***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {1} TYPE A ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya fara da cewa: ==================================== A WANI ZAMANI can baya mai tsawo da ya shude a kasar kisra an yi wani karamin kauye mai suna himsarul aswad ya wanzu a yammacin birnin kisra kuma shi ne gari na karshe wanda yayi iyaka da birnin rum. mutanen birnin himsarul aswad manoma ne wadanda suka sami albarkacin kasa domin agaba daya garuruwan dake kar kashin birnin kisra babu inda ake da arzikin noma kamar himsarul aswad acikin wadannan kauye akwai wani mutum da ake kira hukairu wanda asalinsa dan uwan hakimin garinne amma saboda bambancin ra'ayi da halayyarsu sai hukairu yahakura dazama tare dan uwansa hakimi yakoma daji inda yayi gidansa kusa da gonarsa yaci gabada rayuwa a wajen tare da matarsa guda daya jal wacce akekira humaira shidai hakimin kauyen himsarul aswad wanda ake kira da suna barzuk yakasance azzalumi kuma make taci mai danne hakkin talakawa kamar yadda sarkin kisra ya zamo na wannan lokaci dalilin dayasa kenan ma yadade akan mulkin yana tayin abinda yakeso zanci gaba. Hukairu da barzuk sun kasance hassan da usaini kuma suna matukar kama da junansu tamkar antsaga kara wani abin mamaki shine matansuma yan'uwan junane kuma suma hassana da usainane. Sunan matar barzuk nuzaira. Humaira da nuzaira sun shaku da juna ainun kuma har aka yimusu aure basu rabuba tunda agidadaya suke zaune lokacan da hukairu da humaira zasuyi hijira subar cikin kauyen himsarul aswad da kyar hukaira da nuzaira suka rabu domin kankame junayi suka fashe da.matsanancin kuka A wannan lokaci shima Hukairu kuka yake koda yakama. Humaira yana kokarin banbareta daga jikin yar uwarta nuzaira saita dubeshi alokacinda Fuskarta ta jike sharkaf da hawaye tace "yakai mijina saboda me zaka rabani da yar uwata alhalin tunda aka haifemu Bamu taba rabuwaba Nikam da dai ka rabamu gwara ka barnina zauna anan gidan koda kuwa zan zama baiwar sune. ". Sa 'adda hukairu yaji wannan batu saiya dada kamuwa da tausayin Humaira "yace yake matata ki sani cewa ba a sonraina zan raba ki da 'yar uwarkiba, sai domin mugayen halayen mijinta Nassey ke magana Tabbas bazan iyaci gaba da kallon irin rashin imani da yake yiwa talakawaba tunda banida IKon Hanashi. Ni a rayuwata bantaba marin wani mutumba bare ma muyi kace nace amma shi dan uwannan nawa ba a kwana ba kwai sai yasa ankewa wani hannu kokafa. Sannan yana kwacewa mutane dukiyarsu ko matansu ya maishesu bayinsu. Kituna cewa ahalin yanzu kina da ciki tsawon wata hudu yaza ayina tafi nabarki acikin wannan hali alhalin ina son nakula da lafiyarki da kaina kuma naga abin dazaki haifa. " Sa adda Hukairu yazo nan azancensa sai hukaira ta kara fashe da matsanancin kuka da kyar tayi shiru sannan tace yakai mijina kasani cewa itama 'yar uwata nuzaira a halin yanzu tana. Dauke da juna biyu tsawon watanni hudu dai dai da nawa. Ita haihuwa abuce mai hadarin gasKe. Zan iya rasa rayuwa yayin haihuwar itama zata iya zata iya rasa rayuwarta saboda haka bana son rabuwa da 'yar uwata awannan lokaci, zan so naga ranar da zata haihu. Don haka ina rokonka daka barni na zauna tare da ita har izuwa ranar haihuwarta" hmm soyayya kenan ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {1} TYPE B ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== NA ZAUNA TARE DA ITA HAR IZUWA RANAR HAIHUARTA. Har Hukairu ya budi zaice wani abu sai nuzaira ta tari numfashinsa ta dubi humaira tace yake 'yar uwata kada ki guji mijinki saboda ni domin shima ba shi da kowa face ke, idan babu ke akusa dashi zai iya shiga mugun hali. Ina son ki bishi kutafi tare, kada kidamu dani nayi miki alkawarin komai rintsi bazan haihu ba sai agabanki." Koda jin wannan batu sai farinciki ya lullube humaira takara kamkame nuzaira tafashe da kuka. Haka dai ta hakura sukayi bankwana suka rabu. Tun da hukairu da humaira suka koma daji basu kara ganin mutum ba daga cikin Himsarul Aswad saboda sunyi nesa da garin kimanin tafiyar sa'a bakwai,saidai suna ganin tafiyar fatake. Wani iko na allah yanzu Hukairu da Humaira sunsami tsawon Nassey ke magana wata hudu A wannan daji inda shi dakansa yagina musu wani narkeken gida. Harda garken dabbobinsu dasuke kiwo da rumbu na ajiye kayan amfanin gona amma ko sau daya 'yamfashi. Ko 'yan sumame basu taba kawo musu hari ba. Dalili kuwa shine akwai layar sihiri da wani boka yabashi. Wadda ya binneta a tsakiyar gidansa. Duk wani mugu idan yazo gidan bazai ganshiba koda da ranane tsaka. A ranar da cikin Humaira yacika wata takwas ne laulayi yayi mata yawa har ya zamana takasa yin komai. Ka wai saita zauna. A tsakar gidan tana kallon hukairu alokacin da yake baiwa dabbobi acikin garkensu. Koda ta dan jima tana kallonsu sai idanunta suka ciko da kwalla, Hawaye ya fara zuba. Yayin da Hukairu juyo yaga halin da take ciki sai hankalinsa ya dugunzuma yabar garken da sauri yazo gareta ya tsuguna ya rike hannunta yace matata ina dalilin kukannan naki shin jikin kine yake ciwo. Kokuwa ninayi miki badaidaiba ?"Lokacinda humaira taji wannan tambayar sai ta gyada kai tace Ba wani abu bane yasa kaga ina zubar da hawaye ba face tunanin cewa abune mawuyaci na sake ganin ranar dani kaina zanyi I rin wannan aiki dakakeyi yanzu domin ina ji ajikina abune mawuyaci na rayu daga hadarin wannan ciki danake dauke dashi." Kodajin haka sai Hukairu yayi murmushi yace. Ki daina wannan tunanin naki kisani dawo wata nan bisa umarnin boka nane domin ya tabbatar min dacewa idan kika haihu acikin gari zamu rasa abinda zaki haifa kuma zamurasa duk abinda muka mallaka. Saboda a shekarar daki haihune za ayi mugun fari da cututtuka acikin garin amma mu damuke anan wannan annoba bazata shafemuba. Koda jin haka sai Humaira tayi murmushi cikin karfin hali tace "idan zancenka ya tabbata Nassey ke magana haka ina fatan "yar uwata nuzaira tazo ta haihu tare dani domin kada annobar ta shafi abinda zata haifa." Hukairu yayi ajiyar zuciya yace "nima ina fatan haKan tafaru duk da cewa nasan halin "yar uwarki macece maicika alkawari. Lailai zata zonan ta haihu tare dake cikin kowane hali. Daga wannan rana hukairu yaci gaba da kulada humaira har cikinta ya tsufa sosai harma ranar da nakudarta tazo. A wannan ranane hankalin hukairu ya dugunzuma ainun domin basu da makota bare yasamo mace wadda zata karbi aikin ungozoma. Amma dayake dama can Yasami cikakken bayani a wajen wata tsohuwar mace tunkafin subaro cikin gari sai yayi sauri ya shigar da Humaira cikin daki ya kwantar da ita akan shimfida ya shiga taimakamata. A wannan lokacine hadari yagangamo aka fara walkiya da tsawa kafin ajima ruwan sama ya kece kamar da bakin kwarya kuma asannane humaira tafara kwalla ihu sakamakon nakudar data zomata. Duk da cewa Humaira nacikin tsananin shan wahala duk sanda ta kwala ihu tayi shiru saita kuma kirawo sunan "yar uwarta nuzaira. Al'amarin dayayi matukar dugunzuma hankalin Hukairu kenan domin yana tsoron cewa idan nuzaira bata zoba har bayan haihuwar Humaira zata iya shiga cikin wani mugun halin dazata zamo sanadin salwantar Hankalinta ko rayuwarta.Kwatsam ba zato ba tsammanisai hukairu yajiyo sukuwar doki a wajen gidansa kuma adai dai lokacinne kan jaririn yafito daga jikin humaira. Namfa Hukairu yarude yarasa abinda zaiyi shin zai rabu da humairane. Ya ruga waje yagano ko nu zairace tazo. Kokuwa zai tsayane har sai yaga humaira ta haihu lafiya. Yana cikin wasu wasinne yaji humaira ta damki hannunsa da kyar, tace ya kai mijina maza ka ruga izuwa.kofar gida domin ina ji ajikina 'yar uwata ce ta iso kuma na tabbata kodai ta haihu kukuma tana cikin i rin halin da nake ciki. Karka damu dani zan iya kara sa haihu wa da kaina. Cikin matukar damuwa hukairu yace menene tabbacin hakan? Humaira tace shinna taba maka karyane? Hukairu ya girgi za kai yace baki tababa kuma ina gasgata maganarki kamar yadda nake gasgaga maganar ma haifiyata marigayiya. " Koda gama maganar sai ya mike da sauri yaruga da gudu yana fita ya arba da keken doki. Kwance acikin keken dokin nuzairace kaca-kaca da jinin haihuwa gefe kuma ga jaririn data haifa ko motsi bayayi. Itama a kwai a lamun dogon suma tayi cikin razani hukairu ya ruga gareka ya dauki jaririn ya girgiza shi kuma ya kara shi akunnuwansa yaji ko numfashi bayayi. Sai tausayi yakamashi. Adai dai wannan lokacinne kuma yajiyo kukan jarirai acan dakin da ya baro humaira nantake nuzaira tabude idanunta tayi arba da gawar jaririnta data haifa kuma taga hukairu tsaye akanta. Saita fashe da kukan bakin ciki amma da ta jiyo kukan jariri adakin humaira. Sai ta fashe da dariya cikin hanzari subiyun suka ruga izuwa cikin gidan. Da shigarsu cikin dakin da humaira take kwance saisukayi arba 'yan tagwayen jariranta mata. Guda biyu suna ta tsala kuka.kuma ita humaira ta kasance cikin Koshin lafiya. Fuskarta cike da murmushi. Koda humaira taga nuzaira babu juna biyu kuma babu komai ahannunta Nassey ke magana sai ta yunkura donta mike tsaye. Nuzaira ta ruga gareta da cikin hanzari ta kwanta tace "kwanta ki huta tukunna yake yar uwata kiyi sani cewa kin zubarda jini mai yawa ajikinki. Kafin nuzaira ta rufe bakinta humaira ta tari numfashinta tace ina abinda kika haifa nuzaira ta kalli hukairu takasa cewa komai sai humaira tayi murmushi tace "yake 'yar uwata ai baki da damuwa tunda 'ya'ya biyu na haifa saiki dauki daya ki barmin daya. " Koda jin wannan batu sai nuzaira ta cika da tsananin mamaki ta dubi hukairu shima sai yayi murmushi yace "yar uwarki tayi gaskiya domin abinda ta haifa nakine koda kuwa guda dayane zan iya amincewa ta mallaka mikishi domin zakiyimishi komai kamar yadda zata yi mishi da kanta. Nuzaira tayi murmushi ta dauki daya Jaririyar ta zauna ta shayar da ita. Bayan dukkaninsu sun nutsu sai hukairu ya dubi nuzaira cikin tsananin damuwa yace yaya akai kika baro mijinki kika tahonan ba tare da yasaniba shinkin tabbatar baisa abiyo bayan kiba? Nuzaira ta gyada kai tace aidama tun kafi ranar tazo nayi kyakykyawan shiri domin na hada baki da kuyangina tuni sun tanadi wancen keken dokin danazo dashi. Acan bayan gari kuma acikin dare muka saci jiki muka sulale muka bargarin banyarda wani daga cikin masu tsaro yagammuba kuma suna dorani akan keken dokin na umarcesu dasu share sahun keken dokin don kada aga alamar komai kafinna baro gida kuwa nabarwa mijina wasikar cewa nibazan haihuba acikin garinsa acikin irin wannan lokaci nafari da annoba tun satin jiya gari ya hargitse da wadannan matsaloli. Saboda haka ninasan cewa mijina bazai biyo sawunaba idan yaga wannan wasika. Nikam na zabi na karasa. Sauran rayuwata tare da ku anan har izuwa karshen rayuwata Nassey ke magana. Sa'adda nuzaira tazo nan azancenta sai hukairu ya jawo gwauran numfashi ya ajiye sannan yace yake Nuzara kiyi sani nasan halin mijinki fiye da kowa a duniya. Tabbas sai yabiyo bayanki dan haka zamanki anan abune mai hadarin gaske. Aduniya babu abinda mijinki yakeso sama da samun magaji. Hankalinsa bazai taba kwanciya ba idan baiga abinda kika haifaba idan yazo nan ya iske cewa abin dakika haifa ya mutu. Zai iya hallakamu nida matata da dukkan abida muka haifa. Yazama dole ki dauki wannan jaririya guda daya ki tafi da ita kikoma wajen mijinki. Nayi imani cewa a halin yanzu ya baro gari yataho nemanki. Idan baki tashi kin tafi yanzu ba kin tareshi a hanya. Tabbas zai zo har nan ya riskemu abinda nake gudu ya faru sai ya faru. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {1} TYPE C ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: =================================== TABBAS ZAI ZO HAR NAN YA RISKEMU ABINDA NAKE GUDU YA FARU SAI YA FARU. Kodajin wannan batu sai nuzaira ta fashe da kukan bakin ciki saboda jin cewa zata sake rabuwa da yar uwarta. Cikin tsananin damuwa Humaira ta dubi hukairu tace yakai mijina shin gidan nan na dauke da sihirin mugu bai isa yagan shiba? To ai koda dan uwanka Barzuk yazo nan bazai ga gidan ba kenan. Hukairu ya gyada kai yace ai shima yanada da irin wannan sihirin nawa kuma yana da makarinsa domin tunmuna yara boka saibur yabamu shi sa'adda mai haifimmu yakaimu gurinsa. Nuzaira bamu da ishashshan lokaci dan haka dole ne ki tashi kiyi shirin gaggawa ki koma cikin gari. " Koda jin sai Nuzaira da Humaira suka fashe da kukan bakin ciki kamar bazasu dainaba nan dai hukairu da humaira suka raka nuzaira wajen keken dokinta suka bata abinci da kayan marmari. Nuzaira ta goya jaririyar da akabata ta rungume humaira suka sake fashewa da kukan bakinciki suka kamkame juna. Da kyar suka rabu har nuzaira ta sa kafarta guda cikin keken dokin saita waigo ta dubi hukairu tace. "Yakai mijin 'yar uwata shin baka tsammanin wannan farin da annoba bazai shafi wannan jaririyar da kuka baniba". Hukairu yayi murmushi yace karki damu ba abinda zaisameta kuma ina tabbatar miki nan da kwanaki kadan wannan fari da annuba zasu kau. " Nuzaira tace wana suna zan sawa ya rinyar?" Caraf humaira tace "kisamata suna YAZILA mukuma zamu sawa tamu suna DABIRA. " Nantake nuzaira ta shiga cikin keken dokinta ta kada linzamin da wakanta tayi gaba. A can birnin Himsarul Aswad kuwa lokacin.Hadari ya gangamo a ka fara walkiya da tsa warnan sai Barzuk yatafi dakin nuzaira domin ya ga halin da take ciki saboda sanin lokacin haihuwarta yayi a ko yaushe zata iya haihuwa. Da shigar Barzuk cikin haraba bangaren nuzaira saiyaga abin mamaki. Bakomai yaganiba face dukkanin kuyan ginta akwakw kwance suna ta sharar barci al halin lokacin baccinsu bayyiba. Sannan ya ji warin banju yacika gurin gaba daya. Cikin firgici Barzuk ya toshe hancinsa ya ruga izuwa cikin dakin Nuzaira dazuwa yaga dakin wayam babu Nuzaira babu alamarta. Cikin tsananin fushi ya fita daga dakin da sauri ya kwalawa Dakarunsa kira nan da nan kwa dakarun suka rugo gare shi sai ya dubesu yace "maza kuje ku shirya hawa za afita neman matata lallai anzo an saceta batare da bata lokaciba kuwa barzuk yayi gagarumar shigar yaki mai matukar kwarjini. Daban tsoro ya hauwani farin ingarman doki ya jagoranci dakaru dakaru dari biyu suka fice daga cikin birnin. Babban abinda yatayarwa dasu barzuk hankali shine kokadan ba suga sawon da wakaiba bare su san hanyar daya kamata subi. Koda ganin haka sai barzuk yaja linzamin dokinsa ya tsaya cak, suma dakarun nasa sai suka tsaya a bayansa. Nantake barzuk ya dauko madubin tSafinsa ya shafashi da hannunsa take barzuk yagano hanyar da yakamata yabi amma bisa mamaki saiya kasa ganin hoton komai acikin madubin tsafi face hanya kawai al'amarin daya matukar bashi mamaki kenan domin asaninsa gaba daya kasar kisra in banda sarki Daksur babu wanda ya fishi karfin sihirin tsafi wanda zai iya hada kafada da shi sai dai dan uwansa Hukairu. Hukairu kuwa ya dade dayin hijira gabarin gari gaba daya to wane ha tsabibinne haka yazo har cikin garin sa ya sace masa mata. Nan dai barzuk yakada linzamin dokinsa. Yayi gaba, dakaru suka bishi abaya duu aguje sai da su barzuk suka shafe tafiyar wajen sa'a hudu sannan suka hango wani keken doki yanufo garesu aguJe cikin mamaki su barzuk suka yi tur jiya kuma suka zare maka mansu suna jiran isowar keken dokin. Tun daga nesa kadan barzuk ya shaida keken dokin yagane na matarsa ne Nuzaira dan haka sai jikinsa yayi sanyi ya maida ta kofinsa cikin kube ya sauko da gakan dokinsa ya ruga izuwa keken dokin. A gabansa keken dokin yayi turjiya yayi arba da matarshi Nuzaira rike da linzamin dawakan fuskarta cike da annuri kuma tana dauke da goyan jariri abayanta al'amarinda ya matukar bashi mamaki kenan. Cikin tsananin farin ciki ya kama nuzaira ya sauketa dagakan keken dokin ya rungumeta sannan ya karbi jaririn dake baynta ya kura mata ido yana dariyar farin ciki daga can kuma ya turbune fuskarsa ya dubi nuzaira yace "bani labarinki yake matata wanene yazo ya saceki har cikin gidana, kuma ai na kika haifi wannan tsaleliyar jaririya mai kama dani ainun haka?" Sa'adda Nuzaira taji wannan batu saitayi murmushi tace "yakai mijina kayi sani bansan meya faruba ina cikin turakata sai naji anrufe mini fuska an shaka mini banju ahanci. " Kawai sai farkawa nayi naganni a tsakiyar dokar daji kuma babu kowa a kusa dani sai wasu mutane masu shigar bakaken kaya kuma duk sun rufe fuskokinsu idanunsu kadai ake gani suna rike da muggan makamai. Adadin mutanen yakai dubu. Babban cikinsu ne kawai da Jajayen tufafi bisa jan doki koda naga wadannan mutane sai na firgita abin da jawo tasowar nakudata kenan cikin kankanin lokaci na haifi wannan jaririyar dake hannunka acikin keken doki shugaban wa dannan mutanen ya matso kusa dani yakura min ido sannan ya bushe dadariya. Yace yake matar babban abokin gabata kisani cewa kinyi babbar sa'a da yazamana cewa kina dauke da juna biyu da tuni na hallakaki amma saboda ganin kina dauke da juna biyu shiyasa muka fasa dalili kuwa aduniya bana tausayin kowa sai mace mai juna biyu. Narasa matata ne alokacin da take nakudar haihuwar dana kuma tamutu tabarmin dan, har yau har gobe ina tausayin dan saboda ba shi da uwa. Bisa wannan hujjane zan kyaleki kikoma wajen mijinki wannan karan kan kun tsallake harina amma baza ku tsallake na gababa. Koda gama fadin haka sai ya doki daya daaga cikin da wakan keken dokina take suka zabura sukayi tatafiya dani har na hangoku akan hanya wannan shine iyakar abin da zan iya tunawa ya faru gareni ya kai mijina. Lokacin da nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk yacika da tsananin mamaki kuma yakamu da matukar farin ciki yace tabbas babban makiyin mune sarki Raihan yaturo aka daukeki domin ya dauki fansar yar uwarsa da na kashe amma bai sami nasara ba lallai yazama wajibi naje na sanar wa sarki daksur wannan al'amarin domin mu dauki matakin gaggawa saboda nayi mamakin yadda abokin gabarmu ya shigo har cikin kasarmu ya sace min mata batare da munsaniba yake matata ki sani yau shekara goma dayin auranmu amma bamu taba samun haihuwaba sai yanzu lallai acikin farin ciki nake mara misal tuwa dan haka yanzu da ganan birnin kisra zamu wuce nanunawa sarki wannan kyakykyawar 'ya" dakika haifa mini kuma na gaya masa maganar makiyammu Sarki raihan koda gama fadin haka sai barzuk ya shiga cikin keken dokin ya zauna kusa da nuzaira sannan daya daga cikin yaransa ya hau gaban keken dokin ya fara sarrafa dawakan aka cigaba da tafiya aka nufi hanyar da ta nufi birnin sin. Tunda aka fara wannan tafiya zuciyar nuzaira ta fara bugawa da karfi domin ta tabbatar da cewa da zarar sun isa gaban sarki Daksar asirinta ya tonu bisa karyar data shirgawa mijinta cewa yaran sarki raihanne suka saceta domin shi sarki Daksur ka sur gumin ma tsafine wanda ka iya ganin duk abinda yafaru tun gabannin su isa fadar tasa har aka iso cikin kisra hankalin Nuzaira atashe yake bata da sukuni al'amarin dayasa barzuk ya dubeta kenan yace yake matata lafiya naga kamar kina cikin damuwa? Tunda muka fara wannan tafiya bakice uffanba kuma babu walwala da annu shuwa afuskarki koda jin haka sai nuzaira tayi murmushi tace yakai mijina kasani cewa ban taba shiga fadar sarki Daksur ba da girmanaba saboda tun ina yarinya wata rana sa'adda mahaifina ya je dani naga an sare kan wani mutun a gabana saina firgita ainun na tsandara ihu tun daga wannan rana kullun sai nayi mafarkin wannan abu ina firgita acikin barcina saida ma haifina yanaimi taimako awajen bokansa sannan na daina wannan mugun mafarki yanzu dakace zamu fadar sarki daksur sai mafarkin ya fadomin arai saboda haka nidai bana son shiga fadar sarki Daksur ka samomin masauki agari kafin mu isa fadar. Sa'adda Nuzaira tazo nan azancenta sai barzuk ya bushe dadariya yace kadaki damu yake matata lallai bazanje fadar sarki batare dake. Kamar yadda barzuk yayi alkawari haka abin ya kasance wato da shigarsu birnin kisra sai ya kai nuzaira cikin wani kasaitaccen gida irin na sarakai wanda ke dauke da komai na jin dadin duniya harda barori da kuyangu masu hidima. Al'amarin daya matukar bata mamaki kenan domin bata ga lokacin da aka biya kudin hayar gidan ba kuma da zuwansu kofar gidan ta ga masu gadin gidan sun tsube kasa sun kwashi gaisuwa har nuzaira ta bude baki zata tambaye shi batun wannan gida sai yace saboda me zakiyi mamakin mallakar wannan gida agareni ? Shin kin manta ina daya daga cikin makusan tan sarki? Nuzaira tayi murmushi ta ce bana mamakin mallakar wannan gida agareka amma ina mamakin dalilin da ya hana ka sanar dani labarinsa Barzuk yayi murmushi yace so nake na shammace kine nabaki mamaki kinga kenan zamu tare a sabon gida nuzaira tace yanzu idan katare anan birnin ya zakayi da wakilcin sarki a kauyen Himsarul Aswad? Barzuk yayi dariya yace aiba tarewa zanyi ananba kece dai zaki tare a cikin birnin nan domin na fison 'yarmu tataso da wayewa ta zama cikakkiyar 'yar birni mai wayewar kai in yaso duk karshen mako nazo nata fi daku tare ku biyun. Bayan barzuk ya nunawa Nuzaira bangarenta a cikin wannan gida harta shiga ciki ta kwanta tana hutawa kuyangi suka fara mata shidima sai barzuk yayi shiri ya tafi izuwa fadar sarki daksur. Fadace kasaitacciya wadda aka kawatata da kayan alatu iri iri tamkar aljannar duniya sarki daksur na zaune bisa wata kerarriyar kara gar mulki ta ka saita fadawa sun kewaye shi a tsakiyar fadar ga wasu tsala tsalan 'yammata sai tikar rawa suke cikin mummunar shiga mai baiyana tsaraicinsu. A kaida duk sa'adda sarki ke kallon wadannan 'yammata yayin da suke tikar rawa yana dariya da murmushi amma a yau sai sarki ya turbune fuska babu annuri atare da shi ko kadan kuma tun da ya fito fadar haka ya ka sance cikin rahin walwala da sukuni kallo daya mutum zai masa yasan yana cikin tsananin bacin rai. Al amarin daya matukar dugun zuma hankalin fadawa kenan domin sun sancewa fushin sarki ba karamin tashin hankali bane agaresu gaba daya. Ana cikin wannan haline akaga hakimi barzuk ya shigo fadar cikin farinciki kamar wanda aka yiwa albishir din mulkin duniya cikin sauri har da hardewa barzuk ya isa gaban sarki Daksur ya zube kasa ya kwashi gaisuwa ya dago kai domin yayiwa sarki bayanin abin farin cikin da ya sameshi sai sarki yayi farat ya tashi tsaye kawai sai ya dubi barzuk yace kabiyoni izuwa cikin dakin gani ina son magana dakai a sirrance. Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yanu fi dakin gani nanfa Barzuk ya bishi da sauri aka bar fadawa da jama'ar gari a zazzaune sun yi tsurutsuru da idanuwansu suna mamakin abin da ke faruwa. Yayin da sarki Daksur da Barzuk suka shiga dakin gani sai sarki ya tsaya a tsaye maimakon ya zauna ya juyo suka fuskanci juna shida Barzuk yace kazone kayi mini aibishir bisa cewa matarka ta haifi "ya" mace koba hakaba? Cikin muryar rawar murya burzak yace hakane ya shugabana Daksur yace tokasani kasani wannan "ya" data haifa ba "yar ka bace "yar" dan uwanka ce Hukairu amma ita matarka "da" na miji ta haifa kuma a mace yazo duniya hakika matarka ta yaudareka kuma karya ta shiryama domin ka jaddada magana ta yanzu zan nuna maka duk abubuwan da suka faru azahiri. Kagani da idanuwanka. Gama fadin hakan ke da wuya sai sarki yayi nuni da hannunsa izuwa ga jikin bango take hoton al'amarin suka rinka gudana tun lokacin da Nuzaira tayiwa 'yar uwarta Humaira alkawarin cewa lallai awajenta zata haihu har lokacin da aka bata jariri yarnan koda ganin wannan al'amari sai barzuk ya kwarara uban ihu cikin tsananin bakin ciki jikinsa gaba daya ya kama tsuma ka wai sai ya zare ta kofi ya juya da nufin yaje ya sare kan Nuzaira amma sai sarki daksur ya daka masa tsawa ya tsaya cak ya juya ya durkusa bisa guiwowinsa a gaban sarki daksur ya mayar ka takofinsa bisa kubenta ya sunkuyar da kansa kasa alokacin da hawayen takaici yake zubo masa yace ya shugabana yanzu me ya kamata nayi? Sarki daksur yayi ajiyar numfashi sannan yace ya kai Barzuk kayi sani bisa bin ciken da nayi idan muka ka bar matarka da wannan "ya da aka bata wannan fari da annoba da muke fama dasu a gari zasu kare nan da sati biyu kacal gari zaiyi lafiya amma inda masifar take shine wannan jaririyar da matarka ta zo da ita idan har ta girma zama gawurtacciyar jaruma kuma mayakiya fiye da sarkin yakinmu sadauki Hauzar bin Mausus duk yakin da muka taro sai ta sami nasara amma fa duk sanda ta san sirrin tsafina mun banu mun lalace sai mulkimmu ya rushe. Kuma sai talakawanmu sun zama shugabanninmu sun dauki fansar zaluncin da muka dade muna yi musu tsawan shekara da shekaru ta han ya daya ce ka dai zamubi kada azo da ita fadata kada abari tayi arba da fuskata kuma kada ka nunawa matarka bacin ranka koka gaya mata abin da muka tattauna anan yanzu. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {1} TYPE D ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== A can daji kuwa inda manomi hukairu yayi gidansa sun wayi garine a cikin farin ciki da bakin ciki dalili farincinsu shine na haihuwa da humaira tayi nayaya tagwaye mata duk da cewa tayi kyautar bayar guda ga 'yar uwarta nuzaira shi kuwa mummuna mafarkin wanda himaira tayi a jiya da daddare da safe sa adda humaira ta farka daga bacci ta fara bawa mijinta hukairu labarin mafarkinda tayi a jiya al amari daya matukar dugunzuma humaira duk hankalinsa kenan dalili kuwa shine a iya saninsa da matarsa humaira duk abin datayi mafarkinsa saiya tabbata a gaske. Bawani abu humaira ta ganiba acikin mafarki ba face saukar wadansu dakaru kamar daga sama wadanda suka bukawa gidan wuta ya kone kurmus babu abin da ya tsira. Lokacin da hukairu yaji labarin mafarkin da humaira tayi sai hankalinsa ya dugunzuma ainun rasa abin dake masa dadiya shiga tunani mai zurfi daga can saiya dubi ita humaira yace yake matata kinsani cewa wajibine a garemu muyi hijra mubar gabadaya yankin wannan kasa tamu idan har muna son mu da abin damuka haifa mutsirada rayuwarmu naji ajikina cewa sarki daksar kasurgumin matsafine don haka na tabbatar da cewa abinda ya faru tsaka nimmu da 'yar uwarki nuzaira ya gani kuma ya nunawa barzuk bisa wannan da lilinne za su turo a hallakamu lokaci yayi da zan gaya miki wani sirri wanda bantaba gaya mikiba. Tun muna yara nida dan uwana barzuk bokan ma haifina wanda muka sami sirrikan tsafi a wajensa yace mana cewa agaba daya kasar nan babu wani mahaluki mai karfin sihirinmu face sarki daksar amma duk 'yar da muka haifa idan tayi arba da idan sarki daksar to zata samu duk irin sihirin da sarki daksar yake da shi a cikin kwana uku harta samu nasarar Hallaka shi ta hau kan karagarsa face ya kasheta kafin cikar kwana uku shi kansa sarki daksar ya san da wannan sirri don haka bazai taba barin abun da muka haifa arayeba dun haka ba zai barmuba yazama wajibi muyi shirin gaggawa yanzu muyi hijira mukara gaba. Sa adda hukairu yazo nan azancensa sai humaira ta ce yanzu ina kake tsammanin zamu shiga mu buya ba tare da sarki daksar yaturo an kashemuba Hukairu yace waje daya ne zamu iya zuwa muyi rayu wa acan kuma mu tsira daga sharrin sarki daksar da dan uwana Barzuk. Bawani waje bane face birnin misra inda sarki Raiyan ke mulki. " Koda jin haka sai idanun Humaira suka zazzaro tace "ya ya za ayi muje birnin misra kuma muyi rayuwa alhalin mutanen can sun kasance musulmai mukuma ma abota tsafine da gunki? Humaira tace "shin ka manta ne sarki daksur bashi da wani makiyi wan da yafi sarki Raiyan na birnin misra? Ai idan sarki raiyan ya fashinci cewa mu mutanen birnin kisra ne sai yasa anyi mana kisan gilla domin ya dauki fansar ran 'yar uwarsa gimbiya Numaira wacce sarki daksur ya ka she yayin da aka fafata kazamin yaki da su a shekaru uku baya. " Hukairu yayi ajiyar numfashi sannan yace "duk nasan da wannan al'amari amma abinda nake so ki fahimta shi ne abinda ya koro bera yafada cikin wuta ya fi wutar zafi. " Koda gama fadin haka sai hukairu ya mike tsaye yakama hada kayyayyakinsu domin suyi hijira. Bayan ya gama hada hada komai a waje guda ya dora a kan rakumansa wasu kuma akan shanunsa sai yaje tsakiyar filin gidan ya haka rami sai ga shi ya tuno wata laya. Nan take ya rataya layar a wuyansa, sannan yakira Humaira ta fito da ga cikin daki goye da jaririyarta. Ba tare da bata lokaciba suka hau kan rakumansu biyu sukayi gaba suna janye dabbobinsu. Koda hukairu ya juya ya dubi gonarsa da wannan gida nasa sai idanunsa suka cikoda kwalla saboda takaicin ya tafiya bar kasa mai albarkar noma wadda abu ne mawuyaci ya sake samun irinta. Bayan kamar sa a hudu da tafiyar hukairu da matarsa humaira sai ga sarkin yaki haizar bin mausus bisa doki tare da dakaru dari biyar suna take masa baya dukkaninsa dauke da muggan makaman yaki tun daga nesa haizar ya dauko wani gilashi na sihiri wanda sarki daksur ya bashi ya ce da shi da wannan gilashi ne kadai zai iya hango gidan hukairu. Haizur yasa gilashin a kan idanunsa amma bai hango komaiba dan haka sai suka kara kaimin gudu bisa da wakansu. Jim kadan da faruwar haka sai suka hango gidan daga can nesa. Daya daga cikin daka runnasane ma ya fara hangowa ya nuna masa al'amarin daya matukar ba shi.mamaki kuma yaba shi tsoro ya fara tunanin duk yadda a kayi su Hukairu basa gidan kuma lallai ya tone wannan laya wacce sarki daksur ya bashi labarin cewa hukairu ya binneta a tsakiyar gidansa. Tun da ga inda suka hango gidan Haizar yabada umarnin a fara harba kibiyar wuta izuwa gidan. Ai kuwa cikin kan kanin lokaci gidan gaba daya ya kama ya kama da wuta yana ci balbal. Su sarkin yaki haizar suka karqso gaban gidan aguje bisa dawakansu suka yiwa gidan kawanya kuma suka dana kwari bisa baka suna jira suga wani abu mairai yayi fitar burgu don ceton ransa su harbeshi amma hargidan yagama konewa kurmus yazama toka ko kyanwa basu ganiba. A sannanne sarkin yaki haizar ya sakko daga dokinsa ya duba tsakiyar gidan nan take kuwa yayi arba da wannan rami wanda hukairu tone ya cire layarsa ta sihiri. Cikin tsananin ta kaici da fushi haizar ya kwarara ihu sannan ya dakko mudubin tsafinsa ya shafeshi sau uku yana mai karanta wadansu dalasiman tsafi guda uku. Faruwar hakan keda wuya sai ga fuskar sarki daksur ta bayyana akan madubin suka dubi juna. Kafin haizar ya budi baki yace wani abu sai sarki daksur ya tari numfashinsa yace "maza ku ruga gaba domin tuni Hukairu da matarsa sunyi nisa, taza rarku da su ta kai nisan sa'a hudu. Idan kuka yi sakaci suka shiga yankin kasar misra shi ke nan baza ku taba riskar suba. Tun da hukairu na tare da wannan laya baza ku taba ganin koda sawunsuba amma i dan kayi amfani da wannan gilashin sihiri da na baka zaka i yaganin sawayensu. Idan har kana son kariskesu sai kunyi ta fiyar kwana uku bayada zango babu barci. Idan har kasami nasarar cika wannan aiki kana dawo wa birnin kisra zanbaka wazircina kuma zanbaka dukiya ninkin goman abin da ka mallaka a yanzu. Koda gama wannan jawabi sai fuskar sarki daksur ta bace bat, daga cikin madubin sarkin yaki haizar nan take yaji farin ciki ya lullubeshi dan haka sai yaruga kan dokinsa yayi tsalle ya haye kan dokin ya zabure shi cikin matsanancin gudu koda ganin haka sai suma ragowar dakarun suka sakarwa dawakansu linzami suka rufa masa baya. Tun dasu sarkin yaki haizar suka cigaba da wannan tafiya basu tsaya ba har rana ta fadi, gari yasoma duhu. A wannan lokacinne yunwa da kishirwa ta suka fara addabarsu. Sai da ta kai suna ta fiya da wakansu suna sassarfa domin suma sun gaji dokin haizar ne ka wai bai gaji ba saboda shi ba doki bane na gaskiya, dokine na sihiri. A duk sa'adda daya daga cikin dakarun yayi yun kurin tsaya wa don ya huta kodan ya nemi ruwan sha sai haizar ya da ka masa tsawa ya shiga taitayinsa, idan kwa yaki bin umarni nan take haizar zai zare takobi yasare kansa nan take bisa dole suka hakura suka hakura suka ci gaba da tafiyar a hankan bayan kwana daya ne dakarun suka rinka yanke jiki suna fadowa daga kan dawakansu matattu saboda tsananin yunwa da kishirwa sakamakon basu taho da isasshen gazuri ba masu tsananin juriya da taurinri ai ne suka kai kwana na uku amma suma alfijir na ketowa suka fadi kasa matattu ya rage saura sarki haizar shi kadai bisa dokinsa shi kansa in badon yana tsafiba ya sami ruwansha da tuni ya mutu saboda azababben zafi ranar da ake yi ga shi dazuzzukan da suke ratsawa gabadayan su saharane ko bishiya daya mutum ba zai gani ba. Lokacin da rana ta take ne haizar hango su hukairu a can gabansa tazarar da bata wuce taku dari biyar ba tsakaninsu sun doshi kofar birnins misra koda ganin haka sai haizar ya zare takofinsa yasa karwa dokin sihirinsa linzami ya zabureshi cikin masifaffen gudu. Su hukairu na cikin tafiya sai suka jiyo sukukuwar doki a bayansu. A firgice suka juyo hango wanda ke kokarin kawo musu hari cikin hanza hukairu yazare takobinsa ya tsaida rakuminsa sannan ya dubi humaira ya ce maza ki ruga bakin kofar binin misra ni kuwa zantsaya na tari wannan mahayi da ya durfafomu. Ba wanibane.face sarkin yaki haizar lallai sarki daksur ne yaturoshi ya hallakani. Koda jin wannan batu sai humai tafa she da kuka ta ce ni kam bazan tafiba na barka sai dai mutafi tare. Cikin tsananin fushi hukairu ya dakawa ya dakawa humaira tsawa ya ce idan ban tsaya ba na tareshi zai cimmanane ya hallakamu gaba daya har jaririyar dake goye a bayanki. Fatana shine ke da jaririya kutsira da rayuwarku ai ni nagama cika burina kunda har na kawo kunan bakin birninmu da na misra. " Koda jin wannan batu sai humaira ta zaburi rakuminta da gudu tanufi bakin kofar birnin misra, a wannan lokacin baifi taku arba'in ba haizar ya iso gaban hukairu Hukairu ya juya yayiwa Humaira kallon kar she cikin guntun murmushi, a lokacin da kalla ta cika idanunsa. Wai gawar da zaiyi haka sai yaga sarkin yaki haizar dab da shi har ya kawo masa wawan sara da nufin ya sare masa kai. Cikin zafin nama hukairu ya sunkuya ta kobin haizar ta sari iska shima ya zare takobinsa suka fara a zababben yaki. Nanfa suka fara kai wa juna sara da suka cikin tsananin zafinnama, juriya da bajimta ya zamana cewa dayansu ya kasa cutar da dayan al'amarin da ya matukar baiwa sarkin yaki zaihar mamaki kenan domin bai taba sanin cewa HUkairu jarumine haka ba. Lokacin da ake wannan mugun artabu tsakanin Hukairu da Zaihar tuni humaira ta isa bakin kofar birnin misra amma sai ta ja linzamin rakumin ta ta tsaya cak ta kasa shiga birnin ta juyo cikin tashin hankali tana kallon gumurzun da akeyi tsakanin mijinta da sadauki zaihar. Lokacin da sadauki zaihar yaga wankin hula zai kai shi dare sai ya fusata ya fara amfani da karfin sihiri domin ya hallaka hukairu amma sai ya ga ashe shima hukairu ba kyalle bane abangaren tsafi domin karfi ya zo daya. Haizar yaja da baya yaduru daga kan dokinsa ya tsaya cak a waje daya yana tunanin dabarar da ya kamata yayi. Koda ganin haka sai shima hukairu ya duro daga kan rakuminsa ya gyara tsayuwa yana mai fuskan tarsa sannan ya kyalkyale da dariya yanuna haizar da dan ya tsa ya ce "ya kai wannan tsohon azzalumi ba wan azzalumai ka sani burin mai gidanka bazai cikaba a kan iyalina domin sun tsira daga sharrinkku a yanzu tunda sun haye iyakar kasarku. Ko a yanzu ka kashe ni bani da na damar komai. Yayin da haizar yaji wannan batu sai shima ya kyalkyale da dariya sannan yace "ai kuwa yanzu zan kasheka sannan nabi iyalinka har bakin kofar birnin misra suma na hallakasu tun dadai sun kasa shiga cikin birnin sun tsaya suna kallo domin suga irin mutuwar dazakayi. " Koda jin wannan batu sai hukairu yajuya da sauri domin ya dubi bakin kofar birnin misra kafin ya juyo da kansa tuni Haizar ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da tsini ya wurga masa take wukar ta cake atsakiyar kirjinsa ya dur kushe bisa guiwowinsa koda humaira ta hango abinda ya faru da sai ta tsandara uban ihu al'amarin da ya janyo hankalin masu gadin kofar birnin misra kenan suka rugo waje da gudu rike da makaman yaki suda yawa. Yayin da sarkin yaki ya hango fito war wadannan mayaka sai ya juyo da sauri ya ruga izuwa kan dokinsa na sihiri ya zabure shi da gudu yanufi baya. Ita kuwa Humaira sai ta diro kasa daga kan ra kuminta ta falfala da gudun tsiya tana kuka izuwa inda mijinta yake durkushe. Koda zuwanta gabansa sai ta tabashi sai taji ya bingire kasa ko motsi baiyiba alamar cewa yamutu ba shi da rai nan fa ta rungume gawarsa tasake fashewa da matsanancin kuka. Tana cikin wannan haline dakarun misra suka zo gareta suka banbareta daga jikin gawar da karfin tsiya suka tafi da ita izuwa cikin birnin misra tana ta iface iface da koke koke tamkar sabuwar mahaukaciya. Wannan shine abin da ya faru ga Humaira matar Hukairu bayan srkin yaki ya riskesu ya kashe hukairu, ita da jaririyar sun tsira A can birnin kisra kuwa lokacin da hakimi barzuk ya koma wannan gida nasa inda ya ajiye matarsa nuzaira sai ya shaida mata duk wadannan dokoki wadanda sarki daksur ya shimfida masa a kan jaririyar data haifa ko da jin wadannan dokoki sai ta cika da tsananin mamaki ta dubeshi tace to wai shin laifin me mukayi harda sarki zai kafawa yarmu irin wadannan dokoki masu tsauri dayawa haka?” Koda jin wannan tambaya sai barzuk ya tumbune fuska yace ” ni kaina bansan daliliba amma babu mamaki akwai babbar hujja data janyo mana hakan saboda haka indai kIna son mu tsira rayuwarmu da mutuncinmu lallai kikiyaye wadannan dokoki ” daga wannan rana kowa nuzaira tacigaba da renon jaririyarta da ranar suna tazo sai aka radawa jaririya suna yazila tunda nuzaira ta acikin wannan gida na mijinta acikin birnin kisra batata bin hanyar gidan sarauta ba bare ma taga sarki da idanunta bare kuma jairiyar datake raino. Tafiya sannu sannu kwana nesa darare na wucewa kwanaki na shudewa sai aka wayi gari yarinya yazila ta cika shekara bakwai a duniya nan da yazila tazama sananniya a birnin kisra saboda kasancewarta tataso da tsananin kyau dakuma jarumantaka domin tun a sannan tana iya daga kato komai girmansa ta rankwalashi da kasa har sai datakai cewa ana shirya mata gasar kokawa da mazaje majiya karfi tana zama zakarar gasar daga nan kuma sai lamari nata kara samun cigaba domin ta fara koyon sarrafa takofi`mashi`kwarida baka. Duk mutumin daya fara koya mata amfanida kayan yaki sai yaga tafi kwarewa acikin kwanaki uku kacal. Tun da yazila ta taso taga wata farar laya a wuyanta bata son abin da zai rabata da layarba dare da rana har kwanciyar barci kuwa. A takaice dai batata cire layarba kuma tana iya tuno lokacin da mahaifiyarta hakimi barzuk ya samata layar sa adda batafi shekara biyarba aduniya. Koda wasa yazila batata bin hanyar gidan sarki ba kuma kojitayi sarki zai shigo cikin gari tobazatataba fita daga cikin gidan domin a rayuwarta babu data tsana tagani ko taji zancensa face sarki. Abinda batasaniba shine. Wannan laya da aka rataya mata awuya itace sanadin dataji batason taga sarki. Ana nan cikin wannan hali har yazila ta cika shekara goma sha takwas. Alokacin ne kyawunta yaruda gaba dayan jama ar birnin kisra ya zaman cewa duk inda mutun yaje saidai yaji ana labarinta. Afagen jaruman taka kuwa al amarin maya wuce tunanin mai tunani domin duk sa adda aka fita yaki da mutanen birnin misra tana ya musu mummunar barna wata jaruma guda daya takeci mata tuwo akwarya wadda itace sarkin yakin mutanen birnin misra a wani lokaci ita dai yazila taji ana yiwa jarumar kirari da basadaukiya dabira babban abin takaici a wajen yazila shine bata taba ganin fuskar wannan abokiyar gaba tata ba domin duk sa adda zata fito yaki tana rufe fuskarta ne da hular karfe. Akalla yazila da dabira sun fafata kazamin yaki kamar sau hudu amma duk sa adda suka hadu.kare jini biri jini sukeyi. Koda rauni suka yiwa juna sai kaga raunin yazo adadi daya baya gotawa sukansu suna matukar mamakin wannan al amari babu irin kokarin da yazila batayi ba don ganin ta cire hular karfen datake dabira taga fuskarta amma abu ya gagara. Akwai.wata rana da yazila ta tambayi bokanta wanda ake kira mushrid bin affan tace dashi yakai abin dogarona yaza ayina sami nasara akan abokiyar gabata basadaukiya dabira na kai kasa kuma har na cire hular karfen dake kanta naga fuskarta ?” Koda jin wannan tambaya sai boka mushrid ya kyalkyale da dariya sannan yace ” idan har kina son ki sami wannan nasara sai dai ki cire wannan laya dake wuyanki kije har cikin fadar sarki daksur ku yi arba da juna in dai kikayi haka sai kin nasara akan jaruma dabira har kiyi mata rauni sama da adadin wanda zatayi miki. Kuma ki kaita kasa ki cire hular karfen dake kanta kiga fuskarta amma ki sani cewa ranar da wannan abu ya faru zaki shiga tashin hankali irin wanda baki tabaga shigarsa ba” Koda jin wannan babu sai jaruma yazila tasa hannunta ta kama wannan farar laya dake wuyanta da nufin ta cireta amma sai ta ji kamar an soka mata allura guda dubu a sassan jikinta. Ba shiri ta saki layar ta kama ihu kuma ta fadi kasa a matukar galabaice tana haki kamar wadda aka yi yunkuri zare ruhinta. Nan ta jike sharkaf da gumi da kyar ta dago da kanta ta dabi boka mushrid tace ” me yasa na kasa cire wannan laya daga wuyana kuma taya ya zan iya rabuwa da ita ?” *WACCE AMSA BOKA MUSHRID ZAI BAIWA JARUMA YAZILA? *YAUSHENE JARUMA YAZILA ZATA YI ARBA DA FUSKAR SARKI DAKSUR? *YAYA AKAYI BASADAUKIYA DABIRA TAZAMO SARKIN YAKIN BIRNIN MISRA? SHIN ITAMA TA ZAMA MUSULMA CE? *INA LABARIN MAHAIFIYARTA HUMAIRA? *SHIN NUZAIRA DA HUMAIRA ZASU SAKE GANIN JUNA? MUHADU A JARUMA YAZILA NA BIYU DON JINCIGABAN WANNAN LABARI. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ----------------------------------------------------------------- ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {2} TYPE A ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== Lokacin da jaruma yazila ta tambayi boka musrid bn Affan dalilin da ya sa takasa cire wannan laya daga wuyanta da kuma yadda zata iya rabuwa da ita sai ya yi ajiyar nunfashi sannan yai shiru ya sunkui da kansa kasa cikin halin tunani tsawon lokaci mai tsawo yana tunani baice komaiba daga can sai ya dago kai ya dubeta cikin tsananin damuwa sannan yace ya ke jarumar jarumai ki yi sani cewa yau kin tambayeni babban al amari wanda yafi karfina domin idan na ce zan matsa bincike bisa wannan al amari zan iya rasa rayuwata. Ita dai wannan laya ta wuyanki tun kina jaririya mahaifinki Barzuk ya sanyata a wuyanki kuma duk ranar da kika sami damar cireta a ranar ne zaki san wani babban sirri dangane dake kanki da kuma mahaifinki da sarki daksur har kiyi arba dashi in kuwa kika yi arba da shi duk irin sihirin tsafin da yake da shi sai kin sameshi. Ina tabbatar miki da cewa duk duniya a halin yanzu babu wanda zai iya cire maki wannan laya face abokiyar gabarki dabira ta birnin misra. Sa'adda boka mushrid yazo nan a zancensa sai jaruma yazila ta cika da tsananin mamaki kuma zuciyarta tayi bakikkirin ta dubi boka mushrid ta ce, "yanzu ashe ke Nan akwai wani babban sirri dangane da rayuwata wanda mahaifiyata da mahaifina suka boye mini?" Boka mushrid yace kwarai kuwa akwai wannan sirri kuma kada kiga Laifinsu domin sanar dake bazai haifar da komaiba face tsananin tashin hankali agareki baki daya. Koda jin haka sai hawaye ya zubowa jaruma yazila tace, "Ai kuwa a yau dinnan sai na tambayi mahaifiyata wannan al'amari ko menene zai faru kuma zan yi shiri na tafi birnin misra wajen abokiyar gabata jaruma dabira domin na san dabarar dazan yi tacire min wannan sarka bare bata saniba. " Cikin firgici boka mushrib ya kama kafadun jaruma yazila yace, "yake jarumar jarumai, kiyi sani cewa abinda kike shirin yi tamkar ki aza gammo ne a kanki kice zaki dauki duniyar nan gabaki daya ina mai shawartar ki da ki hakura dayin wannan abu domin a karshe allura ce zata tono garma." Koda jin haka sai yazila ta mike tsaye zumbur! A fusace tace, "ya kai wannan amintaccen bokana kayi sani cewa babu wani abu da ya isa yahanani yin waddannan abubuwa guda biyu face mutuwa kuma yanzu_Yanzu zan tafi na fara gabatar dasu ." Koda gama fadin haka sai yazila ta juya ta fice daga daga gidan boka mushrib tana isa kofar gidansu tayi kicibis da boka mushrib tsaye gabanta fuskarsa a murtuke babu annuri. Mushrid ya dubi yazila yace, "bazan barki kije ki ai'watar da wannan al'amariba domin nifa zaki jefani cikin masifa da bala'i". Yazila tayi murmushi sannan tace, "kayi sani cewa dan zaki ya girma banga ta yadda zaka iya hananiba, idan kuma kana ganin zaka iya toka jarraba". Gama fadin hakan ke da wuya sai ta yun kura da nufin ta wuce ta gabansa. Take mushrid yayi nuni da hannunsa izuwa gareta sai wata irin murtukekiyar sarkar tsafi ta kanannadeta tun daga kan kafafunta har zuwa kanta ta daureta tamau, idanunta da fuskarta ka dai ake gani. Yazila ta girgiza jikinta don ta tsinke sarkar amma ta kasa kwancewa. Koda ganin haka sai boka mushrid ya bushe da dariyar mugunta yace "kika ce dan zaki yagirma kodai dan kyanwane?" Yazila ta kyalkyale da dariya sannan ta ce, tabbas dan zakine wannan ba dan kyanwa bane. " Kafin boka mushrid ya kara cewa wani abu sai yazila ta ambaci wata kalma daya daga cikin da lasiman tsafi. Nan take wannan sarkar tsafi ta narke tazama ruwa. Kafin boka mushrid ya yi wani yun kuri tuni yazila ta fincikoshi da hannu daya tayi hajijiya da shi a sama ta fyada shi da kasa kuma tatake masa wuya da kafadaya ya fara kakarin mutuwa. Yazila ta dauke kafarta guda daga kan boka mushrid tacce, "kaci albarkacin kyautatawar da kayimin abaya da yanzu zan kasheka. Kasani cewa dokata ta farko akan kowa itace, ba ayimini dole, kuma idan nabada umarni ba a ketare shi daga yau idan ka sake saba wannan doka zan kau da batun mutunci dake tsakaninmu na yi maka hukunci dai-dai da laifinka. " Koda gama fadin haka sai jaruma yazila tayi girgiza ta bace bat ! Tamkar bata taba wanzuwaba a wajen. Al'amarin daya matukar baiwa boka mushrid mamaki kenan ya bita da kallo ka wai zuciyarsa cike da wasa- wasi yana mai cewa, "yaya akai yazila ta sami wannan sihirin tsafin mai karfi haka ? Abinda bai sani ba shine, yazila ta ziyarci manyan bokayen duniya ta sami sirrikan tsafi da yawa. Wadan da suka finasa. " Lokacin da jaruma yazila ta isa gida sai ta iske mahaifiyarta nuzaira zaune a turakarta. Ko magana yazila bata mataba sai ta wuce kai tsaye izuwa cikin turakarta, al'amarin da ya matukar baiwa nuzaira mamaki kenan domin a duk sa'adda yazila ta dawo gida da gudu take shigowa turakarta, ta rungumeta cikin farin ciki ta sumbaci goshinta. A rayuwar jaruma yazila babu take kauna sama da nuzaira ko kadan bata son taga abin da zai sosa mata zuciya, haka kuma duk abin da nuzaira ta umarci yazila tayi sai tayi shi bata taba yimata gar dama. Bayan yazila ta shige cikin dakinta sai nuzaira ta mike tsaye ta kira wata kuyanga mai suna rafina wacce itace ke kula da komai na yazila ta ce da ita taje ta kawo mata abincin yazila. Cikin mamaki rafina ta dubi nuzaira tace , "ya shugabata ai yanzu zan je na kai mata abincin". Nuzaira tace yau ni da kaina nake son na kai mata" Koda jin haka sai rafina ta juya da sauri tatafi dakin girki ta dakko abincin yazila bisa faranti ta kawowa nuzaira ita kuma ta karba ta tafi dakin yazila ". Yazila na zaune bisa gefen gadon ta tayi ta gumi cikin halin tunani mai zurfi. Ka wai sai taji anturo kofa an shigo. Yazila ta dago kai da sauri tayi arba da ma haifiyarta Nuzaira kawai sai ta kau da kai ga barin kallonta ta sun kui da kanta kas. Cikin sanyin jiki nuzaira ta matso daf daf da yazila ta ajiye farantin abincin wani benci karami sannan ta zauna bisa wata kujera dake fuskan tar yazila ta dafa cinyoyin yazila tace, "yake 'yata yau kuma wanene yabata miki rai a waje har da fushinsa zai shafeni?" Koda jin wannan tambaya sai hawaye ya zubowa yazila ta kasa cewa komai. Al'amarin da ya matukar razana Nuzaira kenan ta cika da tsananin mamaki. Kawai sai yazila ta kama hannun nuzaira ta dora akanta tace, yake mahaifiyata ina son ki yi ran tsuwa bisa dara jar kaunar dake tsakaninki dani ki gaya mini gaskiyar al'amarin da zan tambayeki a yanzu. Kisani cewa idan kika gaya mini sabanin gaskiya kuma na gano hakan anan gaba lallai zan kashe kaina domin ban ga amfanin rayuwataba a duniya tunda wadda na aminta da ita fiye da kowa bata aminta daniba". Cikin rudewa Nuzaira tace mene ya kawo duk wannan al'amarin haka yake 'yata ? Shin wani ne yace akwai abu dana boye miki ?" Yazila ta share hawayen i danunta tace, "dafarko ina so n'ki gaya mini asalin wannan layar dake wuyana da kuma dalilin da yasa aka sakamin ita. Ina son ki gaya mini sirrin dake tare da rayuwata da taki. Na ran tse da darajar soyayyar da nake miki idan kika boye mini gaskiyar al'amari bazan taba yafe miki ba " Sa'adda Nuzaira taji wannan tambaya sai tacika da tsananin mamaki bisa abin da ya janyo yazila tayi mata wannan tambaya. Nuzaira ta dubi yazila tace, "mene ne dalilin daya sa kika yi mini wannan tambaya?" Koda jin haka sai yazila ta kwashe labarin duk abin da ya faru tsakanin ta da boka mushrid ta zaiyane mata. Sa'adda nuzaira taji wannan batu sai han kalinta ya dugunzuma ta dubi yazila tace, "yake 'yata hakika yau kin zomini da babban al'amari don haka yana da kyau ki bani lokaci. Isasshe nayi tunani tukunna. Yanzu dai ina son ki kwantar da hankalinki sannan kici abincinki inyaso nan da wani lokaci na dawo gareki muci gaba da wannan magana". Har nuzaira ta mike tsaye zata fita daga dakin sai yazila taruko hannunta ta zaunar da ita alokacin da hawaye yaci gaba da zuba akan kumatunta. Yazila tace, "ya ke Ummina ina tabbatar miki da cewa idan baki bani amsar tambayata a yanzu ba ba zan kara cin abinci ba a rayuwata sai dai yunwa da kishirwa su kasheni". Koda jin haka.sai hankalin nuzaira ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe domin ta san halin yazila duk abin da ta ce za ta aikata bata fasawa kawai sai yaZila ta ga hawaye ya zubowa nuzaira sannan kuma ta fashe da kuka al amarin. Da ya matukar dugunzuma hankalin yazila kenan taji ta yi nadamar matsawar datayi mata a kan wannan tambaya batare da nuzaira tace komai basai tamike tsaye taje ta kulle kofar dakin sannan ta kulle tagogin dakin ta dawo daf da nuzaira ta zauna ta fara ba ta labari tun daga lokacin da hukairu da humaira suka yi hijra daga kauyen himsarul aswad suka koma can da birnin kisra suka cigaba da rayuwa kawo izuwa lokacin da nakuda ta kamata ta tafi can inda su humaira ta haifi yan mata tagyaye ta dauki daya ta bata ta dawo wajen mijinta barzuk suka koma cikin birnin kisra da zama da duk irin dokokin da sarki daksur ya kafawa jaririyar har barzuk ya kawo wannan laya aka sanyawa jaririyar a wuyanta. Lokacin da nuzaira ta gama baiwa yazila wannan labari sai yazila ta fashe da matsanancin kuka kamar baza ta daina ba. Kuma tacika da matukar mamaki da bakin ciki da kyar da sidingoshi nuzaira ta rarrashi ta tadaina kukan sannan ta roketa akan tabar wannan magana a zuciyarta domin idan tace zata dauki wani mataki akan barzuk da sarki darkus bazata sami galababa. Yazila ta gyada kai cikin matukar takaici sannan tace yake ummata kiyi sani inda na san cewa niba yarki bace bazan tsaya nayi yaki da mutanen birnin misra ba tsawon shekaru kuma ina tabbatar miki da cewa lallai sai na sami nasarar cire wannan laya daga wuyana kuma komai dadewa sai naga bayan mijinki da sarki daksur. Domin sun kasance azzalumai kuma bara gurbi a doron kasa shin yanzu kina da labari yar uwarki humaira da yar uwata dake tare da ita ?“ Koda jin wannan tambaya sai nuzaira tayi ajiyar zuciya tace ai rabona da su tun sa adda na rabu da su a can gidansu daji amma na taba ji a bakin sarkin yakin garin nada wato sadauki zaihar cewa hukairu da humaira tare da yarsu sun gudu izuwa birnin misra amma ya bisu har ya riskesu kafin su shiga birnin har ya fafata yaki da mahaifin naki hukairu ya sami nasarar kasheshi amma bai sami damar kashe humaira da yar uwarki ba domin dakarun birnin misra ne suka yiyo kansa ya gudu ya yin da yazila taji haka sai zuciyarta ta kama tafarfasa kamar za ta kone tace yanzu sarkin yaki zaihar ne ya kashe mahaifina ?“. Nuzaira tace tabbas haka ne babu shakka “ yazila kuwa indai mahaifiyata da yar uwata suna raye tabbas suna cikin birnin misra ni kuwa ta kowanne hali sai na shiga birnin misra na sadu da su dama ina da burin naje na sadudA jaruma dabira domin ta cire mini wannan laya dag wuyana kuma ina son muyi yakin karshe da ita domin nasami damar kaita kas har na cire hular karfen da take sawa a kanta domin naga fuskarta kin ga kenan ina da manyan bukatu har guda uku acikin birnin misra don haka zama bai kamani ba dole ne nayi shiri na tafi birnin misra". Koda jin wannan batu sai hankalin Nuzaira ya dugun zuma ta dubi yazila cikin firgici tace, "yake 'yata kin sani cewa mutanen birnin misra sun kasance ma'abota addinin muslunci saboda haka zuwanki birninsu abu ne mai hadarin gaske da zarar sun ganki zasu hallakaki tun da kin kasance tsohuwar abokiyar gabarsu. Ki tuna cewa kin kashe musu jama'a ba adadi. A bu na biyu koda 'yar uwarki da mahaifiyarki suna nan araye yanzu kodai suna kurkuku kokumaa suma sun zama musulmai don haka baza suyi mar haban da keba tun da kun banbanta addini da yanayin rayuwa. Ke koma dai babu banbancin komai ai baza sutaba shaidakiba tun da basu sankiba kema baki sansuba. Shekara goma sha takwas ai ba kwana goma sha takwasbane. Na tabbata yanzu 'yar uwata Humaira ta tsufa, kamar yadda nima na tsufa, ta yaya zata shaidaki alhalin rabonta da ke tun kina jaririya?". Lokacin da nuzaira ta zo nan a zancenta sai yazila ta mike tsaye ta kama kai kawo sannan ta tsaya cak ! Ta dubi nuzaira tace, "yake ummina ki sani cewa dan uwa-dan uwane, har abada idan ka hada jini da mutum sai kaga wani abu ya zamo iri daya da nasa bare kuma ni da 'yar uwata mun kasance tagwaye ai dole ne asami kama ni da ita kamar yadda kika bani labari cewa tamkar an tsaga kara muke. " Nuzaira tayi ajiyar zuciya sannan tace, "nidai na umarceki da kada ki kuskura kice zaki ce zakiyi wannan ta fiya izuwa birnin misra kuma ina mai gargadinki da kada ki kuskura kice zaki je kiyiwa sarkin yaki zaihar wani abu, domin kina tabashi mijina da sarki daksur zasu gane cewa na sanar dake sirrin rayuwarki don haka komai zai iyafaruwa a gareni. Yake yazila ki tuna cewa nice na shayar dake harkika girma kika zama mutum, ki tuna nice naci kashinki, na sha fitsarinki, kuma nice na sha wahalar renunki idan kika bari su sarki daksur suka cutar dani lallai kinci amanata kuma kinci amanar zumuncin dake tsakanina da mahaifiyarki." Koda gama wannan jawabi sai nuzaira tayi shiru bata kara cewa komai ba , sannan ta mike tsaye ta fice daga cikin dakin ta bar jaruma yazila a zaune cikin tsananin damuwa, gami da tunani mai zurfi. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {2} TYPE B ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== Haka dai yazila taci gaba da sake-sake acikin zuciyarta ta kulla wancan ta kwance wancen har dare yaraba ya zamana taka sayin barci sai kai kawo kawai takeyi acikin dakin nata tana zarya. Bayan tayi dogon nazari da tunani akan abinda zai fishsheta sai taje ta dakko takadda da alkalami ta rubuta wata wasika ta ajiye a karkashin matashin kanta sannan ta cire kayan jikinta ta sanya wadansu bakaken sulke na yaki ta dauki makamanta na yaki ta soke a jikinta nan take tayi girgiza bace bata bayyana ako ina ba sai a kofar gidan sarkin yaki zaihar da baiyanarta sai taga masu gadi a tsaitsaye suna kan aikinsu kai tsaye jaruma yazila ta durfafosu koda masu gadin suka hangota sai suka cika da tsananin mamaki bisa ganinta a cikin wannan lokaci na tsawon dare cikin ladabi da biyayya masu gadin suka risina suka gaisheta yazila ta dubeshi a fusace tace kubude mini kofa da salama na shiga domin naga mai gidanku idan kuma kuka yi gardama yanzun nan takobina zata sha jininku !“. Koda jin wannan batu sai jikin masu gadin ya kama karkarwa cikin firgita sukayi sauri suka bude mata kofar ta kunna kai ciki da shigar yazila cikin gidan sai tazare takobinta taci gaba da kutsa kai tana leka cikin dakunan gidan domin taga inda sarkin yaki zaihar yake. Karar zare takobin yazila daga cikin kubbenta ne yasa sadauki zaihar ya bude idanunsa alokacin da yake kwance tare da matarsa acikin turakarsa dama bai dade da kwanciya ba bisa bata lokaci da yayi wajen bincike a hallarar tsafinsa. A cikin binciken da yayi ya ga wata gagarumar masifa dake shirin afko masa amma sai ya kasa gane irin masifar da kuma lokacin dazata zo masa abin da ya saya kasa barci ke nan ya kwanta kawai yana tunani cikin fargaba. Koda zaihar yaji karar zare wannan takobi sai yayi wuf ya mike daga kan gadonsa yayi sauri yasanya kayan yakinsa sannan ya zare tasa takobin ya fita waje yana neman wanda ya shigo masa gida cikin wannan tsohon dare. Nassey dey Talk Lokacin da jaruma yazila ta shigo cikin wani katon falo na gidan wanda babu komai acikinsa face shimfidar jan kilishi mai taushi da kujeru na alfarma sai tayi kicibus ! Da sarki yaki zaihar tsaye ruke da takobi a wannan lokaci falon a haskake yake dahasken fitilu tazarar dake tsakanin zaihar da yazila bata wuce taku asirin ba. Koda zaihar ya ga ashe yazila ce ta shigo masa gida acikin wannan dare sai ya cika da tsananin mamaki kuma yaji ajikinsa cewa lallai ba lafiya ba akwai wani abin daya faru da dai dai ba saboda haka saiya tsaya a inda yake ya dubeta yace yake halifata mene ne ya kawoki gidana a wannan dare?“ Yazila ta dubi zaihar a fusace tace ,“ nazo na dauki fansar mahaifina dakakashe ne ya kai babban azzalumi !“ Cikin matukar mamaki zaihar ya dakawa yazila tsawa yace ,” wannan kuma wacce irin maganar banza kikeyi ? Shin ke ba yar mai girma barzuk bace ? Yaza ayi kice na kashe mahaifinki alhalin barzuk na nan araye ?”. Dajin haka sai hawaye ya zubowa yazila tace ” Kayi tunani izuwa shekaru goma sha takwas baya lokacin da kabi bayan hukairu dan uwan barzuk sa adda ya gudu tare da iyalinsa izuwa birnin misra daf da kofar birnin misra kuka fafata yaki kai da matarsa humaira tan goye da jaririyarta to ka sani cewa wannan jaririr yar uwata ce mun kasance tagwaye nida ita kuma hukairu ne ya haifemu ita kuwa nuzaira abin data haifa mutuwa yayi sai humaira taba ta daya daga cikin tagyayen data haifa kuma ni ce jaririyar da aka bata kagake nan hukairu shine mahaifina ba barzuk ? Lallai mahaifina ka kashe , babu makawa sai na dauki fansa a kanka kuma a yanzu ”. Nassey dey talk Sa adda yazila tazo nan a zancenta sai sarkin yaki zaihar ya bushe da mahaukaciyar dariya. Ya ce ” yake yarinya karyarki tasha karya. Ba a zama wane a banza. Kafin na sami wannan matsayi na sarkin yakin birnin kisra sai dana taka mukamai masu daraja da yawa kuma sai dana sha bakar wahala. Duk abin da kike takama da shi a yanzu na mallakeshi tun kafin kizo duniya saboda haka yanzu ga fili ga mai doki idan kina ganin zaki iya daukar fansar mahaifinki ki jarraba ki gani ina tabbatar miki da cewa kamar yadda na kashe mahaifinki haka kema zanka sheki !”. Kafin zaihar ya gama wannan jawabi tuni zuciyar yazila ta fara tafarfasa kawai sai ta daga takobinta sama ta ruga gareshi shima sai ya daga tasa sama ya rugo gareta suna haduwa kowanne su ya kaiwa dan uwansa mugun sara kowannensu ya kare saran da takobinsa da takobinsa tara tsatsin wuta ya fantsama izuwa kas. Nan fa suka rugunzume da azababben yaki ya zamana cewa suna kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama juriya da bajinta. Wohoho ! Idan sabon hannu da tsohon hannu akahadu a gumurzu dolene aga tsagwaran jarumta t ban al'ajabi. Ita yazila tana ta kama da kuruciya gami da sadaukan taka ta zamani shikuwa zaihar yana ta kama da kwarewa da sanin makama ne. Da dabarun yaki irin na tsofaffin sadaukai inda aka sami babban bambanci shine, ita yazila tafi zaihar juriya da dadewa ana gumurzu, shi kuma yafi ta zafin nama. Sai da aka shafe rabin sa'a ana wannan gumurzu dayansu bai sami na sarar komai ba, ya zamana cewa dauki ba dadin da sukeyi yasa gaba daya hadiman gidan sun rugo izuwa falon da suke fafatawa a dimauce. Itama matar zaihar saita farka daga bacci a firgice ta ruga izuwa dakin da danta ke barci, wani karamin yaro dan shekara hudu kawai, saita sungumi yaron a kirjinta taruga izuwa falon da ake gumurzu tsakanin yazila da zaihar. Dazuwa sai ta iskesu cikin masifaffen artabu. Gaba daya hadiman gidan sun ra kabe a tsorace suna kallon abin dake faruwa. Nan fa itama matar zaihar ta kasa yin komai saita tsaya ka wai tana kallon fafatawar cikin tsananin tsoro da fargaba da mamaki bisa ganin wacce ke gumurzu da mijinta. Nassey dey talk Saboda zafin naman zaihar sai ya shammaci yazila ya yanketa acinya. Kafin tayi wani yunkuri ya sake yankarta a damtsen hannunta na hagu. Bisa dole yazila tayi alkafira da baya ta koma nesa kadan da shi ta durkushe kasa bisa guiwowinta a lokacin da ta dafe raunikan jikinta biyu cikin jin zugi da radadi. Koda taga jini na zuba saita fusata ainun kuma tayi sauri. Ta daure raunikan da wani tsumma dake daure a kugunta. Ka wai sai ta mike tsaye ta sake zare wata takobin a kuibin cinyarta ta hagu ya zamana cewa ta hada takubba biyu ahannunta. Koda ganin haka sai shima zaihar yaciro wani gatari dake rataye a bayansa ya hada da takobin hannunsa ya fuskanceta. Kawai sai yazila ta rugo gareshi suka sake kacamewa da sabon azababben yaki amma awannan karon sai yazila ta sauya salon fadan ya zamana cewa tana tsalle tana alkafira a kasa da sama. Nan da nan kuwa ta ruda zaihar, bai ankara ba sai yaji ta dankara masa sara acinyarsa. Take wajen ya dare jini yayi tsartuwa. Zaihar ya rankwala uban ihu yatafi da baya taga-taga ya fadi Koda matar zaihar taga abinnda aka yiwa mijinta zaihar sai itama tarusa ihu ta fashe da kuka. Yazila ta kara rugowa da gudu izuwa kan zaihar ta ci gaba da kaimai sara da suka cikin iya zafin namanta bata yarda ta bashi damar da zai daure raunin nasaba. Nan fa jini ya cigaba da zuba daga cinyar zaihar har jiri yafara dibarsa amma saboda naci da juriya irinta 'YAN MAZAN JIYA sai yaci gaba da yakin a haka. Ya yin da zai har ya fuskanci cewa idan akaci gaba da wannan gumurzun a haka har izuwa wani lokaci mai tsawo zai iya gala baita yafadi saka makon jinin dake zuba a kafarsa sabo da haka sai ya fara amfani da karfin sihirinsa yana watsawa yazila mugayen abubuwa kamar; masu, wuta, kibiyoyi da sauransu. Bisa mamaki sai Nassey dey talk yaga tsafin baya tasiri ajikinta, domin karfin sihirin nasu yazo daya duk abin da ya watsa mata sai itama ta watso masa irinsu sulalata juna. Al'amarin daya dugunzuma hankalin zaihar kenan ya tabbatar da cewa bashi da wata mafita face yayi amfani da iyakar karfin dmtsensa da kwarewarsa ta yaki. Bisa dole yakara ZAGE DAMTSE suka cigaba da bakin gumurzun, yazamana cewa sun tashi hankalin komai da kowa dake cikin falon.(Ni ma dakyar na rakabe a ani lungu) Sai da suka shafe sa'a biyu suna wannan gumurzu ya zamana cewa kowannensu yasake samun nasarar yiwa abokin gwaminsa rauni. Zaihar ya sami nasarar saranta a kirji, ita kuma ta sami nasarar sokarsa agefen kirjinsa na dama alokaci guda duk subiyun suka kwala ihu suka ja da baya taga taga kamar zasu fadi amma sai suka sake rugowa suka kacame da a zababben yaki. Hakika idan mutun ya ga irin wannan juriya, naci da jarumta irin ta zaihar da yazila dolene ya jinjina musu ya tabbatar da cewa sun cika zaratan sadauki ababan misali. Bayan sun dada kwarmazuwa bisa hadawa da naushi da bugun juna sai suka jigata ainun ya zamana cewa da kyarma suke kaiwa juna hari. Duk wannan abu dake faruwa matar zaihar na rakabe a gefe daya rungume da danta ta na kallongumurzu cikin tashin hankali kuma tana kuka. A na cikin wannan fafatawar ne duk su biyun sukA yiwa juna wani irin mugun naushi a fuskokinsu har jini yai tsartuwa bakunansu suka zube kasa kafin yazila tamike tsaye sai zaihar yayi sauri ya zaro wata wuka siririya mai kaifi da atsini ya wurgawa yazila wukar ta tafi tsananin gudu zata cake ta cafi wukar ta maida ita inda aka jehota nan take tsinin wukar ya lume acikin goshin zaihar nan take zaihar ya sulale kasa matacce koda ganin abin daya faru sai matar zaihar ta kwala ihu ta rugo kan gawar mijinta ta ajiye danta a gefe daya ta rungume gawar tana kuka sauran hadiman gidan kuwa sai suka firgice suka kama guje guje suna ficewa daga cikin gidan gaba daya jaruma yazila ta taka kafafunta da kyar ta nufi inda matar zaihar take koda ganin haka sai matar zaihar ta dago kai ta dubeta ba tare da tsoron komai ba tace.” Yake dirkar birnin kisra ma zaki kasaro ki kasheni ni da dana domin na huta da wannan abin takaicin da kika bar mini ban ga amfanin rayuwarmu a duniya tun da kin yanke mana farin cikin rabamuda masoyinmu. ”. Yazila tayi shiru bata ce komai ba har ta iso kan gawar zaihar kawai saitasa hannunta ta zare wannan wukar wacce ta lumamai acikin goshin zaihar sannan ta dubi matarsa a lokacin da hawaye ya zubo mata. Tace ina bukatar alokacin wannan wuka domin da sonki san cewa bazan kashe kiba kuma bazawara kamar yadda uwata humaira ta zama bazawara kuma inason wannan da naki ya zama maraya kamar yadda ni da yar uwata muka zama marayu ina son ki isar da sakona ga sarki daksur cewa ni “jaruma yazila ” na kashe sarkin yaki zaihar bisa sanin cewa shi ne ya kashe mahaifina na gaskiya bisa umarninsa don haka ya saurari ranar Nassey dey talk da zanzo daukar fansa a kansa ki sanar dashi cewa na san sirrin layar da suka rataya mini a wuya tun ina jaririya kuma na tafi inda za ayi cire mini layar koda gama wannan furuci sai jaruma yazila ya goge jinin dake jikin wannan wukar daga jikinsa ta daura a kugunta kawai sai ta juya ta fite daga cikin gidana tana tafe tana tangadi ita kuwa matar zaihar sai ta bita da kallo kawai cikin tsananin mamaki bisa jin abubuwa data zaiyano mata a matsayin sako sarki daksur. * * * Al'amarin hadiman gidan zaihar kuwa, dasu da masu gadin gidan Bayan yazila ta sami nasarar kashe maigidansu Sai suka ruga da gudu izuwa gidan sarki daksur suka isar da labarin abinda ya faru ga man yan hadiman gidan. Ai kuwa acikin wannan dare labari ya riski sarki Daksur. Cikin tsananin firgici da dimauta sarki daksur yamike zumbur yayi shigar yaki ya jagoranci dakaru dubu a shirin da kansa acikin dare suka bazama neman jaruma yazila acikin birnin kisra amma sai da suka duba ko ina basu gantaba. Shikuwa hakimi barzuk yajin labarin abin da yafaru sai ya ruga izuwa dakin yazila a fusace rike da takobi. Da shigarsa cikin dakin sai ya iske matarsa nuzaira atsaye rike da wasika tana karantawa tana zubar da hawaye cikin fushi barzuk ya fisge takardar ya karanta jawabin dake cikinta kamar haka. YAke ummata ki gafarceni bisa abinda zan aikata. Kiyi sani cewa bani da wani zabi face na aikata hakan kuma ki gayawa mijinki da sarki daksur abinda ya faru da sarkin yaki zaihar suma yananan tafe garesu nan da wani lokaci a ko yaushe kuma ina gargadinsu akan idan suka taba lafiyarki nima saina taba lafiyar dukkanin danginsu, sai na tabbatar da cewa na share dukkanin zuri'arsu daga doron kasa. Idan har sun matsu. Da son ganina su nemeni acan birnin misra..........." Koda barzuk yazo nan akara tun Nassey dey talk wasikar sai zuciyarsa ta kama ta farfasa kamar zata kone. Saboda tsananin fushi da bakin ciki ka wai sai yasa hannu ya fyade nuzaira ta fadi kasa sumammiya. Nan take ya kwalawa wasu hadi mansa kira yace su dauki nuzaira su kaita can babban kurkuku na kasar suce asamata sarka atsareta har sai ranar daya nemeta. Nan take kuwa wadannan hadiman suka cika wannan umarni. Bayan hadiman sun tafi da nuzaira sai yafita da sauri ya hau dokinsa yatafi gidan sarki da zuwansa kuwa ya iske sarki daksur ya dawo daga neman gimbiya yazila bai gantaba. Yana zaune a fada shi kadai cikin tsananin fushi tamkar zai kona gidan sarauta gaba daya barzuk ya zube kasa gaban sarki daksur ya sunkui da kansa kas cikin tsananin ladabi alokacin da gaba daya jikinsa ke karkarwa don tsoro kada fushin sarki ya kare a kansa Bazato ba tsammani sai barzuk ya bushe da ma haukaci yar dariya. Al'amarin daya matukar bashi mamaki ke nan ya dago kai a tsorace yana kallonsa. Sarki daksur ya turbune fuska sannan yace , "hakika matarka taso ta watsa mana dukkan shirimmu ta tona mana asiri bisa sakacinka na kula da sa ido akanta. Hakika in ba don kayi mata hukunci ba da kanka kasa ankaita kurkuku da tuni kai da ita duk nayi muku hukuncin kisa. Bisa bincike da nayi a halin yanzu na gano cewa tuni jaruma yazila tayi nisa da barin wannan birnin wannan kasa tamu saura tafiyar kwana daya da yini daya jal ! Ta isa kofar birnin misra. Jaruma yazila tana da matukar karfin sihirin tsafi don haka bani da wa dansu hadiman aljanu da zan turasu su hallakata kafin ta isa cikin birnin misra. A cikin binciken da na yi na gano cewa idan ta shiga cikin birnin misra bazata sami nasarar samun abinda taje nemaba. Kuma zata sha tsananin wahala wacce zata iya zama sanadin ajalinta. A kwai wani lokaci da zaizo muyi yakin karshe da sarki raihan na birnin misra a wannan yaki ne zamu sami nasara akansa mukama birnin nasa gaba daya a sannanne zamu shiga har cikin birnin mukama yazila da mahaifiyarta humaira sannan mu binciko duk inda 'yar uwarta take dabira itama mu hallakata. " Sa'adda sarki daksur yazo nan azancenta sai farin ciki ya lullube barzuk bai san sa'adda ya bushe da dariyar murnaba. Nan fa duk su biyun suka ci gaba da kyakyata dariyar kamar bazasu dainaba. A dai-dai lokacinne matar zaihar ta shigo cikin fadar ita kadai rungume da danta tana zubar da hawaye. Batare da fargabar komaiba ta iso har gaban sarki Daksur ta risina ta kwashi gaisuwa sannan ta zaiyana musu sakon da jaruma yazila tabata. Koda matar zaihar ta gama jawabi sai jikin sarki daksur ya kama tsuma. Nan da nan zufa ta karyo masa. Zuciyarsa ta kama bugawa da karfi kamar zata fado kasa cikin tsananin zafin nama ya zare ta kobinsa ya fille kan matar zaihar ta saki dan dake Nassey dey talk hannunta ya cafeshi da hannu daya. Gangar. Jikin matar zaihar ya sulale kasa alokacin da dan nata ya fashe da kuka. Sarki daksur ya yunkura zai sare kan dan sai barzuk yace, "kayi masa rai ya shugabana ai kankanin yarone" ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {2} TYPE C ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: Sarki daksur ya sauke takobinsa kasa sannan ya bushe da dariyar mugunta ya killawa barzuk wannan yaro ya cafe yace dashi katafida shi izuwa gidanka ka raineshi ya taso a cikin bayinka masu yi maka hidima hakika mahaifiyarsa ta cuceshi data sayi ajlinta a lokacin da yafi bukatarta a rayuwa tayi kuskure babba da tazo gabanmu da mugun lafazi domin itace mace ta farko datata ba zuwa gabana ta fadi mugun sako. “ Koda gama wannan ne abin daya faru sarki barzuk ya nufi hanyar fita daga fadar rike da wannan yaro yana ta tsala kuka bai fasaba. “ Wannan shi ne abin daya faru a birnin kisra tsakanin jaruma yazila dasu sarki daksur bayan ta sami labarin asalinta. Acan birnin misra kuwa tun kimanin shekaru sha takwas da suka gabata wato a lokacin da sarkin yaki zaihar ya kashe hukairu a gaban matarsa humaira saita ruga da gudu izuwa kan gawar mijinta a lokacin da masu gadin kofar birnin suka rugo izuwa wajen suka. Kewayeta suna kallonta kawai cikin alamun tausayawa domin sun fahimchi cewa mijinta aka kashe. Kuma ga jaririya a goye a bayanta. Bayan humaira ta dade tana kuka har ta gaji sai wadannan dakaru suka haka kabari suka binne gawar hukairu a gabanta sannan suka shigar da ita mata jagora har izuwa cikin birnin misra daya daga cikin yayi masa bayanin duk abin daya faru ga humaira a gaban idanunsa bayan Nassey dey talk wannan badakare ya gama jawabi sai sarki raihan ya dubi humaira cikin alamun tausayawa yace wannan bakuwa ina mai yi miki marhaba izuwa wannan birnin. Namu mai albarka wato birnin misra kiyi sani ma abota addinin musulunci ne kuma bisa tafarkin addininmu bamu yarda da zalunci ba saboda haka muna son kibamu labarinki iyakar gaskiya bisa abin dake tsakanin da wancan mutumin wanda ya biyoku har izuwa kofar wannan birnin namu ya kashe mijinki kuma igudu idan har kina da gaskiya akansa da iznin ubangiji duak inda ya gudu zamu tura a kamoshi domin ayi masa hukunci dai dai da laifin da ya aikata kafin sannan muna son muji sunanki da kuma sunan garin da kika fito. “ Lokacin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai humaira ta sunkai da kanta kas kamar bazatace komai ba kuma taji tsoro ya shigeta bisa sanin irin tsananin gabar dake tsakanin birnin kisra da birnin misra amma data tuna cewa sarki raihan yace shi mai adalci ne sai taji dukkanin tsoro ya kau daga zuciyarta nan take ta baiyana masa sunanta da kuma kasardata fito. Koda jin haka sai gaba dayan jikin sarki Raihan yakama tsuma, idanuwansa suka kada, zuciyar sa takama tafarfasa kamar zata kone bisa jin sunan kasar mutanen dasuka zamo sana diyar mutuwar 'yar uwarsa guda daya jal a duniya wadda yake matukar kauna fiye da komai a rayuwarsa. Cikin tsananin fushi sarki raihan ya kai hannunsa izuwa kan kuben takobinsa da nufin ya zare takobin ya sare kan humaira amma sai ya kasa kawai sai hawaye ya zubo masa ya kasa yin komai ya kura mata ido kawai. Daga can sai yayi ajiyar numfashi sannan yace, "yake Humaira hakika kinci albarkacin adalci irin na ma'abota addinin musulunci amma da Nassey dey talk tuni yanzu nasare kanki da takobina. Kiyi sani cewa na tsani kasarku, na tsani mutanen kasar ku domin sarkin kasar ku ne ya kashe min 'yar uwata wadda na fiso fiye da komai aduniya a ranar da mukafara yaki. Haka kuma sarkinku ya tsani mutanena ya tsani addininmu. A duk sa'adda wani daga cikin jama'armu yaje kasar ku koda da zummar fatauci ne sai yasa a kamashi ayi masa Kisan gilla. Ki sani cewa mu bazamu kashekiba bisa tarbiyyar addininmu, amma akwai sharadi mai girma a tsakaninmu daku. Ba zamu yarda kuzauna a kasarmuba face kun karbi addininmu idan kina ganin bazaki iya karbar addininmu to kijuya ki tafi izuwa wata kasar daban inda zasu iya karbarki". Ya yin da sarki raihan yazo nan a zancensa sai Humaira ta fa she da kuka sannan tace, "ya kai wannan sarki mai adalci, kayi sani cewa babu wata kasa dazan iya zuwa na tsira daga sharrin sarkinmu da mijin "yar uwata face wannan kasa taka. A iya abin da na fahimta yanzu a zuwana kasarka nagane cewa wannan addinin naku addinine na adalci gami da tausayi da jin kai, domin da farko dakarun da suke gadin kofar birnin sun kamani da karfin tsiya zasu kawoni gabanka amma dasu fahimci halin dana ke ciki suka an kashe min mijina kuma suka ganni da goyon Jaririyata sai suka tausaya min suka tsaya suka binne gawar mijina sannan suka taho dani izuwa nan fadar ka cikin salama ba tare da cin zarafinaba ko su taba lafiyata ba. Kaima da aka kawoka gabana da kaji cewar na fito ne daga birnin kisra sai zuciyarka tayi baki ka harzuka kamar zaka ka sheni amma saboda tausayi da adalci irin naka sai kakasa kasheni. Tabbas iya wannan karamci dana gani daga gareku ya isa na gamsu cewa wannan addinin naku shi ne addinin da yafi cancanta ga bil'adama a doron kasa. Saboda haka ni yanzu a shirye nake dana karbi wannan addini naku mai daraja. " Koda Humaira tazo nan azancenta sai taji gaba daya jama'ar fadar sun rude da Nassey dey talk kabbara kuma kowa ya kamu da tsananin farin ciki. Shikuwa sarki rai han baisan sa'adda fuskarsa ta fadada da murmushi ba. Nan take sarki raihan ya biyawa humaira kalmar shahada ta maimaita sannan ya umarci wani hadimi nasa yace da shi a kai Humaira cikin gidansa na sarauta abude mata dakin matarsa marigayiya kuma a bata sutura da duk abinda take bukata. Nan take kuwa wannan hadimin ya tafi da Humaira izuwa cikin gidan sarki ya cika wannan umarni. Daga wannan rana Humaira ta tsinci kanta a cikin sabuwar rayuwa mai cike da dumbin farinciki da kwanciyar hankali, domin babu abinda tanema tarasa. Haka kuma sarki yasa wata baiwa masanar addinin musulunci ta dinga koya mata yadda ake ibada kuma ta dinga karan tar da ita addinin musulunci. Humaira taci gaba da renun jaririya dabira tataso a cikin son addini kawaici, fasa ha da jarumta. Tsananin kyawun dabira ya dimauta gaba dayan mutanen birnin misra, don haka tun tana da shekara bakwai 'ya'yan sarakai da 'ya'yan attajirai suka rinka zuwa wajen sarki raihan kamun kafa. Shikuwa sai Nassey dey talk yarika gaya musu dabira 'yace ta amana awurinsa don haka ba shi da ikon bayar da ita face ta girma ta zabawa kanta miji. Lokacin da sarki raihan yaga dabira ta taso da.matukar basirar daukan karatu da kuma jarumtaka taban al'ajabi sai ya ji ya kaunaceta ainun tamkar hi ya haifeta. Bisa wannan daliline yasa yazamana cewa kullum sai ya tura a daukota ta yini a wajensa yana koya mata karatu da kansa kuma yana koyamata yaki. Hakane yasa dabira ta shaku ainun da sarki sarki raihan ta dauka azuciyarta cewa shine mahaifinta, don haka tana kiran sane da "abbanta". Ita kanta Humaira bata gayawa dabira gaskiyar al'amari ba domin kada hankalin dabiran ya dugunzuma ta shiga wani hali. Kai a birnin ma gaba daya in banda wadanda suka san taihi zuwan Humaira garin da yawan matasa sun dauka cewa dabira yar sarki raihan ce ta Cikinsa. Wani abin mamaki shine, a tsawon wadanan shekaru har dabira ta cika shekara goma sha takwas sarki raihan da Humaira basu taba zama tare ba tsawon dakika dari da sittin. A koda yaushe duk su biyun suna gudun faruwar hakan domin gudun kada soyayya ta shiga tsakaninsu. A binda basu saniba shine sun makara, domin tun a ranar da sarki raihan ya musuluntadda ita duk su biyun suka ji suna kaunar juna. Shidai sarki raihan tun da matarsa ta mutu a lokacin da tazo haihuwa ya zamana cewa dan cikin nata ma yarasu sai yaji gaba daya baya sha awar yin aure a rayuwarsa domin a ganinsa ba zai taba samun wacce zata maye gurbinta ba. Tun a sannan ne yayi al'kawari a zuciyarsa cewa bazai sake soyayya ba. Ita kuwa humaira a duk sa'adda ta tuno da tsohon mijinta Hukairu sai taga kamar butulci za tayi idan ta sake yin wani auran. Abu na biyu idan ta tuno cewa itafa ba jinin sarauta bace sai taga babu yadda za ayima sarki raihan ya sota har ya aureta. Bisa wannan daliline ta dunga baya-baya da shi ta na tsoron duk wani abu da zai jawo wata hulda a tsakaninsu duk da cewa sautari ta kanji begensa yana darsuwa azuciyarta domin gaba dayan halayensa suna burgeta. Nassey dey talk Al'amarin gimbiya dabira kuwa lokacin da ta shekara goma sha takwas, kyawunta ya kara bayyana karara a fili fiye da ko yaushe kuma ta zama gawur tacciyar mayakiya kuma jaruma wacce babu kamarta akasar gaba daya. Sai sarki yasa aka bata sarautar sarkin yaki. Tun daga wannan rana ne dabira ta samu damar rufe fuskarta da hular karfe, bata cire wannan hula face tana cikin turakarta amma ko acikin gidan sarauta idan zata je wajen mahaifiyarta ko wajen sarki sai tasa hular sai ta shiga wajen nasu sannan take cire hular saboda yawan kallon da mutane suka yi mata yayi yawa bama maza ba, hatta 'yan uwanta mata da zarar sun ganta sai kaga sun kura mata idanu baza su daina kallonta ba face ta kule. Allah yayi dabira da tsananin kyawu na dirin jiki,sannan gashin kanta baki ne sidik ga kyalli da sheki tamkar madubi ya zubo har kasan kwankwasonta. Saboda tsananin kyallin ga shin idan mutum ya tsaya a bayanta sai ya dinga ganin fuskarsa a cikin gashin. Dabira nada dara-daran idanu farare soll masu dauke da digon baki tamkar yankan wuka. Tana da dogon wuya tamkar na barewa. Kalar fatar jikinta kuwa bata kasance fara ba ko ja ba, wani irin launine na musamman wanda ido bazai iya tantance waba saboda tsananin kyau. Kai a ta kaice dai babu wani da namiji da zaiyi arba da jaruma dabira ba tare da ya kamu da tsananin sonta da begen taba. Lokacin da samari masu isa suka yi caa ! A kan neman auren gimbiya Dabira sai ta taka musu birki tace baza tayi aureba har sai ta sami na sarar yaki a kan mutanen birnin kisra, kuma duk saurayin daza ta aura sai ta tabbatar da cewa yafita ilimin addinin muslunci. Al'amarin daya matukar firgita samarin kenan guiwowinsu sukayi sanyi domin sun san cewa Dabira tasa sharadin abin da ba zai taba yiyuwa ba domin a kasar gaba daya ana ganin cewa babu mai irin iliminta. Hatta manyan malaman kasar ma shakkar ta suke domin tun sa'adda tana yarinya 'yar karama ta rinka kure su yayin da a ke musabaka ta karatun Al'qur'ani da fassararsa.Nassey dey talk A bangaren ilimin tauhidi da fighu kuwa' dabira ta na zarcie littattafai da dama. Wasu ma jama'a da yawa basu taba nazarin suba saboda tsananin yawon neman iliminta da bincikenta da kuma baiwarta ta saurin daukar karatu. Duk abin da aka biyawa dabira ko aka gaya mata ta haddace shi kenan har abada tamkar a littafi aka rubuta shi, komai tsaurin karatu da yawansa kuwa. Kai da yawan mutanen kasar misra sun daina kiran ta da dabira sai dai suce da ita "YAR BAIWA" saboda al'amarinta ya wuce yadda kowa ke tsammani.Lokacin da jaruma yazila ta hango kofar birnin kisra daga can nesa, dabara ta fadomata na yadda zata shiga cikin birnin bisa batar da kamanninta koda wannan dabara tazo mata sai ta tsayar da dokinta ta sauka, sannan ta daure dokin agindin wata bishiya. Dama awannan lokaci rana ta kwalle gashi ta gaji ainun kuma guzirinta ya kare har ta fara jin yunwa da kishirwa. Ka wai sai yazila ta shimfida darduma a karkashin wannan bishiya ta kishingida akai tana tunanin yadda zata shiga cikin birnin misra. Tana cikin wannan hali ne kawai sai ta hango an bude kofar birnin, sai ga tawagar wadansu dakaru kimanin su arba'in sun fito bisa dawakai a cikin shigar yaki kuma sun durfafo inda take zaune. Cikin hanzari jaruma yazila Nassey dey talk tayi girgiza, nan take ta rikide ta zama tsohon mafarauci sanye da walki da rigar fata, kuma. A rataye da kwari da baka. A kafarsa yana sanye da ta kalmin fata. A kan dokinsa kuwa tsuntsayene kala-kala kimanin guda bakwai duk matattu alamar cewa harbosu yayi. Nan take dardumar dake shimfide a kasa itama ta rikide ta zama buzu. tsohon yana ki shingida akan buzun yana hutawa A dai-dai wannan lokaci ne wannan lokaci ne wannan tawaga tazo za ta gifta ta gaban mafarauci. Koda ganin wannan mafarauci sai shugaban tawagar yaja linzamin dokinsa ya tsaya a gabansa. Bawani bane shugaban tawagar face jaruma dabira. Tana sanye da kayan yaki, kuma tarufe fuskarta da hular karfe, kofofin idanunta da hancinta da bakinta kadai ake gani. Jaruma dabirA ta dubi wannan tsohon mafarauci sama da kasa tare da karemasa kallo cikin nutsuwa sannan ta daka masa tsawa tace, "yakai wannan tsohon mafarauci wanene kai, kuma daga ina ka fito sannan menene ya kawoka nan kusa da kofar birninmu?".Nassey dey talk Da jin wannan tambaya sai tsoho yakama makyarkyata cikin alamun tsoro yace, 'ki gafarceni yake shugabata sunana kasim kuma ni bakon mafaraucine na fitone daga kasar rum. Na shigo cikin dazuzzukan dake kusa da iyakar kasarku ne da tamu ina farauta sai guzurina da ruwan shana suka kare shina na zonan na zauna ina hutawa idan rana tayi sanyi na shiga kasarku na sayar da 'yan tsuntsayen dana harbo na sami abin da zan sake yin guzurin na koma kasata". Koda jin wannan batu sai jaruma dabira tayi murmushi saboda jin cewa tsohon daga kasar rum yake domin birnin rum ma'abota addinin musuluncine a wannan lokaci, kuma akwai alaka tsakanin mutanen birnin Rum da mutanen birnin Misra. Dabira ta dubi tsuntsayen da tsohon ya harbo wadanda ke kan dokinsa taji sha'awarsu domin babu irinsu a cikin yankin dazuzzukan kasar misra don haka sai ta dubi tsohon ta ce "yakai kasim nayi sha'awar wadannan tsuntsaye naka saboda haka ni zan siyesu nawa ne? Kuma inaso ka raka mu izuwa dajin daka harbo irin wadannan tsuntsaye domin nima na farauto irinsu domin a halin yanzu farautar muka fito. Zan biyaka da lada na musamman idan kayi mana wannan rakiya " Koda jin haka sai farin ciki ya Nassey dey talk lullube tsoho kasim yayi godiya. Nan take jaruma Dabira tasa aka bawa tsoho kasim abinci da ruwa sha ya cika cikinsa ya koshi, sannan ya hau dokinsa ya wuce gaba yayi musu jagora izuwa cikin daji. A wannan lokaci zuciyar tsoho kasim daka take kamar zata tsaga kirjinsa ta fado kasa domin bai san dajin da zai kai su dabira ba su sami irin wadannan tsuntsaye na sihiri da ya samar dasu. ~MEZAI FARU TSAKANIN YAZILA DA DABIRA A CIKIN WANNAN TAFIYA TA SHIGA DAJI DOMIN FARAUTA? ~SHIN JARUMA YAZILA ZATA CIKA BURINTA BISA ABIN DA YA KAWOTA BIRNIN MISRA? ~YAUSHENE DABIRA ZATA GANE CEWA YAZILA 'YAR UWARTACE TA JINI, KUMA IDAN TA GANE HAKAN MAIZAI FARU ? ~SHIN IDAN HUMAIRA TA HADU DA YAZILA ZATA SHAIDATA A MATSAYIN 'YAR CIKINTA KUWA ? ~YAUSHENE ZATA KOMA BIRNIN KISRA KUMA IDAN TA KOMA MAI ZAI FARU? Muhadu a JARUMA YAZILA littafi na uku don jin cigaban wannan kayataccen labari. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {3} TYPE A ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== Lokacin da tsoho kasim yayiwa dabira da dakarunta jagora izuwa cikin daji domin yin farautar irin wadannan tsuntsaye da ya harbo sai ya ci gaba da wucewa kan gaba zuciyar sa nata. Bugawa da karfi domin baisan inda yakamata ya kaisuba har a sami irin wadannan tsuntsaye. Haka dai suka wanzu suna nausawa cikin daji har tsawon sa'a daya da rabi bai tsaya a ko ina ba. Al'amarin daya sa jaruma Dabira ta kosa kenan ta dubi tsoho kasim ta daka masa tsawa tace "ya kai wannan maharbi ina zaka kaimune haka, har yanzu bamu isa dajimba ne?" Koda jin wannan tambayar sai tsoho kasim yaji kamar hantar cikinsa zata fito ta baki. Cikin karkarwar bAki yace, "ya shugabata ai muna dab da shiga dajin da tsuntsayen suke". Koda gama fadin hakan sai ya sunkuyar da kansa kas yana tunanin yadda zaibi ya sulale yagudu ya barsu a dajin tun da asirinsa yana daf da tunuwa. Hakika allah shine mai rufawa bawansa asiri, idan kuwa ya tona masa, tofa koda duniya kaf zata taru babu wanda ya isa ya rufamasa ba. Kwatsam! Bazato ba tsammani sai ga irin wa dannan tsuntsayen sak! Suna shawagi a saman su dabira. Tsuntsayen sun kasance masu yawan gaske tamkar shagalin biki suke, Nassey dey talk Koda ganin tsuntsayen sai dabira da dakarunta suka tsaya cak a waje daya suka dana kwari da baka suka dinga harbo tsuntsayen suna fadowa kasa shima tsoho kasim sai ya faki ido ya watsar da wadannan tsuntsaye guda bakwai na kan dokinsa. Suna zubowa kasa sai suka bace bat cikin hanzari ya harbo wasu guda bakwan ya dora akan dokinsa. Dayake su dabira sun shagala da harbin tsuntsayen basu lura da abinda tsoho kasim yayiba. Bayan an sami nasarar harbo tsuntsayen da yawa sai sauran tsuntsayen suka tsere. Nan take kowa ya debi nashi tsuntsayen ya dora akan dokinsa cikin mutukar farinciki jaruma Dabira ta dubi tsoho kasim tace, "madallah da wannan tsoho mai bayani na gaskiya. Yanzu sai mukoma da baya mukoma birnan mu domin nacika maka alkawarina agareka kuma zanso na baka masauki agidana da kaina domin kayi koda kwana biyune rak a gidana kaga irin yanayin rayuwarmu ta birnin misra". Kodajin wannan batu sai tsoho kasim yayi godiya yana mai nuna matukar farin ciki Nan take jaruma Dabira ta kada linzamin dokinta baya ta wuce kan gaba tana mai jerawa tare da tsoho kasim suka bi hanyar komawa birnin misra sauran tawagar na rufamusu baya Haka dai akaci gaba da tafiyar inda hira karde tsakanin Dabira da tsoho kasim inda taringa tambayarsa tarihin rayuwarsa dakuma irin gwagwar mayar da yasha a rayuwarsa a cikin daji bisa wannan sana'a ta farauta. Koda jin wannan tambaya sai tsoho yai tashara karya kala-kala haryana ta bayani irin gumurzun da yayi da manyan dabbobin daji yana samun nasarar kashesu. Kodajin wadannan labarai sai mamaki yakama jaruma dabira ta dubi tsoho kasim taga babu alamar sadaukan taka atare tashi saita aiyana aranta cewa duk yadda akai wannan tsoho da kuri Nassey ke magana yakeyi kawai donhaka sai tace aranta, "Nikuwa in allah ya yarda sai na kure wannan tsoho na gwada iyakar jarumtakarsa na gani lokacin da yarage saura tafiya kadan a iso kofar birnin misra sai jaruma Dabira ta sake nausawa cikin wani dajin daban al'amarin da ya baiwa kowa mamaki kenan daya daga cikin dakarun dabira yadubeta yace "ranki yadade meyasa kika komar damu cikin daji alhalin gashi farautar tayi kyau munsamo abinda muka fito nema, koma kinsani cewa wannan daji dakika shiga damu dajine mai hadarin gaske wanda ke dauke da mugayen dabbobi?"™Nasiru Muhammad™ Koda jin wannnan tambaya sai dabira tayi murmushi ta dubi mai tambayar tace , tace """ai gani nayi mun fito bamu sha wahalar komai ba mun sami tsun tsaye ai yana da kyau mu dan motsa jini?". Dajin haka sai hankalin sauran dakarun ya dugunzuma domin sunsan halin dabira idan tace tana son motsa jini dai-dai yake data ce tana son tayi yaki. Shikuwa tsoho kasim ko gezau baiyi ba sai kawai yakara kaimi ya wuce kan gaba ma a cikin dajin. Al'amarin daya baiwa kowa mamaki kenan har ita kanta dabira kuwa tce a ranta "yanzu shi wannan bushashshen tsohon gani yake zai iya wani abu kenan ? To ai inda bakasa anan ake gardamar kokawa. Zamuga iya kar koka rinsa Abinda ya kara baiwa su dabira mamaki shine tsoho kasim ya sakarwa dokinsa kaimi ya zabureshi da gudu ba tare da shakkar komaiba Kwatsam! Sai gasu sun iso tsakiyar wani babban fili dazuwa sai suka ga wadansu manyan kuraye ayari guda akan bishiya. Tsoho kasim ne yafara farga da dabbobin don haka sai yaja linzamin dokinsa yayi turjiya ya daga hannu yana mai yiwa su dabira nuni da su tsaya. Nan take kowa yaja tunga ya tsaya. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin kuraye da tsoho kasim Kurayen sun kasance manya-manya masu matukar kwarjini da ban tsoro sai Nassey dey talk gurnnani suke yi suna wangame baki gami da dalalar da yawu kamar suci babu. Kai dagani kasan cewa yunwa sukeji kamar suci babu. Nanfa kuraye suka fara motsa jikinsu alamar cewa akoyaushe zasu iya daka tsalle su fado kan kasim Tsoho kasim ne yafara zare™Nasiru Muhammad™ takobinsa daga cikin kube. Sannan sauran sauran dakarun dabira ma suka zare tasu takobbinsu itakuwa dabira komotsi bata yiba daga kan dokinta sai murmushi take yi kawai tana kallon kasim da dakarunta alamar cewa tayarda da kanta su takeji. Koda kuraye sukaga su tsoho kasim sun zare takubbansu sai suka dako tsalle gaba dayansu alokaci guda asama suka fado kansu aka rugun tsume da a zababben yaki. Sai gashi kuraye sun jeho yaran Dabira daga kan dawakansu su duka kuma suka turmushe su suna kokarin cinyesu. In badamma dakarun sun kasance zakakuran gaskeba da farad daya kura yen zasu gama dasu. Nan fa akacigaba da bakin artabu ya zamana cewa kuraye sunfara yiwa dakarun Dabira rauni suna kartar jikinsu da faratan hannayensu da kafafunsu kuma suna kai musu cizo suna kaucewa da bugun bakunansu da takobi. Al'amarin tsoho kaasim kuwa, abin al'ajabin da yake yine yasa Dabira takasa motsawa daga inda take ta kaiwa dakarunta dauki kawai sai tabude baki tana kallonsa cikin tsananin mamaki. Tunda kurayen suka afkawa su tsoho sai yazama kamar shaidani a tsakiyarsu ya dinga ra gargazarsu da takofinsa yana kaftara musu sara yana tarwa tsasu suna faduwa kasa, amma saboda naci da taurinkai irin na kurayen saikaga suna dada tasowa suna afkawa tsoho kasim duk da cewa jikinsa yai fata fata da jini. Nan dai tsoho kasim shika dai ya zamewa kuraye alakakai alokacin da suka gallabi sauran dakarun Dabira. Yayinda kuraye. Suka ga tsoho kasim yana yi musu muguwar barna sai duk suka bar da karun dabira suka yiwa tsoho kasim rubdugu Nassey dey talk gaba dayansu suka lullubeshi. Da yake sarkin yawa yafi sarkin karfi sai nan da nan kuraye suka fara ruda tsoho kasim saboda suna kai masa muggan hare-hare ta kowane bangare. Inbadan ma yana yana da tsananin zafin namaba da tuni sun ya galgala shi. A nan cikin wannan gumurzu ne wadansu kuraye guda uku masu mugun naci suka shammaceshi suka karci jikinsa da faratan hannayensu lokaci guda.™Nasiru Muhammad™ Daya ta dankara masa sara akirjinsa waje uku, wajen ya dare har jini yai tsartuwa daya a gadon baya taimasa saran iri daya dana kirjin nasa, dayar kuma a cinyarsa, saboda tsananin zafi da zugin da tsoho kasim yajine ya kwala ihu kuma ya fusata ainun kawai sai yadaka wawan tsalle sama na bammamaki sannan ya sallamo kasa kafafunsa na sama kansa na kasa. A haka ya dinga gididdiga kurayen. Duk wadda yayiwa sara daya sai kaga ya fille mata kai ta fadi kasa mutacciya nan fa jinin kurayen ya dinga fantsama har yana bata jikin Dabira. Kafin ta ankara jikinta gaba daya ya rine da jini. Babbar jarumtar da tsoho kasim yayi shine tunda ya fara sare kan kurayen a sama hannunsa ko kafafunsa basu taba kasaba asaman yayi shawagi a kan kurayen tamkar tamkar tsuntsu mai fuka fukai sai da ya gama kashe kurayen gaba daya ya zamana babu guda daya mai rai sannan ne ya duro bisa kasa. A sannan ne dabira ta lura da wadansu tsofaffin manyan raunika a jikin tsoho kasim wadanda tuni sun warke abin da fara fadowa Dabira a rai shine ta yaya wannan tsoho yake irin wannan jarumta irin ta masu jini a jika wato matasa masu karancin shekaru ? Nan take taji cewa lallai akwai a yar tambaya akan tsohon. Abu na biyu wadannan tabon data gani a jikinsa da gani kasan gumurzu yayi da wani gagarumin sadaukin da ya illatashi. Dabira ta kudurce a ranta cewa lallai sai ta tambayi tsoho kasim yadda akayi yasami wadannan raunika. Bayan tsoho kasim ya gama Nassey dey talk kashe kurayen nan sai yaji Dabira tayima tafi gami da jinjina nan take dabira ta sakko daga kan dokinta ta taho izuwa inda tsoho kasim yake. Sai da tazo daf dashi har suna jin numfa shin juna sannan tatsaya cak tadube shi tace "ya kai wannan gwarzon jarumi kasani cewa rabon da naga jarumta irin taka tun sa'adda nayi gumurzun karshe da babbar abokiyar gabata Jaruma Yazila ta birnin kisra".™Nasiru Muhammad™ Koda jin wannan batu sai tsoho kasim yaji zuciyarsa ta buga da karfi ya tsorata ainun domin ya zata Dabira ta gano ko wanene shi. Kawai sai yaji dabira ta kyalkyale da dariya sannan tace, "ka gafarceni yakai wannan jarumin tsoho, ka sani ina sani nace a shigo wannan dajin domin na gwada iyakar jarum takarka bisa labarin daka bamu kan hanyarmu bisa irin gwagwarmayar Da kayi. Tabbas yan zu na yarda kai jarumine a bin kwatance. Amma duk da haka zan sake yimaka wata jarrabawar ta karshe wadda ina ganin asannanne zanga karshen jarumtakar taka. Koda gama fadin han sai jaruma dabira ta bude jakarta ta guzuri ta dauko wani magani ta mikawa kasim tace, "ga wannan sai kasa a cikin raunin naka ". Nan take kasim ya karbi maganin ya shafa a raunikan da kurayen suka jimasa. A sannanne suma dakarun dabira suka yiwa kansu magani bayan kowa ya kimtsa sai aka hau dawakai aka nufi hanyar birnin misra. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {3} TYPE B ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== Humaira na zaune a cikin harabar gidanta tana hutawa wadansu kuyangi hudu sun zagayeta suna tayata hira kawai sai ta hango Dabira da tsoho kasim sun taho gareta, wani bawa na rike da tsuntsayen da suka farauto. Tun daga nesa da Humaira tayi arba da idanun tsoho kasim sai taji zuciyarta tabuga da karfi. Ba komaine ya haddasa hakan ba face jida tayi a jikinta cewar kamar ta taba ganin irin idanunnan arayuwarta amma sai ta kasa tuno a inda ta taba ganinsa. Shima tsoho kasim tun daga nesa ya kurawa Humaira idanu ko kiftawa bayayi. Koda suka iso daf kuwa sai yaji idanunsa sunkico da kwalla suna neman su zubo da hawaye. Babu shiri kasim ya ™Nasiru Muhammad™ sunkui da kansa kas. Nan take Humaira taji kaunar tsoho kasim ta shiga zuciyarta tamkar dama can tadade da sabo dashi. Cikin fara'a Humaira ta dubi dabira tace "yake 'yata wannan kuma wanene haka kika zo mini dashi?" Kafin dabira ta budi baki tace wani abu sai tsoho kasim ya zube kasa gaban humaira yace "Ni bakone daga birnin rum nake wannan matar sarki. Na zo gareku da salama kuma da yardar allah zan Nassey dey talk barku a cikin salama da karamci ina fatan zaku karbi bakun cina na kwanaki kadan cikin jin dadi?" Koda jin haka sai Humaira ta sunkuya. Da sauri ta kama kafadun tsohon kasim ta tashehi tsaye a lokacin da ta sake kura masa idanu tace, "haba ya kai wannan tsoho saboda me zaka durkusa min alhalin ka haifeni a haife?" Koda jin wannan tambaya sai idanun tsoho kasim suka sake cikowa da kwalla ya dubi Humaira yace, "ai duk inda 'ya mace take dole ne namiji ya girmamata tun da kune kuka haifemu. Duk da cewa shekaruna sunfi naki ina ganinki na tuno da ainahin mahaifiyata wadda kaddara taa rabamu". Dajin haka sai hankalin Humaira ya dugunzuma ta kasa sakin kafadun tsoho kasim tace, "wacce kaddara ce ta rabaka da mahaifiyarka?" Sa'adda kasim yaji wannan tambaya sai hawaye ya zubo masa yace, "makiyane suka rabamu tun ina jaririya har yau har gobe bamu sake saduwaba. Babban abikin cikina shine yanzu idan ma haifiyata na nan araye ko mun sadu ba zamu shaida junaba tunda bata sanni ba nima ban santaba". Koda Jin wannan batu sai hawaye ya zubowa Humaira tace, "ya kai wannan tsoho kayi sani jininka jininkane har abada. Ina tabbatar maka dacewa koda mahaifiyarka bata shaida kaba indai kukayi arba da juna saikun ji wani abu ajikinku, tabbas na tausaya maka matuka bisa jin labarinka domin al'amarine mai ban mamaki"". Lokacin da HUmaira tazo nan a jawabinta sai Dabira ta cika da tsananin mamaki domin a iya rayuwarta tare da ™Nasiru Muhammad™ humaira bata taba ganin ta zubar da hawayeba sai yau. Abin daya kara daure mata kai shine Humaira ta sha jin labarai na abubuwan tausayi wadanda ma suka fina tsoho kasim amma bata yi kukaba. Menene dalilin daya sa Humaira tayi kuka a yanzu bisa jin labarin tsoho kasim?" Nassey dey talk Tambayar da Dabira takasa bawa kanta amsa kenan. Nan dai dabira ta baiwa humaira labarin yadda ta hadu da tsoho kasim da duk abubuwan da suka faru a tsakanin su a daji. " Koda jin haka sai humaira ta kamu da tsananin farin ciki ta sake yiwa tsoho kasim barka da zuwa sannan ta umarci wata kuyanga safina ta tafi da tsoho kasim izuwa dakinsa kuma a kai masa ruwan dumi yayi wanka gami da abinci. Nan take kuyanga safina tatafi da tsoho kasim suka nufi bangaren da ake saukar baki. Har suka kuLe tsoho kasim bai daina waigowa ba yana kallon Humaira tamkar baya son rabuwa da ita. Kai kace 'yar uwarsa ce ta jini. Ita kanta Humaira sai taji bata son tsoho kasim yayi nesa da ita amma sai ta rasa dalilin hakan, mussamman a duk sa'adda ta dubi idanunsa wadanda take ganin cewa basu dace da shiba domin idanune irin na matasa masu karancin shekaru dabasu kai ashirin ba shi kuwa gashi ya kasance tsoho dan kimanin shekaru tamanin da doriya. Bayan kulewar kuyanga safina da tsoho kasim sai dabira ta dubi Humaira ta Baiyana mata sakon sarki cewar yana son a dafa masa wannan tsuntsu kuma zai zo da kansa bayan magariba yaci naman tsuntsun a turakarta. Koda jin wannan sako sai Humaira taji zuciyarta ta buga da karfi kuma ta cika da tsananin mamaki domin ita a zatonta sarki bazai taba zuwa kusa da ita ba sai bayan cikar shekaru ashirin da zuwanta birnin misra. Cikin sanyin jiki da yake HUmaira ta dubi Dabira tace, "shi kenan zan cika wannan umarni na abbanki"™Nasiru Muhammad™ Nan take Humaira ta juya ta nufi turakarta itama dabira sai ta nufi tata turakar zuciyarta cike da tunani da wasi-wasi. Abin da yafara fadomata a rai shine wai shin menene ya kawo sauyin al'amura ne a yau tsakanin mahaifiyarta Humaira da abbanta sarki Raihan alhalin hakan bata taba faruwaba ? Anya kuwa sauyin al'amarin ba shi da nasaba da zuwan wannan bakon tsoho? Koma dai menene zan gani da idanuna kuma zan yi aiki da shawarar abbana nasa ido sosai Nassey dey talk akan wannan bakon tsoho don kada ya mamayemu ya cutar damu duk da dai yace shi musulmine, ai dole ne mu tabbatar da musuluncin nasa da kuma amanarsa. Wannan shine abinda ya faru tsakanin jaruma Dabira da iyayenta bayan ta tsinto tsoho kasim a can bayan gari. Al'amarin tsoho kasim kuwa lokacin da aka kaishi masaukinsa aka shigar da. Shi cikin wani daki mai kyau aka kai masa ruwan wanka kewaye kuma aka kawo masa abinci sai ya mike tsam yaje ya rufe kofar dakin yasa sakatu sannan yarufe duk tagogin dakin gaba daya suma ya samusu sakatu. Bayan ya tabbatar da cewa babu ta inda za a iya hangoshi daga waje sai yayi girgiza nan take ya rikide ya dawo izuwa ainahin siffarsa ta gaskiya, wato siffar JARUMA YAZILA. Nan take yazila ta shiga kewaye ta cire tufafin jikinta gaba daya sannan ta shiga cikin baho tayi wanka. Bayan ta fito daga wankane taje gaban madubi ta tsaya tana kallon fuskarta. Koda taga irin kyawun da allah ya bata kuma ta tuna yadda ta sauyawa kanta kamanni ta zama tsoho tukuf ta boye ainahin kamanninta ga mahaifiyarta Humaira sai ta fashe da kuka. ™Nasiru Muhammad™ Dama tun sa'adda yazila ta taho izuwa birnin misra tayi bincike a cikin tsafinta har ta gano cewa lallai mahaifiyarta na nan a raye a cikin gidan sarauta kuma duk wadda tayi mata jagora izuwa wajenta itace 'yar uwarta ta jini wadda aka haifesu tare. Bisa haka ne yazila ta gane cewar lallai Humaira ce mahaifiyarta kuma Dabira ce 'yar uwarta wadda take dokin gani. Yanzu gashi tana son taga fuskar Dabira a matsayin 'yar uwarta ba akan matsayin abokiyar gabarta ba tana son dabira ta gane cewa ita 'yar uwarta ce ta jini. Tayaya zata biya duk wa dannan bukatu a cikin kwanciyar hankali? Sa'adda yazila tazo nan a zancenta sai ta fashe da kukan bakin ciki kuma hankalinta ya dugunzuma ainun domin ta sancewa a koda yaushe a sirinta zai iya tonuwa idan kuwa asirinta ya tonu kafin humaira da dabira su gano cewa ita jinin suce tata takare wata kila ma zata iya rasa rayuwarta a wannan lokaci. Koda yazila ta aiyana haka a cikin zuciyata sai ta sake fashewa da matsanancin kuka. Bayan an yi sallar isha'i sai Humaira ta caba ado sannan ta shirya kasaitaccen abinci akan teburin dake falonta wanda aka yi shi da farfesun irin wannan tsuntsayen da su dabira suka farauto a daji. Lokacin da Humaira ta gama wannan kintsi sai ta sallami dukkan kuyanginta suka fice daga cikin turakarta gaba daya sannan ta zauna tasa wannan abinci agabanta tana kallonsa kawai a lokacin da jikinta ya kama tsuma saboda mamaki da fargabar zuwan sarki Raihan. Nassey dey talk Tana cikin wannan hali ne taji anyi mata sallama. A razane ta amsa sallamar ta dago kai tayi arba da sarki Raihan a tsaye shima ya caba ado na kure a daka fuskarsa Cike da annuri. Nan take kamshin turaren jikinsa ya cika falon gaba daya. Koda ganin sarki Raihan sai Humaira ta mike tsaye zumbur a lokacin da jikinta yaci gaba tsuma, yayinda ™Nasiru Muhammad™sarki raihan yaga Humaira a cikin wannan hali sai shima ya kasa bude baki yace wani abu har ya zo kusa da ita ya tsaya. Tsawon 'yan dakiku suna tsayen dayansu baice uffan ba kuma kowannensu kansa na sunkuye suna kallon kas, sai sarki Raihan yayi gyaran murya sannan yace, "ya ke ummul Dabira shin na iya zama akan wannan kujera?". Koda jin wannan tambaya sai Humaira ta dago kai ta dube shi cikin mamaki gami da murmushi tace, "ya shugabana ai da wannan kujera da kuma wannan dakin duk a karkashin ikonka suke. " Koda jin haka sai sarki raihan yayi 'yar karamar dariya sannan yace, "A'a ina shakka. Na yarda cewa da wannan kujera da wannan daki a karkashin ikona suke amma banda mai dakin. Ya ke Humaira ki tuna cewa tun da kika zo garinnan tsawon shekaru goma sha takwas ban taba umartarki da wani abuba sai yau, kuma yau ne karo na biyu da muka taba kebewa tare. Kin ga kuwa ashe ke ba a karkashina ikona kike ba, kina dai karkashin alfarmata. Na san zaki yi matukar mamaki bisa ganina ayau na kawo miki ziyara har cikin turakarki, kuma bama keba hatta gaba dayan hadiman gidannan suna mamaki don gudun zargin wani abu shi yasa ban rufe kofar wannan daki ba leka bayanki ki gani". Cikin sauri humaira taleka bayan sarki sai ta hango wadansu dakarunsa mutun biyu a tsaye suna hangen duk abin dake faruwa tsakaninta da sarki amma kuma basa iya jiyo abin da suke tattaunawa koda ganin haka sai humaira tayi murmushi sannan tace. ” Haba ya shugaba ai shi kansa shaidan ba a ko ina yake samun nasara ba na yarda da imaninka da tsoron Allah ka don haka ina da yakinin cewa babu wani mugun abu da zai shiga tsakaninmu face alkhairi yanzu sai ka zauna kaci wannan abinci wanda ka umarceni da na dafama maka ”. Koda jin haka sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Na yarda zan zauna naci abinci amma bisa sharadin cewa zaki cire™Nasiru Muhammad™ dukkan tsoron dake ranki ki daina tsuma haka”. Da jin haka sai humaira tayi yar karamar dariya tace. ” Na amince amma ai bai kamata kaga laifina ba domin kwarjininka ne da mamakin wannan ziyara taka ta bazata su suka janyo mini lokaci guda duk su biyun suka yi dariya sannan suka zauna a tare zamansu ke da wuya sai sarki ya bude kwanukan abincin dake gabansa kamshi ya doki hancinsa ya shaki kamshi cikin farin ciki koda ya wanke hannunsa acikin bakinsa ya yanko loma guda ta abinci ya sa acikin bakinsa ya tauna ya tsaya cak ga barin cin abinci ya kurawa kwanon abinci idanu kawai al amarin da ya dugunzuma hankalin humaira ke nan tayi zaton ko abincin ne bai yi dadi ba. Dag cai saita ga hawaye ya zubowa sarki raihan cikin kaduwa humaira ta dubi sarki kuma ta dubi baki da kyar tace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskuren komai ba a cikin wannan girki ?” Koda jin haka sai sarki raihan ya gyada kai sannan yasa daya hannun nasa ya share hawayensa ya dubi humaira yace. ” Yake umma dabira kiyi sani cewa baki yi kuskure komai ba acikin wannan girki kuma tsananin dadin girkin ne yasa na tuno da matata marigyiya da kuma yar uwarta ina so ki sani cewa rabona da cin abinci mai dadi irin wannan tun daga ranar dana rasa wadannan masoya nawa saboda bakin ciki rabuwa dasu. Ina so ki sani cewa idan har ban zo bana baiyana miki wata muhimmiyar magana dake raina tsawon shekaru a yau bato har abada ba zan sami damar hakanba. Yake ummul dabira kiyi sani cewa tundaga ranar da Nassey dey talk mutane suka zo dake tare da jaririyarki dabira naji ina matukar kaunarki a zuciyata, amma sai naji bazan iya furta miki ba saboda tausayinki bisa ganin halin da kike ciki na bakin ciki rashin mijinki wanda aka kashehi a gabanki dakuma yadda kika bani labarinki naji cewar kin rabu da daya 'yar taki wato usainar Dabira wacce kika bayar da ita ga 'yar uwarki Nuzaira. Tun™Nasiru Muhammad™ daga sannan na ji na kamu da tsananin tausayinki da kuma kaunar dabira, shiyasa na rokeki akan cewa komai dadewa kada kisanar da dabira cewa bani ne na haifeta ba har sai bayan shekara ashirin alokacin da zatayi aure murabu da ita an nuna mini a mafarki cewa a gobe-gobennen allah zai kawo wani sadaukin jarumin musulmi daga can nashiya daban wanda yafi Dabira jarumtaka kuma suna haduwa zasu kamu da son junansu akan wannan daliline na yi kundun bala na shirya wannan haduwa tamu domin na bayyana miki sirrin zuciyata. Idan harkin amince da tayina ina son a daura aurena da ke gobe". Koda jin wannan batu sai humaira ta fashe da kukan farin ciki taji kamar ta rungume sarki raihan humaira ta budi baki domin tace wani abu sai kawai suka ga dabira ta fito daga cikin turakar humaira idanunta sun yi sharkaf da hawaye. Cikin firgici da matukar mamaki sarki raihan da humaira suka mike tsaye suka kura mata idanu. Dabira tasa hannu ta share hawayen ta sannan ta dubesu daya bayan daya tace, "me yasa kuka buye mini wannan sirri tsawon shekara da shekaru ? Na rantse da girman allah duk inda 'yar uwata take sai na tafi nemanta! Waye ya kashemini mahaifina? Kuma ko waye ya kashe mahaifina sai na bincikoshi duk inda yake na hallakashi! Ina tabbatar muku da cewa bazan taba yarda nayi aure ba face na cika wadannan burika ". Koda gama fadin haka sai taji ta tsani birnin kisra da duk mutanen cikinsa saboda jin cewa asalin mahaifiyarta humaira daga can take. Nassey dey talk Koda sarki raihan da humaira suka ga dabira ta fashe da kuka sai han kalinsu ya dugunzuma suka yunkura zasu je gareta domin su rarrasheta amma saita ruga waje da gudu ta nufi turakarta. Da zuwa sai ta shiga can cikin dakinta mai kofa ta rufe ta sake fashewa da sabon kuka. Cikin sauri humaira da sarki raihan suka karaso kofar dakin dabira suka yi ta rokonta akan ta bude kofar amma taki, duk suka hakura suka koma turakar Humaira™Nasiru Muhammad™ suka zauna. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★JARUMA YAZILA★*** Littafi Na Daya {3} TYPE C ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: ==================================== Tsawon lokaci duk su biyun sukayi tagumi basu ce komai ba. Daga can sai sarki ya mike tsaye ya dubi Humaira yace, "yanzu muna cikin tashin hankali da damuwa saboda haka sai gobe naji amsar tayin dana yi miki " Koda gama fadin hakan sai sarki yajuya ya fice daga cikin falon gaba daya. I ta kuwa Humaira ta bishi da kallo kawai cikin damuwa da tunani. Har dare ya raba sosai Humaira bata rintsaba saboda fargaba da tunani bisa jin abinda Dabira tafada cewar duk inda 'yar uwarta take saita tafi nemanta kuma sai ta nemi wanda ya kashe mahaifinta. Shima shi. Abinda ya tayar wa da humaira hankali shine, tasan irin bala'in sarki Daksur da sadauki Zaihar da irin sadaukantakar da karfin tsafinsu,don haka yana tsoron karonta da su don tana ganin cewa zasu iya hallaka farat daya muddin ta kai kanta inda suke. Haka dai humaira ta kasance acikin tsananin tashin hankali ta kasa zaune ko tsaye ta dinga kai komo acikin turakarta. Tana cikin wannanhali ne ta tuno da batun tsoho kasim nan take ta aiyana zuwa dakin tsoho kasim ta tasheshi koda kuwa barci yake yi. Batare da bata lokaciba humaira tafito daga cikin turakarta acikin dare da durfafi bangaren da dakin tsoho kasim yake duk inda ta ratsa sai taga dakaru a tsaitsaye suna kan aikinsu na gadi kuma gaba dayan gidan sarautar a haskake yake da fitilu gwanin ban sha awa duk inda tazo giftawa sai dakaru su ratse su bata hanya babu inda aka dakatar da ita har ta iso kofar dakin tsoho kasim. Da zuwanta sai ta iske kofar dakin a kulle take ruf. Haka ma gaba dayan tagogin dakin. Koda ganin haka sai jikin humaira yayi sanyi ta tuna cewa yau fa tsoho kasim acikin matukar gajiya yake sakamakon artabun da yayi™Nasiru Muhammad™ da kurayen nan har maya sami raunika saboda haka bai kamata ta tasheshi daga barci ba nan take humaira ta juya da baya da nufin ta koma turakarta. Amma sai ta jiyo sautin kuka acikin dakin tsoho kasim kuma sautin na muryar mace ne. Al amarin daya matukar bata mamaki ke nan domin ita a saninta ai tsoho kasim ne aciki wannan daki to mene neya shigar da mace cikin dakinsa ? Cikin fargaba da sanda ta Nassey dey talk koma izuwa kofar dakinta leka ta cikin kafar kubar ai kuwa tana lekawa ta hango zabgegiyar kyakkyawar budurwa ta gaban kwatance zaune akan kujera tana faman sharba kuka a gefe daya daya ga wadannan tufafi na tsoho kasim ajiye a gefe daya wadannda akansu an dora layu da guraye na tsafi humaira ta kurawa fuskar budurwa idanu kawai sai ta lura da idanunta taga iri daya ne sak! Dana dabira. Koda ganin wannan al amari sai zuciyar humaira ta buga da karfi ta dafe kirjinta da hannayenta biyu ta juya baya cikin ajiyar numfashi tace a ranta. ” Duk yadda aka yi wannan yata ce ussainar dabira tazo mana a cikin kamannin tsoho kasim mene ya kawota garin nan ? Shin tazo neta cutardamu ko kuwa ta gano cewa mu jininta ne ta zo domin mu sadu ? ” Nan fa humaira ta kasa baiwa kanta amsar wadannan tambayoyi cikin tsananin fargaba da tashin hankali humaira ta koma dabaya don ta koma turakarta. Lokacin da ya rage saaura kiris ! Ta iske kofar turakarta sai kawai taga dabira tsulum ! A gabanta kamar daga sama ake jefota kafin humaira ta budi baki tace wani abu sai dabira ta dubeta tace. Yake ummata menene ya kaiki dakin bakonmu tsoho kasim ? Ki sani cewa nida sarki duk bamu yarda da tsoho kasim Ba kuma na fuskanci cewar akwai wata alaka tsakaninki da shi. Da shi saboda haka gobe kafin na bar garin nan zaki yi mini cikekken bayani akan rayuwarki kafin ki baro birnin kisra ki da dawo nan misra da wannan kalami nake miki sallama allah ya tashe mu lafiya ” koda gama fadin ™Nasiru Muhammad™hakan sai dabira tajuya ta koma izuwa cikin dakinta tamai da kofa ta rufe nan fa humaira ta sake rudewa ta kidime ta rasa abin da ke mata dadi a duniya domin bata san bayanin daya kamata ta yiwa dabira da sarki ba a goben. Da kyar humaira ta koma cikin dakinta ta kwanta taci gaba da tunani da zullumi. Har aka yi assalatu bata sami damar yin barciba. Kamar yadda humaira ta kasa barci hak shima sarki raihan ya kasa barci saboda tsananin damuwa har yaje masallaci da asuba. Ya dawo turakarsa bai rintsaba. Itama dabira bata rintsa ba wato dai duk su ukun basu yi barciba amma wani ikon allah ita jaruma yazila batasan saadda barci yasace taba daf da lokacin daza ayi sallar asuba. Lokacin da aka idar da sallah a masallaci sarki ya waiga ko ina bai ga tsoho kasim ba sai jikinsa ya sake bashi lallai akwai wani boyayyen al amari a kansa don haka sarki na baro masallaci sai ya tura aka kirawo dabira yace da ita ta tafi izuwa dakin bako tsoho kasim ta fada dakin cikin shammace taga a halin da yake ciki domin baizo masallaci sallar asubaba lallai akwai wani abu na shin gaskiya a tare da shi. Domin tun da ya garin babu wanda ya ga yayi sallah koda jin wannan batu sai dabira tatafi izuwa dakin tsoho kasim a fusace wadansu dakarunta guda biyu na biye da ita. Tana sanye da hularta ta karfe. Da zuwan kofar dakin tsoho kasim sai tasa kafarta guda ta daki kofar. Take kofar ta burma ciki ta fadi kasa. Karar dukan kofar na yasa yazila ta farka firgigit! Kafin tayi wani yunkuri sai kawai taga jaruma dabira tare da dakartunta biyu tsaye akanta rike da makamai koda su dabira sukayi arba da yazila sai suka cika da tsananin mamaki. Gashi dai agefe daya kuma suka ga wannan tsufaffun kayan tsoho kasim ga layu da gurayen tsafi akansu sai al'amarin ya daure musu kai. Nan fa Dabira ta kurawa yazila ido tana tunani a zuciyarta. Abinda ya fadomata a rai shine, tasan fuskar yazila tun da sun gwabza yaki ba sau dayaba, amma ™Nasiru Muhammad™bata taba yimata kallon kurilla ba sai yau. Tabbas dai yanzu ta gane cewa abokiyar gabarta ce tayi bad-da-kama ta shigo birninsu domin ta cutar dasu. Amma kuma me yasa a bokiyar gabar tata take kama da ita? Anya kuwa yazila ba ita ce 'yar uwarta ba? Ai waka abakin mai ita tafi dadi,bari naji daga bakinta. Nan take dabira ta dubi yazila tace, "wace ce ke, kuma meyasa kika batar da kamanninki kika shigo birninmu?". Koda jin wannan tambaya sai yazila ta bushe da dariya tace, "Nice jaruma Yazila babbar abokiyar gabarki! Kuma na shigo wannan birnin naku ne domin kawai nayi yakin karshe dake mu bambance tsakanin aya da tsakuwa!!!". Da jinhaka sai itama Dabira ta bushe da dariya sannan ta hade rai tace, "ke tsohuwar abokiyar gaba kiyi sani sani cewa kinka wo kanki GIDAN MUTUWA! Lallai bazamu kashekiba da azaba ko taron dangi ba, lallai nida ke zamu raba raini a yau dinnan. A matsayin ki na mai laifi, dole ne yanzu nasa a kamaki akaiki kurkuku a tsare ki inyaso yau da farkon yamma yammaci afito dake izuwa filin fada inda zamu fafata yakin karshe ni dake inda za arufe mu a cikin keji har sai dayanmu ya wanda duk ya rayu sai ya bude kejin ya fito. " Nassey dey talk Koda gama fadin hakan sai dabira ta dubi dakarunta dake tare da ita tace dasu su sawa Yazila ankwa sannan su tafi da ita kurkuku, Bisa mamaki sai dabira taga yazila ta tsaya kyam! Ansa mata ankwa a hannayenta da kafafunta batare da tayi wani yunkuriba sai murmushi kawai take har aka tusa keyarta a gaba aka tafi da ita. Al'amarin daya matukar jefata cikin tsananin mamaki kenan da wasi-wasi domin a sanin dabira yazila jarumace ta gaske ko ita kanta ™Nasiru Muhammad™ bata isa tasa mata ankwa ba cikin sauki, amma sai gashi dakarunta sunsa mata ankwar sun tafi da ita. Abin dabata saniba shine yazila tana sane ta saki jiki aka kamata saboda dalili uku. Dalili na farko shine tana son su fafata yaki domin dabira ta cire mata wannan laya dake wuyanta dalili na biyu shine tanason takai dabira kas har ta cire wannan hular karfe ta kanta domin taga kamanninta dalili na uku shine bata son dabira tace zata bita sutafi izuwa birnin kisra don daukar fansa akan sarki daksur shiyasa taki gayamata cewa ita yar uwartace ta jini Bayan an tafi da yazila izuwa kurkuku sai dabira ta tattara wadansu layu da guru na tsafi ta kunna musu wuta nan take suka kune kurmus ! Suka zama toka. Har tajuya zata fita daga cikin dakin sai taga jakar guzurin yazila a rataye ajikin bango kai tsaye ta nufi inda jakar take zata dauko ta duba abin dake ciki sai kawai taji an kira sunanta. Tana waigowa sai taga ashe sarki raihan ne a tsaye da kansa. Sarki raihan ya dubeta fuskarsa babu walwala yace " yanzu kin daina fushi damu zaki iya sauraron bayanin dazan yimiki ?” Koda jin haka sai idanun dabira suka ciko da kwalla. Tace. ” Ka gafarceni yakai abbana. Kayi sani cewa nima nayi nadamar nuna muku fishina. Ina fatan zaku gafarceni ? ” Koda jin wannan batu sai sarki raihan yayi murmushi yace. ” Babu komai yake. Yata yanzu dai kizo muje fada akwai wani gagarumin abu daya taso wanda zamu zauna mu tattauna tare da sauran yan majalista hukuncin da kika yanke yanzu akan wannan abokiyar gaba tamu dataso ta yaudaremu yayi kyau ”. Koda jin haka sai dabira ta taho wajen sarki raihan ta ruke hannunsa suka jera suka fice daga cikin dakin ya zamana cewa gaba daya ta manta da batun wannan jaka ta yazila. ™Nasiru Muhammad™ Ita dai wannan jaka babu komai a cikinta face wadansu kayayyakin tarihi wadanda da zarar humaira tayi arba zata shaidasu. Domin kaya nena yar uwarta nuzaira wanda ayanzu haka tana da irinsu aajiye kuma kullum sai ta kallesu don tunowa da yar uwarta ta. Banda wadanda kayan tarihi kuma. Akwai rigarda aka sawa yazila aranda aka haifeta kuma dabira ma tana da irin rigar wacce har yanzu humaira nanan da ita aajiye don tarihi. Dabira ta sha ganin humaira tana dauko rigar tana kallenta kawai har tana kwallah amma duk saadda ta tambayeta dalili sai tace da ita kawai ta tuno wahalar data sha ne a lokacin data sami cikinta saadda ta haifeta. Lokacin da sarki raihan da jaruma dabira suka iso fada sai suka iske gaba dayan yan majalistar a zaune. Suna jiran karasowarsu al amarin daya razana dabira kenan domin ta san cewa duk saadda taga yan majilista sunyi irin wannan taro ya zamana cewa kowa ya zo to lallai akwai wani abu gagarumi al amari daya taso. Ko dai annoba ta barko. Ko kuma yaki zaayi. Da shigowar dabira da sarki cikin fadar sai suka je suka zauna inda suka saba zama. Zaman su keda wuya sai wazirin sarki Raihan yayi kyaran murya sannan yace, "yaku 'yan majalissar wannan birni namu mai albarka, da yawa daga cikinku sun san dalilin taruwarmu anan. Ga wadanda basu saniba, yanzu sai su sani. Wannan al'amari ba komai bane face a yau dinnan kimanin sa'a daya data shude mun sami rahoton cewar abokan gabarmu mutanen birnin kisra sun taho da zugasama da dakaru miliyan dari hudu da hamsin domin su yakemu. Wannan zuga ta hada da dakarun gudummawa daga sauran kasashen kafirai na wannan nashiya, kuma sun taho da alwashin cewa wannan karo adan za a shekara ana wannan yaki bazasu janyeba har sai sun tabbatar da cewa sun baje birnin mu sun kashe mazajenmu sun kama matayenmu da yaranmu a matsayin bayi sun kwashe dukkan dukiyoyinmu. ™Nasiru Muhammad™ Ku sani cewa adadin wadannan dakarun abokan gaba ya ninka namu sau goma, wato gaba dayanmu bamu wuce kaso daya ba a cikin kaso gomansu ba. Yanzu menene abinyi? Tabbas idan muka ce zamu fita mu tari waddannan abokan gaba za su iya murkushemu a cikin dakika kadan. " Sa'adda waziri yazo nan a jawabinsa sai Jaruma Dabira ta mike tsaye zumbur! A fusace, kuma ta zare takobinta a lokacin da jikinta ya kama tsuma. Cikin fushi ta dubi waziri tace, "yakai waziri kayi sani cewa bamu da wani karfi wanda yawuce karfin allah katuna cewa bayau ne karo na farko da muke fita yaki da abokan gaba da kuma ya zamana sun fimu yawa, amma sai kaga mun yi RAGAS dasu kokuma musami nasara akansu. Duk bawan da yayarda da allah kuma ya sallama al'amuransa a gareshi tabbas allah zai iya masa abinda ya gagareshi. Ina tabbatar muku da cewa koda abokan gaba yawansu ya kai cikin duniyar nan gaba daya idan ni kadai ce na rage musulma a wannan birni na rantse da girman Allah sai na fita na yakesu dan kare martabar addinin allah koda kuwa zasuyi gutsin-gutsin da sassan jikina. Na sani nan dagobe wadannan abokan gaba zasu iso kofar birninmu don haka zan jagoranci dakarunmu mufita mu yakesu wanda duk yake ganin zai bi bayana yabi, wanda ba zai bi ba yayi zamansa!". Koda dabira tazonan azancenta sai sarki Raihan ya zare takobinsa yace, "Ina bayanki ya ke 'yata, lallai dani za ayi wannan yaki gobe!".Nassey dey talk Koda ganin haka sai fiye da rabin 'yan majalissar ma suka yi abinda sarki raihan yayi. Kalilanne daga cikinsu basu yi hakan ba, domin sun gama tsorata da wannan yaki daza ayi, kuma imaninsu ya raunata. Wannan shine a binda ya faru a fadar sarki raihan bayan 'yan majalisar kasar sun yi taro na musamman. Al'amarin yazila kuwa, lokacin da aka kaita kurkuku aka kulleta sai taji ko kadan bata damu ba face kawai tana zumudin yamma tayi a fito da ita a kaita filin fada inda zasu yi yakin keji ita da jaruma Dabira. Har rana ta take Yazila ta kasa tsaye ta kasa zaune a cikin kurkukun. A lokacin ne aka kawo ma ta abincin rana. Ko kallon abincin batayi ba bare ma taci. Ai kuwa bayan an idar da sallar la'asar da kimanin rabin sa'a sai aka bude kofar kurkukun aka tasa keyar yazila izuwa fada. Tana tafe tana jan sarkar da aka daure kafafunta da hannayenta, dakaru na biye da ita. Lokacin da aka iso filin fadar da jaruma YAZILA sai taga filin fadar ta cika makil da jama'a fiye da kullum, harma mutane sun rasa inda zasu tsaitsaya sai akan katangau. A tsakiyar fadar kuwa, an ajiye wannan katon kejin karfe mai tsawo da fadi wanda aka yi masa 'yar karamar kofa ta shiga. ™Nasiru Muhammad™ A can gefe daya kuwa, sarki RAIHAN ne da 'yan majalisarsa a zaume kuma daf da shi JARUMA DABIRA ce a tsaye cikin gagarumar shigar yaki fuskarta a rufe cikin hular karfe kamar kullum. Koda aka ga anzo da YAZILA sai aka yi sauri aka bude kofar wannan keji. Cikin hanzari aka kwancewa yazila sarkokin dake hannayenta da kafafunta aka bata takobi sannan aka ingizata izuwa cikin kejin. Nan take Jaruma Dabira ma ta baro inda su sarki suke ta nufi inda kejin yake. Koda ganin haka sai fadar ta rude da kabbara aka rinka yiwa Dabira Jinjina har ta shiga cikin kejin aka rufe kofar kejin. A sannan ne aka yi tsit! A fadar gaba daya tamkar mutuwa ta gifta. Nan fa aka fara kallon-kallo tsakanin jaruma Dabira da Jaruma YAZILA. Jaruma Dabira ta dubi yazila cikin murmushi tace, "yau mun hadu a inda babu damar gudu, kuma babu yankewar yaki face dayanmu ya sami nasara akan daya. Ina so ki sani cewa tuni na kona gaba dayan layoyinki da gurayenki na tsafi yanzu dame kuma za kiyi dogaro?". Koda jin wannan tambaya sai Yazila ta bushe da dariya tace, "ke yarinya, aikin kashe micijine baki sare kansa ba. Kin ga wannan laya dake wuyana wani malami ma'abocin addininku ne ya bani ita bayan an bashi dukiya mai tsananin yawa. Kuma ya tabbatar mini da cewa in dai ina tare da ita babu wani mahaluki daya isa ya sami nasara akaina ".Nassey dey talk Koda jin haka sai Dabira ta fusata ta zare takobinta ta afkawa yazila suka ruguntsume da azababben BAKIN ARTABU wanda ya dugunzuma hankalin kowa a wajen, domin su biyun babu wanda ke da alamun samun nasara akan abokin gwaminsa. ~WAYE ZAI SAMU NASARAR WANNAN GAGARUMAR HADUWA DA AKAI ? ~SHIN DABIRA ZATA CIRE LAYAR WUYAN YAZILA ITAKUMA TA CIRE HULAR KANTA? IDAN SUN SAMI NA SARAR HAKAN ME ZAI FARU ? ~YAUSHE ZA A KWABSA YAKI TSAKANIN RUNDUNAR BIRNIN KISRA DA RUNDUNAR BIRNIN MISRA? ~A WANNE HALI HUMAIRA MAHAIFIYAR DABIRA TAKE CIKI? ~SHIN DABIRA DA YAZILA SUNA GANO CEWA SU 'YAN UWAN JUNANE ? IDAN SUN GANO ZASU JE DAUKAR FANSA ABIRNIN KISRA AKAN SARKI DAKSUR? Muhadu a littafi mai suna BAKIN ARTABU cigaban JARUMA YAZILA don jin cigaban wannan kasaitaccen labari. Alhamdulillah a yau mun kawo karshen littafin JARUMA YAZILA 1-2-3 Sai mu hadu a cigabansa ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★BAKIN ARTABU**cigaban**JARUMA*YAZILA★*** Littafi Na Daya {1} TYPE A ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya fara da cewa: ==================================== Lokacin da aka kacame da azabebban yaki tsakanin jaruma dabira da jaruma yazila acikin keji sai suka wanzu suna masu kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama. Juriya da jarumtaka tamkar jikinsu bana jini da tsokabane. Sai da suka shafe sa a uku cur suna wannan gumurzu amma dayansu bai sami nasarar koda lakuyar jikin abokin gwaminsa ba. ' Yan kallo kuwa da sarki raihan hankalinsu ya dugunzuma ainun bisa ganin yadda ako yaushe yakin nasu dabira kekara tsamari. Tashin hankalinsu sarki raihan shi ne. Idan jaruma yazila ta sami nasarar hallaka dabira sunyi asarar sarkin yakinsu wacce babu kamarta aduk fadin mayakan birnin. Lokacin da sa a uku ta cika sai dabira da yazila suka tsaya da yakin suka jada baya suka yi cirko cirko suna haki da kallon juna kamar zakaru saboda gajiya. A sannan ne dabira ta fara tunanin hanyar dazatabi ta sami nasarar akan yazila amma kuma bisa mamaki sai taji zuciyarta na bugawa da karfi a duk sa adda ta kalli fuskar yazila. Abu na biyu daya fado mata arai shi ne batun wannan laya dake wuyan yazila anya kuwa wannan laya dake wuyan yazila ba ita ce tasa nakasa samun nasara akantaba ? Yazama wajibi agareni na cire wannan laya daga wuyan yazila tunda dai tace daga hannun musulmi take. Koda gama aiyana haka acikin zuciyarta sai tayi jifa da takobinta gefe daya ta dubi yazila tace , ” tunda dai munkasa yiwa junanmu illa da makami saimu gwada yar kashi domin mu kawo karshen wannan gabatamu ”. Koda jin haka sai jaruma yazila ta bushe da dariyar mugunta irinta ma abota shirka sannan ta murkushe fuska kuma itama tayi wurgi da takobin tace. ” Ai dama haka nakeso. Domin ta haka ne kadai zamu iya bambancewa tsakanin aya da tsakuwa ” ™Nasiru Muhammad™ Nan take duk su biyun suka dunkule hannayensu suka gyara tsayawa sannan suka fara zagaya juna. Kwatsam ! Sai suka kacame da azababban fada suka rinka kaiwa juna naushi da bugu. Hannu da kafa. Babu abinda zai baiwa mutane mamaki face yadda suke bugun jikinsu tamkar suna bugun buhun hatsi. Ma ana ko gezau basayi. Sai dai kaga sun shanye dukan sun maida martani. Aikuwa kafin an juma sun hadawa junansu jini da majina. Ana cikin haka ne suka jada baya alokacin guda suka bayar da tazarar taku shida shida sannan suka rugo da gudu kowacce ta daka tsalle sama. Suna haduwa sai kowacce ta gabzawa yar uwar mummunan naushi a kumatu tun a saman feshin jini yai fitsar burgu daga cikin yanayi mai kama da suma Suma. Al amarin daya sa gaba dayan mutanen dake fadar suka mike tsaye zumbur cikin firgici domin a zatonsu jaruman biyu sunyi ragas babu wanda hankalinsa yatafi na kowa dugunzuma face sarki raihan domin yana mikewa tsaye a dimauce bai san sa adda maya ruga da gudu izuwa bakin kejin dasu jaruma dabira keciba. Al amarin humaira kuwa dama bata fito ba zata iya kallon wannan gumurzu da za ayi ba tsakanin yazila da dabira. Lokacin da gari ya waye taji gaba dayan gidan sarautar tayi tsit tamkar babu mai rai acikinsa sai ta gane cewa lallai kowa na can fada ana kallon wannan fada daza ayi. Dama tun a daren jiya tsakanin yarta dabira da tsohuwar abokiyar gabarta tazila wanda tazo musu a siffar tsoho kasim. Bayan humaira ta gama dan kintse kintsenta saita mike tsam ta fito daga cikin turakarta ta kamaa tafiya acikin harabar gidan sarauta inda ta rinka arba da dai daikun dakaru masu tsaro da bayi masu kai kawokai tsaye humaira tawuce izuwa dakin da aka sayki bako ™Nasiru Muhammad™kasim duk inda ta wuce sai aka ga dakaru da bayi suna rissinawa suna gaisheta har ta isa kofar dakin da zuwa ta iske kofar dakin a bude batayi mamaki ganin hakan ba saboda dama tasan yanzu ankama yazila an tafi da ita. Duk da cewa humaira taga fuskar jaruma yazila ajiya da daddare amma har ayanzu zuciyarta na wasi wasi akan anya kuwa yazila yarta ce? Zuciyar humaira na bugawa da karfi ta kunna kai izuwa cikin dakin ai kuwa tana shiga tayi arba da jakar guzurin yazila wacce ke rataye ajikin bango. Kawai sai ta dauko jakar ta sauketa akas ta bude. Nan take idanunta suka yi arba da wadansu surutu wadanda dabira tanada irin su sak. Sannan kuma taga rigar da aka sawa yazila a ranar da aka haifeta wacce dabira ma tanada irinta. Koda ganin wadnnan tufafi sai humaira ta dubesu ta rungumeshi a kirjinta sannan ta fashe da matsanancin kuka domin a yanzu ta tabbata da cewa lallai yazila yarta ce kuma yar uwar dabira. Tana cikin wani hali ne ta tuno da cewa yanzu haka fa yazila da dabira na can fada suna yaki kuma za su iya kashe junansu. A firgice humaira ta mike tsaye ta juya da baya a guje ta rungume da wannan tufafi ta nufi filin fada. * * * Lokacin da yazila da dabira suka baje akas cikin mawuyacin hali. Sarki raihan ya rugo da gudu izuwa bakin kejin yana isowa sai yai turjiya bisa ganin abin daya faru. Bawani abu bane yafaru ba face tashin yazila da dabira atare lokaci guda kamar wadanda suka farfado daga dogon suma. A tare yazila da dabira suka mike tsaye. Kowacce ta sake dunkule hannayenta kuma suka goge jinin dake yoyo abakinsu. Kawai sai yazila ta kurawa hular karfen dake kan dabira idanu. Itakuma ta kurawa layar wuyanta ido take suka sake rugowa da gudu batare da sunyi ™Nasiru Muhammad™ yunkuri daka tsalle samaba. Cikin bakin zafin nama dabira ta kaiwa layar yazila cafka tayi saar damketa kuwa itama yazila saitayi sa'ar damkar hular karfen dabira . Alokaci guda kowacce ta cire abinda ta damka. Wato yazila tasami nasarar cire hular karfen dake kan dabira. Sai ga kyakkyawar fuskarta ta baiyana a fili dogon gashin kanta mai haske da kyalkyali ya zuba har kasan kwankwasonta. Dabira kuwa sai tasami nasarar cire layar dake wuyan yazila tayi wurgi da ita. Atare duk su biyun suka naushi juna da kafa a kirji kowacce tayi baya taga taga kamar zasu fadi kasa. Amma sai suka cije. Adai dai wannan lokaci ne sarki raihan da sauran gaba dayan jama'ar dake fadar suka kame kamar gumaka saboda tsananin mamaki bisa ganin yadda kamannin yazila da dabira suka zo iri daya sak tamkar an tsaga kara yazila da dabira suka kurawa juna idanu kowacce jikinta na tsuma cikin mamaki. Bisa mamaki kuma sai kowacce ta sunkuya ta dauki takobi suka ruga ga juna suna ihu irin na manyan sadaukai domin su sake kaurewa da sabon yaki. Lokaci guda suka sake tsayawa suka waigo baya sakamakon jiyo muryar humaira wacce ta taho da gudu tana daka musu tsawa bisa umarnin su dakata da wannan yaki. Ai kuwa sai suka kame suka kura mata ido. Da isowar humaira sai tayi sauri ta bude kofar kejin dasu yazila ke ciki ta kamo yazila da dabira ta rungumesu atare ta fashe da matsanancin kuka Gaba dayan jama ar dake wajen sai suka rude da kabbara ™Nasiru Muhammad™ Cikin yanayin rashin fahinta dabira ta janye jikinta daga cikin na humaira ta dubeta tace. ” Yake ummina yanzu kina nufin kice yazila ce yar uwatace da nadade ina son na gani ? ” Humaira ta gyada kai tace. ” Kwarai kuma ga cikkakkiyar shaida ”. Nan take humaira ta tunawa dabira wannan riga ta tarihi tace, "kin shaida wannan riga kuwa ? Irin taki ce da kike ta ajiyarta. Ki gafarceni yake 'yata hakiki na boye miki wani babban sirri na dangane da asalinki da kuma tarihin tawa rayuwar. " Koda humaira ta zo nan azancenta sai hawaye ya zubowa dabira ta dubi yazila tace, "ke kuwa me yasa kika boye kamanninki agareni ? Yanzu ashe ke jini nace amma ban saniba, yanzu inda da tsautsayi da shikenan sai dayammu ya kashe daya". Yayinda yazila taji wannan batu sai itama zuciyarta ta karaya, hawaye ya zubo mata. Kawai sai ta bude hannayenta biyu tana mai fuskantar Dabira. Nan take Dabira ta fada kan kirjinta suka rungume juna kuma suka fashe da kuka a lokaci guda suna dada kankame junansu. A wannan lokaci gaba dayan jama'ar dake fadar suka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda Jaruma Dabira ta rungume babbar abokiyar gabarta. Bayan dabira da yazila sun dan jima a rungume da juna kuma fadar tayi tsit kamar babu mai rai acikinta, sai yazila ta janye jikinta daga jikin Dabira ta dubeta cikin murmushi tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa tun daga ranar da nazo garin nan naku naga irin yanayin rayuwarku naga ya banbanta da irin tamu ainun akan adalci,karamci da zaman lafiya, sai naji nakamu da sha'awar wannan addini naku Ina son yanzu take ki shigar dani wannan addininaku. Ina son yanzu take kishigar dani cikin addinin". Koda jin haka sai Dabira ta cika da tsananin farin ciki batare da bata lokaci ba Dabira ta biyawa yazila kalmar shahada ta maimaita. Koda sauran jama'a suka ji YaZILA tayi kalmar SHAHADA, sai suka rude da kabbara. Shi kansa sarki Raihan bai san sa'adda yakama murmushi ba saboda farin ciki. Nan take sarki RAIHAN maya shiga cikin kejin ya kamo hannun DABIRA da YAZILA yajasu suka tafi izuwa cikin gidan sarauta, HUMAIRA nabiye dasu. A sannanne fadar ta watse kowa ya kama gabansa kai tsaye sarki raihan, humaira, yazila da dabira suka wuce har izuwa turakar sarki raihan suka zauna. Zamansu keda wuya sai wadansu likitoci mata guda biyu suka hau duba Yazila da Dabira suka samusu magani a fuskokinsu inda jini yafito. ™Nasiru Muhammad™ Bayan sun kammala aikinsu na likitoci sun fita sai Sarki Raihan ya dubi Yazila da Dabira cikin murmushi yace, "ya ku wadannan zaratan jarumai kusani yau ni da mahaifiyarku muna cikin matukar farin ciki bisa ganin yadda allah ya hadaku har kuka gane juna. Tabbas shigowar yazila izuwa cikin addinin allah cigaba ne babba a garemu. Yanzu dai kafin na yiwa yazila bayanin halin da muke ciki ke humaira sai ki basu tarihin rayuwarki da yadda yazila da Dabira suka rabu tun suna jarirai, har izuwa lokacin da kika gudo izuwa nan kofar birninmu tare da mijinki aka kashe shi a gaban idanunki". Batare da bata lokaciba Humaira ta kwashe dukkan labarinta ta zaiyane wasu yazila. Ai kuwa tana gama bayar da labarin, Yazila da Dabira suka fashe da matsanaicin kuka saboda bakin ciki kuma suka harzuka ainun. Cikin tsananin fusata Yazila ta mike tsaye ta dubi Dabira tace , "yake 'yar uwata kizo mu tafi izuwa birnin kisra yanzu domin mu dauki fansa akan sarkin kisra da sarkin yakinsa. " Koda jin wannan batu sai dabira ta kama kafadun yazila tace, "yake 'yar uwata kiyi sani cewa zuwa da shiri yafi zuwa da wuri. Ina tabbatar miki da cewa ahalin yanzu wadannan abokan gabar tamu ba a zaune suke ba, harma sunyi gagarumin shirin yaki sun taho nan garin domin su baje wannan birnin namu. Labari ya riskemu....." Kafin dabira ta gama fadin abinda ke bakinta sai sarki Raihan ya tari numfashinta yace, "yake Dabira ai wannan jawabi bana bane, nawane". Dabira tayi murmushi tace, "ka gafarceni yakai abbana hakika na wuce gona da iri". Shima sarki Raihan sai yayi murmushi sannan ya dubi yazila yace, "yake 'yar uwar Dabira kiyi sani cewa a halin yanzu a ko yaushe abokan gaba zasu iya baiyana a kofar birninmu kuma labari ya riskemu cewa sun zo da mayaka masu tsananin yawa da ya wuce misali domin har gudummawar mayaka suka samu daga sauran kasashen makwabtaka. Tabbas yanzu bamu da wani zabi wanda yafi mufita mutari abokan gabar nan tun gabannin su iso". Koda sarki raihan yazo nan azancensa sai yazila ta dubi Dabira tace, "yake 'yar uwata kisani cewa nice sarkin yakin birninmu kamar yadda kike sarkin yakin nan birnin, saboda haka nasan dukkan sirrin mayakanmu da irin yanayin yakinsa, lallai zan bayar da gagarumar gudummawa a wannan yaki daza ayi kuma na tabbatar da cewa ba karamar barna zan yiwa su sarki Daksur ba. Babban burina shine, na kashe sarkin yaki da sarki Daksur da hannuna". Koda jin haka sai Dabira tayi murmushi tace, "ni kaina burina kenan domin dole ne mu dauki fansa akansu bisa bakin cikin da suka jefa mahaifiyarmu a ciki. Ya ke 'yar uwata tunda dai yanzu allah yasa kin karbi addinin musulunci na san cewa zuciyarki zata sake kekashewa ga barin tsoro kuma zaki sami kwarin gwuiwa fiye da da can, saboda haka ina ganin idan muka hada karfi da karfe ni dake a wannan yaki zamu iya samun nasara akan abokan gaba ". Kafin yazila ta budi baki tace wani abu sai sarki Raihan ya tari numfashin Dabira yace, "ba haka bane yake 'yata,ke dai kawai munemi taimakon allah, amma ai karfinmu ko dabarar mu baza su sa musami nasara ba akan makiya ba domin na tabbatar da cewa suma baza su fito ba kai tsaye sai da kyakykyawan shiri irin wanda basu taba yin kamar saba. Yanzu abin da nake so dake yake Dabira ki tafi tare da 'yan uwarki yazila ki tara dukkan mayakan kasar nan ku fara shirye shiryen dabaru na yaki wanda yakamata kuyi, nima yanzu zan je na tara dukkan 'yan majalisata domin mutattauna akan wannan yaki, amma dai kusani nine wanda zan jagoranci wannan yaki inyaso kubiyu kurufa min baya idan allah yasa narayu abayan wannan yaki ™Nasiru Muhammad™ kuma nasami nasara za a daura aurena da mahaifiyarku domin mun daidaita junanmu". Sa'adda sarki raihan yazo nan a jawabinsa sai yazila da dabira suka kamu da tsananin farin ciki basu san sa'adda suka rungume sarki ba a tare lokaci guda suka sumbaci goshinsa. Batare da bata lokaci ba Yazila da Dabira suka fice daga cikin dakin da sauri suka nufi wani bangare daban na gidan sarauta inda suka iske wani barde a tsaye cikin shigar yaki. Dabira ta dubi Barden tace, "ma za ka busa kahon tara mayaka domin yanzu nake son mu shirya yadda zamu bullowa wannan yaki". Koda jin haka sai barden yacika Umarni. Ai kuwa nan take dakaru suka dinga tuttudowa daga wajen gidan sarauta suna rugawa izuwa filin fada suna taruwa da jeruwa a sahu-sahu. Wannan shine abin yafaru abirnin misra bayan jaruma yazila taga mahaifiyarta da 'yar uwarta Dabira kuma ta karbi addinin musulunci. *** *** A can birnin kisra, bayan sarkin yaki da sarki Daksur sun yi bincike a cikin halwar tsafi sun ga duk abinda ya faru ga jaruma yazila wadda ta bijire musu kuma tazama babbar abokiyar gabarsu sai hankalinsu ya duguntsuma ainun domin sun tabbatar da cewa aikin dake gabansu ba kadan bane. Bisa wannan dalili ne sarki daksur yasa aka shiga sauran kasashen kafirai dake makwabtaka don neman gudummawar Dakarun yaki. Duk sarkin da wasikar ta iskeshi sai yaba da hadin kai ya aiko da dakarun masu yawa da makamai da kuma isasshen guzuri. A yamma da birnin kisra akwai wata babbar kasa mai suna tashwar. Birnin tashwar na karkashin mulkin wani sadaukin saurayi ne, kyakykyawan gaske mai tarin arziki da karfin mulki. Wani iko na allah shi dai wannan sarki baya tsafi kuma ™Nasiru Muhammad™tsafi baya tasiri akansa. Bisa wannan daliline gaba dayan sarakunan dake mulki a nahiyar suke shakkarsa domin ba a taba kai masa hari ba ko wargi. Shi dai wannan sarki ana kiransa da suna Uhaisu bn kairuf. Sarki uhaisu yana da matukar karfin damtse na allah ya isa, domin komai girman giwa idan yayi mata naushi daya sai ta fadi kasa idan zai jarraba karfinsa ya kansa karti dari su rufar masa shi kadai, sai dai kaga ya bazarda su gaba dayansu sun baje a kasa suna yoyon jini a hanci da baki. Idan kuwa ya naushi mutun iya karfinsa tofa ko kashin karfe gareshi sai ya karye. Sarki uhaisu bashi da wani addini don haka bai matsawa kowa ba a kasarsa duk addinin da mutun yaga dama yana da ikon yinsa. Wannan ya samo asali ne tun daga iyayensa da kakanninsa, haka ya taso ya samesu, basa addini kuma basa hanawa ayi. Akwai wata rana sa'adda mahaifin sarki uhaisu ke kan gangarar mutuwa wato yana kwance acikin jinyar cutar ajali awannan yammaci da suka ka daita su biyu kacal a cikin turakar sarki sai uhaisu ya dubi sarki yayin da hawaye ya zubo masa yace, "ya kai abbana ina son nayi maka wadansu tambayoyi guda biyu wadanda suka dade suna yawo acikin zuciyata" Koda jin wannan batu sai mahaifin nasa ya kamo hannunsa ya dorasu akan kirjinsa kuma ya kura masa idanu alokacin da shima idanunsa suka ciko da kwalla sannan ya budi baki da kyar yace, "ya kai dana na san tambayoyinka dake ranka kuma na dade ina jiran ranar dazaka gabatar dasu agareni. Tabbas yanzu ne lokacin daya dace kayi mini wadannan tambayoyi domin tun kana karami na boye amsarsu, kuma gashi harka girma kakai munzalin dazaka gajeni amma baka san amsar tambayoyin ba wadannan suke faman damunka acikin zuciya. TAMBAYARKA TA FARKO AKAN ADDINI CE. Kana so kasan dalilin dayasa bamu da addini? Tambayarka ta biyu kuwa itace kana so ka san dalilin da yasa naki yin aure, kuma kaima ban taba nuna maka ina da ra'ayin kayi aure ba? Kasaurara da kyau kaji amsar wadannan tambayoyi naka kuma kayi amfani da basirarka wajen amfani dasu domin idan baka nutsuba har abada bazaka sami daraja da daukaka ba irin wadanda na samu a rayuwata. Dalilin dayasa bamu da addini shine, mahaifina kafin yarasu nayi masa irin wannan tambaya, domin yadda ka taso babu addini. Kuma babu aure haka nataso amsar da yabani itace. "Ya kai dana kayi tunani yanzu addinai sun yi yawa a cikin wannan duniya, akwai masu bautar rana, wata, ruwa, wuta, gumaka, dabbobi da sauransu. Kai wasu ma aljanu suke bautawa. Mahaifina yaga yamin cewa addini guda daya ne, kuma ubangiji daya ne wanda shine na gaskiya mai ikon komai da kowa. A wannan zamani babu wannan addini kuma kaima zaka riski wannan addininne a karshen rayuwarka, abu ne mawuyaci kasan wannan addini amma wata kila in ka sami haihuwa danka yasan wannan addini. To ka gaya masa cewa duk ranar da wani gagarumin yaki ya taso ya halarceshi domin a wannan tafarki ne zai san wannan addini na gaskiya har ya fahimceshi kuma ya aminta da shi " Sa'adda mahaifina yazo nan azancensa sai na cika da mamaki na dubeshi nace, "ya kai abbana ashe baka gaya min cewa yaki ba zai taba zuwa birnin tashwar ba? Ya kuma yanzu kake mini batun yaki ?"™Nasiru Muhammad™ Koda jin haka sai mahaifina yaja numfashi tamkar ransa zai fita, a sannan yace, "bana nufin yaki zai zo har nan ya riskeka, ina nufin za'a aikomaka da sakon gayyata. Lallai ka amsa gayyatar, amma kafita yakin kai kadai, kada ka kuskura ta tafi da kowa idan har kana son kasan addinin gaskiya. Dangane da tambaya ta biyu dake ranka kuwa ba wani abubane face batun aure. Tun da mahaifiyarka ta rasu ban sake yunkurin aureba. Haka mahaifina ya kasance, shima mahaifina haka rayuwarrsa ta wanzu har izuwa kan kakanmu na arba'in da daya. Abinda nake nufi anan shine duk wanda yai aure acikinmu haihuwa daya yake samu kuma sai matarsa ta mutu, shima sai yamutu yabar abinda ya haifa. Lokacinda aka haifeka sai naji babu abinda nake so a duniya sama da kai, kuma naji ina son kayi nisan kwana a duniya. A cikin gidan sarautar nan akwai wani daki guda daya wanda ba'a shigarshi kuma kai ma baka taba ganin an shigeshi ba, haka ne?" Kodajin wannan tambaya sai na jinjina kaina nace, tabbas na san da wannan daki kuma na dade ina mamaki da tunani akansa." Mahaifina ya sake ajiyar zuciya yace, "Akwai wani aljani bawanmu a cikin wannan daki wanda bama bauta masa shima kuma baya bauta mana, amma zaman amana ne da kauna tsakanin zuri'armu da tasa. Duk abinda zai samemu a rayuwa shi wannan aljani ne ke sanar damu. =========================================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani ***★BAKIN ARTABU**cigaban**JARUMA*YAZILA★*** Littafi Na Daya {1} TYPE B ***Nasiru**Muhammad**Tijjani*** Marubucin ya cigaba da cewa: =========================================================== A iya tsawon rayuwata ta duniya sau daya na taba. Ganawa da wannan aljani kuma shine ya gaya mini cewa kada na kuskura na kara yin aure a rayuwata. Idan kuwa nayi sai an kawo harin yaki izuwa kasata an kawar dani. Yakai dana kaima kayi amfani da wannan nasiha wacce wannan aljani yayi mini kuma kada ka kuskura ka shiga dakin da wannan aljani yake domin ku gana sai ranar daza ka fita wannan gagarumin yaki da aka gaiyaceka. " Har kullum sarki Uhaisu baya mancewa da wannan jawabi na mahaifinsa don haka sai ya hakura da batun aure gaba daya a rayuwarsa saboda yana son yayi nisan kwana a cikin daular mulki daya tsinci kansa a ciki. A ranar da wasikar gaiyata izuwa yaki ta riski sarki Uhaisu daga birnin kisra sai yacika da tsananin farin ciki domin yasan cewa lokacine yazo da zai cika babban burinsa na duniya domin yasan mahaifinsa ya gaya masa cewa bayan anyi wannan gagarumin yakinne zai iyayin aure har ya sami magaji kuma lallai zai yi tsawon rai a duniya. Lokacin da maga-takarda ya gama karanta wasikar gayyata a fadar sarki Uhaisu fadawansa suka ga ya cika da farin ciki sai mamaki ya kamasu domin su a saninsu babu sarki ya tsana sama da yaki kuma babu abinda yafi so sama da zaman lafiya. ™Nasiru Muhammad™ Sarki Uhaisu ya kasance mutum mai adalci, tausayi da jin kai, gashi da karrama mutane, wato bai iya wulakanci ba bashi da izza da jin kai irin na sarakai, duk da cewa allah ya bashi karfi, kyawu da dukiya mai yawan gaske. Bisa wannan baiwa da allah ya baiwa sarki Uhaisune ya zama cewa 'yan mata, 'ya'yan sarakai, attajirai da manyann matsafa suka kamu da tsananin kaunarsa, wasu da yawansu a dalilin kamuwa da sonsa ne ma suka kamu da cututtuka saboda rashin samun kaunarsa. Wasu ma sanadin ajalinsu kenan. A duk sa'adda sarki uhaisu ya ci ado kuma yayi hawa ya fito daga cikin gidansa sai dai kaga mata suna fitowa da gudu domin kawai su ganshi. Idan dakaru suna hanasu zuwa kusa dashi sai kaga suna kuka kamar wadanda akayiwa mutuwa. Duk wacce ta sami nasarar koda taba dikin sa ma kuwa sai kaga sauran mata na rungumeta don su sami albarkaci. Idan kuwa maca tasami nasarar koda taba hannun sarki Uhaisu ne sai dai kaga ta yanke jiki ta fadi sumammiya saboda tsananin farin ciki. Daga wannan rana kuwa mata sun dinga kai mata ziyara kenan suna bata kyaututtuka ba adadi. Hakika a tarihin nashiyar kasar tashawar ba a taba samun saurayi mai farin jini ba a wajen mata kamar sarki Uhaisu, kuma labarinsa ya bazu ko ina, har zuwa ake yi daga kasashe daban-daban domin kawai aganshi. Tabbas duk mutumin da yake shakka akansa da zarar yazo ya ganshi dole yake gasgatawa. Komai hassadar mutun da kushensa idan yayi arba da sarki Uhaisu take yake sallamawa. Sukansu maroka idan sarki Uhaisu ya fito suka fara yi masa kirari sai masu rasa irin kalmomin dazasu rinka fada wadanda suka dace da shi akwai wani maroki wanda yafi kowa iya kodashi, shine ya kance dashi: Kaico! Ina gwanin wani ganawa? Ga saurayi uban samari tauraron kyawawa mai magance yunwa da kishirwar yan mata. ™Nasiru Muhammad™ Gaka jarumi. Sarki sadauki mai ragargazar maza yau fa ga mai tekun zinare mai shanye kogunan attajirai. Ga ruwan sanyi mai sanyaya zuciya talakawa kufara nan ga bargon kankara mai kashe gobara daga kogi. Marhaban da babbar gona nomanta sai shekara dubu ! Aduk sa adda marokin ya haukace ya kama sambatu saboda sai da dinare ya rufeshi ruf tamkar an nutsar da shi a cikin yashi tun yana kirari. Ya koma yin waka sannan ya fashe da kuka ya dinga mari da cizon kansa har sai da aka tattarashi shi da dukiyar daya samu aka kaisu gidansa lokacin da sarki uhaisu yaga fadawansa sun cikada mamaki bisa ganin yadda ya kamu da farin ciki don jin sakon gaiyata izuwa yaki. Kuma ya fahim cewa hankalinsu ya dugunzuma ainun sai ya dubesu yayi murmushi sannan yace. ” Yaku yan majalista ku kwantar da hankalinku. Ku sani cewa wannan yaki bai shafi kowa ba awannan kasa tawa face nikadai. Don haka nikadai zan shirya na tafi wannan yaki. ” Koda jin wannan batu sai mamaki da fargaba suka dada kama yan majalistar wazirin sarki uhaisu wanda ake mazwan ya dubishi cikin tsananin damuwa yace. ” Haba ya shugaban kasani cewa mu da sauran talakawanka muna. Matukar kaunarka kuma tunda ka hau kan karagar mulki bamu taba rabuwa da kaiba dai-dai da rana daya. Mun tabbatar da cewa idan babu kai babu wanda zai iya yi mana mulki acikin adalci irin naka. Tayaya kake tsammanin zamu iya barinka ka tafi yaki kai kadai ? Katuna fa cewa baka da mai gadonka bare idan muka rasaka musami halifanka?" Lokacin da waziri yazo nan a jawabinsa sai sarki Uhaisu ya mike daga kan karagarsa yayi tafiya izuwa tsakiyar fadar sannan ya tsaya ya dubi jama'a gabas da yamma, kudu da arewa, kawai sai hawaye ya zubomasa ya ce, "ya ku jama'ar birnin tashwar kuyi sani cewa a iya rayuwata ta duniya babu abinda nake kishinsa kuma ™Nasiru Muhammad™ nake matukar kaunarsa sama da birnina da jama'ata. Yau shekara a shirin da takwas a duniya amma ban taba zuwa yakiba. Duk wannan daukaka da ni'ima wacce nake da ita a duniya bata gani ba sai jitake yi kawai. Yau gashi dama tazo wacce za a sanni. Bugu da kari. Ina mai sanar daku cewa wannan yaki da zan fita ne zan cika babban burina na duniya harna sami damar aure na sami wanda zai gajeni yaci gaba da yi muku irin mulkin da nake muku bayan babuni. " Koda sarki UHAISU yazo nan a zancensa sai fadar gaba daya ta rude da shewa, mutane suka cika da farin ciki asannanne sarki Uhaisu ya sallami kowa fadar ta watse nan labari ya bazu ko ina a kasar cewa gobe sarki Uhaisu zai fita yaki shi kadai kuma ga sakamakon da zai biyo baya idan ya fita yakin. Nan fa jama'a suka yi farin ciki da bakin ciki ba face rabuwar daza a yi da sarki izuwa tsawon kwanaki ko watanni ba a san ranar da wowarsa ba. Haka kuma ba a san irin hadarin da sarki zai gamu da shiba akan hanyarsa, babu tabbacin zai iya tsira da rayuwar sa duk da an san irin gagarumar jarumtakarsa amma kuma ai ba a taba ganin kwazonsaba a filin yaki ba. Dayawa daga cikin jama'ar gari kuwa basu yi bacciba a wannan dare, musamman mata. Duk gidan da kaje sai kaga ana koke-koke tamkar mutuwa akayi. Yayin da dare ya raba sai sarki Uhaisu ya shiga cikin wannan daki na musamman wanda tunda aka haifeshi bai taba shiga ba. Kofar dakin a lullube take da yana gaba dayanta alamar cewa an dade ba'a shigaba tsawon shekara da shekaru. Batare da fargabar komai ba sarki Uhaisu yasa kwagirin sarauta ya share wannan yana sannan yasa daya hannun nasa ya murza marikin kofar dakin nan take kofar ta bude ya kunna kai ciki.™Nasiru Muhammad™ Da shigarsa sai ya ga dakin faba daya a haskake yake da wani irin haske na musamman wanda bai taba ganin irin saba kuma yarasa daga ina hasken yafito. Babu komai acikin dakin face wata farar kujerar karfe guda daya jal a ajiye agefe daya. Sai sarki uhairu ya dubi gabas da yamma. Kudu da arewa na dakin. Amma bai gawata halita nai rai acikiba. Kawai saiya ya juya da baya domin ya fiche daga cikin dakin. Har ya iso bakin kofa yasa kafarsa guda a waje sai yaji an kira sunansa da wata murya wacce tabbas ya taba jin muryar amma sai yakasa tuno mai muryar cikin hanzari da mamaki uhairu ya waigo. Kawai sai yayi arba da wani tsohon aljani. Siriri mai dogon fuska gashin kansa da gemunsa fari ne fat kai da gani kasan cewa yadade aduniya. Aljanin na zaune akan wannan farar kujera fuskarsa cike da annuri. Kallo daya mutun zai yiwa aljanin ya tabbata da cewa yana cikin koshin lafiya domin akwai alamun kuzari a tare da shi babu wata nakasa mai nuna alamu tawaya ko gazawa bisa dalilin tsufa. Aljanin ya sake kiran sunansarki uhaisu akaro na biyu yace. ” Haba dan uwana ya zaka juya ka fito ko gaisawa bamu yiba alhalin yau ne ranar farko da zamu fara ganawa ”. Koda jin haka sai sarki uhaisu ya mai dawa aljanin martanin murmushi yataho gareshi cikin sanyin jiki. Da isowar uhaisu daf da aljanin sai ya mike tsaye cikin girmamawa yayi masa nuni da kujerar da yake zaune akai yace dashi ya zauna. Uhaisu ya dubi aljanin cikin mamki yace. ” Saboda meza kace na zauna akan kujerarka wacce kasaba zama a kanta tun kafin a haifi kakan kakana ? ”. Da jin wannan batu sai kwallah ta ciko a idanun aljanin sannan yace. ” Yakai uhaisu ka sani cewa kaine sarki na arba in da biyar daga cikin sarakan da suka yi sarauta a gidannan kuma kowanne sarki yayi zamaninsa tare dani. Amma gaba ™Nasiru Muhammad™dayansu babu wanda ya shigo cikin dakin nan ya mai da mini da martanin murmushi sai kai kadai. Kai ne kadai sarkin daya shi shigo wajena cikin kwanciyar hankali da saukin kai bada jin tsoro ko izza ba. Turbude fuska kamar wanda aka aikawa da sakon mutuwa yace. ” Bani ne zan sanar da kai wanna addini ba kai da kanka zaka ganeshi zuciyarsaka ta gamsu da shi “. Koda gama fadin haka sai aljani aznaihul markas ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa ba a cikin dakin muryarsa na cewa sai mun sake saduwa idan har ka dawo gida a raye cikin nasara. ”Nan take sarki uhaisu ya fice daga cikin dakin ya janyo kofar ya rufeta. Aikuwa yana rufe kofar sai yaga yana ta sake lullubeta tamkar ba a taba bude kofar ba. Nan dai sarki uhaisu ya tafi izuwa turakarsa zuciyasra cike da sake sake da zullumi abinda ya fara yawo a ransa shine. Bayanin karshe da aljani aznaihul markas yayi masa cewa sai sun sake saduwa idan ya dawo a raye kuma cikin nasara. " Shin wannan batu yana nufin kenan babu tabbacin zai tsira da rayuwarsa ? Kuma babu tabbacin zai sami nasara acikin burinsa na duniya?" Nan take hankalin Uhaisu ya dugunzuma. Ya rasa abin da ke masa dadi aduniya, amma da yatuna matsoraci bashi zama gwani, kuma ya tuna shima jarumine sadauki mai tarwatsa maza, sai yaji dukkan tsoro ya kau daga zuciyarsa. Haka dai sarki uhaisu ya isa cikin turakartsa ya kwanta. Kwanciyarsa keda wuya sai barci ya saceshi domin shidai a rayuwarsa bakin ko kishiyarsa, tunani ko ™Nasiru Muhammad™fargaba basu taba hanashi yin barciba domin ya kasance mutum wanda bai taba sa wani abu a ransa ya dame shiba. Kashegari kuwa tun da dukudukun safiya sarki Uhaisu ya tashi ya kintsa aka kawo masa wani farin ingarman doki gami da isasshen guzuri. A wannan lokaci sarki uhaisu yayi gagarumar shigar yaki, kuma yasa hular karfe wacce ta rufe fuskarsa idanunsa kadai ake ake gani. A lokacin ne gaba dayan fadawansa da jama'ar gari suka taru a fadar don yin bankwana da shi. Fadar tacika ta batse babu masakar tsinke duk inda mutun ya duba fuskarsa maza da mata daga masu kwalla sai masu zubar da hawaye saboda alhinin rabuwa da sarkinsu uhaisu. Yayinda sarki uhaisu yaga jama'arsa acikin wannan hali sai ya kamu da tsananin tausayinsu yaji kamar ya fasa yin wannan tafiya amma daya tuna cewa wannan tafiya itace fa cikar burinsa na duniya sai yaji bazai iya fasa taba. Nan take sarki uhaisu ya cire hular karfen kansa sannan ya hau kan mumbari dake tsakiyar fadar ya fuskanci jama-arsa ya shiga jawabi na rarrashi gami da ban baki, kuma yanuna musu mushimmancin wannan tafiya da zai yi cewar a dalilinta ne zai samu tsawon rai kuma birninsa zai samu daukaka irin wacce bai taba samuba. Duk da jin wannan bushara sai jama'a suka ji sudai basa son su rabu da sarki Uhaisu domin ji suke kamar zasu rabu da hanyar kirjinsu. Lokacin da sarki Uhaisu ya gama jawabinsa ya sauko daga kan mumbari ya hau kan dokinsa ya sanya wannan hular karfe. Koda ya kada linzamin dokinsa ya nufi kofar fita daga fadar sai jama'a suka rude da ihu, kuka da dimauta mata kuwa da yawansu yanke jiki suka rinka yi suna faduwa kasa sumammu saboda bakin cikin rabuwa da masoyinsu wanda suka dade suna begensa a cikin zuciyarsu. Hakika sarki uhaisu ya cika tauraron samari, maganin ™Nasiru Muhammad™ yunwa da kishirruwar 'yam mata, domin babu wata 'ya mace a cikin birninsa wadda bata kamu da sonsaba face matan aure da tsofaffi. Kai wadansu matan auren ma idan sarki Uhaisu zai auresu zasu iya kashe aurensu haka dai sarki Uhaisu yacigaba da tafiya babu waiwaye, kuma babu sassauci har ya fice gaba daya daga cikin birninsa. Sai da ya kwana ashirin ba daya yana keta dazuzzuka da birane sannan ya isa birnin kisra. Kafin ya iso birnin kisra yayi arangama da 'yan fashi iri-iri da kuma muggan dabbobin daji amma komai yawansu da karfinsu sai ya ga ya tarwatsasu ya kashe na kashewa, masu nisan kwana kuwa saidai su gudu. Shikansa sarki Uhaisu yayi matukar mamaki bisa ganin irin jarumtakarsa domin bai taba tsintar kansa a cikin irin wannan haliba na yaki a daji da mutane da yawa ko dabbobi. Lokacin da sarki uhaisu ya iso fadar sarki Daksur sai ya iske fadar a cike makil da manyan baki da sarakai wadanda ke zaune a can saman fadar kusa da karagar sarki Daksur. A kasa kuwa, sauran dakarun yakine masu yawan gaske wadanda suka rako sarakuna don zuwa wannan gagarumin yaki wanda za a yi abirnin Misra. A wannan lokaci fadar tsit, sarki daksur ne kadai yake bayani ana sauraron muryarsa, kwazam! Sai akaga mutun yashigo fadar bisa kan doki sanye da kayan yaki ya rufe fuskarsa da hular karfe. Karar kofatun dokin nasa ne tasa sarki Daksur yayi shiru kuma kowa yajuyo yana kallonsa. Mahayin yaci gaba da tafiya kai tsaye ya durfafi inda karagar sarki take batare daya tsaya ya gabatar da kansa ba. Koda ganin haka sai dakaru sama da dubu suka yunkura zasu afka masa. Cikin hanzari sarki Daksur ya daka musu tsawa suka tsaya cak! Shima mahayin dokin sai yaja linzamin dokin nasa ya tsaya a waje guda. Sarki daksur ya mike tsaye ya tako da kafarsa, yazo har gaban mahayin sannan ya risina a gareshi yace, "lale marhaban da sadaukin sadaukai, kuma sarkin sarakuna na wannan nashiya tamu, mai birnin tashwar wato sarki Uhaisu bin kairuf". Koda akaji sarki Daksur ya ambaci wannan suna sai idanun kowa ya zazzaro aka cika da tsananin mamaki bisa ganin yadda sarki Uhaisu ya iso fadar shi kadai batare da dakarunsa sun rako shiba, sannan kuma sai kowa ya zuba ido domin yaga fuskarsa domin da yawan jama'a basu taba ganinsaba labarinsa kawai suke ji. Abinda yakara baiwa mutane mamaki shine, yaya aka yi sarki daksur ya gane cewa sarki uhaisune wannan har ya taso ya taryeshi alhalin ba a gabatar da zuwansaba. Abinda suika manta shine, sarki daksur babban ™Nasiru Muhammad™matsafine. Nan take sarki uhaisu ya sauko daga kan dokinsa sai sarki daksur ya rungumeshi cikin tsananin farinciki tamkar wanda yaga dan uwansa na jini. Batare da sarki Uhaisu ya cire hular karfen dake kansa ba sai sarki daksur ya jashi suka tafi izuwa har can inda karagarsa ta mulki take take suka zauna akan karagar mulkin su biyu. Abinda ya daurewa kowa kai kenan, domin babu wani mahaluki wanda sarki Daksur ya taba girmamawa haka ya darajashi sai sarki UHAISU. Nan take aka kawowa sarki uhaisu abinci da abin sha iri-iri mai daraja irin na sarakai na alfarma wanda babu kamarsa a wajen sarki uhaisu ya saki jikinsa yaci abinci sosai har sai da yaji ya koshi sannan ya dubi sarki Daksur yace, "a kaini masaukina ina da bukatar na kwanta na huta domin na huce gajiyar tafiyar da na sha ". Batarte da gardamar komai ba kuwa sarki daksur ya kira wani Hadimi yace da shi ya kai sarki uhaisu izuwa masaukinsa, wani wuri wanda shine mafi kyau da tsaruwa a gaba daya gidan sarautar. Nan take kuwa aka tafi da sarki Uhaisu, A she gaba dayan sarakan dake zaune a cikin fadar ransu ya baci bisa ganin yadda sarki daksur ya tarbi sarki Uhaisu cikin karramawa da girmamawa fiye da yadda aka tarbi kowannesu. Bayan bacewar sarki uhaisu da hadimin da ya tafi kaishi masaukinsa sai wani sarki mai ji da kansa wanda ya kasance babban abokin sarki daksur wanda ake kira ma aruf bn saurud ya dubi sarki daksur yace "haba abokina ka tuna fa cewa yau kwanamu arba'in anan muna taruwa kullum muna tattaunawa da shiryawa akan yadda zamu bullowa wannan yaki. Yanzu ne muka yanke shawarar mu tafi izuwa yakin amma sai gashi mutum daya yazo ya tsaida komai. Yanzu shikenan sai dai mujira har sai sa'adda yayi barci ya tashi sannan zamu tafi?" Lokacin da sauran sarakai suka ji wannan batu sai duk ™Nasiru Muhammad™ suka goyi bayan sarki ma'aruf, fadar ta rude da hayaniya. Shi kuwa sarki Daksur sai ya kama murmushi. Daga can sai ya daga hannu sama akayi tsit sannan yai kyaran murya yace, 'yan uwana ina so ku sani cewa sarki Uhaisu ne zai jagoranci wannan yaki da zamu je kuma dukkan nasararmu na tare da shi, idan muka kuskura muka tafi yakin babu shi tabbas baza sami nasaraba ". Koda jin wannan batu sai mamaki ya turnuke gaba dayan jama'ar dake cikin fadar sarkin yaki ya dubi satki daksur cikin biyayya yace, "haba ya shugabana, yanzu duk yawannan namu amma ka ce ba zamu sami nasara ba face Uhaisu ya jagorancemu? Kai da bakinka kace damu yawanmu ya ninka na abokan gaba sau dari ba. Ai kuwa ina ganin cewa koda Uhaisu ko babu shi dole ne mu sami nasara a wannan yaki. " Sa'adda sarki daksur yaji wannan batu sai ya mike tsaye ya dubi kowa dake cikin fadar, sannan yayi ajiyar zuciya yace, "yaku 'yan uwa ina so kusani cewa ni nasan abinda babu wanda ya sanshi a cikinku nan gaba daya A halin yanzu sarkin yakimmu ta da, wato JARUMA YAZILA tana can birnin misra kuma ta karbi addininsu, don haka ita da 'yar uwarta JARUMA DABIRA zasu hada KARFI DA KARFE su yakemu. Tabbbas su biyu kacal sun isa su iya yi mana mummunat barna a wannan yakin, domin a duk fadin wannan nashiya babu wani sadauki ko mayaki wanda wanda ya isa ya taresu face sarki Uhaisu. Ina tabbatar muku da cewa ahalin yanzu babu wani sadauki mai karfin damtse irin na Uhaisu a duk fadin duniyarnan kuma shine mutumin da baya tsafi, kuma tsafi baya tasiri a kansa domin ku gasgata zancena yanzun nan zan nuna muku ku gani da idanunku ". Koda gama fadin haka sai sarki Daksur yayi nuni da hannunsa izuwa ga saman bangon fadar saiga hoton irin gwagwarmayar da sarki Uhaisu yayi da 'yan fashi da masu yawan gaske wadanda adadinsu ya kai dubu ™Nasiru Muhammad™ ashirin da doriya sun yiwa sarki uhaisu kawanya 'yan fashin sun kasance gabza-gabza masu kirar mutanen farko kuma kowannensu na dauke da muggan makamia lokaci guda suka yiwa sarki uhaisu rubdugu shi kuwa sai ya wanzu yana mai gididdigasu cikin tsananin zafin nama irin wanda ido bai taba ganiba. Cikin sa'a daya jal ya ragargazasu duka dayansu bai tsira da rayuwarsa ba, sai gashi filin dajin gaba daya ya cika da gawarwakin 'yan fashin, duk inda mutum ya duba sai dai yaga jini na malala da kwaranya tamkar ruwan sama akeyi. Babban abinda ya baiwa kowa mamaki shine ganin sarki uhaisu a tsaye bisa dokinsa cikin koshin lafiya babu inda jikinsa ya sami rauni koda kwarzanewa kuwa, kai ba ma shiba, hatta dokinsa ma babu abinda ya taba lafiyarsa. Bayan wannan gwagwarmaya sai kuma aka ga wani azababben yaki da sarki uhaisu yayi da wadansu dodanni wadanda yawansu ya wuce misali domin ninka na wadannan 'yan fashi sau biyar. Sai da sarki Uhaisu ya shafe kwana guda da yini daya yana yaki da dodannin bai gajiba kuma bai guduba sai ragargazarsu kawai yake yi, suna zubewa kasa matattu. Yawan dodannin sai ya zama na banza ya yin da bala'I yakai bala'I da kansu suka rinka guduwa suna neman maboya. Nan take sarki daksur ya sake nuni da hannunsa izuwa ga bangon fadar hoton komai ya bace. A sannan ne gaba dayan jama'ar dake fadar suka yi ajiyar zuciya a lokaci guda saboda tsananin mamakin ganin irin wannan a zababbiyar jarumtaka ta sarki Uhaisu wacce ko a tarihi basu taba jin taba kuma gashi jarumtaka ce ta zahiri wacce babu sihiri ko tsafi acikinta. Nan take kowa ya sallama ya gamsu cewa lallai sarki uhaisu nezai jagoranci wannan gagarumin yaki da za a tafi izuwa birnin misra. Sai da rana ta fadi sannan sarki uhaisu ya farka daga barci domin huce gajiyar shi. A sannan ne kuyangi suka ™Nasiru Muhammad™ kai shi kewaye suka yi masa wanka a cikin bahon zinare mai cike da ruwan kamshi na turaren miski da furanni iri-iri. Bayan angama yimasa wanka an shafeshi da mai sai aka kawo masa kayan yakinsa ya sake sanya su ya mayar da hular karfensa yasa a kansa sannan ya taho fada yana zuwa cikin fada sai kowa ya mike tsaye don girmamawa, hatta sarki daksur kuwa. Maimakon sarki uhaisu yaje ya zauna sai dubi sarki Daksur yace, "a kawo mini dokina yanzu zamu kama hanya mu durfafi Birnin MISRA. Batare da gardamar komai ba kuwa sarki Daksur yasa aka kawowa sarki Uhaisu dokinsa ya hau kawai sai ya kada linzamin dokinsa ya juya da baya ya fice daga cikin fadar. Cikin hanzari sarki Daksur ya bayar da umarni ga dukkan sauran mayaka da a fita ayi hawa abi bayan sarki Uhaisu. Nan da nan kuwa aka bi wannan umarni. Kaico! Tashin han kali ba a samasa rana. Inda ace mutun yana wannan wuri idan yaga irin tsananin yawan wadannan mayaka da kuma irin maggan makaman da suka debo dole ne ya firgita domin gani zaiyi kamar zasu iya tashin duniya gaba dayanta a cikin rabin sa'a. Gaba dayan mayakan da suka fito wannan yakin babu abinda suke son gani face fuskar sarki Uhaisu da kuma irin kirar jikinsa amma sai gashi har yanzu bai cire hular karfen dake kansaba kuma bai kwabe kayan yakin da suka rufe jikinsa ba su kansu kuyangin nan da suka yi masa wanka dukkansu dimaucewa sukai suka fita haiyacinsu saboda ganin irin tsananin kyawun surar da allah ya baiwa sarki Uhaisu. MENENE ZAI FARU A WANNAN GAGARUMiN YAKI DA ZA A YI A BIRNI MISRA? WACE CE MATAR DA SARKI UHAISU ZAI AURA? Mu hadu a BAKIN ARTABU na biyu domin jin cigaban wannan kasaitaccen labari. ==================================== Anan zamu dakata Amma Kafinnan nine Nasiru Muhammad Tijjani nake cewa ku kasance tare dani