An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 1 post by Shuraih 99% Godiya ta tabbata ga Allah madaukakin Sarki da manzon sa Annabinmu Muhammad tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi, wanda ya bamu iko ga jama'a domin su samu abin debe kewa da nishadantarwa yayin karantashi. Shi wannan littafin, fassarace daga harshen larabci zuwa na hausa domin jama'a Su amfaneshi. Shi wannan littafi mafi yawancin mutanen yanzu basu sanshi ba, domin Malamai ne ada suke karanta wa jama' a shi idan sunajin nishadi. Zakuji cewa Wannan littafin ya kunshi labaran soyayyaya, nishadi da kuma abubuwa iri daban-daban, wadanda suka kunshi sha'anin bokanci da tsafe-tsafe wanda mutanen wancann lokaci suka kware a kai. Za kuma aji yadda rayuwa take kasancewa ga wannan sarki, tun tasowar sa da kuma girmansa, kama izuwa lokacin daya zama kasaitaccen Sarki da kuma mutuwar sa. Kuma za aji cewa wannan littafin ya shafi bangaren addini da kuma ma'amaloli na rayuwar alumma. halakata. MAALIKUS-SAIF Bin ZIYAZINUN a karan kansa an taba samu rayuwa irin tasa. ldan muka duba tarihin masarautar BORNO zamu samu cewa daya daga cikin wadanda suka taba yin sarauta a wannan masarauta wadanda akeyiwa lakabi da Saifawa Dinas (Wato Daular Saifawa), tayi kimanin Shekara dubu kafin ta gushe, wannan zuria ta saifawa sun samo sunansu ne daga wannan babban Sarki kuma kamar yadda tarihi ya nuna shine ya kafata. Don haka labari da aka bayar akan wannan Sarki SAIF yana iya zama kirkirerren labari ko kuma shi Sarkin ya zamto antaba samunsa A hakikama yankin da wannan sarkin ya zauna wato HAMRA'U YAMEN ko YAMEN wato kamar yadda wannan littafin tarihin ya nuna. A wani zamani mai tsawo daya wuce, zamanin Annabi Nuhu {Alaihissasatu wassalam yayi wa 'ya'yansa addu'ar Allah yasa daya daga cikin 'ya'yansa a samun wanda zai mallaki duniya ya kuma yada addinin Allah. Cikin ikon Allah sai wannan addu'a ta sa ta fada akan babban dansa SAMU, wanda shi SAMU a wannan lokaci zuriyar sa farare ne {larabawa), shikuma karamin dansa HAMU zuriyar sa bakake ne. Bayan Sun bar wajen Mahaifinsu, sai SAMU ya doshi gabashin duniya,yayin dashi kuma HAMU doshi yammacin duniya. Bayan wani lokaci mai tsawo, sai akayi wani Sarki mai suna ZIYAZINUN shi wannan Sarkiire-iren zuriar SAMU ne, kumaya samu tarihin adduar da Annabi Nuhu {Alaihissasatuwassalam} ya yi wa kakansu na cewa "Allah yasa a irin zuriyarsa a samu wanda zai mulkiduniya, kuma a samu wanda zai yada addinin ibrahimiyya, da yake a wannan lokaci zamanin Annabi Ibrahim ne{Alaihissasatu wassalam}. Sarki ZIYAZINUN ya lashi takobin InAllah ya yarda a kansa wannan addu'ar zata fada, saboda haka ya yi ta yake-yake a gabashin duniya kuma ya murkushe kasashe da dama da yaki, har ya fado yammacin duniya. Sai da takai hardai tsufa ya riskeshi. Wata rana Sarki ZIYAZINUN ya sauka a wanı guri, sai yaga yanayin wannan waje yana da kyau kuma yana da dadin zama, saboda haka sai yasa aka gina masa birni aka sa masa suna HAMRA'U YAMEN. Shi wannan birni daya ginaa yana karkashin masarautar HABASHA ne, wanda a wannan lokaci ita wannan kasa tana karkashin wani sarki mai suna SAIFURRA' ADU su kuma ire- iren HAMU ne wato su bakake ne. Sarki SAIFURRA'ADU ya samu labari cewa ga wani farin Sarki can ya sauka a kasar sa harya kafa birni ba tare kuma da izininsa ba. Dan haka sai ya tura yan leken asiri domin su gano masa irin shirin da Sarki ZIYAZINUN yazo dashi. Suka je suka sanar wa da Sarkin su cewa ai Sarki ZIYAZINUN yazo da runduna ta sadaukai masu tarin yawa, kuma suka fada masa cewa bazai iya yakarsa ba. Nan da nan Sarki SAIF yasa a ka tara masa bokayen kasar HABASHA domin su ba musulmai bane, taurari suke bauta mawa. Ya Ya umarci bokayen nan dasu duba masa su gani idan ya yaki wannan Sarki akwai nasara ko babu. Bokayen nan suka dukufa suka fara bincike kowanne yayi- yayi amman babu nasara, karshe dai suka sanar wada Sarki SAIF ya hakura babu nasara. Sarki ya sallamesu suka watse daga nan kuma Sarki yasa a ka kira masa wasu manyan bokayensa masu Suna SAKARADISA da SAKARAJUNA da Wazirinsa mai suna Waziri BAHARU. Nan da nan wannan mutane guda uku suka zo gaban Sarki SAIFI suka zauna. Sarki ya ce **Yana so ne su bashi shawarar yadda zai bullo wa Sarki ZIYAZINUN?". Da bokayen nan suka ji wannan bukata ta Sarki sai sukace "Tauraruwa ta baka nasara, ai abinda zaka yi shine ka dauki daya daga cikin yardaddun bayin ka ka bata guba, ka ce kana so ta boyeta a jikinta yadda kowa bazai iya ganinta ba, idan ta boye sai ka turata izuwa Sarki ZIYAZINUN a matsayin kyauta ta karramawa, ita kuma ka umarceta da idan ta tashi bawa Sarki ZIYAZINUN ruwa ko abinci da ta saka masa wannan gubar daya ci ko ya sha, sai ya mutu kaga shiken ba sai mun yakesa ba. Sarki SAIF yayi murna da wannan shawara daga bakin SAKARAJUNA. Nan da nan yasa a ka kirawo wata kyakykyawar kuyanga wadda tana daya daga cikin yardaddunsa KAMRIYYA. Aka kawo guba mai Suna ya bata ya ce "Ta boye inda ba wanda zai ganta koda cajeta aka yi". KAMRIYYA ta karbi gubar nan ta cusa a gashin kanta yadda inba wanda ya sani ba ba yadda za' ayi mutum ya gane. Daganan ya yi mata bayannin ce wa zaiyi Sarki kyautar ZIYAZINUN, idan ya karbeta ta ga suna tare to tasan yadda za tayi domin ta bashi wannan gubar ko dai a abinci ko kuma ruwan sha yaci ko ya sha. Ya ce "Idan ta aikata hakan zai 'yantata kuma zai bata dukiya mai tarin yawa,idan kuma ta kasa yin hakan to muddin ta dawo HABASHA to sai ya halakata". Da KAMRIYYA taji haka sai ta ce "Zata aikata duk abinda Sarki yake so. Shi kuwa Waziri BAHARU da yake musulmi ne, ya musulunta ne ba tare da sanin Sarki SAIF ba domin da yasan da musuluncinsa daya sa hallakashi, saboda da gudun abinda zai sameshi sai ya boye an musuluncinsa. Saboda kishin addini, kuma ZIYAZINUN musulmine sai yasan Sarki hankalinsa ya tashi, kuma yasan saboda da gudun abinda zai sameshi sai ya boye musuluncinsa. Saboda kishin addini, kuma yasan Sarki ZIYAZINUN musulmine sai hankalinsa ya tashi, kuma yasan lallai Sarki ZIYAZINUN bazai iya gane makircin da aka kulla masa da KAMRIYYA ba. Dan haka sai ya rubuta wasika zuwa ga Sarki ZIYAZINUN yayi bayanin ce wa "Shine Wazirin Sarki SAIF, kuma shi Musulmi ne, ya kuma yi masa bayanin duk irin makircin da aka kulla masa da KAMRIYYA duk ya rubuta a takardar, daya gama shine yayi kiran wani yardajjen bawansa ya bashi wannan takardar, ya ce "Yayi sauri ya riga yan aiken Sarki SAIF zuwa wannan birni na HAMRA'U YAMEN ya kai wa Sarki SAIF wannan takarda ba tare da wani mutumin ya ganshi ba, sannan ya fada masa ce wa "Idan har ya aikata hakan kuma ya dawo to zai 'yantashi, kuma zai bashi dukiya mai tarin yawa'". Waziri ya bashi takarda wannan bawa nasa ya daura sirdi ya sukani doki yabi ta wata barauniyar hanya ya nufi HAMRA'U YAMEN. Cikin dare ba tare da kowa ya ganshi ba... Bayan kwana uku sai akayi sa'a wannan bawa na Waziri ya riga yan aiken sarki SAIF zuwa Hamrau Yameen. Da zuwansa ya isa fada gurin Sarki ZIYAZINUN a kai masa iso gurin Sarki, ya fadi yayi gaisuwa yakuma isar da sakon Waziri BAHARU gurin Sarki ZIYAZINUN, yakuma ce wa Sarki ya sallameshi da wuri domin. kada yan aiken Sarki SAIF suzo su taraddashi anan suyi tunanin wani abu. Nan da nan Sarki yayi masa kyauta ya sallameshi ya juyo izuwa kasar Habasha. Bayan kamar sa'a uku saiga yan aiken Sarki SAIF sun iso kasar HAMRA'UU YAMEN. Da zuwansu suma sai suka wuce fada, akayi masu iso gurin Sarki ZIYAZINUN, da isarsu suka fadi gaban Sarki suka gaidashi kuma suka bashi kyautar KAMRIYYA da Sarkisu Sarki SAIF yaba Sarki ZiYAZINUN. Koda Sarki ZIYAZINUN yaga wannan sako sai ya sake gaskata bayanin da Waziri BAHARU ya fada masa, amman dukda haka sai Sarki ZIYAZINUN ya karbi KAMRIYYA ya nuna kamar baisan makircin da ake shirin kulla masa ba. Yasa aka bawa yan aikennan masauki suka kwana kashe gari suka kama hanya izuwa kasar HABASHA. Bayan ansamu kamar wata daya. Wata rana sai Sarki ZIYAZINUN ya kadaita da kuyangar da aka kawo masa wato KAMRIYYA, a wannan lokaci ya zare takobinsa ya umarceta da ta fito da gubar da aka bata ta bashi in kuma taki to zai halakata, da KAMRIYYA taga zai halakata sai ta ciro gubar daga kanta ya karba, sannan suka kwanta tare a wannan dare dai Sarki ZIYAZINUN bai gushe ba saida kuyanga KAMRIYYA ta samu ciki dashi. Da Sarki yaga ta samu ciki sai ya kira wani malamin sa yace ya buga masa kasa yagani, sai wannan Malamin yaga ai wannan ciki na KAMRIYYA namiji zata haifa kuma shine wanda zai mulki duniya. Sai ya fada wa Sarki wannan labarin, Sarki yayi murna kwarai. Daga nan sai Sarki ZIYAZINUN ya rinka nunawa KAMRIYYA kauna yana tattalinta. Lokacin da cikin KAMRIYYA ya cika wata na hudu sai Sarki ZIYAZINUN ya kwanta ciwon ajali, inda yayi wasiyya cewa idan ya nmutu KAMRIYYA ta hau karagar mulkinsa har ta haihu, idan Dan ya girma ta sauka tabashi mulkinsa. Bayan yan Kwanaki ya cika inda KAMRIYYA taci gaba da mulki kasar HAMRA'U YAMEN. Da aka samu yan kwanaki KAMRIYYA tana kan gadon sarauta sai ta rika dauko mutanen HABASHA dai-dai da dai-dai tana kawosu majalisar kasar HAMRA'U YAMEN tana kuma korar mutanen Sarki ZIYAZINUN suna mutuwa. Cikin dan kankanin lokaci duk ta kori mutanen Sarki ZIYAZINUN daga majalisa ta mayesu da sababbi. Ba dadewa cikin KAMRIYYA yakai wata tara, ta haifi yaro namiji kyakykyawa fari tamkar mahaifinsa. Tun lokacin da KAMRIYYA ta haihu, kuma taga ta haifi na miji sai wani abu ya dinga darsuwa a zuciyarta. Bayan gari ya waye sai KAMRIYYA ta shirya jaririn ta fito dashi fada domin jama'a su ganshi, bayan ta zaunane a bisa karagar mulkinta sai ta ajiye jaririn daga gefe bisa wata shimfida wadda ba kowanne jariri ake kwantarwa akai ba sai 'ya'yan manyan Sarakuna. A wannan lokaci sai jamaar wannan gari suka fara zuwa wajen wannan jariri suna kwasar gaisuwa suna cewa "Yaron kuwa kamarsu daya sak da ubansa suna cewa munyi mubayi'a." Bayan sun gama kwasar gaisuwa gaban jaririn tare da masa adduar Allah ya raya sai kuma su juya kan KAMRIYYA suyi gaisuwa. Gani cewa tun yanzu, tun ba'aje ko inaba gashi anfara mancewa da ita ta wannan jaririn akeyi sai kishi ya kamata, anan sai tasan gaba tubeta zasuyi su nada yaron. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 Part 2 post by Shuraih 99% . KAMRIYYA ta boye abinda ke damunta a zuci da dauki yaron ta koma cikin gida jama'a kowa ya watse. Da isarta gida ta zauna tayi shiru tana tunani, hankalinta yayi kokoluwar tashi domin tasan lallai idan wannan yaron ya taso ya girma ya samu wasiyyar uban sa to lallai sai ya tureta daga gadon sarauta ya hau, kuma gashi ita ta dandana giyar mulki taji da dadi. Saboda haka ta yanke shawarar kawai ta kasheshi shiya fi. Ta dauko wuka zata yankashi amman saita fasa, ta sake yunkurawa zata yankashi sai ta fasa, ana uku data yunkura zata yanakashi sai wata tsohuwar kuyanga ta shigo dakin koda ganin abinda ke shirin faruwa sai tace kai! Keko mai wannan jariri yayi maki da har kike yunkurin hallakashi? Nan KAMRIYYA ta fada wa wannan tsohuwar dalilinta da tsohuwa taji haka sai ta bata shawarar kada ta yankashi ta bari sai dare ya tsala su hau dawakai su biyu su sulale ba tare da kowa ya gansu ba suje can daji su yadashi, kana su ajiye dukiya tare dashi domin duk wanda ya tsincesa yayi amfani da wannan dukiya wajen rainonsa, domin idan ya taso hannun wani bazai taba tunanin shi dan Sarki bane balle ma har yayi wani tashin hankalı. Sarauniya KAMRIYYA ta yarda da wannan shawara ta tsohuwa ta fasa yankashi ta bari har dare ya raba sannan suka sulale kamar yadda tsohuwa ta fada, sukayita tafiya, har saida suka fita daga cikin kasar kana suka ajiye jaririn a gindin wata bishiya, kuma suka ajiye akwatun cike da kudi sannan sukayi komawarsu. Can cikin dare jariri ya farka ya fara kuka shi kadai a cikin daji, can yanata kuka sai matar Sarkin fararen aljanu tazo giftawa tana dauke da yarta mai suna AKISA, wadda a wannan lokacin tana shayar da ita. Da aljanan nan taga jinjirin nan sai tausayinsa ya kamata, sai ta tsaya ta daukesa ta bashi nononta yasha ya koshi, daya koshi sai ya koma bacci, ita kuma ta ajiyeshi ta dauki yarta tayi gaba. Can da asuba tayi jaririn nan ya sake farkawa ya kama kuka yana cikin kukanne sai ga wata barewa mai shayarwa tazo wajen, taga jaririn nan sai ta tsugunna ta kara masa nononta yasha. Yana cikin Shane kawai sai wani maharbi ya hango barewar nan. Aiko ya lallabo ya na sanda saboda barewar bata ganshiba, koda ya matso kusa sai yaga ai barewar nan jariri Dan mutum take bawa nono, sai ya tsaya ya na mamaki hardai barewar nan ta ganshi ta gudu. Maharbin nan ya matso kusa da yaron nan ya tabbatar dan mutum ne, kuma ga wata akwatu kusa da shi, daya bude akwatun yaga dukiya sai ya maida yarufe, ya dora akwatin a bisa Kai, yakuma dauki jaririn ya rungumeshi ya na murna ga dukiya ga kuma Yaro sun samu. Saboda haka ya juya akalarsa zuwa gida. Shi wannan mutumin mutumin kasar DUWAR ne, kuma ita wannan masarsuta ta na karkashin Kasar HABASHA ne. Da Isar wannan Maharbi gida tundaga waje ya Fara kwala wa matarshi Kira harya shiga cikin gidan. Da isarshi ya mika mata yaron, kana ya sakko da akwatun da yake a kansa, sannan ya kwashe labari kaf! Ya bata. Yace kinga shikenan daman bamu taba haihuwaba gashi Allah ya bamu d'a, sannan kuma ga dukiya Allah ya bamu. Da matar tajihaka sai tace "Haba! Mai gida kaika dubi irin.wannan kyakykyawan yaron da ganinsa kasan dan sarakuna ne, KO kuma manyan attajirai ta yaya zamu I ya rikeshi? Kuma kaga shi farine muko duk bakakene ai. Ana gani za ace satoshi mukayi aje a samu a cikinwani hali, kawai yanzu ka daukeshi kaje ka Kai wa Sarki shi domin wannan yaro yafi karfin mu. Da mijin yaji haka sai ya zauna yayi tunani kuma saiya aminta da shawarar matar tashi. Saboda haka saiya kinkimi akwatunan sannan ya dauki jaririn ya nufi gidan Sarki. Yana isa bayan yayi gaisuwa ga Sarki ya kwashe labari Kaf ya labarta wa Sarki. Sarki ya karbi wannan jaririn daga hannun maharbin nan. Shidai wannan Sarki sunan sa AFARA'U, kuma ya kasance karamin Sarki ne dake karkashin babban Sarki SAIF na HABASHA. Sarki AFARA'U daman bai taba haihuwa ba, sai yayi murna da samun wannan jaririn ya baiwa matarsa mai suna DAHASHANATU yace ta rikeshi dukda su bakakene shikuma wannan yaron farine {Balarabe) ne. Ita kuma can wannan Aljanar da taba jaririn nan nono ya sha, data koma gida, sai take bawa mijinta labarin cewa "Tagawani jaririn mutum kwance a daji shi kadai, ta daukeshi ta bashi nononta yasha." Da mijin yaji wannan labari sai yace "Ai tunda kika bashi nononki ai ya zama danki sbd haka yi maza kikoma kidaukoshi." Nan da nan Aljana ta bazama nema. Ta koma kasar DUWAR. Ta duba inda ta bar jaririn nan amman sam bata ganshi ba, sbd haka saita je wurin Sarki Aljanu na wannan gari domin shima a karkashi mulkin mijinta yake. Ta nemi dayabaza dakarun Aljanu su nemo mata wannan jariri duk inda yake. Nan da nan Aljanu suka bazama cikin kasar domin gano inda jaririn nan ya shige. Jim kadan sukazo da labarin cewa ai yaron yana gidan Sarki AFARA'U. Nan da nan aljanar nan ta juye ta koma izuwa sutfar mutane, ta iske matar Sarki tana rungume da jariri, tana shiga sai tace nazone na karbi dana. Koda DAHANASHATU taji wannan batu sai ta fusata, jin cewa wata tazo zata rabata da wannan yaro. Na da nan sai tayi kiran wasu bayi ta fada masu suyita dukan Aljanar nan Harsu fitar da ita. Da Aljana taji haka sai tayi wani ruri wannada ya firgita duk wanda yake gidan, takuma fada masu ita ba mutum bace, saboda haka su bata jaririn nan ko kuma ta halakasu gaba dayansu. DAHASHANATU taji tsoro sai ta kama kukan bakincikin rabuwa da zatayi dashi. Nan ta tura aka kira sarki ta bashi labarin abinda yake faru, nan take shima Sarki ranshi ya baci ya umatci matarsa data mika wa wannan aljanar yaro. DAHASHANATU ta mika mata yaron cikin bakin ciki. Koda aljana taga irin halin da suka shiga sai tausayinsu y kamata, tace masu yanzu zan tafi dashi naci gaba da shayar dashi amman idan ya cika shekara biyu zan dawo maku dashi. Da gama daukar wannan alkawari, sai wannan aljanar tayi sama da yaron bata zame ko ina ba sai a fadar mijinta, wato Sarkin fararen Aljanu. Can kuma a HAMRA'U YAMEN, Sarauniya KAMRIYYA sai ta fada wa jama' arta ai wannan yaro ya mutu. Koda jama' a sukaji haka mafiyawancinsu basu yarda ba, amman saboda zafin mulkinta sai sukayi shiru domin sun san lallai idan suka karyata zancenta, to lallai zasu dandana kuransu. Kuma gashi duk mutanentane a majalisar, wann dalilin ne yasa suka bita a yanda tace. Shi kuwa jinjirin da aljana ta dauka yayin daya cika shekara biyu a fadar Sarki AFAYARU, sai aljana ta yayeshi tare da yarta, kuma tanemi izini a gurin mijinta kan cewa tanason maidashi gun Sarki AFARA"'U. Da Sarki AFAYARU yaji haka sai yace da ita tabar yaron nan a wajensu, ya cigaba da cewa yaron yana da alamura masu girma, domin kuwa dan Sarki ne, kuma shi zai kubutar da yarki daga wata masifa a nan gaba, kuma wannan yaro shine zaiyi yaki duniya baki daya kuma yayi nasara, saboda wannan girman lamari nasa nake ganin bai kamata mukaishi wajen mutane yan uwansa ba domin zasu iya cutar dashi. Koda DASUKATU matar Sarkin aljanu AFAYARU taji haka sai tayi na' am da wannan magana amman kuma sai ta tuna ai ta daukarwa Sarki AFARA'U da matarsa alkawari kan cewa zata maido dashi. Anan sai tace da mijinta eh ta yarda da maganarsa amman itama tana da shawara. Ya tambayeta yace to fadi shawararki muji. DASUKATU tace Kaga mu ba mutane bane, saboda haka halayyarmu data mutane ba iri daya bace zaifi kyau mu mayar dashi gurin mutane yan uwansa domin ya samu taebiyya irin tasu. Sarki AFAYARU ya yarda da wannan shawara ta matarsa, yakuma yi mata izini data mayar da yaro gurin Sarki AFARA'U da matarsa, amman ta ja masa kunne kada ya yarda wani abu ya tabasa. DASUKATU ta dauki yaro ta mayar dashi ga Sarki AFARA'U da matarsa kamar yadda tayi alkawari kuma ta gargadeshi Kamar yadda mijinta ya fada mata. Sarki AFARA"U ya karbi yaro ya shiga dashi cikin gida cike da farinciki ya kira matarsa DAHASHANATU ya mika mata yaron koda ta ganshi sai tayi wuf! ta karbeshi, ta rungumeahi tana kuka domin farinciki da murna da suka kamata. Sannan ya fada mata duk sharuddan da aljana ta fada masa. Anan Sarki da matarsa suka sama wannan yaro suna WAHASHINFALA. Bayan an samu kwananki Kamar kwana Arbain da dawo da WAHASHINFALA wurin Sarki AFARA'U sai matar Sarki ta sami ciki, murna kan murna wurin Sarki AFARA'U da matarsa DAHASHANATU basai an fada ba, gashi suna murna aljana ta dawo masu da WAHASHINFALA gakuma DAHASHANATU tana da ciki. Duk gari akayita taya Sarki murna. Hakadai lokaci yayita tafiya har lokcin haihuwar DAHASHANATU yyi tahaifo ya mace aka saka wa yarinyar suna SHAMATU. Ita wannan yarinyar farace kuma sai ya zamto Kamarsu daya da WAHASHINFALA. Wannan lamari ya baiwa Sarki AFARA"U tare da duk sauran mutane mamaki saboda sudai gasu bakake amman gashi sun haifi farar mace, balarabiya, kuma gashi tayi kama da wannan yaro WAHASHINFALA, haka dai sukayita manaki. A lokacin da WAHASHINFALA yakai shekara bakwai, sai ya bukaci yanason ya fara hawa doki, sarki yasa aka dauko masa wani dan karamin doki, da WAHASHLFALA yaga wannan dokin sai ya rainashi yace shi bazai hau wannan karamin dokin ba, shi babba yake so. Sarki yasa aka mayar da wannan dokin aka kawo masa wani baki ingarman doki mai digo-digon fari a wuyansa da kirjinsa. WAHASHINFALA yace wannan doki yayi masa, yayi tsalle ya dare kansa yayi sukuwa a gaban jama'a yana dawowa gabanSarki yana tirjiya. Daga nan WAHASHINFALA ya fara koyon yaki da takobi kuma cikin kankanin lokaci ya kware a harkar fada da takobi yazama kaf yaran dake sa' anninsa bawanda zai iya ja dashi har manyan ma. Ganin haka yasa Sarki AFARA'U ya dinga alfahari dashi kuma ya ware masa masu yimasa hidima. Wata rana Sarki yana zaune a fadarsa da yan majalisarsa ana fadanci can saiga bokan Babban Sarki mai suna SAKARAJUNA ya shigo fadar sarki da yan majalisa suka mike domin girmamawa ga wannan boka saboda sanin matsayinsa a gurin Babban Sarki wato SAIFURRA'ADU wato shugaban Sarki AFARA'U. Boka SAKARAJUNA ya zauna, bayan sun gaisa da sarki ne sai boka SAKARAJUNA yace masa yazo kasarsa ne ziyara, daga haka akaci gaba da fadanci daga can sai Boka SAKARAJUNA yaga WAHASHINFALA zaune kusa da Sarki. Sai Bokan nan ya tambayi Sarki cikin rada mai ya kawo wannan farin yaron nan, kuma mai yake yi a cikin kasarka? shin baka da labari cewa irinsu ne zasu mulki duniya kuma su maidamu bayinasu bayan sun karkashemu. Nan take Sarki AFARA'U ya fadawa bokan nan maganganu masu sanyaya zuciyar Boka SAKARAJUNA ya yarda, da suka nitsa ne cikin hira sai Sarki AFARA'U yake bawa boka labarin cewa ai matarshi ta haihu shekaru biyar da suka wuce ta haifa masa "ya mace. Nan da nan boka ya bukaci da akawo masa yarinyar ya ganta, Sarki yasa aka kawo masa SHAMATU dan boka ya samata albarka. Da boka ya daga ido ya kalleta sai yaga ai fara ce balarabiya, kuma gashi tayi kama da wannan yaro WAHASHINFALA wanda Sarki yace ba dansa bane. Nan da nan boka yayi tsafinsa ya gani cewa lallai wannan yarin ya SHAMATU yar Sarki AFARA'U ce kuma wannan yaro ba dansa bane. Sai ya umarci daya mayar da wannan yaran cikin gida. Sarki ya tura SHAMATU da WAHASHINFALA suka koma cikin gida. Nan dai Boka ya sake buka rairayi sai yaga ita wannan yarinya wanda zai aureta farin mutum ne, kuma shine wanda zai mulki duniya, sai ya zaci ko WAHASHINFALA ne, sai ya fusata yace wa Sarki ya zama dole ya kashe wannan yaron WAHASHINFALA in kuma yaki to zai aika wa Dan uwansa Boka SAKARADUSA, ya fadawa Sarki SAIF ce wa "Sarki AFARA'U ya ajiye wani farin yaro kuma idan ya taso to duk zai halakar damu ne, sannan kuma ya mayar da wasun mu bayi. Boka SAKARAJUNA ya kare da cewa kaga kuwa idan Sarki SAIF yaji wannan batu to labudda zai halaka ka da ki da jamaaar taka baki daya." Koda Sarki AFARA'U yaji wannan magana daga bakin Boka SAKARAJUNA, sai hankalinsa yayi kololuwar tashi saboda yasan indai har wannan magana taje kunnen Sarki SAIFIRRA'ADU to kashinsa ya bushe. Koda gama wannan tunani sai yace da boka SAKARAJUNA daya bashi nan da kwana biyar zaiyi shawara, boka ya yarda da hakan. Boka yayi wa Sarki sallama ya nufi masaukinsa, yayin da shikuma a bangaren Sarki AFARA'U ya zurfufa kogin tunani na neman mafita, yana cikin wannan haline na tunani Wazirin sa mai suna HARISU ya fado masa arai. Waziri HARISU ya kasance mutum ne mai hangen nesa, saboda sanin yakamata da kuma hangen nesashi ne yasa Sarki AFARA'U ya nadashi Wazirinsa. Wanda ada yake da mukamin Sarkin gida. Koda Sarki AFARA'U yazo nan a tunaninsa, sai ya kira wani barde yace yayi maza gidan Waziri HARISU ya kirashi yanzu yanzu. Bardennan ya amsa da angama ya shugabana. Ya haye dokinsa ya sukwaneshi. Lokacin da barden nan ya dawo shida Wazirin HARISU Sarki yana cikin turakarasa. Saboda haka shima Waziri sai ya zarce inda turakarsa Sarkin take. Bayan ya nemi izini Sarki ya bashi, ya kunna kai cikin dakin. Koda shigar sa sai Sarki ya bashi labarin duk yadda sukayi Boka SAKARAJUNA akan WAHASHINFALA. Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan... Zamu cigaba MALUKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 3 posted by Shuraih Usman @ https://dlhausanovels.com.ng Koda Waziri HARISU yaji haka sai yayi na wasu dakiku tamkar babu kowa a dakin. Daga can kuma sai ya kawo gauron numfashi ya aiye yace "abar bauta zahalu ta kareka, mafita daya garemu akan wannan lamari tunda kaidai kanason yaron nan bakason rabuwa dashi ko kadan. Mezai hana mu jewa da wannan boka kalamai masu sanyaya rai da kwantar da hankali, muyi masa alkawarin cewa Indai har wannan yaro ya girma mukaga take taken shi nason rushe mana masarauta da kuma hanamu bautar zahalu to sai mu kashehi." Koda Sarki AFARA'U yaji wannan zance sai yace "Maraba da fasihin Waziri, hakika hakan za'ayi".Da haka Waziri yayi wa Sarki sallama ya tafi gida. Bayan kwana biyar Kamar yadda Waziri HARISU yayi wa Sarki AFARA'Uu bayani, cikin sa'a kuwa suka shawo kan boka SAKARAJUNA. Sannu a hankali soyayyaya mai karti ta kullu tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU ba tare da Sarki AFARA'U ko boka SAKARAJUNA sun sani ba. Bayan wasu yan shekaru kowa a cikin wannan garin saida ya fahimci soyayyayar dake tsakanin WAHASHINFALA da SHAMATU saboda haka boka SAKARAJUNA ya fara kokarin rabasu ta hanyar alqalaman tsafi amman abu ya farkara. Ganin haka ya shirya mashi makirci ta qarkashin kasa. Sannu a hankali manema suka fara fitowa neman auren SHAMATU, cikinsu kuwa harda WAHASHINFALA wanda shine kan gaba. Saboda haka Sarki AFARA'U ya nemi shawarar boka SAKARAJUNA, koda boka yaji harda WAHASHINFALA sai yayi dariyar qeta yace "Inaso gobe a tattatara mani manemanta a kofar fada". Daga haka Sarki AFARA'U yasa aka rubuta takardu zuwa ga masu neman auren "Yarsa SHAMATU. Yakira wani bafadensa ya aikesa. Washe gari tunda sanyin safiya masu neman auren SHAMATU suka fara bayyana, bayan wani lokaci, suka gama bayyana a bakin fada, cikin mutanen nan kuwa harda WAHASHINFALA dashima ya shiga layin manenan SHAMATU. Bayan wani lokaci suka fara jin bugun tabura gami da busar algaita hakan ya tabbatar masu da cewa Sarki yana tafe. Haka kuwa akayi Sarki AFARA'U ne sanye cikin alkebba, daga damansa Wazirin sa ne mai suna HARISU Sannan daga hagunsa kuma boka SAKARAJUNA. Koda ya karaso bakin fadar, bayan yayi masu barka da zuwa saiya umarci boka SAKARAJUNA daya fada masu abinda ake buqata ga duk wanda yakeson SHAMATU. Boka SAKARAJUNA ya fara magana kamar haka "inayi wa bakinmu barka da zuwa, dalilin dayasa muka taraku anan shine, duk wanda yake son auren SHAMATU to sadakinta shine zai kawo mana kan Shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI, koda wadannan jaruman da yayan attajirai dake neman auren SHAMATU sukaji haka sai suka fara sulalewa, cikin kankanin lokaci wajen ya zama fetal ba kowa sa WAHASHINFALA. Koda ganin haka sai boka yayi murmushin keta yace da WAHASHINFALA jarumtarka ta burgeni sai ka shirya nanda jibi ka kama hanya. Daga haka suka juya izuwa cikin gidan sarautar. Bayan kwana biyu WAHASHINFALA ya shirya cikin bakin sulke, yayi wa SHAMATU da Sarki AFARA'U sallama y kama hanya cike da kewar garinshi da kuma masoyiyarshi SHAMATU. Alamarin SHAMATU kuwa tunda masoyinta WAHASHINFALA ya tafi ta shiga damuwa kasancewar bata da tabbacin cewa ko zai dawo da rai. Ahaka ta kwana ta wuni a rana ta biyune tana bacci tayi mafarki da annabi HALLIRU alaihissasatu, yace mata ai ita taimakon WAHASHINFALA yana hannunta. Cike da mamaki ta kalleshi tace taya ya? Sai yace da ita a gidan akwai wata matattala ita wannan matattalar ta kasance idan ka taka ta farko lafiya ta biyu bazakata lafiya, yacigaba da cewa saboda haka ya zama maki dole kije ki sanar dashi. Koda SHAMATU ta farka cikin dare bata zame ko ina ba, sai bargar dawakai, cikin sanda ta kanto doki ta haye cikin sa'a kuwa ta tadda masu gadin kofar sunata sheka baccisu. Ba tare da tsoron komai ba ta bude kofar ta fice. Kasancewar WAHASHINFALA be dade da lafiya ba ita ta bi bayansa koma dokin data dauko irin na musammanne wanda ba koda wane lokaci ake fani da suba, tadauki lokaci tana tafiya cikin kurmumun daji ba tare da tsoron komai ba. Aiko cikin sa'a ta fara hango WAHASHINFALA wanda yana gab da shiga cikin gidan shahararren dan fashin nan wato SA'ADUNUJJANJI ta kwala masa kira, koda yaji ankwala masa kira sai yayi turus yaja ya tsaya ba tare daya waiwayo ba. Ganin shirun yayi yawa yasashi ya waiwayo koda ganin wadda ta kirasa sai fuskarshi ta fadada da murmushi. Ya tabayeta keko meya sa kika biyoni? SHAMATU tace Zan baka labari amman ba yanzi ba. WAHASHINFALA shida SHAMATU sukayi kokari suka shiga cikin gidan kasurgumin dan fashin nan SA'ADUNUJJANJI can suka hango wata matattakala, nan take WAHASHINFALA ya doshi inda matattalar nan take ya mika kafa ya taka ta farko ya kuma taka matattala ta biyu daga takawarshi sai ya rufta ciki wasu wukake guda biyu masu matukar kaifi, da tsini tare da suka nufoshi zasu rabashi biyu cikin azababben sauri SHAMATU ta rugo da gudu ta rikeshi sannan tayi wuf ta jawoshi waje. Ai koda ya ganta sai ya cika da matukar mamaki ya tambayeta ya akayi kikasan haka? Nan ta kwashe labari kaf ta fada masa. Da yaji haka sai yace gashi yanzu adduarki taci. Nan dai SHAMATU ta ci gaba da bashi labarin wannan matattala tace Ita wannan matattalar idan ka taka ta farko lafiya to tabiyu ta Sharri ce dan haka idan ka taka ta farko to saidai ka tsallake ta biyu ka taka ta uku. To haka sukayi har suka isa can sama da suka isa sai suka riski wata katuwar kofa ta baki karfe saboda haka sai MALUKUSSAIF ya leka ya hango wani mutum baki, kato, mai manyan idanuwa gasu jajaje tamkar garwashin wuta, gashi da katon hanci kamar gwangwani, ga katon kai Kamar mangala Sannan ga manyan labba kai kace fata aka shinfida. Daga gefen damansa mutane arbain ne haka ma bangaren hagunsa. Koda WAHASHINFALA yaga haka sai ya dawo bayan wannan kofar ya labe, koda ganin haka sai SHAMATU tace da WAHASHINFALA shi wannan mutumin na tsaki baki mummunan shine SA"'ADUNUJJANJI. Suna zaune can sai SA'ADUNUJJANJI yace da mutanensa kai kutsaya nifa kamar motsi nake ji fa? Inaga daya daga cikin mutanen da kuka kamo ya kwance, daya daga cikin ku ya tashi ya duba. Yana gama rufe bakinsa, daya daga cikin Sadaukan nan ya tashi domin ya dubo yana zuwa daidai inda kofar nan WAHASHINFALA yayi wuf ya sare masa kai, ita kuma SHAMATU ta janyeshi ta boye gawar, da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yaji shiru sai ya kuma turo wani barden nan ma dai WAHASHINFALA ya sare masa kai kamar yadda yayi wana farko, haka SA'ADUNUJJANJI yayi ta aiko da mutane har akazo kan na biyar nan fa kowa tsoro ya darsu a zuciyarsu aka rasa Wanda zai tashi shikuma WAHASHINFALA dayaga anjima babu wanda ya sake fitowa sai ya kutsa kai ya shiga cikin dakin ya tsaya gabansu koda SA'ADUNUJJANJI yaga WAHASHINFALA sai yace kai kuma wannan karamar halitta daga ina haka? Kuma maiya kawoka nan harka halaka mani mutane? WAHASHINFALA ya amsa masa da cewa babu ruwanka daga inda najo, kuma dalilina na zuwa na wajenka shine nazo ne na kasheka, Sannan na tafi da kanka a matsayin sadaki. Koda SA'ADUNUJJANJI yaji wannan magana sai ya bushe da dari sannan yace kai yanzu wannan yaro har MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 4 post by Shuraih 99% zaka iya fada dani? Dubeka fa ka dubeni na ninka ka sau goma, yanzu kaiko wannan saurauyin wane ne ya turoka ka aikata wannan abu gareni? WAHASHINFALA cikin bacinrai yace ba'a sani ba idan zakayi shirin yaki kayi. SA'ADUNUJJANJI yace zo mu shiga cikin gidana akwai fili isasshe wanda zai ishemu ni da kai. SA'ADUNUJJANJI ya tashi yaransa suka biyoshi a baya, WAHASHINFALA ma ya biyo shi a baya, suka shige wasu manyan soraye guda uku suka riski wani fili, da suka isa wannan fili sai SA'ADUNUJJANJI ya juyo wajen mutanen sa yace idan muna yaki da wannan yaro kar wanda ya kawo mani dauki koda kuwa kunga yana kokarin samu galaba a kaina ne, ku tsaya kawai kuyi kallo. Koda yaran SA' ADUNUJJANJI sukaji haka sai su dukansu suka babbake da wata mahaukaciyar dariya, domin sun san cewa ba ta yadda za' ayi wannan karamar halittar ya iya kai shugaban nasu kasa ko yazo da matemaka bare ya zo shi kadai. Suka amsa da sunji sun yarda. Can kuma SHAMATU data ga sun shiga wannan gida, sai ta fito daga inda take boye ta hau kan wani dutse inda zata iya ganin karawar da za'ayi tsakanin SA'ADUNUJANJI da saurayinta. SA'ADUNUJJANJII ya yiwo kan WAHASHINFALA yana gurnani tamkar zakin dakejin yunwa ya hango nama, WAHASHINFALA shima ya zare tashi takobin yayi dauki kan sa suka kaure da yaki bají-ba-gani har dare yayi rana ta take. Can suna cikin wannan dauki ba dadi dine sai WAHASHINFALA ya taka wani karamin dutse ya durkushe kasa. SA'ADUNUJJANJI ya daga takobinsa ya kawo wa WAHASHINFALA wani wawan sara koda SHAMATU taga haka sai ta tabbatar da cewa indai har saran nan ya dira a kan masoyinta to saidai wani bashi ba. Sai tayi wuf! Ta zaro wani gariyo daga cikin sulkenta ta wulwuloshi ta jefi SA'ADUNUJJANJI dashi, sao gariyon ya sare shi a hannu wanda hakan yayi sanadin faduwar takobin dake hannunsa. WAHASHINFALA ya rike takobinsa a hannu yayi niyyar sarewa SA'ADUNUJJANJI kai amman sai ya fasa yace tashi ka dauki takobinka muci gaba da yaki, domin bazan kasheka ta hanyar yaudara ba, sai kuma ya juya ya fuskanci dutsen da SHAMATU take tsaye yace jinjina gareki ya ma'abociyar bege. Koda SA'ADUNUJJANJIl yaji haka sai ya tashi ya dauki takobinsa suka ci gaba da yaki, haka suka cigaba da wannan gwabzawar har tsawon kwana uku a rana ta ukun ne shuka tsaya domin su huta, ko wannensu ya samu guri ya zauna yana haki. Su kuma yaran SA'ADUNUJJANJI sun cika da mamaki ganin irin jarumta da kuma sadaukartaka ta WAHASHINFALA. Can da aka jima sai SA'ADUNUJJANJI yace "Yaro me yasa lokacin da takobina ta fadi ka samu damar kasheni amman kaki kace bazaka kasheni da yaudara ba? kuma naji kamar kana magana da wani. WAHASHINFALA yace wannan yarinyar da zan aura itace ta cillo mani wuka, kuma da ita nake magana shiyasa nace bazan kasheka da yaudara ba. WAHASHINFALA ya sakko da SHAMATU daga kan dutsen nan ya shigo da ita cikin wannan filin ta zauna kusa da shi. SA'ADUNUJJANJI yace lallai yau zan shayar da ku gidauniyar mutuwa daga kai har ita sannan naje har kasarku na kashe uban wannan yarinya na fatattaka garin gaba daya, na kwashe dukiyoyinsu sannan na koro bayi. Koda sukaji haka sai suka zabura suka cigaba da sara da suka, a takaice dai saida WAHASHINFALA da SA'ADUNUJJAN.JI suka shafe tsawon mako duga cir suna gwabza yaki amman babu wanda ya samu nasara a kan dan uwansa, har saida makamansu suka lalace nan take kowa ya yada nashi suka tsaya sukayi cirko-cirko kamar zakaru suna kallon juna suna muzurai. Can sai SA'ADUNUJJANJI yace "Kai yaro! Yanzu tunda makamanmu sun gaza yanzu sai mu fidda sharadi, WAHASHINFALA yace wane sharadi? SA' ADUNUJJANJI yace sharadin shine yanzu zamuyi kokawa nida kai duk wanda ya kada wani sau uku to shi ya cinye wannan gasar, idan kai ka kadani sau uku to kai ka cinye wannan gasa sai kayi yanda kakeso dani, haka zalika idan ni na kadakai sau uku to sai nayi yanda nakeso dakai. Koda WAHASHINFALA yaji haka sai ya yarda da wannan sharadin, suka fara kokawa kici-kici, can sai SA'ADUNUJJANJI yayi wuf! Ya suri WAHASHINFALA ya daga sama zai fyada da kasa, kawai sai WAHASHINFALA ya Kama kunnen SA'ADUNUJJANJI ya murda cikin ikon Allah sai ga SA'ADUNUJJANJI ya fadi kasa tim!. Haka dai WAHASHINFALA yayi ta kada SA'ADUNUJJANJI har sau uku, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro kayi nasara aikata abinda kakeso dani ya durkusa bisa gwiywoyinsa. Da WAHASHINFALA yaga haka sai ya dauko gariyonsa yayi niyyar sare kansa, da SA'ADUNUJJANJI yaga haka sai yace yaro amman da zaka kyaleni, da raina, ka kuma riqeni na zama bawanka domin kila wata rana zan maka amfani. Da WAHASHINFALA yaji haka sai ya ajiye wannan gariyon yace gaskiya ne na yarda da maganarka. SA'ADUNUJJANJI da kaf yaransa suka jinjina ga WAHASHINFALA sukace "Gaisuwa gareka ya shugabanmu" anan suka kwana. Da gari ya waye SA'ADUNUJJANJI da yaransa suka zo gurin WAHASHINFALA suka kwashi gaisuwa Sannan suka zauna daga gefen WAHASHINFALA. WAHASHINFALA yace da SA' ADUNUJJANJI da mutanen sa to ai saiku tashi mu tafi kasar DUWAR domin kuwa nasan Sarki AFARAU yanacan yaba jirana. Nan da nan SA'ADUNUJJANJI suka dora wa giwayensu sirdi, shi kuma WAHASHINFALA da SHAMATU suka haye kan dawakansu suka kamo kan hanyarsu ta dawowa kasar DUWAR. Bayan sun samu Kamar kwanaki uku suna tafiya sai suka fara hango katangar birnin DUWAR, anan sai shamatu ta rigasu shiga cikin birnin dankada a gane cewar tare suke, takoma gida ba tare da wani ya ganta ba. A wannan lokacin kuma sai akayi sa'a boka SAKARAJUNA yace da Sarki AFARA'U cikin gatse zomu je bayan gari muga ko wannan yaron zai dawo, Sarki, Waziri da sauran fadawa suka fito bayan gari suna diban hanya. Can sai suka hango WAHASHINFALA ga kuma SA'ADUNUJJAN.JI da yaran sa bisa giwaye, "kagani ko gashinan abinda kaja mana kasa wannan yaron ya tsokano mana SA'ADUNUJJANJI, ya matsa mashi ya sanar dashi cewa mu muka turo shi, gashinan sun sakoshi a gaba suzo su halakamu". Koda jin haka sai Sarki, boka da jama'ar gari suka ruga da gudu cikin gari suka rurrufe kofofin gari, da suka karaso sai WAHASHINFALA yasa daya daga cikin yaran nan ya bubbuga kofar amman ba'a bude ba. Koda WAHASHINFALA yaga haka sai yayi tsawa ya umarci SA'ADUNUJJANJI daya karya kofar birnin. Nan da nan SA'ADUNUJJANJI yayi wa toron giwarsa qaimi ya bangaji kofar garin ta karye, suka kutsa kai izuwa cikin MALIKUSSAIFI IBN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 kashi na daya 5 fassarar Aliyu Abubakar Sharfadi rubutawa Mr Hausa Ebooks Da WAHASHINFALA yaga haka sai yace "Baba yanaji kace dani Sarki bayan ba haka bane, kuma ka kirani da wani suna wai MAALIKUS-SAIF bayan ni sunana WAHASHINFALA. Tsoho ya dubeshi yayi murmushi yace "Katahone daga garin DUWAR kuma yau kwananka sittin kana tafiya kafin kazo nan, kuma WAHASHINFALA ba sunanka bane sunan ka wanda Allah ya nufa shine MAALIKUS-SAIF, mahaifinka kuwa shine Sarki ZIYAZINUN mai mulkin kasar HAMRA'U YAMEN wanda ya rasu, kuma kaine wanda adduar Annabi Nuhu zata fada a kansa zai samu mulkin duniya baki daya, ya kuma tambayarsa ya MAALIKUS-SAIF yanzu mai kake bautawa? Ya amsa masa da cewa "Eh nidai naga mutanen nahiyar mu suna bautawa rana da wata ne, amman ni bana bauta masu sabo da nasan Allah ne ya halicceni saidai ban samu Wanda zai koya mani yadda zan bauta mashi bashiyasa ni ban bauta wa komai Tsohon yace "Ka dogara ga Allah yanzu zan musuluntar da kai. MAALIKUS-SAIF yace na dogara ga Allah, Tsohon yace kace na gasgata babu abin bauta sai Allah kuma na gasgata da Annabi Muhammadu Annabi da zaizo a karshen zamani da Annabin wannan zamanin Annabi Ibarahim alaihissasatu wassalam. MAALIKUS-SAIF ya maimaita shahada kamar yadda Tsohon nan ya fada masa. Bayan ya gama sai Tsoho yace masa ni sunana Shehu ZAJJADA, yanzu tunda ka musulunta ka zama dan uwana kuma ya zama dole na taimakeka nasan ka fito neman littafin kogin NIL zan fada maka inda yake amman inaso kafin ka tafi ka kwana a nan domin inason sanar dakai hanyoyin bautar Allah. Shehu ZAJJADA ya koya wa MAALIKUS-SAIF alwala da zikirin Allah suka zauna suna ta zikiri har cikin dare sannan shehu ZAJJADA ya mike ya daga hannu ya roki Allah ya kawo masu abinci daga arzikinsa. Nan da nan sai ga abinci da abubuwan sha iri-iri a gabansu, MAALIKUS-SAIF ya cika da dunbin mamakin ganin wannan abinci saboda baiga yadda ya kawoshi ba. Shehun ya umarceshi da yaci abinci amman kafin ya fara ci yace Bismillah. MAALIKUS-SAIF ya fadi haka ya fara dibar gara abinka da maijin yunwa. Haka yayita ci har saida yaji ya koshi sannan ya sha ruwa, sannan ya kwanta ya huta. Kwanciyarshi keda wuya bacci ya kwasheshi, shi kuma Shehun ya ci gaba da zikirinsa. Can da gari ya waye Shehun ya tada MAALIKUS-SAIF yayi masa wa'azi sannan ya kuma cewa ka dogara ga Allah, zaka kubuta da duk wani yanayi da ka samu kanka. Sannan ya zagaya da shi bayan wannan dutsen ya nuna masa yace yanzu kabar dokinka anan domin baya da amfanin tafiyar da zakayi dashi, ya nuna masa yace kabi gefen kogin nan kayi dama zakayi tafiyar kwana uku zakaga wani fili, bayan ka wuceshi zaka kuma ganin wani kogin mai matukar girma dan girmansa babu iyaka, to saika tsaya a nan. Akwai wata dabba mai suna HATSHA. Ita wannan dabba tunda Allah ya halicceta idan rana ta fito daga gabas tana daga tsakiyar wannan kogin sai tayita tsalle wai sai ta kamo rana, idan rana ta tsaya daidai a sama sai bakinciki ya kamata, sai ta fito da kanta daga bangaren gabas tayita turmutsa kanta a cikin yashi dan hushi, haka kuma idan rana ta koma gabas sai tayita tsalle da niyyar ta kamota har rana ta fadi, idan ta fadi nan ma sai ta fito da kanta a bangaren yamma ta rinka turmutsa kanta a yashi nan ma dan haushi. To idan kaga wannan dabba tana tumurmusa kanta a cikin wannan yashi to kar kaji tsoro ka kana gashin wuyan wannan dabbar ka dafeta, bazataji komai ba saboda girmanta, kai koda cikin idanunta zaka shiga bazataji komai ba. Ka zauna kana makale a kanta har ta maida kanta yamma, bayan ka sauka zakaga wani mutum, to ta dalilin wannan mutumin zaka samu wannan littafin. Daya gama wannan bayanin sai MAALIKUS-SAIF yayi godiya Sannan yabi wannan hanyar da Shehun ya nuna masa, ya shafe kwana uku yana wannan tafiyar har ya isa wannan filin da Shehun ya fada masa.... Anan zan dakata Zamu cigaba zuwa Gobe Ana yin comment yan uwa MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 6 post by Shuraih 99% . Isar sa keda wuya kuwa yaga wannan dabbar tanata tumurmusa kanta a cikin yashi kamar dai yadda Shehun ya sanar dashi. Nan da nan sai yayi maza ya dane kanta har rana ta fadi,takai bakin gabar daga bangaren yamma, koda MAALIKUS-SAIF yaga haka sai ya fado daga kanta ji kake tik!. Ya tashi ya fara tafiya. Can yana cikin yafiya sai yaga wani mahayin doki a sukwane ya yi yo kanshi, koda mahayin yazo gab da MAALIKUS-SAIF da niyyar bankeshi sai MAALIKUS-SAIF yayi sauri ya banke dokin, haka suka rinka yi har sau shidda ko da mahayin dokinnan yaga haka sai ya zare takobinsa ya kaiwa MAALIKUS-SAIF Sara da suka shi kuma yana gocewa, hardai ya harzuqa MAALIKUS-SAIF, MAALIKUS-SAIF ya dubi mayin sai yace kaidai Allah wadaranka ragon banza, ai ba haka ake gwanimtar yaki ba, haka kawai mutum yana tafiya ka tasar masa dan ganin yana kasa Kai kana doki, kuma ga makami a hannunka, bari in nuna maka yadda sadaukai suke nasu sha'anin. MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya damki wuyan dokinnan da hannun dama, ya kuma sake yin wif! Ya shaqo Wuyan mahayin da hannun hagu ya daga sama ya jinjina shi sannan ya saukeshi a hankalı ya ce "Kaga yadda sadaukai suke nasu lamarin". Da ganin haka sai wannan mahayim dokin ya sakko daga bisa dokinsa ya tsaya gaban MAALIKUS-SAIF ya yaye kyallen dake rufe a fuskarshi koda ya yaye sai MAALIKUS-SAIF yaga shema mace ce ba namiji ba ne ya dubeta yaga kyakkyawa ce, sai tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN koda yaji ta kira sunansa sai yace kekuwa yaya akayi har kika san suna na? bani labari mana. Yarinya ta fara da cewa "Suna na DAMATU, na samu labarin kane a wajen mahaifiyata wacce itace Sarauniyar bokayen birni KAIMARA, sunan ta Bokanya AKILA. Wata rana muna zaune da ita sai nace mata ta buga mani qasa taga waye wanda zai aureni, sai ta amsa mani da cewar Wanda zai aureki sunansa MAALIKUS- SAIF na ainahi amman yanzu ana kiransa da suna WAHASHINFALA, kuna asalinsa dan wani Sarki ne mai suna ZIYAZINUN Sarkin kasar hamra'u yemen amman yanzu yana qasar wani sarki mai suna AFARA'U, bayan an kwana biyu, sai tace mani shi wannan wanda zaki aura ya nemi auran wata yar Sarki aka nemi ya kawo kan wani dan fashi kuma gashi can ya dawo. To a wannan lokaci sai na rinka damunta da yaushe zai zo garin nan? Sai ta rinka ce mani ai ya kusa Zuwa, sai yau kuma dana sake tamayarta sai tace dani inyu maza ai gakacan ma ka iso, amman ta fada mani cewa inyi qoqarin yaqarka, indan naga baka da niyyar cutar dani sannan ka kama wuyan dokina sannan ya dagani daga ni har dokin, sannan ya saukemu a hankali to Wannan shine wanda zan aura, saboda haka kaji na kira sunanka kada kayi mamaki. Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan yarinya ta fadi wadannan batutuwa a kansa sai ya gasgata zancenta, amman a fili sai yace da ita "Ke kuwa wannan da qaryar tsiya kike, sannan kin iya shirya batu, domin wannan mutumin da ki ke fada to ni ba ni bane, kedai kawai kinyi niyyar ki yaqeni kikaga babu nasara shine kika shirya wannan zantuka". Koda 'DAMATU taji haka sai tayi murmushi sannan tace "Daman uwata ta fada mani cewa kona fada maka bazaka gasgata ba, kuma kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin NIL, kuma babata itace zata taimaka maka ka dauko wannan littafin. Tana gama wannan bayani sai ta yaye lullubin dake a fuskarta. MAALIKUS-SAIF ya dubeta ido cikin ido yace yanzu ina babar taki take? Tace tana gida, yace to mu tafi izuwa gareta. Sai DAMATU tace "A'a ai a kaidar wannan garin bako baya shiga, domin kuwa tarihi ya nuna wa mutanen wannan garin cewa wani bako ne zai zo ya sace shi wannan littafin tarihin NIL wanda ka fito nema, su kuma wadannan mutanen tun kaka da kakanni wannan littafin shine abin bautarsu, tun lokacin da suka samu labarin cewa wani bako ne zai zo ya sace wannan littafin sai suka tsafe garin, suka sana' anta wani gunki mai suna GAMMAZI wanda duk lokacin da bako ya shigo zai dinga îhu yana Ga... Bako! Ga Bako! Daga nan sai a kama bakon a yankashi wannan dalilin ne yasa bako baya shiga, amman duk da haka, babata ta fada mani cewa idan kazo qofofin shiga garinmu ka lissafa qofa ta tara sai ka duba zakaga wata bishiya a kusa da wannan qofar zakaga akwatu ka shiga ciki sannan ka girgiza igiyar sai mu jawo dakai daga cikin kwatun mu shiga dakai cikin garin. Koda DAMATU ta gama bashi wannan labarin sai ta haye dokinta ta tunkari qofar birnin nasu. Shi kuwa MAALIKUS-SAIF sai ya dinga bin sawun dokinta har ya fara hango katangar birnin KAIMARA. Daga nan sai ya juya bangaren gabas ya fara qirga qofofin shiga garin koda ya qirga ta tara, da ya hango kofa ta goma sai ya dosheta, Kamar yadda 'DAMATU ta fada masa, to daya isa bakin qofar nan sai ya boye ajikin wannan bishiyar da yake duhun dare ne ba wanda zai iya ganinsa, can yana tsaye jikin bishiyar nan sai yaga ana sako akwatu daga kan katangar, koda ya sakko qasa sai yaje ya shiga cikin wannan akwatu, sannan yaja murfin akwatin ya rufe ya girgiza igiyar sau uku. Su kuma can bokanyanya AKILA da DAMATU da sukaji an girgiza wannan igiyar sau uku sai suka jawoshi suka shiga dashi cikin birnin. Da suka isa gida, sai bokanya AKILA ta kawo masa abinci da ruwan sha, bayan ya gama sai ya kwanta, bayan ya huta sosai bokanya AKILA tace barka da zuwa MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN.MAALIKUS-SAIF ya amsa mata da cewa yawwa, kazo wannan qasa tamu domin neman littafin tarihin kogin NIL, kuma nice zan taimakeka saka makon auren yata da zakayi. Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai yace wai meye amfanin wannan littafin da har jama'ar wannan gari suke bashi tsaro sosai kuma har suke bauta mashi? bokanya AKILA tace shi wannan littafin a cikinsa ne akayi bayani yadda za'a zuqo kogin NIL, kuma duk kasar data mallaki wannan littafin to fari na rashin ruwa bazata samesu ba, kuma qasar zata samu arziki da yalwa na albarkacin qasa, haka kuma duk mutumin da wannan littafin ya zamto a hannun sa to shi zai mallaki duniya. Saboda haka tin iyaye da kakanni mutanen wannan qasa suke girmamashi kuma suke bautamashi. Kuma tarihi ya nuna cewa wani baqo zaizo ya dauke shi wannan littafin, saboda haka ake bawa wannan littafin kyakkyawan tsaro. A wannan lokaci sai mutanen birnin KAIMARA sukaji gunki GAMMAZI yana cewa "Yaku mutane birnin KAIMARA ga bako ya shigo maku wannan birn?", ya fadi haka har sau uku nan da nan Sarki.. Ya fito shida tawagarsa aka rinka bincike lungu-lungu, sako-sako har dare yayi amman basuga wannan bakon ba. A can cikin gidan bokanyanya AKILA kuwa, MAALIKUS-SAIF yaji hayaniya ta yawaita sai yace da bokanya AKILA "Amman dai bazasu shigo nan ba ko?", sai bokanyanya tace "Kada ka damu bazasu shigo nan ba ya kuma tambayarta yace meyasa kikace bazasu shigo ba? bokanyanya tace ai duk manyan bokayen Sarki KABRUNU su dari uku da cittin (360) nice shugabarsu, a karkashina suke kuma su waddan nan bokaye sune suke tsaron wannan littafi dan haka ba yadda za' ayi su shigo wannan gida. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 7 post by Shuraih 99% . Da gari ya waye, Bokanya AKILA ta aika DAMATU gidan makwaftansu da yake masunci ne ta siya masu wani katon kifi, da DAMATU ta kawo sai Bokanya AKILA ta yanka kifin ta kwashe duka kayan cikin kifin ta saka qafafun MAALIKUS-SAIF a cikin kifin ta mayar da dinke cikin kifin; sannan ta dauko wani qaton tsutsu ta daura masa a wuya, sannan ta daura mashi igiya a girji, Sannan ta sakashu cikin rijiya, tace kada ka damu nayi maka wannan ne domin na bata hankalin bokaye ma' abota tsafi da Sarki zai sasu bincenka. Bokanya AKILA ta shirya ta tafi fada da zuwanta fada ta iske fada ta cika makil, ta fadi gaban Sarki tayi gaisuwa takoma mazauninta ta zauna. Zaman ta keda wuya sai Sarki KAMARUNU yace da ita daman ke muke jira, domin jiya GAMMAZI yayi mana kuwwa cewa wani bako ya shigo mana birni, to inaso ki sa yaranki su binciko mana inda wannan bako yake. Nan da nan Bokanya AKILA ta umarci wadannan bokayen dari uku da cittin (360) dasu buncika qasa su gamo inda wannan baqon yake. Bokaye suka dukufa suka zana alkalaman duba bisa rairayi suka shiga aiki, haka sukayita yu har tsawon wani lokaci, su zana su goge su sake zanawa su kuma gogewa su shafe... Can sai suka tsaya da wannan duban sukace munga wannan baqon. Koda Sarki KAMARUNU yaji wannan bokayen sunce haka sai yayi farat! Yace a ina kuka ganshi maza ku gaya mani. Can sukace shidai wannan bako gashi mun ganshi cikin duhu kuma kifi ya hadiyeshi, ga kuma wani tsuntsu ya ratayoshi, da sarki yaji haka sai yace wannan wace iriyar maganar banza ce kuke fada haka mara ma'ana. Sai Bokanya AKILA tayi farat ta rufesu da fada tace na fada maku cewa ku daina cin abinci da yawa domin yana hanaku kuyi aikin ku yanda ya kamata amman kunqiji ai ga irinta nan yanzu kun binciko wa Sarki shirme. Koda Sarki yaji haka sai ya fusata yasa hauni ya sare wa Bokaye biyar kawuna, sannan aka tashi daga fadanci. Koda Bokanya AKILA ta koma gida sai ta fito da MAALIKUS- SAIF daga cikin rijiya ta fito dashi daga cikin kifin sannan ta kwance mashi tsutsun data daura masa, kana ta kwashe duk abinda ya wakana a fada ta fada mashi. MAALIKUS-SAIF yace lallai kina da yawan hikima, badan kinyu mani haka ba da da tuni bokayen nan sun gano ni, haka sukayita fira da Bokanya AKILA tare da yarta DAMATU har dare ya raba sannan suka kwanta bacci. Da gari ya waye a rana ta biyu, Bokanya AKLA ta samo wata barewa ta daura mata fuka-fukan tsuntsu, sannan ta sa MAALIKUS-SAIF ya durkusa gaban barewar ta daura mashi ita ta kuma daura wata igiyar ta raba qafafun barewa da qasa, ta shirya ta yafi fada. Da zuwan ta fada sarki ya umarce ta data sa bokayen nan da su buga gasa su nemo inda baqo yake. Nan da nan bokayen nan suka tsundum aikı, can sai bokayen nan suka dago sukace sun ganshi. Cike da zumudi Sarki ya tambayesu yana ina? suka kada baki sukace ai gashi can wata barewa ta tashi sama dashi, nan da nan Sarki ranshi ya qara baci yace me yasa kuke kawo mani wasa ne? Kun tabajin ance yau ga barewa da fuka-fukai?, wannan ai rainin hankali ne yasa aka kuma yanka bokaye biyar nan dai fada ta tashi. Bokanya AKILA ta tafi gida tana dariya, taje ta kwance MAALIKUS-SAIF suka cigaba da hira. A rana ta uku Bokanya AKLA ta samo wata babbar tasa, ta yanka wata dabba ta juye jinin a cikin wannan tasar, ta kuma samun wata tasar da dora a cikin tasar da ta zuba jinin, Sannan ta umarci MAALIKUS-SAIF daya shiga cikin tasarnan zauna, bayan ya shiga ya zauna. Sai ta kama hanya ta nufi fada, isarta keda wuya ta umarci bokayen dake karkashinta akan su fara aiki. Nan suka dukufa, bayan wani dan lokaci suka dago sukace munga wannan baqon a cikin wani kogi na jini, sannan banda wannan kogin da yake ciki akwai wani kogin wanda shi babu komai a cikinsa, jin haka sarki ranshi ya qara baci ya umarci hauni daya kara sare kawunan bokaye goma, sannan yace da bokanya AKILA ke ya kamata ki duba mana inda wannan baqon yake tunda su sun kasa, bokanua AKILA tace to tunda yau saura kwana biyar bikin mu na shekara to a ranar zan kawo maka wannan baqo, koda jin haka sai fuskar Sarki ta fadada da murshi a haka aka tashi daga fada. Bayan kwana biyar yaune Bokanya AKLA tayiwa Sarki KAMARUNU alqawarin kawo masa baqon daya shigo wannan gari nasu. Tunda sanyin safiya MAALIKUUS- SAIF ya fara jin hayaniyar mutanen wannan gari, cikin firci ya tashi yace mekuma yake faruwa ne tace ai na manta ban fada maka ba yaune muke bikin shekarar mu kuma a cikin dakin da wannan littafin yake anan muke bikinmu, saboda haka kayi zamanka acikin gida nida hannuna zan kawo maka wannan littafin. Nan fa MAALIKUS-SAIF yanuna shi sam baiyarda ba saidai ta tafi tare dashi, dole kuwa hakan tayi tatafi tare dashi amman kafin haka saida ta bashi wani bakin ruwa na tsafi tace ya watsa qa jikinsa, watsarshi keda wuya yaga ilahirin jikinsa ya zama baki kamar yadda fatar 'yan garin suke, Bokanya AKILA ta bashi jakarta ta bokanci ya rike, tana tafe yana binta a baya har suka fito daga cikin gidan. Fitowarsu keda wuya suka tadda bokayen nan dake qarqashin Bokanya AKILA a bakin gidanta suna jiranta tana qarasawa inda suke suka dunguma sai dakin bauta, koda suka kusa shiga sai MAALIKUS-SAIF ya qarasa kusa da Bokanya AKILA ya miqa mata jakarta, ita kuma cikin rada ta qara jadda mashi kan cewa kada ya kuskura yayi yunqurin daukar littafin nan ya amsa mata da to amman badan ya yarda da shawararta ba. Koda Bokanya AKILA ta isa cikin dakin bautar sai gaba daya mutanen dake dakin bautar sukayi wa littafin sujjada bayan Sarki KAMARUNU ya fito dashi daga maboyarsa ya dorashi bisa wani taburi, ganin sunyi sujjada ga wannan littafin yasa MAALIKUS-SAIF ya taho a hankali cikin sanda, yazo inda littafin nan yake ya miqa hannu da niyyar ya dauko shi sai kawai yaga littafin ya fado qasa tim! Ya fara zagayeshi. Jin qarar fadowarshi yasa Bokanya AKILA; Sarki KAMARUNU da sauran jama'ar dake wannan dakin bautar suka dago daga sujjadar da suka yi, aiko sukayi ido biyu da MAALIKUS-SAIF, nan fa suka hau dukansa baji ba gani, MAALIKUS-SAIF shima ya hau dukansu, kasancewarsu suna da matukar yawa sai wani daga cikin.dakarun ya zagayo ta bayan MAALIKUS-SAIF ya sammaceshi ya bugesa a tsakiyar kai, nan take MAALIKUS-SAIF ya baje a kasa baiko shura ba, koda ganin haka sai Sarki KAMARUNU yayi godiya ga wannan littafi sannan ya umarci wasu dakarunsa dasu je su jefa MAALIKUS-SAIF cikin wata tsohuwar rijiya dake a bayan gari. Bayan sun dauki gawar sun jefata a wannan rijiyar ne suka dawo suka sanar da Sarki KAMARUNU. Sannan Sarki KAMARUNU yace da jama'a aci gaba da shagalin biki. Ita kuwa Bokanya AKILA koda taga an kashe MAALIKUS- SAIF sai hankalita yayi mugun tashi kasancewar tasan irin son da yarta "DAMATU takewa MAALIKUS-SAIF saboda haka ta sulale ta koma gida ba tare da sanin kowaba. Koda tafada wa DAMATU abinda ya faru a dakin bauta, kuka °DAMATU ta dinga yi da qyar Bokanya AKILA ta shawo kanta. ****** Alamarin MAALIKUS-SAIF kuwa ashe ba mutuwa yayi ba lokacin da aka MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 8 post by Shuraih 99% . dokeshi a tsakiyar ka suma yayi, yana cikin wannan hali na suma wata aljana ta bayyana tsulim! A cikin wannan rijiyar koda ta daga hannunta sama sai wani ruwa ya dinga fita daga wannan hannu yana jiqa fuskar MAALIKUS-SAIF, jim kadan sai MAALIKUS-SAIF ya farfado daga suman dayayi, nan fa ya fara tariyo abinda ya faru dashi a dakin bauta, bai gama tunanin dayake ba yaji anyi sama dashi anfito dashi daga wannan rijiyar. Anan MAALIKUS-SAIF yayi godiya ga Allah madaukakin Sarki daya kubitar dashi daga cikin wannan rijiyar, to bayan ya gode ma Allah, sai ya tambayi wannan mutumin daya fito dashi yace kai kuwa wane ne kai? Mutumin ya dubi MAALIKUS- SAIF yace ni ba Namiji bane ni mace ce, kuma aljana, na kasance diyace a gurin Sarki fararen aljanu mai suna ABAYARU ni suna na AKISA, nan da nan ta juye ta koma budurwa. Kuma nazo nan ne domin wani taimako da zakayı mani. MAALIKUS-SAIF ya dubeta yace wane taimako kikace zan maki? Aljana AKISAA tace ya Dan uwana akwai wani bakin aljani mai suna MUTTADI'U. Shi wannan aljani kafiri ne mukuma musulmai ne, mun samu musuluncin mune a wajen wani bawan Allah mai suna Shehu Abdussalam. Wata rana wannan bakin aljani mai suna MUTTADrU ya sauka a Garinmu yace yazo ziyara, duk da karfin mulkin mahaifina amman yana tsanananin tsoron wannan bakin aljanin, saboda haka mahaifina ya saukeshi suka zauna afada suna fira. Can nazo wucewa da bakin aljanin nan ya dubeni sai yace yana sona, saboda tsananin tsoronsa da mahaifina yake sai yace masa ya bashi ni, ni kuma banason sa, saboda ba musulmi bane, hankalina sai ya tashi, nayi iya tunanina naga babu mai iya kubutar dani daga wannan bala'i da nake ciki, sai na yanke shawarar na tafi wajen wannan bawan Allah Shehu Abdussalam wanda ke garinmu, na fada masa halin da nake ciki na nemi ya taimaka mani. Da Shehun yaji haka sai yace Ai duk duniyar nan babu mai iya kubutar dake daga hannun wannan bakin aljanin sai wani mutum kuma Dan uwane gareki mai suna MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN. Sai na tambayeshi inda zan sameka sai ya ce mani Inkoma wajen babata zata gaya mani inda kake. Dana koma Gida sai na tambayi uwata shine take bani labarin cewa ai yanzu wasu aljanu daga kasar KAIMARA suke bata labarin cewa gashi can a jefashi a cikin wata rijiya, maza jeki ki kubutar dashi to shine kaganni nazo to kaji abinda nakeso ka tainmakeni ka kubutar dani daga wannan baqin aljanin. Da MAALIKUS-SAIF ya gama jin wannan batu daga bakin AKISA sai ya shafa bulalarsa yaji tananan, sai yace in sha Allahu zan kubutar dake daga hannun wannan bakin aljanin. To amma kuma naji kina cewa ni Dan uwanki ne, ya akayi ni ina mutum ke kina aljana har na zama Dan uwanki?. AKISA tace uwata ta sanar dani cewa ai kaima danta ne domin tare ta shayar dani da kai nono lokacin muna jarirai. MAALIKUS-SAIF yace to ya sunan babar taki? AKISA tace DASUKATU. Koda MAALIKUS-SAIF yaji wannan suna sai yace na yarda ke yar uwata ce, to yanzu saikiyi maza ki kaini wajen wannan uwa tamu. Kafin ya rufe bakinsa sai ga DASUKATU ta dira dif! a gabansa yana ganin haka ya rungumeta, yana ce Mata mai yasa kika rabani da ku shekaru da dama. DASUKATU tace ya Dana munyi maka haka ne domin zamanka a wajenmu bazai yiwuba saboda dabi'un mu da naku na mutane sun banbanta, shiyasa ya zama mana dole muka mayar dakai ga mutane yan uwarka, yanzu maza ka hanzarta domin kubutar da yar uwarka. Da gama wannan magana sai tayi masu sallana ta tafi. MAALIKUS-SAIF ya kalli AKISA yace To yanzu sai ki daukeni ki kaini wajen wannan aljani. AKISA ta dauki MAALIKUS-SAIF ta tashi dashi izuwa qololuwar sama tayita tafiya dashi, can sai AKISA ta tsaya da tafiya ta sakko kan wani dutse, ta nuna masa wani tsauni ta ce Kaga wancan tsaunin to akansa gidan wannan aljanin yake. MAALIKUS-SAIF yace "To shiken an tsaya anan ni na shiga na fito", yakama hanya, daya isa gindin tsaunin nan yai zagaye ya rasa inda zai kama ya hau, yana cikin haka sai yaji ana kiran sunan sa daga saman tsaunin nan, ya daga kansa sai yaga wasu yan mata ne suke dago masa hannu suna kiran sunan sa. Sai suka zuro masa igiya ya kama, suka jashi harkan tsaunin nan. Da MAALIKUS-SAIF ya hau kan dutsen nan sai yaga yawan yan matan nan yakai su Arba'in,kuma dukkansu yan matane kyawawa, sai daya daga cikin su wadda kamar itace shugabarsu mai suna NAHIDA tace ai jiya a cikin baccina naga Annabi HALLIRU laihissasatu Wassalam, yace inbada Gaskiya akan addinin Annabi Tbrahim Alaihissasatu wassalam, ya musuluntar dani Sannan ya fada mani cewa yau akwai wani mutum mai suna MAALIKUS-SAIF zai zo ya kubutar damu, ya kuma fada mani cewa ni ina daya daga cikin matayen da zaka Aura, shine na fito ina baiwa wadannan yan uwa nawa labari sai muka leko muka ganka. MAALIKUS-SAIF ya tambayi yan matan nan ku kuma me ya kawoku nan? NAHIDA tace ai mu duk nan daka ganmu yayan Sarakuna ne, ganinmu da kayi anan wannan aljanı shiya kwasomu ya kawomu nan, dama shi dab1arsa shine duk inda yaga yar Sarki kyakkyawa to sai ya daukota ya kawota nan, ahaka duk ya taramu anan. Da MAALIKUS-SAIF yaji wannan bayani sai ya tuna lokacin dashi wannan aljani yaje zai dauke SHAMATU ya sare masa hannu daya, suna cikin haka sai suka ji wani rugugi da hayaqi ya tunkaro su, sai matan nan suka ce wa MAALIKUS-SAIF ya gudu ya nemi wajen buya domin ga aljanin nan ya dawo. MAALIKUS-SAIF ya ce Ku barni dashi babu inda zani, yan matan nan suka shige cikin wani daki suka bareshi tsaye a waje. Jim kadan sai ga aljanin nan ya bayyana, koda yaga MAALIKUS-SAIF sai yace yauwa daman kaine ka taba sare mani hannu yau gashi kazo har gidana, kaga sai na rama na kasheka nima. Koda gama fadin haka sai aljanin nan ya miko hannu d nufin ya kama MAALIKUS-SAIF. Cikin zafin nanma MAALIKUS-SAIF yayi wuf! Ya zaro bulalar sa ya tsula wa aljanin nan. Nan take aljani ya kama da wuta yana kururuwa yana ihu yana ya kasheni! Ya kasheni...! Cikin lokaci kankani aljanin nan ya qone kurmus, ya baje kamar turbaya. Da yan matan nan sukaga haka sai suka fito a guje suna murna, shi kuma ya yi kiran AKISA ta taho ta shigo wajen. Koda taga ya kashe wannan aljanin sai tace Ya Dan Uwana na gode wa Allah, na gode maka daka kubutar dani daga sharrin wannan aljanin, ni kuma babu abinda zanyi na saka maka illa kawai na rika maka hidima. MAALIKUS-SAIF ya umarci AKISA da ta dauki yan matan nan duk ta mayar dasu kasashensu kuma idan ta mayar dasu ta sanar da iyayensu cewa shine ya kubutar dasu. Nan da nan AKISA ta rika daukar yan matan nan tana mayar dasu qasashensu, sannan tayi bayanin kamar yadda MAALIKUS-SAIF ya fada mata, da haka har ta kwashesu kaf ya rage saura NAHIDA kadai. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 9 post by Shuraih 99% . AKISA tazo zata dauketa amman sai taqi. MAALIKUS-SAIF yace Ki tsaya mana ta daukeki ta mayar dake wajen iyayenki. Sai tace "Ai ni tunda Annabi HALLIRU ya fada mani cewa ina daya daga cikin matan da zaka aura to ba inda zani ina tare da kai duk inda zaka kuwa". Da MAALIKUS-SAIF yaji wannan magana ta NAHIDA sai ya tambayeta yace "Ke mutumiyar wace qasa ce'?" ta amsa mashi da cewa "Ita mutumiyar birnin Sin ce, kuma ubana shiyake mulkin wannan kasa". MAALIKUS- SAIF ya amsa da cewa "Naji kuma zan Aureki to ammanfa ki sani bazan aureki ba har saina auri SHAMATU DA 'DAMATU tukunan. Saboda haka yanzu ki koma qasar ku". Tayi nacim duniyar nan amman yaqi, koda ganin yaqi yarda sai tayi masa wata addua tace "To tunda kaki insha Allahu duk lokacin da zaka shiga garinmu, dagakai sai wando zaka shiga". Shikuma sai yace "Ni kuma insha Allahu lokacin kina a makance zan shiga, bazaki ganni a tube ba" Dukkansu kuwa sa aka amsa masu adduarsu. MAALIKUS-SAIF ya umarci AKISA data dauketa ta mayar da ita kasarsu. AKISA ta kaita ta dawo da AKISA ta dawo sai tace da MAALIKUS-SAIF to ya Dan Uwana in kanaso zan kaika birane bakwai mafiya kyau a Duniya?MAALIKUS-SAIF yace "Eh inaso ki kaini nayi kallo, amman kafin nan inaso ki kaini wajen Shehun nan na garinku nayi masa ziyara. AKISA ta daukeshi suka tafi. Da zuwansu, sai MAALIKUS-SAIF yaga wata hasumiya. AKISA tayi sallama sai sukaji daga ciki an amsa masu da cewa Barka dai MAALIKUS-SAIF Dan ZIYAZINUN. Suna tsaye sai wani Tsoho ya fito. MAALIKUS-SAIF ya tambayi AKISA yace Shikuma wannan Tsohon wanene shi? AKISA tace "Ai shine Shehu Abdussalam din da nake baka labari". Suka yi musabiha shida MAALIKUS-SAIF yajashi ya shiga kogon dashi yana fada wa MAALIKUS-SAIF wasu nauoi da sigogi na zikirin Allah. Bayan sun kammala ne Shehun yace ka zauna ka kwana anna ni gobe zan mutu, bayan na mutu kayi mani wanka ka daga kasan shirmfida ta zakaga likkafani sai ka lillibeni dashi. Sannan sai ka fita waje kofar hasumiyar nan kayi kira sallah, zakaga mutane ta sama da qasa sunata zuwa kar kayiwa kowa magana, kuyi zana' ida tare da mutanen nan bayan kun gama, zakaga ba kowa a cikin mutanen nan. Sai kaima ka binneni ka kama gabanka. Haka kuwa akayi gari na wayewa Shehun nan ya cika. MAALIKUS-SAIF yayi jana'idar yadda Shehun nan ya fada masa. AKISA tazo tace Ya Dan Uwana idan ka shirya to zan kaika birno na farko, MAALIKUS-SAIF yace Na shirya. AKISA ta daukeshi suka samu Kamar sa'a daya a suma suna tafiya, sai suka isa ganuwar wani birni AKISA ta sauka tace "To dan uwana gamu a qofar birni na farko, yanzu sai ka shiga ka fito ni bani da ikon shiga wannan birnin, domin akwai kafi wanda zai iya koneni idan har nayi kuskuren shiga. MAALIKUS-SAIF ya kama hanya ya shiga cikin wannan birni na farko. Da shirsa sai yaga nmanyan gine gine masu matukar kyau, sannan da Abubuwa masu balain kyau, yaita yawo yana kallo. Can sai ya iso wani fili yaga wasu mutane sunata fada. Koda suka ganshi sai duk sukayo kashi, daya daga cikin su yace "Yakai wannan baqon sai ka raba mana rikicin dake tsakanin mu. MAALIKUS-SAIF yace Wane rikici zan raba maku? babban yace nida Dan Uwana mahaifinmu ya kasance shine baban malami a wannan birni, sunansa Malam AFLADIN, ya mutu ya barmana gadon wata hula, wadda ita wannan hula ta tasance indai ka sakata to mutum ko aljan babu mai ganin ka. To shine muketa rigima akan ko wannenmu yanason ace shine ya gaji wannan hula, dama kafin kazo mun yanke shawarar duk wanda yazo ya samemu to shi zai Yanke hukunci a garemu, sai kuma gashi kazo, to muna so yanzu ka raba mana wannan rigima tamu. Da MAALIKUS-SAIF yaji haka sai yace "To zan rabamaku wannan rikici, ku bani kwari da baka zan harba ta duk wanda a cikinku ya fara dauko ta, ya kawo mani ita nan to wannan hular tazama tashi. Wadannan yan uwa biyu suka amince da abinda ya fada, suka bashi kwari da baka gami da hular ya rike a hannunsa. MAALIKUS-SAIF ya harba kibiya duk mutanen suka saki dawakansu suka bazam neman kibiya, suka barshi a tsaye da hula a hannun sa, can bayan wani lokaci sai MAALIKUS-SAIF ya hango daya daga cikin mutanen nan ya dawo a sukwane, kafin ya karaso sai MAALIKUS-SAIF ya raya a zuciya sa cewa To niko in gwada wannan hular in gani in gaskiya suka fada mani akan wannan hular, sai MAALIKUS-SAIF ya saka Wannan hular. Koda mutumin ya qaraso wajen sai ya rinka kwada kira yana yakai wannan alkali namu ina kashiga gani na dawo da kibiyar, yayita diri diri. Koda MAALIKUS-SAIF yaga mutumin baya ganinsa sai yace a zuciyarsa "To lallai na yarda da lamarin wannan hula idan kasa mutum baya iya ganinka, yanzu saura na gwadata akan aljani nagani, can sai ya tuna ai AKISA aljanace bari yaje ya gwadata akanta. MAALIKUS-SAIF yai tafiyarsa yabar wannan mutumin yanata diri-dirin neman sa, daya fito ne ya iske AKISA tana tsaye tana jiransa yazo gabanta ya tsaya amman duk bata ganshi ba, saiya kira sunan ta *Ya 'yar uwanta AKISA". AKISA tayi wani turus! "Tace kana ina ne Dan Uwana, kardai ace kasamo hular nan ta Malam AFLADIN? MAALIKUS-SAIF yace kina ganina? "Tace A'a bana ganin ka kana inane?" Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai ya godema Allah daya bashi ikon mallakar wannan hula, Sannan ya cire hular da hanninsa sai AKISA ta ganshi a gabanta, ya kwashe labari kaf game da yanda akayi ya mallaki wannan hula ya fada wa AKISA. "Ai manyan sarakuna da dama na samu labarin sun rasa rayukansu akan neman wannan hula, amman kai gashi ka sameta a sama" AKISA take bashi labari, taci gaba da cewa MAALIKUS-SAIF to yanzu saika shirya na tafi dakai izuwa birni na biyu. MAALIKUS-SAIF yace to yanzu karbi hulata ki ajiye mani, tana karba yace da ita to muje na shirya. MAALIKUS-SAIF da AKISA suka kama hanyar birni na biyu nan ma dai AKISA ta saukeshi a kofar shiga gari yai mata sallama ya tinkari kofar shiga garin, da shigar MAALIKUS-SAIF garin sai jama' ar garin sukayiwo kansa suna ga bako! Ga bako...!Suka taso masa zasu kamashi sai rigima ta barke a tsakaninsu suna dukanshi shima yana dukansu, ahaka hardai sukaci karfinsa suka kamashi suka kaishi wajen Sarkin su. Shi Sarkin wannan gari sunan sa Sarki DUHANI, ita wannan qasa suna da wani zobe wanda duk wanda ya mallaki wannan zoben to shine zai zama Sarkin wannan gari, saboda shi wannan zoben shi suke bauta mawa, sannan idan aka nuna mutum da wannan zoben sai kanshi ya guntule y fadi qasa, a wannan lokaci Sarki DUHAN shiya mallaki wannan zoben, saboda haka ya zama Sarki. Sarki DUHAN ya dubi MAALIKUS-SAIF yace "Kai ko mai ya kawoka qasata?" MAALIKUS-SAIF yace "Nazo ziyara ne da kuma yawon bude idanu." Da Sarki haka sai yace Shine kuma kazo ka fara fada da mutanena harka kashe mani wasu daga ciki. Sarki yayi umarni ga wani babban bawansa da ya tafi da MAALIKUS-SAIF gida yayita gana masa azaba har sai gobe da safe a dawo bakin kogin dake gaban gidan Sarki a fito dashi a kasheshi. BULAKI ya kama MAALIKUS-SAIF ya tafi dashi ya kaishi cikin wani daki yayita azabtar dashi har dare ya raba sannan ya koma dakinsa ya kwanta. MALIKUSSAIFI DAN ZIYAZZANUN littafi na daya 1 part 10 post by Shuraih 99% . Can bayan wani lokaci, MAALIKUS-SAIF yana a daure sai yaga BULAKI ya shigo dakin ya fadi gabansa yace ka gafarceni ya Sarkin Sarakuna MAALIKUS- SAIF Dan ZIYAZINUN ka gafarceni. Koda MAALIKUS-SAIF yaga haka sai yace "Ya ya haka kainefa kayita azabtar dani dazu kuma yanzu kazo mani da wannan maganar." BULAKI ya nisa yace "Ai yanzu cikin baccina naga Annabi HALLIRU ya musuluntar dani kuma yace dole na kubutar dakai. Nan da nan BULAKI ya kwance MAALIKUS-SAIF, ya kawo masa abinci yaci ya koshi sannan ya kawo masa ruwan sha, sannan ya kara jadda musuluncinsa a gaban MAALIKUS-SAIF. A wannan dare BULAKI yabi duk mutanen gidan ya musuntar dasu sai wata baiwa kwaya daya data ki musulunta, akayi akayi amman taki. Nan BULAKI ya kamata ya daure yace "Gobe Zan je ya jefata ruwa a mainakonka." MAALIKUS-SAIF yace "Tunda kai yanzu musulmine Zan canja maka suna daga yau ka koma Abdussamad." Gari na wayewa Abdussalam ya fito da wannan kuyangar lullube dan ayi tunanin MAALIKUS-SAIF ne, yazo da ita bakin kogi ya tsaya. Jim kadan sai Sarki ya leqo ta taga, yai Umarni da Abdussamad daya kashe MAALIKUS-SAIF shi a tunaninsa kenan amman baisan ba MAALIKUS-SAIF bane. Bayan Abdussamad ya kashe wannan kuyanga mai taurin kai. Sai Sarki yayi nuni da hannunsa daya jefa gawar cikin ruwa. Abdussamad ya jefa gawar cikin ruwa ya koma gidansa. A lokacin da Sarki yayi nuni da hannunsa da a jefa gawar cikin ruwa bai saniba ashe a wannan lokaci zobensa ya subuto ya fada cikin ruwan. Zoben na fadawa cikin ruwa sai wani kifi ya hadiyeshi a tinaninsa abinci ne. Da isar Abdussamad gida sai yace da MAALIKUS-SAIF "Mai kake da sha'awa yanzu na kawo maka?" **Yace kifi nakeso naci yau domin naji ina marmarinsa. Abdussamad yace Kash! Sai dai babu sauran kifi a gidan nan amman bari na fita nayi fatsa na kamo maka. Da MAALIKUS-SAIF yaji haka Sai yace kaga kuwa nima ina da sha' awar fatsa bari mu tafi tare. Abdussamad ya yarda da hakan suka tafi wannan kogin da suka jefa wannan kuyangar, can suna fatsa sai suka kamo wani katon kifi ganin kifin yana da girma sai suka hakura suka taho dashi kadai gida. Abdussamad ya yanka cikin kifin a dafa, koda ya kwaso kayan cikin sai yaga zoben Sarki. Nan da nan ya mika wa MAALIKUS-SAIF zoben nan yace Kaga wani zobenan cikin kifin nan koda MAALIKUS-SAIF ya gogeshi, sai Abdussamad yace duk yadda akayi wannan zoben Sarki ne ba makawa. Nan dai ya kwashe labarin wannan zoben yabawa MAALIKUS-SAIF labari yakuma fada masa cewa Duk wanda ya mallaki wannan zoben to ba makawa shine Sarki wannan gari. Koda MAALIKUS-SAIF yaji haka sai yace ba komai Allah ya kaimu gobe zanje fada na tunbike wannan mushitikin Sarki naku. Gari na wayewa MAALIKUS-SAIF da Abdussamad suka kama hanya suka doshi fada, da isarsu sai suka ga fada ta cika makil Sarki DUHAN yana bisa kan karagar mulkinsa anata fadanci. Da shigar su fada Sarki ya cika da mamaki yace "Ya kaida nasa a kasheka kuma naga ka dawo." MAALIKUS-SAIF ya dubi Sarki yayi dariya sannan ya daga wannan zoben ya nuna wa Sarki da Duk jama'ar dake fadar. Koda jama' a suka kyalla ido sukaga zoben, sai suka kama cewa "Aiko zoben sarki ne ai shine. ai tunda ka mallaki wannan zoben ba makawa kaine Sarkin mu, dama ka'idarmu kenan ta samun sarautar wannan gari." Koda Sarki DUHAN yaga haka sai ya mike yana hargagi yana karyata MAALIKUS-SAIF yana cewa wannan zoben na karyane ba zobena bane nawa na barshi a gida. Rufe bakinsa keda wuya sai MAALIKUS-SAIF ya nunasa da hannunsa mai zoben nan take kansa ya gutsire ya fadi kasa matacce. Sarki DUHAN tasa ta kare makomarsa ta munana aka gaggauta zuwa da ransa jahannama. Bayan ya gama da Sarki DUHAN sai MAALIKUS-SAIF yace yanzu bautar wuta ko zobe ta kare kowa ya zai koma bautawa Allah da manzon sa Annabi Ibrahim Halilullah, in kuma kukaqi in halakaku gaba dayan ku. Jama'a gaba daya suka yi mubayia. MAALIKUS-SAIF ya zauna dasu har tsawon wata biyu yana sanar dasu hanyoyin bautar Allah. Ranar da MAALIKUS-SAIF zai bar garin sai ya dora Abdussamad bisa gadon sarauta ya umarci Jama' ar garin da yi masa biyayya. Daga nan Jama'a suka yi masa rakiya har bayan gari sannan suka juya suka koma cikin gari. Shi kuma ya doshi inda yabar AKISA tana jiransa. Da zuwansa sai ya iske AKISA tana jiransa. Koda ta ganshi sai tace ya Dan Uwana na ina kallon lokacin da mutanen wannan qasa sukaso halaka ka, inaso na taimakeka amman bani da ikon shiga garin tilas haka na hakura ina gani zasu kasheka. MAALIKUS-SAIF yace ashe kin ganni, ai yanzu gashi Allah ya kubutar dani, ai yanzu saiki daukeni ki kaini birni na uku. Koda jin haka sai AKISA tace "A'a Dan Uwana bazan iya kaika ba, ina gani a cutar dakai domin kuwa suma birane biyar din bazan iya shigarsu ba, saboda haka koda hallaka za'ayi inaji ina gani babu yadda zanyi, kaga kuwa ya za'ayi na rika kai Dan uwana ga mahallaka bani da ikon taimaka nmasa." Da MAALIKUS-SAIF yaji haka sai ya fusata ranshi ya baci yace kidai ki kaini mana ina ruwan ki. Itako AKISA da taga ran MAALIKUS- SAIF ya baci sai tayi masa dabara tace haba ya dan Uwana kada rudin duniya ya shagaltar dakai abinda kafito nema mana littafin tarihin NIL, koda jin abinda AKISA ta fada sai hankalinsa ya karkata izuwa gida, ya tuno da SHAMATU abar begensa. Sai ya umarci aljana AKISA data daukeshi ta mayar dashi birnin KAIMARA yayi amfani da hularsa ya dauko wannan littafin tarihin. AKISA ta daukeshi sukayi sama bata zame ko ina ba sai bakin wannan rijiyar data fito dashi. AKlSA ta mika masa hularsa BADUHU wadda ya samo Sannan tayi masa adduar Allah yasa ya dauko wannan littafin na tarihin NIL. Sukayi sallama AKISA ta tashi sama, ta tafi shi kuma ya tsaya yana tunanin yadda zai shiga garin KAIMARA yana cikin wannan tunanine can kuma Bokanya AKILA ta hangosa a madubin tsafinta.. YANZU SHIN MAALIKUS-SAIF YANA SHIGA GARIN KAIMARA NE HAR YA DAUKO LITTAFIN NAN KO KUWA HAKURA YAKEYI YA KOMA GIDA? IDAN KUMA YANA DAUKO LITTAFIN TO YA YAKE A SHIGA GARIN TUNDA SUNADA GUNKI MAI TONON SILILI. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels