*Muhammad kabir* Documentation workshop 08160112181 *ZUCIYA* _kowa da irin tasa_ © *NA AYUSHER MUHD* 1⃣ Duk yanda yaso ya taka burki abun ya gagara gashi a kan gada yake sannan ga motoci na wucewa, cikin rikicewa ya zuro da hannunsa ta window yanawa mutane alamar su matsa akwai matsala, wasu sun fahimceshi wasu kuwa basusan ma me yake nufi ba, wani yaro ya gani ya taho gadan gadan yana kokarin tsallake titi horn ya shiga yima yaran hakan yasa yaran ya kalli motar sai dai kasancewar yarone karami kawai sai duk ya daburce ya rasa ina zai nufa tsoro yasa shi ya karkata kan motar wanda tsautsayi yasa ya afka cikin kokin jikake tim mota ta fada ciki nan fa mutane suka taru dan neman yanda za'ai sai dai inaa mota tuni ta tafi can kasan koki, rukicewa yai ganin motar ta cika taf da ruwa, shi kanshi duk ruwa ya fara cikamai baki nan ya fara kokarin fitowa ta glass din motar wanda yai sa'a a bud'e yake, dakyar ya fito sai dai yana fitowa yaji ya bugi wani abu wanda baisan menene ba ga ruwa ya shakka dayawa wanda yasa ya suma..... _A Rigar Datti_ Nafi ta d'ago ta kalli mahaifinta wanda yasata a gaba yana zabga mata masifa cikin yarensu na fulani tace " Baffa kayi hakuri wlh ni bansan ya akai kajin nan suka faracin geron nan ba." Wanda ta kira da Baffa wato mahaifinta cikin tsananin masifa yace " kedai wannan yarinya baki da mutunci dan tsabar wulakanci da asarar abinci har kaza ta samu matsayin cimin gero na? Wanda nine nake wahalar neman kayana bake ba bakuma waccan balagazazziyar uwar taki ba wacce ta d'au kaninki ko kunya ta saida saniya ta ta had'a ta tafi wai saudiya yin takaranci ba? Ni dai wannan masifa ta faru ne tunda na auri waccan tambad'ad'iyar uwar taki wacce ban tambatar da tsatson ta ba." Nafi ta share kwallar ta tace " Baffa kayi hakuri nasan inna taba kyau...." "Gafaracan ni munafuka yimin shiru ai kinji a sara nayi mamakin da zata gudu menene dalilinta na barinki tadau namiji yanzu da alama na fara fahimta." Ya maida numfashi sannan ya cigaba " kidahumar banza kidahumar wofi to wallahi a hir d'inki da min almubazaranci." Yana kainan yai waje a fusace, hawaye ta share sannan ta mike ta d'au kwarya ta tafi garken shannun baffa dan yin tatsa. Tana yi tana 'yan wakenta na fulani, kasan zuciyarta kuwa takaicin tafiyar uwarta da kaninta take sun barta ita kadai a wannan rigar tasu ko tausayinta basayi. Kasancewar Mahaifinta mutum ne mai bala'in gaske in nace bala'i to fa lalai ina nufin bala'i baya ganin mutuncin komai a rayuwarsa banda na dukiyarsa ko da wasa wani ya tab'amai dabba to fa lalai ya shiga uku, saboda tsabar masifarsar ne yasa ya bar cikin mutane ya dawo can gefen kogi ya dasa nasa gidan wanda ake kira da rigar Datti. *Dattin* sunan mahaifin Nafi kenan, Mahaifiyar Nafi ba karamin hakuri tai da Datti ba, auren soyayya sukai sai dai kasancewar ita ba bafulatana bace (Kad'o suke kiran hausawa.)ta samu kalubale da dama gun danginsa, har sukazo suka hakura saboda tsantsar mutuncin ta wanda ya ninka na d'an nasu. Duk yawan shanu da kaji da zabi irin na datti ko da wasa bazakaga an yi abinci mai mutunci agidanba bare har akai da zancen yanka kaxa, koda kuwa ciwo zai kama ta, ya gwammace ya d'au dabbar dabatada lafiya ya fita ya siyar, girkinsu dai baya wuce abin gero ko dawa dan ko shinkafa ba bari yake a ci ba. Iya tsananin hakuri Matarsa tayi dashi ganin bazai tab'a canzawa ba haushi ya kamata ta d'au saniyarsa ta saida ta kuma dauke karamin danta kanin nafi ta gudu dashi Saudiya inda 'yar uwarta take da zama tana kasuwanci (Takaru). Samari da dama suna san Nafi dan in taje Talla cikin gari abin shawa duk da ba kaya dayawa gareta ba sai dai zakaga kayanta kullum tsaf tsaf gata ba laifi tanada kyau. Duk yanda samari suka kai ga santa babu mai iya tunkarar ta dan kowa na tsoron hada zuri'a da Datti acewarsu duk wanda ya aureta sai dai yai kayan daki da kansa sannan har cikin gidansa Datti zai dinga zuwa yana zazzaga masifa. Nafi kam haka nan take zaune da mahaifinta a rana duk shiga da fitar da zaiyi da masifar dazai mata. ****** Ajiyar zuciya Nafi tai a sanda ta gama yin tatsar, ta mike ta dau bokitin tai cikin gida. Tana ajiyewa a ciki ta dau wani bokitin dan d'eboma dabobi ruwa da kuka daura sanwar dare. Tad'anyi tafiya kadan ta isa babban kogi wanda ke bayan gidansu kadan, kallan katon kogin tai yau sam ba kowa ko fulanuwa masu kiwo da suke tsayawa ba dabobinsu ruwa yau basanan, tadanyi tsaki kadan cikin yaransu na filo tace " yau dai da alama banida sa'a ko mutanen da muke 'yar hira dasu wani sa'in ban tarar ba." Takarasa maganar tareda gangarawa kasan Kogin. Zama tai adan bakin kogin tasa kafafuwanta acikin ruwar tanadan bubugasu kadan waka take dan yi tana murmushi ita kadai, rayuwarsu da mahaufiyarta da kaninta Gaddafi take tunowa. Ganin rana na neman faduwa yasa ta mike tadau d'an karamin kokonta ta shiga deban ruwan tana zubawa a bokiti, ta dau bokitinta da niyyar tafiya daga d'an gefe inda ruwa ke korowa taga kamar takalmi, mamaki ya kamata can kuma tadan girgiza kai kadan tace " Oh ni Nafi yanzu kila wani bafulatanin ne ya manta da Takalminsa, ba mamaki gobe yazo yai ta neman inda yake." Karasawa tai kusa da takalmin tana cewa " bari ni in dauka tunda akusa nake sai in ajiye gobe na fito in rataye musus ko a bishiya ne." Mamakinta ya tsaya ca a sanda tasa hannu dan ciro takalmi sannan a daidai lokacin ruwa ya koro sannan ya koma hakan ya bata damar ganin ashe kafa ce ta mutum kwance a cikin ruwa. Da sauri ta saki ta kalmin sannan ta kurma wanu ihu mai kara wanda ruwan sai daya amsa, sai dai abin haushi babu kowa agun, idanunta a runtse suke tam ta had'a hannayenta biyu alamar roko tana cewa " Yahkuri Aljanin ruwa wallahi Allah bansan kai bane kake hutawa, natuba kwai ka yafemin wallahi ba ruwana ba kuma zan sake ba." Tana gama rokonta na shirme ta dan bud'e ido daya cikin tsananin tsoro sai dai yananan a yanda ta barshi, baya ta danyi tana cewa " Kayi hakuri dan Allag ka koma makwancinka in ma fatalwa ne ni wallahi ba ruwana da kai." Nan ma tad'an sake kyalla ido kadan, sai dai yananan a inda yake, dabarace ta fado mata akan lale ta mike ta falfala da gudu hakan zai fi mata sauki, juyawa tai ta ga lalai fa ba kowa ai kuwa da wayau ta tattare zaninta ta juya tai baya a guje kai kace Zaki ne ya biyota ko bokitin ruwan bata tuna dashi ba. Gida ta nufa da uban gudunta, tana shiga ta shiga yin haki na tsabar tsoro, Datti dake tsaye a tsakar gida ya kalleta cikin takaici yace " To dabba da alama kema bakida maraba da tinkiya meye hakan kuma?" A tsorace ta daidaita tsayuwarta tace " Baffa aljani na....." Yace kiga abinda yafi aljani ma makaryaciyar banza da wofi dan tsabar iskanci dama ba ruwa kika tafi debowa ba? Ai kin sani sarai dabobbi ba ruwa a gunsu." Sai a lokacin ta tuna da abinda ta fita yi cikin sanyin jiki ta fita, tana tafi tana dan share kwallarta aganinta ya kamata mahaifinta yaji a wani hali take ciki. Da komawarta idanunta suka sake dira kan wannan mutumin, har ta dau ruwanta zata tafi wata zuciyar tace "Yanzu Nafi in mutum ne fa ya fada ruwa?" Da sauri ta kara kallan gun, tsoro ne fal a ranta, addu'a ta shiga yi tana takawa a hankali idanunta kuma a rufe wai ita a dole so take inta isa idanun nata na rufe zata zare mai takalma ta gani ko da kafafu. Haka tai ta tafiya idanu a rufe jitai ta yi tuntube kafarta ta harde saboda tsoro jikake tim ta fada kan wani abu, bata San sanda ta bud'e idanunta ba cikin tsoro ta kalli inda ta fada, itadai tasan lalai akan abu ta fada hakan yasa ta kallin kasa, ganinta kwance akan mutum yasa ta kara calla wani kara mai sauti...... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _kowa da irin tasa_ © *NA AYUSHER MUHD* 2⃣ Kanta ta sake cusawa kan mutumin duk ta rikice, can ta tuna inda tasa kanta hakan yasa ta mike da sauri, jikinta na rawa, sai dai a wannan lokacin tsoronta yadan ragu ba kamar da ba. Hannu tasa ta zare takalmi mai saucikin dake kafarsa, sannan ta zare safar kafa ta gani kamar ta mutum sai kuma tausayin wanda ke kwance ya kamata, hannunsa ta kamo ta shiga kokarin jawoshi daga cikin ruwan, da kyar da nishi ta samu tadan jawoshi kadan, nan fa ta shiga kokarin murgunashi, nan ma da kyar da numfarfashi ta samu ta juyashi, tsugunawa tai a gabansa tana kallanshi. Tsoro ta fara ji kardai ya mutu? Nan tasa hannunta a sai tin hancinsa ta dan dade kadan jin baya numfashi yasa tsoro ya kara kamata, idanunta suka fara tara kwalla, hannunta tasa a saitin zuciyarsa, dariya ce ta bayanna a fuskarta a lokacin dataji bugun zuciyarsa. Ta rufe fuskarta alamar kunya tace " Da ranta wallahi." Ta sake yin dariya tace " Wlh da ranta Allah da gaske." Ta sake dariya. Fuskarta ta zuro daf da tashi tana kallo, ba fari bane sannan kuma ba baki bane yanada kyau, hancinsa dogone, ta d'an yi murmushi sannan ta kalli kayansa tace " Kad'o ne wannan kam, sannan da alama bama dan nan garin bane daga birni yake." Baki tad'an turo kadan ganin ita kadai take maganarta sannan ta shiga tunanin yanda zatai ta dawo da numfashinsa. Hannu tasa ta shiga danna mai kirji tana san ruwan daya shakka ya futo, sai dai ina, ya shaka da yawa duk yanda ta zake tana dannawa ba alamar motsi a tattare dashi. Idanunta ne suka ciciko, ta kalleshi tace " Dan Birni ya zanyi?" Ga ba kowa a gun, ta kafeshi da ido tana kallo jitake kamar tai ihu, tunawa tai sanda wasu fulanuwa suka ciro wani yaro daya fada ruwa kwanaki, tana kallo bayan sun danna mai kirji bai farfado ba sai wanda ya danna mai kirjin yasa bakinsa a nasa ya huramai iska alokacin mutane sukai ta ce masa dan iska, babar yaran tazo ta kwace danta itama tana masifa. A hankali ta matso itama da shirin kai bakinta, sai kuma ta tsaya ta kalleshi tace " Dan Birni ba iskanci zan maka ba kawai iska zan hurama, kaji? inka warke xan baka hakuri." Nan ta sa bakinta cikin nasa ta shiga huramai iska iyakar karfinta, sai datai tayi sannan can sai yadanyi tari sai ga ruwa dayawa ya zubo daga bakinsa, idanunsa ya bude a hankali ya kalleta, ta kifkiftamai ido tace " Hannu? Kin ganni?" Gani tai ya maida idanunsa ya rufe, sai dai yanzu numfashinsa na fita sai dai dad'an sauri yake fita, tai shiru tace " ya zanyi? Bacci yake? Ga dare nayi?" Jijigashi ta shiga yi tana cewa " Karkiyi bacci anan dan Allah kiyi hakuri ki tashi." Sam bataga alamar motsi a tattare dashi ba, ga gari ya fara rufewa, da sauri ta mike ta suri bokitin ruwanta ta nufi gida, tana shiga ta waiga taga bataga Baffa ba, ajiye ruwan tai ta karasa gun dabobbi ta dauko baro ta fito da sauri. Inda ta barshi anan yake babu alamun ya motsa, nan fa ta shiga kokarin d'orashi akan baron, sai dai ina.....sam ta kasa. Duk wani karfi datake tunanin tanadashi ta sake akan mutumin sai dai daga ta dagoshi sai su fad'i tare, saboda rinjayarta dayake yi, duk su biyon sunyu butu butu dasu da jikakkiyar kasa, banda numfashin wahala ba abinda takeyi, ga duhu ya kawo kai, nan ta cigaba da gwadawa, dakyar da sid'in goshin wahala ta samu ta d'aurashi, tana daurashi hannunta ya kume ajikin baron. Kara tad'anyi saboda zafin dataji, sai dai tsoron rafin ta keyi dan duhu ya fara rufewa, da sauri ta shiga tura baron, sai dai dakyar shima take turawa kasancewar ba siminti bane ko kwalta a gun, iya wahala Nafi taji a wannan lokacin, har ta samu ta isa gida, tai sa'a baffa na kewaye (ban d'aki ) hakan yasa ta tura baron zuwa d'akinta tasani sarai mahaifinta ko wani ne zai mutu bazai taba yanda a kawoshi gidanshi ba koda kuwa dan uwansa ne bare wannan dabatasan inda ya fito ba. Can gefen dakinta ta sa tabirmar datake kwanciya a kai ta shimfida zannuwa guda uku sannan ta shiga kokarin saukeshi, wannan karan batasha wahala sosai ba sai dai shi yadan kumu da bango garin saukeshi. Nan tasamai pillow ta kwantar dashi, itama nan ta zube ta kwanta dan tasha bakar wahala. Batai minti 3 a kwance ba taji muryar Baffa yana kwalla mata kira " Ke Nafi kina inane?" Dasauri ta mike ta kara jan labulen dakinta tai waje tace " ganinan Baffa." Yai tsaki yace " Bakida hankali ne zaki d'ebo ruwa baki zubama dabobin ba shinr zaki dangwarar anan? Ko ni kike jira in kai musu?" Kallan ruwan tai tadan yi kasa dakai tace " cikinane yadan murdamin kadan shiyasa......" "Ciki? Zancen banza kenan, dan cikinki ya murd'a sai ki barmin dabobi da kishi ruwa? Sannan ba madai kina nufin bokiti dayan nan kadai kika d'ebo ba ko?" Idanu tadan kifta na mara gaskiya, Datti ya shiga tafa hannu na mamaki yace " Lalai zance kwal ubanki kuwa a gidan nan, banza wacce mahaifiyarta ta gudu da kayan sata, sannan da auranta ta tafi yawan karuwanci." Idanun Nafi ne suka ciciko tai saurin yin kasa da idanunta a hankali tace " kayi hakuri Baffa wlh ba h......" "Billahilazi kika b'atamin rai goben nan sai in nemi wani can in aura miki, ni dama na gaji da ciyar dake abincin da bakisan darajarsa ba." Yanakainan yai waje a zuciye. Tsugunnawa tai agun ta shiga wani irin kuka mai tsuma zuciya, tadade agun kafin taje ta maka alwalarta wacce batasan ko hakan akeyi ba, itadai kawai tasan ana wanke fuska, hannu da kafa, ta mike ta shigo daki tayi dunguren sallarta da batasan me ake cewa ba. Tana idarwa ta matso kusa da dan birni, kansa takai hannunta sai dai da sauri tadauke hannunta jin wani mugun zafi datai, Mikewa tai da sauri tace " Hande inboni!! Karfa kad'on nan ya mutumin adaki in shiga uku?" Dasuri tai waje ta shiga lelekawa, abin haushi a can gefe suke wanda inzakaje rigar kusa dasu sai kayi tafiya mai dan yawa, gashi tana tsoron mahaifinta kar ya dawo yaga ba tannan. Komawa tai ciki, ta nufi d'akin baffa nan ta shiga duba gayayyakin magani ko zataga na zazzabi, tai sa'a kuwa ta samu nan ta sato rigarsa ta fito daga dakin, wuf ta shige d'akin ta. Tofa nan ake yinta gani take jikaken kayan dake jikinsa ne ya jawo mai zazzabin nan, shiyasa ta dauko kayan baffa, to amma taya zata ciremai kayan dake jikinsa ta samai wannan? Tsayuwa tai akansa tai tsuru tsuru da ido tana tunani, maganin ta dauko ta jika a kofi sannan ta matso kusa dashi ta shiga bashi a hankali da cokali, wani yana shiga bakinsa wani kuma zubewa yake. Bayan ta gama ne ta kalleshi cikin kalaar tausayi tace ya zanyi dake? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 3⃣ Duk ta rud'e ta zauna kusa dashi tare da daura hannunta akan goshinsa, tsoro da fargaba ne suka cika mata zuciya jin yanda jikinshi yai zafi dauuu. Yawo ta had'iya sannan tace " bazamuyi ta zama a haka ba d'an birni kiyi hakuri bazan kalleki ba, zan cire miki riga idanuna a rufe, kinji?" Tana fadar haka ta ajiye rigar Baffa a kusa da ita ta matso kusa tare da rufe ido, irin rigarnan mai dogon hannu da kwala ce, sai botir dake jikin rigar daga sama har kasa, nan ta shiga b'allewa idanunta na rufe tana yi tana magana, "yanzu kaga bana kallanka, sannan namaki laifi guda biyu, na farko nasa bakina a naki sannan yanzu ina cire miki rifa, sai dai inaso karki manta wallahi ba asan raina duk nai hakan ba, banaso ne ki mutu kinji?" Tana kainan ta shiga kokarin zare rigar, jin ta kasa zarewa yasa ta manta ta bud'e idanunta kallansa ta shiga yi, sam ta manta, yauce rana ta farko data tab'a kallan jikin namiji dan kaninta tun daya tasa mahaifiyarsu ta raba musu d'aki, ita ba gurin wasan shad'i ake barinta taje ba, nan ne dai tasan maza basa sa riga sai wando, to ita inama take zuwa banda ta mika nono da madara cikin gari inda mahaifinta yake saidawa, dan rashin yadda irin na datti bai yadda ace wani yasai da mai abu sai dai shi dakanshi, nan shago ya bud'e yake saida madara da nonon shanu. Ganin yanda gabanta ke fad'uwa yasa tai saurin rufe idanunta sai dai wannan karan ta guntse bakinta gum, haka tasamai riga sannan ta fito waje da sauri. Sam bata kula da Baffa dake zaune akan tabirma ba, ta tsaya a waje tare da rik'e inda zuciyarta take, a tsaye take kamar gunki, jitai ance " Wato Nafi kin fara zarewa ko?" Dasauri ta kalli inda maganar ta fito, Baffa ta gani a zaune, hannunta ta zare cikin tsoro ta kalleshi tsoru tsuru tace " Baffa.." " Inajiyoki daga d'aki kina magana ke kadai wato zama ke kadai a gida yasa kin fara zarewa ko? " Tai kasa dakai cikin tsoro batace komai ba, baffa yai tsaki sannan ya juya kansa yace " damomin fura insha dare nayi." Cikin rawar murya tace " to Baffa yauma bazamuci abinci ba......" Katseta yai cikin masifa yace " Inkin gaji dashan fura da nono kiyi zuciya kiyi aure, nifa banga dalilin dazaisa yarinya kin kai aure incigaba da ciyar dake ba, sannan haka kawai inada shanaye dayawa bazanje insai abinci ba ah to." Nafi bata amsa ba ta juya dan shiga d'akin dasuke ajiye fura, nan ta debo, ta d'ebo nono a kwarya ta zauna ta dama, itakam yanzu warin nono ma yafara damunta, tunda uwarta tabar kasar nan kullum abincin da suke ci kenan, sam Baffa ya rufe ido ita kuma tasan inya fita shago yana siyan shinkafa yaci amma ita kullum abinda takesha kenan. Tana gamawa ta zubomai a langa ta rufe ta daura ludayi ta kawomai, sannan ta dauki nata tai d'aki, kallan mutumin dake kwance tai, tace " Nasan kaima yunwa kake ji ko?" Matsawa tai ta kara tab'a goshinsa, da zafi har yanzu, nan ta matsa kusa dashi ta dan dagoshi kadan tasa kafarta ta tareshi, ta dinga deban furar data dama tana bashi a hankali da cokali, wani yasha wani ya zube, ganin yadan sha dayawa yasa ta mik'e jiki a sanyaye ta zare zanen data shimfida na saman ta goge mai jikinsa sannan ta dauke numfashinta itama tasha, dan sam batasan sha. Waje ta fito da kwaryar sannan ta koma ciki tare da tura kofarta ta rufe, kusa da mara lafiyar ta koma ta zauna, ta hard'e cinyoyinta kallansa kawai takeyi, sai dai tunaninta nakan mahaifiyarta, a haka har bacci yai awun gaba da ita. Wajen gabanin asuba ya bud'e idanunsa a hankali, yarinya ya gani kwance kusa dashi ta dan dukunkune jiki tana baccinta, kallanta yai sannan ya shiga kallan dakin, mamaki yashiga yi a ina yake hakan? Yadauka ya mutu shikam, Nan ya shiga juye juye, tare da kallan d'akin dakyau "wannan kuma inane hakan?" Gashidai kamar d'aki sai dai gaba daya baisan dame akai rufin dakin ba, sannan ba komai a dakin banda ta birmar dayake kai sai gefe kuma bakko da 'yan samiru, kokarin mik'ewa ya fara sai kuma yaga kamar yarinyar tana neman tashi, dasauri ya maida idanunsa ya rufe. Nafi ta mik'e zaune tare da sa hannu akan goshinsa, murmushi ne ya bayyana a fuskarta jin zazzabin yaragu sosai, ta kalleshi fuskarta dauke da murmushi tace " Zazzabin ya ragu aradu, dan binni ya kamata ka farfado ko na samu in baka hakurin abinda nai maka." Tai kasa dakai tana murmushi tace " kaga sanda na sa bakina a naka a bakin ruwa wannan taimakon ka nai. " Shikam dake kwance jiyai kamar yasa ihu, bakinki? Yamaimaita a ransa, wayyo ni. Tacigaba " sanda kuma na cire maka kaya har tsautsayi yasa na kalleka wannan shine zan baka hakuri, bansan me yasa na kafeka da ido ba. " wayyo na shiga uku, kallon jikina? Ciremin kaya? Inalilahi, hannu wa na fada haka? Ba dai har wando tacire............? Jiyai ya kasa tunanin komai saboda tsoron abinda yake tunani. Nafi ta mike jin mostin baffa tasan yanzu zaice ta tashi tayi tatsar madara, ta mike hartaje kusa da kofa ta juyo tace " kema kina shan madara? " Sai ta juya tana murmushi. Tana fita ya mike zaune da sauri ya duba wandansa, ajiyar zuciya yai a sanda yaga wandansa nannan ya koma ya kwanta yana hakki kamar wanda yai gudu ba shakka ya tsorata kwarai, tunani ya shiga yi ya zaiyi yai alwala yai sallah? Muryar namiji ne ya katseshi yaji yana cewa " ke nafi? Ke Nafi. " Saurin amsawa tai daga garke tace "Baffa ganinan. " Ya kalli inda take yace " Dan gidan ku jiya bance ki karo wa dabobbi ruwa ba?? " Ta dan matso inda yake jiki a sanyaye tace " Baffa naga jiyan dare yayi nasan kuma bazakaso inje rafi dadaddare ba. " " to yar gidan manyan mutane, kin rika sosai wato ina miki magana shine bakiji kunyar maidamin ba ko??" Duk maganar da sukeyi da yarensu sukeyi hakan yasa baisan me suke cewa ba amma tabbas ya fahimci abu daya masifa akema yarinyar, har kasan ransa yaji tausayinta masifa da sanyin safiyar nan? Nafi tai kasa dakai cikin hausarsa mara fita yace " Kin wuce ko kuwa? " Nan ta shigo ta dau kallabinta tai waje, yana kallan yanda take share kwalla dazata fita. Bokiti ta dauka cikin tsoro t nufi rafi, tayi sa'a gari ya fara haske, nan ta shiga debo ruwa sai datai sawu hud'u ta debo na karshen ne taje shiga gida taga maza carko carko a kofar gidan rike da sanda sunata masifa, cikin mamaki ta kallesu sai dai ganin yanda ransu yake a b'ace yasa ta shige gidan sukuku.... Tana juye ruwan ta shige daki dan da alama wad'annnan mutanen ba alheri ne ya kawo su ba, zama tai a kusa dashi tace " kasan me?" "Bansan me wasu maza sukazo yi ba amma da alama masifa sukazo yi, hmmm basusan halin Baffa bane. " Tad'an tab'e baki tace " ni kaina tsoronsa nake gani nake kamar ba shi ya haifen ba, mahaifiyata ma saboda masifarshi tsoronshi take, hmmm bansan ko su basa tsoron Baffan ba. " Dariya yake a cikin ransa lalai wannan akwai surutu. Jitai an fasa abu yasa ta mik'e da sauri tai waje, yabi bayanta dakallo tareda yin dariya lalai wannan yarinyar ga hausartata mai abin dariya. Tana fita taga mutanen nan ne suka fasa musu randa, ga mamakinta Baffa na zaune a gefe yana kallansu, wani daga cikinsu yace " wallahi kaji na fad'ama Datti ka bani kud'ina tun kafin rai ya b'aci. " Baffa ya juya kai yana murmushi yace " Nina rantar muku kud'i? " Mutumin yace " bakai bane amma ai matarka ce tace injika. " Yasa dariya yace " Matata? Wa kenan? " Haushi ya kara kamasu, Nafi dake tsaye jikin kofa ta matso kadan, ai kuwa Mutumin na ganinta ya matso tare da rike hannunta yace " Uwar wannan yarinyar." Baffa yai dariya yace "Ali kasan Allah ficikata bazatai ciwo ba dan ba ninace ka bata uban kudi ba, banda sacemin saniya datai har kake tunanin zan kara kashe mata wani kud? " Wanda ya kira da Ali shine ya matso a shekaru ya girmi baffa sai dai bai tsufa ba, yace " Datti wlh in har ka cigaba da batan rai to kuwa zan dauki wannan 'yar taka amaimakon kud'ina ne.? Baffa ya bugamai wani kallo, Nafi wanda tsananin tsoro ya kamata ta kalli Baffa hawaye suka fara zubo mata. Baffa ya juyar da kai. Ali yace " Aradun Allah ko ka biyani kud'ina ko kuma a yau d'innan insa a auramin 'yarka sai ka zab'a. Dan binni dake tsaye yana jinsu ya mike cikin tsananin mamaki kasancewar da hausa suke maganar yasa ya fahimta, ya kula su masu masifar kamar hausawa ne, meke faruwa? Muryar Nafi ce ta katseshi tana kuka tana cewa " Baffa dan Allah ka taimakeni kaji? " Baffa ya kallesu kallan wulakanci yace " kuna tunanin saboda 'yata sai in sadaukar da dukiyata? " Ya sa dariya yace " Dama na gaji da ita, in kanaso yanzu ma sai in aurama ita menene a ciki? " Ba Nafi ba ba kuma Dan binni ba hatta 'yan ansan bashi sai da tsananin mamaki ya kamasu, Nafi ta kalli Mahaifinta cikin tsananin mamaki sam tama kasa magana banda rawa da jikinta ya shigayi. Baffa yai tsaki yace " Zancen banza kenan. " Ali ya kalli mutanen gun yace " kowa yaji abinda Datti yace ko? " Duk suka amsa da eh, Ali yace dan haka anjima da azahar zamu dawo a bakin nan za'a daura aure lalai zanga karyar iskaninka Datti. " Suna kainan suka saki Nafi suka juya. Nafi kam haf yanzu jikinta rawa yake, baffa ya kalleta yace " ke menene damuwarki? Ali fa nada kudi da dabobbi sannan matansa uku sai 'ya'ya guda sha shida kinga gwara ki aureshi can ki xauna cikin mutane ko kyafiyin hankali. " Yana kainan ya juya yai waje. Dan binni yai tsuru yana kallan ikon Allah wace irin zuciya ce da wannan mutumin? Bakomai a ransa sai dukiyarsa? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 4⃣ D'akinta ta shiga tana tafe tana layi, shikam yana jin motsinta yai saurin kwanciya dan ya tabbata bazataso wani yaji wannan mumunan abun ba, Nafi na shiga ta karasa kusa dashi ta zauna hawaye ne kawai ke malala a idanunta, can tasa hannu ta goge sannan ta kalleshi cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa tace "Dan binni yazanyi da ke? Gashi baki farfad'o ba bare ki bar wannan gidan mai cike da abin takaici dasan zuciya. " Zuciyarshi ce ta karye da mamakin tana cikin wannan halin amma tausayinsa take? Wannan wace irin yarinya ce wacce zuciyarta take da tsananin kyau? Nafi ta kara sa hannunta ta goge hawayenta sannan ta cigaba " Dan Binni ina cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa, Mahaifina baisan komai ba sai dukiyarsa baya ganin mutunci ko darajar kowa banda ta dukiyarsa, mahaifiyata kuma san kanta ya mata yawa haka na taso a cikin irin iyayen nan, ba wanda ya damu da halin da nake ciki ko wanda zan shiga, a dazu nafijin haushin Baffa akan kin biyan bashin dayai sannan bai damu da in auri sa'ansa ba wanda a cikin 'ya'yansa akwai wad'anda suka girmeni ba. " Tai ajiyar zuciya sannan ta cigaba " yanzu kuwa nafijin haushin Inna ta, tafi kowa sannin halin Baffa amma duk da haka taje ta ranci kud'i da sunansa, ni kuma da ko naira biyar bangani ba bashi na neman............ " Kuka ne yaci karfinta ta kasa karasawa, mikewa tai tsaye tace "bari in samoma madara kasha nasan yunwa kake ji." Tana fita ya bud'e idanunsa ga mamakinsa jiyai gaba daya jikinsa yayi wani mugun sanyi, meyasa mutane basuda imani? Yanzu me wannan yarinyar tayi da hakan ke faruwa da ita? Shiru yai yana tunanin meya kamata yai dan cetan rayuwarta? Bata dade ba ta shigo dauke da kwarya karami da chokali, nan ta dagoshi kadan ta shiga bashi, mamaki tayi dan kuwa yau madarar bata zubewa sai dai batai tunanin komai ba. Shikam sha kawai yake gardin madarar ce kesashi sha sai dai rashin sigari yasa madarar batamai armashi sosai ba. Ganin yadansha dayawa yasa ta gyaramai kwanciya sannan ta mike tai waje. A can bangaren Datti kuwa yatafi rigar Mahaifinsa nan ya shiga suka gaisa da iyayensa da 'yan uwansa ya kuma sanar dasu auren Nafi wanda za'a daura anjima, tsananin mamaki ne ya kama Iyayensa da yayensa, mahaifinsa wanda ya tsufa sosai ya kalleshi yace " yanzu Datti za'ai auren Nahi shine sai ranar auren zaka sanar damu? " Datti cikin halin ko in kula yace " to Kawo menene aciki nima sai yau naji zancen auren. " Gaba daya suka kalleshi cikin tsananin mamakin kalamansa, Aji mahaifiyarsa tace " Datti me kake san kace? " Ya kalleta yace " Aji to menene ban fada ba? Nima aradun Allah sai dazu nan na sani." Tsannnanin akaici ne ya kama Aji ta mike cikin zafi tai gaba hartaje wajen dakinta ta dawo ta kallesu tace " in har na isa da ku babu wanda zaije daurin auren Nahi ta gurin datti sannan ba wanda zai aika mata ko da kwayar samira ce, na sani ba laihinta bane sai dai Datti ya ja mata komai. " Tana kai nan tai gaba a fusace Tanaji Datti nacewa " Karki damu Aji nima ba kai mata samirun zan ba mijinta inya damu ya sai mata. " Yayansa Sambo yace " Datti me kake san fad'a? Bazaka mata kayan daki ba ko me?" Datti ya mike yace " nifa nazo sanar daku ne bawai cewa nai kuzo ba, yar nan tawace ra'ayinane in mata kayan daki ko inki. " Kallan mamaki suka bishi dashi inda sabo sun saba da halin Datti sai dai mamaki suke tunda yanzu abun ya shafi zancen 'yarsa. *********** Sukam su Ali da ragowar abokansa murna suka shiga tayashi akan yasamu abu a bagas, lalai sun yadda Datti baya cikin hayyacinsa, waye zai saida 'yarsa saboda dubu ashirin? Sukam sunje sun sanar da liman nan suka shiga shirye shiryen, Ali yasa aka share mata daki daya acikin gidansa, matansa kansu basuyi kishi ba jin yarinya ce suna ganin baifisu kara samun mai musu girki ba. ************** Nafi ta gama aikin gida tsaf ta gyara dabobbi, shikam zaune yake yana addu'a fatansa d'ayane Allah ya bashi ikon taimakon wannan baiwar Allah, kamar yanda ta taimakeshi, yanaji a kasan ransa kamar Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya ceci wannan baiwar Allah. Tunani guda d'aya ne ya tsayamai dole ne shi ha dauki nauyin biyan wannan bashin kila itace mafita. Mikewa yai ya fito daga dakin, ba kowa a wajen hakan yasa ya fita daga gidan. Toh fah!!!! Ganinsa yai a tsurar daji baya ganin komai sai daji mamaki ne ya kamashi, yanzu ace mutum ne yake rayuwa anan? Sai kace mara gaskiya? Jiyai ance kai waye nan? Da fillo akai maganar, Juyawa yai dan jin yasan kamar mai muryar nan. Ya kalleshi tare da da dan yin kasa dakai sannan ya mikamai hannu alamar gaisuwa, Datti ya bugamai harara sannan yace " me kake anan? " Yaa fada tare da kallan kayan jikinsa kamar yasan kayan nan, shikam dan binni ya daure ya sauke hannunsa sannan yace " Dan Allah cikin gari nake tambaya. Jin yamai hausa yasa Datti yace " Ka mike nan hanyar inkai tafiya mai tsaye zakaga gari. " Bai jira komai ba yace " Na gode yai gaba. " Datti ya bishi da kallo kamar kayansa, sai dai ta ina kayansa zaije gun wannann kad'on? Yayi tafiya mai nisa dan har ya gaji sannan yaga gari, a ransa yace nan ne garin? Kauye ne sai dai yanada girma sosai ga mutane sunata hada hadarsu, wajen wani mai tabir din rake ya tsaya ya mikamai hannu suka gaisa sannan yace " Dan Allah akwai ATM anan kusa? " Kallan mamaki mai raken ya masa yace " A me? " Yadan dafa kansa sannan yace " Banki fa? " Me raki ya kalleshi sosai kana ganinshi duk da rigar dake jikinsa zaka gane ba daga nan yake ba, ya girgiza mai kai alamar bai sani ba sannan yace " amma kaje can gurin masu mashina akwai Dan liti wanda yai karatun boko sai ka tambaye shi. " Yamai godiya sannan ya karasa gun masu mashina, sallama ya musu sannan ya tambayesu waye D'an liti, wanda ke zaune ya sha riga da wando ya wani tsuke shi a dole dan boko ya kalleshi yace " Yes ganinan. " Kallansa yai ya wani daura kafa d'aya kan d'aya akan mashin, dariya tadan so kamashi ya daure yace " Dan Allah tambaya nake san ma. " Dan litti ya dan wani rangwad'a kai sannan yace " what is your ansa? . " wai so yake yace "what is your question?" lol Dariya ce ta kama Dan binni yai kasa da kansa tareda murmusawa jiyai abokansa sunce " Kai Dan litti ka kure gayu fa. " Dan litti ya wani sosa keya irin jin dadin nan, Dan binni ya dago sannan yace " So nake in tambayeka ko akwai ATM anan kusa." Fuska dan litti ya canza yadan gyara zama sannan yace " AT me? " Dan binni yai murmushi yace " ka gane mana inda ake cirar kudi ba tare da anshiga banki ba. " Tafi Dan litti yai yace " Ohhhhhh ATN? Ha ha ha kai ne bakamin bayani ba, akwai amma gaskiya sai dai muje can gwaram. " Dan binni yace " inane kenan? " Dan litti yai murmushi yace " local gommant d'in mu." Kai ya jinjina alamar gamsuwa sannan yace " Zai kai minti nawa kan mu isa? " " A kalla minti 40 inaji. " Shiru Dan binni yai sannan yace " Muje to Allah yasa mu dawo kan azahar. " Dan litti yace " Maganar kudina fa?" " in mun dawo mayi maganar ai tare zamu mu dawo tare. " Dan litti ya kwama glass dinsa sannan yace " Hau muje. " Dan binni ya hau yana tunanin yanda zaiyi tafiyar kusan hour daya da rabi akan mashin shida rabonsa da mashin har ya manta inbadai race suke da 'yan uwansa ba shima race d'in sun dade basuyi ba kasancewar canjin yanayi da suke fuskanta a tsakaninsu. ************ Nafi zuciya d'aya tana gama aiki ta shigo gun D'an binni sai dai me? Ba shi ba alamarsa, tsoro da fargaba ne suka kamata nan ta fito ta shiga nemansa sai dai samm babu shi, idanunta ne suka ciciko da kwalla tace " Wato ya warke shine ko sallama baxai min bako? Me yasa mutane suke min haka? Kowa baya sona? Kowa bai damuwa da halin da nake ciki ko wanda zan shiga? Wato shi kuma wannan zuciyarsa mara rama alkairi ce ko???????? *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 5⃣ Sun fara tafiya akan Mashin Dan litti yace " Amma da alama kai ba dan garin nan bane ba ko?" Murmushi yai sannan yace " ni ba dan garin nan bane kuma yau nakesa ran barin nan." Dan litti yadan juyo sannan yace " When are u fom?" Ya fada cikin irin isar nan wai shi a dole kwarare, Dariya Dan binni yasa hakan yasa Dan litti yace " U don't say English? " Dan binni kam dariya yake yi har ransa hakan yadan sa ran Dan litti ya soso, yace " Malam menene hakan ka sani a gaba sai dariya kake?" Dan binni ya daure yace " A wacce makaranta kau karatu ne haka?" Mazewa dan litti yai yace " Anan makarantar Gomnati ta Gwaram." Yadan kare hade rai yace " what matter?" Dan binni yace " lalai naga kanata kokari ne wajen yin turanci." Dan litti yai wani murmushin isa da takama yace " Kaf garin mu ni kadai ne nai karatu hakan yasa mahaifina ke ji dani kamar kwai sannan yan mata suke sona." Dan binni ya jinjina kai yace " hmmm gaskiya kam a garin Jahilai dama ai......" Dan litti yace " me kace?" Kai ya juya batareda yace komai ba. Inya tuna turancin Dan litti kawai sai ya saki murmushi lalai ana kwab'a a kasar nan. Tun yanajin dadin tafiya yana kalle kallen kauye har ya gaji kawai ya zauna yai dif. Yanaji Dan litti nata bashu labarin makaranta, shidai kam jinsa kawai yake fatansa Allah yasa suje su dawo kafin bakin alkalami ya bushe. Sunyi tafiya sosai kafin su isa Gwaram, nan Dan litti ya karasa bakin banki ya tsaya, ya kalli Dan binni yace " Gashi mun iso." Dan binni ya kalli bankin sannan ya kalli ATM din dake gun guda biyu ne a jere saidai mutanen dake tsaye a gun sunfi 20, wata iska ya furzar sannan yace " Dan litti ba wani sai wannan?" Dan litti ya kalli mutanen gun yace " Kasan karshen wata yayi ko munje wani gun ma hakan ne gwara mu tsaya anan." Dan binni ya kalli mutanen gun sannan ya tuna Nafi wacce ake neman ruguza mata rayuwa, takawa yai yaje har ya tsaya a layi yaga abin kamar bazai yiwu ba, hakan yasa ya karasa ya fara neman alfarma, abinda tunda yake arayuwarsa bai tab'a yi ba kenan wai ace shi ne ya rusunar da kai yake neman alfarma gun wasu, ya taso rayuwarsa ba abinda ya rasa, haka ya daure yai ta neman alfarma har ya dawo na 8, suna nan tsaye har aka zi kansa, ya zaro wallet dinsa dake aljihun wandansa ya ciro ATM card dinsa ya sa. Dubu Ashirin ashirn sau biyu ya cira sannan ya ciri dubu goma ya kama hamsin kenan, ya musu godiya ya karasa gun Dan litti, tafi Dan litti yamai yace " Gaskiya ka birgeni yanzu mu tafi?" Dan binni ya kalleshi yace " yunwa dai nake dan ji." Dan litti yace " Ga mai Yam da Egg can muje sai ka siya." Murmushi yai sannan yace " Lalai Dan litti dan boko." Dan litti ya shafa keya yace " Can we went?" Dan binni ya juya kai sannan suka karasa gun mai doya, kashi biyu yace asa musu wato shida Dan litti, har zasu juya sai ya koma yace a kara samai wani daban, haka kawai yaji zuciyarshi ta tuno mai da Nafi. Dan litti ya shiga godiya nan suka ci sukasha leman kwalba sannan suka mike suka juya. ************ A can rigar Datti kuwa Nafi ce zaune a dakinta banda kuja ba abinda takeyi ga bakin cikin auren da za' a mata gana guduwar dan binni, mamaki ne ya kamata dataji mutane suna sallama, nan ta fito dan tasan su ba baki suke ba tunda Baffa baso yake ba, turus ta tsaya tana kallan kanwan mamanta, sai dai ta kasa farin cikin ganinta sam. Ganin haka yasa ta matso tare da rungume Nafi tace " Nafi shine kina ganina zaki shareni? Bayan har da kawarki Hanne nazo miki da ita? " Nafi ta maida hawayenta sannan tace " Aunty nayi mamakin ganinki ne." Tace" ai daga ke har Datti baku kyauta mana ba wau sai dazu aka turo mana almajiri wai yau ake auren ki? Haba Nafi ai ko Datti bai sanar damu ba ke kya fada mana ai." Nafi kam kasa magana tai dan batasan taka maimai mema zata ceba cewa zatai an bada ita biyan bashi ko me? Hanne ce ta matso kusa da ita tace " Nafi ya naga ba kowa a gidan? Kamar ba biki za'ai ba?" Nafi ta share hawayenta tace " eh kinsan Baffa bayasan mutanene shiyasa." Baki Hanne ta tab'e tace " amma dai duk da haka, sannan ke ma kalleki kamar ba Amarya ba ko wanka ma da alama bakiyi ba." Nafi tadan juya kanta gefe, Nan Maman Hanne tasa Hanne ta debo ruwa, da kanta ta tasata gaba sukaje ta wanketa fes, sannan suka fito, kayan Nafi ta kalla sam bana arziki bare aje ga sabo haushi da tausayi suka kamata ta kalli Hanne tace " Hanne da alama ke zaki taimaka ki ciro kayan jikinki ta saka inyaso ke sai kisa nata." Hanne ta kalli Nafi tace " Allah Nafi shi yasa kike ban haushi ke wai bazaki taba cewa asai miki kaya ba? Ko sanda innarku nanan itama banga ta wani damu da miki dinki ba, yanzu dan Allah meye amfanin hakan?" Nafi tai kasa dakai, Hanne taja wani dogon tsaki tace " sam ita wannan a kidahuman ma ita ta dabance, fa tsinanan kawaici da hakuri, wallahi babu inda zakiji ba'a cuce ki ba indai haka zaki cigaba." Maman ta tace " to ya isheni uwar 'yan masifa." Nan Hanne ta cire kayanta tana masifa. Nafi ta saka kayan sun amsheta kuwa nan Hanne ta shafa mata hoda tana shirin yi mata ja gira da kwalli Nafi tace " Bashi Hanne kema kinsan banasan kwalliya." Hanne ta mike cikin takaici tace " ni dai kam ban taba ganin mutum irin ki ba, gaskiya Nafi kina neman addu'a ni wallahi haushi wannan halayen naki suke bani." Tana kainan tai hanyar waje, jitai Nafi tace " kiyi hakuri Hanne ba bata miki rai naso yi ba." Hanne ta kara had'e rai tace " kinganta ko Goggo? Yanzu me tayi na bada hakuri dan Allah?" Tai waje ba tareda ta jira amsa ba. Maman Hanne ta kalli Nafi tace " Nafi kiyi hakuri kinsan kawartaki akwai masifa." Hanne ce ta shigo cikin mamaki tace " Nafi naga sun fara taruwa inaji yanzu za'a daura, ni ko mijin ban gani ba." Gaban Nafi ne ya fadi tanasan yin kuka ba kuma taso su Hanne da mahaifiyarta susan halin da ake ciki, kasa kawai tai da kanta tana karanta Inalilahi a zuciyarta. Ango kam yasha babbar riga haka kuma ya taho da abokanansa dayawa dama yan uwa da makota, sannan sun taho da liman da maroka, Datti ne yashigo gida fuskarsa a sake wasai ko a jikinsa, ya zura riga babba shima, yanajin Mahaifiyar Hanne na gaisheshi ya shareta yai waje. Ta birma manya aka shimfida musu sannan Ali ya taho da goro nan aka ajiye, Aka dan gagaisa sannan aka zauna. A ciki kuwa mahaifiyar Hanne ce ta kalli Nafi tace " Nafi amma an miki komai na kayan daki ko?" Nafi ta kalleta tare da kakaro murmushi kawai amma batace komai ba, hakan yasa itama tai shiru. An gama addu'oi nan aka ce ina Walliyin Alhaji Ali? Wani kanin mahifinsa yace " Ganinan." Akace walliyin Nafi fa? Datti yace gani. Kallan mamaki suka bishi dashi sukace " Dakanka malam Datti? Ai kyanta wani dan uwanka na kusa zaka wakilta." Datti ya hade rai yace " wannan damuwarku ce amma nine zan zama walliyi a auren 'yata ehe." Sunyi shiru, liman ya kalli Ali, kai Ali ya daga mai akan ba komai a kyaleshi, nan liman yace to shikenan yanzu zamu gabatar da......... Ji sukai ance " Ba abinda zaku gabatar domin kuwa ni na hana wannan auren." Gaba daya suka juyo suka kalli inda maganar ke fito wa, ga mamakinsu wani saurayi ne ya sauka daga kan mashin sannan ya fara takowa gunsu cikin isa da takama, basusan fuskarba sai dai Datti yasanshi dan kuwa bai manta shi ba. Dan binni ya karaso inda suke zaune ya gaida liman sannan ya kalli Ali wanda yasha manyan kaya, ba shakka ya girmi mahaifin Nafi lalai mutanen nan basuda imani. Ali ya harareshi yace " Kai menene kakeyi haka? Ba ka gani aure ake shirin daurawa?" Dan binni yai murmushi yace " Aure? Dama haka ake aure?" Ali da 'yan koronsa suka mike sukace " kai meye hakan? " Dan binni yasa hannu a aljihu ya ciro dubu ashirin daya waresu tun a banku yace " ungo! Ba bashi kake binsu ba har kake tunanin kwace mutum akan wata banza dubu ashirin dan tsabar rashin imani?" Ali ya kalli kudin sannan yace " ni na yafe Nafi nakeso a auren." Dan binni yace " Ai kuwa baka isa ba, yarinya ba sanka take ba kuma baka isa ka aureta ba, kai ko kunya ma bakaji ba kana yayan mahaifinta? Inbanda zuciyarka irin ta yarace ina kai ina neman wace batafi sa'an 'ya'yanka ba?" Datti dake zaune ya mike tsaye yace " Kai wai kai waye ne? Menene naka a ciki? " Dan binni ya kalli Datti cikin takaici yace " nine wanda 'yarka ta taimaka a lokacin da nake kan karagar mutuwa ta." Mamaki ya kama datti dama sauran 'yan gun, Datti yace " to naji, daga taimako sai akace ka isa da ita? Ka dubafa kaga yarinyar nan ta girma amma ba miji, in ka korar mata wannan d'in kai ne zaka aureta ko me?" Gaba daya kallo yakoma kan Dan binni suna jiran amsarsa. Gabansa ne ya fad'i baiyi tunanin abin zai juye haka ba, me kenan? Daga taimako?" Ali ya matso kusa dashi shima yace " eh muna jinka kai ne zaka aureta ko me?" Innalilahi wa ina ilaihi raji'un!!!! Allahuma Ajirni fi Masibati wa aklifni kairan minha...... Addu'ar da Dan binni ya shiga yi kenan a ransa. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 6⃣ Gaba d'aya hankalinsa yakai kololuwar tashi muryar Ali yaji yana cewa " Kai yaro dakai muke magana, Kai zaka aureta amaimako na ko me? Yaran yanzu banda tsugudidi basuda aikin yi inbanda munafirci da shiga shara ba shanu dan ta taimakeka meye naka na shiga shirgin rayuwarta?" Dan binni ya kalleshi cikin bacin rai yace " kai yanzu in 'yar ka ce zata auri sa'anka ko wanda yafika zakaji dadi?" Ali ya kwashe da dariya yace " to menene? Baifi karin zumunci ba." Dan binni zaiyi magana yaji an dafashi, juyawa yai dan ganin waye, ga mamakinsa dan litti ya gani a tsaye a bayanshi, ya kalli Dan litti cikin wani yanayi. Dan litti yace " Abokina ka fita harkarnan tun kafin kuzo kuna arment." Dan binni ya kalleshi yace " meye arment?" D'an Litti ya wani sosa kai su kuma mutane suka kalleshi da sha'awa jin yana turanci. D'an litti yace " baka gane ba? Kar kuzo kuna musu nake nufi." Wani kululun takaici ne ya kamashi dama mutanen gun nan sun gama kona mai rai shikuma D'an litti zai so mai da wani sabon takaici wai arguments ne arment? Kallanshi ya maida kan Liman wanda yake cewa " ni yanzu a wani matsayi nake? Datti yace " Aure za'a daura da Ali yanzun nan." Ali ya gyara rigarsa, haushi ya kara turnuke dan binni yace " in kuma nace zan aureta fa?" Gaba d'aya kowa juyawa yai ya kalleshi cikin tsananin mamaki, Datti yace " Kana nufin zaka aurenta?" Gaban D'an Binni ya fad'i ya daure yace " Eh." Abinda kawaj zuciyarshi take rayamai Allah ya kawoshi garin nan ne dan ya taimake ta." Matsowa D'an litti yai da kansa saitin kunnen D'an binni yace " I am Crazy? Kasan me kake kuwa?" Dan binni ya juya ya kalli D'an litti sannan ya kalli Ali wanda yake hucci kamar zaki, shi a tunanin sa ai dan yace zai aureta baza'ace yanzu ba. Sai dai abinda kunnensa ya jiyo masa ya tada masa hankali, jiyai Datti yace " to Liman yanzu sai a daura da wannan shikuma Ali sai ya amshi kudinsa yai gaba." Kallan Datti yai cikin tsananin mamaki yace " nikam ka tabbatar kaine mahaifinta?" Datti ya had'e rai yace " wani banza zance kake yi hakan? In ba 'yata bace 'yar kace?" Dan binni ya dafa kai zaiyi magana yaji Ali yace " da alama bai shirya ba gwara a daura dani......" Kallan da D'an binni yamai ne yasa yai shiru, yace " na dauka nace a daura dani?" Datti yace " to banga alamar kanaso ba gashi mu kana bata mana lokaci." D'an binni ya ciro d'ayan dubu ashirin d'in wanda ya d'auko domin ba Nafi inzai tafi ya mikama D'an litti yace " Sadaki ne mika musu." D'an litti ya jinjina kai cikin mamaki yace " Lalai I am crazy." Yana kai nan ya karasa gun Liman yace " wai ga sadakin Wancan." Liman ya kalleshi yace " to waye zai mai walliyanta? " Datti ganin damin kudi yasa cikin saurin murya yace " Ladan kawai yamai ai musulmi dan uwan musulmi ne." D'an binni ya bishi da kallan mamaki lalai mutanen nan basuda cikaken hankali kaf cikinsu ba wanda ya tambayi inda yake? Mugu ne shi? Haka kawai suke neman bashi 'ya ba wani bincike. Jiyai Ladan yace " Ya sunan ka? " " ASHRAF" Abinda ya fito daga bakinsa kenan, yana tsaye har aka gama d'aurin auren Nafisa da Ashraf akan sadaki dubu ashirin. Nan su Ali da mukarabansa suka watse cikin tsananin takaici, Datti wanda ya cafki kudin sadaki ne ya matso kusa da Ashraf yace " Ashaf yanzu inane inda za'a kai ma Amaryarka?" Kallan Datti yai cikin mugun takaici yace " Na dauka baka damu da inda za'a kai 'yarka ba tunda banga alamun kanaso ka sani ba." Ya kafe Datti da ido yace " me Nafi take ma wanda kakeso tabar ma gidanka kota halin ka ka?" Datti yad'an had'e rai yace " Kai Ashaf dan ka zama mijinta an fadama kanada damar fadamin magana san ranka?" Ashraf ya kalli D'an litti yace " Please d'an jira ta fito mu tafi ka saukemu, dan banga alamar mashin ba ko zaka samomana d'aya saboda mu biyu ne?" D'an litti yace " ba problem kaje ku shiryo I will came with one. " Ashraf ya d'an yi murmushi kadan sannan ya kalli Datti yace " a sanar da ita ta shirya dan ni ba anan garin nake ba." Datti yace " me?" Ashraf ya juya kai bai kara magana ba, har Datti sai sake magana sai ya fasa ya shiga ciki. Nafi kam ta kule a bayan gida banda kuka batada aiki shikenan Allah ne kadai yasan wace rayuwar zata fara daga yau, ina zata sa kanta?" Jitai Hanne na kiranta, hakan yasa ta goge hawayen ta tafito, Hanne ta kalleta tace " kuka kike?" Nafi tace " a'a." Hanne tai tsaki tace " wato memakon kiyi kuka a gabanmu mu samu damar lallashinki ki gwammace kinyi kuka ke kadai kin share hawayenki? Nafi nikam ina tsananin mamakin halayenki." Tai gaba, Nafi ta bi ta a baya, har sunyi hanyar dakinta ta kalli igiya inda ta shanya kayan D'an binni ka ra sawa tai ta zare rigar ta rike a hannunta. D'aki ta shiga ga mamakinta Datti ta gani zaune akan tabirma wanda rabon da ko dakinta ya leka yaga a wani hali take ciki ita kanta ta manta. Shiga tai kanta a kasa, ta gaidashi sannan ta zauna kusa da Maman Hanne. Datti ya kallesu yace " To aure dai an daura sai dai an samu canji daga Ali zuwa wani Ashaf." Cikin tsananin mamaki Nafi ta d'ago ta kalli Baffa tace " Ashaf?" Datti ya jinjina kai yace " Kwarai nikaina nafisanshi akan Ali da alama yana da arziki sannan kuma shi saurayi ne." Maman Hanne ta kalleshi tace " nifa sam ban fahimci me ake nufi ba, banga ne daga Ali ba an koma Ashaf? Meye ma wani Ashaf? Ni bantaba jin sunan ba." Datti ya buga mata wani kallo yace " meye naki a ciki? ' yata ce ba 'yar uban kowa ba sannan in baki tabajin suna Ashaf ba yau ai kinji." Ya mike rai a bace sannan yace " ke kuma ki shirya yanzun nan dan yace ba agarin nan yake ba zaku wuce yanzu." Kallan mamaki kawai take ma babanta ta sani shi dabobinshi su kadai ne abinda ke gabansa kuma suka dameshi sai dai bata taba tunanin zai ma 'yarsa ta cikinsa haka ba, sai kace wata kaza? Ganin kallan datake mai yasa yace " in tunanin sadakinki kikeyi kima manta dan nima na dauki rabona na satar da uwarki tamin, yana kainan yai waje. Nafi kam kuka ma kasa zuwa mata yai jitai idanunta sun kafe kaf, sai dai rigar dake hannunta kawai ta shiga ninkewa jitake zuciyarya kamar zata tsage, Maman Hanne ta kalleta tace " Nafi ki taimaka ki fadamin abinda ke faruwa dan Allah." Nafi ta kalleta tace " Auntu ko na fada miki menene amfani? Tunda aikin gama ya riga ya gama? " Hanne ta mike cikin takaici tai waje. Nafi kam a zaune kawai take tana jiyo muryar Datti yana cewa suyi sauri. Ashraf kam yana tsaye a waje tunani sun taru sun mai yawa, ina zai sa kansa? Mai zai cewa masoyiyarsa kuma 'yar uwarsa wacce saura wata biyu a daura musu aure? Yasan ta sarai yanda take tsananin so da kishinsa lalai zata iya yin komai inhar taji abinda ya faru, kansa ya dafa wanda yakeji yana sara mai. Karar mashin ne yasa ya kalli hanya, Su D'an litti ya hango nan suka karaso D'an litti ya kalleshi yace " yama kace name d'inka?" "ASHRAF. " D'an litti yai murmushi yace " Gaskiya an cucen da aka samin D'an litti sunan ka yafimin dadi." Ashraf yai musrmushi sannan yace " D'an litti kenan." Datti ne ya fito ya tsaya kusa da Ashraf yace " Ashaf gatannan amma ya za'ayi in anaso aje gunta ina zance? " Ashraf ya kalleshi sannan yace " Kano anan garin nake, sannan ai kasan sunana."yai maganar cikin bacin rai. D'an litti ya tafa mai yace " Haba? Living Kano? I also came to kano." Ashraf ya furzar da iskar takaici yace " nikam D'an litti kadingamin hausa banasan turancin nan." Dariya Datti yai yace " gaskiya kam, yanzu kenan in wasu zasuje sai D'an litti ka rakasu ko?" D'an litti yai murmushi tare da sosa keya. Nafice ta fito sanye da lulub'i Hanne da mamanta na gefenta, Hanne ce ta kalli mazan gun su uku, tace waye mijin a ciki? Ta fada tana fatan Allah yasa ba wannan bane dan ya birgeta Allah yasa D'an litti ne." Gani tai D'an litti ya nuna wanda yai masifar burgeta da yatsa, dukda rigar kauye ce a jikinsa kana ganinshi kasan daban yake, tadan yi yake tace " to a rike mana 'yar uwarmu dakyau, amma bamu zamu kaita ba?" . Datti yace " bakiji me nace ba aciki ko kuma wani sabon kinibibi ne hakan? Ai nace su biyu zasu tafi ko?" Mamaki ne ya kama maman Hanne tace " su biyu? Dama abinda kake nufi kenan? Taya zamu bari 'yar mu ta tafi daga ita sai shi? " Datti yace " karki damu D'an litti yasan gidan." Tai shiru, Nafi kam hawaye ne ya fara zubo mata itakam tana ganin rayuwa? Wasa wasa kaza ma ta fita matsayi itakam. Jitai ance " Ina rigata? Ko kin barmin wannan?" D'agowa tai cikin tsananin mamaki, idanunsu ne suka hadu........gabanta ne ya shiga fad'uwa sai dai ta kasa dauke ido daga kansa, ya sakar mata wani sansanyan murmushi........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *WELCOME BACK ZEE FRESH,* *WE REALLY MISS YOU*😍😘.. 7⃣ Kallansa take cikin tsananin mamaki ya sake murmushi yace " Riga tafa? Ko kin barmin wannan d'in? " Kasa tai da kanta sannan a hankali tace "na d'auka ka tafi ai. " Datti yace " me kuke nufi kenan ka santa dama? Sani bana taimako ba? " Ashraf yad'an yi murmushi dama so yake ya kular da Datti yace " sani kuwa tunda ji jiya a d'akin ta na kwana. " Yai maganar yana kallan Nafi, gaba d'aya kowa ya kalleshi, Datti ya rike haba yace " Kwana? " Ashraf yai wani murmushin rainin hankali sannan ya ya d'aga kai yace " Uhm hum" Hannee da mamanta suka kalli Nafi cikin mamaki, Dan litti shima mamaki ne taf a ransa lalai wannan gayen ashe dan duniya ne? Nafi ce tayi baya da sauri tai cikin gida, kallan kofar data shiga sukai suna tunanin me kuma zatai. Nafi kam tana shiga da sauri tai d'aki tana tafe tana murmushi takasa gane dalilin murmushin nata, rigarsa data ninke d'azu ta dauka abin haushi ba tada turare hakan yasa ta fito, suna tsaye sai gata ta dawo. Datti yai tsaye yace "Gungumar Munafuka ina kika je? " Rigarsa ta mikamai fuskarta a sake tace " danaji bakai min magana ba sai na d'auka tafiyarka kayi. " Ashraf ya amsa yace" ina kuwa zan tafi? Bayan nasan kina cikin wani hali? " Salati Datti yasa yace " yau na shiga uku lalai yarinyarnan ke ba karamar 'yar iska bace, a haka kowa ya ganki sai ya d'auka ke ta Allah ce ba'asan tsantsar munafircin ki yafi na shaid'an ba, yanzu dan iskanci da so kikai ki auri Ali bayan kin gama lalata da wannan? " Cikin mamakin kalamansa Nafi ta dago ta kalleshi, lalata? Me kenan? Maman Hanne ma tace " Gaskiya Nafi kin ban mamaki ban taba tunanin zaki aikata haka ba. " Itakam Hanne harara kawai take makama Nafi. Ashraf ne ya kallesu yace " Gaskiya bakuda adalci, wato kai kana mahaifinta sanda nace ta taimakeni baka shi mata albarka ba ka yabe ta ba, sai yanzu dana fad'i na kwana a d'akin ta kaf cikinku ba wanda yai tunanin lalai kila ba abin banza akai ba. " Ya d'an furzar da iska sannan ya matsa daga inda suke, ta baya ya zaga ya cire rigar jikin sa yasa tashi, tunda ya juyo ya fara tahowa kowa ya kuramai ido, lalai wannan gayen bana karya bane, tafiya yake cikin isa Nafi itama ba'a barta a baya ba gun kallansa, Hanne kam kishi duk ya isheta. Ashraf har ya karaso basu daina kallanshi ba, D'an litti ya dafa yace " Babban gaye me kake tunani ne? " D'an litti ya had'iyi miyau yace " Kai Ashraf gaskiya she is beautiful. " Ashraf ya sakeshi tare da mikama Datti rigarsa yace" mu zamu wuce. " Datti kam sam ya kasa magana, kallan Nafi yai yace " muje ko? " Kallan mamaki tamai dan ita batasan shine mijin ba lokacin kanta ma kasa sai dai ta kasa mai musu nan ta kalli Datti tace "Baba mun wuce. " "Ah to shikenan, sai munzo ganin gida, d'an litti ya kawo mu. "datti yai maganar yana kalle kalle. Nafi tace to. Maman Hanne ta mata sallama sai dai ganin yanda Hanne ta hade rai yasa Nafi ta juya ba tare da ta mata magana ba. " Sunanan tsaye har suka hau mashin, nan suka nufi hanyar Gwaram inda zasu hau mota. ******** Sunyi tafiya sosai kafin su isa, nan D'an litti yakaisu inda zasu shiga mota, wata karamar golf suka samu D'an litti jiyai Ashraf yace " Shata muke so. " Dasauri ya jawo rigarsa yace " Ashraf kasan me kake fad'a kuwa? Inkace shata yana nufin fa ku biyu za'a kai har kano kaga kuwa zaka biya money panty. " Ashraf yai d'an murmushi yace " meye kuma panty? " D'an litti yace " Kudi dayawa nake nufi. " Kafadarsa Ashraf ya dafa yace " Plenty ake nufi. " Yana kainan ya wuce gun driver yace " Muje ko? " Nafi ce ta kalleshi sanda taga ya bud'e mata bayan mota ta shiga, ya dawo inda yabar D'an litti a tsaye kamar gunki ya ciro dubu uku ya bashi yace " Nagode sosai d'an litti Allah ya karama ilimi. " Kallan kudin yai yace " Ashraf ina zan kai kudin nan? " Murmushi yamai sannan ya mikamai wata dubu d'ayan yace " ka ba abokinka. " Ya juya ya nufi motar, tsayawa yai yana tunanin ko dai yabada number wayarsa in case ko iyayenta zasuzo Kano? Kai ya girgiza alamar a'a lalai dole ne ya koya musu sanin darajar yarinyar nan, dan ya kula zaman dasuke tare da ita ne yasa ba wanda yake ganin darajarta da mutuncinta. Shima bayan motar ya shiga, Nafi kam tana zaune duk jikinta a sanyaye, bata taba shiga mota ba sai yau, sai dai taitajin labarin agun Hanne yau gataa ciki, Driver ya tada mota. D'an litti ne ya matso da sauri ya turo kansa ta window yace " Nagodee Ashraf sannan yanzu na rike plenty ko? " Ashraf ya mai murmushi yace " kana burgeni ta yanda kake kokarin yin turancin nan, Allah ya hada fuskokinmu da alkairi. " Murmushi sukama juna D'an litti ya dagamai hannu yace "Sai munxo gidan ka. " Kai ya daga nan mota ta ja suka fara tafiya.......... Sun danyi nisa a hanya kad'an Ashraf ya kalli Nafi sannan yai gyaran murya, d'agowa tai ta kalleshi da idanunta, Yad'an mata murmushi sannan yace " Nafisa? " Gabanta ne ya fad'i jin ankirata da cikaken sunnanta, sai dai bata amsa ba sai dai hankalinta data tattara zuwa kansa. Ashraf ya cigaba " ki nutsu zamuyi magana mai mahimmanci ne. " Ta d'aga kai alamar tanaji. Ashraf yadanyi ajiyar zuciya sannan yace " Nafisa bazan miki alkawarin so ba, ba kuma zan miki alkawarin kulawa ba sai dai zan miki alkawarin ni Ashraf bazan taba bari ki wulakanta ba. " Kanta na kasa sai dai gaba daya gabanta har yanzu bai daina bugawa ba, ya cigaba " Na aureki ne domin ceton rayuwarki daga gun mutanen nan da babu imani a zuciyarsu, sai dai inaso ki kama bakinki kamar yanda nima zan kama. " Dagowa tai cikin mamaki ta kalleshi yace " kada ki kuskura ki fadama kowa na aureki, wannan sirri ne a tsakaninmu ni dake, karki fadama kowa wannan shine abinda zai kareki." Idanunta ne suka fara cicikowa nan ta shiga kokarin maidasu, kai ta daga mai alamar ta fahimta, Ashraf ya cigaba " Nafisa zan ajiyeki a gidanmu har Allah ya kawo miki wanda kike so shima yake sanki, in kun aminta da juna sai in sauwake miki ki aureshi......... " Kallan datamai ne yasa yai shiru shima, me kenan? Abinda zuciyarta ke raya mata kenan? Wani irin aurene a ranar aurenta ake mata zancen saki???? Ashraf yadan juya kai sannan yace " Bazaki fahimci me nake nufi ba yanzu amma na sani nan gaba zaki gane, a inda zamuje zakiga zuciyoyin mutane iri iri sai dai inaso ki daure ki zauna da kowa a yanda yake. " Nafi wanda hawaye yake yawo a fuskarta tai saurin jan mayafi ta tarufe fuskarta, kallanta yai sai dai ya za'ayi? Dole ne ya fadamata gaskiya....... Nafi tai shiru sai dai tunanin dake zuciyarta yawa garesu sai dai tasan abu d'aya dama, tabbas Dan binni ba santa yake ba taimakon ta kawai yai kamar yanda ta taimakeshi, tana ta tunani har bacci yai awun gaba da ita. Ashraf kam yayi shiru yana tunani, tabbas motarsa lafiya kalau ya ajiye ta, to amma mezai sa lokaci daya burkin motar yakiyi? Girgiza kai yai da sauri yace " zato zunubi, ikon Allah ne. " *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 8⃣ Bakin wani katon gida Ashraf yace mai yai parking, daga bakin gate din mutane ne sosai a tsatsaye sannan wasu dauke da speaker da cameras hakan yasa Ashraf yasan 'yan jarida ne a gun, kallan Nafi yai wacce ke zaune yace " Nafisa kin gaji ko? " Kallansa tai sannan ta girgiza kai alamar a'a, ya dan murmusa sannan yace " mun iso. " Ta kalli waje ganin mutane yasa ta kalleshi, ya bud'e motar ya sauka sannan ya zaga ya bud'e mata, a hankali ta fito jikinta duk a sanyaye, ya kalli driver d'in yace " bari in kawo ma kudin ka. " Ya amsa da to, juyawa yai ya fara tafiya, bai karasa gun mutanen ba kawun sa wato kanin babansa ya hangoshi cikin tsananin mamaki da farinciki ya taho da saurinsa, kusa da Ashraf ya tsaya yama kasa magana sai dariya kawai da yake ya kankame hannun Ashraf, mamakin da ya kamani banga Ashraf yana farinciki sosai ba sai dai yace " Kawu na tada muku hankali ko? " Wanda ya kira da kawun ya gari fadada murmushinsa yace " Ashraf duk mun daga hankalinmu ganin jiya a rafin wudil muka wuni cur ana nemanka an rasaka tsoro yasa muka fara tunanin ko ka cika sai dai mahaifiyarka taki yarda sam tace lalai kana nan da rai. " Yad'an yi murmushi kadan sannan yace " Bari na shiga ciki, sannan dan Allah aba mai mota kud'i." Kai ya daga mai cikin farin ciki, Ashraf ya juya ya kalli Nafi dake tsaye yace " Mu shiga ko? " Kallanta kawu yai saidai baice komai ba, Nafi kam a hankali ta karasa inda yake, nan suka fara tafiya, hannu kawai ya dagama 'yan jarida suka nufo inda yake, bai jirasu ba ya nufi gate, ya shige ciki. Inalilahi abinda Nafi ta fada kenan a fili, wani tafkeken gida ta gani, ba wai haduwaa kad'ai ba gida ne kato flat flat dayawa, in ka gani zaka dauka ko gidan hayane na masu kud'i sai dai Ina gida ne na Marigayi Alhaji Saminu wato mahaifin Ashraf, ya gina wannan tafkeken gidan ne saboda yazauna shida d'an uwanshi sannan yayi flat dayawa ne saboda in 'ya'yansu sun taso kowa ya kama flat daya ya zauna da nasa iyalen. Wannan kenan. Ashraf har yad'anyi nisa ya juyo a bakin gate yaga Nafi a makalle tana ta fadin Inalilahi, a hankali ya tako yazo inda take, ya kalleta yaga ta runtse ido tsam, yace " Nafisa muje ko? " Kallansa tai a tsorace tace " Muje ina? " Ya nuna mata hanya yace " ciki mana. " Yawu ta hadiya tace " Dan binni nan din inane? " Ya dan canza fuska kadan yace " badai baki yadda dani ba? " Kai ta girgiza da sauri alamar a'a, yace" good, to in har kin yadda dani muje ko? " Duk da tsoro bai bar ranta ba sai dai bata daina binshi a baya ba, can wani flat sukaje, suna karya kwanar flat din sukaga wata yarinya wacce batafi sa'ar Nafi ba rike da faranti zata shiga ciki, Ashraf yace " Little! " yafad'a tare da daga mata hannu. Cikin mamaki ta juyo, ganin Yayanta batasan sanda ta saki farantin ba wanda ke dauke da lemon kwalli akai ba, da gudu ta karaso gunsa ta rungumeshi, sai kuka. Ya dagota kadan yace " Little kukan fa? " Hawaye take tace " Yaya ina ka shiga? Hankalinmu ya tashi sosai. " Kanta ya shafa sannan yace " to naji ya isa haka, ya dan juya ya kalli Nafi yace " Little zan shiga ciki so nake ki shiga da wannan tai wanka taci abinci ki bata kayankk tasa. " Kallan Nafi tai sannan tace " waccece? " Yace "Zan fada miki, Mumy fa? " Tace " duk fa muna bangaren Umma muna zazzaune, mumy jiya cir ruwa kawai tasha. " Ya dan juya kai, little tace " Yaya ya kamata kaje ka ganta kafin ka shiga ciki dan da alama nan kafara zuwa. " Kai ya juya baice komai ba, Kallansa tai cikin rashin jin dadin yanda sam baya kula mahaifiyarsu sosai bayan kowa yasan yanda take tsananin sanshi, zatai magana kawai ta hango Aneesa ta taho da gudu, ganin tana kallan wani gun yasa Ashraf ya juya hakan yaba Nafi damar juyawa ta kalli gun itama. Da gudu ta taho sai data kusa zuwa inda suke sai kuma ta tsaya daga nesa ta kafe Ashraf da ido idanunta na zubar da hawaye, Nafi ta bi Ashraf da kallo, yanda taga yana kallan ta yasa tasan akwai wani abun tsakaninsu. A hankali Ashraf ya fara takawa zuwa inda take tana tsaye tana mai wani kallo mai tattare da ma'a noni sanda hawaye nabin kuncinta. Nafi tai tsaye jiki a sanyaye tana kallansu, sai da Ashraf yazo kusa da ita kawai ta gifta ta gefensa tasa gudu, ta kusa da Nafi ta wuce, ta nufi inda little ta nufa d'azu. Turus yai agun, jikinsa duk yai sanyi, little ta kama hannun Nafi tace " wuce mu tafi xasu fara abin nasu. " Sun je zasu shiga sai ga mutane kowa ya taho harda Mumy da Umma sun taho gun Ashraf, sudai suka karasa ciki. Kallan fallon Nafi tai, aranta tace " lalai rayuwa tana wani gun. " Sunje shiga d'aki Nafi ta kalli Little jin sheshekar kuka, Little tai murmushi tace" Neesan yaya kenan yau sai yayi lalashi mai karfi kafin abarmu musamu bacci. " Nafi ta kalli kofar d'akin jikinta ya kara sanyi, Little tace" karki damu inda sabo sun saba, ita shagwab'a shikuma saurin b'ata mata rai shiyasa wannan kukan harya fara daina damuna. " Nafi ta jinjina kai sannan tace " Amma kuna kama da ita. " Little tai murmushi tare da tura kofar d'akin tace " Yaya tace ta gurin uba, shi kuma ya Ashraf yaya nane na gun uwa. " Kallan mamaki Nafi ta mata tace " Ban gane ba. " Dariya Little tai tace"Maman Mu ce ta auri baban Ya Neesah bayan Baban Ashraf wato yayan babanmu ya rasu. " Nafi ta zaro ido cikin mamaki zatai magana sai idanunta yakai kan tangamemen d'akin, kallo tabi d'akin dashi cikin tsananin mamaki lalai dukiya tana wani gun, yanzu nan d'akine? Jitai Little tace " Yes. " Nafi ta hadiye wani yawu cikin mamaki, take kallan d'akin. Ashraf kam yana tsaye gurin 'yan uwansa manyan 'ya'ya maza na kanin babansa da kuma kannensa, yake kawai yakeyi dan shikansa yasan ba kowa bane yake farin cikin dawowarsa sannan shi ya kosa subarshi yaje ya lallab'a Neesarsa. Mumy ta kalleshi tace " Ashraf kai wanka sai kazo kaci abinci ko??" Ta sani sarai bazai amsa mata ba sai dai tasan zaiyi abinda tace, kallan yayen sa yai yace " Zan shiga ciki." Yana kai nan ya wuce, nan suka juya, dadi da farin ciki ya kama Mumy da sauri ta nufi hanyar kitchen dan shiryamai abinci, duk wannan kin kulatan da Ashraf yake sam bata ganin laifinsa tasan dole ya ji haushi daga mutuwar mahaifinsa ba dadewa ta sake aure kuma gidan datake da anan take sannan ta auri kanin mahaifinsa. Ashraf har ya nufi bangarensu ya zagaye ya koma bangaren su Aneesa. Nafi dake zaune akan gado sai dan tsalle take kadan taji ana kwankwasa kofa sannan taji muryar Ashraf ya na cewa "Neesah?? " Nafi tadaina wasa da gadon, tai shiru tana jin Ashraf, ya dan dade yana knocking kafin yace " shikenan Neesa na dauka kece ta farko da zaki fara farincikin ganina shine zaki shige d'aki kina jina ina magana? Shikenan na tafi. " Nafi tanaji daga ciki cikin wata murya mai salo da jan hankali tace " Amma yaya kasan halin dakasani kuwa? Jiya ko bacci kasa yi nai ina tsoron kar in fara ace min ga gawarka can. ......." Kasa karasawa tai, Ashraf ya murmusa yace " Neesah ki bud'e inganki please...." Nafi ta sauka daga kan gadon ta zauna a kasa, murmushi ta kakaro da kyar tace " dama ai baice yana sona ba, kuma ya sanar dani hakan, shikenan." Tanajin motsin bude kofar. Ashraf na shiga ya karasa inda take akan gado, tana ganinsa tasa pillow ta rufe fuskarta, Ashraf ya matso sosai saitin kanta ya kwantar da kansa yace " Ko kallo na bazakiyi ba? Na d'auka yau in kika fara kallona sai na kwace kaina? " Ta dago a hankali ta dan harareshi sannan ta dau pillow din ta makamai ta kara makamai, ta daga zata sake na uku yai saurin rikewa, yace " ya isa to dear ai kin huce ko? " Ya fada yana mata wani kallo....... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *For you my dear Friend Asiya Musa (Koxali) luv u soooo much😍* 9⃣ Little ce ta fito daga toilet ta kalli inda Nafi take tace " zo ki shiga kiyi wankan. " Nafi ta mike jiki a sanyaye ta karbi dan towel din da little ta mika mata, kallo tabi towel din dashi tace" dan wannan abun zan daura? " Little tai murmushi tace " to dame zaki daura? Ni shi kadai garen. " Kallan zanin jikinta tai tace " na d'aura wannan. " Little ta saki murmushi tace " ya sunan ki? " Nafi a kasan zuciyarta so take tace Nafisa sai dai ta rasa me yasa batasan akirata da haka tafisan tadinga jin wannan sunan daga bakin Ashraf, "Nafi. "ta fada tana Kallan little. Tad'anyi murmushi tare da mika mata hannu alamar gaisuwa tace "ni kuma Maryam amma little ake cemin ko kice little Maryam, mu biyu ne masu suna maryam babbar riketa akai agidan har tayi aurenta. " Nafi ba tare data mika mata hannu ba tace" li?? Hmm nidai Maryam kawai zan dinga ce miki. " Little tai murmushi sannan ta kara mika mata hannu tace " mu gaisa to. " Nafi ta noke tare da girgiza kai tace " ba maza bane ke gaisawa?" Little ta fizgo hannun Nafi tace "Mata ma nayi ai musabaha ce. " Kai Nafi ta jinjina, little tace "shekararki fa? " "16." Little tad'anyi tsalle kadan tace "nima haka. " Sukai murmushi a tare, Nafi ta daura zani ta nufi inda little ta kira da bayan gida, Da gudu Nafi ta dawo ta kalli Little tace " kina nufin anan zanyi wanka? Ta ina? Ta yaya kuma? " Little ta kalleta tace "muje in nuna miki." Nafi ta ja ta tsaya, Little tace "Nafi muje mana. " Dum Nafi ta mata itadai tsoro take ta ina zatai wanka a wannan gun? Little tadan had'e rai tace "Shikenan bari in je in fadama Ya Ashraf. " Da sauri Nafi ta rike rigar Little jin an anbaci Ashraf tace "Zanje Maryam. " Little tadanyi dariya tace "muje to. " Sunje toilet nan Little ta nunama Nafi yanda zatai wanka, ganin hankalin Nafi yaki kwanciya da shaya yasa little ta tararmata ruwa a baho tace hakan fa? Nafi tai murmushi alamar gwara hakan. Nan little ta fita ta barta. ********** Ashraf kam suna shiryawa da Neesah ya wuce bangarensa, ko ince bangaren mahaifinsa shikadai ne a bangaren saboda duk yanda akaso asashi cikin 'yan uwansa maza kin yarda yai yace " lalai shidai a bangaren Mahaifinsa yake san zama. " Yana shiga ya wuce toilet yai wanka ya zura doguwar riga sannan ya fara rama salolinsa. Bayan ya idar ne yaga sakon meeting a babban falo, in kuwa za'ai wannan taron to acan ake cin abinci. An sanar da kowa akan akwai meeting a babban falo saboda dawowar Ashraf. ********** Nafi ta fito daga wanka ta shafa mai kawai littleta bata doguwar rigar atamfa tasa, saboda little ta fita kiba hakan yasa rigar bata mata kyau ba ga wuyan rigar sai fad'owa yake, ga ta kima daurin dan kwalinta ta matse kanta tamau. Itadai little taso mata magana sai dai tasan daga zuwan mutum gari bazai wuyo ace ya canza abinda ya saba ba, gashi tana tsoron karsuyi latti wajen meeting. Nafi na gamawa little ta kama hannunta tace "muje ko? " Nafi wanda gabanta ke faduwa tace " Maryam gani nake ni bai kamata inje ba. " Dariya Little tai tace"to yaya na kira na tambaya yace muje tare yanasan introducing d'inki. " Nafi ta kalleta da mamaki tace "me? Inkiro me? " Dariya little tai tace "ke dai muje kawai. " Nan suka fito sunyi sa'a Neesah ta riga ta fita, nan suka taho har zuwa babban falo. Katon falo ne sosai wanda gefe aka kawatashi da wani round din dinning table manya guda biyu, d'aya maza ne a zazzaune d'ayan kuma mata ne, sai dai duk a kusa da juna suke. Tunda suka shigo kowa ya zubama Nafi ido yana mata kallan mamaki sai dai banda Ashraf wanda ke zaune fuskar nan tasa kamar yanda ya saba a murtuke, Haka little ta jata har zuwa inda zasu zauna. Zuciyar Nafi kam kamar zata fado saboda tsananin tsoro da ganin mutane dayawa maza da mata, kanta na kasa, sunje zama kawai tai tuntube ta fad'i, kwashewa akai mata da dariya sai ta samu kanta cikin tsananin tsoro ta kasa mikewa, Ashraf ne ya kallesu ran nan a had'e ya kalli Nafi wanda itama shi take kallo ya mata alama data tashi. Jiki a sanyaye ta mike little ta taimaka mata ta zauna. Kanta ta sunkuyar, kawu yai gyaran murya hakan yasa kowa ya nutsu yace "Bismillah." Nan kowa ya fara zubama kansa a binci, Umma kuwa mahaifiyar Aneesa da ita Aneesan sun kafe Nafi da ido. Kowa ya fara zuba abinci, itadai Nafi a zaune take sai gabanta dake ta faduwa, ganin batada niyyar zuba abinci yasa Little ta zuba mata shinkafa da miyar carras sannan ta matso mata da papper chiken da salad, Nafi ta kalle ta sannan ta d'au chokali, ganin yanda kowa yakecin abinci yasa ta fara cin shinkafar a hankali, sai dai lomarta biyu taji inaa bazata iya cigaba da ci ba, gani tai kamar kowa kallanta yake, ta zaune tare da matse kafafuwanta dake rawa, little ta kalleta tace "Nafi tafiya fa kikai kici abinci mana? " Nafi ta kakaro yake tace " a koshe nake ai naci abinci a mota Yayanki yaban doya da kwai. A hankali sukai maganar, Ashraf yadan kalli inda take ganin bataci abinci baiyi mamaki ba, ta ina zata iya cin abinci a cikin mutane? Bayan kowa ya gama ne Kawu yai Hamdalla sannan ya fara magana "Alhamdulila Allah ya taimakemu d'an mu ya dawo da ransa da kuma lafiyarsa wannan ba karamin abin farinciki da alfahari bane, lalai Muna godiya ga Allah wanda yasa muke zaune yau da Ashraf kamar yanda muka saba. " Kowa ya jinjina kai alamar jin dad'i, akace Ashraf yai magana. Shiru yadanyi nawasu dakika kafin yace " Nagode da kulawarku, Sai dai inaso in nuna muku Nafeesa wacce itace sanadiyar zamana anan gurin haka, Itace wacce ta taimakeni a lokacin da nake tunanin yanke alaka da duniya, Allah ya kawomin ita ta taimakeni ta ceci rayuwata. " Jin haka yasa kowa ya kara kallan Nafi wacce kanta ke kasa, sai gabanta daya tsananta fad'uwa. Wani daga cikin mazan gun yace "Lalai Ashraf to dan ta taimakeka shine ka taho da ita nan ko me? Iyayene batadaso ko me? " Ashraf ya bugamai wani kallo baice komai ba, Umma mahaifiyar Aneesa tace "Ashraf ina ganin gaskiya Nuhu ya fada in ta taimakeka sai a bata kud'i ban gane dalilin tahowarka da ita ba. " Ashraf ya dan kalleta kadan nan ma bai tanka ba, Mumy tai murmushi tace " tunda ya taho da ita akwai dalilinsa nayin hakan nasan halin Ashraf sarai. " Kansa ya juya sai dai fuskarnan a had'e take tamau, nan aka dan fara musu wasu suce ya kamata wasu suce bai dace ba, Anisa kam kallan kyana kawai takema Nafi. Cikin wata kakkausar murya mai zafi Ashraf ya mike yace " Me? Dan na taho da yarinya shine ake cece kuce? A kan wani na ajiye ta ko me? Ko kuwa anaso ace ni Ashraf ban isa in kawo wanda na ga dama cikin gidan nan bane? " Wannan kalamai dayai ya gigita kowa itakam Nafi idanunta ne suka ciciko tsoro ya kara kamata, Kawu ya kalli Ashraf yace " Kada ka manta Ashrac akwai iyayenka anan, taya dan ranka ya baci zaka hada da kowa ka fara fad'a? " Ashraf ya kalli Asim sannan ya kalli inda Nafi take yace "Duk wanda yake ganin hukunci na bai mai ba sai ya tareni muyi magana. " Yana kai nan yai waje, Umma tabishi da kallo, Mumy kam da sauri ta mike ta bishi. Nan aka cigaba da 'yan maganganu, little ta kama hannun Nafi tace "Nafi mu bar nan ko? " Suna kokarin mikewa sai ga Ashraf ya dawo daga bakin kofa kawai ya kalli Nafi sannan ya kalli Aneesa yace " Neesah inasan ganinki. " To fa gani nai Nafi ta mike itama Aneesa ta mike, Umna ta kalli Nafi tace " ke yake kira? " Nafi wanda itakam jitai kamar yace "Nafeesa"tai tsuru tana kallan Umma. Aneesa wani haushi ya kamata, a zuciye ta bangaje Nafi tai gaba. Nafi ta tsaya cak kamar gunki sai hawaye, Kawu ya mike shima da zuwanta bai wani burgeshi ba yai waje. Little ta taso ta kama hannunta Asim yasa dariya yace "ko dai akwai wata manufa ne a tahowa da wannan kwailar? " Yai maganar yana kallan Nafi aka kwashe da dariya, sudai sukai waje. Suna fita Nafi tasa kuka. Aneesa kam a gefe taga Ashraf ta karasa inda yake fuska a had'e tace " menene? " Shima fuskarnan a had'e yace " ki fadama ummanki tadaina min abinda takemin menene nata dan na taho da Nafisa? Akan wani zata zauna? Ko kuwa yarinya ce ita daza'ace wanka ma yi mata za'ai? " Aneesa ta kalleshi cikin bacin rai tace " Yaya dama saboda kamin fada ka kirani? Sannan yanzu kace Neesah amma dayake yarinyarcan yar rainin hankali ce ta d'auka wai ita kake kira. " Ashraf ya kalli su Nafi dake tahowa ganin tana kuka ya kalli Aneesa yace " ki fadama Umma tadaina min haka sannan kema na dauka ko me na kawo gidan nan zakibi bayana in har kina sona, na gode da nunamin din dakikai abinda nake tunani ba haka bane. "yana kainan yai gaba. Nafi tabi bayansa da kallo sannan ta kalli Aneesa ta maida kanta kasa. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Kuyi hakuri jina shiru da kukai jiya, na shiga tarone wlh kuma dana dawo na gaji.....na gode kwarai da kulawarku da kuma san da kukema littafin nan*😍😍 1⃣0⃣ Little ce rike da hannunta kawai tana tafiya amma idanunta nakan Ashraf dake tafiya, Aneesa kam har wuya tazo ganin yanda Ashraf ya hauta da fada akan wata banza kucaka, da saninta ta taho ta mangaje Nafi wanda har sai da ta kusa kai kasa, Little ta kalleta tace "Haba Yaya Neesa? " Aneesa ta kalli Nafi tace "Sorry ban kula ba."tai gaba. Little ta kalli Nafi wanda ta kakaro murmushi tace "Maryam karki damu ai bata kula bane, kuma taban hakuri. " Little tai karamin hucci tace" Nafi kiyi hakuri. " D'aki suka shiga, Nafi ta zauna a kasa, little na shirin mata magana wayarta tai kara, da sauri ta d'aga tace "Naam Yaya. " Daga can bangaren Ashraf yace " Little ki samarmata abinci dan banaji taci wani abinci. " To, little ta fad'a tana kallan Nafi wacce itama hankalin ta ke kan Little tunda taji ance Yaya. Little ta kashe wayar sannan ta kalli Nafi tace "kinga Yaya ma ya kula bakici abinci ba." Nafi tad'anyi murmushi, hakab yasa Little tai waje. Ashraf kam yana shiga bangarensa ya kwanta a kan kujera doguwa dake falo, hannu yasa akan goshinsa, meyasa duk sanda akace za'ai meeting indai har saboda shine sai an b'ata masa rai? Yai dan karamin tsaki zai juya yaji sallama, muryar Mumy ce hakan yasa ya amsa sama sama. Mumy ta shigo ciki, shi kuma ya mike daga kwanciyar da yai ya sauka kasa, mumy ta karaso ta zauna akan kujera, kansa na kasa bai ce komai ba. Kallansa tai cikin tsananin kulawa tace "Ashraf kayi hakuri. " Batare da ya d'ago ba yace " Ya wuce ai tunda dai ba wanda ya isa ya fitar da ita daga gidan. " Mumy ta jinjina kai sannan tace" Ashraf a gaskiya nima hukuncinka bai min ba, bana ganin dan ta taimakeka ya kamata ka taho da ita, sai dai in akwai wani dalili bayan wannan. " Bai kalleta ba haka kuma baice komai ba, Mumy ta cigaba " ba komai nasan tausayinta ne yasa ka taho da ita insha Allah nikuma zan kula da ita. " Yanzu kam ya d'ago ya kalli Mumyn sai dai baice komai ba, tai murmushi dan ta gane yaji dadin maganar ne tace "Ashraf zuwa nai muyi wata magana. " Inaji kawai yace. Tace " Baka ganin lokaci yayi da zaka fara aiki a company d'in mahaifinka?? " Kallanta yai cikin mamaki yace " Ba Kawu da Asim suna kula da company d'in ba? Meye kuma nawa na fara aiki acan?? " Mumy cikin damuwa tace " Ash raf mai yasa kake abu kamar bakasan komai ba? Companin nan na mahaifinka ne fa? Kai kad'ai ne d'ansa sannan ya bar maka share d'in sa gaba d'aya kanada 50% na share d'in company d'in kafi kowa, akan me zakayi ta zama a gida bayan ka gama karatu? " Ashraf ya mike tsaye yace " Mumy banasan wannan maganar dan Allah. " Jikinta a sanyaye tace " Ashraf? " Ya d'an kalleta sai dai bai ce komai ba, mikewa tai a hankali tai waje, yabi bayanta da kallo tare da dafa kansa, meyasa kowa ba ya hango abinda shi yake hangowa? Idanu ya runtse yana tuno sanda akace fatiha an d'aura auren Nafi da Ashraf, yai wani hucci sannan ya mike kawai ya zari makulli yai waje. ************ Sosai Nafi ta ci abinci, ji take wani dad'i na ziyartarta, tanaji tunda take bata tab'acin abinci mai dadi irin wannan ba, tas ta cinye wanda little ta zubo mata, ta kwankwad'i lemon kankana mai sanyi da ke cikin jug, wata gyatsa tai sannan tasa dariya ita ka dai. Ita kad'aice a d'akin dan little ta fita, tace " oh yau banyi gyatsar nono ko madara ba." Ta sake yin dariya tace " Kai abincin nan yayi dad'i, wannan kuma ko menene?" ta fada tana d'aga ragowar juice d'in kankanar data sha, tace " Tabdi lalai akwai abin dad'i a birni." Sai dataji abincin ya tsirga mata saboda cin datai dayawa, tad'au tiren kamar yanda Little tace mata ta maida kitchen. Ta fito ta kalli gabas inda little ta mata kwatance, ta fara tafiya, tafiya kawai take, gani tai ta b'ata nan ta shiga waige waige, jitai ance " Ke." Juyowa tai cikin mamaki, Ganin umma uwar Aneesa yasa tai saurin yin kasa dakanta, Umma tace " Dan gidan ku uban me kike anan? " Nafi cikin tsoro ta fara magana cikin in in na tace " Um kitchen nake nema. " Umma ta kalli kwanon sannan tad'an tabe baki tace " Kwarai dole ai, a can kauye ba'a sami damar zakewa aci abinci ba shiyasa ake neman bud'e mana ciki? " Nafi wanda jikinta duk ya gama mutuwa ta kasa magana sai motsa baki kawai take. Umma ta kalleta kallan banza tace " wuce muje kitchen d'in. " Nafi ta kalleta da mamaki, Umma tace " To munafuka bakijini bane kike kif kif da ido? " Nafi tai saurin yin kasa dakai, nan tai gaba Nafi ta bita. Sun isa katon kitchen d'in inda masu aiki keta hidima Umma ta tafa hannun ta hakan yasa duk suka taho, Umma ta kallesu tace " Yauwa dama so nake in sanar daku kun samu kari. " Kallan juna sukai na mamaki, tasa hannu ta finciko Nafi tace " gatannan da safe zatazo ta tayaku aiki sannan da rana ma haka." Nafi ta kara kasa da kanta, Umma tace "na umarceku ku sata aiki sosai, saboda ita ta fiku cin riba dan inda zata kwanta yafi naku haka abincinta da suturarta tafi taku. " Suka amsa da to, ta kalli Nafi tace." Ke kuma dan gidanku kullum da sasaafe in ganki anan hakama da rana, bazaki dinga cin abinci a banza ba. " Nafi ta d'aga kai, Umma taja kunenta tace " kuma wlh inji maganarnan abakin wani ko da Little ce bare Ashraf Allah sai kin gane kuranki. " Tana kai nan tai gaba. Nafi tai shiru, jitai ance ajiye kwanukan ki tafi gobe kya fara zuwa, Nafi ta kalli mai maganar wata babba ce a kalla zatai sa'ar Innarta, ta ajiye tiren sannan ta gaidasu tare da musu sallama. ********** D'aki ta koma ta zauna a kasa tai shiru, bacci ne yai gaba da ita. Ashraf kam bayan ya fito daga d'aki Aneesa yama waya yace ta fito ta rakashi an guwa. Jifatu ya wuce da ita, tanata murna ganin yau gata ga masoyinta, suna tafiya ne ta kalleshi tace " Yaya ya maganar sa ranar da akai ai tana nan ko? " Ya kalleta tare da murmushi yace " eh mana ko musa a kara matsowa da shi? " Idanu ta rufe tace " Kai yaya wata biyu ai kamar yau ne. " Aneesa ta kalleshi cikin tsananin farinciki tace " Yaya wlh ni kad'ai nasan missing dinka danai jiya. " Titi kawai ya kalla baice komai ba sai murmushi da yai. A bakin jifatu yai parking, nan ta fito shims ya fito suka shiga ciki, bangaren kaya na atamfofi lace da mayafai sukai, ce mata yai kawai ta zab'a, hakan yasa tai tunanin nata ne, sosai ta jidi kaya shima yana tayata, suks wuce gun takalmi, nan ne dai yace banda takalmi sai dai jaka, saboda shikam yasan baisan size dinta ba. Itakam Aneesa sai farin ciki take har suka gama zaben suka fito, sun shiga mota ta kalleshi cikin kauna tace " Yaya na gode sosai. " Ya kalleta cikin mamaki yace " name fa? " Tace "na kaya mana. " Murmushi yai yace "Aneesa ke kuma mai zakiyi da kaya? Duk yawan kayanki? " Fuska ta had'e tace " na waye to? " Ya kalli titi yace " Nafeesa. " Gabanta ne ya fad'i cikin tsoro ta kalleshi sai dai gani tai shi ko a jikin sa, ranta yai mugun b'aci........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 1⃣1⃣ Ashraf ne ya kalleta kadan yace "Aneesah tailorn ki kuwa yana nan? " Fuska ta kara daurewa tamau tace " menene? " "kayan Nafisa nake tunanin muje akai mai can naga ba laifi ya iya d'inki sosai. " Jitai zuciyarta na neman tsagewa saboda takaici, rasa ma mai zata cemai tai, kawai sai ido ta bishi dashi, ganin kamar bai ma fahimci ranta a b'ace yake ba yasa tace " Yaya d'anyi parking." Cikin mamaki ya kalleta yace " parking kuma? " Kai ta d'aga hakan yasa ya gangara gefen titi, ta bud'e kofar ta sannan ta kalleshi tace " randa zaka fita domin ni ka d'aukoni amma bazan zauna kusa da kai domin wata ba. " tana kai nan tai waje, ya bita da kallo cikin mamaki, me take nufi domin wata? Yana kallanta ta tari adaidaita, ga magrib ta kawo kai,shima ya ja mota yai gaba. Aneesa na shiga mota ta fara matsar kwalla dan tsabar takaici ita zai d'auka su zaboma wannan kucakar kaya? Tana isa gida ta wuce gun ummanta da gudu nan ta sanar da Ummanta duk abinda ya faru sannan ta d'ora da cewa " Umma kinga lesukan dana zab'a kuwa? Na d'auka nawa ne? Ina wannan kucakar ina sa kayan dubu talatin? " Umma ma da ranta yakai kololuwar tashi tace " kwantar da hankalinki ita d'in banza? Har ta isa tasaki kuka? Bare har ta had'aku fad'a da Ashraf?" Aneesa ta goge kwallarta tace " Umma me Ashraf yake cemin? " "Neesah mana, tun kina karama yake fad'a miki haka shi yasa wasu ma haka suke ce miki." Aneesa tai kwafa tace " to Umma tunda na cemai wannan yarinyar ta d'auka ita ya kira d'azu bai sake cemin Neesah ba har yanzu. " Umma ta kanne ido cikin b'acin rai tace " Aneesa kada ki kuskura ki kara yadda Ashraf yasan bakyasan yarinyar nan, sannan karki kara yimai musu akanta." Aneesa ta mata kallan mamaki, Umma tace " tabayan gida zamu b'ulo mata, ni na fad'a miki bazata cika sati a gidan nan ba zata d'auki tsuman kafafuwanta tayi gaba. " Aneesa ta jinjina kai alamar gasuwa tace " Umma ni ko ganinta ma bana sanyi wlh. " Umma tai murmushi tace " d'aure kinji 'yata, sati d'aya yayi yawa. " Nan sukai murmushin mugunta su dukansu. Nafi kam tana zaune a d'aki ita kad'ai mahaifinta ne ya fad'o mata a ranta tace " ko baffa yana me? " Jitai an kwankwasa kofa hakan yasa ta mike tare da yafa d'an kwalinta ta bud'e kofar, Matar data gani d'azu itace ta gani yanzu, ko ba'a fad'a ba tasan Mahaifiyar Ashraf ce, murmushi ta mata sannan tace "fito falo muyi magana." Tai gaba Nafi ta bita a baya, akan kujera ta zauna hakan yasa Nafi ta zauna daga nesa kadan a kasa, Mumy ta kalleta tace " ya sunan? " "Nafi. " ta fad'a kanta a kasa. Mumy tace " Nafisa kenan ai." Nafi tace " Eh." tai maganar cikin sanyin murya. Mumy ta kalleta da gani batafi sa'ar Little ba tace " kinsan ko ni wacce? " Nafi tad'an kalleta kad'an sannan tace " Mamar Dan Binni ko? " Mumy tai dariya tace " Ashraf kenan? " Kai ta d'aga itama tana murmushi, Mumy tace " Nafi iyayenki fa? " Kallan Mumy tai jiki a sanyaye batace komai ba, Mumy tace " Nafi karkiji komai ki sanar dani duk abinda ya faru babu wani abu, ni mahaifiyar Ashraf ce." Nafi tai shiru me zatace? Me zatace? Jitai Mumy tace " Nafi!! " A hankali Nafi tace " Mahaifiyata ta koma saudiyya da zama, mahaifina shine yake kokarin aurar dani ga babban mutum shine Dan binni ya taho dani. " Mumy tai shiru ba shakka yarinyar abin tausayi ce amma ita tasan Ashraf sarai shi ba mai shiga abinda bai shafeshi bane bare har ya d'auko yarinya daga gaban mahaifinta. Ta kalli Nafi tace " Kidinga kirana Mumy kamar yanda kowa yake cemin, sannan ki saki jikinki kamar nan ma gidanku ne. " Nafi ta d'ago ta kalli Mumy idanunta suka ciciko, Mumy tai murmushi tace " Karki damu kinji? Sannan karki kara cema Ashraf dan binni kidinga cemai Yaya kamar yanda kowa ke cemai. " Ta d'aga kai, ba shakka yanda taga yanayin 'yan gidan lalai in tsautsayi ya sa akasan an d'aura musu aure da Ashraf to fa lalai tanaji ko Mumy bazata sakar mata fuska ba. Nan Mumy ta mike tace " Little ba ta dawo ba? " Nafi tace " eh. " Mumy ta jinjina kai sannan tai waje. Nafi tabi bayanta da kallo sannan tai murmushi. Mumy na fitowa daidai nan Ashraf ya dawo daga masallaci yana shirin yima little magana, ganin Mumy ta fito yasa gabansa ya fad'i, yasan mumy da fasaha da iya bugar ciki da alama taje ta bigi cikin Nafi ta fada mata komai, Mumy na wucewa yai wuf ya shiga bangaren. Nafi lokacin ta mike kenan zata shiga d'aki, jin sallamar Ashraf yasa ta tsaya cak ta kasa juyowa sai dai ta amsa, Ashraf ya shigo da hanzari yazo daf da ita yanda har numfashinsa take jiyowa hakan yasa gabanta ya shiga bugawa, juyowa tai cikin tsoro hakan yasa suka fuskanci juna daf da daf, gabanta ne ya cigaba da fad'uwa har tanaji kamar shima yanajin bugun da zuciyarta yake. Shikam cikin rashin damuwa yace " Nafi me kika cema Mumy?" Kasa magana tai sai bakinta dake motsi shi kadai, Ashraf cikin takaici yace " kin fada ko? " Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ke nake jira me kika ce mata? " Gaba d'aya jitai ta kasa magana, da sauri ta murda kofar d'aki ta shige tabarshi a nan, tana shiga ta sulale ta zauna a kasa, ya za'ai ya matso mata haka daf yace wai tai magana? Ashraf yabi dakin da kallo cikin takaici ya juya yai waje, yana zuwa kofa Aneesa na shigowa, tana ganinshi tai murmushi tace " Yaya sry ina gun Umma ne. " Fuskar nan a had'e dama ransa ya gama b'aci yace "Ni har zaki rainawa hankali muna tafiya dake ki fita ki hau adaidaita? " Kallansa tai cikin mamaki ta d'auka hakuri yazo bata, ta daure tace " Yahkuri Yaya dazun ne raina a b'ace yake. " "Na gane" kawai yace ya wuceta yai gaba. Kallansa tai cikin mamaki. Ashraf yai waje a zuciye, d'akinsa ya wuce. Itakam Nafi anan take a zaune har Little ta dawo wajen Isha'i, ta kalleta tace " Nafi me kike a nan? " Nafi ta mike ba tare datace komai ba ta nufi ban d'aki, sai kuma ta dawo tace " Maryam taramin ruwa inyi alwala dan Allah. " Little tai murmushi sannan ta ajiye takardun data amso ta tara mata. Little ta kula da yanda Nafi take sallah tasan kuma da alama batamasan me ake cewa ba, sunci abinci wanda Little ta d'auko musu sannan suka zauna hira, Little tace Nafi ta bata labarin rayuwar kauye. Nan Nafi ta fara bata labaruruka tace " ni ba shiga mutane nake ba amma fulanuwa masu tsayawa a rafi gunsu nake zama. Little tayi dariya sosai in taji wani labarin cikin labarin ta bige cikinta akan sallah. Nafi tace " Ni kawai yi nake yanda naga Innata tanayi. " Little tace "Zan koya miki yanda akeyi. " Nafi cikin farin ciki ta amsa da to. Sun dade suna hira sosai kafin su kwanta. *********** A bangaren Mumy kuwa ta sanar da mijinta abinda ya faru acan sannan ta karasa maganar da cewa " Alhaji kasan halin Ashraf tunda kaga ya d'auko yarinyar nan to tabbas tausayinta ne yamai yawa gashi ta taimakeshi. " Kawu yai shiru can yace " shikenan Hajiya dama ni ban ce komai ba mamaki nake yanda akai Ashraf har ya shiga abinda ba nashi ba. " Mumy ta ce" nima wannan abun ya ban mamaki sai dai inaji a jikina akwai dalilinsa nayin haka. " Kawu yai murmushi yace " ai dama Ashraf baya laifi. " Ta kalleshi kawai tai murmushi batace komai ba. Ashraf kam ya kasa zama,yanzu in akaji ya auri wannan kucakar ai an gama zubar mai mutunci, hakan yasa ya kira wayar Mumy. Da mamaki Mumy ta kalli mijinta sannan ta kalli wayar, cikin tsananin mamaki ta daga tace "Ashraf? " Gyaran murya yai sannan yace " Mumy dazu me Nafi ta ce miki? " Mumy da mamaki tace " me ya faru? " Yace " ba komai, sai da safe. " Da sauri ganin zai kashe wayar tace " Ashraf!" Naam kawai yace. Nan ta sanar dashi duk yanda sukai, ajiyar zuciya yai sannan yai saurin kashe wayar, mumy tabi wayar da kallo cikin mamaki da rashin fahimta sai dai hakan a tabbatar mata akwai wani abu. Ashraf yabi wayar da kallo tare da furzar da wata iska yace " Da alama tanada wayau." Murmushi yai sannan ya zauna a bakin gadonsa. *THE INNOCENT TEAM* Copied By HAYATU BABA ZUBAIRU (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen2⃣) WHATSAPP NO: +2349030159301 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 1⃣2⃣ Karfe hud'u Nafi ta bud'e idanunta kamar yanda ta saba, shiru tai daga kwance tana tuno mahaifinta ta kalli little wacce take ta baccinta hakan yasa itama ta koma bacci. Har asuba tai Little ta tashi tai Sallah Nafi bata farka ba, ganin ta idar yasa tadan tab'a Nafi, da karfi Nafi tace " Baffah kayi hakuri na tashi wallahi. " Ta fada tare da mikewa zaune da sauri, little tad'anyi dariya tace " Nafi nice! Da alama Baffan nan bulala yake miki. " Ajiyar zuciya Nafi tai ta kalli Little tai murmushi kawai batace komai ba. Little tace " Tashi kiyi sallah. " Nafi ta amsa da to tare da mikewa tsaye tace "kin tarar mi..... " Katseta Little tai tace "Na tarar miki ke da bakya mantawa. " Nafi tai toilet tana murmushi. Bayan tayi Sallah ne ta kalli Little wacce ke kwance kan gado da alama bacci zatai tace " Maryam naga kin kwanta?" "Me zanyi to? Bayan sai karfe sha d'aya zan fita?" Nafi tace" nima me zakiyi a kwancen nake tambaya. " Little ta zauna tare da kallan Nafi tace " Bacci mana. " Idanu Nafi ta zaro tace" Bacci kuma? Mu kwana muna kwanciya yanzu ma ki kwanta? Tab di. " Little tai dariya tace " Uhm hm i kam dai bacci zanyi. "tai maganar tare da kwanciya. Nafi ta kalleta tana mamakin wannan al'amari, mutum ya kwana yana bacci sannan ya kara kwanciya da safe? Shi ba ciwo yake ba? Ganin tana ta zaune ga zaman ya fara isarta yasa ta mike sanye da hijabin datai Sallah tai waje. Ba kowa a wajen garin ya yi hasken gabanin asuba ta kalli katun gida a ranta tace" Masu gini sun sha aiki. " Kitchen ta nufa tana tafe tana kara kallan gidan mai cike da sha'awa, sukam 'yan kitchen sunata hada hadar aiki, ta gaishesu suka amsa cikin sakin fuska, Matar jiyar nan ta kalleta tace " yanaga kinzo da wuri? " Nafi ta dan murmusa tace " in ma na zauna ba abinda zanyi shi yasa naga gwara na taho. " Kai ta jinjina, Nafi ta kallesu tace " me zan fara? " Wata daga ciki ta kalli matar tace " Goggo me zatayi? " Goggo tai shiru can tace " ke wani bangare kika fiso? Akwai masu wanke wanke? Akwai masu bangaren dake dake da yanke yanke akwai masu bangaren girki. " Ba tare da dogon nazari ba Nafi tace "Nafisan b'angaren masu abinci saboda inaso in iya irin abincin jiya. " Dariya suka sa mata, Goggo tace " Bangaren Abinci fa sunfi kowa wahala saboda da safe kowa da abinda yakeso a dafa mai, wani sa'in da rana ko dare ma haka." Nafi tace " Bakomai." Nan ta zauna gun Goggo, takarda Goggo ta dauko ta shiga karanto abinda za'ama kowa yau, sunyi sa'a wasu suna zuwa iri d'aya, nan suka shiga aiki. Nafi dai sai dai juyawa dan ko sunan abubuwan bata sani ba bare ta dinga mikowa. An fara da masu fita karfe takwas, sai da aka gama dasu sannan aka fara ma 'yan gida su kuma nasu aka fita dashi. Nafi kam abin sai birgeta yake, sai wajen karfe tara suka gama, Nafi ta musu sallama ta tafi. Har sanda ta dawo Little na ta uban bacci, Nafi tanasan tai wanka gashi bata iya bud'e famfo ba, dole kawai ta samu guri ta zauna a kasa. Bacci ne yai gaba da ita, wajen 9 da rabi sukaji ana kwankwasa kofa, da sauri Nafi ta mike tare da bud'ewa, Wasu yarane su biyu d'auke da ledoji suka kalli Nafi sukace " Dama Yaya ne yace mu kawo ma Yaya Little. " Little dake zaune akan gado tace "Amra ku shigo mana. " Nan suka fara kokarin jan ledar, Nafi ta amsa ta shiga dashi, little ta kalli kayan tace " me yace?" Wacce ta kira da Amra tace " cewa yai mukawo miki zai kiraki. " Amra na rufe baki kuwa sai ga kiran Ashraf, da sauri tai gyaran murya dan ya hanata wannan baccin, tace "Yaya ina kwana? " Yace " kinga dama kin tashi? " Kallan Nafi tai sannan tace " Yaya ba bacci nai ba. " "Hmm ai inaji gaba ni da kaina zan dinga zuwa ina dubaki." Little ta d'an turo baki sannan tace " Yaya ga su Amra sun shigo da ledoji." Yace " Yanzu za'a kawo manyan, naga su bazasu iya d'auka ba ko kuma turo Nafi ta dauka. " Little tace " to kana ina? " Ina gun motor park, Sai Amra ta rakota. " Little tace " to amma yaya kayan meye? " Kayan Nafi ne so nake da yamma inkin dawo ki d'au driver ya rakaki gun mai d'inkinki sai a gwadata a mata. " Baki little ta bud'e to kawai tace tanaji ya kashe wayar. Nafi ta kalla ta fadamata sakon sa tare da cewa kimai godiya daga nan duk ke ya siyowa kayan. " Cikin mamaki Nafi tace ni kuma? Little tace " eh mana ya san baki da kaya ga nawa sun d'an miki yawa. " Nafi tai shiru tana mamakin ledojin da aka kira da nata. Little ta katseta "ki tashi dan Yaya baisan jira. " Nan suka mike itada Amra. Yana zaune cikin mota kafafuwansa na waje sannan hannunsa rike yake da waya yana dannawa. Nafi ta karasa inda yake ta tsugunna ta gaidashi, kallanta yai kawai maimakon ya amsa sai yace " kema daga baccin kike? " Kai ta girgiza alamar a'a, yace " ki d'au kayan suna bayan mota." Nafi ta mike a hankali har ta je inda zata d'auka sai kuma ta dawo inda yake ta tsaya kyam tana wasa da 'yan yatsun hannunta, Ashraf ya kalleta yace " Nafeesa da wani abun ne? " Yawo ta had'iya sai dai ta kasa magana, ganin haka yasa ya cigaba da danna wayarsa baice mata komai ba shima. Nafi kam tayi tsuru ta kasa magana, Amra kam tafiyarta tai ya rage saura su biyu, ta dade agun kafin ta daure tace " Yaya. " Dasauri ya d'ago ya kalleta, tai saurin yin kasa da kanta dama abinda ta kasa fada kenan. Kallan mamaki ya mata sai kuma ya maida kansa kan waya. Ta kara daurewa tace " Yaya Na gode. " Tana fada ta juya zata d'au kaya, jitai yace " Nafisa!! " Tsaya wa tai cak sannan ta juyo a hankali cikin tsoro, ya kalleta kad'an sannan yace " Jiya me yasa kika rufemin kofa ina miki magana?" Kanta na kasa sai gabanta dayake fad'uwa, Ashraf yace " meye dalili? Ko raini ya fara shiga tsa...... " Katseshi tai da sauri da cewa " Wlh ba haka bane, matsowar dakai kusa danine yasa gabana yaketa fad'uwa shiyasa na rufe. " Da mamaki yake kallanta yace " Nafisa yaushe kika koyi karya? " Idanu ta zaro cikin mamaki tace "Wlh ba karya nakeba Yaya. " Ya d'an kura mata ido hakan yasa tai kasa da kanta, a ransa yace " dole dan da alama namiji bai taba tsayawa kusa da ita haka ba. " Wani abu ya tuno ya d'auke kansa daga kanta a hankali yace " da alama sanda kika ciren riga gaban naki bai fad'i ba " Idanu ta zaro da sauri ta juya ta fara tafiya, ya kalli yanda take sauri yace " kayan fa? " Idanu ta rufe, cikin tsananin kunya ta shiga neman tahowa gun idanunta a rufe, batasan har tazo inda yake ba, jin tayi dan tun tube da kafa yasa ta bud'e ido da sauri, Ashraf ya kalleta yace " Toh da alama gaban naki baya fad'uwa ko? " Tsugunnawa tai da sauri cikin tsoro tasa kanta a cikin cinyoyinta, idanunta suka ciciko, Ashraf ya mike tare da d'anyin murmushi, ya matso saitin kunnenta yace " in kin gama kunyar sai ki rufemin mota. " Tanaji ya tafi, ta dade kafin ta mik'e ta shiga bubuga kanta a hankali a jikin motar, jin goshinta ya fara zafi yasa ta d'au kayan tare da rufemai mota tai gaba. Tana isa d'aki ta taradda Umma da Aneesa a zaune, gefe kuma Little ce tsaye da towel da alama wanka zatai. A hankali cikin tsoro ta shiga d'akin, tare da ajiye kayan, Umma tace " Yauwa Ke muga ledar nan. " Nafi ta mika ma Ummaa taja gefe ta tsaya, Umma ta kalli Aneesa tace " wanene lace d'in? " Aneesa ta ciro wani dankararen lace wanda kana ganinsa zakasan lalai mai tsada ne na gaske. Little ta kalli Umma tace " Umma nikam yaya fa bai fadamin ba?" Umma tai murmushi tace " Little kenan bakiji me nace ba? Nice na aiki Aneesa ta fara siyomin kayan biki ita kuma ta manta ta bashi a cikin kayan wannan. "ta fada tana nuna Nafi. D'aukan lace din sukai suka tafi, little ta shiga toilet ranta duk a b'ace. Nafi kam ko ajikinta dan batasan darajarsu ba, itadai kunyar Ashraf ce ta kara kamata ya zatai inta ganshi? *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *I Sincerely Dedicated This Page To All Masoyan Xuciya, Nagode Kwarai da san da kuke mai.... *😍 *ILYSM*😍 1⃣3⃣ Nafi tanannan zaund har Little ta fito ta kalli Nafi cikin takaici ganin tana murmushi ita kad'ai tace " Nafi bakiji haushin abinda su Umma sukai ba? " Cikin rashin kulawa da abin tace " name fa? " Little ta zauna a gaban madubi tace " kina gani sunzo sun dauki lace mai tsada da sunan wai aike akai? " Nafi ta kalleta tace " lalai Maryam meye abin jin haushi? Kika sani ko da gaske suke? Sannan ko d'auka ma sukai ai sun isa ne naga ita zai aura? " Little tai d'an karamin tsaki tace "Wlh ba wani kayansu, sannan dan ita zai aura sai akace tazo ta d'au abinda ba nata ba? " Nafi ta mike tace " kafin ki shirya bari na anso miki abinci. " Bata jira amsarta ba tai waje da sauri, Little ta bita da kallo a fili tace " lalai wato dan indaina maganar shine zaki gudu? " Nafi kam tana fita tai murmushi tace " ni da naga kaya daga sama? Dan an d'au d'aya menene? " Kitchen ta wuce, ta amso abincinsu kenan zata shiga bangarensu taji ance "Ke!" Juyawa tai dan tasan Umma ce, Umma tace " zo nan. " Ajiye tiren tai sannan ta karasa gunta, Aneesa ta maka mata hararra tare da juya kai gefe. Nafi ta karasa tare da rusunawa tace "gani. " Umma ta mata wani kallo tace " munafuka kinje gun aikin ko kuwa? " Da sauri Nafi tace "Naje wlh. " Duk da dama Umman ta riga ta tambaya ankuma shaida mata taje amma sai cewa tai "in kika min karya na tambaya wlh kinji na fad'a miki jikinki sai ya fad'a miki. " Nafi tai kasa dakai ba tare da ta sake magana ba, Umma ta kara kallanta sannan ta ce " me Little tace bayan mun fita? " dama wannan shine dalilin kiran wancan burga ne so take taji me akace bayan sun fita. Nafi da mamaki ta kalleta tace " Bangane ba. " Da kuwa Umma ta mata ta kara da kinci gidanku, ni zaki kalla kicewa baki gane ba? Nafi tai kasa da kanta a hankali tace "kiyi hakuri. " Cikin takaici Aneesa tace "Dalla malama kara gaba. " Nafi wacce bata fahimci me ake nufi da kara gaba ba tace "Naam? " Cikin kuluwa Umma takaimata wani wawan mari wanda sai da Nafi tai baya tare da rike kuncinta. Umma ta nunata da yatsa tace " kin bar nan ko sai na karya ki? Shigeya wacce asalinta bashida tabbas. " Nafi ta juya ta fara tafiya sai dai tana tafe hawaye nabin kuncinta, haka ta d'au tiren tare da goge hawayenta ta shiga. Little har tana shirin fita sai ga Nafi ta kalleta tace " lalai Nafi sannu da zaman hira. " Nafi tai murmushi kawai batace komai ba sai hanyar toilet data nufa. Tana shiga ta tsugunna sai kuka, itakam Little abincinta taci ganin Nafi bata fito ba yasa taje bakin kofar toilet d'in tace " Nafi na tafi. " Da kyar ta daure tace "To. " Sai dataji alamun fitarta sannan ta dawo ciki, ta dade kafin hawayen su tsagaita taci abinci sannan ta fara gyara d'akin. _A Company_ Kawu zaune a kan kujerar dake tsakiyar dogon tabirin, gefe da gefe mutane ne kowa zaune akan kujerar sa, Wanda ke daga b'angaren hagu na kusa da kawu ya kalleshi yace " A gaskiya Chairman mun gaji da abinda Chief Director(Asim) yake mana, a duk sanda muka bukaci sa hannunsa akan wani aiki ko meeting a b'angaren mu ya dinga mana wala wala kenan, sam baya yin aikinsa na Chief Director." Kawu ya kalli Asim wanda yaketa juyi a kujera cikin rashin damuwar abinda ake kararsa dashi, ran kawu ya kai koluluwar b'aci ya kallu wanda yai maganar yace " kar ka damu Director idan har Asim bai canza halayensa ba nan da one month ni a matsayina na shugaban wannan company d'in zan saukeshi daga matsayinsa. " A zabure Asim ya kalli mahaifinsa wanda yana gama magana ya mike yai waje, Asim cikin tsagali da raini ya kalli mutanen gun yace " ni kuka had'a da mahaifina? Lalai ran kowa in yayi dubu sai ya b'aci. " shima yabi bayan mahaifinsa. Office d'in kawu ya shiga, yana shiga yaganshi a tsaye kusa dashi ya karasa yace "Abba.... " Littafin dake hannun kawu ya makamai iya karfinsa, Asim ya fad'a kan kujera cikin tsoro yace " Yahkuri Abba amma sharri suke...... " Yatsa kawu ya nunamai idanunsa sunyi jaa yace "kai dakikin ina ne? Meyasa sam kwakwalwarka bata aiki? " Yai wani hucci sannan ya cigaba "Company d'in nan na Waye? Kana tunanin dan na rike shi na shekara ashirin yana nufin ya zama nawa? " Kai ya jijiga sannan ya cigaba " A'a, da zarar Ashraf yaso zai zo ya amshi matsayinsa ne babu kuma yanda zamuyi. " Asim cikin b'acin rai yace " ta ina zamu barshi? " Tsaki kawu yai yace " 50% d'in yaya(mahaifin Ashraf) gaba d'aya a gunsa yake, kai kasan duk karshen wata kud'in dake shiga account d'insa ya ninka nawa mai 20%?" Asim wanda ya fara huccin takaici ya kalli Mahaifinsa, kawu yacigaba "In baka rike matsayin ka ba ka nuna ma mutane zaka iya kana tunanin Ashraf mai taurin kai zai bakka ka cigaba da abinda kaga dama in har ya fara aiki anan? " Asim ya mike cikin takaici yace " shiyasa duk duniya ba wanda na tsana irin yaron nan, mahaifinsa kaf arzikinshi sunan sa yasa, kai daka wahala gurin taimakama uban sanda yana da rai bai ma kara ya barma ko da wannan companyn ba. " Kawu ya zauna kan kujera cikin b'acin rai shima ya kalli Asim yace " Ka kula sannan ka dinga kokarin b'oye tsanar da kakema Ashraf dan naga kamar kanka na rawa baka kunyar nuna mai. " Shiru Asim yai baice komai ba....... _A Gida_ Nafi bayan ta gama komai tai wanka dama Little ta fito mata da kaya hakan yasa ta saka ta fito domin zuwa kitchen yin aiki. Ta d'anyi tafiya kad'an taji ance "Ina Zaki? " Tsayawa tai cak ta kasa juyowa, shima bai sake magana ba hakan yasa ta daure ta juya a hankali, daga gefe ta ganshi zaune akan d'aya daga cikin kujerun gun, gani tai ba kallanta yake ba hakan yasa tad'an kuramai ido, duk da bai kalleta ba jitai yace " Kallan fa? " Da sauri ta d'auke idanta tace " na fito ne kawai" Ya kalleta sannan ya mata alama da hannu akan tazo, a hankali ta karasa inda yake, ya kalleta yace " So nake kimin wani abu. " Cikin mamaki ta kalleshi tace " Me kakeso yaya? " Ya bud'e baki zai magana sai ga Aneesa ta karaso cikin salon tafiya da yanga, tana zuwa ta shagwab'e murya tace " Cwt Yaya kaifa nake nema. " Ashraf ya kalli Nafi sannan ya kalleta yace " Anie ya akai?" Baki ta turo tace "ni dai banasan Anie kacemin Neesah na. " Kunne yad'an sosa sannan ya kalli Nafi wanda da alama zaman gun ya isheta yace " Nafeesa jeki kawai. " Wani kasalalen kallo tamai wanda ita kanta batasan ta iya ba, so take ta tambayeshi me yakeso tamai? Ga Aneesa agun ita kuma duk ta rasa mai zatace, Aneesa ta maka mata harara sannan tace " Nafi yace kije zamuyi magana ne. " Kamar tai kuka haka ta juya ta fara tafiya, me yake so? Abinda ke mata yawo kenan. Itakam Aneesa zama tai ta shiga mai salo, wani abun ya biyeta wani kuwa ya juya kai kawai. Nafi kam duk aiki take amma hankalinta nakan Ashraf har suka kammala girki, nan Goggo tace "A d'au na Ashraf akai mai. " Da sauri Nafi ta amshi tiren tace "bari na kaimai. " Goggo ta kalleta tace " kinsan b'angarensa ne? " Haka kawai tasamu kanta da yin karya tace na sani. Nan Goggo ta bata. Fitowa tai tana ta kalle kalle, nan Allah ya had'ata da Amrah murmushi tai ta karasa gunta tace "Amra inane b'angaren Yaya? " Nan Amrah ta nuna mata, karasawa tai tana tafe tana tunani da fatan Allah yasa yana nan. Knocking tai a hankali, Ashraf dake kwance akan doguwar kujera yana kallo a falo yace "in abinci ne ajiye zan d'auka." Nafi ta kalli kofar kamar tai kuka har ta ajiye zata tafi sai kuma ta koma gefe ta zauna a kasa. Shikam ya dade kafin ya taso ya bud'e kofar, mutum ya gane a zaune ya jingina da bango cikin mamaki yace "lafiya? " Da sauri Nafi ta mike ta kalleshi, kallan mamaki ya mata yace " kece? " Kai ta d'aga kawai, yace " D'auko abincin ki shigo. " D'auka tai sannan tabi bayansa, tana shiga ta tsaya a bakin kofar, ya karasa kan kujera yace " turamin kofar. " Rufe kofar tai sannan ta kalleshi, da hannu ya mata alama akan ta ajiye abincin a dinning, nan ta kai sannan ta kara tsayawa tana wasa da hannunta, ya kwanta ba tare da yace mata komai ba, itama shiru tai dan batasan me zatace ba. Shikam kwanciyarsa yai yana jiran tai magana, sun dade sosai a haka shikam bacci ne yai gaba dashi. Nafi tana nan a tsaye jitai kafarta ta fara amsawa, a hankali ta d'an matso kad'an cikin in ina tace "dama d'azu ne.... " Sai kuma tai shiru, Jin shima baice komai ba yasa ta kara daurewa tace "naji kace zan ma abu? " Nan ma shiru, lekashi tai kad'an, gani tai bacci yake, a hankali ta matso inda yake ta kuramai ido, a ranta tace "na sashi yai bacci baici abinci ba. " Kallansa ta karayi, itadai haka kawai tun sanda ta ganshi takesan taga tana kallanshi, batasan sanda murmushi ya bayyana a fuskarta ba ta juya tai waje. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 1⃣4⃣ Sai yamma Little ta dawo, abinci kawai taci suka shiga bubud'a kaya nan Little ta ware mayafai da jaka suka had'a kayan da za'a kai d'inki. Nafi sai murna take a ranta zataga cikin gari. Driver d'in mumy ne ya d'aukesu, a hanya Nafi sai kalle kalle take can ta tuno tahowarsu a mota itada Ashraf murmushi ta saki wanda Little ta kula dashi. Little ta d'an harareta tace "Nafi na kula yau dai a farin ciki kikeyi." Murmushi ta sake sannan ta kalli Little tace "Little dan Allah tambaya. " Inaji kawai little tace sai dai ta maida hankalinta kan Nafi, Nafi tai kasa dakai cikin alamun kunya tace " in mutum yace yanaso kamai wani abu, me zai kasance? " Dariya sosai Little tai ta dade kafin ta tsagaita tace "Hala Ya Ashraf ne ya fad'a? " Nafi ta d'an turo baki kadan tace "shine to menene kike dariya ?" Little tai d'an karamin tsaki tace "in kikaji yaya ya fad'i haka wallahi aiki yakesan saki. " Nafi ta kalleta tace "aiki shine yanasan inmai wani abu? " Little ta girgiza kai tace "Tab bakisan mutumin nan ba, amma duk da haka nayi mamaki dan ni kad'ai yake sawa aiki ni kuma ba abinda na tsana a rayuwa irin inji yaya yace zan mai wani abu. " Nafi ta d'an jujuya kai sannan tace " Meye abin tsana? Nikam dadi zanji inya sani aiki ma. " Little ta mata wani kallo na yarinya da sauranki tace "Nafi bakisan waye Ya Ashraf ba, duk aikin da zakimai bazai tab'a burgeshi ba sannan bazai tab'a cemiki ko sannu ba. " Nafi ta d'an tabe baki tace " to mezai sa sai yayi miki sannu bayan ke kanwarsa ce? " Kallan mamaki Little take ma Nafi itakam Nafi ina ta sani cigaba tai da cewa " Sanna? N da alama ba a mai aikin yanda yake so ne. " Duka little ta kai mata,Nafi tai saurin sa hannu agun, Little ta rike hab'a tace "Lalai ashe kina magana haka? " Nafi tai murmushi batace komai ba, Little ta kalleta tace "Naji ni kanwarsa ce sannan naji d'in bana mai yanda yakeso, ke tunda kinanan sai ki mai yanda yakeso ki kuka tabbatar yacemiki sannu. " Nafi murmushi kawai tai batace komai ba, Little tace "Kinga da Ya Habib ne? Wayyo Allah na. " Da mamaki Nafi ta kalleta tace "Ya Habib? " Little ta saki wani fara'a yacigaba "D'an yayan mumy ne yanazuwa gida sosai ya dad'e yanzu ma na tabbata kila karshen satin nan ki ganshi. " Nafi ta maida kanta titi kawai, Hannu little tasa ta juyo da ita tace " Nafi kinsan me? " Kai Nafi ta girgiza alamar a'a, Little ta cigaba cikin zakuwa "Ya Habib ko Opposite d'in Ya Ashraf ne. " Nafi da mamaki tace "Oppo? " Little ta dafa goshi tace " Kinsan me? Kinga Ya Ashraf bai da san magana shi kuma ya Habib akwai surutu, sannan Ya Ashraf akwai zafin rai shikuma Ya Habib Saukin kai gareshi. " Nafi ta d'an bata fuska tace "Zafin rai? " Little tace " naji ba zafin rai ba, sannan kinga Ya Habib akwai san wasa da mutane, ga mutunci. " Nafi wanda ta rasa dalilin jin haushi Little datai tace "Little da wa kuka fi kusa? " Cikin rashin kulawa tace "Ya Ashraf. " Nafi tai shiru batace komai ba jitai Little tace "Amma Ya Habib zan aura. " Juyowa tai cikin tsananin mamaki ta kalleta, Little ta harari Nafi ta juya. Nafi kam ta kasa magana sai shiru tai. Tanaji Little ta d'aga waya suna hira da wata kawarta akan Lesson d'in da suke zuwa, saboda shirye shiryen Exam d'in Qualifying da zasuyi, ga makarantarsu anyi hutu kuma suna komawa za'a fara jarabawa. Nafi kam sai kallan sha'awa take mata, har suka isa gun d'inkin. An gwadata sannan suka bada kayan akai sai nan da sati d'aya za'a amshi wasu daga baya sai a zo a amshi sauran. _A gida_ Ashraf ya dad'e yana bacci kafin ya tashi, wanka yai sannan ya ci abinci, ya gama kenan Amra ta shigo tace Mumy na nemansa hakan yasa ya mike yai waje. Yana ganinsu Asim da kannensa a zaune d'auke kai yai kamar bai gansu ba yai gaba, yana wucewa kuwa sukaja tsakin takaici. Sun gaisa da Mumy sannan ya gaida Kawu, shiru ne ya biyo baya kafin kawu yace " Ashraf dama maganar auranka ne da Aneesa. " Kallan Kawu yai sai dai baice komai ba, Kawu ya cigaba "saura wata biyu a d'aura auren shine nakesan jin ra'ayinka akan abubuwa guda biyu." Ganin Ashraf bai da niyyar magana yasa yace " Da farko inda zaku zauna, anan kake so ko kuwa a d'aya daga cikin gidajen mahaifinka zaka duba d'aya? " Ashraf kam tambayar ta d'an b'atamai rai sai dai bai nuna ba kawai cewa yai "A tsarin mahaifina yafisan inzauna anan cikin 'yan uwana. " kawu yai murmushi yace " yauwa haka ake so dams banasan tauyema hakki ne, tambaya ta biyu maganar aiki fa? " Ashraf ya kalli Kawu ga mamakinsu murmushi sukaga ya saki, Mumy ta daure tace "Ashraf me kenan? " Kallan Kawu yai yace "Kawu so kake in fara aiki? " Gabab Kawu yad'an fad'i badai yaron nan yasan basaso ya fara aiki ba? Mumy ce tace "wani irin zance kakeyi haka? " Bai amsa mata ba sai maganar sa ta d'azu daya maimai ta "Kawu so kake na fara aiki? " kawu ya saki murmushi yace "in banda abinka Ashraf tun yaushe nake cema ka fara aiki? Ga mahaifiyar ka nan duk ta damu akan rashin aikin ka." Bai kara magana ba kawai kansa ya maida gefe, Mumy kam abin nan na damunta ganin zata sake magana yasa Ashraf yai saurin cewa "Kawu zan shiga ciki akwai abinda zanyi. " Kawu ya kalleshi sannan ya kalli Mumy wanda jikinta yai sanyi, bai jira amsarsu ba yai waje, Umma dake tsaye a kofa tanajin me ake cewa sam batasan Ashraf zai fito ba tana ganinshi ta shiga borin kunya, ko kallan ta baiyi ba yai gaba, duk ransa na dadi. D'akinsa ya wuce ya d'au waya ya kira Little, nan ta sanar dashi sun dawo gasunan shigowa, yace "kuzo keda Nafeesa. "abinda ya fada kenan ya kashe wayar. Little ta girgiza kai tare da kwaikwayan abinda yace, Nafi tace "to me kikeso yace? " Little tace "Inkun iso to kuzo ke da Nafisa ina nemanku. " Nafi ta juya kai tace "meye marabar hakan da yanda ya fada? " Little ta harareta tace "Lalai nafi na kula bakyasan indinga kushe yayan nan nawa." Nafi ta kalleta kawai batace komai ba, Little tai murmushi tace "ko da yake dole ne ganin yanda ya taimakeki. " Sun isa ko bangarensu basuje ba suka wuce bangaren Yaya, a zaune sukaga su Ya Asim hakan yasa suka rusuna suka gaidasu, harsun yi gaba Asim yace "Ke yar kauye? " Nafi ta juyo cikin tsoro alama ya mata da hannu kan ta matso, a tsorace ta matsa inda suke. Asim cikin izgilanci yace "Nemanki yake ne? " A tsorace tace wa? Dariya yasa irinta rashin mutuncin nan ya kalli kannensa yace "kun yadda Ashraf haka kawai ya kawo ta nan ba da dalili ba? " Nafi cikin mamaki ta kalleshi dan bata fahimci inda ya nufa ba. Dariya suka kara mata d'aya daga cikin su yace "amma wannan kwailar? Kalli fa kirjin? " Dariya suka kara sawq hrda tafawa, Nafi kam yanzu tafara ganewa, kasa tai da kanta a hankali hawaye suka zubo mata. Little ce ta matso wacce batasan me suke cewa ba sai dai ganin suna dariya ya nuna mata iskanci suke mata. Tana karasowa tace "Ya Asim yanzu Ya Ashraf ya kira muje ko ince mai ka tsaida ita? " Hararar Little din yai sannan ya kalli Nafi yace dalla bani guri. Nan Little ta kamata sukai gaba, tambayarta tai meya faru? Kai kawai Nafi ta girgiza alamar ba komai, haushi ya kama Little tace "to na fadama ya Ashraf inyaso sai ki fadamai. " Da sauri Nafi ta rike hannun Little tace "Maryam karki fad'amai dan Allah. " Da mamaki Little ta kalleta, Nafi ta goge hawayenta tace "dan Allah mubar maganan nan in yaji ransa ne zai b'aci. " Little tai shiru sai dai tana jinjina hakuri irin na Nafi. Sun kwankwasa sai dai jin muryar mace sukai tace ku shigo, ba sai an fada ba sun san wacce. Fuskar Nafi ce ta canza, a falo suka ganta ta baje a kasa tana cin abinci shi kuma yana gefenta amma a saman kujera yana kallo. Jin sun shigo yasa ya kallesu itama kallansu take ganin Nafi yasa tace "me take anan?" Ashraf yace "d'akinki ne? " Cikin shagwab'a tace "Amma ai ya kusa zama nawa. " Idanunsa akan Tv yace "sai kijira inya zama naki sai ki fad'i haka. " Mamaki ne ya cika Nafi wai haka itakam saurayi yake ma budurwa magana? Jiya da suka dawo sai taga kamar bada wannan zafin yake mata magana ba to ko abin zuwa yake? Ashraf ne ya katsesu da cewa "so kuke inta d'aga murya? " Nafi kam bata fahimceshi ba, Little tace " mu shiga. " Sun karasa Little ta zauna kusa da Aneesa tace "Yaya Neesa nan kika gudu cin abincin? " Ta kalli Ashraf tace "nafisan inci abinci a plate din dayaci tunda bayasan muci tare. " Kasa Nafi tai da kanta da sauri, Ashraf ya kalli Aneesa sai dai bai ce komai ba. Little ta kalleshi tace "Yaya munkai." Gud kawai yace, Little ta kara cewa "Gamu to. " Nafi ya kalla yace "Nafeesa so nake gobe ki gyaramin b'angare na. " Murmushi tai sannan ta d'ago ta kalleshi tace "Toh. " Little tai kwafa aranta tace "kiyi murmushi da kyau. " Aneesa ce ta harareta hakan yasa tai saurin maida kanta kasa, kanta ta maida kan Ashraf tace "Ya Ashraf yanzu me wannan zata maka? " Cikin rashin damuwa yace "to ko zakiyi? " Da sauri tai shiru dan ba abinda ta tsana irin aiki, Ashraf ya kallesu yace "Little kuje." Little wacce dariya ta kusa kamata da yaba Aneesa amsa ta mike itama Nafi ta mike, har sun fara tafiya Nafi ta juyo tanasan tambayarsa. Kallanta yai yace "d'azu yaushe kika tafi? " Aneesa ta kalla cikin tsoro tace " ban dade ba ai. " Kai ya d'aga kawai, ta daure tace "Goben karfe nawa zanzo? " "Sanda kika gama abinda kike. " Juyawa tai bayan ta amsa da to. Aneesa ta rakata da hararar tsana.... Suna fita ta shagwab'e ma Ashraf wai ya dizgata a gaban nafi. Murmushi yai yace "kinsan banasan irin tambayoyin nan ai amma naga in bakimin ba bakyajin dad'i. *THE INNOCENT TEAM*[5/5, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Sry jiya nayi mistake zansa 16 nakara sa 15.* *Nagode kwarai da tunatar dani.... LYSM* 1⃣7⃣ Kwanaki sun d'an tafi yau kwanar Nafi 10 sai dai abubuwa dayawa sun canza, sam yanzu Ashraf yadaina mata magana tundaga wannan ranar ko gaisheshi tai kai kawai yake d'agawa, tana zuwa gyaramai d'aki duk bayan kwana biyu sai dai daga ta shiga yake fitowa, wannan abu na damun Nafi iya tsanani, gida ya mata zafi ga Little yanzu suna jarabawa ba zaman gida take ba, sannan cikin gida kowa zancen biki ne a gabansa, shiyasa yanzu zamanta yafi yawa a kitchen, sosai ta fara iya abinci dan yanzu tana nata iya kokarin. Kamar yanda ta saba yau ma a ka'ida zataje ta gyara b'angaren Ashraf suna gama aiki a kitchen tai wanka ta d'au abincinsa tai gaba, ya bata makuli saboda wani sa'in in bayannan hakan yasa data kwankwasa taji shiru kawai tasa makuli ta bud'e, karfe goma ne shiyasa kanta tsaye tai d'aki ta d'auka ya fita, me zata gani? Ashraf ta gani kwance ya dukunkune jikinsa da bargo, lekawa tai cikin tsoro idanunsa a rufe suke hakan yasa ta karasa kusa dashi, numfarfashi yake fitarwa sama sama, Nafi ta tsuguna saitin fuskarsa, hucin da yake fitowa daga bakinsa yasa tasan yanajin jiki, kuramai ido tai kawai hawaye ne suke zubo mata wanda ita kanta batasan tanayi ba, a hankali yad'an bud'e ido ganin Nafi yasa ya ciro hannunsa da niyyar yi mata bayani, itakam ganin yana miko hannu tai saurin rike hannun, ya kara daurewa ya bud'e ido, yayi mamakin ganin yanda take zubar da hawaye sai dai abinda yakeji yasa ya d'aure yace " rub zaki mikon." Mikewa tai da sauri ta shiga dube dube, hannunsa ya sa ya nuna mata inda yake, da sauri ta d'auko ta mikamai, nuna mata kafad'ar hagunsa yai ya d'aure da kyar yace shafamin anan. " Kallan mamaki tamai sai dai gani tai idanunsa a rufe suke, mikewa tai a hankali ta rasa ta ina zata fara, ganin yanda yake hucci yasa ta d'aure a hankali ta d'an yaye bargon daga b'angaren sa na haggu. Vest ne a jikinshi shiyasa tana iya ganin gun, mamaki ne ya kamata ganin gun ya kumbura, da alama bigewa yai ko kuma wani abun lalai wannan ciwon ne ya sa mai zazzab'i, kallansa tai cikin tsananin tausayi wanda bata tab'a ji ba, yau ce rana ta farko da takeji inama ciwon ya dawo jikinta, a hankali ta d'ebi rub d'in ta fara kokarin shafawa, sai dai daga takai hannunta kan jikinsa sai tai sauri ta d'auke, tasan magani ne da alama kuma yanda takeji maganin zafi zai mai. Cikin wani yanayi wanda Ita kanta bata sani ba tace " Yaya baka ganin zaiyi xafi? " A hankali yace " Nafeesa samin ba zaiyi ba. " Idanu ta rufe kamkam kamar ita za'a sawa a haka ta samai, sam batasan hawayenta na d'iga akan gun ba, Ashraf kam ido ya rufe dan akwai zafi sai dai jin hawayen nafi agun ciwon yasa jikinsa yai sanyi, meyasa? Menene dalilinta? Wata zuciyar tace kasan Nafi da tausayi. Tana gamamai ta maida bargon ta rufe shi sannan ta share hawayenta wanda ita kanta tana mamakin yanda suke zuba haka, cikin sanyin murya tace " Yaya ka tashi ko wani abin kaci. " Kai ya girgiza mata alamar a'a, idanunta suka kara cicikowa tace "Yaya dan Allah, in kumaa da wani abu da kakeso sai in maka yanzu. " Idanu ya bud'e a hankali ya kakaro murmushi sannan yace " me kika iya?" Da sauri tace "duk abinda kakeso na iya kaji. " Ganin baiyi magana ba yasa tace "Dankali aka soyama da farfesun kayan ciki, xaka iya ci? " Kallanta ya sakeyi sannan yace "eh" Da sauri ta mike tai falo ta dan zubo a plate, tazo kusa dashi, kallanta yai baice komai ba. Itama tsayawa tai rike da abinci batasan ya zatai ba. Suna nan a haka har bacci yai gaba dashi, kuramai ido tai a hankali tace "Kayi bacci sau biyu kenan Ina tsaye. " Tai murmushi sannan tace "sai dai duk banajin haushin hakan. " Falo ta fito ta maida abincin sannan ta shiga gyara, har ta gama bai farka ba, itakam zuciyarta na raya mata taje ta sanar da mumy halin da Ashraf ke ciki, sai dai tana tsoro dan kuwa tasan halinsa, ta kuma kula kamar ba wani shakuwa sukai ba. Gashi ta gama aiki kuma sam batasan ta fita tabarshi shi kad'ai, kuma tana tsoron kar azo a ganta matsala ta sake faruwa wanda ita kuma bataso. Haka tanaji tana gani tai waje tana waiwayen d'akin. _Kauye_ Yau tun safe su maman Hanne suka shirya ita da Datti akan lalai yau ya kamata suje ganin muhalin Nafi saboda ai dama bai kamata suje daga farko ba. Sun fito suka tarar da D'an Litti a inda sukai zai jirasu, Kowa ya kalli D'an litti sai ya kara saboda tsananin gayun dayasha, riga ce ta shadda mai dogon hannu yasa wando jeans ya tutura rigar a cikin wandan sannan ya kwama takalmi sau ciki ba safa, ya kawo hula irin tamu ta hausa ya saka, sannan ya kwama glass dinsa, gefen aljihun wandon kuwa ya ajiye wata zargab'ebiyar wuka. Tsayawa yai ya wani karkace, su Datti suka karasa, maman Hanne na rike da gari yai zafi, wanda 'yan uwan Nafi suka harhad'a mata tarkace su fura ne, kayan mata ne, gayayyaki na magani, su daddawa ne, kub'ewa busassa da sauransu. Datti ya kalli D'an litti yace " kai amma wannan yaron kana burgeni, ni kam dama kaine ka auri Nafi ba wannan ba. " Dan Litti ya juyo cikin gayunsa yace "Haba Malam ni ai nafi karfin Nafi sannan ni abinda yasa nake san zuwa rakiyar nan ba komai bane ila I want me to see Ashaf. " Datti ya juya kai tare da tab'e baki yace " mu tafi nikam ba turanci ne a gabana ba. " Sun isa Gwaram suka samu wata bus anata lodi masu zuwa kano nan suka shige, Datti yai dariya yace " Ashe ma abin ba wuya." Me ruwa ne ta leko tana asai ruwa, Dan Litti ya kobare cikin salonsa yace " ke me ruwa Me too want water one. " Ta kalleshi tace " Dan boko banajin turanci. " Maman Hanne tace "Kayi mata da hausa D'an litti kasan ba iyawa tai ba " Yai murmushin kasaita yace " okay, bani ruwa d'aya. " Nan ta bashi, Datti yace "lalai yaro muna zaune dan rashin d'a'a sai ka sai ruwa kai kad'ai ba tare da ka sanmana ba? " Dan litti ya kara gyara zaman glass d'in sa yace "gatannan ka siya kaima." Datti ganin inya siya sai ya saima maman Hanne hakan yasa ya gwara shima ya hakura. Nan mota ta tashi suka fara tafiya.......... _Gida_ Kawu ne ya kalli Mumy wacce ke zaune cikin damuwa, yace "Hajiya lafiya kuwa? " Kallansa tai cikin kulawa tace " Tunani nake yaushe ya kamata asa lawyer d'in mahaifin Ashraf ya kawo sakon wasiyyar nan? " Kawu ya mike zaune tare da dafata yace "Hajiya karki damu da wannan, ai shima Yayan cewa yai abama wacce Ashraf ya fara aura, sai mu bari sai anyi auren kenan ko? " Tai d'an dariya tace "I am really curious akan me ya ajiyema Matar Ashraf wanda ba wanda ya sani sai shi daya tafi. " Kawu yai dariya yace "nikaina na k'osa naga menene wannan, da yace lalai matar Ashraf ta farko ya umarta abama. " Nan suka shiga tattaunawa akan al'amarin wanda ba su kad'ai ba kowa ya kosa yaga menene wannan abun...... To nima daban taba ji ba sai yau na k'osa na gani sai dai ina ta tambayar kaina, Wacece matar Ashraf ta farko?????? *🗣🗣🗣🗣🗣🗣My Beely Badaru, duk Amarcin ne🙈?* *THE INNOCENT TEAM* [5/5, 1:06 AM] ‪+234 703 962 5239‬: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Where are u my Cwt Nafeesa? Ur page is here!!! Hope banyi late ba? Happie Birthday dear wish u long life and prosperity.....* 1⃣8⃣ Duk yanda Nafi taso ta kwantar da hankalinta ta kasa, ganin azahar tayi tai sallah dan yanzu ba laifi Little ta koya mata duk da suratul Iklas kawai ta iya ko hijab d'in datai sallah bata cire ba tai waje da sauri, knocking tai ganin ba'a bud'e ba yasa tasa makuli ta bud'e. Ko kofar bata rufe ba ta shiga da sauri tana fatan Allah yasa ba wani abun bane ya sami Ashraf. D'akinsa ta nufa kofar nanan a bud'e kai tsaye tai nufin shiga sai dai me? Aneesa ta gani zaune kusa da Ashraf ta rike plate a hannunta ta d'ebi Faten dankali tana kokarin kai bakinsa, da sauri ta matsa daga kofar ta tsaya a jikin bango, hannu. Ashraf yasa da niyar amsar cokalin ta noke kafad'a tace " ni zan baka Hubby. " Kallan mamaki ya mata, ta kashe mai ido cikin salo tace " daga yau na daina cema Yaya tunda bikinmu ya matso, Hubbyna zan dinga kiranka. " Ashraf baice komai ba sai kula da hijab dayai a bakin kofa, Nafi wacce ke lab'e tad'an leko kad'an jin abinda Aneesa ta fad'a. Idanunsu ne suka had'u juyawa tai da gudu tai waje, baice komai ba haka kuma bai mike ba sai murmushi dayai. Aneesa ta d'auka cemai Hubby datai shiyasa yai murmushi, ta kalleshi cikin kauna tace "ahhh! " Amsar cokalin yai, ta turo baku cikin shagwab'a tace "Hubby ya maganar sakon Abbanka? Sai yaushe za'a bani. " Kallan mamaki ya mata yace "me? " Ta d'an mai hararrar wasa tace " haba Hubby na kagu inga menene. " Fuska Ashraf ya canza, cikin takaici ya kalleta yace " Get out." Mikewa tai cikin mamaki tace "me kuma nai? " Yace "what? Me kikai? Ina kwance ba lafiya amma ki rasa me zaki ce sai zancen wani abu? Fita nace. " Idanu ta fara canzawa zatai alamun kuka, yace "wlh Anisa kika min kuka anan sai kinyi bala'in dana sani. " Ta kalleshi cikin tsoro tace "Tayaya zaka iya abu kai kad'ai bayan kafad'ar ka a kumbure take? " Ya juya kai yace "da sanda kika gani a mace kika ganni? Fita nace ko? " Aneesa ta mike ta fita cikin takaici. Tsaki yai sannan ya tuno sanda Nafi take hawaye sanda taganshi haka da sanda takesamai magani, tsaki yaja kawai. Nafi kam tana fita d'aki ta koma ta rasa me yasa takejin zafin Ashraf, Hubby? A fili tace ko meye hakan oho.... Harta zauna ta mike tai kitchen. _A Mota_ Tunda suka isa birnin kudu aka tsaya aka ajiye mutane sannan aka d'ebi wasu, kowa ya kalli D'an litti wanda ke sanye da wuka a katara sai ya matsa, sai kuma yasha jinin jikinsa, duk mutane sunyi tsit a mota duk tunaninsu d'aya wancan me zaiyi da wuka? " Haka dai akai ta tafiyar kurma shikam yana nan kwame da glass d'iinsa baicewa komai, haushinshi ma su Datti da suka isheshi da zancen wai gaskiya sun gaji har yanzu ba'a iso ba? Wani gida ne kano haka? Sun isa kachako anan kwandasta ya kalli kowa yace "a kawo kud'in mota." D'an litti yace "nawa ne? " "dari 700." A zabure Datti yace "me? Dari 700?hauka kuke? Kunsan ma miye d'ari bakwai? " Wani ne wanda ke gaban d'an Litti ya d'an mike yace "To wlh anmin sata. " Gangarawa mai mota yai, parking yai sannan akace kowa ya fito, wanda akama sata yace wlh an d'auken kudina a dunkule. D'an litti yaja tsaki yace "kudai kawai baku ajiye kudi ba yanda ya kamata zakuzo kuce am d'auke muku. " Nan aka fara hayaniya kwandasta da kansa yake tambayan kowa ko ya d'auka har akazo kan d'an litti yace "Kai Tsakanin ka da Allah kaika d'auka? " "I am the one. "abinda d'an litti ya fad'a kenan cikin gadara da takaici, shi harga Allah ya dauka i am the one yana nufin ba i am not ne. Nan aka shiga zaginsa wasu na cewa dama su basu yadda dashi ba, hannu yasa ganin ana mai hayaniya da jiyar fito musu da aljihun sa akan su tabbatar ba komai a ciki, da sauri Driver ya rike hannun sa ta baya, yace " me kake shirin d'aukowa? " Mamaki ya kama d'an litti zai magana sai ga 'yan sanda, nan suka fad'a musu, su kansu suna kallan yanda d'an litti yasa wuka zargab'ebiya a gefen riga suka tabbatar da lalai da alamar tambaya. Cafkeshi sukai sukace sai sun kaishi office an charge shi, Datti a zabure yace "Aradun Allah baku isa ba rakamu gurin 'yata fa zai. " Kallansa sukai sukace "sai dai ku koma in ya dawo ya rakaku amma wannan dole me ya bimu." Dan litti sai kokawa yake akan a kyaleshi amma ina...ankwa aka garkama mai akai gaba dashi sai ihu yake yana cewa Wallahi Allah bani bane, Allah I am the one. " Su Datti kam abin duniya ya damesu, maman Hanne tace "Yaya aikam dole mu koma ina mukasan zamu? " Mai mota yace sai sun bashi dari 1000 su biyu, da kyar aka laluba datti aka samo dari 500 cikin takaici suka barsu agun sukai gaba. Datti kam duk ya rikice, shida yakesan suje gun Nafi wannan yaran ya d'an bashi kudi dan yaga da alama akwai kudi a jikinsa. Maman hanne ta kalleshi tace " Yaya wlh ba karamin kuskure kai...... " Tsawa ya daka mata dama yana takaicin bai samu wani kudin ba ga nashi ya kare uta ficika ba a d'auka nata ba yace "ke ni gafara bani guri, banza kanwar mai satan saniya duk ba yayarki bace taja duk abinda ya faru? Zaki wani bud'en baki kice wai nayi kuskure? Nayi kuskuren 'yarki ce? " Maman Hanne tace "Allah ya baka hakuri.... " Nima nace Ameen *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *_Hakika bani da bakin da zan muku godiya, nagode kwarai da so da kaunar da kuka nunamin, ina kara godiya ga masu min ta'aziya ta waya, ta text, da ta chat nagode kwarai Allah ubangiji ya barmu tare......_* 2⃣0⃣ Shiru Ashraf yai a mota bayan sun fito daga Asibiti, tunani yake mai zurfi ina zai sa Nafi a makaranta? A kalaa dai shekarunsu d'aya da Little banbancinsu dai Little nada d'an jiki sai dai Nafi siririyace sosai sai tsayi, ko alphabet bata iya ba. Ya d'an juya kai, ina zai sata? Yarinyar nan dai bamai ansarta ko Js1 ne to a hakan ma Js1 ya mata kankanta saboda ita ba yarinya bace, yai d'an karamin tsaki lalai Malam dama wahala ya d'auramai. Sam baiji sanda Driver yake ta cemai Oga ina zamu? Can bayan ya gama tunani ya kalli Adamu yace "Adamu me muke jira kuma? " Adamu ya dan saki fuska yace " tun d'azu nake tambayar inda zamu banji kace komai ba. " Tsaki ya kara ja sannan yace "Mu tafi gida, tunani ne suka min yawa. " A gida kam kan kace me kowa yasan abinda Ashraf yama Aneesa akan wasiyyar da za'a bata, duk ta yad'ashi tana fadama mutane tana kukan sakalci, anyi carko carko a waje kowa nata fada'an albarkacin bakinsa, sai dai kaf Ashraf suke bama laifi gani suke ai ta cancanci abata ta gani, dan ankusa d'aura musu aure. Mumy kam tana d'aki abin duniya ya dameta itakam ba abinda ta tsana irin taji ance Ashraf yayi abu. Tun da suka shigo Ashraf ya fuskanci da matsala sai dai har sukai parking ya fito bai nuna komai ba, ba kuma yasan ya san meke faruwa, direct hanyar banharensa ya nufa, suna daga tsaye ko kallan inda suke baiyi ba, Ga Aneesa da su Umma suma daga d'an gefe. Asim ne cikin kuluwa yace " Ashraf bakaga dan kai muke tsaye ba? " Kallansu yai ya saki wani mugun smiling na rainin hankali yace " Da alama tsayuwar domin ni tana muku dadi ne. " Ya ci gaba da tafiyarsa, a xabure Asim da kannansa suka matso inda Ashraf yake, Asim ya tafi a zuciye zai shake Ashraf, saura kiris ya karaso Ashraf yace " D'an daba muka samu a gidan? Ka tabbatar kasan me kake shirin yi kafin a samu matsala. " Jin haka yasa kannensa sukai saurin tare Asim d'in shikam sai hucci yake, ya nuna Ashraf yace " Dan kut........ Kai har ka isa kasa kanwata kuka?" Kallan inda su Umma suke yai sai a lokacin ma ya kula da su, cikin zuciyarshi kwarai takaici ya lulube shi sai dai murmushi ya sake saki yace " Kanwarka? Sai kai azama ka bata hakuri sannan kai gaggawar yi mata kashedi akan zubar da hawaye akan wani bare. " Ran Asim ne ya kara dugunzuma, yanzu kam har kannansa abin ya kular dasu, Aneesa ta matso, Ashraf ya d'an buga mata wani kallo sannan ya kalli Asim fuskarsa a sake sosai kamar ba'amai komai ba yace " Ya? Gatannan sai ka tambayeta me baren nan ya mata. " Asim ya kalli Ashraf cikin masifa yace " kai dan rashin mutunci baza ka bata wasiyyar mahaifinka ba? Ko dan tsabar mugunta rikewa zakai? Oh andaiji jiki uba ya mutu ya bar wasiyya amma d'a ya kasa......" Kasa karasawa yai saboda ganin Ashraf yana murmushi harr hakoransa suka fito, cikin tsananin takaici ya kalli Ashraf yace " kut! Dariya ma na baka? " Ashraf ya juya kai tare da shafar kasan kansa da hannun da baya mai ciwo yace " Uba? Sai kuma ka manta wannan Uban nawa ne ko? Sannan banaji a wasiyyarsa yace inba matar da ban aura ba ko? " Aneesa ta matso kusa dashi tace " Yaya?" Matsawa yai daga kusa da ita baice musu komai ba ya juya ya fara tafiya, sai dai abin mamaki kasa cemai komai sukai sai Aneesa data bishi da sauri, tana kiranshi. Ko Kallanta baiyi ba, ransu Umma ya sake b'aci, yana shiga falonsa ta bishi itama tace "Hubby? " Matsowa ya farayi inda take harta isa jikin bango yasa hannunsa ya matseta har sai datai dan kara, sannan yace " wlh ki shiga hankalinki, inkikai wasa Wlh kinji na rantse duk sanda nake miki sai in ajiye maganar auranki, kinfi kowa sannin ni Ashraf nafi karfin mace ta wulakantani ko ta juyani. " saketa yai sannan yai d'akinsa. Da kallo ta bishi dashi, wani mugun tsoro ne ya shigeta,A tsorace tai waje. Ashraf kam yana shiga d'aki ya durkushe agun, kafad'arsa har kasan hannunsa banda azabar zafi ba abinda yake ji, d'ayan hannun yasa da niyyar sa magani, sai dai ina jin gun yai ya kara kumbura, ya tuna abinda likita yace mai. "Ashraf a ina ka bugu haka? " Da mamaki yace" ni ban bugu ba kawai da daddare ciwo ya tashi min." Likitan yai shiru can yace " A 'yan kwanakin nan baka bugu ba? " Ashraf ya kalleshi yace " na dai d'an sanu karamin accident to daga nan ina d'anjin gun ba dadi to amma bawai ciwi ya kemin ba. " Likitan yai d'an ajiyar zuciya yace " Ashraf ya akai haka? Me yasa bakazo checkup ba bayan abin? " Ganin bashida niyyar magana yasa ya mik'e ya bashi magunguna, sannan yace " a sa tsuma a ruwan zafi a dinga matsewa ana gasa ma gun, sai a shafa wannan. " Asharf ya amsa, yacigaba "wannan kuma na had'iya ne. " Nan ya bashi kud'inshi Ashraf ya mike, har ya fara tafiya likitan yace " Ashraf ka tabbatar an gasa ma sannan karkai amfani da jikinka sosai. " Nan yai gaba, ta ina zai iya gasa gun da kansa? Gashi sunyi fada da waccan yarinyar, shikuma kaf mazan gidan bayaji akwai wanda zai iya kira. Wayarsa ya d'aga ya dannan number Little yana fatan Allah yasa ta dawo. Daga can b'angaren Little wacce ke kwance batajin dadi ta daga, bayan tagaisheshi bai amsa ba kawai yace "little kizo yanzu. " Abinda ya fada kenan ya kashe, little wacce da alama ciwon mara take ganin yanda take a durkushe sai dai ita batasan meke damunta ba, ta kalli Nafi wacce ke xaune kusa da ita duk ta rikice kamar ita take ciwo. Tace "Nafi dan Allah jeki yayane ke kirana nikuma kinga cikina murd'amin yake. " Nafi ta kalleta daa idanunta da sukai raurau tace " taya zan tafi in barki? " Little tace " naji muryar yayan ma kamar......" Ai Nafi da sauri ta mike batama jira karashen zancen ba tai waje da sauri, ganin saurin bai mata ba ga ba mutane agun yasa tadan sa gudu, tabbas ciwonsa ne ya motsa abinda kawai tasa a ranta kenan. Sam bata kula da Asim ba wanda ke kokarin shawo kwana ita kuma zata mike, dayake gudu takeyi iya karfinta kuwa ta bangaje shi, Asim ya juyo cikin tsananin mamaki ganin wani kwararen ne? Nafi kam jikinta ya fara tsuma ta kalleshi a tsorace tace " Yahkuri yaya dan Allah. " Asim ya d'ago da niyyar masifa, sai dai me? Can ya ganta ta mai nisa sai sauri take, ta sani bazai kyaleta ba sai dai yanzu abu d'aya ne a gabanta ba kuma taji akwai abinda zai tsayar da ita. Tana murd'a kofar tajishi a bud'e nan ta shiga ta fara sallama, jin shiru cikin tsoro kawai ta dannu ciki, baya falo hakan yasa ta wuce d'akin shi. A zaune yake a kasa ya kifa kansa akan gado, ba riga a jikinsa sai dogon wando hakan yasa Nafi ta juya baya da sauri, a hankali tace "Yaya ga...... " Yanda yakeji yasa bai bari ta karasa ba ya katseta "Little yi sauri ki d'au roba a toilet ki taro ruwan zafi ki sa tsuma a ciki kizo ki dinga matsewa kina gasamin gun nan. " Nafi ta juyo a hankali tana san cemai ba little bace tace " Ya.... " "Little wuce mana" Jiki a sanyaye Nafi ta wuce toilet yanzu ta iya kunna famfo ta kuma san inda ruwan sanyi dana zafi yake, nan ta tara a roba ta saka towel karami dake rataye a ban d'akin ta fito, ganin yanda ya kifa kansa ko d'agowa baiyi ba yasa tasan yanajin zafin gurin, kallan gun tai taga ya kara tashi ba kamar da safe ba, idanunta ne suka fara cicikowa, ta karasa a hankali tai kneel down ta bayansa ta fara matsewa tana gasa mai gun, dun sanda tasa sai taga ya d'an motsa kad'an. Kamar a jikinta takejin ciwo nan, intaga ya motsa sai ta runtse ido. Asim kam wanda ransa yakai kololuwar tashi ya tsaya ya d'auka yanzu zata dawo yaci mutuncinta, jin shiru yasa yabi bayanta a kufule. Bud'e kofar yai a zuciye yai ciki, me zai gani????? Me kuma idanunsa suke gane mai??????? Tofah! Babbar magana........ ¤¤¤¤¤¤¤¤¤¤ A b'angaren su Datti kam haka sukai ta yawo suna neman taimako, kayan da maman hanne tazo dasu suma sai siyarwa tai. Da kyar suka hada kudin mota suka koma Gwaram..... ¤¤¤¤¤¤¤ Shikam d'an litti ya musu bayani har ya gaji amma ina... Sunce dole sai ya fada musu wanda ya sani yazo yayi bailing shi. D'an litti yace " ku nemo min Ashraf. " Officer yace " Ashraf wa? A ina yake? Meye number wayarsa? " To fa! Da masifa D'an litti yace " nidai ba na fada muku ba? Sunanshi Ashraf a kuma kano yake. " Officer yace " me kake nufi to? So kake mu shiga kano mu fara neman masu suna Ashraf ko me? " D'an litti takaici ya kamashi ya zauna a cell d'in kamar yasa ihu, gashi sunce inya sake musu turancin nan nasa sai sun fasamai kai........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *I Sincerely Dedicated This Page To You Billy S. Fari and My Samrah.... ILYSM* 1⃣9⃣ Dakyar Ashraf ya iya watsa ruwa a jikinsa, wajen sa kaya kamar yai ihu, haka dai ya daurw yasa riga, makuli ya d'auka ya nufi hanyar waje da niyyar zuwa asibiti. Yaje fita Umma ta kirashi hakan yasa ya karasa gunta, falo suka shiga bayan sun gaisa ya kalleta yace "Umma ya akai? " Ta d'anyi murmushi tace"Dama tun jiya nakesan magana dakai. " Kallanta yai kawai baice komai ba, ganin haka yasa tace " yanzu saura wata d'aya da sati biyu bikinku da Aneesa shiyasa nake tunanin kamar ya cancanta a bata sakon mahaifinka..... " Wani kallo ya mata wanda ita kanta batasan ke yake nufi ba, sannan murmushi ne ya biyo bayan fuskarsa ya kalleta yace " Ashe har na bada sadaki an shaida kenan? " Umma tace "mene? " Yai wani murmushin rainin hankali yace "a iya sanina wanda ya bada wasiyyar nan cewa yai matata ta farko, banaji yace matar dana kusa aura. " Ta kalleshi sannan ta motsa baki zatai magana, mik'ewa yai sannan yace " inada abinyi Umma sai anjima. " Tabishi da kallo cikin maimaita kalamansa, asanda yai maganar sam kwakwalwarta kullewa tai amma yanzu kam datake maimaita kalaman ta fahimci banda tsananin rainin hankali ba abinda Ashraf ya fad'a mata. Shikam cikin tsananin b'acin rai ya shiga mota, yayi tunanin zai iya tuki sai dai jin zafin da kafad'arsa take yasa ya na driver d'in mumy magana, ba'a dad'e ba ya karaso nan ya jashi suka fita. Kansa ya kwantar akan kujera ya lumshe idanunsa, menene dalilin dayasa mutane suka damu da abinda mahaifinsa ya bari? _Fatiha an d'aura auren Ashraf da Nafisa yar gidan Datti_ Abinda ya fad'o mai a rai kenan, kallan driver yai yace " Adamu kaini wajen malam Yunus " To abinda driver d'in ya fad'a kenan tare da murd'a kan sitiyari, sunyi tafiya sosai kafin su isa wata katuwar makarantar islamiya, nan yai parkin Ashraf ya fita, wani babban office ya nufa ya kwankwasa, daga ciki aka ce shigo, Ashraf ya murd'a kofa ya shiga. Malamin na ganinsa ya mike cikin tsananin farinciki ya karaso kusa da Ashraf tare da mikamai hannu alamar musabaha, shi kanshi Ashraf d'in ya saki fuskarsa sosai, nan shima ya mikamai suka gaisa cikin girmamawa. Nan ya nunama Ashraf guri ya zauna, sunyi gaisuwa tare da tambayan juna bayan rabuwa, dattijon Malami ya kara washe baki yace "Muhammad sam ka daina ziyartata. " Ashraf yai murmushi yace " wlh malam uzuri ne ke hanani zuwa. " Sunjima suna gaishe gaishen su kafin Ashraf yai gyaran murya yace "Malam ina cikin wata 'yar matsala ne wacce duk duniya ba wanda na sanar ma kuma ba wanda zan sanarwa sai kai. " Malam yunus ya kalleshi cikin tsananin kulawa, yace" Inajinka." Ashraf yai shiru, yana tunani. Malam yace "Muhammad karka b'oyemin komai. " Ashraf yai kasa da kai nan ya zayyane mai kaf abinda ya faru sannan ya d'oramai da wasiyyar mahaifinsa. Malam Yunus hankalinsa ya tashi dajin wannan al'amari ya kalli Ashraf yace" Tausayi da Taimako ne yasa ka aureta sai dai Muhammad inasan tunasar dakai aure ko a wasa akayishi indai har anyi auran yanda musulunci yace to fa tabbas wannan auran ya d'auru sannan hakkin matarka na wuyanka. " Kallan Malam yai cikin tsananin damuwa yace " da ina tunanin saki..... " Da sauri Malam yace " kul Muhammad akan me? Ba taimako kakesan yi ba? Meye amfani taimakon kenan? " Ashraf jiki a sanyaye ya kalli Malam yace " me zanyi da ita? A kauye fa take ko ince a riga, yarinyar da banaji sallah cikake ta iya, batasan komai na rayuwa ba, infact shekarunta ma inaji basufi 16 ba Malam me..... " Malam yai murmushi yace " naji duk bata iya komai ba, kamin alkawari d'aya nikuma zan taimaka ma. " Ashraf yace "Name kenan? " Malam Yunus yai murmushi yace " Inaso kasa ta a makaranta inma taa kwana ko ta jeka ka dawo ka kula dacinta da shanta da suturarta har ta kai shekara 20 zuwa da d'aya, inhar aka kai lokacin Bakaji komai a tattare da ita ba inaso ka bata takardarta ita kuma sai ta nemi wani ta aura. " Cikin rashin damuwa Ashraf yace "nama wannan alkawari. " Malam yai murmushi sannan yace " game da wasiyar mahaifinka kuma kasan yanda zakai a rabu lafiya dan kuwa wannan wasiya ta matar daka aurace ba wacce zaka aura ba. " Shiru Ashraf yai yana tunanin lalai akwai chakwakiya inhar yace bazai ba Aneesa wannan wasiyar ba, Malam yaji yace " zaka iya jinkirtawa zuwa sanda ka rabu da matarka." Ashraf yai shiru, sai dai yasan wannan shawarar itace daidai,sunyi Sallama Ashraf ya ajiye mai kud'in talafi na makaranta sannan ya tafi. Mota ya koma nan sukai hanyar Asibiti. *Dan Allah kuyi Hakuri da wannan wallahi rasuwa aka mana shekaran jiya.* Nagode![5/9, 09:58] Ayusher✍🏻: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Dedicated This Page to World of Hausa Novel 1* And *Taskar Lubie Mai Tafsir* 2⃣1⃣ A tsorace Nafi ta mike gabanta sai fad'uwa yake, shikam gogan ko mikewa baiyi ba sai cewa dayai "Little mikomin rigata a kan gado. " Nafi ta mikomai sannan ta fito daga d'akin da sauri tare da ja mai kofar, dan ta kula kamar bayasan asan bashida lafiya. Tana fita falo Asim ya karaso tare da jan hannunta da karfin tsiya, Nafi ta d'an turje sai hawaye da takeyi. Asim ya haska mata wani wawan mari yace " banza karuwa, a ido kamar bakauyiya ashe kinfi karuwai iya iskanci. " Nafi ta shiga girgiza kai hawaye na zubo mata. Kofa aka bud'e, mamaki ne ya kama Ashraf ganin Nafi, sai dai bai bari mamakin ya fito fili ba cikin isa ya karaso ya sa hannu ya rike hannun da Asim ya rike. Asim ne ya kalleshi cikin masifa yace " Me kenan? Kazo karema karuwarka ne? " Nafi kam kanta na kasa, kunyar Ashraf duk ta gama rufeta ta sani sarai bai san ita bace sai yanzu. Ashraf ya kalli Asim yace " Saketa ko? " Nafi kam hannunta sai zugi yake yi, Asim yace " bazan saketa ba sai munje gaban kawu ta sanar mai abinda kai da ita kuke aikatawa. " Ashraf yai wani murmushi ya kalli agogo karfe 6 na yamma, sannan ya kalli Asim yace " ai banaji sai ta bika wajen isar da sakon kai kad'ai ma ya wadatar kaje ka sanar. " Asim ya kara cika baki da takaici yace " Me kake nufi? " Ashraf ya kalli Asim ya mai alama da ya sakar mata hannu, cikin takaici Asim ya saketa, Ashraf ya kalleta yace " wuce ko? " Nafi ta kalleshi idanunta sun cika da kwalla tanasan bashi hakuri sai dai bataga fuska ba, da kai ya mata alama ta wuce mana, jiki a sanyaye tai gaba tana yi tana waigensa. Tana fita Ashraf ya kalli Asim yace " D'an sako mai kake jira? " "d'an sako? Nine d'an sakon? " Ashraf yai wani murmushi yace " Au na d'auka danace kaje ka sanar ai zaka wuce da sauri ka gurfana agaban kawu ka sanar mai. " A zuciye Asim ya kama wuyan Ashraf cikin masifa yace " Ni kake fada ma haka? " Ashraf yad'an juya ido kad'an yace " inmu uku ne to dana ukun nake." Ya ja jikinsa ya koma d'aki dan yin alwala. Asim ya naushi iska cikin tsananin takaici yai waje jiyake kamar ya lumama Ashraf wuka hankalinsa ya kwanta. Ashraf kam alwala yai sannan ya fito waje. Nafi kam d'aki tai tana kuka, Little ta gani ta fito daga wanka, da sauri Little ta karaso tace " Nafi menene? Wani abin ya miki? Laifi kikama yayan? " Kai kawai Nafi take girgizawa, Little tace " to menene?" Nafi ta kalleta tace" me karuwa yake nufi dan Allah? " Little da mamaki ta kalleta tace " Yayan ne ya fada miki hakan? " Kai ta girgiza alamar a'a sannan tai hanyar ban d'aki da sauri, da alama kalmar bata da dad'i ganin yanda fuskar Little ta canza. Little ta bita da kallo, sannan ta d'au always d'in da Mumy ta kawo mata ta sa, zama tai jiki a sanyaye, waye yacema Nafi karuwa? Asim kam ana idar da sallah ya tari kawu acikin masallacin ma ya fad'amai, ran kawu yayi dubu gurin b'aci, ganin haka yasa Asim ya saki wani murmushin mugunta. Kawu ya fito cikin tsananin masifa nan yace Ashraf ya biyoshi, duk da kasan zuciyarsa yaji ba dadi sai dai bai nuna ba, nan Asim yabi bayan kawu. A falo Mumy, Umma, Asim da Ashraf ne a zaune sai kawu. Cikin fada kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf meke faruwa? Wani banzan labari nake ji haka? " Ashraf ya kallesu kaf sai dai kafin yai magana Aneesa ta shigo cikin tsananin kishi ta karaso kusa da Ashraf tace " Yaya me kenan? Ni zakaci amana? " Mumy wacce jikinta duk ya mutu dan ta taba ganinta ta fito daga d'akin, tai shiru yau kam batada halin kare Ashraf. Kawu ya daka mata tsawa yace " Aneesa bakida hankali ne? " Ta kalli kawu cikin tsananin takaici tace " Amma Abba..... " Hannu ya d'aga mata hakan yasa Umma ta zaunar da ita a kusa da ita. Ashraf wanda ke zaune sai dai duk masifar mutum bazai tab'a gane meke yawo a ransa ba, sam babu b'acin rai ko farin ciki a tattare dashi. Kawu yace " Asim fad'i me ka gani. " Hankalin Asim a kwance ya sanar da abinda ya gani har da karin cewa wai suna ganinshi suka tura kofar d'akin suka rufe, sai daya dade kafin su fito. Mumy ta runtse ido zuciyarta na wani irin zafi, Umma ta shiga tafa hannu tana salati, itakam Aneesa kafe Ashraf kawai tai da ido jitake kamar zata mutu dan tsananin kishi. Kawu ya kalli Ashraf rai a b'ace yace " Wani irin iskanci ne hakan Ashraf? " Ashraf ya mike daga zaunan da yake ya kallesu ga mamakinsu Murmushi sukaga ya saki, ya jinjina kai sannan yace" tunda maganar Asim itace gaskiya banaji inada abin cewa. " Yana kai nan ya nemi hanyar fita, Umma cikin kuluwa tace "lalai kuwa Alhaji yarinyar nan dole ne ta bar gidan nan, inshi ba'a isa dashi ba ai ita kam karya take. " Ashraf ya juyo ya kalleta sannan ya kalli Aneesa da ta ke zaune kamar gunki ya bud'e baki zaiyi magana yaji Mumy tace " Gaskiya nima Alhaji yarinyar nan bata kwanta min ba." Fuskar Ashraf ce ta canza, yanzu kam ransa ya b'aci sosai, bai damu inkowa ya mai abu ba amma ya tsani yaga mahaifiyarsa na goyon bayan masu mai abu. Kawu ya kalli Asim yace "Ai ba sai anja da tsauri ba, yanzu nan za'a kirata tabar gidan nan. " Ashraf ya had'iyi wani abu sannan ya d'auke idansa daga kan Mumy ya maidashi kan kawu, ya kalli Kawu yace " Kawu banasan abu yaji da zafi sai dai in aka kaini bango banajin kowa zaiji da dadi a gidan nan. " Yana kai nan yai waje, Mumy ta dafa kanta, tanaji Umma na cewa " Allah wadaran nakaa ya lalace, sam yaran nan yafi karfin kowa a gidan nan? " Kawu yai shiru shikansa ya kasa magana. Ashraf kam yana fita ya kira number Habib, bugu biyu Habib ya d'aga yace " Buddy yau kuma soyayyarce ta tashi? " Ashraf yai tsaki yace " Habib dan Allah makarantar Abbanka wace iri ce? " Da mamaki Habib yace "lalai Ashraf kana nufin bakama san me Abbana yake ba? " Ashraf yace " Malam dole ne sai na sani? Ba gashi ina tambayarka baa yanzu? " Habib wanda baiji dadin kalaman Ashraf ba yace " Primaryce da secondary." Ashraf yace " day ce ko boarding?" Day ce mana. Ashraf yad'an shafi kansa sannan yace " Habib boarding school nakesan asa Nafisa gashi kasan tayi girma ba ilimi na rasa ya zanyi. " Habib yai shiru can yace " karka damu Aminin Abba matarsa itace principal ta makarantar kwana dake nan minjibir, sai a d'an yi mata ciwa ciwa ko Js3 ne a sakata. " Ashraf ya d'an saki fuska yace "yauwa Habib hakan yayi." Habib yai dariya yace " bazaka gode min ba? " Ashraf yace " in komai ya kammala zan gode ma, but please ka tambayi Abban yanzu dan inasan ta tafi a satin nan. " Habib yace Shikenan. Yana kashe wayar yai ajiyar zuciya sannan ya makama inda ya fito wani mugun kallo na takaici, yai gaba. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Su kam a ciki sai tada zancen suke yi, mumy kam duk ranta ya gama da gulewa rai b'ace ta fito daga falon tai b'angaren su Little. A zaune taga Little a kan gado ta zuba tagumi, Nafi kuma ta ra kub'e a gefen gado ta cusa kanta cikin cinyoyinta, abu d'aya ke yawo a ranta tajama Ashraf fada ita abinda ke damunta kenan. Muryar Mumy ce tasata ga d'ago, mumy ta tsaya a kusa da Little tace " Nafi ta fadamiki abinda ya faru? " Jikin little a sanyaye tace " Mumy bakisan Nafi bane, kome ke damunta bazata taba fad'amin ba. " Mumy cikin fada tace " ai kuwa yau dole ta fada tunda gashi can ta jama Ashraf cin mutunci. " Nafi wacce jin hakan yasa ta mike cikin tsoro ta matso kusa da Mumy ta tsugunna a gabanta tace " wlh Mumy ba abinda Yaya ya sani, bai ma san nice naje d'akin ba. " Mumy tace " mene? " Nan little ta fad'a mata ita yace taje ita kuma batada lafiya shine Nafi taje, jikin mumy ne yai sanyi ta kalli Nafi tace " to akace kina d'akinsa? " Nafi ta share kwalla tace "Mumy bashida lafiya fa? " Idanu mumy ta zaro ta kalli Nafi jiki a sanyaye, Nafi wacce idanta ya rufe dasan kare Ashraf tacigaba " Mumy wlh tun safe bashida lafiya kuma wlh yana jin jiki, ni a ganina bai kamata ma ace kaf gidan nan ba wanda yasan halin da yake ciki ba........" Hannu tasa ta rufe bakinta, me take fada? A ranta tace " amma ai Anisa ta sani. Mumy tai shiru a hankali ta juya tai waje batace komai ba, little ta kalleta tace " lalai Nafi dama kin iya zakewa haka? " Nafi ta kalleta tace " Maryam bakisan halin da yaya yake ciki bane sannan ace dake kanwarsa da mahaifiyarsa ba wanda ya sani? Na d'auka in bashida lafiya Mumy ya kamata ya fara sanarwa? " Little tai wani sansanyan murmushi tace " Nafi kenan, bakisan komai ba a kan harkar rayuwar gidan nan. " Nafi ta mata kallan mamaki, little tace " karki damu zan sajar dake komai gobe, in kikaje zaki gane dalilin dayasa Yaya baya shiga harkar Mumy. " Nafi tai shiru batace komai ba.... *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com 2⃣2⃣ Mumy ta fito jiki a sanyaye kanta sai sara mata yake yi, a waje ta hango Aneesa ta taho kamar zaki rike da wata zungureriyar waya tana tafe Umma na mata magana amma da alama bata ma jin me ake cemata, Mumy tana tsaye a kofar su Little har Aneesa ta karaso, idanunta sun canza. Da mamaki Mumy ta kalleta tace " Neesah meye hakan? " Aneesa wacce sai hucci take ta kasa magana sai neman cusa kanta ciki take, Mumy tasa hannu ta riketa tace " Neesa meye hakan wai? " Umma ce ta karaso cikin kinibibi tace" Yauwa gwara da kika riketa wai Nafi zataje ta zane. " Mumy takaici ya kamata tace " in kuma Ashraf d'in yajiki kice me? " kallan Mumy tai kamar mai shirin kuka tace" Mumy amma kina ganin..... " Mumy tace " Laifinkine, in har Nafi ta fiki sanin meke damun Ashraf, ke da zai zama mijinki amma ace ba kece ke kula da shi ba. " Umma tace " wace irin magana kikeyi haka? Haba Amina ya zakisa yarinya a gaba wacce ranta yake a b'ace ki kara b'ata mata." Mumy ta kalli Umma sai dai takaicin abinda yake faruwa yasa ta kasa tanka mata. Umma ta juya kai tace " haba Amina _wace irin zuciya gareki?_ace ke kawai d'anki kika sani? " Mumy ta juya batare da ta sake magana ba. Aneesa ta kara zuwa wuya gani take kamar saboda Nafi itama Mumyn take mata haka. Hannunta ta fizge daga gun Umma tai ciki a zuciye. Nafi kam ta d'auro alwala isha'i kenan, ta zauna a bakin gado ta rasa abinda ke mata dadi, taji an banko kofa da karfi kamar za'a b'ala, da sauri ta kalli kofar. Little dake zaune akan kujera ma ta d'ago da sauri. Aneesa a zuciya ta shigo d'akin, Nafi dake tsaye ta shiga kallanta cikin tsananin tsoro, Little ta mike tace " Ya Neesa meye kuma hakan? " Aneesa ta buga mata wata muguwar harara sannan ta nufi kan Nafi gadan gadan Umma kuma ko kunya tana tsaye a baya. Da karfi Little tace " Wlh Ya Neesa kika daketa sai na fadaki da Yaya. " Cikin kuluwa Aneesa ta wurga mata kallo, Little ta kalleta tare da d'aukan wayarta tace " Wlh kika daketa yanzu zan kirashi." Aneesa kam ta kulu fam kamar zata fashe, Umma ta matso ta gaurama Nafi mari iya karfinta sannan ta kalli Little tace" ni ki tabbatar kin fadamai inyaso ya zo ya rama mata. " Tana kai nan ta fizgi hannun Aneesa tai gaba. Nafi kam ko kuka batai ba dan ganin zabgegiyar bulalar dake hannun Aneesa yasa batama ji zafin marin sosai ba. ¤¤¤¤¤ Mumy kam ana idar da sallah tai b'angaren Ashraf, a hanya suka had'u da Mumy baice mata komai ba sai dai yasan gunsa tazo, nan ya bud'e ya shiga tare da kunna kwan wuta. A bud'e ya bar kofar hakan yasa Mumy ta shiga. Shikam d'aki kawai ya wuce, ya d'au ruwan da Nafi ta gasa mai gun ciwon ya zubar a toilett, sannan ya matse towel d'in ya shanya sannan ya fito. Mumy na zaune hakan yasa yaje d'an nesa kadan da ita ya zauna a kasa, Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tace " Ashraf abinda ya faru d'azu kayi hakuri....." D'agowa yai ya kalleta idanunsa sunyi jaa jikinta ya kara yin sanyi, cikin wata irin murya wanda mai sauraro shi kad'ai zai fahimci abinda ke zuciyar me maganar Ashraf yace " Kin taba yadda dani Mumy? Ko me aka fada a kaina tun ina karami kin taba yin bincike kafin kimin fada? " Mumy idanunta suka cicika da kwalla sai dai tsananin tausayin Ashraf dake yawo a ranta. Hannu yasa a bugi inda zuciyarsa take da karfinsa wanda kana iya juyo karar dukan ya cigaba " Kinsan ya nakeji a raina? A duk sanda kika zargeni da abinda banyi ba?....." Kasa karasa kalamansa yai saboda wani rad'ad'i da zuciyarsa take mai, Mumy wacce ganin yanayin d'anta da bata taba gani ba yasa hawayen datake b'oyewa suka zubo ta gefen idanta. Kallansa tai cikin dauriya tace " ba haka bane Ashraf. " Ya kalleta sannan yai wani murmushin takaici yace " Nafi zata tafi makarantar kwana a satin nan insha Allah. " Mumy bata d'auke ido a kanshi ba tace " amma naga kamar ba tada karatu? " Ya sake yin wani murmushin wanda itakam mumy sam batasan taga yayi saboda bata sani me yake nufi yace "eh hanya za'a mata ta shiga Js ko 3 ne inyaso sai a dinga mata lesson kuma a makarantar. " Mumy ta jinjina kai tace " hakan yayi sai dai baka ganin karatun zai mata wahala? " Ashraf ya d'an tab'e baki yace " wannan kuma ruwanta. " Mumy tace " shikenan in makarantar ta fito sai ka fadamin sai muje a mata shopping Allah ya baka lada ya kuma yi albarka. " A cikin ransa yace Ameen, ta mike tace " bari inje. " Bai amsa ba ko ince tasan ma bazai amsa ba, tana fita yabi bayanta da kallo sannan ya koma d'aki ya d'auko diary d'in mahaifin sa wanda wasiya ce kawai ya barmai. Shafin farko wanda a kullum sai ya karantashi yau ma shi ya karanta " _Ashraf kada ka kuskura kabar mutane susan abinda ke zuciyarka,_ _ka dinga kokarin b'oye bakin ciki ko farin cikin dake ranka, kar ka bari wani yasan sirrinka, wannan ita kadai ce hanyar da zaisa ka kare kanka...ko da kuwa 'yan uwanka ne na jini..._" Ashraf ya share zufar data keto mai duk da sanyin AC d'in da ke d'akin, Murmushi yai wanda kana ganin kasan na bakin ciki ne a fili yace " Dad zan iya jure hakan kuwa? I am really lonely." Ya kwantar da kansa kan gado, kafad'ar sa na masa zugi sai dai zugin dake zuciyarsa tafi karfin wannan....... ¤¤¤¤¤¤ Habib kam da kansa ya samu Abbansa ya mai bayani, Abban Habib na tsananin san Ashraf a lokacin ya kira wayar abokinsa ya sanar dashi, sunyi rashin sa'a matar tashi an mata transfer zuwa Rumfa Collage sai dai ya sanar dasu ai kanwarta ma principal ce ta FGC na kazaure, nan ya sanar musu in suna san can d'in to a yanzu zai kira kanwar matar tasa ya fada mata. Nan Habib ya ma Abba alama da a yadda, sunyi sallama akan zai kira anjima. Ba'a dade ba ya kira tare da sanar dasu ba matsala duk sanda suka shirya ko gobe ne su kaita. Nan Habib ya kira Ashraf yamai bayani. ¤¤¤¤¤ A b'angaren D'an litti kuwa yan sanda sun gaji da ajiyarsa gashi abin haushi bashida alamar sanar dasu Inda Ashraf yake, duk kuwa da dukan da sukamai, hakan yasa haushi ya kamasu suka cilloshi waje tare da kwace wukar dake jikinsa. D'an litti ya sha kuka wiwi gashi ko ficika bashida shi, ga wunya datake damunsa. Dakyar ya mike ya dingisa ya shiga gari, yayi sa'a ya sami wani mutum ya bashi naira d'ari. Nan ya gangara yasai wainar gero kan kace me ya cinye, ta gumi ya baza yace " Oh Ni D'an litti haka rayuwata ta koma? Daga boko sai a nemi halakani? Yanzu ni ina zan nufa in nemo Ashaf d'in? " Ya jingins kansa da bango zafin rana na damunsa. Nace wayyo🤦🏻‍♀ *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Fatie Shafi'u ina tayaki murnar kammala Jarabawarki. May Almighty Allah help and protect u.... ILYSM* Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari. Nan ya taho da shi gidansu Ashraf. Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamman ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta. Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take, sunayi suna 'yar hirarsu da Goggo. Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d'an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace " Wai kizo inji yaya. " Nafi ta kalleta cikin zak'uwa tace " Ya Ashraf? " kai Amra ta d'aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b'angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu, tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai. Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba, sai dai yau gani tai anzo an bud'e da fara'arta ta kalli mai bud'ewa tace " Yaya ina kwa...... "kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi. Jin ta tsaya da magana yad'an kanne ido cikin salonsa yace " Haba Nafi ba ni kika so gani bane? " Da sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta d'ora da cewa " ba haka bane Ya Habib. " Habib ya d'an matso kad'an hakan yasa ta d'an kara matsawa, kara matsowa yai itama ta kara matsawa, sam bata kula tazo karshe ba tayi baya zata matsa kawai taji zata fad'i, da sauri yasa hannu a kugunta ya tarota. Nafi kam har ta runtse idanta kam, jin an riketa yasa ta bud'e ido a hankali, Habib ya sakar mata wani lalausan murmushi, sannan ya matso da fuskarsa yace " Me yasa kika tsaya da maganar ki to? " Yawu ta had'iya da karfi sannan ta d'an motsa baki tace " Ya Habib d'an sakeni. " Jin ta waske bata bashi amsa ba yasa ya d'agota tare da sake cewa " Shikenan na hakura da gaisu.... " Bata jira ya karasa ba tace ina kwana? " Dariya ya d'anyi sannan yace " Nafi kina burgeni na rasa me yasa. " Kasa tai da kai dan itakam tasan wasa ne ace tana burge wani. Ashraf dake zaune a kujera duk yana kallan me sukeyi kasancewar kofar a bud'e Habib ya bata yaja wani karamin tsaki tare da girgiza kai yace " in kun gama sai ku shigo, dan ni inada abinyi. " Nafi ta kalli inda Ashraf yake haka kawai taji gabanta ya fad'i tare da tsananin takaicin ganin ta dayai. Habib ya matso da niyyar rike mata hannu da sauri ta b'oye hannun a baya kallanta yai fuska a sake sannan ya d'anyi gaba yace " Ki shigo. " Da sauri ta shige jikinta duk yai sanyi. Ashraf na zaune yana kallo ta karasa tare da zama a kasa, Habib ya kalleta yace " zauna a kan kujera mana? " Ashraf ya bugamai wani mugun kallo yace " Mu sa'aninta ne? Kai meyasa kake kokarin zubar mana da mutunci agurin yara kanana? " Nafi wacce ko alamar tashi dama batai ba ta d'ago ta kalleshi sai dai zuciyarta ta d'anji ba dadi. Ashraf ya d'auke idansa, Habib ma kasa magana yai, Shiru ne ya d'an biyo baya kafin Ashraf yace " Nafisa! " Gaba d'aya tun daga kan yatsar kafarta har zuwa kanta sai dataji wani abu ya wuce mata, d'agowa tai a hankali ta kalleshi. Ashraf kam ko a jikinsa yace " yau zuwa gobe zakuje da Little da kuma mumy xakuje siyayyar kayan makarantarki. " Kallonsa tai cikin mamaki batasan sanda tace " naam? " Ya had'e fuska sosai yace " bakiji me nace ba? " Tace " Naji kace makaranta. " Yace " eh, in kun gama siyayya da komai zuwa jibi zaki wuce makarantar kwana dake kazaure. " Nafi kam idanunta ne suka ciciko, wani irin farin ciki ne wanda ita kanta batasan irinshi ba yake ratsata, Ashraf yace " meye hakan? " Hawayenta ta goge wanda suka zubo, ta girgiza kai tace ba komai. Habib cikin damuwa yace " Bakyaso ne? " Kai ta girgiza da sauri tace "a'a ba haka bane. " Ashraf ya d'an kuraa mata ido kamar yanasan gano wani abun, idanunta tai saurin yin kasa dasu tace a hankali tace " Yaya babana fa?" Jiyai ransa ya b'aci ya ce " Bansan inda yake ba, kuma bana fata insani, sannan in har da haka kike tunanin yin karatun to gwarama karkije, dan ni na tsani mutum mai raunanniyar zuciya. " ya mike yai ciki. Kallo ta bishi dashi zuciyarta tana dana sanin tambayar datai, sai dai duk yanda taso da daurewa ai dole ne tai rashin mahaifinta. A ranta ta maimaita Raunanniyar Zuciya? Me kenan? Kamar Habib yasan meke ranta yace " karki damu da fadan Ashraf dan shi yawancin maganarsa haka take. " Nafi tabi d'akinsa da kallo tanasan ta bashi hakuri ta kuma tambayeshi ciwon sa, daurewa tai ta kalli Habib tace " Ya Habib meye raunanniyar zuciya? Ma dai san me zuciya take nufi" Dariya yai yace " rauni fa? " Tace " na sani. " Ya sake dariya yace " to sai ki had'asu guri d'aya ki gani. " Tace " Rauni Zuciya? " Wannan karan dariya sosai Habib yai yace " lalai Nafi inkinje makaranta cikin mutane a hankali zaki fahimta. " Tace to, sannan ta sake kallan d'akin Ashraf sai dai ba yanda zatai, mikewa tai zata fita, Habib yace " aiki kikai ne? Naga kayanyi sun b'aci kamar daga kitchen kika fito. " A'a kawai tace tai saurin fita. Tana gaba kad'an sai ga Aneesa wacce tasha kwalliya tana tafe kamar sarauniya. Idanunsu ne suka had'u, gaban Nafi ne ya fad'i bawai dan tsoro ba a'a sai dan ganin kyan datai, a cikin zuciyarta tace " Dole Ya Ashraf yasoki. " Tun datazo gidan bata taba ganin Aneesa ta d'au kwalliya irin haka ba, ba namiji ba ko mace ce ta wuce dole ne ta kalleta dan tayi kyau sosai, Aneesa wacce takura ma Nafi ido cikin tsananin takaici ta karaso. Kwalliya tai dan taje su shirya da Ashraf amma me take gani haka? A zuciye ta karaso tare da kallan Nafi cikin tsananin takaici tace me kike anan? " Nafi ta kalleta sai dai ta kasa cewa komai, Aneesa ta sake kuluwa tace " ke dan gidan ku ba magana nake miki ba? " Nafi ta daure kawai jitai ta sami kanta da cewa" Ya Habib ne ya kirani. " Aneesa wacce bata gamsu da zancen ba tace " Nafi karkiga jiya nazo da niyyar dukanki ki d'auka wai ko kishi nake dake ko wani abun. " Ta d'anyi dariyar kissa tace " Tausayi kike bani, kinfi kowa sanin ni dake ba d'aya bane sannan ke da kanki zaki iya warewa kisan wa ya dace da Ashraf ko ince wa Ashraf yake so, dan haka ina baki shawara in ma da wani shirme ko yarinta akanki gwara tun wuri ki cireta dan kinsan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke ko masu aikin gidan nan sun fiki daraja. " Ta bangaje ta tai gaba, jitai ranta yayi sanyi ta tuno maganar Umma datace " ki nuna mata ita ba komai bace ta hakan ne inma da wani munafircin a ranta zai sa ta shiga hankalinta."juyowa tai ta kalli Nafi tana nan a inda ta barta, ta sake dariya sannan tai gaba. Nafi kam sai juya kalamun take a ranta, tafi kowa sanin Ashraf yafi karfinta, ta kuma sani ko kata sun kare ba abinda zaiyi da ita sai dai meyasa takejin zuciyarta ba dadi? Wata zuciyar tace kema Nafi kina ganin mai mace kamar Aneesa me zaiyi dake? Jiki duk a rame? Gaki yar kauye wacce ake neman biyan bashi da ita? " Da kyar ta karasa d'aki tai wanka sannan tasa abinci a gaba, da kyar takeci ta rasa me yasa batajin dadin abincin sam. Aneesa kam tana shiga taga Habib zaune a kan dinning yana cin abinci, tai murmushi tace " Yaushe a gari d'an uwan Ango? " Habib ya kalleta yace " Amarya irin wannan kwalliyar kamar yauce ranar? Ko dai anzo seducing d'in d'an uwa nane? " Aneesa ta d'anyi dariya har hakoranta suka fito ta d'an karkace kadan tace " me? Kana tsoro ne? Ko kuwa kishi kake ba kada me ma?" Habib ya rike haba yace " tab lalai d'an uwana yana cikin tashin hankali gwara muyi sauri mu kawoki kafin ki burkice mana d'an uwa." Aneesa ta d'an fara tafiya cikin salo tare da cewa " ah to wayace kukai bikin da nisa?" Habib ya bita da kallo yana murmushi. D'akin Ashraf ta murd'a, kai tsaye ta shiga, Ashraf wanda ke kokarin shiga wanka ya kalli kofar kansa tsaye ya d'auka ko Habib ne, ganin Aneesa yasa ya had'e fuska tamau, ta sakar nai wani murmushi tace " Sorry Hubby ashe wanka zakai. " Ya kalleta yace " Aneesa bakisan ya ake sallama ba ko kwankwasa kofa ba? " Ta shagwab'e tare da shiga ta zauna a bakin gado tace " nida d'akin mijina? " Ya girgiza kai cikin takaici yai hanyar toilet sannan ya tsaya ya kalleta tare da cewa " nine mijin kuma banaji na bada sadaki bare a shafa fatiha, dan haka ki kiyaye shigomin d'aki kai tsaye." yana kainan ya shige toilet. Aneesa ta turo baki cikin jin haushi sai dai ta kasa cewa komai sannan tana kunyar fita kar Habib ya mata dariya...... *THE INNOCENT TEAM*[5/12, 6:24 PM] ‪+234 703 962 5239‬: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Fatie Shafi'u ina tayaki murnar kammala Jarabawarki. May Almighty Allah help and protect u.... ILYSM* Washe gari da safe Habib yaje makarantar mahaifinsa yama Nafi takardun karya na primary da kuma Js 1 and 2, sai dai takardun sun nuna sam batada kokari. Nan ya taho da shi gidansu Ashraf. Yau gidan an tashi kowa zuciyarsa ba dadi musamman ma Umma da Aneesa, Little kam ta fita makaranta. Itakam Nafi tana kitchen ta zake sai aikin girki take, sunayi suna 'yar hirarsu da Goggo. Suna gamawa ta fito duk jikinta ya d'an baci Amra ce ta karaso gunta da gudu tace " Wai kizo inji yaya. " Nafi ta kalleta cikin zak'uwa tace " Ya Ashraf? " kai Amra ta d'aga mata ai kam Nafi da sauri ta nufi b'angarensa tana tafe tana gogee fuskarta da hannu, tun jiya takesan ganinshi sai dai ba yanda zatai. Fuskarta a sake ta kwankwasa kofar, ta saba in yana ciki sai dai yace ta shigo in dai har ba makulli yasa ba, sai dai yau gani tai anzo an bud'e da fara'arta ta kalli mai bud'ewa tace " Yaya ina kwa...... "kalamanta ne suka tsaya ganin Habib a tsaye yana mata murmushi. Jin ta tsaya da magana yad'an kanne ido cikin salonsa yace " Haba Nafi ba ni kika so gani bane? " Da sauri ta girgiza kai alamar a'a sannan ta d'ora da cewa " ba haka bane Ya Habib. " Habib ya d'an matso kad'an hakan yasa ta d'an kara matsawa, kara matsowa yai itama ta kara matsawa, sam bata kula tazo karshe ba tayi baya zata matsa kawai taji zata fad'i, da sauri yasa hannu a kugunta ya tarota. Nafi kam har ta runtse idanta kam, jin an riketa yasa ta bud'e ido a hankali, Habib ya sakar mata wani lalausan murmushi, sannan ya matso da fuskarsa yace " Me yasa kika tsaya da maganar ki to? " Yawu ta had'iya da karfi sannan ta d'an motsa baki tace " Ya Habib d'an sakeni. " Jin ta waske bata bashi amsa ba yasa ya d'agota tare da sake cewa " Shikenan na hakura da gaisu.... " Bata jira ya karasa ba tace ina kwana? " Dariya ya d'anyi sannan yace " Nafi kina burgeni na rasa me yasa. " Kasa tai da kai dan itakam tasan wasa ne ace tana burge wani. Ashraf dake zaune a kujera duk yana kallan me sukeyi kasancewar kofar a bud'e Habib ya bata yaja wani karamin tsaki tare da girgiza kai yace " in kun gama sai ku shigo, dan ni inada abinyi. " Nafi ta kalli inda Ashraf yake haka kawai taji gabanta ya fad'i tare da tsananin takaicin ganin ta dayai. Habib ya matso da niyyar rike mata hannu da sauri ta b'oye hannun a baya kallanta yai fuska a sake sannan ya d'anyi gaba yace " Ki shigo. " Da sauri ta shige jikinta duk yai sanyi. Ashraf na zaune yana kallo ta karasa tare da zama a kasa, Habib ya kalleta yace " zauna a kan kujera mana? " Ashraf ya bugamai wani mugun kallo yace " Mu sa'aninta ne? Kai meyasa kake kokarin zubar mana da mutunci agurin yara kanana? " Nafi wacce ko alamar tashi dama batai ba ta d'ago ta kalleshi sai dai zuciyarta ta d'anji ba dadi. Ashraf ya d'auke idansa, Habib ma kasa magana yai, Shiru ne ya d'an biyo baya kafin Ashraf yace " Nafisa! " Gaba d'aya tun daga kan yatsar kafarta har zuwa kanta sai dataji wani abu ya wuce mata, d'agowa tai a hankali ta kalleshi. Ashraf kam ko a jikinsa yace " yau zuwa gobe zakuje da Little da kuma mumy xakuje siyayyar kayan makarantarki. " Kallonsa tai cikin mamaki batasan sanda tace " naam? " Ya had'e fuska sosai yace " bakiji me nace ba? " Tace " Naji kace makaranta. " Yace " eh, in kun gama siyayya da komai zuwa jibi zaki wuce makarantar kwana dake kazaure. " Nafi kam idanunta ne suka ciciko, wani irin farin ciki ne wanda ita kanta batasan irinshi ba yake ratsata, Ashraf yace " meye hakan? " Hawayenta ta goge wanda suka zubo, ta girgiza kai tace ba komai. Habib cikin damuwa yace " Bakyaso ne? " Kai ta girgiza da sauri tace "a'a ba haka bane. " Ashraf ya d'an kuraa mata ido kamar yanasan gano wani abun, idanunta tai saurin yin kasa dasu tace a hankali tace " Yaya babana fa?" Jiyai ransa ya b'aci ya ce " Bansan inda yake ba, kuma bana fata insani, sannan in har da haka kike tunanin yin karatun to gwarama karkije, dan ni na tsani mutum mai raunanniyar zuciya. " ya mike yai ciki. Kallo ta bishi dashi zuciyarta tana dana sanin tambayar datai, sai dai duk yanda taso da daurewa ai dole ne tai rashin mahaifinta. A ranta ta maimaita Raunanniyar Zuciya? Me kenan? Kamar Habib yasan meke ranta yace " karki damu da fadan Ashraf dan shi yawancin maganarsa haka take. " Nafi tabi d'akinsa da kallo tanasan ta bashi hakuri ta kuma tambayeshi ciwon sa, daurewa tai ta kalli Habib tace " Ya Habib meye raunanniyar zuciya? Ma dai san me zuciya take nufi" Dariya yai yace " rauni fa? " Tace " na sani. " Ya sake dariya yace " to sai ki had'asu guri d'aya ki gani. " Tace " Rauni Zuciya? " Wannan karan dariya sosai Habib yai yace " lalai Nafi inkinje makaranta cikin mutane a hankali zaki fahimta. " Tace to, sannan ta sake kallan d'akin Ashraf sai dai ba yanda zatai, mikewa tai zata fita, Habib yace " aiki kikai ne? Naga kayanyi sun b'aci kamar daga kitchen kika fito. " A'a kawai tace tai saurin fita. Tana gaba kad'an sai ga Aneesa wacce tasha kwalliya tana tafe kamar sarauniya. Idanunsu ne suka had'u, gaban Nafi ne ya fad'i bawai dan tsoro ba a'a sai dan ganin kyan datai, a cikin zuciyarta tace " Dole Ya Ashraf yasoki. " Tun datazo gidan bata taba ganin Aneesa ta d'au kwalliya irin haka ba, ba namiji ba ko mace ce ta wuce dole ne ta kalleta dan tayi kyau sosai, Aneesa wacce takura ma Nafi ido cikin tsananin takaici ta karaso. Kwalliya tai dan taje su shirya da Ashraf amma me take gani haka? A zuciye ta karaso tare da kallan Nafi cikin tsananin takaici tace me kike anan? " Nafi ta kalleta sai dai ta kasa cewa komai, Aneesa ta sake kuluwa tace " ke dan gidan ku ba magana nake miki ba? " Nafi ta daure kawai jitai ta sami kanta da cewa" Ya Habib ne ya kirani. " Aneesa wacce bata gamsu da zancen ba tace " Nafi karkiga jiya nazo da niyyar dukanki ki d'auka wai ko kishi nake dake ko wani abun. " Ta d'anyi dariyar kissa tace " Tausayi kike bani, kinfi kowa sanin ni dake ba d'aya bane sannan ke da kanki zaki iya warewa kisan wa ya dace da Ashraf ko ince wa Ashraf yake so, dan haka ina baki shawara in ma da wani shirme ko yarinta akanki gwara tun wuri ki cireta dan kinsan wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa, ke ko masu aikin gidan nan sun fiki daraja. " Ta bangaje ta tai gaba, jitai ranta yayi sanyi ta tuno maganar Umma datace " ki nuna mata ita ba komai bace ta hakan ne inma da wani munafircin a ranta zai sa ta shiga hankalinta."juyowa tai ta kalli Nafi tana nan a inda ta barta, ta sake dariya sannan tai gaba. Nafi kam sai juya kalamun take a ranta, tafi kowa sanin Ashraf yafi karfinta, ta kuma sani ko kata sun kare ba abinda zaiyi da ita sai dai meyasa takejin zuciyarta ba dadi? Wata zuciyar tace kema Nafi kina ganin mai mace kamar Aneesa me zaiyi dake? Jiki duk a rame? Gaki yar kauye wacce ake neman biyan bashi da ita? " Da kyar ta karasa d'aki tai wanka sannan tasa abinci a gaba, da kyar takeci ta rasa me yasa batajin dadin abincin sam. Aneesa kam tana shiga taga Habib zaune a kan dinning yana cin abinci, tai murmushi tace " Yaushe a gari d'an uwan Ango? " Habib ya kalleta yace " Amarya irin wannan kwalliyar kamar yauce ranar? Ko dai anzo seducing d'in d'an uwa nane? " Aneesa ta d'anyi dariya har hakoranta suka fito ta d'an karkace kadan tace " me? Kana tsoro ne? Ko kuwa kishi kake ba kada me ma?" Habib ya rike haba yace " tab lalai d'an uwana yana cikin tashin hankali gwara muyi sauri mu kawoki kafin ki burkice mana d'an uwa." Aneesa ta d'an fara tafiya cikin salo tare da cewa " ah to wayace kukai bikin da nisa?" Habib ya bita da kallo yana murmushi. D'akin Ashraf ta murd'a, kai tsaye ta shiga, Ashraf wanda ke kokarin shiga wanka ya kalli kofar kansa tsaye ya d'auka ko Habib ne, ganin Aneesa yasa ya had'e fuska tamau, ta sakar nai wani murmushi tace " Sorry Hubby ashe wanka zakai. " Ya kalleta yace " Aneesa bakisan ya ake sallama ba ko kwankwasa kofa ba? " Ta shagwab'e tare da shiga ta zauna a bakin gado tace " nida d'akin mijina? " Ya girgiza kai cikin takaici yai hanyar toilet sannan ya tsaya ya kalleta tare da cewa " nine mijin kuma banaji na bada sadaki bare a shafa fatiha, dan haka ki kiyaye shigomin d'aki kai tsaye." yana kainan ya shige toilet. Aneesa ta turo baki cikin jin haushi sai dai ta kasa cewa komai sannan tana kunyar fita kar Habib ya mata dariya...... *THE INNOCENT TEAM* [5/13, 8:19 PM] ‪+234 703 962 5239‬: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Hajja ce! I Sincerely Dedicate This Page to You... ILYSM😍* *24* Tana nan a zaune jugum har ya fito daga wanka, daga bakin kofa ya kalleta fuskar nan a had'e tam yace" me kikeyi har yanzu? " Mikewa tai ta d'anyi rau da ido tace " Haba Hubby na taya na ciwo kwalliya dan in birgeka zaka dinga wulakantani haka? Tunda kaga nazo ai kasan hakuri nazo in baka. " Ashraf ya wani saki murmushin rainin hankali sannan ya mata wani kallo wanda ita da akawa ita kadai tasan me yake nufi yace " Ko? " Tace " bangane ba? " Ya d'an juya kai gefe yace " ke kina tunanin har kinkai matsayin da zaki tozartani a gaban mutane sannan ki biyo ta baya kice zaki ban hakuri? " Aneesa ta d'an canza fuska kad'an tace " Amma Yaya kasan dai ko waye dole yaji haushi, ko bakasan na dinga kishin ka? " Kallanta yai sannan yad'an girgiza kai na takaici hanyar waje ya nuna mata da yatsarsa yace " yi nan. " Ta kare lagub'e fuska, yace " kinfi karfi? " Juyawa tai a hankali tai waje tana fita yasama kofar makuli, tare da jan tsaki. Nan ya shafa maganinsa sannan ya shiga kokawar sa kaya, bayan yasa ma kwanciyarsa yai a kan gado. Itakam Aneesa tana fita Habib ya kalleta tare da guntse dariyar datake kokarin tahomai yace " Badai fada kukai ba? " Ta kalli Habib kamar zatai kuka sai kuma ta daure tace " a'a kaya zai sa. " Habib ya jinjina kai, zama tai a kan kujera shikuma ta mike yai waje, Aneesa ta dade a zaune tun tana irgaminti har ta dawo hour, ganin hour din Ashraf biyu a ciki gashi har bacci yana neman d'aukan ta yasa ta mike kamar ta kurma ihu. Abin haushi taje tana kwankwasa kofar Ashraf sai ga Habib ya shigo, yana ganinta baisan sanda dariya ta zo mai ba. Aneesa takalleshi cikin kuluwa tace " Abokin Ango meye hakan? " Habib ya had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri yace " Tuba nake Amarya amma naga kamar fada kukai da Angon." Aneesa wani takaici ya kara kamata ta kalli kofar Ashraf sannan ta kalli Habib dake juya kai yana d'an dariya haushi yakamata kawai ta tsugunna a gun tasa kukan shagwab'a. Kuka take sosai Habib ganin haka ya kara komawa waje. Ashraf kam wanda kukan duk ya dameshi ya mike jiki a sanyaye ya bud'e kofar, Aneesa tana jin ya bud'e ta kara sautin kuka. Ashraf ya tako a hankali, ya tsugunna shima tare da sa hannu akan kafad'arta, kamar jira take dama ya tab'a ta kawai ta kankameshi tana kuka, Ashraf ya shiga kokarin zare jikinsa amma ta kankameshi tamau sai kuka take. Ganin bata da niyyar sakinshi yasa ya mike da karfi, Aneesa ta d'ago fuskarta wacce duk ta b'aci kaca kaca sakamakon kwalliyar datasha, Ashraf ya dafata yace " Anie na fada miki ba sau d'aya ba kidaina kankameni haka." Ta turo baki tace " kai fa mijinane. " Ashraf yace " banzama ba tukunna, sai an d'aura mana tukunna, sau nawa ina sanar dake hakan? " Aneesa ta kara share hawaye tace " Yaya naji to zan daina amma d'an Allah kadaina wahalar da zuciyata. " Mikewa yai batare da ya amsa ba ya bud'e kofar d'akinsa yace " zo ki wanke fuskarki. " Ta turo baki tace " bakasan kwalliyar? " Kai ya girgiza alamar a'a yace " ki shiga kya gani " Ta mike zuciya ba dadi tai toilet. Tana shiga taga fuskarta a madubi kamar dodo, da sauri ta matso liquid soap ta shiga wanke wa tana yi tanajin haushin ganinta a haka da Ashraf yai. ¤¤¤¤¤¤ Da yamma bayan little ta dawo Mumy ta sasu a mota suka fita shopping, sunyi siyayyar kayan abincinta sannan aka sai uniforms, da house wear sannan suka wuce gun mai d'inki, nan suka bashi sannan suka amshi ragowar sababbin d'inkunenta, wannan kuma akan gobe za'a mata tunda uniform ne bawai style za ai ba. Nafi kam kana kallanta zakasan tana cikin farin ciki dan little ma sai tsokanarta takeyi. Sun gama komai kafin su nufi hanyar gida, Little ta kalli Nafi tace " Nafi kinsan Ice cream?" Kallan mumy tai wacce tai kamar batajinsu sannan ta kalli Little ta girgiza mata kai alamar a'a. Little ta zunguro kusa da Mumy tace " mumy asai mana Ice cream. " Murmushi Mumy tai tace " to. " Nan suka karkata suka gangara 212, Little ta kama hannun Nafi suka shiga ciki, Nafi kam sai sadda kai kasa take, dama Mumy bata bisu ba tana zaune cikin mota sai dai tabi Nafi da kallo wacce ta ke kula da nutsuwarta tunda suka fito. Tana jinta sanda suna siyayya tana tab'a Little akan wai duk kayan na makaranta ne? Ai sunyi yawa ina zata kaisu? Tanaji sai dai Little tai dariya tace "ke dai me ya dameki? " Mumy ta saki fuska tabi bayansu da kallo. Sukam suna shiga Little ta shiga zab'an abubuwan da zasu siya da yake duk sunayen da turanci take fada yasa Nafi kawai ta zura mata ido tanaji inama itama tasan ke ake cewa? Sunyi siyayya sosai kafin su fito, Nafi ta kalli Little tace " ku kam wani irin kud'i gareku? Na ga sam bakwajin wahalar kashesu. " Little ta d'an harareta tace " Ke dai in an miki abu kawai kiyi godiya ki daina cewa ya miki yawa. " Nafi bata amsa ba sai dai ta bita da kallo, nan suka koma mota. Mumy ta ja mota suka tafi, sun isa gida mumy tai parking zasu fito Nafi tace " Mumy angode Allah ubangiji ya kara bud'i." Murmushi Mumy tai sannan ta amsa da Amin. Zasu fita sai ga Habib da sauri ya karaso, shiya rike musu kofar motar, Little kam wani shaukin farin ciki ne ya ziyarci zuciyarta tace " Ya Habib? " Yakwantar da kansa a jikin kofar kad'an yace " My Little Princess i really miss u" Little wacce zuciyarta ta kara yin haske ta juya fuska cikin shagwab'a tace " bayan yaya ya daina damuwa dani? " Habib ya kalli Nafi ba tare daya ba Little amsa ba yace " Nafisa ba magana? " Ina wuni ta fad'a cikin sanyin muryarta, Ya amsa tare da kallan cikin motar yace " Mumy sannu. " Mumy ta fito tare da cilamai makulli tace " akwai kaya a boot ka tayasu kwasa zuwa b'angarensu. " Ya chafe tare da yi mata salute yace " yes maa. " Mumy tai gaba, Little ya kalla yace " Little Princess ba a huce bane? " Tace " Yaya Allah kuwa..... " Ya katseta tare da had'e hannayensa biyu alamar ban hakuri, hakan yasa ta kasa karasawa, itakam Nafi dama tad'an matsa nesa da su kad'an, jitai Habib yace " To gimbiya sai ki matso mu kwashi kayanki ko? " Da mamaki ta juyo tace " Ba dai nice Gimbiyar ba ko? " Habib yai dariya yace " me? Bakyasan sunan? " Zatai magana Little tace " Ni Princess ita Gimbiya? Ya Habib to meye marabarsu? " Ya saki dariya yace " Princess ba dai tana kishi ba? " Da sauri tace " ni dai bance ba. " Nafi itakam ta karaso ta d'au ledoji manya manya ta nufi hanyar ciki, Habib da sauri ya sha gabanta yace " ta ina mace yarinya kamarki zata iya d'aukan kayan nan? " Nafi ta kalleshi tace " zan iya, kai dai kaba Maryam hakuri. " Ya kalli Little sannan ya juyo da niyyar yima Nafi magana sai dai can ya ganta tayi gaba, ya saki murmushi tare da shafar keyarsa sannan ya koma gun Little. A falo Nafi ta tadda Aneesa da kawarta a zaune suna hira, Nafi ta tsugunna ta gaidasu sannan ta nufi hanyar d'akinsu, Aneesa ganin manyan ledoji yasa tace " ke zo nan." Nafi ta juyo ta kalleta sai dai bata karasa ba, Aneesa tace " ke munafuka ba dake nake ba? " Nafi ta ajiye kayan a bakin kofa ta nufi gunta, cikin masifa Aneesa tace " da ke da kayan nakesan ganinki. " Nafi ta koma ta d'auko kayan ta karasa gunta, gyara zamanta tai sannan ta fizgi Ledar da karfinta ta shiga bincikewa, Nafi kam yau ta kulu, har ranta sai dataji haushin wannan abun, tana kallon Aneesa ta juye ledar ma gaba d'aya akan carpet dai dai nan Little ta shigo falon, mamaki ne ya kamata tace "me kenan? " Habib ya karaso shima ya kalli wannam cin mutuncin, ga Nafi a gefe ta tsugunna, Aneesa ta bugama Little harara idanta ya rufe ko Habib bata gani ba tace " Little wa aka saima kayan nan? " Little ta kalleta rai b'ace tace " Ya Neesa me ya dameki da wanda aka saiwa? " Aneesa ranta ya b'aci ga kawarta a zaune a kusa da ita, tace " mene?" Little a zuciye ta karaso tace " Ya Neesa wai meke damunki ne? Taya zakiga kayan mutane kawai ki zubar a kasa? " Kawar Aneesa ta kalli Little tace " lalai Little yaushe kika zama mara kunya haka? Aneesa ba yayarki bace? Sannan yanzu da kika ganni anan tsara shirye shiryen da za'ai da bikinta da yayanki mukeyi ai ko bata zama matarsa ba ai yayarki ce bare an kusa. " Little ta kalleta a kule sai dai ta kasa magana ta kalli Nafi cikin takaici ta wani takure kanta a kasa zatai magana kawai sukaji ance "Tsugunna ki kwashe kayan da kika zubar. " Gaban Aneesa ne ya fad'i ta juyo a tsorace, ba ita ba Little da Nafi ma kofa suka kalla haka ma kawar. Ashraf ne a tsaya kana ganinsa kasan ba wasa a fuskarsa, Little ta kalli Habib wanda ke tsaye daga kofa, a ranta tace " yaushe ya kira shi? " Aneesa ta kalleshi tace " Yaya.... " Wani kallo ya mata wanda yasa ta had'iye maganar ta cikin tsawa wacce ta razana kowa dake falon yace " Kowa ya fita." Nafi kam jikinta rawa ya kauri dashi, bata tabajin yayi tsawa haka ba, Little ta kamata sukai waje a sukwane itama kawar Aneesa da sauri tai waje ta nufi d'akin Umman Aneesa. Ya rage daga Aneesa sai Ashraf a d'akin, ya kara kallanta yace " ba dake nake ba? " Idanunta na kansa kallan mamakin dizgata dayai take, ta daure tace " Yaya ni zaka wulakanta akan Nafi? " Shi baimasan a hannun Nafi aka anshi kayanba, shidai Habib yace yazo akwai matsala a b'angaren su Little, da ya iso shine yake cemai Mumy ta siyo kaya Aneesa ta zubar. Ashraf ya kara kallanta, idanunta suka ciciko tace " Yaya kana san ka nunamin ka fifita Nafi akaina kenan ko me? " Ashraf ya kalleta cikin tsananin takaici zaiyi magana kawai sai ga Asim da Umma sun shigo cikin masifa........ *THE INNOCENT TEAM* [5/15, 7:43 PM] ‪+234 703 962 5239‬: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* *25* Nafi wacce little ke janta akan su tafi b'angaren Mumy tana ganin Umma da Aslam sunyi b'angarensu a fusace yasa ta turje tare da kallan Little tace " Maryam wannan abun duk laifinane, kina ganin abun nan yana neman ya zama babba? Sannan ni kuma in gudu?" Little ta tsaya itama tare da cewa " Laifinki? Ta ina ya zama laifinki?" " laifinane mana tunda dai a hununa aka amshi kayan." Haushi ya kama Little ta rasa Nafi wace irin yarinya ce, ta kalleta tare da dafata tace " Naji a kaddara laifinki ne mai zakiyi in kika koma?" " Hakuri zan bada mana kina ganin su Umma sun tafi nasan kowa laifin yaya zai gani." Ta karasa maganar cikin rawar murya. Little ta kalleta sai dai ta rasa me ma zata ce mata, gani tai Nafi ta fara tafiya nan ta bita tana mata magiya akan su tafi sai dai itakam gani take gwara taje kawai. A falo kuwa Ashraf ne ya had'e rai kamar zai dake Aneesa ita kuma tana tsaye kyam kusa da kaya, ta kalleshi tace " Yaya nice fa?" Ya buga mata wani kallo yace " kece wa? Ko dama a duniya akwai wanda ya isa inyayi ba daidai ba a kasa hukuntashi?" Daga bayansa yaji ance kwarai kuwa, Asim ne yai maganar ya sani shiyasa kuma bai juya ba, Asim ya karaso rai b'ace sannan ya sa hannunsa ta bayan Ashraf iya karfinsa da niyar kai mai duka, Umma tai saurin rike hannun tare da balamai hararra. Ashraf ya kalli Aneesa yace " idan kika bari na irga uku acikin raina wlh sai kinyi dana sanin wannan ranar." Umma tai charaf tace " ai kuwa sai dai tayi dana sanin dan kaf duniya ba wanda ya isa ya sa 'yata ta kwashi kayan wannan yar kauyen." Ashraf bai kalli Umma ba haka kuma bai bata amsa ba sai Aneesa da yake kallo yace " kin amince da abinda aka ce?" Aneesa ta goge kwallarta tace " yaya me zakayi in na ki kwashewa? Badai cewa zakai ka fasa aurena akan wannan shirman ba?" Ashraf ya saki wani mugun murmushi yace " me? Kina ganin bazan iya ba?" Kallan mamaki sukamai su duka ukun, Aneesa wacce duk ta gama rikicewa tace " Ya Ashraf me kake fada haka?" Ya kalleta yace " in kina tunanin bazan iya ba ki bar kayan nan har na karasa bakin kofa, ni kuma zan nuna miki magana d'aya nakeyi." Nan ya juya Aneesa ko kara wata maganar batai ba ta shiga saurin kwashe kaya kamar zata kifa kansu, Ashraf kam ko a jikinsa ya wuce ta jikin Asim ba tare da ko kallan su yayi ba, bai kuma kara duba Aneesa ba dan yasan tabbas zata kwashe kayan nan. Ana kai kofa, Nafi wacce ke tsaye jikinta sai rawa yake ta kalleshi a tsorace, bai kulata ba yai wucewarsa, Little ta dafa Nafi tace " Nafi jikinki rawa yake." Juyowa Nafi tai cikin tsananin tsoro tace " Maryam wani irin mutum ne yayanki? Da gaske sai ya raba auren nan a dalilin da baikai ya kawo ba?" Little tai shiru dan itama abin ya bata tsoro, Nafi ganin haka yasa ta girgiza kai tace " Maryam yayanki na bani tsoro dan ko Baffa banajin tsoronsa kamar yanda nake jin na yayanki." Little ta dafata tace " yayana yaga rayuwa wanda itace ta maidashi haka, baya tausayin kowa ba kuma ya shakkar kowa, abu d'aya ya tsana kuka bayan wannan banaji akwai abinda ke tab'a mai rai." Nafi tabi bayan inda Ashraf yabi da kallo, ace wacce zaka aura kuma kake so ita zaka dizga haka agaban iyayenta da yayanta? Kuma ya juya ya fita kamar ba abinda ya faru? Little ce ta katseta da cewa "Nafi ina zuwa."ta juya da sauri. A falo kam Aneesa tana ganin fitarsa bayan ta gama kwashe kayan ta tsugunna agun tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi, Umma ta karaso kusa da ita jikinta itama a sanyaye ta jawota jikinta. Kuka sosai Aneesa takeyi, Asim ya kalli Umma cikin takaici yace " Umma haka zamu zauna yaron nan yqna ci mana mutunci?" Umma ta kalli Aneesa tace " da kinsani baki kwashe ba inga ta karyar iskanci." Aneesa ta mike daga jikin Umma tace " Umma kamar bakisan Ashraf ba? Kin manta abinda ya faru shekarun baya da suka wuce? Kina sane da ciwon danai tayi a lokacin dayace bazai aureni ba, ya kuma daina kulani." Umma tai shiru, Aneesa cikin kuka tace" alokacin bansan ciwon kaina sosai ba, kina tunanin inya fasa aurena yanzu zan iya rayuwa?" Asim a kule yace " Dalla yima mutane shiru, sai ki kasa rayuwa dan an rabaki da Ashraf?" Aneesa ta harareshi sannan ta mike cikin fushi tana kuka tace " kana tunanin in Ashraf bai aureni ba zai barka a matsayin da kake ne? " Asim yai shiru, Umma tace " ya isa, taya za'ai ma muso auren ya rabu ba, kinsan dalili shima Asim d'in ya sani, mu tabbatar mun rufe maganar nan ma kafin Abbanku ya sani." Nafi wacce ke tsaye duk taji me suke cewa tai shiru jikinta duk yai sanyi, ta fahimci wani abun amma bata gane wani abun ba. Jin alamun zasu fito yasa tai saurin lab'ewa, Umma har tazo kofa ta juya tare da kallan Aneesa tace " karki kara yadda kuyi fada da Ashraf akan wannan kucakar yarinyar wacce riga ma bata fara zama mata ba bare...." Ta juya, Nafi ta kalli rigar jikinta cikin ranta tace " bai fara zamamin ba?" Ashraf kam yana shiga d'aki ya d'au littafin dake kunshe da wasiyar mahaifinsa ya bud'e wani shafi da mahaifin yace " Babban burina a rayuwa bai wuce na hada aure tsakanin d'ana da 'yar Kanina ba." Sannan a kasa aka sa" Ashraf ka taimakeni ka cigaba da kula da zumuncin nan ko bayan raina." Kai ya dafa, a cikin ransa yace " Abba meyasa kakesan wad'anda ba sanmu suke ba? Kasan yanda nakeji a raina in na tuna mahaifiyar Aneesa da tawa Mahaifiyar wai kishiyoyi ne?" Ya kwantar da kansa a jikin gado, a da bai d'auki wasiyyar nan da wahala ba amma yanzu ya gane tafi komai wahala a rayuwar duniya. ☆☆☆☆☆☆☆ A can garin kachako kuwa D'an litti yana kwance a wani kango duk kayansa sun fara yagewa sai ga wani babban mutum yazo wucewa, ganin mutum kwance a kango cikin rana yasa ya karasa inda yake, hannu yasa ya tab'ashi yace " Bawan Allah me kake anan?" D'an Litti ya mike zaune a zabure, yace " Wlh I am the one." Kallansa mutumin yai sannan yai dariya yace " me kayi kuma?" Ganin mutum yasa yasan ba mafarki yake ba, ya kalleshi baice komai ba, Mutumin yace " Sunana Malam Kabiru, ina zaune akarshen layin can, kai fa dan naga kamar ba daga nan kake ba." Nan D'an litti ya kwashe komai ya fadamai, wani gurin yai dariya wani gun ya tausaya mai, nan yace yazo su tafi gidansa inya tara wani d'an kudin sai ya tafi kano ya nemi Ashraf d'in. Sosai D'an litti yaji dadi ya kalleshi yace " Amma ta ina zan tara kud'in?" Malam kabiru yai dariya yace " bakace kana tuka babur ba? Sai muje in baka babur d'in yarona wanda yai tafiya ci rani sai ka d'an tara." Murna sosai d'an litti ya shiga yi cikin tsananin murna nan suka tashi suka tafi..... ☆☆☆☆☆ An anso d'inkunan Nafi sannan Littl da kanta ta zauna ta dinga mata bayani akan yanda zatai amfani da kayayyakin, sun dad'e sosai a daren ranar suna hira dan gobe akesa ran tafiyar ta, murna kuwa agunsu Aneesa da sukaji ba'a magana. Sun nitsa cikin hira Nafi tace " Maryam in na tafi kuma shi kenan ko?" Little ta kalleta cikin mamaki tace " shikenan me?" A ranta tace " kafin in dawo Ya Ashraf yayi aure mana." A fili kuwa sai tace " zamu dade wai bamu had'u ba." Little tai dariya tare da gyara zama tace " Nafi inza'ai bikin yaya inzo ni da Ya Habib mu d'aukeki?" Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " a'a nida na tafi karatu? Sannan shima in yayan yaji ai kinsan fada zaiyi." Little ta tab'e baki tace " shi da yaketa hidimar biki inama zai kula dake? Hmm ai ina cin burin bikin nan sosai wlh." Nafi ta juya tare da gyara kwanciya tace" hmm." Little kam ta zake sai zuba takeyi akan shirin biki, itakam Nafi a kwance kawai take sai eh kawai da take cewa dan itakam ta rasa me yasa batajin dadin hirar ta yanzu...... *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Where are u Maman Shaheed, Jidda Samusa and Classic Feedoh? Ur page is here.... LYSM😍* { *26*} Yau saura bikin Ashraf da Aneesa wata d'aya da kwana 10, a wannan ranar ce kuma Nafi ta shirya tsaf cikin uniform d'inta, Little tayi kokari wajen koya mata komai, Nafi ta fito fes da ita abin sha'awa ga kayan sunsha guga. A wannan lokacin inba fad'ama akai ba ko hausarta kaji ba tabbas bazaka gane daga riga ta fito ba, Little ta jawo a kwatinta tana cewa " Zaki tafi ki barni ni kad'ai. " Nafi tai murmushi a ranta tace da ina riga bana fita, yanzu nazo nan kuma shima gashi zan koma wani gun. Little ta dafata tace " Muje Ya Habib na jiranmu. " Nafi ta kalleta sannan ta d'anyi kasa da kanta tana wasa da hannunta tace " Maryam bazanje inma yaya sallama ba? " Little ta d'anyi dariya sannan tace " kije mana, amma bada ni zaki ba, ni zanje gun Mumy inkin gama sai kizo can mu had'u. " Nafi ta d'aga mata kai alamar eh sannan ta fito da saurinta, tana tafe tana tunanin me zata cemai, sam bata kula da Asim a zaune akan kujera ba, har ta wuceshi taji ance " ke dan kut**** baki iya gaisuwa ba? Ko dan zaki tafi wata kucakar makaranta kike tunanin kinfi kowa? " Nafi wacce tsoro ya rufeta ta kalleshi a tsorace tace " yahkuri Ya Asim wlh ban kula bane. " Ya girgiza kai sannan yace " da alama ma kayan sa miki akai. " Nafi tai kasa da kanta kawai batace komai ba, ya tab'e baki sannan ya juya kai tare da cewa " sai aje ayi sallama da dadiron ki. " Nafi kam bata fahimci me yake nufi sam da dadiro ba shiyasa ma bata damuba, ta juya ta cigaba da tafiyarta a ranta tana mamakin irin zuciya ta wannan mutumin. B'angaren Ashraf tanufa, a hankali ta kwankwasa kofar, daga ciki Ashraf ya amsa da ashigo. A hankali Nafi ta murd'a kofar sannan ta shiga ciki, yana zaune akan kujera rike da laptop da alama aiki yakeyi, bai d'ago ya kalleta ba bare tasa ran zai tanka mata. A hankali take d'agowa tana kallansa sai dai ganin har yanzu hankalinsa nakan laptop d'in ga lokaci na tafiya yasa ta d'aure tace " Yaya zamu tafi. " "To Nafisa Allah ya kiyaye. " abinda ya fada mata kenan har yanzu hankalinsa nakan abinda yakeyi, Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, makullin d'akinsa ta ciro sannan a hankali ta fara takawa har zuwa inda yake, mikamai makullan tai tace " gashi yaya." D'agowa yai ya kalleta, idanunsu ne suka had'u gabanta yai wani irin fad'uwa da sauri tai kasa da ido, shikam har yanzu idanunsa na kanta bai kuma amshi makullin ba sai cewa yai "Sanda na baki cewa nai ki dawon da shi in zaki wani gun? " Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, idanunsa na kanta hakan yasa ta karayin kasa dakai tare da cewa " kafin in dawo kayi aure nasan kuma a lokacin baka bukatar aikina. " Bai san sanda ya saki murmushi ba sannan ya maida kansa kan aikinsa tare da sa hannu ba tare da ya kalleta ba dan ya amsa, hannunsu ne suka had'u da juna, sai dai abin mamaki ya kasa d'auke hannunsa haka itama. Ganin yanda take mutsu mutsu da baki yasa ya rike hannunta tare da makullin. Yanaji sanda ta d'an zabura kad'an shi dariya ma taso bashi, ta d'ago tare da kafeshi da ido, mamaki ne ya kamata ganin hankalinsa ma baya kanta. Idanunta na kansa sam ta kasa d'aukewa, jitai yace " kallan bai isa ba? " Da sauri tai kasa da kanta, yace " ba jiranki ake ba? " Kallansa tai da mamaki taya za'ai ta tafi bayan ya rike hannunta? Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " So kike kuyi dare ko da wani abin da zaki fad'amin? " Nafi ta d'an yi rau rau da ido tace " Yaya Hanuna fa? " Yanda tai maganar ita kanta batasan ta iya ba, ya kalleta sannan ya kalli hannun, sakin hannun ta yai tare da zare makullin, ya kalleta yace "zan ajiye in ko in dawo sai kizo ki amsa. " Ta kalleshi da mamakin kalamansa, ta daure kawaj sai cewa tai " Yaya nagode insha Allah bazan baka kunya ba. " Ya mata wani kallo sannan yace " kada dai kije ki biyewa kawayen banza, sannan kar ki kuskura kiyi kuka da sunan wai kinyi rashin mahaifinki ko nan. " Nafi ta d'aga kai jiki a sanyaye, nan tamai sallama ta juya a hankali take tafiya har ta fita daga kofar. Tayiwa Mumy sallama nan Mumy ta bata dubu biyar wai kudin kashewa, itakam Nafi kin amsa tai sai da taga ran mumy ya b'aci tukunna, nan tai godiya suka fito, b'angaren Umma sukaje. Tana zaune a falo, Aneesa na gefe itada kawarta suna kallan wasu kaya, da kyar aka amsa sallamar ta, jiki a sanyaye ta shiga sannan ta tsuguna tagaida Umma sannan tagaida Aneesa da kyar suka amsa suna mata kallan uku saura kwata, Umma tace " ai anyi dabara da aka saki boarding dan na gaji da ganin yar rigar fulani tana yawo a gidan nan. " Nafi batace komai ba, Aneesa ta harareta tace " Allah ya raka taki gona. " Jiki a sanyaye Nafi ta fito daga b'angaren nan ta karasa kitchen tama su Goggo sallama. A mota ta taradda Little zaune a gaban Mota kusa da Habib suna hira, tasa hannu ta goge fuskarta sannan ta karasa cikin mota. Habib ya juyo ya kalleta yace " Gimbiya Nafeesa irin wannan jira da aka sani haka? " Murmushi ta d'anyi sannan tace " Tuba nake, amma gimbiya ai Maryam ce bani ba. " Habib ya kalli Little wacce taji dadin kalaman Nafi, yace " to me kike so indinga ce miki? " "sunana mana. " Habib yai dariya yace " ai ni bana fadan sunan mutum, kowa da sunan da nake cemai. " Nafi ta kalli little tace " Little ki zabarmin to. " Su dukansu dariya sukai, nan Habib ya tada mota, Nafi dama tana baya, ita kuna Little na gaba. Sun fara tafiya Little ta juyo tace " Kinje kunyi sallama da yayan? " Nafi tai murmushi tare da dg mata kai, Habib ya kalli Nafi yace " me yakeyi? " Tace " na daiga yana danna abu irin na Little a falo. " Suka sa mata dariya sannan Habib yace " Ashraf kenan, yanada kwakwalwa ga iya aiki amma har yanzu na rasa me yake hanashi yin aikinsa. " Nafi ta kalli Habib da mamaki sai dai batasan me zata tambaya ba, jitai Little tace " anya ba abin da bane yake damunsa? " Habib yai ajiyar zuciya yace " nima ina tunanin wannan, ai ko waye dole ne abin ya zamarmai Karma. " Kai Little ta jinjina tace " Shiyasa bana ganin laifinsa in yana fada, itama Mumyn ai.... " Sai kuma tai shiru. Nafi kam ta kasa shiru ta kalli Little tace " Me ya sameshi dan Allah. " Little tai ajiyan zuciya tace " Nafi ki bari sai kin dawo zan sanar dake." Habib ya kalli Little baice komai ba. Har suka isa makaranta zuciyar Nafi fal take da tunani kala kala menene ya faru da Ashraf? Ita kanta tana mamakin Mumy da ta auri kanin babansa kuma harda 'ya a tsakaninsu. Sun shiga makaranta nan Principal ta hadata da wata Copper wacce zata dinga nata extra lessons, sunyi sallama Little ta shiga mota duk tausayin Nafi ya kamata. Nafi kam sai data b'oye hawayenta, Habib ya mata alkawarin zuwa d'aukota shida Little in biki yazo, itakam batace komai ba dan bata wani damu taje bikin ba. Tana nan a tsaye har suka shiga mota suka tafi, ta goge hawayenta sannan ta karasa gun House Captain dinsu da aka kira, nan ta kira yara yan Js 1 suka kwashi kayan Nafi. ¤¤¤¤¤ A gida kam har yanzu Ashraf bai sakema Aneesa kamar da ba, sai dai yanzu tana iya kokarinta wurin ganin ta farantamai rai, sosai take kula dashi, sai dai wannan ba damuwarsa bace in fact gani yakema ta takura mai bayan shi mutum ne dayakesan ya zauna shi kad'ai. Mumy da ita da mahaifiyar Habib suka shiga kasuwan ni kala kala mall da sauransu, suka had'a lefe na gani na fad'a, sunso suje Dubai sai dai Ashraf ya hanasu, yace " shi baiga wani abu da za'a siya da har za'a rasashi anan kasar ba. " Kaya kam anyishi, naira ta gurzu, sai dai wannan ba komai bane a kan irin dumbin kud'in da Ashraf yake dasu. ¤¤¤¤¤¤ An ba Nafi d'aki cikin 'yan ajinsu, gaishesu ta shiga yi dan ita a gunta hakan shine daidai. Dariya sosai suka mata, jin hausarta yasa suka san bafulatana ce, d'aya daga cikinsu wacce kana ganinta kaga wayayyiya tana kwance saman up na gado, sanye da vest da wando ta zuro kai tace " lalai da alama mun sami yar kwana. " Dariya suka kara kwashewa dashi wata tace " Ferry ashe kin gano? Da alama kan ba komai sai iyaye suka sami kud'in gomnati. " tafad'a tana kallan tulin kayan provision din Nafi. Dariya suka kara sawa, Nafi tana nan tsaye idanunta suka fara neman kawo ruwa, watace ta dafata tace " ki shiga da kayanki, sai ki zauna a up gadan dake kallan na Ferry. " Nafi ta d'aga kai alamar to, sannan ta shiga da kayan, daga ganin yanda suke mata kallan wulakanci yasa tasan bazataji dadin wannan zaman ba. Sai dai ya zatai????? Tana gama jera kayanta aka turo wata yarinya akan ta fito karatu karfe 2 tayi, Nafi tayi mamaki ganin ai yau tazo, sai dai ba yanda zatai sallah kawai tai tafita waje tanaji suna gulmar ta. *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Gaisuwa da jinjinar ban girma gareku masoyan arziki, soyayyarku daban take 'yan group d'ina na The Queen Bee da Ayusher Fan Club..... ILYSM💋* { *27*} Sun fara daga kan farkon karatu wato English Alphabet,Nafi ta zake sosai wajen ganin ta koyi abinda ake koya mata, sai karfe 5 sannan wannan matar ta mike akan sai gobe a daidai wannan lokacin zasu sake haduwa. A galabaice ta dawo hostel yunwa duk ta isheta, ba kowa a d'akin hakan yasa taji dadi, cornflakes ta had'a ta zauna tasha, jin cikinta ya d'auka yasa ta fito tai alwala tai sallar la'asar. Tana zaune a kan sallaya tana kara tisa karatunta a ranta sai gashi 'yan d'akin sun dawo. Nan suka mata wani kallo Ferry tace " ke kina nan wato mu muna can an samu wankin toilet ko? " Nafi ta kalleta tace " wlh bam sani ba. " Wacce ta dafata d'azu yanzun ma ita tace " haba Ferry taya za'ayi yarinya tazo yau d'in nan amma kice tai aiki? " Ferryn ta kalleta cikin kuluwa tace " Ke Jibiya banasan salon iskanci, meye naki a ciki? Ko dake nake magana? " Wacce aka kira da Jibiya itama cikin fad'a tace " badani kike ba amma hakki nane in fada miki gaskiya sannan ko yanzu kika kara abinda bai dace ba dole ne in fada miki gaskiya koda kuwa zakiji haushina." Ta ja tsaki a karshen maganarta sannan tai waje a zuciye, Ferry ta bita da harara tace " Yarinyar nan ta gama rainani wlh. " Itakam Nafi tana zaune duk jikinta yai sanyi,ba abinda ta tsana irin taga anyi fad'a a kanta. Mik'ewa tai ta kalli Ferry tace " D'an Allah kiyi hakuri." sannan tai waje inda taga waccan ta fita. Ga mamakinta a zaune taganta cikin mutane suna ta hira da dariya. Nafi ta karasa inda take tare da musu sallama, Jibiya ta d'ago ta kalleta sannan tace " new comer ya akai? " Nafi ta d'an motsa baki alamar tana san magana, ganin haka yasa ta mike taso kusa da ita, Nafi ta kalleta tace " Banji dadi ba daga zuwana kuna fada akaina, d'an Allah kiyi hakuri. " Jibiya tasa dariya sannan ta kama hannun Nafi suka zauna tace " Karki damu da wannan, Ferry yayatace, ubanmu d'aya, indai fad'a ne irin wannan mun saba. " Nafi ta kalleta cikin mamaki tace " Ayya bansani ba. " Hannu ta mika mata alamar suyi musabaha tare da cewa " Sunana Aisha Isma'il. " Nafi tai murmushi sannan ta mika mata hannu itama tace " Sunana Nafisa Abubakar. " Murmushi sukama juna, Jibiya ta kalleta tace " a kano kike? " Nafi ta d'aga kai alamar eh, fara'arta ce ta kara bayyana tace nima haka. " Nafi tai murmushi, jibiya tace " Karki damu da Farida ko ince Ferry kamar yanda ake cemata, a ido ne take haka amma a zuciyarta sam mace ce mai saukin kai. " Nafi kam murmushi kawai tai, suna nan a zaune Jibiya na janta da hira sama sama har magrib tayi. Nam suka mike sukai alwala suka nufi massallaci. Washegari bayan sun shirya da safe suka fito aji dukansu 'yan d'akin, Nafi an shiga cikin Uniform ba laifi tayi kyau dagwas da ita. Sunshiga aji malamin Math ne ya fara shigowa, itakam Nafi kawai iya kacinta kallon duk malamin daya shigo dan ko kad'an bata fahimtar kalma d'aya da take fahimta ba. Sai dai ta kalli Malami ta kuma kalli alo, haka malamai sukai ta fita wasu na shiga har aka tashi, itadai tasan kawai dumama benci kawai takeyi. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Wani mugun kallo Ashraf ya ma wata kawar Aneesa da sauri ta kalli Aneesa a tsorace, Aneesa ta kalleshi tace " Hubby me kake nufi? Events d'in ne bakaso kome?" Ashraf ya kalleta yace " Anie kanki d'aya kuwa? Biki kwaya d'aya shine kike neman yin event kusan guda 10? Sannan kina san ni in hallarci guda 8? Akan me? " Aneesa ta kalleshi tace " bangane akan me ba?" Ya dan rufe ido kad'an sannan yace " tambayar ki ai nake akan me zanje? " Kawar Aneesa ta daure tace " Ashraf amma..... "kallan daya mata yasa tajs bakinta tai dif, Aneesa ta mike rai b'ace tace " Yaya meyasa kake min haka?" Murmushi ya sakar mata sannan yace " me kuma nai yanzun? " Aneesa ta kafeshi da ido ranta duk ya gama b'aci ta daure tace " Ka tab'a ganin mijin daya ce ma matar da zai aura akan me zaije gun bikinsu? " Ashraf ya d'an daga kafad'a tare da d'aukan wayarsa ya fara dannawa sannan can yace " kowa da irin zuciyarsa, sannan dama namiji aka sani dayin kyale kyalen biki ko mace? " Aneesa idanunta ns kansa ranta yakau kololuwa gun tashi, ta bud'e baki zatai magana tags ya d'au waya ya kira wata number sanan taga yaa mike yai cikin d'aki. Idanu ta bishi da shi sannan tai waje fuuu, kawarta ta mike ta biyo bayanta. D'akin Umma ta shiga da gudu ba ko sallama, Umma na zaune tanacin abinci, Aneesa ta fad'o kanta sannan ta saki kuka. Nan Umma duk ta rud'e ta shiga tambayarta abinda ke faruwa, kawarta ce ta sanar ma Umma komai, ran Umma ya b'aci sosaii ta kalli Aneesa rai a b'ace tace " Akan haka ne kike kuka? Ai nasha fad'a miki ki cire san Ashraf aranki kiso kud'insa kawai ba wai shi ba amma nsga alama sam kin kasa fahimtata. " Aneesa cikin kuka tace " Umma ya zanyi? Nafa fad'ama friends d'ina zancen events d'innnan. " Umma ya shafa kanta tare da kama hannunta sukai d'aki. A bakin gado suka zauna, Umma ta kalleta tace" ki rage events d'in daga goma zuwa bakwai, a wannan lokacin kibar Ashraf ya sami duk abinda yakeso, karki kuskura ki b'ata masa rai har zuwa lokacin da zai aureki ki amshi wasiyyar mahaifinsa. " Aneesa ta kalli Umma sai dai batace komai ba, Umma ta cigaba "a sanda kika samu kansa kikasan ya gama mutuwa akanki lokacin ne zamu samu ya barma yayanki company d'insa." Aneesa da mamaki tace "Umma taya zanso mijina yabarma Yayana Company d'in mahaifinsa? " Umma tai wani tsaki na kulawar tace " Aneesa ke yarinyace bazaki tab'a fahimta ba, alokacin da Ashraf ya amshi aikinsa, dukiya da aiki suka fara mai yawa kina tunanin zai samu lokacin ki? " Aneesa ta girgiza kai, Umma ta dafata tace " Aneesa kiyi tunani dakyau a haka ma mutumin da ba aiki yake ba baya ganin wani darajarki bare kunyi aure? Yana ganin shi ke da iko dake? " Aneesa tai shiru sai dai Umma ta tabbatar kalamanta sun ratsa Aneesa sosai...... Nan ta mike ta barta a d'akin, shiru Aneesa tai tana tunani kalakala da wulakancin da Ashraf ke mata duk suna dawowa cikin zuciyarta, kwanciya tai akan gadon zuciyarta na mata sake sake kala kala...... ¤¤¤¤¤¤ Yau satin Nafi d'aya a makaranta, har a wannan lokacin itadai bata fahimtar me ake a aji, sai dai tana kokari sosai a gun karatun da ake koya mata. Yau aka kawo musu wani sabon malami na Computer bayan yayi introducing d'in kansa ne ya fara tashin mutane one by one dan tabbatar da abinda suka sani a gun waccan malamin nasu. "Ke tashi." abinda Nafi taji malamin ya fad'a kenan idanunsa ns kanta, a tsorace Nafi ta kalleshi sai da ya kara ce mata ta tashi kafin ta mike jikinta duk ya fara rawa, Malamin ya kalleta yace "List 3 input of computer." Nafi ta zare ido cikin tsoro, 'yan aji kam gani sukau ba wanda ya samu saukin tambaya irin tata. Nafi tai shiru sai wasa da hannunta data shiga yi, zufa sai keto mata take a cikin jikinta. Ran malamin yakai kololuwa gun tashi gani yake kamar yamata tambayar yara taya za'ai wannan tambayar ta gagari 'yar Js 3? Ranshi ya b'aci yace " get out. " ya fad'a tare da nuna mata hanyar waje. Batasan me yace ba sai dai ganin ya nuna da hannu yasa ta had'a hannayenta biyu tashiga bashi hakuri. Dariya 'yan aji suka saka mata, ran Malam ya kara b'aci ganin taki fita, a zuciye ya d'au bulsla ya fara zuba mata, Nafi kam ta daku sannan yace " ya bata nan da sati d'aya zai kirata a gaban class ya mata tambayoyi, inta kuskura ta kasa to wlh ba shakka sai tayi dana sani mai tsanani." Nafi kam zama kawai tai tana hawaye....... Ni kaina ganin halin da Nafi take ciki sai dayasa hannuna ya fara rawa wanda na kasa cigaba da rubutun nan...... *LYSM MY FANS*😍😍😍😍 *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd* { *28*} Nafi kwance a saman gado, ba shakka taji zafin dukan da aka mata sosai, ita kad'ai ce a d'akin tana kwance Ferry ta shigo, kasancewar ba magana take mata ba yasa Nafi tace " Sannu da dawowa. " Kallan da Ferry ta mata yau ba kamar yanda ta saba mata ba, wato kallan banzan data saba ba, yau kallanta tai cikin mutunci, Nafi tai murmushi sannan ta gyara kwanciyarta, jitai Ferry tace " Nafisa ya akai kika kasa bada amsa d'azu? Baici ace duk dakikantarki kinkasa ba. " Nafi ta mike zaune sannan ta kalleta fuskarta cikin farin ciki, tace " Bansan amsar na Ferry. " Ferry ta shiga cire kayanta tana cewa " to in dai haka ne lalai zakici doka a gun malamai, ya kamata ki samu Jibiya ta koya miki tun kafin a gama raina ki. " Nafi ta jinjina kai cikin farinciki tace " Nagode Ferry. " Ferry ta harareta tace " karkiyi tunanin sanki nake yanzu, ni bana kawa da wacce bata kile ba, bana kawa mara kwalliya, ba kuma na kawa mara aji. " Nafi ta sauko daga sama tace " Ferry nikam kina burgeni wlh, duk da ba kulani kike ba inasan tsarinki yana birgeni. " Ferry ta d'aura towel sannan tace " abinda yake b'atamin rai kenan da mata irin ku, sam bakwa abin mace, bakwa kwalliya, yanzu kamar ke sam duk abinda mutum zai miki ban taba ji kin d'aga ma wani murya ba, komai sai dai ki bada hakuri, ke ba dutse ba." Taja tsaki ta zari kwandon wankanta tai waje. Nafi ta bita da kallo ba shakka abinda ta fad'a gaskiya ne, to amma ya zatai? Bayan haka halinta yake? A satin nan Nafi har sai da ta rame tsabar karatu kala biyu, ga na lesson d'in da ake mata gana computer, a wannan zaman karatun da jibiya take koya mata anan ta fahimci Nafi batai wani karatu ba ganin duk yanda taso tai pronounce d'in kalmomi abun yake gagara, sai dai hakan yasa ta kara tausayama Nafi sannan ta jajjirce wajen kara koya mata. Yanzu kam suna 'yar magana sama sama da Ferry. Sati d'aya ya cika, malam ya kira Nafi gaban black board ya shiga zuba mata tambaya, tambaya 5 ya mata da kyar Nafi ta amsa biyu, wannan dalili yasa Malam ya yanke mata hakunci akan ta dawo gaba kusa da Ferry da zama sannan duk karshen week sati biyu zai dinga mata tambaya. Nafi kam duk ta rame saboda karatu, sam bata samun damar tunanin gida ko wani abu, sai dai ta rasa dalili duk sanda ta tashi daga bacci sai zuciyarta ta rage mata kwana d'aya akan kwanakin bikin Ashraf. *A KANO* An kai lefe sannan anata hidimomin biki, sai dai sam Ashraf abin nan baya gabansa, tabbas yasan a ransa yanasan Aneesa sai dai bayajin wani farin ciki game da wannan auren. Ita kad'ai take kid'anta take rawarta, duk dinkunansa sai Habib ta samu sukaje suka siyo, sam Ashraf baya walwala bare farincikin wannan auran. Duk yanda Aneesa taso daurewa karta nunamai jin haushinta sai data kasa tamai magana, sai dai duk sanda tamau magana kanta abin yake komawa, karshe tazo tana bada hakuri. Gida ya fara taruwa da mutane, little kam sai rawar kai dinkuna tayi yakai kala 10 ta musu kuma anko da Nafi kala 5, murna kam ba'acewa komai agunsu Umma. Yau saura kwana biyu a fara hidimomin biki Mumy ta kira Ashraf zuwa falonta, bayan ya zaunane Mumy ta kalleshi cikin kuluwa tare da tattara hankalinta kansa, ta fara magana cikin kulawa " Ashraf yau saura kwana biyu a d'aura maka aure da 'yar uwarka." Ashraf kansa na kasa sai dai baice komai ba, tace " Muhammad! " D'agowa yai cikin mamaki dan bai tab'aji ta fad'i wannan sunan ba d'an sunan baban mahaifinsa ne. Mumy ta kalleshi tace " kayi hakuri abinda na maka. " Kallan mamaki yake binta dashi, yace "name? " Ta kalleshi idanunta a raunane tace " Ashraf na sani sarai abinda na maka shekarun baya masu yawa shine yasa ka zama haka, sam bakasan 'yan uwanka, kanka kawai ka sani, ba ka tunanin maganar da zaka fad'a ko zai b'atama wani rai. " Ashraf dai kallanta kawai yakeyi, Mumy tai ajiyar zuciya tace " bazaka tab'a fahimtar me yasani na auri kanin mahaifinka ba daga rasuwar Abbanka ba har sai lokacin da kasan komai na gidan nan da kuma abinda ke cikin zuciyar kowa na gidan nan. " Ashraf da mamaki yace " Mumy. " Ta sakar masa murmushi tace " na sani nayi laifi a gareka, na rashin sanar dakai komai danai har sai sanda aka haifi Little, sai dai inaso ka sani komai nai a rayuwa to tabbas d'an kai nayi shi, ban tab'ayin wani abu dan in farantawa kaina rai ba, a ko da yaushe kai nake fara sawa a gaba akan komai na rayuwata kafin inyi tunanin kaina. " Shiru tai sai dai ta kawar dakanta gefe kad'an alamar so take ta b'oye kwallar ta, Ashraf kam kalaman Mumy sun tab'ashi sai dai haryanzu gani yake koma meye dalili shi bai fahimci dalilin auranta da kanin Abbansa ba." Mumy ta d'anja hanci sannan tace " Mahaifinka na tsananin san kaninsa, sannan babban burinsa bai wuce yaga ya had'a zuri'a dashi ba, nasani da yana da rai sai yafi kowa farin cikin wannan abun duk da yasan shi kanin nasa ba sanshi yake ba. " Ashraf ya kalleta cikin mamaki yace " Mumy me kike nufi da basanshi yake ba? " Mumy tai murmushi tace "la ba haka zan fad'a ba subutar harshe nai. " Ashraf yai shiru sai dai tabbas yasan da wani abu. Mumy tai saurin wayancewa da cewa " Ashraf kasan me ake nufi da aure ba sai na sanar dakai ba dan Allah ka rike matarka yanda ya dace, Aneesa na sanka kowa ya sani. " Ashraf bai amsa hakan yasa Mumy tace " Ashraf maganar aiki. " Kallanta yai sannan ya daure yace " Mumy me yasa kike so im fara aiki a company d'in Abba? " Mumy tace " saboda hakkinka ne." Ashraf yai murmushi yace " idan na fara aiki a wani matsayi kawu zai zauna? Sannan ni a wani matsayi employees na company d'in zasu d'auken?" Mumy da mamaki tace " Ashraf me kake nufi? " Yai murmushi sannan yace " zan fara aiki a company d'in Abba sai dai bawai a matsayina na magaji ba inasan ne in amshi hakkina da kokarina bawai dan ni d'an Abba bane. " Mumy ta jinjina kai tace " kana nufin zaka fara aiki a company d'in daga farko? Tun daga kan interview?" Kai ya d'aga Mumy tai murmushi lalai ta yaba da tunanin d'an nata ta sani sarai dama yanada hangen nesa sai dai bata tab'a tunanin zaiyi tunani haka ba. ¤¤¤¤¤¤ Nafi ce zaune tana shafa mai Ferry ta kalleta tace " Nafi yau tunda kika tashi naga kamar bakida lafiya. " Nafi ta kalli Ferry tace " Ferry dan Allah tambaya. " Kai Ferry ta d'aga mata alamar eh tanaji. "Yayanane zaiyi aure a satin nan, na rasa meke damuna sam duk sanda na tuna sai inji raina yana b'aci. " Ferry ta kwashe da wani dariya tace " Innocent Feenah dama haka kike? Oh a ido kamar.... " Nafi tace " ban gane ba, wani abun ne? " Ferry ta fara tafi tace " Innocent girl, yayan naki uwa d'aya kuke ko uba? " Nafi ta girgiza kai, Ferry ta kara sa dariya sannan tace " gaskiya Feena kin tashi daga Innocent kin koma green snake. " Nafi ta mata kallan mamaki tace " ni na tambayeki abu ma baki amsa min ba kin bige da dariya. " Ferry tace " Good haka nakesanki in abu bai miki ba ki fito ki fad'i gaskiya, sannan zancen yayanki ai ba komai bane sanshi kawai kike. " Da sauri Nafi ta mike ta zura hijab d'inta tai waje tana cewa " Ni? Wacce ni? Ni kaza????? *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Hi Fans please Vote me on Wattpad As_AyusherMohd* { *29*} Yau ce ranar da za'a fara gudanar da event, da sassafe Little da Habib sukazo suka d'auki Nafi, sunyi murna sosai da ganin juna sai dai Little ta damu da ganin yadda Nafi ta rame sosai, hatta Habib yaga haka, nan suka taho a hanya Little nata tsokanarta akan ta bata labarin makaranta, Nafi kam sai dai tayi dariya kawai. Haka sukai ta tafiya, Little duk ta isheta da labarin biki, Nafi kam shiru kawai tai sai yake da takeyi, daga kazaure zuwa kano ba wani nisa ne dashi ba amma saboda Little ta kyaleta da zancen bikin nan sai Nafi ta tsiri yin bacci a hanya, hakan yasa Little ta kyaleta sai dai ta maida akalar hirar tata ka Habib. Har suka iso gida Nafi dai idanunta a rufe suke. Tunda suka shigo kuwa tasan lalai biki yazo, dan gida ya cika da mutane, nan Habib yai parking su kums suka fito. Sun fara zuwa b'angaren Mumy suka gaisheta, cikin farin ciki ta kalli Nafi tace " 'yar makaranta kin iso? " Nafi ta d'aga kai, Mumy tace " kije kiyi wanka kice abinci ki huta dan yanzu kinsan da baki dayawa a gidan hutu bazai samu ba anjima. " Nafi ta amsa da to fuskarta cikin farin ciki, b'angaren su suka wuce tana isa ta fad'a toilet tai wanka kafin ta fito Little ta d'auko mata kaya a cikin sababin da Ashraf ya mata bata sa ba. Nafi tai murmushi sannan tasa kaya, taci abinci sosai daj gaskiya tayi rashin abincin gida, ta gama kenan Ashraf ya kira Little a waya, Nafi tanaji Little tace "Hello Yaya! " Taji gabanta yaa fad'i, jitai Little tace "eh ta dawo." sai kuma taji tace to amma yaya..... " Jin shiru yasa Nafi tasan ya katse wayar dan shi dama baya jira. Little tabi wayar da kallo sannan tace " wai kije ki gyaramai d'akinsa, yaba Habib makullin d'akin sannan inkin gama ki ajiye a gunki zai amsa. " Nafi tai murmushi sannan tace " To. " Little cikin b'acin rai tace " Nafi bakiji haushi ba? " Ta kalleta tace name? Little ta ja wani dogon tsaki tace " yau kika dawo bai tambayeki makaranta ba, sai ya saki aiki? " Nafi ta d'an harareta kad'an tace " ke kuma menene naki??? " Little ta kama baki cikin mamaki tasan Nafi indai abu ya mata ko bai mata ba bata tab'a magana sai dai tai kasa da kai, cikin mamaki Little tace " ba komai nawa. " Nafi ta mike tare da wanke hannu tai waje ranta wasai, farin ciki take zataga Ashraf. Da isarta b'angaren taga kofar a bud'e sannan ga kayayyaki nan a waje da alama gyara ma ake, nan ta tsallaka ta shiga falo, mata ta gani su hud'u suna ta jera sababbin kaya a falo, Nafi ta gaishesu, sai dai kowa kallanta yake cikin mamaki, wata daga cikinsu wacce kana ganinta kasan kanwar Umms ce ta d'aure tace " Yarinya ke kuma wacece? Kuma me kikeyi a nan. " Kallansu tai sannan tai kasa dakai, a zahirin gaskiya batasan me zatace ba bata kums san me zata kira kanta ba a gidan nan. Jitai ance " me kike anan ba aiki yasa ki ba? " Da sauri ta d'ago ta kalli inda ake magana Habib ne tsaye a bakin kofar d'akin Ashraf, a hankali ta wucesu zuwa gunsa. Habib ya mika mata makulli sannan yace " gimbiya meye naki na tsayawa? " Ta kalleshi tace " gaishesu nai. " Habib ya d'an matso kad'an yace " ki kiyaye kula mutane irin wannan kar abu ya rutsa dake kisani a tashin hankali. " Da mamaki ta kalleshi, ita zatai abu to shi kuma meye nashi na shiga tashin hankali??? Ta bud'e baki da niyyar tambayarsa kawai taga ya wuceta ya fita. Bayansa tabi da kallo sannan ta shige d'akin Ashraf ta rufe. Ba shakka yan jere sun sha mamaki, wacce wannan zataxo ta shige d'akin Ashraf?? Itakam Nafi tana shiga ta cire hijabinta ta shiga gyara, ba laifi d'akin yayi kura, ta dad'e tana gyara d'akin kafin ta nufi toilet, ta wankeshi tas sannan ta wanke towel d'in dake ciki. Tana gamawa taji bayanta yad'an amsa, murmushi tai har hakoranta suka fito tace wato jikinki ya fara sanyi ko? Ai in a riga ne aikin dayaci uwar wannan ma batajin wahalarsa. Air freshener ta fesa a d'akin, sannan ta jawo mai d'akin ta kulle tare da zare makullin, sallama ta musu basu amsa ba itadai tai gaba. Yau Arabian nights za'ai, bayan magrib kowa ya shiga yin kwalliya ta gani ta fad'a, Nafi kam tana zaune tana karatu, Little wacce kawayenta sukazo sunata shiri. Kallanta Little tai tace " Nafi wai meye hakan? " Tace " name?" "kina ganin kowa yana shiryawa amma ke kina zaune sannan ga kayanki nan na fito dasu banga alamar kinada niyar sa wa ba. " Nafi ta kalli kayan, riga ce da wando sai doguwar riga ce baka (after dress) sai dai an bita da kwalliyar duwatso rigar tayi kyau sosai. Nafi cikin mamaki ta kallesu, kowa riga da wando yasa yanata kwalliya, tace " Little kinsan dai bazan iya fita a haka ba. " Little tai dariya tace " muma ce miki mukai a haka zamu fita? " Ta fad'a tare da ware mata after dress d'in tace "wannan zamusa. " Nafi tai ajiyar zuciya tace " zakuyi kyau nikam ba dani ba. " Little ta d'aga wayarta tace " shikenan bari na kira yaya nacemai kince wai ke bazaki iya zuwa gun bikinsa ba. " Da sauri Nafi ta mike ta kwace wayar, kawayen suka sa dariya. Nafi tai ajiyar zuciya tace " naji zan saka kuma zani sai dai ina gefe. Little ta d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanki. Little da kanta ta zauna ta shiga yima Nafi kwalliya, itakam Nafi bataso gani take kamar ba mai bukatatarta a guri meye nata na wani kwalliya? Nafi tayi kyau sosai, dan zan iya cewa tun datazo birni bata taba yin kyau irin na yau ba, mayafin abayar Little ta nata rolling dashi, tayi kyau sosai da sosai, ba wani kwalliya na kuzo mu gani bane sai dai inkaga Little lalai bazaka tab'a cewa ba a birni take ba. Dukansu wando Ja suka saka, hakan yasa suka sai takalmi ja flat, sannan yar karamar jakar dake rataye a kafad'arsu ma jaa ce, sunyi kyau sosai dan ankon shigar su kad'ai sukai. Sun fita reras dasu, Little na rike da hannun Nafi, tun a gida ma duk wanda ya kallesu sai ya yaba musu, nan suka shiga d'aya daga cikin motocin da aka kawo na d'aukar mutane zuwa gun da za'ai event d'in. ¤¤¤¤¤ A can b'angaren Aneesa kam tana can gidan Aminiyarta ankira mai kwalliya tana tsantasara mata, ganin an kusa gamawa yasa ta d'au waya ta kira Ashraf. Sai data kusa katsewa ya d'aga, cikin salon jan hankali tace " Hubby ka shirya? " Yace " ku mata ai kune aka sani da shiryawa ni wani shiri zanyi? " Tai murmushi sannan tace " ka taho ta gidan su Abida sai mu tafi. Cikin mamaki yace " ban gane ba? " Ta kara shagwab'e murya tace " ba dama kai zaka kaine ba? Ai tare zamuje gun. " Yace " So? " Tace " so shine nake fad'ama ina gidan Abida kazo mu tafi tare. " Yace " ni na kasa fahimtarki, meye zaisa sai nazo mun tafi tare? " Mikewa tai ganin yana neman disgata a gaban kawayenta tai d'aki tace " yaya haka fa akeyi. " Yai d'an tsaki yace " in haka akeyi sai akace dole sai nayi? " Mamaki ya kamata tace "Yaya ka tab'a ganin Amarya taje gun biki daban ba tare da ango ba? " Yace " sai a fara a kanki dan ni kam ba driver bane babu kuma dalilin dazai sa inzo in d'aukeki keda kawayen ki bayan inada abinyi. " Idanun Anisa ne suka canza kala tace "yanzu dai kana nufin bazaka zo ba kenan Yaya? " Yace " ba wai bazan zo ba gaba d'aya, sai dai zaki iya zab'a in har nazo na kaiki to kuwa ina ajiyeki zanyi tafiyata. " Aneesa ta furzar da wani iska ta bakin ciki tace " shikenan zamuzo a motar Abida. " Bai amsa ba ya kashe wayar, bin wayar tai da kallo ranta a b'ace sai dai dan karsu gane yasa ta fito tana zumbure zumbure. Abida tace " Neesa ya akai? Ko keda Angon ne?" Ta kara tab'e fuska tace " wai suna tare da abokansa su kuma shine sukace wai inyi hakuri mu tafi dake akwai abinda zasu bashine da bazai samu damar zuwa d'aukana ba. " Sukasa mata dariya, Abida tace "sai kiyi hakuri ai uzuri ne. " Aneesa ta harareta sannan ta zauna akacigaba da kwalliya. An gama kwalliya suka taso suka taho, Amarya tayi kyau sosai da sosai dan maganar gaskiya Aneesa dama kyakyawace. A gun event kuwa, Amarya ta iso sai dai ango shiru, gashi ba dama ta shiga ta zauna ita kad'ai. Duk yanda Aneesa ke kiran layin sa san bai d'aga ba. Little ta taho rai a b'ace ta zauna kusa da Nafi tace " Nafi wlh yaya nema yake ya ja mana magana." Nafi tace " name? " Little tai ajiyan zuciya tace " an nemeshi an rasa kuma Habib yace " wlh yana cikin gun nan dan tare suka shigo. " Nafi da mamaki tace "an kirashi a waya? " "tun d'azu ake kiranshi amma shiru bai d'aga ba, gasu Mumy can da Umma kamar zasuyi fad'a. " Nafi wacce duk jikinta yai sanyi tace " a nemeshi mana to ko wani abun ne ya sameshi." Harararta Little tai tace " yaro ne shi? " Nafi ta mike da sauri bata ce komai ba kawai tai baya da sauri. Sauri takeyi tana tafe tana addu'a Allah yasa ba abu ne ya sameshi ba, duk ta gama rikicewa, sai kutsawa cikin kuryar gun ga gun ba kowa sai dai akwai fitilo suma masu d'an duhu. Nafi tana tafe tana waigewaige, saura kiris ta fa d'a kwata, Allah ya taimaketa sai dai takalminta d'aya ya fad'a, zare d'ayan tai ta rike a hannu. Ko kulawa batai ba haka taketa tafiya, yanzu kam har gudu take had'awa d'ashi jikake tim. Kafarta ta bige wani dutse ta fa d'i, mikewa tai batare data dubaba ko kula da kafarta wacce taji ciwo sai jini yake batai ba. Daga can bakin wani pool ta hango mutum a tsaye ya kurawa ruwan ido, tana ganinshi ta baya tasan shine, da gudu ta karasa inda yake. Ta tsaya kawai tana hakki, Ashraf ya juyo gabansa jin alamun mutum, Mamaki ne ya kamashi yake kallan Nafi. Idanun ta suka zubo da hawaye, tasa hannu ta share da sauri tare da cewa " ba abinda ya same ka? " Kallanta yai daga sama har kasa, kayanta duk sun b'aci, yabi kafar ta yabi da kallo duk jini ya b'ata kafar. A hankali ya matso daf da ita har tanajin numfashinsa, yasa hannu kamar zai rankwasheta a kai, da sauri ta runtse idanta kam. Ya girgiza kai batai auni ba taji ya sureta. Idanu ta bud'e cikin mamaki da tsoro, a can kan kujera wacce ake hutawa in anyi wanka ya ajiyeta sannan ya karasa bakin ruwan ya debo ruwa a hannayensa ya fara zuba mata a kafa. *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* *Gaisuwa gareku Aminan Arziki Mom Hamra, Mom Farhan, Agra, Mom Farouk and Fresh LUSM* { *30*} Gaba d'aya Nafi ta kasa d'auke ido daga kanshi, har ya gama d'ebo ruwa ya wanke mata duk da rad'ad'in da takeji sai leb'e kawai da take ciza, sannan ya kalli inda ta yanke, sosai gun ya shiga ciki da alama karfe ne ko kwalba ya mata wannan aikin, hannu yasa a aljihunsa ya ciro handkerchief sannan ya d'aure mata gun dashi. Mik'ewa yai tsaye sannan ya kalleta yace " zaki iya tashi? " Kai ta d'aga mai idanunta subyi tsuru tsuru, ta d'aga zata mike taji wani zugi a kafarta wanda sai da tayi 'yar kara saboda azaba, baya tai kamar zata koma kan kujera da sauri yasa hannu ya taro ta, idanunsu ne suka had'u da juna, Ashraf ya kalleta sannan yace " bakya gani ne? " Kallansa tai batare da ta amsa ba, ya girgiza kai sannan yace " taya zaki bari har kiji irin wannan ciwon? " Kasa tai da idanunta, saukar da ita yai ta koma ta zauna kan kujerar da ta mike. Harararta yai yace " yanzu ya kike so muyi? " Tai kasa da kai sannan tace " kaje kai ai jeranka ake ni zan karaso da kaina." Ta d'auka bazai tafi ba ganin ba yanda za'ai ta iya tafiya, amma ga mamakin ta gani tai yayi gaba, kallansa tai idanunta suka ciciko, ta sukunyar da kanta cikin rashin jin dadi. Batai auni ba taji kawai an sungumeta, a tsorace ta bud'e idanunta cikin rud'ewa tace " Yaya saukeni dan Allah. " Ya murtuke fuska yace " kina tunanin bazan iya ba? " Kai ta girgiza alamar a'a, sannan tace " tsoro nake kar wani ya ganmu a haka." Wani murmushin rainin hankali ya mata yace " ke dai kina tsoro kar Aneesa ta miki duka." Nafi tai kasa dakai sannan tace " Allah dagaske nake ka ajiyeni please." Bai kulata ba ya cigaba da tafiya, sun kusa isa filin gun sai ga Little da Habib sun taho ta gun suna Neman Ashraf. Daga d'an nesa kad'an Little taga alamun kamar sune hakan yasa ta karaso gun da sauri. Kallan mamaki ta musu, Habib ne ya karaso gun shima cikin mamaki yace " Ashraf meye hakan? " Batare da ya kalleshi ba yace " name fa? " Habib ya kalli Nafi wacce tai tsuru tsuru da ita yace " event d'in auranka fa akeyi? " Yace " ehen sai me? Abun haramun nai ko me? " Habib ya kara kallansu, sai dai amsar Ashraf yasa ma ya kasa magana, Little ta daure tace" yaya yanzu in mutane suka ganku a haka me kake tunani? " Zaiyi magana kenan sukaji ana zabga salati daga bayansu. Ashraf ya kallesu Umma ce da 'yan uwanta ga Aneesa a tsaye cikin tsananin mamaki. Ashraf wuce su Little yai ba tare da damuwa ba ya gifta su Umma sannan ya ajiye ta a kan kujera daga baya, sannan ya kalli Umma yace" Umma me kuke anan?? " "Kan jakar uba, abinda za ka tambayemu kenan? " Ashraf ya kalli Aneesa wacce ta fara hawayen bakin ciki sannan yace" naga kamar abun yara ne ban d'auka manya ma zasu zo ba. " A zuciye Umma ta matso tace " me kake aikatawa anan kai da waccan munafukar yarinyar a ranar shagalin bikinka? " Ya kalli Nafi cikin salon rainin hankali yace " wacce? Waccan yarinyar? " Umma ta kumbura kam, yai murmushi sannan yace" karamin accident ne ya sameta shine na taimaka mata." Umma ta kalli Nafi cikin kuluwa sannan ta kalli Ashraf tace " accident? Shi accident d'in bai tashi ba sai a ranar bikinka? Ko dai tsabar kinibibi da muafurci ne hakan? " Ashraf bai tanka ba ya kalli Aneesa da take kuka, matsowa yai kad'an sannan yace " muje ko mutane na jira. " Hawayenta ta share sannan cikin b'acin rai tace " Duk wayar danake ma baka d'auka ba dan kana tare da waccan ne ko me? " Kallanta yai cikin rashin kulawa yace " zakije ko kuwa in tafi? Dan naga kamar lokaci na kawai ake b'atawa anan." Wata 'yar uwar Umma ta kalli Nafi wacce tai kasa da kanta hawaye kawai takeyi, tace " waccan munafukar ai d'azu muna jere itace ta shiga d'akinsa ba kunya ta dade aciki kafin ta fito, kun tabbatar ba wani abu na masha'a tsakaninsu? " Umma ta kalli Ashraf sai dai gani tai kamar ma baisan me suke cewa ba waya kawai yake danna wa, zatai magana taga kamar tafiya ma zaiyi. Da sauri Habib ya rike hannunsa yace " Ashraf ka jiraya mana. " Hannunsa ya fizge sannan yace " zamanta nake? Ita har takai in mata magana taki tahowa? " Aneesa ta matso inda yake jiki a sanyaye tace " Yaya amma.... " Cikin fada yace " amma me? Ba ki yadda dani ba ko me? " Kai ta girgiza sannan tace " ba haka nake nufi ba. " Ya kalli su Umma sannan yace " to me kike nufi?" Tace " ba komai kawai dai dama. " Tsaki yai sannan yace " inzaki wuce muje to, in kuma bazaki ba ni inada gun zuwa. " Nan ya fara tafiya, Umma ta maka mata harara alamar kar taje, da sauri Aneesa ta d'auke idanta akan Umma tabi bayan Ashraf da sauri. Ran Umma ya b'aci sosai lalai ta kosa Aneesa ta auri yarannan insun samu kan dukiyarsa su salwantar dashi dan kuwa bazata iya jurar bakin cikin yaron nan ba. Kan Nafi suka dawo a zuciye, gashi Habib ya tafi, duk yanda Little ke ba umma hakuri amma inaa idanta ya rufe duka ta shiga yima Nafi ba ji ba gani, itakam Nafi hawaye kawai takeyi. Gaba d'ayawannan ranar mutane dayawa da bakin ciki suka taso daga gun nan. Su Nafi suna sauka a mota, Little ta sakala hannunta ta kafa'adarta suka nufi ciki,sai dai me? Suna shiga sukaga cincirindon mutane a tsakiyar farfajiya banda masifa ba abinda akeyi, Little ta kalli Nafi tace"ko me aka sake yi oho. " Ji sukai da karfi wata tace " dan kut...... Uban yarinyar ai karyata zakuyi ba barinta zakuyi ba. " Nafi kam ta rasa me yasa takejin gabanta na fad'uwa haka, jisukai ance " wai yarinyar ma daga ina take? Akan ke zaku yadda ta zauna a nan gidan? " Little ce ta kalli Nafi yanzu kam sun gane inda maganar a dosa, Little ta kalleta tace " mu wuce ciki. " Suna shiga ciki Little ta ajiye Nafi sannan ta fito tai gun Mumy. A zaune taga Mumy tayi tagumi ga 'yan uwanta suma sunata magana, Little ta karasa ta zauna kusa da ita tace "Mumy wlh ciwo taji a dalilin neman yaya, ganin bazata iya takawa ba yasa ya d'auketa. " Mumy tai ajiyar zuciya tace" Little ki fadama Nafi gobe ta shirya da safe a maidata makaranta saboda tsoron abinda mutane zasu mata dan nasan 'yan uwan maman Aneesa sarai bazasu tab'a barin maganar nan ba. " Little tai shiru jikinta yai sanyi sosai, sai dai tana ganin hakan ne yafi sauki. ¤¤¤¤¤¤¤¤ A kachako kuwa d'an litti ya zake sosai yana aikin kasuwancin sa na babur, yana kuma jin dadin yanda uban gidan sa yake sanshi, fatanshi d'aya yai sauri ya kammala kud'insa ya taho kano neman Ashaf........ *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* *Gaisuwa gareku 'yan sauyi, 'yar gaya, sankach, nagudu, sharubutu, Aisha Idris, Sub, Zee Sa'id and many more, tunda yanzu kun daina neman Aisha sai Zuciya to ga sakon Zuciya nan tana muku fatan alkairi....lol* { *31*} Little jiki a sanyaye ta fito daga d'akin Mumy tai b'agarensu. A zaune taga Nafi kan sallaya, Little ta karasa gunta tare da sama a kusa da ita, Nafi ta kalleta sannan ta kakaro murmushi tace " Little nayi dana sanin zuwa bikin nan." Dafata Little tai tace " Laifinane dana d'aukoki duk da banga alamun kinasan zuwa ba." Kai Nafi ta girgiza alamar a'a kawai zatai magana taji kamar intai magana kuka ne zai kufce mata. Little ta d'au waya ta kira Ashraf, sai da ta kusa katsewa sannan ya d'aga tace " Yaya." Daga can Ashraf dake zaune kusa da Habib yace " uhm ya akai? " Kasancewar a kusa suke yasa Nafi tana iya jiyo maganar Ashraf, Little tace " dama fadama zanyi gobe Nafi zata koma inji Mumy." D'agowa Nafi tai ta kalli Little, jitai Ashraf yace " to Allah ya kiyaye." Little taso ya hana Nafi tafiya jin ya fad'i haka yasa jikinta yai d'an sanyi tace " Yaya wa zai maidata?" A zuciye yace " da wani karambanin ne ma yasa ku d'auko yarinya tana makaranta? Sai kuje ku sami wanda ya saku ku tambayeshi." Little zatai magana taji ya katse, jiki a sanyaye ta kalli Nafi wacce ke wasa da hannunta a zahirin gaskiya kalaman Ashraf sun mata zafi sai dai tasan koma meye ai laifin ta ne. Ta kalli Little tace taimakamin dan Allah in kwanta." Little ta kalli kafarta tace " Nafi ko muje Chemist? " Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a tace "bafa wani serious bane. " a zahiri kuwa tanajin zafin gun sai dai bataso a cire handkerchief d'in Ashraf daga kafarta. Little ta mike sannan ta shiga taimaka mata ta kwanta, idanu ta rufe kamar mai bacci, hakan yasa Little ta fito daga d'akin. Tana fita Nafi ta fara zubar da hawayen dake cinta, Ashraf ta tuno sanda ya d'auketa, idanu ta runtse kalaman Ferry ta tuna data cemata san Ashraf take, Nafi ta share hawayenta sannan a fili tace " Ina na isa? In kuwa har haka ne lalai ina cikin gararin rayuwa." Kalamansa na mota ta tuna dayace mata zai saketa in ta samu wanda takeso. Ta dad'e tana hawaye kafin bacci ya d'auketa. Washegari da sassafe kuwa Drivern Mumy ya mai da ta makaranta, ko Ashraf bata sa a idanta ba. Nafi ta dage sosai da ta koma makaranta, ba wai a kan karatu kad'ai ba sai dai kullum suna tare da Ferry tana kokarin canza halayenta. A wannan zuwa gidan datai lalai ta fahimci abu biyu, na farko Ashraf wasa kawai yake da ita da jawo mata tsana agun mutane bayan ba santa yake ba, na biyu kuwa lalai in har tanasan Ashraf ya fara santa sai ta zama mace daidai shi. A can kuwa an gama biki lafiya ankai Amarya d'akinta, sannan kowa ya watse. Anyi hutu amma Nafi ta kira Habib akan zata zauna a gidan Principal ya tambayar mata ita, saboda a lokacin hutun ta samu isashen lokaci na karatu, wannan jarabawar ita tazo ta karshe a aji batajin kuma za ta iya nunama Ashraf wannan dakikantar datai. Habib ya tambaya, ba tare da wani dogon Nazari ba ta amince, bayan kowa ya tafi gida itama ta koma quaters. Little taji ba dadi sai dai bayan Nafi ta mata bayani ta waya yasa ta gamsu. Nafi ta dage sosai...... Shekararta d'aya kenan a makaranta, duk hutu ba ta wani zuwa gida, sai dai duk cikin hutu Little na zuwa ganinta da sakon Provision daga Mumy da kud'in kashewa. A iya wannan Shekara d'aya ba shakka Nafi ta canza sosai da sosai, ita da Ferry kam sun zama Aminai sosai, sai dai in a b'angaren karatu ne kuma da Jibiya sukeyi. Yanzu suna S1 Nafi ta canza sosai, bata tunani ko sha'awar zuwa gida duk da kuwa yanda zuciyarta take tsananin rashin Ashraf kamar ranta. Yanzu sun shiga Ss 2 a a wannan lokacin ne kuma Nafi ta shirya dan zuwa gida, Little tace "wannan karan kam gaskiya sai Nafi tazo gida, dan akwai bikin kawar Little ko ince Aminiyarta da za'ai. A wannan lokacin shekarun Nafi 18, duk da ba kiba gareta ba sai dai kirjinta ya cika da dukiyar fulani, Nafi ta goge sosai, kamar ba makarantar kwana take ba, komai nata tsaf dan in Little zata kawo mata kaya har da mayuka masu kyau take cewa ta had'o mata. Nafi tana tsaye kusa da Ferry ga Jibiya a gefensu, Nafi ta kalli Ferry tace " Na nawa kikai?" Ferry tai d'an tsaki tace " Ai Yaya Yusuf ya rainan hankali wai ta 7 dan tsabar rashin mutunci." Nafi tasa dariya ita da Jibiya, Ferry ta had'e rai tace " kubarni da abinda ke damuna." Jibiya ta sake dariya tace " lalai zakisha Fada'a gun Abba dan ni na 2 nai." Idanu Ferry da Nafi suka zaro, Nafi ta kalleta sannan ta had'a hannayenta ta tafa mata tace " wow! Jibiya kina kasheni." Ferry ta harareta tace " Zama ta raya ki, ke Feena na nawa kika ci?" Nafi ta juya kai tace " Secret." Ferry tai dariya tace " badai irin na last term ba na 12 ba?" Nafi ta d'an rangwad'a kai cikin tsokana tace " na 8 nai." Ferry cikin d'aga murya tace " WHAT?" Nafi tai murmushi tare da ware takardar, murna suka shiga yi sosai, can Ferry tace " Kai naji dadi kin daina cin double number, amma da alama sai na dage kar next term ki dawo gabana." Suka sakeyin dariya. Ferry ta kalleta tace " Feena zakizo d'in ko?" Nafi ta d'an juya ido tace " zanzo insha Allah amma banasan zuwa yayanki nanan." Ferry ta harareta tace " Gaskiya Feena bazan juri wulakantamin yaya da kike ba, tunda yazo visiting ya nuna yana sanki amma kike wani disgashi, in bakiyi wasa ba har gidanku zan kawoshi." Nafi ta zare ido tace " wa? Rufan asiri." Jibiya tace " kema kinsan bazata yarda wani saurayin ya bita gida ba saboda sanda takema yayan nan nata." Tsaki Ferry tai tace " wlh Feena in har kika bari ya gane kin mutu akansa haka lalai sunanki sorry." Nafi ta tsuke baki tace " Ke nima yanzu ba daina sanshi yaushe rabon ma da inganshi, kila ma ko a hanya naganshi bazan ganeshi ba." Ferry ta d'aka mata duka tace " ni zaki maida gara? Kullum fa sai kinyi labarin yayan nan naki." Nafi zatai magana ta hango kamar Little ta fito daga wata zukekiyar mota, tana sanye da sun glass tayi kyau sosai da sosai, Nafi tace " anzo d'aukana." Nan suka mik'e suka taimaka mata da kayanta, Ferry tundaga nesa tace " Kai Feena gaskiya Little tana kasheni da gayu, ki bari nika inje gida dattin makarantar nan ya fita daga jikina lalai zan tsorata maza." Nafi tace " Nima ki bari sai nazo gida kin ganni kiga yanda zan kasheki da nawa gayun." Dariya sukai harda tafawa. Sun karasa gun, Little ta karaso cikin murna, ta rungume Nafi. Sunsa kaya a motar sannan Nafi ta leka dan ganin wanda ya kawo Little. Habib ya sakar mata murmushi yace " Tantancewa akeyi ne?" Murmushi tamai itama tace " Ai ba sai na tantanceba dama can jikina yaban kai ka kawota." Nafi kenan ba shakka kim canza wato yanzu bakya kunyar maidamin kalamai na." Ta d'aga kanta batare da ta amsa mai ba, sannan sukai sallama dasu Ferry ta amshi number Ferry da jibiya tasa a wayar Little. Nan suka shiga mota, Habib jefi jefi yana kallanta ta glass d'in mota, ba shakka yarinyar nan ta girma, ganin haka yasa Nafi ta matsa daga setinshi ta koma ta can b'an garen. Little ce tace " Nafi yau ji kad'ai nasan farin cikin danakeyi, nayi missing d'inki sosai." Nafi tai murmushi sannan tace " nimafa kawai daurewa nakeyi jinake kamar na biyoki inkika zo ganina." Little ta harareta tace " ba wani nan kedai kawai kinzama 'yar college tafi gida dadi." Dariya suka d'anyi Nafi ta juya tan kallan window. Little ta juyo ta kalleta tace " Nafi au Feena baki tambayi ina yaya ba, ko visiting nazo bakya tambayarsa." Habib ne yai katsal yace " ita meya dameta dashi bayan yayi aure yamanta da ita." Har cikin ranta Nafi taji haushin maganar Habib amma sai ta daure tace " Ya Habib kenan, dama can ba wani shiri muke dashi ba balle ya nemini." Little ta kalleta tace " Nafi yanzu kin daina shigar ma yaya ne?" Ta tab'e baki tace " ni a wa? Dama can bawai shigar mai nake ba kece baki fahimceni ba, ai Yaya Neesa itace zata shigar mai bawai ni ba." Habib ya saki dariya yace " Gaskiya ne Feena gwara ki fara bayyana musu komai." Nafi ta kwantar da kanta akan window tare da lumshe ido, tace " Little bacci." Little ta d'an had'e rai tace " shikenan nayi shiru." Habib ya kalli Little yace " Ai cewa tai bacci bawai kiyi shiru ba." "Hmm ai tun da dadewa na gane Nafi au Feena in batasan magana sai tace wai bacci." Habib ya juyo ya kalli Nafi sannan yace "yarinyar nan ta canza dayawa." kai little ta jinjina tace " ai naji dadin makarantar nan." Haka sukai ta maganganunsu itakam tana kwance tana jinsu a cikin zuciyarta take magana " Yaya ba sai ka basar da ni ba, nafi kowa sanin rashin matsayi danake dashi agunka, kila ma inya ganni bazai ganeni ba, ba komai Allah ya kawomin wani mai sona nima inyi kokarin ganin na yakece wannan soyayyar da take one_side." Nace Uhmmmm zaki iya????. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *32*} Sun isa gida Habib ya gangara yai parking, sannan suka fito, Nafi ta rataya jakar bayanta uta kuma Little ta ja wo trolly d'in ta. Habib ne ya matso kusa da ita yace " Gimbiya Feena kawo in tayaki mana. " Ta kalleshi sannan ta kalli kanta tace " da me fa? " Nuna mata jakar bayanta yai, tai murmushi sannan tace " ni ai ba kaya na d'auka ba Little ce mai kaya, da alama baka kula ba. " tana fad'a tai gaba. Habib ya bita da kallo, gaskiya yarinyar nan tayi, shi dama tun tana yar kauyenta burgeshi takeyi. Little ce ta karaso tace " yaya mun gode." Ya rufe ido tare da yin mika yace " Princess na gaji. " Ta kalleshi cikin kulawa sannan tace " yaya kaje b'angaren su Asim ka kwanta. " Kai ya girgiza mata yace " a'a gida zan wuce, ai tunda Ashraf yai aure na daina kwana a nan gidan. " Kanta ta sunkuyar kasa alamar rashin jin dad'i ya matso tare da sa yatsar sa ya d'ago kanta yace " sai munyi waya." Kai ta d'agamai, ya mika mata key yace " Ungo kiba Ashraf zan d'auki motata nai gaba nima." Ta d'agamai kai, tana kallo ya koma ya shiga motarsa yai gaba. Nafi kam tana shiga d'akinsu tai wani ajiyar zuciya tace " Kai nayi Missing d'akin nan. " Kaya ta shiga cirewa ta d'aura karamin towel sannan ta fara ninke kayan makaranta. Little ce ta shigo, ta kalleta cikin shagwab'a tace " kina gani Feena har Ya Habib ya tafi? " Nafi ta karasa ninkewa sannan tasa agun kayan datti ta kalleta tace " Little wani irin so kikema Ya Habib? " Little tace " so mai yawa wanda yanzu ya zama jinin jikina." Nafi ta tab'e karamin bakinta tace " Shifa? " Little ta fad'a kan gado, ta d'an mirgina tace " Shifa haryanzu a kanwa ya d'auken." Nafi ta girgiza kai a ranta tace " Little nima matsalar dake damuna kenan, gwara kema banaji kinajin rad'ad'in da nakeji in na tuna Ashraf fa mijina ne sai dai yamin nisa. " Toilet kawai ta shige batare databa Little amsa ba tai wanka. Ta dad'e tana gurza jikinta a cewarta dattin makaranta ya fita. Sannan ta fito, bataga Little a d'akin ba hakan yasa ta zauna a gaban madubi ta fara goge fuskarta da cleanser. Hoda kawai tasa batai wani kwalliya ba, sai dai tayi kyau sosai, ta mike kenan sai ga Little ta shigo ta tiren Abinci, Nafi ta kalleta tace " Little ina kayana? " Little ta bud'e mata inda ta jera mata nata kayan, Nafi tai murmushi ta sani sarai daba dan Little ba lalai da zaman gidan nan ya gagareta, nan ta zab'o wata atamfa riga da siket, mamaki tayi dataga tana sa kayan da kyar, Little tai dariya tace " ai dole kigafa dad'ewar da kikai bakizo ba, ga yanzu kin kara girma bawai kiba ba ina nufin kin girma ta sama da kasa. " Nafi ta harareta tace " lokacin girman ne yazo, da alama Little sai kin ban aran kayanki inyaso sai mukai a bud'amin nawa anjima. " Little tace " ki d'auka mana, sannan kinsan fa yau da yamma zamu kamun Yusra sai ki gwada kayan ko da yake cewa nai a kiki daidai ni kawai dai karya kai nawa fad'i ne saboda nad'an fiki kiba. " Nafi ta saka wata doguwar rigar material sannan ta zauna suka zuba abinci suka faraci. Nafi ta kalleta tace " Little ya gunsu Amarya?" Little ta tab'e baki tace " hmm ke dai bari Nafi bayan kin tafi biki an gamashi lafiya sai dai a ranar da aka kaita sukai fad'a kaca kaca. " Cikin mamaki Nafi tace " fad'a kuma? " Little taja wani tsaki tace " Ita wai a dole a daren takesan ya bata wasiyyar mahaifinsa shikuma yace ba wanda ya isa ya sashi ya bada abinda baiyi niyya ba. " Nafi ta tab'e baki tace " ya suka kare to? " "Hmm kedai bari Dady ne yaje da kansa ya sasanta yace Yaya yai hakuri gobe ya bata tunda dai hakkinta ne, ita kuma karta kuskura ta sake tambayarsa. " Nafi ta d'an juya kai tace " Na d'auka tanasan shi dayawa, meye nata na damuwa da abinda baiyi niyyar bata ba? Indai har tana gudun b'acin ransa? " Little tace " Zigata akai ya Asim da Umma." Nafi ta d'anyi karamin tsaki tace " san da takemai baiyi nisa dayawa ba kenan indai har za'a zigata akan dukiyarsa." Little tai ajiyan zuciya, Nafi tace " yanzu fa? An bata ai nasan hankali ya kwanta. " Little tace "Hmm Yaya wai cewa yai wasiyyar dama mahaifinsa ne yace aba matar sa ta farko million d'aya ko ince wai ya ajiye kud'in a banki, to Yaya yabata kud'in sai dai Umma tace itakam gaskiya bata yarda wai kud'i kawai akace ba." Nafi ta had'e rai tace " shi kuma yayan me yace? " "Uhm bai kulasu ba kinsan shi ai. " Nafi ta kara tab'e baki tace " Allah ya sauwake. " Little ta amsa da Amin sannan ta d'aura da cewa " kigama muje ki gaida Mumy sannan kije kiga b'angaren Amarya. " "wa? Bada ni ba, inje in musu me? " sukasa dariya a tare. ¤¤¤¤¤¤¤¤ A b'anagren Ashraf kuwa ya nemi aiki yanda kowa yake nema ya kuma samu ba babban aiki bane sai dai yanajin dad'in yanda yake fahimtar matsalolin ma'aikatansa tundaga kasa, yana kuma fahimtar abinda ya cancanta da zai musu bayan ya amshi company d'in. Sai dai su Asim da Kawu kam shar take a gunsu, Asim kam gani yake kamar saboda Aneesa ne ya hakura da mukaminsa, sai dai shi kawu haryanzu yana tunanin da wani abu a kasa. Kamar kullum yau ma ya dawo gida daga gun aiki, yana zuwa daidai saitin kofa yaji maganar mutane da karfe, da alama ma musu sukeyi, kai ya dafe cikin tsananin takaici sannan ya kwankwasa tare da murd'a kofar. Aneesa ce zaune cikin kawayenta su uku, sallama yai sannan suka kalli inda yake, Aneesa cikin kissa ta taso da sauri tazo ba kunyar mutane a falon ta rungumeshi tare da manna mai kiss a kunci, Ashraf ya d'an zareta kad'an sannan yace " Bari in shiga ciki.." Hannunta ta sakala cikin nasa sannan suka fara tafiya, shidai takaici ma hanashi magana yai. Yana shiga d'akinsa ya kwace hannunsa sannan ya kalli d'akin yanda ya tafi ya barshi haka dai ya dawo ya sameshi, ya kalleta cikin takaici yace " Anie mekenan? Ba nace ki gyaramin d'aki na ba? " Ta shagwab'e tare da kwantowa jikinsa tace " kana fita su Laila suka zo ni ko tunawa ma banyi ba. " Ya kalleta cikin takaici yace "yau kwanan d'akin nan uku kenan a haka kullum da abinda kike cewa, wasa wasa ma falo da mai aiki bata zuwa ta gyara haka nan zaki barshi da sunan kinada abinyi ko? " Aneesa ta kara shagwab'ewa tace " Hubby kayi hakuri zan gyara. " Wani mugun kallo ya mata yace " banaso fitarmin daga d'aki. " Zatai magana ya nuna mata kofa da yatsarsa sannan ya had'e rai sosai, jiki a sanyaye ta fito, sai dai dankar kawayenta su gane ta saki fuska. Shikam tana fita ya sawa kofar makuli tare dajan wani tsaki yabi d'akin da kallo, ko sanda yana shi kad'ai baya barin d'akinsa haka amma yanzu ji d'akisa? Gadon ya gyrara sannan yai wanka ya kwanta a kai, bai dade ba bacci ya d'aukeshi. Bacci yai sosai harya makara sallar la'asar sai karfe 5 ya tashi, da saurinsa yai alwala ya fito masallaci. Sukam su Nafi ganin anyi sallar la'asar suka shiga yib kwalliya dan tafiya gidan biki, saboda kawar Little ce sosai, sunaso suje da wuri dan a gamama Amarya kwalliya su tafi da ita gun biki. Anko suka saka, light purple d'in wani yadi ne, shiba lace bane sannan ba material bane, riga sukai da siket sannan sai head shima kalar kayan, sunyi kyau sosai da sosai, balle abin kan nasu Little ce ta d'aurama Nafi sannan ta d'aurana kanta, Nafi tace " amma ankon yayi kyau. " Little tai murmushi tace " kawayenta ne kawai zasu sa wannan ragowar atamfa ce. " Nafi ta jinjina kai sannan tace " Farin mayafi zamusa? " Little ta girgiza kai tace " a haka zamu. " Nafi ta kalli kanta sannan ta kalli Little tace " taya zamu fita a haka? " Little tace " haka ake yi ai in ma mun d'au mayafin sai dai mu rike a hannu. " Nafi ta jin jina kai sannan ta zaro wani mayafinta karami golden color tace "ni dai da wannan zani. " Little tace " to. " Sun fito abin sha'awa dan hatta takalminsu iri d'aya ne, sai dai ba kyan kwalliya ba duk wanda ya kalli Nafi sai ta birgeshi, kamar yanda nace Nafi ba fara bace can sai dai tana da kyau gashi batada jiki. Sun fito suka wuce gun Mumy dan amsar kud'in liki inji Little. A lokacin shi kuma Ashraf bayan ya idar da sallah yaga kiran Mumy hakan yasa ya karasa gunta, yana zaune a kasa ta kawomai tiren abinci ya bud'e cikin mamaki ganin ba anan yake cin abinci ba. Ganin d'an wake yasa ya gane dalilin kiran, zubawa yai yafara ci kenan, Little tai sallama, amsawa yai saidai bai d'ago ba, lokacin Mumy ta tashi daga falon, wata sallama ya sakeji bayan ta little sai dai wannan muryar cikin sanyi take. Ya amsa sai dai yanasan juyawa kasancewar hali irin nasa yasa ya d'auke kai sai dai bai cigaba da cin abincin ba. Little ta karaso cikin murna tace " Yaya kaine anan? " Nafi ta kalleshi ta baya gabanta yai wani fad'uwa yaushe rabon data ganshi, Ashraf ya kalli Little yace " ke wato kin girma ko? Sam bakya ma zuwa ganina sai dai inmun had'u a wani gun. " Ta rike hab'a tace ina na isa yaya? Kana gani Yaya Neesa sam batasan muje mata wai muna takura muku nikuwa ina zaka ganni? " Baiyi magana ba, tace"Mumy fa? " Ya ce tana ciki, da sauri Little tai ciki. Nafi ta karaso jiki a sanyaye ta tsuguna daga ta bayansa tace " Yaya ina wuni? " Juyowa yai dan ganin mai magana, kallan mamaki yake mata lalai yasan fuskarnan sai dai wacce ya sani inaa.... She can't be. Nafi ta mike ganin yaki amsawa sai wani kallo da yake mata, tai hanyar waje, dasauri yace " Ke! " Ta tsaya sai dai bata juya ba, ya mike tsaye sannan yace " ke! " Nafi dai tana tsaye bata juyo ba, a hankali ya tako zuwa inda take cikin fad'a yace " ba dake nake ba? " Nafi ta juyo fuska a had'e duk da tana shakkarsa amma ta daure tace " ganinai ba sunana kenan ba." "mene? " Nafi tad'an burtso baki, kallan mamaki ya mata yace " Ba Nafisa bace? " Ta kara had'e rai ta kalleshi tace " au kama mantani? Ka d'aukoni daga garin mu amma kama manta da sunana? " Ta juya cikin takaici zata wuce, da karfi ya fizgo hannunta ya jawota, kallan tsoro tamai, tace " Yaya mai kake yi? " Kallanta ya karayi yace lalai itace ya fad'a a ransa, a fili yace " ancemin kun kusa hutu ashe har kunyi. " Ta d'ago ta kalleshi sai dai batai magana ba, yace " wato yanzu makaranta ta maidake mara kunya ko? " Tace " menai kuma? "yanda tai maganar yasa yace "Lalai yarinyar nan. " Kokarin kwace jikinta tai tace " ni ba yarinya bace. " Ya saketa tare da cewa " ke ya hanaki dawowa har kusan 2yrs. " Ta juya kanta gefe tace " nemana akeyi?" Ya koma ya zauna yace " ina zaku haka? " Biki zamuje. Ya fara cin abincinsa, ya juyo da niyyar magana yaga batannan. Mama ne ya kamashi yace " lalai yarinyar nan, yaushe ta girma haka? Gaba d'aya tama canza kamar ba Nafin riga ba." Itakam tana fita tai d'akinsu, a falo ta zauna ta matse hannayenta, jikinta sai rawa yakeyi, meyasa suka had'u? *THE INNOCENT TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *HWA* *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *33*} A can Little ta ganta falo zaune ta kifa kanta, ajiyar zuciya Little tai tace " Feena meye hakan? Mun taho tare shine zaki taho nan ki barni. " Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tace " Sry My Little wlh jinai kaina na d'an sarawa. " Cikin damuwa Little tace " ayya! Sannu, ko zaki hakura da zuwa? " Kai Nafi ta girgiza tace " Muje nima ina san zuwa ai, kuma kan yama daina. " Nan suka mike Nafi ta kara gyara fuskarta sannan suka fito, sunzo shiga mota shikuma ya fito daga b'angaren Mumy, yana kallansu har suka shiga ya d'an yi wani smiling yace " lalai yara sun girma." abinda ya fada kawai kenan yai gaba. Su kuma suka shiga motar Little 'yar karama wanda Kawu ya sai mata wai murnar gama secondary. ¤¤¤¤¤¤¤ Umma na zaune kusa da Asim acan kuryar d'aki, Asim ya nisa yace " Umma tanashan maganin nan kuwa?" Umma tai murmushi tace " Ai tunda muka bata magani tai b'arin nan na tsoratar da ita akan in har ta haihu yanzu da Ashraf to fa lalai wulakantata xaiyi dan kuwa maza basasan mace mai saurin haihuwa." Asim yace " to kidai tabbatar tanasha dan kuwa in har ta haihu da Ashraf to fa komai bazai yiwu ba, bazata taba bamu hadin kai ba, sannan muma in muka halaka Ashraf bayan mun amshe company d'insa da sauran dukiyarsa in har abinda aka haifa ya girma ya gano nan ma kinga akwai matsala. " Umma ta jinjina kai tace "karka damu da wannan amma nikam har yanzu fa hankalina bai kwanta da wannan wasiyar da ya bata ba. " Asim ya kurawa kasa ido, sannan can yace " karya yakeyi ai ni da farko na yarda sai da naga wani murmushi da Kawu yai bayan ta kawomai haka kawai jikina yaban ba haka bane, sai daga baya nai tunani ta ina mutumin da zai mutu zai bar wasiyar kud'i kawai???? " Umma ta jinjina kai tace " nima yanda naga babanka nayi ne yasa nasan ba haka bane sannan nasan halin Yaya sarai bazai bada kudi kawai haka ba. " Nan suka cigaba da kule kulensu....Nikam nace Allah ya kyauta dama ita zuciya kowa da irin tasa. ¤¤¤¤¤¤¤¤ Su Little kam an d'auko Amarya suka wuce inda za'ai event d'in, suna tafe ana hira saboda duk kawayene, Nafi ma yanzu bata kunyar shiga hira, har suka isa. Guri yayi kyau bayan Amarya tazo ne aka fara gudanar da shagalin biki, Nafi tana zaune daga gefe ganin yanda 'yan mata keta rawa su Little ma an zake sosai, Nafi dai tana gefe rike da wayar Little tana dadanawa, tunanin kiran Ferry ne yazo mata, nan ta mike ta d'an matsa kadan daga inda ake shagalin. Daga can ferry ta d'auka nan suka shiga hira, tana nan a tsaye suna waya sai dai suk sanda ta kalli gun idanunsa na kanta, hakan yasa ta fara tsarguwa, daga gani shima gun bikin yazo yana zaune akan motarsa. Ganin kallan ya fara isarta yasa ta matsa daga gun, bayan sun gama waya Nafi ta juya da shirin komawa. Ganin mutum tai kawai a bayanta tana juyawa suka hada ido, Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace " Malam lafiya? " Wani lalausan Murmushi ya sakar mata sannan yace " Aminci Allah su tabbata a gareki. " Ta kalleshi cikin mamaki sannan ta d'an motsa baki a hankali tace "tare da naka, amma..... " " Shiiii dan Allah karki koreni kar kuma ki nuna bakya sona daga gani na yau d'aya." Nafi cikin mamaki ta kalleshi, sai dai har kasan ranta yaso sata dariya yanda yai, ya cigaba da cewa " Sunana Al-Amin masoyin wannan yarinyar. " Juyawa tai bayanta dan ganin wace yarinyar, ya sakar mata murmushi yace " ina kike dubawa bayan gatanan a tsaye. " Nafi ta harareshi yanzu kam ta gane da ita yake, ya d'an rike kunnuwansa yace " Tuba nake ranki ya dade da alama na b'ata miki rai. " Nafi batasan sanda tai murmushi ba tace " ba wani b'ata rai sai dai kayi hakuri ni matar aurece. " Gani tai ya hau dariya, ya kalleta yace " matar aure? Wow na gode da alama da wuri zamuyi aure in killeceki a d'aki." Nafi ta makamai harara, da sauri ya kara rike kunne, yace " Taya zakice min ke matar aurece? Ina mijin? " Shiru Nafi tai a ranta ta ce " inafa yake? Yana can gun matarsa. " Al-Amin yai murmushi yace " please ki amince dani, zan kula dake yanda bakya tunani, ni d'an Katsina ne, sannan kanwar maman yarinyar da ake aurenta ne. " Nafi ta kalleshi sannan tace " lalai yayi kyau." Hannunsa ya had'e guri d'aya yace " Dan Allah sunanki?????? " *FEENAH* abinda ta fada kenan, yace "wow nice name, a ina kike? " Ta juya kai tace " zan koma ciki. " Bata jira amsarsa ba ta fara tafiya, Biyota ya fara yi sai data juyo tace " dan Allah Al-Amin ka kyaleni. " Kansa ya shafa yace " kai!!! Naji dadi dan sake ki kiran sunana." ta kara harararsa sannan ta juya. Taji dad'i sosai dataga bai biyota ba, haka kawai taji ta saki murmushi. Sai da aka gama, wajen isha'i sannan suka fito zasu tafi, suna fitowa ya taso ya karaso gunsu tare da musu sallama, Little ta amsa tana mai kallan sani sai dai ta rasa a inane, yace " Little manya, can na ganki ai kinata rawa ana bikin Aminiya. " Little ta nunashi da yatsa tace " Ya Al-Amin." "Bingo!" ya fad'a yana murmushi, itama murmushin tai tace " Ya Al-Amin ace kaine, nifa ince na rasaka sam ashe ka zama babba ko a hanya na ganka zanyi wahalar ganeka. " Ya harareta yace " Haba Little a gaban Swt Feenah kike fadar hakan? " Ta kalleshi sannan ta kalli Nafi data juya kanta, tace " yaushe ka ganta?" Yace " gatannan sai wulakantani take ashe kawarki ce." Little ta kalli Naf tace " Feena d'an uwan namu kike wulakantawa? " Nafi ta kalli Little kamar zatai kuka, yace " wlh ina zuwa na ajiye su Hajiya na dawo dan in kaita gida " Nafi ta harareshi tace "cewa nai zan bika? " Ya kara had'e hannayensa yace " Little please." Little ta juya da sauri ta shige motarta taja tai gaba tana dariyar mugunta. Nafi ta saki baki tana kallan Little cikin mamaki, Al-Amin ya kalleta yace " Cwt Feena da alama dai nid'in nan nine zan kaiki. " Ta juya kai cikin takaici tace " da wayace kazo nan ma. " Yace " Matata tana guri ba dole inzo ba?" Nafi ta kalli agoggon hannunta karfe 8 ga gun duk ba mutane, katseta yai da cewa. " Please Cwt Feenah ki taimaka, ai indai gidansu Little ne na sani. " Nafi ba dan ranta yaso ba ta karasa gun motar ta shiga rai a b'ace, tana shiga ya zuge glass tare da kunna mata AC, itakam kanta ta maida gefe tana kallan waje. Sun fara tafiya shi kad'ai yake mata magana, ganin batada niyyar kulashi yasa yai shiru. A daidai kofar gidan yai parking, a wannan lokacin kuma, Ashraf ya fito kenan zai fita, kallan motar yai cikin mamaki, har zai wuce sai yaga alamar mace ce a ciki, badai Little bace? Abinda yazo mai kenan, hakan yasa ya ja motar yai parking a gefe. Itakam Nafi tazo fita yasa lock cikin mamaki ta kalleshi ya kashe mata ido sannan yace " Cwt Feenah shikenan bako sallama?? " Nafi ta d'an turo baki tace" in na fita ai zan ma. " Kai ya girgiza alamar a'a sannan ya mika mata wayarsa yace "a'a na yafe numberki kawai nakeso. " Ta d'anyi murmushi tace " sry Al-Amin sai dai banida waya. " Kallan mamaki ya mata yace " mene? Shikenan wato dan bakyasan ki bani mumber ki shine zaki fad'i haka? " Kai ta girgiza alamar a'a tace "wlh ba haka bane, banida itane. " Kallan mamaki ya mata, shikam Ashraf ya cika fam, me Little take a cikin mota har yanzu? A zuciye ya fito yazo kofar da take shikuma daidai lokacin Al-Amin ya cire sim d'insa na Mtn ya bar glo ya mika mata wayar yace " ga tawa akwai sim a ciki ba wanda yasanni da sim d'in ni in na fita nasai wani..... " Kallan mamaki takemai, zatai magana sukaji an kwankwasa glass d'in motar, inda take, Al-Amin ya zuge cikin mamaki. Cikin tsananin mama ki Ashraf ke kallan Nafi, ransa yakai kololuwa gun b'aci, itakam tunda ta ganshi gabanta ya shiga fad'uwa. Al-Amin ne ya katse mugun kallon da yake mata yace " Yaya Ina wuni? " Wani kallo ya bugamai batare da ya amsamai ba, ya kalli Nafi cikin tsananin takaici yace " kin fito ko sai na karya ki? " Motar ta bud'e zata fita Al-Amin ya sake cewa " Cwt Feenah gashi. " Juyowa tai ta kalleshi haka kawai taji tanasan ansar wayar yanzu a gaban Ashraf, hannu tasa ta amsa sannan tace " Nagode kawai tai waje. " Ta gabansa ta rab'a ta wuce haryanzu gabanta fad'uwa yake, Ashraf ya bita rai a b'ace, hannu yasa ya riko ta da karfi yace " abinda aka koya miki kenan a makarantar??? " Idanunta ne suka dan ciciko ta daure tace " me nayi yaya? " Yai wani murmushin takaici yace " me kikai? Ke harkin kai ki zauna a motar namiji ku zuge glass? Ku kuma dade a ciki? " Nafi wacce hannunta ke mata rad'ad'in rikon da ya mata tace " kawoni yai daga gun biki." Xaiyi magana yaga hawaye sun zubo mata cikin rawar murya tace " Yaya hanuna. " Kallan hannunyai sai a lokacin ya kula da yadda ya matse mata hannu sosai ga agogo agun, nan ya sake mata hannu, agoggon kuwa har ya ji mata ciwo, mamakin kansa ya shiga yi. Ya juya da sauri ya shiga motarsa ba tare da ya kalli inda take ba, Nafi kam agoggon ta cire tabi ciwon da kallo lalai ta yarda Ashraf baya ko digon santa wasu zafafan hawayene suka zubo mata, ta juya a hankali tai ciki. Tana shiga ta cilar da wayar akan gado tana kallan Little tana mata dariya, ta wuce toilet. A gaban madubi ta tsaya bayan tayi alwala ta kalli kanta a cikin ranta tace "dama kema kinyi laifi tun farko, kinfi kowa sanin Ashraf yafi karfinki meya kaiki???? " Hawayenta ta share sannan ta fita jiki a sanyaye..... Bayan tayi sallah little ta dameta da zancen Al-Amin itakam shiru kawai tai, dama bata kunna wayar ba balle ma ya kirata. Ganin taki kulata yasa itama Little d'in tai shiru, itakam Nafi kwanciya tai kamar mai bacci sai dai ranta fal yake da tunani kala kala. Shikam Ashraf yana shiga mota yai wani huccin takaici, meye nashi na zakewa haka? Wata zuciyar tace to yarinyace karama ko karatu bata gamaba ko kunya ace tana xama da saurayi a mota? Ai amanace ita agunsa shi ya d'aukota daga wani garin dolene ya kulada ita kafin mazan zamani su hure mata kunne. Ya d'an bigi sityari kadan yace " me yasa nai haka agaban wannan yaron? Salan ya rainani? Ya kara jan tsakin takaici, haka ya gangara gun abokinsa nagun aiki dazai amshi takardu ransa duk a jagule....... Washe gari Nafi bayan ta tashi daga bacci ta fita zuwa kitchen nan suka gaisa cikin farinciki da kewar juna, ta zake ta shiga tayasu aiyukan girki. Sun gama ta fito kenan sukai kicibis da Umma, had'e rai Umma tai tace "ke wacece a kuma wani dalili kiika shigo mana kitchen? " Nafi tad'an rusuna kad'an ta gaisheta sannan ta mike tsaye tace "Umma baki ganeni ba? " Umma ta kar had'e rai, Nafi tace " nice fa Nafi. " Umma ta kara kallanta ba shakka itace, ta d'an harareta tace " uban me kike anan ba dama kina makaranta ba?? " Nafi tace " ai dama ana hutu nice dai kawai ban dawo ba. " Umma ta kara had'e rai tace " to yanzu gulma ce ta dawo dake ko me? " Nafi kam murmushi ta saki dan itakam bataji haushin kalaman Umma ba ta kalleta tace " Umma na shiga ciki. " Ran umma ya b'aci ganin yanda yanda yarinyar ma ba a kula ba, gashi tasan yarinya da take 'yar riga yanzu ta girma? Gashi dai ba wanka tai ba amma gata tsaf, ba kamar wannan kucakar tada ba. *Anan ne zan dakatar da wannan littafin nawa mai taken Zuciya kowa da irin tasa, ina fatan zaku jirani zuwa bayan sallah in Allah ya kaimu.* *Yanda zamu fara azumi lafiya Allah ubangiji yasa ku gama lafiya, ya kuma bamu ikon yin ibada batare da gajiyawaba, ya karemu daga duk wani abu dazai d'aukemana hankali agun ibadaunmu, ya yafemana kura kuranmu, ya kuma sa mu gama da duniya lafiya.* Ameen suma Ameen..... *Nagode kwarai da irin san da kukema littafin nan, banida abinda zancemuku face godiya, Allah yabar zumunci, ya kara mana kaunar junan mu.* *Duk wani masoyin wannan Littafin ina mika sakon gaisuwata gare ta/shi, na gode kwarai da kauna.* *Sai Allah ya Kaimu Bayan Sallah in Muna da Rai da Kuma Lafiya.* ❤💛💛💙💜💜🖤💟💟[6/28, 1:51 PM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* *Dukan Godiya ta tabbata ga Allah Subhanahu Wata'ala, muna kara godiya gareshi da ya nuna mana watan Ramadan lafiya yasa mukai ibadun mu lafiya, sai fatan Allah ubangiji ya karbi ibadun mu...(Ameen)* *Inama dukan d'okacin masoyana barka da sallah da kuma fatan alkairi a ko ina suke...* Allah Ubangiji ya Maimaita mana Ameen.. { *34*} Umma ta juya cikin takaici da niyyar lalai sai ta sa a kori yarinyar nan kafin ta zamar musu masifa. Nafi kam har tayi gaba ta tsaya tare da juyowa tabi Umma da kallo, kai ta girgiza ta juya zata wuce ta hango Asim ya nufo Umma da sauri kamar zai fad'i da kasa, kallan yanda yake baza sauri take da alama akwai magana da yake san isarwa cikin gaggawa shi yasa yake wannan saurin. Umma tana hangoshi da ganin yanayinsa yasa tai hanyar b'angarenta da sauri itama, Nafi har ta juya zata koma d'aki taji sam hankalinta ya kasa kwanciya, a hankali ta tako tazo wajen b'angaren Umma sai dai ta rasa tayayya zatai karyar da zata shiga? Shiru tai ganin ba halin shigan yasa ta juya da niyyar komawa, Asabe mai aiki a kitchen ta hango ta nufo gun rike da tire babba da kuloli akai, Nafi ta karasa gunta da sauri tace " Asabe ina zuwa?" Asabe tace " Umma zan kaima kumallon ta." Nafi ta amshi tiren tace " Barshi ni bari na kaimata dama ciki zan shiga." Cikin rashin damuwa Asabe ta bata tare da kad'a kanta ta koma inda ta fito, Nafi kam da sauri ta nufi kofar Umma, gabanta kam sai dukan uku uku yake saboda tsoro sai dai ta rasa dalilin dayasa zuciyarta keta tunzurata akan lalai ta shiga. Murd'a kofar tai a hankali ta shiga da sallaha itama ciki ciki tayi ta. Batai mamaki ba dan dama batasa a ranta za ta gansu a falo ba, nan ta wuce cikin tsoro ta ajiye tiren akan dinning sannan ta kalli d'akunan dake falon guda biyu, a ina suke???abinda ta fad'a kenan a ranta. Lalab'awa tai ta karasa d'akin farko,tare da sa kanta a jikin kofar kamar munafuka, jin alamun rashin mutum yasa ta karasa d'ayan, zuciyarta sai kara tsananta take da fad'uwa wannan karan bata sa kanta a kofa ba tana zuwa jikin kofar d'akin taji cikin fad'a wanda yasa ta tsorata taji Muryar Asim yace " Umma nikam bakin ciki kasheni zai yi dan nikam indai har na cigaba da ganin Ashraf to fa lalai inaji ni zan bar gidan nan." Gaban Nafi ne ya yanke ya fad'i me kenan? Ta fad'a a ranta. Kafin ta nemo amsar tambayarta taji Umma tace " ni d'in ce maka akai farin ciki nake in na ganshi? To amma ya zakayi....???" Cikin fad'a Asim ya katse Umma da cewa " Yanzu sam 'yan gun aikinmu basa karramani magana ma ba yimin suke ba, sannan yanzun nan abokina na gun aiki ya sanar dani cewa shareholders na company d'in sun yi meeting akan a dawo da Ashraf matsayina inyaso ni sai a ragemin matsayi, nifa wlh in bakuyi wasa ba zanyi aika aika." Umma ta gyara zama tace "Asim kayi hakuri abi maaganar nan a hankali." Cikin zafin rai yace. " a hankalin me? Ni wlh har yan daba na kira kafin nazo nan na sanar dasu inya fito aiki anjima su tareshi su kawar mun da numfashinsa." Jikin Nafi kam rawa kawai yakeyi, har tsuma takeyi saboda tsananin tsoro da fargabar abinda yau kunenta yake jiye mata. A tsorace ta juya cikin tsananin tsoro da firgici tai waje har kafarta na hard'ewa ta fad'i kasa. A d'aki kam Umma ta kalli Asim tace " Asim yau lahadi naga ba aiki?" Asim yai wani murmushi yace " ai shi zai je saboda akwai wani project da sukeyi shi da 'yan team d'insa." Umma tai ajiyar zuciya sannan tace " baka ganin anyi gaggawa in aka mai illa tun yanzu? Asim yai tsaki yace " Illar me? Shima Abban ai yafi kowa san Ashraf ya mutu." Umma ta jinjina kai sannan tace " Aneesa fa?" Asim ya kara jan tsaki yace " kyale wannan in ya mutu taji ta cafki dukiyaa a hannu kina ganin zata damu?" Umma tai murmushi sannan tace " duk da Neesa na tsananin san Ashraf banaji tana sansa kamar yanda takesan kudinsa dan na tabbata da bashida komai duk sanda takemai bazata tab'a aurensa ba." Asim yai kwafa yace " Ni wlh na tsani ma na gansu tare, nifa inaji duk duniyarnan ba wanda na tsana kamar yaran nan." Umma ma tai tsaki tace " ai nima dashi da uwarsa sune mutanen dana tsana kaf duniyar nan." Nan suka zauna suka cigaba da sake sakensu. Nafi kam dakyar takai kanta falon b'angarensu, ta zauna akan kujera har yanzu jikinta rawa yake, sam kwakwalwarta ta kasa d'aukan abinda ta jiyoma kanta. Dif taji kwakwalwarta ta d'auke sam bata tunanin komai sai da wasu dakiku suka shud'e sannan taja wani dogon numfashi sannan ta mike a zabure tace " Ya Ashraf????" Jitai idanunta sun kawo kwalla ace d'an uwanka na jini???wannan wace irin rayuwace???? Sanar dashi zatai?? Zai yarda da abinda zata fad'a??ko Little zata fad'ama??kai ta girgiza tace"kar itama in tada mata hankali..." Wata zuciyar tace Mumy fa???kai ta girgiza da sauri tace " Mumy kuma da wani idan zata zauna dasu??" Kanta ta dafa dataji ya sara, can tace " Kawu fa???" Hucci ta saki cikin damuwa tace " shikuma matarsa ce da d'ansa." Kan kujera ta fad'a wasu hawayen suka sake zubo mata, Ya Ashraf me kai ake neman halakamin kai???ta fad'a cikin wata irin murya mai ban tausayi. Agoggon bango ta kalla karfe tara, karfa Ya Ashraf ya fita??? Da sauri ta mike kawai ta nufi b'angarensa, hankalinta bai tsaya ba sai da ta isa kofar b'angarensa, me zata cemai??? Shiru tai ta tsaya agun kamar abu mara motsi, dan batada amsar tambayar nan. Tana tsaye ba mafita har dakika goma suka shud'e, motsin bud'e kofa ne yasa ta dawo hayyacinta, idanunta ne suka firfito cikin tsoro, ta kalli kofar. Ashraf ne ya fito, jitai gabanta ya fad'i cikin mamaki ya kalleta, sai dai kafin yai magana sai ga Aneesa ta fito rike da jakarsa, fuskarnan tata a had'e da alama ranta a b'ace yake. Cikin mamaki itama ta kalli Nafi, "Malama wacce ce ke? Me kuma kike anan?" Nafi ta had'iye yawo cikin tsoro ta kalli Ashraf, shima kallan mamaki yake mata, Aneesa ta kara kallantaa yanzu kam kallan rashin mutunci ta mata. Tace " Ke malama wacece ke? A wani dalilin kikazo min kofar miji??" Nafi kam jira take Ashraf yai magana sai dai abin haushi gani tai ya d'auke kansa, tare da amsar Jakarsa zaiyi gaba, jitai idanunta sun fara cikowa ita gani take ai ya kamara Ashraf ya sanar da Aneesa, ganin ya fara tafiya ga tana so ta tsaidashi daga fita waje, sannan ga Aneesa ta tsareta da ido yasa duk ta rikice. Shikam Ashraf haushin abinda tai jiya da daddare ne yasa yaki kulata, Aneesa ta bud'e baki zatai magana kawai Nafi tai baya luuu jikake ta zube a kasa, wannan ita kadai ce mafita a gareta abinda ta fad'a kenan a ranta tare da runtse ido. Aneesa ta d'anyi kara tare dayin baya cikin tsoro, hakan yasa Ashraf ya juyo da sauri, cikin rud'ewa yasa ya karaso inda take, sannan ya d'agota tare da cewa " Nafeesa!!Nafeessa!!." Sai a lokacin Aneesa ta gane waccece, kallan Ashraf tai duk ya wani rud'e haushi da kishi suka kamata a zuciye ta matso tace " Aljanu ne da ita??" Ran Ashraf ya b'aci ganin yanda tai maganar cikin rashin kulawa, yace " bishiyar kuka ce a kanta..." Ya mike a zuciye ya d'agata ya nufi mota da ita, Nafi kam haryanzu gabanta bai bar fad'uwa ba tanaji ya bud'e bayan mota ya sata a ciki. Tanaji ya bud'e gaban mota ya shiga, ya tadata tad'anyi zafi sannan yaja motar suka fita, suna fita daga gate d'in gidan sai taji yace " Will u get up now?" Idanunta ta kara runtsewa a ranta tace " badai dani yake ba?" Ashraf ya kalleta ta madubi sannan yace " abinda kika koyo a makarantar kenan? Pretending??" Nafi kunya da takaici duk suka kamata ta kara danna kanta kujera, gefen titi ya gangara yai parking sannan ya juyo ya kalleta yace " Kin tashi ko sai na fitar dake waje da kaina?" Nafi ta mike zaune tare da zunburo baki gaba kanta na kasa, ya kura mata ido yace " me kike san fad'amin?" Kallan mamaki tamai, tace " ya akai kasan abu nake san fad'a?" Kallanta yai sannan ya kalli window yace " inba abu kikesan fad'amin ba me zai sa kizo b'angarena kinsan inada mata kizo ki tsaya a waje?" Baki ta tab'e a ranta tace " da cewa nai bakada mata?" Ya kalleta sannan taji yace " da alama kin manta inada mata inba haka ba mezai sa kije b'angaren? Ai sai ki kirani a wayar Little ko ta saurayinki." Nafi ta saki baki tana kallan sa tace " to ni menace?" Ya juya kai sannan yace " Ki tambayi abinda kika ce a zuciyarki." Nafi tai shiru rai b'ace. Ashraf yace " to fad'amin? Menene?" Nafi tai shiru tare da maida kanta kasa. Ashraf ya kara had'e rai yace "zan saukeki fa inja motata inyi gaba ko ce miki akai banda abinyi??" Nafi ta kalleshi jiki a sanyaye, cikin wani irin murya tace "banifa da lafiya, xaka saukeni." Wani murmushi ya saki na rainin hankali yace " harda karya kika koyo a makarantar? " Ta kalleshi sannan ta d'an shagwab'e murya tace " nifa Yaya ba karyar dana koyo." Har cikin ransa sai dayaji wani abu, sai dai ya sake dakewa yace " ke jiranki nakeyi ko?" Nafi ta kalleshi tace " Yaya dan Allah kar kaje gun aiki yau." Kallan mamaki ya mata yace " bangane ba? Ke harkinkai matsayin da zaki hanani abu?to ko Aneesa bata samu wannan matsayin ba." Nafi ta kalleshi cikin wani yanayi tace " Na sani Yaya banida wannan matsayin kuma ban kai kaina wannan gun ba, sai dai ba dan nibaaa ba kuma dan halina ba sai dai ka duba darajar Allah ka hakura da zuwa aikin nan yau." Ta karasa magana tare da kawar da kanta alamar idanunta nasan kawo kwalla, kallan mamaki yake mata, sai dai yanzu yasan tabbas da wani abun....... *THE INNOCENT TEAM* 🏌🏻‍♀ [6/30, 12:30 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *35*} Yanda yake kallanta yasa ta had'e rai tare da maida kallanta wajen window, itakam batasan me zata cemai ba, ana san kashe ka? Kuma 'yan uwanka?? Itakam kalaman nan sun mata tsauri. Ga mamakinta jitai yace " tunda karyar ciwo kikai yanzu ai sai ki koma gida." Nafi ta kalleshi a tsorace tace " Sauka zanyi a haka??" Kai ya d'aga mata alamar yes, idanunta ne sukai rau rau ta kalleshi sannan tace " taya zan iya fita ahaka komayafi fa babu a jikina, sannan bani da kud'in da zan tafi da kaina." Ya d'aga mata kafad'a alamar wannan kuma ruwanta ne, Nafi ranta ya b'aci a zuciye ta matsa da niyyar bud'e kofa, har ta zura kafa d'aya zata fita sai taji yace " shigo in ajiyeki ba dan halinki ba inada abinyi." Ta koma ta zauna kamar ba taso sai dai ko kallan inda yake batai ba, Ashraf ya tada mota zuciyarsa fal da tunani, har suka isa gida ba wanda ya sake magana, yana parking ta bud'e kofa zata fita sai kuma ta juyo tace " Yaya ina zaka?" Kallanta yai yace " banaji wannan yana d'aya daga cikin damuwarki tunda dai baki fad'amin me kike nufi da kar inje aiki ba, kin kuma san halina ba a sani abu." Nafi ta kalleshi cikin kulawa tace " Yaya tunda kaga na furta hakan ai kasan da dalili, in ba haka ba meye nawa da zance karkaje aikinka?ni ba matarka ba?" Juyowa yai ya kalleta kalamanta na karshe sun tsayamai a wuya, sai dai ya share yace " ke nake jira zan fita ko?" Nafi batasan sanda wani takaici ya kamata ba ta kafeshi da ido na takaici, kallanta yai sannan ya juya ya d'au wayarsa, bakin ciki ya hanata d'auke idanunsa daga kansa jitai ya tada mota, alamar zan tafi, takaici yasata ta fito daga motar a zuciye tana kallo yaja motarsa ya tafi, tabi motar da kallan takaici. Wannan wani irin mutum ne, duk yanda na damu da rayuwarsa amma shi ko a jikinsa?? Sai ma rashin mutunci ne zai biyo baya?. Sam ta kasa d'auke idanunta daga hanyar daya wuce, jitai an dafa ta a firgice ta juyo, Mumy ta gani tsaye itada Little. Nafi tai saurin share kwallarta sannan ta kakaro murmushi tace " Mumy ina kwana???" tafad'a tare da risinawa, mumy ta amsa sannan tace " Nafi me kike yi anan? Little duk ta damu tanata nemanki?" Nafi ta kalli Little sannan tai murmushi tace " Ayya My Sisto tuba nake." Little ta harareta sannan ta juya tai b'angarensu, Mumy ta kalli Nafi databi bayan Little da kallo tace " Nafisa ina kika je???" Nafi tai kasa dakai, Mumy tai murmushi sannan tace " shikenan, kije gun 'yar uwar taki dan hankalinta ya tashi." Nafi ta d'aga kai sannan tai bayan Little da sauri. A tsaye ta ga Little ta cire kaya daga ita sai towel da alama wanka zata shiga, Nafi ta karasa gunta ta zauna akan gado tana kallan Little wacce ta had'e rai. Nafi tai murmushi tace " Little bazaki kulani ba?" Little ta juya tai hanyar toilet, tanaji Nafi ta kara cewa " My Sisto tuba nake kinji kiyi hakuri." Little ta wuce toilet ba tare da ta amsa mata ba, nan Nafi ta mik'e ta gyara d'akinsu ta gama shara kenan Little ta fito, Nafi ta kalleta zatai magana taji Little tace " ki je kiyi wanka Yusra tun d'azu take kira wai dan Allah muje yanzu." Nafi ta mike ta karaso gun Little ta rungumeta tare da cewa " Little wlh wani abu ne ya taso min dayai gaba da duk tunanina." Little tace " Shikenan Feena ni kin barni anan cikin tsoro tunda na tashi naga banganki ba na kuma fita kaf na zaga ban ganki ba." Nafi tace " Sry nayi laifi." Murmushi sukama junansu, nan Nafi ta saketa sannan itama tasa nata towel d'in ta nufi toilet, har taje zata bud'e kofar ta juyo tace " Little nikam a iya sanina ba wata matsala dake tsakanin Mumy da Umma ko?" Little ta kalli Nafi tace " Feena kenan, a haka dai kamar babu, sai dai inaji a jikina kamar da wani abu." Nafi ta kalleta tace " kamar me??" Little ta d'an tab'e baki tace " kinsan a duniya in har akace kud'i to fa an gama komai, kud'i da kike ganinsu sune matsalolin komai na rayuwar duniyar nan, duk wata matsala inka dubashi daga kasa to fa lalai zakiga kud'i shine silar komai." Nafi ta shiru tana mamaki, can tace " Amma dai nan banaji za'ai fad'a akan kud'i ko? tunda dai naga kowa yanada shi." Little ta furzar da iska sannan tace " Feena kenan ai a gidan da ake da kud'in anfi samun matsala akan kud'in tun balle in dukiyar da mai ita." Nafi ta mata kallan mamaki, Little tai murmushi sannan tace " share kawai." Jiki a sanyaye Nafi ta shiga wanka, sam wanka take amma tanata nanata kalaman Little dukiyar da mai ita? Kawu kenan? To in shine meye na neman kashe Ya Ashraf?" Ta dad'e kafin ta fito, tana fitowa taga Little ta ciro musu dinkin Less anko ne shima, Nafi ta zauna itama ta fara shafe shafe. A b'angaren Ashraf kuwa yana fita daga gidan ya nufi gidan abokin babansa ko ince lawyer d'in babansa, bayan sun gaisa yace " dama so yake ya d'auki mota d'aya daga cikin motocinsa dake gidan. Nan ya d'auko masa keys d'in Ashraf ya d'au d'aya sannan sukai sallama ya fita. Hanyar Company d'insu ya nufa, yasha kwanar karshe ya hango wasu mutane kusan su goma a cikin wata katuwar mota baka kirin sai dai sun sauke glass d'in motar sannan wasu sun zuro kansu suna duba hanya, bakaken kaya garesu haka kuma baza'a ganesu ba saboda tabarau baki dake fuskarsu. Ashraf ya rage gudu dayazo kusa dasu, sam sukam sun d'auke kai daga kallan motarsa ganin ba irin ta bace wanda aka basu umarni. Hakan ya bashi damar ganin yawan mutanen dake ciki, sannan ya wuce, lalai ya tabbatar shi suke nema saboda yazo giftawa yaji wani yace "wai ya haryanxu banga mota kirar Marcedes_Benz C300, wai ya tabbatar nan zai biyo??" Ashraf ya giftasu zuciyarsa fal da mamaki, meke faruwa? Me Nafeesa ta sani? Me taji???? Ya karasa gun aikinsu nan ya tadda 'yan team d'insa sun dad'e da zuwa, nan ya zauns suka fara abinda ya kawo su. Su Nafi ansha kwalliya, suna fitowa Habib na yin parking, tundaga nesa Little ta hangoshi ta saki wani lalausan murmushi na farinciki, Nafi ta kalleta sannn ta kalli inda take kallo ganin Ya Habib yasa tai murmushi itama tace " Little a dinga kokarin dannewa irin wannan nuna soyayya kirikiri haka??" Little ta harareta sannan tace " haka nace miki?" Nafi ta d'an rangwad'a kai tace " Little kenan." Juyowa yai shima ya hangosu, nan ya tsaya tare da kurawa Nafi ido, gaskiya yarinyar nan type d'insa ce ba karya, har suka iso gun yana kallanta, Nafi ta d'an had'e fuska tare da kawar dakai ge. Little ta matsa gunsa tace " Ya Habib daga ina haka?" Idanunsa nakan Nafi yace " wlh wucewa nazo yi shine na shigo." Little ta kalli Nafi dan taga yanda yake kallanta, sai dai bata kawo wani abu ba tace" Nafi tayi kyau ko yaya?" Habib yai murmushi yace " Sosai ma kuwa." Nafi ta matsa daga saitinsa sannan tace " inafa wani kyau dan kowa yaganki yasan kece kikai kyau." Ta fad'a tare da cewa " Ya Habib ko ba haka ba?" Ya kalli Little kunya tad'an kamashi yai wani murmushin burin kunya yace " dama ai Princess daban ce." Little ta saki murmushin farin ciki. Little ta kaleshi cikin kauna tace " Ya Habib yaushe zaka tafi?" yace " zuwa la'assar dan inasan ganin Ashraf." Kai little ta d'aga tace "Allah yasa mu dawo mu sameka." Yace Ameen tare da satar kallan Nafi. Nan sukamai sallama suka shiga motar Little sukai gaba. Su Umma kam da Asim suna zaune a falo suna jiran good news tunda sunga fitarsa daga gidan da motar mercedes wanda hakan yasa Asim ya sanar dasu sunan motar da number ta, sai dai jin shiru har shad'aya ba labari yasa Asim ya kira, sun sanar dashi har yanzu motar bata wuce ba, nan suka kara jinkirtawa zuwa azahar, nan ma akace motar bata wuce ba, cikin takaici Asim ya kira wani ma'aikacinsu na company ya tambayeshi Ashraf yazo? Ga mamakinsa jiyai ance tun d'azu yana nan. Haushi da takaici suka turnukeshi ya kirasu ya hau su da fad'a sannan yace " su tafi daga gun kafin ma a zargi wani abun.?" *THE INNOCENT TEAM*Copied By YAYA HAYAT (admin Hayat hausa novels Hausa novels and fashion Cool novel, makeup and kitchen1⃣ Cool novel, makeup and kitchen2⃣ AND Cool novel, makeup and kitchen3⃣) WHATSAPP NO: +2347039625239 [7/2, 5:42 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ *Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku Haske Writers Association* *©na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *Wattpad As_AyusherMohd* { *36*} Little ta kai bakin gate wayarta ta fara kuka, Nafi ta zaro wayar daga cikin jakarta ganin Sunan Big Bro yasa Nafi tai saurin mika mata, Little ta amsa tare da gaidashi. Nafi duk ta tattara hankalinta kan Little tanasan taji me yake cewa sai dai batajin komai sai amsar da Little ta bashi "Yaya har mun fito fa?" tai maganar tare da had'e fuska, Nafi sai ji tai tace " Yaya dan Allah ka....." da alama katseta akai wanda ta karasa maganar da cewa " To Yaya." Tana kashewa ta kashe motar tare da kallan Nafi ranta duk a b'ace, Nafi ta kalleta tace " ya akai?" Little tace " wai Yaya ne yace kije ki gyaramai b'angarensa." Nafi ta kalli Little da mamaki tace " Ni kuma?" Little ta d'aga kai alamar eh, Nafi ta canza fuska sannan tace " Matarsa fa? Ita bata iya gyaran bane ko me yake nufi?" Little tai karamin tsaki tace " wannan uwar san jikin me zatayi? Banda chatting." Nafi ta d'aure fuskarta tamau sannan tace " Mu tafi kinji?" Little ta kalleta cikin mamaki tace " Me kike nufi?" " Mu tafi inda zamu." Little kam tayi mamakin Nafi dan bata taba tunanin zata iya ture maganar Ya Ashraf ba ganin yanda take girmama shi. Little ta kalleta tace " Feena....!" Nafi tai murmushi tace " Mu tafi kinji, wato matarsa bazata gyara musu muhallinsu ba shine ni zanje in gyara musu, sannan ba kunya su shiga suna farin ciki, sannan gobe ma aa kara kirana in gyara, to ba da ni ba." Little ta jinjina kai alamar ta gamsu da zancen Nafi sai dai tana jiye mata b'acin ran Ashraf, iya kuluwa Nafi ta kulu wato ita da bai damu da ita ba shine yake neman sata gyara musu b'angaren su a lokacin da suke shirin fita, ta d'anyi kwafa kadan a ranta tace " ni d'azu kamar zan zauce jin wani abu zai sameshi ni kuma wato wannan ne sakayyar da zaimin. Bata sake magana ba har suka ita gidan su Yusra sai dai kana kallanta kasan ranta a b'ace yake. A bakin gate Al_Amin wanda ke zaune yana ganinsu ya saki wata fara'a tare da mikewa ya nufo su, sam Nafi bata kula ma da shi ba, har ya iso inda suke Little ta mai murmushi sannan suka kalli Nafi wanda sam hankalinta baya gunsu sai ma ci gaba da tafiya da takeyi. Hannu Little tasa ta rikota wanda hakan ne yasa Nafi ta juyo ta kalleta, ganin Alamin a tsaye yasa ta mai kallan mamaki. Rausayar da kai yai cikin salon soyayyarsa yace " I am disappionted Feena." Nafi ta kakaro murmushi sannan tace " Sry wlh ban kula ba, sam hankalina na wani gurin." Ya d'an shagwab'e kadan yace " in har damuwarki ba akan wani namiji bane na hakura in kuma har akan namiji ne ba ni ba banaji zan hakura." Little ta saketa tai gaba ta barsu ganin Alamin ba kunya agabanta yake wannan sakalcin. Nafi ta juya kai gefe sannan tace " just 4get, ya kaje gida jiya?" Alamin ya kura mata idanunsa wanda ya kashesu kai kace a haka idanunsa suke, Jitai bazata iya kallansa ba hakan yasa tai kasa da kanta, ya kara matsowa sannan yace " Feena jiya na baki waya amma sam ko kunnata ma bakiyi ba, sannan yanzu kin wuceni ko kallona bakiyi ba, Feena please kar ki wahalar da zuciyar dake tsananin kaunarki." Nafi ta d'ago jiki a sanyaye, ganin yanda har yanzu kallan nan yake mata yasa tad'an kalli gefe sannan tace " Ba haka bane, jiya bayan na shiga gida bacci nai da wuri, yau kuma sam ban ganka ba." Alamin yai kasa dakai sannan yace " Ko dai....." Katseshi tai da cewa " Alamin me yasa kake da yawan complain ne? Na fada ma uzuri na why not kai believe da abinda nacema meyas kake neman tursasani akan fadar abinda na shine ba?" Tana kai nan ta juya ta nufi hanyar da zata sada ta da ciki, da sauri Alamin yasha gabanta tare da rike kunnuwansa biyu yace " Sry Feenah please!!" Nafi ta kalleshi bata cemai komai ba sai kokarin canza hanya tai gaba da takeyi, bai san sanda ya riko hannunta ba, Nafi ta watsa mai wani mugun kallo sannan ta fizge hannunta tai gaba. Kai ya dafe cikin tsananin tsoron abinda ya aikata, me zata d'aukeshi? Nafi tana shiga ciki aka nuna mata d'akin da su Little suke nan ta shiga ta taddasu ana ta hira, duk yanda sukaso su jata da hira taki aminta a karshe ma kwanciya tai batasan sanda bacci yai gaba da ita ba. Can cikin bacci taji Little na tashin ta, ta bud'e ido a hankali, Little ta kalleta tace " Feena ya zamuyi?" Nafi ta mata kallan da me fa? Little tace " Ran Yaya ya b'aci yana waje yana jiranki." Idanu ta zaro gabanta ya yanke ya fad'i ta mike zaune da sauri tace " Da gaske?" Little tace " wlh, yace ki fita yanzun nan, in kuwa kika bari ya shigo sai ranki ya b'aci." Nafi ta mike tare da d'aukan mayafinta tai waje. Little tace " inzo muje?" Kai Nafi ta girgiza mata alamar a'a sannan tai gaba. Nafi tana fita ta shiga neman motarsa dan itakam bata ganta ba, horn taji an mata wanda yasa ta juya ta kalli inda taji horn d'in, nan ta karasa gun jikinta duk ya mutu ga bacci ga tsoron me zai biyo baya, tana zuwa jikin motar ya zuge glass d'in motar sannan ya mata alama da hannu akan ta shiga. Nafi ta bud'e motar ta shiga tare da rufe kofar. Bai mata magana ba sai jan motar da yai, sai da sukai nisa ya juyo ya kalleta rai a b'ace yace " wato ni ban isa dake ba ko? Maganar saurayin ki ta fi tawa ko?" Cikin mamaki ta kalleshi ta daure tace " ban gane ba." Wani irin burki dayaja sai da numfashinta yai gaba na wucin gadi. Nafi a tsorace ta kalleshi, ransa a b'ace yace " ban bada sallahu ki gyaramin part d'ina ba?" Nafi ta kalleshi tace " ka fada amma gani nai ni meye nawa na shiga part din mai mata?" Ashraf mamaki ya kamashi yaushe 'yar nan tai baki haka? Yace " to ita kinsan ba 'yar wahala bace dan nace ki taimaka mata shine zaki tafi gidan saurayinki?" Wani mugun kishi ne ya taso ma Nafi, ita ba 'yar wahala bace?" Kallan mamaki take mai, yacigaba da cewa " sannan ke harkin isa in saki abu ki kama hanya kiyi tafiyar ki??" Nafi batasan sanda ta saki wani murmushin takaici ba, ta goge kwaIlar data taho mata, tace " Yaya ba sai ka fadamin magana akan matarka ba, nafi kowa sanin ita ba 'yar wahaka bace, ni da ka d'aukoni daga riga mai shan madara da nono kullum, mai kiwon dabobbi nice 'yar wahala." Jikinsa ne yai sanyi, a zahiri shi gidan saurayin ne bayasan taje ya kuma rasa dalilinsa na rashin san hakan, shi yasa yasata aiki bawai wulakantata yakesanyi ba. Nafi ta share kwallarta sannan ta cigaba da cewa " Yaya ka maidani garinmu inda nake, na fi kowa sanin banda matsayi a gunka dama sauran mutanen gidan, Little ce kadai mai sona dama can ni haka Allah ya halliceni da bakin jini, ubana ma ba sona yake ba, uwata ta d'auki kanina ta tafi dashi ni da bataso ta barni a riga, ban taba samun wani wanda yake sona tsakani da Allah ba in har ka cire little, gwara ka.......... Jitai an jawota an rungume ta, kalamanta ne suka tsaya cak, bama su kadai ba duk wata gaba ta jikinta jitai ta daina aiki, shi kanshi sai daya rungumeta hankalinshi ya dawo jikinsa, me ya aikata? Sai dai ya kasa zare jikinsa.......... *THE INNOCENT TEAM* [7/2, 10:06 PM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA* _Kowa da irin tasa_ © *AYUSHER MUHD* 37 Sun dade a haka kafin Ashraf ya d'agota daga jikinsa, kansa ya maida yana kallan gefen titi, a zahiri kunyar kallanta ma yakeyi, Nafi kam anyi dif kamar kazar data fad'a ruwa, kallansa kawai takeyi, Ashraf ya juyo ya kalleta ganin har yanzu bata dawo daidai ba yasa yai saurin cewa " Ke wai yarinyar nan yaushe kika yi baki haka? Sai magana kike ba tsayawa?" Nafi ta bud'e baki zatai magana sai shakuwa, jikake heee'i, kanta tai saurin sawa a cinyoyinta tana kokarin maida shakuwar, Ashraf yai saurin tada mota suka fara tafiya, shiru ne ya biyo baya Nafi ta d'ago a hankali ta kalleshi, ganin sun wuce hanyar gida yasa tace " Yaya ina zamu?" Kallanta yai sannan ya maida kansa titi tare da cewa " Hotel." A tsorace ta kalleshi sannan tasa hannu a kafafunta ta matse jikinta, ya juyo ya kalleta dariya ta kusa zuwa mai, yace " lalai yarinyar nan me kike tunani?" Kallansa tai sannan a hankali tace " bakomai." A ransa yace " lalai makarantar nan ta b'ata yarinyarnan, bayaji sanda tazo garin nan tama san me ake nufi da aure amma yanzu aga zancen hotek har tana wani matse cinyoyi? Shi me zaiyi da yarinya karama ma kamar wannan? In ma iskanci zaiyi?" Nafi kam aranta abubuwa da dama take ayanawa, ne zai mata a hotel d'in? Tunowa tai da sanda ya rungumeta da sauri ta girgiza kai alamar a'a, Ashraf kam kallanta kawai yake saura kad'a ya bigi wata mota, da sauri yaja burki sannan ya kalleta yace " badai tunani kikeyi ni? Kamar ni Ashraf zanyi miki wani abu ba? Banaji kinkai wannan matsayin ko da kuwa iskancin na keyi." Nafi wanda kalamanta suka b'ata mata rai tace " nima ai bance wani abu zakamin ba, sannan ko wani abun ne ai banaji nakai wannan matsayin." Kallan mamaki ya mata, sannan ya had'e fuska tamau yace " Da alama raini yafara tasiri a tsakanin mu." Juya kai tai batace komai ba sai d'an kunkuni datai, a zuciye ya fizgi motar, lalai yarinyar nan shi take ma kunkuni? Sun isa Hotel din ya karasa gun parking, kallanta yai sannan yasa hannu ya fizgota sam baisan da karfi ya jawota ba wanda hakan yasa ta fad'a kirjinsa, a hankali ta d'ago cikin tsoro, ya kalleta yace " me kika ce d'azu?" D'an karamin bakinta ta turo gaba tace " ni me nace?" Yai wani murmushi yace " bakima san me kika ceba ko rainin hankali? Da alama ma zagina kikai." Idanu ta zaro cikin mamaki ta d'aga jikinta daga nashi tace " ni? Yaushe? Taya za'ai in zageka koda kuwa naman jikina kake yanka?" Ya kura mata ido sannan yace " inkinaso in yadda baki zagen ba to ki fad'amin a ina kikaji zancen za'a tareni a hanyar zuwa office." Kallan sa tai cikin tsoro, ya matso da fuskarsa kusa da nata yace " what? Bazaki iya fad'a ba?" Idanu ta kifta sannan ta had'iyi yawu, ya sa idanunsa cikin nata sannan yace " bazaki iya ba?" Idanunta tai saurin maidawa kasa saboda wani abu dataji ya taho mata, komawa yai yazauna tare da d'aukan wayarsa yace " kijirani ina zuwa." Yana kainan yai hanyar fita, batasan sanda tasa hannu ta riko rigarsa ba, yazo fita yaji an rikeshi, ya juyo ya kalleta sannan ya kalli rigarsa inda ta rike. Nafi cikin tsoro tace " tsoro nakeyi Yaya." Idanunsa ya kankance yana kallanta, ta cigaba " Tsoro nake kar na zama silar jawo gaba ko fad'a a tsakanin ku." Ashraf yai karamai ajiyar zuciya sannan yace " Nafisa me kika sani? Me kika sani game dani da 'yan uwana? Mutane sun d'auka ganin fara'a a fuskar mutane shi yake nuna suna cikin farinciki sai dai abin sam ba haka yake ba, kowa da kike gani shi kadai yasan wace rayuwa yakeyi a cikin zuciyarsa." Nafi tai shiru kanta na kasa bata kuma sakeshi ba, Ashraf ya sa hannu akan hab'arta ya d'agota yace " Asim ne?" Kai ta d'aga mai tare da maida kanta kasa, Ashraf yace " sakini inje in dawo lokaci na tafiya." A hankali ta saki rigarsa, ya fita. Kallo ta bishi dashi jikinta duk ya gama sanyi. Shikam Ashraf sam baiyi mamaki ba dan dama jikinsa ya bashi hakan, ya sani mutane dayawa ba sanshi suke ba a gidan amma kowa na kokarin b'oyewa banda Asim. Yana shiga ya bada takardun dayazo badawa sannan ya fito. Nafi kam abin duniya ya dameta, Ashraf ya bud'e ya shiga, ganin yanda take kallansa yasa ya d'aga mata gira yace " ya akai kuma?" Nafi ta girgiza kai alamar ba komai sannan ya tada mota sukai gidan lawyer d'in babansa, nan ya ajiye wannan motar ya d'au tasa ta da sannan sukai gida. B'angarensa suka nufa, yana gaba tana binsa a baya, sunje wuce wa ta b'angaren su Asim sai gashi. Ashraf ya saki wani murmushin rainin hankali sannan ya cigaba da tafiya, ba wanda yama juna magana har Asim ya gifta Ashraf kad'an. Yaji Ashraf yace " ASIM" Ba Asim ba hatta Nafi wanda Asim d'in ke saitin ta ta tsorata da yanda Ashraf ya kirashi, Asim kam tsoro ne karara a fuskarsa, Ashraf ya tako a hankali yazo kusa dashi sannan ya sa hannu ya dafashi yace " ka tab'aji inda kura ta nemi kama zaki?" Asim yamai kallan mamaki sai dai bai amsa ba, Ashraf yai murmushi sannan yace " Ita kanta kurar da take tsoron zaki kaga kuwa ta ina ta isa ta kama sarkin dabobbi?" Ya kara matsowa kusa dashi sosai yasa bakinsa a saitin kunnensa yace " In har kurar tana neman halaka sarkinta to lalai sai tayi amfani da kwakwakwarta." Ya fad'a tare da nuna tasa kwakwalwar. Sannan ya cigaba " in har batai amfani da nan ba to lalai ita zata fad'a cikin trap d'in datai na kama sarkinta." Yana kai nan yasa hannu ya bubugamai kafad'a sannan yai gaba. Nafi kam a tsorace tabi bayan Ashraf. Shikam Asim anan suka barshi sai dayai kusan minti biyar a tsaye kamar abu kara motsi kafin ya juyo da niyyar kallan Ashraf sai dai sam baya gun. Sun isa b'angaren sa, Ashraf ya kalli Nafi yace " D'akina nakeso ki gyaramin." Ta kalli falon wanda duk yayi kaca kaca ko sanda yake shi kadai baya taba yanda falonsa yai haka bare yanzu. Ta kalleshi tace " nifa d'akinka kawai zan gyara." Yace "Falon fa?" Tace " Wannan kuma matarka sai tayi ai aikinta ne ba nawa ba." Matsowa ya farayi ita kuma tana matsawa baya, tsoro takeyi sai dai itakam bazata taba yadda ta gyara musu falo ba wato ta gyara suzo su zauna suyi soyayyarsu a ciki? Jin tazo jikin bango yasa ta tsaya tare da kallansa a tsorace, Ashraf ya kalleta sannan yace " Maimaita kalamanki." Kasa tai da kanta ba tare data maida ba, ya saki wani murmushi yace " in aka tambayi iyayenki matsayina a gunki me zasuce? Ahh i am really curious." Zaro ido tai cikin mamaki tace " ban gane ba." Yace " Menene matsayina a gunki?" Gabanta ne ya fad'i da sauri tace " Yayana mana." Yace " Good." Menene matsayinmu a gun iyayena da 'yan uwana? Tace " Wanda ya taimakeni." Yace " Bravo!, to menene kuma matsayina a gun 'yan kauyenku da mahaifinki?" Baki ta shiga motsawa tana san magana sai dai bazata iya fad'a ba. Ya juya ya fara tafiya sannan yace " in kina san 'yancinki kimin biyayya sai in baki takardarki cikin sa lama ki auri wanda ranki yakeso." Cikin takaici tace " in naki fa?" Yace " Well! Wannan kuma ya rage naki kinsan dai ba'a aure kan aure ko? Haka nan zakiyi ta zama har ila masha Allah." Yana kainan yai hanyar dinning. Tabishi da kallan takaici, ba ma zaka zauna dani ba sai dai haka zan ta zama har ila masha Allahu, lalai ma Ya Ashraf..... Cikin takaici ta shiga gyaran gida ranta inyayi dubu to fa ya b'aci, takaici duk ya turnuketa, ko inama wannan matar tasa taje? tai maganar ranta a b'ace. Hotunsu ta kalla dake manne a falo sunyi masifar kyau kamar me, taja tsaki sannan tace " Aikin kawai ko kyau ma." Lol nikam ai dariya ce ta kamani na kara kallan hoton wanda yaune rana ta farko danaji an kushe wannan hoton.....Su Nafi ko me yasa akaga munin hoton da ni kaina na bash A1????? *THE INNOCENT TEAM*[7/4, 11:51 PM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*   Kowa da irin tasa    ©Ayusher Mohd..... 38     Tsayawa yai cak cikin tsananin mamakin Nafi yarinyar da a iya saninsa sanda ya d'aukota ko dukanta zakai bazatai magana ba illa ma inka gama ta b'uya a wani gun tai kukanta yau kuma itace........   Katsemai tunani Anisa tai da zanzaro ashar, tace " Lalai yau za'ayi kan babban b*********, ni kika rikema hannu?"  Nafi ta sake mata hannunta batare da ta tanka mata ba sai neman giftata datai zata wuce.  Cikin zafin rai Anisa tasa hannu iya karfinta ta hankad'a Nafi, saura kiris ta kifa taji an tareta tare da rungumeta, nan suka karasa kasa su biyu, basai ta tambaya ba tasan waye ko ince zuciyarta ta isar da sakon waye zuwaga gab'obinta.    Aneesa mamaki ya kamata ta saki baki dalala tana kallan wannan al'amarin shikam Ashraf suna karasa faduwa, ya mike tare da sake Nafi sannan ya kalli Aneesa cikin fad'a yace " kinada hankali kuwa? Yanda kika hankad'ota inta fad'a kan wani abu fa??"    Aneesa kam cikin mamakin kalamansa tace " Ya Ashraf kana nufin tare mata kai ko me?"  Ya kalli Nafi cikin b'acin rai yace " wa zan tare wa? Ina miki fad'a akan zakiyi b'arna wata rana in har baki kula da abinda kikeyi ba kina min wani zancen banza." Aneesa tace " Naji na d'au laifina amma inaso inji me yasa ka tareta kai ka fad'i ita kuma ta fad'i a jikinka?"   Kansa ya shafa da hannu cikin takaici ya kalli Nafi yace " malama kama hanya ki fita, sannan in sakeji kin raina na gaba dake wlh inbakiyi wasa ba sai jikinki ya gaya miki."   Nafi kalamansa sunsa gwiwarta tai sanyi ranta kuma ya sosu sai dai ya ta iya? Mikewa tai jiki a sanyeye tai waje.  Tana fita Ashraf ya kalli Aneesa cikin takaici yace " ke bakiji kunya ba??yarinya karama ita take nusar dake nan d'akin aurenki ne ba wai na wani ba? Akan me zatama gyara miki gun da yazamar miki dolenki?"    Aneesa wacce idanunta suka ciciko tace " Yaya nikam inaji a jikina kamar ba auren soyayya mukai ba, kamar ni kad'ai ce nake sanka kai kuma sanda kakemin kawai na 'yan uwan taka ne."   Idanu ya runtse sannan ya kalleta yace " a soyayyar danasan ina miki da, banaji yanzu ina miki ko rabinta sannan bana tsamannin zaki tambayeni dalili ganin ke kikafi kowa sannin abinda ya jawo hakan."  Yana kai nan ya zari makullin mota yai waje.   Aneesa ta fashe da wani irin kuka na bakin ciki itama ta fito tai b'angaren Ummanta tana kuka wiwi kamar wacce akama duka.   *************   A b'angaren Asim kuwa yana ganin su Ashraf sun tafi yai b'angaren mahaifinsa cikin tsananin tsoro da firgicin kalaman Ashraf.    Yana isa ya kwankwasa tare da murd'a kofar ba tare da ya jira an bashi izini ba.  Kawu wanda ke zaune gaban wani karamin akwati (kit) yana duba wasu takardu yanajin motsin mutum yai saurin rufe takardun tare da maidashi cikin kit d'in, yana kokarin tura kit d'in karkashin gado Asim ya fad'o d'akin tare da kallan mahaifin nasa.  Shikam Kawu da sauri ya karasa turawa sannan ya had'e rai tare da cewa " Kai Asim bakada hankali ne zaka fad'omin d'aki ba sallama?"   Asim ya karaso kusa da mahaifinsa tare da tsugunawa a gabansa yace " Abba ya zanyi?"  Cikin mamaki yake kallansa yace " Da me fa?"  Asim ya share zufa nan ya sanar dashi duk abinda ya faru sai dai ba fad'amai da sanin Umma a harkar ba.   Kawu ya kalleshi cikin b'acin rai sannan yasa kafa iya karfinsa ya ture Asim, ya cigaba da magana cikin fad'a, Asim me yasa ne sam bakada hakuri? Banine nace kabar komai a hannuna ba?"   Asim ya rusunnar dakai yace " Abba kayi hakuri wlh ni sam banasan ganin yaron ne."  Tsaki kawu yaja sannan yace " zancen banza ma kakeyi, yanzu idan wad'anda ka tura sun kama Ashraf kenan 'yan sanda suka zo fa?"  Kana tunanin bazasu sanar dasu kaika aikosu ba? Daganan sai me? Kamaka zasuyi a banza."   Asim yai kasa dakai cikin dana sanin gaggawar daya aikata, kawu yacigaba " ni nace kabar komai a guna, akan me zamu halakar dashi bayan bamu gama sannin iya dukiyar dake karkashin sa ba?"   Asim ya jinjina ma mahaifinsa kai sannan ya bashi hakuri, nan kawu ya sallameshi tare da zama akan gadonsa yai shiru yana tunani, can cikin wata irin murya yace. " Yaya ya zakayi??? D'an da kakeji duk duniya baya shi gashi a tafin hanuna, ya auri 'yata sannan matar fa kake santa kamar ranka ta dawo karkashina." Wata irin dariya ya saki wanda ni kaina saida tsoro ya kamani, da sauri nabar d'akin ina mamakin dama haka mutumin nan yake??? Lalai wata zuciyar akwai hassada da mugunta a cikinta.    Asim na fita yai murmushin farin ciki tare da kara kallan kofar d'akin yace " Kai!!!! Amma Abba karshen mugu ne."  Ya sa dariya sannan yace " ko menene a  akwatin nan???"  Kad'a kai yai ya nufi b'an garen Umma, ya shiga kenan ya zauna yana jiran ta fito daga b'andaki sai ga Aneesa ta shigo da kuka.   Cikin kulawa ya mike ya rungumota yana tambayarta menene? Aneesa kam kuka take sosai, nan Umma ta fito ta samesu a haka.  Itama zama tai suka cigaba da tambayar Aneesa abinda ya sata kuka, Aneesa cikin kuka tace " Umma Ba Ashraf bane ya fifita yarinyar nan a kaina."  Cikin rashin fahimta Umma tace " Ban gane ba?"   Asim yace " Malama dalla daina mana kuka ki fad'a mana menene ke faruwa."  Hawayenta ta share ta shiga sanar da su duk abinda ya faru tun daga farko har karshe."   Umma ta mike cikin fad'a tace " Lalai za'ayi tashin hankali a gidan nan."  Asim ya mike tare da cewa " akwai meeting dole ne yau ayi taron gaggawa na gida dan kuwa Ashraf yayi kadan ya wulakanta mana ke."  A zuciye yai waje......   *****************    Nafi kam tana fita daga b'angaren Ashraf ta nufi nasu b'angaren taje shiga taji ance " Yaya Feena."  Juyowa tai tare da kirkiro fara'a tace " My Amrah kece da kanki?"  Amrah tai murmushi tace " yaushe kuka dawo?"  Nafi tad'an jujuya kai sannan tace " ni kadai na dawo."  Amrah tad'an yi hucci kad'an kamar babba, Nafi tai dariya tace " Yaya Amrah ya akai ne?"  Tace " Mumy ce tace " in mun dawo daga makaranta muzo gun yaya Little ta mana wanka sannan ta d'auko mana kaya."   Nafi ta d'an canza fuska kad'an tace "Amrah naji haushi fa! Wato ni bazan iya muku abinda Little zata muku ba ko me?"   Amrah ta matso kusa da ita tace " Yahkuri Yaya Feenah wlh ba haka nake nufi ba."  Nafi ta kama hannunta sannan tace " naji muje mu taho da Afrah."   Nan suka fara tafiya hannayensu rike da juna.     *************** A can kauye kuwa Datti yana cikin tsananin farin ciki da walwala, a 'yan shekarun nan dabobbinsa sun kara bunkasa sosai yazamo kaf kauyen garin ba wanda ya kaishi yawan dabobbi, shi kadai yake rayuwarsa cikin farin ciki ba wanda zai kashema kud'i bare har arzikinsa ya ragu.    Sam bai damu da halin da Nafi take ciki ba bare kuma matarsa da d'ansa da suka gudu.   Duk sanda aka tambayeshi gidan Nafi sai yace sai dai a tambayi Dan Litti dan kuwa shi bazai iya gane wa ba, hakan yasa duk 'yan garin sun d'auka da gaske yaje gidan 'yar tasa.   Sanda Dan Litti yai wata 5 a garin kachako yad'an tara kud'insa ya shiga garin kano neman Ashaf sai dai duk yanda ya nemesu ya kasa samunsu kasancewar garin da girma sannan baisan wani kwatance ba sai Ashaf mijin Nafi, wannan yasa duk inda ya tambaya sai dai amai dariya gani suke kamar shirme yake ko kansa ne ya tab'u.   Bayan kud'in hannunsa sun karene ya koma garin kachako ya cigaba da achabar sa har ya d'an samu wasu kud'i, ya sanar da uban gidansa akan zaije kauyensu ya dawo.   Mamaki ne ya kamashi ganin kowa ya ganshi sai ya tambayeshi wai 'yar gidab Datti a wani irin gida akai kaita? Wasu ma cewa suke zasuzo ya kaisu.    Datti yanajin labarin D'an litti ya dawo ya taho takanas ya tareshi suka keb'e, Datti ya kalleshi yace " ya kaje gidan?"  Dan Litti ya girgiza kai alamar a'a, Datti yace " ka taimaken duk wanda ya tambayeka gidan Nafi kace musu munje ka taimaka min."   Mamaki ya kama d'an Litti yace " What u say?"  Datti yai tsaki yace " malam ni banasan wannan yaren arnan naka kamin hausa."  D'an Litti yai saurin rufe baki dan yace ya daina turancin shima.   Nan Datti ya lalaba Dan Litti akan yai karya wai sunje gidan Nafi.  Shikam d'an litti ko sati baiyi ba ya koma garin kachako ya cigaba da kasuwancinsa, ganin yayi abokai acan ga uban gidansa na sansa sannan can yafi kawo masa kud'i.    Wannan Kenan....    To be continue ......   *THE INNOCENT TEAM* ( _Dan Allah kuyi hakurin jina dakukai shiru wlh Wayatace tad'an same matsala sai do akai resetting d'in d'inta Tukunna.....Thanks 4 ur Love._ ) [7/5, 6:20 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*   _Kowa da irin tasa_    *Na Ayusher Muhd*   39     Nafi ta shiryasu tsaf sun zauna a falo sunata hirar su, labarin makaranta kawai suke bata itakam kai kawai take d'agawa amma sam hankalinta ba'a gunsu yake ba, abubuwan da suka faru a d'akine suke dawo mata.    Ta zarfafa cikin tunani sam bataji shigowar Little ba, sai jitai an dafa ta, ta d'an xabura kad'an sannan tace " Amrah me kika ce?"  Little ta zagayo ta gabanta tare da harararta tace " Feenah wato baki mayi tunani na ba ko?"   Nafi ta kalleta sannan tai murmushi tace " My Little tuba nake wlh sam hankalina yayi wani gun ne."   Little ta zauna kusa da ita tare da cewa " Alamin yau ai karamar hauka yaso min."   Nafi ta d'an tabe baki tace " Name kuma?"  Little ta girgiza kai cikin takaici tace " wai shi a dole ke da Ya Ashraf akwai wani abu a tsakaninku."   Nafi ta zaro ido tace " kamar ya kenan?"  Little ta d'aga kafad'a tace " ohon masa, shi wai yanda kukeyi keda yaya sam bayaso, hankalinsa bai kwanta da yanayin yanda kuke ma juna ba."   Nafi tasa dariya sannan tace " lalai da alama baisan Ya Ashraf ba shiyasa, me zaiyi dani?"  Little ta d'an harareta tace " kijiki ke kuma, wai ashe yaje gunsa kafin ki fita yana gaidashi amma yaya wai da kyar ya amsa mai."   Nafi tad'an turo baki kad'an tace " wannan kuma ai yanayinsa ne ba wani abu ba."   Little tace " Na fad'amai amma kamar zigashi nake, sam ya hanani zama agun kamun nan shidai wai sai na fad'amai ko kina sansa."   Tsaki Nafi taja tace " daga had'uwa sai soyayya sai kace wata taxi?"  Little ta kwashe da dariya tace " Love at first sight yake so ku zama."  Nafi ta had'e fuska tace " lalai wayaga."  Dariya sukai a tare.     Bayan sallar sukaji kararrawar tarawa, Little cikin mamaki tace " Meeting kuma?"  Nafi tace " Ai nikam kafin ki dawo nayi bacci."  Mikewa Little tai tace " Bazaki ba?"  Nafi ta jawo pillow ta kishingid'a sannan tace " Family Meeting."   Little ta harareta sannan ta mike tai waje.     Nafi ta gyara kwanciyarta tare da kalan wayar da Alamin ya bata, kai ta girgiza alamar a'a dan zuciyarta na raya mata ta kunna wayar.    A can falo kuwa kowa ya hallara, Ashraf ne ya shigo daga karshe, ya ja kujera ya zauna.  Kawu ne ya fara sallama nan ya tambayi dalilin taron?   Asim ne ya mik'e sannan yace " Abba in anci abinci zan sanar da kowa."   Anci ansha kafin Asim ya mike yace " A gaskiya Abba bazan juri ganin abinda Ashraf yakema kanwata ba, yau cin mutuncin har yakai ya fifita wata kucakar 'yar kauye akan matarsa."   Wani murmushi Ashraf ya saki, Mumy kam kallan Ashraf tai cikin damuwa, ganin abinda yai yasa ta fara tsoron karfa ya b'allo wata maganar dan tasanshi sarai.   Kawu ne ya katseta da cewa " Ban fahimceka ba, Fad'an tsakanin Ashraf ne da Matarsa?"   Asim yace " Eh."  Kawu ya kalli Ashraf yace " Ashraf ya akai?"   Kallan Asim yai ba tare da ya d'auke idansa ba yace " Asim za'a tambaya ai kawu ni me na sani banda sani da akai nazo nan."  Kalaman sun ba kowa haushi sai dai ya zasuyi? Kawu ya kalli Anisa yace " ke me ya faru?"   Little kam fatanta Allah yasa ba Nafi ake nufi ba.  Anisa ce cikin sanyin murya tace " yarinyar nan 'yar kauye ce ta nemi kawomin raini dan na sata aiki shine na mata fad'a akan ni ba sa'arta bace shikuma shine ya shigar mata ya wulakantani a gabanta."   Mumy ta kalli Ashraf, Kawu ne yace " Ashraf me yasa ka wulakanta matarka akan tana nunama yarinya karama 'yar kauye laifinta?"   Ashraf ya kalli Anisa sannan ya kalli Kawu yace " wannan kuma itace takeda amsar tambayar, me yasa nabi bayan yarinyar? "    Mumy ta kalleshi tace " Ashraf me yasa kai haka?"  Bai amsamata ba sai juya kai dayai, ya sani sarai dama yarda zatai da duk abinda akace mata yayi.     Anisa ta kalleshi cikin sakalcin magana tace " Yaya kaine fa kamin fad'a akanta."   Ashraf ya mike tsaye cikin takaici yace " fad'a? Ai banaji wanda na miki yau sunanshi fad'a, sannan Umma ki maida 'yarki kusa dake dan banaji tasan me ake nufi da aure, da kuma darajarsa."   Yana kainan yai waje abinsa.  Cikin zafin rai Asim ya mike ya sha gabansa yace " ce maka akai mun gama magana?" Ashraf ya kalleshi yace " Me ya rage?takardar kanwarka? Ko 'yan daban daka turo d'azu?"   Asim ya kalli Ashraf cikin wani irin yanayi, Ashraf ya bubugamai kafad'a sannan yai gaba.   Bakin ciki ne ya cikama Asim ciki a zuciye yai wani irin ihu.        An gama taro kowa zuciyarsa ba dadi, Little ta shigo d'aki. A kwance ta hango Nafi rike da Qur'ani a hannunta. Ta shiga ta zauna kusa da kafarta.  Nafi takai aya sannan ta kalleta tace " kun gama?   Little tace " A kanki ma akai taron."  A tsorace Nafi tace " ni kuma? Me nai? Nashina."   Little tai d'an yake nan ta zayyane mata abinda ya faru......  Asuba ta gari   *[truncated by WhatsApp] [7/5, 7:48 PM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *40* Nafi ta mike a zabure tace " Haka suka ce? Wow! Lalai na jinjina ma matar Yaya." ta fad'a tare da tafa hannunta. Little tai dan dariya tace " hmm dan ma Ya Ashraf suka samu? " Nafi ta koma ta zauna tare da jan tsaki tace " Ni fa gani nake Yaya nada zafi amma baya iya wani abun kuzo mu gani. " Little tai murmushi tace " Nafi bakisan halin Yaya bane, yanada masifar zuciya da taurin kai abu d'aya ne yake hanashi yin komai a gidan nan. " Da mamaki Nafi ta kalli Little tace " me kenan? " "Mumy. " Little ta fad'a fuskarta d'auke da damuwa, sannan tacigaba "Nafi yau zan fad'a miki tarihin gidan nan. " Da jin haka Nafi ta gyara zama cikin zukud'in san taji meke faruwa. *TUNA BAYA.* " Kakan Ashraf wato Sale ya kasance mutumin wani kauye ne dake garin Kila a karkashin jahar Jigawa, ya taso cikin wahala kasancewar mahaifinsa bashida hali sannan shi kad'ai ne namiji kuma babba agun mahaifinsa. Wahala kam na rayuwa ya shata, dan mahaifinsa ba cikaken lafiya gareshi ba, duk wani arzikin gona iin ya samu akan kannensa da iyayensa yake tafiya, hatta kayan da yake sawa sun jeme saboda tsabar wahala. Sam bai taba tunanin aure ba ganin nauyin dake gabansa sun mai yawa, har Allah ya kawo kanwar mahaifiyarsa ita da 'yarta sukazo hutu gidan. Tunda Sale ya ganta yaji ya kamu da santa sai dai ganin ita daga birni take yasa ya kunshe abinda ke ransa. Fanna wanda take 'yar kanwa ce ga mahaifiyar Sale a garin maiduguri suke, yarinya ce wacce ba ruwanta , tunda tazo gidan ta lura Sale kaya d'aya yake maimaitawa sannan sam ta kula baya zaka kullum aiki yakeyi. Ranar yazo fita ta d'au mayafinta tace " zata rakashi. " Ba musu suka fita tare, wannan fitar itace mafarin soyayya mai karfi data kullu a tsakaninsu, iyayenta sunyi takaici sun kuma so hanata wannan auren ganin ba komai Sale ke da shi ba. Fanna ta dage wanda hakan ya kaisu ga aure. Nan aka gyara mata b'angare anan cikin gida aka mata jere. Shekararsu d'aya da aure Allah ya azurtata da d'a namiji sai dai tana haifarsa Allah ya karb'i ranta. Aka sama yaron Abbas, Sale yayi kuka sam rayuwarsa ta canza kullum yana tare da d'ansa ko gona zaiji haka yake d'aukansa sutafi. Gulmar da ake a kauyen ne yasa mahaifin sa ya d'aura mai aure da Ruma 'yar gidan babban wansu. Ruma na san Sale sosai sai dai shi d'ansa ne kawai a ransa, wanda hakan ne yasa Ruma ta d'au soyayya itama tasama Abbas. Ganin yanda takesan d'ansa ne yasa shima ya fara kulata har Allah ya bata ciki ta haifi namiji itama shine aka samai Mansir. Sun taso cikin kulawar iyaye sai dai kowa yasan sanda Sale yakema Abbas wanda sam baya iya b'oye hakan koda kuwa a gaban waye. Abbas na shekara 8, shikuma Mansir na shekara 5 Allah yama Sale rasuwa. Wannan mutuwa ta girgiza kowa, iyayen Fanna sukazo akan a basu Abbas ya zauna a gunsu. Sai dai Abbas ya tubure akan baza'a rabashi da kaninsa ba, hakanan dole suka had'a da Mansir suka taho maiduguru. A can kuwa kowa yafi nuna kulawa da damuwarsa akan Abbas, dan yana isa garin aka sashi a makaranta, Abbas na kokarin ganin duk abinda aka mai an ma Mansir sai dai duk yanda yaso abu ya faskara. Makarantar kud'i aka sashi aka sa Mansir ta government, sannan kafin asai ma mansir kaya d'aya to Abbas ya tara 5 dan 'yan uwa ma na aikomai, wani sa'in haka zai dau saban kayansa yaba kaninsa. Haka suka taso cikin wannan rayuwa, Mansir yana tsananin kishin kauna da Abbas yake samu ta ko ina, a haka har Abbas ya gams karatunsa ya tafi Buk a kano. Mansir kuma yana aji biyar. Mansir tun yana Js1 ya fara san wata yarinya wacce akama mahaifinta transfer daga kano zuwa maiduguri. Yana tsananin santa sai dai ganin yarinyar bata Shiga harkar kowa yasa ya kasa sanar mata, har shima ya gama secondary ya fara poly dake nan garin Maiduguri. A kullum ya taso daga makaranta sai ya biya ta islamiyar su yarinyar wato Ruma, haka zai tabin bayanta har sai sunje gida ba tare da saninta ba. Kwatsam wani hutu Abbas yazo gida lokacin yana level 4 yaga Ruma, ba tare da gazawa ba yaje gidansu ya sanar da ita soyayarsa, cikin sa'a ta amsa masa, bai sanar da kowa ba saboda Ruma tace bataso a sani saboda mahaifinta yace karatu kawai yakeso. Soyayya mai zafin gaske ce ta shiga tsakanin masoyan biyu, a lokacin da Abbas ya sanar da Mansir akwai wacce yake so shima Mansir din yacemai akwai wacce yakeso sai dai shi kunyar sanar da ita yake. Abbas yai dariya sannan yace " Kanina ai yanzu da zafi zafi ake bugan kirji karka kuskura ka jinkirta soyayyarks kar a maka shigo shigo.... " Wannan kalamai na yayansa sun karfafamai gwiwa bayan Abbas yabar gida Mansir ya bugi kirji yaje gidan su Ruma. Sun gaisa kafin cikin fara'a zai fara koro mata abinda ke ransa ta katseshi da cewa " Mansir ko? Kanin Abbas. " Mansir ya washa baki yace " Eh nine. Ruma ta d'anyi kasa dakai sannan tace "Ai koka yai? " Cikin mamaki Mansir yace "a'a. " Ta d'ago sannan tace " ba wani nan, yace bazai fad'ama kowa muna soyayya ba amma wai bazai min alkawarin kin fadama ba. " Gaba Mansir ne ya fad'i yace " Kinsan yaya ai. " Tai murmushi tace " Yana sanka dayawa komai sai ya ambaceka. " Mansir kam jiyai kafafuwansa suna neman Kasa d'aukansa hakan yasa yace mata kansa na ciwo ya tafi. Mansir ya rame, sam karatun ma ya kasayi, a lokacin ne Abbas ya gama nashi karatun, yama Mansir fada sosai ganin takardunsa ba abin arziki, duk yanda yai akan ya sanar dashi matsalarsa ya ki. Hakan yasa ya zauna da kansa yake koyamai karatu. Sai dai abin mamaki ya kula yanzu sam Mansir baya yarda suyi wata magana mai tsawo. Hankalin Abbas ya tashi, yana tsakiyar wannan kangi mahaifin Ruma aka maidashi kano, sannan mahaifinta yace ta fito da miji. Ruma kam kai tsaye ta gabatar da Abbas, nan aka kai kud'i tare da sa rana." Little tai ajiyar zuciya tare da kallan Nafi wacce tai shiru tana sauraranta, tace " Kinsan su waye mutanen nan uku? Nafi tace " Abbas mahaifin Yaya, Mansir kuma Abban ki ko? " Little ta d'aga kai sannan tace " Ruma fa? " Idanu Nafi ta zaro cikin shakkun abinda yazo ranta tace " Don't tell me???" Kai Little ta d'aga tace " Yes! Mumy ce. " Nafi ta zaro ido sosai cikin mamaki, Little tai yake sannan tace " wannan shine mafarin komai dake faruwa. " Nafi kam baki ta saki tana mamaki wannan sarkakiyar..... Little ta nisa sannan ta cigaba.............. *THE INNOCENT TEAM* [7/7, 9:33 PM] YAYA HAYAT: ZUCIYA* Kowa da irin tasa *HASKE WRITERS ASSOCIATION* 41 " Mansir ya shiga wani yanayi ganin anata shirye shiryen auren yayansa da budurwar da yake masifar so, sam ya daina zama a gida wanda hakan ya tada hankalin yayansa. Abbas duk abin duniya ya dameshi ganin kaninsa a wannan hali, ana saura wata d'aya biki Mahaifin Ruma ya nemarma Abbas aiki a wani company na AL-Food.ltd, dan takardun Abbas sunyi kyau sosai. Company ne babba wanda ake ji dashi bama garin kad'ai ba har kasa baki d'aya. Kowa yayi murna sosai da wannan al'amari sai dai wanda ake dominsa sam baya farin ciki, an tsaida bayan aure da sati uku zai fara zuwa aiki a nan garin kano. Saura sati biyu biki Mansir ya shirya bada sanin kowa ba ya tafi kano,address din Ruma daya amsa agun wata kawarta yabi yaje gidan. Ruma kam alokacin ta dawo kenan daga amso dinkunanta na biki ta ganshi tsaye a bakin gate. Fara'arta ce ta karo ta karaso inda yake tace" Mansir yau kaine a garin namu?" Idanu ya kura mata gani yai ta kara wani kyau jiyai santa na kara ratsashi, ita ta katseshi da cewa "Mu shiga ciki mana." Kai ya girgiza alamar a'a, tad'an had'e rai tace "na d'auka mun zama d'aya?" Sun shiga ya fara kallan tangamemen gidansu, lalai yaya ya cuceshi ya kwacemai Ruma sannan an bashi aiki ga iyayenta masu kud'i sosai?auren da yake fata kenan. Falon baki ta kaishi sannan ta shiga gida ta had'omai abinci da drinks. Fita tai ta barshi yaci abinci kafin nan ta koma,suka sake gaisawa sannan tace" D'an lelen Abbas ya akai?" Mansir yasadda kai kasa tare da d'agowa a marairaice yace "Ruma!" Yanda ya kira sunanta yasa jikinta yai sanyi cikin tsoro tace " Badai wani abun ne ya samu Abbas ba?" Kai Mansir ya jijiga alamar a'a tai ajiyar zuciya sannan tace" Kaine ka tsorata ni Mansir." Ya d'anyi yake sannan yace" Wata magana......" Katseshi ta sakeyi da cewa" kasan Mansir ni in na tashi da kai zanyi kishi?" Cikin rashin fahimta yace name fa? Ta d'an rangwab'a kai tace "yanda yayanka ke sanka mana, shifa babban burinshi shine yaga ya samu aiki ya fara kula da karatunka da kansa sannan yaga duk wani abu da kakeso a duniya ya maka shi." Mansir jikinsa ya d'anyi sanyi,Ruma kam zuciya d'aya ta cigaba da sanar dashi tsarindaya shirya na ganin ci gaban ka,sam baya tunanina da kansa." Mansir yai shiru, Ruma tace " ya akai bai fad'amin zaka zo ba??" Kallanta yai da sauri yace " shima baisan nazo nan ba" "Why?"ta fad'a cikin mamaki. Ya kara gyara murya yace "garin na shigo shine naga bari nazo mu gaisa, dan banaji zamu had'u da bikinku." Bata gamsu ba sai dai da alama bayasanya fad'i gaskiyar abinda ya kawoshi. Murmushi tai sannan ta mai alama da ta tauke bakinta tace " nima bazan fad'amai ba" Yai murmushi jiki a sanyaye ya mike zai tafi, ya kalleta yace "Me kikeso game da Yaya? Tai dariya sannan tace " Mutum ne mai mutunta na gaba dashi, yanada ilimi,ga addini, gashi bashida kyashi." Shiru yai, a zahiri gaskiya ta fad'a, yasan kuma yaya yafishi da komai,ya saki yake yace "Allah ya baku zaman lafiya." Da sauri tace "Amin." Ya fito jiki a sanyaye. yayan Ruma shine ya nemomusu gidan haya anan kano dan sam Abbas yaki yadda akan ya zauna a d'aya daga cikin gidan Mahaifinta ko na yayan nata. Ranar d'aurin aure da sassafe Mansir yabar garin maiduguri ya shiga motar Jigawa. Tunda Abbas ya tashi yaga ba d'an uwansa ya shiga wani yanayi nan ya bazana naimansa sai dai sam ba Labari, ga duk wayoyinsa a kashe. Har lokacin d'aurin aure Abbas bai dawo ba nan shima aka shiga naimansa a tasha aka ganshi duk ya rikice da naiman kaninsa,da kyar aka samu aka mai dashi aka shiryashi aka wuce dashi gun d'aurin aure. An d'aura aure sai dai ko jira baiyi ayi gaishe gaishe ba ya fita,wannan abu yaba iyayen Ruma haushi, a maiduguri aka d'aura auren gidan yayan babanta, dan dama mahaifinta ne kawai a kano da iyalansa. Mansir kam ya isa kila sai dai yayi dana sai,babu inda zai zauna kakaninsu sun rasu, mahaifiyarsa kuma tana aure a wani gidan tare da yaranta. Haka aka wuce da Abbas kano yana cikin tsananin tashin hankali, a ranar aka kai Ruma sai dai ganin halin da yake ciki yasa itama hankalinta ya tashi,Abbas ya sanar da ita akan gobe dole zaije Kila neman kaninsa, ba tantama ta amince. Abbas ya isa kila yaje gidan mahaifiyar Mansir nan aka kirashi, da kyar Abbas ya shawo kansa ya yarda suka taho, wannan ma sai da Mahaifiyarsa tasa baki,ganin in ya zauna a garin ma a ina zai zauna yasa ya amince suka koma,Abbas ya dage yanata tambayarsa akan menene matsalarsa sai dai Mansir yaki fad'amai, kano suka wuce,Abbas ya roki mahaifin Ruma akan subar Mansir ya zauna a b'angaren baki dake gidan,Abbas ya naimomai Buk. Haka rayuwa ta cigaba, sam Mansir baya sh ga harkar yayansa, har ya gama karatu shima yai aure, a lokacin Abbas ya kara samun matsayi saboda kwazonsa. Ruma har Mansir yai aure ko b'atan wata batai ba wannan abu na tsananin damunta, har matar Mansir ta haihu ta haifi namiji aka samai Asim, shekarar Asim 3 Allah ya ba Ruma ciki, farin ciki kamar suyi ka ka,a kuma wannan lokacin ne Abbas ya Fahimci ashe Mansir matarsa yakeso tun yana Js1, hakan ya faro ne sanda yaji Mansir suna hira da abokinshi wanda suke a maiduguri sai dai yana gama aji uku aka kaishi makarantar kwana, tundaga nan suka rabu sai yau suka had'u shine yake tsokanarsa ina Ruma kuwa? Dafatan ya aureta. Hankalin Abbas ya tashi ya tausayama kaninsa wanda yake gani kamar shine sanadiyar durkushewar farin cikin kanin nasa. Daga sanda Ruma ta haihu alheruruka sukai ta faruwa da Abbas, ansama d'anta suna Muhammad Ashraf. Dukiyar Abbas tayi yawa a lokacin da Ashraf yakai shekara 8 yanzu company ne nasa na kansa, sanda ya gina tafkekn gidan wanda zai ishesu rayuwa duk yawan 'yayan da zasu tara shi da kaninsa. Ashraf ya taso mai tsananin san mahaifinsa, sun shaku sosai, alokacin ne kuma Abbas yake yawan zancen had'in aure tsakanin Ashrafda Anisa wacce take shekara biyu." " Abbas ya sanar da Ruma akan lalai ko bayan ransa karta kuskura tabar gidan nan sanda ta taimakeshi ya cika alkawari na ganin gidan nan ya zauna lafiya." Mansir kam yana kishin yayansa ta harkar komai ganin duk abinda yakeso aduniya daga arziki, ilimi,mata da sauransu Allah yabad'aj uwansa ba shi ba." Little tai ajiyar zuciya tare da share kwallarta tace "a lokacin Yaya na shekara 9 ne Mahaifinsa ya rasu,hatsarin mota yai, sannan Mumy na gama Takaba aka d'aura mata aure da Mansir wanda kowa bai san dalilin amincewarta ba. Har Baban Yaya ya rasu bayan an kaishi asibiti zancenshi d'aya ne akan Mansir ya yafemai. Nafi ta share kwallarta cikin tausayi, chakwakiya kenan, ta fad'a a ranta.......... THE INNOCENT TEAM*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *42* Shiru sukai can Nafi tace " Little to ai shi Mahaifin Yaya bai sani ba na tabbata daya sani da bazai ci amanar kaninsa ba." Little ta kalli Nafi tace " A ido Abbana yana nuna komai ya wuce sai dai daga yanda al'amura suke tafiya a gidan nan banaji har a wannan lokacin da Mumy take matarsa ya yafema Abban Ashraf." Cikin mamaki Nafi tace " To ita Mumy me yasa ta aureshi daga gama takaba?" Little ta d'aga kafada tace " Allahu a'alam shiyasa sam haryanzu Yaya bai sako ba." Nafi tai shiru tana tunani, little tace " kuma kinsan ba wanda ya fad'ama yaya mumy ta auri Abba na? Shikuma a lokacin baiyi hankalin da zai kawo komai ba har sai sanda Mumy ta haifeni, lokacin shi kuma hankali ya fara zuwa mai." Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace aikam ba'a kyauta ba, amma meyasa Mumy tai haka?" Little ta girgiza kai alamar bata sani ba." Nafi ta daure tace " To naji ana zancen wasiyya har ga matarsa?" Little ta share kwallarta tace " Feena akwai wani sirrin da Mahaifin Yaya ne kawai ya sani saboda ayanda tarihin yazo shekarar da zai rasu lokacin yaya bai dade da shiga shekara 9 ba Abbas ya canza, shiru zaka ganshi yayi shi kad'ai sannan a wannan lokacin yana yawan zama da lawyernsa wanda yake abokinsa, hatta aiki daina zuwa yai sai dai in Ashraf ya dawo ya sashi a gaba suyi ta hira, in baya nan kuma sai dai kaganshi da diary yana rubutu." Nafi tai shiru, can ta ce " me yake rubutawa?" Little tai d'an dariya kad'an sannan tace " Yaya ne kawai ya sani dan shi yakema rubutun, sai dai ganin yanda Yaya bai tab'a nunama kowa ba sirri ne babba a ciki." Nafi tai shiru mamaki duk ya kamata, a cikin ranta tace " ina mamakin abubuwa guda biyu zuwa uku, na farko me yasa Abbas ya barma Ashraf duk wata kadararsa bayan yana tsananin san kaninsa kamar ransa?q Sannan me nene dalilin yin wasiyyarsa ba rashin lafiya yake ba bare yai tunanin ya kusa rasuwa, me ya sashi yin haka? Sannan abu na uku, wato Mumy. Wata irin ajiyar zuciya taja Little ta dafata tace " me kike tunani?" kai ta girgiza alamar ba komai. Little tai dariya tace " Feenah da alama lawyer zamuyi irin wannan tambayoyi da kikamin d'azu? Nafi tai dariya zatai magana sukaji ana knocking, Kallan juna sukai sannan suka kalli agoggo karfe 9 waye a daren nan? Little ta mike tare da bud'e kofar, d'aya daga cikin mai aikinsu ta gani, yarinyar tace " Wai Nafi tazo inji Umma." Nafi dake tsaye tace " ni kuma? A daren nan?" Yarinyar ta daga mata kai, Nafi ta janyo mayafinta ta kalli Little wacce tai tsuru tsuru tana kallan Nafi, murmushi Nafi ta mata tace " karki damu ba komai." Nafi ta wuce waje. B'angaren Umma ta nufa batasan me yasa ba sam ba tajin tsoron ko zasu mata wani abun. Knocking tai daga ciki akace ta shigo, nan ta tura ta shiga da sallama sai dai ba wanda ya amsa mata. Kallan falon tai, Umma ce a zaune ga Asim da Aneesa a gefenta. Nafi ta karasa ta zauna a kasa tare da gaida Umma, batare da ta amsa ba tace " ke yama sunan ki?" Nafi ta d'ago ta kalleta sannan tai d'an murmushi tace " Feenah!" Dariya Anisa ta saki tace " Mee? feenah? Ha ha ha." Asim ya kalleta yace " ke dan.........Har kin kai matsayin da zaki raina Anisa a gidan nan? Ko dan kinga Ashraf na bin bayanki?" Nafi ta d'an kalleshi ta tuna kalamansa ka d'azu da safe akan a kashe Ashraf, jitai wani irin tsanarsa ta kamata tace " banaji nayi abinda zaisa a kirani a daren nan, sannan Ya Ashraf ne ya kawoni gidan nan duk wanda abun bai mai ba sai ya sanar dashi a sallaman." Asim a zabure ya Mike ransa yai dubu gun b'aci, Umma kam da Anisa mamaki ne ya kamasu. Asim ya matso a zabure ya dage ya kai mata duka, Nafi ko gezau batai ba ta d'ago ta kafe shi da ido, ranshi ya cigaba da azalzala yace "ni kike ma wannan kallan?" Nafi ta ki sauke idanta jitai an kifa mata mari wanda sai da falon ya d'au kara, fulani akwai taurin kai balle Nafi wacce wahala tun tana karama take shanta ganin ko gezau batai ba yasa Asim ya tafi a zuciye ya zaro wayar CD ya taho zai fara zabga mata. Nafi ta mike tsaye tace " Ya Asim me na maka kake shirin duka na?" Ya sake zabura yace " tambaya ta ma kike?" Tace " Kanwarka itace zata gyara rayuwar auranta ni banga me nai ba balle insan dalilin dukan nan." Asim yai wata dariyar takaici yace " Umma dama na fad'a muku yarinyar nan karuwar Ashraf ce inba haka ba har takai matsayin da zata dinga magana haka?" Nafi ta kalleshi cikin wani mugun tsana tace " karuwa?" Asim ya matso yace "me? Ba haka bane?" Idanun Nafi ne suka fara neman kawo kwalla ta d'aga kanta sama tare da maidasu sannan ta kalli Anisa wacce itama Nafi take kallo cikin tsananin kishi, har zatai magana kawai tai waje a zuciye. Anisa ta kalli Umma kamar karamar yarinya zatai magana Umma tace " Ai na fad'a miki ki cire Ashraf a ranki yanzu ai kingani yanzu." Anisa ta kalli Asim, ya karaso gunta ya zauna tare da ce mata sau nawa kikasan ina kamasu tare? Shiyasa kikaga sam banasan Ashraf dalili kuwa shine nasan komai, ai kina kallo dai bata musa ba." Anisa ta fashe da wani irin kukan takaici, lalai Ashraf ita zai ma haka? Asim yace " kada ki kuskura ki nunamai kinsani ki cigaba da nunamai yanda kike sanshi har sai mun samu abinda mukeso." Anisa kam kuka take sosai. Nafi kam tana fita taja can gefe ta takure ita kad'ai ta saki wani kukan takaici, karuwa?? Lalai mutanen nan makiyan Ashraf ne na gaske, shi me ya kaishi auren 'yarsu?? Me yasa duk da yasan basa sanshi suna neman kasheshi amma bai kai kararsu ba ko wani abun? Kuka take sosai taga an dalleta da fitilar mota, a hankali ta d'ago jajjayen idanunta, ganin wacece yasa aka rage hasken fitilar. Nafi ta dan karkata ta kalli motar, motar Ashraf ce hakan yasa jiki a sanyaye ta mike ta karaso jikin motar inda yake. Ashraf ya sauke glass d'in motar. Me kike anan? Ta kalleshi da idanunta tace " Yaya gobe nake tunanin komawa skul saboda inyi karatu kafin a dawo, kasan yanzu S3 zamu shiga." Kallan idanunta yai ba tantama yasa kuka tai yace " Wani abun aka miki?" Kai ta girgiza alamar a'a ya juya kai yace " amma me kike anan? Ba dai jirana kike ba?" Ta d'an bata fuska tace " ni a suwa? Akan me zan jiraka?" Yai ajiyar zuciya yace " good daya kasance ba haka ba." Nafi tad'an juya kai sannan tace " Amma yaya daga ina kake a daren nan?" Yace " Ko Mumy inta ganni na dawo a wannan time din banaji zatamin wannan tambayar." Baki ta d'an turo batace komai ba. Ya kalleta yace " ki wuce ki kwanta gobe kizo da safe muyi maganar makarantar." Ta jinjijina kai alamar to, sannan ta juya. Kallanta ya tsaya yi baisan sanda ya saki murmushi ba can yace " me aka mata? Wata zuciyar tace kasan su ai." Tsaki yaja sannan yai 'yar kwafa. B'angarensa ya nufa yana shiga ya shirya tare da kwanciya ya d'auko diary din Abbansa shafin tsakiya ya bud'e. " Ashraf ban taba tunanin abinda naji da kunena ba har kuma a wannan lokacin ina fatan abinda naji ya zama karya ba gaskiya ba, don't ever trust anyone except ur self." Ajiyar zuciya yai yace " Abba me kaji? Me yasa baka rubuta ba?" Idanu ya lumshe zuciyarsa na zafi, a haka bacci yai gaba dashi....... *Fatan Alkairi gareku Masoyana, Allah ubangiji ya barmu tare (Ameen)* *THE INNOCENT TEAM* [7/10, 7:20 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*        _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd*     ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡   *Wannan shafin sadaukarwace gareki yar uwar arziki Lubbabatu Maitafsir, Allah ubangiji ya kareki daga sharrin mutane, yasa ki gama da duniya lafiya....Ameen suma Ameen*   *43*     Da safe bayan nafi ta tashi daga bacci tai wanka sannan ta fita zuwa kitchen, da kanta ta shiryama Ashraf abinci sannan ta d'auka tai b'angarensa.    Tsayawa tai tana mamakin ganin taje kwankwasawa taga kofar a bud'e, shiga tai tare da sallama sai dai jin shiru ba'a amsa mata ba yasa tai tunanin ko wanka yakeyi.   Shiga tai ta ajiye tiren a kan dinning sannan ta karasa cikin falon da niyyar zama, a kwance ta ganshi akan duguwar kujera yana bacci, ta saki murmushi sannan ta karasa gun.    Tsugunnawa tai a saitin fuskarsa ta kuramai ido bacci yakeyi sosai, a hankali tace "Handsome." sannan ta kalli kirjinsa littafine wanda bangonsa ke da kauri kana gani kasan ba irin littafan yanzu bane, hannu tasa ta d'aga littafin, jitai an rike hannunta.   Da sauri ta kalleshi har a lokacin idanunsa a rufe suke, ta sake littafin tare da neman tashi, jawo ta yai wanda hakan yasa ta fad'a kan kirjinsa, idanu ta shiga kiftawa tana kallansa, idanunsa a rufe yace " ina zaki?"    Kallan mamaki tamai ya akai yasan itace? Ko ya d'auka matarsa ce? Katseta yai da cewa " kin gama kallan nawa? Me kika gano?"   D'agashi tai kad'an sannan tace " yaushe na kalleka?"  Murmushi yai sannan ya bud'e idansa a hankali ta d'auka zaiyi mamakin ganinta sai taji yace " kin tabbatar ba kallona kike ba?"  Kai ta d'aga tare da d'an juya kai, ya d'an had'e rai yace " to amma ya akai nakeji kamar anata kallona?"   Ta kalleshi cikin shagwaba tace " dama ba bacci kake ba?"   Ya sakar mata hannu sannan ya d'auke littafinsa tare da mikewa zaune yace " wayacemiki ba bacci nake ba?"  Ta kalleshi idanunsa kuma sun nuna bacci yakeyi, tace " to ya akai kasan ina kallanka bayan bacci kake??"   Ya sa diary din a gefensa sannan yace " ke zan tambaya." Mamaki ya kamata ta kalleshi sannan ta nuna kanta da yatsa tace " ni kuma?"  Ya juya kai sannan yace " amma da alama in babanki ya ganki yanzu banaji zai yarda kece 'yarsa."  "Why?"ta fad'a tana kallansa, yace " komanki ya canza kinsan me ake nufi da komai?" ya karasa maganar yana neman kare mata kallo, mikewa tai da sauri tace " ni bansan wani komai ba sannan me yasa kabar kofarka a bud'e?"   Yace " baki nake jira sai dai nayi mamaki danaji basuzo ba."   Baki? Da safe?  Kai ya d'aga sannan yace " bakin da ba'a sanin zuwansu bare tafiyarsu."    "B'arayi??" tafad'a cikin tsoro, wani murmushi ya saki sannan yace " just 4get,kikace me jiya?"   Tace " cewa nai zankoma skul yau saboda karatu, na saba bana dawowa gida shiyasa yanzu nakejina daban."   Dinning ya kalla ganin breakfast yasa ya mike ba tare da ya bata amsa ba ya d'au diary djn nan ya shiga d'akinsa, toilet ya fad'a yai wanka sannan yai brush ya fito ya shirya.   Nafi kam haushi duk ya isheta taya za'ai suna magana ya tashi ya barta agun ba tare Da yace mata komai ba, ta d'an harari kofarsa kad'an sanna tace " badai bacci ya koka ba? Wata zuciyar tace zai iya kuwa dan kinsan ya tab'a tsaidake yai bacci, ta dan cije leb'e sannan ta mike da niyyar yin zuciya ta fita, har taje bakin kofa ta tuna so take fa ashe tabar gidan nan, komawa tai a hankali tana tafe tana zumbure zumbure, har ta shiga falon zata zauna sai kuma ta kara kallan kofar ta kalli hotonsu da Anisa ta makama hoton harara sannan ta tab'e baki tace " da alama kai kadai kake santa, dan da tana sanka da bazata yarda da sharrin da akama ba wani ni karu.....Tsaki taja sannan ta kara hararar hoton tace " ko meye ma nasa hoto a falo? Sai kace ba'a sansu ba?"    Ta had'e rai tare da kara hararar kofar tace " san maso wani kaima dai kakeyi kamar ni." tana cikin murg'udawa kofar baki Ashraf ya fito, idanu ta zaro ganin ya ganta yanda ta karkace baki, juya baya tai da sauri tare da rufe bakinta da hannu.   Har ya karaso gunta bata sani ba sai kamshin turarensa kawai da takeji yana ratsata,har wani lumshe ido takeyi, saitin kunnenta ya kai bakinsa yace " badai bayan murgud'a bakinba harda zagi?"  Daidai inda yai maganar ta juyo da fuskarta da sauri cikin tsautsayi bakinta ya tab'a nashi, jikinta ne ya hau rawa da sauri ta matsa ta fara ja da baya ta rufe bakinta da hannu tai waje da gudu.   Shi kansa a kame ta barshi ganin yanda ta fita da gudu baisan sanda ya saki wani murmushi ba, da sauri ya girgiza kai yace " me ke damuna? Rainane ya kamata ya b'aci fa ganin abinda ya faru meyasa nake murmushi???"    Kan dinning ya karasa ya bud'e babbar kular dankali ne na turawa sai dai an sarrafashi da nikaken nama dasu vegetables, kamshi ne kawai ke tashi, murmushi yai sannan ya bud'e d'ayar karamar kular awara ce a ido sai dai dayakai bakinsa sai yaji kamar cuscus, ya sake murmushi sannan ya had'a tea yana cin abinci yana santi, a ransa yace " nasan Nafisa ce tai lalai mijinta ya......." kasa karasa wa yai sakamakon jin dayai maganar tamai banbarakwai.     Nafi kam da gudu ta fad'a d'aki a zaune taga little tana waya da alama da ya Habib ne ganin yanda take wani rage murya, Nafi ta fad'a gado sannan taja bargo ta rufe kanta ruf, tanaj Little na cewa " Yaya to ai kaine jiya ka tafi ba sallama, daga fitarmu."   Nafi kam haryanzu bakinta a rufe yake duk da tana cikin bargo, me ta aikata??idanu ta runtse tace " me yasa ya kawo kanshi nan to?" iho ta d'anyi tare da kara dukunkunewa ganin haka yasa Little tai sallama da Habib ta matso tace " Feena meye hakan?" ta fad'a tana kokarin yaye bargon, Nafi kam ta kara kankame bargon ta daddane,Little tace " feenah meye hakan? Wani abun aka miki?ko su umma ne?"  Nafi kam ba magana sai kara kudun dunewa take hakan yasa Little ta mike tai waje, a falo ta tsaya ta kira Ashraf,  shi kuma a lokacin yayi shiru sai abinci da yakeci yana mamakin meya hanash karasa maganarsa wayar Little ta shigo.  Yana d'agawa tace " yaya inaji fa su Umma sun ma Feenah wani abun kaganta ta dawo ta shige bargo ko magana ta kimin.  " karki damu bari nazo sai inji." tace to amma ni Mumy na kirana, zan bwrdai d'akin a bud'e.  Ya amsa da to.   Sai daya gama cin abinci sannan ya d'au key din mota ya fita, b'angarensu ya nufa, kamar yanda tace kofar kuwa nanan a bud'e hakan yasa ya shiga, tare da sallama.  Nafi tanajin sallamarsa ta kara kudundunewa, Ashraf ya karasa tare da tsayuwa a gefen gadon yace " Malama tashi ko? Ko kin fasa tafiyar?"  Nafi ta kara shigewa, ya d'aga kafad'a yace " bari kawai in fadama little mai kikai inaji hakan zai sa ki tashi."  Gaban Nafi ne ya fad'i batai auni ba taji yace " Little kinsan mai yarinyar nan tamin??????"  Ai batasan sanda tai wani irin mikewa va ta rufe mai baki da hannunta duka biyu ba tana faman girgiza mai kai Alamar kar ya fad'a.   Kallanta yai duk ta sake karfinta akansa, wuyansa har kasa yai ya d'an sa hannu ya fara known karin zare mata nata hannun ita kuma ta kankame bakinsa, juyowa tai da niyyar yima Little magana sai taga ba kowa.   Mamaki ya kamata ta juyo ta kallesh.  Hannu yasa ya zare nata hannun da karfi yace " me? Kunya kikeji?" *THE INNOCENT TEAM*   [7/11, 7:33 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*        _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd*     ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡   *44*    Nafi fuskarta d'auke da mamaki ta ke kallansa, ya kalleta shima yace " What?" murmushi tai sannan tace " dama ka iya tsokana? This is the first time i......"   Katsets yai tare da had'e fuska yace " yaushe kika dawo da kike tunanin komawa?"  Tai murmushi sannan tace " Yaya S3 zamu shiga so nake kafin lokacin waec a karamin lesson sosai." Ashraf bai san sanda yace " ai kina kokari sosai, bakiyi primary ba amma gaski kin iya speaking sannan ko a class result dinki ba mai muni bane." a zahirin gaskiya shi ya d'auka a ransa yake fad'a sai dai gani yai Nafi tayi kasa dakai cikin farin ciki tace " Yaya a koda yaushe tsoro nake kar exam ta fito inga banyi abin arziki ba banaso kayi tunanin rashin amfanin kaini makarantar dakai."    Kallanta yai na wasu 'yan dakiku duk da kanta na kasa sai dai yaji dadin kalamanta, yace " yanzu kin daina san kiga Mahaifinki?"   D'agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko sai dai hawayen basu zuba ba, Ashraf ya sake had'e rai yace " Naga alama haryanzu ke raguwa ce." ya juya zai fita, hannu tasa da sauri ta riko rigarsa, ya tsaya cak sai dai bai juya ba.   A hankali ta fara magana " Yaya ba wai dan kayi zancen Baffa bane yasa kaga nayi haka, kuma yanzu ko ni bazance zanje ba harsai na gama karatuna, sai dai naji dadi ta yadda baka manta da komai ba."   Juyowa yai da niyyar yi mata magana idanunsa suka sauka akan wayar da saurayinta ya bata a gabansa, ji yai ransa ya b'aci ya kurama wayar ido ba tare da ya d'auke idansa ba yace " ki shirya ki sameni a bakin mota."  Yana kai nan ya juya, da sauri itama ta juya dan ganin inda ya kalla, waya ta gani da sauri ta dafa kai cikin takaici ta d'au wayar har tana kokarin jefata cikin drawer sai tace " wait a moment..... Me yasa yaji haushi dan yaga wayar?"   Ferry ce ta fad'o matavda sauri ta kuna wayar ta danna number ferry, sai data kusa katsewa ta d'aga cikin muryar iyayi tace " Hello! "   Nafi tai dariya tace " to uwar jan ra'ayin maza nice."  Muryarta  ta sake sannan tace " Feenah amma kin kwafsa."   Nafi tai murmushi sannan tace " Ferry tambaya zan miki."  Tace "me? Akan yayan naki?"  Nafi ta d'aga kai kamar tana ganinta sannan tace " yanzu yaga wayar da wani ya bani sai naga ya had'e rai sosai, me kenan?"   Ferry tai dariya sannan tace " cikin d'ayan biyu ko ya fara kishinki ko kuma kice kika fasara abun haka."   Nafi cikin masifa tace " Nafassara kamar ya?"   Ferry ta sake dariya sannan tace " saboda kinaso yai kishinki mana yasa kikai tunanin haka."   A zuciye Nafi ta katse wayar ta ja dogon tsaki sannan tace " na fassara? A gabana fa naga ya had'e rai."    Wayarce taji tayi kara tana dubawa taga ansa My Number, Alamin ne tai d'am tsaki ba tare da ta d'auka ba ta mike ta hau shiryawa.    Ashraf kam yana fita yai b'angaren Umma, a zaune ya samesu suna breakfast ya karasa ciki bayan anmai izinin shigowa, Anisa dai kawai cakular abincin takeyi ganin Ashraf yasa ta kuramai ido tanaji kamar taje ta rungumeshi, sai dai abin haushi ko kallanta bataga yayi ba, ya karasa ciki ya kalli Asim wanda ya had'e rai yana zubamai harara.   Kowa a falon ya d'auka biko yazo yi, bayan ya gaida Umma ta amsa sai ta d'ora da cewa " Ashraf yanzu meye amfanin fad'an da kukai bayan kowa yasan yanda kuke san junan ku yanzu ......"   Katseta yai tare da kallan Anisa yace " ina kikasamin takarduna na rannan?"   Kowa yayi mamakin wannan kalaman nasa sannan ran kowa ya b'aci, Ashraf ya cigaba " na kira wayarki a kashe, fad'amin inda suke dan inada abinyi." ya karasa maganar tare da mikewa tsaye, Anisa cikin tsantsan kuluwa da takaici tace " Suna drawer d'akinka."   Bai sake cewa komai ba ya juya ya fita, Asim ya daki kirjinsa da karfi cikin takaici yace " Umma yaron nan zai samin hawan jini in har ba'a kawar dashi daga gabana ba."    Ashraf yana fita har zai wuce sai yai tunanin gaida mumy hakan yasa ya shiga, tana zaune itama kusa da Kawu ta zubamai abinci yana ci ita kuma tana zaune kusa dashi, ransa yakai kololuwar b'aci a duniya ba A binda ya tsana irin ya shigo yaga mahaifiyarsa da kanin babansa a zaune suna soyayya duk sai yaji komai yamai zafi, juyawa yai ba tare da ya musu magana ba yai waje, Little dake gyara falon Mumy ta kalleshi tace " har ka fito?"   Kallanta yai da jajayen idanu wanda hakan ya bata mamaki taga yanzu ya shiga lafiya kalau, yace " karkice mata nazo."   Ya juya ya fita, kallo ta bishi dashi sannan itama ta leka wajen dinning din, yanda ta gansu a kasa suna cikin fara'a gasu daf da juna yasa ta fahimci abinda ya sa yayan nata haka.   Ashraf kam yana fita yai bakin mota, tun daga nesa ya hangota zuciyarshi tai haske duk da bai fito kan fuskarsa ba amma ya rasa dalilin dayasa yaji kashi 60 na bakin cikinsa ya yaye.  Cikin atamfa riga da siket take sun zauna a jikinta kalar atamfar akwai orange hakan yasa ta sa mayafi orange tayi kyau sosai.   Yana karasawa ya bud'e mota ya shiga itama ta shiga, Anisa kam da bayan fitar Ashraf ta d'an tsaya kad'an can ganin zata cuci kanta yasa ta fito da gudu ko d'ankwali babu a kanta tana yin kwanar inda ake ajiye motoci ta hangosu sun shiga mota tare.    Wani irin kishi ne ya lulub'eta ta saki kukan takaici da tsana da take musu duka su biyun, a haka ta koma ta sanar dasu Umma nan  suka samu abinda sukeso sukaita zugata yau kam zugar tayi tasiri dan ta d'au alwashin amso zuciyar mijinta da dukiyarsa sannan ta kora wannan kucakar kauyensu.   Suna shiga mota ya kalleta zaiyi magana ringing ya katsesu, jin ba irin ringing d'insa bane yasa ya kalleta, itama cikin nata salon dan da saninta ta d'auko wayar tanasan tabbatar da abinda zuciyarta ke so, kallansa tai cikin shakka sannan ta kalli wayar, ta canzama Alamin suna daga My Number zuwa My Alamin, ganin sunan daya fito kan wayar yasa ransa ya sake b'aci dama gashi bai gama warewa ba a zuciye ya fizgi motar sukai waje.   Nafi kam bata d'auki wayar ba sai tai kamar irin tsoron Ashraf takeyi,sunyi nisa akan titi ba wanda ya kula wani, Nafi ganin haka yasa ta d'aure tace " yaya baka tsaida magana ba akan tafiya..."  Bata karasa ba taji yace " gobe ki shirya ko driver din mumy ne ya kaiki."   She really feel disappointed ganin yanda ya bata amsa ba wani damuwa ko kulawa, wata zuciyar tace " dan kawai ya sake miki fuska yau kin dauka sanki yake? Stop dreaming Feenah."   Kanta ta juya ta kurama titi ido, a cikim ginin Ado bayaro mall yai parking sannan ya fito, a hankali itama ta fito tare da kallan garin, hadari ne ya fara had'uwa.  Ta juyo ta kalleshi taga yayi gaba, tsayawa tai cak ranta inyayi dubu ya b'aci ta bi bayansa da kallo ba tare da ta je inda yake ba, sai dayai nisa sannan ya juyo mamaki ya kamashi ganin bata taho ba tana tsaye a jikin mota sai idanu da ta kafeshi dashi.   Shima tsayawa yai yana kallanta me takeyi acan?"   Nafi ta juya tare da kifa kanta a saman mota ji take kamar tai kuka ko zataji dadi wannan dizgi har ina? Suzo tare amma ba magana sai kawai yai gaba ya barta, so yake ya nunama kowa bashida hadi da ita ko me?   Jitai ance " in bazaki jeba shiga mota in maidake gida ko ki hau adaidaita ki tafi, kina tunanin banda abinyi ne?"   Ta juyo ta kalleshi yana tsaye ya had'e fuska sosai, d'azu ta tuno sanda ya sakar mata fuska wannan wani irin mutum ne?"   Ran Ashraf ya kara b'aci ganin wayar a hannunta, ta d'aure tace " yaya kasan ban taba zuwa ba amma kana ajiyeni kai gaba kabar ni, ya kakeso inyi?"   Ranshi ya sake b'aci yace " bakida kafa ne ko kuwa jaririya ce ke?"   Nafi ma cikin b'acin rai tace " duk da ni ba d'aya daga cikin abinda ka lissafa bace amma ai nima inasan kulawa, taya zamu taho tare ace kana can gaba ni kuma ina can baya?"  Ashraf ya kalleta zaiyi magana yaji tace " so kake ka nunama kowa bakada alaka dani?na sani kafi karfin ajina balle har ka jera dani sai dai na rasa me yasa nakeji zafin hakan aduk lokacin da kamin, nasan da hakan har kasan zuciya ta to why nakejin zafi?"  Ta fad'a tare da juyawa tana neman maida kwallarta, jikinsa ne yai sanyi sam matsalarshi kenan bayasan yaga ya sa mace kuka, kallanta yai sannan yace " zaki iya tahowa yanzu?"   Kallansa tai sannan ta fara takawa a hankali, Yana gaba kad'an tana binshi a baya, har suka isa cikin shop right  nan ya nuna mata babban cart ita kuma ta jawo suka fara zagawa, ita take nunamai abin bukatar makaranta inta sa d'aya sai ya kara biyu a ciki su zama uku, haka suka sai kaya sosai, ita har tsoro take nawa za ace musu in akazo gun biyan kud'i?   Bai bari taji ba ana fad'an nawa ne yai saurin mika Atm card dinsa nam aka cira sannan akasa wani ya kai musu mota.   Suna fitowa sukaga gari ya turnuke sosai, nan sukai sauri suka shiga mota, ko fita daga mall din basuyi ba aka fara yayyafi, kafin kace me? Ruwa ya tsuge sosai ruwa mai karfin gaske wanda ko gaban mutum baka gani.   Nan Ashraf ya gangara gefen titi yai parking, sunyi shiru sai kallan yanda ruwa yake sauka kawai sukeyi, Nafi batai auni ba taji muryar Ashraf cikin sanyi yace " karki sake cemin nafi karfinki wai ko na tafi saboda bazan iya jera wa dake ba."   Kallansa tai cikin wani irin yanayi mai wuyan fassarawa ya juyo shima ya kalleta, ganin yanda take kallansa yasa yaji wani abu na ratsamai jiki, kansa ya d'auke da sauri, ya had'e rai sosai, Nafi ta matso sannan tace " Yaya ni..."  Wayarta ce ta sake katseta ya juyo ya kalleta tare da kallan wayar, number d'azu ce, ta kalleshi cikin tsoro kafada ya d'aga mata sannan ya mata alama akan ta amsa wayarta.   Jiki a sanyaye Nafi ta d'aga tare da sallama, Alamin yai ajiyar zuciya yace " At last kin d'au wayata."  Nafi idanunta nakan Ashraf tace " sry d'azun ma wani abu nakeyi."  Ashraf kam wayarsa ce a hannunsa yana dannawa sai dai hankalinsa na kan wayar da take.   Alamin ya saki murmushi sannan yace " Feenah plz ki daina jamin rai wlh zuciyata zata iya kamuwa da ciwo in har baki tausaya kin amince da ita ba."   Har yanzu idanta nakan Ashraf sai dai jin kalaman Alamin sun sa ta d'an sassauta murya kamar mai rad'a tace " Alamin ya kake so inyi wai?"   Yace " ki amince dani na zama saurayinki ni kadai."   Tace " bangane ka zama saurayina kai kadai ba??"   Ashraf ne ya juyo ya buga mata wani mugun kallo wanda batasan sanda ta sauke wayar ba daga kunnenta hannubya bata akan ta bashi wayar ba musu kuwa ta mikamai ya sa hannu ya amsa tare da kashe wayar gaba d'aya, mamaki ya kamata a ranta tace ko kishin ne??  Jitai yace " ku mata wani sa'in me yasa bakuda tunani ne?"   Nafi ta zaro ido cikin mamaki tace name fa?   Ya kalli wayar yace " ke kina ganin burgewa ne saurayi yaba budurwa waya ba wata magana mai karfi a kasa?"   Nafi ta turo baki batare da ta amsa ba, yace darajarta take ragewa agunsa alama kuke nunawa na abin hannunsa kuke so.   Nafi cikin takaici tace " ai ba ni nace ya bani ba sannan magana mai karfi ai za'ayita in na gama makaranta."   Dariya taga yayi sannan taji yace " kin manta me nace miki kenan ko? Randa zakizo garin nan."  Kallan mamaki tamai yace " cewa nai sai na yarda da yaron sannan zan baki takardarki."   Kallan sa tai sai dai zuciyarta taji ba dadi haryanzu wato yana tunanin bata takarda ko?????? *THE INNOCENT TEAM* [7/12, 12:06 AM] YAYA HAYAT: *ZUCIYA*        _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd*     ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡   *45*   Ranta yakai koluluwa gun b'aci Ashraf bai tsamani ba kawai yaga ta bud'e motar ta fita, ga ruwa ake sosai, da sauri shima ya bud'e kofa ya fita, tafiya kawai take tsabar ruwa batama san ina take sa kafarta ba, Ashraf ya hanzarta ya riko hannunta.    Kallansa tai sannan ta fizge hannunta da karfe ta nemi ci gaba da tafiya, hannayensa biyu yasa ya rike kafad'arta ya juyo da ita saitinsa yace " Nafisa!!" ya fad'a tare da jijiga mata kafad'a, Nafi ta shiga neman kwace jikinta ganin yanda ruwa ke dukansu gashi da alama taurin kai take nemanyi yasa kawai ya d'agata cak yai mota da ita ahakan ma saj wutsul wutsul take, ya bud'e mota ya sata sannan ya zaga  da sauri ya shiga tare da sama motar lock.   Nafi ta juya kanta gefe, hannunta ya kamo yace " menene wai?kanki d'aya kuwa?"   Ta kalleshi da idanunta da suka ciciko cikin wani irin murya ta kalleshi tare da cewa " yaya ni nace ka aureni?"  Kallan mamaki ya mata, ta share hawayenta duk da tasan abanza dan kuwa hawayen sai ma kara zubowa takeyi, ta kalleshi sannan ta cigaba " Yaya ni bw mutum bace?dutse ce ni ko kuwa?"  Kallanta kawai yake sam ya kasa magana, hawayen da takeyi da kalamanta sune kawai ke ratsa shi, ta kara share wasu kwallan sannan ta cigaba " ka tab'a ganin inda mace a ranar da aka daura mata aure miji yake mata zancen saki? Ka taba tunanin yanda wannan matar zataji duk da yarintar dake damunta a lokacin??"    Ashraf jikinsa ya mutu sosai, Nafi ta sake goge kwallar sannan tace " ka bani takarda ta yanzu inaji shine kawai abinda ya kamata, a gun iyaye da mutanen garinmu ne kawai kake mijina waya san abinda ke tsakanin mu? Ni kaina mantawa nake da auren ka akaina, baka tunanin halin da zan fad'a idan na fara kula wani?ku kuwa ba zunubi na aikata ba in nai hakan?"   Ashraf ya kara rike hannunta yace " Nafisa!"   Hannunta ta kwace ta kalleshi cikin idanunta da suke zubo da kwalla tace " na gode sosai daka taimakeni, ka kula dani ka kuma sani a makaranta sai dai ina ganin lokaci yayi da nima nake bukatar zuciyata ta huta da kokwanton ni matar aurece ko bazawara ko kuwa budurwa?ka bani takardata gobe in koma mahaifata."    Idanu Ashraf ya runtse sannan ya bud'esu a hankali ganin yanda take kuka bai san sanda ya jawota jikinsa ya rungumeta ba, kokarin kwacewa ta shigayi sai dai ya riketa sosai ganin ta kasa kwacewa yasa ta rikeshi itama tare da cigaba da kuka, jikinsu ya jike shakaf.   Kuka take sosai wanda ke taba duk wani lungu da sako na jikinsa, kanta ta kwantar a wuyansa a lokacin da ta fara tsagaitawa da kukan, jin jikinta yai ya fara d'aukan zafi ya daure ya d'agata sannan ya riko hannunta ya shiga hura hannunta da bakinsa yana murzasu, kallansa kawai takeyi tanajin wani irin sabon kaunarsa na ratsata, Why?? Meyasa ita da takesan ta daina sanshi amma takejin haka.    Ya kalleta yace " zazzabi ke neman kamaki, me yasa bazaki min magana ba kika shiga ruwa?"   Ta kifta ido sannan tace " yaya ka tab'a tunanin ya nakeji inkamin zancen saki bayan ban tabbatar da matsayin aurena ba ma? "     Ashraf ya kalli yanda jikinta yai sharaf sannan ya kalli idanunta cikin dan fada fada yace " ina miki zancen jikinki kinamin zancen abinda ba shiba?"    Idanu ta kafeshi dashi, ya kalleta shima, kallan juna suka shigayi dukansu wani abu na ratsasu, Nafi ta daure ta d'auke idanta ta juyar da kanta jikin window, Ashraf ya sa hannu ya rikota tare da jawota kusa dashi.   Idanun Nafi ne suka fifito ya kalleta yace " kalleni.!  A hankali ta d'ago tana kallanshi ta maida kanta kasa, jikinta ne ya mutu ganin ya sa kanta akan kafadarsa yace " ki zauna a haka na yan mintina."    Why? Tafad'a a hankali yai gyaran murya yace " zai taimakawa jikinki dake neman kamuwa da zazzabi."   Tai murmushi batace komai ba, ya sake gyaran murya yace " ba kuma cewa nai kiyi hakan ba da wani."   Tace " me yasa? Naga taimako ne."  Ya harareta yace " ni ai haryanzu akwai aurena akanki." Tad'an tab'e baki tace " auren da ni kaina ban tabatar ba."   Me kikeso ki tabbatar? Idanu ta rufe kamar mai bacci dan batada amsa. Ya kalleta sannan yai murmushi.   Ganin ruwa ya fara d'aukewa yasa ya gyara mata kwanciya zuwa kujerarta duk da yasan ba Bacci take ba, sannan ya tada mota ya jata a hankali.    Nafi kam juyawa tai tana murmushi lalai wannan rana ta shiga cikin tarihin rayuwarta ba wai cewa yai yana santa ba sai dai ta rasa dalilin farincikin nata.   Sun isa gida sannan yai parking yasa hannu a wuyanta yaji dumin kadan ne sannan ya kalleta yace " mai baccin karya ki tashi ki shiga ciki ki dan zuba ruwan zafi a jikinki kisa kaya mai dan nauyi."   Kai ta d'aga ba tare da ya juyo ba, sannan tai sumsum tai waje ya bita da murmushi.  Yasa ankai mata kayanta sannan ya wuce b'angarensa yai wanka shima da ruwan zafi sannan yasa kaya ya kwanta akan gado tare da dora hannunsa akan goshinsa, meke damunshi? Me yasa yake abu kamar ba shi ba, me yasa yake yawan murmushi tare da yin abubuwan da bai saba ba in yana tare da yarinyar nan?    Wata zuciyar tace badai kamuwa kafarayi da santa ba? Kai ya girgiza da sauri yace " No way, how can i...."    Shiru yai yana tuno sanda ta kwanta ajikinsa tana kuka, murmushi ya saki tare da lumshe ido......    Nafi kam haka taitayin komai cikin farin ciki har Little ta ke tambayarta yau meya same ta haka?Nafi kawai sai dai tai dariya..   Washegari litinin da safe Ashraf ya shirya ya tafi gun aiki sabosa sunada Meeting yau ranace babba agunsa don project din da yai kusan wata 6 yana planning yau zaiyi presenting dinsa a gaban directors na company din.   Karfe goma ne presentation din dan haka ya isa gun karfe 9 da kansa ya Shiga gyara gun har 10 tai, mamaki ne ya kashi ganin har 10 da rabi ba kowa a gun sai shi kad'ai nan ya fito ya fara dan zazagawa, wani member na team dinsa ya kira yace " ya dubamai ko ancanza lokaci ne."   Yana nan a tsaye sai ga Mansir ya taho, ya karaso inda Ashraf yake yace " har an fara?"   Ashraf yai kasa dakai cikin rashin jin dadi yace " ba wanda yazo shiyasa nake tunanin ko ancanza time ne."   Kawubya d'an nuna rashin jin dadinsa a fili sannan ya d'aga waya ya kira Secretary dinsa, ko me ya cemai ya kashe tare da kallan Ashraf yace " Ashraf ance project dinka plagiarism ne."  Cikin tsananin mamaki Ashraf yace " Ban gane ba?"   Kawu yace haka aka sanar da directors din ciki kuwa harda members na team dinka sannan project din har anyi lunching dinsa ma a comapny din da muke rivals." yana kai nan yad'an bubuga kafadar Ashraf sannan ya juya ya tafi.    Da kallo Ashraf ya bishi ya saki wani murmushin takaici a ransa yace " ko kuma ka d'auka ka basu ba? Kana tsoron hakan zai sa mutane suyi acknowledging dina."   Ya runtse ido saboda wani takaici da ya kamashi, yai kwafa tare da zubar da takardun yai waje.    Mota ya shiga ransa yakai kululuwar b'aci ya dage ya daki sityarin mota da hannunsa tare da kwantar da kanaa jikin kujera ya saki wani huccin takaici.    Little ce ta kirashi sai data kusa katsewa ya d'aga sai dai muryar Nafi yaji tace " Yaya ina kwana?"  Ya amsa a hankali, tace " driver din yazo zamu tafi gashi bakanan bare muyi sallama."   Yace " da inzaki tafi makarantar sai kinyi sallama dani?"   Mamaki ya kamata tace "Yaya gani nai...."  Katse wayar yai sannan ya kasheta gaba d'aya ya runtse idansa da karfi zuciyarsa na kara tafasa.   Nafi kam mamaki ne ya kamata, cikin takaici ta shirya da taso in sukai waya yace ta bari ba yau ba sai dai yanda ya amsa mata yasa taji batasan zaman gidan ma sam a wannan lokacin, ta kalli Little ta mika mata wayar Alamin sannan tace " ki bashi wayarsa kicemai na koma skul inda rabon mu sake had'uwa to inkuma babu Allah ya hada fuskokinmu a aljanna."   Little ta kalleta fuska a hade tace " wai dan Allah bazaki hakura da tafiyar nan ba?"   Nafi ta girgiza kai cikin takaici tace " karki damu little kwana nawa ne?"  Little ta harareta sannan tace " wani irin sako ne wannan haka kikeso in fad'ama al'amin din?"  Tace "eh, bari naje nama Mumy sallama."   Sunyi sallama da Mumy, sannam ta shiga mota ranta duk ba dadi suka tafi.....   *ILYSM MY FANS* [truncated by WhatsApp]*ZUCIYA*        _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd*     ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡   *46*    Ashraf ya gyara zamansa a cikin mota sannan ya kira lawyer kuma abokin babansa, bayan sun gaisa ne yace " Uncle taimako nake san kamin."  Yace "me kakeso Ashraf kasan saboda kai nake ta d'aga time din retire dina."  Ashraf yai murmushi sannan yace " Nasani Uncle please so nake kaje Slc company kace ina tuhumarsu da satarmin project ka basu takardar shaidar sammaci a kotu."   Lawyer yai murmushi yace " da alama yanzu ka shirya fito na fito da su."  Ashraf yai dan kwafa yace " Uncle a duk sanda sukamin abu kalaman Abba daya rubutamin shi ke fad'omin sai dai inaji ajikina yanzu shima Abban bazaiso in barsu su kara b'ata ba."   Lawyer yai dariya sannan yace " Hakane, dama ance Eye for eye, tooth for tooth."  Sunyi sallama Ashraf ya bud'e mota ya fito, Asim ya gani ya nufoshi yana wata tafiyar kasaita.   Ashraf yaja tsaki yace " The biggest fool is here."   Asim ya karaso cikin isa sannan ya shiga tafama Ashraf, kallansa Ashraf yai yace " kai kuma me ke damunka?"   Asim ya saki dariya sannan yace " Ashraf shi yasa nace maka ka kiyayeni ni ba sa'an yin ka bane."   Kallan sa Ashraf yai yace " kana tunanin kaika aikata hakan?"  Asim ya jinjina kai yace " sosai ma tunda ninasa aka sace project din."  Kai Ashraf ya jijiga alamar tausayawa sannan ya matso yad'an bigi kafadar Asim da hannu yace " u are such a big fool, ka daiyi tunani dakyau amma ninasan kanka bashida wannan basirar, kaidai basirarka d'aya ka turo a kasheni." Yana kai nan ya juya yai gaba.   Asim yabishi da kallo cikin kuluwa yace " me? Yasan Abbanane yasani ko me?"kai ya jijiga alamar a'a sannan yace " ai ba yanda zaiyi ya zargi mijin mahaifiyarsa.   Ashraf kam office ya koma ya cigaba da aikinsa, wanda akasa ya saci takardun a cikin members dinsa sai b'uya yake yi, sam Ashraf bai kulashi ba sai ma wani abu dake mai yawo a zuciya, wato kawu abin tsoro ne na gaske, ya tura d'ansa yayi abu yanzu in asiri ya tuno fa? Lalai mutumin nan wato akan abinda yakeso he can use anyone."  Yaja tsakin takaici inya tuna uwarsa ma amfani yake da ita.   Sai yamma ya tashi nan lawyer ya sanar dashi yace Slc ya sanar musu sai dai sunce a jira director ya shigo gobe dan shine yai proposing din project din.   Gida Ashraf ya wuce, yana shiga yai parking sannan ya kira Little a waya, bayan ta d'aga ne yace " turomin kawarki."  Little tace " wa kenan?"   Ashraf ya had'e fuska yace " wace kawa zance ki turon bayan Nafisa."  Da mamaki tace " naga kunyi sallama d'azu ta tafi ai." Da sauri taji yace " bangane ba? Ina ta tafi?"  Little tace "Skul ba ta kiraka ba?" Katse wayar yai sannan yai wirgi da ita gefen kujera sai a lokacin ya tuno mai sukai, yai hucci sannan yace " waya bata permission?"   Kansa ya shafa sannan ya fito ransa duk a jagule, b'angarensa ya nufa ya bud'e kofa ya shiga, kamshin turaren daya jine yasa ya d'ago dan ganin meke faruwa? Anisa ya gani sanye da wasu 'yan iskan kaya riga ce iya cibiya sai wani mini siket a jikinta tayi kyau sosai sannan kwalliyace ta tada hankalin duk wani namiji indai yanada lafiya, duk da shigar ta daki Ashraf matuka gashi dama ya dade rabonsa da ita dan dama ko da tana gidan haushin abinda takemai yasa yake kin kusantarta.   Idanu ya kankance yace " ke kuma me kikeyi anan?"  Cikin takun jan hankali ta taso ta fara tahowa tana tuno shawarar Umma ki maidashi naki, zuciya da gangan jiki bayan mun gama amfani dashi sai mu munamai yayi kuskuren fifita kucakar yarinyarcan akanki."   Ta karaso tare da zura hannayenta ta wuyansa ta kwanto a jikinsa sannan ta saki ajiyar zuciya tace " Hubby do u know how much i miss u?"  Ashraf ya d'agota sannan yace " me kikeyi anan......."   Bakinta ta saka a nashi nan fa kaji tsit malam....Duk yanda yaso ya daure ya ture Anisa ya kasa dan kuwa in zuciyarsa bataso to fa jikinsa naso.   Nan ya sungumeta sukai d'aki........Ni kuma da jawo musu kofa nai gaba.   Bayan sun gama ne sunyi wanka sannan Ashraf ya had'e fuska tamau, ta matso kusa dashi tare da daura kanta akan kirjinsa Tace " Hubby bazaka yafemin ba?"  Kallanta yai sannan yace " Anisa sam ni na rasa mai ke damunki."  Ta cusa kanta a kirjinsa tare da sakala hannunta ta bayansa tace " tuba nake dear, kaji? Bazan sake ba."   Yai shiru hakan yasa ta cigaba " Bakasan yanda nakeji ba in ina zaune a gun Umma."    D'agota yai zaiyi magana Nafi ta fad'o mai a rai, jiya ya tuno sanda ya rungumeta a jikinsa me yasa bayajin irin wannan yanayin inyana tare da Anisa?   Mikewa yai tsaye ya wuce toilet tabi bayanshi da kallo sannan ta tuno sanda tagansu sun shiga mota da Nafi.   Ashraf kam a toilet ruwa kawai ya sakar ma kansa a ya sa hannunsa ya rike bango ruwa na dukansa a bayansa, idanu ya runtse sai dai abin takaici Nafi ya hango sanda ta shiga cikin ruwa, ya bud'e idanunsa tare da kallan madubin dake toilet din mamakin kansa yakeyi ace kamar shi yazauna yana tunanin wata 'yar karamar yarinya?"   **********    Nafi kam tun bayan isarta makaranta sam ta rage ko magana dan daba ba kawar da zatai hira da ita, karatunta kawai takeyi sai dai a 'yan kwanakin nan har rama tai saboda ko abinci takeci tunanin Ashraf takeyi wannan abun duk ya isheta ta kosa su Ferry su dawo ko dan ta samu damuwar dake damunta ta ragu.   ******    Scl hankalinsu ya tashi jin gaskiyar al'amari agun director cewarsa abokinsa ne ya bashi, wannan dalili yasa suka rubuta takardar hakuri suka aika company din su Ashraf wanda hakan ya sa ma'aikatan company d'in suka tausaya ma Ashraf sannan sukai dana sanin abinda suka aikata a gareshi,  matsayinsa ya d'aukaka dan su cewa sukai a bashi matsayi babba wanda ya dace dashi.  Kawu kam duk yanda kaso kasan bakin cikin dake ransa bazaka taba sani ba a fili yafi kowa farin ciki dan har murna aka dinga tayashi ganin yanda yake ta farin ciki kamar me.    Sai dai Ashraf kam kallansa kawai yakeyi dan yasan sarai yafi kowa bakin ciki.   ********* Sati biyu da komawar Nafi makaranta 'yan skul suka dawo, farin ciki agunta kuwa ba'a magana, nan suka had'u da Ferry da Ferry da Jibiya, sai dai Ferry na ganinta tasan akwai abinda ke damunta.   Da daddare bayan jibiya tayi bacci Ferry ta kalli Nafi tace " Feenah meke damunki?"  Nafi tai yake tace " ba komai."   Ferry tasa hannu ta dafata tace " Nafi akan yayanki ne?"  Hawayen da ta dade tana had'iyewa ne suka zubo, Ferry hankalinta ya tashi tace " Feenah menene?"   Nafi ta goge hawayenta sannan cikin muryar tausayi da radad'in zuci tace " Ferry inaji san Yaya Ashraf shine zai zama ajalina."   Ferry ta kalleta tace " Feena me kike fad'a haka?"   Nafi ta kara share hawayenta tace " Ferry ko bacci nake da tunanin mutum nan nake kwana kullum sai nayi mafarkinsa, rashin ganinsa na hanani komai a rayuwan nan na rasa ina zansa kaina."    Ita kanta jikin Ferry sai dayai sanyi tace " Feenah."  Yanda ta kira sunan Nafi ne yasa Nafi ta tattara hankalinta kanta.  Ferry ta cigaba " Na fahimceki sai dai Feenah inaso ki koyama kanki danne so, kada ki kuskura ki bari shi wanda kikema wannan san ya fahimceki in kuwa kika bari har hakan ta faro? Maganar gaskiya ko shima yana sanki zai dinga wulakanta ki."   Nafi ta kalleta tace ta ya ya? Ferry tai dariya tace karki damu zan koya miki yanda zakiyi ki mamaye zuciyar wannan yayan naki, ba tare da kin wulakanta ba.   Nafi tai murmushi tare da rungume Ferry tace " Ferry shiyasa nake ma Allah godiya dayasa kike a matsayin Aminiyata."   Ferry ta harareta tace " ba wani nan bayan nayi nayi kizo muje gidan mu kinki?"   Nafi tai murmushi tace " nafisan zaman skul."  Ferry tace " Shikenan in kinasan kisan komai na kama saurayi sai kin yadda zaki bimu wannan hutun, Ammi nasan ta ganki kuma kinga daga wannan hutun sai extension."  Nafi tace " I will think about it."   Sukasa dariya dukansu.....    ********   A riga kuwa yayyan Datti suka matsamai sai da sukasa shi ya sake aure, ya auri wata bazawara bafulatana, tanada 'ya'ya uku sai dai yace shi bazai rike ba, ita kadai ya d'auko sannan yamata kashedi sosai akan dabobinsa, ko garken ma ya hanata zuwa saboda bayasan ma tasan yawan dabobinsa, in zai fita kwad'o yake sawa a kofar karken sannan ya kakara itace. Itama sam ta nunamai ba ruwanta da shirginsa hakan yasa yakejin dadin zama da ita...... *#THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *47* Su Nafi manya anyi hutun first term da kyar ta yarda tabi su Ferry gida tai hutu, sunyi waec sunyi neco. Yau sun tashi suna ta shirye shiryen graduation ceremony da za'a musu. Zuwan Little biyu d'aya da Mumy d'aya kuma itada driver tana zuwa kawoma Nafi provision. Sun tashi a gida ita kadai zataso dan Mumy tanada biki, hakan yasa ta kira Habib ta fad'amai da sauri ya amsa akan zaizo dan kuwa shima yana san ganin Nafi. Bayan Habib yazo ne ya karasa gun abokinsa wato Ashraf nan ya sanar dashi inda zasu, shiru Ashraf yai yana tunani tabbas yanajin rashin yarinyar nan har cikin jikinsa, amma zuwansa bazai kawo masa raini ba kuwa??" Habib ya dafashi yace " mutumin mu mun wuce." Da sauri yaji Ashraf yace " Nima zani dan ina ganin bai kamata har ta gama skul banje ba." Habib yai dariya yace " ashe kasan abinda ya dace, na tabbata da Little ce acan da kaje yafi a irga." Ashraf bai amsa mai ba ya tashi ya shiga d'aki, bayan ya shirya ya fito, kallan d'aki Anisa yai wanda ya tabbata bacci take har lokacin aya zari key yai waje. Sun tsaya gun ajiye motoci Ashraf yace "ku tafi da motar ku dan ni tawa tafiyar daban sannan banaji zanyi hour d'aya ma acan. Sun fito suka fara tafiya, Habib na gaba shi yana baya, a hankali yake tuki yana tunanin me zai ce mata in sun had'u? Wata zuciyar tace " Sannu? Congrat? Hi? 'yan Mata? 'yan makaranta?" Kansa ya shafa yace " ke zai sa in fara mata magana? Ita zata gaida ni ai nasan ni kuma sai na amsa." Yai murmushi ganin komai yazo da sauki. Har suka isa yana ta 'yan tunane tunanensa. A makaranta kuwa lokacin har an fara programs, su Nafi anshirya cikin kayan 'yan mata atamfa da siket ansha d'auri zasuyi drama ne itace lead, alokacin dasu Ashraf da habib suka iso, daidai nan an fara gabatar da drama din kenan. Nafi sam bata kula sun iso ba ta zake sosai tana gudanar da scene dinta na star din cikin dramar, kowa ya nutsu yana kallo Nafi sai burge mutane takeyi da turanci ga iya acting, bawai dan tafi kowa bane aka sata a'a sai dan yanayin yarinyar yanayin Nafine. Su Little sai fara'a akeyi, Habib kam kallan Nafi kawai yake yana tsananin mamakin yarinyar da batai primary ba itace take turanci haka?? Shi kuwa gogan ya kafe kaf, shi bawai turancin bane yafi tada mai hankali ba, yanda ta girma ne yafi bashi mamaki, bawai wani kiba tai ba sai dai cikar mace kam Nafi tayishi a wannan lokacin, ta kara gogewa. Sam ya sha'afa cikin tunanin yarinyar jiyai Little na tab'ashi, ya kalleta fuskan nan a d'aure. Little tace " Yaya kaga Feena? Dan Allah bata burgeba?" Ya harareta sannan yace " ina wani abun birgewa ta fito kandar kandar ko mayafi?" Ya fad'a tare da juya kai, Little ta d'an turo baki sannan ta kalli inda Nafi take. An gama drama Nafi tun anayi ta hangosu, aikam ana gamawa ta taho gunsu, little ta rike hannunta cikin tsananin farin cikin ganin junansu, Nafi tace " Little!" Little ta saki murmushi tare da kara rike hannun Nafi tace " Yar Uwa Congrats." Nafi tai murmushi sannan ta kalli Habib tace "Ya Habib." Habib yai murmushi cikin kulawa yace " Princess Congrats tun dazu naketa kallanki sai birgeni kike sake yi." Nafi ta maida kallanta kan Ashraf wanda shima kallanta yake tun da tazo gun, kallan sa kawai tai tace " yaya sannu." tana fada ta maida kallanta kan Little. Kallan mamaki ya bita dashi, is that all? Abinda ya fad'a kenan a ransa Cikin mamaki, yaya sannu? Ya kara kallanta gani yai sam ma hankalinta baya kansa ransa yakai kololuwar baci. Nafi kam hannun Little taja tace " ya Habib muna zuwa." Sukai gaba, kallo Ashraf ya bita dashi. Sukam gun su Ferry suka nufa nan suka cigaba da hira ita kuma Nafi taje ta canza kaya zuwa kayan makaranta tare da sa graduation gown dinta. An gama taro suka fito tare da su Habib jikin wata bishiya suka zauna babbar sallaya irin manyan nan suka shimfida suka zauna, Ashraf da Habib kuma suka zauna a kan wani benci dake gun. Ashraf ya d'au waya yana dannawa sai dai jefi jefi yana kallan Nafi, haushi duk ya isheshi ganin yanda sam ta d'auke kai daga kansa ko gaidashi batai ba balle ma yasa ran zasu danyi magana. Had'e ransa yai tamau ya rike wayarsa kawai yana dannawa, Su Ferry ne suka iso suka. Nafi ta kallesu tace " wannan Yayana ne Ya Habib." ta fada tare da nuna Habib, yai murmushi. Su Ferry suka gaisheshi, ta kalli Ashraf tace " wannan ma yayanane sunanshi Ya Ashraf." tafad'a tare da nuna Ashraf, Ashraf ya sake hade fuska wato shi da Habib duk matsayinsu d'aya take nufi ko me? Yayana? Ya Habib? Ya Ashraf?" Wani mugun kallo ya bita dashi, Nafi kam d'auke kai tai tare da kallan Ferry. Yana kallo suka zauna suna hira sam ma ko kallan inda yake batayi. Ashraf kam ya cika fam ko hira da Habib yake neman jansa dashi ya kasa biyemai. Suna nan a zaune suna hira sai ga wani saurayi nan ya iso kana ganinsa kasan yayan Ferry ne dan suna kama sosai, yana isowa ya kalli Nafi sannan yasa hannu a saitin inda zuciyarsa take yace " Feenah zuciyata za za za......" Yai kamar irin numfashin na neman yankewa, Ferry da Nafi sukai dariya, Nafi tace " Ya Nabil zaka fara ko?" Little ta kallesu tace au wasa yake?" Nabil yai murmushi sannan ya kalli Little yace " Yar uwar mu." Little ta zaro ido dan mamaki, yacigaba " ke yar uwar Feena ce kinga kuwa yar uwa tace." Habib yai dariya yace " Lalai guy din nan kana da abin dariya." Nabil ya cigana da magana yana kallan Little yace " Little in baki taimaken ba kinsa kanwarki ta soni ba inaji zakuzo jana'iza ta." Nafi da Ferry suka sake dariya, Ashraf ransa ya kara b'aci a zuciye ya mike ya karasa gun motarsa ya shiga, kansa ya kwantar akan kujera zuciyarsa duk ta gama kuluwa haka take ma maza dariya?" Kallan gun yai ya d'auka zai ga tana ko kallan inda yake sai dai abin haushi hira suke cikin annashuwa da Nabil. Motarsa ya tada, Nafi ta kalli gun da sauri zuciyarta duk ta fara sanyi anya kuwa wannan hanyar itace? Ferry ce ta mintsineta a cinya wanda hakan yasa ta daina kallan motar sai dai zuciyarta duk ta karaya. Little ce ta kalli Habib tace " Ya Habib ina yaya zaije?" Habib ya girgiza kai sannan yace "wlh bansani ba nima." Ashraf har ya fara tafiya yaga bazai iya jurewa ba a zuciye ya fito inda suke hannu yasa ya fizgo Nafi dake zaune suna barkwanci da Nabil. Nafi ta kalleshi, fuskar sa a had'e yace " mike." A hankali ta mike, yai gaba ta bi bayansa, jikin mota ta tsaya, ya kalleta yace " shiga." Fuska itama ta had'e tace " ina?" Yace " za ki shiga ko na shigar dake da kaina? Kallan mutanen gun tai ta had'e rai sannan ta shiga fuska a hade. Shima ya shiga, glass din motar ya zuge, ya maida kallansa kanta yace " i am a joke?" Ta kalleshi itama tace " me nai kuma?" Me kikai?tambaya ta ma kike? Ta turo baki tace " to ni menai? Ka fad'amin" Ashraf ya kura mata ido cikin takaici yace " kinasan kice min bakisan me kika min ba? Sannan ko kunya ma ki fito gaban maza kadar kadar ko mayafi wai ke a dole kina drama ko?" Nafi bata amsa ba sai baki data turo ya kara cewa " shi kuma wancan waye? Meye hadinki dashi zaki zauna kina washe mai baki?" Nafi ta kalleshi sannan tace " Mun saba dashi ne fa." What?kun saba? Meye shi a gunki?" Nafi ta juya kai tare da yin dan yin kunkuni, yace "me kike cewa?" Kallansa tai tace "jirana akeyi nabar mutane." Zai sake magana yaga ta bud'e kofa kallan mamaki ya bita dashi...... A zuciye yaja motarsa da gudu yai waje, Nafi tabi bayan motar da kallo jikinta duk yai sanyi, idanunta suka ciciko, Ferry ce ta matso ta dafata suka kalli juna sukai murmushi. *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 { *48*} Ganin yanda jikin Nafi yai sanyi yasa Little tace " Me ya ce miki?" Nafi tai murmushi tace " tambaya ta yai kawai yaushe zamu dawo nace wasu yau mukuma sai gobe." Little ta dan tab'e baki tace " akan haka ne naga ya zuciya?ni wlh na d'aukama ko laifi kikai." Habib yai dariya yace " kinsan yayan naki ai Gimbiya." Haka dai sukai ta hira sama sama sannan sukai sallama tare da tafiya da kayan Nafi yanda gobe sai dai ta taho ita kad'ai. ******** Shikam Ashraf har ya isa gida zuciyarsa batai sanyi ba, sai ma kara tunano abinda tamai kawai dayakeyi, sannu yaya? Lalai kalman nan ta bala'in b'atamai rai ya cije leb'e tare da yin kwafa lalai yarinyar shi zata dizga??? Da karfi ya shiga gidan ko mai gadin bai kalla ba ya fito tare da rufe kofar motar da karfi yai bangarensa. A falo yaga Anisa tana ganinsa ta taso da sauri tana neman rungumeshi gocewa yai ya wuceta yai gaba. Kallan takaici ta bishi dashi tana kallo ya shige d'aki tare da rufo kofar da karfi, wanda har sai dayasa tadan razana. Yana shiga ya cire kaya ya wuce toilet, ya dade yana zuba wa kanshi ruwa kafin ya fito. Ya kwanta akan gado tare da daura hannu akan goshinsa, Anisa ce ta shigo cikin kissa ta zauna a gefenashi tace " Dear muje kaci abinci ko?" Juya mata baya yai yace " banasan magana yanzu bacci zanyi." Kallansa tai tace " Amma......" Wani kallo daya mata yasa ta mike tai waje. ****** Nafi ce bayan isha'i zaune a hostel itada Ferry da Jibiya suna cin abinci, sai wasa kawai take da cokalinta sam ta kasa kaiwa bakinta, Ferry ta kalleta tace " banga laifinki ba Feena gaskiya Ashraf ya hadu karshe sannan rashin maganarsa da hade fuskarsa charm dinsa ne." Nafi ta buga mata harara, Ferry tace " sai dai bawai ina nufin haduwarsa da charm dinsa ba ko kudinsa sune zasusa yafi karfinki ba ko ki karaya ba, sai dai......" shiru tai batare da ta karasa ba. Nafi jiki a sanyaye tace sai dai me?? Ferry tace " sai kinyi da gaske dan irinsu ko suna san abu in har ka nuna musu soyayya dayawa to fa zakasha wahala, kinada kyanki ga gashi gaki 'yar chas in har kika bi yanda ya kamata Ashraf bazai miki wuyar samu ba." Nafi ta kalleta sannan ta dan yi murmushin yake tace " Ferry ni fa ba 'yar gidan bace, na dade inaso in sanar da ku hakan." Harararta Ferry tai tace " Nasani ai." Mamaki ne ya bayyana a fuskar Nafi ta kalleta tace " How? When?" Ferry tai dariya tace " kin manta nasan sunanki?sannan sanda muna Junior ai kowa yasan bafulatana ce ke kuma kema dakanki kin fada kince daga karamar hukumar gwaram kike." Nafi tai dariya sannan tace " lalai Ferry." Ferry tace " bansan matsayinki a gidan ba sai dai inaso ko ma meye matsayinki karki bari wannan ya rage miki daraja." Nafi ta kalli jibiya tace "Jibiya lalai ki kiyaye yayan nan taki kwakwalwarta a cike take fam da plan." Sukasa dariya, nan suka shiga hirar bikin jibiya wanda za'ayi bayan sun koma ba da dadewa ba. A ranar dai basuyi bacci ba dan hirar karshe a makaranta. Washegari da safe kuwa suka shirya suka kamo hanya, Ya Nabil ne yazo ya d'aukesu, a hanya ma hira sukai tayi Nabil na kara sasu dariya dan mutum ne mai tsananin barkwanci. Nafi suka fara ajiyewa sannan sukai sallama, ganin gidan yasa Nabil ya kalli Ferry bayan Nafi ta shiga ciki yace " Farida dama a gidan Marigayi Abbas Saleh take?" Ferry tace " ka sanshi ne?" Nabil ya juyo yace " kin manta? Ta kalleshi tace me fa? Ya harareta yace " inda Dad yai aiki da ai company dinsa ne." Ta mai kallan mamaki tace " haba?inda ya ajiye aikin bayan mai company din ya rasu?" Nabil yace "Bingo! Kinsan ai da Secretary din marigayin ya fara daga nan har ya zama Chief Director." Jibiya tace " me yasa dan ya rasu ya ajiye aikin?" Nabil ya girgiza kai alamar bai sani ba sannan yace " kawai dai nasan ya taba cewa mutuwar mutumin akwai conspiracy." Sunyi mamakin jin hakan sai dai agun suka bar maganar sukai gaba. ******* Nafi kam bangaren Mumy ta fara zuwa bayan sun gaisa ta mata murnar gama makaranta sannan tace "taje tai wanka ta kuma ci abinci." Nan Nafi ta mike ta fito tai b'angarensu, Little ba tanan dan dama tasan nazata sameta ba sakamakon jarabawar da sukeyi a makaranta. Wanka tai tana fitowa taga an aiko da abinci inji Mumy, sai data shirya tai sallah sannan taci abinci ta kwanta akan gado, ko minti goma batai ba bacci yai gaba da ita. Ashraf wanda ya kasa samun Little yana shigowa gida yai b'angarensu, knocking yai yaji ba motsi bai kawo komai ba dan baima san Nafi ta dawo ba ya murd'a kofar dakin. Tsayawa yai daga bakin kofa ya kura mata ido, a hankali ya tako zuwa cikin d'akin ya tsaya tare da kallan fuskarta, bacci take sosai ba wani kwalliya tai ba, ya kalli jikinta riga ce doguwa mai ba wai ta bacci bace sai dai ta bi jikinta ga hanun rigar karami ya mata kyau sosai 'yar kanti ce. Kansa ya girgiza yace " me kake kallo?" juyawa yai zai tafi yaga tad'anyi motsi, ya juyo ya kalleta sannan ya juya zai wuce. Hannunsa yaji an rike, juyowa yai tare da hadiyar wani abu, Nafi tace "Yaya?" Ta fad'a cikin muryar bacci, kallanta yai tare da dakewa yace "Yaushe kika dawo?" Ta saki hannunsa sannan tace " d'azu." Kai ya jinjina alamar to sannan ya kara kallanta, ta daure tace "me kake anan?" "Little, little nake nema." Batanan, abinda ta fada kenan ta juya mai baya tare da rufe ido, ya kalleta, is that all? Yauma? Ba ko gaisuwa? Ya dauka ko in ya fqra tafiya zata kulashi amma sai yaji dif, ya juyo yaga har yanzu bata juyo bama, komawa yai rai a b'ace yasa hannu da karfi ya zaunar da ita. Kallansa tai cikin tsoro, tace cikin tsoro mai nai kuma?" Yatsa ya nuna mata yace " ni wanene?" Tace "ban gane ba?" A zuciye yace "waye ni? Just answer nake so." Tace " Ya Ashraf mana." Ya ce "ok good, in har zaki kirani da yaya ban isa ki gaidani ba ko me?" Kallansa tai sannan tadan shagwabe fuska tace "Bacci fa nakeyi ka tasheni." What? Tace " sannan naga kamar baka fiya san gaisuwa ba dan naga da in na gaida kai ba koda yaushe ma kake amsawa ba." Wata irin dariya yai yace "And so?" Tace "nima shiyasa naga in kana cikin mood din amsawa sai inyi gaisuwar." Kallan mamaki ya shiga yi mata, kanta ta d'auke ta juyar dashi gefe, a zuciye yasa hannu sai juyo da fuskarta ita kuma tai saurin gocewa gashi gaba dayanshi dama ya gama sakar jiki, ya kara sa hannu ai kam ta matsa da sauri ta koma can karshen gado. Mamaki ya kamashi yace " ni kike gudun ma?" Ya fad'a tare da hawowa gadon yazo kamata ta tai saurin kwanciya, tare da yin rufda ciki. Babbakewa yai ya juyo da ita da karfi, nan shima kuwa ya fada kan gadon sukai facing din juna, kallan juna suka shiga yi, Nafi ta daure ta d'auke fuskarta, cikin wata irin murya yace "Yaushe kika zama haka?" Ta kalleshi gabanta na fad'uwa tace " Na zama me?" Hannunsa yakai kan bakinta yace " fitsarariya mana." Hannunsa ta ture tace " ni ka tashi ka tafi.........." Bakinta taji cikin nata, gaba daya numfashinta ne ya tsaya, shikansa bai san me yakeyi ba, sai dai ya kasa daina abinda yakeyi. Nafi anyi luf ana karbar sako, sai can ta farga da abinda sukeyi, tureshi tai iya karfinta, Ashraf takaicin kansa ya kamashi, da sauri suka mike zaune. Nafi ta sauka daga kan gadon har yanzu hannunta bai bar rawa ba tace "Yaya me kake yi hakan?" Jitai yace " wannan ita kadai ce hanyar saita bakin da bashida kunya, ki cigaba da min fitsara ni kuma zan koya miki hankali." Da sauri tai hanyar toilet tana 'yan kokoni." Ya bita da kallo, cikin takaicin abinda ya aikata ya mike, shikenan yasan ta gama rainashi yanzu kam, ya gaka jama kansa raini, amma me ya sashi yin hakan? Bayan ko Anisa da suke gida daya tun suna kanana bai taba sha'awar tabata ba har sai da sukai aure???? Itakam a toilet, gaban sink ta tsaya jikinta na bari....... *AISHA ISMA'IL JIBIYA* ( _Allah ya raya mana baby ke kuma ya kara miki lafiya Ameen suma Ameen_) *THE INNOCENT TEAM* *ZUCIYA*        _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd*     ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 {  *49*}     Yau kwananta biyu kenan da dawowa, Little na zaune tana karatun jarabawa ita kuma Nafi tana zaune tana ninke underwears dinsu data wanke, Little ta kalli Nafi tace "Feenah haryanzu bakice komai ba."   Nafi tace "Name kenan?" Hararta Little tai tace "Alamin mana kinsan dai yanda yake neman sanin lokacin da zaki dawo."   Nafi ta ajiye ninkin sannan ta kalli Little tace " Little nifa wlh ko kadan ba san Alamin nake ba, banaso sam na yaudareshi ne shiyasa kikaga ina baya baya dashi."    Little ta maida hankalinta kan Nafi tace "I know that, sai dai in har kikace da haka zakiyi soyayya kina ganin zai yiwu?"  Nafi ta mata kallon alamar tambaya ?   Little ta gyara zama sannan tace "tunda kikazo garin nan wa kika kula? Samari dayawa namin zancen suna sanki sai dai ganin yanda kike dauke fuska yasa kowa yake shakkar miki magana, sai yaushe ne zaki saki zuciyarki ki sami mai sanki saboda Allah?"   Nafi a ranta tace "Little bazaki gane bane." amma a fili sai tace " Little nifa soyayyar ce sam bata gabana."  Hararta Little tai sannan tace "ko dai akwai wanda kike so?"  Da sauri Nafi ta mike, sam bata kula karfen bra ya makale a rigar material din dake jikinta ba."    Kallan Little tai da sauri tai hanyar waje tana cewa "lalai Little na kula yau tambaya mara amsa kike neman yi."   Waje tai da sauri tana fita tai ajiyar zuciya daga nesa ta hango motarshi yayi parking, ta dan kurama motar ido sannan tadan harari gun tace "duk laifinka ne kasa Little na neman tsuyeni."    Tafiya ta fara cikin nata salon, shikuma ya fito daga mota ya tsaya kallanta, tun randa abin nan ya faru bai kara sata a idansa ba, sai dai ji yake kamar yayi wata d'aya bai ganta ba, pride dinsa kuma bazai bari ya nemeta ba da kuma tsoron karta rainashi.   Ganin yanda yake kallanta yasa ta kara canza tafiya tare da dauke kai daga gunsa shikuma ya jingina da jikin mota, murmushi tai a ranta sannan ta cigaba da tafiya, sai datazo kusa dashi sannan ta kalleshi tace " Yaya Ina wuni?"   Bai bata amsa ba sai kallanta da yake ta karaso kusa dashi sosai sannan ta hade rai tace "shi yasa banasan gaisheka sai ka ga dama kake amsawa."  Ganin bashida niyar bata amsa yasa haushi ya isheta ta juya zata karasa kitchen, hannu yasa ya rikota harta giftamai kadan, ya dawo da ita gabansa, ta kara bata rai tace "Hanuna."   Bai saketa ba sai dai ya matso da kansa saitin kunenta jikinsa na taba nata kallansa tai gabanta na faduwa, ganin a waje suke.   Jitai yasa hannunsa ta kugunta, tsoro ya kamata a hankali tace "Yaya me kake yi haka?"  Bai tanka mata ba sai kara matsota dayai, tace "Yaya a waje muke fa me kake yi hakan?"   D'agowa yai sannan ya mika kata bra d'in yace " Bakya kunyar mutane susan size dinki?"   Idanu ta zaro cikin tsananin kunya ta wafta tare da b'oyewa a cikin rigarta, da sauri ta juya ciki, tafe take tana sauri, shikuma sai murmushi yakeyi.     Nafi tana shiga ta jefar da bra din akan gado tare da kwanciya itama da karfi ta hau birgima kamar karamar yarinya, Little ta kalleta tace "Me kuma ya faru?"   Nafi tana juyi tace "shikenan na gama nikuma."   Little tace "menene wai?"   Kai Nafi ta girgiza sannan ta d'an jade rai tace "Little bakiga bra ta makale ajikina ba sanda na fita?"    Little tasa dariya tace "haba? Garin yaya!"   Nafi ta baza tagumi tace "shikenan ni kuma."   Kallanta Little tai tare da guntse dariyarta tace "to menene? Ai ba abin kunya bane, wani ne ya ganki?"   Nafi ta dan harareta tace " ba abin kunya ba kamar ya???" wayyo ni...."   Little tai dariya tace " to menene? Ai kowa yasan kinkai lokacin sawa kuma ansan haka kawai da saninki bazaki fita dashi ba."   Nafi ta kwanta tare da rufe kanta da bargo.   Wayar Little ce tai kara ta daga tare da cewa to yaya.  Tana kashewa ta kalli Nafi tace "Yaya yace ki amso kai lunch dinsa ki kaimai."  Ido Nafi ta zaro tace "ni kuma? Ina matarsa?"  Little tace "inkinje wannan kya tambayeshi."   Gyara kwanciyarta tai little tace "ya?incemai bazaki kai ba."   Nafi tace "kice bacci nake."  Little tace "ba ruwana."  Tafi minti 15 akwance kamar bazata mike ba sannan ta tashi fuska a had'e tai waje, Little ta bita da kallo tare da dariya.    Nafi kitchen ta nufa ta amso mai abincinsa sannan tai hanyar b'angarensa.   Bayan ta kwankwasa ya zo ya bud'e tare da komawa cikin falo, Nafi kam tana shiga ta ajiye mai akan dinning ta juya da niyar fita, jitai ance ke zo nan.   Cak ta tsaya bata kuma je ba haka kuma bata tafi ba, Ashraf dake zaune yana kallo yace "bada ke nake ba?"  Nafi bata amsa ba, yace "Ke Nafisa!"  Juyowa tai tace "na kasa tantancewa ko da ni kake shiyasa na tsaya."    Wani murmushi ya saki yace " da alama mu goma ne a falon."  Ta kalli falon sannan tace "na sani ko matarka na kusa?"  Kallan mamaki ya mata yace "Matartawa ke nake ce mata?"   Fuska ta kara daurewa tamau tace " to nima kuwa ba sunana haka ba."  Ta juya, jitai yace "Nafisa bakiji nace kizo ba?"   Kallansa tai batace komai ba, yace "au yanzun ma da bra din kika fito?"  Da sauri ta shiga duba bayanta ya saki  murmushi, ganin ba komai yasa Nafi ta shagwabe fuska tace "haba yaya?"   Mikewa yai ya karaso gunta sannan yasa hannu ya riko habarta yace " ba na hanaki min fitsara ba? Ko rannan baki daddara bane?"  Tace "yanzun kuma me nai?"  Yace " wlh kin canza gaba daya."   Ta kwace fuskarta tace " ni ba wani canzawa danai."   Hannunta ya kama ya jata zuwa dinning  ya nuna mata kujerar dake kallan tasa yace "zauna."     Kallansa tai tace " inzauna inyi me? In ma abinci ne ni naci nawa."   Dariya taga yayi yace "Ohh abinda kikeso kenan? So kike ince muci abinci tare?"  Ta zaro ido cikin mamaki tace "yaushe nace haka ko kuwa haka ka fassara?"   Ashraf ya zaunar da ita sannan ya koma ya zauna, kallanta yai yace " ki zauna ki jirani naci abinci."    Tace "ni? Akan me?"  Yace "haka kawai."    Wata irin dariya tai tace " wannnan kuma banaji aiki nane." ta fada tana neman mikewa.  Yace zauna.  Kallansa tai fuska a hade, yace " ba dake nake ba?"  Zama tai tare da juya kai gefe, yace " zubamin."  Tace "me fa?"  Da ido ya mata alama da abinci.  Tace "yaya nikam menai ma ne yau?"  Kuramata ido yai yace "bansan ni kaina me nakeyi ba sai dai kawai naga inasan inga kinmin abinda nace."   Labanta tadan ciza sannan taja plate ta fara apkamai abinci sai data kusa cika plate din ya kalleta yace " Me kike hakan?"  Gabansa ta tura mai sannan ta mike ta fara tafiya, mikewa yai da sauri ya fizgota, tare da sata a bango, ta kalleshi idanunta sun fara ja, yace "wai Nafisa meke damunki?"   Ta kalleshi tace " na kasa fahimtar dalilin sani abubuwan nan sai dai yanzu na gane, u take me as a joke."     Idanunta ya kalla zuciyarsa na raya masa wani abun, ya daure yace " joke? Taya zaki fassara shi a haka?"   Hannunsa tadan ture batace komai ba ta juya zatai gaba, bai san sanda ya rungumeta ta baya ba, dif kamar an dauke wutar lantarki haka tai.   Cikin wata irin murya wanda bata taba jinshi da ita ba taji yace " Ni kaina bansan me nakeyi ba."    Shiru tai sai dai jikinta duk ya mutu, yacigaba " shiyasa nakesan ki cigaba da zama inda nake har sai na san me nakeyi tukunna."    Shiru tamai hakan yasa ya juyo da ita yace "Uhmm?"   Kallansa tai sannan tace " in zauna a kusa dakai kamar yaya?"  Ya dan juya  kai yace "kamar yanda na kiraki yanzu."   Hannunsa ta dan zare tace " after that?"  Kallanta yai tace " eh after that, then what?"   Ya shafa kansa yace " ban fara wannan tunanin ba."   Murmushi tai sannan tace " I am sorry."  Kallanta yai yace " for what?"  Tace " bazan iya abin da kace ba, me yasa a koda yaushe zuciyarka ita kadai ce mai amfani agunka? Me yasa baka tunanin tawa?"   Ya kalleta yace " Me kike nufi?"  Kai ta girgiza sannan tace " Ka dinga ajiye matarka akusa dakai ba ni ba, nima daga yanzu zan fitar da wanda naga yana sona inyi aure."   Tana kaiwa nan tai waje, kallo ya bita dashi sannan ya runtse ido ya bud'e tare da naushin iska yace " Ashraf meke damunka? Me yasa duk lokacin da ka shirya abu daidai pride dinka ke hanaka????    Wata iska ya furzar ta takaici.....   Nafi kam tana fita hawayen datake boyewa suka fara zubowa tafiya kawai takeyi sam bata kula da Asim ba wanda suke zaune suna hira. Shikuma yana ganinta ya mike tare da shan gabanta yace "ke yar iska?" Kallansa tai da jajjayen idanunta, yasa dariya yace "au har kwarton naki ya fara b'ata miki rai? Ki dawo guna ni zankula da ke sosai." Hararsa taicikin takaici tace " ni nafi karfin karuwa kuma inma karuwancin ne mai zanyi dakai? Tana kai nan tai gaba, Asim kam ya kai kolowa gun bacin rai, ya juyo da niyar zaginta yaga wayam, hucci yai yace "lalai za'a kai gawar 'ya garinsu...." Nace hmmmm...... *#ASHRAFFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 _Godiya gareku 'yan Nice Hausa Novel musamman hajiya admin Aisha Sabi'u Mohd....ILYSM😍_ { *50*} Nafi kam a falo ta zauna ta dafa kanta itakam Allah ya yaye mata wannan abun dan bata ganin akwai riba a cikin wannan san da takema Ashraf. Kwanciya tai daga nan bacci yai gaba da ita akan kujerar. Sai la'asar ta tashi tana shiga taga Little ma bacci take nan tai sallah sannan ta tasheta itama tai, kitchen ta nufa dan kara samun fasaha akan girki. Sai 6 ta fito tana shiga bayan sunyi magrib aka aiko wai ana sallama da ita, mamaki ya kamata ta tsare Little da ido, Little tace " ba Alamin bane Allah dan shi baima san kin dawo ba." Nafi tace "to waye??" Little tai murmushi tace "ki shirya sai ki dubo mana." Harararta Nafi tai tace "wani shiri kuma? Bansan waye ba kawai sai in hau kwalliya sai kace mai neman saurayi?" Little ta sa dariya tace " to da mecece?ai duk budurwa nema take har sai ta samu tsayaye." Nafi ta tabe baki ta zari mayafi tai gaba Little na tsokanarta. Waje ta fita mota d'aya ce a gun hakan yasa ta tsaya daga dan nesa tana tunanin karasawa, fitowa yai tare da zama a saman motar yace "My Feena ko sai na zo da kaina?" Jin muryar Nabil yasa tai murmushi sannan ta karasa, kallansa tai cikin zolaya tace " da alama rashina ya hanaka sukuni?" Ya dafa kai yace "Feenah taba kiji inaji zazzabi ne ke neman kamani saboda missng dinki." Tai dariya tace "Ya Nabil to ya? Nayi mamakin ganinka a daren nan." Ya kalli agogo yace " ko isha'i batai ba shine dare?" Tai dariya sannan tace "Ina Aminiya?" "Tana gida nima wucewa nazo yi nace bari na tsaya mu gaisa." Murmushi ta sakeyi tace "aikam na gode." Ya kalli gidan yace "dama a gidan Marigayi Abbas kike?" Kallan mamaki tamai tace "kasanshi ne?" Dariya yai yace "ina fa mutumin daya rasu kafin muyi wayau." Tace "then?" Yace " A company dinsa dai Dad yai aiki." Cikin mamaki tace haba? Ya daga mata kai sannan yace "Amma tun bayan rasuwarsa shima ya ajiye aikin." Nafi tace "me yasa?" Iska ya dan tara a bakinsa sannan ya furzar yace "bansan dalili ba." Kallo ta tsareshi dashi tace " Kace wallahi." Yai murmushi yace " me nene matsayinki a gidan?" Ta kalli gidan sannan tace "nima bansani ba ganinan ne dai kawai." Dariya yasa yace "ban gane ba." Tace Wallahi dagaske." Kallan mamaki ya mata yace " kiyi a hankali to da irin wannan gidan manakisa da sharrinsu yawa gareshi, dan mutuwar Abbas din........" Bakinsa ya guntse jin yana shirin yin baran barama, Nafi ta kalleshi fuska dauke da mamaki tace " Me? Akwai sa hannu ko me?" Juyar dakai yai yace " Hmm yaushe zakizo gida?" Tace "Ya Nabil?" Kallan gate yai yace "ga wani can ya fito da mota." Nafi ta kalli gun, motar Ashraf ce idanunta ta kaida kan Nabil tace " Ya Nabil dan Allah me ka sani??" Kifta ido yai yace "bazai miki fada ba?" Hade rai tai tace " akan me kenan?" Zaiyi magana yaga an dallesu da fitilar mota wanda sai da Nafi ta juya, ta tabbata so yake yaga waye, shiyasa tana juyawa ta maida kanta gun Nabil. Ashraf kam wanda suka fito shida Anisa. Ya tsaida mota batare da ya kashe fitilar ba, Anisa ta kalleshi ya had'e rai tare da kafe Nafi da ido, mamaki ya kamata.   Shikam Nabil kallan Nafi yai yace " Feenah da alama ke ake jira kar inja a miki fada bari na tafi."    Da sauri tace a'a yaya taimakamin karka tafi please.  Yace "Ba kya tsoro?"  Kallansa tai fuska dauke da murmushi tace " mu shiga motarka mudanyi gaba please, sannan banaji zan barka ka tafi baka karasa fadar abinda zaka fada dazu ba."   Kallan mamaki ya mata, ta shagwabe fuska tace "please "   Sauka yai sannan ya zagaya ya bud'e mata mota ta shiga sannan shima ya shiga tare da tada mota.   Anisa ta kalli Ashraf tace "wai me mukeyi anan ne?"   Bai ma san tanayi ba dan wani irin abu ne ya tasomai yana ganin sun hau kan titi ai kuwa shima ya taho da gudu da mota ya sha gabansu saura kiris motoci biyun su bigi juna, Nafi kam da Anisa duk sun runtse ido kowa na tsoron abinda zai faru shikanshi Nabil ya tsorata, Ashraf a zuciye ya kashe mota sannan ya fito ko kofa bai rufe ba yazo Kofar da Nafi take ya bud'e da karfinsa.    D'agowa tai cikin tsoro tana kallan idanunsa da suka kada sukai ja sai hucci kawai da yakeyi, hannu yasa ya fizgota da karfi, Anisa ganin haka yasa ta fito tare da shan gabansu tace "Ya Ashraf me kakeyi hakan? Ina zaka bayan kasan unguwa zamu?"   Kallanta yai cikin idanunsa da sukai ja bai bata amsa ba kawai ya zagaya ta gefe ya sa Nafi a bayan motarsa ya shiga ba tare da ya kuma kallan Anisa ba yai reverse sannan ya ja motar a zuciye.   Nabil kam wannan abu ya d'aure mai kai shima a hankali yaja tasa motar yai gaba yabar Anisa wacce ta tsaya kamar gunki.   Ta dade agun kafin ta koma gida, gun Umma ta nufa tai sa'a Asim nanan nan ta zayyane musu abinda akai tare da fashewa da wani irin kuka.   Umma ta mike tsaye tace " Asim dole ne musan abinyi dan nikam na gaji da wulakancin wannan dan marasa tarbiyar."   Asim a zuciye yai waje ya nufi bangaren mahaifinsa......   Shikam Ashraf gudu kawau yakeyi, Nafi kam tayi shiru a baya sai dai har yanzu tsoron abinda Ashraf yai takeyi, gashi sai gudu yakeyi ga dare.   Addu'a kawai take a ranta, can karshen titin Naibawa ya tsaya, wajen fly over sannan yai parking ya fito tare da bud'e kofar Nafi.  Ta kalleshi cikin tsoro. "Fito!" Abinda taji yace kenan, ta danne tsoro sannan tace "in fito inyi me??" "What?" ya fada yana kara kallanta. Ta murguda bakinta tace " Haka kawai ka jawoni ka kawoni nan sannan in fito inyi me?" Kallan mamaki ya mata tai saurin kallan gefe, shiga yai kusa da ita tai saurin matsawa tare da harde hannayenta ta maida kallanta gefe. "Waye waccan d'in?" Tace wa kenan? "tambaya ma kike? Wanda yake neman sa ki a mota ku tafi wani guri a daren nan." Baki ta turo tace "Wani ne." Yace "wani? Bakida hankaline bakisan mutum ba kike neman shga motarsa? In ya lalataki fa?" Dariyar da ta nemi taho mata ta guntse tace " to meye a ciki? Tunda so na yake?" Me? Bakida hankali ne?" ya fada a zuciye, ta kalleshi tace " ni so nake ma in aureshi dan na gaji da zama a inda na sona ake ba." " who said that?" shikansa baisan sanda ya fadi hakan ba. Kallan sa tai fuskarta da alamar tambaya, ya juya kai sannan yace " karki kuskura inkara ganinki da wani namijin balle har ki samu mai dariya ko shiga motarsa." Tace" Akan me?" Yace " Tambaya ma kike? So kike wani abu ya sameki ace nine?" Haushi ya kamata ba haka taso ji ba, ta juya kanta tace " bazan iya rabuwa da shi ba." Hannu yasa ya rike kafadarta da karfi tare da juyo da ita saitinsa, yace " ni kike fadawa haka?" Baki ta turo batace komai ba, kallanta ya tsaya yi, batai auni ba taji bakinta cikin nasa, nan ta fara kokarin kwacewa sai dai ya riketa da kyau tun tana kokarin kwacewa har tai la'asar....Wani sakon ni suke ba juna wanda su kadai suka san ma'a narsa, sun dade sosai a haka sannan a hankali suka saki juna, idanuwansu dake lumshe suka bud'e a hankali. Idanunta suka ciciko cikin sanyin murya tace " Yaya why are u doing this to me?" Jawota yai jikinsa ya rungume ta yace " Nafeesa ni kaina bansan me nakeyi ba." Tace " ba so na kake ba me yasa kakeyin hakan to?" Ya kara kankameta yace " Na rasa me ke damuna, ni kaina abin na damuna." Ta dago da jikinta tace " karka sake tabani har sai ka san abinda ke damunka." Kallan mamaki ya mata yace " Ke halal dina ce bawai haram dina ba." Wani murmushin takaici tai tace " Halal? Since when did i became your halal?" Yace " What?" Ta rufe ido sannan ta bud'e tace " Halal din da ba wanda ya sani? Halal din da ni kaina ban san halal bane? Halal din da kake tsoron kar mutane su sani? Halal din da kai kanka baka tabbatar dashi ba?" Kallanta yai sai dai kalamanta sunsa jikinsa yai sanyi, ta sake murmushin takaici tace " ko ma meke damunka nidai karka kara tabani sai ka tabbatar dashi sannan sai na yarda da hakan." Tana kai nan ta juya kanta tare da share kwallar da ta zubo mata. Jiki a sanyaye ya bud'e motar yai waje ya koma mazauninsa ya zauna a hankali ya tashi motar sukai gaba. Yana kallanta ta madubi jefi jefi tana share hawayenta, ya sani sarai shine silar kukan ta, me yasa yake zama dalilin hawayen ta? Why did he always cause her pain?" Jiyai gaba daya jikinsa yai sanyi jiyake kamar ya jawota jikinsa ya lallasheta, bayaso ko kadan yaga tana kuka dan har zuciyarshi abin ke tabawa....... *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *51*    Asim yana shiga bangaren Mahaifinsa yaga Mumy a zaune suna duba takardu, haushi da kishi ya kamashi ya karasa ciki a zuciye.   Kawu ya kalleshi yace " Asim meye hakan zaka shigo ko sallama?"  Asim ya harari inda Mumy take ya kalli mahaifinsa yace " in kuna tsoron Ashraf ni bana tsoronsa, sannan in ku bazaku iya komai ba akan halayensa ni zan gyara su."   Kawu ya daka mai tsawa yace "Kai wani irin hauka kakeyi hakan? Zakazo ka dinga fadamin zancen banza ko ni din abokin ka ne?"    Asim ya kafe Mumy da ido yace " gashi can dan da kuke ji dashi ya ajiye matarsa a titi ya zari karuwarsa sunyi gaba."   Hankalin Mumy ne ya tashi ta kalleshi tace "Bangane karuwa ba?"   Asim yai wata dariya yace " Au ke kika mahaifiyarsa bama kisa abinda d'anki yakeyi ba? Karuwarsa daya dauko daga wani kauyen nake nufi."   Mikewa Mumy tai tace "Nafi?bangane abinda kake nu......"  Bata karasa ba taji ana zage zage a waje, Asim ya juya yai waje, kawu yai wani murmushi ta gefe sannan ya mike yazo kusa da Mumy ya jawota jikinsa yace "Karki damu munfi kowa sannin Ashraf mun kuma san bazai aikata abinda suke fadaba, Anisa kawai suke tayawa kishi ba komai ba."    Idanu Mumy ta runtse jin zage zagen da akeyi yayi yawa, nan suma suka fita, Umma ce taci damara ita da 'ya 'yanta maza, Anisa na tsaye sai matsar kwalla takeyi.     Fada sosai ne ya kaure a waje banda zagi da cima Ashraf mutunci ba abinda sukeyi, mumy ganin bazata iya daure wa ba yasa tasa baki aikuwa kamar jira Umma take har cewa take zata daki Mumy kuma yau dole ne Ashraf ya saki 'yarta dan bazata yarda da cin mutuncinsa ba, sai dai zancen saki burga ce kawai takeyi dan tasan bazai yiwu ba.      Little wacce hayaniya yasa ta fito tai tsiru tana jin su duk jikinta yai sanyi, bata taba ganin gidansu a haka ba.    Suna tsakiyar zage zage sai ga motar Ashraf ta shigo gidan, nan fa kowa yabi motar da kallo dan ganin abinda sukaji, Ashraf kam tunda ya shigo yake mamakin taruwar ta menene, itakam Nafi kanta na kasa sam bata gansu ba, yana fitowa ya zaga inda Nafi take ya bud'e mata ta fito, kallan takaici tamai.   Zata wuce taji kafarta ta hard'e ta kifo zata fad'i ta gaba, da sauri ya tareta, hannunsa yasa a kugunta d'aya kuma ya rike hannunta.   Sallati suka saka, Umma ta shiga tafa hannu tana sallalami, Mumy ma idanu kawai ta rufe, kawu kuwa ko ajikinsa sai ma farinciki da yake.   Nan Asim ya nufoshi a zuciye, Anisa kam zama tai a kasa ta kara sa wani sabon kukan.   Itakam Nafi kallan Ashraf tai sannan a hankali ta zare jikinta ta kalleshi tace "Thanks."   Bai amsa mata ba sai kallanta kawai da yakeyi, kai ta juyar gefe dan batasan kallan nan, Asim ta gani ya iso gun a zuciye ya dunkule hannu zai naushi Ashraf da sauri ta shiga gaban Ashraf ita naushin ya sameta, iya karfinsa ya sake wanda naushin sai daya sa tai baya.   Ashraf ya razana da sauri ya tarota ya shiga kiranta, su Umma ne dukansu suka karaso gun suka cigaba da sallalami, Umma ta kallesu ya wani rungumota yana kiran sunanta.  Tace "Lalai Ashraf bansan haka kake ba sai yau, to dama mahaifinka ya mutu kafin ka mallaki hankalin kanka, uwarka ta kasa hakura ta zauna tai tarbiyarka saboda bazata iya zama ba namiji ba ta auri kaninsa ta ma manta da danta, dama ina zakai hankali?"   Ashraf ya d'ago ya kallesu dukansu, Mumy ya kalla wacce ke matsar kwalla a gefe, ransa ya kara b'aci ya kalli Nafi wacce bata farfado ba, sannan ya maida dubansa kan Umma yace " kun taremun jikin mota ina bukatar fita dan kaita Asibiti."   Asim ya kara zuciya zai kara kai mai naushi wani kallo da Ashraf ya bugamai yasa ya tsaya, Ashraf ya nunashi da yatsa yace "Don't you dare think of something like this again, dan banaji zan yafema inka kuskura ka kara tunanin abu irin wannan, kasan ni kasan kuma abinda zan iya."    Umma ta kutuntumo Ashar ta maka mai tacigaba " dan marasa tarbiya har mu zaka nunawa bariki? Daga kai har wannan tsinaniyar karuwar taka?jiki duk a kya mushe? Zaka wulakanta matarka ta suna akan wata can karuwa?"    Ashraf ya kallesu, sannan yace " In kun gama zaku iya matsawa? inada gun zuwa na dauka na sanar daku."   Kawu ya matso gunsa yace "Kai Ashraf bakada hankali ne? Akan me zaka dinga neman fita da yarinya bayan ka bar matarka ka dauketa kun tafi wani gun?"   Ashraf ya kalleshi yace " Me kuke san ji daga gareni? Kafin ku tambayeni komai na dauka kowa a nan ya amince da abinda zuciyarsa ta fadamai?"   Kawu ya hade rai yace " Ko ma menene dole ne gobe wannan yar kauyen mara asali ta koma kauyensu saboda yarinya guda d'aya bazai yiwu mu cigaba da samun sab'ani ba."   Little ce ta mikamai ruwa a jarka data d'auko ya amsa sannan ya sa mata, numfashi taja sannan ta mike zaune, sai dai gefen fuskarta har ya tashi, Ashraf ya mike tsaye yace " who said that?"   Kawu ransa ya b'aci yace "nine na fad'i haka kuma nine shugaba a gidan nan dolene ta koma kauyensu goben nan, bazan juri ganin tana neman lalata mana zumunci ba, yarinyar da ko asalinta bamu sani ba."   Nafi kam yanzu ta fahimci da ita ake, jiki a sanyaye ta mike zata wuce, hannu Ashraf yasa ya riko nata hannun, cak ta tsaya sai gabanta kawai da yake fad'uwa, Ashraf ya kalli Kawu yace "Zumunci?wanne kenan? Banaji na sanshi, sannan maganar yarinya babu wanda ya isa ya sata ta tafi dan kuwa nine na kawota nine kuma nakeda hakkin sata ta tafi."   Kallansa tai cikin takaici, tasani bazai iya cewa matarshi bace ita, yana gani yana kuma ji ana ce mata karuwa, hannunta ta fizge sannan ta kalli Kawu tace "Kawu kuyi hakuri zan tafi gobe in Allah ya kaimu."   Tana fada ta juya, hannu yasa ya kara rikota nan ta shiga kokarin kwacewa, Mumy tace "Ashraf wai ke kakeyi hakan? Bazaka saketa ba?"   Murmushi ya sakar musu yace " What should i do?"   Kallansa sukai cikin alamar tambayar, yace " ya zanyi? Tunda Nafisa matata ce wacce na aura kafin Anisa, ya zanyi in ban rike hannun matata ba?"     Gaba d'ayansu cak suka tsaya kamar abu mara motsi Nafi kam kallansa kawai take sai dai tsoro ya cika mata zuciya, a da tana so taji ya fada with full confidence akan ita matarsa ce to meyasa yanzu taji gaba d'aya ba haka ba?"   Ashraf ya kalleta yai murmushi yace "muje ko?"  Hannunta ya ja suka fara tafiya binsa kawai takeyi, sukam kowa ya kame ya kasa motsi, suna matsawa daga gunsu Nafi ta had'iyi wani abu tace "Yaya mai ka aikata?"   Murmushi ya sakar mata yace "what? Are u scared?"   Kallansa tai batace komai ba, har d'aki ya kaita yazaunar da ita tare da kallan inda aka nausheta yace "Me yasa kika taremin d'azu?"   Kanta na kasa tace " nima ban sani ba."  Yai murmushi yace " sanda naga kin taremin naushin da ya kamata ya sauka a jikina lokacin jinai komai ya daukemin a kuma wannan lokacin na gane meke damuna."   Kallansa tai kallo mai alamar tambaya, kiss ya manna mata a kuncinta yace " Feena I think I Luv You."     Kallansa tai gabanta ya tsananta fad'uwa baki ta shiga motsawa tana san tai magana ta kasa, Ashraf ya jawota jikinsa yana daga tsaye ita kuma tana zaune akan gado, yace " Be strong dan nasan akwai yaki babba a gabanmu, sai dai karki damu kowa zai gaji ya bari."   Kai ta jinjina mai, yai murmushi sannan  ya saketa ya fita.    Ko kallan inda suke baiyi ba yai b'angarensa.   Anisa da gudu ta mike tai b'angaren Umma ta shige d'aki ta kulle, maganin Umma ta gani kawai ta debi guda 10, ta hau had'iya, kankace me jiri ya debeta ta fadi kasa ta suma, nan su Umma suka tadda ita a kwance, da gudu Asim ya d'auketa ya sata a mota sukai Asibiti.     Nafi kam tana nan a zaune Little ta shigo da sauri bata mata magana ba kawai ta zari mayafi tai gaba, Nafi ta mike da sauri tace "Little ina zaki a daren nan?"  Little bata tanka mata ba tai waje, jikin Nafi yai sanyi ta zauna a kasa ji take kamar tasa kuka, sallama taji ta mike ta leka, mai gadi ne ya miko mata leda yace " gashi inji yalabai."  Yana bata ya juya ya tafi, bud'ewa tai taga magunguna, dana shafawa dana had'iya.   Ta mike tai sallar isha'i sannan tasha, akan sallayar ta zauna kawai tana addu'oi Allah yasa komai yazo mata da sauki......   Nima nace Amin.....   Su Anisa kam dukansu har Mumy aka nufi asibiti, emergency akai da ita, likitoci suka dukufa akanta, sun dade kafin su gama aikinsu, suka kallesu suka ce " Kuna ina duk yawanku yarinya na neman kashe kanta?    Umma ta harari Mumy tace "Likita masifa ce ta taso mana, bamu fargaba ta shiga d'aki."   Yai dan hucci sannan yace "She is no longer in danger amma sai kun jira zuwa anjima kafin ta farfado."   Yana kaiwa nan yai waje, Umma ta kalli Mumy tace " Lalai danki dan masifa ne, bala'i ne kuma annoba ne."   Mumy cikin takaicin kalaman Umma tace " Malama kisan abinda zaki dinga gada nasan yayi laifi amma ko kadan bai cancanci kalamai irin wannan ba daga bakinki ba, dama kowa na gidan." *#ASHRAFEENAH TEAM* *1LOVE💞**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *52* _Ga masu min korafi akan yin da nake sau d'aya, kuyi hakuri inada uzuri ne, ni kaina inaso inga nayi dayawa dan in kamalla littafin, sai dai ina kara baku hakuri, dan Allah kuyi hakuri da page d'ayan da nakeyi, in har na samu dama nima zan yi sama da page d'aya......Nagode da kauna, Allah yasa ku fahimceni._ *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *52* _Ga masu min korafi akan yin da nake sau d'aya, kuyi hakuri inada uzuri ne, ni kaina inaso inga nayi dayawa dan in kamalla littafin, sai dai ina kara baku hakuri, dan Allah kuyi hakuri da page d'ayan da nakeyi, in har na samu dama nima zan yi sama da page d'aya......Nagode da kauna, Allah yasa ku fahimceni._ Sun dawo gida aka bar Umma kadai acan, Mumy ta kalli agoggon jikin mota karfe 12, lalai dole ta hakura sai zuwa gobe ta samu yin magana da Ashraf in ma wasa yake to lalai kar ya sake mata irin wannan wasan. Shikam Ashraf hankalinsa a kwance yai baccinsa, itakam Nafi akan sallaya tai bacci tana jiran Little. Little ta shigo taga Nafi na bacci, shiru tai ta tsaya tana kallanta har ta kai hannu zata tasheta ta koma kan gado ko me ta tuna? Sai naga ta fasa, kayanta ta cire tai kwanciyarta. Mumy tana shiga b'angarensu taga Kawu a tsaye sai zirga zirga yake, yanzu in har da gaske Nafi matar Ashraf ce kenan ko sun kawar da Ashraf itama tanada gadonsa? Gadan me? Bayan ba wanda yasan da auren iya kaci su karyata hakan. Ya zarfafa a tunani sam baiji sallamar Mumy ba sai jiyai ta dafashi, kallanra yai sannan ya zare hannunta ya koma kan kujera ya zauna tare da daure fuska, Mumy ta karasa gunsa tace " Me ya faru?" Ya kalleta yace " Abinda yaran nan yai yana matukar damuna, nasan Ashraf bai daukeni a matsayin uba ba sai dai ban taba tunanin zai wulakantani haka ba." Mumy tai ajiyar zuciya tace " nikaina abin nan ya tabani, sai dai ina gani ya fadane kawai, gobe zanje in mai magana ai aure ba hauka bane."   Washegari da sasafe su Nafi na bacci sukaji buga kofa kamar za'a b'ala kofar, a razane suka tashi, Little ta bud'e kofar da sauri.    Anisa ce a gefenta kuma Umma ce fuskarnan kamar me? Banko kofar sukai tare da shigowa ciki suka gifta Little tare da wucewa gurin Nafi wacce ta mike zaune sai dai kana ganinta kasan a tsorace take, Anisa ta karaso a zuciye ta d'aga hannu zata kifa ma Nafi mari, da sauri Nafi ta rike hannunta duk da tana tsananin tsoron yanda taga fuskokinsu sai dai bazata yarda da duka ba kuma.    Anisa ta kalleta cikin tsananin kishi tace " ke har kin......." Umma ce tai saurin kifa ma Nafi wani wawan mari ba tare da ta zata ba, Nafi ta sake hannun Anisa tare da rike kuncinta ta kafe Umma da ido, Umma cikin mamaki tace " ni kike ma wannan kallan?"    Nafi ta dauke idanta jitai Anisa ta rufe ta da duka gaba daya hannayenta, Little ta karaso zata tare, Umma ce ta riketa tace "meye naki a ciki? Ke bakya kishin cin mutuncin da akama 'yar uwarki?"   Little ta tsaya jiki a sanyaye, Anisa kam ta dage sai sauken takaicin ta take akan Nafi, can Nafi ta mike ta rike hannun Anisa, tace "Yaya Nisa inaji yanzu kin huce ai ko?"    Anisa tai sototo tana kallanta, Umma tace " mene?"  Nafi wacce taji zafin dukan iya zafi ta daure tace " gani nai dukan ya isa haka inkuma ba kasheni takesan yi ba."   Umma a zuciye ta fizgo wayar charger dake jikin socket tai kan Nafi zata daketa, Nafi ganin ba sarki aikam ta sake hannun Anisa tai hanyar waje da gudu, jitai ta bugi mutum, ta tsaya tare da d'agowa ta kalleshi, Umma kuma wacce suka taho itada Anisa rike da bulala zata daketa itama ta tsaya cak.   Ashraf ya kallesu, yace " me kuke tunani kuke aikatawa?"    Umma ta fara hucci, Anisa kuma kallan yanda Nafi ke tsaye a jikinsa take, Ashraf ya kallesu yace "Umma me kukeyi?"   Umma tace " Kai dan marasa tarbiya,kayi kadan ka wulakantamin 'yata akan wata banza yar daji, kuma wlh kaji na fada maka ko ba yau ba sai na mata dukan da sai an kwantar da ita a asibiti kamar yanda aka kwantar da tawa 'yar."    Murmushi ya sakar mata wanda ya bata tsoro, yace "Umma kenan banaji ranar da zakiyi hakan 'yarki ma zata kwana a gida."   Anisa ta matso cikin takaici tace "Yaya mai kake nufi? In umma ta daketa kana nufin nima dukana zakai ko me?"   Hannu yasa ya shafi gefen fuskar Anisa yace " No no no, kinfi kowa sanin banasan harkar duka sai dai ina nufin a ranar zamana dake ya kare."    Baya baya ta fara ja, tana girgiza kai, wannan ba Ashraf dinta bane, Ashraf ya kalli Umma wacce ta saki baki tana mai kallan mamaki yace " i tried really hard inga na boye abinda ke raina, sai dai naga alamar bakusan wannan ba, dan haka daga yanzu i won't tolerate anyone ko da kuwa Little ce."   Yana kai nan ya kalli Nafi yace " koma ciki ki kwanta zanga wanda zai kara gigin tabaki."   Nafi kam yau ta zama kurma, a hankali ta koma ciki, Umma ta kalleta cikin takaici, Ashraf ya kalli Little yace "kin bani kunya." ya juya zai fita jiyai Anisa tace "Yaya karka fita."   Juyowa yai ya mata wani kallo yace " a matsayinki na wa?"  Tace "ni ai matarka ce."  Murmushi yai sannan ya tako a hankali har inda take ya rungumota jikinsa sannan yakai bakinsa kunnenta yace " mata wace take shan maganin hana daukan ciki? Wacce take binciken dukiyar mijinta? Wacce take jiran mijinta ya rasu ta samu gadon sa?"   Kallan tsoro tamai, ya matso da fuskarta wajen kuncinta yace " why? Kin dauka duk ban sani ba?"    Ya kara mata murmushi sannan ya juya yai gaba, zubewa tai a kasa tama kasa kukan sam, Umma ta matso tace "ke ya ce miki?"   Kai kawai take girgizawa, ganin haka yasa umma ta cicibeta sukai waje.   Little kam da sauri tabi yayanta.   Nafi kam ita kanta a d'aki zaka tai dabas tana mamakin abinda Ashraf yakeyi tun jiya, ita kanta shakkarsa take taya za'ai ya dinga fadar bakar magana hankalinsa a kwance? Bata taba ganinsa a haka ba lalai kenan akwai wani hali nashi da ya boyema 'yan gidan.      Ashraf na fita bangarensa ya nufa, yau kam gidan kamar ba safiya ba kowa ya tashi, a bakin kofarsa yaga Mumy hakan yasa ya gaidata kai tsaye ya bud'e kofarsa ya shiga.  Shigowa tai itama, guri ya samu ya zauna itama ta zauna a kujerar da ke kallansa, Little ce ta shigo ganinsu tare yasa ta koma gun dinning ta zauna.      Sunyi shiru kafin Mumy tace " Ashraf!"  Kallanta yai batare da ya amsa ba.  Tacigaba "me kake nufi da kalamanka na jiya?"  Cikin rashin kulawa yace "me nake nufi kuwa?abinda kikaji shine gaskiya."   Ido ta kuramai can tace " kasan me kake fada kuwa? Kasan me ake nufi da aure?"  Dariya yai ya kalleta yace "Mumy kenan, na dauka ko dan shekara 18 yasan me ake nufi da aure, sannan banyi tunanin zaki damu ba in nayi aure ba tare da saninki be tunda kika sake aure ba tare da sanina ba sannan kika fita daga harkata tun ina karami."   Idanunta ne ya ciciko tace " Nasani i am a bad mother to you, sai dai Ashraf kai kanka kasan ba inda uwa zataki danta."   Idanu ya rufe yace "gashi kuwa na gani? Tunda nake dake kin taba tambayata yaya nake?meke damuna?menene matsalata? Banaji tun mutuwar mahaifina kin kara zama dani zama na uwa da danta."   Mumy tai shiru, sai idannunta da suka ciciko, Ashraf ya dan rufe bakinsa sannan ya dan sa hannu ya shafi kansa yace " inaji a jikina ba san mahaifina dani kike ba."   Yana kai nan ya mike zai shiga ciki, sunansa ta kira "Muhammad!"  Tsayawa yai cak jikinsa yai sanyi, tacigaba " bazaka fahimci dalilina na yin hakan ba, sai dai na sani banida wani uzuri da zan kare kaina tunda komai da nai is due to ky selfishness and greed."   Bai amsa ba ya shige d'akinsa, Mumy tabi bayan dakin da kallo tare da share kwalla.   Shima yana shiga ya zauna a bakin gado tare da rufe fuskarsa da hannayensa biyu.   Mikewa yai tare da yin wanka yasa kaya ya dau jakarsa yai waje ganin lokacin aiki yayi.   Little ya gani a zaune bai kulata ba yai waje, itama kasa binsa tai dan jikinta duk ya mutu.   Ashraf a gun ajiye motoci yaga kawu shima zai fita, da saurinsa ya karasa gun kawun wanda har abin yaba kawu mamaki, Ashraf ya karasa tare da cewa "dama gunka zan fara isa in naje Company."   Kawu ya kalleshi yace "me? Ka bada hakurin laifin daka aikata?"   Ashraf yadan yi dariya yace " laifi? Basan na aikata laifi ba, sannan magana ce ta inasan kai appointing dina a matsayin chief director a company."   Kallan mamaki kawu yamai yace " Ashraf meke damunka?"   Baki yadan motsa yace " meke damuna kuwa? So nake inyi sauri in amshi abinda yake a matsayin nawa, me? Laifi ne yin haka?"   Kawu ya saki baki yana kallan Ashraf, Ashraf yace "sai naga takarda." yana kai nan ya shiga mota yai gaba.    Nafi kam yau wunin daki tai da azahar Mumy ta aiko akan taje, bayan sun gaisa Mumy fuska a hade tace " Nafisa so nake ki fadamin gaskiyar meke faruwa."   Shiru Nafi tai, Mumy tace "ki fadamin ko?"  Nafi ta kalleta tace "mumy kiyi hakuri."   Mumy ta runtse ido tace "kina nufin da gaske ya aureki kenan? Tun kafin kuzo garin nan?"   Kasa Nafi tai dakai, Mumy ranta ya b'aci ta mike tai ciki, Nafi jiki a sanyaye tai waje. ********   Ashraf ya taso daga aiki yana cikin mota a gun traffic light, an tsayar dasu, shikuma yana kan mashin ta saitin gun da Ashraf yake.  Ashraf ya leko kansa ganin mai saida ruwan faro ya amsa tare da mikamai dari biyar, yaron yace bari na nemo cangi, kai Ashraf ya girgiza mai yamai alama da hannu akan yaje kawai.   Yaran ya juya yana murna, shikuma dake kan mashin ya leko dan ganin me wannan abin arzikin.  Kallan mamaki yamai da sauri ya sauka daga kan mashin din ya matso inda Ashraf yake yace " Wazob main ba kai bane Ashaf?"   Ashraf yamai kallan mamaki yace " Kamar nasan......"  Dariya yasa yace " bari nama inkiya ta, Do you went?🤔" *#ASHRAFEENAH TEAM**ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *53* *Wannan shafin naki ne Billy Galadanci*......😍😍😍 Idanu Ashraf ya zaro cikin mamaki ya nunashi yace "Dan Littin Gayu?" Keya d'an Litti ya sosa yace " Ashaf nine dai kam." yai maganar yana washe baki. Dariya sukama juna ganin za'a bada hannu yasa Ashraf yace, shiga muje. Da sauri dan litti ya shige bakin nan yaki rufuwa. Gefen titi suka gangara Ashraf yai parking tare da kallan guy din wanda sai washema Ashraf baki yake, Ashraf yai murmushi yace "Dan Littin Gayu." Dan Litti yai dariya yace "inafa gayu? Gayun daya kusan kaini prison." Ashraf bai san sanda dariya ta kwacemai ba yace " Ah haba? Ni ai bantaba tsammanin ganinka a nan ba." Nan D'an litti ya shiga bashi labarin zuwansu da su Datti da kulleshin da akai, da zamansa a kachako, har zuwa komawarsa kauyensu da abinda Datti yai. Ashraf yai murmushi yace " Gaskiya kasha wahala gun nemana, ko da yake alheri ya zamarma tunda gashi nan ai ka canza." Dan litti yai dariya, Ashraf ya cigaba " Shi kuma wannan mahaifin Nafin....." Sai kuma yai shiru. Dan litti yace " Ai datti ni har yau Allah bai hadani da mutum irinsa ba." Shiru Ashraf yai, tausayin Nafi na kara ratsashi. Ya juyo ya kalli Dan Litti yace " yanzu ina zaka?" Dan Litti yace "mun shigo kano ne dama kawai yawo, nida abokaina." Ashraf yai murmushi yace " Dan Litti kenan, kace yanzu an daina sakar mana turanci." Kansa ya kara sosa wa yace " inafa?inasanyi ina tsoron abinda zai jamin." Sukai dariya a tare, Ashraf yace "ba matsala mu tafi gidan mu." Dadi ya kama Dan Litti shi dama burinsa ya gansa da Ashaf. Nafi kam yau gidan duk ya isheta, ga Little bata kulata ba tai wanka tai tafiyarta makaranta, gashi bata isa ko fita tai ba, yunwa ma takeji amma saboda gudun rigima ta kasa fita. Mikewa tai ta shirya ta duba jakarta taga d'ari biyar ta fito ta hau adaidaita tamai kwatancen gidansu Ferry. Tai sa'a suna nan aikam suna haduwa hira ta barke, anan taci abinci suka cigaba da hirarsu. Duk yanda sukai akan ta fada musu meya sameta a fuska taki fada cewa kawai tai faduwa tai, sai dai su sunsan ba faduwa bace Sai dai ba yanda zasuyi. ********* Ashraf sun isa gida yai parking din motarsa sannan ya kalli Dan litti wanda ya saki baki, hanci, ido duk yana kallab tangamemen gidan dai bai taba gani ba a tsawon rayuwarsa. Ashraf ya sa hannu ya zunguroshi, Dan Litti yai firgigitbya kalleshi. Fito mu shiga ko?" A hankali Ashraf ya fito sai kara kallan gidan yakeyi, Ashraf yai gaba, nan yabi bayansa yana tafe yana kalle kalle. Bangaren Ashraf suka nufa, bayan ya bud'e ya kalli Dan Litti yace 'shiga muje ko?" Kai dan litti ya girgiza yace "a'a kadai fara shiga." Ashraf yai murmushi sannan ya shiga, nan Dan Litti ya dan dosana kafarsa a hankali sannan ya shiga, kallan Ashraf yai yace " Ashaf lalai kana bawa gayu kunya, wannan duk haduwarsu suka ganka ko motarka ko gidanka ai dole su shiga hankalinsu kunya ta kamasu." Ashraf bai san Sanda dariya ta zo mai ba yace " Lalai Dan Litti, kai dai baka rabuwa da shirme, shigo insa a kawo ma abinci." Nan ya zauna a tare da kara kallan falon, Ashraf kuma yai ciki. Dariya kawai dan litti ya shiha yi ba kakautawa wanda yasa Ashraf ya fito da sauri, a kasa yaganshi yana dariya, cikin mamaki yace " ya akai?" Dan litti ba tare da ya daina dariya ba yace "lalai Datti zai ci Kw*******" Ya karasa yana dariya, kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, bayan dan litti ya gama dariyarsa ne idanunsa suka fada kan hoton Ashraf da Anisa, nan yace "KAI! Kai jama'a." da karfi yai maganar wanda yasa Ashraf ya sake fitowa ya kalleshi yace " ya akai?" Dan litti yace " Tab, Ashaf amma wannan matar taka tayi, da alama wannan yarinya mai wanke wanke ta koma, yo dama ina kai ina ita?." Ashraf ya dan daure fuska zaiyi magana yaji Dan litti ya sake cewa " lalai Datti zai suma duk randa ya shigo gidan nan." ya kara kwashewa da dariya. Kai Ashraf ya girgiza sannan ya koma ciki, waya ya daga ya kira Little yace " ki sa Nafisa ta kawo min abinci." Little wacce tun dazu take neman Nafi tace "yaya wlh nima nemanta nakeyi." Cikin rashin fahimta yace "kamar ya kenan?" Tace "wlh na dawo daga makaranta naga batannan." Cikin fada yace "to ija taje?" A tsorace Little tace "wlh bansani ba yaya " Tsaki yaja sannan ya kashe wayar, ya zauna a bakin gado, haushinsa da takaicinsa d'aya da ko waya bai sai mata ba, ya rufe ido cikin takaicin kansa yace " why?" Yanzu tayaya zai soma nemanta?to inama ta sani da zata? Kansa ya dafe cikin takaici. Yana fitowa sai ga Little ta shigo da tire ta kalli dan litti mamaki ya kamata bayan Habib ba wanda yaya yake kawowa bangarensa,ina kuma ya samo wannan?" Ashraf ne ya katseta da cewa " ko wa ya dawo?" Kai ta daga alamar eh, fuskan nan tasa a daure yace " ki buga taro." Ta amsa da to sannan ta fita, kallan Dan Litti yai yace " zo ka ci abinci Gayu." Nan ya kaishi dinning ya turamai tiren gabansa sannan shi ya fita. Tunda ake taro agidan yauce rana ta farko da Ashraf ya fara zuwa gun taron da wuri, zuwa yai ya zauna fuskarsa a murtuke. A hankali kowa ya fara shigowa duk wanda ya shigo sai yayi mamakin zuwan Ashraf da wuri. Bayan kowa ya hallara ne Ashraf ya mike yace " bayan fitata waye ya kira matata Nafisa?" Cikin mamaki kowa ya kalleshi, Kawu yace " dalilin taramun da kai kenan?" Ashraf yadan motsa baki sannan yai murmushi yace " matata bayan fitatavna tabbata wani ya kirata, in kuwa ba'a kirata ba anje har inda take anci zarafinta, dan a yanzu haka bata gidan nan, ban kuma san inda ta shiga ba." Umma tace " to menene namu a ciki? Banaji wannan damuwar mu ce, kila ta tafi yawon karuwancinta ne." Ashraf yq shafa goshinsa yace " menene naku a ciki? Ina tunatarwa ne da in ban ganta ba ni kaina bansan me zan aikata ba." Asim ya mike rai a bace yace " kai! Kayi kadan ka taramu akan wata banzar yarinyar da mu bamu san matsayinta ma a gunka ba, wanda babu shaidar ita matarka ce." Ashraf yadan yi murmuhsin da har hakoransa suka fito yace " Little kiramin bakon nan." Nan ta mike tai waje, Ashraf ya cigaba " wlh in har wani abu ya samu Nafisa bani da guarantee din abinda zan iya aikatawa." Mumy ta kalleshi zatai magana kawu yai saurin cewa "nina kiranta bayan ni kuma banaji akwai wanda ya kirata, inka tashi hukuncin sai kamin, tunda yanzu idanka ya rufe akan karamar yarinya sam baka tunanin kowa." Ashraf ya kalleshi sai dai baiyi magana ba, ya gane Mumy ce ta kirata kenan, tunda yasan ai kawu suna tare gun aiki. Kallan Mumy ya shigayi, ta had'e fuska tace "eh nice na kirata, Ashraf wai meke damunka ne kwana biyi?" Idanunsa ne suka fara canza kala, a hankali ya ke fitar da wani hucci dan kar a gane ransa yakai kololuwa gun tashi. Shigowar Dan Litti ne ya taimakeshi da yayi barna dan tibiren dake gabansa mai dauke da cups na tangaran kawai yake kallo. Dan litti ya tsaya daga nesa cikin tsoro ganin duk an zubomai ido, kuma kallan tsana ake mai. Ashraf ya kalleshi yace " karka damu mutumina gani nan anan." Kallan Ashraf yai sannan hankalinsa yadan kwanta, Ashraf ya kalli Kawu yace "to ga shaida na nan na sanda aka daura auren, banaji daga wannan shaidar kuma kuna bukatar wata." Kawu ya Mike ya kalli Dan Litti yace " daga ina kake?" Dan litti yace " kauyen gwaram." Kawu yace " menene hadinka da Nafisa?" Kauyensu na kusa da tamu." Menene ita kuma tsakaninta da Ashraf? Matarsa ce. Wannan kalma ta rikita kowa, Ashraf yama Dan litti alama akan ya koma. Yana fita Ashraf yace " zan nemo matata da kaina, sai dai bazan yafema wanda ya kuskura ya kara shiga harkarta ba." Yana kai nan yai waje...... _Ina mika ta'aziyata ga Aisha Y. Kura na rashin mahaifinta datai, Allah ubangiji ya jikansa, yasa aljanna ce makomarsa ya kuma kai haske kabarinsa (Ameen)_ *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *ASMY I Sincerely dedicated this page to u may Allah help and guide u through the right path always....(Ameen)......*😍😍😍 {54} Ashraf ya fita daga gun taron rai a b'ace, Dan litti ya kalla wanda ke waje yace " muje inkaika b'angaren baki ka huta ina da gun zuwa." Duk da Dan litti bakinsa tam yake da tambaya ganin yanda Ashraf yai yasa ya kasa tambayarsa, nan Ashraf ya kaishi sannan ya aiko da kaya a kawo mai shi kuma yai waje a mota da gudu. Ta ina zai soma nemanta??? Yayi yawo iya yawo ga magrib ta kawo kai, gaba daya hankalinsa ya gama tashi, ina Nafinsansa? Little ce ta kirashi a waya wanda ita kanta ta kasa zama daidai saboda rashin Nafi, bayan Ashraf ya d'auka yace "ta dawo ne?" yai maganar cikin zumud'i. A hankali tace "a'a yaya." Yai tsaki sannan yace " to meye?" Cikin sanyin jiki tace " yaya ina tunanin gidan kawarta ta tafi." Da sauri yace "kawa?dama tanada wata kawa ne?" Little tace "Ferry wannan kawartata ta makaranta, ai a nan kano suke." Ferry??? Tai saurin cewa kanwar Ya Nabil. Duk da yaji haushin inda akace take dan shi ya dauka saurayinta ne, amma yanzu ganin Nafi shine a gabansa yace "ina ne gidan?" Tace "wlh bansani ba amma bari na turo maka number ferryn." Yace "turon to." Ya kashe wayar tare da dafa sityarin mota yace " lalai Nafisa zan gamu dake." Little ce ta turo number da sauri yai dialing sai data kusa katsewa Ferry ta d'auka cikin salon iyayi tace " HELLO!" Ashraf yace "Farida ce?" Tace "nice, wanene?" "yayan Nafisa ne, tana nan kuwa?" Ta kalli Nafi da suke hira da Ummansu tace "tananan amma...." Da sauri ya katseta yace " a wacce unguwa kuke?" "kabuga ta fada." Nan tamai kwatance ya katse layin, tabi wayar da kallo tare da cewa " kai wannan guy din Feenan sai a slow." Mikewa tai ta koma gunsu Nafi, Nafi kam Umma ta kalla tace " Umma ashe Baba acan yai aiki?" Umma tace " Nabil je ya fada miki ko?" Daya dawo ai yacemin a gidan Marigayi Abbas kike. Nafi tai murmushi tace " ba yar gidan bace bafa." Umma ta kalleta a nutse tace "kiyi a hankali da wannan gidan." Kallan mamaki Nafi ta mata tace "Umma meya sa?" Umma ta girgiza kai sannan tace " nidai abinda zance miki kenan, har yau in na tuno da mutumin nan sai naji zuciyata ta karye." Nafi ta kalleta cikin damuwa tace "Umma wai wani abun ne ya faru da Marigayin?" Shiru Umma tai sannan ta mike tace "bari in je kitchen Babanku ya kusa dawowa." Nafi ta bita da kallo cikin kulawa. Tana fita Ferry ta kalleta tace "tashi kiyi wanka." Nafi tace "ke nifa yanzu zan tafi, duk kece kikasa nai dare haka." Ferry ta jata ta turata toilet, Nafi tai dariya dama batasan komawa, da saninta tai dare dan Umma ta hanata tafiya, wanka tai sannan tai alwalar magrib ta fito, wata had'adiyar doguwar riga taga Ferry ta fito dashi, ta mata kallan tambaya sannan tace "zance zaki ko?" Ferry ta matso tace "Feenah gwada rigarnan, Baba ne ya siyomin dayaje umara to kuma abin haushi tamin kadan." Nafi ta ture hannunta tace "naki na gwada din." Ferry tace "shikenan bari na fada ma umma ta saki ki gwada." jin haka yasa Nafi ta amsa sannan ta gwada. Ta mata daidai, gashi kamar dan ita akai doguwar rigar, light pink ce sai dai daga gaban rigar ta sama anye jere da manyan duwatsu har kusan cikinta, ta mata kyau sosai, rigar tanada mayafinta sai dai mayafin plain ne. Nan Ferry ta sata a gaban madubi tace yi kwalliya. Nafi tace "wai ina zamu?" Ferry tai dariya tace "sirri ne." Kai Nafi ta girgiza sannan ta fara kwalliya, tayi kwalliya sosai, ta kuma yi kyau sosai, nan ta mike tai sallah, tana idarwa wayar Ferry nayin kuka, da sauri Ferry ta d'au wayar tai waje. Nafi ta tabe baki tace "ferry kenan uwar soyayya." Shigowa Ferry tai rike da wani turare a hannunta mai masifar kamshi, sanyin kamshi gareshi, nan tazo ta fesa ma Nafi. Nafi tai dariya tace "lalai to ke yaushe zaki shirya?" Tace kedai ki sauka kuyi sallama da Umma. Nafi tace "Au bari na mike na tafi, amma meye ma sani kwalliya haka?" Ferry tai dariya tace "sauko." Nafi wacce batasan tafiya kuma bazata iya fad'aba ta mike a hankali suka sauko. Umma tama sallama nan umma ta bata ledar dauke da turare da kayan kwalliya. Nafi tai godiya suka sauko. Ashraf yana tsaye a jikin mota sai ga motar mai gidan ta iso, ya tsaya kusa da Ashraf dan ganin waye a kofar gidansa. Ganin ya tsaya yasa Ashraf ya karasa tare da gaidashi, gaban Baba ne ya fadi ganin ko wanene, cikin sanyin murya yace "Me kakeyi anan?" Ashraf yai murmushi zai yi magana yaji Baba wanda ya dauka gunsa yazo yace " Ba Ashraf bane?" Kallan mamaki Ashraf yamai yace "nine...Amma???" Baba yace " me kake anan?" Ashraf ya kalleshi yace "a ina kasan ni amma?" Gaban Baba ne ya fadi ya dauka gunsa yazo ai, cikin dan rawar murya yace "na ganka a magazine ne." Yana kainan ya ja motarsa yai cikin gida. Kallan mamaki Ashraf ya bishi dashi, yanda ya kira sunansa da yanda yamai tambayar bai yi kama da wanda aka gani a magazine ba, kallan gate din gidan yai yana mamaki, fitowar yarinyarce yasa ya katse mai komai. Kallanta kawai yakeyi, tunda ta fito, ganin mutum a tsaye yasa ta tsaya itama, ferry tace "muje mana sanyin ranki ne." Nafi ta kalleta tace "ya akai yasan gidan nan?" Ferry ta nuna kanta da hannu, tace "kina wasa dani ko?" Nafi ta harareta, Ferry ta dafata sannan suka cigaba da tafiya, kallanta yake ya kasa d'auke idanunsa, yaushe na zama haka? Meyasa bana iya jure abinda zuciya ta take fadamin akan wannan yarinyar?" Nafi kam kasa kawai take kallo, har suka karaso kusa da gun, Nafi ta tsaya itama a hankali ta d'ago ta kalleshi, idanunsa na kanta tad'an shagwab'e fuska. Ferry ce ta katsesu dayin gyaran murya tace "yaya ni zan koma." Ashraf ya kalleta yace "Farida nagode kwarai amma dole na bada tukuici." Dariya tai tace " ba wani tukuici yaya indai ka kula damu to komai ya biya." Hannu yasa a aljihu, yaji ba komai, ba dai bai d'auko wallet dinsa ba?" Farida ya kalla wacce take mai dariya, Nafi ma dariyar ta guntse, Ashraf yace "karki damu zan kawo tukuicin daga baya." Tace "ba komai yaya." Nan ta dafa Nafi ta rada mata a kunne, "ki tabbatar kin gama kwace zuciyarshi a yau din nan." Tana kaiwa nan ta juya ta tafi, kallan Nafi yai yace "muje ko?" Tad'an turo baki sannan ta karasa ta shiga ta zauna, ya shiga tare da maida kallansa kanta yace " bansan ina fadan da zan miki ya tafi ba." Ta kalleshi fuska a shagwab'e tace " me nai da za'amin fada?" Kasa jurewa yai ya jawota ya rungumeta, a hankali yace mata " Nafeesa ni kaina ina mamakin kaina." Itama a hankali tace "Name fa?" Yace "nakasa controlling din kaina a kanki, ni na san ba haka nake ba, ban kuma san ya akai na koma hakan ba." Idanu ta lumshe sannan tace " nifa ba yau naso komawa ba." D'agota yai yace " kinsan zunubin dake kan matar data fita ba sanin mijinta kuwa?" Kallansa tai tace " ni kam ban saba da zancen miji ba." Ya matso da bakinsa kuncinta yace " ya? Ko kinaso in tabbatar miki ne a yau d'in nan?" Idanu ta zaro da sauri tace " a'a bance ba." Yai murmushi sannan ya tada mota, hannunta ya kamo ya rike d'ayan kuna yana tuki dashi, kamshin turarensa ne ya hadu da nashi sai ya bada wani sansanyan dadi, ga Ac din daya kunna, Nafi kam har wani lumshe ido takeyi, a zuciyarta tace "Allah ka d'auki raina a lokacin da nake irin wannan farin cikin." Har suka isa gida hannunsu na cikin juna yai parking sannan ya kalleta yace " b'angarena zamuje." Idanu ta zaro tace "muyi me?" Hannu yasa ya ja kumatunta kadan yace "uwar tsoro abu kawai zan baki." Tai murmushi batace komai ba. Ya fito sannan ta fito shima, yana gaba tana binsa har suka isa b'angarensa yace "ta zauna, sannan shi kuma ya shiga d'aki." Kayan jikinsa ya cire ya saka doguwar jalabiya. Itakam hotonsu wanda sukai da Anisa kawai take kallo, baki ta tabe, sam bataji zuwansa ba sai ganinsa tai ya zauna kusa da ita. Kallansa tai ta saki murmushi, shima maida mata yai sannan ya nuna mata cinyarsa yace "kwanta." Kallan tsoro tamai, ya kafeta da ido, a hankali ta kwanta a cinyarsa tare da lumshe idanta, ya zame d'an kwalin kanta sannan ya fara shafar kanta a hankali, idanunta a lumshe suke sai dai Allah ne kadai yasan me takeji a wannan lokacin. Ashraf fuskarta yake kallo yace " gobe zamuje musai waya, daga yanzu karki sake fita ba sanina, kinji?" Kai ta d'agamai fuskarta d'auke da murmushi. Idanu ta bud'e a hankali tace " na d'agama hankali da baka gan ni ba?" "Hmm, ban taba zatan zanji haka ba." Tai murmushi tace " I can't help dole ne in sake guduwa wani gun." Harararta yai ya had'e rai yace " in kika sake gwadawa zakiga b'acin raina da baki taba gani ba kuwa." Ta turo baki tace " sai in sake shirya yanda bazaka iya min fada ba." Hararata yai yace " ahh i am dead, abinda banaso ya afko a kaina." Tace "mekenan?" Yai furzar da iska yace "bazan iya fada ba." Murmushi tai sannan ta kara lumshe ido, ji take lalai in abu ya rabasu da Ashraf lalai to kuwa ba tantama mutuwa zatai sai dai wani iko na Allah. A hankali yakai bakinsa ya sumbashi goshinta, ta bud'e ido a hankali suka kura ma juna ido, idansa ne taga ya d'an canza kala, batasan ya akai ba taji tsoro karfa su wuce gona da iri, su biyi a bangare. Da sauri tace " Yaya." A hankali yace "Uhmm." Tace "Abba hatsarin mota yai ko?" Kallanta yai yace "eh." Tace "kaima hatsari kai harkaje garin mu ko?" Yace eh. Tace " Motar Abba alokacin an duba meya jawo hatsarin?" Kallan ta yai gaba d'aya hankalinsa na kanta, idanunsa taga ya kada sosai, ta mike zaune, tace" yahkuri in na ba....." Jawota yai ya rungumeta tsam a jikinsa, yace " me kike tunani?" Kai ta girgiza alamar ba komai. Ya dago ya kalleta hannayensa na kan kafadarta, yace " Nasani Nafisa sai dai banasan ki cigaba da binciken abinda bai shafeki ba." Hawaye ne ya zubo mata na tsananin tausayin Ashraf, idanunta na kansa tace " Na dauka duk abinda ya shafeka ya shafeni?" Hannu yakai a hankali ya share mata hawayenta yace " ba haka nake nufi ba....." Tacigaba da zubar da hawaye tace " Y are u enduring everything by ur self? Can't u share it with me?" Kallanta kawai yakeyi, tacigaba da cewa " kwanaki kasheka ya Asim yaso yi, amma ba wanda ka fadama, abubuwa nawa ka sani wanda baka fadama kowa ba? Kana tunanin in kabar mutanen da sukeyin evil deeds saboda 'yan uwane kana tunanin zasu daina?" Yauce rana ta farko dayakeji har cikin jinin jikinsa lalai yarinyar nan ta damu dashi lalai tana sanshi saboda Allah, lalai zata iya komai domin shi. Jawota yai a hankali yakai bakinsa cikin nata... Wata duniyar suka shiga kiss suke deeply wanda gaba d'ayansu wani feelings sukeji wanda su kadai ne sukasan abinda sukeji tundaga kansu har kafafuwansu......... Ni dai nace to fa ayi a hankali kar a gangara🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣. *#ASHRAFEENAH* 💞*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Someone!!!* *Somewhere!!!* *Is Made For U* {55} Sun yi nisa sosai, Ashraf ya saketa a hankali, da sauri ya shiga d'akinsa, itakam kafafunta ta had'e dan jitai har su rawa suke, tun da take bata taba jin abinda taji yau ba, wani irin feeling ne wannan???" Ashraf kam kwanciya yai rufda ciki akan gado, wata muguwar sha'awa ce take tasomai sai dai bazai taba kusantarta ba har sai ta aminta dashi a matsayin miji, juyi ya shiga yi. Nafi kam ta dade itama a zaune kafin tabi kofar d'akinsa da kallo, ya kamata ta tafi kafin dari yayi sosai, a hankali ta mike tai d'akin. Sallama tai jin shiru yasa ta murd'a kofar d'akin, Ashraf najin haka yai saurin rufe idanunsa, kallansa tai a hankali ta tako tazo inda yake. Zama tai a gefensa takai hannu kan sumar kansa, ta kurama fuskarsa ido, a hankali tace "bacci?" Jin shiru yasa tad'an turo baki tace "shine ka barni a zaune kai ka taho ka kwanta?" Shiru tai tare da cigaba da kallansa a hankali takwantar da kanta saitin fuskarsa suka zama fuskokinsu na fuskantar juna, ta sa hannu a kan kuncinsa sannan tace " please let me be the first person whom you can trust." Murmushi tai sannan ta kai bakinta a hankali kan leb'ensa ta sumbata, sannan tace "Goodnight." Ta mike tare da jamai bargo tai waje, b'angarensu ta nufa a zaune taga little a falo ta matso da sauri zata mata magana taga Little ta mike tayi ciki, Nafi tabi bayanta. Toilet ta wuce direct dan da alama tanajin jikinta ba yanda yake ba, a gun tsarki ta gano lalai abinda ya zubo na sha'awa ne, nan ta wanke wandon ta ta gyara jikinta tasa wani sannan ta fito. A kwance taga Little ta kalleta tace "Little yanzu haka zamuyi ta zama bakya kulani?" Little bata tanka taba, Nafi tace " ban taba tunanin zaki iya kin kulani ba saboda kinji ance ni yar kauye matar yayanki bace, ni kaina nasan ban kai wannan matsayin ba, sai dai........" Little ce ta katseta da cewa " kin dauka saboda matsayinki a gun yaya nake miki haka?" Nafi ta kalleta tace "to menene in ba shiba?" Little ta mike zaune tace " shekararmu nawa tare?nikenan da miki zancen saurayi akan ki kula wane ki kula wane, bansani ba ashe mahaukaciya kika mai dani." Nafi cikin mamaki tace "mahaukaciya kuma?" Cikin zafi Little tace "mahaukaciya mana, inba haka ba da igiyar auran yayana a gunki amma nake neman had'aki da wani?" Nafi ta matso tare da rike hannun Little tace "Little kiyi hakuri wlh ni kaina mantawa nake akwai abu a tsakanin mu." Nan dai Nafi tai ta bata baki har ta hakura, sun dan yi hira kadan kafin Nafi ta kalli Little tace " nikam Little wani abu na damuna." Kallan mamaki Little ta mata tace name kenan?" Nafi tai shiru can tace " Abban Ashraf na ga shine ya fara zancen had'in auren Yaya da Ya Nisa, to menene dalilinsa na ajiye wasiya yace a ba matar Ashraf ta farko bayan yasan ko ince Yaya Nisa yakesan ya fara aura?" Shiru Little tai can ta girgiza kai tace "ban sani ba, ni banma taba kawo abin a raina ba, amma kina ganin da wani abun ne?" Kai Nafi ta girgiza tace "ba komai, bari nai sallah." Ta mike tana tunani tabbas da wani abun, sai dai menene????? ************* A b'angaren Ashraf kuwa tana fita yabi bayanta da kallo yanaji kamar ya jawota ya rungumeta sai dai ina bazai iya hakan ba, bayan yayi sallah ya d'aga katifarsa ya d'auko wani karamin makulli sannan ya zugi wardrobe dinsa ya ture kayan, nan wata yar karamar kofa ta bayana, nan yasa makuli ya bud'e ya zaro wasu takardu a ciki sannan ya koma ya kulle kofar d'akinsa da makulli ya zauna tare da baje takardun nan, bayan ya gama bincikensa da 'yan rubuce rubucensa ya maida ya rufe sannan ya juye fuskarnan a murtuke kamar mai tafiya yaki yace " Mu zuba mu gani." Kan gado ya kwanta ya sa diary d'in mahaifinsa, wani shafi ya bud'e an rubuta _Someone! Somewhere is made for u my dearest son_" Murmushi yai da ya tuna abinda nafi tace da kiss din data mai, hannu yakai kan leb'ensa yace " yarinyar nan kamar ba ruwanta ashe itama killer?" A haka har bacci yai gaba dashi. Da safe ya tashi tare da sawa a kiramai dan litti, sunyi breakfast kafin Ashraf ya kalli Dan litti yace "yanzu me kakeyi?" " Achaba." Ashraf ya jinjina kai yace "mota fa ka iya?" Dan litti ya d'aga mai gira yace "ka sanni ai akwai karambani ai zamana a kachako sai da na koya." Ashraf yace "gaskiya nafa sanka." Dariya sukai kafin Ashraf yace " zaka koma kauyene?" Da sauri yace "a ina?ai ni yanzu i am big for them." Ashraf ya sa dariya yace "u are big?wato baka daina bako?" Ashraf ya mai alamun zip a bakinsa yace "na daina kai kawai nake san ma." Ashraf yace "to in ba matsala nafisan ka zama driver d'ina, saboda nafisan wanda zan yarda da shi." Zaro ido dan litti yai yace " Ashaf kana kasheni in nazama driver dinka ai na zama dan gomna." Dariya sosai Ashraf yai yace " whoa! Dan litti kai kadai ke sani dariya akai akai." Dam litti ya mike tare da yima Ashraf salute yace "yes sir!" Ashraf yai murmushi yace " kaii ban taba ganin mutum irinka ba." Dan litti ya zauna yace "Ashaf karka damu zan zama mutum mai rike ma amana, dama tunda muka hadu nake sanka bazan taba bari wani abu ya cuceka ba." Ashraf yai murmushi sannan ya dafashi yace "thanks, amma kanaso kacemin wai baka iya fadar Ashraf bane ko ya?" Dan litti yai dariya yace "in na cema Ashraf ai mantawa zakai nine d'an littin gayu." Dariya suka sakeyi kafin su mike su fita. Makullin motarsa yaba Dan litti shikuma ya wuce b'angaren kawu. A tsaye ya ganshi shima zai fito, mumy na kusa dashi, wani takaici ya kara kamashi ya matso kusa da kawu ya gaisheshi fuska dauke da murmushi sannan ya gaida mumy. Bayan sun amsa ne kawu yace "Ashraf ya akai?" Kallan mumy yai yace "magana nakeso muyi." Mumy ta kalleshi jiki a sanyaye tai waje, ya matso kusa da kawu fuskarnan a sake yace "naji shiru ne, jiya banga takardar appointment ba." Kawu ya kalleshi yace "wai da gaske kake?kasan fa matsayin Asim ne ya kakeso inyi." Wani murmushin rainin hankali yai tare da jinjina kai yace "ahhhh! Na manta ko da yake ba matsala ka barshi a matsayinsa kai sai ka bani naka, dama ai can nawa ne ko ba haka ba???" Ya fada yana kallan kawu. Kawu ya shiga hucci, Ashraf yai murmushi sannan ya dan girgiza d'an yatsansa yace "No no no, kawu how can u get angry? Bayan a sama kaga komai?wanda ya sha wahalar yana karkashin kasa?" Kawu ya kalleshi sannan yai yake yace "ce maka akai raina ya b'aci?" Ashraf ya d'an kanne idanuwansa yace " why?kunya kake na gano hakan? Hmm ko da yake ba matsala yi zamanka a kujerarka nizansa ka sauka da kanka in har baka ajiye da hannunka ba." Yana kai nan yai waje,yana fita kawu ya shiga hucci, jakarsa ya cillar can gefe sannan ya zauna a kujera yana maida numfashi kamar wanda yai gudu...... Ashraf ya fitowa ya harari d'akin sannan ya juya, jiyai ance "Ya Ashraf." Juyowa yai ya kalli Anisa wace duk ta dan fada a kwana biyu, ya matso yace" ya akai?" Kallansa tai tace " yaushe zaka zo ka maidani b'angare na?" Kafada ya d'aga yace "da nina kawoki nan?" Kallansa tai tace "yaya ni bazan koma bane harsai ka saki wannan yar kauyen dan pride dina bazai bari in iya kallanta ba, kace ta koma kauyensu." Hannu yasa ya dafata yace " a maysayinki na wa kenan?" Tace "yaya!" Yai murmushi yace " karki damu kiyi ta zamanki a gun mahaifiyarki gani nake zatafijin dadin hakan, nima kuma zan samu saukin bincike min d'aki da akemin." Yana kainan yai gaba, kallo ta bishi dashi yasan komai meyasa bai taba magana ba???? Mota ya wuce, dan litti ya bud'e mai baya nan ya shiga ya rufe shikuma ya shiga mazaunin driver. *#ASHRAFEENAH TEAM* 👩🏻‍✈ *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *56* Ashraf yacema dan litti akan su tsaya a wani babban shago na wayoyi, nan suka fita tare. Waya ya d'auka kirar Samsung S7+ karamar ta hannunsa, sannan ya kalli Dan litti yace"kaifa wanne kakeso?" Kai Dan litti ya sosa, Ashraf yace "shikenan in ba ka so." Da sauri yace " ni kowacce ma ina so." Ashraf yai murmushi yace "a d'auko mai Iphone 5." Wani ihu da dan litti ya sake sai dayasa mai wayar ya kwashe da dariya, nan suka sai sim sannan ya kara siyan wani extra sim sannan suka fito. Suna shiga mota ya d'auko wata yar karamar waya daga cikin jakarsa, yasa wannan d'ayan sim d'in a ciki sannan ya maidata jakar. Sun isa gun aiki Ashraf ya fito d'an litti yabi bayansa, Asim ne wanda yake tsaye yake jiran isowar Ashraf ya taso da sauri, ya taho gun Ashraf fuskarnan a had'e. Dan karamin tsaki Ashraf yaja a ransa yace "The fool is here." Asim na karasowa ya kalli Ashraf yace " Kai bakaji kashedena ba ko? Akan kaba yarinyar nan takardarta ta bar gidan nan ba ko?" Dan litti ya matso yace " Malam meye hakan?" Murmushi Ashraf yai yace " barshi magana zamuyi." Nan Dan litti ya matsa tare da had'e fuska kamar irin shi akama abun nan. Kallo Ashraf ya maida kan Asim yace " Mahaifinka yace zai bani matsayinka, mai kake tunani?" Idanu Asim ya zaro tare da kumburo baki yace "matsayina? What do u mean?" Ashraf ya dafashi yace " what do i mean? Da alama sai ka tambayi mahaifinka da ya dage akan bani matsayinka, mayb kuma ya kula ne u are useless." Yana kaiwa nan yai gaba, Dan litti yabi bayansa rike da jakarsa yana hararar Asim. Ashraf ya kalleshi yace " Dan litti kasan kanin mahaifina?" Kai ya girgiza alamar a'a yace "jiya dai na ganshi sai dai banaji zan iya gane shi." Ashraf yace "zan nuna maka shi inaso ka dinga kulamin dashi akan abubuwan da yakeyi da kuma wadanda yake gani, sai dai karka bari kowa ya ganka kar kuma asan abinda kakeyi." Dan litti ya mai salute da hannunsa yace "yes sir." Hannunsa Ashraf ya ture yace " sorry ba a military muke ba." Nan sukai dariya sannan suka shiga. Jakarsa Ashraf ya kaimai sannan ya juyo ya fita. Asim kam yana gama magana da Ashraf yai office dinsa kamar zai fadi saboda sauri, yana zuwa ya ture takardun kan desk dinsa da hannayensa biyu, ciki hucci yace " ni zakama haka Abba?" Kawu kam yana zuwa office yasa aka rubuta takardar ragema Asim matsayi aka aika mai. Asim yai shiru yana kallan takardar, can cikin takaici ya yaga takardar sannan ya mike cikin fishi yai office d'in kawu. A zaune ya ganshi shi da manager suna magana, nan ya tsaya suka gama, manager din ya fita sannan ya shiga. Tsayawa yai a kan mahaifinsa yace "ban yarda da ragemin matsayin nan ba." Kawu yace " kasan complain din da ake kawomin naka kuwa?in ban rage ma matsayi ba mai kake tunani mutane zasu daukeni?" Mamaki ya kama Asim yace " wa zaka ba matsayina? Ashraf?" Kawu ya juya kai yace " haka shareholders da director's suka yanke." Dariya Asim yasa yace " ko kuma ka tsara ba?" Kawu ya had'e rai yace "kai ni kake fadama haka?" Asim cikin hucci yace " ni dai na fada kar a kuskura a ragemin matsayina in ba haka ba zan iya tona abubuwan da na sani." Mikewa kawu yai tare da dukan desk dinsa da hannu yace " me zaka tona?" Yai dariya yace "abubuwan da kai, kana tunanin in Ashraf yaji zai barka?wato yanzu tunda kaga Anisa batada matsayi a gunsa shine kake neman juya mana baya ka koma gunsa ko?" Kawu a zuciye ya d'aga hannu ya kai mai mari, Kallansa Asim yai sannan yai waje rai a b'ace." Kawu ya bi bayansa da kallo sannan ya zauna tare da rike kansa. Asim sama yahau cikin takaici yahau hucci tare da kara, ko aure bai taba kawowa ba saboda yanasan ya gaji Company din nan, shine yanzu mahaifinsa zai fara juyamai baya??" ************ Nafi kam bayan ta gama aikin gyara musu d'aki ta zauna tare da daukan qur'ani tana karatu. Mumy ce ta aiko a kirata, nan ta mike gabanta na faduwa tai waje. B'angaren Mumy ta nufa ta zauna tare da zama a kasa. Mumy ta kalleta tace " jiya ina kika je?" Nafi kanta na kasa tace " Gidan wata kawata da mukai makaranta." Mumy ta kalleta tace " ina sanki a natsayinki na yarinyar da aka taimaka amma ba wai a matsayinki na matar Ashraf ba." Nafi ta d'ago a hankali ta kalli Mumy. Mumy ta cigaba "Ashraf bai samu kulawa daga gareni ba sai bakin ciki dana dinga kunsa mai, mahaifinsa ya rasu hankali bai gama shigarsa ba." Idanun Nafi suka ciciko, Mumy tace " sai dai hakan ba yana nufin zan yarda ya auri mara ilimi ba alhalin aiki babba yana gabansa, yana bukatar matar datasan gari sannam takeda ilimi at least degree, shine wanda zai gaji mahaifinsa." Nafi tai kasa da kai hawaye suka zubo mata, Mumy tace " kije kiyi tunani in har kina san Ashraf to kiyi tunanin menene abinda zaifi amfanarsa a rayuwar nan." Nafi ta mike a hankali tana share hawayenta, b'angarensu ta nufa, da gudu mai gadi ya karaso yace " yallabai yace wai ki mai abincin rana zai dawo da anyi la'asar." Kai ta d'aga sannan ta koma ciki. Ana azahar ta fito tai kitchen ta fara mai girke girken Asabe na tayata. ********* Umma da Anisa kam suna zaune abin duniya ya damesu, Anisa can ta nisa tace " duk laifinku ne Umma, meyasa kuka hanani haihuwa dashi?" Umma tace "mene?" Anisa ta cigaba" da yanzu akwai zuri'a a tsakaninmu ko baya sona ai nasan halin Ashraf bazai wulakantani ba." Umma ta mike tsaye tace " Anisa meke damunki?" Anisa cikin dan fada tace " wlh ni duk ku kuka cuceni, da ace na haihu dashi ai da d'ana shine zai zama yanada gadon dukiyar Ashraf amma dayake ba ni kukeso na gaji dukiyar ba shi yasa ba wanda yai wannan tunanin." Tana gama fadar haka ta mike tai cikin d'aki tare da bugo kofa da karfi, Umma ta bita da kallan mamaki. ******* Karfe hud'u da rabi Ashraf ya dawo, b'angarensa ya nufa, shima dan littibya wuce nasa. Zama yai tare da d'aukan waya ya kira Little, yace "kin dawo?" Tace eh yaya. Yace "ki turomin Nafi." Ta amsa sannan ya kashe. Nafi ta kalla wacce tai wanka tai kwalliya cikin atamfa riga da siket, bata d'aura d'an kwalli ba kanta ba kisto sai dai ta tifkeshi da ribon. Kan nan yayi gwanin sha'awa. Little ta kalleta tace " Yaya na kiranki, da alama dama shi kike jira." Nafi ta harareta tace " ni wai ina mutumin ki? Naji shi shiru kwana biyu. Little tace "tafiya yai wlh amma gobe zai dawo." Nafi ta zari d'an kwalinta tai waje. Kitchen ta nufa ta d'auko tiren data jera mai abincinsa sannan tai b'angarensa fuskarnan fal take da farin ciki, dukda dai kalaman Mumy suna kara yimata yawo a zuciyarta. A bud'e taga kofar hakan yasa tasa kai tare da sallama, Ashraf wanda ke zaune akan kujera ya kalleta fuskarnan d'auke da murmushi, dinning ta wuce ta ajiye sannan ta tsaya daga gun tace "ka taso." Hannu ya mata alamar tazo nan tad'an yi kasa dakai sannan ta make kafada tace " naki ni dai ka taso." Murmushi yai ga mamakinta sai taga ya taso ya nufota, jingina tai da jikin dinning din tana kallansa fuskar nan d'auke da murmushi. Ya karaso kusa da ita batai zata ba sai jitai ya rungumeta. Murmushi tai sannan tace " Yaya ka dawo lafiya?" " Hmm lafiya lau, jiya yaushe kika tafi?" D'agowa tai ta kalleshi tad'an mai hararar wasa tace " ba bacci kai ka shareni ba." Idanu ya zaro yace garin yaya?" Ta turo baki tace "Allah yaya indai ina zuwa gunka kana min bacci ko?" Bakin data turo ya d'an sumbata hakan yasa ta maida shi da sauri, yace " me za amin?" Kallansa tai tace " kazo kaci abinci." Murmushi yai sannan ya saketa ya ja kujera ya zauna tare da nuna mata kujerar kusa dashi. Nan ta zauna ta zuba mai, kallanta yai yace " muci." Tace " am full." Idanu ya kafeta dashi hakan yasa ta mike ta d'auko wani spoon din ta zauna. A hankali suke ci sai dai ya kamo hannunta na hagu ya rike. Bayan sun gama ne ta zubamai juice ya sha sannan suka mike. Hannu yasa a kugunta ta kalleshi tai murmushi a haka suka karasa ya zauna akan kujara tare da jawota kan cinyarsa. Kallansa tai tace " yaya inada nauyi fa." Dariya yai yace " indai kinada nauyi to lalai Afra ma tanada nauyi." Cikin shagwab'a tace " Afran?"" Ya d'aga mata kai sannan ya d'auko ledar dake gefensa yace " Gift." Kallansa tai ta amsa zata bud'e yace " ba anan ba sai kin tafi kya bud'e, yanzu dai tukuicina zaki bani." Yai maganar yana mata wani kallo, itakam in Yaya na mata irin wannan abun mamaki takeyi dan a iya saninta da gani take mutum ne wanda bashida sakin fuska, sai dai ferry dama ta fada mata maza duk daya suke indai a harkar so ne, kenan shi yana santa da gaske." D'an kwalin kanta ne ya zame, kanta ya kurama ido, a hankali yakai hannu ya shafa yace " i like this." Murmushi tamai sannan tai kasa da kanta tace " tukuicin me kake so?" Nesa dashi ya nuna mata yace zauna, nan ta tashi ta zauna a gun, zatai magana taji ya kwantar da kansa kan cinyarta yace " a gajiye nake, so nake inji ya bacci yake a kan cinyar matata." Kallansa tai tare da sa hannunta kan fuskarsa tace " amma ai kana kwanciya akan cinyar yaya Nisa." Yai murmushi bai ce komai ba sai idanunsa daya rufe. Murmushi tai sannan tasa hannu ta fara shafar kansa. Ta ina zata iya rabuwa da Ashraf? Bataji zata iya, in kuwa tai to gaskiya rayuwarta ta gama karewa. *#ASHRAFEENAH* 💋 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Thanks alot My Wattpad fans, i really appreciate ur luv and support.* 57 Tun daga idanunsa take bi da kallo fuskarta sai murmushi ke bayyana, lalai soyayya da dadi amma batajin in har da wani ne zataji dadin soyayyar nan. Ashraf kam bacci ne ya daukeshi, jin yanda Nafi ke shafa masa kai. Bud'e kofar falon yasa ta kallo gun da sauri tana san ganin wanene ya bud'e kai tsaye. Ganin Anisa yasa ta zaro ido sai dai bataji zata iya d'aga Ashraf daga jikinta saboda Anisa. Itakam Anisa tun daga bakin kofa ta tsaya tana musu wani kallo, wani irin zazzafan kishi ne yake damunta, kitchen ta wuce direct ta debo ruwa cikin bokoti ta nufo Nafi. Itakam Nafi ganin tayi kitchen yasa ta saki numfashi na farin ciki, tare da kallan Ashraf, batai auni ba kawai sai ruwa sukaji akansu. A firgice Ashraf ya farka tare da mikewa tsaye, kallan mamaki ya shiga yima Anisa wacce ta shiga yin huccin masifa. Ya maida kallansa kan Nafi wacce dama kanta ba d'ankwali saboda dazu ya cire mata tun daga saman kanta har jikinta duk a jike yake jarab. Yaso yama Anisa magana amma ganin Nafi cikin wannan hali yasa ya wuce dakinsa da sauri ya d'auko towel sannan yazo ya rufa mata. D'aga ta yai ko kallan Anisa bai kuma yi ba ya wuce da ita cikin d'akinsa. Nafi kam tayi lamo har suka shiga ciki, ya kalleta yace " kinji haushi ko?" Kai ta jinjina alamar eh, yai murmushi yace " kinsan......" Ta katse shi da cewa " haushi na d'aya kana bacci an tasheka." Kallanta yai tare da murmushi ya jawota jikinsa, sannan ya kamo hannunta sukai toilet. Kallanta yai ya mika mata towel, ta amsa sannan tace " ka fita to." Baya ya juya sannan yace " ki cire a haka dan ba inda zani, ai ba kallanki nake ba." Ta ce " taya zan yarda bazaka juyo ba?" Yai murmushi yace " in ma na juyo ai abuna na kalla ba na wani ba." Juyawa tai da sauri cikin kunya. Da kyar ta cire kayan ta d'aura towel din sannan ta sa kayan a bokiti, tace kazo ka cire naka sai in wanke mana." Murmushi ya mata sannan ya sa wani takalmin ya shiga toilet din. Juyowa tai zata fita ya riko hannunta. Nan ta tsaya ba tare da ta juyo ba, yace " ina zaki??" Kallansa tai da sauri tace "naam?" Yace " ina zaki nake tambaya, dan nasan kinjini." Tace " waje zani in ka...." Hannunta yaja yai wajen sink da ita kallan sa kawai takeyi, gani tai ya d'auko man wanke kai da alama nashi ne ko na Anisa ne ni dai ban sani ba. Ya mata alama data sa kanta. Ta kalleshi tace " yaya me....." Hannu yasa a bakinsa alamar tai shiru sannan ya mata alama data sa kanta. Nan ta sa kanta tana tunanin me bawan Allahn nan yake shirin yi. Ribbon dinta ya zare sannan ya zuba man ya fara cud'awa a hankali, shiru tai tsantsar mamaki ne yake mata yawo a zuciya, dama haka Yaya yake??? Jitai yace " kina mamaki ne?" Cikin rawar murya tace " ni ban ce komai ba." Ya sake murmushi sannan ya sunkuyo saitin kunnenta yace " na dade ina sha'awar wanke kan nan tun kafin ki koma skul, sanda mukaje siyayya." Tai kamar zata d'ago ya maida kanta kasa yace " kina mamaki ne?" Tace " na fahimci me yasa yaya nisa bazata iya rabuwa da mutumin nan ba." a ranta tai maganar batasan a fili tai ba sai jitai yace " da cewa akai zan rabu da ita? Ko kuwa abinda kike so kenan?" Idanu ta runtse kunya ta kamata, da sauri tace " ni na isa? Na san irin san da kuke ma juna??" Murmushi yai a ransa yace " bantaba san wani ba sai a kanki dan ban taba tunanin zan iya yima mace wadan nan abubuwan ba." Anisa kam wacce tazo daukan kaya sam kasa dauka ma tai ta koma bangaren Umma tana zuba kuka kamar ranta zai fita. Umma ta taso da sauri zata mata magana, Anisa tace "kun cuceni wlh ni bada kudin ba bada mijin ba." tai d'aki tana kukan takaici. Umma ta baza tagumi, a fili tace " kai wannan yar bafilatanan anyi tsinanniya, anya kuwa haka ta barshi? Da alama zan fadama Uwarsa dan banaji ta barshi haka, dama ita inaaa sam bata yarda da ita ba. *Dan Allah kuyi hakuri da wannan wlh wani irin mura nakeyi mai hade da ciwon kai, amma insha Allah zuwa gobe in yai sauki zakuga nayi posting, nagode.* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Where am i going to started? Ayeesh! U really left me without word, Thanks alot for the dedication of the whole book "Jini D'aya", I really appreciate ur love....May almighty Allah help and guide u through the right path...Ameen* 58 Bayan ya gama ne ya sa mata karamin towel ya sa mata akai sannan ya kalleta yace " zaki fita in watsa ruwa ko zaki zo mu watsa......" Ai bata jira ya karasa bama tao waje da sauri, murmushi yai sannan ya tura kofar. Nafi kam kofar tabi da kallo tace "wato yaya sam bashida kunya ko?" Zama tai a bakin gado littafin nan na diary ta gani a hankali ta zaro shi ta bud'e shafin farko "To My dearest Son Ashraf." Abinda ke rubuce kenan tai murmushi ganin wani d'an karamin hoto ba sai an tambaya bama Ashraf ne, passport ne da alama yana nursery aka d'auka tai murmushi sannan ta bud'e shafi na biyu. _Ashraf Allah baiyi zanga girmanka ba sai dai inaji ajikina ko bani zaka zama yaro na gari, mai san 'yan uwansa da na kasa dashi._ Nafi ta sake murmushi tace "Abba ai d'an naka ne ba a gane cikinsa." Tana bud'e d'ayan page rubutu ne sosai, tana kokarin karantawa taji motsin alama na bud'e kofa, da sauri ta maida littafin sannan ta mike. Ashraf ya kalleta sannan ya karaso inda take, yace "matsoraciya." Kanta ta kawar gefe batace komai ba. Toilet ta wuce da sauri, yabi bayanta da kallo zuwa cinyoyinta da suke a waje, kansa ya shafa sannan ya zura riga doguwa ya fita falo. Nafi kam bayan ta watsa ruwa ta fito tare da tsayawa a d'akin to me ma zatasa? Ina kuma yayan yaje? Rigarsa ta gani t-shirt irin mai dogon hannun nan kawai ta zura sai ta sauke towel din kasa ta d'aurashi kamar zani. Tana d'aura kanta da ribbon Ashraf ya shigo, kallanta yai yadanyi dariya yace " da har ina tunanin d'auko miki kayan yayarki?" Da sauri tace " wacce yayar?" Ya d'an bata rai kadan yace "wace yayar kike da ita a gidan nan?" Baki ta tabe tace " bansa kayanta bama an jikani ina kuma ga ta ganni da kayanta?ai inaji kanazir zata zubamin ta kyasta ashana." Ashraf ya danne dariyarsa yace " ke dai tsoronta kawai kikeji da alama, ko da yake baki da laifi Anisa ai akwai zuciya, ga kwarjini kuma bata da tsoro kamar o'o." Nafi ta d'an harareshi kadan tace " nima ai inada zuciyar kuma ba tsoro garen ba kawai dai raga mata nake nima." Ashraf baisan sanda yasa dariya ba, sai dayai sosai sannan ya kalleta ta wani ci magani yace " ayya bansan raga mata kike ba ai, ashe karamar matar tawa ba tsoro." Nafi ta kara had'e rai tace " ai in aka bi ta gaskiya ma nice babba dan nice uwargida." Baki Ashraf ya bud'e sannan yai dariya yace "Uwar gida?" Ta turo baki tace" to wacce in ba ni ba?" Dariya yasa zai yi magana yaji ana knocking, nan yai waje yana dariya, lalai yarinyar nan, uwar gida??? Ha ha ha ni kaina sai da na sa dariya. Dan liti ne bayan ya shigo ne Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ina da ina yaje?" Nan Dam litti yashiga mai bayani, Ashraf yai shiru can yace " shikenan sai zuwa gobe." Dan litti yamai sallama ya fita, Nafi bayan taji rufa kofa ne ta fito, a falo ta ganshi ya zauna tare da sa hannunsa duka biyu akan hancinsa zuwa bakinsa, Nafi ta zauna kusa dashi tace "Lafiya?" Kallanta yai tare da girgiza mata kai alamar ba komai, ya mata murmushi. Itama murmushin tai sannan tace " nikam kun hadu da babansu Ferry ko?" Kallanta yai yace " Inda kikai yaji?" Tai murmushi tace " ka ganshi?" Kai ya d'aga alamar eh, sannan yace " ya akai?" Tace " baka sanshi ba ko?" Kai ya d'aga mata cikin rashin kulawa yace " yeh." Shiru tai hakan yasa yace "ya akai?ya kamata in sanshi ne?" Tai shiru kafin tace " a company din Abba yai aiki da." Kallan mamaki ya mata yace " what?" Tace " kuma da alama abokin Abba ne, dan bayan rasuwarshi ya ajiye aikinsa na company din." Ashraf yace " ko abokinsa ne mai zai sa ya ajiye aikinsa dan Abba ya rasu?" Shiru tai hakan yasa ya dafata yace "Nafisa!" Nafi tace " wlh bansan dalili ba sai dai kamar yana zargin mutuwar Abba ne." Shiru yai hakan yasa tace " menene?" Ya kalleta yace " sunansa Isma'il?" Kallan mamaki tamai tace kasan sunan ne?" Da sauri ya mike yace " zan turo Little ta kawo miki kayanki." Ta mike tace " ina zaka?" Bai amsa mata ba sai makulli daya zara yai waje da sauri. Bayansa tabi da kallo, sannan ta kalli ledar daya bata d'azu, mam ta bud'e ganin kwalin waya yasa wani farin ciki ya kamata, irin wayar hannunsa ce har kalar sai dai ita bata kai waccen ba, wani murmushin farin ciki tai tace "Yaya na gode." Nan ta bud'e wayar ta shiga ta tabata. ******** Ashraf direct a kofar gidan su Ferry yai parking, ya karasa suka kaisa da mai gadi sannan ya tambayeshi ko mai gidan na nan, mai gadi yace " eh yana gida, wa za'ace mai?" Ashraf yace kace " Dan marigayi Abbas ne." Nan mai gadi yai cikin gida, baifi minti 3 ba sai gashi ya dawo wai ya shiga. Nan ya rakashi falon baki, Nabil na zaune kusa da mahaifinsa yana ganin Ashraf ya mike suka gaisa sannan cikin muryar rada yace " rannan ya aka kare kai da budurwata Feena?" Ashraf ya makamai harara sannan shima cikin rada yace " kai saurin gyara bakinka,wacce budurwar taka?" Yana kainan yai gaba, a gaban mahaifinsu Ferry ya zauna, tare da gaidashi cikin ladabi. Dad ya amsa sannan ya kalli Ashraf cikin tsoron abinda yazo dashi yace "Ashraf ya akai?" Ashraf ya d'ago yace " Tun ranar da na fara zuqa gidan nan ka san ni ko?" Dad ya kalleshi bai amsa mai ba, Ashraf yai murmushi yace " Na dade ina nemanka sai dai bansan ta inda zan soma cigiya ba, shiyasa nabarma kaina saninka." Kallansa Dad yai yace " nema na?" Ashraf yai murmushi yace "kasan lawyer din Abbana?Uncle Salim?" Dad yace " Salim?" Ashraf ya d'aga kai yace " ya sanar dani kai da amintar dake tsakaninka da mahaifina sai dai kowa na mamakin barinka company daga sanda Abba ya rasu." Ashraf yad'an tsaya sannan ya cigaba, " sai dai ni ina tunanin ba aminta bace tasa kabar company din sai dai cikin d'ayan biyu, ko dai kasan abinda ya faru da mahaifina? Ko kuma da kai akai abinda akai, sai dai a koda yaushe in zuciyata ta rayamin na biyun ina saurin neman sauki gun Allah daya sa hakan karya zama gaskiya." Dad ya kalli Ashraf ga mamakin Ashraf sai jiyai yace " Ya Mansir?" Ashraf yace " kawu? Yana nan." ya fada yana mai kallan mamaki. Dad yai murmushi yace " me kake tunani gama da Mansir?" Ashraf ya d'an rage idanunsa yace "naam?" Dad ya sake murmushi yace " u are smart, nasan kasan me nake nufi." Ashraf ya kalli Dad yace " nagane me kake san tambayata sai dai bansan meyasa nakeji a jikina ba Kawu bane kadai." Dad yai murmushi yace " As i expected nasan dan Abbas bazai bani kunya ba, u are right sai dai bazakaji komai a bakina ba, sai dai zan baka suna guda d'aya kaje kai amfani da wannan sunan ka gano shi da su waye suka had'u sukama Abbas haka." Ashraf yai shiru yana kallan Dad, dad yace " Auwal max." Kaje kai tunani ka kuma yi amfani da wannan sunan mutumin ka gano su waye ragowar, in ka gano sai ka dawo ni zan sanar da kai abinda na sani saboda a lokacin ne zan gane lalai zaka iya komai." Ashraf ya maimaita sunan "Auwal Max!" Sannan yai godiya ya mike ya fito, a wajen falon ya tsaya yana kallan kofar falon, lalai mutumin nan ya iya d'aure magana, ya maimaita sunan Auwal Max! Sannan ya fito daga gidan yayi sa'a bai ga Nabil ba da sauri ya fada mota yai gaba..... *GODIYA MARA ADADI AKAN ADDU'OINKU.* _Nagode kwarai, insha Allah zaku cigaba da jina kullum._ _Tnx for ur love and support💞_ *ASHRAFEENAH TEAM* *LET'S GO👩🏻‍✈* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 59 Ashraf yana fita daga gidan ya wuce gidan Uncle Salim, bayan sun gaisa ya kalli Uncle yace " Uncle tambaya nazo da ita." Uncle yace " ina jinka, sai fatan Allah yasa na san amsarta." Numfashi Ashraf yaja sannan yace " Kasan Auwal Max?" Kallan mamaki Uncle yamai yace " kwarai kuwa dan driver din mahaifinka ne koda yaushe suna tare." Ashraf yai shiru hakan yasa Uncle yace " menene?" Ashraf yad'an numfasa sannan yace " Yana ina yanzu?" Kai Uncle ya girgiza yace " Allahu a'alam, tun bayan hatsarin mahaifinka ban sake sashi a idona ba." Ashraf ya kalli Uncle cikin mamaki sannan yace " shima yana cikin motar sanda abin ya faru?" Uncle yace " kwarai kuwa, a iya sanina tare suka fita sai dai bansan ya akai ba naga mahaifinka kadai a asibiti, sai dai inaji ko shi wani asibitin aka kaishi." Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya mike yace " sai da safe na gode." Bayan ya fito ya shiga mota ya jingina kansa da kujera, yana nazarin kalaman Uncle, mai zai sa Alhaji Isma'il ya fadamai sunan driver din mahaifinsa???? Ya dade yana tunani kafin yaja mota yai gaba. Nafi kam Little ta kawo mata kaya tare da mata kallan zargi, Nafi ta harareta tace " me kike tunani?" Little tai dariya tace "ah to abin naku dai ba kunya da alama daga ke har yaya." Nafi tai saurin fizgar kayanta tace " me mukai?" Little ta girgiza kai tace "hmm ko sai nazo nayi gashi? Ko kuwa ba tun yau ba aka bud'e?" Idanu Nafi ta zaro sannan ta d'au kayanta ta dan bigama Little tace "lalai wannan kanwar batada kunya, to wlh mu ba ruwanmu salahaine." Little ta rufe baki tace " hmm da alama kam." Nafi ta harareta sannan ta zura kaya suka fita tana kokarin kare kanta agun Little, ita kuma sai tunzurata takeyi. Ashraf yana dawowa gida yai sallah sannan ya kwanta akan kujera yana tunani, can wata idea ta fadomai hakan yasa yai bacci tare da tunani da fatan Allah ya taimakeshi gobe. Da safe ya shirya sun fita shida Dan litti, a hanyarsu ta office ya zaro wayar nan dake cikin jala ya saka number kawu sannan ya turamai sako kamar haka " Yallabai ina bukatar taimakon ka, kudin hanuna sun yanke. daga Auwal Max." Ya dade yana tunani kafin yai shahadar turamai, suna isa office ya kalli Dan Litti yace " ka tabbatar kabi Kawu duk inda zaije, jikina yana ban zai fito yanzu ka bishi duk inda yai." Dan Litti ya amsa da to, sannan Ashraf ya sauka, a hanyarsa ta shiga yaga kawu wanda yake kokarin saukowa daga beni, kallan mamaki yamai ganin yana cikin hanzari. Da sauri yasha gabansa, yace " Kawu sai ina haka?" Kawu ya dan yi murmushin yake yace " akwai aikin dazan je dubawa ne a construction site." Ashraf yamai kallan zargi yace " Hmm naga ne ka fito ba tare da Secretary dinka ba." Kawu yad'an juya kai sannan yace " yana mota yana jirana." Ashraf ya jinjina kai tare da cewa " shekanan a dawo lafiya." Nan yai gaba, kawu ya kalla yaga yana sauri, waya ya daga ya kira Dan Litti yace mai ya tabbatar yabi kawu gashinan ya fito. Ashraf office din kawu ya wuce yai knocking, kamar yanda yai zargi Secretary dinsa ne zaune yana rubuce rubuce, Ashraf yai murmushi sannan yace " Cigaba da aiki dama gun Kawu nazo." Ya mike tare da cemai, bayannan yanzu ya fita, Ashraf ya jinjina kai sannan yace " amma ya akai ya fita shi kadai? Kana aikin ka kuwa?" Da sauri yai kasa dakai alamun ban hakuri yace " wlh nace zan bishi yace in zauna ba dadewa zaiyi ba." Ashraf ya juya ya fita batare da ya amsa ba. Ajiyar zuciya yai sannan yace " ya ga sakon?" Kawu kam yana fita duk ya rikice ganin tun bayan faruwar abun nan bai kara ma tunawa da wani Auwal Max ba bare yasa ran haduwa dashi, menene nashi namai sako yanzu? Rashin kudi? Unguwar Nasarawa ya shigaz yai parking a wani tangamemen gida sannan ya fito da sauri yai cikin gidan yana waya, Dan litti na ganin haka ya kira Ashraf ya sanar dashi ya shiga wani gida. Ashraf yai murmushi tabbas gun wanda suka hada abun yaje daga ganin sako, yai murmushin ganin abun yazo mai da sauki yace " zaka gane gidan?" Dan litti yace " Yes Ma!" Ashraf yai dariya yace " nine Ma?" Dan litti shima yai dariya yace " ganinai tun da ka tashi yau bakai dariya ba shiyasa na saka." A tare sukai dariya kafin Ashraf yace " bayan La'asar kazo mu tafi." ********** Nafi kam ganin Little ta fita skul, yasa taji gidan shiru, dan ma tanata latsa wayarta can ta mike da niyyar zuwa kitchen, a kofar falo suka had'u da Habib, mamaki ya kamata tace " Ya Habib?" Ya sakar mata murmushi yace " Gimbiya i really miss u." Kallan mamaki tamai sannan tace " ni?" Ya d'an hade rai, zai yi magana tai saurin cewa " Little tana makaranta bakuyi waya bane." Ya hade rai yace " cewa nai gunta nazo?" Ta zaro ido tace " inba gunta kazo ba,gunwa kazo to? nadai san ba guna kazo ba." Ya kalletq yace " taya kika san haka?" Tai murmushi tace " haba ya Habib ina nakai wannan matsayin?" Yai ajiyar zuciya sannan ya mika mata leda yace " tsarabarki ce ta Abuja." Ta amshi kayan tana mai kallan mamaki, bata samu tai magana ba taga ya juya yai gaba, ta dan tabe baki tace " Tsarabar Little dai." D'aki ta maida kayan ba tare da ta bude ba sannan ta fita tai kitchen. ****** Ashraf sai yamma bayan sun tashi Dan litti ya wuce dashi gidan da kawu yaje, tun a kan hanya dayaga sun dau kwanar Nassarawa G.R.A yaji gabansa nafaduwa, addu'a kawai yake yi a ransa Allah yasa ba inda yake tunani zasu ba. Tsoronshi ya kara daduwa ne sanda yaga anyi kwanar gidan, idanu ya runtse cikin tsananin tsoro, Dan litti yai Parking sannan ya kalli Ashraf yace " Mun Iso." A hankali Ashraf ya bud'e idanunsa gabansa ne ya yanke ya fadi, da sauri ya fito daga mota yana girgiza kai alamar ba haka bane, ya kalli Dan litti yace " ka tabbatar nan yazo?" Kai dan litti ya d'aga alamar haka ne, Ashraf ya dafa kansa cikin tsananin tsoro can wata zuciyar tace " mayb baiga sakonka ba." Jiyai ance " Buddy." Da sauri ya juya Habib ya gani ya fito daga gidan da saurinshi, yana karasowa ya rungumeshi yace " Ayya Aminina da alama jikinka ne ya baka na dawo ko?" Ashraf ya d'an yi yake yace " lalai kasha hanya." Habib yace "sosai ma, dan ma naje naga gimbiya." Kallan mamaki Ashraf yamai,Habib ya katseshi da cewa " muje ciki ku gaisa da Dady kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai." Ashraf yai murmushi sannan yace " muje to." Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace " dama Dady da Kawu suna shiri??" Habib ya dafashi yace " me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy." Ashraf a ransa yace "then y??????" Jansa Habib yai suka shiga ciki. Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace " wa nake gani kamar d'ana da baya nemana???" Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace " Dady na sameku lafiya?" Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace " Dady ina wuni?" Dady ya dafashi yace " Ashraf nida d'ana amma ganinsa ya min wuya?" Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace " Dady kasan aikin namu ne sai a slow." Dady yai murmushi yace " to ya za'ayi dama komai sai hakuri." Habib dake zaune yace " wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d......." Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace " kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?" Ashraf yai murmushi a ransa yace " shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? " Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta 'yan uwa ko akwai wani b'oyayyen al'amari a kasa???? Hmmmmmmm *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *My Kawa Bilyn Abdul wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah ya kara kareki a duk inda kike* Ameen. *60* Nan Dady yai ta jansa da hira shima yana biyemai kafin daga bisani yamai sallama, Habib yace "muje ka gaida Mum." Ashraf ya dafashi yace " next time kanina." Murmushi sukai a tare Ashraf ya kira Dan Litti suka dau hanya, suna hawa kan titi dan litti ya kalli Ashraf yace " Ashe ma kasan 'yan gidan." Ashraf yai murmushin takaici yace " Gidan yayan mahaifiyata ne " Dan litti yasa dariya yace " ohh shiyasa yazo nan?" Murmushi kawai Ashraf yai ya bud'e window tare da kurama titi ido, suna isa gida ya fito jiki a sanyaye yai b'angarensa. Nafi kam harta gaji da jiran dawowarsa gashi ta mai abinci, ganin anyi sallar isha'i yasa tai tunanin dubawa ko ya dawo. Da yake yanzu tanada makulli bayan ta kwankwasa taji shiru sai ta bud'e kofar, duk wutan bangaren a kashe yake da alama ba mutum a ciki, ta d'an d'aga gira tare da yin ajiyar zuciya tace " bai dawo ba." Tayi nufin juyawa sai taji ringing din waya, ita kuma ba tata bace dan tata na gida, cikin tsoro ta fara yin sanda tana bin inda takejin karar gashi a bin mamaki ba'a d'aga wayar ba. D'akinsa taji karar na fitowa a hankali ta murd'a tare da yin addu'oi a ranta, kwan wuta ta kuna da sauri tana tsoron kafin a maketa gwara taga waye. A binda ta gani ne yasa gaba d'aya jikinta ya mutu, tsayawa tai cak tana kallan Ashraf wanda ke zaune a kasa ya hada kai da gwiwa, ga kuma wayarsa nan a hanunsa yanaji ana kira bai dauka ba, sai dai ta kula ba wayarsa bace da yake amfani da ita. Ganin haske ya kewaye d'akin ne yasa ya d'ago ya kalleta da idanunsa wadanda sukai jaa, a hankali yace " Nafisa can u please get out?" Kallansa tai cikin tsananin mamakin halin data ganshi cikin rawar murya tace " Ya Ashraf?" Idanu ya runtse yace " please can u get out, banasan ki ganni cikin wannan halin....." ya karasa maganar cikin wata irin murya, sakon da aka turo mai yana kokarin bud'e kofa ne yasashi cikin wannan halin. Kawu ne yai reply kamar haka "Max na d'auka kunyi da Yaya akan bazaka kara nemana ba? To shi yace kaje yana nemanka." wannan sako ya d'agama Ashraf hankali, a iya saninsa Kawu mahaifin Habib kawai yake cema Yaya, sai dai tayaya za'ace da hannun yayan mahaifiyarsa????? Ganin bai maida reply ba yasa Kawu ke ta kiransa. Kashe wutar Nafi tai sannan a hankali ta taka zuwa inda yake, ta tsugunna tare da rungumoshi jikinta, idanunta sun cika taf da kwalla tun da take bata taba ganin Ashraf a irin wannan yanayin ba, hawaye ne ya ziraro mata a hankali tace " taya zan iya tafiya na barka cikin wannan yanayin?" Ashraf ya d'an zare jikinsa kadan yace " Nafisa please......" Hannu tasa ta rufe bakinsa sannan ta kara kankameshi hawaye suka fara zirya a idanunta cikin kuka tace " Yaya can u please share ur burden with me? Zuciyata tana zafi idan na duba naga bansan abinda ke faruwa dakai ba, bansan a wani hali kake ciki ba, Yaya ka taimaka ka sanar dani damuwar ka dan Allah...." Kuka take sosai wanda yasa jikinsa yin sanyi, kankameta yai sosai a hankali yaji hawaye ya gangaro ta idanunsa, yace " Nafisa ya zanyi? Ya zanyi da rayuwata, duk wanda nake tunanin yana sona sai na duba sai inga makiyi na ne, duk wanda nake tunanin yadamu dani sai in duba inga ashe amfani yake dani a b'oye, na d'auka i am smart sai dai yanzu na tabbatar i am the biggest foolish in the world, me yasa Allah ya d'auke Abbana ya barni? Meyasa....." Kuka take sosai ta sa hannu ta toshe bakinsa tana girgiza mai kai" Yaya ka daina fadar haka, Allah na tare da kai sannan duk wanda ya zalunceka Allah bazai barshi ba ko shi wanene." Idanu Ashraf ya runtse wasu zafafan hawaye suka zubo mai yace " me ya kaini binciken abinda ya riga ya shud'e, why???" Nafi ta kankameshi tana girgiza kai tace " laifinane yaya ko ma menene laifina ne, please ka yafemin, da ban sanar dakai ba banaji zakai binciken nan, yaya ka yafemin Laifinane, nice na ja maka shiga wannan halin." Ashraf ya sa hannu ya shafi bayanta yace " ba laifinki bane, na dade ina bincikena, iya kace ke taimakamin kikai, karki sake cewa laifinki ne." Nafi shasheka kawai takeyi, bata san me ya jiyo ba amma ta tabbata abin ya shafi danginsa. Sunyi shiru suna manne da juna cikin duhu, Ashraf can cikin wata sansanyar murya taji yace " Thank u Nafisa." D'agowa tai cikin mamaki duk da ba haske ba ganinsa take ba sai dai mamaki karara ya bayyana a fuskarta, wannan itace rana ta farko data tabajin Ashraf yayi godiya bama ga ita ba, a'a bata tabajin yace ma wani bama. Murmushi taji yayi ya d'an ja numfashi kadan yace " kina mamaki ko? Ni kaina rabon danaji na fadi wannan kalma ba naji zan iya tunawa." Hannayenta tasa akan fuskarsa sannan ta hada goshinsu tace " Yaya in kamin godiya akan me kenan? Ni kuma ince me kenan, yarinyar datake yar kauye ka..........." Hannu yasa ya d'an turo kanta bakinsa yakai cikin nata, wani irin salon soyayya suke ma juna wanda kana gani kasan son da sukema junansu lalai a bayyana yake, sun dade suna sumbatar juna kafin a hankali bakin Ashraf ya sauko kan wuyanta, wani irin yarr taji a jikinta wanda yasata yin numfashi, Ashraf sam ya manta da zancen sai ta aminta dashi, sarafata ya shiga yi sai dai itama duk da batasan kan abun ba haka kawai taji lalai tabbas tanasan ba Ashraf dinta farin cikin da yake nema. Soyayya mai karfi suke nuna ma juna sam bata san sanda ya zuge zip din rigarta ba sai jitai yabrabata da rigarta, ba shakka tsoro da fargaba ne ke damunta sai dai bataji duk wani wahala da ake fada zata iya bijirema Ashraf. Ya gama fita daga hayyacinsa haka itama a daidai wannan lokacin mai afkuwa ta amfku............Nikam ganin haka yasa na fito ga duhu wanda yasa ni yin tuntube da kujera😭 ************ A kauye kuwa Datti yau ya dawo ya taradda matarsa Mairo ta yimasa tuwo miyar kubewa bushashiya sai dai da zabuwa akai miyar, mamaki ya kamashi ya kalleta yace "mairo badai da zab......" Katseshi tai cikin salonta na jan hankali tace " Haba Datti bada zabuwarka bane, zabuwa ta ce data kasa na yanka mana ita." Baki taga ya washe yace " kai Mairo Allah ya miki albarka kinsan darajar dan adam." Nan ya yanko malmalar tuwo ya zuba nama sosai da miya ya hau ci, sai uban santi yake zubawa. Itakam sai murmushi takemai. Yaci yai hani'an ya tauna kasusuwa sannan ya kalleta yace " kai Mairo Allah ya barmin ke " Tace " Amin Datti." Ya kara washe baki yace "rabon dana kai nama bakina har na manta sai dai in gani a kwanon wani." Tai dan fari tace " ai banga laifinka ba, yanzu ba gashinan kafi kowa dukiyar dabobi ba duk yankin nan." Ya sake washe baki yace " Zabina guda 20 ne kaji guda 30 banda raguna, saniyoyi da akuya." Ta matso kusa dashi tace " yaushe za ka nunamin ne nima in gansu." Dariya ya kwashe dashi yace " karki damu gobe da kaina zan kaiki ki gansu." Tace to Datti Allah yabarmu tare. Yace Amin Mairoro ta.... Nace inma Maikoko ce...Lol masu suna Mairo tuba nake🤢 *#ASHRAFEENAH* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *61* Ashraf yana fita daga gidan ya wuce gidan Uncle Salim, bayan sun gaisa ya kalli Uncle yace " Uncle tambaya nazo da ita." Uncle yace " ina jinka, sai fatan Allah yasa na san amsarta." Numfashi Ashraf yaja sannan yace " Kasan Auwal Max?" Kallan mamaki Uncle yamai yace " kwarai kuwa dan driver din mahaifinka ne koda yaushe suna tare." Ashraf yai shiru hakan yasa Uncle yace " menene?" Ashraf yad'an numfasa sannan yace " Yana ina yanzu?" Kai Uncle ya girgiza yace " Allahu a'alam, tun bayan hatsarin mahaifinka ban sake sashi a idona ba." Ashraf ya kalli Uncle cikin mamaki sannan yace " shima yana cikin motar sanda abin ya faru?" Uncle yace " kwarai kuwa, a iya sanina tare suka fita sai dai bansan ya akai ba naga mahaifinka kadai a asibiti, sai dai inaji ko shi wani asibitin aka kaishi." Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya mike yace " sai da safe na gode." Bayan ya fito ya shiga mota ya jingina kansa da kujera, yana nazarin kalaman Uncle, mai zai sa Alhaji Isma'il ya fadamai sunan driver din mahaifinsa???? Ya dade yana tunani kafin yaja mota yai gaba. Nafi kam Little ta kawo mata kaya tare da mata kallan zargi, Nafi ta harareta tace " me kike tunani?" Little tai dariya tace "ah to abin naku dai ba kunya da alama daga ke har yaya." Nafi tai saurin fizgar kayanta tace " me mukai?" Little ta girgiza kai tace "hmm ko sai nazo nayi gashi? Ko kuwa ba tun yau ba aka bud'e?" Idanu Nafi ta zaro sannan ta d'au kayanta ta dan bigama Little tace "lalai wannan kanwar batada kunya, to wlh mu ba ruwanmu salahaine." Little ta rufe baki tace " hmm da alama kam." Nafi ta harareta sannan ta zura kaya suka fita tana kokarin kare kanta agun Little, ita kuma sai tunzurata takeyi. Ashraf yana dawowa gida yai sallah sannan ya kwanta akan kujera yana tunani, can wata idea ta fadomai hakan yasa yai bacci tare da tunani da fatan Allah ya taimakeshi gobe. Da safe ya shirya sun fita shida Dan litti, a hanyarsu ta office ya zaro wayar nan dake cikin jala ya saka number kawu sannan ya turamai sako kamar haka " Yallabai ina bukatar taimakon ka, kudin hanuna sun yanke. daga Auwal Max." Ya dade yana tunani kafin yai shahadar turamai, suna isa office ya kalli Dan Litti yace " ka tabbatar kabi Kawu duk inda zaije, jikina yana ban zai fito yanzu ka bishi duk inda yai." Dan Litti ya amsa da to, sannan Ashraf ya sauka, a hanyarsa ta shiga yaga kawu wanda yake kokarin saukowa daga beni, kallan mamaki yamai ganin yana cikin hanzari. Da sauri yasha gabansa, yace " Kawu sai ina haka?" Kawu ya dan yi murmushin yake yace " akwai aikin dazan je dubawa ne a construction site." Ashraf yamai kallan zargi yace " Hmm naga ne ka fito ba tare da Secretary dinka ba." Kawu yad'an juya kai sannan yace " yana mota yana jirana." Ashraf ya jinjina kai tare da cewa " shekanan a dawo lafiya." Nan yai gaba, kawu ya kalla yaga yana sauri, waya ya daga ya kira Dan Litti yace mai ya tabbatar yabi kawu gashinan ya fito. Ashraf office din kawu ya wuce yai knocking, kamar yanda yai zargi Secretary dinsa ne zaune yana rubuce rubuce, Ashraf yai murmushi sannan yace " Cigaba da aiki dama gun Kawu nazo." Ya mike tare da cemai, bayannan yanzu ya fita, Ashraf ya jinjina kai sannan yace " amma ya akai ya fita shi kadai? Kana aikin ka kuwa?" Da sauri yai kasa dakai alamun ban hakuri yace " wlh nace zan bishi yace in zauna ba dadewa zaiyi ba." Ashraf ya juya ya fita batare da ya amsa ba. Ajiyar zuciya yai sannan yace " ya ga sakon?" Kawu kam yana fita duk ya rikice ganin tun bayan faruwar abun nan bai kara ma tunawa da wani Auwal Max ba bare yasa ran haduwa dashi, menene nashi namai sako yanzu? Rashin kudi? Unguwar Nasarawa ya shigaz yai parking a wani tangamemen gida sannan ya fito da sauri yai cikin gidan yana waya, Dan litti na ganin haka ya kira Ashraf ya sanar dashi ya shiga wani gida. Ashraf yai murmushi tabbas gun wanda suka hada abun yaje daga ganin sako, yai murmushin ganin abun yazo mai da sauki yace " zaka gane gidan?" Dan litti yace " Yes Ma!" Ashraf yai dariya yace " nine Ma?" Dan litti shima yai dariya yace " ganinai tun da ka tashi yau bakai dariya ba shiyasa na saka." A tare sukai dariya kafin Ashraf yace " bayan La'asar kazo mu tafi." ********** Nafi kam ganin Little ta fita skul, yasa taji gidan shiru, dan ma tanata latsa wayarta can ta mike da niyyar zuwa kitchen, a kofar falo suka had'u da Habib, mamaki ya kamata tace " Ya Habib?" Ya sakar mata murmushi yace " Gimbiya i really miss u." Kallan mamaki tamai sannan tace " ni?" Ya d'an hade rai, zai yi magana tai saurin cewa " Little tana makaranta bakuyi waya bane." Ya hade rai yace " cewa nai gunta nazo?" Ta zaro ido tace " inba gunta kazo ba,gunwa kazo to? nadai san ba guna kazo ba." Ya kalletq yace " taya kika san haka?" Tai murmushi tace " haba ya Habib ina nakai wannan matsayin?" Yai ajiyar zuciya sannan ya mika mata leda yace " tsarabarki ce ta Abuja." Ta amshi kayan tana mai kallan mamaki, bata samu tai magana ba taga ya juya yai gaba, ta dan tabe baki tace " Tsarabar Little dai." D'aki ta maida kayan ba tare da ta bude ba sannan ta fita tai kitchen. ****** Ashraf sai yamma bayan sun tashi Dan litti ya wuce dashi gidan da kawu yaje, tun a kan hanya dayaga sun dau kwanar Nassarawa G.R.A yaji gabansa nafaduwa, addu'a kawai yake yi a ransa Allah yasa ba inda yake tunani zasu ba. Tsoronshi ya kara daduwa ne sanda yaga anyi kwanar gidan, idanu ya runtse cikin tsananin tsoro, Dan litti yai Parking sannan ya kalli Ashraf yace " Mun Iso." A hankali Ashraf ya bud'e idanunsa gabansa ne ya yanke ya fadi, da sauri ya fito daga mota yana girgiza kai alamar ba haka bane, ya kalli Dan litti yace " ka tabbatar nan yazo?" Kai dan litti ya d'aga alamar haka ne, Ashraf ya dafa kansa cikin tsananin tsoro can wata zuciyar tace " mayb baiga sakonka ba." Jiyai ance " Buddy." Da sauri ya juya Habib ya gani ya fito daga gidan da saurinshi, yana karasowa ya rungumeshi yace " Ayya Aminina da alama jikinka ne ya baka na dawo ko?" Ashraf ya d'an yi yake yace " lalai kasha hanya." Habib yace "sosai ma, dan ma naje naga gimbiya." Kallan mamaki Ashraf yamai,Habib ya katseshi da cewa " muje ciki ku gaisa da Dady kasan yace sam baka zuwa gunsa, gashi kullum sai ya tambayeni kai." Ashraf yai murmushi sannan yace " muje to." Jikin Ashraf kamar wanda aka zubama ruwa haka yake tafiya, sunje shiga ya kalli Habib yace " dama Dady da Kawu suna shiri??" Habib ya dafashi yace " me kake fada, ka manta Dady baya shiri da Kawu har bayan auren Mumy." Ashraf a ransa yace "then y??????" Jansa Habib yai suka shiga ciki. Dady na zaune yana karanta jarida yana ganin Ashraf ya mike cikin tsananin farin ciki yace " wa nake gani kamar d'ana da baya nemana???" Ashraf yai murmushi ya karasa gunsa yace " Dady na sameku lafiya?" Dady ya zauna tare da nuna ma Ashraf kusa dashi ya zauna, Ashraf ya girgiza kai sannan ya zauna a kasa wajen kafarsa yace " Dady ina wuni?" Dady ya dafashi yace " Ashraf nida d'ana amma ganinsa ya min wuya?" Ashraf yai murmushi sai dai a ransa yana kara kallan Dady da tunani kala kala dake yawo a ransa, can yace " Dady kasan aikin namu ne sai a slow." Dady yai murmushi yace " to ya za'ayi dama komai sai hakuri." Habib dake zaune yace " wato Dady kaga Ashraf ka manta dani ko? Dama kullum tambayar ka ya Ashraf yake? Wani aiki yakeyi yanzu? Me yakeyi? Wa da wa ya hadu da d......." Da sauri Dady ya katseshi da dariya yace " kai kuwa ba dole inji halin da dana yake ciki ba?" Ashraf yai murmushi a ransa yace " shiyasa kake barin Habib ke zuwa kwana akai akai saboda kasan me nakeyi???sai dai akan me? " Nima nace lalai fa akan me kenan? Soyayyace ta 'yan uwa ko akwai wani b'oyayyen al'amari a kasa???? Hmmmmmmm *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *62* Nafi kam yana fita ta gyara d'akin sannan ta fito kamar munafuka ta nufi bangarensu, a hankali take tafiya taje kwanar da zata shiga part dinsu taji ance " kan bala'i daga ina kike?" Gabanta ne ya fadi ta juyo a hankali cikin tsananin tsoro, Umma ta karaso cikin huci tasa hannu ta fizgota Nafi ta fadi a kasa. Umma ta kalleta tace " daga gidan ubanwa kike da safen nan???" Nafi ta kalleta tace " ba daga inda nake kawai dai na fito ne." Umma ta nunata da yatsa tace " ke na miki kama da sususu??" Cikin mamaki Nafi tace " Sususu??" Umma ta kara hasala tace " badai a bangaren Ashraf kika kwana ba?" Kasa Nafi tai da kanta da sauri. Cikin tsananin fishi umma tasa hannu ta mangareta da karfinta tace " 'yata tana can ta kasa bacci tabar mijinta saboda ke, ke kuma kinsamu wannan damar kina neman maye gurbinta." Nafi ta d'ago ta kalleta, Umma tace "me? Zaki ramane?? Uban me kikaje yi a bangaren 'yata?" Nafi ta ki dauke ido daga kanta bata kuma bata amsa ba, a zahiri bazata juri dukan nan ba haka kawai ba gaira ba dalili. Umma ta rike haba tace " ke ni kikema wannan kallon??" Nafi tai shiru. Umma ta sa hannu ta kara mangareta tace " dauke idanunki daga kaina." Nafi kam ko gizau idanun nan nakan Umma. Takaici ya kara rufe Umma tasa hannu biyu zata rufe Nafi da duka. Da sauri Nafi ta matsa sannan ta kalleta tace " Umma a matsayina na matar Ashraf banaji zan yarda ki cigaba da dukana kamar wata baiwa." Umma tai sototo tana kallan Nafi, cikin hasala tace " in baki tsaya ba me zakiyi?" Nafi tace " ni dai ki daina dukana, sannan ni ba bangaren 'yarki naje ba bangaren mijina naje, ba kuma naji nayi laifi dan naje can." Tana kaiwa nan ta mike davkyar sakamakon jikinta ta cigaba da dingisawa tai gaba, kallan kafafuwanta Umma tai nan danan ta fahimci komai, tsoro da fargaba suka kamata. Itakam Nafi a hankali ta bud'e kofarsu ta shiga, tana dagowa da niyar ganin Little ko tana bacci, taga Little a tsaye a gabanta daure da towel. Nafi ta zaro ido ta juya da sauri. Little tace " da alama nan gaba kadan zaki gudu daga nan tunda yanzu kunfara dan waken zagaye ke da yaya." ta juya tai toilet." Nafi tadan rufe bakinta sannan ta zauna a gefen gado. Bayan Little ta dawo Nafi ta kalleta tace " kinga sakon ki?" "sakon me kenan?" Nafi ta nuna mata da hannu tace " Ya Habib." Da sauri Little ta mike ta zanyo jakar, ta hau bud'ewa, turaruka ne da wani lace mai masifar kyau, sai dan kunne da sakarsa silver. Little tace " jiya yazo?" Nafi ta daga kai alamar eh sannan tace " do u like him that much?" Little tai murmushi tace " Ni kaina mamakin kaina nakeyi, amma bakya ganin shima yana sona?" Tausayinta ya kama Nafi, Nafi tai yake tace " kin fadamai tsakanina da yaya?" Little ta girgiza kai, Nafi tace " ki fada mai, kar yaji a gari." a ranta tace mayb inyaji ya shiga hankalinsa. Little ta d'aga kai alamar to sannan ta cigaba da shirin makaranta. *********** Umma kam a zuciye tai bangaren Mumy, ko gaisawa bata bari sunyi ba tace " Ruma hankalinki daya kuwa?" Mumy ta kalleta tace " ban gane wannan banzan zancen ba." Umma ta kara yin hucci tace " wai danki yagama fin karfinki ne? Ko kuwa kin sallamashine yabi duniya?" Mumy wacce kalaman Umma suka bata mata rai tace " wani irin banzan zance ne wannan, taya zakizo har d'akina ki dinga fadar magana irin wannan wacce batada ma'ana." Umma ta tabe baki tace " a ido ne kike nuna mana bakyasan wannan tsinaniyar yarinya ko kuwa har ranki?" Mumy cikin kunar rai tace " har raina mana kema ai kinsani." Umma tacigaba " to in bakiyi wasa ba zaki samu jikar daji, wanda rabin asalinsa ya kasance kidahumin bafulatanin da ko hausa bai sani ba." Mumy tace " banasan kunbiya kunbiya me kike san fada." Umma tace " yarinya ta fara kwana a bangaren Ashraf sannan har jiya ya aikata abinda yakeso, ke wai a sunan uwarsa amma bakisan komai ba sai zaman daki kamar wata gumba." Mumy ta kara hasala tace " inkin gama zaki iya fita ai ko." Umma ta juya cikin takaici tai waje. Zama Mumy tai a bakin gado ta dafa kanta tace " Ashraf!!!!!!" ********* Shikam Ashraf yau ya koma sabon office dinsa a matsayinsa na Chief Director, Kawu dan ya nuna ma mutane yanasan Ashraf da kansa yazo wai zai tayashi murna. Bayan ya shiga ya kalli Ashraf yace " Congratulation d'ana." Ashraf ya kalli Mutanen gun ciki harda Asim sannan shima ya mikamai cikin fara'a, bayan sun gaisa ne Ashraf ya matso kusa dashi yace " thanks but not yet." Kawu ya kalleshi yace " what du u mean?" Ashraf ya sake murmushi sannan ya kara matsowa yace " in naje office din Chairman na Company din nan at that time zan amshi taya murnar ta ka." Kawu ya zaro ido cikin mamaki, ya kalli Ashraf wanda ya sake hannunsa ya karasa ya cigaba da gaida mutane Kamar ba'ai komai. Asim kam a zuciye yai waje ran nan nasa a b'ace. Shikam Ashraf ko a jikinsa suna fita ya zauna sannan yasa waya ya kira Dan Litti, ba'a dade ba sai ga Dan Litti nan yazo. Ashraf yace " Dan Litti inaso daga yau sunanka ya koma Auwal Max, sannan ka fadama mutane hakan sunanka yake, ni kuma yanzu inka fita inaso kaje inda Kawu yake zansa a kiramin kai." Dan litti yamai kallan mamaki sai dai bai tambaya ba sai yes sir dayace. Ashraf yace sainya kira ka sau uku zaka amsa. Yana fita ya shiga neman kawu can ya gashi a sama sai ya wayance da aiki a gun. Shikuma Ashraf dama dan litti na fita ba dadewa ya tura masingansa akan ya nemomai driver dinsa sunan sa Auwal Max in ya ganshi ya kira sunan da karfi. Nan masingan ya amsa sannan yai waje. Dan Litti yana tsaye, gefe kuma kadan Kawu ne tsaye da Asim. Kawu ya kalli Asim yace " kai wai meke damunka??" Asim yace " da akai me kenan?" Kawu ya hade rai yace " ba nace ka dinga kokarin boye emotion dinka ba? So kake kowa ya gane bakasan matsayin da Ashraf ya samu yanzu?" Asim ya hade rai yace " Abba wai ni haryanzu bakamin bayani ba akan wani dalili ne zaka ba waccan yaron matsayi haka? Baka tsoron abinda zai aikata? Ko kuwa yanzu ka dawo kana bin bayansa ne?" Kawu ya bud'e baki zai magana yaji ance " AUWAL MAX!" Cikin tsananin firgice har da sakin takardun hannunsa ya fara waiwaigawa. Masinja ya kara kwalla kira, Kawu ya rikice yana kalle kalle, Dan litti ya zubamai ido, shikansa Asim sai daya fahimta yace " Abba lafiya?"" Kawu kam sai dudubawa yakeyi baiga alamun wanda yake zargi ba duk ya gama rikicewa, sako ne ya shigo wayar dan litti. Yana dubawa yaga sakon Ashraf akan kar ya amsa yaje kusa da masinja din kawai su taho. Haka kuwa akai, Kawu ya duk ya gama rud'ewa dajin wannan suna shikuma Dan litti yaje yaja hannun masinja sukai gaba. Dan litti ya shiga gun Ashraf ya sanar dashi halin da Kawu ya shiga daga jin sunan. Ashraf yai murmushi yace "jeka na gode." Bayan ya fita Ashraf yai shiru yana tunani kafin ya dauko wayarsa ya danna number Dadyn Habib." Bayan sun gaisa yace " Dadyn nikam dan Allah tambaya, kasan wani Auwal Max?" Gaban Dady ne yai mugun faduwa duk yadda yaso ya daure sai da muryarsa ta canza cikin rawar murya yace "Auwal Max?" Ashraf yai dan dariya yace " eh wlh, jiya ne akamin sako akan wai anasan magana dani wai driver din Abba ne Auwal Max, shine nikuma nake tunani kar inje karya yake sannan ni bangama dalilin haduwar mu ba nace bari na kiraka." Dady yai sauri cewa " Don't meet him." Ashraf yace ' naam?" Dady yace " hmm karka yadda Ashraf ku hadu da mutumin da baka sani ba, wayasa me zai maka? Ko mugu ne??" Ashraf ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " nima abinda nake tunani kenan, shiyasa nace bari na kiraka." Dady yace " yauwa Ashraf kayi tunani mai kyau." Nan sukai sallama, Ashraf ya kankance ido tare da yin hucci yace " How can u do this to me???? Tayaya duk a cikin mutane ace kaii!!! Har da......" Kasa karasawa yai ya sa hannu ya rufe fuskarsa. *ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 _*MY INTIMATE FRIEND AISHA MUHD UMAR*_💞 *As it's a special day for My Intimate Friend, i just can't express how happie i am today, It's ur wedding day, the day 5th August have become a memorial day for us.* *Allah ubangiji ya baku zaman Lafiya da zuri'a dayiba Ameen suma Ameen* *63* Ashraf yana fita ya wuce gidan su Ferry, yayi sa'a kuwa a lokacin Mahaifin su Ferry ya dawo. Tare suka shiga gidan bayan sun gaisa Isma'il ya kalli Ashraf yace " banyi tsammanin ganinka da wuri haka ba." Ashraf ya dago cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa yace " Kasan komai ko kuwa kaima bincike kakeyi??" Isma'il yai murmushi yace " Bansan komai ba sai dan abinda ba'a rasa ba." Ashraf yai dan huci kadan yace " Auwal Max a ina zan sameshi??" Kai ya girgiza yace " bansan inda yake ba, tun wannan ranar, in fact banmasan ko yana raye ba ko ya mutu, sai dai nasan abu d'aya tabbas shine wanda yaja Alhaji a wannan ranar sai dai abin zargi shine sun fita daga gida tare amma daga baya danai bincike sai naji Alhaji ne kawai a cikin motar sannan a bincike nane na gano Auwal Max mai gadi yana kallansa sanda ya shiga kasan mota, hasashe na ne yasa nasan yayi wani abu bawai proof gareni ba." Ashraf ya matse hannunsa da karfi, tare da runtse ido yace " Shi Abban a ina ya san Auwal max din?" Isma'il ya kara girgiza kai yace " bansani ba, sai dai tun da nasanshi tare nake ganinsu, sai dai a koda yaushe inaji kamar bawai zuciya daya yake zaune da Abbas ba ganin duk wani plan indai mukai kafin mu aiwatar sai muji shi a gari ance Muktar yayi, shi kuma Abbas ba ya kara tada zancen." Ashraf yace " Daga bangaren mahaifiyata akwai wani abu da kasani na gaba ko wani abun a tsakaninsu??" Isma'il ya dan shafi goshinsa sannan yace " akwai case daya faru wanda ya jawo asarar dukiya mai yawa daga bangaren matar Abbas." Idanu Ashraf ya zaro yace " case?? Wani iri kenan?" Isma'il ya girgiza kai yace " i can't tell u, sai dai kai ka nemo menene." Ashraf yai shiru yana tunani, sun danyi shiru kafin daga bisani Ashraf yamai sallama. Yana fita ya shiga mota tare da sa kansa a sitiyari wani irin zafi yakeji zuciyarsa namai. Ya dade kafin ya daure ya tada mota yai gida. ********** Nafi kam yau sam bata fita ba tana kwance a d'aki gani take kamar in ta fita za'a gane abinda ya faru daren jiya. Bayan magrib tai sallah tana zaune ita da Little sukaji ana knocking. Little ta tashi ta bud'e, Mumy ce ta shigo fuskarnan tata a b'ace. Little tace " Mumy ya akai?" Bata kulata ba ta karasa gun Nafi wacce cikinta har ya duri ruwa, Mumy tace " Ki shirya gobe zansa a maidake garinku." Nafi ta zaro ido cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy, Little ta matso tace "Mumy wai meyasa kike haka ne? Matar yaya ce fa....." Tsawa mumy ta mata tace " fita." Little mamaki ya kamata ta fita da sauri, bangaren Ashraf ta nufa tana zuwa tahau bugawa, shiru da alama bai dawo ba gashi ta bar wayarta, jiki a sanyaye ta dawo nan ta hangoshi daga nesa. Da gudunta ta karasa gunsa, Ashraf ya kalleta yace " Little!" Cikin haki tace " Yaya Mumy ce." Yace "Mumy?" Ta daga kai tace "Nafisa...." Ai bai jira ta gama ba yai bangarensu da saurinsa. Yana zuwa bakin kofar dayake a bud'e yake yaji Mumy na cewa " Me zaki iyama Ashraf da har kike tunanin zamq matarsa? Ban yarda da wannan auren ba dan haka dole ne gobe ki koma kauyenku." Nafi kam hawaye ne kawai ke zubo mata. Muryar Ashraf ce ta daki kunnuwansu yace " Inji wa kenan?" Mumy ta juyo har zuciyarta sai dataji dan tsoro sai dai ta dake tace " injini ni mahaifiyarka." Ashraf ya karaso ciki yace " Do you hate us that much? Ni da Mahaifina nake nufi?" Idanu Mumy ta zaro cikin mamaki tace " me kake fada haka?" Yai murmushi yace " me? Ba tsantsar tsana bace yasa kike bakin cikin ganin farinciki na? Na sanar dake matatace, na dauka uwa mai san danta zataso farin cikinsa." Ya girgiza kai cikin takaici yace " sai dai me? Ban taba gani kinso abinda nakeso ba tun da na mallaki hankali na, in har nace gabas nake san yi to burinki kice kekuma yamma kikeso nai." Cikin murya mai zafi ya karasa maganar da cewa " inkinsan da haka meyasa kika auri Abba har kika haifine??" Nafi da sauri ta taso tazo kusa dashi ta dan turashi baya, idanunta na zubar da hawaye tace " Yaya me kakeyi hakan?" Mumy kam gaba daya jikinta ya gama mutuwa kamar wacce aka kwarama ruwan sanyi, Nafi ta cigaba da turashi zuwa waje tanacewa " please Yaya ka bari, kar kai fada da Mumy saboda ni dan Allah." Ashraf ya rike hannunta idanunsa suka kada sukai jajawur kamar jan gauta, ya kalli Mumy yace " na tabbata sanda mahaifina ya rasu kina daya daga cikin masu farin cikin faruwar hakan." Nafi kai kawai take girgizawa tana kuka, Ashraf na gama fadar haka ya fara jan hannun Nafi, har sunje bakin kofa ya juyo yace " in har baso kike nabar gidan nan ba kar ki kara shiga harkar matata." Ya ja hannun Nafi sukai waje, zubewa Mumy tai a gun ta rike inda zuciyarta take jin tana mata zafi ta saki wani irin kuka mai kuna. Ashraf kam jan Nafi kawai yake sunje yin kwana sai ga Anisa ta sha gabansu, ya buga mata wani kalli dan yanda yakejin zuciyarsa tayi sa'a ka da bai mareta ba, itama harararsa tai tace "anji kunya wlh kwartanci da ranar Allah, to wlh baku isa ba naga uban da zai maye min gurbina." Ashraf ya kalleta cikin tsananin bacin rai yace " gurbin inaji nine nake rike da ragamarsa ko? To mai zai faru in na sallami mai gurbin?" Idanu Anisa ta zaro tace "mai kake nufi Yaya?" Yace " zaki matsa ko sai na fahimtar dake abinda nake nufi??" Da sauri ta matsa ya ja hannun Nafi sukai bangarensa, bai saketa ba sai da suka shiga d'akinsa ya kalleta cikin tausayi ya runtse idanunsa, ransa na kara soyuwa, baya ya juya mata yana wani hucci da sauri da sauri. Nafi da sauri ta matso ta rungumeshi ta baya, tasa kanta a bayansa tana kuka tace " Yaya please cool down, me yasa ranka zai baci akan abinda baikai ya kawo ba??" Idanu ya runtse yanajin wani abu na tasomai a ransa yace " ina zaki gane bayan wani bangaren na sanar dani harda Mumy a salwantar da mahaifina, tunda nasan abu ya hadasu da danginta." Nafi ta kara kankameshi ta baya tace " Yaya Mumy fa ba wai tsanar ka tai ba, ka taba ganin inda uwa taki danta? Ni inaji a jikina akwai dalilinta na yin haka." Idanu ya sake runtsewa, Nafi ta zagayo ta gabansa ta rungumeshi tace "please yaya kadaina fadamata magana mai zafi haka tun balle in akainane." Hannu yasa ya zareta daga jikinsa yace " Nafisa, kinsan ya nakeji a raina? A duk lokacin da matar nan tamin haka? Tun da nake da ita bata taba san abinda nakeso ba, bata taba yarda da abinda nace ba, bare in nemi kulawarta ko shawararta." Hawaye ne ya zubo mai, Nafi kam hawayenta sai tsananta gudu suke yi, da sauri Ashraf ya juya dan bayasan taga hawayensa. Kara rungumeshi tai tace " Yaya fitar da duk abinda ke ranka, inaji kamar abubuwan da kake hadiyewa sunyi yawa, shi hawaye rahama ne in kayishi yanasa bakin cikin mutum ya ragu, sannan maganar Mumy ni dai inaganin da wani abu." Ashraf ya hadiye hawayensa yabar idanunsa a runtse, Nafi ta dago a hankali ta danyi dage ta sumbaci bakinsa kadan, tace " i am here with u, ka daukeni a matsayin mutum mara ji mara magana, ka fadi duk abinda kake boyewa a ranka ko ka samu sauki cikin ranka, Yaya na kula bacci ma bakayi yanda ya kamata, kuma ni nasan duk saboda abubuwan da kake hadiyewa ne kai kadai." A hankali ya bud'e idanunsa ya jawota ya rungume tsam, yace " Nafisa I really Luv u." Dagowa tai cikin mamaki, ya kara kankameta yace " kece mace ta farko ko ince mutum na farko da nake jin tabbas wannan itace, itace wacce takesona tsakani da Allah, itace wacce ta yarda dani, itace wacce zuciyata ta aminta da ita, itace nakeji in har tana tare dani i can endure everything." Ya dan yi ajiyar zuciya yace " ban taba tunanin zan taba jin mutum haka a raina ba, ban tabaji na aminta da mutum haka ba, Nafisa please don't ever betray me" Wani hawayen dadi ne ya zubo mata kai kawau take girgizawa tace " How can I! How can I......." Sam ta kasa karasawa ya dago a hankali ya kai bakinsa cikin nata...... _Ni kaina idanuna yau sun ciciko, tabbas Ashraf yaga rayuwa ko ince yana gani, babu abu mafi soyuwar zuciya da kunci irin ka rasa wanda zaka aminta dashi, ka rasa wanda zakai shawara dashi, ka dinga ji kamar kowa na kusa dakai nemab ganin bayanka yakeyi_ Allah ya tsaremu daga sharrin mutum domin kuwa sharrinsa yafi na shedan. Ameen *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *64* Kwance suke tare a kan gado tana makale a jikinsa sun shiga bargo, fitilar d'akin a kashe take sai ta gefen gado da take a kunne, sunyi shiru sunajin dumin junansu. Cikin sanyin murya Ashraf yace " Nafisa." Tana kan kafadarsa tace " Naam." Yacigaba " Abba hatsarin dayai a kwai hadin baki a ciki." Da sauri tai nufin mikewa yasa hannu ya maidata yanda take, shiru tai sai dai gabanta sai faduwa yakeyi, yacigaba " bansan takamaimai dalilin dayasa Abba ya tsole musu ido ba ko ince suka tsaneshi ba sai dai gobe nake sa ran tambayar Uncle Salim in har shima bai sani ba sai inyi bincike da kaina." Nafi tai shiru, Ashraf ya cigaba " tun dana mallaki hankalin kaina nakejin komai ba daidai ba a gidan nan, sam na kasa yarda da yanda al'amuran gidan nan ke tafiya." Nafi ta makalo hannunta ta kwibinsa a hankali itama tace " Yaya ni kaina bayan Little taban tarihin gidan nan na rasa dalilin dayasa na kasa fahimtar abubuwa guda uku." Ashraf yace " me da me kenan?" Ta gyara kwanciyarta tace " Mumy inaji a jikina akwai dalilinta na auren kawu cikin gaggawa." Ashraf yai dan karamin tsaki yace "ba wani dalili dama kila can shi takeso ta yaudari Abba." Nafi ta girgiza kai tace " karka bari zuciyarka ta nemi boyema gaskiya." Kai ya dan kawar gefe sannan yace " next." Tace " Meyasa kafin Abba ya rasu yafi zama dakai, naji hatta aiki ba fita yake ba kullum kuna tare dashi, nasan zai iya yiwuwa jikinsa ne yake bashi hakan sai dai yanda baya zama da kowa sai kai yasa nake tunanin da wani abu, ko yasan akwai manakisar da akemai ko kuma akwai wani dalili da mu bamu sani ba." Shiru Ashraf yai yana tunani, Nafi tacigaba " nakarshe karkace kishi ne ko wani abun sai dai inaganin tayaya Abba dayakesan ka auri yaya nisa zai bada wasiyya akan aba matarka ta farko? Indai har yaya nisa yake so ta zama matarka banaji sai yace matarka ta farko sai dai kawai ya bada yace abawa Yaya nisa in aurenku ya tashi." Shiru Ashraf yai yana tunani lalai wannan abun tambaya ne, Nafi tace " nayi mamaki danaji wasiyyar ta kudi ce ganin ba kudi kuka rasa ba,banaji akwai dalilin dazai sa Abba ya bada wasiyyar kudi." Ashraf yai shiru yana tunani, Nafi ta matso da kanta tace " yaya karka damu da abubuwan danace, zargi nane kawai ba wani abu serious ba." tafada tare da kara shiga jikinsa. Ashraf yai shiru yana tunani, ganin haka yasa Nafi tai bacci, sai daya tabbatar tayi bacci sannan ya jawo littafinsa ya zare jikinsa a hankali ya nufi falo. Can tsakiya ya bud'e inda yaga Abba yasa " Baban burina bai wuce naga na hada zuri'a da Muktar ba." Shiru Ashraf yai ya dade kafin ya dawo ya kwanta. Da sassafe kuwa bayan sunyi sallah sun kwanta sai daya jira tai bacci sannan ya zare jikinsa yai waje. Mota ya fada yai waje. Gidan Uncle ya nufa kafin ya karasa ya kirashi a waya yace " dan Allah ya fito waje zasuyi magana ne." Yana zuwa kofar gidan kuwa yaga Uncle a tsaye. Ashraf ya karasa suka gaisa sannan yace " Uncle zaka iya tuna me ya faru tsakanin Abba da dangin Mumy kafin ya rasu." Uncle ya kalleshi yace " Ashraf a ina....." Hannu ya hade gu daya alamar toko yace " dan Allah kafadamin Uncle, nasan ba yanda za'ai case ya hada su da Abba ace lawyer dinsa baisan komai ba." Uncle yai ajiyar zuciya yace " mu shiga motarka." Nan suka shiga, Uncle ya kalleshi yace " Ashraf mai nene dalilinka nasan jin abinda ya riga ya wuce?" Ashraf ya kalli Salim cikin zakuwa yaji yace " ba komai kawai so nake naji ne." Salim ya jinjina kai sannan yace " Mahaifin Ruma ya fara kasuwanci bayan yayi retire, ko da yake ba wai fara wa yai ba dan dama Hashim(mahaifin Habib) dan kasuwa ne, kasuwancinsu ya bunkasa alokacin da Abbas arzikinsa da matsayinsa yai fice a garin nan. Bazan manta ba bayan ka gama nursery ka shiga primary 1 wannan mumunan al'amari ya faru. Hisham da mahaifinsa sukayo dealer din kaya mai uban yawa wanda ya kunshi kusan duk arzikinsu, sai dai kaya aka hanasu shigowa, Customs suka rike musu kaya gaba daya container's dinsu. Ba karamin tashin hankalu suka shiga ba duk yanda sukai a barmusu kayansu su wuce amma ina... Sam abu yaki yiwuwa." Ashraf ya kalli Salim cikin mamaki yace " sunyo order din abu mara kyau ne?" Ajiyar zuciya Salim yai yace " Kwarai kuwa sai dai sun b'oye hakan, ganin ba yanda za'ai kayan su ya fito ga dukiyarsu duk tana ciki yasa mahaifin Ruma ya yanke jiki ya fad'i, tashin hankali ya kara tsananta. A wannan lokacin nan Hashim ya samu Abbas yace ya taimaka suyi cuwa cuwa a sakar musu kayansu, Abbas mutum ne mai tsaurin gaske jin Hashim ya zo mai da wannan uzuri yasa ya mai duban kurila yace " Hashim mai kuka sako a cikin kayanku?" Ran Hashim ya baci yace " ko ma me muka sako ai ya zamarma dole ka taimakemu ganin mune muka samar ma aiki har kakai matsayin da kake yanzu." Abbas yace " bai zamar min dole ba dan kuwa in har abinda kuka d'auko akwai abin cutarwa to wlh ko d'ana Ashraf ne bazan taimaka mai ba." Nan dai suka rabu zuciya ba dadi, bayan Abbas yayi bincike nan ne ya gano mugayen abubuwan dake kasan kayayyakinsu, ciki kuwa har da hodar iblis da 'yan kanananan makamai." Ba karamin tsorata Abbas yai ba ya samu Hashim cikin tsananin fushi yace " Hashim da hankalinka zaka saro wannan mugayen abubuwan?" Hashin cikin zafin rai yace " ce maka akai nawa ne? Na wani abokin Abba ne dan majalisa ne yace mu taho mai da sakonsa." Ran Abbas ya sake b'aci yace " to meyasa shi baiyi magana an sakar muku kayan ba?" Hashim ya dan shafi kansa yace " tun bayan faruwar abin nan yabar kasar ma gaba daya, ba yanda zamuyi mu sameshi." Abbas yace " kanaso kacemin kaf mugayen abubuwan nan ba naka ko na Abba ko daya a ciki?" Hashim cikin hasala yace " akwai mana, bayan yace mu taho mai dashi nima nai tunanin sawa a dan samomin jin yanda suke da tsada sosai." Abbas ya bud'e baki cikin mamaki yace "Hashim kanka daya kuwa??" Hashim ya mike rai a b'ace yace " me? Yanzu dan ka zama babban mutum kana tunanin zaka wulakantamu? To wlh kayi kadan dolene kaje kasan yanda zakai su sakar mana kaya." Yana kai nan ya nufi hanyar waje, daidai nan Ruma na kawo kai, Abbas ya mike yace " ba dole a ciki, sannan tunda dai bakuji kunyar cutar da mutane ba banaji nima ya zamarmin dole na bi bayanku, kasan inka sai da hodar da makaman wadanda za'a cuta dasu? Kasan bayin Allahn daza'a halakar dasu?mai makon ma ka dauki laifinka akan kuskuren dakai sai ma gani kake baka aikata komai ba?" Hashim ya kalli Ruma yace " ke Ruma!" Mumy ta kalli Yayanta cikin tsoro, yace " wuce mu tafi gida, da alama Abbas ba sanki yake ba inhar bazai taimaki mahaifinki dake kwance a gadan asibiti ba saboda wani shirme can da zuciyarsa ke sanar dashi ba." Nan yai waje Ruma tabi bayanshi. Abbas yai shiru yana mamakin wannan al'amari, sai dai tabbas in har zai taimaki Hashim to lalai sai ya yi nadamar abinda ya aikata." Ashraf ya kalli Salim jin yayi shiru, yace " Uncle sai akai yaya?" Salim ya goge gomin daya keto mai yace " anyi haka da kwana d'aya Allah ya dauki ran mahaifin Ruma, wanda kuma shock din mutuwarta ya kwantar da mahaifiyarta ta samu ciwon paralyze." Idanu Ashraf ya zaro tsananin tsoro ya kamashi, Salim yai ajiyar zuciya yace " Abbas yayi dana sani sosai nakin taimaka musu da wuri, shi kuma yana ganin dolene Hashim yayi nadama saboda gaba. Sai dai faruwar wannan mumunan al'amari ya tada hankalin kowa, yayi nadama takin karawa gani yake daya taimaka da wuri Abban Ruma bazai rasu ba, haka ma Mahaifiyarta bazata kwanta rashin lafiya ba. Sanda Abbas yaje gaisuwa Hashim ya sanar dashi kada ya kuskura yasa a saki kayan basa so sun kuma fahimci abinda yake nufi." Yai dan hucci sannan yace kaji abinda ya faro. Ashraf banda Inalilahi wa Ina ilaihi Raji'un ba abinda yakeyi. Can ya daure yace " Nagode Uncle." Salim har ya bud'e kofa zai fita Ashraf yace " Maganae wasiyae Abba ta matata ta farko fa? Kasan dalilin sa nayin hakan?" Salim ya girgiza kai yace " bansani ba gaskiya sai dai nasan ana gobe zaiyi hatsari kunyi tafiya dakai dashi da malam kunje kauyuka bada taimako, yana dawowa a daren ya bani wannan takardar." Ashraf yai ajiyar zuciya sannan ya kara cewa Nagode. Salim har ya fita ya dawo yace " karfa ka kawo komai a ranka, kasan Hashim na sanka." Ashraf ya daga kai alamar to, Uncle na tafiya ya kwantar da kansa a jikin kujera yana fitar da numfashi sama sama....... *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *65* A hankali yaja mota ya nufi office ji yake numfashinsa na fita da sauri da sauri dole yai parking a gefen titi tare da kwantar da kansa kan kujera, waya ya dauka yama Dan Litti text din inda yake sannan ya maida kansa jikin kujerar. Nafi kam karfe 7 ta tashi saboda tanasan Ashraf yai break kafin ya fita, sai dai me? Bataga kowa a kusa da ita ba hakan yasa ta fito falo da sauri, nan ma ba Ashraf, ta zauna akan kujera tare da kiran numbersa, sai data kusa katsewa sannan taji ya daga cikin wata irin murya mai tsoratar da mai sauraro yace " Hello!" Mikewa tai a tsorace tace " Yaya menene? Me ya sameka?" Sama sama takejin numfashinsa ganin yanda ta rikice yasa yai saurin katse wayar. Zubewa tai a kasa tanajin zuciyarta tana kuna, hawaye ne ya zubo mata ta dafa kanta tace " wannan wani irin masifa ce? Ya Allah ka dubi wannan bawan naka ka sassautamai ka agazamai." Kara kiran wayar sa tai saima tajita a kashe. Mikewa tai da sauri ta nufi bangaren Mumy ba tare da tunanin komai ba. Mumy kam tana zaune kan sallaya tana kallan su Afra sun gama shiryawa zasu tafi makaranta, ta musu sallama sukai waje suna fita ita kuma Nafi tana shiga, Mumy cikin mamaki ta kalleta. Zubewa Nafi tai a gabanta idanunta na zubar da hawaye tace " Mumy dan Allah ki tausaya wa Yaya ki sanar dashi dalilinki nakin shiga harkarsa da kulashi da nunamai soyayya " Mumy ta buga mata wani kallo zatai magana Nafi ta katseta da sauri tare da hade hannayenta cikin sigar roko tana kuka sosai tace " kin taba tunanin yanda yake bacci da yanda yake rayuwarsa? A da na dauka ina cikin bayin Allah wanda suke bukatar a tausaya musu sai dai yanzu na fahimci cewa nice ya kamata in tausayama wasu badai a tausayamin ba, duk wahalar danasha a kauye har yaya ya tausayamin banaji nakai kashe 10 acikin 100 wanda yaya yake fuskanta" Tadan ja hanci sannan ta cigaba " He is so lonely, mutum ne wanda bai yarda da kowa ba sai kansa,Mumy nasan har kasan ranki kina tausayamai sai dai shi akullum kina daya daga cikin mutanen da suke bakin ciki ga rayuwarsa gani yake ba sanshi kike ba, kema kina daya daga kashe 20 bisa 100 na bakin cikin sa da damuwae dake ransa." Nafi ta kara matsowa tana kuka tace " Na rokeki Mumy ki tausayama wannan marayan Dan naki ki sanar dashi dalilinki na mai haka ki kuma ja shi a jiki, mutum ne wanda bai san dadin uwa ba." Idanun Mumy ne suka ciciko, Nafi tai kasa da kanta tare da share hawaye tace "indai nice bakyaso zan bar Yaya har abada zan koma kauyenmu sai dai dan Allah ki duba darajar Allah ki sassautama wannan dan naki, maraya ne shi kice gatansa in har kika nuna bakyasan jininki waye zai soshi? Na rokeki Mumy dan Allah........" Kuka ne ya kufce mata kawai ta kifa kanta akasa tana kuka, da sauri Mumy ta mike tai cikin daki, a bakin gado ta zauna itama tana kuka. Nafi kam ta dade agun kafin ta tashi a hankali tai waje, taje fita daga bangaren sai ga Anisa. Sam bata kula da ita ba saboda hankalinta sam baya jikinta. Ji tai an bangajeta da karfi har tai baya tala tala kamar zata fadi, ta dago idanunta da suka sha kuka ta kalli Anisa. Anisa ta sa hannu ta daki kafadarta da karfi tace " me? Kuka kike dan ance dole ki rabu da mijina? Ko kuwa da kina tunanin banza ta shani ne?" Ran Nafi yakai kololuwa gun b'aci, ta kafe ta da wani mugun kallo, Anisa ta matso tace " ke? Ni kike ma wannan kallon?" ta fada tana kallan Nafi. Nafi ta ki dauke idanta, haushi ya kama Anisa ta daga hannu zata mari Nafi. Nafi ta rike hannun da sauri sannan cikin dakakiyar zuciya tace " kada ki kuskura ki kara tunanin dukana, nice matar yaya ta farko, balle kiyi tunanin na miki kwace, sannan uban me kika tsinana ma Yaya? Bakin ciki? Ko me? Tun da kike dashi kin taba kula da halin da yake ciki? Kin damu da cinsa? Sannan sai anyi magana kice ke matarsa ce?" Ta cillar da hannun Anisa tace " da rashin wayau ne yasa nabar Mijina a kulawar ki sai dai yanzu ni zan kula da abina, ni zan bashi hakkin da mace ke ba mijinta." Tana kai nan tai waje a fusace. Anisa kam kasa motsi tai mamaki da tsoron yanda yarinya karama ta kafeta da ido da kalamai takeyi. Tana shiga d'akinsu ta fada kan gado, Little ce ta shigo rike da flask na abinci a hannunta, Nafi ta kalleta haka kawai taji zafin ganin Little da kular abinci. Ganin kallan da take mata Little tace " Feenah menene?" Nafi ta share kwallar ta tace " Little me yasa bakya jan dan uwanki a jiki?" Little ta mata kallan mamaki tace " wani dan uwana kuma?" Kai Nafi ta girgiza alamar ba komai sannan ta maida kanta kan gado, yau zafin kowa takeji har ita kanta, yanda numfashin Ashraf ke fita da sauri ya kasa barin kunnenta idanu ta runtse cikin kunar zuci tace " Allah ka agazama wannan bawa naka." Nima nace Amin. Ashraf nanan a zaune Dan litti ya iso akan babur. Nan Ashraf ya mike ya matsa daya bangaren shikuma ya shiga. Kallansa Dan litti yai cikin kulawa yace " me ya faru?" Kai Ashraf ya girgiza akan ba komai sannan yace " mu tafi office." Sun isa Ashraf ya shiga office dinsa ya kule kofar tare da ba secretary dinsa umarnin kar abar kowa ya shigo. Takarda ya d'ako babba ya rubuta. ABBAS / | \ Muktar. | Hashim \ | / Rumah Auwal Mask??? Shiru yai yana kallab takardar kafin yace " komai yayi connecting da Mumy, yayanta, mijinta nada, mijinta na yanzu." Itama da ita aka dau fansa saboda suna ganin Abba ne sanadiyar mutuwar mahaifinta?? Da sauri ya girgiza kai yace " it can't be, mijinta ne Abba ai." Shiru yai yana tunani kafin ya mike ya dauko ruwa a fridge a kafa kai, sai daya shanye robar ruwan tas sannan yace " cikin d'ayan biyu, ko da ita akai ko kuma ba a san ranta akai ba." Waya ya dauka da sauri ya kira Dan litti yace " inaso kamin bincike akan dukiyar Alhaji Hashim inda mukaje rannan." Dan litti yace " amma tayaya?" Ashraf yace " zan turo maka number wani dan sanda kaje gunsa zai taimaka ma." Yana kai nan ya kashe, sai yanzu wani abu ya fado mai, in har dukiyar Dady gaba daya ya sata a cikin wannan dealer din da sukai tayaya ya farfado cikin kankanin lokaci? A iya saninsa ko makarantar da yake da ita tun daya taso ya santa, sannan tun da ya taso yasan Dady mai kudi ne. Hmmm Babbar magana. *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Wannan Shafin Sadaukarwa ce gareku My Asmy, My Asy Khaleel da Autar Hajiya, May Almighty Allah always guide u through the right path (Ameen)* *66* Nafi ganin tana ta kiran number Ashraf amma shiru yasa ta mike tai hanyar waje da sauri, Little ta bita da kallan mamak, me ke damun Feenah? Kitchen ta nufa da kanta ta shiga shiryama Ashraf abincin safe tana gamawa ta juye sannan ta fito tai bangarensu, wanka tai ta zura wata doguwar rigar abaya ash color anyi kwalliya da stones kalar silver a jiki, tayi kyau sosai. Little kam mamaki take tace " ina zaki wai?" Nafi tace " dan Allah so nake in zaki fita skul yanzu mu tafi tare ki ajiyeni a gun aikin yaya." Idanu Little ta zaro tace " kije kiyi me?" Tace " gun mijina zanje, hankali na bazai taba dawowa daidai ba sai naga halin da yake ciki." Little ta rike baki cikin mamaki tace " lalai Feenah kinyi nisa bakyajin kira, amma kina gani yayan bazai fada ba in kika je?ki kirashi a waya tukunna." Nafi tai ajiyar zuciya tace " da na sameshi a waya ai hankali na bazai tashi haka ba, sannan in ma yamin fadan zuwan ai dai a kalla na ganshi, bazanji haushi ba." Little ta jinjina kai tace " lalai Feenah wai a 'yan kwanakin nan ne kika mato haka akan san yaya ko kuwa dama can b'oyewa kike?" Nafi ta mike tare da rataya jaka karama mai dogon hannu tace " Little muje please kafin hankali na ya nemi goshewa." Tare suka fito Nafi ta d'auko abincin daga kitchen suka tafi. A hanya ko magana batayi fatanta kawai ta samu Ashraf lafiya, ganin batasan magana yasa Little ma tai shiru. A bakin company din ta ajiye ta tace " ko inzo in rakaki?" Nafi ta girgiza kai alamar a'a tace " zanyi tambaya." Nan Little tai gaba ita kuma ta nufi kofar shiga. Taje shiga taga wani wanda ba tantama tasan fuskar sai dai a ina?? Shi kam Dan litti kallanta yai sam amma bai ganeta ba, to dama ta ina zai gane Nafi kucaka da wannan? Tambayar sa tai tace " bawan Allah." Dan litti har yayi gaba ya dawo, tace " dan Allah office din Ashraf nake nema." Kallan mamaki ya mata lalai gata kamar mutuniyar arzuki ashe neman mijin wata tazo yi, ya had'e rai yace " ban sani ba, sannan yarinya karama bai dace da ke ba irin wannan rayuwar." Ya juya yai gaba, kallan mamaki ta bishi dashi bai dace da ita ba kamar ya? Shiga ciki tai ta sami wani security ta tambayeshi, nan ya mata kwatancen office din Ashraf. A hankai ta murda kofar ta shiga ta gaida secretary din sannan tace " gun yaya nazo." Kallan mamaki ya mata yace " yaya wanne kenan?" Tace " ya Ashraf kace mai kanwarsa ce." Secretary ya mike tare da knocking din kofar Ashraf, daga ciki Ashraf yace " ka manta nace banasan ganin wani in ba urgent bane?" Yace " yallabai kanwarka ce tazo." Ashraf cikin mamaki yace " Little?ba dai wani abun bane ya faru." Da sauri yace " ta shigo." Nan Nafi ta karasa tare da murda kofar ta shiga. Sannan ta maida kofar ta rufe tare da jingina jikinta jikin kofar. Wani nannauyan ajiyar zuciya ta saki, ganin Ashraf a zaune lafiya kalau. Kallan kallo suka shiga yi mamaki yake dama Nafisa ce? Sansanyar murmushi ta saki sannan a hankali ta fara takowa zuwa inda yake. Kallanta kawai yakeyi yanajin wani sanyi naratsa shi. Nafi sai datazo kusa da inda yake kadan sannan ta ajiye abincin akan center table cikin shagwaba tace " Nasan ba farin ciki kai da ganina ba, dama lafiyarka nazo dubawa, tunda na gani bari na juya." Ta fada tare da juyawa, da sauri Ashraf ya taso ya kamo hannunta ya jawota jikinsa ya rungume tsam, sannan ya saki ajiyar zuciya yace " Ban kawo araina zan ganki bane sam." Tace " A wani hali kake tunanin zaka barni bayan ka amsa waya kamar numfashinka zai fita? Sannan daga baya ka kashe wayar ma gaba daya?" Ashraf ya dagota tare da rike kafadunta yace " Sry Baby nasan zaki damu in ban daga ba sannan dana daga kuma sai naga kamar zan fi tada miki hankali inkikaji yanayin da nake ciki." Cikin damuwa tace "mai ya faru wai?" Murmushi ya mata sannan ya kara jawota jikinsa yace " karki damu ba wani....." Kwace jikinta tai tace cikin dan zafin rai kadan " yaya baka yarda dani ba ko?" Jawota ya sake yi ya rungume yace " kema kinsan ba haka bane, kece mutum ta farko dana yarda da ita a duniyan nan." Har kasan ranta taji dadin kalamansa. Sake ta yai ya zauna tare da jawo kular abincin yace " Ahhh bari inga mai matata ta shiryamin." Tai murmushi sannan ta kamar zata zauna a dan nesa dashi. Harararta yai sannan ya bubuga kusa dashi da hannu yace " nan." Kallansa tai tace " in wani ya shigo fa?" Ta fada tare da matsawa inda yake. Hannu yasa ya jawota ta fada kan cinyarsa yace " anaso ana kaiwa kasuwa." Baki tadan turo tace " yaushe nace inaso?" Wani murmushi yai yace " gashi nan waya d'aya ta tada hankalinki gaba daya har kika tsiri kunyar fulani kika biyo mijinki." Idanu ta dan murza tace " yaya wani abu ya shiga idona." Dariya yadan yi yace " ko? Bari in duba miki." Neman mikewa tai tana rurufe ido, hannu yasa ya riko kugunta sukasa dariya a tare. Kan desk dinshi ta kalla taga take-away kallansa tai tace " wancan fa?" Yai murmushi yace " wlh abokina ko ince abokinmu ni da ke shine ya damu wai yaga alama banci abinci ba ya kawo min." Kallan mamaki tamai tace " abokin mu? Ni banda wani aboki namiji." Yai dariya yace " nima ba wai ina nufin abokinki ba na abota abokinmu dai na aure." Kallan mamaki ta sake mai, zatai magana ya matso saitin kunnenta yace " ya? Muyi skipping din aikin yau ne?" Hannu tasa ta rufe mai baki tace " aikin fa?" Yadan sosa kai kadan yace " yau so nake nai spending din whole day din dake." Tai kasa dakai tace " kar mu tafi azo nemanka." Yace " karki damu muje kawai." Abincin ya dauka da kansa ta kwace tace " barshi ni zan dauka." Yai murmushi shi ya fara fitowa ya kalli Secretary dinsa baisan mai zaice dan bai iya karya ba, ganin yana sosa kai yasa Nafi tai murmushi tace " zamuje dubiya bazamu dade ba." Yace " okay sir adawo lafiya." Ashraf ya kalleta sannan yai gaba, tabi bayansa, gudun ma kar asan inda zasu yasa suka tari mai adaidaita. Ta kalleshi tace " ka taba shiga?" Kallanta yai yace " ke dai muje." Ita ta fara shiga sannan ya shiga ya kalli mai adaidaita yace " Shagari Quarters." Kallansa tai mai alamar tambaya yadan matso bakinsa yace " akwai gidana acan na Abba." Kai ta jinjina sannan sukai gaba. Kafin su isa ya kira mai gadi ya sanar dashi zuwansa. *********** Yau Datti ya tashi cikin tsantsar farin ciki saboda jiya da yamma Mairo ta kawo mai shinkafa da miya abinda rabon dayaci shinkafa har ya manta, ga shi harda kaza a ciki, ya gama sannan ta bashi lemo mai dadi ya sha. Sai dai fa tundaga shan lemon nan bai farka ba sai yanzu, agoggon hannunsa ya kalla yaga wai karfe 9 na safe. A firgice ya mike zaune yace tun hudu da rabi na yamma nake bacci?" Mikewa tsaye yai yana kwalla ma Mairo kira, sai dai me? Shiru yaji kamar ba kowa ma agidan. Nan ya fito waje yana kiranta, babu ita ba alamarta. Da sauri ya shiga nemanta sai dai ina sam batannan. Yai dariya yace " da alama wata kazar aka tafi siyomin yau ma zansha dage dage." Garkensa ya nufa da niyyar ganin halin da dabobinsa suke ciki. Idanu ya zaro ganin kofar a bud'e. A tsorace ya karasa ciki.... Jama'a mai Datti zai gani?????? Kaf an kwashe komai dake cikin garken ba komau a ciki sai kashin dabobbi. Wani irin kara ya kwalla da karfi.... Wanda ya razanani yasa na yarda biro na. *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Gaisuwa tare da godiya gareku Miss Softie, Mum Farhan da Fatima Lawan Jet.Nagode kwarai da kaunar da kukema Littafin nan.* _Datti na gaisuwa Softie....Lol_ *67* Datti kam daga wannan ihu shikenan ya zube ya zauna a gun kamar gunki, sam ya kasa ko da magana na ne. Gashi a bayan gari suke hakan yasa ba wand ya shigo, sai can wajen azahar yayansa ya biyo dan yanasan datti yazo ya duba mahaifiyarsu dake kwance ba lafiya. Can ya ganshi zaune, yai tsaki yace " kaji asara wlh kazo kasa dabobbi a gaba kana kallo, ni can na bazama ina nemanka kai ko jina ma bakai ba." Ya karasa maganar tare da karasowa inda Datti yake. Ganin kamar baima san me yake cewa ba yasa yayan ya tabashi da hannu tare da kallan garken. Shikanshi tsorata yai, ya kalli Datti cikin tsananin firgici yace " Datti ina dabobbin?" Datti kam ba magana yai dif kawai sai kallan turkensa yakeyi. Ganin kamar ba a hayyacinsa yake ba yasa yayan ya d'agashi dakyar yai waje dashi, a taburma ya zaunar dashi sannan ya shiga mai fifita. Datti kam haryanzu baya hayyacinsa ganin haka yasa yayan yai waje da sauri dan neman mai magani kafin matsala ta afku. ************* A b'angaren Ashraf kuwa sun isa gidan suka sauka daga kan adaidaita nan ya bada kudi suka nufi gidan. Mai gadi ya bud'e tare da gaidasu. Suna shiga falon Ashraf ya rungume Nafi ta baya yace " ahhh finally we are alone." Ta zare hannunsa daga kugunta sannan ta kama hannun ta zaunar dashi kan kujerar dinning sannan ta ajiye kular tai kitchen ta dauko plate da spoon. Kallo kawai yake binta dashi yana murmushi, ta kawo ta ajiye mai sannan ta bud'e abincin wani daddadan kamshi ne ya daki hancin Ashraf ya lumshe ido tare da kallanta. Dankalin turawa ne aka mai hadi cikin kifi da vegetable ta zubamai a plate sannan ta mikamai spoon tace " a taimaka a ba cikina abinci." Kallanta yai cikin tsananin so yace " nima ko ba'a fadaba nasan nawa cikin yana bukatar abinci." Tai murmushi sannan tace " to ya za'ai kenan? Nima nina zubama nawa cikin abinci baka ganin kaima aikinka ne ka kula da naka?" Murmushi ya saki wanda har fararen hakoransa suka fito, hannunsa ya nuna mata alamar tazo. Ta dan turo baki ya kara nuna mata hannunsa, nan ta mike cikin shagwaba ta karaso gunsa kujerar kusa dashi ya jawo mata ta zauna ya kalleta sannan ya matso cikin rada yace " muci tare gwara na tabbatar da yawan abincin da zakici dan inaji a jikina nayi a jiya a cikina." Kallansa tai cikin mamaki sai dai bata gane mai yake nufi ba, tace " ajiya?tame kenan?" Yai murmushi tare da sa yatsarsa akan bakinsa yace " sirrine." Harararsa tadanyi sannan ta d'auko spoon suka fara cin abinci a plate daya. Suna gamawa ta kwashe kwanukan tai kitchen dasu, cikin tsautsayi garin ajiye cup na tangaran ya fadi kasa. Ashraf dake falo jin kara yasa yace " Baby menene?" Idanu ta zaro duk ta rikice batasan ko kadan ta jawo abinda zai batama Ashraf rai, tana kokarin matsawa dan ta bashi amsa sai jiyai ta dan yi kara. Da sauri ya mike ya nufi kitchen din a rikice. A zaune ya ganta ta rike kafarta ga jini sai zubowa yakeyi a tafin kafarta. Cikin rudewa ya karaso tare da kallan cup din daya fashe. Ya zagayo inda take ya d'aga cak yai falo da ita. Kan kujera ya zaunar da ita ya kalleta da niyyar yi mata fada akan rashin kulan da takeyi sai dai ganin yanda tai raurau da ido yasa yai shiru. Hannu tasa ta dan rike kunnenta tace " Yahkuri." Kallanta yai tare da rufe ido sannan ya kalli kafarta, mikewa yai ya dauko tissue ya ciro kwalbar sannan ya goge jini, sai dai yana gogewa wani na zubowa. Kallanta ya kumayi yace " sai dai mujibko chemist ne." Tace " ta yaya? A adaidaita fa muka zo." Ya kalleta cikin fada yace " Akan me ma tun farko bazaki dinga kula ba? Abu ya fashi kuma kin gani, mai zai sa bazakibi a hankali ba ki zagaye gun?" Yar kara ta saki tace " Yaya zafi." Ya sani sarai ta fadane saboda ya daina mata fada. Mikewa yai ya sungumeta yai toilet da ita. Ruwan dumi ya tara a dan roba sannan ya zuba dettol ya fara wanke mata. Rike rigarshi tai tana dan rakinta, bayan ya gama ya kalleta yace " zaki iya tashi?" Kai ta girgiza alamar a'a, yadan yi murmushi kadan yace " to yanzu ya za'ayi?" Ta dan kara shagwabewa tace " kadaukeni irin na d'azu." Baisan sanda yai dariya ba yace " naki, tunda bazaki dinga kula da kanki ba." Rigarsa ta rike, ya juyo ya kalleta tadan karkatar dakai cikin shagwaba tace " in nai kuka fa?" Kallanta yai batare da ya bata amsa ba, tace " Allah zanyi kuka, bakasan zafin da nakeji ba." Murmushi ya karayi sannan ya d'agata, d'aki ya kaita ya ajiyeta a kan gado sannan ya zauna a gefenta yana kallan yanda take murmushi kasa kasa, ya kura mata ido yace " me kike saka wa?" Mazewa tai ta kalleshi sannan cikin sanyin murya kalar tausayi tace " ruwa nakesan sha kuma bansan ya zan ba." Kallanta yai yace " ruwa?" Kai ta daga da sauri, ya mike yai waje, tabi bayansa da kallo, yana fita tadanyi dariya. Bai dadeba sai gashi da ruwa ya bata ta amsa ta sha, yace " ni danazo dan karamin honeymoon kin maidani mai kula da mara lafiya." Kasa tai dakai tace " ya hkuri yaya nima ba asan raina naji ciwon ba." Ajiyar zuciya yai sannan ya matso kusa da ita, cinyarta ta nunamai tace " kwanta anan." Harararta yai yace " salan anjima kizo kice na sagar miki da kafa?" Baki ta turo tace " tayaya zan fadi haka?" Kwanciya yai akan cinyarta tasa hannu tana shafa kan sumarsa. Idanunsa ya lumshe ba tare da ya bud'e idanunsa ba yace " Mu gudu mubar garin nan gaba d'aya?" Kallan mamaki tamai tace " Yaya." Idanunsa a lumshe yai murmushi yace " mu bar komai a yanda yake in daukeki mu bar garin nan?" Kanta ta sunkuyo ta daura fuskarta kan goshinsa tace " duk inda kake so muje in dai har da kaine bana shakka sai dai ka tabbatar zaka iya hakura da komai? Iyayenka? Kannenka? Company din da mahaifinka ya gina da guminsa?" A hankali ya bud'e idansa ya kalleta yace " Nafisa i am really scared." D'agowa tai cikin mamaki ta kalleshi tace " Yaya!" cikin raunanniyar murya. Idanu ya dan runtse kadan yace " Ina tsoron abinda zan binciko, bansan wani abu mai rikitarwa zan kara cin karo dashi ba." Hannunta tasa cikin tafin hannunsa idanunta suka ciciko tace " bayan kawu akwai wasu ne?" Cikin mamaki ya kalleta yace " ya akai kikasan....." Murmushi tai tace " yaya kenan, da alama da a birni na taso lawyer zan zama ko inzama Agent." Yai murmushi tare da maida kansa saitin cikinta yace " i am always impressed yanda kwakwalwarki ke saurin daukan abu." Murmushi tai tace " naji ance Abba kasheshi akai, to abun ai ba mai wuya bane, waye yafi amfanuwa da mutuwarsa? Duk ta inda aka duba kawu ne, kaga kuwa wannan binciken mai sauki ne na gaske." Dagowa yai kadan ya kalleta yace " whoa! Lalai na yarda matar nan tawa tana ja." Idanu ta rufe yai murmushi sannan ya maida kansa saitin cikin ta, yace " mai kike tunani gama da Mumy?" Cikin mamaki ta kalleshi, tare da tsayawa daga shafamai kan da take, tace " yaya ni fa har yanzu......." Kasa karasawa tai jin bakinsa akan cibiyarta, numfashinta ne taji ya dan dauke, a hankali ya shiga sarrafa ta cikin salon soyayya wanda itama ba'a barta a baya ba............ Ganin yanda suka fita hayyacinsu yasa na jawo kofar ina dariya nace " ko ina ciwon🤔???" ************ Dakyar aka samu kan Datti sai dai tun da ya fara magana zancenshi daya " Mairo Allah ya isa." Abinda yake ta fada kenan, ganin haka yasa yayansa ya taimakamai suka tafi rigarsu dashi. Duk yan uwansa ba wanda ya tausayamai da jin abinda ya faru, kowa Allah ya kara yakeyi wasu kuwa suce dama ai ance in bakai sharar masallaci ba kayi ta kasuwa, bai har matarsa? Yarsa?iyayensa da yan uwansa sunci arzikinsa ba ai gashinan wata katuwa can ta yasheshi." Yayansa yaje kauyen su Mairo sai dai iyeyenta sun sanar dashi suma basu ganta ba yanzu haka 'yayanta ma ake nema. Nam yayam ya gane dama can sun gama tsarawa. Amma Datti yana me? Ala fitar da dabbobi haka masu uban yawa??? *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *68* Kwance yake akan gado ita kuma tana kan cikinsa ya kalli agoggon bangon d'akin azahar tayi yace " tashi muyi wanka muyi sallah." D'agowa tai ta kalleshi tace " yaya sai dai ka kaini toilet kasan kafata ciwo take." Baisan sanda dariya ta kamashi ba yace " au dama haryanzu kafar tana ciwo? Sai naga d'azu kamar kin ma manta da ita." Fuska ta had'e tace " bafa mantawa nai ba kawai daurewa nai." Murgina wa yai daga inda yake ya koma gefen gado yace " hmm na fahimta yanzu." Nan ya sauka tare da d'aura towel sannan ya d'agata sukai toilet. Sunyi wanka sukai sallah, yana zaune kan sallaya yaji wayarsa nata neman agaji. Nan ya mike yai falo, ganin Dan litti ne yasa ya d'aga da sauri yace " mutumin ya an dubo?" Dan litti yace " Yallabai munje makarantar da yake da ita ni da officer din sai dai a can mukaji makarantar shekararta 30 da ginawa." Ashraf yace " 30?" Dan litti yace eh, sannan karamin asibiti din dayake dashi shima haka. Ashraf yace "gidajen hayansa fa?" Dan litti yace " su din ne bamu gama nemo su ba." Ashraf yai shiru can yace " is ok ma hakan, nagode, sannan ina shagari quaters ka kawomin mota please, zan turoma address." Yace " okay." Yana kashe wayar ya zauna tare da kurama wani guri ido yana tunani, wato tun Abba nada rai kenan makarantar take da asibitin. Kan kujera ya kwantar da kansa ya d'aura hannunsa akan goshinsa tunani yakeyi sosai, so yake ya hada puzzle din da yake a rarrabe a kwakwalwarsa. Nafi jin shiru bai dawo ba yasa ta mike tare da dingisa kafa ta fito falo. Ganin yanayin da yake ciki yasa tasan tunani yakeyi, a hankali ta taho kusa da shi ta zauna batace komai ba. Ashraf kam can cikin kwakwalwarsa abu d'aya ke saka masa, wato dady sun hada baki da kawu sun salwantar da rayuwar Abbansa saboda dukiya kenan. Shi kawu yana san dukiyarsa da kuma matarsa, shikuma Dady wato saboda kin taimaka masa da Abba yai da wuri shiyasa yake ganin shine sanadiyar talaucewarsu da kuma rasuwar iyayensa. Wannan dalilin ne yasa suka salwantar da Abba shima dan ya samu nasa kason na dukiyar Abba? Ko kuwa kafin Abban ya rasu ya mallaki dukiyar? Ajiyar zuciya yai tare da sauke hannunsa daga kan goshin sa, jin alamun mutum yasa ya juyar da kansa ba tare da ya d'ago ba. Kallan Nafi yai wacce itama kallansa take. Idanu ya lumshe sannan ya bud'e su a hankali yace " Yaushe kikazo?" Itama kanta ta kwantar a saman kujerar tana kallansa a hankali itana tace " tun dazu." Ya dan murmusa kadan sannan yace " banji motsinki ba." Tai murmushi tace " na kula kana bukatar kasancewa kai kadai ne, ni kuma banasan barinka shiyasa na zauna anan ba tare da saninka ba." Murmushi ya mata sannan ya mata alama da hannu akan ta matso, a hankali ta matsa kusa dashi yasa hannu a kugunta tare da kwantar da kanta akan kafadarsa yace " mu dawo nan da zama?" Kai ta girgiza alamar a'a tace " yaya meyasa kaketa fadan magana irin haka." Kansa ya dan kwantar akanta yace " yanzu dai kawai jinai inasan inganni daga ni sai ke a gidanmu mu biyu." Tace " mu biyu? Ko uku?" Kallanta yai cikin mamaki zai ce mu uku kuma? Sai ya tuna da Anisa, hakan yasa yai shiru. Kallanshi tai tace " ya kamata in daura mana abinci sai dai naga ba komai a gidan na girki." Yace " hmm kayan abinci ba matsala bane sai dai da alama kin warke, kar anjima azo acemin baza'a iya abincin ba bayan an siyo, a nemi sani a kitchen." Dariya tai sannan tace " ko na saka a kitchen din ai bana tunanin akwai abinda zaka iya dafawa." Yace " akwai abinda zan iya dafawa mana." Cikin zumudi tace " haba? Mene? Fadamin dan Allah." Dariya yai sannan yace " matso in rada miki." Da sauri ta kai kunnenta saitin bakinsa, ya jawo kunnen da hannun harsai da tadanji zafi sannan yace " kinasan ji?" Kai ta daga alamar eh, yace " ruwan zafi." Yana fada ya mike yana dariya. Leb'enta ta ciza tace " YaYa." Ta fada cikin fushi. Dariya yasa mata tare da yimata gwalo. Mikewa tai dasauri tana dingisawa ta bishi kafarta ya nuna yana mata dariya. Nan ta kara sauri dan kamoshi. Dariya sosai yake mata ya shige d'aki, itama ta bishi nan suka fara zagaye gado yana tsokanarta wai Nafisa Cogal, ganin ba yanda zatai ta kamashi gashi ta gama kuluwa yasa tace " wayyo kafata." Ta fada tare da durkusawa. Da sauri ya matso yace " Nafisa menene?" Cafkeshi tai tace " wacce Cogal din?" Dariya yai ya jata suka fada kan gadon, dariya suke sosai dukansu kafin daga bisani su tsagaita. Matsowa tai ta daura hannunta kan kirjinsa tana kallansa tace " yaya inaji farin ciki zaimin yawa, ina tsoro kar ya yankemin lokaci guda." Kallanta yai cikin kauna yace " Baby tun da nake, bandai san kafin Abba ya rasu ba sai dai a iya tarihin rayuwata yanzu ne nasan me ake nufi da farinciki, me ake nufi da dariya, me ake nufi da tsokana, me kuma ake nufi da so, Nafisa ban taba tunanin zan yi experiencing wad'annan emotions din ba, sai dai yanzu jina nake kamar yaro dan sha takwas, akanki gani nake zan iya komai." Idanunta ne suka ciciko da kwalla, ya harareta yace " karki soma min kuka please dan banasan kuka ko kadan balle daga wacce nake tsananin kauna." Batasan sanda hawaye ya zubo mata ba, ba shakka bata taba tunanin akwai ranar da zatazo wanda Ashraf zai sota haka ba, kallanta yai tare da kankance ido yace "na dauka nace banasan kukan nan?" Ta share hawayen da hannunta tace " yaya akwai hawayen da suke zubowa in har farinciki ya musu yawa, in har kaga nayi kuka to yanzu akan abu biyo ne, ko dai farin ciki yamin yawa ko kuma kai nakema kukan da zuciyarka ta kasa." Kallanta ya keyi cikin tsananin kauna, kanta ta kwantar akan kirjinsa tace " in har zuciyarka na maka radadi akan wasu al'amuran ni zan ma kukan da zai sanyayata, dan nasan kai bakasan kuka ko kadan." Idanu ya rufe batare da yace komai ba. Tai murmushi itama. Ya bud'e ido a hankali sakamakon wani idea data fado mai, kallanta yai yace " Nafisa duk abinda zan aikata a wadannan lokacin inaso ki kauda kanki, ki kuma yafemin a hankali zan sanar dake dalilin da yasa nai komai, sai dai inaso ki sa a ranki ni Muhammad Ashraf mai san Nafisa ne." D'agowa tai ta kalleshi ba tare da dogon nazarin kalamansa ba ta matso ta sumbaci goshinsa tace " nima inaso kasa a ranka ni Nafisa mai tsananin kaunar Ashraf ce a koda yaushe." Rungumeta yai wani sanyi na ratsa zugakan mutane biyun, sai dai Ashraf yana saka plan dinsa da zai fara gudanar wa. Nace hmmmmmm ************ A b'angaren Mumy kuwa tun bayan tafiyar Nafisa data shiga daki ta dade tana kuka kafin daga bisani ta kwanta. Juyi kawai takeyi san tunani sun taru sun mata yawa akanta. Tana nan a d'aki har yamma kawu ya shigo d'akin ganin bata falo. Kusa da ita ya karaso yana tsaye yace " Hajiya me ya sameki? Naga na dawo bakyanan sannan na shigo banga kin mun sannu da zuwa ba." Ba tare da ta kalleshi ba tace " kaina ke min ciwo." Cikin rud'ewa ya matso tare da cewa kinsha magani? Ko zamuje asibiti?" Kallansa kawai takeyi ba tare da tace komai ba, ya kalleta cikin mamaki yace " menene? Naga kin kuramin ido?" Idanunta ta dauke daga kansa tare da girgiza kai tace "ba komai." Ya karasa kan madubi ya d'auko magani sannan ya fita dan dauko ruwa. Kalli ta bishi dashi wanda ni kaina ban fahimci kallan me take mai ba. Bai dade ba sai gashi nan dauke da ruwa ya nemi d'agata nan tace zata iya tashi, ta mike ta amshi maganin tasha sannan ta kwanta. Yace " bari in fita naga kamar kinasan hutu." Kai ta daga kawai hakan yasa yai waje. Yana fita ta share wasu kwalla da ni kaina ban fahimci kwallar ta menene ba. *********** Datti kam sam ya kasa magana, banda Mairo Allah ya isa ba kalmar da take fitowa daga bakinsa, an kaishi gurin malamai harda yan duba sai dai haryanzu ba sa'a duk hayakin da akemai kuwa, abinci ma sam bayaci sai dai ai ta duramai kunu. Yana zaune kamar gunki sai kalmar Mairo Allah ya isa kawai dayake fada. 'yan gidan ba wanda ya damu dashi banda yayansa guda d'aya. Datti kam duniya ta juyamai baya.......... Mairo ko tana ina??? Abinda ya fado min kenan. *Juma'at karem* *#ASHRAFEENAH TEAM* *one love💞* 🤸🏻‍♀ *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Wannan shafin sadaukarwace ta musamman gareku 'yan Xahra Bukar Novel, nagode kwarai da gaske da kaunar da kukemin da littafaina.........ILYSM😍* *69* Da yamma Dan litti ya kawo mai mota, bai bari ma sun gaisa ba makullin kawai yaba mai gadi ya juya yai gaba. Suma wajen karfe 6 suka fito daga gidan, hannunsu rike da juna, tana dan dingisa kafa kadan kadan. Tuki yake zuciyarta nata sarka masa abubuwa kala kala, Nafi kam ganin haka yasa ta kwanta kawai batace komai ba. Sunje shiga gida ya zaro Atm daga wallet dinsa ya mika mata. Kallansa tai tace " Name nene?" Yace " nasan akwai abinda kike bukata sai kuje ke da Little, sannan ki barshi a gunki incase in akwai abinda zaki bukata nan gaba." Kallan mamaki tamai tace " nan gaba in zan nema ba sai na fadama ba?" Kansa yad'auke baice komai ba. A karamar purse dinta ta saka suka shiga gida. Sunje gun ajiye mota sukaga Anisa da su Umma a tsatsaye sai masifa akeyi, ga Asim nan ya rike kofar motar Anisa shima yana fada. Tunda suka kula da motar Ashraf sai duk suka zubama ma motar ido kowa fuskarnan a murtuke, Nafi kam yau ko a jikinta jitake yanzu bazata iya jurar wulakancin kowa ba. Ashraf na tsayar da motae ya bud'e da sauri tare da kallansu, kafin yai magana Anisa ta matso a harzuke ta cakumi wuyan rigar Ashraf kamar zata fashe saboda tsabar masifa tace " Wlh Yaya yau sai ka zaba ko ni ko wannan yar iskar, har ni zatacima mutunci d'azu? Sannan yanzu ka dauketa kun tafi yawan iskanci, wlh da so nai in ja mota duk inda kuke in nemeku, nagaji da wannan dadirancin da kukeyi." Umma ta matso itama tace " Kai Ashraf a wani matsayi Anisa take a gurinka? Ka maidata kamar ba matarka ba sam ka daina ko shiga harkarta, kana tunanin mu iyayenta zamu barka ne?" Asim kam kallan Ashraf kawai yake yana hucci. Nafi ta bud'e motar ta fito tana kallan ikon Allah, Ashraf ya zare hannun Anisa daga jikinsa a hankali yace " Nisa calm down wannan fadan fa?" Kallansa tai idanunta ya ciciko tace " yaya bazan iya ba, na san ba sona kake ba, ni kuma wlh bazan iya zama da waccen tsinaniyar ba." Ta fada tana nuna Nafi. Ashraf ya dan kalli Nafi kadan sannan ya maida idansa kan Anisa mayafinta da ya fadi kasa saboda masifa ya tsugunna ya d'auko mata, ba wanda ya zata sai gani sukai ya yafa mata mayafin ya kalleta cikin kulawa yace " Nisa kalleni nan." Jikin kowa ne yai sanyi, Umma a ranta tace " dama ta ina za'ace yaron da suka taso tun suna kanana har yafi san wata wacce basu dade da haduwa ba." Nafi kam jitai wani abu ya tokare mata makoshi, kallansu kawai take tama kasa ko motsi. Asim ma mamakin Ashraf ne ya kamashi. Gogar kuwa duk jikinta ya gama sanyi kallan Ashraf kawai take kamar yanda ya umarceta, Ashraf yace " Nisa!" A hankali tace " Naam." Yai murmushi yace " Yauwa ko kefa." Kallansa ta tsaya tanayi, ya saketa tare da juyawa ba tare da ya kalli Nafi ba zai wuce. Da sauri Anisa ta riko hannunsa tace " yaya nidai wlh ka zaba ko ni ko waccen, banaji zan iya ganin tana zama kusa dakai zuciyata bata fashe ba." Ba tare da ya juyo ba ya had'iyi wani abu sannan yace " Karkisata a ranki u r so dear to me." Yana kaiwa nan ya ja hannunsa yai gaba. Nafi kam bata san sanda taji hawaye ya zubo mata ba tana kokarin mai magana taga ko kallanta baiyi ba yai gaba. Yana tafiya Umma ta matso gunta tana dariya tace " ah ah su Amarsu yanzu kin tabbatar da matsayinki?" Kallansu tai ba tare da ta tanka ba, mamaki take mai ya samu Yaya daga shigowa? Umma tai dariyar mugunta tace " ah to da an fada miki barno gabas take? Shi dama namiji kan ya samu abinda yake so ne zai ta lallabaki amma da ya samu shikenan kin zama kashi." Wani irin kallo Nafi ta kafe Umma dashi, Umma ta wanka mata mari tace " A da in mun barki kinyi iskanci saboda mijinki ya baki matsayine bawai yanzu da kike kamar bola ba." Anisa ta matso tace " ke harkin isa dama kice zaki kwace min miji? Yar kauye dake? Mutumin da na taso dashi tun muna yara ke kuwa yar karo?" Nafi wacce ke rike da kuncinta ta daure tace " wannan kuma tunaninku ne ba na yaya ba." Tana kaiwa nan ta fara dingisa kafa tana gaba. Anisa ta matsa ta fizgota da karfi tace " ni kika fadama magana d'azu ko?" Nafi ta kalleta tare da fincike jikinta ta cigaba da tafiya, Anisa tasa dariya tace " yi maza ki je ki shiya yan kayan da kika samu anan kafin insa a baki takardarki." Nafi bata juyo ba tai bangarensu. Tana shiga ta zauna akan kujera a falo, meke faruwa? Tayaya ya Ashraf zai canza mata lokaci d'aya? Da sauri ta girgiza kai alamar a'a tace " Yanada reason dinsa ni na sani, zanje anjima in ma laifi na masa in bashi hakuri." Da wannan shawara taji hankalinta ya kwanta. Anisa kam tana ganin tafiyar Nafi suka kwashe da dariya, Asim ya matso yace " Anisa ina mamaki fa ya akai hakan?" Anisa ta dan yi fari da ido tace " yaya na sona ni nasani kawai abinda ya faru ne yasa ya shareni." Asim yace " to yanzu kije ki lallabashi ki samu kisan yawan dukiyayonsa da kuma inda takardun suke, karki bari ya gane komai." Kai Anisa ta jinjina alamar gamsuwa tace " karka damu yaya ni nasan ya Ashraf a tafin hannuna yake." Dariya sukai dukansu, Anisa ta wuce bangaren Umma da sauri tai wanka ganin magrib tayi tai sallah sannan ta saka wasu riga da siket 'yan kanti sun bi jikinta sosai. Mayafi ta yafa sannan ta fito tace "Umma ya kika ganni?" Umma ta shiga tafa mata tace " yauwa 'yata sai da safe." Nan Anisa ta fito cikin tsantar farin ciki. Bangarensu ta nufa tare da bud'e kofa. Ashraf na zaune ya baza wasu takardu yana dubawa, jin motsi yasa ya d'ago. Ganin Anisa yasa ya sakar mata sansanyan murmushi. Cikin rangwada ta karaso gunsa tace " yaya shine bakazo biko ba ko?" Kallanta yai bayan ta zauna daf dashi yace " sry Nisa kunya ce ta hanani zuwa." Kankameshi tai tace " yaya nagode da ka nunamin kana sona." Zareta yai daga jikinsa yace " Amma kin dawo kenan ko?" Cikin shagwaba tace " anya kuwa?" tafada tana karema takardun kallo, tace " wad'an nan fa?" Tataresu ya farayi yace " ba komai." ya fada tare da mikewa da sauri Ya nufi d'akinsa." Kallan bayansa tai tace "da alama takardune masu amfani ganin yanda ya kwashesu da sauri, sannan da tana dubawa taga kamar takardun fili." Mikewa tai da sauri tabi bayansa, kofar dama bai rufe taba. Yana kokarin sawa a drawer ta jikin madubi sai ga Anisa. Da sauri ya tura yasa key, ta matso gunsa tare da rungumeshi ta baya tace " ka gama?" Makullin ya bari a jiki ya juyo ya kalleta yace " eh muje falo." Nan ta kara kallan gun sannan sukai falo. zama sukai ta zauna akan cinyarsa tare da rungumeshi ta fara sambatarsa, sam hankalinta ya gama tashi saboda rashinsa datai kwana biyu bataji buga kofar da ake ba. Ashraf ya d'an zareta kadan yana kokarin sauketa Nafi ta turo kofa, tunaninta jin tanata bugawa ba'a bud'e ba mayb yana masallaci sai tai tunanin ajiye masa abinci tai gaba. Cak ta tsaya daga jikin kofa tana kallansu. Anisa kam ganin Nafi ce yasa tai wani dariyar mugunta sannan ta kara kai bakinta cikin na Ashraf tana mai wani saban salo. Nafi kam jitai jikinta yana kakkarwa anan bakin kofar ta ajiye abincin tai waje da sauri. Tafiya kawai take batasan inda take sa kafarta ba sam kuma bata kallan gabanta. Saura kiris ta buge da bango taji an jawota, kallan wanda ya jawota tai, jitai yace " Gimbiya me kike tunani haka?" Kallansa take kamar bata cikin hayyacinta ta kwace hannunta tana kokarin ci gaba da tafiya. Gabanta yasha yace "Gimbiya menene? Baki kula dani bane?" Kallansa tai sannan ta kewayeshi tai gaba. Bin bayanta ya farayi yana mata magana sai dai da alama batama san yanayi ba. Sunje shiga bamgarensu, Little kuma na shirin fitowa. Ganin Nafi yasa ta karaso da sari tace " Ni harzan gudu gun Mumy muyi hira dan nasan ke kuma sai gobe ni da na ganki." Nafi ta kalleta sai dai batace komai ba, muryar Habib taji yace " Princess kece?" Da sauri ta matsa daga gun Nafi ta karasa gun Habib, itakam Nafi ciki ta shiga kawai ta zauna a bakin gado. Hoton yanayin datagansu sam ya ki barin kwayar idanunta, ta sani matarsa ce ba kuma ta da hakki akan hanashi yin abinda yaga dama da matarsa sai dai me yasa takeji kamar Ashraf yayi betraying dinta?????? Nikaina bansan me zance ba Feenah👩🏻‍🏭 *Ina mika ta'aziyata zuwa Feedoh Deedoh Allah ya jikanta da rahama yasa Aljanna ce makomarta, ku kuma Allah ya baku hakurin rashin ta.* Ameen suma Ameen. *May her gentle soul rest in peace* Ameen *#ASHRAFEENAH* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *70* Little ta kalli Habin tace " Yaya sai yau fa naganka!" cikin shagwaba tai maganar, ya kalli kofar da Nafi ta shiga yace " Princess nazo ai bamu hadu bane ba kawai." Ta dan turo baki tace "na kiraka ma baka dauka ba." Ya hada hannayensa biyu yace " sry mayb ban kula bane." Ta kalleshi tace " naga sako na gode." Kallan mamaki ya mata yace " sako?" Kai ta daga alamar eh tace " eh mana wanda kaba Feenah ta bani." Shiru yai a ransa yace " au kayan dana bata ma Little taba?" Bai dawo daga tunaninsa ba Little tace " yaya, bari inje inga Feenah da alama yaya ne ya b'ata mata rai, nayi mamakin ganin ta haka." Sannan ta karasa maganar a hankali " Naga they get along with eachother very well, da alama fadan masoya sukai." Ya kalleta yace " Ai Asharaf sai a slow, amma...." Little ta kalleshi jin yayi shiru, kallan mamaki ya mata yace " me kikace daga karshe?" Cikin rashin damuwa ta maimaitamai tace " Allah naga tunda mukasan tsakaninsu kullum suke tare da juna." Cikin tsananin mamaki yace " me kikace?" Yanda yai maganar yasa jikinta yadanyi sanyi tace " oh bakasan fa ashe matar yaya bace fa ko?" Gani tai yadan yi baya tare da rike kansa, cikin wani irin yanayi yake kallan Little wanda yasa tasha jinin jikinta, yace " matar wa?" Kasa maimaitawa tai sai kallansa kawai datakeyi, ganin tayi shiru yasa ya juya jiki a sanyaye yai gaba batare da ya kara cewa komai ba. Little tabi bayansa da kallo me kenan? Ko dai shock ne irin wanda sukaji da suma suka samu labarin?" Ciki ta shiga ta samu Nafi ta sauko daga kan gado ta zauna a kasa tare da d'aura kansa a kan jikin gadon. Little ta matsa kusa da ita tace "matar yaya da alama fada kukai ko?" Nafi ta kalli Little sai dai batace komai ba, Little tai dariya tace " karma ki fadamin nima ba san ji nake ba, na kuma san goben nan zaku shirya." Ta karasa maganar tare da mikewa. Nafi da kyar ta tashi ta watsa ruwa kawai tai sallah ta kwanta, sam ta kasa bacci ita ba wai ganin yanayin da suke ciki da Anisa bane yafi daga mata hankali, kiss din da sukai a gabanta shine ya tsaya mata a kwakwalwarta, ai karama wani abun ce, ta tuna sanda yake ce mata su zauna a shagari su biyu. Wani dogon tsaki taja tace " kamar irin da gaske ya manta da matarsa din nan." Sam kasa barci tai sai juyi kawai take, da kyar baccin ya d'auketa. A b'angaren Ashraf kuwa sun zuba love shida nisa sai dai sam yaki yadda ya kusanceta, ganin ta matso da hakan yasa ya d'an matsa kadan, haushi ya kamata tace " Hubby meye hakan?" Kallanta yai tare da rike hannunta yace " sry Nisa." Ta fizge hannunta cikin fushi tace " me? Kana tunanin matarka Nafisa ne ko me?ko kuwa so kake kace baka sha'awar yi dani bayan kayi da yarinya?" Jawota ta yai jikinsa ya rasa me zaice, baisan sanda yace mata" ba haka bane, banajin dadi ne wanda likita ya hanani saduwa amma inani ina kin matata?" Nisa ta kalleshi cikin zargi tace " me ya sameka? Sannan naji Umma tace ka kwana da Nafi fa!" Kara jawota yai yace " zargin Umma ne kawai karki wani sashi a ranki." Da wannan yasa ta saki ranta, shikuma ya kwanta yai bacci. Tana gani yayi bacci ta mike a hankali ta bud'e drawer din nan a hankali ta zaro takardun nan tai falo. Karantasu tai taga tabbas kuwa takardun filayene da wani babban gona. Tai dariya tace " da alama zan gano komai wannan karan." Nan ta dau hotunan a waya ta turama Asim, sadi ya kara kamashi tace " yaya in sato su?" Yace " a'a ki maidasu sai mungama ganin ragowar tukunna karya gane." Ta jinjina kai cikin gamsuwa sannan ta maidasu a hankali ta koma ta kwanta. Hankalin Ashraf a kwance ya tashi yai asuba, duk yanda yaso ta tashi tai sallah taki, dama inda sabo ta saba dan bata sallah sai rana ta fito. Sai daya gama shirinsa na gun aiki sannan ta farka ta kalleshi yana fesa turare. Mikewa tai tazo ta bayansa ta rungume shi, yai murmushi yace " kun tashi My Neesa?" Wani irin sanyi ne ya ratsata tace " eh hubby." Ya juyo da ita gabansa yace " da fatan kinyi bacci mai dadi." Kai ta daga tace " sosau ma, na dade rabon danai bacci mai dadin haka." Yai murmushi yace " gud, ni zan fita." Kiss ta mannamai a kuncinsa tace " sai kadawo." Kai ya d'aga mata baice komai ba. Yana fita waje yasa hannu ya goge inda tamai kiss din sannan yai waje. A waje yaga Asim da kansa ya karasa ya mikamai hannu suka gaisa wanda hakan yai bala'in ba Asim mamaki, Ashraf yai murmushi yace " Asim dama inasan magana dakai." Asim yace " inaji." Ashraf yace " kamar ya kamata muwa Kawu magana ya karama matsayi inaganin kamar inda aka maidakai yanzu is too low for someone like u." Cikin tsananin mamaki Asim ya kalli Ashraf yama kasa magana, Ashraf ya dan dafa kafadarsa da hannu daya yace " barshi in baka so." Yana kai wa nan yai gaba, da sauri Asim yasha gabansa yace " da gaske kake?" Fuskar Ashraf a maze kamar yanda yake kullum yace " wasa nakeyi to da?" Asim ya sa dariya yace " mamaki nake yi ai bantaba tunanin za ka taimaken bane ba ai naga tun muna yara bama wani shiri." Ashraf yace " ko ba ma shiri ai kai dan uwanane." Yai gaba abinsa daga fadar haka, Asim yai dariya yace " wai yau me nakeji haka?" Bangaren Kawu ya nufa cikin zumud'i ko sallama baiyi ba ya tura kofar d'akin, kawu na gaban wannan akwatin, jin Asim yasa yai saurin rufewa tare da turashi karkashin gado da sauri, ya kalli Asim cikin fada yace '" kai wai sai yaushe zakai hankali ne?" Asim yabi akwatin da kallo sannan ya basar yace " Abba anya kan Ashraf d'aya kuwa?" Kawu yamai kallan mamaki yace " ban gane ba." Asim ya matso yace " yanzu wai yacemin ya kamata muma magana ka karamin matsayi wannan matsayin nawa na yanzu is too low for me." Kawu yai wata dariyar rainin hankali yace " amma ba kada hankali ko?" Asim cikin mamaki yace " bangane ba." Kawu yai dan tsaki tare da mikewa yace " Kanaso kacemin Ashraf ne yace ma haka?" Da sauri Asim ya daga kai, Kawu ya hade rai yace " ba ka cikin hayyacinka da alama mafarki kai." Asim zai sake magana Kawu yace " mu fita ni." Haushi ya turnuke Asim yai waje a zuciye, har yayi nisa ya dawo gun Kawu yace " Abba me kake nufi dani?" Kawu ya kalleshi cikin mamaki ba tare da ya amsa ba, Asim ya cigaba " menene baka yarda dashi ba game da ni? Ni din ne baka yarda Ashraf yayi acknowledging din aiki na ba ko kuwa baka yarda da zan iya wani abun bane?" Kawu ya kalleshi cikin kulluwa da wannan halin nashi, yace " duka, u always disappoint me." Yana kai nan yai gaba yabar Asim a tsaye a gun. Asim yabi Kawu da kallo cikin tsananin takaici da haushin yanda Kawu yake mai. Kawu kam mota ya shiga cikin takaici. *********** Nafi kam bayan tayi wanka tana zaune a d'aki ita kadai duk abin duniya ya isheta ta kira Ferry a waya nan sukai ta hira har Ferry ta sanar da ita jarabawarsu ta fito. Nafi tace " haba?kin dubo?" Ferry tace " a'a amma ya Nabil yau zai dubo min." Naf tace " kice ya dubo da nawa " Ferry tace " to, amma Nafi karfa ki yaudaren kije ki cike wata makarantar ba BUK ba." Nafi tai dariya tace " karki damu duk inda kike nima ina nan, sai dai in samu ne banyi ba amma ina zani?" Sun dade suna hira kafin suyi sallama bayab sun gama tsara bikin Jibiya da za'a fara nan da 2wks, Nafi tace " Zata kawu mata kudin ankon inyaso sai a musu gaba d'aya komai iri d'aya." Tana kashe wayar tai shiru, a ranta tace " Ferry fa batasan ni matar aure bace fa ko? Ya kamata in sanar da ita kar taji daga baya ta d'auka ko yaudararta nai." ********** Ashraf na zaune a office ya dukufa sosai gun aiki yaji an banko mai kofa, Secretary dinsa yana biye da wanda ya bud'e kofar yana cewa " malan meye hakan?" Ashraf ya kalli Habib yama Secretary din alama da hannu akan yaje. Nan yai gaba, Ashraf ya kalli Habib yace " Habib lafiya naganka haka?" Habib cikin fada yace " Ashraf me ake nufi akan kai mijin Nafi ne?" Ashraf yamai kallan mamaki yace " ban gane ba?" Habib yace " baka gane ba kamar ya? Little tace kai mijin Nafisa ne, ni kuma banaj na taba jin wannan labarin." Ashraf ya koma ya zauna fuskarnan a hade yace " yanzu ai kaji." Habib ya matso cikin tsananin kishi ya kamo wuyan Ashraf yace " how can u do this to me? Kasan kuwa yada nake da burin auren yarinyar nan? Taya za'ai kac......." Ture hannunshi Ashraf yai da karfi yace " kai ko kunyata ma bakayi? Taya za'ayi kazo kanamin zancen wai so bayan kasan kanwata yanda take sanka?" Habib ya kalleshi, Ashraf yai wani murmushin yace " badai cemin zakai baka sani ba? Zan iya aminta inka fadi wani abu amma ba wannan kalmar ba." A hankali Habib yadanyi baya, Ashraf ya sake murmushi yace " mubar wannan maganar, ina Dady?" Jiki a sanyaye Habib yace " yana gida." Ashraf yace " Allah sarki Dady baka gani ya kamata a dan ko karamai girman asibitin nan ko kuma a bud'e mai wani babba?" Habib yai dariya yace " tab lalai, dady din?" Wani irin kallo kasa kasa Ashraf yamai, Habib yacigaba " kabar Dady kawai sani ne bayasan ayi amma yanada kudi sosai inaj fa yanada gidajen haya manya kusan guda goma." Ashraf yai murmushi yace " amma wannan ai mayb daga baya ya saisu." Habib ya girgiza kai yace " a'a wlh, ni fa rannan inajinsa da Mumy yana zancen da gidajen lokacin duniya na kwance basa kawo kudi sosai amma yanzu dayake komai ya tashi kudi suke kawowa sosai." Ashraf yai murmushi, kafin daga baya Habib ya tafi. Ashraf ya d'au waya da sauri ya kira Uncle bayan sun gaisa yace " Uncle nikam kasan komai ma dukiyar Abba kuwa?" yai maganar cikin bugar ciki. Uncle yai dariya yace " a iya sanina nasan komai nashi." Ashraf yai shiru jikinsa ya fara sanyi, can ya daure yace " kasan komai nashi tun kafin ya rasu?" Salim ya sake dariya yace " gaskiya nidai a iya sanina nasan komai." Ashraf yai shiru can yace " shikenan na gode." Yana kashe wayar ya mike tare da zuge glass din window yana kallan titi, a ransa addu'a kawai yake Allah yasa ba haka bane......" *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *71* Nafi tana zaune a d'aki taji ana kwankwasa kofa, a hankali ta mike ta bud'e. Ganin Mumy ce yasa tad'anyi baya da sauri tare da cewa " Mumy sannu da zuwa." Mumy ta shigo ciki tare da zama akan d'aya daga cikin kujeru biyun dake d'akin, Nafi ta zauna daga d'an nesa da ita a kasa tare da gaisheta, Mumy ta amsa sannan ta kalli Nafi tace " Zaman kadaici baya damunki?" Nafi ta girgiza kai alamar a'a, Mumy ta dan yi shiru, kafin ta nisa tace " Nafisa!" Yanda ta kira sunan yasa Nafi ta d'ago a hankali tare da shan jinin jikinta, ta sani cewa zatai tabar gidan. Mumy tacigaba " Ashraf yaro ne wanda baisan farinciki ba, bai san soyayyar iyaye ba, bai kuma san soyayyar 'yan uwansa ba." Nafi tai kasa da kai idanunta suka dan ciciko, Mumy tad'an yi ajiyar zuciya kafin ta cigaba " na sani i am not a good mother to him, ban taba tambayarsa ko da damuwarsa bane bare har inkai ga bin bayansa ko nunamai kulawa." Nafi ta kalli Mumy cikin tsananin tausayin mijinta, Mumy ta d'anyi murmushin takaici, tace " duk kuma da wannan abun danake mai ya nunamin ke a matsayin matar da yakesan zama da ita sai dai shima hakan ban bi bayansa ba." Hawayen da ke kwance a idanta ne ya gangaro, tai saurin sa hannu ta goge su, Mumy ta cigaba "A nawa ganin Ashraf matar da yake bukata itace mai ilimi wacce tasan kanta wacce kuma zata kula dashi." Nafi ta goge hawayenta sannan ta kalli Mumy jin tayi shiru, tace " na fahimceki Mumy na kuma sani ba tun yanxu ba Yaya yafi karfina, sai dai ni na kasa fahimtar ki." Mumy ta kalleta, Nafi ta daure duk da tsoron da takeji tace " bakya gani Yaya na bukatar kulawarki? Ko baki nunamai ba a kalla kya sanar dashi dalilinki na kin nunamai soyayya." Mumy ta maida kwallar ta dake neman fitowa tace " me yasa kike tunanin akwai dalilina nayin hakan?" Nafi tai murmushi tace " Mumy ta yaya uwa zata haifi d'anta tace ba ta sansa? Ta yaya uwa tana ganin danta a cikin wani hali tace ba ta damu ba? Ta ya ya uwa zataki d'anta wanda yake maraya ne? Duk inda nakai ga tunanin zai iya yiwuwa sam zuciyata bata yarda da hakan, ni nasan akwai dalilinki nayin haka, sai dai a gun yaya shidai rashin so ne yasa kike mai haka." Nafi da sauri taga Mumy ta mike tayi waje, ta bita da kallon tausayi. Ta dade a zaune agun kafin ta d'au wayarta ta kira Ashraf, sai dai duk yanda wayar ke ringing bai d'auka ba. Ta ajiye wayar tare da kwantar da kanta jikin kujera. *********** A b'angaren Ashraf kuwa yana azahar ya wuce gidan Uncle bayan sun zauna a falo sun gaisa Ashraf ya kalli Salim yace " Uncle a labarin da ka bani kwanaki banaji kacemin an anso kayan su Dady." Salim yai shiru yana kallan Ashraf. Ashraf ya cigaba " nasan asibiti da makarantar sa na Abba ne amma bansan gidajen hayansa nawaye ba." Salim ya shafi fuskarsa da hannayensa yace " Ashraf you are very smart,ban taba tunanin zakai zargin wani abu ba game da wannan, shiyasa ma ban sanar dakai komai ba." Ashraf ya kalli Uncle yace " me ke faruwa?" Salim yaja numfashi yace " a lokacin da mahaifin Ruma ya rasu bayan an gama zaman makoki Hisham ya shiga gararin rayuwa, kaf kudinsa sun kare bayan rashin kudin ashe har loan yaci a banki wanda ya jinginar da gidansa. Bayan an gama zaman makoki 'yan bankin sukazo amsar kudinsu kamar yanda ya sanar dasu lokacin dazai biyasu. Sai dai a lokacin gidansa abincin ma dazasuci nema yake ya gagaresu. Da yake Ruma na gidan ita ta kira Abbas ta sanar dashi halin da ake ciki nan ya je bankin ya biyasu kudinsu sannan makarantar da yake masifar so ya mallakama Hisham duk dan ya farantamasa, sai dai kwanansa d'aya da bashi makarantar Allah ya d'auki ran Abbas." Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " asibitin fa?" Salim yai ajiyar zuciya yace " Ashraf wannan sai bayan rasuwar mahaifinka sukazo min da takarda akan Abbas ya mallakama Hisham asibitinsa da aka gama ginawa ko fara aiki ma ba'ai ba." Ashraf cikin rashin fahimta yace " ta yaya ya bashi makaranta mai girma irin wannan ya sai mai gida sannan ya kuma bashi asibiti?" Salim ya kalli Ashraf yace " nima da naki yarda da bada takardun asibitin to amma abin mamaki rubutun mahaifinka ne." Cikin fada Ashraf yace " zasu iya sa expert su kwaikwaya ai." Salim yace " yes shiyasa naki yarda sai dai mahaifiyarka itace tace tabbas Abbas ne ya rubuta." Shiru Ashraf yai kafin yace " gidajensa fa?" Salim yace " bansan wannan ba gaskiya sai dai bayan mutuwar Abbas naji jita jita akan bai daina safarar bindigogi ba zai iya yiwuwa da su ya siya ko kuma gadon Ruma ne." Cikin mamaki Ashraf yace " gadon Mumy?" Salim yace " ban tabbatar ba amma tunda kace gidaje dayawa nasan tanadasu dan Abbas tun yana da rai yake siyan gida da sunanta sannan da ya rasu aka bata gadon wasu." Ashraf yai shiru baice komai ba, Salim ya dafashi yace " Ashraf mahaifinka burinshi kai rayuwa mai dadi ba wai ta wahala da kunci haka ba." Murmushi Ashraf yai yace " Uncle kana tunanin zanyi rayuwa mai dadi bayan duk 'yan uwana makiyan Abba da ni suna zagaye da ni?" Salim baice komai ba sai kallan Ashraf dayake yi. Ashraf ya sake murmushi yace " ka binciko min inda Auwal Max din yake?" Salim yace " eh to wanda yake binciken yace yana zariya sai dai yace in kara mai 1day ya tabbatar da shi din ne." Kai Ashraf ya jinjina sannan ya mike yace " kace kafin Abba ya rubutawa matata wasiya munyi tafiya zuwa wani kauye dashi ko?" Salim ya jinjina kai yace " kwarai kuwa saboda bazan manta lokacin ba nayi mamaki kwarai daya kawon wasiyyar da daddare." Ashraf yace " Malam Mahmud ko?" Salim ya daga kai alamar eh. Ashraf yai godiya kafin yai waje. Mota ya fad'a ya d'aga wayarsa sakon Nafi ne yaga ya shigo kamar haka " _Yaya dafatan kaci abinci?_" Ya dade yana kallan sakon kafin ya ajiye wayar ba tare da ya mata reply ba. Makaranta ya wuce, yai sa'a kuwa yana zuwa Malam na kokarin fita, nan ya ajiye mota ya karasa suka gaisa, Malam yai murmushi yace " Muhammad daga ina haka?" Ashraf yai murmushi yace " gaisawa nazo muyi." Malam yai dariya yace " nagode da baka manta da wannan tsohon ba." Nan sukai dariya, Malam yace " Ina Matar taka?" Ashraf yace " tana nan." Malam yace " yarinyar fa nake nufi." Ashraf yadan sosa keya. Malam yai murmushi yace " da alama tana nan." Ashraf ya kalleshi yace " malam tambaya nazo da ita." Malam yace " Allah g yasa na sani." Ashraf ya nisa sannan yace " kafin Abba ya rasu munyi tafiya ni da kai da shi ko?" Malam yace " Hakkun." Ashraf yace " Malam zaka iya tuna abinda ya faru a lokacin?" Malam yai murmushi yace " shekarun da yawa na dai san munje zagaye da taimakon bayin Allah dake da bukata, wannan shine tafiyarsa ta karshe." Ashraf ya jinjina kai yace " ba wani abu na mamaki da ya faru game da ni?" Malam yai shiru kafin yace " tabbas akwai na tuna, abinda ya dade yana bani mamaki." Ashraf ya kalleshi cikin zakuwa da sanjin menene. Malam yace " mu shiga ciki." Nan suka nufi makarantar. ********** Yau Datti yana tsakiyar bacci ya tashi cikin firgice tare da kwallama Nafi kira, sai kuma ya saki wani irin kuka mai ban tausayi. Yayansa ya shigo d'akin a tsorace ganin tsakar dare ne gashi ya tashi mutane da dama. Datti yana kuka yana cewa " a kiramin Nafi dan Allah ku taimaken ku kiramin Nafi." Yayansa ya shiga lalabashi yana cewa kai shiru Datti da alama ka samu lafiya tunda ka fara magana. Sai dai ina Datti kam abin ya canza salo daga kuka sai a kira masa Nafi kawai yake cewa. Nan suka shiga tambayarsa a wani gari Nafin take a kirata?" Kai kawai ya girgixawa alamar bai sani ba. Mamaki da tsoro ya kamasu. Mahaifiyarsa dake kwance ba lafiya tace "kila saidata yai saboda tsabar san kudinsa nikam na shiga uku na." Datti kam cewa yake a kira masa Nafi...... Nace ta yaya kenan?🤔 *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *72* Bayan sun zauna Malam ya kalli Ashraf wanda ya nutsu yana kallansa. Ashraf ganin Malam na kallansa baice komai ba yace " Malam ya akai?" Malam yai murmushi yace " tunowa nai lokacin da mukai wannan tafiyae bakafi dan haka ba " ya fada yana gwada tsayin Ashraf a lokacin. Ashraf yai kasa dakai yana murmushi. Malam yace " A wannan rana munje kauyuka da dama na kusa da na nesa, a karshe muka isa wani gungurmin kauye, wanda 'yan garin kana ganinsu kasan suna cikin tsananin wuya da talauci, nan muka isa gun mai garin aka tara 'yan garin aka fara basu sadaka, kaima kana mikawa. Gun yayi cunkoso wanda ya janyo turereniya agun, wasu suka dinga faduwa saboda karfin da kowa yake gwadawa. Ganinka mukai kabar gun rabon da dan gudunka. Nan Abbas ya leka ya ganka gaban wani bawan Allah, tsoho ne tukuf gaba d'aya gashin kansa fari ne ya tsufa sosai, wanda aka tureshi garin rigima ya fadi kasa. Da saurinka ka karasa kana neman d'aga mutumin, tsohon wanda kowa yake kyararsa sai cimai mutunci akeyi. Nan Ashraf ya taimakamai ka maidashi gefe, wani mutum ne ya jawoka yace " kai yaro ka raba kanka da wannan tsohon maye ne." Ashraf ya kalleshi shikam yarinta baisan ma me ake nufi da maye ba ya koma gunsa tare da d'auko abin sadaka guda biyu ya kaimai. Duk inda Ashraf yai sai mutumin nan ya bishi da kallo wanda hakan yasa muma jikinmu yai sanyi. Bayan kowa ya watse mutumin nan na nan a zaune ya taso dakyar yazo gun mu. Abbas ya kalleshi yace "Baba lafiya?" Tsoho ya kalli Ashraf wanda ke gefe yana alwala ya kalli Abbas yace " kaine babansa ko?" Cikin mamaki Abbas yace " ya akai ka sani?" Tsoho yai danyi dariya sannan ya kara kallan Ashraf ya kuma kalli Abbas yace " kwanakinka basu da tsayi, ko ince kwanakin ka sunzo karshe." Malam cikin b'acin rai ya kalli tsoho yace " kai miye hakan? Ta yaya zakazo ka samu mutane ka dinga fadamusu zancen banza haka? Kai Allahn masaru ne?" Tsohon ya girgiza kai sannan yace " ko d'aya ba kuma na fada bane dan ranka ya b'aci ba sai dai kanada makiya dayawa na jikinka kuma." Abbas ya kalleshi cikin shakkun kalamansa tabbas yasan yanada makiya amma bayasan aminta da maganan wannan tsohon da ya kai kusan shekara 100. Tsoho ya kalli Ashraf yana murmushi yace " kayi dacen d'a sai dai rayuwarsa zata zama a kewaye take da makiyansa." Abbas da Malam kawai kallan tsoho sukeyi, tsoho yacigaba " sai dai akwai farinciki a rayuwarsa in har ya rike matarsa ta farko, in kuwa ya rabu da ita banaji akwai wani farinciki da zai samu a rayuwarsa." Abbas ya mike cikin mamakin mutumi yace " malam wani irin zance kakeyi haka? Tayaya daga ganin yaro zaka fara cewa wai ba farinciki a rayuwarsa? Kasan me kake fada kuwa?" Tsoho yace " kamar yanda makiyanka na jini basa sanka kana tunanin zasuso d'anka?" Yana kainan ya juya zai tafi sai kuma ya kara juyowa yace " D'anka zai zama abin alfahari ga mutane, matar da zai aura ta farko itace zata zamar mai farincikinsa nan gaba." Yana kainan yai gaba, Abbas ya bishi da kallo kafin cikin tsoro yabi bayan mutumin sai dai babu shi ba alamar sa. Mai gari dake zaune yanajin komai ya kalli Abbas yace " Mutumin nan da kake gani ba wanda ya sanshi, shekararsa kusan d'ari ba aure ba zuri'a ba komai, ba wanda yake kusantar ko da magana dashi ne, sannan abun tsoro ga mutumin in dai ya fadi abu to fa sai dai wani iko Allah, shiyasa muke tsoron harka dashi, wasu sunce maye ne, wasu sunce baiwa gareshi wasu sunce kambun baka wasu sunce aljani ne, a zahirin gaskiya kowa da abinda yake fada sai dai Allah ne kadai masani." Malam ya kalli Ashraf wanda gaba d'aya shi hankalinsa nakan Malam. Malam yai murmushi yace "munyi mamaki kwarai da abin al'ajabi na wannan tsohon sai dai abinda ya tsoratamu shine mun gama sadaka muna kokarin tahowa aka sanar da mai gari mutuwar wannnan tsoho." Idanu Ashraf ya zaro yace " muna garin ya rasu?" Malam yai ajiyar zuciya yace " ban taba ganin abin al'ajabi irin wannan ba." Ashraf yai shiru yana kallan malam. Malam yace " shiyasa dakazomin dazancen rabuwarka da matarka ta farko naki aminta saboda inaji a jikina itace farin cikinka, bawai dan na yarda da abinda wani bawa na Allah ya fada ba sai dai shi dan Adam Allah ne kadai yasan baiwar dayama kowa." Ashraf yai shiru kafin daga bisani yace " to inkuma da ace Anisa na fara aure fa?" Malam yai murmushi yace " shiyasa nacemaka baiwar dan Adam Allah ne kadai yasan yawanta, dama can Allah ya tsara ba ita zaka fara aura ba." Ashraf yai shiru, tunaninsa ya tsaya cak. Malam yace " muje inada gun zuwa." Ashraf ya fito jiki a sanyaye ya shiga motarsa, idanunsa ya lumshe a zuciyarsa yace " kaddarace ta kaini kauyen garinsu, shi dama d'an adam rayuwarsa a tsare take." Sako ne ya shigo wayarsa ya d'aga wayar ya karanta kamar haka " _yaya inasan zuwa gidansu Ferry in ka bani izini, sannan zan kai mata kudin anko_" Kallan sunan daya sa mata yai Baby Feenah, a hankali ya goge sunan ya maidashi Nafisa. Yana kallan sunan daya canza mata ya furta a fili, I Am sorry Nafisa sai dai wannan ce hanya kadai dazaisa inyi fooling din kowa, inhar na sanar dake plan dina ba zakiji pain ba akan abinda zanyi sai dai hakan zai sa a gane ba gaskiya bane. Yai ajiyar zuciya tare da cewa " I am sorry for using u." Mota ya tada sannan yai gaba. Gidansu Habib yai ya tsaya a wajen gidan ya kurama gate din gidan ido, bakincikinsa yanda yakesan Dady da Habib, yanda yakesan kannen Habib, ya kara kallan gidan yace " Dady kaci amanata." Ya dade kafin daga bisani yaja motarsa yai gaba. Gida ya wuce, direct bangaren Umma yai, Umma tanajin sallamarsa mamaki ya kamata cikin zumudi. Bayan ta bud'e ya shiga kamar yanda ya saba fuskarshi a daure. Zama yai sannan ya kalli Umma tare da gaisheta. Umma ta baje baki tace " Ashraf yau da kanka?" Kasa yai dakai yace " Umma hakkinane ai." Ta kara washe baki yace " Anisa fa?" Tace " tad'an fita dazu." Murmushi yai yace " ok ba damuwa bari na wuce." Tace " a'a ka zauna insa a kawoma abinci." Ba musu ya amince da hakan." Da sauri Umma ta fita kamar ya sani sai ta sanar da Mumy, yana zaune kuwa ya fara cin abinci kenan sai ga Afra. Ta gaisheshi sannan yaga ta juya, ya sani mumy ce ta turota akan ta tabbatar ko yana can d'in. Ashraf yai murmushi ya cigaba da cin abincinsa. Ya kusa gamawa sai ga Asim. Asim mamaki ya kamashi cikin tsananin mamaki ya karaso yace " Kai kuma me kakeyi anan?" Ashraf ya kalli Umma. Da sauri Umma tace " ni nace ya zauna yaji abinci." Asim ya mata kallan mamaki, kallansa tai tamai alama da yaje d'akinta. Nan yai gaba ta bishi a baya suka rufo kofa. Ashraf ya mike ya bi bayansu. Asim ne ya kalli Umma yace " Umma meye hakan?" Tai dariya tace " Asim bansan meyasa kanka baya ja ba yaron nan yanzu ya san matsayin Anisa a zuciyarsa baka tunanin lokacine daya kamata muyi amfani dashi dan jansa a jikinmu?" Cikin fada yace " mujashi a jikin mu kamar ya?" Tai dariya tace " yanda zai saki jiki damu har ku gama gano komau kafin musan abinyi akansa." Asim yai dan tsaki sannan yace " Ni Abba ne ke ban haushi sam yana nuna ni ba komai bane." Umma ta kalleshi tace " kamar ya?" Ya kara tsaki yace " share, amma Umma menene a cikin wannan akwatin na kasan d'akin Abba?" "Shiiiiiiii" tamai alama da hannu tace " bakada hankali ne? Sai an jika? Ni kaina saboda wannan akwatin yasa inaji baya barin matansa sudinga shiga mai d'aki, inaji akwai wani sirri babba a ciki." Ashraf ya kalli kofar kafin ya juya yai gaba, akwati??? Ya maimaita a ransa. B'angarensa ya nufa, a bakin kofa ya hango kamar Nafisa, hakan yasa ya had'e rai tamau. Ko kallanta baiyi ba ya bud'e kofa ya shiga. Nafi wanda ganin yanda ya shareta kamar shara yasa jikinta ya kara sanyi, yau tun safe ruwan zafi kawai tasha sam ta kasa cin ko abinci. Ganin ya shiga yasa tabi bayansa, ta ajiye masa tiren abincin data kawo mai akan dinning sannan ta tsaya daga nesa tana kallansa. Gani tai ya d'auke kai daga kanta kamar baisan tana gun bama. Har ta bud'e baki zatai magana taga ya mikr ya shiga d'aki tare da rufo kofa. Hawayen da suka zubo mata ta share sannan ta fito a hankali tai b'angarensu. A falo taga Little tana kallo, bata ce mata komai ba tai d'aki. Little ta taso ta shigo tace " Yaya yace kije sannan in zakiyi amfani da kudi ki daina tambayarsa." Nafita dago a hankali ta kallu Little. Little tace " wai fada kukai? Akan me zai turob text bayan kinada waya?" Mikewa Nafi tai ta shiga toilet. Tsugunnawa tai sai kuka. *#ASHRAFEEMAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *73* Kuka take sosai a cikin band'aki tana tuno irin soyayyar da Ashraf ya nuna mata a 'yan kwanakin nan, ko dai da gaske ne dan ya riga ya santa a mace shiyasa yake mata haka? Jin yanda wayarta taketa kara ga Little sai kiranta takeyi yasa ta daure ta share hawayenta ta fito. Wayar ta d'auka tace " Ferry ya akai?" Ferry cikin zumudi tace " albishrinki?" Nafi ta daure tace " goro." Ferry tace " 8 credit gareki including math and English." Wani sanyin dadi ne ya kamata tace " haba?dagaske?" Ferry tace " wlh goegraphy ne kawai kike da pass." Nafi tai hamdallah sannan tace " kefa?" Ferry tace " 7 credit nima da maths da English." Nafi ta kara hamdallah sukai sallama. Little ta fadawa nan little ta taso da sauri ta rungumeta tana tayata farinciki. Nafi kam murmushi kawai take yi aranta fadi take inama yaya na kusa da farincikin yafi min dadi. ********** A b'angaren Ashraf kuwa tun bayan fitar Nafi ya zauna shiru yana tunanin ta anya kuwa ya dace abinda yake aikata mata? To amma ya zaiyi? Yasan sarai zata iya taimakamai wajen plan dinsa sai dai yana ganin in har tasan ba gaske bane yana ganinta a kusa dashi bayaji zai iya jure wulakantata, yafisan tai fishi dashi har ya cimma burinsa sannan ya nemi yafiyarta ya kuma amshi punishment din da zata bash na using dinta dayai. Anisa ce ta shigo d'akun ba ko sallama ta zo ta zauna kusa dashi tana zubamai shagwaba wai tun safe bata ganshi ba sai yanzu. Daurewa yai yace " nima nayi missing dink ai sosai." Kwantowa tai kan jikinsa tace " Yaya kaje asibiti?" Cikin mamak ya kalleta yace " Asibiti kuma?" Kallansa tai cikin dan hade rai tace " ba kace bakada lafiya ba? Jiya da daddare." Tunowa yai ya dan mike da sauri yace " eh naje anma ban magani." Ta dan turo baki tace " ka warke?" Ya juyo tare da dafata yace " daga shan magani sai warkewa?" Ta zumburo baki tace " nifa....." Waskewa yai ya jawota jikinsa. Bayan sun kwanta tana jikinsa itakam tayi missing dinsa, Ashraf cikin dabara yace " nikam kina shiga d'akin Kawu?" Kallansa tad'anyi tace " ba sosai ba dai." Yadan yi shiru hakan yasa tace " menene? Wani abu kake so?" Kai ya girgiza alamar a'a yace " bashi kawai banasan kowa yaji ne." Mikewa tai ta zauna tace " me kakeso?" Yace " dama akwai akwatin Abba na a kasan gadansa ne to kuma naga kamar Kawu bayasan in dauka, kinga in yaji na dauka ba da saninsa ba zai iya jin haushi." Anisa cikin rashin damuwa tace " menene a ciki?" Yace " kayan Abba ne na da can, su kadai ne ba'a bada ba na rasa me yasa kwanan nan nake san ganin su." Tausayinsa ne ya kamata tace " karka damu zan daukoma amma sai dai kana gama gani mu maida yanda bazai ma san ka dauka ba." Ashraf yai murmushin tausayi ya jawota jikinsa yace " Nisa nagode." Wani dadi ya kamata tace " yaya in akwai wani abu da kakeso ka sanar dani." Yace " abinda yasa ma ban fada miki da wuri ba banaso ne kowa ya sani, na kuma sanki komai sai kin fadama umma." Kai ta girgiza da sauri tace " wlh wannan bazan fada mata ba ko da kuwa kamani Kawu yai bazan taba fadan kaine kakesan gani ba." Cikin sanyin murya yace " Nagode Nisata." Nan sukai murmushi dukansu. ************ Washe gari kuwa kafin kawu ya fita gun aiki Anisa ta shiga d'akinsa, bayan sun gaisa ya kalleta cikin kulawa dan yanasan Anisa sosai yace " Anisa ta yau kuma ganina aka zo yi?" Kusa dashi ta zauna tace " Abba ba kai bane ka daina nemana?" Yai dariya yace " ina na isa in daina neman 'yata Anisa?" Itama dariya tai tace " Yaya na koma fa." Ya kalleta yace " Ummanki ta fadamin amma ni hankalina bai kwanta da Ashraf ba kina ganin fa abinda yamana akan yarinyar can." Dariya ta sakeyi tace " Abba kenan bakasan yanda Yaya ke kula dani ba yanzu komai nakeso shi yake min." Kawu ya kalleta yace " shiyasa ai banyarda dashi dinba." Anisa tadan tabe baki tace " Abba kenan." Kallan agogo yai yace " mu tafi ko?" Ta kwanta akan gadonsa tace " ni bacci ma zanyi anan." Cikin mamaki yace " anan din?" Kai ta daga tace " ina missing din kanshin Abba nane." Dariya yai yace " ni inada meeting bari naje inkin tashi kya kullemin kofar ki ajiye makullin agunki, karkuma ki bari kowa ya shigo, ki rufe kofar kafin ki kwanta." Tai dariya tace waye ma agidan dazai shigo. Yace " tashi muje ki kulle kafin ki kwanta." Ta tashi yana fita ta kulle sannan ta kira Ashraf tace "Yaya kana ina?" Yace " ina d'aki." Tace " in kawo ma." Da sauri yace " A'a Nisa in kika fito dashi wani ya gani fa?" Tace " ah haka ne, to ya za ai?" Shiru yai kafin yace, bari nazo nan din in yaso sai kije gun Umma in na gama gani sai in kiraki." Tace "bazan iya tsayawa mu gani tare ba?" Yace " banaso ne ki ga yanayin da zan shiga." Tai murmushin sannan tace " shikenan sai kazo." Yana fita ta leka karkashin gadon, karamin akwati ta gani dab kit, tai dariya tace " wannan ai karamin akwati ne nasan baifi kala daya bane a ciki " Ashraf na zuwa sukai canje ita tai bangaren Umma shi kuma ya shiga. Akan gado yaga akwatin jikinsa ne ya fara rawa a hankali ya karasa gun akwatin cikin shakku da tsoron abinda zai gani. Bayan ya zauna ya dade kafin ya daure ya bud'e akwatin. Idanunsa ya bud'e a hankali ya kalli cikin akwatin. Waya ya gani, da kuma envelope guda biyu. Wayar ya d'aga waya ce irin ta da jiki a sanyaye ya kunna wayar, hotonsa yana karami ne ya bayyana akan wayar idanunsa ne suka fifito, wayar mahaifinsa ce kenan? Envelope daya ya d'auko hotuna ne a ciki nan ya fito dasu, kana ganinsu kaga hoton da dan farare ne irin black and white din nan. Na farko hoton Kawu ne shida wani mutum suna tsaye jikin wata mota suna gaisawa da alama ma basusan an d'aukesu ba. Na biyu kawu ne da Dady da kuma wannan mutumin sun fito daga wani gida nan ma kana gani kasan basu san an daukesu ba. Na uku kuwa hoton Abbansa ne da Kawu ga Mumy a tsakiya. Kallan hotunan ya tsaya yi sai kuma ya d'auko wayarsa dake cikin jaka ya d'auki hutunan hoto. Sannan ya bud'e d'ayan envelope din, wasika ce. Mamaki ya kamashi ya kalli kasan wasikar an rubuta daga D'an uwanka Abbas. Idanu ya zaro da sauri ya zari takardar sannan ya nemo wata takardar a cikin jakarsa plain ya sa a ciki. Sannan ya sa waccan a aljihunsa. Wayar ya sake dauka, ya jujuyata sannan ya maidata, ya rufe sannan ya fito. Anisa yama waya ta dawo sannan yai office. Wanene wannan mutumin?abinda yake ta mai yawo kenan. Da sauri ya kira wayar D'an litti bayan sun gaisa yace " Dan Litti kana ina?" Yace " ka manta kace inje gidan Lawyer din nan inji ko mutumin ya dawo?" Ashraf ya dan shafi kansa yace " bar wannan kazo company yanzu akwai abinda nakeso kai da wannan dan sandan ku nemo min." Dan Litti yace " Yes sir." Nan ya juyar da kan mota yai gun Ashraf. Bayan ya shiga office dib Ashraf ya turamai hotob Kawu da wannan mutumin yace " wannan mutumin nakeso a nemomin inda yake, ni kuma zanje gub Uncle inji wanene shi." Dan Litti ya mai salute sannan ya fita. Ashraf ya zaro wasikar nan daga aljihunsa ya kura ma wasikar ido, a zahiri tsoron karantawa yake dan baisan mai zai jiyo wa kunnensa ba. Sai dai ko dan ya dawo da Nafisan sa kusa dashi dole yai saurin yib solving din wannan case din. ************ Nafi kam ita kadai tana kwance a d'aki yau ma ruwan zafi kawai tasha sam ta kasa cin komai taji an banko mata kofa. D'agowa tai a hankali dan ganin wanene. Anisa ce da Umma hakab yasa tadanyi tsaki kadan tare da maida kanta. Umma da Anisa suka shigo, Umma tace " ha'a su bora ashe ananan? Ko da yake anci jan miyan anci nama anci shinkafa inafa za'a yarda a koma riga a sha fura da kunu?" Nafi ba tanka musu ba, Anisa tai dariya tace " Umma ina tunanin ince yaya ya d'aukeni muje honeymoon ko paris ne muyi ko 1week ne." Nafi barasan sanda ta dago ba ta kalleta wani irin kalli wanda ita kanra batasan ta yi ba." Umma ta sa hannu ta hankadata kan gadon tace " me? Kishi kike? Ji kike kamar ki daketa?" Nafi kam shiru kawai tai, Anisa tai dariya tace " karki damu zan kawo miki takardar sakinki." Nafi ta mike tsaye ta musu wani kallo tace " in kun gama please kuyi waje." Anisa tace " mene?" Nafi tace " inda saura kuma ku gama kafin ku fita." Tana kainan ta kwanta akan gado tare da rufe idanta. Haushi ya turnukesu, Umma tace " Kyale ta zamugani ko bakin nanan in har aka bata takardarta." Dariya suka sa sannan sukai waje. Nace uhmmmmm *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *74* _Zuwa ga Muktar_ _Ba sai munja duguwar magana ba, na sani bazan tashi daga kwanciyar nan ba._ _Da farko dai ina mai baka hakuri abisa rashin sanina na san Ruma da kakeyi wanda kai baka aureta ba ta kuma zama matar yayanka, Allah shine shaidata ban taba sanin kana santa ba ko da kuwa da wasa ne._ _Abu na biyu shine kayu hakuri abisa rashin kula dakai da banyi ba, ganin yanda ka canza hali ka rikid'e zuwa mutum mai tsananin buri da kuma neman sai ya samu abinda yakeso ko ta halin ka ka ne yasa na shiga tunanin laifinane da ban kula dakai da kyau ba, Muktar ita rayuwa da kake ganinta ba'a mata buri mai yawa, ba kuma a cewa komai sai an samu, na sani sarai kaine kai manakisa ka sanar da abokinka da yake aikin custom akan su Hisham sun saro miyagun abubuwa, bayan rasuwar mahaifin Ruma nai bincike akai anan na gano kaine kasanar da abokinka, na fahimci so kake ka hadani fada da Hisham da iyayen Ruma wanda harzai sa su rabani da Ruma._ _kai ka zuga dan siyasa wato Chirman Santa akan ya ba Hisham makudan kudi ya kuma nemi ya taimakamai da saro miyagun abubuwa, sannan ka karkata ka sanar da abokinka, duk daga baya na gane trap ne ka shirya dan rabani da Hisham da iyayensa._ _Muktar na dade ina mamaki akan wannan al'amari, na d'auka ka hakura da Ruma ganin akwai zuri'a a tsakaninmu, sai dai daga a yayin da nai hatsari na gane lalai ba hakura kai da ita ba shiri kakeyi ta yanda zaka sameta ko ta halin kaka ne._ _Muktar na sani sarai da kai da Hisham kune sanadin wannan hatsarin nawa, domin kuwa na san komai, kun samu Auwal Max akan ya lalata birkin motata sai dai a lokacin da na sani lokaci ya riga ya kuremin domin kuwa ina cikin mota nayi nisa da fara tafiya, Isma'il ya turomin da hotunan ku gidana wanda Ruma ta kirani cikin gaggawa sai dai lokaci ya riga ya kuremin, ko ince dama can kwanana ya kare._ _Ban taba tunanin tsanar da kakemin zatakai ga hallakani ba, na maka komai na rayuwa, na kuma nemi 'yarka da ta zama matar d'ana, sai dai a wannan lokacin na janye zancen auren Anisa da Ashraf, banaso d'ana ya fiskanci kiyayya da wahalar danasha a gunku, ya rayuwarsa zata kasance inhar yaji Mahaifin matarsa shine yai sanadiyar nasa mahaifin?_ _Muktar nayi iya bakin kokarina wajen farantamaka da janka a jiki duk da nasan tsananin kiyayyar da kakemin akan Ruma da dukiyata sai dai ina rokonka kar wannan kiyayar ta koma kan d'ana, na yafe maka duk abinda kamin, amma bazan taba yafemaka ba in har ka cutar da Ashraf._ *Daga D'an uwanka Abbas* Da sauri Ashraf ya saki takardar yana girgiza kai cikin tsananin firgice, lalai Kawu mutum ne wanda dole aji tsoronsa, kasa ya sauka jikinsa sai rawa yake ya jingina da bango tare da hade kafafunsa yana girgiza kai kenan Kawu shine yasa aka kama kayan su Dady dan yasan halin Abbansa bazai taba taimakon su ba akan harkar miyagun aiyuka ba. Kansa ya cusa cikin cinyoyinsa a hankali hawaye ya fara zubo mai, wayarsa ce take ta kara sai dai sam ya kasa ko da mikewa, yanaji wayar har ta gaji ta katse. Ya dade a wannan yanayi kafin ya daure ya d'au wayarsa da taketa faman kara, Dan litti ne da kyar ya daga batare da yace komai ba. Dan litti yace " Oga Auwal Max ne a hoton nan." Kai ya daga kawai dama jikinsa ya gama bashi nan ya katse wayar tare da yin shiru, ya akai hotunan da aka ba mumy suka kare a hannun kawu? Da sauri ya mike ya zari makulli yai waje cikin tsananin rudani. Bangaren Mumy ya nufa zuciyarsa na masa wani irin radadi, banko kofa yai da karfin tsiya wanda ita kuma tana zaune rike da karamin hoto, tana jin yanda aka banko kofar ta mike da sauri hoton ya fadi kasa, kallan hoton yai ganin Abbansa ne a jiki. Wata irin dariyar takaici ya saki ya matso kusa da ita ya tsugunna ya dau hoton ya kalleta cikin tsananin takaici yace " me kikeyi da wannan?" Kallansa take cikin wani yanayi, ganin yanda ya rikid'e gaba daya, tace " Ashraf." Kallanta yai idanunsa sunyi jaa sosai yace " me kikeyi da hoton mahaifina? Bayan da ke aka hada baki akai komai?" Kallansa tai tace " Ashraf wai meke damunka ne kwanan nan da baka iya boye emotion din ka?" Ha ha ha ha! Yai tafi da hannunsa yace " Emotion? Kamar yanda kikeyi? Ku halaka min uba sannan ki wani dauki hotonsa kina kallo?" Idanu ta runtse cikin wani yanayi, wayarsa ya bud'e ya shiga nuna mata hotunan nan, yace " hoton nan ke Isma'il yaba shaidar shirin da Dady da kawu sukeyi na halaka mahaifina, tambaya ta anan shine tayaya akai hotunan nan suka isa gun Kawu?" Kallansa tai sai dai ta kasa magana sai hawaye kawai takeyi, Ashraf yace " Good! Dama nasan bakida amsa, sai dai Mumy dukanku sai kun amshi laifinku a gaban hukuma an muku hukunci." Yana kai nan ya juya zai fita, haryaje bakin kofa yaji tace " Kana tunanin duk a san raina nake komai?" Tsayawa yai cak ba tare da ya juyo ba, tana kallan bayansa ga hawaye na zuba sosai a idanunta tace " me kake tunani? Banasan Mahaifinka? Ashraf na auri mahaifinka ne saboda soyayya ba dan komai ba." Juyowa yai yace " a'a kin aureshi ne saboda kudin sa." Cikin zafi tace"lokacin dana auri Abbas kana tunanin yanada kudi? Mahaifina shine ya neman masa aiki har ya zama abinda ya zama." Ashraf ya kalleta baice komai ba. Mumy ta zauna jabbas akan kujera ta share hawayenta tace " Zauna." Jikinsa a sanyaye ya zauna yana kallanta. Mumy ta kara share kwallarta sannan tace " Muktar bakasan wanene shi ba haryanzu, mutum ne wanda inyace yanasan kaza to fa sai ya sameshi ko da kuwa ta wani hali ne, bayan aurena da mahaifinka har Allah ya azirtashi ya gina wannan gidan baisan Muktar na sona ba, ni kaina sai bayan mun zauna tare sannan nai dana sani sosai dana amince da wannan hadin gidan. Muktar haka zai zo bangarena ya dade duk yanda naso ya tafi bazai tafi ba, anan zaici abinci ni kuma sai dai in shige d'aki. Danama Abbas magana sai yace kar in damu ba komai. Tsoro na ya fara yawa ne daga sanda Muktar ya shigomin d'aki ina bacci ya zauna kusa dani, idona a rufe na dauka Abbas ne inaji yana ta shafamin kai ina murmushi, sai dai daga sanda na bude ido na ganshi na mike da sauri na sa hijab na fara mai masifa. Abinda ya tsoratani shima cikin masifa ya matso ya turani jikin bango gaba daya idanunsa sun canza kamar bashi ba yace " Ruma kinsan tun yaushe nake dakon kaunarki? Banaji duk duniya akwai wanda ya isa ya rabani dake, wlh kinji na rantse miki sai na mallakeki ko ta wani hali ne." Ya sakeni yai waje a fusace. Tun daga wannan rana na fara rufe bangarena sai kuma awannan lokacin Abbas yasan komai sai dai bai taba kawowa Muktar zaiyi tunanin mun wani abuba." Mumy taja wani numfashi tacigaba, a sanda suka hada plan din halaka mahaifinka matar Dady taji komai, sanda aka kawomin hoto ina kokarin kiran Abbas matar ya hisham ta kirani nan ta sanar dani komai. Cikin rikicewa na kira Abbas na sanar dashi sai dai alokacin yana mota, bayan yayi hatsari ne ya sanar dani inyi a hankali da muktar lalai zai iya yimaka illa." Ashraf jin Mumy tayi shiru yasa yace " naji na kuma fahimta sai dai tambayata anan shine ta yaya hotunan nan suka je gun Kawu?" Tace "Dauka yai da ina asibiti." Ashraf yace " menene dalilin dayasa kafin Abba ya rasu ya bar zama dake kullum sai dai ya zauna dani?" Kallan Ashraf tai cikin wani yanayi tace " Ashraf wlh sharri akamin, Muktar ne ya d'aukoni daga gidan Ya hisham sai yace yanada abinda zai kai Tahir Guest palace shine muka shiga, ni a mota ma na tsaya ya shiga ya fito amma bansan ya akai ba wani ya dau hoto ya turama Abbas, tundaga lokacin naga ya daina shiga harkata sam nikuma ban kawo komai a raina ba, sai bayan yayi hatsari ya sanar dani dalili." Kallan rashin aminta Ashraf ya mata sannan ya mike tsaye yace " kinsan yana sanki akan me zaki yarda har ya daukoki? Sannan akan me zaki aureshi bayan kinsan shine ajalin mijinki?" Kuka Mumy tasa sosai tace " Ashraf bazaka taba fahimtata ba, Na auri Muktar ne dan na kareka, na auri Muktar ne dan na kare yayana na auri Muktar ne dan kare dukiyar da mahaifinka ya tara da guminsa." Ba tare da ya zauna ba ya mata kallan mamaki. Mumy kuka take sosai tace " Muktar shi yaba Ya hisham shawarar a halaka Abbas sai dai ya Hisham shine ya sanar da Driver din Abbas, wanda ashe cikin shirinshi ne ya dau recording din maganar Ya hisham a sanda yake bada umarni, bayan anyi sadakar bakwai ya kawomin ya bani naji yace bazai kuma yadda da kashemai dan uwa da hisham yai ba, sai dai alokacin banida evidence da zai nuna hardashi, shi kuma yanada wanda inyakai kotu kama ya Hisham ba wani abu bane." Ashraf ya kalli Mumy baice komai ba. Tacigaba " Ashraf." Idanunsa ne suka ciciko da kwalla yace " what about me?" cikin wani yanayi yake maganar, yace " nifa? Wanda baki taba ba kulawa ba, baki taba sanin matsalata ba? Nifa?" Hawayenta ya tsananta sosai da sosai, sai dai ta kasa magana, Ashraf ya daki inda zuciyarsa take yace " yanda baki taba kula da halin da nake ciki ba banaji kinsan matsalar mahaifina, tunda har shima zai dauke miki kafa amma baki tambayeshi dalili ba, wace irin rayuwa kuka jefa Mahaifina a ciki? Ke da kike matarsa bakisan matsalarsa ba kamar yanda bakisan ta danki ba, shi da yake dan uwansa yana neman illatashi, kamar yanda yake neman illatani." Ya juya cikin wani yanayi ya fara tafiya yana hard'e kafa saura kiris ya fadi yaji an rikeshi. A hankali ya dago ya kalleta, kuka take sosai, ta taso da niyyar zuwa gaida Mumy taji maganar Ashraf cikin b'acin rai daga bakin kofa. Kallan ta ya tsaya yi zuciyarshi na tafasa, dagewa yai yana neman maida kwallarsa, Nafi kuka take sosai idanunta na kansa. Lumshe idanunsa yai ya bude su ya kalleta yace " Nafisa ya akeso inyi da rayuwata? Me yasa ba wanda yake fahimtar kuna da radadin da zuciyata keyi?" Kuka takeyi cikin kuka tace " Yaya Allahn daya hallacemu yafi kowa sanin halin da kake ciki kuma shi zai kawo maka mafita." Murmushi yai sannan ya zare hannunta daga jikinsa ya mike yai waje. Mota ya fada yai waje da gudu, tafiya kawai yake, babban burinsa bai wuce yaga Nafi a jikinsa ba tana lallashinsa sai dai ya zai yi? Ya fahimta Mumy ba da ita akai komai ba sai dai bazai taba fahimtar selfishness dinta ba na kin kula da mijinta da danta ba. *********** Mumy kam yana fita ta tsugunna tana kuka, cikin kuka tace " Ashraf nasani sarai laifinane sai dai tsoro nake in nuna maka soyayya kishin Muktar ya motsa ya nemi halakamin kai." Nafi ta kalleta tace " Mumy na fahimceki sai dai duk da ba hurimina bane zance abu daya, rashin nuna soyayyarki ga Yaya bai hana Kawu tsanarsa ba da san halakashi, wannan dalilin shi zai sa Yaya ya kasa fahimtar dalilin ki na kin nunamai kulawa." Tana kainan tai waje tana share hawaye. D'akinta ta nufa ta zauna ta bude wani shafin kukan, ya zatai da Ashraf? He is soo pitiful, ita tsoronta ma kar wani ciwo ya kamashi. Jitai gefen cikinta ya rike, ta san matsalar sarai rashin cin abincine sai dai ta ina zata iya tauna abinci bayan yanzu tasan yaya ko ruwa bataji zai iya hadiya a halin daya tsinci kansa?" *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 _Maman Shaheed wannan shafin sadaukarwace gareki, Allah ya kareki a duk inda kike Ameen_ *75* Ya dade a waje kafin zuciyarsa ta daidaita ya dawo gida, har ya kusa isa gida ya kira Anisa, ta d'aga cikin tsananin farin ciki, yace " Nisa kina ina?" Tace " ina nan gidan su Zee." Yace " bari nazo na daukeki." Wani dadine ya kamata suna kashe waya ta saki wani ihu na farin ciki gaskiya yanzu ta aminta da san da Ashraf yake mata, nan Zee taita tsokananta wai ta dinga ja mai class, itakam ita kadai tasan abinda ta gani da yanda taji asanda ya juya mata baya. Ashraf yai shiru bayan sun gama waya har yanzu yana mamakin kawu, ya sani sarai mutum ne mai tsananin ambition sai dai bai taba tunanin haka b'oyayyun halayensa suke ba, da har zaiyi threatening din mahaifiyarsa da yakeso akan laifin da yayanta dashi suka aikata akan ta aureshi, shiru yai yana tunani kafin yai gwafa sannan ya kira Dan Litti, bugu biyu ya daga. Ashraf yace " Dan Litti ka nutsu sosai ka ji mai zanje maka." Nan ya shiga mai bayani da ni kaina bansan me suke cewa ba sai dai sunkai kusan minti 20 suna waya kafin daga bisani Ashraf yace " Ka fahimceni?" Dan Litti yace " yes sir, yanzu zakama Lawyer din maganar ko inje?" Ashraf yace " karka damu kai dai ka samo mutanen da zamu yarda dasu wanda kuma baza'ai suspecting dinsu ba." Nan suka karasa bayanansu sannan sukai sallama. Gidansu Zee ya wuce ya d'auko Anisa tana ta zubamai sakalci a hanya shidai sai kokari yake kawai yana biye mata. Nafi na zaune a barandar b'angarensu tana jiran taga shigowar Ashraf dan sam hankalinta ya kasa kwanciya ganin yanayin da ya fita. Shigowar motarsa ce yasa ta saki ajiyar zuciya tare da mikewa tana kallo yai Parking sannan taga ya fito. Murmushi ta saki ganin fuskarsa dauke da fara'a, sai dai me? Anisa taga ta fito ta d'aya b'angaren ta matso kusa dashi ta sakala hannunta cikin nasa, kallan juna taga sunyi suka sakarma juna murmushi. Jitai wani abu ya tokare mata a makoshinta da sauri tai ciki tana kokarin kakaro numfashi. Da kyar ta samu numfashinta ya daidaita kafin ta saki wani irin kuka, tace " ni ina nan hankalina ya kasa kwanciya saboda kai amma kai kana gun matarka kuna soyayya? Yaya ya kakeso inyi da rayuwata?" Wajen karfe shabiyu na dare taji ta kasa bacci wani irin ciwo cikinta yake mata, dakyar ta iya daukan waya ta kira Little. Little ta dauka da sauri tace " Feenah tun dazu nake nemanki, yau bazan dawo gida ba ina hostel, gobe 7 zamuyi text ga malamin ba shida sauki." Da kyar Nafi ta iya cewa "to" Ta yarda wayar tanaji Little na kiranta sai dai azaba ta hanata dauka. Little da sauri ta kashe ta kira Yaya, wanda shikuma alokacin suna kwance da Anisa ya samu dakyar ya lalabata tai bacci wai ita adole sai sun gwada ko ya warke, da kyar ya samu ya shawo kanta ta hakura. Yanajin ringing din wayarsa ya zare jikinsa daga nata yai falo, ya daga cikin mamakin ganin number Little. Cikin rud'ewa Little tace " Yaya inaji Nafi bata da lafiya dama tun jiya na kula ba tacin abinci sai ruwan zafi to yanzu kuma ta kirani naji muryarta ba dadi." Cikin rud'ewa yace " kedin kina ina?" Tace " makaranta." Tsaki yaja sannan yai waje da sauri ya manta ko kaya bai canza ba, yana zuwa ya bud'e kofar yajita kuwa a bude da alama ta barma Little kofar ne inta dawo. Da sauri ya shiga ciki ya bude kofar d'akin. A durkushe ya ganta a kasa tana murkusus, da sauri ya karasa gunta a kid'eme ya d'agota cikin tsananin firgice. Nafi kam azaba kawai takeji, hannunsa ta rike kam tace " yaya cikina." Kara rud'ewa yai yace " Nafisa? Me yasamu cikin? Bakici abici bane?" Kasa bashi amsa tai a rude ya dawo falonsu ya hada mata tea mai kauri ya dawo gunta ya kwanto ta jikinsa ya fara bata, sha kawai takeyi dan bazata iyamai musu ba, haka yai ta bata har ta shanye sannan ya d'auketa ya maida ita kan gado ya kwantar tare da ja mata bargo. Kanta ya shiga shafawa a hankali bacci ya dauketa. Ido ya kura mata cikin wani yanayi na dana sani da yakeyi, idanunsa ne suka kada sukai jaa a hankali yace " Am sry Nafisa, it's all my fault." Ganin kamar baccin ya fara nisa yasa ya mike a hankali zai tafi, hannunsa ta riko, wanda hakan yasa ya tsaya ba tare da ya juyo ba. Nafi ta bud'e ido a hankali tace " Yaya ina rokon Allah ya kawomin cuta a kullum indai har hakan ne kadai zaisa inganka a kusa........." Saurin matsowa yai gunta yasa hannunsa ya toshe mata bakinta yace " Nafisa me kike fada haka? " Lumshe ido tai ta bud'e sannan ta zare hannunsa daga bakinta tace " in har hakane zai sa inganka zan iya horar da kaina da abinda yafi yunwa ma." Kallan mamaki ya mata yace " Kada ki kuskura ki sake dan kuwa bazan yafe ma kaina ba inhar wani abun ya sameki." Kallansa tai tare da daura kanta kanta kan cinyarsa a hankali tace " Yaya ban iya san abu ba, in har nai nisa asan abu jinake bazan iya rayuwa ba tare da abun nan ba, tunda nake a rayuwata ban taba san abu ba kamar kai, juyamin bayan dakai jinake kamar duk duniyar ta juyamin baya, sam..........." Matsowa yai da kansa batai auni ba taji bakinsa cikin nata,lalai sunyi missing din juna, jiyai sam ya kasa tsaida hankalinsa nan kowa ya shiga nunama dan uwansa tsantsar rashin junansu da sukai......... Sai bayan komai ya kammala sannan bacci mai nauyin gaske yai gaba da ita bayan sunyi wanka, kura mata ido yai yanaji a ransa shifa yafi santa akan yanda takeji akansa, shikadai yasan ya zuciyarsa takeji inya ganta. Ya dade a gunta sai wajen karfe 3 sannan ya fito daga d'akin yai bangarensa. ************* A kwance ya tada Anisa da alama ma ko farkawa batai ba kallanta yai yanajin tsantsar tsanar mahaifinta na kara ratsashi. Falo ya fito ya kwanta yadanyi bacci kadan kafin asuba. Nafi kam tunda ta tashi taji ciwon cikin ya tafi sai wani tsantsar farin ciki da takeyi, idanunta a rufe ta fara shashafa gado dan jin masoyinta, jin ba alamunsa yasa ta farko baki ta turo ganin ba ya nan, a ranta tace "mayb masallaci yaje." Sallah tai sannan tadan kishingida, wani bacci ne ya kara gaba da ita. ********** Asim yaje shiga office yaji wasu mutane daga gefensa suna magana. "kai amma na tausayama Zakari, yanzu duk girman company din nan nasa haka zai saidashi da arha?" D'ayan yace "nikaina tausayinsa nakeji, to ya zaiyi duk kadarar tasa ta karye." Matsawa kusa dasu Asim yai yace " wani Zakarin?" Wanda ya fara magana yace " Yallabai Zakari dai mai company din sabulai da mayuka na jiki, lotion da sabulu." Asim yace " garin yaya?" Mutumin yace " wlh karayar arziki ce ta sameshi komai nashi ya kare sai company din gashi dansa ba lafiya." Asim cikin zakuwa yace " kuma nawa zai saida?" Mutumin ya danyi shiru kafin yace " million 190 dai naji ana cewa, shiyasa kowa yake tausaya mai ganin guri ne babba mai kyau ga kayan aiki da komai a kalla gun nan yakai million 250 amma mutumin nan ya karyar da shi." Asim yai shiru kafin daga bisani ya shiga office dinsa, shiru yai yana tunani kafin yace " in nasai company din nan lalai ba karamar garabasa zan samu ba, yanda zan nunama Abba nima na fara abin kaina ba wai dashi na dogara ba." Ya danyi murmushin mugunta yace " gaba ko Ashraf ya kwace company dinsa nidai inada makafa" wayarsa ya zaro ya duba account dinsa, million 30 ne a ciki kansa ya dafa cikin takaici yace ina zan samu kudi bayan ko rabi bandashi?" Sauri yai ya kira Anisa yace " kanwata wannan takardun haryanzu sunanan a inda suke?" Ta mike tare da dubawa tace " eh." Ajiyar zuciya yai yace " guda nawa ne ma?" Ta fito dasu tace " da alama ma ya kara wasu a gun da guda biyar ne yanzu kuwa sunkai 8." Yace " ganinan zanzo yanzu in amsa." Tace " amma yaya....." Yace " karki damu bazai gane ba, inma ya gane sai musan karyar da zamuyi ko kuma yau da yamma kiyi kuka ki kirashi kice barayi sun shigo." Tace "to." Can kuma yace " a'a ba haka ba yau da daddare zansa a shigo gidan sai ki bar kofar a bud'e muyi kamar yan fashi ne suka zo." Tace "yauwa hakan dai yafi." Shiru yai yana tunani dole duk da haka yana bukatar wasu kudin ya tabbata wannan bazai isheshi ba, fitowa yai ya samu Secretary dinsa yace " yana bukatar account book na Company din nan." Nan yai waje dan amsowa, Asim yai murmushi yace " ko na dau kudin Company ba abinda Abba ya isa ya min." Nace hmmmm ********* Nafi kam sunyi waya da Ferry tace " Little ta kaimata kudin, harta je kasuwa ma ta siy musu." Nafi tace "to ina amarya?" Ferry tace " tana gun dangin mamanta taje sallama." Jin ance mamanta yasa jikin Nafi yai sanyi, haka dai sukai ta waya har suka gama, Nafi tana kashe wayar ta kwantar da kanta kan kujera tace " ko ina ni tawa uwar?" *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *_Gareku 'yan Group d'ina The Queen Bee & Ayusher Fan Club.....Really luv u ol ❤_* *76* Ashraf na tasowa daga gun aiki ya wuce ban gareb Mumy, bai sameta a falo ba sai Afra ce tace mai tana d'aki tun jiya batajin dadi, nan ya wuce d'akin. A kwance take sai dai jin kwankwasawa yasa ta mike ta bud'e, Ashraf ya shigo tare da zama a kasa ya gaisheta, ta amsa a hankali sannan ya kalleta yace " Mumy tambaya nazo da ita." Gabanta ne ya fadi dan itakam tsoron tambayoyin Ashraf take, ya kalleta yace " gidajen Dady na waye?" Kallansa tai bakinta yadan motsa kadan tace " wasu nawa ne wasu kuma nashi ne." Kallanta ya sakeyi yace " asibitin Dady ya akai shima yaje hannunsa?" Gabanta ne ya fadi ta kallu Ashraf cikin dan rawar murya tace " Mahaifinka ne........" Katseta yai yace " sanda Abba yaki taimakama Dady har abin yazama ajalin Mahaifinki bakiji haushin Abba ba?" Kallansa tai sai dai ta kasa magana, Murmushi yai sannan yace " Kince bakyasan kawu saki yai kika aureshi a dole saboda Dady meyasa kina aurensa kika hada zuri'a dashi bayan a fadarki ba sanshi kike ba ga haushin ya yi sanadin mijinki?" Idanunta ta runtse a hankali hawaye ya zubo mata, Ashraf ya mike tsaye yace " no matter what i can't understand u Mumy, ke kanwar Dady ce, sannan matar Abba ta da sannan matar Kawu ta yanzu, duk inda na duba kina tsakiya." Mikewa yai jiki a sanyaye yai waje har yaje fali ta fito da sauri tace "MUHAMMAD." Tsayawa yai jiki a sanyaye idanunsa sun rukid'e, tace " zo." A hankali ya koma d'akin ta zauna a bakin gadi shikuma ya zauna kusa da ita a kasa,Mumy tace " Ashraf duk na fahimceka sannan koma wanene dole ne indai yanada zarfafa tunani yai mamakin wad'an nan abubuwan." Ashraf cikin zafin rai yace " bayan mahaifinki ya rasu ba shine dalilinki na fara kula Kawu ba har ya jawo zargi tsakani........." Batasan sanda ta mareshi ba, bai dago ba sai dai yana ji dole ne ya fada mata abinda zai kona mata rai ko dan ta sanar dashi abinda ke b'oye. Mumy ta share kwallarta tace " Kana nufin da aure na nai tarayya da kanin mijina? Dan kawai in rama abinda yamin kome?" Ashraf a ransa yace " kiyi hakuri nima maganar ba har raina na fada ba." Jin yayi shiru tacigaba " Tunda nake ban taba shakkar wani abu ba kamar ka, gashi dai ni na haifeka amma ina tsoron halayenka na zuciya da fadar magana ta yadda kai ra'ayi, ko Mansir da nasan zai iyayin ko menene a rayuwarsa bana shakkarsa sai dai ina tsoron abinda zai maka." Kallanta Ashraf yai, tai murmushin takaici sannan tace " tabbas idan nace maka banji haushin Abbas ba alokacin nasan dole bazaka yarda ba ko ince ba ma mai yarda da ni." Tai ajiyar zuciya kafin ta cigaba " Bayan rasuwar mahaifina ga mahaifiyataba kwance yasa ya Hisham ya kirani cikin fishi yacemin Ruma haryanzu kina tunanin Abbas nasanki?duk abinda ya mana?" Kallansa nai cikin kunar abinda ya faru sannan nace " Yaya amma......." Ya Hisham ya katseni da cewa " Abbas dukiyarsa ce kawai ke rudarsa in bakiyi wasa ba nan gaba kadan kema zaki rasa matsayinki a gunsa." Kalamannan sun tsorata ni matuka wanda yasa na kalli Mansir wanda yake zaune a falon, Mansir yai ajiyar zuciya yace " ke kanwar Hisham ce ta jini dolene ki taimakeshi ya samu ya farfado dan kuwa makarantar da Abbas ya bashi ba abinda zata iya mai." Na dau kudirin taimakama ya Hisham wanda hakan yasa nabarmai gidajen da Abbas ya dinga bani kadan kadan tun farko da ya sai karamin gida na haya dama ni yaba, tun daga nan yake bani kusan duk shekara. Bayan naba yaya ne nace zan dawo gida sakamakon hakurin da Abbas yai ta zuwa yana bawa yaya. A wannan lokacin shine Mansir ya daukoni dan Abbas baya kasar a lokacin. Ban taba tunanin Mansir ya shiryamin gadar zare ba ya kaini Tahir guest Palace da sunan dauko abu ashe yasa a dau hotonmu a ba Abbas. Ashraf ya kalleta yace " amma wa yasa?" Tace " Driver din Abbas yanda yasan in har Abbas ya gani dole yai zargina saboda yasan yaron bazai kai karya ba, sai dai abinda bai sani ba, Mansir da Ya Hisham sun riga sun siye zuciyar yaron." Tai dan hucci sannan ta cigaba " maganar gidaje kenan." Maganar asibiti kuma wannan tabbas nasan laifinane dan nina sanar ma yaya zan sa Abbas ya bashi asibitin sai dai a ranar da zan sanar da Abbas a ranar yai hatsarin mota, gashi a lokacin ya Hisham ya gama sanar da matarsa da wasu nashi na kusa akan an bashi asibiti, bayan rasuwar Abbas ne yaya ya samen yace ban kyautamai ba sai dana bari kowa ya sani ashe ni ko fadama Abbas banyi ba. Jiki na yai sanyi, shine mansir ya bamshawara akan tunda kai yaro ne sannan d'anane ba wani abun bane in na dauka na ba yayana. Sunje sunsa anyi rubutu irin na Abbas wanda ni kuma nai shaidar hakan. Kwallarta ta goge tace " Ashraf nasani nayi ba daidai ba sai dai ina tsoron abinda ya samu Abbana ya samu dan uwana, iyayenmu duk sun rasu shi kadai ya ragemub wanda nakeji bazan iya yarda abin duniya yasa in rasashi ba. Ashraf ya kalleta sannan yace " Mumy kina tunanin saboda kunyi amfani da dukiyar da take gado na nake fadar haka? Ko kadan dukiyar nan bata gabana dan wlh zan iya barinta in dauki matata in bar garin nan, sai dai abinda ke damuna ya zakuyi da zunubin da kuka daukarma kanku? In ni ina raye zan iya yafemuku Abba fa? Ya kuke tunanin Little da Habib zasuji in suka ji komai?" Idanu ta runtse tace " Nasani munyi ba daidai ba sai dai ba yanda zamuyi tunda abu ya riga ya faru." Ashraf yai shiru kawai yana kallanta, ta nisa sannan tace "maganar zuri'a kuma dana hada da mansir nasani shine babban kuskuren dana tafka a rayuwa sai dai ya zanyi? Allah ya riga ya rubuta akwai 'ya'ya a tsakaninmu dashi." Mikewa Ashraf yai ya shafi kansa sannan yace " kujira hukuncin da Kuto zata muku dukanku, banaji zan iya yafe muku dan kun ci amanar Mahaifina sannan hukuncin da za'a muku shi kadai ne zai sa a kama kawu akan babban laifin daya aikata." Yana kainan yai waje. Sama ya kura ma ido zuciyarsa na tafasa lalai shikam ya gaji da jin abubuwa kala kala, sai dai yanzu komai ya ware mai kuma tabbas ne ya gurfanar da kawu gaban hukuma ko da kuwa komai nasa zai kare. ************ A ranar kuwa da daddare Asim ya turo 'yan fashi suka sashe takardun nan Ashraf kam ya nuna da gaske yaji ba dadi sai dai a ransa yana mamakin lalai Asim sam kansa baya ja, ace mutum duk yanda aka nemi ayi amfani dakai ba ka wani tunani sai ka bi? Anisa kam kuka tasa wai ita a dole tana tayashi bakin ciki, ya jawota jikinsa yace " karki damu Nisa sai dai please karki fadama kowa abinda ya faru banasan azo ana kace nace." Kai ta daga alamar to. ****** Asim yaje ya ga filaye manyan gaske sannan ga gonaki, nan ya ba wani dilallinaka sasu a kasuwa, bai wani tsula musu kudi dayawa ba wanda hakan yasa aka sai dasu cikin kankanin lokaci, ya amshi kudinsa Million 20 cif ya hada da nasa yaga million 50, takaici ya kamashi ganin ko rabi bai hada ba, gun Umma yaje ya mata bayani har ta gamsu itama ta dauko tata kadarar aka harhada aka saida, ansamu an hada 90 million, nan fa ya shiga neman yanda zaiyi ya samu ragowar gashi yaje yaga Company din ya birgeshi sosai wanda ya kara rinjayarsa, sannan ance akwai mutane da sukeso dayawa, nan ya samu Zakari ya bashi 90m yace zai ciko nan da 2dyz. ************ Nafi kam tun daga ranar da Ashraf ya tafi ya barta washegari bayan sunyi waya da Ferry akan shagalin biki Ferry take tambayarsa Ashraf, Nafi tai ajiyar zuciya tace " Ferry sam yanzu ya canzamin, jinake zuciyata kamar zata fashe." Ferry tai tsaki tace " wato nema kike ki koma Nafi ko?" Cikin mamaki tace " bangane ba." Ferry ta kara ja mata tsaki tace " kin manta yanzu Feenah kike ba Nafi ba? In ya canza miki kema ki canza masa an fada miki kowani namijine yake so yaga an like masa?" Nafi tace "Ferry bazaki gane bane yaya na cikin......" Ferry tace " ni kin bani kunya ma wlh shiyasa yake miki abinda yaga dama tunda kin gama nunamau shine rayuwarki gaba d'aya." Nan ferry tasata a gaba da fada. Tundaga wannan rana Nafi bata kara bari sun hadu da Ashraf ba, sai dai tana ganinsa a b'oye ganib hankalinsa kamar a kwance yake yasa itama ta kara kwantae da nata. ********** Yau Ashraf na zaune a office Salin ya kirashi ya sanar dashi tabbas Auwal Max an ganshi yanzu ma suna tare da wanda yasa ya nemoshi suna hanyar zuwa kano tare. Dadi sosai ya kama Ashraf ya kira dan sandan nan abokinsa yace " ka nemomin Dan siyasan nan dana ce maka?" Yace " haryanzu dai ranka ya dade ba labari." Ashraf yai ajiyar zuciya. Nan sukai sallama, Ashraf ya kalli Dan Litti dake tsaye yace " ana azahar kazo mu tafi." Yace " ok sir, amma maganar Asim." Ashraf ya kalleshi yace " ya? Ya d'ebi kudin company din?" Dan litti yace " inaji dan d'azu Zakari ya kira yace yakaimai cikon kud'in." Ashraf ya hada hannayensa yace " good, kace ya bashi takardun company din ya kuma yi signing." Dan litti cikin mamaki yace " amma in akai haka ba a bashi company din ba?" Ashraf yai murmushi yace " ai dama so nake ya zama nashi." Dan litti yamai kallan mamaki sannan yace " ko da yake Ina ni ina sanin abinda Kake tunani?" Dariya sukama juna kafin Dan Litti ya fita. Nace Hmmm *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *77* Ana azahar Dan Litti yazo suka fita shida Ashraf, gidan Salim suka wuce. Falo suka nufa inda Salim yace musu Auwal max na ciki, Ashraf ya kalli Dan Litti yace " dole ne ka hade rai ka maida abu serious." Dan litti ya jinjina kai sannan suka shiga. Ashraf da sauri ya isa gun Auwal ya kama hannunsa cikin nuna tsananin kulawa yace " Uncle kana lafiya? Badai abinda ya sameka ko?" Auwal cikin tsananin mamaki ya ke kallan Ashraf. Ashraf yace " ko ba Auwal bane?" Yace " nine Auwal Max" Ashraf ya zaunar dashi sannan ya zauna a gefensa ya kama hannunsa yace " nine Asim, babban d'an gidan Mansir." Sai a lokacin Auwal ya saki fuska, Ashraf ya kara rike hannun sa Yace " Abba ne yace in tabbata na samoka kafin Ashraf ya fara samunka." Auwal yace "Ashraf D'an....?" Ashraf ya karasamai " dan Abbas marigayi." Idanu Auwal ya zaro cikin tsananin tsoro yace " ya akai ya sanni?" Ashraf ya dan saki fuska cikin yanayin damuwa, Dan litti yace " bincike yake akan abinda ya faru a baya." Auwal cikin tsananin rud'ewa yace " inalilahi ya zanyi? Nikam na shiga uku, banda masifun da suke afkuwa akaina yanzu kuma wannan?" Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Abba yace inkula dakai sannan yace in tambayeka ranar meya faru? Har dakai akai hatsarin ko yaya?" Auwal ya kalli Ashraf yace " mantawa yai? Ai na sanar dashi komai." Shiru Ashraf yai yana tunani, sai jin Auwal yai yace " bayan mun shiga mota ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, aikuwa tana kira yace inje shi bari yaja motar, da alama dai Mansir ya manta da hakan." Ashraf yai dariya yace " da alama kasan yanzu abubuwa sunmai yawa dole ne mantuwa ta dinga shiga." Auwal ya jinjina kai, Ashraf yace " amma ai ba wata hanya da Ashraf zai gane kaine ka lalata birkin ko?" Auwal yai shiru yana tunani kafin daga bisani yace " kai, babu sai dai in mahaifiyarka." Cikin mamaki Ashrad yace " Umma?" Auwal ya jinjina kai yace " ita kadai ce ta ganni lokacin da nake aikin, bayan ita gaskiya ba kowa." Ashraf yai murmushi yace " ai bakomai indai Umma ce, amma Dady fa?" Auwal yace "Dady?" "Hisham nake nufi." Auwal yai dariya yace " shi ai bashi ya sani ba shine dai ya bani kudin aikina." Ashraf yace " nasan wannan wai nufina baku kara haduwa ba?" Auwal yace " ina zanganshi nida na koma garinmu?" Ashraf ya kara rike hannunsa yace "karka damu Abba yace inkula dakai ba abinda zai faru." Auwal yai ajiyar zuciya sannan yace "tunda na taho gabana ke faduwa sai yanzu hankalina ya kwanta." Ashraf yamai murmushi. Auwal ya kalli Ashraf yace " Amma kafi kama da Abbas, sam baka kama da mansir." Ashraf ya shafi fuskarsa yace " duk ba jini d'aya bane su? Kowa haka yake cemin wai nafi kama da Marigayi, shikuma Ashraf din inka ganshi abin mamaki kamarsu d'aya da Abbana." Auwal yace " ikon Allah, ai nikam bazan taba mantawa da Abbas ba, naci amanarsa na yaudaresa shiyasa nake ganin ishara kala kala." Ashraf yace " karka damu ka kwantar da hankalinka." Auwal ya daga kai. Ashraf ya kalli Dan litti yace " ka maidashi gidana na Darmanawa." Dan litti ya amsa da to, sannan ya kalli Auwal yace muje ko? Ashraf ya mikamai kudi yace kasai mai abinda zai bukata na nan da sati d'aya. Kallansa Auwal yai yace "har sati zanyi anan?" Ashraf yace " tsoro nake kar mu maidaka Ashraf ya sa a kamaka." Jin zancen kamawa yasa yace "to ai ba laifi satin ma." Nan sukai waje Ashraf ya bishi da wani kallo na takaici, sannan ya zaro wayarsa dayai recording ya sa a computer ya yanke maganar daga inda yace " _Nine Auwal Max_" Ya tura ma Kawu da d'aya wayarsa. Kawu wanda ya fito daga meeting kenan ya ga anturo mai email yana bud'ewa yaji muryar Auwal da abinda yace. Mamaki ya kamashi, meye hakan kuma???? Bai kawo komai ba yai gaba. Salim ya kalli Ashraf yace " amma kana tunanin zaiji wani abu dan yaji suna kawai?" Ashraf yai wani murmushi yace " it won't be fun in na turamai komai a lokaci d'aya, so nake naga yanda hankalinsa zai fita daga jikinsa a kowace rana, yana wannan case din ga kuma na d'ansa." Salim ya dafa Ashraf yace " U are very smart Ashraf sai dai please kayi a hankali dan ina tsoron wannan kawun naka." Ashraf yace " karka damu Uncle, sannan ina tunanin Mumy ne, in barta anan ko inkaita wata kasar, kar ya hanani komai saboda ita." Salim yai shiru sannan yace " tabbas kayi tunani dan kuwa zai iya cewa zai mata illa inkaki bin umarninsa." Ashraf yace " shi nake tsoro." Uncle yace " ka sata kawai ta tafi umara, taje ma ta nemi yafiya tai ibada ko ta samu rangwame." Ashraf yace " nagode Uncle." Nan ya fito. ********** Su Asim an mallaki company murna a wannan rana ba'a magana, dashi da Anisa da Umma da sauran kannansa sunje sunga guri kowa ya yaba sannan ya kira mahaifinsa ya sanar dashi. Mamaki ya kama Kawu a ina Asim ya samu kudin siyan Company? Sai dai haka ya karasa company din dan tabbatarma idanunsa. Mamaki sosai yakeyi ganin wannan katon guri wai mallakin d'ansa ne, ya kalli Asim cikin zargi yace " ina ka samu kud'i?" Asim yai shiru yana tunanin karyar da zaiyi, sai dai kafin ya furta komai sai ga wasu mutane ne nan su hud'u sanye da kayan 'yan sanda sunzo kusa da Asim. Nan fa kowa ya matso ana san ganin menene. Na gabansu ya zaro id card dinsa yace " I am Sergeant Kabir." Asim ya mai kallan banza yace " me ya damen da sunan ka?" Ankwa ya ciro yace " u are under arrest." Asim ya kalli Kawu sannan ya kallesu yace " ban gane ba, me nai?" Kabir ya cafki hannunsa ya fara kokarin sa mai ankwa Asim na turgewa. Kawu ya rike hannun Kabir yace " me yai?" Kabir yace " an kai kararsa akan d'eban kudin company dayai " Kallan mamaki Kawu yama Asim yace " me kenan?" Asim ya shiga jijiga kai yana cewa " Abba ba Company dinmu bane, ai ba wani abun bane in na ranci kudi a ciki." Hankalin kawu ya tashi yace " ku tsaya ayi magana." Kabir yace " i am sry sir, bayan wannan yana dauke da laifin satar kayan da ba nashi ba." . Asim cikin rud'ewa yace " mena sata kuma?" Kabir yace " filayen daka saida takardun ba na gaskiya bane bayan kuma ka riga ka amshi kudin mutane." Asim ya rikice ya kalli Kawu yace " Abba." Kawu wanda gaba d'aya yama rasa abinyi yace " yanzu me kuke bukata?" Kabir ya karasa datsamai ankwa yace " am sry sir dole ne ya biyomu." Yana kai nan yaja hannun Asim. Umma wacce ta saki wani ihu tare da bin bayansu tana kira sai dai ina.....Sunyi gaba, Anisa ma kuka take sosai, Umma ta matso gun Kawu ta rikemai kwallar riga tace " malam ka wuce ka amsomin d'ana." Kawu ga runtse ido cikin takaici, Umma ta kara rikicewa tana masifa. Kawu ya fizge jikinsa yace " me yasa kwatakwata kwakwalwar yaron nan kamar ta kifi take? Bashida hankali ne ko me? Ke ma kina ina da kika kasa bashi shawara,?in har bazaki iya dashi ba ai sai ki sanar min, yanzu wani irin abune wannan?" Ya fada cikin tsananin takaici. Nikam nace 🤷🏻‍♀ ko a jikina. Lol masoyan Asim amin afuwa, duk da banaji yanada masoya.....Lol *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *78* Asim kam duk ya gama rikicewa sai rokon Kawu yakeyi, Umma kam kuka kawai takeyi tana itadai a anso mata d'anta. Sun isa police station akasa Asim a wani dan karamin d'aki dan yin bincike kafin a rufeshi. Kawu ya karaso a tasa motar ya umarci a barshi ya fara magana da Asim, ba musu kuwa suka barshi. D'akin ya shiga ya kalli Asim yace " ina kasamo filayen gidaje da gonaki haka?" Gabansa ne ya fadi, ta ina zai iya cewa satarsu yai? Cikin rawar murya yace " siya nai." Kawu ya bugamai wani kallo yace " Asim kana wasa dani, wlh akan kai kadai bazan yi asarar abinda na tara da kyar ba, zan iya yanke tsakanina dakai in har naga kana neman zubarmin da kemata." Asim ya kara rikicewa yana rokon Kawu akan yai hakuri, kawu yace " kasan nawa kaci kudin company kuwa? Banda zubarmin da mutunci dakai, dole haka nan nizan yi kashin wad'an nan kudin, kafi kowa sani dukiyar Abbas a karkashin Ashraf take ba ni ba ai." Asim ya sauka kasa ya rike kafafun Kawu yace " Abba dan Allah ka taimakeni, bazan iya zama a wannan gurin ba, kafi kowa sani kaf 'ya'yanka bamai maka biyaya dayin abinda kakeso farat d'aya kamar ni, saboda haka ko aure ban taba sha'awar yi ba karma matata tazo tanemi samin wani ra'ayi." Abba ya kwace kafarsa da karfi wanda hakan yasa Asim fad'uwa, yace " na rasa wace irin kwakwalwar tumakai gareka, mema ya kaika siyan wani company? Meka rasa na rayuwa?" Asim kuka kawai yake yana rokon kawu, kawu ya nunashi da yatsa yace " wannan damuwarka ce da alama zaka ziyarci prison." Yana fada yai gaba yakai wajen kofa Asim yace " wato ka gama shan mangwaro shine kakeneman yadda kwallan?" Kawu ya juyo ya kalleshi, Asim yace " me kake tunani Abba? Bansan komai game da kai ba? Nafa sani kaine ka sa aka lalata birkin Ashraf a sanda ya b'ata, ba kasheshi kaso kai........." Kawu ne ya matso cikin zafin nama ya toshemai baki tare da jinginashi da bango, yace " bakada hankali ne? Me kake fada haka?" Asim ya dan shiga kakari saboda yaji matsar, Kabir da yake zaune yana kallo da jinsu a d'akin da ake ganin komai through computer ya mike tare da kallan su ya kashe abin CCTV din da microphone din sannan ya kira Ashraf ya sanar dashi komai. Wani Murmushi Ashraf yai yace " karka damu ganinan ma shigowa gun." Suna gama wayar dama yana kokarin ajiye mota ne, nan ya fito hankalinsa a kwance yai ciki. Anisa ya gani a bakin kofar da Umma sun zauna a kasa kamar marayu, Anisa tana ganin Ashraf ta taho da gudu ta rungumeshi tana kuka, Ashraf yadan zare jikinsa tare da ce mata "Nisa a waje fa muke." Da kyar ta d'agashi sai dai haryanzu kuka take, Umma ta mike ta kama hannun Ashraf tace " Ashraf ka taimaka ka anso mana yaron can, da alama Mahaifinsa bashida niyar ansoshi." Ashraf ya kalleta cikin kulawa yace " karki damu Umma bari naje naji yanda ake ciki, amma ku me kuke anan?" Umma tace " banasan shiga ne, bansan da wani ido zan kalli Asim a cikib wannan gun ba." Ashraf yace " bari na shiga naji." Nan yai cikin station din. D'akin da suke ya kwankwasa, Kawu ya sake Asim sannan yace ya shigo. Ashraf ya shiga cikin nuna kulawa yace " Kawu meke faruwa?" Kawu ya kalli Ashraf sannan ya kalli Asim cikin takaici yace "ohon masa, nema yake kawai ya zubarmin da mutunci." Ashraf ya kallu Asim yace " Asim a ina ka samu takardun filayen? Wannan ita kadaice hanyar da zaisa a warware komai." Asim ya hadiye yawon wahala, ina zai iya furtawa da bakinsa yace shi ya turo 'yan fashi. Kawu takaici ya kamashi a zuciye yai waje. Asim ya matso kusa da Ashraf yace " Ashraf dan Allah ka taimakeni wlh bazan iya zama anan ba ko da na awannine ka taimaken dan Allah." Ashraf yace " karka damu zamusan yanda za'ai." Ya fito waje. Kawu ya gani yanawa Kabir magana, nan ya matsa gun, yanaji Kawu yace " kana nufin kudin Company din ma sai na biya double?" Kabir yace " sry sir amma haka ka'ida take, duk wanda yai embezzlement din kudin Company dolene ya biya double." Gumi ne ya karyoma Kawu, nan yai gaba ba tare da yace komai ba, aransa fadi yake lalai Asim bashida hankali, haka kawai baici ba baisha ba asashi biyan kudi har million 200 a yini d'aya? Ashraf ne ya d'au wayarsa dake aljihunsa ya turamai voice note din Auwal Max daya d'auka. Kawu yana ganin sako gabansa ya fadi, da sauri yai waje yanaji su Umma namai magana amma ko sauraransu baiyi ba yai waje, ya kunna sakon. _Ai ko layin bamu fita ba na sa matata ta kirani a waya akan batada lafiya dan nasan yallabai zai barni, da alama dai Mansir ya manta da hakan._ Gaban kawu ne yai mugun faduwa, cikin tsananin rikicewa ya shiga waiwaigawa, zuciyarsa ce tacemai Ashraf. Nan ya koma cikin station din da sauri, can yaga Ashraf zaune kusa da Kabir suna magana, matsawa yai gunsu jiyai Ashraf yace "Yanzu Officer ba yanda za'ayi?" Kabir yace" dolene sai ya biya kud'ad'an nan dan kuwa hakkin jama'a ne." Kawu yai ajiyar zuciya da alama dai ba Ashraf bane nan yai waje. Kabir ya kalli Ashraf ya sa dariya. Shima dariya Ashraf din yai yace " Kb ka tabbatar ka tsareshi dakyau." Kabir yace " karka damu mutumina." Ashraf yazo ya lallaba Umma da Anisa ya kaisu gida, yana fitowa zai shiga b'angaren Mumy ya hango Nafi daga nesa. Ta sha kwalliya sosai da sosai, ya shagala sosai wajen kallanta tana tafe tana lallatsa waya, gani yai kamar ta kara wani irin mugun kyau. Ya shagala sosai da kallanta yaji alamar sako a wayarsa. Nan ya duba, daga Nafi ne, _Yaya zanje gidansu Ferry._ D'agowa yai da sauri dan ya kara ganinta sai dai me? Wayam ya gani ba Nafi. Da sauri ya matso yana nemanta, sai dai bai ganta ba. Gun mai gadi ya nufa da sauri yace " Nafisa ta fita ne?" Mai gadin yace " eh yanzun nan." Ashraf ya leka waje da sauri, yana ganinta ta shiga motar Nabil, jiyai ransa ya sosu sai dai kafin ya karasa fitowa sunyi gaba. Motar yabi da kallo sannan ya juya jiki a sanyaye. B'angaren Mumy ya shiga, tana zaune a falo tana cin abincin rana. Fuska ya daure tamau sannan ya zauna suka gaisa. Ta amsa a hankali tace " kaje gun Asim ne?" Bai amsa tambayarta ba sai cewa yai, passport dinki nake so." Kallan mamaki tamai tace " me za'ai dashi?" Yace " umara zakije kida Nafisa." Tace " Umara?" Ya kalleta yace " garin nake so ki bari, saboda in na barki anan Kawu zai yi tunanin amfani dake wajen tsaidani daga kamashi, sai dai banaji akwai abinda zai tsaidani, shiyasa nakesan ki bar garin in na kamashi sai ku dawo." Kallan sa tai cikin wani yanayi, yace " karkiyi tunanin yafe maki laifinki nai, in kika dawo kema zaki je kuto a miki naki hukuncin." Hawayenta ta maida sannan ta d'aga kai tace " ni naji nawa dalilin amma nafisa fa?" Yace " Tsoro nake kar wani abu ya sameta, duk da na juya mata baya saboda banasan mutanen gidan su damu da ita, amma a zuciyata kullum da ita nake kwana nake tashi, ku tafi tare ko Allah zaisa ma taga mahaifiyarta." Mumy ta jinjina kai alamar gamsuwa tace " Ya Hisham fa?" Yace " Duk wanda yai laifi dole ne ya karbi hukuncin shi a duniya, shine kadai gatan da zan iya muku." Yana kaiwa nan yai waje. B'angarensu Little ya nufa, dan yanasan ganinta. Daga lungun kofar ya ganta tsaye itada Habib, kasa karasawa yai yatsaya kawai jikinsa duk yai sanyi, ya zasuji in komai ya fito? Ya sani Habib ba wai san Little yake ba amma ita fa? Gata yarinya ya zatai??? ************* Nafi kam Nabil na jan mota yace mata " mutuminki fa ya fito, ina kallansa ta madubi." Murmushi tai tace " share kawai Ya Nabil, shima hidimar gabansa ta mai yawa." Nabil yai dariya yace " ko dai fadan masoya kuke?" Tai dariya tace " ba wani fada, ko dan kaga nace inzaka wuce kazo mu tafi? Wannan ma ai dan naji kana anguwarmu ne." Nabil yai murmushi yace " Feenah Allah nikam Ashraf ya gama kwafsamin, da ya kwaceki." Harararsa tai tace " Ya Nabil ba nace ka daina min wannan zancen ba? Nifa kanwarka ce." Yai ajiyar zuciya yace "ya zanyi tunda an maidani yayan karfi da yaji." Zatai magana taji sako ya shigo wayarta. Ashraf ne hakan yasa ta bud'e da sauri _Wajen karfe 4 za'azo a d'aukeki akwai inda za'akaiki._ Ta dan turo baki tace " ina za'a kaini??? Nabil ya kalleta yace " ya akai?" Tace "bakomai." Shikam Ashraf Dan Litti ya kira ya sanar dashi karfe 4 yaje ya d'auki Nafisa ya kaita inda akeyin passport akwai wani abokinsa daya kira yace suje 4 lokacin mutane duk sun ragu. Dan Litti yace "da alama yau zanga Nafinmu kenan." Nace lalai anfa dade ba'a gamu ba.....Lol😄 *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 _Sakonku ya isa gareni masoyana, insha Allah zanyi kokarin kammalawa zuwa sallah, ni kaina nakosa ingama, fatana dai kutayani addu'a Allah ya bani ikon gamawa lafiya...._ *Nagode kwarai!* *79* Da yamma kuwa Dan Litti ya nufi addreshin da Ashraf ya turomai na gidan su Ferry. Nan ya kira Ashraf ya sanar dash ya isa shikuma ya ma Nafi sako akan ta fita wanda zai kaita ya iso. Sunyi sallama dasu Umma sannan ta fito itada Ferry, ganin motar Ashraf yasa ta nufi motar. Dan Litti yana ganinsun iso ya fito sanye da sunglasses, zaresu yai ya kallesu, Nafi kallansa take cikin mamaki shima kallanta yake. Fuska ya hade tamau yace "malama lafiya?" Nafi tace " bangane ba?" Dan litti ya maida glass dinsa ya kalleta yace " Na fada miki bai kamata ki dinga bin mijin dake da aure ba, a kalla dai mutum ya dinga sanin darajarsa." Nafi ta hade rai itama tace " kai kuma a wani matsayin kenan kake sanar dani haka?" Mota ya bud'e yace " malama dan Allah kiyi gaba akwai wacce nake jira ne, tunda kinga ba mai motar bane ai sai ki kara mai." Nafi da Ferry suka kallu juna, ferry tace " ruwa zata kara ba mai ba, sannan kai wanene ma?" Ya kalli Ferry cikin isa yace " The Hand Right of Ashaf." Dariyarsu suka guntse Ferry ta kalli Nafi tace " ke kuma fa?" Nafi ta kalli Dan Litti tace " As his wife." Duk da kalmar taba Ferry mamaki sai dai ta dauka ko dan ta kular da Dan Litti ne yasa ta fadan haka. Idanu Dan Litti ya zaro yace " matarsa? Amma matan Ashraf ai na sansu." Kai ta juya, da sauri ya kira wayar Ashraf yasa a hands free. Ashraf ya daga yace " mutumin ya akai?" Dan Litti ya kalli Nafi yace " wata ce take tutiya wai matarka ce." Yace " wata kamar ya?" Ferry ta fizge wayar ta mikama Nafi. Nafi tace " Hello." Ashraf yace " Nafisa? Ya akai? Kinga Dan Littin?" Kallan juna sukai daga ita har Dan littin. Cikin mamaki tace " Dan Litti?" Shima yace " Nafisa?" Ashraf yai murmushi yace " Da alama baku hadu ba sai yau." ya kashe wayar. Dan Litti tsananin mamaki ya kamashi, kallan Nafi ya shiga yi. Nafi cikin mamaki tace " Dan Littin gayu? Kaine?" Kansa ya sosa yai kasa da kai yace " Hajiya Nafi wannan ko a mafarki naganki akacemin kece ai bazan yarda ba." Dariya tai, Ferry tace " au dama kunsan juna?" Nafi tace " Kauyenmu d'aya." Ferry tai dariya tace " lalai yau akwai hirar gida kenan, ni nayi ciki." Nan ta musu sallama tai gaba. Ashraf ya bud'ema Nafi gidan baya ta shiga. Mamaki har yanzu bai barsu ba. Ya ja mota yana tambayarta ya akai bai taba ganinta ba? Tace " wai da gaske a nan gida kake? Nima ban taba haduwa dakai ba a gidan mayb shiyasa bamu fahimci juna ba." Hira suke sosai har suka isa inda zasu, waya ya kira akace su shiga. Nan suka shiga ciki aka mata hoto sannan aka basu form da sauran abubuwa. Ba musu take yin komai, sai dai tana bukatar amsar tambayoyinta daga bakin Ashraf. Sun dade sosai sai bayan magrib suka fito, akan sai zuwa gobe azo a amsa. Gida suka wuce, ta kalleshi tace " kana zuwa gida kuwa?" Yace " nadaije kwanakin can da dadewa." Tai shiru kafin tace " Baffa fa?" Shiri yai shima kafin ya daure yace " yayi aure sannan ya bata labarin zuwansu da kamashi da akai." Tayi dariya sosai jin turancinsa abinda ya ja mai. Suna isa gida sukai sallama sannan tai bangarensu, duk da tana san magana da Ashraf sai dai tana tsoron zuwa bangaren tagansu da Anisa. ********** Washe gari da safe, Ashraf yai wanka ya fito, bangaren Umma ya fara zuwa, tana kwance ba lafiya dan hawan jininta ya tashi, Anisa na zaune kusa da ita. Ya gaishesu sannan yace zaije station yaji ya ake ciki, Umma tamai godiya tare da rokon ya taimaka ma Asim. Ashraf yana fitowa ya kira Habib yace " mutumin kana ina?" Yace " ina gida." Yace " Dady fa?" Yace " wlh dazun nan ya fita wai banki zaije, nace zan rakashi ma yaki." Ashraf yai murmushi dan dama jikinshi ya bashi za'ai haka. Mota ya fada Dan Litti yace mu tafi? Ashraf ya girgiza kai yace " yanzu kawu zai fito so nake kabi bayansa ka sanar dani inda zaije." Dan litti ya amsa da to, sannan yai waje shikuma Ashraf ya ja motar yai gaba. Wayarsa ta jaka ya dauka ya kara turama Kawu sakob Auwal. Kawu wanda ke ta zirga zirga a falon, hankalinsa duk ya gama dugunzuma bacci ma kasa samu yai jiya, yanajin sakon Auwal hankalinsa ya kara tashi ainun, da sauri ya kira number Dady. Dadu ya dauka yace " Ya akai Mansir?" Kawu yace " ya ya? Ka ciro kudin?" Dady yace " ganinan na fito daga bankin yanzu sai dai ina za'a kawoma kudin? Sannan kana tunanin inkaba Auwal zai kyalemu kaga wlh duk na tattare kudina na sa a jakar nan." Kawu yace " ni zansan yanda za'ai, sannan karka damu nace zan san yanda za'ai wasu kudin su shigo." Dady yai ajiyar zuciya sannan ya kashe. Kawu ya runtse ido yace " yanzu na samu kudin da zan taimaki Asim, in na gama dashi sai in dawo kan Auwal." (Azahiri gaskiya Ashraf dama ya sani sarai, yasab duk yanda kawu yaso ga san Dansa bazai tava yadda ya tattare arzikin daya tara dakyar ba ya taimaki Asim ba, ya kuma san kawu zaiyi amfani da sakon magana na Auwal dayake turamai yai blackmailing din dady akan Auwal ne yake bukatar wannan uban kudi ko kuwa ya toba musu asiri.) _Wannan kenan_ Kawu ya fito da sauri ya fada mota sannan ya turama Dady sako akan inda yake so su hadu. Dan litti kam yana biye dasu har suka isa Mariri gun da gidaje ma kwayanune a gun. Nan ya kira Ashraf wanda ke zaune a office hankalinsa a kwance yanashan tea, jin inda kawu yai yasa ya kira Kabir ya sanar dashi inda suke tare da cewa " ku tabbatar kun kwace." Kb yace " karka damu abokina yaran danasa bazasu baka kunya ba." Nan ya kashe wayar ya cigaba da shan shayinsa cikin annashuwa. Kawu kam ya isa wani kango ya kira Dady yace " ya ya? Ka taho?" Yace " ganinan na gangaro." Daf da gun kadan Dady na tuka mota ga gun hanyar duk batada kyau wasu mutane ya gani a gabansa sanyi da kyalle baki sun rufe daga hancinsu, tsoro yasa ya taka burki tare da kallansu. Nan suka zo suka bud'e motar d'aya yasamai bindiga d'ayan kuna ya d'auke jakar kudin, suka hau mashin sukai gaba. Dady kam hannu kawai ya dora akai sam ya kasa komai. Wayarsa ce tai kara ya duba ganin kawu ne yasa ya daga cikin tsananin tashin hankali yace " Mansir na mutu, na shiga uku, million 80 din dana dauko an kwacesu." Yana kainan ya kasa magana. Kawu ya fito a rikice, nan ya hangoshi ya isa inda yake cikin tsananin tashin hankali. Ashraf ya gama shan shayinsa ya kwantar da kansa kan kujera tare da lumshe ido yace " Dady taya zaka bari Kawu ya dinga juya ka? Da na dauka kai ne mai wayau akansa sai dai yanzu na gane kai din a ido ne kake da cikar zati amma kawu ya fika nesa ba kusa ba." Kawu cikin kunci da bakinciki ya isa station shikam Dady dakyar ya karasa gida idanunsa da jikinsa duk sun nuna alamar damuwa Da karayar zuci. Kawu yana shiga station din wani tunani ya fado mai, ya akai aka kwace kudin da su biyu suka san da shi? Da sauri ya kira Secretary dinsa yace " dubamin ka gani Ashraf yazo?" Nan yaje ya dubomai aka sanar dashi ai tun safe daya shiga office ma bai fito ba. Hannunsa ya dunkule ya naushi bango wanda wani radadi da zugi suka ziyarceshi, yace cikin takaici "To waye? In har ba Ashraf bane wanene wannan da yake neman dimautani?yake neman ganin karshena?" Zufa ce ta karyomai ya karasa cikin station din ya samu kabir yace ya ake ciki? Kabir yace " yaki fadar inda ya samu wannan filayen, sannan wadanda suka bashi kudi sunce tabbas suna bukatar kudinsu yau zuwa gobe." Kawu yace "in aka ki fa?" Kb yai dariya yace " ai dole ne ma abiya dan kuwa kuto za'a shiga dashi wani satin dokene yabiya kudi sannan asan kuma hukuncin da za'amai " Kawu yace " hukunci?" Kb yace " kwarai dan in har satarsu yai to fa lalai sai ya ziyarci prison." Hankalin Kawu ya kara tashi, jiki a sanyaye ya fito ko Asim bai gani ba. Da yamma Dan Litti ya amso passport din Nafi nan Ashraf ya sa aka musu visa na umara wanda zasu tashi jibi nan, dan dama yafisan su tafi da wuri to sai yai sa'a ya samu International saboda ya tabbata daga Asim ya sanar da kawu a inda ya dauko takardun nan to fa babu makawa yasan shikenan Kawu zai san shine ya shirya komai... Hmmmmmm😷 *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *80* Mikewa yai daga zaman da yake tare da furzar da wata iska sannan ya d'au wayarsa yama Nafi da mumy sako akan su shirya saboda tafiyarsu. Nafi kam kallan sakon take tayi, duk da tana masifar san zuwa kasa mai tsarki sai dai abin ya zo mata a ba zata, na farko ga bikin Jibiya wanda ya matso daf sannan ita a iya saninta Hajj ake fara yi tunda shine farilla. Sai dai taci alwashin yima Ashraf magana in ya dawo. ********* Sai Yamma ya fito daga office station ya wuce inda acan ya samu Umma, kana ganinta kasan tana cikin wani halin kusa da ita ya karasa yace " Umma lafiya?" Hawaye ne ke zubowa a idanta tace " Ashraf banga alama Mansir nada niyyar taimakama Asim ba, na sanshi sarai akan dukiyarsa zai iya hakura da Asim a matsayin d'ansa ni kuma na tattare dukiyata naba Asim ya sa a kudin company din da ya siya." Ashraf yai shiru tabbas ganin halin da take ciki ya sa ya tausaya mata sai dai bazai taba yin bailing Asim ba dan kuwa shine key dinsa na kama Ubansa. Umma yaji ta kamo hannunsa tace " Ashraf na sani tun kana karami ba sanka nake ba, ban damu da harkarka ba sai dukiyarka, har rayuwarka na nemi salwantarwa ni da Asim, sai dai a yanzu ina dana sanin hakan, banida wanda zan iya roka akan ya taimaki Asim sama da kai, ka sani iyayena ba masu karfi bane ga girma ta zo musu, ni kuma banida uban kudin da ake bukata, Ashraf ka dubi girman Allah ka taimaki Asim." Ashraf ya kalleta cikin kulawa zuciyarshi ta farayin sanyi, sai dai tunowa dayai ita kadaice taga Auwal Max a yayin da yake lalata birkin mahaifinsa yasa ya dake. Yace " Umma karki damu muna tattaunawa da 'yan sandan insha Allah komai zai yi daidai." Idanu ta runtse tace " Nagode Ashraf ban taba tunanin zan nemi taimako a gunka ba." Ashraf yai murmushi sannan ya mike. Gun Kb ya nufa, Kb yace " ya za'ai da kudin nan?" Ashraf yace " ka kai banki a jiya bayan komai ya kammala zamu maidamai kudinsa." Kb ya jinjina kai alamar gamsuwa sannan yace " what are u planning to do next?" Ashraf yace " D'an Siyasan nan fa? Har yanzu shiru?" Kb yace " yau muke sa ran dawowar yaron daya tafi binciken." Ashraf yace " Allah yasa a sameshi wannan karan." Kb ya amsa da Amin. Gun Asim ya shiga, Asim har yayi baki ya rame, dan tunda yazo gun nan ya kasa cin abincinsu. Ashraf ya kalleshi yace " Asim ance baka cin abinci, kasan dai dole ne kaci abinci ko ma samu mu gama wannan fadan da ya tunkaromu lafiya ko?" Asim wanda kansa ke kwance kan tabir din ya dago ya kalli Ashraf yace " Nasani ni kuma tawa ta riga ta kare." Ashraf yace " Haba Asim da hankalinka kuwa?" Asim yai wata dariya ta tsantsar takaici, yace " rayuwa kenan, mahaifina da na dauka duk duniya yafi damuwa dani sai gashi lokacin da nake bukatar kulawarsa ya nunamin karema ya fini matsayi a gunsa, sannan kai da nake ganin kaine babban makiyina a duniya yau gashi kaine kake kula dani." Ashraf ya hade rai yace " kai dai ka daina wannan tunanin na shirme ka kula da kanka har Allah ya kawo mana mafita." Asim yai murmushin takaici baice komai ba. Ashraf tare suka taho da Umma a motarsa tana sauka shima ya sauka yai bangarensa. Ya sani Anisa na gun Umma hakan yasa ya fito falo bayan yayi sallar magrib sanyi da singlet da kuma gajeran wando. Tv ya kunna yana kallan labarai, sai dai ya rasa ke yasa yau yakejin tsananin kewar Nafisansa, gyara kwanciyarsa yai ya koma rufda ciki, duk da yasan ba'asan kwanciyar sai dai yana ganin ita kadaice mafita. Ganin hakan ma ya kasa kwantar mai da hankali kawau ya mike ya hau exercise, kwankwasa kofa yaji, sam ya manta shigar dake jikinsa ya karasa ya bud'e. Nafi ya gani a tsaye fuskarta a maze. Bari kofar yai a bud'e shikuma yai ciki, ta shigo tare da maida kofar ta rufe. Sai da sukaje tsakiyar falo sannan ya tsaya tare da juyowa ya kalleta, Nafi itama kallansa tai, Ashraf kam wani abu ya dingaji yana taso mai, Nafi ta daure ganin kamar zuciyarta na neman yin rauni da kallan da yake mata, wanda shi kansa bai san yanayi ba. Ta daure tace " Yaya mai kake nufi da zancen tafiya jibi?" Ashraf kallanta kawau yake baice komai ba, ta dan motsa baki sannan tace " Yaya ke ka daukeni? Kaza? Tattabara? Ko me? Ba ka damu da ni ba, ka daina shiga harkata sannan kawai sai ka min sako akan inshirya wai jibi zanyi tafiya? In har a matsayin mutum kadaukeni banaji zaka dinga min abu haka, na rasa ya kakeso inyi da raina, ka daina kulani, na dauka na huri zuciyata nima na jure da kulaka, ka daina ko amsa wayata wannan ma na huri zuciyata na jure sai dai inma sako yanda kake min, sai dai banaji duk wannan abun da..........." Yanda bakinta yake motsi tana magana gashi tasa jambaki light pink kawai yake kallo, kasa jurewa yai ya kai bakinsa cikin nata, wanda ya hanata karasa maganar da takeyi. Wani irin salo yake mata wanda duk yanda taso taki biyemai ta kasa, kiss suke sosai wanda kana gani kasan lalai masoyan sunyi rashin juna da yawa. Bakinsa na cikin nata suna mikama junansu sakon ni mai cike da kewa Ashraf kam duk ya rikice, ya saka controlling din kansa kan kace me? Ita kanta ya rabata da kayan jikinta, nan suka fada kan kujera........Hmmmm babban al'amari nikam ina ganin haka nai gaba. Ashraf ya dade yana kwasar garar da ya dade bai ji ba, sai dai ya rasa dalili yau jinta yake daban ita kanta yau tasan Ashraf yayi missing dinta. Suna gamawa ya rungumeta tsam a jikinsa, yana fitar da wani numfashi na farinciki, Nafi ma idanunta ta lumshe tanajin kaunarsa na kara ratsata, cikin wata irin murya mai cike da ma'anoni da yawa yace " Baby i really miss u." Hannu ta runkule ta dan naushi kirjinsa tace " then y?" Ya kara jawota jikinsa yace " dole ce ta sani hakan, saboda inasan amfani da Anisa." D'agowa tai ta kalleshi idanunta suka ciciko tace " rashin yarda dani ne yasa baka sanar dani ba?" Kai ya girgiza mata alamar a'a yace " Duk duniya kece mace ta farko dana yarda da ita 100% banaji dar a kanki, sai dai ina tsoron abinda ke zuciya." Kallan mamaki tamai tace " kamar ya?" Yace " in har kikasan ba da gaske nake ba, bazaki taba nuna jin haushin ki da kishinki ba yanda zasu aminta ba." Ta dan maka mai harara tace " shine nima kai using da feelings dina?" Sumbatar lebenta yai fuskarsa da daf da tata yace " do u think it's easy?" Murmushi tai, tace " amma duk da haka ka wahalar dani." Sumbatar idanunta yai yace "am sry Baby, na wahalar dake ni kaina na sani, shi yasa nace zan amshi punishment dina." Ta sake murmushi tace " maganar tafiya fa?" Yace " Yanzu it's eye for eye, thooth for thooth, we are in a war ni da kawu i am afraid kar wani abu ya samarmin ke ta dalilin revenge dina." Baki ta turo tace " Amma......" Hannu yasa ya toshe mata bakinta yace " Baby please." Idanunta ta rufe sannan a hankalu ta bude jiki a sayaye ta daga kai alamar to." Mikewa yai ya dauketa yai toilet da ita. Sai daya cika musu bahon wankan sannan ya sa kayan kamshi na ruwa sannan ya sata a ciki shima ya shiga. Ta kalleshi tace " Allah baiyi zan tsaya bikin Jibiya, thanks to someone." Idanu ya kankance yace "someone? Do u mean me?" Ta dan murguda baki tace " nidai ban fadi suna ba." Kallanta ya tsaya yi, ta debi ruwa a hannunra ta watsa mai tace " yallabai kallan fa?" Dariya yai yace " fada kikeso?" Ta tsuke baki, shima hannu yasa duka biyu ya riga watsa mata ruwa, nan itama ta dage tana watsa mai, dariya sosai suke yi wanda kana ganinsu kasan suna cikin tsananin kaunar juna. Bayan sun gama wanka, ta jawo towel d'aya ta rufa sannan tace " na fita." Kallanta yai yace " nifa?" Tamai gwallo tace " ka dauka da kanka." Tai d'akinsa tare da zama kan gado tana dariya. Ashraf ya fito yana zuwa ya sa hannu a gugunta ya matse da karfi, wanda ya sa ta saku kara yace " ni kika ki daukoma towel?" Tana ihu da dariya tace " sry Yayana na tuba na daina." Yace " inaa baki dainaba sai na hukuntaki tukun na." Ganin yaki saketa yasa tace " Yaya Nisa?" D'agowa yai da sauri ta mike da gudu tana dariya. Murmushi yai sannan ya mike sambal akan gado tare da rufe idansa. Ahhh na kosa in gama wannan case din in ganni tare da matata kullum. Abinda yake fada kenan a ransa. *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *Gareku yan gro din World of Hausa Novel, Mumbari M.Jabo, Maryam mai dala grp na gode kwarai da yanda kuke san littafin nan. ILYSM😍* *81* Washegari da safe bayan Kawu ya fita, Dan Litti yazo ya dauki Mumy da Nafi yai abuja dasu dan tacan zasu tashi gobe. Little kam taji takaici sai dai Nafi tace mata ai ita saboda makaranta, tunda su sai nan da 1mnt akace list dinsu ma zai fito. Ashraf sai dayaga tafiyarsu sannan ya kira Kb yace " a ina kace an samu Dan Siyasan?" Kb yace " yana nan asibitin Murtala ashe bashida lafiya ne shiyasa akaita nemansa aka rasa." Ashraf yai murmushi sannan yace " ganinan zuwa ka turon ward din da yake da number d'akinsa." Nan take Kb yamai Text Ashraf yaja mota yai gaba. Bayan ya isa asibitin ne ya tafi ward din masu cancer sannan ya duba number d'akin. Knocking yai nan akace ya shiga, a hankali ya tura kofar d'akin, wani ne a kwance jikin nan duk ya rame kamar me kanjamau sannan ga wani matashi a kusa dashi a zaune. Jiki a sanyaye Ashraf ya shiga tare da karasawa bakin gadon. Matashin wanda baifi shi ba yace " ban gane ba?" Ashraf yai murmushi sannan ya dauko complimentary card dinsa ya mika mai yace " sunana Ashraf." Kallansa yai, wanda hakan yasa Ashraf yace " ba Dan siyasan dayai House of rep bane da?" Matashin yace " shine." Ashraf ya kalli mara lafiyan yace " Alhaji Uba ka san Mansir?" Kallan Ashraf yai fuskarsa dauke da alamar tambaya, Ashraf yace, " Mansir kanin Abbas marigayi mai A&A Food. Ltd?" Haryanzu dai bai fahimta ba sai dai ya maimaita kalmar A&A?" Ashraf yace " eh wanda yake auren kanwar Hisham." Jin sunan Hisham yasa ya fara kokarin mekewa zaune, hakan yasa d'ansa ya taimakamai ya zauna, kallan Ashraf yai yace " ina Hisham? Ka taimaka ka kiramin shi." Ashraf yace " baya kasar ne yanzu haka ma shiya turoni nadubaka, baisan baka da lafiya ba." Hannun Ashraf ya kama guda d'aya wanda Ashraf ya dana start da d'ayan hannunsa a wayarsa dake aljihunsa. Mutumin yace " Yaro ka ba Hisham hakuri, a zahirin gaskiya nayi laifuka da dama a rayuwata ta duniyar nan, wasu na nemi yafiya wasu kuma banma san inda mutanen dana cuta suke ba, na hau mulki, dadinta yasa na manta da Allah na kwashi dukiyar jama'a sannan na cuci jama'a Hisham na d'aya daga cikin mutanen da bazan taba mantawa ba saboda nine sanadin talaucewarsa." Ashraf yai shiru tausayin mutumin ya kamashi, ita dama rayuwa haka ne, yau in kaine gove ba kai bane. Mutumin ya cigaba, ka san kanin mijin kanwarsa?" Ashraf ya ce "eh shine Mansir din ai.", Mutumin yai ajiyar zuciya yace " kacema Hisham wlh wannan mutumin shine ya sani komai, shawara yazomin da ita ta neman kudi, nikuma alokacin idona ya rufe, zuciyata ta zarme ina ganin zan samu kudi mai yawa da xai sa inyi campaign ba tare da matsala ba, shi yasa na dauki shawararsa, sai dai dalilina yasa aka kama dukiyarsu mai yawa har hakan yakai ga ajalin mahaifinsa, wanda tsoro yasa nakasa fadar abinda ya faru a lokacin, ina tsoron kar nima azal ta fadamin." Kuka ne yaci karfin mutumin ya shiga yin tari a hankali,yace " yanzu gashinan kowa ya gujeni, wannan yaron shi kadai ke taimaka ta, shi kuma ba jinina bane rikonsa nai, nawa 'yayan duk sun gudu sun barni." Idanun Ashraf ne ya ciciko, yasa stop sannan yace "amma wace irin cancer ce ke damunka?" Murmushin yake yai yace " blood, anyi maganin har an gaji shiyasa nace shima yaron nan ya barni kawai a gida in kwanana yazo in tafi." Ashraf ya kalli matashin, hawaye yaga yana gogewa, tausayi ya kara kamashi, ya kalleshi yace " ya sunanka?" "Abdulmalik." Ya fada Ashraf yace " wani aiki kake?" Yace " kasuwanci nake a kwari, inada karamin shago." Ashraf ya kara tausaya mai, yace " aure fa?" Yace " shekarar Alhaji 5 kenan ba lafiya ina ni ina tunanin aure?" Ashraf yai shiru kafin daga baya yace " ka zo ka sameni a address din dake jikin katin, inada sha'awar kasuwanci inyaso sai in bude ma babban shago sai ka dinga mana." Kallan mamaki Abdulmalik yama Ashraf, shikam Uba kuka kawai ya saka yana godiya kamar me, Ashraf yace ba komai, sannan ya ajiye musu kudi dubu 30 ya fita. Yana fita ya runtse ido cikin tsananin tausayi yace " Rayuwa kenan." ********** Kawu ne zaune kusa da Asim ya kalleshi yace " wlh kaji na rantsema yau itace rana ta karshe da zaka ganni anan, in har baka fadamin inda ka samu takardun nan ba." Asim jiki a sanyaye cikin tsoro yake kallan Mahaifinsa. Kawu yace " to shikenan, ka karashi rayuwarka anan ni dakai kuma......" Da sauri Asim yace " Sata nai a d'akin Ashraf." Idanu kawu ya zare cikin tsananin mamaki yace "mene?" Nan Asim ya bashi labarin abinda ya faru. Hannu kawu yasa cikin takaici ya wankama Asim wani wawan mari yace " bakada hankali ne? Me yasa ne nikam kwakwalwar kifi Allah ya d'orama? Kana tunanin Ashraf Shine zai ajiye takardunsa a fili? Yaron da nafi shekara 10 ina sawa a min bincike akan ma yawan dukiyar Abbas daya barmai amma sam hakab ya faskar saboda tsananin wayau da takatsantsan irin na yaron, shine kakeso kacemin ya ajiye takardu a d'akinsa?" Asim yai shiru, Kawu ya naushi iska cikin takaici yace " kana xaune sokon banza ya kamaka cikin ruwan sanyi, kai wannan yaro nikam bansan jakantarka ba." Waje yai da sauri cikin takaici, yana fitowa Anisa ta kirashi tace "Abba nikam Mumy tayi tafiya ne?" Cikin fada yace " kamar ya?" Tace " a'a naga bangarenta ansa kwado ne sannan su Afra sun koma bangaren Little shine dazu da Afra tazo tacemin ai Mumy tayi tafiya." Cikin tashin hankali yace " ina Ruma zataje ba da sanina ba? Sannan d'azun nan fa na barta a gida." Kashe wayae yai a zuciye ya kira wayar Mumy a kashe ya jeta, nan fa idanunsa suka kada. Ya na kokarin saukowa daga steps din gun sai ga Ashraf. Kallansa ya dingayi harya iso, Kawu ya kalleshi yace " ina Uwarka?" Ashraf yai dariya yace " haba kawu wannan ai wayan zagine, kace ina matarka dai?" Kawu ya fara huccin takaici, Ashraf yai murmushi tare da girgizamai dan yatsa yace " no no no ai bai kamata ka nuna tashin hankalinka tun yanzu ba, inkai haka u will spoil the game, it won't be fun." Ya sake murmushi sannan yai ciki. Wani irin ihu kawu yasa na takaici, Ashraf ya wani murmushi sannan yai ciki😏 *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞*ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *82* Kawu cikin tashin hankali yai gida, b'angaren Mumy ya nufa ko mota ma bai rufe ba, yana zuwa kuwa yaga kwado a kofar da zata sada ka da b'angaren, Ruma! Ruma! Ruma! Abinda kawai yake fada kenan cikin tsananin tashin hankali, kofar ya taba tare da rike kwadan. Ya dade a haka kafin ya koma na sa bangaren cikin takaici, ba shakka dolene ya nemo Ruma dan kuwa in har bai ganta na kwana biyu ba bayaji hankalinsa zai kwanta, a iya saninsa mutane kan ce in har ka auri mutum ka zauna dashi na shekaru to fa soyayya na gushewa sai dai zaman hakuri da na 'ya'ya, shikam a yanda yakejin zuciyarsa gaskiya bai yarda da hakan ba, kaunar Ruma da yakeyi bayaji ko tsufa yai da ita zai daina santa. Ashraf kam gun Kb ya shiga Kb yace " kaje kuwa?" Ashraf yace " naje sai dai abin ba dadi." Ganin bayasan maganar yasa Kb yace " yanzu mutuminka ya fita." Ashraf yadan yi tsaki kadan yace " na ganshi, ya waccan fa?" Ya fada yana kallan inda aka killace Asim." Kb yace " yanacan." Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje inada abinyi." Nan ya fito, baiga kawu ba hakan yasa yai murmushin mugunta yace " ko kaifa, dan banaso ka badani." "********** Kawu kuwa gida ya taho da gudun gaske yana zuwa ya ajiye mota ya fito, ko kofar bai rufe ba saboda tsananin firgici, bangaren Mumy ya nufa, kwado kuwa ya gani daga kofar da zata sadaka da bangarenta, kofar ya shiga jijigawa cikin wani irin kunar rai, ba shakka bazai taba yarda a dauke mai Rumansa ba, shifa a iya saninsa yaji ance in har mace da namiji sukai aure na wasu dan shekaru to fa soyayyarsu na tafiya sai dai kimma da hakuri yasa zama ya d'ore, sai dai shikam abin ba haka yake ba, yanaji dole ne ya zauna da Ruma ko ya samu nutsuwa, kofar ya dinga jijigawa, ganin ba yanda zaiyi yasa yai b'angarensa cikin tashin hankali. Waya ya dauka ya dinga kiran layinta sai dai duk a kashe, tashin hankali kam ya shigeshi a wannan ranar. ******** A can bangarensu Nafi kuwa, sun isa Abuja lafiya, sai dai tun da suka sauka Nafi ke kwara amai, gashi sam ta kasa cin komai, Mumy cikin damuwa tace " Nafi anya kuwa ayi tafiyarnan dubifa yanda kiketa amai." Murmushin yake Nafi tai tace " Mumy karki damu, tafiyar mota ce kawai ta sani haka, kinsan mu filanuwa akwai mu da hararwar mota." Mumy ta gamsu da zancen Nafi, a haka har suka kwanta bacci. Da safe kuwa jirginsu ya d'aga. Sai kasa mai tsarki. *********** Shikam Ashraf da safe bayan ya tashi ya fito daga gidan shi da Dan Litti, wata envelope ya mikama Dan Litti yace " yaje gidan Dady kawai ya ba mai gadi yace a bashi, ya juyo karya bari Habib ko wani daga cikin gidan ya ganshi." Dan Litti ya amsa da to, sannan ya ja mota yai gaba, yana zuwa kofar gidan kuwa yai sa'a ba kowa a gun sai mai gadi, hakan yasa ya mai horn, mai gadi ya taso da sauri, Dan Litti ya kwama sunglasses tare da kallansa ya mikamai envelope din nan yace " kaga mai gidan." Mai gadi ya amsa yana kokarin tambayarsa inji wa, yaga Dan litti ya ja mota yai gaba. Cikin rashin kulawa ya koma ciki ya nufi ban garen Dady, Dady lokacin yana kishingide a falo abin duniya duk ya taru yamai yawa yaji kwankwasa kofa, nan yace a Shigo. Mai gadi ya shiga a hankali ya gaidashi tare da mikamai sakon, Dady yace " inji wa kenan?" Mai gadi ya dan sosa keya yace " wlh ni kaina ban sani ba." Dady ya sallameshi sannan ya bude wannan envelope din wata karamar Mp3 ce ta fado tare da yar karamai takarda. Fuskarsa dauke da mamaki ya sa earphone din a kunnensa tare da danna play. Kallo d'aya zakamai kasan yana cikin tsananin tashin hankali da jin abinda ake fada, mikewa yai tsaye cikin tashin hankali idanunsa suka kada sukai jaa, mamaki tare da firgice ne suka kamashi, takardar ya sunkuya ya dauka a kasa bayan ya gamajin sharhi daga bakin Alhaji Uba, address ne kawai rubuce a jiki na asibiti tare da number d'aki. Makullin mota kawai ya dauka ya fito da sauri tare da fadawa cikin motarsa, ya ja ta da gudu yai waje. Bai tsaya a ko ina ba sai asibitin Nassarawa. Nan yabi address har zuwa inda ya isa number d'akin, jikinsa ne yai sanyi ya kasa bude dakin, ba shakka in har abinda yaji gaskiya ne shikam rayuwarsa ta kare, kenan ya zalinci Abbas akan hakkin da ba ruwansa, kenan duk yanda ya dauki Mansir ashe shi ne babban soko yana zaune ana amfani dashi. Dashi Mansir yai amfani yai achieving din duk abinda yakeso a duniya. Yana tsaye rike da kofar yaji an bude kofar daga ciki, wata nurse ce ta fito, kallansa tai ta gaisheshi sannan tai gaba. Kofar a bude take hakan yasa daga waje yana kallan Uba wanda ke kwance duk ya tsome, shikanshi Uban kallansa yake dan tabbas bazai iya manta fuskar Hisham ba. A hankali Hisham ya fara takawa zuwa ciki har ya isa kusa da gadon ya kalli Uba zaiyi magana Uba yai saurin katseshi da cewa " Hisham na gode da ka ziyarceni kafin rayuwata ta kare, ka yafemin abinda ya faru." Dady kallansa yai cikin wani yanayi yace " me nakeji game da Mansir....." Uba ya kamo hannunsa hakan yasa Dady ya zauna kusa dashi, Uba ya kara zayyanamai komai daya faru tare da doramai " nayi babban laifi, sai dai ba'a maida hannun agogo baya, Ka yafemin Hisham." Hankalin Dady yayi mugun tashi, ya mike jiki a sanyaye ba tare da yace komai ba yai waje. Tafiya yake kamar mara laka a jiki, har ya isa motarsa, ya shiga ciki ya zauna tare da dora kansa akan sityarin motar, me na aikata? Abinda zuciyarsa ke tambayarsa kenan, waya ya dauka dan kiran kanwarsa, sai dai a kashe ya jita, haka nan ya tada mota cikin karyewar zuciya yai gidansa. Yanzu kam ya gane komai daya faru dama trap ne da Mansir ya shirya. ********* Ashraf bayan ya ga Dady ya koma gida dan yana biye dashi shima ya nufi gun aiki." Bayan azahar suka shiga meeting, sai 4 suka fito, sun fito dukansu Kawu na tsakiyar mutane suka dan tattaunawa, Hisham ya karaso gun. Hisham nada tsananin zuciya wanda duk itace tasashi yin abubuwan da suka faru a baya, sam ransa ya gama b'aci baima kula da mutanen dake tsatsaye a gun ba, ya karaso gun Kawu. Cikin tsananin mamaki kawu ya kalleshi yace " Yaya ya......." Mari yaji an tsinkamai nan fa kowa ya kallesu, kawu mamaki ya kamashi, ya rike gun yace " Hisham ba kada hankali ne?" Dady yai wani murmushin takaici yace " au yanzu dakaji mari ka manta da yayan?" Kawu ya kalli mutanen dake gun ciki kuwa harda Ashraf wanda takaici ya kara kamashi, ya daure yace " yaya muje office dina da alama ranka ne a b'ace." Dady sai a lokacin ya kula da mutanen gun, suka hada ido da Ashraf, nan sukai office din Kawu. Ashraf yai murmushi yace " Whoa lalai Dady ba sauki." Nan yai nashi office din hankalinsa a kwance. Kawu kam suna shiga yasa key ya kalli Dady yace " Yaya meye hakan.....?" Idanun Hisham sunyi jaa na takaici yace meye hakan? Dady yace " wai me......" Jiyai Hisham ya karamai wani marin, dady ya fusata yace " malam meye hakan?" Dady yace " waccan marin na farko na rainamin hankali dakai ne, wannan kuma na takaicin hada zuri'ata dakai danai ne." Kawu ya hada rai yace " wannan wani irin banzan zance kake? Mu bayara ba ba komai ba?" Hisham ya nuna Kawu da dan yatsa cikin kunar rai yace " wlh kaji na rantse maka bazan yafe ma rainin hankalin daka min ba, ba zan yafema sanadin mahaifina dakai ba, bakuma zan yafema amfani dani dakai ba ka auri kanwata, ba kuma zan yafema na amfani dani dakai ba wajan kashe Abbas ba." Kawu kallan Hisham kawai yake, sai yanzu ya fara gane inda zancensa ya nufa, cikin rashin damuwa Kawu yace " ni ban fahimceka ba." Hisham yace " naji komai daga Alhaji Uba, munafikin banza da wofi, wlh Mansir nayi danasanin saninka a rayuwa, kai kani ne ga Abbas sai dai ko kadan halayenku ba iri daya bane, shiyasa a koda yaushe kake losing akansa, dukiyar da kake takama da ita ficika ba kai ne kai wahalarta ba, tarawa akai ka kwaceta karfi da yaji, matar da kake takama da ita, ba sanka take ba, ita ma karfi da yaji ka kwace ta, ko da wasa bazaka taba zama Abbas ba duk wannan abun daka kwata kuwa." Idanun Kawu suka rikide babban takaicinsa a duniya ace mai daga dukiyarsa har matarsa ba nash bane, wani irin abu ya fara da fuskarsa, hannu yasa ya shake Dady. Cikin wani mugun yanayi yace " karyane, komai nawane, uban waye ya isa yace dukiya da Ruma ba nawa bane?" Hisham da kyar ya fizge hannun Mansir, cikin tsananin mamaki ya kalleshi yace " kana tunanin wannan abun da kakeyi shi zai sa su zama naka? Ruma da kake tunanin wai hakan santa kakeyi yanzu na fahimci obsession ne ke damunka, lalai kana cikin gararin rayuwa, kuma wlh ka gaggauta ba kanwata takardarta." Yana kaiwa nan yai waje. Wani irin ihu Kawu ya saki yana cewa " waye ya isa yace ba nawa bane?" Ya dade a haka kafin hankalinsa ya dawo jikinsa, nan fa ya shiga tunani uban waye ya sanarma Dady abinda yake a b'oye?" Fitowa yai ya nufi office din Ashraf. *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *83* Kofar ya bude ba tare da kwankwasawa ko sallama ba, a zaune yaga Ashraf yana aiki yana kuma kurban tea dake gefensa, kana ganinsa kasan hankalinsa a kwance yake, jin yanda aka bude kofar ne yasa ya kalli gun, ganin kawu ne yasa ya sakar mai murmushi tare da dagamai hannu yace " Hi!" Ran Kawu ya kara b'aci matsowa yai gunsa ya kuramai ido. Ashraf ya kalleshi cikin rainin hankali yace "ya akai? Ko shayin zan hada ma?" Kawu yanasan ya tambayeshi ko shine ya fadama Hisham sai dai yana tsoron karya buloma kansa aiki, yaje haka kawai Ashraf din bai san komai ba ya sanar dashi. Daurewa yai ya juya, har ya kai tsakiyar gun yaji Ashraf yace " Ba tambaya kazo kayi ba?" Kawu ya tsaya cak tare da juyowa ya kalleshi, Ashraf ya mike tare da matsowa inda kawu yake cikin gadara, ya dan tafa hannayensa biyu a hankali yace " Ohhhh kana tsoron kar inji?" Kawu ya buga mai wani kallo, Ashraf ya dan rike kunne yace " sry kanin Abba, sai dai ya zamuyi? Da alama Dady fa yasan komai." Idanu kawu ya zaro cikin rawar murya yace " kai kai ne ka....." Dariya Ashraf yasa yace "kawu meye hakan? Kar ka badani mana, ya muryarka zatai rawa daga nan?" Kawu ya daure ya nuna Ashraf da yatsa yace " Ashraf wannan shine last warning dina akanka, ka shiga hankalinka dani, kada kai tunanin komai yana tafiya yanda kakeso kai tunani kaci riba akaina, wlh kayi min kadan, tsohon ka ma bai isa yaja dani ba bare kai da aka haifeka a gabana." Hannu Ashraf yasa ya kankame jikinsa yace " Ahh so Scary!!" Kawu ransa ya kara baci yace " ina tausaya ma dan wlh......." Ashraf ya hade hannayensa biyu yace " plzz na rokeka kar ka tausayamin dan Allah, Dan Allah na rokeka kana kwafsamin in naji zancen tausaya war nan." Zuciyar kawu ta cika taf da takaici, a zuciye yai hanyar fita, Ashraf yace " ka tabbatar kanacin abinci mai kyau kafin ka shiga prison dan naji labarin abincin can ba dadi." A zuciye kawu ya bankade kofa yai waje. Yana fita ya kara kallan kofar cikin takaici yai kwafa yace " in ni banje ba kai ka ziyarci kabarin ka ai." Daga ciki kuwa yana fita Ashraf ya furzar da wata iska tare da zama akan kujera Ya kira Uncle Salim. ********** Su Nafi an isa kasa mai tsarki sai dai Nafi kam jiki yaki dadi sam, haka suka shiga d'akin da aka basu a kasar madina ita kam duk ta gama fadawa. Mumy cikin kulawa tace " Nafi ya kamata muje asibiti nikam naga hararwan nan ta isa ga ba abinci kike ci ba." Nafi ta dago tace " Mumy Allah in na huta nasan komai zai tafi." Kallanta Mumy tai tace "kinga yanda kika rame kuwa?" Nafi tai murmushi tace " Allah ba komai Mumy." Shiru Mumy tai jikinta yai sanyi. Nafi kam gata dai a kasa mai tsarki garin da take masifar san gani amma gashi tazo a kwance ba lafiya. ************** Da yamma Ashraf ya koma gida, yana fitowa daga mota yaga Anisa na tahowa, hade rai yai jakarsa ya dauka yai kamar bai ganta ba, Anisa ta karaso da saurinta ta rike rigarsa ta baya. Dole hakan yasa ya tsaya, juyowa yai ya kalleta yace " ya akai?" Idanunta ne suka ciciko tace " yaya." Kallanta yai yace " ya akai?" Ta share kwallarta tace " jikin Umma ba dadi, ga ya Asim har yanzu shiru." Kallanta yai kawai baice komai ba. Anisa ta rike hannunsa tace " yaya muje dan Allag ka duba Umma, itama tun dazu take nemanka." Bai musa ba nan suka nufi bangaren Umma. Tana kwance a d'aki tana ganin Ashraf ta shiga kokarin mekewa zaune. Ashraf ya kalleta sannan ya kalli Anisa yace "dan bamu guri ko?" Anisa ta juya ta fita. Umma ta karasa zama sannan ta kalli Ashraf tace " Ashraf ya maganar Asim?" Kallanta yai sannan yace " Asim? Ina zan sani in har ku iyayensa baku sani ba?" Mamaki ne ya kamata tace " Ashraf na rokeka dan Alla......." Ka tseta yai yace " duniyarnan al'amuranta na bani mamaki, har kasan zuciyarki daga ke har dan naki banaji akwai daidai da kwayar zarra da san 'yan uwantaka da kukemin, banda neman halakani da kukeyi, amma wai ko kunya ni kike cewa in taimaki danki?" Umma jikinta yai sanyi dana sani suka ziyarceta tace " Ashraf na sani sai dai......" Katseta ya sake yi yace " ni a wannan lokacin ba abinda zaki fada da zan aminta dashi, abu d'aya nazo fada miki yanzu, in har kinason danki ya fito, sannan kinasan farincikin 'yarki to inaso nima kimin abu d'aya." Da sauri tace " zan maka shi ko menene." Ya kalleta yace "inaso idan na nemi shedarki akan mutuwar mahaifina ki bada shaida yanda kika sani tsakaninki da Allah." Cikin tsoro ta kalleshi tace " Ashraf me kake fada haka?" Yace " wannan ba damuwa ta bace, iya abinda zance da ke kenan, in kuwa har kikaki bada shaida kamar yadda nace to ki jira abu biyu, na farko danki dolene ya ziyarci gidan yari, na biyu kuwa ki jira takardar mutuwar auren 'yarki kinsani sarai yanda Anisa take sona, na tabbata bazata taba yafe miki ba inhar taji kece sanadiyar mutuwar aurenta." Hankalin Umma ne yai mugun tashi,Ashraf yace " sai ki zab'a da mijin da bai taba sanki ba, bai kuma damu da ke ba da 'ya'yan da kika haifa kike sansu kamar ranku suma haka, sai ki duba kiga wanene zai fi miki amfani nan gaba." Yana kaiwa nan yai waje. Hawaye ne ya biyo kuncin Umma lalai yau tana ganin tashin hankali ina zata sa kanta da rayuwarta??????? ************ Dady zaune a d'aki kusa da matarsa cikin kunar rai yake sanar da ita komai, hankalinta yayi tsananin tashi da jin abinda ya faru sai dai abinda basu sani ba, Habib wanda ya taho d'akin, cak ya tsaya jin zancen da sukeyi. Hankalinsa yayi mugun tashi da jin abinda ya faru, muryar mahaifiyarsa yaji tace " Dadyn Habib yanzu ya zamuyi da hakkin maraya da kuma wanda ya rasu?" Dady cikin mamaki ya kalli matarsa yace " dama kin sani?" Kallansa tai cikin kulawa tace " najiku a ranar da abin ya faru da safe kuna zancen, wanda hakan yasa nai saurin kiran Ruma na sanar da ita sai dai bakin alkalami ya riga ya bushe dan alokacin Abbas ma yana cikin mota." Jikin Habib ne ya shiga rawa, muryar Dady yaji yana cewa " Na shiga uku, tunda nake a rayuwata ban taba tunanin zan hada kai in kashe wani ba sai gashi nayi akan mijin kanwata wlh kinji na rantse miki tun bayan faruwar wannan abun duk sanda na kwanta sai nayi mafarkin Abbas yana min murmushi wanda hakab ke kara karyamin zuciya sai dai san abin duniya yasa na kasa yin nadama sai ma tunanin yanda zan kara mallakar wata dukiyar tasa da nakeyi." Gaba d'aya jikin Habib ne ya shiga rawa, da kyar ya iya saukowa daga saman dakin, d'akinsa ya nufa ya zube a kasa sam kwakwalwarsa ta dauke ya rasa ma tunanin mai zai fara abu d'aya kawai yake mai yawo a zuciya mahaifinsa da mahaifin Little sune suka hadu suka kashe mahaifin Ashraf wannan wani irin mugun al'amari ne????? ************ Kawu ne a d'aki sai safa da marwa yakeyi dole yasan matakin dazai dauka akan wannan yaron, dan kuwa baiga mai rabashi da Ruma ba baiga kuma bai rabashi da dukiyarsa ba. Akwatinsa ya dauko na karkashin gado, sai dai ya zaro takardar wasikar da Abbas yamai yaga tagardar ba komai, hankalinsa ya tashi matuka ya fito daga d'akin ya nufi bangaren Umma. Anisa ce kadai zaune a falo, ya shigo kallansa tai tace "Abba kazo duba Umma ne?" Fuskarsa a hade yace " ke kika bud'emin akwatin kasan gado na?" Gabanta ne ya fadi cikin i-ina tace " ba ni bace." Tsawa ya daka mata yace " tun bayan shigarki d'akina ba wanda ya kuma shiga bazaki fadamin gaskiya ba." Shiru tai sai gabanta dake faduwa, jitai yace " Ashraf kika ba?" D'agowa tai ta kalleshi a tsorace tace " wlh ba ruwan yaya ni......" Lebensa ya ciza da karfi yai waje a zuciye. Bangaren Ashraf ya nufa wanda rabansa da bangaren har ya manta. Jin kwankwasa kofa yasa Ashraf ya mike dan dama yana zaune ne tun dazu yana neman wayar Nafi tunda yasa layin Mumy shi ya amsa da kansa to na Nafin kuma sam ya ki shiga. Yana bud'e kofa yaga kawu a tsaye. Ashraf cikin mamaki yace " lafiya?" Hannu kawu ya mikamai yace " bani wasikar daka dauka a d'akina." Ashraf ya mai kallan mamaki yace "wasika?" Kawu yace " wanda kasa Anisa tadaukoma." Ashraf yace " ohhh wannan? Nikaina bansan inda yake ba." Kawu yace " mene?" Ashraf yace " kunya kakeji kayi karya ka b'oye akan Mahaifiya yace karna auri 'yarka?ko kuwa kunyar mai illa dakai kakeyi?" Kawu ya juya bai kara magana ba cikin takaici lalai dole ya dau mataki akan yaron nan dan kuwa da alama ya gama sanin komai. *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *84* Rayuwa tayima mutane 4 zafi, na farko Kawu wanda yake tunanin yanda zaiyi ya halaka Ashraf ba tare da sanin kowa ba. Na biyu Habib wanda kunnensa ya jiyomai tashin hankalin dayafi karfinsa. Na uku Umma wacce ta rasa ina zata sa kanta, 'ya'yanta zata ceta ko kuwa mijinta. Sai na karshe Hisham wanda nadamada danasani suka taru suka mai yawa. Yau kwanan su Nafi 4, da barin gari, jikinta dai haryanzu ba wani sauki sai dai ba kamar da ba, yanzu tana dan cin kayan itace (Fruit) Mumy kam ta kasa daurewa ranar suna zaune a d'aki ta kalleta tace " Nafisa anya ba ciki gareki ba? Nafi cikin tsananin mamaki ta kalli Mumy gabanta ya fadi. Mumy ta matso kusa da ita tace " bakida kowa a garin nan da ya wuce ni, shiyasa nima na cire kunyar surukantaka na tambayeki, Nafi a matsayin 'ya na daukeki ba sirika ba, nayi dana sani sosai na kin amincewa dake danai tun farko har nake nuna miki cewa mace mai ilimi itace ta dace da Ashraf." Kan Nafi na kasa ta kasa dagowa. Mumy ta dafata tace "muje asibiti." Da sauri Nafi tace " a'a Mumy." Dariya Mumy tai tace " me? Kunya kikeji?" Nafi tai kasa dakai. Haka Mumy ta matsa mata dole da yamma suka nufi asibiti. An mata gwaje gwaje nan aka tabbatar musu tana da ciki na sati bakwai, farin ciki agun Mumy baya misaltuwa, ta kalli Nafi cikin zumudi tace " kinsanar da Ashraf?" Kanta ta girgiza alamar a'a tace " ni ai ko waya bamuyi ba tunda muka taho." Mamaki ya kama mumy tace " akan me?" Nafi tace " wlh bakomai, kawai dai nasan yanada al'amuran dake gabansa ne dayawa." Mumy tai shiru, jikinta yai sanyi ba shakka kam yanada su dayawa. Nafi ta kalleta tace " Mumy karmu fadamai harsai ya gama." Kai Mumy ta daga alamar amincewa. ************ Ashraf na zaune gidan Uncle Salim dashi dasu Auwal Max. Ashraf ya kalli Auwal yace " kayi hakuri kaga haryanzu bamu maidakai ba." Auwal ya girgiza kai yace " ba komai, acan din ma me nakeyi banda wahala, matata ta rabu dani ko ince tunda taga banida komai ta fitineni sai dana bata takardarta, 'ya'yan da muke dasu guda biyu ta kwashesu, ni ba sana'ar arziki ba sai dai inyi can inyi can." Ashraf ya kalleshi cikin tausayawa, Auwal yai murmushi yace " na sani alhakin Abbas ne ke bina, mai gida ya kula dani sosai amma naci amanarsa." Ashraf ya mike jin idanunsa na rawa ba shakka an zalunci mahaifinsa dayawa, shiyasa akullum in ya tuna akwai ranar hisabi sai yaji zuciyarsa tayi wani dadi. Sako ne yashigo wayarsa daga Little. Cikin mamaki ya bude _Yaya dan Allah kazo gidan gona na Mumy dake bayan gari akwai matsala._ Abinda aka rubuta kenan a sakon, shiru yai yana kara kallan sakon. Kb ya kalleshi yace " ya akai?" Ashraf ya mika masu wayar, sannan yace Auwal ya shiga ciki. Kb ya karanta yaba Salim shima ya karanta, Ashraf ya kalli Kb yace " bari inje." Uncle salim ya kalleshi yace " anya Ashraf baka tunanin da matsala kuwa?" Ashraf yai murmushi ya kalli Dan Litti yace " Mutumin muje?" Dan Litti ya mike, Kb ne ya dafa Ashraf yace " Ashraf." Ashraf yai murmushi yace " karka damu, kawai dai nan da 20mins ka kira 'yan sanda kuzo gurin." Kb ya kalleshi cikin kulawa, Ashraf ya kalleshi sannan ya kalli Uncle yace " cikin abu biyu akwai d'aya, ko dai da gaske wani abun ne ya samu Little kaga kuwa in naki zuwa ko me ya sameta daga baya bazan iya yafema kaina ba, ko kuma trap ne Kawu ya shirya min." Salim yai shiru tabbas ya gamsu da bayanin Ashraf, ya mike yace to muje tare. Ashraf ya girgiza kai yace " A'a Uncle karka damu ba abinda zai faru." Sun fito dashi da Dan litti suka shiga mota sukai gaba. A hanya ya turama Little sako akan gashinan zuwa. Sun isa can waje gari inda gidan gonar Mumy yake, da sauri ya fito ya shiga ciki. Yana shiga cikin gun yaji daga baya ta waje an datseshi. Tsayawa yai cak ya kurama kofar kallo. Sannan ya kalli cikin gun, ba komai agun, kajin ma babu ga kajinan nan wayam. Dan Litti daya taho yazo yin kwana yaji an kwadamai wani katako. Nan ya fadi kasa a sume. Ashraf kam da sauri ya koma bakin kofar ya fara jijiga. Wayarsa ce tai kara, nan ya zarota. Ganin number Little yasa ya daga da sauri. Jiyai an sheke da dariya, da sauri ya danna record a jikin wayar sannan yace " Kawu ina Little?" Kawu ya sake dariya yace " kai da Little sai dai ranar tashin kiyama, dan kuwa kai daga nan sai kabarinka." Ashraf cikin mamaki yace " me kake shirin yi?" Kawu ya sake dariya yace " me? Are u scared?" Ashraf yai shiru. Kawu yace " Kasan dai Maryam 'ya tace, 'yata kuma wacce na haifa da Ruma, kana tunanin zan iya halakata ne? Na dauka u are smart ashe kaima kan baya jaaa." Ashraf cikin fada yace " me kake tunanin yi?" Kawu yasa dariya yace " kanada sako gun tsohuwarka ne?" Ji yai alamar kauri hakan yasa ya jujuya mai zai gani? Wuta ne ya fara ci ta waje. Kawu yace " ina jiranka." Ashraf yace " ka kashe mahaifina yanzu ni zaka kashe? Sannan kacigaba da zama da mahaifiyata?" Kawu yai murmushi yace " it's unfair ko? To amma ya zakai, wannan itace kaddararka Abbas na kasheshi ne saboda ya kwace komai da nakeso a rayuwa, kai kuma zan kasheka ne saboda kana neman rabani da abinda ya zama mallakina." Ashraf zai sake magana kawu yace " kaje kai lokacinka yayi mu ba yanzu ba." Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Dariya ya karayi sannan ya fito daga bangarensa ya goge last call din dayai ya kaima little yace " Little wayar Nafin ma shiru, na kasa samunsu duka." Little tace " insun kira zan kawoma Abba." Yace "yauwa my Little sannan yai gaba." *********** Ashraf kam suna gama waya da kawo ya kalli wayarsa sannan yai wani murmushi tare da kiran Kb, yace "kuyi sauri." Nan kb ya amsa da to. Ashraf nan ya shiga tuno abinda ya faru. A safiyar yau ne ya samu Little da kansa har bangarensu. Ya kalleta yace " duk sanda Kawu yace ki bashi wayarki karkiyi musu ki mikamai sannan karki tambayeshi me zaiyi dashi." Ta amsa da to. Sannan ya fito ya tafi shida Dan litti sukai gidab Salim. A hanya ya kallu Dan Litti yace " mutumin nasan baka da tsoro sai dai abinda nake shirin yi har lafiyarmu zai taba." Dan Litti yace " karka damu yallabai ai komenene indai har bai sabawa shari'a ba to bazan taba yima musu bama bare inkiyi." Bayan sunga wannan sakon Ashraf ya mai murmushi kafin ya mikamai, dama Kb ya san komai. Murmushi ya sakeyi yace " abinda nakeso kayi ka taimaken kayi cikin gaggawa Alhaji Mansir, dama burina shine kayi nufin kasheni wanda hakan zai kaimu gun 'yan sanda daga nan kuma komai zai fara fitowa dala dala." Zafin wutar ne ya fara damunsa gashi har ya fara shigowa ciki. Tari ya shiga yi dan hayaki sai shigamai hanci yakeyi duk ya dameshi. Tari yake sosai wanda hakan ya kaishi ga suma. Dakyar su Kb suka iya b'alla kofa, nan suka ciroshi akai asibiti dashi. 'yan kwana kwana dama suka kira. Dan Litti kam ana samai ruwa a hanya ya farka, sai dai gefen kansa sai jini yake yi. Sun isa asibiti da sauri akai emergency dasu. Dan litti aka mai dinki shi kuma Ashraf har drip aka samai. Nan Kb ya kira shugabansu na gun aiki ya sanar dashi ga report nan ankawo musu anyi anyi attempting din kashe wani. Nan shugaban yace "yanzu zai turo Team dinsa su dau case din." *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *85* Bayan Ashraf ya farfado 'yan sanda suka zagayeshi aka fara mai tambayoyi, hankalinsa akwance yake amsawa nan ya sanar dasu akan sako kanwarsa tamai ya kuma nuna musu sakon. Nan suka bukaci anuna musu kanwar. Ya sanar dasu tana gida. Kb ya jasu suka nufi gidan. ******** A bangaren Kawu kam tunda wadanda yasa aiki suka sanar dashi cewa 'yan sanda sunzo hankalinsa yai kololuwa gun tashi, ya kasa zaune ya kasa tsaye tsoro da fargaba duk sun dameshi. 'yan sanda sun shigo nan suka tsaya daga waje suka umarci a kira musu Little. Ba'a dade ba sai gatannan, tsoro duk ya kamata, me zaisa 'yan sanda su nemeta. Bayan ta iso ogan cikinsu ya kalleta fuskarnan a hade rike da littafi yace "Ke kika turama Yayanki sako akan kina san ganinsa?" Cikin mamaki tace " a'a." Yace " ina wayarki?" Hankalinta a kwance ta mikamai, ya duba wayar babu sakon, ya kalleta yace " ki tuna sosai ina kika ajiye wayarki? Ko kuma wa kika ba?" Tace " ni ban ajiyeta a ko ina ba, mahaifina dai ya amsh wayar dazu." Kallan juna sukai, yace " mahaifin naki yana nan?" Tace " eh." Yace " kira mana shi." Nan ta tafi bangaren Abba. Yana zaune duk hankalinsa a tashe yaji kwankwasa kofa. Hankali a tashe ya bud'e kofar. Little ta kalleshi tace " Abba ana nemanka." Yace " su waye?" Tace " yan sanda ne, ni kaina bansan me ke faruwa ba." Cikin tashin hankali yace " me kika ce musu?" Tace " tambaya ta sukai a ina na ajiye wayata ko wa naba shine nace kai naba kawai." Hankali Kawu ya kara tashi cikin fada ya kalleta yace " bakida hankaline??me yasa zakice ni kika ba? Ko kema kin hada baki da yayanki ne???" Cikin mamaki tace " me ya faru?" Tureta yai ya wuce cikin takaici yana tunanin me zaice? In ya gudu kuma tabbas yasan zasuyi zargin wani abu. Fitowa yai ya isa gunsu, tare da mikamusu hannu alamar gaisawa. Bayan sun gaisa wannan officer din na dazu ya kalli Mansir yace " bincike mukazo yi." Mansir ya kalleshi, Officer yace " kaine ka amsh wayar 'yarka wato Maryam dazu?" Kawu ya danne tsoro yace " nine, amma menene dan uba ya amshi wayar 'yarsa?" Officer ya kuramai ido kafin yace " kaine ka turama Ashraf sako ta wayar?" Kawu yai alamar mamaki yace " ban gane in turama Ashraf sako ba? Akan me zanyi hakan?" Officer yace " zaka biyomin office da kai da 'yarka dan tsananta bincike." Kawu zai yi magana officer din yace " in har kana san kar a zargeka kenan, in kuma har da abinda kake b'oyewa to." Kawu yace " muje, bari na canza kaya." Nan ya koma bangarensa, ya canza kaya cikin tsananin firgice, tsoro ne fal a cikin zuciyarsa, nan suka taho da Little suka shiga mota suka bisu a baya. Ashraf kam ya ware sai dai yaki yarda a sallameshi, sun hada baki da likitan akan yace har yanzu bashida lafiya. Su Little zaune a station duk tayi tsuru tsuru, shikansa Officer din yasan ba ita bace dan dai ya zama dole ne ayi tambayar nan da ita. Wayarta ta karba ta kira Habib. Ta dade tana ringing kafin ya daga, tace " yaya kana ina?" Yace " ina gida ya akai?" Tace " dan Allah kazo ina police station tsoro nakeji." Mikewa yai daga kwanciyar da yake cikin rikecewa yace " ban gane ba me kikeyi acan?" Alama aka mata akan ta miko wayar hakan yasa tai saurin mai kwatance ta mika musu. Kan kace me sai ga habib ya danno mota a guje da gudu ya shigo cikin station din, sam bai kula da Kawu ba gunta ya nufa da saurinsa ya rike hannayenta yace " Little are u alright?" Kai ta girgiza mai hawaye suka zubo mata tace " yaya ka kira ya Ashraf kaji ko yana lafiya naji ance yana asibiti." Cikin mamaki yace " asibiti kuma?" Kai ta d'aga mai, zaiyi magana suka hada ido da Kawu, wani irin kalli yamai cikin takaici baisan sanda yace " ka gama lalata rayuwar wasu yanzu ta 'yarka kake san lalatawa?" Cikin mamaki Little ta kalleshi, kawu ma kallan mamaki yake mai. Habib ya dauke kai sannan ya matsa gun officer dan jin abinda ke faruwa. Sosai officer yamai bayani, ran Habib ya baci cikin fada yace " Ai ba sai kunyi wani bincike akan wannan baiwar Allahr ba tayayya ma yarinya karama zatai tunanin yin haka? Sannan yayanta ne fa ubansu d'aya banda yanda suke tsananin san juna, shi kuma waccan mahaifinta ne sai dai im shine." Little cikin mamaki ta kalli Habib tace " Yaya ya zaka ce Abba ne? Mai zaisa Abba ya cutar da Yaya?" Habib bai amsa mata ba ya kalli Officer. Kawu kam ya ma rasa mai zaice, aransa yace "like father like son dukansu sai zuciya basu iya controlling din fishinsu ba sam. Sai yamma wanda yaje bincike ya dawo dauke da doguwar takarda, duk abinda ya faru a wayarta ne da wanda aka kira da time din kiran da kuma texts. Kawu kam yana zaune ne kawai. Bayan an kawu ne aka ga tabbas an kira Ashraf bayan kuma texts da akamai. Mamaki ya kama Little duk da Yaya ne yace taba Abbanta wayarta inya tambayeta bata kawo komai a ranta ba. Officer ya kalli Little yace " me zaki iya cewa gameda sako da kuma waya da akai da layinki?" Abbanta ta kalla sannan ta daure tace " nidai wlh ban kira Yaya ba." Officer yace " mahaifinki fa?" Tace " shima nasan bai kira yaya ba, saboda me zaisa ya kira yaya a wayata bayan ga wayarsa? In ma ya kira wani to sai dai in Nafisa ya kira." Officer yai murmushi yace " hakane abinda kika fada me zaisa ya kira yayanki a wayarki bayan ga wayarsa? Wannan itace kalma ta farko da take bukatar bincike." Kawu kam gabansa sai faduwa kawai yakeyi. Officer yace " kuje gida zamuyi bincike zuwa gobe." Habib ya jata suka shiga motarsa sukai gaba. Kawu ya shiga tashi cikin tashin hankali. ************* Datti kam jiki ba dadi da kanshi yake bi gari gari kauye kauye kauye sai dai ba Nafi ba labarinta ba kuma Dan Litti. Hankalin Datti ya kara tashi nan ya fara zuwa gun malamai akan amai addu'a akan yarsa ta fito. Sai dai haryanzu ba labari, Datti duk ya canza magana ma ba damunsa tai ba, ba dukiya, ba 'yarsa dama wadancan sun gudu, duk ya zama abin tausayi. *#ASHRAFEENAH TEAM* *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *SECOND TO THE LAST PAGE* *ILYSM MY FANS* *86* Yau kwanan Ashraf uku a asibiti, 'yan sanda sune suke tsaron d'akinsa sai dai duk abinda ke faruwa Dan Litti na kawo mai rahoto, Little kam tayi kuka sosau ganin yayanta cikin wannan hali, haka ma Anisa, duk yanda taso akan ya barta ta zauna agunsa yaki sai ce mata yai ai Umma ma ba lafiya gareta ba kuma tana bukatar ta. Umma kam neman yanda zata fito da Asim kawai takeyi, sai dai duk inda taje ta nemi taimako akaji wannan uban kudin sai kaga kowa yana dauke kai. Yau da kanta ta shirya tazo gun Ashraf, bayan sun gaisa ta kalleshi tace " Ashraf in har nai abinda kace zakasa a saki d'ana?" Ashraf yace " zan biya kudin da ake binsa zai kuma yi bailing sa " Tace " naji yaushe kakeso in fada?" Murmushi ya mata yace " zan sanae dake lokacin." Cikin damuwa tace " Yaushe to zaka sa a fito da Asim din?" Yace " karki damu saboda ankusa a cikin satin nan ne insha Allah." Nan ta fito tai gida. Dady shima yazo, kuka sosai yai agaban Ashraf magana d'aya yake cewa "Ashraf ka yafemin, kalmar da kawai yake fada kenan." Ashraf ya kalleshi yace " karka damu Dady ko ma menene na yafema." Yau 'yan sanda suka isa company din da Kawu yake, shi kam a wannan lokacin nema yake ya tattara komai na company din ya gudu, bai taba tunanin za'a zagayo kansa da wuri haka ba. Yana zaune a office suka iso, ID dinsu ogan ya fito dashi yace " u are under arrest." Kawu ya daure yace " akan me kenan?" Officer din yace " mun kama daya daga cikin yaran da ka sa su sa wuta a ginin sannan ya bamu tabbacin kaine ka sasu." Kawu ya rikice yace " a ina? Karya yakemin, Ashraf ne ya zugashi." Baiyi auni ba yaji ansa mai ankwa, nan fa hankalinsa ya tashi ya shiga sambatu yana cewa a kira masa Ruma, shifa bai san me ke faruwa ba. Sudai sukai waje dashi. A cell aka garkama shi, sannan aka umarci Ashraf dayazo. Bayan ya zo ne nan ya basu wayarsa sukaji duk abinda ya faru a lokacin. Hankalin kawu ya tashi, ya dinga musu hauka. Nan aka shigar da kara kotu. Kawu kam anga rayuwa, bai taba tunanin zama a cikin dan dakin nan ba duk tsawan rayuwarsa. Duk yayi baki ya jemi, Ruma kawai yake kira, ya ma rasa inda zaisa kansa, yayi tunanin basu kudi su fitar dashi, sai dai inaa duk inda ya bula abin yaki yiwuwa. Har ranar zama a kotu. *********** Nafi sun fito daga masallaci a garin makka, suna tafe ita da Mumy, Mumy ta kalleta tace " gashi har mun kusa komawa banga ko waya kunyi da Ashraf ba." Nafi tai kasa dakai tace " Nasan zai nemimu in har ya nutsu." Mumy tai murmushi tace " Nafisa kina birgeni sosai, kinama mijinki uzuri ba kamar wasu matan na zamani ba." Nafi ta kalli takaru yanda taga anbiyosu sun smkwashi kayan da suka baza akan titi da gudu kamar me suna zabga gudu, ta kalli Mumy tace " nikam Mumy wai haka duka takaru suke zama agarin nan sam ba daraja?" Mumy tai murmushi tace " ba duka bane suke rayuwa haka, sai dai akasarinsu abinda suke kenan, sai dai addu'a." Nafi sunzo tsallakawa wata ta taho da kayan saidawarta da gudu ta bangaje ta da karfi wanda sai da ta fadi. Matar ta tsaya tana ba Nafi hakuri, Mumy ta kalleta tace " haba baiwar Allah kudinga abu da hankali mana." Nafi ta dago dan yima matar magana, mai idanunta zai gani?" Mahaifiyarta ce sanye da wata kodadiyar doguwar riga da hijab tana rike da kayan saidaiwa a hannunta tanayi tana waigawa, ganin an biyosu yasa ta juya zata tafi. Cikin zafin nama Nafi ta kama hijabin ta. Matarta kalleta tace " Malama kiyi hakuri nace." Nafi ta kara kura mata ido, tace " Inna?" Kallan mamaki matar ta mata tace " ban gane ba." Hawaye ne ya fara zubo ma Nafi tace " Inna nice fa Nafi." Idanu matar ta zaro cikin tsananin kidima tace " Nafi?" Mumy kam ta fahimci me ke faruwa ganin an biyosu yasa tace " mu wuce d'aki kwayi magana." Nan suka karasa hotel dinsu. Nafi hannunta na cikin na mahaifiyarta kuka kawai takeyi, ita kanta matar kuka take. Nafi ta daure tace " rayuwar da kikeso kenan ki ka barni a kauye ni kadai?" Inna ta share tata kwallar tace " Nafi ki yafemin wlh nayi dana sani sosai na barinki." Nafi cikin kuka tace " menene abin birgewa anan?sannan ina kanina Mudan?" Uwar ta share kwallarta tace " Mudan tun daya girma ya bi abokai suka shiga hidimar duniya, har abu yake sha, nayi fadan har na gaji, nayi dana sani har ba iyaka, rannan Aka zo min da labarin hadarin mota da sukai." Hankalin Nafi ya tashi kwarai tace " meyasa baki koma ba bayan rasuwarsa?" Tace " da wani idan zan koma? Bayan kayan Datti dana sata na bar iyayena sannan na barki, na kuma yi sanadiyar mutuwar dana, nikuwa mai zan koma inyi?" Kuka sosai takeyi wanda hankalin Nafi ya kara tashi, nan suka shiga yin kuka sosai. Mumy ta tausaya musu, nan taba mahaifiyar Nafi shawara akan ta dawo nan da zama tunda sun kusa tafiya kuma International ne zata biya kudi au wuce da ita. Godiya sosai Inna ta dinga yi haka ma Nafi. ************* Anyi zama a kotu inda Lawyer din Ashraf ya dinga fito da shaidu na garari ciki kuwa harda Auwal Max, Umma, Dady, Alhaji Uba sannan ga wasikar mahaifinsa ga kuma yaran da aka kama yasa wuta. Ga maganar Kawu wanda Ashraf ya dauka, hankalin Lawyer din Kawu ya tashi ganin ba wata mafita, nan fa kowa ya san abinda kawu yai ma Abbas da d'ansa. Kotu ta umarci dole ne ayima Dady da Mumy hukunci sannan Umma ma. Kawu an yanke mai hukuncin daurin rai da rai, saboda ya kashe Abbas sannan ya nemi kashe Ashraf banda dukiyar maraya dayake amfani da ita. Dady kuma an yanke mai hukuncin shekara 10 saboda shima dashi aka hada baki gunyin kisa, sannan shima yaci kudin maraya. Mumy kuna an yanke mata hukunci kala biyu, ko ta je gidan yari ta zauna na shekara 2 saboda karyar da tai akan gadon maraya duk da kuwa danta ne, ko kuma ta biya kudi million 30. Umma kuma an yanke mata hukuncin biyan kudi dubu 200 saboda kin fadar gaskiya datai. Auwal Max ma an mai hukuncin zaman gidan yari na shekara 8 saboda yayi laifin taimako gunyin kisa. An sanar da Mumy bata kasar sai dai ana sa ran nan da kwana 3 zata dawo. Alkali yace tana dawowa a killaceta. Da wannan zaman kotu ya tashi. Littke tayi kuka kamar ranta zai fita jin wannan sabon al'amari, hankalinta ya tashi, labari kuwa ya bazu a gari ko ina ka zaka abinda ake fada kenan. Su Ferry ma Nabil yazo ya basu labari, hankalin kowa ya tashi na mamakin wannan al'amarin, anyi bikin jibiya waccan satin. Shikam kawu maganarsa daya shifa Ashraf ya cuceshi akuma kiramai Rumarsa. Hmmmm nace su kawu sai ai zaman yari lafiya.....lol😂 *#ASHRAFEENAH TEAM* 💞 _Barkanmu da shan ruwa, Allah ya bamu ladan ibadar amin_ *ZUCIYA* _ĸowa da ιrιn тaѕa_ © *na Ayυѕнer Mυнd* ayushermohd.blogspot.com *HASKE WRITERS ASSOCIATION*💡 *87* Little tayi kuka kamar ranta zai fita, Anisa ma haka, haka suka rungume juna itada Little a kotu suna kuka, Ashraf daga gefe yana zaune yana kallansu, shikansa abinda yake tausayi da tsoro kenan bayasan Little tasan abinda ke faruwa sai dai ba yanda zaiyi. Habib wanda ke zaune kusa dashi idanunsa sun kada sunyi jaa kamar goro, yasa hannu ya buga kafadar Ashraf baice komai ba ya mike zai fita, hannu Ashraf yasa yamaidashi ya zauna sannan a hankali yace " ina zaka?" Duk yanda Habib yaso ya b'oye hawayensa kasawa yai tun balle daya kalli Little yaga yanda take wani irin kuka, a hankali hawayensa suka ziraro ya kalli Ashraf kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa. Ashraf ya mai murmushi yace "karkace komai Buddy nasan abinda ke ranka, so stop feeling guilty, ba laifinka bane haka fatanmu dai Allah ya yafe mana kurakuranmu." Rungumeshi Habib yai alokacin hawaye ya fara zubomai sosai, cikin takaici da tsantsan tausayi yace "Ashraf na na......." Kasa karasawa yai dan kukan yamai karfi, Ashraf ya bubuga bayansa a hankalu yace " karka damu abokina in har zuciyarka ta karye haka, Little fa?" A hankali Habib ya d'ago ya kalleta sannan ya kalli Ashraf. Murmushi Ashraf ya sakar mai sannan yace " kalli Dady ka gani shikanshi murmushi yakema." Nan Habib ya kalli mahaifinsa wanda za'ai waje dasu, da sauri ya dauke kansa yace " ni ai bansanshi ba." Ashraf ya hade fuska yace " ka tashi kaje kamai sallama, ko kamanta mahaifinka ne?" Habib ya kalli Ashraf yace " Haba Ashraf kisa fa?" Sosai Ashraf ya tamke fuska yace " ka tashi ko kuwa?" Jiki a sanyaye Habib ya mike ya karasa gun mahaifinsa. Yana matsowa Dady ya kama hannunsa yace " Habib kayi hakuri." Habib ya kalleshi cikin takaici yace " Dady ban taba tunanin haka halayenka b'oyayyu suke ba." Dady ya daure yace " Ni kaina bansan me ya sameni ba, sa dai fatana kada kasa wannan abun a ranka harya xamemaka wani abun, sannan duk da abinda ke tsakanina da mahaifin Little bazai hanani yimaka sha'awar auranta ba." Habib ya dago cikin mamaki yace " Kanaso kace in auri Little bayan abinda kukama mahaifin Ashraf?ai ba Little ba banaji ma zan iya auran wata a duniya." Yana kainan yai waje da sauri, Dady ya bishi da kallo hawaye suka zubomai. Nan akai gaba dashi, kawu kam ba wanda yaje gunsa haka aka fita dasu aka sasu a mota Sai gidan yari. Anisa kam tana isa gida ta rufe kanta a d'aki banda kuka ba abinda takeyi, tayaya mahaifinta zai kashe mahaifin Ashraf? Itakam ba wani uzuri da zatama mahaifinta ace d'an uwanka?duk da ba uwarsu d'aya ba ai jini jini ne, itakam bataji zata iya ko da cutar da Little ne bari har akai ga kisa. Duk yanda Umma ke buga mata d'aki taki bud'ewa, a yanzu kam ta tabbatar da aurenta da Ashraf ya kare haka kuma tasan rayuwarta tazo karshe ba tantama. Ganin taki bud'ewa yasa Umma ta koma falo ta baza tagumi tana kallan tsakar falon, lalai ba shakka duniya abin tsoro ce, itakam komai da yake faruwa jinsa take kamar a wani mumunan mafarki ne da takeyi. Little kam zazzabi ne mai zafi ya rufeta wanda sai dayakaita ga kwana a asibiti. ************ Mumy da kanta ta nemi mahaifiyar Nafi akan ta zauna da su sannan su tafi tare, Inna kam ta amince da hakan dan batada wani uzuri sai mamakin yanda 'yarta ta zama takeyi balle yanda taga Mumy na ji da ita. Nafi ta ba Inna labarin duk abinda ya faru wanda yasata kuka kamar ranta zai fita dan kuwa tasan laifinta ne duk abinda ya faru ba shakka itace sila sai dai tayi farinciki na ganin yarta cikin wadata haka da farinciki. Sun shirya tsaf Mumy ta biya kudin komawa da Inna. Nan suka shirya suka baro kasa mai tsarki suka dawo gida Nigeria. A ranar da zasu dawo Ashraf sam ya kasa zaune ya kasa tsaye dama tun washegari kafin su dawo ya dau Dan Litti suka shiga manya manyan company's na yin furnitures yasa kaf kayan bangarensa aka canza ma Nafi, sannan ya sai akwatuna saiti ya zubamata kaya kala kala, dinkakune, wadanda ba'a dinka ba, dogayen riguna da English wears. Ya dauko masu gyara aka gyara bangaren sosai kana gani kasan amarya za'a kawo. Kayan Anisa na sawa kuwa aika mata b'angaren mahaifiyarta yai, wanda hakan ba karamin tada musu hankalu yai ba, Anisa kam ko abinci bata iya ci kullum kuka kawai takeyi. Yau tun safe ya shirya dan sunyi waya da wani abokinsa da suka tafi tare ya sanar dashi yanzu zasu taho. Bayan ya kintsa tsaf Dan Litti sai tsokanarsa yakeyi wai wannan zumudi haka? Shi bai taba ganin Ashaf a cikin wannan yanayin ba. Ashraf dariya kawai yakeyi, ganin akwai sauran lokaci sosai yasa kawai ya wuce police station nan yai bailing Asim bai tsaya ya ganshi ba yai gaba. Asim yayi baki sosai kamar ba shi ba ya rame sosai, ya fito ya tari adaidaita yai gida kamar wani almajiri. Airport ya wuce suka hau jirgi shida Dan Litti sukai Abuja. Sun saita abin suna isa ba dadewa Jirginsu Nafi ya iso. Tunda Jirgin ya fara alamun sauka Ashraf ya kafe jirgin da ido, har ya sauka sannan a hankali alhazai suka fara fitowa kallan mutane kawai yakeyi yanasan ganin matarsa. Bayan sun sauko ne suka taho ahankali aka musu checking nan ya hango Nafi. Wani irin sanyin dadi ne ya dinga ratsashi ba shakka bai taba tunanin akwai 'ya macen da zatasa yaji irin wannan yanayin ba amma yanzu ya bada kai bori ya hau. Su Nafi suna fitowa daga gun daga nesa ta fara kalla kalle, nan idanunta suka hango mata abin begenta. Tsaya wa tai cak tana kallansa idanunta suka ciciko da kwalla, shikansa kallanta kawai yakeyi, Mumy ganin haka yasa taja hannun Inna sukai gaba. A hankali suka fara takowa idanunsu nakan juna, Ashraf sam bai kula da wani agabansa ba sai jiyai ya bige wani, ya d'ago ya kalleta dariya ta sakar mai shima yai dariya sannan ya cigaba da takowa, sai da suka zo daf da juna ya kai hannu da niyyar rungumota, ta matsa da sauri tare da cemai "yaya mutane." Kallan mutanen gun yai sannan yadan sauke fuska alamar takaici, tai murmushin farinciki ya matso kusa da ita yace " ni fa gaskiya so nake na jiki a kusa dani." Kallan mamaki tamai tace " yaushe yayana ya zama haka?ba kunya?" Mutanen gun ya kara kalla cikin takaici yace " muje masaukin da nasa a kama mana sai yamma jirginmu zai tashi." Nafi ta daga kai nan suka fara tafiya a jere, ganin tana jan yar karamar trolly dinta yasa yakai hannu ya amsa. Mamaki abin ya bata sai dai bata musa ba ta sakar mai tana murmushi. Can inda yabar Dan Litti ya karasa nan yaga Mumy, da sauri ya mikama Nafi jakarta shifa sam idanunsa sun rufe bai kula da ita ba. Nafi tai saurin matsawa daga gun jakar tai kamar bata ganshi ba. Mumy tai dariya tace " Ashraf jakar zata fadi." Kallan Jakar yai ya harari Nafi wacce ta matsa dan yasan da saninta, da sauri ya waske yace " Mumy lallabani tai akan in rike mata wai ta gaji." Nafi ta zaro ido tace " a ina kenan akai hakan?" Harara ya buga mata nan aka kwashe da dariya dukansu harda Inna dan ta gane lalai wannan shine sirikin nata. Ashraf ne ya kalleta ba shakka ba sai an tambaya ba akwai kama sosai tsakaninta na Nafisa. Nan ya gaida Mumy ya gaidata sannan suka shiga taxi suka nufi hotel din da suka kama. D'aki uku yasa aka kama d'aya shida matarsa, daya Dan Litti dayan kuwa Mumy. Sanda zasu kama D'an Litti har tsokanarsa yai yace "amma dai Mumy da Nafi ka kamama d'aya ko." Harara ya bugamai yace " to wa ya sani?" Ana zuwa Mumy ta kama hannun Inna sukai d'akinsu dan tasan da alama Ashraf ba kara a harkarsa ta yau. Shikam ko a jikinsa ya kalli Nafi yace muje. Tsayawa tai tace " ina zamu? Yaya tarefa muke da mumy?" Ya hade rai yace " to ko gabanta zamu in jawoki jikina?" Idanu ta zaro tace " ba kace yau zamu koma ba?" Yace " dan yau zamu koma sai aka ce a hanani jin dimin matata?" Zatai magana taji ya ja hannunta ya turata d'akin ya rufe. Ita dariya ma abin ya bata tace " yaya wai yaushe ka zama haka?sam ka manta da wata kalma a hausa wai kunya." Rungumeta yai ya saki numfashi yace " Ahh lalai nayi missing matarnan tawa." Jikimta tadan janye kadan tace " nifa yaya a gajiye nake sannan wanka nakesan yi." Zama yai akan kujera tare da juya kai gefe. Nafi ta dauke kai itama ta dau towel ta cire kayanta ta d'aura sannan ta matso kusa dashi ta manna mai light kiss a lab'ansa tace " is that okay?" Juyawa tai zatai gaba da sauri yasa hannu ya kamota ta fada kan cinyarsa ya kalleta ido cikin ido yace " Are u kidding me?" Zatai magana taji bakinta a cikin nasa, wani salo yake mata wanda yasa itama dole ta fara bashi murtani, nan fa ya rabata da towel dinta ya shiga sarrafata ta nayanda yakeso, sai numfashi yake fitarwa itakanta tasan yayi missing dinta........ Sai da suka gama tukunna ya jawota jikinsa ya rungume yace " I really Miss u Feenah." Yanda taji ya fadi sunan sai da tsikar jikinta ta tashi, idanu ta kafeshi dashi, baki yasa ya hura mata iska a idanun yace " kallanfa?" Bata dauke idanunta ba tace " yayan dan kara fada." Ya kalleta yace "mene? I miss u?" Kai ta girgiza tace "a'a d'ayan." Kallan mamaki ya mata yace " to mene?" Tace " d'ayan please." Yace " wai Feenah?" Kai ta daga da sauri tace "bantabajin dadin sunan ba a bakin wani ba kamar kai." Idanu ya kanne yace " badai so kike kicemin haka kikesan indinga ce miki ba?" Shiru tai sannan tana wasa da gashin kirjinsa tace "mene? Bazan iya ba?" Yace " sosai, dan ni Baby nake san cemiki dan haryanzu u are a baby." Baki ta turo tace " salan ka faracemin baby daga na haihu ka koma cemin Nafisa?" Cikin mamaki yace " saboda kin haihu sai kawai na daina cemiki?" Tace " sosai ma dan nasan abinda na haifa zaka koma cema Baby, haka kawai a fara cemin suna ba wani dadewa a canza." Kallanta yai yace " to amma?" Sai kuma yai shiru kafin da sauri ya kalleta yace " ba wani dadewa? Ya akai kika san haka?" Kanta ta cusa cikin kirjinsa tace " ya za'ai bazan sani ba bayan lokaci kawai suke jira?" Idanu ya zaro cikin tsananin mamaki ya d'agota shima ya zauna akan gadon, ya rike hannayenta yace " Baby me kike nufi?" Harararsa tai tace " sai nayi dala dala? Agunka fa na koyi murda magana." Yawu ya hadiya sannan ya kalleta cikin wani yanayi yace " Nafisa bana san........." Kiss tamai a kunci sannan ta kai hannunsa na dama kan cikinta batace mai komai ba. Kallanta kawai yake kamar a mafarku yakejin abun, da sauri ya jawota ya rungume tsam yace "Nafisa yaushe?" Tace "sai da mukai tafiya sannan na sani." Wani irin tsantsar farinciki ne ke ratsashi ya kara kankameta, cikin zolaya tace " kaga banshirya ba na samu ciki sannan gashi ance a satin nan zafa a kafe mana list na makaranta." Ashraf ya dagota yace " makaranta?" Kai ta daga da sauri. Fuska taga ya canza yace " da babyn nawa za'a dinga zirga zirga?salan karatu yasa a ki kulamin da babyna?" Cikin mamaki ta kalleshi tace " ban gane ba?" Yace " ki bari dai sai kin haihu." Kallan tsantsan mamaki tamai tace "yaya mai kake fada haka?" Dariya taga yasa yace " me? Kinji haushi? Nima ramawa nai ina murnar zanyi d'a ko 'ya amma kidinga min zancen wai karatu? Nima shiyasa na rama." Hannu tasa tadan bigi kirjinsa tace " yaya harfa ka tsoratani." Mikewa yai ya daga ta cak yai toilet da ita yana cewa gwara tsoron ya tsaya daga ke karki kaimin shi ciki." Yana ajiyeta a bathtub ta kalleshi tace " ka gani ko? Dama nasani ina haihuwa zaka daina sona." Murmushi yai yace "sorry Feenah dan da alama zan daina kuwa." Haushi ya kamata ta kafeshi da ido, goshinta ya matso ya sumbata yace " in banda abin ki ai soyayyar da muke ma juna ita zamu yi karo karo mu ba babyn mu." Ta kalleshi tace " hmm gashi nan har ka daina cemin baby, shi yasa ma nace kar a fara." Shigayai cikin bathtub dib ya sakar musu shaya ya jawota jikinsa ya rungume a hankali yace " Nafisa bansan irin farincikin da nake ba yau lalai ina cikin farinciki mara misaltuwa, ji nake kamar bayani farinciki a duniyarnan." Murmushi tai ta kara shigewa jikinsa. Bayan sunyi wanka dakansa ya shafa mata mai sannan ta saka wata doguwar riga baka dake cikin jakarta sannan sukai order na abinci aka kawo musu. Shi dakansa ya dinga bata bayan ta koshi sannan shima yaci, ya koma kusa da inda take zaune ya jawota suka kwanta a kan gado, a hankali tace " yaya ya kuka kare?" Nan fa ya zayane mata duk abinda ya faru Nafi kam tasha kuka kankameshi tai tsam taba kuka tace " Yaya." Murmushi yai yace " karki damu ai komai ya wuce." Cikin kuka tace " wace irin rayuwa ce wannan ace duk mutanen dake zagaye dakai ba sanka suke ba? Ace mutum ya fifita dukiya akan jininsa" Ya sake murmushi yace " _zuciyar kenan ai kowa da irin tasa_, wani akan kudi ba abinda bazai iyayi ba." Tai murmushin takaici sannan tace " yaya wato da rayuwa ta da taka is so similar inaji tamu kaddarar kenan, bamu da kowa sai junan mu, nima daga mahaifina har mahaifiyata kowa rabuwa yai dani saboda san abin duniya." Ashraf ya kalleta yace " ya akai naga kamar mahaifiyarki?" Nan ta bashi labarin abinda ya faru, kai ya girgiza cikin takaici yace " Kaddarar da Allah ya daura mana kenan, ikon Allah ne yankaini garinku har na hadu dake, duk da rashin mutanen da ke sona tsakani da Allah a kalla ina alfahari da matata Nafisa na sona tsakani da Allah." Murmushi tai tare da goge hawayenta ta kai fuskarta saitin tasa sannan tasa hannayenta ta kare bangare biyun idanunta a rufe suke sai ta bud'esu a hankali tana kallansa, shima kallanta yakeyi tace " nima ina alfaharin kasancewa dakai." Murmushi ya Mata yace " Nafisa tnx alot 4 not living me." Wani sansanyan murmushi ta saki sannan ta zare hannayenta ta kwantar da kanta akan kafadarsa tace " zaka cigaba da sona duk da banda komai?" Murmushi yai sannan yace " zaki cigaba da sona duk da yanda nake?" Idanu ta lumshe tace " duk rintsi bazaka wulakantani ba?" Murmushi ya sake yi yace " duk rintsi bazaki gaji dani ba?" Kallan juna sukai suka saki murmushi Nafi tace " yaya amma Little dita fa?" Ajiyar zuciya yai yace "sai dai kinje." Ta jinjina kai tace "yaya nisa fa?" Kallanta yai yace "tana gun tsohuwarta." Cikin mamaki tace " amma dai ba wai ka saketa bane ba ko?" Ya hade fuska yace " kinmanta abinda na fada miki? Banda maganin hana daukar ciki datai dani harda ita fa aka hada baki akaina." Nafi tai murmushi tace " amma yaya kaima ai kasan yanda take sanka ina sanin da kai tana masifar sanka shi yasa kai amfani da ita gun kama Ya Asim? Da kuma ganin akwatin Kawu?" Ashraf yai shiru bai ce komai ba, Nafi tai murmushi tace " kabarta ma da abinda takeji plx karka saketa." Hannu yasa ya tureta ya mike tsaye yace " wato ke ko kishi ma bakyayi, a iya sanina murna ya kamata kiyi." Tasowa tai ta rungumeshi ta baya tace " ni kuwa nake kishinka shine ma yasa na fadi haka, dan ina kishin komai daya shafeka ciki kuwa harda kishin kar idanunka su rufe ka aikata ba daidai ba." Kanta ta kwantar a bayansa tace" amma yaya nikam maganar wasiyya ta fa?" Juyowa yai ya kalleta yai dan murmushi sannan ya bata labarin abinda ya faru. Dariya sosai tai tace " amma dai ai bai kamata Abba yabi maganar wani mutum ba." Ashraf yai dariya yace " nima da farko na dauka maganar mutumin nan ce ta sashi barin wasiyyar sai dai yanzu na gane ba haka bane, fahimtar dayai su kawu sune sillar halakarsa shine yasa ya mai wasika akan ya janye maganar aurena da Anisa, shi a tunaninsa kawu zai janye, to fatan Abba shine wasiyyar ta isa gun matar da zan aura." Nafi ta jinjina kai alamar gamsuwa sannan tace " amma yaya kasan akwai mutane masu baiwar haka kuwa? Duk da bance wannan gaskiya ya fada ba sai dai Allah yana hallintar mutane da baiwa kala kala, wasu in basusan ya zasuyi amfani da baiwar tasu ba sai kaga sun koma harkar duba da bokanci da tsubbu." Ashraf yace " haka ne, amma bakya ganin ya kamata mu maida Inna gun mijinta ta nemi yafiya?" Nafi tai shiru, Ashraf ya dagota yace " karki damu ba abinda zai faru, iya kaci inyace baisan aurensa da Inna sai mu dawo da ita nan gida." Kallansa Nafi tai sai dai batace komai ba, tana matukar tsoron Datti gani take bazai taba yafema Inna ba tunda ta satar mai saniya. Da yamma sun taso sun iso garin kano, ya kuma sanar ma Mumy hukuncinta, a da taso ta zabi zaman gidan yarin dan gani take bata kyautama Ashraf ba a rayuwa, sai dai shi da kansa yace gidajenta za'a saida a bada rabi shi zai bada rabi a biya kudin, sai dai sam tace bata yarda ba, sai dai a saida duk kadararta a bada bazata taba yarda ya biya kudin laifin data aikatamai ba. Sun isa gida inda Nafi ta shiga gun Little da sauri, a kwance ta ganta a d'aki ita kadai su Afra suna falo suna kallo, Nafi da sauri ta karasa gunta ta rungumeta tsam a jikinta a tare suka saki wani kuka, kuka suke sosai kafin daga baya Nafi ta shiga ba Little hakuri. Little tace " Nafisa da wani ido zan kalli Yaya? Da wani ido zan kallu Ya Habibda mumy?" Nafi ya rike hannayenta tace " Little bakiyi komai ba fa, baki san me ya faru ba, ta yayya zaki daura wa kanki laifin da baki aikata ba?" Little hawaye na zubo mata tace " ta ya zakice ban aikata ba bayan mutuwar Abban Yaya itace sanadiyyar haihuwata?" Kai Nafi ta girgiza mata tace " karkiyi sabo Little kaddarace ta riga ta faru fatanmu Allah yasa mu gyara." Da haka Nafi tai ta ba little baki harta kwantar da hankalinta, nan ta jata bangaren Mumy. Little na zuwa ta fada kanta tana kuka. Asim kam tunda ya isa ya samu abinci agun Umma ya hau ci ba kakkautawa, Umma kam tausayin dan nata takeji ganin yanda yake tutura abinci kamar zan cinye har kwanon, sai da ya koshi sosai ya tam sannan tace yaje yai wanka. Yana fita ta saki kukan takaici itakam ina zata sa kanta, basuda komai sai gun zaman nan yanzu in har Ashraf yace su bar gidan nan fa shikenan tasu ta kare. ********** Da daddare Ashraf yana zaune ya bugama Nafi waya, ta dauka tare da mikewa daga gun su Inna da Mumy da take, cikin rada tace " yaya ya akai?" Yace " wai bazaki taho gun mijinki ba?" Tace " gun mijina?" Yace " da kina so kicemin a gun Little zaki kwana?" Tace " naga da acan nake kwana?" Yace "da kenan yanzu ai kayanki zaki tattaro ki dawo bangaren mijinki." Murmushi tai tace " ni dai kunya nake ji gaskiya." Yace " kunya ko? To ni bari nazo na daukeki." Yana kaiwa nan ya kashe wayar. Dariya tai tace " in zaka iya kenan ba." Ta koma suka cigaba da hira, batai minti 10 da zama ba suka ji sallamar Ashraf. Little tai kasa da kanta, shigowa yai ya zauna kusa da Little tare da dagota yace " kanwata ko neman Habib kike ne?" Dagowa tai da sauri tace "ni kuma?" Murmushi yai yace " to ni kike nema?" Kasa tai da kanta tana murmushi, Ashraf ya harari Nafi yace " malama tashi ko?" Nafi ta zaro ido ta kalli Mumy da Inna cikin tsananin mamaki, wai keke damun Ashraf? Abinda tafada kenan a ranta. Mumy tai murmushi tace " Ashraf bafa inda zataje." Kallan Mumy yai cikin mamaki. Mumy tace " Nafisa tana bukatar wani shagalin biki dan a kara shaida auranku, mutane dayawa basu san matarka bace, ita kanta kunya ya hanata sanar da kawayenta." Cikin tsantsan mamaki ya kalli Mumy yace " to ai...." Mumy ta hade rai tace " mun yanke hukunci da mahaifiyarta nan da sati d'aya za'ai ko yar walima ce sannan ta tare." Haushi ya kama Ashraf yace "har sati?" ya fada yana kallan Nafi. B'oyewa tai bayan Little tamai gwalo, haushi ya kamashi ya mike yace " hmm amma da ina tunanin gobe zamuje kauye tare da Inna dan ta nemi yafiyar Datti." Mumy tace " hakan yayi kyau, inyaso sai Little ta rakaku." Yace " amma mu biyu ma....." Mumy ta katseshi zan ma Habib magana shima kila zaiso yaje kauyen kaga sai kuje da armashin ku sai ku dauki babbar mota, gashi Afra nan ma xasuyi rakiya." Haushi ya kama Ashraf yai waje cikin takaici, bangarensa ya nufa ya kalli yanda ya tsara musu bangarensu yace " har wani sati? Sannan goben ma baza'a barmu mu biyu ba???" ********** Washegari haka suka shirya suka dauki mota babba, Little, Inna,Nafi, Afra da Amra, Dan Litti Habib da Ashraf suka nufi kauyen su Nafi. A hanya Ashraf yai musu siyayya sosai duk da Habib ne ya sashi dan shi gani yake bazai iya kaima Datti komai ba, haka suka isa kauyen A kauyen su Dan Litti suka fara sauka aka saukeshi mutane sai kallansu sukeyi, sannan suka wuce rigar Datti. Sun samu ba kowa a gidan gidan ma a rufe yake nan fa hankalinsu ya tashi sai ga wani yazo wucewa nan ya sanar dasu ai yana gidansu. Nan suka shiga mota suka gangara, Datti na kwance a karkashin bishiya shi kadai abin duniya duk ya isheshi yana ganin mota ma ta tsaya amma ko alamar mikewa baiyi ba, mutane suka zagaye motar, nan fa su Nafi suka fito ba wanda ya ganesu gwarama Inna yayan Datti na ganinta ya ganeta. Sai da aka musu iso suka zauna a ciki sannan yayan datti ya aika a kirashi. Ba'a dade ba sai gashi nan, nan yaga inna sai dai maimakon masifa gani sukai ya saki kuka yana ce mata " innar Nafi mun shiga uku na saida ma masu yankan kai Nafi." Kuka yake sosai wanda saida yasa Nafi ma kuka, Ashrad ya kalleshi yace " baka gane ni ba baffa?" Kallansa yai yanasan gano fuskar sai dai ya kasa, Ashraf yai murmushi yace " mijin Nafi ne." Nan fa aka dau salati, nan Ashraf ya zayyane musu komai, Inna ta nemi yafiya shima datti ya nemi yafiyar ta data Nafi. Sun dade kafin daga bisani suce zasu tafi,Datti yace ai auransa nanan da matarsa, jin matsalar data sameshi yasa Ashraf ya ciro kudi masu yawa ya bashi yace ya sai wasu dabobbin, sannan suyi shawara in sunfisan zaman nan to in kuma sunfisan birni sai ya turo a daukosu. Nan ya musu sha tara ta arziki suka fito, kowa sai sha'awar Nafi yake, nan Hanne ma dataji labari tazo taganta alokacib itakuma 'ya'yantama 2. Su kadai suka taho dan dan litti yace sai yayi kwana biyu, zai dai dawo lokacin bikinsu da Nafi. *********** Duk yanda Ashraf yaso su kebe da Nafi abin yaci tura har ranar zagayowar sati, Nafi tayi rabon Iv gida ya cika sai dai Anisa da Umma sukam suna zaune a bangarensu ko fitowa ba sayi. Nafi da kanta ta sai kusu kayan da zasu sa a cikin kudin dake katin da ASHRAF ya bata. Ta aikama Anisa da umma. Hall aka kama, ga innarta ta zo itada mahaifinta da hanne, dama ta shirya musu dinkuna. Su ferry da Little amara kirjin biki kenan sai hidima sukeyi, duk inda Little ta wuce Habib binta kawai yake da ido, sosai guri ya cika Abdulkadir wanda ke kula da dan siyasan nan shima yazo dan yanzu ya zama babban mutum Ashraf ya bude mai shago babba anan titin Zoo road inda yake saida kayan masarufai yanzo ko motar da yake hawa ka kalla sai ka kuma kallo, tunda ya iso shikuma ya kyalla ido yaga ferry hankalinsa ya tashi, sosai ta birgeshi. Anyi shagalin biki sosai mutane kowa ya tayasu murna, sai dai Nafi tunda ta zauna Ashraf ya hanata tashi, ko kiranta Dj yai sai yace a mata uzuri haushi duk ya isheta datai magana sai yace wai bazai yarda a wahalar mai da baby ba. Haka aka gama taro aka watse, Little da Ferry sune suka kai Amarya Nafi bangarenta inda Little tai ta mamakin sanda aka canza komai na bangaren. Duk yanda Habib yaso suyi magana da Little abin ya faskara, haka suka kai Nafi bayan sun ajiyeta Little ta juya zata tafi Habib yai saurin binta suna fita yace " Little haka zamu dawamma ko magana babu?" Kallansa tai tace " yaya da wani idon kakeso na kalleka bayan mahaifina shine sillar lalacewar rayuwar Dady?" Habib ya kalleta yace " amma wannan ba ya wuce ba?" Kai ta girgiza mai tai gaba zata wuce, hannu yasa ya rikota da sauri ta tsaya cak gabanta na faduwa yace " Little bantaba tunanin ina sanku haka ba sai bayan faruwar wannan abun." Juyowa tai ta kalleshi tace " nifa?" tafada hawaye na gangaro mata, tace " nifa da nake sanka tun ina yarinya?" Wani irin kallo suka shiga yi ma juna....... Ferry kam da Abdul bansan ya akai ba can na gansu tare suna hira mamaki ya kamani nace hmmm lalai...... Shikam Ango ana watsewa ya yaye mayafin dake rufe a fuskar Nafi yace " su Amarya am gama gudun?" Tai kasa dakai wai kunya, dariya yai yace " au abin Amaren gaske zakimin?" Ta turo baki tace " ba amaryar bace?" Yai dariya yace lalai su Amarya bari in kaiki ciki in gwada ingani ko Amarya ce da gaske." Zatai magana taji ya sureta.......... Washegari da safe taga bangarenta sosai taji dadi sai dai tace ya dawo da Anisa, ya aminta da shawarar sai dai yace sai dai a gyara mata wani bangaren dake cikin gidan dan kuwa inhar ta zauna dasu gaskiya itace a wahale dan kuwa bazai iya adalci ba zai kuma sanar da ita hakan. Da zai fita zuwa gun Anisa ne ya zaro takarda ya mika mata yace " uwar gida ga wasiyyar ki." Yai gaba Kan kujera ta kwanta a hankali ta bude takardae. _Zuwa ga sirikata_ _Bansan me zance miki ba, ban kuma san dalilina na yin wasikarnan ba sai dai nasan abu d'aya shine ke rinjayata, dan Allah ina rokonki da kularmin da wannan yaron nawa, amanace na baki kisoshi saboda Allah bawai dan dukiyarsa ba, ki nunamai kulawar dazaisa yamanta shi marayane, wannan ita kadaice rokon da zan iya miki a rayuwa._ _Ga nawa gudun mawar na auranku, ba yawa sai dai wannan nine nake daburin baki ba wanda yasan da zamansu sai ni sai ke sai Lawyer na Salim, nagode kwarai._ Murmushi tai sannan tace " Abba zan kula da yaya sosai, zan sadaukar da komai nawa a kansa." Nanta zaro takardar dake bayan wasiyyar, takardace ta nuna mallakin wani gida da kuma shago, mamaki ya kamata, da alama kuma gida ne babba sosai hakama shagon. ************** Bayan shekara d'aya, sauri take sosai tana hada breakfast Ashraf da babynta mace wato Zainab suna zaune akan dinning ya daurata a cinyarsa yana bubuga mata kan dinning da cokali wai tai sauri su yunwa sukeji. Nafi ta taho da sauri rike da plate ta ajiye a gabansa ta sa hannu ta ja kunnensa da karfi yadanyi kara kadan yace " muguntar ta motsa kenan?" Harararsa tai ta rike kugu tace "Yaya daga nan ina zaka?" Yace " zama zanyi in huta kadan kafin na fita aiki." Ta hade fuska tace " dama shigaban Company an bashi damar kin zuwa da wuri?" Yace " an fara akaina?" ya fada yana murmushi tace " ni kuma fa daga nan ina zani?" Yace " makaranta zaki." Ya fada tare da sumbatare Zee, Nafi tai kwafa tace " kai da zaka zauna a gida, mu da zamu fita shine kake min kidan yunwa?" Ya tabe baku yace " to ya zamuyi Zee ma yunwa takeji." Ta kalli agoggo ganin lokaci yayi yasa tai daki da gudu ta dauko mayafinta da jakarta ta zo kusa dashi tamai kiss a kunci sannan tama Zee tace "yaya inkun gama wasab naku ka kaita gun Ya nisa." Ya mata salute yace " yes ma." Dariya tai sannan tai waje. Motarta ta fada sannan ta kata key tai gaba. Little ansa ranar auransu da Habib. Dan Litti kuma Ashraf ya turashi kasar Spain dan yin karatu. *ALHAMDULILA* _Nan ne na kawo karshen littafina na zuciya kowa da irin tasa, darusan dake ciki Allah ya bamu ikon fani dasu, kura kuran da ke ciki Allah ka yafe mana, Ameen suma Ameen._ Godiya ta musamman ga *Yan Haske Writers Association* Ina godiya kwarai da duk wani mai kaunar littafin nan, na gode kwarai da kaunar da kuka nunamai, naji dadi kwarai. Gaisuwa ga duk 'yan gro din da nake ciki dan yawansu bazai sa na zayyanosu ba sai dai ina mika gaisuwa ta Allah ya barmu tare Ameen.... Masoyana na gode kwarai da kulawarku, da kaunar ku, Allah ya karemin ku a duk inda kuke. *ILYSM* *URX AYUSHER MUHD* 💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋💋 Masha'Allah barakallah, a madadin dubban masoyanki dake zaune a mk hausa novels, Muna tayaki farincikin kammala wannan littafin mai farinjini, Addu'ar mu a gareki shine, Allah ya ƙaramiki hazaƙa, da basira, ya kareki daga dukkanin abunƙi ko abun ƙyama.. Daga Muhammad kabir 08160112181. Yake miki fatan alkhairi. Muna jiran sabon littafin dake tafe. Allah ya taimaka ameen.