[3/27, 9:56 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *02* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, Sako zuwa ga mabiya novel dina: *gaisuwa mai dumbin yawa, godiya da jinjina, ga wani ya zo fatan zaku karbe shi, taku ce, SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... A darare ta juyo tana kallon mahaifiyar tata Inna na karasowa ta jawo hannunta daga cikin gidan kadan, cikin yannayin lalaba ta ce" WUJDANE , karki fita ki yi masa rashin mutunci , du layin nan bawan Allahn nan shi ya ji ya gani ya nace, karki ringa aiki da kyakyawar halitarki yanzu fa duniya tafi karfin tunaninki, Wujdane ki yi fatan gamawa da duniya lafiya, karki yi masa rashin mutunci ba.a yiwa dan adam hakan baki san irin baiwar da Allah yayi masa ba Kanta a kasa tamkar gaske take amsawa mahaifiyar tata, dokar malan ce ba.ai masa zance da dare, sai dai da safe ko yama , hakan ya saka Sule mai tahuna lokacin zuwansa da safe ne ya zo ya sha darga da yar rigimar tasa Fitowa tayi da hijabinta baki yauma har kasa, shi dai ne hijabin nan tun na salarsu ne da Malan ya saya masu dan kanti ne Sai da ta gama harararsa daga nesa kafin ta karaso Tana zuwa cikiciki ta ce" ina kwana Cike da murnar ganninta yake amsa mata ya shiga wasata kamar yanda ya saba Ga mamakinsa a yau bata yi masa tsawar ya isheta ba, saima wani gu da take kallo kadan kadan tana dan juyowa ta kale shi A ranta ayanawa take" sam baiyi mata ba, shi dai ba qani tsayi ba ga wasu idannuwa micik micik, kuma banda wannan shegen mugun halin tsiya ne da shi, matarsa Aliya yar masifa ce duda tana shayin Wujdane din aman bata da aiki sai masifa A hankali ta juyo ta ce" zan tafi gidan yawa Yana murmushi ya ce" tototo ba damuwa ai ina fatan yau za.a karbi kudin nawa Ya fada yana miko mata yan hansin hansin watar har ta cire dan wuyar da ta sha, Kudin ta karewa kallo, Wujdane ko yayunta bata rokq kudi ko iyayenta ita dai barta da jarabarta aman ba dai na kwadayi ba Dagoshi tayi da firgitatun idannuwanta da mutane da dama ke tsoron kallonsu ta watsar gefe , bata ce da shi komai ba ta juya ta nufi gidan yawa *Wacece Wujdane?* *Wujdane* jika take wajen Malan Hamza marigayi, mahaifin nana Fatima matar Malan Laminu Malan Hamza irin bayin Allahn nan ne wanda ya gaji kujerar mahaifinsa a wani kauye dake arewacin Maiduguri, Bafilatani ne na usul , wani irin fari gare shi da wata irin halitar idannuwa , kwayar idannuwansa tamkar na mage ko maciji kala daban sannan yana sheki, Malan hamza ya tara iyalai matansa hudu wanda du cikinsu ba wada ta taba haihuwa sai matarsa ta farko wace ake kira da Ya, Allah ya bata ciki har ya cire tsamani Malan Hamza mai almajirai yana zaune a gidansa dake cike da almajirai yakan fita daji yayi watanni ya kilace kansa sosai ya jima a can kafin ya dawo hakan ya saka ake kiransa aljan domin jejin kansa abin tsoro ne Tafiyar da yayi *Ya* nada cikin wata uku harda doriya aman bata fada masa ba domin ko kadan bata kawo hakan a ranta ba sun cire tsamani Wannan fitar sai da ya dauki wata bakwai wanda yana zuwa ya tarar sa yanda aka mayar da *Ya* tamkar banza dan ta haihu a cikin matansa Sannu a hankali zama ya gagara da sauran matan inda suka sako su a gaba da shi da Ya da yar yarsa wace ya saka mata sunnan yar ma.iki Nana Fadima Daya bayan daya sai da suka bar masa gidansa dan gani suke baya son haihuwar ne da su, ya kasance a gidan Malan Hamza daga Ya sai yarta Fadima sai almajirai yan matasa Haka Fadima ta taso cikin gata da karatu, domin a cikin almajiransa akoy wanda suka fi shakuwa sosai da sosai har ake ce masa dan malan wato Laminu Haka rayuwa take tafiyar masu, tunda Fadima ta taso sai ta taso da wani kyau sosai idannuwanta kuwa tak irin na mahaifinta ne, Samari da dama suna son kyakyawar fuskarta aman kalar idannuwanta ya saka aka canfa su ko wani gida sai a hana yaro neman aurenta da nufin kamaninsu sun hada iri da maciji Kauye da ake aurar da yarinya tun tana shekara goma watar sha daya idan kin jima sha uku sai ya kasance Fadima har ta kile sha biyar shiru, sai abin ya zama na zunde idan dai ta fito daga gida sai dai ta dawo tana kukan irin wulakancin da aka yi mata a waje Sosai abinnan ke ciwa malan tuwo a kwarya, cilon yarsa a irin wannan rayuwar sai ya kasance abin na nukurkusarsa na damunsa har yakan jajantawa Laminu dan malan Wani lokaci suna zaune Laminu dan malan ya zowa malan da labarin ya samu aiki a birni na tsaron kofar gidan wani Elhaj, Sosai malan yayi murnar hakan yayi masa sha tara ta arziki Tunda Laminu ya tafi sai ya samu gurbi mai kyau ya kasance a wajen aikin nasa masha Allah ya samu karbuwa, Ya kan yiwa malan aike du wata sannan Ya kuwa ya turo mata da su magi da makaroni da shinkafa cimar yan birni dai yakanyi sayayarsa daidai gwargwado ya bayar a kawo Hakan ya kara dadada ran Malan gannin irin yanda Laminu bai zubar da zumunci ba sannan bai manta alkhairi ba domin Laminu maraya ne na uwa da uba tun yana dan karaminsa ruwa ya cinye iyayensa da dabobinsu Wani zuwa da Laminu yayi ya jewa malan da muradin Auren Fadima, ba dan yana tausaya mata ba sai dan soyaya ta tsakani da Allah Malan yayi dogon bincike inda yayi ta istihara, banda alkhairi da kwaituwar hada auren ba abinda yake gani du kwanan duniya hakan ya saka ya daura masu aure Laminu ya dauko matarsa suka kama dan gidan haya suke rauwarsu Sannua hankali Fadima ta haifi yaronta na fari Malan ya saka masa Hamza, shekara biyu tsakani ta samu wani aka saka masa Abdul Fatah, daidai nan malan yayi dan ginninsa a wata anguwar talakawa tukuf suka koma wanda ya dauki daki hudu yan madaidaita sai bayi da zaure da balbalin gida, da rijiyarsu Bayan Abdul Fatah ta jima ta kai shekara bakwai shiru har ta fara tunanin haihuwar ta tsaya ne sai Allah ya bata wani cikin , Sanu a hankali cikinta ke girma ta kai wata tara da kwanaki kwatsam mumunan labari ya sameta rasuwar mahaifinta da sati mahaifiyarta itama tace ga garinku Du irin yanda ta kai ga hakuri da juriya taci kuka sosai da sosai ba.a jima da hakan ba ta haihu, wannan karan ya mace Malan ya saka mata Aisha Basu kai ga yada wanka ba Aishar ta rasu ta koma, sannu a hankali ta kuma samun wani cikin wannan karon sai ya saka mata *Wujdane* Wujdane na da shekara uku ta haifi wata macen malan ya maida mata Aisha sunnan Ya Tun daga wannan lokacin sai haihuwar ta dauke bata kuma koda batan wata ba Yayan Malan Laminu sun taso da karatu da tarbiya sosai da sosai domin a anguwar ba kowa ya san cewar a cikin gidan yan matan biyu bane sai dadaya wa.ina suke shiga Cikin ikon Allah sai Allah ya basu Tsagaira, Wujdane ja rigima Wujdane shiga sabgar da ba tata ba, har siyan fada take du girmanka kuwa sai ta daku da kai cikin ikon Allah ta nausaka da kasa Wujdane ta kwashe gaba daya kyan kakanta domin har idannuwansa bata bari ba, Wujdane ta kasance yar matsakaiciya bata da wani tsayi sosai sannan ba gajeriya bace, bata da rama ko kadan jikinta daidai da ita ne, haka yannayin kirar jikinta a tsare take sosai das da ita Wujdane gashin kanta ba baki bane kalar ja ne sam bashi da baki hakan ya saka take saka masa lale baki dan yayi baki aman baya sati zaya fara dawo da kalarsa, Gashinta har bayanta sannan sam baya kitsuwa hakan ya saka mahaifiyarta ke yi mata doka sai ta kindime kan bata bude shi A kulun ta Allah sai an kawo karar wujdane, domin ko mai hucewa ne bata bari ba, sannan ga shiga gidan yawa gidan da ba mai tarbiya kowa gashin kansa yake ci, gidane a unguwa da suka yi kaurin suna ba mai shiga sai gagarare domin a ciki ne zaka ji kani na lailayawa yayansa zagi idan uwa ta shiga itama a bata rabonta da fitsara da komai A nan cikin gidan Wujdane tayi kawa suke zaune a ciki tana kara darisan rashin mutunci da tsayaya Yayanta Abdul Fatah idan da abinda ya tsana bayan halayarta to wutar jahannama ce, baya son halayarta yakan ya saka yake yi mata dukan jaka idan ya shiga yin kwalo da ita sai ka rantse idan ta tashi ba zata kuma ba aman abinda zata aikata sai ya ninka wanda tayin A kulun yayanta Hamza yakan yi mata gargadi bayan mahaifinta yayi mata aman mahaifiyarta a kulun takan yi mamakin wai shin Wujdane wace irin mutun ce? Ita da ba dan *BATA DA ZABI* ba da ta jima da rabuwa da WUJDANE tun kafin ta kashe ta Wannan kennan [3/27, 9:57 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *01* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, Sako zuwa ga mabiya novel dina: *gaisuwa mai dumbin yawa, godiya da jinjina, ga wani ya zo fatan zaku karbe shi, taku ce, SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Zaune take bakin rijiya bayan ta janyo ruwa ta cika buta , hannayenta bibiyu ta dafe kuncinta tana duban daidai kofar gidan, yar datijiwa ce zata kai shekara arba.in da dori, gaba daya yannayinta yannayin cikin damuwa take domin lafiyar kirki ma bata da ita A hankali take takowa har ta karaso kusan wannan mata ta tsuguna a kusa da ita, ta ce" INNA ki tashi ki yi alwallar kin saba yi da wuri kinga kina zaune har an fara kiraye kirayen sallar magaribar shi kuwa a makaranta malan ya ce a gagauta shan ruwa a jinkirta yin sahur Dago da kanta tayi ta sauke kwayar idannuwanta masu wani irin kala tamkar na mage saman yar tata, ajiyar zuciya ta sauke ta ce" Aisha shin da kika je baki cewa Uwa ni nake nemanta ba? Wace aka kiraya da Aishar ta furzar da iskar takaici ta ce" Inna na fada mata, aman bara na koma ko wani abin ne ya rike ta Kai ta kada tana kokarin mikewa ta ce" kiyi sallah tukunnan, ba kyau tarban magariba, Haka ta shige bayin nasu na laka wanda yayi kasakasa sosai aman an saka wani yadi an rufe shi bazaka hango na ciki ba Uwata kika zaga? Ke Binta kin san na fiki rashin mutunci ko gaban babarku sai na bi ki na daki banza, na yi maki kashedi kula Hamza, ke har kin isa saurayin fa nace bana so ke ki so shi? Ai Hamza ya kade sai dai ya fita ya auro wata ba dai a nan layin ba, shi ne dan na fada zaki ce wai idannuwana girma tamkar na mujiya kwayar ciki sai kace kalar na mage??? Ni? Ni jarin... Kau kake ji an dauketa da mari, tana dagowa ta ga yayansu ne Abdul fatah, ai kuwa ta nade hijabinta ta artaya a guje ,, Dubansa ya kai kan Binta dake yashe a kasa tana share hawaye, ya kada kai ya ce" ki tashi ki yi hakuri kin ji??? Binta ta danyi murmushi ta ce" ba komai Abdul Fatah daman bata fahimci zancen bane kuma sai Anasiya tace da ita wai na zage ta Kai ya girgiza ya juya ya bi bayanta Tunda ya shigo ya kasa ya tsare yana jiran ta gama sallar da ta kabarta a dakinsu ita da kanwarta, aman kamar mai sauke alkur.ani a cikin sallar bata da alamar gamawar shi kuwa baya so yayansu Hamza da Babansu malan Laminu su shigo su hana shi yi mata dukan mutuwa Juyowa yayi wajen mahaifiyarsu, ya karaso ya zauna a kusanta yanai mata barka da shan ruwa Cike da kulawa take amsa masa ta tura masa kankanar da ya shigo mata da ita tsarabar yan azumi, Kalon yannayinsa take ta ga sai shan mur yake tayi dan murmushi dan ta san kwannan zancen bazai fice Kanwarsa ta tabo shi ba Asalamu alaikum warahamatulah A tare suka dago suna amsa salamar Malan da ya shigo da carbinsa , ya gama jan salar isha.i kafin ya karaso gidan, bayansa kuwa yaya Hamza ne rike da dardumarsa Yana zama dadaya suna gaishe shi Inna ta mike tana gabatar masa da kayan buda baki dankalin hausa ne ta dafa ta yanyanka danyen tumatur da yar albasa sune mahadinsa Budewa yayi yana murmushi yana yi mata sannu, aman bai ga *WUJDANE* ba Dubansa ya kai wajen Aisha, a hankali ya ce" MAMANA, shin ina yayarki ne? Ko bata shigo gidan ba?? Inna ta juyo ta juyar da kanta tana sauke ajiyar zuciya, bata ce komai ba, AISHA ta mike tana fadin " bara na duba Aba ko ta gama sallar? Tana nan Cike da murmushin yau ta dawo gidan da wuri yake fadin "Masha Allah, Sannan ya bi Abdul fatah da kalo ya mike yayi gaba cike da fushi can cikin ransa yake yiwa yayan nasa gaba daya adu.ar shiriya A hankali ta fito cikin hijabin nata baki wanda ya tsufa iya tsofewa sosai, ta karaso ta duka kusa da mahaifin nata cike da ladabin karya kanta a kasa tace" barka da shigowa baba, an sha ruwa lafiya??? Yana murmushi yake amsa mata da" lafiya lau WUJDANE ya gida, na same ku lafiya? Cikin nutsuwa take amsa masa Ya dago yana hangen fuskar Innarsu, ya ce" Allah ya shirye ki Wujdane , Allah ya kara nutsar min da ke kin ji? Inna ta juyo cikin yannayin sanyin nata ta ce" uhum, Malan nutsuwar munafurcin? Kallonta yake yana salamar yaren dan baya son suna irin wannan maganar a gabansu Bayan sun tafi ya nisa yana kallonta ya ce" ba sai na tambaya ba yauma tayi halin, aman da sauki tunda ban tardo ana jirana a kofa ba, sannan ina tsakar ganawa da iyalina ba.a katse ni ba, Fatima Allah yakan jarabtar bayinsa ta hanyoyi daban faban dan ya auna imaninsu, idan sun yi hakuri sun jure sun kawar da kansu sun mika lamarinsu wa shi , zai wanke masu zukatansu, Kaf cikin yayanmu ba wanda ya kai *WUJDANE* konya, aman karatun bokon ya gagara ke kin san na islamiya ba.a rabarta cikin ikon rabah tana da konya, wannan halaya na yau da kulun wanda na sani koda namiji ne sai hankalinmu ya tashi bare a mace, sai mu dauka tamu Salon jarabawar kennan, mu bi ta da adu.a Fatima sai Allah ya shiryar mana da ita Inna ta sauke ajiyar zuciya, a hankali ta ce" malan, ai *BANI DA ZABI* , aman ina tsoron rayuwar WUJDANE, ke mace ? Macen ma mai rauni sosai? A shekarun Wujdane goma sha takwas da doriya yaci ace tana gidanta aman du ba wannan fitinar nan ita ta saka a gaba ya zamu yi??? Malan ya lumshe idannuwansa ya ce" ADU.A, ita zamu ci gaba da yi, jinkiri ba kin amsawa bane, Allah ya shiryar mana da ita ya bata miji na gari Ka.ida ne, karfe hudu na bugawa Wujdane zata bude idannuwanta , ita zata bi dakunnan yan uwanta du ta tashe su daga baci dan su fito balbalin gidan nasu su yi karatu kafin lokacin sallar asuba su tafi masalaci su kuwa su yi sallah su yi zaman azkar Yauma hakan ta faru, zaune suke suna karatu kowa a hankali Malan na gefe shima ya bude alkur.aninsa Inna na zaune itama rike da carbinta tana ja Wujdane ta juyo tana kallon Innarsu, juyawa tayi ta maida kanta wajen mahaifinsu ta ce" Baba, ni mai yasa inna bata karatun ne,? Dago da kansa ya yi yayi mata nuni da ta maida hankalinta kan karatun ba tare da yayi magana ba, hakan ya saka ta mayar da kanta bata ko lura da irin hararar da Abdul fatah ke watsa mata ba Safiya na yi ta fito ta shiga aikin tsakar gidansu, Wujdane akoy kin ji aman kuma shegiyar tsafta tamkar wata mai aljannun tsafta, Yaro ne yayi salama karfe goma na safe ya gota, Yana gannin Wujdane ya dan rabe yana raraba idannuwa dan tsoro Dago da kanta tayi bayan ta kwashe shara ta wurga masa harara ta ce" shege mai kai tamkar duniya, ubanme kuma kake nema a gidan da safiyar nan? Anzo a ga yau mun samu abin karin ne ko aa ko??? Jikinsa ne ya fara bari yana kallonta ya ce" Mama, ( sunnan da ta dorawa du yaran anguwar nan cewar koda wasa shegen da ya kirayeta da sunnanta sai ta karya masa wuya, tsabar balakinta ya saka yaren dake kiran sunnayen iyayensu ma idan suka hadu da ita sai kaji sun ce *mama* dan idan ka fadi sunnan nata har gaban mahaifiyarka zata bika ta daki banza), yaci gaba mama yaya sule ne ke magana a kofa Ido ta zaro a fili ta ce" Kan Uba, da safiyar nan ubanme yake nema a kofar gidanmu? Ai kuwa yau zai san bashi da wayo Saurin saka hijabinta take dan ta fita innarsu kuwa na kokarin fitowa da sauri dan ta tsayar da ita Har ta saka kafa guda a zauren gidansu ta ji muryar inna na fadin" *WUJDANE WUJDANE!* ........ [3/27, 9:57 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *04* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Cike da takaici ta dago da kanta ta sauke idannuwanta a fuskar saurayin da ya duka gefenta kowa na gudunta banda shi, ya zuma mata ido yanai mata wani kalo irin ka hadu da wani abin da ya mugun birge ka Bakinta ta murguda ta banka masa harara sai idannuwan suka yi wani wulikwulik da su, Tsarki ya tabata ga ubangijin da ya halici wannan halita Muryar wannan bawan Allah ta kuma dakar kunnenta Juyowa tayi wannan karin da yannayin mamaki shinfide a fuskarta, har zuwa lokacin bata furta masa kalma daya ba, kallonsa kawai take a ranta tana mamakin kowa na gudunta ya akayi shi ya tsaya ko bai ji sunnan da suke kiranta da shi bane? Wato Aljannah??? Sosai ya gyara zamansa ya ce" aljannah da yamacin nan a tsakar gari? Aljannah har ta tsaya ayi haka da ita? Ni koda ke aljannah ce kin yi min Dago da kanta tayi wannan karin ta shiga kokarin mikewa cike da jin haushinsa a ranta tana fadin" banza bata gari Idannuwanta ne suka sauka saman Mairo dake kokowa da wasu almajirai na nama, sosai ta cire dan mayafin sai dakuwa suke ta warta su warta Wani uban tsaki ta ja ta mike ta kama hanyar tafiya ranta a matukar bace tana tsinewa halayar Mairo Biye yake da ita a saman mashin dinsa irin ash colar din nan, shi fa yarinyar nan sai ta kula shi Ita kuwa sauri take zabgawa domin bata da kudin mota ko sisi a hannunta kuma ba zata jira Mairo ba domin har magariba ta kawo kai Ki bari na kaiki, kin ga tun dazu muke tafiyar nan da alama gidan da nisa ko? Idan tayi magana to tabas titin da take takawa yayi magana, ita fargaba ce ta fara dirar mata jin ana salame sallar magariba, Ba ita ta karaso anguwarsu ba sai da aka gama isha.i, kafafuwanta du sunyi jajajir haka take baza hijabi Wannan gayen na biye da ita , shigarsa ba wata muguwar shiga bace, dan saurayi matashi zai kai shekara ashirin da takwas, yaro mai sunna Lukman dan kasuwa ne yana siyar da su atampa da yan daidaikun kayan mak.up a banban layi, sosai yake neman na kansa domin tunda ya tashi ya taso da hakan shi ke ciyar da gidansu Juyowa tayi ta kale shi daidai kusa da gidansu, Biye yake da ita tamkar jela, ta ja wani tsaki tayi masa kallon sama da kasa ta nuno shi da yatsa ta ce" Kai malan ka barni haka, lafiya? Sata nayi maka ne ko me? Ya zaka kama bina tun daga anguwar nan har gidanmu? Nayi maka kama da yan iska ne? To ka barni haka karka shafan bakin penti! Kallonta yake cike da matsannancin abinda ya taso masa na kaunarta, dama haka muryarta yake? Ya salam ya furta kafin yayi wani yunkurin ta fada gidansu Zama yayi a jikin babur ya jima har ya samu wani yaro yace da shi dan Allah ya shiga gidan nan ya kirawo masa wata budurwa fara mai bakin hijabi yanzu ta shiga Zaro ido yaron yayi harda kama haba ya ce" wai kana nufin gidan su *WUJDANE MAMA?* Bai tsaya ya bashi amsa ba ya ci gaba" ai kama tafi kawai domin basa zance da dare, kuma inai maka adu.ar Allah ya sa ba WUJDANE kake nufi ba Ya sa kai yayi gaba da bakar ledar man ja da ya sayowa mamansa Ajiyar zuciya ya saki a fili ya furta" zan dawo Tunda ta shige zaure ta jima a tsaye kafin ta saka kai cikin gidan da adu.a a bakinta sannan tayi salama kasa kasa Inna ce zaune a balbalin cikin gidan tana zaune saman darduma, kwai ne a gefenta dan ya kara haska mata tsakar gidan domin da abin hadari hadari garin sai yayi duhu Zuru tayi cike da tsoro tana kallon yannayin tafiyar y.ar tata, yar da tafi kusanci da ita har cikin zuciyarta dalilin kamar da duka yayanta basu yi da ita ba sai ita, ta dauko komai na mahaifinta harda tsagar idannuwansa, yar da kulun ta Allah take jaza mata bacin rai tunani fitina kala daban daban Tsoro ne ya darsu a zuciyarta harma ta baiwa kanta amsar shikenan da Alama Wujdane ta zubar da mutuncinta domin wani tafiya ne take tana harharde kafafuwa Cike da sanyin jiki Wujdane ta karaso kusan mahaifiyarta ta tsuguna, murya na rawa ta ce" inna, ina yini? Ya gida? Kallonta innar take, sam Wujdane bata tsoron zuciyarta haka take ayannawa a ranta, ace y'a mace ta fice a gidansu tun safe sai yanzu zata dawo abinda ko wani namijin baya kai magariba a waje? Cike da muryar karaya da takaici inna ta ce" Allah ya shirye ki WUJDANE, bata ce komai ba kanta a kasa , ta jima a tsugunan nan kafin ta mike ta shige dakinsu A cikin fashin sallah take hakan ya saka ta lalubo maganinta na ciwon mara ta hadiya, sai a lokacin cikinta ya bada wani kuuuuuu na yunwa alamar ba.a saka masa komai ba a wunnin ranar kwata kwata Konciya tayi ta takure jikinta tana sauraron muryar Aisha na karanta AL.IMRAN. Aisha karatu ne take tana tilawa bayan ta gama sallar isha.i, a hankali ta kai dubanta wajen yayarta, a rayuwa tana tausayawa rayuwar yayarta, wannan wace irin rayuwa ce ta daukarwa kanta ne? Yaushe zata farka ta daidaita nutsuwarta? Ita ba wuni a gida ba, ita ba cin abinci ba sai wani lokaci lokaci, haka take galari tamkar tinkiya, bata saka komai a ranta, yayansu ya jibge ta, Dan hawayen da ya zubo mata ne ta share tana mikewa ta fita Jim kadan ta dawo dauke da roba ruwan blue yar madaidaiciya Gefen katifar ta zauna ta ce" tashi Aunty ki ci abinci dan Allah Shiru tayi mata tamkar ba da ita take ba sai da ta kuma maimaitawa A hankali Wujdane ta dago da kanta, tana sha.awar rayuwar Aisha aman ita ba zata iya yinta ba, domin kuwa ko cikin gidansu takan jita tamkar ba a inda ya dace ba, kalar idannuwanta idan yayanta na dukanta yakan kirayeta da banza wawa wace bata kama da mutane mai siffar mutan boye, Hakan na sakawa tayi nesa da kowa Ki yi hakuri ki mike kinji? Ki yi hakuri dan Allah, A hankali ta mike ta karbi robar, macaroni ne ce ta sha man ja da yaji, Zama ta gyara tayi bismillah ta fara ci cikin nutsuwA Bayan ta gama ta dauki ruwan da Aisha ta zubo mata a kora ta sha , nan ta fara samun nutsuwa na shigarta Inna ce ta yi salama ta shigo dakin nasu, waje ta samu ta zauna tana kallon su gaba daya A hankali ta shiga jawabi kamar haka" Wujdane, ki sani a duniya mace yar gida ce, yar a kilace ce, mace yar mutunci ce, kin ga, du isar mace du takamarta idan har ta zubar da mutuncinta na ya mace ta gama, wujdane baki da wani abin tunkaho da ya fi wannan, ki sani saurayi du abinda zai rudeki da shi idan ya gama da samun abinda yake nema ya gama da rayuwarki, ki rufawa kanki asiri wujdane, ki rike tarbiyar mu Kanta a kasa take gyadawa irin tana daukan abinda ake fadi din nan, Ajiyar zuciya ta saki ta miko mata rubutun da Malan ya wanke wanda du kwanan duniya ake yi mata dan ta nutsu , Hannu ta saka ta yi bismillah ta shanye ta mikowa innar kwannon Haka inna ta mike ta fice gwuiwarta a sace Washe gari a daki Wujdane take, du tana ji lokacin da mazan gidan suka fice kowa ya yiwa inna salama , Kafafuwanta ne suka dauki ruwa, sun yi luhu luhu da su basa takuwa, Inna mamaki take har karfe goma sha daya Wujdane bata fito ba? Sai ta shiga adu.ar Allah ya sa ta ji jawabi ne wannan karin Aisha ce ta dawo daga makaranta karfe daya tana shigowa dakinsu cike da mamaki take kallon Wujdane, Zama tayi gefenta tana tambayar lafiya kuwa yau take gida??? Haka kawai ta ji ina ai itama makarantar zata shiga , makaranta ce mai hade da islamiya, sosai ake karatun islamiyar komai da larabci, a can ake kusan wuni su duka aka saka aman ita ta ki A hankali take bin Aishar da kalo har ta gama cire uniform dinta ta kara zama kusanta ta nace kan sannin mai ke damunta Hijabinta da ta rufe kafarta ta budewa Aishar cikin yannayin gajiya da konciyar ta bata labarin doguwar tafiyar da tayi Cike da mamaki Aisha ta shiga dakin Malan ta dauko man zafi ta zo ta shashafa mata har bayanta sannan ta fice ta barta ta huta Kai.kawo kofar gidan su Wujdane ya fi a kirga da tayi tana son shiga tana tsoron yayansu, domin wani lokaci da ta shiga Abdul fata da ya kama kwalo da ita tamkar ya samu jaki, ita tsoronta daya jiya yaya wujdane din ta yi ne? Mairo mairo. .. [3/27, 9:57 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *03* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Tana saka kafarta cikin gidan ji kake wur kwatsam karar cilo langa fada ne ake na kirki ana dambe tsakanin lami da Hajara Sosai ta shake wuyanta inda yaransu ke tsatsaye suna ta ihu suna ke daki hancin ke dakii bakin ke daki tatasai da kubewa wanda ya fasa ba shi bane Dan tsayawa tayi ta kare masu kallo ta kada kai tayi wajen zanar su kawar tata Tana shiga da salama a bakinta Mairo ( Mariam ce aka mayar da sunnan Mairo ) Dake zaune da daurin kirji tana ta kokarin yin kwaliya ta juyo ta saki baki tanaiwa Wujdane wani kalo Wujdane ta murguda baki ta ce" kallon fa?? Mairo ta ce" yanzu tsakaninki da Allah danine ( Wujdane) kin san dalilinki aka gayace mu wajen sunnan nan, tunda aka yi haihuwar nan nake tara kudi dan mu samu na mota aman shine har yanzu baki shirya ba??? Wujdane ta yatsina fuska da kalar an dameta ta ce" ke ni nama manta da wani wajen suna, ke yanzu dan su Abu sun ce ana dafa shinkafar gwomnati shine kike wannan rawar kafar? Kinga karfa mu tafi mu jazawa kanmu raini, ni bana son irin shiga cikin yan gayun nan yanzu za.a fara yi maka kallon saman hanci ni kuwa ba dauka ba zanyi Mairo ta juyo tana kallonta ta cacaba hodar ruwa mai sunna iman a fuskarta irin ta cub din nan mai danko sai wani firirita take da idannuwa tana kokarin jan gira ta ce" kai Danine, kar ki ce dan hinkafar gwomnati ne ni daman can Aradu ina da sha.awar shiga cikin yan gayun ne a dama da ni dan Allah ki je ki shiryo mu daga kar rana tayi sosai a shishige cikin gidan Kai ta girgiza , tana matukar mamakin irin yanda Mairo bata gani ta kyale ko ta kawar da kai, kwadayi kuwa ba.a magana, waje ta samu ta zauna tana cewa" idan xaki je da ni a haka ki je idan kuwa ba zaki ba ba damuwa sai nayi zamana aman bikin gayar sodi Abua itama mai aikin gidan ta gayace ta muma aka gayace mu bazan tsaya kyalkyale kyalkyale ba irin wa.innan fa daman sai dai kai kayi musu wahalar aman su basu iya yiwa mutun ba, dan haka ke da kika ga zaki iya ki ci gaba Bata kai ga rufe bakinta ba aka jefo wata rigar mama da har ta sandadare dan dati, wani irin tsami take fitarwa jikinta harda kamar wata kwalkwata , Da sauri Wujdane ta mike tana sakin rigar mamar kasa tana kakabe hijabinta Kanta ta dago cike da bacin rai ta ce" Kan Uba, wannan wace yar kwal uba ce ta jefeni da wannan abin??? Tana fadi tana nuna rigar mamar Mairo ta mike ta dauki rigar mamar ta leka ta jikin zanar ta jefa masu tana fadin" banzaye fitinanu, wai fa Adamu ne zai kara aure kuma na budurwa shine ya basu naira dubu dadaya harda dari bibiyu abinda bai taba yi masu a matsayin kishin laifi dan ya kawo amaryarsa, toh shine Hajara ta ajiye nata kudin ta tafi dauko markade kafin ta dawo ta tarar ba dari biyun shine wannan fadan tace ai Lami ce tunda su kasai suka san da kudin sannan da ta fita ba kowa a gidan sai su din, tun safe suke wannan ragabzar mijin ya fice abinsa yayi tafiyarsa, umanmu kuwa ta hane mu da shiga domin tunda adamu ya taba nuna yana son nan nawa suka sha masifa da umanmu sai bama shiga sabgarsu Wujdane ta tabe baki cike da kyankyannin Adamun kansa, bata cewa Mairon komai ba Mairo ta saba da halayar kawarta hakan ya saka itama taci gaba da shiryawa tana tayi mata labarai dan karta daina tafiyar Tunda bus ta ajiye su suke tafe har anguwar sunnan, Anguwa ce irin ta daidaikun masu hannu da shuni, irin anguwar nan ce dake cakude da masu abin da talakawan Ja tayi ta tsaya sanadiyar hango gugun samari a kofar gidan Mairo da ta shan jan baki ta juyo tana kallonta daman ta san a rina wai an saci zanin mahaukaciya domin du dabararka da Wujdane bata bi ta tsakiyar maza koda a idi ne zata rakube ne, aman da mata ne koda sun cika anguwar nan sai ta bi kuma ka tsakwaleta ku daku Waje ta samu ta zauna gindin wata bishiya tana fadin" sai kin fito Mairo bata tsaya magiya ba domin ta san kare kukanka ne ba zata bita ba hakan ya saka ta juya kawai ta tafi cikin sake salon tafiya wai ita yan mata🤔 Zaune take tana kallob kasa,tunani take tana fatan su koma kafin yama Yaya Abdul fatah bai dawo ba dan yana da haushinta ( ita bata ma damu da daga fita gaisawa da saurayi ta fice mai gaba daya ba) Yan mata ne su biyu, sanye da ankin gidan sunnan da wani saurayi a gefensu suna tafe suna labari suna dara na darawa na jin haushi su ji Wace ke gefe ta juyo da biyar dinta a hannu ta ce" bara na bayar da sadakar biyar nin nan zaifi gyara ni da na je na jefar idan ya so khalifan ya zo nema sai na amsan masa a wajen mama Saurayin ne yayi dariya ya ce" ke da aka baki ajiya zaki yi kyauta da shi? Bakya gudun rigima ko??? Gaba tayi ta Nufo wajen wujdane itama tana dariyar ta miko tana fadin malama karbi sadaka Ta maimaita ya kai sau biyar Wujdane na kallon kasa bata dago da kanta ba sannan gaba daya ta nanade kafafuwanta da hannunta a cikin hijabinta baki, Jin mai maganar taki ta bar wajen ne ya sakata dago da kanta cike da bacin rai ta sauke idannuwanta a fuskar yarinyar Ihu ta saki ta saki naira biyar din tana fadin" Aljanna wayo aljanna wayo na shiga uku Aljanna Mutannen dake gefe da wannan saurayin suka yo wajenta suna tambayar a ina aljannar ne,????? Wujdane da 5ake nunawa suke kallo, wani irin fari tamkar bata da jini a cikin jikinta, sai idannuwanta kalar maciji, wannan saurayin dake tare da su ya shiga janyeta yana fadi tun karfinsa" Inahu sulaimana wa.inahu bismilahi rahamani rahim Shi kansa ya tsorata da yannayin halitarta, abinka da farin mutun ya saka bakin hijabi, Du kama guduwa suka yi suka bar wani saurayi shi daya dake kallon Wujdane wada ta cika da takaici A hankali ya duko ya ce""""""""":""""""""":::""""""" [3/27, 9:58 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *05* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... A wunin ranar nan Wujdane ko kofar gida bata leka ba, tana ta bacin gajiya daman tana fashin sallah Can da malan ya zo ya tarar da fara.a a fuskar Inna da ya tambayi dalili ya gano ta fara samun kan yar tata ne, cikin murna ya dube ta ya ce" innar Wujdane, koda kinyi kokarin boye soyayarta a zuciyarki a idannuwana bata boyuwa, Allah ya inganta Kanta ta sada tana murmushi bata ce komai ba, haka ya mike ya leka dakinsu ya tarar har sun yi baci su dukansu kan Aisha na saman cikin Wujdane ya yi masu adu.a ya rufo dakin Yau ta kama talata, tun karfe bakwai Wujdane ke zaune kofar dakin mahaifinta, kanta a kasa tana dan kallon yanda tsuntsaye ke saukowa su ci geron da innarsu ke zubawa du asuba ta Allah a tsakar gidan hakan ke janyo tsuntsaye kala kala su yi ta ci suna dan waken su Yau ba bakin hijabin bane a jikinta, kayan makaranta ne irin na Aisha, blue din dogon wando sakake da hijab fari har kasa da riga blue a ciki, gefenta nikaf dinta ne da ya sha wanki kaf jikinta kalkal bata da dati ko kadan, Malan Laminu ne ya fito da shigarsa na jalabiya fara da rawaninsa dan madaidaici kamar yanda ya saba Da mamaki yake kallon Wujdane, idan dai ba idannuwansa sun samu matsala bane kayan makaranta ne ta saka, toh aman mai ya canza mata ra.ayinta ne? Ita dake maganar makaranta sai dai a aljannah idan tana cikin bayin da zasu shiga, dalili kuwa shine, a makarantar ya kasance wasu malaman na wawar neman soyayarta, wasun lalata da ita, wasun su tsangwami rayuwarta , haka dalibai idan dai ta fice sai an tsokane ta da zagin mai idannun kurukuru ya na mage, mai farin zabaya da sauransu Amsa gaisuwarta yake yanda ta kara dukawa har kanta, Wujdane ba dai ba ladabi da biyaya bata da raina mutun koda a waje ne sai idan ka tabota nan fa zaka gane bata da wayo Tsaye suke da innarsu malan na kallon yanda take zaune bata furta masa muradinta ba, aman shi ba sai ta fada ba tsakanin da da mahaifi fuskarta kadai zai kalla ya gane yarenta Malan, ni kam ba katsalandan nake son yi ba, aman ka fi kowa sannin halayar Wujdane, nafi kowa murnar ta je makaranta ko dan yawon nan da ta saka a gaba, aman Malan kar ka manta zuwanta na karshe fa, ta yiwa yaya da kanwarta dukan tsiya ta tare hanya sai da aka kirawo ka, malan yara ba zasu daina tsokanarta ba, haka nima nayi rayuwa kai shaida ne, a kauye ma an hana ni zama bale ita a birni? Malan kana gani yaran anguwar nan dan dole suke ce mata MaMa, idan rigimar Wujdane ta fita nesa ba lale ne a yi hakuri da ita ba, ita kuwa ba zata iya mayar da komai ba komai ba ta kawar da kanta har yanzu tamkar wata yarinya karama Inna ke mitar nan ta dage kan kawai kar ma a soma kai Wujdane Makaranta Malan ya dago da kansa yana sauraronta, shi kam yana mamakin halayar mata har yanzu, innar yara dai ba wata yarinya karama ba aman cikin ikon Allah du girman mace ana yi ana tarota ne, cikin tausasashiyar murya ya ce" haba innar yara, idan fa hakan na cikin adu.armu na ta nutsu? Ke ganau ce ba jiyau ba Wujdane rabonta da wuni a gida har an manta cikin ikon Allah yau ta farka da muradin komawa makaranta sai a jaraba a gani, ina mai yi miki nuni da a kulun kwanan duniya adu.arki wa Wujdane ita ce abar so ba magana ba, sai mun dawo Haka ya saka kai Wujdane na biye da shi da Aisha Bayan ta saka nikaf dinta, inna ta yi masu Allah kiyaye ta shiga dan aikacen aikacen cikin gidan cike da zulumin yanda za.a kaya da yarta A makaranta Malan ya yankawa Malan lamunu kudade wa.inda dole a bayar idan dai ana bukatar Wujdane ta ci gaba da daukan karatu a aji Bayan dogon nazari ya basu lokaci wanda da yardar Allah zai dawo da wa.innan kudade sannan ya nemi alfarmar ta fara daukan karatu kafin ya cika alkawari da yardar mai duka Malamin mai mutunci ne, sannan ya san irin kwazon Wujdane, duda yana tsoron dayan halin aman ya yarjewa Malan Aminu ya yiwa Wujdane rakiya har kofar aji sannan ya koma kasuwa dan bubuga abinda ya samu Du cikin ajin ba mai nikaf, sannan kowa dake zaune sai surutu suke, Can gefe Wujdane ta samu ta rakube ta sada kanta tana dan juya bironta Shiru kake ji ajin ya dauka hakan ya saka ta dan dago da kanta, Malam yusuf ne ya shigo mai koyar masu maths Rubuce rubuce ya fara a allon makarantar cike da kwarewa yana yi yana kwatanta masu sosai da sosai yanda zasu fahimta Juyowa yayi yana tambayar ko da wanda bai fahimta ba? Nan ya hango wujdane zaune da nikaf Cikin yaren turanci ya ce" wannan mai nikaf din fa? Shin bata san dokar makarantar ba cewar ba.a shiga aji da nikaf??? Shiru Wujdane tayi tamkar bata wajen, ko bata san abinda yake nufi ba Wata yar matashiya mai suna Salima take fada masa cewar bakuwa ce mai yiwuwa bata san abinda yake fadi ba, domin Malan Yusuf akoy rigima sosai bashi da sauki Cikin bacin rai ya fara fadi yana nufota da hausa cewar" idan har bata iya turanci ba uban me take nema a school din nan kuma ajin nan? Malama ki cire nikaf din idannuwanki mu nan bamu taru a nan dan fuskarki ko wani abin ba, Cike da kunan rai ta kai hannunta da sauri dan kar ya cire mata ta cire nikaf din kanta a kasa Tsaki ya ja yana fadin" useless kawai A hankali Wujdane ta dago da kanta, wani banzan harara ta bala masa wanda ya saka idannuwanta suka yi wuluk da su , ciki ciki take gunaguni wanda Allah kadai ya san mai take fada, ta kada kai ta buda litafinta da niyar rubutu Sam malan Yusuf bai gani ba, aman daliban da suka juyo kowace kallon mamaki take yi mata, kasa kasa Aisata ta cewa makociyarta" ke kinga wata tamkar ba mutun ba? Ji fa farin fuskarta ko dai wata hoda ce haka ta shafa bayan an hana mak up a makaranta???? [3/27, 9:58 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *07* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Haka kuwa suka yi suka fitar da sauran jama.ar nan suka bar daga Wujdane sai Balki Mairo na fita ta shiga surfa sauki ta dauki adaidaita ta yi masa kwatance har kofar masalaci baba wanda Malan kan je ya bayar da karatu manya manyan mutane da du talata da yama yakan yi hakan Tana sauka ta nemi gu ta rabe, ita bata ma san ya zata yi ta samu malan din ba, sannan jama.ar dake kai kawo ba wasu kananan mutane bane bale ta nemi alfarmar a yi mata magana da Malan Can dai tana zaunen nan wani dan saurayi fari dogo ya zo shigewa , Da sauri ta mike ta ce" bawan Allah dan Allah ka ce da malan yarsa na kofa na yi masa magana Dan dakatawa yayi yana kallonta, a firgice take da alama ba lafiya hakan ya saka ya shiga cikin masalacin cikin nutsuwa ya yiwa Malan dij magana Cike da mamaki Malan ya fito yana ayana yayansa basu taba zuwa nemansa ba du rintsi, wannan ya tabata ba lafiya ba Yana fitowa Mairo ta zube jikinta na bari ta kwashe masa komai yanda aka yi ta fada masa ta dodoka rantsuwar cewa ba Wujdane ce ta fara tsokanar ba Malan baima san mai zai ce da ita ba, cikin sasarfa ya yi mata hani da fadawa Inna, sannan ya juya cikin masalacin dan yi masu salama Wannan dan saurayin ke kallon yannayin malan, daman akoy shakuwa sosai tsakaninsa da malan, sarai yana mutunta shi domin shi dai bai taba gannin ko jin wani abu marar dadi a tare da malan Mikewa yayi da sauri ya biyo bayansa gannin yanda yake tafka sauri Cikin daga murya ya ce" MALAN, MALAN , domin shi har ya fara shesheka bazai iya irin tafiyar nan ta malan ba Dakatawa Malan ya yi ya juyo, cike da mamaki ya amsa da " na.am *JAMAIL*? Karasowa Jamail ya yi ya ce" malan sai na ga kamar ba lafiya ba, ka yi hakuri haka kawai ina sonka a raina malan, Allah dai ya sa lafiya? Murmushin yake malan din ya saki, shi kansa bai san lokacin da ya furta " police station na hanyar yan Babura zan je Kara matsowa Jamail ya yi cike da mamakin mai zai kai malan can, wajen aikin yayansa ne, baban office ne yayansa Anwar ke jan wajen , aman ba zai yi masa tambayar mai zai je ya yi ba sai dai ya ce" Lah ai wajen aikin yaya ne, yaya Anwar din nan? Shima yana zuwa nan din ranar lahadi yana daukan karatu Murmushi malan yayi ya ce " masha Allah Jamail, masha Allah Dan dakatawa ya yi, shi bai ce wani abin ba , shi kuwa jamail haka kawai ya ga ba zai iya barin malan ya tafi haka ba Jamail ya ce" Malan mu tafi na kaika mana, da nisa sosai kuma ka ga kafin ka samu abin hawa a anguwar nan an hana motocin haya shigowa sai ka fita sosai wanda a kala zaka yi tafiyar awa ko fi wai danma kana saukin nan, dan haka mu je na kaika dan Allah Ya karashe yana mai hada hannayensa waje guda Ajiyar zuciya malan ya saki ya ce" mu je Jamail Juyawa Jamail din ya yi malan na biye da shi dan zuwa gidansu ya dauko mota Malan dan dardar yake a bayan Jamail, bama zai iya daga kansa ya karewa ginin katangar kalo ba bale har ya ga tsayinta, da alama daga ciki hawa hawa ne, wani irin zane ne aka yiwa ginnin daga kofa wata fulawa manya manya, kofar shigar kuwa glass ce, irin glass din nan da bata fashewa ko da bindiga sai bomb, sannan kalar blu mai duhu ce ba.a gannin mai ficewa, Wata yar camera ce a jikin kofar daga sama wada ke haska mai shigowa da mai fita komai da ya shafi kofar gidan, Ham Malan ke kallon wannan gini kaf anguwar bai ga ginnin da ya kai nan tsaruwa girma shiga ido ba, wai baima shiga ciki ba , kennan nan ne gidan yayan nasu da Jamail ke yawan zuwa yana wuni domin yayan nasu na yawan yin rashin lafiya, Yatsarsa ya dora kan wani abu, babar yatsarsa , sai da abin yayi zuzu scan sannan ya bada wani pippp sai kofar ta budu A hankali malan ya daga kafarsa ya saka ya bi bayan Jamail bakinsa cike da adu.o.i yana mai fatan Allah ubangiji ya datar da mu a janatul firdaus, wai wannan gidan duniya ne? A gaskiya fadin tsaruwar cikin gidan nan bazai yiwu ba, just ka kiyasta iya hangen ka ka saka a ranka ya fi gaban hakan, gaba daya ginnin tsarin fallon ba a kasa yake ba a tsakiya yake, Malan tsoro ne ya rufe shi ya ja ya tsaya yana tunanin wai mai yake haka ne? Ya biyo yaro haka kawai bayan ga Wujdane dinsa can a rufe???? Lalalal broth, yanzu ka dawo mu kuwa yanzu zamu je ai wajen aikin naka, ka ga Malan ne wanda ke bada karatu a masalacin yaya, shine zai je na shigo na dauki mota na kaishi domin da nisa Matsowa Anwar yayi yana dan dukawa yana mikawa Malan hannun irin girmamawar nan yana gaishe shi cike da mutuntawa Malan yayi mamakin tarbiyar yaren nan, mafi yawancin yayan masu fada a jin nan sukan dauki talaka tamkar wani abin kyama aman wa.innan yaren sun mutunta shi sosai, yayi murna gannin hakan Har Anwar ya juya zai fice ya dawo ya ce" Ni malan, lafiya zaka je can office din? Domin na fito idan abin sai an ganni ne kar ku je ku wahala sai na baku lokaci gobe da safe insha allah ko??? Cike da fargaba Malan Aminu ya dago kansa yana duban Anwar, hannayensa ya hade waje guda ya ce" yaro kar dai ka ce min sai kana nan za.a iya sakin mutun? Yarinyata ce ta yi fada aka kaita tana wajen naku abokiyar tafiyar tata ta zo tace min ance sai iyayenta sun zo? Yaro idan sai gobe ai sai dai nima na je kofar wajen aikin mu kwan tare da safen sai mu shiga gidan tare dan ban san ya innarsu zata dauki zancen ba Malan ya karashe yana dan sada kansa kasa Gaba daya Anwar ji yayi ba dadi, kansa ya dafe tabas cikin yan matan nan biyu ne, tausayin malan ya darsun masa a zuciyarsa har ya fara tunanin da shi ne da ya zai yi? Da dukan alamu kuma Malan din a ganninsa ba wani abin kirki a hannunsa hasken alkur.ani ke kara cika haibarsa a idannuwa, Juyawa ya yi ya kali Jamail ya shagwabe fuska tamkar zai saki kuka ya juya falo yana tunanin shi da ya zo ne dan gannin jikin broth dinsa Please yaya karka bar mace mai rauni dan kawai rigimar fada ta kwana a cel, plz mu tafi yaya, cewar Jamail yana hade hannayensa waje guda Kai Anwar ya dan girgiza ya ce" Bismillah malan Ya yi gaba ya budewa Malan gidan gaba shima ya zagaya dan yayi driving, dar Jamail ya shige baya yana sasada kai dan kar a kore shi Suna karasawa direct office dinsa ya karasa da su Malan , ya yi umarnin a fitar masa da su Wujdane a kawo su office Har yama ta yi sosai cike da mamaki suka shiga domin fitar da su Balki ta ci kuka har ta gode Allah, Wujdane kuwa ta ja hijabinta dan sama sama ta kuma rufe daga goshinta, ita damuwarta daya innarta da kuma Malan Ku fice mu tafi , wani bakin police ya yi musu tsawa Cike da dan fargaba ta dago da idannuwanta, ta sauke su a bayansa ya juya baya zai fice yana nufin su bi bayansa Balki ce ta mike jikinta na rawa ta ce" wujdane kar mu bi shi wly ance fada yayan mutane suke yi fa??? Wata harara Wujdane ta banka mata ba tsoro ko dar ta bi bayan shi duda a kasan zuciyarta banda adu.ar tsari da take ita kanta a tsoracen take aman bata nunawa ko daya Bayan ya shiga suka shigo su ma, kanta a kasa bata daga bama bale ta ga mutanen da ke ciki Anwar ya ce" Malan wacece yar taka???? Malan ya nuno Wujdane ya ce" ga tanan Da sauri Wujdane ta dago da fuskarta tana jan hijabinta baya, bata taba jin kunyar mahaifinta kamar na yau ba, kwarai da ake cewa yaro ke jawa iyayensa, yanzu ko su Yayanta Abdul fatah basu kawo malan police station ba sai ita? Wani abin bai taba kawo shi ba yau sanadiyar ya haifeta gashi tsamotsamo a tsaye a wajen, Sada kanta ta yi hawaye na ziraro mata wanda haka kawai ta ji shi na mahaifinta , bata san nawa aka yanka masa kafin ya fitar da ita daga wajen nan, wani haushin Balki ya tirnuke ta ta dago da kanta ta Bankawa Balkin harara na tsana ta ja dan karamin tsaki Malan ya girgiza kai, ya juya wajen Anwar ya ce" wato yaro, cikin ikon Allah ka haifi da ne baka haifi halayensa ba, ita dai wannan yarinya idan ka ga mahaifiyarta sai ka rantse da ba ita ta haifeta ba , domin fadima akoy hakuri da kawar da kai, Wujdane tunda ta tashi ta tashi da rigima daidai geargwado, cikin ikon Allah bata da hakuri idan dai ka shiga sabgarta toh zaka tarar, a kulun adu.a muke binta da ita Allah ya sanyaya, yau anyi abin kirki aman sai yamacin ya karashe da haka, Ja nunfashi ya ce" Alhamdulilah, na san Allah na boye wani lamari a tare da ita, a kulun ina gode masa da ya malaka min ita, sannan ina adu.ar Allah ya shiryar min da ita ya saja mata nutsuwa a duk inda take Cike da kaunar datakon Malan Anwar ya bada umarnin Balki ta fice ta koma itama gidansu, bayan dogon kashedi da gargadin kar ya kuma gannin kafar wata cikinsu a police station din nan domin ba zasu kwashe lafiya ba, Haka Balki ta juya har gudu take ta tafi tana godewa Allah da ya takaita tashin hankalin nan Kallon Wujdane suke gaba dayansu, shi Jamail gaba daya ta gama birge shi, yana son ya ga macen da bata daukan raini, shi kuwa Anwar a wani hali ya shiga, yarinyar ta yi masa fiye da tunanin bawa, kallonta yake a ransa yanai mata adu.ar samun nutsuwa , Cike da farin ciki Malan ke yi masu godiya wada ya umarce ta da ta yi wa Anwar da Jamail godiya Dago da kanta ta yi bayan ta goge fuskarta wanda ya baiwa hannunta damar fitowa , yanda farin fuskarta yake haka na hannunta , faratunanta dogaye ne tsar , Idannuwanta ta dago a karo na farko ta sauke su a fuskar Anwar, gashin idannuwanta sun jike da hawaye hakan ya saka suka dan harhade suke kyali tsaf bakinsu ya fito radau, sai zagayen idannuwan ya yi jajajir kamar ya kode domin ba wani kwali a idon, Murya na rawa ta ce" jazakallah Bai san lokacin da ya lumshe idannuwansa ba, tamkar sarewa haka muryar ta yi masa rada a kunensa, a hankali ya furta" wa.iyaki Ky din ya mikawa Jamail dan ya kaisu gida bayan an sha darga da Malan kan abin ya yu yawa, da kyar suka shawo kansa ita kuwa wujdane sai kumbura take tana karawa, Nan suka bar Anwar zaune ya jinginar da kansa yana ta tunanin to ya aka yi basa kama ko kadan da Malan din,, ????? Jin tunanin yarinyar zai dame shi ya saka ya mike ya fita ya harhada takardu ya fara dubawa yana kara zagaye police station din Tafe suke malan na kara yi mata nasiha, cike da kula , Jamail kansa yayi tsam yana sauraro yana mamakin du abin nan da ta aikata malan yanai mata nasiha, uhum da wani uban ne ba mai hana shi dakata Har suka karaso gidan wanda yara yu suka biyo motar suna ihun jirgi a anguwarsu domin irin motar nan ce mai tsayin nan, Motar na tsayawa Wujdane ta bude ta fito a bayan ai kamar an watsa su suka fara guduwa ta ko.ina suna ihun walahi *MaMa* da malan ne a motar, du suka warwatse dan mai dukan yaro ce va zata saurara masa ba Yauma bata tsaya cin abincin daren da su ba, ta fada dakin ta shiga baci Malan bai fada ma inna ba, sannan bai fadawa kowa maganar ba bayan a titi da Mairo ta dan barbada cewar Wujdane na rufe sai ta yi wata , ganninta ta dawo ya saka ake zuwa har gidan su mairon anai mata ihun makaryaciya ta ji kunya Da safe kofa ka san fitarta bayan ta shaidawa Aisha cewar ta tafi makaranta dan ta samu ta gama rubuce abubuwan da ya kamata bata da a litafinta Sai da Malan ya fito take shaida masa ai ta fice makaranta da ya tambaya Dan jim ya yi sannan ya fice har inna na tambayar lafiyar malan kuwa du wani sukuku take ganinsa??????????????????????? Konci tashi yau wajen sati........... [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *09* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Wujdane dake konce mamaki fal cikin ranta, mamakin yanda aka yi su malan suka sake da wannan bawan Allah, har wani dan uwanta inna ke cewa, a ina ya zama dan uwan nata???? Cike da jin haushi ta fito jin inna na kuma kiran sunnanta, wannan karin ba nikaf din aman da hijab dinta har kasa Silbar wajen Malan da a ciki ake zuba masa ruwa idan ya zo domin ya fi kowanne haske ta dauko , ta bude randar cikin dakin inna tsaftataciya da kulun sai ta wanke ta ta juya wani ruwa sanyi karai da kanshi ta zuba masa ta kawo ta ajiye masa Can gefe ta zauna ta turo baki ta hade fuska ta sada kanta kasa, Kallonta Jamail yake can kasan zuciyarsa dariya tamkar ta kashe shi, shi kam ba zata bashi wuya ba domin yana zaune da wanda ya fita miskilanci, dan ita idan ta hana kanta abu akoy wa.inda suke tursasata, shi kuwa yaya Alaidine sai dai a hakura dan ko kalonku ba zai yi ba bake ka saka a kokon zuciyarka zai yi abin A hankali ya ce" kanwata wujdane, Da gangan ya fadi dan sau goma zai fadi hakan sai ta dago ta watsa masa harara dan ita ta tsani a mayar da ita yarinya, duda ya girme matan ya bata shekara biyu a kala aman sai tana ganin ya raina ta danme ba zai kirayi sunnanta kawai ba Bata dago da kan ba, sannan bata amsa ba, Murmushi yake saki na samun nasarar ya hauda ta, zai kara magana Aisha ta shigo da salama Da fara.a yake mata oyoyo ya ce" lale da mamana,(kamar yanda su Malan ke fada mata), ya ci gaba haba yanzu bakina zai daina tsami kin ga inna na fama da kicin dinta Kanwats kuwa idan ta kulani toh wannan dutsen ya kulani Aisha dariya ta saki tana karasa shigowa, dukawa ta yi ta ce" ina yini yaya Jamail, Amsawa yake cike da fara.a , ta juya wajen Wujdane ta shagwabe fuska ta ce" aunty shine kika yi tafiyarki kika barni? Na saba kwana biyu da dawowa da ke har na watsar da abokan tafiyar tawa yau ni kadai na bi hanya ina ta waige Wujdane ta dan dago, bata da niyar tankawa a yau sanadiyar Jamail dake guri wanda ta radawa natace, Yana shirin kara tunzurata wayarsa baba ta dauki tsuwa Da sauri ya zaro ido ya daga Kafin ya yi magana daga dayan bangaren aka ce" ka zo Kit aka kashe kiran, Mikewa yayi yana dan sauri yana salamar su inna da fadin" Inna baban yaya na kirana bara na artaya kar ya daki banza, Yana fada ne yana kokarin cusa wani abu kasan kwannan ruwan sannan yayi ficewarsa yana dariyar inna na yi masa adu.a har soro Tuki yake na garari yana adu.ar kar ya kagauta, Da gudu ya haura ya shige fallon yayan nasa da salama a bakinsa Zaune yake yana ta faman danna laptop aman wani dan yaro da ba zai fi shekara biyu da ba na ta kokowa da wuyansa da jikinsa, shi kuwa sai dai ya dan kawar da kansa ya ce" boy stop it! Kamar wanda yake fadin" Boy ka yi kokowar, domin kara makale shi yake Jamail na shigowa ya san kwannan zancen ya hana shi aiki ne, cikin hikima yake kokarin janye shi a jikin yayan nasa, aman yaron sai ya kuma makale shi yana ihun shi park shi park gashi ranar ranar aiki ce park din ba wani dadi ne da ita ba, du yawanci matan aure ne da yan mata yan school da samarinsu irin masu dan hannu da shunin nan Kansa ya dafe ya furta " oh goshhh🤦🏻‍♂ Mikewa ya yi tsaye , dan zuwa bedroom dinsa ya dauko abu, a nan tsayinsa da kirar jikinsa ta bayana, Ya salam, wannan bakin mutun ne a africa ko mai? *ALAIDINE* ba fari bane, Aman ya fi duka yan uwansa haske, irin fatar nan ce ta yan ethiopia, domin sam ba zaka kiraye shi da bakin mutun ba, Alaidine dogo ne zambak , har ya dara Anwar a tsayi, Ba zaka taba kusanto jikin Alaidine da rama ba sannan ba irin jikin nan ne mai tumbi ko wani loko loko na kiba ba, aa hasalima jikinsa irin na yan dambe ne, hannunsa a wani murde yake dalilin excercise da yake ba dare ba rana du lokacin da yake jinsa a irin yannayin kadaita ko tunanin rayuwa yakan mike ya shige dakinsa na sports ya zagine ya gurzu , yana gamawa lipton kawai zai dan sha ya konta ya huta domin ba kasafai yake fita aiki ba dan irin mutanen da suke zube shagunnansa , Alaidine na da idannuwa masu girma sai dai a ko da yaushe cikin ja suke, sannan akoy shi da rashin tsoron saka idannuwansa cikin na mutun koma waye, hakan ke kayar da gaban mutane da dama Shin menene tarihin rayuwar wannan familly??????????????? Elhaj Kadri ganninka riba, miji a wajen Hajiya Marwa mahaifan ALAIDINE, ANWAR da JAMAIL, Hajiya Marwa Ya ce a wajen Elhaj Muhamadu itace auta ita da yar uwarta marigayiya Shafa, Matarsa daya, wace tayi ta hayayafa cikin ikon Allah tayi ta yin yan bibiyu har sau hudu sannan ta yi daya ta kuma samun su Marwa Daga Marwa haihuwar ta tsaya sannan su uku kadai ne mata Shafa ta koma ya yi sauran biyu kuma Marwar ce auta Marwa cikin wani irin gata ta tashi, takan fita ta je makotansu gidan Elhaj Abdallah mahaifin Elhaj Kadri, Elhaj Abdallah ya ninka Elhaj Muhamadu arziki nesa ba kusa ba, sannan mutun ne mai mutunci yana da sadaka da zaka, Yayansa biyu kawai maza Elhaj Kadri ne baba sai kanninsa Elhaj Abubakar, Ragamar kulawa da kasuwancin Elhaj Abdallah a hannun yayansa, sosai yake saka su a hanyar koyan aiki su koyi neman na kansu, sai dai saken yayi mugun yawan da su Elhaj Kadri sukan yi wuta a cikin gari ba laifi Marwa da Elhaj Kadri soyaya suke irin mai karfin nan, wanda da wuri ya nemi a aura masa ita sai dai abin takaici mahaifinta ya nuna ko kusa kawai sai ta gama karatunta na university Tafiya ta yi tafiya, Elhaj kadri na ci gaba da kula rayuwar Marwa du da irin kashedin da mahaifinsa ya yi masa na cewa idan an hana shi aurenta ya nemo wata mata yawa ne da su a duniya aman fir zuciyarsa da gangar jikin na wajen Marwa wace itama du kwanan duniya takan sha darga da mahaifinta kan kul ta kiyaye duda mahaifiyarta bata da yanda zata yi ne da lamarin nan dan ita sam bata goyi bayan ace budurwa kamar Marwa da yar uwarta sai sun gama karatu ayi masu aure mata ba maza ba, a wannan zamanin Ya kasance kusancin Marwa da Elhaj Kadri ya kara kusantuwa, takan tardo shi idan bai zo ba yakan bi ta baya ya ganta idan bata zo ba, harma su fice yawonsu idan ta fito makaranta Elhaj Abdallah mahaifin Elhaj Kadri ya nemawa Kadri auren yar abokinsa wanda suka shiga shagulgulan shirin biki nan da wata biyar Labari na tarda Marwa ta rikice ta shiga tashin hankali wanda ta kasa boyewa, da farko fushi take da shi mai tsanani daga baya suka shirya har suka shirye shedan ya kara himma aka kauce a lokacin da ba.a shirya ba Bayan wata biyu rashin lafiya ya tsannanta a wajen Marwa, kulun yan cututuka, wata safiya yar uwarta ta fesa turare da sanyin safiya amai ya ce bismillah Tun tana yi da karfinta har karfin nata ya kare ta galabaita, cike da tsoro mahaifiyarta ke kallonta mahaifinta ya rike yana maganar a je asibiti zazabi ne Luuuu mahaifiyarta ta je zata fadi yan uwanta suka rike, cike da tashin hankali ta saki kuka tana innalilahi wa.ina ilahi raj.une, shikenan son zuciya ya kaimu ga halaka, cike ne ai da Marwa, Marwa kin bata kuruciyarki, kin zubar da mutuncinki, kin kawo kanki cikin bakar rayuwa Wani kwalo mahaifinta yayi ta yi da ita har ana rikeshi, yar uwarta na gunzar kuka Sai da ya gama dukanta ya jawota a kasa har cikin gidan Elhaj Abdallah, Yana zuwa suna karyawa a falo ya hankadota Jiki na tsuma ya nunota da yatsa ya ce" tunda kika zabi rayuwar iskanci har kika dauki cikin yaron da ake shirin aurarwa sai ki zauna idan kin haife ki bar masa abin ki nemo mijin zan aura maki, aman daga yau na haramta maki saka kafa cikin gidana idan kuwa kika sakan sai dai a kwashi gawarki Yana gama fada ya fice ya bar Marwa nan yashe Haka take rayuwa a takure cikin gidan su Elhaj Kadri, du yanda yake so dan gannin ta samu sa.ida abin ya gagara, mahaifiyarsa ta kasa ta tsare ko abin ci ne sai dai a boye ya miko mata, har ta kai watan haihuwa Elhaj Kadri zuwa wannan lokacin ya gama yanke hukuncin yanda zai yi a washe gari, sai dai a cikin dare nakuda ta kama ta , Sun yi tunanin zata haife a nan abin ya ci tura har ta fara fita a hayacinta Cikin tashin hankali Elhaj Kadri ya nufeta ya kinkimeta Mahaifinsa cikin bacin rai ya nunosa da yatsa ya ce" kar ka kuskura, idan har ka yarda ka fita da yarinyar nan na yafe ka, Jikinsa a mace yake kokarin basu hakuri da nuna masa halin da take ciki aman fir suka kiya Har kasa ya duka yana basu hakuri ya fice a motarsa da takardunsa na banki ya nufi asibiti da Marwa Cikin ikon Allah aka bata taimakon gagawa ta haifi sambalelen danta namiji, a nan Mahaifinsa yayi masa kiran sallah yayi masa huduba da sunnan *ALAIDINE* Ci gaban labarin a next page i.a [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *06* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Haka Wujdane ta jure ta kawar da kanta ga daliban nan ta dauki rubuce rubucen nan har aka dana karaurawar fitowa a karya Wujdane bata yi gigin fita tarin daliban nan ba domin tayi imanin idan ta fitan sai wani ya nemi shiga sabgarta ita kuwa ba zata lamunta ba, Cikinta sai kugi yake yi mata wani kuuuuuuuuu na yunwa domin ko abincin dare jiya bata ci ba, a hankali ta dora hannunta saman rigarta tana dan kokarin danar da yunwar Tana nan zaune sai ga Aisha da wata kawarta fauziya, sun shigo da leda a hannunta Zama tayi tana fadin " Aunty kinga na sayo maki abin kari ko zai yi maki?? Tana fada ne tana bude abincin a ledar tana nuna mata Kasa kasa take hararar Fauziyar nan domin ta wani raja.a gaba daya a kallonta, Kai ta juya gefe ta ja dan tsaki bata taba ledar ba bata ce komai ba Aisha ta dan saki murmushi tana kallon Fauziya ta ce" am ni freind leko mana ajin su ely ki gani idan ta gama rubuta exercise ki karbo mana plz Juyawa Fauziya tayi tana dan mamakin yayar kawarta Tana fita Wujdane ta juyo ta bude ledar ta dan fara ci da bismillah Haka Aishar ma ta saka hannunta fankasu ne da yaji suna ci ba wani hira suke ba sannan Wujdane tana dan kakawar da kanta A hankali Wujdane ta ce" kinsan jiyan nan yara suka yi ta yi min ihun aljannah, shin halitata ta muzanta har haka ne ? Mai yasa mutan3 basa kallon kansu sai dai su damu da tawa halitar har su zo sunai min tsokana? Wannan abin na damun rayuwana Ta karashe tana sada idannuwanta alamar she is sad Aisha cike da tausayi da kaunar yayar tata, ta kale ta, ta ce" aunty, ba halitarki ce ta muzanta ba, aa , Allah ne ya yi ki cikin bayi masu baiwa, aunty karki manta abinda aba ke fada mana idan yana sufanta mana kamanin ma.aiki, idannuwansa tamkar na mage, Aunty baki da wata halita karkataciya, haka Allah ya yo ki wanda du mai kallonki sai ya razana da tsarin halitarki, ki kawar da kanki bi.izinnillah komai zai huce Kallonta Wujdane take, a duniya Aisha ta zamanto mutun ta uku a masu tausaya mata sannan kaunar da take nuna mata sosai da sosai ce, Allah ne ya hada ko a cikin yan uwanta ta tabata aisha mai rungumarta ce, Bata kuma furta wani abin ba har aka dawo inda Aisha ta fice dan zuwa ajinsu Sosai Inna ta yi mamakin Wujdane dinta ce aka je makaranta aka dawo ba.a yi fada ba, Yanzu haka fura take kirbawa a turminsu, furar da idan malan ya dan yi samu yakan sayo inna kuwa tayi abinta a gida ba ta mashin ba, Kirbawa take tun karfinta hannunta du yayi jajajir , Aisha na gefe tana gyara shinkafar hausa mai cike da tsakuwa innar kuwa na bakin murhu tana iza wuta Wulgawar Mairo ta gani ta kofar gidansu wAda ta wulgar ya fi a kirga hakan ya saka dam ta silale ta fice innar bata ma ankara da ita ba Tana fitowa Mairo na tsaye tayi saurin riko hannunta tana fadin" Kan uba, wai Danine da gaske kenan ana ta zunden kin koma makaranta na karyata kinga kuwa, aman yanzu in ba rigimarki ba mai zaki yi da makarantar nan? Yayan talaka dai ba wani yanci ne da su ba a nahiyar nan , sai ka gama karatun ka dawo aikin hannu dan baka da dogon hannu, shi ne zaki wani koma yau anguwa an wuni ana camama banda ke??? Wujdane ta yatsina fuska suna tafe ne Mairo ke zubar nan, sai ga balki fitsara yar gidan indo Balki daman na hakon Wujdane tun wani lokaci da ake bata labarin irin masifar Wujdane tayi tsanlan albarka ta yi alkawarin ita kuwa sai ta cima Wujdane din, Tsayuwa tayi kikam a gabansu bakin baban titin da za.a tsalaka age kantin yan gayu dan su sayo mayafin da ake yayi a layin nasu naira dari hudu wada Mairo ta samo dari shida zasu je su gwada ko za.a siyar masu ita da Wujdane Da sauri Mairo ta ja ta tsaya jikinta ya soma bari, hangowar su Yinusa saurayinta sun aza zaman yama da suke yi da abokanansa, sannan ta san halin Balki sarai ba dai masifa ba domin Balki idan ta rike ka ta gala maka cizo har cire fata take dan balaki kuma idan ta makaleka sai an yi da gaske za.a raba ku Cikin fuskar tsoro Mairo ta ce" kinga dai Balki bamu tana higa sabgarki ba, dan haka ki yi hakuri dan Allah kar ki higa tamu har a zo anai mana taro Balki ta zaro ido ta ce" ke yar kundun uba, ke har kin isa na tare ki ki yi min iyaka da ke? Yau zan gwadawa yan matan layinku karyar rashin kunya ne da ku daga ke har zabayar nan Girgiza kai Wujdane ta yi ta juya dan bin bayan Mairo dake janta dan karta biyewa Balkin Balki na gannin hakan ta kamo hijabin Wujdane daga baya ta janyota cike da izgili da neman fitina sai kara fifitar da idannu take tana kada girji ita ga mai balaki Wani irin juyowa Wujdane ta yi da hannunta bata sauke yataunta ko ina ba sai fuskar Balki, ta kara wanka mata wani marin tamkar yarta, Ai kuwa suka kacame kowa na dukan dan uwansa nan a cuci mazan Balki ya fado kasa tarin tsumakwarai harda pant baki kurin Ai kuwa yara suka dau ihu da soya Balki na gannin hakannan ta shiga kokarin sai ta cirewa Wujdane hijab dinta wada a ranar bata da dan kwali a ciki hijab din ne kawai ta dora saman kitsonta na doka da inna ta yi mata Jama.a ne ke kokarin sai sun raba fadan nan wanda abin ya gagara har sun kai kasa sosai Wujdane ta shake wuyan Balki ta hanata katabus Ihu ake karta kasheta , sai manya suka fara tsoron saka hannunsu aje tayi kisan kai , A bakin titin akoy polisawa da suke aiki a ranar, su suka zo suka runtuma jama.a da wanda ya ji da wanda bai ji ba du suka kame wanda harda su Wujdane a bayan mota kuri suka nufi police station Zaune yake da wayar office din ya sada kansa kasa ya dafe habarsa, amsa waya yake cike da tashin hankali, Anwar kenan, saurayi ne matashi, baban ma.aikacin polisai mai ji da kansa da jini a jika, magana yake da mahaifiyarsa tana fada masa jikin Sultan ya tashi, gashinan dai da kyar an samu malan ya yi masa adu.ar nan ya samu baci aman zuciyarsa bata sauka ba Ajiyar zuciya Anwar ya sauke ya ce" Mom, wannan zuciya ta yaya na rasa kanta, ace mutun a gidan duniya ko gardama ya yi da wani shikenan sai ya sansandare dan idan mutumen ba na ya daka bane sai abin ya zama matsala idan kuwa na ya daka ne sai yayi kamar ya kashe mutun? Yanzu ita Mardiyar ta tafin ne?? Ba.a dai jin abinda mahaifiyar tasa ta fada , sai shi ne ya sauke ajiyar zuciya ya ce" sunar ma.aiki ne, wanda du musulmi zai so ace ya zama cikenken mutun, Mom yayana uku a duniya, yaya ya nace kan idan dai ba macen da zata shirya da boy ba zai taba zama da mace ba? Mom rayuwar nan sai a hankali daman yanzu duniya da ta zama haka da wuya ka samu macen da zata soka domin Allah har ta so yaronka, auri sakin yaya ya yi yawa da har ina murnar wannan an jima da ita har an kai wata uku ashe sakin na nan zuwa? Idan ba yaya ba dole ya kawar da kansa da wasu abubuwan ya ci gaba da kulawa da dukiyarsa, kin sani ne Mom ni aikina na nan ma ya iya da shi bale har na iya da tarin dumbin dukiyar nan ta yaya? Aman ba komai zuwa yama zan shigo dan Allah ki yi masa abinci da kanki Mom zai ci sannan masu aikin nan du su koma bangarensu kar ya farka ya sauke a kansu Yana tsaka da maganar ta computersa yake kallon yanda ake tuntunkuda mutane a cel, harda mata da yara, kansa ya dafe yana fadin" Ya Allah, mai kuma suka yi wa..innan ? Ni da na aike su su duban hanya shine zasu fara kame? Mikewa ya yi sai a sannan na ga tsayinsa, dogon namiji ne zambal, bashi da rama ko kusa, kakarfa ne mai aji, idan ba fada maka yayi ba ba zaka taba kawowa ranka cewar yana da aure harda yara uku, aikin police na cikin tsarin mafarkin rayuwarsa ne wanda a dole ya takurawa yayansa har ya amince masa ya je ya fito police din yake bautawa kasarsa, Ba zai fi shekara 29 ba, domin mahaifinsu *Elhaj Kadri ganinka sa.a* baya barin yaro ya kai wani lokacin kafin ya yi masa aure, yakan cewa abinda ake muradi za.a samu, a kasan zuciyarsa yana yin hakan dan gujewa yayansa fadawa halaka wato tarihi ya maimaita kansa a tsautsayin da ya fada masu shi da matarsa uwar gidansa kafin su yi aure, Du duniya yayansa uku Sultan wanda ainayin sunnansa shine *ALAIDINE* suka lakaba mai sultan ba dan komai ba sai dan yannayin rayuwarsa ta sadaukai ce ta sarakai, sai Anwar sai kanninsu Jamail, Haka ya fito da sauri ya nufo wajensu wanda polisawan na ganninsa du suka kame suna sara masa Aikin da kuka je yi kennan? Wa.innan fa? Su waye su??? Cikin zazakar muryarsa mai sanyi yake jero tambayoyin nan aman fuskarsa a hade take tamau Baban cikinsu ne ya mike ya shiga fada masa ga yanda abin ya kasance , Juyowa yayi yana kallon mutanen da aka ce suna fada harda dambe, wai mata Balki sai tsuru tsuru take da idannu Wujdane kuwa ta sada kanta kasa ba,zaka ce ga kamaninta ba domin hijabinta ua rufe har kafafuwanta Cike da takaici ya dafe kansa a ransa yana fadin kamar ta Allah da shigar nan take fada a titi, sannan ya tambayi kansa anya wannan aikin ba ajalinsa ya sako kansa a ciki ba?????? Cike da jin haushi ya bada umarnin a saki wa.inda fadan bai shafe su ba a bar su Wujdane kadai har iyayensu su zo, Yana gama fada ya juya ya dauko wayarda da ky din motarsa rang rover ya fice dan zuwa gidan dan uwansa ya ga ya jikinsa To fah Wujdane a cel🤦🏻‍♀ [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *08* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Konci tashi ikon Allah, yau har ya kama sati na hudu da Wujdane ta dage kan hanyar makaranta, ba wai ta daina fita bane aa kunyar Malan ke sakawa ko kadan ta kasa daina zuwa makarantar, sannan kwazo irin na Wujdane ko nace baiwa ba abinda bata fahimta, sosai take gane karatun malansu aman a yi tambayar duniyar nan ba zata daga hannunta ba, haka kuma har yau bata da kawa a ajin bata shiga sabgar kowa Yau Malan yusuf ya tashi da rashin mutuncin, tunda ya shigo yake kora koda takalminka ba na makarantar bane zai yi waje da kai ne sannan ya baka punishment, Dalubai du sun nutsu, kowa ya kama kansa ba mai garajen wani yunkurin bale har kilu ta jawo masa bam Cike da jin haushin Wujdane yanda take yi masa wani kalo da ya fasara a zuciyarsa kallon raini ne ya rubuta wani excercise na math a blackboard, Kafin ya tayar da wanda zai je ya yi masa excercise din sai da ya tambaya wa zai je kamar yanda ya tsamata va wanda ya daga hannu domin a gaskiya akoy yar wahala Kanta na kallon kasa kamar yanda ta saba, ba wanda zai ji muryarta sai ma ya rantse shi bai taba ji ba ba shi kadai ba du jama.ar ajin, Ya jima yana kallon wajen wanda ya saka du daliban shan jinnin jikinsu domin da gani sun san zai zabo mutun ne ya tura Kamar daga sama ta ji yana fadin" *WUJDANE MALAN LAMINU* A firgice ta dago da kanta , ta sauke idannuwanta a fuskarsa Cikin daure fuska ya ce" ki taso ki yi mana excercise din nan sannan kina yi kina kwatanta mana yanda aka yi kika yi hakan, idan ba haka ba zaki fuskanci tsatsauran hukunci na hutun sati guda A cikin ranta take ayana" ka koreni ma idan kana so, sai wani gefe na zuciyarta ya tunatar da ita Malan fa ba zai ji dadi ba Cike da jin haushi ta mike ta nufo shi, ta karba ta dan dakata ta karanta , Cike da kwarewa ta dora equation din ta shiga gabatar masu da harshen turanci, Ba kalacin daliban dake yi mata kallon may be kwakwaluwar ba komai sai majina ba, harta malan Yusuf da ya kawo karan tsana ya dora mata a tunaninsa bata da kwakwaluwar zama a nan hanya ce aka yi mata kansa ya cika da mamaki, ta iya turanci a bakinta, to yaushe ta koya? Ni kaina na cika da mamakin yaushe ta koya? Larabci dai ba mamaki idan tana yinsa tamkar balaraba har wani khal khal take da harshe sai ga abin mamaki wujdane da turanci sosai a bakinta Har ta gama ta dawo kujerarta da ido suka rakata har ta zauna, ba mai bakin magana du ta kashe shi Malan Yusuf ya shiga tafi a hankali, wanda wani irin kunyarta ya rufe shi, a fili ya shiga yi masu kwatance da ita a can kasan zuciyarsa ya shiga yaba mata , yaba kwazonta, nutsuwarta, tsarinta Haka ya gama ya fice aka bi shi da kayansa har wajen motarsa yar madaidaiciya ya shige ya tafi abinsa Zaune take a wajen pampo, tana kallon yanda wasu yan mata ke kalkalce kalkalcen kafafuwansu dan tafiya gida, sai dan waigawa take wajen ajin su Aisha aman har zuwa lokacin ba.a sake su ba Tsaki ta ja ya fi a kirga ta dan waiga ta waigo Ke wai bakya cire nikaf ne? Ya akayi kulun da nikaf?? Wata yar budurwa kyakyawa ke fadin hakan tana kokarin zama gefen Wujdane Dago da kanta ta yi ta kali gefen budurwa, dan tura bakinta ta yi ta matsa kadan tana kawar da kanta gefe Murmushi budurwar ta yi ta ce" ni kuwa ina son na yi kawance da ke, domin na yaba da nutsuwarki plz ki yi hakuri idan na takura maki Kuma juyowa ta yi tana kallonta, still dai bata yi magana ba, Ta yi murmushi ta ce"ni sunana Rumaisa, ina gefen pharmacy ne, na jima ina ganinki kin shiga ajin can, kina san zama nurse ne??? Kai wujdane ta dan girgiza ta kuma kallon kofar ajin su Aisha, bata cewa Rumaisa ufan ba Rumaisa ta buda baki dan ta kuma yin magana Wujdane ta mike ta kakabe hijab dinta ta juya ta nufi kofa dan tafiyarta gida domin yau bama zata jirayi Aishar ba, Tana tafe tana mitar ta rasa jarabar wasu yan matan Tana zuwa kofar gidansu ta yi kicibus da Lukman, ya sha yadinsa fari kal ya caje gashin kansa ya saka agogonsa baki da bakin takalminsa, yana saman babur dinsa yana dan kada kafa har zuwa lokacin ya rasa yaron da zai taimaka masa ya shiga yayi masa magana da Wujdane Kokarin rabawa ta gefensa take ta shige gida ya yi tsalen albarka ya tsaya a gabanta yana zuba mata murmushi A fili ya ce" Alhamdulilah, yau dai Allah ya yarje min ganinki, Bata cire nikaf din ba, kanta na kallon gefe tana fadin wannan akoy natace mai kuma ya zo yi gidan nan Wannan zuwana na biyar ne yan mata, na samu ribar jin sunnanki ma abin ya gagara na rasa ke ce *AISHAR KO WUJDANE MAMA?* dago da kanta ta yi tana mamakin Wujdane mama, wani dan murmushi ya subuce mata, wato yaran anguwar nan nema suke su lakaba mata sunnan da zai bi ta ko??? Dan Allah ki saurareni, shi mutun daraja gare shi, Dan Allah na yarda da ja min aji ina neman alfarmar na san sunnan kawai a hankali za.a amince da soyayata Mamaki ne ya cika mata zuciya, a ranar da ya ganta ma bai nuna tsoro ba, shi ne harda maganar soyaya? Haka kawai ta ji ya birge ta ko ba komai ya nuna mata kauna a fili Dan gefensa ta bi ta ratsa shi ya juyo yana kallonta ya harde hannayensa fuskarsa kalar tausayi Murmushi ta kuma saki wanda baya gani shi domin da nikaf, kasa kasa ta ce" *WUJDANE MAMA* Wuf ta shige cikin gidan ita kadai sai murmushi take dokawa ta cire nikaf din Inna dake bakin murhu tana iza ice ta dago cike da mamaki tana kallonta, murmushi na matukar kawata fuskar yarta, itama sai ji ta yi nata murmushin na fitowa domin fuskar mahaifinta sak ta fito a fuskar yar tata Karasowa ta yi ta duka har kasa tana gaishe da innar Cike da kulawa inna ta ce" ina Maman kuwa? ( Aisha ) Bayanta ta juya ta juyo ta ce" a can na barota ni gajiya na yi inna Inna ta ci gaba da kallonta , sam Wujdane bata iya karya ba idan dai zaka tambayeta toh zata fada ne kai tsaye, ta yi imanin wannan murmushin kuwa da dalilinsa Kallonta ta yi ta ce" mai ya saka ki nishadi haka,???? Wujdane ta dago da kanta cike da wani abu da take ji kadan kadan na taso mata , ta buda baki zata yi magana kenan sai ga muryar Jamail yna kwala salama Kanta ta dafe irin na takurar nan ta mike ta yi dakinsu inda inna ke amsawa jamail salamarsa cike da murnar ganninsa, domin Jamail yayi tuwo ya yi tsaki har tsakar gida yake shigowa shi kawai gidansu ne Tabarma inna ke shinfida masa tana amsa gaisuwarsa, Dakin su wujdane ta juya ta kwala mata kira tana fadin ki fito ki ba dan uwanki ruwa mana Wujdane! [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *10* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Haka ya daukosu ya nufi gidansa da ya gina boyaye wanda ko mahaifiyarsa bata san da shi ba, ya kai su Marwa sannan ya nemo wata tsohuwa ya hada su Komawa ya yi wa mahaifansa da mahaifan Marwar, aman cikin ikon Allah mahaifansa ko kalo bai ishe su ba, daga karshe mahaifinsa yayi rantsuwar idan ya kuma gannin kafarsa a gidansa toh lale zai tsine masa tunda ya nuna mace ta fi su, cike da tashin hankali ya dauki carte sin banki da mahifinsa ya bara masa wada keda kudadensa a ciki na kasewa ya karbe duka sauran abinda ya bashi kan sharadin in dai ba watsar da Marwa zai yi ba ya je ya bara mata shi Cike da tashin hankali ya nufi gidan su Marwar, a nan ma dai zancen daya ne, ta yar da dan ta dawo gidan ida bata yarda ba ya yafe ta, mahaifiyarta ce ta biyo bayansa a boye ta bashi yan zannuwa tana kuka ta fada masa dan Allah ya kula da Marwa, karta yada kautar da Allah ya yi mata, ba laifinsa bane, kadara ce sai a karbe ta, insha Allah idan mahaifinta ya huce zata dawo Haka ya dawo gidan ya zauna da Marwa ya sanar mata komai, Ta jima tana kuka, ta jima tana astagafari tana rokan Allah ya yafe mata, ta rungumi yaronta inda Elhaj kadri a dakin kofa yake zaune idan ya shiga gidan sai dai dan ya ga lafiyarsu ne ya yiwa yaronsa wasa sannan ya fice, Haka har ta yaye Alaidine cikin ikon Allah a masalaci ya nemi alfarma wajen liman ya fada masa duka yanda ake ciki Liman din da kansa ya je wajen iyayensu dan gannin ko za.a sasanta, aman suna nan kan bakansu, sai dai shima mahaifiyarsa ta sauko aman tana mugun tsoron mijin nata Du yada liman ya so ya kwatantawa iyayensu a sasanta basu saurare shi ba, kowane ya hau dokin zuciya duda shima mahaifin Marwar ya dan sauko aman gannin mahaifin Kadri bai sauko ba ya saka shima ya botsare Liman ya wakilce su bayan salar juma.a aka daura masu aure, inda suka ci gaba da rainon Yarensu mai wani irn hali tun yana yaro, Alaidine baya son hayaniya, ko dan ya rayu daga shi sai mahaifiyarsa da mahaifinsa ne , Alaidine bashi da tankiya, gumgum da shi baya shiga sabgar kowa ko da wasa Mahaifinsa ya ci gaba da juya dukiyarsa wanda Allah ya saka mata albarka ta yi ta habaka, Makarantar biya yake , yana da shekara takwas mahaifiyarsa ta sake haihuwa aka sakawa yaron sunna Anwar Alaidine girmansa abin al.ajabi ne, bai jawowa iyayensa magana ko sau daya, kwazo gare shi a makaranta wanda hankalinsa ya fi karkata a kasuwanci, Yana da shekara 18 aka yi masa gori a anguwa, wata mata haka kawai ya zo wucewa ta ce" wannan ai shine shegen gidan cen, sai dagin kai tamkar wani tsarkakake Wannan magana ta saka su a tashin hankali domin a ranar ya san ko shi wanene , ya yi kuka har ya gode Allah, inda mahaifinsa ya dauke su da mahaifiyarsa da dan kanninsa msi shekara goma da tsohon cikinta suka koma sabon gidansa nesa da anguwar da yan uwansu da kowa suke zaune suna rayuwarsu Alaidine ya saka wannan magana a ransa, hakan ya saka yake kauracewa mutanne domin yanai masu kallon wa.inda basu da uzuri shima sai ya daina yi masu uzuri Tun yana da shekara goma sha tara ya nemi jari wajen mahaifinsa Cike da farin ciki Elhaj Kadri ya bashi ya ja sana.a, wada suke mamakin husa.a ta yanda yake kirkirar abubuwa kala kala Nan da nan sunnansa ya fito a yaro da kudi, farin jinninsa ya daukaka, lungu da sako maganarsa ce ake ana radin yaro da kudi yaro da kudi Gashi ya dauko kyau da hutu, nan da nan ya rikide ya kara zama wani hamshaki mai aji Sosai mata ke wawarsa, abinda ke dagawa mahaifiyarsa hankali kennan, domin har gida wasun ke zuwa nemansa Du da irin taurin halin Alaidine akiy sadaka, zaka, yana taimakawa marayu, ya gina masalaci tankameme a unguwar da ya gina gidansa wanda yan anguwar kansu ke kiran gidan da ko a turai, domin babu ne kawai babu Wani lokaci mahaifiyarsa ta saka shi gaba tana ta mita harda kuka kan ya fitar da mace, shi ko budurwar bashi da ita, mahaifinsa dake saukowa daga sama yana sauraron su, shi kansa ya lura da yannayin halitar Alaidine, ya dace ace da mace a kusan sa zuwa wannan lokacin aman shi sam baya ra.ayin yin aure bisa dalilinsa nasa na kansa, Cike da fushi ya dago da kansa yana kallon mamansa ya ce" Mom, kina tsoron tarihi ya maimaita kansa a kaina ne? Ki yi hakuri da yardar Allah hakan ba zata faru ba Cikin tsananin bacin rai da tir da halayarsa na fadin gaskiya kwadokwado baya shayi koma wanene ta wanka masa mari ta kara masa, muryarta na rawa ta nuna shi da yatsa ta ce" dan ka ga ana gudun zuciyarka dan kar ranka ya bace ka yi rashin lafiya ba wai tsoronka bane ya saka ko ka fi karfin mu bane, haihuwarka aka yi Alaidine kuma dole ka yi biyaya, idan har baka dauki kadarar rayuwarka ba kai ta gano aman baka isa ka jefe mu da wata kalma ba bayan kadara ce *Bamu da zabi* dole muka dauka, kaima haka zaka dauka Tana gama fada ta haura sama da gudu mijinta ya tare ta yayi ta rarashinta Bayan wannan da kwanaki mahaifinsa ya shaida masa an bashi auren yar gidan amininsa wanda ya san komai kuma ya yi amana da hada auren Bayan sati biyu aka daura masa aure da khadija Shi kansa bai san haka yake da muradin mace ba sai a kan Khadija, khadija ta kawo masa mutuncinta sannan tana gannin girmansa Wai dai wani mugun abin , mahaifiyarta ta ji labarin ko wanene alaidine, nan fa ta kama hure mata kune har Khadija ta fara fito da halayen da bai santa da su ba Daman ba aikin fari take ba bale na baki, domin da ma.aikata birjik a gidan masu kula da komai, sai ya kasance shi Khadija ta fara kauracewa a shinfida, Da ta lura da ciki ya shigeta sai tashin hankali na kulun kala daban, tayi ta kuka idan ya tambayi ba.asi sai ta furta" ni dai an cuce ni an lalata min rayuwa Abu tamkar wasa cikinta ya girma ta haife ta samu yaro namiji aka saka masa" *Huzaifa* suke kiransa da boy Tunda ta haihu sai sabon kulafuci, ita ce wannan ita ce wancen, Alaidine bai taba kai kashenta ko kararta ba, kudi kuwa tamkar wuta haka take kashe su, shi kansa baya kashe kudin da take kashewa, boy kuwa tamkar ba ita ce ta haife shi ba, ta banzatar da shi bata damu da shi ba Wata safiyar Asabar, Mahaifinta ya zo nemansa har gida dan ya kasa samunsa a waya kan harkar business, ya tarar da Khadija sai sababi take Alaidine kuwa yana sama yana hangenta ya harde hannu a kirjinsa yana tir da halayenta a kasan zuciyarsa harma yana mamakin kansa da yake iya kawar da kai yanai mata uzuri Cike da masifa ta wsnkawa Huzaifa mari , wanda ya ji tamkar ta watsa masa wuta a fuska, cikin azama yake saukowa inda mahaifinta ya labe yana kallon ikon Allah Yana saukowa ya dauki yaronsa idannuwansa har sun canza launi, ya nunota da yatsa ya ce" rashin mituncin naki har ya kai ki tsalake banzatar da aurenki da kike ki dawo dukan min yaro? Why Khadija? Mai yasa bakya gannin irin yanda nake kokarin gannin na fita a hakin ki na kula da amanar mahaifina? Idan bakya iya rayuwa ne da ni ai gwara ki fada da ki cutar da yarona, idan ni ne ki je ki yi bani da damuwa aman harda dan da kika haifa khadija? Cike da bacin rai ta ce" eh man, dan me ba zan dake shi ba? Shi dan *Shege* ? Tamkar an dauke wuta haka abin nan ya dirar masa, wanda ya yi sanadiyar kara nutsawarsa a rayuwar duhu, Hannu ya daga ya wanka mata lafiyayen marin da ta kai kasa bakinta ya fashe take gefen kuncinta ya sundume Hannunsa na rawa ya nunata ya ce" *na sake ki saki biyu* idan kin samu miji zaki iya aure domin baki da idata A lokacin mahaifinta ya bayana a fallon yanda ya mayar da ita tamkar ganga, yayi alkawari ba dai a gidansa ba Cike da tashin hankali ta nufi gidan su Alaidine din ta fadawa mahaifiyarsa da kanta komai, Duda ta ji haushi hakan, aman sai ta ga idan ta kiri khadija ta yi butulci , domin itama da aka kore ta mijinta ya rungumeta, hakan ya saka ta bata daki take zaune tamkar gidansu A haka aka yiwa Anwar aure da matarsa Bahija, yarinya mai daraja mai daraja mutane, Tun daga wannan lokacin sai Alaidine ya dawo sabo, yakan zubawa mace kudi domin ya gama fasara su a kudinsa suke so, ya aura idan kun jima ku yi wata biyu ya salame ki domin yakan gwada mace cikin hikima, idan bata tangarde wajen rikon xilon dansa ba, toh zata nemi fitina wajen gididige sannin waye shi hakan yake sakawa ya bale igiyar ya dauki wata Yaro da shi auri saki ya mayar da shi tamkar a jininsa, abin nan na ciwa mahaifansa tuwo a kwarya, dan gujewa ya afka zina yake saka mahaifinsa nemamasa auren da anje an kwan biyu a gundule shi, domin zuciyarsa ta fi karfinsa ba zai yiwa wara banza uzuri ba Wannan kennan, Ci gaban labari Haka ya fito da katon jirginsa na wasa ya mikawa Jamail ya ce" plz ka je da shi kawai, ya kwana wajenka aman karka yarda ka je da shi gida ( dan kar Khadija ta hadu da shi ) Daukansa ya yi yana ta yi masa dabara inda boy ya karkata hankalinsa gannin za.a fita yawo Jamail na fita bai zame ko.ina ba sai gidan inna, dan ya je ya ci dambun da take domin ba karamin tafiya da imaninsa ya yi ba Yana shigowa ya tarar da mutuniyar tasa tana yanyanka albasa, Aisha kuwa tana daka yaji, Bayan ya gaisar da innar ya samu waje ya zauna Boy na lilike masa dan rashin sabo Inna ta fito da kuli a leda baka tana fadin" yau ga miji yau ga miji, tana kokarin yiwa boy wasa aman ya lafe ya ki yarda ta dauke shi haka ma Aisha Wannan ledar ta mikawa Jamail ta ce" yarona haka zamu fara da kai? Kul ka kiyayi fara hakan da ni sai na ji ba dadi Cike da gannin girman tsohuwar yake kallonta, ya yi murmushi ya ce" inna, yaya ne ya fitar sadakar da yake bayarwa, shine na karbo maki naki, inna kennan idan Abdul fatah ya kawo ba zaki karba ba??? Wata kunya ce ta kamata, haka yake mata wannan wayon sai ya nuna kenan dan shi ne ya yi mata abu ba zata karba ba, Mikewa ta yi dan zuba dambun tana adu.ar allah ya sa ya gama da duniya lafiya da shi da mahaifansa Ihu boy ya saka wanda ya saka Wujdane saki wukar da take dan yanyanka albasa tana kallonsa Fitsari yake ji sai ihu yake kuma ba zasu taba shi ba Cike da jin haushi Jamail ya ce" zan fa wanwanka maka mari Boy meye hakan? Ka nutsu a cire maka wandon ka yi mana Aa shi ya dage sai ihu yake shi jacuzzi jacuzzi, Tsaki Wujdane ta ja ta mike ta nufo shi, cikin yaren turanci ta miko masa hannu tana fadin" zo nan boy dina na kai ka ka yi fitsarin na baka chocolate Ai yana jin hakan ya dare gannunta yana sauke ajiyar zuciya ta yi bayi da shi Gaba dayansu da ido suka bita na mamaki, duda sun san dan ya daina ihun nan ne ya daina damunta da ihu ya saka ta lalaba shi, domin itama ba wani onuwa daya take sha da yara ba, basa shiri da yara hakan ya matukar basu mamaki, Jamail ya juyo wajen inna ya ce"":: ........☹ [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *11* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Jamail ya juyo wajen inna da mamaki fal a shinfide a fuskarsa ya ce" inna, daman kanwata tana shiri da yara? Inna ta yi dariya ta ce" kanwar taka a abin mamakinta baya karewa Suna tsaka da maganar inna ta zuba masa dambun a plat dan madaidaici ta fito da Boy ta gyara masa wandonsa ta dawo ta zauna tana kallon kofa wani abu na fizgarta kan ta ficewarta Wani yaro ne ya yi salama da naira goma a hannunsa, yana dan rakubewa ya ce" inna wai ana salama da MaMa, Inna ta dago da kanta tana kallon yaron ta ce" wa ke salama da ita? Yama fa ya yi bana son fitar nan Yaron yana dan bari da hannayensa ya ce" wai ya ce ace lukman ne Firgigit ta dago da kanta daga kallon kasan da take a tare da Jamail, shima bai shirya ba ya dago cike da mamaki da karyata kunnayensa, Lukman? Waye lukman? Daman Wujdane na zance da saurayi??? Tunaninsa ne ya katse daidai lokacin da Inna ke fadin" to ai tana jin ka Harara ta watsa masa ta ce" ka je ka ce ta yi baci Tun kafin ta rufe bakinta yaron ya juya a guje yana maimaita maganar da zai fadi din dan kar ya manta Tsam Jamail ya tsame hannunsa daga cikin abincin ya mike ya darwaye ya yi hanyar kofa Da harara Wujdane ta bi shi ta ja tsaki ita kadai tana fadin natace Yana fita ya tarar da Lukman na faman buga babur dinsa Salama ya yi masa ya mika masa hannu suka yi musabaha Lukman kallon Jamail yake, a yannayin girman jikinsa ba zaja bashi shekara 20 ba sai dai sama, ga cika ido Murmushi Lukman ya saki ya juya a hankali a can kasan ransa yana ayana du da soyaya ba ruwanta da kyau mulki ko arziki ba, zab gwada nawa sa.ar ( toh fa ) Zaune yake cikin falonsa ya dafe kumatunsa da hannu bibiyu yana sauraron mahaifiyarsa hajiya Marwa, cike da hikima ta ci gaba" Haba Alaidine, ka ringa sasautawa zuciyarka, yanzu tsakani da Allah mahaifiyar boy na zaune ita ta ki ta sake suren wani, kai kuwa ka yi rantsuwar ka gama zaman aure da ita, du bama wannan yanzu dan tana gidan shikennan ba za kana leko mu ba? Ni yaya kake so nayi ne? Cike da kaunar mahaifiyarsa wace bata taba nuna kyamarsa ba ya ce" Mom, idan ta yi aure ta bar gidan zan koma zuwa, mom To kai ya maganar auren naka ne? Ta katse masa hanzari, ta ci gaba da fadin" ko na zaba maka ne??? Dago da kansa ya yi wannan karin, yana kallonta ya ce" Mom aa, bana so ki zaba min na dawo na kuma saka ki kunya, zan yi auren kwananan insha Allah Kallonsa take tana jin ciwon irin rayuwar nan nasa, arziki dai na gidan duniya Allah ya malaka masa, wanda yana cikin mutanen da ake maganarsu a kasar, aman ka kasa zama cikeken mutun ta fannin ajiye iyali???? Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga kiran layin mijinta dan jin a goben zai taso kuwa daga abujar wajen meeting? Malan na shigowa d fara.a fiye da da cikin gidan, Bayan sun gagaishe shi inna ta dauko kudin nan da ko kirgawa bata yi ba ta ajiye da niyar malan ya zo ta danka masa, Kafin ta yi masa bayani ya karkace ya ciro kudi a aljihunsa yana ta aikin murmushi ya miko mata Ido ta fitar waje bata karba ba ta ce" Malan wannan fa?? Fuskarsa wadace da murmushi ya ce" Masalacin da nake bayar da karatu, wato wanda yayan Jamail ya gina, a yau aka shigo aka nemi malaman dake bayar da karatu da masu kula aka bamu dubu ashirin ashirin, sannan a lokacin elhazen kamar hadin baki suka shiga bamu kyaututuka, kinga dai cikin ikon Allah yau a masalaci kinga abinda Allah ya bamu baki daya malaman na bada shawarar a hade kawai a raba domin akoy wa.inda yau basu samu halarta ba, su din ma ba masu karfin bane, sai aka bi shawarar nawa aka hade aka kasa kinga na tashi da wajen dubu arba.in da shida Kallonsa kawai take a can kadan zuciyarta cike da tausayin mijin nasu da kuma godiya ga Allah, ta san dai ko ba komai a yau ya kara samu domin ma.aiki, Murmushi ta yi ta mika masa na hannunta ta yi masa bayanin yanda suka yi da Jamail Adu.a kawai yake yiwa bayin Allahn nan yana ta godewa Qllah kafin ya sake kallonta cike da fara.a ya ce" kin ga sai na kai kudin makarantar Wujdane, dubu bakwai ne da dari hudu da Malan din ya lisafa abinda ya dace sai na cike, sannan ku samu ku yi sabin dinki ku sayi su mai su dan turare sannan a sayo abinci ko??? Cike da murmushi take kallonsa tana amsa masa, da insha Allah, sannan ta gyara zamanta a dukan abinda ya zana bai sako kansa ba, domin cikin ikon Allah samarin gidan suna iya kokarinsu wajen yi masa sutura da su kansu, danma karatu na dauke hankin Abdul Fatah, Mika masa gaba daya kudin ta yi, ta ce" malan du abinda Aka zana Allah ya idasa nufi, Tana gama fada ta mike fan gabatar masa da shinfidarsa Da ido ya bita, yana kara godewa Allah, matarsa, uwar yayansa, abin alfaharinsa, mai gane matsalarsa mai kula da fara.arsa, ita irin zumudin nan na ta ga kudi ma bata da shi, yana kara godewa Allah da du irin murdaden halayen Wujdane kudi baya gabanta, haka ya mike ya kara daura Alwallah ya shige dakinsa dan gabatar da salolinsa ya kuma kara godewa Allah da wannan budi da ya yi masa Da sasafe kamar kulun, Wujdane ta fito daga wanka ta yi turus dalilin inna da ta ganni a dakin nasu zaune, dukawa ta yi har kasa ta kuma gaishe ta da kwana, innar na amsawa Mikewa ta yi tana son saka kaya inna na binta da ido, Dan murmushi inna ta yi a can kasan ranta take fadin kunyar karya irin ta wujdane, ita ba za.a ga tsiraicinta ba, gannin ta kasa saka wandon ya saka innar juyar da kanta tana kallon kofa Aishama dariya take kasa kasa tana kokarin murza man kuli dake cikin wata yar farar roba a jikinta domin shine mansu idan man ya kare Yan dari biyar biyar biyu ne a hannun innar, ta juyo ta mikawa Aisha sannan ta mikawa wujdane Tsai suka yi suna kallonta, da alamun neman karin bayani Zama ta yi ta ce" a jiya cikin ikon Allah sosai Allah ya yi budi a gidan nan, shine yau mahaifinku du irin kiye masa da nayi kan ba za.a baku hakan ba ya tirje min kan ai samu aka yi, shi ya sa ya bada wannan kudin ya ce na baku ku adanna idan bukatar sayen wani abin ya taso maku sai ku saya, ko dan saboda makaranta ma Murmushi Aisha take ta saki, tana godewa Allah a fili ta ce" masha Allah, masha Allah, Allah mun gode maka, Allah ya kara budi , ya kara arziki mai anfanni Amsawa inna take ta juyo wajen Wujdane, ta ga ta ajiye dari biyar din a nan kusan innar sannan tana kokarin saka hijabinta, inna ta ga yanda kitsonta ya tsufa sosai haka, to aman dan me bata dauki kudin ba ko ta raina ne? Inna ta ce" toh ke sarauniya, ya zaki jefar min da kudin a nan ne? Ko kin raina ne? Juyowa Wujdane ta yi da sauri tana kallon inna wai ta raina, ta dan girgiza kanta bata ce komai ba Takaici ya cika inna , yau miskilancin na banza harda ita za.a yiwa, ai kuwa ta shiga fada inda take shiga ba ta nan take fita ba, Aisha du ranta ya bace gannin inna na yiwa yar uwarta fada da safiyar nan, ita kuwa ta sada kanta ta yi zuru tana sauraron fadan innar na rashin dalili a wajenta, bayan inna ta gama tana harararta ta dan dago, ta sanyaya muryarta ta dauko kudin ta mikawa innar ta ce" innata, ba wai rainawa na yi na, koda baba ya dage kan sai an bamu sai ki rike a wajen ki, cikin ikon Allah koda wata rana abinci ya dauke da ajiya ai za.a yi anfani da shi, mu ba kudin mota muke biya ba dan zuwa makaranta, ko a makaranta Aisha ke sayo min abincina, kenan inna na wajen Aishar ya ishe mu har ya yi yawa, insha Allah idan ta sayo manta na shafawa vaseline dari da hamsin sauran sai ta ajiye mana a wajenta tana sayo abincin a makaranta kinga sai ki huta da bamu kwana biyu ko?? Tana gama fadar haka ta sakawa inna kudin ta mike ta fice da ledarta ta mauludu da aka yi a anguwar aka raraba ita ce jakarsu ta makarantar ta saka litafinta da biro Da ido inna ta bisu bayan fitar su, shar ta ji dumin hawaye a gefen idannuwanta, a hankali ta goge ta daga hannayenta sama ta shiga karanto adu.o.i wa yayanta baki daya Malan kam yau fara.arsa ta ki ta yanke, bayan ya biya kudin makarantar Wujdane ya zarce masalaci dan akoy karatun safe da zai bayar, Bayan ya gama ya yiwa mutane salama ya fito , ya shiga doka sauri dan zuwa kasuwa domin a lokacin har karfe biyu na rana ya yi, Oda ya ji ana yi kamar da shi ake hakan ya saka ya dan waiga Anwar ne da wani saurayi a cewar malan shima mai cikar kamala a gefen Anwar din sai dai wannan tamkar ya fi shi girma da isa, bakin gilas a fuskarsa da waya yana dan dadanawa Malan barka da warhaka, za.a je gida ko na ga sai sauri ake, cewar Anwar yana gaisar da malan din cikin mutuntawa Malan ya amsa yana mai dan sakin fara.a , Alaidine ya dago da kansa, sai ya samu kansa da cire glass din idannuwansa, a hankali shima ya furta" barka da rana Malan, ka shigo mu saukeka man na ga ana rana Murmushi Malan ya saki ya ce" aa ba komai yaro, ai kasuwa ma zan je ba gida na yi ba Anwar ya matsawa malan kan ya shiga ko kasuwar ce su sauke shi domin suma can suka nufa, hakan ya saka malan shiga motar tasu da ya karewa kallo sannan ya bada nutsuwarsa wa bakin titi yana kallon yanda motar ke gudu aman tamkar bata motsawa dan irin motocin nan ne da idan ba wani baban gargada aka shiga ba ba zaka san an shiga ba Anwar ke dan jan Malan da zance inda Alaidine ya yi shiru yana mamakin surutun Anwar Ni Malan ina Yar rikici ne take??? Cewar Anwar Malan ya dago da kansa ya saki murmushi jin an ambaci Wujdane ya ce" ai fa ana nan, sun tafi makaranta da yar uwarta, Wujdane rigima ba, aman an dan kwana biyu ba.a yi ba mai yiyuwa adu.a ta ci karfinta Anwar ya yi ta dariya abinsa, Haka suka karaso suna dan labari da Anwar aman Alaidine yayi kif, tun gaisar da Malan din da ya yi bai kara komai ba Daidai babar kofar suka sauke Malan inda suka juya dan karasawa shagonsa na atamfofi Malan ya yi masu sayaya daidai gwargwado harda su macaroni ta zamani, da fulawa da shinkafa da su magi mai gishiri , sosai ya yi masu tsince tsince sannan ya karasa shagon masu sayar da kaya Nan ya sayawa inna atamfa da hijabi biyu, ya sayawa su Wujdane hijabai suma da atamfar kala biyu ,shine harda abaya yar dubu da dari biyun nan da yan takalma plate masu kyau da turare da mai na shafawa, rigi rigi almajiri ke binsa da kaya har ya zo fita ya ga yan abubuwan hannu, ya dakata ya sayowa Wujdane da Aisha sannan ya sayi sabulu sinki guda, Malan dai ya yi sayaya ya kashe kudi bai fi dubu shida a aljihunsa ba ya nemi adaidaita ya yi shata har gidansa Zaune suke Inna na tsefe mata dokar kanta da ta tsufa sosai har sai ta laluba take jin tufkar kitson tana yi tana mitar gaskiya Wujdane sai kin canza hali, ke daki yi tsaftar ko ina aman bakya so a taba maki kai?? Idannuwanta a rintse, jin taba kan nan nata take tamkar inna na yankan naman jikinta Malan ne ya shigo da ledoji Aisha ta tashi ta tarbo shi, ya koma dan dauko sauran kayan Yana daukowa Motar Jamail na tsayawa daga dan nesa da gidan kadan (Talauci ba zai hana yin walwala a cikin gida ba idan har an gina rayuwar gidan a kan tubali mai kyau) [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *13* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Mom dake sama ta lumshe idannuwanta ta shiga yiwa yaronta adu.ar shiriya bayan komai da ya faru a idannuwanta duda bata ji takamaiman mai ya bata amsa ba ta san dai ba maganar dadi bace, tana adu.ar Allah ya sa wannan auren ya kasance ya shiga ransa, ya sota tamkar ransa, sannan ya shinfida shakuwa a tsakaninsu, tana adu.ar ta samu sarakuwar da zata zamo tamkar yarta, matar Anwar akoy mutunci da mutunta su, damuwar nesa ga yara sai ya kasance weekend kawai suke samun yi Gaisuwarsa ta katse mata tunanin da take ta bada hankalinta kacokam kansa Wujdane, Wujdane, ki saurareni mana, haba Wujdane ya dace a ce na samu karbuwa a wajenki daidai wannan lokacin, ki tuna fa a kala na kwashe wata biyu na bin bayanki, haba Wujdane dan adam daraja gare shi, ki saurare ni Juyowa Wujdane ta yi, tana dan dubansa ta cikin nikab dinta, a can kasar zuciyarta tana aiyana" ya salam, yanzu Baba da ya fitar da maganar wani ta tsayar da miji wai ya yake so ta yi ne? Ko dai Lukman din nan kawai zata fadawa idan har yana son nata kawai ta aureshi ta huta da wannan rayuwar, Ki ban amsa mana Wujdane, cewar Lukman yana kalar tausayi Kanta ta dan dafe hango su Jamail sai a lokacin suka shigo kwanar shi da Aisha, ta juyo wajensa ta ce" ka ga dai azumi ne, ba.a sha ruwa ba ya zaka tare ni da azumina kanai min wasu maganganun soyaya? Na fada maka ni ban santa ba, ni ban iya ba, sannan ai ba ni na takuraka kan sai ka bi ni dole ba ko??? Tausasa muryarsa ya yi , ya ce" kwarai na san da azumi a bakin mu , aman maganar da nake miki na neman aure ne, kinga dai da dare ba samun ganninki zan yi ba, ki taimaka ki lamunce min na turo iyayena bayan sallah insha Allah da sannu zaki so ni Wujdane Ido ta dan zaro gabanta na faduwa, daidai su Aisha sun karaso inda Aisharma ke gaishe shi cikin mutuntawa, Inna ta aikesu Jamail ya dage sai ya yi rakiya, Dan jerawa ta yi da Aisha inda Lukman ya biyota da kalo da kalar tausayi, Ko mai ya tausasa mata zuciya, ta juyo a hankali daidai da Lukman, murya a can ciki ta ce" Allah, ya dayaba, ya sa nufin da ka bayana alkhairi ne, ya nuna lokaci Tana gama fadar haka ta daga kafarta sosai inda ta wuce su ta fada gida, Da ido suka bita gaba dayansu, inda Lukman ya saki wani lalausan murmushi da ya bayanar da hakoransa waje, a fili ya furta Alhamdulilah, yanzu adu.arsa daya Allah ya sa mahaifin baban nasa ya yarda da wannan magana domin ya nace kan sai ya aura masa yar uwarsa Zuhra wace sam baya jinta a layin matan da yake sha.awar rayuwar aure da su Haka suka karaso suka tarar da inna na ta tatar koko Wujdane na gefe tana gyara dambun shinkafar da zasu yi, ta zagine ta ce ita zata yi komai bayan Jamail ya nemi alfarmar a yi masa ya kaiwa yayansa dan yana da son dambu Jefi jefi takan saci kallonsu da Aisha dake famar gyaran lemo na shan ruwa, a daidai wannan lokacin Abdul Fatah ya karaso cike da gajiya shi kan idan yana azumi akoy son jiki Shima nan ya tile wajen su Aishar ana ta labari da Jamail wanda sosai a gidan ba wanda bai yi sabo da shi ba, tsananin yana son wannan zuri.a Inna ce ta dan dago da kanta, ta yi ta yi ta hani kanta yi masa magana aman ta kasa, dan zama ta yi kafin ruwa ya tafasa tana kallonsa, a hankali ta ce" Jamail, ka yi hakuri, aman na kasa jurewa, shin Jamail wannan kayan abinci da ka kawo mai kennan? Dago da kansa ya yi da sauri, daman ya san a rina shi ya sa yaki yarda ya zauna daga shi sai ita a gidan, wannan kayan kuwa yayansa ne ya bude yana talafawa talakawa shima yaje masa da bukatar a deba masa ya kawo gidan malan dake bada karatu a masalacinsa, hakan ya saka aka cika mota da su shinkafar gwomnati, hatsi, gero, macaroni, cuscus, kai harda su man kuli a babar jarka da su magi, kafin ya karaso sai da ya biya wajen malan ya fada masa da kuma fadin sakon yayan nasu na kar kowa ya tafi gida da wuri dan yana can baban shagonsa na abinci ana ta fitar da sadakar kafin ya karaso anguwar nasa, duda ba shine ke rabawar ba, domin a cikin masalacin mutane dadaya ne suka san shine mai taimakon nan, da yawa ba zasu shaida shi ba a boye yake Kafin ya yi magana inna ta ci gaba da fadin" ina jin tsoron hakan Jamail, tunda aka haifeni har zuwa yau da furfurana a kai ban taba tara kayan abinci irin haka ba, Jamail ba wai ban yarda da kai bane ko wani abin, iyayenka basa tuhumarka da dawainiya da kake da gidan nan yau da kulun? Shin baka gannin ya yi yawa ne duda ka fadan cewa kai kana yi ne idan ka ga yin hakan ya dace, ka daukeni tamkar mahaifiyarka ne, malan mahaifinka, kana son talafawa mu, aman Jamail ya dace ka sasauta, ka ga da ba dan Wujdane na gidan nan yau ba da tuni layin nan sun cikani da kai kawo dan tsegumin mai ke faruwa a gidan nan, Jamail bana son abinda zai zo ya jagula kyakyawan zumuncin nan dan Allah Jamail ya yi murmushi, a hankali ya juya wajen Abdul fatah ya ce" ni yaya a kasuwar sabon gari ma kana dan taba kasuwanci a can ko??? Abdul Fatah ya ce" sosai ma, ai nan din yafi kwari kasuwancin domin a da soso nake kaiwa yanzu tsaron shago nake na siyar da irin turarukan nan na mata na shafawa Jamail ya gyada kai ya ce" Masha Allah , Allah ya taimaka, aman yaya ka san wani da ake cewa Elhaj ALAIDINE MAI KAYA? Abdul fatah ya ce" tap, ai wanda bai sanshi ba toh ka tabatar bako ne, domin tun daga kan hausawa da inyamurai dadaya ne basa bin reshen kasuwancinsa, suma dan basu samu ba, aman du yawancin haraka sai ka bi ta gefensa idan kana son ka ga komai ya je maka da sauki ga biyan bukata Jamail ya ce" madallah, kuma ba tonan asiri ba, dan Allah yaya Abdul fatah, yana da tausayin na kasa da shi? Abdul fatah ya ce" a kishin kishin din da ake yadawa wai ba wanda Allah ya cida haduwa da shi ba, aa, koda sako yake na bayar da zaka ko sadaka Allah ya sa ya biyo layin ka warke, yauma fa ana can store dinsa karka so ka ga layin jama.ar, ai sabko zan yi dan na samu gaba gaba, ba wani bambanci ko almajiri ko baba ko yaro ana sadaka ne da zuciya daya, aman ba wanda ya gansa ance yana ciki, mutane da yawa layin da suka yi dan su gansa ne da idannuwansu domin alkhairinsa ya jima da tardo su aman ka ga bawan Allahn nan ko mai yasa baya son a gansa Sosai Abdul fatah ya dage yana bada labarin Alaidine, sai da ya koro da surutu ya dakata ya ce" aman kai ya aka yi ka tambayeni sunnansa? Ko ka sanshi ne?? Jamail ya saki murmushi, ya juyo wajen inna da Aisha da suke kallonsu sun rataba masu hankalinsu dan gane inda wannan labari ya nufa, Wujdane kuwa na daka tsidahu a zuciyarta tana aiyana mai kuwa zai hana shi banda girman kai irin na masu kudi, Jamail ya ce" inna, kinga masalacin da malan ke bayar da karatun nan toh nasa ne, a wajensa na karbo kayayakin nan, ina fada masa a kawo na gidan Malan yace na je gidansa na fitar wai danma matarsa mugun hali ne da ita bata son kyauta wa wasu da ba yan gidansu ba, domin yan gidansu sun cika gidan tana ta fitarwa aman idan wani ya zo sai ka ga ranta ya baci, bata son ana rabar mata miji, ni na san da shine ya fitar ko yana tsaye aka fitar da bansan bama ya zamu kare da ku inna, Inna ta dafe kuncinta ta ce" toh ikon Allah, shi kuwa wannan bawan Allah haka yake da sannin romon sadaka? Allah ubangiji ya jibanci lamuransa, ya bashi ladan sadakar da yake ta kasance masa haske a gobe kiyama, aman a anguwarku yake ko??? Jamail ya ce" shine mahaifin boy Su duka sun cika da mamaki har wujdane dake daka sai da ta dan dago ta dan kale su, ta mayar da kanta sai ta tsinci kanta da cewa ai gwara da bai zama aku ba irinka(🤦🏻‍♀🤣) Haka sukai ta labari tsakaninsu, wanda Inna ta yi gum da mitar kayan nan sun yi yawa ta bi su da adu.a, Abdul fatah da ya ji dambun nan shi za.a kaiwa sai ya lalubo dubunsa guda ya fice, bai dawo ba sai da sayaya niki niki ta su kifi da albasa yanda za.a yi yar jijibar miyar ci da dambun Aisha kuwa cike da murna ta karba ta shiga gyarawa Konci tashi ba wuya, azumi har ya zo karshe wanda ake saka ran wayewar gari da sallah za.a tashi, Idan ka shigo layin su Wujdane abin sai ya baka mamaki, duda karamar sallah ce aman cikin ikon Allah ko.ina ka wulga yara ne da yan mata da samari kowane na faman gyara kansa kunshi wa.inda basu samu yi a shekaran jiya da jiya ba Aisha ce zaune ta gama hada sibkarta, tana bin Wujdane da kalo, ta san ita zata yi mata kunshin aman sai dan kai kawo take tana kara share gidan da baida dati ko kadan, su Mairo ma sun yi aiken dan girman Allah ta taimaka wannan salar ta dan yi masu komai kadan dinsa , fakat ta furta ba zata yi ba Aisha ta kali ledar ta kuma dagowa ta shagwabe fuska ta ce" yanzu aunty ba za.a yi min ba kunshin nima Aishar ki? Dan harare ta jefeta da shi, inna dake dakin malan tana ta faman gyara masa domin ana saka ran a ranar zai dawo daga masalaci da yayi kwana goma sha biyar , ta ce" ai fa sai ki zauna jiran ta yi maki, ba sai da na fada maki ba ki nemi mai kunshi mai neman na kanta wace ba zata wulakantaki ba tayi maki abinki tunda ke kin amince mace ce ke kina son gyara ki barta da shirmenta aman ke kin nace sai nata dan ta iya take yiwa mutane yanga, ita ta zauna a yi mata kitson ma ya gagara ta kunce dokar kuma ta daure gashin duda ba inda zaku ai ana samun baki, sai ka kimtsa kaima ka ji dadi irin na kowa, aman kiri kiri ta hade fuska ba damar yin wani abin na jin dadi Kai wujdane ta dafe, ita dai ta rasa mai ya sa innarta komai ta yi sai ta ga rashin dacewar hakan Bata shirya yiwa Aisha kunshi a lokacin ba aman dan ta rufe bakin innar ta zauna ta shiga zana mata Aisha murna fal cikin ranta, a zahirin kuwa sai doka murmushi take, domin kunshin ya zanu, nima masha Allah na furta domin idan ba miskilancin Wujdane ba ta iya kunshi ashe har haka, tamkar wata amarya Aishar ta koma anyi mata kananuwan kitsonta ga yalwar gashi sosai, fuskarta ta jayu da kyau, ga kuma kunshi, Inna na gamawa ta dora ruwan zafi a murhu, wanda yana yin zafin ta juye ta silka shi da ruwa ta zuba yodo a rabin, a sauran kuwa ta juye a buta, fir ta yiwa wujdane jan ido ta zo ta darje mata kan, wanda har wani zafi fatar kan nata ta fara, aman wata iska mai dadi na shiga kofa kofa na gashin nata, sosai ta ji dadin yanayin nata har innar ta gama daga nan wajen tun kafin ya bushe ta shafa mata mai mai maski maski ta hade shi ta daure mata shi a tsakiya sosai ta ja shi yanda fuskar zata dan fito, sannan ta tufke shi ta laulaye mata shi sosai Zo ka ga wuwurga idannuwa wajen wujdane, kan nata ya dauki ciwo a lokacin wai anyi mata kitso, har wani lumshe shanyayun idannuwan magenta take tana cije lebenta dalilin hayaniyar anguwar Wani yaro ne Saminu ya shigo a guje tun daga kofa ya kwala salama, yana shigowa ya ja ya tsaya, Saminu ba dai firirita ba, akoy shi da taurin kai , Yana kale kalen gidan ya ce" wai aka ce ana magana da Wujdane Ji tayi tamkar saukar aradu a kanta, kwal uba sunnana gatsal din nan ya kama dan uwarsa? Ai kuwa tana dago da kai Saminu ya lura ashe ita ce a zaune da hijab dinta da ya jike da ruwa, ido ya zaro bazai manta dukan da ta yi masa ma wanda ko babansa bai taba yi masa irinsa ba duda dukansu da yake, ido ya kwalalo waje ya hade hannayensa waje guda Ina ai gani ya yi hakan ba zata fishe shi ba, ganin irin yanda ta mike a zazafe ta nufo shi, daman a cike take da haushi tamkar ta fashe sai ga mai kan dauka ya tsokale ta, Arcewa Saminu ya yi a guje yana ihun kiran sunnan mahaifiyarsa yana fadin" mama wujdane ce zata dake ni Ai kuwa innna bata ankara ba sai giftawar Wujdane ta gani da gudu ta marawa yaron nan baya, da azuminta, da girmanta, da bakinta a kofa Lukman da abokinsa sun zo mata da kayan sallah Kaka kara kaka wujdane nayi zaton kin nutsu ashe konto kika yi?😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲 [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *15* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Yana zuwa masalaci jama.a sai harama ake ana mimika dabino ga gefe manyan jarkoki ne cike da su kunu ko tukudi masu sanyi wa.inda mutane ke kawowa sadaka, wasun kuwa daga can gefe suna ta kokarin gannin dan jaririn watan dake kokarin bacewa domin fitowar ranar ne Nan da nan aka shiga musabaha ana godiya ga rabil izati, jama.a na neman yafiyar junnansu sannan ana ta buda baki Shigewa ya yi cikin tarin mazan nan, ya zauna ana ta mimiko kunnu a kofuna Karba ya yi yana hangen wasu tsofafi dake zaune gefensa, da alama dare duka yi har shan ruwa ya riske su, Kansa ya juyo wajen MLan dake magana da Hamza, suna yar dariya da alama maganar mai dadi ce, Haramar sallar da ladan yake maimaitawa a lasifika ya saka kowa mikewa masu kuskurar baki na yi, wa.inda a kuskuren suke har sun bi sahun sallah Muryar Malan ne, wanda a ranar shi ya yi limanci yana jan sallar inda Alaidine yake ji gaba daya wata nutsuwa da tsoron Allah sun saukar masa, muryar malan ta saka shi nutsuwa fiye da tunanin mai karatu, haka ya samu kansa da zama bayan an gama sallar , almajirai sun bude karatu kamar kulun , wasun kuwa na zuwa kara daukan karatu qajen malan, A hankali ya dauko alkur.ani shima, ya zauna har aka zo kansa ya je gaban malan, aka biya masa karatu wanda kwarai ya ji dadin hakan Yana lure da malan sai da kowa ya watse kafin shima ya mike ya tafi bayan ya yiwa jama.a da dama salama, cike da fara.a ya fito ya kuwa dauki hanya yana doka sauri Ajiyar zuciya Alaidine ya sauke, ga dukan alamu sun nuna mutumen kirki ne, aman zai kara nazartarsa, ya tabata idan har na gari ne matarsa ma haka toh zasu baiwa yaransu tarbiya, duda yanzu zamani ya zama na tir, domin kana tarbiyantar da yaron ne, a waje idan ya hadu da mugayen abokai suna warware maka tarbiyar yaro, shi dai abinda ya sani shine, bazai taba yarda irin rayuwar da yake ciki na rashi dacen macen aure ta kirki kanninsa ma ya fada a haka, Shi dai adu.arsa shima ya samu mai dama damar kamar mayar anwar Washe gari an tashi da sallah, inda cikin ikon Allah du jama.a sun ajiye azumi an tashi da sallah baki daya, Zo ka ga yanda mutane ke shigo da fici, Malan ya sha sabon farin yadinsa da Hamza ya dinka masa, ya dora sabuwar hularsa da takalminsa da Abdul Fatah ya kawo masa, sai sabon carbi da turare, fuskarsa na fitar da annuri Yana fitowa ya tarar inna sai gyaran kayan miyarta take, da zabi biyu a gefe wa.inda ya saka aka kawo mata, sai aikinta take cikin nutsuwa, ta sha sabuwar atamparta ta saka kwali a idannuwanta, sai ta fito radam da ita sai sheki jikinta ke yi na mai da ta shafa vaseline dinsu sabo, ga turare da ta fesa yau ranar sallah kowa kwaliya yake Cike da fara.a malan yake amsa gaisuwar yayansa, kyam kuwa yana karewa matarsa kallo wace ta fitp masa a yarinyarta, masha Allah shi kam ya godewa Allah da ya bashi innar yara a matsayin matarsa malakinsa Haka samarin suka fice wajen idi , inda yan matan suka shiga taya inna aikin cikin gida da zabin nan da ake shirin tsantsara masu dafuwar cire kune🤣 Yau sallah kwana uku kenan, Jamail bai samu lekowa gidan malan sai a ranar nan domin hidomomin sallah gidansu a cike yake da yaya da jikoki ana ta shagali ana ta murnar sallah, harda Alawiya ma kanta ta zo bisa umarnin Alaidine wace take taku daidaiya tana yabawa khadija magana, itama tana ramawa Shiru ya yi yana sauraron inna na yiwa Wujdane fada kan tace ba zata bi su yawon sallah ba shi da Aisha dake shiryawa da yayan ysyunsa da ya dauko yaran wajen Anwar da Boy, du sun sha shigarsu ta manyan kaya kamar ka sace su ka gudu Mikewa Wujdane ta yi ta fito ranta a bace ta fada wanka, ko maganar ma yau bai samu ba domin sai take ganin ai laifinsa ne shi ya jaza aka takurata wani yawon sallah Fitows ta yi ta shige dakinsu, tana sauraron yanda yaren suka cika gidan da surutu Mai ta shafa, ta dauko bakar abayar da Malan ya kawo masu ta walwale tana niyar sakawa A hankali Aisha ta rike hannunta ta ce" Aunty, ki yi hakuri dan Allah na dan gyara maki fuskar ki, kin ji auntyna dan Allah ba dan ni ba Yatsina fuska ta yi ta zauna , Aisha taa dan samu ta dan gyara mata fuskar duda kwali ne kawai sai girarta da ta caje mata ta daidaitata, fir ta ki a saka mata jan baki a pink din lebenta sai dan lips aka dan goga mata, Abayar ta saka bayan ta daura zani daga ciki don karta like mata a jiki, Gashin kanta take faman sai ta dunkule waje guda dan ta daure aman idan ta gwada nada mayafin abayar sai gashin ya cunkushe, Tsaki ta ja da ta saki gashin ta nanada ta ga ya yi dan cicif a jikin nata tana ayana wannan ai sallon iskanci ne Kallonta kawai Aisha take, sam kalar Wujdane ba ta bahaushiya bace, ba ta yan africa bace, tamkar wata balaraba haka ta fito ga kalar adon jikin abayar duwatsu ne blue da fari sai suka haskaka idannuwanta masu kwayar ido blue Dan takalminta plat ta saka, suna yiwa inna salama wace ta yi masu gargadi sosai , ta kara kawa Wujdane kune banda fada, Haka suka fito inda Jamail ya kasa daina kallonta, a kasan zuciyarsa yana ayana daman haka take ? A hankali ya lumshe idannuwansa bayan ya bude mata gaba ta shiga da Boy a hannunta ta zauna a kasan zuciyarsa ya furta" ya Allah, idan har inna da rabon auren wannan baiwa taka , Allah ka kadara min shi kafin nayi kaura gareka Haka ya zagaya ya shige ya ja motar ya fara nufar gidansu domin can zai fara kaisu kafin su karasa park Yana zuwa mamaki ya kashe shi irin yanda gidan yayo tsit, tamkar ba mutane bayan a fitarsa ma ya barsu a barbaje suna ta shalakwalinsu harda yayan kawayen Mom dinsu Juyawa ya yi sai ya hango motar yayansa, wace ranar idi ya fara takata, a fili ya furta" yawa ga dalili dodonsu na gidan Su dai ba wanda ya fahimci maganarsa, sannan Aisha da Wujdane sun kasa fita a motar, mamaki, tsoro, da komai ya zubun masu, tambaya suke yiwa kansu, wai daman Jamail nan nw gidansu? A irin gidan nan yake rayuwa aman yake zuwa ya zubar da kansa ya dangwali abincin tukunyarsu ya sha labarinsa ba abinda ya dame shi? Ku fito mana, muryar Jamail yana kallonsu, yaran ma haka suna kallonsu A hankali ta sako fara kal din kafarta wace bata yi mata kunshi ba, hakama Aisha ta zuro tata da ta sha kunshi masha Allah Suna fitowa Wujdane ta ja ta yi tsaye da Boy a hannunta taki bin bayansu tana kallon kasa Boy kuwa na ta yi mata magana yana murnar yau ya zo wajen kakaninsa Daga saman gidan yake tsaye, ya dage labulen kofarsa yana kallon balbalin gidan Alawiya a gefe tana shan jus tana kada ido tanai mai bayani adadin kudin da take bukata dan kaiwa yan gidansu barka da sallah, A kan idannuwansa suka fito, Kwarai ya ware idannuwansa yana kallon su, har du suka shige banda yarinya daya da ta tsaya da Boy a hannunta, Mamaki yake, su waye wa.innan kuma? A ina boy ya sansu boy da kin yarda shine harda yarda da baki haka? Bai gama tunaninsa ba ya ga Jamail ya dawo ya harde hannunsa daya a kirjinsa yana ta zuba murmushi da alama lalaba ta yake Gabansa ne ya yanke ya fadi , wani haushin yarinyar ya darsu a zuciyarsa , a fili ya furta" rashin tarbiya ne ko kwadayi ne zai kai budurwa gidan su saurayinta kafin ma a yi masu baiko???????? Alawiya dake zaune ta dago tana kallonsa dan sai ta ji kar ya yo magana, a fili ta furta magana ce???? Kafin ya bata amsa ya juya ya fito dan tabatarwa zarginsa, idan kuwa hakane sai ya sabawa Jamail, daman ba yar gidan mutunci ya je ya dauko ba? Mai yake son mayar da kansa da su kansu ne?????????????????????? Toh fa [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *14* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Wani irin fitowa ta yi da gudu, burinta ta damki yaron nan ta jijiga masa jiki ya gane bashi da wayo ko ta samu sa.ida a cikin zuciyarta Wani wawan birki ta ja ta tsaya, ta yi saurin sada kanta kasa tana sauke ajiyar zuciya , zuciyarta tamkar ta fashe, Lukman da ya yi mutuwar tsaye, ya rasa mai zai cewa abokinsa da ya saki baki da hanci yana kallon katuwar budurwa haka na bin yaro da gudu, yaran zamani bata ko jin tsoron ya kaita kasa Hularsa ya cire Lukman ya shiga fifita zufar da bai san lokacin da ta sabko masa ba, Dago da kanta ta yi, kallon da abokin Lukman ke jifanta da shi ya tsaye mata a wuya, Saurin janye rufar nata ta yi ta dago da idonta sosai tana kallonsa irin kallon meye?? Ya salam ya furta yana waiwayen Lukman ya ce" Lukman jibi halaitar Allah Lukman ya dan kada kai ya ce" eh ita ce Wujdane dina Dahiru ya dan waigo ya kali Lukman da alamar tambayar wasa kake min? Lukman ya dan girgiza kai yana kokarin karasawa wajen Wujdane Dariya ya bushe da ita, ya ce" aman abokina baka da mutunci, kyan ne zai kaika ko mai? Kana gannin yanda yarinyar bata da nutsuwa har zaka wani kwaso ni? Juyowa Lukman ya yi cike da jin haushin Dahiru, sai dai mai kafin ya yi magana Wujdane ta bude fuskarta da kyau, Gaba dayansu ta yi masu kallon sama da kasa, yawu ta tatara a bakinta ta yatsina fuska sosai ta karaso kusa da Dahiru kadan ta zabga masa harara wace ya tsorata ainun dan shi ya fara zargin ko aljanna ce, ? Yawun bakin nan nata ta tofar a fegensa ta wani kada ido ta ja tsaki , Kokarin juyawa take sai ta hango Jamail, wanda ya ja ya taka birki yana kallonta da samarinta, Har cikin ransa yake jin tsanar lukman din nan, wani wawan birki ya ja ya tsaya ya bude glass din motar A tare suka juya wajensa, wanda hakan ya bashi damar yi masu kallon sama da kasa, ya zabgawa Wujdane harara ya ja motarsa da karfi wanda sai da ya bude su da kura Da kalo suka bi motar, kowa da abinda yake sakawa a ransa, Wujdane mamaki take wannan sabon salon wulakancin fa? Kan Uba, ka ga an gwada maka ba sa.ar yinka bace wannan dan haka abokina kawai mu tafi Juyowa Wujdane ta yi, a yau dai ta godewa Allah, kalolin abinda zai saka ta ciwon kai ta hadu da dama, Ji take tamkar ta shake wuyan wannan marar ta idon abokin Lukman din, juyawa ta yi ta fada gidansu wanda ta tarar da inna na zaune tana kallon daidai kofar shigowar Duke yake gaban malan, du ya wani rikice masa yana koro masa bayani Malan cike da mafificin mamaki da zai iya tsinta a takaitaciyar rayuwarsa a gidan duniya yake kallon Jamail, Murmushi ya dan saki dan harga Allah sai ya dauka Jamail ya shiga yi masa wasa irin na kakanu Cike da murmushi Malan ya ce" kai Jamail, ka cika tsokana kai dai, Dago da kansa ya yi, idannuwansa cike da hawaye ya ce" ba zancen tsokana Malan, ba zancen wasa, dan girman Allah ka karbi bukatata ka cika min burina tun kafin na bar duniya, Malan wannan shine baban burina tun ranar da idannuwana suka sauka a kanta, na sani kana tunanin nayi yarinta ko wani abin? Malan na shiga shekara ta ashirin da biyu, ina da sana.a, a gidan mu ba za.a hana ni ba, ka dubi girman Allah ka yarjewa bukatata Daidai wannan lokacin kam Malan ya daina murmushin sai tsoron furucin Jamail, cike da nazarinsa ta ce" kana nufin Jamail kana bukatar auren Wujdane? A shekarunka? A wayewar nan ta zamani? Ya za.ai iyayenka su aminta da hakan? Ya kake hasashen faruwar wannan diramar? Lale aure nufi na Allh ne, kuma namiji namiji ne, aman Jamail zamanin ne idan na rinste idona nakan budewa cikin gagawa, domin sam ban hango yin hakan ba, dan Haka ka sakawa ranka nutsuwa ka je ka yi tunani ka ji yarona??? Dago da kansa ya yi, zuwa wannan lokacin ya yarjewa tunkarar koma waye dan kar yana kallon ruwa kwado ya yi masa kafa, Wujdane sai ta zama malakinsa sai dai idan baya nunfashi a doron kasa Farawa da iyawa Jamail bai tunkari kowa da maganar nan ba sai yayansu, wato Alaidine Gidansa ya tunkara wanda ya tabata a wannan lokacin yana gida dan kuwa yama ta yi sosai Yana zuwa ya faka sabuwar daleliyar motarsa da Alaidine ya canza masa Budewa ya yi ya fito cikin nutsuwa yake salama Shiru ba.a amsa shi ba hakan ya saka shi shiga kai tsaye , Alawiya ya tarar tana zaune kafa daya kan daya, kalo take a tv da manyan kayanta a jikinta wa.inda tafi jin dadin jikinta da su bayan rigimar da suka gama tafkawa da Alaidine, ta kai masa korafin dan me yake kauracewa shinfidarta sai ya nuna mata cewar dalilin azumi ne ta yi hakuri bayan sallah, sai hakan ya kona mata rai ta yi masa tambayar da ya saka shi korarta daga falonsa domin tambayarsa ta yi ko bashi da lafiya ne? Bayan ta fita ya yi kwafa ya konta yana kallon Boy dake bacinsa hankali konce Dauke kansa ya yi, domin tunda aka kawota gidan nan ba wani amsa gaisuwarsu take ba, idan an gaisheta bata wani amsawa hakan ya saka ya daina ko a gaban waye zai yi mata salama dai Ficewa ya yi ya shige bangaren yayansa da salama daga bakin kofa Alaidine da yake konce yana ta lumshe ido ya mike yana amsawa fuskarsa na kalon kofar shigowar, Jamail ya shiga ya duka har kasa ya gaishe shi Amsawa Alaidine ya yi, cike da kaunar autan nasu, shi dai a duniya jinninsa ya hadu da Jamail sosai, kai duka yan uwansa nema, kallonsa yake yana jiran jin bayanninsa domin jamail baya zuwa ba da dalili ba har cikin dakinsa Kansa ya dukar, sai da ya ganshi gaban yayan nasa kwarjinninsa ya tsirka masa, aman ya ya iya idan bai tarbi wannan rigi.ar ba da alama sai ta fi karfinsa Dago da kansa ya yi gabansa na dukan casa.in casa.in murya na rawa ya ce" yaya , maganar aure ne na zo da..... Sai ya yi shiru yana kifta idannuwa Kallonsa Laidine yake, yana jiran jin karin bayani, gannin bai karasa ba ya ce" maganar aure? Wani aure? Cike da gargadar murya ya ce" nana....nawa! Kikifta ido Alaidine yake yana kallonsa, can cikin kwakwaluwarsa kuwa kokowa yake da tunaninsa, shin yau mai ke damunsa haka yake haduwa da abubuwan tsayar da zuciya ne??? Baima san mai zai cewa Jamail ba, shi dai abinda ya sani shine akoy shakuwa tsakaninsa da kanninsa ta mamaki, aman babu zancen tsokanar juna ko wasa da juna, suna wasa tsakaninsa da Anwar aman da shi babu wannan tsakaninsu Ajiyar zuciya ya sauke, gannin yanda Jamail du ya rikice ya takura, a hankali ya ce" Aure zaka yi? Jamail ya sada kansa kasa, yama rasa mai zai bayar amsa, Mikewa ya yi a hankali ya ce" yaya ba komai Niyarsa ya fice a dakin tun kafin ya rasa nutsuwarsa, Alaidine ya ce" dawo ka zauna Dawowa jamail ya yi, ya zauna yana kallon kasa, Alaidine ya ce" bazan hanaka yin aure ba Jamail, tabas na doraka kan kasuwanci bana shayin zaka kasa iya rike gidsnka, ba zanyi shaidar hankalinka ba, sai dai ina da tambaya , mainene makasudin ingiza tunaninka a wannan lokacin da baka cika shekara 22 ba a duniya har mararin yin aure ya darsu a zuciyarka?? Wani banbarakwai ya ji tambayar, sho dai bai san takamaiman amsan ba, baban abinda ya sani shine yana son Wujdane tun ranar da ya dora idannuwansa a saman fuskarta kuma baya bukatar ko da wasa ta kubuce masa, shi ya saka shi kokarin yiwa tufkar hanci Sun dauki mintuna a haka, shi bai ce ga dalili ba, shi kuma bai sake wata tambayar ba, Yar gidan waye??? Dago da kansa ya yi jin wata tambayar yayan nasa, A hankali ya furta" yar gidan Malan liman ce mai bayar da karatu a masalacin gida sunnanta *Wujdane* Alaidine ya dan daga kansa ya ce" kana iya tafiya, zan waiwayeka insha Allah Mikewa Jamail ya yi jar kamar ya kife dan sauri ya kama hanyar fita sai sauri yake, Bayan fitarsa Alaidine ya jinginar da bayansa jikin gadon, a hankali ya furta" ba zan hanaka aure ba, may be halitar du guda ce, kar a je tarihi ya maimaita kansa Kiraye kirayen sallah ya saka shi mikewa inda ya fito ya nufi masalaci dan ya sha ruwa sannan yana da bukatar gannin wannan malan, domin yan gidansu du sun karbe shi yana son karantarsa............. [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *16* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Salama ta yi ciki ciki, wanda ta samu Aisha zaune da yaran nan na anwar sun zagaye ta sai labari suke bata, itama ta sake da su sosai A hankali ta karasa kusan Aishar ta zauna, ta sada kanta kasa a lokacin ta yi shiru tana tunani Dakin kanshi ne yake fitarwa na turaran wuta irin dan maidugurin nan, ya garwaye da sanyin ac sai yake fitar da sanyi mai dadi, Mom kennan ba dai kulawa da tsaftar gidanta ba A hankali take saukowa, bayan ta gama shan dargu da Alaidine ya tokare daga sama ya harde hannayensa yana kallon ikon Allah Boy yaki ya saki jikin wannan munafukar domin kanta a kasa shi jar yanzu bai ga kalar fuskarta ba hakan ya saka shi amincewa cewa ba mutuniyar kirki bace Mikewa suka yi gaba dayansu daga saman kujerar bayan mom ta karaso ta yi masu salama A tare kamar sun hada baki suka koma saman capet din domin Mom ta hau kujerar Aisha ce ta fara gaishe da mom, wace ke amsawa cike da fara.a malale a fuskarta A hankali Wujdane ta dago da kanta muryarta can kasa kamar yanda ta saba idannuwanta suna dan kallon Mom ta ce" Barka da sallah mama, Allah ya maimaita mana Mom ta amsa tana kallon Wujdane, masha Allah take maimaitawa a kasan zuciyarta tana fadin Allah ya raya Wani irin ja da baya Alaidine ya yi, sanadiyar bugawar da zuciyarsa ta yi, a hankali ya laluba ya fada dakin dake kusa da shi sai dai kash, ashe dakin Khadija ne Murmushi Khadija dake konce saman bed dinta ta yi tana kallon yannayinsa, a hankali ta taso gannin zai fita ta taho kusa da shi ta dafe kofar fitar tana kallonsa Idannuwansa ya lumshe, har ya samu ya saisaita nutsuwarsa, kallonsa ya dawo wajen Khadija wada habanta ya yanke ya fadi sanadiyar kwayar idannuwansa da ta ga sun canza launi Bude min na fita Ya fada fuskarsa a hade Gwuiwowinta ta kai kasa, bata bar jikin kofar ba ta fashe da kuka, murya a matukar raunane ta ce" danme ba zaka mayar da ni dakina ba? Na tuba Aban Huzaifa, dukan abinda na yi maka yarinta ce da zuga, yanzun na gane ko kai wanene a cikin rayuwana, ina neman dan girman Allah ka ji kaina ya yafe min, ka mayar da ni dakina Kallonta yake, a can kasan zuciyarsa yana hangen nadamarta kamar da gaske, dan dukowa ya yi ya rage murya ya ce" kina nufin koda da halin mayar da ke din zaki iya zama da shege? Khadija ta kara sada kanta ta ce" ka daina tunawa, na yi kuskure, na nemi gafararka, ka manta ka mayar da ni dakina ko na samu sukuni a zuciyata Alaidine ya mike ya kama kofar ya juyo ya ce" a saki uku ana komen aure kennan? Bayan nan ni bazan iya auren mai uba ba, dan haka ummu Huzaifa ki samu miji ki yi aure kin ji?? Dago da kanta ta yi, muryarta cike da rauni ta ce" dan kawai baka son mayar da ni zaka ce ka yi min saki uku bayan biyu ka yi min? Shin kai ba musulmi bane da ba zaka manta rayuwar da muka yi ka mayar da ni ka ga a yada zan zauna? A yanzu da na gama sannin manyan sirikanka na rayuwa nake amana da su nake jin haushin yarintar da na zuba har ka sake ni, Zuwa wannan lokacin ta kusa samun galaba a kansa, juyo da kansa ya yi, q hankali ya furta" da ba dan rantsuwar da na gindaya ba da na waiwayeki, ba maganar rike ki ne ba aa, maganar a lokacin raina a bace na yi muguwar rantsuwa harda haramta ki a rayuwana, Khadija ke ce ta farko da na rayu da ita a matsayin mace sannan ke kika bani kyautar da har yanzu nake jina cikeken mutun, ba zan yarda ki wulakanta ba, ni da kaina zan nema maki yafiyar su abanki, sannan daga millon goma abinda ya yi sama bukatarki zan biya maki, ki samu miji malamuncinki ki yi aure kin ji? Tana kallonsa tana ji tana ganni ya fice a dakin hakan ya saka ta zubewa a nan ta saki kukan nadama( magana zanar bunu ce) Yana saukowa ya tarar da Mom ita kadai zaune, Karasowa ya yi a hankali ya zauna bayan ya yi mata sannu da gida Amsawa ta yi cike da kulawa, tana murmushi ta ce" idan baka zo ba nakan shiga wani yannayi na rashin ganninka a kusa da mu, idan ka zo kana zo mana da tsare tsare masu wuyar gani, yanzu son dan Allah kawai sai ka kora yara daki suna shagalinsu? Ai sallah ce sai ka barsu su dan huta kadan ko? Kallonta ya yi, bai ce komai ba ya dan kawar da kansa a kasan zuciyarsa yana ayana ai bazai yiwu dan sallahce su kunna kida a cikin gida haka ba dan basu da tarbiya Ta san ba zai tanka ba, domin ya ki jinnin sha.annin kida da abubuwan da suka shafi jakan, kawar da kanta ta yi itama ta ci gaba da kallon tvn Mom ina Jamail ne? Dago da kanta ta yi tana kallonsa, ita bata ga abin takurawa kai a lamarin Jamail, ita kwarai yaran sun shiga ranta ba yanda bata yi ba dan su karbi abin barka da sallah fir suka ki har rigai rigai suke wajen fita, sun nuna idan suka je gida da shi innarsu ba zata saurara masu ba, yaran sun shiga ranta daman fil azal take sha.awar tara yara tumba mace ba, aman cikin ikon Allah ukun ne su ne rayuwarta Murmushi ta yi ta ce" ai ya tafi ya mayar da su Wujdane Dago da kansa ya yi da alamar bacin rai bayane karara a fiskarsa ya ce" yanzu fisabililahi Mom sai kace wasu jininsa na jiki? Ya zai fito yawo da yara haka cikin gari, nawa yake Jamail din da zai fitino da wannan rayuwar, meye abin sha.awa a bibiyar yara haka? Mom kuma har ki yarda da hakan dan Allah? Ai wannan da gani basu da tarbiya idan ba haka ba ta ya zasu shiga motar namiji haka ba wani yayansu ba ba wani muharaminsu ba su bi shi zikau zikau su shiga gari da shi? Yanzu fisabililahi haka ake rayuwa? Kuma sai ya dauki boy yana cakula shi a shirmensa ko? Sannu mai da, maganar Mom ra katseshi wace ta zubawa sarautar Allah ido yana bambamin balaki dan kawai Jamail ya kawo yaran da a kulun ta Allah idan dai zaka zauna da shi maganar gidansu ce tarbiyar gidansu, mahaifinsu mahaifiyarsu, komai, yarinyar da yake muradin aure a rayuwa, yarinyar da a yanzu ita kanta zata yiwa iyalanta sha.awar ajiyeta a matsayin mata, bai ko zauna da mutun ba bai san halinsu ba aman ya dage yana zuba masifa a kan hakan Hade fuska ya yi tam, ransa ya gama baci, gannin zaman nasu da mahaifiyarsa ba zai ci gaba da yin dadi ba tunda sun yi baran baran ya saka shi mikewa ya fice a gidan gaba daya Ni fa na fada maka ba zan je wani park ba, ka mayar da mu gida na gaji da yawon haka, Wujdane ke fadawa Jamail cike da masifa a muryarta Ajiyar zuciya ya sauke, shi fa har wani shayinta yake idan tana fada bai san dalili ba, Karkata motar ya yi ya dauki hanyar gidan nasu wada ta fitar da kanta gefe sai cika take tana batsewa, fitar ce ma bata saba ba an takurata ne Suna karasowa ya ja ya tsaya aman maimakun ya bude masu sai ya rufe gaba daya motar Kowanensu ya ja ya ja ya kasa budewa hakan ya saka su waigowa wajensa Kansa a kasa yana kokowa da zuciyarsa kan abinda zai furta a daidai wannan lokacin Yaya Jamail ka bude mana taki buduwa, muryar Aisha ce ta doki kunnansa cikin sanyinta yanda ta saba Ta madubin motar ya dan kaleta ya marairaice murya ya ce" dan Allah sisterna ki dan dakata ki tayani yaki da auntynki kin ji? A tare suke yi masa kallon rashin fahimta, yaki, na me fa? Kiwace tambaya take yiwa kanta a kasan zuciyarta aman ba amsa hakan ya saka Wujdane dago da kanta a karo na barkatai wannan karin da yannayin rashin son raini ta ce""" [3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *18* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Yau kwana uku kennan shiru ba Jamail ba labarinsa a gidan malan, inda inna ke ta jajen rashin zuwan sa sai dai aisha ta sauke ajiyar zuciya bata ce da inna komai ba, Bangaren Wujdane ta bi ta takura rayuwarta a tunani, ita bata son auren yaro karami ba dan komai ba sai dan kar a zo a rasa waye baba a cikin gidan domin tana ra.ayin auren mai shekaru dan ana fada cewar sun fi hakuri, kawar da kai, ga mace, ita kam ta tsayar da shawarar zata baiwa Lukman damar ya fito Konce take a dakinsu ta mayar da dakin nan wajen rayuwarta, Yaro ne ya yi salama yana fadin ana salama da Wujdane Yama ce, magariba ta kusa shigowa, duda hakanan ta dauki hijabinta ta zura ta fito waje dan amsa kiran da ake yi mata Tana fita ta tarar da Lukman, kamar kulun yauma ya sha shirinsa masha Allah, daga nesa ta kare masa kallo kafin ta karaso kusan shi Dan dukar da kanta ta yi tana fadin" barka da yama, da fatan ka yini lafiya Kallonta yake cike da mamaki, bata taba yi masa irin gaisuwar nan ba tunda ya santa, hakan ya saka shi amsa mata cike da fara.a da sakin fuska Hi Zance yake zuba mata, wanda a wannan rana Wujdane ta bashi gaba daya nutsuwarta, ta tatara dukan hankalinta a kansa harma tana bashi amsa cike da kulawa, wanda har cikin zuciyarta rake ji ta yi amana da shi ko ba komai shi din zai bata wata shekara goma ya dara Jamail A hankali Jamail ya ja motarsa ya tsaya da malan a cikin motar, wanda ya zubawa Wujdane ido yana nazartarta, wannan yaro ya ganta da shi bila adadin A hankali ya dan juyo da kansa yana kallon Jamail wanda har ya dan wani fada dan ya sakawa kansa damuwa Malan ya ce" Jamail, na gode, ka fadawa Aban naka cewar ka sanar min, aman idan da hali ina bukatar ganninka nan da kwana biyar insha Allah, kafin mu yi magana da abanka, aman ka fada masa ai ba sai ya nemi alfarmar gannina ba ko yaushe ya tashi kawai zai ganni da yardar Allah Haka Malan ya fito daga motar daidai lokacin da Wujdane ta shige gida sai Lukman ne ya tsugunna har kasa yana gaishe da malan cike da mutuntawa Malan ya amsa masa , har ya daga kafa da niyar tafiya sai kuma ya dawo ya dan dakata ya nisa, can ya tambayi Lukman shi din dan inane, da kuma sunnan mahaifinsa da komai sannan ya shaida masa ya soke zancen nan da Wujdane idan har ba hanyar kirki suka bi ba Cike da murnar jin haka Lukman ya bar gidan malan inda ya nufi gidansu da wannan albishir wanda a wajensa kadai yake albishir mai dadi Jamail da kyar ya kai kansa gida, yana parking din motar ya fito a hankali ya samu jikin motar yayansa da yake da duhu duhu ya silale a nan ya hade kansa da gwuiwarsa Alaidine dake zaune yana amsa kira ya dakata ya kurawa Jamail ido, ya shiga tunanin bashi da lafiya ne? Yana yunkurin sako kafarsa dan ya fito ya tsinci muryar Jamail na fadin" shin da me Lukman ya fi ni Wujdane? Da me ya fini? Danme zaki ce na yi maki kankanta ne? Aisha bata dai fahimce ki ba idan har shekarun ne ai Lukman bai wani girme min da yawa ba a ganninsa, kawai dai da inda maganarki ta dosa Wujdane, aman danme zaki yanken hukunci baki yi hakuri kin ga yanda ni nake ba? Da sauri Alaidine ya dafe kansa a can kadan zuciyarsa yana furta: innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, dama yar iska ce har haka? Dama rashin tarbiyar nata har ya kai ta furtawa namiji cewa wai ya yi mata kadan? Muryar Jamail ce ta katse shi cikin kasalaliyar murya yake furta" ni kam zanci gaba da adu.a, domin so kwaya daya tal ke na baiwa, idan har da rabon ki dubeni Allah ya nuna min Haka ya yi ta sambatunsa har ya gaji ya mike ya share hawayensa ya shige ciki Wata irin guguwar tsanar Wujdane ce ta darsu a ran Alaidine, a fili cike da bacin rai ya furta" da ubanwa take takama ne wannan yar iskar? Ai daga jin yannayinta sannan ka ganta ka gama gannin rikakiyar yar iska, ohke da iskanci take takama da alama? Ba laifi ni zan nuna maku gaba dayanku ruwa ba sa.an kondo bane, dan kin samu yana bibiyarki toh wly ni zan hana ya aure ki idan har na isa da shi, soyaya ta fi ta ma.AIKI ta Allah, ta iyayena banga wata soyaya ba, karya kake kaima .....fuuuuuu ya fice a motar wsnda ya bankota ya nufi samansa Yau kwana biyu da wannan diramar, inda Malan ya gama fahimtar Wujdane ta fitar da Lukman ne a matsayin zabinta, a kulun idan Malan ya yi sallah adu.arsa daya ce Allah ya sa wannan zabi shine alkhairi a rayuwar yarsa, sannan ya hane shi jin kunyar Jamail da iyayensa, haka kuma Lukman ya ci gaba da zuwa zancensa tunda an tsayar da magana har aure ya kusa , aman har wa yau ba.a kawo lefe ba, ance sai ranar daurin aure sannan bata ga keyar mutun daya nasa ba, ko abokannansa wanda ita hakan ya yi mata domin ba zata hadu da wulakancinsu ba Baifi kwana hudu auren Wujdane ba, wanda du a wani wai take daukansa, inda malan ke ta faman kokari dan gannin ya intata a rayuwa Zaune yake a masalaci, yauma ya yi samako, du ba.a fara fitowa ba, ya mayar da gabansa yama ya yi zuru, a can kasan zuciyarsa yana tunanin dangin mijin Lukman sam basu da kulawa shi jadai ke murnarsa Salama ce ta katse masa tunanninsa, ya dago da kansa inda idannuwansa suka sauka a fuskar wannan mutun mai kamala,da girma a idannuwansa sai Alaidine dake rike da jakar laptop karami Musabaha suka yi kafin suke zama su yi gaisuwar mutunci Malan da wata kunya ta lulube shi kansa a kasa , ya shiga shaida masu yanda lamarin ya kasance, wato Wujdane dama ta fotar da miji ne sai ga zancen Jamail Alaidine dai kallonsa yake a mutumin da du irin kamalarsa ya yarda yarinyarsa take juya shi haka? Aba ne ya yi gyaran murya yana murmushi ya ce" ai Malan duka an sanar min , yanzu haka da wata magana ne muka zo wace insha allahu da alama za.a dace domin dai kafin na yarjewa shawarar yayan nasa sai da nayi ta istihara, nan dai suka shiga tataunawa wace ni kaina ban ji mai suka tsayar shawarar ba sai dai gannin sun fito gaba dayansu Malan ya yi masu rakiya har wajen motarsu sannan ya dawo masalaci ya zauna yana mai adu.ar Allah ya sa hakan shi ya fi zama alkhairi Shirye shirye ake a gidan Malan, inda inna ce da Aisha ne kawai suka yi lakwas, ba dan komai ba sai dan inna ta san abinda ke faruwa ita kuwa aisha Abin ne ya zame mata goma da gomiyatara, domin Wujdane dai kamar ba amarya ba, idanma inna ta bata wani abin dan ta sha sai dai ta nace kan sai sun raba hakan yake saka Aishar sha dan kawai dai ta yarda ta sha ita dinma, sai abinda ke bata mamaki, yan gidan su mijin Wujdane har wa yau ba wanda ya leko su, sai Lukman ne ke kai kawo shima yanzun ya rage dan sai an kwana biyu yake zuwa aman ita Wujdane ko a tsuman ranta Wujdane dai ba kawaye ba, Aisha ce ta gayaci gawayenta na makaranta da na anguwa ta fitar da anko zawarawa na wunnin bikin wanda malan ya basu suma suka sayo, sai abu na gaba, lefe ne aka kawo wanda inna ta aike su aiken da ta san zasu jima, suna dawowa suka tarar da wasu rantsatsun lefe na mamaki, wa.inda suka firgitasu, lefe ne na alfarma sannan inna taki shaida masu kan lefen saima takursu da ta yi kan a yi masu kitson amare da kunshi Wujdane fir ta sakawa idannuwanta toka kan bata yarda da wannan tatsuniyar ba, ba za.a yi mata kitso ba, da kyar ta amince aka yi mata kunshin shima inna ta nuna mata jan ido sai Aisha ce aka yarfawa kitso da kunshi abinta Zaune suke bayan salar magariba, du sun yi shiru suna tunani ba mai cewa dan uwansa ufan, inna ba komai ke yi mata yawo a can kasan zuciyarta ba sai shin inna dangin mahaifinta ne? Ance yana da dangi guduwa ya yo daga garinsu kan wani dalili daban, yai gashi zata aurar da yaya anman daga ita sai makota sai yayan a cikin gida? Sosai ta rufe kanta a daki ta ci kuka na ban mamaki ta gode Allah kan wannan rayuwa tata Wujdane ta yi shiru, tunani take inna lukman ya shige kwana biyu ne? Mai ke damunsa ba zuwa ba labari? Inna ya shige ne? Wannan shi ya tsaye mata a rai domin itafa a gaskiya tana jin soyayarsa a can kasan zuciyarta , Aisha kuwa tunani take na faduwar gaban da ta tsinci kanta a ciki, ta yi imanin dan zata rabu da yayarta ne hakan ke faruwa da ita shi ya sa ta matso sosai jikin wujdane ta dora kanta saman cinyarta tana sauke ajiyar zuciya Ranar Daurin Aure................. To jama.a Shin ina Lukman ne? Zai fito ne ko yaya? Yaya makomar daurin Auren Wujdane ne? Alaidine bai yiwa kansa shigo shigo ba zurfi ba kuwa? Domin Alaidine ya tarwatsa auren Wujdane da Kanninsa Jamail du da irin yanda ya dauki soyaya ba a bakin komai ba, bayan ya kula kyakyawar alaka tsakanin mahaifinsa da Malan sannan ya manta haihuwarsa aka yi wato an isa da shi? Ina Jamail ne? Ina ya shige ne? Jamail kuwa fa haka za.a barshi? Comment dinku ninkin typing😲🤪🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🌚🚶🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀ [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *19* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Ranar daurin aure A kofar gidan Malan, shinfidar tabarmi ne na leda , kofar ta sha shara kalkal da ita Daga cikin gida kuwa jama.ar ba wani yawa ne da ita ba, yan anguwa ne sun shishigo, sai kawayen su Aisha da ta gayata Ausha ta sha kwaliya, ma.abociyar kwaliya ba, ta hade cikin atamparsu ita da wujdane wada Malan ya saya masu domin kayan cikin lefen nan ba.a ma taba su ba Zaune Wujdane take, ita kanta ba zata fasara irin halin da take ciki ba, aman aure komai taurin zuciyarka sai ka ji ka yi lakwas, zuwa wannan lokacin ne tunani kala kala ya fara darsun mata harma ta yiwa kanta tambayar shin mai ke faruwa da ita ne? A cikin dakinsu suke, sun dage labule da window, yan mata sai gwali ake inda Aisha ke tsakiyarsu suna shan shapter Wujdane kuwa na gefe tana dan murmushin da iyakarsa lebenta Ta rasa mai bata amsoshin tambayoyin dake daskare a can kasan zuciyarta Dirar motoci kake ji da karan babura da mai lasifika a hannunsa yana isar da karasowar jama.ar ango dan daura aure Tsuru suka yi da Aisha da Wujdane, domin da mamaki, motocin nan fa? Duda malan mutumin mutane ne, aman hakan bazai fasara musu tarin motocin da ake ta rangadadin karasowarsu wai harma da masu daukan vidio dan sakawa a tv A bada guri ga baban yayan ango, Elhaj kowa, Elhaj ganninka an huce, Elhaj kaji da nasu ka ji da naka, farin zaki mai hakoran dinary, gaba dai gaba dai dawisu mai kyan kwaliya, na je haji iyalina sun je muna godiya, Wannan mai lasifika ne ke tarban Alaidine wanda Aba ya rigaye shi karasowa, shi zai zo da sadaki da komai na daurin auren kannin nasa Zazaune ake, malan idannuwansa kyam a kan hanya, ba komai yake hange ba sai ta ina Lukman zai bilo ne shi da jama.arsa? Bayan ya kwana da sannin yau ne, sannan an sanar masa sai an daura nasu kafin ake daura dayan Abinka da birni, jama.a har sun fara dan kosawa domin kowa da shagalin gabansa tumba yan anguwar da suka zauna wajen malan ba sai tambaya ake ina dayan angon da yan uwansa gashi har an dora awa a saman lokacin da za.a daura auren Uzuri malan ya nema , na hanyar fadin mai yiwuwa go slow ne ya hade a hanyar zuwan su aman a bashi dan lokaci zai nemi yaron Mikewa yayi cikin shigarsa ta alfarma, wada Aba ya yi masa dinki na mutunci ya bashi a matsayin dinkin fitar biki ya shiga cikin gidansa inda direct ya shige dakin yaransa yan mata Yana shiga yan matan suka fara ficewa a dakin suna bashi waje Idannuwansa ya sauke kan Wujdane cike da tarin tausayinta, sai a yau yake tuhumar kansa shin gazawa ne yayi da halayar wujdane har ya yanke hukuncin yi mata aure da gagawa haka har gashi ana nema a wulakanta ta ko me? Shin bai dauki rayuwar wujdane a matsayin kadarar da Allah ya dora masu ba be ya lamunce yanda take ne har yaa saka gagawa a lamarinta bayan ya kwana da sannin gagawa aikin shedan ce? Ina tunaninsa ya je har ya bari fushinsa yayi rinjaye a yarsa mafi soyuwa a cikin zuciyarsa? A hankali ya karaso daidai lokacin da inna ta shigo, itama ta sha shigarta ta alfarma ta zauna tana kallon yannayin mijin nata murya a raunane ta ce" Malan, ni lafiya kuwa ake kananun magangannun ne? Dago da kansa daga kallon yayansa da suka zubo masa idannuwa ya yi, ya hadiye wani yawu mai wuyar fita , a hankali ya ce" innar yara, yaron nan ne shiru na wajen Wujdane, ko lafiya? Gabansu ne ya fadi gaba dayansu, Wujdane ta jimke hannun Aisha wace jikinta ya dauki dumi ta kontar da kanta saman bayan Aishar tana wani nishi ciki ciki na bacin rai Malan ya ce" abinda nake so da ku shi ne ku gaba dayanku shine kar ku yarda ku tayar da hankalinku kam komai, ku yi tawakali da dukan abinda zai samu bawa mai kyau ko mara kyau kadararsa ce daga ubangiji, ki zauna da su bara na je kawai Mikewa Malan ya yi ya fice, zuciyarsa a matukar karye ya fita wajen jama.ar dake zaune abin har ya zama na magana sai dauka ake danma wa.inda suka zo da Alaidine basu tarki yin wani cece ku ce bisan lamarin ba suna dai mamakin danme idan dayan bai zo ba ba za.a daura da daya ba? Zama Malan ya yi, inda a hankali ya dan duko da kansa wajen Aba, da kuma Malan ishak ya ce" ina gannin Elhaj kawai a daura Na Jamail din, domin wa.innan basu da niyar zuwa, da alama ko sun fasa ne Kafin Aba ya yi magana sai ga karan wani tsohon babur furrrrrrrrrrrr ya tunkaro anguwar, direct wajen jama.ar ya karaso, sai dai abin mamaki Lukman ne a saman Babur din nan Suturar jikinsa yau kam ba tsari, Lukman mai son wanka yau kam ba wannan daukan wanka Bai damu da irin yanda aka zuba masa ido ba, haka ya sauko ya ratso har gaban malan kafin yake zubewa nan kasa Du girma irin na Lukman ya saki kuka mai cin zuciya yana bin jama.ar dake wajen da ido Kallonsa Malan yake bai iya hana shi kuka ba, saima dan langwabar da kai da yayi Abdul Fatah ji yake kamar ya kama da wuta a zaunen nan da yake, yana son yin magana aman Hamza ya tsare shi da ido Hamza ne ya mike ya karaso wajen da Lukman yake ya kama shi ya mikar da shi, suna kallon juna ya ce" Lukman, lafiya? Mai yake faruwa haka ne? Lukman ya sada kansa, yafi son su kasance daga shi sai Malan sai wujdane dan sirinta abinda ke faruwa, hakan ya bukata sai dai ina , malan ji yake daga inda yake ba zai iya motsawa ba Aba ya dago da kansa ya mike a hankali ya ja hannun lukman, domin a duniya komai yana bukatar sirri, koma menene, sannan a yau rana ce ta zulumi.cike da zuciyar Malan, gannin Hamza ba zai dauki wannan ragamar ba, Malan kuwa zuciyarsa bukunta ya matar masa da jiki ya saka Aba mikewa inda ruuu aka bi su da ido harda Alaidine da ya cika da mamakin shi kuwa Aba ina ruwansa, daman ya za.a yi ya gama mora a waje sannan ya aura? Yayi yaya da ita? Shi ai ba mahaukaci bane, da gani a yanda ya gama shagalinsa da ita yanzu zai zo masu da wani bayani, shi dai komai za.ayi ba zai yarda Aba ya canza abinda yayi niya ba, wato ya aurawa Jamail Wujdane haka kawai a bata masu zuri.a? Haka kawai? Ai yau za.a yita ne a wajen nan Lukman na kebancewa da Aba ya shiga koro masa bayani kamar haka" yau kwana biyu da mahaifina ya dauran aure da yar uwata, bisa sharadin sai an auran ita za.a barni na auri Wujddane, du ban fadawa su Malan ba domin ona son Wujdane bana son abinda zai rabani da ita, tun jiya nake gannin abubuwan da basu dace ba, inda mahaifiyata ta bukaci na jawo kudin sadakin Wujdane din su adana, Kawai ina zaune nake jiyo magangannunsu suna labarin ai lefe ma da na tara na wujdane aka ce min an kawo ashe ba ita aka kawowa ba gidan su yarinyar da aka aura min suka kai, karshe ma kudin sadakin na Wujdane da na bayar ajiya mahaifiyata ta sayo keken dinki da kayan dinki wai zata shiga koyon dinki da na auro mata yar iska Hakan ya bakantan rai na ritsasu cike da bacin rai na saki yarinyar saki daya, Wannan ya tunzura zuciyar mahaifana suka yi rantsuwa da idan dai na zabi auren Wujdane ba ni ba su duniya da kiyama Hakan ya tayar min da hankali, ya fitini tunanina, ya fitar da ni a nutsuwata, ba inda ban je ba dan a zo a baiwa su mahaifana hakuri aman abin ya ci tura shine tun jiya zuwa yau na zama tamkar mahaukaci yawo kawai nake, ni yanzu ga sadakina na samo a aura min ita kawai mu yi tafiyarmu shikenan Sauraronsa Aba yake cike da tausayi, sai kawai yake gannin kamar rayuwarsa ke maimaituwa a nan, Kamo kafadunsa ya yi ya ce" karka yarda, koda wasa karka kuskura ka ki bin abinda suka fada, tunda har kai kadarar taka ta fito a haka, ka rungumeta kawai Lukman, ka sani a duniya babu kuskuren da zaka tafka sama da take maganarsu, Wujdane dai mace ce wada take gaban iyayenta, ysu ba zata kaunaci namiji ya tsameta ya kaita a rayuwar wahala ta gaban abada, shin baka tunanin abinda zaka cewa Allah? Da ace mahaifinka ya aminta ni zan dauki nauyin aura maka Wujdane, aman ina hakinsu dake kanka? Aljanarka tana karkafin digadigensu, basu kore ka ba, zabinka ne bai yi masu ba, ka nutsu ka farka giyar soyaya ke dibanka, babu innuwar da ta kai ta iyayenka lumshi da dadi ko a nan duniya bale a kiyama, lale auren wace ake so yana da dadi aman kuma zaman lafiya da iyayen mu ya fi dadi dadi, Lukman idan ka samu nutsuwa ga numberna ka nemi gidanna mu tatauna, ni ina baka shawara ne wai ba a matsayin dan na girme maka ba aa, sai a matsayin wanda ya san me hakan ke nufi, dan haka idan muka zauna zan baka tarihin rayuwana Wani irin sanyi jikin lukman ya yi, ya dubi Aba kimar Aba kadai zata haneka karyata lafuzansa hakan ya saka shi fadin" Malan fa? Kenan na bashi kunya? Wujdane fa? A me zata dauke ni na cuce ta ? Elhaj ka san hausa yanzu abinnan sai ya yi ta bin Wujdane har ka ga ta rasa miji a sanadina? Aba ya yi murmushi ya dafa kafadar Lukman ya ce" *ALLAH ZAI HANA* Yana gama fadar haka da hanzarinsa ya dawo ya bukaci a nutsu za.a daura aure Hannunsa ya mikwa Alaidine ya miko masa kudin sadakin Jamail Aba ya juyo ya raba kudin hannunsa gida biyu wato dubu hamsin hamsin, ya mikawa malan isyaku ya irga ya ce dubu hamsin, ya sake miko dayan ya irga ya ce" wato dubu dari kudin sadakin.... ABA ne ya katse shi da fadin " *AA, DUBU HAMSIN BIYU, WATO KUDIN SADAKIN YARINYA BIYU, YA JUYA WAJEN MALAN YA CE" MALAN INA NEMAWA YARONA........* 🌚 [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *17* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Kallo suke yi masa na rashin fahimtar inda zancensa ya nufa, Zuciyarsa yake dana, tunda ya fara ai sai ya gama, a hankali ya dan matsa hularsa baya wanda ya baiwa sauran gashin gaban goshinsa damar fitowa, Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Wujdane a hankali ya furta" dole na kirayi hakan da yaki, yaki ne na zuciyar mutun guda, ina son shiga yakin da na san zan jigata aman kila wa kala zan cima burina,, Aisha kam daidai wannan lokacin zuciyarta tamkar ta balo ta bar kirjinta, kallonsa take cike da faduwar gaba inda wujdane bata ma san inda maganarsa ta nufa ba Kai ta dan dafe ta ce" wai yau abinda ka tashi da shi kennan Jamail? Ka bude mana mota mu fita ka ga an fara lekowa daga bango da kofa ana lekomu na san an fara cicira mu ne, ni shi ya sa bana son matse maka guri, yanzu a anguwa za.a dauka wani abin ne har a zo anai maka tambayar rainin hankali, *Wujdane i love you* Katsewar mitar Wujdane kennan, wanda yayi daidai da wani irin bugawa da zuciyar Aisha ta yi, haka zuciyar Jamail ta shiga luguden duka ba kakautawa Shatata Wujdane ta yi tana kallon Jamail, ita bata ma san me kunuwanta suka ji takamaimai ba, hakan ya saka ta sakin wani malalacin murmushi tana kallonsa ta ce" ban ji mai ka fada ba? Jamail ya sauke ajiyar zuciya ya dan waiga gefen Aisha ko zata taimake shi, aman ina kanta a sade a kasa wanda ba zaka fahimci halin da take ciki ba, Juyowa ya yi yayi kundubala da tsoron dake dukan zuciyarsa ya ce" cewa na yi ina son ki Wujdane ko laifi ne?? Wujdane ta dan kada idannuwanta irin tambaya da idannun nan, tana kallonsa kafin ta furta" mai kake nufi da maganar nan naka ne? Jamail ya tsareta da ido, wanda itama cikin idannuwan nasa take kallo, ya ce" shin hausar ce baki fahimta ba Wujdane ko menene??? Wujdane ta dafe kanta da ya dauki sara mata, ta kuma dago da kanta ta ce" yanzu fisabililahi ka rasa wace zaka ce kana so sai ni? Shekara uku kacal fa ka bani a nan gidan duniya, ni kuwa ba bakin uwa ba ba na uba ba zan auri yaro? Ai ni ba zan soma soyaya bama da yaro domin ko lukman hakan ya saka na yi watsi da shi, Look Jamail, ka ga dai ina gannin girman ka, dan haka dan Girman Allah karka soma irin wannan abin ba zai fishemu gaba dayanmu ba, danme zaka yi kokarin kawo min irin wannan wulakancin daidai wannan lokacin? Shin ganni ka yi bani da mai tayawa ko? Jamail idan na yi soyayay da kai ka fadan mai na gane mai? Jamail ni idan ba shekara arba.in da biyar namiji ya yi ba, bana jin zai iya zama da ni a matsayin mata domin sai an samu mutumin da ya fara manlakar hankalin kansa kafin yake gane zama da ni a rayuwa, Please buden kofa na tafi, Kallonta yake, cike da mamakinta, yanzu shi take gannin ba zai iya rayuwa da ita ba,? A irin hakurinsa , zai iya ciyar da ita ya yi mata sutura ya biya mata dukan bukatunta na gidan duniya, shin a mai ta dauke shi? Tana nufin ya yi mata kankanta ko me? Aman ai NAMIJI BAYA KADAN , dan me zata fara fasara shi ta haka, Hannunta ta mika inda ta ga ya dana ya kile motar ta dannan ta bude ta fice abinta ta nufi wajen Mairo da ta tarbota an sha kayan sallah Kokarin bude motar Aisha take, dan ta fice itama, sai jin muryar Jamail ta yi yana fadin" Aisha ta ina na kasa? Shin menene makusata? Aisha ki taimake ni dan girman Allah ki fada min menene aibuna? A hankali ta dago da kanta dan bashi amsa, sai dai mai a lokacin da suka yi ido hudu da Aisha wani iri yanda gabansa ya yanke ya fadi har sai da ya katse tunaninsa na sakonni, A hankali ya bude idannuwansa da ya dan lumshe ya sauke su a fuskarta, Murmushi Aisha ta sakar masa ta ce" yaya Jamail baka da wani makusa, kawai sai a hankali aunty zata fahimci inda maganarka ta nufa ka ji? Kar ka sakawa kanka damuwa domin Aunty ta jima da irin wannan ra.ayi nata na cewar sai dai ta auri mutun mai shekaru shi ne zai iya rayuwar zaman aure da ita, ka yi hakuri insha Allah zanyi kokarin gannin na karkato maka da hankalinta ka ji? Cike da sanyin murya ta yi maganarta wanda ya kashe masa jiki, sam bai san dalili ba, a haka yana kallo Aisha ta bude motar ta fito inda ta hango babur din Lukman ya faka yana faman shawo kan Wujdane kan ta yi hakuri ta saurare shi Ba Wujdane ta dawo gida ba sai da ta saurari Lukman harma suka shirya kan fadan da suka yi , daga nan ma ta bi bayan mairo suka shiga yawonsu a cikin anguwar wace ba ita ta dawo gida ba sai can da dare sosai Malan ne zaune, a yau km Wujdane ta tabo masa ransa, bayan ya fada masu gaba dayansu su hadu bayan sallar magariba su yi adu.a wace sukan yi du bayan azumi, sannan a ci abinda ya samu, wannan karin harda dan akuya ya sayo da tarin kayan miya wanda sai su kadai ne suka yi adu.ar shekarar sannan suka shiga shirye shiryen yankansu suna ta shagalinsu banda Wujdane dake anguwa yawon fitinar fada Salama ta yi , wanda sai a lokacin gabanta ya yanke ya mugun faduwa, dalilin hango tarin karan dake ci ya haske tsakar gidan nasu, ga kuma gefe kai da kafafuwa na akuya a aje ga Aisha sai aiki take ita da inna gefe kuwa Hamza ne rike da wayarsa yar nokia yana amsa kira Kallon da inna ta yi mata ya sage mata gwuiwar nufar su, hakan ya saka ta nufi dakin mahaifinta dan ta bashi hakuri A hankali ta dakata ta yi salama daga kofa Kafin Malan ya amsa mata salamarta ta ji dau an fauketa da wani gigitacen mari, Kafin ta ankara ya shiga balata da kafarsa ransa a matukar bace Da sauri malan ya fito daga dakinsa ya karaso wajen Abdul fatah dake jibgar Wujdane tamkar an aiko shi su inna kuwa ko su dago kansu sai aisha ce ta mike tsaye jikinta na bari tana kallon yayan nata na dukan yayarta Malan na karasowa ya ce" aa, aa, Abdul Fatah me haka? Baka da hankali ne? Ka daina kafin na wanka maka mari fa? Du irin yanda Wujdane ta kai ga taba ran mahaifinta abu na farko ne da ya fi tsana a taba lafiyarta Cike da bacin rai Abdul Fatah ya nuno Wujdane da yatsarsa ransa a bace ya ce" Aba, shin yaushe yarinyar nan zata yi hankali ta samu nutsuwar zuciyarta ne? A yau wajen samari ana labari har ta kai an daina jin nauyin nawa a gabana ake cakalkalarsu ita da wancen jakar kawar tata, shin a mai kika dauki rayuwarki na ya mace ke wujdane,,? Ko maza a wannan lokacin suna kofar gidajensu aman ku yanzu kuka fito daga gidan mai alaro wai kun daki amaryarsa? Shin Aba yaushe zaka bari yarinyar nan a koya mata hankali? Sai fada yake yana huci inda Wujdane ke zaune dangagar a kasa tayi zaman yan bori, kuri da idannuwanta sai kallon yan gidan nasu take, ta jibgu dan jibguwa aman ba ko digon kwallah a idannuwanta sai cicije lebe take A hankali.Malan ya ce" duka ba shi ne magani ba, daga hannu da kake a kanta yana iya jawo maka raininta a lokacin da kake bukatar ta girmamaka, ni kaina a yau Wujdane ta taban zuciyata, bani da wani uzuri da zan yi mata a gabannan sai maganata ta karshe shine ta fitar da mijin aurenta nan da sati biyu kacal, idan ba haka ba ni zan yi mata miji, Malan na gama fadar haka ya shige dakinsa ya zauna yana hangen Wujdane wanda yake kokowa da zuciyarsa kan kar ya fito ya lalasheta, Itama kifar dakin nasa ta tsurawa ido, zuciyarta na halbawa, irin halbawar nan mai sauri sauri, da sauri ta juyo da idannuwanta ga innarsu, aman inna bata kallonta daga karshe ma innar daki ta shige, yayi sauran daga ita sai yayunta da kanwarta wanda cikinsu idan ka cire Abdul fatah kowane ji yake kamar ya rugo ya rungumeta ko zata daina jin zafin dukan da aka yi mata, Hamza kuwa cike yake da jin haushin dukan da abdul fatah ya yi mata duda ya hana shi daga hannu samanta aman shine zai yi ta kwalo da ita a haka din nan baya gannin yanda jikin wujdane yake tamkar na jariri zai kama dukanta haka Wujdane ji tayi wani abu na bun fuskarta, a hankali ta kai hannunta daidai gurbin idannuwan nata ta lalubo Da sauri ta kai idannuwanta tana kalo, eh da gaske hawaye ne, hawaye ne take , hawaye ne a fuskarya, ai bata san lokacin da ta mike tsaye ba ta....... Readers, i.k so sorry, hidindimu ne suka yi min yawa, insha allah da na samu sasauci page zasu ninniku sannan a kan lokaci, daga sajidarku [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *20* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Aba ya ce" Malan Laminu ina nemawa dana *Alaidine* auren yar wajenka *Wujdane* A tare suka dago da Malan da Alaidine, wani irn faduwa da gabansa ya yi har sai da ya dafe kirjinsa, ya dago da dara daran idannuwansa daga wayarsa da yake duba ball da aka yi Barça da Reel, a wani haukace ya juyo wajen abansa wanda ya yi masa kallo daya ya dauke kansa ya mayar wajen Malan Laminu wato Malan, da malan ishak Kamar da wasa Alaidine na zaune dangalgal a gabansa da kudin aljihunsa mahaifinsa ya daura masa aure da yarinyar da a ranar da ya ganta tsanarta ta darsu a ruhinsa, a yanda ya fahimci rayuwarta bata da kamun kai har tana furtawa namiji ya yi mata kadan kennan ta san mazan ne, yarinyar da shi bama zai nuna kamaninta ba, yarinyar da kanninsa Jamail ke so kamar ya mutu, yarinyar da yayi yanda yayi dan karta shigo zuri.arsu a matsayinta na wada sam bai yarda da lamarinta ba, yarinyar da a duniya idan da akoy abinda zai nuna da kyama toh tabas itace domin kawai haka ta darsa masa rayuwarsa a zuciyarsa sai gashi An daura auren *Elhaj ALAIDINE abdul kadri, DA WUJDANE Laminu bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan* , da *JAMAIL ABDUL KADRI DA NANA AISHATU LAMINU A BISA SADAKI NAIRA HAMSIN LAKADAN*, Nan fa ya ci gaba da yadawa ya zo kan soron gidan Malan ya rangada wannan labari Aisha ta zabura ta mike tsaye jikinta na wani irin bari, kallonta ta maido wajen innarsu da itama ta yi zuru cike da mamakin sunnan Alaidine da aka kira da sunnan mijin Wujdane, tambayar kanta take shin waye Alaidine kuma? Ko dai malan sadakar Wujdane ya bayar? Wujdane ce ta fado jikin inna, ta kankameta sosai domin wani irin sanyi sanyi ne yake ziyartarta, da wata irin faduwar gaba, kanta yayi mata wani irin nauyi, haka ma zuciyarta, bakinta yayi wani daci ta rasa gane kanta, a hankali ta dago da idannuwanta da kwayar cikinsu ke ta wulgawa tamkar zasu fado, zufa na keto mata ta zube idannuwanta cikin na mahaifiyar wace itama sak irin idon Wujdane din ne , murya a shake ta ce" innata, Lukman dina bai zo ba ko innata? Innata wanene *Alaidine* kuma???????? A hankali Aishama ta fado samansu itama ta saki kuka, kuka na abinda ya riske ta, farin ciki take da bakin ciki, idan ta tuna Jamail ba ita ce a zuciyarsa ba, ta tuna halin da yayarta ke ciki sai ta ji komai ya fice mata, idan kuwa ta hango ita Aisha itace matar Jamail muradin ranta sai kawai wani dadi ya rufeta, hakan ya hadun mata ya bata wani irin nauyi a zuciyarta itama ta fashe da kuka Inna sauraron magangannu take, yanda ake kaikaikai ku leko ku ga wanda aka daura aurensa da Wujdane, iye lale Allah na sonta, kaikaikai aman shima bai sani ba mahaifinsa ne, toh dama auren harda na Aisha? Toh sunnan mahaifinsu daya ko dai yayan mijin Aishar ne, aman ba.a ga mijin Aishar ba, iye angon Wujdane din ya tafi a mota a guje kamar baya son auren, Rungume yayanta ta yi a jikinta ta saki labulen dakin ji take tamkar ta fita ta cewa jama.ar tsakar gidan su tafi ya isa hakanan ta gode, sai dai abin haushi yanzu ne ma wasu ke kara zuwa dan gulma A kofar gida kuwa wasa sabon kallo, shagali kawai ake, sosai da sosai, daga nan aka kwasa dan zuwa masalaci wajen sauka, zo ka ga malan da Aba fuskokinsu fayau shagalinsu kawai suke suna amsar barkar da aminnan arziki ke yi masu Dugunzuma suka yi inda Malan bai samu damar shigowa dan ya karawa inna bayani, harda su Abdul Fatah du suka yi masalaci kowane na mamakin wannan iko na Allah ( haka ne, wani baya auren matar wani, wani baya haihuwar dan wani tun ran gini tun ran zane ) Wuni aka yi gidan inna ana ta dafe dafe na abubuwan da ya sawaka, makota sun bude ciki sun yi nak, domin a gidajensu ba samun hakanan zasu yi ba, kowa mamakin ana dafa shinkafa da makaroni a sabgar gidan Malan sai kace wani atajiri harda nama da isasun kayan miya, idan ka ga yanda jama.a ke wawa sai abin ya baka mamaki Kawayen su Aisha sun yi gefensu daban sun dora tukunya a zuwan na yan matan amarya ne Kamar daga sama wajen yama sosai kake jin murya sama sama na tashi, ana zubar da tijara kala daban daban, muryar ta mutun biyu ce hakan ya saka inna a hankali ta sauke su Wujdane daga jikinta ita a tunaninta baci ma suka yi sai dai ta ga Wujdane ta bita da ido, a ranta tana mamakin taurin rai irin na Wujdane har yanzu ta ki ta yi kuka sai dai zuru zazabi kuwa ya rufeta ruf Inna na fitowa ta ga wata datijiwa ce da jan hijabinta, sai wata budurwa ita kuwa da bakin hijab, cikin shigarsu ta mutunci shigarsu ba wani tsiraici ko rashin mutunci a cikinta, sannan masha Allah a wanke kal da su Budurwar ce ta yiwa inna kallo daga sama har kasa ta ja wani uban tsaki ta juya wajen datijuwar ta ce" gogo ai inajin wannan itace uwar yar iskar domin a yanda aka kwatantata ance kama da aljannu ne da su Juyowa Gogon nata ta yi ta ce" ohoooooo aho itace, to yayi daman ke muka zo ganni, ke yanzu in ba rashin hankali ba, yar taki ta gama yawon anguwa anguwa gida gida, ance watarana bama a gida take kwana ba idan tayi daren yawonta, shine kuka yiwa yarona asiri kuka shanye mana shi har ya kasance baya ji baya ganni sai ita ko? To ta Allah ba taku ba domin Sabra aka aura masa kuma itace matar Lukmanu har gaban abada, mutanen banza mayu, idan ba son zuciya ba baku haifa min dan ba baku rainar min ba aman da anga yana da dan abin hannunsa hikenan an like mas har ana tarda hi wajen aikinsa dan a kara damke hi? Ai idan takamarka sauko wani a kan hanya ya kwana Inna kam yau ta ga rana gannin idonta, a yau ta ga jarabawa kala daban daban, a hankali ta matso tana kokarin gannin ta kontar da wannan tarzomar, ta shiga lalaba su Mahaifiyar Lukman Sabra matar da aka aura masa aman sai tirjewa suke suna kara zubar da rashin mutunci suna zage zage , ba inna kadai ba harda Malan sai sun kama sunnansa su zuba rashin mutunci Du taron jama.ar nan dake wajen bikin kawai an taru kowace na dauka da idannuwanta , da kunnuwanta dan ta ji dadin bayar da labari, ba wace ta yi yunkurin shiga, ba abinda ya kawosu kennan ba, shigarwa wani fada? Aa, inna baiwar Allah zuciyarta ta karaya haka hawaye ke silalo mata wani na korar wani tana sharewa tana kokarin basu hakuri kan su tafi Wujdane ce firgigit ta mike zaune, ta sauke idannuwanta saman Aisha dake zaune jikinta na bari, tana son fita tana tsoron maganar anguwar nan nasu, mai za.a ce da su idan ta fita? Dama an yi masu sunna yau yau din nan idan ta fita ai sai a kara a sama A hankali Wujdane ta yunkura ta mike, hijabin dake jikinta ta cire inda gashin kanta ya yi lambar a gadon bayanta da dan ribom dinta, doguwar riga ce aka yi mata ta atampa wace ta yi mata das a jikinta ta fitar da wani kyau nata, idannuwanta ba kwali aman kamar ta saka, lips dinta kuwa ainahi ma pink kolor ne ga cicije su da ta wuni yi sai suka kara yin ja suna sheki abinsu, idannuwanta sun rufe da wannan tijara da take tsintowa, Yelemun kuwa tana daga labulen dakin ta ga du yan anguwar sai kus kus suke suna dariya kasakasa, yan matan amaryar kansu sun cakulu da su , innarta na faman ta tsayar da rogimar aman wa.innan mata biyu tamkar zugasu take Yaye labulen dakin ta yi gaba dayansa ta fito ta karaso gaban mutanen su duka ta ja ta tsaya, Idannuwanta ta dago ta yarfawa Sabra dake magana wace tsitttt sai da ta katse maganar nata kafin take ci gaba daga inda ta tsaya tana kara matsawa kusa da mahaifiyar Lukman Ai gogo kin ganta, irin jan fatan nan karuwan kasashen waje an gama shaye shay............ ......tsittttty kake ji maganarta ta katse, da sauri du aka kalo Wujdane wace ta dauketa da mari, du sai mamakin daman haka wujdane ta keru suke, Gaba dayanku kowace ta tatara ku fice a gidan mu, walahi talahi yanzu yanzu ko na gwada maku na fi ku rashin mutunci yan kwal uba kai, Wujdane ce ta fada idannuwanta kyar a kan daga iyayen har yayan, Gannin sun tsaya suna shewa ana tafawa ana kallonta irin an raina maka hankalin nan ya saka ta juya da gudu wajen murhu da ake dori, Wujdane bata damu da zafin tukunyar da suka kuma dorawa ba ta ruwan zafin ta dora hannunta ta tunkude tukunyar, marfinta ta dauko ta shiga kwasar garwashin da yayi jajajir yana ci da itace ai kuwa tace da wa Allah ya hadata idan ba su ba Nan da nan sai ihu da kururuwa ya tashi na jama.a haka suke fitowa a guje ita kuwa kamar sabuwar kamu tana nufosu tana dana masu ashar ranta a matukar bace tana fadin .......? [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *23* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Haka suka raba dare ba wada ta samu rintsawa a cikin su , Kamar yanda suka saba gidan inna tun karfe shida suka fito falo, nan fa suka nemi kayan aiki wanda Lami mai taya Mom shara da wanke wanke ta gama sallah tana jan carbi ta basu kayan aikin tana mamaki a ranta, amaren ne zankada zankada haka da su zasu yi aiki? Gum dai ta yi da dan bakinta gulma na cinta Fitowa suka yi daga kicin din domin tare suka shiga ta fitar masu da kayan aikin harda na goge goge bayan shara Falon Mom ba dai girma ba, hakan ya saka su rabuwa suka kamo gefe gefe suna shararsu Aisha ta cire hijabinta ta ajiye nan kasan capet din inda Wujdane kuwa ta daure shi a tsatsonta dan su yi aikinsu cikin nutsuwa Cikin kankannin lokaci suka hade sharar waje guda kafin suke raba abin gugar suka kamo tun daga lungunnan wanda rabonsa da hakan tun sallah Daga masalaci suka sauko, kiran gagawar da Aba ya yi masu, Alaidine ne da Jamail sai Aba Aba ke gaba, Alaidine na biye da shi a baya sai Jamail, kowanne da carbinsa yana dan ja Zuciyar Alaidine cike take da tambayoyin kar dai a je Aba kiransu ne yayi su tafi da matan da ya kakaba masu? Aba kiran menene wannan ya yi masu haka? Lafiya tun karfe biyar ya umarcesu da yake abin hawa ne da su, gashi yanzu asuba na yi zaka ga musulmai na ta fitowa domin zuwa masalaci, dan haka yana bukatar du gabatar da sallah a masalacin anguwarsa dan yana son yin magana da su, abinda dai ya fi basu tsoro gaba dayansu shine aba ya kasa hakura har safiya ta yi ? Suna shigowa gidan ya kara umartarsu da su je , wato su biyo bayansa ciki Aba ya fara sako kafarsa falon da salama a bakinsa, domin koda ba kowa ya dace du musulmi zai shigo waje ya yi salama, balatana ya san Momyn yara da kuma sabko dan ta yi masa break, aman me, sai yan mata biyu yake ganni suna ta faman gugan capet Da sauri Aisha ta janyo hijabinta a saman kujera ta zurmuka wanda hakan bai bata damar mikewa ba, Wujdane dake zaune dangalgal saman nata ta saka hannunta tana ja , tana ja , gannin ba zai fito fa ya saka ta mikewa tsaye a hankali kanta a kasa , gashin kanta da aka yiwa parking har gaban goshinta ya zubo sosai daga gaban rigarta har ya fice tsayin wajen mamarta, Zani ne a jikinta wanda ta tumurmure shi da hijabin, kokarin koncewa take harda zannin dan dimaucewa da gannin maza har uku wanda Jamail ne kadai ta sheda a cikinsu , domin ko Aba ita bata taba haduwa da shi ba Kamar wanda aka dasa yake kallonta, gannin abinda take shirin yi ya saka shi sada kansa kasa sosai tamkar yana gaban hukuma kuma ya aikata laifi, tsaki yake ja can kasan zuciyarsa na wannan bata da hankali zata kuncewa mutane wani bakin zani, domin saman doguwar rigarta ne ta dora zannin Lami mai dati dan kar abayarta ta yi dati Aba kuwa tuni ya haye sama dan kiran Mom, Jamail kuwa juyar da bayansa ya yi tun lokacin da Aisha zata saka nata hijabin yana irga bugun zuciyarsa, Lalalalala, na shige su yau nayi baci har haka , kai gajiya da bashin baci basa barin bawa sai sun bi shi, ohohoh ni yasu jikarsu har yayan nawa suka tafka aikin nan? Dan na san Lami dai ba guga take har can ba, Tana yi tana karasowa domin sai a lokacin ta gama azkhar, danma jiki da sabo shi ya ta tashin domin an gaji iya gajiya A tare suka kai kasa Aisha da Wujdane suna gaishe da Mom da Aba wanda a lokacin sun fahimci shine Mahaifin su Jamail Amsawa yake cike da kulawa, yaran sun shiga ransa domin da gannin dan yannayin da suka nuna suna da tarbiya ya samu mai gaishe shi haka a tsugunen nan har kasa abinda baya samu wajen sauran sirikansa Mom kuwa kamo su ta yi tana mikar da su tana amsawa , ta nufi kujera da su ta zaunar da su , babar kujerar dake facing din su Aban Tana juyawa suka silale kasa saman capet din suka zauna irin zaman makaranta A rayuwa idan Alaidine zai gaisar da mahaifiyarsa sai ya duka har kasa, wannan haka ya taso tun yana yaro bayan ya gama gaisar da ita a tsugune sannan yake zuwa ya rungumeta a jikinsa yayi dan lamo, baya taba daina hakan ko daya a rayuwarsa Yauma hakan ne ya yi , daga karshe ya rumgumeta a jikinsa yayi shiru yana sauke ajiyar zuciya, uwa uwa uwa, ita ce mace kwaya daya da ya san idan ya rungumeta ba zancen cutarwa da zai biyo baya ko ta danna mai wani mugun abin ko idan rigimarsu ta hada su ta kiraye shi da *Shege* Haka Jamail ma ya gaisar da kowa, kanna ya dan juyo wajen su Aisha da Wujdane, muryarsa a dan sake ya ce" aa, yau su Aunty Wujdane anyi kwannan gidanmu? Mom ta yi murmushi ta ce" aa, gidanku fa? Kai ai ba yauba muka mika ka wajen yayanka, yau shima zai mika ka wajen matarka ai yanzu kuma yanzu zaka san an yaye ka da gaske, Dan sinne kansa ya yi, wanda jin ance yayansa ya saka Wujdane dan dago da idannuwanta wajen mom inda take tunannin nan yake yayan nasa, sai kuwa suka hada ido, domin so yake shi sai ya tantance ta ya ga abinda ke kayar masa da gaba a wajenta Wani mugun kallo, irin kallon kaskancin nan ne ya wurga mata, wanda a take a lokacin gabanta ya yanke ya bada bam, ya gama bata mata rai, bata wani dauki lokaci ba ta zabga masa wani uban harara ta kawar da kanta, ta mayar wajen Aisha da ta lalubo hannunta ta rike jikinta na dan bari, tsoro ne ya darsun mata a kasan zuciya na yanda Jamail bai ko kali inda take ba, baiyi mata wata magana ba Mamaki kamar ya kashe shi, a kasan ransa yake tambayar kansa wai da ni take hararan nan? Ni ta harara? Aman lale yarinyar nan bata da kunya, shine zata wani juyan ido ita ga tsaurara ko? Zata gane bata da kunya ne Aba ya gyara zamansa ya ce" asalamu alaikum warahamatulahi wa barakatuhu A tare suka amsa salamarsa wanda hakan ya saka su bada tunaninsu wa shi, Ya ci gaba" kamar yanda a jiya na yi maku bayannin yanda hulunci Allah subahannu wa.ala ya yi aiki a kan maganar auren da na dauro muku a jiya, shine zan dora da bayanaina a gaban mahaifiyar ku, Alaidine, kai ne baba, sannan a rayuwa ka yi aure aure, a yanzu haka kana zaune ne da macen aure a gidanka , dan haka aure da zaman aure ba sabon abu bane a wajen ka, sai dai sharadin a nan shi ne, wannan aure da na je na nema maka ni mahaifinka, ba talar yarinyar aka yi min ba, ba sadakarta aka bani ba, aure aka nema nata aka bani cikin ikon Allah bisa hanyar da musulunci ya hukunta mana, Alaidine a jiya na fada yau zan maimaita, ban lamunce maka sakin yarinyar nan ba, kamar yanda ba zan tauyeka kara wani auren ba, Alaidine ka ji tsoron Allah , ka kare mutuncin kanka da na iyalinka, ka nemi lahirarka ka manta da du wani shirme *Wujdane* Aba ya yi kiran sunnan Wujdane wada ta dago da kanta a hankali tana amsawa a hankali, can kasan ranta tana fadin" shi dinma auren ne da shi kennan, ABA ya ce" wannan shi ne mijinki da aka daura maku aure jiya, shi dai aure ibada ne, wato hakuri hakuri da kawar da kai, da kaskantar da kai, ta haka zaka cima burinka cikin ruwan sanyi kin ji? Ki yi hakuri, ki karbi aurenki, ba yanzu zaku tare a gidanku ba, domin na fada masa tsarin gidansa ba na ajiyar mace biyu bane, ko ya kara wani ginnin a ciki ko da gidajensa ya saka a gyara guda ku tare kamar yanda aka shiga gyaran na su Jamail Sai kai Jamail , ina so ka sani du dan adam Allah yakan jabartarsa ta hanya daban daban, idan ya yi hakuri ya jure zai ci ribar jarabawar cikin ruwan sanyi Komi kake ciki ka mika lamarinka ga rabil izati, ka rungumi aurenka , kar ka wulakanta yar mutane, sannan yanzu ka fara shiga rayuwar auren ka yi kokarin shinfidata da kyawawan dabi.u dan kuwa abinda ka sabawa kanka da matarka zaka ga da kowace ma hakan ne, aman idan da fahimta da dadin rai zaka ga aurenka shine babar kyautar da Allah yayi maka ta saka nutsuwa farin ciki a rayuwarka domin aure ga wanda fa ya bi koyarwar ma.aiki ni.ima ne, nutsuwa ne, farin ciki ne, dan haka ina mai shawartarka domin idan kaima na ji wata baraka ba zata yi mana kyau ba daga kai har ni *Aisha* nana Aisha, ki yi koyi da halayen mai sunnanki kin ji? Ki kasance mai hakuri mai biyaya kin ji? Karki raina mijinki ko abinda ya kawo maki, ki tausasa lafuzanki ki kyautata halayenki zaki ga da kyau a rayuwarki kin ji? Amsawa take kanta a kasa, wanda har wani hawaye yake zubo mata a kumatunta, Mom ta ce" Allah ya saka da alkhairi Aban yara, Allah ya biya mun gode mun gode Aba yana amsa mata yana yi mata dan murmushi Kiran Lami Mom ta yi [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *21* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Kallonta kawai inna take, inda Aisha ta fito da gudu ta ja ta tsaya itama domin du sai wani tsoro ya darsun masu kar a je ta haukace Ba wujdane ta tsagaita korar mutane ba sai da kowa ya fice a gidan ta bi bayansu ta jawo dan kayuran gidan nasu ta rufo ta saki dan yololon labulen dake kara rufe gidan ta juyo da marfin tukunyar nan a hannunta da garwashin nan a ciki, ya dauki zafi iya zafi ko da kalo zaka gane Tana shigowa tsakar gidan da sauri Aisha ta matsota da niyar karbe marfin sai dai ina, yayi zafin da ba zata iya kama shi da hannunta ba, Da sauri inna ta karaso ta karbe ta juya tana ajiyewa ta juyo sai suka hade da Wujdane ashe biye take da ita zungwai zungwai, Inna na juyowa Wujdane ta fada jikinta ta rukunkumeta, ta ja wani numfashi mai nauyi, Innna ta rufe idannunta, da sauri ta ciro Wujdane a jikinta ta dagota, murya a raunane ta ce" Wujdane ki yi kuka kin ji? Idan kana jin ciwo irin haka kuka kake yi sai ka ji sasaucin zuciyarka, ki dan zubar da hawaye koda kadan ne sai ki ji kin saku Danine, Kyafta ido kawai take, can ta dafe kanta ta ce" inna kaina ciwo, sannan ta dafe kirjinta ta ce" inna nan dina ma ciwo, inna ina jin ciwo sosai Inna ta rungumota jikinta sosai, a hankali ta ce" kin san Wujdane, muna sonki fa, kar ki yi tunanin iyayenki basa sonki, da farko halayenki muka guda, daga baya muke jin tsoran yanayinki, aman karki dauki wannan abin da ya faru a yau ki kakabawa zuciyarki kin ji? Ki dauki hakuri ki sakawa ruhinki ki yi imanin cewa kadarar ki ce, Allah ya rubuto haka zata faru ne da ke Wujdane, ba wai dan mun tsane ki ba, kar ki ji haushin mahaifinki, ni na tabata idan ya dawo zai zo mana da dadadan albishir domin Wujdane kin ga tun ina yarinya nima, yake kula da ni, mutun ne mai son mutanensa yana fita hakinmu, ki yi hakuri kin ji? Sai a wannan lokacin zuciyar Wujdane ta karaya, wata zufa ta karyo mata, bugun zuciyarta ya karu, ai kuwa sai ga hawaye wasu na korar wasu, ta buda baki da niyar yin magana sai kecewa ta yi da kuka, wanda hakan ya yiwa mahaifiyarta dadi, ko ba komai zata samu sasaucin zuciyarta ,Alaidine, Tamkar mahaukaci haka ya shigo gidansa, yana tsayar da motar ya bude ya bar wayoyinsa da komai harda su passport dinsa da yake da niyar yin tafia a ranar, Falonsa ya ratsa ya fice sama ya nufi dakinsa na can kurya ya shige ya rufo yayi ruf da ciki Tunani yake so yayi, so yake ya tsayar da tunaninsa, so yake ya gane a wani yannayi yake ciki so yake ya farka a mafarkin da yake , aman ina ba hali, zuru ya yi ya zubawa hoton boy ido dake mane da jikin bangon dakin, a yannayinsa kamar wanda yake son fitar da wani abin a jikin hoton , ya dauki lokaci mai tsayi wanda shi bai furta um bare um.um ba Jamail ne zaune gaban tv yana kallo, duda a yau din nan ya tashi da wata faduwar gaba, aman yana dan jin karfin jikinsa kadan hakan ya saka shi mikewa ya watsa ruwa ya zo ya saka tv gaba yana kalo, Direba ne ya tsayar da motarsa a harabar gidan Alaidine, Mom ta fito inda Aba ke tsaye yana jiran karasowarta ya fito daga cikin masalaci Tana fitowa ta karaso fuskarta cike da tambaya, Aba ya gyara tsayuwarsa, ya shiga shaida mata abinda ke faruwa, Gim tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta san da kwannan zancen Alaidine fir ya ki Jamail ya auri Wujdane dan yana shaida bata da tarbiya, sai gashi abin ya kasance a shi, wato dai Wujdane ta gidansu ce gwara ma su daina jayaya da hakan Mom ta fara shiga Falon inda ta tarar Da Alawiya na zaune saman kujera tana shan fruits, ta sha kananuwan kayanta domin ana dan zafi zafi a garin, tana kalon series a tv Mom ta yi salama ya kai sau hudu hakan ya saka ta shiga , Ido hudu suka yi da Alawiya dake zaune dangalgal ba wai dan bata ji salamar bane aa, cikin tsarinta kenan idan bata san da zuwanka ba ba wani tarba da zata iya yi maka Gannin Mom bai saka ta irin zaburan nan ba, na gannin sirikinka a cikin gidanka, saima wani kara kalonta da tayi ta ce" au da Mom ce? Haba ni da naji salamar a raina nake fadin ko waye haka da wannan lokacin bayan lokacin hutu ne??? Mom ta danyi murmushi, ta ce" Alaidine fa? Yana gidan ne? Alawiya ta dan daga kanta benensa, ta dawo da kan nata ta ce" toh ni dai na ga motarsa kuma na ji kamar budewar bangarensa, aman ban san ko yana nan ba, kin san baya son ana shiga lamarinsa idan har ba shi ne ya jawoka ba Da mamaki Mom ta gyada kai ta koma ta yiwa Ba iso kawai , wanda yana shigowa Alawiya ta gaisheshi shima ba a wani mutunce ba , ya amsa yana kawar da kansa suka haura sama falon Alaidine Ratsawa suke domin du dakunan da ya shige kawai a bude ya bar su, suna yi suna salama, har suka karasa dakin da yake zaune Salama Mom ta yi ta maimaita, hakan ya saka shi dago da kansa yana amsawa fuskarsa na kan fuskar mahaifiyarsa Kokarin mikewa yake yana fadin" Mom, ke ce?? Karasa shigowa suka yi gaba dayansu, Mom ta zauna daf da shi ta kamo hannunsa na dama da ta ji ya gauraye da zafi, Aba ma waje ya samu ya zauna, inda gaba daya suka yi shiru ba wanda ya furta ci kanka A hankali Alaidine ya dago da kansa ya sauke kallonsa kan Mahaifinsa, murya a shake ya ce" aman aba, bayan na sanar maka ga dalilina na kin ta shigo zuri.armu why Aba zaka aura min ita? Ita ce fa abinda Jamail yafi so a duniyarnan bayan ku, Aba ka ga irin yanda yake ba ci ba sha ba wani walwalar kirki dan kawai ta furta masa bata son sa ina da ya ji wannan labarin? Aba kuma bama wanu daban ba sai ni Aba? Ban wani takamaiman santa ba aman na ji bana sonta a cikin gidan kanina ko a abinda ya shafi yan uwana sai gashi Aba ka hada ni da ita? Abana la bani dama na yanke igiyoyin nan da ka daura min Abanna, Elhaj Kadri bai katse shi ba, sai bayan ya gama, a gankali cikin muryar kontar da hankali ya ce" ni Alaidine danme yasa ka tsani yarinyar nan haka bayan kaima ka furta yanzu cewar bata yi maka komai ba? Alaidine ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Aba yarinyar nan munafuka ce, bata da nutsuwa, Aba ta wulakantar da kanta, sannan ai Allah ma yayi mana nuni da mu zabawa yayanmu iyaye na gari Aba Aba yayi murmushi jin ta inda Alaidine ke son bilo masa, ya ce" ka san menene Alaidine, yarinyar nan ita ce ta biyu da na je da kaina nema maka aurenta har na dauro maka cikin ikon Allah, mahaifiyar Huzaifa ka saketa dan kawai ta jefe ka da kalmomi bayan kai namiji ne, kayi karatu mai zurfi kana cikin kara yi , a musulunci an fada mana cewa mace ana yi ana tankwasota ce, a nasarance an gwada hakan, aman cikin ikon Allah sai ka zamo wani mai auri saki wanda matan da ka aura ni ban taba kawowa raina cewar wai zaka yi hakan ba, to ka ga dai Wujdane amanata ce, ni kuwa zan gargadeka da babar murya, walahi Alaidine karya kake ka mayar da Wujdane karamar bazawara, idan na kawo maka ita gidanka karshen ki ka gutsutsura namanta, aman fa na hane ka, na haramta maka sakinta Alaidine, idan ka kyautata zamanka da ita ka so kanka da nutsuwarka idan ka muzanta kuma ka san hukuncinka Mom ce ta dago da kanta gannin Aba maimakun ya lalaba Alaidine din aa, sai fada yake surfawa, yannayin tausayi ta yi da fuskarta ta ce" Aban Alaidine.... Hannu Aba ya daga mata ya dawo da hankalinsa wajenta, ya ce" na gaji da zubawa yaron nan ido yana auri sakin nan, yau da ace yana da kane mata aka yi masu haka yaya zai ji? Baya tunanin haihuwar mace a nan gaba? Ke kar na kaiki nesa Momynsu baya dora abin a kanki yayi tunanin idan hakan ya same ki yaya zai ji? Da sauri ya dago da kansa , daman idannuwansa sun gama rinewa, shi ya tsani ana jan magana guda, aman shine Abansa zai saka momynsa? Shi du duniya ai ba wanda ya kai momynsa zama mutumin kirki, sannan ira kadai ce macen da ya sani ba munafuka ba, Mikewa Elhaj Kadri ya yi ya fice, wanda bai tsaya ko.ina ba sai bangaren da Jamail yake, zuciyarsa cike da tausayin yayan nasa, aman idan bai fitowa Alaidine ta bayan gida ba ya aika ya saki Wujdane a yau yau din nan domin bata ce masa komai, A hankali Mom ke kontar masa da hankali, wanda yana sauraronta a kasan zuciyarsa yana ayana yanda zai koyawa yatinyar nan hankali, Mom ta ce" idan ma kana zarginta koda idannuwanka sun nuna maka da ba mai zama dam bace, ka yi hakuri ka rungumeta sanadiyarka sai ka ga ta shiryu son, yau da ace mahaifinka yayi watsi da ni, da yanzu bansan inda kake ba, mai yiwuwa a watsar da mu gaba dayan mu a raraba mu, Ta karashe zancen tana kallon kasa tana gannin tamkar yanzu ne abin ke sake faruwa da ita Tausayin mahaifiyarsa ne ya tsarga masa zuciya, a hankali ya dora kansa saman cinyarta ya ce" Mom, ke kadara ce, karki hada kanki da wannan banzar , tana shafa sumar kansa tace" kowa ma kadarar ce ke afku masa kafin daga bisani idan yaci gaba to wannan kuma yana neman izgili, sannan yau kowa da ka ganni yana son ya zama dan mutunci, yana son ya rayu a cikin mutunci, karka yi gagawar yanke hukunci dine,, ka bi mahaifinka a hankali ka ga dai yanda ya dauki zafi da kai, dan haka ka faranta masa kar ku fito rana fa, Shi dai sauraronta yake, sannan abinda ya sani ne bai isa ya rabu da yarinyar yanzu yanzu ba, a hankali idan hankalin mahaifinsa ya konta zai nemi ya raba auren nan, shi fa ba zai iya zama da yarinyar da kanninsa ke so tamkar hauka ba, shi yama zai iya wannan cin amanar, ga yarinyar fitsarariya ai idan ta samu hakan birgeta ma zai yi Sosai Jamail ke kuka rungume a jikin mahaifinsa, wanda ya gama jin abinda ya faru, harma Aisha na zaune a matsayin matarsa Wujdane kuwa matsayin matar yayansa, ya sani ne shikenan Wujdane ta kubuce masa, domin da wani ne aka aura mata shi sai yayi jiranta, aman sai ya fado kan yayansa kuma a yanda abansa ya fada yayan nasa ya tsaneta tamkar ransa, ya san wanene Alaidine, idan ya tsani abu ya fiya zurfafawa a lamarin hakan ya saka shi jin tsoro matuka a kasan zuciyarsa, koma wa zai auri Wujdane dinsa baya so ta wahala, duda Alaidine ya kasance wanda ya raine shi, ya bashi tarbiya, ya kaunace shi, ya bashi dukan bukatu na nan gidan duniya, mutumin da ya sha salwantar da farin cikinsa wa su, ya san ba wani rabo kuma tsakaninsa da Wujdane, ya hakura da Wujdane, aman zai roki alfarmar kar a wulakanta masa da wujdane, hakan ne ya saka shi fashewa da kuka ya rungume mahaifinsa, Sosai yayi kukansa har ya gode Allah, kafin yake tsagaitawa yana share hawayensa, a hankali ya ce" Abana, Allah ya sa hakan shi yafi zama alkhairi, Allah ya saka maku da alkhairi ya kara lafiya, Allah ya biya duniya da kiyama Wani irin abu ne ya saukowa Aban wanda ya matukar kashe masa jiki, Jamail, jamail, ba dai hakuri ba, jamail ba dai daukan girma ba, haka Aba yayi ta lalaba shi, ya samu ya dan ware kafin yake iza keyarsa ya kimtsa suka fice tare masalaci Bayan salar magariba, sosai ake ta rabon abincu na sadaka da godiyar allah, Aba ne ya zubawa Alaidine ido gannin bashida niyar tayar da motoci a je daukan amaren bayan gidan cike yake da jama.a, wanda alaidine din na can yana fama da Alawiya wace sai a lokacin ta ji mijinta yayi aure ta tare shi da koke koken sam bata san zancen ba, yayi zuru yana kallonta........ [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *22* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Idan Alaidine ya tanka mata toh tabas bangon dakin nan ma ya tanka mata, kawai kallonta yake yana mamakin yaushe ta ga damarsa har haka? Dan yayi aure sai me? Ita da ya je aurenta yayi mata alkawarin ba zai kara wata bane? Ko an gaya mata auren soyaya ne da zai ji tsoron fada mata? Jan tsaki yayi ya lura idan ya biye mata zata ga damarsa ne hakan ya saka shi mikewa ya lulobo lambar wani yaronsa samir Samir ya daga cikin mutuntatawa yake gaisar da Alaidine Alaidine ya ce" kana ji? Wajen da muka je da safe aka daura auren nan ka samu mutane ku dauki motoci a je a dauko amaren, gidan Aba can zaku je a hada ku da mutane, sannan idan kun dauko gidan Aban zaku kai su ka ji? Samir ya amsa masa yana mai fadin " yanzu kuwa oga, daman nace wai mutanen nan da suka dauki labarun daurin auren nan, suna jiran saka hannunka dan su gabatar a gidan tv Cikin karaji ya ce" kar su soma, du wanda ya yarda ya yadani a wannan abin sai na yi shara.a da shi, , kittt ya katse kiran yana huci Shiru Alawiya ta yi tana kallonsa, a hankali ta fice dan amsa kiran wayar mamarta Toh fa amare kam sun fito a amare domin inna baiwar Allah zaginewa ta yi ta shirya yayanta, da wasu abayoyi bakake wa.inda ta ciro a cikin akwatunnan nan, akwatuna dai na Aisha ne wa.inda aka yi mata na lefe daga wajen Jamail, abayoyin an mugun kawata su da duwatsu farare tun daga wuya har kasan dinkin sannan a hannuwa da bayan rigar, haka mayafansu gaba daya duwatsu ne masu kyalin gaske Turare ta fefesa masu, ba wani mak.up a fuskarsu su duka sannan ba fuskar wace take fara.a Ana haka su Malan suka shigo da su Hamza du da alamar gajiya a tatare da su Tabarmar leda katuwa inna ta shinfida a tsakar gidan wace du suka zazauna, wajen ya dauki shiru Ajiyar zuciya malan ya sauke sannan ya umarcesu da su yi adu.o.i inda Hamza ke ja suna amsawa gaba dayansu Bayan an gama Malan ya dago da kansa yana kallon su Wujdane da Aisha, ajiyar zuciya ya kuma saukewa kafin yake gyara zamansa ya ce" kunga sha.anin Allah ko? Wujdane da Aisha a wannan lamari ni bani da ta cewa sai dai kawai kamar yanda Allah ya juya abin nan haka Allah ya sa alkhairi ne aka yi, wato duniya bawa ke haukansa sai ka ga mutun na tsara idan nayi kaza sai na yi kaza da rayuwana, du a cikin hakan yana tsarawa Allah na zartar da yanda ya zana tun ran gini ne, Shi aure sunna ce, aure nada daraja madaukakiya, miji kalmar da kowa ya sani ne aman ba kowa yake daukanta a hakan ba, Allah yace da ina umartar wani ya yiwa wani sujada tabas da na umarci mata ta yiwa mijinta sujada, bauta na kaiku ku yi, ku bautu aikin gidan mijin ku domin ibada ne, ku fita a hakinsa da na iyayensa da na jama.arsa, Wujdane Aisha, ku sani neman aljanarku zaku tafi, daman ba wani kawaye kuka cika ba, bana so ku fara a yanzun, kar in ji kar in gani kuna fitar da sirin gidanku, koda wani abin ya hada ku da mazahenku ku gagauta fadawa Allah shi zai sanyaya maku lamarinku, kar ku soma kwaso matsalarku tsakaninku da mazajenku kuna fada fada mana, shi dai hakurin nan da ake jadada maku fa sai kun yi shi dole, Haka Malan yayi ta yi masu nasiha, yana kara nuna masu girma da darajar mazajensu a gare su, yana kara tsoratar da su da su kara kiyayewa, yana kara nusar da su kan su yi biyaya A haka har motoci suka zo, zo ka ga mamaki Samir sai da ya cika anguwa da motocin daukan amaren, Aba ya kara karfafa abin da mata sosai na rakiya, haka suna ji suna gani suna kuka tamkar ransu zai fita aka raba su da iyayensu wanda inna kukanta na biyu ne, da rabuwa da su da kuma kukan bata da shakikin dan uwa ko aminiyar da ta yiwa yayanta mata rakiya gidan miji, sai su sai masu daukar su haka malan ya lalabata ta shiga daki ta hade kai da gwuiwa tana rizgar kuka, tana mai yi masu adu.ar Allah ya sa wannan aure da aka yi masu gaba dayansu ya kasance farin ciki wa kowanensu sannan silar tsirar su duniya da kiyama, ita dai ta sani Aisha akoy hakuri, wace ta fi daga mata hankali Wujdane ce, ko ya zasu kaya?????? A haka har aka iso tankamemen gidan Elhaj Kadri, layi aka yi inda motar amaryar farar motar Alaidine, wace ya saka aka kawo masa ita a cikin satin nan , yana son ya fara gwadata da fita da ita idan ta karbu yayi odarta Tunda aka tsaya ba.a kashe fitilolin motocin ba, sai kyali suke suna yi suna mutuwa suna kunnuwa, hayanaya ce ke ta tashi sosai mutane sai fitowa suke ana tsatsaye Mom ce ta fito, da abayarta fara mai duwatsu, a hankali ta karaso har wajen motar ta saka hannunta ta bude marfin motar Hannun ta mika tana murmushi ta ce" Marhababikum yayana, ku fito da kafar dama da bisimillah A hankali suka fito kowace kanta a kasa, tun bama Aisha ba jinta take tamkar iska ta dauketa, Wujdane kuwa tana yi tana dan daga kanta, bata wani jin wani abin da ya fi na rabuwa da su inna, Mom ta shiga tsakiyarsu ta riko hannayensu, ji take yau ba wanda ya kaita murna, saima da Aba ya dora cewar a gidan zasu tare har ya ga hankalinsu ya daidaita, ji take yau ta samu yaya matan da take nema, jinsu take har can kasan zuciyarta A haka suka shiige ana ta rangada buda, Wani zaman aka kuma dorawa sai can aka watse kowane da murna aka sada amaren da dakunansu wanda tare suka raka kowace ta ga mazaunin yar uwarta kafin suke amincewa da baci a sabon guri Alwallah Aisha ta dauro tana bin dakin da kallo, ita tsoro ma take wai nan ace dakin da zata rayu ne? Allah kenan mai rahama mai ji kai, yanzu ita tana cikin daular nan da nepa da sanyi da kayan dadin nan haka su innarta kuwa suna can cikin duhu da yololuwar katifa , ko mai suka ci? Gagawar astagafari ta shiga yi duba da a cikin duhun itama ke rayuwarta, a haka da hasken salati basu wani damu ba, a hankali ta zauna ta shiga adu.o.i tana rokon Allah ya sakata a zuciyar mijinta, ya bata ikon kyautata masa, Bangaren Wujdane kuwa daman fashin sallah take, haka al.ada lan zo mata sau biyu a wata, wanka ta yi ta dawo ta rakube jikin bed din ta kasa hawa, carbinta take ta ja a hankali ta daga kanta sama sai ga wani siririn hawaye ya surnano mata, a fili ta furta" Lukman ka ga abinda ka jaza min ko? Mai yasa ka san ba aurena zaka yi ba takura ka shiga rayuwana? Gashi an hada ni aure da namijin da ban san kamaninsa bama bale halayarsa Lukman, dan me ka koya min jin dadin kalamanka? Ka koyan sauraronka? Ka fada min akoy namijin da zai iya jurar halayanna harma ya koya min shakuwa da shi? Ka yi min alkawarin idan mun yi aure kulun zaka kaini wajen innata , a yanzu ka jaza min wannan ka fadan wa zai kaini? Kanwata da muke baci katifa daya a yau an raba mu sannan an barmu da kadaici rayuwar yan gayu ka fada min wa zai dora kansa saman cinyana yanai min labari? Wa zau dake ni idan nayi laifi yau an raba ni da yaya abdul fatah? Wa zai yi hawaye a boye idan na yi laifi an raba ni da yaya Hamzana? Wa zai yi min nasiha kan halayana da ni kaina ban san ina aikatawa ba sai idan inna na jaje ya lalashe ni yayi min nasiha ya nunan cewa ni baiwa ce, kyauta ce daga Allah yau an rabani da Babana? Wa zai wanken kaina, ya tsare ni da rubutu kafin na konta baci, du irin yanda zan bata mata rai ta dube ni ta ce min Allah ya shirye ni yau an raba ni da innata? A ina zan ga tsantsar so? A idannuwan wa zan ga tsantsar kaunata a yanda nake? Ina zan dosa na ji sanyi yau Lukman ka wargaza ni, a yau tsal nayi kuka fiye da tunaninka, ashe har aure ka yi bayan ni? Ashe daman maza butulu ne basu da tabas? Ashe daman maza haka suke?................... 🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚🌚 [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *25* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Sosai ya yiwa Alawiya filafila dan ya kula ta fara kokarin fice gona da iri, dan yana daga mata kafa ne bata san cewar bata fi karfinsa ba Kuka take tun karfinta ta kasa koda motsa yatsanta, a can kasan zuciyarta kuwa Allah ya isa ne take jero masa yafi cikin kondo tana aibata shi iya karfinta Mikewa yayi ya kare mata kallo, ko va komai ya rage wani zafin, a hankali yake haurawa samansa ya shige bayi, Wanka ya yi na sabulu kafin yake tsaftace jikinsa ya fito da tawul a daure a kugunsa yana tsane ruwan wankan da ya yi Wayoyinsa ne suka fara kawo hari kan sakunna sai kira, a hankali yake shirya kansa bai daga wayar ba sai da ya gama ya dauko jaridun da mai gadi ya kawo na ranar ya sauko kasa ya dora kafa daya kan daya ya shiga karantawa bai bi ta kan woyoyin nan ba Tsam ya yi ya shiga tunani, haka kawai hankalinsa ya raja.a a menene suke fada suke yiwa juna murmushi haka? Ji yayi yana kokarin nutsewa a zargin kaninsa hakan ya saka shi mikewa ya fito ya nufi masalaci Yauma wannan datijawan da suka yi dare suka sha ruwa a masalaci ne suka kuma zuwa, sai dai wannan karin sun zo ne da alkhairi wa masalacin sun bayar da sadaka sannan sun zauna ana yin karatu da su, Sosai yake satar kalonsu dalilin gannin dayan wanda ya fi tsufan ya matsa masa da kallo irin kallon nan na kure mutun A hankali Alaidine ya mike ya fito ya ja gefen wata bishiya ya zauna yana kallon masu hucewa tamkar hankalinsa na kansu bayan tunaninsa kaf a wani wajen, Bayan sati da daura auren su Alaidine , Jamail kam yana ta kokari koma nace alhamdulilahi yanzu sai abinda ba za.a rasa ba, domin sun shaku sosai shi da Aisha, yana jinta a kasan zuciyarsa, soyayar da yake ji tata irin ta a jinninsa take ne, sam baya son ko kuda ya rabi jikinta ko wani abin, yana girmama yanda take girmama shi, yana mutuntata kamar yanda ta ga tanaiwa mamansa, yana ji da su su duka yana girmama su Malan a kasan zuciyarsa domin su suka basu tarbiyar a yaba, Aikace aikacen gidan nan sun dauke shi, basu da damuwa face na rashin mahaifansu wanda har zuwa wannan lokacin sun kasa sabawa a tsakaninsu suke jajantawa Mom na iya kokarinta dan gannin ta dauke masu kew sannan sun saki jiki irin sosai din nan da ita, ba laifi ana samun ci gaba sai dan abinda ba za.a rasa ba a wajen Wujdane wanda shi kuwa miskilanci ne irin nata Abinda ke birge Mom, yaren nada tsafta, ga tarbiya, suna girmamata suna kulawa da du wani abin da ya shafeta, Mama suke kiranta da shi hakan ya saka take jinta a damuwarta sun debe wani wajen sosai sai abinda ba za.a rasa ba, sannan itama take lure da dukan lamarinsu Alaidine kuwa rabonsa da gidan yau kwana na hudu kenan, yanzu haka boy ne ya tisa shi a gaba da kukan shi uncle dinsa domin Jamail zamansa ya zama kalilan a gidan Yayi rarashin, yayi gadan aman Boy ya nace shifa uncle dinsa, cike da jin haushi yake kara buga number Jamail aman a kashe, haka anwar yana wajen aiki, ya rasa ya zai yi da shi kuma abin haushin Alawiya na kallonsa ko ci kanka bata ce da shi ba bale ayi tunanin rarashi daga wajenta A hankali yake bala botiran rigarsa yana hangen yanda boy ke kuka hannunsa bibiyu a saman kansa, ajiyar zuciya ya saki ya fesa turare a jikinsa ya juyo da tissu ya gogewa boy fuskarsa sosai, ya dauko shi a hannunsa suka shiga mota suka kama hanyar gidan Aba Yana karasowa bayan ya parka motarsa ya juyo yana kallon yanda Boy ya daina kukan yana dan wasansa, wato anyi masa abinda yake bukata? Kansa ya dago yana dan duduba gidan, kamar ance ya daga kansa can wajen shukokin mangoro abarba da sauransu sai ganninsu yayi a zaune Jamail da Aisha a waje guda suna shan ice cream sai Wujdane a dan nesa da su tana ta jifan mangoro tana son ya fado ta sha Ba wani hijabi a jikinta, doguwar riga ce ta saka irin gown din nan, ta dan yane kanta da dan kwalin rigar, rigar kalar fara ce kal dan kwalinta ma haka , sannan ta dan kama ta daga wajen mamarta sai ta baje kasa, kallonta yake kamar an kunna masa tv yana jin dadin yannayin sosai, Boy ne ya tabo hannunsa ya kwabe fuska ya ce" dad Uncle☹ Ajiyar zuciya ya saki a hankali ya bude motar ya dauko shi ya nufi wajen Jamail da shi Gaishe shi suke cike da girmamawa ya amsa fuska a dan sake har yana yiwa Aisha tsiyar cewa ta sake abinta Sai ta danyi murmushi tana sada kanta kasa bata ce komai ba Boy kuwa da gudunsa ya nufi wajen Wujdane gannin tana kokarin baso mangoro, yana zuwa ya gane ta ya ja ya tsaya yanai mata murmushi Juyowa Wujdane ta yi ta zuba masa ido, haka kawai yaron tun ranar a gisansu ya shiga ranta irin yanda ya makale matan nan, a kulun tunanin ina yake take a kasan zuciyarta Murmushi ta sakar masa sannan ta miko masa hannunta na dama ta ce" zo, Kallonta yake bai motsa ba, sai ta dan girgiza kai ta miko dayan hannun nata da niyar tana son daukansa Ai kuwa da gudunsa ya karaso yana bangale bakinsa ya ga dauka Daukansa ta yi tana kakabe masa wandonsa da ya dan yi kura, bata bi ta kansu ba ta nufi falo dan so take ta yiwa boy wanka domin yaron da dati a jikinsa , dan kuwa mai yi masa wankan daman Jamail ne Alawiya ba wani damuwa ta yi da lamarinsa ba Alaidine kuwa baima san ta inda zai fara ba Biye yake da bayansu a hankali, idannuwansa kyam a kanta, shi yakan manta cewar ya tsayar da kalonsa a saman kanta, yakan manta cewar ya shagalta da damuwa da yannayinta , har dan murmushi ya saki jin labarinsu da Boy, yana son mai kula dansa abinda ya sa yafi shakuwa da Jamail kennan irin yanda ya shaku da Boy sannan ya sakar masa aljihunsa har shima ya malaki na kansa yake wadaga da aljihunsa, yana girmama girman du wanda ya damu da rayuwar yaronsa A hankali ta tura kofar gilas din dakin ta shiga, hankalinta a wajen Boy dake jan jelar gashinta Kan uba, ke sauke min yaro sauke min yaro, ko kunya bakya ji? Mai ya hada ki da yarona? Khadija ce ke hargowa tana nufo wajen Wujdane dake rike da Boy, abin mamaki shima yaron sai ya riketa gam yana dan cusa kansa a kirjinta Ja ta yi ta tsaya tana kallon Khadija, a kasan zuciyarta tana mamakin wannan irin tsana haka, kuma a hankali take fahimtar ba wani abu tsakaninta da Alaidine din kuma ita dinma ta lura ta ganni ba wani abin tsakaninsu da shi ba wani kula juna suke ba aman ita sai kishin hauka take zubawa ta hanata sakat, ita kuwa kawar da kai take bata son kula ta dan tana tsoron abinda zai iya faruwa tana matukar jin kunyar Mom Kokarin sauko Boy take, ya ririke rigarta ya saki kuka yana fadin " no no bana so bana so sauka ni................ Dan tsai ta yi da shi a hankali ta ce" ka ga mamanka na son daukanka my Boy, ka je mamanka ta yi maka wankan ka ji? Boy yaki cika ta sannan yaki yarda ya saukan, Ba sai kin sauke shi ba, ki tafi da shi kawai Murya ta daki kunnenta, a hankali ta mike da Boy ta dan juyo dan gannin waye ya yi maganar,? A tare gabansu ya yanke ya fadi bata tankasa ba ta nufi dakinta da boy Ya zaka yi man haka aban Huzaifa? Ni da yarona har ka fifita wata a kaina a wajensa sannan a gabansa? Ya kake so ya dauki lamarina ne ? Ni fa na haife shi! So what? Dan kin haife shi a da baki nuna masa kulawa ba sai yanzu? Idan ke kika haife shi zaki haife shi ke kadai ne? Ko kin san kashin sa da fitsarinsa? Bana son yawan haye maki kina kokarin tura ni rami, *MATATA CE* wannan, tana da damar daukan yarona ta kula da shi Idannuwa ta kankance ta ce" matarka fa ka ce? Matarka fa? Yaushe ma ka aminta da matar taka? Ai a sanina bata amsa kiran matarka ba domin bata ma san kalarka ba a zahiri, auren hadin? Kema ai auren hadi ne ko kin manta? Ya katseta, tsam ta yi ta juya zuwa dakinta Zama ya yi a wajen , shi bai haura saman ba shi bai tafi ba, Can yake jiyo dariyar Boy har kyakyatawa yake, tsam yayi yana hangen saman a kasan zuciyarsa yake tambayar abinda ke faruwa? A hankali ya mike ya nufi saman, du takunsa daya sai zuciyarsa ta buga masa wannan lamari na rage masa karfin jikinsa, yana saka shi a damuwa ainun A hankali ya tura dakin ya shiga, bayanta kawai ake iya gani, ta cire mayafin na kanta ya kasance gashinta a baje a gadon bayanta, cakulkuli take yiwa boy wanda har daga kafafuwa yake yana ihun dariya Tsam yayi da ransa, wani irin nishadi ya tsinci kansa a ciki, kallonsu yake inda ya ja a hankali ya rufo kofar dan kar su gansa sai dai me yana juyowa suka yi ido hudu da Mom.........😳 [3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *26* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Ido ta tsurama yannayinsa, kamar kallon tuhumar nan haka take jifansa da shi wanda ya saka du ya wani kawar da kai, can ta basar ta ce" sai nake jin kamar dariyar mai gidan? Juyowa ya yi ya ce" eh shi ne yake dariyar nan Mom ta yi murmushi ta ce" eh lale, wa ke yi masa wasa ne??? Du da gangan take tambayoyin nan, dan kawai ta dabirtar da shi ta kuwa yi sa.a ya daburcen, Kai ya sosa ya ce" am em ..... ina jin bakuwar nan ne🤷🏼‍♀ Mom ta kale shi da kyau ta ce" bakuwa? Muka yi? Ko su Aisha suka samu ziyara ne??? Wannan karon tsayar da kallonsa yayi a kan Mom din yana nazarinta, kirkiri ya lura Mom din na kokarin sai ta kure shi ne, a hankali ya sauke ajiyar zuciya gannin Mom fa amsarsa take jira, a hankali kamar ba zai yi magana ba ya ce" aa fa, wannan dai wada aka aura min...... Yana fada ya juya da saurinsa dan ya bar mata wajen , Mom ta saki murmushi ta dan daga murya dan ya jita ta ce" ai Wujdane da Aishana ba baki bane, sai dai su sauki baki , gidansu ne harma sun fi mutun yanci! Murmushin ya yi shima yama fice a falon kwata kwata wanda wani abu ya mugun bashi mamaki, wato Jamail ne ya dora Aisha saman cinyarsa a hankali ya cafke lebenta sai kissing yake, Idannuwansa ya kawar da sauri daga bangarensu mamaki kamar ya kashe shi ya fada motarsa ya ja ya fice a gidan Yauma kamar wasu lokutan , parka motarsa ya yi dan nesa da gidan ELHAJ MUHAMADU DA KUMA ELHAJ ABDALLAH, wato kakaninsa shi fa ba zai ce ga kamaninsu ba aman yana iya shaida yayan gidajen, shi Elhaj Muhamadu shine mai yaya da dan dama shi kuwa Elhaj Abdallah dansa daya wanda ya yiwa aure matar ta haifi yaro daya, aman a yau sai yake gannin ana ta shigi da fici a yannayon tashin hankali Motarsa irin mai glass din nan ce mai duhu, ba zaka iya gannin na ciki ba sai dai shi ya ganka hakan ya bashi damar mayar da hankalinsa yana gannin datijai na shiga cikin sauri wasu na fitowa wasun su na kara shiga cikin gidan Elhaj Abdallah Haka kawai yake jin wannan ba lafiya ba dan haka sai ya kara zama yana kallo, Ganni ya yi an fitar da babar makara irin ta manya, an nufi cikin gidan da ita Gabansa ne ya yanke ya fadi, ya bude motar kamar zai fito ya dan dakata yana kallon wajen kofar gidan Elhaj Abdallah, jin an bude kofar Datijon nan da ya gani sau biyu a masalaci ne, wannan wanda ya kafe shi da ido yana kallonsa ya fito daga gidan ya maida kallonsa kofar gidan Elhaj Abdallah, Wata mata ce ta fito da bakin hijabinta har kasa, du yanda ta kai ga tsufa sai da gabansa ya fadi dan hango tsantsar kama da mahaifiyarsa Hajiya Marwa, tsai yayi da ransa yana kallonta ta dan dakata daidai wannan datijon ta kamo hannunsa ta yi masa magana wada ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya shafa kansa sannan ya yi gaba ta bi bayansa har gidan Elhaj Abdallah Mayar da hankalinsa ya yi, yana nan zaune aka shinfida tabarma lakadediya Ba.a jima sosai ba aka fito da gawar a cikin makara, Shi dai ba zai ce ga wanda ke cikin makarar nan ba, domin ba sannin tsohon gidan ko tsohuwar gidan ya yi ba, Saurin fitowa yayi, gannin ana kokarin salatar gawar, da saurinsa ya dauki butar ya bi layin masu azamar yin alwallah dan gabatar da sallar gawar Da Alaidine aka salaci gawar nan, aka dauketa yana kalo wani baban saurayi ne a gaba wajen rikon gawar Bai tambayi kowa ba, ya shiga motarsa har ya dauki mutane aka nufi makwontai, har zuwa lokacin bai san wanda ya rasun ba A makontan ne ya ji ana ya Abdallah, ya Abdallah, ya Abdallah, hakan ya tabatar masa cewar namiji ne ya rasu Cikin ramin ya ga wani datijo fari da wannan saurayin suka saka gawar a cikin ramin suka gyara mata konciyarta hakan ya nuna masa cewar sune mafi kusanci da gawar Fitowa suka yi a hankali aka yiwa wannan bawa sutura, jama.a suka fara watsewa ana ta yiwa mamata adu.a Da dayadaya du aka watse aka bar sai yan tsirarku da suma suka dan bazu wajen sauran kaburan Mutun uku ne a zaune daidai da kabarin nan, wannan tsoho wato Elhaj Muhammad sai yaron nan da dayan tsohon A hankali Elhaj Muhamadu ya dora hannunsa a kafadar Elhah Abdallah ya ce" ka yi hakuri, ka tashi mu tafi a yi ta masa adu.a Allah ya bashi ikon amsa tambayoyin kabari, Allah ya bashi haske da ni.imar dake cikinta, shi da ya rigaye mu bai yi sauki ba, mu da muke jira bamu yi jinkiri ba, Saurayin nan ne ya fada kan Elhaj Muhammad ya saki kuka ya ce" yanzu shikennan Abanna ya rasu? Shikenan bani da kowa? Sai su kaka da umana? Shi kennan na rasa jigon rayuwana? A hankali ya shafa bayansa ya ce" ba.a yiwa mamata kuka haka, a cikin makontai muke ba.a son yin yawan magana a makontai idan har ba adu.a ba, aman ka sani *ABDUL KADRE* Allahn da ya amshe shi ya fi mu son sa, sannan bai barka kai daya ba, kana da wani uban mai sunnanka! Da sauri Elhaj Abdallah ya dago da kansa ya sauke idannuwansa a kan Elhaj Muhammad, bai iya furta komai ba ya mike ya nufi fita a makontan inda suka biyo bayansa Alaidine dake zaune gefe ya dukufa a kusan wani kabarin yanaiwa mamata adu.a sannan hankalinsa na kan magangannun su elhaj , a nan ya fahimci cewar Kanin mahaifinsa ne ya rasu, wanda su biyu kawai iyayensu suka malaka a duniya, sannan wannan tsohon shine mahaifin mahaifinsa yaron nan kuwa dan mahaifinsa, a takaice dai rasuwar nan ta shafe su, mutuwar nan su aka yiwa Cikin mutuwar jiki ya dawo kusan kabarin nan ya zauna, adu.a yayi ta zubawa kamar ba gobe, bayan ya gama ya dora hannunsa ya ce" Aba, baka sanni ba, ni dan dan uwanka ne, ina mai yi maka adu.ar samun nutsuwa a cikin kabarinka, Allah ya karbi bakuncinka ya sa mu ma mu cika da imani Yana gama adu.ar nan ya mike a hankali ya fito, zuciyarsa du a mace, yana duba irin tarin kaburburan dake konce yana aiyanawa a ransa cewar " *KULU NAFSIN ZA.IKATUL MA.AUT* ba wanda ya isa ya tsira fa, mutuwar nan sai an yi ta dole (😭) Tuki yake zuciyarsa tamkar ta bale, yana tafe yana tuna yannayin da Elhaj Abdallah ya nuna da aka tsankwalo sunnan abansa A haka har ya karaso gidansu, yana sauka ya nufi falo Abansa ya tarar a zaune a falon, yayi zugum yana kallon tv, Karasowa yayi ya gaishe shi ya nemi waje ya zauna ya rasa ta inda zai fara Mom ce ta fito daga kicin ta taho da jus a hannunta , tana karasowa ta mikawa Aba tana kallon Alaidine ta ce" ka dawo? Amsa mata ya yi yana kallon Abansa, Hankalinta ta maida wajen aba ta ce" Aba yara idan zuciyar taka bata daina bugawar ba ai gwara a tafi asibiti ko? Dan na ga tun jiya kake jin yannayin nan A hankali ya muzkuta yana kallonta ya ce" Momyn yara, ai faduwar gaba ne kawai ba komai insha Allah Gaba daya jikinsa ya gama mutuwa, tausayin mahaifinsa ne ya tsarga zuciyarsa, bai san ta inda zai fada masa rasuwar kanninsa kanninsa uwa daya uba daya, wanda may be ya jima rabonsa da shi, mai yiwuwa ya jima bai saka shi a ido ba, aman yaya zai yi? Mutuwar nan dai an yi ta, sannan shi dolensa ne , kuma musulmi ne du abinda zai faru zai yi hakuri ne Muzkutawa ya yi ya ce" ABA, A tare suka dago suna kalonsa wanda ya kara kayar masa da zuciya, daurewa ya yi ya ce"....... [3/27, 10:01 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *24* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Happy happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday to you *YAYA HAYAT* happy birthday to you@ *Allah ya sa wannan shekara ta zamo daya daga cikin shekaru da zasu zo maka da cikar lafiya, su kara maka daraja, su kawo arziki mai anfani, hsppy bufday* Mom ta yi kiran Lami, Lami ta fito tana gyara hijabinta dan tunda ta kyala ido ta ga Alaidine a gidan da safen nan ta shiga kimtsa kanta tun kafin ya fita bayanta Tana zuwa ta raba tana amsawa Mom ta yi dan murmushi ta ce" ki fitar min da zabi a cikin frij ki saka min su s ruwa yanzu zan fito na hada breakfast , yau na yi rana Amsawa Lami ta yi ta juya insa Wujdane ta kama hannun Aisha ta mikar da ita dan su bi Lami Mom ta cel" aa, yar gidan Mom ina zaku tafi ne? Ku fa je ku huta kar ku kwashi gajiya da yawa kun ji? Wujdane ta dan juyo, ita kam da alama zafa a saka ta yawan magana ne s gidan nan, s hankali ta ce" zamu hada kayan karin ne *Mama* Mom ta yi murmushi, ta lura aikace aikacen nan sabonsu ne, dan haka sai kawai ta barsu suka tafi kicin, aka bar su Alaidine da su Mom , nsn Aba ya dora daga inda ya tsaya a jawabinsa mai shige da gargadi, sannan ya basu umarnin su tsaya su karya kafin su tafi Raba aikinsu suka yi, Wujdane kam bata iya wani dogon rarashi ba aman idannuwanta kyam a kan du wani motsi na Aisha, Aisha ke feraye dankalin turawa ita kuwa Wujdane na gyaran naman da take kokarin dora shi silale Sosai ta kara wanke naman, duda daman ba wani dati ne da shi ba, ta kawo tukunyarta ta zuzuba shi, ta kawo su kayan yajinta , su gishirinta kadan ta zuzuba sannan ta dan zuba ruwa kadan bayan ta saka albasarta Lami ce ta kunna mata gaz wanda har sai da ta tsorata yanda wutarsa ke da zafi, ta dora ta rufe tukunyar ta zauna tana daka atarugun da zata hada vinaigrette da shi tana kallon yannayin Aishanta, yanzu da zuciyarta da dadi da tuni ta cika mata kune da labari A hankali ta matso kusa da ita ta kama mata yankan dankalin turawan, Kanta a kasa bata wani dago ba ta ce" *kar ki kwalafa da gannin daidai fa a wajen da namiji, sannan ki cire damuwa a ranki insha Allahu Jamail zai so ki kin ji?* Dago da kanta ta yi tana klon yayar tata, sai ta sakar mata murmushi, sai a lokacin ta farga da irin yanda ta tayar da hankalinta bayan ta san a yanda aka yi auren nan, tausayin Wujdane ne ya ratsa mata zuciya, ita sam bata wani nuna damuwarta ba bayan ta sani sarai itama bata wani jin dadin hakan dake faruwa da ita Hakan ya saka ta saki ranta ta shiga aikinta da kazar kazar dan su yi su kamala, suna yi suna tambayar Lami irin abubuwan da Mom din ke yi ( iyaye mata, mu kula, kana da shi ko baka da shi idan baka koyawa yaron naka ya wahala ba, idan baka koya masa abubuwan ba, ba lale ne ya je gidan hutu ba, kuma yau ko gidan hutun ya je zai so ace shima yana shiga kicin dinsa yana sarafawa mijinsa kalolin girkin da zasu kara shakuwa a tsakaninsu ba wai kawai mai aiki ya girko ya kawo masa ba, idan yaron naka ya horu da wahalar tun a gida, aikace aikacen ku, wankinsa, du inda zai je ba zai sha wahala ba, sannan kai kanka sai dai a bika da adu.a, Allah ya sa mu dace) Dankalin nan suka soya, bayan sun yiwa zabin nan suyar sama sama inda suka yi wani taushi, sai vinaigrette, sannan suka hada jus na kwakwa da madara pink suka markade kwakwar suka tace ta tas sannan suka hadeta da madarar nan sai kankara da dan siga da suka hada domin Mom bata hada jus da irin kayan kanshin nan , Lami ta jera masu saman katon plat suka kama suka fito Direct wajen table din suka kai suka ajiye wanda su Mom suka bi su da kallo, a can kassan zuciyar Mom tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa, tana ta faman yi masu adu.a sannan tana so ta dandanna girkin su Kiransu ta yi ta fada masu cikin sif akoy kaya su kimtsa su sauko a karya Sama suka hau , wannan karin fakin Wujdane suka fice a tare Wujdane ta fara yin wanka, kafin take fitowa Aisha ta ciro masu atampa da hijabai, irin hijaban nan masu hannu da tsakiya a hannun sannan da dan tsayinsu domin sun dan zarta gwuiwa, ta dorawa wujdane kalar ruwan anta a saman atamfarta ita kuwa ta dora fari, duka yanda zasu hau atampopin ne Nan da nan suka shirya abinsu, sai bayan ta dage ta sakawa Wujdane kwali wada idannuwan suka cika da hawaye na kwalin domin ba wani sabawa ta yi da sakawan ba Sai da ta jima kana take bude idannuwanta ta sauke su a fuskar Aisha Mirmushi Aisha ta saki tana kallonta, a can kasan zuciyarta kuwa tana taslima ga wannan tsarin Halita na yayarta Girar Wujdane a tsare take, bata taba asketa ko wani daidaita ta ba, ba baka sidik bace maroon ce sannan ta daidaita tsaf a zagayayiyar fuskarta Idannuwanta tsarinsu sai dai ace masha Allah, idan ta saka kwali kuwa har wani kyalkyalin kwalin suke su kara haskawa, sai lebenta kuwa ainayinsa pink color ne, ga motsi kadan takan dan laso shi hakan yake sakawa koda yaushe a danyace yake koda bata saka man lebe ko jan baki ba, gashin idannuwanta kuwa gazar gazar haka suke da tsayi da shanyewa, a hankali suke saukowa suna dan magana kasa kasa kasa Har sun hau table din, Mom tana zuba masu abincin Khadija ma an tasota daga bacinta, tana zaune kanta daure da dan kwalin shadar dake jikinta, wace ta kwana da ita abinta, Aba kawai ne da Mom ransu fes, idan ka duba yannayin Alaidine du kamar ya fasa ihu ya bar wajen yake ji, Jamail kuwa du zuciyarsa a karaye na irin yanda Aba ya yi ta yi masu nasiha, Khadija kuwa daman da kyar ta samu bacin, tana jin haushin bayan gata a gidan Aba ya je ya aurowa Alaidine wata matar, ai kuwa ta dauki aniyar sai ta koyawa Wujdane hankali sannan zata jata a jiki ta fada mata sirrin Alaidine din dan idan fada ya hada su itama ta kiraye shi da shegen ko ya saketa ta huta, A hankali suka zauna, a kujerun da ba kowa wato tsakiya suka saka khadija dake zaune, sai ya kasance Wujdane tafi kusanci da Jamail dake kusan Mom, sai Aisha ta zauna kusa da Alaidine dake kusan Aba, aman kuma suna facing din junna wato kowane na iya kallon dan uwansa sak idan hakan ta kama Abincin aka fara ci, inda kake jin karar cokula na kara a cikin plat, Khadija kam yayi mata dadi a baki, Alaidine ya ki ya kai bakinsa dan kyankyami sai da suka hada ido da Mom ta yi masa nuni da idannuwanta kan ya ci, hakan ya saka shi cin a tunaninsa ba zai ji yanda yake so ba Sai dai ga mamakinsa wani taushi, kanshin kayan kanshin nan da dan gishirigishirin ya saka shi lumshe ido, a boye ya saki ajiyar zuciya ya dan gyara yana fakaitan idannuwan mutane yana dan tsakura Sosai jamail Jamail yake cin abincinsa dan ya san girkinsu daman, a hankali ya dago da idannuwansa cikin sa.a kuwa suka sarke da na Aisha wace ta dago dan zuba ruwa Sun yi kallon cikin ido na wajen sacond biyar kafin ya sakar mata murmushi mai kayatarwa wanda ya sakata jin kunya ta yi saurin mayar da kanta wajen abincinta ta kasa dauko ruwan sannan ta kasa ci gaba da cin abincin Kamar hadin baki suka miko hannayensu dan daukan baban flask din jus din , ita ta san jus ne a ciki, shi kuwa a zuwan ruwa yayi masa, hannunsa ne ya doru saman nata,wani irin dago da kai yayi jin hannu tamkar na jariri, caraf suka hade idannuwansu, Idonta ta rintse jin hannun namiji a saman hannunta, ta yi gagawar budewa, shi kuwa shagalta ce yayi da kallon idannuwanta, yanzu kuma sai suka bashi sha.awa mainakun haushi, aman abinka da miskili sai ya watsa mata hararar da ya saba Bakinta ta yatsina ta dan karkace shi ta murguda masa shi kana ta janye hannunta tama fasa daukan jus din, Mamaki taru ka kashe Alaidine mana, tambaya yake yiwa kansa" wai dam fitsarariya ce har haka? Daga hararanta sai ta murguda min baki?? Tashin Aba ne ya katse masa tunaninsa, inda Mom ta mike ta mara masa baya suka haura gefensa Kokarin mikewa yake, wanda kafin yayi wani yunkurin har Khadija ta gifta shi ta shige kicin Gannin du ana tashi ya saka su harhada kayan da aka ci abincin, sai Wujdane ta fara tafiya dan kaiwa kicin Hadewa suka yi da Khadija ta fito a kicin din, Khadija ta yi mata kallon kaskantaciya, sannan ta dan saki buda a hankali ta rage muryarta ta ce" farin ya kaishi wannan karon kennan, zaki gane baki da wayo idan ya shige ki tamkar gonar talaka sannan ya rataba maki saki uku, ni din nan dai ni ce a yi a gama ina kallonku, domin nice kadai na iya daukan cikinsa na haifa masa Boy, du wata ta bayana karya ce ko yar gidan wanene balarana na ji a labari cewar ba.a tara aka tayar da kai ba Tana gama fada ta fice bagazan bagazan ta tafiyarta dakinta Zuru Wujdanw ta yi tana antayowa kanta tambayoyi, wannan ita ce matar tasa ko mai? To aman ya akayi bata ga wata shakuwa ta matar da har suka samu yaro da shi ba tsakaninsu? Ko tana matarsa danme zata fafada mata magangannu haka mararsa dadi? Ko an gaya mata son mijin nata ake ne? Daman sakin nawa yayi tun yanzu da bani da kamarsa a masoyana Kwafa ta yi ta shige kicin din tana ayanna bafa zata dauki iskancin matarsa ba, du a tunaninta Khadijan matar Alaidine din ce Tana dawowa ta tarar sai Jamail kadai , Aisha tana kicin din bata fito ba, A hankali ta karaso wajensa tana murmushi ta ja ta tsaya ta ce" yayana, ina neman alfarma Dago da kansa ya yi ya sakar mata murmushin shima, ya ce" Au, yau kuma? An amince na girman ne ko mai? Oh aunty wujdane manya Kawar da kanta ta yo tana dan turo bakinta ta ce" dan Girman allah kar ka wakanta min Aisha, Jamail Aisha yarinya ce, bata da wani tunani in ba na kuka ba, kuma karka manta itama sai da ta jo hukuncin da aka zartar a kanta, karka wulakanta min ita na roke ka Sai da ta gama, Jamail ya ce" na san Aishana yarinya ce, duda da farko ba ita na so ba aman ina mai tabatar maki zan kula da dukan lamuranta, karki wani damu kin ji? Murmushi ta saki, wanda har sai da hakoranta suka bayana, Aisha da ta lafe ta rabe tana sauke ajiyar zuciya domin komai a kunnanta ya fito, sai Alaidine dake sama ya tsura masu ido, shi dai bai san mai suke cewa ba, aman a yannayinsu sai kawai yake hango tsantsar nishadi a tatare da su, gabansa ne ya fadi ya shiga tambayar kansa, ko dai yarinyar nan ta bata masa kani shi ya sa ya haukace shi yana sonta, Aba ya tashi ya aura masa kanwarta kar dai su dora daga inda suka tsaya ( ku ji fa😳😳) Ficewa yayi a gidan ba tare da ya yiwa kowa magana ba ya nufi gidansa Zaune Alawiya take, ta sha ado da doguwar rigarta ta atampa, Alawiya fa ba baya ba wajen kyau, sannan fara ce tas itama, gashi dai ne bata da shi, shima dan ta wakanta shi ya kakarye yama dadage, bata samu yin girki ba ta tashi da fitinar ina ya je, dan du a tunaninta bama a gidan ya kwana ba Tana sakar zucinta sai gashi ya shigo , ransa a kololuwar bace, Alawiya kuwa ta mike ta tarbe shi da sabon salon iskanncinta Kallonta ya tsaya yi tana furta masa kiri kiri cewar" daman auren da ya kara ita ta san dan sex ne, aman ko kunya baya ji ya tafi gidansu ya dane mace sannan ya dawo mata gida ya wanke dauda? Domin ba alamar ya wanke daudar da ya kwaso a jimin wata karuwar,........ Dago da idannuwansa da suka yo jajajir yayi, ya sauke su a kan Alawiya dake masifa ita an taba ta, Nufota ya shiga yi tana ja da baya, domin idan akoy abinda bata marari a rayuwarta shine kasancewa da shi, dan kuwa a lokacin da ta nace baya kulata da ya kula tan ya kusan halakata, harma ta yi dana sani ta ci kuka, tun daga lokacin take tsoron kasancewa da shi, bata ma mararin hakan ko kadan Murya a marairaice ta ce" karka taba ni plz, baka fa yi tsark............ .....kafin take karasa maganarta ya cafkota, muryarsa da ta soma gushewa da kyar ya furta mata" idan na hada da naki da nata kin ga sai na yi mai dalili............ ... ... Nan ya....... 🌚 [3/27, 10:01 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄 *27* WRINTING BY *SAJIDA* Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai, *SAJIDARKU CE* MARUBUCIYAR: *YAR MAHAUKACIYA* *DUK KARYAR KADA* *DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA* *NEMAN NA KAINA* ................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH.... Cike da fargaba Alaidine ya ce" Aba, ka fi ni sannin duniya mun zota ne na dan lokaci kalilan, dukan mai rai sai yayi kaura zuwa kiyama, ba ran da ba zai yi wafati ba, hakuri shi ne Allah yayi mana nuni da mu yi, domin dole ne bamu da yanda zamu yi Kallonsa kawai Aba yake, bai iya furta masa komai ba, kallo na tsoro, kallo na tsoron jin abinda zai fito a bakinsa Mom kam jikinta ya gama rikicewa da rawa, tsoron fal ranta ji take tamkar ta kwato magana a bakin Alaidine aman ya tsaya sai kwana kwana yake, cike da kosawa ta ce" kai Alaidine,.lafiya? Mai yake faruwa ne? Wani ne ya rasu? Ka fadawa mutane ka tsaya kana ta jan maganar bayan ka ga halin da Abanka ke ciki? Ta karasa maganar tanai masa tsawa tsawa Ajiyar zuciya ya sauke ya ce" Aba, rasuwa ne aka yi, kaninka ne ya rasu yanzun ma daga makabarta nake Zurbat suka mike daga Mom har Aba suna kalon Alaidine wanda ya sada kansa kasa yana dan damanma bai je anguwar ba Ajiyar zuciya kawai aba ya saki ya zauna yarab a kasa ya kurawa kasa ido Mom nan da nan ta fara sharar kwallah, ta kasa cewa komai banda innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, tana gannin kannin mijin nata a idannuwanta, Aba ya jima bai yi wani motsin kirki ba , har sai da abin ya fara basu tsoro , a hankali ya ce" Alaidine yaushe ya rasu ne? Alaidine ya sauke kansa kasa ya ce" Aba yanzu na tarar za.a yi sutura aka yi da ni sai bayan an gama ne na fahimci shi ne Mom ta dago da idannuwanta da suka yi jajajir ta ce" kai kuwa wa ya nuna maka gidan? Ya aka yi har kake zuwa? A ina ka san gidan? Ajiyar zuciya ya saki yana kallon mahaifinsa ya ce" Mom ai ina lekawa wani lokacin, nakan je na tsaya gefe guda dan gannin halin da suke ciki, to yauma na je ne na ga ana fitar da gawar Kanta ta mayar wajen Aba, a hankali ta sanyaya muryarta ta ce" Aba ka yi hakuri, ka yi masa adu.a sannan mu tafi mu yi masu gaisuwa Aba, dukan mai rai mamaci ne karka rike a ranka domin karka manta muma jiran tamu muke Aba ya sauke ajiyar zuciya yana kallonta, can ya ce" tabas *MARWA* na yi imanin wanda ya amshe shi ya fi ni son sa, abinda ya tsaye min a rai shi ne rashin lafiya ya yi? Ya adinninsa ya canza wasu halayan? Ya wajen yiwa iyayenmu biyaya ya daina taurin ran nan nasa? Shin yana tuna ni nima kamar yanda nake tuna shi duda bamu wani mugun shakuwa ba a lokacin har na bar gidan? Ina cike da zulumin mutuwar kanina ne, ina adu.a ne a kasan zuciyata kan Allah ya datar da shi, Allah ya karbi bakuncinsa, sannan inna koka ranar tawa mutuwar harma ina adu.ar Allah ubangiji ya sa ranar mutuwarmu ita ce ranar farin cikin mu, ranar shiga kabarin mu itace ranar hutun mu, A tare suke amsawa da amen ya rabeel Alamen Nisawa ya kuma yi ya ce" ba zamu tafi gidan ba Momyn yara, domin karki manta Abana yayi furucin idan har ya kuma ganin kafata kalata koma mai kama da ni sai ya tsine min Albarka sannan sai ya kwana sallah kan Allah ya yi mana hisabi idan har ba sakin ki na yi ba na dawo gare su a lokacin da kike cikin halin rayuwa sanadiyana, daga baya da na koma ya rantse cewar ya kare da ni ya cire ni a yayansa, Kawai zamu yi zaman mutuwar dan uwana a nan, mu yi masa adu.ar uku da na sati mu bi shi da adu.a sannan mu yi kokarin gyara namu zuwan, Allah ya sanyaya Yana gama fada ya ciciba ya mike ya haye sama da niyar shiga dakinsa Ajiyar zuciya Mom ta saki ta kashe Tv ta kirayi kaf mutanen gidan ta sanar da su cewar an yi rasuwa a yi kokari a samawa gidan nutsuwa na zaman makoki Sosai ake zaman makoki a gidan Aba, mutane da dama na zuwa yi masa ta.aziya, adu.a kam mamacin na shanta ta sosai da sosai, tun daga kofar gida wajen Aba har cikin gida wajen su Wujdane wa.inda suka bude tsantsar sauka a kulun ta Allah sukan yi sauka wa mamacin nan su yi masa adu.a a wuni zikiri ana hailala da kurhuwalahu ana nemawa mamata rahamar ubangiji ( ya Allah 😭, ina rokonta dan sunayanka tsarkaka, Allah dan girman zatinka Allah, idan wani ya ji labarin mutuwata ko a ina yake, Allah ka bashi ikon bina da adu.a sannan ka bashi ikon furta alkhairi a kaina da ni da dukan bawan da zai amsa da amen da kuluyin musulmi ya ziljalalu wal ikram 😭) Dalilin zaman nan da ake, sai ya kasance Alaidine kulun yana gida, da shi da Anwar da matar Anwar da yayansa, dama Jamail ba yauba yake kokarin kaurowa gaba dayansa Alawiya har zuwa wannan ranar bata zo ba, ta tsiro karyar cewa bata da lafiya hakan ya saka ya kyaleta bai takurata ba, idan ya fice a gidan ta mike ta shiga sabgar gabanta hankalinta konce a fili takan furta wani zaman makoki na kin Allah bayan mutanen ba wani sannin zamanku suka yi ba? Boy na wajen Wujdane, yaron yana matukar sonta domin tana kyautata masa, tana yi masa wanka ta saka masa sutura tsaftatatu, ta bashi abinci a baki ta bashi chocolate t goya shi a batanta du irin girman shi kuwa, ita haka kawai take jinsa a ranta, domin Huzaifa irin yaran nan ne masu shiga rai, cikin jikinsa yake bulbul da shi, ga kyau masha Allah sannan ya maida Wujdane tamkar mahaifiyarsa ko baci ya dauke shi ta shinfide shi yana farkawa sai ihun mama mama yana nemanta, haka yake kiranta da sunna Mama kamar yanda ya ji suna kiran Mom. Khadija ba yanda bata yi ba dan ta hana shi rabar jikin Wujdane aman matsalar ita bata iya rarashi ba, bata iya jan yaro ba sai dai da yayi abu ta duke masa baki ko hannu shi yasa sam ba wata shakuwa a tsakaninsu Yau da wuri Alaidine ya dawo gidan dan ya farka da wuri ya tafi wajen sadakar bakwai, Tunda ya dawo yake lure da taketaken Alawiya, kazar kazar dinta take sam ba wani alamar rashin lafiya a tatare da ita Da wuri ya konta baci abinsa bayan ya gama nafilfilunsa, sai dai mai yarinyar nan tana yawan fado masa a cikin idannuwansa koda idannuwansa a bude suke, haka ya kwana juyi yana jawa kansa tsaki yana jin haushin kansa, harma ya yiwa kansa tambayar wannan wani irin tashin hankali ne haka? Sai dai ba amsa Da safe yana fitowa Alawiya ta sha kwaliyarta tana zaune tana shan shayi, Tsayawa ya yi a kanta ya mika mata hijabi, fuska a tanke ya ce" yau ko mutuwa kike a hanya sai kin je wajen rasuwar kannin mahaifina, dan haka ki mike mu tafi Ranta a hade ta saka hijabin ta mike ta bi bayansa, idan ranta yayi dubu ya baci da wannan lamarin, dan me yake son takura mata a rayuwa ne? Haka har suka karaso kowane bai cewa dan uwansa ufan ba Aba mutum mai mutane, sosai kofar gidan ta cika da mutane , a haka ta ratsa ta shige shi kuwa ya ja ya tsaya Malan Mahaifin su Wujdane sai jero adu.o.i yake suna amsawa har aka gama aka wawatse Matan cikin gidan ne ke ta fitowa har ya kasance du an fito sai na gida kawai Mikewa yayi ya shige gidan, Matar Anwar ce zaune saman tabarma, gefenta Wujdane ce rungume da Huzaifa tana bashi madara a bakinsa sai Aisha dake zaune itama da carbi a hannunta tana ja suna dan taba hira tsakannin matar Anwar da Wujdane Dan tsai ya yi daga nesa yana kallonta, yanda Boy idan ta kai bakinta ya dan zubun mata a habarta zai lashe abinsa yanai mata daria idan kuwa ta hana shi lashewar sai ya fashe da kuka, Ajiyar zuciya ya saki a can kasan zuciyarsa ya ce" Alaidine, ka san cewar a duniya ka yiwa kanka hani da soyaya da wata diya mace , ba dan komai ba sai dan gudun ta san sirrinka ta yi maka gori harma ta guje maka, Alaidine yarinyar nan lale mace ce, ta isa mace, aman konciyar hankalinka shine mafi girman bukatarka, so ka kawar da kanka a lamarinta , ko ba wannan fa karka manta ko ita wacece? Fitsarariya ce, yarinyar da kanninka ya so tamkar ransa har suka shaku, yarinyar da ta watsa kanta a banza , so plz ka fitar da tunanin nan, ka watsar da shi ka rufe idannuwanka a kyanta domin kyan dan maciji ne.... Toh fa readers kun ji dalilin Alaidine...........,,,,........ ku kanku kun san irin fitsarar Wujdane, toh aman ai Woujdane ba jahila bace🤔