[01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association (Uniterd we stand & succed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers) This novel Dedicated to saldefi student 2016 Bismillahi rahmanir raheem Ya Allah yadda ka bani ikon fara novel dinnan lafiya kasa na karesa lafiya .Ameen Page1⃣ A garin katsina Alhaji Jabir ya taso haifaffen garin ne iyayensa babu laifi sunada yali yana da amini wato Alhaji Aminu sun taso tun yarinta. Sunyi karatunsu na boko da arabi sun samu ilimi daidai kima ,bayan dawowarsu daga masters Allah yayiwa iyayen Jabir rasuwa ta hanyar hadarin mota. Kasan cewar shi kadai suka haifa yasa ya gaji duki mai tarin yawa na daga kamfanoni gidaje . Yakan yasa Aminu ya fara jin haushinsa saboda ya fiyeshi da komai. A haka sukayi aure Jabir ya auri wata buzuwa mai suna Fatima. Shiko Aminu ya auri Asma'u anan kusa dasu take kuma Allah yasa halinsu yazo daya. Wata tara daidai su duka suka haihu inda Jabir yasa sunan mahaifinsa wato Kabir ake kiran yaron da Manab. Aminu kuwa yasawa Dansa suna Jawad . Amintarsu tayi karfi sosai komai tare sukeyi sun zama tamkar uwa daya uba daya duk wani sirrin Jabir Aminu ya gama saninsa,gashi beda shaki da dukiyarsa komai zai iya aekatawa a cikinta. Shekarun su Manab 8 Fatima ta sake haihuwar santaleliyar yarinyarta kyakyawa ta karshe gata fara tas ,don duk ta fisu kyau nesa ba kusaba,ranar suna yarinya taci sunanta Saudatu suna kiranta Minad. Minad ta taso cikin gata da soyayya da kulawa ,kowa na matukar sonta musamman Abee dinsu daya ke sonta fiye da komai nasa. Ko kadan Minad bata da hayaniya dukda gatan data samu bae hanata samun tarbiyyah ba,wata iriyar soyayya sukewa juna ita da Manab. Some years latter Minad takai shekara 3 a duniya,nan mahaifinta ya sakata makaranta tare da yan uwanta. Da sallama Abee ya shigo gida ,yayinda Minad ke zaune a chair tana game da tab din dake hannunta kirar iPhone, gashi tasha kwalliya tayi matukar kyau. Da gudu ta taso ta fada jikin Abee tana fadin"Abee oyoyo" Rungumeta yayi sosai a jikinsa kafin yace"sannunki da gida Maman baba". "Yauwa Abee,muje kaci abinci na baka labarin school dinmu kaji" Minad ta fada Tsaye Amma tayi tana binsu da kallo kafin tace"sannunku da labari a tsaye,ko tunawa damu ba'ayi balle musan ka dawo". Dariya yayi kafin yace"ina nan da Mama na muna labartawa ne". Da murna Manab ya iso wurin ya karbi bag din Abee tare da masa sannu da zuwa. Minad na ganinsa ta duro ita saiya goyata dama nemansa take. Dariya Manab yayi yadanja karan hancinta yace"see u shiyasa na buya naki donna samu nayi homework rigimammiya" Goyata yayi suka wuce ciki suna dariya. Gidan Alhaji Jabir gidane mai cike da farin ciki,gashi wani irin tabkeken gida ya tsaru iya tsaruwa. M'I love u all 💘💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 . 💘💘 💘💘💘💘 💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association (United we stand and succeed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers) Page2⃣ Bayan Abee yayi wanka ya gama cin abinci ne ya fito parlo da niyan ya huta,sallamar Alhaji Aminu ne da iyalansa ya janyo hankalinsu shida Amma,maraba da zuwa suka farayi masu suka karaso cikin fara'a da murna. Bayan sun gaesa kafin kace me tuni masu aeki sun cika masu gaba da kayan makulashe. Kallo Amma Jawad yayi yace"Amma ina minad ?". Kafin Amma ta bada amsa tuni Minad ta fito da gudu tana saukowa a stairs tana fadan"ga Yaya oyoyo". A nitse Manab ya take mata baya ya iso ya duka gaban Daddy wato Alhaji Aminu, ya shiga gaishe dasu shida Momy. Minad kuwa kai tsaye ta makalkale Jawad tana murnar ganinsa dukda fushin da take dashi na ya daina zuwa ,hakan be hanata farin cikin ganinsa ba,dukda kankantar shekaru irin na Minad hakan besa ta kasa gane abunda take so ba,gata da masifar wayo sosai. Bayan sun gama cin abinci ne,suka tashi zuwa dakin wasansu,su Amma kuwa suka wuce zuwa dakinta suna labartawa. Anan ne Alhaji Aminu ya kyara zama ya tuskanci Alhaji Jabir yace"nazo ne neman wani abu wurinka ,kuma inada yakinin zan samu samoda iriyar tarayyar dake tsakaninmu". Nan Alhaji Jabir ya tattaro duk natsuwarsa yace"ina jinka ,kuma Allah yasa zan iya yi maka". Murmushi Alhaji Aminu yayi yace"wani abokin harkata ne yaga companyn ka na *MINAD INVESTMENT* ,yana so ka sayar masa dashi ". Kallonsa kawai Alhaji Jabir yayi kafin yace" nasan kafi karfinsa a wurina amma kayi hakuri ba mallaki na bane ,kasan na Mamana ne na malka mata shi tuni ka bashi hakuri". Wani kululun bakin ciki yai wa Alhaji Aminu tsaye a rai,yana tuna asarar makudan kudin da zaiyi,wata irin sabuwar tsanar Jabir ta sake darsa a zuciyarsa,amma ya daure yaci gaba da lallabashi. Ko kadan Alhaji Jabir yaki sauya ra'a ya tsaya kan maganarsa ta farko. Wayancewa Daddy yayi yace"to ae shi kenan saiya yakura dama jarabawa nayi,karka damu komai ya wuce". Haka suka karashi firarsu har tsawon yinin ranar kafin suka tafi gida,inda sukayi maganan anan Abee yabarta. 2:30pm Daddy ne keta safa da marwa a tsakiyar tankadedan dakinsa hankalinsa tashe yana tuna irin dumbin asarar da zaiyi . Kallonsa Momy tayi tace"ae wannan ba masoyinka bane wanda zaisa kayi asarar makudai haka,kuma ka zuba masa ido kana kallonsa,bazai yiwuba kasan nayi Daddyn Jawad". "To me zan masa,naga dai nasane kuma yace bazai sayar ba dole muyi hakuri..." Kafin ya idasa maganarsa Momy ta dakatar dashi ta mike tsaye ta fara zagaye shi kafin tace"kada kaban kunya mana,ba haka nasan Mijina ba,a maka wannan asara kuma kace kayi hakuri, never ya kamata ka masa abunda bazai taba mantawa dakai ba ka koya masa hankali". Lumshe ido Daddy yayi yace"me kike tunanin zan masa dazai tsaya masa arai". Dariya tayi kafin ta daure tuska tace"badai companyn Minad bane,kuma ka manta yafi sonta da komai nasa,to kanta zaku huce Ku dauketa Ku lalata mata rayuwa Ku rabasa da ita na tsawan shekaru,ta tashi a matsayin kafura,wacce batasan ta kalli gabas ba ,Ku fitar da ita daga kasar nan,kasan babu abunda zaisashi bakinciki ,kuma yai masa taban da bazai taba goguwa ba,ya hanaku kamtanin Minad,toku Ku nisan tashi da Minad din baki daya". Wata irin dariyar mugunta ya fashe da ita,sannan yace"gaskiya inajin dadin zama dake,dama kinga Samol zai koma,sai kawai ya tafi da ita America ".yana gama fadar haka ya fita daukar wayarsa a parlo. Wani irin farin ciki ya ziyarci zuciyar Momy ganin tasa Mijinta farin ciki ,haka ta kwanta cike da murna a ranta. M'I love u all 💘💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 💘💘 💘💘💘💘 💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers. Page3⃣ Daddy kuwa yana fitowa parlor ya dauki wayarsa ya kirawo Mr samol kuma ya amince zai dauketa subar kasar,sannan ya kuma kiran amintattun yaransa ya fada masu mai yake buka,ya kuma ja kunnensu akan kada a samu matsala kuma ya zama dole su kawo masa Minad duk rintsi.haka Daddy ya kwana cike da farin ciki dajin dadi. 7:10am Nani din Minad ta futo rike da ita sanye cikin uniform, sunyi masifar karbar jikinta siket din iyakarsa gwaiwa red sai farar riga da kwalliyan red a jiki ,gyaran gashi aka mata sai y'ar karamar hula a kanta red. Daga stairs suka sauko iske Abee tayi yana karatun jarida idonsa sanye da white glasses, sai Amma da Manab a dining table Manab na break fast,shima yayi shirin school da irin colour din Jikin Minad,saidai shi ya saka suit red da ratsin White students din little angle kenan. Cikin sauri ta isa ga Abee ta rungumesa tace"Good morning Abee". "Morning My Dear,maza aje ayi break fast kada kuyi latti". Gyada kai tayi ta wuce ta gaeshe da Amma da Yayanta Manab,nan fa aka soma rigima da ita ita bazatayi break ba,da kyar Abee ya lallabata yasa tadanci Irish potatoes da stew din egg. Cike da girmamawa Nani ta shigo tace"Hajiya driver din ya shirya kada suyi latti". " OK suna zuwa yanzu"Amma ta fada. Har sun kusa fita Minad ta dawo tayi hugging Abee da Amma a tare kafin tace"I'm going to miss u". Dariya sukayi kafin Abee yace"Allah yayi maki albarka ayi karatu sosai saikin dawo" Ta tsaya surutu Nani ta sab'eta tana fadin"sai kinsa kun makara ko". Dariya suka fita sunayi,girgiza kai Amma tayi tace"inasan Minad na kasancewa da Nani ,tana matukar farin ciki suna son junansu". "Ae gaskiya Jamila tayi tana kula da Mamana sosai". Haka suketa dan fira jefi jefi. Dai dai wannan lokacin ne yaran Alhaji Aminu suka takewa Motar su Minad baya,har suka shiga cikin makaranta,su kuma sukayi parking suna tsara yadda za'ai su dauketa. 1:30pm Jazi ya shiga cikin little angle yana zagayawa donko an tashi yaran kanana dake primary, nan yai sa'ar hango Minad na dososhi a nutse,murmushi yayi da yaga ta iso dap dashi ,nan ya zubar da kudin dake hannunsa ya juya ya soma tafiya sannu sannu. Dafe kai Minad tayi time din data iso wurin kudin tace" oh my God kuji wancan Yayan ya yarda kudinsa ,maybe ma bashi da wasu".ganin zai bace mata yasa ta dauki kudin ta bisa da gudu tana kiran"Yaya,Yaya". Lokacin data iso gate ba gateman yadan zaga bandaki hakan ya bata damar fita ,tsaye ta hangesa ta isa gunsa da sauri tace"Yayana kana neman kudinka ne ko?". Daga mata kai yayi alamar eh ,kafin tace"gasu ka zubar dasu a cikin school dinmu ka rika kula da kudi kaji ko suna da mahimmanci a rayuwarka" Da sauri ya ruko hannunta yace"na gode" "Ka godewa Allah ,bani na taemako kawai nayi". Da murmushi ta juya wani abu Jazi yai saurin shaka mata a hanci ,ba jimawa ta lankwabe zata fadi,saurin daukarta yayi ya fada da ita mota inda su Tiger suke da sauri suka fizgi motar suka bar wurin. A kuma daidai lokacin Driver dinta ya shigo wurin ya shiga don daukarta,duk fadin Makarantar aka duba babu Minad ,Manab dayaji labari da sauri ya fito idanuwansa sunyi jawur ,a nanne y'ar ajinsu ke fadar taga fitarta waje,wasa wasa har wurin 3:00pm babu alamun Minad a school din,a dole aka sanar da Abee dinta. A rude ya shigo makarantar yana goge gumi nan aka fada masa duk abunda ya faru a take ya Ciro waya ya shaidawa police abunda ke faruwa suka bazu don fara bincike a kanta. Kamar sunsan haka zata faru kai tsaye airport suka wuce da Minad anan suka samu su Alhaji Aminu ,kai tsaye suka mika Minad hannun Lisa wato matar Mr samol,hannu biyu ta karbeta kasancewar bata taba haihuwa ba gata da son yara. Kallo Mr Samol Alhaji Aminu yayi yace" gata nan amana kada ka ruguza mana plan please,kada Ku dawo har nan da tsawon shekaru masu dama". Murmushi Mr Samol yayi ya fada a gurbatacciyar hausarsa"baka da damuwa zanyi hakan". Bankwana sukayi suka shiga jirginsu dazai tashi yanzu zuwa America, Alhaji Aminu na tsaye har jirgin ya tashi sannan ya juya zai tafi karar wayarsa ta tsayar dashi nan yaga amininnasa ne ya dauka tare da sallama. "Kazo Minad ta bata har yanzu ba labarinta" Abee ya fada. "Subuhanallah sai kace wasu kaya,bazai taba yiwuwa ba,ganinan zuwa school din" Bai jira ansa ba ya kashe wayar tare da bushewa da dariyan mugunta sannan ya nufi school din. Lokacin daya isa school din bala'i ya shigayi anata rarrashinsa amma Sam ya tubure yaki saurarawa yana fadan laifin makarantar ne da suka barta ta fita. Da kyar Abee ya lallabashi suka koma gida. A parlo suka samu Amma zaune kallo ta bisu dasu ganin kowa fuskarsa cike da muwa sannan ta fara tambayar ko lafiya. Murmushi Abee yayi yace"dole mu dauki kaddara Amma,Allah shi yasan me take nufi da hakan". "Wait Dr wani ne ya mutu ko yaya ina Minad ?". "Sai hakuri Amma ,Minad ta bata tun dazu ba'a sameta ba". Alhaji Aminu ya fada. Da sauri Amma ta mike hawaye suka gangaro mata a fuska tace"never duk inda y'ata ta shiga dole a fito da ita bazan taba lamunta ba" Tana karashe magana jiri ya soma dibarta basu ankara ba sai ganinta sukayi kasa a sume. M'I love u [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succeed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers. Page4⃣ Da sauri sukayi kanta Manab ya dauko glass cup da ruwan sanyi yana zuba mata yana fadan "Amma na ki tashi don Allah". A hankali ta soma bude ido tana binsu da kallo,sosai ta rike Abee tana kuka lokacin da ta tuna abunda ke faruwa. " yanzu kana nufin Minad ta tafi ta barmu?,wanne irin bakin ciki ne wannan me ta aekatawa wani". "Kiyi hakuri kaddara ce ta kama haka idan Minad rabanmu ce zata dawo garemu,kuma kinga yan sanda na bincike akan lamarin" Alhaji Aminu ya fada. Nan dai sukaita ta bata baki harta hakura ta rungumi kaddarar data iso garesu. Wasawasa abun yaci tura duk inda ake tunanin Minad ba'a sameta ba har sun hakura sun fallafawa Allah al-amarinsa suna addu'ar samun zabin alkairi dukda damuwa na damunsu. Rike da plate din abinci Momy ta fito kai tsaye dakin Jawad ta nufa ,can jikin bango kusa da bed ta gansa ya hada kai da gwaiwa,a hankali ta dafasa tace"Mike damunka Jawad ka duba yadda ka koma,baka cin abinci kullun sai damuwa". Hawayen idonsa ya goge yace"Momy yanzu mun rasa Minad kenan?,gaskiya Wanda ya dauketa bashi da imani,kuma na ganesa sai munyi shara'a don bazan taba yafe masa ba". "A'a Jawad ka daina fadan haka,Ku mata addu'a zaifi " Nan ta lallabashi yadanci abinci,har bacci ya saceshi ,nan ta soma tunanin yadda zata bullowa lamarin Jawad. America Tunda su Samol suka isa America Minad ke masu kuka a kaita Abee,wani irin son yarinyar ya darsu a zuciyar Lissa tana matukar son Minad tana bata kulawa musamman daya kasance basu taba haihuwa ba. Yanayin kulan da suke da ita yasa cikin kankanin lokaci Minad ta mance wacece ita, minene ASALIN TA,tuni sunanta ya tashi daga Minad ta koma tana ansa suna *SARENA* kwata kwata kamanninta duka sun rikede,tana zaune cikin gata da kula da soyayya taban mamaki komai take bukata shi take yi ,musamman Samol da yake yana da kudi sosai,tuni ya riketa kamar y'ardaya haifa,ya sakata makaranta mai kyau gata ta koyi riko da addini sosai bata wasa da addinsu. *SOME YEAR'S LATER* 💘💘💘💘💘💘💘 Cike filin makarantar yake duk inda ka juya zakaga dalibbai da kayan bautar kasa(N Y S C).ko wanne cike yake da farin ciki,da iyayen zagaye da wurin. Wata doguwar kyakyawar yarinya na hango fara tas gashinta har tsakiyar baya yasha gyara fuskarta babu wasu tarkacen makeup a jiki kayan bautar kasane jikinta tayi tokkin da farar green din na daure ga kugunta rike take da sateficate dinta da gudunta ta iso wurin iyayen nata ta rungume wani dattijo Dan gayu dashi tace"I miss u Dad" Sannan ta rungume matar dake gefanta tace"Mother I made it". Dariyar farin ciki sukayi suka rungume juna tare,suna kukan farin ciki.pic sukaci gaba da dauka kafin suka taho gida cike da farin ciki dajin dadin da soyayyar juna. Nigeria Yanzu kam alhamdullih Amma ta daina damuwa ta boye abun a ranta, ta rungumi kaddarar da Allah ya dora mata. Jawad da Manab a kamfanin Abee suke aeki sun karanci Architecture sun zama manyan samari kyawawa saidai Jawad black beauty he ba fariba sosai ,zumuncinsu sai karuwa yake bacci kawai ke rabasu. Haka zalika ga iyayensu ma suna gudanar da rayuwarsu cikin jin dadi da soyayyar juna,yayinda Daddy da Mommy suka zama masu fuska biyu . M'I love u all Muhphat love 💘💘💘💘💘💘💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers Page5⃣ Da karasowar su Sarena gida da murna ta fada a chair tana fadin"I miss u home". "Ke nasan kin gaji ko,kizo kiyi wanka ki huta mana" Mother ta fada tana kamota. Tayata tayi ta cire kaya tare da daura dan karamin towel a jikinta before ta shiga toilet ,tuni Mother ta fitar mata da kayan da zata saka kafin ta fita,gidan ya kauraye da kamshin girkegirke kala kala da sukayi don tarbar Sarena. A hankali ta zuro kyakyawar kafarta daga toilet zuwa cikin tankameman dakinta daya hada komai ya kawatu,karamin towel ne a hannunta tana goge gashin kanta dake jike da ruwa,bakin mirrow ta tsaya ta shafa mai tare da powder jikinta ta feshe da turere kafin ta dauko kayan da Mother ta fitar mata,wando ne iyakarsa rabin cinyarta kalar brown sai riga marar nauyi fara iyakarta kugu,gashin kanta ta shafe damai ta sakesa har gadan bayanta ,fashion silifas ta saka kafin ta kara gyara yar siririyar sarkar zinarin dake zanan kuroz a wuyanta sannan ta fito parlo. Zaune ta samu su Dad suna jiran ta fito suci abinci,da murmushi ta karasa tace"kuyi hakuri na barku kunata jirana ba". "Kinga zo nan y'ata ,ba wani damuwa ae wannan ranarki ce" Dad ya fada. Kusa dashi ta zauna ta dora kanta a kafadarsa tace"ina sonka Dad". "Idan aka biye maku zamu kwana bamuci abinci ba,don murnar dawowar Sarena,gashi har Furanko ya iso ma". Mother ta fada. " wa kuma yace dashi na dawo?".Sarena ta tambaya "Nice mana,ki tsaya Furanko yaron kirkine y'arta kinji" Bata sake fadan komai ba,suka mike suka tafi dining area ,da sauri Furanko ya shigo gidan da murna yana fadan"welcome back home my Dear". "Thank u ta fada ,sannan suka rungumi juna,kafin suka soma cin abincin da aka tara musu. Furanko ya kawo mata gifts sosai duk abunda yasan tana so saida ya siya mata duk a matsayin murnar dawowarta gida. Zaune suke a parlo suna fira anan ne Dad ke fadawa Sarena zasu koma gida Nigeria akwai wani aeki da zaiyi tsawon 2years,zasu farayin gaba suga komai ya daidaita before ta biyosu. Wata irin tsalle ta daka da murna zataga Mona kawarta da sukayi karatu anan America tare,rungume Dad tayi tana masa godiya tunda zasuje gobe ita zatazo jibi,key din mota ta zira ta fice domin zagaya gari bag kawai ta dauka. Nigeria Zaune suke a desk suna duba wani Zane da sukayi aekinsa.mika Jawad yayi yace" kai Broz na gajifa ga yunwa da nakeji" Murmushi Manab yayi yace"aekin kenan kaida ba mata ka ajiyeba sai son kaje gida kawai". "To ae daya muke donko babu mai aure cikinmu ,balle ka fadan haka". Cewar Jawad. " zauna nan saidai kaji ana ayyiriri Manab yayi aure" Dariya sosai Jawad yayi kafin yace"da y'ar fura ba". Duka Manab ya kaimasa ya goce,haka sukaitayin firarsu kwanin birgewa. Yau tun safe Dad da Mother suka shirya don jirginsu na safene,tare da Sarena sukazo airport din har suka shiga jirgi tana daga masu hannu,hawayen idonta ta share jin wayanta na kara yasa ta laluba aljihun wandonta ta zaro Furanko ta gani ta dauka da fadin"hello" Banji meya fadaba sai naji tace"no bana gida ma hadu anjima"kafin ta kashe wayar. Shima Abee da safe ya shirya ya tafi airport don zaije America ya duba wani aeki zai dawo jibi. Dad da Mother sun sauka a garin katsina a JRA kafin su iso an kyara ko ina a gidan kasancewar gidan babban gida ya tsaru iya tsaruwa ko ina sai Wanda ya gani ,a gajiye sukayi wanka,sukaci abinci,nan Mother ta soma waya da Sarena tana fada mata yanayin gidan da yarda Nigeria take. Dariya Sarena tayi tace"na kagara nazo Nigeria Mother,kinsan ban taba zuwaba,amma hakanan naji ina matukar son kasar nasan zaiyi dadin zama,musamman idan muka hadu da Mona" "Ki kwantar da hankalinki ba jibine tahowanki ba,ae karki damu kanki mana,ina kewarki y'arta. Fira sukayi sosai sannan sukayi bankwana. M'I love u all Muhphat love 💘💘💘💘💘💘💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succeed: our ambition is to entertain & motivate the mind of readers. *Ina kike Yusra Jafar wannan page din naki ne na gode da soyayyarki ga ASALI na ,(my Junior tnx ones again)* Page6⃣ Yaune ya kama zuwan Sarena Nigeria kasar data dade tana mafarki a rayuwarta wani irin farin ciki take ciki,ta hada komai daya kasance zata bukata,jirgin safe zata bi,shiri tayi cikin wani farin wando iyakarsa gyaiwa ,pink din Riga ta saka medan siririn hannu irin na vest ,gashin kanta ta gyara ta daure da white rebom pink din tooms ta saka a kafarta kafin ta jawo akwatinta ta fito parlo. Zaune ta samu Furanko a parlo yana jiran fitowarta,da mamaki ta karasa wurinsa tace"yaushe ka shigo ne". "Dama bazaki sani ba,don nace su barki ki shirya tunda murna kike zaki tafi ki barni" Furanko ya fada. Dariya tadanyi kafin tace"kada ka dauka haka Furanko kasan inason kasancewa dakai ur my best friend u know". Kamo hannunta yayi ya zaunar da ita,abincin da Nani ta ajiye ya dauko zai bata a baki,rike hannunsa tayi tace"I will do that ".karba tayi ta soma ci kadan tadanci da sauri ta mike kasancewar agogon hannunta data duba taga time ya tafi,bankwana tayima su Nani kafin ta shiga motar Furanko suka wuce airport. Fitowa tayi daga motar don yanzu zasu tashi,kallonta Furanko keyi cike da tsantsar soyayya wani irin kara jin sonta yake a ransa,hura masa iskan bakinta tayi ,firgigit ya dawo daga duniyar tunanin daya afka. " me kake tunani nixan wuce"ta fada . Rungumarsa tayi tace"I'm going to miss u". Karfin hali Furanko yayi yace"miss u too,ki kula da kanki sai wani lokacin" Murmushi tayi ta shafa gefan fuskarsa kafin ta juya ta tafi. Har jirginsu ya tashi Furanko yana wurin tsaye tunanin ya zaiyi da soyayyar Sarena yake,tun suna yara suke tare amma ya kasa fada mata yana sonta gashi hartatafi ta barshi dole yasan abunyi. A jirgi zaune take cikin farin ciki ta rasa meye dalili,sitmate dinta ta kalla Dattijone mai kyau yasha manyan kaya bamai haske bane sosai saidai kyakyawa ne farin glass ne a idanunsa yana duba jarida,haka kawai taji mutum ya burgeta kallonsa kawai takeyi har suka iso. Juyowa yayi zai dauki bag dinsa karama dake gefanshi da sauri ta rike tace "Bari zanyi ,zan dauka maka". Murmushi yayi yana jin son yarinyar a jikinsa har cikin ransa yake sonta,tare da tata ta hada ta dauko suka futo,tsaye tayi cak jin wata iriyar sanyayyar iska da bata tabajin irinta ba tana ratsata har cikin kwakwalwar kanta,furzar da iskan bakinta tayi sannan tabi bayan mutumin har inda ya zauna,aje masa bag din tayi sannan tace"zan wuce Daddy ". Wani irin yar yaji a jikinsa data kirasa da Daddy dukda hausarta bata fita sosai ya fahimci abunda take nufi" ki tsaya y'ata yaro na yazo,saimu ajeki gida". "Na gode Daddy ,ban taba zuwa Nigeria ba,ballantana na fadi inda zanje,Driver dina ya karaso ". Murmushi Abee yayi sannan yace" na gode Allah yayi maki albarka kinji". Batasan me zata fada ba amma tadai San addu'a yayi mata "na gode" ta fada sannan ta juya ta tafi. Binta yai da kallo ya fada a fili"yarinya mai kirki da musulmace dataji dadi kuwa akwai taemako". Tafiya takeyi ta isa wurin driver dinta don ta ganesa ta hanyar waya da sukeyi ,a hankali take tafiya kanta a kasa ji tayi ta bugu da mutum luuuuuu tayi kasa zata fadi,cikin sauri Manab ya ruko hannunta yana bata hakuri. Wani kallo ta bisa dashi don bata fahimtar abunda yake fada siririn tsaki taja ta wuce.gyada kai kawai yayi ya wuce wurin Abee. Daukarsa yayi a mota sai faman sannu yake masa suka wuce gida. Itama mota ta shiga suna tafiya tana bin ko ina da kallo before su karaso katsina daga kano. "Kaga Jawad ka tashi daga wannan yamutsin abuncin da kakeyi da saika shekara kana yi sarkin bakin rai kawai,kuma kasan yau Nabila zata dawo gidan nan ,saran idan tazo ka mata wannan bakin mishkilancin da rainin wayan daka saba,kuma kasan halin innarku sarai kan Nabila babu abunda bazata iya ba. Kawar dakai yayi gefe cikin sanyin murya yace" ae dama gulma ta kawota sai inga Uwar da zata dauka a gidan". "Haka zaka kare sarkin bakin rai ,Allah ya shiryeka". Be sakebi takan Ummanba ya mike ya nufi part dinsa ya zube bisa tafkeken gadonsa,kallon pic din Minad yakeyi yana sakesake arai yadaiyima picdin zuro,ga kuma murmushin da yakeyi. Duk kwakwata dole na kyale Jawad donko na kasa gane komai yake fada. A gajiye su Sarena ta karaso gida dake GRA da sauri ta hada iyayen nata ta rungumesu tana fadin irin missing dinsu datayi. Cike daso da kauna da farin ciki suka tarbi y'ar tasu suna jin kaunarta. Da gudu Nabila ta shigo gidan tana kwalawa Umma kira ,ba laifi tana da kyau saidai daka kalli farinta kasan bleecing ke aeki ya maida ita fara bata da kiba doguwa ce tayi kyau kwalliyan datayi,da gudu ta rungume Umma tana jin dadi " keni karki karyani kinjiko ,duk murnar ne" Tabe baki Nabila tayi tace"kinsan nayi missing dinki shiyasa nace zan dawo nan da zama fa Umma". "To Allah ya bamu ikon rikeki da gaskiya y'ar albarka,zako muji dadi".Umma ta fada M'I love u 💘💘💘💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we sand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's Page7⃣ Some days later Sarena ta fara zama y'ar gari domin Mona na nuna mata wurare da dama a gare,magana taiwa iyayen akan cewa zata nemi aeki a companyn da Mona ke aeki,ko kadan badan ransu yasoba suka barta domin basa son bacin ranta. Tun sassafe ta shirya cikin riga da siket ,siket din yellow colour mai roba iya karsa rabin cinyarta ,riga ta saka yellow mai hannun Vest sannan ta dauko boyfriend jaket black colour ta saka ,daure gashinta tayi ,dogon takalmi Mae tsini black colour ta saka tare da bag dinshi ,Key din motarta ta dauko tayo waje tana duba agogon hannunta . Da sauri Mother ta tareta tace "haba bazaki break ba,kuma ki bari driver ya kaiki banason fitanki ke kadai". " is OK Mother zanyi break anjima,kuma na soma gane gari nasan inda zanje basai kin damu dani ba".Sarena ta fada Bude baki Mother tayi zatayi magana,da sauri Dad ya rufe mata baki yace"ki barta taje,bana son kina matsa mata". Rungumesu tayi tare tace"bye bye"bata jira cewarsu ba ta fice daga gidan,kai tsaye wurin Motarta ta nufa kirar Vive black colour ta shiga ta fita daga tankamemen gidan.kai tsaye companyn ta nufa tasan anan zata iske Mona. Ajiyar zuciya Mother ta sauke tace "kawai na damu da itane" "Na sani Lissa amma karki damu ,babu abunda zai sameta" Samol ya fada yana rungume Lissa a jikinsa. Titowa yayi sanye da black suit sai farar inner wear yayi tokin jikar laptop dinsa na a hannunsa yayi masifar kyau ga wani sihirtaccen kamshin dake fita a jikinsa,kai tsaye dianing area ya nufa,anan ya iske su Daddy ,gaeshesu yayi,cike da zumudi Nabila tace"Yaya Jawad ina kwana". Ba yabo babu fallasa yace"qlau".zama yayi a chair yana furzar da iskan bakinsa. "Kiyi saving dinshi kinji Daughter" Momy ta fada. Tam ya daure fuska wani mtsssss yaja tsaki ,wani irin mugun kallo ya bita dashi ,ya tashi ya dauki bag dinsa ya fice ko bankwana. "Uban yan bakin rai,baka daiji dadi ba". Umma ta fada. Murmushi Daddy yayi yace" sai kunbi yaronnan a hankali domin kunfi kowa sanin halinshi ,ke kuma Nabila saikin daure kin hada da hakuri akan Yayan naki". Yana fita kai tsaye company ya nufa office din Manab ya wuce dayake shine M.D na company, Jawad kuwa Director ,fuska daure ya shiga office din ya zauna ba tare dayace kala ba,Shima Manab bai tankashiba saida ya ida yan danne dannensa a laptop sannan yace"yadai mutumin yau na ganka a fusace". Mtsssss tsaki yaja before yace"Momy ce mana,sai ta rika saka wannan yarinyar tanamin abu bacin sunsan bana so". Dariya Manab yayi yace "to minene a ciki ba kanwarka bace sarkin son girma". " kaga kaima karka batamin rai malan"Jawad ya fada a fusace. "Iz OK,yanzu ba wannan ba,yau sabuwar ma'aikaciyarmu zata fara aeki ,a America tayi karatu result dinta yayi kyau komai da muke bukata tana dashi,don haka itace ,assistant Director, mataimakiyarka,tunda dama a kujeran ba kowa". " ba damuwa"kawai ya fada ya fice ya nufi office dinsa. A parking space tayi parking sannan ta Ciro waya ta kira Mona ba jima ta karaso suka shiga ciki,office din Manab suka shiga,kallonta kawai yake yanason tuno inda ya taba ganin face dinta amma ya kasa itama haka,sharewa yayi ya ida mata abunda zaimata ya turata office dinta.zata fara aeki daga ranar.godiya sukayi suka futo,Mona kam wucewa tayi office dinta itama. Tsayawa tayi a bakin office din nasu sannan tayi knocking, "yes come in" ya fada. A nutse ta fara taku zuwa cikin office din ta isa kusa da table dinsa,tun daga kan santaleliyar kyakyawar kafarta ya soma kallonta har zuwa kyakyawar fuskarta wani irin dummmm yaji a kirjinsa lokacin da suka hada ido da ita,itama hakan taji ya faru da ita,daurewa tayi tace"Morning sir,nice sabuwar office mate dinka da zamu fara aeki tare". Dan murmushi yayi da gefan baki yace"your welcome". Hannu ta mika masa tace"thank u,I'm Sarena Samol nice to meet u". Shima hannun ya bata suka gaesa yace"I'm Jawad Al-Ameen,nice to meet u too" Wani irin yar yaji lokacin da hannunwansu suka hadu,wurin table din daya nuna mata ta nufa ta zauna,tasowa yayi ya Dan nununa mata aekin dake garesu da yarda suke aekin,godiya ta masa ta soma aekin. M'I love u all [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers *IT UR DAY YAYA HAYAT* *when a year is dead,a year is born,when poverty dimishes,riches overflows,when sadness is gone ,happinesses is all that u have so as u have achieved from the past..happy birthday! Yaya hayat ones again.* Page9⃣ Suna isowa asibitin da gudu aka iso da gadon daukar mararsa lafiya,aka dorashi a sama aka soma turashi zuwa emergency da gudu Sarena ta juya zata bisu riko hannunta Manab yayi ya jawota,jikinsa ta fada tana kuka mai tsima zuciya,rarrashinta ya somayi yana bata hakuri yace"kiyi hakuri dama yanayin haka cos yana da ciwan zuciya ,kada ki damu zaiji sauki". Share hawayen idonta tayi tace"ciwan zuciya,me kuma ke damunsa meya rasa haka". Shiru Manab yayi yana kallonta ya kasa fada mata komai,tunani yakeyi da yanzu Minad takai kamar haka ko ,kuma da yanzu suna tare,ji yayi hawaye na neman zubo masa yayi sauri ya kauda kai gefe dai dan fitowar Salim suka wuce office, anan akabar Sarena tanata saka da warwara a ranta. Gaesawa sukayi da Salim sanan yace"yanzu kuma me akayi masa,ciwansafa yana kara gaba fa". Murmushin yake Manab yayi yace"look at u kaima kasan damuwar ae basai an masa komai bama yana tashi". Dafe kai Salim yayi yace"wallahi Manab i don't want to lose my friend, ya kamata I yanzu mu fallafawa Allah lamarinsa domin shikadai yasan inda Minad take kuma shizai kareta". "Haka ne friend buh kasan yanda Jawad da Minad suka taso,abun yafi karfinmu saidai mu tayasa da addu'a,bari na kirawo su Umma". Lokacin aka fito da Jawad a bed yanata sharar baccinsa daki aka canza masa,da sauri Sarena ta shiga dakin tana kallonsa cike da fargaba da tsoro,addu'an ya tashi kawai takeyi wayanta ne ya soma ringing tana duba taga Mom ,dauka tayi jin tana kiranta emergency yasa ta sauke wayar a kunne ta juya tana duban Manab dake bayanta. " don't worry, Ummansa tana zuwa yanzu zaki iya tafiya,kiji kiran da ake maki,hannu tasa ta janye gashinkanta zuwa baya,ta duka ta sumbanji Jawad a goshi"tace,fatan samun lafiya,kawai na damu dakai, I will be going"ta fadawa Manab "Ga car key dina kije da ita". " no am ok zan dauki mota naje company na dauki tawa"bata jira mezaice ba ta fice daga dakin da sauri tana duba Jakarta,ashhhhh naji ta fada tana dafe gefen kanta yayinda Nabila itama taja baya rike dakai tace"ke dabbar inace bakya ganine ko hanyan ance ta tsohoce kafura kawai". Juyar dakai Sarena tayi ta duka ta dauki wayanta tabi ta gefanta ta wuce,da sauri Nabila ke shirin binta Umma ta riko mata hannu tace"kiyi hakuri muje muga yayanki". "Umma harta isa wacece ita,aena rike face dinta zamu hadu wata ran" Nabila ta fada tana kumfar baki. Sarena kau taje company ta dauki Motarta tuna maganganun Nabila a kanta ya tilasta mata ta yanke hukunci dole ta samu Wanda zai koya mata Hausa sosai ko biyansa zatayi,da wannan tunanin ta isa gida. Tana shigowa parlo ta saki Jakarta a chair ta dauki glass cup mai dauke da ruwan sanyi ta kurba,da sauri Lissa ta nufo ta kamata tace"ke Sarena meke damunki naga kin damu da yawa haka?". Murmushi Sarena tayi tace"a'a Mom kada ki damu ba komai bane ,kawai na gaji ne" "Ki samu kiyi wanka ki huta kinsan na damu dake sosai" kama hannunta tayi suka shiga dakin Sarena,taimaka mata tayi ta cire kaya ,saida ta tabbatar ta shiga toilet sannan ta baro dakin,kai tsaye kitchen ta nufa wutin Nani kas tasa ta hadawa y'arta abinci takai mata daki. Tana fitowa wanka taci karo da abinci a table ,tsane jikinta tayi sannan ta saka vest da karamin sikat rabin cinya ta feshe jikinta da turare ko bra bata saka ba,sama sama taci abincin sannan ta kwanta a bed tana tunanin Jawad da haka har bacci ya kwasheta. Su Umma kam suna shiga sukayi kan Jawad ,Umma ta soma shafa masa fuska,a hankali ya fara bude idonsa yana binsu da kallo harya isa kan Manab"ina Sarena?".abunda ya fada kenan. Murmushi Manab yayi yace"ta samu emergency call ne taje gida wurin Mamanta,kada ka damu tana lafiya" Sai a sannan ya kalli Umma yace"sannu da zuwa". Murtuke fuska tayi tace"ae nasa baka ganniba,tunda saida ka gama tambayar wacce ta fini". "Kiyi hakuri " kawai ya fada.Nabila ta soma masa ya jiki cikiciki ya ansa kafin yace"nifa mu koma gida bazanyi zaman hospital ba,ina Salim din yake". A dole suka sallamesa a ranar badon sunso ba saidon kafewarsa don tunda ya fada sunsan zai iya tafiyarsa gida ne. Bayan wani lokaci Jawad ya warke tas yau tun sassafe yake shiri zai koma office as everyday wankan suit yayi white colour da inner black yayi masifar kyau sosai kaman ba shiba fitowa yayi yadanyi break ya kama hanyan company, parking yayi ya fito yana takun kasaita kai tsaye office dinsu ya nufa a kofa sukayi karo da Sarena tsaye sukayi suna kallon juna,sanye take da White wando har kasa sai black riga mai Dan karamin hannu gashinta a gyare yake ta zubosa har gadon bayanta yanata sheki plat shoe ne kafarta baki tayi kyau sosai sai zuba kamshi takeyi,kallon juna sukeyi kamar a yau suka fara ganin juna. Wai Allah kuyi hakuri da wannan M'i love u all Ur comments is needed shizaisa mu zage my gane kuna so mitayi maku typing ba ji ba gani 💘💘💘💘💘💘💘💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers. Page8⃣ Cikin sauki Sarena ta gane komai da company ke bukata da aekinta ,ba laifi sun saba da Jawad yana sakan mata fuska har labari sukeyi a tare cikin kankanin lokaci sukayi wani mugun sabo da ita. Zaune take a chair dinta ,tana sanye da dogon riga iyakarsa rabin cinyarta purple colour ta daure kanta da purple riboms dogon takalmi ne kafarta farare tas fuskarta tadanyi simple makeup sai kamshi take kallon farar agogon dake hannunta tayi taga tuni time ya wuce gashi Jawad bezo ba haka nan taji ta damu,Ciro wayarta tayi kirar IPhone ta soma kiran layinsa harta tsinke ba'a daga ba,kara kiran layin tayi. Nabila dake gefen wayan ta juya ta dubi fuskar Jawad dake sharar bacci akan makeken gadonsa sannan ta dauko wayan *Special* ta gani ya bayyana akan screen din wayan,wani bakin ciki ne ya turniketa ta daga wayan. Ajiyar zuciya Sarena ta sauke sannan tace"thank god,meke faruwa bakazo office ba,duk kasa na tsorata". Wani murmushi meban takaici Nabila ta saki idanuwanta suka canza kala tace"Ke malama dakata kin cikamin kunne,idan kinason zama cikin farin ciki ki fita daga hanyan mijina,karuwa kawai"bata jira cewar Sarena ba ta katse wayar. Bin wayan da kallo Sarena tayi tana nazarin maganganun da aka fada mata,bata wani fahimci abunda aka fada ba amma tasan fadane ake mata,ji tayi babu dadi kawai saita share taci gaba da aekinta. A hankali Jawad ya soma bude idanuwansa ya saukesu akan Nabila dake rike da wayarsa,kara tamke fuska yayi yace"uban meye ya hadaki da wayata?". "Dama haka zaka fada ae,komai zan maka baka gani ya kamata a yanzu ka gane cewa *ina sonka*Yaya Jawad so kake sonka ya kasheni,ka tausayamin mana". Mikewa yayi zaune yana binta da mugun kallo yace" ke ina wasa dake ne?,yaushe har kika samu daman fadamin haka zan takaki a wajen nan,ubanwa yace kika shigoman daki".fizge wayansa yayi ya tankadata kasan bed din kanta ya bugu da kasa. Hawayen bakin ciki suka fara gangaro mata a fuska ta dafe kai"tace ko kasheni zakayi bazan taba daina sonka ba,kuma zanga ita y'ar iskar yarinyar dake kiranka"da gudu tabar dakin ta toshe bakinta ta nufi dakinta tana kuka. Hankalinsa a tashe ya duba wayan yaga wacce ta kirashi ganin number din Sarena yasa ya dafe kai yana tunanin meta fada masa.shawara yayi yaje office din yanzu,da sauri ya mike ya fada toilet jiki ba kwari yayi wanka ya futo ya shirya cikin shadda kaftan blue colour ya saka hula ya feshe jikinsa da turare ya dauki carkey dinsa ya fice daga gidan. Waya take da samol yana fada mata zaizo Nigeria, ganin Manab ya shigo ne yasa ta yanke wayan tace"I will call u back". Mikewa tayi tace"morning sir" "Morning ,dama nazo na fada maki, abokin aekinki bashi da lafiya but he is getting better". Zaro ido tayi tace"oh my God,ciwo ba dadi,ina masa sannu". Gyada kai Manab yayi ya fice daga office din. Cikin harabar Company din yayi parking ya futo jikinsa babu karfi ko kadan tafiya ya somayi a hankali har ya isa office din Manab,zama yayi a chair yana dafe zuciyarsa yana maida numfashi sama sama,saida ya huta sannan yace" akwai damuwa fa,Sarena ta kira wayana Nabila ta dauka and nasan doke wulakanci zata mata". Dariya Manab yayi yace"meye na damuwa anan,inba son Sarena kake ba meye na damuwa don an fada mata magana". Mugun kallo Jawad yawa Manab yace"ae ban fada maka ina sonta ba,and ba dariya nazo kamin ba". "C'mon kadaina sanya damuwa a ranka,kasan ciwan dake damunka,ka saukakawa ranka inaga zaifi" Mikewa Jawad yayi ya fita daga office din ganin babu mafita a wurin Manab saima iskancin da yake masa,tsaye yake wurin stair's lokaci daya zuciyarsa ta wani irin buga da karfi ya dafeta kasa ya tafi luuuu ya fadi a sume da sauri mai kula da wurin yayi sama ya fadawa Manab,da gudu ya futo yayo wurinsa yana kiran sunansa. Dai dai a idan Mona da sauri ta kira wayan Sarena tace"ki fito kasa Mr Jawad ba lafiya". Bata jira Mona ta ida magana ba ta jefar da wayar ta fito da gudu tana isowa tasa hannu ta janye Manab gefe ta kankame Jawad ta fashe da kuka tana kiran sunansa. Manab yai karfin hali yace "Is OK,mu tafi asibiti yanzu". Mota aka sakashi har lokacin Sarena tana rike dashi tana kuka ,kafin su isa Manab ya kira Salim ya fada masa,Salim abokinsu ne tare sukayi makaranta. M'I love u all Ur comments iz needed pls 09030953294 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers Page1⃣0⃣ Saida suka dauki tsawan lokaci a haka kafin Sarena ta kauda idonta daga kallonsa,kama leban bakinsa yayi yana tsotsa sannan yace"u didn't Miss me right ?". Murmushi tayi ta goge kwallan dake gangaro mata a kyakyawar fuskarta ta fada a faffadan kirjinsa ta rungumesa tace"ka daina fadan haka,kasan ka tsoratani kada ka sake wannan ciwan kaji". Dariya yayi har hakoransa suka bayyana yace"Ashe kin damu dani". Dukan wasa takai masa tace"ban damu ba"kama kunnensa tayi tajashi zuwa ciki tana fadin"ka barni zan mutu da aeki ,to yau har 6 muna office saika gama aekinka. Shagwabe fuska yayi yace"Special I can't do it today". "C'mon my Dear u must,iz ur problem ,zauna ka fara aeki time na tafiya". Dariya sukayi duka ya zauna ya soma aeki yayin da Sarena ta zauna kusa dashi tana kallon kyakyawar fuskarsa data dade tana mararin ganinta. Da sauri Lissa tasha gaban Samol tace" hakan bazai taba yuwuwa ba,inason Sarena ka sani,duk ranar rabuwa da ita ka saka a ranka ranar mutuwar Lissa kenan". "Bawai ina nufin haka ba Wife ,nima ina Son Sarena kin San wannan,kuma bazan taba bawa Aminu damar ya gane tana raye ba,tuni ya dauka ta mutu" Samol ya fada. "To indai haka ne,meye nasa na kiranka mezai maka ,kayi kokarin rabuwa dashi pls". Lissa ta fada idanuwanta cike da hawaye.kama hannuwanta biyu yayi yace" na dauka maki alkawari kin"sumbatarta yayi ya tashi ya tafi zuciyarsa cike da tunani. A gidan hutawar Alhaji Aminu suka hadu ,musabaha sukayi suna fuskantar juna a makeken parlor dinsa,kallon yaransa yayi tuni suka fice suka barsu su biyu kadai,nuna masa wurin zama yayi ya mika masa glass cup dake dauke da lemon me sanyi,karba yayi yadan kurba. "My friend, na kiraka ne don na tabbatar da magana akan Minad". Murmushi Samol yayi yace" u know Minad ta dade da mutuwa,ganinai tana kokarin tona mana asiri tana komawa kalar Babanta kamanninsu sak,kuma taki sakin jiki damu,kuma aena fada maka lokacin dazan badata a kasheta". Dariyar Mugunta Alhaji Aminu yayi yace"kayi daidai shiyasa nake sonka,amma wacce yarinya CE a wurinka kake riko budurwa". Saida gabon Samol ya fadi amma ya daure ya dauko wayarsa ya kunna tuni pic din shi da Sarena ya bayya a gaban screen din ya nunawa Alhaji Aminu yace"y'ar 6ter din Lissa ce data rasu". "Karka damu I trust u,na dauka Minad ce ka boyemin gaskiya,da kuma haka ta faru dakasan abunda zan iyayi". Dariyar rashin tsoro Samol yayi yace"ni da kai kowa yasan kowa so nima ae kasan abunda zan iyayi kar tasan kar ne". Dariya sukayi tare da tafawa sannan sukayi sallama Samol ya taho gida. Alhaji Janir ne zaune yana duba jarida a tankamemen parlonsa Wanda fasaltashima bata lokacine sai Wanda ya gani,dago kai yayi ya kallo wani tankamemen pic dake manne a bangon na wata kyakyawar yarinya y'ar shekara biyar,Amma ce keta faman gogeshi tana kallo da alama tana matukar son yanayin. Tasowa Abee yayi ya kamota ya zaunar da ita yace"ke kullun bakya gajiya da aekin goge photo?". Murmushi Amma tayi tace" wannan pic shine Minad dina,shi nake kallo nakejin dadi dole na kula dashi indai ni da gaske mahaifiyar Minad ce,dukda a yanzu na fidda rai da samun ta",ta fada tana share hawayan daya gangaro mata a fuska. Rikota Abee yayi yana goge mata hawaye yana bata hakuri,kafin yace"ba'a fidda rai da rabo kuma inaji a jikina Minad zata dawo garemu,kuma tana kusa damu. M'I love u all. Ur comments iz need 09030953294 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers. Page1⃣1⃣ Share hawayen idonta tayi ta rike hannun Abee tace"ina fatan haka,ranar kuwa Allah kadai yasan irin farin cikin dazan shiga Abee narh". Rungumota yayi suka wuce part dinsa tuni ta manta da damuwar dake damunta. "Kana ganin Sarena tana sonka yanzu,kada kayi abunda zaka cutar da ita mana". Manab ya fada tare da duban Jawad. Murmushi Jawad yayi yace" sure an zaka gani"kamo hannun Manab yayi suka fito daidai saitin inda Sarena zata iya kallonsu ta kumaji muryarsu. Waya Jawad ya fito da ita ya soma magana"eh Swt kinsan yanayin aekin namune,buh yau da dare zanzo kinsan nayi missing dinki Baby nah,amma kinsan na daure da rashin ganinki ko 2days" Wani irin mumunar faduwar gaba ta dirarwa Sarena wani irin gugumin abun taji ya tsaya mata a zuciya ,hawayene suka soma gangarowa ga kyakyawar fuskarta ta fada a zuci"dama ba sona yakeba,yasa nina kamu da sonsa "jefar da file din hannunta tayi ta figi Jakarta tayo waje da gudu. Kiran sunanta Jawad ya somayi amma ko juyowa takiyi,tana isa ga mota ta bude ta shiga ta figi Motar da wani irin mumunar gudu, a tsorace Jawad yace" kada tajiwa kanta ciwo fa". Harara Manab ya masa yace"to laifin waye komai zai faru"yana fadan haka ya wucewar sa office. Ikon Allah ne yakai Sarena gida ko parking bata daidaita ba ta futo tayi part dinta da gudu daki ta shige ta banko kofar ta danna mata key kafin ta wurgar da Jakarta ta sake fashewa da kuka ta duke a wurin tana yamutsa lallausan gashin kanta tana kuka mai tsuma zuciya tanawa kanta ala wadai data kamu da soyayyar Wanda bata ita yake ba,a haka bacci ya dauketa a wurin. Zaune Jawad yake amma damuwa ta hanasa sakat yana tunanin halin da Sarena ke ciki gashi sai kiranta yakeyi bata dauka,ta wani bangaren kuma yana farin ciki da irin son da take masa. "Nani kas naga motan Sarena ta dawo ne?" Mom ta tambaya "Eh amma inaga bata jin dadi naga ta shigo ba dai dai ba" Nani ta fada. A tsorace Mom ta nufi dakin Sarena tana kiran sunanta tare da buga kofan. A firgice ta farka daga baccin da takeyi tana zare ido jin muryar Mom yasa tayi hanzarin shigewa toilet ta wanko fuskarta ta tattara bag dinta before ta bude kofan,suka soma kallon kallo tsakaninsu inda Mom ke kallonta cike da tuhuma. Kuyi hakuri da wannan kwanannan ina busy sosai. Don't forget to Like Comments and Share M'I love u all [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to enatartein & motivate the mind of readers Page1⃣2⃣ Ina bada hakuri na jina shiru kwana biyu hakan ya farune ta dalilin wasu hidimomi da suka shiga gabana ,ana tare "Meke damunkine Sarena,kwanannan na kasa gane maki at all kin canza ". Mom ta fada. Riko hannun Mom Sarena tayi tace"Mom i'm OK kawai banajin dadi yaune kada ki damu". " bazan taba yarda da hakanba Sarena,yaushe kika zama kina boyemin damuwarki har haka"Cewar Mom. Raurau da ido Sarena tayi kafin kace me hawaye suka soma ambaliya a kyakyawar fuskarta Da sauri Mom ta jawota tace"ya isa haka, bana son kukanki kin sani bazan taba jurar zubarsu ba".goge mata fuskan ta somayi kafin ta rungumeta tana bata hakuri saida ta tabbatar ta natsu kafin ta sakar mata Murmushi tace"ki shirya Furanko ya iso yana dakinsa". Wata iriyar razananniyar fadin gaba ya ziyarci zuciyarta amma ta kasa furta komai har Mom ta bace mata daga kallonta. Daki ta koma ta zauna kan bed tana sharar hawaye Wanda ta rasa meke dalilin zubarsu,tunani tayi ya zatayi ta sake gujewa Furanko ba mafita dafe kai tayi tana juyi a wurin. Banko kofar dadin Nabila tayi ta shigo tana taunar gum ta tada daurin kai a sama,kai tsaye jikin Jawad ta nufa ta zauna,jaki yaja ya tureta ya tashi a bed din yana binta da mugun kallo kafin yace"ban hanaki kusantoni ba,karki sakemin haka". "To my Swt am sorry dama Umma ce tace na fada maka Hajiya tazo ka futo Ku gaesa". Nabila ta fada tana kashe ido. Sake daure fuska yayi yace" OK fitarmin anan bazanzo ba".Jawad ya fada rai bace. Bude baki tayi zatayi magana ganin ko kadan bataga alamar wasa a tare dashiba yasa ta mike ta fashe da kuka tayi waje. Har rigan tambayarta sukeyi meya sameta,jikin Hajiya ta fada tana fadin"Hajiya ya tsaneni wallahi baya sona,ki duba irin cin mutuncin da yakemin da ranku". Mikewa Hajiya tayi tace"ina wallahi be isaba,bamusan hakaba kuma bazamu taba sani akansaba" taso muje Jan hannun Nabila tayi suka wuce part din Jawad da isarsu ta bankada kofar tana huci bakin cikine ya kara kamata data gansa kwance yanata faman duban wayarsa. "To Dan iska marar mutunci ,kai harka isa kace zaka juya mana ra'ayi to ba'ayika ba,idan Aminu ne ya turo kiranka zakace baza kajeba ,mai zubin munafukai amma ko kadan albasa batai halin ruwa ba,to bari kaji ko Aminu uban naka be isa ya tsallake maganata ba,ballantana kai,auranka da Nabila ba fashi kama shirya" dungure masa kai tayi ta figi hannun Nabila suka fice. Tsaki Jawad yaja ya dauki carkey dinsa tare da phone dinsa ya fice daga gidan ta baya kai tsaye gidansu Manab ya nufa yana shiga yayi parking mota ya futo da Amma ya hadu gaesheta yayi cike da ladabi before ya wuce part din Manab. A zaune yake a lallausar royalchair dinsa yana latsa waya,ko kallonsa Jawad beyiba ya wuce Bed room ya fada a bed yana huci saboda tsabar dacin da zuciyarsa take masa kuma yake kara jin tsanar Nabila a ransa. Ajiye wayar Manab yayi ya shiga bedroom din murmushi yayi da yaga yarda ya kwanta,karasawa yayi ya soma kwance masa igiyar takalmansa kafin yace "yaron Umma meke damunka haka rai bace". Shiru kamar bazaiyi magana ba candai yace" Hajiya CE" "C'mon ka yarda mana me Nabila ta rasa yarinya y'ar gata dalla ka bada kai bori ya hau".cewar Manab. A firgice Jawad ya juyo yana watsawa Manab mugun kallo ya fizge kafarsa ya tashi ya soma cire kaya saida yaje kofar toilet sannan yace" marar kirki kawai,idan bazaka bawa mutum hakuriba kaja bakinka kayi shiru". A hankali ta iso dining area din tana binsu da kallo ko kadan babu lakka a jikinta sanye take da maroon din Riga mai hannun Vest iyakarta cinya gashin kanta a sake yake sai plat shoe black colour dake sanye a farar kafarta,da sauri Furanko ya taso ya rungumeta yana mata sannu da futowa,Murmushi kawai tayi ,chair yaja mata ta zauna suka soma zuba mata abinci,ko kadan bata jin dadin abincin wasa kawai takeyi da spoon din tana juyashi. M'I love u all Gaskiya na raina comment dinku akan book dinnan. Fatan alkairi gareku 💘💘💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈Kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein $ motivate the mind of readers Page1⃣3⃣ Kallonta Dad yayi yace"meke damunki meyasa ba zakici abinciba?". "Bakomai Dad karka damu,kawai banason cine,inaso naje saloon ne". " banda abunki Sarena an taba tafiya da yunwa?"cewar Mom "Mom kina wani damuwa,nixan wuce". Bata jira cewarsu ba ta wuce daki ta dauko bag dinta da key na mota ta futo ,wucewa zatayi Mom ta rike hannunta ta zuba mata kudi masu yawa a bag dinta tace"ki kulamin da kanki". Murmushi kawai tayi ta rungumi Mom da Dad sannan ta rungumi Furanko tayi waje,mikewa yayi da sauri Dad ya rike hannunsa yace" kada ka damu ka bari ta dawo inaga wani abu na damunta kwanannan". Motarta ta shiga kirar corolla ash colour ta figeta tayi waje kai tsaye wurin saloon ta nufa da gyaran jiki ta shiga aka soma gyara mata kanta tare da saka mata kunba ta kafa da hannu red colour. Tsaye Nabila take tsakar daki tanata kaiwa da komowa a dakin ranta a matukar bace ta fada a fili"bazai yuwuba zaman me nakeyi wacce Sarena daharta fini a wurin Ya Jawad dame ta fini ,ko wacce tayi karya bazan taba bari ta rabi abunda nake soba"Dan figigin gyalenta ta fizga da jaka da key na mota tayi waje tafiya takeyi tana sakesake kai tsaye Companynsu ta nufa da izza ta shiga ciki anan taci sa'ar haduwa da Jamila dake aeki Companyn da farko taso taki bata hadin kai amma da yake Nabila y'ar duniya ce tuni ta siye Jamcy da kudi ta samu duk wasu details da take bukata akan Sarena wata muguwar dariyar mugunta ta saki tana ganin alamun nasara a tare da ita musamman da taji ba Musulma bace tuni sukayi musayar number da Jamcy don da gani y'ar hannu ce tasu zatazo daya, cike da farin ciki ta koma gida tana Allah Allah gobe tayi ta dirarwa Sarena. Zaune yake a Bed yana shartar lallausar gashin kansa yana daure da towel yana kallon Manab dake damunsa akan yaci abinci. Daure fuska Manab yayi yace"kana son Sarena har haka harka rayu bayan batan Minad to meyasa son Sarena zai hanaka cin abinci ka shiga damuwa har haka". Tuni fuskar Jawad ta canza ta rikide zuwa bakinciki marar musaltuwa hawayene suka soma bin kuncinsa yace"amma ka cuci Minad dina ina matukar sonta ,son daba zan taba yiwa wata mace shiba ka daina hadata da ko wacce irin mace". "Meyasa bazaka mata irin son Minad ba" Manab ya tambaya. Harararsa Jawad yayi yace"saboda ita ba Minad bace bakuma zata taba zama irin Minad ba,kawai abunda yasa nakeso Sarena wani zubi takan man kama da Minad dina". "Kayi hakuri zan kira Sarena yanzu nace gobe ta shigo office da wuri sai nida kaina na fada mata gaskiya". Wayarsa ya zaro ya kira number din Sarena bugu ukku ta dauka tare da fadin" hello Sir,ina wuni" "Lafiya " bayan sun gama gaisawa yace gobe ta shigo office da wuri yanason ganinta,kamar ta masa musu don ko kadan bata son zuwa amma kuma ta daure ta amsa da too. Next day Tsaye take gaban mirrow ta saka Red colour din riga iyakarta rabin cinyarta bata da hannu kuma robace dai dai jikinta gashin kanta a yasha gyara sosai an dauresa da kananun ribom red and black simple makeup tayi but yau ta shafa red janbaki hannunta daure yake da black clock dadaddiya dayan kuma da karamin yan yannu red,shoe dinta hills ne sosai black colour glasses ta saka radow baki me kyau kafin ta dauki black bag ,tayi matukar kau sosai abunka da farin mutum gashi sai fidda sihirtaccen kamshi take. Saida ta gaishe da kowa na gidan sannan tayi break sama sama ta shiga motarta marcidiz black ta nufi hanyar companynsu. Ur comments iz needed Comment Share M'I love 💘💘💘💘💘 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of readers Page1⃣4⃣ A hanzarce Nabila ta fito sanye da dogon riga na atamfa makeup ne sosai a face dinta ga hills ta saka wani Dan karamin gyale ta daura a kanta ga gashin doki baje a tsakiyar baya jakk'a ta dauka da key din mota ta fita, cikin mintoci kadan ta isa companyn a bene ta hangi Jawad da Manab da labe ta iske Jamcy suka buya saitin da zasu iya ganin shigowar kowa a companyn. Parking tayi amma tadan jima bata fito daga motanba kafin daga bisani ta soma ziro da kyawawan k'afafuwanta da sukasha ado da hadaddun hillsshoe,kafin ta fito gaba dayanta Masha Allah shine abunda na fada domin irin haduwar da tayi ga kayan jikinta sun karbeta,tafiya take a nutse ta nufi office din Manab. Sosai Nabila ta gane Sarena nan take ta tuno ranar da suka hadu asibiti wasiwasi ta shigayi anya a ranar ba Jawad taje gani ba,nan take tsanar Sarena ta kara d'arsuwa a zuciyarta musamman data lura Sarena ba sa'arta bace ta fita tako wanne fanne,saidai tayi farin ciki da kasancewar Sarena ba musulma ba dominko ta kara samun hujja,anan tabar Jamcy tahawo stairs tana labe dabin bayan Sarena. Baya ta dawo kadan tare da dafe kai lokaci daya ta furta ashhhhhhh kafin ta dago kyawawan idanuwanta tana kallon fuskar Jawad Wanda shima yake dafe dakai sanadiyar bigewan dasukayi. Murmushi ya mata kafin yace"see u zaki fashemin kaine ko". Daurewa tayi tadan wayance tace"kai bakaji tausaina ba,daka bugamin katon kannan naka"ta fada da sigar tsokana. Zaro ido yayi tahowa yayi da niyyar kamata ta zille ta shige office din Manab. Gaisawa sukayi kafin Manab ya dubeta yace"Sarena kinada boyfriend? ". Tambayar tazo mata a bazata a firgice take dubansa tuni hawaye sun soma wanke kyakyawar fuskarta murya dishe ta furta" No". Kallonta dakyau Manab yayi ya gama fahimtarta yace"to wani friend dina ya ganki yanaso ,zaki soshi?". Kallonsa tayi kafin tace"idan har yayi daidai da ra'ayina da kuma iyayensa zasu karbi addinina". "To baki tambayi ko waye ba,kinga sai aji auran rana daya dana Jawad barima na nuna miki matarsa kiga ko tayi". Gabantane yayi mumunar faduwa idanuwan hawaye kawai suke fitarwa babu tsagaitawa yayinda zuciyarta ke mata zugi ji takeyi kamar ta rusa ihu a wurin saboda tsabar bakin ciki. Wayarsa yake mika mata ki duba gata,ko kallonsa ta kasayi bare ta karbi wayar,da k'yar ya samu ta karba tana tababar kallon phone din,daurewa tayi ta soma kallon pic din ,zumbur ta mike tana karewa picture din kallo cike da mamaki da tababa shin barcine ko mafarki tana kara goge idanuwanta kodai sun fada mata k'arya ne. Wani pic dinsune ita da Jawad da sukayi dago ido tayi tana kallon Manab dake mata magana" comedown Baby my friend is in love with u I hope zaki soshi kamar yadda ya soki tsawan lokuta". Kasa amsa masa tayi tuni kallonta ya koma ga Jawad dake bakin kofa yana daga mata gira,Murmushi yayi ya bude hannuwansa yace"come to ur husband Baby". Hawayen farin ciki suka zubo mata ta saki kayan hannunta ta ruga suka rungume juna ,dagota yai yana goge mata hawaye yace"l love u Sarena,do u love me?". Murmushi tayi tace" I love u more than u love me Jawad". "Ayyye harkun manta dani a nan to yayi kyau,ko kunyata bazakuji ba ko" Dariya sukayi duka suna makale da juna. Nabila dake hangensu tuni fuskarta ta jike da hawaye bata gane komai bare ta saurari wanne irin yaraye yake yawa a kanta dafe zuciyarta tayi dake barazabar tarwatsewa da gudunta ta ida shiga office din, iya karfinta ta daga hannu ta kwashe Sarena da mari har biyu kafin ta ingizata kasa ta fadawa chair kafin tace"Mazinaciya kafura harkin isa, ki shigo cikinmu da najasar jikinki,Wanda munafurci bazai taba barin zuciyarku ba makiya Allah to ina fada maki ki fita daga harkar mijina jahila kawai". Kafin takai k'arshe Jawad ya daka mata tsawa"kima mutane shiru a wurin,me kike tinanin kinyi yanzu ,akwai jahilar data fiki ne,ko a cikin dabbobi sai an tona za'a samu wacce zatayi abunda kikayi" Wurin Sarena ya karasa ya tasheta tsaye yana goge mata hawaye. Ihu Nabila ta kumayi kafin tace"akan kafura wacce bata sallah zaka wulakanta jininka,wallahi bazan taba bari kuji dadin rayuwa ba" Zuciyace ta tunzuro Jawad ya fada da karfi"ko sunanta kikaji dole ki girmama Nabila indai ni jininki ne,ki fita anan tun kafin na bata maki rai". Tasan halinsa sarai tuni zai iya lakad'a mata duka ,yasa ta fita da gudu ta fada mota ta fita a guje. Dafe kai Manab yayi yace"kaji yadda take tuki kada wani abu ya sametafa" Tsaki Jawad yayi kafin yace"to saime damuwarta ce ae"Sarena ya kama yanata bata hakuri. Rufe masa baki tayi tace"kada ka damu a kanka zan jure fiye da haka"kafin ta dora kanta a kafadarsa Nabila kuwa a kofar gida tabar Motar ta shigo ta kofa a guje ta shiga parlo ta fada jikin Umma ta fasa ihu tana fadin"Umma ya gujeni kafura yake so,idan ban auresa ba wallahi zan iya mutuwa". Da sauri Hajiya ta shigo parlon Wanda ta gama jin me suka fada tana fadin"kwantar da hankalinki marar tarbiyar yaronnan marar mutunci be isa ba" *ALK'ALAMIN MARYAMA*✍🏻 Share and comments [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers Page1⃣5⃣ Huci kawai takeyi tanaso Jawad ya shigo gidan ita kadai tasan me take rayawa a zuciyarta. Yayinda Nabila ke jikin Umma kwance tana sheshek'ar kuka hawaye nabin fuskarta.Umma kuwa sai faman lallashi take. Gefe Abba ne yanata kai komo yana tunanin meke damun Jawad dahar yakeso ya wulakantashi yaki y'ar uwarsa. Sallama sukayi da Sarena cike da k'auna ,Car dinta ta shiga ta tafi gida ranta cike da sakesake tana tunanin ya lamarinsu zai kaya. Tsaye yayi a wurin yana tunanin mezai iske inyaje gida but yadai San babu abinda zaisa ya rabu da Sarena a wannan lokacin. Dafasa Manab yayi yace"karka wani damu ka zama jarumi,kasan ya dace ka zabawa kanka macce ta gari,nina tabbata Sarena zata iya musulunta koda bayan auranku ne ka fuskanci kalubalan rayuwarka ". Murmushi yayi sukayi musabaha ya shiga mota ya tafi gida. A hankali ta futo daga mota rike da jakkar ta saita laptop a d'ayan hannun da sauri nani ta k'arbi jakkan tana mata sannu,murmushi kawai tayi ta shige cikin gida. Zaune mutan gidan suke a parlo suna labari ganinta yasa Furanko tasowa da sauri ya kamota ya zaunar da ita a chair sannan yace" meke damunki haka?" "Babu,kawai na gajine" cewar Sarena. Daga gefan hannunta Mom ta hango ciwan da taketa boyewa,zaro ido tayi ta taso da sauri ta rike hannun a tsorace tana fadin"meye wannan daga ina kikaji ciwo". Sorota tsaya tana dubanta sai kuma siraran hawaye suka soma bin kyakyawar fuskarta. "Kinga kada kiyi kuka ,nasan ba zafin ciwo kikewa kuka ba,watakilla zakiga na takura maki amma komai nakeyi inayi donke kuma nasan zakiji dadi sosai a rayuwarki a gaba,ki kuma gane mamanki na sonki sosai kuma ina zama donke ne". Murmushi Sarena tayi ta tungume Mom ,kafin ta kira Doctor a waya yazo ya duba hannun nata. Da sallama Jawad ya shiga parlon babu Wanda ya amsa masa,dama yayi tsammanin haka juyawa yayi zai wuce da sauri Hajiya ta tari gabansa ta fizgosa baya suka tsaya suna duban juna. " me kuma na maki haka Hajiya?". "Ubanka kaman shege marar mutunci ". Cewar Hajiya. Tsakiyar parlon ya dawo ya zauna yana dubansu yasan nufinsu kenan. Numfasawa Abba yayi yace" yanzu abunda kayi ka kyauta kenan,dubi halin daka saka y'ar uwarka a ciki,Jawad yaushe ka zamo marar tausayi a rayuwarka". "Abba babu abunda na mata tak'i fahimta ne". " rufeman baki matsiyacin yaro Wanda baya kishin kansa,to aure babu fashi kokaso ko karkaso".cewar Hajiya. Tuni launin Jawad ya dade da canzawa donko ya soma gajiya da masifar Hajiya a daure yace"Abba ka bani dama daya, gobe na kawo wacce nakeso Ku ganta,daga nan sainaji me zaku yanke a kai pls Abba na kayi wannan domin ni". Girgiza kai Abba yayi yace"to kuyi hakuri zuwa gobe muga kan wacce ake abun donsu". Badon Hajiya tasoba amma sai tayi wani tunani kuma ta hakura taga gobe mezai faru. Ta waya Jawad ya sanarwa Manab komai ke faruwa ,baki ya bashi da kuma ya zama mai hakuri ya jira yaga abunda Allah zaiyi. *NEXT DAY AT 4:30PM* zaune yake a car yasha manyan kaya shadda blue colour ba k'aramin kyau yayi ba,phone dinsa ya ciro ya fada mata isowarsa,mintuna kad'an na hangota. Sanye take da dogon wando har kasa blue colour sai farar riga iya kugu,kanta a daure batayi makeup ba sai plat shoe din dake k'afarta shoulder dinta rataye take da tsadaddiyar jikka inda wuyanta ke daure da sarkar jinari but me zanan kuroz sai zuba kamshi take tayi masifar kyau. Da murmushi ta k'araso suka gaesa kai tsaye gidansu suka nufa cikin mintuna kad'an suka iso katafaren gidansu a gate suka samu Manab ya rigasu isowa,gaesawa sukayi daidai zasu shiga taja ta tsaya cak ta rike hannun Jawad tace"ina tsoro fa". "C'mon babu abunda zai faru muje" Da sallama suka shiga itako tayi shiru binsu kawai take a baya main parlon gidan suka shiga anan suka samu Umma da Nabila nuna Umma yayi yace"Sarena look at my Mother". Da sauri ta isa gabanta ta duk'a har k'asa tace cikin gurbatacciyar hausarta"ina wuni Umma na sameku lafiya". Babu yabo babu fallasa ta amsa mata da lafiya kafin tace Nabila kira Abbanku da Hajiya. Yamutse fuska tayi kafin ta fita ta kirasu tanabin Sarena da kallon tsana. Ba jimawa suka shigo yadda Sarena ta gaida Umma haka ta gaeda Abba da Hajiya, shikam Abba ya amsa tsakaninta da Hajiya kuwa sai harara. "Uhum ina jinka Jawad". " Abba wannan itace Sarena kuma itace wacce nakeso saboda naga bai sabawa addininmu ba". "Ina h'ar a bada baka isaba bakuma zaka taba isaba,kafura a familynmu kayi k'arya,makiya Allah zaka aura" cewar Hajiya. "Kaban Mamaki Jawad yanzu wannan itace abun aure d'ana na ciki ka rasa wacce zaka aura sai kafura wacce bata sallah,indai inada rai babu kai babu wannan auran"Cewar Umma. *ALK'ALAMIN MARYAMA*✍🏻 Share Vote Comment Love u all [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers *ASALI NA* NA *MARYAM ISMAIL* PAGE1⃣7⃣to1⃣8⃣ Kare mata kallo Momy tayi tsab sannan tace"meke damunki?,ki fadamun kinsan duk duniya bakya da wacce ta wuceni kinsan zan iya sadaukar da komai domin farin cikinki,bazan taba jurar hawayenki ba" "Momy sun rabani dashi,ina sonsa sosai amma sunce bazan auresa ba....." Kuka yaci karfinta tayi shiru. Cike da tuhuma dason gano meke faruwa Momy tace"wayeshi?,meya fiki gata ko kuwa *ASALI* ". Girgiza kai kawai tayi sannan ta share hawaye tace"wai donni ba musulma bace...." Daga mata hannun da Momyn tayi shiyasa tayi shiru ta natsu . Maimaita maganan Momy tayi sannan ta fada rai bace"kin bani mamaki kuma kin bani kunya,yaushe kika fara soyayya?,kuma ki rasa Wanda zakiso sai Wanda ba addininku daya ba,ya kikeso nayi,kema kinsan bazai taba yiwuwa ba,my last word indai na isa dake babu ke babu shi"ta ida nagana rai bace ta wuce part dinta. Dafe kai kawai Sarena tayi wani bacin ran ya kauda wani tuni ta nemi hawaye ta rasa idanuwanta suka kekashe zafi kawai suke mata wani irin zafine ke ziyartar zuciyarta ta nemi hawaye ta rasa, da gudu ta nufi dakinta tasa key ta sake rushewa da kuka mai tsuma zuciya. "Kaima kasan abunda bazai taba yiwuwa ba kenan,kafasan *ASALIN* Sarena a kasarnan yake, kuma zanyi duk abunda zanyi don ci gaban boyuwar sirrina,bazata auri musulmi ba final". " Lissa ki fahimceni bana nufin tonuwar sirrinmu saidai bana so ki matsawa y'arki akan wannan hakan zai iyasa mu rasata Wanda nasan bazakiso hakan ba kibi a hankali kar kisata a damuwa".Samol ya fada da alamar rarrashi. Numfasawa Lissa tayi sannan tace" zanyi me kace amma bazata taba ganin fuska akan wannan ba,inko haka ta faru zan dauketa mu koma America ta kuma auri Furanko". ********************** Dab dashi Nabila ta matso tana shirin dafashi,dagowar da yayi ne suka hada ido taga yadda launinsu ya tikide zuwa ja ga hawaye kwance lub a cikinsu,babu abunda take hangowa sai tsantsar tsana da kiyayya wacce Jawad ke mata da sauri ta kauda idonta tabar wurin........Jan hannunsa Manab yayi suka wuce part dinshi sannan ya shiga basa hakuri yace"Jawad ka saurareni babu abunda yafi biyayya ga iyaye dadi,na tabbatar kafi son iyayenka akan Sarena,kayi addu'a Allah zai zaba mana mafita". Girgiza kai Jawad yayi "bawai biyayyane bazanyi masu ba,ka gane Nabilarta na tsana ko kadan kafi kowa sanin bata cikin jerin matan da nakeso,me akeyi da mace marar aji ballagaza wacce zatasa a tursasawa namiji auranta wallahi n tabbatar Sarena tafita duka wannan abun dana fada,shima wai ko kasan meyasa nakeson Sarena?". Girgiza kai manab yayi alamar a'a. Murmushi takaici Jawad yayi kafin yace"iliminta ,natsuwarta ,hankalinta kalinta duk irina Minad ne,kuma kasan ba sauki bane zama kamar Minad komai nasu iri daya at all har kama sunayi son da nakewa Minad shine ya shafi Sarena,pls karku rabani da ita kamar yadda na rasa Minad". Hakuri Manab yaita bashi yana nuna masa da bashi shawarwari masu inganci sannan sukayi bankwana ya tafi. Next Day Kamar kullun cikin suit ya shirya black colour yayi masifar kyau sai zuba kamshi yake dukda yadan fada daga jiya zuwa yau jakarsa da key ya dauka ya fita ta kofar baya ya tafi office. A sanyaye Momy ta tura kofar dakin Sarena ta shiga cike da tausayin yadda ta isketa take amma saita daure tace"ba zakije office ba?". Gaesheta tayi sannan ta bata amsa da eh. "OK inkin shirya ki fito kiyi break nizan fita zuwa office". Saikin dawo ta mata,Momy na fita hawayen tausayi ya zubo mata ta share fuska donko kadan bataso yanayin data iske y'ar tata ba. Zaune yake a office din Manab sai tsaki yakeyi kamar zai tsinke harshe yana kallon agogon hannunsa ganin har time ya wuce Sarena bata zoba gashi sai kiran wayarta yake a kashe. " kayi hakuri,nasan dama bazata iya zuwa yauba,amma Mae zai hana damun tashi office mu wuce gidansu"Manab ya fada.haka suka tsaida shawara don haka 3:00pm a cikin tankameman gidan Mr Samol tayi masu tsaye suke jikin mota a parking space ,ganin baki a wurin yasa Nani kas isowa wurin da murmushi ta kallesu tace"sannu da zuwa,na ganeka Kaine Mr Jawad ina yawan ganin picture dinka a wayan Madam" Gaesawa sukayi sosai before tace"ka natsu ka jini ka saurari zuciyarka karkayi garaje ka yanke hukunci a hankali kabi maganar zuciyarka da shawara mai amfani amma ka sani babu abu mai mahimmanci a rayuwarka daya wuce iyayenka,zan turo maka Sarena yanzu"bata jira cewarsa ba ta wuce abunta. *ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻 Don't for gate to Like Comment Share Ga masu bada shawara 09030953294 [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 *ASALI NA* 💘💘💘💘 💘💘💘💘💘 Na *MARYAM ISMAIL* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers *HAPPY SALLAH,FATAN ALLAH YA KARBI IBADUNMU* Page1⃣6⃣ Dago ido Jawad yayi yanabin Umma da kallo Wanda a time din idanuwansa sun rikide sun koma jawur saka makon bacin ran dake kwance luf kyakyawar fuskarshi,kafin ya dauke kallonsa yaji Nabila tace"to mayya y'ar gidan mayu zaki iya tashi ki fita ae kinsan hanyar da kika shigo aurene ba'ayi" Murmushi Daddy yayi yace"to an sanya ranar auranka da Nabila nanda 2weeks ,n gama magana". Hawaye ne suka soma fitowa a fuskar Jawad take yaji kafafunsa basa daukarsa anan ya duke kawai y kasa furta komai yana jujjuya kai,da gudu Sarena ta iso ta rikeshi tace"karka damu indan nice zan iya jure komai amma banda ganin kukanka ko bacin ranka pls ka daure". Cikin sauri Nabila ta fizgeta daga jikin Jawad ta wurgar d ita can gefe kafin ta furta "karuwar banza". Tsawa Manab ya daka mata yace" ke baki d hankali koko meke damunki sai kinji mata ciwo,ana so dolene?ke yanzu so kike nunawa Jawad ko k'i". A hankali Sarena ta mike don ta gaji da bakaken maganganun da takeji ana fada mata kuka kawai take kamar zata cire ranta yanzu tanaji tana gani an rabata d Jawad dinta kenan saboda b addininsu daya ba,hanyar fita tayi ,da sauri Jawad y mike zan bita. Cikin tsawa Umma tace" kana fita binta banice mahaifiyarka ba ,bani bakai" Da gudu Sarena ta fice daga gidan tafiya kawai take a layin bata gane komai bata ko gani sosai tafiya kawai take tana rangaji ,horn kawai ake mata ta baya ida rudewa tayi ta zube anan tana rusa ihu tare d kiran sunan jijoz. Da sauri Furanko ya fito a motar ya rungumeta ,tana ganinsa ta makalkalesa tana huci mota y sakata hankali tashe don tunda Jawad ya daukota yake biye dasu, kai tsaye gida suka nufa. A rike ya shiga da ita cikin gida da sauri Momy ta taso ta riketa hankali tashe tace"meke damun y'ata Furanko" "Mama" Sarena ta fada ta fada jikin Momy ta sake fashewa da wani irin razanan kuka mai tsuma zuciya. Anan take hankalin Momy ya kuma tashi don duk duniya ta tsani bacin ran Sarena itama hawaye taji yana bin kuma tunta. *ALKALAMIN MARYAMA*✍🏻 Don't for get to Like Comment And share [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* NA *MARYAM ISMAIL* 🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION* *united we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers* Page1⃣9⃣to2⃣0⃣ Da kwarin gwaiwa ta shiga dakin Sarena . Zaune ta sameta a gefan bed ta zabga uban tagumi ,kiran sunanta ta shigayi amma shiru,hakan yasa ta dafata. Firgigit ta dago ta goge hawayen idonta tana fadin"Momy n daina fa". Ganin Nani kas a gabanta yasa ta saki sanyanyar ajiyar zuciya ta zuba mata kyawawan idanuwanta. Zama kusa da ita Nani tayi sannan ta rike hannayenta duka biyu suna fuskantar juna tace"meke damunki?,ba munyi alkwari ba zaki daina damuwa ba". Shiru Sarena tayi sannan tace "nima bansan me zanyi ba,kinga Momy bataso kuma banason tayi fushi dani,kuma inaso n rabu dason Jawad amma ba Abu mai sauki bane a gareni". " karki damu Mamanki bazayi fushi dake ba,nasan tana sonki ,amma kibi a hankali tashi muje waje yazo yana jiranki". Bude baki tayi zatayi magana,Nani ta rufe mata baki ta kama hannunta suka fito,turata tayi wurinsu ita kuma ta wuce kitchen. A hankali take tafiyan kanta a kasa sanye take da wando baki rabin cinyarta sai y'ar karamar riga marar hannu wacce ko cibinta bata rufeba gashin kanta kwance a bayanta sai sheki yake, plat shoe ne a kyakyawar kafarta sai faman zuba kamshi take a sanyaye ta iso wurin ta tsaya ba tare data furta komai ba. Kallonta yayi dakyau dukta fada ta danyi duhu kafin ya kira sunanta"Sarena". Bata da niyyan ansawa ko dubansa . Hakan yasa yaci gaba da cewa"yanzu abunda ya faru zaisa ki soma ganin laifina ko kiyi fushi dani?,har yakai bakya son ganin fuskata?". Da sauri ta dago tare da fadin"pls Jawad stop it". "To me hakan yake nufi,nidai nasan ina sonki,kuma zan aureki babu abunda zai hana,zakizo ta biyu a gidana bayan nabi zabin iyayena ,shin zaki iya yarda da aurena a haka?". Langwabe kai tayi tace" addinika ya yarda da hakan wace ni da zance bazan yarda ba zan aureka a haka kodon samuwar farin cikina da kuma naka". "Never Sarena,ban raineki donki bijire ma umarni na ba,ko kadan banason ki auri Wanda ba addininku daya ba,kuma banaso kisha wahala,Furanko shine mijin daya dace ki aura" cewar Momy ta fada tana ida karasowa inda suke. Tunda Momy ta fara magana idon Sarena na kanta kwata kwata bata fahimtarta a hankali ta iso gaban Momy tace"what do u say Mommah?" Gyada kai Momy tayi"nasan kinji mena fada" "Pls Mommah can we stop this,Furanko baya sona we are just friends, irin haka be taba shiga tsakaninmu ba". Dariya Momy tayi sannan tace" ko zaki iya yin shiru,kina nufin kicemin bakisan Furanko yana sonki ba,to tun yarinta yake sonki yake kula dake kuma yafi kowa cancantar auranki akan wannan abun"ta ida magana tana nuna Jawad da hannu a wulakance. Share hawaye Sarena tayi"Momy kina sona?,kinsha fadamun zaki iya sadaukar da komai naki domin farin cikina,zaki bani komai nakeso amma yau gashi da ranar tazo Momy kin kasa bani ko d'aya,ke kike neman rabani da farin cikina,na dauka daga Daddy zan samu matsala,sai gashi shiya goyamun baya fiye dake,Jawad mutumin kirkine auransa baya nufin zan bar addinina a'a zaiyi nashi zanyi nawa, tuni kuka ya kwace mata,cikin kuka taci gaba da fadin pls kiyi wannan domin ni 👏🏻". Yanzu kam zuciyar Momy ta soma karaya daurewa tayi ta dagota daga duken da take tace"meya kawo wannan Sarena?,Mamanki tana sonki kuma zatayi komai domin ke,kawai baki fahimceni bane,zan yarda da auranku domin farin cikinki bawai don inaso ba,a'a saidon banason ganin bacin ranki". Rungume juna sukayi suna hawaye,amma Momy tana aekawa Jawad da wata iriyar harara dake cike da tsantsar tsana da kiyayya zahiran. Daurewa yayi sukayi ma Momy bankwana suka tafi. Yanzu kam no way farin cikin Sarena yasa iyalanta dason auranta da Jawad. **************""" Kai tsaye wurin Ammi suka wuce ba bata lokaci sukayi mata bayanin abunda ke faruwa sunyi sa'a ma Abee yana nan yace suje anjima zasuje gidan suka su Abban kada ya damu. Yanzu kam zuciyar Jawad tadanyi sanyi domin ya fara ganin alamun nasara a cikin tafiyarsa. Duke hajiya take gaban bokanta tuni ya gama sanin meya kawota,bushewa yayi da dariyar mugunta yace"kinsan idan abu zai yiwu zan fada maki amma idan kika saba babu wani bokan dazai maki aekin saidai kawai yaci kudinki,inaso ku sani auran Sarena da Jawad bazai fasuba don duk a sama gashi anata daura auran, tauraronta nada karfi naga wani abu zagaye da ita a yanzu bamuda nasara a kanta,saidai Ku tsaya ayi auran saimu San yadda zamu bullo mata tabar duniyar baki daya". Kallon Nabila,Hajiya tayi suka hada ido,wani kululun bakin ciki ya tsayawa Nabila a zuciya tace"Hajiya tashi muje barta ta shigo gidan bala'i ma kadai zaisa tabar gidan,donko tayi bankwana da farin ciki har abada indai zata kasance da Jawad". Godiya Hajiya tawa boka suka tashi suka wuce. Tofa ana wata ga wata Da sallama Abee da Ammi suka shigo tankameman parlon Aminin nashi,cike da farin ciki Umma ta tarbesu suka zauna,kayan ciye ciye aka cika masu gaba dashi. Kallon Abba,Abee yayi yace"ba wannan ta kawoni ba,nazone akan maganar Dana da kake neman tauyewa hakki kasan kuma ba lafiya ce dashi ba". Murmushi Abba yayi yace"kayi hakuri ina fatan kasan neke faruwa". "Kwarai kuwa dama zuba ido nayi,Jawad yabi umarninku na auran Nabila,to meyasa shi zaku tauye masa hakkinshi?,ko kunaso mu rasashi,abunda zaiyi be sabawa addini da shara'a ba,kuka sani idan taji dadin zama dashi kota musulunta,tunda bata da wani mumunan hali ko abunki a tare da ita,to wallahi karkuyiwa Allah shishigi cikin lamurransa idan kuma kun shirya bugawar zuciyarsa ya mutu da bakin cikinku to bismillah". Haka Abee yaita kwanta masu har jikinsu yayi sanyi suka aminta da shawarar Abee. Washe gari sukaje Neman auran Sarena a gidansu an masu tarbar arziki sosai anan suka gane ashe y'ar Samol ce kuma sunada sanayya su duka ,aka sanya ranar aure nanda 2weeks rana daya Dana Nabila. Farin ciki wurin Sarena da Jawad har ba'ae don murna. Tuni Furanko ya hada kayansa ya koma America. Nabila kuwa tasha kuka kamar ta kashe kanta don takaici. *ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻 Don't for get to Comment Like and Share [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* 🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION* *united we stand and succed:our ambition is to entartein and motivate the mind of readers* Page2⃣3⃣to2⃣4⃣ Da huci ta kare maganar tana jin tsantsar bakin ciki a ranta,main parlo suka fito suna surutu da habaici suna sheke ayarsu dukdan su Sarena su jiyosu. Sarai su Serena na jinsu amma suka share babu abunda takeyi sai tsananin kuka domin rabuwa da Momy yana mata zafi arai sosai. Ba jimawa gida ya watse aka bar Nabila da Sarena kadai,Manab da Salim suka rako ango dakinshi,suna dauke da manyan ledoji a hannunsu ,ciki ya shiga ya kira Sarena before y kira Nabila,bada bata lokaci ba suka fito tare da dukawa gabansu,sannan Sarena ta gaeshesu,ita kuwa uwar gayyar a chair ta zauna tayi daya kan daya tana taunar gum,kota kanta Jawad bebi bare y tanka mata,haka suka karaci gaesawarsu babu Wanda yabi takan Nabila Wanda hakan kuma ba karamin haushi ya bata ba,kafin sukayi sallama suka tafi. A shekeke ya kalli Nabila yace"ke ki saurareni kiji,bawai n taraku nan donku maidamin gida dandalin fada bane,don nasan kece fitsararra kece bakyada hakuri,ya kamata ki sani kece karama anan ya zama dole kiwa yar uwarki biyayya,in kinason zama dani,komai tayi maki ki sanarmin zan dauki mataki da kaina amma babu batun rashin kunya tsakaninku" Baki bude Nabila tabi Jawad da kallo murmushi kawai tayi tace"tab". "Sarena nasanki da hakuri,inaso ki kara kan Wanda kikeyi Ku zauna lafiya in kuna fada bazanji dadi ba,kuma kinga kece babba duk laifi dole ki dauka kiyi hakuri daduk sharar da kanwar taki ta ebo a kanki"Jawad ya fada. Numfasawa yayi sannan yace" maganar kwana ya kukeso ayi" Karaf Nabila tace "ae abun a bayya ne yake,kwana bibiyu zakayi ko ina kawai". Beko kulata ba yace" Sarena dake nake fa". A hankali ta dago dara daran idanuwanta tayi murmushi tace"gashi Nabila ta fada hakan yayi ae". "OK zan fara da dakinki tunda kece babba,Allah yayi maku albarka ya hadamun kawunanku wuri daya". Saidai shi ya amsa da Amin don Sarena batasan me zata fadaba,itako uwar gayyar bakinci ke damunta wai Jawad zai fara kwana da Sarena dole tasan abunyi,cikin ledojin ya dauka ya mikawa Nabila ya kwashi nasu yaja hannun Sarena,kafin sukawa Nabila saida safe suka wuce daki.wani kululun bakin ciki ya taso mata wani irin rushewa tayi da kuka ta ebe ledojinta tayi daki da gudu ta fada a bed tana kukan bakin ciki. Shiko suna shiga part din Sarena wanka yace taje tayi shima zaije yayi a part dinsa,kafin ya wuce,toilet ta shiga ta wanke jikinta sosai tazo gaban mirrow ta shafe jikinta da mayuka masu dadin kamshi kafin ta feshe jikinta ko ina da body spray masu dadin shaka sannan ta dauko kayan baccinta mararsa nauyi yan sharashara ta saka ta nannade lallausan gashin kanta ta koma gefan gado ta rakube. Bangaren Jawad ma wanka yayi ya dauro alwala ya shafe jikinsa d mai sannan ya feshe jikinsa ko ina da turarukansa masu daukar hankali da dadin kamshi jallabiya kawai ya saka ya fito tare da kulle part din nasa. Da sallama ya shiga part din Sarena isketa yayi inda take ya jawota yana goge mata hawayen da takeyi ,zaunar da ita yayi yace"bari nayi sallah kinji baby na" Tana kallonsa har yayi sallah raka'a biyu yayi addu'o'in shi ,sannan ya jawota tare da lallabata yana bata gasasshiyar kazar daya siyo tare da fresh milk harta koshi,sannan yaci shima tare sukayi brush kafin yazo ya kama goshinta yayi mata addu'a ,kafin suka haye bed yana dan mata wasanni ,ganin da nayi wasa ya soma canzawa don Sarena harta fara kuka tana magiya yasa na jawo yan matan kafafuna nayo waje,oga ko ya rude bayama sauratonta burinsa kawai ya jefa kwallo a raga🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀🏃🏻‍♀. Saida Nabila ta karaci kukanta ta gaji sannan ta tashi taci kazarta ta watsa ruwa ta sheme tana bacci daure da towel. Sai dab da asuba naga Jawad yayi wanka tare da alwala,itako Sarena sai sharar bacci take,jijiyoyin kanta duksun tashi fuskarnan jajir alamun anci kuka an gaji,sunbatarta yayi sannan ya wuce masallaci. Koda ya dago kofar dakin Nabila ya tura baccinta take hankali kwance ga ledoji a barbaje gashi tayi daidai a bed tana bacci hankali kwance,tashinta ya somayi ,a galabaice ta bude idanuwanta dake cike da bacci tace"meye yaya". "Tashi kiyi sallah" ya bata amsa. "Nayi anjima pls k barni n gaji". Ganin ya daure fuska yasa ta mike tana guguni ta nufi toilet mintuna kadan ta fito hijab ta zira ta fara sallanta ,ko kadan babu natsuwa a ciki batama iyaba don ita kanta ba zata nuna yaushe rabon da tayi sallah ba harta soma mance karatun sallah.sallama tayi ta zo ta zauna kusa dashi tace " ina kwana". Beko ansaba yace"Nabila sallah nace kiyi ba wasa ba". "Wallahi yaya nayi,ita kadai na iya irin wannan Allah kuwa". Girgiza kai yayi cike da tausayi da jimami ina iyayenta zasu da hakkinta,lallai akwai aeki gabansa," OK zan koya maki don baki iya komai ba". Murguda baki tayi tace"ba garani ba da wacce bata kallon gabas dinfa nifa ba takurani nazo kayi ba"ta wurgar da hijab din ta haye Bed taja blanket. Tashi yayi ya wuce part din Sarena ,har yanzu bacci takeyi,zama yayi yana azkar yana jero addu'o'i. Wurin karfe10:00am Mama tayi knocking kofar Sarena,Jawad ya fito ya bude,ganin Mama yasa ya gaesheta ,itama ta gesheshi tace"an gama shirya abincin karin kumallonku".godiya ya mata ya koma ciki. Note:Mama itace ke zaune a gidan Jawad tana masa girki,asalinta mai aekin Abba ce,da Jawad yayi aure shine y daukota tana masu girki,gata da kirki da son mutane dama tun suna gida mutuniyar Jawad CE,hakan yasa ya fitar mata da daki a gidan. Iske Sarena yayi ta tashi ,taimaka mata yayi tayi wanka ta shirya cikin doguwar riga marar nauyi takai har gwaiwa,sannan ta gyara gashin kanta tayi kyau sosai,har yaja hannunta su fita ta tsaya cak,baya tayi da Dan Saudi taje inda aka ware mata wurin addu' a cikin dakin ta hada hannu biyu ta rufe ido,saida ta gama addu'o'inta sannan ta shafi gunkin dake wurin ta shafa a fuskarta ta fito suka wuce dining. Anan suka samu Nabila ,Sarena ta gaesheta taki amsawa ,haka sukecin abincin sai aekawa Sarena harare takeyi. *ZAMAN GIDAN JAWAD* TURKASHI *ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻 *gaskiya n raina comment dinku a book dinnan,in bakwaso saina daina* Yawan comment yawan typing. Luv u all masoyan Asali na. [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* NA *MARYAM ISMAIL* 🌈 *KAINUWA WRITER'S ASSOCIATION* *United we stand and succed:our ambition is to entartein & motivate the mind of readers* Page2⃣1⃣to2⃣2⃣ Satin biki ya taho ko wanne bangare shire shire suke musamman bangaren Nabila don tana kudirin yin bikin da duk layinsu va'a tabayi ba dukda cewa kowa a layin yanaji da kudi. Sarena kuwa babu abunda ta shirya zatayi bayan walimar da zasuyi a coci bayan an gama daura aure,don Momy ta buga kai kasa tace in an daura a masallaci dole azo ayi irin nasu don sai tafi samun natsuwa. Nabila shagali take ba kama hannun yaro tasha lalle ga uban kitson gashin doki tasha,tunda satin bikinta ya kama take program, yau ya kasance daran biki kuma zasuyi Dinner a dole Umma ta matsawa Jawad akan yaje tunda hada yan uwa. Badon ransa yasoba,ya shirya cikin maroon din shadda tsadaddiya tasha aeki black hula ya kafa black da takalma d agogo duk black yayi masifar kyau sai zuba kamshi yake. Manab da Salim suka saka shadda blue colour anko sunyi masifar kyau komai nasu iri daya. Tsaye Jawad yake yana fesa tirare, da sallama Manab da Salim suka shigo suna fadan Ango kasha kamshi. Yamutse face yayi kota Kansu bebi ba. "Wait mlm ,ya za'ae ayi Dinner ace ba dayar amaryar kamata yayi ace Sarena ta halarci wannan taron" Salim ya fada. Mumfasawa Jawad yayi sannan yace"Bari n kirata". A waya ya sanar mata akan ta shirya yanzu zasu biyo daukanta. Still tayi tanabin wayan da kallo,sannan ta dubi Moona ta fada mata me yace. "OK bari n samu Momy" Moona ta fada tana fita. Da murmushi Momy tazo dakin ta dafata"OK my Daughter bari naje siyayyan kayan da zaki saka yanzu gamai Makeup nan tayi maki". Rungume Momy Sarena tayi don Dadi cos ta dauka zata hanata zuwane. Momy bata jima da fitaba aka soma cancadawa Sarena kwalliya. Nabila n hango sanye cikin pink din dogon Riga har kasa mai kama da gown tasha make up tayi kyau ba laifi sai blue head da aka nada nata ga yar karamar Jakarta blue itama hills ta saka kayan sun matseta sosai hakan yasa take tafiya kamar tana sanda. Waje ta fito cikin gate anan ta samu su Jawad ,Salim ne yadan bugo Jawad yace"ango dago kaga kwalliyar Amaryar taka mana" Tsuka yaja kamar zai tsinke harshensa ya bude mota ya shige tare da kullewa,Manab ne zaija Motar sai Salim a kujerar mai zaman vanza. A sanyaye ta bude dayan side din ta shiga don taga muguwan hararar da Jawad ke aeka mata. Gaishesu tayi ,suka amsa but banda Jawad da yaketa faman kallon waya komai yakeyi oho ,tafiya kawai sukeyi ta rasa gane inda suka dosa gashi tana tsoran tambays Jawad y tsinkata. Kofar wani tankameman gida taga sunyi parking, waya taga Jawad ya kara a kunne ba jimawa taji yace"Baby muna kofar gida". A hankali take taku zuwa wajen gate din Moona n rike da d'ayan hannunta,sanye take cikin tsadaddiyar weeding gown black colour bata da hannu daga sama ta kamata kasa ya bude wuyanta n kallah goals be zube sai kyalli suke, gashin kanta yasha gyara sai sheki yake an dauresa da bantis sai red net aka rufa mata a kai saidai ka kalli face dinta da tasha make up a ciki ,hannunta rike yake da flowers, masha Allah abun sai Wanda ya gani donko Sarena tayi masifar kyau. Da sauri Jawad ya bude Motar ya iso gareta da murmushi ya kama hannuwanta ,rungumar juna kadan sukayi . Murmushi Moona tayi tace"to oga ga bride dinka nan mu zamu taho daga baya". Gyada kai kawai yayi ya jawo hannunta zuwa motar sun bala'in dacewa da juna musamman da suka jera. Wani kululun bakin ciki ya tsayawa Nabila a rai,a zuciya tace lallai inada aeki ,marar adalci kawai kun kusa yiwa juna kallon bankwana don vazan taba zama koma baya a cikin gidan aurena ba. Shine a tsakiya ,kafin Manab yaja Mota sai soli center, wuri yayi wuri taro yayi taro isowar ango da amare kawai ake bukata ,hangosu nayi ya shiga tsakiya sunyi masifar kyau sai dai Sarena tawa Nabila zarra tako ina. A hankali suke taku sunzo wucewa wurin kawayen Nabila da gangan Aysha ta sakawa Sarena kafa daidai akan idon Jawad,tafiya tayi zata fadi da sauri ya rikota ya dagata sama cak kamar Baby ya kaita sit dinsu kallon juna kawai suke cike da soyayya ,wani irin mahaukacin kishi da kululun bakin ciki suka dira a zuciyar Nabila Jan kafa kawai tayi ta isa ta zauna rakwaf,a dayan Side dinsa. Casu kawai ake anyi barin nairori musamman Momy da aka fiddo Sarena fili saida kallo ya dawo wurinsu don barin dukiya kawai take mata. Wuri yayi kyau ba'a tashiba sai wurin 10:30pm sannan kowa ya watse. Washe gari. Da misalin karfe 11:00am aka daura Auran Jawad Al'amin da Sarena Samol da Nabila muh'd,akan sadaki ko waccensu dubu Dari. Daurin auran yayi mutane har wurin 12 sannan suka soma ragewa before ya wuce coci ya karbo auran Amanar Sarena ya saka mata ring itama ta saka masa. Anata shagali gidansu Nabila sai cashewa takeyi tana takadarci da yamma aka lullubeta cikin hijab Abba ya mata fada sosai before yai shirin daukarta. Har gidansu Sarena Abee yaje ya karbota wurinsu Momy kuka kawai sukeyi dakyar aka rabasu ya dakkota ya kawota gidansu dake newlowcost . Gate ne babba saika shiga kaga kofa idan ka shiga babban parlo ne da yasha ado sai part Ukku na tsakiyar ne na Jawad n right side naga Abee ya shiga da Sarena ,fada ya kara mata sannanya fito ya tafi kafin Moona ta iso gidan. Ba jimawa da zuwansu Abba ya karaso da Nabila a kagare take su shiga ya fito ya tafi donko hijab din jikinta dukta dameta,shima fada ya mata sannan ya tafi . Kamar jira take ta yakice hijab din ta jefar tace"Aysha Allah yasa BA's kawo shegiyar aljanar yarinyar nanba". Tsuka Aysha taja tace"na nawa kuma ae kece amarya tun dazu Abee ya kawota". Ihun haushi Nabila ta daka tace "wlh wannan shirin Jawad ne mugu kawai donta rigani zuwa ya tsaidamu ,to wallahi zatan tayi sallama da farin ciki tunda hartai kuskuren hada miji dani". *ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻 Luv u all [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* 🌈 *KAINUWA WRITERS ASSOCIATION* Page2⃣5⃣to2⃣6⃣ *zaman gidan jawad* Zaman gidan Jawad zamane da kokadan bayawa Sarena dadi kowa kansa ya sani musamman yacce take hakuri da halin Nabila da irin izgilancin da take mata,tana goronta mata ita kafura ce. Wayan dake kusa da ita yayi kara dubanta takai kareta ganin sunan Mom ya bayyana a kan screen din ya sata sakin murmushi da sauri ta dauka tana shaukin jin muryar Mom,saida suka gama gaesawa sannan tace"Sarena kizo muyi bankwana karfe 9:00am jirginmu zai tashi zuwa America ,Daddynki ya gama aekinsa zamu koma kasarmu". Wata iriyar faduwar gaba ta iske Sarena a hankali tace"Mom zaku tafi Ku barni ni kadai".sai hawaye suka soma bin kuncinta,sallama sukayi ta kashe wayar tana tunanin ina zataga Jawad ta fada masa zataje gida,rabonta da ta saka Jawad a idonta koya kulata tun daran farkon da aka kawota gidan,text ta masa ta waya ta tashi ta fara shiri. Yana zaune office text dinta ya shigo wayarsa kamar ya duba kamar y bari ,haka kawai ya duba koda yaga me take fada,text ya mata (ki je ae akwai driver kuma kinada mota a gidan kije inda kikaso). Futowa tayi sanye da dogon Riga iyakarta cinya fara kal gashin kanta yasha kyara dukda ta rame amma hakan besa taki yin kyau ba,ba wata makeup a face dinta amma tayi masifar kyau ,hill shoe ta saka baki ta dauki bag dinta black colour, duba text din da yayi mata tayi,haka kawai taji zuciyarta ba dadi key ta dauka ta fice daga gidan ganin time ya tafi yasa sukayi mahada airport. Da gudu ta bude motar ta nufi wurin su Mom ganin jirginsu na haramar tashi tun kafin ta isa wurinsu hawaye ke ambaliya a kyakyawar fuskarta,rungume Mom tayi tana fadin"Mommy narh". Karfin hali Mom tayi tace"a'a Sarena ba kuka yanzufa kin girma,matar aurece,ba yadda za'ayi mu tafi dake, idan kin haihu saiki kaimun Baby na na rike"ta fada tana Jan kumatunta. Kunya ta kamata ta rufe fuska ta kuma rungume Mom ,sannan ta rungumi Daddy,nan kam Mom ta kasa daurewa haka Daddy yaja Mom suka shige jirgi sukabar Sarena a wurin,tanaji tana gani jirginsu ya tashi,a jirgi Mom kuka take kamar ranta zai fita tana kuma Allah wadai da auran Jawad da Sarena tayi gashi yanzu sun rabu. Kuka take a haka ta karasa Mota da kyar ta iya shiga mota ta nufi gida ,tana isa da gudu ta fito ta fada part dinta bakinta cike da amai ga wani irin kasala da tashin zuciya dake damunta amai ta zazzaga ba kadan ba da rairahe ta iso a bed ta fada ta rufe jikinta tana kyarmar sanyi har bacci yayi awan gaba da ita. Tafa hannu Nabila da Hajiya sukayi kafin Hajiya ta sassauta murya tace"waya fada maku barno gabas,take saima tabar gidan kafa zage,yanzu dai ga wannan maganin ki bashi shi a abinci yaci ,dole ya tsaneta ta rika masa warin jaba yaji ko ganinta bayasonyi a gidansa kedai ki dage kiga yaci". Ansa Nabila tayi tana boyewa a side drower tace"Allah ya barman ke Hajiya ta kin maidani mace na karbe mijina". Haka sukaita fira marar amfani sai yamma likis Hajiya ta tafi gida. Bancin Mama ta gama abinci ta jera a dining ,Nabila tazo ta zuba maganin kamar yadda Hajiya ta umarceta,kafin taje tayi wanka,ta shirya cikin atamfa Riga da siket Wanda dasu gwara babu duksun matseta . Da sallama ya shiga part din Nabila da gudu ta iso wurinsa ya rungumeta yana washe baki yana kara kankameta a jikinsa yana bin wuyanta yana sinsina tare dadan lasarsa. Zame jikin tayi tace"kaidai baka gajiya muje kayi wanka kaci abinci sannan na baka"ta fada tana kashe ido. Wanka yayi ya shirya cikin 3kwata da vest ya feshe jikinsa da turare sannan suka iso dining suna makale da juna ,zama yayi ta zuba masa abincin jolluf rice CE da hadadden sobo ,yanaci yana wasa da ita hankalinsu kwance yaci ya koshi yana faman rirriketa. Sarena dake lekensu ta taga wani irin bakin ciki ya ziyarci zuciyarta ga cikinta dake mata ciwo tanata tashin zuciya zafafan hawayene suka ci gaba da ambaliya a kyakyawar fuskarta da tayi jajir ta sauya launi a kasa ta zauna dishan ta kuma fashewa da kuka tana rike cikinta. *ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻 Share and comment Luv u all [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* 🌈kainuwa writers association United we stand and succed: our ambition is to entatein and motivate the mind of readers Na Maryam Ismail Muhphat Page2⃣7⃣to2⃣8⃣ A ranar batayi isashen bacci ba,ga dai tsananin ciwo ga kuma kewar iyayenta uwa uba da mijinta ya juya mata baya,har safiya tayi Sarena bata kara sanin inda kanta yake ba,donko tasha amai dukta galabaita ciki ciki take numfashi. Da misalin karfe11 na safe,Mama dukta damu tun jiya rabon data saka Sarena a idanunta amma ba halin tambaya,suko gasu a parlo sai sheka dariya suke suna fira,karaurawar dakin ta shiga kara alamar damai shigowa,yunkurawa yayi yana fadin"Manab harya karaso kenan".yana budewa kuma zatonsa ya zama gaskiya musabaha sukayi sannan ya shigo cikin gidan a parlon suka zauna,Nabila kuwa kara matsewa a jikin Jawad take ko kunyar fingilallun kayan dake jikinta batayi tana wani narkewa a jikinsa. Wani bakin cikine ya ziyarci zuciyar Manab a kufule yace"friend ina Sarena?" Wata faduwar gaba ta ziyarci zuciyar Jawad dandanan ya daure fuska yace"oho ka duba part dinta zaka wani dameni". Mikewa yayi ya isa part din nata buga kofan yake amma shiru babu ko motsi kasada kawai yayi ya tura ,parlon a gyare sai zuba kamshi yake ko ina tsab,jiyo nishinta da yakeyi a hankali a hankali yasa ya kara isa kusa da bedroom nata aeko itace zaro ido yayi ,da sauri ya karasa ya tura kofar,yadda ya ganta ya masifar tada hankalinsa da sauri ya dawo main parlo yana kwalawa Jawad kira, Yatsine fuska Jawad yayi a hankali ya furta "Menene kuma". " lallai Jawad,ka kosan me kake aekatawa da iliminka zaka kashe y'ar mutane,Sarena ba lafiya sosai ko tashi bata iyayi "cewar Manab " to mezan mata ko yarinyace karama da batasan hanyar asibiti ba,goyata kakeso nayi,nifa malan ba cewa nayi ka daman ba"Jawad ya fada. Wani far da idanu Nabila tayi sannan tace"haba Habibi nah,ya kamata ka dubata,sannan ka kaita asibiti pls mana" Tsaki yaja yace"Hada ke za'a tursasani wify gaskiya bazan iyaba ,aetanada hankali karki kara saka kanki a irin wannan don Allah". Duk yadda Manab yaso Jawad yazo ya dauko Sarena fafur yaki saima ya tashi yaja Nabila suka wuce daki yace inya fita yaja masu gidan.sosai ran Manab ya baci waya ya ciro ya kira Salim ya tambaya ko yana hospital, ya amsa da eh,cikin hanzari ya koma wurinta a lokacin ko motsi batayi,babu yadda ya iya a dole ya dauketa ya fito yana gudugudu ya sakata bayan mota yaja da gudu sai hospital din salim. Cikin gaggawa aka shiga da ita emergency a rude Manab ya rike hannun Salim yana fadin"pls Salim do ur best ,banaso Sarena ta mutu wallahi ina jinta tamkar ciki daya muka fito banaso na rasata". Dafa kafadarsa Salim yayi ya daga masa kai ya shiga ciki. Safa da marwa ya shigayi yana tunanin shinwai meya shiga kan Jawad wannan wanne irin cin zaline haka,yafi awa hudu a nan yana jiran Salim sannan ya futo suka wuce office. "Wai aekin me Jawad yakeyi yakeson kashe y'ar mutane da ranta" cewar Salim. "Hm inako zan sani tsohwan Dan iskan ya biyewa wannan y'ar iskar yarinyar ita ke juyashi fuska kamarta biri". Manab ya fada. " to gaskiya Sarena tana bukatar kula,kagadai ya ciwan zuciyar data samu da ba'a kawota Asibiti ba at anytime zata iya rasa ranta,uwa uba ga cikin dake jikinta tana fama da laulayinsa". Da sauri Manab ya dago kai yace"Ciki ,kuma da Cikin sa a jikinta yabarta tana wahala gaskiya Jawad ya canza ban taba tunanin zewa Sarena haka ba inka duba irin son da yake mata amma bari mu gani" Waya ya Ciro ya fara kiransa ,harya fitar da rai akan zai dauki wayarsa sannan ya dauka ajiyar zuciya Manab yayi sannan yace"Jawad wai meke damunka kanaso ka gama da duniya lafiya kuwa?,ka sakawa yarinya ciwan zuciya har yana baraza a rayuwarta,ga Cikin daka dirka mata kuma ka barta cikin wannan halin". "Dakata Manab tadai sakawa kanta me nake mata,nifa ko sunanta banaso kana ambatamin indai kanaso muci gaba da zama wuri daya,sannan ni tunda aka kawota so d'aya na rabeta sannan kacemin tanada Ciki,toni ban karba ba ba Cikina bane,taje ta nemi Wanda yayi mata shi" be jira ansar Manab ba ya tsinke wayarsa. Murmushi Salim yayi yace"karka damu Manab wannan bayin kansa bane mudai muyi masa addu'a mu kula masa da matarsa har Allah ya sauketa lafiya shine kawai". Dakin da aka kaita Manab ya shiga,Sarena yakebi da kallo tayi fari tas abunta ta kara kyau drip ne like a hannunta ,hankalinta kwance tana bacci sai fitar da numfashi takeyi. Salim ya saka masu kula da Sarena dare da rana,bata da matsalar komai a asibitin ta murmure tayi kiba abunta,kullun Manab da Salim suna tsaye a kanta kwananta biyar aka sallameta,Manab ya dauketa ya maida ita gida yayi mata fada sosai akan tayi hakuri kuma kada ta saka damuwa a ranta. ******** Parlo ta fito dama tunda ta dawo take dakon ganin Jawad ,zaune ta samesa har kasa takai ta gaeshesa tayi masa banza. A hankali tace"idan bakaji tausayinaba ae kodan D'anka da yake Cikina ka tausayamin my Love ". Tsawa ya daka mata wacce tasa ta firgicewa lokaci daya tana kyarma.sannan yace" karki kara kirana My love ,Cikin Jikinki ba nawa bane,kije ki nemi Uban danki karuwa kawai,kuma daga yau kin daina zaman banza a gidannan duk wani aeki ke zaki rika yinsa bance ki zauna ki hutaba ,inko naga akasin haka zaki gane kuranki,wannan kadan daga hukuncin Cikin shegen da kika kawomin ne"kafa yasa ya halbeta harta fadi ya wucewarsa. *ALKALAMIN MARYAMA* ✍🏻 Gaisuwata a gareki kawar alkairi masoyiyar Asali na,Khadija Haruna Abdulkadir alkairin Allah yakai maki inayinki irin sosai dinnan. Share and comment Muhphat luv [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's Na Maryam Ismail Muhphat Page2⃣9⃣to3⃣0⃣ Wani irin kuka ke shirin kubuce mata,da sauri ta toshe bakinta ,sai wasu zafafan hawaye da suka kwaranyo daga idanuwanta ,bakin ciki cike da zuciyarta ,kallon Jawad kawai take harya bacewa ganinta,kasa mikewa tayi daga inda take saida Mama ta kamata sannan dishi dishi ta soma gani a haka tabi bango zuwa dakinta a kan chair ta kifa kanta ta fashe da kuka. Nabila kuwa duk abunda yake faruwa tana ta window tana lekensu ganin tahowar Jawad yasa tad'anyi baya ,yana shigowa suka rungumi juna kallonta kawai yake ,sannan ya hada bakinta da nashi ya soma tsotsa kamar ya samu sweet daga nan wasa ya sauya,na jawo kafafuna nayi waje😀 *AMERICA* Zaune take a chair iskar garin na ratsata ,yanayin yayi dadi ga Wanda yake kwanciyar hankali,hango fuskarta nayi idanuwanta rufe suke cikin bakin glass tayi kyau sosai ,saidai hawayen dakebin gefan fuskarta kallo daya zaka mata ka tabbatar tana cikin tashin hankali sosai . A hankali Mr Samol ya karaso gareta kamata yayi yana goge mata hawaye yace"meke damunki wify". Bakin Lissa na rawa ta furta"Sarena ,inason y'ata anya banyi kuskuren barinta a Nigeria ba,gashi inata kiran wayarta bana samu". Murmushi kad'an yayi yace"ki daina damuwa,kinsan mijinta na sonta sosai zai kula da ita,kuma muma zamuje ganinta kada ki damu" Da kalamai masu dadi ya shawo kan Lissa harta daina kuka ta dauki tunani irin nashi. Some months later. Cikin Sarena ya shiga wata na tara a kowanne yanayi zata iya haihu,bayan hanyoyin da su Hajiya sukabi wurin kasheta ita da cikin Amma basuyi nasara ba,hakan ya basu dama suka maisheda Sarena cikakkiyar baiwa a gidan,ko kadan idan bakayi mata mugun saniba bazaka taba ganeta ba tayi baki, ta rame, ta fita daga hayyacin ta koma kazama don a sati so daya take wanka,ga wasu kaya da basu da maraba da tsunma su take sakawa,daki daya suka bata a part din masu aeki wata guntuwar tabarma CE shinfide a dakin sai gefe kullin kayanta na sakawa,rayuwa kenan. Zaune take a gefan tabarmarta kanta a gwaiwarta hawayene kebin fuskarta daduk ta koje . Banko kofar dakin Nabila tayi tana yan harare harare tare da toshe hancinta ,wankin dake hannunta ta watsa a jikin Sarena tace "ke dallah tashi ki wankemun kayannan sannan ki wankemun Mota zan fita". D'ago kanta tayi tanabin fuskar Nabila data gama konewa da mayukan kara fari na kanti" tace haba,wai bakya tausayina kiji yadda nake amma ko'a jikinki kamar kema ba y'a mace ba". Saurin dakatar da ita Nabila tayi sannan ta kwashe da dariyar mugunta tace"tausayi aeni ban sanshi a kanki ba,na tsaneki yadda na tsani mutuwa ta,dama nace zan sakaki kukan wuya tunda har kikayi kuskuren had'a hanya da abunda nikeso". Mikewa Sarena tayi sannan tace"tir da irin wannan rayuwa taki,sai naji ke keyi nikejin kunya shin baki girmama addininku ,kobashi ya basu damar auran mace fiye da d'aya ba,amma ke kike jayayya,kodayake ae addinin ba kama jikinki yayi ba" Dukawa tayi ta kwashe kayan wanki tana tafiya da kyar ta soma wankin kayan tanajin kunar rai a tattare da ita. Jawad kam ya zama saniyar ware banda Hajiya da Nabila babu mai rabarsa su kadai ke morarsa harta Manab da Salim sun rabu dashi donko kadan bazasu iya daukar halayyarsa ta yanzu ba ko sallah bata damesa ba ,saidai daga gefe suna masa addu'a Zagaye kawai Umma take tsakar d'aki abun duniya ya dameta ace d'anta na cikinta ko kadan yanzu be damu da itaba yau kusan wata biyu bata sakashi a idonta ba,bazai yiwuba dole tasan abunyi gaskiya ,dole Jawad ya dawo gareta. Da sallama Momyn Manab ta shigo gidan cike da fara'a mata meson mutane,cikin mutunci Umma ta taryeta suna murnar yaushe gamo,part din Ummu suka shiga a bed suka zauna A hankali cike da nazari Momy tace"wai meke damunki ?,kika wani fita hayyacinki". "Ba dole ba,yaufa wata biyu banga Jawad ba,kuma yana cikin garin nan ,an rabani dashi ko ta waya baya iya kirana gaba daya ya koma bashiba" cewar Umma. Murmushin takaici Momy tayi tace"haka nikejin labari donkoni ya daina zuwa wurina,ya kuma rabu dasu Manab, dama idan na gansa yake d'an debeman kewar *MINAD* to nima ya gujeni,ki tashi ki kama addu'a babu abunda yafi karfin Allah d'anki ze dawo gareki. Haka Momy tayita bata shawa ta gari,sannan suka rabu akan cewa zasuje gidan jibi. Flowers duksun cika gidan and'an jima ba'a gyara wuriba,me kyara aka kirawo yazo yayi masu aski,a lokacin kuma Nabila ta fita zuwa wurin bokanta akan ya kashe mata Sarena tunda hartayi bakin maida mata magana. Askin yake Mama da Sarena suna Sharar flowers din dake zubewa a kasa,sauri Sarena tayi ta dago a firgice har cikin kwalwarta abun ya ratsata ga wani irin mumunar faduwar gaba,a hankali ta dago kafarta daga tudun data taka. Riketa Mama tayi sannan tace Bari na tona wurin naga menene a ciki,tsab Mama ta tone ramun,wani irin ihu suka rigaji yana fita faga ramin, hannunta na kyarma ta kwaso kayan dake ciki,layune iri iri ,ga katon abu gunki sak sai wani gashi,ga kuma rigar Sarena data Jawad an dauresu wuri daya. Duk abunda ke cikin layun saida Mama ta karantasu tasan makarar asiri bata nunawa kowa ba facce Sarena ,wuta ta hada ta konesu kurmus tare dayin addu'o'i har suka cinye sannan tasa ruwa ta wanke tokar tas. Bacci yake tare da mafarki,hannu taketa miko mashi daga cikin bakin ramun da take,tana kuka tana fadin ka tai makeni,zuwa yayi cetonta ya mika mata hannu sai aka janyeta kasa,ga jarirai har biyu sai binsa suke suna kuka,suna kiransa da Abba. Firgigita ya farka yayi zufa sharkaf a hankali ya furta *MINAD* ina kika shiga kika barni ,zumbur ya mike jikinsa ko kadan ba kwari ga jiri yana gani,tunani yakeyi yaushe rabon da yayi sallah Alwala ya dauro ya soma jero salloli. Nabila kuwa bokanta ya tabbatar mata saiya sadu da ita maniyinsu shine mahadar gubar kisan Sarena,bako musu ta bishi suka shige bukkarsa suka soma masha'arsu dukda warin da bokan yakeyi haka ta daure har sukayi ya samu maniyyin ya hada maganin a kwalba ya bata tare da sharadin ta tabbatar Sarena tasha wannan maganin cikin ruwa ko abinci.cike da farin ciki ta dawo gida hankalinta bekai kan wurin ajiyarta ba ,ta wuce part dinta tayi wanka don tsabtace jikinta bayan ta gama take shedawa Hajiya yadda sukayi. Umma kuwa ko kadan taki bacci yanzu ko ta fara saluda zaune take a sallaya tanata yiwa danta addu'o'i,addu'ar uwa akan danta. Typing ba dadi kuyi hakuri da wannan pls Comment Share Like Muhphat luv [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* Na Maryam Ismail Muhphat 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's Page3⃣1⃣to3⃣2⃣ Cike da kisisina Nabila ta mike ta nufi dakin Jawad tana zuwa kai tsaye ta tura kofa,ta shige ciki ,kan sallaya ta hangosa,gabanta yayi wata mumunar faduwa tuni kyarma ke shirin kwace mata,daurewa tayi ta karasa garesa zata kwanta a jikinshi,wata iriyar tsawa ya daka mata Wanda yasa sora kadan ta zubo fitsari. Binta yayi da mugun kallo sannan yace"uban waye tsaranki da zakizo ki kwanta a kaina,kuma daga yau karki kuma shigomin daki babu sallama tashi ki fita ki bani wuri Jaka kawai". Kallonsa kawai take tana hawaye a zuciyarta tana fadin na shiga ukku ni Nabila ya akai haka ta faru,mikewa tayi ta fice da gudu tana isa daki waya tayi saurin dauka tana kiran number din hajiya,bugu daya ta dauka baki na kyarma take fadin"Hajiya na shiga ukku na,Yaya Jawad ,duk abunda nayi masa Hajiya ya warware sallah fa yakeyi yanzu kumani yake kora daga dakinsa tsantsar tsanata tananan kwance a zuciyarsa"kuka ya kwace mata. "Rufe bakinki kinji,daina damun kanki bazamu gaji da bannatar da miliyoyi ba akan farin cikinki,kije kiyi aeki akan wannan mayyar kafurar yarinyar,ki fita harkar Jawad ni kuma zanje wurin malam karki damu" Da irin wannan maganganun gurbatattu Hajiya ta kwantarwa Nabila hankali harta Dan daidaita sannan sukayi sallama. Fitowa tayi don duba ajiyarta kamar yadda ta saba ,ganin an tone wurin batasan lokacin data kurma uban ihuba,tare da zaro ido ta dafe kai,ba damar tayi tambaya a gane da saka hannunta a abun da suka gani wurin,rai bace ta juyo zuwa part dinta. Duk abunda takeyi akan idanun Mama da Sarena take yinsa suna kallonta ta window,numfasa Mama tayi tace"Allah ya shiryi mai hali irin naki,ke kuma Allah ya juyo da hankalin mijinki a wurinki". Murmushi kawai Sarena tayi tace a gurbatacciyar hausarta"na gode,Amma ni kasarmu zan koma Mama ,na fasa auran dashi". Ko kadan Jawad bayajin karfin jikinsa kwance yake rufda ciki hankalinsa tashe,abubuwa da yawa sunata dawo masa akai,ji yayi daga kwance kamar ana juyashi ga tashin zuciya,da gudu ya fada toilet ya soma kwarara amai,bakinkirin dashi ga wari,ya dade yana yinsa,kamar fitar wani abu take a lokacin yajishi ya koma sawat har wani karfi yakeji a jikinsa,wanka yayi ya fito ya shirya cikin kananan kaya,ya feshe jikinsa da turaruka masu dadin kamshi yayi matukar kyau cikin wando black da riga red ,wayarsa ya dauko ya soma kiran layin wayan Manab. Shiko Manab zaune yake gaban Ammi sunata fira akan matsalar Jawad din tana fada Masa anjima zasuje gidan ita da Ummansu suga meke faruwa. Karar wayarsa yasa yakai dubansa garesa cike da mamaki ya furta Jawad,dauka yayi a sanyaye jin muryar Jawad a sanyaye yasashi sakin ajiyar zuciya yace"friend ya kake". "Nrml kana ina ,zanzo yanzu" Jawad ya fada. Murmushi Manab yayi yace"Angon Nabila da wuri haka,ina gida". Wani irin tsaki Jawad ya saki sannan yace"banza kawai ,dallah ka daina fadamun haka"be jira amsa ba ya kashe wayarsa ya dauki key din motarsa yayi waje. Gefe take tsaye ita da Mama ya fito hankalinsa bekai Kansu ba,Mama zata gaeshesa Sarena ta rufe mata baki ,kallonsa kawai takeyi yayinda wasu zafafan hawaye kebin kuncinta.harya ja Mota ya fita akan idanuwanta. Nabila ganin ba kowa da gudu ta shiga dakinsu Sarena ganin kwanon abincinta a gefan katifarta da alama shizataci ,cikin sauri ta warwaro kullun maganin ta zuba ta motse abinci ta rufe,ta fito da sauri ta koma part dinta. Kallon Sarena Mama tayi, tace"har yanzu kina son mijinki,amma kuma kince zaki rabu dashi". Goge hawaye Sarena tayi tace"ina sonsa,Amma bazan zauna dashi ba,baya sona" "Kinga kada kiyi kuka,kinga kinada ciki banaso kina damuwa,muje kici abincinki kada yayi sanyi kinji y'ata". Kai tsaye dakinsu suka shiga ,zaunar da ita tayi ta jawo kwanon ta mika mata ta dauka spoon ta bata,ta wuce waje don ida aekace aekacenta.ita kuma ta soma cin abincin. Jawad yana isa gida ya gaeshe da Ammi,sannan yake fadawa Manab mike faruwa kuma shi yanzu besan yazaiyi da Sarena ba harta saurareshi,sannan ya roki Ammi dasuje gidan,wucewa sukayi suka dauki Umma,suka wuce gidan Jawad. Sarena kam ta cinye abinci tsab,kai tsaye taji cikinta ya soma juyowa kamar zai fito kai tsaye jini ya soma bin kafarta wani azababban ciwan ciki ya taso mata,Mama ta soma kwala ma kira,Amma bazata jitaba kasancewar tana kasa,a hankali ta soma rairafe tayo hanyar waje. Da Sallama su Jawad suka shigo main parlor din,Mama ce kadai gaesawa sukaci gaba dayi sannan Ammi tace"ina Sarenan takene". " tana ciki abinci takeci bari na kirata"kafin Mama ta rufe baki,suka hango Sarena tana fito da rairafe a hankali ta dafa kofa ta mike bakinta na rawa tana so ta furta sunan Mama. A razane Ammi ta dago tana kallon cinyarta dake dauke da wani bakin tabo a jiki ,bakinta ta kyarma ta fada da karfi"Minad". A razane kowa kebinta da kallo suna maimaita sunan data fada Minad. Cikin Sarena ya kuma murda mata ta saki wani razanan ihu ta tafi zata fadi,dukansu sukayi kanta,kafin kowa ya isa gareta Ammi harta isa ta riketa,tana kuka tana fadin"Ku taimaka mun kada Minad dina ta mutu don Allah",tuni Sarena ta some a hannun Ammi,Nabila na gefe tana kallonsu . Cikin sauri Manab ya fizgeta yayi mota da ita,da gudu suka rufa masa baya. Comment Share Like Muhphat luv [01/08, 8:54 PM] Cweet Mrym Mhphert: *ASALI NA* 🌈kainuwa writer's association United we stand and succed:our ambition is to entertain & motivate the mind of reader's Na Maryam Ismail Muhphat Godiya gareku masoya TABON D'A NAMIJI,ina bada hakuri na jina shiru kwana biyu da kuka jini naji dadi sosai wasu sun kirani,wasu sunman text,insha Allah ranar Sunday zaku rika jina kullun Alhmdllh yanzu shine gabana. 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Last page 🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚 Sadaukarwa ga kainuwa writers Allah ya kara hada kanmu. Mota Manab ya shiga suka rufa masa baya,kowa da abunda yake fada sabanin Jawad da tunda aka ambaci Minad ya rasa gane komai yanaso yasan tayaya Sarena zata koma Minad dinsa wannan wanne irin rudadden Asali ne a tattare da ita. Da kyarma Manab yake kiran Salim yana fada masa ga Sarena ba lafiya su taimaka mata,kai tsaye Emergency suka shiga da ita yayinda kowa ke safa da marwa a wurin suna jiran saka mako. Su Mr Samol kuwa yaune jirginsu ya sauka Nigeria saboda rigimar Lissa kullun kuka take tace wai tayi mafarki Sarena na cikin damuwa da kunci hakan ya tilasta masu tahowa don duk jiya basu rintsaba,kai tsaye gidan Jawad suka nufa nan Mama ke sanar musu Sarena na asibiti,tun kafin su isa Asibitin Lissa ke kuka suna isa ko parking basuyi ba ta bude murfin mota ta fito tana tambayar sisters din wurin,a rude suka isa da ita wurin hakan yayi daidai da turowar da akayiwa Sarena a Bed an fito da ita daga Emergency zuwa wani dakin na daban,wani irin ihun kuka Lissa ta saki lokacin data gama bin jikin Sarena da kallo duktayi baki ta lalace kwatakwata batayi kama da Sarenar data bari ba,kai tsaye Jawad ta nufa tana dukansa tana fada masa mugayan kalamai da nuna masa irin tsanar data masa,dakyar Mr Samol ya riketa ta fada jikinsa tana fadin"I will never forgive u inhar Sarena ta mutu,kaima ka jera sunanka a matsayin matacce I promise u this". Kallonsu Salim yayi yace muje Office,Manab da Jawad sai Mr Samol suka bisa nan ya masu bayanin gubar da aka bata,amma Allah ya taimaka sunkaita asibiti da sauri gubar batayi tasiri a jikinta ba Alhmdllh ita da abunda ke cikinta suna cikin koshin lafiya. Wata sanyayyar Ajiyar zuciya Jawad ya saki yana godewa Allah ,sannan suka fito,a dakin da aka kai Sarena suka shiga har Daddy da Abba sun iso rigima na neman ta balle tsakanin Ammi da Lissa. Cikin kuka Ammi tace "wannan tabon na cinyarta akwaishi tsakiyar bayanta,kuma Ku duba wannan Minad ce,". Nanfa ido ya soma raina fata ana bude bayan Sarena saiga tabo ya bayyana. Matsowa dab da ita Ammi tayi tace" ki tashi Minad,yauga mahaifiyarki a gabanki tana cike da kewarki da soyayyarki dama ban taba sakawa raina kin mutu ba,ina matukar sonki nasan zaki dawo gareni" Wani irin nishi Sarena tayi a hankali ta bude idanuwanta da suka lumshe ta fara bin kowa na dakin da kallo baki na rawa take mikawa Momy hannu tana fadin"Momy na,ki tafi dani banason nan ". Matsowa kusa da ita Momy tayi ta dafata tace" share hawayenki gatanki ya dawo Mind ki kalli wannan itace Mahaifiyarki bani ba ki bude kunne ki saurareni". Lissa bata jira neman Shawar mijinta ba ta fadi komai ke faruwa da tun ranar da suka dauki Sarena har kawo yau,gaban Ammi taje tace"kiyi hakuri bama da zabin daya wuce wannan,komun dawo da ita,zasu iya cutar da ita kumani Soyayyar ta ta shiga raina, amma kuyi hakuri". Kowa na dakin hankalinsa tashe yake masu kuka nayi ,Abba ko da Umma sunyi sufa sharaf suna faman kamekame,ananme kuma Mama ta shigo dakin ta kalli Nabila da Hajiya kai tsaye ta mika video din dake hannunta kowa ya kalli duk abunda ke faruwa,ganin ba sarki sai Allah yasa Nabila saluda tana Neman afuwa da fadin abubuwan dake faruwa. Da sauri Abba da Hajiya sukayi waje kankice me suka shige Mota suka fita da gudu be kallon ina yakeyi da mota horn wata babbar Mota ke masu, basuji ba kafin motarsu Daddy ta iso motarnan ta murjesu tas jikinsu yabi kwalta dakyar aka tattarasu aka sallacesu zuwa kabarinsu,tashin hankali da sauyin yanayi yasa Sarena shiga labour room bata shirya ba ta haifo yaranta yan Maza guda biyu masu masifar kama da Jawad sosai . Nabila kuwa kai tsaye ciwo ya sakota gaba ta kamu da HIV ga wasu kuraje da takeyi suna fitar da ruwa mai wari duka jikinta ta rame tayi baki ta lalace,a cikin mabaratan asibiti suke zama, Umma ko ta dade da saluda,ta zauna tana istigfari ta koma ga Allah,sosai Ammi ke tausaya mata kullun cikin sadaka da ibada take. Alhmdllh Sarena ta koma Minad a ranar sunan yayanta suka karbi musulunci ita da Daddy da Momynta,yaranta kuma sukaci sunan Abba da Daddy suna kiransu da Ashman da Ashwan,Mama ke kula dasu. Some years later Farin ciki ya dawo wa family dinsu,hankali kwance tuni Minad tayi sauka,yaranta sunyi wayau sosai Alhmdllh sun zama yan uwa dasu Mr Samol, soyayya tsakanin Jawad da Minad ta kara karfi hankalinsu kwance duk wani damuwa ta yaye masu Minad tayi kyau tayi fari yar gata a wurin iyayen ta da yayanta ga kuma mijinta rayuwata hankalinsu kwance. Godiya ga sarki Allah daya nunamin karshen wannan littafi. Muhphat luv