AAn dauko wannan littafi daga shafin https://gistrog.com.ng ku ziyarci shafin na https://gistrog.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348141702912 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://gistrog.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348141702912 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://gistrog.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.gistrog.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/SuleimanUsmanKurya Twitter : https://twitter.com/Kuryaloaded_Ng Telegram : https://t.me/+Um7CIRmWSIU2NTg8 SIRRINSU Littafin Maje el hajeej hotoro Shekarar bugawa:- 1999 Ebook creator and design by:- Shuraih Usman Publish by:- Shuraih 99% . SIRRINSU Littafina daya Chapter 1 By♥ Shuraih Usman A A 3~4~'99 . *_ASABAR_* Maryam!A'isha! Sai yaushe ?" Kawata banga jakata ba "Faruk ! Banda kwacen budurwa" Boss ! Muhade a tropicana Ka-ce-na-ce, rudu da kuma hayaniyar dasuka ringa tasowa daga bakunan dimbin mata da mazan dasuka halarci filin wasan kwallon kafar, datafi kowace girma da kayatuwa a Nigeria (sulere). Bayan antashi daga wasan costarica da nigeria agasar cin kofin duniya na matasa Cikin halin hargowa da matsananciyar bugun zuciya kamar ta faso kirjina don tsananin bugu da takeyi tun da nake Arayuwata. Ban taba tsintar. Kaina ahalin danake ciki awannan lokciba Domin aranar na hadu da wacce na kirawo mutumce , Aljana ce ko kuma fatalwa , bayan an tashi daga wasan. Anan ne. Na wadata idanuwana da abubuwa da dama. Shuraih Usman Shugaban askarawan nigeria janar Abubakar Abdulsalami da tawagarsa. Sune suka fara ficewa daga filin wasan 'yan jaridu da ma'aikatan gida jen sadarwa nata daukar hotunansu. "Shuraih usman"Alokacin da wasu ke shirye-shiryen tafiya , wasu ke shirin zantawa da sababbin 'yan matan. Da sukayi Turawa kuma na ta daukar hotuna. Sai idanuwanta suka hasku ga kyakkyawar fuskarta Farace doguwa mai matukar yalwar bakin gashi, ta mallaki dara-daran fararen idanuwa kamar madara ,sannan tana da dirarriyar cikar halitta da kan dau hankalin dukkan da na miji Dogon hancinta harbaka da dan karamin bakinta na daya daga cikin abubuwan da suka tona asirin kyawunta kallo daya zaka yi mata ka gamsu cewar duk daga inda tafito tahada dangi da shuwa Ina ganinta sai da wani abu ya taso daga kafufuwana ,har zuwa cikin kwalkwalwata,wanda hakan yasa jikina yayi yarrr! Na wasu lokuta sannan ganinta ya jefa zuciyata a cikin wani irin da tun dana. Shaki iskar duniya ban taba tsintar kaina. A wannan yana yiba. Shuraih Usmanbawai ina nace ban taba ganin macen data fi ta tsarin kyan halitta ba,ko tsarin iya sa kaya ba. Haka kawai ina ganinta na ji kamar akwai wani abu gare dayake fizgeta zuwa wajenta . Babu abin da yafi bani mamaki game da ita, irin duk cikar dakin wasan da yayi , da zunzurutun kabilu daban-daban , maza da mata daga kowane bangare na nigeria , da kuma kasashen ketare kowa na farin ciki da nishadi .Amma ita tana can gefe guda jin gine. Jikin bakar marsandi,ta sunkuyar. Da kanta kas , kamar.duk al'ummar dake wajen bata san da su ba , bata kuma damu da Suba. Hayaniyar kuma da sukeyi bata dameta ba. Wanda wannan na nuni da cewar shakka babu tana cikin matsananciyar. Da muwa arayuwarta . Na dada yin matukar mamaki lokacin dana fahimci duk taron samarin dake wajen babu wanda yakula da kowa. Shuraih Usman bakar kwat da siket dinta da ke sanye a jikinta ,sun mata matukar kyau,da tayi kama da gimbiya LAILA. Kyakkyawan takalmi ne mai launi uku PRINCE sanye a kafarta. Kai tsaye na nufi inda take gabana na faduwa , jikina na rawa kamar mazari,kuma bansan dalilin hakanba . Sai dai abinda bansaniba. Shine ,zuwa wajenta danayi,shine ya jefa rayuwata cikin gagrumin tashin hankali,kamar mutumin daya bude dakin dake cike da mayunwatan kuraye bai sani ba. "Hello".na fada ina murmushin karfin hali a tunanina bata yi kama da wanda ke jin hausa ba. Har nayi magana dago kanata ba. "Yau wa sannu".Ga mamakina naji ta fada ,lokacin data daga kanta ta kalleni ,sannan ta mayar da hankalinta. Ga hannunta. Sannnan ne na fahimci ba hannun take kallo ba ,wani kyakkyawan zare ne mai launin ja, baki da kuma fari, dake hannunta .ni kaina nayi mayukar sha'awar zaren. "Zanyi matukar farinciki idan har zuwana wata matsala arayuwarkiba " "Kwarai kuwa , domin ni kaina na ji dadin zuwanka ,wanda zai debe min kewa dama nake nima "shuraih usman"wannan maganar tafi bani mamaki, fiye da zunzurutun kyanda ta mallaka , wanda ita kanta ta fahimci hakan. "Maganar tabaka mamaki ko?" "Shakka babau, tun ba ma da ta fito dagga bakin mace irinki ba " nafada ina kallon fuskarata. "Kamar yaya mace irina ?" Tunda ta kalleni sau daya har yanzu hankalinta. Nakan kyakkyawan zaren dake hannunta. "Kinsan mu maza mun gama yarda. Cewar duk inda mace take bata kasancewa ita kadai " " To yaya aka yi ka sameni ni kadai" "Ni kaina nayi mamakin hakan ,yanzun ma na dauka wani kike jira" zaka iya sauke abun daka dauka don ni bana mu'amala da da namiji " Na kalleta kallon da ita kanta ta fahimci ban yarada da abin data fadaba ." Shuraih Usman "na san bazaka yarda da. Abin dana fada ma ba ,nikaina. Ba'a son raina hakan ya kasance arayuwata ba saidai don babu yadda zanyi" "Yanzun nan fa kikace kin yi farinciki da zuwana ,daman wanda zai debemaki kewa kike nema ,kuma kince ba kya mu'amala da namiji"• Nafada ina mai kwadayin fahimtar abinda take nufi ,yayin da ita kuma tayi daya mayar da fuskarta ,fuskar data dace data wacce ,wani abu ke kuntata rayuwarta. "Babu abin dana fiso arayuwata irin hira da da namiji,sai dai bani dawannan daman arayuwata .kasancewar. Takunkumin alakakai , data gindayawa rayuwata . Yanzu haka daza ta ganni da kai sai na dandana kudata ,bata son ganina da namiji kwata-kwata arayuwata . Abin yana damu na saidai don babu yadda zan yi ne " Tana rufe bakinata hawaye suka fara zuba daga idanuwanta . Wanda ba karamin bani mamaki yayi ba . "Wace ce ke takura maki ?" Na tambaya cikin mamaki. Kawai saita cigaba. Da kuka tana kallon zaren dake hannunta . "Wai shin yaya sunanki? Ni sunana HABIB?" "FARIDA" Cikin shisshikar kuka ta fada Sirrinsu Littafi na daya Chapter 2 By Shuraih Usman . Babu irin magiyar da banyi mata ba don tafada min amsar wacce ke takura mata .Amma taki bani amsa . Kawai takurawa zaren dake hannunta ido,kamar tana mamakin ganinsa ahannunta "Shin dama Farida ke mutuniyar legos ce?" Na tambaya don canja hirar. Gyada kanta tayi alamar a'a ce amsar tambayata . "Daga ina kikazo" "Kaduna" "Wacce unguwa a kaduna " "Tudun wada " "So nake ki kwatan tamin gidanku" *Shuraih Usman*"kana zuwa tu dun wada ,kusa da makarantar marigayi sheikh Abubakar gumi,duk inda katambaya gidan Alhaji adam za'akaika, shine gidana uku" Tun data fadi wadannan maganganu,bata kara cewa komai ba,sai kawai tacigaba da kukanta ,ga kyakkyawan zaren, kamar aranta yake sainaji. Ina son mallakarsa. Sai naciro zoben azurfa dake hannuna,wanda fatima yayata tabani "Farida" Nakira sunanta lokacin dana mika mata zoben tadaga kanta ta karba ta saka adan yatsanta na hagu.sannan taci gaba da kallon zaren. "Farida"ina son kema kibani zaren dake hannunki,don tunawa dake kafin mukara haduwa" Nasamu dogon lokaci ina tambayarta Amma in da kasan dutse nakeyiwa magana.ko kallon inda nake bata yiba, bata dakuma niyyar kara yin magana . kwata-kwta hankalinta na kan zaren,ganinyadda ta tatattara hankalinta ga zaren saina mika hannuna na rike zaren. Inda kasan aranta yake ,domin ina tabawa ta daga kanta ,sannan tayi wani irin ajiyar zuciyar da sai da na tsorata ,Amma dauk da haka ban saki ba.* Shuraih Usman*. "Mene ne haka ?" Naji wata irin murya mara dadin ji tafada daga bayana , cikin sauri na waiwaya a tsorace ganinta ya dada jefa tsoro da fargaba azuciyata. Kodaddiya ce mummuna gajeriya kuma kakkaura ,mai wasu irin jajayen idanuwa kamar garwashin wuta . Sannan ta mallaki faskeken kai, da burgujejen hanci.tun dana dora idanuna afuskarta ,naji kwata- kwata na tsane ta ,na kuma tsani ganinta da nakeyi . Sai na ji bana bukatar hada ido da ita ,domin da zarar na kalleta sai wani irin kunci yakai farmaki zuciyata . Lokacin dana. Mayar da hankalina ga farida ,sai na fuskanci har yanzu ta daga kanta sama ,idanunta arufe jikinta na matukar tsima kamar tsohon dan taurin da tsiminsa ya motsa . Kuma na fahimci zuwan kodaddiyra matar ce ,kuma nafahimci ita ne ke takura wa farida'kuma na fahimci shakka babu tana matu kar tsoron matar . Saidai abin daya bani mamaki mene ne hadin farida da wannan mummunar matar dako ta ina basu dace agansu tare ba ba?* Shuraih Usman* A fusace kodaddiyar matar takama hannun farida,cikin sauri tabude motar da farida ke jingine ta tura ta ciki da karfi sannantayi min wani irin kallo da ya dada tsoratani sannan taci taya da karfin daya tayar da kura awajen . Kamar fitan harsashi daga bindiga motar ta bace daga harabar dakin wasan . Abin kamar aikin sihiri , awannan ranar babu abinda ke zuciyata . Sai yawan tunaninta ,duk abinda nake yi kwatsam,saita fado min a zuciyata . Sai dai ba zan taba mantawa da haduwata da ita ba ,domin rikirtaccen abin daya faru arayuwata .nakasa gane shin farida ,MUTUMCE KO ALJANA KO KUMA FATALWA Sirrinsu Littafi na daya Chapter 3 By Shuraih Usman B *_SIR.AHMADU BELLO STADIUM_* ,na cikinjerin kayattattun dakunan wasa dake najeria. Shakka babu wannan haka yake. Na yarda da hakan ne don halartar wasan ghana fa crotia. Amma kwata-kwata hankalina baya na kan wasan da ake bugawa yake ba, burina kawai ata shi natafi tudun wada neman gidan su farida .* Shuraih Usman*Tunda jirginmu yata so daga legos ya dira a kaduna ,na so na bincika amma kasancewar Ahmad mijin yayata wanda shine ke daukar dawainiyarmu ni dashi, halartar wasanin da ake gudanarwa. Yabukaceni dana rakashi ziyartar kayatattun hotels,da wuraren hutu,da kuma barikin sojoji. Ana tashi daga wasan ko komawa masaukinmu banyiba ,kai tsaye na wuce unguwar tudun wada . Sai dai kash ban san cewar zan gamu da gawurtaccen al'amarin da zai birkita kwalkwalwata ba . Shadda ce launin ruwan kwai,sanye a jikina. Kamar yadda ta kwatanta min ban sha wahala wajen gane gidansu ba. Babban gidane dayake da bakar kofa,ankuma yi masa shudin fenti. Banyi minti daya da zuwa ba kofa tabude ,wata kyakkyawar yarinya wacce suka yi matukar kama da farida ,sanye da shudiyar doguwar riga tafito daga gidan. Rike da Naira hamsin guda uku ahannunta . A yadda na fahimceta zata kai shekara goma shadaya.* Shuraih Usman* "Sannu"nafada bayan nakirawota . "Yauwa sannu" "Yaya gida?" "Lafiya ta Amsa tana yimin kallon rashin sani. "Ko don Allah nan ne gidansu Farida?" Tayi shiru kamar tana mamkin tambayar ,kafin ta amsa min da cewa nan ne" 'Ke kanwarta ce ?" "Eh" "Yaya sunanki?" "Meenat"Ta fada har yanzu bakon kallon na fuskarta. Ko don Allah ta dawo?" "Wa?"Ita ma ta tambayeni cikin mamaki. "Ina nufin farida" "Daga ina ?" Wannan karon mamakin yafi bayyana afuskarta. "Jiya muka hadu da ita a lagos ,shine ta kwatan ta min gidansu ,idan kika ce habib wanda suka hadu ........ Ni kaina na fahimci matukar razana ,data bayyana karara a fuskar meenat, atunanina kodon farida ta ec bata mu'amala da maza shine take mamakin zuwana .Amma bata tsaya saurarar ragowar abin dazan fadaba , sai * Shuraih Usman*ta ruga gida a guje ,kamar wacce kare ke niyyar cizo. A lokacin da nake tunanin kokirawomin farida ta tafi yi,sai kofa tabude wata mace sanye da fararen kaya ta leko,da farko na dauka farida ce don kamaninta dana gani. Sai daga baya na sauke ashe mahaifiyarta ce. Ta yi min wani irn kallon matukar mamakn kamar yadda meenat tayi min,shin ko tana mamkin nine saurayi na farko da na taba zuwa wajen 'yarta ? A dai de lokacin dana nufi inda take don mu gaisa ,saitayi sauri arazane ta mayar da kofar ta rufe . Haka kawai sai zuciyata ta fara matsananciyar bugu ,jikina yayi wani irin sanyi.har na yi niyyar tafiya ,sai kofar ta kara budewa . Wannan lokcin nayi tsammanin ganin kodaddiyar matar nan,ga mamakina sai wani dogon saurayi fari kimanin dan shekaru goma sha takwas . Sanye dafarar singileti da shudin wando jeans yafito. Tun kafin ya karaso inda nake nafahimci irin kallon mamakin da meenat da mahaifiyarta kemin,shine shima. Akan fuskarsa.* Shuraih Usman*"ko kaine ke neman farida ?"Yatamabye ni bayan ya miko min hannu mun gaisa. "Shakka babu"nafada bagun zuciyata na karuwa. "Kuma kace itace t kwatan ta maka nan gidan" "Shakka babu" "Jiya kuma kuka hadu?" "Shakka babu" Na kara mai maitawa ina mamakin tambayoyin. "A Lagos kuma kuka hadu?"Ya tambayeni cikin shakkar abin dana ke fada "Shakka babu" Yayi shiru yanayimin wani irn kallon mamki,kamar ni ne mutum daya taba gani arawursa. Nikaina kallon mamakin da yake min sai yasa na rika yi masa kallon mamaki. "Ba wani abune yasa nake maka wadannan tambayoyiba , Shuraih Usman saboda agaskiya wani irin. Rikitaccen al'amarine ka zo da shi. Hakika nan ne gidan su farida,saidai ina mai tabbatar ma faridan dake nan gidan ta dade da MUTUWA" SIRRINSU Littafina daya Chapter 4 By Shuraih Usman Cikin matukar mamaki idona yazzaro,bakina a bude na kalleshi kallon da ya karyata Abin daya fada. "Shakka babu,zuciyata bata amince da abin daka fada ba. Na rantse da wanda raina ke hannunsa jiya mun hadu da farida a Lagos ,kuma ita ce ta kwatan ta min nan gidan har na bata zobena .shin ba farida ce doguwa fara mai yalwar gashi ba? Ina ganin meenat nasan kanwarta ce ,don kamar da sukayi" Kallon mamakin dake fuskarsa yai hijira sannan kallon akwai matsala a kwalkwata ya ziyarci fuskarsa. "Dankari! Agaskiya kazo da babban magana ,domin ita meenat daka tambaya har tanzu a tsorace take,a tunaninta kai mahaukacine, tabbas tasan farida ta mutu" Wani dattijo yazo zai wuce yana jan tasbaha , biye dashi wasu almajiraine su uku "Alaramma! Wai kaga wannan ne bai yarda cewa farida ta mutu ba "saurayin yafada lokacin da wannan dattijo yazo gabda mu zai gifta. "Kamar yaya bai yarda. Ta mutu ba ?" Ya tambaya "Malam anshakka babu jiya na hadu da farida a Lagos ,kuma itace ta kwatantamin nan gidan" Shi da almajiran Shuraih Usman suka kura min ido,suna yi min kallon anya ban tabu ba. A gaskiya sai dai kowata faridar,amma wace kenan gidan ta dade da mutuwa kuma mata tace ta wanke gawarta. ******* Na yi shiru ina birkitaccen tunani lokacin da saurayin yashiga gida. Wasu yara suna gara taya,suka zo wucewa na tsayar dasu. "Kai don Allah anan unguwar kuke ?" "Eh"suka amsa "Ko kunsan Farida tanan gidan?" "Mun santa amma ta dade da mutuwa" Adaide wannan lokaci sai saurayin yafito ,rike da kundin adana hotuna (album). "Duba sosai kaga ko wata kagani mai kamar Farida"ya fada lokacin dana fara buda kundin hotunan.*Shuraih Usman* "Shakka babu faridan dake jikin wadannan hotunan ita ce Faridar data kwatanta min wannangidan,kuma ita ce ta karbi zobena a Lagos,wannan ko shakka babu" Narika fada lokacin dana ke nuna hotunanta. Kamar na fita daga hayyacina . "Shinyaya sunanka malam"ya tambayeni. "Habib" "Nikuma Nasir"~ Anya habib ba mafarki kayi kunhadu da ita ba?" "Jiya an yi ball tsakanin Nigeria da Costrica a Lagos?" "Tabbas" yafada. To shakka babu jiya na hadu da farida a Lagos,kuma ita ta kwatantamin nan gidan" "To ai ni abin dake bani mamki shine babu abin da yada farida da Lagos ko da tana da rai domin bamu da kowa aLagos" Ya. Zura hannunsa a aljihun wandonsa ya fito da kundin rubuta muhimman al'amura ,don tunawa gaba(Dairy)ya miko min bayan ya budo inda yake so naduba* Shuraih Usman* RANAR ALHAMIS 1-2-96,RANAR BAKIN CIKICE GAREMU.RANAR DA FARIDA TA KOMA GA MAHALLICCINTA,ALLAH YAJI KANTA,YAYI MATA GAFARA DA RAHAMA. Cikin matukar fargaba da mutuwar jiki kwalkwalwata ta kasa tabuka komai,namika masa littafin. "Don na kara gamsar da zuciyaka,Farida kwananta biyu a hafsat private Hospital ta mutu,zamu iya zuwa can don su kara yimaka bayani ko ka sami cikakkiyar gamsuwa" Ban yi masa musu ba muka nufi hafsat private Hospital. Mun samu likitan dogo siriri wankan tarwada,mai gashin baki sanye da kayan aiki na likitoci a jikinsa.mutum ne mai fara'a wanda yafi dacewa da malami akan likita . "Ka shai dani?"Nasir ya tambaye shi. Bayan mungaisa "Kwarai kuwa. Bakaine kanen farida. Wacce ta mutu anan asibitin shekaru uku da suka wuce ba. SIRRINSU Littafina daya Chapter 5 By Shuraih Usman "Tabbas nine,dama don Allah muna bukatar shaidar cewar anan ta mutu,fatan dai kuna ajiye irin wadannan takardun?" "Hakika muna ajiyewa ,domin dokar asibitin ce ,ku danyi min hakri mintuna biyar,ina zuwa" "Yafada lokacin yanufi wani daki Shakka babu wannan al'amari haka yake,na duba wadannan takardu kuma na gamsu,sai dai har yanzu mamakin al'amarin ya sa kwalkwalwata ta birkice . Na hadu da mace jiya ace ,yau shekarunta uku da mutuwa?" Har zan tafi sai yace na tsaya ya kirawo babarsu,don ita ma ta tabbatar min cewar farida ta mutu. Babu abin da ya kara ba ni mamaki ,irin matukar kama da farida ta yi da mahaifiyarta , Kamar ka tsaga kara gida biyu. Kundin adana hotunan da nasir ya kawo min,har yanzu shine a hannunta. Bayan mun gaisa ta miko min kundin adana hotunan ,tace na kara dubawa,ko dai wata faridar ce . Bayan na duba na kara gamsuwa, sai na zari daya daga cikin hotunan batare da sunsani ba. Sanye take da doguwar bakar riga ,data yi matukar dacewa da jar fatanta. Tasaki yalwataccen gashinta ya zubo har gadon bayanta,sannan tayi amintaccen murmushi dakan dau hakalin kowane namiji. Sannan na mika mata kundin adana hotunan* _ Shuraih Usman _ * "Shakka babu, wacce ke jikin hotunan nan ,itace faridar dana hadu da ita a Lagos. Kuma iace ta kwatantamin nan gidan,kuma har zobena nabata . Wannan ko shakka babu na rantse da wanda ya aiko Annabi dagaskiya ,duk abin dana fada gaskiyane" Tayi shiru tana kallon fuskarta,kallon dake nufin matukar mamkin abin dana fada. "Shakka babu aljana ce ta fito maka a siffar Farida. Wacce kuka hadu da ita ,tabbas ba farida bace . Farida yatace,ni na haifeta kuma yau shekarunta uku akarkashin kasa. Sauda yawa sukan fito ma mutane a siffar mutane ,kamar yanzu yafaru yanzu akanka . Ba mamki so take ku hada gwiwa don gudanar da wani al'amari,domin da cutar dakai zata yi shiga jikinka zata yi. Wanda wannan bakon abu ba ne* _ Shuraih Usman _ *sau nawa aljanu ke shiga jikin mutane? Abu daya kawai za kayi,shine samun cikakken bayani daga masana akan _SIRRINSU_ " Bayan nayi mata godiya ,mun yi sallama ta koma, sai nasir yace muje makabartar da akabinne farida,don naga kabarinta ko na kara gamsuwa . Katuwar makabarta ce da aka katangeta , muna shiga makabartar sainaga kamar film din ban tsoro (Horrow) nake gani kokuma mummunan mafarki nakeyi. Wani tsamurarren mutum gashin kansa amurmurde ya nufo mu ,ashe shine mai gadin makabartar. "Don Allah zan raka wannan kabarin yayata"nasir yafada. "Farida?"Maigadin yafada cikin muryar tausayi. Simin taccen kabari Nasir yanuna min ajerin kabarurruka na takwas. * Shuraih Usman *"kaga kabarinta" maigadin yanuna min. Daga kusa da kabarin kafaffen katako ne anyi rubutu ,balo-balo ajikinsa kamar haka:- *_FARIDA TA MUTU RANAR ALHAMIS 1-2-1996._* Nakurawa kabarin ido ina mamkin,yanzu faridar dana hadu da ita jiya itace a kwance anan!shinfitowa tayi ta tafi Lagos muka hadu?ko kuwa fatalwarta ce_(hmm nima amsar danake ni ma kenan)_ Wani abu dake sheki akan kabrin,shine ya katsemin tunanina ,cikin mutuwar jiki sannu ahankali nanufi kabarin. Na tsinci kaina cikin tangamemen tafkin abin mamakin daya girgiza rayuwata,tunanina da kuma hankalina .Shakka babu abin dake kyalli akan kabarin *_ZOBEN_* dana bawa farida ne jiya a Lagos SIRRINSU Littafi na daya Chapter 6 By Shuraih Usman C 4~3~'99. *_KARFE TARA NA DARE_* Ahmad mutum mai matukar farinjini, da mutunci a idon al'umma .kuma shi yake da hakkin mallakar kamfanin jarida DANKARI,kamfanin jarida mai zaman kansa a hausawa sabontiti dake birnin kano. Kamar yadda yake da farinjini haka ma jaridarsa , tayi matukar karbuwa a wajen al'umma . Jaridar DANKARI,ta kan taba kowanne bangare na rayuwar dan adam,sannan kuma tana kunshe da labarirrikan abubuwan abin mamaki. Da suke faruwa aduniya,wadanda idan badon sun faru ba,idan wani yafada baza'a yarda da shi ba. Ahmad shine yake auran yayata fatima ,saboda shakuwar da mukayi da shi agidansa nake kwana ,kuma a kamfaninsa na ke aiki. Wasu lokutan tare muke shawagin dauko rahotanni,kamar yadda ya tafi dani Lagos da Kaduna . Mexico da Ireland na gama wasansu na karshe muka dawo kano. Gidansa kayattacce ne kuma yalwatacce,bene hawa daya dake fuskantar bakin titi a unguwar. Tara daidai na dare ina zaune a falon gidansa,kwanukan abinci a girke. Akan tebirin dake gabana . Babu abin ke matukar jefa nishadi a zuciyata game da aurensa da fatima ,irin zunzurutun *_SO*_ da kaunar juna da suke yi. Tun data ajiye min abincin ko kara tunawa da shi banyiba ,sakamakon zuzzurfan tekun tunani dana zurfafa. Na tuna lokacin dana mika hannu hankalina a tashe,jikina na rawa na daunko zobena ,dake kan kabarin Farida.*_ Shuraih Usman *_ Shi kansa Nasir da maigadin makabartar sunyi matukar fahimtar razana da kidimewan dana yi. Shakka babu na hadu da farida jiya a legos,kuma shakka babu na bata zobena ,sannan shakka babu na tabbatar ta mutu ,sannan shakka babu zoben dana tsinta akan kabarin shine wanda na bata ta kuma saka ahannunta .(Shakka babu nima shuraih wannan al'amri ya kidimani) Shin yanzu wa zan gayawa wannan birkitaccen al'amari ya gaskatani? Wane ne zai yarda dani idan na ce jiya na hadu da mace a Lagos ,kuma shekarunta uku da mutuwa ?"*_ (shakka babukoni bazan yadda dakaiba )_* "Shine zoben daka bata" nasir yatambayeni cikin kaduwa. "Shakka babu"cikin kidemewa na fadamasa. "Nasir bana son kowa ya yarda da wannan rikirkitaccen al'amari daya faru gareni,domin nasan shakka-babu babu wanda zai gaskatani" "Habib ! Ba na shakka,bana kokwanto wannan al'amari daya faru zuciyata ta gaskatashi." "Shin yanzu aljana ce ta fito min jiya a siffar farida?"*_ Shuraih Usman _* "Shakka babu amsar kenan domin farida ta riga ta mutu" *********** Sai da muka dawo kano na tuna ban tambayi nasir game da kodaddiyar matar dana gansu da farida ba. Shakka babu aljanu na hadu da su,domin kallo daya zaka yi wa mummunar matar nan,ka san cewar aljana ce . Natuna yadda na tsorata lokacin dana ganta ,da kuma yadda naji na tsaneta . Har muka dawo kano hoton farida da zobena da na bata , na kuma gan shi akan kabarinta , Sune abin da hankalina da tunanina suka tattara akai. "Tunanin me kake yi habib?" Fatima fara mai matsa kaicin tsayi da kauri,sanye da a tamfar Holland dinkin sirfani,ta tambayeni tana murmushi. "Tun dana kawo maka abnicin,har yanzu ko taba shiba kayiba " Nayi ga wurtacciyar ajiyar zuciya ,lokacin dana fito da hoton farida daga aljihuna ,na kuma dora zoben akai,sannan na mika mata . *_ Shuraih Usman _* Shakka babu kaki cin abinci kuma kamanninka sun birkita ,wannan irin zukekiyar yarinya ,gaskiya kyakkyawa ce " Ta fada lokacin data dawo min da zoben, hoton har yanzu na hannunta . "So nake kikare ma zobennan kallo" "Kamar ya nakare masa kallo,ba shine zoben dana baka ba ?"Cikin mamki ta fada . "Kin tabbatar shine " "Shakka babu shine" Ta fada bayan ta kare masa kallo sannan na kara zura shi a dan yatsana ,tun lokacin dana daukeshi ban mayar dashi hannu na ba . "Fatima ! So nake na yi maki wasu tambayoyi" "Allah yasa ina da amsarsu" Fatima ta kasance mace ma'abociyar ilmin Addinin islama, ta bangaren tarihi,littatafan fiqhu,hadisai dakuma Alqur ani. "Shin ko a karance -karancen da kika yi na hadisai,dana tarihi,da kuma na fiqhu zuwa Alqur'ani ,kokintaba karo da cewar mutum idan ya mutu an binne shi,kan iya tasowa yaci gaba da rayuwa?" SIRRINSU Littafi na daya Chapter 7 By Shuraih Usman Tayi dan shiru na wasu lokuta ,wanda hakan yasani tsammanin ko gaskiya ne ana mutuwa a taso. "Mutuwa dai na nufin rabuwar ainihin rai da gangar jiki. Ku ma ahakikanin gaskiya idan har ubangiji ya umarci mala'iku,suzare ran mutum,suka kuma zare,shakka babu wannan mutum bazai kara tasowa duniya don cigaba da wata rayuwa ba. Har sai lokacin da ubangiji yakara dawo masa da ransa,don tsaiwar ranar ALKIYAMA. Yana faruwa mutum yai doguwar suma a zanta ya mutu,har sai an masa wanka ana kokarin binneshi sannan ya farfado. Wasu idan suka yi wannan suman sukan sami har kwana daya kofiye da haka. Amma idan har an zubawa mutum kasa aka binne shi , Shakka-babu wannan tasa takare. A kwai rayuwa da akeyi idan anmutu(HAYATU-B ARZAKIYYA)rayuwace da mamaci ke yi idan aka binne shi ,duk wanda aka binne shi akan dawo masa da ransa ,don sanin cewar wani matsayi yake . Idan aljanna ne akan hada masa wani dausayi na aljanna,kamr yadda akan hadawa dan wuta wani narko daga jahannama .*_(wa iya zu billah)_* Shuraih Usman Idan har mutum ya mutu to bashi da wata dama ,da zai cutar da rayayyu ko kuma ya amfanar dasu. Shi wannan tasa ta kare sai yadda Allah yayi da shi" "Shin dagaske ne idan mutum ya mutu,ya kanyi fatalwa ya dawo duniya?" Wannan karonma. Shiru tayi na dan lokci. "Aduk lokacin da mutane suka ji ance fatalwa,abin da kawai suke dauka shine ,bayan mutum idan ya mutu idan ya kasance yana da matukar buri,ko ba'a yi masa sadaka . Sai yakara dawowa,yana tsorata al'umma. Wanda a zahirin gaskiya wannan al'amari bahaka yake ba. A bin dake faruwa shine ,aljanu ne ke fitowa a siffar wanda ya mutu don surika tsorata al'umma ,suna jefa zukatansu cikin rudani" Tana fadin haka sai gabana yai mummunar faduwa. "Wasu lokutan idan shahararren mutum ya mutu,sai aljanu su rikida da siffarsa,da zarar al'umma sun ganshi sai su rude , su razana suna fadin fatalwar wane ta fito. Shuraih Usman Ko kuma idan mutum yana hulda. Dasu,kuma jama'a sun san hakan kuma ya mutu,sai shi masu rikida da siffarsa,su rinka razana wadanda suka sanshi. Ubangiji yayiwa aljanu baiwar rikida daga wata siffar kuma su wadan su irin halittu na da burinsu kawai su cutar da mutane ,su kuma jefa su cikin rudani. Sai dai abin dubawa shine ,babu yadda za'ayi aljani idan ya rikida a siffar mutum,ya bayyana da cikakkiyar kama ba tare da ansami tawayaba .dole ne idan suka rikida kasamu wani bangare jikinsu,baiyi dai dai da na mutane ba ,komai kyan siffar da suka bayyana. Wasu idan suka fito a siffar mutane zaka samu idanunsu na mage ne,ko kura ko kuma sauran namun daji ,ko kuma ka ga kafafuwansu irin na doki,ko daya tafi daya girma da dai sauransu. Amma mafi yawancin sunfi rikida amunanan siffofi. Kamar mummunan tsohon dake cikin matsanancin talauci,ko kuma siffar halittun tsoro. Shuraih Usman Nayi shiru ina fargaba da mamakin,rikirkitaccen al'amarin daya faru akaina,wanda da wani ne yafadamin ba mamaki zuciyata takasa gaskatawa. To amma ni ai banga wasu kamanni jikin farida,wadanda ba su dace dana mutane ba sai dai matar dake tare da ita,wacce kwata-kwata na tsani na tuna kamanninta a zuciyata. "Fatima! Wani abune ya girgiza rayuwata" Kamar wani abu kenan"cikin doki ta bukata . 'Jiya ne bayan antashi daga wasan Nejeria da costrica a Lagos ,sai muka hadu da yarinyar dake jikin hoton dake hannunki. Mun yi hira da ita ta fadamin sunanta, da kwatancen gidansu a kaduna ,nakuma bata zoben nan dakika bani yau bayan antashi daga wasa naje gidansu kamar yadda ta kwatan tamin. Ina ganin kamwarta da babarta ,naga kamarsu daya,ba wani bambanci, dana nemi akirawo min ita sai suka tabbatar min shekarunta uku da mutuwa. Da farko ban yarda ba sai da suka gamsar dani da hujjoji. Lokacin da aka kaini kabarinta ,sai na ga zoben dana bata akan kabarin. Wannan hoton da kike gani cikin kundin hotunanta na dauko. To waishin wannan da me ya yi kama? Kuma na duba jikinta tsaf,babu abin da bai yi kama dana mutane ba. A takaice ma har taba jikinta nayi" Ta kurawa hoton ido wasu lokuta,ta dawo da hankalinta kan zoben dake hannuna,sannan ta zurfafa atunani. Shuraih Usman "Shakka babu ,wannan al'amari ne babba ,kuma da aljana ce ina ganin ba zata fito cikin taron jama'a ba . Koda yake to idan ba aljana ba ce ,yaya mutum zai mutu shekaru uku kuma aganshi a wani waje daban? Gaskiya al'amarin da rikitarwa" A dai dai wannan lokci sai Ahmad doga dan baki kakkaura fari kyakkaywa sanye da farin boyel doguwar riga da wandonta . Bayan fatima ta cire masa takalmin kafarsa ,ta kwance masa agogonsa,ta sumbaci fuskarsa,sai ta harhada tawagar abincinsu akan tebur. Ko da yaushe tare suke cin abinci. Shi kansa daya samu labarin al'amarin ya girgiza shi. "Wannan sai yayi dai da labarin *_SHAKKA-BABU_*" A gaskiya al'amarin kunshe yake da riktarwa. Ahmad yafada. Kwarai kuwa abinday faru akaina yaso yayi dai de da labarin BABBAR MAGANA. Har fatima da ahmad suka gama cin abinci suka shiga harkokinsu,ina zaune zuciyata makil da tunani ,al'amarin sai faman kai kawo yake cikin kwalkwalwata .idan na kalli hoton Farida sai naga kamar moysi take yi, don gudun kada na zautu ,sai najuya bayan hoton.rubutu ne dara-dara ajikin hoton REST IN PEACE. SIRRINSU Littafina daya Chapter 8 By Shuraih Usman D 5~3~'99 *_ LITTININ_* Shakka babu , al'ummar kano na matukar kishin yan kwallon kafar england. Zuciyarka zata iya gamsuwa da hakan idan ka halarci wasan da aka buga tsakanin AMERIC da ENGLAND,a dakin wasa na *_GENERAL SANI ABACHA_*,daka kofar mata . Wajen yadinke da dimbin al'umma bakamar lokacin da aka buga wasa tsakanin camerou da japan ba . Shakka babu dakin wasan ya yi haduwar ,da ba za a kushewa wadanda suka yi aikin ba . Har aka gudanar da wasan farko babu cikakkiyar nutsuwa,a zuciyata da ruhina da kuma kwalkwalwata . Idan har farida aljana ce mene ne dalilin yin kuka ,har da zubar da hawaye ? Mene ne baiyi kama da halittan mutum ajikin taba?..... Bana mu'amala da da namiji" Me wannan kenufi ? Nasan baza yarda da abin dana fada ba ...... Ni kaina ba'ason raina hakan ya kasance ba " "Sai dai babu yadda zanyi" Shin wadannan zantuttuka ke nufi ? Shin farida mutumce ? Idan mutum ce yaya ta mutu ta dawo? Nayi iya bakin kokarina don samawa wadannan tambayoyi amsoahinsu,yayin da kwalkwata da kuma tunanina . suka gaza don samar da amsa tambayoyin. Da har yanzu dada rikitar da rayuwata sukeyi. Shakka babu na hadu da farida ,nayi hira da ita ,wannan ba mafarki bane $ To kuma na samu gamsassun hujjoji kuma kwarara cewar farida dana gamu da ita shakka babu ta mutu. To mene ne wannan? Wanne suna ta dace aradawa al'amarin? Wannan suma tambayoyine ma bukata amsar dazat gamsar da tunani. Shuraih Usman Da ga ranar dana hadu da'ita izuwa yanzu ,idan kasanni kallo daya zakayiwa fuskata ka tabbatar shakka babu rama ta ziyarceni. Saboda tsagwaron kaduwa da rudewa ,da tunani da hankalina suka yi,wanda hakan ya haifarwa da kwalkwalwata nutson bazata cikin rudu da matsananciyar birkita. Duk don faruwar birkidadden al'amarina. Shakka babu dolene tunanina ya zurfafa ,rayuwata ta girgiza,hankalina ya galaibaita . Ka gamu da mace jiya kuyihira ido da ido,kabata abu ta karba ,ka tambayeta ,ta baka amsa ,karewa ka tabata ,sannan kana daya kacal da haduewar ka daita ka samu tabbacin mutuwarta ,shekaru uku da suka gabata. "Shin wace mummunar matar dake tare da farida" Mene ne hadinta farida? Mene ne dalilin da yasa take takurawarayuwarata ." Shuraih Usman Babu abin dana fiso a rayuwata irin hora da namiji,sai dai bani da wannan damar arayuwata "banda maganganun da mukayi da farida ,kwata kwatakwalkwawata ba ta tuna wasu muhimman al'amura . Shuraih Usman Kwatsam! Sai naji farida ta a zuciyata. Babu abindayafi ban mamaki irin tun dana ganta ,sonta ke dada ruruwa a rayuwata . Maimakon idan tunanin matacciya nakeso,sai ya ziyarci zuciyata na kori son,sai son yakara bunkasa. Kiri kiri,ina ganin ana shiga dakin wasan,yadda za'a fafata tsakanin England da USA,kuma ni kaina ina matukar ra'ayin wasan ,na hakura natsaya a waje ,kuma nakasa tafiua ko ina ,idan ka ganni tsaye ko tunanin gajiya banayi,na kurawa dakin wasan ido ,sai ka dauka so nake nashiga bani da kudin shiga . Shine na kasa daurewa na tafi , nake kallon masu damar shiga.na shiga ,nikuma ina kallon takaicin babu yadda zan yi. Sai dai da ace wani zaizo inda nake ,zai san na zurfafa a tangamemen tekun zunzururutun zuzzurfan tunani. Da ace nasan awajen wani al'amari zai kara faruwa,har ya girgiza rayuwata,fiye da yadda na tunzura jiya da yau ,da ban tsaya tsimayin faruwar tsorataccen al'amarin ba. Amma ina gama ya gama ,uba yayiwa yarsa ciki. Al'amarin yariga. Ya faru. Tun lokacin da na zari hoton farida ,har zuwa wannan lokaci,duk lokacin dana kura mata ido, ina mai maita tambayoyin da amsarsu bazata samu awajena ba,ina dago kaina sai naji zuciyata ta yi tsayawan wucin gadi. Shuraih Usman Kamar lokacin nafara ganinta ,ranta amatukar bace ,kodaddiyar fuskarta ta kara muni,har yanzu idanuwanta jawur suke kamar tira su take yi. Sanye d katuwar rigar shan iska da matan turawa ke sawa,hannun ta rike da makullin mota tana dan karkadawa. Ina ganinta tsoro da matukar fargaba suka lillbe zuciyata ,dukkan jikina ya dau rawa tamkar mutuwa ta na ke gani; Babu abin da ke bani mamki irin yadda nake matukar tsorata da zarar naga matar. Shakka babu na tsani mummunar matar,bana bukatar ganinta a rayuwata. Cikin tsoro ina tunanin guduwa daga wajen ,sai farida sanye da shudayen kwat riga da siket,ita ta fito daga dakin wasan .hankalina yayi matukar girgiza,tunanina ya dagule ,zuciyata bugun ta ya tsananta sannan jinin jikina ya zafafa. Farida ! Shin ba wannace akace tamutu ba ?shinyanzu ma mafarki nake yi?idan dai har aljanu basa rikida batare da na sami wani bangaren jikinsu , Shuraih Usman da baiyi kama dana mutane ba ,farida ba aljana bace .ko ina ajikinta irin na mutane ne ,wannan ko shakka babu. Domin kura mata ido nayi,babu inda ban kalla a jikinta ba . SIRRINSU Littafina daya Chapter 9 By Shuraih Usman Kyan fuskarta ya dada karuwa akan nada ,sannan amintaccen murmushina bayyana adan karamin kyakkyawan bakinta "MINAL JINNATI WAN NAS" Abin da kawai narinka fada kenan. Sannu ahankali ta rinka nufo wa inda nake ,har nayi niyyar cika wandona da iska ,ga mamakina sai kafafuwana suka nauyaya ,ba zan iya gudu ba . A dai dai lokacin da ta zo daf da ni sai ita da hasken suka bace,A ranar kwana nayi ina wuridi don na razana bacci yayi hijira daga idanuna Shakka babu ina cikin rudu babba. Shuraih Usman F LARABA 7~3~'99 Mahaifiyata Nana safiyya ta kasance ma'abociciyar turare ce , Aduk lokacin da zatayi maka gagarumar kyauta turarene Duk lokacin daka hadu da ita ,hancinka zai wadatu da kamshin hadadden turare. Fatima ce babbar yarta. Sannan ni,sai kuma karamin kanen mu sadiku. Kuma shine yafi farin jini a gidanmu sakamakon baiwar hikimar zance da zuzzurfan tunani daya mallaka. Wata rana mahaifinmu da abokansa na hira,kowannen na fadin wanda yafi tsana arayuwarsa,da dalilin daya saya ya tsane shi,kamar wasa sai daya daga cikin abokan mahaifinmu yatambayi sadiku dake zaune kusa da mahaifinmu "Sadiku wanene babban makiyinka aduniya ?" "Sulman rushdie"ya amsa masa "Musamman ya wallafa littafi yasa masa suna ayoyin shaidain(SATANIC VERSES), Acikin littafin yakirawo fiyayyen ANNABIN RAHAMA, Mayaudari mazinaci,ya kuma ambaci tsarkakkan matansa da Allah yakirawo IYAYEN MUMINAI,da cewar karuwai ne. Sannan yanuna cewar yayan gidan ANNABI(SAW) yayan zina ne, Musulmi da suka rasa rayukansu a yak-yaken daukaka kalmar ALLAH,ya kirawo su batattu.(Kai amma Allah ya tsine ma sulman rushdie- kowa ya tsine mai) Shuraih Usman Shaidan salman rushdie bai tsaya nanba ,sai daya kirawo littafin ALLAH mai tsarki al'kur'ani da cewar ayoyine na shaidan. Ayanzu shine littafin dayafi kowanne littafi tsada , Wannan abu da shaidan salman rushdie yayi,ko fir'auna baiyi wannan bakar aniya ba . Azaba mai matsananciyar radadi,da la'anta mai matukar yawa ,su tabbata ga shaidan salman rushdie da yan barandansa" Abokan mahaifinmu sai dai suka shawarce shi ,da ya wadata sadiku da wataccen ilmi,saboda nan gaba zai zama malami mai wadataccen tunani. Aduk lokacin dana saya mata turare,takan dade tana nuna farincikinta ,ganin haka sai na mai dasaya mata turare dabi'ata . Aduk lokacin da nake bukatar daddadan turare ,kai tsaye NAFISATU FASHION nake tafiya . NAFISATU FASHION kayataccen tangamemen waje ne da mata ke matukar alfahari da ziyartarsa. Sakamakon zunzurutun kayan kyale-kyalen,mata masu matukar kyau sai dai tsada . Koda yake nafisatu ta tabbatar musu cewar arha bata ado,kuma sayen nagari mai da kudade gida. Kuma dimbin matan dake narkar da kudinsu a nafisatu fashion sun dade da yin amanna da wannan maganar Shuraih Usman Idan kana bukatan kayan mata masu kayatarwa,ko kuma mace na bukatar hadadden gyaran gashi ,ko tsararren tsari da salo salon kitso,ko kuma amintattun zanannun furanni(Flowers) a hannu da kafa ,idan ta ziyarci nafisatu fashion zuciyarta zata samu gamsuwa daga masana akan sirrin harkokin. Karfe sha dayan rana na tsaida motar honda civic a kofar nafisatu fashion sanye nake da kubta riga da wando ruwan kasa,kaina da hula. Kamar yadda nasir yafada cewar ya gasgata al'amarin daya faru gare nine ,ganin yadda kamannina suka yi mutukar birkita cikin kankanin lokaci tundaga ranar dana hadu da farida. Hakama Ahmad da Fatima suka kara maimaitamin, Kuma ni kaina shakka babu na shaida akan hakan. Dayake unguwar gadonkaya da gidan Ahmad babu yawan mutane , Kuma ni da shi mun kasance masu yawan zirga zirgar daukar rahotanni ,bani da abokai kamar unguwar Albasa da gidan mahaifiya ta yake. SIRRINSU Littafi na daya Chapter 10 By Shuraih Usman Na san da zarar naje Gandun albasa abokaina na ganina sai sun tambayeni game da ramar da keyi. Na samu dogon lokaci ina zaune cikin motar, Amma na kasa fitowa saboda zurfaffan tunani da na yi. "Nan ne gi dan su dela din? Yanzu ku dama shegantaka. Kuka kulla min? Ina zaune lafiya kuka yimin karya kun san ba gidan delar zaku kaini ba ! To mene ne nufin ku da yin hakan?" Wata yamutsastsiyar murya da kaji kasan wacce ta mallaketa , Shekaru sun wada ceta aduniya ta kaste min tunanina . Ina waigawa sai na ga wata tsohuwa ce sanye da riga da zani na atamfar English, Tayi wani irin baudadden daurin fatala. Sannan zanen ma maimakon yatafi daidai sai ya kauce kamar arazane yake ,sakamakon wani irin dauri da tsohuwar tayi masa. A tsaye daf ta wata marsandi ruwan toka , Fuskarta da idanuwanta amsoshi ne na cewar ta dade aduniya. Kusa da ita wasu kyawawan 'yanmata ne guda biyu, Babba da karama kana ganinsu kaga ya da kanwa, Farare sal dasu. Babbar sanye take da burgujejiyar riga da wandon wani zani mai kyalkyali a jikinsa , Kanta babu fatala. Karamar kuma bakin wandon jeans ne ajikinta , Da kuma farar rigar yadi mai hudahuda,da yake baiyanar da bakar shimin dake jikinta ,tayafa katon bakin fatala a kanta.(Tambaya dan Allah mata mene fatala don ni bansan shi ba Shuraih Usman ) Tsohuwar da ke tare dasu duk ta rude kamar tana nuna alamun sato ta sukayi. "Wannan shegantaka har ina ? Kawai ku tashi ku zunbuda min karya ,wai gidan su dela zaku kaini, Shikenan sai ku kawo ni wata uwa duniya ku ajiyeni! Kunsan ba son shiga mota nake yi ba, Wannan dinma dan kunce gidan su dela zaku kaini ne" Tsohuwar take fada lokacin datake kokarin tafiya daga inda yaran suke . "Tsaya kiji Goggo" Babbar tafada . "Gidansu delar zamuje , Mun tsaya anan ne muyi saye-sayen biki, Mukuma gyara gashinmu a kuma zana mana flowers. Sannan kema tunda gobe biki sai a gyara miki gashin ki, Gobe ba sai ki fito fes ba" "Ban gane a gyaramin gashiba ! Da me za'a gyara min gashin nawa ? Kai kunga bana son iya shege da wasu tsarabe- tsaraben banza dana wofi. To ina ma hausar a gyaramin gashi ? To ama gyara min gashi kamar ya ? Shuraih Usman "Kinga Goggo cigaba aka samu , Wani irn inji nasara ya yiwo musamman don gyaran gashi. Za'ayi matukar wanke miki gashinki ,afitar da kowanne irin datti,sannan sai ki zura kanki a cikin injin ya gyara miki gashinki ya rinka sheki , Ya kuma canja miki duk irin fasalin da kike bukata " Ita kanta budurwar sai da ta fada ta gane kuranta. "Allah ya sitiri bukwui! Yanzu don Allah ,Don annabi ina zaman zamana kuka yaudareni babu sidi babu sadada, Wai na zura kaina cikin inji! Wato ya markade min kaina kenan? To idan kun gaji dani alhaji bai gaji da ni ba". "Na zura kaina cikin inji akan wane dalili? Tsohuwar ke fadi lokacin data bar inda matan suke , Ni kuma a daidai lokacin na fito daga motar na fara nufar nafisatu fashion. "Kubarni Allah yakawo wanda zai mayar dani gida, Babu ruwana daku,kuje tsiyarku ta kare akanku ,nazura kaina cikin inji turkashi!" Karamar yarinyar tayi saurin tasha gabanta, Ta fara lallaminta ni kuma adaidai lokacin nazo zan gifta. Bawan Allah kaji zancen nanfa" Tafada lokacin dakai tsaye take fuskantar fuskata( Shuraih Usman ) "Cewa sukayi na shirya su kaini gidan kanwata ,shikenan sai kuka woni nan waina zura a inji, Wai acanja min fasali"ina jin yadda injin makotanmu ke burari, Sannan yanzu don sunana saratu na garkama kaina cikin injin nasara , Ina ruwana da wata gayyar tsiyar nasara". Kafin nayi magana karamar yarinyar tarigani. "Goggo ba markade miki kai zaiyiba , Mutane nawa akayiwahakan? Yanzu zamani ya canja , Abin da babu shi da yanzu an samu bawani abu tattare da hakan?" "Zamanin banza dana wofi,haka kawai garin neman gira a rasa ido. To wai mene ne yayi zafi gira ke hayaki,idoke cin wuta" "Shakka babu tafiku gaskiya ,yaya ga abin da mutun ya saba dashi ,haka kawai rana tsaka ,yarinka nemowa kansa abin da bana saba. Tun da dai ku kuna bukata kuje kuyi, Ita dabataso tayi zamanta a mota, idan kuka fito ku kaita gida. ( Shuraih Usman ) Nafadi hakanne don na kwantarwa. Da tsohuwar hankali. "Sannu dan gari•haka kawai babu gaira babu dalili,kilu ta jawo bau" Tafada lokacin da tafara komawa wajen motar. "Kaduba rannan ina zaune lafiya suka kawomin wata tsinanniyar aba wai ita talabijin, Dalbijin ko masifa? To inbanda masifa kawai sai gani nayi wannan ya cakawa wancan wuka. Wancan ya sari wannan da takobi,a duko bindiga a zunduma wa wannan ,kaga tsiya ! Mutum yafadi ya mutu. Can kuma sai wuta ta kama zaal! Zaal! Zaal!!!" "Kwanana uku ina mafarkin wannan masifar,kuma tun daga ranar nace in Allah yayi duniya don dan Abdullahi ni da talbijin munyi sallama . ( Shuraih Usman ) Tafada lokacin data shiga motar,'yanmartan sai faman dariaya sukeyi suna kallon fuskata. "Ni dadina da Goggo ,haryanzu kanki yaki wayewa " Babbar tafada cikin zolaya . "Fatalar uwarki!kan nawa bai wayeba kullum kike zuwa ki ce na koya miki yadda zaki mallake mijinki ki hana shi fita ?" "Ahayye ! Ayyururi ! Kyale su haka Goggo" Suka fada suna shewa, lokacin da suka shiga Nafisatu fasion ,ina biye da su a baya . Mata ne dinke cikin nafisatu fashion,kowacce na kai- kawo, Don zabin abin da suke bukata . Dayake na san abin daya kawon,kuma nasan inda zan sami turaren kaina tsaye ban tsaya bata lokaci ba na nufi matattarar turarikan. Ina zuwa wajen tirarikan 'yan matan suma suka zo inda nake . "Zainab ! Ni ma fa ina bukatar turare" Babbar ta fada wa karamar,lokacin dasuka fara duddubawa. "Kaima turaren zaka siya ?' Zainab din ta tambayeni. "Shakka babu " Nafada ina murmushi. "Na zaba maka" "Zaki iya yin hakan" SIRRINSU Littafina daya Chapter 11 By♥ Shuraih Usman Queen da heart da kuma daimond , Sune turarikan da zainab ta zaba min. Shakka babu ,nayi matu kar yaba zabin da zainab ta tayi min ,domin tsarin kwalaben kadai sun gamsar idanuwa . A dai dai lokacin dana rike ina dada dudduba , sai naji wata irin daddadan dariya ta diki dodon kunnena . Kwalaben turaren suka kubuce daga hannuna suka tarwatse a kasa, Tsarwatsewar da ta jawo hankalin matan cikin kantin kaina . Hankalina a birkice , Tunanina arazane ,bugun zuciyata yayi matukar tsananta lokacin danaga wacce nake gani , Shakka babu farida ce , Kasancewar nafisatu fashion tangamemen wajene akwai tazara tsakanina da su. Babu abin daya fi tunzurani fiye da komai, Irin duk inda naje sai na ganta . Shakka babu , Dole hakan ya tunzura rayuwata, Dole rayuwata ta rude, Dole rayuwata ta gigita, Tun ranar da Nigeria da costrica,suka yi wasansu a lagos , Kullum sai mun hadu da farida ? Kuma bayan na samu tabbacin mutuwarta . ( Shuraih Usman ) Sanye take da kayan babe bari dogwaye har kasa, Ta nannade jikinta da dogon kayataccen mayafi, Kamar dama zuwanta kenan daga maiduguri. Abin daya dada jan hankalina gareta ,wannan lokacin cikin farin ciki da nishadi farida take, Bakamar ganina da nayi mata a sani abacha stadium da kuma hawan dabar gidan sarki ba . Saboda kada na kara gamuwa da ita, Ahmad yatafi Lagos don dauko rahoton wasan Nigeria da Germany.sannan kuma zai wuce ibadan don halartar wasan gwana da argentina . Babu yadda bai yi dani don mutafi ba , Na dage akan gaskiya na hakura , Kawai do tsoron haduwata da Farida . Wannan lokacin ma tare suke da ko daddiyar matar ,ita ma sanye da zurma zurman bakaken kwat riga da siket. A lokacin nake kollosu,kudin sayayyar da sukayi mayar ke biya . A lokacin dana yi yun kurin zuwa inda suke , Saboda na ga suna kokarin fita sai naji hannuwa sun rikeni. Ina wai gawa saina ga wasu rusa-rusan karti guda hudu, Kowanne fuskarsa a tirbine suna yi min kallon rashin yarda. Sai daga baya na fahimci masu tsaron nafisatu fashion ne . Ai a anan na dawo hankalina na fuskanci ta'adin danayi . Har yanzu zainab da yayarta na tsaye suna mamakin,yadda cikin kankanin lokaci na birkita . Kwata-kwata sai kunya ta lillibeni,dana waiga inda su farida suke tuni sun fice daga wajen. Shuraih Usman Bayan nanemi afuwan ta'adin danayi , Na biya kudin tirarikan sai na kara sayen wasu,sannan cikin sanyin jiki da kunya na nufi inda motata take . Na sami dogon lokaci cikin motar , Na kasa tukawa na tafi. Shin menene dalilin da duk inda nayi sai na hadu da farida? Tambayar da zuciyata tayi ta maimaitawa kenan, Na rasa amsarta har sai da wata murya a sanyaye tace; "Hala wani abu ya tunzuraka?" Zainab ce an matukar kayata gashinta , Sannan hannunta data dora akan murfin motar, Shima ya kayatu da kyawawan furanni lokacin dana waiga. Bayan nayi ajiyar zciya sai nayimata murmushin gaskiya kin-hadu-zainab. Ganin haka ita ma sai ta yi murmushin. Mahaifiyata tayi farincikin turarikan dana kai mata , Kuma ta tambayeni dalilin rama da nakeyi . Ban boye mata ba , Na sanar da ita komai, Kuma shakka babu tayi matukar mamki kamar yadda duk wanda na gayawa sai yayi mamaki. Shuraih Usman Sannan tabani addu'o'in da zan rika yi don neman tsari, Sannan kuma ta shawarceni da kada na aiwatar da wani yunkuri da zai iya kaini ga halaka ,ko kuma ya cutar da rayuwata. Abokaina ma sai da suka tambayeni halin dana ke ciki. Shi kansa mahaifina sai da yayi min tofin wasu ayoyin AL'QUR'ANI a dukkan jikina ,sannan ya tofa min wasu aruwa na sha. Ya kuma umarceni da karanta QUL'HUWALLAHU uku, FALAQI uku, NASI uku,idan nayi sallar asuba. Sannan idan nayi sallar magriba , Da kuma idan nazo bacci . Ya kuma kara umarta ta da karanta AYATUL KURSYU da kuma suratul YASIN. Bayan na dawo daga gandun albasa wajen mahaifiyata ,a ranar idan na runtse ido saina ga kaman farida tana kuka , Idan na bude sai na ganta tana murmushi. Sai dana samu dogon lokaci ina zubar da hawaye sannan na fahimci kuka nake yi. "NA SHIGA UKU" Kalmar dana yawaita fada kenan awann rana. SIRRINSU Littafina daya Chapter 12 By♥ Shuraih Usman G ALHAMIS 8~3~'99 Mata ne dake tinkaho da ilmi, Masu takama cewar mazansu masu fada ajine , Suka dinke dakin taron na makarantar Rumfa College, Don gudanar da taro na musamman akan tallafawa iyali. Maimuna isa kwantagora matan ,kantomar jihar kano,ita ce tayi jawabi na karshe a taron. Kamar yadda Ahmad ya umarceni don na dauko muhimman abubuwa a taron , Na cika wannan umarnin, domin na halarta. A burin Ahmad duk wasannin da za ayi a dakunan da Nigeria ta tanada don gudanar da wasan cin kofin matasa na duniya sai mun halarce su. Da farko nayi matukar farincikin hakan, Amma daga baya na fatattaki farin cikin daga zuciyata,don matukar tsoron kara haduwa da farida. Sanye na ke da farin jeans riga da wando,kafata daure da kito baki Wasan da za ayi tsakanin cameron da England a kano, Bashine a gabansa ba . Wasan japan da USA da za ayi a bauchi, Da wasan zambiya da spain daza a gudanar a calabar,da kuma wasan honduras da brasil da za ayi a por shine abin daya dame shi. Kuma babu yadda za,ayi ya halarce su rana daya ,shine babban abin bakin cikinsa da kuma kekasa kasa danayi nacewa bazan kara halartar kowane dakin wasa ba . Shakka babu baiso hakanba ,don matukar shakuwa da mukayi da shi. Bayan na gama gudanar da abin daya kawoni ina kokarin tafiya hausawa sabon titi,in da kamfanin jaridar Ahmad take ,sai na'urar daukan hoton ta subuce daga hannuna ta fadi. Da farko na bayar faridace,sai daga baya na karbo ashe mahaifiyarta ce , Ita ma tana daya daga cikin matan da suka halarci taron. Nayi matukar girgiza da mamakin ganinta ,wanda ita kanta ta fahimci hakan rubuce a fuskarta. Kuma ita kanta tayi mamakin ganina a wajen Har muka gaisa da ita gabana na faduwa ,shakka babu idan kaga mahaifiyar farida kaga farida . "Da ma anan kake" Tafada cikin mamaki. Shuraih Usman "Wallahi anan nake " "Daukar rahotanni kake yi?" "Da man kai ma'aikacin jaridane?" "Shakka babu" Nafada . "A wanne kamfani kake aiki" "Dankari" "Dankari?" Tasake maimai tawa. "Shakka babu" "Kana nufin jaridar dankari wanda dimbin al'ummma ke alfahari da karantata?" "Shakka babu" Na maimaita. "A gaskiya shakka babu ,ta shiga bakinka "(nima haka daenagani) Tafada tana murmushi. "Shakka babu" Nima nafada cikin murmushi. Murmushin datayi sai ya koma dariya , Nikuma a wannan lokacin zuciyata a farida take daukanta . Duk da cewar tafi farida kaurin jiki da shekaru,gani nake yi zata rikide ta koma farida. "Ina nasir?" Na tambayeta don katse dariyar da takeyi . Shuraih Usman "Tare muka taho,har ma da meenat ,duk suna tarauni" "Tarauni wajen ina " Na bukata . "Don inason gaisawa da nasir" "Kana zuwa daidai masallacin juma'ar tarauni,ka tambayi shagon askin sulaiman ,agidansu sulaiman din muka sauka .sai gobe zamu koma yace yana son ganin wasan England." Abin dayabani mamki har muka rabu bata yi mani zancen ganin farida danace ina yiba . Wanda hakan na nufin TASAN FARIDA TA MUTU ,KUMA TASAN SHAKKA BABU WANDA YAMUTU KAWAI YAMUTU. WACCE NAKE GANI A TUNANINA ,ALJANACE TAKE FITO MIN A SIFFAR FARIDA. TO AMMA ABIN TAMBAYA ANAN WACECE WANNAN KODADDIYAR MATAR SIRRINSU Littafina daya Chapter 13 By♥ Shuraih Usman Bayan naje hausawa sabon titi na bawa ma'aikata rahotannin dana dauko , sai na wuce gida nayi wanka na sauya kayan jikina , da shadda riga da wando launin sararin samaniya ,sai na shiga wata motar Ahmad din TOYOTA CAMRY sai tarauni. Kamar ta kwatanta min,ina tambaya aka nuna min shagon askin sulaiman. Sulaiman farine amma ba dogo ne sosai ba,yana da yawan fara'a da 'yar saurin magana. Kaset din wa'azin AHMAD DEEDAT ne ke tashi a katuwar rediyon dake shagon yana yi wani yaro aski. "Don Allah nasir dayazo daga kaduna nake nema" Na fada bayan ya rage karar sautin rediyon. "Ok,kwarai yana gidanmu. "Nasir ko?" Hakika yana nan. "Don Allah barina gama askin sai mutafi,dama ina zon zuwa gida" Cikin saurin magana yafada,yana sauri don ya gama wa yaron askin. "Bismillah,zauna mana ,nakusa gamawa ,saura kadan" Yafada lokacin da yayi min nuni zuwa ga kujera . Bayan ya gama askin,ya kulle shagon,sai muka nufi gidansu. "Tun dana ganka nake tunanin,kamar na so na sanka " Sulaiman yafada lokacin dana tsayar da motar a kofar gidansu" "A ina fa ?"Na bukata "Shin ko kataba yin karatu a 'yargaya ?" "Shakka b babu" "Haba ni fa tun dana ganka ,nake ma kallon sani,nima a 'yargaya nayi karatu" Shuraih Usman A daidai wannan lokaci sai nasir,sanye da farar riga ya dora mata bakar falmaran ,da wando launin kwai ya fito daga gidan. "Aah! Habib! Yaya aka yi kasan ina nan ?"Cikin mamaki yafada ,lokacin daya nufo in da muke. "Nasir!" Na kirawo sunansa bayan mungaisa. "Ya yi habib ,wallahi ina da saurin mantuwa,mama fa ta fadamin kun hadu dazu a rumfa college " "Shakka babu" "Ok sai anjima ,nizan shiga daga ciki"sulaiman ya fada. "Nagode sai anjima "na amsa masa. "Nasir! Kasan kuwa farida tana kano? Domin jiya sai da nakara haduwa da ita ,a nafisatau fashion dake nan kofar nasarawa. Kuma shakka babu. Bani kadai nake ganintaba ,jama'a da yawa suna ganinta ,kawai dai don basu san tabane " Nafada Shuraih Usman "Habib wannan al'amari yana da matukar mamaki da rikitarwa. Ni kaina idan na tsaya nayi tunani,sai zuciyata ta cika da al'ajabi. Ni dai nasan farida ta mutu,kuma inhar mutum ya mutu ,shakka babu tasa takare . Kuma gashi kai kana haduwa da farida ,abinda yafi mamaki ma ai dole kwalkwalwa da zuciya suyi" Cikin matukar mamki yafada . "Kasan abin dayafi dagula min lissafi nasir? Farida ba aljana bace ,kamar yadda masana SIRRINSU suka sanar dani. Dole idan aljani ya rikida asiffar mutum ,sai ansami alamun daza su tona masa asiri cewar ba mutum bane . Na ga farida har sau hudu,kuma shakka babu ,babu wata alama a jikinta da bata dace da mutane ba". Kuma babu yadda za'ayi aljani yarinka bayyana a bainar jama'a yana hulda dasu . Duk ganin da nake yiwa farida acikin jama'a nake ganinta ". Nasir yayi shiru na wasu lokuta ,nikaina na san tunani ne ke birkita kwalkwarsa. "To shin habib idan wacce kake gani ba aljana bace ,kana nufin farida kake gani, wacce muka binne kuma wacece?" Shuraih Usman "Nikaina wadannan tambayoyin ina matukar kwadayin amsoshinsu"cikin sanyin jikinafada. "To ai sani zaka sake nema daga masana akan SIRRINSU" "Shakka babu,ina ganin abinyi kenan" Bayan mun tattauna akan wannan da waccan,sai naga yadace nakoma . "Habib ,zaka halarci wasan Camerou da England kuwa" "Shakka babu , na kauracewa halartar kowanne kallon wasa,don matukar tsoron haduwa da farida" Ya dan kalli fuskata ,kallon dana so nasan abin da yake nufi. "Ba mamaki kaima kuhadu da ita acan" Nafada ina kallon fuskarsa,bai yi magana ba amma yanayin fuskarsa na nufin shakka babu da mamaki. Shuraih Usman A daidai wannan lokaci sai zuciyata takara kadawa sabida ganin meenat sanye da atamfa,riga da zani ruwan madara,ta nufo in da muke . A wannnan lokaci dana ganta sai dana tsorata ,a tunanina farida ce ta rikida takoma karama ,domin idan ka san farida,kana ganin meenat ka ga kanwar farida. Ta na zuwa ta rakabu da jikin nasir,tana kallon fuskata. "Habib ! Ko zan sami kasa-kasan fim din hausa a wajenka?" Nasir ya bukata. "Shakka babu,amma sai dai a gida ,idan kanaso zamu iya zuwa" Dani dashi da meenat muka nufi Gandun Albasa. "Habib mama ta gayamin wai a kamfanin jaridar dankari kake aiki" "Shakka babu" "A jaridar ne ake buga labarin BABBAR MAGANA ko ? Agaskiya akwai matukar rikitarwa ,da jefa mutane cikin rudani,kuma kagaya yi daidai da abin dake faruwa akanka " "Shakka babu ,maganarka ba musu" Nafada lokacin dana shigar da motar haraban gidan ahmad. "To mene ne dalilin dayasa kai baza ka buga wanda yanzu yake faruwa akanka ba ?" Nasir yafada lokacin da muka fito daga motar. Shuraih Usman "Saboda babu wanda zai yarda da ni" "BABBAR MAGANA ma da farko mene ne jama'a basu fada akansa ba " Har sai lokacin da aka karanta karshen labarin" Bayan munci abinci saina bashi MUNKAR da TSUNTSU MAI WAYO da kuma SAI DAI MUTUWA. "Baka da NAIRA DA KWABO?' Yabukata "Wallahi bani da shi nasir ,sai dai nahada ma da littafin SAI DAI MUTUWA da kuma WUYA BA TA KISA" Fatima na ganin meenat tace kanwar faridace,haka ma faruk(BBJJ) da bala Barde,muna fitowa zamu tafi suka ce meenat kanwar faridace . Abokaina ne kuma sunga hotonta a wajena . SIRRINSU Littafina daya Chapter 14 By♥ Shuraih Usman Abin mamaki da rikitarwa ya farune adaidai KANO LINE a kan hanyarmu ta komawa tarauni don kaisu nasir gida. Kwata-kwata nasha'afa babu wadataccen mai amotar ,kawai sai ga ni nayi malejin mai nayin nuni cewar mai yakare ,yayin da motar ta tsaya . A lokacin karfe biyu da rabi,ina sauri na kai su nasir gida don ganin wasn England da yake da niyyar zuwa. Sanin cewar akwai 'yan cuwa-cuwa a diga ,sai muka nufi can don sayowa ,nasir rike da hannun meenat. "NASIR ! NASIR !! KAGA ! KAGA !! Arazane meenat ta rinka fada ,tana nuna wata mota kirar volvo da mata biyu keciki. ""FARIDA ! FARIDAAAAAA......" Shima Nasir arazane ya rinka fada ,idanuwansa sun zazzaro ,farida ce ke tuka motar,kodaddiyar matar agefenta kuma titin sabo bakin zuwo suka nufa ,inda muma zamu. Lokacin danayi kokarin duba lambar motar,zundumemiyar harafin "L" ne a makale. Shakka babu meenat da nasir sunyi matukar razanar da tunda suka shaki iskar duniya basu taba razana fiye da haka ba. Shuraih Usman Cikin gaggawa jikina na rawa ,na tsayar da wata taksi babu kowa aciki . Don kada ya bata mana lokaci nazaro damin kudi na bashi, na nuna masa motar ta fara nisa ,nace duk inda tayi yabita . Na saka meenat wadda duk ta fice daga hayyacinta a motar ,sannan shima nasir afirgice na kama hannunsa muka shiga motar. Cikin zumudin da na ba shi ,direban ya zaburi motar cikin matsanancin gudu. A daidai lokacin da muka isa garesu ,sai motar ta shiga matan fada road,kuma adaidai lokacin danja ta tsayar da mu. Cikin matsananciyar gaggawa direban ya kutsa kan motarsa, GARAM!!! Yakade wani dan acaba da zai gifta ,dana duba motarsu farida sun bace. "Shit!" Na fada lokacin dana daki kan motar. A ranar kallon wasan da nasir bayyiba kenan sai da aka masu allurar bacci sannan suka sami nutsuwa. (Lol sun karyata sun ga zahiri) Duk da ina kara razane,sai son farida yadada karuwa a zuciyata .shakka babu ina matukar sonta. Shuraih Usman H JUMA'A 9 ~ 3~ '99 Juma'a babbar rana , wannan juma'ar shakka babu ,koda wani bata zama babbar rana agareshi ba ,a wajen Al'ummar kasar Nigar babbace . Domin da sanyin safiyar juma'arne ,shugaban kasarsu BA'ARE MAINASARA, ya koma ga mahaliccinsa . Sakamakon ruwan harsashi daya fuskanta daga jami'an tsaronsa. Fantsamuwar labarin a duniya keda wuya ,Ahmad yaga muma yadace musamawa jaridar DANKARI kanun labaran tun da dumiminsa. An katse gidajen rediyo,an hana jirage tashi a kasar Nijar, wanda hakan na nufin dole muyi amfani da mota idan muna bukatar shiga kasar. Kada ka dauka mun samu shiga kasar cikin sauki,bayan nune-nunen shaidar cewar mu ma'aikatan jarida ne ,saida wasu kudade daga aljihunmu sukayi balaguro zuwa ga aljihun masu tsaron boda. Shuraih Usman Bayan munyi yanzirga zirga nan da can ,mun kalato abin da muka dawo kasar Nigeria . Duk da cewar Ahmad yayi tukin motar , jikina ya samu wadatacciyar gajiya . Karfe hudu da mintuna takwas,muna cikin birnin dabo a wannan lokaci rana tafara sanyi sai dai babu wani alamar sanyi a zuciyata da kwalkwalwata . Har muka je Nijar muka dawo,zuciyata taf take da tunanin farida ,da kuma tunanin halin da meenat da nasir suka shiga . A wani bangaren zuciyata na so faruwar hakan saboda shakka babu Nasir,da meenat da kuma mahifiyansu za su fi gaskata al'amarin,domin gani ya kori ji. Bayan nayi sallah naci abinci wanka yabiyo baya bansan lokacin dana zurfafa a zuzzurfan kogin bacci ba . Ba don fatima ta tasheni ba, daban san lokacin farkawata ba . Saboda wadataccen baccin danasamu darana ,da daddare sai barci yayi hijira daga idanuwana. Karfe tara daidai naji ina matukar sha'awar fita yawan shakatawa,SULJAM PALACE shine wajen da kai tsaye yayi ungulu a zuciyata. Shuraih Usman Sai dai da nasan akwai mummunan al'amarin da zai sake faruwa akaina dana hakura . Sai bayan dana samu wasu lokuta zaune wajen su nasir ,don ganin halin da suke ciki. Ina fitowa da niyyar tafiya tarauni ,sai ma'aikacin wajen ya zaburo a guje yagaya min wai wasu mata na kirana a ciki. "Wasu mata?" Na rinka maimaitawa har lokacin dayanuna min inda suke zaune . Sannu a hankali zuciyata na mamakin kiran na karasa inda suke. "Wa nake gani kamar habib ?"Daya daga cikin mata uku dake wajen ta tambaya. "Idan dai ba wanine yayi kamama dani ba ina ganin shakka babu nine "na fada lokacin dana fahimci raqeebah da saratu da kuma jameelah ne ,dukkaninsu 'yan unguwarmu ne . "Dama kana zuwa irin wadannan wuraren?" Saratu ta bukata ,lokacin data kurbi tataccen lemu. "Ku yakamata nayi wa wannan tambayar " nafada. Lokacin dana zauna kusa da su raqeebah. Shuraih Usman "Saboda me kafadi haka ?" "Saboda da namiji yana da yancin irin wadannan wuraren musamman ga irinmu marasa aure ,amma ga mace ziyartar gidajen kawayenta zaifi mata martaba akan irin wadannan wuraren" "Kiji son kai" jamila tafada . "Wato ku maza ku zo ku nemi mata koh? Mukuma mata mutafi gidajen kawayenmu?kana nufin kenan mu muje muyi soyayya atsakaninmu ko? To waye baya son hutu ! Koda dutse aka halicci mata ?"(Kujifa yan'uwa) Dukkaninsu sai suka kyalkyale da dariya . " Baki fahimci abin danake nufi ba ,ina nufin kamar yadda yake al'ada ,idan har akaga namiji a irin wadannan wuraren,kawai ana daukarsa mai neman matan banza. Koda kuwa ba hakan ne ya kawoshi ba .to ina ga mace ?da zarar an ganta cewa za'ayi 'yar harkace ma'ana mazinaciya ce" Shuraih Usman Wannan hirarce ta jawo mana musun da ya sha'afar dani harsai dana fahimci daya da rabi na dare ,sannan hankalina ya tashi ,banzo da abin hawaba . Nafito cikin hanzari ina tunananin komawa gida ,sai motar da muka gansu jiya aciki VOLVO,haryanzu zundumemyar harafin "L" din na makale ,suka gifta ta daya bangaren titin. "Farida !"A kidime na kwala mata kira ,sai dana kirata na fahimci gaba dayan gilasan motar arufe suke ,ina rufe bakina sai dan-acaba ya bayyana . Kamar yadda nayi wadan taksi,shima sai naba shi kudi ban san nawa bane , na sanar dashi yabi dukinda motar tayi. SIRRINSU Littafina daya Chapter 15 By♥ Shuraih Usman Hikimar yin hakan zaka ga kasamu biyan bukata da wuri ,don kada a bata lokaci wajen tsadancewa ,sannan idan da zargi a zukatansu,kudin zaiyi saurin fatattakarsa. Ratar dake tsakaninmu bata da yawa sosai ,kasancewar babur dinsa Yana da ingancin inji ,sannan Kuma farida ba gudu take sosai ba. Babu abinda yayi saurin bani mamaki ,irin yadda na gane su farida nan da nan. Suna zuwa wajen wasu yansanda dake tsattsaye kan titi ,mummunar matar ta mika musu kudi ,suka Kuma kyale su suka wuce. Don gudun kada muma su batamana lokaci ,tun kafin mu karasa na zaro kudi ,muna zuwa wajensu na mika musu muma suka kyale mu muka wuce. Haka muka yitayi,duk yansandan da msuka taremu sai mun basu kudi , Har sai da motar su farida ta shiga harabar VILLA GUEST INN . Kai tsaye na umarci dan-acaban, shima ya shiga ciki. Cikin sauri Dan acaban yafice daga wajen bayan na sauka ,don gudun kada nabukaci ,wasu daga kudin Dana bashi. Sai da mummunar matar ta fito daga motar ,sannan na fahimci a matukar buge take . Ganin yadda take tangadi, har sai da farida ta rika taimakamata. Suna shiga reception din, ma'aikacin wajen ya mika wa farida makulli ,wanda na nufin makullin dakin da suke ne. Nayi sauri na zaro kudi daga aljihuna ,nanufi inda yake. Shuraih Usman "wannan kyakyawar yarinyar nakeso ,Kuma na tsara ta yarda ,Amma wannan matar da suke tare ta kawo mana cikas .lambar dakinsu zaka gaya min" Nafada lokacin Dana mika masa kudin . Kafin na san me yayi tuni ya rarume kudin daga hannuna ,kamar yadda kadangare ke yiwa kuda cafkar bazata . "No. 11, dakin dake fuskantar yamma ,daga hannun damanka " Ga mamakisa sai yaga na fice daga wajen ,har na fito Yana lekena .nasamu dogon lokaci ina tsaye ina tunani. "shin menene hadin farida da wannnan mummunar mata ? Nasir yabani tabbacin basu da wata yar'uwa datayi kama da wannan matar ,kai kanta kallo daya zaka yi wa matar kasan babu abin da ya hada ta da farida . Ganin farida danakeyi kullum Akano ya tabbatarmin suna Kano . Abin tambayar shine ,shin akwai wajen dasuke zaune musamman ? Kokuwa tun farko anan Villa guest inn din suke ? Wannnan tamabayar ma'aikacin yadace nayiwa. Banyi mamaki Dana tambayeshi yace yaune zuwansu na farko ba . Kuma sannan kudin kwana daya kawai suka biya ba. Motocin dasuke shiga ina suke samunsu ?farida ta mutu, Kuma kullun suna tare da wannan matar. shakka babu akwai wani kullallen al'amari tattare da matar nan .domin kana ganin matar ,kasan ba mutuniyar kirki bace ,yanzuma ba acikin Maye nagantaba? Shuraih Usman Kuma kana ganin farida kasan bata yi kama da mutuniyar banzaba . Wani bangare na zuciyata ya shawarceni da kai tsaye na wuce wajen yansanda na sanar dasu cewar ,ina zargin wannan matar da sace farida . Tun da iyayenta da kannenta na Kano . Kuma zasu gane yarsu ,tunda dama sunganta sun ganeta ,shiken sai azo acafke matar . Daga nan Sai a sani shin faridar data mutuce kokuwa ? Wani bangare na zuciyata ya bijirewa wannan shawara da cewa na fara sanar da mahaifiyarta . Mu zo mu kama . Sai mu tuntubi hukuma . Kuma da wannan shawarar na yarda , nayi ta jiran Dan-acaba . Har sai Dana fitar da rai da samu Shuraih Usman A daidai lokacin da tsinken agogona ya tsaya akan biyu da minti dudun dare ,saina hangi hasken fitila na nufo ni, sai daya kusa zuwa na fahimci babur ne . Babu Irin daga masa hannun da banyiba ,don ya tsaya ammma ko alamar tsayawa bai yi ba . Inda Allah ya taimakeni sai a she sabi'u ne da muke kira [lastman]. A wajensa ne muke sayen katin duk wani wasan kwallon kafar da ake gudanarwa indai anan Kano ne. "lastman!lastman!! Na rinka zunduma masa kira har sai da jiyo sannan ya Dan tsaya . Abin daya sana tsayar da shi ,na sani sani sokoto road yake , tun dani tarauni zanje sai na yi farincikin hakan . Komai dare komai dare nayi niyyar sanar da mahaifiyar farida inda farida take . Don gudun kada na tafi gida kaddara tasa na makara ,kafin naje tarauni su Kuma su kama gabansu "Dan Allah wasu muhimman takardu ne na manta su a tarauni ,Kuma a Daren nan ake bukatarsu ,ka taimaka ka ajiye ni a nan sokoto road din sai na karasa" Na yi masa karyane don gudun kada ya cikani ta tambayoyin me zan je yi atarauni?bayan ya san unguwarmu . Shuraih Usman 'bawani abu hau mu je " Yafada kafin yarufe bakinsa na dare Vespa din, Saboda ,matukar kaguwa Dana yi ,na ganni a tarauni. Har muka zo sokoto road bamu sokoto road bamau hadu da yansanda ko daya ba . "tarauni wajen ina zaka ?"ya tambayeni. "kasaukeni anan na karasa" Ba wani abu na karasa dakai " "masallacin juma'a na tarauni zani" nafada. ya ajiyeni adaidai masallacin sannnan ya juya . "nagode " nafada . "bawani abu ,Allah ya bamu alkhairi." Banda haushin karnuka da ke tasowa nan da can , babu wani sauran motsi da kunnena ke iya ji . Dayake na gane hanyar da muka bi jiya da sulaiman ,sai na bi har kofar gidan . Koda irin 'yan tauran dake yawon dare , ban gani a layinba ,kowa ya garkame kofar gidansa,kamar har abada bazasu kara budewa ba . Nayi ta faman kwankwasa kofar gidan har na gaji ,in da kasan kofar makabarta nake kwankwasawa, babu wani motsi da ya biyo baya .ganin haka sai na hakura ,da niyyae zuwa bakin titi na samu babur na koma gida, nayi matukar kokari na dawo da asubah. Ina zuwa daidai masallacin juma'a .sai wata bakar Peugeout ta tsaya a gabana ,tun kafin su fito na fahimci......................................... SIRRINSU Littafina daya Chapter 16 By♥ Shuraih Usman Ina zuwa daidai masallacin juma'a .sai wata bakar Peugeout ta tsaya a gabana ,tun kafin su fito na fahimci ,yansanda ne ,Kuma nayi matukar bakin cikin manta I.D. CARD dina a gida . Subiyu ne a motar , mai kakin 'yansanda ajikinsa shine ke tuka motar ,fari kakkaura mai gashin baki . Nakusa da shi Kuma baki kakkaura Mara gashin baki,sanye da fararen kaya. "hey !daga ina ! Zaka ina a wannan tsohon Daren?" Kafin na amsa masa tambayoyin da yayi min, bakin ya fito ya cafi kuguna . "shegiya ! Barawo ,sata zata " yafada lokacin da yake kokarin turani motar . "officer" nafada ,ina son yimusu bayani. "close your goddam mouth" bakin yakara zunduma min tsawa a sukwane ,lokacin Dana shiga motar . "in banda barawo , me mutum yake a waje har yanzu bai kwanta ba ? " Dansandan mai kaki ya fada , wanda sai daga baya na fahimci ashe D.P.O ne . Shuraih Usman Ni dai bance musu komai BA ,kawai ni dai abin daya dameni, kada su farida su kubuce min . Yanzu idan aka kulle ni kafin mana fiti kawai su farida sun min adabo. Kai tsaye D.P.O ya nufi kasuwar tarauni kamar akwai abinda yake nema ,ya zazzagaya kasuwar , sannan ya tuka muka hau titin maiduguri, kana ahankali ya gangara da motar muka shiga layin farko na kusa da lambun tarauni. Ya tsayar da Motar a daidai shagon wani gida ,da wani saurayi sanye da gajeren wando ke shan sigari. D.P.O na fitowa saurayin na fahimta dan sandane .YIP " yafada shagon a tsorace tamkar wanda yaga mutuwarsa . D.P.On bai tsaya bata lokaci BA yabi bayansa, yayin da dayan ya fito daga motar ya tsaya Yana gadina . Babu yadda D.P.On bai yiba don Yafito da saurayin Amma abin ya faskara . Sai ya fito bakin kofa ya umarci dayan ya shiga ya fito da shi. Shuraih Usman Bayan ya shiga , sainaga kwata-kwata hankalin D.P.On ya tattara akan shagon, sakamakon bololon da saurayin keyi. "baba! jamilu ! Wayyo niba barawo bane " Kai idan kaji burarin dayake cikin tsakar dare ,sai ka zata ana kai shi harbe shi za'ayi. Sannan a hankali jikina na rawa , Na bude motar na rufa aguje kamar zantashi Sama . Na sami dogon lokaci ina gudu , sannan na hango hasken fitilar motar na haske min gaba . Nayi matukar gajiya , zuciyata kamar ta faso kirjina ta fado ,sannan tsabar haki yariga ya gama da ni ,Kuma nasan idan har suka kama ni hukuncina sai yafi da tsananta . Saboda babu abin da 'yansanda suka tsana irin su kamaka ka Kuma gudu. Da kyar na sha wata kwana kamar zan kife , ina shiga kwanar dabara tazo min nashiga cikin wani katon tanki dake ajiye kofar wani gida . Sai Dana shiga na fahimci shara ake zubawa a cikin . Sun dade suna zazzagaya unguwar don nemana ,ni kuwa ina cikin tankin gabana na dakan sittin sittin , hankalinsu bai zo gareni Ba. Sai dana tabbatar babu wani sauran motsi dA kunnena ke iya ji, sannan jikina manne da shara na fito, gabana na faduwa . Na fara 'yar tafiya kenan ban yi tunanin ,shin yanzu takamaiman ina. Zani ba , sai na kara hango hasken mota na nufo inda nake banyi tunanin kara komawa cikin tankin dana fito ba ,na kara rufawa aguje . Ina dada gudu gunjin motar na kara kusantoni,har sai lokacin dana zo. titin makarantar sekamdiren tarauni. Sai da motar ta gifta ni, sannan na fahimci honda,ce kuma wani mutum ne shi kadai a ciki. Duk da haka ban tsaya ba sai lokacin dana kai daidai gindin gawo ,ina kokarin tsayawa sai nayi tintiben daya wuntsilar dani har kasa. Shakka babu, naji matukar zafin buguwar da kaina yayi. Kamar ajiyeta aka yi a gabana ,sai ganin motar,sai ganin motar nayi ta tsaya , har 'yansanda hudu sun fito daga motar kowannen su rike da bindigarsa ahannunsa. Ka-ka-ka-Kaf! Karaf !" Shuraih Usman Naji bindigogin sunyi shirin yin ta'addanci,sannan suka cuccuna minsu akaina da bayana . Da kyar na dago kaina motar ,zuciyata takasa tuna komai saboda tsoro. Inter-state-Anti-crime-patrol. Abin dake rubuce kenan ajikin motar, can. Sai naji wata murya kaman na taba jinta tace. "Don't move ,you are under arrest" Babu yadda zanyi kawai sai narufe idanuwana ,jikina kamar ba laka na koma na kwanta ,shakka babu na kamu. 'Ka daka aiwatar da wani yunkuri da zai iya kai ka ga halaka ,ko kuma ya cutar da rayuwarka " Na tuno da gargadin da mahaifiyata tayi min. Anan muka kawo karshen Book 1 sai kun jini a book 2 mai taken MUN-JI-MUN-GANI Authour: Maje~el~hajeej Hotoro ( ya hajeej) Written: Shuraih 99% Shekarar bugu : 1999 Post by: Shuraih 99% An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels