An dauko wannan littafi daga shafin https://gistrog.com.ng ku ziyarci shafin na https://gistrog.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348141702912 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://gistrog.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348141702912 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://gistrog.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.gistrog.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/SuleimanUsmanKurya Twitter : https://twitter.com/Kuryaloaded_Ng Telegram : https://t.me/+Um7CIRmWSIU2NTg8 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Bismillahir Rahmanirrahim. Ina farawa da sunan Allah me Rahma mejinkai. GARGADI....... Banyarda wani ko wata su juyamun littafina ko su canzamun sunanshi ba. Wannan labari kirkirarre ne, banyi dan wata ko wani ba, zanyi shine domin yazama darasi ga kai, ke,ni, su da kuma mu baki daya. Allah yasa yanda zanfarashi lafiya in gamashi lafiya amin. Season 1 🔱 5 Zaune yake agefe guda yayi tagumi hawaye suna bin fuskarshi, idanu yazuba ma mutanen dasuke yi masu watsi da kaya. Kallon dayan gefenshi yayi ganin yanda matarshi kuma abin sonshi, take kuka. Duk da itace sanadin fadawarsu wannan hali amma yana tausayinta sosai. Kuma haryanzu duk da irin halin data sakasu bayajin digon sonta yaragu azuciyarshi. Wannan wulakanci na korarsu daga gidan haya shine na 3 tun bayan aurensu. Goge idonshi yayi, wasu hawayen suka kara zubowa alokacin daya tuna magana mahaifiyarshi. Abbas kada kabiyema Son dakake ma wannan yarinyar, ze kai ka yabarokane, idan bazata iya zama da kai ayanda kake ba to kahakura da ita. Kanshi yacigaba da girgizawa hawayen idonshi suna kara zubowa, yarasa inda zesa kanshi, gashi ta dalilin matarshi gaba daya sun bata da abokanshi, mutum daya ne, yarage mashi wanda yake temaka mashi. Karar faduwar wani abu dayaji ne yayi saurin dawo dashi daga tunanin dayakeyi. Ihun matarshi yaji tana fadin dan Allah kuyi hakuri kada kuyi mana banna. Saurin tashi yayi yanufi gurinta. Jawota yayi ya rungumeta yana bata hakuri, mutane dayawa yan unguwar harma da makota sun tausaya masu. Wani daga gefe ne yace kai gaskiya abokina megidan nan beda mutunci, kamar ba musulmi ba, haba dan Allah yaza,a rika watsi da kayan mutane kamar besan darajarsu ba. Abokin yace uhm abokina beda laifi, kama dena tausayin ABBAS ALEE, domin acikin rukunin unguwar nan mutane dayawa sun san halinshi, Ace mutum beda tunanin kanshi sena matarshi. Haba wace irin rayuwace haka, ai so ba hauka bane, a iya sanina wannan shine gidan haya na 2 danasan ana mashi irin wannan korar wulakancin. Kuma duk lokacin da aka tashi korarshi seyayi asara ba kadan ba. Yanzu kaduba kayansu, sekace wadanda suka shekara 10 dayin aure. Duk sun kare ayawon haya. Wlh kaganni nan babu yanda za,ayi inyarda inyi aure batare dana mallaki MUHALLI na nakaina ba. Aishi MUHALLI DARAJA gareshi. Maganar daya daga cikin mutanen dasuke masu watsi da kayan ne taja hankalin masu wannan maganar. Ina me tabbatar maku ko kukan jini zakuyi wlh kun gama zama acikin gidan nan. Ai ko da kudin ubanku aka sayi gidan inde ance na haya ne, dole kubiya idan lokaci yayi, damma kunsami Oga mesauki ne har ya iya yafe maku na watannin da kuka kara. Acikin kudinku na shekara har seda kuka kara wata 4, sannan duk da haka bakuga adalcin da megida yayi maku ba. Sa,a kukaci da besa aka daure kuba. Maza ku kwashe tsummokaran kayanku kubar kofar gidan nan. Shide Abbas Alee yayi shiru bece komai ba, yana rungume da matarshi, yama rasa yanda zeyi, gashi ko sisi bashida ita bare yakira me mota yadaukar masu kayansu. Yana kallo mutane yan kallo suka fara watsewa, da haka har gurin yazamto saura yara kanana, kama matarshi yayi yazaunar da ita gefe, tana ta faman goge kwallan datake zubo mata. Aranta tana danasanin wannan hali nata marar kyau, da yanda tabiyema karyar zamani tasaka mijinta cikin wannan yanayin. Matsawa yayi gurin kayansu yafara tattara akwatinansu yana kawosu gefe guda, sannan yakoma yahada sauran kayan daya bayan daya yatarasu suma agefe guda. Kusa da ita yadawo yazauna, yace LABIBA dan Allah kidena wannan kukan haka, banason kina kuka domin kukanki yafi wannan hali damukeci, sakani cikin damuwa. Kallonshi tayi tace dole inyi kuka Abbas, duk nice sanadiyar sakamu cikin wannan rayuwa, gashi yanzu duka shekararmu 4 da aure amma haryanzu babu gidan damukayi sama da shekara 1 acikinshi. Tun muna zama gida me kyau, har muka fara zama marar kyau, yanzu gashi wannan dinma danake rainawa, shima ankoremu, yanzu kuma wayasan wane iri zamu samu? Kuka takara sakamashi. Jawota yayi yace karki damu, Allah shine yasakamu acikin wannan halin kuma yana sane damu insha Allah bazamu tozarta ba, abinda nakeso dake ki kara hakuri dani aduk halin dazamu tsinci kanmu aciki. Banason talauci yasa kijuya mun baya, nayi maki alkawarin zan zauna dake akowane hali nake ciki, inaso kema kimun wannan alkawarin Labiba. Shan majina tayi takamo hannunshi tace nayi maka alkawarin zan zauna da kai koda acikin bukka zamu zauna matukar zan jika akusa dani, kuma nayi maka alkawarin insha Allahu bazan kara bijire maka ba aduk inda kasama mana domin muzauna. Murmushin jin dadi yayi yakara rungumeta yana fadin nagode maki masoyiyata Allah yabarmu tare. Dafashi yaji anyi dasauri ya juya yana kallon bayanshi. Murmushi yayi yace sannunku masoyan asali, wato kuna cikin wani hali amma kuna soyayya ko ABBAS ALEE?. Murmushi Abbas yayi yace to abokina yakake so muyi, ai gara muyi soyayyar kozamu samu saukin abinda yake damun mu. Zama yayi kusa da Abbas fuskarshi dauke da damuwa yace ina kasuwa ashago nasamu labarin abinda akai maku, hakan yasa na taho,kuma tundazu nasamu labarin. Abinda yasa banzo dawuri ba, seda nabiya nafara sama maku wani gidan dazaku zauna sannan nataho da motar dazata dauki kayan. Wasu hawayene suka zuboma Abbas dayaji bayanin babban abokinshi. Kallonshi yayi yace Jafar nama rasa dawane baki zan maka godiya, akullum bakada wani buri daya wuce ka kyautatamun. Tabbas kai abokine nagari, Allah yayi maka albarka, yabaka duk abinda kake nema. Jafar yace amin. Dama kwana 2 banga kaje shago ba, shine naje gurin Alhajin na tamabayeshi, Shine yake cemun wai ya sallameka, amma meyasa baka fadamun ba? Girgiza kai Abbas yayi yace haba Jafar yazanyi tasaka cikin damuwa, bayan kana kokarin temako na akowane lokaci. Jafar yace koma menene yakamata kafadamun, ina da wani bayanka,ne? Kai wane irin temako,ne bakamun ba, seni yanzu inkasa temaka maka. Wlh nayi bakin ciki da gidana be kasance me dakuna dayawa ba, da aciki zaka zauna har abada har kasamu naka nakanka, kai koda ace dakuna 2 ne, zan iya daukar daya inbaku daya. Sede kash!!!, nima da kyar nasamu nagina ciki da falo da bandaki , kana ganin haryanzu kitchen dinma bankarasa ginashi ba. Abbas yayi murmushi yace Jafar ka godema Allah dayaba ikon mallakar MUHALLINKA na kanka. Kuma babu komai, wannan abun ma dakamun kadai ya isa, nagode sosai, nima kaddara ce tafadomun harna rasa nawa MUHALLIN, se ayanzu nake gane DARAJAR MUHALLI. Amma bakomai, tunda na tsira da abin sona hakan ma ya isheni. Girgiza kai Jafar yayi cike da tausayin abokinshi, yarasa wane irin sone yakema Labiba. Matar da itace silar shigarshi cikin wannan yanayin. Kamar daga sama yaji muryar Labiba tace Jafar awace unguwa ka sama mana gidan, Allah de yasa tana da kyau, kuma babu kowa aciki? Saurin kallonta Abbas yayi domin beji dadin maganar datayi ba, shiru yayi dan bayason yayi mata magana ranta ya baci. Jafar kuwa jiyayi kamar ya shakota. Daurewa yayi yace acikin burget gidan yake, kuma abokina sede kuyi hakuri domin gidan dakuna 4 ne aciki guda 3 akwai mutane, dayan ne nakama maku, sede ciki da falo ne, amma babu bandaki aciki. Yana waje, sede kuyi hakuri kafin Allah ya hore asamu wani se acanza maku, kasan yanayin da ake ciki, yanzu kasuwa tayi kasa. Abbas yayi murmushi yace haba abokina meye na bada hakuri sekace da kudinmu aciki. Nagode sosai Allah yabar zumunci. Yace amin. Wata irin zufa ce tafara keto ma Labiba jin irin gidan da aka kama masu, yoko gidansu na da ai yafi shi daraja. Idonta ta kulle wasu zafafan hawaye suka zubo mata, tana kara tsanar kanta. Da haka aka saka masu kayansu acikin mota suka nufi sabuwar unguwarsu. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady ) 08028525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 5 🔱 10 Labiba tana tsaye aka gama shiga da kayansu cikin gidan, wani irin bakin ciki ne ya turnuketa, tunda taga sun shigo cikin unguwar, gaba daya layin beda fasali, Ko acikin Burget dinma yana daga cikin kazaman layi, har cikinta seda taji yana yamutsawa saboda warin kwata, kara kallon gidan dazata zauna tayi, Ko kofar kirki babu agidan, hatta da simintin gidan duk ya karce, kwalla taji ta cika mata ido, tunawa tayi alokacin da Abbas yakama masu wani gida kafin su zauna a wanda aka koresu, Gidan yana da kyau, mace daya ce aciki kuma kowa da part dinshi, tsakar gida kadai ta hadasu, amma tace bataso ita bazata iya zama da kowa acikin gida ba. Haka nan yanaji yana gani ya hakura da gidan alokacin har seda suka kusa yin fada da Jafar dan shine ya sama mashi gidan, ganin ran Abbas ze baci yasa Jafar ya kyaleshi. Haka yaje ya kara samo masu wani gidan, wanda shine aka koresu aciki yanzu. Ajiyar zuciya tayi, setaji dama ta hakura sun zauna awancan gidan, tunda Jafar yace gidan dan uwanshi ne, yasan baze koresu ba, idan basu biya ba, Segashi aranar da sukaki zama gidan aranar wasu suka karba. Hijabinta tasa tagoge fuskarta. Aranta tace oni Labiba, haka kuma ni tawa kaddarar tazo mani. Allah yajikanku mama na da Babana, danabi shawarar ku da duk haka bata faru dani ba, segashi yanzu narasaku, banida mesona se mijina, dangin Babana ma sungujeni, Dafata taji anyi, kobata kalla ba, tasan mijinta ne, hannunta yakamo yana fadin haryanzu bazaki dena kukan ba ko? Kiyi hakuri dan Allah, duk wannan abun wata rana ze wuce, kinji Labibata. Haka yajata suka shiga gidan, mata 2 tagani atsakar gidan, wadda bawani fadi gareta ba, kowacce tana aikinta, babu wanda yadaga kai yakallesu, Abbas yayi sallama sannan suka dago suka amsa. Da kallo suka bisu, har suka shige, dariya daya tayi tace wayyoni duniya, ke Laraba kina ganin wani sabon salo agidan nan yau, ke daganin yanayin kayan wannan mata ba amarya bace, Amma kalli yanda yawani rungumota ita kuma tana kuka sekace wadda akama dole. Dariya wadda aka kira da labara tayi tace, uhm kede ganemun hanya Laure, Inde gidan haya ne, ya isheka riga da wando, duk wasu masu kilibibi haka zasu kare, shewa suka saka harda tafawa. Duk abinda sukeyi Labiba da Abbas sunajinasu, Jafar dayake zaune afalo bisa kujera yace dan Allah Labiba kada ki kula wadan can matan, kinsan gidan haya yagaji haka, saboda kowa yana takamar kudinshi yasa yakama gida, babu ruwanki dasu, kinga kece me zama acikinsu. Shiru tayi tana ta kuka, haka sukayita bata hakuri hartayi shiru. Jafar yace abokina bara inje inkawo maku abinda zakuci tunda nasan bazata iya girki yanzu ba, kuma gashi yamma tayi har ankusa kiran sallah. Kuma gobe inaso muhadu akasuwa ashagon danake kazo idan yaso se aduba maka abinda zakayi, bazaka zauna hakanan ba, amma sekayi hakuri kasan nima shagon banawa bane. Abbas yace haba Jafar, wai meyasa komai zakamun seka bani hakuri? In badan kai ba, ayau ma bansan inda zamuje ba, kasande bazan tunkari Ummata infada mata halin danake ciki ba, dan itama gidan da take ciki ita da kanina bawani girma gareshi ba, Saboda haka ni kowane irin aiki nasamu zanyi, matukar aikin halal ne, banida abinda zance maka sede Allah yakara daukaka. Jafar yace amin, bara inje sena dawo, yace to. Tashi sukayi suka shiga daki suka kara gyara kayansu, Abbas ya bude tagar dakin, domin zafi yakeji dan dakin babu fanka ancireta, saukinsu ma akwai wuta, gaba daya kayan kitchen din Labiba adaki aka sasu, wasu kuma afalo bayan kofa. Damma kayan bawani yawa garesu ba, duk ta saida wasu, kujerunta ma biyu kadai suka rage, alokacin dazasu tashi daga wani gida basuda kudi suka saida guda 2 manyan, hakan yasa falon be cunkushe ba. Abbas yace Labiba ina ganin tunda falon yana da dan girma kawai musa labule daga can sekirika girki agurin banason kifita waje kina girki naga alamun matan gidan nan basu da kirki. Murmushin jin dadi tayi, kamar yasan abinda yake damunta kenan, shima seda yayi murmushin ganin yasata farin ciki. Yace tunda muna da babbar robar zuba ruwa semu rika cikata, kinga babu ruwanki da fita waje debo ruwa, Daya kusa karewa se azuba, bandaki ne, kadai zerika fitar damu, bakomai ai, ni dama fita inyi girkinne banaso, nagode, maganar bandaki kuma zan kula da lokacin da suke shiga se inkiyaye. Abbas yace hakane, ko kuma kawai zansa alarm awayata kamar karfe 4:30 se murika tashi, muyi wankan mu muyi alwala kinga zamu samu saukin bin layi, dan naga alama akwai yara agidan. Rungumeshi tayi tace gaskiya naji dadin wannan shawara taka, yace bakomai, Labiba, idan ban jiya maki dadi ba, wazan mawa? Nikadai kike dashi, kuma kinbani duk soyayyarki banida abinda zance maki, se fatan Allah yakara mani budi inmaki abinda yafi haka. Tace amin. Jafar ne yayi sallama Abbas yace bismillah shigo, mamakine yakama Abbas ganin Jafar dauke da kaya, kama mashi yayi yasauke sannan yazauna. Abbas yace Jafar kaida kace zaka kawo abinci shine naganka da kaya haka?. Murmushi yayi yace haba ai bakomai, kayan shayi ne, nasiyo maku da galan din kananzir, se kuma sabulai, ga kuma guga nan se kurika ajeta agurinku, kunsan gidan haya kowa da kayanshi, Abbas yace mungode, anan yafada mashi dabarar dasukayi,Jafar yace gsky ne, hakan ma yayi tunda bawani yawa gareku ba, inafatan rishow din baya hayaki ko? Labiba tace a,a bayayi kaga tukwanena haryanzu basuyi baki ba, Yace yauwa, Allah yabaki hakurin zama agidan nan,insha Allahu bazaku dade aciki ba, duk da kudin shekara na bada, amma idan nasamu hali zaku tashi idan yaso se yamaido mana kudinmu, dama nayi dashi ahaka. Mikama Labiba cooler din abincin yayi yace abokina muje masallaci ko, yace to muje, Jafar yace to Labiba ni daga can zan wuce Allah yabaku zaman lafiya keda mutanen gidan, babu ruwanki dasu, kuma kada ki kyamace su, Sede kar kije dakin kowa, amma inkinfita kirika gaishesu, hakan zesa kifisu, idan ma suna nufinki dawani abu, Allah ze kareki. Tace to Jafar nagode. Abbas yace tashi kije ga bandakin can naga bakowa dauki pure water kizuba abuta kafin indawo se inzuba mana ruwa. Jafar yace a,a bazaka fara jan ruwa tun yanzu ba, muje naga akwai masu ruwa se suzo suzuba, fita sukayi ita kuma ta dauki buta tanufi bandaki. Tana fita wani yaro daya fito daga dakinsu shima da buta ahannunshi yarugo da gudu har yana shirin bangajeta, saurin bashi hanya tayi, kawai yashige bandakin yarufo. Tsayawa tayi akusa da bandakin, ga wani irin wari agurin, wasu hawayene suka zubo mata na bakin ciki, yanzu idan wani babban uzuri gareta sede tayishi awando. Share hawayenta tayi tace agaskiya bari Abbas yadawo acikin bokatai na, farare na fenti zan dauki daya inrika fitsari aciki, tunda de suna da murfi, idan yaso se inrika fitowa waje ina alwalar, Gara inrika wahalar wanke bokitin dade irin wannan iskancin yaran gidan nan, ta dade atsaye kafin yafito, har wata yarinya zata shiga taji wata mata tace ke Zainab kitsaya ta fito tunda tarigaki, Juyawa tayi ta kalli me maganar, dan alokacin da suka shigo gidan bataji muryarta ba, murmushi tayi mata tace nagode, ita murmushin tayi tace bakomai. Bayan tagama sallah taji sallamar mace, tashi tayi tafita falo tana amsawa, fuskarta tasaki ganin wannan matar tadazu, tace a,a maman Zainab kishigo mana. Bayan sungama gaisawa, maman zainab tace sannu da zuwa, wlh bansan kunzo ba, nade san ance za,a kawo wasu yau, dayake ina cikin daki bansan lokacin dakuka zoba. Labiba tace ai bakomai, Maman Zainab tace ya sunanki? Tace Labiba, tace sannu da zuwa Labiba, kema Allah yakawoki gidanmu babu abinda zance maki sede ince kiyi hakuri da duk yanda kika tsinci kanki agidan nan. Kinganni nan yau shekararmu daya agidan nan, diyata daya se mijina, akullum ina addu,ar Allah yakawo mana karshen zaman gidan nan. Zamane mukeyi kowa da mijinta amma yanda kikasan kishiyoyi haka ake wannan zama. Agaskiya kafin insamu yanci agidan nan nasha wahala, shiyasa nayi alkwarin fadama duk wadda tashigo gidan nan halin yan gidan, bazanso acutar da itaba kamar yanda suka mani, domin anan nazo nasamesu. Kin ganni nan nasha wahalar matan can guda 2, afarkon zuwana, dayake mijina idan yafita tun asuba baya dawowa se gurin 10, hakan yasa banida abokin fira, sede infita gurinsu. Babu kalar wayon dabasu yimani ba, hatta girki kinga de mijina abincin dare kadai yakeci, mu 2 kawai zanma girkin safe dana rana ko, amma duk da haka sena dora babbar tukunya, Haka zan gama abinci sena zuba ma kowace ita da yaranta, amma idan sune suka dafa abincin dazasu bani ko zainab yayi mata kadan, Tun mijina baya maganar saurin karewar abinci har yafara, sede inbashi hakuri,dayake mijina mutum ne me hakuri haka ze kara kawo mani, nice share tsakar gidan nan, wanke bandaki, Idan suka tashi rancen kudi agurina suke karba, idan aka tashi maido mani da 20, 50 haka za,a biyani, wani lokacinma rabi ake bani ace inyi hakuri, nikuma dan kawai insamu fuska agurinsu yasa nake bauta masu, Kuma hakan be hana surika zagina, ga yaransu basuda kunya, kinsan idan akace mutum yazo cikin mutane 2 shine na 3 dole ya kwantar da kai, in bahaka ba, sede kulluma yayita zama shikadai. Tun ina hakuri dasu, har nafara gajiya, wlh saboda su, nadena amfani da rishow, sede da gawayi, aikuwa wata rana yaron Laure yaduki Zainab, wai ni naga munzama daya shine nakamasu na dan dokesu nace sudena fada. Kawai Laure da Laraba suna fitowa Laure ta daukeni da mari, cike da masifa tacemun meyasa zan dakar mata yaro, nace mata fada sukeyi ban idasa rufe baki ba, takaramun wani marin, Ai bansan lokacin da nima nadauketa da mari ba, na jawota nadaga ta na maka da kasa, dama bawani kiba garesu ba, ganin haka yasa Laraba tayi baya, aiko nahau ruwan cikinta, Haka nayita jibgarta nakoma kamar me aljanu, dakyar laraba ita dawasu suka kwaceta, akayita bani hakuri sannan naja zainab muka shiga ciki. Tun daga ranar muka dena magana dasu, haka nasa mijina yazagayemun wancan kitchen din da kikegani da langa langa, nakai rishow na nafara girki aciki, Komai nawa yana daki, hatta da rishow sezanyi girki nake daukoshi, ina gamawa indauke komai in kai daki, ko bandaki zanje sena kulle kofata, ko Zainab bana bari tsaron falo, waje nake fiddota. Idan nafito mushiga ciki, bana basu abinci kuma bana zuwa gurinsu, gara inzauna adaki nida Zainab muyi kallo ko,karatu ko,muyi fira, ko yaran gidan nahanata wasa dasu. Tundaga ranar nasamu lafiya, abincina yafara yimani auki, kuma inci abinda nakeso, domin agaskiya babu abinda mijina yarageni dashi, sede suyita gulma, nikam babu ruwana dasu. Labiba tayi ajiyar zuciya tace gaskiya nagode dakika fadamun halinsu, kuma ni dama tunda mukashigo naji abinda suka fada kawai naji banyarda dasu ba, hakan yasa nima mijina yace anan zanrika girkina. Maman Zainab tace shikenan kin huta, ai zaman gidan haya beyiba, barema ace irin wannan. Wlh nayi dana sanin ziga mijina, alokacin da aka raba masu gadonsu, to dayake shikadai ne, mahaifiyarshi ta haifa, Kuma ta rasu, to da babansu yarasu akazo rabon gado, dama gaba daya yaranshi agidan suke zaune suda matansu, su 3, maza, 2 dakinsu daya, se mijina shi kadai, Alokacin da aka raba gadon, kowa aka yankar mashi bangarenshi, kinsan wace shawara nabama mijina, dan kawai banason muzauna tare da matan yayyanshi?. Cemashi nayi kawai ya saida masu nashi gadon, akwai wata mata a unguwar sallari, dama mu a Janbulo muke, nace mashi naji tace zata saida gidanta kwanaki, idan suka bashi kudin seya hada da nashi musiya hakan zefi. Da farko yacemun a,a da kyar nasamu ya amince dayake yanada sonkin kai. Alokacin daya samu babban wansu da maganar, yabashi shawara yayi hakuri yazauna, ba,ason saida gidan gado. Amma yace mashi shide kawai saidawa zeyi, ganin yaki yarda haka suka hada kudi shida kaninshi suka biya suka anshi kasonshi. Haka mukaje muka sami matar, setace ai bayanzu zata saida ba, sede idan munaso zamu siya mufara zaman haya na shekara 1. Idan yaso daga baya seta saida mana da farko yace beyarda ba, haka nayita lallashin shi harya yarda. Haka muka fara zama agidanta, sauran kudin gadonshi muka rika cin dadi, da haka har suka kare. Alokacin da muka cika shekara 1 tace idan zamu siya to mubata kudin domin tanaso tabar unguwar, anan muka fara zare ido domin ko kudin dazamu kara karbar haya bamu dasu bare na sayan gida. Hakuri muka fara bata tabari musamu kudi amma tace batasan maganar ba, alokacin kuma wani mutum yazo ze siya, shine tace tabamu wata 1 musami gurin zama. Kuka mijina yasakamun, yana fadin na cuceshi, hakuri nayita bashi, nace mu koma gurin yan uwanshi nasan zasu bamu gurin zama. Dayake mijina yanada zuciya yace wlh bazejeba, koda ace dakinsu daya, kuwa. Haka yayita buga buga har yasamu wannan gidan muka dawo, kinji dalilin dayasa muke zaune agidan nan. Kuka sosai Labiba takeyi, jin labarin maman Zainab. Share hawayenta tayi tace lallai kunga rayuwa, amma inaji bakiga komai ba kan....... Gyaran murya tare da sallamar Abbas ce tasata yin shiru, saurin tashi Maman Zainab tayi tana fadin kinga fira tasa bamuji kiran sallah ba. Gaisheda Abbas tayi tace Labiba seda safe ko. Bayan tafita Abbas yazauna akusa da Labiba wadda haryanzu kuka takeyi, jawota yayi, yace haba Labiba ya isa haka, kuma na dade atsaye, naji firanku, abinda nakeso dake, Ki koyi boye sirrinki, duk yanda kike da mutum kada kiga yafada maki sirrinshi kema kiyi saurin fada mashi naki, yau kikasan wannan mata, duk dade naga tanada hankali, amma banyarda kifada mata labarinmu ba, har se nan gaba idan nakara karantarta. Banaso labarinmu yazama ana fadinshi babu sirri, bakisan kila lokacin dazaki fada mata ko wani yanaji ba, yanzu kila babu wanda yasan labarinsu seke, amma gashi nima naji, Kuma bakusan najiba. Dan Allah Labiba kada kiyarda kifada ma kowa labarinmu kinji my dear? Tace to yace yauwa muma Allah ze kawo mana mafita. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 10 🔱 15 Washe gari kamar yanda Abbas yace karfe 4:30 suka tashi, alokacin babu wanda ya motsa acikin gidan, haka sukayi wankansu suka gama, bayan sungama shiryawa sukayi nafila har aka kira sallah sannan yafita masallaci. Seda gari yafara wayewa sannan yadawo, alokacin Laure da Laraba suna bakin toilet suna jiran yaron laure daya shiga bandaki, da ganinsu basuyi sallah ba. Da kallo suka bishi har yashige, Laure tace kai Laraba amma wannan mutum yana da kyau, laure tace ashe kema kin gani, wlh tunda naganshi nima naji yatafi dani, Ina ma ace dan hannu ne, ai da munshana. Laraba tace kai wannan yafi karfinmu kina ganinshi kinsan akwai ibada, ko kallonmu fa betaba yiba. Uhm kede ba,a nan take ba, kibarni dashi kawai kiyi kallo. Da sallama yashiga Labiba tana kwance bacci yafara daukarta, zama yayi yace Labiba da alama bacci be isheki ba ko? Murmushi tayi tace wlh kuwa, yace to nima matsamun in kwanta tunda bada wuri zanfita kasuwar ba. Hayaniyar yara da matan gidan ce ta hanasu baccin kirki, gurin karfe 7 suka tashi, Labiba ta dafe kanta tace wlh Abbas kaina ciwo yakemun, gsky mutanan nan suna shiga hakkinmu. Abbas yace ai se hakuri, kinsan gidan haya yagaji haka, Allah de ya hore mana mubar masu gidansu, tace amin, bari intashi indora mana ruwan zafi, yace to bari inje insiyo mana biredi ga wasu kudi nan da Jafar yabani jiya. Tace bazaka shiga bandaki ba? Yace kai a,a idan nafita nashiga bandakin masallaci. Acikin bokitinta tayi fitsari bayan tagama ta kunna rishow ta dora masu ruwan zafi, bayan tagama tajuyeshi a flask takai masu kofuna afalo, bayan yadawo suka karya, Misalin karfe 8 yace bari yatafi kasuwa kada Jafar yajirashi, kallonshi tayi tace mezan dafa mana? Murmushi yayi yace kidafa abinda kikeso nasan se da yamma zandawo idan yaso sekiyi mana na dare tare. Kudi yabata yace gashi kiyi cefane sekiyi mana miya kinga anjima seki dafa shinkafa, wannan kuma kisiyo kifi da salak. Murmushi tayi tace yauwa nagode, amma kuma kaga bansan wazan aika ba, Sede infita da kaina. Yace a,a to bari inje insiyo maki kawai amma anjima idan zandawo inde nasamu kudi kawai zanyo mana siyayya sbd banason siyan abu cire cire, tace to. Fita yayi, dayake acikin unguwar akwai masu kayan miya, Bayan yakawo mata yace kiyi sauri ki markada a blender kafin su dauke wutar, idan kuma sun dauke seki tambayi Maman Zainab inda ake kaiwa, tace adawo lafiya mijina. Murmushi yayi yace yau babu rakiya ko? Tace a,a naga yanzu gidan bamu kadai bane, yace koma mu nawa ne, ni bandamu ba, yanda muka saba kirakani haka zakimun. Tashi tayi tasa hijabinta tabishi suka fita yana rike da hannunta, suna fita suka cikaro dasu Laraba, zaune acikin inuwa, ko kallonsu beyi ba, yajata har zaure sannan yayi mata kiss a kumatu yatafi. Bayan tadawo ta matsa kusa dasu tace sannunku ina kwananku? Ya mutsa fuska sukayi sukace lafiya lau, bakuwa se yanzu muke ganinki? Daure fuska tayi tace tunda kun ganni yanzun ma ai ya wadatar, wucewa tayi abinta tashiga dakin Maman Zainab. Laure tace kan uban nan kai yasa, ke Laraba, kinajin wannan kwailar yarinyar me kama da karas har mu zata kalla tafada ma wannan maganar? Laraba tace aini nama kasa magana. Kuma kina ganin tashige dakin waccan munafukar, to wai yaushe ma ta santa? Laure tace kinsan halin munafuka, jiya ina kallon lokacin data shiga dakinta, kuma ta dade aciki har seda mijinta yadawo tafito. Laraba tace lallai damu suke magana, har mu za,a yima bariki, ai duk wanda yasanmu a unguwar nan anan yasamemu, kuma dole muyi yanda muke so. Kibarni dasu, ninasan mezanyi masu. Zaune suke akasuwa shida Jafar, dan tunkafin yazo Jafar yayima uban gidanshi magana kuma ya amince, ze dauki Abbas aiki adayan shagonshi, dan shima yatausaya mashi dayaji labarinshi. Jafar yace Abbas ina sarkin rigima Labiba? Murmushi yayi yace baiwar Allah tana can, nasan kadaici ya isheta, gashi bamuda kayan kallo duk mun saida bare tayi kallo, amma insha Allah idan komai ya dedeta zan siyamata. Kai Jafar ya girgiza yace wato Abbas har yanzu bazaka yima kanka fada ba ko? A tunanina yanzu base wani yabaka shawara akan abinda yakamata kayi da kudi ba, domin ayanzu kafi kowa sanin DARAJAR MUHALLI. Murmushi Abbas yayi yace wlh nima Jafar ina son inga na mallaki MUHALLI na, badan kowa ba, sedan Labiba, amma kasan halinta yanda kasan ta taso gidan masu kudi kwata kwata batasan babu ba. Kana gani ko abinci bata yarda taci marar dadi ba, shiyasa wani lokacin hakanan nake hakura inbata ita taci medadi, kasan irin son danake mata, wlh bana so inga nabata mata rai, gaba daya se inji nashiga damuwa. Kasan mutane dayawa acikin abokanmu har cewa suke wai Labiba bata barni haka ba. Nikuma nasan ba haka bane, nida Labiba akwai so me tsanani atsakaninmu, sede nasan sona yafi nata sosai, duk da itama tanamun so dede gwargwado. Jafar yace hakane, nima sheda ne,akan irin son da kukema junanku, sede duk da haka, kasan son da take maka, da wanda kake mata be kai son Uwa da danta ba. Idan har Uwa zata iya sa hannu ta duki danta, saboda ta gyara mashi kuskuren dayayi, Ina ganin babu wanda zece dan batason shine ta dokeshi, tayi hakane dan kada tarbiyarshi ta lalace. Ina ganin kaima danka hana Labiba wani abu, baza,ace bakasonta bane, arayuwa dole se mutum yarasa sannan yake samu. Idan har zakaji ta tawa kadaure ka koyi hanata abinda takeso, bance kada ka kyauta tamata ba, idan ace yau katashi da naira 100, to kuyi hakuri kusami abinda zakuci na naira 50 kai kuma karike 50 a aljihunka, sbd tsaran laruri, ko kuma kasata cikin asusu. Kasuwa bata da tabbas, ba kullum,ne muke samu ba, kaga duk ranar da bamu samu ba, zaka iya daukar cikin wanda kake tarawa kuyi amfani dasu, idan kasamu seka maida, da haka mutum yake iya tara nakanshi. Amma wlh duk wanda yace zebiyema mata, yana tare da wahala, idan kana cikin budi zaka iya yimata komai, idan kuma babu se ku hakura, hakan ze koya mata samu da rashi, kuma koda wata rana bakayi mata ba, zata maka uziri. Amma tun farko kaine ka koya ma Labiba duk abinda take maka yanzu, amma haryanzu lokaci be kure maka ba, tunda ko haihuwar farko batayi ba, zaka iya daurewa ka gyara rayuwarku, duk da nasan zaka fuskanci matsala, amma na tabbata idan har son datake maka na gaskiya ne, zatayi fushi daga farko, amma daga baya dole ta sauko. Jinjina kai Abbas yayi bece komai ba. Dafashi Jafar yayi yace zaka iya abokina, kadaure dan Allah kayimun wannan alfarmar inaso daga yau kazama namiji kamar yanda nasanka abaya kafin haduwarka da Labiba. Wannna ita kadaice alfarmar dana keso awajenka, nasan banida sama da kai, kuma kaima haka, ina tsoron ranar da mutuwa zata daukeni inbarka cikin wannan halin, nasan duk duniya babu wanda ze iya fada maka irin gaskiyar danake fada maka. Duk wani wanda zezo gurinka dan ya cuceka zezo, dan Allah Abbas,,,, kwalla ne suka zubo mashi daga ido, dasauri Abbas ya kalleshi yace haba Jafar meye na kuka, kayi hakuri, nasan aduk duniya banida sama da kai, ko Ummata ayanzu bazata yimun abinda kake mun ba. Nasan son da kakemun daga Allah ne, haduwar jininmu, ma dagavAllah ne, na dade ina rokon Allah kada yakawo ranar dazaka rokeni wani abu ni kuma banida halin yimakashi. Alhamdulillahi, nagodema Allah dayasa yau ka tambayeni alfarmar dazan iya maka. Ni ABBAS ALEE nayi ma abokina JAFAR alkawarin daga yau zan canza halina, zan koma asalin duk wani da namiji me zuciya. Zanyi kokarin tara kudi na halak koda zan kasance banci me kyau ba, insha Allahu sena kara mallakar MUHALLI nawa na kaina. Dariyar farin ciki Jafar yayi ya rungume Abbas harda kwallanshi yana fadin nagode abokina, Allah yabaka ikon cika alkawarin daka dauka, zanfi kowa farin ciki. Insha Allah sekazamo abin kwatance acikin abokanmu dasuka juya maka baya. Se duniya tayi alfahari da kai ko bayanzu ba. Tashi muje kada Alhaji yajika shiru. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 15 🔱 20 Misalin karfe 6 Abbas suka tashi daga kasuwa, dari 500 Alhajin yabashi, hakan yasa Jafar yasiyo mashi wani katon asusu, dari 300 yabashi,yasaka 200 acikin asusun. Cefane yayi masu na kayan miya na naira 50 yawuce gida bayan sunyi sallama da Jafar. Kafin yaje gida ankira magriba, hakan yasa seda ya tsaya masallacin unguwarsu yayi sallah sannan yashiga gida. Kamar kullum suna zaune tsakar gida suna sana,ar tasu, da sallama yashiga yana ganinsu yayi saurin dauke kashi dan wasu kananan kayane ajikin Laraba, kanta ko dankwali babu, dasauri Laraba tace sannu da zuwa. Ko kallon inda take beyi ba, yashige falo, dariya Laure tayi tace ai nafada maki wannan mutumin baze taba kulaki ba, shiyasa ma na hakura. Laraba tace wlh bazan hakura ba, inde muna cikin gidan nan zakiga yanda zanyi dashi, ai kowama ya iya kissa. Abisa sallaya yasameta tana addu,a zama yayi harseda ta idar sannan yashafa, tashi tayi tana cire hijabi tace sannu dazuwa Abbas ya kasuwa? Murmushi yayi tare da jawota jikinshi yace lafiya lau, Labiba ta. Yazaman kadaici? Dariya tayi tace babu dan muna tare da maman Zainab munsha fira da kuma kallo, murmushi yayi yace nikam inaji maki tsoron mutanan gidan nan, Fuskarshi ta shafa tace kada kadamu Maman Zainab bata da irin halin sauran mutanan, itama kanta guje masu takeyi, kuma ni nayaba da hankalinta, tana sona sosai, yace toshikenan Allah yatemaka, tace amin. Tashi tayi takawo masu abinci, anan suka zauna sunaci, kallonshi tayi, dan taji shiru haryanzu befada mata nawa yasamo akasuwa ba, kamar yanda yasaba. Abbas yau naji shiru, ko baka samu komai akasuwar bane? Kallonta yayi ta gefen ido yayi murmushi yace kasuwa lafiya lau mana, gashi kina ganin har cefane nayo mana na abincin gobe da rana. Shiru tayi tana kallonshi, duk seya tsargu dan besaba yimata haka ba, Hannunta yakamo yace yade Labiba naji kinyi shiru? Hannunta tacire, tace wlh bakai bane Abbas, tabbas akwai abinda aka koya maka a kasuwa yau. Murmushi yayi yace bangane me kike nufi ba? Shikenan kawai dan nace maki kasuwa lafiya ai bawani abu bane, dannace haka. Tashi tayi ta daure fuska tace shikenan yayi maka kyau, daki tashige aranta tana fadin nasan yanzu zaka biyoni. Murnushi yayi yace insha Allah Jafar zan cika maka alkawarinka. Tashi yayi yanufi masallaci, domin yin sallar isha'i. Shiru taji be shigo ba, tashi tayi ta leka, amma bata ganshi ba. Dawowa tayi gaba daya hankalinta yatashi, tace meke samun Abbas zeshigo mani da wani hali wanda besaba mani dashi ba? Kalli dan cefanan daya kawo mana,ko nama babu bare kifi, wanda ada bahaka yake mani ba. Komin kadan din kudi yana siyo mani abun dadi inde ze dawo, lallai bari yashigo inji dalili, tashi tayi ta kabbara sallah. Bayan yadawo sukayi shirin kwanciya har yanzu tana fushi dashi, shikam yamaki kallonta dan kada ta karyar mashi da zuciya. Abbas,yaji takirashi, inajinki Labiba meyafaru? Wai meyasa naga kamar kacanzamun ne? Ada bahaka kasaba mun ba, baka boyemun komai, amma ayau naga kacanza meye dalili? Bakomai Labiba, dan Allah kibarni inyi bacci gobe dawuri zanfita banason damuwa, juya mashi baya tayi tasa kuka. Saurin runtse ido yayi, domin kukan jiyake tamkar ana zuba mashi garwashi. Shima juya mata baya yayi dan bemanta halin dasuke ciki ba, runtse ido yayi yanajinta tana kuka amma haka yashareta dan be manta alkawarin daya daukarma Jafar ba. Ganin beda niyar kulata yasa tayi shiru da haka bacci yadauketa. Washe gari tunda asuba sukayi wanka bayan ankira sallah yafita masallaci, yana dawowa tagaishe shi ya ansa mata yana fadin Labiba rigima, baki ta turo tana dira kafa tahaye gado. Murmushi yayi shima yakwanta tare da jawota suka koma bacci. Da gari yawaye yafita yasiyo masu biredi na 100 yana kawowa, Labiba tace haba Abbas kasan fa jiya biredi mukaci, kuma kasan bana iya jera kwana 2 ina cin biredi , nadauka ma zaka taho mani da dankali tunda haka kasaba mani, kuma naga kayan miyan basuda yawa kuma baka siyo nama ba. Shiru yayi yana kallonta dan zuwa yanzu tabbas tafara bata mashi rai, wanda ada betaba jin hakan ba, kome ze kawo mata idan takusheshi bayajin haushi, amma ayau yafara jin haushinta. Wasu kwalla ne yaji suntaho mashi, ganin zata bata mashi rai kawai ya aje mata biredin yadauki wayarshi yayi waje. Zama tayi ta buga tagumi duk setaji babu dadi aranta, domin tana ganin lokacin da idonshi yakawo ruwa, kwanciya tayi tasa kuka, dan duk abunta batason taga bacin ran Abbas, kasa karyawa tayi, ruwan tea kawai tasha ta kwanta. Akasuwa kuwa Abbas duk wanda yaganshi yasan yana cikin damuwa, hakan yasa Jafar yajashi gefe guda yana tambayarshi, anan yafada mashi duk yanda sukayi da Labiba, Sosai Jafar yaji dadi ganin abokinshi yafara canzawa, haka yayita kara mashi kwarin guiwa akan yakara daurewa komai zezo karshe, alokacin seya nuna mata duk wani jin dadi. Abbas yace Jafar ina tsoron kada Labiba takasa daurewa tabarni, Jafar yace bazata taba barinka ba, domin kunama junanku so me tsanani, kaide kawai karika nuna mata bakadashi, bawai kayi shiru ka kyaleta babu bayani ba. Idan kana fadi mata tunda akwai so zata rika tausaya maka. Dan Allah Abbas. Murmushi yayi yace shikenan Jafar, naji zan gyara, kuskuren da nayi shine dabanyi mata bayani ba. Dariya yayi yace nagode abokina. Tun daga ranar Abbas yakara dagewa gurin canza tsarin rayuwarshi, domin yanason yaga yasamu nakanshi, kuma akullum yana nunama Labiba takara hakuri samunshi nayanzu bakamar na da bane, Tun tana jaje, har tafara hakura, domin kota bata mashi rai, saboda son datake mashi bata iya dogon fushi dashi, kuma akoda yaushe Maman Zainab tana kara nuna mata halin rayuwa, hakan yasa tafara saukowa, domin itama tafara gajiya dazaman gidan. Kwata kwata basa shiri dasu Laraba, shikam Abbas bawan Allah yana aiki sosai dan ganin yasamu yatara kudi masu yawa, har kaya yana daukar ma masu siya yana kai masu bakin mota, duk da Alhajin yana hanashi, dan gani yake kamar yayi girma dayin hakan. Amma shi gani yakeyi yana samu da hakan, tunda kowa da irin alkhairin dayake mashi idan yayi mashi dako, sannan kuma ga kudin sallamar shi da Alhajin yake bashi, hakan yasa yanzu yake zuba kudi masu yawa a asusun shi, dan har 1000 yana sakawa. Jafar ne, tsungunne gaban Mamanshi tana ta faman fada, da kai nake kanaji na kamun shiru, ko kana tunanin duk halin da kake ciki kaida abokinka banida labari? To wlh baka isa ba, bazan haifama wani daba, Ita uwar tashi meyasa bazata jashi gidanta yazauna ba, se kaine zaka rika yawon kama mashi gida duk bayan shekara, to kaji namaka rantsuwa wlh yazo karshe, dama ai nadade dasawa arika dubamun kai, Ina sane wannan shine gida na 2 daka kama mashi, yanzu kuma har kasuwa aka cemun ka kaishi gurin Alhaji kanaso yazo yafika arziki ne? Dan haka daga yau naraba wannan alakar datake tsakaninku. Kai barima kaji inyi maka megaba daya, wlh, wlh, wlh. Daga yau idan nakarajin labarin anganka kaida Abbas Allah ya isa banyafe maka ba, kuma inaso kaje gurin megidan daka kama mashi haya agurinshi, ya lissafa kwanakin dayayi yacire kudinshi. Yabaka sauran, kuma tunda Alhajin dan uwanane zanyi mashi magana karyakara barinshi yayi aiki agurinshi. Idan kuma bakaji ba, daga yau kamanta cewa kana da Uwa. Haka nan kai baka da zuciya, kajawo mutum jikinka yazo yafika arziki. Kuka sosai Jafar yakeyi kamar karamin yaro, haka yafara rokonta amma sam taki ta saurareshi, shi babban damuwarshi ma yasan Abbas yana zaune kofar gida yana jiranshi, Dan tunda suka shigo bayan sun gaisa mamanshi tace ma Abbas yajira awaje zatayi magana da danta. Shikam Abbas dama tunda yaji haka yasan akwai wani abu, dan dama yadade da sanin maman Jafar bata sonshi. Jafar ganin bazata saurareshi ba yamike tsaye, yanufi hanyar fita, seda ya tsaya zaure ya goge fuskarshi sannan yafita, ita ko mamanshi tana ganin yafita tabishi zaure. Abbas yanajin alamun fitowarshi shima yayi saurin goge idonshi, dan duk abinda sukeyi yajisu, Jafar yakaraso gurinshi yana murmushin karfin hali, yace yi hakuri abokina Mama ce take bani sako. Uban sako nake baka munafuki, ubanka neshi dabazaka iya fada mashi abinda nace ba? To tsaya kaji Abbas kake kowa? Daga yau narabaka da Dana Jafar, tunda ba ciki daya kuka fito ba, idan har son dakake mashi na gaskiya ne, kuma kanason kada fushin Allah yahau kanshi to karabu dashi. Dan wlh bazan yafe mashi ba, matukar yacigaba da kulaka, kuma kaje kanemi gurinzama domin zansa a anso mani sauran kudin hayar daya biya. Haka kawai kaje ka goga mashi kashin tsiya, yo inba kashin tsiya ba, haryanzu ka kasa Mallakar MUHALLINKA. Wannan itace maganata ta karshe, da kai. Haka tajuya takoma gida, gaba dayansu kuka sukeyi, bakamar Jafar, jijiyoyin kanshi duk sun fito, da kyar Abbas ya tsaida kukanshi yadafa Jafar yace, Abokina kada kadamu, ninasan aduk duniyar nan banida kamarka, kayi mani abinda babu wanda yataba munshi, wlh kanada matukar muhimmanci arayuwata, kuma bazan taba mantawa da kai ba. Babu komai, zanyi kokarin yin nisa da kai, bazanso ace saboda ni kasamu matsala da mama ba, zaka iya canza ni, amma bazaka iya canzata ba, bakomai insha Allahu gobe zanbar gidan damuke, koma ina ne, zankoma da zama, Kuma zanbar kasuwarku gaba daya zankoma wani gurin insamu wani aikin tayanda bazamurika haduwa ba, ina rokonka dan Allah aduk inda kaganni, kayi kokarin boyewa, nima zanyi haka, Domin Mama tace bata yarda ka karamun magana ba, dan haka idan har kanaso inji dadi to kabi abinda Mama tace, kada ka kara nemana, har se ranar da mama da kanta tace kanemeni, nasan bazan taba wulakanta ba. Allah yahada fuskokinmu da alkhairinsa. Kuka Abbas yasa sosai, Jafar ya rungumeshi suna kuka, Jafar yace wata alfarma 1 nakeso kamun Abbas, inaso ka koma gidan Umma, duk da nasan daki daya ne agidan, Kaninka ma ashagon kofar gida yake kwana, amma nasan zaka samu yanda zakayi. Abbas yace zanje Jafar dole ne, canne kadai yaragemun inda yazamar mani dolena,amma bazan iya takura Ummata ba, zanje induba asusuna nasan yanzu suntaru da yawa. Insha Allahu komun lalacewar gida zansamu muzauna kafin Allah yakawo mana wani budin. Jafar yace toyanzu wace kasuwa zaka koma? Abbas yace ayau zanyi tunanin amma bazakaji ba, dan banason kama fara nemana. Sakinshi Abbas yayi yana fadin Allah yasadamu da alkhairi Jafar, juyawa yayi yana goge idonshi yafara tafiya, Jafar yace Abbas,,,, yana juyowa yace narokeka da girman Allah kada talauci ya rudi zuciyarka kafada wata harka, bazan taba yafe maka ba, idan kabi hanyar haram domin kaji dadi. Abbas yayi murmushi hawaye suna zubo mashi yace namaka alkawarin kozan kwana banci ba, bazan ci haram ba. Nafiso ingina rayuwata da halal. Haka yajuya yatafi, harseda Jafar yaga ya bille sannan yaduke anan yasaki kuka meban tausayi. Tafiya yakeyi acikin adedeta amma gaba daya hankalinshi baya jikinshi, seyanzu yake kara ganin wautarshi daya biyema soyayya da kuma mace yazabeta yabar MUHALLINSHI. Daya sha wahala kafin yasameshi. Maganar dan adedeta yaji yana fadin malam munshi unguwar, kudinshi yaciro yabashi yafita, har anfara kiran magriba, hakan yasa yashiga masallaci, koda aka gama zama yayi, yana tunani, har akayi isha'i sannan yanufi gida. Da sallamar shi yashiga, sede besamu kowa awaje ba, hakan yasa yashige dakinsu, zaune yasamu Labiba tana linkin kaya, sallama yayi mata tace sannu dazuwa Abbas, yau naga ka dade, uhm kawai yace mata yashige daki, domin yanajin kanshi kamar ze tsage. Tashi tayi tabishi, akwance tasameshi, yana kalon sama, tsayawa tayi tace Abbas yanaga kashigo hannu biyu, bakasiyo komai ba, kuma dazu nace maka kasiyo mana abinci awaje dan nayi wanki nagaji banajin zan iya dora wani abinci, Amma naga kashigo haka, kuma gashi ka kwanta, katashi kaje kasiyo mana ko awara ce to. Shiru yayi bece mata komai ba, tace Abbas da kaifa nake magana amma kamun....... saukar marin dataji ne,yasata kasa karasa maganar datakeyi. Hannu 2 tasa tarike kuncinta, hawaye suna zuba daga idonta, kallonshi take cike da tsoro, dan gaba daya fuskarshi tacanza kamar ba Abbas din data sani ba. Abbas, yau nika mara? Hannu yadaga zekara mata tayi saurin yin baya, yace wlh kika kara wata magana senayi maki abinda baki zato, haba, wannan wace irin masifa ce,duk kece sanadiyar jefani cikin wannan wulakantatar rayuwar. Ya isheki hakanan,wlh yanda nakeji ayanzu zan iya daukar kowane mataki akanki, kinsan irin masifar danake ciki yanzu? Amma dayake bakida hankali nadawo kina ganin yanda nashigo zaki faramun wata maganar banza. To idan bazaki dafa abinci ba, sede ki kwana da yunwa, amma babu inda zani, kuma bari kiji, idan har kinason cigaba da zama dani, dole kicanza halinki, duk wannan wahalar danakeyi danwa nakeyinta? Kina tunanin inda ni kadai ne, bazan iya rayuwa me dadi ba? Kuma inaso ki,kwana da sani zuwa gobe zamu bar gidan nan, zamu koma can gidan Ummata, nabaki daga nan zuwa gobe, kiyankema kanki hukunci idan har zaki iya cigaba dazama dani. Saurin rungumeshi tayi tana kuka, tace haba Abbas wace irin magana kake fada haka? Yau da bakinka kake fadin zaka rabu dani. Ina alkawarin dakamun? Kasan irin son danake maka bazan iya rayuwa idan babu kai ba. Dan Allah kayi hakuri kayafemun. Kuka tasa takifa kanta saman kirjinshi, hannu yasa yakara rungumeta shima yana kukan, sun dade ahaka kafin yacireta suka zauna, Hannunta yakama yace kiyi hakuri Labiba, yau na aikata maki abinda bantaba yimaki ba, ayau ina cikin damuwa, amma muje intayaki kisamu wani abu kidafa kici, kallonshi tayi tace kaifa? Kanshi ya girgiza yace banajin akwai abinda ze iya shiga cikina. Itama tace nakoshi, bari indafa mana ruwan zafi musha lipton yace toshikenan. Kwanciya yayi yana kara jin haushin marin dayayi ma Labiba, tabbas ayau yasan bakaramin so Labiba take mashi ba. Bayan sungama shan tea suka kwanta, haka yabata labarin duk abinda yafaru. Sosai take kuka, tace Abbas kayi hakuri da duk irin abinda namaka, tabbas nasan nice silar saka ka cikin wannan halin dakake. Amma wlh nayi nadama, kuma hakan bazata kara faruwa ba, rungumeta yayi yace bakomai karki damu kanki, wannan kaddara tace, ko babu ke tunda Allah yarubuta hakan zefaru dani to seya faru. Tace nagode megidana, kuma namaka alkawarin duk inda zaka kaini zanyi hakurin zama. Washe gari da asuba, bayan angama yadawo gida, yana zuwa dede kofar dakin Laraba,yaji an saka ihu ana fadin nashiga 3 maciji, har yawuce yaji ancigaba da ihun, saurin daga labule yayi yashiga. Yana shiga falon yaji anturo kofar, abinda be saniba dama Laraba tun jiya tashirya plan dinta ita da Laure, sanin mazajensu basa nan, hakan yasa ta tura yaranta dakin laure, tunda yafita masallaci take lekenshi, Yana tahowa, tayi saurin shigewa daki, gashi babu wuta. Saurin juyawa yayi alokacin dayaji antura kofar, Laraba yagani babu ko kaya ajikinta tana nufoshi fuskarta dauke da murmushi, saurin rufe ido yayi yana karanta addu,ar neman tsari, ita kam kamar yana kara mata karfi, haka tanufo kanshi gadan gadan. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 20 🔱 25 Hannu yasa yadauketa da mari, anan tafadi kasa, yayi saurin bude kofar yafita, cikin ikon Allah babu wanda yaganshi, yana fita yashige dakinsu. Afalo yazauna gaba daya ranshi yagama baci, hankalinshi yatashi, aranshi yake fadin inbadan Allah yasoshi ba, dayanzu ankamashi yazecema mutanan gidan? Yazeyi da Labiba wanda yasan saboda kishi zata iya aikata wani abun. Godiya yayi ma Allah daya kareshi, aranshi yana fadin agaskiya koda maman Jafar batace subar gidan nan ba, da ayau seya barshi. Ihu sukaji atsakar gida, ana fadin mutanen gidan nan kufito wlh yau Allah yakama kwarto adakin Laraba, kuma abun kunya acikin gidan nan, Kowa yafito yaganshi da idonshi gashinan acikin dakinta. Dasauri Maman Zainab, tafito itama Labiba fitowa tayi daniyar fita setaga Abbas zaune afalo, Kallonshi tayi tace Abbas bakaji ana ihu ba amma kazauna bazakaje kate makesu ba, kasan mazajansu basanan. Kallonta yayi yace tunda ke kinfito ai sekije, Tashi yayi yace idan kingama kallon kishigo muhada kayanmu, anjima kadan zanje infada ma Umma, dan nasan mutumin nan yana iya zuwa akoyaushe yayi mana wulakanci, gara mucema mutanan gidan nan munsamu wani guri. Jiki asanyaye tabi bayanshi, aranta tana fadin Abbas yasake hali, yanzu komai fada. A waje kuwa Laraba tanajin Laure tafara ihu tayi saurin tashi tasa rigarta ta bude dakin tajawota tana fadin ke bakida hankali ne, zaki tara mana mutane? Idan kuma sukazo basu ga kowa ba yazance masu? Laure tace yo bake kikace danaji anfara dawowa masallaci ba, idan aka dan jima infito inyi ihu zaki san yanda zakiyi Abbas yashigo dakinki, sekija mashi sharri. Laraba tashare zufar datakeyi tace kede bari kawai nibanja mashi sharri ba, shiya kwasamun mari, anan tafada mata duk abinda yafaru Hannu maman Zainab tafara tabawa jin irin mugun abunda wadannan mutanen sukaso su hadama Abbas, komawa daki tayi ta dauko hijabinta tafito tanufi dakinsu Labiba. Da sallama tashiga falon, seda Labiba tajita ne ta fito, tana ganinta suka gaisa, Maman Zainab tace Labiba, yanaga kamar kuna hada kaya?. Murmushi tayi tace wlh tashi zamuyi, Maman Zainab tace bangane tashi zakuyi ba, kuma shine baki fada mun ba, seda nashigo nagani da idona. Zatayi magana taji muryar Abbas yana fadin dole ce tasa zamu tashi Maman Zainab, zaman gidan nan ba namu bane, domin mutanan gidan nan basuda halin kirki, Gara inbar masu gidan tunkafin sujamun dauri,Labiba tajuya tana kallonshi dan ita batasan abinda yake faruwa ba. Maman Zainab tace wlh nima abinda kunnuwana suka jimani ne, nashigo infada maka. Gaskiya Abbas ka tsallake rijiya da baya, tabbas Allah ya kubutar da kai daga sharrin Laraba, anan tafada masu maganar dataji sunayi data fito. Kuka Labiba tasaka dajin wannan abu, Abbas yace to Maman Zainab kinji dalilin dayasa zamu tashi, gara mukoma gidanmu kafin musami wani gurin, domin nan gaba bansan wane irin sharri zata jamun ba. Maman Zainab tace gaskiya kam nabaka goyon bayan kutashi, nima insha Allah Abban Zainab yana dawowa zanbashi shawarar mutashi, tunda yanzu abubuwa sun fara canzawa, Kuma dama shima yafara maganar tashinmu, amma dayake yacemun sunfara cinikin wani karamin gida yanaso yakarasa tara kudin yasiya duk da yacemun gidan kasa ne, kuma daki daya ne me hade da falo, bandakinma yace ba rufaffe bane. Amma yace gara mukoma can da zaman mu anan, ina maku fatan alkhairi, kuma insha Allahu tunda inada number dinki aduk inda kike wata rana zanne meki. Abbas yace babu komai Maman Zainab, mungode da kulawarki, kuma shawarar dazan baki, ki kara karfa fama mijinki guiwa akan yakara dagewa yasayi wannan gidan, gara kukara hakuri anan din wata rana se labari. Tace bakomai bari intayaku hada kayan, Abbas yace toni bari inje gida kafin kugama, fita yayi yabarsu suna hada kayan su. Labiba kuwa haryanzu kuka takeyi, Maman Zainab tace haba Labiba godiya yakamata kiyima Allah daya tsare maki mijinki amma wannan kukan ya isa haka. Labiba tace hakane, amma wannan kukan harda kukan rabuwa dake. Hakika bantaba zama da wata wadda naji tashiga raina ba, kamar ke, kuma babu wadda take fadamun gaskiya komin dacinta seke, abaya nayi kawaye dayawa amma babu abinda suka kareni dashi sema jefani cikin tashin hankali da sukayi. Namaki alkawarin duk lokacin da kika ziyarceni zanbaki tarihin aure na da Abbas. Maman Zainab tace bakomai, insha Allahu wata rana rayuwarku zatayi kyau, harse mutane sunji sha,awarku. Nide abinda nakeso ki kara hakuri aduk inda kike, kuma kizama me rike sirrinki dana mijinki, kada kibari wata kawa tazo tashiga jikinki tasamu damar rabaki da halayenki masu kyau. Kuma kada kiji kyashin bada wani abu da kika mallaka ga mijinki domin ku rufama kanku asiri, ba maganar tonon asiri ba, amma duk abinda nasan ina dashi nabama mijina domin yasamu yahada danashi ya mallaki MUHALLINSHI. Domin nice silar rabash danashi, shiyasa banajin haushin temakonshi, domin nasan irin wahalar damuka sha agidan nan. Allah yahada fuskokinmu. Itama kukan tasa haka suka cigaba da hada kayansu, Maman Zainab tana kara bama Labiba shawara. Zaune yake adakin Ummanshi bayan sungama gaisawa yayi shiru kanshi yana kallon kasa. Cike da kulawa tace Abbas bakinka da magana amma naji kayi shiru, idan baka fadamun damuwarka ba wakake dashi dazaka fada mawa?. Gyara zama yayi yafada mata duk abinda yafaru tundaga korarsu da akayi daga wancan gidan har yanda Jafar yakama masu wannan gidan, da aikin daya sama mashi akasuwa, har zuwa abinda Maman Jafar tace. Kwallan idonta ta goge domin bata taba sanin halin da danta yake ciki kenan ba, tun lokacin daya sake komawa gida na 2 bayan aurenshi datayi mashi fada akan yadena biyema mace yana kashe mata kudi yakasa tara komai, tundaga lokacin Abbas bekara fada mata halin dayake ciki ba. A duk lokacin dayazo sede yafada mata suna lafiya, sam bayason abinda Ummanshi zata ce, yadena yima Labiba, hakan yasa yadena fada mata komai. Kallonshi tayi tace yanzu Abbas da halin da kake ciki kenan amma baka fadamun ba? Har wata mata tana yimaka cin fuska saboda kawai kaddara tafada maka karasa naka MUHALLIN. Ashe dama baka daukeni amatsayin uwar dazaka fadama damuwarka ba? Waye yafada maka duk duniyar nan akwai wanda ze iya rufa maka asiri inbanda mahaifiyarka? Lallai kayi kuskure Abbas, wanda batun yau nasha fada maka matukar kabiyema mace tabbas kana tare da wahala, domin mace itace silar jefaka cikin wannan rayuwar, Kawai namaka uzuri ne, saboda irin son da kake mata, kuma ina tsoron rabon dayake tsakaninku kada yazama ajalina shiyasa ban matsa ba, amma da tuni nasaka karabu da ita. Amma babu komai, koda awaje zamu zauna yafiyemun kadawo kusa dani kazauna da kaje wasu suna walulakanta mun kai, ita Labiban seta zauna adakina, kai kuma sekaje dakin Umar kurika kwana duk da dakin bawani girma gareshi ba. Amma abinda zan fada maka inaso kayi amfani da wannan abun daya faru da kai yazamar maka ishara, kayi kokarin dagewa gurin neman halak, kaima kasamu kasamu nakanka. Godiya yayi tamata, yace Umma dama akwai wani asusu danakeyi, nasan kudin sun taru, zan fita gobe inje neman aiki, idan har nasamu zancigaba da tarawa, idan yaso ko daki daya ne, zanyi kokarin ginawa daga gefen tsakar gidan nan. Murmushi tayi tace Allah yate makeka Abbas, Allah yasa kafi haka, babu komai, kayi hakuri insha Allah wata rana mutanan dasuka gujeka sesun dawo karkashinka. Tashi kaje kada suzo sumaku wulakanci. Wata mota yasamu irin ta daukar kaya yatafi da ita, yana zuwa yasamu harsun gama, haka aka fara fita da kayansu, Laraba da Laure duk sunyi tsuru tsuru abakin kofa, dansu atunaninsu saboda abinda Laraba tayi ma Abbas ne, yasa zasu bar gidan, Laraba duk tashiga damuwa, hakan yasa tana ganin Abbas yashiga dakinsu, taja Laure suka nufi dakin, afalo suka samesu suna sallama da Maman Zainab, se kuka sukeyi ita da Labiba, Da sallama suka shiga dakin kamar mutanan arziki, suna shiga Laraba ta tsungunna tafara kuka, tace dan girman Allah Abbas kayi hakuri kayafemun, wlh nayi nadamar abinda na aikata maka, gashi ta dalilina zaku bar gidan nan. Dan Allah kayafemun kada kutafi da hakkina. Murmushi Abbas yayi yace bakomai, Allah ya yafe mana gaba daya, kallon Labiba tayi tace kema Labiba kiyafemun, nasan tunda kukazo gidan nan babu abinda mukayi maki na kyautatawa, dan Allah kiyi hakuri. Labiba tace bakomai nayafe maku Allah yahada kowa da rabonshi, kallon Maman Zainab sukayi itama suka nemi yafiyarta. Anan duk suka yafema juna. Sallamar dasukaji anayi ce hade da kuka yasa sukafito dasauri. Yarinyar Laraba ce da Yaron Laure, tare da wani mutum wanda yarikosu, se kuka sukeyi, mutum yakara tallabar keyarsu yana fadin bazaku mana shiru ba, mutanan banza. Laure tace malam lafiya zaka shigo mana gida da yara karika dukansu, aikensu fa mukayi su siyo mana koko da kosai. Laraba tamatsa kusa da diyarta tace meyafaru kike kuka?. Mutumin yace siyen kosai kuka aikesu ko kuma yawon iskanci? Hakanan kawai kuna aiken yara bakusan halin dasuke ciki ba, tonide abinda nagani yasa nakasa hakura shine na bigesu kuma nasa su kawoni gidansu dan su fada maku abinda sukeyi. Mamn Zainab tace dan Allah kayi hakuri kafada mana abinda sukayi. Mutumin yace to nazo wucewa tagurin wani kango senaji magana, kamar ance inleka, senaji yaron yanacema yarinyar kicire wondonki, yauma inkara yimaki irin abinda mukayi jiya, wanda nace maki haka Babana da Mamana naga sunayi. Abun ya tsoratani sosai, ganin yarinyar tana shirin cire wondonta, shine nayi saurin shiga nakamosu, ga dukkan alamu ba wannan bane karo na farko dasuka fara, shiyasa amatsayina na uba nace gara inkawosu inma iyayensu magana. Domin sudauki mataki, kuma su gane kuskuren dasukeyi, nizan koma, Allah ya kyauta gaba, amma ina baku shawarar kusaka yaranku makaranta, kuma ku gyara tarbiyarsu, hakan ze rage bannar da ake samu ayanzu. Girgiza kai Abbas yayi, aranshi yana fadin Allah da manzonsa sunyi gaskiya, idan kazamo na kirki danka ko yarka zasu zamo na kirki. Addu,a yayi kan Allah yakara tsaresu daga sharrin shaidan. Juyawa yayi yacema Labiba, muje mun tsaida me mota. Allah yakara kyautawa, mude semu cemaku sadon alkhairi, maman Zainab tabi bayansu tana kuka, su laure ma kuka sukeyi, suna kara dana sanin irin mugun halin dasuka aikata. Bayan suntafi maman Zainab tashigo tana kuka, tsaye ta iske su suma suna kuka,tace wannan kukan baze kaiku ko ina ba, yakamata ke kiduba diyarki, idan akwai wata matsalar kutafi asibiti, Allah yakara shirya mana zuri,a. Hannun Zainab takama suka koma ciki. Laure tace Laraba munga ta kanmu, tunkafin muje lahira Allah yafara nuna mana kuskuren mu tun aduniya. Laraba tace ni narasa abinda ma zance, insha Allahu daga yau, nadena aikata duk wani mugun abu danakeyi, ba yara kadai ba, mukammu yakamata mu koma makaranta, domin mukara samun ilimin dazamu bama yaranmu tarbiya. Laure tace Allah ya yafe mana. Nace amin. Tun ahanya Labiba tacema Abbas, kada asauke da kujerunta da gadonta, asauke masu kayan sawarsu da katifa da sif dinsu, kawai. Kallonta yayi yace meyasa kikace haka? Murmushi tayi tace kawai inaso akaisu kasuwa asaida. Murmushi yayi yace mezakiyi da kudin? Tace nide dan Allah nace, idan ka kawo kudin zakaga abinda zanyi dasu, kaga yanzu ko munje babu inda za,a sakasu dan Allah kada kace a,a. Jinjina kai yayi yace shikenan, tace yau nagode, shima aranshi yaji dadi sosai, dama tundazu yake tunanin inda za,a ajesu, bayason a ajesu awaje ruwa yabatasu. Kuma bayason yafara kawo mata maganar asaida dan tunda suke betaba saida mata wani abunta ba, se idan itace tace, ko kujerunta dasuka saida itace tace asaida suka sayi abinci. Haka akayi, suna zuwa gidan yakira kaninshi Umar suka sauke kayan aka bar sauran amota, Umar yasa yashiga dasu shi kuma yawuce kasuwa dame motar, suna zuwa yaci sa,a aka siyesu da daraja, naira dubu 15 aka bashi kudin gado, kujeru kuma 18, cike da murna ya sallami me mota yahau adedeta yanufi gida. Koda yaje harsun gama shirya kayan adakin Ummanshi. Duk da dakin beda wani girma amma kayan sun shiga, abinci Umma takawo masu dumamen tuwo, fita waje tayi tabasu guri dansuci. Labiba kawai Abbas yake tausayi, dan tunda sukayi aure yau shekara 3 basu taba cin tuwo da safe ba, kallonshi tayi taga ita yake kallo, hakan yasa tayi murmushi ta tashi tadebo mashi ruwa akwano, Hannunshi takama ta wanke itama ta wnke nata, sannan tafaraci, harda lumshe ido tace gsky Umma ta iya girki, jin hakan yasa yayi murmushi yasa hannu yafaraci. Amma azahirin gsky miyar babu magin kirki, hakanan Labiba take daurewa tana ci saboda Abbas. Shikanshi sabo da cin girkin Labiba, hakan yasa yaji miyar babu dadi sosai, Labiba kuwa aranta take fadin bazata kara barin Umma tayi girki ba, gara tarika yimasu, kodan surika cin medadi. Bayan sungama yadauko kudin kayanta yabata, yafada mata yanda aka siyesu, murmushin jin dadi tayi tace Allah yayi masu albarka, dubu 20 ta mika mashi, tace karba karike inaso kasa kasu cikin asusunka, bayan kasamu aiki seka fasa muga abinda aka samu nasan zasu isa kayi ginin dakin. Wannan dubu 13 kuma inaso kamun izini infara abincin saidawa amma acikin gida, zanrikayin na safe dana rana, kaga babu ruwanmu da neman abincin safe da rana, sede na dare kawai, hakan ze kara temaka mana. Amma dan Allah kada kace a,a nasan komeye wata rana ze zama labari. Wasu kwallan tausayi ne, suka zubo mashi, besan lokacin daya jawota ya rungume ba, itama kukan takeyi, yace nagode Labiba, bansan dame zan saka maki ba, fatana Allah yamun budi na alkhairi injiya maki dadi. Bakomai nayi maki izini, Allah yasa kifara asa,a Allah ya kareki daga sharrin mahassada. Tace amin, yace bari inkira Umma infada mata, Sosai Umma taji dadin abinda Labiba tayi, anan tayi masu addu,a dama Umma tana sana,ar saida magi dasu barkono, kuka gishiri. Tace se insa asamo maki almajiri dan kada wahalar tamaki yawa. Haka Abbas ya karbi kudin yaje kasuwa yasiyo mata kayan abinci da robobi, cokula, yakawo mata, dama Umma tana da babbar tukunya da kaskon tuya. Umma da kanta taje makarantar wani malami anan kusa dasu tace yabata almajirai 2 haka yasamu masu hankali yabata. Waken da zata rika kosai dashi Umma tasa aka kaishi barza dan kada Labiba tasha wahalar surfawa, ana kawoshi ta bakace shi, suka aje. Umar shine yafara yimasu talla agurin yan unguwar matasa. Koda dare yayi Labiba kasa bacci tayi, domin yau itace rana ta farko dazata kwanta batare da Abbas ba tunda sukayi aure. Shima hakan ta kasance agareshi, shiyasa yayi alkawarin zeyi ginin dakin da kanshi, tunda beda kudin biyan masu aiki, dama kuma yariga daya saba. Addu,arshi daya Allah yabasu sa,a aduk abinda zasuyi, dayaji baccin yakasa zuwa haka yafita yayo alwala yafara nafilfili, yana rokon Allah sa,a. Itama Labiba haka tayi, sallah tafarayi tana neman sa,a agurin Allah, gaba daya daren sun rayashi ne, da ibada. Nikam nace ai duk me nema yana tare dasamu, kuma Allah yace duk wanda yarokeni nikuma zan amsa mashi. To Allah yabama su Abbas da Labiba sa,a. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08927525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 25 🔱 30 INA FATAN KOWA YAYI SALLAH LAFIYA? ALLAH YA MAIMAITA MANA, YA KUMA SA IBADARMU KARBABBIYA CE. AMIN. Washe gari tunda asuba suka fito anan suka hada kayan kosai gari yana fara haske aka bama almajiri yakai nika, yana kawowa Umma da kanta ta hura wuta sannan Labiba tahada kullun tafara bugashi. Lokacin da gari yakara wayewa sungama hada komai, Labiba tafara tuyar kosai, koko Umma ta dama masu, tazuba ma Abbas da kosan taba Labiba takai mashi, ita kuma ta anshi tuyar. Cikin ikon Allah sega mutane sunfara shigowa siyan kosai, dayan almajirin shine yake karbar kudin yana zuba masu. Afalo tasameshi zaune, zama tayi tace sakko kaci abinci kada ka makara zuwa kasuwa, murmushi yayi, yana kallonta cike da tausayawa, Hannunta yajawo, yace Labiba kiyi hakuri da duk wani hali damuke ciki, nasan nine silar sakaki acikinshi, yanzu gashi ta dalilina kinayin abinda baki taba yiba. Murmushi tayi tace haba Abbas, nice yakamata infada maka haka, amma dan Allah daga yau, banaso ka kara tuna abinda yawuce, koma menene inaso mu manta da rayuwarmu ta baya hakan zesa mu fuskanci rayuwarmu tayanzu. Abinci yafara ci yace toshikenan Allah yashige mana gaba, tace amin, fira tarika yimashi har yagama, tadauke kayan, bayan tadawo yace Labiba nizantafi kimun addu,ar samun sa,a. Inaso inde nasamu aiki akasuwa infara ginin dakinmu, domin jiya banyi bacci ba, nasaba kwanciya tare dake, amma dalilin rashin MUHALLI jiya na kwanta batare dake ba. Insha Allahu gobe zanyi ma malam musa megini magana semufara da wadannan kudin amma na kasa zanyi domin kudin su isa, nasan idan muka hadu nida Umar dashi malam musa zamuyi saurin gamawa. Kinga kudin aikin malam musa kawai zan samu, tunda shine yafi sanin takan gini. Labiba tace hakane, gara de asamu ko marar tsawo ne sosai agina, inde ze ishemu rayuwa nida kai, zefimun dadi, da,ace baka kusa dani. Yace insha Allah, bara intafi. Sallama yayi ma Umma tayi mashi fatan alkhairi sannan Labiba tara kashi har kofar gida, sukayi sallama tana yimashi addu,a sannan tadawo. Koda karfe 7:30 tayi tuni har sun saida kosan, almajiran sukayi wanke wanke suka share tsakar gidan aka basu abincinsu suka nufi makaranta karatu. Bayan sungama karyawa suka fita domin gyara kayan miyan abincin rana. Abbas kuwa yana fita yatari me adedeta yatambayeshi ina ze kaishi? Shiru Abbas yayi, yama rasa wace kasuwa zece mashi, sam bayason kasuwar dazatayi kusa datasu Jafar. Kawai jiyayi bakinshi yace WAPA zaka kaini, duk da yasan ba kasuwa bace amma yasan acan ma ze iya samun aikinyi tunda gurin yan canji ne. Tafiya suka fara Abbas yana ta tunanin ta inda zefara. Abakin gurin ya ajeshi, kudinshi yabashi yayi mashi godiya sannan yayi bismilla tare da addu,ar shiga kasuwa yafara tafiya, koda yashiga gurin, mutane yafara gani kowa yanata hidimarshi. Haka Abbas yayi ta zaga yawa cikin Wapa amma yakasa samun inda zenemi aiki, wani katon shago yagani, da yara acikinshi sunata aiki, hakan yasa ya matsa kusa da gurin. Sallama yayi masu, daya daga cikinsu yayi saurin tasowa, dan atunaninshi customer ne, hannu yabashi, bayan sungaisa yace ya Malam kanason canji dala ne ko sefa? Shiru Abbas yayi yace a,a ina neman megidanku ne, kallon 3 saura kwata yaron yayi mashi yace bangane kana neman megida ba. Idan wani abune kafada nine babban yaronshi. Gyara tsayuwa Abbas yayi tare da sosa kai, yace to bawani abu bane dama nafito neman aiki ne, nafi awa 2 ina zagaye cikin Wapa amma nakasa samun wanda zan tunkara da bukatata. Shine danazo wannan shagon hankalina ya kwanta da gurin shine nace bara ingwada sa,a ta. Wani murmushin rainin hankali yaron yayi yace lallai kuwa malam wannan sa,ar taka bazata karbu anan ba. Sede ka kara gaba, Abbas yace haba bawan Allah, naga kaima fa gurin nan banaka bane, shiyasa danazo nace megidanku nake nema, inda shine yafadamun haka zan iya hakura, amma kaima akasanshi ka keci. Dariya yaron yayi, yace ka gyara kalamanka, domin duk wani wanda ka gani yana aiki a shagon nan ta hanyata yashigo, idan kana da wani abu me kauri kamiko kawai amaka hanya, idan kuma babu zaka iya karama kafarka iska. Shiru Abbas yayi, tabbas yanason aiki amma yariga da yayima Allah alkawarin baze taba samun aiki ta haramtacciyar hanya ba, kuma wannan kudin da yaron yake magana tamkar cin hanci ne, amusulunci kuwa Allah yaharamta cin hanci. Tsaki yaron yayi yace bakada magana tunda naga kayi shiru, dan haka kayi saurin barin kofar shagon nan tunkafi megida ya iso dan wlh zan jamaka sharrin dazakayi dana sanin zuwanka gurin nan. Haka nan kawai daga zuwanka guri a kama adauke ka aiki, wama yasani ko barawo ne kai, ko kuma dan 4 1 9, kashigo jikinmu ka cucemu. Juyawa yayi yashige shago yana masifa. Wasu zafafan hawayene suka zuboma Abbas, wai yau shine ake kira da barawo da dan 419 saboda yana neman aiki. Lallai wannan rayuwa idan baka dashi komai ma za,a kira ka dashi, Yanzu wannan yaron ko kunyarshi bejiba amma yafada masa wadannan maganganun. Juyawa yayi yatafi, sede haryanzu zuciyarshi bata hakura da neman aiki ashagon ba, dan tunda yashigo layin yakejin gabanshi yana faduwa. Alokacin daya iso bakin shagon kawai seyaji kamar ana ingizashi yashiga, nesa da gurin yasamu yazauna, kanshi ya kifa da guiwarshi, yana kara tunanin irin wannan rayuwa, Ace yanzu aduniya idan kana neman aiki dole seka bada cin hanci za,a daukeka? Kasuwanci ma kenan, inaga aikin gwamnati? Addu,a yashiga yi yana neman temakon Allah, yana nan har aka fara kiran sallar azahar, hakan yasa yatashi yanufi masallacin dayake kusa da wannan shagon dayaje. Akusa da wani mutum ya tsaya, bayan sungama sallah kowa yakama gabanshi, shikam Abbas zama yayi yanata addu,a yadade azaune agurin har wannan mutumin dayake kusa dashi wanda shima zama yayi bayan angama sallah, har seda yagama addu,oinshi sannan yatashi. Bayan Abbas yagama yatashi da niyar zuwa yasiyi abinci, tashin dazeyi yaga wata babbar waya a inda mutumin nan yayi sallah, dukawa yayi yadauka yanakara juyata ahannunshi, ko ba,a fada mashi ba, yasan wannan wayar bata kananan mutane bace, domin daganinta zatayi tsada. Aranshi yace tabbas naga mutumin damukayi sallah tare dashi, sede bazan iya gane fuskarshi ba, amma de naga kalar shaddarshi. A aljihu yasaka wayar yafita, yana fadin nasan za,a kira bara inje inci abinci. Agida kuwa su Labiba kasuwa tayi riba, domin mutane da yawa sunzo siyan abincinta, kuma sun yaba da iya girkinta, domin Labiba akwai iya abinci kuma ga tsafta. Tas abincin yakare har ana nema. Bayan sunyi wanka sunyi sallah, sukaci abinci, almajiran suka kwashi kwanukan suka wanke suka share gurin. Anan Umma da Labiba suka kirga kudin suka fitar da ribar, sannan suka cire Uwar, anan Umma tabama Umar kudin yaje kasuwa yasiyo cefanan gobe. Labiba har kuka tayi dan murna, ganin sun sami riba sosai, kudin gishiri da magin Umma daza,ayi amfani dasu gobe tabata, domin tace agurinta zata rika siye yafi aje waje asiya. Asusun da Umma tabata tadauko tazuba ribar data samu, sannan ta kwanta dan gaba daya tagaji, Umma se dariya take mata, tana fadin yaran yanzu bakusan wahala, abu kadan zakuyi ya gajiyar daku. Bayan Abbas yagama cin abinci yana zaune nesa da wannan shagon dayaje dazu, zuwa yanzu yafara fidda ran ze samu aiki, har yafara tunanin ko yatafi kasuwar kwari kila adace acan, dan anfi samun dako,gara yaje yafara da dakon. Mikewar dazeyi yaji wayar aljihunshi tana kara, sam shi yama manta da ita, dama tunda yaduba yanaso yakira seyaga akwai pass word hakan yasa kawai ya maidata yajiye. Hamdala yayi, dan dama bayason tafiya batare daya bama me ita abinshi ba, dauka yayi tare da sallama. Shiru yayi yana sauraran abinda ake fada, yace e wlh nima a masallaci naganta, shine na aje inajiran akira. Eyanzu haka ina bakin wani babban bene, shiru yayi can kuma yace to bari intambaya danni bakone , e insha Allah zan kawo maka, tunda kai sananne ne, dama abinda yakara tsaidani kenan, toshikenan inazuwa. Kashe wayar yayi yakara maimaita sunan da,akace yatambaya. ALHAJI ABBAH HALA? Matsawa yayi jikin wani shago yayi sallama, da fara,a mutumin ya amsa mashi, yana fadin malam barka dazuwa, kanason canji ne? Murmushi Abbas yayi yace a,a tambaya de nakeyi. Yace to Allah yasa nasani. Dama shagon Alh, Abbah Hala nake nema. Bata fuska yayi yace kaga malam idan canji kakeso kona nawane nima inayi, yanda zebaka nima haka zanbaka, kanama iya zuwa su kara maka farashi. Kallon mutumin Abbas yakeyi cike da mamakin bakin ciki kiri kiri. Kai ya girgiza yace niba canji nazo ba, kawai shagon nake nema. Mutum yace to nima bansan shagon ba. Juyawa Abbas yayi yace to nagode. Fita yayi ranshi yana me mamakin mutanan yanzu, wai ace babu kunya babu tsoron Allah arika maka bakinciki akan sana,arka, yanzu inda da gaske canji yazoyi haka ze kwacema Alh, ciniki. Seda Abbas yashiga shago 3 amma duk irin abinda wancan mutumin yafada ake fada mashi, lokacin daya fito shagon karshe yayi alkawarin baze kara tambayar kowa ba, juyawa yayi yakoma masallacin dayayi sallah yazauna yace gara injira idan yakara kira ince yazo yakarba. Ko minti 5 beyi dazama ba, aka kara kira, yana dauka yace mashi idan da hali yaturo atafi dashi shagon, ko kuma yazo da kanshi yakarba. Bansan me akace ba,naji yace toshikenan inajira. Tun daga kofar shigowa masallacin yagane wanda yake shigowa, domin bemanta kalar kayan mutumin ba. Da sallama ya isa gurinshi, amsawa Abbas yayi, mutumin yamika mashi hannu suka gaisa. Wayar Abbas yamika mashi yana fadin ai tunda kashigo nagane kayan, domin dazu akusa dani kayi sallah, dama fuskar ce kawai bazan iya shedawa ba. Murmushi mutumin yayi yace gaskiya nagode da wannan abun dakamun. Domin azamanin nan bakowane ze tsinci babbar waya ba ya mayar ma me ita, kai koma karama ce, yanda ake cikin talaucin nan babu wanda ze maido maka. Nagode sosai, gaskiya, kuma hakan dakayi ya nunamun kanada amana. Idan bazaka damuba intambayeka mana? Ya sunanka? Sunana Abbas Alee, murmushi yayi yace da kyau, amma kai bakone ko, naga kace bakasan shagona ba? Abbas yace hakane, nibakone, amma agurin nan, dan agarin nan nake amma bancika shigowa nan ba, yauma neman aiki ne yakawoni nan tunda safe, amma gashi har la,asar takusa bansamu ba. Hakan yasa nayanke shawarar tafiya kwari kozan dace,to wannan wayar dana tsinta ce tasani zaman jira, gashi ansa key bare ni inkira. Jinjina kai mutumin yayi yace Allah sarki, ni sunana Alh, Abbah Hala. Kuma ina aiki anan Wapa, shagona yana daga nan baya, ina canjin dala ne, gaskiya naji dadin haduwa da kai, kuma nayaba da hankalinka, ayanzu duniya ta lalace, kana zaune da mutane, amma suna maka bakin ciki shiyasa bazaka iya gane dawa kake tare ba. Abbas yace tabbas hakane Alh, nikaina ayau zaman danayi agurin nan nakara fahimtar mutane, anan yabashi labarin abinda mutanen gurin suka mashi, jinjina kai Alh, yayi yace Abbas zaka iya nunamun shagunan mutanan?. Kai ya girgiza yace kabarsu kawai Alh, yafi kyau mutum beson makiyanshi ba, da,ace yasansu, hakan zefi mashi dadin rayuwa, amma duk yanda akace kasan makiyinka kuma ace kuna zama guri daya dashi, tabbas ko bakada niyar mashi wani abu shedan ze iya rinjayar zuciyarka har yasaka maka wani mugun tunani. Kuma nima idan har nafadesu tabbas nazama annamimi me hada fitina, domin bansan meze faru ba, bayan nafada. Kayi hakuri kawai, kamar yanda kake zaune da kowa lafiya to kayi kokarin zama dasu da zuciya daya. Hakan zesa Allah yate makeka akan makiyanka, kuma kadage da addu,a da neman tsari daga sharrin masu sharri. Tsayawa Alh, yayi yana kallon Abbas cike da burgewa, hakan dayayi seya tuna mashi babban yaron shagonshi, akullum beda wani aiki se son yakawo mashi gulmar mutane da son ya bakanta wani agurinshi, shi kuma yasamu shiga. Maganar Abbas takara ankarar dashi abinda yaronshi yakeyi kenan badede bane, murmushi yayi yace, nagode Abbas da tuna tarwarka, hakika samun masu zurfin ilimi irinku, kuma ace suna aiki dashi ayanzu akwai wahala, dan zaman danayi da kai yanzu, nakaru da abubuwa dayawa, inaga ace nazauna da kai har abada? Idan bazaka damu ba, nizan daukeka aiki ashagona, ina fatan zaka rikeni da dukiyata bisa gaskiya da amana? Abbas besan lokacin daya kai goshin shi kasa yafara sujjadar godiya ga Allah ba. Hakan da yayi bakaramin burge Alh, yayi ba, seda yayi addu,a sannan yadago yafara yimashi godiya, haka suka jera suka nufi shagonshi. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 30 🔱 35 Mamaki ne ya rufe Abbas ganin sun nufi shagon daya fara zuwa wannan yaron ya koreshi. Tunda suka shiga mutane suke yima Abba Hala sannu, fara,a dauke a fuskarshi yake amsa masu. Auwal, shine sunan da Abba yakira bayan yazauna, yayi ma Abbas umarni daya zauna, daga waje wanda aka kira da Auwal yashigo, shima mamaki yayi ganin wanda ya kora dazu amma yanzu gashi agaban megidansu. Alh, Abbah yace yauwa Auwal munkara samun sabon ma aikaci, sunanshi Abbas, kuma nizan bashi aiki da kaina, ba daya yake da sauran ma aikatan gurin nan ba. Dan haka inaso kuzauna dashi lafiya, daga yanzu shine PA na, dama haryanzu kasan tunda wancan PA yarasu ban sake dora wani ba, duk da nace kaine zan bama, amma naga alamar gara inbarka matsayinka na mekula da ma,aikata. Wani bacin raine ya rufe Auwal, ya dade yana jiran wannan ranar, tunda tsohon PA yarasu yake jiran anadashi, amma gashi yanzu daga zuwan wannan mutumin yabashi, kuma da alama besanshi ba. Murmushi Auwal yayi yace ai bakomai Alh, Allah yahada kanmu, kallon Abbas yayi yamika mashi hannu yace abokina kayi hakuri da abinda yafaru dazu. Murmushi yayi yace haba ai bakomai. Alh, Abbah yace dama kasanshi ne? Auwal yace wlh dazu yazo neman aiki, nikuma nakoreshi, kasan yanzu duniyar ta baci. Alh, Abba yace haka ne, amma duk da haka banaso kuna wulakanta duk wanda zezo nemana. Koma wanene kubashi dama yaganni, domin ba,a taru akazama daya ba, bakasan darajar da Allah yayi ma wanda zaka kora ba, sekaje ka kori wanda shine nagari, idan nabanzan yazo kuma ka karbeshi. Yanzu gashi nan, kayi mashi ranshin kyautawa dazu, cikin ikon Allah kuma yanzu Allah ya dauka kashi har yafika matsayi agurin aikinka, kaga yanzu kaji kunya ko? Kai Auwal ya sosa yana fadin ayi hakuri megida. Yace shikenan ya wuce, ka kiyaye gaba,jeka zan nuna mashi duk abinda yakamata. Fita Auwal yayi yana cizon hannu, wato aikin ma, megida da kanshi ze nuna mashi, Amma ada shine yake kula da komai, to kode wannan mutumin wani abu yayi ma Alh, ne? Gaskiya da sake, dole insaka mashi ido, baze yuwu yazo yafini fada agurin megida ba. Anan Alh, Abbah yadauko file yarika nuna ma Abbas yanda komai yake, dayake Abbas yayi diploma akan accounting, shiyasa abun yazo mashi da sauki. Sallar la,asar kawai ta tadasu, suna dawowa suka cigaba da aiki,seda misalin karfe 5, sannan sukayi shirin tashi. Alh, yace bakomai naga kana da saurin fahimtar abu, nan da wani lokaci zaka kara sanin komai. Idan Allah ya kaimu gobe se mucigaba. Ina wayarka insa maka number ta? Wata Nokia Abbas yamika mashi, Alh, yace lallai Abbas gobe zantaho maka da babbar waya, saboda dole zaka bukaceta. Abbas yace godiya nake Alh, yace bakomai, atare suka fito, yana rike da jakarshi, har bakin motarshi yarakashi, Alh yace wace unguwa kake ne Abbas? Yace anan Darmanawa nake can gurin gandun Sarki gaba da primary alayin wanzamai. Murmushi yayi yace kace muna kusa, nima kusa daku nake, muje se in ajeka ko? Abbas yace badamuwa, haka suka tafi, suna zuwa Abbas yace ya ajeshi akwai abinda zeyi abakin titi. Dubu 5 Alh, yabashi, haka Abbas yayi tamashi godiya yamashi sallama. Seda ya tsaya yasaya masu lemu da kankana sannan yahau adedeta yanufi gida, se kara godema Allah yakeyi da wannan nasarar daya samu ta yau, lissafin yanda zefara gininshi kawai yakeyi. Hamdala yayi tunda yasamu aiki, kawai zesa malam Musa yasamo wani wanda zetayashi aikin se Umar yarika kula dasu, tunda beda lokaci kuma yanason agama dakin dawuri. Da fara,arshi yashiga gidan, bakinshi dauke da sallama, abakin murhu yasamu Labiba tana kokarin dora tukunya, saurin aje tukunyar tayi tanufeshi fuskarta dauke da murmushi. Tana zuwa tafada jikinshi tana fadin sannu dazuwa, rungumeta yayi yana fadin yauwa Labibata, sannu da kokari, ina Umma ne? Tace tashiga bandaki, yace shiyasa ai naga kinshige jikina, nasan intana daki bazakiyi ba. Hannunshi taja suka nufi falon Umma tana fadin Abbas daga ganin bakinka akwai alkhairi, yace sosai ma Labiba, kede muje in kimtsa kusha labari, Ruwa takawo mashi yasha, sega Umma tafito, fita waje Labiba tayi tahada mashi ruwan wanka, Umma tace Abbas kadawo? Yace wlh kuwa Umma, zama tayi tace tundazu bakina yakasa dena maka addu,a Allah yasa kasamu narasar fitar? Yace sosai ma Umma, ai sede kawai muyima Allah godiya, bari infito wanka kusha labari. Umma tace Alhamdulillah, Allah shine abin godiya,jeka fito. Bayan yagama wanka ya nufi masallaci, bedawo gida ba, seda akayi isha,i, akofar gida yahadu da malam Musa, bayan sun gaisa yayi mashi maganar ginin daki, malam musa yace ai babu damuwa akwai wanda zankira semuyi tare, Abbas yace muje kaga filin inaso idan ze isa ayi mana hada bandaki aciki, kasan bandaki daya beda dadi agida, sbd matsuwa ake gudu. Tare suka shiga gidan, yadauko fitila ya haska masu. Malam musa yagama dubawa, sannan yace kwarai kuwa za,a samu bandaki, Abbas yace yauwa amma naji dadi, yanzu agajiye nake, gobe ana fitowa asuba zan nemeka, tunda bamu fita kasuwa se 8 semuji yanda za,ayi. Malam Musa yace shikenan babu damuwa, yanzu idan nafita zansamu me zanen infada mashi, abokin aikina ma zan fada mashi. Abbas yace nagode sosai, sallama yayi mashi yatafi. Bayan sungama cin taliyar da Labiba tadafa masu, suna zaune afalon Umma, anan Abbas ya basu labarin duk abinda yafaru, kuma yafada masu gobe za,a fara ginin dakinsu. Sosai sukayi farin ciki da labarin Abbas, suma suka fada mashi abinda yafaru da bayanan, sosai yaji dadi, dajin irin canji daga gurin Labiba. Umma tace babu abinda zamuyi ma Allah se godiya, dan haka ayau inaso muyi kokari mutashi muyi godiya ga Allah. Domin duk abinda kasamu daga Allah yana da kyau kayi wata ibada wadda zata nuna godiyarka agurin ubangijinka. Allah yatemakeka, ya kareka daga sharrin masu sharri. Dole Abbas ka kara dagewa da addu,a domin Allah ya kaika gurin da dole saka dage da addu,a. Gashi kaje gurin asa,a kashiga gaban mutane dayawa, dole ne suji haushinka, amma kaide babu ruwanka da kowa, kazauna da kowa lafiya, Allah ze temakeka akan makiyanka. Abbas yace insha Allah Umma, bari inje inkwanta nagaji dayawa, Umma tace gaskiya kam, nima bari inleka gidan Zulai indubata. Abbas yace Umma bata da lafiya ne? Tace lafiyarta kalau, kawai zanshiga mugaisa ne. Abbas yace amma Umma naga har 9 takusa, mikewa tayi tadauki mayafinta tana fadin aikuma sekayi fita waje tayi batare data kara kulashi ba. Dariyar da Labiba take boyewace ta fito, Abbas yace wato ma dariya kikemun ko? Matsowa tayi takwanta saman kafarshi tace kaima de Abbas naga alamar bakaje ghana ba, aini tunda Umma tace zataje gidan Zulai nagane abinda take nufi. Amma kai ka tsaya ka isheta da tambayoyi, bakinshi yarufe yana zaro ido yace kai hakanefa, gakiya Umma tana da kula, tashi muje kidanmun tausa inji duminki kafin tadawo, Allah sarki Ummata, muma munkusa komawa dakinmu. Infada maki hada bandaki nasa ayi mana. Labiba tace da gaske? Yace da gaske mana, kara rungumeshi tayi tana fadin nagode sosai Abbas, dariya yayi yadauketa suka shiga daki. Washe gari kamar jiya haka su Labiba suka fara aikinsu da wuri, yau harda kunu sukayi, dan mutane sunce arika hada masu da kunu. Shikam Abbas tunda suka dawo sallah suka nufi gurin ginin, bayan me zane yazo haka aka kiyasta komai, tundaga kasa, ruwa da sauran kayan gini, haka yadauki kudin yabama Umar, yace yarika kula dasu. Bayan yagama wanka ya karya sannan yayi masu sallama yafita, haka jama,a suka rika shigowa suna shiyan kosai da kunu, kafin wani lokaci tuni sun kare. Abbas kuwa yana zuwa shagonsu yafara aiki, haka mutanan shagon suka rika shigowa suna gaishe shi, sosai yaji dadin abinda sukayi mashi, Auwal kam yama kasa zama agurinshi, gani yake kamar idan baya kusa za,ayi wani abun.. Se karfe 10 sannan Alh, Abbah ya iso, bayan sungaisa yamika ma Abbas sabuwar waya akwalinta, infinix hot 4 lite, sosai Abbas yaji dadin wayar, haka yayi ta mashi godiya. Auwal kuwa kamar ze hadiyi zuciya dan bakin ciki, Abbas ya mika mashi wayar yana fadin katayani godiya, Auwal yayi murmushin yake yace gaskiya waya tayi kyau, angode megida. Kallon Abbas yayi yace ai seka bani tsohuwar taka, Abbas yayi dariya yace wannan ai se Labibata. Dariya Alh, Abba yayi yace bama zaka bashi ba, shima yana da ita, Alh, yace Abbas tashi muje banki akwai wasu kudi dazamu ciro, Haka suka fita Auwal se bata rai yakeyi, tunda wancan tsohon PA yarasu dashi ake zuwa bank amma yanzu shikenan yakoma dan tsaron shago. Fita yayi yakira wani abokinshi kuma amininshi yace abokina zokaji babbar magana. Anan yafada mashi duk halin da ake ciki, Saddik yace lallai dole musan abinyi, kai dolema yabar shagon nan wlh. Dariya Auwal yayi yace yauwa abokina haka nakesonka, wlh be isa yazo yasamemu yace ze nuna mana kano ba, zamu gwada mashi mu yan asalin Fage ne. Muje zuwa. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:09 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 35 🔱 40 Haka Abbas yacigaba da aiki a shagon Alh, Abbah Hala, sosai yake kara gane takan aikin, Auwal da abokinshi akullum kokari sukeyi su sami hanyar dazasu kullama Abbas sharri. Sede idan Allah ya tsare bawansa babu wanda ya isa yaja dashi. Labiba da Umma sosai san,arsu take cigaba, aduk sanda suka dafa sesun saida, acikin sati 2 aka gama ginin dakin Abbas, ba laifi yayi kyau, duk da ko fenti ba,ayi ba, amma anyi shafen farar kasa. Bayan sati 1 da gama ginin suka koma, sosai sukaji dadin komawarsu domin bakaramun takura sukayi ba adan zaman dasukayi, haka suka cigaba da sana,arsu. Acikin haka ne ciki ya bayyana ajikin Labiba, bayan sunje asibiti akace wata 3. Sosai Abbas yayi murna da samun cikin Labiba, yakara godema Allah da seda yasamu gurin zama sannan Labiba tasamu ciki, haka Umma tahana Labiba aiki sosai, itace takeyin girki. Jafar kuwa tunbayan rabuwarsu da Abbas bekara ganinshi ba, akullum yana son yanemeshi amma yana tuna maganar Mamanshi, hakan yasa yake hakura, sede kullum yana mashi addu,a kuma shima yanzu samunshi yayi kasa sosai, Yarasa dalilin dayasa yanzu ko kudi yasamu basa zama, abu kadan zesiya zasu kare, ko mamanshi dayake daukar dawainiyarta yanzu yafara kasawa, tun tana fada hartafara gajiya, domin ba kullum yake kawo mata abinci ba, shima gidanshi wata rana so 2 suke ci, dan ma matarshi tana yar sana,a. Sosai arzikin Alh, Abbah yake karuwa, tunda yafara aiki da Abbas yake ganin budi, dan Abbas yakawo mashi cigaba aharkar canjinshi, hatta abokan kasuwancinsa sunajin dadin harka da Abbas, inhar Alh, Abbah bayanan basa ganin kowa se Abbas, hakan bakaramin batama su Auwal rai yakeyi ba. Wata rana Abbas yakarbo ma wani baturen mutum abokin Alh, canjin Kudi daga bank, dala ya canza mashi, kudin zasukai million 10, bayan sunyi waya da mutumin yace yakai mashi office dinsu anjima zezo ya karba. Abbas yafadama Alh, Abbah yanda sukayi da baturen, suka kirga kudin, se Alh, yace shikenan ka aje mashi, nizanje gida akwai inda zanje amma anjima zandawo. Cikin office din yashiga ya aje mashi kudin ta yanda babu wanda zesan anyi ajiya. Ashe duk maganar dasukeyi Auwal yanajinsu. Lokacin da aka kira sallah, kamar yanda Abbas yamaida tsarin office din inde ankira sallah babu abinda za,a kara jira za,a kulle office atafi sallah, kuma hakan yana daya daga cikin cigaban dasuka samu akan kasuwancinsu. Haka yau ma Abbas yafito yace masu akulle office atafi sallah, dama akwai wani yaro shine yake kulle office din kullum kuma ya bude, tare da Auwal da Abbas suka jera suka nufi masallaci, bayan kowa yafita yaron ya kulle kofa shima yanufi masallaci. Bayan sundawo ne, wannan baturen yazo karbar kudinshi, haka Abbas yadauko jakar inda ya ajeta, kara fitar da kudin yayi zekirga, baturen yace a,a inde yasan sun cika yabashi kawai, Abbas yace a,a ka,idar kudi anaso arika kirgasu, Baturen yace shifa sauri yakeyi yabashi ai yasaba harka da Alh, kuma betaba samun failure dashi ba, haka Abbas yadauki jakar kudin yabashi. Auwal ne, yashigo yace kaga nagaban goshin megida. Dariya Abbas yayi yace, Auwal baka rabo da tsokana, ai kowa yasan kafi kowa kusanci da Alh, Auwal yace ada kenan, amma yanzu kaine babba, mukam munzama yan kallo, murmushi kawai Abbas yayi yacigaba da aikinshi. Da yamma bayan Alh, Abbah yadawo office, yana zama sega wannan baturen yashigo, bayan sungaisa yacema Alh, yayi mamakin ganin kudinshi basu cika ba,Alh, yace kamarya baku kirga bane kome? Yace ai yasaba dashi hakan yasa betsaya ankirga ba, Anan Alh, yace nawa ne, babu? Yace mashi 2 million. Mamaki ne yakama Alh, tunda yafara aiki da Abbas ba,a taba samun haka ba, anan yakirashi yafada mashi abinda yake faruwa, wata irin zufa ce, tafara ketoma Abbas, Innalillahi Wainna ilaihirraji,un kawai yake fada. Hankalinshi yagama tashi, dan tundazu dama yakejin faduwar gaba, Alh, yace Abbas kayi magana mana, naga duk hankalinka yatashi, ka kwantar da hankalinka, ninasan akwai abinda yafaru, kamun bayanin yanda abun yafaru tunbayan ka aje kudin. Ajiyar zuciya Abbas yayi, harseda kwalla tazubo mashi, anan yafada masu yanda akayi, sallah kadai sukaje. Alh, yace akira mashi yaran office din gaba daya, danshi ba,a taba samun irin wannan a office dinshi ba. Yade san yasha aje kudi a office idan yazo dauka seyaga sunrage, dayake becika kirga kudi ba, hakan yasa baya sanin konawa ne, amma kuma tunbayan zuwan Abbas bekara ganin hakan ba, amma ace wani customer yazo karbar kudi yadawo yace basu cikaba, shine abinda ba,a tabayi a office dinshi ba. Shiyasa abin yadaga mashi hankali. Bayan kowa yazo, anan Alh, yafara bayanin abinda yafaru, sosai kowa hankalinshi yatashi, anan guri yacika da surutu,kowa da abinda yake fada, shikam Abbas yana gefe guda, inbanda kuka babu abinda yakeyi. Baturen yace, Oga inaganin wannan yaron daya bani canji shine yacire wani abu aciki, bantaba harka dashi ba, se yau, kuma gashi ayau nasamu failure, kawai kabarni dashi zan kiramashi police, idan yaje can zeyi bayanin inda kudina suke. Auwal yayi saurin fadin hakane yallabai, mude tunda muke aiki ba,a taba samun matsala ba, amma gashi ayau antaramu ana tambayarmu kudi. Saddik yace gaskiya megida kabari kawai afitar da bara gurbi acikinmu, hakan zesa asamu zaman lafiya, nidama tuntuni banyarda dashi ba, tun lokacin daya kawo dokar dole se antafi sallah atare. Idan aka tafi kuma seya riga kowa dawowa, tun daga nan nafara zargin shi, kuma gashi ayau gaskiya tafito. Wani daga cikin yaran yace amma kuma koda muke tafiya tare yake riganmu dawowa, ai bashine yake kulle office din ba, kuma bashine yake kullewa ba. Idan har akace shine yadauki kudin ba,a mashi adalci ba. Wani yace kaga malam dalla kamana shiru, ni aganina ba,a cikin office din nan aka dauki kudin nan ba, domin babu wanda yabishi bank, shikadai yaje, dan haka babu wanda yasan lokacin daya dauki kudin. Haka kowa yarika kawo uzurinshi, Tebur Alh, yabuga yace ya isa hakan bankiraku nan danku yanke hukunci ba, nakiraku ne saboda acikin office dinnan aka dauki kudin nan, dan lokacin daya karbosu nidashi muka kirga kuma dede muka kirga, dan haka zanyi maku tambayar karshe, idan har babu wanda yadauka nizan biya kudin, amma kusani duk ranar da aka gane wanda yadauki kudin nan wlh, nikadai nasan abinda zanyi mashi. Kunyi shiru, babu wanda yadauka? Auwal ya hadiyi muyau da kyar, zufa tana zubo mashi yace megida to sede atambayi dan Bala, domin shine me kulle office din nan, kuma kowa yasan shine muka bari akarshe, kuma tare suka dawo da Abbas. Kallon dan Bala Alh, yayi yace tsakaninka da Allah bakasan inda kudin nan suke ba? Kai yashiga girgizawa hawaye suna zubo mashi, yama kasa magana. Baturen yace Oga kana batamun lokaci, zantafi dasu duka 2, idan ansamu wanda yadauka seya biya. Alh, yace a,a nizan biya kudin kayi hakuri, idan katafi nizan gano wanda yadauka da kaina, wata durowa yabude yakirgo 2 million yabashi, anan yafita. Alh, yace kowa yatafi gurin aikinshi. Kallon Abbas yayi wanda yaketa kuka yace kayi hakuri Abbas, ninasan bakai kadauki kudin nan ba, kasan arayuwa idan akaga mutum yana samun cigaba, yafi samun makiya, kada kadamu, nizance naji dadin daukar kudin nan da akayi, domin insha Allah zamu gano makiyanmu. Bazanyi kasa aguiwa ban zanyi kokarin nemo wanda yadauki kudin nan, kodan inrabu dashi. Abbas yace shikenan nagode Alh, nima insha Allah ayau zan dage da addu,a harse Allah yatona asirin wadanda suka dauki kudin nan. Haka kowa yarika kallon Abbas amatsayin wanda yadauki kudi, gaba daya yakasa samun sukuni haka yacema Alh, zeje gida, shikanshi Alh, yatausaya ma Abbas, hakan yasa ya kyaleshi yatafi. Koda yaje gida daki kawai yawuce ya kwanta, domin kanshi ciwo yake mashi sosai, ganin hakan Labiba ta tashi tabi bayanshi, tana zuwa tazauna kusa dashi tare da dafa kanshi tace Abbas lafiya naga kadawo gida da wuri?. Wahaye ne, suka sake zubo mashi, cike da tashin hankali takamoshi tace Abbas kowani ne yarasu? Shiru yayi bece mata komai ba, tashi tayi takira Umma, atare suka shigo, anan suka cigaba da tambayarshi. Da kyar yatashi yafada masu abinda yafaru, sosai hankalinsu yatashi, Umma tace ammade ai ba,a koreka daga aikin ba ko? Kai yadaga mata, jinjina kai tayi tace dama nafada maka, yanda Allah ya daukaka ka alokaci guda dole kasamu makiya, nagode Allah dayasa shi Alhjin yake da hankali har ya iya yanke wannan hukuncin. Kayi hakuri Allah yana tare da kai, insha Allah babu wanda ya isa yayi maka wani abu, kuma dole karika zuwa gurin aikinka, addu,a kadai ta isheka kariya duniya da lahira, kuma insha Allah za,ayi walkiya Allah zetona asirin wanda yadauki kudin nan. Da haka suka lallashi Abbas har yasamu ranshi yayi dadi. Cikin dare Abbas, Labiba da Umma suka tashi sukayi nafila suna rokon Allah yatona asirin wanda yadauki kudin nan, se asuba sukayi sallah suka kwanta. Washe gari haka Abbas yatashi ranshi yayi tas, babu abinda yake damunshi haka yayi masu sallama yatafi office, koda yaje office besamu Auwal ba, Alh, ma bezo ba, daya tambayi dan Bala yace bezo ba, kuma da kyar idan zezo, haka yacigaba da aikinshi har Alh, yazo. Bayan sun gaisa yace ina Auwal fa? Yace shima yazo besame shiba, ya tambaya ance bezo, murmushi Alh, yayi bece komai, ba, yazauna yafara duba wasu takardu, yace Abbas akwai abinda nake zargi amma insha Allah komai zezo karshe. Godiya Abbas yayi mashi yace Allah yasa adace nikaina inaso Allah yatona asirin wanda yadauki kudin nan, kodan insamu nutsuwa araina. Alh, yace karka damu akwai Allah. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:10 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 40 🔱 45 Mukullin mota Alh, Abbah yadauka ya kalli Abbas yace muje karakani wani guri, fita sukayi anan ya tambayi wani ina Saddik, yace ai shima bezo ba. Murmushi yayi yace shikenan bara muje bank mudawo,suna fita Abbas yace wai Alh, ina zamuje? Murmushi yayi yace Fage zaka rakani. Shiru Abbas yayi suka tafi. Adede majalissar su Auwal suka tsaya, fitowa sukayi, wani abokin Auwal da yasan Alh, Abbah shine yayi saurin tasowa yana gaishe shi. Bayan sungama gaisawa yace yau banga abokinka ba agurin aiki shine yasa nazo inji ko lafiya? Mamaki abokin yayi, dan sunyi sallama da Auwal yace mashi yatafi gurin aiki, kallonsu yayi yace aikuwa tundazu mukayi sallama dashi yace yatafi aiki, har nake cemasa yau kafita dawuri, shine yace wai aiki garesu sosai. Mamaki Abbas yayi, shikam Alh, dama yasan za,ayi haka, kallon abokin yayi yace nagode,dama munzo muji ko lafiya tunda mutum yana zuwa kullum kuma mukaji shiru ai dole mubiyo. Wani ne yazo wuce wa shima abokin Auwal ne, bayan sun gaisa dayan yace mashi megidan Auwal ne, yaga shiru bezoba shine yabiyo yaji ko lfiya. Yace aikuwa tare muka shiga adedeta dashi dazu, harmuka dauki wani abokinshi awancan layin shima inajin gurin aikinsu daya. Amma dama ni Fam Center zanje kuma suma can naga sunnufa. Alh, yace shikenan nagode bara mutafi, haka suka nufi mota Alh, shikadai se murmushi yakeyi. Abbas ya kalli Alh, Abbah ganin yadauki hanyar Fam Center yace mezamuyi acan kuma? Yace kaide kayi addu,ar musamesu acan, domin zuciyata tana kara sakamun wani abu. Shiru yayi sukaci gaba da tafiya. Suna isa kai tsaye suka shiga wani babban layi inda ake saida manyan wayoyi suka nufa, cikin sa,a sunzo wuce wani shago Alh, yaga Auwal yana kirga wasu makudan kudi daga aljihunshi. Tsayawa yayi tare da kamo hannun Abbas yayi mashi nuni da Auwal, sosai yayi mamakin ganin yanda yake zaro kudi daga aljihunshi, can daga gefe sukaga Saddik shima yana zaro nashi. Cikin sauri Alh, yanufi gurin Auwal, dama ya aje wayar daya siya akan table yana kirga kudi, hannu Alh, yasa ya dauki wayar yana fadin kai abokina kaga wata hadaddiyar waya kuma daga ganinta zatayi tsada. Saurin dagowa Auwal yayi jin muryar megidanshi, ai besan lokacin daya saki kudin hannunshi ba, dukawa Abbas yayi yakwasho mashi yana fadin hankali kana zubar da kudinka. Saddik kam yadauko wayarshi yataho gurin Auwal yana fadin abokina nifa nariga natsaya anan, kalla kagani idan tayi inbashi kudin dubu 250 yace ze saidata, nide ina........... Ai be karasa maganar ba ganin megidansu akusa da Auwal. Gaba dayansu zare ido suka farayi, dan Auwal jiyake kamar yasaki fitsari agurin, sosai suka tsorata, basuyi tsammanin ganinsu anan ba, shiyasa ma Auwal yace suzo wannan kasuwar dan yasan babu abinda zesa suhadu da Alh, dan baya shiga irin wannan kasuwar. Murmushi Alh, Abbah yayi yace Saddik ashe kaima kana nan, ni hankali na, duk yatashi yarana basuje aiki ba, ashe kuna nan kuna shagalinku, to muma munzo ayi damu. Shiru sukayi, dan gaba dayansu zufa ta wanke masu fuska, maganar meshago ce tadawo da hankalinsu, yace dan Allah kabani kudina sekucigaba da maganarku kabarni inajira. Alh, yace kabashi kudinshi tafiya zamuyi dama wani abu mukazo dubawa kuma munsamu zamu wuce muka ganku shine mukazo, idan kungama kuzo muwuce office ko?. Hawaye ne, suka fara zuboma Auwal, cike da nadama yakalli Alh, yace dan Allah kayi hakuri karufa mana asiri wlh zanyi maka bayanin amma kada katona mana asiri acikin jama,a. Alh, yace dan Allah kayi shiru, niban tambayeka komai ba, kabashi kudinshi mutafi, kallon meshagon Auwal yayi yace dan Allah kayi hakuri mun bata maka lokaci, munfasa sayan wayar kayi hakuri dan Allah. Meshago yace bakomai, tunda bakutafi ba, shima Saddik jin haka yasa yajuya yamaida ma meshagon wayar shi. Murmushi Alh, yayi yaja hannun Abbas suka nufi mota, yace kuzo mutafi. Kamar munafukai suka bi bayansu kowa sedafe aljihu yakeyi, haka suka zauna acikin mota kamar kurame, wani guri daban sukaga Alh, yanufa ba hanyar office ba. Kuka Auwal yasa yana fadin dan girman Allah megida kayi hakuri kada ka kaimu police station, wlh zanyi maka bayani, kuma kudinka ko kwandala basuyi ciwo ba, yanzu haka muje gida indauko maka sauran, dama dede na wayar muka dauko nida Saddik, dan Allah kayi hakuri. Murmushi Alh, yayi yajuya kan motar suka nufi Fage, suna zuwa Auwal yafita segashi yafito da wata leda, yana zuwa suka tafi, sede duk da haka Alh, be nufi office ba, can wani guri suka nufa wani filinshi acan yayi parking, yajuyo yana kallonsu, yace Auwal inajinka banason boye boye kafadamun komai. Ajiyar zuciya Auwal yayi yace wlh lokacin da Abbas yashigo Office dinka da kudin,duk maganar da kukayi naji hakan yasa na labe har seda naga inda Abbas ya ajiye kudin. Alokacin da yafita yace akulle kofa ankira sallah, alokacin nayi saurin dibar kudin, kuma cikin sa,a har na dauki million 2, anan nayi saurin fita mukatafi masallaci tare da Abbas, kuma sanda muka idar da sallah narike Saddik mune karshen dawowa office din. Dama agaskiya nida Saddik mun dade muna so muga mun kullama Abbas sharrin dazesa akoreshi daga aiki, amma bama samun nasara akanshi, ninasan mundade muna maka sata a office, kuma baka taba magana ba. Dan Allah kuyi hakuri, ni nayarda ka koremu a aiki amma dan Allah kada ka kaimu gurin yan sanda, wlh nasan Babana tsinemun zeyi, tun ranar dana samu aikin nan kullum idan zanfita seyace kada inbari inyi wani abu dazan jawo mashi magana, idan har hakan tafaru, wlh bazan yafe maka ba. Dan Allah kada kabari mahaifina yaji wannan maganar, nasan inde aka kulleni dole yasamu labari. Saddik yace dan Allah megida kayi hakuri, tabbas munyi kuskure amma wlh, wlh, wlh, kaji nayi maka rantsuwa 3, daga yau mundena aikata duk wani abu marar kyau, amma karufa mana asiri bazamu kara ba. Abbas kuwa kuka kawai yakeyi,Alh, yace shikenan yanzu hadamun kudin kabani, kuma inaso kusani nibazan koreku ba, zamu cigaba da aiki tare, kuma insha Allah kamar yanda mukayi maganar nan mu 4 babu wanda zejita se idan kune kuka fada. Kuma banaso afadama kowa angano kudin, nida kaina zanyima sauran bayani, nide tagurina nayafe maku, amma inaso kuji tsoron Allah, bawai zanbarku kucigaba da zama dani bane sbd ina tsoronku, nayi hakane kawai dan in nuna maku ba,a kyamar mutum dan yayi wani abu marar kyau. Nasan idan nakoreku zaku iya shiga wani hali, kaga anyi ba,a yiba amma idan har halinku ne, wata rana zaku kara sede alokacin wlh ba mutanan office kadai zasu jiba, kotu zan kaiku yanda kowa zesan halinku. Yanzu seku nemi yafiyar Abbas, dan kun cutar dashi. Kallon Abbas sukayi sukace yayi hakuri. Abbas yace bakomai shi yayafe masu, haka suka nufi office cike da kunya. Suna zuwa Alh, yatara duka yaranshi anan yace masu dazu abokinshi baturen nan yasameshi da wadannan kudin yamaido mashi yana bashi hakuri ashe acikin motarshi kudin suka zube, shine yamai domin wanda nabashi kuma yace abaku hakuri da Abbas yaja maku bacin rai. Hamdala kowa yafari, anan wadan da sukace abinciki Abbas suka fara bashi hakuri, shikam mamakin irin halin kirki na Alh, yakeyi, sukansu su Auwal sunyi mamakin abinda yace. Anan kowa ya yafi kowa aka koma aiki, sede haryanzu su Auwal sunkasa sakewa, ganin haka yasa Alh, yace idan baku sake ba, Zakusa kowa yafara zarginku, haka suka saki jikinsu, sede tsakaninsu da Alh, da Abbas sun koma tamkar surukai, Auwal kuwa yaran shagon sunfara mamakin canjin dasu kagani daga gareshi sam yadena masu fadan dayake masu, yakoma tamkar bashi ba. Bayan Abbas yadawo gida yafada ma su Ummanshi abinda yafaru, sosai sukaji dadin abun, Umma tace ai Allah baya bacci inde kadage kamaida al,amuranka gareshi tabbas zekareka. Allah yakara karemu daga sharrin mahassada. Haka Abbas yacigaba da aiki agurin Alh, hankali kwance,yakara samun daukaka akan mutane, yaran office dinsu sosai suke bashi girmanshi dan yakawo cigaba sosai a kasuwar. Haka suka cigaba da renon cikin Labiba kuma arzikinshi sosai yake karuwa dan albashi metsoka Al, yake bashi, hakan yasa asusun dayakeyi yakaru, itama Labiba tana asusu, sam yanzu tayi hakuri darashin cin dadi, sede cikin datake dashi yasa akullum Abbas seya siyo mata nama da kayan marmari. Alokacin da cikinta yacika wata 9 duk wata siyayya Abbas yayi mata, hatta da ragon suna yasiya ya turkeshi, duk wani abu daza,a nema yasiya, dan ayanzu yahana Ummanshi yin abincin saidawa sede duk wani abu da ake amfani dashi ya saro masu, ita da Labiba. Umma da kanta taraba masu kowa da abinda zerika saidawa, idan akazo siyan wani abu idan Umma kesaidashi ita zata basu, idan kuma Labiba ce gurinta za,aje. Sosai sukejin dadin zamansu, dama shi Umar kasuwar kwari yake tafiya. Saboda yawan Customers da Abbas yake dasu hakan yasa Alh, yace yanaso shima yabude mashi nashi office din, Abbas yace a,a Alh, kabarni incigaba da aiki akasanka, hakan ma ya isheni inajin dadin zama da kai. Alh, yace ai ba rabuwa zamuyi ba, inaso nida kai mukara daukaka kasuwancinmu, karka damu wlh na daukeka tamkar jinina, kana da amana, karka damu akwai wani zabe ma daza,ayi mutane dayawa suna son infito amma ni kuma nafison intsaidaka, danni bana son mulki ko kadan, Kuma gaka bana zama sosai. Abbas yace amma Alh, ina tsoron mutanan gurin nan kalli fa yanda suke nuna maka kiyayya afili, nide ina tsoro wlh. Murmushi yayi yace kada kadamu, banayin abu da ka, aduk lokacin dazanyi wani abu, sena fara neman yarda daga gurin Allah, dan haka nabaka nan da sati 1, kaje kafara tsayuwar dare, nima zan tayaka, danni bazance banasa amun rokon Allah ba. Ina sawa amma gaskiya nafiyi da kaina domin nine me neman bukatar, dan haka mudage muyi wannan istaharan idan har akwai alkhairi aciki insha Allah zamu gani, amma banaso kafadama kowa, senan da sati 1. Godiya Abbas yayi mashi sannan suka tafi. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO ( Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 45 🔱 50 Bayan sati daya dayin maganarsu shida Alh, Abbah suna zaune a office wasu manyan mutane suka shigo office din, abokanan kasuwancin Alh, ne kuma suna daya daga cikin wadan da suka fito zaben daza,ayi. Bayan sun gaisa daya daga cikinsu yakalli Abbas yace bawan Allah idan bazaka damu ba kabamu guri zamuyi magana da megidanka. Har yatashi Alh, yace karku damu PA nane, zaku iya maganarku. Abbas yace a,a Alh, bara inje dama akwai abinda zamuyi nidasu Auwal, Murmushi Alh, yayi yace shikenan. Bayan yafita yajuyo gurinsu yana fadin inajinku. Gyara zama,sukayi daya daga cikinsu yafara magana. Dama bawani abu bane yakawo,mu gurinka, munsan de kasan nida Alh Bashir munfito cikin wadanda zasuyi takara, wato ta chairman din Wapa. Kuma inaso Alh, Bashir yasamu shiyasa na barmashi sauran jama,ata kaga zesamu kuri,a. To munsamu labarin kaima ba kaine zaka anshi mukamin ba, sede haryanzu bamu san wanda kake tayawa ba. Shine mukazo muroke ka kabarma Alh, Bashir mutanenka ko nawa ne zamu baka. Murmushi Alh, Abbah yayi yace tonaji bayaninku, sede inaso kusani niba saboda kudi nace zanyi wannan zaben ba. Kuma shima ba saboda kudi zerike mukamin ba, kawai nazabeshi ne saboda can cantarshi. Dan haka ina ganin babu kudin dazasu saka inbama wani kuri,ar mutane na. Inafatan kun fahimci abinda nake nufi? Shiru sukayi gaba daya ransu yagama baci, babu kamar Alh, Bashir dama shi beyi niyar zuwa ba, hakanan yabi shawarar abokinsa sukazo, tashi yayi yana huci yakalli abokinshi yace katashi mutafi, dama ai nafada maka Alh, Abbah baya cikin irin mutanan dazaka nemi alfarma agurinsu. Fita yayi abokin yabishi abaya. Murmushi Alh, Abbah yayi, dan ya riga yasan wanene Alh, Bashir, waya yadaga yakira Abbas, yana zuwa yafada mashi yanda sukayi, gaba daya jikin Abbas yagama sanyi. Kallon Alh, yayi yace wlh dama nafada maka ni bana son wannan mukamin, kawai kabar masu, banason ina zamana nida iyalai na wani abu yazo yasame mu, wlh Alh, bakasan irin wahalar dana sha arayuwata tabaya ba, shiyasa yanzu dana samu wannan aikin nake jin dadi sosai, kuma ina alfahari dashi. Banaso sanadiyar wannan zaben nazo narasa aikina gaba daya, ko kuma wani abu yasameni. Murmushi Alh, yayi yace karka damu Abbas, insha Allahu babu abinda ze faru, kada kamanta kafin mufara wannan zaben seda muka nemi yardar Allah sannan. Banaso kasaka tsoro acikin ranka, idan har mutum yana neman wani abu, kuma yamika al,amuranshi agurin Allah, to abinda yafi kawai kayarda cewa babu wanda ya isa yayi maka wani abu se Allah. Idan kuma har kaga bamu sami wannan mukami ba, to kadauka daga Allah ne, kada kayi zargin wani dan adam ze iya baka ko ya hanaka. Ka tsaida zuciyarka aguri daya Allah yana tare damu. Ajiyar zuciya Abbas yayi yace shikenan nagode Allah yashige mana gaba. Wayarshi ce tayi kara, yana dagawa yaga Ummanshi ce, saurin dauka yayi, bayan sun gaisa take fada mashi yazo asibiti ankawo Labiba zata haihu. Yana ajiyewa Alh, yace yade Abbas naga kamar akwai matsala ko? Kai yadaga mashi yana fadin wlh Labiba ce akace ankaita asibiti zata haihu. Saurin tashi Alh, yayi yace to ai semuyi sauri muje kada anemi wani abu. Sallama sukayi ma su Auwal suka tafi, koda sukaje harta haihu, anma kaisu dakin hutu, suna zuwa suka sameta ita da danta cikin koshin lafiya. Sosai Abbas yayi murna ganin Labibanshi ta haifa mashi yaro me kyau, yana kama dashi sosai, atare suka shiga da Alh, shima yatayashi murna, Abbas yadauki yaron yayi mashi huduba sannan yamikama Alh. Addu,a shima yayi mashi yacema Abbas suje gurin likita subiya kudaden da aka biyosu. Bayan sungama da likita yace ai zasu iya tafiya tunda dukansu suna lafiya. Haka suka hada kayansu suka nufi gida amotar Alh, amota Umma se godiya takema Alh, Abbah akan irin abinda yakema Abbas, addu,a kam yashata, sosai yaji dadi, har seda kwalla tazubo mashi, daya tuna mahaifiyarshi wadda ta dade da rasuwa. Har kofar gida yakaisu, sosai ya tausaya ma Abbas, ganin irin gidan dasuke zama, kamar daga sama yaji Umma tace Alh, kashigo mana, haka yabi bayan Abbas suka shiga. Bayan sun shiga gidan zuciyarshi takara tsinkewa da tausayin su, afalon Umma suka zauna, ita kuma Labiba Umma tace suje dakinta, ganin sun nufi dakinta yasa Alh, yagane nan dakin Umma ne. Yadan jima Umma takawo masu abinci, bayan sungama yace ma Abbas ze koma. Dubu hamsin ya ajemasu, sosai sukayi godiya yace seya dawo anjima da iyalanshi suma suzo ganin jariri. Har mota Abbas yarakashi, yana fadin anjima zezo. Alh, yace a,a yabari se gobe. Da yamma haka Alh, Abbah yazo da iyalinshi motarshi cike da kayan abinci sosai su Umma sukaji dadin zuwanshi, itama matarshi dubu 20 tabama Labiba, haka sukayi tamasu godiya, suka tafi. Ranar suna Abbas yasama yaron sunan Alh, Abbah na gaskiya wato Hassan, ana kiranshi da Ansar, sosai Alh, Abbah yaji dadin karar da Abbas yayi mashi, haka yasiyama yaron kaya masu kyau, shida mamanshi, hatta Umma seda yasiya mata kaya, Abbas kuwa kudi yabashi dubu 100. Yan gurin aikinsu ma kudi suka hada dazasu zo ganin jariri suka kawo, Abbas yaji dadin abinda sukayi mashi. Haka ya hada masu kayan suna yabasu. Ba laifi sunan yayi taro, yan uwan Labiba ma sunzo. Maman zainab itama da yamma sosai tazo sunan, domin Labiba tafada mata. Labiba sosai taji dadin zuwanta haka suka shiga daki. Bayan sungama gaisawa Maman zainab take cemata ai suma suntashi. Labiba tace Allah Sarki inasu Asabe da Laraba? Maman zainab tace wlh tun bayan tafiyarki suka koma abin tausayi, sosai muke shiri dasu, baki gani ba sunkoma makarantar islamiyya duk wannan halin banzar sun dena, sede matsala daya su duka suke fuskanta. Daga gurin maza jensu, kinsan dama yan kasuwa ne, ranar kawai sega mijin Laraba yadawo gida abuge, haka yakamata yayi mata shegen duka, da kyar aka kwaceta. Da safe tazo tana fadamun ita gidansu zata tafi haka nayita bata hakuri, nace idan ta tafi ya, yanta kuma batasan wadda zatazo tarike mata suba. Da kyar nasamu ta hakura, bayan kwana biyu kuma aka kama mijin Asabe yashiga dakin wata mata abayan layinmu, ashe dama sun dade suna aikata masha,arsu, aranar Allah yatonu asirinsu. Seda aka kulleshi da kyar aka bada belinshi, itama tace zata tafi haka mukai ta bata hakuri. Alokacin Baban Zainab ya hada kudin gidanshi, haka nayi masu sallama se kuka sukeyi, ni kaina seda nayi kuka, haka muka rabu. Yanzu kam Alhamdulillah babu laifi arzikin mijina yafara dawowa, shiyasa duk wata hanya danasan zata kawo mashi cigaba nake nema mashi, domin nice sanadiyar shigarmu halin da muke ciki. Yanzu haka nadage da sana,a kudi komin kadan dinsu, bana kashewa ina ajiye wasu a asusu. Wlh, Labiba nakoyi darasi sosai arayuwata, duk yanda kaga mijinka yana da abu kada ka rainashi, kayi kokarin tayashi son abun, se Allah ya buda maku nan gaba. Da banyi rashin hakuri ba, da yanzu arzikin mijina yafi na yanzu. Amma gashi nan yanzu munkoma baya, ina addu,ar Allah ya kara karemu daga zaman Haya. Labiba ta goge kwallan dasuka zubo mata tace amin. Maman Zainab tace Labiba kince duk ranar damuka hadu zaki bani labarinki. Murmushi Labiba tayi tace, kiyi hkr, kinga yanzu akwai mutane, kuma dare yafarayi, nasan Abbas yakusa shigowa. Inaso infara tambayar Abbas idan har ya yarda duk ranar da kika kara zuwa zanbaki labarina nida Abbas. Maman Zainab tayi murmushi tace bakomai, amma akwai gyaran danakeso inmaki, haba Labiba kamar ba auren soyayya kukayi keda mijinki ba, kuma gashi de ku yan zamani ne, bare ace mutanan da ne. Ai yakamata ki canza ma mijinki suna, tunda kukayi aure yakamata ace kindena kiranshi da Abbas. Idan kuma kun haihu se ki kara canza mashi suna kamar yanda kikaji ina fada ma Baban Zainab. Kinga dayawa mutane yanzu zakiga ya,yansu suna kiran iyayensu da sunansu, kuma hakan yana samo asali tundaga gurin iyayen. Yanzu tunda kun haihu yakamata kirika kiran Abbas da Abban Ansar, kinga idan ya girma shima da Abba zerika kiranshi, kema kifada mashi yakiraki da Momyn Ansar ko kuma wani suna. Hakan zesa yaranku surika kiranku dasunan dakuke fada. Labiba tace nagode Maman Zainab inasha Allah zan gyara kuskuren danayi, ada nadauka badole bane seka canza ma mijinka suna ba, wlh kunya nakeji shiyasaya nakasa canza mashi suna. Murmushi Maman Zainab tayi tace lallai Labiba naga akwai abubuwa dayawa daya kamata ace kin sansu amma kuma gashi ina ganin baki sansu ba, ai ita rayuwar aure tasha bam bam da rayuwar gida, duk min son da mijinki yake maki dole sekin bada taki gudummuwar sonki zekara shiga zuciyarshi. Amma bakomai, insha Allah namaki alkawarin duk sanda nasake zuwa zan kawo maki abubuwa dayawa wadan da zakiji dadinsu, kuma zan sawo maki littatafai kamar su Gyara da kanki, Sirrin Mijina, harma da na koyon girki, domin girki shine mace. Kada kiga kin iya miya, tuwo, dafa shinkafa da iya saka magi amiya kice kin iya girki, akwai sauran girke girke daya kamata ace kinkoya, kada kice wai bakuda hali, yanzu kam mijinki nasan shima duniya tafara canza mashi. Bakisan meze zama nan gaba ba, ke koma bakuyi kudi ba, zaki iya sarrafa maku abinci masu rai da lafiya, mata dayawa suna kuskure suna ganin dole semasu kudi ne, zasu iya yima mazajensu kalar abinci me dadi. Ko Fulawa kadai kike da ita zaki iya sarrafata, yanzu in tambayeki, dame dame kika iya na Fulawa? Sosa kai Labiba tayi tace ito na iya cincin, wainar fulawa se dan waken fulawa. Dariya Maman zainab tayi tace lallai kam, kinada aiki. Kin ganni nan, bawai seda nayi aure na iya abinci ba, tun kafin nayi aure nake zuwa gidan wata makwabciyar mu, dayake mijinta yanada hali, hakan yasa nake zuwa, inde naga zata shiga kitchen ina rokonta tabarni inbita. Da farko taji tsoro, amma dataga inason koyon girki ne, hakan yasa tajani ajiki tarika koyamun girki da yanda zan gyara jikina, alokacin da zanyi aure, bakiga irin littattafan data bani ba, duk da nasan ba me kudi zan aura ba, hakan besa na zubar dasu ba. Amma kibari yanzu magriba tayi, duk ranar danazo zakisha mamaki na, amma matsala daya ce, bazan dawo nan kusa ba, saboda Baban Zainab yace wannan karon idan yaje Lagos ze dade sosai, megidanshi yace zasuyi yawo shine yace yataho da iyalanshi akwai boys Quarters dinshi semu zauna. To gaskiya bansan yaushe zamu dawo ba, amma ai akwai waya, kome kenan zakiji. Sosai Labiba tayima Maman Zainab murna, kuma taji dadin shawarar data bata, haka tahada mata kayan suna sukayi sallama, har kuka seda sukayi. Bayan suna da sati daya aka tsaida ranar zaben su Abbas, sosai hankalinshi yatashi, musamman daya tuna kashedin dasu Alh, Bashir sukayi mashi, dan tuni sungano cewar shine Alh, Abbah yake nemama kujerar, hakan yasa sukayi mashi kashedi, sede Alh, Abbah yace kada yadamu. An tsaida zabe ranar asabar, duk wanda yaga Abbas yasan baya cikin natsuwarshi, abinci ma baya iya ci sosai, duk yarame. Bawai mulkin yake tsoro ba, barazanar dasu Alh, Bashir suke mashi ce take damunshi. Ana gobe zabe Abbas yadawo daga office, dan yau batare da Alh, suka taho ba, yana cikin adedeta kawai yaga me adedetan yawuce hanyar unguwarsu. Kallonshi yayi yace malam bakaji menace maka ba? Darmanawa nace amma naga kawuce, waigowar da me adedeta zeyi kawai ya hura mashi wani abu afuska, nan take Abbas yafara ganin dishi dishi, anan ya kwanta asume cikin adedeta, dariya me adedata yayi yakira waya yana fadin Alh, nagama aikina, gashi nan zankawoshi inda kace. Shiru yayi sekuma yace e akwai mukulli agurina. Kashe wayar yayi yana dariya. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 50 🔱 55 Cike da mamaki Alh, Abbah yabi adedetar da Abbas yake ciki da kallo, saboda alokacin da Abbas ya hau adedeta shi kuma Alh, yafito yana bayanshi, har suka hau kan titi yana binsu abaya. Lokacin da akazo kwanar daza,a shiga da Abbas ta Gandun Sarki, shi kuma Alh, ze wuce gidanshi dayake can gaba dasu, ganin adedetar bata shiga kwanar ba, ta wuce shine abun yabashi mamaki, gashi de yaga yamma tayi. Aranshi yake fadin Abbas ko wani guri zeje? Haka yabi bayansu har sukazo kwanar dazata sadashi da gidanshi, seyaga sun wuce, har yashiga kwanar tacikin madubi yaga kamar Abbas akwance yake acikin adedetar. Jikinshi ne, be bashi ba, hakan yasa yayi saurin juya kan motarshi yabi bayansu, mamaki ne yakara kamashi ganin yanda me adedetar yake wani irin gudu gashi yasauka daga titi yadauki hanyar wani guri. Ganin abun yaki karewa yasa kawai Alh, yadauki waya yakira police, anan yayi masu kwatancen inda yake, yace zerika fada masu duk inda yayi, kashe wayar yayi yacigaba dabin bayansu. Mamakinshi be karuba seda yaga sunshiga wani gate wanda da kaganshi kasan fili ne, aka zagaye ba,ayi gini ba. Matsawa yayi daga gaban gidan yayi parking. Zuwa yanzu hankalinshi yagama tashi, waya yakira yakarayi masu kwatancen inda yake, yana gamawa yaga wata bakar mota tazo gaban gidan, budewar gate din keda wuya yaga anshiga da motar. Wata zufa ce tafara fitoma Alh, aranshi yake tunanin kode yan yankan kai ne? Shiru yazauna azuciyarshi se addu,a yakeyi akan Allah yakare Abbas daga dukkan sharri. Adede lokacin motar yan sanda ta iso, fita yayi, yasa mesu, anan yayi masu bayanin abinda yagani, ogansu yace karka damu insha Allah zamu kamasu. Anan ya raba yaranshi suka zagaye gidan, shikuma shida wasu mutum 3 suka bi bayanshi, Alh, cike da fargaba shima yabi bayansu. Kwan kwasa kofar ogan yayi, anan megadin yafito. Yana ganin yan sanda cikinshi ya kada, da sauri yayi niyar komawa ciki, anan wani dan sanda yayi saurin cafkoshi, se zare ido yakeyi. Murmushi ogan yayi yace kana tunanin guduwa ne? Kai yashiga girgizawa. Ogan yace ina megidanka yake? Yace suna ciki, dan Allah kuyi hakuri, tasa keyarshi sukayi yashiga nuna masu hanya. Mamaki sosai sukayi ganin katon filin dayake zagaye. Abbas kuwa bawan Allah suna zuwa Alh, Bashir yasa aka daureshi jikin wata bishiya, ruwan sanyi yasa aka dauko mashi amota, tundaga kan Abbas yafara zuba ruwan me bala,in sanyi. Cike da firgici Abbas ya farfado, gaba daya jikinshi rawa yakeyi, begama wartsakewa ba yaji saukar wani katon icce akanshi, nan take jini ya wanke mashi fuska. Dariya Sukayi, Alh, Bashir yace da kadauka wasa nakeyi maka? Uhm, kai yarone, kuma bako acikin harkar canji, shiyasa bakasan koni waye ba. Ayau zakayi asarar mahaifiyarka matarka da kuma danka. Kana tunanin bansan komai akanka bane? Da farko mahaifiyarka naso indauke da danka harseka yarda kabarmun matsayin danake nema sannan insake su. Amma daga baya senayi tunanin gara indauke ka gaba daya daga duniyar, hakan zesa nadena ganinka gaba daya, dan nasan ko kabarmun wannan matsayin nan gaba Allah ze iya dagaka. Amma idan ka mutu, nasan banida sauran fargaba. Kallon wani kato yayi wanda sukazo tare dashi, yace gama dashi, banason yakara ko minti 5 aduniya. Matsowa yayi hannunshi rike da igiya. Yana zuwa yashake wuyan Abbas da ita, tuni Abbas ya runtse idonshi yafara kalmar shahada, kamar daga sama sukaji karar bindiga, cike da tsoro wannan katon yayi saurin sakin Abbas, wanda har yafara jin kamshin mutuwa. Gaba dayansu tsoro ne ya bayyana azuciyarsu, Alh, Bashir kam da gudu ya nufi hanyar motarshi, wani dan sanda yaruga ya cafkeshi, sauran ma kamasu akayi, Alh, Abbah kam gurin Abbas yanufa hankalinshi atashe. Yana zuwa ya kwanceshi, rungumoshi yayi, dan gaba daya jikinshi rawa yakeyi, ga kanshi dayake sarawa sosai, haka ogan yabasu umarni suka tasa keyarsu zuwa motar yan sanda. Abokin Alh, Bashir se kuka yakeyi yana fadin shikenan Alh, kajamana, seda nace kada kayi wannan abu amma dayake zuciyar kafirci gareka bakaji maganata ba. Tsawa ogan yadaka mashi, yana fadin kamana shiru koma menen idan mukaje office zakuyi bayani. Alh, Abbah kam zaunar da Abbas yayi yafita dauko motarshi. Abakin gate suka hadu, yacema ogan su wuce office zekai Abbas asibiti idan sungama zezo, haka yaje yadauki Abbas suka nufi asibiti, sukuma suka wuce office din yan sanda. Suna zuwa asibiti aka ansheshi, dressing ciwon aka fara yimashi sannan aka jona mashi ruwa, haka Alh, yakasa zaune duk tausayin Abbas yagama kamashi, aranshi yake fadin shikenan da bezoba sede suji akanshe Abbas. Agida kam hankalin Labiba da Umma duk yatashi, ganin har magriba Abbas bedawo ba, haka suka rika kiran wayarshi amma akashe, Umma tace muyi hakuri agama sallah kila tsayawa masallaci yayi. Labiba kam tade amsa mata kawai, amma jikinta yana bata akwai abinda yasamu Abbas dinta. Su Alh, Bashir kuwa ana zuwa aka anshe komai nasu aka sakasu a cell aka kulle, Alh, Bashir se magiya yakema Ogansu akan yabari su sasanta ko nawa ne. Yayi alkawarin zebashi. Amma dayake ogan abokin Alh, Abbah ne, sam yaki amincewa da bukatarsu, haka suka zauna kowa da abinda yake damunsu. Se bayan isha,i Abbas yadawo dede, alokacin leda 2 ta ruwa takare ajikinshi, yana tashi, Alh, yace sannu Abbas. Kai yadaga, yana kara kallon dakin, ahankali yace Alh, naji sauki mutafi gida, nasan hankalinsu atashe yake ganin bandawoba. Alh, yace hakane, nima nayi tunanin haka, gashi banida numbernsu, naduba aljihunka kuma banga wayarka ba, kuma banaso intafi inbarka, shiyasa banje nafada masu ba. Amma bari inje gurin likita yazo yaga jikinka semutafi. Bayan likita yagama dubashi ya rubuta masu magunguna yace zasu iya tafiya, bayan kwana 2 sudawo acire daurinda akayi mashi. Godiya Alh, yayi mashi, suka tafi, seda suka biya ta police station sukayi magana da abokinshi. Alh, Abbah yace dan Allah kada kabada belinsu, abarsu, zuwa monday da gobe asabar munada zabe, jibi kuma lahadi babu aiki, inaso akoyama sauran mutane darasi, kotu zamushiga dasu ranar monday, nafiso alkali ya yanke masu hukunci, suje suji ya gidan yari yake. Police din yace badamuwa Alh, koda wani ne, yasani wannan aikin zanyi, bare kuma nakane, gara akaisu kotun hakan zesa mutane dayawa su dauki darasi. Godiya yayi mashi, suka tafi. Tun amota Abbas yakema Alh, magiyar kada yabari abashi wannan mukami dan gaba daya yagama tsorata. Murmushi Alh, yayi yace Abbas kenan, gashide kana da rikon addini, amma har yanzu ka kasa yarda da kaddara. Kamanta dan adam mumuni baya taba samun abinda yakeso cikin sauki batare da Allah ya jarabceshi ba? To kaima hakan ne yafaru da kai, kuma tunda kaga Allah be kashe ka ba, to yanaso kayi wannan mulkin, dan haka banaso ka kara cewa bakaso. Allah shine wanda yake bada mulki ga wanda yaso, kuma inaji ajikina kaine zakayi nasarar samun wannan matsayi, dan haka addu,a itace makaminka, dani gaba daya. Kai Abbas yadaga alamun gamsuwa yace nagode Alh. Da sallama auka shiga gidansu Abbas, acikin rumfa sukaga su Umma sunyi tagumi, dakagansu zakaga tashin hankali kwance afuskarsu, ai Labiba mantawa tayi da kowa haka ta tashi da gudu idonta na zubar da kwalla ta nufi Abbas, tana zuwa ta rungumeshi. Kuka tasaka tana kara shigewa jikinshi, gaba daya shikam kunya tagama rufeshi, ga Umma kuma ga Alh, Abbah. Ahankali yayi saurin zareta daga jikinshi, yakama hannunta suka zauna. Umma kuwa tashi tayi tadauko ma Alh, kujera yazauna, bayan sungama gaisawa cike da damuwa umma takalli Abbas tace bade hadari kayi ba, naga andaure maka kai?. Alh, ne yayi gyaran murya yace, umma ba hadari bane, wani tsautsayi ne, yafaru dashi, sede Allah yakareshi abun yazo da sauki. Anan Alh, yafada masu duk abinda yafaru. Salati Umma tafarayi, tana kuka, Labiba ma Kukan takeyi, Umma tace Oh ni, shikenan dayanzu mummunan labari yazo mana, lallai mutane yanzu basa tsoron Allah, saboda duniya ka kashe mutum?. Nikuwa Alh, idan har hakane, kawai ahakura da wannan zabe, kabar masu, suje su cinye, aide duk mulkin dazasu samu aduniya zasu barshi. Banaso inrasa dana, tunda yataso yake gamuwa da tashin hankali kala kala, narokeka kabarshi yacigaba da aikinshi agurinka ku hakura da wannan mulkin dan Allah. Kuka ne, yaci karfinta tayi shiru, gaba daya jikin Alh, yagama sanyi, Abbas kanshi kuka yakeyi. Alh, yace Umma addu,arki bazata bari wani mugun abu yasamu Abbas ba, bashi kadai ba, harni dana rasa iyayena, nasan addu,arki tana tasiri ajikina. Dan Allah kada ki hana Abbas yakarbi wannan matsayi, wanda bamune zamu bashiba. Allah shine yazabeshi kuma shine zebamu sa,ar cin wannan zabe, kicigaba dayi mana addu,a insha Allah wata rana se rayuwar Abbas tazama tarihi, duk da bansan komai agame da rayuwarshi ba, amma nasan Abbas yasha wahalar rayuwa. Kuma nayi alkawarin temaka mashi da dukkanin karfina da dukiyata, tun lokacin dana fara ganin Abbas naji hankalina ya kwanta dashi, hakan yasa nayi saurin jawoshi jikina. Umma idan har kinyarda dani, kinyarda bazan taba barin wani abu yasamu Abbas ba. Idan har kinyarda nima danki ne, ina neman alfarmar kibar Abbas ya karbi wannan matsayi da za,ayi zabenshi gobe, wanda nakesa ran babu wanda za,a bama Chairman na WAPA se Abbas. Idan har kinyarda da wannan abun dana fada maki, dan Allah ki amince da bukata ta badan na isa ba Umma. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 55 🔱 60 Ajiyar zuciya Umma tasaki, shiru tayi nawani lokaci sannan tadago kai ta kalli Abbas wanda tundazu idonshi yafara zubar kwalla, sakamakon tuno irin wahalar daya sha arayuwarshi ta baya. Kai ta girgiza tace shikenan Alh, na amince, saboda nasan kai me son Abbas ne, bazaka taba barin wani abu yasameshi ba, mungode da irin kaunar daka nuna mana, Allah yajikan mahaifanka. Kuma Allah yabaku sa,ar wannan zabe da za,ayi gobe. Murmushi Alh, Abbah yayi yace amin Umma, nagode kwarai, Allah yasaka da alkhairi, kuma insha Allah bazan bari wani abu yasami Abbas ba. Nadaukeshi tamkar kanina uwa daya uba daya, domin a zamanin nan duk mutumin da zerike maka amana bakaramin sonka yakeyi ba. Wlh Umma ayanzu kodan uwanka baze iya rike maka amanar da Abbas yake rikemun ba, nasha gwada Abbas Umma batare daya saniba, amma bantaba samunshi da ha,inci ba, wanda tunda nafara wannan kasuwancin bantaba haduwa da merikemun amana kamar Abbas ba. Shiyasa nadauki alkawarin shima zannuna mashi gata kamar yanda akema kowa, insha Allah watarana Abbas seyazama abun kwatance agurin mutane, zakiyi alfahari dashi Umma, fatanmu Allah yayi mana jagora aduk abinda zamusa gaba. Umma tace amin, tashi yayi yace Abbas kasamu kayi wanka ga magungunanka nan kasha seka kwanta ka huta, Allah yakara sauki. Abbas yace amin nagode, hannu yasa a aljihu yaciro kudi masu yawa ya ajema Umma. Sallama yayi masu yafita, da addu,a tabishi tana masa godiya. Umma tace sannu Abbas Allah yakara tsarewa, tashi kaje kayi wanka, haka tafita Labiba tahada mashi ruwan wanka yashiga. Maman Jafar ce zaune tabuga tagumi tana kallon tukunya, tunda safe take jiran Jafar yakawo mata abunda zata dafa amma haryanzu shiru, da kyar tasamu aka samo mata koko na 20 tasha, ajiyar zuciya tayi tace kai wannan wace irin rayuwa ce, ace abincin ci ya gagari dan adam. Nida ada har zubar dashi nakeyi amma yanzu insamu nazubarwa ma babu. Sallamar Jafar ce ta katse mata zancen zucin datakeyi, amsawa tayi tabishi da kallo, duk yarame yayi baki, zama yayi daga gefenta yana fadin Mama sannu da hutawa. Bayan sungama gaisawa yace Kinjini shiru ko mama? Tace wlh kuwa Jafar tun safe kokon 20 ne kawai acikina, saukina ma daya banida yara da har bansan yanda zanyi da kaina ba. Jafar yace wlh Mama abubuwanne se ahankali, Allah ma yasoni Ummansu Abdul tana sana,a da bansan inda zansa kaina ba. Tana iya kokarinta, wani kallo tayi mashi tace e dole kace haka tunda kai kasamu matarka tana bama yaranka abinci kaima kuma kanaci dole kamanta da Uwarka. Idan maganar gaskiya ce nima afitarmun da kwano daya arika kawomun mana. Jafar yace wlh mama suma bawani abinci suke ciba, nikaina ba kullum nake karyawa ba, haka ma ba,a gida nakecin abincin rana ba, shiyasa nake kokarin kawo maki duk abinda nasamu, tunda naga ita tana sana,a zata iya rike kanta da Abdul. Ya mutsa fuska tayi tace kwaji dashi, nide bani abinda kasamo inje insiyo abinda zanci. Hannu yasa a aljihu yaciro dari 500 ya mika mata yace gashi mama nasan zata isheki harzuwa gobe, idan yaso jibi se inyo maki cefanan kayan abinci sunfi da arika bada kudin. Amsa tayi tace a,a ni banason wasu kayan abinci karika kawomun kudin nafi sonsu dan banason dora girki, Jafar yace shikenan zanyima Umman Abdul magana setarika dafawa dake arika kawo maki, dama can haka naso amma kikace kinfi son ki girka da kanki. Tace ni banason akawomun abinci kabani kudi kawai insayi abinda nakeso, taya zanrika jira se lokacin da tagama abinci sannan za,a kawomun. Kai Jafar ya girgiza yace shikenan Mama duk yanda kikace haka za,ayi, nixan koma, tace to nagode agaida Abdul. Washe gari haka WAPA tacika da mutane, kowa da jama,arshi, mutanen Alh, Bashir se zare ido sukeyi amma haryanzu basuga megidan nasu yazoba, wasu daga cikinsu tunjiya suke kiranshi amma bata shiga, har gidanshi sunje matanshi sukace bedawo ba. Alokacin da Alh, Abbah da Abbas suka karaso haka jama,a suka zagayesu, da kyar suka karasa office, wasu manya daga cikin mutanan Alh, Bashir suka shigo, bayan sungaisa suke tambayar Alh, Abbah shiru megidansu bezo ba. Murmushi Alh, Abbah yayi yace ai bazezo ba, yana police station shida abokinshi, mamaki ne yakamasu sukace kamar ya? Anan Alh, Abbah yaciro wayar shi ya kunna masu vedion da yayi masu jiya. Kowa seda yayi mamakin ganin abinda Alh, Bashir yayi, babban cikinsu yace ai shikenan yajama kanshi, kuma ni bantaba sanin haka halinshi yake ba, da ban bata lokacina gurin tsayawa zabenshi ba, wayarshi yadauko yace atura mashi domin yanuna ma sauran jama,arsu kowa yasan halin da ake ciki, kuma yayi alkawarin shima yakoma bayan Abbas. Gaba daya gurin ya yamutse da hayaniyar jama,a kowa da abinda yake fada, hakan yasa mutane dayawa suka dawo bayan Abbas, amma wasu dayake akwai kishi da kiyayya azuciyarsu cewa sukayi gara ayi asarar kuri,arsu dade su zabi Abbas, haka suka watse suka tafi gida. Bayan komai yalafa wadan da zasuyi zaben suka iso anan aka fara gudanar da zabe, duk da haka akwatin Alh, Bashir seda aka samu wadan da suka saka mashi, sukansu jami,an zaben dasuka samu labarin abinda yayi basuji dadi ba, hakan yasa akama kulle akwatin zabenshi. Bayan angama zabe agaban mutane aka kirga kuri,a inda Abbas ne yasamu damar lashe zaben Chairman na WAPA, mutane dayawa sunji dadin matsayin da Abbas yasamu, musamman abokan aikinshi, su Auwal da saddik suna daya daga cikin manyan yaranshi dasuka tsaya mashi akan zaben. Bayan komai ya lafa mutane sukarika yima Abbas murna da fatan alkhairi,Abbas seda yayi kuka ya rungume Alh, Abbah yana mashi godiya, shima seda idanunshi suka kawo kwalla. Haka kowa ya watse suma suka nufi gida shida Abbas. Koda sukazo shiga kwanar gidansu yaga Alh, ya wuce, kallonshi yayi, Alh, yace wani guri zaka rakani. Murmushi Abbas yayi, gaba da unguwarsu Abbas kadan sukaje, dede wani kwaton fili da aka zagaye aka samashi gate suka tsaya. Fitowa sukayi Alh, yabude gate din suka shiga, babban filine babu komai cikinsa, shide Abbas kallon gurin kawai yake. Hannu Alh, yasa a aljihu yaciro wata bakar leda, wasu ta kaddu ya fiddo yamika ma Abbas, yace wannan filina ne, halak malak. Kuma ayau ni Alh, Abbah Hassan Hala na mallaka maka shi halak malak, inaso kazabi irin ginin da kakeso nikuma daga gobe zansa afara zanenshi. Zankira sauran ,yan uwana infada masu suma su zama sheda, harma da hukuma zan sako suzama sheda saboda kasan yanayin rayuwa. Shiru Abbas yayi yana kallon Alh, idanunshi suna zubar da kwalla. Murmushi Alh, yayi yace kada ka damu Abbas, idan ina raye zanmaka abinda yafi haka. Ka Kosan irin yawan dukiyar dana samu azuwanka office dina? Kasan yawan mutanen dasuka dawo gurina saboda aiki da kai?. Tabbas haduwata da kai alkhairine, samun irinku aduniya bakaramin abu bane, shiyasa banajin kyashin yimaka duk wani abu na kyautatawa, fatana Allah yakaramana budi. Muje gida kada su Umma suga ka dade. Rungumeshi Abbas yayi tare da sakin wani irin kuka, yace bansan da wane baki zan gode maka ba Alh, kayimun abinda Uba yake ma danshi, kayimun abinda wani dan Uwa baze iya yima dan uwanshi ba. Tabbas kazama babban jigo arayuwata. Nasha matukar wahala arayuwata, sanadiyar rasa MUHALLI na danayi, nashiga damuwa sosai, mutane sungujeni aciki hada manyan abokaina, nayi yawon gidan haya wanda daga karshe seda aka kusa jamani sharrin Zina, Allah yakareni. Nafitar da ran zankara mallakar MUHALLI nawa na kaina, amma gashi alokaci guda Allah cikin ikonshi yasake mallaka mun MUHALLI. Babu abinda zance maka sede fatan alkahiri arayuwarka, Allah ya tsareka da iyalanka aduk inda kake, yakara daukaka ka, yasa kafi haka. Alh, yace amin Abbas, nagode nima da irin amanar da kake rikemun, sede idan bazaka damuba, inason duk lokacin da muka sami nutsuwa, komai yazama dede inaso kabani tarihin rayuwarka. Abbas ya goge kwalla yace nayimaka alkawarin zan baka labarina nida Labiba,Alh yace shikenan nagode, kuma inaso daga yau kadena kirana da Alh, zanfi jin dadi idan ka kirani da YAYA Abbas yace insha Allah Yaya. Murmushi yayi suka nufi gida. Umma seda tayi kuka saboda farin ciki, Labiba ma haka, addu,a kam Alh, Abbah yashata, haka yabarsu suna ta murna, bayan yatafi Umma ta kalli Abbas tace tabbas babu abinda yakamata musakama Alh, dashi sede murika binshi da addu,a. Yayi mana abinda babu wani dan uwanka dazeyi maka shi, amma gashi baka hada komai dashi ba, ya zama sanadiyar dauka karka,saboda haka inaso kamar yanda nasanka kada kabari wasu sushiga jikinka su canza maka hali. Kasan tunda kake baka taba samun matsayi irin wannan ba, kuma mutane da dama suna canza hali alokacin da arziki yazo masu, bazan maka baki ba, amma inaso kayi kokari gurin yin yakida zuciyarka, domin idan kayi yaki da zuciyarka ko shedan yayi kadan ya kusanceka. Kada kabari rudin dukiya ko zuciya sudebeka kazama butulu ga Alh, ko kuma kazama butulu ga mutanan dasuka zabeka, ka tsaya tsakaninka da Allah kayi aiki, babu ruwanka da karbar cin hanci, nasan akowane guri inde ance akwai shugaba dole za,a saka doka, to wadanda basa san gsky sukan bada cinhanci dan abarsu suyi abinda sukeso. Nasan aduniya duk me gaskiya shine abin ki agurin wasu mutane, kuma yafi kowa samun makiya, dan haka bawai kasamu cigaba ba, kabari ibadarka tayi baya, ayanzu ne ma yakamata ka kara karfafa ibadarka. Bacci beganka ba, amma zaka iya kwanciya da wuri kodan kasamu katashi cikin dare kanemi abinda kakeso agurin ubangijinka, kuma nima zantayaka, babu ruwanka da duk wanda zekawo maka maganin tsari, idan yana bada maganin tsari to yafara tsare kanshi. Babu wani dan adam dayake iya tsare mutum se Allah, kanemi yarda da tsaro agurin Allah seya tsareka. Ka gyara mu,amalarka da ubangijinka seya kareka. Manzan Allah yace kaci moriyar kuruciyarka tunkafin tsufa yazo maka. Kaci ribar lafiyarka tunkafin mutuwa ta riskeka, narokeka amatsayina na mahaifiyarka, kada kudi yasa kacanza halinka, kada kabari mutane su rabaka da Alh, hakan shine kadai hanyar dazaka iya saka mashi yaji dadi. Kuka sosai Abbas yakeyi tunda Ummanshi tafara yimashi nasiha, itama seda taji idonta yacika da kwalla, Labiba kam itama kukan takeyi. Abbas yace naji duk abinda kikace Umma, kuma nayi maki alkawarin bazan taba bari wasu su canzamun halayyata ba, addu,arki itace garkuwa arayuwata. Umma tace naji dadin hakan, Allah yayi maka albarka, yabaka ikon rike wannan amana da,aka baka, yakareka daga sharrin masu sharri, yace amin. Kallon Labiba tayi tace kema Labiba inaso infada maki wani abu. Nasan baki manta irin abinda kika yima Abbas ba, wanda kowa yayi mamakin barinki danayi kika cigaba da zama da dana, kuma kema kanki kinsan bantaba yimaki magana ba, ko na canza maki fuska, wanda duk wata uwa bazata iya saka ido ta kyale wata tasaka danta cikin irin halin da kika saka Abbas ba. Nayi haka ne, saboda shima ya dandana yaji yakuma gane da kanshi bakomai ne akema mace ba, nasan alokacin konayi mashi magana baze saurareni ba, saboda inasane da duk irin maganganun da mutane harma da abokanshi sukeyi mashi akanki amma yaki amincewa harseda yabi gurguwar shawararki, wadda daga karshe babu inda ta kaiku. Kuma alokacin na kyaleki ne, saboda banason inzama kamar sauran iyaye mata dasuke tauye hakkin ,ya,yansu, kuma banaso nazama sanadiyar rushewar farin cikin dana, nasan kuna son junanku, alokacin dana rabaku nasan nashiga hakkinku, kuma kila dayanzu wannan babban rabon yazama ajalina. Tunda Allah yarubuta rabo atsakaninku, hakan yasa nadanne zuciyata na hakura nabarku, dannasan koma menene tare zakusha duk wata wahala, kuma kece zakifi shiga damuwa, domin ke macece. Alhamdulillahi yanzu komai yafara zama tarihi, nasan ayanzu kindauki darasi sosai, kuma kingane DARAJAR MUHALLI, koyazu zaki iya bama wasu shawara, kuma azamanku gidan nan yasa na fahimci kema kuruciya da son zuciya tare da biyema shawarar kawaye sune suka jaki harkika aikata abinda kika aikata. Domin nafahimci kina da halaye masu kyau, kuma kina son mijinki sosai, dan haka ina kara rokonki kada kibari shedan ko wata kawa tazo jikinki ganin mijinki yasamu babban matsayi su saki ki kara canza hali. Kiyi hakuri da duk halin dakike ciki, baruwanki da kawaye, yanzu duk wadda zatazo jikinki wai kuyi kawance wlh, ba masoyiyarki bace, dan duk wanda ze gwada maka so alokacin daka samu wadata karya yakeyi. Lokacin da kake cikin wahala alokacin kake bukatar mutane, kizama me dora mijinki akan abu me kyau, kada kiyi amfani da son dayake maki kisashi ya aikata abinda beda kyau, wlh, kinji na rantse maki awannan karon bazan hakura ba, idan har kika sake maimaita kuskuren da kikayi abaya, koda zerasa ranshi idan narabaku sede yarasa. Amma bazan bari Abbas yakara shiga matsala ba, inafatan kinfahimceni? Goge kwallan idonta tayi tace naji Umma, kuma namaki alkawarin bazaki sake jin makamanci wani abu irin nabaya yafaru tsakanina da Dadyn Ansar ba. Murmushi Umma tayi tace naji dadi, kuma nagode maki, Allah yayi maki albarka, tace amin Umma. Haka jama,a suka rika shigowa suna masu murna, harda wadan da suke gulmarsu ada, Umma de kallonsu kawai takeyi, dan tasan komai game dasu. Washe gari haka Alh, Abbah yazo da mezanen gida Abbas yazabi irin fasalin dayakeso ayi mashi, sannan suka wuce, yadauko wasu yan uwanshi 2 suka nufi police station, anan yafada masu yabama Abbas filinshi, agaban abokinshi aka kafa sheda yayi rubutu kowa yasa hannu daga karshe officer yasa hannu. Godiya Alh, yayi mashi yace se sun hadu gobe akotu. Washe gari aka shiga kotu dasu Alh, Bashir, bayan ankawo shedu kuma suka amsa laifinsu, Alkali ya yanke masu hukuncin daurin shekara 1 agidan yari, da tarar dubu 50 ga Alh, Bashir, sakamakon tashin hankalin dayasaka Abbas. kowa seda yayi Allah wadai da halin Alh, Bashir, shi kanshi kunyar mutane yakeyi, abokinshi se kuka yakeyi yana danasanin biye mashi dayayi, iyalansu se kuka sukeyi, haka aka tasa keyarsu zuwa gidan yari. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 60 🔱 65 Ranar monday Abbas yafara shiga office dinshi dayake cikin Wapa, sosai yake aiki saboda bakaramin aiki yasamu a office din ba, ga mutane dasuke shigo yimashi fatan alkhairi. Sosai Alh, Abbah yake kara nuna mashi abubuwan da suka shige mashi duhu. Manyan yan Wapa se so suke suhada kai da Abbas, amma shi sam yaki sakar masu fuska, asalima yana karbarsu kamar yanda yake karbar kowa, abubuwan kyautatatawa har gida suna aika mashi dasu. Sukam su Auwal sunzama yan gaban goshi, se godema Allah suke daya shiryesu dayanzu suma sunzama yan kallo. Sosai Abbas yakawo canje canje a Wapa, mutane marasa karfi sunji dadin wannan canji da Abbas yakawo, ayanzu duk wani canji idan kazo Wapa bakada matsala. Marasa gaskiya sosai abun yafara damunsu. Haka Abbas yacigaba da gudanar da aikinshi hankali kwance, ta gefe guda kuma Alh, Abbah yana kokari gurin ganin an kammala ginin Abbas, gida ne, babba ake ginawa, part 3 ne kowane part yana dauke da falo da dakuna guda 2 hade da kitchen da toilet acikin kowane daki. Guda daya ne kawai babu kitchen wanda yakasance bangaren Abbas ne, kuma yana hade da bangaren Labiba kofa ce kawai tarabasu, dayan bangaren kuma na umma ne, yana daga gefen na Labiba, daga gefe guda na gidan kuma boys quarters ne guda 2, ginin yayi kyau sosai, dayake anzagayeshi hakan yasa ba,a ganin irin ginin da akeyi daga waje. Kwance Abbas yake saman kafar Labiba suna fira, kallonta yayi yace momyn Ansar wlh bakaramin farin ciki nake ba da Allah yasa seda wahalarmu tazo karshe Allah yabamu Ansar. Sam banason dana yasha irin wahalar dana sha arayuwa,sede inaso inrokeki wata alfarma dan Allah kada kizamo irin mutanan dasuke sangarta yaransu akan dukiya, tabbas nasan ayanzu kudi sunfara zama ajikina, inaso Ansar yataso cikin kulawa da kyakkyawar tarbiya. Ta yanda bazeyi alfahari ba, bare kuma yasamu damar raina na kasa dashi, kinsan halin da wasu yaran masu kudi suke ciki kenan, shiyasa nace aduk sanda kikayi sallah kirika yima Ansar addu,a hakan zesa Allah ya tsare mana shi. Kinsan azamanin yanzu tarbiyar da namiji tafi wahala akan ta mace, kuma bawa be isa ya kare wani daga fadawa halaka ba, dole se yahada da addu,a Allah ne kadai yake iya shiryar da bawansa alokacin dayaso. Dan haka kada kiyi sake da addu,a. Allah yayi mana jagora, tace amin Dadyn Ansar, nide tsorona daya murmushi Abbas yayi yakamo hannunta yace tsoron mekikeji?. Baki ta turo tace aikaima kasani,dariya yayi yace to dana sani zan tambayeki. Dora kanta tayi saman kanshi sega hawaye suna zuba daga idonta, ai dasauri Abbas yatashi yakamota ya rungumeta yace Labiba meyafaru kuma? Shiru tayi sema sautin kukan data kara, gaba daya hankalin Abbas yagama tashi, haka yayi ta lallashinta dakyar yasamu tayi shiru, yace dan Allah Labibata kifadamun abinda kikeso. Share kwllanta tayi cike da shagwaba tace shikenan nasan yanzu zaka kara aure, dan nasan masu kudi basa zama da mace daya. Wata irin dariya Abbas yasaka yana kallonta hada rike ciki, ganin yamaidata abun dariya yasa ta tashi tadauki pillow. Tashi yayi yana dariya suka fara guje guje, ganin takasa kamashi yasa tafadi tarike kafa tana fadin wayyo kafata, ai dasauri yakaraso gurinta yana fadin muga kafar, hannunshi takama tasa dariya tana fadin wana kama?. Dariya yayi yajawota suka zube akasa, bayan sungama dariya ya kalleta ahankali yakira sunanta, kallonshi tayi sede bata amsa ba, hannunta yakara matsewa yace Labibata inaso kiyarda da duk wata magana dazan fada maki. Wlh babu karya acikinta, kuma kinsan koni wanene, kudi ko mulki bazasu sa nacanza daga Abbas Alee dakika sani abaya ba, nasan talauci baya canza mutane kamar yanda kudi yake canzasu. Ni nakine har abada, kidauka saboda ke kadai Allah yayini, kema haka, babu wata mace dazata burgeni ayanzu domin nasamu zabin raina, kinzauna dani alokacin da bani dashi. Kinzauna dani alokacin da ake mana korar wulakanci agidan haya, kinyi hakuri dani wanda bakowace mace za,a samu awannan lokacin ba tayi irin abinda kikayi, idan har ban saka maki da alkahiri ba, banida wani amfani aduniya. Duk wata mace dazata zomun da wata kalma ta so nasan yaudara ce, domin babu wani sauran so azuciyar mutane ayanzu, duk wanda zece yana sona ayanzu tamkar ya furta kalmar kiyayyace agareni. Domin basu soni lokacin danake cikin matsala ba. Wlh Labiba banida burin zama da mata 2 arayuwata, kin isheni rayuwa, sede idan kincanza hali, hakan kadai zesa nima na karya alkawarin dana maki, inafatan kin fahimceni? Rungumeshi tayi tana murmushi tace insha Allah zaka sameni fiye da yanda kasanni abaya, nasan na cutar da kai, kuma kayi hakuri dani, bazan bari inkara maimaita kuskuren danayi abaya ba, fatana Allah yabani ikon yimaka biyayya akowane hali. Yace amin MATATA. Bayan wata 4 dafara ginin gidan Abbas, ayaune Allah yasa aka kammala komai na gidan, babu abinda ba,a zuba aciki ba, na more rayuwa, tsayawa fadin kyawun cikin gidan kauyencine, amma iyakar haduwa ya hadu. Hatta sutura seda Abbas yazuba ma Labiba da Ansar tamkar sabuwar amarya, dayan bangaren shine na Ummanshi itama kaya kala kala yazuba mata, sannan aka daukar mata me aiki, dazata rika yimata hidima, tundaga abinci, shara gyaran daki dasauransu. Labiba kam cewa tayi me wanke wanke da shara kadai takeso, ita zata rika girkinta, sosai Abbas yaji dadin abinda tafada, kaninshi Umar a daya daga cikin BQ din gidan aka bashi daya, dan Abbas yace rushe tsohon gidansu za,ayi seya koma can kafin shima yayi aure. Aranar da suka koma seda Alh, Abbah yashirya walima, mutane da yawa suka samu halartar walimar, anci ansha, kowa ya yaba da gidan Abbas Alee, da masu gulma damasu tsegumi duk sun halarci gurin. Anan Alh, Abbah yayima Abbas kyautar wata mota me tsadar gaske, wasu daga cikin mutane har cewa suke kode asiri Abbas yayima Alh, dan suna ganin kyautar dayake mashi tayi yawa, wanda agurin Alh, yana ganin beyi mashi komai ba, idan akayi la,akari da irin halarcin da Abbas yayi mashi. Bayan kowa ya watse Alh, dasu Umma suna zaune afalo, Umma se godiya take ma Alh, yace Umma bakomai dannayima Abbas wannan ai bawani abu bane, Allah yakara hada kanmu, tace amin. Abbas kuwa seda yayi kuka, haka Alh, yayi masu sallama yatafi. Aranar kasa bacci sukayi, saboda tsananin murna, hakan yasa Umma tace kowa yaje yayi alwala suyima Allah godiya abisa sauyin rayuwar dasuka samu. Haka suka raya wannan dare da ibada, Labiba gani take kamar amafarki ne abun yake faruwa, akowace addu,a seta roki Allah yasa kada Abbas yayi mata kishiya. Nikam nace Allah yasa LABIBA Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 65 🔱 70 Zamansu gwanin dadi suna cikin farin ciki, hankalinsu ayanzu akwance yake, acikin sati 2 da dawowarsu gidan harsun murmure. Labiba da yaronta tubarkallah yaro yayi girma kyanshi se kara fitowa yakeyi, Abbas kuwa duk wanda yasanshi awatannin baya idan yaganshi yanzu baze iya ganeshi ba, Umma ita kanta jikinta yayi kyau, batada wata damuwa, komai yimata akeyi, Umar kuwa Abbas yabude mashi wani babban shago abakin titi ya zuba mashi kayan provision hakan yasa yadena zuwa kasuwa yakoma zaman shago, shiyasa Umma tace bazata iya zama bata komai ba, shiyasa tafara yin cincin da zobo na roba tana bama Umar yana tafiya dashi. Zaune Abbas yake shida Auwal a office suna lissafi, kasancewar Alh, Abbah yabama Abbas Auwal dan yace yasan takan aiki kuma sundade tare gashi kuma yacanza hali, zefi jin dadin aiki dashi akan yasamu wani. Hakan yasa Auwal yadawo office din Abbas shi kuma Saddik ya zauni matsayin Auwal, kuma sosai Abbas yakejin dadin aiki da Auwal, dan yanzu tsakani da Allah yake zaune da kowa. Kallonshi Abbas yayi yace Auwal ina ganin abar lissafin nan haka, kaje ka kai wadannan kudin bank, idan kadawo anjima akwai wanda yace zezo karbar canjin dala, shine Yaya yahadani dashi, idan kadawo se ahada mashi. Auwal yace angama megida, murmushi Abbas yayi yace Auwal baka rabuwa da abin dariya, sallama sukaji abakin kofa, hakan yasa Auwal yayi surin rufe jakar kudin datake hannunashi. Amsa sallamar Abbas yayi yace bismillah shigo, wasu manyan mutane ne suka shigo irin Alhazawan nan, da sauri Abbas yatashi murmushi dauke afuskarshi yace a,a Alhaji Kallah sannunku dazuwa. Gurin zama yanuna masu yace ga gurin zama, bayan sun zauna yakarasa kusa dasu yamika masu hannu suka gaisa, Auwal ma hannu yabasu suka gaisa se bata fuska yakeyi, dan yasan kosuwaye acikin Wapa. Bayan Abbas yazauna yace Alh, inafatan lafiya ko? Gyara babbar rigarshi yayi yana murmushi yace eto lafiyar kenan, tunda kaganmu munzo office dinka adede wannan lokacin ai kasan akwai dalili. Abbas yace haka ne, to meke tafe daku? Wanda aka kira da Alh, Kallah yace agaskiya Abbas bamajin dadin irin wannan canji damuka samu tunbayan hawanka wannan kujera. Kasuwancinmu banda karyewa babu abinda yakeyi, kasan halin dan kasuwa, akullum munfison ace kaya suna tsada akasuwa bawai karika kokarin sauko dasuba, ayanzu dala tafadi, bama samun komai idan munyi ciniki. Kullum cikin bacin rai muke, sabanin nakasa damu wadanda akullum suke cikin farin ciki, gsky muna ganin ayi hakuri akara mana koda kaso 20 ne acikin 100, idan akayi hakan muma ante makemu. Kaga kaima zaka samu, muma musamu, idan kabiye ta talakawa wlh damu da kai bazamu taba samun abinda mukeso ba, kuma kaga wannan kujerar taka lokaci gareta, idan kayi sake babu abinda zaka tara. Ni kaina dana rike irin matsayinka danayi irin abinda kayi ai da lokacin dana sauka nazama abin dariya agurin mutane, amma gashi haryanzu ina cikin wadan da suke damawa. Amma gashi ayanzu daga hawanka arzikina yafara sauka, jiya dana duba account dina bakaramin tashin hankali nashiga ba, harseda hawan jinina yakusa tashi. Nasaba kudi basa yanke mun, hakan yasa nadauki ATM dina nabama Matata, amma jiya dana duba kudina bakaramin fadawa sukayi ba, gaba daya abinda ke ciki baze wuce million 30 ba, jiya ko bacci kasa yinayi, kamata ace 30 million ne a account dina. Gashi yanzu mutanan danake harka dasu sunfara barina, shiyasa nace muzo gurinka ayi mana wannan temakon, ko ba haka ba Alh, Bukar?. Wanda aka kira da Alh, Bukar yace kwarai ma kuwa Alh, wannan itace maganar gaskiya, damu akayi zabe, mune muka amince aka zabeka dan haka dole muma ayi mana abinda muke so. Murmushi Abbas yayi yana kare masu kallo, Auwal Kuwa jiyake kamar yarufe su da duka, babu abinda yafi bata mashi rai kamar wai sune suka tsaya aka zabeshi, kuma su suka zabeshi, wanda yana sane akwatin Alh, Bashir suka sama kuri,arsu. Abbas yayi gyaran murya yace hakane, naji duk abinda kukace, amma zan maka gyaran magana daya Alh, Bukar, ni babu wani daga cikinku wanda ya tsayamun nasamu wannan matsayi, asalima ni bansanku ba, inba yanzu ba, dan magana ta fatar baki bata taba hada muba. Garama Alh, Kallah, shi inajin labarinshi, kuma nataba ganinshi so 2 amma akoina zanfito da babbar murya infada cewa Alh, Abbah Hassan Hala shine mutumin dayayi sanadiyar hawana wannan matsayi, dan haka kadena ikirarin kuntsaya mun. Abu na 2 kuma Alh, kallah naji korafinka, sede ina mamakin mutane irinka, kanada kudi har million 30 amma kake fadin wai baka da kudi, har hawan jininka zetashi, kana cikin katon gida, babbar mota, amma duk da haka kake fadin bakada kudi. Inaga wanda yakeda iyali sama da mutum 10 agidanshi, be aje ko kwarar masara ba, balle kudi agidanshi, haka kullum yake tashi beda ko kwandala kuma ga nauyin mutane akanshi haka zetashi yafara tunanin abincin karyawa. Daga nan yafita neman abincin rana, shi beda burin ma yatara agidanshi, burinshi inde zesamu abinda iyalinshi zasuci alokacin zeyima Allah godiya, na tabbatar idan aka bude store dinka na kayan abinci ya ishi wani yabude karamin shago dasu. Talaka fa? Wanda dayawa azamanin nan sede suyi awo bade su siyo abincin yau da gobe ba, yakake ganin idan muka kara farashin dala, wane hali mutane zasu shiga? Akullum kada kayi tunanin kanka, kayi tunanin nakasa da kai hakan ze kara maka karfin imani. Mu muna kokarin muga yanda Dala zata kara karyewa domin talakawa su samu saukin rayuwa kana sane da idan dala ta tashi komi seya tashi, amma ku kunaso akarata, so dayawa ba daga sama komai yake tashi ba, wani lokacin laifin yana garemu yan kasuwa. Kullum burinmu tayaya zamu samu karuwa, babu ruwanmu da sauran bayin Allah, to agaskiya ni bazan iya daukar wannan maganar taku ba, kuma kamar yanda muka zauna da sauran manyanmu aka tsayar da farashin Dala. Kuma aka kafa doka duk wanda aka samu da laifin yakara akan afarashin da akasa ze fuskanci hukunci, to haryanzu doka tana nan, babu wanda zezo yakawo mana wani bakon al,amari, inafatan kunfahimce ni? Gaba daya zufa da bacin rai sun gama wanke fuskokinsu, Alh, Bukar ne yayi karfin halin dauko wata jaka dasukazo da ita, share zufa yayi, yace haba Yallabai, ai abun be kai nan ba, muma bamuzo ba, seda muka shirya, Amma laifinmu ne, kamata yayi mufara baka wannan kafin mufadi bukatarmu, ga wannan bayawa, million 2 ne, asa mai, sauran bayani kuma daga baya zakaga sako insha Allah har gida, dora jakar yayi saman table din Abbas. Cike da bacin rai Abbas yatashi tare da dukan table din wanda har Auwal seda ya tsorata, dan betaba ganin Abbas cikin bacin rai kamar haka ba, idanuwanshi har kankancewa sukeyi saboda bacin rai. Cikin bacin rai yace Bukar kutashi kubarmun office daku da cin hancinku, kuma wlh, wannan shine karo na farko kuma na karshe dazakuzo office dina da magana irin wannan, idan kuma bakuji ba, tabbas zakuyi dana sani, zannuna maku waye Abbas Alee. Cike da bacin rai Alh, kallah yatashi yakalli abokinshi yana huci yace dauko jakar mutafi, kallon Abbas yayi yace kaine, matsiyaci, wanda begaji arziki ba, shiyasa zakayi watsi da kyautarmu. Murmushi yayi yace kodayake ba laifinka bane, kai sabon shiga ne acikin arziki, domin dama talaka be iya samun guri ba, duka yaushe kafara farfadowa daga talauci? Ko kamanta in tuna maka, kadauka bamusan komai akanka, ba? Sanin ko kai waye yasa muka hana abaka wannan kujera, domin bama son abama talaka marar arziki yazo yanuna mana halin naku. Segashi tukafin ayi nisa munfara gani, aini atunanina yanda kasha wahala arayuwarka bazaka taba bari wata dama ta arziki tashigo maka batare dakayi amfani da ita ba. Ko kamanta ko wata 1 bakayi da mallakar MUHALLINKA ba? Kodayake bazakji ciwon wannan ba, saboda bada guminka ka ginashi ba, kasan duk wani dan halak yakanyi kokari yaga yagina MUHALLINSHI da gumin kanshi. Hakan zesa aduk lokacin daya kwanta zerika alfahari da abunshi, amma kana gefe anmaka gini ansamaka komai kashiga ta yaya zaka iya alfahari dashi? Tambayarka nake ka amsamun idan har kasan da gaske abinda na fada badede bane? Wasu zafafan hawayene suka fara zuboma Abbas, kasa yayi da kanshi, murmushin mugunta Alh, kallah yayi dan yasamu abinda yake so, hakan yasa yacigaba. Idan zaka fadi tsakaninka da Allah, alokacin da aka koreka daga gidan hayarka na karshe, kadawo gidanku, dakin daga gina da guminka, ranar daka fara kwana acikinshi kozaka iya fadamun wane irin farin ciki kayi aranar? Shin zaka iya hada farin cikin ranar da wanda kayi aranar da ka kwana agidan da babu ko sisinka aciki? Uhm kobaka fadamun ba, nasan bazaka iya hadasu suzama daya ba. Idan kamanta bara intuna maka, tunda kake arayuwarka baka taba kwanciya a karkashin inuwar data kasance guminka ne, kayi bacci me dadi aciki ba se ranar daka kwana acikin dakin daka gina na gidanku. Ko kamanta gidanka daka gina dazakayi aure, hakanan kasha wahalar banza amma ko zaman. Yini guda bakayi aciki ba, bare kuma ka kwana aciki? Uhm Abbas kadena yaudarar kanka, MUHALLI koda kudin haram ka ginashi inde daga aljihunka suka fito, seyafi daraja akan adauki sadaka abaka,nasan zakayi mamakin yanda nasan waye kai ko? Karka damu, siyasar kenan, munbarka lafiya, duk lokacin daka shirya tafiya damu kofa abude take, asha inuwar gidan SADAKA lafiya, dariya Alh, Bukar yayi yadafa kafadar Abbas yace semunjika, haka suka fita suna dariya. Zubewa saman kujera Abbas yayi yana wani irin kuka wanda betaba yinshi ba, tunda yazo duniya, ze iya cewa koda mahaifinshi yarasu beyi irinshi ba, hatta da Auwal seda yayi kuka jin irin bakaken maganganun dasuka fadama Abbas, koshi dasuke tare betaba sanin labarin Abbas ba, amma saboda yashiga harkar siyasa yau anzo har office dinshi ana mashi tonon asiri. Shiru office din yayi, banda sautin kukan Abbas babu abinda akeji, Auwal ne, yagoge kwallanshi yamatso kusa da Abbas yadafashi yace yallabai dan Allah kayi shiru haka nan, Kada kadamu da irin maganar dasuka fada maka, dama ita siyasa tagaji haka, dole se mutum ya toshe kunnanshi sannan ze iya zama lafiya, kuma maganar gidan da Alh, yabaka dasukeyi karabu dasu, Bakin ciki kawai sukeyi,da sune aka bama gidan karba zasuyi, kuma ai kafisu, suda suke zaune akarkashin inuwar haram, kaifa? Kyauta aka baka gidan, kuma kowa yasan yazama mallakinka halak malak. Dago kai Abbas yayi, yashare hawayenshi yana murmushi wanda yafi kuka ciwo, yace a,a Auwal, basuyi karya ba, tabbas farin cikin dana tsinci kaina aranar dana mallaki dakin dana gina agidanmu, yafi wanda na kwana agidan da yaya yabani kyauta, Bantaba lura da haka ba se ayau da akamun tuni, aranar dana kwana asabon gidana, naji dadi, amma wlh be kai dadin danaji ba, aranar dana kwana adakina. Goge kwallan idonshi yayi yace haka ne Auwal, Kyan MUHALLI ka ginashi da guminka, sekafi farin ciki da alfahari, sede nayima Allah alkawari ba zan taba bari haram tashigo cikin dukiyata ba,amma naji dadin wannan tuni da Alh, Kallah yayi mun, Kuma insha Allah zan dauki shawarar daya bani, duk da agurinshi yana gani cin fuska yamun, ni kuma nayi alkawari, inaso kazama sheda, insha Allah nan dawani lokaci zanyi kokarin gina MUHALLI na da gumi na, kuma acikinshi nakeso incigaba da rayuwa, nasan tabbas MUHALLIN daka gina da guminka yafi DARAJA akan wanda kasamu daga sama. Nasan yaya zeji ba dadi amma zansameshi inmashi bayani, nasan ze fahimceni. Uhm Alh, kallah, inaso kasa aranka wata rana zakaga cin fuskar dakamun alkahirin dazata janyo mun. Dan ayanzu nafika sanin DARAJAR MUHALLI. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 70 🔱 75 Dukar da kanshi Abbas yayi yacigaba da kuka me tsuma rai, Auwal duk tausayin shi yagama kamashi, turo kofar da,akayi ne yasa Auwal saurin kallon kofar, Alh, Abbah ne yashigo fuskar shi cike da damuwa, harya zauna Abbas besan yashigo ba,seda Auwal ya gaisheshi sannan Abbas yayi saurin dago kanshi. Hannu yasa yana goge fuskarshi, yana fadin sannu da zuwa Yaya, kai Alh, Abbah yadaga yace sannu Abbas, shiru yayi ya dukar da kanshi. Alh, yace Abbas kayi hakuri da duk wani abu dayake faruwa akanka, da kuma wanda zefaru nan gaba, dama haka siyasa ta gada, naji duk abinda yafaru, Tundaga shigowar su Alh, Kallah, alokacin nataho zanzo gurinka naga sun shigo nan, hakan yasa na tsaya abakin kofa, duk abinda yafaru akunnena naji komai, Alokacin dazasu fito nayi saurin boyewa, sanda suka fito basu san inajinsu ba, Alh, Bukar yace yaji dadin abinda Alh, Kallah yayi maka, dama shiyasa suka saka akayi masu bincike akan rayuwarka, Domin susami hanyar dazasu daga maka hankali, Alh, kallah yace ka kyaleshi tunda nafara mashi maganar naga tashin hankali da bakin ciki a idonshi, dan haka ta wannan hanyar zamu bullo mashi, da kanshi seya nememu, Kaga semuci karanmu babu babbaka, dariya suka sa suka wuce, nazo zanshigo senaji kuna magana da Auwal. Karka damu, ni kaina raina bakaramin baci yayi ba, da irin wannan cin fuska da sukayi maka Amma ka kyalesu, suna ganin kamar sun cimaka fuska, naji dadi sosai da kadauki wannan mataki, dama kuma haka akeso ga duk wani dan halak, kuma namiji me kishin kanshi yayi. Kuma banaso kasaka wannan abun aranka har kowa yafahimci kana cikin damuwa, hakan zesa suji dadin abinda sukayi, kuma zasu samu damar hanaka aikinka, dan idan har mutum beda kwanciyar hankali to komai nashi yana ja baya ne, Narokeka kosu Umma da Labiba kada kabari suji domin suma hankalinsu zetashi musamman Umma kasan ayanzu hankalinta akwance yake, dan haka kamar yanda kake addu,a kacigaba insha Allah makiyanka sede subiyo bayanka. Maganar gida kuma banaso ka kara tada hankalinka saboda abinda suka fada, nide harga Allah bada wata manufa nabaka wannan fili ba, kuma lokacin da aka fara gini babu wanda yasan nine nake gina maka. Kai ko yan uwana babu wanda yasan cewar nine nayi maka wannan ginin, kuma ina me tabbatar maka suma basani sukayi ba, sunde san nabaka fili agurin mutane. Amma sunfadi haka ne, kawai dansu kara daga maka hankali, Kuma naji shawarar daka yanke, Abbas bazan hanaka ba, domin kowa zeso ace ya mallaki MUHALLINSHI da gumin kanshi, idan har yana kishin kanshi, kuma naji dadi daka zamo daya daga cikin irin masu kishi, Bakomai, wlh raina be baci ba, na fahimceka, kuma ko nine matakin daka dauka shizan dauka, sede inaso kasani, banaso saboda wannan maganar kadaga hankalinka kafara ramewa abanza, Kasan zafin nema baya kawo samu, kabi ahankali insha Allah zaka mallaki gidanka, wuyar abun ace mutum bayada abunyi, alhamdulillah yanzu kawuce tunanin me tunani, nasan ko ayanzu cikin account dinka za,a samu kudin dazasu saya maka fili, babba har kafara gini menisa, Dan haka kabari abi komai asannu, kuma ko kagama gininka bayarda kabar gidanka ba, sede kabama Umar shima yayi aure hakanan, sesu zauna agidan, Allah yamana jagora aduk abinda mukasa gaba, kada kabari makiyanka surika gane fushinka afuska, Kowane irin bacin rai suka saka ka, kayi kokarin dannewa, hakan zesa karika kona ransu. Kallon Auwal yayi yace kaje ka kai kudin bank, idan kadawo se ahada ma wannan mutumin kudinshi, kuma abinda nakeso da kai, Inaso kasaka ido akansu Alh, Bukar, inaso musami kwakkwarar shedar dazatasa mu fallasa su agaban mutane, kowa yasan halinsu, kaga dakansu zasu daure kansu, zaman Wapa seya gagaresu. Tashi Auwal yayi yadauki mukullin motar Abbas yatafi, anan Alh, Abbah yayita lallashin Abbas harseda yaga yasaki ranshi, Har Auwal yadawo yana nan, suna gama hadama mutumin kudinshi yakirashi yazo, bayan sungama yayima Abbas da Auwal kyauta me tsoka, dan bature ne mutumin, Bayan sun gama yayi masu sallama tare da alkawarin zekawoma Abbas sauran abokanshi suma zasu dawo gurinshi dayin canji, sosai Abbas yaji dadi, anan sukayi musayar number, hakan yasashi yamanta da bacin ran dayake ciki, dama kuma shi bame riko bane. Jafar ne, yake ta sauri yasamu yakaraso kofar gidan mamanshi, dan tun daga nesa yahango dandazon mutane akofar gidansu, hakan yasa yayi saurin karasowa. Da kyar yasamu yakutsa ciki, mamanshi yagani tayi dammara da mayafi se ruwan bala,i takeyi ita da wata mata, mutane se hakuri suke basu, yana zuwa dayar matar tana kwashe mamanshi da mari. Besan lokacin daya daga hannu yakai mata naushi afuska ba, nantake tazube asume, gaba daya mutana gurin suka dau salati, ga jini daya fara zuba ta hancinta, ashe shima danta yaiso gurin akan idonshi Jafar ya naushi Babarsa, Ai kamar walkiya shima yafado cikin filin, anan ya cakumi wuyan Jafar suka fara dambe, hankalin mutane yakoma kansu, nan aka shiga kokarin rabasu, ganin fadan yaki karewa yasa wani mutum yayi waya yakira yan sanda, Da kyar, aka samu aka rabasu, duk sunjima kansu ciwo, anrikesu sosai amma kowa soyake yakaima dan uwanshi kafa, wasu ne suka dauko ruwa suka rika zubama dayar matar data suma. Adede lokacin yan sanda suka karaso, nan akayi masu bayani, hakan yasa suka tasa keyar Jafar da abokin fadanshi, da Mamar Jafar, harma da dayar matar, wadda bata dade da farfadowa ba, hancinta duk jini, Gaba dayansu abayan motar yan sanda ka sasu, Jafar da dayan ansaka masu ankwa suka ja motar, maman Jafar se kuka takeyi, yau gashi adalilin son zuciyarta tajama danta zuwa police station, mutane se magana sukeyi dan wadanda abun yafaru agabansu sun san Mamar Jafar ce bata da gaskiya. Adede inda ake bada hannu motar dasu Jafar suke ciki ta tsaya, mutane se kallonsu sukeyi, gaba daya kunya tagama kama Jafar, abinda tunda yake arayuwarshi betaba yin fada ba, amma gashi yau shine hada ankwa, Dukar da kanshi kawai yayi kwalla tana zubar mashi, abokin fadanshi banda harara babu abinda yake aika mashi, dama kuma can bawani shiri sukeyi ba, dan wancan irin yan zafin kan nan ne, kuma Jafar ma ya girmeshi. Zaune Abbas yake agaban motar Alh, Abbah dan tare suka fito, motar Abbas kuma Auwal ya tukata, tsaye suke suma a inda ake bada hannu, kamar ance Abbas yajuya, karaf idanunshi suka sauka akan fuskar maman Jafar abayan motar yan sanda, kara gyara zama yayi, yana kara kallon motar, kawai yaga Jafar hannunshi daure da ankwa, ga fuskarshi duk jini, Mamaki da tashin hankali ne suka bayyana afuskar Abbas, kafin yayi magana aka bada hannu, besan lokacin dayace Yaya dan Allah kabi waccan motar yan sandan, Alh, Abbah yayi saurin kallonshi cike da mamaki, Abbas yace dan Allah Yaya, girgiza kai Alh, Abbah yayi yabi bayansu Jafar,gaba daya hankalin Abbas baya jikinshi, kallon Jafar kawai yakeyi, Alh, Abbah ne, ya kalleshi yace Abbas wai lafiyarka kuwa? Meya hadaka da motar yan sanda, kasani sebin bayansu nakeyi kuma kai bakamun bayani ba? Kallonshi Abbas yayi yace Yaya wlh wani aminina ne da mahaifiyarshi nagani abayan motar yan sandan kuma ga ankwa ahannun shi, kalli fuskarshi duk jini, rabona dashi mundade seyanzu dana ganshi awannan halin. Kabari muje idan mundawo zakaji komai agame dashi, Alh, Abbah yace to Allah ya kyauta, haka suka rika bin bayansu, har suka isa bakin station,bayan sunshiga suma su Abbas sukabi bayansu, kai tsaye office din DPO aka yidasu, Da sallama su Abbas suka shiga, gurin wani dan sanda sukaje, bayani sukayi mashi, yace sujira yafito, bayan minti kadan yafito yace sushiga, atsugunne suka samesu, maman Jafar se kuka takeyi, Bayan sungama gaisawa da DPO yabasu guri suka zauna, Abbas yace Jafar, ai dasauri Jafar yadago kai ya kalli wanda yakira sunanshi, cike da mamaki yace Abbas, ita kanta Maman Jafar seda tadago kai tabi Abbas da kallo, mamaki dauke akan fuskarta. Alh, Abbah yace yallabai munzo ne, muji meyafaru da wadannan bayin Allah, muna tafiya muka hadu da yaranka sun kamosu, shine muka biyo muji ba,asi. DPO yace to nima de yanda kagansu haka aka shigo mun dasu, yanzu ko bayaninsu ba,ayi mani ba kuka shigo. Kallon dan sandan daya kawosu yayi yace kai muke sauraro. Gyara tsayuwa yayi yace yallabai muma waya aka mana aka fada mana ana fada, shine mukaje, koda mukaje wani yayi mana bayanin wannan, yanuna Jafar, shine yadake waccan matar harya sumar da ita, shine itama danta yakamshi suka fara fada, Toshine muka daukosu duka muka taho nan dasu, semuji daga bakinsu. DPO yakalli Jafar yace kai kafada mana abinda yake faruwa, da har baka kalli girman wannan matar ba ka iya ware karfinka kamar zakayi fada da sa,anka har ka sumar da ita. Jafar yayi kasa da kanshi yace wlh yallabai tsautsayi ne, nima zuwana unguwar kenan na hangi mutane kofar gidanmu, dasauri nakarasa gurin, zuwana yayi dede da wannan matar tadaga hannu ta kwashe mamana da mari, Ni kuma idona yarufe, bansan lokacin dana nausheta ba,shine ta suma, ashe danta yana gurin shine yarufeni da duka muka fara fada. Jijjiga kai DPO yayi yace kai kuma fa? Yace nima zuwana kenan gurin nasamu Jafar yakaima Ummana naushi, agabana naga ta suma shine nima nakai mashi duka. Murmushi DPO yayi, yace atakaice de kuduka babu wanda yasan abinda yahada fadan, kawai de kowa yashigarma Babarsa? Kai suka daga su duka, DPO yace amma gaskiya kun kyauta, ko nine abinda yakamata inyi kenan, musamman idan akace nine aka sumar da Babata. Murmushi Alh, Abbah yayi yace habade yallabai, yace emana, ai Uwa batafi Uwa ba ko? Alh, Abbah yace hakane, ammade ayi hakuri muji abinda yahada fadan, kasan mata. Kallon iyayen DPO yayi yace kowa ta matsa kusa da danta, bayan sun matsa, yace yauwa, ayanzu nagane wadda aka sumar, dan haka zan fara da ita, baiwar Allah meya hadaki fada da waccan matar? Gyara zama tayi tace yallabai, wannan matar kowa a layinmu yasan halinta, akwaita da karbar bashin mutane, ta dade tana karbar bashin kudi ko kayan amfani agurina, ayanzu haka inabinta dubu biyar, bayan kudin sabulu da omo datake amsa, wanda akalla zasu kai, dubu biyu. Tun ina hakuri da ita har nagaji, ayau naje gidanta karbar kudina shine tarufeni da masifa, wai ita batada hanyar samun kudin dazata bani, ganin tanamun masifa nace to zan kaita gurin yan sanda, shine taci dammara ta turoni waje tana ta fada, Nima sena biye mata muka cigaba da rigima, nan mutane suka taru, abinda yafi bani haushi yanda agaban mutane take fadin wai nice naci mata bashi naki biyanta shine kawai na mareta. Amma wlh banyi niyar fada da ita ba, kowa yasan irin zaman danakeyi da kowa a unguwar nan, DPO yace naji bayaninki, kallon maman jafar yayi yace kefa? Kuka tasaka tace wlh hakane duk abinda tafada babu karya, Kaichona banzama Uwa tagari ba, Allah yabani yaro nagari, me zuciyar imani, da son temakon wanda bedashi, amma nayi amfani da damar da Allah yabani amatsayina na Uwa na tauyeshi, Segashi tun lokacin dana hanashi aikata aikin alkhairi nima Allah yajarabceni, gaba daya samun da Jafar yake dashi ada yanzu babu, kunga laifina yashafeshi, Abbas ka gafarta mani, tun daga ranar dana sa Jafar yarabu da kai, nasa aka koreka daga gidan hayar daya kama maku, Wlh tundaga ranar kome yashigo hannuna baya albarka, shima Jafar haka kasuwancinsa yafara lalacewa, abincin ci seda yafara gagararmu, duk da Allah yabani sirika tagari, amma narufe idona dole sede Jafar yakawomun kudi inyi girkina, Tun yana samu akullum har yadena samu, gashi duk abinda nace haka yake kokarin sama mani, duk kokarin dayake akaina be hanani cin bashi ba, wanda bansan menake dasu ba, Segashi ayau ta sanadiyata yarona yazo gurin yan sanda, kayafemun Jafar, nasan na cutar da kai, kaima Abbas haka, kayafemun, narabaka da abokinka, narabaka da aikinka, gashi tunkafin aje ko ina Allah yanuna mun shine kadai yake iya azurtawa kuma ya talauta, Ko baka fada ba, nasan baka cikin talauci, dan girman Allah kuyafemun, Talatu kema nasan nacutar dake, kinmun rana daga karshe nayi maki butulci, kuka tasaka, wanda seda tabama kowa tausayi, Abbas da Jafar kuwa tuni suke kuka. Shiru gurin yayi nawani lokaci, sannan DPO yace tabbas baiwar Allah baki kyauta ba, kinzamo uwa marar tausayin danta, kuma kin zamo mace marar kyautatama makotanki, Kisani Allah yabama iyaye amanar ,ya,yansu kuma ranar gobe kiyama zetambayesu wane irin riko suka masu, kamar yanda iyaye suke da hakki akan ,ya,yansu, haka ,ya,ya suke da hakki akan iyayensu, be kamata iyaye surika amfani da damar da Allah yabasu ba, suna cutar da ,ya,yansu, musamman iyaye mata. Ki godema Allah daya barki da ranki harkika samu damar neman afuwa agurin wadanda kika cuta, dan haka yanzu wata dama Allah yakara baki, idan kinso kiyi amfani da ita gurin gyara lahirarki, Idan kuma kinso zaki iya yin yanda kikaso, sbd haka niyanzu abinda zance, yarage tsakaninku da wannan mata, kibiyata kudinta, sauran kuma idan tayafe shikenan, dama mu aikinmu shine sasanci. Alh, Abbah yace hakane yallabai, kallon matar yayi yace baiwar Allah nawane kike binta? Matar tace dubu biyar ne, wanda nasan nabata adunkule, sauran kuma kana nane, agaskiya abazan iya fadinsu ba, namanta, tabani dubu 5 din nayafe mata sauran. Mamn Jafar tasa kuka tace nagode Allah yabiyaki, Alh, Abbah yaciro dubu 10 yabata yace tarike, godiya tayi masa, yakalli yaronta yace kaikuma kayi hkr da abinda akayima mahifiyarka, Kasan duk da nahalak bazeso yaga anwulakanta mahaifanshi ba, kayi hkr, yace shikenan ya wuce, Jafar yamika mashi hannu suka gaisa, nan DPO yabasu takarda suka cike yasallamesu, Alh, yaciro kudi yabashi suka fito. Amotar Alh, suka shiga su duka, har kofar gida suka kaisu, anan Abbas yakarbi number Jafar yace mashi zasuyi waya, godiya sosai Jafar yayimasu, Alh, yaciro kudi yabama maman Jafar, shima Abbas yabata, yakuma bama Jafar, hada kukanta tana kara fadin kayafemun Abbas, Haka suka nufi gida, amota Alh, Abbah ya kalli Abbas, yace agaskiya yau dinnan naji ina matukar son inji labarinka, na dade inaso kabani labarinka, dan nasan dole akwai abubuwan ban tausayi aciki, Musamman ayau danaji kadan daga tarihinka, Abbas yayi murmushi yace bakomai Yaya insha Allah ayau zakaji labarin rayuwata, Alh, yace yauwa bara inkira gida infada masu bazan dawo da wuri ba. Labiba tana zaune afalo tana kallo, Ansar da metayata aiki suna zaune akasa tana yimashi wasa, daga kofar falo, sukaji sallamar megadi, Labiba tace yashigo, bayan sun gaisa yace hajiya dama wata matace tace gurinki tazo, shine nace ta tsaya inyi mata iso. Labiba tace to Baba kace tashigo, yana fita segashi sunshigo tare dasauri Labiba ta tashi tana fadin Maman Zainab, tace na,am momyn Ansar, Dariya sukayi suka rungume juna, bayan sungama murnan ganin juna, Labiba tasa aka kawo mata lemu da abinci, zama tayi tafaraci,suna gaisawa. Maman Zainab tace ikon Allah se kallo, naje gidanku akacemun kuntashi, gashi wayata na manta ta agida, Allah yatemakeni nasamu wanda yasan nan, shine yarakoni, Kobaki fada ba, nasan Allah yakawo maku sauyin rayuwa kamar yanda yakawo mana, tabbas ba karamin farin ciki nayi ba, alokacin dana ganni agaban gidan nan kuma akacemun nakune, Labiba tace wlh kuwa maman Zainab kinga yanda Allah yakawo mana sauyi cikin kankanin lokaci, koyanzu nakoyi babban darasi arayuwata, ya Lagos ban tambayeki ba muntsaya labari, Maman zainab tace wlh lafiya lau, ai zuwanmu Lagos bakaramin nasara Baban Zainab yasamu ba, Allah yahadashi da megida nakirki, yau watanmu guda da dawowa, Kinsan wani abin farin ciki? Tunkafin mudawo Baban Zainab yazo yasaya mana gida akusa da tsohuwar unguwarku, amma mu a gandun sarki muke, wlh bakiga gidan ba, babba gsky babu abinda zamuce sede muyima Allah godiya, Ayanzu har mota muke da ita, gaskiya arziki kam yazauna mana, saboda karatun Zainab yasa muka dawo nan, dan Babanta yace yafison tayi karatunta anan kano, Nima kuma nagaji dazama cikin yare, bansan kowa ba, ai gida yafi komai dadi, koba komai zakaga yan uwa da abokan arziki, labiba tace gaskiya kam, ni kaina na kosa kidawo, dan akwai abubuwa dayawa danakeso agurinki. Dariya maman zainab tayi tace nikaina kina raina, amma insha Allah babu inda zamu kara zuwa, koma zamuje wani guri sede idan Zainab tasamu hutu, yanzu de ba wannan ba, nifa yau nazo acikamun alkawarina, Wlh har kosawa nayi mudawo, na matsu inji labarinki, musamman danaji kince labarinki yafi nawa. Labiba zatayi magana wayarta tayi kara, tana dauka Abbas yace momyn Ansar gamu nan afalo tare da Yaya, Akawo mana abinci, tace to yallabai, murmushi maman Zainab tayi tace e lallai nafara ganin canji, dariya Labiba tayi tace ba dole ba, ai naji dadin shawararki, Baride indawo kisha labari, ammade Baban Zainab zezo daukarki ko? Tace e nama yimashi kwatancen gidan tunda nazo yace yagane, idan mungama zezo yadaukeni, shima yana gurin abokinshi. Dariya Labiba tayi tace to bara indawo kisha labarina da Abbas. ASALIN LABARIN ABBAS ALEE DA LABIBA. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 75 🔱 80 ASALIN LABARIN ABBAS ALEE DA LABIBA. Abbas Alee su 2 ne, agurin iyayenshi, shida kaninshi Umar, mahaifiyarsu ita kadaice agurin mahaifinsu, Abbas shine babba, mahaifinsu Mal. Alee bawani arziki gareshi ba, kasuwa yakezuwa yana kasuwanci, Duk da rashin wadatarshi behana yasa yaranshi makaranta ba, Ummansu Abbas tana sana,ar cikin gida, kasancewarta mace me kirki batada nuna kyashi akan abun hannunta, Idan har yaranta suna bukatar wani abu na makaranta inde befi karfinta ba, ita take basu, alokacin da Abbas yagama secondary school haka mahaifinshi yasashi gaba suka rika zuwa kasuwa, kafin takardunshi su fito, Abbas mutum ne, me ladabi da biyayya, gashi da hakuri, da juriya, akullum maganar mahaifinshi daya ce, Abbas aduk lokacin dakasamu kudi kada kabari ka kashesu abanza, kasamu kasayi fili kobaka ginaba wata rana zeyi maka rana, Kana ganin yanda na dage nagina wannan gidan damuke ciki, nasan bawai yana da girma ba, ciki da falo ne, kawai nasamu na gina se bandaki, haka muka rayu da Ummanku, Se bayan an haifi Umar ne, naga dakin baze ishemu ba, shine nasamu nayi maku wancan dakin azaure, Abbas shi MUHALLI dakake ganinshi daraja gareshi kafin insamu nawa nasha wahala nida Ummanku, Hakan yasa lokacin da mahaifina yarasu, aka raba mana gado, dama ni daya ne agurin mahaifiyata, kuma dama dana auri Ummanku agidanmu muka zauna, bayan anraba mana gado sauran yan uwana sukace basu yarda abar gidanmu ba, sede asayar abama kowa kudinshi, Da mutane sukaga abun ze zama rigima shine aka kaimu gurin megari, bayan anyi bayani masu rabon gado sukace gidan baze tsagu abama kowa ba, se megari yace shikenan ayima gidan kudi shize siya, Bayan yabada kudi aka raba kowa ya anshi nashi, megari kuma yabamu kwanaki mubar mashi gida, haka nadauki wannan kudin na kama mana haya, sauran kuma nasaro kaya dasu nafara saidawa, Cikin ikon Allah kasuwan cina yafara yawa, haka narika tara duk wata riba dana samu, bama cin abinci medadi, haka Ummanku tayi hakuri dani, har Allah yasa kudina suka taru nasayi fili, Ahankali nacigaba da tara kudi, wannan ginin da kake gani, da hannuna na ginashi, akwai wani abokina shine kadai nasan ya temaka mun agurin ginin, aranar dana gama gina gidan nan, aranar aka haifeka, Bakaramun dadi naji ba, farin cikina yazamo biyu, seda akayi sunanka sannan muka koma sabon gidanmu, acikin yan uwana haryanzu babu wanda ya mallaki gidan kanshi, Shiyasa aduk sanda na kwanta nakejin wani farin ciki yana rufeni idan natuna wannan gidan nawa ne, da gumina na ginashi, shiyasa nayi alkawarin tsayawa akanku inga nabaku ilimi wanda zaku dogara dashi, Dan haka Abbas kaga yanzu girma yafara zuwa maka, koyanzu zaka iya yin aure, tunda sa,anninka biyu sunyi aure, shiyasa daka gama makaranta nace murika zuwa kasuwa da kai, nafiso tun daga yanzu kafara tara kudin siyan fili, Bazanso ace zakayi aure bakada MUHALLI, idan kasamu naka, nasan ko bayan raina zaka iya kula da kaninka, Abbas yace insha Allah Baba zanyi kokari in mallaki gidan kaina, Wannan labarin daka bani kadai ya isa yazamo darasi akan kowa, fatana Allah yabani ikon samun takarduna, kaga idan nagama karatuna nasamu aiki zantemakeku sosai, murmushi Babanshi yayi yace Abbas kenan, Allah yatemakeka, amma kasani banaso ka dogara da wannan karatun, nafiso kabada karfi akan kasuwan cinka, dan kasuwanci yamun abinda har in mutu bazan manta ba, Inda ace nima karatun nayi kaga dole senajira nagama, sannan inzo inyi zaman jiran samun aiki, kafin infara daukar albashi inyasi gida, dan haka koda kasamu shiga makaranta nafiso ka cigaba da kasuwancinka, Kaga seka hada biyu, Abbas yace shikenan Baba zanyi yadda kace, tundaga ranar Abbas yakara dagewa akasuwa, duk kudin daya samu Babanshi baya karba, asusu yasaya mashi, Akullum yake zuba kudi aciki, ana cikin hakane wata rana yahadu da LABIBA tafito daga gidan kakarta, tunda Abbas yaganta yaji sonta yashiga zuciyarshi, Alokacin suna zaune shida abokanshi, Jafar yana kusa dashi, hakan yasa yayi saurin tabo Jafar yace abokina kasan waccan yarinyar? Jafar yakalli inda Abbas yake nuna mashi, Dariya yayi yace gaskiya ban santa ba, daya daga cikin abokanshi yace ai Labiba ce, bata dade da dawowa nan unguwar ba, agurin kakarta take, Abbas yace Jafar gaskiya inasonta, Dariya suka saka daya daga cikinsu yace haba Abbas, duka yaushe ka gama secondary da har zaka fara maganar soyayya? Daure fuska Abbas yayi yace amma naga nida Usman shekararmu daya amma shi haryayi aure, Jafar yace rabu da Buba kasanshi da tsokana, kabari anjima zan rakaka gurinta, bade munsan sunanta ba, kuma munga gidansu ba, murmushi Abbas yayi yace yauwa abokina, dama nasan kai kadai kake goyon bayana, Aranar Abbas da Jafar sukaje gidansu Labiba, bayn tafito Jafar yayi mata bayanin abinda yake tafe dasu, itama tunda taga Abbas taji ya kwanta mata, babu bata lokaci ta amince mashi, Sundade kafin suka tafi, tundaga ranar soyayya me karfi tashiga tsakaninsu, abokanshi babu wanda besan suna soyayya ba, kakar Labiba tasan Abbas, kamar yanda Ummanshi tasan labarin Labiba, Sede koda tafadama Babansu yakira Abbas yace mashi, Abbas naji wani labari agurin Ummanku, bazan hanaka abinda kakeso ba, amma shawara daya zan baka, idan har yarinyar tana sonka, to tayi hakuri kasamu gidan kanka, Wannan shine babban burina arayuwa, bazan so ace kayi aure bakada MUHALLIN dazaka zauna ba, Abbas nasan ciwon rashin MUHALLI, hakan yasa duk wani wanda zeyi aure nake mashi sha,awar samun MUHALLINSHI, Wlh gara ace bakada abincin dazakaci, bakada sana,aryi da ace bakada MUHALLI, duk wadan nan abubuwan dana lissafo maka, masu sauki ne, idan kanada MUHALLI koda bara kakeyi kuna samun abinci kasan de akarshe gidanka zaka dawo ka kwanta, Kuma idan kafita bara dole kasamu wani yabaka, amma idan bakada MUHALLI, babu wanda ze dauki gida yabaka, ko kuma yarika biya maka haya, Yau ko nine nake biya maka haya wata rana dole ingaji, bare kuma ace wanine wanda baka hada komai dashi ba, sannan idan bakada sana,a hankalinka zefi kwanciya idan katuna babu wanda zezo yace kabiya kudin haya, Wannan ma bakaramin abu bane, dan haka nide bazance kada kayi aure ba, amma nafiso ka mallaki gidan kanka, idan har kanason yarinyar, nizanje innema maka aurenta, amma da sharadi, Nafarko seka gama ginin gidanka sannan za,ayi aurenku, kuma idan har kasamu makaranta zaka cigaba dazuwa, idan har kayarda da haka, ni kuma zanje insamu iyayenta muyi magana. Abbas yasauke ajiyar zuciya yace bakomai Baba na amince, nidama ba ina nufin inyi aure yanzu ba, kawai ina tsoron kada wani wanda yashirya aure yazo yacanza mata ra,ayi, kasan mata sunfison da sunsami saurayi suyi aure. Murmushi Babanshi yayi yace Abbas shifa rabon mutum baya taba wuceshi, duk abinda kaga mutum yasamu ba wayonshi ko dabararshi bace tasa yasameshi ba, Idan har Allah yarubuta seka auri Labiba, to kozakayi shekara nawa baka aureta ba, babu wanda ze aureta se kai, dan haka ka kwantar da hankalinka, banaso kasaka wani abu aranka wanda zekawo maka matsala arayuwarka, Kuma ka dage da addu,a idan Labiba alkhairice agareka Allah yabaka ita, idan kuma babu alkhairi atsakaninku Allah yayi maka canji da mafi alkhairinsa. Abbas yace amin Baba,kuma naji dadin wannan shawara, Insha Allah zandage gurin ganin na mallaki muhallina na kaina, Babanshi yace Allah yasa, anjima zamuje gidansu nida abokina semuyi magana, Abbas yace ai agidan kakarta take dazama, Babanshi yace to idan munje setayi mana bayanin inda zamuje, sosai Abbas yaji dadin maganar Babansu, Bayan magriba sukaje gidansu Labiba, dayake Labiba tafadama kakarta, hakan yasa ta aika aka kirawo kawun Labiba, koda sukazo sun sameshi, Bayan sungama gaisawa sukayi bayanin abinda yake tafe dasu, kawun Labiba yace ai babu damuwa, tunda yara suna son junansu, mu namu addu,a ce, kuma duk lokacin da yaro yashirya, babu damuwa se adaura auren, Naji dadin abinda kukace, kuma dama duk wani Uba me kishin danshi, bazezo ace suna zaune agidan haya ba, mutane ne basa ganewa ka mallaki MUHALLINKA Yafi kaje kana biyan kudinka awani guri, Allah yayi mana jagora, Sukace amin, anan suka bada kudin neman aure, sukayi addu,a sannan suka tafi, da Abbas yasamu labarin abinda yafaru rasa inda zesa kanshi yayi saboda farin ciki, Tundaga ranar soyayyarsu da shakuwarsu takara yawa, kuma kullum yake zuwa kasuwa, sosai yakara dagewa gurin saka kudi a asusu, ada koya saka seya ciro idan yaji bayada kudi, Amma ayanzu gara yazauna beda ko sisi daya taba kudin asusunshi, sede yaje Ummanshi tabashi, duk wani kayan kyale kyale ya hakura dasu, shiyasa acikin abokanshi yazamo baya agurin gayu, har tsokanarshi sukeyi, amma baya nuna damuwarshi, Duk da abun yana damunshi, dan wata rana suna zaune zakaga kowa yana siyan abu sunaci, sede suyi mashi bismillah, sam baya cin abunsu, sede idan Jafar ne, Yabashi, Ganin abun nasu yana kona mashi rai, hakan yasa yarage zuwa majalissarsu, sede su hadu da jafar, ana cikin haka yasamu admission a poly sunbashi fannin kasuwanci, Bakaramin dadi yaji ba, sede babban tashin hankalinshi yasan dole yataba asusunshi, tunda Babansu bawasu kudi gareshi ba, alokacin da kyarma aka samu rabin kudin registration din, ganin dole seya taba kudin asusunshi yasa yace yafasa karatun. Babu yanda Babanshi beyi dashi ba, akan yadauka aciki zekara samun wasu, amma yace ya hakura, lokacin da Jafar yaji abinda Abbas yace, hakan yasa yadauko wasu kudinshi dayake tarawa, be bari Mamanshi tasani ba, Haka yakawo ma Abbas yace yaje yabiya, Abbas yace bazan karba ba, haba Jafar, kai meze hana kabiya ma kanka kaima kayi karatun, nimafa inadasu, kawaide nasan idan natabasu zan iya rasa damar auren Labiba, Nikuma da inrasa Labiba gara na hakura da karatun, wanda nayi ya isa, zan cigaba da kasuwancina, mutane nawa ne, sukeda kudi ta hanyar kasuwanci, Wasuma ko aji basu taba shiga ba, dan haka nima na hakura, jafar yace haba Abbas, kasande nine banida ra,ayin wucewa makaranta, shiyasa nabaka kudin, ni nafison kasuwanci, Kaifa nafi kowa sanin dole ce tasaka kake zuwa kasuwa, tun muna makaranta nasan bakada ra,ayin kasuwanci, kawai kana bin umarnin Baba ne, dan haka ka anshi kudin nan, kuma ni kyauta nabaka, banaso kafada ma kowa nine nacika maka kudin, kawai kace asusunka ka fasa, Abbas yace Jafar, wlh ada ne, banason kasuwanci, amma yanzu haduwata da labiba inason kasuwanci sosai, domin ta dalilinshi gashi ina tara kudin dazan samu Labiba, Ayanzu nagane cewar kasuwanci abune me daraja, dan haka kabar kudinka, jafar yace naji, amma bara kaji, wlh, idan har baka anshi kudin nan ba, babu ni babu kai, Juyawa yayi zetafi, dasauri Abbas yarikoshi yace yi hakuri abokina, naji zan amsa, nagode sosai da kulawarka, tabbas kai abokine nagari, Allah yabani ikon yimaka koda rabin abinda kake munne, Murmushi Jafar yayi yace amin, rungume juna sukayi, washe gari Jafar ne. Yarakashi sukaje sukayi komai, bakaramin dadi Baban abbas yaji ba,alokacin dasuka fada mashi sungama komai, Aranar monday Abbas yafara zuwa makaranta, daya dawo da yamma kuma yawuce kasuwa, yana dawowa yanufi gurin abun sonshi. WACECE LABIBA? Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 80 🔱 85 WACECE LABIBA? Labiba yar asalin kano ce, ita kadai iyayenta suka haifa, tayi primary da secondary, babu laifi iyayenta suna da rufin asiri, mahaifanta suna sonta sosai, Duk wani abu najin dadi suna yimata, akusa da gidansu akwai wata kawarta, mesuna Hauwa, tare sukayi karatunsu, komai zasuyi tare sukeyi, kawayene sosai, A unguwar sallari suke dazama, mahaifinta dan jigawa ne, kasuwanci yakawoshi kano harya hadu da maman Labiba sukayi aure, alokacin Labiba tana aji 3 asecondary school, Sosai mahaifinta yake kaita gurin yan uwanshi ajigawa, kasancewarshi su 2 mahaifiyarsu ta haifa tarasu, dagashi se kanwarshi, sauran duk ubansu daya, Kanwarshi agurin haihuwa itama tarasu, hakan yasa yadawo beda wata yar uwa makusanciya, sede yan uba, yana sane da irin bakin cikin dasuke nuna mashi, amma hakan besa ya yanke zumunci dasu ba, Idan Labiba tasamu hutu, yakan kaita tayi ko sati 2 ne, duk da mamanta bataso amma hakanan take hakuri dan tasan yanda mijinta yakeson yan uwanshi, Acikin kannanshi mutum daya ne, yabiyoshi kano shima yafara kasuwanci, shine Labiba take kira da Kawu karami,shi beda irin halin sauran yan uwanshi, Hakan yasa yake zaune da yayanshi lafiya, ahaka yasamu yasayi gidanshi yayi aure anan kano, lokacin da Labiba tayi J,S,C,E tasamu dogon hutu, Hakan yasa Mahaifinta Alh, Lawal yakaita jigawa gidan yaynshi tayi hutu, alokacin har kuka tayi dan batason zuwa gidanshi, kuma bataso arabata da kawarta Hauwa,tace mashi yabarta taje gidan kakarta acan darmanawa, yace tayi hkr idan tadawo setaje, Seda tayi sati 2 sannan iyayenta suka shirya zuwa daukota, akan hanyarsu ta zuwa jigawa sukayi hadarin mota, babu wanda yarayu, lokacin da labari yasami yan uwanshi bakaramin tashin hankali suka shigaba, Labiba kuwa sumanta 3, da kyar aka samu tasamu sauki, anan jigawa akayi zaman makoki, acan kano kuma iyayen mamar Labiba sukayi nasu zaman makokin, Bayan sati daya da rasuwarsu, Kawu karami yace abashi Labiba yatafi da ita gidanshi, tunda bata gama karatunta ba, sam babban yayansu yace beyarda ba, ayanzu shine yakeda hakkin rike Labiba, Domin shine babba, makaranta seta cigaba anan, Kakarta ma tace abata ita amma yaki yarda, haka tayi hkr tabarta, Labiba kuwa kuka tasa tace ita tafiya zatayi, dan tasan halin Kawunta, Sam beda kirki, shida matarshi, hakade yadage dole seda aka barmashi ita, shida kanshi yasa akayi rabon gado, bayan angama yace yaza,ayi da na Labiba? Sauran yan uwanshi sukace ai shine zerike mata, Tunda shine marikinta, murmushi yayi, aranshi yace nasan za,ayi haka ai, shiyasa nadauki rikonta. Da kanshi yasama mata makarantar gwamnati, bakaramin haushi Labiba taji ba, Dan kawai babu iyayenta shine za,a maidata makarantar gwamnati, aranar tasha kuka, hakanan ta hakura tafara zuwa makarantar, data dawo gida kuma tayi aiki, Sam kawunta baya bata kudi, na makaranta ma kudin zuwa kawai yake bata, nadawowa kuma ta dawo akafa, acikin lokaci kadan kamanninta suka canza, haka tacigaba da hakuri, harta shiga aji 5, Alokacinne tace bazata koma makarantar ba, saboda wahalar datake sha, aranar tafita makaranta kawai ta gudu zuwa kano, koda taje kakarta har kuka tayi ganin yanda jikarta ta koma, hakan yasa tasa aka kira kawunta karami, Shima ranshi bakaramin baci yayi ba, yacema kakar tarike Labiba zeje yasamu yaynsu kome sukayi ze fada mata. Alokacin daya samu Yayansu da sauran yan uwanshi da maganar, kowa ranshi yabaci, gani sukeyi yanaso yacima yaynsu fuska, ya goyi bayan bare, Yayansu yace shikenan, yayarda ze barma kakar Labiba ita, amma da sharadi, babusu babu ita, kome za,ayi mata kada anemesu, kuma maganar gadonta tariga data cinye abunta, Tundaga kudin makarantarta harzuwa abincin dataci, dasauran kayan daya siya mata, dan haka yanzu babu ko sisi nata agurinshi, Kawu karami har kuka yayi, dayaji bayanin yayansu, Jiyake inama ace mamansu daya da mahaifin Labiba ba yayansu ba, yanaji yana gani ancinyema yarinya kudinta, goge kwallanshi yayi yace shikenan yaya, amma inaso infada maka kaji tsoron Allah, Duk wanda yaci kudin maraya wlh wuta yacima cikinshi, kuma insha Allah zamu rike Labiba, domin mahaifinta yayi mani gata, harma daku kanku, amma zaku saka mashi da sharri, Saukar marin dayaji ne yasashi yin shiru, Yayansu yana huci yace banason sakarci, tsakanin Lawal dani wanene makusancinka, da harzaka rufe ido kana fadamun abinda kaga dama, to kaima bara kaji, kada insake ganin kafarka agidana, kaje kacigaba da zama akano. Tashi Kawu karami yayi ranshi abace yace naji Yaya, bazaka kara ganina ba, kuma insha Allahu yarinyar da kuka cuta wata rana setazamo abin alfahari acikin al,umma, Haka yafita, ranshi bace, koda yafada ma Kakar Labiba abinda yafaru itama har kuka tayi, tarokeshi akan yabar mata Labiba, yace shikenan amma dan Allah duk wani abu daya shafeta arika sanar dani, Nayi alkawarin zan zame mata Uba, kuma maganar makarantar ta zata cigaba, sosai Kakar taji dadi, bayan yatafi Labiba tashigo Kakar tabata labari, itama kuka tasaka,kakar tace bakomai kanshi ya cuta, nide Labiba kobayan rai na, kada kiyarda kawunki, aduk yan uwan mahaifinki babu mesonki kamarshi. Bayan kwana 2 kawu karami yasamo mata makaranta, haka tacigaba da zuwa, nan suka cigaba da kawancensu da Hauwa, Labiba tana da hankali, sede tana da saurin yarda da shawarar kawayenta, hakan yasa batada ra,ayin kanta, kome zatayi seta tambayi Hauwa, Ita ko Hauwa, tana da wayo sosai, shiyasa kome zatayi tafiso itama Labiba tayi irinshi, ahaka har suka gama makaranta, sede Labiba ba ruwanta da kula samari, sabanin Hauwa, ita akwai kula samari, Duk wani abun bukatar ta samarinta suke mata,ita kuma seta bama Labiba, dan tanaso itama tafara kula samari, Labiba duk abinda tanema kawunta yana mata hakan yasa tasaba da jindadi. Ana cikin hakane kuma suka hadu da Abbas. CIGABA.......... Sosai Abbas yake gane karatunshi, ga kasuwanci yanayi, alokacin da Babanshi yasashi yabude asusunshi sun sami kudi masu yawa, hakan yasa yaje yayi mashi cinikin wani fili kwata ne acan kasan unguwarsu, Sede gidanjen gurin duk na talakawa ne, shiyasa fili yake arha agurin, sosai Abbas yaji dadi aranar da akasiya mashi fili, hakan yasa yanufi gidansu Labiba da murnarshi. Zaune suke afalon baki bayan sungama gaisawa Abbas yace Labibata albishirinki, tace goro, murmushi yayi yace yaude Allah yanufa na mallaki Fili da kudina, Dariya tayi tace da gaske Abbas? Yace da gaske, kinga ma takardun filin, abinda yaragemun yanzu infara gini, Labiba tace amma gaskiya naji dadi sosai, awace unguwa kasayi filin? Allah de yasa unguwar yan gayu kasamu. Saurin kallonta yayi yace Labiba kenan, kinsan banida kudin dazan iya siyen fili a unguwar masu kudi, wancan ma dana siya kwata ne, ko rabi be kaiba, kinga yanzu dana kara samun kudi se infara mana gini koda na kasa ne, se inyi mashi shafen siminti, Bata fuska Labiba tayi tace haba Abbas, wato gidan ma ba,a unguwar yan gayu ba, sannan kuma ginin kasa zakayi mana, haba ai sekasa kawayena suyi mani dariya, nide ina ganin kawai kasaidashi kaje wata unguwar kasiya mana wani. Wata irin zufa ce yaji tafara zubo mashi, kallonta yayi yace haba Labiba, banzaci wannan maganar daga bakinki ba, tashi tayi tace shikenan, sekayi yanda kakeso, Saurin rike hannunta yayi yace yihakuri, haba Labibata, daga magana zakiyi fushi, shikenan zanje induba kinji abinso na, murmushi tayi tace tonaji, haka sukayi sallama gaba daya ran Abbas abace yake. Kai tsaye gidansu Jafar yawuce, harwani jiri yake gani saboda tashin hankali, yasan Labiba tana sonshi, amma akan wannan gidan zata iya rabuwa dashi, dan tasha fada mashi, Tana son rayuwar yan gayu, tana son gida mekyau, hakan daya tuna bakaramin tashin hankali yaji ba, yana zuwa dakin jafar yasameshi akulle, kasan cewar yana da mukulli hakan yasa yabude, yana shiga ya kwanta, Wasu zafafan hawayene suka fara zubo mashi, jiyake kamar yarasa Labiba yanzu duk irin wahalar daya sha kafin yatara kudin fili yanzu haka ze hkr dashi, lokacin da,aka bashi Labiba har dako yake dauka duk dan yasamu yatara kudi masu yawa. Kai yafara girgizawa, aranshi yace gara inrasa komai da inrasa Labiba, haka yayita sake sakenshi har Jafar yadawo, lokacin dayaga Abbas seda gabanshi yafadi, dan betaba ganinshi cikin irin wannan yanayinba, Zama yayi yace Abbas lafiyarka kuwa? Tashi zaune yayi yace shikenan Jafar zan rasa Labiba, dan Allah muje asamu wanda zesayi filina Labiba batason shi, kuma kasan akwai manyan masu kudi da suke sonta, Ni nasan saboda wannan matsalar zata iya hakura dani, kasan babu abinda Labiba takeso kamar hutu. Jafar yace wai lafiyrka Abbas? Ka nutsu kafada mun abinda yake faruwa, share hawayenshi yayi nan yafada ma Jafar yanda sukayi da Labiba. Tsaki Jafar yaja daya gama jin labarin Abbas. Cike da takaici, hade da tausayin abokinshi yace haba Abbas, kanka daya kuwa? Wai me kamaida mace ne arayuwarka? Shikenan kadauki son duniya kadorama Labiba, Inaji ko Umma baka mata irin son dakake ma Labiba, ayanda kasha wahalar tara kudinka ninasan ko Ummace tace kasaida filinka bazaka yarda ba, wlh Abbas inajimaka tsoro akan son da kakema Labiba, duk da nasan itama tana sonka, Amma bazata taba yimaka irin sadaukarwar da kake kokarin yimata ba,yanzu idan kasayar da filinka, ina zaka samu kudin dazaka cika kasayi wani? Ai ko Baba baze taba barinka karabu da filinka ba, Shawarar dazan baka, idan har kanason ka mallaki Labiba dole ne kayi abinda zan fada maka, ai dasauri Abbas yace fada inji, zan dauka, inde hakan zesa insamu labiba. Murmushi Jafar yayi yace lallai Abbas kayi nisa bakajin kira, to da farko de dole sekayi karya, abinda nake nufi ka gwada mata cewar ka saida filin kasayi wani, kuma ahankali zakayi gini me kyau, Kuma inaso daga yau kada ka kara fada mata halin da kake ciki akan gininka ko kuma wani abu naka, hakan zesa kasamu sauki, idan kagama gininka ai bazata zo tagani ba, asalima se ankawota zata san gidan, Kaga alokacin tariga tazama taka ko agidan bukka kasata zata zauna, inde tana sonka. Murmushi Abbas yayi yace kai amma nagode, harnaji dadi, shiyasa nake sonka, Allah yabarmu tare, Yace amin, anjima sekazo muje ninasan mezan cemata, kasan mata se anayi masu karya, dariya Abbas yayi yace hakane, shiyasa takemun yanda taso kasanni ban iya karya ba, yanzu kai ya maganar Maryam? Dariya Jafar yayi yace lafiya lau, gobe ma su Kawu zasu kai kudin neman aure, kasan nima acikin satin nan zanfara gini, Abbas yace to Allah yate maka, muje ka rakani induboma Umar jarabawarshi ance tafito, Allah de yasa yasamu abun kirki, dan kasan Umar hankalinshi baya kan karatu yafison kasuwanci, Jafar yace ai da gaskiyarshi, tunda de yasamu na YES da NO ai yawuce komai, Kaga ko ina ze iya shiga beda damuwa, dama amfanin mutum yasamu ilimi ko kadanne kafin yafara kasuwanci baza,a cuceshi ba, Abbas yace ai shikenan muje mugani idan basuyi kyau ba, kawai seya cigaba da kasuwancinsa. Seda suka uba mashi, kamar yanda Abbas yayi zato haka suka samu. Daga Hausa se islamic kawai yakeda pass, Abbas yace shikenan Allah yabashi sa,ar kasuwancin. Daga nan sallar magriba kawai sukayi suka wuce gidansu Labiba, bayan sungama gaisawa Labiba tace Jafar kwana 2 ka boye, dariya yayi yace naje unguwane, dazu nadawo, naje gurin Abbas shine yake fada mun wani abin alkhairi, Natayashi murna dayace yasayi fili, amma yana fadamun unguwar daya sayi filin raina yabaci, Labiba tace yauwa kaima beyi maka ba ko? Jafar yace wane irin ma yi, haba yama za,ayi inbar Abbas yazauna a unguwar nan, Aise abokanmu suyi mana dariya, kinsan Allah yanzu ma dande dare yayi da ayau za,a maida masu takardunsu subamu kudinmu, Nifa tuni nayi mashi cigiyar wani fili a sallari kawaide tafiyar danayi ce tasa ban fada mashi ba, dariya Labiba tayi tace wlh Jafar har kasa naji dadi, ai dama nasan bada kai Abbas yasayi filin ba. Jafar yace kibarshi kawai, gobe zamu maida masu, tace amma nagode sosai Jafar, yace ba komai bara inbaku guri, kallon Abbas tayi tana murmushi tace harnaji dadi wlh, murmushi yayi, yana tausayin kanshi duk ranar da Labiba tagane gsky. Bewani dade ba yayi mata sallama suka tafi, ahanya yace amma gaskiya Jafar ka iya karya, dariya yayi yace kaide kazauna komai gaskiya, aikasan akwai karyar da mutum zeyi dan ya ceci kanshi. Tun daga ranar hankalin Labiba ya kwanta, bakamar da Abbas yace ansayi wani filin, tundaga lokacin tadena yimashi maganar gida, haka sukaci gaba da soyayyarsu, alokacin Abbas yashiga shekarar karshe amakarantarsu, Kasan cewar shekara 2 ce, ahankali yafara yin bulo na kasa shida Jafar da Umar sukeyi, sosai mahaifinsu yaji dadi ganin zasu fara gini, hakan yasa shima yarika tayasu kwaba kasa, Hauwa ce da Labiba adaki suna fira, hauwa tace Labiba jiyafa aka kawo kayan sa ranata, Labiba tace kai da gaske? Shine ma baki fadamun ba seda aka kawo, Hauwa tace kiyi hkr wlh abunne yazo akure, Bafa daniyar sa rana sukazo ba, kawai Abban mu yace asaka rana, kuma kinsan wata guda aka sa, Labiba tace amma naji dadi, wanene wannan me sa,ar? Hauwa tace wlh baya cikin samarina, bamu dade da haduwa ba, Yanuna mun da gaske yake, amma yacemun a Dambatta yake kasuwanci yakeyi acikin kano, shine ma yakama haya a irin gidan gwamnatin nan yake zaune aciki, To yace yanada gida a Danbatta, idan can nakeso akaini to, ai kinsanni da son gidan yan gayu, gidan gwamnati fa harda gurin sa dining table, ke bama wannan ba ya za,ayi ina cikin kano inyarda akaini kauye, Shine nace mashi nafison nan toyanzu anan zaya ajeni. Dariya Labiba tayi tace kai amma kinburgeni, yama za,ayi akaiki kauye,ai ko cikin birni bazamu yarda akaimu unguwar talakawa ba, nan tabata labarin yanda sukayi da Abbas. Hauwa tace kinmun dede ai yanzu ba soyayya ake ciba, kawai kasamu gidan hutu, Labiba tace a,a wlh kema kinsan ina mutuwar son Abbas, kawaide dan banason zama irin unguwar nan dabazan hanashi ba, Amma nafison nayi auren soyayya akan na kudi, Hauwa tace tonaji nizan tafi, bikina baza,ayi anko ba, dan lokaci ya kure, idan kinsamu lokaci kishigo muyi sauran shirye shiryen. Abbas ne zaune abisa kujera suna fira da Ummanshi, kallonta yayi yace wai Umma tundazu naga kamar akwai abinda yake damunki? Ajiyar zuciya tayi tace wlh Abbas tundazu nakejin gabana yana faduwa, Murmushi yayi yace kila kishiya Baba zeyi maki, murmushi tayi tace tazo mana, kaga se kubar mata dakinku, dariya yasa, zeyi magana yaji ana sallama, amsawa yayi yafita, Bayan sungama gaisawa, mutumin yace mashi dan sanda ne, anyi mashi kwatancen gidan nan amatsayin gidan Mal, Alee, Abbas yace hakane. Nan ne gidan, kuma nine babban danshi. Mutumin yace to dama yasamu hadarine. Ahanyarshi tadawowa gidan wata mota tadaki adedetarsu, sede yafi kowa jin ciwo, wanda suke tare dasauki dan shinema yayi mani kwatancen gidan. Cike da tashin hankali Abbas yace inazuwa, gidan yakoma yasanar ma Ummansu, tashi tayi tace zata bishi, yace kiyi hkr Umma shima amashin yake bari inje inga jikin nasu, ance Umar dasauki nashi, fita yayi, yabarta tana kuka. Ko kafin suje asibitin har Babansu yacika, suna zuwa Abbas yazube akanshi yana kuka, da kyar aka cireshi daga jikinshi, nan akayi duk wani rubutu, sannan suka bada mota domin akaishi gida, dan wanda ya kadesu guduwa yayi. Ummansu Abbas bakaramin tashin hankali tashiga ba, nan da nan gida yacika da mutane, dayake magriba batayi ba, hakan yasa aka shiryashi aka kaishi MUHALLINSHI na gaskiya. (Lallai MUHALLI YANADA DARAJA, SHIYASA HATTA GAWA SEDA AKA SAMA MATA MUHALLINTA. ALLAH KABAMU IKON CIKAWA DA IMANI AMIN). Haka akayi zaman makoki harna kwana 7 kafin kowa ya watse, Abbas duk yafita hayyacinshi, Jafar ne, kadai yake lallashin shi, haka suka cigaba da zaman jimami, har suka hakura Abbas yacigaba da zuwa makarantarshi, Umar kuma yacigaba da zuwa kasuwa, Ayanzu dole ginin Abbas yaja baya, saboda yanzu shine yake rike da gidansu, damma Ummansu tana sana,a shiyasa ba kullum suke aiki ba, shiyasa ma yakirawo me zanen gida aka fidda mashi ciki da falo se kitchen da bandaki, kasancewar filin ba babba bane hakan yasa gidan beyi wani girma ba, haka suka fara gini shida Umar, dan jafarma yana gurin nashi ginin, dande shi masu aiki yadauka. Duk ranar da babu makaranta ranar agurin aikin gidan suke wuni, dan shima Umar aranar baya zuwa kasuwa, abokanshi har magana sukayi mashi akan yasamu masu aiki su gina mashi amma yace beso, Danshi aganinshi kudin daze biya masu aiki sun isa yayi wani abun dasu, gara yanzu suyi da kansu. Idan lokacin da zesa masu aikin yazo seya biya su karasa mashi. Gulmar da abokanshi sukeyi ne yasa Jafar yace sudena zama agurinsu tunda basu da kirki, tun daga ranar suka dena zama gurinsu, acikin haka ne akayi bikin Hauwa, Ranar da aka kaita gidanta shima Abbas yaje gurin Labiba da dare, tunda tafito take fadin gaskiya Abbas unguwarsu Hauwa ta burgeni, kalli gidajensu ba ruwan kowa da wani, kowa yana gidanshi, Kalli kowace hanya akwai titi, damma bakaga cikin gidan ba, komai acikin gida yake, kai koruwan sama akeyi mutum bazesan anayi ba, dan babu ta inda ruwa zeshigo, basuda tsakar gida, ko rana mutum seya fito nan waje zesan anayinta. Itakam Hauwa taji dadinta wlh, dama nice nasamu wannan gidan, tunda tafara magana Abbas yake kallonta, seda tagama sannan yace amma kuma gidanshi ne? Kai ta girgiza, Murmushi yayi yace ai kinfita, tunda ke gidan daza,a sakaki gidan mijinki ne, itafa? Shekara tana cika idan be biya kudin haya ba, za,a iya korarshi daga gidan, bata fuska Labiba tayi tace aide nasan gidan dazaka gina mun baze kai wannan ba, Kuma dade ace mutum yana irin gidanka ai gara ace haya yakeyi inde gidan hayar yana da kyau nide yafiyemun da,ace mallakin mutum ne, sakin baki Abbas yayi yana kallon Labiba, zuciyarshi yaji tana bugawa dasauri. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 85 🔱 90 Hannu biyu Abbas yasa yadafe kirjinshi, kanshi yaji yasara mashi, da sauri yadafe kanshi, yasamu guri yazauna, hankalin Labiba yatashi ganin yanayin da Abbas yashiga, Dukawa tayi tana fadin, lafiyade Abbas ko kanka yake ciwo? Kai yadaga mata dan baze iya magana ba,wayarshi yadauko yakamo number Jafar yabata, karba tayi tace kiranshi zanyi? E yace mata, Kira biyu Jafar yadaga, nan yaji muryan Labiba, tana fadin dan Allah Jafar kazo wlh Abbas beda lafiya ko magana yakasayi, Cike da damuwa Jafar yace kuna ina yanzu? Kwatancen gidan Hauwa tayi mashi, yace gashinan zuwa, Adedeta yadauka suka nufi unguwar, fifita Labiba take tayima Abbas, se jera mashi sannu takeyi, shikam yama kasa amsawa, zufa kawai take fito mashi, Adede lokacin Jafar ya iso, shida me adedeta ne suka kama Abbas suka sakashi adedetar, Labiba tace zata bisu, Jafar yace a,a tazauna dare yayi, kome kenan zasuyi waya, Kuka tasaka mashi ganin zata bata masu lokaci kawai yace me adedeta sutafi, nan suka barta tana kuka, kai tsaye asibiti suka wuce, suna zuwa aka kaishi wani daki, likita aka kira yazo yayi mashi aune aune, Sannan yasa aka kawo mashi allurai yayi mashi, aka saka mashi karin ruwa, nan take bacci yadaukeshi, likita yacema Jafar suje office, Bayan yagama rubutunshi, yadago ya kalli Jafar, cire glass din idonshi yayi sannan yace, agaskiya wannan dan uwan naka jininshi ya hau sosai, nayi mamakin abinda yasa jinishi ya hau har haka, Irin hakanefa zuciyar mutum take bugawa, gaskiya seyayi ahankali, bekamata ba, ace ashekarunshi yana gamuwa da irin wannan lalaurar, Ajiyar zuciya Jafar yayi yace wlh, Dr, nima bansan abinda yake damunshi ba, ada de nasan yana cikin damuwar mutuwar mahaifinshi, amma daga baya ya hakura, Amma kawai ina zaune sega wayarshi, ina dagawa naji wadda ze aura tacemun beda lafiya, inaji idan ma akwai wata matsala, to kila tsakaninsu ne, sede zan tambayeshi idan yafarka, Likita yace to gaskiya kabashi, shawara yayi ahankali, kada yayi wasa da rayuwarshi, inde macece wlh zata kaishi tabaroshi, godiya Jafar yayima Likitan, sannan yabashi wasu magunguna yace yasiya, Idan yafarka zasu iya tafiya, godiya yayi mashi yafita zuwa siyan magani, daga nan yaje yabiya sauran kudin, yakoma dakin da Abbas yake yazauna yana jiranshi, ganin dare yafarayi, yakira Ummansu Abbas yace ga Abbas nan agidansu Yasha maganin mura ne kuma bacci yadaukeshi, ze kwana nan, Umman tace ai bakomai, Allah yabashi lafiya, kashe wayar yayi yacigaba da kallon Abbas,yana me kara jin tausayinshi, yasan irin son dayake ma Labiba, yanzu haka wani abun tayi mashi. Segurin karfe 10 Abbas yafarka, sosai yaji dadin jikinshi, sam babu ciwon kan, nan wata nurse tazo takara dubashi sannan aka sallamesu, ahanya Jafar yafada mashi yanda sukayi da Umma, hakan yasa suka wuce gidansu Jafar, Seda Abbas yayi wanka Jafar yahada mashi tea ya sha, sannan yasha maganinshi, kwanciya sukayi, anan Jafar yake tambayarshi abinda yafaru. Ajiyar zuciya Abbas yayi yace Jafar inajin Labiba ita zata zamo ajalina, wlh bantaba jin tashin hankali irin na yau ba, bansan meyasa Labiba takeson ta canza hali ba, Ni nasan Hauwa ce take zugata, inaji wata rana zan iya rasa Labiba, nide dan Allah katemakeni kada inrasa Labiba, Jafar yace yanzude kafadamun abinda yafaru, Nan Abbas yabashi labarin abinda yafaru, Jafar seda yazubar da kwalla saboda bakin ciki, jiyake dama shine Abbas, da babu abinda ze hana berabu da Labiba ba, tuna irin Son da Abbas yakema Labiba yasa Jafar yashiga kwantar mashi da hankali, Sosai yabashi shawara akan yanda zekara hakuri da ita haryasamu ya mallaketa, Jafar yace kasan duk abinda kakeso dole sekayi hakuri kake samunshi, Kaima idan kayi hakuri wata rana komai ze wuce, Abbas yace shikenan insha Allah daga yanzu data fara mun irin maganar nan kawai zanyi mata sallama, hakan shi zekawo mani mafita, haka suka cigaba da tattaunawa har bacci yadaukesu. Labiba kam aranar kasa bacci tayi, jitake datasan asibitin da sukaje data bisu, hakade tayi hkr, har bacci barawo yadauketa. Washe gari bayan sungama karyawa Abbas yayi wanka yasha magani, yace ma Jafar zetafi, sallama yayi ma Mamansu Jafar, se harararshi takeyi, Dazasu fita tace ma Jafar idan ka rakashi kazo inason magana da kai, Jafar yace to, bayan yarakashi yadawo, yana zama tace bangane kwanan da Abbas yazo yayi agidan nan ba? Nifa banason jaye jaye, Jafar yace wlh Mama beda lafiya ne, yasha magani shine bacci yadaukeshi, kinji abinda yasa ya kwana, amma kiyi hakuri baza,a sakeba, tsaki taja tace shikenan jeka, nibanga abinda yasa ka nacema Abbas ba, inbanda talauci babu komai ajikinshi, Ga sauran abokanka nan, ka kyalesu kana biyema wancan talakan, tashi jafar yayi yana bata hakuri yafita, sam bayajin dadin yanda Mamanshi takema Abbas, idan shine yaje gidan su Abbas, Ummanshi kamar zata hadiyeshi dan murna, amma shi Mamanshi ta kasa gane irin son dayakema Abbas. Abbas yana sauka kofar gidansu yaga Labiba zaune abisa dakali tabuga tagumi, idanunta har sun kumbura saboda kuka, dasauri yanufi gurinta har yana tuntube, Tsugunnawa yayi kusa da ita, yace Labibata meyake faruwa na ganki anan? Saurin dago kai tayi jin muryar Abbas, wani kukan tasaki batasan lokacin data fata jikinshi ba, Kasancewar atsugunne yake hakan yasa suka fadi kasa, tana samanshi, cikin sauri ya tureta ya mike tsaye hankali tashe, waige waige yafarayi, ajiyar zuciya yayi ganin babu kowa awajen, Hannu yasa yatada ta tsaye, janta yayi suka shiga zauren gidansu, suna shiga yasaketa, ahankali yakara kiran sunanta, dagowa tayi tana share hawayen idonta, Labiba kifadamun meyake faruwa naganki da sassafe haka, kuma ma ba gidan Hauwa kika kwana ba, amma naganki anan yanzu, kalli yanda fuskarki ta kumbura, dan Allah kifadamun abinda yake faruwa kinsan fa banda lafiya? Idanu tazuba mashi, ahankali tace dan Allah Abbas kayi hakuri, ko baka fada ba, nasan maganar dana fada maka jiya ita tayi sanadiyar shigarka awannan halin, wlh nima daga baya nayi dana sanin abinda nafada maka, Kayi hakuri bazan kara ba, kaji. Murmushi yayi, yana kallonta, yayin da soyayyarta take kara yawa azuciyarshi, hannunta yakamo yace bakomai, Labibata, nayafe maki, son danake maki baze taba barin zuciyata tayi fushi dake ba, Akullum ni meyafiya ne, agareki, tundaga laifin da kikamun, harma da wanda zakimun nan gaba nayafe maki, fatana Allah yabani ikon mallakarki, murmushi tayi tace amin Abbas dina. Sakin hannunta yayi yace muje ciki ku gaisa da Umma sekici abinci nasan bakici komai ba, turo baki tayi tace ni gida zantafi, bacci nakeji, jiya kasa bacci nayi, kuma Jafar yace zekirani yafadamun halin da kake amma bekira ba. Dariya Abbas yayi yace ai naji sauki, kallonshi tayi tace wai meya sameka? Gira yadaga yace bakomai, kawai ciwon Son Labiba ne, yake neman halakani, duka takai mashi tana fadin bawani dan Allah kafadamun, kaga se inkiyaye idan laifin daga gareni ne. Abinda likita yafadama Jafar shiyafada mata, rau rau tayi da ido tace tokayi hakuri kaji, insha Allah bazan kara bata maka rai ba, murmushi yayi yace Uhm Labiba kenan Allah yasa, tace amin, Fita sukayi seda yarakata har gida yace zaki koma gidan Hauwa anjima ko? Tace e amma senayi bacci sannan, yace yauwa gara kihuta, banason kina wahalarmun da kanki, tace angama Abbas dina, gida tashige tana dago mashi hannu, murmushi yayi yawuce gida. Haka sukaci gaba da soyayyarsu, babu abinda yakara hadasu, sosai Labiba take kiyaye duk wani abu dazesa Abbas bacin rai, hakan datakeyi bakaramin rura wutar kaunarta yayi ba, azuciyar Abbas, Gininshi yayi tsawo dan har ankai linta, rafta kawai za,ayi asa kofofi da windors, ayi shafen siminti se fenti, ba laifi ginin yayi kyau, hakan yasa suka tsaya da ginin dan sungama nasu, saura namasu aiki, kuma seya hada kudin daze biyasu, saukinshi ma yagama siyan kayan aikin. Sosai yakara dagewa wajen neman kudi, damma yanzu basa zuwa makaranta sosai, dan last semister exams zasuyi, tuni yagama project dinshi, hakan yabashi damar dagewa gurin zuwa kasuwa, Yanzu ba sosai suke haduwa da jafar ba, dan shima yana zuwa gurin masu gininshi dan nashima saura kawai yarage,saboda nashi akwai kudi, dan yafi Abbas samu sosai, kuma mamanshi tanada kudi, Idan kaga Abbas zakasan yarame, dan yanzu se yayi kwana 2 beji gurin Labiba ba,ga karatun exam, ga aikin kasuwa, ga rashin bacci, dan baya samun lokacin karatu se yadawo da dare, haka ze bata lokaci yayi karatu, duka baccinshi kadan ne. Sosai ummanshi take tausayinshi, duk yanda taso yakarbi wasu kudinta datake tarawa akan yabiya masu aiki kin karba yayi, tace Abbas meyasa bakasan kowa yatemakeka akan gininka? Murmushi yayi yace Umma inaso inyi alfahari da gidana kamar yanda Baba harya rasu yake alfahari da wannan gidan nashi, Baba yafadamun babu kwandalar kowa acikin gidan nan, Gumin kanshi ne, shiyasa aduk lokacin daya kwanta yakejin dadi, kuma yake alfahari da wannan gidan nashi, to nima haka nakeso, shiyasa bana karbar kudin kowa, ranar nan ma Jafar yabani kudi inkara insayi langa langa amma wlh Umma koda na karba bansaya dasu ba, Sune nasaya mana kayan abinci, daya tambayeni nasaya nace mashi e dan karyaji haushi, dan haka kema ki aje kudinki, zasumun amfani, idan nazo hada lefen Labiba. Murmushin Jindadi Umma tayi, tace ina alfahari dakai da Umar, akullum ina godema Allah daya bani ku Allah, yayi maku albarka, kuma yabaku wadanda zasu yimaku abinda kuka mana, Abbas yace amin Umma. Ayau ne, aka kai kayan saka ranar Labiba gidan Kawunta wani abokin Baban Abbas wanda tare sukaje neman auren Labiba shida Babansu Abbas,Kawunta yaji dadi sosai, yace toyanzu yaro shine yakeda hakkin aji daga bakinshi lokacin daya shirya, Se asaka rana, anan suka tsaida idan Abbas yafidda rana zasu aikama sauran yan uwa, godiya sukayi, suka masu sallama, Alokacin da Abbas yasamu labari, agurin Ummanshi yace to Umma kinga jibi zamu fara jarabawa, kuma bankarasa ginin ba, amma acikin week end damun gama jarabawa zasu fara aikin, kuma bazasu tsaya ba, dan natara kudi dayawa. Seda idon Ummanshi yacika da kwalla tace Allah sarki Abbas, insha Allah wannan wahalar dakasha arayuwarka wata rana seta zamo labari, insha Allah seka daukaka, kalli, yanda ka koma saboda kawai neman na kanka, Shima kwalla ne suka cika mashi ido yace amin, Umma, Umar ne, yayi sallama bayan sun amsa yashigo,yace Umma sannu da hutawa, tace yauwa sannu auta, zama yayi yace yaya sannu, yace yauwa autan Umma ya gajiya? Yace lafiya lau, dama kasuwa zantafi, nace ko akwai wani aiki dazan maka? Murmushi Abbas yayi yace a,a bara inshirya mufita tare nima zanleka kasuwar, sallama sukayima Ummansu, tabisu da addu,a. Kamar wasa ayau Abbas yagama jarabawarshi takarshe, yana fitowa seda yayi kuka, alokacin daya tuna kalaman Babanshi........ Abbas inafatan Allah ya nunamun ranar dazaka gama karatunka, aranar senayi maka sadaka, domin burinka yacika, tunkana yaro kakeson kayi karatu, Aduk lokacin dana kwanta bacci, idan natuna nasaka amakaranta, nakanji farinciki tunda zancika maka burinka....... wani guri Abbas yasamu, besan lokacin da kuka meyawa yataho mashi ba, sosai yake kewar mahaifinshi awannan rana, Seda yayi kukanshi yagaji sannan yatafi gida, ahanya ya tsaya yasayi dabino kwano daya sannan yawuce gida, wata makarantar allo dake unguwarsu yaje, bayan sungama gaisawa da malamin yabashi yace ayimashi sadaka ayima Babanshi addu,a. Umma bakaramin dadi taji ba, alokacin da Abbas yadawo yace mata sungama lafiya, itama kosai tace zatayi na sadaka. Acikin kwana 4 aka gama rufin gidan Abbas, anyi wearing, ansa kofa da windor, anyi fenti, sosai gidan yayi kyau, abandakin gidan harda broken tyles aka saka, kitchen din har kanta aka buga, sosai Abbas yayi kokari, Gida dede na talakawa yayi kyau aranar da aka gamashi, Abbas kasa fita yayi aciki, haka yazauna yaketa kuka, saboda yatuna da Babanshi, dayanzu seyafi kowa farin cikin kammala ginin, domin yaci buri akan yaga angama gidan, Jafar ne, yayi sallama dan yaje gidansu ance baya nan, hakan yasa yataho sabon gidanshi, dasauri yakarasa gurin Abbas, kafadarshi yadafa yace lafiyarka Abbas? Kallonshi yayi tare da goge idonshi yace lafiya lau, Jafar, kawai na tuna da Babane, Allah beyi yana raye zan gama ginin nan ba. Jafar yace kayi hakuri Abbas, addu,arka Baba yake bukata, tashi muje. Kasan yau ne, zamuje gurin Kawun Labiba atsaida rana, Tashi yayi yace muje gida inyi wanka idan munyi sallar magriba semuje, jafar yace amma bawani dogon lokaci za,a saka ba ko? Abbas yace gaskiya kam, dan dama wannan ginin ne ya tsayamun, Yanzu abinda yaragemun kawai lefe ne, nasan inde akasaka bikin nan da wata 2 ya isa ingama hadashi, Jafar yace haka ne, nima zanso asa bikinmu rana daya, kaga semuhuta gaba daya,Abbas yace hakane, fita sukayi. Bayan sunje gurin kawun Labiba aka tsaida ranar biki wata 2, bayan suntafi yaje gidan kakar labiba bayan sungaisa, yace dama nazo ne, infada maki zanje gurin su yaya infada masu za,ayi bikin Labiba kada suga anyi ba,a fada masu ba. Kakar tace gaskiya ka kyauta, dama ba,abiye ta mutum,gara kafada masu, koma menene kafita hakkinsu, godiya yayi mata yatafi, Kamar yanda yafada, washe gari yaje jigawa, ko kadan beji dadin yanda yasamu yan uwanshi ba, gaba daya rayuwa tafara juya masu baya, yayanshi har tsufan talauci yafito mashi, sede abinda yadaure mashi kai, yanda haryanzu basu sauko daga fushin dasuke dashi ba. Duk yanda yaso ya fahimtar dasu amma sam sukaki saurararshi, yanaji yana gani haka yahakura yafito ranshi abace yanufi kano tare da alkawarin baze kara zuwa inda suke ba, zeje ko abokananshi sun isheshi yayi hidimar biki. Haka bangarorin biyu suka cigaba da shirye shiryen biki, Abbas gaba daya bayada lokacin kanshi, kullum akasuwa yake wuni, dan burinshi yatara kudin dazeyima Labiba kaya masu kyau kada kawayenta su rainata. Labiba ce take tafiya kakarta ta aiketa magana tarikaji abayanta anakiranta, juyawa tayi dan taga mekiranta, murmushi tasaki ganin abokin Abbas Buba, bayan sungama gaisawa yace amaryarmu bakya laifi koda kinkashe dan megida, Dariya tayi tace Buba kenan hada zolaya, yace ai gaskiya nafada, ina mutumin naki kinsan yanzu yayi mana wahalar gani tunda yafara gini, Kallonshi tayi tace ai nasan kuna haduwa amajalissarku idan yadawo kasuwa, gini kuma shida aikinshi kawai yabiya masu gini, Dariya yayi yace haba Labiba,ai Abbas shine yakeda ruwa agini, mutumin dayake kwaba kasa da kanshi, yayi bulo nakasa sannan yahau shida kaninshi suyi gini ai shine keda aiki, Cike da mamaki ta kalleshi tace wane irin kwabin kasa kuma? Abbas din daya sayi filinshi a sallari kuma yace ginin bulo da bulo zeyi yama za,ayi kace yayi na kasa. Dariya yayi yace lallai da alama kece yamaida sallari, acikin unguwarsu fa yasayi wani kwatan fili, kuma tunkafin Babanshi ya mutu suka fara kwabin kasar dazasuyi bulo da ita, Kuma koyanzu zan iya rantse maki da Abbas ginin kasa yayi maki, kawai shafen siminti ne akayi asaman ginin kasar, jiya jiyan nan mun wuce tagaban gidan daya gina, Sede kiyi hakuri dan gaskiya gidan bawani girma gareshi ba, amma kuma fa yayi kokari dan gidan yasha fentin ruwa,dan irin wannan fentin da anyi rywan sama yake wankeshi. Toni zanwuce dama wani guri zani na ganki shine nace bara inkaraso mugaisa, Amma idan baki yarda ba, zaki iya hawa mashin dina inkaiki har gidan kigani. Wata irin zufa ce tarufe Labiba, tace muje wlh nafasa zuwa aiken idan nadawo zanje, hawa mashin din tayi Buba yana dariyar mugunta yaja mashin suka tafi, Kuka Labiba tasaka alokacin dasuke shiga unguwar, hijabinta tasa tarufe hancinta saboda wari, da kyar suka isa kofar gidan saboda hanyar duk tayi rami, Kallon gidan takeyi cike da takaici, ga rufin gidan ba irin nazamani bane, langa langa ne, akayi rufi dashi, kuka takeyi, tace dan Allah Buba muje ka kaini gida, Haka suka tafi, zuciyar Labiba kamar zata fito, tun ahanya tayima Abbas message yazo tana son ganinshi, har kofar gida Buba ya ajeta, yana mata sallama amma bata kulashi ba, tashige tana kuka. Dariya Buba yayi yace muje zuwa Abbas. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 90 🔱 95 Zaune Abbas yake asaman dakalin kofar gidansu Labiba, yayi mamakin yanda sam Labiba taki yarda su shiga cikin gidan kamar yanda suka saba, Gashi tunda yazo take kuka yama rasa yanda zeyi da ita, kallonta yayi yace Labiba kitashi mushiga ciki kinga nan mutane zasu ganki kina kuka, Kai tadago tace maganar danakeso muyi bana so kaka taji, hakan yasa nace muzauna anan, kuma ai akwai duhu bakowa zeganni ba, Ajiyar zuciya Abbas yayi yace tonaji, yanzu share hawayenki kifadamun abinda yake faruwa, tunkafin nima nafara kukan, Gyaran murya tayi tace Abbas meyasa zakamun karya? Meyasa zaka ha'inceni? Wannan abun daka mun munafunci ne, cike da tashin hankali Abbas yace haba Labiba me kuma nayi maki? Dan Allah kimun bayani yanda zangane. Uhm Abbas kenan dadina da ramin karya kurarrene, atunaninka karyar dakayi bazata fasu ba? Wato kaso ka cuceni, harse andaura mana aure ankaini gidanka sannan zanga irin gidan dakamun ko? Anufinka dole inhakura inzauna tunda anriga da andaura. To bara kaji, wlh, wlh, wlh, kaji namaka rantsuwa 3, duk yanda nake sonka da ace seda aka daura aurenmu aka kaini wannan kaskantaccen gidan amatsayin gidan dazan rayu, Wlh da aranar zan barmaka gidanka, kuma koyanzu infada maka da babbar murya wlh inde awancan gidan dakayi zaka sakani, wlh gara sonka yakasheni dade inzauna acikin gidanka, kai gara in mutu banyi aure ba da ace ankaini wancan abun dakake kira gida. Barema nasan koyanzu nafasa aurenka inada wadan da zasu aure ni, aciki ma hada masu babban gida, kawai de saboda son danake maka ne, yasa nayarda na zabeka, Amma kuma duk irin halarcin dana maka shine zaka sakamun da wannan gidan? Haba Abbas, ai nadauka yanda kake sona zakayi duk yanda zakayi kanemi kudi kodan kasama mun gurin hutu. Shiyasa dazu da Buba abokinka yafadamun abinda kake boyemun bakaramun dadi naji ba, dan nasan duk wannan munafuncin wannan Banzan Jafar din ne, ya hadashi, Ni nasan irin son dakake mun bazaka iya munafunta ta ba, kuma idan gaskiya ne, meyasa shi beyi ginin kasa ba? Shine kai ze zuga ka kayi mani, dan haka wlh nibazan zauna awannan gidan ba. Dan haka zabi yarage naka, kode kasaidashi kasayi wani, ko kuma ka hakura da aurena, kamanta kataba sanin wata Labiba. Fuskar Abbas da jikinshi kamar wanda aka kwarama ruwa, kuka yakeson yi amma zuciyarshi tabushe, Innalillahi Wainnailaihirrajiun kawai yake fada aranshi, Yafi minti 10 ahaka bece komai ba, kuma be motsa ba, ganin yakasa motsi yasa Labiba tafara tsorata, hannu tasa ta dafa kafadarshi, saurin kallonta yayi, ganin ya motsa yasa tayi saurin daure fuska. Ahankali yafara magana, Labiba dan girman Allah kada kimun haka, kinsan ina matukar sonki, nasha wahalar da tunda nake bantaba shanta ba kafin in mallaki wannan gidan nawa, Idan kika sani nasayar da wannan gidan bansan inda zansamu cikon kudin dazan sake siyan wani ba, kuma ga lefe zan hada, ga kudin biki, kinsan de yanayin da gidanmu yake ciki base nayi maki karya ba, Wlh Labiba da ina da kudi Allah kadai yasan irin gatan dazan nuna maki, amma kidena fadin zaki rabu dani kinsan da inrasaki gara inrasa komai na duniya inde zan sameki, zan iya hakura da komai. Kuma kinsan duk abinda kikeso shinake so, dan haka kigoge kwallanki kifadamun duk yanda kikeso wlh na maki alkwari zanyi, kinsan ina sonki kamar rai na. Murmushin farin ciki Labiba tasaki, wani irin son Abbas ne da tausayinshi taji sunkara shigarta, wata zuciyar tace mata tabarshi suzauna agidan, amma data tuna gidan Hauwa da yanda kawayensu suka rika yabon gidan setaji bazata iya hakura ba, Kallonshi tayi tace yauwa Abbas dina shiyasa nake sonka sosai, kana son duk wani abu danake so, nima wasa nake maka danace zanrabu da kai, kasan inasonka dayawa, dan Allah duk abinda zan fada maka banaso kafadama kowa, Kagade babu wanda zetayamu zama, idan akayi auren nan kowa tafiya zeyi yabarmu, dan haka kadena biyema Jafar kana shawara dashi akan aurenka, yace to Labibata fada inajinki, ni kuma bazan fadama kowa ba. Gyara zama tayi tare da rage murya tace Abbas meze hana kasaida gidanka, tunda baka da kudin dazaka cika kasayi wani, nasan kudin zasuyi yawa, kaga semuje ka kama haya a irin gidan su Hauwa tacemun dubu 150 ne ashekara, kaga sauran kudin sekasayi mashin, shima baze wuce dubu 150 ba, Kaga har yanzu kanada sauran kudi, seka ajesu acikin asusu, kaga bayan biki sekacigaba da tarawa, nasan kafin kudin hayarmu yakare arzikinka yafi nayanzu, kasan annabi yace idan talauci ma ya isheka ka kara aure, To kai yanzu ma zakayi auren, kaga nan da wani lokaci zamuyi arziki, kaga zamu sayi gida me kyau, babu ruwanka da bata lokaci gurin gini, aginan nanshi zaka siya,mashin dinka ma zaka iya saidashi kasayi mota, Shikenan fa, kaga kasameni, kasami gida kuma kasami mashin, kaga kawuce raini acikin abokanka. Shiru Abbas yayi zuciyarsa se bugawa takeyi dasauri, zufa haryanzu taki dena fito mashi, Matsawa kusa dashi Labiba tayi takamo hannunshi takara rage murya tace, nasan Umma kake tunani, dannasan aduk duniya ita kadai zata iya hanaka yin abinda kake so, Kasan ance tsakanin uwa da danta se Allah, kada kabari tasan zaka saida gidanka, nasan zataji haushi amma kuma yanda take sonka bazatayi fushi da kai ba, kasan Umma Akwai dogaro ga Allah. Idan har zakayi abinka cikin sirri ko Jafar kada kabari yasan abinda zakayi, idan sukazo daukar amarya zasu sani, dan Allah Abbas kayarda da shawarata, kada kabari shedan yahanaka yin abinda nakeso, yin hakan dede yake da rasani na har abada, kuma...... Hannu yasa ya rufe mata baki, kallonta yake atsorace, yace Labiba kinaso zuciyata ta buga ne? Wlh gara kice inbada gidan dana gina kyauta, dakice zaki rabu dani, tunda har narasa mahaifina na kuma hakura babu abinda bazan iya sadaukarwa ba akan soyayyarki, Naji kuma nayarda, amma inaso kema kada kifadama kowa zan saida gidana, insha Allah babu wanda zesan wannan maganar, kuma zamu rayu cikin jin dadi, zanmaki yanda kikeso, kibani sati daya zan gama komai. Rungumeshi tayi tana fadin inasonka Abbas dina, tashi yayi yana murmushi sukayi sallama yatafi, tsallen murna tayi tadauko wayarta takira Hauwa, tana dauka tace wlh dole inbaki kyauta, wannan shawara taki tayi. Hauwa tace, a,a wai da ke kintsaya soyayya, ai dama nabarki kunyi auren an kaiki wannan rubabbar unguwar, idan fa akayi ruwan sama haka zakiga ruwan kwata yana shigowa gidajen mutane, Gashi gininku nakasa ne, wata rana kuna ciki gini zefado maku, shikenan ku mutu abanza, ai dama nafada maki, Abbas yana maki wani irin so, idan kinso zaki iya amfani da wannan damar kiyi abinda kikeso. Yanzu gashinan dayake yaga yana shirin rasaki ya amince da bukatarki, ai wlh sekinyi da gaske, idan bahaka ba, ko kunyi aure shawarar abokinshi Jafar zerika dauka, garama tun wuri kirika hanashi shawara da kowa seke. Labiba tace ai yanzu kam nadauki shawararki, bazan kara biyema so ba in cuci kaina, idan munyi auren mayi soyayyar, Hauwa tace yauwa yar gari. Godiya tayi mata takashe wayar tashige gida. Aranar Abbas kasa bacci yayi, yarasa yanda ze bulloma wannan matsala data taso mashi, wani barin na zuciyarshi yana gargadinshi akan kada yasaida gidanshi, amma barin da son Labiba yafi yawa yakasa yarda da maganar dayan barin. Daga karshe kawai ya yanke shawarar, gara ya saida gidan, ze iya gina wani, amma Labiba baze taba samun taba idan har yarasata, da wannan gurguwar shawarar bacci barawo yadaukeshi. Washe gari tunda safe yana gaisawa da Ummanshi yace mata megidansu yana son ganinshi, addu,a tayi mashi yafita, Yama rasa acikin abokanshi waze dauka suje neman mesiyan gida, yasan idan za,a saida gida mutum daya baya tsayawa shikadai, maganar Labiba yatuna datace Buba ne, yafada mata gidan dayayi. Hanyar gidansu Buba yadauka, yana zuwa yasameshi yana shirin fita, bayan sungama gaisawa yafada mashi abinda yake faruwa. Wata irin dariya Buba yayi, yace yauwa abokina kokaifa, yanzu ne zaka shigo cikin manya, Amma saboda kawai kanaso ka mallaki MUHALLINKA sekaje kayi ginin kasa, kuma kazauna aciki, haba Abbas, aishi MUHALLI da kake ganinshi, da kasameshi awulakance gara kazauna ana haya, ahankali seka mallaki naka. Kana ganin komasu kudi yanzu basu cika son gina gida ba, sunfi so su kama haya, hankali kwance. yanzu kam dole intemaka maka, da fitama zanyi amma nafasa, muje gurin wani abokina dillali ne yanzun nan za,a siyar da gidanka. Abbas yace amma nagode, dan Allah kada kafadama kowa. Buba yace haba Abbas babu wanda zan fadamawa, kaide muje zuwa. Cikin sa,a suka sami abokin Buba kuma yafada masu dama akwai wanda yakeson gida, nan yayi mashi waya, babu bata lokaci yace gashi nan zuwa. Bayan yazo suka tafi ganin gida, mutumin yana ganin gidan yace yayi mashi, nan akayi ciniki gida yakama dubu dari 550, Abbas yanaji yana gani yadauki takardun gida yabayar, Aka bashi takarda yarubuta shedar yasayar da gidan, Kuka sosai yakeyi, kallonshi sukayi cike da mamaki, dillalin yace Buba mekuma yafaru naga yana kuka? Buba yace bakomai, kawai yatuna da mahaifinshi, sukace Allah sarki, tafiya sukayi dan sukarbi kudin. Bayan anbasu kudin Buba yace yauwa munason gida na yangayu kasan bikinshi saura sati 3, to kuma sebayan biki zefara gina babban filinshi, shine yakeson gida me kyau wanda base anyi gyara ba, dan sufara zama shida amarya. Dillali yace ai wannan ba matsala bane, akwai wani gida.... Abbas yace a,a ni nafison irin gidan gwamnati, dillalin yace me irin gininshi kake so ko? Yace E, To gaskiya kaga yanzu lokaci yakure, amma akwai wani gida anan kasan gida na, kuma yana da sauki gaka de unguwar ba laifi tana da kyau, kuma zakuji dadin gidan, duka dubu dari 2 ne ashekara. Abbas yace muje inga gidan, haka suka tafi, suna zuwa yaga gidan yakira Labiba yafada mata ansamu gida, Buba yabama wayar yayi mata bayanin yanda gidan yake, dariya tayi tace ai nayarda da kai, kawai akama. Haka suka gama komai aka bama Abbas mukullin gida, sukayi mashi sallama, akan hanya Abbas yace Buba mashin nakeso insiya, tunda kaga yanzu kudin saura dubu dari 300 da kadan, sauran kudin kuma zan ajesu, Buba yace kai amma dagajin wannan shawarar dakake fadi ba daga bakin Jafar tafito ba, dan nasan Jafar baze iya baka wannan shawarar ba? Murmushi Abbas yayi yace kaide kafadamun. Buba yace haka ne, muje musiyo, amma ka kawoshi gidanka ka ajeshi bayan biki sekafara hawanshi, haka sukaje akayi cinikin mashin lifan baki, suka biya sabon gidan Abbas aka aje mashin din, dubu 10 Abbas yabama Buba, godiya yayi mashi suka rabu. Haka Abbas yacigaba da shirin bikinshi, sam baya barin sudade suna magana da Jafar, siyayyar lefenshi ma shikadai yakeyi, damma Jafar shima yana tashi hidimar, amma shi lefenshi mamanshi ce take hada mashi. Biki yana takara matsowa, har akayi jeran Labiba babu wanda yasan Abbas yasayar da gidanshi, haka yan uwan Labiba sukaje sunata yabon gidanta, ita kam se dadi takeji. Jafar da Buba sune suka kai lefen Labiba, shikuma Jafar nashi mata ne, suka kai, kowa ya yaba kayan da aka sakama Labiba. Umman Abbas dataga kayan tace amma Abbas kayi kokari wannan kaya haka, lallai ka hana kanka ci da sha, Abbas yace Umna hada gudummuwar abokaina na hada, Tace gaskiya sun kyauta Allah yabiyasu yace amin, kallonshi tayi tace inafatan babu wata damuwa ko Abbas, nasan yanda hidimar biki take kuma banji kace inbaka wannan kudin dakace in aje maka ba? Abbas yace bakomai Umma tunda inada kudi kibarsu kema kiyi hidimar biki dasu, tace ai shikenan Allah yatemaka, yace amin. Ayau ne aka daura auren Abbas Alee da Labiba Lawal, akan sadaki dubu 30, da misalin karfe 12:00, suna gama na Abbas kuma karfe 2:00 aka daura na Jafar da Maryam. Da misalin karfe 5:00 aka dauki Labiba zuwa gidanta, shima Jafar alokacin aka dauki tashi amaryar, hakan yasa besan inda aka kai Labiba ba. Kawayenta se yaba gidan Labiba sukeyi, Hauwa tace gaskiya Labiba kin more gida dama nawa, Dariya Labiba tayi tace, kinji Hauwa duk haduwar gidanki amma kike santin nawa? Wata kawarsu tace inde Hauwa ce, ai tacika ruwan ido, dariya suka saka. Umar ne yashigo gidansu, hankali tashe, alokacin anyi magriba, yan biki duk sun watse, dama yawanci yan unguwa ne, se wasu yan uwan Umma mata guda biyu, Umma tna ganin umar ta taso tana fadi lafiya nagana kamar kana cikin damuwa? Kwalla ne suka zubo mashi cike da damuwa taja hannunshi suka koma gefe guda, tace Umar kafadamun meke faruwa? Umar yace Umma yanzu awaje agurin abokan yaya nakejin wani labari, wai Yaya yasayar da gidanshi yakama haya da kudin gidan,saboda Labiba tace bazata zauna agidan kasa ba, Lokacin danaji banyarda ba, haka natafi gidan inazuwa nasameshi abude, sallama nayi sega wani mutum yafito, tambayarshi nayi ko da gaske gidanshi ne, yace mun ai tun sati 3 da suka wuce yabiya kudin gidan. Wlh Umma........... bekarasa maganar ba, Umma tazube agurin sumammiya. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 95 🔱 100 Cike da tashin hankali Umar yanufi gurinta, dagata yayi yashiga kiran sunanta amma ko motsi batayi, tashi yayi da gudu yanufi hanyar fita, azaure sukaci karo da Abbas shida Jafar sunzo yima Umma seda safe. Rikeshi Abbas yayi yana fadin lafiyarka Umar zaka bige mutane baka gani ne? Kuka yasaka mashi yana fadin shikenan Yaya zamu rasa Umma, cike da fargaba Abbas yasakeshi yana fadin meyasamu Umman? Da hannu yashiga nuna mashi hanyar cikin gida, ai shida Jafar har rige rigen shiga suke, kwance suka sameta yanda Umar yabarta, kusa da ita Abbas ya duka yasaka kuka. Jafar ne, yayi saurin dauko ruwa yashiga yayyafa mata, cikin sa,a tasaki ajiyar zuciya, fita Jafar yayi yataro me adedeta, yana zuwa yacema Abbas yakamata sutafi asibiti. Yan uwanta ne suka fito jin hayaniya, suma hankalinsu yatashi ganin abinda yake faruwa, nan Jafar yace masu zasuje sudawo, haka aka fita da Umma dan haryanzu bata dawo dede ba. Suna zuwa asibiti aka karbeta, wani daki aka sata aka kwantar da ita saman gado, likita aka kira, yana zuwa yafara yimata gwaje gwaje, ya dauki lokaci kafin yagama, Allurai yayi mata nan bacci yadauketa, fitowa yayi yace su sameshi office, bayan yagama rubutunshi yace menene sanadiyar sanyata tasuma? Shiru sukayi, Jafar yace wlh bama gidan lokacin da abun yafaru, Umar ne, kuma yana gida. Dr, yace to da alama anfada mata wani abu wanda yadaga mata hankali har yayi sanadiyar sumanta. Damma tana da karfin jini abun yazo dasauki, kunci sa,a bata da hawan jini da wannan faduwar datayi zata iya jawo mata matsalar shanyewar barin jiki. Amma nayi mata allurai insha Allah zata samu sauki, tana farkawa ma zaku iya tafiya, sede a kula da duk wani abu daze daga mata hankali, domin akare lafiyarta. Takarda yamika masu yace kusiyi wadan nan magungunan tashasu insha Allah babu wata matsala, godiya sukayi mashi suka fita, bayan sun dawo daga siyen maganin suka zauna akusa da dakin. Abbas yakalli Jafar yace kozakaje gida kada Maryam taga kadade? Murmushi Jafar yayi yace haba Abbas, ai koba Umma bace aka kawo asibiti wani naka ne, bazan iya barinka kai kadai ba, Bare kuma Umma, idan kuma mamanace aka kawo zan iya tafiya inbarta? Ai ko kwana zatayi bazan tafi ba, bare kuma yau zamu tafi, kawai zankirata, kaima ka kira Labiba kafada mata. Haka suka zauna suna jiran Umma ta farka, gaban Abbas se faduwa yakeyi, yayi duk wani tunani amma yakasa gano dalilin dayasa Umma tashiga wannan halin, haka ya hakura. Gurin karfe 9 ta farka, hakan yasa suka kira wata nurse bayan tagama dubata tace zasu iya tafiya, Abbas se sannu yake mata amma taki ko kallonshi, haka suka tafi gida abun yana damunshi, sede yadauka ko bata son magana ne. Suna zuwa gida tashige dakinsu Abbas dayake zaure, mamaki ne yakamasu, Abbas yace Umma dakinmu ne fa kika shiga, kallon Jafar tayi tace kirawomun Umar kuzo nan inason magana daku can akwai mutane. Zama Abbas yayi gabanshi se faduwa yakeyi, Umar yana zuwa Jafar yace to nizan tafi Allah yakara sauki Umma, dago kai tayi tace dawonan kazauna kaima maganar tashafeka, Zama yayi shima gabanshi yashiga faduwa, shiru dakin yayi, can Umma tace Umar maimata abunda kafadamun dazu, dasauri Abbas yakalli Umar, saurin dukar da kai Umar yayi yafara magana. Kaf yafadi abinda yafadama Umma dazu, wata irin zuface tafara zuboma Abbas, Jafar kuwa jiyake kamar amafarki, saurin kallon Abbas yayi dan yatabbatar da maganar Umar gaskiya ce. Kwallan daya gani suna fitowa a idon Abbas ya tabbatar da maganar Umar gaskiya ce, Murmushin takaici Umma tayi tace amma Jafar meyasa kai bakazo kafadamun abinda Abbas yake shirin yiba tun kafin ya aikata? Saurin kallonta Jafar yayi yace wlh, Umma yanda kikaji maganar nan daga sama haka najita, har garake tundazu kikaji nikam yanzu ne nasan da ita, kallon Abbas yayi wanda zuwa yanzu kukanshi ya tsananta yace, Kayi magana Abbas dan Allah kacemun da wasa Umar yake baka saida gidan dakasha wahala kafin ka mallakeshi ba, kifar da kanshi Abbas yayi saman cinyoyinshi yacigaba da kuka. Umma cike da bacin rai tace wlh ko katashi kayi mana bayanin yanda abun yafaru ko kuma idan kabari nafita daga dakin nan, wlh gidan zanbari kuma kungama ganina har abada, Bazan tsaya bakin cikinka yakasheni ba, nagama da iyayena lafiya, nagama da mijina lafiya, saboda kai bazan bari hawan jini yakashe ni ba. Saurin dago kai Abbas yayi yace dan Allah Umma kiyi hakuri wlh zanfada maki komai, ba laifina bane, kiyafemun, gyara zama yayi yashiga fada masu duk abinda yafaru. Salati Umma tasa tana tafa hannu, Jafar da Umar kuwa kuka suke sosai, shima Abbas kukan yakeyi, Umma tace lallai Abbas kayi wayon banza, ashe dama duk hankalin dakake dashi na banza ne? Ashe dama mace karama zata iya yimaka wayau? Wlh, wlh, wlh, kaji namaka rantsuwa har 3, da ace kafin adaura aurenku ne, nasamu wannan labarin da ko awajen daurin auren ne, senasa anfasa auren, Sede rashin aurenta yazamo ajalinka da kake ikirari dashi, innalillahi wainna ilaihirrajiun, wannan abu dame yayi kama? Amma wannan yarinya bansan mezan cemata ba. Kuka tasaka, hankalinsu gaba daya yagama tashi, matsawa kusa da ita Abbas yayi yana kuka yarike hannunta yace Umma nasan ban kyauta ba,na munafunceku amma dan Allah kada kiyimun baki, Yau gashi ta dalilina kinzubar da hawayenki, dan Allah kiyi hakuri kada Allah yayi fushi dani, nasan nayi kuskuren da bazan iya gyarashi ayanzu ba, amma addu,arki kadai zatasa in gyara laifin danayi nan gaba. Kallon Jafar yayi yace Jafar kayi hakuri, nasan ban kyauta maka ba, amma wlh sharrin zuciya ne, da son danake ma Labiba, wlh alokacin jinayi kamar raina zefita idan narasata, hakan yasa nayi saurin karbar sharadinta, Dan Allah kazo katayani bama Umma hakuri, wlh idan yanzu kikace inrabu da Labiba nayarda zan rabu da ita inde hakan ze sanyaya zuciyarki, amma kada kiyi fushi dani Umma, Matsowa Jafar yayi hada Umar suka shiga bama Umma hakuri, shiru tayi tana goge idonta yayin da tausayin Abbas yakamata, hakika tasan Abbas yarone me ladabi, kaddara ce da kuma sharrin mace yasashi ya aikata wannan abu, Kamo hannunshi tayi tace shikenan Abbas na hakura, bazan ja da kaddarar da Allah yadora maka ba, kuma bazan rabaka da farin cikinka ba,tabbas nasan kana tsananin son Labiba, Hakan yasa take amfani da wannan damar tana maka abinda taga dama, amma bakomai, nayafe maka, kaje kacigaba dazama agidan haya, sekayi kokari kasamu katara wasu kudin kasayi wani gidan, Idan bahaka ba, wlh inde kabiye mata bazaka taba mallakar gidan kanka ba, kuma zaka ce nafada maka, duk ranar daka fara zama namiji ka iya tsayawa kaki bin yanda takeso to daga ranar zaka fara tara abun kanka. Amma ayanzu soyayya ta rufe maka ido, bazaka taba gane abinda za,a fada maka ba akan matarka, amma kayi ahankali nibazan maka baki ba, addu,ata zata bika aduk inda kake, Allah ya tsareka daga sharrin mace, kuma bazan raba aurenku ba, Allah kadai yasan rabon daya boye atsakaninku. Allah yabada zaman lafiya. Kuka sosai Abbas yakeyi idanunshi har sun kumbura, Jafar se lallashinshi yakeyi, dago kai yayi yace nagode Umma da kika fahimceni, Allah nagode maka daka bani Uwa me saurin fahimta, Insha Allah Umma bazan baki kunya ba, zan dage inga namayar da gidana dana rasa, sede idan wani hukunci na ubangiji. Umma tace Jafar kutashi kutafi dare yayi, Allah yayi maku albarka. Magungunanta Jafar yabama Umar yace gashi da safe kabata tasha da rana ma haka, sallama sukayi mata, suna godiya suka fita, da kallon tausayi tabi Abbas. Kallon Umar tayi tace Umar karika saka Yayanka acikin addu'arka, Allah ya jarabceshi Umar yace to Umma, muje ki kwanta, kuma dan Allah kada kisa abun aranki yadameki, kinga bakida wani ciwo ayanzu. Seda Jafar yabi Abbas har gidanshi dan yaga gidan, tausayin abokinshi yakamashi ganin irin gidan da aka sashi yakama, yasan inba wani iko na Allah ba, Abbas baze iya biyan kudin gidan ba idan suka kare. Jafar yace to Abbas asha angwanci lafiya nizan tafi, kamo hannushi yayi yace inafatan baka fushi dani? Jafar yace haba Abbas, wlh bana fushi da kai, sede inaso daga yanzu kasa aranka zaka cikama Umma alkawarinta, zakayi kokarin maida gidanka daka rasa? Abbas yace insha Allah, murmushi Jafar yayi yace naji dadi, seda safe muhadu agidan Umma, Abbas yace angama, hannu yabashi sukayi sallama yashiga gida. Bacci yasamu Labiba tanayi babu kowa dan dama yace mata idan suntafi ta kulle gidan tunda yana da mukulli idan yazo seya bude, tashinta yayi, tana tashi tace haba Abbas ina katsaya haka kalli agogo fa? Zama yayi yace muna asibiti Umma badata lafiya, saurin tashi tayi tace meyasameta? Nan yafada mata duk abinda yafaru, kwalla ne suka fara zubo mata cike da tausayin Abbas tace dan Allah kayi hakuri, nasan nice silar komai, Amma kayafemun, kuma gobe zamuje inbama Umma hakuri kaji? Murmushi yayi yace bakomai Labibata Umma batayi fushi ba, tace nide duk da haka dan Allah. Yace shikenan Allah yakaimu goben tace amin, wlh duk shawarar Hauwa ce amma kasan ba halina bane, yace nasani Labiba, kuma insha Allah zan maida gidana, tace Allah yasa. Washe gari tare sukaje duba Umma, sede abun mamaki sam Umma bata canza ma Labiba fuska ba, asalima ko maganar batayi mata ba, hakan yasa Labiba duk ta tsargu, Dukar da kai tayi tace Umma nasan nayi maki laifi, amma dan Allah kiyi hakuri, wlh sharrin zuciya ne, da kuma bin shawarar kawa, amma nagane kuskurena insha Allah hakan bazata kara faruwa ba. Murmushi Umma tayi tace bakomai Labiba, dama haka akeso idan mutum yayi badede ba, yagane kuskurenshi, inafatan zaki kiyaye da bin shawarar kawaye? Tace insha Allah Umma. Sun dade kafin suka tashi suka tafi, gidan kakar Labiba suka wuce, tana ganinsu tace wane irin mutane ne ku? Duka yaushe aka kaita har zaka fara fitowa da ita? Abbas yace kaka gida mukaje duba Umma bata lafiya shine nace muzo mugaidaki. Bayan sungaisa Abbas yace bari yaje yakarbo wani abu, Kaka tace to kada kadade kasan zakuyi baki yan ganin dakin amarya, yace to kaka. Yana fita Labiba tafada mata duk abinda yafaru, salati kaka tafarayi takaima Labiba duka tana fadin ammade anyi yar banzar yarinya wlh, aini dama tuntuni wannana yarinyar Hauwa bata kwanta mun ba, Ashe seda tasaki hanyar banza hankalinta yakwanta, ke kuma dayake 'yar fari ce kika biye mata tamaki wayau, bakisan bakin ciki take maki ba, ke naki mijin gidan kanshi zesaki, ita kuma gidan haya ne, hakan yasa tasaki kika aikata wannan shirmen. To bara kiji,wlh kanki kika cuta, baki cuceshi ba, domin shi namiji ne, kowace irin rayuwa, tazo mashi ze iya daukarta, kefa? Macece wadda batasan wahalar rayuwa ba, Zakiyi kuka da idanunki wata rana, da kinyi hakuri da wannan gidan wata rana daukaka zata iya zo maki, domin kowa da haka yafara, wasu ma da gidan kara suka fara arzikinsu, Amma ke kinsamu kikayima Allah butulci, to wlh kobayan raina zakice nafada maki, wata rana sekin nemi gidan da bekai wanda kika raina ba, amma yafi karfinki, Labiba idan har kinaso kisamu rayuwa medadi, tabbas sekin koma ga Allah kuma kinsake wannan rayuwar da kika dorama kanki ta karya, sannan Allah ze kalleki. Kuka Labiba takeyi sosai, Kaka tacigaba, MUHALLI da kike ganinshi wlh kona tsumma ne, daraja gareshi musamman idan mutum da gumin kanshi yayishi,kinko san irin farin cikin da mutum yake tsintar kanshi aciki aranar daya mallaki MUHALLINSHI? kina ganin ko mahaukaci beyarda yazauna awaje ba, koda icce da tsummuna seyayi kokari yahada gidanshi, amma ke kinsamu me daraja kika wulakanta. Hakuri tashiga bama kakarta, da kyar ta hakura dan ranta bakaramin baci yayi ba, shawara tayita bata, Abbas ne yayi sallama, yashigo, shima nan Kaka tarufeshi da nashi fadan, tace, Kabani kunya da har ka iya biyema mace, kuma meyasa ma ni baka fadamun ba? Hakuri Abbas yayita bata, tace ai shikenan ku kuka sani, kutashi kutafi, Allah ya kyauta gaba, haka suka fito suna mata godiya. Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya suna cin amarcinsu cikin jin dadi, Abbas duk abinda Labiba takeso shiyake mata, ko girki batayi sosai, sede yasiyo masu, soyayya kawai sukeyi, Ko fita yayi baya dadewa zedawo, hatta kasuwa ba kullum yake fita ba, Jafar yayi maganar harya gaji, Abbas ganin Jafar ze matsa mashi yasa yabar kasuwar dayake zuwa shida Jafar da Umar Kwari, ya koma sabon gari. Da Jafar yamashi magana Abbas yace yasamu wani ubangida kuma yamafi samu acan, sosai Jafar yaji dadi, dan yanason Abbas yarika samu, Umma ma taji dadi da Umar yafada mata. Ganin babu wanda yake matsa mashi hakan yasa seyaga dama yake zuwa kasuwar, dama kuma babu wani uban gida daya samu, idan yajema dako yake danyi, daya samu yan kudi zetashi yakoma gida. Sauran kudinshi daya aje sune yake dauka suna cin dadi dan kullum seya sayama Labiba kaza da madara, sosai sukayi kyau, bakamar Labiba, hutu ya karbeta. Haka rayuwarsu tacigaba da tafiya, sannu ahankali suka cinye kudin Abbas duka, saukinsu ma sunada abinci dan ba kullum suke girki ba, ganin beda kudi ahannu Labiba tace yasaida mashin dinshi se yayi jari. Babu gardama ya amince da shawararta, kayan gwanjo yasaro yafara saidawa, sosai yake ciniki sede kudin basu azuwa ko ina, kafin wani lokaci kudin suka kare. Zaune suke afalo suna cin abinci, wayar Abbas ce tayi kara, yana dubawa yaga kawun Labiba ne, bayan sungama gaisawa yafada mashi Allah yayima kakar Labiba rasuwa tunda dare, sakamakon ciwon ciki seda safe aka balle kofar akaga tarasu. Salati Abbas yayi yace gasunan zuwa, yana fadama Labiba tasa kuka, haka sukatafi, lokacin dasukaje har angama shiryata, sosai Labiba take kuka dan sun saba sosai da ita, Bayan anyi mata sallah aka kaita gidanta na gaskiya, haka akacigaba da karbar gaisuwa, dangin baban Labiba mutum 2 sukazo, sosai Kawunta yaji dadi, dan bedauka zasuzo ba, daya fada masu. Bayan sadakar 7 kowa ya watse, sosai Abbas yakara dagewa gurin bama labiba kulawa,saboda bakaramin tausayinta yake ba. Rayuwa tafara yimasu zafi domin yanzu se Abbas yaje kasuwa amma da kyar yake samun dari 500, aciki ze cire kudin mota yadawo gida, gashi koyaya yasamu kudi seya sayama Labiba abun dadi, wani lokacinma shibaya ci, sede sam bebari Jafar yasan halin dayake ciki ba, duk sanda suka hadu yana gwada mashi yana tara kudi a asusu, Jafar kam dadi yakeji idan yaji haka. Lokacin da shekara tacika akazo karbar kudin haya, nan suka fara zare idanu, dan Abbas beda ko dubu 500 bare yasamu dubu dari 200 kudin haya, hakuri yafara bama megidan, amma yace idan basu da kudi kawai su fita dan yanzu haka akwai meson kama gidan, dan haka yabasu nan da sati daya sufita, nan yabar Abbas zufa tagama jikashi. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 100 🔱 105 Tagumi Abbas yayi hannu 2, hawaye ne kawai suke sintiri a idanunshi, Labiba tana zaune gefenshi itama kukan takeyi, tanaso tayi mashi magana tsoro takeji, dan gaba daya tasan koma meyafaru laifinta ne. Sallama yaji akafor gida, sanin muryar wanda yayi sallamar ne, yasa gaban Abbas faduwa, domin kobe fita ba yasan Jafar ne, shiru yayi yakasa tashi, kofar da aka rika kwankwasawa ce tasashi saurin tashi ya goge idonshi. Akofar gida yasamu Jafar karasawa yayi yace Jafar sannu dazuwa, hannu yabashi suka gaisa yazauna kusa dashi, kallonshi Jafar yayi amma sam Abbas yaki bari su hada ido, Jafar yace Abbas lafiyarka kuwa, kode bakada lafiya ne? Kai ya girgiza. Ai duk wanda yaganka yasan akwai damuwa atare da kai. Shiru Abbas yayi bece komai ba, dafashi Jafar yayi yace kamun magana Abbas, kasan de baka da wani wanda yawuceni, wanda zaka fadama damuwarka, Ko Umar sunan yana kaninka ne, amma bakomai kake fadamashi ba, saboda haka kafadamun damuwarka, ashirye nake inmaka koma menene inde befi karfina ba. Kwantar da kanshi yayi saman kafadar Jafar yasaki wani irin kuka me ban tausayi. Cikin tashin hankali Jafar yadagoshi, yana tambayarshi lafiya? Kasa cewa komai yayi inbanda kukan dayakeyi, hakan yasa Jafar yarabu dashi yasan kila kukan ne zesa zuciyarshi tayi sauki. Yafi minti 5 yana kuka kafin yadago kanshi yana goge fuskarshi, se ajiyar zuciya yake saukewa kamar wani yaro. Kallon Jafar yayi wanda shima tuni hawaye sun fara sauka afuskarshi, hannunshi yakamo yace, Shikenan Jafar abinda Baba yake gudarmun yafaru, Labiba ta cuceni, narasa gatana, daga yau zuwa wani lokaci zan iya tozarta agaban mutane, banda komai Jafar, megidan hayarmu yabamu lokaci mubiya komutashi. Kuka yacigaba dayi, Jafar yashiga bubbuga bayanshi yace dan Allah kayi shiru Abbas, inde ina raye bazaka taba tozarta ba, Allah yana tare da bayinsa masu gaskiya da hakuri, kayi shiru musan ta inda zamu bulloma wannan matsalar, kaifa namiji ne, Idan kana kuka Labiba tace me? Kama dena cewa Labiba ta cuceka, duk da tana da laifi, amma kadauka kawai wata jarabawa ce Allah yayi maka, kayi hakuri ka rungumeta se Allah yasaka maka da abinda yafi alkhairi, Kafadamun gaskiyar abinda kake boyemun, tunbayan barowarka kasuwarmu? Tashi Abbas yayi yafara fada mashi duk gaskiyar abinda yafaru azamansu da Labiba. Ajiyar zuciya Jafar yayi,yace gaskiya Abbas bazan boye maka ba, Wlh, Son da kake nunama Labiba yayi yawa, ba,ace kada mu nunama matanmu soyayya ba, amma wadda kakeyi tawuce misali, taya zaka dorama kanka abinda yafi karfinka duk dan kawai kafaranta ma matarka rai?. Kasan sufa mata basu san wanda yake masu ba, wlh, duk yanda kake kyautata masu duk ranar da bakayi masu ba, se sunnuna maka bacin ransu, garama karika nuna masu zafi wani lokacin, zakufi dedetawa dasu. Amma yanzu mubar wannan maganar, abinda nakeso da kai zannema maku wani gidan, sede kayi hakuri ba,a wannan unguwar ba ne, kasan nima bawasu kudi gareni ba, zanyi kokari insama maku gida mesauki a burget, Acan za,afi samun gidan dazaku zauna ku kadai mesauki, dan gaskiya banaso kuzauna da wasu, ammafa sekunyi hakuri, ba dadi kunsaba zama anan kuma yanzu kusake wani gida. Murmushi Abbas yayi yace haba Jafar, niyanzu ko gidan bukka nasamu ai wlh, zama zanyi sede idan Labiba bazata zauna ba, ai namafi son musami kaskantaccen gida kodan yazama darasi agareta. Nasan yanzu kowane gida nasamu zata zauna, domin nine gatanta, da ace kakarta tana raye nasan bazata yarda tabini ba, to kasan bata shiri da yan uwan babanta, kawunta kuma baze taba goya mata baya ba. Nayarda kasama mana duk inda kaga zemaka saukin biya, kada kadamu dani Jafar, kasan ni namiji ne, zan iya kowace irin rayuwa ce, nasan inason Labiba amma zanyi kokarin dannewa domin itama ta gyara halayenta. Amma dan Allah Jafar kada kafadama Umma wannan abun daya faru, nasan Umma tana da kawaici, bata zuwa gida na, kawai zance mata munsake gida saboda inaso intara kudi wannan gidan kudin sunyi yawa, Nasan zataji dadi sosai. Jafar yace karka damu, babu wanda zesan anyi wannan magana,zanje anjima da yamma zandawo seku fara hada kaya, rungumeshi Abbas yayi na fadin nagode Jafar tabbas kai abokine nagari, Allah yabani abinda zan saka maka dashi na alkhairi, tashi Jafar yayi yace kada kadamu, sena dawo. Gida Abbas yashiga yana me cike da farinciki, hankalinshi kwance, akwance yasamu Labiba tana kallo, dariya da tausayinta ne zuka kamashi, kusa da ita yazauna, yace tashi zakiyi mufara hada kaya, Ai kamar ya watsa mata ruwan zafi haka ta tashi zaune, kallonshi tayi tace Abbas yanzu babu yanda za,ayi asamu kudin hayar dole semun,,,,, wani kallo yayi mata hakan yasa takasa karasa maganarta, Kasa tayi da kanta tace awace unguwa zamu koma? Daure fuska yayi yace ai nadauka tambayata zaki farayi inda nasamu kudin kama wani gidan, amma zaki faramun wannan maganar banzar, Labiba kisan ina sonki, kada kibari kifara batamun rai, koma menene ai kece sanadi, dan haka kiyi abinda nikeso idan har kinason zama dani, ayanzu bamu da wani zabi, duk abinda yazo mana dole mu karbeshi hannu 2, koda kuwa acikin kango ne, dole muyi hakuri muzauna. Kuka tasa mashi me bantausayi, gaba daya seyaji be kyauta ba, tausayinta yakamashi,saurin kamota yayi yace yishiru mana, kallonshi tayi tace dan Allah Abbas kada ka kara cewa idan inason zama da kai, Kasan ayanzu bani da kowa se kai, da kawuna, idan muka rabu ina kakeso inje? Kuka tacigaba, rungumeta yayi, seyaji sam be kyauta ba, lallashinta yacigaba dayi, yace naji kiyi hakuri nima wasa nake maki, aikinsan bazan iya rayuwa babuke ba. Amma kema kimun alkawarin duk inda nasamu gurin zama zaki bini kuma ranki baze baci ba? Kai tadaga mashi tace namaka alkawari bazan kara maimaita kuskuren danayi maka abaya ba, yace yauwa Labibata, tashi muje kada Jafar yazo yajiramu, anan yafada mata komai, Jafar yana zuwa sungama hada kaya, dama da mota yazo, haka sukarika kwasar kayan har suka gama, Labiba kasa shiga makwafta tayi don suyi sallama, haka Abbas yaje yakaima megidan mukullin gidan suka tafi. A unguwar burget wani karamin gida suka tsaya, ciki da falo ne, bandaki atsakar gida, se kitchen din langa langa, sosai Labiba tayi bakin cikin gidan, hakanan tadanne kada sugane halin datake ciki. Kayan suka sanya aciki, sauran kayan kitchen dinta aka sasu daki, kayan ruwanta aka saka wasu bandaki, wasu awaje, Jafar yakira me ruwa yazuba masu, dan sun saba inda suka baro akwai famfo, seda suka gama shirya komai Jafar yace zetafi, Gobe su hadu kasuwa yasama mashi wani aikin, godiya sukayi mashi Abbas yarakashi, bayan yadawo sukayi wanka dama Labiba ta dafa masu abinci acan gidan sukaci, Abbas yace naga abincin gidanma yakare ko? Labiba tace E. Shiru yayi dan yasan beda kudi, Labiba tace kawai kadauki kujerun nan kanana guda 2 kasayar semu sayi kayan abinci, Abbas yace nagode Labiba, tace kadena godemun nice silar komai. Washe gari seda ya saida kujerun yasiyo masu kayan abinci sannan yanufi kasuwa, sede aikin daya samu bekai wanda yakeyi ada ba, haka Jafar yayita bashi hakuri yace yacigaba dayinshi nan gaba zesamu wani. Bayan suntashi kasuwa gidansu yawuce dan yagaida Umma, bayan sun gaisa tace Abbas meyake faruwa da kai naga duk karame? Cewa yayi bakomai Umma nayi rashin lafiya ne, tace Allah ya kyauta, Nan yafada mata suntashi, amma yanuna mata soyake yatara kudi shiyasa suka tashi, Umma tace to Allah yate maka, amma kaima seka rage kashema matarka kudi sannan zaka iya tara abin arziki, Abbas yace to Umma, tashi yayi yatafi. Da kallon tausayi tabishi, dan tasan akwai abinda yake damunshi, kawai baze fadaba, amma tayi alkawarin yimashi addu,a. Haka rayuwar su Abbas tacigaba datafiya, yanzu samunshi yayi kasa sosai, dan ba kullum yake samu akasuwa ba, gashi Labiba tasaba da cin dadi, hakan yasa tafara saida kayan kitchen dinta suna siyen abinci. Wasa wasa haka shekara takare Abbas betara wasu kudi ba, domin koyatara Labiba zatasa su cinyesu saboda hidimarta, ada ma yadauka ko ciki gareta shiyasa yake siya mata duk abinda takeso. Duk wasu abokansu yanzu sungujeshi, hatta Buba baya kulashi, dan kowa yanada rufin asiri, Jafar ne kawai yake temakonshi, alokacin da kudin hayarsu yakare alokacin matar Jafar ta haihu. Ganin hakane yasa Abbas yacema Labiba baze iya yima Jafar maganar kudin haya ba, hakan yasa Labiba tace su saida kayan kallonsu da sauran kayan falonta se su biya, alokacin daya saida kayan dubu 30 yasamu, Kuma gidan dasuke ciki dubu 45 ne, hakan yasa yashiga neman wanda bekaishi ba, da kyar yasamu wani gida irin masu yawan nan, amma yace bayason zama da mutane, Hakan yasa megidan yace akwai wani part amma zaka kara dubu 500 asama danshi nazagayeshi daki daya ne se bandaki awaje, dubu 25 zaka bada, Abbas yace bakomai yayi, Zuwa yayi yaga gidan, dakin babbane, haka yabada kudin aka bashi makulli, me kura yasamu suka rika daukar kayan dayake abayan layinsu gidan yake, haka suka gama kwashe kayan yakaima megidan makullinshi. Labiba seda tayi kuka dataga gidan, haka sukaci gaba dazama aciki, langa langa Abbas yasamu akayi mata kitchen, saboda ruwa, ga dakinsu inde ana ruwa zuba yakeyi. Alokacin idan kaga Labiba zakasan rayuwa ta canza mata, duk tarame, damma Abbas yana kokarin yimata abinda takeso, hatta da wayarta tasaida danyanzu batada wata kawa, Hauwa ma sunrabu tunda suka taso bata kara nemanta ba, Kiran datake mata ne, yasa tasaida wayar, dan bataso tazo taganta agidan datake, alokacin da Jafar yasamu labarin suntashi fada yayi tama Abbas, shikam hakuri yayita bashi yace Jafar kaima fa hidima tayi maka yawa, ga haihuwa anmaka, Badamuwa yanzu ma muna cikin farin ciki, Jafar yace duk da haka Abbas banajin dadin ganinka cikin irin wannan rayuwar, wlh da ace gidana yanada dakuna dayawa can zaku koma. Abbas yace bakomai Jafar, ni inajin dadin wannan rayuwar kodan saboda Labiba, inaso takara sanin DARAJAR MUHALLI, kaga duk sanda Allah yaye mana wannan matsalar bazata kara maimaita kuskuren datayi abaya ba. Jafar yace shikenan, amma meze hana tunda takardunka sunyi kyau muje kasami ko makaranta ce nasan zasu baka ko dubu 10 ce, Abbas yace a,a niyanzu kasuwanci yafiyemun komai. Nasan aduk rana zan iya samun kudi, aikin gwamnati fa? Dole se wata yayi, kabarshi kawai ina jindadin halin danake ciki nasan kaddarata ce haka wata rana komai zewuce. Jafar yace Allah yasa. Haka suka cigaba da rayuwa, tausayin Labiba da kuma soyayyarta sune suke sa Abbas yana kasa tara kudi, bayajin ze iya hanata wani abu inde yanada kudi, wannan itace babbar matsalar data hana Abbas tara abun kanshi, Haka suka rika cinye kwanakinsu batare dasun tara komai ba, har lokacin biyan kudi yazo, da kyar suka samu aka kara masu sati 2, Abbas duk hankalinshi yatashi, yarasa yanda zeyi, gashide gidansu daki daya ne cike da falo kuma na Ummansu ne, Gashi basuda sauran abinda zasu saida se gado da kujeru 2, kuma yace ma Labiba baza,a saidasu ba, ranar da sati 2 suka cika tunda safe masu karbar kudi sukazo suka fara masu wulakanci, Jafar yafito kasuwa yahadu dawani dan unguwarsu Abbas, shinema yake fada mashi abinda yake faruwa, gida yakoma yadauki wasu kudinshi dayake tarawa zesayi mashin, bekoma gurinsu Abbas ba seda yaje fage yakama masu gida, Sannan ya samo mota suka nufi unguwarsu Abbas, suna zuwa suka samesu awaje ankulle gidan kayansu awatse, shine Jafar yadaukesu yakaisu gidan daya kama masu me mutane 3. WANNAN SHINE ASALIN LABARIN ABBAS ALEE DA LABIBA. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 105 🔱 110 CIGABAN LABARI. Kuka sosai Abbas yakeyi alokacin daya gama bama Alh, Abbah labarinshi, shima Alh, seda yazubar da kwalla, bakaramin tausayi Abbas yabashi ba. Gyara zama yayi yace kayi hakuri Abbas, tabbas kaga rayuwa wadda bakowane namiji bane ze iya jureta, ko kuma yacigaba da zama da Labiba ba. Tabbas duk wanda yaji labarinka dole ya tausaya maka, Allah ya jarabceka kuma kayi sa,a kaci wannan jarabawa domin bakaramin me imani bane ze iya haye wannan jarabawa. Jafar ba abokinka bane kadai, yazama dan uwanka najini, azamanin nan kafin asamu irinsu gaskiya za,a sha wahala, yayi maka abinda bakowa ne ze iya yinshi ba. Kai intakaice maka wlh ko dan uwanka ciki daya bakowane baze iya yimaka abinda Jafar yayi maka ba,kuma ayanzu ne, kaima zaka temaka mashi kamar yanda kayi addu,a Allah yabaka damar dazaka temaka mashi wata rana. Gaskiya Abbas kayi namijin komari da har ka iya cigaba da zama da Labiba, duk da itama tana sonka, dan bako wace mace bace zata iya yin abinda tayi, itama ya cancanta a jinjina mata. Kuma banga laifinka ba, idan kace bazaka iya yimata kishiya ba, duk da itace silar duk wata wahala daka sha amma itama tabada gudummuwa sosai arayuwarku. Kuma ayanzu ne nima zankara baka goyon baya wajen ganin ka mallaki MUHALLINKA da guminka, domin kacikama Baba da Umma burinsu, kuma kanuna ma su Alh, Bukar cewa kai dan halak ne. Bazamu bata lokaci ba, kafadi a unguwar da kake so kayi gininka ni kuma zan nema maka kuma zan baka dama kayi gini da kudinka kodan kasamu farin cikin da kowa yake samu alokacin daya mallaki gidanshi da guminshi. Goge ido Abbas yayi yace zanso insamu fili akusa da kai, idan har akwai Yaya, domin kaima kazama daya daga cikin yan uwana, murmushi Alh, Abbah yayi yace badamuwa ni kaina zanfi son hakan, Zan nema maka insha Allah, sede akwai wata shawara danakeso inbaka agame da yan uwan matarka, duk da sune suka yada zumunci zanso ka tsaya mata wajen ganin ta aikata aikin lada. Kashige mata gaba kuje ku sasanta tsakaninta da yan uwan mahaifinta, domin sune abun ado ga kowa, kuma ayanzu dole zasu karbeta kodan arzikin datayi, shima Kawunta kuje hadashi. Abbas yace insha Allah Yaya zanyi yanda kace, Allah yasaka maka da alkhairinsa, yabaka abinda kake nema duniya da lahira, Yace amin,nizanzo intafi, labarinka yasa nayi dare agidanka. Abbas yace Yaya ka tsaya muci abincin dare mana. Tashi yayi yace a,a naci na rana kanaso inyi laifi agurin uwar gida ne? Kasan bakowace mace takeso mijinta yaki cin abincinta ba, nagode tunda naci., tashi Abbas yayi yace nima nagode muje inraka ka. Sauke ajiyar zuciya Labiba tayi, fuskarta ta jike da hawaye, ita kanta Maman Zainab kuka takeyi, ada tadauka tafi kowa shirme datasa mijinta yarabu da gidan gadonsa, segashi ayau taga wadda tafita wauta. Kallon Labiba tayi tace lallai Labiba ayau naji labarin daya bani tausayi da kuma tsoro, ada inaganin kamar babu wata mace data fini wauta, amma ayau na jinjina maki, dole zakice labarinki yafi nawa. Gaskiya ki godema Allah daya baki miji nagari kuma mesonki, wlh da ace wanine da tuni kun rabu, gaskiya bakaramin wauta kikayi ba, da har kika iya daukar gurguwar shawarar Hauwa. Kodayake idan Allah yariga yarubuta abu zefaru dole seya faru, bawa baya iya kaucema kaddararshi, amma ina fatan wannan yazama darasi agareki, bakowace shawara ake dauka ba ta kawa. Duk wata wadda zata baki shawara kifara tsayawa ki kalleta kiga shawarar data baki ita tana binta kokuwa kawai son zuciyane, dan wlh dayawa yanzu kawaye basa bama kawayensu shawara tsakaninsu da Allah. Kawai dasun duba sunga kafisu wani abu, ko kuma zaka daukaka shikenan se sufara bakin ciki, to itama Hauwa abinda tagani kenan har tabaki wannan shawarar, ita meyasa bata bama mijinta shawarar yasaida gidanshi na danbatta ba? Ashe kenan tana sane har tabaki wannan shawarar, saboda taga ke acikin gari zaki zauna, itafa? Akoda yaushe zasu iya komawa garinsu, kuma kilama karya tayi maki babu wani gida da mijinta yake dashi, kawai dan ta yaudareki ne, Kiyarda da ita. Amma bakomai kanta tayi mawa, yanzu gashinan Allah ya daukaka ku, dama hausawa suna cewa hassada game rabo taki ce, nasan ayanzu Labiba kin dauki darussa da dama, domin ko babu Hauwa kema kina da naki halin. Amma yanzu da kikaga duniya na tabbata kinkoyi darasi? Share hawayenta tayi tace haka ne Maman Zainab, wlh ayanzu nadauki darasi meyawa arayuwata, nasan idan Hauwa tana da laifi nima inadashi, Na cutar da Dadyn Ansar sosai, kuma yayi hakuri dani, shiyasa ayanzu banida wani buri wanda yawuce insan duk wata hanya dazan faranta mashi, koda rayuwata zata kare gurin bauta mashi, bazan damu ba, inde zeyi farin ciki. Ayanzu babu abinda yake damuna kamar yanda nake yawan mafarkin Babana, aduk sanda nayi mafarkinsa yakan cemun Labiba ina yan uwana, haka kawai yake cemun seya bace, Kuma kinga ai banida laifi ko? Murmushi Maman Zainab tayi tace haka ne, bakida laifi amma manzon Allah yace duk wanda ya yarda zumunci aranar lahira idan ze tsallaka siradi igiyar zumunci seta kamoshi, Dan haka idan har bakiso kizamo daya daga cikinsu kidage kinemi yan uwanki, koda zakije suna jifarki kada ki hakura, harse idan abun yayi yawa to wannan zaki iya kyalesu domin Allah yaga zuciyarki. Labiba tace insha Allah zanyi kokarin ganin mundedeta tsakaninmu da yan uwana, nagode sosai da shawararki kuma zanzo domin ki kara koyamun yanda zan kula da mijina, Domin ayanzu shine abinda ke gabana, dan yanzu Allah yabamu duniya, saura nikuma indage innemi aljannata agurin mijina. Maman Zainab tace karki damu, yanzu ma ga wasu littatafai nan nakawo maki kibisu daya bayan daya, Inda baki ganeba ki kirani zan maki bayani. Amma kada kiyi sake da abincin mijinki, kinga de mijinki dan kasuwa ne, ba kowane dan kasuwa bane yake iya dawowa gida suci abinci rana ba. Amma kidage ko direba ne kisa mijinki ya aje maki, kirika dafa mashi abinci yana kaimashi, hakan bakaramin kara maki daraja zeyi ba agurinshi, kuma sauran mazaje ma zasuyi sha,awar hakan har susa matansu suyi koyi dake. Sannan duk wata kunya kicireta kirike mijinki, kingade yanzu yayi kudi yakara zama dan gayu, mata dayawa zasu rika kawo mashi kansu, kema sekin dage, shigar kananan kaya, kwalliya, sarrafa magana duk sekin koya, Ke duk akwaisu acikin littafin nan, zaki sami komai, ada nasan bakiyima Abbas komai najin dadi ba, dan haka yanzu kidage, hakan zesa mijinki yadauke idonshi akan kowace mace, ba boka ba malam zaki siye zuciyar mijinki. Labiba tace nagode sosai Allah yabar zumunci, insha Allah zanyi yadda kikace, zakisha mamaki na, shiyasa yanzu nima nadage kallo da karance karance bakaramin karuwa kuma nakeyi ba. Maman Zainab tace bara inkira Baban Zainab, kinga dare yayi, waya tadauka takira mijinta yace aigashinan ma yakusa zuwa, dariya tayi tace sekazo abin alfaharina. Kallonta Labiba tayi tace maman Zainab manya, Tace sosaima aiyanzu soyayya bata tsufa, duk wadda kikaga takoma baya agurin mijinta ita taso, dariya Labiba tayi ta tashi tace inazuwa to. Sabulai da turaruka tahado mata, tana fitowa sukaji sallamar Abbas, amsawa Labiba tayi, zungurarta Maman Zainab tayi, murmushi tayi bata tashi ba, harara tasakar mata ahankali tace bazaki tashi ba? Murmushi tayi ta tashi taje ta rungumeshi tana fadin sannu dazuwa megidana na kaina abin alfaharina, kara matseta yayi yace yauwa amaryata, kallonshi tayi tace yaude anboyemun kai, Sakinta yayi yakamo hannunta suka shigo yana fadin ashe Maman Zainab tana gidan nan, yanzu mijinta ya tsaya kofar gidan nan, seda yafito naganeshi, shine yake cemun ai nan gidan yazo daukar matarshi. Nace mashi ai gida nane, bakaramin mamaki yayi ba, yanzu haka yana falona, nace bara inzo inkirata, zama yayi, yana fadin sannu dazuwa Maman Zainab, tace yauwa Dadyn Ansar, mun wuni lafiya, yace lafiya lau, Nan tayi mashi murna da fatan alkhairi, tashi sukayi suka nufi falon Abbas, bayan sun gaisa shima yakara yimashi fatan alkhairi sukayi musayar number suka rakasu tare da alkawarin zasu zo. Bayan sun koma Labiba ta hada mashi ruwan wanka, yace ai sekizo muyi tare ko? Tace to muje, murmushi yayi yana mamakin canjin dayake gani daga Labiba, ada yasan kafin suyi wanka tare seyasha fama amma ayanzu wasu abubuwa yake gani, haka suka shige bandaki dan suyi wanka. Washe gari bayan yagama karyawa Labiba tace mashi tanason direba zata rika aikenshi, kallonta Abbas yayi yace amma ai mota daya ce agidan ko? Turo baki tayi tace nide to ko me adedeta ne, kasamu se arika biyanshi duk wata. Dariya yayi yace Labiba rigima to wai mezaki da direban? Kwantawa tayi saman kafadarshi tace abincin rana zerika kaimaka banaso daga yau karika cin abinci awaje. Murnushin jin dadi yayi yace ashema niza,ayima gata, nagode sosai My dear da irin kulawarki agareni, tabbas ayanzu nake bukatar kulawarki musamman dana kasance akoda yaushe cikin aiki, Bakomai zanrika turowa adaukar mani, kafin Allah yakara budewa insayi wata motar, kinga idan akace za,a dauki me adedeta za,a bata mashi lokaci, idan lokacin daze dauki abinci yayi kuma baya kusa da gida kinga dole ze bata lokaci. Amma idan turowa zanyi dakin gama sekimun waya kawai se inturoshi, dariya tayi tace yauwa nagode, yace nikeda godiya, muje mugaida Umma intafi kada in makara, wato yanzu de Ansar yadena kwana anan ko? Dariya tayi tace ai yayeshi ma zanyi, yace dama yafi, kinga se asama mashi kanwa ko? Tashi tayi tashige daki tana murmushi, gyalenta ta dauko zuka wuce, bayan sungama gaisawa Abbas yace Umma kinji wai Labiba yaye Ansar zatayi. Dariya Umma tayi tace nima haka nagama fada jiya, tunda yanacin komai, kuma baya shan nono da dare gara ayayeshi haka nan koyasamu kani ko kanwa, dariya Abbas yasa Labiba kuwa rufe fuska tayi. Gyara zama Abbas yayi yace Umma anjima zandawo dawuri, zamuje gurin Kawu inaso muje da Labiba dashi Jigawa domin mugaida Iyayenta. Umma tace amma gaskiya kayi tunani, tunda su sunyarda zumunci gara kuje Allah zebaku ladar zumunci. Kuma kema Labiba ai gara kije kigansu tunkafin ta Allah takasance, kada kidamu da duk abinda zasu maki, ayanzu tunda kinsamu arziki kitemaki yan uwanki Allah yanason meyin zumunci. Abbas yace zamuyi waya da Kawu, anjima gurin karfe daya zandawo semutafi, Umma tace to Allah yakaimu, tashi yayi yace natafi Umma, addu,ar data saba yimashi akullum tayi mashi, tashi Labiba tayi dan tarakashi. Murmushi Umma tayi aranta tace su Labiba anfara cire kunya kenan, amma ace dan kina gaba na bazaki iya raka mijinki ba, sekace kina cikin mutanan da, Allah ka kara hada kawunan wadannan yara nawa. Bayan yaje Office yaje gurin Alh, Abbah, bayan sungaisa yake fada mashi ansamu fili babba miliyan daya da rabi, Abbas yace badamuwa yaya yayi, anjima zamuje jigawa munyi waya da Kawu yace semunzo, Nasan kafin mudawo dare yayi zuwa gobe semuje abiya kudin ko? Murmushi Alh, Abbah yayi yace hakan ma yana da kyau, kuma naji dadi dazakuje, bakomai Allah yakaimu goben semuje. Da karfe daya bayan yayi sallah yanufi gida, wanka yayi yaci abinci suka yima Umma sallama suka dauki Ansar suka nufi gidan Kawu, koda sukaje yashirya, haka suka dauki hanyar jigawa, Labiba da Kawunta gabansu se faduwa yakeyi dan basu san mezasu tarar ba. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 110 🔱 120 Mamaki ne, yakama kawu lokacin dasuka sauka gidan Yayansu, gaba daya ginin gidan ancanza shi, yakoma gidan yan gayu, gate din gidanma kanshi abin kallo ne, Sauka sukayi suka kwankwasa gate din, wani mutum ne yafito, bayan sun gaisa Kawu yace dan Allah ko Yaya yana ciki? Kallon mamaki mutumin yayi masu yace wane yaya kuma? Abbas yace megidan muke tambaya. Murmushi mutumin yayi yace ai megidan yana dubai shida iyalanshi, kuma senan da sati 2 zasu dawo, amma nayi mamakin da bansanku ba, kuma gashi har kuna kiranshi da Yaya? Kawu ya goge zufar datake zubo mashi yace e Yaya nane uwarmu daya ubanmu daya, mutumin yace kai shifa wannan danake magana beda wa ko kani namiji, yan uwanshi duk mata ne, kuma bama anan suke zama sosai ba, Aikine yakawoshi garin nan shine yasayi gidan nan agurin wani. Cike da mamaki Kawu yace ikon Allah, yi hakuri malam, wlh na dade banzo bane, bansan yasaida gidan ba, shikenan mungode bara muje can gidanmu mugani, sallama sukayi mashi suka tafi. Labiba tace Kawu kode Abba yasamu budi ne har yasaida gidanshi kila wani yasaya? Murmushi Kawu yayi yace kila, ammade bara muje gida muji abinda yafaru. Akofar gidan suka ci karo da mutane ana ta rigima, can kawu yahangi yan uwanshi guda 2 suna tayima Yayansu masifa, shi kuma yana zaune saman wata kujera kuka kawai yakeyi, ga mutane sunzagayeshi. Cikin sauri kawu yaratsa tacikin mutanan ya isa gabansu, adede lokacin da wani kaninsu yakama kujerar yayansu yana shirin kadashi. Rike kujerar yaji anyi, hakan yasa yayi saurin juyowa, cak ya tsaya ganin dan uwansu, Kawu yace haba Kabir mekakeyi haka? Kalli yanda kuka tara mutane akofar gidan nan, idan wata matsala ce tafaru ai yakamata ku tsaya cikin gida ku warwareta. Amma yanzu kunfito kuna tonama kanku asiri, wanda aka kira da Kabir yace bazaka gane bane, wannan mutumin wane irin wulakanci ne beyi mana ba, lokacin yanada arziki shida matarshi da yaranshi, Amma yanzu duniya tajuya mashi baya mun temakeshi shine zeyi mana rashin mutunci. Kawu yace ya isa dan Allah, yanzu tare mukeda sirikinku amma abun kunya munzo munsamu kuna fada. Kallon mutanan gurin yayi yace dan Allah jama,a kowa yasan inda dare yayi mashi tunkafin inkira yansanda, ana fada kunkasa rabawa amma kunzo kuna kallon gulma, ai ko idasa rufe bakinshi beyi ba, kowa yakama gabanshi. Kallon Yayansu yayi yace yaya tare mukeda baki kumu shiga ciki, haka yajuya yayima su Abbas iso suka shiga ciki, ababban falon gidan suka sauka, babu komai cikinshi se tabarma, Kawu ne yabada aka siyo masu ruwa, bayan sungama gaisawa kawu yakalli Yayansu da tundazu beyi magana ba, se hawaye dasuke sintiri afuskarshi. Yace Yaya wannan fa Labiba ce diyar marigayi Yaya Lawal, wannan kuma mijinta ne shine chairman na WAPA akano, wannan kuma dansu ne. Cike da mamaki kowa yabisu da ido yana kallonsu. Kuka Yayansu yasaka, se alokacin yabude baki yayi magana, Labiba kece haka? Dan Allah kiyafemun, nasan na cutar dake, gashi ba,aje ko ina ba, hakkinki yafara tambayata, Kalli yanda nakoma, banida komai, babu mata ba, yara babu gida, kuma duk wannan nasan yafaru ne, saboda hakkinki dana cinye, tabbas duk wanda yaci hakkin maraya se Allah ya tambayeshi, kuka yasaka. Kawu ya kalli Kabir yace wai meyake faruwa haka? Gyara zama Kabir yayi yafara basu labarin abinda yafaru. Tun bayan da kazo mukayi fada akan Labiba, tun daga ranar shima Yaya yafara samun matsala, Gaba daya kudinshi basa mashi albarka, matarshi da yaranshi inbanda sata babu abinda suke mashi,yaranshi maza gaba daya suka lalace da shaye shaye, matan kuma su 2 duka sukayi ciki, suka gudu. Ahankali komai nashi yafara karewa, gashi ya aje aiki haka yaje yaciyo bashin banki yasayi mota kuma ya gyara gidanshi, mukammu seda mukayi mashi magana akan yabude shago da kudin yafi mashi, Yayi mana wulakanci yace kudinshi ne bana wani ba, babu wanda yabama kudinshi dasuka fito, haka suka kashe shida matarshi, akwai lokacin da aka kwantar da yarona asibiti ana bukatar dubu 20, naje na tambayi Yaya amma seya koreni, Yace shi kudinshi bana biyama mutane kudin asibiti bane, inaji ina gani yarona yarasu, tundaga ranar nadena zuwa gurinshi. Bayan wani lokaci matarshi ta sace mashi duka kudinshi ta kuma hada baki da wasu yanfashi akazo aka dauke motarshi. Ta gudu, tundaga lokacin Yaya yazama wani iri, kuka kawai yakeyi, hankalinshi bekara tashi ba, seda banki tazo karbar kudinta, anan yashiga tashin hankali kuma banki baruwanta, haka tasa gidanshi kasuwa wani yasaya tadauki kudinta ta koreshi. Shine yazo mute makeshi, ni kuma nace babu inda zan bashi yazauna, haka yayita bamu hakuri shine nace sede inbashi daki daya haya, kuma zan tausaya mashi yarika bada dubu 5, tofa shine yau sati 3 kenan ina mashi maganar biyan kudi amma daga karshe yafara mani fada, shine nikuma nace yabarmun gidana. Ajiyar zuciya Kawu yayi yace ikon Allah, yaya Allah yakyauta gaba, damashi haka alhaki yake, gashi tunkafin aje ko ina Allah yanuna maka kuskurenka, kaima Kabir inamaka ta,aziyar danka, bansani ba, Kodan kuncireni acikin yan uwanku saboda kawai son zuciya, kasa sukayi da kai, Kabir yace wlh ba haka bane, duk laifin Yaya ne, shine yake mana huduba akan mu kyaleka dan yaga kadauki Labiba shi kuma yana tunanin zaka iya kwatar mata hakkinta shiyasa yace muma murabu dakai, Hakan zesa kashiga damuwa har ka kasa ansar mata hakkinta, amma wlh munyi dana sanin abinda muka aikata, gashi acikinmu babu wanda yasan gidanka akano, babu number waya hakan yasa bamu nemeka ba. Amma dan Allah kayafe mana, kema Labiba kiyafe mana alhakinki yanata bibiyarmu, kudinmu basa mana albarka, kiyafe mana kozamu samu sauki. Kawu yace bakomai Allah yayafe mana baki daya, dama haka rayuwa take, wanda ka raina wata rana shine yake maka rana, yanzu ku kalli Labiba ita kadai ta isa tazame maku ishara, Wace irin wahalace baku bata ba, amma yanzu tana auren me kudi, sede Kabir akwai abinda banji dadinshi ba, koba komai Yaya dan uwammu ne, bamuda kamarshi aduniya, kome zemana bekamata kuyi mashi haka ba, Meye daki daya? Ba daki ba, idan kanada hali gida ma zaka iya bashi, amma saboda zuciya wai seka anshi kudin hayarshi. Gaskiya banji dadin wannan abun ba, aduniya idan baka rufama dan uwanka asiri ba, babu wanda zaka rufamawa kaji dadi. Kuma daga yau inde inada kaso acikin gidan nan to abama Yaya yazauna agurina bance yakara biyan komai ba, dukar da kai Kabir yayi yace kayi hakuri yaya insha Allah daga yau komai yawuce. Mungode da tunatarwar daka mana, hakika dan uwa abin sone, munso mubiyema son zuciya kamar yanda Yaya yayi amma katunatar damu, kallon Yayansu yayi yace dan Allah yaya kayi hakuri da abinda mukayi maka. Murmushi yayan yayi yace nikeda neman gafararku, na cutar daku amatsayinku na yan uwana wadan da muke ciki daya, ko Lawal wanda bamu fito ciki daya ba, betaba nuna mana bambanci ba, segashi nida nakasance babba acikinku nine azzalumin. Kuyafemun dan Allah, mika hannu yayi yakarbi Ansar yana kuka, rungumeshi yayi yana fadin Labiba bakiyi magana ba, kiyafemun,wlh da ace inada kudi dazan biyaki kudinki dana cinye, amma ayanzu banida komi, wani lokacinma kudin abinci gagarata sukeyi. Goge idonta tayi tace bakomai Abba nayafe maku Allah yamana gafara, kallon Abbas yayi yace mungode da yanda karike mana diya, koba,a fada ba munsan tana cikin kwanciyar hankali, Allah yabiyaka. Abbas yace amin Abba,Kawu yace tomu zamu koma, nan da kwana 2 zandawo induba ku, hannu Abbas yasa yaciro kudi masu yawa yaraba masu, anan yace susa yara suzo sudaukar masu kayan abinci amota. Godiya sukayi masu sosai, bayan sunfita Kawu ya kalli Kabir yace dan Allah kada ku kara barin Yaya yayi kuka, kuduka kuna da mata sekunbama yaya muhimmanci matanku zasu bashi, dande kwano daya so 3 arana dan Allah kudauke mashi. Kabir yace insha Allah Yaya zaka dawo ka iske komai yacanza, zamu koma kamar da, Yaya baze kara kuka ba, komai ze canza, sosai kawu yaji dadi, haka shima yayi masu kyauta yafita, alokacin har ansauke kayan abincin haka suka tafi zuciyarsu cike da farin ciki. Sosai Umma taji dadin abinda suka fada mata, kuma aranar aka yaye Ansar aka bama Ummashi yaye, su Abbas suka bude sabon shafin soyayya. Washe gari su Abbas sukaje suka sayi fili shida Alh, Abbah, anan ne yake fada mashi yanda sukayi da yan uwan Labiba, shima yatausaya ma Yaya kuma yaji dadi dasuka shirya, bayan sunkarbi takardun fili duka shedu suka sa hannu, Gidan Alh, Abbah sukaje, bayan sunci abinci mezanan gida yazo Abbas yazabi irin ginin dayake so,Alh, Abbah yace shikenan insha Allah gobe za,a fara zagaye filin. Tashi sukayi suka koma office. Duk yanda su Alh, Bukar sukaso su hana Abbas aikinshi abu ya gagara, babu irin abunda basuyi mashi ba, amma hakansu becima ruwa ba, hakan yasa suka kara farashin Dala da kansu batare da kowa yasani ba, duk wanda yayi canji agurinsu to da tsada zeyi, Zaune Auwal yake shida Saddik suna fira, dan Auwal tunda Alh, Abbah yace yarika sakama su Alh, Bukar ido yarage zama a office din Abbas sede idan zeyi aiki, wasu mutane sukaga sunfito daga office dinsu Alh, Bukar. Daga ganinsu baki ne, tsayawa sukayi da jaka ahannunsu sunata magana, Auwal yace Saddik kana kallon wadan can mutanan kuwa? Naga sun fito daga office dinsu Alh, Bukar amma kuma suna magana. Saddik yace kaine bakaga lokacin dasuka shiga tare da Alh, Bukar ba, tundaga waje naga suntaho dashi, har sauri yakeyi, kila sababbin costomers ne, shiyasa yake sauri yatarosu kada suje gurin wani. Tashi Auwal yayi yace inazuwa, Saddik yace kai kuma ina ruwanka? Auwal yace kaide kazo muje idan zaka, haka suka nufi gurinsu, bayan sun gaisa Auwal yace ammade ku bakine ko? Daya daga cikinsu yace wlh kuwa bakine mu, dan bamu san gurin nan ba, mundauko me adedeta mukace yakawomu inda ake canjin dala shine yakawomu nan, ana ajemu muka hadu da wani mutum shine muka tambayeshi, Aiko bari beyi ba muka karasa maganarmu yace mubiyoshi, toshine yayi mana canji, amma abun mamaki yanda mukaji ance dala ta sauko semukaga agurinsu bahaka bane, shine kuka gammu anan, Shawarar damukeyi mukoma mu karbi kudinmu dan gaskiya tafiyace gabanmu kuma kudin bazasu ishemu ba. Murmushi Auwal yayi yace kuzo muje gurin megidanmu acan za,a kwatar maku hakkinku. Sosai Alh, Abbah da Abbas sukayi mamakin abindasu Auwal sukace, murmushi Alh, Abbah yayi yace ayau ne zaka nuna masu kanada iko dasu, tashi yayi yace kuzo muje office dinsu, idan sunso za,ayi abun cikin lalama, Amma idan sun nuna taurin kai kowa zesan halin dasuke ciki kuma za,ayi zama da manya ayimasu hukunci, suna fita sukaga taro akofar office dinsu, mutane se hayaniya sukeyi, Ganin Abbas agurin yasa kowa yayi shiru, tambayar su Abbas yayi abinda yake faruwa, anan wani yafada masu wasune sukazo canji shine aka basu bayanda aka tsaida farashin Dala ba, kuma su Alh, Bukar ne suka basu. Wani irin kallo Abbas yayima su Alh, Bukar, tuni zufa tafara keto masu, cikin in ina Alh, Bukar yace kaga wannan magana bekamata ayita anan ba, kumuje ciki muyi magana. Wani daga cikin yaran wajen yace wlh babu inda za,a je dama duk cikin Wapar nan kowa yasan irin zalincin da kuke ma mutane, se wani yazo yin canji gurin wanda yasaba dashi haka zakusa yaranku surika taresu, To wlh bazamu yarda ba, ayau se an dauki mataki, Abbas yadaga hannu yace kuyi hakuri muma abinda yasa mukazo nan kenan, munsamu sun cuci wasu baki, dan haka kuyi hakuri yanzu zamu zauna da manya, Kuma kowane irin hukunci yakamata ayi masu za,ayi masu, bazamu yarda da duk wani ha,inci ba acikin Wapar nan, dama kuma kowa yana sane da dokar da akasa alokacin da aka tsadai farashin Dala. Kallonsu Alh, Bukar yayi yace kumu hadu adakin taro, kuma wadanda abin yafaru ku biyomu, se wakilan matasana Wapa, juyawa yayi yatafi office. wayarshi ya dauko yakira Jafar, bayan sun gaisa yace Jafar kayi hakuri tunjiya bankira kaba, wlh munje Jigawa ne, Amma yanzu idan baka komai kazo wapa muhadu, idan kuma kana aiki kabari idan muntashi zanzo nan gidanka. Jafar yace a,a ina kasuwa bari intaho, Abbas yace a,a kayi aikinka nizanzo gidanka Jafar yace anyi haka? Dariya Abbas yayi yace amma gama. Kashe wayar yayi yadauki wasu takardu yanufi dakin taronsu. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 120 🔱 125 Manyan yan kasuwa ne, na Wapa azaune, bayan sungama sauraran korafin dasu Abbas suka kawo, anan wani babban mutum kuma daya daga cikin manyan wakilai na Wapa yafara magana. A sakamakon samunku da akayi da cin amanar mutane, ha'inci da kuma zalunci, wanda kunriga da kunsan dokar gurin nan dan kuba baki bane, asalima kai Alh, karike wannan mukami na Chairman agurinnan, Amma kuma abun kunya ace hada kai acikin wannan zalunci, dan haka dole za,a yanke maku hukunci dede da laifinku, sannan kuma mubazamu koreku daga gurin nan ba, amma kuda kanku zakuji gurin ya isheku, Domin ayanzu kowa yariga daya san mekuka aikata, dan haka kamar yanda mukace duk wanda aka kama da kara farashin Dala za,a cajeshi tara ta naira dubu dari, kuma haka zaku biya, munyi haka ne, domin mu nunama sauran mutane doka tana aiki, kamar yanda Chairman tun farko yaroka akafa wannan doka, wanda bamu taba samun cigaba kamar na wannan Chairman dinba. Kuma zaku maida ma wadan nan mutane kudinsu dakuka karba, nagama maganata. Wani daga cikin mutanan yatashi yace shawarar dazan baku guda dayace, wannan hali dakuka dauka ba abu bane me kyau, zaku batama kanku sana,a ne, dan haka ku gyara tunda wuri. Chairman ko akwai abinda zakace? Tashi Abbas yayi, fuskarshi dauke da murmushi, suna hada ido dasu Alh, Bukar sukayi saurin dukar da kai, gyaran murya yayi yace tonide abinda zance bawani abu bane, Nasan ku duka agurin nan kungirmeni, dan haka zanyi maku tuni akan abinda kuka rigani sani, kawaide kila son zuciyane yasaku take sani, Alh, ina ganin kamar zalunci bayasa mutum yatara arzikin da Allah be bashi ba. Kuma koya tarashi baze taba alfahari dashi ba, saboda bada gumin kanshi yatara ba, ni aganina mutum yatara kudi ko MUHALLI da gumin kanshi, kudin halak bana haram ba, wannan shine abin alfahari. Amma duk abinda aka tarashi ta hanyar haram wata rana seya lalace, garama ace mutum maula yayi aka bashi zefi yin alfahari dashi, dan be cuci kowa ba, kawai kyauta aka bashi, kunga kuwa baza,a taba hada abinda aka bama mutum kyauta ba, da wanda mutum yatara ta hanyar zalunci, cin amana, ha'inci da yaudarar mutane. Daga karshe ina baku shawara dakuji tsoron Allah, shi arziki idan Allah yace zakayishi kota yayane sekayi shi, mutane dayawa farkonsu talauci ne, amma daga baya Allah yana dagasu har suzo suwuce wadan da aka haifa cikin arzikin kudi. Shiyasa arayuwa kada ka raina mutum daraja ce dashi, inafatan wannan abun daya faru zezame maku darasi, kuma zaku daukeshi amatsayin Allah yana sonku shiyasa yasa asirinku yatonu kozaku gyara halinku. Allah yatsare gaba, kuma yakaremu daga sharrin son zuciya. Gaba daya jikinsu yagama sanyi, sosai maganar Abbas ta ratsa jikinsu, yaro karami amma yafada masu maganar dasuka kasa ganeta tun farko saboda idonsu yarufe, tashi Alh, Bukar yayi yana goge zufa dan shi Alh, yama kasa motsi. Alh, Bukar yace hakika bamu kasance mutanan kirki ba, kuma wannan abu daya faru zanso kubamu dama domin munemi yafiya agurin mutanan gurin nan, domin tun bayau ba, muke zaluntarsu, tun lokacin da Alh, yarike mukamin Chairman muka kasance azzalumai, Amma Allah yarufa mana asiri haka mukacigaba da tara dukiya ta haram, wadda babu wani abu dazata iya yimana alokacin dazamu tsaya agaban Allah ranar gobe kiyama, dan haka wannan magana inaso inyita agaban jama,a. Tashi sukayi suka fita, aikuwa dama mutane duk sun taru agaban office din sunajiran suji hukuncin da aka yanke masu. Anan alkalin Wapa yayi ma mutane jawabin abinda aka yanke, Nan guri ya rikice da hayaniya, mutane sunata jinjina ma Abbas, saboda andade ba,a samu Chairman me adalci kamarshi ba, ansha kama masu laifi irin haka abaya, amma da anshiga dakin taro anfito sekaji magana tawuce, amma yau gashi Abbas ya tsaya seda aka yanke ma masu laifi hukunci. Anan Alh, Bukar yafara rokon gafarar mutane yana kuka, duk irin abubuwan dasuka aikata seda yafada masu. Bayan yagama abokinshi yatashi, danshi yama kasa kukan sede zufa datake tafaman zubo mashi. Bayan yanemi gafarar mutane, yakalli Abbas, hannushi yakama yace, hakika ba girma bane hankali, kwakwalwa ce mutum, gashide kai yaro ne, amma kana da tunanin manya, lallai da ace za,a samu irinka acikin manyan kasar nan, da kasarmu ta cigaba. Dayawan mutane, tsoro da Son zuciya shine abinda yake hanasu suyi yaki darashin adalci, amma kai bakada kodaya acikinsu, alokacin danake Chairman, nasan ana abubuwa dayawa agurin nan, Amma saboda tsoron manyan gurin nan da kuma son zuciya irin tawa, nakasa daukar mataki, saboda ina tsoron kada inrasa matsayina, kamar yanda manyan gurin nan sukeyi mani barazana. Aranar da mukazo mukayi maka barazana nadauka washe gari zaka zo gurinmu, amma abun mamaki se banga wani bacin rai da damuwa atare da kaiba washe gari, nan yafada ma mutane irin cin mutuncin dasuka yima Abbas a office dinshi. Kowa seda yatausaya ma Abbas, kara rike hannun Abbas yayi yace kayi hakuri da irin abinda mukayi maka, da wanda kasani dama wanda baka sani ba, tabbas gara abani kyautar MUHALLI senafi ganin darajarshi da ace mallaki nane, amma bata hanyar halak na mallakeshi ba. Munsami labarin ayanzu haka zaka fara gini naka na kanka, kuma hakan yasamo asaline saboda gorin damukayi maka, munyi hakane dan muci maka fuska, amma gashi agurinka yazamo alkhairi, Tunda gashi zaka mallaki gidanka da guminka, dan Allah kayi hakuri, hannunshi yadaga sama yace inama duk kanin matasan gurin nan sha,awar zama kamar ABBAS ALEE. Mutum me gaskiya da rikon amana, mutum me zuciyar nema, marar kasala, mutum marar tsoron dan uwanshi dan Adam, inafatan ka zarce abisa wannan matsayi da Allah yabaka, hakan zesa mukara samun canji acikin gurin nan, kuma kasuwarmu tazamo zakara akan sauran kasuwanni. Gaba daya gurin aka dau tafi, kowa yana jinjina ma Abbas,masu daukar vedio taxwaya sunayi, hatta da yan jarida seda suka sami zuwa gurin, hakan yasa dan danan suka fara daukar abinda yake faruwa suna aikawa. shikam Abbas seda kwalla tazubo mashi, anan kowa yace yayafema su Alh, Bukar kowa yakama gabanshi. Kallon su Alh, Bukar Abbas yayi yace bakomai, nayafe maku, Abinda kukamun baku zalunceni ba, asalima temako na, kukayi, dabaku fadamun haka ba, bazan yi wannan tunanin ba, amma gashi ta dalilinku zan sake cikama iyayena burinsu, nagode Allah yabar zumunci. Hannu yamika masu sukayi musabaha, kowa yawuce suname yimashi godiya. Wannan abu daya faru bakaramin kara daukaka darajar Abbas yayi ba, dan har a redio, gidan Tv, da jaridu seda aka buga, wannan shine abinda yasa Abbas yakara samun daukaka da suna agurin mutane. Mutane daga guri daban daban suka rika zuwa kawai dan suganshi, manyan mutane kuwa duk gurinshi suka koma dayin canji, duk da kudin dayake samu baya rike mutane agurinshi, Haka yake rarrabasu agurin sauran abokanan kasuwancinsa, domin kowa yasamu, wannan abunma dayayi yakara mashi daraja agurin yan Wapa. Dama kuma hakane, idan kayi niyar cutar bawan Allah, abun seya zamemashi alkhairi. Bayan suntashi daga aiki yawuce gidan Jafar, acan yayi sallar magriba yadaukeshi suka nufi gidanshi, amota Abbas yabama Jafar labarin abinda yafaru dashi bayan rabuwarsu. Sosai Jafar yaji dadin abinda Abbas yafada mashi, anan shima yafada mashi irin wahalar daya sha, sosai Abbas ya tausaya mashi, kallonshi yayi yace wlh Jafar dede da rana daya bantaba mantawa da kai ba, A kullum ina cikin tunaninka, kuma inaso inzo inda kake, sede dana tuna da maganar Mama se inji tsoron kada injamaka bakinta yabika, haka nayita hakuri. Jafar yace ni kaina ina tunaninka, sede maganar da Mama tafada ne, take hanani zuwa gurinka, amma yanzu tagane gaskiya, ita da kanta take maganarka yanzu. Naji dadi sosai Abbas da Allah ya nunamun kai acikin kyakkyawar rayuwa, nafi kowa farin ciki, yau gashi Allah yadawo maka da MUHALLINKA daka rasa, kuma yakara maka da babban matsayi wanda ayanzu cikin garin nan harma da wajenshi mutane dayawa sun sanka. Dazu ina kasuwa naji ana maganarka, abun da kukayi ayau, naga ana turashi awaya, wlh har kukan farinciki seda nayi dana ga yanda ake yabonka. Dariya Abbas yayi yace haka rayuwa take, kaima daga yau kabar kwari, zaka dawo kusa dani domin bazan kara barin kamun nisa ba, dariya Jafar yayi yace wato zaka rabani da aikina ko? Kai Abbas yadaga yace tunda muka taso muke aiki akwari, gara yanzu asamu canji. Jafar yace hakane, nagode sosai Abbas, Allah yabarmu tare. Murmushi Abbas yayi yace haba Jafar, ai harmu mutu bazan taba biyanka abinda kamun ba, ka temake ni alokacin dana rasa gatana, kaine farin cikina Jafar. Nagode ma Allah daya barni araye har nima zan samu damar yimaka kadan daga cikin alkhairan daka mun, da bazance zan maka abinda kamun ba, wannan Allah ne kadai ze iya biyanka. Abakin gate din gidan sukaga wasu mutane su 3, suna jingine da katangar gidan, hasken fitila ya haske su, Jafar yace kaga yallabai, ga wasu mutane can suna jiranka, Abbas yace habade, ai bankai wannan matsayin ba. Kilade hutawa sukeyi, Jafar zeyi magana yaga sun nufosu, hakan yasa Abbas yafasa shiga da motar cikin gidan, parking yayi suka fito, da sallama mutanan suka karaso gurinsu. Cike da mamaki Abbas yace suwa nake gani kamarsu Buba? Saurin kallonsu Jafar yayi, yace aikuwa Abbas sune, hada Usman, hannu Abbas yabasu suka gaisa, Jafar ma yamika masu hannu, yana kallonsu, daga ganinsu duniya ta juya masu baya. Abbas yace ya kuka tsaya anan baku shiga ba? Buba yace wlh mun tambayi megadinka shine yace baka dawo ba, muka tambayeshi yaushe zaka dawo yace haka kawai besammu ba, zamu mashi wannan tambayar, shine yace mutafi, Shine muka zauna muna jiranka dan musan kana gari, ko dazu munganka kana jawabi awaya. Murmushi Abbas yayi yace yana da gaskiya kasan yanzu duniya abun tsoroce, kuzo mushiga ciki to. A falonshi suka zauna, nan Abbas yasa Labiba tabama me aikinta abinci da ruwa da lemu takawo masu, Buba sekara kallon falon yakeyi yana mamakin arzikin da Abbas yayi. Bayan sun gama cin abinci, Buba yakalli Abbas yace dan Allah Abbas kayi hakuri da duk abinda mukayi maka, wlh munyi nadama, babu kamar ni, nine nafadama Labiba komai agame da gidan daka gina, gashi nazamo sanadiyar dayasa karabu da gidanka. Segashi nima nasamu mata dede dani tasani narasa komai, ita bama sawa tayi narabu da gidana ba, yaudarata tayi harseda tasa namaida sunan takardun gidan da sunanta, daga baya tayi mani rashin mutunci wanda seda yasa nasaketa har saki 3, Anan nace tabarmun gidana, se alokacin data dauko takardun gidan natuna da abinda nayi, haka mukayita rigima wadda takaimu har kotu, kuma alkali yabata gida, tunda ansamu sa hannuna abisa takardun. Inaji ina gani haka nabar mata gidan, dama kuma bata bari mun haihu ba, haka rayuwa ta juya mun baya, hatta da mashin dina seda na saida, da kyar nasamu wani shago nake kwana aciki, yanzu haka bani da komai, dan Allah Abbas kayafe mani. Sosai Abbas ya tausayama Buba, yace bakomai, ya yafe mashi, kuma yadauko kayanshi yadawo gidanshi akwai daki daya me hade da bandaki a boys quarters din da Umar yake ciki, Godiya yayi tamashi, haka ya tambayi su Usman, sukace su sunada gidansu, kawaide kasuwancinsu ne, babu jari, anan yace suma zebasu jari, godiya sukayi mashi, tare da bashi hakuri akan abinda sukayi mashi, yace babu komai. Kudi yabasu yace gobe su sameshi a office. Bayan sun tafi, Jafar yace Abbas kaga rayuwa ko? Abbas yace nagani Jafar, kalli Buba yanda yarasa gidanshi daya dade yana ginawa, akalla gidan nan yayi shekara 4 yana ginashi, tunkafin musan zamu fara gininmu. Jafar yace ai ita duniya yanzu tunkafin mutum yabarta take koya mashi hankali, Kaga yanzu shima yadauki darasi, kuma naji dadin abinda kamashi dama haka akeso mutum yazama me saka alkhairi akan sharri. Abbas yace nimafa gobe zanfara sabon ginina, jafar yace wannan bemaka bane? Kai Abbas ya girgiza yace wannan babu ko sisina aciki, kyauta Yaya yabani filin kuma yagina munshi, ada nakarbeshi amatsayin gidan dazan zauna, amma sanadiyar wani gori da akamun, yasa zanyi ginina da kaina. Nan yabama Jafar labarin abinda yafaru, seda Jafar yayi kwalla, yace kayi dede Abbas, Allah yataya ka yabaka ikon kammalashi, Abbas yace amin Jafar, Muje kugaisa da Labiba ko? Dariya Jafar yayi yace Labiba sarkin rigima ba, Abbas yace haba yanzu tazamo sarkin biyayya, Jafar yace da gaske? Abbas yace wlh kuwa aiyanzu nakara godema Allah dayasa banyi fushi abaya ba, nasan dayanzu bama tare da ita. Amma gashi danayi hakurin daba kowane namijin zamanin nan ze iya yinshi ba, gashi yanzu ina cin ribar abun, dan ayanzu de bazan iya samun mace kamar Labibata ba, nan yafada mashi yanda take mashi biyayya da kuma kyautatawar datake mashi. Jafar yace shiyasa nake kara baka hakuri, nasan Labiba tanada halin kirki, kawaide kasan halin wasu matan dasaurin yarda da kawaye, gaskiya natayaka murna Allah yabarku tare, Kaga yanzu seka fara shirin karo ta 2, duka Abbas yakai mashi yace se lokacin dakayima Maryam kishiya zanyima Labiba, Jafar yace haba aini da Maryam takalmin kaza, mutu karaba. Abbas yace nima haka nida Labibata, dariya suka sa suka fita, gurin Umma suka fara zuwa, taji dadi sosai ganin Jafar, Ansar da gudu ya haye Abbas yana gwarancinshi, jafar yace ikon Allah, gaskiya mundade bama tare, yanzu wannan danka ne? Abbas yace a,a Ummace tayi aure shine ta haifeshi, pillow din kujera Umma tasa tajefeshi dashi, tashi yayi yana dariya yace ai da gaskiyata Umma, inbanda iskanci na jafar yaze tambayeni bayan ko makaho ya taba yasan Anasar dana ne. Dariya Umma tayi tace wannan kuma tsakaninku, daukarshi Jafar yayi yace rabu dashi Umma, zan ramane, sallama sukayi mata zuka nufi gurin Labiba. Sosai Labiba tayi farin cikin ganin Jafar, bayan sungama gaisawa yayi mata barka, anan yafara tsokanarta akan abinda yafaru abaya, dariya suka rikayimata shida Abbas, tashi tayi tana turo baki tana fadin wlh, zan rama akanka Dadyn Anasar. Hannu 2 yasa yarufe bakinshi yana fadin nayi shiru laifin Jafar ne, dariya tasa tashige ciki, Jafar yace to seda safe tunda kinshige, haka suka fita da Abbas yatafi maidashi, kudi masu yawa yabashi yace semun hadu gobe a wapa, godiya yayi mashi yatafi. Bayan yakoma yayi wanka suka kwanta, Labiba tace amma naga kamar Jafar yana cikin damuwa ko? Abbas yace wlh kuwa, anan yafada mata abinda yafaru, hada labarin su Buba, sosai ta tausaya masu, yace amma gobe zefara aiki a office dina, tace amma ka kyauta gaskiya, Allah yabiyaka, Yace amin Labibata, tace dan Allah inaso gobe idan zaka fita ka kaini gidan kawu, idan kadawo se kadaukoni, Abbas yace angama matata, zata kara magana yarufe mata baki yace muyi bacci. Washe gari bayan sun gama karyawa sukayi wanka Labiba tashirya cikin wani less mekyau da tsada, suka nufi gurin Umma, bayan sungama gaisawa Abbas yace dama Labiba ce zataje gidan kawu, shine zamu fita tare in ajeta idan natashi se indaukota. Umma tace hakan yanada kyau, gara kirika zuwa dubashi, to Anasar dinfa? Labiba tace badashi zanje ba, Umma tace aiko sede kifasa tafiyar, inba kina zuwa dashi ba, yaza,ayi surika ganinshi? Turo baki Labiba tayi tace Umma kawai kibarshi zanje dashi wani lokacin, kuma kinga zaki rasa dan fira. Umma tace nibawani dan fira dazan rasa, maganar ma me ya iya dazanyi fira dashi? Dariya Abbas yayi yace nide zantafi tunda bazakije ba, saurin tashi tayi kamar zatayi kukaUmma tana dariya tace kayanshi kawai zaki dauko anyi mashi wanka, haka tadauko kayanshi sunkayi mata sallama, Turare da sabulai Umma tabada akai masu, godiya Labiba tayi mata sukatafi, amota Abbas se dariya yake mata, yace meyasa bakison tafiya da yaro? Tace wlh takura gareshi, dariya yayi yace damma kinsamu ba,a gurinki yake ba, amma aigashinan zaki haifo mashi kanwa kwanan nan. Dariya tayi tace nibani da komai, yace shikenan Allah ya kaimu ni naga komai ai, da haka suka isa gidan kawu, fita sukayi, Abbas yadauko tsarabar dasu kayi masu, daga gefen gidan su kawu sukaga wata me kosai, Labiba tace Dadyn Ansar wlh kosan can nakeso. Dariya yayi yace mesan kosai ne, kenan? Baki ta turo tace kaide kacika fassara, kayan yamaida mota yace sede muje tare dan bazanje ni kadai ba, bayanshi tabi yana tamata dariya. Sallama Abbas yayi yace baiwar Allah bamu kosai, dagowa tayi zata anshi kudin, karaf suka hada ido da Labiba, har suna hada baki gurin kiran suna, Labiba tace kamar Hauwa? Hawayene suka zubo mata tace itace Labiba, mamakine yakama Abbas, yace karbi kudin kisamata muje sauri nakeyi kada inmakara a office, kosan tasa mata tace kabar kudin, ajemata yayi ya karbi kosan yace a,a dauki kudinki. Kallon Labiba yayi wadda idonta yacika da kwalla yace muje ko, harsuntafi tadawo tace idan kingama kisameni gidan kawu zanso inji labarinki, hauwa tace yanzu kuwa. Bayan sun shiga suka gaisa Abbas yabama Kawu kudi yayi masu sallama, godiya sukayi mashi, har bakin mota Labiba tarakoshi Hauwa sekara lekensu takeyi, hannunta Abbas yakamo yace banyarda kije gurin waccan ba. Labiba tace bazanje ba, amma kayi hakuri nace tazo tasameni agidan kawu inaso inji labarinta dan Allah. Kai yadaga yace shikenan amma da sharadi, bance ki nuna mata gidanmu ba, koma menene tafada maki gidanta se asa akawo mata temako, zanfadama su kawu kadama sufada mata inda gidanmu yake, Awannan karon bazan yarda da kawancenku ba, kuma bazan hanaki temakonta ba, nida kaina ma zan tayaki temakonta, amma maganar kawance babu ita, ina fatan kin fahimceni? Kai tadaga mashi tace na fahimceka, kuma nima bazan bari wani abu yakara hada muba, kawai zanso inji labarinta, kuma intemaketa dan Allah badan halinta ba, kodan tagane duk irin cutar datamun gashi nayi mata rana, Abbas yace shikenan idan nadawo nima zaki bani labarinta. Murmushi tayi tace angama yallabai, adawo lafiya. To masu karatu kunga laifin Abbas daya hana kawancen LABIBA DA HAUWA AKARO NA 2? ZAMUJI LABARIN HAUWA A NEXT PAGE. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263 [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 125 🔱 130 Zaune suke adakin matar Kawun Labiba, seda Hauwa taci abinci takoshi sannan ta kalli Labiba tace dan Allah kifara bani labarinki kafin inbaki nawa, domin nasan naki seyafi nawa dadin sauraro. Ajiyar Zuciya Labiba tayi tafara bama Hauwa labarinta tundaga ranar dasuka rabu ta ita datazo gidanta har zuwa yanzu, su dukansu kuka sukeyi kamar an aiko masu da mutuwa. Goge kwalla Hauwa tayi tace lallai Labiba kinga rayuwa, na cutar dake, kindauke ni amatsayin babbar kawarki amma ni bahaka nadaukeki ba, na cuceki, Tun ranar da kika nunamun Abbas amatsayin wanda zaki aura nafara jin haushi, ban kara jin haushinki ba, seda kika fadamun Abbas yana maku gini, tundaga ranar nafara tunanin yanda zanyi insa kiraba Abbas da wannan gidan, Kema yazamana haya ze kama maku kamar yanda mijina ba gidanshi bane ka .Wlh Labiba karya nake maki danace mijina yanada gida a Danbatta, asalima beda wani gida, kuma dan garin nan ne. Dalilin dayasa na zabeshi amatsayin wanda zan aura saboda naga kinsamu miji,kuma duk cikin samarina babu wanda yashirya aure, hakan yasa nima aranar da muka hadu dashi kawai nayanke shawarar inrigaki aure. Alokacin danayi mashi maganar aure yacemun shifa be shiryaba, asalima beda ko gidan daze sani, ayanzu haka gidan dayake aiki gidan wani uban gidanshi ne, baya zama sosai shine yakama gidan gwamnati idan yazo yake sauka amatsayin guest house nashi. Yace mun da ace yanada gurin daze ajeni daya aure ni, kudin aure bazasuyi mashi wahala ba. Nikam dajin haka na tambayeshi awace unguwa yake zaune idan megidanshi yazo, yacemun anan unguwar yake alayin bayansu kawunki. Kuma gidan daki daya ne se bandaki, shima gidan kakarshi ne, kuma danta ne yaci gidan data rasu, kasancewar dan nata yanada gida shiyasa yabashi yarika zama. Alokacin har na hakura, amma wata zuciyar ta hanani, tambayarshi nayi wata nawa megidanshi yakeyi kafin yazo? Yacemun yanzu ma baya nan yayi tafiya kuma wata 6 zeyi bedawo ba. Murmushi nayi nace mashi meze hana muyi aurenmu kawai akaini can kafin yadawo? Kallona yayi bece komai ba, nace mashi kada yadamu son danake mashine yasa bazan iya hakura dashi ba, nayarda idan megidanshi yakusa dawowa semutashi mukoma gidan kakarshi, dajin haka shikuma ya amince. Kinji yanda akayi mukayi aure harna zauna agidan gwamnati, babban dalilin dayasa na zugaki kada kiyarda Abbas ya kaiki gidanshi saboda nasan nima zamana agidan nawani lokaci ne. Haka muka zauna dashi harna tsawon wata 5, alokacin damuka shiga wata na 6 megidanshi yayi mashi waya yakusa dawo wa, kuma yasamu mata agarin nan daya dawo zasuyi aure kuma agidan ze ajeta. Babu bata lokaci muka tashi muka dawo nan unguwar, kayana ko rabi basu shiga gidan ba, haka nayanke shawarar sayar da wasu. Da haka muka cigaba da zama acikin gidan, Gaba daya rayuwa ta canza mani, dama dadin danakeji saboda kayan garata ne, amma suna karewa muka shiga cikin kunci, mijina koya fita baya samo komai, idan ma yasamo awaje yakecin abincinshi. Ahaka har muka shekara daya da rabi, duk na rame nayi baki idan baki manta ba akwai sanda nazo gidanki kike tambayata meyasameni, nace maki rashin lafiya nayi, ganin zaki matsamun da tambaya nace maki zantafi. Hakan yasa nadena zuwa gidanki, lokacin da wahala tamun yawa na yanke shawarar inzo insameki inroki gafararki, amma inazuwa na iske kuntashi, nakiraki bana samu, har nan gidan nazo suka ce basu san inda kuka koma ba. Wlh Labiba har bara gidan mutane seda nafarayi, danaga hakan bazemun ba,shine nafara shiga gidan masu kudi ina neman aiki, nasamu aka daukeni, anan nafara samun sauki, kinsanni da son banza, Wata rana matar gidan ta aje kudinta tashiga daki, inazuwa ni kuma nadauke, ashe tazo fitowa ta ganni, tun daga nan ta koreni, haka na koma rayuwar baya, mijina idan yatafi seyafi wata bedawo ba. Ana cikin haka wannan dan kakarshi yazo ganin gidanshi, ganin yanda gidan ya koma yace mutashi zeyi gyaran gidanshi, mowakan mijina yabashi hakuri seya rufe ido yarika mashi rashin mutunci, nan ya fusata yace semunbar gidan. Alokacin na koma gidanmu, seda nayi wata guda, kinsan kishiryar mamana batada kirki, ganin mamana tarasu shiyasa tashiga matsamun, gaba daya aikin gidan yadawo kaina, 'ya'yanta basa ragamun, Ga Babana baya zama se dare, bayan wata guda mijina yazo gurin Babana yace yasamu angama gyaran gidan, dama haka muka cemashi, nan na bishi muka tafi. Ashe hakuri yaje yabama dan uwanshi, shine yace gyaran gidan yakeyi yajira yagama zebashi daki daya, kinsan yanda ya gyara gidan? Ciki da falo ya maidashi, yazuba yan haya daga zauren gidan yayi wani karamin daki yaja karamar katanga daga gaba yayi mana wani karamin bandaki. Ko gado na beshiga ciki ba, bare katifa, hakan yasa mijina yace sede mu saidasu musayi karamar katifa, haka yadaukesu yaje yasaido, ahanyarshi ta dawowa wata mota ta kadesu a adedeta, dagashi har me adedetar babu wanda yarayu. Bakaramin tashin hankali nashiga ba alokacin da aka kawomun shi, haka dan uwanshi da mutane suka shiryashi aka kaishi, nasha kuka, duk da irin rashin kyautawar da yayi mani, amma daya rasu naji alokacin nake son zama dashi, Sonshi da kaunarshi kamar alokacin aka dasamun su, haka nacigaba da karbar gaisuwa, tare da sadaka daga gurin mutane, Bayan sadakar 7 dan uwan mijina yasameni yabani kudin da aka samu ajikin mijina da kuma sauran sadakar da aka samu, anan yake tambayata zan koma gida ne? Nace mashi inde zebarni inaso inzauna anan. Yaji tausayina yace bakomai incigaba da zama, kudi nabashi nace yasayomun karamar katifa, kin karbar kudin yayi yaje yasiyomun yakawomun. Haka nacigaba dazama ni kadai, alokacin da Babana yace kozan dawo gida, nace mashi yayi hakuri yabarni inzauna inyi takabata da iddata anan, shima tausayina yaji dan yasan zaman damukeyi da matarshi, haka yakawo kudi masu yawa yabani. Ahankali ina cin kudina, har nafara maida jikina, kinsan zara bata barin dami, haka kudin suka dauko karewa, ganin idan suka kare zanshiga wahala yasa nayanke shawarar fara kosan saidawa. Kasan cewar layinmu beda mutane siyasa nazo nan layin nafara kosai, ba laifi ina samu, da haka nake rike kaina harzuwa yanzu. Kiyafemun Labiba, nasan hada hakkinki dana Abbas yake bibiyata, kuyafemun kona samu sauki. Kuka ne yaci karfinta, Labiba ma kuka takeyi sosai, tausayin Hauwa duk yakamata, wayarta ta dauka takashe recording din datayima Abbas, dan bazata iya bashi labari ba, hakan yasa tayi mashi recording. Hakuri tashiga bata, tace kiyi hakuri Hauwa, dama haka rayuwa take, duk wanda ya cuci wani shima seya ga rayuwa, nima na cuci Abbas shiyasa na tsinci kaina ahalin damuka shiga abaya, wannan abun daya faru ya ishemu darasi. Ina maki ta,aziyar mijinki, Allah yajikanshi, Hauwa tace amin, nagode Labiba, dan Allah kicema Abbas ya yafemun, Labiba tace bakomi munyafe maki, Allah yakara yafe mana. Amma shawarar dazan baki Hauwa mace duk inda take dole setana da me kula da ita, kibar ganin kamar kin girma, haryanzu yarinyace ke kawai wahalar rayuwa ce ta maidaki haka, Kyan mace gidan iyayenta ko gidan mijinta, ko gidan 'ya'yanta, komin girman mace bata iya rike kanta dole seda mate maki, ina guje maki sharrin shaidan,duk yanda kikaso ki kame kanki zuciya batada kashi, Wanda yake cikin wadata ma yana bin masu kudi bare kuma ma bukaci, kiyi hakuri da duk irin rayuwar dazaki tsinci kanki aciki wata rana komai ze wuce, gara ki koma gaban mahaifinki kowace irin wahala matar babanki zata baki bazata taba rabaki da numfashinki ba harse lokacinki yayi. Ajiyar zuciya Hauwa tayi tace hakane Labiba, maganarki gaskiya ce, zuciya batada kashi, nagode da shawararki, insha Allah ayau ba gobe ba zanbar gidan danake, zanyi hakuri inzauna agidanmu kafin Allah yakawomun canji. Kudi masu yawa Labiba tabama Hauwa tace takara jari tasayi wani abun tarika sana,a kuma tasayi kayan amfaninta. Godiya Hauwa tayi mata tace, awace unguwa kuke dazama yanzu? Labiba tace karki damu zanzo har gidanku indaukeki muje can, ai yanzu kingama iddarki ko? Hauwa tace E, tashi tayi tace bara inje infara hada kayana, Labiba tace to sekin ganni. A Office Abbas ya iske Jafar,bayan sun gaisa ya nuna mashi wani table yace daga yanzu kazama PA na, dan haka ga kujerarka can, dariya Jafar yayi yace kai amma nagode, ashede Allah zenunamun ranar dazan samu aiki a office, ranar dazan rika shan iskan AC. Abbas yace haka Allah yake al,amarinshi, Jafar yace amma kuma Auwal fa ? Abbas yace yana nan amatsayinshi, sede shi mefita ne, kai kuwa kana office, tashi muje gurin Yaya dan yacemun yau za,a fara gini. Haka suka fita suka nufi gurin ginin Abbas, sosai Alh, Abbah yaji dadin irin matsayin da Abbas yabama Jafar. Bayan sun gama Abbas yanufi inda ake saida mashin, yasayama Jafar Lifan, sosai Jafar yaji dadin kyautar da Abbas yayi mashi, daga nan yayi masu siyayyar kayan abinci. Seda suka fara zuwa gurin maman Jafar suka aje mata nata, hada kuka tayi tana kara rokon Abbas yafiya, yace bakomai, anan Jafar ya gwada mata mashin din da Abbas yasaya mashi, Abbas yasha addu,a haka yadauki kudi yabata yawuce dauko Labiba. Bayan sundawo gida suka mika Ansar gurin Umma, wanka sukayi, Umma tabada abinci aka kawo masu, seda suka gama cin abincin sukayi brush suka kwanta, Abbas yace to azo abani labarin, kawarki. Dariya Labiba tayi tace Allah sarki Hauwa, ai labarinta baze badu da baki ba, hakan yasa nayi maka recording dan insamu sauki, amsar wayar yayi ya kunna, shiru sukayi suna sauraro. Tunkafin yakare hawaye suka fara sintiri afuskar Abbas, yaji tausauyin Hauwa sosai, bayan yagama ya ajiye wayar, itama Labiba kuka takeyi. Abbas yace Allah sarki, gaskiya na tausaya ma Hauwa, hakika taga rayuwa, Allah yajikan mijinta da rahma. Labiba ko kin kula aduk cikin mutanan dasu kayi sanadiyar sakamu cikin rayuwarmu ta baya duk sunfimu fuskantar wulakanci? kinsan kome yasa? Saboda mu bamuda hakkin kowa akanmu, bamu cuci kowa ba. Dama kuma haka rayuwa take, duk wanda yace tukunyar wani bazata tafasa ba, to tashi ko zafi bazatayi ba, yanzu inasu Alh, Bashir dasuka so halaka ni? Suna can suma sunga rayuwa, gobe ne wa,adinsu yake cika zasu fito, kinga koba komai sun rasa abubuwa da dama. Amma kuma naji dadin shawarar dakika bama Hauwa, kuma insha Allah nima zantemaketa, zanga abinda zanyi insha Allah. Labiba tace Dadyn Ansar, nikam tundazu nake wani tunani, Yace inajinki, dama naga shima Buba beda aure shine nacemeze hana muhadasu,murmushi Abbas yayi yace saboda kucigaba da kawance ko? Kai ta girgiza, yace hmmm, Labiba bazan boye maki ba, wlh, Hauwa ta cutar dani, inbadan Allah yaso ba dabazan aureki ba inda ace nabiyema zuciya, Dole inyi duk wani abu dazanga na nisantaki da ita, amma kiyi hakuri, tunda ta gane kuranta, zanyi tunani akan maganarki, amma fa ko hakan yakasance dole zan sama masu gida nesa damu, dan shima Buban bangama yarda dashi ba, koda nace yadawo gidana, dande kawai akwai hidimar danakeyi yanzu, Amma da komai ya kammalu shima zetafi, gara inbashi jari, idan kuma aurensu ya yuwu, itama zambata jari kuma insama masu gida nesa damu. Labiba tace hakan ma yayi nagode, yace bakomai. Washe gari su Alh, Bashir suka fito daga gidan yari, duk sun kode, sunkara tsufa saboda wahala, acikin abokansu babu wanda yazo tarbarsu, mutum daya ne aka samu cikin yan uwan Alh, Bashir yazo daukarsu. Tun amota yake tambayarshi ina yaranshi da matarshi, babu abinda yake cewa illa suna nan lafiya lau Alh, mujede gidan ka huta. Haka nan yarika jin gabanshi yana faduwa. Ur's. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263. [10/7, 6:11 PM] nabilalady5: 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 DARAJAR MUHALLI 🏡🏡🏡🏡🏡🏡🏡 Nah Marubuciyar Zamani NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) @House of Novella Association (H,O,N,A) www.NabilaLady5@gmail.com Season 130 🔱 135 LAST PAGE!!!! A firgice Alh, Bashir yafito daga mota yana kara murtsike ido domin tabbatar da abinda idanunshi suke nuna mashi, faduwa yazoyi dasauri suka rikeshi zufa ce tafara keto mashi, Kamashi sukayi suka sakashi mota yana fadin ina zaku kaini kubarni inje akwai abubuwan dazan dauka acikin dakina, dan Allah kada kucemun komai yatafi. Lallashinshi suka farayi, kallon driver yayi yace dan Allah Kasim meyafaru kafada mun, tunkafin zuciyata ta buga? Kai Kasim ya girgiza yace Alh, kayi hakuri muje can gida na zakaji komai. Zaune suke afalo Alh, Bashir yana zaune kasa rigarshi duk ta jike da zufa, idanu ya zubama Kasim yana sauraronshi. Gyaran murya Kasim yayi yace wato Alh, abinda yafaru shine, yau tsawon shekara daya kenan iyalanka sukatashi cikin tashin hankali, sakamakon gobarar data tashi acikin gidanka. Kuma ba komai bane ya haddasa ta ba, se karamin danka, ankunna inji da dare shikuma yadauki ashana yana wasa da ita, se mamarshi ta anshe, ta ajeta ashe yagani, bayan ta tafi yadauka seyatafi can baya inda ake aje injin, Wata takarda yagani shine ya kunna ashanar ajikinta, dayake babu rabon ya kone, yana ganin takama shine yaji tsoro seyadauketa ya wurga ta baya shikuma ya ruga cikin gida, ashe kusa da injin yajefa, Kafin mutanan gidan su ankara kawai aka ga wuta takama, nan kowa yafara neman yanda zeyi yafita, saukin da aka samu wutar tabaya tafara ci, haka kowa yafita, babu wanda ya tsaya daukar wani abu, Matarka ce kawai tayi kokarin daukar kayan sarkokinta da jakarta, gashi alokacin mu muna masallaci sallar isha,i kasan wutar fetur, nan take gaba daya gidan yakama da wuta, Lokacin da mutane sukazo aka fara zufa ruwa amma kamar ana kara mata mai,kafin akira masu kashe wuta tuni wutar tacinye gidan, haka sukazo aka kashe wutar babu abinda yayi saura na amfani, motocinka duka sun kone. Kuka sosai Alh, Bashir yakeyi kamar karamin yaro, kallon Kasim yayi yace yanzu ina matata da yarana suke, nasan acikin jakarta akwai ATM dina, kuma nasan za,a iya samun wani abu agurinta, wlh Kasim bayan wannan kudin na account dina bani da sauran wani abu. Kasan ni ba ma,abocin siyan kadara bane in aje, nafison inga zallar kudi a ahannuna ko acikin account dina, nasan narasa kudade masu yawa acikin dakina, amma dasauki tunda na cikin account sun tsira. Dukar da kai Kasim yayi yace Alh, nibansan mezan cemaka ba, domin bayan komai yalafa Ummar mu tace da Hajiya sudawo gidanta su zauna kafin asamu agyara gidan ko kuma su sami wani gurin. Kwananta 2 tace zataje unguwa, tun ranar data tafi haryanzu tsawon shekara daya babu ita babu labarinta kuma munsami labarin tasayar da filin gidanka daya kone, kuma kanina yafadamun yaganta aranar data tafi taje bank. Alokacin da muka sami labarin tasayar da filin mukaje muka sami wanda yasayi gidan,takardun gidan yadauko mana kuma tabbas sune ga sunan matarka nan ajiki, hakan yasa mukashiga nemanta, amma babu labarinta, sauran yaran haryanzu suna gurin Ummarmu. Innalillahi wa inna ilaihirrajiun shine abinda Alh, Bashir yake maimai tawa, idan kaga kayanshi kamar akwara mashi bokitin ruwa, duk da fankar datake aiki afalon amma bata isar shi. Kai yadafe yama rasa abin cewa, abokinshi ne, yace hakuri zakayi kasan duk abinda Allah yaso ga mutum seya faru, dan haka kayi hakuri se Allah yasaka maka, shiru yayi ya tuna firar dasukayi da Alh, Bashir ajiya daren dazasu dawo. ( Zaune suke acikin dakin dasuke kwana, Alh, Bashir yace kasan kuwa ayanzu idan nakoma gida ina da kudin dazasu isheni kafin incigaba da kasuwancina? Dariya abokinshi yayi yace lallai Alh, ainasanka da dabara, nasan kayi ajiya acikin account dinka sosai, dariya Alh, Bashir yayi yace wane account? Ai tun sanda nabama Hajiya ATM dina narage saka kudi aciki, adakina nake ajiyarsu wani guri wanda babu wanda ya isa yaganosu seni.) Ajiyar zuciya yayi alokacin daya gama tuna maganar dasukayi jiya, gaba daya tausayin Alh, Bashir yagama kamashi, duk wani buri nashi Allah yaruguza mashi. Maganar Alh, Bashir ce ta katse mashi tunanin dayakeyi. Hannun Kasim Alh, Bashir yakama yana kuka yace Kasim tabbas wannan abun daya faru dani hada hakkin marayu dana danne, anyarda dani naci amana dan Allah kuyafemun, amtsayina na kanin mahaifinku ban iya rike amanar Allah ba, nine yakamata inrikeku amma senazamo mecinye maku abinda aka barmaku. Idan baka mantaba, alokacin da Yaya yarasu, acikin account dina aka turo dukiyarshi datake kasar waje, nine nayi maku canjin kudin da kaina, wlh ko rabin abinda aka turo ban baku ba. Haka na boye kudin nan acikin dakina segashi nima dayake ba hakkina bane ko kwandala banci ba acikin kudin haka suka kone gaba daya. Kai cona nayi asara natara dukiya da kudin haram duk kadarorina dana tara babu wanda babu kudin haram acikinsu. Allah na gode maka dabaka bani ikon cin wannan kudi na marayu ba, dan Allah Kasim kuyafemun, yanzu ba se anjima ba zamuje inbama hajiya hakuri, wlh nayi nadamar abinda na aikata, yanzu ni Bashir ina zan dosa? Kifa kanshi yayi yacigaba. Alh, kabar kuka, inde nine nayafe maka, sede muje gurin yan uwa na ka tambayi gafararsu. Kuma kadena maganar inda zaka zauna, insha Allah bazamu barka ka tozarta ba,Allah ya yafe mana gaba daya, bara insa akawo maku abinci kuci. Alh, yace a,a muje gurin hajiya nafison innemi yafiyarsu. Tashi sukayi suka nufi gidansu Kasim, dayake Ummansu tana zaune agidan dasuka samu agadonsu. Gaba daya falon kuka sukeyi dasuka gama jin abinda kanin mahifinsu yayi, yaranshi guda 3 suna jingine ajikinshi suma kukan sukeyi, haka yayita basu hakuri, anan kowa yace ya yafe mashi, godiya yayi masu. Kasim ne yafara magana kasancewar shine babba, Kallon Ummansu yayi yace Umma inaso zantafi da Alh, gidana tunda akwai wani part seya zauna aciki, yaran kuma yabarsu anan tunda kince zaki rikesu. Goge kwallan fuskarta tayi tace bakomai, Allah yayi maku albarka, kutafi tare nizan rike yaran, Allah yatayani riko, ita kuma hajiya abinda tayi itama zata hadu da dede ita. Godiya Alh, Bashir yayi tamata yana kuka, haka suka nufi gudan abokinshi suka saukeshi sannan suka wuce gida. Haka rayuwa tacigaba da tafiya ginin Abbas ba dare ba rana dayake akwai kudi, katanga daya ce amma part 2 akeyi aciki, komai iri daya, Alh, Abbah yadauka ma aure Abbas zeyi shiyasa bema tsaya tambayarshi ko nawaye dayan part din ba. Sosai Jafar yake aiki a office din Abbas, suna samun cigaba a kasuwan cinsu, dan danan Jafar ya murje yakara kyau, su Alh, bukar duk sunzama abin tausayi basosai suke samun ciniki yanzu ba, Damma Abbas yana tura masu mutane, hakan da yayi masu bakaramin dadi sukaji ba, kuma yakara sakasu jin kunyarshi, wani girma suke bashi tamkar shine babbansu. Su Alh, Bashir har gida suka sami Abbas suka nemi gafararshi, anan yace masu bakomai, kuma zasu iya dawowa kasuwa suci gaba da aikinsu, kudi yadauko yabasu yace sukara jari, godiya sukayi mashi suka nufi gidan Alh, Abbah. Shima kudi yabasu kuma yace ya yafe masu, da haka suka yanke shawarar su koma kasuwarsu kawai, koma me mutane zasu ce masu gara sunemi halak dinsu hakan zefi masu. Sosai Labiba take aikama Hauwa da kayayyaki da kudi, duk yanda Hauwa taso tasan gidan Labiba abun ya gagara, hakan yasa ta hakura, dan tasan Abbas ne baya son sucigaba da kawancensu. Sosai Hauwa ta murmure domin ayanzu tana cin abinda take so, danko girki bata cin nagidan, sunan tana zaune agidanne, amma abangaren mamarta take komai dama ita kadai ta haifa, Bata fita tayi aikin gida hakan yasa matar babanta tahanata abinci, ko yaranta bata barin suje gurinta, amma ganin irin abubuwan da ake aikoma Hauwa, da irin girkin datakeyi yasa matar babanta tafara saukowa. Dan wani lokacin idan yaranta sukaje gurin Hauwa idan tayi wani abu medadi tana basu, hakan yasa matar babanta tanemi gafararta kuma ta nemi suyi zaman mutunci. Ba laifi su Alh, Bashir sunfara samun mutane, kuma suna ciniki, sede a dar dar suke zaune acikin mutanan gurin sunzama tamkar mujiya cikin tsuntsaye, ganin haka ne yasa Abbas yake jansu ajiki da kanshi yake tura masu mutane. Zaune Abbas yake shida Jafar da Buba, bayan sungama jin bayanin Abbas Jafar yayi dariya yace amma wlh abokina ka iya tunani me kyau, wannan magana taka haka take, babu wani tsayawa shawara ni Jafar na bama Hauwa Buba. Dariya Abbas yayi yace e lallai sannu da kokari, kabarima shi Angon yayi magana amma kai har kabadashi, kafadar Buba Abbas yadafa yana fadin na Hauwa kayi magana mana. Hannun Abbas Buba yature yace dan Allah karabani da Hauwa, ni nasan babu wata shiryuwa datayi kawaide dadin bakine zatayi maka saboda tashiga yanayi, amma wannan matar irin abinda tayi maka ai bazan yarda na aureta ba. Kude sake duba mun wata, ni wlh ko me tallar Awara ce inaso amma banda macen da idonta yabude sosai. Dariya Jafar yayi yace wai kai kana kallon masu talla wadanda basu waye ba ko? Ai inaji macen datake talla tafi macen datayi master's budewar ido. Kaide kawai kayi addu,ar Allah yabaka tagari, amma maganar wadda idonta be bude ba, ma bata taso ba, karewar budewar ido seka auri karuwa kuma kuzauna lafiya, amma zaka iya auren macen da tunda ta taso agidansu bata fita. Karatu ma acikin gidansu tayi, islamiya ma cikin gida, idan zata fita seda driver, batasan kowa ba, babu wanda yasanta amma wlh, idan ka aureta tsiyar dazata maka setafi me yawon duniya. Ai yanzu kawai kadage kada ka cuci wani, kazauna da kowa lafiya, zuciyarka daya akan kowa, kamika al,amuranka agurin Allah, seya zaba maka abinda yafi maka alkhairi, Amma wayonka, dabarar ka basu isa su zaba maka abinda kakeso ba. Zakaga akwai mutane dayawa suna aikata alfasha da yaran wasu, amma yaransu se su sanya masu matakan tsaro, waisu aganinsu hakan dabara ce. Idan zanbaka shawara wlh, gara ka auri Hauwa, koba komai ansanta, munsan halinta, kuma duk wanda kaga Allah ya jarabta da irin abinda yasamu Hauwa, amma be tuba ba, to kadauka beda rabo agurin Allah. Ni nasan yanda Hauwa taga rayuwa, kuma tayi nadama bazata kara barin ta maimaita makamancin kuskuren data aikata abaya ba, amma kaje kayi tunani kuma karoki Allah zabi akan lamarin. Buba yace hakane, kuma nagode da shawararka, kuma harga Allah nayarda da zabinku, fatana Allah yashige mana gaba. Abbas yace yauwa ko kaifa NA HAUWA. Dariya sukayi. Babu bata lokaci itama Hauwa ta amince alokacin da Labiba ta kaimata maganar Buba, tabata shawara sosai, kuma ta amince tace idan Babanta yadawo zasuyi maganar. Sallama Labiba tayi mata tawuce gidan Maman Zainab, dama Auwal ne yakawota. Sosai maman Zainab taji dadin zuwan Labiba,dariya sukayi ganin su duka suna dauke da ciki. Maman Zainab tace Lallai mun dade bamu hadu ba, ashede da wuri za,ayima Ansar kani ko kanwa?. Zama Labiba tayi tace wlh kuwa, Dadyn Ansar yace yana son yara, maman Zainab tace ai gara, ke dama kika dade baki haihu ba, ai gara kibari kisamu yaranki, domin sune abin alfaharinki. Ina fatan de ana kula da megidan, yanzu wannan kunyar taki duk kincireta? Dariya Labiba tayi tace kai Maman Zainab, ande cire ta cirewa amma bazata ciru duka ba, kinsan Dadyn Ansar yana son kunya. Maman Zainab tace e hakane gaskiya kunya tana karama mace kima agurin mijinta, amma kuma kada tayi yawa hartasa ki kasa yimashi abinda ze kasa kallon wasu awaje. Yanzu ya maganar girkin,inafatan kina bin wadan nan littattafan dana kawo maki? Labiba tace sosai ma, kuma nashiga wani group ma na koyon girki, sosai nake karuwa, duk abinda ban sani ba ina tambaya. Maman Zainab tace amma kin kyauta, Allah yakara yi mana jagora, anan Labiba tabama Maman Zainab labarin Hauwa, sosai ta tausaya mata. Maman Zainab tace dama haka rayuwa take duk wanda ya cuci wani shima Allah seya tambayeshi tun aduniya, haka sukayita fira, har lokacin tafiyarta yayi, sukayi sallama ta tafi. Alh, Bashir ya kalli Kasim yayi murmushi yace haba Kasim wannan magana taka ai bame yuwa bace, niyanzu nafiso inkarasa rayuwata haka yaran da nakedasu Allah yaraya mun su. Kasim yakara kasa da murya yace dan Allah Alh, wlh banyi wannan shawarar ba seda nafara magana da Umma. Kuma ta amince, kai muke jira, nide gara Umma ta aureka da ace ta auri wani, dan danginta sun dameta da maganar aure, dama kuma tunbayanzu nake wannan tunanin ba, kawaide alokacin nasan bazaka yarda ba. Banaso kannena suje agolanci wani gida dan Allah. Murmushi Alh, Bashir yayi yace shikenan Allah yasa haka yafi zama alkhairi. Dariya Kasim yayi yace amin, nagode. Dama nayima Kawu magana, shine yace idan ka amince wannan asabar din se a daura auren. Alh, yace da wuri haka? Kasim yace tome za,a jira, Alh, yace naso insami gida sannan, Kasim yace haba Alh, mufa masu baka gida ne,tunda akwai gidanmu wanda Umma take ciki kawai kuyi zamanku. Alh, yace shikenan babu damuwa Allah yakaimu. Ayau ne aka daura auren Hauwa da Buba, kuma yayi dede da aurensu Alh, Bashir. Mutane dayawa sunyi mamakin aurenshi da matar yayanshi, masu gulma sunayi, masu addu,a sunayi. Aranar da dare aka kai Hauwa gidan su Abbas, wanda shine yadauki nauyin yimata kayan daki, Umar kuma yakoma bangaren Ummansu da zama. Sosai Hauwa ta canza halinta, zamansu da Buba, shima yanajin dadin zama da Hauwa, sanin Abbas bayason tana shige ma Labiba yasa bata cika shiga part dinta ba, sunfi haduwa part din Umma. Buba tare suke aiki da Umar a provision store din da Abbas ya budema Umar, aiki yake sosai babu ha'inci, kuma yana kokarin tara kudinshi, dan shima yaci burin siyan gida koda nakasa ne. Zaune suke afalon Umma, Abbas yace Umar yakamata fa kafara tunanin aure,idan ma bakada budurwa to kanema, dan da muntashi zanyi maka aure. Dariya suka sa, Umma tace ai garade kayi mashi aure shima yashigo sahun manya. Labiba tace yanama da ita, kawai mu ake jira, dariya Umar yayi yatashi yafita, Abbas yace idan nafito zamuyi magana, gara muje mu tambayo maka, kada suga kamar wasa kakeyi. Umma tace Allah yayi zabi mafi alkhairi. Abbas ne da Labiba suka fita, gidan su Jafar sukaje da yamma, ahanyarsu ta dawowa suna tafiya Labiba cikin sauri tace dan Allah Dadyn Ansar ka tsaya, burki yataka yace waike anfada maki mota kamar keke take? Dariya tayi tace yi hakuri wlh, wata nagani kamar Laraba ta tsohon gidanmu. Bude motar yayi yace ai seki fito idan kuma ba ita bace duka zansa tamaki, Aikuwa tana karasawa jikin shagon data ganta, sallama tayi hakan yasa Laraba tajuyo domin ganin me sallamar. Cike da mamaki tace Labiba! Dariya Labiba tayi tace ashede kece dama zamu wuce naganki nace bara induba ko kece, Laraba tace amma wlh, kin kyauta, amsar abinda tazo siya tayi tace muje daga can. Labiba tace oni Laraba ina kawarki Laure? Laraba tace wlh tana nan, amma yanzu ba gida daya muke ba, duk muntashi daga wannan unguwar, su sun koma Fage, ni kuma muna rimin kebe, yanzu ma da kika ganni anan gidan wata yayata nazo shine nafito zantafi gida na tsaya insayi wani abu anan. Murmushi Labiba tayi tace Allah sarki ya rayuwa? Laraba tace Alhamdulillah gata nan munata shanta, yanzu kam munsami cigaba sosai dan nida Laure duk da munyi nisa amma muna kasuwanci sosai kuma muke samun alkhairi, sede haryanzu muna gidan haya, amma kuma mukadai ne agidan. Yanzu kam mazajenmu gaskiya suna zuwa kasuwa sun maida hankali sosai. Kallon Labiba tayi tace ke kam koba,a tambaya ba, kunsami canjin rayuwa ko? Dariya Labiba tayi tace gaskiya sede mu kara godema Allah, Muna cikin rufin asiri, ai muna haduwa da maman Zainab muna zumunci sosai, itama sunyi gidansu, Laraba tace Allah sarki, wlh naji maku dadi, muma Allah yahore mana, wace unguwa kuke ne? Labiba tace agaban Darmanawa muke kadan, Laraba tace bade seyanzu zaki haihu ba, dan naga cikinki yayi girma? Labiba tace a,a na biyu ne, wannan akwai Ansar yana gida, muje kugaisa da Dadyn Ansar gashi can. Laraba tace ashe tare kuke, nide ki gaisheshi wlh kunyarshi nakeji, hannunta Labiba takama tace haba Laraba yau shekara nawa ai komai yawuce, muje dan Allah ai zaman taren kenan. Fitowa Abbas yayi yana murmushi yace ashede Larabar ce kika gani, risnawa tayi tana gaisheshi, bayan sungama gaisawa Abbas yaciro kudi masu yawa yabata yace ga wannan, ayima yara tsaraba, Labiba tace Dadyn Ansar Laure ma ta tashifa, amma suna haduwa da Laraba, murmushi yayi yace Allah sarki to ki gaisheta, hannu yasa Aljihu yaciro wasu kudin yabata yace takaima Laure, har kasa ta duka tana godiya, Haka sukayi mata sallama suka tafi, da ido Laraba tabisu cike da mamakin irin kyan motar dasuke ciki, jinjina kai tayi tace Allah sarki, rayuwa shiyasa kazauna da kowa lafiya yafi, da,ace sharrin da mukayi niyar jama Abbas yayi da shikenan yanzu bazasuyi mani kallon arziki ba, Allah na gode maka daka tsare bawanka. Ayanzu Wapa tazama abun kwatence a garin kano, mutane basuda tsoron shiga gurin kowa suyi canji, zuwa yanzu Abbas Alee sunanshi ya daukaka agarin kano, mutane dayawa suna yimashi lakabi da mai gaskiya. Gidan Tv, da Redio babu inda ba,a kiranshi ayi fira dashi kuma yabada shawara, yanzu Costomers dinshi daga ko ina yana dasu, fararan fata da bakake, ayanzu babu sauran zalinci a Wapa. Abbas ganin ya kammala gininshi yasa aka rushe gidansu na gado akwai wani babban fili akusa dasu, siyenshi yayi yasa aka fara yimashi ginin bene dan yayi alkawarin seya gina gidan haya. Bakaramin kyau gidan Abbas yayi ba, babu abinda ba,a zuba ba, komai ya kammala, hakan yasa Alh, Abbah yace dole se anyi walima abokanansu na Wapa sunzo domin kowa yasa albarka. Alh, Abbah shiya dauki nauyin walimar da za,ayi, sosai yakashe kudi domin yanaso walimar ta kayatar, ranar lahadi aka sa walimar su kuma zasu tare asabar. Abbas ne zaune shida Jafar agaban Mamansu Jafar sungama cin abinci, Abbas ya kalli Mama yace Mama insha Allah ranar asabar nida Jafar zamu tare asabon gidanmu. Kuma hada ke zamutafi, dan nayi maki dakinki acikin gidansu Jafar. Mamaki ne dauke akan fuskar su Jafar, yama rasa bakin magana, mama kuwa kuka tasaka tana fadin ikon Allah, Dama akwai ranar dazan zauna akarkashin inuwarka Abbas? Hakika abunda ka raina wata rana shine yake maka amfani, na wulakanta ka saboda MUHALLI, yau gashi kaine zaka bani gidan da ko a mafarki bantaba tunanin samun shiba. Nagode Allah yayi maka albarka, yabaka abinda kake nema, kuma ina kara rokonka kayafemun akan abubuwan danayi maka. Abbas yace haba Mama babu komai, matsayin uwa kike agurina, Jafar kuwa dan uwanane na jini, babu abinda bazan iya yimaki ba. Jafar matsowa yayi yakama hannun Abbas, idanunshi suna fitar da kwallah yace, Abbas bani da bakin magana, sede ince......hannu Abbas yasa yarufe mashi baki, yace bana son daga yau ka karamun godiya akan duk wani abu dazanyi maka. Duk abinda zanyi maka baze kai wanda kamun ba, domin ayanzu ina yimaka ne, kana dashi, nifa? Katemakeni alokacin dabani dashi, dan haka kadena banaso, tashi muje kafada ma maryam, kaga gidanka seka sa yan haya, kema Mama wannan gidan yan haya za,a saka ciki, Seki rika amsar kudin. Mama tace hakane, Allah yabiyaka, amin, yace suka tashi suka fita. Alh, Bashir ne da Kasim suka fito daga kasuwar wambai, suna shirin shiga mota sukaji ana fadin bayin Allah kutemaka mani da kudin magani, juyowa sukayi suna kallon wadda tayi maganar, Kallo daya zaka mata tabaka tausayi,hannunta guda daya ya kumbura ciwo ne, ajiki ga wani tsumma da,aka daure hannun dashi, se wani ruwa yake fita daga jikinshi. Matar duk ta yamutse gwanin tausayi, kai Alh, Bashir ya girgiza cike da tausayi ya ciro dubu daya yamika mata, dayan hannun tasa zata karba, tsayawa tayi cike da mamaki tace Alh?. Sake kallonta yayi yace baiwar Allah karbi sadakarki mu wuce, kuka tasaka tace ikon Allah Alh, baka ganeni ba? Sake kallonta yayi yace gaskiya banganeki ba, kallon Kasim tayi ta kira sunanshi tana fadin kaima baka ganeni ba? Kai Kasim ya girgiza yace gaskiya kam, kuka tasaka tana fadin Alh, matarka ce uwar yaranka, Hajiya Binta ce fa. Saurin cire glass din idonshi yayi yakara kallonta, se alokacin ya ganeta, sede yanayin datake ciki bazaka taba gane taba inba fada tayi ba. Kasim yace ikon Allah, Hajiya ina kuma kudin naki kika kare abara? Cikin kuka tace dan Allah Alh, kayi hakuri zan fada maku wlh nima banci kudinka ba. Kasim yace Alh, kada mutara mutane kaga kasuwa ce, mudauketa muje gida se ayi maganar acan. Alh, kasa magana yayi se Kasim ne yabude mata baya tashiga, gaba daya seda kamshin motar yacanza, haka suka shiga suka nufi gida. Seda Alh, yasa Ummansu Kasim ta nuna mata bandaki tayi wanka tabata kaya tasa sannan taci abinci suka zauna falon, balaifi harta fito datayi wanka. Yaranta se kallonta sukeyi suna kuka, Alh, yace ke muke saurare. Goge kwalla tayi tace kamar yanda nayi maki sallama Hajiya akan zanje indawo, alokacin kudin account din Alh, da filinshi naje nasayar, kudin kuma na kwashe su duka. Domin alokacin da gobarar takama ina daki, jin ana ihu wuta yasa. Bandauki komai ba, se jakata da gwala gwalai na, dama takardun suna cikin jakata. Haka na hada kudina masu yawan gaske, kuma alokacin banyi tunanin insaka su a account dina ba, gani nake za,a iya rufeshi idan Kasim yagane na gudu, tafiya nayi gidan wata kawata da niyar inkwana acan washe gari inbar garin. Ashe dana fada mata abinda nayi tayima mutananta waya, cikin dare muna kwance mukaji yan fashi, ba bugu ba zagi haka suka hada komai danazo dashi suka anshe, ko kwandala basu barmun ba. Itama kudinta da gwal dinta suka ansa, ashe duk cikin shirinsu ne, haka muka kwana muna kuka, washe gari tacemun ita tafiya garinsu zatayi seta kwana 2 zata dawo, dama kuma bata da miji. Nima haka nafito daniyar indawo, adede gidanmu daya kone, nazo wucewa naga Kasim da mutumin dana saida ma filin suna magana, ko ban tambaya ba nasan maganata sukeyi, Hakan yasa naji tsoron zuwa gidan, juyawa nayi dasauri na rika tafiya, gashi banda kudi bare in hau adedeta, seda nayi nisa sosai, nazo zan tsallaka titi wani me mashi ya kadeni, ina faduwa kuma ashe akwai wani abayanshi shi kuma yatakamun hannu. Haka aka kaini asibiti hannun yakare, ga ciwo ajiki, nan sukayi mani dinki ahannun suka mun allurai, sukace idan ciwon ya warke za,a gyaramun hannun, sannan sukace bayan sati indawo akwance dinkin. Dama wasu ne suka kawoni masu mashin din sun gudu, magungunan da,aka rubutamun suka siyamun, anan suka bani dubu daya sukace inyi kudin mota, godiya na masu suka tafi. Haka nafito narasa inda zani ga yunwa tana damuna naso intafi garinmu amma ganin kudin bazasu isheni ba, yasa nasayi abinci naci, nace idan nasamu kudin mota se intafi. Haka nayita gararamba, bana wannan rumfa bana waccan, haka nakoma me bara karfi dayaji, dana fara tara kudin mota se sutafi asiyen magani da abinci, har sati yacika bankoma asibiti ba, haka nayita zama da hannun yana damuna. Ganin yafara ruwa yasa nasa tsumma na daureshi. Dan Allah Alh, kayafemun, nasan hakkinka ne, yake tambayata, alokacin kana da kudi baka rageni da komai ba, asalima ATM dinka agurina yake, amma segashi nakasa zama inrike yaranmu, daga karshe ma naci amanarka, Ta hanyar bin mazan banza alokacin da aka kulleka, har cikin gidanka nake kawo maza, yanzu ga karshena nan, kayafemun dan Allah. Kowa seda ya girgiza dajin abinda Hajiya Binta ta aikata, wai bin maza. Cike da bacin rai Alh, Bashir yace bakomai Hajiya, kanki kika cuta, wlh da ace iyakar satar da kikamun kika tsaya babu abinda ze hana ban maidaki dakinki ba. Amma wannan babban zunubin da kika dauka bazan iya cigaba da zama dake ba, na sakeki saki 3, sannan kuma nayafe maki abinda kikamun, domin kema bakici kudin ba, kuma dalilin yaran damuke dasu, zan kaiki asibiti, aduba hannunki, bayan kinwarke zan daukeki inmaidake garinku, Zamfara, Wannan shine iya alfarmar dazan maki, saura kuma yarage keda ubangijinki. Kuka tasaka tana fadin nagode, yaranta ta kalla wadan da suke kuka tace kuma kuyafemun, hajiya nagode da rikon yaran da kikamun, kema kiyafemun. Seda tabama kowa tausayi, haka Alh, da Kasim suka dauketa suka nufi asibiti, suna zuwa akace ai hannun ya rube dole ayanke shi, kuka tasaka Alh, yace kiyi hakuri hakan ne kadai zesa kisamu sauki idan ba haka ba, zama cikin mutane seya ga gareki, saboda wari. Tanaji tana gani akayi mata allura aka yanke hannun damtsenta kawai aka bari, dressing akayi mata sannan suka nufi gida ita kuma aka bata gado. (Allah ya kyauta, karshen maci amana kenan). Ayau ne su Abbas da Jafar suka tare asabon gidansu, Maman Jafar seda tayi kuka dan dadi, Umman Abbas kuwa cewa tayi abarta agidan Autan ta,Hauwa ma seda tayi kuka saboda zasu rabu da Labiba.(Nikam nace Allah yasa kukan iyakan nan ya tsaya). Hada Maman Zainab cikin masu gyaran gida, sosai tayaba kyan gidan Labiba, iyakar tsaruwa ya tsaru, Abbas kuwa bakinshi ya kasa rufuwa saboda ayau ya mallaki gidanshi da guminshi ba nawani ba. Washe gari haka aka kafa rumfuna aharabar gidan da kujeru, dan walimar karfe 4: 00 ce, komai na kayan ci da sha an tana da, masu abinci na musamman Alh, Abbah yadauko, kuma sune masu rabawa. Walima ce wadda ta tara mutane dayawa, dan Alh, Abbah da kanshi yayi gayyata, din kunan dazasu saka shida Abbas da Jafar duk iri daya suka saka, sunyi matukar kyau, Hatta da gidan Tv seda sukazo walimar, anci ansha, duk wanda yazo yasan an karrama kowa, Abbas har kuka yayi saboda farin ciki, haka aka gama walima kowa yarika zuwa yanama Abbas murna. Bayan an natsu ne yan jarida suka fara yima Abbas tambaya akan yanda yakeji daya mallaki MUHALLINSHI? Tashi yayi nan mutane suka matso, masu dauka awaya suka fara seta Abbas. Gyaran murya Abbas yayi tare da farawa da bismillah, godiya yafara yima mutanan dasuka halarci walimar, bayan yagama daya daga cikin yan jaridar yace Alh, Abbas wane irin farin ciki kake jin kanka awannan ranar daka mallaki MUHALLINKA na kanka, duk da de mun sami labarin ba wannan bane gidan daka fara mallaka kusan ma ince shine na 3? Murmushi Abbas yayi yace haka ne, wannan shine gida na 3 daya kasance amatsayin mallakina. Hakika ina cikin farin ciki marar misaltuwa. Rubutu yayi bayan yagama yace amma ayau kafi jin farin ciki akan sauran gidajenka. Tunda wannan gidan shine yafi kowanne gida tunda ance da guminka ka ginashi kasancewar gorin da akace abokan adawarka sun maka? Abbas yace hakane, gidana na farko bantaba jin farinciki ba arayuwata ba kamar ranar da na kammalashi. Domin shine gidan dana gina da zufata kuma da kudina nasha wahala kamar yanda masu gini sukeyi, na kwaba kasa da hannuna , nayi bulo kuma nadaukeshi akaina najerashi da haka har muka kai tsawon gini. Agaskiya bazan taba samun farin ciki aduk gidan dazan gina kamar gidana nafarko, amma koyanzu ma ina cikin farin ciki, kuma inama Allah godiya. Jinjina kai yayi yace Alh, Abbas kozaka iya fada mana dalilin dayasa karabu da gidan daka sha wahala kafin kagama ginashi, kaje kana yawon haya?. Kai Abbas ya girgiza yace wannan nabarshi amatsayin sirrin rayuwata,kai ya jinjina yace hakane, to wace irin shawara zaka bama mutane agame da muhimmancin MUHALLI?. goge kwallar data zubo mashi yayi yace hakika babu abinda yafi MUHALLI muhimmanci arayuwar yanzu, inabama duk wani matashi shawara yadage ya mallaki MUHALLINSHI, domin idan kanada MUHALLI duk wata matsala dazata taso maka me sauki ce. Arayuwa da mutum yabaka kudi gara ya nuna maka hanyar da ake samunsu kaje kasamo aduk inda su, domin zasu iya karewa, amma idan kaine kake nemansu bazasu kare ba, domin akullum kana fita nema. Daga karshe ina mika godiyata ga mutane biyu masu matukar muhimmanci arayuwata, ba wasu bane se wadannan mutanan guda 2 nakusa dani, bazan taba mantawa dasu arayuwata ba. Sunzama babban jigo arayuwata, akullum ina rokon Allah daya saka masu da abinda yafi komai alkhairi arayuwarsu, nagode sosai inama kowa addu,ar yakoma gidanshi lafiya, kuka ne yaci karfinsa hakan yasa yazauna. Gaba daya gurin yadauki tafi, godiya yan jarida sukayi mashi suka tafi, haka taron ya watse kowa yana jinjina ma Abbas abisa rayuwar dayayi. Bayan angama kwashe kayan gurin Alh, Abbah yayi masu sallama yatafi, godiya sukayi mashi yatafi, nan kowa yanufi gidanshi. Wanka Abbas yayi yanufi masallacin cikin unguwa, akofa suka hadu da jafar suka nufi masallaci, bayan sunyi sallah zuka zauna seda akayi isha,i suka tafi. Abinci kawai yaci ya kwanta, domin bakaramar gajiya yayi ba, cikin dare suna bacci Labiba ta tashi da nakuda, tashin Abbas tafarayi, cikin bacci yaji ana tashin shi, dasauri yatashi, ganin halin da Labiba take yasa yayi saurin tashi yasaka jallabiyarshi. Jafar yakira awaya yafada mashi, kafin sufito harsu Jafar sunfito shida Maryam, nan suka nufi asibiti, suna zuwa aka ansheta dan takusa haihuwa. Ko minti 30 bata yiba, ta haifi diyarta mace, albishir akayima su Abbas, cike da farin ciki suka nufi dakin, bayan takara minti 30 aka sallamesu, gida suka nufa cike da farin ciki. Ranar suna yarinya taci sunan mamar Labiba Aminatu ana kiranta da MINAL, sunan yatara mutane dayawa, su Maman Zainab da Hauwa sune iyayen suna, harsu laure da Laraba seda sukazo dan sun hadu da Maman Zainab akasuwa ita take fada masu, kwatancen gidan tayi masu segashi sunzo, ita ma Maman Zainab cikinta ya tsufa. Bayan suna da sati 2 akayi bikin Umar da amaryarshi Halima, sosai Abbas yakashe kudi abikin agidan da Ummansu take aka kai amarya abangaren Labiba na da, shikuma Umar yadauki bangaren Abbas, yarinya ce me hankali da ladabi, hakan yasa suke zaune lafiya da Umma. Buba ne tare da Abbas yana fada mashi yasamu wani gida acikin darmanawa can layin wanzamai, nasayarwa ne, sede karamine, kuma yayi ciniki, shine yace zesiya. Murmushi Abbas yayi yace meze hana kuyi zamanku anan, nida bazan tasheku ba, Buba yace wlh tunda naga rayuwa kuma naji labarinka tundaga lokacin nasama raina gida kona kara ne, insha Allahu sena mallakeshi da kudina, domin na lura babu abinda yakai MUHALLI DARAJA. Kaduba kaga irin gidan daka gina amma fadi kake har duniya tanade bazaka gina gidan dazakayi farin ciki dashi ba kamar gidanka na farko, shiyasa nima nakeso insamu gida nawa na kaina, wanda kudi nane suka sayamun, komin kankantarshi nasan zuwa gaba zan samu wanda yafishi. Kai Abbas ya jinjina yace amma Buba gaskiya ka burgeni, haka akeso mutum yazama me zuciyar nema, duk yanda mutum zebaka aron abu matukar ba kyauta yabaka kada kadogara dashi, domin rayuwa tana iya canzawa ko mutuwa tazo, kaga dole mutum yatashi yabar gidan. Bakomai kaje kasiyi gidan ni kuma nadauki nauyin gyaranshi da komai, godiya Buba yayi mashi yatafi, sosai Abbas yaji dadin yanda Buba yayi wannan tunanin dan dama yaso ya bashi wannan shawarar, amma gudun kada Buba yace yana mashi kora da hali yasa ya kyaleshi. Ayau ne, za,a kara zabar wadan da zasu sake fitowa takarar Chairman na Wapa, mutane dayawa Abbas sukace sunaso yafito, dan acikin yan takarar ma mutum daya ne, yafito, ada Abbas cewa yayi baze sake tsayawa ba, dan bayaso yashiga hakkin masu nema, amma yanda mutane suka rika damunshi, Har gidan Alh, Abbah sukaje sunaso yasa baki Abbas yasake fitowa, ganin hakan ne yasa Alh, Abbah yayi mashi magana, baya iya musu da Yayanshi shiyasa ya amince. Aranar da akayi zabe Abbas yacinye kuri'ar, kowa farin ciki yakeyi da wannan zabe, yasamu kyaututtuka dayawa, haka kowa ya watse Jafar da Abbas suka nufi gida. Bayan wata 2 Abbas ya kaddamar da gidanshi daya gina afilinsu na gado, babban gida ne yayi me hawa 2, dakuna ne masu yawa yayi asama da kasa, kuma kowane daki ciki da falo,ne se bandaki da kitchen aciki, ginin yayi kyau, Alokacin da akayi tallar gidan, babu bata lokaci mutane suka fara neman hayarshi domin Abbas yasaka kudin babu yawa sosai, dan dama yace saboda marasa karfi ya ginashi amatsayin sadaka ga Babansu. Mutane sunyi mamakin yanda yayi wannan gida me tsari amma yasa mashi kudi kadan, domin gidan babu ruwanka da wani kowa da gurinshi, gate ne kawai daya se filin gidan, shima kuma Abbas da kanshi yadauki megadin gidan da kuma wanda zerika kula da tsaftar gidan dan gudun kada abarshi ya lalace. Zaune suke afalon Umma sunzo dubata, su duka hadasu Jafar da Maryam, tare suke da Alh, Abbah da matarshi, Umma taji dadin wannan ziyara dan hada Maman Jafar. Bayan sungama gaisawa Umma tace gaskiya naji dadin wannan ziyara, Allah yakara hada kanmu baki daya, Mama tace aminde, gashi Allah beyimu dayawa ba, acikin zuri,ata amma yau gashi mutanan arziki sunzama cikin zuri,ata. Alh, Abbah yace dama haka rayuwa take, idan karasa ta wani guri, se Allah ya baka tawani gurin, kallon Abbas yayi yace kasan dazu wasu mutane sukazo gurina, irin dillalan nan ne, suna zama a tsohuwar unguwarku. Wai sunzomun ne, da maganar gidanka daka bada haya, wai suna ganin bekamata ace kayi wannan gidan me kyau da tsari, wanda manyan mutane yakamata ace kabama haya amma kasa mashi kudi kadan, kuma kaje kabama talakawa hayarshi. Kasan me nace masu? Kai Abbas ya girgiza, Alh, yace cemasu nayi acikinku akwai wanda yazuba jarinshi cikin gidan ne? Nan suka fara zare ido, suna kame kame,nace masu tunda de babu ko sisin ku aciki dan Allah kusama kanku salama kuje kuyi abinda yake gabanku. Da de sukaga bazasu samu fuska agurina ba, shine sukatafi, dariya sukayi Jafar yace kasan yanzu mutane basuda wata sana,a se saka ido akan hidimar wani, ka duba kaga babu ko sisin su aciki amma sukazo suna gulma. Nima jiya seda wani yace mun wai bekamata Abbas yasa kudi kadan ba, gida kamar kana cikin gidanka amma kuma kudi kadan, nima ban bashi fuska ba, haka yatafi. Abbas yace duk ku kyalesu zasuyi sugama, Kuma insha Allah bazan kara kudin hayar ba, ina rokon Allah ya albarkaci wanda zasu bani, domin ba cika kudi agidan haya shine riba ba, albarkar kudin ita akeyimawa, wlh, tun lokacin da muka zauna agidanmu na karshe azaman haya, tun daga lokacin irin gidan ya fucemun arai. Ace gidan mata 4 kowa da mijinta da yaranta amma dukansu abandaki daya zasuyi amfani, babu kitchen tsakar gida se wanda yaga dama ze shareta, ko wace irin matsuwa kake da ita sekajira wanda yashiga bandakin yafito. Haba shiyasa akullum nake kara rokon Allah ya tsaremu daga sharrin zaman haya irin wancan . Bayan da Allah ya azurta ni, babu abinda yafadomun arai kamar in gina gidan haya, alokacin daza,a fara ginin me zanan yatambayeni wane iri nakeso, tunawa da irin wahalar da mukasha yasa nafada mashi irin wanda nakeso. Wlh koyanzu na kwanta bacci da farin ciki nake kwana idan natuna mutanan dasuke haya agidana suma suna cikin wadata da farin ciki, agaskiya zaman haya beyi ba, matukar ba gidan mutum daya bane, kai gaba daya ma Allah yayi mana tsari dashi. Umma tace amin, Abbas, Allah yakara buda maku kuci gaba da temakon nakasa daku, domin idan mutum yana da dukiya bayajin farin ciki meyawa idan har yatasata yacinye dagashi se nashi. Amma matukar kafitar da ita kayi sadaka alokacin zakasamu farin ciki meyawa, Allah yakara shige mana gaba, sukace amin. Abbas yagama gyarama Buba gidanshi, yayi kyau sosai, se godiya yake mashi, kuma aranar da aka gama saka kujeru da labulale suka koma gidan, Hauwa de har aranta taso suzauna agidan su Umma, duk da a boys quarters suke amma gani take yafi nasu, tunda akwai komai, ga wuta ga ruwa, idan babu ma akwai generator, hakade tayi shiru tabar abin aranta, dan kada tayi magana tajama kanta.( Lalai me hali baya taba barin halinshi, naga alamar Hauwa wannan halin nata ajininta yake, sede muce Allah yashiryeta, amin). Motar da Abbas yake hawa yabarma Umar, motoci guda 3 yasa aka kawo mashi, 2 iri daya se dayar daban, cikin biyun yace ma Jafar ya zabi daya, sosai Jafar yaji dadin kyautar, baki yabude zeyi godiya, Abbas yace wlh idan kasake kamun godiya batawa zamuyi sosai ma. Murmushi Jafar yayi yace towai kai ko haihuwar mutum kayi yamaka abun alkhairi ai godiya tazama dole, balle ni da ba haifaka nayi ba. Abbas yakara daure fuska yace toni banaso, kawai kamun addu,a senafi jin dadi, amma idan kanamun godiya banajin dadi araina, se inga kamar irin nabaka sadakar nan,kai kuma kafi karfin haka agurina. Dariya Jafar yayi yace shikenan angama Allah yabarmu tare, yakara tsaremu daga sharrin ma hassada, murmushi Abbas yayi yace yauwa kokaifa, amin. Zaune suke shida Labiba bayan sungama cin abinci, Abbas yace kulle idonki, murmushi tayi tace naki wayonka haka nan kaci zalina kuma ka gudu, dariya yayi yace wlh babu abinda zan maki, amma idan baki kulle ba, zanje gurin mejin maganata insata ta kulle, kinga se inyi mata abinda zan maki. Saurin kulle idonta tayi, dariya yasa yace ashede yan matan tawa tana tsoron kishiya? Hannunta yakamo yasa mata mukullin mota, yace bude, cike da mamaki tace kamar mukullin mota? Yace shine, kuma takice, jiya nasa aka kawo mana ita. Su Umma da Maman, Jafar da Kawu karami kuma nabiya masu hajji, idan Allah ya kaimu wata shekarar kuma mu semuje. Rungumeshi tayi tana fadin bansan dawane baki zanmaka godiya ba, duk irin yanda na kuntatama rayuwarka abaya amma bakada burin daya wuce ka faranta mun. Hakika Dadyn Ansar kai mijine da kowace mace yakamata tayi alfari da samun irinka, wlh nasan da wani nayima irin abinda namaka, ko be sakeni ba, idan ya tsinci kanshi a yanayinka nayanzu wlh seya auro mata har 3, kodan yabani haushi, amma kai inbanda alkhairi babu abinda kake bina dashi. Nagode Allah yabarmu tare, yabani ikon faran tamaka akoda yaushe. Abbas yace amin matata, ai kema kin cancanci inyi maki duk wani abu daya kamata saboda kinyi mani halarcin daba kowace mace bace zata iya yimani abinda kikayi mani,akullum banida burin dayawuce infaranta maki, fatana Allah yabarmu tare, Kuma daga yau banaso ki kara tuna rayuwarmu tabaya, kidena tunanin kinsani narasa MUHALLINA, dama can arubuce yake a kaddarata, ko ba ta dalilinki ba sena rasa gidana, kuma hakan daya faru kinga yazamar mun alkhairi tunda har na karbi kaddarar da Allah yadoromun, kinga canjin dana samu. Ko ayanzu nasamu darasi, kuma nakara sanin DARAJAR MUHALLI, fatana Allah yashige mana gaba, Labiba tace amin mijina abin alfahari na. ALHAMDULILLAH!!! Ina mika godiyata ga Allah daya bani ikon kammala wanna littafi nawa mesuna DARAJAR MUHALLI. Kurakuren dasuke ciki Allah ya yafe mana, duk wanda yasamu wani guri wanda bemashi dadi ba, koya bata mashi rai, iname bada hakuri, domin dan adam ajizi ne. Ina mika godiyata ga dukkanin masoyana, da wadanda na sani dama wanda bansani ba, nagode da kulawarku da kuma addu'arku agareni, Allah yabar kauna da zumunci. SADAUKARWA!!! Na sadaukar da wannan littafi nawa DARAJAR MUHALLI ga Mahaifita HAJIYA RUKAYYA MUSA KALLAH. Allah yakara mata lafiya da daukaka, amin. Sekunjini alittafina mezuwa insha Allah me suna RAYUWAR MATA AYAU. BISSALAM. UR'S. NABILA RABI'U ZANGO (Nabeelert Lady) 08028525263. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels