirya bayan ya fito daga wankan,duk da baici abinci ba amma sam baya jin yunwa,muryar amna yakeson ji,yayin da wani sashe na zuciyarsa kuma a yau yake cike da kewar shaheedansa,ya feshe jikinsa da lallausan turaransa bayan ya gama gyara sumarsa dake samun gyara na musamman,ya dauki wayarsa ya danna kiran number ammansa. Bugu biyu aka daga,salma ce,ta shaida masa amman tana wajen abbi,sai ya nema ta hadashi da amna,ta kuwa hadasun,yarinyar ta dinga masa hira sosai,abinda yasa ya samu relief daga abinda yakeji kenan,yadan sake shima yana tayata. Ya kusa minti talatin tare da ita,ya samu sauqi sosai cikin ransa,harma ya samu qwarin gwiwan jin son shan coffee,don haka ya diba takardun da zai duba da system dinsa ya nufi falon. Janye idanunta tayi daga fuskar tv din tana sakin murmushi,jarumin film din yana mata mugun yanayi da J dinta,yadda ya iya soyayya ta tabbatar J zai iya finsa,saidai shawo kansa da qwato hankalinsa abune mai wahala ta sani kuma,dai dai sanda take shirin sake maida idanunta ga film din,sai suka sauka ga babban hoton shaheeda dake rataye cikin falon,zuba ma kyakkyawar fuskarta idanu tayi,murmushin da take a cikin hoton tajiyana tabata,sake waiwaya tayi wani sashe still hotonta ne ita da twins dinta amna da amra,daga daha bangaren kuma shi da ita ne,sunyi masifar kyau cikin qananun kaya,karon farko data fara ganin wani abu me kama da murmushi saman fuskarsa,yana rungume da ita ta baya,da gani ba'a qasar nan aka dauko hoton ba,yana sanye da uniform da matuqan jirgin sama,kyau iya kyau yayishi,uniform din sun karbeshi matuqa da gaske,hoton ya fusgi hankalinta,ya kuma saka kishin shaheeda mai yawa cikin ranta,har sai data miqe ta isa ga hoton dake can wani kusurwa na falon,ta tsaya a gabansa tana sake qare musu kallo. Da farko daya fito bai lura da ita ba,sai daya kusa isa inda ya ajjiye na'urar hada coffe dinsa take,yadan tsaya kadan,kamar zai magana sai ya fasa,ya isa inda coffee maker din yake,ya soma hada abinsa,saidai abun mamakin har ya hada ya dawo ya zauna saman kujera bata ankara da wanzuwarsa,abunda yayi masifar bashi haushi,saidai zaiga iya gudun ruwanta da nata qwaqwqwafin da kuma sanya idon. Hannu ta sanya zata daga hoton don ganin date din jiki sosai "Don't dare touch it" ya fada da kakkausar muryar data ankarar da ita yana wajen,tadan zabura kadan tana juyowa,idanunta suka sauka akansa, sipping coffee dinsa yake hankali kwance,idanunsa kan tv din daya sauya tasha zuwa ta news,kai baka ce da ita yake magana ba. Wani mugun kyau yayi mata,sai ta dinga jin inama ace zai rungumeta,ko ita ya bata wannan damar?,qoqarin dai daita kanta tayi,sannan ta fara takowa cikin salo na canjin tafiya zuwa inda yake zaune "Welcome home" ta fada tana sakar masa murmushi,saidai kuma abun haushin,baiko kalleta ba bare ya fahimci kwainanen da takeyi,hasalima tambaya ce ta biyo baya "Who gave you permission to enter my room?" Tambayar data sanyata yin sak,kafin kuma ta saki murmushi tana ci gaba da takowa "am your spouse fa,mene ne a ciki?" ta fada tana isowa dab dashi,shirinta shine ta zauna daura dashi din. Idanun nan nasa masu matuqar nauyi da kwarjini ya daga ya watsa mata su,abinda ya sanyata tsaiwa ta kuma kama kanta,bata sake gigin yunqurin zama kusa dashi ba yadda taso a baya,kamar bai shirya yin magana ba,saidai zuciyarsa tana gaya masa,ita kadai ce a yanzu zata zame masa damuwa cikin gidan baiyi wasa ba,itakam waccan bashi da damuwa da ita ya tabbatar,don ya gama da babinta,unaisan ke kallon kanta a ta cika macen da zata kutso kai tayi tarayya dashi cikin rayuwarsa,abu mafi wahala da tsada da diya mace ke nema ko ta samu daga wajensa,yana jin komai nasa kebantacce ne na musamman "Am warning you for the second time,stay away from me,banason kutse cikin al'amurana,Live your life,I live mine,banason kutse cikin al'amurana,ki kiyaye" ya fada da sautin dake nuna gargadi mai qarfin gaske. Har cikin zuciyarta maganganunsa suka soketa,tanason ta maida masa raddi amma kuma ya mata kwarjinin da ko bakinta ta kasa motsawa "Am saying in respect, get out of my room" ya fada with his husky voice. Jikinta a sanyaye ta fara takawa zuwa bakin qofa,gefan ranta a quntace,sai ya ajjiye cup din idanunsa na sauka kan tray din data ajjiye,ya janyo wata qaramar dawer daga jikin kujerarsa,wadda ba kowa ne zai kula da ita ba,ya ciro kudi kusan adadin wanda ya baiwa maimunatu ya dora mata a kai,sannan yace "Dawo ki dauke kayanki" cak ta tsaya,kamar ba zata dawo din ba saboda yadda qwalla ke neman cika mata ido,to amma ba zata iya tafiyar ba,saboda yadda muryarsa ke iya canza duk wani nufi naki,ta dawo ta dauka din kamar yadda yace sannan ta fice. Cup din ya dangwarar a wajen,yana furzar da iska daga bakinsa,shi kansa yana jin baiyi dai dai ba,amma kuma hakan shine dai dai a wajensa,gwara tun wuri kowacce a cikinsu tasan cewa bata da gurbin zama cikin rayuwarsa,yafi kyau ya nesanta kansa dasu akan ya sake musu su sanya ransu a kansa. Tun a falonta ta watsar da komai suka tarwatse sukayi nasu waje,ita kuma tayi daki da sauri tana sakin kuka,wayarta ta laluba,ta kuma kira anty talatu,kukantanya daga mata hankali sosai,don da qyar ta iya ta mata bayanin abinda ya faru. Murmushi anty talatun ta sake,alamun hankalinta a kwance yake "Hmmmm,yaro man kaza,ke haka kike unaisa?,baki da haquri?,ga shegen gaggawa?,daga fara wasan saiki saare?,waya gaya miki abu mai daraja da tsada yana samuwa ta sauqi haka?,in just a minutes amma kin gaza?,haka zaki nunawa kishiyar taki har ta fuskanci kema kin kasa?,to kiyita kukan,idan kin gama kya kirani na fada miki abinda zan gaya miki" sai ta kashe wayarta,itama bata sake kiran nata ba,sai data gama kukan nata,ta kuma huce sannan tayi kiran nata. ********Cikin kwanakin ya maida kansa busy qwarai da gaske,duk wani tunani nasa da kulawarsa na ga companies dinsa dake nan gombe kano da kuma lagos,kusan tun daga ranar yama mance dasu cikin lissafin rayuwarsa,basu kuma sake haduwa da kowacce a cikinsu ba,kamar yadda suma kowacce rayuwa take a sassanta ba tare da 'yar uwarta ba,duk da cewa sau tari maimunatu takanyi kamar ta leqa su gaisa da unaisan,amma kuma sai taji tsoron yin hakan,musamman idan ta tuna da me gidan kansa "Qila itama irin halinsa ne da ita" abinda zuciyarta take raya mata kenan,saita juya ta koma. Daga gidan dr marwan ake kawo musu abinci kullum,safe rana dare babu gajiyawa,kullum maimunatun ke amsa,ta kuma barshi saman dining na main parlor na gidan idan ta diba yadda zai mata,wanda yawanci ma idan ta diba na rana ita shike kai mata har dare,bata sake neman wani kalar abincin. Ba kasafai yake dawowa gidan da wuri ba,yakan kai tara ko goma,kuma daya dawo ya haye samansa yake rufewa,idan ba wani babban uzuri ba baya saukowa sai washegari,takwas na safe ya fice sabgoginsa,saidai lokaci lokaci yakan sauko ya duba cikin gidan ko akwai wata matsala,sai ya tabbatar da babu wani abu da ake buqata sannan ya sake komawa,a hakan suka kwashi sati biyu cur,a ranar suka tashi shuru babu saqon abinci,dama kuma maimunatu ta tsammaci hakan,don haka qarfe sha daya saura bayan tayi wanka,ta danyi gyare gyarenta cikin daki wanda basu da yawa,tayi wanka ta shirya kanta cikin wata army green din atamfa me maroon din ado saita fita zuwa kitchen don samawa kanta abinda zata saka a bakinta. Ruwan tea ta dora,ta kuma hada kayan qamshi kamar yadda ta koya daga wajen baba tabawa,sannan ta juya ta laluba dankali ta debo bayan ta kwashe wadanda suka lalace saboda kwanakin da suka dan dauka ba'ayi amfani dasu ba,ta dauko qwai guda biyu ta fara aikinsu. Tana aikin tana kuma tunane tunane,abinda ya zame mata jiki,a zaman kwanakin da tayi cikin gidan,zaman kadaici,da za'a irga adadin tunanin da tayi zata tashi wani dan qaramin littafi,ta saqa burika masu yawa da takeson cimmawa a rayuwarta,wadanda bata da tabbas din wanzuwarsu,tunda dai bataga hanya ko qofar da hakan zata kasance ba,nan din tana wani zama ne kwatankwacin zaman mutumin da aka kai prison. Bata dauki lokaci ba,ta gama komai,tuntuni ta juyr tea din a flask,dankalin kuma ta zuba akwando don ya tsane,ta matsa gaba tana neman plate da zata xuba,tana ta kokwanton ma zata iya cinyeshi kuwa. A dan hanzarce ta turo qofar kitchen din saboda wata mahaukaciyar yunwa dake sakadar cikinta,ta duba saman dining inda kullum take tadda abinci ta diba ba tare data damu da wanda ke girkawa ba. Motsinta ya sanya maimunatu dake dauko plate dakatawa ta waiwayo,idanunsu suka hadu waje guda lokaci guda,lokaci na farko kenan da kowacce taga 'yar uwarta,kuma kowacce a cikinsu jikinta ya bata. *HUGUMA* 34 *Arewabooks chapter 39* https://arewabooks.com/chapter?id=63637876d52c9563f3289fda _______________________________ Wani kallon qurilla me dauke da mamaki da kuma fargaba unaisa ke bin maimunatu dashi,zuciyarta na qiyasta mata wannan ce maimunatun?,wannan itace kishiyar tata?,yarinyar da duka duka bata wuce qanwarta ta uku biyu ba?,a qalla zata iya bata good five years,wannan zata kalla a matsayin kishiya?,no saidai ta dauketa tamkar 'yar aiki,amma kuma...... she's very beautiful,tana da wani irin kyau daya daki zuciyar unaisan,kyan da idan tace maimunatun ma 'yar aikinta ce ba shakka babu wanda zai yarda,don yarinta kam yarinya ce,amma batun tace 'yar aikinta ce ma bata taso ba,kyan yarinyar ya daketa,ya kuma tsole mata idanu tun daga kallon farko,abinda ya hanata sukuni,ko bayan data qarasa kitchen din tayi abinda zatayi ta fito,wanda gaba daya ruwan zafi ta iya dafawa ta juye a cup ta hada tea ta dauki five slices of bread ta hada dashi ta fita. Ji tayi sam bata jin taste na tea din,sai ta aje ta dauki waya ta kira anty talatu,ta kuma rattaba mata komai "Keba macace bace?,meye na daga hankalinki?" Ajiyar zuciya unaisa ta saki "Ba zaki gane bane anty,ni da nake mace ma kyanta ya tabani,ina ga da namiji?" Murmushi me sauti ta sake "Bakisan namiji ba kenan,shi kam idan zuciyarsa ta qyasa da abu babu ruwansa da kyansa ko muninsa,abu daya ne da zakiyi shine ki kama zuciyarsa da kyau ta duka hanyoyin da suka dace,ba da bakinki kike gayan tafi marigayiyar matarsa kyau ba?" Kai ta gyada kafin tace "Haka ne anty" "To amma me yasa wannan kyan bai sanya ya sota ba har yanzun zuciyarsa naga marigayiyar?" Tambayar da tun kafin ta amsawa kanta ita taji gamsuwa "Exactly" "Da kyau,abu daya ne yanzun zakiyi,ki tabbatar kawai yarinyar bata sake cikin gidan ba,duk yadda zakiyi ki nuna mata a qasanki take,matsayinku kuma ba daya bane,wanna zaisa ta kasa kallon kanta a matsayin cikakkiyar mace da har zata maida hankali wajen ganin tayi tarayya dake akan mijinku,sannan kinfinkowa sanin daga inda ta fito,bata da cikakkiyar wayewar da zaki kasa juyata yadda kikeso,cikin ruwan sanyi zata zame miki kamar qasqantacciyar 'yar aikin ba tare da ta ankara ba" dukka wadan nan maganganun na anty talatu dama wadanda suka biyo baya sunwa unaisa dadi,sai ta saki jikinta suka sha hirarsu,tana sake bata haske game da wasu abubuwan. Cikin zuwan da yakanyi gida wasu lokutan idan ya tashi a aiki da wuri anni tace ya kawo unaisa da maimunatu su gaida surukansu,hikimar hakan kuwa,tayi ne don taga kamun ludayinsa da kuma yadda su din suke zaune,don tun daga washegarin randa aka kaisu ba wani dan gidan daya sake komawa gidan nasa. Baya buqatar magana da kowacce a cikinsu,baisan ta yadda zai sanar musu su shirya ba,don haka sai kawai ya sanya driver ya dauki laila yace ya kaita gidan su taho tare,shi kuma ya wuce aikinsa abinsa. Kamar a mafarki maimunatu taga lailan,ta saki ihun murna ta rungume lailan duk da baqunta da rashin sakin jiki irin na maimunatun,sanda ko ta gaya mata inda zasun ji tayi kamar anyi mata bushara,sati na uku nason cikewa ko farfajiyar gidan bata qara leqawa ba tun randa sukazo tayi musu rakiya,nan da nan ta hau shiri,kafin ma unaisa ta gama laqai laqai dinta ita ta gama shiryawa,cikin wata jar atamfa data haskata sosai. Duk inda maimunatun ta motsa laila na binta ne da ido,tayi wani fresh sosai,fatarta kamar babu abinda yake hawa,saidai kuma babu wata qiba ko murmurewa da tayi,kuma tana da tabbacin inda maimunatun ta qara qiba lallai zama zatayi abar kallo,don komai na jikinta ya soma cika da alamun girma da budurci tare da kwarjini na aure. Sanda suka fito zasu wuce laila ta leqa yiwa unaisa magana,sai ta sameta bata ma shirya ba "Kaina kemin ciwo,kice ina gaishesu,zan sanya lokaci sai mu shigo ji dashi" amsar data bawa laila haushi matuqa,ta kuma fito tana mita,wannan ai tsabar rainin wayo ne,ita dai mainunatu batace komai ba,daga bisani ma sai ta janyo mata hirar islamiyya,wadda takejin kewarta qwarai da gaske,tana jin inama za'a barta taci gaba da zuwa,tana jin rashin dadi kan yadda haddarta ta tsaya cak,duk da tana tilawa a gida. Tsaki unaisa taja bayan jin tashin motarsu,me suka maidata ne?,ko sun manta matsayin ubanta a qasar nan,banda soyayyar da takewa J da ta yaya ma zata zauna a inda take yanzu?,ta yaya zata yarda ta hada kishi da wata bafulatanar ruga?,idan gaisuwar surukai ne ai basai ta hada kafada da 'yar qauyen yarinyar ba,cikin motocinta zata ja daya takai kanta gidan idan fa shirya gaishesun basai an mata jagora ko an tusata a gaba ba. Sai data shiga ta gaida amma da ammi sannan ta yada zango wajen anni,annin na karance da maimunatun sarai duk da ita bata fahimta ba,ta kuma samu gamsuwar gabatarwa da ja'afar qudurinta,don haka sanda yazo washegari gidan,akaci sa'a safiya ce,saboda yau din da yunwa ya tashi,don jiya bai samu tsaiwa yaci abinci a inda ya saba tsaiwa cin abincin ba "Makaranta nakeso ka dauki maimunatu da kanka ka sanyata" ta bashi umarni nakai tsaye idanunta a kansa sanda yake zaune gabanta amna na saman cinyarsa yana bare mata chocolate. A hankali ya daga kansa zai kalleta,sai ya samu itama shi take kallo,ba tun yau ba,yasan anni sarai,yasan kuma tunda ta tada zancan nan akwai abinda ta taaka,kamar zaice wani abu sai kuma yace "Ba damuwa" a taqaice,yadda yayi saurin amsawar ya bawa anni mamaki,ya kuma tabbatar mata akwai wata a qasa,kuma ruwa baya tsami banza,amma kuma zata zanya idanu taga me zai aikata "Idan ka tashi ka hada mata da waya,don ya kamata ace tana waya da 'yan uwanta,bawai don ta taho ta taho kenan ba" "To" ya sake cewa da ita "Kiyi picking ledojin chocolates din ki biyoni mota zaki rakani unguwa" yace da amna bayan ya sauketa daga kan cinyarsa ya kuma miqe,ta sauka kuwa da sauri tana murna,ta hau tsincewar tana ta yiwa anni da ta bishi da kallo surutu,hankalinta bai kwanta ba,tasan halin ja'afar itama,wannan saurin amsawar da yayi ba'a banza ba,amma koma meye ya shirya yi,indai cutuwa ne ga maimunatun ba zata bari ba. Shegen miskilanci gami da zurfin cikinsa yana nan har yanzu,yana da wannan nuna shakulaton bangaron kan abubuwan da yana sane dasu sarai,suna kuma cikin ruhi da zuciyarsa,amma sai yayi kamar bai damu ba,kamar baya ankare da abun,kuma kamar baya gani,saidai duk randa ya magantu ko ya dauki wani action akai kowa zaiyi mamakin hakan,wannan ya sanya anni ta sake sanyama ranta zata kula da komai da irin abinda zai biyo baya,ta sauke ajiyar zuciya tana hade hannayenta waje daya,fuskantar ja'afar ko yin gaba da gaba wajen saukeshi daga ra'ayinsa ya zuwa wani babban aiki ne da ba kowa zai iya shi ba,fatanta ubangiji ya dubesu,rayuwarsa ta sai saita,ya kuma riqe amanar yaran mutane kada suji kunya. *********Kwanaki anni tayita qirgawa tana jiran taji yace wani abu,ko kuma ya tanka game da maganar da sukayi da ita,saida har ta gama irga kwanaki bakwai baice komai akan maganar ba. A daren ranar ya koma gida da wuri kai tsaye daga wani gidan saukar baqi,inda suka tattauna da wani babban mutum da ya bawa company dinsa kwangilar ginin wata university da zai bude. A gajiye ya shigo gidan,ya wuce sassansa kai tsaye ya fidda kayan jikinsa ya watsa ruwa,duk da gajiyar da yayi amma yanason yaje gida wajen anni,don haka sai ya shirya cikin wani irin straight leg jeans da shirt masu azaban kyau,ya kuma sakaya qafarsa cikin wani rufaffen sneakers daya dace da kayan jikinsa,ya sake gyara sumarsa tsaf,kai bakace dare bane,ya dauki maqullansa da wayarsa guda daya a gurguje ya sauko,yana so yaje yayi ya gama ya dawo ya kwanta,don gobe yake sanya ran zai wuce lagos. A nutse yake tuqinsa,yana kuma amsa wayar da suke da jabir ta speaker din motar har ya isa gidan,sai daya tura hancin motar zuwa farfajiyar gidan sannan sukayi sallama dashi,ya dai daita tsaiwar motar a parking lot na gidan yana duban inda masu gidan ke ajiye motocinsu,akwai kotar hisham data abbi duka a wajen,da alama suna gida,sai ya balle murfin motar ya fito zuwa cikin gidan,cikin takun nan nasa dake nuni da qasaitarsa da kuma aji da yake dashi cikin jininsa,duk inda ya gifta sai ya bada ajiyar qamshinsa a wajen,wani qamshi na musamman da zaiyi wahala ka jishi jikin wani,turare na musamman yake amfani dashi,na jiki kuma ya banbamta dana kaya,hakanan na gashin kansa daban da wanda yake shafawa qirjinsa,dama can haka yake,dan gayu ne daya zarta kowa cikin gidan dama familyn khalid akko. Jifa jifa ma'aikatan gidan ke kawo masa gaisuwa har ya dangana da sassan ammansa,wanda kusan ko da yaushe yazo gidan wajenta yake fara zuwa,ya sameta zaune a falon gidan,sanye da hijab,yatsarta kuma sarqafe da da tasbah counter,idanuwanta na kan tv. Fuskarta fadade da fara'a ta gyara zamanta tana masa maraba "Kaine a daren nan?" Ta fada tana ajjiye masa ruwan data dauko masa da kanta,sai yasa hannu ya karba,duk da baya jin qishi amma kuma bazai iya wucewa tayinta ba,saboda kima da martabar da take dashi a wajensa,ya gaidata cikin girmamawa "Lafiya qalau,yasu maimunatu?" Sunan yajishi tamkar baqo a wajensa,don bai gama tantance wacece maimunatun ba,wadda ya lura duk zuwa shine suna na farko da take fara tambayarsa "Lafiya qalau" ya amsa mata,yana zarcewa da shan ruwan daya tsiyaya din,sai daya ajjiye cup din sannan ya dubi amma "Amna fa?" "Ina zaton tana wajen ammi,suna can sassan babanku da ita,yau rigima takeji tun yamma,wai sai an kaita gurin adda maimunatu" bai fahimci gundarin abinda maganar ta amma ke nufi ba,yadai dauka key dinsa ya maqala a yatsan hannunsa yana shirin tashi,dai dai lokacin da salma ta fito daga dakinsu,ta kuma ratso cikin falon cikin kwalliya,tana baza qamshin turare. Kafin ta qaraso ta ankara dashi,sai duka karsashinta ya zagwanye,ta sake saita kanta da kyau don kada tayi wani laifin,ta qaraso ta rusuna tana cewa "Barka da dare yaaya" "Yauwa barkanki dai" sum sum tafara takawa zuwa gaba,sai a sannan ya waiwaya zuwa inda take "Ke!" Ya kirata da nannauyan muryan nan tasa da take sanyasu cikin rudani da tsoro "Na'am yaaya" "Zo nan" ya fada yana mata sign da hannu ba tare daya sake dubanta ba,gabanta nata dukan uku uku ta dawo,ta sulale saman carpet din ta zauna tana dubansa yana danna wayarsa,sannan ya karata a kunne,second uku kacal yace "Ka bude ka shigarmin dasu sassan anni" iya abinda ya fada kenan ya katse wayar,sannan ya maida dubansa ga salma,sai tayi qas da kanta,yana da wani irin kwarjini wanda ba kowa ke iya sanya idanunsa cikin nasa ba "Ina zakije?" Dan muskutawa kadan tayi,duk sanda ya sanyata gaba da wata tambayar komai qwace mata yakeyi,kamar ba ita salman ba,'ya gayu me aji,wadda take kadawa maza ganye,'yar jami'ar dake gab da kammala degree dinta "Yaa..... Ahmad ne yaxo" wani kallo ya watsa mata,wanda yasa tayi dana sanin bashi wannan amsar "Koma ciki ki saka hijab dinki" iya abinda yace da ita a taqaice kenan,ya maida dubansa ga wayarsa,bata da iko ko qwarin gwiwar musu dashi,don dole ta miqe ranta a bace kan yadda zai bata maka kwalliya ta koma dakinsu,ahmad din nan ba baqo bane,koshi kansa yasan da zamansa,tunda sai da iyayensa sukazo nema masa izinin fara zuwa wajenta,amma shi da yake wani irin mutum ne mai shegen tsari da qa'ida,ji yadda yayi kamar bai ganeshi ba. Da sallama ya shiga sassan annin,tana zaune a qasa,ta dora qafafunta saman tuntum,daya daga cikin masu aikinta na mata yankan farce,fa'iza khadija da laila na zaune daga gefe suna kallo duka harda annin. Sallamarsa tasa dukkansu suka gyara zamansu,hadi da hada baki wajen amsa sallamar tasa,anni ta waiwaya ta zuba musu harara "Ya'yan nema marasa kunyar Allah,ni da yake marainiyar wayonku ce magana nayi muku har babu adadi amma ba wadda na samu ta tankani,amma da yake dodon naku ke magana har hada baki kuke wajen amsa sallama kamar na Allah....." Laila daketa motsi tana yiwa anni sign na tayi shuru don Allah amma tayi kamar bata gani ba takasa shuru "Amma anni don Allah ba cewa nayi bari mu qarasa ganin wannan ba?" Da yatsa annin ta nunata "Ke arcan,kiyi ta kanki yarinya,ni zaki yiwa sanabe?" "Barka da dare" mai rahila me aikin ta gaidashi kanta a sunkuye "Kina lafiya" ya maida mata yana daga tsaye "Alhmdlh yallabai" "Ajjiye ki tafi" ya fada mata kansa tsaye,da hanzarinta ta miqe bayan ta ajjiyr nail cutter din,sai data bace a falon sannan ya waiwaya ya dubesu duka su ukun,ya sauke kallonsa ga fa'iza babbar cikinsu "Xoki dauka ki qarasa mata" cikin sauri ta taso ta zauna inda rahila ta tashi "Nidai ki bini a hankali,kada garin rawar jiki ki yankemin jiki ina lallaba rayuwata". "Tashi kije ka karbomin abinci wajen amma,idan kinso ki xauna ko kiyi mistake" ya fada cikin gatse,yana zama a qasan carpet daura da anni tare da duba agogon hannunsa,saura minti daya a fara haska wasan tseren dokuna, favourite thing nasa kenan,ya yiwa khadija umarni da ta bashi remote,tana miqa masa ta samu ta sulale daga falon,ya canza tashar yana jin anni na mitar me zasu kalla a nan?,shi dai baice da ita komai ba ya maida kansa ga kallonsa,har zuwa sanda laila ta dawo da wani qaramin kwando kamar na kaba,saidai an saqa wannan ne da wata irin roba me kyau,ta ajjiye masa a gabansa,sannan ta duqa ta fara shirin serving dinsa. "Stop" ya fada da sauri,a dan tsorace ta daga kanta,sai ya sauke dubansa ga yatsunta ba tare da yace komai ba. A tsorace ya dunqulesu cikin tafin hannunta,sai a sannan ta tuna,babu abinda yafi tsana irin tara farce "Na baki minti biyar ki tabbatar sun koma kamar na hannun kowa" abinda yace da ita kenan,ta gyada kanta tana miqewa,bataso ya gani ba,saboda bikin rumaisa za'ayi,cousin dinsu,diyar uncle umar,mai bin dr marwan. *Ku bibiyi shafina na arewabooks don samun sabbin shafuka* *AREWABOOKS:HUGUMA* INAYA(Riba biyu)___mamughee SANADIN LABARINA___Rano BABU SO___Billynabdul FARHATUL K'ALB___Miss xoxo GURBIN IDO____Huguma *ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?* *_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_* Biyar:::1k Hudu:::700 Uku::::500 Biyu::::400 Daya:::300 *_zaki saka kudin ta wannan account number din_* HAFSAT UMAR KABIR 2270637070 Zenith bank *Saiku tura shaidar biya zuwa ga* 07040727902 *IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR* 09134848107 *_THANKS FOR CONTINUES PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰 35 _INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._ _TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_ _A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_ _AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_ _SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_ _BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_ _AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_ _AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_ _SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._ _KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_ _NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_ _INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_ _YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_ _________________________________ Ficewarsu sai falon ya zamana daga shi sai annin,yaja kwanukan yayi serving kansa da kansa,ya dauki plate din ya dora saman qafafunsa ya fara ci. Duka anni na karantarsa ba tare da tace komai ba,yadda yake cin abincin nasa ya sake tuna mata da ja'afar din,har yanxu qasaitarsa da jan girman nan nasa yana nan,rashin daukan wasa qarancin magana da rashin walwala,saidai kuma baya wasa da cikinsa,har yanzunma haka abun yake,yadda taga yana cin abincin ya tabbatar mata babu komai a cikinsa "Ni na rasa wanne irin wayo da dabara ne wannan,ka baro abincin mata har biyu a gidanka kazo kana cinyewa bayin Allah abinci?" Idanunsa ya sauke ka fuskar anni,da gangan take musu gorin abinci,duk sanda kaji tana gorin abinci to 'yan rigimar nata ne a kusa,batasan cewa shima yau da tasa rigimar yaxo ba,don haka baice mata ta tafas ba,sai daya gama yana goge hannunsa da tissue,duk da ba da hannun yaci ba,ya janyo takardun da yasa a shigo masa dasu ya ajjiye a gabanta. Kallon takardun tayi sannan ta maida dubanta gareshi tana bata fuska "Meye wannan din?,kasan dai ba wani bokonku nayi ba da zaka turon takardu gaba ko kana wani cushe fuska kamar tsohon kashi" can qasan ransa ya murmusa,amma ko days ba alamun murmushin a saman fuskarsa,yasan zata fadi sama da haka ma idan tana jin rigimarta "Takardun makaranta ne da kika nema a samar mata" fuska ta yatsine "A samarma wa?" Ta fada tana jifansa da kallo "Kin manta maganar da mukayi kenan?" "Na manta,saika tunamin" hannu ya miqa ziwa gabanta zai janye takardun nasa yana fadin "Duk randa kk tuna zan dawo saimu qarasa tattaunawar" "Kaniyarka.....kaniyarka nace" ta fada bayan ta danqe hannunsa "Ka kirata da maimunatun kake ganin asara?,manya....manya ka kiyayeni" sakar mata takardun yayi,ya koma baya yayi relaxing yana dubanta cikin calmness din nan nasa,har ta gama fadanta,sannan don kanta tace "Ina jinka,wacce makaranta ce?" "Pen resources academy" ya amsa mata a taqaice,shuru ta danyi don makaratar ta kwanta mata,kafin ta sake cewa wani abu hisham yayi sallama falon,saita diba takardun ta miqa masa tana cewa "Dubamin da Allah,wacce makaranta ce wannan?,tana da kyau ko kuwa lullubin biri ce?" Qunshe dariyarsa yayi,da alama yayan nasa ya yiwa anni halin nasa,sabgarsu shida annin babu me shiga,idan ka shiga kunya zakaji wajen anni,saidai kuma idan suka tashi al'amarinsu saisu. Duba biyu ya yiwa takardun ya gama fahimtar komai,me yasa yayan nasa zai dauki maimunatun ya kaita boarding school,duk da cewa ba nisa bane a tsakaninsu,amma koma meye ita din a yanxu ai matar aure ce,eh makarantar nada kyau da kuma tsari me kyau,saboda private ce da ake biyan maqudan kudaden da sai dan wane da wan ke yinta,to amma ya manta igiyar aurensa dake kanta?. "Ya ka tsaya?,tana da kyau?" "Sosai ma anni,makaranta kwana ce,tana gombe bauchi road" da fari a zafafe ta daga kai ta dubi ja'afar din da niyyar qare masa tatas,saidai kuma yadda ya kashingida hankali kwance kamar baisan abinda ke faruwa ba ya tabbatar mata da biyu ya aikata hakan,saita jinjina kai,ta kuma maida dukka wani fadanta data debo niyyar yi masa,zata bishi ta yadda ya biyo,amma kuma tabbas yaci bashi ne,zai kuma gane ta yaro kyau take bata qarko. **********washegari******* Daya idar da sallar asuba bai koma ba,saboda tafiyan dake gabansa,zaibi flight ne da zai tashi qarfe goma na safe,waya ya amsa me dan tsaho da CEO na wani company da yakeson zuba hannun jarinsa a kamfaninsu,yaci a qalla awa daya cikin wayar,har sai daya fara murza goshinsa saboda maganar ta fara hawan masa ka,bai fiya jurewa doguwar magana ba,ya bashi excuse kan cewa idan ya gama abinda yake bayan ya shigo lagos din zai nemeshi,da haka sukayi sallama. Ajiye wayar yayi yana lanqwasa yatsun hannunsa da yaji sun sage masa,ya kalli agogo,qarfe takwas da ashirin,yana son shiga gym room amma lokaci bazai bashi dama ba,don haka ya miqe yana nufar falonsa don ya hada koda coffee yasha ne ya dumama cikinsa. Coffee powder din ya duba yaga ya qare,dole kenan sai ya sauka kitchen dinsu ko zai samu wani,sai ya zura slippers dinsa masu taushi,ya nufi qofa yana gyara maballin pyjamas din dake jikinsa. A hankali yake saukowa daga stairs din,falon shuru yake kamar kowanne lokaci,ya ratsa ta cikinsa ya wuce dining area ya wuce kitchen,hankalinsa da tunaninsa yana can ta wani waje daban. Dai dai lokacin da take kwashe gasashen dankalin data hada masa wata 'yar source data wadata da albasa da koren tattasai da nama da aka yiwa yankan cube shape,tana sanye da wata night gown mai taushi,me dogon hannu ce data sauka mata har qasa,ta sanya baby hijab dinta shima kalar rigar,abinda yasa baby face dinta sake fitowa sosai,quruciyar dake tattare da ita na sake fitowa. Kusan a tare suka daga kai suka kalli juna,saura kadan ta saki frying pan din dake hannunta,tayi hanzarin ajjiyeshi,sannan ta duqa har qasa ta fara gaidashi kamar yadda take masa. Ciki ciki ya amsa idanunsa na sauka kan dankalin,ya mishi wani kallon qyanqyami yana matsawa gaba ya fara duba kayan da suka kawoshi kitchen din,ci gaba tayi da tsugunnawa a wajen,turarensa na cike ilahirin kitchen din,kamar a yanzun ya fesa shi a jikinsa,ya gama daukan abinda zai dauka,ya nufi qofa. Har ya kusa fita ya tsaya,yadan tako baya kadan yana cewa "Ki shirya anjima kadan hisham zaizo ya daukeki,zai kaikai makaranta zasuyi miki interview,next week zaki fara zuwa,ko ince za'a kaiki keda kayanki,after every Three month zaki dinga dawowa hutu kafin ki koma" ya mata maganar gwari gwari,saboda gani yake babu abinda ta sani,babu kuma abinda take ganewa,idan ma yace mata boarding school ba lallai ta fahimceshi ba. A ba zata albishir din yazo mata,don ko a mafarki bata taba kawo hakan ba,bata taba tsammanin haka ba,tunda a society din data tashi bata ga ana hakan ba,cikin ruhinta ta dinga jin wani farinciki da bashi da misali yana kutsawa,ashe dai tana da rabo,ashe dai burinta zai cika?,tana shirin buda baki tayi masa godiya ya fice abinsa,yana fitar ta miqe cikin farinciki,tayi wani dan tsalle,ta qanqame jikinta waje guda tana fadin "Alhamdulillahi,miyatti Allah" cikin walwala karsashi da kuma kuzari taci gaba da aikin nata,Allah Allah take ta gama ta shirya,batason yaa hisham din yazonya jirayeta,tunda bai gaya mata qarfe nawa zaizo din ba. Sanda ta kammala girkin unaisa ta shigo,kamar ko yaushe cikin takun taqama isa da jin cewa NA FIKI FA,ta qarasa inda maimunatu ta adana warmers din,tasa hannu tana budewa,kafin ta zaqulo faranti cikin nata kayan kitchen din tasa serving spoon ta fara diba ba tare data ce da maimunatun kanzil ba. Bata daga kai maimunatun ta kalleta b,don kusan ta saba da hakan,ita ke girkin safe da kuma na dare amma unaisan tana rigata ci,da farko iya cikinta take,ganin unaisan tana diba ya tabbatar mata itama tana buqata,duk da bata taba budar baki ta gaya mata hakan ba,shi yasa idan ta tashi yi takeyi harda ita "Ina kwana?" Ta gaidata kamar yadda kowanne lokaci take mata,ganin cewa ya girme mata,ita kuma tana mata kallon yaya ne a wajenta,tunda shekaru da tazarar dake tsakaninsu tana da yawa. Bata amsa mata ba,saima dawowa da tayi ta dubeta "Daga yau idan kin gama girki,a cikin warmers dina nakeso a dinga xubashi,banason amfani da kayan kowa" ta fadi tamkar me magana dame aikinta. Maimunatun bata kawo komai cikin ranta ba,hakanan ranta bai wani baci ba,cikin girmamawa ta amsa mata da to,sai tasa kai cikin izza tana fita daga kitchen din. A kan lokaci maimunatun ta gama komai,ta gyara wajen ta wuce dakinta,daga nan toilet ta fada ta soma wanka. Yana gaban madubi yana amsa wayar muzaffar, cousin dinsa,kuma daya daga cikin ma'aikatansa dake aiki companynsa na lagos,gyara tie din suit dinsa yake,yana dai daita wuyanta yadda ba zata dameshi ba,ya gama ya dauki comb yana sake gyara qawatacciyar sumar kansa wadda take fidda sassanyan qamshi tare da wani sheqi na musamman da takeyi. "Okay,zan kiraka idan na iso,ka zama ready,banason jira" ya fada yana jefa comb din inda ya daukoshi tare da gyara hannun suit din nasa wanda aka yiwa wani ratsi daya sake qawata ta tare da nuna ainihin tsadar da take dashi,jikinsa sai fidda qamshin turaren bad boy yake na kamfanin carolina Herrera yakeyi,nan gaban madubin ya zauna,ya janyo sock dinsa ya sanya,sannan ya dauko takalminsa qirar qasar Italy dake daura da inda yake ya saka,sai ya miqe daga durquson da yayi yana furzar da iska cakude da ajiyar zuciya daga bakinsa,hadi da lumshe idanunsa yana tuna shaheeda,baisan dukka irin wadan nan wahalhalun ba muddin suna tare,komawa yake dan lelenta,bata barinsa yayi komai. Karar da yaji cikin wayarsa ya sanyashi hanzarin duba fuskar wayar,sai ya miqe yana daukan wayarsa,ya kuma janyo trolly dinsa zuwa qofar dakin,yana dora handle dinsa a bakin qofar unaisa tana turowa itama. Da kallo kadan ya bita dashi bayan ya janye mata baya,tana sanye da wata doguwar riga mai budadden hannu silk material butter color,tayi ado sosai wanda ya bayyanar da zallar hutu da jin dadin data samu tun daga gidan mahaifanta,saboda yadda farar fatarta take a kwance very smooth,bakinta sai qyallin lip gloss yake,tana tauna chewing gum a hankali. "Gud morning dear" ta furta tana murmushi tare da sake takowa gabansa,sai ya dan goce kadan yana amsa mata can qasan maqoshinsa "Morning" idanunta ta sauke kan akwatin hannunsa,da alama tafiya zaiyi,wanda ko alama itakam batasan da zamanta ba,tadan bishi da kallo sanda ya sanya hannu ya bude aljihun gaban trolly dinsa,kudade ya ciro,ya matso daura da ita kadan ya ajjiye yana cewa "am going to travel somewhere,zaku iya kiran number dake jikin nan whenever you need something" binsa tayi da kallo sanda ya gama jawabinsa,ya kuma taka cikin cikakkiyar nutsuwarsa ya soma barin falon "Ba wannan nake buqata,ba kudi nake so ba,ba kuma shine ya kawoni ba" cak ya tsaya daga tafiyar da yake,hannunsa daya na soke a aljihun wandon suit dinsa yana kallon qofa ba tare daya juyo ba,kamar kuma bazai juyo din ba,kamar yadda kuma yanayinsa ya nuna baida niyyan yin magana,saidai kuma faaida trolley din yayi,ya waiwayo ya kuma fara dawowa,cikin wani irin yanayinsa dake saurin sanya karaya da karyar da duk wata zarra jin kai da jin isa na 'ya mace ya aza mata idanunsa,a gabanta ya tsaya yana dubanta,ya sake sakaya daya.hannun nasa dake waje cikin aljihun wandon nasa,yadan raba qafafunsa kadan "Me kike da buqata?" Ya furta with husky voice,wadda bata sauka ko ina ba sai tsakiyar zuciyarta,ta kuma nada ajiyar wani yanayi mai tsauri ga zukata. Nata idanun ta daga da niyyar gaya masa abinda yake ranta quru quru,saidai inaaa,zarrar ba daya bace,don kuwa kasa qarasar da kallonta tayi izuwa fuskarsa,saita zube idanunsa a qirjinta,wanda iya nata tsahon kenan "Iya abinda zaki samu shi nake baki,indai wannan jikin kikeso,to a shawarce ki koma gida,don abune da bazai taba samuwa ba wajen wata har abada....." Daga haka ya juya abinda hankali kwance,ya riqe trolley dinsa ya fara turata waje,sai a sannan yace mata "Idan kin gama abinda zakiyi kina iya ki rufemin dakina" sai ya qarasa tura akwatinsa ya fice. Wani wawan kuka ga saki sannan ta sulale a waje ta zauna,ya Allah,itakam wanne irin abune J yakeso tayi?,wanne abu zatayi taja hankalin ja'afar,saita kifa kanta saman kujerarsa tana sheshsheqa. A shirye tsaf cikin Egyptian hijab ta fito ruwan golden yellow,tayi matuqar kyau qwarai,kyakkyawan fuskartan nan me dauke da wani lafiyayye kuma boyayyen kyau tayi fayau tsakiyar fuskar hijabin. Yana zaune cikin motar w farfajiyar gidan,don bai shiga ciki ba tunda yasa daya daga cikin masu gyaran farfajiyar yayi mata sallama,wayarsa na a hannunsa yana chart,ya bude qofar mazaunun gaba dake daura dashi,takun tafiya ya sanyashi daga kansa,ya sauke su ga madubin dake gefan murfin motar,fes ta fito a ciki,tana takawa cikin nutsuwa inda yake tsimayinta din. Gabansa yadan fadi,ya lumshe idanunsa yana sauke ajiyar zuciya,kana ya kauda dubansa daga gareta,kasancewar yasan haramcin aikata hakan a yanzu,har yau yana jinta a ransa,kuma har yau yana jin zafin rasata,tun daga randa zai shiga dakin anni yaji tana masa tayin auren yayan nasa yakejin wani abu ya tsaye masa a wuya,saboda tabbacin rasatan da yayi,amma yayi namijin qoqarin ganij ya fidda komai daga ransa,tunda yana da tabbacin ya rasata rashi na har abada. Baisan me yahau kan yayanshi ba daya kasa gane baiwar da Allah yayi masa,ya kuma yi masa musaya na abinda ya rasa,duk da baisan gaibu ba,amma yana da yaqinin idan maimunatu batafi marigayiya quality ba,to tabbas marigayiya ba zata fita ba,ko yanzun driver yaji yana zancan ya kaits makarantar,sai yaga rashin dacewar hakan yace zaije. Sauke qafafunsa yayi ya gyara zamansa gami da ajjiye wayar sanda ta iso dab da motar,ya sanya hannu yana laluba maqullin tare da amsa sallamarta sanda take yunqurin shigowa cikin motar cikin nutsuwa da kamewa "Ina kwana ya hisham?" Murmushi ya sakar mata "Haba anty moon,ai kya bari na fara gaidaki dai ko?,matar babban wa yayace itama" kunya ce sosai ta kamata,tayi qasa da kanta tana yaba karamci da kirkinsa,shi kam halinsa yasha banban dana dan uwansa,tasan hakan tun ba yau ba,tun tana gidan dr. Motar ya kunna suka fito daga unguwar gaba daya suka hau main titi da zai kaisu pen resources,rashin sabo ya haifar da shuru a tsakaninsu,duk da yaso yadan jata da hira ko zata sake amma sai ya fasa,sabon album na wani waqar hausa ya sanya musu,duka sai sukayi shuru kowa yana saurare,musamman maimunatu da batasan waqoqin ko kuma mawaqin ba,ta dinga bin duka baitukan cikin zuciyarta tana nazartarsu,sai taji waqoqin sun mata,suna kuma motsa mata wani da wani abu ckin zuciyarta,duka baituka ne da suka shafi soyayya da qauna,masu taba zuciyar duk wanda yake cikin soyayya. Sanda suka isa makarantar ayi mata dukka abinda ya dace,an kuma ce next week ne zasu fara daukan sabbin dalibai kamar yadda ja'afar ya gaya mata,sosai farincikinta ya nuna,har hisham yana tsokanarta,ya zaci hukuncin da yayan nasa ya yanke bazai mata dadi ba,sai kuma yaga akasin hakan,tabbacin mutum ce ita mai tsananin son karatu. Kasancewar batasan hanya ba yasa bata gane inda ya nufa da ita ba sai da suka je,gidan anty maama,abinda ya yiwa maimunatu dadi qwarai,ko babu komai zata miqe qafarta ba zata koma waccan kurkukun da wuri ba,karon farko data soma zuwa,qawataccen gida mai bala'in daukan hankali da nuna gayu da kuma dukiya,cikin tafkeken falonta na alfarma ta saukesu,farinciki fal zuciyarta,ta rasa wacce irin sauka zatayi musu,take tasa masu aikinta suka cika musu gabansu da kayan ciye ciye har babu adadi "Amma dai ba daga gida kuke ba,don nasan J bazai barku ba" anty maama ta tambayi jabir sanda maimunatu ta shiga toilet don tayi futsari ta kuma hado da alwalar sallar azahar,saboda mukhtarinta ya shiga,yana bare ayaba mutuniyar tasa ya amsa mata "Daga makaranta,na kaita sun mata interview" "Makaranta?,wacce?" "Pen resources boarding" "What?" Anty maama ta fada cikin mamaki tana kallon hisham,kai kace shine ja'afar din "Bama day din ba?" Ta sake tambaya "Yadda dai kikaji haka ne" ya amsa mata yana tauna ayabar,don shima bashi data cewa akan al'amarin J din "Meye hakan yayi kenan?,mtseew lemme call him,wannan sam bai dace ba,yana son yayi avoiding nata ne akwai a fakaice,ya Allah.....wanne irin mutum ne J din?,kuma anni ta sani ta barshi?" "To ya zata masa,badai matarsa bace?" Wayarta ta janyo ta fara laluban layin jaafar din,wanda a dai dai lokacin yana kwanye bayan lafiyayyar motar company dinsa datazo daukansa,a nutse ya daga wayar yana duba me kiran,sai ya daga ya kara a kunnensa. *GURBIN IDO* 36 *Arewabooks:HUGUMA* https://arewabooks.com/chapter?id=6364b7c12730d61e09816f8b __________________________________ "barka da warhaka" anty maama ta fada,yadan saki muryarsa kadan,duk da haka akwai heaviness din nan a cikinta dake qara masa kwarjini ya amsa mata "Barka kadai,yasu hamood" "Kowa yana nan lafiya qalau" "Ma sha Allah" ya amsata a taqaice,sai ta danyi shuru kuma,ita kanta wani lokaci kwarjini yake mata,duk kuwa da cewa duk irin miskilanci da zafin kai irin nasa bai taba qin bata girmanta ba,saidai babu wani dogon magana me yawa tun dacan a tsakaninsu,shi yasa lokuta da yawa hisham dinne abokin maganarta,amma tuna wannan attitude din nasa na respect ya bata nutsuwar cewa "Muna tare ne da hisham,yanzun yake gayamin wai kaine kace akai maimunatu boarding school?" "Maimunatu?"ya dan maimaita sunan,sai kuma yace "Oh.....eh,hakane,abinda anni ta buqata kenan,komawarta makaranta" "Amma sai nakega anni bawai tana nufin a kaita makarantar kwana ba ko?" Ta fada cikin kwantar da murya "Ban sani ba gsky,na duba kawai makarantar dake da kyau ne,kuma sai naga kamar abun arziqi nayi" shuru tayi ta jinjina kai "Shikenan,Allah ya rufa asiri" "Qarata ya kawo kenan?" Ya jefa mata tambayar,saita gyada kanta da sauri "A'ah sun dai biyo ne shi da ita mu gaisa" "Ok,yayi" ya fada kana ya sauke wayar yana kashewa ba tare da yabi ba:asin me yasa suka biyo din ba,tunda basu gaya masan xasu biyo ba. Gefe ya aje wayar yana duban titin lagos da suke ratsawa cikin sa'a yau babu cinkoso da yawa,sai yake jinsa sakayau,ya rufe case din wannan,saura dayar,ita dinma da bata wuce lavel don boarding din ba hadasu zaiyi ko xai samuu peace of mind,haka kawai ya samu yana lallaba rayuwarshi annin ta hadashi da aiki. **********Bakwai da rabi na safiyar litinin a pen resources academy tayi musu ita da hisham wanda shine ya kawota da kanshi,sanye take da uniform dinta da duk wani abu da sabon dalibin boarding na private school zai buqata,ba wasu kaya bane masu yawa,saboda makarantar suna da tsari ba kamar government boarding school ba,makaranta ce ta wadanda sukaci suka tada kai,saboda haka duk wanda ka gani a cikinta ba dan kuci ku bamu bane. Tunda suka shiga makarantar ta tabbatar da haka,duba da irin motocin da suke sauke daliban da a yau suka dawo daga hutun zangon qarshe na shekara. Sai da aka kammala komai hatta daki aka bata hisham yana zaune,bayan ya tabbatar komai yayi settling ya dubeta,murmushi yadan qwace masa ganin yadda idanunta suka tara qwalla "Zan koma matar babban yaaya,Allah ya bada sa'a,yasa a fara a sa'a" hakanan sai taji zuciyarta ta karye,kamar wadda aka kai nisan duniya,tana qoqarin maida qwallarta ta amsa da amin,tana nan a tsaye har ya isa motarsa ya budeta ya shiga,har ya tadata sai kuma ya kashe ya sake fitowa,hannunsa dauke da madaidaicin kwali ya miqa mata "Na manta,ga waya koda zaki buqaci communicating da mutanen gida" wayar ta kalla sannan ta maida dubanta gareshi,wannan shine karo na farko da aka soma malllaka mata waya a rayuwarta,sai tasa hannu bibbiyu ta karba tana masa godiya "Babu komai fa" ya sake amsa mata yana murmushi,har zuciyarsa yana jin tausayinta,tun dava randa laila ta bashi labarin wacece ita,sai data ga fitarsa a makarantar,sannan ta juya jiki a sanyaye,saita duba agogon dake daure tintsiyar hannunta,lokacin shiga aji yayi,don haka ta ciro school bag dinta dake saqale a bayanta ta cusa wayar a ciki sannan ta kama hanyar da classes dinsu yake. Da sallama ta shiga ajin,sai ta dan tsaya tana dawurwura,don ajin adan hargitse yake da hayaniyar dalibai,wanda basu ma lura da wanda ya shigo din Ta gefanta taji alamun shigowa,saita waiwaya kadan,daliba ce kamarta take shigowa ajin,hannunta dauke da water marker da kuma wasu litattafai,suka hada idanu saita dauke kanta,ta isa gaban allo ta zube marker din,sannan tazo zata giftata,har tadan gota ta waiwayo ta dubeta "Sabuwar daliba?" A hankali maimunatun ta gyada mata kai,sai ta waiwaya tana duban cikin class din sannan ta sake maido dubanta gareta "Ga seat din muje ciki" hakan ya bata damar bin bayanta,har suka isa gaban wani seat,sai taga ta zauna daga gefe,kamar yadda ta karanci duk set daya yana daukan mutum biyu ne "Zauna a nan,akwai abokiyar zamana,amma dawowarmu wannan hutun ashe ba zata dawo ba,an canza mata makaranta,saiki maye gurbin wajenta" tace da maimunatu tana dauko jakarta gami da zugeea tana fiddo da sabin exercise tana dorsawa saman desk din "Na gode" ta amsa mata a taqaice,cike da tsarguwan kallon qurillar da daliban ke binta da shi. Tun zamansu a wajen ta fuskanci lokaci bayan lokaci sukan hada idanu da class captain din,wadda taji suna kira da afrah Ateeq Muhammad,tana taqaitawa da afrah A muhammad,duk sanda suka hada idanun sai ta dan sake mata murmushi kawai taci gaba da abinda takeyi,itama maida mata martani take,sai taji kallon bai dameta ba. Lokacin break har tayi gaba sai ta dawo ganin maimunatu a zaune "Zamuje dakin cin abinci,ko kinsan hanya?" Kai ta girgiza "Okay,kina iya tasowa mu tafi" "Na gode" ta fada tana miqewa,ta ajjiye jakarta tabi baya afran. Abinda ta lura afra nada kirki,tana kuma da kyakkyawar mu'amala da jama'a,hakanan tana da mutane sosai,a nutse take,bata da tarin hayaniya ko rawar kai,tare suka gama cin abincin sannan suka dawo aji. Karfe biyu aka tashi daga makaranta,masallacin cikin makaranta taga yawancin daliban suna tafiya,bataga afran ba,don gab da zaa tashi ta fita a class din,tana buqatar koyon wasu abubuwan da kanta,don haka sai kawai tabi sahun daliban itama ta wuce zuwa masallacin. Batayi gaggawar barin masallacin ba sai data fuskanci lokacine na komawa daki kowa ya huta,ta dauki jakarta ta nufi inda dakunan kwanan dalibai mata yake,tana tafiya ne a hankali don kada ta bace a dakin,jifa jifa tana cin karo da dalibai a verender,duk wadda tazo giftatan kuma sai ta bita da kallo,a haka ta isa dakinsu,ta murza handle din sai taji qofar a bude take,ta tura da sallama tana shiga. Madaidaicin daki ne,mai dauke da gadon kwanan dalibai guda hudu,shimfidadden tiles qaramin toilet da kuma locker ajiyar kaya da aka bawa kowanne dalibai,wutar na'urar solar da fankar sama dake juyawa a hankali,fes dakin yake sai qamshin freshener da yake fiddawa. Gadon da yake qasan nata gadon tunda a sama take taga mutum a kwance,ta motsa sannan ta dago tana amsa sallamar tata,suka hada idanu,sai taga afra dince,murmushi tayi mata tana miqewa daga kwanciyar da tayi "Ah,baquwa,ashe dakinmu daya?" Murmushin itama maimunatu ta maida mata "Ban sani ba nima sai yanzu,dazun da nazo ajjiye kayana babu kowa a dakin" "Yanzun ma saini kadai,su feena basu shigo ba,sun tsaya karbomin magani a pharmacy" afra ta fada tana dan yatsina fuska "Ayyah,baki da lafiya ashe?" "Wlh,yau duka daurewa kawai nakeyi,da ciwon mara na tashi" ta fada tana cije labbanta,da alama ciwon ya motsa mata ne "Sannu,Allah ya sawwaqe" "Ameen na gode" ta fada tana kwantar da kanta saman qafarta,maimunatu kuma ta matsa gaba kadan,ta taka gajerun steps din da suka sadata da gadonta,ta ajjiye jakarta ta kuma canza uniform din jikinta zuwa kayan gida a dan wajen da suka kebe saboda sauya kaya. Leqawa ta sakeyi tana yiwa afra sannu,dai dai lokacin da wasu 'yammatan guda biyu suka shigo dakin bakunansu dauke da hira cai cai,da alama wata gulmar suka qunso daga waje suka shigo da ita. Bin maimunatu sukayi da kallo,duk da a dazun sun ganta a aji,da alama suma suna mamakin ganinta a dakinsu,duk da dama sunsan akwai sauran space na abokiyar karatunsu data canza makaranta. Itama dan bin nasu tayi da kallo,dukkansu kana dubansu zakasan cewa kowacce daga gidan gata ta fito basai an gaya maka ba,ta amsa sallamarsu tana debe idanunta daga kallonsu,suka qaraso kusa da afra,kusan a tare suka ce da maimunatu "Sannu New roommate" murmushi tayi musu "Sannunku" "Sunana fatima baqo" sai dayar ma ta kama "Ni kuma ummu ayman buhari" ta qarashe maganar tana miqa mata hannu "Maimunatu Abubakar muhammad" ta amsa musu tana miqa musu nata hannun itama "Nice meeting you" suka amsa fuska sake kaman sun saba da ita dama can. To hausawa sukace juma'ar da zatayi kyau tun daga laraba ake ganeta,dukkan alamu sun nunawa maimunatu zataji dadin zama da abokan karatun nata ainun tun a waninsu na farko,wasu irin mutane ne masu sauqin kai da kuma dadin zama ainun,yadda suke nan nan da ita da kuma haba haba sai ka zaci an jima da haduwa tare. Takeaway mai yawan gaske suka zube musu sukaci,sunayi suna duba jikin afrah,duk da cewa da sauqi saboda maganin data sha,har sukayi sallar la'asar,sannan suka fara shirin tafiya islamiyyar cikin makarantar,wadda suke shiga hudu na yammaci "Inaga tunda ku kun saba zuwa,kuje kada ku rasa karatunku na yau,ni zan zauna da sister afra(ta fadi kamar yadda taji suna kiran juna),idan yaso ko zuwa gobe sai na fara zuwa"abunda ya yiwa afran dadi qwarai,ta kuma sake jin maimunatun cikin ranta fiye da daxun farkon zuwanta,bayan fitarsun kuwa hira suka dinga yi sosai da afran,a nan ta fahimci dukkansu 'ya'yan manya ne,sai maimunatun taji a ranta ya kamata ta kama kanta,tunda ita din ba 'yar kowan kowa bace,amma duk da hakan sai ta saki jikinta,ta dinga dan tambayar afran game da wasu abubuwa na makarantar,ta samu haske kuwa sosai,don su tun daga js one suka fara,ba kamar ita ba data datsi ss one. Ta fahimci team ne na masu son karatu aka hada daki guda,afra ayman da fatima,wannan yasa itama ta sake jaddada niyyarta na zage damtse tare da yin karatu tuquru haiqan,son karatunsu ne ya sanya a aji suka raba set,don kada suje kasa maida hankali,kowacce a cikinsu akwai babban alqawarin da aka yi mata daga gida na idan ta gama ta fita da sakamako me kyau a dukka record nata,to zata zabi duk abinda takeso kuma shi za'a bata,wannan yasa a tsakaninsu duk term ake samun first second and third position,saidai sukanyi exchange a tsakaninsu wata ta karbe position din wata. Fadan me uwa inji hausawa sukace,idan ana masa mara uwa labewa yakeyi ya saurara ya kuma yi aiki dashi,dama da niyyar karatun ta shigo,haduwarta dasu afra yasa ta sake ninka qudurinta. Kusan abinda ya tashi hirar qarar wayar afran dake daman katifarta,ayman ce ta miqo mata,tana duba number ta miqe ta haye gadonta basu sake jin motsinta ba,maimunatu dai na jinsu suna mata tsiya amma bata fahimta akan meye ba,don tayi nisa a tunanin yadda zata tafi da tata rayuwar,qarar wayar ya sanyata tunowa da tata wayar da yaa hisham ya bata,ta miqe ta haura,ta dauko tata jakar ta bude ta ciro wayar ta bude kwalin. Ido da baki ta saka tana kallon kyan wayar,sai takega wayar tafi qarfinta,ko ba's gaya mata ba tasan mai tsada ce ainun,don haka ta bude cikin locker dinta ta turata ciki ta mayar ta rufe. ********Cikin kwanaki qalilan sabo mai qarfi ya shiga tsakaninsu,musamman tsakaninta da afra,irin sabon da ita kanta maimunatu tayi mamaki,saboda sabo ne da tun zuwanta duniya batayishi da kowacce halitta ba idan ba mahaifiyarta ba,tunda kusan a tsangwame ta tashi,batasan dangin mahaifinta ba,dangin mahaifiya kuwa babu wannan fuskar,wajen inna furera ma kam ba'a wannan maganar,bata jima sosai tare dasu anni ba bare ta gama tantance wannan,duk da dai alhmdlh,ta samu sakewa sosai dasu,don ma ta gaza sakin jiki dasu,wala'alla don tana musu kallon iyaye,su laila kuwa sun dan girme mata kadan,fa'iza da khadija ne kusan sa'anninta. Yadda suke rayuwa basa boyewa junansu komai,infact tama lura kusan kowa yasan family din kowa,don ko waya daya tayi da gida zatace wance tana gaidaku,kusan tasan labarin kowa a cikinsu,har da na mahaifin afra da bashi da lafiya,wannan yasa itama bata boye musu ko wacece ita ba,ta shaida musu,saidai bata gaya musu tana da aure ba. Zamansu tare ta fara koyon abubuwa daga garesu,kowacce nada tarbiyya gwagwadon iko,hakanan itama sun fara koyon nata dabi'un,ada basu wani damu da islamiyya ba,bata dadasu da qasa ba,suna zuwa,amma suna mata asha ruwan tuntsaye,zuwan maimunatu da yadda sukaga ta maida hankalinta ga zuwan,shine yaja hankalinsu,ita da kanta data fuskanci yadda malamin yake da sauqin kai fahimta da kuma iya koyarwa ya sanya ta roqeshi da kanta ya sanya musu wasu litattafan,hakan yayi masa dadi shima,saboda kusan itace daliba ta farko data fara mai da hankali kan karatun,harta nema a sanya musu wasu litattafan bayan qur'ani da ake musu,ba bata lokaci kuwa ya laluba litattafan da suka shafi fiqhu hadis da sira ya saka musu,tun dalibai da dama basu wani damu da karatun ba,sai gashi sannu sannu abun yana jan hankalinsu,ba'a wani bata lokaci ba islamiyya ta cika da dalibai,abun da ya fara tambara sunan maimunatu a makarantar,haziqa ce sosai musamman ta fannin islamiyya,bangaren boko ne yake dan bata kashi,saboda kusan jumping tayi,a sannan taga amfanin lesson din da anni tasa aka dinga yi mata lokacin da tana gida,ya taimaka mata matuqa da gaske,da batasan yadda zatayi da karatun makarantar ba. *GURBIN IDO* 37 *AREWABOOKS:HUGUMA* https://arewabooks.com/chapter?id=6364b8542730d61e0981706d ______________ Sanda sukai jarabawar first semester ta goma sha biyar tazo cikin su arba'in,ko kadan hakan bai mata dadi ba,saboda ta saba,har ta gama rayuwar primary dinta bata wuce ta biyar,bata nunama kowa ba sai aminanta kuma roommates dinta,afra ce tace "Naga qoqarinki ma maimoon(sunan da suka koma ce mata kenan),a wata uku kacal kin doke mutum ashirin da biyar?" Kai ya girgiza sanda take hada kayanta,don a gobe kowa zai wuce gida hutu "Ina qoqari a nan afreen(sunan da ita dinma take kiranta dashi),bazan iya nunawa kowa result dina ba" "Zaki iya maimoon,i trust you,duk wanda ya iya arabic,boko bazai bashi wahala ba sam sam sam,boko minor abune akan arabic" "Next time I will try my best in sha Allah" ta amsa mata tana sakar mata murmushi,tare da jin dadin irin qwarin gwiwar da ko yaushe afra take bata. Washegari tana ta zuba idanun ganin wanda zayazo daukarta saiga yaa hisham,ya fito suka gaisa dasu afra,ya kuma gabatar musu da kansa da kansa a matsayin yayan maimunatu,sosai abun ya mata dadi,ya girmamasu ya kuma mutuntasu a mazauninsu na aminanta,su kansu sun nuna jin dadin hakan,afra taso su gaisa da 'yan gidansu,suga kuma sabuwar aminiyarta,to amma ya hisham din ya bada uzurin yana da patient da zai gani,dole sukayi sallama suka shiga mota. Yana qoqarin tada motar ya lura da envelope din hannunta,wadda ke dauke da tambarin makarantar,sai ya miqa hannu "Duk da ba'ayimin tayin ganin result din ba,nayi shishshigi,a bani na gani" idanu tadan zaro,ta yima kanta alqawarin babu wanda zai gani,har sai tayi abun arziqi,amma tana jin nauyin hisham din "Ya hisham,don Allah.....ka bari sai next term saina hada maka da wannan din duka ka gani gaba daya" ta fada tana marairaice masa,wanda har ga Allah ita din batasan tayi ba,kamar yadda batasan mugun kyan da hakan ya qara mata ba,har sai daya janye idanunsa da sauri daga fuskarta yana fadin "Subhanallah" cikin ransa ya furtata a hankali "Ba matsala,Allah ya nuna mana" yadda taga yayi maganar yana tada motar ba tare da ya sake waiwayowa ba yasa taji babu dadi cikin ranta,sai taji kamar bata kyauta masa ba,don haka ta zaro ta miqa masa,sannan tayi qas da kanta tana jiran jin maganar da zai fada mata "Kinyi qoqari sosai,ma sha Allah,wannan ne karonki na farko fa?" Ya fada cikin nuna qwarin gwiwa da kuma qarfafata,maganar tazo mata a ba zata,ta kuma bata mamaki,sannan kuma taji dadi gaki da sake samun qwarin gwiwa. Ta zaci gidan abbi zai kaita,sai taga ya wuce da ita gidanta,bata tambayi dalili ba,bayan ya aje ta tayi masa godiya,ta kuma bashi saqon gaisuwa wajensu anni,tare da roqonsa a kawo mata amna. Gyare gyare ta shiga yi,irin na mutumin da ya kwan biyu baya waje,sai data gama komai sannan ta sake wanka,ta kuma wuce kitchen ganin azahar har ta gota don ta samawa kanta abinda zataci. Har zata shiga ta tuna da unaisa,sai taga bai dace tana cikin gida ba amma batasan da dawowarta ba,ko banza ta girme meta a shekaru,wannan tunanin yasa ta karkata akalarta zuwa sashen unaisan. Knocking biyu aka tambayi waye,kai tsaye ta amsa da itace maimunatu,sai da aka dauki mintuna sannan ta bata izinin shigowa. Zaune take saman doguwar kujerar falon nata,ta miqe qafafunta akai tana shan lemon fata,da alama tun dazun a hakan take a zaune,kawai dai batayi niyyar bata izinin shigowar bane,kallo daya tayi mata ta canza fuska ta kuma kau da kanta taci gaba da kallonta ga tv. Koda ta gaisheta sama sama ta amsa "Na dawo,nace bari na shigo na sanar miki" wata dariya ce ta zowa unaisa,ya tabbata ja'afar din mugun dan rainin hankali ne,hakazalika da biyu ya dauki yarinyar ya kaita makarantar kwana saboda ya raina ajinta da kwanyarta,to amma hakan yayi mata ita din,tunda ko banza kawo yanzun tana dan samun wasu sauye sauyen,duk da cewa ko sau daya bau taba hada dakin kwana da ita ba "To yayi" tace mata kawai taci gaba da shan lemonta tana kada qafa gami da ci gaba da kallonta,ganin babu wani magana data sake hadasu sai maimunatun ta miqe zata fita "Agwai" ta kirayeta da sunan da maimunatun tafita sanin me sunan yake nufi,sunan yadan sosa ranta,amma bata nuna ba ta waiwayo tana dubanta "Am please idan kin tashi girkinki,ki dinga yi iya cikinki,wanda naci a baya ma shahada nayi,don ba abinci kowanne irin mutum nake ci ba,so ina da masu aiki,zasu dinga yin komai" kai ta gyada sannan tayo gaba tana bar mata dakinta. Ga mamakinta sai taji maganganun unaisa sun dan sosa ranta kadan,abinda tun tasowarta da irin cin zarafin data gamu dashi a rayuwa bata taba jinsa akan kowa ba,ko hakan yana da nasaba da zama dasu afra?,hakan na nufin ta fara sanin kanta da kuma sanin mene ne rayuwa?. Muje zuwa dai. Tunda ta dawo gidan bataga koda gilmawar J ba,abinda ko sau daya bai ɗaɗata da ƙasa ba,sau tari mancewa take dashi kwata kwata cikin rayuwarta,tasa litattafanta a gaba tana ta haddar hadisan data daukarwa malamin islamiyyarsu alqawarin zata kawo masa su kafin a koma hutu,da kuma izifin data diba shima zata daw da haddarsa,don hatta haddar qur'aninta bata bari ta tsaya ba,tana ganin wannan damar ta roqa alfarma,yake mata qari kuma tana kawo masa. Ta fannin boko ma litattafan da zasu sake inganta mata koyo da gane turancinta ta karba aro masu yawa daga library din makaranta ta taho dasu,wadan nan abubuwa sune abokan hirarta,kewar da tayi fama da ita zamanta na baya a gidan yanzu duka babu,mantawa ma take da inda take,wani lokaci ma idan tayi breakfast bata sake neman abinci saina dare,batajin yunwa sam idan ta duqufa karatunta,bare kuma ba wani motsi zatayi me yawa ba bare ya zazzage mata cikinta ya jawo mata yunwar ba,tana daki kwance,saman gado idan ta gaji ta dawo falo saman kujera,ba kasafai take shiga kitchen din ba,dalilin da yasa har zuwa sannan batasan ma kalar 'yan aikin da unaisa ke maganar ta kawo ba,don sanda zata shiga da safe basu soma nasu aikin ba,lokacin da zata sake komawa kuma dare yayi sun gama nasu aikin sun bar kitchen din. To da wannan damar data samu yasa tayi karatu me yawan gaske,wanda ita kanta batasan ta yishi ba,hutun da akazo gida don yinsa nata hutun kadanne. Randa tayi sati a gidan,tana daga bakin window dinta ne taji cewa ja'afar din tafiya yayi ashe,ta bakin unaisan sanda tayi baqi take rakasu zuwa parking lot na gidan xasu shiga motarsu,saita janye zuwa ciki,ta bude shafin gaba na littafinta taci gaba da karatunta. Sai da tayi kwana takwas da dawowa sannan su fa'iza suka zo mata,harda amnanta,ranar kamar sallah haka ta jita,sun sameta anata sana'ar wato karatu,amna na jikinta ta dauketa zuwa kitchen don ta sama musu abun sha,kafin tayi tunanin me zata girka musu. Sanda suka shiga amnan nata mata tambayoyi da zuba mata surutu,tabbacin yarinyar tayi kewarta matuqa,bata lura da unaisa dake tsaye riqe da cup da yoghurt a hannunta ba har sai data kirayi sunan yarinyar,tare suka waiwaya zuwa gareta ita da maimunatun,maimunatun ta dubi yarinyar data zubawa unaisa idanu tana kallonta,duba na rashin sani da kuma rashin sabo "come-on baby,new mom dinki ce" unaisa ta fada tana murmushi gami da miqawa yarinyar hannu,karon farko da yaro ya burgeta,kasancewarta ba ma'abociyar son yara ba,tsantsar kamanninta da silly mahaifinta din nan ya bayyana,tana fatan batayo miskilanci irin nasa ba. Kamar kuwa yarinyar tasan me take rayawa a zuciyarta,sai ta noqe kafada tana ci gaba da kallonta "Zo mu gaisa mana,haba amna,nace miki new mon dinki ce" ta sake maimaitawa dai,sai ta sake maqale mata kafada,wannan karon kallon fuskar maimunatu dake duba lemon da zata dauko musu tayi "Wannan ce new mom dina,ke ban sanki ba" ba unaisa da yarinyar ta fadawa maganar ba,ita kanta maimunatu taji mamakin maganar,ta dago kanta tana duban fuskarta,waye ya gaya mata itace new mom dinta?,ya akayi ta fahimci haka?,duk da dai yarinyar nada wata muguwar kwanya da kaifin basira,wanda maimunatu tafi tsammanin daga wajen mahaifinta ta gajeta. Sauke amnan tayi qasa tana dubanta "Itama new momma ce,kije ki gaisheta kinji" saita gyada kai,duk da bata sake jikinta ba amma haka ta nufi unaisan,abun ya yuma unaisan ciwo sosai,yarinyar ma ba zata zo wajenta ba sai wannan agwai din ta yarje mata,ta kuma yi mata umarni?,ta zabgawa maimunatu harara sanda ta riqe hannun amna,hararar da maimunatun bata ma san tana yinta ba,da hilata ta samu ta janye amnan zuwa part dinta,saidai suna tsaka da hira sai ga daya daga cikin masu aikin unaisan sun dawo da amnan,idanu fici fici da alama rigima ko ma kuka tayi musu. To hutun kwata kwata na sati hudu ne,suna gama satittikansu suka sake diba suka koma makaranta,maimunatu ta sake dasa yaqin neman karatu,babu ji babu gani,bakin rai bakin fama,su kansu su afrah sunyi mamakin yadda qwaqwalwar maimunatun ta sake budewa daga zuwanta hutu zuwa dawowarta,ta dings musu dariya ganin yadda dukka suke mata duban mamaki,a wani yammaci suna hanyar zuwa islamiyya,bayan ta bada amsar wata tambaya cikin subject din math,shi kansa malamin sai data burgeshi yadda ta amsa question din a gaban allo. To bata qarasa basu mamaki ba sai da sukaje islamiyyan,duka ta zubewa malaminsu haddar hadisan data yo,a washegari kuma zai karba na qur'ani,wannan yana daya daga cikin abinda ya sake zaburar dasu suma,sannan kuma farat daya sunan maimunatun ya fara tambari cikin makarantar,tun daga juniors dinsu zuwa seniors,cikin watanni shida kacal ta fara zama sananniya,duk wanda kacewa maimunatu abubakar muhammad zaiyi wuya yace maka bai santa ba,dalibai maza da kuma mata,saboda zuwan da tayi da tarin baiwarwarki a lokaci qalilan,kyakkyawar bafulatar usul,wadda ke dauke da wani irin kyau mejan hankali,musamman da a yanzun take zaman makarata,daga dakunan kwanansu sai ajujuwansu na boko sai kuma masallacin makarantar inda a nan suke gudanar da islamiyyarsu,fatarta ta sake wani irin haske,kamar zata tabata jini ya fito,jajayen labbanta da bata sanya musu komai sun sake ja,hakanan idanunta masu wani irin kyau da suke dauke da golden din qwayar idanu,ita kanta takan jima gaban mudubi tana kallon kanta,tare da tambayar kanta ita dince kuwa?,itace maimunatun rugar ummaru?,itace maimunatun inna furera?tabbas ta canza,canji me nisan tazara kuwa. Duk da cewa gayu da wasu dabi'u nasu afrah sun ratsata,har sun zame mata jiki itama ba tare data sani ba,amma hakan bai hanata yin takatsantsan da kanta ba,qwarai ta sani cewa ba daya suke dasu ba,ita din akwai auren wani a kanta,zuwa yanxu ta sake samun ilimi sani da kuma wayewa kan muhimmancin aure da girman matsayinsa saman kan kowacce diya mace,duk da cewa takan manta sosai da cewa ita din matar wani ce,don shi kansa wanda aka daura mata igiyar ta sanadinsa ba ganinsa take ba,wani lokaci sai taje hutunta har ta dawo baifi su hadu sau daya cikinn gidan ba,idan an samu akasi ne suke haduwa biyu,gaisuwa kusan itace maganar da take gilmawa tsakaninsu,har yau har gobe basu taba wata magana data gota babin gaisuwa da amsa ba. Tana qoqarin tunawa kanta cewa ita din me aure ce,bawai don damuwa ko soyayya ba,haka kawai cikin ranta takeji bai kwanta mata ba ko kadan,me yasa bai dauko halin hisham ba?,hisham din mutum ne da take matuqar ganin kima mutunci da kuma martabarsa,bata ga alama koda ta kuskure da zata nuna maka yana mu'amala da wani abun maye ko shaye shaye ba,sabanin shi da tun ranar data fara ganinsa tasan cewa mazuqin taba sigari ne,sauran abinda kuma yake sha wannann Allah ne kadai ya barwa kansa sani,tunda ita a nata hasashen,duk wanda yake shan sigari to yana shan komai ma na kayan maye. Abu na biyu hisham din mutum ne me kimanta dan adam da darajtashi,koda yaushe yana faran faran da ita dama sauran qannansa,a gu daya take ganin kamewarshi da nashi salon miskilancin shima,idan ya fita cikin mutanen da suke ba ahali a garesa ba,ko kuma baqin fuska,a duk sanda zai dawo da ita makaranta ko kuma zai maidata,hira ce me tsafta take wanzuwa a tsakaninsu,yakan bata shawarwari da qarin haske akan karatunta,labarai da suke da nasaba da karatu,kamar labarin lokacin da yake dalibin secondary kamar ta,takan iya sakin jiki dashi kadan yanxu,wannan baquntar da take masa a da yanzu ta ragu sosai,yayin da shi kuma yake girmamata kamar yadda zai girmama dan uwansa,har wani lokaci yakan bata kunya ainun,ganin cewa ya girme mata nesa ba kusa ba,ita yafi cancanta ta bashi wannan girman. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels