An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MATSATSUBI 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part A ***************************************** Bayan iskar KUNDIN TSATSUBA ta gama zuƙe su Jafar, sun faɗa cikin shafi na goma sha biyu, sai suka tsinci kan su a tsakiyar wani makeken gari mai manya-manyan gine-gine iri-iri na zamani. Wasu gidajen an gina su ne da dutse zallah wasu da ƙarfe wasu kuma da itatuwa. Duk ginin da ka duba sai ka kamu da sha'awarsa saboda tsananin kyawunsa da irin hikimar da aka yi wajen gina shi. Dirar su Jafar ke da wuya a cikin garin sai ga jama'a na ta ɓulɓulowa daga cikin gidajensu, kai ka ce ramukan tururuwa ne ya bude suka yi fitar burgu. Kafin ƙiftawar ido miliyoyin jama'ar sun kewaye su Jafar suka zamo tamkar mitsitsin tsibiri a tsakiyar teku, koda su Jatar suka dubi jama'ar garin sai suka ga ashe halittar jikinsu wata iri ce, ba irin ta bila'adama ba sak. Kowannensu na da zagayayyen ƙaho guda biyu a gefen kunnuwansu, tamkar lauje,kunnuwansu fankama-fankama ne, haka kuma hancinsu dogaye ne sirara tamkar sillan kara, amma sauran abubuwan jikin na su irin na mutane ne sosai,babu wani bambanci. Mazan su da matan su na ɗauke da makamai kala-kala. Wasu sun rike takubba, wasu gudumomi manya-manya, wasu masu, kowannansu sai muzurai yake kamar su cinye su Jafar ɗanyu. A wannan lokaci tuni jikin Yelisa, Mashrila da Gulzum ya fara karkarwa. Jafar ne ka dai bai tsorata ba, domin tsayawa yai ƙyam ya riƙe ƙugu yana kallon mutanen kawai. Ba zato ba tsammani sai ga wani ƙaramin yaro wanda bai wuce shekara tara ba, ya fito daga cikin mutane ya iso gaban su Jafar akan sa akwai hular karfe irin ta sarakai. Cikin ɗagawa da nuna isa ya dubi su Jafar yace, "Ba ma maraba da baƙi a garin nan, in zaku iya komawa inda kuka fito ku koma don bamu yarda da ku ba." Ko da jin wannan batu, sai Jafar ya dubi yaron cikin mamaki yace, "Me ya sa ba ku yarda da mu ba?" Yaron ya ce, "Saboda za ku iya zama irin mutanen Galbasa." "Waye kuma Galbasa, mene ne tsakaninku da shi?" Ko da jin wannan tambaya sai yaron ya matso kusa da Jafar ya tsikare shi da tsinin farcen hannunsa mai kama da allura. Jafar ya ƙwala ihu saboda jin zafin tsikarin, domin har sai da jini ya fito. Ƙaramin yaron ya bushe da dariya, sannan ya tsikari Yelisa, Mashrila da Gulzum, kamar yadda ya yiwa Jafar suma kowannensu ya yi ihu,jini ya zuba a jikinsu. Nan take gaba dayan jama'ar garn suka bushe da dariya suna cewa, "Ba su ba ne, ba su bane." Lokaci guda ƙaramin yaron nan ya ɗaga hannu sai kowa ya shiru,wurin ya yi tsit, kamar babu mai numfashi a wajeu, sannan yace, "Ni sunana sarki Azbir, gaba ɗaya jama'ar garin nan a ƙarƙashin mulkina suke.Yaku waɗannan baƙi ku biyo ni izuwa fadata domin mu zauna mu tattauna na sanar da ku halaiyarmu, rayuwarmu da kuma masifar da ke adddabarmu, ko za ku iya kawo mana ƙarshen ta." Nan take ƙaramin yaron ya juya ya yi gaba jama'a suka dare hanya ta samu ya keta ta tsakiyarsu. Ba tare da wata fargaba ba su Jafar suka bi shi a baya. Suna tafe suna kalle-kalle. Nan fa suka fara ganin abubuwan al'ajabi iri-iri. Abin da suka fara gani shi ne wata ƙatuwar mace mai nono goma sha biyu a zaune tana shayar da jarirai goma sha biyu, a cikin wata rumfar kasuwa, sannan suka ga wani gabjejen mutum ya goyo jaki, jakin na riƙe da wata igiya a bakinsa wadda ta sarƙale wuyan mutumin. Koda ganin sa sai Jafar ya bushe da dariya yace, "Tabɗi jan yau kuma garin da dabbobi ke mayar da mutane abin hawansu muka zo, kai amma fa an ci mutuncin mutuntaka a wajen nan......" Kafin Jafar ya gama rufe bakinsa sai suka ga wani mutum a kwaɓe tsirara kare na zane shi da wata tsumagiya. A can gefe guda kuma sai suka ga birirrika na tallan ya'yan itatuwa bisa faranti,mutane na siya, suna ba su kuɗi, har ma sai sun ƙirga kuɗin, sannan suke bayar da kayan. Nan fa su Jafar suka daɗa cika da tsananin mamaki. Yayin da suka ƙara gaba kuma sai suka ga curin dinare, lu'u-lu'u, jauhar da demon tsubi-tsubi kasuwar boka,yara na wasa akai wani ma saika ga dabbobi na yin kashi da fitsari akai, irin n kuɗin da mutanen garin ke amfani da su kuwa ba komai bane face guntattakin fatar damisa. Haka dai su Jafar suka yi ta ganin abubuwa al'ajabi iri-iri har suka isa wata tangamemiyar fada mai tsananin ƙawatuwa,komai ka gani a cikin gadar an yi shine da dangin su lu'u lu'u,hatta shimfiɗun fadar kuwa. A inda aka ajiye karagar mulki kuwa bisa wani gilashi ne mai kaurin gaske a cikinsa ruwa ne da kifaye iri-iri,manya da ƙanana suna ta zilliya, idan mutum bai lura da kyau ba, sai ya yi zaton ƙaramin teku ne a wajen domin tuni su Jafar sun fara tattare rigunansu suna zaton ta cikin ruwan sarkin zai ratsa da su,amma bisa mamaki sai suka ga ya taka fadamar da ƙafafuwansa yana tafiya akai har ya isa kan karagar mulkin ya zauna a binsa. Take ya yi musu nuni ga wasu kujeru da ke kewaye da karagar ta sa. Cikin alamun ƙauyanci su Jafar suka ƙarasa suka zazzauna akan kujerun,cikin ɗari-ɗari, su Jafar suka yi ta kalle-kalle don gani suke kamar a ko yaushe gilashin da suke kai zai iya ruftawa da su. Sarki Azbir ya dube su ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Yaku baƙina ku kwantar da hankalin ku domin ko girgizar ƙasa za'a yi wannan fada tawa ba za ta ruguje ba, wannan gilashin da kuke kai ba gilashi bane,ƙarfen deman ne zalla. Kamar yadda na gaya muku a baya cewa ni da jama'ata muna cikin mummunan tashin hankali sakamakon farmakin jama'ar Galbasa. Galbasa wani tsohon maye ne wanda ya shahara a zamaninsa, don sai da ta kai ta kawo cewa ya mamaye dukkanin ƙasashen da ke nahiyarsa. Galbasa ba ya cin komai baya shan komai face jinin bil'adama. Babu wani makami da ke iya saran jikinsa kuma yana iya juya siffarsa izuwa ga kowanne irin siffa,duk mutumin da Galbasa ya zuƙi jininsa, shi kenan wannan mutum ya zama maye, kamarsa kuma zai iya yin duk abin da Galbasa zai yi na rikiɗa da rashin saruwa da makami. Kai komai kaifin makami da tsininsa baya huda jikin mutanen Galbasa, idan ma kuwa ya huda sun sai ka ga sun zare shi sun yar kuma in da ya huje a jikin nasu sai ya koma ya manne tamkar ba a taba sukar wajen ba. Suna tashi sama kamar tsuntsaye, kuma mutum ɗaya daga cikinsu na iya surar mutum goma ya tafi da su izuwa can fadar Galbasa inda za'a shanye jininsu, su kan zo mana nan bayan kowanne mako guda. Da saukar su za su fara yi mana ɓarna su hau shan jinin mutanenmu, duk wanda suka sha jininsa ya zama na su, sai ka ga shima ya afkawa mutanenmu, sai sun sha jinin mutum dubu sannan su ɗebi mutum hamsin su tafi da su. Babbar illar waɗannan mutane ita ce yawan jinin mutanen da suka sha shi ke ƙara musu girma, karfi da tsawon rai, wanda ya fi kowa shan jini a cikinsu yafi kowa girma, shi yasa har kullum ƙoƙarin kowanne shi ne ya sha jinin mutane da yawa." Yayin da sarki Azbir ya zo nan a zancen sa sai Mashrila ta tari numfashinsa tace, "Yanzu kenan kana nufin cewa Galbasa yafi kowa girma da ƙarfi a cikin mutanensa?" "Ƙwarai kuwa domin a lissafi yanzu Galbasa ya sha jinin bil'adama miliyan dubu casa'in daidai,idan aka bari ya cike dubu ɗari sai gaba ɗayan mutanen duniya sun zama irinsa. Yau saura kwana uku jama'ar Galbasa su kawo mana farmaki, shin kuna da wata hikima da za ku iya ceton rayuwarmu?" Sarki Azbir ya tambaya yana mai duban fuskokin su Jafar,ɗaya bayan ɗaya. Jafar yace, "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa me rai baya rasa motsi,lallai zamu yi tunanin mafita kafin kwana ukun, amma ina son ka sanar da ni wai shin mutum na wane suka kawo wannan farmakin?" Sarki Azbir yace, "Ai mutum biyar ne kacal kuma mata ne,waɗanda masifarsu ta wuce iyakar tunaninku." Koda jin wannan batu sai Gulzum ya yı tsaki yace, "Yanzu saboda abin kunya a ce mata biyar kacal suke addabar duk miliyoyin jama'ar garin nan." Cikin fusata Azbir ya dubi Gulzum ya daka masa tsawa, yace, "Kai shashasha ka bar ganin kai aljani ne, kai tsammanin za ka iya kafsawa da su ne? Na rantse da girman wannan karaga tawa idan aka tura mace ɗaya daga cikin mutanen Galbasa za ta iya hallaka gaba ɗayan aljanun da ke duniyarku." Azbir na gama faɗin haka ya juya ya dubi wata doguwar kuyanga da ke tsaye a gefen hagunsa yace, "Yake Marzul ki kai waɗannan baƙi masauƙinsu, domin su hutu in ya so gobe mu ci gaba da tattaumawa." Nan take kuyanga Marzul ta wuce gaba su Jafar suka bita a baya, har izuwa wani ɓangare daban, na wannan fada. Inda suka tarar da wani ƙasaitaccen gini mai tarin ɗakuna bila adadin, domin ko a kwana uku mutum bai isa ya ƙirga yawan su ba. Insha'Allahu zamu cigaba nan ba da jimawa ba. Fatan alheriMatsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part B A jiya mun dakata:- "Nan take kuyanga Marzul ta wuce gaba su Jafar suka bita a baya, har izuwa wani ɓangare daban, na wannan fada. Inda suka tarar da wani ƙasaitaccen gini mai tarin ɗakuna bila adadin, domin ko a kwana uku mutum bai isa ya ƙirga yawan su ba." ######## Kai tsaye Marzul ta shige da su cikin ɗaya daga cikin ɗakunan. Da shigarsu suka cika da mamaki domin kawai sun tsinci kansu ne a cikin wani ƙaton falo wanda kiris ya rage girmansa ya ninka na fadar sarki Azbir. Duk wani abu na jin daɗin rayuwa akwai shi a cikin falon. Koda ganin haka sai Mashrila ta dubi kuyanga Marzul tace, "Shin idan na yi miki tambaya za ki ba ni amsa?" Marzul ta yi murmushi tace, "Faɗi tambayarki amfanina kenan a gareku." "Shin duk sauran ɗakunan da muka gani a waje haka suke da girma kamar wannan da muke ciki yanzu?" "Ƙwarai kuwa,kuma sun fi wannan ɗin ma girma, abin bi da bi ne, ma'ana na gaba ya linka na baya har izuwa na ƙarshe." Koda jin haka sai Mashrila da su Jafar suka dubi junansu cikin tsananin mamaki kowa ya jinjina kai. Yelisa tace, "Nima ga tawa tambayar in ba zaki damu ba." Marzul ta sake yin murmushi a karo na biyu ta ce, "Ai na faɗa muku amfanina kenan a tare da ku duk abin da ya shige muku duhu ni ce zan wayar muku da kai, face akan abin da ya wuce sanina saidai sarki da kansa." Yelisa tace, "Yake Marzul kin ga dai kusan halittar jikinku da tamu iri ɗaya ce bambancin kawai shine kuna da ƙaho a ka bamu da shi, kuma kuna manyan kunnuwa da dogayen hanci, shi ne dama can haka kuke ko kuwa wata masifar ce ta sauya muku kamanni?" Marzul tace, "Haƙiƙa wannan tambayar taki tana buƙatar dogon bayani a ƙalla muyi kwana goma ina baku labari,zai fi kyau ku bari mu ga abinda zai faru nan da kwana uku,idan mun tsira da rayukan mu daga sharrin mutanen Galbasa,zan baku labarin na ɗauki alƙawari akan hakan,yanzu sai ku zauna ku ci, ku sha idan da mai buƙatar yin wanka ga kewaye can." Marzul ta yi musu nuni da wata ƙofa ta zinare, sannan ta fice ta bar su a tsaitsaye sun yi cirko-cirko suna masu kalle-kalle da al'ajabin wannan wuri. Kawai sai Gulzum ya dubi Jafar yace, "To sarkin kankanba ɗazu ka ce za ka yi tunani a kan hanyar da za'a samu nasara akan mutanen Galbasa? Shin ka yi tunanin ne ko kuwa sai nan gaba?" Jafar ya dubi Gulzum cikin yanayın raini yace, "Wannan tambayar ai ba taka ba ce, domin wanda ya yi min ita da farko shi ya cancanta ya san amsarta." Koda faɗin haka sai Gulzum ya fusata, ya yunƙura da nufin ya cafko Jafar da yatsu biyu, amma sai ya haɗa fuska da Yelisa ya ga ta daka masa harara. Bisa dole Gulzum ya maida nufinsa zuci,cikin alamun takaici ya ja da baya ya koma gefe guda yayi tagumi, kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa. Yelisa ta matsa daf da Jafar suka fuskanci juna sosai, ta yi tattausan murmushi a gare shi tace, "Ya kai masoyina shin wace dabara ka ke ganin zamu yi mu tsira daga sharrin waɗannan mutane da aka ce za su zo nan da kwana biyu?" Jafar ya yi shiru bai ce komai ba. Sannan ya dubi Mashrila wacce ke tsaye a gefe guda zuciyarta cike da kishi saboda ganin irin kallon da Yelisa ke yi masa ya ce, "Yake Mashrila shin kina da wata dabara ko wani tunani akan mutanen Galbasa? Maganar gaskiya fa ni har yanzu ban tuno wata dabara ba." Koda jin wannan tambaya sai Mashrila ta tuntsire da dariya,sannan ta haɗe fuska tace, "Ni kam ina da dabara amma sai idan kai da Yelisa da Gulzum kun gaza sannan zan faɗi tawa." Caraf sai Gulzum yace, "Ni kam kadama ku sani a cikin wannan magana, ku na ji fa ɗazu sarki Azbir ya ce ɗaya daga cikin mutanen Galbasn zai iya hallaka gaba ɗaya aljanun garinmu,ai kuwa kunga kenan ba ni da wata dabara akan su." Jafar ya dubi Yelisa yace, "Ke kuma fa me za ki iya cewa?" Yelisa ta yi shiru tana tunani, har tsawon ɗan lokaci, sannan ta ɗaga kai ta dubi Jafar cikin alamun karayar zuciya ta ce, ''Gaskiya tunanina ya ƙare na kasa gano mafita." Jafar ya sake duban Mashrila yace, "Na dawo gareki, ki sani cewa nima fa bani da wata dabara don haka mun baki wuƙa da nama." Mashrila ta ƙyalƙyale da dariya, sannan ta juya baya tayi tafiya taku uku cikin ƙasaita da yarda da kai,sannan ta waigo ta fuskance su su uku tace, "Ba zan faɗi hikima ta ba sai gobe a fadar sarki Azbir kuma bisa sharaɗi guda." Cikin fushi Yelisa tace, "Mene ne sharɗin ki?" Mashrila ta yi murmushi, tace, "Sharaɗina shi ne ba zan faɗi hikima ta ba har sai idan ku ukun nan kun amince cewa idan har hikimar tawa ta yi nasara zan zama shugabarku a cikin tafiyarmu ya kasance za ku dunga bin umarnina, har mu gama karance sauran shafükan KUNDIN TSATSUBA." Koda jin haka sai Yelisa ta kurma ihu, cikin fushi ta ce, "Ƙaryar ki ta sha ƙarya yarinya, ki dube ni da kyau ki sani cewa ba ki fini kyau ba, kuma ba ki fini shekaru ba, ya za'a yi na yarda ki zama shugabata mai bani umarni, kuma in ban dama tsaurin ido da rashin kunya ya za ki dubi Jafar da Gulzum ki ce kin zama shugabarsu alhalin ko a haihuwar tumaki baki isa ki zama tattaɓa kunnen Gulzum ba." Wannan furuci ba ƙaramin fusata Mashrila ya yi ba, don haka sai suka fara kace-nace kafin Jafar ya ankara tuni Yelisa da Mashrila sun kaure da faɗa. Nan fa suka hau bugun juna, suka hau kokowa da ƙyar Jafar ya sami damar raba su ya tsaya a tsakaninsu, shi kuwa Gulzum abin ya bashi dariya kawai sai ya hau ƙyaƙƙyatawa har sai da Yelisa ta daka masa harara, sannan ya yi tsit, kamar wanda ruwa ya cinye. Jafar ya dubi Mashrila da Yelisa yace, ''Abinda nake so da ku shi ne ku bar wannan gardama taku izuwa gobe babu mai warwareta face sarki Azbir." "Ƙwarai kuwa." Gulzum ne ya faɗi, yana muzurai. Nan take Jafar ya tafi kan wata shimfiɗa ya kwanta,kawai sai Yelisa ta je kusa da shi ta kwanta,kawai sai itama Mashrila sai ta a kwanta a bayansa, koda ganin haka sai Yelisa ta ƙara fusata ta mike wuf da shirin ta cakumi Mashrila,cikin zafin nama Jafar ya ruƙota ya ce, "Bana son ɗaya daga cikinku ta kwanta kusa da ni, don haka sai duk ku sauya makwanci." Cikin alamun borin kunya da fushi kowacce ta miƙe ta je ta kwanta a waje dabam. Kashe gari da hantsi su Jafar suka ƙara hallara a fadar sarki Azbir inda suka iske fadar ta cika maƙil da gaba ɗayan mutanen garin. Al'amarin da ya matuƙar ɗaure musu kai kenan suka shiga tunanin dalilin taruwar jama'ar haka. Haka kuma sai suka ga an ajiye wani dogon kejin ƙarfe a tsakiyar fadar, A can karshen saman kejin an rataye wata takobi tana reto. Ganin wannan keji ma ya ƙara jefa su Jafar cikin jimami, tun kafin su ƙarasa gaban sarki Azbir sai suka ga ya miƙe ya tare su yana mai murmushi. Kafin ɗaya ya buɗi baki ya ce wani abu,sai Azbir ya tari numfashinsu yace, "Yaku waɗannan baƙi namu masu albarka kuyi sani cewa duk abinda ya faru a tsakaninku jiya da daddare mun gani don haka yanzu ba tare da ɓata lokaci ba ina son na warware gardamar da ke tsakanin Yelisa da Mashrila, don kowa ma ya san matsayinsa. Ku yi duba izuwa ga wannan keji mai tsawo, ina son Yelisa da Mashrila su shiga cikin wannan keji sannan su kulle ƙofar daga ciki, duk wadda ta sami nasarar hawa har can saman kejin ta ɗauko takobin da ke rataye, ita ce ta yi galaba bisa gardamarsu." Yayin da sarki Azbir ya zo nan a zancensa,sai Jafar ya dube shi cikin yanayin al'ajabi yace, "Ya kai wannan sarki ya aka yi kuka ga abin da ya faru tsakanin Yelisa da Mashrila jiya da daddare alhalin bakwa tare da mu, asalima a cikin ɗaki muke a kulle mu huɗu kacal?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Azbir yayi murmushi, ya ce, ''Yakai Jafar ka yi sani cewa a halin yanzu bamu da lokaci na zama yin bayani face mun ga mun sami mafita bisa masifar da ke tunkarar mu nan da kwana biyu, ka yi haƙuri za ka ji abubuwan al'ajabi idan har kai da yan'uwanka kun sami nasarar yi mana maganin mutanen Galbasa." Yana gama fadin haka sai ya dubi Yelisa da Mashrila ya ce, "Ku muke jira sai ku shiga cikin kejin domin kuna ɓata mana lokaci." Yelisa, Mashrila suka dubi kejin wanda tsawonsa ya kai zira'i ɗari, sannan suka dubi junansu sai kowacce jikinta ya kama ƙyarma. Koda suka dubi Jafar ya fuskanci sun karaya sai ya yi murmushi a gare su yace, "Nasararku itra ce karin matsayinku a wajena." Yayin da suka ji wannan furuci sai kowaccen su ta ji ƙwarin gwiwa tare da rashin tsoro don tsananin kishin ƙaunarsa, domin su a zaton su yana nufin cewa duk wadda tayi nasara itace zata samu soyayyarsa. Cikin hanzari suka ruga suka shiga cikin kejin suka rufe ƙofar. Kafin Mashrila ta yunƙura Yelisa takama kejin ta fara hawa tamkar biri akan bishiya, cikin zafin nama Mashrila ta daka tsalle ta kama ƙafar Yelisa da hannu ɗaya sannan ta riƙe kejin da hannu guda ta fara ƙoƙarin finciko ƙafar Yelisa don ta jehota ƙasa. Yelisa ta ƙanƙame ƙarfen kejın da hannayenta biyu,iya ƙarfinta.(😅😅😅) Nan ta fadar ta ruɗe da shewar jama'a. Masu goyon bayan Yelisa na yi, masu goyon bayan Mashrila nayi,kai wasu ma sai suka fara caca, kowa ya zaɓi gwaninsa. Gulzum ya matso kusa da Jafar yace, "Kai shegen duniya, amma fa ka yi tsiya yanzu duk saboda kai ake wannan tataɓurzar, yanzu a ganinka wacece za ta yi nasara?" Jafar ya dubi Gulzum ya yi masa murmushi a karo na farko tun sa'adda suka haɗu yace, "Babu wadda za tayi nasara sai mai rabo." Gulzum ya yi dariya, sannan yace, "To wa ka fiso ta samu nasara?" "Duk su biyun nake so su sami nasara,amma in san samu ne a yanzu nafi ƙaunar Mashrila ta samu nasara." Koda jin haka sai Gulzum ya turɓune fuska,ya ce, "Amma baka da mutunci yanzu duk irin son da maigidata Yelisa ta nuna maka a baya da irin taimakon da ta yi maka har ka mallaki KUNDIN TSATSUBA, duk ka manta har ka yi watsi da ita kafi son wacce ka gani daga baya a cikin halin wahalar da muka fara sha tare, tun kafin mu haɗu da ita." Koda jin haka sai Jafar ya turɓune fuska, yace, "Kai Gulzum ɗan baƙin ciki ne kai, inda ka san dalilin da ya sa na fi son Mashrila ta ci wannan gasa yanzu da baka fadi haka ba." Cikin tsananin fushi Gulzum ya dunƙule hannunsa ya ɗaga sama da niyyar ya daki Jafar, kawai kuma sai ya fasa, ya kama huci da ciza leɓe, cikin tsananin fushi. Shi kuwa Jafar ko gizau bai yi ba. Jafar ya yi murmushi ya kau da kai ga barin kallon Gulzum yana mai cewa, "Me ya hana ka tatsice ni, ai da ka yi nadama irin wacce baka taɓa yin kamarta ba." Duk da cewa Gulzum na cikin tsananin fushi bai san sa'adda da dariya ta ƙwace masa ba, saboda mamakin wannan batu na Jafar. Ba wani abu ba ne ya bashi mamaki face wai shin nadamar me zai yi dan ya kashe wannan banzan Jafar? Wanda ba zai iya tsinana musu komai a cikin wannan tafiya ba. Asalima shi ne ya jefa su a cikin masifar KUNDIN TSATSUBA. Kuma duk bala'in da șuka shiga Jafar baya iya tare musu komai face ya ƙara janyo musu bala'in. Gulzum ya ƙudurce a ransa cewa duk ranar da suka gama karanta KUNDIN TSATSUBA, sai ya tambayi Jafar wai shin wace nadama zai yi don ya kashe shi? "Ka ci albarkacin uwagidana Yelisa na san idan na kashe ka ta rasa masoyi kuma har abada ba zata yi min afuwa ba,ƙarshe ma ta halaka ni." Gulzum ya faɗi cikin alamun takaici. Jafar yace, "To me zai hana in ka kashe ni itama ka kashe ta ka ga shi kenan ka huta da fargabar komai,tunda yanzu tsafi baya tasiri sai ƙarfin damtse?" Gulzum ya yi murmushi, ya ce, "Kai yaro ne abin dana hango baka isa ka hango shi ba, idan na kashe ku yanzu ai na rasa abokan tafiya ni kaɗai zanci gaba da shan azabobin cikin KUNDIN TSATSUBA,kaga kuwa ai ance mutuwar yawa kaka ce,haka kuma ni na san in dai na kashe Yelisa koma daren daɗewa sai mahaifinta ya ɗauki fansa, kai nifa ba wawa ba ne da hankalina, na kan yi tunani kafin nayi abu." Lokacin da Yelisa ta ga Mashrila na neman jefota ƙasa, sai ta yi amfani da ɗaya ƙafarta tana ta dukan fuskar Mashrila. Koda Mashrila taji raɗaɗin zafi a fuskarta ta sai ta sake ƙafar Yelisa. Cikin sauri Yelisa ta ci gaba da ƙoƙarin hawa saman kejin don ta isa inda takobin nan take. hhh Yayin da Mashrila ta ɗaga kanta sama ta ga Yelisa tayi mata nisa,sai hankalinta ya dugunzuma. Ba zato ba tsammani sai aka ga Mashrila ta kama tsalle tana hawa saman kejin ba tare da taka ƙarafan ba da ƙafafunta tamkar biri. Al'amarin ya yi matuƙar baiwa kowa mamaki kenan. Cikin ƙanƙanin lokaci ta riski Yelisa. Nan fa suka kacame da sabon faɗa, wannan ta naushi wannan, kai suka yi ta bugun juna hannu da ƙafa. Sai da suka shafe rabin sa'a suna gumurzu ya zamana sun galaɓaita tare. Ana cikin haka ne Yelisa ta suɓuto ƙasa. Koda ganin haka sai Jafar ya kurma ihu, cikin firgici don ya tabbatar da cewa in dai ta faɗo ƙasa daga nisan saman kejin ta zama gawa. 🥺🥺🥺 Nima ganin wannan abin firgici ne yasa zan dakata anan,sai wani lokaci idan Allah ya kaimu. Fatan alheriMatsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part C A baya mun tsaye ne a inda; Nan fa suka kacame da sabon faɗa, wannan ta naushi wannan, kai suka yi ta bugun juna hannu da ƙafa. Sai da suka shafe rabin sa'a suna gumurzu ya zamana sun galaɓaita tare. Ana cikin haka ne Yelisa ta suɓuto ƙasa. Koda ganin haka sai Jafar ya kurma ihu, cikin firgici don ya tabbatar da cewa in dai ta faɗo ƙasa daga nisan saman kejin ta zama gawa. ###### Tuni a wannan lokaci Jafar ya runtse idanunsa ya fara kuka, amma bisa mamaki sai ya ji gaba ɗayan fadar ta yi tsit, tamkar babu wani abu mai rai a cikinta. Cikin hanzari Jafar ya buɗe idanunsa kawai sai ya ga Gulzum a cikin kejin Yelisa na shimfiɗe akan tafin hannunsa guda tana haki. Ashe mamakin zafin naman Gulzum ne ya sa jama'a suka yi tsit. Kafin Yelisa ta fado ƙasa tuni ya ruga ya banke ƙofar kejin ta ɓalle ya shiga sannan ya tara hannunsa ta faɗo a kai. Nan take fadar ta ruɗe da shewa da tafi, ana yiwa Gulzum jinjina. Ita kuwa Mashrila tuni ta ɗauko takobin nan har ta sauko ƙasa,lokaci guda suka fito daga cikin kejin gaba ɗaya. Sarki Azbir ya miƙe daga kan karagarsa ya tari Mashrila ya karɓi takobin sannan ya jata izuwa wata kujera da ke daf da karagarsa ya zaunar da ita sannan shi ma ya zauna. Zaman sa ke da wuya ya dubi sauran jama'ar fadar yace, "Yaku jama'a ku yi sani cewa a halin yanzu Mashrila ta ci gasa don haka ta warware gardamar ta tsakanin ta da Yelisa. Tabbas ta samu damar sanar da mu hikimar da ke ranta wacce da ita ne zamu samu nasara akan maƙiyan mu,kuma idan har muka yi amfani da hikimar aka dace zata shugabanci su Jafar yayin da suka ci gaba da tafiyarsu. Yake Mashrila yanzu ke muke sauraro sai ki sanar da mu wannan hikima ta ki." Koda sarki Azbir ya zo nan a zancen sa sai fadar ta sake yin tsit, kowa ya kasa kunnuwansa aka ƙurawa Mashrila idanu. Ita kuma Yelisa wacce ke zaune a gefe kusa da Jafar sai hararar Mashrila take zuciyarta na tafarfasa, kamar ta miƙe ta je ta rufe ta da duka.(😅😅😅su Yelisa iyayen kishi,inye kaga mai masoyi😝😝). Mashrila ta yi gyaran murya, sannan tace, "Hanyar da ta dace ta samun nasara akan mutanen Galbasa, kamar yadda kuka yi sani cewa makami baya tasiri a jikinsu haka kuma wuta bata ƙona su,wato dai a taƙaice basa mutuwa, komai aka musu a suna iya tashi. To ga dabara guda ɗaya,ina so a ƙera kibiyar ƙarfe mai kaurin bishiya kuma mai akwa tsananin nauyi wacce za'a rinƙa harbata daga jikin akwatin ƙarfe, mai kama da nau'ura, ina son karshen kibiyar ya kasance dunƙulallen ƙarfe ne mai faɗi da surar faranti. Na tabbatar idan aka harbi mutanen Galbasa da wannan kibiya za ta iya fasa cikinsu ko ƙirjinsu ta ɓullo gadon bayansu. Na tabbata ba za su iya zare kibiyar ba daga jikinsu saboda kaurinta da nauyinta. Kun ga daga sannan sai mu yi ta jarraba hanyoyin hallakar da su har mu dace, tun da ba za su iya guduwa ba, ba za su iya ceton kansu ba." Koda Mashrila ta zo nan a zancenta, sai mamaki ya kama kowa da kowa, har shi kansa sarki Azbir. Fadar ta sake yin tsit aka rasa wanda zai ce uffan kowa sai tunanin al'amarin yake a zuciyarsa. Ita kanta Yelisa duk da tana adawa da Mashrila sai da jikinta ya yi sanyi, don ta tabbatar da cewa haƙiƙa Mashrila ta zo da babbar hikima. Sarki Azbir ya miƙe tsaye, ya yi tafiya yana mai kaiwa da komowa a gaban Mashrila, sannan ya tsaya cak ya fuskanceta sosai yace, "Yake Mashrila haƙiƙa kin zo da dabara babba to amma fa ki sani cewa bana zaton maƙerana suna da hikimar da za su iya ƙera wannan kibiya da na'urar harbata a cikin kwanakin nan biyu kacal, da suka rage mana." Koda jin haka sai Mashrila ta yi murmushi tace, "Abin da na ke so da kai kawai kasa a kaini maƙerarku kuma a sanar da maƙeran cewa duk umarnin da na basu su bi ba musu, ko gardama,kuma zan yi aiki tare da su dare da rana." Sarki Azbir yace, "Wannna mai sauƙi ne." Nan take aka kira wani mutum wai shi Karfan wanda shi ne sarkin maƙera aka haɗa shi da Mashrila kuma aka umarce su da tafiya maƙera. Jafar ya dubi Mashrila yace, "Ina neman alfarmarki ki amince mu biku ni da Yelisa da Gulzum koma ƙaru da irin hikimarki da basirarki.'' Mashrila ta yi murmushi tace, "Wannan ai ba matsala ba ce ai dama bai kamata a ce baku ga komai ba da idanunku. Babu mamaki ku sami basirar kare mu daga wata masifar ta nan gaba albarkacin wannan basirar tawa." Ba tare da ɓata lokaci ba Karfan ya wuce gaba Mashrila,Yelisa da Gulzum suka bishi a baya. Bayan fitarsu daga cikin fadar sai da suka yi tafiya mai nisan rabin zango, sannan suka iso bakin wata kullaliyar rijiya. Da zuwa sai Karfan ya zaro wata kuba daga cikin aljihunsa ya buɗe rijiyar, kawai sai suka ga ashe matattakala ce a ciki, kai tsaye Karfan ya sanya ƙafafunsa ciki ya kutsa kai ciki ba tare da fargabar komai ba, su Jafar suka bi bayansa. Koda suka gama ƙure matattakalar, sai suka tsinci kansu a cikin wani sabon babban gari wanda ya ninka inda fadar sarki Azbir take sau uku. Babu komai a garin face maƙera da kayan ƙira,ga jama'a nan fululu amma babu guda ɗaya mai zaman banza,kowa ka gani a cikin aikin ƙira yake mazan su da matansu, yara da manya. Lokacin da Karfan ya fuskanci cewar su Jafar sun zama 'yan ƙauye don banda kalle-kalle da al'ajabi babu abin da suke yi sai ya ƙyalƙyale da dariya ya dube su, yace, "Ina yi muku marhaban da shigowa birnin ƙirarnmu, ku yi sani cewa fiye da shekaru dubu baya haka wannan birni yake a kullum dare da rana. Babu wani kalar ƙarfe da babu shi anan kuma muna iya sarrafa shi izuwa duk abin da muka so." Nan fa suka yi ta shiga saƙo-saƙo, lungu-lungu, gida-gida suna kalle-kallen kayayyaki iri-iri har da masu ɗumbin tarihi. Bayan sun gama kewaye ne Mashrila ta sa aka kawo mata tahuda da alƙalami da takarda, ta zana taswirar wannan ƙaton mashin da na'urar harba shi. A wannan lokaci gaba ɗayan manyan maƙeran mafiya basira sun kewayeta, koda suka ga taswirar sai duk suka kiɗime saboda tsananin mamaki. Nan fa kowannansu ya shiga faɗin albarkacin bakinsa. Wani ya ce zai iya kera kibiyar a cikin wata biyu, wani sati biyu, ita kuwa na'urar babu wanda ma ya ce zai iya ƙerata a cikin wata uku. Yayin da hayaniyar maƙeran ta yi yawa sai Karfan ya daka musu tsawa, kowa ya yi shiru,sannan yace, "Yaku mutanen birnin ƙira ku yi sani cewa ban taraku anan don ku yi hayaniya da faɗin abin da kuke so ba, sai don kawai ku bi umarni. Abin da nake so da ku kawai shi ne ku yi abin wannan yarinya Mashrila ta umarce ku." Karfan na gama jawabi ya juya ga Mashrila yace, "Mene ne abin yi?" Ba tare da ta ce uffan ba, ta shiga ware maƙeran nan ta kasa su izuwa kaso uku. Kaso na farko su ne mafīya basira don haka sai ta dube su tace, "Ku na zaɓa ku ƙera mini na'urar harba kibiyar,ina son ku haɗa basirarku waje guda kuma kada ku yi komai face abin da na yi muku nuni da yi." Mashrila ta dubi kaso na biyu tace, "Ku kuma ku na zaɓa ku ƙera mini wannan babbar kibiya, kuma ku yi amfani da umarnina kawai. Ku kuma kaso na uku ba za ku yi komai ba, face zuwa ɗebo irin ƙarafunan da na umarce ku." Nan take Mashrila ta fara zayyana musu irin ƙarafan da take buƙata da kuma irin kayan aikin da take buƙata. Sai da ta lissafa ƙarafa kala ɗari uku arba'in sannan ta lissafa kayan aiki kala ɗari bakwai da sittin da huɗu. Al'amarin da ya matuƙar ɗaure kansu Jafar kenan, suka yi ta mamakin ya akayi Mashrila ta san harkar ƙira haka. Kai bama su ba,su kansu maƙeran sun tsorata da al'amarin Mashrila, domin waɗansu kayan aikin ma ko sunansu basu taɓa ji ba, sai a bakinta kuma ba sa ganewa sai tayi musu kwatance da cikakken bayani. Nan da nan kaso na uku suka baza neman ƙarafa da kayan aiki. Ai kuwa rabin sa'a bata cika ba,suka zo da dukkanin abin da ake buƙata. Nan take Mashrila ta shiga basu umarni ta nuna musu yadda za'a sarrafa ƙarafan. Masu aikin kibiya na yi,masu aikin na'urar harba kibiya na yi. Haka dai aka ci gaba da aiki ba dare ba rana har tsawon kwana guda da yini ɗaya. A sannan ne aka kammala ƙera na'urar kuma aka kammala ƙera ƙatuwar kibiyar guda biyar. Koda su maƙeran da su Jafar suka dubi waɗannan abubuwa da aka gama ƙerawa sai suka ruɗe da shewa aka ɗaga Mashrila sama ana yi mata jinjina. Koda jiwo shewarsu sai sarki Azbir da sauran jama'ar garin suka rugo izuwa cikin birnin ƙira, don su ganewa idanunsu abin da aka ƙera. Kowa ya zo ya ga kibiyoyi biyar da na'urar harba su sai ya yi turus ya zama cikakken ɗan ƙauye. Ita dai na'urar babbace ainun kuma za'a iya ɗana gaba ɗaya kibiyoyi biyar a jikinta. A jikin na'urar akwai wani kwarkwaro wanda ake wana shi, yana nannaɗe da wata igiya wadda ita ce ke taɓe kibiyoyin,sannan akwai kunama a ƙasan kowacce kibiya wacce da zarar mutum ya jata sai ka ga kibiyar ta yi fitar burgu. Sarki Azbir ya dubi Mashrila yace, "Yake wannan yarinya mai dumbin basira haƙiƙa mun ga aikinki, kuma ya yi kyau mun gamsu da cewa wannan makami zai ya yin tasiri akan mutanen Galbasa. To amma muna son a yi gwaji don mu sami nutsuwa." Koda jin haka sai Mashrila ta yi murmushi tace, "Ɗauko kibiyoyin a aza su akan na'urar, kuma a ɗana su." Sannan a fito da na'urar izuwa saman gari inda fadar sarki Azbir take. Nan fa ma'aikata suka karɓi umarni. Kowacce kibiya guda sai da mutum hamsin majiya ƙarfi suka taru, sannan suka iya ɗaukarta. Da ƙyar aka ɗorata akan ƙatuwar na'urar mai ƙafafun keken doki. Sannan aka tura izuwa fadar sarki Azbir. Sai da aka zo tsakiyar fadar sannan aka ajiye na'urar. Mashrila ta yi umarni kowa da kowa ya koma gefe guda, sannan ta hau kan na'urar ta zauna. Ta saita wata ƙatuwar bishiya mai tsananin kaurin gaske da tsawo ta sakar mata kibiya guda. Tamkar tauraruwa mai wutsiya haka ƙatuwar kibiyar ta yi fitar burgu ta je ta sami tsakiyar bishiyar ta huda ta ta ɓullo ta can ƙarshen ta. Saboda ƙarfin harbin da kuma kaurin kibiyar sai da bishiyar ta ɓaɓɓako daga cikin ƙasa gaba ɗaya,jijiyoyin suka tunɓuko waje ta faɗi ƙasa rikica. Nan fa jama'a suka ruga gaban bishiyar suna kallon abin al'ajabi. Sai da aka shafe sa'a uku cur ana ƙoƙarin zare kibiyar daga jikin bishiyar. Da ƙyar da siɗin goshi mutum ɗari biyu suka haɗa ƙarfi suka zare kibiyar, suna gama zareta bishiyar ta ratattake. Koda ganin haka sai gaba ɗaya mutanen garin suka ɓarke da shewar farin ciki. Ita kuwa Mashrila wadda ke zaune akan na'urar sai murmushin murna kawai take yi. Sarki Azbir, Jafar, Yelisa da Gulzum kuwe duk sun kasa rufe baki don tsananin mamaki da al'amarin Mashrila. Ana cikin wannan hali ne kawai aka ji wata gagarumar guguwa ta taso daga sama. Koda jin guguwar nan sai gari ya hargitse, jama'a suka fara guje-guje da iface-iface, shi kansa sarki Azbir wurgi ya yi da hular sarautarsa ya cika wandonsa da iska. Cikin hanzari Mashrila, Yelisa,Jafar da Gulzum suka ɗaga kawunansu sama ai kuwa sai suka yi arba da su. Ba wasu ,ba ne face mutanen Galbasu mutum biyar. A rayuwar Gulzum ta duniya bai taɓa ganin ɗan adam mai siffa irin ta waɗannan mutanen ba. Domin girmansu ya kai girma. Suna da manyan fükafukai tamkar na jemagu masu tsananin ƙwari,domin da zarar sun bugi ginin gidaje da fukafukan sai ka ga gidajen suna rushewa. Kuma ko iskar bakin su suka huro sai ka ga ta kwashi mutane sama ta fyaɗa su a jikin gini. Mutanen sun kasance da siffofin mata suna da dogayen gashi da cikakken ƙirji amma zanƙala-zanƙalan hannayensu da faratansu sun kara musu muni ainun. Haka kuma haƙoransu zaftara-zaftara ne masu tsini tamkar allura. Nan fa suka fara ɗauki ɗai-ɗai sai dai ka ga sun cafko mutum kamar kare ya danƙi kyanwa. Da zarar sun kafa haƙoransu a wuyan mutum sai ka ga sun zuƙe jinin jikinsa nan take. Koda ganin abin da ke faruwa sai Jafar,Yelisa da Gulzum suka ruga kan na'urar inda Mashrila take suka zauna tare da ita, ita kuwa dama tuni ta fara ƙoƙarin saita su da kibiyoyin. Yayin mutanen Galbasan suka hango wannan na'ura waɗanda ke kanta kuma suka fuskanci manufarsu suka rinƙa huro musu iskar bakinsu, saboda ƙarfin iskar sai na'urar ta kama katantanwa. Take iskar tayi wurgi da Mashrila,Jafar da Yelisa ta maka su a jikin bango suka zube ƙasa sumammu. Gulzum ne kawai ya rage akan na'urar shi ma don yana da ƙarfi ne sosai,kuma ya riƙeta gam iya yinsa. Har yanzu mutanen Galbasan ba su daina ɓarna ba. Kai ko ƙarƙashin ƙasa mutum ya shiga saidai ka ga sun soka hannunsu cikin ƙasar sun zaƙulo shi, sun zuƙe masa jini. Mutane kuwa ba su fasa gudu da îhu ba. Cikin tsananin juriya Gulzum ya saita ɗaya daga cikin mutanen Galbasan ya sakar mata kibiya. Ai kuwa aka yi sa'a kibiyar nan ta nutse a tsakiyar ƙirjinta ta hudo gadan bayanta, ta faɗo ƙasa tana kururuwa. Idan ta yi kururuwa sai kaga wuta na fita daga bakinta. Ta yi, ta yi iya ƙarfin ta akan ta zare kibiyar daga jikinta ta kasa. Koda ganin haka sai sauran 'yan uwanta mutum hudu suka kai mata ɗauki suma suka yi iya yinsu suka kasa cire mata kibiyar,suna cikin ƙoƙarin hakan ne Gulzum ya sake harbo kibiyoyi biyu,yayi nasarar cake biyu daga cikinsu suka zube ƙasa suna gurnani da kururuwa. Guda biyun da suka rage suna ganin abin da ya faru ga 'yan uwansu suka firgice suka yi sama da niyyar guduwa. Nan ma Gulzum ya ɗaga na'urar nan sama ya saito ɗaya daga cikinsu ya harbota ta faɗo ƙasa. Ita kuwa ɗayar tuni ta ƙule a cikin sararin samaniya. Gulzum ya ciza leɓensa cikin tsananin baƙin ciki yayi takaicin ƙarewar kibiyar akan nau'urar,domin inda akwai sauran kibiya da guda ɗayar ma ba ta tsira ba. Dama kibiyoyin guda biyar ne kacal kuma an yi amfani da guda ɗaya sa'adda aka yi gwaji akan ƙatuwar bishiyar nan ta kuka. Anan zamu dakata,sai wani lokacin idan Allah ya kaimu. Fatan alheriMatsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part D A baya mun tsaya inda; "Gulzum ya ciza leɓensa cikin tsananin baƙin ciki yayi takaicin ƙarewar kibiyar akan nau'urar,domin inda akwai sauran kibiya da guda ɗayar ma ba ta tsira ba. Dama kibiyoyin guda biyar ne kacal kuma an yi amfani da guda ɗaya sa'adda aka yi gwaji akan ƙatuwar bishiyar nan ta kuka. Koda aka ga babu sauran mutanen Galbasa sai mutane suka dawo cikin hayyacinsu. Nan da nan sarki Azbir ya sa aka tattare gawarwakin mutanen da aka shanye jininsu aka bunka musu wuta. A lokacin ne su Jafar suka farfaɗo daga doguwan suman da suka yi, suka ga sarki Azbir da jama'arsa sun taru a waje guda sunyi zugum-zugum suna kallom mutanen Galbasa guda huɗu waɗanda ke kwance kibiya ta tsire su har yanzu ba su daina kururuwa ba,kuma ba su fasa ƙoƙarin cire kibiyoyin ba, amma sun kasa. Koda Jafar ya ga ana ƙona gawarwaki sai ya ruga gaban sarki Azbir yace, "Yakai wannan sarki ina dalilin ƙona waɗannan gawarwakin?" Sarki Azbir yace, "Ashe ka manta da bayanin da na yi muku tun a farko. Ai idan ba mu ƙone su ba,suma zasu zama irin mutanen Galbasa ne su zoƙe mana jini." Azbir ya dubi Mashrila ya ce, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan mutanen Galbasan waɗanda ba su mutu ba, kuma ba su kasance rayayyu ba, tun da ba za su iya tsinana komai ba?" Mashrila ta yi ɗan jim, ta ce, "Babu abinda zamu iyayi akan su face sa ido domin zamu iya aikata kuskuren da zai janyo su tashi." Azbir ya yi ajiyar zuciya, sannan ya sake duban Mashrila yana mai murmushi, yace, "Godiya gareki ya ma'abociyar hikima, haƙiƙa kin cece mu daga shairrin mutanen Galbasa. Yanzu zan bayar da umarni a shirya ƙasaitacciyar walimar girmamawa a gare ki,saboda wannan gagarumar nasara da kika kawo mana, kuma a wajen walimar ne zamu gabatar da babbar kyauta a gare ki da kuma ta Aljani Gulzum bisa ƙoƙarin da ya yi na harbo waɗannan mutanen Galbasa guda huɗu." Koda jin haka sai mutane suka ɓarke da shewa. Cikin hanzari Jafar ya kama mumbarin ya hau can sama, sannan ya ɗaga hannu sama. Take wurin ya yi tsit. "Ku yi sani cewa da ku da mu baƙin ku muna cikin mugun haɗari. Ku tuna cewa ɗaya daga cikin mutanen Galbasa ta tsere,kuma tabbas zata je ta sanar da Galbasa abinda ya faru ga 'yan uwanta. Shin bakwa tsammanin cewa Galbasa zai yi gagarumin shiri ya taho da kansa ya zo ya ƙarar da mu gaba ɗaya,tun da ya san cewa in ya ƙyale nan gaba ma za'a iya yiwa jama'arsa ɓarna?" Sa'adda Jafar ya zo nan a zancesa, sai hankalin kowa ya tashi aka fara kace-nace. Koda ganin haka sai sarki Azbir ya miƙe ya ce, "Yaku jama'ata haƙiƙa batun wannan yaro gaskiya ne,amma ina son kowa ya kwantar da hankalinsa domin kafin labari ya riski Galbasa sai nan da kwana bakwai. Kun ga ashe muna da isasshen lokaci na tunanin abin yi." "A'a ranka ya daɗe bamu da wani lokaci lallai tun daga yanzu ya kamata mu fara shirye-shiryen tunkarar gagarumin yaƙin da ke gabanmu." Koda jin haka sai sarki Azbir ya yi murmushi ya dafa kafadar Jafar, ya ce, "Yaro kar ka damu babu abin da zai faru." Nan take aka fara kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, masu shirya walima kuwa suka tafi suka fara aiwatar da aikinsu. Jafar, Yelisa,Mashrila da Gulzum kowa suka yi zugum cikin tsananin damuwa. Ita kanta Mashrila da Gulzum kuwa waɗanda ya kamata su fara farin cikin walimar da aka shirya musu sai suka kasance masu taya su Jafar jimami. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar yayin da suka faɗa cikin wani gari shafi na goma sha biyu na KUNDIN TSATSUBA. Al'amarin macen nan guda ɗaya wadda ta tsira daga harin kibiyar nan wadda Mashrila tasa aka ƙera, wato ɗaya daga cikin cikon mütum biyar na Galbasa, wacce ake kira Darzil sai ta ƙara ƙaimi,taci gaba da tafiya a sararin samaniya, har tsawon kwanaki bakwai sannan ta iso fadar Galbasa. Sarki Galbasa na zaune bisa karagarsa ta mulki, fadawa sun kewayeshi, sai ga-Darzil ta faɗo gabansa tana haki da numfashi. Cikin fushi da zafin nama Galbasa ya cakumo gashin kanta ya kara fuskarsa daidai tata, ya ce, "Ke Darzil ina sauran abokan tafiyarki kuma ina mutane hamsin ɗin da kuka saba kawo mini a kowanne mako?" Cikin ƙarfin hali Darzil tace, "Ya shugabana ka yi sani cewa wannan karon sabon al'amari ya faru domin wasu baƙin shaiɗanun mutane sun bayyana a birnin Azbir har sun ƙera wata ƙatuwar kibiya wadda ta hallaka abokan tafiyata da ƙyar na tsira da rayuwata." Jin wannan batu sai Galbasa kwarara uban ihu, wanda ya sa fadar gaba ɗaya yin girgiza. Cikin tsananin fushi ya yi wurgi da Darzil tamkar yayi jifa da 'yar tsana,sannan ya ɗauko wani zagayayyen farin dutse ya shafa shi da tafin hannun sa. Nan take hoton abinda ya faru tsakanin su Darzil da su Gulzum ya bayyana. Galbasa ya ƙarewa su Jafar kallo tsaf ya jinjina kai sannan ya waigo ya dubi babban bafadensa Barzuzu yace, "Yakai Barzuzu ka yi sani cewa waɗannan baƙin mutane ba ƙananan shaiɗanu ba ne. Haƙiƙa mun fi ƙarfinsu to amma sun kasance masu matuƙar hikima. Lallai ina so ka je ka yi tunani akan yadda zamu iya hallaka wannan mugun makami da suka ƙirƙira domin mu, sannan mu yi gagarumin shiri mu je mu shafe garin gaba ɗaya yadda ko a tarihi ba za'a tuna da shi ba." Yayin da Barzuzu ya ji wannan batu sai yace, "Ya shugabanmu yanzu don wannan ɗan makamin na su guda ɗaya zamu yi gayya da shiri. Ai ina tabbatar maka da cewa ni kaɗai ma idan ka turani zan iya hallaka su, na ƙone makamin na su." Koda jin haka sai Galbasa ya yi murmushi ya ce, "Kai ƙaramin mayaƙi ne baka san tuggun yaƙi ba. Kar ka yi tsammani za su tsaya ne jira kawai,suma sabon shiri za su yi don sun tabbatar da cewa ba zan kasa ɗaukar mataki ba. Ka yi sani cewa waɗannan mutane sun karya mana darajarmu a wannan duniya tamu, domin fiye da shekaru dubu baya ba'a taɓa cinmu da yaƙi ba, don me za mu yi sakaci wasu mitsatsan mutane kuma baƙi daga wata duniyar su shigo har tamu duniyar su cimu da yaƙi. Lallai ka hanzarta yin abin dana umarce ka." Barzuzu ya sunkui da kai ƙasa, ya ce, "An gama." Barzuzu ya miƙe tsaye ya fice daga cikin fadar. Galbasa ya dubi Galadimansa ya ce, "Ya kai Hutum ka je kasa a yi shela a gari cewar ban ɗaukewa kowa wannan yaƙi ba, babba da yaro,mace da namiji. Lallai kowa ya fara shiri nan da kwana bakwai za mu ɗunguma ƙwanmu da kwarkwatarmu mu tafi birnin Azbir sai mun shafe garin gaba ɗaya, mun zuƙe jinin kowa da komai, kai ko tsuntsu guda ba zamu bari ba a garin face ya zama maye kamar mu." Hutum ya risina, ya ce, "An gama ranka ya daɗe." Nan take fada ta watse, kowa ya kama gabansa. Lokacin da sarki Galbasa ya shiga cikin gidansa zuciyarsa baƙin ƙirin take, kuma tana tafarfasa, kamar za ta faɗo ƙasa, sai ya iske matarsa Hatimal tare da kyakkyawar 'yarsa, Mazalish zaune sun yi jugum. Koda ganinsa sai Mazalish ta miƙe zumbur cikin yanayin damuwa ta tare shi, tana mai cewa, "Ya kai Abbana wane irn yaƙi ne ya taso mana haka har da za ka ƙi ɗaukewa kowa da kowa yaro da babba?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Galbasa ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Yake 'yata mafi soyuwa a raina, kin sani cewa a duniyar nan tamu kaf babu abin da nake so sama da ke, saboda tsananin son da nake yi miki ne ya sa na raba ƙarfina da tsafina na baki rabi-rabi. Kuma saboda tsananin son da nake yi miki ne na cire miki maita ya zamana ke kaɗai kika fita dabam da kowa a garin nan. To ki ƙara sani ke ma ɗin ban ɗauke miki wannan yaƙi ba,domin da na yi asarar wannan yaƙi gwara na rasaki. Asarar wannan yaƙi daidai take da asarar mulkina,ƙasata da al'ummata gaba ɗaya. Tabbas idan ba mu yi nasara a wannan yaki ba, shi kenan sai dai a tuno da mu a tarihi domin hatta ƙasar nan tamu shafe ta za'a yi." Yayin da sarki Galbasa ya zo nan a zancensa sai hankalin Hatimal da na Mazalish ya ƙara dugunzuma fiye da da. Nan take idanun Mazalish ya ciko da ƙwallah, ta dafa kafaɗunsa da hannu biyu tace, "Ya kai Abbana ka tuna cewa ni a iya sanina ban taɓa ganin jarumi mai tsananin ƙarfin damtse da iya yaƙi kamar ka ba. Haka kuma ban taɓa ganinbmashahurin matsafi irin ka ba, domin a matsayinka na bil'adama har takai cewa ka juye ka zama ruwa uku. Za'a iya kiranka aljani ko fatalwa ko maridi,domin ba ka mutuwa ko an kasheka tashi kake yi. Ga shi shekarunka a duniya sun linka irin na bil'adaman wannan zamani, don na tabbata kafi shekara dubu biyu a duniya. To don me wani mahaluƙi zai zo lokaci guda rana tsaka har ya firgitaka ka ce da jama'arka kowa ya fito da ki bacin ni a zatona kai kaɗai ma zaka iya tashin ƙasa guda ta bil'adama?" Sa'adda sarki Galbasa ya ji wannan tambaya daga bakin 'yarsa Mazalish sai ya yi shiru gami da sunkuyar da kai ƙasa, cikin yanayin damuwa, sannan yace, "Yake 'yata ki yi sani cewa kamar shekaru goma sha tara baya lokacin da ya rage saura shekara ɗaya a haifeki na yi wani dogon nazari a cikin bincikena na tsafi na gano cewa akwai wasu irin mutane da za su zo daga wata sabuwar duniya dabam su yaƙe ni har su cini da yaƙi. Tabbas ba wasu ba ne waɗannan mutane face waɗanda zamu tunkara yanzu. Ina tabbatar miki da cewa siffofinki irin na waɗannan mutane ne domin in kikai tunani duk a ƙasar nan babu mai ƙaramin jiki irin na ki. Babu irin ƙoƙarin da banyi ba akan na gano hanyar da zan bi na hallaka waɗannan mutane idan sun zo,amma na kasa. Da naga haka sai na ci gaba da bincike akan ya za'a yi na tsira da rayuwata idan sun zo ɗin, sai na gano cewa in dai ina son tsira saidai idan na haifeki na cire miki maita kuma na raba ƙarfin jikina da tsafina na baki rabi. Tabbas indai ina tare da ke zan kuɓuta. Haka kuma na gano cewa a sanadiyar wannan yaƙi ne zan rabu da ke rabuwa ta har abada, amma ban ga yadda zamu rabu ba." Ko da Galbasa ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka kaɗa suka yi jawur, suka fara shirin zub da hawaye, ita kuwa Hatimal tuni ta fara kuka tun sa'adda ta ji batun ccwa za ta rabu da 'yarta. Mazalish ta rungume Galbasa tana mai rusa kuka, tace, "Yanzu in na rasaka ina zan sami uba kamar ka?" Koda ganin haka sai ita ma Hatimal ta ruga gare su ta rungume su gaba ɗaya tana mai taya su kuka. A can birnin sarki Azbir kuwa sai da aka kwana ana walimar farin cikin samun nasara akan mutanen Galbasa. Har aka ƙare walimar su Mashrila ba su saki jikinsu sosai ba, domin duba ɗaya za ka yi musu ka san cewa suna cikin damuwa, kai ko murmushin arziƙi ba sa iya yi, sai dai ka ga suna yaƙe. Ana ƙare walimar ne Mashrila ta ce babu wanda zai je ya kwanta sai dai a ci gaba da ƙera kibiyoyin nan da na'urorin harba su kuma ba za'a tsaida ba,dare da rana. Hakan kuwa aka yi domin sai da aka kwana shida ana wannan aiki har aka kai gacin ƙera kibiyoyi dubu ɗari uku da sittin da na'urorin harba su guda dubu ɗari shida da arba'in, wato dai na'urorin sun fi kibiyoyin yawa. Nan take aka ware mutane da yawa adadin yawan na'urorin aka koyar da su sarrafa na'urar da iya harba kibiya. Ba'a gama wannan shiri ba, sai a daren kwana na bakwai. Yayin da dare ya raba, mutane sun gaji saboda gajiyar wannan gagarumin aiki da suka sha fama a dalilin hakanne aka fara tafiya ana kwantawa. Mashrila,Jafar,Yelisa,Gulzum,sarki Azbir da manyan dakarun ƙasar kuwa basuje sun kwanta ba,duk sai suka hau kan na'urar harba kibiyoyi suka yi fako suna jiran farmakin mutanen Galbasa don sunsan ako yaushe suna iya zuwa. Da yawa daga cikin suma gyangyaɗi sukeyi, amma har gefin asuba basu ji motsin komaiba kuma kusan ko yaushe hankalinsu akan sararin samaniya yake, kai har gari ya waye rana ta buɗe sosai ba'aji komaiba ba aga komaiba, wannan tasa mutane suka fara sakin jikinsu,Karfan yazo gaban sarki Azbir ya ce "Ya shugabana ina ganin Galbasa da Jama'arsa sun tsorata damu baza su sake kawo mana hariba." Koda jin wannan batu sai sarki Azbir ya turɓune fuska yace, "Ashe baka da hankali to dakata na gayamaka kaji har abada karka saki jiki da abokan gaba komai shirinka da ƙarfin ka. Kai a tsammanika don munyi musu ɓarna zasu ji tsoronmune su daina zuwa. Dubi canfa kagani mutanen sune guda huɗu tsire da kibiyoyi a kwance,har yanzufa da ransu motsi sukeyi inda zasu iya cire kibiyoyin jikinsu da tuni sun halakamu, ina tabbatar maka da cewa tuni labari ya isarwa Galbasa kuma tabbas zaiyi shirin ɗaukar fansa. Babu mamaki yana kan hanyarsa ta kawo mana mamaya.........." Kafin Karfan ya ƙara buɗe baki yace wani abu sai suka ga wasu abubuwa acan ƙololuwar sama kamar tsuntsaye. Saboda yawansu sun lulluɓe saman wajen gaba ɗaya har sun dusashe hasken rana kuma sun tsaya cak su ba su sauko ƙasa ba kuma basu ƙara yin samaba,nanfa kowa ya ɗaga kansa sama hankali ya dugunzuma kowa ya fara faɗin albarkacin bakinsa,wasu suce ai tsuntsaye ne wasu kuma suce wannan dai wata sabuwar masifarce, cikin tsawa mashrila tace, "ku shashashai ku nutsu kowa ya ɗana kibiyarsa, waɗancan abubuwan da kuke hangowa ba komai bane face gungun dakarun Galbasa." Anan zamu dakata, sai wani lokacin idan Allah ya kaimu. Fatan alheri. Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part E A jiya mun tsaye ne inda; mashrila tace, "ku shashashai ku nutsu kowa ya ɗana kibiyarsa, waɗancan abubuwan da kuke hangowa ba komai bane face gungun dakarun Galbasa." ##### Koda jin haka sai kowa ya saita na'urarsa ta dubi sama cikin firgita wasuma gashi sun ɗora hannayesu akan kunamar harbin amma hannayen na ta karkarwa saboda tsananin tsoro. Maso abinka yafika dubara, a ɓangaren Galbasa da jama'arsa makamin mutuni sunyi tunani akan hanyar daza su ɓullowa makamin mutanen sarki Azbir wato sun samo dabaru guda biyu na lalata waɗannan manyan kibiyoyi. Abu na farko shine sun ƙera wata irin ƙatuwar garkuwar ƙarfe wanda aka yita da zallan ƙarfen đemon saboda girman garkuwar kowace ɗaya mutun ɗari tara da saba'in da bakwai ke riƙe da ita. Babu wani abu dazai iya bugun wannan garkuwa ya hudata. Abu na biyu sunzo da wata irin majajjawa itama mai girman gaske wadda zata iya haɗiye na'urar harba wannan ƙatuwar kibiya ta ɗauketa tayi sama da ita kuwa wannan majajjawar guda miliyan ɗaya da dubu ɗari uku da talatin da uku ce kowa ce majajjawa ɗaya mutum dubune ke iya sarrafata. Bayan kamar daƙiƙa sittin sai kawai aka ga tsuntsayen nan na sama sunyo ƙasa riƙe da wasu manyan garkuwoyi irin wanda ba'a taɓa ganiba. Koda suka zo ƙasa ƙasa sai akaga ashe mutanen Galbasa ne. Nanfa aka fara sakar musu manyan kibiyoyin nan amma a banza domin da kibiyoyin sunyi karo da garkuwarnan sai su ɓaɓɓalle,sukuwa mutanen Galbasa sai suka fara ɗauki ɗai ɗai sai dai kawai kaga sun suri mutum da hannu ɗaya sunyi sama dashi, cikin daƙiƙa guda sun zuƙe jininsa. Nanfa gari ya hargitse aka fara iface iface da guje guje. Ana cikin hakane mutanen Galbasa masu majajjawa suka sauka ƙasa suma suka fara nasu aikin sai dai kawai kaga majajjawar ta nannaɗe na'urar harba kibiya da mutanen dake kai ta suresu tayi sama dasu ko ruɓurɓushinsu ba zai dawoba,wannan al'amari yasa hankalin su jafar ya dugunzuma suma bisa dole suka sauka daga kan na'urar harba kibiyoyin nan suka ruga izuwa ƙarƙashin ƙasa inda birnin ƙira yake don neman mafaka suka bar sauran jama'a a filin daga ana tayi musu ɗauki ɗai-ɗai. Acan sararin samnan kuma sarki Galbasa tare da 'yarsa Mazalish da uwargidansa Hatimal da kuma manyan baraden yaƙin sane a tsaitsaye cak kamar gumaka suna jiran aka masu bayanin abin dake faruwa a ƙasa. Ai kuwa basu ɓata sama da daƙiƙa đari biyu da arba'in ba sai ga wani gwarzo da ake Gardus yayo sama ya dira a gaban Galbasa cikin yanayin garmamawa fuskar sa cike da annuri yace, "ya shugabana ai muna samin gagarumin nasara akan mutanen nan kuma ina tabbatar maka da cewa nan da rabin sa'a zamu gama dasu gaba ɗaya,haƙiƙa kayan yaƙin nan da Barzuzu ya ƙirƙira sunyí babban tasiri." Koda jin wannan batu sai sarki Galbasa ya tuntsire da dariya cikin tsananin farin cikin ya dubi Gardus yace, "saboda wannan labari da ka kawo mini mai daɗi nabaka 'yata Mazalish muna komawa gida za'a ɗaura aurenku." Koda jin wannan batu sai Gardus ya ƙwala ihun farin ciki yayi sujada ga sarki Galbasa yana mai tayin godiya kamar bazai dainaba. Take ya buɗe fuka fukansa yayi ƙasa dan ya isa inda ake ta ɗauki ba daɗi. Dama tuntuni gardus ya daɗe yana nuna wa Mazalish so da ƙauna amma sai aka sami akasi domin yadda ta tsaneshi haka ta tsani mutuwarta kai ko haɗa fuska tayi dashi to a wannan rana bazata iya ci da sha komai ba don tsananin ƙiyayya,kai ta kan kira wannan rana da muguwar rana ta rashin dace don koda tayi sharri zai zama mata. Babu irin baƙin cikin da Gardus baiyiba saboda ganin irin ƙiyayyar da Mazalish ke nuna masa har takai cewa kusan kullum sai yayi kuka ya zubar da hawaye dominta. A yau da Gardus yaji sarki Galbasa ya bashi Mazalish sai yaji kamar shine sarkin duniya. A gaba dayan mayaƙan sarki Galbasa babu saurayi kyakkyawa mai matuƙar Jarumta kamarsa. 'Yan mata da yawa sun kashe kansu bisa sonsa,sai gashi gimbiya Mazalish bata da ra'ayinsa ko kaɗan. Al'amarin da ya jefa gaba ɗayan mutanen ƙasar kenan a cikin al'ajabi duk sa'adda Galbasa yayi wa Mazalish batun aure sai tace dashi, "ya kai Abba na kabar wannan batu domin har yau banga ɗa namijin daya burgeniba, cikin matuƙar damuwa sarki Galbasa yakan tambayeta yace, "haba 'yata" yaushe ne zaki ga wanda zai burgeki tunda duk faɗin kasar nan tawa babu inda baki shigaba. Haka kuma babu wata ƙasa dake cikin wannan duniyar da baki shigaba, haka kuma babu wata ƙasa dake cikin wannan duniyar da baki shigaba,amma ace duk kyawawan samarin dake cikinsu da Jarumai da matsafa har yanzu baki ga gwaniba." Duk sa'adda sarki Galbasa ya faɗawa Mazalish wannan batu sai tayi murmushi tace, "yakai Abbana ina so ka tuna cewa bayan wannan duniya da muke ciki akwai wasu duniyoyin waɗanda kai kanka baka taɓa zuwaba. Tunda ban samu gwani anan tamu duniyar ba tabbas zan samu a wata duniyar. Abin da nake so dakai kayi mini uzuri domin ko mai na da lokacin sa. Nayi maka alƙawari komai daren daɗewa zan samu gwanina. Wannan batu na Mazalish na jeta sarki Galbasa cikin tsananin mamaki da damuwa to amma saboda tsananin sonta da yake ne ya ƙyaleta bai tilas ta mata auren doleba. Ako ina ba'a rasa munafiki lokacin da sarki Galbasa yayiwa Gardus alƙawarin Mazalish sai wani bafade ya dubi Mazalish yaga idanunta sun ciko da ƙwallah ya tabbatar da cewa tana cikin baƙin ciki bisa hukunci da mahaifinta ya yanke, shi dai wannan bafade sunansa Dauduf. Take Dauduf ya matsa kusa da sarki Galbasa yayi masa raɗa a kunne yace, "ya sarkın sarakai ina sanar dakai cewa hukuncin dake yanke a kan Mazalish baiyi mata daɗi ba don naga ƙwallah a idanunta ina mai ba da shawara cewa a zuba a idanu akanta don karta sulale ta gudu ba'a sani ba, kasancewar ko kaɗan bata ƙaunar Gardus." Sarki Galbasa ya jijjiga kansa alamar cewa, wannan shawara ta shige shi, sannan shi ma ya yiwa Dauduf raɗa a kunne ya ce, "Na yarda da wannan shawarar ta ka ɗari bisa ɗari, kuma na danƙa tsaron Mazalish a hannunka, in ta ɓata kaima ka ɓata." Dauduf yace, "An gama ya sarkin duniya." Kawai sai ya koma bayan Mazalish ya ja dunga. Tun lokacin da Dauduf ya dubi idanun Mazalish ya ga ƙwallar nan ashe ta lura da shi kuma tana nazarinsa don haka duk abin da ya gayawa sarki Galbasa cikin raɗa sai da ta aiyana shi a zuciyarta tamkar a fili suka yi maganar. Nan take Mazalish ta ce a ranta, "Komai za ka yi sai dai ka yi ni kam na gama yankewa kaina hukunci,na san abin da zan yi,da dai na auri Gardus gwamma na hallaka na yi asarar rayuwata gaba ɗaya." Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin Mazalish da mahaifinta sarki Galbasa a can ƙololuwar sama yayin da aka tafka yaƙi a birnin sarki Azbir. Al'amarin su Jafar kuwa lokacin da suka shige ƙarƙashin ƙasa inda birnin ƙira yake, suka zube ƙasa suna haki cikin mugun tashin hankali,sai kawai suka ga sarki Azbir na tare da su, Koda ya haɗa idanu da Mashrila sai yace, "Yake ma'abociyar hikima yanzu dai kin ga irin dabarar da mutanen Galbasa suka zo mana da ita. Ma'ana sunzo da ƙatuwar garkuwa da ƙatuwar majajjawa waɗanda ke lalata kibiyoyinmu da na'urar harba su. Yanzu mene ne abin yi? Wace hikima za ki sanar damu,mu hanzarta amfani da ita domin nan da rabin sa'a kacal zasu gama da mu gaba ɗaya?" Yayin da Mashrila ta ji wannan tambaya sai ta yi shiru tsawon daƙiƙa biyar tana tunani daga bisani ta dubi sarki Azbir tace, "Ya kai wannan sarki ka yi sani cewa babu wata dabara face abu ɗaya. Abin kuwa shi ne in dai muna son mu samu galaba mu ƙwaci kan mu a hannun mutanan nan saidai mu ƙwaci majajjawar dake hannayensu mu yaƙe su da ita." Koda jin haka sai ran sarki Azbir ya sosu yace, "Haba yarinya wannan wace irin magana kike ta rashin hankali, ta ya ya zamu iya ƙwatar makami a hannun mutanen Galbasa alhalin sun fi mu ƙarfi,kuma sun ninkamu girma sau goma." Cikin fushi Mashrila ta nuna Azbir da hannu ta ce, 'Wace ce yarinya shin kana tsammanin za ka girme nine? Dube kafa kamar a kife da kwando!" Koda jin haka sai Azbir ya yi murmushin ƙarfin hali, ya ce, ''Au dan kin ganni ɗan guntu shi ne kike tsammanin ke sa'a ta ce, ko kuwa don kin ga fuskata irin ta yara ce? To tsaya kiji a wannan watan da muke ciki na cika shekara dubu ɗaya da dari shida da hamsin. Wani matsafi a wata duniya da ake kira Makuk ya gaya mini cewa a wannan duniyar tamu babu wanda zai girme ni face sarki Galbasa." Koda jin wannan batu sai jikin Mashrila yayi sanyi, ta kasa cewa komai. Gulzum ya dubi sarki Azbir yace, "Ka ga ku bar batun musun shekaru don na san a shekaruna baka ɗauki kaso ɗaya ba. Abinda nake so da kai shi ne mu yi amfani da shawarar yarinyar nan domin ita ce kaɗai mafita. Ku sani cewa a barin tayi akan bar araha, kuma da mu zauna a zo a ci mu da yaƙi gwara mu jarraba iya ƙoƙarin mu don wani lokacin sai an gwada ake dacewa, kuma ai himma ba ta ga rago. Ni na san na fiku ƙarfi da juriya don haka zan yi amfani da damata da kuma dabarun yaƙin da na koya irin namu na aljanu na ƙwato majajjawa ɗaya. In dai kuka ga na yi nasara to ku tsaya a bayana. Yanzu zan yi fitar burgu daga ƙarƙashin ƙasa, amma kar ku fito sai bayan daƙiƙa đari da ashirin." Kafin wani daga cikinsu ya ce wani abu tuni aljani Gulzum ya daka tsalle ya yi sama. Ɗayan su bai yi motsi ba sai bayan sun kintaci lokacin da Gulzum ya faɗi, sannan suka leƙo sama. Ai kuwa suka sha mamaki, domin kuwa aljani Gulzum suka gani riƙe da majajjawa guda yana baƙin gumurzun yaƙi, duk inda ya kai farmaki sai dai ka ga ya shaƙo wuyan sama da mutum ɗari na Galbasa ya shaƙe a cikin majajawa yana wulwula su a cikin sararin iska. A cikin hanzari Jafar, Yelisa,Mashrila da Azbir suka daka tsalle suka ɗane bayan aljani Gulzum. Koda sauran mutanen Galbasa suka ga irin ɓarnar da Gulzum ya soma yi musu, sai da yawansu suka yi kukan kura suka afko gare shi, amma kafin su cim masa tuni sun makara domin har ya sami nasarar finciko waɗansu majajjawun guda biyu. Kawai sai ya miƙawa su Jafar guda, sannan ya riƙe guda a hannunsa, ya zamana shi kaɗai yana amfani da guda biyu. Koda Jafar, Yelisa, da Mashrila suka kama majajjawar da niyar riƙeta sai nauyin ta ya rinjaye su, suka suɓuto daga kan aliani Gulzum za su faɗo ƙasa. Cikin tsananin zafin nama sarki Azbir ya riƙe majajjawar da hannu đaya sai ga su Jafar suna reto a jikin majajjawar. Azbir ya dawo da su kan Gulzum kowannensu ya zauna daram, sannan shi kuma ya kama majajjawar da hannu biyu ya fara kaiwa mutanen Galbasa farmaki kamar yadda aljani Gulzum ke yi. Al'amarin da ya jefa su Jafar cikin matuƙar mamaki kenan. Jafar ya dubi Mashrila ya ce, "Ke kin ga wannan mutumin da kike rainawa ko, ashe ma duk ya fimu ƙarfi ba mu sani ba. Lallai sai miya ta ƙare sannan ake sanin maci tuwo." Yelisa ta yi ajiyar numfashi, ta ce, "tab ɗijan daga yau na daina raina ƙananan mutane ni kam ban taɓa tsamanin cewa wannan mutum zai iya ɗaukar wani abu mai nauyin mutum ba, sai ga shi yana sarrafa wannan ƙatuwar majajjawar wadda nauyinta wuce na gawarwakin bil'adama guda dubu, kuma manyan ƙarata ababan kwantace." Cikin ƙanƙanin lokaci Gulzum da Azbir suka tashi hankalin mutanen Galbasa suka ƙuntata musu, suka hana su saƙat, duk da cewa kuwa suma ba su fasa ɓarna ba, domin sun sha jinin sama da mutum miliyan uku da ɗoriya. Yayin da masifa ta yi masifa, gumurzu, runguntsumi, artabu, đauki ba daɗi da tsananin turnuƙu ya yawaita, sai Dauduf ya sake yin sama cikin tsananin gudu ya isa inda su sarki Galbasa suke. Wannan karon sai ga shi ya zo cikin mugun tashin hankali yana ta haki ya risina gaban Galbasa yace, "Ya shugabana wani baƙon aljani tare da sarki Azbir da wađannan baƙin bil'adama sun sami nasarar ƙwatar majajjawa guda uku, daga hannun jama'armu har sun yi mana gagarumnar ɓarna. Gaba runtuma ihu yake, yana rusa kuka jin azaba. Cikin tsananin mugun gudu tamkar an harba tauraruwa mai wutsiya, Mazalish ta bi bayan su sarki Galbasa amma kafin ta isa tuni Galbasa ya riski su Gulzum. Anan zamu dakata, sai wani lokacin idan Allah ya kaimu. Fatan alheriMatsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part F A baya mun tsaya inda:- Cikin tsananin mugun gudu tamkar an harba tauraruwa mai wutsiya, Mazalish ta bi bayan su sarki Galbasa amma kafin ta isa tuni Galbasa ya riski su Gulzum. #### Da zuwa ya yi wani tsafi sai ga shi ya fincike majajjawar hannnunsu tamkar mayan ƙarfe ya zuƙe guntun ƙarfe da ke ajiye a gefe guda. Nan take ya sake yin wani tsafin sai igiyar tsafi ta ɗaɗɗaure su tamau, suka kasa motsi. Anan ne fa Yelisa ta tuna cewa ita ma fa matsafiya ce 'yar babban matsafi,kawai sai ta rufe idanunta ta yi kiranye-kiranye da 'yan tsatsube- tsatsube amma sai ta ji shiru kamar maye ya ci shirwa. Sarki Galbasa ya dubeta ya tuntsire da dariya yace, "Ke yarinya daina ɓata lokacinki, babu wani irin tsafi da zai yi aiki anan in ba irin namu ba. Kin manta ne cewa a wata duniyar kuke dabam ba irin taku ba. Lallai zan tafi da ku izuwa fada ta, don na yi muku mugun kisa, sanadiyar ɓarnar da kuka yi mini." Sarki Galbasa na gama faɗin haka ya bada umarnin a ci gaba da shan jinin mutanen garin. Nan aka sa musu wawa tamkar an ajiyewa karnuka akan yankan nama guda đaya cal. Nan fa gari ya sake hargitsewa da iface-iface, sai dai ka ga jini na ambaliya da fantsamuwa tamkar teku ta ɓalle. Ana cikin haka ne Mazalish ta iso tamkar walƙiya. Cikin abinda bai wuce daƙiƙa guda ba ta tsitstsinka igiyar da ta ɗaure su Jafar da ƙarfin tsafi, sannan ta sure su ta ɗora su a gadon bayanta ta kuma suri kibiya guda irin wacce Mashrila ta sa aka ƙera tare da da na'urar harbata, duk da hannu guda ta ɗora su a gadon bayanta kusa da su Jafar ta sake cillawa da gudu ta ɓace, a cikin sararin sama tamkar walƙiya. Su dai su Jafar sai ganı suka yi sun daina hango birnin sarki Azbir gaba ɗaya. Suna cikin tafiyar ne Mazalish ta ce da su, "Kar ku yi zaton mun tsira da ni da ku. Daga yanzu zuwa kowanne lokaci za ku iya ganin mahaifina sarki Galbasa domin shi kaɗai ne zai iya cim mani. Ƙarfin gudunsa da ƙarfin damtsensa iri đaya ne da nawa, amma dai a cikin baradansa babu wanda zai iya zuwa nan ya riske mu. Abin da nake so da ku ku ɗora wannan kibiya akan na'urarta ku saita ta da zarar kun ganshi a bayanmu ku harbe shi. Lallai ku tabbata kun same shi a karon farko, in kuwa kuka kuskure tabbas dani da ku rayuwarmu na cikin haɗari." Koda jin wannan batu, sai mamaki ya kama su Jafar gaba đaya. Yelisa tace, "Yake wannan maiya ke kuwa me ya sa kika ceci rayuwar mu alhalin kince ke 'ya ce ga wannan azzalumin sarki masha jini?" Koda jin haka sai Mazalish ta ce, ''Ai kin san ruwa baya tsami banza don haka akwai dalilin faruwar hakan sai dai yanzu babu lokacin bayani,kuma ina son ku kwantar da hankalinku domin ni ba maiya ba ce, kamar mahaifina da jama'arsa. Ni mutum ce kamar ku amma zan yi muku bayani nan gaba in dai muna da sauran numfashi " Ai kuwa Mazalish ba ta gama rufe bakinta ba, sai suka ga sarki Galbasa biye da su cikin tsananin gudu tamkar an harbo musu kibiyar tsafi. Jikinsu Jafar na karkarwa suka shiga saita shi da kibiyar nan dama tun ɗazun sun ɗana ta, amma da sun saita shi sai ya ɓace, ko kuma ya zama haske. Shi kuma sai ya dunga harbo musu kibiyoyin tsafi da wutar tsafi ba don Mazalish na zillewa da gocewa ba da tuni sun hallaka gaba ɗayansu. Kai in da a ce mutum na ganin wannan artabu sai ka yi zaton kare ne ya biyo kyanwa a tsiyace, tana neman tsira da rayuwarta. Sai da aka shafe sa'a biyar cur ana wannan gumurzu sarki Galbasa bai cim musu ba,suma ba su sami damar harbinsa da kibiyar ba. Ba zato ba tsammani sai wutar tsafin Galbasa ta fara ƙona su Jafar. Sai da ya zamana babu wanda bai ƙone ba daga cikinsu. Yayin da Mazalish ta tabbatar da cewa in dai aka ci gaba da wannan gumurzu a haka Galbasa zai samu nasarar hallaka su sai ta juyo cikin shammace da zafin nama ta kama bakin kunamar harba kibiyoyin nan da hannunta ta saita mahaifinta ta sakar masa harbi a tsakiyar ƙirjinsa. Nan take kibiyar ta huda ƙirjinsa ta ɓulla har gadon baya, sai ji suka ji ya kurma uban ihu, sannan yayì ƙasa luuu....... Tun suna hango shi har ya ɓace musu da gani. Dama a wannan lokaci Mazalish ta tsaya cak a sararin samaniya. Nan take idanunta suka ciko da ƙwalla ta fara zubar da da hawaye. Kafin waninsu ya ce wani abu ta fashe da kuka tana mai nadamar abin da ta aikata. A daidai wannan lokacin ne shi ma sarki Azbir ya fashe da kuka, Jafar ya dafa kafaɗarsa yace, "Ya kai wannan sarki ina dalilin kukanka?" Azbir ya yì ajiyar numfashi ya ce, ''Ba komai ne ya sani kuka ba face sanin cewa a halin yanzu gaba đayan mutanen ƙasa ta sun zamą mayu domin na tabbata babu wanda zai tsira daga sharrin mutanen Galbasa, nì kam na san bani ba komawa ƙasata har abada, shi kenan na rasa iyalina, dangina,mutanena, mulkina da ƙasata." Yayin da sarki ya zo nan a zancensa, sai tausayi ya kama su Jafar gaba đaya. Ita kuwa Mazalish sai da ta ci kukanta ta ƙoshi, sannan ta ci gaba da tafiya a sararin samaniya, tana đauke da su Jafar a gadon bayanta. Ba ta gushe tana tafiya ba, sai bayan sun shuɗe sa'a bakwai, sannan ta sauko ƙasa suka a tsakiyar wani irin jeji mai ababan al'ajabi kala-kala. Bayan su Jafar sun sauka daga kanta, sai ta girgiza ta dawo cikakkiyar siffa irin ta mutane sosai. Mazalish ta dubi su Jafar har yanzu hawaye na zuba a idanunta tace, "Yanzu na dawo cikin ainihin halitta ta siffar da kuka ganni da ita ɗazu ba komai ba ce face sirrin tsafi." Yayin da Mazalish ta zo nan a zancenta, sai Jafar ya dubeta yace, "Yake 'yar uwa ya akai kika zama mutum kamar mu alhalin kin kasance jinsin mayu?" Nan Mazalish ta basu labarin yadda aka yi mahaifinta ya cire mata maita da kuma yadda ya bata rabin ƙarfin damtsensa da rabin tasirin tsafinsa. Jafar ya sake duban ta ya ce, "To mene ne dalilin da yasa kika ceci rayuwarmu kuma har kika harbi mahaifinki da hannunki?" Koda jin wannan tambaya sai Mazalish tayi ajiyar zuciya sannan tace, ''Ba wani abu ba ne ya sa na ceci rayuwarku face hujjoji guda biyu. Huja ta farko itace mahaifina ya bayar da ni ga wani bafadensa wanda na tsana fiye da komai a rayuwata. Kuma na san cewa idan na aure shi har na sami ciki dole ne maita ta dawo jikina,ni kuwa da na zama maiya irin mahaifina da mutanensa gwara na rasa rayuwata. Hujja ta biyu ita ce kimanin shekaru biyar baya na taba ziyartar wani boka a wata babbar ƙasa na sanar da shi cewa ni kam na gama kewaye wannan duniya tamu amma ban ga wani namiji dana ji ina ƙaunarsa a zuciyata ba, har na iya aurensa, shin ina ne zan ga wanda zai iya aurensa? Lokacin da bokan ya ji wannan tambaya tawa sai ya ƙyalƙyale da dariya,sannan ya yi nuni da hannunsa izuwa ga wani ƙaton madubi sai ga hoton wani kyakkyawan saurayı yana gagarumin yaƙi tare da wani hamshaƙin barde kuma matsafi, a cikin wata duniya dabam ba irin wannan da muke ciki ba. Ina ganin wannan saurayı na ji ina mutuwar sonsa. Boka Arjiwala ya dube ni yace, "Ya kika ga wannan saurayi kina sonsa?" Cikin tsananin murna nace ai tunda nake ban taba jin SO ya shiga zuciyata ba sai akan wannan saurayi, ya kai wannan boka maza ka sadani da duniyar wannan saurayi ni kuwa na saka maka da duk abin da kake buƙata iya tsawon rayuwarka. Boka Arjiwala ya sake bushewa da dariya yace, "yake wannan 'yar sarki ki yi sani cewa ba ni da ikon kai ki duniyar da wannan saurayi yake amma idan kika yi haƙuri nan da shekara biyar masu zuwa waɗansu mutane za su zo daga can kuma sanadiyar sune za'a yi gagarumin yaƙi tsakanin mutanen ƙasar sarki Azbir da mutanen ƙasarki,zaki rabu da mahaifinki da ƙasarki da kuma wannan duniya amma idan kina son ki je ki ga wannan saurayi wanda zuciyarki ta kamu da son sa sai kin ceci rayuwar waɗannan baƙin mutane, ki sani cewa hanyar da suka bi suka zo hanya ce mai matuƙar wahala, domin ta cikin wani sihirtaccen littafi ne da ake kira KUNDIN TSATSUBA ba kuma za su fita daga cikin sa ba,su koma duniyar su sai bayan shekara ashirin daidai. Za su yi ta ziyarar duniyoyi iri-iri ne suna shiga masifu kala-kala." Lokacin da boka Arjiwala ya zo nan a zancensa sai na dube shi cikin matuƙar damuwa nace, "Ya kai wannan boka ka yi sani cewa koda zan tsufa tukuf a yawan neman wannan masoyi nawa ba zan kasa ba. Zan jira waɗannan mutane nan da shekara biyar har su zo kuma zan jure kowacce irin masifa da zamu tunkara a cikin littafin KUNDIN TSATSUBA. Abin da nake so da kai shi ne kawai ka sanar da ni sunan wanann saurayi. Boka Arjiwala yayi murmushi yace, "sunansa Hubalru, kuma ya kasance ma'abocin wani addini da ake kira Musulunci. A yanzu haka yana tsakiyar soyayya da wata kyakkyawar mace wai ita gimbiya Sima." Koda jin wannan batu sai kishi ya turnuƙeni nace, "wacece kuma gimbiya Sima? Shin ta fini kyaune ko kowa mahaifinta yafi nawa ƙarfin mulki?" Arjiwala ya ce ba ta fiki komai ba, amma za ku iya yin kunnen doki a fagen kyau. Babu ruwana da ita abin da na șani kawai koda zan zama baiwa mafi ƙasƙanci sai na auri Hubairu. Nan take na kawo alheri mai yawa na baiwa boka Arjiwala sannan nayi masa bankwana na tafi. Daga wannan rana na cigaba da jira har izuwa yau ranar da na sadu da ku." Yayin da Mazalish ta zo nan a zancenta sai Jafar ya dubeta cikin mamaki yana mai tunani. Mazalish ta dube shi tace, "Tunanin me kake yi?" Jafar yace, "Ai sunan da kika faɗi na saurayin da kike so nake tuno mai shi. Tabbas mun san waye Hubairu kuma mun yi hulɗa da shi." Koda jin haka sai murna ta kama Mazalish tace, "Ba ni labarinsa na ji." Jafar yace, "Haƙiƙa ya cika kyakkyawa kuma cikakken jarumi ne, domin shi ne ya taimake mu ya kashe sarki Lu'umanu har muka samu damar sato wani aljani wai shi Markahul sabus wanda ya đauko mana kubar MIFTAHUL ZARBIL wacce da ita ne muka buđe littafin KUNDIN TSATSUBA. Littafin daya zame mana alaƙaƙai kuma shine sanadin zuwan mu wannan duniya taku." Koda jin haka sai Mazalish ta dubi Jafar cikin rashin fahimta ta ce, "Ban gane wannan jawabi na ka ba?" Jafar ya nuna Mashrila ya ce, "Kin ga wannan a cikin KUNDIN TSATSUBA muka haɗu da ita,kamar yadda muka haɗu da ke." Nan take Jafar ya kwashe labarinsu kaf tun daga farko, har ƙarshe ya sanar da Mazalish. Bayan ya gama ne ta cika da tsananin mamaki, kuma ta ɗauki alƙawarin tafiya tare da su har a gama karanta shafukan KUNDIN TSATSUBA, don ta haɗu da masoyınta jarumi Hubairu bin Mas'ud wanda ba ta taɓa ganinsa ba sai a madubin tsafi kusan shekaru biyar baya. Bayan Jafar ya gama baiwa Mazalish labarinsu, sai suka miƙe gaba ɗaya suka nausa cikin wannan jeji suka yi ta tafiya ba tare da sanin inda suka dosa ba. Kwatsam sai suka ga wata rijiya,dama ƙishirwa ta addabe su. Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da ƙaton murfin ƙarfe. A bakinta an yi rubutu da ruwan zinare kamar haka. "BABU MAI BUƊE WANNAN RIJIYA YA SHA RUWAN CIKINTA SAI BAƘIN DA SUKA ZO DAGA WATA DUNIYAR." Topah,ko mai faru??? Anan zamu dakata,sai wani karon idan Allah ya kaimu,fatan alheri. Ina muku fatan alheri da nasara.Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part G A baya mun tsaya ne a inda:- Kwatsam sai suka ga wata rijiya,dama ƙishirwa ta addabe su. Ita dai wannan rijiya tsohuwa ce ainun kuma an rufe ta da ƙaton murfin ƙarfe. A bakinta an yi rubutu da ruwan zinare kamar haka. "BABU MAI BUƊE WANNAN RIJIYA YA SHA RUWAN CIKINTA SAI BAƘIN DA SUKA ZO DAGA WATA DUNIYAR." ###### Koda gama karanta wannan jawabi sai Jafar ya dubi Yelisa da Gulzum yayi murmushi ya ce, "Ai domin mu aka yi rijiyar nan. Yakai Gulzum maza ka buɗe mana mu sha ruwa ko ma huta da ƙishirwa." Cikin fushi Gulzum ya ce, "Waye bawanka har da za ka bani umarni na bi?" Koda jin haka sai Yelisa ta dakawa Gulzum tsawa, ta ce, "Daga yau umarnin Jafar umarnina ne,maza ka yi abin da yace." Cikin hanzari da biyayya Gulzum yasa hannu ɗaya ya ɓanɓare murfin rijiyar da ƙarfin tsiya. Yana yaye shi wata irin iska mai tsananin ƙarfi tayi fitar burgu daga cikin rijiyar ta zuƙe Jafar,Yelisa, Gulzum, Mashrila da Mazalish, ta bar sarki Azbir shi kaɗai, su ka zama 'yan ƙanana suka shige cikinta, sannan murfin rijiyar ya koma ya rufe kansa. Azbir ya fashe da kuka. Su Jafar dai ba su tsinci kansu a ko'ina ba sai a cikin ainihin tasu duniyar gaban KUNDIN TSATSUBA. Har yanzu shafi na goma sha biyu ne a buɗe. Koda Mazalish ta miƙe ta ganta a cikin wata sabuwar duniya sai ta kama kalle-kalle kamar ɗan ƙauyen da bai taɓa shigowa birni ba. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar bayan sun shiga shafi na goma sha biyu a cikin KUNDIN TSATSUBA. ***************************************** Al'amarin su Jarumi Hubairu kuwa lokacin da sarki Hudais ya haɗa shi da manyan dakarun Musuluncin nan don zuwa gidan bokanya Samaratu ɗauko gimbiya Sima wacce har yanzu tana nan a kwance tana barcin tsafi, saura 'yan sa'o'i kaɗan ta rasu in dai ba a tashe taba daga barcin. Sai suka ƙara himma wajen gudu da sauri a cikin samaniya. Ba su isa gidan Samaratu ba sai da ya rage saura sa'a đaya da rabi gimbiya Sima ta rasa rayuwarta. Da zuwa suka iske hadiman Samaratu a shirye suna tsaron gidan. Da yake an fi ƙarfinsu. Nan da nan aka kashe su a cikin abin da bai wuce daƙiƙa ɗari da ashirin ba. Daga nan su Hubairu suka shiga neman inda gimbiya Sima take. Ɗaki-ɗaki, lungu-lungu, sako-sako,nan ma sai da suka shafe sa'a guda da kusan rabin rabi na sa'a sannan suka risketa a cikin ɗakin tsafin Samaratu kwance bisa wani gadon ƙarfe wanda wata irin tsafaffiyar wuta ta kewayeshi sama da ƙasa. Hubairu ya ruga da gudu don isa gareta,koda yaje daf da gadon sai ja da baya da sauri saboda tsananin zafin wannan tsafaffiyar wuta domin ji yayi kamar naman jikinsa zai narke, koda ganin haka sai wani dakare waishi labahan yace, "ya kai Hubairu shin kamanta cewa mun shigo gidan ma'abota tsafine,lallai bazaka iya dosar wánnan gado ba face da neman tsari daga Ubangiji." Sa'adda Hubairu ya ji wannan batu sai kawai ya fara karanta addu'o'i,kai tsaye ya nufi wannan gado. Yayin da ya tunkare shi sai yaji zafin wutar na raguwa ya yin da yake kusantarsa, a hankali sai wutar ta rinƙa zuƙewa da kanta tana ƙanƙancewa,koda ya je daf da gadon kuwa sai wutar ta ɓace gaba đaya. Ba tare da ɓata lokaci ba Hubairu ya soma karanta addu'ar nan wacce sarki Hudes ya bashi yana tofawa a jikin gimbiya Sima. Yana gama tofawa kuwa sai hannayenta da ƙafafunta suka fara motsi, daga can kuma sai idanunta suka buɗe a hankali. Cikin firgici ta miƙe zaune zumbur tana mai kalle-kalle, koda taga jarumi Hubairu a gabanta sai tayi hamdala ta rungumeshi cikin farin ciki sannan tace "ya kai masoyina ina wazirina Kuddaru,ina su Jafar, wai shin nan ma a ina muke, su waye waɗannan a tare da kai?" Ya yin da jarumi Hubairu ya ji wannan tambaya, sai ya janye jikinsa daga nata suka fuskanci juna sannan yace, "yake abar ƙaunata kiyi sani cewa yau kwananki casa'in da huɗu kina barci sai yau Allah ya nufa kika tashi, su kuwa su Jafar da wazirinki Kuddaru bansan a inda su ke ba,nima ina da sauran shan ruwa a duniya shi yasa muka sake saduwa." Cikin tsananin mamaki gimbiya Sima ta tattaro nutsuwarta ta ƙurawa Hubairu idanu ta ce, "Ban gane wannan batu na kaba. Ya akayi nayi barci har na tsawon kwana casa'in da huɗu aini tsammani na duk bai wuce suman 'yan daƙiƙu bane." Hubairu ya yi murmushi sannan ya kwashe labarin duk abin ya faru garesu shi da waziri Kuddaru lokacin da sarki Lu'umanu yasa aka đauresu don ya hallakasu har mahaifinsa Mas'ud da aljani Abtarul Hudes suka kawo muşu ɗauki ya kawo izuwa lakacin da suka yi gumurzun faɗa shi da sarki Lu'umanu har a karo na biyu da yadda ya koyi yaƙi a wajen sarki Hudes har ya sami labarin inda take yazo yanzu don ceton rayuwarta. Koda Hubairu yazo ƙarshen labarinsa sai farin ciki ya lulluɓe gimbiva Sima ta fashe da kuka ta sake rungumeshi tana mai cewa, "da yardar Allah wannan karon babu mai rabamu har sai mun zama miji da mata." Sima ta ƙara da cewa, "kai amma fa lamarin sarki Lu'umanu akwai al'ajabi. Yanzu ashe bai mutu ba yana nan a raye. Ni fa a gaban idanuna ka karya masa wuya. Tabbas wannan mutum ya cika shaiɗani kuma hatsabibn matsafi." Hubairu yace, "ƙwarai kuwa ai abin da na fahimta shine duk wannan artabun da nayi dashi ba dashi bane da wani aljanin dabam nayi. Gangar jikin tasa ce kawai amma ba ruhin saba ne. Yake masoyiyata ki sani cewa yanzu bamu da wani lokaci na doguwar hira zaifi kyau mu hanzarta tafiya." Kafin gimbiya Sima ta buɗe baki kawai sai suka gaba đayan ginin ɗakin da suke ciki an daukeshi can ƙas an barsu a tsakiyar fili tamkar a ɗauke murfin tukunya a ajiye a gefe guda. Kawai sai ganin waɗansu jibga-jigan aljanu kimanin su miliyan ɗaya sun yi musu ƙawanya kowannensu riƙe da mugun makami. Ba zato ba tsammani kuma sai ga sarki lu'umanu bisa dardumar tsafi ta sauke shi daf da jarumi hubairu suka fuskanci juna sai ya murtuke fuska yace, "ya kai babban maƙiyina kayi sani cewa babu inda zaka shiga a cikin duniya nan ka ɓace mini,ka tuna cewa munyi gagarumin faɗa ni da kai har sau biyu ko kuma nace sau uku munyi kare jini biri jini, ina tabbatar maka da cewa wannan karan na zo da cikakken shirin irin wanda ban taɓa yi ba don haka dole ne naga bayanka. Tabbas yau sai nayi gunduwa-gunduwa da sassan jikinka. Ita kuwa masoyiyar taka dole na mallaketa ko tana so ko bata so." Jarumi hubairu ya dakawa lu'umanu tsawa yace, "kai tsohon maƙiyin ALLAH babban mushiriki ma'abocin fasiƙanci domin ina tare da ubangijin musulunci addinin da ya zamo shugaban addinai kuma tafarkin gaskiya. Duk wanda ya riƙe shi yafi ƙarfin masu yin waninsa da izinin Allah zan samu rinjaye akanka kuma da sannu zamu ƙarar da ire-irenku a doran ƙasa mu kawar da kafirci mu shimfiɗa musulunci ya baibaye duniya gaba ɗaya." Koda jin wannan batu sai sarki lu'umanu ya sake tuntsirewa da dariya sannan ya dubi waɗannan dakarun aljanu guda miliyan ɗaya waɗanda Shamharu ya tsafance su tsahon shekaru dubu kuma ya tsuma makamansu a tsumin dafi tsawon shekaru dubu yace dasu, "me kuke jira ne da abokan gabarmu maza ku ragargaza su ku ratattakasu banda gimbiya Sima kaɗai har sai sun zama ruɓurɓushi. Nan take wuri ya yamutse aka fara ɗauki ba daɗi. Jarumi Hubairu da sarki Lu'umanu kuwa suka ware gefe ɗaya suna zagaya juna da kallon kallo kowennan su na tunanin irin harin da zai kai. Ita kuwa gimbiya Sima an barta ita kaɗai a tsaye a waje guda jikinta na karkarwa don tsananin razana domin tunda take bata taɓa ganin gwarazan aljanu ba irin waɗannan. Su kansu dakarun Musuluncin sun isa abin tsoro ballantana kuma kafiran aljanun guda miliyan đaya waɗanda sun ninka musulman sau arba'in. Nan fa aka shiga bugegeniya da sokaiya, ƙarajin aljanu dana makaman su ya cika dodon kunne. Jini ya rinƙa fantsama tamkar ana ruwan samansa. Haƙiƙa gumurzu ya kasance kare-jini-biri-jini domin kowane ɓangare suna wahala da asara, kuma kowane ɓangare na aiki da abin dogaransu. Su kafiran aljanun nan na tsafi suke tayi da amfani da ƙarfin damtse,su kuwa musulman aljanun suna kiran sunan Allah ne tare da nuna tsantsar jarumtaka. Duk sa'adda suka ambaci sunan Allah saidai kafiran na ɓace ɓat, sai dai kawai a sake ganinsu tsulum sun baiyana ta hanyan shammace. Idan kuwa suka yi nasu tsafin sai ƙarfin addu'a ya hanashi tasiri, saboda haka babu abin da yake tasiri a filin dagar sama da ƙarfin damtse da iya yaƙi. Sarki Lu'umanu da jarumi Hubairu suka ja da baya taku bakwai-bakwai sannan kowannansu ya rugo da gudu don a haɗu a tsakiya riƙe da makami a sama,shi dai Lu'umanu ihu yake yi da kururuwa mai firgita gungun mayaƙa shi kuwa Hubairu babu abin dake fita daga bakinsa face kabbara. Yayin da suka haɗu a tsakiya takubbansu suka gwaru sai tartsatsin wuta ya tashi ƙasa tayi girgiza gaba ɗaya wajen ya hau tambal-tambal kai kace naɗe ƙasar wajen za'ayi. Tabbas kasancewa manyan baradene suka yi karo, nanfa sukaci gaba da kaiwa juna sara da suka cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta tamkar jikkunansu bana jini da tsoka bane, na karfene. Sai da suka shafe sa'a shida cur suna wannan mugun gumurzu amma ɗayansu bai samu koda karcewa ba a jikinsa ba. Da kansu suka rabu kowa ya ja da baya yana haki da tunanin dabarar da zata fishsheshi. Tabbas ƙarfi yazo daya,mamaki ya kama sarki Lu'umanu ya ce a zuciyarsa yanzu duk irin shirin nan da mai girma Shamharu yayi mana ni da waɗannan dakarun nasa ya tashi a banza kenan,kai lallai waɗannan mutane sun cika hatsabibai kamar yadda sarki Lu'umanu ke wannan tunanı haka shima jarumni Hubairu ya kasance domin ya tsinci zuciyarsa na mai cewa dashi kai waishin su Lu'umanun nan waɗanne irin hatsabibai ne. Haƙiƙa Allah ya ara musu lokaci amma in ba don haka ba ya za ai ace mun kasa samun nasara a kansu har yanzu duk da cewa kuwa muna addu'o'i da kiran sunan Allah akansu. Bayan kamar daƙiƙa ɗari da tamanin Lu'umanu da Hubairu na kallon juna sai kawai Lu'umanu ya sake yin kukan kura ya tasammasa suka sake garƙamewa da azababben yaki. A wannan lokaci yaƙi ya ƙara tsamari tsakanin kafiran aljanun da kuma musulman masu taimakawa Hubairu domin kusan kowane ɓangaren sun rasa rabin adadinsu, har yanzu gimbiya Sima na nan a gefe guda tana ganin abin dake wakana, tun tana tsaye har sai da ta faɗi ƙasa kuma tun tana iya yin addu'a har sai da ta kasa da saboda ƙura da hayaƙin yaƙi wanda ya turnuƙe wajen gaba ɗaya domin bisa đole ta toshe kunnuwanta saboda ƙarar makamai da ihun mazaje. Ana cikin hakane Lu'umanu ya faɗo inda Sima ke kwance,sa'adda jarumi Hubairu yayi masa wani wawan duka da ƙafa a ƙirji koda Lu'umanu ya ganta daf dashi sai ya kamobta yasa takobinsa akan wuyanta ya dubi Jarumi Habairu yace in ka ƙara kusantata zan yanke mata maƙogaro. Bisa dole Hubairu yaja da baya kaɗan. Nan take yaƙi ya tsaya cak tamkar babu mayaƙan a wajen,baka jin komai sai nishin naƙasassu waɗanda suka rasa sassan jikin su. Gawarwaki kuwa gasu nan birjik babu adadi,jini kuwa sai malala yake yana gudu kamar idaniyar ruwa. Nan take sarki Lu'umanu ya dubi daddumarsa ta tsafi wacce ke tsaye a cikin iska take daddumar tazo gaban sa ta shimfiɗa kanta,kawai sai ya hau kanta tare da gimbiya Sima har yanzu bai cire kaifin takobinsa daga wuyan ta ba kuma ya ƙurawa jarumi Hubairu idanu don tsoron kada yayi wani yunƙuri. Daddumar tsafin ta bar doron ƙasa ta dira akan ɗaya daga cikin baraden aljanun nasa kawai sai Lu'umanu yayi wani tsafi gaba ɗaya wajen ya gauraye da tsananin duhu cikin abinda bai wuce daƙiƙa ba,kafin su jarumi hubairu suyi wani yunƙuri tuni su sarki lu'umanu sun ɓace kuma sun ɓace ne tare da gimbiya sima. Cikin hanzari jarumi hubairu ya karanta wata addu'a sai wannan duhu ya yaye haske ya baibaye tamkar ba'a taɓa yin duhu ba. Koda hubairu yaga babu su lu'umanu kuma babu gimbiya Sima sai hankalinsa ya tashi cikin sauri ya bada umarni abi sawun su. Ai kamar an harba kibiyoyi dakarun musuluncin suka harba jikkunansu suka luluƙa cikin gajimare suna masu tsananin gudu cikin sahu sahu abin gwanin ban sha'awa kaikace tsuntsaye ne ke bikin gasar gwada tsere. Wannan shine abina ya faru tsakanin su jarumi hubairu da su sarki lu'umanu yayin da aka fafata baƙin gumurzu a gidan bokanya samaratu don ɗaukar gimbiya sima. ***************************************** Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu. Fatan alheriMatsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part H A jiya mun tsaya ne:- Wannan shine abina ya faru tsakanin su jarumi hubairu da su sarki lu'umanu yayin da aka fafata baƙin gumurzu a gidan bokanya samaratu don ɗaukar gimbiya sima. ***************************************** Tun sa'adda aljani durfus ya tafi ya barsu a cikin kejin tsafi bisa sharadin cewa idan sun amince ya zama shugabansu zai dawo ya kuɓutar dasu. Sai suka kasance cikin halin damuwa da shawarwari. Markahus sabus ya dubi ummansa bokanya samaratu yace, "yake ummina tun ɗazu boka Jinshan da boka sulbaini sunata faɗin albarkacin bakinsu bisa shawarar da ya kamata mu yanke akan sharaɗin da aljani durfus ya gindaya mana. Amma ke kinyi shiru ba kice komai ba ko kina da dalili?" Samaratu tayi murmushi tace, "yakai ɗana kayi sani cewa shifa aljani Durfus bawa ne ga boka sulbaini don haka ya fi saninsa shi ya kamata ya bamu shawarar abin da ya dace muyi." Koda jin haka sai sulbaini yayi farat yace, "haba Samaratu ai in ki ka faɗi haka baki yi mini adalci ba. Ki tuna fa cewa wannan durfus din na yanzu ba shine na da ba wanda na sani ma'ana ina nufin cewa a halin yanzu aljani Durfus ya taka matsayin da ban sani ba. Ni ina ganin kawai mu amince da zama bayinsa in yaso bayan ya kuɓutar damu sai muyi masa tawaye ta hanyar yaudararsa har mu kai ga samun nasara akan SHAMHARU." Yayin da sulbaini yazo nan a zancen sa sai boka Jinshan ya tuntsire da dariya yace, "wai shin kai ina ka kai tunaninka ne ka ajiye shi har ka manta dashi. Tsaya na gaya muku gaskiya na gaba yayi gaba na baya sai labari. Ai dama ance wanda duk ya rigaka barci dole ya rigaka tashi idan har muna so mu sami nasara akan shamharu dole ne muma mubi irin hanyar da yabi ta neman zama MATSATSUBI." "Ta yaya zamu zama MATSATSUBAI kaima ka zo da zancen banza abinda ba zai yiwu ba." Markahus sabus ne yayi wannan furuci. Jinshan yace, "to shi shamharu ya aka yi ya shahara har ma yake bin hanyar zama MATSATSUBIN? Duk abin da yayi ya shahara muma shi zamu yi domin ance sannu ba ta hana zuwa sai dai a dade ba'a jeba." Koda jin haka sai Samaratu ta sake tuntsirewa da dariya a karo na biyu tace, "haƙiƙa na fuskanci kuna neman zautuwa shin kun manta ne cewa shi SHAMHARU aljanine ba mutum kamar ku ba. Ku tuna fa sai da shafe ɗaruruwan shekaru yana tara ilmin tsafi sannan ya shahara. A cikinku nan waye zai iya daɗewa a duniya kamar yadda ya daɗe? Waye zai iya zuwa wuraren da ya je? waye zai iya jure irin wahalar da ya sha? Tabbas ni kaɗai ce a cikinku nake da damar zama MATSATSUBIYA sai kuma ɗana gashi tunda mun kasance aljanu kamar boka Shamharu." Ko da jin wannan batu sai jikinsu boka Jinshan ya yi sanyi suka yi shiru ba su ƙara cewa uffan ba. Markahul Sabus ya yi ajiyar zuciya cikin alamun matuƙar damuwa ya dubi mahaifiyarsa Samaratu yace "ya ke Ummina ki yi sani cewa ni yanzu babu abinda ya dame ni face batun masoyiyata gimbiya Sima. Tabbas idan ban mallaketa ba zan iya haɗiyar zuciya na mutu. Yanzu gashi yau kwananmu biyu a cikin kejin nan aljani Durfus ya zo ya ce damu zai dawo don ya ji ta bakinmu har yanzu shiru ba mu ƙara ganin sa ba,anya kuwa lafiya? Ni kam na fara tunanin ko shima ya faɗa hannun aljani Rafkanagu." Samaratu tace "Komai zai iya faruwa amma abin da nake so da kai ɗana shi ne ka sa a ranka cewa in dai ina numfashi a doron ƙasa sai na mallaka maka Gimbiya Sima ko ta halin ƙaƙa. In.kuwa kaga baka mallaketa ba, ba na raye a duniya." Lokacin da Markahul Sabus ya ji wannan batu na mahaifiyarsa bokanya Samaratu sai farin ciki ya baibayeshi ya rungumeta yana mai fatan su samu damar kuɓuta daga cikin wannan tsafaffen keji. Suna cikin wannan hali ne suka ga aljani Durfus ya bayyana gabansu jina-jina, duk jikinsa raunuka ne, sai numfarfashi yake kamar ba zai rayu ba. Cikin ƙarfin hali ya dubesu yace, "Ku yi sani cewa yau kwana biyu kenan ina tafka yaƙi da wasu dakarun boka SHAMHARU waɗanda ya turosu su hallaka ni. Da ƙyar da siɗin goshi na samu na karkashesu, ko ɗayansu ban bari ya tsira ba. Nayi bincike na gano cewa rayuwata da taku na cikin mugun haɗari don haka dole ne mu haɗa kai idan har muna son mu ga bayan wannan babban maƙiyi namu wato SHAMHARU SHAHARARRE." Yayin da Durfus yazo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya dubeshi yace, "To yanzu yaya batun sharaɗin daka gindiya mana?" Darfus ya yi murmushin ƙarfin hali yace, "Ka bar wannan magana yanzu. Abin da nake so da ku shine ku saki jiki dani zan tafi da ku izuwa fadar tsafin a can ne zan iya fito daku daga cikin wannan keji sannan sai mu tattauna akan hanyar da zamu ɓullowa al'amarin." Ko da jin haka sai murna ta kama su boka Sulbaini. Gaba ɗaya suka amsa da cewar sun amince da wannan shawara. Ba tare da ɓata wani lokaci ba aljani Durfus ya suri tsafaffen keji sannan ya buɗe fukafukansa ya yi sama. Cikin daƙiƙu kaɗan ya ƙule a cikin sararin samaniya. Aljani Durfus bai iso fadar tsafinsa ba sai bayan yayi tafiyar sa'a bakwai sannan ya sauko ƙasa ya dira a wani baƙin daji mai dogayen tsaunuka da dogayen bishiyoyi. A gaban wata mitsitsiyar bishiya ya dira, a jikinta akwai wani mitsitsin rami wanda saboda ƙanƙantarsa ko allura aka zura a ciki ba za ta shige ba. Nan take Boka Durfus ya shafi tsafaffen keji, da shi da kejin da mutanen dake cikin kejin duk suka zama siriririn farin hayaƙi. Hayaƙin ya dinga shiga cikin wannan mitsitsin rami na bishiyar har ya ƙule gaba đaya. Ba zato ba tsammani sai su Samaratu suka tsinci kansu a cikin wata tangamemiyar fada wadda aka ginata da zunzurutun đanyen gwal. Ko ina ka duba abubuwan al'ajabi ne iri-iri birjik ba adadi. Boka Sulbaini ya ƙarewa fadar kallo tsaf ya tuna tasa fadarsa wacce ya ke taƙama da ya ga cewa wannan fadar ta ninka tasa sau arba'in a komai don haka sai ya sallamawa Durfus. Cikin alamun karayar zuciya ya dubi Durfus yace "Ya kai Durfus haƙiƙa yanzu na tabbatar da cewa ka taka babban matsayi a harkar tsafi. Ko da yake ban yi mamaki ba domin ai dama almajiri na iya fin malaminsa wata rana." Yayin da ya ji wannan batu na tsohon maigidansa sai ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Ya shugabana ai kun yi sake đan zaki ya girma. Koda yake dole ne na girmamaka a matsayinka na ubangidana na da shi ya sa ma na yi kiranka shugabana domin sai ɗan halak ke tuna alheri. Haƙiƙa na ƙaru sosai da kai to amma fa abin da na sani a hallarar tsafi ba ka san kaso ɗaya daga goman sa ba." Ba tare da ƙara cewa komai ba sai ya ɗebo waɗansu garin hoda kala uku ja, fari da shuɗi ya zuba su a cikin wani kasko sannan ya ɗebo wani tafasasshen ruwa ya zuba a ciki. Nan take wannan gari kala uku ya cakuɗa kansa ya rikiɗe ya zama tiriri. Shi kuwa tiririn sai ya lulluɓe wannan tsafaffen keji wanda su Markahul Sabus ke ciki. Kawai sai kejin ya narke ya zagwanye ya ɓace ɓat. Tiririn ya sake lulluɓe jikin su Markahul Sabus waɗanda sun kasance yan ƙanana mini-mini. Kawai sai kowannensu ya dawo izuwa ainihin siffarsa,cikin tsananin farin ciki suka gurfanar da kansu gaban Alhaji Durfus kuma cikin haɗin baki suka ce "Mun sallamaka maka ya shugabanmu. Bamu da abin yi face bin umarninka, yanzu menene abin yi?" Aljani Durfus ya ƙyalƙyale da dariyar mugunta sannan ya haɗe fuska yace, "Kamar yadda na faɗa muku a baya dole ne mu haɗa kanmu idan muna son mu sami nasara akan Shamharu. Abu na farko dole ne mu dawo kan batun mallakar littafin KUNDIN TSATSUBA na biyu wanda ke tare da Rafkanagu. Kun sani cewa ba zamu mallakeshi ba har sai mun mallaki abubuwan nan uku wato Tsumin Dodo Kirayanu, aljani Rafkanagu da kuma makamin farko wanda aka ƙera a duniya wato tsafaffiyar adda ce dake ajiye a fadar boka SHAMHARU wacce ke can tsibirin Bahar Zus. Amfanin aljani Rafkanagu a wajenmu shine mu tsafeshi ya je da kansa ya sato mana wannan adda to amma fa bincikena ya nuna min ccwa yanzu ba zamu iya mallakar aljani Rafkanagu ba, domin shirinsa ya fi namu. Aljani ɗaya ne rak a duniyar nan wanda zai iya zuwa fadar SHAMHARU ya sato mana wannan adda. Ba wani bane face aljani Balbus Sarkin ɓarayin aljanu. Shi kuwa Balbus yana zaune a can wani jeji da ake kira Zarwal a ƙarshen birnin Hindu. Tabbas zai iya zuwa tsibirin Bahar Zus a cikin kwana arba'in kuma zai iya shiga tsibirin Bahar Zus a cikin kwana arba'in kuma zai iya shiga cikin fadar SHAMHARU ya sato wannan adda. To amma fa ku sani ƙarfi ko tsafinmu ba zai iya tilasta Balbus ba akan ya yi mana wannan aiki face mun yi masa alƙawarin wani abu guda đaya wanda ya gagareshi mallaka shekara shekaru. Wannan abu ba komai ba ne face wani kambu dake jikin hannun Sarki Lu'umanu na birnin Teheren. Balbus ya san cewa idan ya mallaki wannan kambu zai iya sace gaba dayan dukiyar sarakunan duniyar nan ya ɓoyeta a wajensa ya zamana babu wani attajiri kamar sa. Yayin da Durfus ya zo nan a zancensa sai Markahul Sabus ya daka masa harara yace, "amma ka ɓata rawarka da tsalle. Haƙiƙa baka san waye sarki Lu'umanu ba, shi yasa kake zaton zaka iya mallakar kambun." Durfus ya ce dakata ai nasan ba zan iya mallakar kambun tsafinsa ba, amma kuma ai zan iya yaudarar Balbus ya gamsu cewa zan iya ɗin, indai buƙatar mu ta biya ai shike nan tunda munfi ƙarfin kowa a sannan babu yadda Balbus ɗin zai yi da mu yi shirin kwana biyu sannan mu tafi jejin zarwal domin ganawa da aljani Balbus, kar ku sami damuwar komai, ni ina tabbatar da cewa zamu samu nasara akan sa." Wannan shine abin da faru tsakanin aljani Durfus da su aljani Markahul Sabus bayan ya kuɓutar da su daga cikin tsafaffen kejin aljani Rafkanagu. (Matsalar page,yazo a blank amma dai zan iya summarizing nasa). ***************************************** A can fadar sarki Dujalu kuwa,bayan kuyanga ta kawo shayi an zubawa kowa ya sha,sai Ruziyal da boka Hajarul makurus suka yi gyatsa tamkar waɗanda suka ci nama suka ƙoshi. Boka Hajarul makurus ya dubi sarki Dujalu yace, "Ya kai wannan sarki mai tarin hikima,kayi sani cewa haƙiƙa yanzu ma mun sake jijjige gajiyar da take jikinmu,kuma babu yunwa ko ƙishirwa a tare da mu ko kaɗan. Don haka sai ka fara bamu labarin/hikaya ta uku mu ji abin al'ajabin dake cikin ta." Sarki Dujalu yayi murmushi sannan ya dubi tsoho Rafkangu,shima tsoho Rafkangu sai ya girgiza kai alamun ya gamsu da shayin da ya sha yace, "Tabbas nima na ji abinda sauran 'yan uwana suka ji a jikin su." Sarki Dujalu yayi gyaran murya sannan yace, "To sai ku kimtsa, kai mai rubutu ka aza alƙalamin ka akan takarda domin wannan hikayar da zan baku na ɗauke da matukar abubuwan jarumta,tausayi da kuma ban al-ajabi. Ni kai na ko tunowa nayi da labarin sai nayi kuka. Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira NAZMIR bin HALUFA da gimbiya LUZAIYA 'yar sarki FAHALUL BAHAFUS. Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu. Fatan alheri.Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part I A baya mun tsaya inda:- Hikaya ce ta wani kyakykyawan saurayi kuma jarumi wanda ake kira NAZMIR bin HALUFA da gimbiya LUZAIYA 'yar sarki FAHALUL BAHAFUS. ***************** A wani zamani can mai tsawo da ya shuɗe anyi wata babbar ƙasa wadda ake kira DUHAMUL. Wannan ƙasa ta bunƙasa a girma,arziƙi da kuma ƙarfin mayaƙa. A bisa wannan dalili ne ƙasar DUHAMUL ta shahara kuma ta zama Gagarabadau a cikin dukkanin ƙasashen kewayenta. Ya zamana ana matuƙar tsoranta. Sarkin da ke mulkin a wannan ƙasa ta Duhamul wani azzalumin sarki ne ana kiransa Bashakur. Sarki bashakur ba tsoho bane kuma ba yaro bane domin shekarunsa ba zasu gaza arba'in da huɗu ba zuwa da biyar. Saboda zalunci irin na bashakur ko a cikin garin nasa indai mutum bai shafi jinin sarauta ba ko kuma bai zamo ɗaya daga cikin attajirai ba to yana cikin tashin hankali,domin ba ka da 'yancin kan ka. Dukiyarka da matanka zasu iya zama na sarki a koda yaushe. Haka kuma ana ɗorawa talakawa haraji mai yawa ta yadda ko kaɗan basa morar arziƙin su baya ga wannan idan sarki bashakur ya bushi iska sai ya tura mayaƙa izuwa wata ƙasar ya basu izinin murƙushe ƙasar a kamo masa bayi kuma a ɗebo dukiya mai yawa. Bisa wannan halayya ne ya tara dukiya mai tsananin yawa wacce shi kansa bai san abin da zai yi da ita ba. A wannan zamanin na sarki Bashakur tsafi bai shahara ba a cikin al'umma. Babu abinda ke tasiri face ƙarfin damtse da ƙarfin yaƙi. Sarkin yaƙin wannan birnin na Duhamul wani tsoho ne ɗan kimanin shekara saba'in da shida wanda yayi suna a duniya saboda tsagwaran jarumtarsa da kuma iya yaƙinsa. A tarihin rayuwarsa bai taɓa jagorantar yaƙi an rasa nasara ba. Ana kiran sa da suna HALUFA. Da yake Allah ya kan yi mutane iri-iri kowa da hali dabam. Halufa ya kasance mutum mai tausayi da taimakon talakawa. Duk irin zaluncin da sarki Bashakur ke yi ba'a son ransa ba ne. Duk da kasancewar Halufa sadauki, kuma babban mayaƙi bai son ya ga ana cin zali, sau tari idan ya je yaƙi gari sai ya nemi sulhu da sarkin garin akan ya miƙa wuya ta lallami don bai son zubar da jini face bisa dole. Wannan halaiya ta Halufa na matuƙar baƙanta ran sarki Bashakur domin akwai wani lokaci kamar shekaru ashirin baya, wata ƙasa mai nisa bisa izinin ya yanko kan sarkin da na duk 'yan majalisarsa sai ya ƙi zartar da hakan. Kawai sai ya kamo su ya zo da su a ɗaure kuma ya kai su kurkuku a cikin dare. Yayin da sarki Bashakur ya sami wannan labari sai ransa ya ɓaci, ya harzuƙa ainun. A daren ya tura aka kirawo Halufa ya rufe shi da faɗa,sannan ya ce da shi lallai ya je ya fito da wannan sarki da jama'arsa ya sare musu kawuna kuma ya kawo masa kawunan yanzu. Cikin matuƙar damuwa yabi umarni ya tafi izuwa wannan kurkukun. Halufa ya tafi yana mai saƙe-saƙen zuci har ya sami dabara. Kafin ya ƙarasa kurkukun sai ya sauya kamanni yayi wata irin shiga ta baƙaƙen kaya ya naɗe fuskarsa da rawani in banda ƙwayar idanunsa ba'a ganin komai ba. Kawai sai ya zare takobi da isarsa kurkukun ya hau masu gadi da sara. Duk da cewar yawan masu gadin ya haura dubu sai da ya tarwatsa su da ƙarfin tsiya ya ɓalle ƙofar ɗakin da aka sanya wannan sarki da jama'arsa ya fito da su sannan ya nuna musu wata ɓarauniyar hanya ya ce su gudu. Sarkin da jama'arsa suka waigo suka dube shi cikin tsananin mamaki sai shi sarkin yace, "kai kuwa wane ne kai? Mene ne dalilin da yasa ka kuɓutar da mu?" Halufa ya cire rawanin fuskarsa suka yi arba dashi sai mamaki ya daɗa turnuƙe su. Ai kaine wanda ka je har cikin ƙasarmu ka cimu da yaƙi,kuma ka kamo mu da ƙarfin tsiya, to ya kuma yanzu ka kuɓutar da mu?" Halufa ya yi murmushi ga wannan sarki yace, ''Abin da ya sa na kuɓutar da ku shi ne bana son zaluncin da sarkina ke aiwatarwa. Ku yi sani cewa sarkina ya umarce nine da in je ƙasarku na murƙushe mulkinku kuma na yanko kawunan ku ba dan komai ba sai don bakwa yin biyayya ga umarninsa na haraji mai yawa duk shekara. Ni kuma da naje gareku sai na ƙi kashe ku na kamo ku nazo da ku aka kai ku kurkuku. Koda labari ya riski sarkina sai ya tura aka kirani ya rufe ni da faɗa kuma ya ce lallai yanzu a daren nan na zo na yanke kawunanku na kai masa. Maimakon na yi hakan ne na yanke hukuncin kuɓutar da ku. Yakai wannan sarki ka yi sani cewa ban kuɓutar da kai don komai ba sai don naga kana da wata 'ya ƙarama kyakykyawar gaske wadda kake matuƙar so itama kuma na fuskanci ta shaƙu da kai don haka ba zan so na zama sanadin raba wannan soyayya ba ta ɗa da mahaifi domin nima ina da ɗa wanda nake matuƙar so fiye da komai a rayuwata. Ba zan so a ce ya zama maraya tun yana ƙarami ba." koda Halufa yazo nan a zancensa sai ƙaunarsa ta mamaye zuciyar wannan sarki da jama'arsa. Dukkaninsu basu san sa'adda idanunsu ya ciko da ƙwallah ba. Nan take suka yiwa halufa godiya sannan suka yi bankwana dashi. Halufa ya kamo musu dawakai suka haye suka kama gabansu. Tafiyarsu keda wuya yayi sauri ya sauya kayan jknsa sannan yayi wa kansa raunuka a jiki ya koma gidan sarki. Koda sarki bashakur yaga jini na zuba a jikin Halufa sai ya miƙe zumbur ya tareshi cikin firgici yana mai cewa, "ya kai sarkin jarumai me ya faru gare ka?" Halufa yace, "ya shugabana ai lokacin da na isa kurkukun sai na iske mayaƙa dubu biyu sun afkawa masu gadi har sun buɗe ɗakin da aka kulle fursunoninka sun fito dasu. Koda nayi ƙoƙarina akan na hana su tafiya da fursunoninka amma sai abu ya gagara don kasan sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi. Da ƙyar ma na kuɓutar da kaina. Kafin na dawo cikin gari na nemi mataimaka tuni sunyi mana nisa." Koda jin wannan mummunan labari sai zuciyar sarki bashkur tayi baƙiƙƙirin ya cika da baƙin ciki kawai sai ta sallami Halufa ya shiga tunani mai zurfi. Daga can sai ya miƙe ya yi hawa ya tafi can kurkukun da kansa. Da zuwa ya iske masu gadin a kwankwance cikin jini magashiyan. Da ƙyar ya samu mutum ɗaya wanda bai raunata ba sosai. Sarki ya durƙusa gabansa ya cakumi wuyan rigarsa cikin tsawa yace, "wane ne ya zo yayi muku wannan ɗanyen aiki?" Mai gadin ya bude baki da kyar da ƙyar yace "ai wani mutm ne shi kaɗai cikin shigar baƙaƙen kaya ya zo ya tarwatsamu ya fito da fursunoninka ya kuɓutar dasu." Koda jin haka sai sarki bashkur yayi jifa da mai gadin yace, "wannan zancen banza ne duk faɗin ƙasar mahazus babu wani sadauki mai irin wannan jarumtarkar. Lallai ka tabbata maƙaryaci." Kawai sai sarki bashkur ya zare takobi ya fille kan wannan mai gadin. Nan take ya sake hawa dokinsa ya sukwane shi cikin fushi ya koma cikin gari. Da zuwa bai zame ko'ina ba sai gidajen manya mayankan garin yana tambayar su ko jarumi Halufa yazo neman taimakon su a cikin wannan daren bisa farmakin sumame da aka kaiwa kurkukunsa? Kowa sai yace shi ba a neme shiba hasalima yanzu yake jin labarin abinda ya faru. Yayin sarki bashkur ya gaji da yawan tambaya sai ya koma gd ya kwanta cikin tsananin baƙin ciki kashe gari da safe sarki bashkur ya tara dukkan 'yan majalisar sa ya sanar dasu duk abinda ya faru jiya da daddare kuma ya tabbatar musu da cewa shi kam yayi tunani kuma yayi bincike ya gano cewa ba kowanne ya aikata wannan mummunan aiki ba face jarumi Halufa. Nan take ya kawo hujjojinsa guda biyu hujja ta farko itace babu wani sadauki a gaba ɗaya wannan nahiya wanda zai iya tarwatsa barade dubu face jarumi Halufa. Hujja ta biyu itace halufa yayi masa ƙaryar cewa ya dawo cikin gari ya nemi taimakon wasu mayaƙan amma da aka tambaye su sai suka ce ba wanda ya nemi taimakonsu. Duk wannan bayani da sarki Bashakur yake Halufa na zaune gefe guda yana saurara kawai sai yayi shiru bai ce komai ba yana muzurai kawai. Sarki bashkur ya dubi fadawansa yace to kunji laifin da Halufa ya aikata don haka sai ku yanke masa hukunci da kan ku. Gaba ɗaya 'yan majalisar suka yi tsit aka rasa wanda zai ce wani abu. Daga can sai waziri yace, "ya sarkin sarakuna ai ni a ganina wannan hukuncin ba zai yanku ba yanzu muna buƙatar muyi zama na musamman." Koda jin haka sai sarki yace, "Ƙwarai kuwa nima na amince da wannan shawara." Suma sauran 'yan majalisar suka amince akan hakan. Daga nan fada ta watse kowa ya kama gabansa. Sai da aka shafe kwana arba'in ana mahawara a majalisa akan irin hukuncin da za'a yankewa halufa. A ƙarshe dai aka yanke masa hukunci cewa an dakatar dashi daga kan matsayin sa na sarkin yaƙi har tsawon shekara ashirin masu zuwa nan gaba. Kuma dukiyarsa aka raba ta kaso biyu aka ɗauki kaso guda aka raba wa masu gadin gidan kurkukun aka bar masa guda. Daga wannan rana Halufa ya cire hankalinsa daga harkokin fada gaba ɗaya ya maida nutsuwarsa akan ɗansa guda daya wanda suka haifa tare da matarsa Zuwaisa. Wannan ɗa an rada masa suna NAZMIR. Nazmir ya taso yaro mai kwarjini ƙwazo da basira ya zamana mahaifinsa na koyar dashi kyawawan ɗabi'u kuma yana koya masa juriya,jarumta da dabarun yaƙi. Nazmir ya shaƙu sosai da iyayensa domin dare da rana yana tare dasu kuma ko kaɗan baya son abinda zai ɓata musu, domin ya kasance mai tsantsar biyayya a gare su. Yayin da Nazmir ya cika shekara sha huɗu sai ya zamo jarumin gaske kuma farin jininsa ya yawaita tsakanin al'umar garin, saboda irin kyawawan halayensa na tausayi da jin ƙai da kuma biyayya ga na gaba dashi. A ɓangaren jarumta kuwa sai da yabar abin tarihi a kasar Duhamul domin shi kaɗai yake shiga daji ya yi farautar manyan dabbobin dawa masu haɗari. Sai dai aga yazo da gawarsu. Tun yana jarraba jarumtarsa a tsakanin sa'anninsa har ta kai cewa yana tunkarar manyan baraden ƙasar ɗaya bayan ɗaya. Duk wanda suka gwada yar ƙashi ko tsagwaron yaƙi sai ya sami galaba akan sa. Cikin ƙanƙanin lokaci labarin jarumi Nazmir ya yadu ko'ina a fadin ƙasar ya zamana ana zuwa ganinsa daga gari-gari. Shi kuwa Halufa da matarsa Zuwaisa suka kasance cikin tsananin farin ciki bisa wannan da Allah ya baiwa ɗan su. Lokacin da nazmir ya cika shekara ashirin a duniya sai kyawunsa ya ƙara bayyana a fili ƙarara. Jarumtakarsa ta ninka ta da ya zamana bashi da abokai sai 'ya'yan sarautar ƙasar amma da yake shi mutum ne na mutane mai sauƙin kai bai yar da wasu abokansa ba su shida waɗanda suka taso tun yarinta. Wandannan abokai gaba ɗaya 'ya'yan talakawa ne. Kuma dare da rana suna tare da Nazmir duk da cewa mahaifinsa yafi iyayensu arziki da ɗaukaka. Daga cikinsu akwai Sharhil, Bagwan, Hasuf, Iklam, Bardil da kuma Huzaik. A cikin su gaba ɗaya babu wanda yafi shaƙuwa da Nazmir sama da Huzaik domin maƙotan juna suke,gidan su Huzaik yana kallon gidan su Nazmir. Babu abinda ke raba su face kwanciyar baccí kai wani lokacin ma har musayar kwana suke,wato yau idan Nazmir ya kwana a gidan su Huzaik,kashe gari kuma sai Huzailk ya kwana a gidan su Nazmir. Dama mahaifin Huzaik yana zumunci sosai da Halufa. Sai dai tsoho ne tukuf don a ƙallah ya baiwa Halufa tazarar shekara goma sha đaya. Mahaifiyar Huzaik ta rasu tun yana jariri, a halin yanzu Huzaik ba shi da kowa a duniya face wannan mahaifi na sa wanda ake kira Marnush, kuma ko ƙuda bai son ya taɓa lafiyar Marmush ɗin. Huzaik yaro ne mai juriya da bajinta, amma ko kaɗan bai kama ƙafar jarumi Nazmir ba. Da yake an ce zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai. Shaƙuwar Nazmir da Huzaik ta sa shi ma Huzaik ɗin ya zama cikakken jarumi, kuma mara tsoro, domin duk sa'adda da Nazmir zai fita farauta jeji tare za su fita. Yayin da Halufa ya fuskanci amincin da ke tsananin Namzir da abokansa guda shida ya kai ainun sai ya rinƙa koya musu yaƙi tare ko yaushe. Haƙiƙa kowa da irin baiwar da Allah ya yi masa,Nazmir ya ƙware wajen iya sarrafa takobi matuƙa gaya, kuma duk ya fisu jarumta da juriya shi kuma Huzaik ya ƙware ne akan iya harbin kibiya, sannan ya kasance magujin gaske. Komai gudun dabba yana iya ƙure mata gudu ya harbota. Idan kuwa ka kabi bayansa da gudu to in dai ya baka rata har abada ba za ka kamo shi ba. Haka kuma yana da juriyar gudun don yana iya shafe sa'a goma yana gudu a cikin jeji ba tare da ya tsaya ya huta ba. Shi matsalarsa guda ɗaya ce indai babu ruwa a tare da shi ƙishirwa na galaɓaitar dashi nan da nan. Don haka wani lokacin ma yana cikin gudu yana shan ruwa abinsa. Shi kuwa Sharhil ya ƙware ne a fagen iya faɗa da mashi. Shi kaɗai yana iya shiga tsakiyar mutum đari ya tarwatsa su da mashi guda, ko da kuwa za su rufar masa da sara da harbi don yana da zafin naman iya kaɗe harbin kibiya kuma ya kare saran, idan kuwa ya taɓe ya harba mashinsa in dai ya caki bishiya komai kaurinta sai ya nutse a cikinta. Sharhil na iya cake mutumin da ke nesa da shi tsawon kamu ɗari uku daga inda yake tsaye. Husuf, Iklam, Bagwan da Bardil kuwa cikakkun mahaya doki ne,in dai suna kan doki komai yawan taron abokan gaba za su iya ratsawa ta cikinsu su yi ta sara da suka ba tare da an samu galaba a akan su ba. Haƙiƙa sun ƙware ainun akan yaƙin kan doki. A ranar da Nazmir ya cika shekaru ashirin cif a duniya, sai Halufa ya shirya masa walima,a wannan rana Zuwaisa ta sha ɗawainiyar girke-girke. Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu. Fatan alheri Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part D A baya mun tsaya inda; "Gulzum ya ciza leɓensa cikin tsananin baƙin ciki yayi takaicin ƙarewar kibiyar akan nau'urar,domin inda akwai sauran kibiya da guda ɗayar ma ba ta tsira ba. Dama kibiyoyin guda biyar ne kacal kuma an yi amfani da guda ɗaya sa'adda aka yi gwaji akan ƙatuwar bishiyar nan ta kuka. Koda aka ga babu sauran mutanen Galbasa sai mutane suka dawo cikin hayyacinsu. Nan da nan sarki Azbir ya sa aka tattare gawarwakin mutanen da aka shanye jininsu aka bunka musu wuta. A lokacin ne su Jafar suka farfaɗo daga doguwan suman da suka yi, suka ga sarki Azbir da jama'arsa sun taru a waje guda sunyi zugum-zugum suna kallom mutanen Galbasa guda huɗu waɗanda ke kwance kibiya ta tsire su har yanzu ba su daina kururuwa ba,kuma ba su fasa ƙoƙarin cire kibiyoyin ba, amma sun kasa. Koda Jafar ya ga ana ƙona gawarwaki sai ya ruga gaban sarki Azbir yace, "Yakai wannan sarki ina dalilin ƙona waɗannan gawarwakin?" Sarki Azbir yace, "Ashe ka manta da bayanin da na yi muku tun a farko. Ai idan ba mu ƙone su ba,suma zasu zama irin mutanen Galbasa ne su zoƙe mana jini." Azbir ya dubi Mashrila ya ce, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan mutanen Galbasan waɗanda ba su mutu ba, kuma ba su kasance rayayyu ba, tun da ba za su iya tsinana komai ba?" Mashrila ta yi ɗan jim, ta ce, "Babu abinda zamu iyayi akan su face sa ido domin zamu iya aikata kuskuren da zai janyo su tashi." Azbir ya yi ajiyar zuciya, sannan ya sake duban Mashrila yana mai murmushi, yace, "Godiya gareki ya ma'abociyar hikima, haƙiƙa kin cece mu daga shairrin mutanen Galbasa. Yanzu zan bayar da umarni a shirya ƙasaitacciyar walimar girmamawa a gare ki,saboda wannan gagarumar nasara da kika kawo mana, kuma a wajen walimar ne zamu gabatar da babbar kyauta a gare ki da kuma ta Aljani Gulzum bisa ƙoƙarin da ya yi na harbo waɗannan mutanen Galbasa guda huɗu." Koda jin haka sai mutane suka ɓarke da shewa. Cikin hanzari Jafar ya kama mumbarin ya hau can sama, sannan ya ɗaga hannu sama. Take wurin ya yi tsit. "Ku yi sani cewa da ku da mu baƙin ku muna cikin mugun haɗari. Ku tuna cewa ɗaya daga cikin mutanen Galbasa ta tsere,kuma tabbas zata je ta sanar da Galbasa abinda ya faru ga 'yan uwanta. Shin bakwa tsammanin cewa Galbasa zai yi gagarumin shiri ya taho da kansa ya zo ya ƙarar da mu gaba ɗaya,tun da ya san cewa in ya ƙyale nan gaba ma za'a iya yiwa jama'arsa ɓarna?" Sa'adda Jafar ya zo nan a zancesa, sai hankalin kowa ya tashi aka fara kace-nace. Koda ganin haka sai sarki Azbir ya miƙe ya ce, "Yaku jama'ata haƙiƙa batun wannan yaro gaskiya ne,amma ina son kowa ya kwantar da hankalinsa domin kafin labari ya riski Galbasa sai nan da kwana bakwai. Kun ga ashe muna da isasshen lokaci na tunanin abin yi." "A'a ranka ya daɗe bamu da wani lokaci lallai tun daga yanzu ya kamata mu fara shirye-shiryen tunkarar gagarumin yaƙin da ke gabanmu." Koda jin haka sai sarki Azbir ya yi murmushi ya dafa kafadar Jafar, ya ce, "Yaro kar ka damu babu abin da zai faru." Nan take aka fara kaɗe-kaɗe da bushe-bushe, masu shirya walima kuwa suka tafi suka fara aiwatar da aikinsu. Jafar, Yelisa,Mashrila da Gulzum kowa suka yi zugum cikin tsananin damuwa. Ita kanta Mashrila da Gulzum kuwa waɗanda ya kamata su fara farin cikin walimar da aka shirya musu sai suka kasance masu taya su Jafar jimami. Wannan shi ne abin da ya faru ga su Jafar yayin da suka faɗa cikin wani gari shafi na goma sha biyu na KUNDIN TSATSUBA. Al'amarin macen nan guda ɗaya wadda ta tsira daga harin kibiyar nan wadda Mashrila tasa aka ƙera, wato ɗaya daga cikin cikon mütum biyar na Galbasa, wacce ake kira Darzil sai ta ƙara ƙaimi,taci gaba da tafiya a sararin samaniya, har tsawon kwanaki bakwai sannan ta iso fadar Galbasa. Sarki Galbasa na zaune bisa karagarsa ta mulki, fadawa sun kewayeshi, sai ga-Darzil ta faɗo gabansa tana haki da numfashi. Cikin fushi da zafin nama Galbasa ya cakumo gashin kanta ya kara fuskarsa daidai tata, ya ce, "Ke Darzil ina sauran abokan tafiyarki kuma ina mutane hamsin ɗin da kuka saba kawo mini a kowanne mako?" Cikin ƙarfin hali Darzil tace, "Ya shugabana ka yi sani cewa wannan karon sabon al'amari ya faru domin wasu baƙin shaiɗanun mutane sun bayyana a birnin Azbir har sun ƙera wata ƙatuwar kibiya wadda ta hallaka abokan tafiyata da ƙyar na tsira da rayuwata." Jin wannan batu sai Galbasa kwarara uban ihu, wanda ya sa fadar gaba ɗaya yin girgiza. Cikin tsananin fushi ya yi wurgi da Darzil tamkar yayi jifa da 'yar tsana,sannan ya ɗauko wani zagayayyen farin dutse ya shafa shi da tafin hannun sa. Nan take hoton abinda ya faru tsakanin su Darzil da su Gulzum ya bayyana. Galbasa ya ƙarewa su Jafar kallo tsaf ya jinjina kai sannan ya waigo ya dubi babban bafadensa Barzuzu yace, "Yakai Barzuzu ka yi sani cewa waɗannan baƙin mutane ba ƙananan shaiɗanu ba ne. Haƙiƙa mun fi ƙarfinsu to amma sun kasance masu matuƙar hikima. Lallai ina so ka je ka yi tunani akan yadda zamu iya hallaka wannan mugun makami da suka ƙirƙira domin mu, sannan mu yi gagarumin shiri mu je mu shafe garin gaba ɗaya yadda ko a tarihi ba za'a tuna da shi ba." Yayin da Barzuzu ya ji wannan batu sai yace, "Ya shugabanmu yanzu don wannan ɗan makamin na su guda ɗaya zamu yi gayya da shiri. Ai ina tabbatar maka da cewa ni kaɗai ma idan ka turani zan iya hallaka su, na ƙone makamin na su." Koda jin haka sai Galbasa ya yi murmushi ya ce, "Kai ƙaramin mayaƙi ne baka san tuggun yaƙi ba. Kar ka yi tsammani za su tsaya ne jira kawai,suma sabon shiri za su yi don sun tabbatar da cewa ba zan kasa ɗaukar mataki ba. Ka yi sani cewa waɗannan mutane sun karya mana darajarmu a wannan duniya tamu, domin fiye da shekaru dubu baya ba'a taɓa cinmu da yaƙi ba, don me za mu yi sakaci wasu mitsatsan mutane kuma baƙi daga wata duniyar su shigo har tamu duniyar su cimu da yaƙi. Lallai ka hanzarta yin abin dana umarce ka." Barzuzu ya sunkui da kai ƙasa, ya ce, "An gama." Barzuzu ya miƙe tsaye ya fice daga cikin fadar. Galbasa ya dubi Galadimansa ya ce, "Ya kai Hutum ka je kasa a yi shela a gari cewar ban ɗaukewa kowa wannan yaƙi ba, babba da yaro,mace da namiji. Lallai kowa ya fara shiri nan da kwana bakwai za mu ɗunguma ƙwanmu da kwarkwatarmu mu tafi birnin Azbir sai mun shafe garin gaba ɗaya, mun zuƙe jinin kowa da komai, kai ko tsuntsu guda ba zamu bari ba a garin face ya zama maye kamar mu." Hutum ya risina, ya ce, "An gama ranka ya daɗe." Nan take fada ta watse, kowa ya kama gabansa. Lokacin da sarki Galbasa ya shiga cikin gidansa zuciyarsa baƙin ƙirin take, kuma tana tafarfasa, kamar za ta faɗo ƙasa, sai ya iske matarsa Hatimal tare da kyakkyawar 'yarsa, Mazalish zaune sun yi jugum. Koda ganinsa sai Mazalish ta miƙe zumbur cikin yanayin damuwa ta tare shi, tana mai cewa, "Ya kai Abbana wane irn yaƙi ne ya taso mana haka har da za ka ƙi ɗaukewa kowa da kowa yaro da babba?" Koda jin wannan tambaya sai sarki Galbasa ya yi ajiyar zuciya, sannan ya ce, "Yake 'yata mafi soyuwa a raina, kin sani cewa a duniyar nan tamu kaf babu abin da nake so sama da ke, saboda tsananin son da nake yi miki ne ya sa na raba ƙarfina da tsafina na baki rabi-rabi. Kuma saboda tsananin son da nake yi miki ne na cire miki maita ya zamana ke kaɗai kika fita dabam da kowa a garin nan. To ki ƙara sani ke ma ɗin ban ɗauke miki wannan yaƙi ba,domin da na yi asarar wannan yaƙi gwara na rasaki. Asarar wannan yaƙi daidai take da asarar mulkina,ƙasata da al'ummata gaba ɗaya. Tabbas idan ba mu yi nasara a wannan yaki ba, shi kenan sai dai a tuno da mu a tarihi domin hatta ƙasar nan tamu shafe ta za'a yi." Yayin da sarki Galbasa ya zo nan a zancensa sai hankalin Hatimal da na Mazalish ya ƙara dugunzuma fiye da da. Nan take idanun Mazalish ya ciko da ƙwallah, ta dafa kafaɗunsa da hannu biyu tace, "Ya kai Abbana ka tuna cewa ni a iya sanina ban taɓa ganin jarumi mai tsananin ƙarfin damtse da iya yaƙi kamar ka ba. Haka kuma ban taɓa ganinbmashahurin matsafi irin ka ba, domin a matsayinka na bil'adama har takai cewa ka juye ka zama ruwa uku. Za'a iya kiranka aljani ko fatalwa ko maridi,domin ba ka mutuwa ko an kasheka tashi kake yi. Ga shi shekarunka a duniya sun linka irin na bil'adaman wannan zamani, don na tabbata kafi shekara dubu biyu a duniya. To don me wani mahaluƙi zai zo lokaci guda rana tsaka har ya firgitaka ka ce da jama'arka kowa ya fito da ki bacin ni a zatona kai kaɗai ma zaka iya tashin ƙasa guda ta bil'adama?" Sa'adda sarki Galbasa ya ji wannan tambaya daga bakin 'yarsa Mazalish sai ya yi shiru gami da sunkuyar da kai ƙasa, cikin yanayin damuwa, sannan yace, "Yake 'yata ki yi sani cewa kamar shekaru goma sha tara baya lokacin da ya rage saura shekara ɗaya a haifeki na yi wani dogon nazari a cikin bincikena na tsafi na gano cewa akwai wasu irin mutane da za su zo daga wata sabuwar duniya dabam su yaƙe ni har su cini da yaƙi. Tabbas ba wasu ba ne waɗannan mutane face waɗanda zamu tunkara yanzu. Ina tabbatar miki da cewa siffofinki irin na waɗannan mutane ne domin in kikai tunani duk a ƙasar nan babu mai ƙaramin jiki irin na ki. Babu irin ƙoƙarin da banyi ba akan na gano hanyar da zan bi na hallaka waɗannan mutane idan sun zo,amma na kasa. Da naga haka sai na ci gaba da bincike akan ya za'a yi na tsira da rayuwata idan sun zo ɗin, sai na gano cewa in dai ina son tsira saidai idan na haifeki na cire miki maita kuma na raba ƙarfin jikina da tsafina na baki rabi. Tabbas indai ina tare da ke zan kuɓuta. Haka kuma na gano cewa a sanadiyar wannan yaƙi ne zan rabu da ke rabuwa ta har abada, amma ban ga yadda zamu rabu ba." Ko da Galbasa ya zo nan a zancensa sai idanunsa suka kaɗa suka yi jawur, suka fara shirin zub da hawaye, ita kuwa Hatimal tuni ta fara kuka tun sa'adda ta ji batun ccwa za ta rabu da 'yarta. Mazalish ta rungume Galbasa tana mai rusa kuka, tace, "Yanzu in na rasaka ina zan sami uba kamar ka?" Koda ganin haka sai ita ma Hatimal ta ruga gare su ta rungume su gaba ɗaya tana mai taya su kuka. A can birnin sarki Azbir kuwa sai da aka kwana ana walimar farin cikin samun nasara akan mutanen Galbasa. Har aka ƙare walimar su Mashrila ba su saki jikinsu sosai ba, domin duba ɗaya za ka yi musu ka san cewa suna cikin damuwa, kai ko murmushin arziƙi ba sa iya yi, sai dai ka ga suna yaƙe. Ana ƙare walimar ne Mashrila ta ce babu wanda zai je ya kwanta sai dai a ci gaba da ƙera kibiyoyin nan da na'urorin harba su kuma ba za'a tsaida ba,dare da rana. Hakan kuwa aka yi domin sai da aka kwana shida ana wannan aiki har aka kai gacin ƙera kibiyoyi dubu ɗari uku da sittin da na'urorin harba su guda dubu ɗari shida da arba'in, wato dai na'urorin sun fi kibiyoyin yawa. Nan take aka ware mutane da yawa adadin yawan na'urorin aka koyar da su sarrafa na'urar da iya harba kibiya. Ba'a gama wannan shiri ba, sai a daren kwana na bakwai. Yayin da dare ya raba, mutane sun gaji saboda gajiyar wannan gagarumin aiki da suka sha fama a dalilin hakanne aka fara tafiya ana kwantawa. Mashrila,Jafar,Yelisa,Gulzum,sarki Azbir da manyan dakarun ƙasar kuwa basuje sun kwanta ba,duk sai suka hau kan na'urar harba kibiyoyi suka yi fako suna jiran farmakin mutanen Galbasa don sunsan ako yaushe suna iya zuwa. Da yawa daga cikin suma gyangyaɗi sukeyi, amma har gefin asuba basu ji motsin komaiba kuma kusan ko yaushe hankalinsu akan sararin samaniya yake, kai har gari ya waye rana ta buɗe sosai ba'aji komaiba ba aga komaiba, wannan tasa mutane suka fara sakin jikinsu,Karfan yazo gaban sarki Azbir ya ce "Ya shugabana ina ganin Galbasa da Jama'arsa sun tsorata damu baza su sake kawo mana hariba." Koda jin wannan batu sai sarki Azbir ya turɓune fuska yace, "Ashe baka da hankali to dakata na gayamaka kaji har abada karka saki jiki da abokan gaba komai shirinka da ƙarfin ka. Kai a tsammanika don munyi musu ɓarna zasu ji tsoronmune su daina zuwa. Dubi canfa kagani mutanen sune guda huɗu tsire da kibiyoyi a kwance,har yanzufa da ransu motsi sukeyi inda zasu iya cire kibiyoyin jikinsu da tuni sun halakamu, ina tabbatar maka da cewa tuni labari ya isarwa Galbasa kuma tabbas zaiyi shirin ɗaukar fansa. Babu mamaki yana kan hanyarsa ta kawo mana mamaya.........." Kafin Karfan ya ƙara buɗe baki yace wani abu sai suka ga wasu abubuwa acan ƙololuwar sama kamar tsuntsaye. Saboda yawansu sun lulluɓe saman wajen gaba ɗaya har sun dusashe hasken rana kuma sun tsaya cak su ba su sauko ƙasa ba kuma basu ƙara yin samaba,nanfa kowa ya ɗaga kansa sama hankali ya dugunzuma kowa ya fara faɗin albarkacin bakinsa,wasu suce ai tsuntsaye ne wasu kuma suce wannan dai wata sabuwar masifarce, cikin tsawa mashrila tace, "ku shashashai ku nutsu kowa ya ɗana kibiyarsa, waɗancan abubuwan da kuke hangowa ba komai bane face gungun dakarun Galbasa." Anan zamu dakata, sai wani lokacin idan Allah ya kaimu. Fatan alheri.Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part J A baya, mun tsaya a inda:- A ranar da Nazmir ya cika shekaru ashirin cif a duniya, sai Halufa ya shirya masa walima,a wannan rana Zuwaisa ta sha ɗawainiyar girke-girke. #### In ba don ma ta sami taimakon ƙawayenta ba iyayen su Husuf da aikin yafi ƙarfin ta, gaba ɗaya 'ya'yan sarakan garin sai da suka halarci wannan walima. Kai daga wasu ƙasashen ma haka 'ya'yan sarakai suka yi ta shigowa cikin birnin Dahamul duk da cewa kuwa da yawansu ba gayyatarsu aka yi ba. Kawai sunzo ne don su ga jarumin da labarin sa ya cika duniya wato Nazmir bin Halufa. Yayin da taro yayi taro sai jarumi Nazmir tare da abokanansa suka yi ta gaisawa da baƙi ana bashi kyaututtuka,kai har saida ya gaji da karɓar kyaututtukan ya wakilta su Huzaik suka cigaba da karɓa. Nan take aka shigo da kayan ciye-ciye da shaye-shaye,makaɗa da mawaƙa kuwa suka hau aikinsu. Nazmir ya koma inda iyayensa ke zaune cikin farin ciki suma abokansa suka koma gefe guda ana kallon masu yin rawa. Anan cikin tsakiyar wannan shagali ne aka hangi sarkin dogarai ya shigo wajen kai tsaye riƙe da wata takarda a hannunsa. Nan take wurin yayi tsit kowa ya ƙame tamkar babu mai numfashi a wurin kai kace mutuwa ce ta gifta. Sarkin dogarai ya ƙaraso gaban Halufa ya risina ya kwashi gaisuwa sannan ya miƙa masa takardar yace, "saƙo ne daga majalisar sarki." Koda Halufa ya karɓi takardar sai ya miƙawa Nazmir ba tare da ya duba ta ba yace, "ya kai ɗa na buɗe takardar nan ka karanta abinda ke ciki a fili mu ji." Cikin biyayya Nazmir ya buɗe takardar ya fara karantawa kamar haka:- "DAGA MAJALISAR BIRNIN DUHAMUL ZUWA GA SARKIN YAƘI,JARUMI UBAN JARUMAI, SADAUKI HALUFA. YA KAI GARKUWAR MUTANEN DUHAMUL KAYI SANI CEWA HAR KWANAN GOBE WANNAN MAJALISA NA ALFAHARI DA KAI A MATSAYIN KA NA SARKIN YAƘIN TA DON HAKA GAISUWA,YABO DA KARAMCI SU TABBATA A GARE KA, KAMAR YADDA KA SANI CEWA SHEKARUN BAYA AN SAUKE KA DAGA KAN AIKIN KA HAR TSAWON SHEKARU ASHIRIN. TUN DAGA WANNAN LOKACI KAWO IYANZU BA'A NAƊA SABON SARKIN YAƘI BA. MAJALISA NA SANAR DA KAI CEWA WA'ADIN DA AKA ƊIBAR MAKA YA CIKA DON HAKA ANA UMARTARKA DAKA DAWO BAKIN AIKI. DA FATAN ZAKA KASANCE MAI BIYAYYA GA MAJALISA." Yayin da Nazmir ya gama karanta wannan wasiƙa sai ransa ya harzuƙa,har ya yunƙura zai yayyaga takardar sai Halufa yayi masa wani irin kallo. Nazmir ya ajiye takardar a gefe guda shi kuwa Halufa sai ya dubi sarkin dogarai yace, "kaje ka sanar da majalisa cewa saƙo ya zo mini kuma gobe da safe zan hallara a fada." Sarkin dogarai yayi godiya ya fita cikin farin ciki. Shi kuwa Halufa sai ya bayar da izinin a cigaba da walima. Take wuri ya sake hautsinewa da hayaniyar kaɗe-kaɗe da raye-raye. Ba'a gama walimar ba sai da duhu ya fara sannan baƙi suka fara yin sallama suna bankwana ɗaya bayan ɗaya. A haka dai wuri ya ɗaɗe aka bar su Halufa kaɗai. Nan take halufa ya koma kan kujera ya zauna sannan ya umarci su Nazmir da su zauna. Dama Zuwaisa na can gefe ɗaya a zaune. Halufa ya dubi Nazmir yace, "ya kai ɗana haƙiƙa na fuskanci zuciyarka ta sosu sa'adda saƙo yazo mini daga majalisa. Lallai ina son ka yayyafawa zuciyarka ruwan sanyi." Yayin da Nazmir yaji wannan batu sai yace, "ya abbana ai dole ne zuciyata ta sosu domin ban ga dalilin da zai sa majalisa ta buƙace ka ba yanzu,alhalin ta wulaƙanta ka a lokacin da kake ganiyar sharafinka wace gwaninta zaka iya yi mata a halin yanzu da tsufa ya riske ka wacce ba ka yi kamarta ba abaya." Halufa yayi ajiyar zuciya yace, "yakai ɗana haƙiƙa kayi tunani mai kyau nima kuma jikina ya bani cewa lallai akwai babbar buƙata da ta tasowa sarki wadda dole sai da taimakona zata biya shi yasa aka neme ni." Huzaik yayi murmushi yace, "abba ni kam ina ganin babu wata buƙata kawai ana so a yaudare ka ne a tura ka wani wurin inda zaka hallaka don a bayar da sarautar ga wani." Halufa yayi murmushi yace, "a'a ina ganin ba haka bane koma dai mene ne nayi mku izini gobe da safe ku zo ku duka kuyi mini rakiya zuwa fadar domin ku gani kuma ku ji komai da kunnenku." Da wannan furuci ne Nazmir da abokan sa suka yi sallama suka bar Halufa da Zuwaisa zaune su kaɗai a harabar gidan. Zuwaisa ta dubi Halufa tace, "ya kai miji na kayi sani cewa ni da kai duk tsufa ya riskemu ga shi ɗan mu guda ɗaya ne kacal a duniya, saboda me za ka ja shi izuwa fada alhalin tun da yake bai taɓa zuwa fadar ba. Shin baka tsoron ya zama bawan azzalumin wanann sarki namu?" Yayin da Halufa ya ji wannan batu na Zuwaisa sai hankalinsa ya dugunzuma ya yi shiru bai ce da ita komai ba, har tsawon lokaci. Daga bisani sai ya miƙe tsaye ya juya mata baya yana mai cewa. "Yake matata ki yi sani cewa ko mun so ko mun ƙi dole ne mai rabawa ta raba mu da ɗan mu domin tsufa da mutuwa aminnan juna ne. Zuwan Nazmir fada ɗaukaka ce a gareshi amma kuma wata sila ce da za ta iya zama sanadiyar rabuwarmu da shi ta har abada." Koda Halufa ya zo nan a zancensa sai ya juya suka haɗa idanu da Zuwaisa kawai sai ya ga hawaye na zuba a idanunta. Nan da nan shi ma zuciyarsa ta karaya, idanunsa suka ciko da ƙwallah. Zuwaisa ta miƙe tsaye suka rungume juna, suna kuka tana mai cewa, "Haƙiƙa mafarkina ya zama gaske, ranar da nake tsoron ganin zuwanta ne ya yi." Kashe gari fadar sarki Bashakur ta cika maƙil da jama'ar gari,domin tuni labari ya bazu cewa yau ne sarkin yaƙi jarumi Halufa zai dawo kan kujerarsa ta fada. Sarki Bashakur na zaune fadawa sun kewaye shi, yana mai tunƙaho da ƙarfin mulkinsa sai ga sadauki Halufa ya shigo, jarumi Nazmir tare da abokansa guda shida na take masa baya. Koda ganinsu sai sarki Bashakur ya ƙarewa Nazmir kallo sama da ƙasa, ya ga irin halittar da Allah ya yi masa ta kyau da surar jarumta, sai ya cika da ɗumbin mamaki domin bai taɓa ganinsa ba sai yau kawai dai yana jin labarin bajintarsa ne amma bai taɓa sha'awar ya sa shi a idonsa ba saboda kishi da girman kai irin na sarakai. Koda zuwan su Halufa sai suka risina a gaban sarki suka kwashi gaisuwa. Sarki Bashakur ya karɓi gaisuwar yana mai farin ciki da nuna walwala yace, ''An gaisheka sarkin yaƙi kuma muna murna da ka amsa kiranmu da gaggawa muna fatan ka karɓi abin da muka dawo maka da shi bayan ka rasa shi tsawon shekaru ashirin baya." Cikin nutsuwa sadauki Halufa ya yi gyaran murya ya ce, "Ya sarkin sarakai haƙiƙa na yi farin ciki da wannan saƙo, to amma ina da uzuri guda,ina son sarki ya dube ni da kyau don ya gane cewa jiya ba yau ba ce. Haƙiƙa yanzu tsufa ya riskeni, ba zan iya yin abin da na yi ba a shekarun baya. Ina neman alfarma da a baiwa ɗana Nazmir wannan sarauta a maimakona domin ya cancanta,kuma na tabbatar da cewa zai iya yin abin da yafi wanda na yi." Koda jin wannan batu sai sarki Bashakur ya tuntsire da dariya, sannan ya ce, "Ai shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama, domin dama akwai wani gagarumin aiki da ya taso don biyan wata muhimmiyar buƙata tawa. Ya yarda zan baiwa ɗanka sarautarka amma sai bayan ya je ya biya mini buƙata ya dawo cikin nasara. Yana dawowar zan sa a shirya bikin naɗa shi wannan matsayi na sarkin yaƙin ƙasata. Idan kuwa ya kasa samun nasara zan kashe shi tun da ban ga amfanin đan da ya kasa gadon mahaifinsa ba. " Koda jin wannan batu sai jarumi Nazmir ya dube sarki Bashakur ido da ido ya ce, "Na amince da wannan tsari kuma ina mai rantsuwa da darajar mahaifina kowacce irin buƙata ce kake da ita zan biyata, domin na nuna cewa na cika ɗan halak, ɗan da ya sha jarumta a nonon mahaifiyarsa." Koda jin haka sai fadar ta ruɗe da shewa ana yiwa jarumi Nazmir jinjina. Sarki Bashakur ya ɗaga hannu aka yi tsit. Sannan ya ce, "Nima na amince da hakan, shin akwai wanda zai ce wani abun?" Huzaik ya risina ya ce, "Ya sarkin sarakai ina son na roƙi wata alfarma da yawun abokan Nazmir." Sarki Bashakur ya yi murmushi ya ce, "Faɗi buƙatar ku na ji." "Muna son inda za ka tura Nazmir tafiya biyan buƙatarka a yi mana izini mu yi masa rakiya." Koda jn haka sai sarki ya ƙyalƙyale da dariya ya ce, "An yi muku izinin. Yanzu na sallame ku amma ku dawo nan fada gobe war haka cikin shirin barin ƙasarman don aiwatar da buƙatata." Da wannan furuci ne aka sallami kowa fada ta watse. Kowa ya kama gabansa. Tun da su Nazmir suka dawo gida ya kasance cikin tsananin damuwa har ma ya rufe su Huzaik da faɗa yana mai cewa, "don me zai jefa kan su a cikin wannan masifa. Ya sani cewa aikin da za'a tura shi ba ƙaramin bala'i bane,duk da cewar bai san mene ne ba, duk za su iya hallaka." Koda jin wannan batu sai Huzaik, Sharhil,Bagwan,Husuf,Iklam da Bardil suka haɗa hannyensu waje guda suka buɗe baki a lokaci guda suka ce, "Mun kasance abokan juna tun ƙuruciya mun shaƙu da junanmu kuma bama rabuwa komai ruwa komai iska. Ya kai Nazmir gamu mu shida da kai ne cikon na bakwai shin kana tare da mu ko kuwa za ka ware daga cikin mu ne?" Yayin da Namzir ya ji wannan jawabi daga bakin abokan sa sai zuciyarsa ta karaya idanunsu akan na su ya ce, "Ina tare da ku har abada,zumuncinmu da soyayyarmu ga juna ta ratsa jini da tsoka." Take suka rungume juna gaba ɗaya cikin kukan farin ciki. A wannan rana su jarumi Nazmir suka gama kimtsa kayansu don yin tafiyar da ba su san inda zasu je ba. Bayan sun tanadi dawakai da guzuri da kayan yaƙi, sai suka ɗunguma suka tafi gidan su Huzaik don yin sallama da mahaifinsa tsoho Marnush. Da shigarsu inda yake sai suka iske shi a zaune yana sharɓar kuka. Gaba ɗayansu sai hankalinsu ya tashi, suka durƙusa a gabansa, Huzaik ya kama hannayensa ya riƙe yana mai zubda hawaye ya ce, "Ya kai Abbana ina dalilin wannan kuka naka?" Tsoho Marnush yace, "Ya kai ɗana ka yi sani cewa kai kaɗai nake da shi a duniya, ga shi har tsufa ya riskeni ban ga auren ka ba. Yau dare ɗaya labari ya zo mini cewa za ku yi tafiya mai haɗari. Idan rayuwarka ta salwanta shi kenan, ba ni da kowa a duniya, in da za ka haƙura da wannan tafiya da hankalina yafi kwanciya." Huzaik ya kasa jurewa zuciyarsa bai san sa'adda ya fashe da kuka ba, yana mai cewa, "Ka yi haƙuri Abbana na rigaya na yiwa abokaina alƙawarin wannan tafiya. Babu abin da zai hanani yinta face mutuwa. Ina son ka kwantar da hankalinka ka sani cewa lallai zamu dawo gida lafiya,kuma zan zo maka da kyakkyawar sirika." Koda jin wannan batu sai tsoho Marnush ya rungume Huzaik a ƙirjinsa ya ƙara fashewa da kuka yana mai cewa, "Ina fatan abin da ka faɗa ya kasance." Bayan Huzaik ya gama ganawa da mahaifinsa sai kuma suka ɗunguma suka tafi, gidan su Sharhil. Da zuwa suka iske mahaifiyara Ushaiya wacce ta kasance makauniya mai kimanin shekaru sittin da shida. Suna shiga suka risketa ita ma tana kuka. Cikin hanzari Sharhil ya matsa daf da ita ba tare da sanin sun shigo ba. Koda ya durƙusa a gabanta ya taɓa gwiwarta sai tace, "Wane ne?" Maimakon ya bata amsa sai shima ya fashe da kuka,cikin sauri ta shafa fuskarsa da tafin hannunta ta ce, "Au ɗana ne,yaushe ka shigo ban sani ba?" Sharhil ya ɗago kai ya dubeta, idanunsa cike da hawaye ya ce, "Yake Ummina haƙiƙa na san kina kuka ne saboda samun labarin tafiyar da zan yi." Ushaiya ta share hawayenta ta ce, "Ƙwarai kuwa ai dole ne na yi kuka, ka tuna cewa tun dana haifeka ban taɓa ganin kamanninka ba, kuma taɓa rabuwa da kai ba tsawon kwana guda ba. Kai kaɗai gare ni a garin nan ga shì na kasance makauniya, tun sa'adda ka zama mutum ka ɗauke wahalar cina da shana, kuma ka kula da lafiyata. Yanzu idan baka nan waye zai samo mini abincin da zanci, ka sani cewa a yadda girma ya kamani ba zan iya yiwa kaina komai ba,kai ne gatana, in na rasaka na rasa komai, babu wanda zai iya taimako na in babu kai face abokanka to kuma ga shi na ji ance gaba ɗaya za ku yi wannan tafiya." Sa'adda Ushaiya tazo nan a zancen ta sai gaba ɗaya jikin su Nazmir ya yi sanyi, suka kamu da tausayinta. Sharhil ya ce, "Yake Ummina ina mai ƙarfafa miki ƙwarin gwiwa da ki kwantar da hankalinki ki, sani cewa ni da abokaina mun kasance jaruman gaske,don haka kowacce irin masifa da zamu shiga zamu dawo gida lafiya." Ushaiya ta rungume Sharhil sannan ta fashe da kuka tana mai cewa, "Na san kuna da jarumta amma ai ba ku san in da za ku je ba, da kuma abinda za ku tunkara." Haka dai su Sharhil suka yi ta lallashin Ushaiya har suka shawo kanta ta daina kuka,daga nan kuma suka tafi gidan su Bagwan. A cikin waɗannan abokai guda bakwai waɗanda suka taso tare kai ɗaya Bagwan ne kaɗai ya yi aure, koda yake ya yi aure da wuri sakamakon ya taso a matsayin maraya, domin tun bai fi shekara bakwai ba iyayensa suka yi haɗarin jirgin ruwa, suka rasu. Bagwan ya sha wahalar rayuwa domin tun yana ƙarami ya ke sana'ar dako, leburanci da sauransu don kawai ya riƙe kansa. Lokacin da ƙarfi ya zo masa sai ya yanke shawarar ya yi aure da wuri don ya sami zuri'a ya huce takaicin rashin dangi. Cikin dacewa ya gamu da wata budurwa mai suna Muslaiya wacce lokaci guda suka kamu da matuƙar ƙaunar juna. Muslaiya baiwa ce ta wani attajiri, wanda tsufa ya riske shi ainun amma yana da tarin iyali. Lokacin da attaiirin ya fahimci cewar Muslaiy na soyayya da Bagwan sai ya 'yanta ta ya yarje mata ta taje tayi aurenta kuma ya taimaketa lokacin aure. Bagwan suka zauna cikin kwanciyar hankali har tsawon shekaru biyu. A halin yanzu Muslaiya na dạ tsohon ciki wata takwas don haka kusan ko yaushe Bagwan na tare da ita, yana taimaka mata wajen aikace-aikacen gida. Batun soyayya a tsakaninsu kuwa tamkar yanzu suka haɗu da juna. Lokacin da su Nazmir suka isa gidan Bagwan sai suka iske Muslaiya zaune a ƙofar gida ta haɗa kai da gwiwa tana ta sharara kuka. Koda ta hango zuwan mijinta sai ta yunƙura ta miƙe tsaye da ƙyar ta nufo shi. Shi kuwa sai ya ruga gareta suka rungume juna kuma suka fashe da kuka. Muslaiya tace, "Yakai mijina abin dogarona, ka tuna cewa ni baiwace bani da kowa a garin na, yanzu haka za ka tafi ka barni da tsohon ciki, waye zai kula da lafiyata har na haihu? Na sami labarin cewa tafiyar da zaku yi mai haɗari ce, ba lallai ba ne ku sami nasara har ku dawo gida lafiya. Ya kai masoyina yanzu idan na rasaka shi kenan abin da zan haifa ya zama maraya kenan?" Bagwan ya janye jikinsa daga nata,sai ya sa hannayensa biyu ya share mata hawaye ya ce, "Yake matata ki kasance mai ƙarfin zuciya da kyautata zato na alheri, kisa a ranki cewa zan dawo lafiya kuma ki cigaba da yi mana fatan nasara. In kika yi haka nima zan sami ƙwarin gwiwar jajircewa iya yina don na tabbatar da dawowata." Muslaiya ta yi murmushin ƙarfin hali, ta ce, "Shi kenan zan yi duk yadda ka ce." Daga nan sai ta ɗaga kanta ta dubi jarumi Nazmir ta ce, ''Ya kai babban jarumi ina son ka yi mini wani alƙawari." Cikin mamaki Nazmir ya dubeta, yace, "Wane irin alƙawari kike son na yi miki?" Muslaiya ta taka ta matso daf da Nazmir suka fuskanci juna sosai, sannan ta ce, "Ina son ka yi iya ƙoƙarinka wajen kare rayuwar mijina yayin da kuka yi wannan tafiya idan kuma ƙaddara ta yi halinta na roƙe ka da k da ka bar mini gawarsa a jeji, lallai ka zo mini da ita, domin idan ɗansa ko 'yarsa ta taso ta ga kabarin mahaifinta." Yayin da suka ji wannan batu sai duk suka kama zubar da hawaye. Cikin ƙarfin hali Nazmir yace, "Na ɗauki wannann alƙawari, kuma komai tsanani zan cika shi in dai ina numfashi a doron ƙasa." Nan take suka yi mata sallama, sannan suka ɗunguma izuwa gidan su Husuf. Husuf ba shi da kowa face ƙanwa, kuma yarinya ce, wacce ba ta wuce shekara goma sha ɗaya ba, sunanta Lamiz. Tsiran sa da ita bai wuce shekaru tara ba. Tun Suhuf na da shekara goma sha huɗu mahaifiyarsu ta bar masa amanarta lokacin da ita mahaifiyar ta su take kwance cikin cutar ajali. Bayan rasuwar mahaifiyar ta su kuwa sai Suhuf ya ci gaba da kula da Lamiz ainun ko kaɗan baya yarda wani abu ya taɓa lafiyarta, kuma komai take so sai ya yi iyakar ƙoƙarinsa ya samo mata,kai tun a wannan lokaci Suhuf ne ya zamo tamkar uwa da uban Lamiz,domin shi yake mata wanka da wanki ya sa mata kaya, sannan ya ciyar da ita dare da rana. A kullum sai ya ga ta yi bacci lafiya, sannan shi ma ya kwanta har Allah ya raya su gaba ɗaya, suka kawo iyanzu. Sa'adda aka iso gidan sụ Suhuf tun da Lamiz ta hango su tun daga nesa don haka sai ta rugo da gudu gare su tana mai kuka. Koda ganin haka sai shima Suhuf ya ruga gareta ya ɖurƙusa ƙasa ta faɗa ƙirjinsa, suka rungume juną, sụna kuka tare. Al'amarin da ya ƙara jefa su Nazmir cikin tsananin tausayi da damuwa kenan, domin dukkaninsu sun san cewa irin shaƙuwar da ke tsakanin waɗannan 'yan uwa ta kai ainun,cikin shishshiƙar kuka Lamiz tace, "Ya kai yaya na me zai hana ku yi wannan tafiya tare da ni, domin idan har ka tafi ka barni anan ni kaɗai tabbas zan ji tamkar đaukeni ka kaini tsakiyar dokar jeji ne in da babu gida gaba da baya,ka sani kai ne gidana, kai ne jina da ganina, kuma kai ne numfashina, in babu kai babu rayuwa." Nazmir suka cika da mamakin hikimar zancenta a matsayin ta na yarinya ƙarama,kuma suka ƙara kamuwa da tsananin tausayinta,Husuf yace, "yake ƙanwata ki yi sani cewa ba zan iya yin wannan tafiya tare ke ba, saboda haɗarin da ke cikinta. Lallai zan barki a hannun iyayen abokina Nazmir tabbas za su riƙe ki amana kamar yadda nake kula da ke. Ina son ki kwantar da hankalin ki kisa a ranki cewa lallai zan dawo gida lafiya." Yayin da Lamiz ta ji haka sai ta janye jikinta daga na Suhuf sannan ta dube shi cikin nutsuwa tace, "Ya kai yayana na sani cewa iyayen Nazmir zasu kula da ni ainun amma kana tsammanin za su iya bani nutsuwa da kwanciyar hankali írin wacce ɗan uwa ke ji yayin da yake tare da ɗan uwansa na jini? Yayana ka sani cewa jini-jini ne na rantse da darajarka babu wani mahaluƙi da zai nuna mini soyayya a duniyar nan zuciyata ta yi fari face kai, ai kama da wane bata wane." Koda Suhuf ya ji haka sai jikinsa ya yi sanyi gaba ɗaya ya kasa cewa da ita komai. Kawai sai ya sake rungumeta, suka ƙanƙame juna, suna rusa kuka. Da ƙyar su Nazmir suka raba su sannan ya yi mata bankwana suka tafi suka barta tana mai ɗaga musu hannu, shi kuwa Suhuf yana waigenta hawaye na cigaba da kwarara a idanunsa. Har sun yi nisa sai Lamiz ta sake rugawa da gudu garesu. Da zuwa sai ta cire mayafin jikinta ta miƙawa jarumi Nazmir, shi kuwa sai ya karɓa cikin yanayin mamaki ya ce, "Mę zan yi da wannan?" Lamiz ta ce, "Ina son ka riƙe shi yayin wannan tafiya ta ku. Idan har yayana ya dawo a raye ka bashi mayafin nan ya dawo mini da shi, idan kuwa ya rasu a can ka ɗaura mayafin nan a gashinka." Tana gama faɗin haka ta sake fashewa da kuka, kuma ta juya ta ruga gida. A can gidan su Iklam kuwa sun iske mahaifinsa tsoho Kamshur wanda ya kasance gurgu mai ƙafa đaya, kuma shekarunsa sun haura casa'in yana iya tafiya ta hanyar dogara sanduna guda biyu waɗanda ke maƙale a hammatarsa hagu da dama. Kamshur shahararren mayaƙi ne a birnin Dahamul, kuma ya yi shahara a lokacin da sadauki Halufa ke kan sharafinsa Kamshur shi ne na biyu wato daga Halufa sai shi. Don haka sun kasance aminan juna. Anan zamu dakata, sai wani karon idan Allah ya kaimu. Fatan alheri.Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part K A baya mun tsaya inda:- Kamshur shahararren mayaƙi ne a birnin Dahamul, kuma ya yi shahara a lokacin da sadauki Halufa ke kan sharafinsa Kamshur shi ne na biyu wato daga Halufa sai shi. Don haka sun kasance aminan juna. ###### Kamshur ya sami wannan naƙasa ne a wasu shekaru can baya sa'adda sarki Bashakur ya tura shi kai sumame wani gari da ake kira Lamar. Lambar birni ne wanda waɗansu tsirarun fatake suka ƙirƙira,ƙasar ta kasance mai albarka domin akwai ni'imar ruwa da shuke-shuke kuma akwai daɗin faurata, saboda yawan dabbobin jeji. Bisa wannan dalili ne fatake ke ya da zango a wajen har ma suka fara zama. Da kaɗan-kađan kuma sai suka fara yawa har wajen ya zama mahaɗar cinikaiya. Shi dai wannan gari yana kusa da birnin Dahamul domin tsiransu bai wuce tafiyar kwana tara ba. Lokacin da sarki Bashakur ya sami labarin kafuwar wannan gari sai ya aiko musu da saƙon cewa su dunga kai masa haraji mai yawa, a duk wata guda. Su kuwa mutanen wannan birni sai suka karɓi saƙon hannu biyu amma sai da wata uku cur ya shuɗe basu aika da harajin ba. Wannan tasa sarki Bashakur ya fusata ainun ya aika jarumi Kamshur tare da wasu barade su ɗari uku akan cewar su je su rushe garin su kashe mazaje kuma su kamo bayi,a ɗebo ganima. Ashe lokacin da sarki ya bayar da wannan umarni akwai wani baƙo a wajen kuma ɗan wannan gari ne na Lambar. Nan da nan ya sulale ya hau dokinsa ya nufi birnin Lambar cikin tsananin sauri. Baƙon na isa ya sanarwa da 'yan uwansa abin da ake ciki. Nan fa suka fara tunanin abin yi domin sun san cewa kafin su tattara inasu-inasu su bar garin tuni mutanen sarki Bashukur sun iso. Bisa wannan dalili ne suka yi shirin yaƙi, kuma suka yi kwanton ɓauna, a bayan gari. Sai da su jarumi Kamshur suka shigo tsakiyarsu sannan suka farmusu da harbi. Daga bisani kuma suka afka musu da yaƙi. A wannan yaƙi an yi gagarumin gumurzu kuma daga cikin mutun ɗari ukun nan mutum goma sha biyu ne suka tsira da rayuwarsu, kuma jarumi Kamshur ne mafi sauƙin samun naƙasa da ya rasa ƙafa đaya, amma duk da haka sai da ya ci garin da yaƙi. Wani babban abin baƙin ciki shi ne lokacin da jarumi Kamshur tare da dakarunsa guda goma sha ɗaya suka dawo birnin Dahamul sai gasu ɗauke da tarin mata bayi da kuma ganima, mai yawan gaske,amma dukkanninsu sun zama naƙasassu. Daga wanda ya rasa ƙafa da hannu sai wanda ya rasa ido ko kunne. Koda isarsu fada sarki ya karɓi bayin gaba đaya ya sa aka kai su gidansa. Ganimar yaƙin kuwa aka zubata a baitul mali. Su kuwa su jarumi Kamshur aka yi musu ritaya daga aikin sojan sarki batare da an ba su wata kyauta ba, ko girmamawa bisa wannan gagarumin yaƙi da suka yi. Koda shigowar su Ikhļam turakar tsoho Kamshur sai suka iske shi a zaune yąna rusa kuka,kamar ƙaramin yaro. Cikin tashin hankali Ikhlam yaje gare shi yace, "Ya kai Abbana ka yi sani cewa tun tasowa ta ina ƙarami zuwa girmana ban taɓa ganin hawaye a idanunka ba, amma yąu ga shi kana rusa kuka, ina dalili?" Kamshur ya kama hannun Ikhlam ya riƙe da kyau, sannan ya ce, "Ya kai ɗana haƙiƙa zancenka gaskıya ne, amma ka sani cewa dole ne na yi kuka yanzu ba dan komai ba sai dan sanin cewa da ni da zuri'ata zamu gushe a banza cikin wannan babban birni kuma har abada ba za'a tuna da mu ba. Na san wannan bayani a dunƙule yake ba lallai ne fahimce shi ba. Ya kai ɗana ina so ne ka sani cewa na yi bauta ga sarki Bashakur tsawon shekaru, amma ga yadda ƙarshena ya kasance, wato cikin talauci,ƙunci da naƙasa. Kai kaɗai nake gani zuciyata ta yi sanyi, domin na san cewa ko na mutu na bar baya gashi an wayi gari kai ma ɗin an rabani da kai, kuma an saka ka a irin tafarkin da aka sani ka ga ashe ni da zuri'ar tawa mun gushe kenan har abadan abidina." Koda Kamshur ya zo nan a zancensa sai Ikhlam ya fashe da kuka, kuma ya rungeume Kamshur yana mai cewa, "Ya Abbana haƙiƙa ba zan yarda abin da ya same ka ya sameni ba. Lallai ni zan dawo gida lafiya, kuma sai na yì tsawon rai har na yi aure ka samu jika. Tabbas zan kafa maka zuri'a wacce za ta bar abin alfahari, kuma abin tarihi a doron ƙasa." Kamshur ya sake fashewa da kuka yana cewa, "Fatana kenan, kuma shi ne babban burina." Haka dai suka ci gaba da alhini har su Nazmir suka lallame shi suka tafi suka bar tsoho Kamshur in da ya ci gaba da kuka abinsa. Sa'adda suka isa gidan su Bardil sai suka iske mahaifiyarsa Yaluz, wacce ta kasance 'yar shekara arba'in da đoriya. Macece mai ƙwari da ƙarfin zuciya, sai dai ta sami naƙasa guda hudu. Abu na farko gurguwa ce. Gaba ɗaya ƙafafunta biyu a yanke suke iya gwiwa. Hannunta guda na hagu ya shanye, shi kuwa na daman yatsu biyu ne kacal a jikinsa. Da jan jiki take tafiya a harabar gidan, kuma da yatsun nan biyu kacal take iya yin komai. Koda shigar su Bardil sai Yaluz ta ɗago kai ta yi arba da ɗanta. Take idanunta suka kaɗa suka ciko da ƙwallah. Shi kuwa Bardil dama tuni ya fara zubar da hawaye. Kawai sai ya ruga gareta suka rungume juna, yana mai cewa, "Yake ummina ki kasance mai haƙuri da juriyar rashin ganina izuwa tsawon lokaci, har mu dawo daga wannan tafiya." Yaluz ta yi ajiyar numfashi, ta ce, "Ya kai ɗana ai haƙuri tuntuni a cikinsa nake, tun ma kafin na haifeka, kuma a cikinsa zan mutu. Ka tuna cewa an haifeni cikin ƙaddara shanyayyen hannu guda ɗaya, kuma ba cikakkun yatsu. Sannan kuma 'yan fashi suka zamo sanadiyar yankewar ƙafafuna biyu. Ai ko da wannan naƙasa guda huɗu aka barni ta ishe ni shan wahalar duniya da takaici. Yau sai ga shi kuma kai kaɗai da ka rage mini a duniya an rabani da kai. Waye zai ji ƙaina kamar yadda ka ke yi mini? Waye zai ci gaba da yi mini wahala ba tare da ya yi ƙyanƙyamina ba? Ai na ka sai naka tabbas ɗana in babu kai mutuwa zan yi domin takaicı ma kaɗai zai iya kashe ni." Koda jin haka sai Bardil ya sake fashewa da kuka, ya ƙanƙame Yaluz a ƙirjinsa yana mai cewa, "Ki daina kiran mutuwa. Tabbas ba zan tafi na barki a duniya ke kaɗai ba. Komai rintsi sai na dawo gare ki don na ci gaba da taimakon ki, ina kula da lafiyar ki." Yaluz ta ce, "Kaico! Ai bakin alƙalami riga ya bushe. Ya kai đana ka sani cewa nayi mummunan mafarki bisa wannan tafiya ta ku, tabbas an nuna mini cewa in ka tafi ba za ka dawo ba. Haƙiƙa yanzu muna yin bankwana ne,daga yau mun rabu kenan har abada." Koda jin haka sai gaba ɗaya hankalinsu Nazmir ya dugunzuma suka fashe da kuka, domin Bardil ya sha gaya musu ire-iren mafarkin da mahaifiyarsa ke yi, kuma mafarkin ya sha tabbata a gaske suna gani ko sau ɗaya ba'a taɓa samun saɓani ba. Bardil da Yaluz suka ƙara ƙanƙame juna, suka yi ta kuka har tsawon lokaci, sannan suka rabu. Daga nan kuma su Nazmir suka sake ɗunguma su bakwan suka tafi gidansu Halufa. Anan ne Halufa da Zuwaisa suka yi bankwana da ɗan su Nazmir inda suka yi musu fatan alheri da nasara,kuma Halufa ya ƙara tunasar da su irin abubuwan da ya kama ta su kiyaye yayin da suke yaƙi ko kuma suka fuskanci bala'i. A ƙarshe dai Halufa na kuka, suma su Nazmir suna yi aka rabu kowa ya je ya kwanta,domin a lokacin dare ya raba. Babu sauran abin yi sai jiran wayewar gari a tunkari fada don wannan gagarumar tafiya. A yau fadar ta cika ta batse, an yi mugun gangami irin wanda ba'a taɓa irin sa ba,kai ka ce gaba ɗayan mutanen ƙasar ne suka hallara babbba da yaro, mace da namiji. Idan ka duba tsakiyar fadar babu abin da za ka gani face jarumi Nazmir da abokansa guda shida, a tsaitsaye kuma a jere cikin shigar yaƙi. Kai da ganinsu ka san cewa manyan barada ne waɗanda za su iya shafe gari guda,sun kasance masu matuƙar kwarjini da ban tsoro. A can sama kan tudu inda karagar mulki take sarki Bashakur ne a zaune yana murmushin ƙeta, dakaru da fadawa sun kewaye shi, sauran jama'ar gari kuwa sai hayaniya suke kowa na faɗin albarkacin bakinsa,fadar ta cika da hayaniya. Kawai sai sarki Bashakur ya ɗaga hannunsa sama take fadar ta yi tsit kamar babu wani abu mai rai a wajen. Saboda tsoro da biyayya a gare shi. Bashakur ya miƙe tsaye yana mai murmushi,ya tako da ƙafafunsa takan matattakalar da ke gaban karagarsa ya sauko ƙasa, inda su jarumi Nazmir ke tsaye. Sannan ya dube su daya bayan ɗaya, ka ƙare musu kallo kawai sai yace, "Yaku waɗannan zaratan samari haƙiƙa na gamsu cewar za ku iya aiwatar da wannan aiki mai muhimmanci, kuma kun fto da kyakkyawan shiri. Duk da haka zan ƙara muku ƙarfi ta hanyar baku barade dubu goma domin duk yadda kuke zaton wannan aiki yafi haka. Wannan aiki ba komai bane face ina son ku tafi izuwa wani birni da ake kira Mahazus ku ɗauko mini 'yar sarkin garin ku kawo mini ita nan don na aureta. Ita dai wannan 'yar sarki sunanta gimbiya Luzaiya. Masu bincike sun gano cewa a halin yanzu duk duniya babu wata 'ya mace kyakkyawa kamarta ku sani cewa tsakanina da mahaifin gimbiya Luzaiya tsohuwar gaba ce wacce samo asali fiye da shekaru ashirin baya. Tun a wancan karo na so na ga bayansa amma ban sami iko ba. Saboda ni san da ke tsakanin ƙasa ta da ta sa,domin tafiya ce ta wata bakwai, da kwana tara. A halin yanzu wannan sarki ya ƙara bunƙasa ainun a ƙarfin mulki da ƙarfin mayaƙa, kuma a duniya babu abin da yake so sama da wannan 'ya tasa gimbiya Luzaiya. Ina son idan kun je ku kashe shi, kuma ku yanko mini kan shi sannan ku taho da kan tare da 'yar ta sa. ldan kuka saɓa wannan umarni ko kun dawo a raye zaku zama matattu. Idan ku kai nasara zan cika alƙawari na akanka jarumi Nazmir,suma abokan naka zan raba musu sarauta tare da dukiya mai yawan gaske wadda zaku yi taci iyakar rayuwarku ta duniya, na sallame ku zan kasance mai sauraronku nan da wata goma sha huɗu da 'yan kwanaki. Sarki Bashakur na gama wannan jawabi ya koma kan kujerarsa ya zauna,sannan su jarumı Nazmir suka kama dawankansu suka ɗare,dama tuntuni an shirya dakaru dubu goma waɗanda za su take musu baya. Nan take jama'a suka dare aka basu hanya ana buga musu tambura,maroƙa nayi musu kirari,kai idan kaga wannan zuga sai kayi zaton yaƙin duniya za'a yi saboda kwarjininsu. Daga wannan rana su jarumi Nazmir suka kama hanya suka yi tafiya suna ratsawa ta cikin dazuzzuka,gari,ƙasa-ƙasa. Duk inda suka iski 'yan fashi ko namun daji sai sun tarwatsasu sun kashe na kashewa, amma duk inda suka riski gari basa yiwa mutane komai kuma basa taɓa dukiyarsu sai dai su tambayi hanyar zuwa birinin Mahazus a nuna musu. Tafiya kwanci tashi har suka shafe wata bakwai da kwana tara kwatsam suka hango ganuwar birmin Mahazus acan gaba nesa đa su. Nan take farin ciki ya lulluɓesu, kawai sai shugaban tawaga jarumi Nazmir ya bada umarnin a sauka. Nan fa aka sassauka aka kafa tantuna kowa ya buɗe guzurinsa aka ci aka sha aka shiga hutawa. Acan cikin birnin Mahazus kuwa tuni labari ya riski sarki Falalul Bahafus cewa ga wata tawaga can ta rundunar mayaƙa ta sauka a bayan gari ba'asan da wacce suka zoba. Cikin kwanciyar hankali da taƙama sarki Fahalul Bahafus ya dubi wani bafadensa mai suna Jambu yace, "maza kayi hawa ka tafi ga wannan runduna ka tambayesu abin da ke tafe dasu." Jambu ya rissina yace, "an gama ya mai duniya." Cikin hanzari ya fita daga fadar ya hau doki ya nufi wajen gari. A daidai wannan lokaci ne gimbiya Luzaiya ta shigo cikin fadar kuyangi na take mata baya. Nan da nan hankalin kowa ya koma kanta domin ta tafi da tunanin masu tunani. Tsananin kyawunta ko yaushe yana zare imanin dukkanin wani 'da' na miji kuma yana kankare baƙin cikin zuciya wanda ya dafe tsawon shekaru. Gimbiya Luzaiya na sanye da wata doguwar riga ce ruwan ɗorawa mai shara-shara, daga ƙasa tayi bazar bazar kamar ɗawisu ya buɗe fukafukansa. Mutum na iya ganin cikar surarta inda ta kasance mai shamulallen ciki da faffaɗan ƙugu, kirjinta a cike yake kuma ta kasance doguwa mai dogon gashi wanda ya sauka har gadon bayanta, fara ce sol kamar tsada, ko'ina fatar jikinta sumul suɓul tamkar ta jariri. Tana da ƙwala-ƙwalan idanu a ƙarƙashin gira mai ƙyallin baƙi kuma sun kasance masu haske sosai, hancinta dogone siriri kamar alƙalami a ƙasansa an dasa mata ƙaramin baki mai ban sha'awa.(🙄🙄🙄🙄 wannan bayani haka 🙄🙄). ldan tayi murmushi sai kaga kamar kyawun nata ya linka kansa.(Wata sabuwa😝😝😂). Nima fa ganin wanga bayani ne yasa zan dakata anan,zan je hasaso yadda kyawun wannan yarinya yake😜😜 Sai wani karon idan Allah ya kaimu. Fatan alheri.Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part L A baya mun tsaya ne a inda ake zayyana bayani akan gimbiya Luzaiya😏😏:- Tana da ƙwala-ƙwalan idanu a ƙarƙashin gira mai ƙyallin baƙi kuma sun kasance masu haske sosai, hancinta dogone siriri kamar alƙalami a ƙasansa an dasa mata ƙaramin baki mai ban sha'awa.(🙄🙄🙄🙄 wannan bayani haka 🙄🙄). ldan tayi murmushi sai kaga kamar kyawun nata ya linka kansa.(Wata sabuwa😝😝😂). ##### Tana tafe a hankali cikin izza ta iso gaban mahaifinta shi kuwa sai ya miƙe ya tare ta sannan ya kama hannunta na dama ya sumbaci kan yatsunta sannan ya zaunar da ita kusa dashi suna masu duban juna cikin murmushi da nuna zunzurutun ƙauna. Luzaiya tace "Ya kai Abbana ina can gidana yanzu ina shirin fita rangadi bayan gari sai ga saƙonka ya riskeni cewar na dakatar da fita shin lafiya kuwa?" Sarki Fahalul Bahafus yace "E, to lafiyar kenan amma ba ƙalau ba. Abin da yasa nace ki fasa fita shine labari yazo mini cewa rundunar mayaƙa ta sauka a bayan gari kuma ba'a san me ya kawo suba. Don haka yanzu na tura aje aji dalilin zuwansu ƙasata." Koda jin haka sai Luzaiya tayi murmushi tace "Ai koma dame suka zo dai dai muke dasu, ya kai Abbana ni kam nasan cewa a halin yanzu yadda kake da tarin gwarzaye mayaƙa babu wata runduna da zata iya cin mu da yaƙi." Sarki ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Tabbás haka zancenki yake 'yata domin inda na kasance azzalumi da tuni yanzu na mallaki duk ƙasashen dake maƙwabtataka damu." Sarki na gama faydin haka kenan sai ga Jambu ya dawo ɗauke da wasiƙa,da zuwa sai ya miƙa takardar ga sarki shi kuma ya baiwa magatakarda ya umarceshi daya karanta ta. Take magatakarda ya warware ya fara bayani kamar haka:- "DAGA JARUMI NAZMIR BIN HALUFA ZUWA GA SARKI FAHALUL BAHAFUS NA BIRNIN MAHAZÜS. GAISUWA TARE DA BIYAYYA A GAREKA YAKAI WANNAN SARKI, KAYI SANI CEWA NI MANZO NE DAGA SARKI BASHAKUR NA BIRNIN DAHAMUL KUMA BAI TURONI GARE KA DAN KOMAI BA SAI DON NA YANKE KANKA NA KAI MASA KUMA NA TAFI DA KYAKKYAWAR 'YARKA GIMBIYA LUZAIYA DON TA ZAMA SAƊAKARSA,INA MAI SHAWARTARKA DA KASA A YANKO MINI KAN NAKA A HAƊO TARE DA 'YARKA A KAWO MINI DOMIN KA TSIRAR DA RAYUKAN JAMA'ARKA NA TAFI SALIN ALIN IDAN KUMA KA ƘI BIN WANNAN UMARNI NI DA BARADENA ZAMU SHIGO CIKIN BIRNINKA DA ƘARFIN TSIYA MU CIKA UMARNIN SARKIN MU." Tun sa'adda jama'a suka ji ma'anar wannan wasiƙa fadar ta yamutse da surutu da kuma al'ajabi saida sarki Fahalul Bahafus ya rinƙa daka tsawa sannan magatakarda ya sami damar kammala karantawa, yana gamawa ne sarki Fahalul Bahafus ya bushe da mahaukaciyar dariya. Itama gimbiya Luzaiya tare da sauran manyan fadawa suka yi tsit,Luzaiya ta dubi mahaifinta tace, "ashe mahaukata marasa lissafi da tunani basa ƙarewa a cikin duniyarnan. Yanzu in banda ɓatan basira yaushe wasu mutane zasu yi tunanin cewa zasu iya shigowa har har cikin garin nan suyi mana wannan wulaƙanci. Sarki Fahalul Bahafus yayi gyaran murya yace, "yake 'yata ai kinsan shi maƙiyi har abada baya fitar da ran samun nasara akan maƙiyinsa, ki sani cewa fiye da shekaru ashirin baya sarki Bashakur ya yi iyakar ƙoƙarinsa akan yaga bayana amma abu ya faskara sai yanzu kuma yake ganin ya yi cikakken shirin da zai iya samun galaba a kaina bai san cewa jiya ba yau bace nima nawa shirin ya linka nasa. Sarki Fahalul Bahafus ya dubi Jambu yace, "Menene adadin waɗannan dakaru?" Jambu ya ce "Ya sarkin sarakai ai gaba ɗayansu ba zasu wuce dubu goma da ɗoriya ba domin shi shugaban tawagarma matashine ba zai fi shekara ashirin ba shi ne jarumi Nazmir ɗin. Sai kuma waɗansu mutum shida waɗanda su kadai ne ma suke da cikar sura ta jarumai." Koda jin wannan batu sai sarki ya sake bushewa da dariya yace, "Maza a rubuta takardar raddi a kaiwa wannan mara kunyar jarumi kuma a shirya mayaƙa dubu duari su je su maishe dasu abincin tsutsa." Nan da nan kuwa aka cika umarni daga nan fada ta watse kowa ya kama gabansa. Lokacin da takardar raddi ta riski jarumi Nazmir sai suka cika da baƙin ciki, domin ba sa son abin da zai janyo a zub da jini mai yawa,cikin matuƙar damuwa Nazmir ya dubi su Huzaik yace, "Kaicon wannan sarki amma fa ya yi gurguwar shawara wacce za ta janyo masa babbar nadama. Huzaik yace, "Ƙwarai haka ne amma kuma fa ni ya burgeni domin abin da ya yi shi ne daidai." Koda jin haka sai Sharhil ya ce, "Haba Huzaik saboda me za ka faɗi haka? Shin idan kai sarki ne za ka so ka ga an zubar da dumbin jinin talakawan ka, kuma a rushe ƙasarka a yi maka kisan gilla?" Huzaik ya ce, "Ba zan so haka ba, amma ina so ka ƙaddara cewa kai ne wannan sarkin da zamu yaƙa. Kana da ƙarfin mulki da mayaƙa rana ɗaya a zo a ce za'a rabaka da rayuwarka da kuma 'yarka guda ɗaya tilo da kake matuƙar so, shin ba za kayi yunƙurin komai ba na kare kanka?" Sharhil ya yi shiru ya kasa bada amsa. Ba zato ba tsammani sai suka ga idanun Nazmir sun ciko da ƙwallah. Koda ganin haka sai Bardil ya taso daga inda yake zaune ya dafa kafaɗar Nazmir yace, ''Haba abokina me ya sa kake da tausayi ne mai yawa,gaka ka kasance cikakken jarumi mai ragargazar maza. Ka saba da tsinke wuya, kuma ka saba da raba gangar jiki. Ka tuna fa kai ne mai cisge sassan jikin bil'adama da ƙarfin damtse, yayin da ka yi mummunar fusata." Nazmir ya share ƙwallar idonsa,sannan yace, ''Abokina ka sani cewa fishina yafi tabbata akan azzalumai. Wannan sarkin da aka turomu mu ruguza farin cikinsa muraba shi da rayuwarsa da kuma 'yarsa ai ba azzalumi ba ne. Ni kam ina jin kunyar zaluntar wanda bai zalunce ni ba." Bardil yayi ajiyar numfashi, sannan yace, "Nasan da haka amma ka sani cewa babu yadda zamu yi dole mu cika umarnin sarkinmu tun da in muka ƙi tamkar mun salwantar da tamu rayuwar ne,domin hukuncin kisa ne zai tabbata akan mu. Ya kai abokina ka tuna da ivayenmnu da 'yan uwanmu waɗanda muka baro su a cikin tsananin ƙunci da baƙin cikin rabuwa. Tabbas har yanzu suna nan a cikin begenmu dare da rana, ba za su daina ba har sai mun koma sunga lafiyarmu. Ai kuwa ko dan saboda su dole ne mu tsare rayukanmu mu cika umarnin sarkinmu.' Da wannan jawabi ne jikinsu gaba ɗaya yayi sanyi,kowa ya tuna da danginsa na gida kuma ya yarda ya rabu da su kawai sui suka kama zubar da hawaye. Cikin ƙarfin hali jarumi Nazmir ya dubi abokansa, sannan ya dubi dakarun nan guda dubu goma yace, "Kowa ya zauna cikin shiri gobe zamu farwa mutanen garin nan ko sun tare mu ko ba su tare mu ba." Kashe gari tun kafin su jarumi Nazmir su aiwatar da nufinsu suka ga an buɗe ƙofar birnin Mahazus sai ga rundunar mayaka ta fara fitowa suna jeruwa sahu-sahu. Koda suka gama jeruwa su Nazmir suka ga yawansu sai zuciyoyinsu suka karaya. Huzaik ya matso kusa da jarumi Nazmir yace, ''Kai anya kuwa ma yi wannan yaƙi? Dubi yawan dakarun nan fa, na rantse da darajar mahaifina sun linkamu sau goma." Nazmir ya dubi Huzaik ya daka masa tsawa yace, "Ka zamo namiji mại ƙwarin zuciya,faɗuwar gaba asarar namiji ce,in dai muka daure zamu iya gamawa da su,a cikin sa'a biyar." Kafin wani ya ƙara cewa wani abu jarumi Nazmir ya yi kukan kura ya sakarwa dokin sa linzami. Dokin kuwa sai ya nufi tawagar sarki Fahalul Bahafus a sukwane cikin mugun gudu. Koda ganin haka sai Huzaik, Sharhil, Bagwan,Husuf, Ikhalam,da Bardil suma suka sakarwa nasu dakawan linzami suka bi bayansa suna masu ƙoƙarin su riske shi, kafin ya ƙarasa cikin abokan gaba don kada su yi masa sarkin yawa su halaka shi,tuni jarumi Nazmir ya basu rata mai yawa. Kafin kace me tuni ya kutsa cikin baradan sarki Fahaul Bahafus ya hausu da sara ba sassauci,su kuwa suka yanyame shi kamar ansa kyanwa ɗaya a tsakiyar karnuka dubu. Sai dai wannan kyanwar ta zamewa karnukan alaƙaƙai,domin sun gaza cim mata. Duk inda jarumi Nazmir ya kai sara sai dai kaga kawuna na zubewa kuma duk inda ya durfafa dole a dare hanya ta samu a gare shi bisa dole. Kafin su Huzaik su ƙaraso tuni jarumi Nazmir ya yiwa wannan runduna mummunar ɓarna. Ai kuwa sa'adda su Huzaik suka ƙaraso sai wuri ya ƙara hautsinewa, mummunan yaƙi ya rincaɓe ban da ƙarajin mazaje da na ƙarafa babu abin da mutum ke ji. Jini kuwa ya rinƙa fantsama kai ka ce feso shi ake yi daga sama. Kafin dakarun nan guda dubu goma masu taimakawa su Nazmir su iso tuni an gama da dakarun sarki Fahalul Bahafus guda dubu ɗari gaba ɗaya sun zama gawa. Ana gamawa da su ne aka ga Huzaik ya dafe ƙirjinsa yana sunkuyawa ƙasa, cikin yanayin jiri. Kafin wani ya ƙarasa gare shi tuni ya faɗa ƙasa. Koda ganin haka sai jarumi Nazmir ya ƙwala ihu mai firgitarwa ya ruga inda yake ya tashe shi zaune ya ɗora shi akan cinyarsa, sai ga jini na ɓulɓula daga cikin ƙirjin Huzaik. Cikin ɗimaucewa Nazmir ya yaga rigar jikinsa ya toshe ƙirjin Huzaik yana mai cewa, "Abokina tashi muje cikin tantina in sa maka magani, lallai za ka sami lafiya." A wannan lokaci ne su Sharhil suka ƙaraso gabansu cikin tsananin tashin hankali da matuƙar damuwa. Cikin ƙarfin hali Huzaik ya riƙe hannun Nazmir idanunsa na lumshewa, hannunsa na karkarwa ya ce, "Ya kai abokina ka gafarce ni ba zan iya tashi ba, kuma kada ka ɓata lokacinka akan yi mini magani. Tabbas tawa ta ƙare mutuwa zan yi,kuyi haƙurin rashina,idan ka samu ikon komawa gida ka sanar da mahaifina cewar ga yadda tawa ta kasance ya rungumi ƙaddarar rashin cikar alkawarina na zuwa masa da sirikarsa. Lallai kayi mini wannan aiki amanace na baka." Koda jin haka sai Nazmir ya fashe da kuka yana mai cewa, "Huzaik na karɓi amanar ka kuma tabbas zan danƙata ga mahaifinka." Rufe bakinsa ke da wuya idanun Huzaik suka ƙafe, ko'ina a jikinsa ya daina motsi kawai sai suma su Sharhil suka durƙusa gaban gawar suka fashe da kuka. Wannan shi ne abin da ya faru tsakanin su jarumi Nazmir da dakarun sarki Fahalul Bahafus guda dubu đari bayan an fafata baƙin gumurzurn yaƙi a cikin 'yan daƙiƙu bayan garin birnin Mahazus. Sarki Fahalul Bahafus yana tare da matarsa Munaiya wato mahaifiyar Luzaiya suna hira cikin nishaɗi a turakarsa sai ga gimbiya Luzaiya ta faɗo cikin yanayin tashin hankali. Koda ganinta sai sarki miƙe zumbur ya tare ta yana mai cewa, "Yake rabin jikina me ya faru kika zo garemu a cikin siffa mara daɗin gani haka?" Luzaiya ta yi ajiyar numfashi tace, "Ya kai Abbana ga ɗaya daga cikin masu tsaron ƙofar gari yazo da mummunan labari cewar dakarunka daka tura guda dubu ɗari don su yaƙi maƙiyanmu mutum bakwai kacal sun gama da su.'' Cikin firgici sarki Fahalul Bahafus ya saki Luzaiya ya ja da baya kaɗan yace, "Wace irin maganar banza kike faɗa mini haka? Ya za'a yi a ce mutum bakwai sun kashe mutum dubu ɗari a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci da bai kai rabin sa'a ba. Ai kuwa koda mutum bakwan aljanu ne su aikin yafi ƙarfinsu." "Ya kai Abbana wannan labari ba ƙarya bane ka je ka gani da idanunka domin ni na gani,ganau ce ni ba jiyau ba." Cikin sauri da ruɗewa sarki Bahalul Bahafus ya ɗauki rawaninsa ya tuma aka sannan ya fita waje da sauri-sauri, gudu-gudu. Yana zuwa ƙofar fada yaga gaba ɗaya 'yan majalisarsa a tsaitsaye sun yi tsuru-tsuru suna tattauna wannan al'amari. Ko tsayawa gabansu bai yi ba ya sa aka kawo masa doki ya hau ya nufi ƙofar fita daga gari. Cikin hanzari suma 'yan majalisar suka yi hawa suka bi shi. Da zuwa suka iske gawarwakin dakarun nan guda dubu đari,gaba ɗaya filin wajen ya malale da su da kuma jini abin ba kyan gani. A lokacin su Nazmir sun koma tantin su. Nan take zuciyar sarki Fahalul Bahafus ta hau tafarfasa. Kawai sai ya dubi wazirinsa ya ce, "Mene ne abin yi?" Waziri yace, ''Ranka ya daɗe babu abin yi face gobe mu sake turo wasu ɗari uku." "A yi hakan." Abin da Fahalul Bahafus ya faɗi kenan, ya kaɗa linzamin dokinsa ya juya da baya ya nufi cikin gari a sukwane suma 'yan majalisar suka bi bayansa. A wannan rana dai su jarumi Nazmir sun sha kuka mai yawa. Ga shi dai sun sami nasarar yaƙin amma saboda sun rasa abokinsu kuma amini wanda suka taso tare tun ƙuruciya sai suka zamo cikın mugun baƙin ciki,mara misaltuwa.. Har aka haƙa kabari aka binne Huzaik su shidan nan ba su daina kuka ba. Bayan an binne Huzaik ne jarumi Nazmir ya đauki takobin Huzaik din ya sumbace ta sannan saka ta a cikin kayan sa. Daga nan ya koma gefe ɗaya ya zauna shi kaɗai yana tunano irin abubuwan da suka faru a baya tsakaninsa da Huzaik tun suna ƙanana kawai sai ya sake fashewwa da kuwa. Sharhil,Bagwan,Husuf,Ikhlam da Bardil suka taso daga inda suke zaune suka zo suka rungume Nazmir suna masu taya shi kuka. Nazmir ya buɗi baki cikin murya mai rawa yace, "Mu bakwai ne yau ga shi mun zama mu shida. Haba mutuwa ya za ki rabamu da masoyinmu,me zai hana ki ɗaukemu gaba ɗaya a lokaci guda,don mụ huta da baƙin cikin rabuwa?" Sa'adda Bardil ya ji jarumi Nazmir na irin waɗannan zantuka sai ya shiga rarrashinsa yana bashi baki gami da ƙara masa ƙwarin gwiwa don tsoron kada begen Huzaik ya jefa shi cikin zautuwa. Haka dai suka ci gaba da kuka da baƙin ciki har dare ya tsala sosai,ɗaya daga cikin su bai rintsa ba,kai yadda suka ga rana haka suka ga dare. Kashe gari tun kafin alfijir ya keto suka fara jin hayiniyar dawakai a can ƙofar gari cikin hanzari su Nazmir suka miƙe suka hau dawakansu cikin shirin yaƙi, suka nufi ƙofar garin. Da zuwa kuwa suka iske gaba ɗaya an kwashe gawarwakin dakarun jiya. Tsaitsaye akan dawakai dakaru dubu đari uku ne cikin mugun shirin yaƙi. Shi kansa jarumi Nazmir sai da zuciyarsa ta buga ys đubi abokansa guda shida,sannan ya dubi dakarun nan mataimaka su dubu goma ya ce, "Yau fa abin na yi ne, maza mu afka musu muga abin da zai yi hali daga nan zuwa Magariba." Ai kuwa nan take kowa ya saki linzanmin dokinsa,ƙura ta tashi, dawakai suka yi ƙaimi kai kace gasar tsere ake yi, suka nufi ƙofar birnin. Koda mayaƙan sarki Fahalul Bahafus suka ga waɗannan tsirarun dakaru sun taso musu sai suma suka ruga gare su don su tare su,kafin su iso ai kuwa sai aka gamu a tsakiya. Gamuwar kowa ta zamo matsiyaciya,domin tafi gaban karon batta, turnuƙu ko ruguntsumi sai dai a kirata annoba. Domin buɗe kasuwar asarar rayuka,aka yi. Tabbas a wannan rana Nazmir da abokansa sun nuna tsantsar jarumta,juriya da sanin makama. Wataƙila saboda fushin rasa abokin su ne ya sa suka zage damtse įyakar ƙarfinsu,idan kaga yadda suka rinka ragargazar dakarun sarki Fahalul Bahafus sai kayi zaton ba mutane suke rugargaza ba,ƙwaiƙwayen kaji ne,saidai ka rinƙa jin ƙarar fashewar kan bil'adama,tus-tus, raƙaƙaƙa! Sai da aka kwana aka yini ana wannan yaƙin sannan aka gama da waɗannan mayaƙa na sarki Fahalul Bahafus. Ana gamawa da su ne jarumi Nazmir ya shiga dube-dube don ya tabbatar da lafiyar abokansa. Cikin sa'a sai duk ya gansu a tsaitsaye amma duk sun samu raunika sai dai ba wanda zai zamo abin fargaba ba ne. Kowa ka duba sai ka ga gaba ɗaya jikinsa ya rine da jini. Dakarun nan kuwa guda dubu goma masu taimakawa su Nazmir sun dawo saura su đari uku kacal,wato an kashe dubu tara da ɗari bakwai. Jarumi Nazmir ya tara abokan sa waje ɗaya ya fara dudduba raunikan jikinsu gami da sa musu magani. Koda ya zo kan Sharhil sai ya ga gumi na tsatstsafowa a goshinsa kuma yana ciza leɓensa alamun yana cikin jin raɗaɗin ciwo. Nan take hankalin Nazmir ya dugunzuma ya ci gaba da duba ko'ina a jikin Sharhil, kawai sai yaga sukan mashi a ƙasan cibiyarsa jini na zuba ta wajen,Nazmir ya rusa îhu ya yi sauri ya sa magani a wajen. Sharhil ya kamo wuyan Nazmir ya ce, "Yakai abokina kar ka damu zan rayu ba zan mutu ba." Kawai sai suka ga ya miƙe ƙyam,ya tsaya bisa dugaduginsa. Cikin farin ciki suka kama shi aka tafi dashi izuwa tanti sannan aka zaunar da shi. Sai da aka sami rabin sa'a ana ta hira da Sharhil tamkar babu wani rauni a jikinsa domin har ana wasa da dariya. Daga can sai Sharhil ya ce, yana jin ƙishirwa. Koda faɗin haka sai Bagwan ya miƙe ya fito don kawo ruwan,aka ci gaba da hira amma wannan karon sai Sharhil ya daina sa bakinsa a cikin hirar ya yi shiru. Ashe ciwon jikinsa ke nuƙurƙusarsa don kada su Nazmir su ka gane halin da yake ciki ne ya yi shiru. Jim kaɗan sai ga Bagwan ya dawo ɗauke da ruwa a cikin ƙoƙo. Koda ya miƙawa Sharhil ruwan sai suka ga bai miƙo hannunsa ya karɓa ba. Kawai kuma sai suka ga idanunsa a kafe suke basa motsi. Cikin tsananin firgici Nazmir ya girgiza shi amma ko motsi bai yi ba. Gangar jikin ta laguɓe ta fadi ƙasa. A lokaci guda su rusa uban ihu su duka suka fashe da tsananin kuka wanda ya sa ragowar dakarun nan guda ɗari uku suka rugo cikin tantin a guje riƙe da makamansu tsirara don zaton ko maƙiya ne suka kawo sumame. Da zuwa suka iske ashe jarumi Sharhil ne ya mutu. Baƙin cikin da su Nazmir suka yi a wannan karo har ya fi wanda suka yi lokacin mutuwar jarumi Huzaik domin sai da gaba ɗayansu suka ɗebi makamai suka nufi hanyar ƙofar birnin Mahazuz da niyyar ɗaukar fansa. Da ƙyar dakaru masu taimako suka lallame su suka haƙura. Kuka kuwa tun suna zubar da hawaye sai da hawayen ya ƙare,idanuwansu suka kumbura suka yi suntum. Duk wanda ya gan su a wannan lokaci dole ne ya tausaya musu. Bayan an ginawa Sharhil kabari a kusa da na Huzaik an binne shi sai jarumi Nazmir ya dubi su Bagwan yace, ''Yaku abokaina yanzu dai kun gani saura mu biyar maimakon mu bakwai. Shin haka zamu ci gaba da binne junan mu ɗaya bayan ɗaya,ya zama dole mu yiwa tufkar nan hanci mu kawo ƙarshen yaƙin nan." Iklam ya yi ajiyar numfashi yace, "Hanya ɗaya ce zamu bi mu kawo ƙarshen wannan yaƙi,sai dai mu je mu ɓalle kofar garin da ƙarfin tsiya mu banka ciki mu yi kan mai uwa da wabi har sai mu kai ga gidan sarki mun sare kansa,sannan mu kamo 'yarsa mu tafi da birninmu." Husuf ya ce, ''A'a wannan shawarar ba zata kai mu ga gaci ba. Ku sani cewa ba mu san sirrin garin nan ba, idan muka ce zamu shige shi kai tsaye zamu iya faɗawa cikin tarkon da zamu kasa fita,ni ina ganin a wannan yaƙin mun yi musu mummunar ɓarna babu mamaki su tsorata su su bamu abin da muka zo nema, mu tafi salin-alin,domin saboda rai biyu kacal ba za su yarda mu ƙarar da su ba." Sa'adda Husuf ya zo nan a zancensa sai jarumi Nazmir ya dubi Bagwan da Bardil yace, ''Ku kuma me za ku iya cewa?" Cikin haɗin baki suka ce, "Mun yarda da shawarar Husuf." Anan zamu dakata sai wani karon idan Allah ya kaimu. Fatan alheri.Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part M Sa'adda Husuf ya zo nan a zancensa sai jarumi Nazmir ya dubi Bagwan da Bardil yace, ''Ku kuma me za ku iya cewa?" Cikin haɗin baki suka ce, "Mun yarda da shawarar Husuf." ##### Kashe gari ihun mazajen ne ya sa su Nazmir miƙewa ba cikakkiyar nutsuwa. Cikin hanzari suka hau dawakansu suka nufi ƙofar birnin. Tun daga nesa suka rinƙa hango gungun dakarun yaki waɗanda adadinsu ya ninka na jiya. Ban da tsinin masu da kaifin takubba babu abin da suke gani. Sai kuma tulin kuttun kibau da baka-baka. Jarumi Nazmir ya ja linzamin dokinsa ya tsaya, suma abokan tafiyar ta sa sai duk suka tsaya a bayansa. Nazmir ya waigo ya dubi abokansa guda biyar sannan ya dubi ragowar dakaru guda ɗari uku,yayi ajiyar zuciya,sannan yace, "Mu ɗari uku ne da biyar zamu tunkari mutum kusan dubu ɗari shida,bana sa ran wannan karon gaba ɗayanmu za mu tsira da rayuwarmu amma ku sani ba gudu ba ja da baya. Mu ƙarfafa zuƙatanmu,mu cire tsoro da fargabar wahala ko mutuwa. Lallai ko ba muyi nasara ba za mu yi gagarumar ɓarna. Idan mun yi nasara mun kafawa iyayenmu da danginmu tubalin sabuwar rayuwar duniya. Idan muka faɗi mun ruguza zuri'o'inmu kuma za'a manta da tarihinmu a doron ƙasa." Koda gama faɗin haka sai Bagwan, Husuf,Iklam da Bardil suka ji wani sabon ƙarfi ya shige su irin wanda ba su taɓa jì ba. Zuciyoyinsu suka ƙeƙashe ya zamana babu sauran shakkar komai a tare da su. Kafin jarumi Nazmir ya yi wani motsi tuni sun sakarwa dawakansu linzami sun nufi ƙofar birnin Mahazus cikin gaggawa. Nazmir da dakaru đari ukun suka rufa masa baya. Wohoho!, a wannan rana sai da su jarumi Nazmir suka zamo tamkar ifiritai a cikin tsakıyar bil'adama domin kamar masu sassabe a gona haka suka kasance. In banda girba da share kan kawunan bil'adama babu abin da suke yi cikin tsananin zafin nama,juriya da bajinta,idan aka harbo musu kibiyoyi komai yawan kibiyoyin sai dai ka ga suna karkaɗe su suna zubewa ƙasa. In kuwa suka kai suka saidai ka ga a lokaci guda sun ɓurma ƙirjin mutum uku. A wannan yaƙi ne sarki Fahalul Bahafus tare da 'yan majalisar suka zo kan ganuwa suka tsaya suna ganin abin da ke wakana a filin yaƙin,sai da aka kwana uku ana fafatawa ya zamana an yi fata-fata da mutanen sarki Fahalul Bahafus. A lokacin ne fahalul Bahafus ya hango fuskar jarumi Nazmir sai sai ya tuno da fuskar mahaifinsa,wato sadauki Halufa. Nan take ya tuna lokacin da Halufa ya kuɓutar da shi daga kurkuku sai hankalinsa ya dugunzuma,gumi ya tsatstsafo masa. Ba zato ba tsammani sai aka ga sarki Fahalul Bahafus ya sauko daga kan ganuwa a guje ya hau dokinsa ya nufi bakin ƙofar gari. Da zuwa sai ya dakawa masu tsaro tsawa ya ce su buɗe masa ƙofar. Jikinsu na rawa suka buɗe masa ƙofar ya sukwani dokinsa ya nufi inda su jarumi Nazmir ke gumurzu. A lokacin saura 'yan tsirarun barade a filin. Koda aka hango tahowar sarki Fahalul Bahafus bisa kan doki sai kowa ya tsaya da yaƙin aka zuba masa idanu cikin mamaki,yayin da sarki Fahalul Bahafus ya zo gaban jarumi Nazmir sai ya ja tunga ya sauko daga kan dokin ba tare da ya riƙe wani makami ba. Kawai saí ya durƙusa a gaban Nazmir bisa gwiwoyinsa yace, "Yakai wannan jarumi ka yi sani cewa na sallama kaina da 'yata a gareka. Ina umartarka da ka sare kaina ka kaiwa sarkinku kamar yadda ya umarce ka, amma ina son ka yi mini wata alfarma guda ɗaya." Cikín sanyin jiki da sanyin murya jarumi Nazmir yace, "Wace irin alfarma kake so na yi maka?" "Ina son idan ka koma ƙasarku ka fara kaiwa mahaifinka kaina ka gaya masa cewa ni sarki Fahalul Bafus na sallama rayuwata, domin ta ka." Koda jin wannan batu sai mamaki ya kama jarumi Nazmir ya ce, "Yakai wannan sarki ban gane manufarka ba." Fahalul Bahafus yace, "Yakai gwarzon jarumi ka yi sani cewa kamar shekaru ashirin baya mahaifinka sadauki Halufa ya taɓa zuwa nan ƙasata ya kamani da ƙarfin tsiya ya kaini kurkukun sarkinku aka kulleni,amma da ya ji cewar sarkinku yace dole ne ya kashe ni sai ya je kurkukun cikin dare ya tarwatsa masu gadi ya kuɓutar da ni. Yayin da na tambaye shi dalilin da ya sa ya kuɓutar da ni sai ya ce saboda ya san ina da kyakkyawar 'ya guda ɗaya wacce nake matuƙar ƙauna kuma ita ma ta shaƙu dani ainun,saboda haka ba zai yarda ya zama silar raba soyayyar da ke tsakanin đa da mahaifi ba,domin shi ma yana da ɗan da baya son ya zama maraya,kasancewa har yanzu baku kashe kaso ɗaya daga cikin kaso ɗari ba na yawan mayaƙana,na rantse da darajar karagata idan mayaƙana suka fito gaba ɗaya yanzu sai sun ƙarar da ku koda kuwa kun kasance aljanu ba mutane ba. Ya kai wannan jarumi haƙiƙa ba zan yarda na raba soyayyar dake tsakanin ka da mahaifinka ba,domin ya ceci rayuwata a lokacin da nake son na rayu,don rayuwar 'yata. Dole ne yanzu na sakawa mahaifinka da irin alfarmar da ya yi mini. Lallai ina son ka rayu ka koma gare shi,maza ka sare kaina kuma kaje ka kamo 'yata ka tafi da ita. Babu wanda zai hanaka yin hakan face ni." Sa'adda sarki Fahalul Bahafus ya zo nan a zancensa sai jarumi Nazmir ya yarda takobin sa wadda ta rine da jini idanunsa suka ciko da ƙwallah ya kasa yin komai. A daidai wannan lokacin ne a kaga ƙofar garin ta sake buɗewa sai ga gimbiya Luzaiya bisa kan doki tare da dubban ɗaruruwan mayaƙa sun fito. Cikin sauri sarki Fahalul Bahafus ya miƙe tsaye ya yi musu nuni da cewar kada kowa ya zo. Gaba ɗaya dakarun suka yi cirko-cirko amma ita gimbiya Luzaiya bata tsaya ba sai ta sukwano dokinta ta zo gaban mahaifinta tace, "Ya kai Abbana don me za ka dakatar da mayaƙan ka ka bari kawai a yiwa waɗannan tsirarun rubdugu." Cikin yanayin damuwa sarki ya dubi Luzaiya ya ce, "Ba zan iya bari ba a hallaka su domin in akai hakan na ci amana." Cikin tsananin mamaki Luzaiya ta dubi sarki tace, "Me kake nufi da cin amana? Shin ka manta ne cewar waɗannan mutane maƙiyanka ne, sun zo ne fa su sare kanka kuma su tafi da ni." "Ban manta ba, ina sane da komai, yake 'yata ina roƙonki domin ƙaunar da ke tsananina da ke da ki amince kibi wannan jarumi da ke tsaye a gabana ya kai ki wajen sarkin su don ya aureki. Kuma ina son kiyi haƙurin rashina domin yanzu tamkar ina bankwana da ke ne. Lallai ina son a sare kaina yanzu-yanzu." Sarki Fahalul Bahafus ya sake duban jarumi Nazmir yace, "Kai nake jira ka sare kaina, idan baka yi hakan ba ka cuceni ka sa na ci amanar mahaifinka." Jarumi Nazmir ya juya masa baya yace, "Ba zan iya aikata wannan ɗanyen hukunci ba da hannuna. Haƙiƙa mahaifina ya taɓa bani labarinka da duk abin da ya faru a tsakaninku." Koda Bardil ya ga cewar jarumi Nazmir bashi da niyyar sare kan sarki Fahalul Bahafus sai shi ya shammaci kowa da ke wajen ya fille masa kan. Koda ganin hakan sai gimbiya Luzaiya ta faɗi ƙasa sumammiya. Cikin hanzari Bardil ya sureta kuma ya đauki kan sarki Fahalul Bahafus ya ɗora akan doki shima ya hau dokin yana mai baiwa abokan tafiyarsa umarnin su yi sauri su gudu cikin tsawa. Ai kuwa nan da nan kowa ya haye dokinsa ya sukwane shi. Kafin dakarun nan masu yawan tsiya na sarki Fahalul Bahafus su iso filin yaƙin da niyyar cim musu tuni sun yi nisa sun ɓace sai ƙurarsu kađai ake hangowa. Su jarumi Nazmir ba su gushe suna gudu bisa dawakansu ba,sai bayan kwana guda da yini đaya. Koda suka tabbatar da cewa sun yiwa mutanen sarki Fahalul Bahafus tazarar da ba zasu iya riskarsu ba,sai aka tsaya a bakin wata korama don kowa ya huta,a wannan lokaci tuni gimbiya Luzaiya ta daɗe da farfaɗowa daga suman da ta yi. Koda ta ga cewa tana hannun maƙiya ne sai ta fashe da kuka,tayì ta kuka har aka zo bakin wannan ƙorama. A sannan ne kowa ya sauko daga kan dokinsa. Bardil ya sauko da gimbiya Luzaiya sannan shima ya ɗebi ruwa ya zuba akansa kuma ya sha haka suma su jarumi Nazmir suka yi,bayan an sami nutsuwa sai jarumi Nazmir ya fara neman abokansa don ya tabbatar da lafiyar su. Nan take ya ga Bardil da Bagwan amma baiya Husuf da Iklam ba,nan fa hankalinsu ya dugunzuma suka fara tunanin ko sun rasune a filin yaƙi,nan take jarumi Nazmir yace dasu Bardil su tsaya anan shi zai ɗan duba baya kaɗan ko wani abu suka tsaya yi. Kawai sai ya hau dokinsa ya dawo da baya, ai kuwa bai daɗe ba yana tafiya ya hango Husuf a can gabansa kaɗan a kwance yana kakarin mutuwa,ga dokinsa a tsaye kusa dashi. Cikin sauri jarumı Nazmir ya ruga inda yake ya sauko daga kan doki ya ɗaukeshi da nufin ɗora shi akan doki,a lokacin jini na zuba ta cikin kafar bakinsa da hancinsa. Koda Husuf yaga Nazmir sai ya yi murmushin ƙarfin hali yace, "ya kai abokina karka wahalar da kanka a kaina domin tabbas mutuwa zanyi yanzu,ka sani cewa abokinmu lkam ya mutu tun a filin yaƙi naga gawarsa da idanuna,ina mai fatan zaka riƙe ƙanwata Lamiz amana kuma ina son....." Koda Husuf ya zo nan a zancensa sai jikinsa ya sandare, idanuwansa suka ƙafe suka daina motsi. Nan take jarumi Nazmir ya kwarara uban ihu wanda ya cika dajin gaba ɗaya yayi ta amsa kuwwa har su Bardil suka jiyo ihun daga inda suke. Koda jin ihun sai Bagwan da dakaru biyar suka biyo sawu suka bar Bardil tare da gimbiya Luzaiya da sauran baraden nan a wajen. Koda zuwan su Bagwan inda jarumi Nazmir yake sai suka iskeshi zaune a gaban gawar Husuf yana ta rusa kuka. Shima Bagwan sai ya fashe da kukan,anan dai akayi ta rarrashinsu da ƙyar suka bari aka haƙawa Husuf kabari aka binne shi. Bayan an binne shine, jarumi Nazmir ya fiddo mayafinnan na Lamiz ƙanwar Husuf daga cikin kayansa,koda ya dubi mayafin ya tuno da sa'adda Lamiz ta danƙa masa kuma ya tuno da irin kalaman da tayi musu a wannan rana sai ya sake fashewa da kuka, cikin ƙarfin hali jarumi Nazmir ya ɗaura mayafin akansa sannan ya kama dokinsa ya hau,Bagwan ne da sauran barade suka hau nasu dawakan suka nufi inda suka baro su gimbiya Luzaiya. Tun daga nesa Bardil ya hango mayafin Lamiz akan jarumi Nazmir kawai sai ya fashe da kuka don ya tabbatar da cewa abokinsa Husuf ya mutu. Yayin da su Nazmir suka iso sai Bardil ya dubi Bagwan ya ce "Ina kuma labarin Iklam." Cikin alamun karayar zuciya Bagwan yace, "Kafin Husuf ya rasu ya gayawa Nazmir cewar yaga gawar Iklam a filin yaƙi." Koda jin haka sai Bagwan ya kurma ihu irin wanda jarumi Nazmir yayi ɗazu sannan ya rugo gaban Nazmir da Bardil ya rungumesu,yana mai cewa shike nan saura mu uku kacal. Dukkaninsu suka cigaba da kuka,duk wanda ya dubesu a wannan lokaci dole ne tausayisu ya kamashi. Kowa da abin da ya dameshi, kamar yadda su jarumi Nazmir ke kuka da baƙin cikin rasuwar abokansu haka gimbiya Luzaiya ta kasance cikin tsananin baƙin ciki rasuwar mahaifinta. A duk sa'adda ta ɗaga kai ta dubi Bardil sai taji ta tsaneshi bama shi ba har su jarumi Nazmir ɗin duk ta tsanesu inda tana da iko da tuni ta hallakasu gaba ɗaya sannan ta kashe kanta ta huta da takaicin duniya. Anan zamu dakata, sai wani lokacin idan Allah ya kaimu. Fatan alheri Contact 08167757245 Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part N A baya mun tsaya a inda:- A duk sa'adda ta ɗaga kai ta dubi Bardil sai taji ta tsaneshi bama shi ba har su jarumi Nazmir ɗin duk ta tsanesu inda tana da iko da tuni ta hallakasu gaba ɗaya sannan ta kashe kanta ta huta da takaicin duniya. #### Haka dai suka ci gaba da tafiya,su kwana nan su tashi can. Gimbiya Luzaiya da su jarumi Nazmir basu daina kukan baƙin ciki ba har sai bayan kwana bakwai,domin duk sa'adda suka tuno da masoyan nasu sai dai kawai ai sun fashe da kuka. Tsawon kwanakin gimbiya Luzaiya bata yi magana da kowa ba kuma bata ci komai ba face ruwa sai kuma ƙwayar dabino guda uku kullum. Nan da nan ta fita haiyacinta ta rame sosai. A yammacin kwana na bakwaine sa'adda suka ya da zango a ƙarƙashin wani dogon tsauni. Luzaiya ta zauna ita kaɗai a gefe guda tana rawar đari, ashe zazzaɓine ya rufeta. Koda ganin halin da ta shiga sai tausayinta ya kama jarumi Nazmir,da yake sun gasa naman wata barewa a jiya da daddare kuma akwai sauran naman acikin jakarsu sai ya fiddo dashi yaje ga Luzaiya ya miƙa mata yana mai cewa yake wannan 'yar sarki ya kamata ki rungumi ƙaddara haka ki fara cin abinci mana." Kamar za taci kawai sai tayi wurgi dashi izuwa cikin wata ƙorama wadda ruwanta ke gudu bisa duwatsu cikin ɗacin rai da kakkausar murya ta dakawa jarumi Nazmir tsawa tace, "Ina ruwanka da lafiyata ka ƙyaleni na mutu mana,daku da mutanenka duk na tsane ku kamar yadda na tsani rayuwata a yanzu. Tsakanina daku sai gaba har abadan abidina kune kuka dakusar min da farin cikin rayuwa kun kashe mahaifina kun rabani da ƙasata da kuma mulkina kun rabani mahaifiyata da duk dangina,mene ne ya rage agareni." Ko da ta zo nan a zancenta sai ta fashe da kuka har tsawon 'yan daƙiƙu sannan ta cigaba da cewa, "Yanzu ku shi kenan buƙatarku ta biya kun rabani da kowa nawa ku kuma za ku koma ga iyayenku da 'yan uwanku ku ci gaba da rayuwar duniya cikin jin daɗi da kwanciyar hankali. Kun cuceni kun gama dani. Na roƙeku da ku kasheni yanzu ku jefa gawata cikin kwazazzabon nan." Haka dai ta ci gaba da surutai tana kuka amma ko ci kanki babu wanda ya faɗa mata. Haƙiƙa maganganun Gimbiya Luzaiya sun ratsa jarumi Nazmir kuma ya ƙara kamuwa da tausayinta amma sai ya dake ya ƙi nuna tausayin a fili ya yi ta maza. Tun sa'adda ta fara surutan ya koma can gefe guda ya zauna yana kallonta har ta gaji ta yi shiru. A lokacin ne tunanin iyaye ya faɗowa jarumi Nazmir kuma ya tuno da abokanansu guda huɗu waɗanda suka mutu duk a sanadiyyar wannan mugun yaƙi wanda sarki Bashakur ya turosu. Kawai sai hawaye ya zubo masa. Sa'adda Bagwan da Bardil suka ga hawaye na zuba a idanun jarumi Nazmir sai suka taho gareshi suka zauna tare da shi. Bardil ya dubeshi yace, "Ya kai abokina yanzu saboda tausayin Gimbiya ne ka ke zubar da hawaye?" Nazmir yayi murmushi yace, "Ba don haka ba ne. Na tuno da irin halin da muka baro iyayenmu ne kuma na tuno da abokanmu waɗanda suka rasu na tahbatar da cewa har abada ba zamu sake samun masoya kamar su ba. Kuma ba zamu samu masu đebe mana kewa irin su ba." Bagwan ya numtasa yace, "Lallai kam ba zaku iya samun abokan shaƙuwa ba kamarsu amma babu mamaki nan gaba ku haɗu da masoya waɗanda zasu ɗebe muku kewa su cire muku baƙin cikin rashinsu kuma ku ƙarasa sauran rayuwar ku ta duniya tare dasu." Koda jin wannan batu sai Jarumi Nazmir yace, "Nifa bangane manufarku ba." Bagwan yace, "Ina nufin zaku iya haɗuwa da 'yan matan da zaku aura kuma kuyi gagarumar soyayya dasu iyakar ƙarshen rayuwarku." Koda faɗin haka sai Nazmir da Bardil suka bushe da dariya sannan Nazmir yace, "Ni tunda nake ban taɓa jin ina son wata ya mace ba a zuciyata kuma bana zaton zan iya soyayya nan gaba a rayuwata." Bagwan yayi murmushi yace, "Haba abokina ai bakasan meye so ba shi yasa ka faɗi haka kaga ni nayi soyayya kuma ina kan yinta harma naci ribarta tunda nayi aure. Tabbas yanzu ina sa ran cewa idan mu koma gida zan iske ɗana ko 'yata tunda na baro matata Muslaiya da tsohon ciki,tabbas yanzu ko mutuwa nayi,za ana tunawa dani ina so kusani cewa babu abinda yafi soyayya daɗi a duniyar nan domin idan kana da masoyi duk irin baƙin cikın daka shiga kana ganinsa sai zuciyarka tayı sanyi ka manta da komai yanzu idan muka isa gida kuka sadu da iyayenku wane irin daɗi zakuji a ranku? To ina tabbatar muku da cewa wannan daɗin da zakuji bai kai kaso ɗaya ba daga cikin đari na irin daɗin da mai masoyiya yake ji yayin da ya sadu da ita bayan doguwar rabuwa. Ni kam yanzu ji nake kamar na zama tsuntsu nakai kaina gida dan na sadu da matata Muslaiya." Sa'adda bagwan yazo nan a zancensa sai duk jikin su jarumi Nazmir yayi sanyi suka kasa cewa komai domin maganganun na sa sun ratsasu kuma sun gamsu cewar gaskiya ne. Haka dai tafiya taci gaba da wakana suka cigaba da ratsa dazuzzuka gari da ƙasa ƙasa har tsawon wata uku,wata rana hanya tabi dasu ta saman wani dogon tsauni wanda ƙarƙashinsa na da nisan gaske kuma ruwane ke kwarara a kan tsaunin yana zuwa ƙasansa inda wasu manyan duwatsu suke da magudanar ruwa. Bìsa dole suka sauka daga kan dawakansu suka fara tafiya a hankali sai da suka zo kan tsakiyar tsaunin kawai sai gimbiya Luzaiya ta faki numfashin su ta daka tsalle ta faɗa ƙarƙashin tsaunin nan ba tare da yin wata shawara ba jarumi Nazmir ya kwaɓe rigarsa da sauri shi ma ya daka uban tsalle yabi bayanta. Al'amarin da ya firgita su Bagwan kenan, suka leƙo ƙasan tsaunin cikin ɗimauta da baƙin ciki don sun tabbatar da cewa Nazmir da gimbiya sun halaka kenan. Kafin Luzaiya da jarumi Nazmir su faɗo ƙasan tsaunin nan sai da suka yi tafiyar daƙiƙa dubu biyu a sama, tuni a lokacin ƙarfin iska ya sa Luzaiya ta suma,shi kuwa Nazmir bai suma ba sai da ya isa ƙarshen ramin, kafaɗarsa ta fado kan wani dutse. Cikin sa'a Luzaiya ta faɗo akan ruwa. Gaba ɗayansu su biyun ruwa ya jasu ya tafi da su izuwa gaɓar kogi ya watsar da su. Bayan kamar rabin sa'a sai gimbiya Luzaiya ta farfaɗo. Tana buɗe idanunta ta miƙe zumbur a firgice. Ta hau kalle-kallen daji tana mamakin yadda aką, yi ta rayu. Ba zato sai ta ga jarumi Nazmir kwance a kusa da ƙafarta. Ta dube shi cikin mamaki tace a ranta, ya akai wannan ya zo nan alhalin ni kaɗai na faɗo ƙarƙashin tsaunin nan. Na tabbata ba zai jeho kansa ba tunda yana son rayuwarsa. Koda taga wata ƙaramar wuƙa a jikin Nazmir sai ta cirota ta tsaya tana kallonta tana mai yin shawara da zuciyarta tana mai cewa, "Tun da dai na jeho kaina cikin rami ban mutu ba, ai sai na kashe kaina da wuƙar nan dan na huta da takaicin duniya." Tana gama faɗin haka sai ta zare wuƙar daga cikin kufenta ta daga sama ta saita cikinta zata burma. Caraf ta ji an riƙe hannunta. Cikin sauri ta waiga suka yi arba da juna. Ba wani ba ne ya riƙe hannunta face jarumi Nazmir. Cikin tsananin fushi tace, "Don me ka damu da rayuwata ka ƙyaleni na mutu mana." Nazmir yace, "rayuwarki ita ce rayuwata da ta abokaina da suka rage. Idan ban kai ki ba ga sarkinmu a raye ba muma kashe mu za'a yi." Yana gama faɗin hakan ya sunkuceta sama ya đora a kafaɗarsa ya shiga laluben hanyar đa zai bi ya koma inda abokan tafiyarsa suke." ************************************* Koda sarki Dujalu yazo nan a zancensa kawai sai aka ga wata ƙatuwar damisa ta shigo cikin fadar a guje kuma a haukace, kawai sai ta daka tsalle da nufin ta dirga kan sarki Dujalu. Cikin tsananin zafin nama tsoho Rafkanagu ya shaƙo wuyanta da hannu đaya ya fyaɗata da ƙasa. Ko shurawa ba ta yi ba,ta zama gawa. Al'amarin da yayi matuƙar jefa sarkí cíkin tsananin mamaki kenan,domin ba su taɓa ganin tsoho mai ƙarfi irin na wannan ba. Sarki Dujalu ya tambayi kansa cikin zuciya, ''An ya kuwa wannan tsohon mutum mutum ne?" Wani bafade ya je kan damisar ya duddubata sannan ya dubi sarki Dujalu yace, ''Ranka ya daɗe ai wannan damisar kace wacce ake kiwo anan gidan. Lallai duk yadda aka yi jiya mai bata abinci ya mance bai kulle ƙofar kejinta ba." Koda jin haka sai sarki Dujalu ya fusata yace, maza aje a kamo mai bata abincin,a tsire shi tunda har ya yi sakaci haka ya janyo tashin hankalin sarki,kuma ya zamo sanadin katse wannan labarí mai daɗi na hikayar jarumi Nazmir da gimbiya Luzaiya. Bazan cigaba da baku labarin ba sai bayan an ƙaddamar da mai kula da damisar nan. Wannan shi ne abin da ya faru a fadar sarki Dujalu na birnin Misra sa'adda su Ruziyal ke aikin rubuta sabon KUNDIN TSATSUBA na biyu. ***************************************** Al'amarin su Jafar kuwa bayan Mazalish ta gama kalle-kallenta suka faɗo duniyar su Jafar sai hankalinta ya koma kan KUNDIN TSATSUBA, wanda ke buɗe a gabansu ta ƙare masa kallo tsaf a cikin nutsuwa. Sannan ta dubi Jafar,Yelisa,Mashrila da Gulzum tace, "Yanzu a cikinku nan babu wanda zaí iya tsayar da littafin nan daga ci gaba da buɗe kansa don na tafi neman masoyina jarumi Hubairu." Koda jin wannan batsu sai Yelisa ta yi tsaki tace, "Wannan kuma wace irin maganar banza kike yì, inda muna da wannan ikon ai da tuni muma mun yì ko dan mu huta da tsananin azabar da muke sha a cikinsa." Jafar ya ƙyalƙyale da dariya yace, "Haba yayata ai kawai ki rungumi ƙaddara kawai domin kin sayi wahala da kuɗinki tun da kika yi gangacin biyo mu. Da dai kin yì zamanki a can duniyarku ta mayu da ya fiye miki kwanciyar hankali." Gama faɗin haka ke da wuya sai shafin KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha uku inda suka yi arba da hoton wani surƙuƙin daji a samansa an yi rubutu kamar haka: "WANNAN JEJI, JEJI NE NA ABUBUWAN MASIFA IRI-IRI. AN ƘIRƘIRESHI NE KIMANIN SHEKARU DUBU BAYA." MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO." Wata siririyar murya ce ta karanta wannan jawabi. Muryar na đaukewa iskar cikin kundin zuƙe su Jafar suka zama 'yan mini-mini suka faɗa ciki. Kawai sai suka tsinci kansu a tsakiyar wannan jeji irin wanda ba su taɓa gani ba a rayuwarsu,domin komai na cikin sa ya kasance babba mai girman gaske. Ma'ana bishiyoyi, duwatsu da tsirai. Manya-manya ne, girmansu ya wuce ƙima domin bishiya ɗaya sai kaga girman ta ya ninka irin ta duniyar su Jafar sau arba'in. Kuma kowacce bishiya siffar fuskar mutuntaka wato tana da ido,baki da hanci har da ma kunnuwa,kuma suna motsi wato suna harkokinsu kamar yadda sauran halittu masu rai da jiki keyi, saidai ka ga bishiya na tafiya da ƙafafunta ko kuma ka ga tana aiyuka iri-iri. A cikinsu kuma akwai manya da ƙanana. Ba zato ba tsammani sai gaba ɗayan bishiyoyin dake wajen suka yi wa su Jafar ƙawanya ya zamana babu wata hanya da za su iya bi su tsere. Mafi girma daga cikin bishiyoyin ta buɗi baki tace, "Yaku waɗannan mutane mene ne ya kawo ku duniyarmu? Shin kun zo neman wani abu ne ko kuwa kun zo leƙen asiri ne?" Cikin firgici su Jafar suka ƙurawa bishiyar idanu aka rasa wanda zai bada amsar tambayar har sai da bishiyar ta daka musu tsawa gami da maimaita tambayar. Jafar ya ɗaga kansa sama ya dubi wannan ƙatuwar bishiya mai kama da tsauni a gabansa yace, "Yake wannan bishiya ki yi sani cewa ba mu kawo kanmu nan ba kawo mu aka yi, kuma bamu da nufin komai a kanku kuma ba mu zo neman komai anan ba,muna neman alfarma idan har zaku iya mayar damu in da muka fito to ku taimakamana." Koda jin wannan batu sai babbar bishiyar ta tuntsire da mahaukaciyar dariya mai kama da tsawa. Nan take sauran 'yan uwanta bishiyoyin suma suka tayata dariyar. Al'amarin da ya hargitsa jejin gaba ɗaya kenan,ya kama girgiza kamar ƙasa zata daddare. Wata irin ƙara mara daɗin ji ta cika kunnuwansu Jafar bisa dole suka toşhe kunnuwansu suka farfaɗi ƙasa. Lokaci guda bishiyoyin suka daina dariyar,komai ya tsaya cak. Babbar bishiya tace, "Yaku waɗannan bil'adama ku yi sani cewa mun san duk irin makircinku da wayonku lallai ba ku isa ku yaudare mu ba, domin a shekarun baya ire-iren ku sun zo mana don leƙen asiri da nemạn wasu abubuwa don bunƙasa harkokin ƙere-ƙerensu na zamani wanda da sune suke yi mana ɓarna. Bisa wannan dalili yanzu zamu tafi da ku izuwa fadar sarkinmu don a bincike ku,a gane ko kuna ɗaya daga cikin irin waɗannan mutane. Kafin wani daga cikin su Jąfar ya ce wani abu tuni wasu bishiyoyi guda biyar sun jeho rassansu sun kanannaɗesu kamar yadda ake naɗe tabarmå,kuma kowacce bishiya mutum đaya ta ɗauka. Kawai sai suka ga bishiyoyin sun tashi da su sama kamar ɓacewar taurari,sannan aka bayyana da su a wani jejin dabam wanda babu komai a cikinsa face jerin bishiyoyi irin waɗannan masu tsananin yawan gaske. Ko'inà ka duba sune iya hange ba adadi. A can gefe guda bisa kan wani ƙaton tsauni wata jibgegiyar bishiya ce wadda duk ta kere sauran a girmą. Nan take gaba ɗayan bishiyoyin suka yi mata sujjada alamar gaisuwa. Jibgegiyar bishiyar ta buɗe baki tace, "An gaisheku mutanenn birnin tsirrai." Daga nan sai aka gurfanar da su Jafar a gaban bishiyar. Ɗaya daga cikin waɗanda suka ɗauko su tace, "Ya sarkin sarakai ɗazu ne muka kama waɗannan bil'adaman a cikin gonarka ta bayan gari,muna zargin suma sun zo ne leƙen asiri, ko neman ma'adanai babu mamaki ma suna daga cikin al'ummar Sukardas." Koda jin haka sai sarauniyar bishiyoyi ta dubi su Jafar ta ƙare musu kallo cikin nutsuwa,sannan ta buɗe baki cikin wata irin siririyar murya mai taushi tamkar ta ƙaramar yarinya 'yar shckara huɗu,tace, "Ammą dai fadawannan nawa kun cika shashashai. Shin makafi ne ku ba ku yi nazarin waɗannan mutanen bą sosai? Ai ko kaɗan ba su yi kama da irin waɗancan masu zuwa leƙen asiri ba,ko ncman ma'adanai haką kuma ba su yi kama da irin al'ummar Sukardas ba." Sarauniyar ta dubi su Jafar tace, "Yakų waɗannan baƙi ina son ku saki jikinku damu lallai ba zamu cutar da ku ba, kuma ku matso nan kusa dą ni." Nan take su Jafar suka ƙarasa gaban sarauniyar bishiyoyi suka zazzauna. Sarauniya ta sa aka-kawo musu ruwan sha da 'ya'yan itatuwa masu zaƙi da daɗin ɗanɗano,irin wanda ba su taɓa ci ba,suka kimtsa cikinsu. Bayan sun nutsu ne sarauniyar ta sake dubansu tace, "To ina son yanzu ku bani labarinku da yadda kuka zo nan." Ba tare da wata gardama ba Jafar ya kwashe labarinsu tun daga lokacin da suka ɗauko KUNDIN TSATSUBA a rijiyar gidan Riziyal shi da Yelisa kawo i yanzu ya zaiyane shi. Koda ya gama bada labarin sai sarauniyar ta hau yi musu tafi suma sauran bishiyoyin sai suka yi koyi da ita. Daga can kuma sai suka daina tafin tace, "Yakai Jafar haƙiƙa kai da abokan tafiyarka kun cancanci yabo da jinjina domin kun yi matuƙar ƙoƙari wajen kare kan ku abisa wahalar da kuke sha a cikin KUNDIN TSATSUBA,kuma kun cika jarumai. Muma yanzu zamu sanar daku masifar da ke addabarmu a garin nan,kuma muna fatan zaku taimaka mana mu kawo ƙarshenta,domin idan ma ba ku taimaka mana ba in ta zo sai ta haɗa da ku. Mun sani cewa ku bil'adama kuna da basira da hikima fiye da kowacce irin halitta shi yasa muke son ku taimaka mana,ku yi sani cewa a bayan kowanne kwana goma akwai wasu irin mutane masu kawuna irin na batoyi da kuma fufafukai irin na jemagu suna zuwa mana su yi ta feso mana wuta daga sama suna ƙonemu. Sai sun yi mana ɓarna mai yawa sannan suke tafiya. Babu irin hikimar da ba mu yi ba,don mu harbosu ko mu kama su amma abu ya faskara domin komai ƙarfin makami baya iya huda jikinsu. Haka kuma jikin na su na da matuƙar santsi baya ruƙuwa." Koda jin wannan batu sai Mashrila tace, "Ai wannan matsalar taku mai sauƙi ce ni na san hanyar da za'a bi a iya kama waɗannan halittu." Topah,wace dabara uwar hikima Mashrila zata kawo,mu haɗu a babi na gaba don jin yadda zata kaya. Ahmad Munir ke muku sallama. Fatan alheri. Contact:- 08167757245Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part O A baya mun tsaya ne inda:- Koda jin wannan batu sai Mashrila tace, "Ai wannan matsalar taku mai sauƙi ce ni na san hanyar da za'a bi a iya kama waɗannan halittu." ### Cikin zumuɗi sarauniyar bishiyoyi tace, "Yarinya maza ki sanar da mu wannan hanya domin yau saura kwana uku waɗannan halittu su zo." Mashrila tace, "Kada ku damu yanzu dai ku barmu mu huta tukunna domin mun sha wahala mai yawa a duniyar su Mazalish. Nan da wani lokaci kaɗan zan sanar da ku hikimar da ke raina." Sai da su Jafar suka yi baccin sa'a bakwai sannan suka farka. Farkawarsu ke da wuya aka sake kawo musu nau'in ya'yan itatuwan suka ci suka ƙoshi. Sannan Mashrila tace aje a samo mata ɗanyar jijiyar bishiya mai tarin yawa. Nan take wata ƙatuwar bishiya ta bugi ƙirji tace, ita ta yarda a yanki tata jijiyar. Kawai sai ta fiddo da jijiyoyinta aka yi ta tsinka sai da aka tara mai yawa, a sannnan ne bishiyar ta faɗi ƙasa summmiya sai da aka yayyafa mata ruwa ta farfaɗo. Mashrila tace, "Waye gwanin iya saƙa a cikinku?" Wata mitsitsiyar tace itace. Mashrila tace mata, "ina so ki ɗauki jijiyar nan ki saka mini raga mai ƙananan ƙofofi kuma mai girman gaske, kuma ki yi mata mariƙai guda huɗu a ƙarshen bakunanta. A ƙallah ina son ki yi ragar guda dubu." Mitsitsiyar bishiya tace, "An gama" Nan take ta zauna ta fara aiki. Ai kuwa a cikin rabin sa'a ta kammnala abin da aka umarce ta,koda ta gama sai Mashrila ta dubi sarauniyar bishiyoyi tace, "To kin ga waɗannan abubuwan da su zamu yi amfani muna lulluɓe waɗannan halittu muna ɗaure su a jikin duwatsu. Ko sun fesawa wannan raga wuta ba za ta ƙone ba,saboda danshin ruwan da ke jikinta." Koda jin haka sai mamaki ya kama kowa a wajen. Sauraniyar bishiyoyi tace, "Haƙiƙa wannan yarinyar kin cika mai basira, tabbas wannan hikima ta ki za ta yi aiki sosai." Kwana uku na cika sai ga waɗannan halittu masu kan batoyi da fukafukan jemagu,sun iso sai shawagi suke a sararin samaniya. Suna feso wuta tana ƙone bishiyoyi. Nan da nan jejin ya hargitse gaba ɗaya bishiyoyin sukai ta guje-guje da iface-iface. Idan mutum na wajen ya ga yadda rayukan bishiyoyin ke salwanta dole ne ya tausaya. A wannan lokaci su Jafar tare da wasu manyan bishiyoyi sun ɓuya a cikin wani kogon dutse ɗauke da waɗannan raga-raga guda dubu. Sai da suka barí halíttun nan sun fara saukowa ƙasa-ƙasa,sannan suka yi fitar burgu suna lullube su da ragar,sannan su ɗaure su a jikin duwatsu, cikin zafin nama da sauri. Kafin a jima an kama halittun sama da guda ɗari tara. Sauran kuwa duk saí suka tsere. Waɗanda aka kama ɗin sai suka kasa ceton kansų daga cikin ragar suka yi ta ruri suna fesa wuta,amma a banza don ba su sami damar kuɓuta ba. Koda ganin abin da ya faru sai gaba ɗayan bishiyoyin garin suka rugo suka hau tsalle-tsalle da waƙe-waƙe don murna. Sarauniyar bishiyoyi ta zo gaban Mashrila ta tsaya tace, "Yanzu ya zamu yi da waɗannan halittun da muka kama?" Mashrila ta ce, "Haka za ku bar su su yi ta zama a cikin ragar nan har yunwa da ƙishirwa su kashe su." Nan fa bishiyoyi suka yi ta godiya ga Mashrila da abokan tafiyarta,bayan an nutsu sai Jafar ya dubi sarąuniya yace, "Yanzu ya za'a yi mu fita daga wannan garin naku,mu shiga wani?" Koda jin wannan tambaya sai sarauniyar bishiyoyi ta dubi wata basamudiyar bishiya tace, "yake Kalbaladu na uwarce ki da ki fitar da su daga birnina." Tana gąmą faɗin hakan saita zuro rassanta ta suri Jafar,Yelisa,Mashrila, Mazalish da Gulzum ta yi sama dąsu sannan ta wangame bakinta ta jefa su a ciki. Kawai sai su Jąfar suka ga an watso su cikin duniyar su ta KUNDIN TSATSUBA. Har yanzu shạfi na goma sha uku ne a buɗe. Gaba đayansų suka dubi juna kamar waɗanda suka farka daga mafarki. Jafan ya ce, "Kai amma fa wannan shafin na goma sha uku ya zo mana ɖa alheri domin ba mu sha wata wahala mai yawa a cikinsa ba." Yelisa tace, "Ƙwarai kuwa ai sai ka buđe mana shafin gaba babu mamaki mun fita kenan daga cikin wahala." Caraf Mashrila ta tari numfashinta, tace, "Waye ya gaya miki cewar mun fita daga wahala? Ina tabbatar muku da cewa yanzu ne ma zamu fara shiga wahala duk wadda aka sha a baya sharar fage ce." Gulzum yace, "Kun ga ba hira zamu tsaya yi ba aikin shekara goma sha tara da wata shida ne a gabanmu,ku yi sauri ku buđe mana shafin gaba ko mun ragewa kanmu tsawon lokaci." Cikin yanayin mamaki Jafar ya dubi Gulzum yace, "Ya akai ka san cewa sai mun shafe wannan lokacin muna karanta KUNDIN TSATSUBA?" Gulzum yace, "Kai dai na ga alama daƙiƙiyar ƙwaƙwalwa gareka. Yanzu ashe har ka manta cewa an gaya mana shekaru ashirin za mu yi muna karanta littafin kuma duka-duka yanzu a cikin wata na huɗu muke?" Kafin Jafar ya ƙara cewa wani abu sai Yelisa ta yunƙura ta buɗo shafi na goma sha huɗu inda suka yi arba da hoton wani kogon dutse. A samansa an yi rubutu kamar haka. "WANNAN KOGO,KOGO NE NA MASIFA DA BALA'I IRI IRI. AN ƘIRƘIRESHI FIYE DA SHEKARU DUBU GOMA BAYA. MAI KARATU SHIGO CIKINSA KA SHA KALLO." Koda Yelisa ta gama karanta wannan jawabí a fili sai iskar KUNDIN TSATSUBA tayi fitar burgu ta zuƙe su gaba đaya su biyar ɗin suka zama 'yan ƙanana mini-mini suka faɗa ciki. Kawai sai gani suka yi sun faɗo cikin wani jeji mai girman gaske,babu komaí a cikinsa face wani katafaren dutse mai ƙaton kogo. Ko'ina ka duba a jejin iyakar ganinka wannan dutse ne ba'a íya ganin ƙarshen sa. Lokaci guda su Jafar suka mimmiƙe tsaye suka yi nazarin dutsen sannan suka dubi junansu. Yelisa tace, "Yanzu mene ne abin yi?" "Abin yi kawai mu shiga cikin kogon nan tunda babu wata hanyar da zamu iya samu a jejin nan ko ina dutse ne." Mashrila ce ta ba da wannan amsa. Gulzum,Jafar Mazalish suka amince da wannan shawara ta Mashrila. Ba tare da ɓata wani lokaci ba,suka kunna kai cikin kogon. Wani abin mamaki shi ne koda shigar su cikin kogon sai duhu ya yaye haske ya baibaye cikinsa ya zamana suna ganin komai. Babu komai a cikin kogon face tsiraron duwatsu,ƙananan bishiyoyi, da kuma gurɓatattun damomi. Haka dai su Jafar suka yi tafiya a cikin kogon be tare da sun ga komai ba,kuma ba su ji motsin komai ba har tsawon sa'a hudu. A wannan lokaci duk sun gaji ainun Gulzum ne kaɗai bai gaji ba. Jafar da Yelisa kam har haɗa ƙafa suke suna rangaji a hanya tamkar waɗanda suka bugu da giya. Kwatsam sai suka yi kiciɓis da wata ƙatuwar rijiya wadda aka rufe ta da murfin ƙaton mummulallen ƙarfe mai nauyin tsiya. Dukkaninsu sai suka yi turus a gaban rijiyar. Jafar yace, "Me ya kamata mu yi da rijiyar nan?" Mazalish ta ce, "Kawai mu buɗe ta ai dama duk muna jin ƙishirwa sai kowa ya jiƙa maƙogwaronsa." "Kai anya kuwa za'a iya samun ruwa a cikin rijiyar nan ku duba fa ku gani bakinta a bushe yake ƙyamas babu alamar ana ɗiban ruwa a cikinta.'' Yelisa ce tayi wannan jawabi. Ita kuwa Mashrila sai ta daka mata harara tace, "Ke dai kin cika tsoro,to ki sani har abada matsoraci baya zama gwanı." Cikin fushi Yelisa tace, "To na ji ni matsoraciya ce, tun da ke jaruma ce ai sai ki buɗe mana rijiyar ko." "Wannan kuma aikin sarkin ƙarfi ne Gulzum." In ji Jafar. Gulzum ya murtuke fuska duk da cewar an yabeshi. Nan take Gulzum ya sa hannu ɗaya da nufin ɗauke murfin rijiyar amma sai ya kasa. Mamaki ya kama shi ya saka hannayensa biyu ya taƙarƙare iya ƙarfinsa ya ɗago murfin,amma sai ya kasa đaga shi gaba ɗaya. Nan fa su Jafar suka cika da mamaki, domin ba su taɓa ganin aikin ƙarfin da ya gagari Gulzum ba sai yau,tun sa'adda suka shigo cikin KUNDIN TSATSUBA. Koda ganin abin da ya faru sai Mazalish tace, "Gulzum gafara nan ka bani wuri tunda ka kasa buɗewa." Gulzum yace, "To 'yar sarkin mayu ai sai ki jarraba ƙarfin maitarki anan mu gani." Mazalish ta daka masa tsawa,tace "Kar ka sake kirana maiya tunda dai ni ba maiya ba ce, kuma na baro maita a can mahallinta." Kawai sai Mazalish ta nuna murfin rijiyar nan da ɗanyatsanta guda. Take wata siririyar iska ta fito daga cikin ɗanyatsan ta ɗaga murfin rijiyar nan sama ta ajiye shi a gefe guda. Mazalish ta dube su gaba ɗaya tace, "Ni kaɗai ce zan iya yin tsafi ya yi aiki a cikinku saboda na sami tsafina ne a cikin duniyar KUNDIN TSATSUBA,ku kuwa kun samo naku tsafin daga wata duniyar dabam." Mazalish na gama rufe bakinta kenan sai wasu irin halittu suka yo fitar burgu daga cikin rijiyar nan suna yin wata irin ƙara mara daɗin ji wacce ka iya kashe dodon kunne. Su dai waɗannan halittun 'yan ƙanana ne mini-mini,domin girmansu ba zai wuce na fara ba,amma kuma surar aljanu gare su. Gaba đaya jikinsu,hannaye ne masu zaƙwa-zaƙwan farata. Adadin su ya kai dubu,kuma gaba ɗayansu suka fito waje daga cikin rijiyar nan. Ai kuwa nan take suka hau yakusar jikin su Jafar. Cikin ƙanƙanin lokaci suka yi musu fata-fata,kowa ka duba jini ke zuba a jikinsa,kuma jiri na ɗibarsu suna faɗuwa da miƙewa da ƙyar. Koda Mazalish taga zasu hallaka gaba ɗaya sai tayi tsafi suka zama hayaƙi. Hayaƙin ya shige cikin rijiyar nan,sannan murfin ijiyar ya taso daga inda yake ya rufe rijiyar ya zamana halittun ba su sami damar binsu cikin rijiyar ba. Sai duk suka yanyame kan rijiyar suna ta yin wannan ƙarar ta su mara daɗin ji. Yayin da hayaƙi ya faɗa cikin rijiyar sai ya rikiɗe ya zama Mazalish,Yelisa,Jafar,Gulzum da Mashrila. Cikin fushi Jafar ya dubi Mazalish yace, "Don me za ki shigo da mu cikin rijiyar nan bakya tunanin za mu iya riskar abin da yafi waɗancan halittun haɗari?" Mazalish tayi ƙwafa tace, "Kash! Dana san zaka faɗi haka da na barka a can kai kaɗai. Shin baka taɓa jin an ce abin da ya koro ɓera ya shiga wuta,yafi cutar zafi ba? Ai da masifar da ka sani gwara wadda baka sani ba." A daidai wannan lokaci ne kuma hankalin su gaba ɗaya ya koma kan inda suka tsinci kan su sai suka ga ashe a tsakiyar wani ƙaton gari ne. A cikinsa ga gidaje nan da kayayyaki irin na rayuwar mutane sosai,amma kuma ba su ga koda mutum guda ɗaya ba a garin. Garin ya yi tsit,ko kukan gyare babu. Al'amarin da ya yi matuƙar jefa su cikin mamaki kenan. Kawai sai suka cigaba da tafiya su shiga nan su fita can,har tsawon sa'a uku sannan suka iso ƙarshen garin inda yayi iyaka da gaɓar wata teku. Kwance a bakin gaɓar tekun wasu gumaka ne bila adadin masu surar ifiritan aljanu. Anan su Jafar suka tsaya suna kallon waɗannan gumaka cikin al'ajabi. Jafar yace, "Kai amma fa abin al'ajabi baya ƙarewa,wai shin to ina mutanen wannan birnin,kuma me suke yi da waɗannan gumakan?" "To wa kake tambaya ka san dai a cikin mu nan kaf babu mai iya baka amsa." Gulzum ne ya faɗi haka cikin ɗacin rai. Jafar ya fusata yace, "Wai kai me na tare maka ne a rayuwarka kake tsangwamata ko kuwa mun haɗa neman aure ne?"(🤣🤣🤣🤣 Tambaye sa dai Jafarun mu🤣) Koda jin wannan tambaya sai kowa ya bushe da darıya har shi kansa Gulzum ɗin. Yelisa tace, "haba Jafar yanzu in banda daraja ta ina kai ina yin hamaiya da Gulzum ai yafi ƙarfin ka ta ko'ina." Mazalish ta ce, "Kun ga ba hira zamu tsaya yi ba gwara mu yi abin da zai fishshe mu." Kawai sai ta nufi inda gumakan nan suke. Da zuwa sai ta hau duba su tana tattaɓasu,ko zata ga wani abun da yake akwai raunika a jikinta kuma har yanzu jini bai daina zuba ba sai jinin jikin nata ya ɗiga akan ɗaya daga cikin gumakan. Faruwar hakan ke da wuya sai ruhi ya shiga jikinsa nan take,ya miƙe tsaye ya yi kururuwa yana mai zazzago harshen bakinsa wanda girmansa ya kai na ƙatuwar bishiya. Cikin firgici su Jafar suka juya da baya suka runtuma da gudu suka bar Mazalish nan tsaye gaban ifiritin ta kasa gudu don tsananin razana,sai ihu take faman yi kawai. Ifiritin nan ya sake taƙarƙarewa ya wangame ƙaton bakinsa yana mai ruri ya rinƙa aman mutane daga cikin bakinsa. Sai da ya amayar da kusan mutum dubu. Sannan hankalinsa ya dawo kan Mazalish wacce har yanzu tana nan tsaye a gabansa tana ihu. Cikin zafin nama ya kawo mata wafta don ya ɗauke ta,ita kuwa ta goce cikin zafin nama sannan ta ruga da gudu ta nufi inda suka Jafar suka yi. Ifiritin nan kuwa ya bita a guje suka kasa tsere. ldan tayi gudu,tayi gudu,sai ta ga ifiritin nan daf da ita yana jeho harshensa waje don ya lasota, kawai sai ta ƙwala ihu ta ƙara ƙaimin gudu. Haka dai ya cigaba da binta har suka riski su Jafar. Koda su Jafar suka waigo suka ƙaton ifiritin ya kusan cimma Mazalish sai suka ƙara ƙaimin gudunsu. Kawai sai wasu fukafukai guda biyu suka fitar da kansu daga jikin ifiritin nan ya tashi sama ya riski Mazalish ya lasota da harshensa sannan ya haɗiyeta. Daga nan ya bi su Jafar ɗaya bayan ɗaya duk ya haɗiye su. A gaban KUNDIN TSATSUBA su Jafar suka tsinci kansu,har yanzu jini na zuba a jikinsu sakamakon raunukan nan da 'yan mini-mini aljanu sukai musu. Kuma shafi na goma sha huɗu ne a buɗe jikin tafin KUNDIN TSATSUBA. Nan take su Jafar suka yanke jiki suka faɗi ƙasa kamar sumammu. Sai bayan sa'a guda sannan kowannansu ya dawo cikin haiyacinsa. Yelisa ce ta fara miƙewa zaune ta dubi kowa tace, "Tabɗijam amma fa wannan karon mun sha baƙar wuya." Mashrila tayi tsaki tace, "Ai in dama wahalar ce zallah babu tashin hankali ai da sauƙi." Shi kuwa Jafar sai ya dubi Mazalish yace, "Wai ke ina ƙarfin tsafin naki ya tafi,me ya sa baki cece mu daga sharrin wannan ifiritin ba?" Mazalish tayí murmushi,sannan tace, "Lallai yanzu na tabbatar da cewa kai yaro ne. Ai idan ka ji ana cewa ga ƙi gudu to sa gudu ne bai zo ba." Jafar yace, "Wai ina ruwan filfilwa ai ban san cewa Gulzum na da gudu ba, sai sa'adda ifiritin nan ya biyo mu,kafin na waiga bayana tuni Gulzum ya wuce mu gaba ɗaya,duk girman nan na sa da nauyin jikinsa bai hanashi gudu ba, don sai ya zamo kamar soso akan ruwa." Gaba ɗaya aka tuntsire da dariya,shi kuwa Gulzum sai ya turɓune fuska yace a ransa, 'Ina fatan naga ranar da zamu gama karanta KUNDIN TSATSUBA sai na nunawa yaron nan cewa bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne. Tabbas rainin da ke tsakaninmu yayi yawa." Kafin wani daga cikin su ya ƙara cewa wani abu KUNDIN TSATSUBA ya buɗe kansa izuwa shafi na goma sha biyar. Nan take suka yi arba da hoton wata alƙarya. A ƙasanta an yi rubutu kamar haka.... ".....WANNAN ALƘARYA,ALƘARYA CE TA BALA'I, AN SAMAR DA ITA KIMANIN SHEKARU DUBU HUƊU. MAI KARATU SHIGO CIKINTA KA SHA KALLO..." Topah,me zai faru gasu Jafar a wannan alƙarya? Mu haɗu a babi na gaba idan Allah ya kaimu. Fatan alheri. Contact:- 08167757245 Matsatsubi 1 Typing:-Ahmad Munir Muhammad Posting:-Ahmad Munir Muhammad Part P Takun ƙarshe A baya mun tsaya a inda:- A ƙasanta an yi rubutu kamar haka.... ".....WANNAN ALƘARYA,ALƘARYA CE TA BALA'I, AN SAMAR DA ITA KIMANIN SHEKARU DUBU HUƊU. MAI KARATU SHIGO CIKINTA KA SHA KALLO..." ###### Siririyar muryar nan ce ta karanta wannan jawabi. Muryar na ɗaukewa iskar cikin KUNDIN TSATSUBA ta sake zuƙe su Jafar gaba ɗayansu. Kawai sai tsintar kansu suka yi a tsakiyar wani babban birni mai yawan cikowar mutane,maza da mata,yara da manya,duk inda suka duba sai su ga kowa na ƙera kwale-kwale ɗan ƙarami daidai shigar mutum ɗaya. Duk inda suka wuce sai dai su ga ana kallansu kawai,amma babu wanda ya kula su. Al'amarin da ya jefa su cikin mamaki kenan. Haka dai suka yi ta yawo a cikin garin har suka gaji,sannan suka sami wuri suka zauna, don su huta. Jafar yace, "Kai ku tsaya fa an ce ruwa baya tsami banza. Ina ganin zai fi kyau mu ma kowannan mu ya ƙera nasa kwale-kwalen domin an ce idan ka je gari kaga kowa ya ɗaura jela a bayansa kaima ka ɗaura." "Ƙwarai kuwa ka zo da shawara mai kyau domin babu mamaki akwai masifar da zata zo kuma in mutum ba shi da kwale-kwalen hallaka zai yi." Ba tare da wani da gardama ba suka miƙe tsaye gaba ɗaya don tafiya neman kayan aikin ƙera kwale-kwale. Kawai sai suka ga wani babban mutum ya tunkaro su yana sanye da hular saurata akansa,mutane na biye da shi. Koda zuwansa gare su sai yace, "Yaku waɗannan baƙi ku yi sani cewa kun kawo kanku mahallaka,domin akwai masifar da zata zo mana nan da kwana biyu,damu daku babu wanda zai tsira da rayuwarsa, sai mai nisan kwana." Cikin mamaki Jafar ya dubi mutunin yace, "Wace irin masifa ce wannan take zuwa muku?" Mutumin ya yi gyaran murya yace, "Ni sunana sarki Makanul Habasi,gaba ɗaya mutanen garin nan a ƙarƙashin mulkina suke,muna da wata matsala guda ɗaya. Kimanin shekaru dubu huɗu baya wani taƙadarin maridi ya taɓa zuwa mana, koda zuwansa sai ya kama gaba ɗayan mazajen garin nan ya ɗaure su tamau da sarƙoƙi. Su kuwa matayen mu ya bisu ɗaya bayan ɗaya yayi lalata da kowacce. Da ya gama wannan ɓarna sai ya ɓace aka neme shi sama da ƙasa aka rasa. Bayan tafiyarsa ne matayenmu suka yi ta kuka da baƙin ciki,da ƙyar suka samu suka kwankwance mu daga ɗaurin sarƙar da muka sha. Haka dai muka rungumi ƙaddara muka ci gaba da rayuwa har tsawon wata tara bamu ƙara ganin wannan maridiba. Koda wata taran nan ya cika sai gaba ɗayan matayenmu suka kama zubar da jini tamkar annobar amai da gudawa. Wannan jini ya rinƙa yawo a cikin gari ya malale ko'ina kai ka ce teku ce ta ɓalle. Ba zato ba tsammani kuma sai jinin ya rinƙa rikiɗa yana zama tsutsutsi masu girman gaske, waɗanda ka iya haɗiye mutum. Nan fa tsutsotsin nan suka hau yagar naman jikin mutane,aka yi ta guje-guje da iface-iface. A wannan rana babu waɗanda suka tsira face waɗanda suka faɗa cikin teku. A cikin tekun ma wasu da yawa sun mutu saboda haɗuwa da muggan halittun cikin ruwa. Waɗannan tsutsotsi ba su iya shiga cikin teku. Daga sannan wannan masifa ta ci gaba da wakana bayan kowanne kwana arba'in. Wannan shine dalilin da ya sa kuka ga muna ta ƙera kwale-kwaleka ba don komai ba ne sai don mu shiga cikin teku akansa don neman tsira da rayuwarmu. Yaku waɗannan baƙi gashi yanzu kun zo a rashin sa'a domin yau saura kwana biyu rak wannan masifa tu zo." Yayin da sarki Makanul Habasi yazo nan a zancensa sai hankalin su Jafar ya dugunzuma suka rasa abin dake musu da daɗi,Yelisa tace, "Yakai wannan sarki yanzu wane irin taimako zaka yi mana?" Makanul Habasi yace, "Babu abin da zan iya yi muku face na baiwa kowannen ku kyautar kwale-kwale da zarar kun ga wannan masifa tazo sai ku ruga izuwa cikin teku,idan kuna da nisan kwana sai ku rayu. Idan kuwa ba ku da shi a cikin tekun zaku hallaka. Yana gama faɗin hakan ne ya sa aka kai su Jafar masauki aka ba su abinci da abin sha,kuma aka sa musu magani a jikin raunikan da ke jikinsu. Kwana biyu na cika wannan annoba ta wakana wato matayen garin suka kama zubar da jini,jinin ya rinƙa malala yana yawo a cikin garin ya game ko'ina sai dai ka ga mutane na ta guje-guje akan jinin kowa na ƙoƙarin zuwa bakin teku. A wannan ranar har dasu Jafar ake wannan gudun ceton rai,sai da ya rage saura ƙiris gaba ɗayan mutanen su riski bakin teku sannan tsutsotsin suka rinƙa ƙurewa mutane gudu suna kama su,suna yagar naman jikinsu suna ci,kai kace karnuka ne ke walima da naman ɓeraye. Lokacin đa su Jafar suke ƙoƙarin isa bakin teku wata tsutsa guda ɗaya ta tuso su a gaba tana neman ƙure musu gudu. Gulzum ne a gaban kowa,sai Jafar ne ya zamo na ƙarshe, sai da ya zamana tsakanin Jafar da wannan tsutsa bai wuce tazarar taku biyu ba. Duk inda ya đauke ƙafarsa sai ka ga ƙafarta ta dira a wajen ta caki ƙasa. Take wurin zaiyi rami zururu kamar an haƙa rijíya. Sa'adda Jafar yaga tsutsar ta kusan cimmasa sai ya rinƙa ihu yana kiran sunan Gulzum,yana roƙonsa daya kawo masa đauki. Duk da cewar Gulzum na cikin tashin hankali saida dariyar mugunta ta ƙwace masa yace, "Shegen yaro sai yau ka san ina da amfani to ai ni ba wawa bane bare na koma da baya a ƙoƙarin cetonka ayi biyu babu." Da yake Yelisa na kan kafaɗar Gulzum ne sai taji abin da ya faɗa. Nan take ta dakawa Gulzum tsawa tace, "Maza ka juya da baya ka ceto rayuwar masoyina Jafar in kuwa ka ƙi na rantse da darajar mahaifina duk sa'adda muka koma duniyar mu sai nayi maka hukunci mai zafi." Koda jin wannan batu sai Gulzum ya fashe da kuka don tsananin takaici,domin babu abin da ya tsana a rayuwarsa sama da Jafar. Gashi kuma yanzu an tilasta shi akan ya juya ya ceto rayuwarsa. Wanda yin hakan na iya jefa tasa rayuwar cikin ƙila-wa-ƙala. Bisa dole Gulzumn ya juya da baya cikin tsananin gudu har ya riski Jafar ya sure shi ya aza bisa kafaɗarsa kusa da Yelisa,sannan ya juya cikin zafin nama don ya cigaba da gudu. Kafin ya juya tuni tsutsar nan ta kawo sara kawai sai ta zabtare wani ƙaton nama a duga-dugin Gulzum. Gulzum ya ƙwalla ihu,cikin tsananin juriya da jarumta ya daɗa mannewa da gudu jinı na zuba sharaf daga dugadugin nasa,amma bai fasa gudun ba,har suka isa bakin teku kowa ya shiga kwale-kwalensa suka miƙa cikin ruwa. Shigarsu cikin tekun ke da wuya wata irin ƙatuwar macijiya mai tsananin tsawo,kuma mai kawuna bakwai ta taso sama daga cikin ruwan ta rinƙa bugun mutane tana farfasa kwale-kwalensu. Kafin wani lokaci ta zama sanadiyari gawarwaki akan ruwan. Lokaci guda ta wangame bakinta ta haɗiye su Jafar su duka biyar ɗin hár ma da kwale-kwalensu gaba ɗaya. Su Jafar dai sai gani suka yi an jefo su cikin ta su duniyar tare dá kwale-kwalensu sun faɗo gaban KUNDIN TSATSUBA. A dugadugin Gulzum akwai wannan ƙaton rauni,kuma jini bai dai na zuba ba. Köda raɗaɗi da zogi ya ishi Gulzum sai ransa ya ɓaci yace, 'Ai kuwa tunda na shiga wannan hali a dalilin ceto rayuwar wannan yaron banga amfanin hưtún mu ba,gwarama mu ci gaba da shan wahala kówa jikinsa ya gaya masa." Kafin wani yace wani abu tuni aljani Gulzum ya daka tsalle ya buɗe shafin KUNDIN TSATSUBA na goma sha shida. Take suka yi arba da hoton wata guguwa. A samanta an yi rubutu kamar haka........ "WANNAN GUGUWA,GUGUWA CE TA MASIFA DA BALA'I. ẢN HALICCE TA KIMANIN SHEKARU DUBU SHIDA BAYA,MAI KARATU SHIGO CIKI KA SHA KALLO........." Gulzum na gama karanta wannan jawabi a fili sai iskar cikin KUNDIN TSATSUBA tayi fitar burgu ta zuƙe su gaba ɗaya suka zama 'yan mini-mini suka faɗa cikin KUNDIN TSATSUBA. YAYA ƘARSHEN HIKAYAR JARUMI NAZMIR DA GIMBIYA LUZAIYA ZATA KASANCE?? SHIN JARUMI HUBAIRU ZAI IYA SAKE ƘWATO GIMBIYA SIMA DAGA HANNUN SARKI LU'UMANU?? INA LABARIN BOKA SHAMHARU WANDA HAR YANZU BAI FITO BA DAGA HALWAR TSAFIN SA TA ZAMA MATSATSUBI?? SHIN YAUSHE NE ZA'A GAMA AIKIN RUBUTUN SABON KUNDIN TSATSUBA?? SHIN SU BOKANYA SAMARATU ZASU SAMI NASARAR SAMO ABUBUWAN DA SUKE NEMA DON YIN GALABA AKAN SHAMHARU?? WACE IRIN MASIFA SU JAFAR ZASU GANI A CIKIN WANNAN GUGUWA?? Mu haɗu a cikin MATSATSUBI littafi na biyu don jin cigaban wannan labari. DAGA MAI ƊEBE MUKU KEWA ABDUL'AZIZ SANI MADAKIN GINI Masha'Allah,anan muka kawo ƙarshen littafin Matsatsubi na ɗaya, Allah ya bamu ikon kawo muku littafi na biyu. Zaku iya yin sharhi. Fatan alheri. Contact:- 08167757245 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels