💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 Story & written By Mss Lee 💖 07041879581 BOOK 2 NOT EDITED Page 1 UNITED KINGDOM OXFORD A guje wata matashiyar budurwa tashigo cikin wani babban falo me shegen kyau, tana faman ‘kwalla kiran “momy ,momy”, shiru ba a amsaba, wata ‘kofa ta nufa bayan ta ajje wata hand bag d’inta meshegen kyau,”Momy,Momy” ta ‘karan ta fad’a da ‘karfi, wata babbar matace da taji wanka material peach colour me shegen kyau, kyakkyawar budurwar data ke faman ‘kwalla mata kira ta kallah, cikin hausarta da har yanxu bata gama zama a bakinta ba ta furta “ Mimi, Yaushe zakiyi hankaline , bana hanaki wannan guje guje ba?”, a shagwa’be wacce a kira da Mimi ta ‘karaso zata rungume ta , Momy tayi saurin ja baya “ wallahi Mimi ki fita a idona , kinsan halina sarai “, tsayawa Mimin tayi kamar zata sa kuka “ Haba Momy na, kwanana biyu ban ganki ba amma da Alama ke ko missing d’ina bakiyi ba ,” ta’be baki momyn tayi , “ Allah ya shiryamunke “ dariya mimin ta saki tana cewa “Amin” kafun ta ‘kara da “ Momy albishirinki”, murmushi momyn ta saki kafun ta ce mata goro” momy gobe bro zai dawo, already nayi missing d’insa sosai wallahi kamar nayi shekara ban gansaba”,murmushi momy ya saki “ ya fad’a miki kenan, ai kwanda yazo yayi mun maganinki, duk kinbi kin dami kowa ,” kamar wata yarinya fa fara dure ‘kafarta “ Haba momy , gskiya dady ya fi sona , dole na kira sa ma nace ya dawo kafin bro ya dawo ku had’e kanku”, tana karasa kalamanta ta d’auki handbag d’inta tayi sama dagudu, girgiza kai momy tayi kafin a fili ta furta “ Allah ya shiryeki Mimi bansan lokacin da zakiyi hankali ba , har ynxu bakisan kin girma ba”, . Asama kuwa wani d’aki mimi ta shiga me girman gaske , komai na cikin d’akin pink colour ne , jakar hannunta ta yar a ‘kasa bayan ta d’akko kantamemiyar wayarta , number MY BRO 💖da tayi saving da heart tayi dialling, ringing biyu aka d’aga wayar, tun kafin na cikin wayar yayi magana cikin d’aga murya Mimi ta furta “ Bro d’ina nayi missing d’inka and karka manta mun da tsarabata” cikin kamilalliyar murya Wanda ya d’aga kiran yayi sallama batare da ya amsa mata maganganunta ba ,saurin toshe baki Mimi tayi cikin ‘yar dariya ta furta “ Sorry yayana, am really sorry Wa’alaykumussalm “, shiru kawai yayi Mata batare da yace mata komai ba , kamar zatayi kuka ta furta “ Haba mana Yaya nace maka fa am sorry , kayi hakuri kajiiiii , nayi missing d’inka”,a jiyar zuciya ya d’an sauke “Mimi ba kyajii ko, kina so my ‘bata ?”, girgiza masa kai tayi har hawaye ya fara sakko mata a fuska “ kayi hakuri yaya , na rage rashin ji fa,” yanxu ina aiki, okay bye “, ya fad’a tare da hanging kiran, bin wayar tayi da kallo kafun ta rungume wani babban teddy dake kan gadanta shima pink colour , number wata number da tayi saving da dady tayi dialing amma har kusan 2 missed calls ne d’auka ba , ganin be d’aga bane yasa ta saka music tare da ‘Kure karfin Ac d’in dakin. ✨✨✨✨✨✨✨ NIGERIA LAGOS Gabaki d’aya hankalin kowa a tashe yake musamman neman Tahee da akai aka rasa , a d’aya ‘bangaran king ma haryanxu yana cikin COMA d’in da ya fad’a gabaki d’aya Abeey ya raba hankulansa waje daban daban, ga tashin hankalin da Ammey suka shiga na rashin lapiyar king ,ga ‘batan Tahee itama, a wannan karan gabaki d’aya ummey ta cire kawaicinta Sabida ta na tsoran rasa king kamar yadda yadda ta rasa akhiee d’inta, Ammey ma gabaki d’aya abincin ma bata ci dataga wani ya zo kusa da ita zata soma kiran sunan Tahee , Dada gabaki d’aya ta tarar da hankalinta, gefe d’aya ga fargabar farkawar king da akace zai iya farkawa ako Wana lokaci, gabaki d’aya abeey yashiga damuwa. Gabaki d’aya anzuba matakan tsaro akan binciken inda Tahee take, hatta sojojin da suke guarding d’in gidan saida zaki ya kamasu gabaki d’ayansu sai angama bincike,kaf cikin familyn NAHYAN babu Wanda be shiga tashin hankali ba , hatta Amrah da Basma da sukaji labarin Accident d’in king kamar wasu zautattu haka suka koma , acikin su babu Wanda ya damu da Tahee gabaki d’aya ita da amrah hankalinsu na kan king. Ganin dare ya farayi ne Doctor yasa doctor Arween da tun d’azu yake zaryar duba king ya kebance da Abi duk da Abeey Yasa an boye zancan gudun kar wani ya kara kai masa hari, cikin wani d’aki ne shegen tsaro a ka kai king da ko hannunka ka d’aga akwia masu kallanka ta camera. Cikin girmamawa Doctor Armeeen ya sanar wa Abeey mutum d’aya ake bukata da zai kula da king tunga zama da king tunda har yanxu yana cikin coma , lokacin da Abeey ya sanar da su Ammey cikin zuciyar ta wani d’an iskan dariyar mugunta ta saki kafin ta furta damata tazo, cikin sha’kewar murya kamar mara lafiya Ammeey ta bud’e baki daniyar magana ummey ta rigaka, sosai kallar ummey ta Dakar mata zuciya , ‘kara maimaita maganar ta ummey tayi “ ZAN ZAUNA DASHI”, da mamaki Ammey ta kalli ummey da gabaki d’aya hankalinta baya kanta , murmushi Abeey ya saki dan yaji dad’in maganar ummey batare da ya ja zancen ba ya kalli Dada cikin girmamawa , itama Dadan cewa tayi zata zauna a asibitin , duk yadda Su Abeey sukai da ita akan ta koma tace ba inda zata hakan da tayi kuwa ba ‘karamin ‘kara ba’kanta ran Ameen yayi ba ,’ko’karin danne fushinta kawai take . Gabaki d’aya Abeey ya bada umarnin akoma gida bayan uban tsaran da aka kuma sawa a asibitin, duk da babu Wanda yasan abunda ya faru a asibitin sai manyan likitoci gabaki d’aya asibitin a nutse take musamman ko ina mutum ya juya zai ga soja har tsoran kuskure suke. WASHE GARI Gabaki d’aya kusan yan gidan gabaki d’aya basu runtsaba ,ana idar da sallahr asuba su Abeey suka nufi hospital shi dasu uncle saleem,har lokacin kuma babu labarin inda Tahee take , su uncle saleem sai faman tausar Abeey suke ganin yadda ya shiga damuwa suma a nasu ‘bangaran sosai Suka sa cigiyar Tahee , har lokacin kuma King baya motsi sai wani irin haske da she’ki da fatar jikinsa ta ‘karayi kamar bashi ba. Sai da gari ya fara haske ne mutanan gidan suka fara zuwa asibitin wannan karan Ammey bata biyosu ba Sabida yadda take jin zuciyarta , amma kwata kwata bata nuna musu afili ba sai ma ‘karyar zazzabi datayi duk da Abeey yace tazo a duba ta a asibitin taki, A bangaran Abeey ma bece mata komai ba sai umar ta ummey yayi da taje ta huta a gida, tazo turjewa amma kasantuwar bata masa musu yasa ta koma gida ita da su dada wannan karan aka abar su Abeey a d’akin da king yake . Lokacin da Abeey yaga king wasu irin zafafan hawayene suka sakko masa , ga bugun zuciyar sa da take yawaita, abunda ya faru tsawan shekarune ya soma dawo masa musamman idan ya kalli halin da king yake a ciki, ganin yana ‘ko’karin ‘karawa kansa damuwa ne yasa ya fara tasbihi cikin zuciyar sa yana neman za’bin Allah. Ummey tana shiga part d’inta ta zaro ido sabida ganin wacce batayi tsammaniba, kyakkyawa matashiyar budurwar da a ‘kalla bazata hakura shekara 35 a duniya bace ta d’ago kanta, fatabarakkallah ahsanin khalikin,kyakkyawar matashiyace da Hutu ya gama ratsa gabaki d’aya sassan jikinta, sosai take kama da ummey wani abun nata kuma sak irin na zoya , murmushi ta saki ganin ummey kafun ta taso kamar ‘karamar yarinya ta rungume ummey , cikin wata daddad’ar murya ta furta da yaran larabci ta furta “ ummey na nayi kewarki gabaki d’aya na dunga kira wayar ku ban samu ba, hatta waccan uban fad’in ran number d’insa a kashe yake abunda be ta’ba faruwa ba “wasu zafafan hawaye ne suke ‘ko’karin sakkowa ummey tayi saurin dakatar dasu, cikin murmushin ta da bai kai zuciya ba ta kalli matashiyar budurwar” Samreen Yaushe kika zo , ko sanarwa bakiyi bafa “, murmushi samreen d’in ta saki , tana bud’e hannayenta “ surprise!!! King ne kad’ai yasan da zuwana Sabida nace bazata zan muku ammeey, tunda kun hanani ganin amaryarsa ai ganinan nazo ganinta da kaina , wannan karan sai nayi good 2 month kafun nabar gidannan”, jinjina mata kai ummey tayi cikin katse maganar “ ya kamata ki huta yanxu, Nima ina bu’katar watsa ruwa “ , ta kara she zancanta da barin Wajan. Bin bayanta da kallo samreen tayi,Anya lapiyar ummey kalau kamar akwai abunda yake damunta , musamman da na shigo naga kamar akwai abunda yayi missing, ta fad’a cikin zuciyar ta amma sanin halin ummey yasa bata bita d’akin ba ta nufi nata da yake a gyare kamar ansan da zuwan ta. Har ta kwanta bacci ta farka bata ga ummey ba sosai mamaki ya ‘kara shigarta, kai tsaye bedroom d’in ummey ta nufa , ta d’aga hannu da niyar kwankwasa mata ‘kofa taci abunda ya kusa buga mata zuciya, da sauri ta tura ‘kofar d’akin ummey, ba ummey dake hawaye ba hatta Abeey tashi tsaye sukai ganin yadda hawaye ya ‘bata mata fuska, cikin kuka ta soma magana “ ummey ? Abeey? Meyasa?me yasa zaku ‘boyemun halinda d’an uwana yake? Meyasa ?ummey banaso na rasashi kamar yadda na rasa Akhieee “, ta karasa tana sakin wani saban kukan me ta’ba rai , itama ummey kuka ne ya kwace mata da kyar Abeey ya lallashesu sukai shiru, yana d’akin kiran mahma yashigo wayarsa, ko ba’a fad’a masa ba yasan tana Lagos kuwa , yana d’aga wa abunda ta fad’ane yasa guntun murmushi bayyana a kan fuskarsa kafin ya kalli ummey, “ ki zauna ki huta zuwa anjima sai kuzo da samreen “, ba ummey da akai wa magana ba hatta samreen girgixamasa kai ta soma , “ zamreen tana asibitin yanxu haka “, yana kai karshe be kuma kallansu ba ya bar d’akin sai a sannan ummey ta saki ajiyar zuciya , tun halinda taga d’anta yake a asibiti kawai taji bata yadda da kowa ba shiyasa ta ce zata zauna amma tunda taga mahma taje babu Wanda zai taba mata d’a da yardar Allah, amma ko kadan bata nuna ko a fuska ba, samreen gabaki d’aya tundata zube a kasan bata tashi ba saida ummey ta dawo tausarta da kanta. ******** ************ TAHEEE Tun data bar gidan ta soma gudu, ita kanta bata san ina taka do saba sai lunguna take wucewa ko wahalar tafiyar bata ji, har wajan karfe goma sai lokacin sallah yayi zata tsaya tayi sallahr ta , tana idarwa kuma zata cigaba da tafiya abinta ,sosai ta dunga kutsa layuka tana tafiya tafiya , duk irin cigiyar ta da ‘yan sanda suke har yanxu babu Wanda Allah yasa ya ganta, duk Inda ta kutsa shiga kawai take har tazo wani lungu da yake da mugun duhu, kan wani ‘karamin benci ta zauna tare da buga uban ta gumi , zoban hannunta ta zuba ido kamar tana san tuna wani abu, sai kuma ta ‘kara maida kallanta kan abun hannunta da sai faman walwali yake, da Sauri ta cire zata jefar ko me ta tuna sai kuma ta mayar dashi hannunta tana zuba masa idanuwa, wasu mashayen maza ne suka zo wuce wa gabaki d’ayansu a buge su, d’aya daga cikin sune ya nuna musu Tahee dake zaune kan benci, gabaki d’aya had’a ido sukai, d’aya daga cikinsu har ya fara cire belt d’in jikinsa . Cikin sanda suka fara nufar inda Tahee take da har yanxu hankalinta yana kan abun hannunta,d’aya daga cikinsu ya d’aga hannu daniyar ta bata kawai yaji saukar mari, da Sauri ya dafe kumatunsa cikin azaba, gabaki d’aya kallan tahee sukai amma abun mamaki tana yadda take d’azu ko alamar motsawa batayi ba , d’aya daga cikinsu ne yayi ‘ko’karin taba Tahee yaji wani gigitaccen mari a kumatunsa dama da hagu, shima cikin azaba ya dafe kumatunsa,ganin har yanxu tananan a yadda take yasa d’aya daga cikinsu rugawa a guje yana fad’in “ wallahi babu ruwana aljanace “, suma ragowar matasan daga jin haka suka saka gudu suna fad’in “ Aljanace Aljanace”. Taheee kuwa ko ajikinta sai ma Tashi da tayi ta ci gaba da tafiya abunta har taji kafarta ta soma yi mata zafi, wani waje ta samu ta zauna duk sanyi ya gama rufeta sai faman karkarwa take , fashewa tayi da kuka tana kankame jikinta, har wajan karfe biyu da rabi Tahee bata runtsaba tafiya kawai take yi ita kadai ga baccin da take ci amma da ta zauna sai ta tashi a firgice ta cigaba da tafiyar ta. Gabaki d’aya gari yayi shiru baka jin hayaniyar komai sai kukan karnuka kowana mahaluki a irin wannan lokacin ya samu makwanci ya kwanta ban da Tahee da ke ta faman tafiya cikin lungu. Daidai tafi wani babban Titi ta had’u da wasu maza uku da mata guda biyu ko wanne hannunsa da makami a jikinsa. Suna ganin Tahee suka nufo inda take basu tsaya bata lokaci ba suka fesa mata wani abu a fuska matan suka kinkimeta sai cikin ba’kar motar da suka faka . A guje suka ja motarsu da mugun tsiya , ta cikin wani jeji sai gaman sharara gudu suke ko tsoran hanya basa yi har gari ya waye suna tafiyar nan , d’aya daga cikin mazan ne ya d’aha wayarsa da take ‘kara , banji me aka ce masa ba sallan Tahee data kwance yayi “ Eh Boss mun samo yarinya kamar yadda kace, ynxu haka muna cikin niger, zamu kamo hanyar niamey “, ban san me aka ce masa ba sai “ toh oga” da nayi yace yana kashe wayar. Kallan sa d’aya daga cikin matan sukayi “ wizi me oga yace “ Wanda aka kira da wizi ne yaja d’an ‘karamun tsaki , cikin d’aga murya sak d’an daba ya soma magana “ Kunsan halin oga da shegen zumud’i yace duk yanda zamuyi mu’karaso da yarinyar nan kafun gobe , dan haka munti goma na bawa kowa , yaje yayi abunda zeyi mu cigaba da tafiya kunsan muna cika aiki ze bamu kud’in mu”. Hakan kuwa akai gabaki d’aya fita suka cikin motar yayi saura sai Tahee , muntuna goma sha biyar ne ya dawo dasu motar suka cigaba da tafiya cikin jejin , kowa da jakar abuncinsa. Karfe 6:30 pm na yammane ya shigo dasu Niamey, anan ma saida sukayi tafiya me Nisan gaske , lokacin yunwa ya farkar da Tahee amma ta kasa motsawa sabida yadda jikinta ya mutu, ga yunwa d’aya cika mata cikin ta. Wani wayar aka yiwa Wizi , basu dad’e suna wayar ba ya kashe kiran tare da kallansu. “ ku Samu waje mara mutane muyi parking , Sabida yanxu su oga xasu karaso su d’auketa “, amsa masa sukai kafin su isa inda babu mutane da yawan, fita wizi yayi daga cikin motar, “ kusaka idanuwanku akanta ynxu zan dawo”, be jira amsarsu ba ya bar wajan, dogon tsaki wata mace taja “ ni Wlh wani lokaci oga wizi haushi yake bani, kalli fa abunda muke d’urawa cikin mu gaskiya ni ma zanje na dawo dan abinci nake bu’kata. Me tukin ne ya tsayar da ita “ amma Baby kinsan halin wizi”, kanta ta d’aga masa tare da barin motar , ita d’ayar da Sauri tabi bayanta, yayi saura maza guda biyu, shima d’ayan kallan drivern yayi “maganar su gaskiya ce kuma kaga babu mutane da yawa wajan, nasan har mu dawo yarinyar nan bata farka ba kawai muma mu bisu dudu du bazamu wuce mun tuna ashirin ba “. Gyada masa kai driver yayi suka fito cikin ikon Allah kuma sai ya manta be kulle motar ba ya barta a bud’e. Mintuna biyar da tafiyarsu tahee ta mike zaune , kallan inda take yayi da sauri ta zabura ,jikin kofar motar ta soma bubbugawa da karfi, take a Wajan motar ta bud’e , tana ganin ta fito daga cikin motar ta zubawa Wajan kallo , sai kuma ta cigaba da tafiya abunta, cikin wani lungu ta soma tafiya , saida tayi tafiya me shegen Tazara da Inda motar su wizi take kafun ta yanki wata kwanar ta cigaba da tafiya . Lokacin da su Baby suka dawo ba ‘karamun tashin hankali suka shiga ba lokacin da Suka ga tahee bata cikin motar, cikin tashin hankali suka bazama neman ta amma gabaki d’aya basu sametaba, lokacin da wizi ya dawo saban rikici yasaka musu kowa hankalinsa a tashe yake musammman Alhajin su da ya fara kiransa a waya Amma ya kasa d’aga wa , cikin mota suka shiga , suka fara yawan neman inda take kafun mutane su ankara dasu . Akan wani dakali dake kan babban titi tahee ta zauna gabaki d’aya ta galabaita,sai faman lumshe ido take , wata bakar mota da tun dazu take faman wucewa ne tayi parking inda Tahee take a tsaye , wata babbar matace ta fito bayan motar ganin yanda tahee take agalabaice na yasa ta nufeta Amma duyin duniya tahee bata kulasu ba , kama hannunta matar tayi suka shiga motar dan lokaci d’aya taji yarinyarta kwanta mata ga tsoran kada wasu su cutar da ita yasa ta tafi da ita cikin motar ta. 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 MSS LEE 💖 BOOK 2 Page 2 NIAMEY , NIGER Cikin wani madaidaicin gida motar da tahee take ciki aka bud’e gate, Daidai madaidaicin harabar wajan da mota zata iya tsayuwa akai packing. Matar ce ta fara fitowa ganin tahee bata motsa daga inda take bane Yasa matar ru’ko hannunta suka fito tare, babu kowa a wajan har matar ta bud’e kofar falonta suka shiga ciki ita da Tahee, cikin sakin murmushi ta kalli Tahee” kiji rani ba dad’ewa zanyi ba kinji”, ta fad’a tana kallan Tahee da kwata kwata batasan me take ba,”Kara maimaita mata matar tayi tare da nufar cikin bedroom d’inta har da saka key, da sauri tayi dialing wata number da bugu biyu aka d‘aga kiran cikin ‘kasa ‘kasa da murya ta soma magana “ kuna ina? “ banji amsar da aka bata ba saima ‘kara ‘kasa ‘kasa da murya da tayi “ Nasamo babban kaya yanxu, nasan ‘kungiya ba ‘karamun jinjina mun zasuyi ba sabida yadda suke bukatar akawo musu kayan na samu, yanxu haka tana falan gida na , zan yi ‘ko’karin duk yadda zanyi na ajjeta agidan nan zuwa gobe ,” banji me aka ce mata ba sai ma jinjina kai da tayi “ idan hakan zai samu babu matsala , amma kunsan mutane da sa ido kuma saura kwana 4 ayanka mutane goma da ake bu’kata , yanxu me muke jira tunda na samo cikin ta gomar?”shiru tayi tana sauraran abunda ake ce mata , cikin ‘kara ‘kasa da murya ta furta “ ba matsala ku hanzarta, na barta a falo karta ji ni shiru “, tana kai ‘karshen zancenta ta kashe wayan tana sakin murmushin farinciki, abayyane ta furta “ Tsuntsu daga sama gash she , fridge d’in d’akin ta bude tare da d’akko wani exotic me shegen sanyi, hand bag d’inta ta bude ta ciro wani allura , a cikin lemon tayi wa allura kafun ta ‘kara jijjiga lemon, fuskarta ta daidaita tare da fitowa daga d’akin.gaban tane ya fad’i bata san lokacin da ta yar da leman hannunta ba , duk da girman da jikinta yayi mata hakan be Haka ta yin gudu ba , ban d’akin falon ta duba wayan babu Tahee babu alamarta, da sauri ta fito harabar gidan nan ma babu kowa gashi bame fadi ne da itaba ballantana ta tanbayeshi, wayarta da ta soma ‘kara ce ta d’auka sai faman hard’a gumi take , bata jira me za a ceba tayi saurin bud’e kofar gidan ta , motar data gani ta nufa cikin Sauri, ba kowa bane face su wizi da ke cikin motar kowa kagani fuskarsa a cin kushe tun lokacin da suka nemi Tahee suka rasa , zu’kar sigari wizi yayi kafun ya furta “ Hajiya ina kayan suke , kinsan fa gobe za a fitar dasu “, a rud’e hajiyar ta soma duban hanya “ wizi ta gudu, ta gudu kuyi Sauri ku dubata nasan batayi ni saba “, cikin matsiyacin gudu driver ciki ya tada mota suka soma duba layin ko zasu ganta. Adaidai lokacin da suke nemanta ,ita kuma ta dad’e da yin nisa hawaye sai faman sakko mata yake akan fuskarta , ita kadai sai faman tafiya take ga duhu da ya somayi sosai , hannunta d’aya dafe da cikinta. Wasu manyan ba’ka’ken motoci ne guda uku Suka wuce , sai kuma ta dawo Daidai inda take sukai parking, wasu kamilallun mata da mijine suka fito cikin motar dattawa dasu, sai masu tsaran lapiyar su dattijuwar matarce ta matso inda take tahee take , “ baiwar Allah ya naganki, akan titi ke d’aya sai faman kuka kike “ shiru tahee bata ce mata komai ba sai tafiyarta data somayi, dattijan mutuminne ya saki murmushi kad’an , “ ai bazata baki amsa ba “, da mamaki matarsa ta kallesa , shima kallan nata yayi yana jinjina mata kai alamar Hakane abunda yace kafin ya duba agogan hannunsa , “ dare yayi sosai mu tafi da ita gida , insha Allah ko zuwa gobene sai asan abunyi amma barinta anan zai zama illa agareta da abunda yake cikinta “, cikin gamsuwa matar ta jinjina masa kai kafin ta kama hannun tahee da ke kokarin tafiya suka tada motar sai unguwar Francophone dake cikin Niamey , sosai babbar unguwace da ta tara manyan mutane sabida gidajen da suke wajan ya isa ya tabbatar wa mutum haka , wani soja ne ya bud’e musu babban gate d’in gidan Daidai parking lot motocin sukai parking, cikin dattako matar nan tafito hannun ta d’aya rike da na Tahee da har yanxu bata dena hawayeva, matar ta juya daniyar nufar part d’inta da Tahee amma mutumin ya hanata, cikin kamilalliyar muryarsa ya nuna mata wani part “ ki kaita d’akin maganina “, toh kawai tace masa tare da nufar wani madaidaicin flat, dattijan nan na biye a bayanta , duk yadda akai da tahee akan tashiga kin shiga tayi saima ihun da ta fara yi a gigice da Sauri matar ta damki hannunta ta shigar da ita, kafun tayi wani motsi Tahee ta saka ihu tana neman hanyar fita , “jeki kira mun Isma’il, bai jira amsarta ba ya kunna wani hayaki da yasaka Tahee zubewa ‘kasa tana sakin nunfarfashi kamar ranta zai cire , cikin kankanin lokacin wani farin magidancin buzu yashigo d’akin bakinsa d’auke da sallah, yana ganin Tahee zuciyar sa ta buga , wani irin yanayi na taso masa , danne wa kawai yayi kafin ya ‘karasa wajan mutumin “ baba Malam Ance kana ne mana “gyada masa kai tayi tare da nuna masa wasu turaruka “ su zaka had’a” cike da girmamawa kuwa ya had’a turarukan da ya cika d’akin da hayaki har wani irin rawa jikin tahee ya soma bata soma zabure zabure sai lokacin da aka saka karatun Alkurani, ‘kara ta somayi kamar me aljanu cikin wani irin murya ta soma magana “ ku tsaya, ku tsaya karku ‘konani , ku tsaya “, basu tsaya d’Inba sai ma wani magani da isma’il Yasaka ,cikin shakewa ta cigaba da magana “ ku tsaya , ku tsaya “, cikin tsawa baba Malam ya furta “wanene ya aikoku, me yasa kuka shiga jikinta”, shiru Tahee tayi , suma su baba malam karatun suka cigaba tayi saurin da katar dasu “ Munshigq jikinta sabida muzubar mata da cikin jikinta ne , mu hanata zaman lapiya “, a kan me ? Baba Malam ya tanbaya “ cika aikine kawai namu bama tanbayar dalili”, murmushi baba Malam ya saki “ tafiyarta kuma fa “, nan ma kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta bud’e bakinta “ wannan ba mu mukayishiba wacce tayi mata asirin ce ta binne da kanta ,”Menene illarsa “bama fadar…..”, be karasa ba baba Malam ya daka matsa tsawa tare da cigaba da karatun sai da ya tabbatar ya jigata kafin ya soma amsa masa tanbayoyinsa “ bazata taba zama a kusa da kasar da take ba Sabida asirin da akai mata “, yanxu ina umartarka daka fita daga cikin ta yanxu, idan ba haka ba zan ‘kona’ka da ayoyin Allah”,gardama yasoyi Baba Malam ya soma karatun alkuraninsa hankali kwance shi kuma alhaji isma’il yana kara saka turaran wutar maganin ? Cikin azaba ya furta zan fita , zan fita “, sharesa baba Malam yayi sai da ya saka karar azaba Sabida yanda jikinsa ya soma konewa “ zan fita , zan fita “. Yana kai karshen zancansa sai Tahee ta soma atishawa, sai da tayi atishawa kusan sau uku kafin bacci ya d’auketa a Wajan , kallan tahee alhaji isma’il yayi abu na fad’o masa arai amma yayi kokarin kawar da hakan lokaci zuwa lokaci yana kallan fuskarta , take a wajan tahee ta shiga ransa . Gyaran murya baba Malam yayi, dare yayi sosai ya kamata muje mu kwanta , kallan wajan da tahee take Alhaji isma’il yayi, shima baba Malam ita d’in ya kalla kafun ya saki murmushin sa na dattako “ su Ameerah zasu kwana da ita , zuwa safe sai muga abunda Allah zaiyi”, cikin gamsuwa Alhaji isma’il yayi wa baba Malam sallama , shima baba Malam wasu yan mata ya kira a waya suka canzawa Tahee d’aki. NIGERIA WASHE GARI Haryanxu babu irin neman da ba a yiwa Tahee ba amma babu ita babu alamarta atta ma’kotan da suke kusa da Lagos sai da Abeey ysa aka bincika , sosai abeey ya saka kud’i akan neman Tahee babu inda ba a dubaba ba’a sametaba, hatta airports sai da aka bincika amma batanan . A ‘bangaran king ma har lokacin be farka ba yana cikin coma abunda ya ‘kara tayar da hankalin mutanan gidan , tsakanin mahma da ummey kuwa sai aka rasa wanene yafi kula da king , dan a wannan karan ummey kunya ta cire ta dunga kula da d’an ta , momy taji dad’in abinda ummey sukeyi sabida wani dalili nata , kusan suma a asibitin suke yini, su sumayya ma ko wa kagani zakaga irin damuwar dake kan fuskarsu, kabeer da haroon ma kusan suke kula da gidan yanxu . Sosai hakan ya ‘kara ba’kanta ran Ammey da har zazzabi saida tayi, atunanin mutanan gidan Sabida halin da king ya shiga ne da kuma ‘batan tahee , amma a zahiri sam ba hakan bane , tsantsan bacin rai ne da bakin cikin bata ‘karasa hallaka king ba gashi babu damar hakan sabida yadda mahma da ummey suka tsaya akansa ga dada da kullum cikin rubuto masa rubutu take ana shafa masa , Hakan kuma ba ‘karamin barazana bace a gareta. ✨✨✨✨ UNITED KINGDOM Momy zaune cikin akan kujera jikinta sanye da Abaya da yayi mugun yi mata kyau, Mimi ce ta zakka a guje daga kan steps tare da d’anewa jikin momy har saida ta tsorata , cikin fad’a momy ta tureta “Mimi meke damunki, baki da hankali ne Yaushe zaki dena jin magana ? Ban hanaki wannan guje gujen ba ? “, a shagwa’be Mimi ta turo bakinta “ Haba momy , rungumeki fa kawai nayi amma duk kin tsorata “,’karamin tsaki Momy taja “ banga lokacin da zakiyi hankali ba Mimi , bari ya yanki ya dawo, aure zan sa ayi miki da driver ko kinyi hankali “, a zabure Mimi ta mike tsaye tana bubbuga ‘kafa fuwanta “Haba , Haba momy wai me yasa ni kike mun haka kullum, gaskiya ni yanxu ba ‘kyaso na bari dady ya dawo , ni bansan me nayi miki Haka ba sai kace ….”, bata ‘karasa maganar taba sabida tsawar da aka daka mata , da Sauri ta juyo tana kallan Wanda yayi tsawar a tsorace , kyakkyawar guy ne fari tas dashi kamar ka tabasa Jini ya fita , kyakkyawane shi sosai , kyawawan idanuwansa yabi fuskar Mimi da kallo da take ‘kokarin ‘buya a bayan momy,” fito “ muryar kyakkyawan guy d’in ta ratsa mata kunnuwa , a ra’be ta fito daga bayan momy kamar mara gaskiya , murmushi momy ta saki tana nufo inda yake “ wannan bazata haka son , kace mun sai anjima zaka dawo”, murmushin da ya saka jerarrun ha’koransa fitowa yayi,” nayi kewar kune momy shiyasa ban bari Daren yayi ba “, murmushi ta sakar masa tana karban trolley d’in sa,” yanxu dai ka fara yin wanka son , kafun nan sea kaji abinci “, yanxu ma murmushi ya sakar mata “ okay ma”. Har ynxu Mimi na inda take ganin ya’ki kallanta kamar zatayi kuka , shima bece mata komai ba yayi wucewarsa,da Sauri ta ‘karaso Inda momy “ Bro ya’ki kulani please ki bashi hakuri”, hararar ta momy tayi tabar wajan , fashewa da kuka mimi tayi , da gudu ta nufi d’akinta Asama tare da saka masa key. Har guy d’in ya fito sanye da wasu kayan alamar wanka yayi mimi bata fito ba , tsakanin shida momy babu Wanda ya tanbaye inda take har ya kammala cin abincinsa, kallan momy yayi “ Ina Mimi momy”, wani saban murmushi momy ta saki, “Dakar barta ai Son , nasan tana can tana halinta na kullum, nakusa maganinta ai”, murmushi yayi tare da mikewa, kallansa momy tayi “ ina zaka “, kanshi ya d’an sosa kadan yana murmushi “ yanxu zan dawo momy”, gyada masa kai batare da tace masa komai ba , ita kad’ai tana murmushi abinta. ‘Dakin Mimi ya nufa ,sau d’aya ya murd’a yaji shi a kulle , nasa d’akin ya nufa tare da d’akko wani mukulli ya koma dakin mimin, sau d’aya ya saka key d’akin ya bud’e . A tsugunne ya same ta tahad’e kai da gwiwa tana shash she’kar kuka , har ya shigo cikin d’akin bata sani ba , kan kujerar gaban mudibin ta ya zauna tare da crossing Legs d’insa , “me akai miki kike kuka ?”, da sauri ta d’ago fuskarta ganinsa zaune a wajan tayi Sauri goge fuskarta “ ba kuka nake ba , abune ya shigar mun ido”, tafa har yanxu muryarta kamar zatayi kuka , gyad’a mata kai yayi tare da mikewa, itama da Sauri ta mi’ke tare da ri’ko hannunsa “ am sorry yaya moh “, kallanta yayi akaro na biyu ya ‘kaya maimaita maganarsa” me yasaki kuka ?”, sun kuyar da kanta tayi ‘kasa , shima d’auke hannunsa yayi daga cikin nata “ well “ da Sauri ta furta “Naga kana fushine and yaya moh , momy ce tace fa zata sa ka aure min driver”, ke kuma ba kyaso? Kanta ta d’aga masa alamar eh , murmushi ya karmata “ kar na ‘karaji momy na magana Kema kin d’aga muryar ki? Okay ? “ na dena , and yaya moh ina tsarabata? Goshinta ya d’an dallah “ in my room “, bata jira karashen maganar saba ta fita a guje , giirgiza kansa yayi “ Allah ya shirye ki mimi “, daga nan ‘kasa ya sakko inda momy take suka soma hira Yaushe gamo da ita. ********** ************* ✨✨✨✨✨✨ NIGER Tunda Tahee ta farka take kuka ita kadai lokaci zuwa lokaci sai ta zabura zata mi’ke wasu ‘yan mata suna ri’keta , abun mamakin kuma da kanta tayi sallahr asuba daga nan kuma ta mike hawaye cike a cikin idanuwanta , duk yadda taso barin Wajan sun hanata jintake kamar zatayi hauka fad’i take su rabu da ita amma sun ‘ki sai ma baba Malam da suka kira , kallo d’aya yayi mata ya saki murmushi “ ku kyaleta “, suna sakin ta kuwa ta mike a zabure zata nufi ‘kofa ya daka mata tsawa, da Sauri ta nutsu, abincin da aka kawo mata ya nuna mata , cikinta har rawa yake lokacin da ta soma cin abinci har saida Alhaji isma’il d’in yace taci a hankali, gabaki d’aya sai data basu tausayi, rubutu baba Malam yasa aka bata , ita kad’ai sai sakin ajiyar zuciya take , karatun alkurani aka sa a d’akin , matasan ‘yan matan suka zauna da ita , baba Malam da alhaji isma’il kuma suka fita. Cikin wani d’aki suka shiga Alhaji isma’il ya kalli baba malam,”baba Malam idan ba damuwa ina san ro’kan wani Alfarma”, murmushi baba Malam yasaki kafin yace “ina jinka “,shiru yayi kamar bazai ce komai ba sai kuma ya soma magana “ baba Malam idan babu matsala inasan tafiya da wannan yarinyar can wajan iyalaina sai su cikaga da zama tare ,tun da alamu sun nuna zamanta anan kamar zai iya zamar mata had’ari ita da abunda yake cikin ta, tunda asirin da akai Mata ba iya nigeria bane har kusa da ita , kaga idan bata kusa da nan zata samu nutsuwar zuciya ko zata dawo hayyacinta sosai, ko ba dan itaba dan abin cikinta “. Yan Zuma baba Malam murmushi ya saki tare da gyara zaman sa “ Naji duk abunda kace isma’il, kuma na yaba da hankali da nutsuwar ka , amma kasani kamar Marainiyace kake kula da ita tunda bata da kowa , idan kaci amanar Allah , Allah bazai barka ba , ka kula da amanar Allah wannan kamar jarabawace Allah yakeso ya kwadaka”, sunkuyar da kai alhaji isma’il yayi “ insha Allah baba malam , nayi maka alkawari zan d’auketa kamar ‘yar cikina sannan na bata tar biya kamar ni na haifeta “, Allah yayi maka albarsa, yaushene tafiyar?” Cewar baba malam , “Jibi nake san komawa insha Allah “, jinjina masa kai baba Malam yayi “ sai a sanar wa iyali “cewar baba Malam,cike da girmamawa ya “amsa da insha Allahu”. 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 MSS LEE 💖 BOOK 2 Not edited Page 3 &4💖 Yinin ranar gabaki d’aya kula suke da Tahee tun tana zabura har ta dena sai dai har lokacin babu Wanda tayi wa magana , babu Wanda ya damu da rashin maganarta ta Sabida umarni da baba Malam ya basu, kana kallan Tahee zakagane tana cikin damuwa saidai babu Wanda take cewa komai . Haka Suka ci gaba da kula da ita harzuwa ranar da Alhaji isma’il zea koma , bayan ansiya wa Tahee itama abun anfani, sosai tafito tass da ita duk da bata yiwa kowa magana sai bin fuskar kowa da take da kallo. A cikin jet d’in wani amininsa Alhaji isma’il zai koma shiyasa tafiyar tasu taxo musu da sau’ki, suna zuwa jirginsu ya tashi cikin sararin samaniya zuwa UK. 6 hours 18 minutes ne ya kawo su Uk cikin babban filin Airport d’in kidlington date Oxford, duk inda ya saka ‘kafarsa nan Tahee take sawa , cikin wata katuwar Audi aka zo d’aukarsa, bakowa bane yazo d’aukarsa face Ya moh, yana ganin Alhaji isma’il ya rungumeshi “ welcome back dad”, shima Alhaji isma’il d’in rungumesa yayi a jikinsa , “ Thank you my son, “ gabaki d’aya yah moh bai kula da Tahee dake kusa da Alhaji isma’il ba sai da ya bud’e masa mota, suna had’a ido da tayi yaji zuciyarsa ta buga yana neman nutsuwarsa yarasa , cikin Sauri ya soma karanta adduar da ta zo bakinsa, nuna wa Tahee cikin motar yayi ame makon ta shiga sai ta tsaya kallansa, fahimtar hakan yasashi shiga cikin motar , sai gashi itama ta shiga , ta cikin mirror yah moh yake kallan abunda ke faruwa , azuciyarsa yana ayyana me yarinyarnan take tare da dady duk da yasan da zuwan ta . Mintuna 15 ne ya kawosu gida , tunda Mimi taji saukar mota ta fito a guje zata fita momy ta hanata, ita kad’ai sai faman kunburo baki take , da sallama Yah moh yashigo falon bayanshi kuma Alhaji isma’il ne , Mimi na ganinshi ta saki ihu , dagudu ta nufo Alhaji isma’il daniyar rungume shi amma kallan da yah moh yayi matane yasata dakatawa a sanyaye ta furta “ welcome back dady , nayi missing d’inka sosai..” bata ‘karasa ba idanuwanta suka sauka kan Tahee da ke ra’bewa, kallan dady tayi sannan ta kalli Tahee, kafun tayi magana momy ta fito cikin Adon less meshegen tsad’a , wuyanta kuma sarkar gold ne tare da ma had’inta , ita kadai sai faman walwali take ,ganin sun tsaya ne yasa momy sakin lallausan murmushi “ ku shigo daka ciki mana , gabaki d’ayansu cikin falon suka shigo Tahee na bayan Alhaji isma’il, cike da murmushi momy ta nuna Tahee alamar tabbatarwa “ Itace bakuwar tamu?”, jinjina mata kai Alhaji isma’il yayi , inda Tahee take tanufa, daniyar ta’bata , da Sauri Tahee mi’ke tana kallanta amma ta kasa yi mata magana , Ri’ko hannunta momy tayi cikin tausasawa ta furta “ karki damu daughter na ki kwantar da hankali babu abunda zai sameki insha Allah “, Ajiyar zuciya Tahee ta sauke duk da ta’ki yin magana sai bun fuskokinsu take da kallo, kallan Mimi da ta zuba musu ido momy tayi “ MiMi zoki kaita d’akin da aka gyara nakusa da naki”, Girgiza mata kai Alhaji isma’il yayi , for now akai ta d’akin Mimi , sai ta taima ka mata, idan nahuta zamuyi magana “, Toh momy tace , Mimi zatayi magana Yah moh ya kalleta, d’an ‘karamin bakinta ta turo waje tare da ri’ke hannun Tahee dake binta da kallo, a hankali suka nufi sama tare , Tana shiga d’akin Mimi ta saki hannunta tare da nuna mata ‘kofar Toilet “ ga ban d’aki nan, and nan kuma wajan sallah ne ,ga dadduma da sallaya “, tana gama mata bayani tabar d’akin. Bin ko ina nad’akin tahee tayi da kallo kafun ta tsugunna ‘kasa tana fashewa da kuka , kukan da yake zuwar mata tundaga ‘kasan zuciyar ta , kukane take yinshi me rad’adi, da Sauri sauri numfashinta ya soma yin sama da ‘kasa kamar zai d’auke , cikin Amincin Allah bakinta ya fara kirawo sunayen Allah , a hankali wata iriyar nutsuwa ya fara ratsata tana sakin ajiyar zuciya, ban d’akin da Mimi ta nuna mata ta kalla kafin ta mike ta shigeshi, mintuna kad’an ta fito daga toilet d’in, inda sallaya take ta nufa tare da kabbara sallah, saida tazo Daidai tahiyar‘karshe kuka ya kwace mata , lokacin da Mimi take shigowa d’akin d’auke da tray a hannunta , yadda taji shashshe’kar tahee ne yasa ta kallanta, mamaki abun ya bata ganin tana sallah tana kuka, da sauri ta fita daga d’akin , ita kuwa tahee batasan tanayi bama , har ta idar da sallarta tana kuka gwanin ban tausayi, a haka wani wahalallan bacci ya d’auketa kan sallayar. Shima Dady wanka yayi ya huta kafun yaci abinci , a ‘ka idar gidan duk lokacin da wani yayi tafiya tare ake zama ayi hira , hakan ce ta kasance a ‘bangaran dady , tunda ya soma cin abinci yake bin fuskokinsu da kallo , kowa kaga fuskarsa zakaga alamar tanbaya tattare dashi, maida kallansa yayi kan Mimi, kin kai mata abincin ?” Eh dady amma da nashiga naga tana sallah tana kuka sai tabani tausayi”, cewar mimi, kallanta momy da yah moh sukai alamar ‘karin bayani , ita ma Mimi kanta ta d’aga musu alamar gaskiyar zancenta. Ajiyar zuciya Alhaji isma’il ya sauke , kafun ya soma labarta musu abinda ya faru har dalilin na tahowa da ita , tunda ya soma basu labarin Mimi take kuka , shima yah moh sosai idanuwansa suka kad’a, hatta momy saida ta share hawaye “ wannan bala’I har ina ? Yar mitsitsiyar yarinyarnan ma baza a barta ba , koma wanene wannan ya cika babban azzalumi Allah bazai barsaba wallahi”, cewar momy, itama Mimi cikin shesh she’ka ta soma magana “ Dady kabar mana ita anan kaji? Zan dunga kula da ita nima “,kallanta yah moh yayi ya d’auke kansa batare da yace komai ba , kallansa dady yayi, “son baka ce komai ba ,” Dady duk ynda kace hakan yayi , ya kamata ta zauna anan d’in gudun karwani ya lahantata “, cike da gamsuwa dady ya jinjina kansa, gabaki d’aya sai suka canza hirar tasu zuwa kan tahee , anan ne dady yake sanar ma momy juna biyun dake jikinta kasan tuwar ta Doctor ce itama . Duk da Mimi batasan taba , ba ‘karamin murna tashiga ba , hatta dady sai da yayi mamakin murnar ta, yau bata dad’e sosai ba ma ta tafi d’akinta , har lokacin bacci Tahee take , babban blanket Mimi ta d’au ta lullu’be jikin tahee dashi, zata kwanta kenan momy ta shigo d’akin, ganin Tahee kwance a kan daddumane momy ta furta “Subhanallah , me nake gani haka ?”, da Sauri ta ‘karasa inda Tahee take , a hankali ta soma tashin ta, cikin firgita Tahee ta farka da har sai da momy ta ri’keta “ kwantar da hankalinki babu abunda zai sameki kinji”bin momy da ido Kawai tahee tayi , nan ma batace mata komai ba , kama hannunta momy tayi ta mikar da ita zuwa saman bed Inda Mimi take ta kwantar da tahee tare da lullu’barta , kallan mimi momy tayi “ Samuku karatun alqur’ani”, hakan kuwa mimi tayi ta kure volume din yadda zasu fi ji sosai, ‘kasa ‘kasa momy ta furta “ ki kula da ita”, kafin kafin ta kashe musu light d’in ta bar musu mara haske , tunda Mimi ta saka karatun alkuranin nan take Tahee ta soma sauke ajiyar zuciya ita kad’ai, a hankali takai hannunta kan cikinta, ganin haka yasa Mimi saurin mikewa , inda tray din dazu yake ta nufa , milk din kan tray din ta suka tare da wasu fruit ta mikawa tahee , karba tahee tayi ta soma cin abincin, sai da ta ci fruit da milk din sosai kafin ta soma ajiyar zuciya , sai a lokacin bakinta ya bud’e, daga sama Mimi taji muryar Tahee “Nagode “, kallar nagode din da ta fad’a masa yasa Mimi kara sakar mata murmushi cikin murna ta furta “ kije ki kuskure bakinki” , hakan kuwa tahee tayi sai da ta kuskure bakinta, ta sake wani alwalan kafin ta kwanta a gefen Mimi duk da har yanxu zuciyarta bata gama sakewa ba . WASHE GARI Momy da kanta tazo tashin su mimi, lokacin da ta shigo d’akin a kan dadduma ta tarar da tahee na sallah, murmushi ta saki dan sosai ta burgeta, ‘karasa shigowa ciki momy tayi tare da nufar inda mimi take a kwance tana shakar bacci, “Mimi…,Mimi”, cewar momy, d’an motsi Mimi tayi kafun ta furta “Uhmmm “, girgiza kai momy tayi kafun ta furta “ oya ki tashi lokacin sallah yayi “, motsi mimi ta farayi da idanuwanta kafun ta bud’e gabaki d’aya akan momy, a hankali ta mike zaune , sai a lokacin idanuwanta suka sauka kan tahee da ke sallah,sai kuma ta mayar da kallanta kan momy da ta mike ta fita ganin har lokacin sallah tahee take , itama mimin ganin lokaci na tafiya ne yasa ta mikewa , bata dad’e a toilet ba ta fito , lokacin tahee ta idar da sallanta, itama sallahr ta tayar tahee na gefenta kamar mara lafiya sabida yanda tayi shiru kamar me tunani sai kuma hawaye suka soma sakko mata akan kumatunta, duk da ba sosai Tahee ta girmi Mimi ba amma dukda haka cikin tsokana saida mimi tace mata “ Ina kwana Aunty”, d’an kallanta Tahee tayi kafin ta du’kar da kanta kasa , kusa da ita mimi ta matso kafun ta kama hannunta “ ki saki jikinki kinji? , Babu Wanda zai ‘kara ta’baki, duk Wanda ya ‘kara ta’baki sai nayi gunduwa gunduwa da namansa “ kawai kallanta tahee tayi hawayen da take ri’kewa ya fara gangaro mata, zuciyarta ba dad’i tun jiya da tabar Nigeria komai da ya faru na ‘kara yawo a cikin kwakwalwarta, batasan Wana hali mijinta yake ciki ba , Wana hali zai shiga, ya yake ynxu, oummanta , Taheer , gabaki d’aya farincikinta ya rushe , abu d’aya yayi mata saura yanxu, babynta, babynta da mijinta yake matukar ‘kaunar gani, babynta da mijinta yake so , so asalinsu, babynta da yake wa kallan d’an uwansa da yarasu, Amma gabaki d’aya ta rushe musu farin cikinsu da suke ginawa , farin cikin da suke Bu’Kata, ta cutar dasu , cuta sosai , an bata Amana amma taci wannan amanar, ta zalincesu ,sannan tana ‘ko’karin ‘kara salwantar da wani ran , babynta , ace auntyntace ta kashe mata uba, yanxu ma tana ‘ka’karin kashe mata d’a, wani tsantsar tsanar Ammey ne ya ‘kara shigarta, tayi alkawari sai ta koma, sai ta koma ta Nuna wa Ammeey bata isa ta cutar da su ba , idan Allah be nufa ba,hannun da taji akan kumatuntane yasa ta dawo daga duniyar tunanin da ta fad’a,kallan Mimi data share mata hawaye tayi, itama Mimi kallan tayi tare da sakar mata murmushi” kukan nan ya isa haka Aunt, ya kamata ki watsa ruwa , kafin ki fito zan ajje miki kayan da zaki sa, komai da kike bu’kata gashinan agaban mudubi idan kinasan wani abu sai ki tanbayeni kinji”, binta da kallo tahee tayi har ta gama maganarta , kafun ta furta “Nagode “ da kyar, jinjina mata kai Mimi tayi , ita tafita tahee kuma tashiga toilet d’in. A palour kuwa Momy tsaye a wajan dinning tana shirya breakfast d’insu, Mimi na zuwa kawai ta rungumeta a jikinta, tureta momy tayi “ Mimi har yanxu baza kuyi hankali bako? Kishiga taitayinki fa”, baki kawai mimi ta turo kafun ta furta “ Good morning momy”, ita momy “ morning “, wani ma daidaicin tray Mimi ta d’auka ta fara had’a kayan breakfast a ciki , ko me ta gani sai ta d’inta , kallanta momy tayi alamar ‘karin bayani, turo baki Mimi tayi “ Ni momy batare da ku zan ci abinci ba yau, zan je naci da sabuwar sis d’in da nayi, in dady da yah moh sun fito kice ina gaishe su “, tana gama fad’ar Hakan tabar wajan, binta da kallo Momy tayi “ yau kuma mimi ? Anya Itace kuwa ?” Abin ba ‘karamin mamaki ya bata ba sabida tasan mimi ko cikin mutane batasan shiga amma yau da kanta take furta agaishe da Yah moh , hmmmm, murmushi kawai momy tayi. Mimi kuwa tana shiga d’akin wata abaya ta d’auko wa Taheee blue colour me adan flowers pink colour , sosai rigar tayi kyau, bud’e kofar toilet d’in da akai ne yasa mimi ta d’ago kanta,”Yauwa Aunt ga kayanki nan, anjima sea naje nayi miki siyayya kinji, yanxu zan dawo “, bata jira amsar tahee ba ta kara barin d’akin bayan ta ajje tray d’in hannunta, kallan rigar da Mimi ta ajje tayi daga gefe wasu set d’in underwear pink colour sababbi’kal dasu a cikin Leda , ajiyar zuciya ta sauke , kafin ta saka kayan kamar dan ita aka yisu duk da tana cikin damuwa kayan ba ‘karamin kyau sukayi mata ba , sosai da sosai kayan sukai mata kyau, kallan fuskarta tayi a gaban mudubi kafun ta ta’ba gashin kanta da yake a jike , momy ce ta shigo d’akin bakinta d’auke da sallama bayanta kuma mimi ce , ganin bataci komai da aka kawo mata bane yasa momy d’aukan tray tare da kamo hannun tahee tana zaunar da ita , cikin raha momy ta furta “ nifa banaso naga daughter na tana cikin damuwa , ki saki jikinki kamar ni na haifeki, ga Mimi nan ki d’auketa kamar kanwar ki kinji”, sunkuyar dakanta tahee tayi kafun a hankali ta furta “ Ina kwana “, sosia momy taji dadin gaisuwarta amsa mata tayi cikin sakin fuska kafin ta d’auko spoon da niyar bawa tahee abinci a baki , kallanta tahee tayi itama momy ta jinjina mata kanta , da kanta momy ta shiga bawa tahee abinci abaki, tana ci hawaye na bin fuskarta , ko saud’aya momy bata hanata ba dan tasan shine kadai hanyar da zaisa nauyin dake zuciyar ta ya sauka , sai da ta tabbatar ta koshi sannan momy ta ‘kyaleta, hand dryer Mimi ta d’auko tare da sauran abubuwan gyaran gashi, dakanta ta busarwa tahee kanta, tare da gyara mata uban tulin gashin da ke kanta,kallan Mimi, momy tayi , “idan kun gama ku samemu a part d’in dadyn ki”, yana kai karshen zancanta tabar d’akin tare da tray din abinci. Saida Mimi ta gyara mata kanta sosai tayi mata packing d’inshi kafun ta kama hannun tahee suka fito, sai binta da kallo tahee dake , wani waje suka nufa ,tafiya kad’an ya kawosu wani babban falo me shegen kyau da tsa ruwa da yaso yafi Wanda yake a farko, suna shiga mutane uku ne a falon daga Alhaji isma’il sai momy da yah moh da yakw gefe, idanuwan tahee na sauka akan yah moh saida gabanta ya fad’i addua kawai ta soma yi cikin zuciyar ta , kafin ta zauna inda momy take nuna mata, da’kyar tahee ta gaishe da Alhaji isma’il tana bin fuskarsa da kallo da mamakin da ita kadai tabarwa kanta sani, cikin fara’a ya amsa mata, gaishe da yah moh tayi da yake zaune shima, cikin sakin fuska ya amsa mata kamar Mimi, mintuna biyu falon ya d’au shiru kafun Alhaji isma’il ya bud’e taro da addua , sai da ya tabbatar kowa ya nutsu kafun ya mayar da kallansa kan tahee, “baiwar Allah ko zamu iya sanin sunanki”a hankali ta bud’e bakinta “ sunana taheera muhammad “, jinjina kansa Alhaji isma’il yayi alamar gamsuwa kafun ya ‘kara yi mata wata tanbayar da ya ta’bo mata abunda take dannewa a cikin zuciyar ta, hawayen da take kokarin takatarwane sukayi nasarar zubo mata, babu Wanda ya hana ta yin kukan sai ma ‘kara maimaita maganarsa da Alhaji isma’il yayi” ko zamu iya sanin wacece ke , me ya faru har kika bar gidan mijinki da ciki”, share hawayenta tahee tayi tana sakin ajiyar zuciya , ko ba komai sunyi mata hallaci , sun kubutar da ita daga azabar da take ji a jikinta lokacin da take Niger , a hankali ta soma labarta musu labarinta, tun zuwanta gidan su king, da yadda tayi rayuwa dasu , tabin hankalin da ta samu har zuwa auranta da sanadin barowarta gida “, ba momy da Mimi da suke mata ba , hatta Alhaji isma’il da yah moh saida suka goge mata kwalla, momy da Mimi kuwa kuka suke iya ‘karfinsu, itama tahee du’kar da kanta tayi ta cigaba da kukunta, murya a raunane momy ta soma magana “ Wannan mata anyi shed’aniyar mata , insha Allahu sai taga hukuncinta tun a duniya , cikine kuma insha Allahu sai kin haifoshi kuma sai yayi rayuwa kamar kowa da yar dar Allah” kafun ta mayar da kallan ta kan dady “ daga yau ta Xama d’ata, duk abunda uwa take wayarta zan dunga mata shi da yar dar Allah sannan zan ci gaba da bata kulawa har ta haihu”,itama Mimi cikin kuka ta furta “Nima zan zauna da ita bazan ‘bata mata ba , komai tare zamu dungayi har ta haifar min baby”, murmushi Dady ya saki , dan shima sosai yaji wani irin Kaunar yarinyar ya shiga ransa kamar ‘yar da ya haifa a cikinsa , yah moh kuwa babu abunda ya furta sabida yadda kansa ke masa ciwo, lokaci zuwa lokaci yana kallan tahee ga ransa yadda yyi mugun baci,basu wani dad’e a Wajan ba Mimi ta kama hannun tahee suka bar falon dady, sai faman jan ta da hira take , ita de tahee sai binta da kallo take kawai, duk surutun tahee mimi ta dameta sosai tun bata amsa magana maganarta harta dawo amsawa da “eh ko ah ah”, a hankali kuma tana d’an amsawa Mimi hirarta, gabaki d’aya yinin ranar tahee sai tama tamkar wata sarauniya hatta ruwa idan momy ko mimi suka ga za Tasha da kansu suke bata a baki, tun tana jin wani iri harta d’an sake dasu ganin yadda suke kila da ita, da tayi wani motsi momy zatace mata akwai abinda take so, da yamma kuwa da kanta Mimi ta fita driver ya kaita shopping, kome ta gani indai ya burgeta d’aukowa take sosai ta suyo abubuwa masu yawan gaske tundaga kan kayan sawa har zuwa turaruka , gabaki d’aya kuma siyayyar ba tata bace , siyayyar tahee ce. Data koma gida tahee sosai tayi kuka , tun momy na zuba mata ido har ta dakatar da ita ganin kukan nata bana karewa bane , da daddare ma Mimi bata zauna a palour ba , sama ta koma wajan tahee anan Suka ci abincin da ta kawo musu. ******koda gari ya waye haka momy da Mimi suka ci gaba da kula da tahee , ko sau d’aya basu nuna mata basu da alaka da ita ba , sai ma wani irin kulawa da suke bata, hatta Alhaji isma’il da shima lokaci zuwa lokaci zai tanbayi momy ko akwia abunda suke so, hatta yah moh da ya dawo gida da wasu kayan ciye ciye ya dawo masu shegen yawa cikin ledoji na tahee , sabida yasan masu ciki da ciye ciye , hakan da yayi ba ‘karamin faranta ran momy da Alhaji isma’il yayi, gabaki d’aya sai ya zama kowa tahee yake bawa kulawa, babu Wanda zai ce bata da ala’ka dasu, tun tana no’kewa har ta soma sakin jikinta dasu ganin yadda suke nuna mata kulawa babu hantara ko nuna banbanci. 💕💕💕💕 AFTER ONE MONTH NIGERIA LAGOS STATE NAHYAN HOSPITAL. A hankali d’an yatsan king ya soma motsi a hankali , kafun ya fara motsa idanuwansa shima , lokacin gabaki d’aya su Abbey suna d’akin, mahma ce ta fara lura da yanayinsa, cikin sauri ta matso inda yake tana kiran sunansa, a hankali ya bud’e idanuwansa kafun yayi saurin kallesu sabida hasken da ya Haska masa cikin idanu,kara bud’e idanuwansa da suka ‘kara girma yayi, a hankali ya soma bin su Abeey da suka matso Inda yake da kallo, ‘kara dubawa yayi amma still be gantaba, murya a dushe ya furta “ my wife “, duk da rashin lapiyar da yayi babu abunda ya canza daga yanayinsa , fuskarsa ba asake take ba , kuma ba a d’aure take ba , yana bin su oummey da kallo ganin yanda ko wannan su yayi shiru, ‘kasa ‘kasa ya ‘kara furta “ where is she? And my child ?”, yanxu ma babu Wanda ya amsa masa sai ma cikin sauri da abeey ya kallesa , zamuyi magana daka baya bari a fara kiran doctor ya duba ka, be kuma cewa komai har doctor ya shigo cikin d’akin kallan sa king yayi fuska ba fara’a ya furta “for how long?”, cike da girmamawa doctor din ya furta 1 month and 4 days , shiru king yayi yana dafe goshinsa da ya soma sara masa , so yake ya ganta , so yake yasata cikin idanuwansa ko zai ji dady, ‘karasowa su oummey sukai gaban gadon , “ya jikinta “ jinjina musu kai yayi kafun ya lumshe musu ido, sai da doctor ya dubasa yaga ba matsala tukunna,wasu sababbin kaya king yasa a kawo masa , wani toilet ya nufa kamar ba a cikin hospital din yake ba , su kuma su Abeey suka fito zuwa falon inda king yake sabida abarshi ya shirya, cikin murna abeey ya kira samreen da ke tare da dada ya sanar da ita good news din farkawar king, lokacin a kwance ukhti take amma sai da ta mike tsaye da saurinta, har dada saida ta tsorata, “ amma dai anyi yar iskar yarinya, Menene kike mana wannan ihun haka “, murmushi ukhti ta saki lokaci d’aya hawaye na sauka daga cikin idanuwanta “ dada king ya Tashi “, mikewa dada tayi da saurinta “ mu tafi asibitin yanxu “, zasu fita kenan su ilham suka shigo cikin palour , ukhti ce tab kallesu “ Yawwa kwanda da kuka shigo, maza kuje ku cewa su mamy zamu je hospital king ya farka “, ihun murna ilham da su sumayya suka saki har dada tana zaginsu, sumayya ta nufi part din mamy lokacin suna zaune su da momy, sosai sukai farin cikin suma , momy har da mikewa ta kalli mamy “ ya kamata a had’a musu wani abu ko suna bukata “, hakane cewar mamy, firdausi kuwa part din Ammey ta nufa lokacin ta fito daga cikin kitchen hannun ta d’auke da wani plate na tangaran, cike da farin ciki firdausi ta fad’a mata farkawar king , bata jira jin amsar Ammey ba tabar part d’in, a rud’e Ammey ta saki plate din hannunta, kan ‘kafarta ‘karar azaba ta saki ganin yadda yaji mata mummunar rauni amma duk wannan be dametaba, farkawar king ne yafi komai ‘kuntata mata , azuciye ta nufi d’akinta dukda azabar da ‘kafarta ke mata. Lokacin da su dada suka ‘karasa cikin hospital d’in cike da farinciki suke tanbayar inda king yake , abbey ya sanar da ita yana shiryawane, Maya finta dada ta kama ta d’an goge kwallar fuskarta “ oh ni ‘yasu , gashi ya farka , Kema Allh ya bayyana ki tahura ta , Allah Yasa kina hannu na gari, nayi musum (missing) d’inki wallahi,Allah ya bayyana ki duk inda kike “, bata ‘karasa zancanta ba Sabida fashewar abu da suka ji, gabaki d’aya maida kallansu sukai wajan , ba komai bane ya fad’i face kantamemiyar wayar king, idanuwansa gabaki d’aya sunyi jajur lokaci ‘kan’kanin, kamar wani zaki ya nufi dada, jijiyoyin kansa gabaki d’aya ta mi’ke , sam ya manta wacece a gabansa, babban glass din dake kusa dashi ya buga hannunsa da ‘karfi har saida hannunsa ya fashe glass d’in ya tarwatse, babu Wanda be tsorata da yanayin da king yake cike ba , da ‘karfi ya furta “ ina matata?”. 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 07041879581 MSS LEE 💖 BOOK 2 Page 5&6 Da Sauri Abeey ya nufi king da jini ke zuba a hannunsa, idanuwansa sun ‘kara rinewa, kallan dada kawai yake da tafi kowa firgita , a zuciye ya ‘kara furta “ ina matata ?”, yanxu ma babu Wanda ya iya amsa masa, Abeey na ri’ke hannun Ya fusge ko kallansa be yiba , dada ya nufa kamar zai tsakota, ya ‘kara furta “ ina matata?”, yanxu kam dada rud’ewa tayi ganin yadda ya canza mata kamar ba shiba , itama sai ta ‘kara rud’ewa har tana bugewa sabida yadda tayi baya baya kamar zata fad’i abeey yayi saurin tarota, duk da haka king be hakura ba ya ‘kara nufarta fadan fadan , gabaki d’aya idanuwansa sun rufe , zai ‘karayin wani maganar Abeey ya d’auke shi da mari, azuciye ya juya kan abeey,jijiyoyin kansa na ‘kara Tashi, shi kansa Abeey da yayi marin saida yayi danasanin marin nasa , lokaci d’aya yaji shakkar d’an nasa, kallo d’aya king yayi wa abeey ya nufi kofar fita ko takan wayarsa be biba , gabaki d’aya ukhti da ummey ‘ko’karin tsayar dashi suke musamman ydda Jinin hannunsa yake ‘kara zuba, doctor d’in da ya shigone yana ciwan king, ‘kokarin dakatar dashi doctor yayi, shima king ya d’auke fuskarsa da mari, yana fitowa zaki yabi bayansa cikin sauri ganin yadda ransa yake a had’e , da gudu ya bud’e wa king mota suka bar hospital d’in, tunda ya shiga cikin mota idanuwansa suke a rufe har suka ‘karaso cikin gida, Daidai part d’insa zaki yayi packing, kusan 5 minutes idanuwansa suke a lumshe , cikin kakkausar muryasa ya furta “ Me ya faru?”, sanin ba a ‘bata masa lokacine yasa zaki labarta masa abunda ya faru, tunda ga accident d’in da yayi har zuwa ‘batan Tahee, da yadda aka bincika ba a sameta ba, har kama sojojin da yayi saida ya sanar masa, lokacin da king ya bud’e idanuwansa shi kansa saida ya tsorata da ya nayinsa, gefen wuyansa wata Jijiyace ta fito masa , door d’in kofar ya bud’e tare da sakko da’kafarsa , cikin Sauri sauri ya shiga Cikin building d’in nasa kamar yana so ya gasgata abinda yaji da kun nansa “ Almost a month ?, itama ya rasata kamar yadda ya rasa shi”, tafiya ya soma yi cikin falon da yake da d’an duhu, da ‘karfi yake furta “ No hakan bazaiyuba, I don’t kiss them , bazan iya ba , my wife , my baby, Innalillahi wa inna ilaihi raji’un “, yadda zuciyarsa take bugawa da sauri sauri ne yasashi yin baya , ga wani irin jiii da yaji yana neman kayar dashi, wani show glass da ya turene ya fashe gabaki d’aya akasa , muguwar yan kan da yayi sai faman zubar da Jini yake, gabaki d’aya Wajan ya baci, saitin zuciyar sa ya dafe, yana rintse idanuwa, bai da mu da yadda Jini ya ‘bata saba , tsugunnawa kasa yayi tare da runtse idanuwansa , da sauri abbey dake shigowa ya nufi inda yake , idanuwansa sun ‘kan’kance kamar yayi wa king kuka haka yake ji, araunane ya furta “ Am so sorry Tahnoon, Allah yayi bazamu ganta yanxu ba , but har yanxu ana kan bincikenta , nasan duk lefi nane da na sani lokacin da zamuje asibitin har da ita, kayi hakuri..” rufe wa abeey baki yayi tare da sakar masa kyakkyawan murmushi, kyakkyawan murmushin dake d’auke da abubuwa masu yawa a ciki, yadda idanuwansa sukayi mugun canzawa ne yasa be kalli abeey ba , ya kara sakar masa wani saban murmushi “ ba laifin ka bane Abeey, I lost Akhieeee for long time, yana sona sosai, and now I lost my wife again, and also her baby?, No Abbeey, tabbas a wannan karan abunda ya faru had’I, I don’t need anyone now , duk Wanda na tabbatar da sa hannunsa, I swear Abeey ko wanene bazan ‘kyalesa ba, the accident, and also ‘batan matata duk zan bun cika ..” rufe masa baki abeey yayi, “ ka dena fad’an irin haka , bana jin dad’i Allah ya ji ‘kan muhammad, na ro’keka da Allah da manzan sa karka yiwa kanka illa, tun lokacin da kayi accident dinnan Ummey bata bacci sosai, bata cin abinci sosai, kasan halin samreen idan ta sawa kanta abu, tana tunanin zata rasaka kaima , na ro’keka ka kwantar da hankalin ka ko suma nasu zai kwanta “, murmushi ynxu ma king ya saki be ce wa abeey kuma ba ya nufi stairs , a Jiyar zuciya Abeey ya sauke kafun ya kira sumayya ta gyara Inda glass d’in ya baci, gabaki d’aya falon ta had’a ta gyara , sai gashi ana shigo da kayan abincin daga part d’in Mamy da momy, su firdausi na shigowa dashi bayansu kuma samreen ce itama d’auke da wani ‘karamin tray a hannunta , kallan abeey tayi abun tausayi murya a hankali ta furta “ Abeey yana ina ?”, yana sama , ki bashi 20 minutes sai kije and please ki tabbata yaci abincin sannan ki masa dressing d’in hannunsa, Nima zan dawo nayi baki, jinjina masa kai samreen tayi sai da dau kusan mintuna 30 tukunna sannan ta nufi saman d’akinsa, gabaki d’aya ya faffasa glass da yawa na d’akin, sosai ya har gitsa d’akin yana zaune kan sofa idanuwansa a lumshe Jini na ta zuba daga hannunsa , da sauri samreen ta ajje tray d’in hannunta, da ‘kyar take wucewa Sabida in mutum be kulaba zai iya jin ciwo, first aid box ta d’auka zata rike hannunsa ya fincike, ‘kara ri’ko hannunsa tayi ya ‘kara fincikewa, a karo na uku da ta ri’ko hannunsa zai fuske itama a zuciye ta daka masa tsawa, kallanta yyi da mamaki gnin hawaye a fuskarta sai kuma cikin sanyin murya ta furta “ Dan Allah ka tsaya ba danni ba “, kallanta yayi be ce mata komai ba har ta gama dressing d’in ciwansa,tray d’in abincin ta d’auko shi kuma ya mi’ke tsaye zatayi masa magana ya ‘barar da tray d’in abincin, a zuciye cikin d’aga murya ya furta “ get out of my room" da mamaki samreen ta kallesa hawaye a kan fuskarta, “ Ni kake cewa na futar maka a d’aki? Yayi kyau , zan fita daga d’akin ka bani 10 minutes “, bata jira amsar saba ta fara gyara d’akin yana tsaye shima dafe da goshinsa, tana cikin gyarawa kwalla ta caketa da har saida tayi ‘kara da Sauri ya nufeta zai ta’basa ta dakatar dashi” kana ka kuskura ka tabani, kayi abunda ka keso “ Tana gama fad’ar hakan ta nufi kofa da niyar fita ya ri’ko hannunta “ Ukhtii why please? Zuciya ta ba dad’i, I’m feeling lonely, ina jin kad’ai ci, ina ji kamar….”, rufe masa baki ukhtii tayi itama hawaye cikin idanuwanta” komai yayi zafi maganinsa Allah, karka damu jikina yana bani zata dawo, zaku haifamana baby da yawa , ummey da abeey zasu zama grand parents, dada zata zama grand grand ma , ummey bata ci abinci ba tun jiya na ro’keka ka kwantar da hankalinka ko natama zai kwanta kaji?” Kanshi ya jinjina mata, itama saida yayi mata dressing d’in hannunta kafun ta bar d’akin cike da tausayinsa. ************ ********************* A ‘bangaran Abeey kuwa babban Amininsa tun na ‘kuruciya ne yazo duba king, sabida tafiyar da yayi kafun al’amarin ne yasa bezo ba , Abbey yana zuwa falourn sa ya tarar da Aminin nasa , kamar yara haka suka rungume juna , ba kowa bane face Alhaji kabeer, gefenshi kuma khaleed ne , shima hugging din Abbey yayi , cike da alhinin abunda ya faru, kallansa Alhaji kabeer yayi” ban ji dad’in abunda ya faru da son d’ina ba ,shiyasa nace dole na zo na duba shi da kaina dan nasan halinka kamar yadda ka’ki zuwa d’aurin aure na dukda nasan kana da babban dalili, to wannan karan dole a ‘kara d’aura zumunci, suma iyalina insha Allah wata rana zan kawo su,” murmushi abeey yyi “ baka canza ba har yanxu , ina zahra ta ? Nayi kewar ‘yata “, gaishe Abeey Khalid yayi, Daidai lokacin da ilham take shigowa falourn bakin ta d’auke da sallama , gaishe da Alhaji kabeer tayi , kafun ta gaishe da khaleed da ya tsareta da idanu, a fakaice ta dalla masa harara da yasakashi sakin murmushi, tana fita Alhaji kabeer ya furta “ kamar ilham ? “ Aushe baka manta sunayensu “ cewar abeey “ tana zan manta sunayen ‘yayana” tana fita da munti biyar khaleed ya mi’ke gabaki d’aya kallansa sukayi , “ zan d’an sha iska a waje ne , kafin king ya fito” jinjina masa kai sukayi a tare , ajiyar zuciya ya sauke shima kafin ya fito daga falourn, yana fita ya nemeta ya rasa gabaki d’aya bata filin Wajan, ‘karamin tsaki ya saki, tare da bugun ‘kafarsa har zai juya sai ya hangota tafito daga part d’in su zata nufi na dada da sauri ya ‘karasa inda take , d’aure fuska ilham tayi shikuma ya sakar mata murmushi “ kinyi kyau “, banza tayi dashi zata wuce ya dakatar da ita “ me yasa kike haka ? Nasan kin sanni , inaso muyi magana “ sai yanxu ta gane fuskarsa sosai , a hankali tace “ yaya khaleed ?”, oh da baki ganeni ba? , kai ta d’aga masa , ka canzane naga ynxu har d’an ‘kiba da kumatu kayi shiyasa ban gane ka ba sosai , sai anjima “, saurin me kike ? Ba komai , cewar ilham ,” amma kike guduna?” A hankali ta furta “ kayi hakuri “ kai ya jinjina mata kafin ya mi’ko mata kantamemiyar wayarsa “ samun phone number d’inki akwai maganar da zamuyi”, ba musu ta saka masa number d’in tai masa sallama ta bar Wajan, murmushi khaleed ya saki yana bin bayanta da kallo shi kadai yana sakin murmushi, king da ya hango ne yasashi sakin murmushi duk da yadda ya ga fuskar sa a had’e ba fara ‘a yasan daman za a rina , duk da yanayin da king yake ciki hakan be Hanasa hugging d’in khaleed ba kamar yadda shima khaleed d’in ya yi , fuskarsa d’auke da murmushi ya furta “ sorry dude “ be ce masa komai ba ya jinjina masa kai, tare suka nufi falon abeey, Alhaji kabeer na ganinsa shima yayi hugging d’insa “ my son? Ya kake? Ya jikinka? Take heart komai zai daidaita please bana san ganin ka cikin wannan yanayin”, shima king bece masa komai ba bayan gaisuwar da ta had’asu , minti 5 ya mi’ke zai fita khaleed yabi bayansa direct part din ummey suka nufa , gabaki d’aya jiyai yana bukatar mahaifiyarsa yau ko tunanin Ammey be yi ba , ummey na ganinsa shida khaleed ta saki murmushi , shima khaleed na ganinta yayi hugging din ta “ ummey nayi kewar ki sosai da sosai “, wani murmushin ummey ta saki tana kallan king “ Nima nayi kewarka sosai my son “ Ni kuma fa?” Cewar samreen da ke fitowa, murmushi yasakar mata “ Ukhti waya isa ya manta dake kin manta kece ta gaban goshina “ hararar sa tayi , kana dai guduwana sabida nace Kayi aure ko? “ kai ya d’an sosa kadan “ karki damu ankusa insha Allah “ Allah yasa cewar ummey. King na zaune ba abunda yace mikewa ummey tayi batace komai ba ta kama hannunsa zuwa dinning, mamaki ne ya kamasu samreen , ukhti har da yi musu vidoe ganin abun mamaki, abunda ummey ta dad’e batayi ba , da kanta ta zubawa king abinci, shima mamaki ne ya kamasa Amma be nuna hakan ba, mamaki be gama kamasu ba sai da ummey ta d’auki spoon zata bawa king abinci a baki da kanta , ukhtii harda tsallan murna ita da khaleed kamar wasu yara suka fara musu vidoe , murmushi ummey ta sakar wa king kamar wani ‘karamin yaro ta furta “ haaw” bud’e bakinsa kuwa yayi ummey ta fara feeding dinsa, 5 spoon yayi ya d’auke face dinsa amma ummey ta hanasa Tashi saida ta tabbatar yaci sosai , shima king saban abinci ya zuba ya d’auki spoon zai fara bawa ummey abinci, samreen kamar ta taka rawa Sabida ganinsu da tayi cikin wannan yanayi, d’an harararsu king yayi , itama ummey bata bi ta kansu ba ta kama hannun king sukabar Wajan . Ai khaleed kam saida ya taka rawa ko ba komai hankalin abokinsa zai kwanta. ✨✨✨✨✨✨ BUNKURE Tsawan wata d’aya abubuwa da dama sun faru cikin wannan yanayin, ciki har da islamiyya da Matan gidan Suka koma , da yamma kuma suna awarar siyarwa, idan babu makaranta kuma da safe suna yin Koko da ‘kosai, gabaki d’aya rayuwar gidan ta canza , babu Wanda zakaji yana fad’a da d’an uwansa, duk Wanda yyi sallah yanxu sai yayi wa oumma addua dan tayi musu Hallaci sosai , ta mayar musu da alkairi akan sharri, ta tallafesu a lokacin da suke bu’katar taimako, gabaki d’aya sun zanca , ga gyaran gida da Alhaji kabeer yake musu bayan kasuwa da ya saka mazan, duk wannan abun da ke faruwa oumma bata san yanayinsu. Har zuwa tsawan lokacin nan kuwa babu Dije ko bintalo babu alamarsu, Suma mutanan gidan gabaki d’aya babu Wanda ya damu da su, kullum Burunsu Allah ya ‘kara had’a kansu dan ba ‘karamin azabtuwa sukai wajan Dije ba ,yanxu ma marka d’an awara aka kawo musu matan gidun suke yi, kaka tabawa ma yanxu kullum cikin addua take wa oumma da muhammad, bata aikin komai sabida ciwan kafar ta , yan gidan ne Suke komai , babu nuna hantara a tsakaninsu, gabaki d’aya babu Wanda zaice akwai wani abu da ya ta’ba had’asu , sai ma insunga mutum yayi ba Daidai ba suyi kokarin dakatar da shi nayi masa nasiha . ********* ************* ****************** AMMEY 👺👹👹👹👹👺……. Lokacin da Ammey ta samu labarin farkawar king zaucewane kawai batayi ba , a har gitse ta shiga cikin d’akinta tana neman zoban tsafinta, bata Ankara ba taji ansha’ko wuyanta ta baya an bugata da ‘kasa, bata Ankara ba taji an ‘kara sha’ko wuyanta, mutumin da suke magana kwanaki ne yanxu kamar kullum fuskar sa a rufe , cikin ‘bacin rai ya furta “ kikace zaki kashesa kafin farfad’owarsa, me yasa kike ‘ko’karin ‘Bata mana aiki ? , ya mukayi dake ?karde kin fara tausaya musu?” A wahala Ammey ta fusge kanta daga sha’kar da akai mata,” karka ‘kara sha’keni haka ? me ya kawo ka d’akina ? Ka fice ka bani waje” wata ‘yar iskar dariya ya somayi kafun ya fincikota ya turata kan gado, girgiza masa kai tayi “ karka matso Inda da nake “. ‘Dauke fuskar Ammey yayi da mari” kinaso kisan me ya kawo ni ko? Yanxu zaki ga aiki da cikawa ai “ yana kai ‘karshen zancenta ya hau kan Ammey duk yadda taso turesa abun ya gagara, shima cike da mugunta ya fara faffarkewa Ammey kayan cikinta, be tsaya bi ta kanta ba ya shigeta da mugun ‘karfi cike da mugunta, wata gigitacciyar ‘kara Ammeey ta saka Sabida azabar da taji amma duk da haka be saurara mata ba , cike da mugunta Yake binta, saida ya tabbatar bazata moruba ya mayar da wandan sa ya ‘bace gabaki d’aya inda Ammey take Jini ya ‘bata wajan dan ba ‘karamin ‘barna ya mata ba dukda kasan cewar ba yau suka fara ba, amma yau ko sabuwar amarya 🤣( Allah shi ‘kara Ammeey 🤣🤣😂). ✨✨✨✨✨✨✨ Kwanan khaleed biyu a lagos ya fara shirye shiryen komawa Abuja , already alhaji kabeer ya tafi shi tun aranar, sosai khaleed da king suka saka bincike tahee har yau babu ita babu alamar ta , gabaki d’aya ya canza ya koma asalin king d’insa mara fara’a , da surutu, tsakanin su ummey da abeey sai aka rasa wanene yafi kula da king, hatta su momy da mamy ba a barsu a baya , uncles dinsa ma sosai suka bada rawar ganin Wajan bincikar Inda tahee take, aunty ma tazo ta duba sa lokacin Amrah taje kidan su batasan da farkawarsa, Ammeey ce kuwa har yanxu bata shiga ba dan acewarta bata da lapiya, hatta abeey sai da yazo dubata amma bata ko ‘kafar king bata gani ba , dan har yanxu ko ‘kwakkwaran tafiya batayi sosai Sabida yadda ta ke tafiya kamar ‘yar kaciya,kowa na gidan yazo dubata banda king da hankalinsa yake kan iyalinsa. Karfe 2:30pm jirgin su khaleed zai Tashi, 12:20pm yana zaune falan dada , yana danna wayarsa su sumayya suka shigo falon, gaishe dashi Suka yi amma gabaki d’aya hankalinsa yana kan ilham , sanye take cikin doguwar rigar atampa, ta yi d’aurin zahra buhari, bakinta sai shinning yake , yadda yake kallan ilham yasa sumayya kallansa a fakaice tana danne dariyar ta da ido tanunawa firdausi, ka she mata ido ta tayi suka mi’ke a tare , kallan su ilham tayi” Ina zaku?” Danne dariyarta firdausi tayi kafun ta furta “ karki damu ynxu zamu dawo “ basu jira amsarta ba suka bar falon, da harara ta bisu zata mi’ke taji saukar muryarsa” please ko zan iya samun ruwa ?” Jinjina masa kai tayi kafun ta nufi fridge , ruwan ta d’auko masa had’e da lemo sai cup,tana ajje masa yace ta zuba masa kamar zatayi ihu haka ta zuba masa , “ kinyi kyau sosai kamar sarauniya”, da Sauri ilham ta kallesa zuciyarta na bugawa da sauri sauri, shima idanuwan nasa ya zuba mata, da Sauri ta d’auke nata , “nagode “, har yanxu be d’auke kallansa akanta ba , zata tafi ya furta “ please ki zauna” gabaki d’aya sai nutsuwarta ya d’auke ga bugun zuciyar da take samu , idanuwansa har yanxu akanta, waje ta samu ta zauna ba dan taso ba “ yanxu zan tafi, amma zanyi kewarki”yanxu kam gabaki d’aya ya gama kwancewa ilham notikan kanta, “ me yake nufi ?” Take tanbayar kanta , bata ‘kara sham mamaki ba sai lokacin da ya furta “ please ki kalleni ko zanji dad’i” kunya ce ta kama ilham kamar ta saka ihu, kujerar next to her ya dawo yana kallan yadda ta sunkuyar da kanta ‘kasa “ please baby kalleni “, yadda taji zuciyarta na tsanan ta bugu ne yasa ta mi’kewa zata gudu yayi saurin shan gabanta “ ba sai kin gudu ba ni bari na tafi tunda bakya bu’katar gani na, wani ‘karamin box ya d’auko ya ajje mata akan table , “ gift d’in kine wannan, please ki kulamun da kanki”, yana kai ‘karshen zan cansa ya soma tafiya, zuciyar ilham ce ta soma bugawa ga wani abu da take ji ‘kasan zuciyar ta ganin kamar be ji dad’i bane yasa ta zauna wa kan kujera tana bin ‘karamin box d’in da kallo, sumayya da firdausi ne suka fito daman ba tafiya sukai ba , cikin tsokana feedy ta furta “ please Baby”dariya summy ta saka itama kafin ta furta “ ki kulamin da kanki”, pillow ilham ta d’auka ta jefa musu, Wana ta suka ‘karaso tare da d’aukan box d’in zasu bud’e tayi saurin fusgewa , da ‘karfi ta furta “ banasan gulma”, tafawa summy da feedy sukai lokaci d’aya ganin yadda ilham ta gudu. 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 07041879581 Mss Lee💖 Book 2 Page 7&8💖 Kai tsaye khaleed yana fita daga part d’in dada part d’in ummey ya nufa itama ya mata sallama bayn gift d’in da ta basa ya kaiwa zahra, mahma ma da dada gabaki d’aya sai da suka bawa zahra gift, king baya gida shiyasa basuyi sallama sea ta waya, lokacin da zai tafi sai kallan part d’insu ilham yake ko zai ganta amma babu ita babu alamarta, murmushi ya saki lokacin da ya tuna kunyarta, ji yake kamar ya je part d’insu ya dubata amma yasan hakan ba meyuwa bane . 2:30pm na rana jirginsa ya tashi zuwa Abuja, 1hour 15mins ne ya kawosa Abuja , yana fitowa harabar Airport ya tarar da zahra na jiransa, hannu ta mi’ka masa kamar wasu friends sukayi shaking , fuskarta cike da farinciki ta furta “ Nayi missing d’inka yaya”. Nima nayi missing d’inki cewar khaleed , suna zuwa gida ya tarar da oumma ta had’a masa favorite food d’insa wato dambu da kuma zo’bo da yake matukar so, sun d’an ta’ba hira kad’an bayn ya bawa zahra gift d’inta kai tsaye d’akinsa ya nufa ya watsa ruwa, so yake ya runtsa amma kuma ya kasa Sabida muryarta da yake san ji, phone d’insa ya d’auka kamar zaiyi dialing wata number da yayi saving da MINE 💞 sai kuma ya fasa , sau biyu yana ‘ko’karin kiran wayar , daga karshe ajje wayan Kawai yayi yana lumshe ido , shi kad’ai yana sakin murmushi abunsa. *******Ilham ko data gudu, kai tsaye part d’insu ta wuce har mamy na tanbayarta lapiya amma bata amsa musu ba sai faman sakin murmushi take ita kad’ai , tana shiga d’aki ta kulle ‘kofar tare da kallan d’an ‘karamin box din brown colour meshegen kyau, yana bud’e wata sarki ce aciki sai faman walwali take yi ita kadai, zaro idanuwa ilham tayi sosai sarkar tayi mata kyau musamman Heart d’in da ke jikin sarkar ya fi komai d’aukan hankalinta, gaban mudubinta ta’karasa har Zata saka sarkan sai ta fasa , yar ‘karamar letter d’in dake jikin box d’in ta bud’e , wasu ‘kananan flowers ne Suka fara fitowa daga jikin paper ne me design din flower a jiki, kan gadanta ilham ta koma tana sakin ajiyar zuciya , letter d’in ta soma karantawa cikin zuciyar ta, daka ‘karshe ma pillow d’inta ta d’auka taba boye fuskarta ita kadai sai faman sakin murmushi take, lokaci zuwa lokaci tana kallan sarkar da ya bata da kuma letter d’in, gabaki d’aya yinin ranar da tunanin khaleed ta yini , ko me zatayi sai ya fad’o mata arai musamman lokacin da yake furta “ ki kulamun da kanki”, rufe idanuwanta tayi gabaki d’aya tana tuno abunda ya faru d’azu, sai taji kamar bata kyauta ba, amma wani zuciyar na fad’a mata Daidai ne abunda tayi. ✨✨✨✨ karfe 9:00pm na dare gabaki d’aya familyn Nahyan suna falon dada banda king da gabaki d’aya ynxu baya shigowa part d’in ko wannan su, a wannan karan har da Ammeey a falon, duk Wanda ya kalli fuskarta zai san tana cikin damuwa, amma babu Wanda ya kawo wani abune yake damunta sai canzawar king da kowa yasan tafi kusan ci dashi, hatta part d’in ta yanxu baya shigowa , abunda ya ‘kara tayar mata da hankali sabida ‘kullun maganin da bokansu ya bata, indea ba a cikin abinci tabasa ba nan da sati d’aya toh komai zai iya lallacewa, a binciken da tasa ayi mata akan tahee kuwa , hatta bokansu baya iya ganin komai a duk lokacin da yake bincike a kanta cikin abun tsafinsu, sai hasken da yake kashe masa idanuwa da tsoratar dasu, bakomai ne yafi d’aga mata hankali ba musamman dawowar tahee da boka ya tabbatar masu, sannan a wannan karan tabbas idan ta bari tahee tashigo cikin gidan komai nata data d’au shekaru tana ginawa zai rushe rushewar da bazea ta’ba gyaruwa, duk da maganar boka ya girgizata sosai amma duk da hakan bata karaya ba , sannan tayi Al’kawarin bazata ta’ba barin tahee ta cikin familyn nan ba , yanxu burunta kawai king yaci gubar da bakan tsafinsu ya bata, shiyasa ta fakaice da had’a wa duka family d’in dinner , sannan ta had’awa king favorite kunun a yarta da ta zuye duka gubar a ciki yanda ci d’aya zai tsinka masa komai na jijiyoyin jikinsa. Amma gabaki d’aya babu king babu alamar sa gashi ta hana kowa ta’ba zoban da tayi masa, sau hud’u Ammeey tana gwada kiransa a wayrta , amma ko sau d’aya be d’aga mata kiran ba, hakan ba ‘karamin ‘bata mata rai yayi ba , har wajan 9:30 king ne shigowa , kowa ya damu da’kin shigowarsa Amma duk sun masa uziri, gumine ya soma gesowa Ammeey ganin saura mintu na kudun ayar data sawa magani ya canza zuwa launin’baki,rai a’bace Ammey ta d’auki kunun ayar zata tafi, gabaki d’aya mutanan falon kallanta sukai, murmushi tasakar musu cikin rarrabewar murya ta furta “ zan sa masa a fridge ne kafun ya dawo”, girgiza Mata kai abeey yyi, “ no karki damu ki dawo kawai kiyi zamanki “, a rud’e Ammey ta kallesa “ Dama akwai abunda nakeso na saka a ciki sai yanxu ya fad’o mun”, ki barshi kawai, cikin zuciyar Ammey kamar taje ta sha’kesa ta furta bazan dad’e ba yanxu zan dawo ai, gudun kar ya sake magana tayi saurin juyawa , lokaci d’aya momy da ummey suka bita da kallo, hakanan kawai ummey take jin kamar akwai abunda ya kamata ta sani , amma kasan cewar ta mace me ‘boye komai sai ta ajje zancen a gefe, wayar ilham ce ta soma ‘kara gabaki d’aya sai hankalin kowa ya koma kanta, ganin number ba suna ne yasa ta d’an mi’kewa “ Dama husna ce ta kira ni”, gida mta kai sukayi kafun ta wuce , kallan juna sumayya da firdausi sukai, da ido suke nunata Suma ‘kunshe dariyarsu. Saida ta tabbatar ta shiga d’akinsu ta rufe , alokacin kiran farko har ya katse, kafun wani ya sake shigowa kamar bazata d’auka ba , sai kuma ta d’auka bakinta d’auke da sallah, ajiyar zuciya taji an sauke ajiyar zuciya, gabantane ya soma fad’uwa jin anyi shirune yasata cire wayan a kunnan , still ba ayi magana ba , ‘karamin tsaki taja zata kashe taji ance mata “sorry “, da Sauri ta ri’ke wayarta dake neman fad’uwa ‘kasa dan sam batayi zatan shi bane , da ‘kyar bakinta ya iya furta “ yaya khaleed barka da dare ya hanya “, shiru be amsa ba, kara maimaita tayi nan ma be amsaba,hararar wayar tayi kamar ta kashe sai taji saukar muryarsa kuma “ I missed you “, shiru ilham tayi tana saurarar bugun zuciyarta, me yake nufi da maganganunsa,” Ba’amsa?” Ya tanbaya nan ma shiru tayi ta kasa amsa masa murmushi yasaki kad’an kafin ya furta “ shikenan, kula mun da kanki kinji? Good deary “ sea Kuma kit ya kashe kiran , bin wayar tayi da kallo kamar me jira ya ‘kara kira , ita kadai sai tsaki take ga wani irin feeling dataji yana tasoma ta tunda ‘kafarta har zuwa saman kanta, a gefe ta ajje wayar lokaci zuwa lokaci tana dubawa, a haka bacci ya d’auketa tare da wayar a hannunta. A ‘bangaran Ammey kuwa wani bakin cikine ya tokare mata ma’koshi , tana komawa part d’inta a zuciye ta jefarda jug d’in take a wajan ya fashe gabaki d’aya kunun ayar ya zube a’kasa , ko cikakken muntuna biyu be ba daga kalar kunun ya koma ba’ki ‘kirin dashi, sai a lokacin ta ankara da abunda tayi, cikin mummunan ta shin hankali ta d’ora hannayenta aka tana kwarara ihu ko damuwa da Ajiyata batayi, gabaki d’aya ta fita hayyacinta, zoban hannunta ta murza take a wajan ta ‘bace battttt. YOLA Cikin matsanan ciyar tashin hankali Ammeey ta bayyana cikin babban falonsu dake cike da kayan shirka , sabida tashin hankalin da ta shiga a wannan karan ko damu da kulle fuskarta batayi ba kamar yadda ta saba ,ragowar abokanan shirkar tata ko wannansu na zaune cikin jajan ‘kyalle daga cikin su zuwa ‘kaurinsu ko kaya babu a ciki, cikin kururuwa Abar kauna take kiran sunan gunkinsu, kusan sau uku be amsa ba kuma babu Wanda yayi magana cikin mutanan wajan, a na hud’in ne data kara kiran sunanta taji saukar tsawar da tunda Tashi ga cikin kungiyar ba a ta’ba yi mata ba Sabida ita d’in kullun me nasara a fagen aikinsu. Cikin kausash shiyar muryarta mara dad’in ji ta daka wa Abar ‘kauna tsawa da har saida tayi suman wucin gani, cikin muryarta mara dad’in sauraro rai a’bache ta kalli Abar’kauna “ kinyi sake , kinyi sake , kin yi saken da damar ki ta kubuce miki, tabbas kisaka aranki daga rana irin ta yau , ginin ma sarautar da kike ‘ko’karin kammala lawa ta rushe, rushewar da bazata sake tashi ba har sai kin dawo da yarinyar ta kikayi sanadiyyar barin ta gidan, tabbas Abar ‘kauna kina cikin tsaka , Sabida lalatawa dodan tsafi aikin sa, idan baki kashe sa nan da kwana bakwai ba , to tabbas yayi miki nisa hakan na nufin lokacin tonuwar asirin ki ya bude, dama d’aya kike da ita , ki dawo da yarinyar cikin gidan sannan ki bawa dodan tsafi Jinin ta dana cikinta, Idan ta dawo kuma zaki iya shiga kasada komai zakiyi kuma baze kara tasiri akanta ba , sabida tana tare da Jini guda hudu da kikayi kokarin rusawa, dawowarta kamar tonuwan asirinkine,ta ‘karasa tana sakin wata yar iskar dariya mara dad’in ji, lokaci d’aya wani ‘bakin hayaki ya cika falon tsawan mintuna kafun ya washe babu wannan Matar, wata iriyar kururuwa Ammeey ta fara a haukace kamar ta ‘babbiya, sam ta fita cikin hayyacinta, fad’i take sai na kashe ka , sai na ka she ka, gabaki d’aya bata jikin hayyacinsa , suma sauran mutanan zagayeta suka somayi suna wani irin surutai kafin lokaci taya gabaki d’ayansu su bace duka . ✨✨✨✨ A ‘bangaran king gabaki ya ‘kara sauyawa sama da ydda aka sansa a baya , kwata kwata baya murmushi , baya fara’a sannan baya yiwa kowa magana sai dai ya zuba maka narkakkun kyawawan idanuwansa masu ladaftar da mutum,gabaki d’aya ya sauya ya zama wani irin Miskili na bugawa a jarida , ga saurin zuciya da ya koya , hatta abinci yanxu baya sai ummey ko samreen sun soma kusa sannan da d’ar zaici spoon kad’an , yana shiga sabgar kowa a gidan shiyasa kowa ya kara shiga taitayinsa, lokacin da Amray ta samu labarin farfad’owarsa da murnarta ta dawo gidan, alokacin dada ta sa masa kukan sai yasha furar da ta dama masa ganin baya cin komai hatta furar da yake mugunso, cikin iyayi Amrah ta shiga cikin falon,sabida tsananin farincikin da ta shiga lokacin da taji labarin ‘batan Tahee , shiyasa tazo da confidence d’inta bayan kwallin da mamanta ta bata acewarta Indai suka had’a ido da king daga lokacin ta mallakeshi komai zata iya sasa, tana shigo wa kai tsaye ta sauke idanuwanta da suka ji kwalli , Daidai lokacin da yake d’ago idanuwansa, cikin sa’ a idanuwanta suka shiga cikin nasa , da Sauri ta d’auke nata idanuwan sabida wani irin abu daji ya shigeta, lokaci d’aya farin ciki ya kamata ganin sun had’a idanuwa dashi, cike da kwarkwasa ta ‘karaso inda yake mo motsawa beyi ba , kai tsaye kan kujerar da Yake ta nufa tare da zama daga gefensa, be ce mata komai ba , har ta rangwafo daniyar ta’basa , bata Ankara ba sai saukar gigitaccen marin da yasaka kunnuwanta toshe wa lokaci guda , ga wani jiri jiri da ya soma d’i barta bashiri ta saki wani gigitaccen ihu Sabida azabar marin da taji, bata gama jin zafin marin ba ta sake jin saukar wani lafiyayyen marin dama da hagu , a wannan karan ihun da tayi saida mahma da dada sukaji, da sauri suka fito alokacin da ya ‘kara dagewa ya tsinka mata mari, d’an kwalin kanta ya dam’ka da karfi dayasa attachment dinta Fito wa , wani irin ball king yayi da ita , mahma da ya fara bata tsoro da sauri tazo zata ri’keshi yanda yake a zuciyen nan bai san lokacin da ya hankad’ata ba itama , a rude dada ta la’be bayan kujera cikin tashin hankali ta fara danna wayar ta da’kyar ta lalubo number abeey sabida rud’ewa, lokacin yana falonsa shi da ummey, da sauri suka nufi part d’in dada , lokacin da king ya ‘kara saukewa amrah kyakkyawan marin da se da hannunsa ya Fito a fuskarta, cikin ‘bacin rai da kausash shiyar murya dake firgita mutum ya daka mata tsawa “ minti biyar na baki daki bar gidan nan, wallahi ko me kama da ke na ‘kara gani a cikin gidan nan , sai dai uwarki ta sake Haifo wata, Tashi kiban waje “ cikin azaba da fitar hayyaci amrah ta mike da kyar ga hawaye da majina dasuka ‘bata mata fuska, ko bin takan jakarta batayi ba ta arta a guje ko tunanin inda zataje batayi , cikin tashin hankali ta fita daga cikin gidan tayi tafiya me dogon zango rai a bace ta d’auko coccine me tafawa zuga, tun tana tuni har ta soma ganin biyu biyu amma bata hakura ba , ta cigaba da shaye shayenta tana tu’ki , bata Ankara ba wata mota tazo ta bangajeta, sai motar tata ta soma kifawa kanta ya bugu Sabida abun shaye shayen da ta Shaka me ‘karfi d’aya sata yin accident d’in. ***** Abeeey na zuwa falon dada rai a ‘bace ya wanke fuskar king da mari, ummey ba hatta dada da mahma saida sukayi suman tsaye shima king a zuciye ya d’ago fuskarsa ya kana kallan abeey “ Ni ? Mari?” Shima sai alokacin abeey ya kula da abunda yayi, amma be nuna ba sai ma had’e fuskarsa da yayi , cikin sama sama da murya ya furta “ Ina iliminka yake da zaka saka hannu ka mari mace? Akan Wana dalili zakace karta kuskura ta ‘kara dawowa cikin gidan nan, kar ka manta wannan gidan gidanane da kudina na Gina sa , baka da hurumin da zakace kar Wanda yafita “, murmushi king ya saki da ya bawa kowa mamaki, “ really? Gidan ka ko? Toh kasani zan bar maka gidan naka inyaso ko wa kake so sai ya shiga “, zamewa ummey tayi a kasa ta kasa cewa komai, mahma ce tayi saurin shan gabansa ganin yana kokarin tafiya hankali a tashe “ No son , please ka kwantar da hankalin ka , let’s talk”, gabaki d’aya idanuwansa ya rufe ransa yayi mugun baci, cikin murmushi da bekai har zuciya ba ya furta “ why ? Me zan zauna nayi? I lost my beloved brother ? I lost my wife ? My baby ? And mahaifina yana fad’a mun gidan sane , to ki fad’a masa zan bar masa gida, long time ago na rasa farin cikine ? Menene yayi saura?nothing”, yana kai zancensa ya soma tafiya , mahma zata dakatar dashi abeey shima cikin daka tsawa yace ya rabu dashi ya tafi, tashin hankalin da ba ‘a sa masa date , sai a lokacin dada da tayi suman tsaye ta saka sallallami , ganin king yanar part d’in, cikin kuka ta furta “ yanxu zayyadu baka da imani? Duk halin da yaran nan yake cike bazama lalla’basa ba shine zaka kore sa ? Toh wallahi bari na fad’a maka , idan har tahanuni na yabar gidan toh Nima na barshi kenan “, da mugun shock abeey ya kalli dada da ranta ya baci itama cikin daka tsawa tace wa mahma ta d’auko mata mayafinta , dole mahma ta d’auko ganin yadda ran dada ya baci, Allah sarki ummey abun tausayi ta kasa cewa komai sai binsu da kallo da take . Kafun Abeey yasa a dakatar da king har ya fice daga gidan a zuciye, hakuri ya fara bawa dada da tace itama tafiya zatayi, da ‘kyar suka samu suka shawo kan dada har da ummey dake bata hakuri, akan cewa ran sane ya ‘baci Amma zai dawo insha Allah. Gabaki d’aya a cikin gidan babu Wanda y samu labarin futar king har Ammey data ci alwashin ganin bayansa a yau, har dare kuma king ne dawo ba hakan ne yasa kowa yaji abunda ya faru, hatta Ammey sai a lokacin ta Samu labari take a Wajan wani irin zazzafan zazzabi ya kamata da ko motsi bata iyayi Sabida bakinciki da yake kokarin kashe ta . ***** king kuwa rai a mugun bace ya bar gidan cikin mugun speed ko zaki be d’aukaba, kai tsaye airport ya nufa cikin jirginsa , ba ‘bata lokaci jirginsa ya Dashi zuwa America. AMRAH Da kar aka samu wasu suka kira police station Sabida hatsarin da ya faru , suma suna zuwa aka dauki amrah sai asibiti, likitocin ne suka bukaci ganawa da yan uwan Amrahn amma aka sanar musu basu san kowa nata bai wayarta da ita mata lallace , Take a wajan likitoci suka tabbatar musu da matsalar kwakwalwa da amrah ta samu sabida mugayen kwayoyin da take ta ammali dasu . Har washe gari babu king babu alamarsa sai a lokacin hankalin abeey ya kara tashi, d’aya daga cikin masu kula da jirginsu ya kira , abakinsa yaji labarin tashin jirgin king , kuma babu Wanda yasan wata kasa ya tafi, take a Wajan shima Abeeey ya yanke jiki ya fad’i. Sau da yayi 2 days yana jinya , tun suna sa ran dawowar king harkowa yashiga damuwa , lokacin da khaleed ya kira ilham , kuka ta fashe masa dashi cikin tashin hankali ya tanbayeta me yafaru gabaki d’aya ta kwashe ta fad’a masa da ‘kyar ya kwantar mata da hankali akan cewa zai ne mosa. Babu inda khaleeed be duba ba da binciken da yasa ayi masa ko akwai Wanda yaga king amma kowa ce masa yake ya dad’e basa king a cikin idanunsa ba . Kowa da abunda yake sakawa cikin zuciyarsa ummey Sosai ta shiga cikin damuwa , samreen ce kawai me kwantar musu da hankali dukda natan ma a tashe yake . Ammeey tun tana irga kwanaki ko zai zawo har sati d’aya ya zago hakan yasa har ciwo sai datayi kowa ya d’auka sabida barin king gida amma tsantsan tashin hankali ne ya kwantar da ita . Saida amrah tayi 2weeks a hospital kafun mamanta ta samu labarin hatsarin da tayi cikin tashin hankali da doctor yace dole sai ankai amrah asibitin mahaukata sabida anan za afi kulawa da ita , ba ydda mommynta ta iya dole haka ta hakura aka kai amrah asibitin mahaukata, suma lokacin da familyn NAHYAN suka samu labari gabaki d’aya sai da Suka je dubata banda Ammeey da ynxu ta zama shiru shiru abun duniya ya dameta. Haka rayuwa ta cigaba da kansancewa cikin familyn , kusan kullum sai khaleed ya kira ilham , tun yana boye mata feelings dinsa har ya fito ya furta yana santa. Sosai suke zuba soyayyarsu wani lokaci har hira suke da zahra idan ya kirata har maganar taje kunnan dadi, sosai kuwa sukai farinciki da hakan Watanni sun cigaba da shud’ewa har lokacin king be dawo gida ba , sai 5 month suka san yana America dukda kome suke ciki yana sane amma ya sharesu, ba yadda ba ayi dashi ya dawo ba Amma yaki , a cikin wannan lokacin ne Abeey yasan da soyayyarsu ilham shima sukai hakan yayi masa dadi. ✨✨✨✨✨✨ 4 YEARS LATER 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 Mss Lee 💖 BOOK 2 Page 9 💖 4 YEARS LATER Abubuwa da dama sun fara cikin tsawan wannan lokaci , har zuwa lokacin kuma babu Wanda ya ‘kara samun labarin Tahee sai addua da kullum ake mata, gidan sai ya ‘karayin shiru babu Tahee babu king,Amrah da king ya Koreta sai da tayi good 2 years a gidan mahaukata kafun Allah ya bata lapiya amma duk da hakan ta d’an tabu , lokuta zuwa lokuta tana abu kamar na marasa hankali, yan kiran sunan king akai shiga taitayin take har lokacin kuma bata ‘kara kuskuran koda tako ‘kafarta gidan ba ,ga wani irin abu da take ji lokaci zuwa lokaci a ‘kasan ta na mata zutt zutt Amma babu Wanda ta ta’ba fad’awa sai ma harkar less da ta koma ita da wata friend d’inta ,kullum suna manne da juna ko basa waje d’aya toh kullum suna cikin yin vidoe call. Cikin Shawan shekarun nan wani irin soyayya khaleed yake yi shida ilham da basa kwana d’aya basuji muryar zunansuba , tun ana d’auka abun da wasa har saida khaleed ya nufi dady da cewar a Aura masa ilham . Dady ba ‘karamin farinciki da mamaki yashiga ba , sosai kuma yayi farincikin hakan . Zarah ma yanxu an zama big girl duk wannan surutun da rashin jin ta dena su da wuya kaji surutun ta inva a wajan oummey da ta zame musu tamkar uwa ba , me share Masu hawaye , sau da dama idan aka gansu tare sai a yi tunanin oumma ce ta haifeta musamman gogewa da oumma ta ‘karayi sosai ta zama babbar hajiya , ayanxu bayan mall din da take Dashi ta ‘kara gida guda biyu da gida guda uku dayake duk mallakinta,sai kuma filayen da take siyarwa, babu Wanda zai ga oumma yanxu yace Itace a baya sabida yadda kudi da kwanciyar hankali ya zauna mata dukda har yanxu tana yiwa ‘ya’yanta addua kuma batacire rai a sake ganinsuba, lokaci zuwa lokaci tana zuwa bunkure kuma , yanxu wani irin zumunta suke yi abunsu kamar babu abunda ya ta’ba faruwa a tsakaninsu , lokaci zuwa kuma suma suna kawo mata ziyara har Abuja sannan tasa a mayar dasu gida, ynxu gabaki d’aya sun sauya suma kamar basu ba , iya rufin asiri yanxu Allah ya basu sai faman cikawa da Imani , gabaki day sun mata da Dije ko wata bintalo da dad’ewa sun kira sabuwar rayuwar da oumma ta zama sanadin farin cikinsu.Ganin yadda khaleed yake bawa oumma labarin ilham kullum Yasa oumma tanbayar dadi akan auransu , shima yayi na’am da barin alokacin har ya samu Abeey da zancan, ba ‘karamin farinciki Abeey yayi da hakan ba , amma duk da hakan be yanke hukunci ba saida yakira uncle musaddiq da har da kukan sa Sabida farinciki, babu dad’ewa aka saka auren 7 month , a yanxu gabaki d’aya biyan saura 3month, duk lokacin da sukai waya da ilham sai yace mata lokacin yayi tsawa zaije ya zamu Abeey yace a rage , da ‘Kyar ta lallashe sa akan saura ‘kan’kanin lokaci Amma dukda hakan baya hana gobe ya ‘kara ce mata lokaci baya sauri. A ‘bangaran king tun bayar ‘batan Tahee gabaki d’aya ya ‘kara sauyawa kwata kwata baya zama a gida , saida yayi 3 years be je ko da Nigeria ba ,babu Wanda be kira ya lallashe saba Amma gabaki d’aya ya sharesu hatta small mom dake Dubai itama sai da takira sa amma babu abunda ya canza ganin ummey da dada na ‘kara shiga cikin damuwa yasa Abeey da kansa yaje U.S.A ya lallashesa akan ya dawo gida , still dukda ya dena fushin amma yace bazai iya zama babu matarsaba idan ba haka ba zai iya samun ciwan zuciya , sosai abeeey ya tausayawa son d’in nasa shiyasa be takura masa akan sai ya dawo ba , shima koda ya koma gida kwantar musu da hankali Abeey yayi , amma kusan kullum sai sun kira sa , dukda rashin magana da ya koya hakan baya hana in yana free ya kira ummey ko abeey, wani lokacin kuma ya kira dada da kullum sai tayi masa adduar Allah ya bayyana tahura . AMMEEY Cikin kwana bakwai d’in da abun bautar su ya bata ba ‘karamin shiga damuwa da rud’ani Ammey tayi ba , ganin har lokacin king be dawo ba , sosai ta shiga matsanan ciyar damuwa , da ‘kyar ta iya dannewa take kiran sa ko dan tace masa ya dawo amma itama amsarsa kamar ta sauran ce , “ he can’t, bazai iya rayuwa babu matar saba “, wannan kalla tasa ba ‘karamin sosa ran Ammeey yayi ba Amma cikin bariki itama ta nuna damuwarsa tare da baza goyan baya . Sosai ta saka ayi mata binciken a nemo mata tahee cikin SIRRI yadda zata kammala aikinta na ‘karshe amma duk magana d’aya ce ba a gantaba. Tun Ammeey na sa ran dawowar tahee har ta cire gabaki d’aya tare da shinfid’a sabuwar rayuwa acewarta abunbauta ya Mata ‘karya may be taheen ta dad’e da zama Matacciya shiyasa sosai ta saki ranta, kwarton ta da yake kulle fuska kuwa kusan kullum sai yayi sex da ita, ita kuma ko a jikinta ganin ta salwartar da mutanan da sukeso su zama cikas a rayuwarta, yanxu buri d’aya ne yayi saura ta cika, su kwashe gabaki d’aya dukiyar Abbey hatta ta king da ummey da suke hari sai kuma bayan Abeey da yafi komai tsaya mata arai da takeso ta kawar. **************** UNITED KINGDOM 🇬🇧 A wata mata shiyar budurwace so classy sanye cikin doguwar rigar material, farace kyakkyawa , hannunta na d’auke da siririyar fashion pose red colour , kantamemiyar tsadar wayarta ma pod d’in ta ma red colour ,cikin taku irin na wayayyiyar budurwa meji da kanta ta soma sakko wa cikin heels dinta shima red , agogon hannunta take dubawa tun d’azu, tana sakkowa daga steps ta soma kwalla kiran sunan “ momy kuna ina lokacin na tafi , nasan sister tana can tana jiran mu”, wani kyakkyawar baturan yaro ne ya fita daga wata ‘kofa cikin gudu gudu, yake furta “ My love , junior is hear “, kallan inda yaran yake tayi, tubarkalla Masha Allah , wani kyakkyawan yaro ne , sosai yake da kyau fari tass kamar a ‘bula Jini ya fita , sanye take cikin Red suit na yara da ya ‘kara yi wa kyakkyawar fuskarsa kyau, gashin kansa kuwa wani irin gyara akayi masa ne shegen kyau da ya kwanto masa har wajan goshinsa, d’an mitsitsin bakinsa pink colour sai faman shining yake , da Sauri itama matashiyar budurwar ta ‘karasa Wajansa, lokaci d’aya sukai hugging d’in juna , duk da hills d’in dake kafarta Hakan be hanata juyasa ba sai faman dariya yake , dimples dinsa na both side na lotsawa, fararan jerarrun hakoransa tass dasu. “Mimi?” Da Sauri matar shiyar budurwa ta juya , sai yanxu na ganeta sabida wani irin kyau da tayi gabaki d’aya ta canza ta zama so classy, yaron naganin guy din daya kira mimi yayi saurin sauka daga Wajan Mimi ya ruga a guje zuwa wajan guy d’in , shima hugging d’insa yayi cikin turanci ya furta “ Big Dady”, sai yanxu fuskar mutumin ta fito, bakowa bane face Yah moh , shima sosai ya canza ya zama wani kyakkyawan guy , sanye yake cikin wasu ‘kananan kaya shima , sosai kayan sukayi masa kyau . Murmushi ya sakar wa boy d’in “ you look so wow sweetheart “, kashe masa ido d’aya yaran yayi kafun ya ja masa kumatunsa “ and also you my Big dady”,suna tsaye momy da dady da Hutu ya kara rutsa jikinsu fitowa , gabaki d’aya ko wannansu tashi kalar d’aukan wankan , a wannan karan ma kyakkyawan boy d’innan wajan su momy da dady ya nufa cikin hausarsa da bata fitowa sosai ya furta “grandparents kun dad’e tun dazu muna jiran ku”, jan hancinsa momy tayi “ toh ai gamu mun fito sai mutafi ko ?” Kanshi ya jinjina mata kafun ya kama both hannunta dana Dady suka fito baban harabar gidan , motoci biyu kawai suka d’auka d’aya yah moh da Mimi , d’ayar kuma dady ne da kanshi zaiyi driving din sai momy da junior a gefenta. A hankali cikin tafiyar nutsuwa a mota suka hau kan babban titin da zai kaisu **The inner temple ** lokacin da Suka je mutane sai fuffuto wa suke daka ciki zuwa harabar filin Inda kowa zai had’u da family d’insa , da yawa daga cikin mutanan sanye suke da suit a jikinsu sai wig and gown na lawyers da ko wanne ya saka, fara dudduba sukai suna jiran Suga ta Inda zata fito tun suna sa ranganinta har Mimi tayi *kokarin kiranta a waya “daga bayansu sukaji wata daddad’ar siririyar murya ta furta “‘momy”, gabaki d’aya su lokaci guda suka juya zuwa inda muryar ta fito , kyakkyawar matashiyar budurwace ta a jikin karshe fara sol da ita , tsabar farin ta har yellow yellow jikinta yake , sanye take cikin suit ita ba’ka sai wig and gown dinta da ta ri’ke a left hand dinsa , fashion swag bag dinta ma nakegen hannunta na hagu black colour , sosai hill din data saka yafito da kyawun ‘kafarta , idanuwanta sanye yake cikin farin glass da kemar medical, siririyar cute lips dinta ya ‘kara fito tas dashi, duk da suit ne a jikinta hakan be nuna sura ko wani Shati na baiwar da Allah ya bata ba, da Sauri junior ya saki hannunta su momy yaruga wajan matashiyar budurwannan da kudi da jin dadi suka gama zama a jikinta, yana zuwa wajanta yayi saurin hugging d’inta, “ My love ! I missed you “, kyakkyawan murmushi ta sakar masa da ya ‘kara mata kyau lokaci guda both dimples dinta suka lo’ba, “ missed you too” cewar matashiyar budurwar tana sakar masa peck a goshi, inda su momy suke ta nufa cikin ta kunya na d’aukan hankali , tana zuwa ta rungume momy kafun ta koma kan mimi itama ta rungumeta , cikin jin dadi mimi ta furta “ Congratulations sis tahee , you’re now a barrister “, wacce aka kira da tahee da kalla da mugun shock , tabbas Itace Amma gabaki d’aya ta canza ta zama wata babbar mace meji da aji ga baiwar karatun da Allah ya bata na zama babbar Barrister, itama momy congratulations dinta tayi kafun yah moh da dady kowa yayi congratulations dinta, cikin farin ciki suka fara d’aukar hoto gabaki d’ayan su , junior ya ta’ba tahee kadan , kallan sa tayi da dara daran idanuwanta da suka ‘kara haske da kyau , alama yayi mata data matso, d’an rankwafo tayi batayi auneba taji saukar kiss a goshinta , cikin harshen turanci ya furta “ I love you mom”. 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 Mss Lee 💖 BOOK 2 Page 10 Da Sauri na ‘kara maida hankali na kan junior , daga nesa idan ka kallesa sak zaka ga tsantsan asalin balarabe, sai da ya matso da fuskarsa daidai inda tata yake kafun kamanninsa ya kara fitowa dukda kasan cewarsa yaro , amma sosai zaka hango tsantsan kamannin king, sosai suke kama , kamar tasu hartaso baci , banbancin shi junior har yanxu yaro ne , hatta yadda king yake kallan mutum haka shima junior yake , sosai suka d’auki pictures, sun d’anjima a Wajan kafun su kama hanyar komawa gidan bayan siyayyar da yah moh ya kaisu. Tahee na shigowa direct dakin ta tanufa sabida ba ‘karamin gajiya tayi ba , tana shiga wanka tayi kawai ta kwanta , amaimakon tayi bacci sai kawai ta fashe da kuka, Kukane take yinsa tundaga ‘kasan zuciyar ta , diamond ring d’inta da abun hannunta shima diamond da king ya bata take bi da kallo, lokaci d’aya kuma ta saki murmushin da dimples dinta suka lo’ba “ Ammi kin cucenii, kin rabani da farin cikina , why ? , me yasa “, ita kadai take tanbayar kanta,sosai take jin ‘kuna cikin ranta, yau ta kasance mata ranar farinciki da bakin ciki,sosai take sa’ke sa’ke cikin ranta , hannun da taji a kuma tunta ana share mata hawaye ta kalla , junior ne fuskarshi shi kamar zaiyi kuka “ Ammu me yasa kike kuka ?” Girgiza masa kai kawai taheee tayi wasu hawayen na ‘kara sakko mata , duk lokacin da ta kalli fuskar junior fuskar mijinta take gani, he’s eyes , mouth , cute face,he’s everything sak irin na king ne ,” Tohm ki dena kuka kinji “, ynxu ma kanta ta jinjina masa ta kasa magana , rungumeta yayi a jikinsa shima a hankali ya furta “ I love you!!!!!! Ammu”, a hankali ta furta “ Love you more and more my baby“. Kusan 3 minutes suna rungume da suna kafun da Sauri junior ya kalleta “ Ammu na manta, abinci fa zamuci grandpa yace na kira ki”, girgiza masa kai tayi “ Allah ya shiryeka son , bari na wanke fuskata sai mutafi”, tana kai karshen zancantawta wanke face d’inta tare da daukar junior kamar wani baby suka fito down stairs, gabaki d’aya kowa da kowa ya hallara tahee da junior kawai ake jira , kallan fuskarta Dady da momy sukai, duk da alamu ya nuna kuka tayi babu Wanda yayi magana , daman ta sabayin kukan , yau da kanta Mimi tayi serving d’insu abinci, tunda suka soma ci babu Wanda yayi magana sai junior da lokaci zuwa lokaci yake magana , suna kammalawa kowa ya bawa tahee gift ta zamowarta barrister , a nan d’in ma wani saban kuka ta fashe da shi, sun d’an jima a Wajan kafun dady ya mike , momy ta bi bayansa , yayi saura tahee da Mimi, daman yah moh shiya fara futa da junior. ********* *************** ********** *************** FLASH BACK Tun lokacin da tahee ta dawo Uk wajan Alhaji isma’il suka cigaba da kula da ita, tun tana kin sakewa dasu har ta fara sabida yadda ko wannan su yake janta a jiki, A bangaran momy ma sosai take bawa tahee kulawa kamar ‘yar da ta haifa da cikinta kome zatayi wa mimi shi zatayiwa tahee, sosai suke bata kulawa babu me nuna mata banbanci, kullum momy cikin dubata take kasan tuwarta kwararriyar Doctor . Shima yah moh kullum cikin siyo mata kayan kwad’ayi suke shi da dady. Gabaki d’aya family sai suke bata kulawa ta musamman. Lokacin da dady yakezo sa tahee a makaranta ta wayarta da baba Malam ya basa yayi anfani ya Fito da soft copy din makaranta dake cikin wayar, duk da yar hanzu be fad’a mata wayar na hannunsa ba . Koda sukaje school sabida kokarin ta yasa aka za tayi iya tafiya university, sosai tahee tayi farinciki da hakan, take a Wajan ta cike ‘bangaran law department, mimi ta cike nursing, haka rayuwa ta cigaba da tafiya cikin ahalin kullum tahee da tunanin a halinta take kwanciya take tashi , fatan ta Allah yasa suna cikin ‘koshin lapiya. A haka rayuwa tacigaba da tafiya da tahee tana samun kyakkyawar kulawa daga mutanan gidan , mimi ma sosai take janta a jikinta har soyayyar da suke wa juna tayi ‘karfi, lokacin da tahee ta fara labour gabaki d’aya family babu Wanda hankalinsa be tashi ba amma cikin iko na ubangiji ta sum’bulo d’anta kyakkyawan gaske fari tass dashi kamar ka ta’basa Jini ya zuba sabida kyansa, hatta Doctor d’in kowa ya gansa sai ya furta “ the baby is so beautiful” basu wani dad’e a asibitin ba aka basu sallama suka koma gida , gabaki d’aya familyn momy saida sukazo hatta wata sister d’in momy Itace tayiwa tahee wanka sabida yanda suke ‘kaunarta suma musamman da momy ta basu labarinta . Sosai dady da yah moh suka nuna bajintarsu ranar sunan kamar d’ansune ya haihu haka akayi tafi nagani na fad’a , baby da maman baby sosai suka tara gift sbd yaro yayi goshi sai san barka . Hatta friends d’inta na school wasu duk sunzo mata , ranar suna yaro yaci suna mohammad , Sabida shine sunan da kullum king yakece mata yanaso ya sa wa babynsu, sai suke masa la’kabi da junior .kullum momy da mimi ne suke kula da junior , har yaro yayi wayo sabida baiwar saurin fahimta da yake dashi, a haka tahee taci gaba da karatunta har zuwa ynxu da ta kammala karatunta amatsayin barrister. ✨✨✨✨✨✨ BACK TO STORY Karfe 9:30 na dare dady yabu ‘kaci ganawa da kowa da kowa na cikin family d’in, gabaki d’aya taruwa sukai cikin babban falon dady, lokacin junior na jikin momy yana bacci , taro dady ya bud’e da addua bayan salatin annabi da sukayi, shiru dady yayi yana juya maganar da zaiyi , itama momy shiru kawai tayi batace komai ba , gyaran murya dady yayi kafun ya soma magana , “Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah , ina ‘kara gode wa Allah da ya bani ikon ganin ranar nan, ha’ki’ka nayi farincikin kammaluwar karatunku, ina ‘kara gode wa Allah, sannan ko wannan ku gift d’insa da na basa yana wajan momy a Wajan ta zaku karba , abi na biyu kuma maganata akankine tahee,” lokaci d’aya zuciyar tahee ta buga jin ya ambaci sunanta, amma bata ce komai ba sai ‘kasa da ta ‘karayi da kanta.Ba sai na maimaita abunda suka faru shekaru bayaba, amma yanxu lokaci yayi da za’a wuce wannan ga’bar, lokaci yayi da tabon mutanan da suke cikin‘kuncin ya goge, ko ba’a fad’a ba nasan kinsani junior ya fara wayo, yana bu’katar sanin mahaifinsa, yana bu’katar salin ahlinsa, ke matar aurece na tabbata Indai mijinki na raye to tabbas yana cikin kuncin rayuwa, mahaifiyarki tana cikin bakin cikin rayuwa haka ma d’an uwanki, lokaci yayi da zamu koma Nigeria gabaki d’ayan mu. Ba tahee data d’ago kanta ba hatta yah moh a mugun firgice ya kalli dady kansa na sara masa , cikin zuciyar sa ya maimaita “Nigeria ?”, kamar dady yasan me yake fad’a ya ‘kara maimaitawa “ eh Nigeria, Nan da 2 weeks duk Wanda yasan yana da abunyi yayi kafun nan da 2 weeks dan tafiya ba fashi “, idanuwan ya moh har sun fara yin ja, itama tahee da wani irin shock take maimaita Nigeria cikin zuciyarta. Wata waya ya ciro daga cikin aljihunsa tare da wani ‘karamin hoto da ya fad’i batare da sanin saba , wayar ya mi’kowa tahee “ Nasan bazaki manta da wannan wayar ba ko? Sabida tare da ita aka sameta cikin aljihunta”, ita tahee kuwa gabaki d’aya bata san me yake cewa ba , hankalinta yana kan hotan da ya fad’i a kasa , hakanan zuciyar ta take san ganin hotan, saida dady ya ‘kara kiran sunan ta kafun ta saka hannu zata kar’ba wayan ya su’buce mata a hannu sabida bud’ewar da hotan yayi ita kuma wayar ta gangara inda yah moh yake, da Sauri tahee ta d’auki hotan zuciyar ta na bugawa da sauri da sauri , gabaki d’aya sai suka maida hankalinsu kanta, kallan Alhaji isma’il tahee tayi kafun ta mayar da hankalinta kan hotan, shima a Daidai lokacin da yah moh ya d’auki wayar tahee da ta fad’i, cikin wani irin zabura tahee ta furta “Oumma?”, da sauri Alhaji isma’il ya mi’ke tsaye yana ‘ko’karin yin magana wayar tahee tayi haske, cikin wani irin shock yah moh ya mi’ke take a wajan ya soma ganin jiri jiri na d’ibarsa , babu abunda yake maimaitawa sai “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”, nuna wayar tahee kawai yake yana ja da baya ga juwar da take ‘ko’karin kayar dashi , mimi har ta soma kuka babu abunda take fad’i sai yaya moh , meke damunka” . Ga baki d’aya sai abubuwan yaso d’aurewa dady kai musamman Wayar tahee da yah moh yake nunawa, kamar daka sama ya furta “ King” da ‘karfi, take a wajan kuma ya sulale ‘kasa . Da sauri dady da su momy suka nufa inda yake, tahee kuwa kasa ‘karasawa inda yake sai fuskarsa da ta tsurawa ido, kusan 2 minutes tana kallan fuskarsa kafin cikin shock ta mayar da kallanta kan junior dake bacci, sosai tashiga rud’ani kanta itama ya soma juyawa take a Wajan itama ta sulale. Tashin hankalin da ba’a sa masa date, sai suka rasa kan wa zasu tahee data suma ko yah Moh daya suma , babu abunda dady yake furtawa sai “ruwa ! Ruwa !” Da Sauri mimi ta nufi kitchen , cikin ‘kan’kanin lokaci ta dawo d’auke da bottle d’in ruwa guda biyu, momy ta karbi d’aya shima dady ya karbi, ruwan suka shafamusu gabaki d’aya suma sun rikice ganin abunda yake shirin faruwa . Tahee ce ta soma ajiyar zuciya har yanxu hotan data d’auka yana hannunta ta ru’keshi gagam. Yah moh kuwa har yanxu baya motsi abunda ya ‘kara tayar da hankalinsu, abunda ya bawa kowa mamaki, tahee tana farkawa inda yah moh yake a kwance ta zube tana fashewa da wani saban kuka , cikin murya kuka take furta “ Na ro’keka katashi, katashi dan Allah”, kasa magana dady yayi ganin irin kukan da tahee take ,sai abu yaso had’e masa ga momy data tayar da hankalinta ga mimi itama da take masa kuka, a ‘bangaran tahee ma gashi tana bashi tsoro ganin yadda take kuka akan Moh ya Tashi. Yana kara fesawa yah moh ruwa , ya fara motsi a hankali, bakinsa babu abunda ya ke am bata sai “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un, Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un “. Temaka masa dady yayi ya zauna sosai , da sauri tahee ta d’auki wayar tata tana nunawa yah moh, cikin rawar murya take nuna masa wayar , da ‘kyar ta samu bakinta ya furta “ yaya king” sannan ta nunasa a hankali kamar tana tsoran magana ta furta “ Akhieee?” Shima Fuskarsa gabaki d’aya tayi jawur bakinsa yayi nauyi ya kasa cewa komai sai d’an motsa mata kai da yayi alamar eh , murmushi da hawaye tahee ta fara lokaci d’aya sai momy da dady da kuma mimi suka zuba musu idanu gabaki d’aya sun kasa magana , maganar yah moh ne ya ‘kara rikitasu da ‘kyar ya kalli tahee kafun ya nuna junior dake kwance yana bacci, sai kuma ya nuna wayar hannunta “ junior !? Is my son”,murmushi tahee ta sakar masa tana d’aga masa kai , duk da haka sai da ya ‘kara furta “ junior is my brother’s son? ‘Dana ne ? ‘Dan king d’ina ? My dearest brother is now a father ?finally zan ‘kara ganin king d’ina ? Ummey? Abeey?Samreen? Dada?” Kai kawai tahee ta d’aga masa dan gabaki d’aya ta kasa magana , Sabida farincikin da ta shiga “ her lovely husband zai ‘kara samun farinciki? Wana irin farin ciki zai shiga idan ya ga brother d’insa , together with his wife and his baby?” Duka wad’an nan tanbayoyin kanta tahee take yiwa . Dakatar dasu momy tayi kafun ta furta “ kunsa mu cikin duhu, daman kun san junane?” Lokaci d’aya suka girgiza mata kai alamar a’ah . A sanyaye , dady ya furta “ kuyi mana bayani yadda zamu gane amma kafun nan inaso na tanbayeki tahee, naji kinkira matar cikin wannan photon da oumma ko kinsan me kama da ita ne?”. Sai yanxu hankalin tahee ya dawo kan hoton tana sakin murmushi, Oumma tace tare da brother d’inta da ya ‘bata “ da Sauri dady ya kalleta tare da nuna hotan “ oumman ki? “ yanxu ma kai tahee ta jinjina masa murmushi kwance a kan fuskarta. “ Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un” cewar dady, hotan hannunta ya nuna sannan ya nunata , a hankali ya furta “ ke.. ke yar maryam ce ?”, dukda tahee tayi mamakin yadda yasan sunan oummanta hakan be hana ta amsawa da “eh” wani irin farin cikine ya kama dady har ya kasa ‘boyuwa akan fuskarsa “ Alhamdulillah!!! Alhamdulillah!!” Kawai yake furtawa , kallan momy dady yayi itama da take murmushi “ ina tare da Jinina tsawan lokaci Amma ban sani ba ?” Da Sauri Mimi ta furta Dady wacce ?”, farin cikin da ya dad’e beyi bane kwance a fuskar dady , amsawa Mimi ba sai ‘kara kallan tahee da yayi sosai , tabbas tana kama da maryam d’insa , alama yayi mata data matso, ba musu kuwa ta matso d’in hotan hannunta ya kar’ba kafun ya nuna mata oummanta , “ Maryam ‘kan wa tace , nine nan a kusa da ita “, yanxu ma su mimi zubawa sarautar Allah ido sukai har yah moh kallansu yake lokaci zuwa lokaci yana sakin murmushi idan ya kalli junior . Nunasa tahee tayi kafin ta nuna hotan , a hankali ta furta “ uncle isma’il?”, murmushi ya sakar mata sosai yana jinjina mata kai , cikin farin ciki ya furta “ Allah ya ‘kaddara zan ‘kara ganin ahalin Maryam Alhamdulillah, yanxu dare yayi zamu tattauna gobe da safe “, badan sun soba duk suka mi’ke dan gabaki d’aya baccin ya gudu sabida farinciki, kallan tahee ya moh yayi , kafun ya kalli junior “ please ki barshi yau a waje na “, dariya yaso bata kamar yau ne suka soma kwana tare kanta kawai ta d’aga masa , itama fuskarta cike da murmushi ta furta “ bari na d’auko kayan baccin sa “, kafun ta ‘karasa ma Mimi har ta hau sama taje d’auko masa , d’aukan junior yah moh yayi , Daidai lokacin da Mimi ta dawo d’auke da kayan sa, mi’kawa yah moh da yake binta da d’an kallo kawai tayi, har yanxu kanta a tushe yake , ganin komai take kamar a mafarki , jira take kawai gobe tayi . Gabaki d’ayansu kowa goodnight yayi wa junansa kafun su nufa d’akunansu, yau Mimi d’akin tahee ta nufa , lokacin da suka kwanta Mimi sai kallan tahee take har hakan yasa ta tsargu , d’akawa Mimi duka tayi “ wannan kallanfa?” Murmushi Mimi tayi kafin ta sha gefan fuskar tahee , a mai makon ta amsawa tahee tanbayarta “ ban ta’ba ganin farin ciki sosia haka a fuskar dady ba , ya dad’e yana neman ku, da ya samu free time zaice zai tafi Nigeria , wani lokacin har kishi nake , sai na dunga tunanin ko dady yafi sansu akan mune ? Amma yanxu sosai nake farinciki, finally Nima naga familyn dady na “d’an harararta tahee tayi wato da mu kike kishi?” Murmushi kawai Mimi tayi mata , shiru tahee tayi kamar me tunani kafun ta furta “ Yah moh fa”, juya mata baya Mimi tayi tare da kashe light d’in dakin kafun ta furta “ good night, ni bacci nake ji”, dariya ce ta so su’buce wa tahee Amma tayi ‘ko’karin dannewa so take washe gari Kawai tayi, “ one side d’an uwan mijinta da kowa yayi tunanin ya mutu, the other side yayan mamanta.”, a hankali yadda Mimi bazata ji ba ta furta “ ya Allah ! Allah ka bayyana mun su , ko zan ‘kara ganin farincikinsu. Gabaki d’aya ahalin gidan sai kowa ya kasa rintsawa kowa da abunda yake sa’kawa aransa , yah moh tunda suka kwanta yake bin fuskar junior da kallo lokaci zuwa lokaci yana kissing forehead d’insa. ✨✨✨✨✨✨✨✨ ✨✨✨✨✨✨✨✨✨✨ BUNKURE 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 MSS LEE 💖 LEESHARH DATA HUB BUY DATA AT AFFORDABLE PRICE: MTN AIRTEL 500mb-120. 500mb-140 1gb-240. 1gb-300 2gb-440. 2gb-600 3gb-620. 3gb-900 5gb-1200. 4gb-1200 10gb-2200. 5gb- 1500 Validity : 30 days ACCOUNT DETAILS : 2681892316 AISHA UMAR , ZENITH BANK . For more information contact me through my phone number: 07041879581. BOOK 2 Page 11.💖 ✨✨✨✨✨✨ WASHE GARI Tunda suka tashi kowa da farinciki kwance akan fuskarsa , kowa kaganin cikin fara’a junior tsalle yake idan ya juya ya kalli Ammunsa tana murmushi sai ya juya ya kalli Mimi itama yaga tana murmushi, sai ya tsaya kuma ya fara bin kowa da kallo tun daga kan yah moh harzuwa su dady, shima sai murna yake abunsa. Kowa jira yake dady ya ‘kara kiransu amma dagari ya waye sai sukaji shiru har sukai breakfast suna jiran tsammani, sai wajan 11:30am dady ya Bu’kaci ganinsu , gabaki d’aya familyn sun hallara , bud’e taro dady yayi da addua kafun yayiwa Allah kirari yana ‘kara Godiya ga Allah kafun ya soma magana “ nasan ko wannan ku a cikin ku yasan abunda ya faru jiya basai na maimaita ba , cikin iko na ubangiji ya nuna ikonsa ,yar uwata da nake nema cikin iko na ubangiji sai ya fara nuna mun jininta , tabbas zuwanki cikin family d’innan alheri ne babba, ta sanadiyar junior komai da komai zaizo ‘karshe , insha Allah babu wani abun cutarwa da zasu ‘karayi muku cikin ikon ubangiji”, kafun ya mayar da hankalinsa kan yah moh da ya d’an sunkuyar da kansa kad’an “ Mohammad , inaso nasan Menene ya faru har matar mahaifinta take ‘ko’karin salwantar da rai, Menene ya faru a wannan lokacin?” A hankali ya d’ago idanuwansa da sukai jajawur sabida ‘bacin rai, amma bece komai ba har sai da dady ya ‘kara maimaita tanbayarsa kafin ya sauke a jiyar zuciya yana shafa kan junior da ya lafe a jikinsa , cikin sanyayyiyar murya ya soma magana “ cikakken sunana Mohammed zayed Al-Nahyan, mahaifina mu hud’u ya haifa Ni, samreen, king, sai baby d’in da har yanxu ban sani ba tana raye ko akasin hakan, familyn Nahyan babban family ne da gabaki d’aya a halin mu suke rayuwa a ciki , cikin so da ‘Kaunar juna, sosai muke san junanmu musamman ni da king dukda be cika magana ba Amma gabaki d’aya familyn sunfi jin shakkarsa, gabaki d’aya cikin family din babu Wanda baya tsoran yi wa king kuskuren koda sau d’aya ne musamman idan hakan ya shafeni ko samreen, shiyasa muke matu’kar san junanmu mutane da yawa idan suka ganmu tare sai suyi tunanin ‘yan biyu ne mu duk da shi duka kamannin parents dinmu ya d’auka , a haka muka cigaba da rayuwa cikin san junanmu kwatsan sai Abeey ya tado da maganar ‘kara aure , babu Wanda beyi mamakin zancen ‘kara aurensaba musamman yadda kowa yasan soyayyar abeey da oumma , alokacin sosai ran king ya ‘baci duk da Nima banso auren ba amma haka na cigaba da kwantar masa da hankali, still ina tausar ummey duk da bata fito fili tayi magana ba sai albarka data sawa auren bata ‘kara ce wa komai ba.Ba’ai 2 weeks ba sai ga zancen auren ya ‘kara tashi har aka d’aura Auran ta da Abeey, shigowarta gidan sosai take nunawa kowa so da ‘kauna , hakan ya janyo soyayyar yaran gidan har ya zamto kullum suna part d’inta ban dani da king da ko kallan inda take bayayi bare gaisuwa ta had’asu, hakanan Nima naji gabaki d’aya matar bata kwanta mun arai ba amma gudun d’aukan Alhaki yasa na cire zancen Arai na saka harkar makarantana a gaba, 2 weeks da auren abeey abubuwa da dayawa suka soma canzawa , cikin har da wata irin soyayya da gabaki d’aya familyn suke mata kowa kaji maganarsa d’aya biyu sai ya had’a da sunan abeey , hakan shike ‘kara tunxura king sau da dama Ammey idan ta gansa ko da ace tare yake da abeey shi zata farayi wa magana , abun mamaki ba’afi 1 week ba sai gashi yawanci lokuta king yana part d’insa da yana tanbaye sa sai cemun ai tana da kirki sosai , sannu a hankali king ya fara janzawa har yazamto kullum a can part din yake cin abinci ya dena ci a wajan ummey, har yazamo baya cin komia na ummey gabaki d’aya rayuwarsa a part din Ammey yake yi hakan ne ya fara samun zarginta duk da banfito fili na fad’a ba , kwatsan wata rana ina neman king amma ban gansaba ranar da na fara tunanin shiga part din Ammey a rayuwa,ko da na shiga babu kowa a cikin falon har zan juya sai na dunga jin motsi da surutu cikin wani d’aki da ba kullesa sosai ba , kamar na share sai zaciyata ta’ki bani damar hakan, abunda nagani ne yafi komai tadamun hankali kasancewar computer software na karanta cikin Sauri na soma yi mata vidoe , ba komai naga Ammey na yi ba sai shan wani Jini da take ta zagaye d’akin da wasu nan fitulo jikinta duk sanye yake cikin jan kara, sam hankalinta be kawo kaina ba gabaki d’aya hankalinta yana kan tsafin da take yi, abun glass din da na bege nesani sakin ‘kara kadan da Sauri Ammeey ta jiyo cikin tashin hankali mukayi ido vidoe da ita, kururuwa naga ta farayi ni Kuma cikin sauri na far wajan ina kiran sunan Allah . Ranar da matsanan ciyar ciwon ‘kafa na yini gabaki d’aya na rasa wa zan tun kara da nayi kokarin tunkarar abeey ko ummey sai naji ma’kogarona kamar ana sukamun wu’ka, sai da nayi kwana biyu duk lokacin da zan kwanta sai na dunga ganin wad’ansu abubuwa kamar masu rai, hakan yasa na dawo kulla kurani a d’akin,vidoe da nayi mata kuma sai na sashi cikin memory. Har zuwa lokacin ban had’u da Ammeey ba. Sai ranar da na ‘kara kwanta wa rashin lapiya sabida yadda naji jikina kamar ana huramun huta ta ciki gabaki d’aya sai faman gumi nake yi, a fakaice Ammey ta kalleni ta kashe mun ido d’aya ganin su ummey basa kallanta ,cikin bariki ta dunga nuna Al’ajabinta tana mun sannu. Haka muka ‘kara sati d’aya da ita tana harin rayuwata Allah na kareni. Ranar da bazan ta’ba mantawa da ita ba ranar Sunday lokacin dana ro’ki king ya rakani company zan d’aukowa abeey wasu mahimman document , alokacin kuma bamu d’auki masu tsaro ba nida king kawai muka fita har nasashi driving, munyi nisa a tafiyar mu wata babbar trailer tayi ta kan motar mu, gabaki d’ayan mu saida muka bugu sosai , Allah ya bawa king sa’a ya ‘balle motar da ta fara ci da wuta kad’an kad’an, Amma duk da haka hannu yake mi’komun nima cikin mawuyacin hali na mi’ka masa nawa da nayi nasarar balle ‘kofar Nima, bamuyi aure ba wasu mutane sanye da ba ‘kaken kaya suka soma dukan king amma duk da haka bata su yke ba so yke ya cece , king beyi aune ba kawai sai motar da nake ciki ta saki ‘karar bom Adaidai lokacin da suka harbi king, ni muma d’aya daga cikinsu ne da ya kula dani yayi saurin te maka mun tare da turani wani rami gudun kar sauran su ganni take a wajan kaina ya bugu da bishi yar wajan , ban ‘kara sanin inda kaina yake ma sai muryoyin mutanan da yake tashi sama sama d’aya daga cikin sune yake “ mun kashe shi hajiya “, Wannan ne abunda ya faru harnabar gida tsawan lokaci ,duk da nasan akwai wani na jikin mu da yake temaka mata da har ynxu bangane ko wanene ba , nasan zuwa yanxu kowa yana tunanin na mutu ko? “ ya ‘karasa yana tanbayr tahee da take d’aga masa kai itama da Mimi gabaki d’aya kuka suke , Mimi ji take da zata samu shegiyar Matar nan da babu abunda zai hana taci ubanta, shegiya me idan agwagwa,” abunda Mimi take rayawa a zuciyar ta , yah moh kuwa sai faman sakin murmushin takaici yake , ran taheee ma ba ‘karamin ‘baci yayi ba sosai . Shiru gabaki d’aya falon ya d’auka tsawan mintuna biyu, babu abunda ya ke tashi sai kamshi freeshner da sanyin Ac da ke ratsa ko ina na falon, momy ce ta katse shirun “ wannan matar bata da Imani hartana iya salwantar da rai , ai ta kai ma’kura wajan tantiranci”, sauke ajiyar zuciya dady yayi “ tabbas a mawuyacin hali na sameka ko sunanka baka iya fad’a har Allah yasa ka samu lafiya , wannan mata babu d’igon Imani a ranta sam sai san zuciya , budulci da ‘kyashi kuma , Amma Allah ya fita cikin iko na ubangiji zai nuna mata bata da wayo ko dabara “. Yanxu ma shurune ya biyo falan na tsawan mintuna kamar daga sama suka ji muryar tahee “ uncle inasan komawa Nigeria Sabida na tona mata asiri”, gabaki d’aya falon duk kallan tahee sukai , Mimi ma tayi saurin furta “ nima dady zan bita “, da Sauri momy ta katsesu” babu inda zakuje , kunsan matarnan mushrikace bazan juri rashin kuba , sam Hakan ba me yuwa bane “kallan junior daya soma bacci yah moh yayi “ Momy karki damu zan kula miki dasu gabaki d’aya “, sakin baki momy tayi “ kana nufin kai ma binsu zakayi? Ni kuma ku barni an ina ? Kafata kafarku babu me rabani da ‘ya’yana “, .gabaki d’aya kuma sai suka maida kallansu kan dady,ganin yadda suka kafeshi da kallone yasa shi yin gyaran murya “ Naji ta bakinku gabaki d’ayanku, amma bazan ‘karayin gangancin barin ku zuwa Nigeria ba , banasan jin wani ‘korafi na sallami kowa da kowa “,yana kai karshen zan cen sa ya bar falon, gabaki d’aya bin bayansa sukai da kallo mimi zata ‘Kara yiwa momy magana itama ta tashi ta bar falon, a shagwa’be ta maida kallanta kan yah moh, hararar ta yayi shima ya mi’ke ru’ke da junior , falon yayi saura tahee da Mimi, Mimi kamar ta saka kuka haka takeji daman bata ta’ba zuwa Nigeria,ga rashi ga samu. Haka kowa ya nufi d’aki yana sa’ke sa’ken hukuncin dady. Gabaki d’aya yinin ranar tunanin kalaman yah moh ne ya tsaya musu arai musamman Mimi da lokaci zuwa lokaci idan ta tuna abunda Ammeey tayi wa yah moh sai taji kamar tayi fiffike tajita a nigeria , Tahee kuwa jurfin tunanin yadda zata tonawa Ammey asiri take , tuna kalmar akwia wani bayn Ammeey acikin gidan da yke temaka mata yasa tahee ta rubuta sunayen ‘yan gidan kaf tana bin sunansu d’aya bayn d’aya a cikin zuciyar ta da halayyar kowannansu, sosai ta zura tunanin ta ydda zata gano koma wanene babu abunda yke Tashar da ita sai sallah , sai kuma abinci da Suka ci. ******* Da daddare Dady da wani envelope yashigo gidan gabaki d’aya yana lura da yanayin kowa da yadda suke binsa da kallo, be ce musu komai ba harya kammala cin abincin ya koma falo, suma da d’ad’d’ai suka dawo falon saida yaga kowa ya hallara kafun ya d’akko envelopes dinki, ciki ma wasu envelopes dince a ciki ‘kanana ko wannan su da abu aciki da sunansa , saida ya bawa kowa nashi kafun ya basu umarnin bud’ewa cike da zumud’i suka soma bud’ewa abunda suka ganine yasasu zaro ido suna kallan dady , dariya yayi musu kafun ya furta “ surprises !!! Nan da one week insha Allah zamu tafi Nigeria gabaki d’aya mun , wani irin ihun dadi suka saka mimi da tahee , Dady sai dariya suke , junior ne ya kallesu “ Ammu , Aunt , you’re shouting and dare yayi babu kyau”, gabaki d’aya dariya suka saka , haka suka zauna suna hira a tsakaninsu Mimi har ta matsu one week d’in ma tayi . Cikin wannan 1 week din gabaki d’aya babu abunda suke sai yadda tafiyarsu zata kasance duk da ba wani abun suke bu’kataba, amma dady yace bazasu zauna a lagos ba gudun kar a gansu , saidai su sauka a gidan sa na Abuja , gabaki d’aya sunyi na’am da zancensa, batare da kowa ya sani ba Mimi da tahee suka je wani supermarket , Suka siyo wani abu da suke ta ‘boyewa kar su momy su gani, ita da tahee sosai suka had’a plan dinsu. Yau yakama Sunday kuma a yau ne jirginsu ya tashi zuwa Nigeria 🇳🇬 ✈️. 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 Mss Lee LEESHARH DATA HUB BUY DATA AT AFFORDABLE PRICE: MTN 500mb-120 1gb-240 2gb-440 3gb-620 5gb-1200 10gb-2200. AIRTEL 500mb-140 1gb-300 2gb-600 3gb-900 4gb-1200 5gb-1500 Validity: 30 days Account details : 2681892316 Zenith bank , Aisha umar. For more information contact me through my phone number: 07041879581 . BOOK 2 Page 12💖 NIGERIA 🇳🇬 6 hours 10 Minutes ne ya kawosu Nigeria, gabaki d’ayansu babu Wanda be lumshe ido ba da ya sha’ki iskar Nigeria musamman Yah moh da tahee da suke ganin komai kamar a mafarki, Mimi da momy ma sai bin ko ina suke da kallo dan wannan ne karansu na farko da suka zo Nigeria. Wata Blank tinted cars ne guda uku suka zo d’aukarsu, momy da dady suna guda d’aya , Mimi da tahee ma d’aya sai Yah moh tare da junior , kai tsaye motocin kan babban titin da zai sadashi da mai tama suka nufa , cikin wani ‘kayataccen gida meshegen kyau , duk da kallo d’aya zaka masa kasan saban gidane amma sosai yayi kyau tun daga wajan sa . Suna cikin main gidan Suka ga komai na anfanin rayuwa akwai a cikin gidan kamar ana rayuwa cikinsa , ko ina tass sai faman kamshi da sanyi ke tashi, gabaki d’aya 5 bedrooms ne acikin gidan sai 3 palour ne had’e da bedroom da toilet a ciki, momy da day nasa ma suka hau , tahee da Mimi suka d’auki d’aya me falo, daga ‘bangaran hagu shima yah moh ya d’auki d’aya , yau junior baki ya mutu sai bin ko ina ya ke da kallo, gabaki d’ayansu agajine suke shaf shaf mimi tayi wa junior wanka , suma sukayi kafun su rama sallolin da ake bunsu, basu tsaya cin abincin da aka kawo musu ba sukabi lapiyar gado su uku, junior rungume da tahee . Kiran sallah isha’i ne ya tayar da tahee , Mimi alokacin ta farka , sai da Suka idar da sallah kafun kowannansu ya samu nutsuwa sai lokacin suka d’auko abincinsu, shima junior Tashinsa tahee tayi duk da ‘karancin shekarunsa ta koyar dashi yadda zai yi sallah da su karatun, Alhamdulillah kuma yna ‘ko’karin yin hakan.suna gama cikin abincin suka fito babban falon, momy Suka tar kawai, “ har kun tashi daga baccin kenan”, cewar momy , amsa mata sukai gabaki d’aya da “eh”, kafun mimi ta furta “ momy Dady da yah moh fa? Sunaga bangansu ba”, batare da momy ta kalleta ba ta bata amsa “ sun fita zasuyi d’an shopping “, kamar wacce aka zabura Mimi ta matso kusa da momy “ Haba momy amma kuma kika ‘ki tashin mu? Muma sai da sai muzaga gari”,hararar ta momy tayi “Ance miki kowa bashi da hankaline kamarki?sabida kece amarah yawo daga zuwa sai fita yawo ,kishiga taitayinki”, turo baki Mimi tayi kamar wata ‘karamar yarinya “ Haba momy, kinsan fa wannan ne karo na nafarko dana fara zuwa Nigeria, mai yasa kike mun hakane ,” momy bata, bata amsa ba sai hararar ta da tayi , tahee tana gefe sai faman dariyar dramarsu take , inda sabo sun saba da wannan rigimar, shigowar su dady ne ya katse musu hanzarinsu, gabaki d’aya sannu da zuwa sukai musu bayan junior ya gudu wajan tahee “ momy munje yawo babu ke, Big dadi ya siyo mum guns da cars, if I saw an evil person , I will just shoot them all”, gabaki d’aya dariya suka saki , kafun tahee ta furta “ but hope kayi masa Godiya ?” Kansa yayi nodding kafun ya furta “ yes nayi , bari ma Kigani “, sai ya ‘kara juyawa ‘bangaran yah moh “ Big Dady thank you for everything “, hancinshi kad’an tahee taja “ good boy”,shima hancin nata yaja “ good momy , I love you !”, sai yai mata peck a goshi , gabaki d’aya kuma sai kowa ya tsaya kallansu dan ba ‘karamin kyau sukai ba . Muryar Mimi ce ta dawo dasu hankalinsu “ Dady shine kuka tafi yawo ko kafad’amun mu biku ko, kasan wannan ne karo na nafarko zuwa Nigeria , and nayi complain momy tace wai haryanxu bangirma ba”. Murmushi dady ya saki “ rabu da ita , gobe kushirya driver ya fita daku, haka nan momy bazata yi muku kulle ba ,ko?” Ya kalli junior , girgiza masa kai junior yayi “ junior is a good boy”, gabaki d’aya dariya suka saki , ledar da suka shigo dashi suka bawa kowa , ganin dare nayi, junior a wajan yah moh yace zai kwana shiyasa tahee suna shiga suka bace tsirensu gwanin burgewa suna ci Suna hira suna shirya yadda plan d’insu zai kasance, dan kansu suka hakura ganin dare na ‘karayi suka kwanta. (Asuba tagari ) 🥱. WASHE GARI Tun ‘karfe sha biyu Mimi ke ro’kan tahee su shirya zaga gari Amma tahee tayi Burus da ita acewarta futar yamma tafi dad’i, hakan ne kuwa ya faru basu suka fita ba sai bayan sallar magaruba lokacin gari yayi sanyi duk da yanayin kamar damuna na ‘ko’karin shigo wa , gabaki d’ayansu kowa ya ci wankansa kana ganinsu kaga kyawawan yan mata da kud’i da nera ya gama zama a jikinsu.dukansu kwalliyr abaya sukai Tahee red colour, Mimi kuma Rambo colour ta saka ,junior kuwa shima wankan ‘kananan kaya Mimi tayi masa , idan ka gansu su uku bazaka ta’ba cewa Tahee tana da aure ba , sabida yadda ta ‘karayin wani fresh musamman junior da yake da shekara uku.BMW d’insu ba’ka da dady ya bar musu da Wanda zai kasu suka hau, kai tsaye babban mall din JABI LAKE MALL ya nufa nasu, dukda kasashen da suke zuwa sai mimi taga mall din yayi mata kyau , Tahee kam murmushi kawai take “ Yaushe zanganka ? I missed you badly, please “, ita kad’ai take tunaninta cikin zuciya bata ankara ba sunzo shiga sukai karo da wata , gabaki d’ayansu lokaci d’aya suka d’ago suna bawa junansu hakuri , ganin barin da tahee tayi matane ysa ta tsugunna tana kwashe mata kayanta , junior da Mimi na taya ta, juyowar da budurwar zatayi sai naga ba kowa bace face Zahra , dukda tsawan shekara hudu itama ta canza sosai ta zaba budurwa abunta , cikin sakin murmushi tahee ta furta “ kiyi hakuri ban kula ba”, itama zahra murmushi ta sakar mata “ Haba wallahi karki damu ai ba ke kadai ce me lefi ba hardani”, sai ta tsaya kallan tahee kuma kafun ta furta “ fuskarki sai tayi mun shige da ta oumman mu kamar ita tahaifeki, kaman ninku har ya baci” da Sauri tahee ta kalleta bata san lokacin da ta furta “ oummanku ?”,zata kuma mata wata tanbaya idanun zahra ya sauka kan junior , eyes dinta ta zaro gwanin ban sha’awa “ Kanin kune wannan?kyakkyawane shi. Koda yake karna cika ku da surutu sunana zahra ku fa “, ganin yadda take da fara’a ga tahee na ‘ko’karin share ta yasa tayi saurin cewa Sunana Mimi, sabida wani tunani da yazo mata , da murmushi ta kalli tahee “ kefa ?” Tahee zatayi magana junior yayi saurin cewa “ sunanta SweetLove”, Ajiyar zuciya Mimi tayi jin abunda junior yace , itama murmushi Zahra tayi zata kuma magana khaleed ya fito , shima bin fuskar tahee yayi da kallo yana tunanin inda yasan ne fuskar Amma sai kuma y share ya kalli zahra“ tun d’azu nake nemanki kinsan oumma na jiran mu”, kayansa zahra tayi “ sorry yaya khaleed , bari na d’auki kayana “, tana kai ‘karshen zancanta ta d’auki kayanta tayi wasu tahee sallama , suma daga nan suka shiga sukayi siyayyar da zasuyi, sosai suka zaga abuja ba lefi kafin su koma gida a gajiye . **Haka suka ci gaba da rayuwa batare da kowa yasan da zamansu ba hatta shima yah moh yana taka tsan tsan da inda zai shiga , sai da suka shafe 1 month guda a Abuja, hakan yayi Daidai saura wata d’aya da sati uku bikin yah khaleed. Mimi da tahee na neman hayyar da zata sadasu da gidan Nahyan amma gabaki d’aya babu wannan damar. Suna zaune shiru kowa yana neman mafita saiga yah moh ya dawo gida , kana kallan fuskarsa zakaga yana cikin annashuwa,” yah moh meyasa ka farin ciki haka ?” Wani murmushin ya ‘kara saki “ kun shirya fara aikin ?”, kallan juna sukai alamun basu gane ba , hakan yasashi ‘kara sakin wani murmushin tare da tura musu wani file “ ku shirya gobe zaku goma Lagos amma ba da wannan fuskar ba , musamman ke tahee zata ganeki, face d’in da kuka taho dasu za a kawo miki artist tasa miki, “ har yanxu basu fahimci abunda ya ke nufi ba shiyasa tahee tace “ yah moh har yanxu ban gane me kake nufi ba “, mikewa tsaye yyi “ duk plan d’in ku nasanshi, kuna neman yadda zaku shiga gidan ai ko, suna da biki nan da 2 month , naji labarin Ammeey tana neman yar aiki, nasan yanxu kinfi kowa sanin halinta keya kamata keje ame aikin ta shiyasa nace za’a sa miki face, ke kuma mimi ummey itama tana bukatar me aiki sai ki bar fuskarki, kubi ta ka tsantsan , bata da Imani ko kadan , na ruga nasanar wa momy da dady , ina ‘kara Jaddada muku , kubi a hankali duk abunda yake faruwa kuyi ‘ko’kari kusanar dani , later on akwai cameras da zan baku ‘ kanana inaso kowani part kusaka batare da sanin kowa ba musamman Ammeey , tana da wani lumbu shima a part d’inta ki tabbata kunsaka . Abu na biya da zan sanar daku Aikine zai had’a ku ba ‘yan uwantaka ba , kada kuyi gangancin da za a gane shirin ku ko asan kuna da ala’ka “.yana kai Karshensa yabar falon. Wani irin daka tsalle Mimi tayi “ yes finally zanga ummey”, itakam tahee wani irin farinciki da annashuwane ya kamata ko bakomai zata ga farin cikinta , zata ‘kara sashi a idanuwanta , ita kadai take tanbayar kanta , ya yake ? Har yanxu be manta taba?” Da wannan tunanin suka shiga shirin zuwa lagos gobe bayan uban kayan gwanjon da Suka je suka siyo kamar na almajirai, tabbas sun shiryawa kowa, musamman tahee da take jin ta kamar tayi tsuntsuwa. Washe gari kamar yadda aka tsaya da wuri artist tazo ta saka wa tahee fuskar,idan ka ga fuskarta bazaka ta’bacewa Itace ba. har wani mai artists din ta basu da zasu shafa , suna shafawa kuwa fatarsu tayi dan duhu kamar sun taso daga wahala . Amaimakon subi jirgi Sabida fuskar da aka sa musu da wuri suka bi tamota, suna shiga matar da Ammey tasa, takawo mata mai aiki aka kai tahee duk da cikin zuciyarta tana mamakin yadda Yah Moh yasamo wad’annan information din gabaki d’aya , Tahee tana shiga cikin gidan ta fara washe ha’kora kamar wata sauna daga ga abu sai ta fara binsa da kallo kamar ‘yar ‘kauyen gaske , wani ne ya rako tahee shima kana ganinsa kaga me aikin a fakaice ya bawa tahee letter sabida acikin gidan yake aiki kafun ya fara washe baki ganin ta hajiyar tafito har ‘kasa ya dur’kusa” hajiya ran gida , hajiya sarautar mata, hajiya ga yar aikin da kikace kina bu’kata” kallan tahee tayi da Sauri itama ta zube ta fara yiwa matar kirari kamar wata marokiya, yadda take mata kirarin ne yasa hajiya sakin murmushi, “ kincinye jarabawa an d’auke ki , yanxu zan kaiki gidan”, damn hajiyar bata damu da ko wace me aiki bace tunda an bata kud’in ta class a hannu. “ fargaba da farin cikine ya bi ya tsayawa tahee a zuciya tana tunanin gamonta da shi idan ta shiga gidan ,” kallanta matar tayi “ taso mu tafi “ da Sauri tahee ta d’auko daurin kayanta tana bin bayar hajiyar “, basu d’au dogon lokaci ba suka suka kama hanyar BANANA ISLAND , mintuna kad’an ne ya kaisu .Tahee naganin kofar gidan zuciyar ta ‘kara tsinkewa take awajan wata iriyar iska tafara ratsata, gudun kar hajiya saude ta fahimceta yasa tafara washe baki ganin babban gida . Gate d’in farko da ‘ aka bud’e ne yasa tahee ta firgita da har saida hajiyar ta kalleta amma batace komai ba… 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 07041879581 MSS LEE BOOK 2 Page 13 ********* Tunda suka fara shiga cikin gidan wani irin gumi ya fara tsats tsafowa tahee kamar ana ‘Kona ruwan jikinta, babu abunda take sai karanta adduar duk da tazo bakinta, ganin yadda lokaci d’aya jikinta ya fara rawa ne yasa hajiyar tunanin sabida ganin babban gidane yasata rud’ewa haka , bin part d’in gidan tahee ta farayi da kallo , da Sauri ta had’iye kwallar da take ‘ko’karin sakko mata gabaki d’aya ta kafe idanuwanta akan part d’in sa har aka ‘karaso part din Ammey bata sani ba sai da hajiyar ta jijjigata “ ke Menene sai faman kiran ki nake Amma gabaki d’aya hankalin ki baya jikinki?” Amaimakon tahee taji haushi maganar ta sai ta Washe mata hakwaranta da suka sawa abu, da farko idan ka kalla sai ka d’auka hakwaranta haka suke dar harwani baki baki sukai kamar na kod’ewa,”tuba nake hajiya,arabu gidan nagani kamar Aljanna “tsaki hajiyar ta saki kafun tace” fito”ajiyar zuciya Tahee ta sauke kamar cikakkiyar na’kauyiya tafara kici niyar yadda zata bud’e motar harsaida hajiya tazo bud’e mata tana Jan tsaki ,bin ta abaya tahee ta soma tanayi tana ‘kara bin part d’insa da kallo kamar anan ne Zata gansa . Lokacin da zasu shiga part d’in Ammey sai datayi addu’o’in neman tsari tukunna tasaka kafarta da Bismillah, Ammey na zaune kan kujera kafa d’aya da sauri ta tashi tsaye sabida yadda ta jiya zuciyar ta , ta tsinke ga wani bugawa da take yi sosai da sosai , kallan kallo suka tsaya yi ita da tahee da taji kamar taje ta sha’keta mutu , tsanarta na ‘kara shiga cikin zuciyarta Amma gudun kar agano yasa ya wajance da kallan falon tana zazzare idanuwa kamar yadda ‘yan aiki sukeyi, ajiyar zuciya Ammey tasaki dukda lokaci d’aya taji jikinta ya mutu tana bu’katar Hutu shiyasa cike da fara’a tace wa hajiya su shigo ciki, Tahee a ‘kasa ta zauna tana ‘kara bin Ammeey da kudi ya ‘kara zauna mata da kallo , muryar hajiyace ta dawo da ita hankalinta lokacin da taji tana gaishe da Ammey , itama tahee cike da sokwanci da bar kwanci ta gaishe da Ammeey tana bud’e mata hakwaranta ba’ka’ke , da Sauri kuma Ammeey ta kawar da kanta sabida yadda taga bakin tahee , a fakaice tahee ta danna wani abu a wuyanta lokacin da zata agaishe da Ammeey, cikin ikon Allah kuwa sai ga muryarta ta canza kamar ba ita ba , Ammey bata jira jin dogon zance ba bayan sunan tahee da ta tanbaya, yanxu ma tahee washe mata baki tayi kafuntace “ ai aradu hajiya sunana kande kina ganina a ‘kauyan mu nafi kowa cin gasar ‘kyau, “ girgiza kai Ammeey kawai tayi hakanan taji batasan hayaniya musamman kanta da taji ya fara sara mata , sama ta hau shaf shaf kafin ta sauko da wata jaka a hannunta tana mi’kawa hajiya “ zaki iya barin ta anan , duk yadda ake ciki nan da kwana biyu zan sanar dake , idan ta cancanci zama dani shiknn, idan ina bu’katar wata kuma zan sanar dake “ cike da girmamawa hajiyar tayiwa Ammey Godiya bayan shatara ta arzikin da ta bata, falon yayi saura daga tahee sai Ammeey dake bin tahee da kallan ‘kurinla.” Kikace sunanki kande ?” Yanxu ma tahee hakwaran ta washe duk da ydda taji zuciyarta tana tafarfasa kamar gawashi ganin Ammey a gabanta .” Eh hajiya sunana kande , kuma a radu hajiya kome zaki sani a gidan nan zan miki indea zaki dunga bani abincin ku na birni”, wani lallausan makirin murmushi Ammey ta saki tana ‘kara bin fuskar tahee da kallo, wayarta ta d’aga kafun tace ina jiran ki yanxu “, basu ‘kara mintuna biyar ba tahee sai faman barkwancin ta take mata, Asabe ce ta Fito daga wata ‘kofa kamar kullum shigarta na ‘yar aiki ne a jikinta,nuna mata tahee Ammeey tayi “ kikai ta dakin can na ‘kasa ita kadai banaso a had’ata da kowa sannan ai mata abunda ya kamata zanje na huta kafin anjima , cike da girmamawa asabe ta amsa da toh Ammeey , itama tahee har da dur’kusawa wajan godewa Ammeey. Bin d’akin da aka kawo ta tahee tayi , katifa ce kawai a d’akin sai wardrobe da gaban mudubi , koda asabe zata fita ynxu ma sai da ta gode mata, maida kallanta tahee tayi kan gaban mudubin d’akin tana ‘karewa fuskarta kallo, duk Wanda ya ganta tabbas zai d’auka yar ‘kauyece musamman yadda jikinta yake da bakin wahala, guntun murmushi ta saki “ idan kinsan wata ai baki san wata ba “ cewar tahee cikin zuciyar ta , dawowar asabe ne yasa tayi saurin ‘karasawa ta kar’bar mata kayan cike da girmamawa “ ga wannan abincin Ammey tace a baki kici ki huta zuwa anjima kafun ta nemeki, amma gaskiya gaskiya kin cika mai sa’a sabida ni banta’ba ganin hajiya ta saka wani a wannan d’akin ba .hajiya na da kirki kiyi mata duk abunda tace ko kinsamu ‘karin albashi “,cewar asabe , tahee kuwa sakin baki tayi tana kallan asabe kafun cikin mamaki ta furta “ Dagaske kike ? Gaskiya hajiya nada kirki, kuma ko me tasani zanyi mata “, itama asabe washe mata baki tayi kasantuwar ta da shegen surutu” gaskiya dai ya kamata,kinga yanxu shirye shiryen biki ake sai kisamu ko atanfa da Jan baki kishiga sabida Kema ki fito cas dake , yanxun kama tahee batacewa asabe komai ba sai hakwaranta data Washe har ta bar d’akin “ tabbas befi wata biyu bikin sis Ilham ba kamar ydda yazama Kema zaki fara irga ranar tonuwan asirinki” cewar tahee cikin zuciyarta. ‘Dakin ta ‘karewa kallo kafun ta kalli tray d’in abincin da aka kawo mata , har zata ‘kici kuma sai wata zuciyar tace karta zauna da yunwa karba fuskanci wani abu, saida ta zauna tayi addu’o’in neman tsari da yanxu bata gajiya da yunsu cikin Bismillah ta zauna taji lafiyayyan abincin da aka dafa tunda tasan aikin asabe ne , kunun ayar da ta gani ne yasata binshi da ido kafin cikin Sauri ta d’aukesa ta juye a sink gabaki d’aya ta dawo da medium abun kunun, katifar da aka ajje mata ba , amaimakon ta kwanta akai sai ta samu gefe tayi kwanciyarta bayan ta kulle d’akin, bata jima ba bacci ‘barawo ya d’auketa. 3:40 tahee ta farka da Sauri ta mike tanufi toilet shaf shaf tayi abunda zatayi tayo alwala, kafin ta d’auko face d’inta da abun bakin ta shash shafa a cikinta , sallar asahar ta rama , Daidai lokacin da ake kiran la’asar shima , tana idarwa ta bud’e ‘kofar takin kamar wata ‘barauniya ta fito daga cikin dakin tana bin ko ina da kallo, “ kina bu’katar wani abune ?”, cewar asabe da take ‘ko’karin kiranta, cikin waske wa tahee ta soma kinkina “ dama dama na d’auka akwai aikin da zanyi ne sabida zama waje d’ayan danayi duk jikina ciwo yake na saba da Noma da ayyukan gida shiyasa nake neman hanya “, Washe mata hakwara asabe tayi “ Allah sarki Aushe baki da ‘kiwa kinga kuwa duk abunda hajiya tace miki kiyi toh shiknn zaku shirya da ita sosai nake fad’a miki yanxu ma catai na kiraki , ina ‘kara jadda da miki kiyiwa hajiya biyayya tana da kirki matarnan,” cikin gamsuwa tahee take d’aga mata kai har suka ‘karaso cikin falon ita kuma asabe ta juna , cikin girmamawa cike da ‘kauyancin tahee ta soma yiwa Ammeey karari, Ammey kuwa sai faman sakin murmushi take kafun ya kalli Tahee da mugun kallan nan nata “ kikace kome aka saki zaki iyayi?” Da Sauri tahee ta jinjina mata kai “ Aradu hajiya kome kika sani zanyi miki ,” yanxun ma wani murmushi Ammeey ta saki kafun ta ciro wasu Abu a cikin jakar gefanta da wasu ma’kudan kudi ta fun ta nuna tahee “ idan kika bi abunda nace toh tabbas zaki samu ninkin su ba masu ba “. Sai ta nuna wasu wani abu Aroba “ yanxu idan nace ki zubawa wani wannan fiya fiyan zan baki 50k zakiyi”, waro idanuwanta da aka sawa ‘kwayar iho tahee tayi , da farko Ammeey ta d’auka ihu zatayi ne sai kuma tafa sa’banin hakan “ Haba hajiya yo ai wannan me sau’kine , dubu hansin ba ? Idan akai mun kayan d’aki nida iluna ai sai nafi kowa gata , Nidai kome kika sani hajiya zanyi miki dan saida a kaimun fad’a a gida akan duk inda kud’i suke innemo ,”yanxu ma murmushi Ammeey ta saki tana raya wani abu acikin zuciyar “yanxu nice shugabanki, duk abunda nasaki shi zakiyi , idan kika kuskura kika sa’bamun sai dai in wata bake ba , sannan maganar ta tsaya tsakanina dake idan kika kuskura najita abakin wani toh tabbas daga lokacin bazaki ‘kara magana ba “cikin tashin hankali tahee ta zaro idanuwanta tana had’e hannayenta biyu “ tuba nake hajiya aiko me kika sani shi zanyi miki ni babu ruwana da kowa umarnin ki kawai zan bi “, wata yar iskar dariya Ammeey ta saki ita kad’ai tasan me take rayawa cikin zuciyarta , kafin ta danna wani abu? Babu jimawa asabe ta ‘kara fitowa “ kinuna mata yadda ayyukan suke , da tsare tsaran komai bana san kuskure”, insha Allahu hajiya ai duk abunda kika ce shi za’ayi , kafun tayi wa tahee alamar ta taso, cike da ‘kauyanci tanayi tana ‘kara kallan falon haka suka bar falon . Duk abunda take akan idan Ammeey shiyasa ta d’auko wata kanta memiyar wayarta , wata number ta saka , ba a jima ba a ka d’auka , bata jira jin maganar me wayar ba ta soma magana cike da ‘kosawa “ tabbas muna gab da cika burinmu dan nasamo wacce zatayi mana komai namu kawai umarnine “, banji me aka ce mata ba sai ‘kara sakin wata dariya da tayi kafun ta kashe kiran , jinta take yau sakayau ga wani farin ciki da ya cikata ganin burinta yana ‘ko’karin cika cikin sau’ki. A’bangaran tahee kuwa yadda ake anfani da komai na kitchen asabe ta koya mata shima saida asabe taci uwar kwakwa kafun tahee ta nuna mata tagane dan har yadda ake kunna gas sai da sabe ta nuna mata ya kai sau goma dan data kar’bi asha na zata kunna gas sai taja baya wai wuta zai kamata, Asabe ba ‘karamin wuya Tasha ba kafun tahee ta fuskanci abunda ta Goya mata , duk tsarin part din Ammey sai da ta sanar da ita da inda ake shiga da inda ba a shigar mata musamman lambunta da ba a shigarsa. Cike da bin umarni kuwa tahee take furta ta gode , sai wajan 6:30 sannan suka gama , lokacin da asabe zata ‘kara nuna mata d’akin da take dan cewa tayi ta manta hanyar, d’akin da yah moh ya sanar dasu ta kalla kafun ta saki wani lallausan murmushi , har ta koma masaukinta. Shima sai data kulle ‘kofa tukunna tayi sallah kafun ta ‘kara shafa ba’ki ba’kin abun nan , tasan tabbas idan tace zatayi wanka ynxu zasu iya fahimtar wani abun shiyasa ta hakura da yi, bata fito ba har saida tayi sallar isha’i, lokacin da Ammey ta sanar dasu tafiyarta part d’in dada . Kamar tahee zata kurma ihu haka take ji ganin babu damar fita . Zagaye ta somayi cikin d’akin nata, tunanin mafita akwai take yi ita kad’ai , ranta har soyuwa yake idan ta kalli Ammey, tana san fita falo amma tana gudun kar Ammey ko asabe su Fito , wani ‘bangare na zuciyar ta kuma yana bata ‘kwarin baiwar fitar danji take idan bata nakasa abeey ba, bazata ji dad’i ba . Shahada Kawai tayi kuwa , cikin ikon Allah kuwa babu kowa a falon, hanyar d’akinsu su asabe ta kalla nan ma shiru da Sauri ta nufi kitchen tana ro’kan Allah yasa kar Wanda ya fito, Daidai ta zuba man gyad’a a cikin ledo kuwa ta soma jin motsi alamar ana nufo kitchen d’in da Sauri ta rufe man gyad’an ta shige ‘kar’lashing dinning din, wata ce itama da kama kallanta kasan yar aikice, cikin sand’a ta bud’e fridge duk akan idan tahee , Ayaba da kankanar da ta gani ta ‘iba kafin cikin sauri ta bar kitchen d’in tana waiwaye , tahee dariya ce taso ‘kwace mata amma ganin bata da lokaci ne yasata fitowa ita daga ma’boyarta . Babu kowa a falon har yanxu da Alama Ammeey ma bata dawo ba . Bakin ‘kofar shigowa tahee ta nufa cikin Sauri Sauri kafun ta d’iga wannan ta ydda ba Lalle hankalin mutum ya kawo wajan ba . A cikin abun flowers ta jefa ledar tare da komawa d’akinta hankali kwance, dan tayi alkawari daga rana irin ta yau Ammey sai ta fara fuskantar hukunci. Gudun kar axo Tashinta yasa ta saka lock ta cikin d’akin har yanxu kuma bata kwanta akan catifar ba , dan bata yarda da komai na Ammeey ba . AMMEY Ammey kuwa ba ita ta dawo part d’inta ba sai wajan 10:30, da ka kalli fuskarta za kasan ranta a ‘bace yake amma kasantuwarta shu’umar mata sai ta ‘boye hakan da murmushi akan fuskarta.har ta dawo part d’in ta tana tuna maganganin bikin da aka ‘kara tattaunawa na ilham , ba komai ne yafi ‘bata matarai ba kamar yadda su momy suka zage suna yin abu gabaki d’aya sun toshe ko wace hanya, tazo zata shiga cikin falonta kafarta ta hagu ta zamar da ita sai ji kake kafff , Ammey ta kife tsakiyar bakinta ya daki ‘kasa take jini ya fara zuba , wata gigitacciyar zafin azaba Ammey ta saka ganin yadda ‘kugunta ya bugu ga ha’korinta da take ji kamar babu su a bakinta. Kwalla kiran sunan asabe take amma babu asabe babu labarinta , lokacin da ta fad’i kuwa akunnan tahee dan itama taji ‘karar, ganin aikinta ya cikane yasa taje tayo alwala ta kwanta. Ammeey tun tana faman ‘kwalla musu kira har tayi shiru Sabida azabar zafin da yake ratsata , tafi munti 10 kwance a wajan gashi ba damar kiran wani, da’kyar taja jikinta har ta nufi d’akin tafinta sai kuma ta dakata dan tasan cikin sharad’in boka duk Wanda yake da ciwo toh tabbas ranar Jininsa za a zu’ke cike da wani ‘karin takaici ta Nufi d’akin kusa dashi, hankalin ta gabaki d’aya be kawo kan man gyad’an ba , ga baki d’aya takaicin ta kaicin dake cin zuciyar ta ya hanata ganin hakan. Tana shiga cikin d’akin taji abu kamar abakinta masu kauyi da sauri ta tufosu waje, cikin gigita ta saki ‘kara ganin hakwaranta biyu sun cire tana ‘kokarin fara karanta maganganun tsafinta hakwaran suka ‘bace duka . A gigice ta fara dubawa d’akin ko zata gansu Amma gabaki d’aya babusu babu alamarsu, da Sauri ta ‘karasa gaban mudubin d’akin cike da tsoro ta bud’e bakinta kad’an, ha’kwaranta biyu data ga babu yasa ta sulale a ‘kasa sumammiya. WASHE GARI Kiran sallahr azuba a kunnan tahee , dama bata da magagin bacci saida ta fara yin wanka tukunna kafin ta yi sallah, gudun kar azo kiranta yasa cikin sauri sauri ta mayar da fuskarta da kwayar idanunta da yake canza mata kamanni, man da zai yasa jikinta duhu ta shash shafa , tsaf ta fito kande ‘yar aiki abunta, tunawa da muguntar da tayiwa Ammeey ne yasata kwashewa da dad’i, ‘boye abubuwan anfani ta tayi kafun ta fito daga cikin d’akin ynxu ma cikin sand’a , Asabe bata fito ba shiyasa cikin sauri ta ‘karasa inda ta zubar da man, tana zuwa taga Jini Jini alamar harda ciwo Ammey taji , cikin Sauri ta d’auko abu ta goge wajan tass babu ne cewa azuba wani abu a Wajan , dabara ce ta fad’o mata tayi saurin komawa d’akin gudun kar a zargeta , kusan mintuna 10 ta fara cin motsin mutum da Sauri ta kwanta . Asabe ce ta bud’e d’akin ganin har yanxu tahee bacci take kuma a ‘kasa yasa ta fara tashinta, ban’karewa tahee tayi tana bud’e kafun ta waro su duka ganin asabe a kanta “ ya naganki kwance a ‘kasa bayn ga katifa “, kallan katifar tahee tayi cikin zuciya ta furta “ hauka nake ?” A fili kuwa washe ha’kwaranta tayi ,”yo ba ance duk Wanda yake kwana akan irin wannan abu me yaushi aljanin dare na zuwar masa ba , kuma ni inna kwanta a irin wannan abun ai mutuwa zanyi “, dariya asabe ta saka “waya fad’a miki haka ?” Cike da barkwanci tahee ta furta “ malamin Allon mune ya sanar damu kuma yace har ciki a keyi “ ta ‘karasa tana toshe bakinta . Yanxu ma dariya asabe ta saka gudun kar Ammey ta Fito ne yasa ta kallan tahee “ kande ya kamata mu fara aikin mu tun ynxu , kar Ammey ta fito “, toh kawai tahee tace mata suka Fito , suka fara shirin abincin safe kasan tuwar daman akwai masu shara da wanke wanke , farfesun kifi asabe tayi da hot chips sai plantain din da tayi , tahee sai kallan yadda take ai tayi a zuciya ita kad’ai tunanin shigowar king take amma shiru”, a fili kuwa da asabe tayi abu sai ta tafa mata , sai ‘karfe 80:20am Suka kammala asabe sai faman nuna mata ydda ake jere tayi , ita kuwa sai bin motsin kowa take so take taga fitowar Ammey amma har yanxu shiru. Suna tsaye wasu ‘yan mata kyawawa suka shigo falon ko wannansu sanye cikin material gabaki d’ayansu babu Wanda be hadu ba acikinsu, Hutu da kud’i duk ya nuna a jikinsu. Da Sauri asabe ta gaishesu, tahee ta durkusa daniyar gaishesu taji ta farkon ta furta “ gaskiya ilham baki da mutunci ki duba kiga da sassafe kinsa duk mun wani shirya “, da Sauri tahee ta d’ago ta kalleta , cikin Sauri kuma ta bisu da kallo” ilham ? Sumayya? Firdausi?”, Dagaske kunake gani?” Duk wad’annan tanbayoyin kanta take yiwa su, firdausi da ta kula da kallan da tahee take musune yasata sakin murmushi “ ya sunanki?”cewar fiddy, ‘kwallar da take ‘ko’karin zubo mata tayi saurin tare wa cikin washe baki ta furta “ sunana kande “, atare gabaki d’aya yan matan uku suka kalleta , haka kawai suka ji burgesu kodan wani abu da ya ta’ba faruwa da bazasu manta dashi ba . “ Ammey fa?”, da Sauri tahee ta juya wajan asabe , cike da girmamawa ta furta “ har ynxu bata fito ba “. Okay cewar ilham, cike da girmamawa suka bar wajan har yanxu taheee tana tunanin me ya hanasa zuwa part d’in , ta’bata da asabe tayi ne yasata tashiga taitayinta , su ilham basu wani dad’e ba suka bar part d’in sai alokacin Ammey ta fito fuskarta duk a kunbure , dariya ce ta so ‘kwace wa tahee amma ta danneta ganin yadda le’ben Ammey ya kunbura, ganin yadda suke sunkuyar da Kai Ammey cike da kuluwa ta furta Menene kuke sunkuyar da kai, d’agowa sukai a tare suka kalli Ammey ganin babu ha’kwara biyu a bakinta yasa gabaki d’ayan su fashewa da dariya . 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 Mss Lee BOOK 2 Page biyu na had’e muku na jiya da na yau …. 🙏 Page 14&15 Ita kanta tahee bata san lokacin da dariya ya kwace mata ba musamman yadda ta hango wawulon Ammey ,daka musu tsawa Ammey tayi rai a ‘bace , sai a lokacin suka kula da abunda Suka ai kata , gabaki d’ayansu shiga taitayinsu sukayi ganin yadda ranta ya ‘baci, wata dariyarce ta so kama taheee amma take ‘ko’karin danne ta gudun kar Ammeey ta ‘kara zuciya, cikin muryar fad’a ta ‘kara daka musu tsawa “ ku ‘bace mun dagani”, bashiri kuwa suka bar Wajan , tahee na shiga d’aki ta ‘kara fashewa da dariya ita kadai idan ta tunano bakin Ammeey sai ta ‘kara fashewa da dariya , knocking d’in dakin asabe tayi kafun ta shigo ciki kai tsaye, Allah ya te mako tahee bata cire face d’in ta ba , abincin ta asabe ta mi’ka mata itama idan ka kalleta zaka san da fara’a a kan fuskarta, lokaci d’aya kuma tahee da asabe suka ‘kara fashewa da dariya sai da sukayi me Isarsu tukunna asabe ta bar d’akin,breakfast d’inta tahee taci hankali kwance tana tunanin shirin da zata yi nagaba kar Ammey ta gano ta . 12 : 10 asabe ta ‘kara zuwa kiran tahee , yanxu ma abincin rana suka fara shirye shiryen yi fuskar kowa da annashuwa musamman tahee da take yi da biyu, har lokacin kuma tun da Ammey ta shige d’akinta bata kuma fitowaba hatta breakfast kai mata a Kai. Yanxu ma lafiyayyen lunch suka yi kusan rabin aikin asabe ce ke yi,sabida kallan tahee da take a bata waye ba bata san yadda ake abincin ‘yan gayuba , suna Kammala girkin asabe ta zubawa Ammeey cikin babban tray bayn ta zuba komai da komai cikin warmer, mi’kawa tahee jug d’in juice tayi ita kuma ta d’auki tray d’in “ Abincin Ammey ne tace na kai mata d’akinta ni kuma sun mun yawa shiyasa zaki rakani kinji”, toh Kawai tahee tace mata dan ko ita da Ammeey ta kawo ta bata ta’ba shiga d’akin ba sai ynxu da zata shiga , bakinta d’auke da addua ‘kasa ‘kasa ta biyo bayan asabe lokacin data bud’e mata kofar d’akin, Ammeey dake kishingid’e kan gado ce ta d’ago azabure , cikin firgita da tsoro gabaki d’aya ta Amma ta da hakwaranta da Suka jire , jikinta har mazari yake da ya bawa tahee mamaki, wani tsawa ta daka musu da Suka ji har saman kansu “ Me ya kawo ku d’akina na rawa asabe ta nuna tray d’in hannunta , a rarrabe ta furta “ da daman abincin ki ne muka kawo miki ganin baki fito ba…” bata ‘karasa ba Ammeey ta kwashe fuskarta da mari sakin jug d’in hannunta tahee taji jiki na rawa zata soma bawa ammey hakuri ta nuna musu kofa “ kafun ranku ya ‘baci banasan ganin d’aya daga cikin ku anan , ku ‘bace mun dagani” cike da Tsoro tahee ta nuna jug d’in da ya fashe “ hajiya bari na fara kwashe abun tangaran nan “, bata kai karshe ba Ammey ta ‘kara daka musu tsawa “ nace ku fita ko?” Bashiri gabaki d’ayansu suka bar d’akin, tahee harda janyo mata ‘kofa, tana ganin ‘bacewarsu ta zu’be ‘kasa tana dafa kanta “ nashiga uku meyake shirin faruwa dani? “ ‘ko’karin danna zobanta take amma ciwan bakinta ya hanata dan tasan abunda zai biyo baya , tana tsugunne a wajan kamar wani aljani ya bayyana a d’akin, inda Ammey take ya nufa shima gabaki d’ayansu a firgice “ me kike shirin aikatawa? Tonuwar asirin mu kike so ko kuma me?kinfi kowa sanin ‘ka ‘idojin bokanya, kara na biyu da kika ‘kara ‘bata mana shiri, bazan lamunta ba “ , na fad’a miki bazan lamunta ba, idan kika ‘karayin kuskuran akaro na uku to tabbas jininki ya zama salwantaccen,” yana kai ‘karshen maganar sa yayi wurgi da ita saida kanta ya bugu, shima gabaki d’aya hankalinsa a tashe ya ‘kara ‘bace wa daga cikin d’akin. Cikin d’aga murya da fita hayyaci Ammey ta soma magana “ bazeyu ba tabbas Kema kande lokacin aikin ki yayi , shirina bazai ‘baci ba, daga rana irin ta yau , aikin da ke kanki zai fara “ ita kad’ai sai surutai take yi . Tahee kuwa ranta fess suka ci gaba da ayyukansu bayn sunyi sallah, har yanxu idanunta na kan kofar da yah moh ya sanar da ita akai amma har ynxu shiru Ammey bata shiga ciki ba . Sai wajan yamma Ammey ta fito daga cikin dakin , daka kalli fuskarta kamar hadarin kaji, har lokcin le’banta daya kumbura be saceba, “ kande , kande “ , Ammey ta dunga kwalawa tahee kira , jiki na rawa tahee ta zo ta zube mata , kare mata kallo Ammey tayi ganin yadda jikinta yake rawa , kafun ta mi’kawa tahee wata ‘yar ‘karamar jaka , da Sauri kuwa tahee ta karba “ zaki ga bangarori da yawa , ki irga na ukun ciki daga hagu , idan kinga ‘yan mata a falon kice kina neman dada sai kibata, karkiyi kuskure fa “, ba’kin hakwaranta tahee ta bud’e mata “ insha Allahu hajiya bazanyi ba “, kamar sa kai Ammeey tayi daga ganin hakwaran tahee. Da Sauri tahee ta nufi kofar fita , da’kyar ta iya bud’e kofar acewarta wahala ne da kofar ‘yan gayu tana fita har zata nufi part din dada ki tsaye sai ta fara irgawa kamar tanasan cinkar part d’in, sai da tayi almost 5 minutes tana ‘karewa ko wane part kallo kafun ta nufi part d’in dada wani irin sanyi da iska me kamar hadari yana busata. Tana shiga kuwa ta tarar da su ilham sai baman za’ban kaya suke , da sallama tahee tashigo palour gabaki d’aya kallanta sukai lokaci d’aya kuma suka amsa mata sallamarta.jakar ta mi’ka musu cike da barkwanci ta furta “ wai hajiya ce tace a bawa dadu(dada)”,gabaki d’ayansu kwashewa sukai da dariya kafun ilham ta furta “ dada ko?”, washe baki tahee tayi “ kwaran kwatse haka tace , sunan yan gayun ne nakasa fad’a shiyasa “, yanxun ma wani saban dariya suka saki , Daidai lokacin da dada take Fito wa daga cikin d’akin, binta da kallo tahee tayi “ itama ta ‘kara tsufa, farin gashin kanta ya Fito sosai “, cike da girmamawa tahee ta tsugunna ta gaishe ta lokacin da taji hawaye ya sakko mata a ido , da Sauri ta goge gudun kar wani ya gani a gidan , itama dada ba yabo ba fallasa ta amsa mata kafun ilham ta mikawa dada jakar da tahee ta shigo dashi “ Allah sarki , kilishi bata gajiya da d’awainiya , toh Allah yayi albarka “, gabaki d’ayansu amsawa sukai da Ameen banda tahee . Zata tafi ilham ta tsayar da ita , “ kande bari na d’an aikeki part d’in ummey ki kai mata wannan”, tsayawa kallan bakinta da ta furta ummey tayi , zumudi nasan fito mata Amma tana ‘kara dannewa, ta mi’ka hannu daniyar kar’ba taji sallama a bayanta,da Sauri ta juya batasan lokacin da bakinta ya furta “ you!?”, tsayawa kallansu su ilham sukai , tahee sam ta manta suna wajan sai tayi saurin wayancewa da “ You You!! Nayi daidai ?”, yar dariya sukai tare da kawar da shashancin tahee, ajiyar zuciya Tahee tayi tana ‘kara bin Mimi da tashigo cikin shigar ‘yar aiki itama a fakaice ,” Yawwa shikenan tunda kinzo , ita kande ta koma wajan aikinta inyaso ke sai ki kai wa ummey kayannan “, kar’ban kayan Mimi tayi tana cewa toh , dariya duk ya cika mata ciki wato haka tace musu sunanta kande , ita kanta tahee saratu da aka kira Mimi sai da yaso bata dariya Amma tana dannewa , a fakaice ta yadda babu Wanda zai gansu Mimi ta d’aga mata gira d’aya da Sauri tahee ta d’auke idanuwanta tana musu sallama, ita kad’ai a ranta take magana “ yarinyar nan so take asirin mu ya Toni take mun signal ko ? Zan kamata , amma Yaushe ta zo gidan nan itama ?”da wannan tunanin tahee ta koma part d’in Ammey. Yanxu ma Ammey bata falon shiyasa kai tsaye ta nufi makwancinta, kan ‘karamin karfe d’in Wajan sai kayanta datayi fulo dasu har yanxu ta’ki yadda ta hau kan katifar sabida hakanan kawai bata yadda da katifarba. Da daddare ma asabe ce ta kawo mata abinci tunda babu wani aiki da zasuyi, ita kad’ai tana tsaya yadda zatayi magana Ammey. Part d’in king ne ya fad’o mata arai, “ kana ina nayi kewarka sosai !!!!!! Plx kana ina “, duk da acikin zuciya tayi magana dole ka gane kad’ai cin da take ji aranta , sosai yau take missing d’insa so badly, so take kawai tajita a jikinta, bata san lokacin da ta rungume jikinta ba tana lumshe ido gabaki d’aya tsananin kewarsa shida junior d’inta ne ya cika mata cikin zuciya . Bata san lokaci ya ja ba saida ta kalli agogo taga ‘karfe 9, da Sauri ta Tashi tayi sallahr isha’i tare da kulli ‘kofar da lock , sai da ta zauna tayi addu’o’in neman tsari sosai kafun ta soma akaratun alkurani a hankali a hankali, a haka bacci ya d’auketa tana karatun. Karfe 2:30am na safe tahee ta soma jin wani irin bugun ‘kofa a d’akin ta, tun anayi a hankali har aka somayi da ‘karfi kamar za’a ‘balla ‘kofar d’akin, a rud’e tahee ta soma karanto duk adduar data zo bakinta , ‘karar abubuwa da jijjigar’kofar da ake ne ya ‘kara tsoratar da ita amma duk da hakan sunan Allah ne a bakinta . Kamar ‘kiftawar ido aka koma side d’in window shima a haukace aka dunga bubbuga windows din kamar za’a ‘balla ga wasu irin kuka da suke tashi ta ko ina, side d’in kofar aka koma shima nan d’in bubbbuga wa akeyi had’e da kuru ruwa , mintuna kad’an kuma ya koma window , haka y dunga yi tsawan lokaci, sai wajan 3:10 kafun abun ya lafa , har yanxu tahee addua ce a bakinta daman tasan za ‘a rina , Ammey bazata ta’ba barin ta Haka ba . Gabaki d’aya tsoran komawa baccin take , saida bacci ‘barawo ya kwasheta. WASHE GARI Yau kam Ammey ta rigasu fitowa tunda suka fito take bun fuskokinsu da kallo kamar tana san fuskartar wani abu.har izuwa lokacin kuwa ciwan bakinta be gama sacewa ba, abun dariya facemask d’in da tasaka a rabin face d’inta,amma duk da haka idan tayi magana sai alamun rashin ha’kori ya fito mata. Gabaki d’aya yinin ranar kuwa Ammey a falo ta zauna duk yadda tahee taso had’uwa da Mimi abun yaci tura kamar dama Ammey ta san plan d’insu, duk yadda taso Zillewa Ammey bata , bata wannan damar ba , gabaki d’aya yinin tahee bata had’u da Mimi ba sai hakura tayi . *****Haka tahee ta cigaba da zama a part d’in Ammey matsayin yar aiki , ga biki da yake ‘kara kusantowa ,duk yadda taso ta Samu evidence akan Ammey abu ya ci tura gabaki d’aya babu wan sheda da zai nuna maka Ammey tana yin wani abu , har lokacin kuma bata ‘kara had’uwa da Mimi ba tun bayan had’uwar da sukayi a part d’in dada . Yau sati d’aya kenan da zuwan tahee , gabaki d’aya lamarin Ammey ya fara d’aure mata kai , duk dare idan ta kwanta wannan buga ‘kofar da ake a haukace me yake tashin ta daga bacci amma Sabida kariyar ubangiji babu abunda ya sameta, tsawan sati kenan har yanxu taheee bata kwana akan katifar d’akin, kome zatayi cikin taka tsan tsan take yinsa gudun kar asirinta ya tonu. ✨✨✨✨✨✨ Yau ya kama Monday,batasan me ke faruwa ba, sai ayyukan da Ammey ta sasu na dafe dafe da soye soye kamar za’ayi wani babban taro gabaki d’aya Ammey yinin ranar a tsaye take sai faman rawar kai take ga wani farinciki da ya kasa ‘boyuwa akan fuskarta, abinci kuwa kala kala tasa su asabe aikinyi, 6:30 ta saka su asabe zaryar kai abincin part d’in Ammey , ban da wani kunun ayan da ta had’a da kanta sai faman tashin ‘kamshi yake , tahee na tsaye tana kallan ikon Allah ganin ita ba’a sata aikin komai ba , sai umarnin jiranta da Ammeey ta bata . Kiran sallar da akene yasa ta komawa d’aki saida ta kulle ko’ina tukunnan sannan ta cire fuskar, take kyakkyawar fuskarta tafiya kwanin burgewa gudun kar wani ya shigo ya sameta yasa ta yin alwala , tana idar da sallah ma ta mayar da face d’in , sosai take kewar su junior da momy gabaki d’ayansu. Kamar yadda tayi zato taba kammala sallar asabe ta kawo mata abincin Daren, ba musu kuwa ta ‘kar’ba duk da agaban ta akai komai ,snacks din da tayi da hannunta kawai ta ydda taji shima sabida yunwar da take ji hatta leman da aka bata, bata shaba sai ma juyeshi da tayi a cikin toilet. Har lokacin Ammey bata ‘kara nemanta ba , sai bayan kiran sallahr isha’i da ta da asabe kiranta. Tana fitowa taga Ammey ta sha uban kwalliya sai faman walwali take amma ba’kin zuciyarta ya hana a ga kyaun ta sai mununta cewar tahee . “ kande “ cewar Ammey tana katse wa tahee tunanin da ta fad’a , da Sauri tahee ta ‘karasa Inda tace cike da biyayya ta tsugunna , jug d’in kunun ayar Ammey ta nunawa tahee , “shi zaki d’aukomun ki biyo ni dashi”, da Sauri tahee ta amsa sa da to hajiya tana mamakin ne ya hana akai kunun ayar lokacin da ake kai abuncin, babu me bata amsa shiysa ta cire zancen cikin zuciyarta . Tunda suka fara nufar hanyar part d’in dada haka kawai zuciyarta ta soma tsinkewa , ka ‘kafafuwanta da sukai sanyi kamar me shirin zubewa ‘kasa , duk da Haka bata karaya ba addua take karantowa a ‘kasan zuciyarta . Suna shiga falon saura kad’an ta saki jug d’in hannunta, ganin gabaki d’aya ilahirin familyn suna Zaune kamar yadda suka saba , shi kad’ai ne babu sai zoya da samreen da basa nan sai kuma mahma , a d’ad’d’ai da d’ad’d’ai ta soma bin ko wannan su da kallo kafun ta sauke idanuwanta akan ummey, hakanan ummey ta tsinci kanta da sakin wa tahee murmushi , itama tahee murmushi ta d’an sakar mata , kafun ta tsugunna har ‘kasa tana gaishe da ko wannan su d’aya bayan d’ayan kukan da yake shirin kwace mata take ‘ko’karin dannewa sabida kar su fahimci halin da take ciki, gabaki d’ayansu cike da kulawa kowa yake amsa mata gaisuwarta.d’ago idanuwanta tayi ko zataga Mimi Amma gabaki d’aya ba Mimi babu alamarta. A wayance Ammi take Kare bakinta ta yadda basu fahimci cirewar hakwaranta ba, amma abunda bata sani ba Abbey da ummey sun gani shiru kawai sukai da bakinsu ganin kowa na cikin falon. Basu dad’e da zuwa ba gabaki d’ayansu suka nufi dinning area , kallan tahee ummey tayi kafun ta ‘kara sakar Mata murmushi “ idan kika fita ‘nan gare na biyu ki kiramun saratu kinji ?” Da Sauri tahee ta amsa mata gudun kar Ammey tayi magana yasa ta juya cikin sauri sauri ko tunanin ajje jug d’in batayi gabaki d’aya ta manta da wani jug a hannunta. Hadari hadari ne ya soma kad’awa ga wata sanyayyiyar iska da take kad’awa itama , part d’in king da yake d’an nesa da ita ta ‘kurawa ido , ynxu hawayen da suke zubo mata batayi ‘ko’karin dakatar dasu ba , tafi tsawan mintuna 5 tsaye a wajan ga inda take da d’an duhu duhu,batayi auneba taji an janyota baya an toshe mata baki ta yadda bazata iya ‘ko’karin guduwa ko yin ihu ba . Batasan ko wanene Sabida yadda aka rufe mata baki sosai har lokacin kuma jug d’in kunun ayar na hannunta.kai tsaye bayan part d’in uncle musaddiq aka jata ta ydda bazata iya Saurin guduwa ba , saida ya nisantata sosai daga wajan masu tsaro , kafun ya gwara kanta da jikin bango, yana ‘ko’karin ‘kara ta’bata kawai ta watsa masa kunun ayar hannunta gabaki d’aya . Duk da fuskarsa a kulle take hakan be hana jajayen idanuwansa fitowa ba , rai a ‘bace ya ciro knife d’in jikin wandansa yana nuna ta da ita, cikin muryarsa mara dad’in saurare ya soma magana “ dole aikina ya cika yau kamar yadda nake cika ko wace makafa haka Kema zanyi anfani da jikin ki wajan biyan bu’katata, idan kika gigin guduma sai na kasheki , na kashe banzan sannan na binneki ta yadda babu Wanda zai ga ko da sassan jikinki ne .”a tsorace tahee take bin fuskarsa da kallo tana san ganin fuskar wanda yake yake magana , ganin ya fara matsota ne yasa ta soma ja da baya, wata shegiyar dariya ya saki ko ‘ko’karin akamasa bayayi, gadan gadan ya nufo tahee da niyar yaje hijab d’in jikinta , take a Wajan kokawa ya ‘Barke tsakanin mutumin da tahee , adduar da take sanyima sai taji bakinta yayi nauyi ta kasa , suna cikin wannan kokawar taji ya saki ‘kara ya koma gefe , da Sauri ta kalli gefensa ,Mimi ce d’auke da dutsen da ta buga masa , da Sauri ta furta tazo mugudu, da Sauri tahee ta mi’ke ko takan jug din Ammey bata biba sai ma wani abu danaga ta du’ka ta dauka kafun su saka gudu ita da Mimi Suka bar mutumin kwance a wajan dafe da kansa. Direct basu tsaya a ko ina ba sai a part d’in ummey suna sakin ajiyar zuciya, dukda da wahalar gudun da suka sha hakan be hana Mimi kwashewa da dariya ba , “ amma anyi d’an iska da banga lokacin da yaje janki ba da uban me zai miki? Wallahi Allah ya temaketa babu makami a wajena da babu abunda zai hana nayi masa sabuwar kaciya, wani saban dariya Mimi ta ‘kara kwashewa da shi , harararta tahee tayi “ dad’ina dake wani lokaci kamar auta Sabida wauta,shima d’an iskancan koma wanene zan nemo shi, sai kuma ta bud’e ta fun hannun ta tana ‘karewa zoben data d’auka na mutumin kallo, wani irin jan zobe ne mara kyan gani , sai hotan idanu ako ina najikin zoben , kallan mimi tayi tana ‘kokarin yin magana tahee tayi mata alama da tayi shiru, shirin kuwa tayi tana bin tahee da kallo, cikin dabara yadda ba’a ji sauti ba ta nunawa mimi lokaci da kiran da ake mata , da Sauri itama Mimi ta d’aga mata kai alamar ta soma ta fiya, hakan kuwane ya faru tahee ta soma tafiya bayan ta ‘boye zoben da ta samu lokacin da take kokawa da wannan mutumin, gabaki d’aya hankalinta a tashe yake “ kenan akwai me bibiyata? Wanene wannan mutumin da ya kesan ta’bamun martabata? Me yake nufi da cikar burin sa?”, batayi aune ba kafarta ta daki wani d’an step d’in da zata hau , Adaidai lokacin da aka fara ruwa kamar da bakin ‘kwarya, azabar zafin da tajine yasa ta saki ihu tare dayin baya zata fad’i, gabaki d’aya ta sada’kar faduwa zatayi , batayi auneba sai jinta tayi ta fad’o jikin mutum . 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 07041879581 MSS LEE BOOK 2 Page 16 Runtse idanuwanta tahee tayi tana jiran jin fad’uwarta , batayi auneba sai ji tayi ta fad’o jikin mutum, kamshin turaran da bazata ta’ba mantawa ba yana dukan hancinta,’kara runtse idanuwanta tahee tayi , idan mafarki take ma bata so ta farka, a hankali ta soma kiciniyar bud’e idanuwanta da sukai mata nauyi, Daidai lokacin da ruwa me ‘karfi ya fara sakkowa , ita kanta tahee bata san lokacin da ta rungumesa a jikinta ba , tana faman sauke ajiyar zuciya. King kuwa kasa motsi yayi gabaki d’aya sabida yadda zuciyar sa take bugawa da sauri Sauri, shikansa besan dalilin ba , har ynxu kuma be kalli wadda take jikin nasa ba , amma tabbas sai yau zuciyarsa ta motsa, irin motsawar da bata ta’bayi ba sai a kan mutum d’aya sauyin bugun zuciyar ke canzawa . Da Sauri ya hankad’ata baya batare da ya kalli ko fuskarta ba . Adaidai lokacin da ya hankada tahee kuwa bata san lokacin da ta ri’ko rigar jikinsa ba gabaki d’aya Sukai baya zasu fad’i yayi azamar ri’ko ‘kugu ta tare da zuba mata narkankun eyes dinsa za Suka canza kala zuwa ja, gabaki d’aya king ya canza sosai , Hutu da kud’i duk sunbayyana a jikinsa Amma gabaki d’aya fuskarsa babu d’igon murmushi ko alamun ya ta’ba fara’a a rayuwarsa , bin fuskarta ya soma yi da kallo kamar yadda itama ta zuba masa na ta eyes d’in, yarda fuskarta ta nuna alamun tsorone yasa shi lumshe idanuwa tuno fuskar tahee duk lokacin da take cikin tsoro, da Sauri kuma ya ware idanuwansa akan kande da gabaki d’aya hankalinta na kan kallan kyakkyawar fuskarsa, wani gajeran tsaki king yaja da sauri ya d’auke hannun sa a cikinta take a Wajan ta fad’i kasa Sabida yadda kwankwasanta ya bugu sosai har da ‘yar ‘kararta, yadda tayi karan ne yasashi juyawa a Suka ne yana kallanta, amaimakon ya shiga part d’in dada kamar ydda yace musu zai shigo sai kawai ya juya zuwa part d’insa . Yana shiga part d’in gabaki d’aya jijiyoyin kansa suka mimmike kamar yadda ya saba tun lokacin da ta ‘bata , fresh ruwa ya d’auko tare da fito da wani robar magani a jikinsa , tablet uku ya had’a lokaci d’aya ya shanye su tare da jefar da ragowar magungunan, gashin kansa kawai yake cikurkud’awa ,bai san dalili ba , he just need his wife back, lokaci d’aya kuma ransa yayi mugun ‘baci ganin be tsinka wa kowace mari ba ydda ta fad’o jikinsa haka, “ why ! Why ! Why !” Shine abunda king ke furtawa ,sai kuma ya dafe kansa tare da lumshe idanuwansa. TAHEE Ganin yadda yabar wajan yasa hankalin tahee tashi sosai fatanta Allah ya sa yana lapiya , kamar ta bishi taga halin da yake ciki Haka take jin ranta amma babu dama ganin duhu na ‘karayi , da’kyar ta samu ta lalla’ba ta mike Sabida zafin da ‘kugunta yake mata dan ba ‘karamun buguwa tayi awajan ba, da ‘kyar ta Samu ta Daidai tafiyar, ganin yadda lokaci ya ja haka sosai jikinta da ya bara ‘baci, tana shiga gabaki d’aya suka zuba mata idanuwa, sosai ta tsargu da hakan dan batasan me zatace musu ba , amma amaimakon taga ‘bacin rai wajan ummey sai kyautar murmushi da ta samu , tun kafin tayi magana ummey ta Rigata “ Hala ruwan sama da aka soma yine ya tsayar daku?” Wata ajiyar zuciya Tahee ta sauke da inka kalleta sosai zaka fahimci Hakan , da Sauri kuma ta d’aga musu kai tana sassaita muryarta " wallahi hajiya na fita ne sai zuwa ya somayi sosai shine na d’an tsaya, da ya ragu kuma sai na manta ‘bangaran sai da nayi ta dubawa sannan na gane “, jinjina mata kai ummey tayi “ Ina saratun?” Zatayi magana saratu ta shigo cikin falon itama cikin girmamawa ta gaishe da gabaki d’aya familyn,tare da bawa ummey hakurin rashin zuwanta da wuri, ummey bata ‘kara cewa komai ba ta mayar da hankalinta kan abincin da take ci, “ ina leman da nace ki taho mun dashi ?” Cewar Ammeey tana kallan tahee , sai alokacin tahee ta tuna da leman da ta watsawa Wanda ya bita , cikin d’an rawar jiki tace “ hajiya dan Allah da manzan sa kiyi hakuri , nazo sakkowa daga matattakala shine ‘kafata ta zame ya zube…” ta ‘karasa a hankali ganin wani irin expression d’in kallon da ta samu wajan Ammeey , Ammey bata san lokacin da ta d’aga murya kamar zata sha ‘kota ta furta “ ya zube ? Menene ya zube ? Leman da nace ki rike ne kika zubar ? Kisan kuwa yadda akai na samo wannan maga….” Bata ‘karasaba tayi saurin toshe bakinta ganin ‘baran ‘baramar da take ‘ko’karin tafkawar ganin gabaki d’aya ilahirin falon sun zuba mata ido , sai ta wayance da “ hope baki ji ciwo ba !? Kinsan irin wannan abun sai kina bi a hankali karya ji miki ciwo “, murmushi abeey ya saki ganin yadda Ammeey ke kula da lapiyar kowa na gidan , Sabida juyawr da tayi yasa yan falon basu kula da gibin taba , ummey kuwa idanuwanta ta zuba Ammeey na d’an sakanni kafun ta d’auke eyes d’inta, itama Ammeey kan kujerar ta koma ta zauna ranta na mugun ta farfasa , wannan ce damar ta ta’karshe da ta samu maganin da zata kashe king, sabida ba ‘karamar guba bace da ko tava ka yayi sai yayi maka illah musamman idan Akace wanine yasha a hankali take tsitstsinka jijiyon cikin mutum,ranta yayi mugun ‘baci sai ‘ko’karin wantar da hankalin ta take , so take ciwan bakinta ya ‘kara kwanaki kafun taje wajan bokanya. Wayarsa Abeey ya d’auka tare da danna wani kira kafun ya kara a kunnansa , bansan me nacikin wayar yace masa ba sai amsar da abeey ya basa “ No son, you have to, zan sa akawo maka can side d’inka “, kafun ya kashe kiran , yana kallan ummey “ ku shirya masa abincinsa akai masa part d’insa yanxu. Hakance kuwa ta faru da kanta ummey ta shirya masa tray d’in hakan ya ‘kara ‘kuntata ran ammey sai bun idanuwansu Kawai take da kallo rai a’bace, ‘yan Matan kuwa kowa sai kakkaucewa yake gudun kar ace shi zai kai abincin dan sunsan tabbas da kun burarran fuska zasu dawo yau ma , gabaki d’aya king ya canza kuskure kadan Kayi masa sai ka gane kuranka a wajansa.kallan sumayya ummey tayi “ sumayya taso ki mi’kawa yayan ku abinci”. Summy kamar zatayi ihu amma badamar yi haka ta kar’bi tray din kamar zatayi kuka, wata dabara ce ta fad’owa summy tayi saurin kallan tahee “ kande d'an zo ki rakani”. Kallan Ammey tahee tayi , taga ta sakar mata ya’ke alamar suje, ajiyar zuciya ta sauke bayan ta kar’bi tray d’in hannun summyn , tunda suka soma tafiya babu Wanda yayi magana a cikin su musamman yadda tahee taji zuciyarta na bugawa da Sauri sauri, Daidai part d’in king sumy ta tsaya tare da nunawa tahee part d’in “ ki shiga ki kai masa abincin sai ki dawo kinji? “, Toh Kawai tahee ta ce mata, sanyi na ratsa zuciyarta , “ zata gansa? Zata ‘kara san yasa cikin idanuwanta?” Gabaki d’aya tanbayoyine suka taru suka tsaya mata a zuciya ganin tana ‘bata lokacine yasa ta nufi dole d’insa a hankali ta tura ‘kofar tashi sannan ta rufuto, a kan kujera ta hangosa dafe dakansa ga idanuwansa da yake a lumshe , ci gaba da kallansa har ta ‘karaso kan center table d’in bayan ta yi sallama a hankali amma ko motsawa baiyi ba , balan tana tasaka ran amsawar tasa, inda yake ta nufa cikin sand’a ganin idanuwansa a kulle, atunaninta ko yayi bacci ne shi yasa batare da tsoro ko fargaba ba ta nufeshi, fuskarta ta Daidai ta da tasa da take a kulle tun daga kan kyakkyawar sumar kansa ta soma bi da kallo har kyakkyawar fuskarsa tasa,ita kanta batasan ya akai ba sai jin hannunta tayi cikin sumar kansa tana sosa masa kan,da Sauri ya bud’e eyes d’insa , lokaci d’aya sukai eye contact da mamaki yake kallanta “ how dare she?” Ita kuma tahee tsorone ya hana ta motsawa ganin tsananin bacin ran dake kwance kan fuskarsa , da Sauri kamar wacce aka tsikala kuma tayi baya zata fad’a kan center d’in cikin azama yajanyota da hannu d’aya , bata fad’a ko ina ba sai kan cinyarsa , ajiyar zuciyar da besan ko ta menene ba yasauke, itama taheen ajiyar zuciya ta sauke daddad’an kamshin turaransa da bazata ta’ba mantawa ba yana ‘kara shigar hanci, a ydda take tana jin yadda zuciyarsa take bugawa da Sauri da Sauri, gabaki d’aya ta shagala hannunta d’aya ta d’ora a Daidai saitin zuciyarsa, cikin raunin murya hawaye na fara sakko mata ta furta “ we missed you so much “, king be san lokacin da ya fincikota yayi wurgi da ida ba , dukda kalamanta sun shiga kunnan sa , cikin azama ya nufeta da shirin tsinka mata mari tayi saurin kulle fuskar tata cike da tsoro, yadda ta tsoratar ne yasa shi tsayawa kallanta , “ why is she behaving like her ? Why ? Me hakan yake nufi ?” Tana ganin ya janye hannunsa ta mi’ke a guje zata gudu ya ri’ko hannunta, tasan tabbas ta tsaya komai zai iya faruwa da azaba ta fincike hannunta saka gudu, jikinsa ba kwari sosai shiysa ta iya fincike hannun ta , gabaki d’aya ‘ko’karin rasa control d’in kansa yayi lokaci guda, mamakin wacce yarinyar ya soma yi , a tunaninshi aljana ce ma dan yadda ya gani kamar aljanace take masa gizo , da ya kulle idanuwansa yadda ta saka hannunta a saitin zuciyarsa ne yake fad’o masa da lokacin daya d’ora hannunsa a kan kugunta, yanasan ya hukunta koma wacece koda kuwa aljanar ce , amma duk lokacin da yayi yukurin yin hakan , wifey d’inshi ce take masa gizo, why?” Yake tanbayar kansa kafun yasaka both hannayensa cikin gashin kansa yana ya mutsasu. Tahee kuwa tana fita sai da ta sassaita nutsuwar ta kafun ta nufi part d’in dada lokacin gabaki d’aya sun kammala cin abinci suna tattaunawa , dining din data ga su mimi suna gyarawa ta ‘karasa wajan, cike da iskanci Mimi ta ‘kurawa tahee kallo kamar tasan fuskantar wani abu, hararar da tahee ta buga wata lokacin da d’aya daga cikin masu aikin ne Yaso saka Mimi dariya amma ta danne tare da d’aga wa tahee gira d’aya , d’auke idanuwanta tahee tayi akan Mimi tasan ta biyewa Mimi zasuyi abunda zai jawo hankalin mutanan gidan ne Wanda ko kad’an bata san hakan ya faru. Sun dad’e sosai a part d’in dada gabaki d’aya yadda bikin ilham da wasu abubuwan suke tattaunawa akai. Sai wajan 11 suka koma part d’insu , har lokacin Ammey bata ‘kara ce mata komai ba , itama taheen bata damu da hakan ba ta nufi makwancinta , sai da ta tabbatar da ta kulle ko ina na dakin kafin ta cire abun fuskarta, tunaninsa abunda ya faru a tsakaninsu ne yai ta kaikawo cikin zuciyar ta, ita kad’ai sai faman sakin murmushi take , jan zoban nanne ya fad’o mata a rai da Sauri ta d’auko shi a inda ta ‘boye tana ‘kara binsa da kallo haka kawai taji zuciyarta bata kwanta da zoban ba, da Sauri ta sallaba ta shiga kitchen bayan ta mayar da face d’inta , ashana ta d’auka ta koma dakin nata ganin babu Wanda ya ganta sai faman sakin ajiyar zuciya take , gabaki d’aya windows d’in d’akin ta kulle hatta fanka sai da ta kashe ta yadda iska bazata motsa ba , zoban ta d’auko cike da Bismillah tana kunna masa asha guda d’aya kawai ya soma ci da wuta , ci sosai kamar Wanda ake fesawa kalanzir, abunda yfi bata mamaki ganin yadda tana kunna ashana tun kafin ta kai wajan zoben ya soma ci da wuta sosai , ‘karane ya soma karad’e ko ina na cikin kunnuwanta, me kama da ihu ihu na abun tsoro, lokaci d’aya ‘kofar d’akin ta soma jijjiga kamar zata cire kanta da kanta , windows d’in d’akin ma sosai suka soma jijjiga da ‘karfi, saurin toshe kunnuwanta tahee tayi tana ambatan sunan Allah sosai , ganin duk lokacin da tayi adduar sai zoban nan ya ‘karaci da wuta, tsawan a wanni biyu , har tsawan lokacin kuma kofar d’akin da windows din basu dena jijjigaba ka guru ruwar da take tashi. Lokaci d’aya kuma sai komai ya dakata , ihun ya dena tashi, ‘kofa da windows din ma kamar ba’a ta’basuba, inda zoban yake ta kalla ganin yadda ya koma ‘baki ‘kirin ga wani hayaki da ya soma Tashi daga cikinsa yana ‘bacewa , lokaci d’aya kuma gabaki d’aya zuban ya ‘bace kamar be ta’ba wanzuwa ba awajan. Addua Tahee ta somayi tun tanayi a zuci har ta soma yi a fili tana ‘kara bin ko ina na d’akin da kallo, Ta dad’e tana addua a bakinta kafun bacci ‘barawo ya d’auketa. ****** Lokacin da tahee take ‘kona zoban nan da yawa akwai mutanan da basu runtsa ba , musamman mutanan da suke da ala’ka da wannan zoban babu Wanda ya runtsa a cikinsu sabida tashin hankali,ko wannansu cike yake da fargabar abunda zai biyo baya , gabaki d’ayansu kasa ha’kura gari ya waye sukai , karfe 3:00am lokcin da kowa na mahalu’ki yana hutawa gabaki d’aya banda masu ala’ka da zoban da suka bayyana cikin falon su kamar kullum a yola , cike da tashin hankali sai faman kururuwar kiran boyankarsu suke tsawan lokaci, amma babu ita babu alamarta , duk da haka basu ha’kura ba suka dunga kiranta cike da tashin hankali, sun dad’e sunayi kafin suji saukar tsawa akansu , gabaki d’aya suka sunkuyar da kansu alamar girmamawa , bata bayyana ba kamar yadda ta sababa sai amon muryarta mara dad’in ji da ya cika ko ina na falon “ tabbas kun aikata babban kuskure da kuka bari zoben nan ya ‘kone , tabbas lokacin tonuwar asirin ko wannan zai fara daga lokacin da zoben ya ‘bata , yanxu komai ya dawo hannunku Amma kusani gabaki d’aya muguntar da kuka dad’e kunayi tun daga yanxu ya fara warwarewa , ta dawo , ta dawo , bazata ta’ba barin kuba , wannan karan a shirye suke , shirin da bazaku ta’ba warwaresaba,na fad’a muku a farko dawowarta kamar tonuwar asirin kune , toh lokaci yazo , lokacin tonan asirin ko wannan ku yayi “, sai kuma ta ‘barke da dariya mara dad’in ji da saurare. ‘D’aya daga cikinsu ne cike da fargaba ya soma magana “ tuba muke , tuba muke “, sai gabaki d’ayansu suma suka d’au ka , wata tsawar ta daka musu , tun farkon shigowarku na sanar da ku abinda zai biyo baya Aduk lokacin da kuka ‘Kona abun aljanu, kutabbata yanxu lokaci yayi sannan cikin zuri’arku zasu dunga shan jini “ ta sake sakin wata dariyar da ya rud’asu gabaki d’aya. Cike da fargaba d’aya daga cikin su ya soma magana “ ya shigabar mu wannan laifin na abar ‘kauna ce da masoyinta “, yimun shiru , ta fad’a kafun ta cigaba “ babu ruwana da matsalar ku , kanku a had’e yake , duk hukuncin da kuka ga dama kuyi mata babu ruwana , sabida itama yanxu lokacin tonan asirinta ne yazo , lokacin sadaukar da jininkune ya fito , hahahhahahahh, hahahahhahaha jinii, jini,jini , aljanun mu suna bu’katar Jininku, ku tabbata kun gyara abunku a tsakanin ku hahahhahaha “, share gumi kawai suke gabaki d’aya sun rasa bakin magana “ amma wacece wannan shegiyar da take ‘ko’karin ‘bata mana shirin mu ?”, yanxu ma dariya bokanyar tasa kafin ta bud’e musu tafukan hannunta, amaimakon suga wacce ta ‘Kona zoban sai haske ya kashe musu idanuwansu gabaki d’aya , har ‘yar rigan kulle ido suke “bansan taba , bansan wacece ba , sabida duk kogin tsafin mu sun kasa ganin fuskarta, kuma bazaku ta’ba sanin ko wacece ba sai ranar da asirin wasunku zai tonu “, tana kai ‘karshen maganarta ta ‘bace ‘bat. Gabaki d’ayan su babu Wanda hankalinsa be Tashi ba , ko wannansu duk da fuskokinsu da yake a kulle hakan bazai hana tsantsan tashin hankalin da suke ciki bayyana ba . WASHE GARI Kamar kullum kiran sallar asuba ne ya tasheta, hakanan take jin zuciyar ta a sake kamar ancire mata wani dutse me nauyi a ‘kirjinta, ga farincikin ganin masoyinta kuma mijinta da tayi , wani irin dad’i take ji cikin kasan zuciyar ta musamman idan ta tuna abunda ya faru jiya , komai take yi yau zaka ga fuskarta tana sakin murmushi lokaci zuwa lokaci, ko da bata ga fitowar Ammeey ba hakan kwata kwata be dameta ba , damuwarta d’aya ganin har yanxu be shigo part d’in Ammeey ba kamar yadda ya saba , tun d’azu take kallan hanyar shigowa ko zata gansa amma babu shi babu alamarsa , duk da hakan bata karaya sai da ta ‘kara kusan 30 Minutes, nan ma still shiru be shigoba, a sanyaye ta juya har ta kar kwanar d’akinta taji kamshin turaransa ya ratsa mata hanci , da Sauri ta juyo , shi d’inne kuwa , kamar kullum yana sanye cikin ‘kananan kayan yake ‘kara masa kyau da kwarjini, gabaki d’aya ta maida hankalinta kansa shi kad’ai kawai take kallo, shi kansa yaji alamun ana kallansa , a hankali ya d’ago da dara daran eyes d’insa , zuwa inda taji alamar mutum, yana d’agowa idanuwansu ya shiga cikin na juna , gabaki d’aya babu Wanda ya janye idanunsa daga shi har ita, kallon kallon kawai suke yiwa junansu, shi mamakin da yake me yasa tun da ya ganta nauyin da ya tokare masa ‘kirji ya sauka kamar wata aljana ? “, da hannu d’aya yayi mata alamar tazo, a sanyaye tahee ta nufi inda yake, tana zuwa ta saukar da inanuwanta , kallan yadda ta sunkuyar da kai tayi kafun a hankali ya furta “ Ammey ?” , bakinta har rawa yake wajan furta “ tun safe bata fito ba ,”kanshi kawai yayi nodding a hankali kafun ya sauke ‘kafarsa d’aya dayi crossing , lokaci d’aya ta bugu da wani glass na ado a wajan , tun kafun ya motsa tahee tayi saurin ta’ba kafartasa Tanaso taga inda yaji ciwan kamar zatayi kuka ta ke furta sorry , da mamaki ya ke kallanta kafun ya furta “ are you mad ? How dare you ? “,ya ‘karasa da d’aga hannunsa zai mareta , yadda ta kulle idanuwan hawaye na sauka akan fuskarsa ne ya tuno masa lokacin da tahee ta zuba masa coffee, the same reaction d’in da ya gani yanxu , cikin d’aga murya yake furta “ why ? Why ? Me yasa komai irin nata ? Why ?” Ynxu kam tsorone ya kama tahee , batasan me yasa ba , duk lokacin da tagansa sai ta kasa controlling kanta . Muryar Ammeey ce ta katse mata tunaninta tare da ajiyar zuciya , shi kuwa har yanxu idanuwansa na kan tahee da ta kasa kallansa , kallan tahee , Ammey tayi tare da yi mata alamar ta bar wajan, cikin gudu gudu sauri sauri kuwa tabar wajan . Samun waje Ammey tayi ta zauna a gefensa , duk Wanda ya kalleta zai san ko bata da lapiya ko wacce take cikin damuwa Sabida yadda tayi zuru zuru, kallanta king yayi na tsawan 1 minutes kafin ya furta “ Ammey baki da lapiya ?”, da sauri ta girgixa masa kai “ nashiga cikin damuwa ne ganin yadda gabaki d’aya ka canza , kwata kwata baka damu da rayuwar ka ba kamar da hakan yana sani cikin damuwa “, amaimakon ya amsa mata sai kallanta da ya ‘karayi “ the mouth ?”, da Sauri ta toshe bakinta, ranta a mugun ‘bace amma tana ‘ko’karin tannewa , murmushi ta d’an sakar masa “ karka damu son, burgewa nayi na daki hakwarana”, lumshe mata ido yayi a hankali kafun ya furta “karki damu za’ayi fixing d’insu da wasu, anytime you’re ready go and meet doctor maryam zan sa tayi miki cikin sauki “, cike da murya Ammeey ta amsa masa kafin ta ‘kara kallansa “ son kaci abinci kuwa ? Kalli yadda ka ‘kara Ramewa fa ?” Shiru yayi mata ba tare da ya amsa mata ba , cike da damuwa ta furta“ zansa yanxu kande ta kawo maka , ka tabbata kaci idan ba haka ba bazan samu kwanciyar hankali ba ,” yanxun ma bece mata komai ba sai lumshe mata eyes da yayi “ am going Ammey , ki kula “ , yana kai ‘karshen zancansa ya bar part d’in , da wani irin shu’umin kallo Ammey ta bi bayansa dashi , kafun ta saki wani murmushin da ita kadai ta san ma’anarsa, d’akinta ta shiga bata jima ba ta fito da wani abu a hannunta , batare da ta nemi temakon kowa ba soma girka masa lafiyayyan abinci , kamshi sai tashi yake , tana kammalawa ta ajje a dinning tare da komawa ta d’auko wani abu, warmers din ta bud’e tare da bar bad’a wani abu d’an kad’an a ciki,duk abunda take akan idan tahee dake kallanta daga nesa yadda Ammey bazata ganta ba , da Sauri kuma ta koma d’aki zuciyarta tana bugawa da Sauri Sauri , kwalla kiranta da taje Ammey nayi ne yasa ta saki ajiyar zuciya, da Sauri ta fito tare da karasowa Indai Ammey take , kamar kullum sai da ta gaisheta cike da bar kwanci, kallanta Ammey tayi sosia kafun ta nuna mata trays din, “ part d’in da kukaje jiya kuka kai abincin nan xaki kai and ki tabbata yaci abincin , kinjini ko ?” Kamar da gaske tahee ta zaro ido tana dafe kirjinta “ Ni hajiya ? Kwarankwatsi ballani zaiyi , ki temaka kiyi hakuri “, ajiyar zuciya Ammey ta saki daman abunda take san ji kenan daga bakinta , d’an had’e rai Ammeey tayi kafun ta nuna mata abincin “ maza ki Tashi kikai “ , cike da tsora tahee ta kalli Ammey , cikin zuciyar ta kuwa dariyar Ammeey Kawai take , zata sake ro’kan Ammey ta daka mata tsawa da Sauri tahee ta mi’ke ta nufi dinning , jikin ta sai karkarwa yake ta nufi hanyar part d’in nasa , sai da tayi nisa sosai sannan ta tsaya tana daidaita kanta , a hankali ta bude babbar ‘kofar falon , bakinta d’auke da sallama, sanyin ac da kanshin turaran wutane ya daki hancin sa , gefe guda kuma ga ‘kamshin turaransa da baya fita daga palourn. Babu kowa a cikin falon kai tsaye dinning ta nufa ta ajje tana tuna lokacin da take bashi abinci a baki , gabaki d’aya sai ta zubawa falon idanu tana tuna rayuwar su da sukayi a baya , sai data gama ‘karewa falour kallo, cikin sand’a ta nufi bedroom d’inta na sama , ko tsoron ya zo ya sameta a wajan batayi , tana shiga nan ma d’akin fess yake sai faman tashin ‘kamshi yake , d’akinta yananan kamar yadda yake , babu a bunda ya canza , nan ma bata tsaya ba , ta nufi d’akin dressing room dinta , tana bin ko ina na wajan da kallo , sai data gama ‘kare masa kallo ko tsoran ya shigo ya same ta a haka batayi , tasan yana part d’in abeey shiyasa gabaki d’aya bata damuba ta kutsa kai cikin toilet d’in , bataji alamun motsin mutum ba , sai ji tayi an fusgo hannunta da ‘karfin gaske , ta bud’e baki zata sa ido taji an toshe mata bakin nata da ‘karfi anjin ginata da jikin toilet d’in , zaro idanuwanta tayi a kansa ganinsa sanye da towel kawai , da Sauri kuma ta kulle idanuwanta, azuciye ya furta “ bud’e idanuwanki” da sauri kuwa ta bud’e idanuwan, amma bata kallesa ba sai ‘kasa da ta kalla , akau sashe ya furta d’ago ki kalleni, har yanxu ta ‘ki yadda ta kallesa sai jikinta da ya soma rawa , da ‘karfi ya furta “ ba dake nake magana ba ?” , kuka tahee ta saka masa tana d’ago da idanuwanta, hawayen da ya gani akan fuskarta ne yasashi kulle idanuwansa “ why ? Me ke shirin faruwa dani ? Me yasa nk ganin aljana me irin behavior d’inki? Why? “ ya furta cikin zuciyar sa , kafun ya matsa baya kad’an yana nuna mata hanyar waje , “ idan na ‘kara ganin me kama da fuskarki, uhmm” be ‘karasa ba ya nuna mata kofar da finger d’insa , da Sauri zata kwasa a guje , santsi ya nemi kayar da iya , cikin azama ya ri’kota yadda ta fad’o jikinsane yasa towel d’in kugunsa kwance wa , jikinta da nasa suka hadu waje d’aya ,a tsorace tahee ta saki ‘kara jikinta gabaki d’aya ya dena motsi alamar ta suma . Be san me yasa ba , sai kawai ya tsinci kansa da sakin murmushi, murmushin da ya dad’e beyi irin saba , da hannu d’aya ya d’auketa ya fito daga toilet d’in , akan sofa ya ajjeta ya shirya mintuna kad’an ya dawo d’auke da bottle water d’in gabaki d’aya ruwan ya juye mata a jiki a firgice ta farka zata kurma ihu ya daka mata tsawa “ shut up “,yana kai ‘karshen zancen sa ya juya bayar dakin, tunanin abunda ya faru d’azu tayi kafun ta d’auki hannunta d’aya ta mari fuskarta “ why ? Me yasa bana jin magana “, tunanin yadda zata fita ta soma ganin bata da wata hanyar fita , abincin data kawo masa ne ya fad’o mata arai , yanxu idan yaci abinci fa ? “, dukda yadda jikinta yake a ji’ke Hakan be hana ta saka gudu ba , da Sauri Sauri take taka steps, lokacin da ta sakko har ya gama zuba food d’in da zaiji, ganin yana shirin d’aukar spooon ne yasa tayi Sauri kwalla kara da karfi “ No karkaci “, be gama fahimta me take ba kawai sai ganin tahee yayi ta ture tray d’in gabaki d’aya hatta abincin da ya zuwa sai data ‘barar dashi , rai a ‘bace ya d’ago da eyes d’inta, batai aune ba sai saukar marin shi taji a bothside kumatunta, da Sauri ta dafe wajan tana binsa da kallo ganin yadda ransa ya ‘baci, ‘kara d’aga hannu yayi zai mareta sai kuma ya fasa a kausashe ya soma magana “idan na sake ganin ki cikin part d’in nan zakiga abunda zai faru,leave now “, ya daka mata tsawa , ita kanta ta tsorata zata gudu ya tsayar da ita “ washe kwashe miki Wannan trash d’in “, jijjiga masa kai tayi ta nufi haryan kitchen , duk da yayi mamakin yadda akai tasan hanyar kitchen d’in bece komai ba sbida yadda ransa yake a ‘bace , be san dalili ba amma yaji zuciyarsa tana masa ba dad’i, kayan kashe shara tahee ta kwaso tashare Wajan ta goge kamar babu abunda ya zube , komai a nutse take yinsa gabaki d’aya akan idanuwansa yana kula da movement d’inta hawayen ta da suke fitowa ne ya fi komai tsaya masa arai , ko data gama bata kalli indayake ba tayi hanyar fita , “ hey !” , yace mata , jiyowa tayi har yanxu hawayen be dena sauka ma , yadda ta saukar dakai sosai zata baka tausayi , zai yi magana sai kuma ya fasa “ get lose “, da Sauri ta juya tana goge hawayen fuskar tata , ta ‘kasan ido yake kallanta har ta fice , hannunsa ya d’ora akan saitin zuciyarsa , yadda take hawayene ya soma ya dawo masa akai , at the same time yana tuno hawayen tahee d’insa , he don’t know why he feel bad , kamar ya kira ta , but he will never do so, mamakin kansa yake yadda idan tayi abu take d’aga mata ‘kafa , abunda ya faru a toilet ne ya fad’o masa arai da lokacin da ta taho da gudu ta ‘barar da abincin . Abunda ya faru shekarun baya ne ya soma dawo masa kai “ dady no”, shine abunda ya fad’o masa lokacin da tahee ta ‘barar masa da coffee d’insa . Dafe kansa yayi da hannaye biyu sabida yadda yaji kansa ya fara sara masa , gabaki d’aya memories d’inshi shi da tahee na dawo masa cikin brain d’insa. **** Tahee tana futa ta gyara fuskarta , zuciyar ta bata mata dad’in musamman abincin da taga beci ba , tana tafiya tana tunanin mafita har ta ‘karasa part d’in Ammeey , tana shiga ta tarar da ita a tsaye tana ganin tahee ta ‘karaso inda yake , “ yaci abincin ?” Shine abunda Ammey ta fara tanbayarta , ‘yake tahee ta sakar mata sabida bata cikin mood d’in “ eh hajiya sai da na tabbatar yaji sosai sannan na fito “, murmushi Ammeey ta saki , kafun ta furta “ zaki iya tafiya “, a sanyaye tahee ta koma d’akinta . Gabaki d’aya rinin ranar tunanin yadda ta bar king take , hannu ta tasaka ta shafi face d’inta da ya mara , kamar wata ‘karamar yarinyar ta turo bakinta waje . ******** ************* Yau ya kama Wednesday , ayau ne kuma aka kawo lefin ilham , gabaki d’aya mutanan gidan sun shiga busy , kowa yana harkar tar’bar baki musamman abeey da take part din su dada da za’a kawo lefen , tun lokacin da king ya mareta kuma basu ‘kara haduwa ba amma kullum da tunaninsa take tashi , a cikin lokacin da ba’ki suke zuwane kuma mimi ta samu ta bawa tahee sa’kon yah moh , duk da batayi wani mamaki ba ta ydda kayan suka shigo Amma gabaki d’aya sai da ta saka ‘kananan camera a falon Ammey, hatta d’akinta lokacin da asabe ta bata ta kai mata abinci , Allah ya temaketa ta shiga d’akin Ammey ta saka mata sound recorder d’in da yah moh ya basu , d’akin da har yanxu bata ga Ammey ta shiga ba ne kawai bata sawa , hatta wajan sha’katawar Ammey sai da ta saka . Yau ne kuma take plan d’in yadda zata shiga cikin d’akin da ba mahalu’kin da yake shiga sai Ammey ita kadai. Ganin yadda kowa yayi busy hatta mutanan gidan kowa yana part d’in dada da ummey masu aiki ma sai faman kai kawo suke , da Sauri Mimi ta shigo palour Ammey tana kallan tahee da ke faman jiran ta “ tahee kiyi sauri bamu da time , zan miki gado gadi, bamu da time kiyi sauri ,” jinjina mata kai tahee tayi bayanta d’auki cameras din da sound record ta nufi d’akin tana tava door d’in taji wani irin zafi ya ratsa mata hannu , ‘kara saka hannunta tayi a karo na biyu wani s azaban da ya fi na farko ratsa mata hannu, da Sauri ta ja baya jin yadda hannun yake kamar an ‘Konashi. Lokacin da tahee ta ta’ba kofar nan sai da zuciyar Ammey ta buga , wani matsananciyar tashin hankali ya ziyarceta , mi’kewa tayi dan ta dawo part d’in ta ummey ta tsayar da ita , jitayi kamar ta sha’ke ummey , tarar ba’kin sukai lokaci d’aya , Adaidai lokacin da tahee ta ‘kara ta’ba ‘kofar . Wannnan karan kasa hakuri Ammey tayi ko sauraran ummey batayi , a hau kace ta fito daga part d’in dada . “ kiyi sauri tahee bamu da lokaci , kiyi sauri “, jinjina mata kai tahee tayi tare da ‘kara ta’ba kofar, alokacin da ta ta’ba sabida tashin hankali Ammey har fad’uwa kasa tayi a firgice . Runtse idanuwanta tahee tayi tare da furta Bismillah ta bud’e d’akin , tana bud’ewa wata iriyar guguwa ta karad’e d’akin , addua tahee ta soma jin yadda jikinta yasoma d’aukar karkarwa kamar zata rasa kanta , hatta ‘kafarta da ta taka , wani irin zafi ne yake ratsa mata kafafu, adduar datake cikin saurine yasa lokaci d’aya guguwar ta tsaya , da Sauri tahee ta soma bin d’akin da kallo komai na cikin d’akin jane kamar yadda yah moh ya fad’a musu , jin muryar Mimi na fad’in Kiyi Sauri tahee . Da Sauri ta fara duban inda zata saka cameras din, tayi sa’ar saka recorder din , zata saka camera d’in bata sani ba ta buge wasu abu kamar tangaran , take a Wajan suka fad’i kasa suka fashe , suna fashewa wani irin ba’kin hayaki yafito daga ciki lokaci d’aya kuma suka ‘bace batt , a rude tahee ta ke duba d’akin inda zata saka cameras d’in kamar zata haukace haka take jin kanta sabida azabar zafin da ya fara ratsata ji take kamar ta kurma ihu dan hauka . A lokacin kuwa da ta kurma ihu da babu abunda zai hana tahee ta haukace , wani d’an waje ta samu daga ba kowa ne zai san da wajan ba ta li’ka cameras din , duk dubawarka bazaka san dasu ba .dai dai lokacin da zatafito daga d’akin ‘kafarta ta buge wani abu take a wajan shima ya fashe , still wani ba’kin haya’kine ya karad’e kafin ya ‘bace , sabida yadda ta rud’e bata san lokacin da ‘kafarta ta zame ba Zata fad’i, Adaidai lokacin kuma Ammey ta saka hannu kan handle d’in kofar shigowa falon, tahee batai aune ba sai ji tayi an funcukota da ‘karfi an toshe mata baki …….. 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 07041879581 MSS LEE BOOK 2 Page 17 Da Sauri ta dafe hannun da ya toshe mata baki ga baki d’aya ta tsure ,zuciyar ta sai bugawa yake da Sauri Sauri , Ammey na saka hannu akan handle d’in Wanda ya rufe wa tahee baki ya shige wata ‘kofa har yanxu hannunsa na kan bakinta da ya toshe , a haukace Ammeey ta shigo part d’inta har da sawa kofar pin Sabida kar Wanda ya shigo , haukane kawai ammey batayi ba alokacin, har wani zazzafan zazzabi taji yana kamata , da Sauri ta nufi ‘kofar d’akin tsafinta , tana ta’ba ‘kofar taji an d’aga ta an buga ta da bango , cikin azaba Ammey ta bud’e baki zatayi ihu taji saukar mari zafafa a kumatunta duka biyun , fitsarin da take ri’kewane ya kwacemata , bata gama shiga cikin tashin hankali ba sai data ga an ‘kara d’aga ta sama kamar wata kayan wanki an fara hajijiya da ita , wata murya taji kamar tana jari rai ta soma yi mata kuka a kunne , tana saka hannu zata toshe kunnen taji saukar mari, da Sauri ta sauke hannunta majina duk ya ‘bata mata fuska ga wata guda wa da take neman kwace mata, muryoyi ta soma ji mabanbanta suna kiran sunanta , ihu Ammey ta saki kamar mahaukaci ta fara zagaya d’akin , ita kanta batasan me take cewa ba “ ku bari ,bani nace akashe saba , itama bani ce Nace a kashe shiba , woolllhh , hahahahahha”, ita kad’ai sai faman surutai take wani irin wa wan harbi da akai matane yasata fashewa da kuka , hakorinta guda d’aya shima ya cire , ga zafin ciwon hakori ga zafin buguwar da tayi , azaba bata ‘kare mata ba sai ma wani irin ‘kai ‘kayi da jikinta ya fara yi kamar kamar wacce akayi wa feshi, gabaki d’aya nema take ta haukace lokaci guda . ****Tun lokacin da aka kulle wa tahee baki ta nemi ta rikice tsoran tama kar Ammey ce ta kamata , yadda taji ana tafiya da Itace ya hana ta bud’e fuskarta sai ma ‘kara runtse idanuwanta da tayi, duk adduar da tazo bakinta shi takeyi, jin an tsaya kuma an saki bakinta ne yasa ta bud’e idanuwanta da Sauri taja baya har tana ‘ko’karin faduwa jikinta har karkarwa yake wajan juyowa , yadda tagansa a tsaye sanye da ba’ka’ken kayane ya ‘kara rud’ar da ita , hannunta da ya soma rawa ta d’aga ta fara nuna shi, batayi auneba taji ta rungume a jikinsa ,yadda ya rungumeta kamar za’a kwace masa ita , shi kad’ai sai faman sakin ajiyar zuciya yake , sosai jikin tahee ya soma rawa , gabaki d’aya ta rasa tunanin da zata yi, cikin sauri ta raba jikinsu tana dube duben ta inda zataga Mimi , ganin yadda take dube duben ne yasa cikin cool voice ya furta “ tana part d’in ummey “, hannunsa ya d’ora kan kumatunta da ya mara , da Sauri taja baya gudun kar asirinta ya tonu yasa tayi Sauri juya wa zata gudu. “ I missed you wifey ?”, ya furta mata a hankali, cikin wani irin expression tahee ta juyo tana binsa da kallo har yanxu jikinta be bar karkarwa ba , yadda taga yana matsota ne yasa ta soma ja da baya,still be dena bin nata ba yaci gaba da matsota, itama gabaki d’aya ta rud’e ga zafin da jikinta yake mata tun lokacin da shiga d’akin tsafin Ammey , jiri ne yayi ‘ko’karin kayar da ita ya ru’kota a jikinsa , wata nannauyar ajiyar zuciya ya Sauke kafin ya d’auketa gabaki d’ayanta yayi sama da ita zuwa bedroom d’insa . Yana shiga akan sofa ya zauna tare da d’orata saman cinyarsa , hannusa na dama ya mika a hankali har zuwa wuyanta, daidai Inda ban d’in abun fuskarta yake ya cire tare da yaye fuskar gabaki d’aya ya wurgar da ita , ai nahin fuskar tahee tafito fess da ita kamar zatayi kuka ganin tun ba’aje ko ina ba asirinta ya tonu shikenan yanxu zai fad’awa su ammey , tashi tayi daniyar barin wajan ya ‘kara dawo ta ita kan cinyarsa tare da saka both hannayensa biyu ya rungumota a jikinsa , cikin rad’a rad’a ya furta “ fushi kike dani? I can’t take it please”, da Sauri tahee tajiyo tayi hugging d’insa tana fashewa da kuka , cikin muryar kukan ta fara magana tana dukan ‘kirjinsa “why?, kamanta dani?,ka dena sona? Bakaso nazo wajanka? Nayi missing d’inka, me isa da ka gano ni ka ‘boyemun?” ,lumshash shun idanuwansa da ya zuba mata ya lumshe tare da hugging d’inta sosai a jikinsa , “ I’m sorry for the slap , I don’t meant to , but I have to sabida ke kanki baki san ana bibiyarki ba “, d’ago da kallanta tayi ta ‘kara zuba masa , gabaki d’aya yana so brain d’inta ya dena aiki “ taya ka shigo falourn? And taya kasan nice nazo ina bincike a part d’inta ?” Be amsa mata tanbayoyin taba , sai kallan cikin ta da yayi ya shafa a hankali “ the baby?”, itama tahee shafa cikin nata tayi kafun ta furta “ I lost it “, tana kai ‘karshe ya lumshe idanuwansa , jiyayi zuciyarsa na neman tsinkewa sabida babyn shi da ya rasa , hannunta d’aya tahee ta saka a kan fuskarsa da ya sashi bud’e , sosai eyes d’insa sukai ja d’an murmushi yasaki kafun ya shafa nashi cikin “ wifey , I’m hungry “, kanta kawai ta gyada masa , zata d’auki face d’inta ya hanata hakan, tare suka tafi 2 second floor cikin kicin d’inta da yake kamar sabo kullum , simple food ta girka masa , cikin Sauri sauri kar Ammey ta zargi wani abun amma taga ko ajikinsa be damu da hakan ba , ko da ta gama abincin still be bartaba har saida tayi feeding d’insa da kanta , sosai ta ga lokaci ya fara ja ,” I have to go, Ammeey zata zargi wani abun “, be kulataba ya ‘kara d’aukar a barsa kamar wata baby ya nufi bedroom d’insa da ita , yanxu kam hankalinta ya gama tashi , zata ‘kara magana ya katseta, “ nayi hakuri for long years , kina tunanin zan ‘kara kwana batare da Matata ba ?Simple No ! “ da Sauri ta girgiza masa kai “ No please! Ammey zata iya fuskantar wani abu , please am sorry kalb “ you’re sorry ? Ya tanbayeta yana ‘kara kallanta , ganin ta yi masa shiru tana ‘kara binsa da kallo ne Yasa shi d’auke kansa daga kanta , a hankali ya soma taku har yazo wajan gaban mudubin d’akin, daga jikin mudubin ya danna wani abu take gaban mudubin ya rabe gida biyu wata ‘kofa ta bayyana “ follow me “, abunda yace Matt kenan kafin ya shiga cikin d’akin da yake cike da cameras ta ko ina, wani white chair ya ja mata nan ma seat kawai yace mata , ba musu kuwa ta zauna sai faman bin d’akin take da kallo , tunda take bata ta’ba sanin cewa a kwai door awajan gaban mudubinba, yadda yake yarrafa computer din gabansama abun kallo ne , kafun ya ran’kafo Daidai saitin ta yana danna wani keyboard , take a Wajan palourn Ammey ya bayyana , abunda ya faru tun bayan barin ta palourn ya saka mata , sosai ta kurawa palour Ammey ido tana kallan abunda ya faru , ita kad’ai sai faman dariya take , ganin dariyar tata tana ‘ko’karin sha’keta ne yasa yayi saurin tsayar Dashi, da Sauri ta kalleshi a marairaice , alamar ya kunna mata , d’auke kansa yayi akanta yana nufar hanyar fita , Daidai zai saka ‘kafarsa a waje yaji saukar muryarta “ka dad’e kana bibiyarta? Me yasa da kasan true colour d’inta baka tonata ba , kake behaving a matsayin king dinta ? Har poising d’in da take sa maka kasan da haka ? “, fasa fita yayi ya jiyo ya d’an kalleta , yana sakin wani killer smile akan fuskarta “ if my brave barrister tana da basirar shigowa cikin gidan nan har ta ya’ki ma’kiyarta , me kike tunani akan mijin ta kuma ? A husband? Ko kuma a doctor? Da aka ‘batar masa da matarsa ? Shi kuma ya kasa ha’kura ya bar ‘kasar without doing anything?”, zai juya tayi saurin ri’koshi “ Tana kasan ni barrister ce !?”, hancin ta ya ja kad’an , kafun ya furta mata “ I don’t know “, yanxu ma ya juya zai fita ta ‘kara rikoshi sosai “ please “, yadda tace please d’innan gabaki d’aya saida tsi’kar jikinsa ta Tashi, lumshe mata ido yayi daidai saitin kunnanta ya furta “ from the start”, bai jira ta ce masa komai ba ya juya ya bar d’akin , da Sauri tabi bayansa itama har ya zauna kan sofa tayi saurin d’anewa kan cinyarsa tare da sakar masa wani peck a goshi, eyes d’insa ya zuba mata shi kad’ai yasan illar da kissed d’in nan zai ja masa , a shagwa’be ta furta “ please ka fad’a mun please “, what will I get in return ?” Shima ya furta har yanxu kuma yana binta da wannan kallan nasa da yake kashe Mata jiki, “ me kakeso?” Something “, ya fad’a yana d’age mata gira d’aya duk da tagane abunda ya ke nufi sai tayi kamar bata fahimce saba “ Menene kuma something ?” Murmushi ne ya bayyana akan fuskarsa , wai Menene something, “ I will tell you after I give you the story “, gyara zama tayi sosai yadda zata ji dad’in labarin , shima both hannayensa ya zuwa cikin stomach din ta yana shafawa , wani murmushi na sauka akan fuskarta “ kina tanbayata Yaushe naganota?” Nodding kanta tayi masa a hankali , shima bai damu ba ya soma magana “ the day I missed you! Yes lokacin da kika bar gida bayan sun had’a plan d’in accident d’insu akai na , sunyi ‘ko’karin kasheni for a long time amma basu samu damar hakan ba , a time d’in naji rauni sosai Amma gabaki d’aya ina cikin hankali na , but babu Wanda ya fuskanci hakan sabida umarni da na bawa doctor arwan akan cewa nayi coma, and yes it works kowa ya yadda nayi comma d’in , aranar Ammey bata zo hospital d’in ta duba ni ba sai ummey, duk da itama naso na barta a comma din , to my very surprise ta ganoni lokacin da ta tabbatar kowa ya tafi , she was like “ nasan baka cikin coma , Sabida na ydda da d’ana nasan yana da dalilinsa nayin hakan , amma karka manta ni mahaifiyarkace, komai sirrin ka nawa ne “, a lokacin wani raunin mahaifiyata ya kamani bansan lokacin da na bud’e eyes d’ina ba , lokacin da take shafan kan , Aranar naga farin ciki da kuma ‘kunci a fuskar mahaifiyata, musamman raunin da yake cikin idanuwanta “, shiru king yayi yana sauke ajiyar zuciya Sabida dogon maganar da yayi yanzu , tahee ma sosai ta nutsu tana sauraran sa. Saida ya d’auki tsawan 2 minutes kafin ya cigaba da magana “ ban fad’a mata dalilin da yasa nayi haka ba , and itama bata nemi sanin dalilina nayin hakan ba , tsawan lokacin da akace Ina cikin coma gabaki d’aya nasan meke faruwa a cikin gidan batare da sanin kowa ba sai zaki dake kawo mun rahotan duk abunda yake faruwa , hatta mutanan da sukayi kidnapping d’inki suna hannu, har zuwanki Niger na sani, da tafiya Uk d’in ki”, da Sauri tahee tajiyo ta kallesa, cute kumatun ta ya d’anja kadan ganin mamakin da yake kwance akan fuskarta , bai jira jin me zatace ba ya cigaba da maganarsa, “ nasan komai da yake faruwa , all this while ba nabar Nigeria Sabida sa’banin da muka Samu da abeey ba , No!!, this is my plan for the whole time “, itama murmushi tahee ta saki tana shafa gefen kansa “ kuma ka dad’e kana bibiyar Ammey, and the cameras suma , ka dad’e da sanin me ke faru ko ? Sweetheart who are you “, murmushi ne ya kwace masa “ kina zargin mijin naki ?” , da sauri ta girgiza masa kai “ idan mijina zai iya ganoni, how comes bazan gano akwai abunda yake ‘boyemun acikin idanuwansa ba ?”, lips d’inta ya sumbata lokacin da take magana , “ kin ‘kara girma, and you’re too brave now “, hannu san ya d’ora kan cikinta “ zuciya ta bata mun dad’i , tunda nayi loosing baby na , amma haka Allah ya ‘kaddara , Allahn da ya bamu ya fi mu bu’katarsa , and question here is wanene guy d’in da yake cikin gidan ku ? And the small boy d’in da ake ganin su tare ?”, kallansa sosai tahee tayi kafun ta sauke ajiyar zuciya kad’an yadda bazai gane ba , bakinta har Sauri yake wajan furta “ babban yayan mimi ne , junior kuma niece d’insune mamansa ta rasu tun yana baby “, a hankali ya nanata sunan junior a bakinsa , itama kallansa tayi tasan ko giyar wake Tasha bazata fad’a masa Akhie d’insane ba da d’ansa tasan zai iya lalata gabaki d’aya shirin ya d’auko d’ansa “, yadda take binsa da kallo ne yasa ya hure mata eyes d’in nata , lumshe su tayi tana ‘kara kwanciya akan ‘kirjinsa “ akwai abunda kake ‘boyewa matar ka ? Who are you ?”, Tashi yayi tare da ita akan jikinsa har zuwa kan bed d’insu , sai da ya kwantar da ita kafun ya d’an sumbaci bakinta, yana kallan cikin idanuwanta , cikin rad’a rad’a ya furta “ JAMI’IN SIRRI “, yadda yaga ta zaro idanuwantane ya so bashi dariya , zatayi magana ya had’e bakinsu waje d’aya tare kashe light d’in d’akin ya bar dumm light kawai . ******** ************ Tun lokacin da Ammey tabar part d’in dada ake nemanta, ummey ce ta basu uzurin ko akwai abunda ya ri’keta shiyasa kowa ya fita daga harkar nemanta ya cigaba da harkar gabansa. *** Ammey kam kamar wata zautacciya haka ta koma jikin abun ya lafa ta d’ora hannu akai tana faman saki ihu, duk wannan ihun da take babu me jinta da Sauri ta raru wayarta har fad’uwa take , ko kallan gabanta batayi ta nufi d’akin tsafinta , ydda taga abubuwanta masu mahimmanci sun faffashe ne yafi komai d’aga mata hankali, wani number ta d’aga ta kira , amma har kusan 2 missed calls ba’a d’agaba , hankalinta ba ‘karamin tashi yayi ba , duk da hakan bata hakura ba sai da ta ciga da kiran number sai faman zafa d’akin take , cikin sa’a kuwa wannan karan aka d’aga kiran nata , banji me aka ce mata ba sai wata kururuwa da ta saki tana ‘kara yin ball da kayan wajan , ita ka d’ai faman surutu take , tun tana shirmenta harta fara to nawa kanta asirin abunda suke aikatawa da ita da na wayar da ga ‘karshe ma ball tayi da wayar tata , ta fashe tass a ‘kasa , tsugunnawa Ammey tayi gabaki d’aya ta fita a hayyacinta musamman idan ta bud’e bakinta sai mutum ya d’auka ‘yar biri ce ga gashin kanta da ya mimmike tsaye sai kace fika fikin tattaba , yanxu kan kamar me aljanu haka ta Tashi a guje ta nufi d’akinta ta saka masa key. ❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥❤️‍🔥 King kuwa tun lokacin da ya kashe fitilar d’akin be saurarawa tahee ba , sai da ya fanshe tsawan shekarun da yayi batare da shi ba , tun tana dukansa tana ihu har ta dawo ya kushi, still king ko gezau beyi ba aikinsa kawai yake yi baji gani, azabar da tajine tasaka duka ‘karfinta ta gantsara masa ciwo amma duk da haka kamar ba mutum ta cijaba, tun tana neman hanyar guduwa har ta kasa motsawa sai hawayen da yake bi mata fuska. 11pm lokacin da komai ya lafa tahee na kwance a jikinsa tana sakin masa kuka kad’an kad’an , shima kansa yasan ya mata lefi dan be raga mata ba amma ba lefunsa bane hakan , ha’kurinsa ya ‘kare bazai iya kasancewa babu ita ba , “ sorry sweetheart! I can’t hold it! Bazan iya jure rashin kasan cewa dake ba ! Am sorry please wannan kukan ya isa haka “, banza tahee tayi dashi sai ma ‘kara ‘karfin kukan ta da tayi , kamar da gaske yayi ‘ko’karin mi’kewa “ shikenan tunda bazaki ha’kura ba , bari nakira ummey ko abeey su zo su baki hakuri “, ‘karamun duka ta kai masa da ya sashi ‘kara rungumeta , cikin tsokana ya soma “ummey , oumma kuzo ku temakeni zai kasheni, abeey, taheer ya dena Sona “, ganin yana neman tona mata asiri yasa ta rungumeshi tana dariya , “ I love you “, cewar king, “ I love you too”, tahee ta mayar masa da amsa tana ‘kara rungumesa , sai kuma tayi saurin d’agowa “ JAMI’IN SIRRI ? Yaushe kazama? “ mayar da kanta yayi kan chest d’insa kafun shima ya bata amsa “ Long time ago!” Bata kuma cewa komai ba ta lafe a ‘kirjinsa Kawai tana sha’kar daddad’an kamshin turaransa , bayan sunyi wanka wani kayan ya saka mata duk yadda taso ta hanashi gudun kar Ammeey ta ganeta be kulataba , hatta guduwa da tasoyi ‘kin bari yayi , dole ta ha’kura tun tana magiya har bacci ya d’auketa a jikinsa . Kiran sallah asuba ne ya tashe su gabaki d’ayansu, da Sauri tahee ta sakko daga kan gadon har saida king ya ri’kota, lumshash shun eyes d’inta da suke cike da bacci ya zuba mata , a hankali ya furta “ ina zaki?”, wai ina zaki, tasan halinsa da Sauri ta furta “ zan koma kaga bansa nayi bacci anan va , please “, gado ya nuna mata alamar ta koma ta kwanta ,zai ‘kara nuna mata bed ta fashe masa da kuka , gashin kansa ya shafa , kafun ya zuro ‘kafarsa ya nufi inda take “ oya goge hawayen ! Shiknn zaki koma amma da condition “, da Sauri ta furta “ na yadda “. Kanshi ya jinjina mata kafun ya d’aga ta gabaki d’ayan ta duk mutsu mutsun da take be sauketa ba har saida yashi toilet da ita . Acikin toilet d’in ma da kanshi yayi mata wanka ya hana tayi da kanta , sai da yaga jam’i na ‘ko’karin wuce shine yasa ya ha’kura ya ‘kyaleta, saida sukai alwala suka canza kaya tukunna kafin ya jata zuwa wata ‘kofa ta part d’insa bayan ya mayar mata da face d’inta ,har suka ‘karasa part d’in Ammey , anan d’in ma saida suka sha daru da yace zai d’auke ta , da ‘kyar ta Samu ta gudu, shi kuma ya dawo part d’insa kafun su tafi masallaci shida zaki. Tana shiga part d’in Ammey kamar wata mara gaskiya ta yi Sauri shigewa d’akinta ,ganin babu Wanda ya ganta ne yasata sakin ajiyar zuciya , kafin ta cire face d’inta ta tayar da sallah, tana idarwa wani dad’i ne ya kamata , finally mijinta ya dawo gareta , tuno oummanta da taheer ne yasa ta sakin kuka kuma , sosai tayi kewarsu, ga kewar su junior ma da ya cika ta , amma duk da hakan bazata karaya ba , da Sauri ta mayar da face d’inta ta gyara ko ina na d’akin lokacin gari ya soma haske sannan tafito. Tana fitowa suka had’u da asabe tare suka soma ayyukan gidan . Alokacin da tahee ta dawo part d’in Ammey sai alokacin ita kuma Ammey ta samu ta runtsa, sabida yadda ta kasa bacci , data kulle idanuwanta zataji wani irin kuka da gurnani yana biyota. A firgice zata bud’e idanuwanta ko addua bata tunanin tayi , tana bud’ew kuwa zataga wasu ‘kananun halitta na biyo ta gadan gadan, a rike zata mi’ke tayi ta ‘kwalla kiran neman agaji amma babu Wanda yake zuwa dan gabaki d’aya wannan ihun da take babu Wanda zai jita , a gabaki d’aya cikin Daren nan Ammeey bata runtsaba da tayi gigin yin bacci zataji saukar mari ko duka a jikinta, haka ta zauna zuru zuru kamar me ta’bin hankali , sai wajan sallah asuba abun ya lafa , take a Wajan wani wahalallan bacci ya d’auketa ko tunanin gaida uban gijinta batayi aranta. ********* *************** Har Wajan 10 babu Ammey babu alamar fitowarta, ko ajikin tahee sai ma d’aki data koma taji a bincinta hankali kwance, kafun ta kwanta kwana daddad’an bacci ya d’auketa . Cikin bacci taji an ta’bata da Sauri ta bud’e idanuwanta zata saka ihu ya sakar mata kiss abaki , cikin rad’a rad’a ya furta “ matsoraciya “ da Sauri ta tashi zaune tana sakin ajiyar zuciya , “ Ina Kwana “ , ta furta a hankali , amsa mata gaisuwar tata ba sai ma tanbayar da ya jefa mata “ me yasa kike kwana a ‘kasa ?”, ganin be amsa mata gaisuwar taba ne yasa ta d’an turo masa bakinta kamar yadda ta saba “ kawai banasan kwanciya akai , ni ban yadda da komai na part d’innan ba “, bakinta da ta d’an turo masa ya d’an ‘bille mata shi “ kika ‘kara turo mun bakin nan zamu ‘karayin second round , “ ta Sauri ta saka hannunta toshe bakinta , bece mata komai ba sai hannu daya sa ya jawo katifar daga inda take zuwa side d’in tahee. Ita kuma idanuwanta basu sauka ako ina ba sai a kan d’an tudun dake ‘kasan katifar , da Sauri ta tashi ta ‘karasa wajan, zata d’aga yayi saurin dakatar da ita shima ya ‘karaso wajan , d’an mat d’in da yake wajan ya yaye , wani Jan ‘kyalle suka soma cikin karo dashi, nuni yayi wa tahee da ta ja baya , Hakan kuwa ta faru tana ja baya yayi Bismillah tare da yaye jan gyallan, wani ramine ya bayyana cikinsa kuma tulune a ciki, bakin sa d’auke da adduar ya d’auko tulun, be ‘bata lokaci ba ya fasa tulun da aka nanna d’eshi da jan ‘kyalle , yana fasawa wata Jan laya guda biyu suka fad’o sai wani ‘karamun maciji da aka sossoka masa allura , zafi hannunsa ya soma kamar Wanda ake ‘konawa fata amma duk da hakan be hakura basai da ya kwance layar, gabaki d’aya sunan dada da ummey da abeey layar farko, alaya ta biyu kuma duka sunan abeey ne a cike da wasu irin rubutu, hatta macijin da aka sossoka wa allura sunan abeey ne a jiki, kallan tahee yayi kafin ya furta “ d’auko mun ashana “, da Sauri ta d’auko masa ashanar data d’auko kwana kin baya , bai damu da a inda yake ba , ya had’asu waje d’aya ya kunna musu wuta . Sosai wutar da soma ci ,sai ga wani sautin tass yafito da ‘karfi cikin macijin ya fashe wani ‘bakin ruwana na fitowa daga cike me wari. Sun dad’e suka ci a huta kafin gabaki d’aya su ‘bace batt babu su daga layoyin har randar da ya fasa da ‘kyallan, kanshi yaji ya fara sara masa , a hankali ya d’auko phone d’insa da ake kira , number uncle musaddiq daya ganine yayi picking call d’in bansan me aka ce masa ba sai mi’kewar da naga yayi , a hankali ya furta “ on my way “ sai kuma ya kashe kiran ya nufi hanyar ‘kofa da Sauri tahee ta kallesa , “ Ina zaka ?” Kallan inda ya ‘Kona abun nan yayi kafun ya maida kallansa kanta “ ina tunanin abunda na ‘konane yayi affecting Abeey, Ance yana cikin magana dasu uncle musaddiq ya fad’i , so I have to go “. Zan raka ka” girgixa mata kai yayi “ no ki zauna anan kinji “sai yayi pecking d’inta a baki ya bar d’akin. Yana fita tamayar da kallanta wajan da ya ‘Kona layoyin, kamar babu abunda akai , ajiyar zuciya ta sauke , Allah ya temaketa bata kwana akai ba , da Sauri ta gyara Wajan ta mayar da katifar wajan kamar babu abunda ya faru. Ba’kin macijinnan kuwa da ya fashe me kwari be tsaya a ko ina ba sai a bakin Ammey a haka ya dunga shegewa bakinta tana bacci. ✨✨✨✨✨✨ Har bayan sallah azahar Tahee tana faman tsammanin zaman jiran king amma babu shi babu alamar sa , gashi babu waya a hannunta balantana tayi tunanin kiransa , tunanin taje part d’insa ne ya fad’o mata a rai, tana fitowa ta tarar da Ammey zaune kan kujera kamar mara lapiya harta d’an fad’a , saita nutsuwarta tahee tayi kafun ta ‘karasa cikin falon tana saka fake smile akan fuskarta , “Hajiya ina wuni”, shiru Ammey bata amsa gaisuwar da tahee tayi mata ba , akaro na biyu Tahee tana gaishe da Ammey , still bata amsa ba , sai akaro na uku da ta d’an kirata ne Ammey ta firgita sabida tunanin da ta fad’o, gabaki d’aya tayi zuru zuru, bata amsa mata da baki ba sai da kai kawai ta amsa mata ,itama tahee ko ajikinta sai ma ‘kara tanbayarta da tayi “ hajiya ko akwai abunda kike so ?”, nuni Ammey tai da tafi,har yanxu tana kan tunanin da ta fad’a tun safe ko abinci bata samu sa saka a bakinta ba . Itama tahee kamar wacce aka sa dole zata ‘karayi Mata magana ta daka mata tsawa “ nace banasan koma ki ‘bace mun dagani yanxu “ yadda tayi tsawar saida ta nemi tsoratar da tahee , juyawa tahee tayi zata bar wajan sukai karo dashi, ba Kayan d’azu ne a jikinsa ba ya canza , kamshin turaren sai shawagi yake cikin falour , sau d’aya ta kallesa ta d’auke kai ta nufi d’akin ta , sai dayaga wucewarta kafun ya lumshe eyes d’insa , kan d’aya daga cikin kujerun falour ya zauna yana bin Ammey da narkakkun idanuwansa masu wuyar fassara,kamar kullum saida ya daidaita kansa kafun ya furta “ Ammey?” Shima shuru bata amsa ba , sai a karo na biya da ya kira ta ta firgita dan yanxu magana kasan akai mata furgita take “ meke damunyi “, zaro masa ido ta fara , batasan ma amsar da zata Bashi ba gabaki d’aya , a rarrabe ta furta “ gajiya ce da kuma d’an ciwan kai da nake faman dashi “, gyada mata kai Kawai yayi dan ya gaji da saurarar muryarta , be jima ba ya bar falon batare da ya nemi inda tahee take ba. Tahee kuwa a tunaninta zai biyo ta d’akin amma sai taji shiru , gashi bata da dalilin da zai da taje part d’insa tunda Ammey na falon, har akai sallahr la’asar sai faman fita take tana dubawa ko Ammey ta koma d’akinta , amma har yanxu tana falourn ba kamar koda yausheba da sai tayi wanka sau biyu ko uku, yau tun rigar data saka har yanxu bata cire ta ba. Ai akai sallah magariba , shiru bai sake dawowa ba , akayi isha’i shima still shiru , ko abinci tahee bata Ciba ta kwanta , ita kad’ai har bacci ya d’auketa , duk Wanda yaganta yasan ba jin dad’in baccin take ba . 8:30pm yashigo cikin d’akin ynxu ma ya canza kayan , ganin yadda take baccin a takure ga fuskarta kamar a had’e yasashi sakin murmushin da ya ‘kara masa kyau , gabaki d’ayanta ya d’auketa kamar wata baby , ko da zai fito saida ya kulle mata d’akin sannan ya nufi ‘kofar da yashigo , babu kowa a falourn shiysa yayi wuce warsa kai tsaye da ita a hannunsa , har shiga cikin palourn sa bata farka ba , yana ajjeta akan kujera ta bud’e idanuwanta , da Sauri ta Tashi zaune sai faman kunbure kunbure take kamar zata fashe , “ am sorry ai gashi yanxu nazo ko?” , ‘kin kulashi tayi ta nufi stairs , tana shiga d’akinta shaf shaf wanka tayi ta saka wata yar finginan rigar hutawa , dogon gashin kanta ma ta saka wa reborn, sannan ta saka wata hula me shegen kyau , tana Fito wa ta tarar dashi tsaye , yanxu ba mata kulashi ba , zata wuce ya janyo ya jikinsa , a kunne ya rad’a mata “ wifey ynxu da kin koyi fad’a ko d’azu na saka miki saban baby ne ?” Da Sauri tahee ta rungumeshi , ga wata kunya data kamata lokaci d’aya , “ ni ka bari banaso “, okay ki tsaya na kalleki ni banga wannan ba ai ko zaki mun nima ?” Duka ta kai masa kirji tana sakin dariya , a kan sofa ya zauna , kafun ya zaunar da ita akan cinyarsa, “ yajikin abeey ?”, saida ya lumshe idanuwansa kafun ya furta “ da Sauri , zuwa gobe zai dawo normal “, hannunta ta tusa cikin gashin kansa “ am sorry! Nasan ka yadda da ita sosai , ka dena ‘boye abunda ke cikin zuciyar ka ! You can always cry on my shoulder! Da wahala mutumin da ka yadda Dashi yaci amanarka! Kayi kuka please “, da Sauri ya kawar da zancen ta hanyar furta “ yunwa nake ji “, duk da taga yadda idanuwansa suka sauya be kuma cewa komai ba, shima bai kuma ce mata komai ba sai tray d’in da ya shigo dashi,” baki ci abinci ba , kina so ki mun azara ko ? Oya open your mouth “ a hankali ta bud’e bakinta ya saka mata gas meat d’in da ya d’akko , itama wani ta d’auka zata saka masa ya nuna mata fingers d’inta , fork ta ajje ta saka hannun, tana sa masa a baki ya rike hannun, saida ya sid’e abunsa tas sannan ya saki hannun , haka suka cigaba da jiyar da juna , sannan ya bata fresh milk, saida suka ‘koshi kafun ya d’auki babbynsa zuwa kan gado, yanxu ma duk gardamar da ta so yi be saurare ta ba . Ba ita ta koma part d’inta ba sai da akai kiran sallah asuba . ✨✨✨✨✨✨✨ Haka rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin farinciki kullum idan yazo ya d’auki babbynsa baya bari ta dawo sai bayan sallah asuba . Ammey ko damu da inda tahee take ynxu batayi sabida ita kanta a firgice take , duk dare idan tace zata kwanta bata iya bacci Sabida furgicin da yake haka ta bacci, kullum cikin dare haka zatayi ta ihu , tana neman temako amma babu alamar za’azo , ba ita take runtsa wa ba sai bayn kiran sallah asuba , shiysa king da tahee suke sharholiyarsu, yanxu bata damu ba dakanta ma zuwa part d’insa take duk lokacin da taso dan yawan cin lokaci a part d’insa take yini. A gabaki d’aya basu zauna ba Sabida aikace aikacen da suke a part d’in ummey, har yanxu ummey bata ce mata komai ba , amma mimi ta sanar da ita komai , maganar yah moh ne da na junior kawai itama bata sani ba , haka suka ci gaba da aikace aikace Sabida gobe ba’kin da zasu zo , gobe mahma da sha’aban zasuzo, a gefe d’aya small mom da su zoya zasuzo, samreen ma a gobe zatazo Nigeria , ga dangin ango da zasu zo , dan abbey ya fad’a wa dady bikin ‘ya’yansane yana bukatar ganin kowa da ko kafun bikin. Tun lokacin da abbey ya suma , zuwa safiya ya farka ,tunda ya farka yake nuna wa ummey soyayya kamar lokacin da suke amare ko sau d’aya be tanbayi inda Ammey take ba , hatta dada tsawan lokacin nan kamar bata ta’ba wanzuwa ba , babu Wanda yake nemanta.itama Ammeey bata zuwa sbida wannan abunda yake faruwa da ita a cewarta sai ta nutsu ta saita kanta zataje wa abeey. 💖💖GIDAN AUNTY 💖💖 07041879581 MSS LEE BOOK 2 Page 18 WASHE GARI Yau ma gabaki d’aya basu zaunaba suna kan aikace aikacen da za’ayi na tar’bar bakin da zasuzo, gabaki d’aya yagowar manyan part d’in gidan guda biyu an gyarasu, yau tun safe bata sanya shi a idanunta ba , bata d’aga hankalinta sosai ba itama dan Tasan hayaniyar ba’kin ce zata sakashi ‘kin fitowa . Sosai akayi wa baki abubu da yawa na har sai kowa ya ajje , ‘karfe 12:30am na safe aka je a aka d’auko Mahma da sha’a’ban a airport, mahma bata tsaya a ko ina ba sai cikin part d’inta ta da take sauka a ‘bangaran dada , sha’aban kuma daman yana building Dinsu haroon a nan d’akinsa yake Duk lokacin da yazo shima a cikin d’akin nasa yake sauka , ko wannansu part d’insa aka kai masa abinci sabida kar’a takura wa ko wannansu Sabida gajiya , karfe 2:20 itama samreen ake d’akko ta a airport , sai a lokacin tahee ta san ta , sosai kuma take mata kama da king d’inta dan dai ita macace sai fari da king ya fita sosai duk da cewar itama fararce, a ‘bangaran ummeynta ta sauka itama , a wannan karan mimi da tahee ne suka kai mata abincinta, sosai taji dad’in hakan kuma ta gode musu, dan gabaki d’aya ukti bata da wula’kanta d’an Adam tun lokacin da Akhiee ya rasu hakan ya ‘kara shiga cikin ranta . Tun safe su tahee suke abu d’aya dad’insu familyn ango da akace zasuzo sai 8 jirginsu zai shigo Lagos dan ko tasowa basuyi ba su, small mom ba jirgin ‘karge 10 ne zai shigo dasu cikin Garin lagos. Allah sarki duk yadda ummey tayi akan su huta haka tahee da Mimi su’kayi komai dasu akan dunga aikace aikace wannan karan har ita kanta ummey bata zauna ba , sai dasu tahee suka amsar mata aikinta, kamar wasu aljanu ko gajiyar jikinsu basaji sannan ko afuska babu basa nuna alamar kajiyawa da aikin da suke yi duk da tsananin gajiyar da sukayi, babu abunda yake tsayar dasu sai sallah , shima da sun gama zasu cigaba da aikinsu , ‘karfe 8:25pm na dare familyn ango suka shigo cikin Al-nahyan, babban part d’insu da aka gyara musu aka kai musu Kayansu , tahee da Mimi suna ta zuci zuci suga familyn d’in Amma basu samu sun gani ba suma Sabida ayyukan da suke yi, ‘karfe goma da rabi ma sai labarin zuwan small mom sukai tare da zoya da wani had’ad’d’an kamar balarabe da suka zo tare da zoya , kowa sai faman kud’i kyan da zoya tayi, duk rigimar nan babu yanxu ta zama ‘yan Mata , yadda suke tafiya cikin gidan lokaci zuwa lokaci zoya tana yiwa kyakkyawan guy d’in zakaga ba ‘karamin burgeka sukai ba . Itama ummey bata had’u da small mom ba , sai su momy ne suka tar’beta zuwa part d’inta itama , kowa yana mamakin yadda zoya ta koma budurwa abunta , ga mamakin inda small mom ta samo balarabe suke duk da duk cikinsu babu mu nana . Tunda aka soma hidimar nan a marya bata fito ba , itama kamar yadda akai wa tahee d’auke ta akai Sabida kar a dunga zuwa ganinta .basu tahee ne suka samu kansu ba sai wajan ‘karfe 11 na dare , ko wannansu makwanci yake bu’kata tun lokacin da Ammey ta saka su d’ibar abincin su dukda sun ce mata ba yunwa suke jiba Amma haka ummey ta zuba musu da kanta , musamman tahee da ta saka mata cikin tray , sai faman saka musu albarka take, Mimi da tahee basu wani tsaya hira ba kowa ya nufi makwancinsa , ita tahee d’auke da tray d’in da aka zubo mata abinci ta nufi hanyar part d’in Ammey duk da batasan ta yadda zata shiga da tray d’in ciki ba , batare da Ammey ta kula Dashi ba . Mamakinta rashin ganin Ammey da tayi , inda da ne tana cikin masu yin ayyukan tar’bar baki amma ko ayanxu tana da tabbacin Ammey ta san duk abunda yake wakana na ba’kin da akai , fitowa ne Kawai batayi ba . Ta’be baki tahee tayi irin alamun don’t care d’innan itama , zata ta’ba handle d’in kofar taji anri’ko hannunta , saura kad’an ta saki tray d’in hannunta . Sanye yake cikin wasu ba’ka’ken kananan kaya da suka fito da hasken fatansa sosai, sai black p-cap d’in fuskarsa da ta ‘boye , tray d’in hannunta ya karba da Sauri ta zaro idanuwa ga idanuwanta dasuka fara lumshewa alamar gajiya , ganin tana ‘bata masa lokaci ne yasa ya ri’ke mata hannu ya nufi part d’insa da ita , Allah ya temaketa babu kowa da babu abunda zai hana wani ya gansu . Yana shiga part d’insa tray d’in abincin ya ajje kafun ya cire p-cap d’in kansa ,lallausan gashinn kansa ya fito fess dashi, kallan yadda take layi yayi kafun ya d’auketa gabaki d’ayanta ya nufi toilet da ita , da kansa yayi mata wanka ya shiryata , lokacin har ta fara bacci sabida yadda ta gaji, abinci ma da ‘kyar ta Samu taci sabida baccin da takeji. Sai daya lalla’ba kayarsa tukunna kafun ya kashe duka light ya d’auki babyn sa zuwa bedroom , ganin yadda take ta faman lumshe ido ne yasashi d’ora kanta akan chest d’inshi, ya ja musu blanket, yadda taji d’umin jininsa kuwa hakan ba ‘karamin dad’i yayi mata ba shiyasa ta ‘kara rungumeshi a jikinta daddad’an kamshinsa na ratsata, ko cikakken mintu biyu tahee batayi ba bacci ya d’auketa . Shima sabida ayyukan da ya tsaya yi be dad’e ba yayi bacci rungume da babynsa. Kamar ko da Yaushe sallahr asuba ne yake ta yar dasu , wannan karan shi kad’ai ne ya farka tahee sai baccinta take. Kallan yadda take bacci hankali kwancane yasa ya ‘kyaleta ya nufi toilet ,har yayi wanka ya shirya cikin farar jallabiyar sa tahee bacci take , sau biyu yana tashinta tana koma wa, saida yayi da gaske tukunna tahee ta tashi, saida ya tabbatar da ta shiga toilet tukunna ya bar part d’in , tahee ma wanka tahee ta ta yar da sallar ta , tana idarwa bayan tayi azkar d’in safe ta ‘kara bin lafiyar gado yau ko tunanin ammey zata nemeta batayi ba tacigaba da sha’kar baccinta hankali kwance . Lokacin da ya dawo ya tarar da ita tana baccin ta be tasheta ba , shima kwanta wa yayi a gefanta, be jima ba bacci ya d’aukesa . Karfe 9:30am tahee ta farka , idanuwantane suka sauka kan agogon d’akin da Sauri ta tashi zaune tana zare idanu, ta tashi daniyar sauka daga kan gadon ya ri’ko hannunta tare da jawota jikinsa, zatayi magana yayi mata alamar tayi shiru, shirin kuwa tayi tana binsa da kallo a tunaninta zai saketane sai taga itama ya ja mata blanket ya rungumeta a jikinsa , cikin rad’a rad’a a kunnanta ya furta “ go back to sleep “, itama cikin rad’a ta futurta “ nasan Ammey zata nemeni fa “ shima amsa ya bata “ and so ? Akwai Wanda zai hanani kasancewa da matata? So keep silent ok and sleep”, ganin ba wasa yayi maganar shiyasa itama bata kuma cewa komai tayi hugging d’insa a jikinta , daman baccin ba isarta yayi ba , and ga d’umin jikinsa shiyasa bata jima ba bacci ya ‘kara d’aukar ta. A cikin gida kuwa ko wanna part ankai musu breakfast d’insu , har part d’in family d’in ango duk sai da aka kai musu breakfast d’insu , duk da har yanxu family d’in basu had’u waje d’aya ba. Darana ma haka aka kaiwa kowa lunch d’insa kamar yadda akai da safe , lokacin ne Abeey ya bada umarnin kowa da kowa su had’u a babban falournsa anan za’a yi dinner gabaki d’aya family din. Duk wannan abun da yake faruwa babu Wanda ya saka Ammey a cikin idanuwansa , abun mamaki kuma babu Wanda ya tanbayi inda take . A ‘bangaran Ammey kuwa jin labarin dinner d’in da za’ai tsadaddiyar gezna d’inta tasaka a ka Fito mata da ita tare da had’ad’d’an gold d’in me shegen tsad’a dan tayi al’kawari babu Wanda zai fita had’uwa yau da daddare , yau ko neman Tahee batayi ba sabida gyara kanta da take sosai har da saka cream d’in fuska. Itama tahee gabaki d’aya yinin ranar a part d’in king tayi shi , yadda ya hanata fitan ba ‘karamin mamaki da d’aure mata kai yayi ba , bata gama shiga mamakin yanayinsa ba sai lokacin da ya bata wata rantsantsiyar abaya da duk yadda mutum ya motsa sai tayi walwalin stone d’in, ba ‘karamun kyau da tsaruwa abayar tayi ba red colour sai stone d’inta da suke shinning, hatta takalmi da jaka suma red colour aka kawo mata rantsatstsu masu shegen kyau . Duk yadda taso guda ya toshe wannan kafar har mamakin yadda ake kawo masu abincin da suke ci take , ganin bata da wani Za’bi ne yasa ta rungumi mijinta su kad’ai sai faman soyayyarsu suke me tsayawa arai. ✨✨✨✨✨✨✨ Karfe 8:30 aka fara harrala cikin babban falourn Abeey da ya gama tsaruwa da had’uwa , babban falour ne sosai me set d’in kujeru kusan biyar aciki, daga gefen dama Kuma wani step ne da za’a taka befi biyar ba zai kai ka babbar dinning table d’in da a kallah zai d’auki sama da mutane 30 sabida girmanshi, ga kalolon abinci da aka saka , ta ko ina ‘kamshi ne yake tashi, ga sanyin acn da yafi komai dad’ad’a zuciyar mutanan wajan. Su ummey ne suka fara zuwa part d’in abeey, daga ita sai samreen, bayan su kuma dada ce sai mahma da ya sha’aban da suka shigo ciki suma kowa kagani cikin shigar alfarma zaka samesa , bayan su kuma familyn uncle musaddiq da uncle saleem ne Suka shigo , yau hatta amarya da su firdausi har dasu aka hallara Dan abbey yace wannan dinner d’in ta gabaki d’aya family ce , kowa da kowa ya hallara , yanxu ma small mom ce ta shigo falourn bayanta zoya ce sai had’ad’d’an matashin saurayin da a shekaru bazai wuce shekara 22 to 23 ba shima kyakkyawa ne , kana kallansa shida zoya zaka ba ‘karamun sabuwa sukai ba . Daga su kum babu Wanda ya sake shigo wa palour kusan mintuna biyar kafun suma su ango su shigo palour shida zahra kawai, banda oumma , kana kallan fuskar khaleed zaka ga annashuwa kan fuskarsa sai faman satar kallon amaryar sa yake. A cikin falour su abbey kawai babu a ciki sai haroon da bai shigo cikin falourn ba dan tukuni kabeer yazo shima dan ya gaji da neman haroon shiyasa yayi tahowarsa. Tunda zahra ta shigo cikin falourn sha’aban yake binta da kallo duk motsin da zatayi akan idanunsa , tun bata kula da shi ba har ta gane kallanta yake , ganin yadda ya ‘kura mata ido ko kunyar aka masa bayayi Yasa zahra a fakaice ta murgud’a masa baki, murmushi ya sakar mata yadda baza’a gane ba sannan ya nuna kansa , ‘kara murguda masa bakin tayi ‘kasa ‘kasa ta furta “Kurwata dai kur sai wani bina kake da kallo sai kace kaga wata sabuwar halitta, daga ‘karshe ma zahra had’e ranta tayi wai dan karya ‘kara kallanta , Hakan da tayi ba ‘karamun kyau tayi masa ba , shiga ya d’auko phone d’insa yayi snapping yadda ta had’e rai ba tare da kowa ya ankare da shiba. Sai da aka gama gaggaisawa kafun uncle saleem da uncle musaddiq shigowa falourn bayan su kuma Abeey ne tare da dadyn su zahra da abeey ya je ya d’auko shi dakansa, ko wannansu cikin shigar dattako amma da ka kalli uncle saleem zaka ga kamar yayi rashin lapiya Sabida yadda ya fad’a, aunty ba duk yanda take yatsine yatsinen ta saka kaya masu tsad’a lokacin da ta shigo cikin falourn saida jikinta yayi sanyi dan babu me shigar banza a cikinsu. Falourn yayi Sauri daga su oumma sai su tahee ne basa cikin falourn , a wannan karan hatta Mimi itama bata cikin falourn gabaki d’aya tun safe . Lokacin da su abeey Suka shigo ‘kara gaggaisawa akai gabaki d’aya familyn , tunda dama ba gabaki d’ayan su ba , ba’kin juna bane , Dady ne ya d’an bada uzurin su hajiya akan cewa mu fara cin abincin tunda tun safe zahra ta fad’a masa ciwan kan da oumma ta kwana dashi, tunda suka shigo kalon kuma yake bin saurayin nan da kallo amma be ce komai ba , daman abeey yasan halin king ba Lalle ya shigo cikin mutane haka ba duk da ya bashi umarnin shima ya shigo cikin falourn kamar kowa , umarni abbey yayi da a nufi dinning, gabaki d’aya familyn kuwa can suka nufa har lokacin Ammey itama bata shigo cikin falourn ba , a wajan dinning ma yadda sha’aban yaga zahra tana faman kunbura baki duk lokacin da ya kalleta hakan ba karamun ‘kayatar dashi yayi ba , saida ya daidaiti kujerar da zata zauna kafun shima ya zauna a wacce take facing d’inta, su momy ne sukai serving d’in kowa na falourn , and tunda suka soma cin abinci babu Wanda ya yi magana, shi sha’aban tunda aka soma cin abincin ma tsakura kawai yake sabida yadda yake kallan zahra kamar zai had’iyeta, ganin yadda ta ta’be fuska kamar me shirin kuka kuma tana ‘ko’karin Tashi daga Wajanne yasa sha’aban kallanta, tare da girgiza mata kai alamar kar ta tashi, duk da yadda take jin Haushin kallan da yake mata sai ta kasa musa masa ta zauna d’in, khaleed ma ba’abarsu a bayaba , shima tunda suka zauna yake kallan ilham da har saida yasa ta jin kunga gabaki d’aya , duk abunda suke shi da sha’aban a idanun abeey da ummey, babu abunda suke sai sakin murmushi, a haka gabaki d’aya familyn suka gama cikin abinci kafun su koma falourn gabaki d’ayansu ana hira . Zoya ce ta mi’ke tsaya amarairaice takalli abbey “ shima murmushi yasaki “ auta har yanxu baki girma ba ko, Menene kike?, ganin ya ganota ne ysa ta saki dariya “ Abbey a kwai film d’in da zan kunna mana gabaki d’aya kaji?” Hararar ta ummey tayi “ baza ki iya kunnawa anan ba sai kinje wani wajan ?” Kamar zatayi kuka ta kara kallan abbey ta ‘ki yadda ta kalli ummey ba , “ ah ah far kusa mana auta kuka , maza auta jeki kunna mata muyi kallo abunmu”, cewar dady yana d’an kallan Abeg , shima abeey Alama yayi mata akan zata iya zuwa , har ta soma tafiya tayi saurin tsaya wa tana kallan wannan matashin da suke tare “ bro Dan Allah kazo ka rakani”, d’an harararta yayi kafun ya tashi ya biyo bayanta, kallan small mom abeey yayi “ wannan son d’in naki ya burgeni, ko zaki bar mana shi”, zai yi magana shima dady ya furta “ Nima dai abunda zan fad’a kenan ka rigani, amma bari muga wazata bawa, ita small mom dariya ma suka bata , wai wazata bawa , ai me rabata da son d’inta sai Allah, tana ‘ko’karin yin magana Ammey ta shigo cikin falourn taci ado na kece raini harda ‘yar ‘karamar makeup tayi wa fuskarta, gabaki d’aya mutanan falourn zuba mata idanu sukai har ta ‘karaso cikin falourn , suna had’a ido da abeey , abeey ya had’e rai lokaci guda ransa ya baci yana binta da wani irin mugun kallo , ita kanta dada mamakin ganin ammey tace cikin falourn Amma dai bata ce komai ba sabida bataso tsaran da aka had’a yau ya ‘baci sabida wata ,gabaki d’aya sai Ammey ta tsargu da kallan da suke binta dashi amma kasancewar ta shu’umar mace sai ta ‘boye hakan a fuskarta ta Samu waje itama ta zauna tana d’an sakin masu murmushi, haka kawai taji zuciyarta na tsanan ta bugawa , ko magana ta kasa yi, lokaci zuwa lokaci kuma a wayance tana d’an sosa jikinta ta ydda bazaa gane ba . Sallar su zoya ce ta katse mata tunanin da ta fad’a , da Sauri kuma Ammey ta d’ago da idanuwanta kansu , gabantane ya fad’i ya tsinke aranta take furta meke faruwa ? , saurayin dasuka shigo tare da zoya Ammeey ta soma bi da kallo har suka shigo cikin falourn gabaki d’aya , a mugun zabure da tsananin firgita Ammey ta mi’ke tsaye tana tunanan saurayin, kirjinta da yake neman fashewa ta dafe bakinta har rawa yake wajan furta “ TAHEER !?” A Daidai lokacin da oumma ta ke shigowa falourn ita da Mimi da suka had’u a hanyar shigowa , kallar taheer da aka ambata ne yasa ta kara saurin tafiyarta, gabaki d’aya falon sai aka zuba musu idanuwa kowa yana mamakin inda tasan sa , kalmar taheer kawai oumma take maimaitawa a cikin zuciyar ta bakinta har rawa yake ‘kafafuwanta gabaki d’aya sunyi sanyi kamar sata fad’i haka take jinta , da d’inta d’aya ma Mimi dake tare da ita , itama tana shigowa cikin sar’kewar murya me cike da rauni ta furta “ taheer “ tana tunasa, muryar wacce bata ta’ba tsammani bane Ammey taji da Sauri ta kalli ‘kofar, oumma da tagani ne yasa bata san lokacin da ta hantsula ba sabida shiga tashin hankali, gabaki d’aya kokarin fita take daga hayyacinta ga susar da take ya ‘kara yawa , jiki na rawa shima taheer ya soma nuna oumma , hawaye har ya fara ‘bata masa fuska, zahra ce ta kasa yin shiru ta furta “oumma kinsanshi?”, kanta kawai oumma ta gyad’a mata a hankali ta furta taheer d’ina , taheer d’inane , Aushe zan ‘kara ganin ka taheer ? “ shima taheer kuka kawai yake da Sauri ya nufi inda oumma take ya rungumeta , sai alokacin kowa ya fahimci wanene musamman su zahra da suka gane taheer d’in da oumma take basu labari ne , sosai zahra ta cika da farin ciki kuwa finally sun ga taheer d’in umma, bata gama zancan xucin nata ba sabida ‘karar da Ammey ta saki tare da tsige d’an kwalin kanta , hankali a tashe cikin fitar hayyaci ta soma magana “ bazai yuwa ba , me ya dawo daku? Baku mutuba ? Nace me yasa baku mutuba?” Gabaki d’aya falon babu Wanda beyi mamakin furucin Ammey ba sai ma binta da kallo da suke , zata nufi hanyar fita daga falon ta ji muryarta cikin babbar tvn falon kamar wata almara. Da Sauri ta ‘kame jikinta har rawa yake yake lokacin da taji muryarta , jikin abeey har rawa yake lokaci guda , gabaki d’aya familyn kuma hankali a tashe suke kallan tvn da basu san wanene ya kunna tava , Ammey ce zaune cikin lambun sha’katawarta tare da abokin sharholiyarta da ba a Ganin fuskarsa , labarin yadda zasu kashe king da abin cikin taheera suke tattauna , da irin tsarin muguntar da Suke shirin yi suke tattaunawa , cike da tashin hankali falon a ka d’auki salati, basu gama shiga cikin tashin hankali ba sai lokacin da next vidoen ta y shiga lokacin da take kamar a haukace ta shiga d’akin tsafinta gabaki d’aya batasan ana ganin tava lokacin da take waya tana zayyane abubuwan da sukai , tun daga kashe baban tahee har da kashe yah moh da sukai , da ‘kokarin kashe king da abunda ke cikin tahee duk saida ta lissafa su ita kanta bata san lokacin da take zayyano gabaki d’aya bad’alar da sukai, next da ya shiga ba su abbey ba hatta su taheer jikinsu rawa yake lokacin da Suka ga Ammey na shan Jini, dariyar da ta ‘kyalkyalene ysa suka mayar da kallansu gabaki d’aya Kanta daske dariyar take da ta kalli d’aya daga cikinsu zata kara saka wani dariyar tana nuna su , da ‘karfi ta furta “ na kashe su , eh na kashe su, bokanya ta cika mun aikina , saura kad’an aikina ya cika kuka ‘batamun, gabaki d’ayanku sai na kashe ku, saina kashe ku da kuka ‘bata mun shiri , lokaci d’aya kuma sai ta cigaba da susar jikinta da takejin kurajan da suke jikinta suna mata ‘kai’kayi, kallo d’aya tayi Musu sai kuma ta saka gudu daniyar barin falon , tun kafun abbey ya bada umarnin a tare sukai karo da tahee da tashigo cikin falourn sanye da abayar da king ya bata , ga baki d’aya falon mi’kewa tsaye sukai su dada har yar rigan furta “ tahee suke “ Sabida tsananin mamaki, yadda Ammey taga tahee ne Yasa ta fara dukan kanta tana ja da baya cike da rud’ani , itama tahee kallon ummey da taheer kawai take hawaye na sakko mata akan fuskarta, yadda idanuwanta sukai Jane saka gane ranta ba ‘karamin ‘baci yayi ba , a zuciye takalli Ammey , “ me mukai miki? Me muka tsare miki? Me mahaifina yayi miki da zaki kashe shi? “ sai kawai tahee ta saki wata irin kara da ta razana kowa nacikin falon , kafin kace me ta sha’ko wuyan Ammey da mugun ‘karfi, taheer ma da idanuwansa ya juye zuwa ja inda Ammey mn take ya nufa amai makon ya cire hannun taheera daga sha’karda tayiwa Ammey shima ai yasaka duka karfinsa ya dam’ki gashin Ammey , damka ba irin na wasa ba , har har fatar kanta sai da ta nuna haka sabida yadda ya dam’ki gashin kanta , a d’aya bankaran tahee kuma ta sha’ke mata wuya , cikin wata murya kamar ta namiji tahee ta soma magana “ me mukai miki zaki kashe mu? Me mukai miki? Me Nona tayi miki zaki rabamu da ita? Me mukai miki da zaki rabani da lulu?nace me mukai miki?” Ammey sabida yadda Tasha azaba gudawace ta kwace mata , gabaki d’aya nunfashinta neman d’ajjesa yake a cikin falon babu Wanda yyi ‘ko’karin da katar dasu dan gabaki d’aya jikin kowa yayi sanyi a falon , cikin wani irin ‘karfi tahee ta wulwula Ammey ta buga ta da ‘kasa, bakinta da ya kasance babu hakwara biyu kawai tahee take bugu gabaki d’aya bata cikin hayyaacinta, taheer ma da idanuwansa suka sauya hannun sa ya saka da mugun ‘kafi ya daki hanci Ammey take a wajan hancinta ya fashe da Jini gabaki d’aya Ammey bata iya kwakkwaran motsi Sabida ydda ta jigata a hannunsu tahee , ganin sunan’ko’karin yin kisa ne yasa su khaleed suka nufi taheer da niyar ‘ban’bare hannun da ya kama gashinta,abun mamaki duk yadda suke da wannan girman gabaki d’aya yayi jira dasu , su mahma ma da sukayi niyar zuwa wajan ta kallo d’aya tayi musu suka sha jinin jikinsu , kafun tahee ta mayar da kallanta kan Ammey da ta gama jigata , cikin muryar kuka ta furta “ me mukai miki? Me yasa kika cutar damu haka ? “ nan ma shiru tayi ta kasa magna sai faman zare idanu da take , hannayenta biyu taheee ta had’a ta bawa Ammeey wani gigitaccen mari a fuskarta da ysa Ammey suma take a Wajan , wani marin ta bata take a Wajan Ammey ta farka, ganin abun zai wuce hankali ne yasa mahma kiran layin king Amma gabaki d’aya bata shiga number tasa . 💖💖GIDAN AUNTY💖💖 07041879581 MSS LEE BOOK 2 Page 19&20 🔚 Gabaki d’aya anrasa Wanda zai kwace Ammey , oumma ce dakanta a wannan karanta karasa inda suke , da ‘karfi ta dam’ki hannun taheee , itama tahee zata kwace hannunta oumma ta d’auketa da mari tare da daka musu tsawa ita da taheer , gabaki d’ayansu sunkuyar da kansu sukai kamar had’in baki , musammann hannun tahee da oumma ta ri’ke , alama tayi wa su khaleed akan su d’auke taheer, hakan kuwa akayi khaleed da sha’aban ne suka d’aukeshi, sai faman zazzare idanuwa Ammeey take musamman wajan idanuwanta da ya fara kunbura ga le’benta shima da ya tashi, duk adon da tayi ya ‘baci sai muninta ya fito sosai, zahra tayiwa alama da tazo , taso wan kuwa tayi dan ita abunda su tahee sukai wa Ammeey taji dad’in sa, a cewarta ma dama idanuwan Ammey suka tsokale kowa ma ya huta. Tana ‘karasowa oumma tayi mata nuni da ta d’akko mata Rubutun ta, kai zahra ta d’aga mata kafun ta bar falon da Sauri , sha’aban yana ganin futarta da minti d’aya shima ya bi bayanta, taheer kuwa gabaki d’aya tashi zai bar falourn oumma tace ya koma, ko da ya koma d’in Wajan small mom yaje , itama small mom gabaki d’aya jikinta yayi sanyi da abubuwan da suke gani yanxu kamar almara , shiyasa ta ri’ke hannun taheer d’in kar yace zai ‘kara tashi, itama tahee da fuskarta take a had’e kallan Ammey da haryanxu take sauke nunfashi tayi, ‘kara tahee ta saki tana dafe kanta , tare da fincike hannunta a hannun oumma , gadan gadan ta nufi ammey, ydda take abu kad’ai zakasan ba ita kad’ai bace , da Sauri cikin mawuyacin hali Ammey ta mi’ke zata musamman yadda taga tahee ta nufota, itama taheen bata dena binta ba daina Sauri da ta ‘karawa tafiyarta, Daidai lokacin da king ya shigo falourn , gabaki d’aya falon sauke a jiyar zuciya sukai tunda suka ga yashigo , shima fuskartasa gabaki d’aya babu walwala da rahma akan fuskar tasa , Ammey na ganinsa ta nufo sa da Saurinta tana sakin masa kukan ‘karya “ son kaga abunda yarinyar nan tayi mun? Bazaka ‘kara zama da ita ba , ka duba kaga yadda tayi mun son ? Kalli irin dukan da tayi mun”, bata ‘karasa ba tayi kamar zata cafkota Sabida fusatar da tayi , da hannu d’aya king ya saka ya janyota jikinsa , shima d’in ‘ko’karin kwace wa take kamar wacce ta fita daga hayyacinta, ganin Dagaske hannunta zata kwace ya sa duka hannunsa biyu ya ri’ke ta sosai tare da daka mata tsaya , a Daidai lokacin da yayi mata tsawan alokacin jikinta ya tafi kamar zata fad’i ya ri’kota , take a lokacin tahee ta suma a jikinsa. Tallafe ta yayi sosai kafin ya kall Ammey da idanuwansa da suka gama yin ja Sabida ‘bacin rai, su zahra ne suka shigo ita da sha’aban da yake d’auke da ruwan da oumma tace, a d’an kausashe king ya furta “ come in”, zaki ne ya shigo cikin falourn bakin sa d’auke da sallama , hannunsa kuma wanine da ya gama cin duka wajansu fuskarsa a kulle , kwance abunda fuskar zaki yayi kafin ya hankad’o mutumin ‘kasa ,gabaki d’aya salati falourn suka d’auka , bakin Abbey har karkarwa yake wajan furta “ saleem?”, d’ago da kansa uncle saleem yayi da ya gama cin duka a hannun su zaki, itama dada salati ta soma taki “ tahanuni me nake gani haka ? ‘Kanin baban naka zaka sa ayiwa wannan dukan? Lapiyar ka ‘kalau kuwa ?”, yadda ran king yake a ‘bace ne yasa gabaki d’aya be bawa dada amsar taba sai ma jijiyoyin kansa da suka tashi sosai, “ DADA”, muryar da dada tajine yasa ta mi’ke tsaye a firgice abbey da su dady ma duk mi’kewa sukai tsaye ,ummey gabaki d’aya jikinta karkarwa yake tana nuna sa da d’an yatsa, Allah sarki samreen da Sauri ta ‘kara inda yake kafun ta furta “ Akhiee”, yadda tayi hugging d’insa ne yasa ta d’an sakar mata murmushi duk da ransa da yake a jagule, kallan ummey da jikinta ke rawa yayi , kafun ya kalli abbey yana sakar musu murmushisa kamar da, hawaye ne suka fara sakkowa akan ummey, kafun ya kalli king da shima shi yake kallo, sai alokacin uncle saleem yaja dogon nunfashi a wahale daga suman zaune da yayi, Ammey kuwa gaba ki d’aya jikinta karkarwa yake , lokaci d’aya ‘Kai’karin jikinta yafu na farko , da Sauri ta fara susar jikin ta Sabida azabar zafi da yake mata, arud’e uncle saleem ya fara duka yah moh , be san lokacin da bakinsa ya furta “ baka mutu ba ? Me yasa baka mutu ba ? Da nasa su kashe ka basun nuna min vidoen ‘konaka da sukai ba ?” Murmushi akhie ya sakar masa tare da girgiza kai “ har yanxu ina raye tun lokacin da kasa a kasheni kai da ita sabida asirinku da na sani “, ya ‘karasa yana nuna Ammey da ke faman susa, d’an kwalin kanta tuni ya cire ya koma gefe shima . Rai a’bace abbey ya kalli uncle saleem “ kai kasa a kashe mun d’ana dama? Me nayi maka da na cancanki wannan cin amanar”, shima uncle saleem a zuciye ya kalli abbey tare da nuna masa dada “ duk ita tajanyo komai , da bata bari naji cewar ba Itace ta haifeniba da duk hakan bata faru ba , me yasa komai sai tace kai kai kai ? Idan zan tanbayeta kud’i da yawa sai tace zanyi almabur ziranci, dan nayi yawo da ‘yan mata ko dan ina kwana dasu zata hanani? Rayuwa tace fa bata kowa ba , duk yadda naga damar jin dad’in rayuwa hakan zanyi , ni ban ta’ba sanku ba, na tsaneku dukanku shiyasa nayi ‘ko’karin kashe ka ,na kashe ‘yayn naka gabaki d’aya ,” sai kuma ya mayar da kallansa kan uncle musaddiq ya ‘kyal’kyale da dariya “ kai ma yanxu haka ka fara shirin jana’izar d’anka dan yanxu haka na tabbata ya zama matacce, idan ya mutu kaje kabarinsa kasanar dashi bana san bin kwakkwafi , tun farko banyi niyar kashe saba , shish shigin da yayi mun lokacin da nake tattaunawa da masoyiya tace yasa na sa a akashesa “ da Sauri momy da uncle musaddiq suka mi’ke tsaye , momy har ta soma hawaye sai ga muryar haroon a bayansu” uncle saleem ban mutu ba , da saura na Sabida yaya king ya ku’butar dani “, gabaki d’aya falan ajiyar zuciya suka sauke , ganin haroon. Had’iye maganar da zaiyi yayi ganin haroon a gabanshi be mutu ba , cikin kuka dada ta soma magana “ ka cuceni saleem kaci amanar ta , na d’auke ka kamar d’an da na haifa amma kaci amanata, na d’auka Amintar dake tsakanina da mahaifiyarka zan ri’keka a matsayin d’ana batare da kowa ya san hakan ba , amma kashhh kai d’in butulu ne saleem , Allah ya isa tsakanina da kai Allah ya tsine maka albarka “, da Sauri abeey yayi ‘ko’karin da katar da ita amma saida dada ta ‘karasa tsine masa , dariya ya saki tana nunata da ya tsa “ idan kin tsinemun sai me ? Nace miki sai me ? Tsinuwarki bazata yi mun komai ba “, ta ya kara sakin wata dariyar kafun ya kalli aunty da gabaki d’aya zuba ta gama jika ta “ Kema duk ‘Kulle ‘kullen da kika akai na nasani , hatta zuwa Wajan boka yan da kike akan kina san king na sani , shiyasa na fara huce haushi na akan amrah, kamar yadda nake kwana dake haka nake kwana da ita kamar matata, sannan tun wuri ki fara zuwa wajan Likita ke da karuwar ‘yar ‘yar uwarki sabida dukanku kuna da cuta me karya garkuwar jiki duk da dama Kema lokacin da na auro ki kin gama bin maza , sannan daga karshe ina miki albishir da cewa na dad’e da sakin ki saki uku, boyanka ce tace na cigaba da kwana dake a haka burina zai cika shiysa na ‘kyaleki kika zama karuwata”. Wannan shi ake kira da tashin hankalin da ba’a sa masa rana , ihu aunty ta saka ita kad’ai kafun itama ta fad’i kasa sumammiya , duk da halin azabar da uncle saleem yake ciki hakan be hanashi sakin dariya ba , ran king ba ‘karamin ‘baci yayi ba , be san lokacin da ya kwantar da tahee akan kujera ba tare da dora mata doguwar rigarsa, inda uncle saleem yake ya nufa gadan gadan, da iya duka ‘karfinsa king ya d’aga ya saukewa uncle saleem a fuska take a Wajan hanci da bakin sa ya ‘kara fashewa , a kausashe king ya soma magana “ magana kake akan wancan ‘kungiyar daku ? Yanxu me yayi muku saura ?” Ya fad’a yana nuna masa tvn da zaki ya kunna , gabaki d’aya hankalin kowa ya koma kan tvn hatta Ammey dake Susa maida kallanta tayi kan tvn, uncle saleem ya ganin abunda yake baruwa ya kurma ihu kamar ba na miji ba , bakomai ne yasashi shiga tashin hankali ba yan ‘kungiyarsu da aka kama , abun mamaki kuma gabaki d’ayansu manyan masu fad’a a jine da attajirai,ga kayan tsafinsu gabaki d’aya an ‘Kona , mutane da yawa sun taru akan sai anbasu mutanen su kashe su da kansu, a firgice Ammey ta bud’e baki zatayi magana bakinta ya karka ce ga hannun ta d’aya da ya lankwa’be kamar wacce bata da jini, babu Wanda be shiga rud’ani ba acikin falon, shima uncle saleem cikin azama ya zari bindigar dake jikin wani soja , take a Wajan ya harbe kansa , wani irin shure shure ya somayi abun tsoratar wa gabakinsa da ya soma futar da wani ‘bakin abu me wani wari, ya dad’e yana shure shuren kafun ya dena motsi gabaki d’aya , gawarsa kuma ta soma tsotsewa kamar Wanda ake tsotsewa Jini. Ammey ma da ta soma wari sai faman burgima take sabida wani irin azaba da take ji a jikinta, kurajen da suka fito Mata sai fashewa suke suna yin wari, da Sauri king ya bara umarnin afutar dasu daga wajan dan ba’karamin warin Ammey take ba kamar matacciyar ja’ba , gabaki d’aya familyn babu Wanda be shiga tashin hankali ba , babu Wanda zai ce tsoran Allah be shigeshi sosai ba musamman irin mutuwar da uncle saleem yayi ga yadda Ammey ta koma itama . Shiru abeey yayi sabida tashin hankali , Dady ne yayi ‘karfin yin magana “ ya kamata abar komai zuwa gobe tunda tare yayi sosai yanxu “, gabaki d’aya naam sukai da zancensa ita zahra tunda taga uncle saleem ya harbe kansa ta ‘buya a bayan yah sha’aban. Gabaki d’aya kowa nufar makwancinsa yayi , oumma hannun zahra kawai ta kama suka tafi, shima zoya da taheer suka nufi part d’insu shida small mom kamar ydda suka zo , sai alokacin aka yayya fawa aunty ruwa , azabure ta farka sai faman kuka take akan uncle saleem ya mayar da auransu tayi nagama. Shima king taheen sa ya d’auka ya bar part d’in gabaki d’aya . Yana zuwa part d’insu ma direct bedroom ya shiga, ko motsi tahee batayi, shinfid’ata yayi akan gadon su , kafun ya cire kayan jikinsa ya saka bathrub , itama taheen saida ya cire mata Komai na jikinta kafun ya d’aiko ruwa ya shafa mata akan fuska , saida yyi hakan sau biyu kafun ta saki ajiyar zuciya, da kuka ta farka shiyasa yayi saurin hugging d’inta “ it’s okay gani a kusa dake , ki dena kukan nan ya isa haka , okay ? “ kanta kawai ta gyad’a masa , be kuma cewa komai ba Sabida yadda ransa yake a da gule, d’aukar ta yayi suka shige toilet, ko da Suka yi Wanda kayan baccinsu suka saka kala d’ala babu Wanda ya nemi abinci a cikinsu, itama be neme taba sai ma hugging d’inta da yayi a jikinsa taya tapping bayanta , tafi 30 minutes kafun bacci ya d’auketa , sai da ya tabbatar baccin ya dauketa sosai kafun ya kwantar da ita agensa yana sauka daga kan gadon, zuciyarsa zafi take masa sosai ga idanuwansa da lokaci d’aya ya juye zuwa kalar ja, jijiyoyin kansa sosai suka fito rud’u rud’u ajikinsa, hannunsa biyu ya tusa cikin gashin kansa , shi kad’ai yasan rad’ad’in da yake ji cikin zuciyarsa. Dafashi da tahee tayi ne yasashi’ko’karin controlling kansa , sosai ta mike zaune tare da hugging d’insa, ahankali ta soma sosa masa gashin kansa kafun ta soma magana “ cry! Cry!kayi kuka ko rad’ad’in zuciyar ka zai ragu”, lumshe idanuwansa da sukayi ja king yayi da zai samu yayi kukan haka yake so, yadda take tapping d’in bayansa ne yashi wasu hawaye sun fara sakko masa , sosai shima yayi hugging d’inta , rana ta farko tsawan shekarun sa tun yana yaro , sai yau yaki kukan na zuwan masa , sosai ya rungumeta a jikin nata yana kuka ko zai samu zuciyarsa ta rage rad’ad’in da yake ji, kusan 10 minutes yana kukan kafin ya soma sauke ajiyar zuciya, gyara musu kwanci ya tahee tayi sosai tare da dora kansa akan kafadunta ahaka bacci ya d’aukesu bayan adduar da tahee tayi musu. A cikin gida ma kusan hakance ta faru da kowa da kowa , da kyar suka runtsa, Ammey kuwa a part d’inta aka kulle ta zuwa gobe . Washe gari tunda Suka je masallaci suka ji part d’in Ammey sai faman wari ke Tashi acikinsa irin warin ja’ban nan , umarni abeey da aduba me nene a Wajan , ana shiga aka ga Ammey duk ta kunbura babu alamar ko rai a tattare da ita ga wasu tsutsa da suke futo mata masu shegen wari, rai abace abbey yasa itama a d’auke masa gawarta a gida harsa dady ya taushesa akan babu kyau maida sharri da sharri, duk da abeey beso hakan ba amma ya kasa musawa aminin nasa , amma yace babu abunda ya had’asu dan haka babu wani dallah da zai musu, king ba sam duk dayya akai dashi akan ya sallace yace bazeyi ba sai Dady ne da kanshi ya bad’a umarnin Akira Wanda zasu yi musu kwanka. Sai alokacin suka ga babban tashin hankali dan gabaki d’aya an rasa Wanda zayyiwa su ammey Wanka Sabida wata iriyar ‘katuwar maciji da ya nannad’eta, ita kad’ai macijiyar sai faman saran jikin Ammey take , uncle Salem ma duk yadda akai akan za a yi masa wanka sai abun yaci tura musamman kawarsa da take da zafi kamar karwashi da an Watsa mata ruwa zai tsotse sabida zafin da tayi har hayaki take , sai da aka d’auko kusan mutane uku amma duk abu d’aya , macijiyar da ta nannad’e jikin Ammey ta ki bari hakan , shima jikin uncle saleem da yake da zafi ya ki bari a ta’basa , babu yadda za’ayi sai dai abunnesu a hakan. A hakan kuwa aka bunnesu batare da ansallace suba sai rami da aka ha’ka aka rufesu. INNALILLAHI WA’INNA ILAIHI RAJI’UN, ALLAH KA NESANTA MU DAYIN MUMMUNAN KARSHE , ALLAH KASA MUNA CIKIN RAHAMARKA ALFARMAN ANNABI MUHAMMAD( S.A.W). Menene anfanin zalinci,ka mutu ranar tashin Allah agaban ubangiji, me zakace masa akan al’ummar da ka cuta , Allah mun tuba , Allah muntuba😭😭. *****Duk wanda yaji labarin irin mutuwar da su ammey sukai sai jikinsu yayi sanyi ba kad’an ba , hatta manyan mutanan da suke tare da su ammey an wayi gari inda aka ajjesu ya kama da wuta gabaki d’ayan su babu Wanda yayi rai sabida yadda wutar ta’konasu gabaki d’ayansu. Gabaki d’aya wunin ranar kowa yana part d’insa babu Wanda ya ‘Kela part d’in junansu. Sannan abeey be bu’kaci ganawa da kowa ba har saida akai kwana uku da faruwar abu kafun ya tara kowa da kowa a falon kamar kwana uku da suka wuce , duk Wanda ka gani zakaga jikinsa yayi sanyi ba kad’an ba . Taro abeey ya bud’e da addua , kafun ya soma yin nasiha tare da fad’akarwa. Ya dad’e yana yin nasihar kafun shima dady ya d’ora nasa wa’azin. Suna zaune akai sallama cikin babban falon , da Sauri oumma ta juyo zuwa inda taji maganar, jin muryar da bazata ta’ba mantawa da ita ba , su Alhaji ismail ne suka shigo palourn sai momy da Mimi sai kuma junior da ke ri’ke da ita , gabaki d’ayansu zuba musu ido yan falon sukai musamman junior da suka fi ‘kurawa ido, yadda suka ga ya kwace hannunsa da gudu ya nufi cikin falon ne ya ‘kara d’aurewa kowa kai, inda tahee take ya nufa,lokacin tana gefen king, a tunaninta ita zai rungume sai kowa ya ga ya rungume king, cikin muryarsa ta yara ya fura “ I missed you dad ! Kace mun zaka zo shine baka zo ba kamun wayo ko?”, d’an hancinsa kawai king yaja lokacin da junior yayi king d’insa , da Sauri kuma junior ya juya wajan tahee da ta d’auke fuskarta ita a dole tayi fushi ga mamakin inda junior yasan babansa take , itama hugging d’inta yayi “ I love you mom! “, gabaki d’aya sai kowa ya zuba musu ido sun kasa magana , abbey yayi wa su uncle ismail iso cikin falourn suma , har yanxu kuma idanuwansa suna kan junior da yaji san yaran yashigeshi lokaci d’aya , kowa sai bunsa da kallo yake kwanin ban sha’awa, binsu da kallo junior yayi sai muna ya gaishesu gabaki d’aya kamar wani me hankali, idanuwansa da Suka sauka kan yah moh ya zaro kafun ya taho da gudu yana rungumeshi “ Big dady , na kamaka bazaka ‘kara guduwar mun ba “, shima yah moh rungume junior yayi abunda , dada ce ta kasa yin shiru ta furta “ kuyi mana bayani yadda zamu gane , ni sai nake ganin yarannan kamar tahanuni d’ina yana yaro”, murmushi yah moh ya saki kafun ya nuna mata junior “ dada wannan da kike gani jikankine d’an tahanuni d’inki ne ,” sai gabaki d’aya kowa ya zubawa su king ido cike da farin ciki, abbey murya har rawa take wajan furta “ d’an sa na cikinsa shida tahee?” Ynxu ma amsa musu yayi da eh, wani irin garin cikine ya kama family d’in kowa so yake ya d’aukesa , lokacin da kowa yaji sunansa ba ‘karamun farin ciki Sukai ba oumma har da kwallar ta , itama ummey saida tayi kuka “ yau Allah ya nuna mata jikanta , Aushe raban zataga nata jikin”, anan ne yah moh ya sanar dasu tun ‘batansa har zuwan tahee da haihuwar junior da kula dasu da familyn uncle ismail sukai, anan shima uncle Ismail yake sanar dasu yadda ya rabu da oumma har ya dawo nemansu ne gansu , da yadda yasamu tahee . Hajiya dada itama Tasha kuka wai taga d’an tahanuninta, ko yanxu ta muku zatayi farinciki. Lokacin da uncle Ismail yace zasu koma abbey yace babu inda zasuje yana da magana da su nan da sati d’aya , sannan alokacin ysa aka gyara musu ‘ban garan da zasu zauna , dan yace babu me tafiya yanzu sai an gama zumunci . AFTER ONE WEEK Junior ya zama d’an gari kuma d’an gata idan yau baya hannun ka kanninsa toh zaka gansa a hannun uncle d’insa,kowa sai nuna masa kauna yake , tsakanin su oumma da ummey kuwa wani irin zumunci ne ya shiga tsakaninsu su uku , oummey , momy , sai kuma oummansu tahee, idan ka gansu bazaka ta’bacewa ba ‘yan uwa bane , gabaki d’aya familyn sai suka had’e kansu, tahee , mimi sai zahra da suke kai d’aya suma sai suka had’e kansu kamar wasu yan uwa haka suke mu’a malarsu, su ihsan da Suka girmesu ma suma sun had’a Kansu su uku kamar wasu twins , ilham , sumayya da firdausi, momy ma da mamy suna ynzu suna zaman su cikin lapiya kamar ba kishiyoyi ba . Small mom da mahma suma ba’a magana , kullum tare zaku gansu , ga taheer da zoya ma da kowa yazama sanin sha’kuwarsu.Mazan ma gabaki d’aya sai suka had’e kansu, king , khaleed , sha’aban, yah moh, sai zaki da king ya sanar dasu amatsayin best friend d’inshi dan tun suna yara zaki yake tare da king, tabbas zaki ya cika d’an Halak na gaskiya Dan sosai a da king yake kwadasa amma kwata kwata duk tsawan lokacin da sukai tare be ta’baci masa Amana ba musamman zaki da ya kasance marayane shi, har kuka sai da yayi lokcin da king yace a wannan karan bazai ‘karayin aiki a ‘kar ‘kashinsa , duk da ad’a d’in ba da yaso haka zakine yace shi yafi jin dad’in aiki a ‘kar kashinsa. Iyaye kullum zaka ga suna tare kusan tare suke cin abincin rana da na dare , Abbey , Dady,uncle Ismail, uncle musaddiq ,a cikin sati d’ayan nan kullum zaka gansu a tare. Aunty ma ynxu gabaki d’aya ta zama abun tausayi duk da abbey yasa likita ya dinga kula da lapiyar ta , sosai tayi nadamar abunda tayiwa familyn sannan gabaki d’aya sai da taje ta nemi yafiyar kowa tare da neman alfarmar komawa gida , tayi jinyarta acan, babu Wanda ya musa mata hakan abeey yasa aka mayar da ita can gida tare da d’ora likitan da zai dunga dubata. Yau tun dasu abbey suka shiga falour suke tattaunawa duk da babu Wanda yasan abunda suke tattaunawar akai sai yan samarin gidan da suka umarci gani da kuma matan suma . Amma sun ce basa bu’katar iyayen mata da ‘ya’yansu Kawai xasu gana , sudai su ummey babu abunda suke musu sai dariya , mahmace me basu amsa idan tayi wari zasuji. Lokacin da gabaki d’aya suka had’u a falon uncle Ismail ne ya bud’e taro da adduar, kamar kullum akai salati ga annabi muhammad (S.A.W), kafun abeey ya fara maganar da ya had’asu, kallan khaleed da ilham yayi kafun ya soma magana “ kamar yadda kuka sani abubuwa da yawa sun faru mara dad’in ji amma sai dai mu god’ewa Allah(SW.T), sannan kuma kuyi hakuri da d’aga muku bikinku da akayi, kamar yadda akasa a lokacin baya satin da ya wuce za’a d’ora muku aure toh Insha Allahu, nan da kwana shid’a wato asabar ne zuwa za’a d’aura wa gabaki d’aya aure ,” da Sauri suka d’ago suka kalli abeey banda tahee da king , da suke musu dariya , Mimi, zahra , sumayya , firdausi, gabaki d’aya jiki ba ‘kwari suka amsa sa musu, “ kuna da Wanda yake tsayayye?” Ga baki d’ayansu shiru sukai sun kasa bashi amsa , sau biyu yana tanbayarsu amma sun kasa bashi amsa “, murmushi yayi kafin ya mayar da kallansa kan ‘yan mazan, tanbayar da yayiwa matan shi yayi musu, shima sau biyu yana musu tanbayar, d’an sosa kai sha’aban yayi kafun cikin girmamawa ya soma magana “ abbey ni ina da wacce nake amma ban fad’a mata ba har yanxu “, ashsha cewar dadyn zahra, “ wacece haka ? Dole muje mutanbayo maka ita “, kasa d’ago da kansa yayi Sabida kunyar dadyn zahra da yaji “ wacce ita ?” Uncle Ismail ya tanbaya , d’an sosa ‘ke yarsa yayi kafin ya furta “ zahrace “, wata iriyar kunya ce ta kama zahra sai tayi saurin sunkuyar da kanta ‘kasa ko motsi ta kasa yi, murmushi iyayen sukayi gabaki d’ayansu , babu Wanda yayi magana aciki kafin abbey ya ‘karacewa sai kuma wa?d’an d’agowa yah moh yayi kafun ya furta “ Abeey ni fa ina da mata tuntuni” , dariya ce taso kwacewa tahee dan ta ganosa, sai da king shima ya harareta, kamar wani mara gaskiya yah moh shima ya furta “ abeey mimi ce “ , itama Mimi da Sauri ta sunkuyar da fuskarta, nan ma su abeey murmushin su na manya suka saki kafin ya abbey ya ‘kara furta sai kuma wa? Babu Wanda ya ‘kara magana a cikinsu , king ne ya kalli abbey , “ abbey saura zaki, “ da Sauri zaki ya kallesa kafun ya sunkuyar da kansa kasa “ muhammad wacce kakeso a ciki? “ kasa magana zaki yayi sai ma sunkuyar da kansa kasa da yayi sai da abbey ya kara nanata masa maganar kafun ya furta “ sumayyace “ gabaki d’aya iyayen had’a baki Sukai wajan furta Masha Allah, kafun abbey ya kalli firdausi “ jiya iyayen doctor anwar sunzo mun magana akan aurenki? Hope bazaku bamu kunya ba ?” Sun matan sunkuyar da kansu sukai , Allah yayi muku albarka cewar dady da uncle musaddiq, kafun asalla mesu, suna fita sha’aban ya ce zai yi magana da zahra, mimi ma yah moh ne ya kirata, zaki kasa yiwa sumayya magana yayi , sai da king ya had’e masa rai dan gani yake kamar bazata so shiba , a lokacin itama firdaushi doctor anwar ya kirata, daman su khaleed tuni suka wuce , king ma babynsa ya ja , suna shiga part d’insu ya d’auke abarsa. Bayan kwana uku wace irin soyayya ce ta shiga tsakanin su duk lokacin da basa tare to tabbas suna na nike da waya a kunnansu , biki ya kama saura 3 days a yau ne kuma gabaki d’aya suka kama hanyar zuwa bunkure , koda sukaje sai da tahee da taheer suka sha mamakin canzawar kaka ta bawa Dan ba ‘karamin saurin suka gani ba , gidan ma sosai aka ‘kara masa girma musamman makociyarsu data rasu d’an ya siyar musu da gidan shiyasa gidan ya ‘kara girma sosai , anan ma sai da su kaka tabawa suka nemi yafiyar du tahee , su dada an samu ‘kawa sai faman hirarsu suke su uku, da hajiya kakarsu zahra, suna zaune gabaki d’ayansu wata gurguwar almajiran tazo musu gidan gabaki d’aya abar tausayi matar , tun daga waje da ta manyan motocin da suka tsaya a cikin gidan take ta rusar kuka sai da zaki yace abarta ta shigo cikin gidan kafun sojoji su ‘kyaleta, tana shiga ta fara kuka gabaki d’aya ta kasa magana har saida abbey yayi magana “baiwar Allah lapiya ? Kike wannan kukan ?” Yanxu ma kuka take sosai saida ta d’ago sosai kafun oumma tace Dije ? Dije tana d’agowa taga oumma , yadda ta ga oumma tayi fess abun ta ga Hutu da ta samu ta ‘kara sakin wani kukan tana neman yafiyarsu kafun ta fara basu labarin abunda ya faru da ita . Aushe lokacin da ta bar gidan burni suka shiga ita da ka warta , basu tsaya a ko ina va sai a gidan karuwai dage Garin borno, sosai harka tayiwa Dije ta dad’i Sabida yadda take samun kudi ko damuwa da sa’bawa Allah da take batayi , haka taci gaba da rayuwarta cikin bariki duk wacce ta samu labarin zataje wajan boka, itace gaba gaba wajan kai su, sosai ta samu kudin karuwancinta , ranar da zasuje Niger a hanyar su ta zuwa wajan wani boka yan fashi suka tare musu hanya , gabaki d’aya dukuyarsu saida Suka kwace sannan sukayi musu wani mugun fyad’e mara kyan gani, sauran yan sharholiyarta gabaki d’aya sun mutu sai ita da suka sarewa ‘kafa,gabaki d’aya Dije talaucewa tayi ta koma bata abincin da zataci ma gagararta yake ga cutar cancer da akace tana dasu akan nonuwanta, hakan ya ja aka yanke Mata su gabaki d’aya guda biyu,gashi bata da kudin siyar magani, kusan 2 biyu da suka wuce ta fad’a mummunan yanayinnan sai ayanxu da wani ya temaka ya sata ciki vot din mota , ya shigo da ita garin Kano, duk Wanda yaga Dije yanzu tabbas yasan ba’karamin shiga tashin hankali ta fad’a ba , sai kuka take tana neman tafiyarsu , gabaki d’aya kowa yace ya yafe mata duk da irin mugancin da ta shuka musu, suna cikin wannan yanayin ne wani yaro ya shigo da gudu wai ga wasu yara sun kawo bintalo, samarin mazan ne suka fita , ganin yadda aka taru sosai yasa sojoji korar mutane, dogon bugun da yake a shinfid’e zaki ya bud’e take wata gawar mace ta fad’o daga ciki, ga idanuwanta da zuciyar ta da yake a bud’e da Alama ciresu akai daga gangan jikinta. Lokcin da Dije taga kawar bintalo fad’uwa tayi a sume tunda ta farfad’o kuma take kuka akan bintalo ta yafe mata ita tasaka ta cikin wannan mummunar rayuwar, gabaki d’aya babu Wanda be tausaya mata ba duk da irin mugancin da ta tabka ko wa sai alawadai yake da hali irin nata. A haka aka Samu aka sallace bintalo jikin lunkafanin duk Jini ya ‘batashi. Ko da su king zasu koma gida sai da suka barmusu kudi masu mugun yawa , su dada har da karbar number kaka tabawa. Suma su kaka tabawa basu guje Dije ba kamar yadda oumma ta nuna musu Halacci haka suka bawa Dije d’aki guda itama . Sosai ta zama abar tausayi dan ba ‘karamin nadama ta karashiga ba musamman gawar bintalo da tagani. ✨✨✨✨✨✨✨✨ Yau ya kama asabar kuma ayau ne dubban jama’a suka shaida d’aurin auren Mohammad zayed Al-nahyan da maryam Ismail, sai auran sha’aban Ahmad da amaryarsa zahra kabeer, sai khaleed kabeer da ilham musaddiq, sumayya musaddiq da angonta Mohammad Mohammed, sai kuma amare na karshe firdausi musaddiq da angonta Dr anwar Auwal. Abun burgewa da mamaki duk irin dukiyar da Allah ya basu basuyi wani bidi’a ba acewarsu Albarkar auren suke bu’kata dukda haka sai da su abbey suka had’a msu gagarumar walima tare da kyaututtuka. AFTER 3 YEARS gabaki d’aya familyn su ‘kara haduwa musamman yanxu da suka ‘kara yawa , acikin shekara ukun nan Allah ya ‘kara albarkar tahee da samun twins mace da na miji, macen ansa mata suhaima wato taci sunan ummey ana kiranta da Baby Fayha, namijin kuma da yaci sunan zayed ana kiran sa da Aahil, ynxu junior kuma ya Xama yaya dan yace baby’s din kannensa su dai na ce masa junior, su mimi ma sun Haifi ‘yar su guda d’aya me sunan mahma wato zarmin ana ce mata Haida , sai zahra da ta haihu itama mace aka sa mata sunan dada ana kiranta da Afra. Zaki ma sun haihu d’a na miji Yasa sunan king wato tahnoon amma ana ce masa little king, shiyasa duk lokcin da kagansu zaka gansu a tare , a yanxu ne kuma firdausi da ilham suke d’auke da ciki suma haihuwa yau ko gobe . Cikin yan shekarun nan kuma taheer ya cika 25 years shiyasa shima akace yana karasa services dinsa za ayi musu aure shida zoyan sa. Haka rayuwar ahalin nan ta cigaba da tafiya cikin farinciki da ‘kaunar juna, lokaci zuwa lokaci kuma suna had’a family meeting inda gabaki d’aya familyn za a had’u koda kuwa baka nan zakayi settling lokacinka. **** wasu kyawawan yara ne maza biyu sai mata biyu da suke faman yin gudu, matan sai faman kwalla kiran ammu suke cikin hausarsu da bata fitowa sosai , kofar dana ga an bud’e ne yasa na mayar da hankali na kan kofar, wata kyakkyawar budurwace ta fito daga cikin dakin idanuwanta sanye da farin glass , sosai na zaro idanuwana lokacin da naga budurwar, ba kowa bace face tahee da Hutu da kwanciyar hankali ya ‘kara mata wani irin kyau da kwarjini kallan yaran tayi cikin had’e rai , Fayda , Haida ba na hanaku yin guduba, da Sauri suka had’a baki cikin hausarsu “ ammu su yaya Aahil da yaya small king ne suka biyo mu” Daidai lokacin da mazan suma suka ‘karaso kyawawa dasu , suma ba wani Hausa suka iya sosai ba Amma ahaka suke furta “ ammu baza jin maganane “ hararar su tahee tayi , “ su wanne suka taba mun littles dina ?” Da Sauri suka juya kyakkyawan guy din da suka gani ne suka fara ihu da nufarsa a guje suka rungumeshi bakowa bane face king da ya ‘kara kyau har wani ‘kiba da haske sai da yayi, ledojin hannunsa ya mi’ka musu, suna karba suka saka gudu tare da barin falon girgiza kai king yayi kafun ya kalli tahee da take kunbura fuska daman fushi take dashi , yana zuwa ya d’auke ta tare da king d’in goshinta”baby na tana fushi dani? But nasan zata dena “ yana shiga d’aki ya kwantar da ita ya soma yi mata cakulkuli tana dariya, shima dariyr ya somayi kafun lokaci d’aya su canza alakar jakulkulun zuwa wani abu daban. ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH! ALHAMDULILLAH!!! Komai yayi farko zai yi ‘karshe anan na kawo karshen book dina me suna GIDAN AUNTY. Ina mika Godiya ta ga Allah SWT da ya kawoni wannan lokacin da rai da lapiya , sannan ina godewa duka my people na gidan aunty da kuke biye dani nagode nagode ! Masoyiya 😍😍 all the best a cikin Romeo Boss bature ( kurkukun kaddara ). Mom sajeeda Mom sayyid Ummu bulun😹 Aunty sadiya Mom sayyid Auta da saura ku da bazaku lissafuba , na gode nagode nagode sosai da sosai . SEE YOU ALL ON MY NEXT NOVEL ME SUNA IBTISSAM 😍😍🥺❤️. Heart you all.