*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ _ina farawa da sunan Allah Mai Rahma Mai Jin Ƙai._ *(1)* *_ƘADDARA! kalma ce da ta amsa wani suna, wannan sunan mai tarin ma'anoni da yawa...Kowanne bawa na ɗauke da kundin ƙaddararsa, wadda ke ɗaure a wuyansa, kuma kowanne ɗan Adam da yanda salon shafin kundin ƙaddararsa ke buɗewa, inda ta kan buɗe da siffofi guda biyu, ko ta siffantu da alkhairi ko kuma ta siffantu da jarabawa kala daban-daban....ka zalika acikin kowanne duniya kuma kowacce rayuwa, ƙaddara na tafiya ne dai-dai da rayuwa, kuma ta rayu damu cikin farinciki ko akasin hakan, sannan babu wani bawa da yake iya gujewa ƙaddararsa, cikin kowacce rana da kowanne lokaci ƙaddararmu na gudana ne ajikinmu tamkar jini, kuma kamar yanda rayuwarmu ta ke mabanbanciya haka ita kanta ƙaddarar ta ke...yanda kundin ƙaddararsu ya buɗe yasha banban dana saura, kuma tabbas da ace suna da iko, da sun ɗau wannan kundin ƙaddarar sun shafe komai dake cikinsa, tukunna su ƙara tsara shi zuwa wata sabuwar rayuwar da ba zata haɗa hanya da waccen ba...WAYE NI? wannan tambayar me kalmomi biyu da harufa shida ke yawo kullum a cikin kan AL-HUSSAIN, da su yake kwana yake tashi, kuma acikin tsumayin jiran lokacin da ganyensa zai bushe ya faɗo zuwa ƙasa, daga nan shikenan sai ya zama tarihi...sai dai abinda AL-HUSSAIN bai sa ni ba shine; zaren wata ƙaddarar na sauyawa ne a sa'ilin da adu'a kaɗai ke iya sauyata...to amma a ɓangaren SABINA da ta san WACECE ITA fa?, idan har ƙaddara na ɗaure a wuyan kowanne bawa to abun tambayar shine mecece tata ƙaddarar? ya ya ta ke? da yaushe zata fuskanceta? ta wanne irin yanayi zata zo ma ta? mai kyau ce ko kuma mara kyau? zata iya karɓanta ko ba zata iya ba?...wata ƙaddarar kamar zanen dutse ta ke da babu abunda ke iya sauyata!..._* *Kano, 3:00pm.* sanye nake da maroon hijab wanda ya ɗauki kyawuna matuƙa, a yayinda Farhana ke yafe da ƙaramin gyalenta wanda itama yay ma ta kyau sosai. Cikin takun natsuwa da hankali muke fitowa daga cikin Sahad Store da ke nan anguwar zoo road. Ledar hannun Farhana kawai zaka kalla ka gane cewa ba ƙaramar siyayya ce muka yi ba. muna tafe muna ƴar magana a cikin nishaɗi, duka fuskokinmu kewaye da glasses, sai dai akwai banbanci a tsakanin glasses ɗina da nata, domin nawa na magani ne wanda ake kira da medical glass, ciwon idon dana gada a wurin Kakata mahaifiyar Abbana, ita kuma Farhana na gayu ne, wanda bata iya rabo da shi a kullu yaumin. zuwanmu bakin jar motar da ta ke mallakin Farhana ce muka tsaya, sannan Farhana ta buɗe booth ta sanya ledar kayan hannunta, tukunna na buɗe gaban motar na shiga, bayan Farhana ta rufe booth sannan itama ta zagayo ɓangaren mazaunin driver ta shigo ta zauna tana yiwa motar key. "wash Sister wallahi na gaji da yawa yau, kai ni kam sai na kwan biyu ban kuma zuwa wani biki ba". na faɗa a sa'ilin dana ke kunna Ac'n motar. "yanzu ai zamu ƙarasa gida, nima da kika ganni duk a gajiya na ke, buƙatata kawai na jini cikin shower". cewar Farhana tana karya kan motar zuwa kan titin da zamu hau. na ƙara cewa,"ke kin san ma za ki samu ruwa a gida, ni yanzu na koma da wuya idan ba sai na fita neman mai ruwa ba, saboda anguwar mu muna cikin matsalar ruwa...Gwamnati gaba ɗaya bata tausayin rayuwar talaka, ba wuta ba ruwa a inda talaka bawan Allah ke rayuwa, kai Allah kayi mana magani". na numfasa kamin na ƙara cewa,"Allah sarki Gwaggo nah nasan yanzu tana can tana tsumayin dawowa ta, kuma kin san fa sai da ta ce ka da na jima". Farhana ta ce,"kinga ba wannan bama, ni damuwar ma Allah yasa mu tarar da telan nan yana shago, kar musha wuyar banza ga wannan uban go slow ɗin, kalla fa tun ɗazu danja ta ɗaga amma har yanzu motoci sun gagara wucewa". "to amin dai, Allah ya nufemu da ritsa shi a shagon ɓuyarsa". na faɗa ina yatsine fuska alamar gajiya sosai a tare dani. Direct sharaɗa muka wuce shagon da Momin Farhana ta aikemu amso ma ta ɗinki. Ba ƙaramin takaici muka ƙunsa ba da muka je ba mu sami me ɗinkin ba, tsabar haushi ma ko jiran yaron shagonsa dake mana bayani bamu yi ba muka fice dukanmu rai a ɓace, danni har ji nai kaman na gwaɓe bakin saurayin dana san ƙarya ce kawai yake gilla mana. tun fitowarmu daga shagon nake ta duban jefi-jefin jama'ar da ke layin, kasancewar sa layi ne da bai tara mutane ba, sai ƴan tsirarru haka, unguwa ce bata masu kuɗi ba amma kamar wata babbar estate shiru kake ji. nace da Farhana, "ni kam kiyi sauri mu bar layin nan ina tsoronsa, kin san yanzu kidnappers sun yi yawa a gari, mutane ba tsoron Allah". itama tace,"hmmm sauri ai kece zance kiyi, kina tafiya kamar ba za ki taka ƙasa ba, kee ni ko dai kina da matsalar ƙafa ne?". na harareta sannan nai murmushina mai sanyi ba tare dana ce ma ta komai ba, muka ci gaba da tafiya hannunmu riƙe dana juna kace mu twins ne, sai dai muna gab da ƙarasawa inda mukai parking naji ƙafafuna sun tsaya cak daga tafiyar, yayinda hannuna ya zame daga cikin na Farhana, na bi gefen haguna da kallo kafin naji ƙafafuna na jana suna tafiya da ni zuwa wani wuri, wani wuri da ban san me zai iya faruwa ba idan na riske shi, na bar Farhana naci gaba da tafiya tana ta maganarta ita ɗaya duk tunaninta tare muke. sai da tayi gaba sosai sannan ta fahimci tafiyar tamu ba tare muke ba, ta waigo da kanta sai kawai taga babu ɓurɓushina ma a wajen, kuma a wannan lokacin ɗaga idon da zatai can gefe ta hangeni ina tafiya cikin sauri-sauri har ina harɗewa, saurin da a duniyarta zata rantsewa wani bata taɓa ganin nayi shi ba tun yarintarmu. tsananin mamaki sai yasa ta riƙe haɓa, cikin zuciyarta na ayyanawa da me zanje yi a cikin bola?. "Sabina! Sabina!! ke Sabina wai ina ki ke neman zuwa haka? bola fa naga kina neman shiga, wai kin yi hauka ne? Keee!!". zan iya cewa a sama-sama naji abunda ta ke cewa, dan haka hannu na ɗaga ma ta ta baya kawai ba tare dana yi yunƙurin tsayawa ba, kuma zagin da ta ƙunduma ta wurgo min shi yasa ni ɗaga ƴar muryata ina cewa da ita,"Farhana ba fa bolar zan shiga ba, ki biyo ni ko ki jira ni yanzu zan dawo". Farhana ta sauke numfashi tana zubawa sarautar Allah ido, tabbas banda tasan wace ƙawarta lallai zata iya cewa aljanu ne da ita ko kuma tana da ciwon hauka ne, amma a yanzun ma ba zata ƙi cewa Sabina ta sami matsala ba. Gani tai sam ba zata iya barinta ita ɗaya ta shiga cikin wannan bolar da shigarta babu abinda mutum zai kwasowa kansa fa ce musiba, hakan yasa ta bi bayanta itama cikin sauri, abunda ya ƙara bata mamaki kuma hangenta da tai ta tsaya gaban wani mutumi da ke zaune saman bulon wani kango a jikin bolar. Farhana tai turus ta tsaya domin ita kuwa al'amarin ya fara bata tsoro, gwara ta tsaya daga nan ɗin idan taga abin bana tsayuwa bane saita arta ana kare, domin ta fara tantama da lafiyar ƙwaƙwalwar Sabina. Saurayi ne kyakykyawa na ajin ƙarshe zaune saman bulo a bakin wani kango, shekarunsa zasu kai 27-28, shi ba fari ba kuma shi ba baƙi ba, hasken sa dai-dai misali, jikinsa sanye da yadi me arha ruwan madara wanda ya amshi jikinsa, a kallo ɗaya zaka yiwa kayan jikinsa ko da ace daga nesa ne ka gane cewar yadin a koɗe yake, irin koɗewa da jemewar da suka gaji da duniya, Farin silifas ne wanda ya ɗanji jiki sanye a doguwar ƙafarsa me ɗauke da zara-zaran yatsu, Kansa a ƙasa yake hannunsa riƙe da taba sigari, cikin ƙwarancewa yake zuƙa yana fesar da hayaƙin ta gefensa. zai kuma zuƙa kenan yaji an ƙarɓe ta daga hannunsa, ya ɗago jajayen idanunsa domin ganin mahaluƙin dake da ikon karɓe masa abokiyar rayuwarsa. Idonsa ne yay tozali da ƴar kyakykyawar budurwa tsugune gabansa, tana sauke masa kyakykyawan murmushi, da wannan idanun nata masu zurfi, kallo ɗaya yay ma ta yay saurin ɗauke idonsa saboda faɗuwar gaban daya tsinci kansa a ciki, ba tare da sanin dalilin hakan ba, kuma haka kawai sai yaji ƙirjinsa na bugawa da sauri da sauri abinda bai taɓa riska ba tsawon shekarun rayuwarsa. ina lure da shi da yanda yake bina da kallo ta ƙasan ido, wucewar sakan ɗaya, biyu, uku, ya ɗago da kansa gaba ɗaya yana sauke kallonsa gaba ɗaya akaina, har yanzu ban bar yi masa murmushi ba, hakana ban ɗauke idona daga ƙwayar idonsa ba dake haskawa da ƙyallin mamakina ba, kuma zan iya rantsewa a wannan lokacin abinda yake rayawa acikin ransa shine _ko dai ni mahaukaciya ce?._ na gyara zaman glass ɗina sannan nace da shi, "Hy Mr Man". na faɗa ina ɗaga masa gira sama, sai dai shi idonsa na kan tabar dake hannuna da ban yar da ita ba, sai na kalli tabar tukunna na maida kallona kansa kamin na shiga ce masa. "wannan tana cutarwa, ba ta amfanar da mai shanta, Almubazzaranci ce, tana cutar da na kusa da kai. a bisa haka Malamai suka ce tunda duk abinda ta ke haddasawa haramun ne to itama ta zama haramun". ina gama faɗa na jefar da sigarin a ƙasa, na ta ke da takalmina, sannan na maida glass ɗina dana cire nai cleaning ɗinsa. yaji sanda iska ta ɗebo abunda tace ta shigar cikin kunnensa, kuma yaji yanda kalaman nata suka sami zama acikin kansa, ya tantance maganartata cikin kowanne futar harafi, sai dai ya kasa tantance zaƙin sautin daya fita acikin amon muryartata. ni kuwa ƙura masa ido sosai nai ko tsoronsa ma banji, kuma shi ma sosai yake kallon ƙwayar idona, sai dai Allah masanin gaibu, dan ban san me zuciyarsa ke karanta masa ba. sai kawai na ƙara murmusa kuncina a karo na babu adadi, tare da harɗe hannayena a ƙirji ina faɗa masa abunda bai tambayeni ba, haka kuma babu nuni na yana baƙatar sanin hakan. "Sunana Sabina Auwal, anan garin kano nake. And you?". a wannan lokacin abinda Sabina bata sa ni ba shine, zuciyarsa na gaya masa cewar_anya ita mutum ce kuwa._ bai bani amsa ba, babu kuma yunƙurin hakan a tare da shi, abu ɗaya ne kawai ke ɗawainiya dani, aiwatar da wasu abubuwa da bana sanin lokacin da nake yinsu ba...matsowa kusa da fuskarsa nai, na ɗaga masa kai alamar ina jiran cewarsa akan tambayar sunansa da nai. sai naji shi da saɓanin abunda na tambaye shi ɗin. "me yasa ki ka faɗan sunanki bayan ban tambaye ki ba?". "ka fara bani amsar tambayata tunda ni na fara". na faɗa ina ɗan karayar da kai gefe. a hankali naji muryarsa na fita, kuma a lokacin so nake na toshe hancina saboda warin sigarin dake fita a bakinsa, amma na kasa saboda bana so na nuna masa walaƙanci. "duk da bana jin yaren da kika yi min tambayar, amma zai iya yiwuwa na fahimta. indai yanda na fahimci tambayar taki ne to ni ba ni da suna, kuma bani da sunan Baba, ban san kuma garin da na ke ba". sai kawai na saki baki galala ina ƙare masa kallo da maɗaukakin mamaki, kuma ƙwayar idona na haska masa da cewar ban yarda da abunda ya faɗa ba. "tun ina ƙarama kamin Mama nah ta rasu, ina tunawa kamin ta rasu ta gaya mun babu kyau ƙarya, don haka kar na yi kuma kar na koyi yinta, kuma kar nayi tarayya da me yinta. Sannan da na girma, Gwaggo nah wata rana ta yiwa Yaya nah faɗa cewar Babba baya ƙarya. So dan haka kaima karka yi ƙarya kaga babba ne kai, kuma ni yarinya ce, idan kayi zan koya a wurinka, kuma nasan ai ba zaka so hakan ba ko Yaya?". ina masa maganar ne da yanayi irin na yara. "me ya kawo ki nan wurin?". Ya tambayeni yana mai tsareni da ido da alamu na tuhuma. na tsarota sosai, kuma tsoron bai sa ni yi masa ƙarya ba, na faɗa masa ainihin abunda ya kawo ni. "na zo ne domin na hanaka shan sigarin da ta ke haramtacciya". "to ki tashi ki tafi, ni ɗin bana son kowa a kusa da ni, ki tafi kar naji miki rauni". yanayin da yay maganar kuma ya ke dubana ba ƙaramin kaɗa ƴaƴan cikina yay ba, ina kallo ya zura hannu a aljihu ya ɗauko kwalin sigari ya buɗe ya ɗauki ɗaya, sannan ya ƙyasta lighter ya kunna, zai kai baki kenan na miƙe da zafin nama na ƙwace ina yin jifa da ita. kamar zan fashe da kuka nace, "don Allah kar kasha, ba zan iya ganinka kana shan abunda zai cutar da kai ba. Kazo mu bar nan wurin don Allah". na faɗa ina kamo hannunsa don mu tafi. a tsawace yace da ni,"kar ki ƙara cemin Yaya, ni ba Yayanki ba ne". "shikenan ba zan kuma ba. Amma sai ka faɗa min sunanka idan ba haka ba ni kuma bazan daina ce maka Yaya ba, tunda kai ɗin ka girme ni ka yi sa'a da Yaya Abba, tarbiyar gidanmu bata koyar damu faɗan sunan na gaba damu ba gatsal". Ƙwace hannunsa yay anawa yana doka min tsawar da tasa naja baya babu shiri, yana faɗin, "ki tafi ki barni ko. Nace miki bana da suna bana kuma da sunan Baba, banda kowa, na tsinci kaina ina rayuwa ne ni ɗaya kawai...dan haka bana son kuma jin maganarki anan wurin ki wuce ki bar nan". na kawar da tsoronsa ina kuma kamo hannunsa, roƙonsa nake kamar tsohuwar mayya ina cewa, "Yaya kar kayi fushi ka duke ni, na maka alƙawarin ba zan kuma tambayan sunanka ba tunda baka so. Amma yanzu ka zo mu tafi gida, zamanka anan zai cutar da kai, ga warin bola ga sigarin da kake sha, abun yayi yawa". cikin wata razananniyar muryar ya ƙara ce min. "shekaruna goma sha tawas ina rayuwa anan Wurin, anan nake yini nake kwana, sigari itace abincina kuma itace abokiyar rayuwata, Allah shi ke tallafe da rayuwata, maƙociyata da nake jin daɗin mu'amala da ita wannan bolar, warinta shi nake shaƙa naji daɗi. Duk tsawon wannan shekarun ban cutu ba sai a yau da kika zo?, to wace ke? me kika isa ki sauya a rayuwar da Allah ya tsarata a haka tuntuni?...kinga ki shige ki tafi ki bani wuri tun ban maki rauni ba". Tsantsar tausayinsa naji ya kamani, da wani firgici da kalamansa suka haifar min, saboda ganin yanda damuwa ta kuma bijirowa a saman fuskarsa, har yana maganar tana rawa kamar zai fashe da kuka saboda ɗacin rai. saina sauke kaina ƙasa ina goge ƙwallar da ta tarar min, wucewar sakanni uku na ƙara kamo hannunsa naja shi da ƙarfin da Ƙafafunsa basu iya yin gardama ba. yayinda a lokaci ɗaya naji ihun kukan jariri na ƙwala ƙara acikin kunnena, ƙarar kukan da yasani saurin gimtse ido, tare da damƙe hannunsa da ƙarfi babu shiri, inda hasken hoton wani jariri ke giftawa acikin duhun idona, sai naji kaina na wani mugun sarawa da wannan tsala kukan da jaririn yakeyi...wani abu da ban fahimta ba a lokacin shine, wataƙila anyi amfani da gatari ne wajen sara shi a tsakiyar kaina ya rabe gida biyu, ta yanda yin gaba da komawa baya zasu gagara a tare da ni. **** _Hey Guyz how are you doing, hope you are all doing fine. how was the first charpter? loving the story already bah? encourage me by comments and voting, thats the only way i will know my effort is beaing appreciated...it's not a new story buh an old story am updating, i just changed the story name, kuma no disappointment insha'Allahu☺....ina fatan zan sami haɗin kanku daga farko har zuwa ƙarshe. Allah ya bani ikon gamawa lafiya, amin Ya Rahman...mai karantawa kuma Allah ya cire shi daga sahun mugwayen da zasu karanta littafi suƙi appreciating, dan mugunta ne da munafurci ai karatu aƙi appreciating, mutum sai ya nuna kaman bai karanta littafin, honestly speaking babu daɗi irin hakan...promise you ba zanyi delaying maku posting ba, so you people ma karku ji ƙyashin yin vote da comment.👏👏_ #love you my readers😘 #mikiyawriter's #2022. #Share.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(2)* kusan daƙiƙa huɗu kaina na juyawa kafin na iya sakin hannunsa na ɗan matsa gefe da shi na dafa jikin gini. sama-sama nake jiyo muryan Furhana na faɗin,"wai Sabina kin san shi ne?". ta faɗa tana ƙarasowa inda nake. na buɗe idona da ƙyar na dubeta ina cewa,"a'a ban san shi ba, ban ma san waye ba". cikin ƙarfin hali nai magana ina dafe da kaina, ta matso kusa gareni da tashin hankali tana dafa kan nawa da shiga jera min tambayoyin,"lafiya?". a wannan lokacin babu abinda nake so irin a cire min kaina a dire shi a gefe, in yaso a barni naci gaba da rayuwa a haka idan da yiwuwa kenan, idan kuma har cire kan zai zama silar rasa raina to tabbas zaifi min sauƙi a cire shi dan na rabu da wannan tsananin sarawar da yake min, da kuma amsa kuwar kukan jaririn da har yanzu ban bar jinsa ba. "na shiga uku menene naga kina dafe kai? innalillahi wa'inna ilaihi raji'un...kinga abinda kike neman jawa kanki ko Sabina, ni uban me ma kika gani da kika yo cikin bola sai kace mahaukaciya". muryar Farhana na fita ne cikin faɗa sosai da kuma tsananin nuna kulawa gami da matuƙar nuna damuwa. magana nake so nayi amma na kasa, sai laɓɓana dake aukin yin rawa, ko idona dake buɗe kaɗan dishi-dishi nake gani da su, jiri ya ɗebeni na nemi na zube a wajen tai saurin riƙeni ta zaunar akan bulo ɗin da Yaya ya tashi. hawayen azaba ya shiga min sintiri a saman fuskata, Farhana ma ko da bana kallonta amma a yanda muryarta ke fita da rawa nasan kuka ta ke, ta kama kaina tayi min adu'a, sannan ina jinta ta miƙe tana surfa zagi da bala'i ga bawan Allah'n dana san bashi da hannu a wannan halin dana shiga. ta dage akan sai ya faɗa ma ta abunda yayi min ko kuma ta kira masa ƴan sanda yanzun nan, shi dai bai saurareta ba dan banji yayi ma ta magana ba...kuma haka ta ƙyale shi ta dawo kaina duk a ruɗe tana ƙara faɗa masa wallahi komai ya sameni sai inda ƙarfin shari'arsu ya ƙare ita da shi, dan ba zata ƙyale shi ba. da ace tasan irin azabar da nake ji acikin kaina, da kuma hoton dake haskawa cikin duhun idona, da bata tsaya tana wannan jarabar ba, kamani kawai zata yi mu tafi gida a sama min lafiyar ciwon da nake ji. "na banu ni Farhana, ban san me kika shigo yi wajen nan ba, yanzu duba matsalar da kika jawa kanki...yanzu me zan faɗawa Gwaggo". kuka ta ke yi sosai a sa'ilin, kuma har ga Allah maganartata na ƙara ƙarfin iskar guguwar dake wucewa ta kacikin ƙoƙon kaina ne. sai dai cikin lokacin da ba zai haura sakanni takwas ba na manta da halin da nake ciki da duk wani abu da naji yana damuna, hatta hanzarin miƙewar da nayi ban san nayi ba dalilin jin Farhana tana cewa da shi. "ina zaka je? ina zaka tafi? kasan Allah ka ƙara ɗaga ƙafarka daga nan saina yi maka ihu, kazo ka sakar min ƴar'uwa dan nasan koma menene kaine sila". duk da cewar ba sosai nake gani ba, amma a taku biyu na cimma inda yake tsaye, kuma ban manta da wannan kama hannun nasa da nayi ba gudun kar ya tafi ya kai kansa wajen da zaici gaba da cutuwa, hakan zuciyata ke ce min, "barinsa nan wurin zai kai kansa ne inda yafi nan muni". shi yasa komai zai ƙara faruwa dani ba zan sakesa ba, ko da ace zan dawwama anan babu tafiya. amma ga wani maɗaukakin mamakin da al'ajabi, damƙar hannunsa da nai sai kawai naji komai na washewa, ciwon yana tafiya, komai na janyewa, kuma a hankali komai ya tsaya cak, kamin ya tafi gaba ɗaya. sai naji ni nayi sanyi ƙalau, haka kuma wani abu da ban san menene ba na tsargawa a jikina. na buɗe ido ina dubansa, yana nan dai tsaye a wurin, kenan tun a ɗazun bai motsa ba, sai dai wannan karan hannayensa duka biyun na zuɓe ne cikin aljihun wandonsa. sai kawai na ƙara kamo hannun nasa a haka naci gaba da jansa,kuma a yanzu bai min gardama ba, bai yi yunƙurin ƙwacewa ba, kawai bina yake kaman yaron dake bin uwarsa. ni kuwa ƙara saurin tafiyarmu nake dan mu bar cikin bolar da wuri, saboda zuciyata faɗa min kawai ta ke karki tafi ki barshi nan, sai dai komai zai faru ya faru dake. gaba ɗaya na manta ma da wata Farhana sai dana jiyota tana faɗin, "Allah kayi min maganin abunda ke neman yafi ƙarfina...yanzu da kike janshi ina za ki da shi?". ba tare dana tsaya daga tafiyar ba ko kuma na juyo nace da ita. "tare zamu tafi. bana son zamansa anan". "Allah uwar da ta haife shi". sai kuma ta ƙara da cewa,"amma dai kinyi hauka ko Sabina? ba ki san mutum ba, ba ki san shi ɗin ko aljani ne ba, ko kuma macuci kawai dan ɗebarwa kai masifa da nemarwa kai jaraba shine kika wani kama zuwa inda yake harda ƙarfin halin riƙo hannunsa za ki tafi da shi, to ki kai shi gidan uban wa uwar masu son taimako ta duniya...yanzu wannan ɗan wiwin har ina dalilin da za'a taimake shi". "kenan Farhana kawai idan mutum ya tsinci kansa a irin wannan halin sai aƙi danganta hakan da jarabawar rayuwa? saboda hakan kuma sai aƙi taimakon mutum?". na faɗa ina tsareta da ido a sanda na tsaya da tafiyar. "oho ni bance haka ba amma wannan dai ai baiyi kama da wanda za'ace ƙaddara ce tasa shi shiga wannan yanayin ba...dan haka kawai ki sake shi mu tafi, karki so ki tona zuciyata kiga takaicin da ke ciki". "ohhh Farhana ki fahimce ni mana, duk abinda zaka yi kayi shi don Allah kuma zuciya a tsarkake, wataran baka san ta inda za'a taimake ka ba kaima. Nifa kawai na tausaya masa ne, naga kuma bai dace muna ganin halin da yake ciki ba mu tafi mu barshi a haka. Yanzu tafiya zamu yi da shi sai mu sauke shi a gidansu". ta galla min harara tana faɗin,"mtswww ƴan wiwi nawa ki kai arba da su ba ki taɓa yunƙurin taimaka musu ba sai akan wannan mahaukacin". kuma furucinta na ƙarshe ya tsaida ƙafafuna, na rufe ido kaɗan sannan na buɗe, magana nake so na yaɓa ma ta, amma ba zan iya ba, bata cancanci hakan daga gareni ba, kuma hakan ba halina ba ne sam. sai kawai na kaɗa kai da cewar,"su sauran basu yi kama da waɗanda suke biɗar a taimaki rayuwarsu ba ne shiyasa kika kalla banyi hakan ba. shi kuwa sai dai idan idon mara imani ne ya sauka akansa, amma a hoton fuskarsa na farko daka kalla zaka shaida ɗan adam ne da yake cikin wata jarabawar rayuwa, ki kalla ƙwayar idonsa da kyau ki gani, ita kaɗai me shaida miki halin ƙuncin da yake ciki ne, balle shi yanda ba ki ɗaya abunda ke zuciyarsa ya bayyana a saman fuskarsa...Farhana ko kaffara ba zanyi miki ba mutumin nan yana da ciwo a tare da shi, wannan ciwon na damuwa da yake roƙon Allah dare da rana ya magance mishi, kuma wataƙila Allah ya sakoni cikin rayuwarsa dan na zama sila...shi yasa ko dana ganshi naji ba zan iya yin yanda kike so ba...so please lets go, i beg you". ganinta nai kawai ta wuce ta gabanmu bakinta na faɗin,"tabɗijam, ko duniya za'a tasa tafiya da wannan ɗan wiwin ba'a motata ba, don babu abinda zai sanya ni yayibar mahaukaci na kama tafiya da shi, ai yasan da gidan nasu yazo ya zauna anan....mtswww ke da kin kalla ma fa kinga alamun rashin lafiya a tare da shi, saboda haka kinga tafiyata". "kece ki ke masa kallon mara lafiya amma ƙalau ya ke kamar yanda muke". "a'a ba dai kamar ni ba kam, me lafiya dai ba zai zo kusa da bola ya zauna ba har yana shan sigari. Ai da gani kin san waye, cikin biyun dole ɗaya, mahaukaci ko kuma riƙaƙƙen ɗan daba, ki sake kallonsa da nazari tukunna ki dube yanayinsa da idon fahimta". ta ƙarasa faɗa tana nuna shi da baki a yatsine. Kallon Farhana kawai yake yana ganin yanda ta ke banka masa wata uwar harara. na san yaji rashin daɗin abinda tace, amma gani nake kamar nafi shi rashin jin daɗin hakan. "haba don Allah Farhana, ya za ki dinga aibata ɗan'uwanki musulmi da irin waɗannan kalmomi marasa daɗi, bayan ba ki da masaniyar komai a kansa. Ki tuna fa addininmu ya yi hani da tozarta musulmi". "hmmm! lallai har yanzu ba ki da wayo Sabina, kuma indai za ki ci gaba da biyewa wannan zuciyar taki zata kaiki ta baroki akan saurin taimako da kuma tausayi. kuma ina mai gaya miki tun wuri ki bar wannan ɗan shaye-shayen kizo mu tafi, don wallahi irinsu ne tantiran ƴan iskan nan masu lalata ƴaƴan mutane, waɗanda bakin uwa ya gama binsu". maganarta ta ƙarshe tai wani dukan ganga a zuciyar Alhussain, dan haka yay saurin rumtse ido da gaggawa ko ya sami sassaucin raɗadin da maganarta ta haifar masa. yau rana ɗaya kuma rana ta farko da aka taɓa faɗa masa kalma mafi muni da ɗaci a rayuwarsa. lalata! bakin uwa!, to shi da bai taɓa ma yin gaba da gaba da wata ƴa mace ba ta ina zai lalatata? wama ke raɓarsa daga maza har Mata? Babu! Shi ɗaya ne a rayuwarsa, kuma bashi da iyaye balle yace yana da uwar da bakinta yabi shi...amma sai gashi yau har ana kiransa da ɗan daba, zai iya rantsewa a iya tsayin rayuwarsa baya tunanin ya taɓa riƙe wuƙa ko makami, yaji yana shan wiwi amma baya taɓa ɗarawa daga kanta, itan ma dan ya kanji sauƙi ne idan yasha...sai gashi yau ƙanƙanuwar yarinya na gaya masa son ranta ba tare da ta san shi ɗin waye ba kamar yanda shima bai san kowaye ba. ƙwayar idonsa tai masa nauyi kamar an baɗa masa ƙasa a ciki, buɗe su yayi da matsananciyar damuwa gami da ɓacin rai, bai da ikon yi ma ta komai saboda ya cancanci a faɗa masa dukkan wasu kalmomi masu muni. idonsa yana bin Farhana da kallo da saƙa wasu abubuwa cikin ransa, yana jin tsakin da ta ke taja acikin kansa. sai ya cire hannunsa daga nawa, na dube shi da rashin jin daɗin abinda Farhana tai, tausayinsa naji ya daɗa kamani, ko da wannan ɗaga ƙafar kaɗai da yayi mata zan iya shaida na rantse yana cikin wannan halinne kawai dan bashi da yanda iya, amma ba da son ransa ba. Muryarta a sanyaye nace da shi, "don Allah Yaya kayi haƙuri da abinda ƙawata tayi maka, rashin fahimta ne ya janyo hakan, amma a madadinta ina mai baka haƙuri, na san kowane aka yi masa ba zai ji daɗi ba, karda ka sanya ɓacin ran hakan a ranka ya kuma haddasa maka damuwa". sai kawai naji ya buɗi baki yana cewa, "kema kar da ki damu, dama na shirya fuskantar wannan ƙalubalen, irin wannan kalaman ba zasu dameni ba, ko da finsu ne ma ba zanji ciwo ba...da sannu kema za ki faɗa min su ne, wataƙila yanzu, wataƙila zuwa wani lokaci". "Allah ya kiyaye bana fatan hakan ko da ba akanka ba". sautin muryarsa ya washe da ce min, "ke kam wai ba kya da tsoro ne?". Ya faɗa murya da ɗan ƙarfi. sai nace, "Allah shine abin tsoro ai, kuma kai ɗin ai ba kayi kama da mugu ba da har zan tsorata da kai. Yanzu dai kazo mu tafi kaga magriba na gabatowa kuma Gwaggo nah zata mani faɗan ban dawo da wuri ba". "baki sanni ba, baki san wane ni ba amma kina nema na raɓe ki, nace miki bani da gida, anan wurin nake rayuwa ta. Shin wai baki gudun na cutar dake ne ke kam?". na marairaice idanuwa ina dubansa da rashin jin daɗi nace, "Annabi S.W.A yace *KAMATUDINI TUDAN* (duk abunda kayi sai anyi maka). kai ɗin kana da Mama, kana da Ƙanwa, ƙilan ma kana da Yaya mace, nan gaba zaka auri mace, kuma ta iya yiwuwa ka haifi ƴa mace. Kaga kuwa nayi amanna da cewar ba zaka cutar dani ba saboda ba zaka so wani ya cutar da naka ba". sai yaja dogon numfashi ya sauke sannan yace min, "ki dinga kiyayewa. Yanzu kibi bayanta ku tafi gida, kar Gwaggo'n ki tayi miki faɗa". maganarsa ta haddasa jikina yin sanyi, naji raina fayau, nai ƙasa da idona ina kallon yatsun ƙafata nace,"to idan na tafi kai fa?". "so nake ki yarda dani, bana magana balle har ta kai ga nayi ƙarya. inda kika ganni anan nake rayuwata tsayin shekarun dana faɗa miki, idan har nabi ki bani da wani gida da zan nuna miki nace ina da alaƙa da shi. don haka ki tafi kawai ki ƙyaleni". "to amma kayi alƙawari idan na tafi na barka ba zaka kuma shan wannan abar me cutarwa ba?". sai ya rufe ido ya ɗan kauda kai gefe, ba zata taɓa fahimtarsa ba, ba zata taɓa ganewa ba. "akan mene zan ɗauki alƙawarin da bazan iya cika shi ba? Kawai ni dai ki tafi kuma karki kuma dawowa inda nake". "kana nufin ba zaka iya daina shanta ba kenan? Na faɗa maka fa shanta haramune, ko ka fi so ka aikata abunda Allah ya haramta?". idonsa a kulle ya shiga girgiza min kansa alaman A'a. "to in dai haka ne, don Allah kar ka kuma shanta daga yanzun nan. Kaga shi yasa ma mutane ke maka kallon ɗan iska, kuma alhalin kai ɗin ba shi bane. Wannan ba zata yi maka maganin damuwa ba sai dai ta cutar da kai, ka miƙa lamuranka ga ubangiji sai kaga ya yaye maka damuwar dake tare da kai. Ƙilan mu kuma haɗuwa ƙilan ba zamu kuma haɗuwa ba, amma ina roƙonka da Allah karka kuma shan taba, ka nisance ta nisa na har abada kaji Yaya". kawai sai na kalla ya runtse ido yana jijjiga min kansa alaman yaji kuma zaiyi yanda nace. har cikin raina sai naji daɗi, na saki Murmushi kana nace masa, "na gode Yaya nah. Kuma ka sani idan ni bana ganinka Allah yana kallonka, dan haka ka riƙe alƙawarin daka ɗauka...alƙawari yana da girma, kayana ne karka manta da wannan". na juya cikin rashin kuzarin jiki na barshi a tsaye, yayin da nake jin kallonsa da yake bina da shi ajikina, kuma har sanda na shiga mota na zauna idonsa na kaina, zuwa lokacin da Farhana ta yiwa motar key sannan naga ya juya ya koma inda muka fito. kuma tun bayan zaman Alhussain da kuma bayan tafiyar Sabina, tunaninsa guda ɗaya ne yake yi, _dama akwai ranar da zata zo wani ya kusance shi da nuna kulawa gami da tausayawa irin haka? Dama a cikin Mata akwai masu uzuri da kirki irin haka?_ tambayoyin da yay ma kansa kenan, a yayin da hoton Sabina ke haska mishi a ido da amsar tambayar tasa. ta kasance a tare da shi alhalin bata san shi ba, bata san waye shi ba, ba zagi, babu ƙyama, babu walaƙanci, babu tozarci, sai ƙoƙarin janyo shi a jikinta domin ta nuna masa illar halin daya jefa kansa ciki, halin daya na zaune acikinsa ne ta dole bisa ƙaddara. ayau kuma sanadinta yaji yana bala'in son kasancewa da ahalinsa, ya gansu ko da ace ba zasu kalle shi ba, ko da ba zasu karɓe shi ba, ko da zasu wulaƙanta shi. Wani abu mai zafin gaske yaji ya taɓa zuciyarsa, *SHIN WANENE SHI?*, *SU WAYE IYAYESA?*, *MENE SILAR KASANCEWARSA A WANNAN HALIN*, *YAUSHE ZAI FITA DAGA WANNAN ƘANGIN RAYUWAR?*, *HAR TSAWON WANNE LOKACI ZA'A ƊAUKA KAMIN ƘADDARARSA TA SAUYA FUSKA?*... sai yaji zuciyarsa ta matse sosai, ta yi rauni, ya dafe goshinsa ya kuma runtse idonsa da ƙarfin gaske, ya cije leɓensa na ƙasa hawaye masu zafin gaske suka shiga malala a fuskarsa, sai kuma ya fashe da kuka mai ƙarfi tare da kifa kansa a saman cinyarsa yana riƙe da kansa dake mugun sara mishi tamkar zai bar jikinsa. wannan yanayin, wani yanayi ne da yake tsintar kansa a duk sanda ya rasa amsar waɗan can tambayoyin, ya ɗau tsawon lokaci a haka cikin rera wannan kukan mai ƙaramin sauti tamkar ba matashin saurayi ba, tukunna ya miƙe ya tafi masallaci dalilin kiran sallar daya ji ana yi, bai baro cikin masallaci ba har sai da akayi sallar isha'i kana, nan ma sai da za'a rufe masallacin sannan ya fito. A dawowarsa ya tsaya a dai-dai inda motar su Sabina tayi parking ɗazu, kallon wajen yake da haskawar hoton abunda ya faru a ɗazu, bai san dalili ba, amma haka kawai yaji yana so yarinyar ta ƙara kasancewa da shi. sai yasa hannu ya matse idanunsa dake rufe, ƙasan zuciyarsa na raya masa da cewar _ko zata sake dawowa?._ *Please don't forget to comment, vote and share.* *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(3)* da wannan tunanin ya samu wuri ya zauna, zuciyarsa tana cigaba da tunani iri-iri, tunanin duniya, tunanin rayuwarsa da tunanin yarinyar da ta fara raɓarsa tun bayan sanin kansa da yay. motar Farhana na tsayawa ban ce komai ba na buɗe murfin motar na fita cikin fushi ba tare da ko na dubi inda Farhana ta ke ba, can ƙasan murya na furta,"nagode ki gaida su  Hajiya". tace da ni,"zasu ji insha'Allah, amma ba ki ɗauka kayan da muka saya ba”. wani irin kallo na bita da shi ta ƙasan ido, ban ko yunƙurin amsa ma ta ba, dan abunda tayiwa wancan bawan Allah'n ji nake tamkar Yaya Abba da muke ciki guda ta yiwa, shi yasa tun tahowarmu nake fushi da ita, kuma ina ganin kaman ba zamu shirya ba har sai mun koma wajensa ta bashi haƙuri yace ya haƙura tukunna. ban rufe ma ta ƙofa ba sai dana ja tsaki tukunna na fara tafiya na ɗauka hanyar gida, ganin hakan yasa Farhana fitowa daga motar ta buɗe boot ta ɗauko kayan da muka saya ta biyo bayana da shi. A ɗan ƙaramin tsakar gidanmu wanda yasha shara baka ganin ko da ɗigon datti, na tarar da Gwaggo tana goga kuɓewa, sallama kawai nayi na shige ciki, ban ma san ta amsa ba ko bata amsa ba, kuma ajikina nake jin yanda Gwaggo ke bin bayana da kallo, kuma shirunta ya bani tabbacin tana tunanin yanayin da ta ganni aciki ne. Farhana ta shigo, Gwaggo ko amsa sallamarta ba tai ba tace mata,“yauwa yanzu kuwa zance to ya akayi baki shigo ba, ashe kina bayanta, meye sa me ta ne? naga daga sallama ta shige ciki, Allah yasa lafiya ne". Farhana tace, “lafiyarta lau, ai kin san halinta da ɗan banzan saka damuwa a rai, wai fa wani mahaukaci ta gani a hanyarmu ta dawowa gida shi ne ta ɗaga hankalinta haka". ta duƙa a gaban Gwaggo ta aje ledar hannunta da cewa,"ni dai zan wuce Gwaggo sai wani lokacin, ga shi wannan nata ne”. Gwaggo ta maida hankalinta kan kuɓewar da ta ke gogawa tace, “to madalla, kyace ina gaida Hajiyarku”. Daga haka Farhana ta gyara zaman glass nata ta fice. Maganar Farhana ta tsayawa Gwaggo a rai, don kuwa sarai ta san halin Sabina, zata iya yin komi akan wannan mahaukaci kamar yadda Farhana ta faɗa mata, to amma meye nata na damuwa haka, koma meye dai zata ji. ina kishingiɗe jikin pillow naji Gwaggo na Ƙwala min kira, kaman ba zan amsa ba sai kuma na buɗe ba ki nace da ita ina zuwa, na miƙe jiki babu ƙwari kamar mara lafiya na fito. na rakuɓe gefe guda ina jiran abinda zai fito daga bakin Gwaggo, abunda naji tana faɗi ne yasa na ɗaga ido ina dubanta. “wanne Mahaukaci ne wannnan har da zai ɗaga maki hankali haka?, Sabina kin san halina fa sarai, ina da sauƙin kai amma bana son shashanci, waye shi?”. sai naji zuciyata tayi min nauyi saboda kalmar mahaukaci da Gwaggo tayi amfani da ita wurin kiran Yaya da shi, na turo baki gaba ina daɗa dubanta ta cikin glasses nawa nace. “don Allah ku daina kiran shi da mahaukaci, baku san yadda zuciyata ta ke duka ba, kalmar mahaukaci ai bata danganci mutum musulmi ba, mahaukaci ai sai dabba, shi kuma mutum ne mai kamala, don a maganar shi bata yi min kama da mai taɓin hankali ba, kawai halin rayuwa ne ya mayar da shi haka”. Zuru Gwaggo tayi tana dubana, maganganuna sun bata mamaki matuƙa gaya, cikin faɗa-faɗa ta kama cewa, “yo wai ke shin kin yi hauka ne, a ina ma kika gan shi ne tukun har kike faɗin haka, kin san dai Farhana ba zata maki ƙarya ba ko?”. “Gwaggo Allah ba mahaukaci bane, kawai dan ta gan shi a cikin kango kan bola shikenan sai ta kira shi da mahaukaci, idan ita aka faɗawa ɗan uwanta haka ai ba zata ji daɗi ba, ni idan bata yi wasa ba ma sai na daina kulata akansa wallah”. Gwaggo ta wurgo min daƙuwa tana faɗin,"ungo wannan, nace ungo, yau naji Mace, ke anya ma kuwa da kike je wurin shi bai shafa maki haukan ba, wannan wace irin macece ke, wai ke baki san duniya ta lalace haka ba, waye ke yadda da irin su musamman ma masu zama cikin kango, wannan waya san adadin yaran daya lalata daya fake a cikin nan, kar na sa ke jin wannan maganar a bakinki, kar in kuma jin kin amabace shi da sunan Yaya’n ki balle damuwa akansa...ince ko kin jini da kunnen fahimta?”. na muskuta gefe guda, ji nake kamar nayi kuka da kalaman Gwaggo, ƙasan zuciyata tuni yayi baƙi tana bugawa da sauri da sauri kamar zata fito waje. Bance da Gwaggo komai ba na Miƙe haɗe da buga ƙafa a ƙasa na bar wurin, ta biyo ni da faɗin, “ai ba ki buga ƙafar da kyau ba, da kinyi yanda zan shaida kin zama mara kunya, sai na san ta inda zan karɓeta". da faɗin hakan ta miƙe ta nufi inda wutar gawayi take ta zuba kuɓewar, kana ta shiga toilet dake tsakar gidan don ɗora alwalar magriba. ni kam shigewa ɗaki nayi na faɗa kan gado ina kukan irin cin zarafin da Gwaggo tayiwa Yaya, yau da ace ba Gwaggo bace ta faɗa haka da ko waye mun rabu da shi kenan. Washe gari da Safe kuwa ina gama ayyukan gida nace da Gwaggo zanje gidan su Farhana, bata yi yunƙurin hanani ba, sai ma ɗumamen tuwo data zuba a plask tace na kaiwa Hajiyar Farhana saboda ta san tana son ɗumamen tuwo. fitowana na tari mai napep, tunda na hau ko passenger bai ɗauka ba har muka isa ƙofar gidansu Farhana, na fito na ba shi kuɗin shi na shiga gidan. A parlon gidan na iske su duk, suna ta hira gwanin burgewa, gaishe da su nayi har yayunta Maza suka amsa suna min tsiya. na miƙa plask ɗin hannuna gaban Mamansu ina cewa,“Hajiya gashi inji Gwaggo tace na kawo maki”. Hajiya ta amsa tana murmushi ta buɗe, ƙamshin ɗumamen ya daki hancin Hajiya har da lumshe ido tana faɗin, “kaii Masha Allah, kuma kamar kin san yanzu nake cema Farhana ta kiraki ko Gwaggo tuwo tayi yau ashe kuwa shi ɗinne, kaii madalla nagode ƙwarai Allah yayi albarka”. na amsa da Amin sannan muka haura sama nida Farhana inda ɗakinta yake. kamar bani nai fushi da ita ba jiya, itanma kaman ba itane ta shareni ba, tunda muka zauna hira kawai muke zubawa ba ƙaƙƙautawa, sai ma can da ta lura ne kaman hankalina ya rabu gida biyu ta ke faɗin, "wai wani abunne kuma?”. na girgiza mata kai, ta ƙara cewa,"to sai ki bani complete attention ɗinki dan ban iya ta magana alhalin ba sanin me nake cewa kike ba". sai na ɗan yamutsa fuska nace,"ke ni yanzu ma zan wuce, amma tukunnama me kuka dafa yanzu?”. tana hararata tace,"ban sa ni ba. wannan wanne irin kuturun wulaƙanci ne, muna hirarmu me daɗi kawai kice za ki tafi. hala fushin da kike da ni ne har yanzu bai baki daina ba?". "dilla ni ba haka bane, kawai dai ina so zan tafi ne. idan ban bar fushi dake ba ai ba za ki kalla ma nazo ba". "to amma daga zuwa sai tafiya abinda ba ki taɓa ba, to ina ma zaki je wai wanda ban sani ba?, dan dai ba za ki zo ki wuce gida da wuri haka sanin cewar za kisha tambaya gun Gwaggo". naja tsaki cikin ƙosawa nace,"ke dilla Malama ni ina tambayanki me kuka dafa kina wani tsareni da tambayoyinki kamar kin kama me laifi, na faɗa maki bana son irin haka, idan kuma abincinne ba za ki banba ki faɗa min na sa ni, daɗin abun gidanmu ma akwai". duba da yanda raina ya ɓaci kuma nake magana a hasale yasa tace,"ahh ba rami me ya kawo zancen rami?, kinga ni ba baƙuwar zafi bace Allah ba ki haƙuri. indai abinci ne irish potato ne da ƙwai, kawo maki zanyi ko da kanki zaki zubo tunda Allah yasa kin san inda yake?". na kuma jifanta da harara, ban saki fuskata ba sai ƙara ɗaureta da nai, na miƙe ina cewa,"muje kitchen ɗin". itama kuma sai ta ɓata tata fuskar, tai kicin-kicin da ita har muka sauko muka shiga kitchen, kuma da yake zuciyar kowa a wuya take ko Hajiya dake mana magana ma bamu saurara ba muka shige Kitchen, na ƙarasa drowern dana hangi ƙaton cooler ɗinsu da anan ake zuba abinci, ita kuma ta tsaya gefe tana kallona, ƙaramin plask na ɗakko na zuba dankalin da ƙwan a ciki, na samu wani plask na tea ƙarami bayan na haɗa tea ɗin na zuba a ciki sannan na dubi Farhana nace,"muje ki raka ni". tana dubana da mamaki tace,"gida ko ina? ban fahimce ki ba, cin abincin ne ba zakiyi anan ba ko me?”. na ƙara jan ɗogon tsaki saboda tana neman ta ɓata min lokaci da wannan shegiyar tambayar tata. "kinga Gwaggo Farhana, wannan abincin ban zuba dan cikina yaci ba...so rakiya zaki yi min, idan baza ki raka ni ba sai na tafi ni ɗaya ba komai bane ai tunda ni ba makauniya bace balle tafiyata ta zama dole saida ɗan jagora". na faɗa ina bin gefenta zan fice, sai tayi saurin kamo hannuna tana faɗin,"daɗina da ke kenan, babu baya ni sai saurin fushi. kin shigo da damuwa tare dake, ke biki yi min bayani ba sai neman sauke fushinki kike akaina...ina zamuje dama?”. "anguwa”. na bata amsa a taƙaice. tai ɗan jim tana min kallon tsanaki, sai da ta gama nazartata tsaf tukunna tace,"wurin mahaukacin jiya zamu koma?". tayi tambayar da rainin hankali. a ƙufule kuwa nace da ita,"kin faɗa sau biyu kenan, karki gigin ƙara jingina shi da wannan mummunar kalmar a karo na uku, ina faɗa miki ne dan kinji da kyau. Farhana mamaita kalmar can daidai ta ke da yankewar alaƙar dake tsakaninmu, i dont fucking care dan mun rabu". ina faman huci nasa kai zan fita taƙi matsawa,"ki ban hanya zan wuce. ina ce kince ba ki rakani ko. kinga ki daina ganin kamar idan babu ke ba zan iya tafiyar nan ba, nasan hanya sarai, so da ace jagora za ki min sai na tsaya ki gama faɗa min baƙaƙen maganganunki...kinga tafiyana". ina kaiwa nan na tureta na fita, ta ƙofar baya nabi yadda Hajiyarsu ba zata ganni ba. nayi sa'a yanda nake saurin nan ina fita na sami napep, Allah ya taimaka bai tsawwala min kuɗi ba, dama ba isashshen kuɗi ke garen ba, shi yasa ma nace Farhana tazo muje tunda ita a motarta ne. ina sauka daga napep ɗin na nufi cikin bolar, kai tsaye kuma cikin kangon na faɗa, a tunanina zan ganshi amma sai ban ganshi ba, na fito ina ƙara dudduba bakin bolar da gefe da duk inda dai idona idan ya wurga zaiga mutum, amma sam babu shi, sai naji wani abu mara daɗi na bin jikina, na koma cikin kangon na aje basket ɗin abincin na fito ina ƙara dube-dube. ta hannun haguna na gange shi can ƙarshen bolar kwance shame-shame, da sauri na nufi wajen, ina zuwa ban kula da komai ba na durƙushe a wurin na rarumo shi jikina ina faɗin, "subhanallah! Yaya meye sa kazo nan ka kwanta, baka da lafiya?". na tambaya duk a ruɗe ina taɓa kansa, amma babu zafi. "Yaya tashi mu bar nan dan Allah". Kallona kawai yake yi, yayinda ko leɓan shi bai samu damar furta kalma ɗaya ba, yayi min nauyi amma a hakan nake ƙoƙarin ganin na janyo shi da iya ƙarfina, sai dai sam na kasa, kuma ganin hakanne yasa shi miƙewa zaune kafin ya dubeni da kyau yace,"tashi”. muryarsa na fitowa da kaifi kamar na reza. na miƙe lokacin da idona ya cika tapp da ruwan hawaye, sannan shima ya miƙe, nai saurin kama shi ganin kamar zai faɗi, kayan jikinsa duk wari suke amma wannan sam bai dameni ba, haka nake kamashi ajikina bana ko lura da ɓacin da kayana zasu yi da najasar wurin. ya ƙwace a jikina yana cewa,"bar nan wurin". ƙwayar idonsa ce ta shaida min baya so ya ƙara maimaita min, hakan yasa naja da baya har na sauka daga saman bolar, tukunna naga ya fara takowa a hankali har ya sauko daga kan bolar shima, bai ko kalleni ba ya wuce ya shige cikin kangon, ganin haka yasa nima nabi shi na shiga ciki. A ƙasa na same shi zaune, nima na samu wuri na zauna ina duban shi kafin na furta, “Yaya baka da lafiya?...au ina kwana". bai amsa ba, sai ido daya kafe ni da shi yana nazarin rashin hankali irin nawa, tsawon wasu daƙiƙu kaina yana ƙasa na jiyo muryar shi na fita da faɗin, “Sabina ko?”. nai saurin ɗago kaina, “eh” .na bashi amsa. sai kuma muryarsa tayi ƙasa, "me yasa kika dawo inda nake?, wai meye sa baki da tsoro ne?, ke bari kiji na faɗa maki, nifa ɗan iska ne, ɗan yan kan kai ne, ina yanke kan mutane na kai ayi tsafi dasu, ki daina zuwa wuri na idan ba ki son na yanke kanki, ko nayi maki fyaɗe, dan duk na saba yinsu”. abunda zance a wannan lokacin maganarsa ta bani nishaɗi, furuci ne da ko kusa baiyi kama da shi ba, ya faɗa ne kawai dan ya tsoratani, dan da ƙyar ma ya dinga haɗo kalmomin. na saki ƴar ƙaramar dariya ina faɗin. “Yaya ai babu mai yiwa bawa wani abu fa ce abinda Allah ya rubuta zai sa me shi, kuma idan kai ɗan yankan kai ne, ai da baka zauna a haka ba, da baka zauna anan ba, da tuni kana da dukiya mai yawa kamar yadda masu yi suke da ita, ni bana jin tsoronka, hasali ma sai ƙaunarka da nake yi. tun jiya dana ganka zuciyata ke faɗa min ko me zaka yi min kar na rabu da kai, tana faɗa min akwai wani abu da zai kasance a tsakaninmu, tana faɗa min kai mutumin kirki ne, tana faɗa min an halicceni ne domin na tambayeka...so ka bar tsorata ni, ni bana tsoron kowa da komai saboda ina tare da Allah. yanzu dai ga abinci nan kaci mu tafi gida”. Kanshi ya kai duba ga plask ɗin da nake turawa gabansa. “Bana ci, ki ɗauka ki tafi, idan baki so nayi maki fyaɗe”. "banda lokacin ɓatawa". abunda nace da shi kenan ina buɗe jaka na ɗakko pure water, na miƙe na isa har gaban shi tukunna na kama hannunshi na wanke mishi, shi ko sai bina yake da ido yana ganin ikon Allah, sai dana wanke masa duka biyun sannan na buɗe plask ɗin na saka mishi a gabansa, na ɗakko kofi na zuba tea shima ta ajiye a gabansa ina faɗin, “Oya Yaya kaci mu tafi gida”. shi dai yayi shiru na zame masa abar kallo, zuciyarsa na cika da al'ajabina. ni kuwa ganin baida niyyan ci yasa na ɗauki tea cup ɗin na nufi bakinsa ina faɗin,"haaa". sai kawai ya koma kamar ɗa me biyayya ga uwarsa, babu musu ya buɗe baki ba tare da yasan ya buɗe ba, na saka mashi dankali da ƙwan ya taune ya haɗiye sannan na bashi tea ya kora. haka na dinƙa feeding nasa yana ci, ci sosai, kuma duk wannan bashi ɗin da nake ina jin yanda idonsa yake akaina, ni kam cin abincin da yake sai naji kamar ina tare da wata matsala me a rayuwata amma ta akan hakan ta yaye. har saida ya cinye irish ɗin nan tass baima sa ni ba, sai ji yay ina goge masa baki ina faɗin,"yauwa Yaya Nah ko kaifa...yanzun idan ka huta sai mu tafi gida ko?”. Tsaye ya miƙe da yanayi na fusata yace,"ba zan iya zama da mutum mara yadda ba, Sabina fice anan, ki fice anan wurin kamin nayi miki abinda har ki mutu ba zaki bar kuka ba. Kuma daga yau kar na ƙara ganinki anan na faɗa miki wannan". Ya faɗa a tsawace yana nuna min hanyar fita. Kallonsa na tsaya yi a lokacin da idanuna suka kawo ruwa, sannan na duƙa ƙasa na kwashi kwanukan abincin, zuciyata sam-sam ba daɗi, na fita na bar kangon ina mai waigen shi, maganganunsa na min yawo acikin kaina. Sai bayan fitowana tukunna ruwan hawayen da suka gama cika idona suka sami damar zuba, na sanya gefen hijabina na goge, sannan na saita kaina naci gaba da tafiya. shi kuwa tana fita ya sauke dogon numfashi, idonsa a rufe ya nemi wuri ya zauna yana mai jin ransa da zuciyarsa duk babu daɗi. to amma ya zaiyi, ita macece, yanzu idan tana zuwa wurinsa sai ta ɓaci a idon mutane, a dinƙa yi mata irin wannan kallon da akeyi masa, kuma ya tabbata iyayenta suka san da hakan zasu iya saɓa mata, kuma kamar yanda ta faɗa ne, shi ba macuci bane dan haka ba zai taɓa iya cutar da ita ba. hasalima abu guda ɗaya ne yake nan, Allah ya sani, yana so ya dinƙa kasancewa da yarinyar ko da ba koda yaushe ba ne...bai yi tunanin zata kuma dawowa wajensa ba, amma ya tashi da tunaninta a yau. sai ya rumtse ido ya shafo sumar kansa yana fesar da iskar baki, wanda hakan ke ɗabi'arsa ce, kamin nan ya nemi waje ya zauna yana bin wurin da ta zauna da kallo, inda hoton zamanta a wurin ke haska masa cikin ido, maganganunta masu taushi kuma na yawo cikin kansa. #Vote. #Comment. #Mikiyawriters.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(4)* hidimar aikace-aikace nake tayi tun wayewar gari, yau babu inda ban gyara ba acikin gidan nan lungu da saƙo, hakan yasa ɗan ƙaramin gidan namu ya sake yin fayau da shi yay ƙal-ƙal, haka nake sam bani da ƙiwar aiki, Gwaggo na yawan faɗa min Mamana na gada, amma duk wata bauta da nake yi a gidan nan Yaya Abba baya ganinta dai-dai da misƙala zarratan. wuyarta nayi wuyarta ya ɓata kuma ya kushe, wani binma idan ya ɓata yay ficewarsa nai zuciya nace ba zan gyara ba, to bala'i ko sai dai idan bai dawo gidan ba, amma sai ya sauke min shi, ya dinga cewa Gwaggo wai tana sangartani, zan lalace na zama ƙazama. Gwaggo tace masa to ubanwa ke faɗawa idan na gyara, ta hakanne kawai nake samun salama, amma ni kaina na san banda ciki guda muka fito da shi la shakka ba zan ke raga masa ba, ina da haƙuri dai-dai gwargwado amma ba kanwar lasa bace. kiran sallar azahar ɗin dana jiyo yasa na shiga sauri-sauri na kammala aikin kamin lokacin tafiya islamiya yayi, dan lokaci babu wuya yanzu agogo ya buga ƙarfe uku, dama da safe naji Gwaggo na cewa da Yaya Abba ya saka mata sabon batiri a agogonta, agogon me shegiyar ƙara da zarar cikar daidai yayi zai kama kiɗinsa me hawar min kai. Gwaggo ta fito zata shiga banɗaki tace da ni, "Sabina sannu da aiki". na amsa, "yauwa Gwaggo, kin fito alwalar ne, bari na zuba miki ruwan". Ɗaya daga cikin botikan dake nan tsakar gida na buɗe na zuba ruwa cikin buta kana na bawa Gwaggo. Alwala Gwaggo tayi ta koma ɗaki domin ta gabatar da sallar azahar. Idarwarta kenan sai ga sallaman Baba, ɗakin ya shigo inda ya zauna nan bisa kujera yana gaida ita. na shigo a lokacin na durƙusa na gaida shi tare da ajiye masa ruwa da abincin dana kawo mishi. bayan ya amasa min yace,"Yau ba makaranta ne?". nace, "a'a da akwai, ai da sauran lokaci. Amma yanzu ma zan shirya da mun gama cin abinci". "to madallah. Ana dai dagewa ko?". "ehhh Baba muna yi sosai". Fuskar Baban ta washe da fara'a yace, "Allah ya bada nasara, ya kuma yi muku albarka...ai ba'a bina kuɗin makaranta ko?". Ya faɗa a yayinda yake zuba ruwa a cup zai sha. "amin amin Baba na gode. ehh ba'a binka". na miƙe naje na ɗauko namu abincin ni da Gwaggo, ina cin abincin ina satar kallon mahaifina da nake jinsa mafi soyuwa a gareni. kusan tare muka cinye abincin da shi, saboda muna ci ana hira, nan da nan muka tashi kan shinkafa da waken daya ji haɗin kayan lambu. na tashi na haɗa kan kwanukan da muka ɓata na kai kitchen, na dawo na gyara wurin duk da ba wani ɓata shi muka yi ba, sannan na wuce zuwa ɗakinmu da muke kwana ni da Gwaggo. nai wanka na shirya cikin uniform ɗina na islamiya milk colour, kayan sun mun kyau sosai, jakar littafaina na ɗauka na rataya kana na fito nace da Gwaggo da Baba zan tafi. a gaban Baba na duƙa ina cewa da shi, "Baba kayi mani adu'a". Ya dubeni cike da soyayyar uba ga ƴarsa sannan ya ɗora hannunsa saman kaina yace, "Sabina Adu'a ta zama dole, kije Allah yay maki albarka, ya baki masara a rayuwarki. Allah ya kaiki lafiya ya dawo dake lapia ya kareku a duk inda kuke". ina murmushi nake amsa mishi da,"amin Baba nah na gode sosai, Allah ya ƙara maka lafiya da nisan kwana". Gwaggo ma tayo tata adu'a sannan na fita, Har naje soro sai kuma na dawo, saboda tunawa da nai akwai inda nake son zuwa kuma banda kuɗin mota, satina guda kenan rabon dana fita waje, dama inda makarantar boko ne nake ɗan samun canji a hannuna, to anyi hutu, itama kuma islamiyar sai yaune muke komawa. to yanda na ƙwallafa rai da zuwa inda nake so naje yau ai yacce Baba ya shigo dole na nemi kuɗi. ganin na dawo Baba ya shiga tambayana me ya dawo dani, ni kuma kai tsaye nai masa ƙaryar zan siya littafi ne na manta ban karɓi kuɗin ba. na faɗa masa ina tsoron kar yace babu kuɗin a hannunsa amma naje zai shigo makarantar anjima yaywa Malam Saminu magana su bada bashi kaman yanda aka saba. Allah ya taimakeni sai naji kawai yana tambayana nawa ne kuɗin, da yake ban saba da ƙarya irin haka ba sai na rasa nawa zance, na tsaya ina kame-kamen kamar 200 kamar 150, sai kawai ya zaro 500 ya bani yace na riƙe canjin idan yayi saura, na kuwa amsa murna fal raina inata zabga masa adu'a. shima kuma ya shiga yi min adu'ar Allah ya jiƙan mahaifiyata ya haɗani da miji na gari. ko da naje islamiya bayan an gama yi mana ƙarin karatun ƙur'ani mu ƴan manyan aji, sai aka kiramu aka rarraba mu zuwa sauran ajujuwa domin kula da yara sakamakon Malamai zasu shiga meeting. Sai biyar da rabi kana Malamai suka gama meeting, kuma a ciki ne har aka tattauna akan cewar za'a ɗauke ni gasar musabaƙar qur'ani ta ƙasa domin na wakilci makaranta kasancewata gwarzuwa. A lokacin da Malamai suka dawo daga meeting muka koma zuwa ajinmu, ina zaune Malam Hussain ya kira ni, nan ya sanar min abinda hukumar makaranta ta tattauna akaina na ga me da zuwa musabaqa, saboda haka saina sanar da iyayena idan zasu bani damar zuwa, kuma duk da hakan suna da buƙatar ganin mahaifina ko kuma wani babba a gidanmu. ina ta murna da farinciki na miƙe daɗi duk ya isheni, dan ni kaina ina alfahari da baiwar ilimin da Allah ya ban. Ƙarfe shida aka tashemu, a bakin gate ɗin makaranta na sami Farhana tsaye tana jirana, ƙirjina rungume da qur'ani na ƙaraso inda take, nan muka jera muka fara tafiya. shiru shiru babu wanda yay magana acikinmu tsawon tafiyar da mukai, kamar bamu ɗin nan da bama rabo da abin faɗa ba idan muka haɗu, hasalima idan aka tashi muka taho bamu da aikinyi sai gulmar Malam wane da wane. can dai Farhana da bata iya haƙura da yin shiru ta nisa cikin ƴar murya tace,"Ƙawata wai lafiya naga kwana biyu kina sha re ni, laifin me nayi miki ban sani ba ƙawalli?". ta faɗa tana dafa kafaɗa ni kuma ina zamewa, fuskar nan tawa na ƙara cukuleta dan sarai na san ta san dalilin ɗauke mata wutar da nai, amma saboda rainin wayo da neman magana take tambayana. dan haka nima saina raina mata nawa wayon da cewa, "ba komai, me kika kalla dama?". nayi mata tambayar kaina na gaba ina tafiya cikin sauri-sauri. ta ƙara cewa,"aikam dai da wani abu, domin ba haka muke da ke ba, amma a ƴan kwanakin nan duk kin wani sauya min". kaman zance mata a'a ko nayi mata shiru, sai na tuna da maganar malaminmu da yake cewa mutumin daya fi kowa shine wanda idan mutum yay masa ba zai ƙullace shi ba, zai samesa ya faɗa masa wane kayi min abu kaza da banji daɗinsa dan Allah karka sake, amma duk wanda zai ƙullaci mutum akan yay masa laifi ya riƙe abin a ransa yaƙi faɗa maka, ko kun haɗu a zuciyarsa zai gaisa da kaine ta dole yay maka yaƙe to wannan mugun mutum ne, ni kuwa bana so na kasance cikin mugwayen mutane. dan haka na ɗan waigo nai mata kallo ɗaya sannan na ɗauke kaina nace,"Farhana ba magana ta wasa ba, da gaske nake faɗa miki bana jin daɗin aibanta min Yaya da kike ko kaɗan, bana so kike faɗan mummunar kalma akansa, ki daina walaƙanta min shi a wajen mutane, idan kene na yiwa Yayanki haka zaki ji daɗi ne?". nayi maganar raina a matuƙar ɓace, sai tayi saurin dafe ƙirji tana faɗin, "ni ko ina na isa na yiwa Yaya Abba haka, rufa ni ki saya". ta faɗa tana nuna kamar bata gane inda maganata ta dosa ba. na jijjiga kai nace, "nasan kin san akan wanda nake magana, amma saboda kina so ki mayar dani ƙaramar ƴar iska shine zaki nuna wani waskewa ko". nai maganar dai-dai lokacin da muka ƙaraso inda motarta ke ajiye, kuma kamin ta buɗi baki tace wani abu sai kawai gani tai na wuce gaba abina, ina jinta tana jera min kira nai mata shiru ban tsaya sauraronta ba, dan banda lokacinta. sai gata ta tsaya da motar a gabana tare da zuge glass ta min magana. "Sabina wai mene kike yi haka don Allah, ya wani banza can zai ƙoƙarin rusa abotar mu tun ta yarinta...". Maganarta ta katse a lokacin dana juya ina cewa da ita cikin masifa,"Malama shi ba banza ba ne, ki fito kai tsaye ni ki kirani da banza tunda ni na shiga rayuwarsa. Kuma karki damu da tafiyata a cikin motarki domin nima ina da ƙafa, dama ban saba da ita ba saboda ban ganta a gidanmu ba. Kije kawai abinki". Daga haka na wuce nayi tafiyata, raina duk a dagule na shiga gida, saboda na gama tsara bayan an tashi makaranta zanje wurin Yaya domin ganin lafiyarsa, tun wancan ranar da yay min gargaɗin kar na ƙara zuwa ban koma ba yau gashi kwana takwas kenan, sai dai hankalina da tunanina duka na kansa, ga yau ɗin dana ƙwallafa rai da zuwa lokaci yay halinsa dan magriba tayi, ga itama Farhana ta ƙara ɓata mani rai, shi yasa duk kaina ya cunkushe. ina ɗaga labule nayi sallama cikin parlo, lokacin Gwaggo na zaman tahiyar ƙarshe na sallar magriba da ake, bayan ta idar da adu'ointa ta juyo tana kallona da yanda nake ta faman ɗacin rai. ta gefen ido na kalla Gwaggo na girgiza kai alamu na Allah ya kyauta kana tace min, "saboda kina fushi ba za ki yi sallar ba kenan ko mene uwar ƴan nurƙufanci". "ina hutu ne". na bata amsa a taƙaice. "to tashi ki ɗauko mana tourchlight a ɗaki, ga battery can kan abun tv ki saka na ciki yayi sanyi". na miƙe naje na ɗauko na kunna haske, sannan na koma kan kujera na zauna, ko uniform ban iya cirewa ba kuma banda niyyar zan cire, sai faman kumbure-kumbure kawai nake. Gwaggo dake ankare dani tai min banza bata bi ta kaina ba, Taci gaba da harkar abinda ke gabanta, can data gaji da ƙwafar da nake jerawa babu ƙaƙƙautawa ta juyo ta wurgo min harara da cewar,"ke wai ƙalau ki ke kuwa, kinzo kin sani gaba kina ta aikin ƙwafa, ko sallama ma fa ina jinki a ciki kika yi ta. Sabina bafa zan ɗauki wannan sabon halin naki ba, ke da waye a makarantar?". ina aikin tsuke baki nace, "ba Farhana ba ce". Gwaggo tayi tsaki tace, "Allah ya gyara ki idan kina da rabon gyaruwa, tun kuna cin ƙasa rabonku da yin faɗa ke da ita amma saboda mahaukacin yaron nan kina son zama fitinanniya ko Sabina. To wallah tun wuri ki shiga hankalinki, ki fita a sabgarsa tunda kinji dai yanda yake, amma zan gyara miki zama ne karki dawo kan layi ki gani". sai kawai na hau bori ina dukan ƙafa a ƙasa kamar zan fashe da kuka. "na rantse da Allah Gwaggo shi ba mahaukaci ba ne kuma ba ɗan iska bane, wallahi da gaske nake miki da kin kalle shi kinga mutumin kirki, sam bai ma yi kama da ƴan daba ba, kawai tsintar kansa a cikin ƙangi na rayuwa yasa ya jefa kansa cikin wannan yanayi, shine ita kuma Farhana saboda rashin sanin daraja ta ɗan Adam ta ke cewa mahaukaci ne. Amma wallah ba shi ba ne, kallo ɗaya zaki yiwa yanayinsa ki gane, kuma ma ai yace min ba zai kuma shan taba ba". baki buɗe tace, "au ya tabbata lahu dai ɗan daba ne kenan, to ai gwara da kika faɗa da kanki na ji. To bari kiji ko ki fita harkarsa ki manta da shi ko kuma na haɗaki da ubanki, tunda ni yanzu ban isa na faɗa kiji ba, zamanin na faɗa miki kiji ya jima da shuɗewa tun ba ki balaga ba". na sakko daga kan kujerar na dawo kusa da Gwaggo na zauna, na kamo hannunta ina cewa,"kiyi haƙuri Gwaggo nah, ba wai bana jin maganarki ba ne. Allah Gwaggo kika kalla bawan Allah'n nan sai kin tausaya masa, har kuka sai kin yi mishi wallahi, kuma ke da kanki za kiji kina son taimaka mishi". "mtswwww". Gwaggo taja tsaki tana watsa min harara tare da ƙwace hannunta. "tashi ki ɓace min anan wurin ko ranki ya ɓaci...insha'Allahu zan kaiki masallaci ai miki sauka". saina miƙe ina faman yarfar da hannu na wuce ɗaki, na kwanta kan katifa nai shiru ina mai jin raina duk babu daɗi, ni kaina na rasa dalilin damuwa da mutumin da ban san wane shi ba, haka kawai nake jin tsananin tausayinsa da son taimaka mishi, har sanda bacci ya fara ɗaukana, sai dai wani abu na ban mamaki dana rufe ido saina dinga ganin hoton fuskarsa na bayyanar min. Washegari ya kasance Asabar, ƙarfe 9 na shirya domin tafiya Tahfeez, ina yiwa Gwaggo Sallama sai ga sallamar Farhana, ɗauke kai nayi daga kallonta a lokacin data ke shigowa, itama bata kula ba ta duƙa tana gaida Gwaggo. Gwaggo tace da ita, "ya haƙuri da halin ƙawarki duk da nasan kina yi. amma yanzu lamarinta ƙara ta'azzara yake sai an kai zuciya nesa zama da ita...kin ganta nan tun jiya rabonta da min magana, gaisuwarma yau ko samu banyi ba, ni kuwa tunda Ubanta dai yazo ya gaisheni tata ba abar damuwa bace". Farhana tayi murmushi Kawai ta miƙe a tsugune tana dubana tace, "mu tafi ko". na ɗan harare ta gami da murguɗa mata baki kana nace, "ni ai bance ki biyo min ba. Kiyi tafiyanki kawai". Gwaggo ta rarumi mafici zata ƙwalo min nai saurin miƙewa na fice. "ƴar ƙwal uba da ki zauna mana. Farhana indai tayi wani shirmen ki faɗa min dai-dai nke da ita". Farhana na dariya ta amsa da, "to". tunda muka shiga mota babu wanda ya kula ɗan'uwansa, sai da muka kusa zuwa makaranta ta kama ce min. "wai ke don Allah mene na damuwa da wannan mahaukacin, ɗan daba kawai, ɗan iska wanda bakin uwa yay tasiri akansa, haka kawai yazo zai sanya min ƙawa a damuwa, ni Allah da ace nasan haka zata faru da bamu je amso ɗinkin ba a ranar". na juyo na harareta ace, "ni ina mamakin rashin imaninki Farhana. Duk wanda yaga wannan bawan Allah'n sai yaji tausayinsa, amma ke na rasa dalilin bushewar zuciyarki akansa. kuma kina ta bada shaidar zirrr akansa kina ganin kaman burgewa kike, to tunda Allah yasa islamiya za kije kya tambayi Malami makomar irinku". "irinmu? makomarmu ta me?". "kice Malam Ali mene makomar masu shaidar zirr zai baki amsa". "Sabina zirr fa shaidar ƙarya kenan". "to me kike yi banda ita?". sai tai guntun murmushi tana cewa, "To ni dai tausayinsa ne ba zanji ba, kuma abunda na gani da shi zanyi shaida, mutumin da baya jin tausayin kansa kan me kuma kai zaka tausaya masa. Ai sarai yasan shaye-shayen da yake cutarwa ne a gare shi amma yake yi. Shege ɗan iskan banza kawai". ban san lokacin dana kai hannu na daki stearing motar ba har ina ƙoƙarin ƙwace shi daga hannunta, tai ƙarfin riƙewa da kyau tana tureni. na ɗaga murya cikin masifa nake ce mata, "Farhana na faɗa miki babu kyau aibata musulmi ko da ya kasance yana aikata mummunan halaye bai kamata aibata shi ba. Farhana na roƙe ki karki ƙara furta mummunar kalma akan Yaya, idan ba za ki iya masa adu'ar shiriya ba don Allah kiyi shiru da bakinki akansa...karki ga ina roƙonki, na rantse miki gaba ba zata mana daɗi dake ba". na ƙara maganar ina jan ƙwafa. ita dai ta min shiru bata ce komai ba, domin ta lura akan wannan banzan mutumin zamu iya ɓaɓewa ta har abada. kuma har muka isa makaranta ban bar surfa mata masifa da bala'i ba. kuma ci kanki bata ce min ba sai ma earpice data maƙala a kunne naci gaba da haushina ni ɗaya, aiko sai dana tsinka shi. Ƙarfe 2 aka tashemu a makaranta, maimakon nai gida saina tari napep nace ya kaina sharaɗa, ban ko bari mun haɗu da Farhana ba dan Malam na fita na fito kasancewar bamu zauna sit guda da ita ba. Dai-dai kan layi nace mai nepep ɗin ya saukeni, na ciro kuɗinsa a jaka na bashi, ina yankowa wajen bolar kuwa na hange shi a bakin wani tanki ya kunna famfo ya duƙa yana shan ruwa, yauma dai jikinsa fes yana sanye da yadin dana ganshi tun a ranar farko, da alama dai siturarsa ɗaya ce, sai Allah masanin lokacin da yake cirewa ya wanke su. yana gama shan ruwan kuma ya koma can inda ya ke zama ya zauna, da zamansa ya zaro taba sigari cikin aljihu ya kunna ya fara zuƙa. haka kawai sai naji zuciyata tayi matsewar da bata taɓa yi ba, sam-sam bana ƙaunar ganinsa da wannan sigarin ban san me yasa ba, sai naji ƙafafuna na saurin tafiyar da zance basu taɓa yi ba har na ƙarasa gare shi. kansa na duƙe kamar yanda ya saba idan zai sha, ina isa na zare sigarin daga hannunsa a hankali na jefar, fuskana a haɗe. abunda ban sani ba tun ɗazu ya hangeni sai dai baiyi tunanin ni bace kasancewar niƙab ne lulluɓe a fuskata, sai yanzu dana zo na ƙwace masa sigari ya gane ni ɗince shi yasa ya kawar da kansa. yanzu na riga na saba da wajen da yake rayuwarsa, bana jin ƙyanƙyami ko kaɗan, warin sigarin ma yanzu na saba da shi, na naɗe hijab ɗina na durƙusa a gabansa dai-dai saitin inda fuskarsa take. sai ya sake ɗauke kansa ya maida ɗayan gefen, nai murmushi na ɗaga niƙab ɗina ina sunkuyar da kai na leƙa fukarsa nace, "Yaya ni ce fa, fushin na menene? ƙanwarka ce fa Sabina ka juyo ka kalleni". bakinsa ya motsa a hankali kamar ba maganar zaiyi ba yace,"na san kece ai". sai na ɗan shagwaɓe murya ina faɗin,"to amma shine kake ɗauke kai daga gare ni". Yace,"bana kula mara jin magana ne". "Yaya rashin jin maganan me nayi kuma?". na faɗa ina ɗan marairaicewa. ya ɗago ya duben sau ɗaya wanda ya sanya shi jin faɗuwar gaba yace, "bana hanaki zuwa wurina ba, kina so na yi miki fyaɗe ko?". Da mamakin dake haskawa cikin ƙwayar idonsa na rashin tsorota da irin wannan furucina yasa ya tsareni da ido. sai nai siririyar dariyar data bayyanar da fafaren haƙorana kamin nan nace. "Yaya ba zaka fasa tsorata ni da wannan kalman na fyaɗe ba, haka ba zan fasa faɗa maka kai ɗin baka yi kama da macuci ba, kowa ya ganka yaga mutumin kirki, dan haka ka aje barazanarka a gefe". sai yace,"shi dama mugu yana da kama ne?". saina girgiza masa,"ko kusa, hasalima sai kake rayuwa da mugun mutum tare da kai ba tare daka sa ni ba...amma ko menene dai kai ba mugu bane". da ƙaramar murya naji ya kirayi sunana, "Sabina". na amsa, "na'am Yaya nah". "don Allah ki daina zuwa wurina, kar mutane suyi miki mummunar shaida irina, kinga ke ɗin halinki mai kyau ne". Na gyara zamana ina dubansa nace, "Yaya nah ni macece da bana mu'amala da wanda baya jin kunyar Allah, wanda yake saɓon Allah, amma yau gaka kai kuma ka tsaya min a rai, irin tsayawar da har na fara tsorata, ina tsananin tausayinka, hakan yasa na kasa barinka domin kai ɗin ina jinka ne tamkar jinina". Yace, "na gode da har kika iya fahimtata saɓanin mutane da yawa. Amma ni dai ina roƙonki da ki bar rayuwata". "Yaya bazan iya barinka ba a halin da kake ciki". Na faɗa ina zura hannuna cikin aljihunsa ba tare daya sani ba, sai a lokacin dana ɗauko kwalin sigari na nuna mishi ina cewa. "Yaya wannan hatsari ce ga rayuwarka. Kaji tsoron Allah ka daina shanta, Hakan da kake yi yana nuna cewar baka tsoron Allah ne, nasan cewar halin rayuwar daka tsinci kanka shi ya jefa ka cikin wannan halin, amma me yasa ba zaka amshi ƙaddarar da Allah ya jarabce ka da ita da hannu biyu ba? Bayan kasan cewar yarda da ƙaddara Mai kyau ko mara kyau suna cikin shika-shikan imani. Manzon Allah S.W.A yana cewa da ace zaka ciyar da kwatankwacin dutsen uhudu na zinare cikin ɗaukaka Addinin Allah, lallai ba zai karɓa daga gare ka ba har sai kayi imani da ƙaddara. Yaya nah don darajar Allah ina so daga yau kaji tsoron Allah ka daina saɓa mishi, ka nisanta kanka ga waccen abar mai cutarwa". sanda nai shiru na ɗago ina kallonsa, wanda idanunsa suka cika da ruwan hawaye a dai-dai lokacin kuma suka sami nasar zuba. Tausayinsa ya ƙara damƙar zuciyata, Allah kaɗai yasan wanne hali wannan bawa nasa ya shiga a rayuwa, a raina nayi adu'ar _Allah ka kawo mishi mafita._ Tunda ta fara magana ya kasa ɗauke idanunsa akanta, wani abu a ga me da ita na shiga zuciyarsa, tunaninsa ya katse sanda naci gaba da cewa,"Yaya nah zaka iya min alƙawarin daga yau ka daina shan sigari?". kamar wanda yake acikin tsoro da furgici sai yay saurin ɗaga min kai alamar ehhh. Murmushi na saki nace, "da gaske daga yau ba zaka kuma shan sigari ba?". amon muryarsa ya fito da faɗin, "Nayi miki alƙawari, Allah ya bani ikon cikawa". na lumshe ido na buɗe, har ga Allah sautin muryarsa na min daɗi shi yasa wani lokacin nake jan maganar da zai tilasta shi yay magana. ina dubansa da washewar murya nace,"Yaya idan har ka daina shan sigari zanji daɗi, amma fa ka sani duk ranar da na kuma ganin kana sha ina mai tabbatar maka da nima zanyi koyi da kai, dan sai na sha taba sigari naji wanne ɗanɗano kake ji a cikinta". abunda bai taɓa yi ba, yay Miskilin murmushi mai ɗan sauti wanda hakan yasa na buɗe ido ina dubansa, na ɗaga masa gira da faɗin,"murmushin na mene? kana tunanin ba zan iya ba?, ko kuma ce min da kai ba zaka ƙara ba yaudarata ne kayi?" "duk ba haka bane, ina so na koyi irin yanda fuskarki ta ke ne kullum cikin murmushi shiyasa na gwada, kuma sai naji ya haɗe da ciwon dake maƙale a zuciyata kenan yafi ƙarfina. yanzu dai Sabina tashi ki tafi gida". laɓɓana na motsawa na saka hannuna duka biyu a kumatunsa na talasu ina cewa,"indai ka saka a ranka cewar Allah zai maka magani to kullum wannan fuskar zata kasance a haka. ai ba abu ne mai wahala ba". yana ɗauke hannuna yace,"ni dai nace ki tashi ki wuce gida". "Kai Yaya daga zuwa na kuma sai ka kore ni, ni ai bamu gama hira da kai ba, kaga shi Yaya Abba baya bani lokacinsa kullum.yana wurin ball". yace, "aini ban iya hira ba, kuma kinga ke macece ya kamata ace kina cikin gida idan ba makaranta za kije ba. Gaki nan ma da alama makaranta za ki tafi". "a'a na dawo daga tahfeez ne yanzu sai dai ta ƙarfe huɗu". "to ki tashi ki tafi lokaci ya kusa". na miƙe ina gyara zaman jakata nace, "tom Yaya sai wataran?". Gani nayi shima ya miƙe yana zura hannu cikin aljihu, ya kalleni kaɗan yace, "ki ɗaura niƙab ɗinki mana". ina yamutsa fuska ina karayar da kai nace, "Yaya zafi akeyi ne yanzun, ɗazu ba zafi shi yasa na saka". "ki ɗaura don Allah, saboda kan hanya akwai mutane, idan kika je gida sai ki cire". ina marairace fuska nace,"Yaya Allah...". bai bari na ƙarasa maganata ba ya katseni da tashi,"ni dai don Allah". "tom shikenan na ɗaura". na faɗa a sanda na gama ɗaura niƙab ɗin, sannan nace da shi. "na tafi sai wataran". "muje na raka ki". ina kallonsa ta cikin niƙab ɗin zanyi magana ya tari numfashi da cewa,"bana son mutum me musu". Hakan yasa na fasa maganar da zanyi, nan muka jera tare muna tafiya. yau kam ya sake dani sosai, dan harda ce min wai na cika magana, nace masa ai kaima kana da surutun gashi nan tunda muka taho kana magana. sai ya tala laɓɓansa da cewa,"wannan ne karo na farko a rayuwata". "me yasa?". "saboda banda wanda zanke magana da shi". "har ƴan gidanku?". sai yay ɗan jim kamin ya gyaɗan kai, wani ciwo dake ƙasan zuciyarsa na nunawa a fuskarsa kamin yace,"na faɗa miki ban taso na ganni ina rayuwa a gidanmu ba. zuciyata ma faɗa min ta ke wataƙila daga sama na faɗo". ayau gam na gama gasgata shi da wannan furucin nasa, dan haka ɗaya naji zuciyata ta gamsu da shi ɗin. muka ci gaba tafiya ina bashi labarin zaɓata da akai acikin waɗanda zasu yi musabaqa a wannna shekarar. #Vote. #Comment. #Share. #mikiyawriters.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(5)* "Allah ya bada sa'a". abunda yace dani kenan, kuma har muka isko titi ba wanda ya ƙara magana cikinmu. ya faɗa min abunda bai taɓa yi ba iyakar tsayin rayuwarsa shine tsayar da mota ya hau, duk inda zaije ƙafarsa ke kai shi balle ma babu inda yake zuwa. ni kam na dage akan sai ya tsayar min, haka ya miƙa hannunsa na rawa ya tsaida me napep ɗin daya taro, daga hakan na yarda da maganarsa, dan kana kallon ma yanda yake tsayarwar da yanda yakewa mai napep ɗin magana zaka san frin shiga ne. "ɗan dakata Malam". yace da me napep ɗin sanda na shiga ciki na zauna shi kuma yana ƙoƙarin ja, sia ya tsare ni da ido yana kallona kamar ba zai ɗauke idonsa akaina ba. Yanayin kallon nasa yasa ni sadda kaina a ƙasa ina wasa da yatsun hannuna ina murmushi, ji nake kamar kar na tafi na barshi ko kuma kawai mu tafi tare, domin ina jinsa ne tamkar wani ɗan'uwana na jini. "Sabina". Ya kira sunana a hankali cikin zazzaƙar muryarsa. Ɗagowa nayi na dube shi tare da faɗin, "na'am Yayana". "kiyi haƙuri bani da kuɗin biya miki". Ina murmushi na gyaɗa masa kai, "karka damu Yayana, na gode". Yana kallon mai motar yace, "don Allah ka tuƙata a hankali, ka kula da ita amana ce na baka". Ya faɗa yana ɗauke hannunsa daga ƙarfen motar zai juya. nai saurin riƙo hannunsa da sauri ba tare dana sa ni ba, ya juyo yana kallona, nima ɗin kallonsa nake kaman zanyi kuka nace,"Yaya don Allah kazo muje gidanmu, bana son tafiya na barka anan". sai ya tala leɓensa da murmushi, a cikin magana ta rarrashi yace min, "kin kalla yanzu ai makaranta zaki je, ki bari sai kin dawo wataran sai mu tafi tare". Cike da murna da kuma zumuɗi nace, "da gaske Yayana?". Shi kansa ya lura da yanayin farincikin dana shiga, kansa ya jijjiga min alaman ehh da gasken yake. Sai kuma na kwaɓe fuska ina marairaicewa a hankali na furta, "to ai Yaya kace kar na kuma dawowa inda kake, idan ba haka ba zaka yi fushi dani". Idonsa naga ya ɗan rumtse ya buɗe ya zuba su akan hannuna dana riƙe nashi gam. Na lura so yake ya zare hannun nasa amma naƙi bashi damar hakan saboda riƙo na masa kamar wanda za'a ƙwace shi. "ya kamata ki tafi karki makara". Ya faɗa muryarsa a sanyaye. "tom shikenan yaushe zan kuma dawowa?". "a'a karki dawo don Allah, kinga ke macece mutuncin ki zai zube idan kina zuwa wurina, alhalin kuma mutane ga kallon da suke min". Na tari numfashinsa, "to ni ina ruwana, ai na san Yayana ba yanda suke tunani bane...". Ban kai ga ƙarasa faɗin Abinda zan faɗa ba naji yana kiciniyar cire hannunsa daga nawa, riƙewa na sake yi har ina ɗan cije leɓena, ganin naƙi sakar masa yasanya shi sunkuyo da kansa saitin fuskata, idonsa na kallon gefe guda yace, "ke ɗin ba muharramata bace, ni dake gaba ɗaya mun kai munzalin daya zama haramun wani ya taɓa wani, duk da ba lallai kina sanin lokacin da kike aikata hakan ba, amma riƙen hannu da kike saɓon Allah ne". Sai naji kunya ta rufeni, jikina kuma yay sanyi, zuciyata ta motsa, na kasa raba hannu na dana shi sai shine ya cire nasa. Ɗago idon da zanyi naga har ya tsallaka kwata, ido na zubawa bayansa ina jin kamar na fita na bishi, Allah ya sani ina tausayinsa kuma ina sonsa, irin son da nake ma Yaya Abba. gashi shi ɗin dai ba wani ba, ba kuma ɗan wani ba, amma yana da matuƙar burgewa, domin komai nasa me kyau ne, yanayin rayuwar daya tsinci kansa ne kawai ya maida shi wani kala, amma tabbas da ace shi ɗin a gidan gata ya fito, to lallai da anyi namijin gaske, nayi murmushi mai sanyi. na shiga duniyar tunanin ta ina zan iya taimaka masa, zuciyata na faɗa min taimakon da zan masa shine sada shi da ahalinsa, aina zan gansu? ta ina zan fara?, wani abu daya shigo ta cikin kaina ya wuce shi yasa na kulle ido tare da kwantar da kaina jikin kujera, Dai-dai lokacin kuma wata mata tai mani sallama na matsa ciki itama ta shigo ta zauna sannan napep ɗinmu yaci gaba da tafiya. A gadon ƙaya muka sauketa, daga nan kuma mai napep ɗin bai kuma ɗaukan kowa ba, ina jinsa yana ta mani surutu ni dai bance masa komai ba, kasancewata ba ma'abociyar magana da kowa ba, har muka isko ƙofar makarantarmu ya sauke ni, na bashi kuɗinsa ya tafi ni kuma na juya na shiga makaranta, Allah ya taimake ni kuwa ban makara ba. Ina shiga aji sai ga Farhana ta shigo, ashe taga lokacin da nake shigowa ta tagar ajinsu, kallo ɗaya na mata na ɗauke kaina akanta, nifa alallai fushi nake da ita tunda har ta ke aibata mun Yayana. Ta dafa kafaɗana tana ƙaramar dariya tace, "ƙawata wai ina kika je ne? Na biya maki ɗazun Gwaggo ke cewa ai baki dawo ba, sai nace ma ta ƙilan kin zauna bada hadda ne don bamu haɗu ba". "ummm". Shine abunda nace ma ta kawai ina maida kaina a window. "to daga ina kike?". "daga inda kika aike ni".Na bata amsa a taƙaice. Bata damu da sha re ta ɗin da nake ba ta kuma matsowa kusa dani, hannuna dake kan littafin ta dafa, ta fara mani magana cikin damuwa da kuma nuna kulawa. "Sabina tun muna ƙananun yara muke tare, mun riga mun zama tamkar ƴan'uwa, muna bawa junanmu shawara kuma mun zama sirrin juna. Shin mene yasa lokaci ɗaya wani zai sanya ki sauya daga yanda kike a gareni, kawai akan ina faɗan gaskiya...". "karki yaudari kanki da cewan kina faɗan gaskiya akansa, ko za ki Kawon hadisin daya ce ka aibata musulmi? Ina sauraron ki". Na faɗa idona tarr akanta. "babu". "to Kin san da cewan babu kenan amma kike taƙarƙarewa kullum kina aibata shi akan abunda baki da masaniya akai, ko kin san asalin rayuwarsa ne?". "ai ba wai ƙarya nayi ba. Zahiri fa na gani, don nace masa ɗan iska ko ɗan daba ai banyi ƙarya ba". "wallahi da ace kin san yanda nake jinsa a zuciyata ba za kike jifansa da waɗannan kalaman ba. Da kin san matsayinsa a wurina da tuni kin jima da rufe wannan dogon bakin na ki". Na faɗa ina kawadda da kaina bayan na jefeta da banzan kallo. Tayi wani munafikin murmushi sannan tace min, "wato Sabina idan banyi kuskuren hasashe ba son wannan ɗan wiwim kike ko?" .ta tambaye ni tana kafe ni da ido cike da rainin wayo. Tsaki naja ina faɗin, "Kinyi hauka ne hala? Taya za ki ce mani ina sonsa, To akan mene ma zan so shi? Kawai ban san shi ba ban san daga inda yake ba na wani kama sonsa, abunda na sani kawai shine ina tsananin tsausayinsa na kuma damu da shi". Murmushin rainin hankali ta ƙarayi tace, "to ai dama ke ba za ki gane ba, amma tuni kin faɗa a son wancan ɗan isakan, sai dai zan faɗa miki tun wuri ma idan haka ne karki bar abun ya girmama ki cire shi a zuciyanki domin ba zan taɓa yarda da hakan ba, tunda shi ɗin ba mutumin arziƙi bane". Sosai naji zafin maganarta a zuciyata, daurewa nayi na sha re ta ban saurare ta ba, sai ƙwafa da nake ƙasa-ƙasa. "kinsan Allah Sabina, idan har baki fita a harkan wannan ɗan shaye-shayen ba na rantse miki saina faɗawa Yaya Abba, wai akan mene zaki ke kai kanki inda baki dace da nan ba. Ke ni walla ma tsab zan iya ɗauko masa police su kamashi ai dama ɗan wiwi irinsa bai dace da zaman cikin anguwa ba". Nan ma shiru na mata ban tanka ta ba, haushin hakan yasa ta shiga zaginsa ta inda ta ke shiga bata nan ta ke fita ba. Babu zato babu tsammani taji na sauke mata zazzafan mari saman kuncinta. A zabure ta ɗago ido tana dubana da nake faman huci akanta. "tashi ki fita a ajin nan tunda bana ku bane". Na faɗa ina ma ta nuni da hanyar ƙofa. "ni kika mara Sabina? Akan wani banza ɗan iska wanda bakin uwa ya bishi kika mare ni?". Cakumar kwalar hijabinta na ƙarayi, raina a matuƙar ɓace nake dubanta, dukan mu huci muke tun ba ma yani. "Farhana kinyi kinyi karki kuma kiransa da ɗan iska, idan ba haka ba na rantse zan miki abunda bazaki taɓa mantawa ba. Kuma shi ɗin da kike kira ɗan iska bari kiji ya fiki matsayi a wuri na, wallahi ina mai gargaɗin ki karki ƙara kiransa da shege ko makamancin haka". Ta yarfar da hannuna dake ciwkwikwiye da Hijabinta. "ni kika mara ko? Za ki san kin mare ni, kuma kinyi da ƴar halak. Kuma indai ɗan iska ne yanzu na fara faɗa duk abunda zakiyi karki fasa". Cikin zafin nama na shaƙo wuyanta ina kaɗa mata kashedi. Kan kace mene wannan idon ƴan aji ya dawo kanmu, tuni akaje aka sanar da Malaman makaranta. _Short Update☹️. Anyway lets just say i don't feel motivated anymore🥴, like i just stop the typing mu huta gaba ɗaya ko? becx i dey see you people you dont like the story at all...ina gani daga comment & voting naku wanda yanda kuke yi baya encouraging nawa gaskiya...so please and please you guys should changed or you just tell me to stop westing my precious time._*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(6)* kamin a kawo mana rahoton Malam na kiranmu, masu jin haushin alaƙarmu da Farhana sai zugata sukeyi, mu kuwa lokacin shaiɗan ƙara buga mana ganga yake a kunnuwa, faɗa kamar ƙananun yara, abunda zamu iya rantsewa wani bamu taɓa yi ba tun wayonmu. gashi dai haushin hakan nake ji a ƙasan raina, amma kuma na rasa dalilin daya sa ko na nemi na huce sai zuciyata ta kuma ingizoni da zigar kar na raga mata, wataƙila shi Yayan da take zagi wani abu ne mai muhimmanci da Allah ya turo shi cikin rayuwata. kuma a hakan bakin Farhana bai mutu ba, dagewa take tana ƙara zaginsa, ni kuwa ina ƙara ƙuluwa har na rarumo wata kujera zan buga ma ta Allah ya kawo Malam Isma'il. Office ya kaimu, raina idan yayi dubu to kuwa tabbas ya ɓaci, sai cika nake ina faman batsewa. Malam Hamza principal ya shigo office ɗin ya gyara zaman shi akan kujera da hularshi irin ka fiya nacin nan, ya dube ni tsaf, sannan ya juya ya duba Farhana, a iyaka saninsa da mu yasan duk ɗinmu bamu da hayaniya, daga ni har Farhana, wani lokacin idan har ana faɗa da ɗaya, ɗaya yakan shigar wa wani, gashi a wannan karon abinda ya bashi mamaki mu da kanmu muke faɗan. wanda ada saboda irin kyawun alaƙar dake tsakaninmu da yawan Malamai da ɗalibai zatonsu gida guda muke. Malam Hamza yayi gyaran murya ya dubi inda nake tsugunne yace,  “Sabina lafiya yau kam, kuda ba’a jin kanku sai kuma gashi yau anji?”. Bance da shi komi ba, saboda ina da saurin ƙwalla duk da nakan mayar da martani, amma a wannan karon muddin nace zan buɗe baki nayi magana to fa zan iya yin kuka, saboda irin kalaman cin mutumcin da aka dinƙa faɗa min, ana cewa Farhana wai dama tsiyar abota da ɗan talaka kenan, shi yasa tuntuni suke nusar da ita munafukarta ce ni, ba dan Allah nake zaune da ita ba sai dan kuɗin gidansu, ita kuma lokacin ban san meke shiga zuciyarta ba har ta ɗauki huɗubarsu ta yaɓo min maganar data tsayan a rai, wadda ba dan da kunne naji daga bakinta ba, wallah ba zan taɓa yarda ba. Malam  Hamza ya dube ni ya kuma faɗin, “Ko ba zaku iya magana ba ne sai nasa muku bulala, sanin kanku ne baku fi ƙarfin hukuncin makaranta ba". Farhana zata yi magana kenan nai caraf na tari numfashinta, saboda nasan idan na barta tsab zata iya faɗin abin da ya haɗamu. “Malam yau dama ban koma gida ba, na zauna bada hadda wurin Malam Ibrahim, tana ta tambayata, ni kuma yau banjin magana, ita kuma ta takura min da magana shine muka fara faɗa, kuma kaja mata kunne idan ta kuma gani na a irin wannan yanayin ta daina kula ni”. Malam Hamza yace, “to shikenan ke Farhana kinji abinda tace saboda haka ki kiyaye karku ƙara bari shaiɗan ya shiga tsakaninku, ku tashi ku bani wuri”. Farhana zata yi magana Malam Hamza ya dakatar da ita, na faki idon shi nayi mata gwalo wanda nasan ya sosa ranta, ta girgiza kai tare da yin ƙwafa muka nufi hanyar fita. Bayan fitar mu shi kuwa Malam Hamza murmushi yayi gami da girgiza kai. Kafin mu ƙarasa aji kuwa, muna tafe ina banka mata harara itama tana aikomin da martani a haka har kowa ya isa ajinsu. Ƙarfe shida saura kwata aka tashi, kamar kullum tana inda ta saba jirana, ni kuma na gama cin alwashin ko ita ne mai mota ɗaya a duniya wadda dole sai na hau zanje gida sai dai na shekara ban isa gida ba. Ina kallonta ta gefen ido, tana bina da kallo, ni kuwa har wani sauri na ƙara tamkar zan kifa, ƙafafuwana har sarƙewa suke yi, amma hakan baisa na daina sauri ba. Ina tarar mai napep nayi sauri na shige don ko bayanin inda zai kaini ban samu damar yi ba sai da nashiga muka fara tafiya. A ƙofar gida ya sauke ni inda ina sauka su Adda Karima suna fitowa ita da Mardiyya daga gidan mu, ko kallo Addan bata ishe ni ba bare nasan Allah yayi ruwan halittarta a wurin, da hanzari na ƙarasa da fara’a fal shimfiɗe kan kuncina na shiga gaida. Itama anata ɓangaren Murmushin baƙin cikin tayi asanda ta kafe ni da ido tana neman inda zata samu makusa, saboda macece wanda Allah ya dasa mata zuciyar kushe, akwai fara’a amma fa irin mai ɗauke da taɓe bakin nan. ta dube ni sannan ta dubi Gwaggo tace, “Wai ni Yaya me kike bama yarinyar nan ne gaba ɗaya sai ƙiba take kamar ana hura ta, billahillazi idan baka santa ba sai kace ba ita bace, ke duba min yadda take kumatu ta ke cika tana ɓatsewa kamar wadda take shan sha ka fashe”. Yadda ta ke sababinta ni kuma yana saka ni nishaɗi, ita kuma idan duniya akwai abinda ta tsana tana faɗa ina dariya, duk da kasancewar ta itama Kaka ce a gare ni, Gwaggo tayi murmushi ta dube ni tace, “Karima wannan kuma ai gaki gata, yo me zan bata ni kuwa, abin ma da ba wani ci take yi ba, gaba ɗaya makaranta ta saka ta gaba, ko baki kula ba yanzu ma daga can ta ke”. Adda Karima ta gwame baki tace, “kuma fa haka, ita wai huda-huda, gara dai ayi aure duk sa’anni sunyi sun dire ku kuma kunce karatu to ayi dai mugani, lafiya ƙalau”. Saboda tsabar gulma nacin ta bata samu damar amsa gaisuwar da nai mata ba sai da ta gama habaicinta. ni kuwa ina dariya nace, "7Adda Karima kenan, ke dai ba’a raba ki da abin faɗa, to abinda kema kina da iko akaina, miji ai sai kimin wannan abu ɗan sauƙi..”. Kafin na ƙarasa tuni Adda Karima tace,"abu ɗan sauƙi fidda wando ta ka, Sabina ai shikenan tunda haka kika ce”. ina jinta na shiga ciki, duk bakin Gwaggo idan Adda Karima tana wuri tofa nata mutuwa yake yi muɗus. Napep ɗin dana sauka shi ya ɗauke su, ita kuma Gwaggo ta dawo ciki daga rakiyarsu. ina ɗaki ina canja kaya Gwaggo tayi sallama ta shigo ɗakin, gefen gado ta zauna tana faɗin, “ina raba ki da mayarwa Karima martani idan tana maki magana, kinsan dai kaf dangi babu wanda ya kaita shiga abinda babu ruwanta, saboda haka ki kiyaye ta wallah”. Ina gyaran zaman rigata, na miƙa hannu na ɗakko hula na sanya akaina sannan na dubi Gwaggo nayi mata kallon tsaf nace, “to karki damu Gwaggo zan kiyaye, wai da naga itama matsayin Kaka take a wuri na shisa ma nake yi da ita, baki ga ita wancan ko kallo bata ishe ni ba”. Gwaggo tace, “au yo to ni ai nazaci baki ganta ba, kinga fa bana son iya shege, sai kace baku san juna ba, kai ku dai ko miji kuka haɗa iya ka abin da zakuyi kenan, Allah ya shirye ku to”. Miƙewa tayi tana faɗin bari nayi alwala, har ta kai bakin ƙofa ta ɗaga labule ta dawo tana faɗin, “au ke la ɗazu kuwa Farhana tazo zaku tafi, nace mata baki dawo ba, ƙila ko kin tsaya bada hadda ne”. saboda kar taja zancen da sauri nace, “eh, hadda na bayar saboda jiya ban bayar ba, kuma bana son tayi min yawa shisa”. “au to madalla, ai na zaci ko wurin ɗan iskan yaron can kika koma, dan ta kawon ƙorafin hakan”. Sai da zuciyata ta buga, bugun da ban taɓa jin tayi ba, zuciyata bata son ana zagin bawan Allah'n nan ko kaɗan. Rumtse ido nayi ta dubi Gwaggo da wani irin kallo, da ƙyar leɓena na ƙasa ya samu nasarar motsawa kana na sama ya motsa suka haɗu suka samu nasarar furtar kalmar a’a ga Gwaggo. Bata kuma yinƙurin cewa komi ba ta saki labulen ta fita. ni kuwa na dafe kaina saboda yanda naji yana sara min na furta,“Ya Salam!”.*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(7)* "kinga farar singlet ɗina?". muryar Yaya Abba ta amsa a cikin kunnena. "ban ganta ba, bani na kwashe kayan ba sai dai ka tambayi Gwaggo". na ƙaraso wajensa ina ƙara faɗin,"Yaya Abba dan Allah zuge min". ya kama zip ɗin rigata ya zuge min sannan yasa kai ya fice ya zabga mitar da baya rabo da ita. ban dai ji Gwaggo ta tanka masa ba kuma nasan saboda karta yi magana suyi da shine shiyasa ta share shi, ni kuwa da ina gyara naga singlet ɗin amma na manta inda na ajeta shi yasa nace masa ban gani ba, dan ina cewa ban san inda na aje ba na shigesu da jaraba yau. bayan na gama shirina na fita parlonmu da yake madaidaici, na zauna naci sauran ɗumamen tuwon da Gwaggo tace ta rage min, ina gamawa kuma na dawo ɗaki na ɗauki littafin da nayi renting shekaranjiya na shiga karatu, tun a daren jiya na gama karanta book 1 ɗin, Sumayya Abdulƙadir ce ta rubuta shi ina masifar son littafanfa. sai wajen sha biyo na miƙe, na fito falon ina gyaran ɗaurin ture kaga tsiyana sai ga Farhana ta shigo bakinta ɗauke da sallama. fuskarta na washewa da siririyar dariya ta ƙaraso inda nake, wanda ni kuma ganinta yasa na cukule fuska, na dakata da waƙar da nakeyi, ina faman cika ina batsewa, saita hannu tasa da nufin ture ɗaurin nawa tana faɗin, "bari na ture sai naga tsiyar". Na wani bankama mata uwar harara sannan nace, "da kuwa kinga tsiya ganin idonki". Tayi dariya tana kama hannuna da nufin mu zauna kan kujera, na turje ina daɗa nuna mata nifa ban bar fushi da ita ba. cikin daɗin baki ta kama cewa, "haba mana Sabina wai mene kike hakan...wai so kike sai duniya ta jimu ts mana dariya". ta faɗa tana duba na tare da manno min kiss a goshi. ganin dai kamar ba zan sauko daga kan dokin fushin dana hau ba sai fuskarta ta sauya zuwa damuwa, nan fara'arta ta ɗauke gaba ɗaya, ni kaina na sa ni Farhana na tsananin so na, haka nima, bama iya faɗan minti biyar bamu shirya ba, kai hasalima bama yin faɗan, mukan yi ƙoƙarin kiyaye duk wani abu na ɓacin ranmu, duk da cewar wani lokacin ni na kan kasa haƙuri amma ita ko menene haƙuri takeyi. sai dai a wannan karon ina mamaki da silar abunda yasa nake faɗa da ita har nake irin wannan fushin haka, fushi da ita akan mutumin da ban sa ni ba, na tsince shi ne kawai a hanya, har kuma nake jin zan iya rabuwa da ita akansa, bama ita kaɗai ba, kowanene gani nake zan iya rabuwa da shi muddin bai samawa Yaya lafiya ba. Na kauda fuskana gefe guda domin bama zan tankawa maganar da tai ba. tana ƙara riƙe hannuna da nake son ƙwacewa tace, "kinga indai akan Yaya'nki ne kwantar da hankalinki, daga yau ba zaki ƙara jin bakina akansa ba. Wannan alƙawari ne na maki". jin hakan yasa na juyo ina dubanta, idan na kalla shin maganartata da gaske ne, ganin na zuba mata ido ina karantar fuskartata yasa tace, "wallahi da gaske nake miki, ni bazan yarda wani ya lalata mana zumuncinmu ba. Tsakanina da shi Allah ya shirye shi kawai, ko ba hakan kike so ba?". na saki fuskata ina murmushi, kamar yanda muke yi ada yanzu ma haka mukai, domin kuwa tafin hannuna ɗaga na bata muka tafa ina faɗin, "yauwa ko kefa, yanzu naga haskenki". sai tamin harar wasa da cewa, "ji min walaƙanci, duk wannan uban hasken nawa baƙi kike ganinsa dama?". Ina dariya nace, "yo da kike wani kaurara hasken naki, ai na bogi ne tunda na bature ne". Ina faɗa cike da tsokana, ina kaucewa biyo ni da tayi. Har ɗaki ta biyo ni muna dariya, Gwaggo na linke kaya ta bimu da ido. Sai dana ɓuya a bayanta ta sami damar yin magana tana duban Farhana. "ƙalau kuke kuwa?". Farhana na riƙe da ƙugu take ce mata, "wai Gwaggo saboda kuturun walaƙanci ni yarinyar nan zata cewa fari na bature ne". "ai ba ƙarya nayi ba, uban tulin robobin mayukan ɗakinki na mene?". Ina dariyar ina magana kuma cike da tsokana. Gwaggo ce ta juyo ta dube ni, ta wani yatsine fuska kana tace, "kema ai banda Allah ya rufa maki asiri gyatuminki ya ɗauko hasken Sahibina da ba'a san kalar da zaki kwaso ba, da har kike tsokanar wata, ki bar ganin Samari na aikin sunturi akanki duk tabarakin Sahibina kika ci. Ah tou". tai maganar dan ta ramawa Farahana, amma sai taji ba ki ɗayanmu mun sheƙe da dariya, Na buɗi baki nace, "Wai naci tabarakin Sahibinki, Abunda tarihi ma ya nuna shi Sahibin naki Kawu Baffa Sule ma ya fishi kyau, kinga kuwa in haka ne ai da an gani ajikin sauran Ƴaƴan nasa. Kawai dai shi Babana Allah ya zaɓe shi ne, gashi nan santalele kamar balarabe, Shi yasa ake kishi da shi, don ko Sahibin naki da kike koɗawa albarka". Na faɗa ina ƙunshe dariya ta saboda yanda naga Gwaggo na aika min wani kallo mai kama da harara. Gajeran tsaki ta saki tace, "Ki kiyayi ramata Sabina, shi gyatumin naki har kishin mene zanyi da shi, banda aikin wofi na haife shi kuma na kama kishi da shi". sai kuma ta ɗauko mifici ta shiga dukansa a ƙasa tana faɗin, "Kuma In faɗa miki ƙaryar tarihi ya faɗi abin kushewa akan Sahibina Allah ya jiƙansa da gafara. Ke idan a wannan zamanin naku ne ma ai sai na dinga tofe shi da li'ilafi ƙuraishin, ko da yake a wancan zamanin ma me aka fasa, yanda ƴan mata ke tururuwa akansa kamar ƙuda ya sami zaƙi tsabagen tsantsar kyawunsa da farin jini. Amma haka ya miƙe ya dire yace sai ni, haka ya dinƙa bani tabara ana aika min da yasin a gidanmu, Ɗan baiwa kenan wallahi shima Zaɓin Allah ne domin kuwa Allah ya bashi. Ai naga zallar soyayya a wurinsa, Allah sarki Allah yay maka rahma abin ƙaunata". Kawai sai ganin Gwaggo mukai ta fashe da kuka tana matse ido. Niko mai zanyi banda dariya da tafawa harda ƙwalla. "Allah ya jiƙansa, kice Dai Gwaggo kunsha ƙauna ke da Kakanmu". Farhana ke mata wannan tambayar tana ƙunshe dariyarta. "Hmmm". Gwaggo tace tana juyowa ta fuskanci Farhana."amin ƴar aljannah, ai ke kam mutunci ba daga nan ba, ki godewa Allah da baki ɗauko halin ƙawarki ba na rashin kirki". Farhana na daɗa riƙe dariyarta tace,"Gwaggo yau kuma Sabinan taki guda". Gwaggo ta harari gefena da cewar,"Wannan ai ƙaunar da take min a baki ne kawai... kina ganin ta haka sam bata ƙaunata. Yo banda rashin ƙauna ana zancen marigayi kina dariya saboda ɗibar albarka, ai yau Sabina ta nuna min matsayina a zuciyarta". Ni dai dariya nake kawai  bance mata komai ba, dan yanzu ina ƙara yin magana zata kuma hawa. dama Gwaggo sarkin zuba zance, sai dai idan baku zauna da ita ba, Nan ta hau bawa Farhana Labarin Kakanmu wato mijinta kenan. "ina faɗa miki Farhana ai naga zallar soyayya daga wurin Sahibina, soyayya ba irin ta ƴan yanzu ba irin ta aljanu. Babu irin kalar walaƙancin da ban masa ba amma bawan Allah'n nan haka ya nace yace idan babu ni sai rijiya. ke abokansa har ce masa suke babu zuciya a ƙirjinsa saboda irin wulaƙancin da nake masa. ni kuwa abunda ma yake ƙara ƙona min rai nake ci masa fuska idan naji yana faɗin wai in bani rijiya zai faɗa ko kuma ya rungumi tiransufo ma. idan ya faɗi hakan raina yana sosuwa, saboda lokacin ina jin tashen ƴan matanci, gani kyakykyawa gashina har gadon baya, idan ba kiyi min farin sani a matsayina na buzuwa ba to zaki rantse kice baƙar balarabiya ce, gidanmu fa Maza dandazo suke a ƙwar gida sai akai asuba ana jiran fitowata, ni kuwa dama ta samu nayi ta juya su kamar waina a tanda, tunms layi yazo kan Sahibina Allah ya jiƙan rai, shi dama ya kwashi buhunhunan rashin mutunci a wurina, amma don tsiya da tusa min takaici duk sanda nayi masa sai yace ai indai ba ƙona shi zanyi ba ya zama toka, to ba zai daina zuwa inda nake ba kuma ba zai fasa furta min soyayya ba. Watarana dana shirya masa mugunta, Ina jin ance yana sallama da ni Na kaɗa karkashi na fita ta bayan gida na sami dakalin ƙofar wani gida na sheƙa a wurin, Sannan na dawo naci gayu na yafa gyale, na fito waje ina tafiyan rangwaɗa sai faman yauƙi nake kyace tarwaɗa kin san mu buzaye bada ganan ba. Shi ko yallaɓai tunda ya ganni yake faman murmushi yana nuna jin daɗi, Ji yake kamar ya sure ni mu shilla sama, ina isa wurinsa na wani kashe masa ido ɗaya sannan nayi masa sigina da hannu ina masa nuni da ƙofar gidan da zamu yi zancen. Hmmm haka ya biyo ni sai wani nishaɗi yake a tunaninsa yau ya taki sa'a ya mallaki zuciyata ne bai san mugunta na shirya masa ba, ɗan Fillo'nka na hawa saman dakali jinsa kike timmjim ya zame ya faɗo cikin kwalbati, salati yake yana neman ɗauki ni kuwa sheƙa masa dariya nake kamar zararriya saboda mugunta, nayita iya kuɗina na kaɗa masa mazaune nace gobe ka ƙara dawowa inda nake". duk yanda naso dariya a wannan lokacin sai ya gagara, saboda yanda Gwaggo ta saito faranti a fuskata, jira take na ƙyalƙyale ta kwaɗo min. Farahana da biye ta dakakke sai ce ma ta tayi, "ohhh Allah sarki Kakanmu, amma dai daga ranar bai kuma zuwa wurinki ba ko Gwaggo?". Gwaggo ta jawo robar goro ta ɓalla ta Kai baki, tana tauna tana cewa, "ai ɗiyar Aljannah ina kai ki bana baroki, daga inda na sallamawa mutumin nan a faɗuwar da yayi sai da yay karaya biyu targaɗe ɗaya amma yana warkewa sai gashi ya dawo yana kuma zayyana min irin soyayyar da yake min, Kuma fa ko da yana kwance kullum sai ya aiko azo duba mishi ni, in taƙaice miki dai ƙarshe ai sara mishi kawai nayi nace Sahibina ai kai bai kamata a kiraka da masoyin zuciya ba, da masheƙin rai da zuciya ya kamata a kiraka". "to fa! garin ya ya cancanci wannan sunan Gwaggo?". Farhana ta faɗa tana waro ido, tana ƙara tunzura Gwaggo. Ina duban Gwaggo ina dariya na miƙo mata hannu ta sammin goron sai ta make hannun nawa, yau harda su murguɗa min baki bayan harar da ake watsa min. Nan taci gaba da bawa Farhana labari, "ai ɗiyar Aljannah ya cancanci wannan sunan shi yasa na raɗa masa. Akaina fa yay faɗa da ƴan daba talatin saboda sun kawon hari, duk wuƙaƙen da suke tare dasu haka yay masu fata-fata, Ya kamo hannuna cikin kulawar so ya dawo dani gida, kamar zai yi kuka yake roƙona don Allah Sahiba karKi sake fitowa waje bare wani banza ya kuma kalle mani Ke, take a wajen naji wani ƙahon sonsa ya huda zuciyata ƙaunarsa ta nemi waje tai malemale, naja da baya na matso kusa da shi na yi masa kirarin so mai jijjiga ruhin masoyi, sannan na koma gida. Ina shiga na cewa mahaifiyata Adi, nifa Fillo zan aura, kowa daya ji haka sai da yayi mamakin abun saboda ada nace akan me zan auri wani matsolon rake, ai ƙwamma na sami ɗan'uwana usulin buzu kakkaura mai ƙwarin ƙashi na aura. Farhana ai banga so da ƙauna ba sai dana je gidan Sahibi na Sahibarsa, Kishiyoyi suka sanyo ni gaba amma sam Sahibina baya bi takansu, ni kuwa haka na dinga tsula tsiyata a gidannan ina gasa su son raina da tawa salon kissar, kuma fa gani ƴar figigiya amma haka na zame musu ciwon idanu. sanda na sami ciki na fara laulayi ai Kamar na zazzagawa kishiyoyina wuta a jiki saboda yanda Sahibina ke Tattalina kyace wata ƙwai". Gwaggo ta numfasa tana kuma fashewa da kuka tace, "Allah ya jiƙan Sahibina, ya mutu yana cikin mayen so na". Wayyo Allah cikina ni Sabina, yau nayi dariya na godewa Allah saboda dramar Gwaggo, na ƙara tsokanota da cewa, "to amma kuma Gwaggo ai tarihi ya nuna Kakanmu kamar yafi son Uwar gidansa Addagana, akace ma yana kan cinyarta ya mutu". Ba shiri naja bakina nai shiru saboda kallon da Gwaggo ta wurgo min haɗe da jefo min murfin bokiti. "to duk wanda ya faɗa miki wannan zancen ƙarya yake munafikin Allah ta'ala. Ke Sabina zanfa iya haɗa ki da D.P.O yau ɗin nan, saboda haka ki fita a idona, ke kiji wata makirar ƙarya, a gidan ubanwa ya mutu akan cinyarta, wanne shegen ne ya faɗa miki haka?". ni dama ba don komai yasa na faɗi hakan ba sai dan kunnata, saboda nasan yanda take tsakaninta da kishiyoyi, gashi dai shekaru da dama amma kamar waɗanda mijin ke aurensu yanzu. Gwaggo dai kamar nai mata me, haushin maganata da dariyata suka tsaya mata a rai. alhalin ita kanta wadda ake bawa labarin dariya ta ke, amma tawa dariyar ita ta zama laifi, na buɗi baki zanyi magana kenan ta dakatar dani cikin kwazazzafa. "ke kin san Allah zan miki adu'a bakinki ya tsaya a haka na tsawon shekara guda, sarai kin san na gada a wurin Kakana na biyu na ɓangaren kishiyar Babata Adi, kasancewar sunyi zaman mutunci sai muka zama kamar ƴan uwa, don haka ahir ɗinki da ni a yau ɗin nan. Ki tambayi kishiyata Hussaina kisha labari, da tayi min ba dai-dai ba sai da ta kwan talatin da bakwai ba tayi kashi ba, shima banda ta bani haƙuri sai dai ta shura a haka". Nai shiru ban kuma magana ba, ina latsa wayar Farhana. Ina jinsu Suna ta shan hirarsu. Ya Abba ne ya shigo ɗakin ɗauke da sallama a bakinsa, muka amsa masa ya shigo ɗakin ya tsaya yana zuba hannayensa a aljihu. Sannan ya shiga buɗe kwanuka da alama abinci yake nema, ya ɗago yana kallon Gwaggo yace, "ina abinci na?". a hasale tace da shi,"Ka kawo ka aje ne, ko kuma aure na kake da zaka shigo min gida har cikin ɗakina kake tambayana abinci". Ya kama ƙugu ya riƙe yana dubanta babu alamar wasa a fuskarsa kamar wani mijin gaske, yay gyaran murya yace, "naji koma mine kice, ni dai ina abinci na, yasin yau na kwaso yunwa baki ga yanda nai wani laushi ba kamar lagwani". Ta harare shi tace, "To ai kai dama lagwanin ne, saboda kullum a yamushe kake Kamar lawashi. Ni wannan yaro don dai Allah yay maka halittar maza ne amma da sai nace mace ne kai". Ya Abba ya ɓata fuska yace,"nifa sai na rubuta miki takarda akan irin wannan cin fuskar da kike mani. Kuma idan kina wasa ki kuma cewa tak ki kalla idan ban sake ki ba...ya zaai a gaban ƙannena kike faɗa min irin wannan maganar". Gwaggo tayi tsaki ta doki cinya tare da tura masa mazaunai tace masa, "karka fasa saki na ɗin, kaine zaka ji haushi. Saboda ina fita zan sami rangaɗeɗen saurayi mai rai da lafiya yayi wuff da ni, kai Abba kana raina wannan Sauran yarintar dake jikina ko, to Rabon kaji na aure shugaban ƙasarku ne". Ya Abba ya kaɗa kai kawai, idan ya biye tata abincin daya dawo ci ba zai sami cinsa ba. Ya dube ni yace, "ke tashi ki ɗauko min abinci na". Kamin na miƙe Gwaggo tace, "ke yi zamanki, yau kam sai dai ya nemi wani gidan yaci abinci. Abba ba dai ni zaka nunawa tsiya ba, zaka ganta iya ganin idonka, dama kowa ai da ranarsa. Idan kaji haushi ka koma can filin ball ɗin su dafa su baka, ko kuma kaje can gidan su budurwar taka daka saci ɗankwalina ka kai mata matsayin toshin sallah saita baka...kana faman ɓoɗara hanci kamar gajeran wando, da wasu idanuwanka ƙifi-ƙifi kamar na ƙaramar touchlight ɗin masu gadi, har na zaka nunawa fushi Abba". Haushi ya tuƙe Ya Abba, don haka ya juya kawai ya fice yana jijjiga kai. Gwaggo tabi bayansa da ido tana murmushi tayi ƙwafa tace, "ɗan ƙwal uba dani kake zancen ai". Muna haka muka jiyo sallaman Baba, da sauri na sakko a saman kafita na fita cikin hanzari ina amsa sallamar tasa, kamin Gwaggo da Farhana su mara min baya. Yana zama kan kujera na ƙaraso da fara'ata ta nuna jin daɗin ganin mahaifina nace, "Baba sannu da zuwa". Ya amsa min da, "yauwa Sabina". Farhana ta ƙaraso itama tana masa sannu da zuwa. Lokacin da Gwaggo ta ƙaraso ta zauna kan kujera, Baba ya sauko ya gaida ita, tana amsa masa tana sanya masa albarka. Baba yace, "Mama mene ya haɗaki da jikin naki, yace kinƙi bashi abinci". "auto kaga masu ɗa, ai ban san kana tuhuma ta ba sai naga ka sanya mini ankwa, sai naji daɗin maka jawabi...amma yanzu ban ganka da kakin ɗan sanda ba ina zan san kana yi Awwalu. Abinci ne na dafa bazan bashi ba, har ni yaron nan zai tsulawa tsiya na roƙe shi nace yazo ya siyo min kayan miya Sabina na makaranta, amma ya buɗi baki yace ai filin ball zaije, koma ba haka ba ai yayi girman a aike shi wurin me kayan miya, ƴan mata ai sai su raina shi. Ranar haka na zauna ban girka na rana ba sai da Ƴar arziƙi irin albarka ta dawo, wadda tayo gadon kirki a wajen mahaifiyarta". Baba yace, "to ayi masa afuwa Gwaggo ba zai ƙara ba. ba'a horo da yunwa ke kika faɗa mana hakan, kuma shi idan baici anan ba aina zaici". ta taɓe baki kamin tace, "ya tafi can wajen matan ubansa yaci, ko kuma tunda Allah ya kawoka ka ciri ashirin ka bashi ya sayo awara, abincina ne dai yau Abba ba zai ci ba". Baba baice komai ba, dan yasan tun da ta kafe kam bata sauya ra'ayinta. ya dai kalla Ya Abba da ido sukai magana, nan ya tashi ya fita bayan Baba ya bashi kuɗi a ɓoye, in ba haka ba Yanzu Gwaggo sai ta kuma sauke masa sababi idan ta gani. Baba ya kira ni yace nazo, na taso na dawo kusa da shi, kasa ɗauke idona nayi akansa duban yanda naga yana ta zabga murmushi da alamu yau ɗin yan cikin farin ciki, don tunda ya shigo na lura da hakan, ni kuma abunda yake min daɗi kenan a rayuwata, naga mahaifina acikin farinciki da kwanciyar hankali. Baƙar jakar hannunsa ta laptop ya buɗe ya zaro wasu takardu ya miƙon yace na karanta. Habawa ai ina karanta layi biyun farko na miƙe tsaye nai wani tsalle nai juyi ina ihun murna, Farhana na fizgo na nuna ma ta itama, tsabar farinciki mun kasa ƙarasa karanta sauran rubutun. baki ɗayanmu tsalle muke muna murna, kamin daga baya na koma na zauna ina hamdala ga Allah, maimaitawa nake, "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Allah mun gode maka abisa ni'imar da kayi mana. Ya Allah kaci gaba da bawa mahaifina nasara a rayuwarsa". Gwaggo tace, "wai meke faruwa ne, ni duk kun barni a duhu, ko abin farincikin banda ni ya sama. An baki aba kin wani ƙwaƙwame ke kaɗai, ina ce dai ɗa nawa ne tunda sai dana haifa kika sa me shi a uba". nace, "oh Allah na! nikam yau gwaggo ban san me na maki ba. to gashi nan".Na faɗa ina tasowa na bata takardar. Sai da ta gama mani kallon sama da ƙasa kana ta karɓi takardar, hannu ta miƙa saman abun tv namu ta ɗauko akwatin glass ɗina, ta buɗe shi ta ɗauko glass ɗin ta ƙwaƙwuma a fuska sannan ta wani harɗe ƙafafu ta hau kallon takarda kace gaske karantawar take. Dariya muke so muyi daga ni har Baba amma gudun sababinta yasa muka gimtse kayarmu. ta ɗau kusan mintina biyu sannan ta sauke takardar daga kallonta, ta cire glass ɗin, tana faman juya takardar ta kalla Baba tace, "Kai Auwalu, tunda ta gama nata zagin kai sai ka sami damar min bayanin abinda ke ƙunshe aciki. Sarai ai kasan babu abinda na iya karantawar amma ka barta ta miƙo min saboda cin fuska, dama ranar nan tace min ni ai bana ganewa, kamar Addagana haka nake. Yo Allah na tuba duk lalacewa ai nafi wannan lukutar matar tunda ni nayi makaranar Allo. Ita yarinya ce har yanzu bata san mene kishi ba shi yasa take haɗani da waɗanda suka kusa rabani da mijina". O'o, niko na riƙe baki ina kallonta har tagama magana. Gwaggo ba dai mita ba, wannan zancen anyi wata da yinsa amma duk sanda ta tashi sai tace ai nace bata ganewa Addagana tafi ta jaa, kuma ba komai bane saboda na haɗata da kishiyarta. Baba ya numfasa yace, "Mama wannan takarda ce daga wurin aikinmu...". Ai tun Baba bai ƙarasa ba ta dafe ƙirji cikin tashin hankali tace, "na shiga uku na Auwalu ba dai sun kuma korarka bane, wannan ƙaddara da me tayi kama". tana faɗa tana shirin yin kuka. Ina dubanta ina gwame fuska nace, "kai Gwaggo hakanne zaisa kiga ina murna kuma. Abuja fa zamu koma". Tayi min wani kallon sheƙeƙe na ban gane nufinki ba, "me kuma zai maida mu Baba Ja?". Gwaggo bata taɓa cewa Abuja sai dai tace Babaja, saboda acewarta ai cin mutunci ne yasa aka lanƙwaya sunan ubanta aka maida shi Abuja daga Abubakar. Baba yaci gaba da mata bayani, "ehh Gwaggo zamu koma Abuja ne da zama saboda ƙarin matsayi da ma'aikata ta bani". "kai don manzan Allah??". ta faɗa har tana zamowa daga wurin zamanta. "wallahi kuwa Gwaggo, an bani muƙamin MD na ma'aikatar wutar lantarki. Sun bani gidaje biyu acan Abuja, da motoci uku, da kuma miliyan uku, ta buƙaci na ɗauki iyalaina mu koma can da zama gaba ɗaya nan da sati guda". _Please Share, Vote and Comment let me know what you think._*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(8)* Gwaggo ta rangaɗa wata uwar guɗa data amsa a gaba ɗaya cikin gidan, hamdala take ta jerawa ga Allah, har da miƙewa ta taka rawa irin tasu ta tsofaffi. "Allah maji kukan bayinsa...kai gaba ɗaya ma na rasa wacce iriyar murna zanyi". Yaya Abba daya shigo yace da ita,"tsohuwa kina ta ihu fa dare ne, maganarki har soro, dama ke muryar kamar cakwaikwaiwa". tace da shi,"umm Abba ai yau sai dai kayi da wata bada ni ba kam...dan lokacinka dai ban da shi". Murna nake yi sosai kamar babu gobe, amma ɓangare guda na zuciyata yana tunanin halin da zan shiga zai kasance. wannan mutumin, wannan bawan Allah'n da Allah ya haɗani da shi ta ayar da ban san fassararta ba, wannan mutumin da nake jin kamar ina da wata babbar alaƙa da shi, mutumin da babu ƙarya tun a ranar farko nake jin tasirinsa a tare dani a kullu yaumin, mutumin da tunanins akaɗai a sanda bana tare da shi yake sakani zubar hawaye saboda rashin sanin dalilin wanne hali yake ciki. Gaba ɗaya murnar da nake yi tsayawa tayi cak, saboda tunawa da nai zan tafi na bar Yaya, tunanin daya haifar da wani ɗan ƙaramin tashin hankali a zuciyata, ta fara bugu kamar zata fito waje. dai-dai ta nutsuwata nayi saboda ina gaban wanda bana son ya fahimci yanayin da nake ciki. dan duk wanda ya kallen a yanzu dole sai ya ɓazgo wani abun, Ina kallon Farhana ma yadda ta kafe ni da idanunta, tana son gano sirrin dake zuciyata, amma sam na kafa na tsare saboda yanzu sai ta ruguza min tsari, dan ita bata iya sirri ba. Ganin hakan yasa ni furta, “Yauwa Baba barin zuba maka ruwan alwala, na kalla magriba ta gaba to”. ina gama faɗar haka na miƙe na nufi hanyar fita, idon Farhana na kaina har a lokacin, yayin da Gwaggo take ta faman zuba kamar kanyar da ta samu jeje da iska. Ina fita na samu damar dai-dai ta nutsuwata, amma fa sam hakan ya gagara, don tuni hawaye sun fara zubo min, dama ni Allah ya hore min kamar famfo, hawayena a wajen tausayi da rauni basu da wahalar sauka. ina zuba ruwan na dawo, na samu gefen Gwaggo na zauna ina sauraron hirar ta su, ba wani fuskantar hirar nake ba, tunanina da neman mafita bai wuce yadda za'ayi tafiyar nan tare da Yaya ba. kallon Farhana nai, nayi mata sigina da ido, saboda mu fita mu samu abin faɗa, amma sai naga ta basar kamar bata ganni ba. Ganin haka yasa na miƙe na kama hannunta ina faɗin, “tashi mu shiga ciki”. Hannuna ta kama muka nufi hanyar ɗaki, muna shiga ta dube ni sheƙeƙe tace, “ya dai uwar ɗorawa kai damuwa”. harara na watsa mata ina faɗin. “ke fa ƴar rainin hankali ce Farhana, meye nufinki dama?”. ta ɗan harare ni tace, “Oh oh jimin rainin tunani, ke zan tambaya dai meye ke damunki, naganki sukuku, don tun ɗazu na fuskanci damuwar da kika shiga bayan kin gama murna”. na ɗan ja ƙaramin tsaki kaɗan na miƙe tsaye ina safa da marwa kana na kama ƙugu na tsaya nace, “ba zaki gane ba Farhana, kin san halina sarai, ina da saka damuwa akan abinda nasa a raina but..”. ban ƙarasa faɗin abinda zance ba Gwaggo ta bankaɗo labule tana faɗin, “an kira sallah ko baku ji ne wai, ko kuwa ba zaku yi ba ku duka?”. nace, “kaii Gwaggo mai baiwa, yo waye yace maki bamu ji ne wai, banda abinki Gwaggo kuma anyi ta rashin sallar kenan?”. tace, “oho maki marar kunya, na sani ko ba zaku yi ba, tunda ku ko yaushe a cikin jini kuke. abu da a zamaninmu iwar haka ma yara kamar ku basu fara abin mata ba sai an wuce haka...amma ku yaran yanzu nan da nan sai ku nemi kufi ƙarfin kan mutum”. “gaskiya Gwaggo Allah ya baki baiwa, baiwa ba ta faɗe ba, ina ruwanki ne ke kam, don Allah kije, na san abin da kike nufi gamu nan kije abinki”. na faɗa sanda nake ƙara riƙe ƙugu. Farhana kam dariya kawai take tana faɗin, “ni kam dramar ku tana burge ni, muje muyi alwala kafin ta dawo”. muna idar da Sallah Farhana tace zata tafi, Gwaggo ta zuba mata tuwon shinkafa da miyar kuɓewa tace ta kaima Hajiyarsu. Ta karɓa tana godiya, har mun kai soro naja na tsaya ina faɗin,“muje kice ma Baba zan kwana a gidanku in yaso sai mu tattauna abinda zamu tattauna kinji”. Farhana ta ɗanyi jim kafin tace, “Gwaggo dai nasan zata yarda amma kina ganin Baba fa?”. “ke kam muje zai amince insha'Allah”. na faɗa da ƙosawa, da wani abu dake bin jikina wanda ban san menene shi ba. muka koma ciki, Gwaggo bata gama lazimin da take yi ba, sai da ta gama sannan ta juyo da kallonta kanmu tace, “oh yau naga abinda ya ishe ni, yo bakwa iya zama sai dai ku tsaya min haka aka ƙi ƙam sai kace kunzo ɗaukar fansa”. Farhana tayi dariya ta zauna kan kujera, ni kuma na tsugunna a lokacin da nake jin kamar nai fiffike na isa ga Yaya. Farhana tace da ita, “Allah ya huci zuciyar Gwaggo, ina abin ɗaukar fansa anan, sauri muke yi shisa muka ga ba sai mun zauna ba”. Gwaggo ta ajiye carbin dake hannunta tace, “to naji sarakan iya tsari, meye ne dama?”. tana tambayar ga Farhana ne a lokacin da take kafeni da ido. na ɗan ɓata fuska gudun karta harbo jirgina nace,"bafa ni kika tambaya ba da kike jiran amsa daga bakina". ta watsa min Harara kana ta juya inda Farhana take tana faɗin, “ina jinki Farhana meye ne?". “Gwaggo dama tare da Sabina zamu je gida gobe insha'Allah sai mu dawo, ina so zata rakani taron get together da zamu yi ne a school”. Gwaggo ta gwame baki tana kauda kai, sannan ta samu damar furta,“ta jira ubanta ya shigo in yaso sai taji daga gare shi”. nasan sarai ta faɗa ne dan bata so naje, kuma ba zata iya cewa Farhana a'a ba, domin a rayuwarta in akwai abunda bata so shine na kwana ba kusa da ita ba. na yamutse fuska nace, “Gwaggo dan Allah”. na rufe ido ina ƙara faɗin,"Gwaggo, Gwaggo, Gwaggo wai ce nake kece ke da iko da ni, to kuma why zaki ce sai Baba ya amince". tayi ƙwafa bata ce min komai ba, ta ɗau carbi taci gaba da lazimi. duk na ƙosa ta bani attension ɗinta na fara yi mata magiyar dana saba, amma gaba ɗaya sai naga ta sauya fuska, har Farhana ta miƙe tace ita kam tafiya zata yi, nai saurin riƙo hannunta ina roƙonta sai ga Baba yayi sallama muka amsa mashi, ya samu wuri ya zauna, yadda ya ganmu ya sashi faɗin, “duk yadda aka yi akwai abin da kuke buƙata ko...ko kuma wata matsalar ce?". ni dai nayi ƙasa da kaina, Farhana kuma tace,“Baba dama..dama muna son zuwa..”. Baba yana murmushin manyance yace, “ina jinku meye ne dama?”. tana sosa gira tace,"Baba dama ina so mu tafi gidanmu ne tare da Sabina tunda kun kusa tafiya ku barni". ina kallon yanda Gwaggo tai saurin juyowa tana kallon Farhana da ɗumbin mamaki, tama kasa rufe baki, saboda jin furucin daya banbanta da wanda ta faɗa mata a ɗazu, fuskarta kuma na haskawa da rashin yarda damu, dan yanda maganar Farhana ta banbanta tasan dole kwai wani abu da muke ɓoyewa. laɓɓanta suna motsawa da son faɗin wani abu amma sai bata faɗa ba, ta ɗauke kai ta kama ƴan waƙoƙinta na ɗan ƙwairo. "mai zai hana ni ƙin amince miki Farhana, ba ke ɗaya da kuke aminan juna da Sabina ba, ko dan mutunci da karamci irin na mahaifinki babu abinda zaki nema ki rasa daga gareni. dan haka kuje Allah yay muku albarka, gidan ku ai kaman gidansu ne itama...kya gaida Abban naki don na kwan biyu bamu haɗu ba". godiya muka yi masa sannan muka miƙe muna nufar hanyar fita. “au ko sallama don iya shege ba zaku min ba, shi ne kuka miƙa kai kamar ƴaƴan zabi”.dariya sosai Baba yayi, ita kuwa Gwaggo ko dariya bata yi ba, Farhana tace, “wallah Gwaggo kin iya yanka, salon muce wani abin kice mun ce”. “yo ai gaskiya na faɗa, ina kallo fa ko kaya bata ɗauka ba. Ko haka zata tafi babu kaya? ko da yake zumuɗi na gaba da suturta jiki ai”. na manta da Baba yana wajen nace da ita,"Allah Gwaggo kin fiya sa ido, haka zanje ɗin ni don Allah ki ƙyale ni...Baba mun tafi”. ina faɗa naja hannun Farhana zamu fita. Gwaggo ta kuma cewa, “yo ai sai kiyi kuma, da wuyanki kamar mariƙar lema, na san dai kayan Farhana ba zai maki ba ko ɗaya, dan haka ki dawo ki ɗauki dai-dai ke”. duk wannan maganar da take saboda dai a fasa tafiyar ne, dan haka ban tsaya tanka mata ba balle ta sami abinda take so, naja Farhana muka fice, muna jinta tana faɗin,"Allah dai na kallonku, ni bance sai kunji tsorona ba amma kuji tsoron Allah". A mota kuwa muna tafiya Farhana sai dariyar kalaman Gwaggo takeyi, yayin da ni ko kaɗan dariya bata zo min ba, tunanina kaf bai wuce neman mafita ba. idan muka bar garin nan sai yaushe zamu ƙara dawowa?, idan na tafi ba tare da nayi sallama da Yaya ba shin idan na dawo zan sake ganinsa?, ban ɗau tsawon lokaci tare da shi ba, amma ya fara sakewa na san da wannan, ba kullum nake kasancewa da shi ba, amma a jikina nake jin rayuwarsa ta fara sauyawa, haka zalika ajikina nake jin sauyin rayuwarsa na gab da zuwa, gab, kusa-kusa, kusan da bata da wuya wurin Allah, sai da a wurinmu ƴan adam...to amma abunda na kasa ganewa shine, tun a ranar farko zuciyata ke faɗa min kece wannan ƙaddarar, kece ƙaddarar da zaki sauya rayuwarsa, silarki komai nasa zai warware, wataƙila yanzu wataƙila sai an ɗau tsayin lokaci. kuma ayau da wannan abin farin cikin ya samemu, tun bayan dana gama murnata, haka zuciyar tawa ke faɗa min, ki tafi da shi, karki barshi anan, acan inda zaki je, acan inda zaki je zaren wata ƙaddarar zai warware, zuwa Abuja alkhairi ne...abinda zuciya faɗa tana ƙara faɗa kenan tun a ɗazu. kuma maganar Farhana data kutso cikin shirun da nai yasa ni rufe ido ina sauke numfashi, tukunna furucin nata daya fito ya tsaya a iska ya sami damar shiga kunnena.     _Masu Karatu what do you think will happen on this trip?_ _ta yaya zamu fassara kalaman zuciyar Sabina?_ _kuna ganin akwai yiwuwar ƙara haɗuwarsu da Al-hussain kamin tafiyarta?_           #Vote. #Comment. #Share. #Mikiyawriters*AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(9)* "Sabina tun a washegarin ranar da idanuwanki suka sauka akan ɗsn wiwin kan bola na kalli wani abu acikin ƙwayar idonki akansa, sai gashi ayau abunda na gani a saman fuskanki ya ƙara tabbatar min da shi...Sabina a haƙiƙanin gaskiya ba tausayinsa kike yi ba, sonsa kike, irin son da kika kasa ganewa balle har ki gasgata shi". Nai mata wani kallo na rashin fahimtar maganar tata sannan nace,"ina kika dosa kenan? i din't get you well". tai wani guntun murmushi da ya tsaya iyaka leɓenta sannan tace,"wanda kike kira da Yayanki mana...Sabina Whether you agree or not; you love him. Kuma irin son da kinyi zurfi a ciki, since za ki iya shiga wannan yanayin na tashin hankali becouse you are going far away from him. Tun a ɗazu fa ina lure da yanda Mood naki ya sauya lokaci guda bayan kin gama murnarki, kuma dana gama karantar fuskanki, i saw nothing beyond love full of compassion". Naja wani uban dogon tsaki, wanda yasa har mai napep ɗin dake janmu sai daya juyo ya kalle ni. Cikin masifa nake ce mata,"kina raina min ajawali da yawa Farhana. Wai me kika ɗaukeni ne hala ma tukunna, kawai kin bi kin Haɗa da wani hasashenki mara kan gado kin dage akan cewan Sonsa nake. Well, I dont like him at all, I just know I feel very sorry for him. And I can do anything to see that I change his life to a world of happiness unlike the one he is in now". sai ta saki wata dariyar ƙeta tana kallona tace, "ta ya kenan?". ta kuma harzuƙa ni, na wulla mata harara na ɗauke kaina, ina kallon waje nace da ita, "I just told you karki kuma cewa ina sonsa, otherwise kuma zamu yi faɗa". "ke wallah bazan bar cewa kina sonsa ba, ai labarin zuciya a tambayi fuska, ba wai na ƙirƙiro na faɗa ba ne". Na kaɗa kaina ban kuma ce ma ta komi ba, the way I heard her hypocritically laughed, saina tsaida mai nepep ɗin na sauka, dan ba zan iya tafiya da ita tana ci gaba da faɗan wannan banzan zancen nata ba. Allah yaso na fito da sauran kuɗi a hannuna na bashi, ina jinta tana min magana nai mata banza, saboda ma karta takura ni nayi saurin tsallaka titi, har cikin ranta nasan ba taso hakan ba, to amma kuma ya ta iya, dama ni na nema mu tafi tare kuma nace na fasa. Wani mai napep ɗin na kuma tara na faɗa masa unguwarmu, yana sauke ni ƙofar gida mukai karo da Ya Abba, shi ya biya kuɗin motar saboda ni babu a hannuna. Fuskata a turɓune na shigo ina sallama a ciki, sai dai duk ɓacin ran da nake ɗauke da shi, show ɗin Gwaggo da Baba sai ya kawar da shi, take na fara ƙyalƙyala dariya. Sai a lokacin ne ma suka san da shigowata, Baba ya dube ni zai yi magana Gwaggo ta riga shi tana ce min, "mutan kan naki sun sauya miki ra'ayi kenan?". Ina zama kan kujera nace, "ɓata min rai tayi shi yasa na fasa binta, dama ba wata uwar zata tsinana min ba, bare ta sani gaba tana min dariya kamar taga mahaukaciya sabon kamu". tace, "oho miki dai, mai jure ma halinki sai ita ɗin. Ke nifa da ni ce ita da tuni mun jima da gama ɓaɓewa dake, yo ina dole a nan, zamaninmu idan naga ƙawa na min iya shege saboda taga ina sonta sai na nuna mata ba'a haifi wanda ya haife ta bama". "to su Hajiya Gwaggo Allah yasa ba ke ɗin bace, kuma Allah yasa bata nan bare ki zugata. Nima fa Gwaggo ko ni ɗin, da kece ƙawata yasin ba zan iya zama dake ba". Ai tun ban rufe baki na ba tace, "yo ga mai mugun hali ke kuwa ai dole kice haka. Yanzu ai idan baki zauna dani ba kya zauna da matan ubanki da basa ƙaunarki". Yaya Abba dake shigowa yace da ita, "don zamu koma can ai ba yana nufin zamu zauna gida ɗaya dasu bane". Gwaggo ta taɓe baki tace, "to dan masu iya magana ai bani na faɗa ba, ubanka shi ya faɗa gashi nan a zaune sai ka tambaye shi". tana maganar tana hararsa. Sai kuma taci gaba da wa Baba faɗa tana cewa, "nan inace lokacin da Allah ya jarabceka da karayar arziƙi, cikin ƴaƴan su babu wanda yayi yunƙurin taimaka maka har zuwa yanzu da muke ciki, ni kaina daga lokacin suka bar zuwa gaishe ni saboda baka da abinda zan sanya kayi musu. Amma kake ambaton zamu tafi da iyayensu, saboda gaka wanda yafi kowa zuciyar imani, to ni ban yarda ba". Ni dai ban gane akan mene suke magana ba, amma yanda naga Gwaggo ta rikeɗe nasan maganar kishiyoyinta akai, domin Allah'n daya halicci Gwaggo bata ƙaunar sunan kishiyoyinta, sai kace yanzu ne ta ke zaune da su suke bugawa, idan tayi wani abunma sai kai zaton ko ita ɗaya ne aka taɓawa kishiya. Baba ya numfasa, cikin magana ta sigar lallashi yace, "Gwaggo ai ita rayuwa idan zakama mutum abu karka dubi halinsa, duba Allah sai kayi masa, kuma idan Ubangiji ya azurtaka da shi, the more kana badawa the more kana ƙara samu. Hadisi ne fa guda karka rama sharri da sharri...". Ai tun bai kai ba Gwaggo ta dakatar shi, tana jefa goro a baki tace, "kai ba dama a fara magana sai ka nemi yanda zakayi ka kashewa mutum zuciya da faɗin Allah da ma'aiki. To naji na yarda amma fa da mutum guda zamu tafi, kaje goben kaiwa Addagana magana ita kawai nace bance da wannan mai zubin sauron ba. Domin ita a rayuwarta sam bata da mutunci, itama Addagana arziƙi ɗaya taci ta taɓa sammin gishirin miya amma wallah da bazan yarda ta ɗanɗani arziƙinka ba Auwalu, saboda matar nan lokacin zaman mu iya shaƙa na shaƙa a wurinta, to da yake ma ni ɗin ba kanwar lasa bace sai muka yi dai-dai da ita. Itako waccen mai yanayin dusar awarar ko bayan raina ban yarda da sisinka ka kashe mata ba, domin ta cutar dani iya cutarwa saboda tana gani na ƙwaila dani a lokacin, haka ta haƙa rami ta binne borkono da citta da sauran barbaɗenta ta ƙyallo mu ta mudubi ni da Sahibina amma da yake Allah ba azzalumin bawansa bane sai kaidinta ya koma kanta, hakan bai isheta ba sai da tayi nasarar haɗani faɗa da shi na tsawon mako guda, ya daina min magana ya daina saurarona. Kai Allah ya isa tsakani na da Hussaina, insha'Allahu sai ta wayi gari idonta ɗaya ya koma ƙeyarta na gaban kuma ya ma ce". ta faɗi hakan tana matsar ƙwalla, Baba kuma na bata haƙuri, ni da Yaya Abba muka tafa muna kwasar dariya muka ce, "Gwaggo; Gwaggo; Gwaggo; ikon Allah...Hajiya Gwaggo a daina ruƙo dan Allah, duk abunda ya wuce ya riga ya wuce, shekaru aru aru kinƙi cire abu a ranki". ta ɗago ta kalleni aka wurgan harara aka ce, "Sabina ina jiye miki ranar da zaki wayi gari ki kalla kishiya a cikin gidanki, ina mai faɗa miki karda ki sa ke kizo wurina na baki tofin Allah tsine don kifi ƙarfinta, saboda kina ɗaya daga cikin masu cutar da zuciyata, duk sanda nake bada labarin zamana da kishiyoyi maimakon ki tausaya min, a'a sai dai ki bushe da dariya kamar wadda aka bugawa guduma a tsakiyar ka jini da ƙwaƙwalwa suka gauraya suka haɗe. Ko da yake yau ai kin nuna min matsayi na a wurinki, tunda mutuwar Sahibina ma baki iya cewa Allah ya jiƙan rai ba sai dariya to ai kuwa babu abun alkhairin da za ki iya min". ta dubi Baba shima ta jefe shi da harara tace, "kai kuma saboda ƴarka ce shi yasa ba zaka iya tsawatar mata ba akan tsiyar da take shuka min. Wannan yarinya ai da miji ɗaya muke aure baƙin cikinta ne zaisa na bar mata gidan". Baba yace, "Gwaggo ke da jikarki ai bana shiga zancen ku ba. Kefa kika ce duk wani mai ƙaunarki to ya zuba muku ido a sha'aninku ke da ita, saboda tsakaninku ko aure ba zai raba ba, ƙaunace ta har abada". tace, "wannan magan kuwa na soke ta a yau ɗin nan. Saboda itama halin Hussaina gareta, a fuska su nuna suna yinka amma a zuciyar su kamar su kasheka, ta bayan gida su dinga maka mugun ƙullin da zasu daina ganinka a raye". Ina dafe ƙirji nace, "kai Gwaggo yanzu duk wannan mugun halin ni ɗaya, Ki sassauta min mana kona sami rangwamen zafin zuciya". "karki samu sauƙin zuciya ki shekara ki shekare a cikin zafinta ba damuwata bane, mara kirki kawai". Yaya Abba yace, "Gwaggo mita; to wai ita Inna Hussaina me tayi miki haka ne da kika sanyo ta a gaba, kika kasa mancewa da abunda tai miki tun kina amarya". sai ya riƙe haɓa yace,"kai Allah ya raba mu da riƙon abu a rai irin naki". ai yana rufe baki ta furzar da goron bakinta ta hau sababi,"au wato ni ce ma na sanyota a gaba kenan. To dan yayar ubanka bari kaji abinda tayi min, matar nan saboda baƙar azzaluma ce, na wayi gari wani dare na aza sanwar tuwo, nazo kaɗa kuka bani da ita, gashi ana ta ruwan sama bare na aika yara a sayo min, haka na dinƙa safa da marwa a tsakar gida ina gudun Sahibina ya dawo ban kammala girki ba, Ashe idonta na kaina, taje ta ɗauko kuka a ɗakinta kamar ta Allah ta bani, ina godiya ina jin daɗi nazo na kaɗa miya, tun ina kaɗawa naji jiki na yay sanyi saboda duk babu yauƙi amma sai na barta a ko tsohuwar ajiya ce, sai da Sahibina yazo cin lafiyayyan tuwon dana tuƙa, miyar kuka tace shani kaji daɗi, ashe ƴar tahalikar nan lalle ta bani na kaɗa, tana jin Sahibina ya fara faɗa ta fito tana ce min kayya amma Hannatu wannan abu baiyi daɗi ba, dama sai dana ce miki karki saya wannan kukar bata da kyau ashe ma ƙarshe lalle ne, da tun farko kin karɓi guntuwar dana baki da ba haka ba. kai kuji min baƙar makira, ai ranar naga ƙarshen makirci da iya kissa ganin idanuwana biyu, ranar dai ban ƙwaci kaina ba a wurin Sahibina ba, amma nima dana tashi nayi ƙundun bala sai dana juye mata Maɗaci rabin kwano a cikin damun kokon safe, akan hakan sai data karɓi farar takarda a wurin Sahibina, tsabagen farinciki sai dana yi sadakar ƙuli... Saboda haka wallahi ba za'aje Babaja da ita ba, sai dai ta dawwama a ƙauyen ɗan kande". ta dubi Yaya Abba dake dariya cikin ƙufala tace, "ɗan banza mai kama da ƙosai". Wani abun mamakin sai gani muka yi Gwaggo ta fashe da kuka, duk sai kuma hankalinmu ya tashi, na matso kusa da ita muna ta jera mata tambaya. sai cewa Baba tai, "wallah Auwalu ina tunanin tafiyar nan ne na bar bazawari na, Ya'u mai kayan miya mutumin nan na ƙaunata har ransa, sai dai bazan iya cin amanar Sahibina, domin kuwa har Aljanna shi ɗaya ne zaɓina. Yanzu dai shi Ya'u ka bashi haƙuri kace ya nemi wata amma ban yaudare shi ba, babu yanda na iya ne da ƙaunar Sahibina, duk wanda na aura bayansa tabbas naci amanar ƙauna". Kunyar maganarta a gaban Baba yasa na miƙe na wuce ɗaki ina dariya, banma san lokacin da Baba ya tafi ba, sai can na fara bacci naji shigowarta itama zata kwanta. To haka muka fara shirye-shiyen tafiyarmu, ni dai duk bana cikin hayyacina, idan ka ganni kamar wadda tayi sati tana rashin lafiya, duk na faɗa, ramin idona ya ƙara zurfi. Tafiya ce ta farinciki amma ni babu wannan farincikin sai tarin damuwa daya farma ni, walwalata duk ta tafi, nayi wani suku-suku dani, Gwaggo na lure dani amma bata ce min komai sai dai ta bini da ido tana faɗin, "hmmm". Farhana itace mai kwantar min da hankali idan ina damuwa, itama yanzu bata tani saboda tana cikin damuwar zanyi mata nisa, ni kuma ina fushi da ita. Ko gidanmu bata zuwa yanzu, idan ta kirani a waya ma ƙarƙari tace, "Ina fatan kina lafiya". Da zaran nace ma ta, "ehh Lafiya, hope kema lapia?". shikenan zata kashe wayanta ba tare da ta bani amsar tambayana ba. Yauma naje wurin Yayana na dawo, cikin ɗakinmu na shigo na sami Gwaggo na haɗa sauran kayayyakinmu, kasancewar gobe ne tafiyan mu, na nemi wuri na zauna na haɗe kai da gwiwa ina rera kuka, kun san mene ya sani kuka? Yayana! Karo na huɗu kenan yau ina zuwa wurinsa bana samunsa, babu shi babu dalilinsa, babu kuma wanda zan tambaya yace min ga inda yake, wannan dalilin yasa hankalina tashi, na nemi natsuwar zuciyata na rasa, sai aikin bugawa da sauri da sauri da take, tambayar da nake wa kaina wai anya zan iya ci gaba da numfashi ba tare dana san halin da yake ciki ba? ina ya tafi tsawon wannan kwanakin? Na rasa amsar hakan, sai na kuma fashewa da kuka, ina rayawa a raina in har Baba ya dawo zance masa mu fasa tafiyar nan har sai zuwan ranar da Allah ya dawo da Yayana, idan yaso sai na fa ke masa da wata ƙaryar dana san zai ɗoru akanta, tunda duk abinda nace yanayi. Ina wannan kukan ne naji Gwaggo na cewa dani, "ke ɗago ki kalle min nan ki bani amsa sai ki koma ki ɗora daga inda kika tsaya". Tana faɗa da nuna halin ko'in kula akan kukan nawa, wanda ni kuma hakan ke ƙara bani haushi, dan atleast ina so a kula dani a wannan lokacin. "yo baiwar Allah ina miki magana ne fa, kuma nasan kin jini amma kinyi uwar kunnen shegu dani". ta kuma cewa dani, sai a sannan ne na ɗago, a tunani lna wani abun arziƙin zan gani, sai ta wani nuna min gajeran wandon Yaya Abba tana faɗin, "kema naga ƴar ƙwallo ce, za ki san takan amfanin kayan, wannan naga ya tsufa da yawa zai yiwa Abba amfani ko nasawa almajirai saboda naga mazaunansa duk sun ɓuɓɓule, kuma wannan rigar ma naga hammatar ta ɓeke, kuma duk bashi-bashi suke, na bayar ko na bar masa kayansa?". Haushi baisa na bata amsa ba, na maida kaina naci gaba da kukana, sai dai a wannan karan kukan zuci ne nake bana hawaye ba. ina jin Gwaggo na doka tsaki tana faɗin, "karki bani amsa ɗin. Idan kinji haushi kin amsa ke ɗin ba rainona bace, miskila kawai uwar nurƙufanci, kici damuwarki ke kaɗai tunda babu wanda ya isa ya tambayeki abunda ke damunki ki faɗa masa. Ni kuma idan na ƙara tambayanki tagwagwa ta gwagutse min". Har dare Gwaggo bata sake kulani ba kuma nima ban kulata ba, ni haushina ɗaya akanta da taƙi zuwa ta lallasheni naji sauƙin abinda ke damuna, sai dai ina jinta tana ta kai komon haɗa kaya, tana yi tana waƙarta cikin nishaɗi, tai waƙar Mamman shata da ɗan ƙwairo, ta kuma juya tayi ta yarensu na buzanci. Idan tayi ta gaji ta hau mitar ni da Yaya Abba bamu da tausayi sam, tana tsohuwa da ita amma mun barta da hidimar haɗa kaya, to walle ba don ta gaji da wannan gidan mai rufin kwano da yoyon ruwa ba, sai dai a fasa tafiyar. haka Ina jinta da Yaya Abba ya dawo yana tambayarta abincin dare, tace yaje ya duba kitchen akwai daddawa ya daka yay kwaɗo idan zai iya ci kenan, idan kuma ba zai iya ba ya bar mata abinta idan aljanun kaina sun sake ni ƙila ni naci, idan kuma duk ba zamu ci ba sai a barshi ya zama rabon almajiri, domin itama baci zata yi ba, ita da abinci sai na sabon gida. Baba daya zo yaji ni shiru ban fito ba, suna tsaka da hira shi da Gwaggo da Yaya Abba yake tambayana ina ina, tace da shi, "tana can ƙuryar ɗaka tana fama da aljanun miskilancinta, yau ban san uwar da akayi mata ba har suka zo ɗaukan fansa. Ƙilan kai idan ka kira ta tazo tunda suna jin maganarka sa tafi, amma ni da basa gani na da gashin ido ko ta kaina ma basa bi". Tana maganar ne tana shan raken da Yaya Abba ke ɓare mata. Baba ya ƙwala min kira, na ansa ina miƙewa, ban fita ba sai dana saita natsuwa ta, na sami guntun ruwan ledan pure water na wanke fuskana, saboda a rayuwata bana so naga Baba ya fuskanci ina ɗauke da damuwa, yanzu sai hankalinsa ya tashi. Duk yanda naso ɓoye damuwan abun yaci tura, domin kuwa ina zuwa Baba ya shiga tambayana abunda aka mani, kamar nace masa bana son tafiyarmu sai kuma naga rashin dacewan hakan, na ɗago na dube shi nace, "Baba babu komi". "ba kya min ƙarya karki farata a yau, mene aka yi miki?". sai na tsinci bakina da faɗar abun kwata-kwata babu lissafinsa cikin kaina. "Baba ina fargaban zaman mu da su Aunty ne". Yace na taso na dawo kusa da shi, cike da kulawa da kuma lallashi yake ta bani baki har naji zuciyana ta fara sanyi. Washe gari tunda ƙarfe takwas Baba ya kira waya yace to mu shirya ƙarfe sha ɗaya ne zamu tafi. zai aiko mana driver ya tafi damu, shi kuma zai tafi da matansa. Ina jin hakan nayi maza na faɗa wanka, cikin sauri na shirya na fito na gillawa Gwaggo ƙaryar data hau ta zauna akai, domin kuwa ce nayi ma ta Malam Albani ne ya kira yace yanzu naje makaranta suna son ganina, da yake zancen na makaranta ne bata musa ba tace,"Sai kin dawo Allah ya kiyaye, amma kiyi sauri kin dai ji abinda gyatuminki yace". "insha'Allahu yanzu zan dawo Gwaggo. Amma fa sai kin bani kuɗin mota saboda nafi sauri, kinga bada Farhana zamu tafi ba, koma da ita ne ɗin motanta ya lalace". Nan da nan ta kunce gefen zanenta ta ɗauko dalleliyar ɗari biyar ta bani, yanzu tana ji da tashen kuɗi, saboda ko jiya Baba dubu biyar ya bata da daddare. Ina fita na tari mai napep ya kaini Sharaɗa, a mazaunin Yayana a wurin nace ya ijje ni, na sauko na taka na ƙarasa zuwa wurin, ina ta dube-dubena da lalube na ban ganshi ba banga inuwarsa ba, ji nayi kamar na kurma ihu, idona ya ciko da hawaye, cikin zuciyata nake rayawa ko dai Yaya ya daina zaman wurin nan ne saboda ni, tunda yace na bar zuwa wurinsa naƙi, lokaci guda hawayen da nake ƙoƙarin dannewa suka sami nasarar gangarowa, nasa hannu na goge, shikenan yanzu yay min nisan da bazan kuma tozali dashi ba kenan, yanzu nasan yana can yana shan tabarsa, naji zuciyata kaman zata fito waje saboda ɗacin da take min. Sai kuma nayi wani tunani, Yayana zai iya tsere min ne a iya lokutan daya san zan iya zuwa wurinsa, amma tunda ba shi da ko'ina jazaman dare yayi zai dawo wurinsa domin kwanciya, Da sauri na buɗe jakana na ɗauko wata takarda da nai rubutu tun a gida mai ɗauke da taƙaitattun bayani kaman haka. _ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya Yayana, don Allah idan kazo ka nemi waya ka kira ni, zamu bar garin kano mu koma abuja da zama, ina maka fatan alkhairi. Ƙanwarka Sabina._ sai daga can ƙasa na zuba numbobin wayana guda biyu, wayar da a daren jiya Baba ya bamu ni da Yaya Abba. Kangon na shiga na sami inda zai iya katari da ita daya shigo na soke a wurin. Tukunna na fito na koma cikin napep ɗin muka juya, damuwar duniya ta tarar min aka, gefe guda rashin sanin taƙamaimai halin da Yayana ke ciki, ɗayan gefen fargabr zamanmu da Matan Babana, daga Anty har Umma babu mai sona a cikinsu, ko me na tare musu oho, sai dai nafi alaƙanta hakan da irin son da Baba yake min shine yasa Anty ta tsaneni, ita kuwa Umma haushinta da ni sunyi zaman kishi da Mamana. har ƙofar gida ya ajeni, lokacin da naje driver'n mu har ya iso a cikin mota ƙirar Sienna mai azababben kyau, ta burgeni sose sai dai yanayin damuwan da nake ciki ba zai barni nuna jin daɗina ba a fili, amma mamaki na cewar motar mallakinmu ce bai barni ba. Ina shiga Gwaggo na cewa, "yauwa kin dawo". "ehh". Shine nace da ita a taƙaice ina goge hawayen gefen fuskana. Na wuce zuwa ɗaki tabi bayana da kallo tana karantar yanayin nawa. "ke lafiya kuwa, ko wani abun ya faru a makarantar ne na ganki a haka?". Gudun kar ta hauni da tarin tambaya sai nai maza na ɗau buta na faɗa toilet. Na wanko fuskana kana na fito ina ƙaƙalo murmushi, ina kallonta nace, "Gwaggo wai har an fito". "ehh ke kaɗaima muke jira. ina tambayanki kin mani shiru baki bani amsa ba, nace lafiya naga kin dawo kamar wadda aka yowa akaina uwa da uba sun mutu lokaci ɗaya". "Gwaggo na biya ne munyi sallama da Farhana". tana taɓe baki tace, "uhmm shine idonki yay wannan jawur ɗin haka. to naga dai kashin awakai ma suna rabewa bare ku da zaku iya ziyartar juna a duk sanda kuka so...kai Wannan lokacin aurenku kwai lusin". Ƙarshen furucinta ya bani dariya wai looking zata ce shine lusin. Mu uku muka ɗunguma zuwa mota, Yaya Abba a gaba ya zauna, mu kuma muka shiga baya. Da la'asar muka isa Abuja, gidanmu a wani estate yake na manyan mutane, cikinsa baki ɗaya gidaje ne na alfarma, kai daka shiga kaga estate ɗin masu muƙami, a gida na tsakiya mai lamba uku mukai horn, aka buɗe mana tangamemen gate ɗin gidanmu, ya ilahil alamina, Aljannar duniya kenan, mai karatu karka so kaga haɗuwa da tsaruwar gidanmu, wai tun bamu shiga cikinsa ba kenan, ta ko'ina fitilu ne ke haskawa, yayin da wasu haɗaɗɗun flowers ke mana maraba. Part part na gidan ya kai kusan 7, nan Baba ya fara mana lissafi, part ɗaya nasa, ɗaya ni da Gwaggo, ɗaya na Anty da ƴaƴanta, ɗaya na Umma da nata yaran itama, sai na Yaya Abba, sai kuma na masu aiki, sai ɗayan da babu kowa. Nan ya kuma zagayawa damu zuwa wajen parking lot, wayyo Allah nah, wasu tsadaddun motoci ne cikin wata rumfa kamar a ƙasar turai, in taƙaice muku dai ginin gidan kamar a saudiya. Baba ya nuna min wata arniyar mota fara mai tintend glass ƙirar lambogini, ya juyo ya dube mu ƴaƴansa mu shida, yace" ina kike Sabina". Na matso kusa ina faɗin, "Gani Baba". Maƙullin mota ya miƙo min, nasa hannu na amsa, abinda nake rayawa a raina shi kuwa ya tabbata. Domin buɗar bakin Baba cewa yay dani, "wannan farar motar taki ce Sabina". Kan ubancan, ai ban san lokacin dana buga tsalle nai sama na dire ƙasa ba, na kaiwa Gwaggo wata muƙura na ƙanƙameta, saura kaɗan ya rage ta zube ƙasa na riƙo kayata, daɗiɗin duniya ya gama baibayeni, ihun murna nake ina kwaranyowa Allah godiya daya mana wannan arziƙi, na sake ta na dawo wurin Baba, a kunyace naje jikinsa na rungume shi, adu'a nake masa da kuma tarin godiya, shima yasa nasa hannu ɗaya ya rungume ni yana sanya min albarka. Hmm wani abun dariya sai kunga matan gidanmu, yanda suka kumbura kamar an hura baloon tana jiran fashewa, kowacce sai faman aika min da saƙon harara take, baƙin cikinsu na daɗa fitowa ƙarara, har Umma ta kasa danne zuciyarta tace. "to amma Alhaji ga sauran yara a gabanka sai ita ɗaya ne zaka ma kyauta daga zuwanmu, kuma kyauta ma harta irin mota mai shegen tsada, motar da sai a ƙasar turai ake ido huɗu da ita". cikin rashin nuna gane lissafin nata yace,"banda abinki Hajara ai cikinsu itace Babba, suma za'a basu amma ba yanzu ba". Baba na shiru Gwaggo tace, "to shi mai sunan Sahibina ba zaka bashi bane?". Baba yace, "shi da yake magajin gida Gwaggo, ai ragamar komai na hannunsa, da kansa zaizo ya zaɓa". tai wani murnushi na ƙulawar sannan tace,"auto yanzu naji bayani. Tunda ka gama da marayun ƴaƴana, can ta matsewa sauran, su samu ko kar su samu ko a katarina". Ta dubi Yaya Abba, cikin mutunci yau ake masa magana tace, "mai sunan Sahibina zo ka zaɓa ka dirje, kamin ƴan baƙin ciki su haɗiya zuciya su mutu ba suga arziƙinka ba. Hakan ba zai min daɗi ba sam". _Hmm Ya kuke ganin zaman wannan gida zai kasance?_ _Ina Alhussain ya shiga?._ _shin ko zaiga takardar da Sabina ta bar masa?._ _Ko zasu ƙara haɗuwa?. idan da rabon zasu ƙara haɗuwa to aina?_ *Please Comment, Vote and Share.**AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(10)* baba ya girgiza kai, a yanayin yanda Gwaggo tai magana fuskarsa ta nuna rashin jin daɗi, to amma babu damar yayi magana, dan yanzu zata dire masa tace dama shike ɗaure musu gindin zaluntar marayu, duk wani abu da suke da sanya hannunsa a ciki, shima dama ba ƙaunarmu yake ba, kuji fa, wai mu da ubanmu amma abu kaɗan zaiyi za tace baya sonmu. Ni dai da har yanzu daɗi bai gama saki na ba tuni na nufi motana na buɗe na shige ciki ina dubawa, shi kuwa Yaya Abba na daga zaune kan wata kujera ya zuba ido yana kallon abinda ake. Anty da ta ƙware wajen iya kissa nan da nan ta kawar da baƙincikinta ta hau borin tayani murna, Anty macece da ta tsanemu sosai ni da Yaya Abba, don da tana da ikon kawar damu da tuni ta aikata hakan, amma kuma fa duk wannan ƙiyayyar ta ƙware wajen iya kissa da makirci, domin bata taɓa nunawa tana ƙinmu a gaban Baba, Ta inda tafi Umma wayo kenan, domin ita Umma agaban kowa nunawa take bata son ƴaƴan mijinta. Shi yasa Baba idan zaka kwana dubu kana ce masa Anty tayi Laifi baya yarda, Ita kanta Gwaggo da ba ta yarda da laifinta, saboda Anty makirar macece, Kuma ko laifi tayi to tasan hanyar da zata wanke kanta, amma itama tun a inda Gwaggo ta rafkowa lamarinta, ranar da tace Ya Abba ya shigar Mata ɗaki. Anty ta taho inda nake tana ta fara'a tana ce min, "Masha'Allahu mota tayi kyau sosai, inye su Sabina an zama ƴan gayu, lallai arziƙi mai daɗi, gaskiya na tayaki murna wallahi, Babanki ya gwangwajeki ƙwarai matuƙa, duk randa aka fara driving ni za'a fara ɗanawa, sai ki masa adu'an Allah ya ƙara wadata arziƙinsa ya kuma kare shi daga sharrin maƙiya mahassada, kema kuma Allah ya rabaki da sharrin ƙarfe". Duk tana faɗaɗa fara'arta take tayani murnar, wanda sam bai kai har ƙasan zuciyrta ba. hmmm amma kunsan me? saboda baƙar mugunta kunsan kuma abin ba don Allah take ba, hannunta na kan wuyana tana bani wani mugun mintsini, da naga tana neman raunana min wuya sai na fito a motar ina yaƙe domin shegen mintsininta ya shigeni, na sauke hannunta daga wuyana na riƙe a hannuna, inama ta murmushi nake cewa, "ameen Anty na gode sosai". Na faɗi hakanne saboda Baba dake tsaye a wurin, nima kuma cike da mugunta na ganyarata ma ta mintsini a hannunta dake cikin nawa, ba shiri ta janye hannunta tana yaƙe da dukkan alama ya shigeta kamar yanda nata ya shige ni. Na juya wurin ƙannena nace su zo su ga motar, dan suna tsaye ne kamar gumaka, to dake kowacce ta ɗauko halin uwarta haka suka zo suna leƙa motan suna tayani murna, fuska babu yabo babu fallasa, ni dai a raina nace oho muku, ni bana riƙo da irin yanda kuke min, kuma Allah ya ganar daku. Sai da Baba ya gama nuna mana komai na gidan sannan kowa ya wuce part nasa. Ina shiga side namu na raka Gwaggo ɗakinta, na nuna mata yanda ake amfani da duk wasu abubuwa musamman ma na banɗaki, ni ɗin ma ba kowanne abu na san ta kansa ba sai dai na jarraba musamman Ac. Duk wannan abun gwananintar da nayi ma ta ban burgeta ba, Sai da tayi min tsiyarta da ta saba. Harda cewa ai ruwan zafin hita da akasa yake zuba a famfo da gangan aka saka don ya salluɓe ma ta fata ne saboda an san ba iya amfani zata yi da shi ba, to ita a cire shi kawai. ni dai bance ma ta komai ba, ita kanta dariyar ƙeta take min harna gama na fito. Ɗakina na wuce kai tsaye, ina shiga na hau cire kayana domin yin wanka saboda duk a gajiye nake. Wanka nayi da ruwa mai ɗumi sirke da turaruka masu ƙamshin gaske, da aka jere su a toilet ɗin, ban wani jima a ciki ba na fito, ina fitowa na shafa mai da kuma faran powder. closet na nufa na zage domin ciro kaya, cak na tsaya ina riƙe da baki na saboda mamaki, kamin na buga tsalle na kurma ihu saboda daɗi, ashe shiyasa Baba yace babu buƙatar mu taho da kaya, mu bada duk waɗanda muke da su, kayan na shiga dubawa ɗaya bayan ɗaya, shegun kaya ne na alfarma kamar wata amarya aka zuba min a ciki sunfi set 30, Kuma duk abayas sunfi yawa dama sune favorite nawa, ban san lokacin dana zube kan gado ba ina hawayen farinciki ina kuma kwaranyo Baba adu'a, oh ni Sabina ban taɓa mafarkin tsintar kaina a irin wannan daular ba, ko da kuwa a gidan miji duk kuwa da ina fatan samun miji mai yalwar arziƙi na halal, sai gashi ashe zanyi katari da shi tun a gidan ubana, lallai arziƙi na ubangiji ne, shike badawa da hanawa a duk lokacin daya so. Wata dark blue abaya na ciro mara nauyi na saka, sannan nabi lafiyayyan gadona na kwanta, nan take kuwa bacci yayi awon gaba dani. Bani na farka ba sai da ana sallan isha'i, da sauri na diro akan gadon tunawa da nayi banyi sallar magrib ba, ina toilet ina ta ma kaina dariya, Ƴar ƙauye an haye gado anji laushin katifa, naji daɗin baccin da ban saba yinsa ba. Ina zaune bisa sallaya ina karatun qur'ani sai naji landline ɗin dake aje a drowern gefen gado na ƙara, banma lura da zamanta ba sai ayanzu, na miƙe da sauri na ƙarasa don ɗauka domin nasan kiran baya rasa nasaba da Baba tunda dai shine yay mana connecting baici ace kowa na da numban kowa ba. Ina ɗagawa naji Baba yace, "ki fito parlo ki same mu". Na amsa masa da, "to Baba". Daga haka shi kuma ya kashe wayan. ina gyara zaman veil na fita zuwa parlo, yanda na sami duk ƴan gidan kowa a zaune kan kujera yaran kuma a ƙasa, na san magana ce mai muhimmanci Baba ke so yayi damu. wuri na samu na zauna nan ƙasa da gefen ƙafar Gwaggona, sannan na ɗago da kaina na gaida su Umma. Anty na washe min haƙora ta amsa min gaisuwar tawa, saɓanin Umma data amsa min a ciki-ciki kuma fuska a turɓune. Baba yay gyaran murya yace da Yaya Abba yayi adu'a. Bayan gama adu'a Baba ya fara magana akan abinda yasa ya tara mu, maganar duka akan nasiha ce da kuma faɗa akan zaman lafiya,. Ƙwalla na taruwa a idona nace, "insha'Allahu Baba zaka same mu da yin abinda kake so, ko domin farincikinka da kuma kwanciyar hankalinka". Yace da ni, "Yauwa Sabina haka nake son ji, Allah yayi miki albarka. Dama nasan ke baki da hayaniya". na amsa da, "amin". Cikin farincikin adu'ar da yayi min. kishin wannan adu'ar yasa ƙannena suma suka ce, "insha'Allahu Baba, ba zamu yi abinda zai ɓata maka rai ba". Amma ba wai don sunyi niyya ba saboda da yayi maganar babu wadda tayi yunƙurin magana. Anty ma tace, "karka damu Baban Abba, adu'an kawai da zamu yi shine Allah ya bamu zaman lafiya. Amma ni ta ɓangarena babu wata matsala". "nima haka". Umma ta faɗa murya can ƙasa fuskarta na nunawa da abinda ke cikin ranta. Sai da kowa ya gama magana sannan Gwaggo ta gyara zamanta, ta taɓa kafaɗata tace, "ke hayo nan". Na miƙe na hau kujera kusa da ita na zauna, ta kuma dubana tace, "kinji daɗin zaman?". Nace ma ta, "ehh Gwaggo". ta dubi Yaya Abba tace, "kai Abba tashi ka kashe min wannan na'urar sanyin, kasan ina da mara lafiya, ba zai yiwu ni a ruɓar dani ba, ita kuma Albarkar tawa da nake ji da ita a bar min ita da jinya". Yayi kamar bai jita ba yaci gaba da danna wayarsa, domin yasan sarai rigima ce irin tata yasa tace a kashe, gari dai bana damuna bane babu sanyi ko kaɗan, Yanzu haka zafi-zafi ake, to amma ni kuma jikina baya son sanyi ko kaɗan, idan kowa zaice yana jin zafi ni kuma zance sanyi, ita kuma Umma jikinta irin shirgegen nan ne, bata shiri da zafi ko kaɗan, duk sanyin da ake zaka same ta tace a kunna mata fanka ko kuma ta fito shan iska, Ko bini-bini kaga ta yayi mi mafici ta hau firfita, yanzu haka ma saboda yanda ta ɓaɓɓashe iska na shigarta ta ko'ina yasa Gwaggo tace a kashe Ac. ta haɗe rai ta kuma cewa, "Abba dan ubanka Auwalu dake gabana a yanzu, nace ka miƙe ka kashe min na'urar bada sanyi ko". Baba yace, "kai Abba ba magana ake maka bane". Sai a sannan ya miƙe yaje ya kashe Ac'n ya dawo ya zauna, Gwaggo kuwa ta fusata ta hau masifa tana faɗin, "yo ni idan na faɗa maka Abba baya ganin girmana ai baka yarda. Amma yanzu da yayi a gabanka sai ka tabbatar". Yaya Abba yace, "nifl fa ba ƙin tashi nayi ba Gwaggo, ba kiga ina ƙoƙarin miƙewa bane, kuma tunda nake dake kin taɓa sa ni abu naƙi yi ne". "yo Abba na nawa kuma, kuma ai ba yau ka saba ƙaryatani ba. Kaci mutunci na agaban waɗannan marasa kirkin kaji ko, in yaso kai da su sai ku haɗu kuyi min fitsarar san ranku". jan baki yayi yay shiru bai tankata ba. Gwaggo tabi kowa da kallo ta taɓe baki sannan ta juya ta dubi Baba tace, "to Auwalu ni magana ce nake son nayi, wadda gaba ɗayanta kashedi ce da kuma jan kunne. A tou; ƙwamma a buɗe kunne da kyau a saurareni". "to Gwaggo muna jinki ai". Ya faɗa cikin rissinawa da girmamawa. "a'a ni fa kai tsaye bada kai nake ba, su wancananka ai sun san kansu, uwayen kilibibi da iya kisisina". ya sake cewa "Gwaggo a dai yi haƙuri, shi yasama na taramu anan ɗin gaba ɗaya". "oho dai, ni ka tara ko karka tara dama ina da niyyar isar da wannan saƙon tunda Allah ya haɗamu zama wuri ɗaya. gida dai arziƙin ɗana ne dole na zauna a cikinsa tunda bana uban kowa bane, gida kuma na uban Sabina ne zamanta cikinsa daram dam-dam ehe, babu shege daya isa ya raba inuwarta da ubanta". Anty da ta san dasu ake ta kwantar da murya tace, "Hajiya Gwaggo kiyi haƙuri, duk abunda ya faru a baya ya wuce...". Ai bata kai aya ba Gwaggo ta dakatar da ita tana faɗin, "munafuka ke kika kaini Hajji dana zama Hajiya, kina wani kwantar da murya da sadda kai kamar ta Allah, baƙar makira Allah a fuska Fir'auna a zuci, Yo Zara'u ni ai sai dai ki gayawa wani baƙin halinki, domin farin sanin dana yi miki ko uwar data haife ki bata sanki ba, saboda haka ki daina wani ƙumbiya² ki fito sak a mutum ki faɗa musu sabon tuggun da kike shiryawa a zuciyarki, saboda ni bana karantar fuskar Mutum sai dai na karanci zuciyarsa, wannan baiwar tawa ce ni ɗaya da Allah ya bani. ki sa ni da kyau saboda ki kiyaye gaba, domin kina ƙara aikata abunda ban gamsu da shi ba zan sanya Auwalu ya yanka miki Jan kati, akan Sabina babu abinda ba zan iya ba". Kuka Anty ta saka tana faɗin, "wallahi Gwaggo ba sanin da kika yi min da bane, ki bar yimin wannan mummunar fahimtar a yanzu". Gwaggo ta taɓe baki tace, "ki bar ɓarnatar da hawayenki a banza kina kukan munafurci, Kina yaudarata kina yaudarar kanki, da kika ganni nan na zauna cikin kishiyoyi babu kalar kissa da makircin da ban sa ni ba, don haka kisan a inda za kiyi". Baba yace, "Gwaggo ke fa uwace, faɗa ya kamata kiyi musu da nasiha, amma duk wannan ƙananun maganganun basu taso ba". Ta kalle shi ta kuma kallonsa, sannan ta bishi da kallon sama da ƙasa, kamin nan ta ciro Goro a gefen zanenta ta wurga a baki tana faɗin, "to Auwalu nuna min yanda zanyi kaji kai da kasan dai-dai, har ni dana haifeka zaka nunawa kafi ni sanin abinda ya kamata, ahh lallai ne, aikuwa to ka ƙara magana a wurin nan zan tattatara komatsaina na koma ƙauyenmu, tunda na lura kafi ƙaunar ka zauna da Matanka a sabon gida sama da ni da nayi naƙudarka". "ba haka bane, kiyi haƙuri Gwaggo Allah ya huci zuciyarki". "Ameen". Ta faɗa a taƙaice. sannan ta ƙara cewa, "yauwa ana jina ba. Naji ana cewa babu wata matsala Allah ya bada zaman lafiya, ehh to ameen amma ba anan gizo ke saƙar ba, Ita dai Sabina da bakwa ƙauna ta zame muku ciwon ido domin babu yanda kuka iya da ita, saboda ina tsananin ƙaunarta Mahaifinta kuma na mutuwar sonta, saboda haka muddin ana son zaman lafiya a gidannan dole a ɗauke baƙin ido da mugun baki a kanta, gata nan ita kaɗai mahaifiyarta ta haifa mace, ni kuma na maye gurbin uwarta, A kiyaye ɓacin ranta, domin a duniyar nan idan ana ƙaunar aga ɓacin raina to a taɓa min ita. kun san da wannan amma yana da kyau na maimaita muku don naga baku da hadda. Farincikinta kaɗai nake son gani a gidan nan, kar a kuskura naga saɓanin haka, kallon banza wannan kuka yiwa inuwarta billahillazi ina shaida muku sai kun bar Habuja kun koma gidan iyayenku, musamman ma ke kumbusa (Umma kenan), saboda haka muddin ana son zaman lafiya da kwanciyar hankali ta ɓangarena to kar a taɓan marayun Ƴaƴa, duk da dai shi Abba ba kirki ya cika ba amma a ha nake sonsa, saboda haka a kiyaye, a tou; domin ni nafi ɗan iska iya shege, yanzu sai aga ba dai-dai ba". Sannan ta koma kan ƙannena ta kira sunan su ɗaya bayan ɗaya, "Aisha, Aminatu, Zainab da ke Khadija. Allah ya halicce ku a mutanen kirki amma kun rikiɗe kun koma na tsiya duk kun ɗauko halin uwayenku, to kuma kuji ni da kyau. Sabina dai da kuke gani ba sa'ar ku bace, saboda haka dole ku bata girmanta, ku manta da batun cewa ita zata dinƙa baku kamar yanda kuke so, ita ba waina bace da zaku dinƙa juyata son ranku saboda kunga tana da haƙuri. Ƴan banza masu zubin Ƴaƴan kwaɗi. to dai-dai da rana ɗaya akasin abinda na faɗa ya faru saina kai yarinya ƙauye nayi sadaƙar ta ga tsohon daya kusa shuɗewa, in yaso Yarinya ta zama bazawara da ƙuruciyarta ni babu ruwana". Zainab na turo baki gaba tace, "to ai Gwaggo ba laifinmu bane, mu yanda ake nuna banbanci a tsakaninmu ne bama so, tsakani da Allah muna uba ɗaya amma sai a dinƙa nuna anfi sonta taya za'ai muji daɗi". ta gwame baki tace, "idan so kuke a so ku ai sai ku zama mutanen kirki irinta". ta juwa ga Baba tace, "ni na gama magana. Kaima idan ka gama taka sai kowa ya tashi ya bar min parlo". Baba yace, "ehhh Gwaggo ai tunda kin gama shikenan". tace, "ka dai ƙara dubawa ko kana da ta cewa". "babu Gwaggo". "tom shikenan". Har zata miƙe sai kuma ta koma ta zauna, "au nayi mantuwa, sai batun girki kuma. Bana son wani girkin ƴar aiki a gidan nan, kowacce zagewa zata yi ta dunƙa dafawa marayun Ƴaƴana suna ci suna ƙoshi, tunda ba auroku akayi dan kuci kuyi kashi ba. A tou; nan dai ba tsohon gida bane bare ayi abinda aka ga dama, kar aji laushin katifa da sanyin AC ace za'ake jaɓarewa ana ƙara kumbura". Baba ya dubi Yaya Abba yace, "kai Abba sai ka dinga fita da Sabina kana koya mata mota B4 ending of this month, saboda already na sama mata addmission next month zata fara lectures". "tom Baba, Allah ya kaimu". Baba ya ɗauko wata baƙar leda a wurin, kwalin wayoyi ne a ciki, takan ƙananun ya fara bawa, ya kira Khadija ya bata tata ƙirar Tecno Spark 4, Zainab kuma Infinix S5, Aminatu da Aisha iri ɗaya suma, infinix Zero5 sannan nima ya miƙo min tawa ƙirar iphone 11 yace na bashi waccen daya bamu, kwacce da sim card ɗinta ya bata, kuma take a wurin yay mana recharging ta bank kowaccen su 2k, ni kuma 3k". Dukanmu muna murna muke masa godiya da adu'a. Daga haka kowa ya watse aka tafi kwanciya. _Na Sadaukar Da Page Ɗin Gareki Siddeeqer Oumar Barde, kiji dadinki kuma ki sani ina yinki over._ *Please Comment, Vote amd Share.**AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(11)* Shirin sauri nake tayi Yaya Abba na jirana zamu fita koyan mota. Baki ɗaya na hargitso da kayan sawata na rasa wanda zan saka, saboda na riga na saba tun muna tsohon gida bana iya saka kaya idan zan fita sai wanda Gwaggo ta zaɓa mani, gashi ita kuma yau ta shige toilet tayi zamanta kamar ta shiga labour room. Kiran wayar Yaya Abba ne ya shigo a karo na ba adadi, kai na dafe na share ban ɗauka ba, saboda idan na ɗauka fa raina zai iya ɓaci matuƙa, shi mutum ne wanda ya tsani delay a rayuwa, shi yasa ma ba kasafe ya fiya haɗa fita da wani ba. har lokacin da nake tsaye kamar nai kuka banga alaman Gwaggo zata shigo ɗakin ba, kayan na yayiba na fita da su zuwa ɗakinta, a bakin gado na sameta zaune ta riƙe baya tana ta sauke nishi, kayan na zube a gabanta bakina a gaba ina daɗa turɓune fuska. ta ɗago tayi min kallo mai kama da harara sannan tasa ƙafa ta shure kayan. tukunna a ƙufule tace da ni, "ke fa ba ki iya ganin mutum cikin wani hali ki masa sannu ba ko ki tambayi meke damunsa, a'a ke fatanki a biya miki buƙatarki, to sai ki jira sai na gama wartsakewa". "Eyyah Gwaggo tah wallah nai zaton ko kinyi training ne, ban kawo wani abu ke damunki ba". Wani wawan kallo ta wurgo min wanda yasani yin shiru da sauran maganata. "to idan kin aza sai ki sauke ba training nake ba, zawo nake fama da shi, shiga ta banɗaki na huɗu kenan a cikin rabin awa. Ban yarda da abincin jiya da muka ci ba, ina tunanin waɗannan ƴan iskan sun fara mana barbaɗe a abinci". Da sauri na ƙarasa wurinta cike da tausayawa, duba da yanda idonta ya faɗa lokaci ɗaya. "Subhanallahi, Gwaggo Zawo kuma? to taya akayi hakan? me kika ci da za ki kwanta?". ta ƙara kufula tana cewa,"da wanne yare nayi miki maganar da kika kasa fahimta, ko kuma ƙara maimaita miki kike so nayi, ba kiji nace ina zargin masu kama da tantabarun can ba. Mutum na fama da kansa dole sai kinsa yayi magana". taja guntun tsaki, "ke sam ba ki da saurin fahimta, dole idan za'ai miki bayani sai an faɗaɗa shi, kisa aita doguwar magana". nace, "Gwaggo to aini ban zargesu ba ne, tunda abincin nan dai nima na ci shi, wataƙila dai ko cikinki ne ya ɓaci kawai". ƴar maganar da nai kuma sai ta jawo masifa da sababi, faɗi ta ke,"auto ni za ki gayawa cikina ya ɓaci dake ban san takan cikin nawa ba. Da can da nake girkina naci lafiya na miƙe lafiya fa, da kika ganni sarai nasan takan lafiyar cikina, wannan girkin dai dole anyi wani barbaɗin a ciki domin nasan halin mugwayen matan Babanki, so suke su ƙarasa ni kuma ba yanzu ba, kema Allah ne ya kiyayeki, saboda haka bazan iya ci gaba da wannan haɗakar girkin namu da su ba, anyi an gama daga jiya, kowacce cikin su tayi nata taci da iyalanta, mu kuma yazo ya samo mana wadda zata dinga yi mana namu, wacce zuciyarta ta cika fal da tsoron Allah". Ni dai ina dafe da bayanta nayi murmushi, saboda ban isa na hanata wannan mitar da masifar ba sai kuma ta samu lafiya, cike da tausaya ma ta nace, "Sannu Gwaggo, bari a kira Baba sai ya turo likita". "ehh kirawo shi ɗin, dan cikina a ɗaure yake ni ɗaya nasan irin azabar da nake ci. Ba don ina gudun haɗa rigima ba ai da saina zayyane masa wannan muguntar da aka haɗa min, amma Allah dai...". sai kuma tayi shiru tare da yin ƙwafa. Cikin faɗa kuma taci gaba, "ni dai kaf cikin Yarana babu mai halin kirki irin Auwalu. haƙuri, mutunci, karamci komai ya haɗa, amma kuma duk cikin Ƴaƴana shi ɗaya ne bai yi sa'ar Mata ba, Mahaifiyarku kaɗaice ta ƙwarai, sauran auran nasa kam sai dai a kira shi da auran ƙaddara, jiya na gama yarda da duk wani mugunta nasu da kuke faɗa nake ƙaryataku, saboda kwana nayi ban runtsa ba ina kokawa da cikina. dama duk wani iya shege da suke ina ɗaga musu ƙafa ne saboda darajar Auwalu da suke ci amma na kusa yiwa tufkar hanci, kaf ɗin su za su gane shayi ruwa ne. Hmmm banda ma dai ina da tausayi ai da sai naja musu Allah ya isa, to idan naja musu binsu zatayi su zo su ƙara lalacewa, ni kuma gyaruwa nake so suyi kar a tafi lahira da tarin zunubai, tunda dai Allah ya ƙaddara auren su da Ɗana". ta juyo ta kalle ni, wadda nayi shiru ina sauraronta, ince tace nace shi yasa ma nayi gumm. tana wurgan harara tace, "kinyi shiru ba ki ce komai ba". nace, "to Gwaggo ni me zance". "ki faɗi abinda yake zuciyarki karta kasheki, saboda ina faɗar gaskiya shine kike jin haushina, to sai dai ko me za kice kice ehe, sirikaina ne amma bana sonsu, saboda mutanan sun cutar min daku, yanda bana manta akhairi haka bana manta sharri. ai tsakanina da su Allah ya...". Sai kuma tai shiru bata ƙarasa ba, ni kuwa dariya ce ta taho min, duk masifar da Gwaggo zata yi akansu da zarar tazo kan Allah ya isa to fa ba zata ƙarasa ba sai tayi shiru. "ki sa ki dariyarki mana ki bar ƙunsheta kina cutar kanki, ina faɗa miki gaskiya tausayinsu nake ji ne saboda bakina kaifi ne da shi kamar wuƙar daba, inaja musu Allah ya isa binsu zatayi kuma tabbata lahu sai sun lalace, ai nayi na gani ne, tunda najawa kishiyata Hussaina har kwanan gobe gata nan halinta bai sauyawa ba, iskancinta sai ƙara gaba-gaba yake taƙi tayi dai-dai". na sauke numfashi ina cewa,"yanzu dai Gwaggo kiyi haƙuri ki rabu da su, kowa yayi na gari kansa, ki barsu da halinsu, kuma insha'Allahu kamin nan kamin anjima za ki sami sauƙi, na kira Baba yace Family doctor zai zo". tace, "ai shikenan nayi shiru tunda kinsa baki, amma batun haɗakar girki kam ya ƙare, ni lokacin hutuna ne yazo tunda Allah ya kawo mu cikin wannan ni'imar, kema kuma bana so ki wahala, wannan aikin gajiyar kin gama shi tun a tsohon gida sai kuma bautar gidan mijinki. Saboda haka zan kira Karima idan zata zo ta samo min ƴar budurwar yarinya mai hankali da tsoron Allah". Kamin na buɗi baki nayi magana Zainab ta shigo ɗakin ɗauke da sallama bakinta, Ta tsuguna har ƙasa ta gaida Gwaggo. "lafiya". Gwaggo ta amsa mata fuska a haɗe, murya a can ƙasa. Nima tace min, "Yaya ina kwana". "lafiya lau Zainab". Na amsa mata fuskata ɗauke da fara'a. Yaran dukansu sun hankalta tun jan kunnen da Gwaggo tayi musu, don sun san sarai zata iya aikata komai, ba kasafai ta ke faɗa bata aikata ba, abu ne mai sauƙi a wurinta tai musu auren ƙauye. "kin shigo min ɗaki kin wani tsareni da idanu lafiya aka mutu kai na motsi, ko wani kinibibin ne?, ko kuma an aiko ki gulma ne?. To idan ma itace aka aikoki sai a sami damar juyawa don babu abinda za ki ɗauka". baki Zainab ta turo gaba, bata tanka ma ta ba tace min, "Yaya". nace, "na'am". "Yaya Abba says if you did'nt come out he will leave, becouse you are westing his time". na dafe goshi nace, "Ya rab, tell him yayi haƙuri dan Allah, am comming out now". kuma bata kai ga fita ba Gwaggo ta Gwame baki tana cewa. "idan ka haɗu da abinda ya isheka sai ka zubawa sarautar Allah ido. wannan barbaɗin rashin mutunci har ina?, a shigo min har cikin ɗaki a dinga sauya harshe a gabana, to duk wanda ya zageni kansa ya zaga tunda dai ba iyawa nayi ba bare na rama, ni dama tunda na ganki a ɗakin nan nasan ba alkhairi ne ya kawoki ba...ke kuma da ba ki da wayo kiyita biye musu suna ɗoraki a hanyar lalacewa, kaf gidan nan dai kin san babu mai ƙaunarki sama dani, amma tunda ubanki yay arziƙi kike neman juyawa min baya, to indai waɗannan makiranne gaki gasu nan". Zainab tace,"kai Gwaggo bafa zagi ne akai ba". sai ta kauda kai tace,"sarai ai na sani, Abba ne yayo aike yana jiran ta fito, banji yaran ba amma na fahimci me akace tunda naji an faɗi sunansa...to hakan da kika ga nayi gargaɗi ne nayi saboda kar a ƙara kwatanta hakan wataran, dan baza'a ji daɗin martanin da zan mayar ba...bana son sauya yare a gabana wannan halin munafukai ne". Zainab dai tai murmushi ta juya ta fice. "to ni kam Gwaggo tunda kinji sauƙi zaɓar min kayan na fita, kin san halinsa yanzu zai ƙara yo aike ko kuma yay tafiyarsa". "wa yace miki sauƙi naji, ƙarfin hali ne fa kawai nake...ni matso da kayan na gani". na tura mata kayan gabanta, ta ɗaga wata red ɗin riga tawa ta aje a gefenta tana faɗin,"wannan kamar sawarki uku ko. bari na bawa ƴar aikin gidan can da aka aikota t gaishe dani". tukunna ta zaɓar min wata doguwar riga ta shadda wadda taji aikin stones a jiki, ɗinkin yay kyau sosai. na ɗauka na saka na zaɓi gyale na yafa, na duƙawa nayi zan kwashi kayan tace, "ki barsu idan na miƙe zan gyara miki na kai miki, ko ba ki kalla duk karin guguwar ya hargitse bane, kuma kika tsaya cewar sai kin kai ɗaki wancan ɗan masu kwazazzafan sabon aike zai kuma danno miki, ma za jeki sai kun dawo Allah ya kiyaye". nai mata wani hug irin wanda ta gani a tv sanda muna kallo, yanda Patriva ta rungume kakarsu shine tace to nima nake yi ma ta hakan tana so dan Allah. nace,"Gwaggona na gode, Allah ya bar min ke ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Na faɗa fuskana ɗauke da murmushin jin daɗi tare da bata sumba a kumatu. Sauri-sauri na isa dressing mirrow na ɗauka faran powder na shafa, na ɗora da man leɓe sannan na zira takalmina. Duk abinda nake idon Gwaggo akaina, ina ƙoƙarin fita tace. "ke wai dan manzon Allah wacce kalar macece, kina nufin a haka za ki fita da wannan buyagin gashin naki da ba kya so a taɓa shi, ke kin ganki kuwa kamar sabuwar kamu". na yatsine fuska nace, "Gwaggo wancan satin fa aka taje shi, kuma naga baiyi komai ba ne, kuma fa na sanya hula babu mai ganewa sai ɗan sa ido". tace, "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi. to Sabina da aka taje shi wancan satin ma ai tsami yake, Ina taje shi fa ina tara yawu a bakina, kuma yanzu har kina faɗin kin saka hula, ke dai kin shiga uku da ƙazantar kai wallahi, samu ki kai ma shi yasa. to kizo ki wuce ki ɗauko wannan abar mai kama da indararo kizo ki busar da shi ki taje don bazan gayara miki ba, kuma baki isa kin fita a haka ba bare kija min zagi ace Gwaggo bata gyara ki". kamar zanyi kuka na maƙale jikin ƙofa ina roƙonta akan ta ƙyaleni, don ni wallahi idan da abinda na tsana taɓa kaina, da ace Gwaggo ta bani dama tuni na jima da aske shi, to sai tace wallah bazan aske ba haka kawai na rasa mijin aure, tunda ta lura mazan yanzu idan ba gashi ba ƙirji sai su raina mace. "wai kuwa ba za ki zo kiyi abinda ya kamata ba ki wuce kije ku tafi sai kunyi yamma. Kin wani tsaya kina turon baki gaba kamar wadda za'a bawa nono, to bari na kira Abban nace masa gaki anan ba uwar da kike kawai dai ba za ki fito bane". nai saurin cewa, "don Allah Gwaggo ki bari sai na dawo, ko a yanzu zafi yake min, kuma kin san ko ya na taɓa sai ciwon kai". "ai kuwa dai kika je gidan miji da wannan ƙazantar baƙar wuya za ki sha, a tou ni dai gaskiya nake faɗa miki. dan ba zai juri ganinki tsab-tsab ba yana jiyo tashin ƙamshi ta ko'ina a jikinki sai ya doshi kai yaji hammm, yasin sai to miki hanyar gidanku zai yi, idan za ki gyara tun wuri gwara ki gyara". na ƙara cewa, "to Gwaggo nace ki barni na aske ba shikenan sai na huta ba kema ki huta da mita". "yo dama aini ban isa na faɗa maki gaskiya ba, shikenan sai ki ce na cika mita. to kije Allah ya kiyaye, ina kuma faɗa miki karki yarda da tuƙin ganganci irin na Abba, da kinga yana neman wuce gona da iri ki sauka ki nemi mota ki dawo gida, ranki ɗaya ne ba biyu ba...sai kun dawo". Fita nayi ina jinta kuma tana ci gaba da faɗa akan rashin gyaran gashin, idan na dawo ya zama dole ta kaini wajen bayerabiyar nan ta gyara min kai, ba zan kasheta da tsamin kai ba lokacinta bai ba, kuma wallah kaina ba wani wari da yake sharri ne irin nata kawai. ni na lura sababin Gwaggo ma ƙaruwa yayi tunda muka dawo gidan nan. Ina isa ƙofan parlo kiran wayar Farhana ya shigo, ina murna na ɗaga domin mun kwan biyu ba muyi waya ba, hiran yaushe gamo muka hau har tana bani labarin exams ɗinsu ta fito ta sami second class, na tayata murna sosai, na tambayeta yaushe zata zo suga gidanmu tace sai anyi hutun islamiya, nace ma ta Allah ya kaimu, har na bata labarin nima an samo min addimission, tai min congratulations tare da bada shawarwari saboda karatun Uni ba ɗaya yake dana Secondry ba. tun fara wayarmu so nake na tambayeta Yayana amma gudun kar ran junanmu ya ɓaci na haƙura, mu kai sallama na kashe wayar raina ba daɗi. ina ƙarasawo parking lot gabana naji ya faɗi, ƴaƴan cikina naji sun kaɗa har jakar hannuna ta kusa faɗuwa ƙasa, na kuma yin ƙasa da kaina ina takawa kamar bana son tafiyar, don ina ƙwaƙwƙwarar tafiya zan kifa ƙasa, gaba ɗaya a tsorace nake da Yaya Haidar wanda tunda na taho idonsa ke kaina, fuskar nan tasa a haɗe kamar hadarin gabas ya taso, sai wurgan wani mugun kallo yake. Ni dai har na iso inda yake tsaye jingine a jikin mota ƙirjina bai bar duka ba, tsorona da fargabana kar dai ace da shi zamu fita yau. sam shi mutum ne mara daɗin sha'ani, miskilanci da masifa su kaɗai yasa a gaba, kuma tunda yazo gidan ya hanamu sakewa, Amina ce ma take iyawa da shi saboda mara kunya ce ta ƙarshen gaske. ni kam da magana ma bata isheni ba, sai dai yay min son ransa, shi yasa duk na ƙagu ya koma gidansu. kuma tsawar daya doka min ita tai sanadiyar gurɗewar ƙafata. "kin bar mutane tsaye kamar aikinki suke kina biyansu, za ki ɗago ƙafa ko kuwa nima sai nayi tafiyata". A ruɗe nace, "Yaya Haidar to ina Yaya Abban?". bai bani amsa ba ya wurgan harara ya zaga ya buɗe gaban mota ya shige, dana tashi nima na buɗe baya na shiga. ta cikin madubi ya jefo min harara yace, "who is your driver?". Na haɗe fuska ina shirin fashewa da kuka, muryata a sanyaye nace, "Ohh Yaya Haidar then where should i stay? ". "dilla Malama fito ki dawo gaba, sai anyi magana ki nemi ki ɓarewa mutane baki, ki jawa mutane masifa a wurin waccan tsohuwar da bakinta bai gajiya da magana. a'a ke gaki ƴar gwal ba'a isa an taɓa ki ba. Kamar akan ki ne aka fara yin mutuwar uwa". matsalar ɗaya ni ban iya rashin kunya ba, furucinsa na ƙarshe shi yay sanadin taruwar ruwa a idona, na fito na dawo gaba na zauna, ko ƙarasa rufe kofan banyi ba ya figi motar kamar wanda zai tashi sama. kuma tsoratar da nayi ya haɗe da sakkowar hawayena, shi ko a jikinsa ma dan ba lallai ne ma idan ace na faɗa waje ya lura ba. har muka hau titi ban bar kuka ba don sosai maganarsa ta bani haushi, idan shi bai damu da tashi mutuwar uwar ba aini na damu da tawa, sam Yaya Haidar baiyi halin Uncle Sulaiman ba don ba haka Babansa yake ba. Shi ko tausayi ban bashi ba, saima tsaki daya dinƙa ja yana shafo sumar kai har muka isa wurin koyan motar, hakan ya ƙara bani haushi, saboda ni fa ina takaicin naga ina kuka aƙi lallashina, nafi so ko ya na fashe to a karkato da hankali kaina, ta irin haka ne ma muke faɗa da Gwaggo wataran, idan na bata haushi sai tayi biris da ni. Ni dai yau nayi dana sanin fitowa koyar motar nan, gaba ɗaya ma naji koyon ya fice min a rai, kullum da murna nake fitowa nake komawa indai da Yaya Abba ne, kuma muna wasa da dariya yake koya min, amma yau tsabar tsoron Yaya Haidar koyan kwanar da na kasa yi sama da sati biyu sai gashi cikin rabin awa na iya, mu kanyi awa biyu zuwa uku idan muka zo amma yau ko ɗaya bamu cika ba naji yace tafiya zamuyi shi ya gaji. muna ɗaukan hanya na ɗago na dube shi, murya a ɗarɗace nace, "Yaya Haidar ai bada wuri fa muke komawa ba, Baba yace Yaya Abba yake tsawa ya tabbatar da na iya sosai kamin mu koma". Farko banza yayi min, sai can naga yayi wani miskilin murmushi yayi revers, a bakin filin wurin yay parking, kansa na gaba kamar bada ni yake ba yace, "buɗe ki fita". nai sororo ina kallonsa. ya ƙara ɗaga murya wanda na tabbata har na waje sunji. "nace ki buɗe ki fita. in yaso ki sami wani ya koya miki sai ki biya shi, ko kuma ki kira shi Abba'n ya koya miki shi daya ga zai iya aikin wahala amma ni ba kalata bace sanya daƙiƙiya a gaba ina koya mata abu tana kasawa". "Amma tsakani da Allah Yaya Hydar ai kasan koyon driving ɗin nan da wahala, kuma ma yau ai nayi ƙoƙari dai, gashi kai baka encouraging ɗin mutum, sai dai kai ta faɗa. kuma fa ni ba daƙiƙiya bace Allah, saboda ina da ƙoƙari akan komai, kaje makarantarmu ma ka tambaya, har na gama first class nake ɗauka". Na faɗi hakan ina turo baki gaba, na san wannan ƴar maganar da nayi ba zai barni ba, ile kuwa ina rufe baki ya ɗalle min laɓɓana da yatsansa wanda sai daya sani yin ƙara ina sosa wurin. "karki yi min rashin kunya saboda ni ba Abba bane, tun kamin a haifeki nazo duniya, sai da nayi shekara ɗaya-ɗaya har 13 kana aka haifeki a tsumma, kashinki da tunbuɗinki babu kalar ƙazantar da ban gani ba, saboda haka ki iya bakinki wajen yimin magana, ni ba sa'anki bane". Haushi ya tuƙeni hakan yasa na shiga ƙunƙuni. ina jinsa yana faɗin, "banda kinci darajan Baba daya ce na kawoki, kuma motar ba ta gidan mu bace, ai da sai kin fita in yaso ki daɓa a ƙafa ki koma gida...mara kunya fitsararriya ana magana kina tura baki gaba kamar shantu, ke ai gaki goyon Kaka goyon gata, to ba gata wannan tsohuwar ke nuna miki ba, dan a nan gaba wuya za ki sha da wannan halin naki". Ni dai bance masa komai ba har muka iso gida, bare ya kuma gaya min no sugar, na cika nayi fam saboda haushi, Allah ko da kuɗi, kai ko shi ɗaya ne mai koyar da mota a duniya ba zan ƙara binsa mu fita ba sai dai har na mutu kuwa ban iya motar ba. Yana yin parking na buɗe na fice, Ina ji yana min magana nayi masa banza kome ma yake cewa oho, ɗakina na wuce kai tsaye na kifa kan gado ina kuka, to fa dama da biyu kukan nan nawa, tun jiya kewan Yayana ya isheni, ga shi yau kuma wannan matsolon raken ya ɓatan rai. Ina kwance ina faman shashsheƙar kuka Gwaggo tayo sallama, ina jinta ta buɗe wadrobe ta zuba kaya ta mayar ta rufe, kana ta karkato kaina tana faɗin. "ke kuma yaushe kika dawo? Me akayi miki kike kuka? Me Abban yayi miki? Ko kuma shigowarki wata a cikin gidan nan tai miki hali na rashin kyautawa?". Duk a jere ta jefa min tambayoyin, na miƙe zaune ina goge hawayena ban dai ce ma ta komai ba, ƙaramar wayata dake gefena kawai nake kallo naga ko kira mai sabuwar numba zai shigo, don a kullum bana yanke tsammani da kiran Yayana. ta kama ƙugu tana faɗin,"yau naga sarautar Allah". "keee to ko kin gamu da ciwon baki ne da kika gagara bani amsa? Ina daɗa tambayarki me Abba yayi miki? Za ki bani amsa ko sai na ƙwala miki wannan murfin tasar". Sanin zata aikata yasa da sauri na buɗe baki nace, "ba Yaya Abba bane, Yaya Haidar ne". "Haidar dai! shi Haidar ɗin da yake baƙo ya ɓata miki rai? To me ya haɗa ku? Ki faɗan gaskiya ke dai ban sanki da rashin kunya ba". ina goge ƙwalla nace, "ni fa ba abinda nayi masa, tunda na fita yake tayi min masifa har muka je muka dawo, har cemin yake wai kinyi min goyon lalacewa, banda taɓara babu abinda na iya, da anyi min abu dana fashe da kuka sai kace a kaina aka fara mutuwar uwa". sai ta shaki ƙugu ta kama haɓa. "shi Haidar ɗin ne ya faɗa miki haka?". na ɗaga kaina, "ehh mana. Ni dai daga yau bazan ƙara binsa ba in dai shine zai koya min mota, acan ma harda ce min daƙiƙiya, ya bige min baki saboda na faɗa mishi gaskiya ni ba daƙiƙiya bace, Gwaggo har muka je muka dawo fa ba abinda na iya wai shi ai ba bawa bane, hakan ma daya fito dani darajar Baba naci". ta shiga tafa hannaye tana faɗin,"iko sai lillahi, duk shi Haidar ɗin yayi miki wannan rashin kyautawar yaci zarafinki da yawa haka?". "Allah Gwaggo ba zan ƙara binsa ba, ki faɗawa Baba indai Yaya Abba bayanan na haƙura". ta dire farantin dake hannunta, tana gyara ɗaurin zane tace, "yo dama ai ba za'a kuma na biyu ba, anyi na farko anyi na ƙarshe. yo ni kuwa ina dole irin wannan cin mutunci har haka, idan kuka ci gaba da fita tare waya san irin cin kashin da zai yi miki agaba, daga ke sai shi sai Allah'n daya ke kallonku. gashi ke ba ki iya halin rashin kirki ba bare ki rama. Saboda haka kwantar da hankalinki, ki sha re hawayenki haka kar ya rainaki, ni nasan yanda zanyi da shi, kuma idan shi gyatumin naki ya dawo ki sa me shi ki faɗa masa...ina dalili wannan ɗibar albarka har ina". Na kuma turɓune fuska ina fizgar numfashi, ta matso kusa ta cire ɗan kwanlinta ta gogen hawaye tana lallashina. "ki kwanta ki rama baccin safiyar da Abba ya azalzale ki, kamin anjima muje wurin bayerabiyar nan ta wanke miki kai, domin ba zan iya da wannan ƙazantar gashin naki ba, haka kawai muna zaune ƙalau ki jajuɓo mana abinda yafi ƙarfinmu, kwarkwarta ta shafeki. na rasa inda zan saka kaina, nan dai ba tsohon gida bane bare nasa miki omo, yafi nai ta kaiki inji suna dirje shi yanda ya kamata, tunda ba ƙaunar kitso kike ba". ni dai duk ba wannan zancen nake son ji ba, so nake ta fusata ta tafi wurin Yaya Haidar kai tsaye, ita da shi hali ɗaya ne, ya kaishi bango ya fusata ya kwashi kayansa ya tafi shine kawai abinda nake so. sai na shiga rera kuka a hankali, hakan kuma yasa ta hauni da banbami tana faɗin tunda dai na faɗa ma ta ba shikenan ba, na zuba ido kawai naga abunda zata yi, ai nasan bata barin ta kwana akaina. na goge hawaye na Kwanta, Gwaggo ta gyara min abinda zata gyaran a ɗakin...har ta gama idona na kanta, godiya nake ga Allah daya bani Kaka kamar Gwaggo tunda ta fita nai luff jikin pillow na tafi duniyar tunanin Yayana da nake matuƙar kewarsa. Gwaggo na fitowa ta sami Haidar zaune kan kujera a parlo, ya harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya akan centre table, hannunsa riƙe da cup yana kurɓan lemu yana kallon tv yana ssuraron labarai. bata ko bi ta kansa ba saboda tana jin haushinsa ta wuce ɗakinta. ta ɗau tsawon mintuna a ɗakinta yana nan, kuma har ta shiga kitchen ta gama abinda zata yi ta fito still yana nan zaune, amma yanzu waya yake latsawa saboda an gama news ɗin. tsayawa tayi tana tunanin abinda zata yi masa ta huce takaicinta, Amina ta shigo parlon ɗauke da sallama bakinta, hannunta kuma riƙe da basket na kayan abinci. Gwaggo ta ansa gaisuwartata a ciki, ta nufi Dining zata aje abincin Gwaggo tace, "ke tsaya, mene wannan?". "Gwaggo abincinku ne". "to koma da shi, jiya kwana nayi ban runtsa ba har safiyar yau lafiya bata ishi cikina ba, kuma duk sanadiyar abincinku da naci ne. don haka tsautsayi ba zai kuma sawa naci ba, dan ban san me zai kuma faruwa ba, ki koma da shi kice Allah ya amfana, kuma daga yau kar a kuma kawo min". A ciki Amina ta saki dariya, burin Ummanta ya cika, dama girkin jiya da gayya ta rambaɗa masa attaruhu yanda zai kasa ciyuwa ko kuma ya ɓata ciki, ta yanda Gwaggo zata ce a raba girki. Haka Amina ta juya da abincin tana mai jin haushin Gwaggo, tana kuma dariyar mugunta, kuma da alaman yanda ta fita sai ta ƙara akan abinda Gwaggo tace ma ta. Kujerar da Haidar ke zaune ta nufa, kansa ta tsaya ta ƙare masa kallo tukunna tace da shi. "Mulkakke, hamshaƙi, ɗan masu isa da taƙama. ka wani hakimce min a kan kujera kamar ɗakin uwarka, sarai dai kasan wannan jibgegiyar ƙafar taka mai kama da doya tafi ƙarfin wannan teburin nawa, amma saboda mugun hali kazo ka ɗora min akai. don haka ka sami damar ɗauketa kamin ka fasa min glass, tunda babu sisin Sulaimanu a siyota". Yaja guntun tsaki a ciki, da yayi niyyar ɗaukewa amma tunda ta haɗa da sunan ubansa ba abinda zai sa shi ɗaukewa. cikin hasala tace, "ɗaukewar ce aiki ko kuma ɗaukewar ne ba zaka yi ba Aliyu?". Nan ma shiru yayi ma ta, hakan yasa ta duƙa ta ɗauke ƙafafun nasa ta watsar a ƙasa. ta hau sababin cewa,"ni dai duk a cikin jikokina ku biyu ne banyi sa'ar samu na kirki ba kai da Junaid, to gwara Junaidu ma sdaya zo ya tafi naga ya ɗanyi sanyi, inaga rayuwa ce ta fara gara shi. kai kuwa rashin mutuncinka ƙara hauhawa yake. To baka isa ba kayi kaɗan tunda dai ni na haifi ubanka ba kai ka haife ni ba, kuma ka ajiye min kofi, lemun dana aje ai ba kai na ajewa ba amma saboda hannun ɓera gareka shine kazo ka ɗaukar min ba tare da neman izininina ba. to ko Abba baya yi min haka shi da ubansa ma ya siya kenan, saboda haka kake fara neman izini kamin ka taɓa min abuna". Cup ɗin ya aje ya ɗauke kansa gefe yaci gaba da kallon tv. "to waima da ka shigo min wuri kayi sallama ne saboda ina ɗaka banji sallamarka ba?". can ƙasan maƙoshi yace, "amsata ne yake wajibi ba yinta ba". "yo to kai Aliyu dama ai ba mutunci ka cika ba, dan na faɗa ka faɗa wannan ba komai bane a wurinka, kuma dai kasan nafi ƙarfin kayi min rashin kunya tunda dai ni na tsuguna na haifi ubanka. ni ban taɓa gasgata rashin kirkinka ya kai intaha har haka ba sai yau, tsakani da Allah ka kama marainiyar Allah ka duketa ka sata kuka, haka ake rayuwa fisabilillah, kawai saboda kaga tana da haƙuri bata raina na gaba da ita shi yasa ka zageta son ranka, da ka san ba zaka koya mata ba ai saika faɗawa shi Auwalun daya saka, bawai ka juye haushinka a kanta ba,  to ka kiyaye ni Haidar, ka kiyayi ramata, ka kiyayi abunda zan aikata. kuma Allah ya saka mata". Ya waigo gareta yace, "ita maƙaryaciyar haka tace miki na daketa ko na zageta?". tace, "ai ba ƙaryata tayi ba, cikin abunda ka lissafa wanne ne baka yi mata ba?, to kaga ni ba zuwa nayi nai doguwar magana da kai ba, Zuwa nayi na faɗa maka muddin kana so zamanka ya ɗore a cikin gidan nan to ka kiyayi ɓacin ran Sabina, idan kuwa ba haka ba sai ka tattara komatsanka kaje can ka kama wani gidan ka zauna zuwa randa zaka gama shi aikin naka ka koma. Haka kawai kazo kana cin arziƙin uban yarinya kuma sai ka nemi ka takurawa rayuwarta, yo ina dole anan sai ka bar gidan Wallahi, ni ba zan ɗauki ɓacin rai ba". Kan Haidar a kan wayarsa har ta kammala baice ci kanki ba, hakan kuma ya ƙara bata haushi. "ina maka magana baka ce komai ba, wato gani banza a wofi ko, ina ihun kare. kai baka iya bada haƙuri akan laifin da kayi ba, ta inda Junaid ya fika kenan, yasan na gaba da shi amma kai dai banda Ubanka Sulaimanu babu wanda kake gani da gashin ido". "to me kike so nace miki Gwaggo, salon nayi magana kice kema na zageki. Ita dai da kike ɗaurewar ƙugu takewa mutane sharri ba rayuwa ce mai kyau kika ɗorata akai ba, randa babu ke wuya zata sha Wallahi". "ɗan baƙin ciki, kamin ta rasa ni insha'Allahu na damƙata a hannun na gari mai gaskiya da amana". ta kama gefen zane tana gyara ɗauri. "Kaga ni tashi tsaye ma, kaji wani laushin kujera kana neman kassara min ita saboda ba'a saba ganinta a gida ba, zaka tashi ko kuwa? Haidar in maka magana kana gyara zama". "wai idan na tashi me zanyi miki? kina fa da takura Gwaggo. Naga dai nima gidan nan na ubana ne, kuma ɗakin nan mallakin kine kuma ke ɗin Kakata ce". "Laaa kaji min mutum; ta ina gidan nan ya zama na ubanka?, wannan gida dai na uban Sabina ne bana ubanka ba, bana son kalen jaraba". sai kuma ta fara faɗa sosai, faɗa na gaske bana wasa ba. "ka miƙe na nuna maka hanyar fita, idan ka fice kuma bana so ka ƙara dawo min sashena har ka bar gidan nan, tunda ba naka bane, mara mutunci kawai, wanda bai tausayin maraya...na rantse Aliyu idan ka ƙara taɓa min Sabina ba zamu kwashe ta daɗi da kai ba, banza wanda bai girmama kansa. shashasha kawai dogon wofi". Haidar Yaja ƙaramin tsaki ya miƙe yana zura wayoyinsa a aljihu ya raɓa ta gefenta ya fice fuuuu kamar mai shirin tashi sama. Gwaggo ta daki cinya tace, "oho dai tafi nono fari, Idan kayi zuciya har ka bar gidan nan karka ƙara shigo min sashe ko da kuwa gaisuwa ne, ni idan mutum naso muyi shiri to ya kiyaye ɓacin ran marainiyata". Yazo fita ni kuma na fito, bamu lura da juna ba muka bugi goshi, na saki ƙara da ihu ina dafe wurin, shima dafe goshinsa yayi da alama yaji zafi, ina niyyar bashi haƙuri naji ya doka wani uban tsakin daya daki dodon kunnena, ya sanya kai ya fice bayan ya jefan mugun kallo. a wannan lokacin banda a ƙule yake da ba abinda zai hana shi kawo min hannu. *_Masu Tambayan Littafaina kuna da yawa, kuma a haƙiƙanin gaskiya novels ɗina a yanzu idan kuka cire Sirrin Ɓoye da Al'amari Book 1 to banda documents nasu, sai dai kuje wattpad @ Oum_Ramadhan, ko kuma kuje Arewa Books ananne ma zaku sami kowanne book nawa free da paid, shi yafi sauƙi...ina godiya da soyayyarku gareni..._* https://play.google.com/store/apps/details?id=com.arewa.arewabooksapp                  [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(13)* Anty ce ta fara shigowa sai Umma da ta biyo bayanta. Suka nemi wuri suka zauna, Umma ta wani karkace sai faman hure-huren hanci ta ke, ta ɗauke kai tana kallon gefe daban kamar bata ga mutane a wurin ba, sai da taji Anty ta miƙa gaisuwa ga Gwaggo kana itama ta juyo tana kumbure-kumbure ta gaidata. "lafiya". ta amsa musu babu yabo babu fallasa. Gwaggo ta miƙe ta gyara ɗaurin zanenta tukunna ta koma ta zauna, kamin ta kalla Umma ta Kalla Anty, sannan ta maida kallonta ga Baba cikin murya mai bada umarni tace. "ka sami damar yi musu bayani, yau ɗin nan nai magana da yawa na gaji". tana gama faɗa ta jefa goronta a baki tana ci. Baba ya zayyane musu kaf abinda Gwaggo tace akan zarginsu da ta ke na ciwona. Yana gama bayani Anty ta rushe da kuka kamar wadda aka yowa aiken mutuwa, faɗi ta ke. "wallahi ina ga kaf duniyar nan bayan iyayen Sabina to duk wani mai sonta ya biyo bayana domin ni zanzo a bayan Gwaggo, amma sam-sam kin gagara fahimtata Gwaggo, gani kike kamar ba ƙaunarta nake ba, kullum cikin haɗa ma ta mugun abu nake, Bayan ba haka bane, Ko abubuwan da suka faru a baya sharrin sheɗan ne, Gwaggo har yanzu kina min mummunar fahimta akan yaran nan. Yanzu fisabilillahi taya za'ai nayiwa ƙaramar yarinya turen aljanu kamar bani da ilimi". Ta ƙarasa maganar tana kuma fashewa da kukan munafurci, Sai kuma taci gaba da cewa. "tunda naga abinda ya sami yarinyar nan hankalina ya kai ƙololuwar tashi, har zuwa yanzu ban samu natsuwa ba saboda damuwar dana shiga, abinci wannan gagarata yayi ina zaune suku-suku saboda hankalina na kan Sabina da kuma hanyar da za'abi ai ma ta maganin wannan lalurar da ta sameta. Amma ƙarshe sai zargi ya shiga tsakani". hmm ni kaina ban san lokacin dana sa ki baki galala ba, lallai Anty ta ƙwarai a iya makirci, tab wannan kafce nata sai ka rantse gaske ne. Umma dake zaune a shirge tace,"to aini gaba ɗaya na rasa abun cewa, yanzu kayi magana ne abun yafi haka tsauri. Sai dai nace Allah ya kyauta ita kuma ya bata lafiya, Allah kuma yayi gaggawar bayyana gaskiya, domin ni gaskiya an shiga da hakkina. Ko wani daban bazan iya cutarwa ta hanyar masa turen aljanu ba bare Sabina da take ƴar mijina, to ni ina nasan ma hanyar wurin bokaye, ai duk rashin son da nake ma ta bana ɗora mata wannan ciwon wahalar ba, amma Allah yana ji yana kuma gani". inaaa ai Gwaggo sai ta saki Baki, hanci da idanu ta zuba musu tana kallon sarautar Allah, duban mamaki takewa Umma, kamin ta dubi Baba tace, "kaga irinta ko, idan na faɗa maka baka yarda, yanzu tunda Allah ya haɗa mu gida ɗaya ka dinga gani ai, ka kalla fa a gabanka nema ta ke tayi min rashin kunya saboda bata ganin girmana, to dama ta ina zata kalle ni da gashi ni ba Asiya(mhaifiyar Umma) ba, amma dai ko ba komai ai ni na haife ka, ta girmamani idan tana neman albarka aure, ta inda nake yabon Halima kenan, Har ta mutu kamar uwar dana tsuguna na haifeta haka ta ke girmamani, babu fitsara ko ɗaya a lamarinta, ga ƴaƴanta nan ma sun ɗebo halinta, dama hali ai tushe ne". Umma ta zumɓuri baki ta ɗauke kai, Gwaggo ta dubi Baba tace, "wai baka ji irin maganganun da ta yaɓa min bane, kana jinta fa wai Allah yana ji kuma yana gani, to me ta ke nufi da hakan? Kai kuma kaga solon namiji ba zaka iya tsawatar mata ba". Allah sarki Babana bawan Allah, cikin muryar nan tasa ta rashin son magana yace, "Hajara ki iya bakinki a wurin nan, da mahaifiyata kike magana ya kamata kisan irin furucin da za ki dinga yi". Gwaggo tai siririyar dariya, ta shiga magana ita kaɗai. "hmm wai faɗa yake yi ahaka, yana magana a hankali kamar matsoraci, ta inda nake takaicin haƙurinka kenan, Kai dai anyi dolon namiji, da ace Sulaimanu ne sai ta karɓi hukuncinta wallah". "kiyi haƙuri Gwaggo". Yace da ita, sannan ya juya gun Umma yace, "ki bata haƙuri". Tana faman ɓata rai tace, "To ni me nace, gaskiya ce kawai ba'a son mutum ya faɗa". A tsawace Baba ya katseta, "wai ke me yasa baki da mutunci ne, zaman tare kuka yi da Halima, haka kika ga ita tana yi?". Sai data ga ransa ya ɓaci sannan tace da Gwaggo, "Allah ya ba ki haƙuri". Gwaggo ta jaddada kai kamin tace,"Uhmmm, kowacce sai tayi rashin kyautawa sai su juye abin tausayi idan a gaban mijinku ne, saboda kuna tsoron takardar cika, yo wannan kiran da ace ni kaɗai ce a wurin ai sai iya abinda kuka wanke ni da shi na gani, amma ba komai Allah dai ya bani ikon gano gaskiya. Ku tashi ku tafi makirai". Umma ce ta miƙe ta fita kamar ana hankaɗata, amma Anty har lokacin tana zaune ta kifa kai da gwiwa tana kukan rashin kyautawar da akayi mata. Gwaggo tace da ita,"ke kin dawo nan ɓangaren da zama ne, mu miƙe mu baku wuri ke da mijin naki?". Anty tana goge hawayenta tace,"a'a Gwaggo Allah ya huci zuciyarki". "to kuma zaman mene kike da ba za ki tashi ki tafi ba, ba ki kalla waccen jibgagar mai jiran kaɗan ita har ta kwashi ƙafafuwanta ta tafi ba. ko kuma kina jiran kiji me nake tattaunawa tsakanina da ɗana ne, tsakani da Allah wannan ma ai raini ne". Anty ta nemi rufin asirin Allah tace,"Gwaggo ba haka bane, kawai dai ba zan iya tafiya bane ba tare da zargin da kike akaina ya goge daga zuciyarki ba. Ko dana miƙe ƙafafuna ba zasu iya ɗaukata ba, ko kaɗan bana ƙaunar fushinki". Shi dai Baba yayi shiru kallo kawai yake. Gwaggo ta taɓe baki, ta kau da kai gefe tana cewa da Baba, "kacewa Matarka ta ɓace min anan". "Zahra'u tashi kije". Yace da ita ba tare daya kalleta ba. Kamar munafuka Anty ta miƙe ta fice. tana fita kuma Gwaggo ta ɗauka da cewa,"ko kunnuwa duka jikina bazan taɓa yarda da waɗannan makiran matan naka ba. Sarai nasan wata acikinsu tai wannan aikin, Mugwayen banza insha'Allahu duk wani sharri sai ya koma kansu, ai kaf na gama karantar zuciyoyinsu". Baba ya numfasa yace, "haba Gwaggo ki bar wannan maganar, Zarginsu ne fa kawai kike, kuma zato zunubi ko da ya kasance gaskiya". "to Auwalu tunasar da ni hadisin dana manta, kai gaka mai Mata wato na taɓa Matanka shine zaka ɓata rai. To ni dai wallahi duk wanda ma yay silar cutuwar Jikata bazan yafe masa ba". tasa gefen ɗan kwalinta tana sharar ƙwalla,"Auwalu har mutuwata bana tunanin zan kuma son Matanka, sai dai kayita jin haushina, yanda basu da kyan gani haka zuciyoyinsu basu da kyau, yo akan mene zan so su, ina zaman dole ne da su kawai saboda Allah ya ƙadarta rabo a tsakaninku, amma da kowacce sai ka bata jan kati. Har yanzu bana manta baƙin sharrin da kowacce tayiwa marayun ƴaƴan nan, waccan shirgegiyar mara kyan fasali tace Sabina tayi mata sata, ita kuma Ƴar-wadar can tace Abba ya shigar mata ɗaki, ko me zaiyi da waɗannan zubabbun nonuwan nata oho, kai kuma ka hau ka zauna akan maganarsu saboda kana tsoronsu, kaci zarafin Yaranan, to ta ina kuwa kaima zan daina jin haushinka, da wani ƙaton kanka tun na haihuwa". Baba ya ɗago yana duban mahaifiyar tasa da ta ke ta matsar ƙwalla, yana mai takaicin abinda ya aikata mana a baya yace, "kiyi Haƙuri Gwaggo, ni kaina nasan nayi kuskure amma na tuba". ta galla masa harara tace, "ka riƙe haƙurinka kai zai yiwa amfani. Na gama maganar da zanyi da kai, sai ka tashi ka tafi kaje can ka ƙarata kaima". Ganin Baba yaƙi tafiya ita ta tashi tana cewa da ni, "ke tashi mu wuce". Ta juya ta kalla Baba tace, "idan ka ƙaraci zaman naka sai ka kashe min tv da fitilu, kuma ka rufe min ƙofa". Ni dai yanda naga jikin Baba yay sanyi sai na kasa tashi, jira nake Gwaggo ta wuce na samu zantawa da shi, har tayi gaba sai ta juyo tana dubana tace, "aufa na taɓa ubanki shine za ki nuna min matsayina ko, ina magana kinyi banza dani ga susu na magana, yo acikin abinda na faɗa ƙarya nayi masa ne, ba watsi yayi da ku ba akan matansa, kamar marasa gata haka ya watso ku waje, shine yanzu dan nayi magana za ki ɗaura gaba da ni". ina kallon gefenta nace, "ni fa ba wani abin kika ji nace ba Gwaggo. to ma dai ina ce mun yafe masa abinda yay mana, ba sai ki bar tuna bayan ba, tunda ba shi da laifi amma da an fara zance sai kice yay kaza-kaza, tsakani da Allah bama jin daɗi ki daina". tsawatar min Baba yayi, hakan yasa nayi shiru ina goge hawayena. ita kuma ta ɗora faɗanta, "da ka barta taci gaba ai, itama aljanun nema suke su koya mata fitsara, bakaga tana yi kamar zata watsa ni gefe ba, kuma fa wannan ba halinta ba ne, amma yanzu tana neman koyar mummunar ɗabi'a irin ta Abba, ni tsoro na ma kar naje cikin dare su tashi su rufe ni da duka, gashi mu biyu ne kawai ban san ya zanyi ba, ita Allah ya jarabce ni da sonta ba iya barinta ita zanyi ta kwana ita ɗaya ba a cikin wannan halin ba, yanzu dole dai a san abin yi". Ni kam fashewa nayi da kuka, na kifa kai da gwiwa, har ga Allah bana so naji tana ambatar min aljanu, yanzu nai magana ta kuma cewa nayi mata rashin kunya shi kuma Baba ya rufe ni da faɗa. Baba yace, "to Gwaggo ko yaran zan tado daga ɓangaren su, sai suzo nan su tayaku kwana". da saurin baki tace da shi,"su wa ka ke nufi kenan?". "su Aisha". Yace da ita. Da sauri Gwaggo tace, "a'a rufa min asiri, waɗannan ai da gayya zasu tashi su illata ni, kai baka san yanda suke jin haushi na ba musamman ma Aisha, dan kawai ina fifita Sabina akan su, to su akan mene zan so su bayan basu ɗauko halin ƙwarai ba. kaga in baka labari, Ɗazu fa yarinyar nan Amina kaɗan ya rage ta rufe ni da duka, saboda ta kawo abinci nace ta mayar da shi ba zamu ci ba, kuma fa ba walaƙanci ne yasa nace ta mayar ba, abincin nan nasu barbaɗe suke masa yana sani cikin wani hali, baka ji yanda suka tugunzuma masa yaji ba kuma sarai sun san bana so, abinci ya koma kamar na mayu, jiya kwana nayi ban runtsa ba ina fama da ciwon ciki, faɗa maka ne kawai ban ba gudun kar ranka ya ɓaci, amma har yanzu gani nan ban wartsake ba. Shi yasa ma nace zan faɗa maka wannan haɗakar girgin namu kawai a barshi bazan iya ba, haka kawai ina zaman-zama na lafiya lau a dinga ɗora min lalura". ran Baba a ɓace yace, "wace tayi abincin?". "wannan bunkusar matar taka mana, itama ɗayar shekaranjiya da ta kawo nata maggi bai ji ba. Abba kansa kasa ci yayi sai wani ya dafa, ni dama ba kaina nake ji ba, marayun Ƴaƴan nan da basu da uwa nake tausayawa, su na lura basa tsoron shiga hakkin maraya, to ita dai mutuwar nan na kan kowa. Wallahi raina yana ɓaci matuƙa idan naga irin walaƙancin da sukewa ƴaƴan nan, kai kuma baka ɗaukan mataki, yanzu idan na mutu ya zasu yi, shi yasa nake roƙon Allah ya kawowa Sabina mijin ƙwarai kamin wucewa ta". Ta ƙarasa maganar tana fashewa da kuka sosai, kukan da duk sai daya taɓa zuciyoyinmu. Tausayinta ya kamamu duka, lallashinta muka shiga yi har tayi shiru. sannan tace da Baba ya tashi ya tafi dare yayi, Baba ya miƙe yay mana sai da safe sannan ya fita. Ranar dai ban kwana a ɗakina ba, saboda Gwaggo cewa tayi bata yarda ba, bata san me zai iya faruwa ba cikin dare, haka dole na bita ɗakinta, har kuka sai dana yi dalilin hayaƙin da ta saka min, ita wai so ta ke su barni tun abun bai yi tsamari sosai ba, ganin zan cutu na miƙe zan bar ɗakin da gudu, ta damƙo ni dalilin harɗewar da nayi. Hawaye na sakko min nace, "Gwaggo don girman Allah ki ƙyale ni, wannan hayaƙin fa yana cutarwa". "ke dallacan rufen baki, ɗazu da baki hayyacinki da Haidar ya banka miki ai ba ki ce komai ba". "to amma yanzu ai lafiyata ƙalau. Allah likitoci na bayani sosai aka shaƙar hayaƙi". ta taɓe baki, Bata tankani ba ta lakuto wani mai a cikin kwalba ta shiga mulka min, gaba ɗaya warinsa babu daɗi, hannunta nake turewa tasa hannu ta make ni taci gaba da aikinta. Bata ƙyaleni ba sai dana sha maganin islamic kusan nawa, sannan ta barni. sai bayan da muka kwanta kuma ta ke min maganar cewar. "ni Hannatu yanzu nazo na kori Haidar da shigowa ɓangarena, idan aka sami matsala ko me zanyi dan ya kawo agaji ba zuwa zaiyi ba saboda akwaishi da ƴar banzar zuciya, lamarinsa yafi kama dana mahaukata, ba zai gane a ɓacin raine yasa nayi masa haka ba don ya kiyaye gaba ya gyara, to Allah dai ya rufa asiri". Ni dai ina jinta bance mata komai ba, har bacci ya fara ɗaukata naji tana tambayana. "yauwa ke ɗazu ice ko a iya tsotse miki baki Haidar ya tsaya?". Nayi kamar ba zan ansa mata ba, sai ta miƙe zaune tace, "idonki fa biyu kuma nasan kinji me nace". Ina turɓune fuska kamar tana gani na nace, "ehhh, bayan shi bai yi min komai ba". "to gwara da Allah ya tsayar a haka. Kuma dai kina jina da faɗan dana saba yi miki kullum, ki kiyayi ɗa namiji a duk inda yake, Shi iskancinsa ado ne, kina gani dai ɗazu a gabana saboda bashi da mutunci bashi da kunya ya nemi ya kuma maimaita miki, to babu ruwanki da shi tunda mummunan halinsa ya fito fili, kinga ke dai ba halinki bane rashin kunya, karki ce za ki soma, Duk abinda yayi miki ki kawo min ƙararsa ni zanji da shi, kina dai jin me yace idan kika kuma masa rashin kunya abinda yafi haka zaiyi miki, to yana nufin ciki zai ɗirka miki don haka ki kiyaye wallahi, kuma ni fita zanyi a sha'aninki nama bar muku gidan, atoh ni gaskiya nake faɗa miki, ɗan uwanki ne ban isa na raba zumuncinku ba amma dai ki san irin mu'amalar da za ki dinga yi da shi". Na rungumeta ta baya ina kuka nace mata, "ai makamancin hakan ma ba zai kuma faruwa ba, tunda na lura rashin kunya ce baya so ba ruwana da shi, ina tare dake har abada Gwaggo ba za ki taɓa tafiya ki barni ba". Na ƙara ƙanƙameta tsam a haka har muka yi bacci. *** Ɓangaren Alhaji Auwal kam tunda ya koma yakewa Munubiya faɗan yajin da ta saka a abinci, ya kuma ce kar a ƙara girki da yaji, kowa ya haƙura da cin yajin, ai sun san mahaifiyarsa bata so saboda rashin adalci suka tashi suka saka. aikuwa maganar tasa ta tada balli, nan da nan ta kawo wuya ta miƙe ta kama masifa. "haba Baban Alhaji, kowa fa acikin gidan nan da nasa ra'ayin. Ita da bata ci ta dafa nata mana, ko kuma ta saka wannan yarinyar ta dafa mata tunda ita girkin ne ta ke jin ƙyashin yi, kowa ba ɓangarensa daban ba, to da wama yake dafa musu, ni wallahi ba za'a takurani ba, abinda nake so shi zanyi, dan haka banga dalilin da zaisa ace dan wata bata son yaji ba nima ba zanci abinci da yaji ba". shima cikin hargowa yace da ita, "to shikenan kiyi son ran naki, ni kuma kiga yanda zanyi dake, kuma dole a duk sanda aka yi girki a kaiwa mahaifiyata...kuma in har kina ƙaunar Allah karki fasa girka mata abinci da yaji kiga yanda zamu kwashe dake acikin gidan nan". Ko haƙuri bata bashi ba, yana gama faɗan ta tashi ta bar masa wajen yaci kansa, itama ba cin yajin ta ke ba saboda Gwaggon ne dama ta saka, to kuwa duk bala'in da za'ai indai girki da ita ne ba zata fasa sanyawa ba. *Please Vote and Comment and Share.* [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(12)* Buguwar da nayi da goshin Yaya Haidar ashe ba ƙarama bace, dama ga kansa kaftarere, sosai kaina ya shiga juyawa nai sauri na dafe bango ina ganin wasu abubuwa na wucewa a duhun idona, na ɗaga ƙafana zan ɗora saman steps sai idona ya rufe gaba ɗaya, nayi baya zan faɗi sai gani na faɗo a hannun Yaya Haidar, caraf ya cafeni kamar wata ƴar Baby, to ni kam tunda na buɗe ido na kalle shi dishi-dishi na mayar da murfin idona ban kuma sanin inda kaina yake ba, sai dai kamar na jiyo salatin Gwaggo. Shuɗewar wasu awanni na farka, na ganni shimfiɗe a ƙirjinsa Ya kewaye ni da hannayensa, kuma a cikin ɗakinsa, na rufe idona yafi sau ƙirgen hannu ina kuma buɗewa don tabbatar da abinda nake gani, ni ce dai a tsakankanin cinyarsa kuma kwance bisa ƙirjinsa, bacci yake ko mene oho, idonsa dai a rufe yake, da sauri kuwa na miƙe daga jikin nasa a zabure na dira ƙasa daga kan gadonsa, domin zuwa wannan lokacin dukkan wani tashin hankali ya gama bayyana a zuciyata da gangar jikina. Duk tsoro ya gama cika ni, idona ya taru da ƙwalla yana shirin zubar da hawaye, Dama ni Allah ya horen ruwan hawaye kamar ruwan famfo, sai na koma kamar wata taɓaɓɓa, kaina fa ko ɗankwali babu kuma ba a yanda nake ɗazu ba da rigar t-shirt a jikina, wannan riga ce doguwa aka zumbula min ta atamfa, bama ta ɓangarenmu bace, don ko Gwaggo rigar nan tayi mata yawa, sai dana ƙare ma ta kallo kana na tuna atamfar sallar bara da Baba yayi mana, kenan ta Umma ce ma, ƙofa na nufa gadan-gadan sai na jita a rufe da key. Zubewa nayi a wurin na ɗora hannu aka na kurma ihu ina faɗin, "innalilllahi wa'inna ilaihi raji'un, na shiga ukuna Gwaggo tah, wayyo Allah nah shikenan Yaya Haidar ya ɓata ni, Gwaggo kizo ki taimaka min, ya rufe ƙofar, kizo kar ya ƙarasa abinda bai cimma ba". Ihu nake sosai ina shure-shuren ƙafa kamar ƙan-ƙanuwar yarinyar da aka hana shan nono. Jin yadda nake kurma ihu ina buga salati cikin fizgar numfashi, shi ya farkar da Yaya Haidar, Ganinsa nayi a gabana a tsugune don ko tasowarsa ban sani ba, ƙoƙarin saita min yanayin da nake ciki yake, kallon da yake min sai naga kamar da tsoro a cikinsa, abinda yake kawowa a ransa daban, abinda nima nake kawowa a nawa ran daban. sai matsawa baya nake ina ƙanƙame jikina, shi kuma yana daɗa matsowa kamar zai shige jikina, amma fa gefe guda idan na gasgata abunda idanuwana ke gani cikin idonsa tausayi ne tsantsa, sai dana kai maƙura a mannuwa da jikin ƙofa kana na haƙura, jikina nata karkarwa, wallahi tsoronsa nake sosai, inda za'a auna jinina a wannan yanayin tabbas jinina ya hau, shima ɗin sai daya kawo gab dani numfashinmu na gauraya dana juna tukunna naji ya kamo hannu na guda ya damƙe, ya ɗaga kofin ruwan dake ɗayan hannunsa ya watsa min, ba shiri na rumtse idona tare da kurma wani sabon ihu ina roƙonsa. "wayyo Allah nah, Allahumma ajirni fi musibati waklifni kairan minha, don girman Allah Yaya Haidar karka kuma yimin komai, kaga dai ni ƙanwarka ce". Sakin hannuna da yayi shi ya dakatar da ni daga ihun da nake kwaɗawa, ban dai buɗe idon ba sai shashsheƙar kuka da nake ina daɗa faɗin, "Yaya Haidar babu kyau kaji tsoron Allah, duk wanda ya ɓata ƴar wani shima za'aiwa tasa bare ni da nake ƙanwarka, idan ka lalata min rayuwa kai kanka ba zaka sami kwanciyar hankali ba, ka saka rigarka bana son ganinka a haka, babu kyau kallon tsiraicin wani, ko riƙe hannuna da kayi haramunne...". Saukar marin da naji a kuncina ya katse sauran surutan da nake, a zabure kuma na miƙe tsaye ina rarraba ido ina neman hanayar fita, dan duk Yaya Haidar ya gama razana ni. kuma cikin abunda bai wuce sakan huɗu ba naji murya na fita da ɓacin rai yana faɗin,"wallahi idan ba ki rufe min wannan shegen bakin naki ba sai na zare belt na zane miki jiki a wurin nan, mahaukaciya kawai, an gaya maki kowa ɗan iska ne irinki". da ƙyar na iya saita idanuwana na tsayar dasu wuri ɗaya suka tsayar da kallonsu akansa, na gwame fuska zan sake fashewa da kuka, ina dukan ƙafana a ƙasa raina na sosuwa, naji haushin ƴar iska daya kirani, to amma babban baƙin cikina daya gama ganina, abunda ba nasa ba ya gama kallewa mai shi, kai Allah ya isan mai shi, nasa hannu na goge bakina kamar yace min yayi min kiss. Bani da tabbas ɗin abinda nake zargi, banda kuma wata hujjar kafawa akan hakan, kawai dai ganina da nai jikinsa nake jin kamar komai ya faru, dan haka kawai ba zai kawoni ɗakinsa ba, ɗakin ma kan gadonsa kuma ajikinsa. saina daɗa ƙanƙame ƙirjina wanda wuyar rigar yay min yawa, na zumɓuro baki gaba ina hararsa ta ƙasan ido, shi kuma ya saki wani munafikin murmushi daya tsaya iyaka leɓensa, ya juya yaci gaba da saka maɓallan rigarsa. "tsakani da Allah Yaya Haidar me kayi mini?". Na faɗa ina zubar hawaye. "ni me zanyi da wannan ƙazamin jikin naki?, Ki dai tambayi aljanun kanki dalilin da yasa suka zo min ɗaki". Na kalla jikina nace, "ni ba ƙazama bace, Kuma ba mai aljanu bace. Lafiyata ƙalau, kuma indai ba kaine ka kawo ni ɗakinka ba wane zai kawo ni". na faɗa ina hararan bayansa kamar yana gani na. rashin amsa min da yay naci gaba da cewa, "to ma babu abinda kayi min mene ya kawo ni ɗakinka? Bayan ni bana shiga ɗakin wanda ba muharramina ba, ɗakin naka ma wai a jikinka. Gaskiya ni dai ka gama cutata wallahi, duk tanadin dana gama yi sai daka kusa rusa min, kawai kasani a jikinka bayan jikina ba naka bane". Bakina ya matse min da ƙarfi cike da mugunta, na rasa yanda zanyi na ƙwaci kaina hakan yasa na bashi mintsini a bayan hannu, babu shiri ya sauke hannunsa yana yarfewa, yana ƙarewa jikina kallo ya taɓe baki yace. "iina abin yake da har kike wani banzan tunaninki, ni ko da kuɗi aka haɗani dake aina fi ƙarfin wannan ƙazamin jikin naki... kuma wanne dare ne jemage bai gani ba kike faman ɓoye-ɓoye, karki manta a gabana kika girma, hasalima ni na fara saya maki pad, to maye ne ma za ki ɓoye min wanda ban sanda da shi ba, to idan ba ki sani ba ki sani akan idona komai naki ya haɓɓaka Yarinya". Sai kuma yaja tsaki yana cewa, "mtswwww wani ne can dai zaiyi sha'awarki amma bani Aliyu Haidar ba, wata ƴar ƙanƙanuwa dake ma ni mai zanyi sha'awa to". Amma Yaya Haidar ɗan iska ne, wai a gaban idonsa komai nawa ya gama haɓɓaka, wayyo Allah nah anya kuwa bazan kurma ihu ba ko na sami sassauci, Wani sabon baƙin ciki ya kuma tsaya min a wuya, kai tasowar yarinta a gaban namijin da gida guda kuka tashi bai yi ba, ƙunƙuni na shiga yi wanda hakan yasa shi matse min fatar ciki a salo na mugunta. Ƙara na saki ina cire hannunsa daga wurin, ya bige hannun nawa yana faɗin. "maimata me kike cewa?". "ni fa ba abinda nace". "ƙarya kike yi, ki faɗa a fili mana idan kin cika mara kunya". "to ai kaine kana cewa babu abinda zaka yi da ni, kuma dai ni nasan ba haka bane sai dai idan baka da lafiya ne. Kana ganina ba ƙwaila ba, yanda nake ƴar duma-duma da ni ai duk wani mai cikakkiyar lafiya sai yayi sha'awata. Kaima dan na taso a gabanka ne shiyasa kake raina girmana". Na faɗa ina zumɓuro baki gaba, sai faman ƙifta idanu nake, kuma duk a tsora ce nake da shi, kallon yanda yake jan gemunsa nasan wani shirin salon muguntar yake haɗawa a ransa, domin wannan munafikin murmushin nasa ba na Allah bane. "ni dai ka matsa min na wuce tunda Allah ya kiyaye ni baka yi min komai ba. Amma fa kasani sai na kwashe komai na faɗawa Gwaggo". Na faɗa ina mai ƙoƙarin ɗauke hannunsa daya tokare ni a jikin bango. Ƙwafa naji yayi wadda tasa na ɗago ido ina kallonsa, ban ankare ba kawai naji saukar bakinsa cikin nawa yana kissing ena da salo na mugunta, ture shi nake ina dukansa a kafaɗa amma yaƙi sakina saima cizo daya bani a leɓe, kuka na fashe da shi ina buga masa Allah ya isa acikin zuciyata, Zare bakinsa yayi ya ɗago yana kallona fuska a ɗaure yana aika min harara. ni ko na kai masa duka nace, "Allah ya isa ban yafe ba". Na faɗa ina ture hannunsa zan wuce, Raina a matuƙar ɓace, tunda uwata ta tsuguna ta haifeni Gwaggo ta raineni babu wani namiji daya taɓa riƙen ko da hannu, sai Yayana kawai dana taɓa riƙe nasa, shima kuma wallahi bana sanin lokacin da nake riƙe masa hannu, amma yau wani ƙaton banza ya haɗa bakinsa da nawa, bayan naci burin mallakin zuciyata ne kaɗai yake da wannan damar. Allah ya isa dana ja ita ta bashi haushi, ya fizgoni ya haɗani da jikin bango, sai daya ɗalɗalle min baki kana ya kuma manna bakinsa da nawa, Yanzu kam harshena ya kamo yana dannewa da haƙorinsa yana cizawa, sosai nake jin zafi amma bai ƙyale ni ba sai daya tabbatar jikina yayi laushi kana ya rabu da ni. "kinga yanzu sai kiji daɗin yima Gwaggo bayani, mara kunyar banza kawai". Ya faɗa hakan yana nufar ƙofa yasa key ya buɗe, bai ko kalli inda nake ba yace da ni, "zo ki fice min a ɗaki, ko na ƙara maki wanda yafi wannan". Yo baima kuma wani yunƙurin magana ba nai wufff na fice da guduna har ina waiwayan bayana kar ya biyoni. "mugu azzalumi ɗan iska kawai, kuma na rantse sai na faɗawa Gwaggo". Shine abinda nake faɗa har na iso side ɗinmu, Haka kawai ban iya rashin kunya ba yau yasa na farata, ina zuwa bakin ƙofa na saita kaina sannan na buɗe ƙofa na shiga, a parlo na sami Gwaggo zaune tana sauraren karatun ƙur'ani suratul baƙara, ta taso da sauri tana min magana ni kam nayi mata shiru na wuce ɗakina. Ina shiga na faɗa toilet na ɗauka brush da macline na shiga goge bakina kamar zan ɗaye fatar jiki. Sai dana tabbatar na goge ƙazantar bakinsa kaf sannan nai wanka na fito, ina fitowa naji wani warin turare mara daɗi ya daki hancina nayi saurin toshe hancina da bakina da towel ɗin da nake goge ruwan kaina. _"to wannan hayaƙin fa na mene?"_ Na tambayi kaina, sai naji Gwaggo ta shigo tana faɗin, "Sabina kin fito?". Ni dai ban mata magana ba saboda duk warin turaren nan ya isheni, makunnan AC naje na ware haɗe da fanka, sannan na ɗauko air freshner na feshe ɗakin, sai dana juye kwalbar duka amma fitar warin nan ko gezau, naji ba zan iya ba na buɗe closet na ɗau hijab na fice da gudu a ɗakin ina tari, ina sauke numfashi kamar wadda taci gudu, ga amai dake taso min. "sannu". Gwaggo kawai ke jaramin duk bata cikin natsuwarta, sai firfita take min. "Gwaggo wannan wane irin turare ne aka saka min a ɗaki, nafa aljanu ne ma, kinji kuwa kamar kayan cikina zasu fito". Na faɗa ina jera tari, maƙogarona har yaji yake min. Tausayina ya cika Gwaggo, bata iya amsa min ba sai ji nayi ta kirani, "Sabina". Muryarta a hankali kuma cikin damuwa. Na ansa mata ina ɗagowa na gyara ɗaurin towel ɗina, ajiyar zuciya ta sauke tana faɗin, "to masha'Allahu, Allah ya ƙara miki lafiya ya yaye miki lalurar dake damunki". "amin". Na amsa saboda adu'a ce tayi min me kyau ba tare da sanin inda adu'ar tata ta dosa ba. sai dai dubanta nake da rashin fahimta, saboda yanda damuwa ta bayyana ƙururu a fuskarta, cikin wani yanayi na tashin hankali da ban taɓa gani a ƙwayar idonta ba. "Gwaggo menene? ko kina tunanin banda lafiya? Allah lafiyana ƙalau ki daina tada hankalinki kinji, kinga zuciyata zata shiga damuwa da wannan sabon yanayin naki...ko kuma wani abu ya faru ne?". na faɗa a sanda na taso daga mazaunina na dawo kusa da ita, na dafa hannayenta dake kan cinyarta, ina tsareta da idanuwa. sai tace da ni,"a'a ba abinda ya faru, kuma ai ko ƙalau kike abune mai kyau nayi miki adu'ar samun lafiya Sabina". Ta ansa min tana miƙewa daga kusa da ni ta isa friedge ta ɗauko wani jarka da ruwa a ciki, a cup ta tsiyaya min ruwan ta miƙo min tace,"ungo nan shanye". ni dai kallonta nake da sauyin da nake gani a tare da ita, na amsa na kafa kai zan kurɓe, ɗacin maganin yasa nai saurin ɗauke kofin zan miƙe naje na zubar dana bakina saboda ruwan ba daɗi wanda sai yanzu na fahimci na magani ne. murya a ɗage tace, "dawo ko na saɓa miki, ruwan magani ne maza haɗiye shi, idan ba so kike ranki ya ɓaci ba to karki dawo min da shi". Fuskar Gwaggo babu wasa ta ke min wannan maganar, gaddama na saka mata sai da naga da gaske ta ke kana na haɗiye don dole, kuka ne kawai ban sanya ba. Ina faman yatsine fuska ne nace, "to ni wai don Allah Gwaggo taya ma za ki haɗani da magani bayan lafiya lau nake, ai ba haka ake rayuwa ba, ni dai gaskiya karki kuma min haka domin wannan cuta da cutarwa ne". "ai ban san kina min faɗa ba sai kin rufe ni da duka Sabina". "ni fa ba faɗa nake miki ba Gwaggo, ina gaya miki gaskiyar abinda bana so ne". Na faɗa ina yin narai-narai da idanu. "hmm nayi miki uzuri ƙila har yanzu ba ke bace, da kika taho Haidar yana ɗakin nasa ne?". Baki na turo gaba bance mata komai ba, ta doka min tsawa, "ba tambayar ki nake bane ki ka wani turo min baki gaba kamar zumɓutu, za ki maida shi ko saina bige miki laɓɓa". "to ni ina zan sa ni ne?". "ke kr ki maida ni sha uku, ba daga ɗakinsa kike ba?". "ni mene zai kaini ɗakinsa to, ni tun ɗazu da muka dawo ban kuma ganinsa ba, ƙila yaji faɗanki yaji haushi ya tafi gidansu". Ƙaramar dariya kawai naga Gwaggo tayi ta miƙe tana magana ita ɗaya, "wato da mai aljanu da mahaukaci dai basu da maraba, ni dama tunda naga kin shigo kin wuce fuuu kamar tashin iska nayi tunanin bake ɗaya bace, ile kuwa haka yake, to Allah ya sauƙa amma ni wannan abu naki da mamaki da kuma tsoro. Bari dai Haidar ɗin ya shigo naji sauran bayani daga bakinsa". "au wai Gwaggo kinma san ya sace ni ya kaini ɗakinsa kenan, bayan sarai kin san shi ɗin mugu ne. Kuma fa kene kike min faɗan ko ɗakin Yaya Abba baki yarda na dinga zuwa ba". "hmmm ba za ki gane bane, ni dai yau na gode masa saboda ya taimakemu. Ɗan ƙwal uba ashe yaron nan kwanyarsa cike ta ke da baiwar ilimi. Ai naga ranar Haidar yau, kuma na gode masa, dan da ace Abba ne kawai a gidan nan abin ba zai yi kyau ba tunda shi wannan bayan karatun sallah babu abinda ya iya sai buga ƙwallo". Ni dai taɓe baki nayi na gyara zamana ban ce mata komai ba. "aike Yau ki manta da duk wani rashin kyautawa da Haidar yay miki a rayuwa, ki gode masa saboda ya taimakeki". "a tsotse min bakin nawa da yay shine ya taimake ni?". A zabure naga ta yar da tsumman dake hannunta wanda ta ke goge ruwan daya zube. ta tsare ni da tambayan, "ban gama gane ya tsotse miki baki ba, bakinki dana sa ya haɗa yana tsotsa ko me?". "ehh mana, kawai ya kamani ya haɗani da bango yay ta totse min baki kamar ya sami alawa, ina ta ihu ina kiran sunanki ba ki kawo min ɗauki ba, har da cizar min leɓe yayi saboda mugunta gashi nan wurin har jini sai da yayi". Na faɗa ina kaurarra maganar yanda Gwaggo zata fusata. tsumman ta ɗauka taci gaba da goge ruwa tana cewa, "to ya zaiyi dole ce ta saka, sai yayi hakan za ki sami kanki". sai nace, "Gwaggo idan na fahimceki haɗa baki ku ka yi dai da shi kenan, shi yasa da nace zan faɗa miki ya ƙara totse min baki yace sai na faɗa miki da hujja...". sai tai saurin Katse min maganata da cewan, "keee ni fa ki daina ambatar min tsotsar bakin nan haka. Ki dinƙa cewa yayi miki tofi shine kawai, amma kya dinƙa cewa ya tsotse miki baki kamar wani ɗan iska". Ban ƙara ce mata komai ba na miƙe na bar wurin cikin fushi ina faɗin, "kuma sai dai idan Baba bai dawo ba, sai na zayyane masa komai. Ai Allah ya hana ko da riƙe hannun mace ne wanda ba muharraminta ba yayi, amma shi kaɗan ne ya rage bai min ciki ba". Ashe ta jiyo ni, tace, "kamin ki zayyane masa ni zayyane masa, ai dama dole muyi zama da shi akan wannan baƙon lamarin naki. Gaɓuwa kawai". Da daddare bayan mun kammala cin abinci, muka zauna kallo a parlo, Yaya Abba ne da Yaya Haidar suka shigo, kowanne kujera ya nema ya zauna, nayi mamakin ganinsa, amma sai na bar mamaki duk yanda akayi sun shirya da Gwaggo ne. Yaya Abba na zama yace da Gwaggo, "ina abincina?" tace, "acici mala'ikun tauna, kai daka shigo gida ina abincin ka an dafa ko ba'a dafa ba, to jeka kitchen ka ɗauka, Matarka dai ta shiga uku da ɗora sanwa dan ba zaka sassauta mata ba". Ya miƙe yana dariya ya wuce. Shi kuwa goga uban ƴan ji da kai tunda ya shigo ya zauna bai magana ba, sai faman latsa waya da yake yana wani harhaɗe rai, ni duk haushi ma yake bani, saboda bana son mutum mai faɗin rai, ni yanzu ma bana ganin girmansa tun abin ɗazu daya mani, a hakansa kamar salihin bawa nan kuwa iskanci ne fal a cikinsa. Naji Gwaggo tace da shi, "Haidar ina fa daɗa godiya a gare ka kaji". "ba komai, ki godewa Allah kawai".Ya faɗa a taƙaice, still kansa na kan wayarsa. tace,"uhm ai dama godiyar Allah ta zama dole bare ka gayamin magana. Kaine dai da nake mamaki ya kamata na maka godiya, saboda yau ka shayar dani ruwan mamaki, yanda naji kana rera ƙira'ar nan kamar Sudais". Sannan ta juyo kaina tace, "Sabina ki masa godiya kinji ko". Sai yanzu na ɗago kaina dake kan waya, ina faman murguɗe-murguɗe da harare-hare na ɗaga idona na kalle shi, karaf muka haɗa ido, sai dana tsuke fuska na taƙarƙare na murguɗa masa baki, hakan yasa shi sakin ƙwafa mai ƙarfi yana jijjiga kai. Gwaggo ta sake cewa da ni, "ke wai yanzu ba'a isa ace kiyi abu a lokacin ba kiyi ne?". yace da ita, "ba ki kalla murguɗan baki ta ke yi ba saboda bata da kunya, to wallahi ni tashi zanyi na fasawa yarinya baki babu ruwana". yay magana yana kallon Gwaggo kamin ya maida kallonsa kaina yana min kallon za ki sani. "kaga ni kuma sharri ne bana so. Yarinyar na gabana kace ta maka rashin kunya, ta ina to ni ban gani ba. Kai dai ka dinga jin tsoron Allah, Mutuwa ake yi. da ace kana da zuciya ma fa ba zaka dawo part ɗin nan ba". Murmushi kawai yay baice mata komai ba, ta ƙara cewa nayi masa godiya, godiyar da ni ban san akan mene ba, ina ɓata rai nace masa, "na gode". Yay min shiru kamar bada shi nai magana ba, na tashi ina bige-bigen ƙafa zan wuce yasa ƙafarsa ya taɗe ni na faɗa jikinsa, ina faɗowa ya aje wayarsa gefe yasa hannunsa ɗaya ya matsoni jikinsa, ɗayan kuma da mugunta ya matse min baki har na gagara yin ihu, sannan ya kai bakinsa nawa ya kamo leɓena na ƙasa da haƙorinsa ya gartsamin cizo mai shiga jiki. Ganin wannan abu ya sanya Gwaggo tashi da sauri ta iyo kanmu tana tafa hannu tana zabga salati. "ni Hannatu yau naga abinda yafi zare tsayi, ,yo dole yarinya mana tace ka tsotse mata baki, tana faɗa ina basarwa ashe maganar gaskiya ta ke faɗa min, nake cewa tofin magani ne kake mata. ba zaka sakar mata baki ba sai ka cinye mata leɓe". Shi kansa maganar ta Gwaggo ta bashi dariya, ni kuma yana mamakin rashin hankalina da kuma rashin wayona, ashe da nace zan faɗa mata sai dana faɗa. "Allah Haidar ka bari na ƙaraso nan baka rabu da ita ba kai zan shaƙe na yiwa ruƙiya ba ita ba, idan aljanun iskancin ne kaima akanka sai naji, mara ɗa'ar yaro kawai". Dariyarsa ya gimtse yana tankaɗani daga jikinsa na miƙe ina hawaye, Gwaggo na ƙarasowa na faɗa jikinta na fashe da kuka. Ɗagoni tayi tana dubana, ta kalla Yaya Haidar ta zabga masa harara, ta ɓata rai sosai tana ce masa. "nan gidan dai baka ga an rubuta gidan kashe awu daga waje ba, saboda haka ka ajiye barbaɗin iskancin ka acan inda ka baro, tunda nake da Sabina wani ƙaton gardi bai taɓa riƙe mata hannu ba amma kai saboda tantirancinka ya kai intaha a gabana ka ke cafke mata baki saboda rashin kunya irin naka, kaga baki ɗan ƙarami da shi gwanin sha'awa, to billahillazi karka ƙara tunda dai ita ba muharramarka bace. a hakan ma kaje kai da Allah, zunubin daka kwasa ma ya isheka, kuma na dawo kan bakata kar ka sake zuwar min ɓangarena tunda bana ka bane, ruƙiyarka bana so tunda na lura irin ta ƴan iskan Malaman nan ce, Malaman gaibu, to zan nemo sabon Malami da kaina wanda zuciyarsa ta cika fal da tsoron Allah. Yanzu ka tashi ka fice min kamin na sassaɓa maka kamanni dan iya ƙololuwar ɓacin rai ka gama ɓatan rai, Ban san haka halinka yake ba, a gabana ka kama bakin yarinya da tsotso kamar ka biya sadaki, kai ai da sunan ƙanwarka, to da take ƙanwarka ai akwai aure a tsakaninku ko". yace, "idan ni kince na daina iskanci itama sai ki faɗa mata ta daina rashin kunya. Don gaba yarinya ta ƙara murguɗa min baki abinda yafi haka zanyi mata". Dogon tsaki Gwaggo taja, Haidar yana dariya yana ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yace, "Easy Hajiya Gwaggo". Wani dogon tsakin ta kuma ja tana zabga mishi harara a karo na ba adadi, cikin faɗa take ce masa, "kai da Easy ɗin na haɗaku na zazzabga muku mari, Wallahi ka fita a idona Haidar, akan Sabina zan saɓa maka yanda baka zato, sarai kasan halina idan raina ya kai ƙololuwar ɓaci, zan ɗauki komai amma bazan ɗau lalacewa ba, don haka kayi gaggawar miƙewa ka bar min parlo, kuma ko sahun inuwarka kar na sake gani a ɓangarena, abinci kaje can matan gidan nan su baka idan sunga dama, idan ba su so ba su barka da halin iskancinka ya ƙosar da kai, nk dai har ka bar gidan nan na gama saka kwano da kai". Yaya Abba na dariya ƙasa-ƙasa yace, "idan kuma ya dawo gidan gaba ɗaya fa?". Kansa ta juyo da faɗan da ta ke Yaya Haidar, tasa ƙafa tayi fatali da plate ɗin abincinsa, ta haɗa sunansu dana ubansu gaba ɗaya ta zage, da alama dai ran Gwaggo ya ɓaci matuƙa, dan faɗa takewa Haidar sosai, tana nuna masa kuskuren abinda yayi, wanda shi kansa sai da yayi dana sanin abinda ya aikata. A tsawace cikin ɓacin rai tace da su, "ku tashi ku ɓace min daga gani". za su fita Baba ya shigo, Gwaggo tace,"yauwa ƙwara da Allah ya kawoka, tunda ni basa ganina da gashin ido bare suji maganata, kaja musu kunne kar su ƙara zuwar min ɓargarena tunda babu tsiyar da suke yi min, duk su biyun bana son sake ganinsu anan dai inda nake, suje can su ƙarata da halin su na rashin ƙwarai, dama ance abokin ɓarawo ɓarawo ne to abokin ɗan iska ma ɗan iska ne. Ko kwanon abinci sun daina ɗauka a wurina, idan zaka dinga basu kuɗin saya sai ka basu, idan ma da matanka zaka haɗasu ka haɗasu, kai idan ma aure zaka yi musu ku dai kuka jiyo kai da su, ni ba damuwata bace, babu ruwana, buƙatata dai a daina zuwa inda nake, idan ba haka ba kuma duk abinda nayiwa mutum shi yasa ya da kuɗinsa". Baba ya dube su yay musu kallon tsab, kansu yana ƙasa sun sunkuyar yace da su, "mahaifiyata ce fa, rashin kyautawar mai kuka yi mata?". Da sauri Gwaggo ta ɗaga masa hannu tana cewa, "n ifa bana buƙatar sulhu, su fita kawai kuma ka gaya musu karsu ƙara dawowa". "shikenan kun dai ji abinda tace, ku fara bata haƙuri kamin ku tafi". "Gwaggo kiyi haƙuri". Suka faɗa tare. tayi musu kallo mai harara, tana nuna Haidar da yatsa tace da Baba, "kai Auwalu wancan yaron idan aikinsa ba mai ƙarewa bane a kusa to ka nema masa wani gidan ya koma can da zama, bana son ganinsa a gidan saboda bashi da mutunci". Ƙaramin tsakin da Yaya Haidar yaja duk sai da muka jiyo, Baba ya juya zai masa magana yaga har ya fice, Gwaggo na jijjiga kai tace, "kagani ko, sam bashi da mutunci. Banda Allah yasa a gabanka ne da zagayowa zaiyi ya bangaje ni tukunna yasa ƙwalelen kansa ya fice. Ɗan banzan yaro mai kama da alkaki sam baiyi halin ƙwarai ba, shi Sulaimanun zai zo ya same ni, naji idan akan hanyar daya ɗora shi kenan". Baba ya nemi wuri ya zauna, nai masa sannu da zuwa, yana kallon yanayina yasan faɗan Gwaggo da su Yaya Abba akaina ne. Gaisheta yayi yay mata sannu da gida, "yauwa". ta ansa mishi. "ya aikin naka?". "Alhmdl". sai naji yana cewa, "Gwaggo tun ɗazu kika ɗaga hankalina, da kika kira kika ce akwai matsala nayi gaggawar tahowa, lafiya dai ko?". "tun a lokacin da na kiraka mai ya hanaka dawowa?". ta faɗa muryarta na nuna ɓacin rai. "kiyi haƙuri ko a lokacin mun riga mun shiga meeting ne, to naso tahowa sai kuma naji kince na kwantar da hankali na amma dai na dawo gida, jin haka nace ba babbar matsala bace har na kammala komai ma". "to dama akan Sabina ne". Na ɗago da sauri ina kallon Gwaggo, gabana na faɗuwa, to ni kuma ƴar gidan Gwaggo na mai nayi. Baba naji yace mata, "me Sabina ɗin tayi?". tace da shi, "kaji na taɓa kawo maka ƙararta ne da zaka tambaye ni me tayi, to ita bata laifi salahar baiwa ce, ka dai ce me ya faru da ita". Baba ya haɗiyi yawu yace, "to mai ya faru da ƴar lelen taki?". "aljanu ne da ita". "aljanu kuma Gwaggo". Baba ya faɗa yana zare ido, don maganar sosai ta dake shi. "ƙwarai kuwa, amma basu yi nasarar shigarta ba, sun dai shafeta ne, wancan fitsararran baƙon yaron shi yay mata ruƙiyya kasan Malami ne, ƙwaƙwalwarsa taf da haddar qur'ani amma babu tsoron Allah a zuciyarsa, amma haka dai na haɗashi da ita yay mata karatu da adu'oi, sannan ya fita cikin gaggawa yaje islamic chemist ya haɗo magunguna da turare aka haɗa mata, nan da nan cikin ikon Allah komai ya lafa. amma farko fellawa tayi da gudu, da ace babu mai gadi ma ba'asan inda zata nausa ba, nan ta faɗi tana aikin shure-shure da buge-buge da ife-ife. Ashe ajiye shirgegiyar mace ma acikin gida yana da amfani, don wannan ƙatuwar matar taka ita ta ɗaukota duk uban nauyin da suka sa Sabina tayi, don ni dana ɗaga hannunta ma banyi zaton hannun mutum na ɗaga ba...yau ai Ƙatuwar can tayi min rana". jin abunda ta ke cewa yasa na fashe da Kuka, gaba ɗayan su hankalinsu ya tattaro ya dawo gare ni, musamman ita da ta ke bada bayani. "me kuma aka yi miki?". ta jefo min tambaya. ina shashsheƙar kuka nace, "Gwaggo aljanu fa kike cewa ina da su, kinsan kuwa mene aljanu, na rantse ni lafiyata ƙalau". Wata harara ta jefa min kamin tace, "nufinki ƙatuwar mace da ni zan zauna ina gillawa ubanki ƙarya ne, to ribar mai zan samu idan nayi miki fatan wannan lalurar da ba'a so, mtswww shi yasa ɗazu nake gaya miki da ku masu aljanu da mahaukata ɗaya kuke, tunda duk bakwa sanin abinda kuka aikata a lokacin da kuke kan ciwo. To a faɗuwar da kika yi ɗazu sune suka zo, Allah shaidata, Haidar Shaidata, Matan gidan nan shaidata, a tou balle ace nayi ƙarya, ƙwamma na sanar miki gaskiyar komai kamin ki ƙullaceni a zuciya". Shiru nayi ina ci gaba da kukana, ƙasan zuciyata kuma ina tantamar anya Gwaggo bata fara daina ƙaunata ba. "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un". Shine abunda Baba ke nanatawa cike da al'ajabi da kuma tsoro. "Sabina garin ya haka ta faru, me yasa kikayi sakaki da azkar?". "Allah ni Baba bana da wata iska, kawai dai faɗar gwaggo ce kuma ka kira shi Yaya Haidar ɗin ka tambaye shi, anyi haka ko ba'ayi ba, tare ma mukaje koyon mota, kuma har yanzu ma muna zaune da su shida Yaya Abba babu abinda ya sameni. Ina jin dai ko Gwaggo ta fara rikicin tsufa ne, shine ta fara rikicewa ta kaina". Ta kalleni ta jijjiga kai, "to ai kaji, itama ta hau sahun waɗancan fitsararrun yaran, amma ba laifinta bane ita zan mata uzuri, tunda yanzu ta zama ba ita ɗaya ba, adu'a kawai zan bita da ita, idan na fahimci kuma sune sai na hauta da duka". Ta kalle ni tace, "ki sami damar yimin shiru, Allah yasa a gaban ubanki ne bare kija ace zane miki jiki nayi, kin ɓare baki kina kuka mara daɗin saurare, Kefa dama haka halinki yake wani zubin, sam-sam ba ki da daɗin sha'ani". na kuma fashewa da sabon kuka na miƙe zan bar wajen. "dawo". Tace da ni. Na koma na zauna ina jin kamar nayi me saboda baƙin ciki. "to yanzu Gwaggo mene abunyi?". Baba ya tambayeta. tace, "abunyi shine ka tattaro min kawunan Matanka suzo nan. Don ina tantama da wannan Al'amarin, ni dai ba aljanu ba, kai ba su ba, uwarta har ta mutu babu wata alama data nuna tana ɗauke da aljanu, kai kafatanin dangina ban samu labarin wanda ke ɗauke da su ba, kaga kuwa bana gado bane. Bugu da ƙari shekarar mu nawa a wancan gida kamin mu dawo nan, babu wata alama da taɓa nunawa tana da mutanen ɓoye sai da muka zo nan. To da sake a wannan lamarin, su zo idan acikinsu akwai mai su sai ka kwashe su daga gidan nan, kuje can kai musu magani idan sun warke sa dawo. Idan kuma ma wani mugun ƙullin aka ɗaura to azo a warware shi anan, don wallahi aka kuskura na gano ture ne akayiwa Jikata ba za'aji da daɗi ba". Baba yace, "To amma Gwaggo ai a cikinsu kaf babu mai aljanu". a harzuƙe tace, "shine ai nace maka ka kirasu suzo koma wace acikinsu, to ta kunce baƙin ƙullin da tayi tun wuri, dan billahillazi bani da kyau, ni gaskiya ce nake faɗa babu ruwana. Kar na ɗau mataki kai tsaye ace nayi rashin kyautawa...dan kai kanka ba zaka ji da daɗi ba". *Please Vote, Comment, and Share.* [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(14)* *Monday Morning.* kasancewar yau monday tushen aiki, kuma yau ɗin da izinin Allah zan fara ɗaukan lectures, dan haka tunda na kammala azkhar ɗina ban koma bacci ba shiri kawai na fara yi, kwalliya nayi sosai wanda ta ƙarɓe ni matuƙa musamman dana ɗora da medical glass ɗina, dama gani ƴar son kwalliya da ado, tabbas duk wanda ya kalle ni dole ya so kuma gani na. Tunda na fito parlo na kalla yanayinsa nasan Gwaggo bata tashi ba, saboda indai ta farka ta fito zata sa karatun ƙur'ani ta kuma saki turare. jakata da mayafina na aje kan kujera na wuce kitchen don samarwa kaina abinda zanci, dai-dai da zan shiga nayi karo da Yaya Haidar zai fito, da sauri naja baya nayi gefe a tsorace, Allah ya taimake ni ban tankwaɓar masa da tea cup ɗin dake hannunsa ba. Na murguɗa baki gefe don banda niyyar gaida shi, sai naji kamar na koma idan ya fita sai na dawo, sai wata zuciyar tace min kawai na tsaya na ƙara bashi hanyar wucewa, ina kallonsa ya wani haɗe rai yana jifana da harara, bai yi niyyar saurarena ba amma saboda neman magana yaja tsaki yana kallon kayan jikinsa kamar nayi masa ɓari a jiki. Ya ɗago ya kalle ni yana kuma hararata, ya ƙara jan tsaki yace, "ba kya gani ne da ba za ki iya lura da tahowar mutane ba". Na kalle shi kaɗan nace, "ai ban san da tahowan naka bane, kuma ina sauri ne". Tsaye yayi yana kallona ta ƙasan ido, "stupid girl". Ya faɗa yana ƙare min kallo ta ƙasan ido, ni dai zumɓuro baki nake ina alla-alla ya wuce, wayarsa ce tayi ƙara, ya ɗauka yana waya, sai daya gama wayar kana ya bar wajen, nabi bayansa da murguɗa baki. Ni dana shiga kitchen ɗin ma rasa me zan dafa nayi, na duba agogon dake saƙale a wurin, lokaci ƙara tafiya yake kuma yau tara ne zamu shiga lectures, ga time har takwas tayi, na doki ƙafa a ƙasa, ko me fa zan dafa sai yaja min lokaci tunda ni bacin Indomie nake ba, ko da tea ɗin zan dafa it will take time too, tunawa nayi da Yaya Haidar zai fita da tea Kettle a hannunsa, da sauri na suri cup da spoon, na zuba madara da bounvita da nescape na fita, ina zuwa kuwa na sa me shi kan kujera yana kurɓan shayinsa, naje gabansa na tsaya ina sosa gefen kunnena. Ya saci kallona ya ɗauke kai kamar bai ganni ba, na turo baki gaba na duƙa gaban table zan zuba tea a tsawace yace da ni,"kee". Na ɗago ina marairaice fuska nace, "Please Yaya Haidar, Makaranta zan tafi and idan nace i will wait to cook something i will be late. tea ɗin da yawa, barinsa ma za'ayi tunda Gwaggo is not drinking". Na faɗa ina ɗaga kettle ɗin na jijjiga naji yawansa. "wallah idan ba ki aje min kayana ba sai na zabge ki da mari, ke kika dafa min da za ki zo kice na ba ki, mara kunya kawai ana magana kina turowa mutane baki, me zai hana ki jira Kakar taki tazo ta dafa miki, ko kuma ni sa'an kine da zan dafa abu kici". ya faɗa yana ƙara tamke fuska. Na aje ina ƙunƙuni ina cewa, "to amma ai dai a kitchen ɗin Gwaggo tah aka dafa". Ashe ya jiyo ni, hakan yasa yace, "an dafa a kitchen ɗin nata kuma baza'a bayar ba, bar min nan wuri ko kuma nayi ball da ke". Na miƙe na bar masa wurin, cikin raina ina faɗin mutum ba abinda ya iya sai shegen ci, tunda yazo gidan nan kamin kowa ya tashi zaka kalla ya tashi ya dafa abincinsa, kuma aikinsa kenan shan tea ko da rana ko da dare, sai kace wani balarabe. Kitchen na wuce na ɗora ruwan zafi, yana tafasa na sauke na dama curstad, na fito na wuce dining nayi zamana ina shan kayana, Gwaggo ta fito ta sameni, tana kallona ta fahimci akwai abunda akai min. dan haka ta dakata daga gyaran ɗaurin zane tace min, "ke kuma me aka maki kike faman ɓata rai da sanyin safiyar nan? duk daƙe dama uwar miskilanci ce, ko ba'a taɓa ki ba iskokanki zuwa ɗaukar fansa suke". Na aje cup ɗin na ture shi daga gabana, daga tashinta zata hauni da faɗan da baya ma ta wahala. Taja ƙaramin tsaki tai juyawarta zata bar wurin tana cewa, "ke dai kika sa ni da halin nurƙufancinki da baida kyau, tashi na kenan ban bawa cikina ba, ba za ki sa ni magana ba". Na fara shashsheƙar kukan ƙarya nace, "to ba Yaya Haidar ba ne". Cak ta tsaya ta juyo tana kallona, "aina kuka haɗu da Haidar ɗin har kika masa rashin kunya, ban hana ki shiga sabgarsa ba, ina ce na miki faɗan babu ruwanki da shi ko". "ni fa ba sabgarsa na shiga ba, shine don nace ya sammani tea yaƙi, kuma nace masa na makara a school amma duk da haka ya hanani yace zai zabga min mari, yace naje na taso Kakartawa tazo ta dafa min". a wani sukwane ta dawo da dubanta kaina gaba ɗaya. "to shi aina ya sami tea ɗin bayan su ba kitchen garesu ba, kuma dai matan gidan nan basu isa tashi ba bare ace sun dafa sun bashi". "anan fa yazo ya dafa, na fito zan wuce na gansa ya fito daga kitchen". ta jijjiga kai kamin tace,"shi Haidar ɗin wai? Kai wannan yaro akwai baƙin hali, ruwan shayin da zai sammaki ba wata tsiya ba, ɗan ƙwal uba ina ce ma arziƙin ubanki yazo yake ci. tukunna ma ban ce masa kar ya kuma zuwar min sashena bane". "to dai ai gashi can yana kallo". Ta juya ta nufa inda yake, tana zuwa ta ƙarasa gaban socket ta kashe tv ɗin da yake kallon news ɗin da bai gajiya, ni nama rasa uwar me yake ji da news ko da yaushe, yana ganinta baice mata komai ba haka itama bata kula shi ba. Sannan ta kirani, ina zuwa tace, "kashe min wannan na'urar sanyin". Na jawo ƙaramin table na ƙara tsayi na kashe. Ita kuma ta ƙarasa taje ta janye table ɗin da ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, ƙafafunsa suka zube a ƙasa, ina kallon yanda ya cika yay fam ƙiris yake jira ya fashe, nasa hannu na toshe dariyar dake ƙoƙarin fitowa, tasa hannu a aljihun gaban rigarsa ta ciro handkerchf nasa sai tashin ƙamshi yake, ta shiga goge table ɗin daya ɗora ƙafafun nasa tana ta magana kamar bada shi take ba. "Haka kawai a dinga shigo maka wuri da sanyin safiya ko tashi baka yi ba ana takura maka. kuma ba taya aikin fari bare na baƙi, sai dai a hakimce a ware maka na'urar sanyi a kunna maka tv ana sauraren yaren da kai ba jinsa kake ba. Kuma Duk abi a zuba maka dattin ƙafa akan glass, ka yiwa mutum magana ya daina zuwar maka wuri amma saboda ba shida zuciya zuwa yaƙi ya daina, dole dai sai an saka magana, to na kashe kayayyakina kar na soma naji an ƙara kunna min kayan kallo". Maganar ta ke kamar bada shi ta ke ba, tana gamawa ta wurga masa hanky nasa. Ina dariya ƙasa-ƙasa naje kusa da shi na ɗauka mayafina da jaka ina cewa. "Gwaggo zan tafi, ai mana adu'a Allah yasa mu shiga a sa'a". "to kin ƙoshi ne? ko za ki sha shayi ga saura naji a cikin butar nan, ƙila wannan yaron ne ya dafa". Na kalla Yaya Haidar naga ya ɗago yay mata wani kallo, ran nan nasa a haɗe, kawai dan na makara ne amma ko dan na ƙara ƙular da shi da sai na sha, na cije Leɓena ina dariya nace. "a'a Gwaggo bana sha, na ƙoshi ai". "to shikenan yana da kyau na tambayeki ne. Saboda ni ba sha zanyi ba ƙarshe zubar da shi zanyi. ban san ma wane shishshigi ne yasa aka zo aka wani yimin girki a kitchen ba tun gari bai washe ba, kamar ka saka mutum, a dai dinga jin tsoron Allah almubazzaranci babu kyau. kuma wani abin dariya da takaicin kai ɗin dai da aka raina duk tsiya wurinka ake zuwa". ni dai kamar kar na tafi haka nake ji, idan kuga yanda Gwaggo ke magana zaku rantse da kanta ita ɗaya takeyi, saboda yanda ta nuna tamkar babu inuwar Yaya Haidar a wurin, shi kam ina da tabbacin a zuciyarsa ji yake inda ace yana da iko baiga me hana shi saka mata hannu ajiki ba. maganarta ta dawo dani daga tunanin sakanni biyun dana lula. "ki shige ki tafi Allah ya bada sa'a". na ansa da,"amin". Zan fita kenan Yaya Abba na shigowa, na gaida shi ya ansa min, ni kuma fice. Part ɗin Baba na wuce, Anty na samu a parlo tana jera masa kayan breakfast, ina zama kan kujera nake gaisheta, amma ƴar matar nan ko iskar da ta kwaso ni bata kalla ba bare nasa ran zata amsa min. nima na bawa banza ajiyarta, sai can dai dana ga zaman ba zai kai min ba nace da ita,"Anty ina Baba?". tace, "ba dai kinzo ɗakinsa ba, sai ki jira ki gani idan zai fito ko ba zai fito ba. Ni bana son kinibibi". ta faɗa tana wucewa ɗaki ta barni zaune anan, nafi minti goma zaune banga alaman Baba zai fito ba, hakan ya tabbatar min bata sanar masa da zuwana ba. Raina duk yay ba daɗi, na ɗauka wayana na kira Baba, ringing biyu kam ya ɗaga, yanayin da yaji muryana ya shiga tambayana ko lafiya. na kauda ɗacin dake ƙasan maƙoshina nace,"lafiya lau Baba, nazo wurinka ne kuma ban sameka a parlo ba". sai muryarsa ta far fita da sautin faɗa-faɗa. "a'a to wannan wane irin shirme ne, ba sai ki hauro saman ba. Tun yaushe kike nan a zaune?". Dan dai ban iya haɗa rigima ba da nace masa Anty tasan da zuwana, to amma saboda bana son ɓacin ran Baba kuma ni bana so naga ana fitina acikin gidan sai kawai nace masa,"tun ɗazu ne, kuma zan tafi school ne gashi harma na makara". "sorry my daughter gani nan bara na sakko". Ko minti biyu ba'a ƙara ba sai gashi ya sakko, ya zauna kan kujeran da nake, kaina na ƙasa yasa hannu ya ɗago da fuskana, ganin idona ya ciko ya ɗaga hankalinsa. "whats wrong?". Ya tambaye ni. na girgiza masa kai alaman ba komai. "no no ba kya min ƙarya fa". Ina goge guntun hawayen daya sakko min nace, "ban ganka bane". nai mas aƙaryar hakan, wanda a haƙiƙanin gaskiya a lokacin ina kewar mahaifiyata ne, sai Yay murmushin manyance yace, "rainon Gwaggo sarkin shagwaɓa, to yanzu gani me kike so?". Dai-dai lokacin da Anty ta ƙaraso da tea flask hannunta, ta aje kan dining sannan tazo ta zauna itama, tana murmushi ta ke ce min. "Ƴar gidan Babanta har an fito, yau za'a fara shiga makaranta ko, to Allah ya taimaka a maida hankali sosai kinji, banda wasa don Allah, abinda aka je yi shi kawai za'ayi". Tsabar mamaki kasa ce ma ta komai nayi, nai kamar ban jita ba don kar ma Baba yace wani abun. Nace da Baba, "dama zan wuce makaranta ne nace bari nazo na gaisheka". "oh yaune fa za ku fara taking lectures ko, eyyah sorry dear na ɓata maki lokaci". Ya zaro 2k a aljihu ya bani, na amsa ina sambaɗa masa adu'a da kuma godiya. Nace masa ko zaisa Yaya Abba ya kaini, idan naje yau naga yanda yanayin school ɗin namu sai na fara zuwa da nawa motan. Ya kira Yaya Abba a waya yace masa ai yanzu ya tashi ko wanka bai ba. "ina Haidar fa?". Ban san me Yaya Abba yace masa ba naji yace, "to kace masa ya fito ya kai Sabina makaranta, yay sauri tayi late". Mu kai Sallama da Baba na tashi zan tafi, Anty tace, "Sabina tsaya kisha tea mana nasan ba lallai kinyi break ba". "na ƙoshi". nace da ita ataƙaice. cike da ƙwaracewa na kissa tace, "a'a ni dai nasan ba ki ƙoshi ba, saboda ba ki ci komai ba tunda ban kai muku ba, ki daure kizo ki zauna ga plantain nan kici ko kaɗan ne, ba kya tafi makaranta a haka ba". Shi dai Baba wayarsa yake dannawa, ni kuwa mamakin kisisinarta nake. ta kuma cewa, "to ko na zuba miki a flask ne sai ki wuce da shi?". Ƙaramin tsoki naja, na ɗaga kai na jefa mata harara nai tafiyata. sai ga su Aisha sun shigo, suma jikinsu sanye da uniform, Zainab da Khadija ne kawai suka gaida ni, amma Aisha da Amina da suke ganinmu kai ɗaya kallo ɗaya suka mani suka ɗauke kai suka wuce inda Baba ke zaune. Kuɗin makaranta ya basu, ina ji kuma yana musu faɗan latti da suke kullum. Suka bashi haƙurin kan zasu daina. Aisha tace, "Baba yau Umma bata da lafiya tace ba zata iya kaimu ba, sai dai ko Anty ta taimaka mata ko kuma kasa Yaya Abba". Anty tayi karaf tace, "a'a ga Haidar nan zai kai Yayarku, sai ku tafi tare ya saukeku". Baba yace, "ehh hakan ma yayi, kuje Allah ya bada sa'a". A bakin mota muka tsaya muna jiran fitowarsa, ni dai kamar na haƙura da binsa na hau motana kawai na wuce, tun fa ɗazu Baba ya kirashi ko shirin me yakeyi ai yaci ace mun fito mun same shi ma yana jiranmu, kuma duk dan ni zai kai ne shi yasa yake wannan delay ɗin. "Yaya anya kuwa Yaya Haidar yana nan. Kalla fa morethan 5minutes muna tsaye nan muna jiransa bai zo ba. Ni kam yanzu ma nasan an rufe gate". Khadija ta faɗa kamar zata yi kuka, da yake itane autarmu. Har na taka ƙafana zan bar wurin sai gashi ya fito yana gyara zaman hularsa, fuskar nan a ɗaure babu alaman kawo wargi, sai wani takun ƙasaita yake kamar jinin sarauta, na taɓe baki na harari inda yake, ya ƙaraso ya buɗe motan, na buɗe da sauri na shiga. Ya duba su Aisha dake ƙoƙarin shiga yace, "ku kuma fa?". "Baba yace ka aje mu a hanya". Amina ta bashi amsa, ya wurga musu harara ya shigo cikin fushi ya figi motar, Allah yasa na rufe ƙofar da ba abinda zai hanani faɗawa waje. su muka fara saukewa tukunna muka wuce tamu makarantar, sai daya raba tafiyar biyu naga yaja yay parking, ya kashe motar yana danna wayarsa, naga bashi da alamar ci gaba da tafiyar na kalle shi nace, "Yaya Haidar ya dai, ko wata matsalar ce ta sami motar?". Shiru yay min kamar bada shi nake ba, sai dana ƙara magana a karo na uku tukunna ya juyo a fusace yace, "Get out". Na tsaya ina kallonsa, zan kuma magana ya doka min tsawa, "ba za ki fita ba". Na buɗe motar na fice, dama jira yake ina fita ya figi motarsa ya buɗe ni da ƙura. Na samu na tari mai napep ya ƙarasa da ni. Yau na kuma yarda da cewan karatun university bana wasan yara bane, sai na tuna Farhana tah da idan ta dawo tana min complain nayita ce mata raguwa, ita dai bata son karatun ne kawai. Ashe abin ba haka yake ba, lectures uku muka yi ayau kuma duk masu zafi, Har sai dana ji dama ba Accounting na zaɓa ba. Ƙawar da nayi Asma'u tai dariya tana cemin, "to ce miki akayi sauran courses ɗin sauƙi gare su, kowanne da irin nasa wahalar, ke dai Allah ya bamu sa'a kawai". "kuma fa haka ne". Na faɗa ina zura sauran littafaina a jaka. Nace ma ta, "muje ko". Har titi muka zo ni da Asma'u, Anan ne muka rabu, ta hau mota ta wuce ni kuma na tsaya jiran wani, saboda hanyanmu ba ɗaya ba. Sai dana jima tsaye rana duk ta gama zane ni sannan na sami taxi na hau. A matuƙar gajiye na dawo gida, ina shiga parlo nai wurgi da jakata na haye kan kujera dan ko ɗaki bazan iya ƙarasawa ba, takalman ƙafata ma ban cire ba. "Lazy lazy". Yaya Abba yace da ni cikin sigar tsokana. "Yaya Abba wallah ba wani zancen Lazyness, kaga wuyan da muka sha kuwa, Allah ya haɗamu da wani lecturer mara mutunci mugu harda mana test". "to yace ko kinyi abin arziƙi?". "ahh na rubuta masa abinda na iya, na bar masa wanda ban iya ba. Allah tun ƙwaƙwalwata na ɗaukar komai har nazo na daina kwashewa". "dagewa za kiyi yarinya. Karatun bana yara masu lalaci bane". Nai murmushi kawai na juya na gyara kwanciyata, kamar an tsikare ni na zabura na miƙe, na duba Yaya Haidar wanda ke kwance shima kan kujera, na sauko na buɗe jakata na ɗauko littafina na nufi wurinsa. "Yauwa Yaya Haidar kaine kayi Statistic, Please help me to solve this". Kamar bada shi nai maganar ba, "Yaya Haidar please mana". Ya kuma share ni. Na miƙe da sagaggiyar gwiwana zan tafi sai kuma yace, "lem me see". na dawo da ƴar murnata na miƙa masa yace, "i dey hear you; readout". ya faɗa ba tare daya dubi ko inda littafin yake ba balle ni. ina waro ido waje nace, "tabɗi ai bazan iya karantowa ba, wasu numbers ne fa a watsaltsale". sai ya saki wani Silent smiling, ya miƙe zauna ya amsa littafin yana dubawa. tamkar wanda na matsewa baki na masa dole haka yake magana, to ni me ma nake ji, shi ɗaya yake maganarsa a cikinsa, kuma nan wai bayani yake min yana aikin buga calculator, na kallesa na zabga masa harara kamar yana ganina, na haɗe girar sama da ƙasa na warce littafina na tashi na bar wurin nayi ɗakina, Gwaggo dake fitowa daga kitchen ta bini da kallon yanda nake ɓata rai ina jiran fashewa da kuka. Ta juya ta kalla Yaya Haidar daya koma yay kwanciyarsa, sannan ta kalla Yaya Abba wanda ke ɓaɓɓaka dariya ko akan mene oho, shi dai da wayarsa ne, tayi ƙwafa ta koma kitchen da plate ɗin abincinsu da zata kawo musu. Ta hau sababin. "yanzu fisabilillahi yarinyar daga dawowarta makaranta dan zalunci aka ɓata ma ta rai, ko hutawa fa ba'a barta tayi ba ta numfasa, kawai saboda ana Ma ta baƙin ciki, to mutum yaje shi da Allah dan ni dai ba yarda zanyi ba, kuma abincina ne ba zan bayar ba, aje wani wurin aci". Ta sawa kitchen ɗin ƙaton padlock ɗin da tace Baba ya sayo mata ɗazu, saboda Yaya Haidar daya ke zuwa yay mata ɓarna a ciki. Yaya Abba daya jita tana wannan sababi ya taso yana bata haƙuri, saboda shi baya wasa da cikinsa, akan abinci zai maka ladab iya ladab, Gwaggo ta masa wani kallo ta ɗauke kai. "kauce ni zan wuce". "haba Gwaggo, bafa a wasa da yunwa, kina kallo har ƙarfe biyar bamu ci abincin rana ba, ni dai don Allah kiyi haƙuri ki bamu abincin nan. Waccan yarinyar babu abinda aka mata halinta ne kawai". "mtswww babu abinda aka mata zata zo ta wuce ni haka fuuu kamar tashin iska babu magana, ko fa sannu da gida bata yi min ba. Kuma sarai nasan kune kuka ɓata mata rai, dan wannan ba halinta bane na rashin kyautawa, saboda haka idan kana so na baku abinci kaje ka taso wancan mara kunyar yaron kuje ku sameta ku bata haƙuri, idan ta haƙura shikenan idan bata haƙura ba kuje wani wurin kuci". "please mana Gwaggo". Ya faɗa yana haɗa hannayensa. "please ɗin gidanku, dilla ni gafara min ina da abinyi, ai ni Abba kana bani mamaki, irin girmamawa da biyayyar da yarinyar nan ke maka wallahi sam bata cancanci wani abu ɓacin rai daga wurinka ba, a rayuwa bata da wani zance sai Yaya Abba, wanne kalar bauta ne bata maka ba, bini-bini tana cikin maka wanki da guga, har gajeran wandonka wankewa take, amma ka rasa da me zaka dinƙa saka mata sai dai ka taƙarƙare ka ɓata mata rai, babu batun sanyata farinciki. To kaje kowa dai yay na gari kansa". Ta ture shi ta wuce, taje ta ɗauke mayafina da jakata ta barsu anan da yunwarsu dan ta rantse ba zasu ci abincin ba. *Please Vote, Comment and Share.* [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(15)* *Kano, Bompai Police Station.* *9:00pm, Officer Office.* "wallahi ba zan yarda ba, kuma ba zan yafe ba, dan haka Officer kayi moving case ɗin nan zuwa court a gobe". Dattijon dake zaune kan kujerar dake fuskantar Officer Yahya Murtala ya faɗa, cikin hargowa yake maganar, yayinda fuskarsa ke ɗauke da tsananin ɓacin rai da kuma tashin hankali. wannan tashin hankalin daya sameshi tun a ranar da aka sami gawar ƴarsa da aka yiwa fyaɗe. Officer ya sauke numfashi sannan ya koma baya ya jingina daga jikin kujerarsa dake juyawa da shi gefe zuwa gefe. biron dake riƙe a hannunsa a saman leɓensa yay shiru yana nazari, tsawon wucewar daƙiƙa uku tukunna ya sake sauke numfashi ya fuskanci Alhaji Musbahu Wasai yace da shi,"Alhaji karfa ka manta har yanzu bamu da wata ƙwaƙwƙwarar hujjar da zamu tura wannan yaron kotu, zarginsa kawai muke, har yanzu bamu tabbatar ba". Alhaji Musbahu Wasai ya taso masa sama acikin muryar faɗa yana cewa,"Officer babu wani batun zargi anan. akwai wata hujja da za'a samu ne bayan wacce muka da ita?...sai dai kuma idan wanda yay wannan aika-aikar ne ya biya...". bai kai ga ƙarasa maganar ba Officer ya ɗaga masa hannu. "Alhaji ba'a ɗakin matarka kake ba, saboda haka ka iya bakinka anan wurin". sai kuma shiru ya sake ratsa ofishin gaba ɗaya na wucewar wasu sakanni. kamin daga bisani Officer ya ɗaga waya ya kira, cikin daƙiƙar da ba zata haura ɗaya ba Corporal Murshid ya shigo, tsaye daga gefen table ɗin Officer ya sara masa, sannan muryar Officer ta fito cikin bada umarni. "Corporal". "yes Sir". "kaje ka faɗawa Sergeant a ƙara komawa kan yaron nan. ayi duk yanda za'ai musami abunda muke so ayau ɗin nan". Corporal ya ƙara sarawa yana cewa,"Oak Sir". daga hakan ya juya ya buɗe ƙofa ya fita. Officer ya kalli Alhaji Musbahu yace,"kai kuma kaje zamu nemeka...sai dai abunda nake so kayi keeping a mind ɗinka shine, hukuma bata gudar da aikinta ta irin tsarinka...mun san abunda muke, mun kuma san abunda ya dace...i hope you get me". Alhaji Musbahu bai ce komai ba ya miƙe tsaye yana bin Officer da wani irin kallo sannan ya taka ya wuce zai fita, sai daya je bakin ƙofa maganar Officer ta dakatar da shi. "ina fatan kasan inda ka kawo case ɗinka, Bompai!". Alhaji Musbahu ya jijjiga kansa kawai sannan ya buɗe ƙofar ya fice. *9:30pm, cikin Cell.* kansa duƙe yake a ƙasa, yayinda hannayensa ke riƙe da kumburarriyar ƙafarsa, ciwon dake saman goshinsa na zubar da jini kaɗan-kaɗan. yaja dogon numfashi ya sauke tare da rumtse idonsa sakamakon zafin ciwukan dake ratsa ilahirin jikinsa. _"Ya Rahman ka kawo min agaji, ka kawo min ɗauki, ubangiji ka wanke ni daga wannan laifin da ake zargina da shi. Allah ka bani ikon cinye wannan jarabawar"._ zafin ciwon dake kafaɗarsa yasa shi ƙara rumtse ido sosai, wanda ya tabbata idan ba karaya bace to ya sami targaɗan ƙashi. _"Ya hayyu ya qayyum"_ itace kalmar da yake ta nanatawa a fili har zuwa lokacin daya fara samun sassaucin zafin ciwon. sannan ya ɗago da kansa ya jinginar jikin bango yana sauke numfashi a hankali a hankali. kuma lokaci ɗaya hoton Sabina ya shiga haska masa acikin ƙwayar idonsa, maganganunta kuma na waccen ranar suma suka haska a kansa, ranar data zama ta ƙarshe daya gargaɗeta akan karta ƙara zuwa inda yake, har yay mata rakiya zuwa titi ta hau mota. a dawowarsa, mazauninsa inda yake rayuwa, wata sabuwar ƙaddarar da zai iya kiranta da mafi muni ta kama ƙafarsa, kuma bata sake shi ba har sai data kawo shi nan, cikin wannan cell ɗin da kwanaki ashirin da biyar kenan yana cikinsa, ba zaman daɗi ba, zama na wahala da uƙuba, zaman da a kullum yake cewa inama mutuwa tazo ta ɗauke shi. sai dai a kullum abu guda zuciyarsa ke faɗa masa, ba zaka mutu yanzu ba, ba zaka mutu ba Alhussain har sai gaskiya tayi halinta, ba zaka mutu ba har sai ka fita daga wannan zargin. lokaci ɗaya yaji wani abu da bai san menene shi ba ya wuce ta maƙogoronsa, yayinda Sabina ta tsaya masa a ƙirji ta tokare wucewar komai ta wurin. ya sani! ya san cewar zuciyarta me kyau ce tun kamin ya kai ga kallon kyawun surar dake saman fuskarta...wataƙila ta sake komawa wurinsa tunda bata jin magana, duk da jikinsa na bashi cewar ta koma ɗin fiye da yanda yake lissafawa...tunda yazo nan hankalinsa da tunaninsa suna kanta, suna kan zuwanta wurin zamansa daya zame masa baƙar ƙaddara, yana tsoro, a tsorace yake sosai, shi yasa tunanin halin da take ciki ya kasa barin ruhinsa da gangar jikinsa gaba ɗaya. ya sake kulle idonsa gam sannan yaja wata doguwar ajiyar zuciya ya sauke, cikin ransa yana adu'ar. _"Ya Allah ka kula da ita, ka tsareta daga dukkan wani abun cutarwa"._ kuma buɗe ƙofar cell ɗin daya ji anayi yasa komai dake cikin kansa ya tsaya cak, illa bugun zuciyarsa daya ƙaru sosai. har yanzu ya kasa sabawa da wannan horon da akeyi masa, bai kuma san ranar da zai saba da shi ba. abu guda ɗaya ne kawai yake anan, a duk sanda yake ansar wani tsatstsauran hukunci, ya kanji yana samun sauƙin abun idan yana ambatar sunan Allah, kuma ya kanji kamar zafin komai na yayewa ne ya zama kamar babu idan ya tunata, jikinsa yana bashi cewar zata zo ta goge komai, zata zo ta ɗauke shi, zata zo ta fitar da shi, wataƙila nan kusa ko da jimawa...amma da jimawar shi yake lissafawa kuma yake hangowa. maganar Captain da suke shigowa ciki tare da Sajent ta ratsa cikin kunnensa. "Yallaɓai duk wani bincike da ya kamata muyi munyi shi. kuma har yanzu abu guda muke samu, irin bayanin da yake fita daga bakinsa...ƙwarai ba shi da alaƙa da kano, haka kuma mun kasa gano daga wacce ƙasa ko kuma garin daya fito har ya shigo nan. abunda yafi ɗaure kai shine rashin sanin sunansa kaman yanda shi kansa yake faɗa". Sajent jin bayanan Captain yake har sanda ya sami kujera ya zauna, kujerar dake fuskantar Alhussain. "me yasa ba zaka yarda ka ansa wannan laifin ba?". Sajent ya jefa tambayar ga Alhussain wanda kansa ke ƙasa. "saboda bani na aikata ba". ya bashi amsar kai tsaye, kuma ba tare daya jira ƙara cewar Sajent ɗin ba yace. "inaji zan iya ansar wani laifin da ƙaddara zata ɗora min shi, amma banda laifin aikata fyaɗe. bani nayi ba, dan haka babu dalilin da zaisa na amsa cewar ni na aikata. dan haka zaifi muku kyau ku kashe ni ko kuma ku bar wahalar da kanku akan tambayata kuyi abunda ya dace". shirunsa ya haɗe da dukan da Captain ya bashi a gadon baya da gwiwar ƙafarsa, hakan yasa shi saƙin wata azababbiyar ƙara tare da ambaton sunan Allah. "ka yarda kai kayiwa Yarinyar nan fyaɗe, ka yarda kai kayi mata fyaɗe kuma baka ƙyaleta ba har saida ta mutu". "ba zan yarda ba tunda bani nayi ba". "idan ba kai kayi ba to waye yi?". "nima ban sani ba, Allah shine masani". "amma me yasa aka sami gawarta acikin kangon da kake zama? bayan jama'a sun bada shaidar kai kaɗai ne kake rayuwa acikin wannan kangon". "wataƙila Ubangiji ya jarabceni ne da wannan jarabawar saboda ta kawo sauyin wannan ƙaddarar dake ɗaure da rayuwata...jikina na bani cewar rayuwata zata sauya silar wannan jarabawar". Sajent yay wni murmushi yace, "ba fa zamu taɓa yarda da kai ba...duk da cewar likitoci sun bamu tabbacin babu semen ɗinka ajikin yarinyar amma hakan bashi zai wanke ka daga wannan laifin na fyaɗe ba". Alhussain ya rufe ido hoton abunda ya faru a wancan lokacin na haskawa a duhun idonsa. bayan ya raka Sabina ya wuce masallaci, bai dawo ba sai gefin magriba, kuma yana zuwa kai tsaye ya shige cikin kangon don ya samu ya kwanta kasancewar kansa da yaji yana masa ciwo sosai. ya tuɓe rigarsa ya saƙaleta a jikin garun wajen kawai sai yaji jiniyar motar ƴan sanda, bai kawo komai a ransa ba ya wuce ya shiga zuwa ɗaya ɓangaren dake cikin kangon, inda yana shiga yay tozali da budurwar yarinya kwance shememe acikin jini, tsoro da firgici suka sa shi ya razana yaja da baya yana zazzare ido. bai taɓa gani ba, a baki kawai ya san kalmar ta Fyaɗe!. sanda yay yunƙurin saurin fitowa lokacin ƴan sanda suka faɗo ciki, aikuwa nan da nan suka saita shi da bindiga suna faɗin hannu sama, ta ke anan yaji duniyar na juyawa da shi sannan ta tsayar da komai nasa ya tsaya cak, haka ƙwayar idonsa ta komai kan yarinyar. wani ɗan sanda yazo ya wuce ta gabansa ya durƙusa ya ɗauki wayar yarinyar dake yashe a gun, wadda ta bin lokacation ɗin wayar ne ya kawosu gurin. kuma duba da yanayinsa wanda yake daga shi sai gajeren wando yasa ƴan sanda taso shi ƙeyarsa aka sa shi a mota aka taho da shi nan. "kanata wahalar da hukuma. ka faɗa mana gaskiya ka hutawa kanka haka muma ka sawwaƙa mana". Maganar Sajent da dukan day kawo masa na kulki suka baro shi daga duniyar tunanin daya tafi. "har yanzu amar guda ɗaya ce a wurina shine bani na nai fyaɗen ba, haka ban san ya akayi komai ya kasance ba". kuma buɗar bakin Sajent zaiyi managana wani ɗan sanda ya faɗo cikin cell ɗin yana faɗin, "Ranka ya daɗe ɗaya daga cikin waɗanda suka aikata laifin Fyaɗen nan ya kawo kansa...yace shi yaron Alhaji Musbahu Wasai ne". jin hakan yasa Sajent saurin miƙewa suka fita daga cikin cell ɗin cikin hanzari. yayinda Alhussain yabi bayansu da kallo, zuciyarsa na wucewa da wani abu mai kama da sanyi. *Bayan Wata Biyu.* To alhamdulillahi karatunmu na ta tafiya yanda ya kamata, kuma na raba ƙawance da Asma'u saboda ita shirme ne ta sanya a gaba, na samu sabuwar ƙawa mai hazaƙa da ƙwazo kamar ni muka ɗinke da ita, sosai nake jin daɗin harka da Intisar, saboda yarinyar akwai hankali da natsuwa, ita ɗin ce dai-dai da ra'ayina. sosai na maida hankali a karatuna babu wasa, Yaya Abba da Yaya Haidar ƙwarai matuƙa suke taimaka min akan abinda ban gane ba, dama ga shi ni tun a secondry school sarkin read ahead ce, yanzun ma haka ta ke, ko ajikina dan Malami ya shigo yace zaiyi unexpected test saboda bani da shakku akan abinda zan rubuta, karatu ne nake wanda babu dare babu rana shi yasa komai ke zuwar min cikin sauƙi. Gwaggo tayi ta bambami tana takaici, "karatun da bana Allah da Annabi ba a dinga bauta masa, yo ina kuwa jiki zai yi kyan gani, gaki nan duk kin bi kin ƙare kamar ragowar yaƙi". Ni dai bana ce ma ta komai sai dai nayi murmushi, mafi akasari ma Yaya Abba ke bata amsa idan yana kusa, yay dariya yace, "to ai Gwaggo karatun ita zaima amfani ke kuma kiji daɗinsa". sai tayi masa kallo mai harara, idan taso ta bashi amsa idan bata ba so ba tayi masa banza. Yauma kamar kullum nasa littafi a gaba ina karatu, kawai naga an ɗauke shi daga gabana, ina ɗagowa na kalla Gwaggo tsaye ta ɓata rai, tana min faɗa tace, "tashi kije ki kwanta ki matse idonki, kar ki soma farkawa sai na zo na tasheki, wallahi idan ba haka ba sai na ɓata miki rai". Zanyi gaddama naga babu fuskar hakan, na miƙe na wuce ina faman buga ƙafafu a ƙasa, ina ji tana ta faɗin,"ƙarshen buga ƙafa ki fasa tiles ɗin ki faɗa ciki, haba Mutum idan ba so yake ya haukace ba wannan karatun ai yayi yawa, tun takwas kike anan a zaune ga ƙarfe ɗaya na neman kawo kai, duk kinbi kin wani sukurkurce kamar ba ke ba, ƙashi kamar kayi magana su amsa maka, ɗan kumatun nan naki babu shi, su kansu dukiyar fulanin naki sun rame, yo to ni ai ba mahaukaciya bace da zan barki kina lalacewa ba, nifa idan ma babu dole wannan karatu sai ki barshi, tun farko da nasan haka yake ba za ki soma ba, iya wanda kika samu a baya Allah ya amfana". taja tsaki ta ƙarasa wurin Yaya Abba, tana zama kusa da shi tace, "kai kira min Babanku, kace masa idan zai taho ya taho min da tsire irin wanda yaji ƙuli a jiki sosai, Ita kuma Sabina ya sayo mata kaza mai nagartaccen haɗi da kuma youghrt shima mai kyau, ya haɗo da kayan marmari ma namu ya ƙare". Ya ɗago ya ƙura mata ido yana kallonta, jin yayi shiru ta waigo daga kallon tv ta kalleshi, "to abinda na faɗa ne ba dai-dai ba dana zama abar kallo, ko kuma ƙa ƙa?". yace,"a'a Gwaggo, ke da kuɗin ɗanki, duk wani faɗi tashi fa kece kika yi a kansa har ya samu ya kai wannan matsayi, don haka ko garin Abuja kike son ci gaba ɗaya ai dole ya saya maki". Ta masa kallo mai kama da harara ta ɗauke kai, "to aini ba Gara bace da zan kama cin gine-gine, idan zaka kira min shi ka kirawo shi, idan kuma baka iyawa na tashi naje na sami Haidar ya kira min shi, tunda shi yanzu sai dai na taka ƙafata naje inda yake, ban kai matsayin da zai zo wurina ba, sam yaron nan baya girmamani". Abba ya fashe da dariya, bayan itace ta kora Haidar da muciya tace idan ya kuma zuwa inda take saita mummuƙa masa muciya aka, ta gaji da zuwan da yake yana mata dafe-dafe a kitchen, kuma tunda ta kore shi ɗin ya daina zuwa, tana cewa ta sami lafiya amma kullum zancenta ina Haidar, har zuwa ɗakinsu ta ke ta gani ko yana lafiya, shi kuwa yay biris da ita ko a compound suka haɗu ɗauke kai yake. Abba ya zura hannu a aljihu ya ɗauko wayarsa, sai bayan daya kira Baba yake roƙon Gwaggo akan don Allah ta barni nake karatun nan, hutun yana gaba yayin dana gama exams, yanzu jarabawa ce zamu fara dole take ganina ko da yaushe akan littafi, kuma hakan shine dai-dai, dole sai na dage zan cimma nasara. "sai na barta jikinta ya lalace saboda ba kai zaka aureta ba ko, mtswww ni karka ɓata min rai Abba. Akan wannan karatu yarinyar nan ko lokacina bata da shi, to yanzu dai na ware masa lokacinsa, ba zan ɗauka ba, kuma fa karatun nata lissafi ne naji Zahra'u na faɗa, tace har hauka yana sanya mutum, ta kwatanta min da ƙanenta tace idan na ganshi ai zan lura bai cika hankali ba, to itama haka kake so ta zama? ko da yake kai dama ba ƙaunarta kake ba, aikinka shine kasata gaba kana faman tayata dukan wannan abar ta lissafi sai kace za ku ƙirge kuɗin duniya". Baice mata komai ba sai dariya da yake ƙasa-ƙasa, sababin Gwaggo na saka shi nishaɗi, idan ta fara magana baka ce zata yi shiru ba, taita jera zance kenan. a ƙufule tace da shi, "nifa kasan Allah na tsani ina magana naga ana min dariya kamar anga sha uku-sha uku, abin yana ƙonan zuciya, wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya taɓa haɗani da wani saurayina nace na fasa aurensa, Sahibina shima wataran haka ya taɓa min, na kuwa doka yaji na wuce gidan Kakanni na, sai daya sha fama kamin na dawo". Yanzuma dariyar yay ba tare daya bari ta lura ba, ya miƙe ƙafa ya kwantar da kansa saman cinyarta, tana shafa sumar kansa take faɗin, "Abba ya kamata ka aske wannan sumar taka haka kaji ko, haba tayi yawa ai, gashi sai kace bana ɗan musulmi ba". "tom Hajiya Gwaggo". Yace da ita. saiga hawaye ya shiga sauka saman kuncinsa, hankalinta ya ɗaga ta shiga tambayarsa ko lafiya, yay shiru baice mata komai ba, itama saita fashe da kukan, ganin haka yace, "Gwaggo ina kewan mahaifiyata ne fa". Ya faɗa yana sa hannu ya goge mata hawaye. Ta mayar da shi saman cinyar tata, tana shafa kansa, "kayi haƙuri Abba, Allah ya jiƙanta da rahma kai kuma ya haɗaka da abokiyar zama ta gari wadda zata dinga ɗebe maka kewa". Ta kuma fashewa da sabon kuka, "yanzu haka dole nima wataran zan tafi na barku, mutuwa rigar kowa ce. Allah ya bamu cikawa da imani ya kuma nufe ni da ganin aurenku, ina son Allah ya ara min rai da lafiya naga hannun waɗanda zan damƙa ku". Ya miƙe zaune ya riƙe hannunta, "insha'Allahu Gwaggo za kiga aurenmu har da ƴaƴanmu, duk da mutuwa bata barin wani don wani yaji daɗi amma ai ta bar mana ke tunda ta ɗauke mana Mama, so ki bar kuka don Allah kar Sabina ta jiyoki". Hakan daya ce tai saurin sa hannu tana sha re hawayenta. ***** Yaune zamu zana last papper, kwana nayi ban runtsa ba ina karatu da nafila, amma fa a hakan sai da muka yiwa Gwaggo dabara tukunna, saboda tuni ta hanani karatun cikin dare, Yaya Abba ne ya sayo maganin bacci muka sa mata a lemu ta kwankwaɗe gashi har gari ya waye sai sharar baccinta ta ke. Allah sarki Yaya Abbana abin ƙaunata, kamar yanda naga rana naga dare haka shima ya gani, da daddare da Gwaggo zata kulle ƙofa ya ɓuya ga bayan labule, bayan ta wuce ɗaki ya fito, nima ko da na wuce kwanciya sai dana tabbatar tayi bacci kana na fito parlo muka hau karatu ni da shi, kamar shima exams ɗin zaiyi. Shap-shap nayi wanka na fito, ko mai ban tsaya shafawa saboda bani da lokacin wannan, mayafinma a bai-bai na yafa, sai dana fito Yaya Abba ya gyara min, shi yace zai taimaka yau ya kaini, da zamu fita muna jiyo ƙira'ar Yaya Haidar na tashi a masallacin cikin gida, na kirashi a waya nace idan ya idar ya sani a adu'a, yace "toh, Allah ya bada sa'a". Ƙarfe takwas dai-dai muka shiga ɗakin jarabawa, ba ƙaramin tsaro aka sa mana, duk an tarwatsa mu, wannan course ko bala'i, Allah dai ya bamu ikon hayewa, tun ba'a fara ba sai haɗa zufa muke, kwanciyata nayi kamin a raba peppers, har bacci ya fara ɗaukata, ganin Malamarmu ta taho da sauri Intisar ta dokoni, dama tazarmu da ita 1seat ne. Na farka a gigice na miƙe zaune, "masha'Allahu". wannan kalmar ko da yaushe ita nake furtawa a duk sanda nai tozali da Malama Muhsinah, ta ko'ina bata da makusa matar nan sai dai ban sa ni ba ko a halinta, amma iyakar kyawun halitta Allah ya bata, farinta tamkar wani madara-madara haka yake, amma a duk sanda nake zuzuta kyawunta sai Instisar tace wallahi na fita kyau, ko da yake dama ance wai mutum bai ganin kyawunsa, nayi dariya kawai idan naga tana ɓata rai ita alalle ba zance banda kyau ba. Inda nake Malama Muhisina ta ƙaraso, "get up". Shine abinda tace min, na miƙe, tace, "follow me". Na kwashi kayan rubutuna nabi bayanta, seat ta sauya mini ta maidani front seat, har wani lokaci ba'azo an raba mana script ba, nasa biro a bakina ina kallon wani bawan Allah dake zaune kan wheelchair a saman stage, ya juya baya baka ganin fuskarsa, Allah sarki ya bani tausayi sosai, shi kuma tasa jarabawar kenan, _Allah ka barmu da lafiyarmu, Alhamdulillah._ na faɗa a cikin zuciyata. Script aka fara raba mana, gabana ya faɗi, na runtse ido ina karanto wasu ayoyi da Baba ya bani, har aka gama raba mana questions pepper, kun san dai yanda ake tsintar kai a lokacin da aka shiga ɗakin jarabawa idan aka miƙo takardar tambaya musamman ma ace na course mai wuya ne, wani murmushin jin daɗi na saki da naga tambayoyin duk na sansu, aiko inata faman murmushi na duƙa kai na fara amsawa, cikin awa guda da farawarmu wasu suka fara submitting, kuma ni ce ta kusan 6 a gamawa. Ina sakkowa daga steps naji a jikina ana kallona, don koya aka ƙura min ido bada sanina ba sai naji a jikina, na ɗan dakata da saukar ina yatsine fuska, Supervisor namu naji ya doka min tsawa, "hey my friend what are you still waiting there?". Na tura baki gaba naci gaba da sauka ina murguɗa baki, na san dai koma wane mai kallona ya gani, ni ban son saka ido, dan bana buƙatar sanin koma wane dana ɗago na banka harara. Na ƙarasa na miƙawa Malama Muhsina script ɗin, har nai gaba naji ta kirani, na dawo tsna cewa da ni, "are you stupid?". na ɗago ina kallonta, tana nuna min script ɗin ta ke cewa, "what about your name and regestration number?". *Please Comment, Vote and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(16)* ban ko bi ta kan Malama Muhsina dake bina da banzan kallo ba, abunda ya dameni shi ya damen, dan haka a wannan lokacin dafe goshi nayi cikin fargabar abunda ka iya faruwa da ace basu lura da rashin rubuta sunana ba. wallah shaf ni na manta da batun suna saboda zumuɗin fara ansering, daɗin question ɗin ya mantar da ni. na bawa Malama Muhsina haƙuri na amshi script ɗin na duƙa ina rubutawa, haka kawai sai na tsinci gabana da faɗuwa a lokacin, ga kallon da ake min ya tsananta yawa, naja tsaki ni ɗaya, sannan na ɗaga kaina sama nai harare-harare da murguɗe-murguɗe, yanzu kam dai koma wane nasan ya gani ya kuma san da shi nake, sannan na ɗago na miƙa mata. "your ID card". Ta ƙara cewa da ni, na miƙa mata ta duba abinda zata duba ta bani na wuce na fita. A ƙofar class na tsaya jiran Intisar, babu daɗewa itama ta fito, hangoni yasata ta fara dariyar dake ƙunshe da murna, tana ƙarasowa muka tafa da ita, exams dai tayi mana daɗi gaba ɗayanmu, muna tattaunawa akan wata question sai ga wata ƙawarmu ƴar carryover ta fito, muka jera muna tafiya. Intisar tace, " kallah wani bawan Allah, Allah ya bashi kyau sai dai babu ƙafa". Muka juyo ni da Rahinat don kallon mutumin da take magana akai, ana tura shi a kekensa na guragu, har sun wucemu, kamar ɗazu dai bayansa kawai na gani, da tausayawa nace,"Allah sarki wallahi nima ya bani tausayi, har ƙwalla sai dana masa ɗazu, kamar shine muka yi exams tare ko?". Na faɗa da muryar tausayawa ina daɗa bin bayansa da kallo. "ehh shine". Intisar ta faɗa. "baki ga akan stage aka ɗora shi ba daga shi sai halinsa, wannan exams idan baka yi karatu ba ai kana tsakiyar ruwa". ta ƙara faɗa. sai Rahina tace, "ke he is not a student, He is the Financial Accounting lecturer, baya ɗaukan ƴan Level one lectures until level two, Becouse he can't walk bare ya miƙe yay explaining a board, So at level two kuwa bayani ne zaizo yay maku verbally using projecter, ita Malama Muhsinah ƙanwarsa ce, ita ke karɓa masa a L1 nd also she is the one taking care of him at school". "eyyah Allah sarki, Allah ya bashi lafiya". Muka faɗa a tare ni da Intisar. "amma dai baida mugunta ko?". Na tambayi Rahina ina waro ido waje. "ehh to gaskiya bashi da mugunta, amma fa ya iya tsara questions, aima kun gani yanzu, kuma gashi da fara'a murmushi har tunbuɗinsa yake, kuma ba'a faɗuwa course nasa gaskiya saboda kunga yadda ake dagewa, nima ƙaddara ce ta dawo da ni". Muka ci gaba da tafiya muna hirarmu, daga bayanmu muka ji ana mana magana, muka dakata da tafiyar muka juyo. Saurayin yace da ni, "Beauty Malama Muhsina is calling you". Ya faɗa yana nuna ni. Na kallesa ina yamutsa fuska saboda ranar data haskemu. ina nuna kaina nace, "kuma ni tace ka kira, ai ba sunana Beauty ba, sai dai ko ƴan gabanmu ta ke nuna maka". Na faɗa ina maida kallona ga ƴan gabanmu dake tafiya. Murmushi naga yayi yana cewa, "na san ba ainihin sunanki bane, nima ce tayi min na kira mata beauty gata can tana tafiya with pink veil, ai farko dana kira ku Sisters kuka ji ina cewa ko?". Su Rahinat suka ce masa "ehh". Ya kuma cewa,"to da ku ka juyo na kalleki sai naga ehh lallai kin cancanta da a kira da suna Beauty, hakan yasa nima na ɗana. Allah ya tsare miki wannan kyawu naki". Ya faɗi hakan yana wucemu. Na kalla su Intisar da suke kallona suna murmushi, na sauke numfashi na ɓata rai sannan nace. "sarai kun san Malama Muhsina bata da kirki, maimakon ku tayani jimami ku abinma daɗi yay maku, ban san kiran akan mene ba Allah dai yasa ba laifi na mata ba". "amin dai". Suka amsa. Intisar tace, "amma ai ɗazu ta tuna maki baki rubuta suna ba, kiyi gaggawar zuwa may be kin kuma mantawa da rubuta wani abun". Na dafe ƙirji na furta, "na shiga uku na". "Beauty ki dai wuce ki tafi kiran Malama kar ki ƙarama kanki laifi". Rahinat ta faɗa da sigar tsokana. Na kalleta na mata harar wasa, ko mene abin tsokana anan oho. "na san zaman da zanyi dake". Na faɗa ina barinsu. Tsaye na sameta a bakin admin block, dama bamu da nisa da wurin a tafiyan da mukai, ta harɗe hannaye a ƙirji tana jiran isowata, gabana ya faɗi da irin kallon da ta ke mani, na kuma sadda kaina ƙasa na ƙarasa gabanta, ina rissinawa nace. "Maa Someone said you were calling me". Na faɗa har muryata na rawa. Da alama dai tana da izza, tana jijji da kai tace min, "and now you have the opportunity to come After you finish westing my time, right?". Shiru nayi ban ce mata komai ba sai tsilli-tsilli da idanu da nake. ina kallo ta taɓe baki haɗi da maƙe kafaɗa cikin ɗagin murya tace min, "Comon jor my friend, ki wuce Proff want to see you". "Maa waye proff?". Na tambayeta da son ƙarin bayani. ai kamar na zageta saita ɗaga murya a zafafe tana faɗin,"wane proff kike tambayana? Duk faɗin waƴanda ke maku lectures akwai Malami Proff ne sama da mutum ɗaya, mtswww this girl you don't have manner of etiquette at all". Taja tsaki tana kamo kunnena ta bani ranƙwashi,"to daga yau ki san wane Proff, daƙiƙiya kawai, comon to write your name on script ɗazu ma kika kasa, and that is how you got in to university, kamata yay ace kina primary school. Ana magana kina zumɓurowa mutane baki, maida shi ko na bige miki laɓɓa". Nai saurin maida bakina, na ɓata rai ina jin kamar nayi mata mene, ta gallan harara tace,"ki same shi a office nasa". "aina office ɗin yake?". Bata ce min komi ba tai juwarta ta shiga admin block ɗin, na bi bayanta, muna zuwa office na huɗu tai min nuni da yatsanta sannan tai gaba abinta, nabi bayanta da murguɗa baki kana nayi knocking door. "Yes, come in". Aka ce dani, hakan yasa na buɗe na shiga ƙafafuna na rawa saboda duk a tsorace nake ban san laifin da nayi ba, ni da ko wani Proff ma ban taɓa sani ba. Ina wurga idanu nake taka ƙafata, ƙaton hotonsa na gani an rubuta Proffessor Muhsin Muhammad Na kowa, _"fatabarakallahu ahsanal khaliƙin"._ na faɗa a zuciyata. sai dai kuma kan na kai ga ɗauke idona akan hoton ƙirjina ya buga dummm, hakan yasa na murza idanu ina ƙara kallon hoton da kyau kamin wata faɗuwar gaba ta musamman ta riskeni. na sauke idona daga kan hoton kamin su ƙara tsayawa akan ƙatuwar calender ɗin dake gefena, ina daɗa kallon fuskar hoton na tsawon wasu daƙiƙu kamin na tsayar da tunanina akan abunda ke wucewa ta cikin kaina. ƙwarai na san wannan fuskar, na santa farin sani, nayi mata sanin da zanenta ba zai taɓa ɗaukewa a idona ba, to amma mene alaƙarta da mamallakin wannan ofishin?, tukunna ma wannan sunan da muƙamin daga ina ya samo su? a yaushe?. mamaki ya kamani zuwa nisan da ba zai kwatantu ba, wani abu ya daki ƙwaƙwalwata a lokaci guda, Yaya! Yaya dai!, dama waye shi?. dukkan tunanin dake cikin kaina da ma abinda zuciyata ke rayawa ya tsaya acak a sanda idona ya sauka akansa, lokacin daya juyo ya fuskanceni, dan sanda na shigo ya juya min baya. sai na zama kamar wadda aka dasa a wurin, idanuwana na gaza ko da ƙiftawa daga kallonsa, kallon fuskarsa dake ɗauke da ƙayataccen murmushi da yake, irin murmushin nan daya taɓa yi a waccen ranar da yace zaiyi koyi da ni. kuma a take dukkan faruwar wani abu ya shiga haskawa cikin idona, tun daga ranar dana fara ganinsa zuwa ranar ƙarshe da naje wurinsa, da ma sauran ranakun dana ɗiba ina zuwa ban same shi ba. waccan rayuwar dana sansa ba irin wannan bace, haka zalika wancan yanayin da na sansa da shi ba irin wannan yanayin ba ne. yanayin da yake ɗauke da shi a yanzu yanayi ne na nuna yana cikin nishaɗi da jin daɗin rayuwa. kuma da dukkan wata alama wayar da yake ne yasa shi hakan. _ko dai mafarki nake?_ zancen da zuciyata keyi kenan, dan haka saina sadda kaina ƙasa na rufe ido, sannan na buɗe da dukkan yaƙinin zanga saɓanin abunda nake gani. sai dai wannan muryar tasa da ba zan taɓa mancewa da ita ba ta shigo cikin kunnuwana ta sami mahalli acikin ƙoƙon kaina. "Beauty bismillah come have a sit". Ya faɗa har zuwa wannan lokacin bai bar wayar da yake ba, na ɗago ina duban kujeran da yake min nuni da shi, sannan na ƙara masa wani kallon, kallon dana kasa fassara shi da irin yacce zuciyata ke lissafi. abu guda ɗaya kawai da na sani shine a lokacin da ma guda ɗaya nake nema da zanyi masa wulaƙancin da har mutuwa ba zai manta da shi ba. a rayuwata na tsani mutane guda uku, munafuki! maƙaryaci da kuma mayaudari. dan haka na ɗaga ƙafafuna na ƙarasa na zauna akan kujerar, gaba ɗaya ma zuciyata ta kasa lissafa abunda zanyiwa wannan bawan na Allah, duk da a gefe guda zuciyar tawa ta kasa gasgata shi ɗinne. dan wancan da na sani, ko kusa bashi da wata alama da ke nunin yana da wata rayuwar ta daban bayan wacce yake acikinta. sai dai har yanzu tunanin guda biyu ne acikin kaina. idan wancan dana sani ne to wanene shi?, haka idan ba shi bane to wannan wanene?. sai dai a irin alamomin da nake gani kamar ba mutumin da nake tsammani ba ne, dan shi wannan nunawa yake kamar bai taɓa sanina ba?, beside ma Yaushe ya zama gurgu? ko kuma hakan duk na cikin takun basajarsa?. na ɗago ina ƙare masa kallo, me yasa nake jin bugun zuciyata na tsananta ne idan ina kallonsa, alhalin shi wancan bana tsintar kaina a irin hakan. gaba ɗaya yay shiru yana sauraren maganar da ake masa ta cikin waya, ya ɗago karaf muka haɗa ido da shi, ya sakar min sanyayyan murmushi, hakan yasa na ɗauke nawa idon daga kansa cikin ɗaurewar fuska. zuciyata gaya min ta ke Wannan ba wanda na sani bane, domin ba zan taɓa manta duk wasu abubuwa da suka danganci Yayana ba, sai dai tsananin kamarsu da wancan ya ɓaci, tamkar an tsaga kara, ba su da wata maraba daga kamannin fuskar har surar jikin, hatta muryarsu iri guda ce, kawai shi wannan gurgu ne kuma yana da fara'a, to amma shima wancan ai halin rayuwan daya tsinci kansa ne yasa baida abubuwan da wannan yake da su. ban san lokacin dana miƙe tsaye ba, na tsaya akan ƙafafuna, fuskata a turɓune babu wani ɗigon annuri na zagayo gabansa, don in samu in tabbatar da zargina, yazo nan yana musu basaja kamar yanda yake yi a garin Kano. Ina tsayawa gabansa na kama ƙugu da duka hannu biyu ina faman jijjjige-jijjige, ƙiyasto abinda zan masa nake idan har na tabbatar da shi ɗin ne. sai dai nayi istigfari sannan na kamo hannunsa, saboda na san hakan da zanyi haramunne ya saɓa da shari'an musulunci, sai dai bani da yanda na iya, fatana kawai na fita daga duhun da nake ciki, links ɗin hannun rigarsa na ɓalle na yaye hannun rigar tasa. shi dai bina da ido kawai yake yana kallon ikon Allah, saboda farko dana riƙe ya janye saina kuma janyo shi na damƙe, na kuma tsorata da yawan gargasar da na gani a hannunsa, wanda wannan gargasar ita ta ƙara tsoratani har na ɗan ja da baya, babu shakka wancan mutumin da nake kira da Yayana ne. amma me yasa yaywa rayuwar masu saurin yarda irina haka? Yaudara!. sai dai har yanzu ina cikin shakku, ban gama yarda shi ba ne, haka kuma ban yarda ba shi bane. sai kuma na ƙara kamo ɗayan hannun nasa daya ke riƙe da waya, na amshe wayan na aza masa a ɗayan hannun yaci gaba da wayarsa, kuma a wannan hannun ne na sauke a jiyar zuciya, saboda hannun hagun wancan mutumin da nake kira da Yaya akwai lamɓaceciyar ƙunuwa a wurin, wannan kuma babu wata alama ta hakan. Na rufe ido ina aikin sauke numfashi, sai kuma kunya ta baibayeni nasa hannu na rufe fuskana, na ma kasa ɗaga ƙafa na koma mazauni na. sai naji ya kamo hannuna, nai saurin buɗe fuska ina kallonsa, sai naga yana ƙoƙarin miƙewa amma ya kasa, ta ke naji ruwan hawaye sun cika min ido saboda tsantsar tausayinsa, shima kuma yanayinsa ya koma zuwa na damuwa. "mene? Me kake so?". Na tambaye shi cikin sanyin murya da tausayawa. a wannan lokacin na manta da tunanin ruɗanin dana shiga cikin wucewar wasu daƙiƙu. baiyi magana ba sai nuni da yay min da kansa, saboda haka dana fahimci me yake nufi saina duƙa, ina tsugunawa gabansa naji yana faɗa acikin wayar. "Mom ga Beauty zaku gaisa". Ya faɗi hakan yana kara min waya a kunne, kenan da mahaifiyarsa ne yake waya tun a ɗazu, dole ya kasance cikin nishaɗi, _me mahaifiya a raye shike jin daɗin rayuwa,_ na faɗa a zuciyata ina sanya hannu na goge ƙwallar idona. Na maida hankali kan maganar da Mom ke yimin. "Beauty nah". Itama naji ta kirani da wannan sunan, duk da mamakin daya kamani sai na kawar, ban san lokacin da muryana ya koma na shagwaɓaɓɓu nace, "Mom ba sunana Beauty ba". tai murmushin manyance tace, "to ya sunan ɗiyar tawa?". nace, "Sabina, Sabina'n Gwaggo". maganar tawa ta sakata yin murmushin mai sauti, sannan tace da ni. "Allah ya albarkaci rayuwanki Sabina tah, ya kuma dawwamar dake a farinciki". na amsa da,"ameen Mom, na gode sosai. Kema Allah ya ƙara maki lafiya da nisan kwana". Ta amsa min da, "amin ɗiyar kirki". Sai yanzu na tuna ban gaidata ba, nai saurin rufe bakina ina zaro ido na kalla Proff dake aikin kallona, a hankali nace, "Mom ina yini. Kiyi haƙuri don Allah tun farko ban gaida ki ba". tace, "dont worry my daughter, jin muryanki ya fiye min gaisuwan, tabbas yau ɗin nayi farinciki da jinki. Ina Yayan naki?". Tana faɗar haka na ɗago na dube shi, zuciyata na kuma tsinkewa da lamarin, dan da Mom tace Yayana sai naji kamar wancan Yayan nawa ne da gaske. "Daughter". Nai firgigit daga gajeran tunanin dana tafi, "na'am Mom". "ina Yayan naki?". ta kuma tambayana. "Mom gashi nan". "oak bashi wayar, Idan kinje gida ki gaida min da Gwaggo sosai kinji". nai knodding kaina kamar a gabanta nace, "tom Mom zataji". lokaci ɗaya saina sami kaina da yin wasu abubuwa da ban san lokacin da nake yin su ba, shi kansa abunda nace mata a yanzu sai daga baya na san na faɗa. "Mom ki cewa Yaya ya daina ƙarya ba kyau, shi dai babban mutum ne". Nai maganar ina masa kallo mai harara. murmushi naji ta sa ki kana tace, "shikenan zanyi masa faɗa, daga yau ba zai ƙara ba Beauty nah, oak Bye bye". "aha Bye Mom". Na faɗa ina miƙa masa wayar, yana ansa kuma na miƙe daga tsugunen da nake da zummar barin wajen ya maidoni na zauna. Ina faman cin magani nake kiciniyar ƙwace hannuna daga nasa amma yaƙi bani damar hakan, su kai sallama da Mom, cikin ɗaurewar fuska yace dani, "ba ki da kunya dama? Sa'anki ne ni da kike hararana? Ko dan kinji nace a kira min ke, yanzun nan sai na baki carryover, kuma idan aka faɗi course ɗina har spilling". Wayyo Allah nah ni Sabina, a wannan lokacin ji nayi kamar na ɗora hannu akaina na kurma ihu, domin maganar da yake a cikin tamkewar muryar nan sai ya kuma rikeɗe min zuwa Yayana. to ni maganar carryover ma bata bani tsoro ba kamar yanda shi yake bani tsoro, babu maganar da na tuna sai ranar da Yayana yace karna kuma zuwa inda yake idan ba haka ba sai ya mani fyaɗe, sak da irin wannan sautin muryar ne. a yanzu cikin ɗaurewar fuska yace da ni, "binciken me kika mani ɗazu a jikina?". nace, "na duba ne naga ko kai ɗan yankan kaine". Na faɗa cike da jin haushinsa. sai Yay siririyar dariya yana cewa, "shine sai kika zo kina bincike ni right?, ta yanda Koda ni ɗin ne kamin na gama waya da Mom kin arce ba? Ke gaki me wayo ko, to yanda kika shigo office ɗin nan kin shigo kenan har busa ƙaho kina nan". na nuna masa ko kaɗan ban kaɗu da maganarsa ba, dan na lura irin Malamn nanne watsatstsu da idan mace ta biye musu zasu kaita su barota. dan haka kai tsaye na jefa masa tambayan,"kiran nawa na menene?". na faɗa ina miƙe da ƙoƙarin ƙwace hannuna daga riƙon da yay min. kuma muryarsa ta fito kai tsaye zuwa kunnena da cewan,"zamu je gidanku ne na faɗawa Daddy'nki, daga shiganki exams hall kika yi min sata, hakanne ma yasa na binciko files naki na duba address na gidanku, ko da idan na tambayeki za ki min ƙarya". *Please Comment, Vote & Share.* [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(17)* a lokaci guda furucinsa ya daki tsakiyar kaina. Na zaro ido a tsorace ina dubansa nace,"na shiga ukuna, ni ɗin na maka sata?". Ya ɗaga min gira ɗaya alaman ehh, a ruɗe na shiga ce masa,"wallahi ko Gwaggona tasan bana sata, Kuma ban taɓa yunƙurin yi ba. kuma don Allah karka je kace ma Baba na maka sata, ba zai tsaya jin komai ba zai ɗauka tsatstsauran mataki akaina. Ni dai nasan ban maka sata ba amma ka faɗa min ko mene indai kuɗin account ɗina ya kai zan biyaka ta ke anan". Ina faɗa duk na rikirkice, tsorona Allah tsorona Baba ya kuma korata daga gida. a wannan duniyar tashin hankain da Proff ya jefani naji maganarsa na shiga kunnuwana da cewa,"kuɗi ko kuma wata kadara ba zata iya biyana abinda kika satar min ba, dole Baba da kike tsoro shi zansa Daddy nah yaje ya sama ya faɗa masa, ta yanda Baba da Daddy nah zasu yi saurin yanke hukunci dai-dai da buƙatata". kawai saina fashe da ina faɗin, "wallahi tunda uwata ta haifo ni duniyar nan ban taɓa yiwa kowa sata ba. ko wancan karanma sharri Umma tayi min. dan Gwaggo nah ta bani tarbiya mai kyau wanda ko kallon abinda ba nawa ba bana iya tsayawa yi". Sosai nake kukan har sai dana kifa kaina a gwiwata, wannan wacce iriyar ƙaddara ce. Naji ya cika bakinsa da iska ya furzar, a cikin siga ta lallashi yake ce min, "ohhh Beauty please stop crying mana, am just kidding you ba zan faɗawa Baba satar da kika mani ba". na ɗago idona masu ruwan hawaye nace,"au da gaske ne ma na maka satar? To mene na satar maka?". y gyaɗa kansa sau uku kamin nan yace,"ofcourse kin sace min abu mai muhimmanci a tare da ni, amma i promise you i will not tell your Dad for now, but for sure zan faɗawa Momy nah, what ever she decide akai then...". Bai ƙarasa ba ya kanne min ido guda yana cije leɓensa na ƙasa, yana abu kamar Yaya Haidar. Ni kam na shiga uku, wannan rana ta yau bata zo mani a sa'a ba, na kuma fashewa da kuka, naji yana cewa, "shikenan idan kina so na bar maganar to ki bani haƙuri". Ai da sauri na ɗago nace, "kayi haƙuri". "haka ake bada haƙuri?". Na karayar da kai, na kama kunnuwana nayi exactly yanda nake bama Yaya Abba haƙuri idan na masa laifi, "Don girman Allah kayi haƙuri". Hasken flash yasa na ɗago ido ina kallonsa, ƙyasss naji ƙarar ɗaukar hoto, zanyi magana kawai na ƙyaleshi, ba buƙatata kenan ba. "Sabina Auwal right?". Ya jefo min tambaya. na ɗaga masa kaii "ehhh". "nice name Beauty". Na murguɗa masa baki, ya tari numfashina da cewa, "yauwa and i will also tell Baba kina murguɗawa manya baki". Na ɗago zan bashi haƙuri na tuna abinda Gwaggo tace min duk sanda wani yace ina murguɗa masa baki. Na turo bakina gaba nace, "ai dai ko Gwaggo tasan ina yi, kuma ma ai a wurinta na koya. Saboda haka ko an kai ƙarata wurin Baba ba abinda zaice, "Ƙaramar dariya naga yayi, ina marairaice fuska na haɗa hannuna nace, "don Allah kai wane?". a karo na babu adadi ya janyo leɓensa na ƙasa ya cija sannan ya shafo sumar kansa yace, "sunana Muhsin Muhammad Na kowa...". Bai ƙarasa abinda zaice ba na wurga masa tambayan, "a kano kake?". Ya kaɗa min kai, "nop, ni banma taɓa zuwa Kano ba. Mahaifina balaraben sudan ne, also my Mother she's shuwa arab, mu 6 duk an haifemu a misra, wata harƙallar aiki ta kawo Daddy nah nan Abuja, ataƙaice bamu haura 4years ba anan, like you see me ina da asali, kuɗi, gata da duk wani abu na jin daɗin rayuwa, sai dai banda lafiyan ƙafa, as soon kuma zamu koma can ƙasarmu da zaran Daddy ya kammala abinda yake. So kema sai ki shirya becouse we are going along with you, acan ne za ki amsa hukuncin satar da kika mani". Zan buɗi baki nayi magana Malama Muhsina ta shigo. "Brother is time for the meeting". Na kalla ya duba agogonsa yace,"oh shet". Sai kuma ya kalle ni ya kalleta yace, "Sister zo ki tayani lallashin Beauty tun ɗazun ta ke kuka taƙi yin shiru, kuma kin san na tsani kuka bare nata ma da babu daɗin ji kamar kukan shanuwa". Ya faɗi hakan yana wani toshe kunne, Zumbur na miƙe tsaye na ƙwace hannuna daga nasa, don cin mutunci kukana ne mai kama dana cow, ina tura baki na raɓa Malama na ɗauka jakata dake kan kujera nayi ƙofa. Sai dai a rufe take, na juyo na kallesa naga yanda yake dariya ƙasa-ƙasa, na kawar da kaina cike da jin haushinsa. Malama Muhsina ma tayi siririyar dariya ganin yanda na cukule tace, "Soryy Beauty ki rabu da Brother nah, idan kika biye masa zai ta sanyaki kuka ne. Bari nazo na buɗe maki". Ina kallo ta kamashi sosai kana ta ɗora shi kan wheelchair nasa, da alama dai ƙafafunsa basa aiki kwata-kwata, mutum ba isashshen lafiya sai ɗan banzan surutu da neman magana". tana buɗe ƙofa nayi ficewana raina duk a dagule, gefe ɗaya kuma ina saƙa abubuwa da dama a raina ina warwarewa, a wannan lokacin kowaye ya ganni yasan kwai abinda ke ƙasan raina saboda yanda nake zabga ƙwafa. ina kan hanya Yaya Abba ya kirani, na ɗaga wayan nace masa gani nan zuwa, Allah sarki bawan Allah ashe har yanzu yana jirana. Intisar ma ashe tun ɗazun tana waje zaman jirana, tana hangoni ta taso da sauri tana aika min tambayan me ya faru, ni dai shiru na mata ban saurareta ba nayi tafiyata ina sha re hawaye. ina zuwa mota na buɗe na shiga, da shigana na ƙara fashewa da kuka, tambayar duniya Yaya Abba yace me aka mani shima na masa shiru, gaba ɗaya ba komai ke damun zuciyata ba sai kewan Yayana, tausayinsa na kuma ratsa ni, ganin wannan mai kama da shi ya matuƙar ƙara tada min da kewansa, ya zama dole naje naga halin da yake ciki, bazan dawo ba har sai idan da shi ne, Allah yay mana wannan arziƙin da ba zan taɓa barinsa a wahala ba. dan Na gama gane Proff ba Yayana bane shi ya fiya surutun wofi, Yayana kuwa magana ma wahala ta ke masa. a ƙufule Yaya Abba yace, "ke ban san iskancin banza fa. Ina miki magana kin min shiru, exams ɗin ne tayi wahala?". Kai kawai na girgiza masa, sai yaja tsaki ba tare daya ƙara ce min komai ba. ganin yanda ransa ya ɓaci yasa nace,"Yaya Abba dama ana halittar mutane iri guda ko da ba identical twins bane?". Ko kallo na bai ba, sai guntun tsaki daya kuma ja, bai ƙara saurarena ba har muka isko gida. Ina shiga parlo na faɗa jikin Gwaggo dake zaune, ko ta kaina bata bi ba sai taɓe baki da tayi, ganin dai kukan nawa bana ƙarewa bane tace. "ke wai Ubanki Auwalu aka yi miki da za ki zo ki sani a gaba kina faman kuka, bayan kin san ba abinda ke ɗagan hankali a duniyar nan sama da kukanki, za ki faɗan mene ko kuwa?". na mata shiru ina ƙara ƙanƙameta, a gaskiya ina bala'in son ganin Yayana, dan a yanzu jin zuciyata nake na wani matsewa sa zafi. Ta tureni da ƙarfi tana cewa, "je can ki ƙarata da halinki ke ɗaya, idan kika ƙarar da hawayen kya rasa na zuwa ɗakin miji ace ba ki da kunya, ke baza'a taɓa tambayanki mene ke damunki ba ki faɗawa mutane ba a lokacin, sai kin gama iskance-iskancenki tukunna. to Wallah ki ka kuskura kishiya ta gane ma ruwan hawayenki gasa ki zata dinƙa yi". Sai a sannan ne nayi shiru, nace mata, "Gwaggo tunda munyi hutu yau don Allah ina so naje naga Hajiya da Mami da su Uncle Nasir". Ina nufin dangin mahaifiyata. Taja tsaki tace, "amma ke kuwa kina da abin haushi, dama abinda kike wa kukan kenan?". "a'a bashi bane. Wani Malaminmu ne yace na masa sata, har da kirani ofishinsa ya ƙara min wulaƙanci, shine nasa kuka sai yace wai Kukana kamar kukan Shanuwa, ita kuma ɗayar Malamar tamu tace min daƙiƙiya". Gwaggo tai wani zabarin gyara zane tana furzar da goron bakinta tace,"shi Malamin naku? Yace kin masa sata kuma kukanki kamar na shanuwa?". na ɗaga mata kai alamar tabbatarwa. ta jijjiga kai da kyau sannan tace,"To sata ta ƙare a ahalinsu, kuka kuma nasa ne ke kama dana tumaki. Ita kuma Malamar itace babbar daƙiƙiya da ta kasa fahimtarki. Kuma suje da halinsa na rashin kyautawa Allah zai saka miki, yanzu kije ki wanke fuskarki kizo kici abinci, na san babu abinda kika ci ki ka fice karatun da ba lada ba zunubi". na goge hawayena ina tambayanta cewa,"to Gwaggo zanje ɗin?". "za kije mana, ba kunyi hutu ba?". "ehh munyi har na wata guda ma". "to kinga kuwa kina da lokacinma da za ki je ki zazzaga musu. Ki bari idan Karima tazo sai ku wuce tare idan zata koma". Na miƙe ina cije leɓe nai ɗakina, gado na faɗa ina jin farinciki da nishaɗi, zanje naga Yayana, kuma mu taho tare da shi don bazan kuma barinsa acan ba, dole ne ma ya biyoni. Na rugume pillow inata murmushi ni ɗaya, dana rufe idona babu hoton dake haska min sai nasa, zumuɗi duk ya hanani sukuni, na ɗauka waya na kira Inna Karima na tambayeta yaushe zasu tace sai nan da sati biyu, ina jin haka ban san lokacin dana gilla mata ƙaryar ai Gwaggo bata da lafiya ba, aiko hankalinta a tashe tace min suna kan hanyar zuwa gobe ko jibi. Na kashe wayar ina dariya sai kuma na fara Allah na tuba Allah ka ƙarawa Gwaggo tah lafiya, ina haka ta shigo, hannunta ɗauke da kwanon abinci, yanayin da ta riske ni yasa tace, "ke lafiya?". "lafiya lau Gwaggo". Ta dire min abincin saman table tana faɗin, "da dai sauƙi kam, Allah ya bada lafiya inda rabon samunta". Ta juya za ta fice na dakatar da ita da tambayata. "Gwaggo kin taɓa ganin Halitta ɗaya a mutum biyu?". ta wani juyo a sukwane tana ambaton sunana, jin na amsa yasa ta cewa,"ohh ke ɗince dai". sai na ɓata fuska na turo baki gaba nace,"wai Gwaggo ba zaki bar ce min mai aljanu ba". tana gyara ɗaurin zanen da a ko yaushe nake takaicinsa tace,"to ai tambayar taki ce Sabina ta a bincika ce". "to ni dai ki bani ansata". "ansar me zan baki Sabinan Gwaggo?". na ƙara jefa mata tambayar, a wannan karon daya kasance tana fuskantata ne sai kawai ta bini da ido tana kallona da kyau cike da nazari, sai kuma tasa kai tayi hanyar fita tana faɗin,"to Allah yasa ba gamo kika yi ba...ni dai Rakiya Allah kayi min maganin abubuwan da suke neman fin ƙarfina". *Please Vote, Comment and Share.*[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(18)* bayan fitar Gwaggo kuwa raina fes nake jin shi, murmushi kuwa idan ka kalla fuskana kai kace gonar auduga ce saboda yadda haƙorana suka gagara rufewa. Har sai da Gwaggo ta dawo ɗakin ta iske ni kwance kan gado still dai murmushin nake, ina kuma ta faman juyi akan gado, sai da ta ƙare min kallon tsaf kafin ta samu gefen gadon ta zauna kana tace. “Allah mai girma da ɗaukaka, yau naga Mace. Anya Sabina lafiyarki kuwa, na fita kina dariya haka zalika na shigo kina dariya, to ki daiyi a hankali don wallah dariya illah ce, kuma kin san bana son dariya”. matsowa nayi kusa da ita, na kuma sakin murmushi. Sai naga ta miƙe tsaye zata nufi hanyar fita nayi caraf na riƙe hannunta, ina ƙunshe dariyar da ta ciyo ni, don nasan sarai abinda ke ranta nace,“wai Gwaggo me kika gani, ina zaki je dana ga kin miƙe?”. tace, “yo Sabina na sani ko aljanun ki ne suka dawo, wannan dariyar haka sai kace an maki bushara da shiga aljannah”. “yo Gwaggo kika sani ko busharar aka min, kinga ai sai mu tafi tare”. sai kuma na kwaɓe fuska nace,“amma fa gaskiya Gwaggo kibar cewa ina da aljanu, waye ke son su, amma ke duk magana ɗaya sai kice aljanu, mutum ba zaiyi dariya ba sai ya zama jinnu”. na faɗa ina yin ƙasa da kaina tamkar zanyi kuka. Ganin haka yasa Gwaggo kamo hannuna tace, “haba ƴar lalen Gwaggo, kinga kece naga sai murmushi kike ke ɗaya kuma kin san Allah da yayi ni ina da tsarguwa shisa kika ga nace haka, ko kuwa akan maganar ɗazu shi ne duk kike faman wannan murmushin, ko dai a makaranta kin samu ɗan..”. bata ƙarasa maganar ba muka haɗa iɗo, sarai na gane inda ta nufa sai na waske nace. “Gwaggota kenan mai abin mamaki, ki bama mutum daɗi ki bashi haushi, nasan fa abinda kike nufi, to ni bashi yake sakani nishaɗi ba, kawai dai ina son zuwa Kano saboda naga Farhana, kuma naga dangin Mama shi ke sani nishaɗi wallah. Kuma duk lokacin dana tuna yadda Kike tattalina kamar ƙwai sai hakan ya kuma tsundumani cikin nishaɗi da jin daɗi, ke dai Gwaggo Allah kaɗai zai biyaki ya kuma ƙara maki nisan kwana mai amfani ya ɗora ki kan maƙiyanki. Ina son ki Gwaggota”. na ƙarasa faɗa ina bata sumba a goshi. Gwaggo ita ma ta shafa bayana tana saka min albarka tana faɗin, “ai kema kin san indai akan kine sai inda ƙarfina ya ƙare, Allah dai ya haɗaki da miji nagari. Oh Allah ka nuna min wannan rana, gaskiya ranar akwai shagali, ke ranar sai na kwaso shoki, don ma wai babu Sahibina a kusa da nake faɗi maki abin sai yafi armashi”. Dariya nayi na janyo kwanon abincin da ta kawo min ɗazun na fara ci kafin nace, “ɗakko wata hirar don yanzu idan kika fara labarin Sahibin kin nan sai mu kwana mu yini baki gama ba, sai kace Sahibin kin nan yafi kowa”. ta ɗan dungure min kai, “munasira!, yo har kya faɗi min wani zancen Sahibina, baki ji akace kowa da bazarsa yake taka rawa, to ni tawa rawar da ta Sahibina ce, yo Allah na tuba ke har kya yimin zancen zan ɗakko maganar Sahibi, kema fa idan kika samu wuri tsaf nasan sai kin zarce ni, yarinya baki san loɓe ba(love)”. wata dariya ce ta suɓuce min wadda yayi sanadiyar zubar da abincin da nake ci waje, Gwaggo tamin duban sheƙeƙe kafin tace,“kinga ba nayi magana kice ke baki san zance ba, yo meye abin dariya anan?”. ta tambaya babu wasa a fuskar ta, da alamu ta ƙulu, don haka nayi gaggawar tsayar da dariyar da nake yi kafin nace,“yo Gwaggo kece da fama, sai kice sai kinyi turanci kuma baki iya ba, ai sai ki haƙura haka, idan kuma ba haka nace maki zan fara koya maki haruffan hausa shima kinƙi da duk kin san yadda ake faɗan words a hankali”. “ke kika san wani was(words), hakan ma tunda zan faɗa a gane ai shikenan tunda ba wurin wani naje na faɗa ba, bare naji kunya ato”. “yo ai kuwa wataran zaki faɗa a wurin wani wallah idan baki daina ba”. Gwaggo tace, “yau naga iya shege, ke Sabina fice min da gani”. Daga haka na miƙe ina dariya har na fice a ɗakin, dama yau na gama shiri na ba zan kwana wuri guda da Gwaggo ba duk tabi ta dameni da hayaƙi. Kai na tsaye nake tafiya dariya nacin cikina, har na isa corner da zata sadaka da kitchen kaina a ƙasa naji nayi tuntuɓe da abu da sauri na ɗago kaina ina duban meye ne, karaf muka haɗa ido da Yaya Haidar, da sauri na zaro ido shima ni yake kallo da irin kallon wanne abu zan maki na huce. ni kam ganin kallon da yake watso min tuni na sauya hanya, nayi gefe da niyyar wucewa yace,“dutsen da kika taka hala bai ji maki ciwo ba?”. Na ɗan ɓata fuska nace, “eh bai jimin ba”. ina faɗar haka na kuma niyyar wucewa. aiko a zafafe ya damƙo hannuna, tuni ido na ya raina fata, duk lokacin da muka haɗu sai naga kamar zai kuma tsotsen baki ne, fuskata ta cika da tsoro, baki na fal in-ina nace, "ka..kaj..kaji tsoron Allah kaga dai ba abinda nayi maka karka tsotson baki don Allah”. ina gama faɗar haka hawayen da suka cika ido na suka samu nasarar sauka kan ƙafar Yaya Haidar ya kuma ƙulawa fuskarsa tamkar ta bijimin sa yace,“an faɗa maki kowa ɗan iska ne kamar ke, da za’ayi tayin abu guda, ko an faɗi maki kowa maye ne kamar ke sha uku kawai, goge min ƙafa na ko na zane maki ƙaramin mazaunanki nan”. takaici ne ya ishen, a zuciyana nace, _wallah kamar na zabga maka mari nake ji._ zaro idon da Yaya Haidar yayi yasa ni tsorata ba ƙarama ba, don wata iriyar damƙa ya kuma yima hannuna ya matsa min ya kuma galla min mintsini, take na buga tsalle idona ya cigaba da zubar da hawaye da ƙarfi ya buga min tsawa yace,“ni sa’an kine, Sabina ina wasa da ke ne, ni zaki kalli tsabar idona kice za ki mara?”. ya ƙarasa maganar yana nuna kansa. “wallah zancen zuci ne ya fito fili ban san na faɗa ba, don Allah kayi haƙuri please Yaya Haidar Allah ban san ya fito ba”. ɗan cif-cif gemunsa ya kama yaja kana ya kawar da kanshi gefe guda, ban ankara ba yaja hannuna fuuuuu sai ɓangaren shi. ina ta bashi haƙuri amma sam bai kulani ba, saboda maganar tayi mashi ciwo, yana shiga yasa key a ƙofar ya saki hannuna, nan na shiga bashi haƙuri akan ya barni na tafi kar ya kuma tsotson baki, sai kawai na tsinkayo muryar shi yana faɗin,“abinda yau yafi tsotsar maki baki shi zan maki, za ki gane shayi ruwa ne zalla, za ki san kince ni za ki mara marar kunya kawai”. Nan ta ke ya shiga cire rigar shi ya zama daga shi sai gajeran wando, na saka hannuwa na rufe idona, gabana sai dukan dubu-dubu yake yadda kasan ana surfe akan ƙirjina, zuciyata kamar zata faɗo ƙasa tayi dancing haka nake jin yanayin yadda ta ke duka. Ta cikin hannuna nake ganin shi yana takowa, sai daya iso har inda nake naji ya cafki hannuna, sai ji na kawai nayi ya wulla ni kan gado, yana ƙoƙarin hawa gadon nace,“na rantse da Allah idan ka hawo gadon nan kamar a bakin Baba, tunda na kalla sam baka tsoron Gwaggo ka mayar da ita sakarya Kuma wallah Allah indai...”. Ban kai aya ba na jiyo muryar Gwaggo tana ƙwalo min kira. Da sauri ya mayar da rigar shi da wandon shi ya samu wuri ya zauna ni kuma yace min, “tashi ki shiga toilet ki tabbatar kin wanke fuskarki ta wanku, zance ma Gwaggo kina wanke min toilet kuma wallah idan naji kin faɗa mata magana ɗaya akan abinda na maki”. ya nuna ni da yatsa alamun kin san sauran. Cikin hanzari kuwa na diro daga gadon na faɗa toilet ina shiga Gwaggo ta turo ƙofar ɗakin ta shigo tana faɗin, “a’a Zainab tace min Sabina’n tana nan, ko kuwa tayi wani ɓangaren?”. “Eh tana nan, tana wanke min toilet ne”. ya bata amsa ataƙaice, kansa na ƙasa kamar me yankan farce. “Tolet kuma?, yau kuma ƴar wankin tolet ka mayar da ita bayan wulaƙancin duk da kake mata a baya bai ishe ka sai ka haɗa da folishwan?”. ina toilet amma yadda ta faɗi kalmar Punishment ba ƙaramin dariya ya bani ba. Yaya Haidar yace,“Gwaggo wai yaran nan idan ba’a basu aiki dame zasu horu idan sunje gidan miji, ki riƙa kawar dakai akan Sabina mana bafa ita ɗaya ne ƴa ba”. “au tou, haba sai ka ce min kai kayi ƴaƴan ai har daka san horo, tunda har ka iya tsayawa tsegege ina faɗa kana faɗa, Aliyu ka shiga hankalinka dani, wai bance ma ka daina zuwa gefe na ba har ka ganta ka saka min ita aiki ba, Aliyu ka fita idona na rufe billahillazi tun kafin nayi maka abinda har ka koma ga ubangiji bazaka manta ba wallah”. tana ida zancenta, ta ƙwala min kira, ni kuwa dama ƙiris nake jira na fito muna haɗa ido tace,“jakar uban can, kar kace min kuka ka bata, don wallah mai barinka ka ƙara kwana gidan nan sai ikon Allah”. da sauri na girgiza kai ina tuna sharaɗin daya gindaya min nace,"a’a fa Gwaggo, ina wanki ne ƙwaro ya faɗa min a ido, shine kika kalla yayi ja haka, amma na fitar sai dai bai daina min zafi ba, muje”. naja hannun ta muka wuce don nasan zata iya fahimtar abinda ya faru. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(20)* *Kano.* "idan ka gama ka kulle masallacin". limamin masallacin da ke tsaye akan Alhussain yace da shi. Alhussain da kansa ke ƙasa kan ƙur'anin dake hannunsa yana karantawa bai ɗago ba sai daya kai aya tukunna. sannan ya ɗago da kansa dake masa nauyi ya kalli Liman ya amsa mishi da,"tom Malam". har Liman ya kai bakin ƙofa sai ya dawo ya duƙa ya ajiyewa Alhussain naira 200 a kusa da shi. tsawon wucewar mintuna talatin sannan ya kammala karatun ƙur'anin, ya shafa adu'ar da yay sannan ya mayar da ƙur'anin ya kai cikin drower ya aje. ya dawo ya tsuguna ya ɗauki kuɗin da Liman ya aje masa yana tayi masa adu'a cikin ransa. sannan ya fita ya rufe duka ƙofofin masallacin ya ɗora mukullin a inda ake ajiyewa. bayan sallar isha'i ne lokacin, dan haka unguwar ta daɗa yin shiru sai haushin karnuka da kake shi, haka kowanne layi duhu saboda rashin wutar nepa. tafiya yake yana takawa a hankali saboda yanda ƙafafunsa ke yi masa tsananin ciwo, haka har ya fito bakin titi, anan ya hangi wata ƴar tsohuwa mai siyar da tuwa ya ƙarasa wurinta ya siyi tuwo da miya na hamsin, a wurin ya zauna yaci sannan ya tashi ya koma bakin masallaci inda yake kwana anan yanzu tun bayan fitowarsa daga cell. kuma a wannan zaman da yay ne gyangyaɗi ya fara ɗaukarsa, cikin baccin dake neman ɗibarsa yaji kamar hayaniya, dan haka ya buɗe idonsa da sauri, dai-dai lokacin da motar ƴan sanda ta tsaya a wurin, a gabansa, dan haka ƙwayar idonsa akansu ta sauka. bakinsa da zuciyarsa suka shiga furta kalmar innalillahi wa'inna ilaihi raji'un a sanda yaga Ƴan Sanda na tunkaro shi, wasu matasa kuma a tare dasu na faɗa musu cewar,"ehh shine, wallahi shine". kalmar shine ta bada tartsatsin tsawa acikin kansa, yaja numfashi ya sauke tare da lumshe ido. a cikin duhun idonsa abunda ya faru da shi kwanakin baya da suka shuɗe ya shiga haska masa, ko kaɗan baya fatan hakan ta ƙara maimaituwa masa, ko da a mafarki baya fatan ƙaddara ta ƙara kaishi hannun ƴan sanda. zuciyarsa a yanzu faɗa masa ta ke akan ya tashi ya gudu, ya tashi gudu tun kamin su cimmasa su kama shi, bai san dame suka zo ba wannan karan, idan har ya ƙara shiga hannun hukuna taya za'ai ya fito?. ya buɗe idanuwansa ya suke kan ƙafafunsa biyu, ɗaya ta kumbura suntum ɗayar kuma ta ɗan sace ba kamar da ba. ya ƙara maimaita kalmar innalillahi a cikin ransa, ko daya miƙe tsaye, ko da yace zai gudu, la shakka babu inda zai kai ga ɗora ƙafarsa zasu cimma masa, da ƙyar ya takawa, irin takun da ko kusa ko kaɗan ba zai iya yin gudu ba. maimaituwar kalmar innalillahi a bakinsa ta haɗe da damƙwar kwalarsa da ɗan sanda yayi, ya fizgo shi ya miƙe tsaye, sannan ɗayan ɗan sandan daya ƙaraso shi da wasu mutane ukun da bai sansu ba ya kama hannunsa ya saka masa ankwa. sannan suka tasa ƙeyarsa zuwa cikin mota suka tafi. _"gani nan Yaya. Yaya gani nan, karka bari ƙwallar ta zubo dan Allah"._ maganar daya ji na shiga kunnensa kenan, muryar Sabina ce, daga ina?, tana ina?, ya rumtse ido da ƙarfi ya kuma buɗesu, acikin motar dai yake, cikin motar dai daya ji ana faɗar direct gidan gyara hali za'a kai shi. bai san lokacin daya daki kansa da jikin motar ba, inda tasan abunda ta ke haifar masa, da ta hana ganinta da jinta suna yi masa gizo, da ta hana sunanta ambatuwa acikin zuciyarsa. kuma buguwar da yay a wannan lokacin shi yay sanadiyar ɓallewar jini daga kansa, saukar jinin da yay sanadiyar tsayar komai acikin kansa, ya daina ji da ganin komai. *Abuja.* "haka za ki fita ba ki ci komai ba?". "ina tsoron layi ne shiyasa, idan naje can ɗin na sami resturant a kusa saina saya na ci". "hakan yayi, a dawo lafiya. Idan kinga mutane ba sauƙi a wurin ki dawo ya ba ki kuɗi a hannu kawai saiki amfani da shi". "ameen..tom Gwaggo". Na amsa ina gyara yafa mayafina. Da sauri na fito compound, ina zuwa na tarar motana babu mai, na daki kai ina jan tsaki, ni yanzu ya zanyi? Shine tambayar da nayi ma kaina, ga Yaya Abba baya nan, ni kuma bana son kula Yaya Haidar bare nace ya ara min tasa, to ya zanyi dole haka zan haƙura neje wurin nasa tunda dai babu wata motar a ajiye sai ta matan gidan, su kuwa ba shiri muke ba bare nace zan ari tasu, shi yasa nacewa Baba a ɗaukar mana driver a aje, yace a'a baida amfani tunda dai kowa ya iya motar nan kuma ga Yaya Abba da Yaya Haidar ma. Har na nufi part ɗin su Yaya Haidar na hango Anty na shirin fita, na dawo da sauri na ƙarasa wurinta lokacin harma ta shiga mota tana ƙoƙarin fita, na tsayar da ita, ta zage glass tana jiran cewata sai faman haɗe rai ta ke tana min gani-gani. cikin ƴar murya nace,"Anty please bari na biki ki ajeni a bank, motana babu mai aciki, jiya su Yaya sunyi tafiya ina tunanin basu san ya ƙare ba basu tsaya sunsha ba, idan nace zan bari aje a sayo zan ƙara yin late". Nace da ita ina maganar da sigar roƙo na lallami. "tunda ubanki ya saya min motar ai dole ne na zame miki driver, to ko na rasa abar ɗauka a motana bana yayibi mai aljanu ba na kwasarwa kaina matsala". Ta faɗi hakan tana ɗauke kanta akaina taja motar ta fice a gidan. Oh ni Sabina, yanzu har ta kai ake min gorin mai aljanu, na goge guntun hawayen daya sakkomin, _Allah ka yaye min da ni da sauran ƴan'uwana ba ki ɗaya._ nayi adu'an a zuciyana ina nufar hanyar gate, saboda na san idan na koma Gwaggo cewa zata yi na fasa zuwa, ni kuma nafi so nayi abuna yau na huta, don akwai terming ɗin da nayi. Har na kai gate zan buɗe ƙofa na jiyo Gwaggo na ƙwala min kira, na juyo na ganta tsaye tana jan kwandon shara, ko ina zata da shi oho, rigima dai irin tata kawai, Baba yace su Zainab suna zuwa suna mata aiki tace bata son marasa mutunci suke zuwar mata inda take, Inna Karima zata kawo mata mai aiki. daga inda ta ke tsayen tace, "idan kin gama ƙare min kallon, nace har yanzu ba ki tafi ba dama?". "ummm motan nawa ne babu mai, zanje na hau ta haya sai na tafi". "to zuwan yau dama dole ne ko ƙaƙa?". ina ɗan marairaice fuska nace, "nafi so ne nayi yau ɗin, please Gwaggo ki barni na tafi". Ina kallo ta taɓe baki, "wai please, dole dai idan za'a maka magana sai an haɗa da ɗan iskan yaran da ba jinsa kake ba, yare bana uwa ba bana uba ba, shegen bature duk ya lalatawa ƴaƴan musulmi harshe, banda kece ma da sai nace zagi na akai". Ina nesa da ita banji mai tace ba, na juya zan tafiyata tace, "riga Malam masallaci ai ban gama maganar da ke ba, ina Abba ko wannan yaron Haidar?". Tana rufe baki Yaya Haidar na fitowa daga ɓangarenta, yana gyara maɓallin hannun rigarsa fuska a haɗe yace, "ni fa ba yaro bane karki kuma ce min yaro". "to ubana". Tace da shi tana hararsa. Sai kuma tayi masa kallon tsab kamin tace, "fita zaka yi ne?". "umm". Yace da ita yana tafiya. "yauwa to ga Sabina nan zata je banki, sai ka ajeta a can motarta ce babu mai". "ni ba driver bane, taje ta nemi nepep ta hau mana". Tace da shi, "yanzu Haidar ni zance kayi abu kai tsaye kace min ba zaka yi ba saboda banda girma a idanunka. Wannan yarinyar fa ƙanwarka ce, me yasa kake nuna mata tsana da yawa har haka ne, idan baka ɗauketa ba ai kaje ka ɗauki wata ƙatuwar banza. Kuma motar nan dai naga ai Babanta ne ya saya maka ita, amma saboda kai mutunci bai gama ratsa jininka ba shine zaka ce ba zaka kaita inda take so ba". cikin jin haushi yace da ita,"da nayi magana sai kice bana ganin girmanki, shi yasa idan kina magana nake miki shiru. Kuma shi Baban daya saya min motar ai ba cewa yayi gata nan ka zama driver'n Sabina ba. And again motana bata ɗaukan marar kunya ne". "idan bata ɗauka mara kunya ba ai ta ɗauka fitsararru". Gwaggo ta sa ki wani guntun murmushi kamin tayi ƙwafa tace, "hmmm ina jiye maka ranar ƙin dillanci. Ina roƙon Allah kar ya jarabce ka da son wannan yarinyar kayi tunanin zan baka ita Aliyu, ko da zanga ledar jini gefe, ledar ruwa gefe babu zancen mallaka maka Sabina, atoh ka jini da kyau". "nima kar Allah ya nuna min wannan ranar, dan babu abinda zanyi da wannan mummunar jikar taki. Da za ki ce mata ma ta daina kwalliya idan zata fita may be ta ke yin samari, wannan kwalliyar babu abinda ke ƙara mata sai girman ƙwailancinta, ƙwaila kamarta ace babu mai so, ki miƙe tsaye ki samu ki haɗata ta farfaɗo don tayi tsala da yawa". "akwai babban tsala ma irinka, kai wacce asararriyar macen ma zata iya aurenka, cikakkiyar mace dai cewa zata yi baka girma ba, tunda gaba ɗayanka yaushe ne ma aka cire maka shayi". Wani shu'umin murmushi naga yanayi yana cizon leɓe, yayi ƙwafa murya can ƙasa yace, "to Gwaggo koma wace a bamu ɗaki ɗaya da ita a jira wata tara a gani. Anan za'a tantance darajar kaciyar tawa". ni kaina kalmarsa ta ƙarshe ba kaɗan ɗin kunya ta bani ba. Gwaggo kam sheƙeƙe tayi tana kallonsa kafin tace,"kai dama ai ba kunya gareka ba, Allah dai ya shiryeka idan na shiryuwa ne, idan kuma bana shiryuwa bane yay mana maganinka". Murmushi kawai yay mata baice komai ba, yasa key ya buɗe motar, tana dubana tace, "to ki taso ku tafi". Yay saurin waigowa ya kalleni ya kalleta, "ni fa babu yarinyar da zata shigar min mota, tunma wannan jikar taki mara kunya. Yarinyar da gaba ɗaya kayan jikinta suka girma a gabanka amma ji take kamar ita ta baka nono". kawai saina Durƙushe a wajan na fashe da kuka, idan da kalmar dana tsana naji yana cewa na girma gabansa, ranar nan haka yace min tun twins ɗina na ƙifil-ƙifil ya sansu amma saboda yanzu sun cika min ƙirji shine nake ganinmu kai guda da shi. masifa naji Gwaggo na masa na ɗago ina dukan ƙafa a ƙasa ina ƙara sautin kukana. "ni dai Gwaggo Allah na gaji da ganin Yaya Haidar da Anty a gidan nan, duk su biyun sun tsaneni". "ita kuma guntuwar me tayi miki?". "ɗazu itama fa daga nace ta rage min hanya take cewa ba zata yayibi mai aljanu ba...". Ban ƙarasa ba ta tareni da cewar, "ita Guntuwar ta gaya miki wannan kalmar mai ɗacin saurare?". Na ɗaga kaina ina ƙara cewa, "kuma ai duk ke kika jawo min koma wacce magana ce, ina zaman zamana kin tashi kina yaɗawa mutane wai ina da aljanu". Jikinta naga yay sanyi, sai kuma ta duba Yaya Haidar tace, "kira min Auwalu a waya kace yazo ya sameni cikin gaggawa, ke kuma tashi muje ciki". Ta ƙarasa maganar tana dubana. Na miƙe zan bita sai ga Baba ya ƙaraso wurin, ta zuba masa ido tana faɗin, "yauwa Ashe kana cikin gidan?". "ehh inan ban fita ba. Daga wurinki nake naga duk baku nan, ina fitowa kuma na hangoku anan". Ta shiga goge hawaye, a cikin muryar ƙonewar zuciya take faɗa masa. "yanzu tsakani da Allah abinda matanka suke a cikin gidan nan suna kyautawa, kwata-kwata basu san hakkin maraya ba, kai kuma gaka sun gama shanyeka babu abinda kake iya tsinanawa, ni kuma gaba ɗaya baka tausayina, nasha wuyar kishiyoyi zan kuma sha ta matanka, to wannan a baya ne akayi baza a kuma ba. Babu shegiyar da zan zubawa ido acikin gidan nan tana cin zarafin marayun yaran nan, wanda suka yi a baya ma su da Allah. Ƴar nan ko ɗumin hannun uwarta bata ji ba da ta zo duniya amma hakan baisa aji tausayinta ba, Yanzu har ta kai da su dinƙa goranta mata akan tana da aljanu, to ita ta ɗorawa kanta ne? shi dai ciwon nan bai wuce kan uban kowa ba, to Kaja musu kunne su shiga hankalinsu da taɓa yarinyar nan idan ba haka ba kuma billahillazi zan ajiye sanyin da nayi a gefe na zazzage musu buhun rashin mutunci, na zama kalar uwar mijin da ba'a so. Wannan ƙiyayya da ake nuna mata haka tun ina da rai, to randa babu ni kuma fa? to ni wallahi da a taɓa min Sabina ƙwamma a fito fili ace min Hannatu na tsaneki, in yaso ayimin zagin ƙare dangi zanfi jin daɗin hakan, ɓacin ranta yana damuna haka kukanta yana ɗaga min hankali, ka gayawa wannan guntuwar karta ƙara yin abunda tayi saboda hukuncin da zan ɗauka akanta ba zaiyi mata daɗi ba". Baba dake tsaye yana sauraronta ya ɗago ya kalleta yace, "ni dai don Allah Gwaggo ki bar wannan kukan bana so, ki kuma yi haƙuri zanyi musu faɗa hakan ba zai kuma faruwa ba". "karka kuma bani haƙuri akan laifin matanka domin cutata kake, kai da ubanka marigayi babu abinda kuka iya idan an cuce ni sai bani haƙuri, to ni wannan mugun kalmar na gaji da jinta, tun ina zaman gidanka wancan Zamanin na zaman Halima da Hajara kake zaluntata da wannan kalmar, karka ƙara idan ba haka nayi maka irin yanda nama Sulaimanu. Maganar ƙarshe da zanyi wallahi wallahi kaji na rantse ko, duk ƴar wofin da ta kuma shiga harkar Sabina a gidannan sai ka saketa ta koma gidan koko da wainar gero". Ya buɗe baki zai ƙara bata haƙuri sai kuma yay shiru. Ya kuma kalleni yace, "ke acikinsu wace ta gaya miki haka?". "Anty". Nace da shi. Wani kallo yay min wanda na lura da alamar bai yarda da maganar ba, domin baya taɓa yarda da laifinta. Na miƙe ina gyara ratayen jakata nace, "Gwaggo zan tafi". "kin bari sai gobe ko kuwa?". ta faɗa tana min wani kallo. Na zumɓuri baki ina kallon Yaya Haidar da shima ya ɗago a lokacin yana kallona. Baba har zai wuce kuma sai ya dakata da faɗin, "Gwaggo ina ce na hanaki shara, me tsintsiya keyi a hannunki da safiyar nan?". ya faɗa yana ƙoƙarin ƙarɓar tsintsiyar hannunta. tace da shi, "ban son shishshigi da ƙwala kai a faranti, bada tsintsiyar hannuna zaka ji ba da wannan abin zaka ji". ta faɗa tana nuna masa Yaya Haidar dake kusa da ita. kamin ta ɗora da faɗin,"Tun ɗazu nake fama da yaron nan akan ya ajiye Sabina a banki, yaƙi ya tsaya sai karta min maganganun banza yake, ka san jinsa yake kamar sa'nni muke". Kamin Baba yay magana da sauri Yaya Haidar ya kalleni yace,"kin fasa tafiyar ne?". Yay maganar kamar bashi ba, ni kuwa nayi kamar ban jisa ba, na ɗauke kai gefe ina hare-hare, shima kuma sai hararata yake ta ƙasan ido. Baba yace, "ita ina motar tata?". nayi saurin cewa, "Baba ciwo fa naji a ƙafana, bazan iya driving ɗin ba nace ya kaini don Allah tunda Yaya Abba baya nan, shine yace aishi ba driver bane, naje na hau napep, har Gwaggo ma sai da tayi masa magana yace shi ba zai ɗau mara kunya ba". Ina yin shiru shima yace, "Baba ƙarya ta ke yi babu wani ciwo da taji, Gwaggo tazo ta samemu ne muna maganan zanje na sayo petrol a zuba mata a motan nata tunda ni ina sauri ne". Gwaggo ta riƙe haɓa tana faɗin, "iko sai lillahi, au yau kuma ni zaka ƙaryata Aliyu, yau naga makirci a wurin ɗa namiji. To Auwalu ai ka gani da idonka, shi da Abba don suyi min rashin kunya su ƙaryata ni wannan ba komai bane a wurinsu, yau gashi harda su kissa. wannan yara dai ai albasa batayi halin ruwa ba musamman Aliyu, dan ba haka uwarka da ubanka suke ba, Allah zai kawo Sulaimanu gidan nan zanji idan shine ya ɗaure maka gindin yimin fitsara". ta numfasa da ƙara cewar, "to koma menene dai kaje dan kanka. ni ba wannan ne buƙatata ba, kawai Auwalu kace ya ɗauketa ya kaita inda ta ke son zuwa, ya jira har sai ta gama kana ya dawo da ita, don na tabbata maka babu inda za shi bacin shegen yawonsa da ba ƙararre bane". Baba ya dube shi yace, "wurin aiki zaka ne?...". Gwaggo tai saurin cewa,"ai kaji tsiya, shi har ƴaƴansa ma tsoronsu yake, kai da zaka balbale shi kamar wuta amma kana masa magana a ruwan sanyi". Baba baice mata komai ba, Yaya Haidar yace masa, "ehh Baba amma ai har zan iya ajiyeta, tunda ban makara ba". Baba ya dube ni yace, "ke mene ma za ki yo a Bank ɗin da wannan safiyar? Idan kuɗi za ki amfani dasu ba saina ranta miki ba, ko kuma kije wurin Anty'nku ta ba ki aro". Na zaro ido ina faɗin, "tabɗi, wannan matar ce zata ara min kuɗi, zanko mutu babu kuɗi a hannuna". Baba ya galla min harara, Gwaggo ta gyaɗa kai tace, "ah to gaya masa dai, ita wannan munafukar ɓoyen gani yake kamar ƙaunarki ta ke". Baba ya girgiza kai kawai ya wuce. Yaya Haidar kuma yace, "kizo mu tafi".ya faɗa yana shiga mota. Na zagaya na shiga ya tada motar muka tafi. ba ƙaramin da nasanin biyoshi nayi ba, fitowar da muka yi tun tara sai sha biyu ya kawoni bank, sai daya gama zagaye-zagayensa tukunna, kuma duk saboda ya ɓata min rai yayi hakan. Ni kuwa ko parking bai ƙarasa yi ba na buɗe motar na fice, ko da na isa layi ne maƙil a wurin, kamar zan koma kawai na haƙura, sai dana shafe awa guda kamin azo kaina, ranar waje duk ta gama zane min jiki. Haka na shiga cikin bank ɗin, nan ma wani layin ne na musammman a wajen customer care, shima mutanen dake gabana sunfi goma sha biyar, na durƙusa ina danna wayata. "who is Sabina?". Naji one of the customer ɗin na magana. Na miƙe tsaye ina ce masa gani, "come to the front". Yace da ni. na ƙarasa gabansa security ɗin wurin na biye da ni a bayana, aka ja min kujera na zauna akai, security ɗin yaywa na bayana tsawa akan duk su ja baya, na faɗi complain ɗina, in few minutes aka kammala min komai, nayi masa godiya yace babu komai Madam. Haka na fito daga wajen customer care, securities na biye da ni baya da gefe, ni dai abin na ta bani tsoro da mamaki, mutane kuwa kowa kallona yake, wasu na raya ko sata nayi wasu kuma na tunanin wacce mai babbar matsayin ce wannan. ATM machine na wuce shima na tsaya bin layi, ina tsaye nan sai ga wani security na daban yazo yace kowa ya bar kan layi yay baya, duk mutane na ta jan tsaki sukayi baya, sai naji yace da ni nazo na cira, abin sai ya bani mamaki, haka a ciki ma aka mani kamar wata ƴar mai faɗa a ji a nigeria. Hayaniya ta kaure tsakanin mutane kan ba'ayi musu adalci ba in har akayi haka, sai na duba security ɗin nace karka damu zan jira har layi yazo kaina. Duk da cewan dattijo ne amma haka yake rissina min, kuma cikin girmamawa yake min magana yace, "duk abinda ke wakana ta nan oga yana gani ta cikin CC, kuma idan har na saɓa umarnin shi zan iya rasa aikina ta dalilin hakan saboda yace ke ɗin mai muhimmanci ce, ki taimaka min wannan aikin da shi na dogara nake ciyar da iyalina". Abun ya ɗaure min kai, na ɗaga ido ina kallon CC camera ɗin dake hasko mu, to wane shi ɗin? na sauke ajiyar zuciya na ƙarasa wurin ATM machine ɗin saboda karna ɓatawa jama'ar wurin lokaci, na ciri kuɗina na bar wurin, zan fita a gate maroon ɗin mota ƙirar accord sabuwa fil tasha gabana, ina jiran ta wuce sai driver ɗin ya fito ya buɗe bayan motar yace na shiga. Wani duba na tsaya ina yi masa, a yayin da duka idanun mutane ya dawo kaina, banyi maganar da zanyi ba ya miƙo min waya yace ana magana. "wa...?". Ban ƙarasa tambayar ba Kawai naji an ɗora min wayar a kunne, na waigo don ganin waye haka, mace na gani da black skirt with white longslip a jikinta kuma ba musulma bace, da alama itama security ce, ni dai mamaki duk ya baibayeni, ta cikin wayar naji yana cewa,"don Allah Beauty ki shiga motar ya sauke ki a gida, bana so kina tafiya wani halittar ɗa namiji na kallonki, bana son gardama". Yay maganar cikin sigar roƙo. laɓɓana suka haɗe wajen furta, "kana school kana nan, to kai ɗin wane? Kuma nazo kasa anyiwa mutane rashin adalci, sunyi sammako sunzo wuri suna jira, ni kuma da ban haura rabin awa da zuwa ba nayi na gama, hakan da kayi adalci kenan matsayinka na shugaba? Ni ɗin nafi kowa ne?". Ajiyar zuciya naji ya sauke, muryansa a hankali yace, "idan har akanki ne to a wurina nayi babban adalci, babu ta yanda za'ayi ina da iko a wuri kuma na barki da shan wahala. Yanzu awajen nan idon kowanne banzan namiji akanki yake, ki taimaka ki shiga mota ku tafi, idan kin ƙarasa gida za muyi waya". Maganar ya ƙarasa min ita yana ɗan ɗaga murya. "Beauty". Ya katse min shirun da nayi. "mene kuma? Nifa babu motar da zan shiga, ai da zanzo bada taimakonka nazo ba, kuma Gwaggon bata bani wannan tarbiyar ba". Nace da shi. Sai naji ya fitar da iska daga bakinsa, "da ace ina da lafiyar takawa da nazo da kaina na kama hannunki na tilasta miki, sai dai bani da damar hakan". Na taɓe baki, kiran wayar Yaya Haidar ya shigo wayata, na ɗaga yace, "Malama kina tsayuwar mene anan da ba za ki fito ba, ko zanyi ta zaman jiranki ne?". murya a kumbure nace, "to ni nasan kana nan ne, kuma ai naga bance kazo ɗaukana ba". banma ƙarasa faɗar abinda zan faɗa ba ya kashe wayar. nayi nazarin ƙwamma na fita na bishi, wannan proff ɗin na gane yana min wayo ne so yake na yaga gidanmu. Don haka na raɓa deiver'n dake tsaye gabana na fice da sauri, Yaya Haidar na ƙoƙarin kunna motar na buɗe na shiga, ko magana baiyi min ba bare kallona. Nace da shi, "Yaya Haidar wai zaman jirana kayi ko kuma dawowa ɗaukana kayi?". Kansa na kan tuƙin da yake yace, "ko hakan bai maki bane na saukeki?". "a'a kawai dai dama na tambayeka ne". Haka na dinƙa masa hira yana amsa min jefi-jefi har muka iso gida, ina kallon wayana na ringing ban ɗauka ba tunda na lura numban proff ne a jiki. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(19)* Washe gari da safe bayan mun karya ina ɗaki muna waya da Farhana ina faɗa mata zanzo kano ba ƙaramin daɗi taji ba, Gwaggo ta shigo ta samu gefe ta zauna tana jiranmu gama wayar, kuma da alamun fuskarta tana so tai magana dani ne, Amma sam babu alamun zamu ƙare wayar, da ta gaji da jira tace. “yau naga ikon ubangiji, yo sai kice min Gwaggo tashi ki fita ba yanzu zan gama wayar nan ba”. Ina jin haka nace da Farhana. “ga Gwaggo ku gaisa”. Washe baki tayi kana ta ke faɗin,“ahh haka za ki ce min Farhana ce mutan kano”. Farhana ta gaishe da Gwaggo ta amsa mata, Gwaggo tace,“Farhana ki gaisar min da Hajiyarki sosai da sosai, insha'Allah idan na shigo kano zanzo har gida mu gaisa, eh kifa gaishe ta don nasan halinki sarai kamar yadda nasan na ƙawarki ato”. Ni dai karɓa nayi ina dariya Gwaggo tace nayi na gama Baba yana jirana. Jin haka yasa na katse kiran duk da ina son tambayar Farhana ya Yayana yake, kamar wadda na bata ajiyarsa, amma ban samu damar hakan ba, saboda Gwaggo ta kafa ta tsare. Ina fita na iske su Gwaggo da sauran matan gida duk a parlo ni ɗaya ne babu, gefe guda na samu inda Gwaggo ta ke bayan na gaisar dasu Baba da sauran Matan gida da Yaya Abba. Ko kallon inda Yaya Haidar yake banyi ba, Gwaggo ce kawai ta lura da haka. Gwaggo tace, “yauwa dama ba komi bane, Sabina ce zata je ganin dangin ta shi ne nace barin sanar daku, har tafiya ta tashi ace bamu sanar ba, ato idan damai sha’awar zuwa shima sai yaje yaga nasa dangin”. Gwaggo tana rufe baki Umma tace, “ah ai kuwa ba za’a rasa masu zuwa ba, su Zainab ma zasu je dama suna son zuwa dama ce basu samu ba”. Baba yace, “sunyi hutu ne?”. ɗan sosa ƙeya Umma tayi kafin tace, “ai wai da naga Gwaggo ce tace idan damai sha’awar zuwa shisa na faɗa haka”. Gwaggo tace, “ai sanin asali shisa kare yaci alli, yo ai nasan kwanan zancen, dama na faɗa ne kawai don naga hankalinku kuma sai gashi nagani. To ku babu ma mai zuwa ita da Abba kawai ya isa su tafi su lafiya insha'Allah, ato ni na gama magana kunga tafiyata”. Tana rufe magana bata jira cewar Baba da kowa ba ta ja hannuna muka bar wurin. Baba yayi ƴar dariya yace, “ni zan fita babu mai magana?”. Baba ya tambaya da buƙatar amsa. Shiru suka yi, alamu ya bashi babu mai magana suka yi mashi fatan alkhairi ya fita. Bayan komawar mu ɗaki kuwa Gwaggo ta shiga haɗa min kayana da duk wani abin buƙata ta kuma jaddada mani akan na riƙe azkar sosai kar nayi wasa da shi, ta kuma haɗa min magungunan da zan riƙa sha ina shafawa, duk da tasan bai yiwu lallai nayi amfani da shi ba. Na dubi Gwaggo nace, “naga Gwaggo sai haɗa kaya kike, kuma naga ba yau ne tafiyan ba sai gobe”. “yo ke banda ke da abinki, ai saboda karki manta wani abin, nifa idan zanyi tafiya tun ya rage sati nake kimtsa komi nawa, saboda gudun mantuwa, bare kuma Sahibina Allah sarki, Allah ka jaddada Rahma a gare shi". da Amin na amsa mata bayan na samu wuri na zauna. Gwaggo ta ɗakko wancan ta ɗakko wannan duk tana yi min bayanin wanda zan bama idan Allah yayi tafiyan nawa gobe. *Ɗaya Ɓangaren.* Kwance yake a makeken gadonsa, mai kyau da tsari, kayan alatu sun wadatu a ɗakin babu ƙarya, alaƙalami ba zai iya bayanin yadda ɗakin ya wadatu da tsaruwa ba sai ido in ya kalla. Sallama tayi fuskar ta ɗauke da murmushi. Ta samu gefe guda kan kujera a kusa da gadon ta zauna kana tace, “Bro barka da hutawa”. ɗan juyo da fuskarsa yayi gareta kana ya motsa bakin shi tamkar baya son magana fuskar shi babu yabo babu fallasa yace, “Barka dai Sis, dafatan an samu biyan buƙata ko?”. “umm an samu, amma sai an bani tukuici zan bayar don Mom haka tace”. ɗan murmushi yayi kafin ya furta,“me kike buƙata ki faɗi min, duk da nasan kinfi ƙarfin komi a wuri na, but tell me um”. “to shikenan, na yafe sai dai nayi fatan asha soyayya lafiya yasa kuma ita ne Aunty’nmu”. Amin ya amsa da shi kafin yace, “duk kinsa ni ƙaguwa, kin gagara bani na gani”. Ƴar ƙaramar takarda ta miƙa mashi, ya ɗakko wayan shi yayi dialing number, da ike yana Amfani da true caller a ta ke sunan ta ya bayyana, ba shiri wani ƙayatatcen murmushi ya samu muhalli a fuskarsa. “bari naje wurin Mom kafin nan ka gama”. da to ya amsata sannan ta fice a ɗakin. Sau biyu yana kira bata ɗauka ba sai ana uku ya yi sa’a ta ɗaga tare da yin sallama, sallamar da tayi barazar ɗauke numfashinsa cancakas, da gaggawa tare da nasarar ubangiji ya samu ya dawo gareta ya amsata yana faɗin. “Ina fatan ban katse ma Beauty baccin da ta ke mai cike da farin cikin ganina a cikinsa ba”. Jin kalmar Beauty yasa tuni na gano wanda ke magana, hakan yasa nace,“Barka da Safiya Sir, ina kwana, na tashi a bacci tun ɗazu, yasu Mom?”. “Masha Allah, Mom tana lafiya. How was your nyt?". "Alhmdl Sir". Na faɗa ina jin wani yanayi na jin nauyi a tare da ni. wucewar wasu sakanni na katse shirun daya ratsa nace,"amma Sir where do you got my number?". Murmushi naji yayi, bai kuma ce komai ba. Na kuma cewa, "Sir ina tambayanka ne fa, answer me please". murya a ɗan murɗe yace,"Do you think I will let you go without paying me for what you stole from me. Abune fa mai muhimmanci kika sace min, so I have to find you wherever you are, even if it's not on the phone. Ko da kuwa zan murɗa keke nane naje har birnin sin". Gabana ne ya buga ras, naji kamar an karza min magogin kaushi, tuni idona ya ciko, muryana a raunane nace,“nifa wallah ban maka sata ba, kuma ma naga nace ka faɗi min ko nawa ne Allah zan biyaka, amma ka daina cewa nayi maka sata, har ga Allah bana so ake dangantani da wannan kalmar”. ba tare da na bashi damar magana ba na karawa Gwaggo wayar a kunne ina faɗin,“Gwaggo ki sanar da shi ban taɓa sata ba, ya daina cewa na masa sata...". "shine muna malamin da yace kin masa sata?".Ta tambaye ni tana dafa katifa ta miƙe daga kwancen da ta ke. Kamin na bata amsa yace, "Gwaggo ina kwana". Naji ya faɗa cike da girmamawa. Gwaggo ta ƙura min ido, na ɗaga mata kaina alamar ehh, tayi gyaran murya sannan tace da shi,"Kai kuwa bawan Allah tsakani da Allah haka ake rayuwa, haka kawai saboda ɗaukar alhaki kace ɗiyar albarka tayi maka sata, to gaskiya ka sauya hali saboda wannan ba halin ƙwarai bane. Ni Ƴar jikalle tah ko tsinke bata taɓa sata ba, atoh sai kaje can ka nemi wanda yayi maka sata, idan ba haka ba hukuma ce zata raba ni da kai, ba zan lamunci ganin ka ɓatan sunan Jika ba, a hakan ma ƙazafin da kayi mata kaje kai da Allah, yo wannan ai kai fitinannen bawa ne". Daga inda Muhsin yake yay dariya mara sauti, yanzu ya gane Gwaggo Kakata ce ba mahaifiyata ba, ya buɗi baki zai magana Gwaggo ta tari numfashinsa da faɗin,"yo tsaya yanzu mene na kiranta a waya ma, ko wani sharrin zaka kuma ƙulla mata?". Nayi caraf nace, "Gwaggo haka fa yace ba zai taɓa barina ba duk inda na shiga, dole ne sai ya nemo ni ko da kuwa a keken guragunsa ne". tai wani zabura ta ƙara gyara zama kan tace,"au gurgu ne ma shi? Kai amma wannan anyi Fitinannan gurgu, ko da yake kunfi masu ƙafa iya shege, to ai sai ka fito sak a mutum kace mata kana barar na abinci ko na magani, sai a taimaka maka, amma ka wani fa-ke da tayi maka sata saboda rashin tsoron Allah. To na riga na gama gano ka taimako ne kake buƙata, sai kazo har gida ka roƙi Ubanta ya taimaka maka, ka daina bibiyar min ita da baƙin sharri, idan kuma ka ƙara cewa tai maka sata zanyi adu'ar kekenka ya wuntsula da kai a tsakiyar ruwa". Naji yay ƙaramar dariya, farinciki a tattare da shi yace, "Hajiya Gwaggo ai dama ni nafi so ta faɗa min inda gidan nasu yake, yanda idan iyayena ma suka zo Baba zaifi taimaka min". tana gutsurar goro tace, "aiko dai Auwalu zai taimaka maka sosai, kazo da kai da iyayen naka insha'Allahu duk wani kuka da kuka zo da shi zai share muku hawaye. Gidan ba wani wuya gare shi ba ai da kunzo...". Tunawa nayi da abinda yace min a wancan rana, Nai saurin saka hannu na rufe mata baki, duk na ruɗe nace,"Gwaggo karki faɗa masa inda gidan nan yake, wallah haka yace indai yazo sai ya faɗawa Baba na masa sata kuma ina murguɗawa manya baki". "iye". Ta faɗa tana jijjiga kai tare da cewa,"yo ai ce min za kiyi me haɗa husumiya ne shi kamar waccan shirgegiyar matar uban naki. To ɗan gurgu kana jina ba, laqad ja'akum baƙin sharrinka ya koma kanka. Kinga Sabina kashe min wannan wayar kar raina ya tugunzuma ya ɓaci nayi tattaki naje har inda yake". Na sauke mata wayar daga kunnenta ina dafe ƙirjina dake bugawa, ina jinsa kamin na kashe wayan yana roƙon Gwaggo don Allah ta masa kwatance, ni kuwa na kashe ina hararan wayar. Na lumshe ido na kwantar da kaina bisa pillow ina kallon sama, ina jin wayata na ringing naƙi ɗagawa, saboda nasan shine, sai dana ji ƙarar shigowan text tukunna na miƙa hannuna na ɗauka, na buɗe ina karantawa. _Please Beauty help me pick my call, na rantse za kisa naje na yiwa Mom kukan dana jima ban mata ba. My eyes are desperate to see your beautifull face, ba zan iya juriyan har sai an koma school kamin na kuma ganinki ba, i can't bear it anymore, dole sai kin biyani satar da kika mani zan ƙyaleki._ Ina gama karantawa na taɓe baki, na kuma murguɗawa saƙon nasa baki shima. Na jefar da wayar gefe na mayar da murfin idona na rufe, ina jin Gwaggo na min magana nai mata shiru. Gaba ɗaya tunanina da ɗokina ya tafi akan naje kano naga Yayana, idanuwana can see nothing fa-ce fuskarsa, haka zalika my ears can hear nothing but the sound of his golden voice wanda yake iri guda dana Proff, da ace zanje Kano na rasa Yayana tabbas zan dawo na kama Proff nace shine, saboda ban manta da wani kallo da Proff yayi min ba a wancan rana, sak kallon da Yayana yay min a ranar da nake bashi abinci a baki. Naja doguwar ajiyar zuciya na sauke, na miƙa hannu zan jawo pillow na rungume naji an ɗala min duka a bayan hannu, a zabure na miƙe naga Gwaggo na wurgan harara, na bo-ne fuska ina turo baki gaba sai fama ƙifta idanu nake. Yau rana ta farko da tace da ni, "mutum sai shegen turo baki gaba kamar shantu...in har ba ki daina wannan mugun abun da kowa ke ƙorafi akansa ba wataran sai jaɓa tayi miki kiss". na tuntsire da dariya sosai. nan ta kuma hau bambamin bata son wannan ƴr iskar dariya, Allah kuma ya rabani da sababinta a sanda ta jiyo motsi a parlo, ta fita da sauri tana faɗin,"ga Aliyu can ya shigo yi min ta'adi da sanyin asuba, yo ta'adi ai sata ne. wannan yaro dai da gani Unguwar Zoma bata gasa shi da kyau ba". [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(21)* Bayan Kwana biyu, Zaune nake kan plastic chair a balcony dake upstairs namu, ina karanta wani haɗaɗɗan novel mai ɗauƙe da wata iriyar soyayya mai burgewa, da kuma sawa kaji kana buƙatar kasancewa da saurayinka a lokacin, banma san sunan littafin ba sai da shafin ya yanke min, da sauri nayi scrolling back na duba sunan novel ɗin. *ƘADDARA TA RIGA FATA* naga an rubuta daga haziƙar marubuciyar nan mai suna Anty Nice, cikin sauri na Kunna da ta na buƙaci da a turo min sauran, babu ɓata lokaci kuwa sai ga Oum Ramadhan ta turo mani, godiya nayi mata sosai sannan na kashe datan naci gaba da karatuna, ban ɗau wani lokaci ba na kammala karanta shi, Soyayyan Hummy da Dr ta ƙayatar da ni, sosai littafin yayi daɗi ya kuma faɗakar, ba ƙaramin jinjinawa marubuciyar nayi ba. Daga nan kuma na ɗora da littafin Al'amari, tunda naci karo da page ɗin da ake zayyano kamannin Hammah Saddam na fara shiga wani yanayi, Gaba ɗaya yanayin kamannisa da ake lissafawa sai yake min kama da Yayana, Banbancin su ɗaya Yayana yafishi haske sosai, wani sanyayyan murmushi na sa ki ina ƙara gyara zaman karatuna, Saurin lumshe ido nayi a lokacin da nayi katari da wurin da Hammah Saddam ke nunawa Tasleem ɗinsa tsantsar so, Na jinginar da kaina bisa kujera ina daɗa lumshe ido ina ƙiyasto ni da Yayana. Ta ke kuma naji ruwan hawaye na cika min ido, kewar Yayana ta dakar min zuciya, ina shirin fashewa da kuka na jiyo ƙarar hayaniya a compound, tashi nayi na leƙa, su Aisha na hanga sun kewaye Inna Karima suna murnar zuwanta, tsallen murna na buga na wurgar da wayata akan gado na fice da gudu ina, "oyoyo Innah". Ina zuwa na ɗafe jikinta. "laaa kunga yarinya zata kada ni". Ta faɗa tana dafe jikin mota, Sakinta nayi ina dariya. Ita kuma ta bini da wani kallo tana taɓe baki, Kamar dai yanda na faɗa muku a baya, Inna Karima macece da Allah ya dasa mata zuciyar kushe, a hakan ma kallon da take mini tana taɓe baki neman makusa take a jikina, kai ni dai na godewa Allah da Gwaggo bata yo halinta ba, na basar kamar ban san tanayi ba, ina ƙara faɗaɗa fara'ar fuskata ina masu sannu da zuwa. Jakar hannunta na amsa, ina kallon Mardiyya a gefe sai wani shashshan ƙamshi ta ke, ko takanta banbi don ba shiri muke ba, na kalla yarinyar da suka zo tare, wanda na fahimci itane ƴar aikin da aka kawo mana, ina mata murmushi nace muje ciki ƴar ƙanwata, ina ta jin daɗi na sami abokiyar hira duk da ni bana zaman kaɗaici tunda ina da Gwaggo. Inna Karima ta yaba gidanmu sosai, ni dai hankalina na kan naji batun kwana nawa zasu yi. Ta kalla Gwaggo tace, "wai Matan gidan basa nan ne?". "suna nan mana". "amma naga babu wadda tazo ta gaida ni". "ni kaina da nake zaune da su ba gaida ni suke ba, gani dai uwar miji, basa ganina da girma wannan tarihin kin sani ba sai na ƙara ba ki ba, don haka kinga ni dai bana son magana don na san halinki, nima adu'a nake musu Allah ya shirya su". Abincin da Inna Karima keci ta tashi akai, ta fita compound tasa aka kira mata su Umma, tayi musu tatas wanda har dukanmu sai da muka ji dama bata zo ba, saboda yanda tasa Baba a gaba tana masa faɗa tana zaginsa, su kuwa kowacce haƙuri ta shiga bata don suna tsoronta, ita bata wasa kamar Gwaggo da ta ke ƴar barkwanci. Har dare Inna Karima bata bar masifa ba, Gwaggo dai bata ce mata komai ba, don dama idan tana masifa duk bakin Gwaggo mutuwa yake. mai aikinmu Iklima na kusa da ni a zaune, saboda ni bani da ƙyama, tunda suka zo nasa tayi wanka na bata kaya masu kyau ta saka, cikin lokaci kaɗan har mun fara sabawa da ita, yanzu haka ma kallo muke a wayata, Mardiyya na gefenmu tana waya da saurayinta, na bawa Iklima wayar nace taci gaba da kallon kamin na dawo. A parlo na sami Inna Karima tasa Baba gaba sai zazzage shi take akan yaƙi aurar dani, ya barmi sai kumbura nake ina jera kafaɗa da shi da matansa, ba zai aurar da ni ba sai karatun boko ya gama lalata ni tukunna, wannan kayan haushi da yawa yake. Shi dai Baba haƙuri yake bata yana kuma ƙoƙarin ganar da ita, amma kwata-kwata taƙi fahimta, har cewa ta ke da mahaifiyata nan ba zata taɓa zuba ido tana ganina a haka ba ban cika mace ba har yanzu, saboda ita tasan ƙimata kuma tana ƙaunata... "ni kuma da nake riƙonta ai kin san ba ƙaunarta nake ba". Gwaggo ta faɗa a ƙufule. "ni ba haka nake nufi ba Yaya, amma dai zuwa yanzu kam ya kamata ku gane yarinyar ta girma, kuna tare da ita amma kamar ba kwa ganinta". "yo ke da kike ganinta kuma kika gane ta gama haɓɓaka me zai hana ki aurar da ita wai, ni duk kinzo kin isheni da hayagaga baki sai warin goro yake. To ki sami damar yimin shiru tunda bake ce a gaba dani ba, da za ki sa ni a gaba kina min faɗa kamar wata uwata". Ta juya ga Baba tace, "kai Auwalu tashi ka tafi, ɗiyar albarka ce dai ba yanzu zan aurar da ita ba dan haka sai a bini da ido kawai. A jira har sai randa ta kawo min wanda yay male-male a zuciyarta tukunna". Baba ya miƙa ya fita bayan yay masu sai da safe, Gwaggo kuwa taci gaba da sababinta a yayinda Inna Karima taja baki ta tsuke, alamu dai taji haushin maganar da Gwaggo tayi mata. Gwaggo kam bata fasa maganarta ba, sai ta koma ma kamar bada Inna ta ke ba. "shi mutum bashi da shanka bare cinka amma duk yabi ya damu da zamanka a gidan ubanka. To ki faɗi kwanon shinkafarki nawa take ci sai a biyaki tunda kin gaji da ci da ita". "yo na kuma magana kice bakina na warin goro Yaya, gaskiya ce da kai ba'a son ka faɗa. Amma ita ai ba dutse bace da har zuwa yanzu zata ce ba wani abu dake tsikarinta". "yo Allah na tuba shekarun nata nawane gaba ɗaya, sha tara ne fa ta ke yanzu, girman kajin gona tayi shi yasa duk tabi ta tsone miki ido. Ga shi ita ba kazar ba ballantana kice za ki siya ki dafa kiyi mata cin yunwa, wannan luhu-luhun tsokar haka za ki ganta ki mayar da ƙwaɗayayyan yawunki". Dukansu haushin juna suke ji, Sai harar juna suke. Abin nasu yaso bani dariya, Na zauna kan kujera na ɓata fuska ina turo baki daka ganni kaga wadda ke cikin fushi. Inna Karima da baki bai mutuwa ƙara faɗa ta ke, "ji dan Allah yanda nono ya cika ƙirjin yarinya, komai yaji zamzam a halittarta amma an take gaskiya an Kama huɗubar bature. Ga sa'aninki nan a ƙauye duk sunyi aure, harda masu ƴaƴa Kin tsaya nan kina daka ta ubanki". Gwaggo dai ta taɓe baki, ni kuma na ƙara haɗe gira nace, "to wai Inna da kika damu da nawa ita Mardiyya da take jikarki mene yasa ita ba za ki sa mata ido ba". "au saboda ba ki da kunya ni kike faɗawa wannan maganar, yo ba ƙwamma ita bazawara ce ba, ke kuwa fa. Shekaru 19 kina ƙoƙarin dosar ashirin amma ba ki taɓa leƙan gidan miji ba. Ba tun yanzu ne nake tambayar yaushe ne za kiyi aure ba? Ganin sa'anninki duk sunyi aure, Amma ganin laifina ake ba'asan mutunci nake nema miki ba". abun yay min ciwo, ban san lokacin dana fara ce ma ta, "Addah Jummai, Inna Talatu, Gwaggo Ladi, Hajiyan Jos. Inna Sa'anninki da yawa duk sun jima a ƙabarburansu, mene yake faruwa dake ne? Ya akai ke shiru haka? Ya naki labarin tafiyar? Yaushe ne za ki mutu? me yasa aka zuba maki ido har yanzu ba ki mutu ba?". Ina dubanta naga tayi shiru, nace, "Inna tambayarki nake ki bani amsa". Nan ma shiru tayi min, na sake cewa, "To Innah Yanda mutuwa bata da lokaci haka ma aure, yanda mutuwa ba gasa bace hakama lokacin aure, yanda burin kowa Aljannah haka burin duk wani marar aure abokin rayuwa nagari. Yanda ba'a rubuta ma kowa lokacin mutuwarshi a goshin shi ba, hakama wasu ba'a rubuta musu rabon aure a rayuwarsu ba, kuma ba'a rubuta musu lokacin auransu ba a goshi. Ni kuma bana rasa mijin aure bane, ban shirya yi yanzu ba, ki bar ganin banda mashinshina. Don Allah Innah ki sakar min mara kiji da Mardiyya ita da zaman ɗaka kawai ta ke babu arabi babu boko". Ina kallon Gwaggo na dariya ƙasa-ƙasa, ni kuwa na miƙe nai wucewa ta ɗaki, ina jinta tana faɗin, "to aini da na shigo wannan daular niyyata na jima ina shan jar miya mai naman ɗawisu acikinta, ashe tafiyata dole ta kama gobe goben nan". Gwaggo tace da ita, "kofa mene ke kika ja ta gaya miki haka, akan me kuma za ki ji haushinta". Kwanan Innah biyu muka wuce kano, naji daɗi da bamu taho da Yaya Abba ba, a gidan Hajiya na sauka wadda ta haifi Mamana, tayi farincikin ganina sosai. Abinci kawai naci na miƙe na shiga wanka, ban ɓata lokaci ba a shirin da nake yi, nayi kwalliya mai kyau, hijab ɗina sai tashin ƙamshi yake na fito, Hajiya dake kishingiɗe a parlo ta dube ni tace,"ke kumburin burodi ina zuwa kuma daga saukarki? Ko abincin da kika ci fa bai gama tsarga miki ba". Ni kam bana son wannan sunan da Hajiya ke kiran da shi, da yake itama ƴar ayi ce irin Gwaggo, na ɓata rai ina cewa, "Hajiya na fa yi girman da ya kamata ki daina ce min kumburin burodi". "to Mama'nki ma har ta mutu ban daina ce mata kumburin burodi ba, kinga kema kuwa banga ranar daina faɗa miki ba tunda kinyo gado". Na turo baki gaba ina yin kamar zanyi kuka, ta kamo hannuna ta zaunar dani Saman cinyarta, ko nauyina ba ta ji. "haba jikar Hajiya da Gwaggo sarkin shagwaɓa, ƴar lelen Babanta, maida bakin naki kar ya tsaya a haka samari suce basa so, kinga yayi dogo da yawa sai kace payis". Ta faɗi hakan tana ɗan yimin cakulkuli, na ƙyalƙyale da dariya kamin na kuma cewa,"amma dai kin daina cemin Kumburin burodin ko?". Tace, "kema kin san ba zan iya ba, saboda duk sanda na tsokane ki da haka kina tuna min da marigayiya ne, komai naki sak na mahaifiyarki har wannan shagwaɓar. Itama idan nace kumburin burodi haka zatai ta aikin buga ƙafa tana cewa bata so, Babanta kuwa hake yake ce mata kazar gona, shi kam daya faɗa zata fashe da kuka sai ansha da ƙyar zata yi shiru, Sabina wallahi komai naki babu maraba da Halima". "Allah sarki Mamana Allah ya jiƙanta. Hajiya naso ace naga Mama ko da sau ɗaya ne, amma ko da yaushe sai dai na kalleta a hoto ina jin kamar na fito da ita tayi min magana". Ta goge min hawayen daya sakko tana cewa, "karki kuka mana kuma ki ɓata kwalliyar taki, ba gashi Allah ya bar miki mu ba. Ina za ki ne haka kamar wadda ta shirya gasar kyau?". "da gaske Hajiya nayi kyau?". "wallahi sosai ma kinyi kyau, tsab za kisa ɗa namiji tuntuɓe a hanya. amma ni kin san bana son fice-fice ina zuwa haka?". Ina roƙonta nace, "don Allah Hajiya yanzu zanje na dawo, gidansu Farhana zanje". Da ike itama tasan Farhana tace to saina dawo amma kar na jima. ina tsokanarta nace, "to Hajiya idan kinji shiru sai ki bini Abuja". Dariya kawai tayi ni kuma na fice, sai dana bari nayi nesa da gida kana na tari mai napep saboda kar Uncle Musbahu ya ganni, don naji yana shago yana ɗinki. Sharaɗa nace masa ya kaini, har inda Yayana yake zama ya sauke ni, na fito ina kallon wajen har ya fara sauyawa saboda yanda aka yiyyi gine-gine, shi kansa kangon da Yayana ke zama ciki har an fara sa masa dakin, waje ma anyi masa fulasta. Ƙafata tayi sanyi, ƙirjina na bugawa na ƙarasa ƙofar kangon, gaba ɗaya na dudduba banga alamar ƙyallin ko inuwar mutum ba. Tuni naji komai na duniya ya daina min daɗi, na shiga tsananin damuwa, ina taka ƙafa da ƙyar na ƙarasa wurin wani mai shago, sallama na masa ya amsa min, na tambayeshi don Allah ko yasan wani bawan Allah dake zama a kangon nan na kusa da shi. "wani ɗan shaye-shaye ko?". Ya tambaye ni. banji daɗin tambayar da yay min ba, domin da a hayyacina nake zan gaya masa babu daɗi, na ɗaga masa kai kawai. Yace, "Ayyah ai wannan ƴan sanda sun jima da yi mana maganinsa...". Bai ƙarasa ba na katse shi, "ban gane me kake nufi ba?". "ina nufin yana gidan maza, kusan wata shida da kamashi kenan". Nai ƙoƙarin tare kukan dake neman fito min nace, "a bisa wanne laifi aka kama shi?". Yana ƙulla madara a leda yace, "yo Hajiya irin waɗannan ai annoba ne a unguwa, hukuma tayi ram da su shine dai-dai". Ban iya cewa da shi komai ba na juya na fita da ƙafafuna da suka min nauyi, idanuwana na tsananta zubar hawaye, zafin da nake ji a zuciyata ba zai iya misaltuwa ba, ni ɗaya nasan tashin hankalin da nake ciki, saura kaɗan wani mai mashin ya bigeni naji an jawo ni, mutumin ya hauni da masifa ina tafiya ina tunanin banza zan haɗa accident. Sam ban san halin nake ciki ba sai a yanzu da yay maganar, na kalla inda nake tafiyar na kalleni tsakiyar hanya da ababen hawa ke wucewa. "kayi haƙuri don Allah". Ina faɗa ina ƙoƙarin barin wajen. "idan ba damuwa ki tsaya zanyi magana dake. Zan shiga wancan shagon naga kin fito kina kuka, na tambayi mai wurin yake gaya min wanda kike nema". Ni dai bance masa koma ba, sai dafe kaina da nayi wanda naji juwa na neman ɗibata ta zubar a ƙasa. Maganar da yay ne ta dawo dani hayyacina nayi saurin ɗagowa ina dubansa. "ya ce mashayin bakin bola kike nema?. Duk abinda ya faɗa miki gaskiya ne amma bai san da cewar an fito da shi ba. Sai dai ya bar wurin da yake zama, idan kika zaga bayan masallacin nan daga wajen wata bishiya za ki gansa zaune a wurin, yanzu muka fito daga masallaci tare da shi". Ban jira sauran maganarsa ba, haka Ko godiya ban tsaya yi masa ba, tuni na juya ina tafiya cikin sauri har na isa inda yay min kwatancen. Ina zuwa kuwa na hangi mutum zaune akan dutse ya juya baya, ban san lokacin da murmushin jin daɗi ya subce min ba, na ƙarasa wurinsa ƙafafuna na rawa, na tsaya a bayansa ina jin kamar na rungume shi saboda yanda nake jin wani farincikin a raina. "Yayana". Na kira sunansa ina mai jan harufan ta wani irin siga ba tare da nasan nayi hakan ba. shi da yake zaune yaji muryar da har mutuwarsa ba zai taɓa mantawa da ita ba, yay shiru yana jiran ƙara sauraron zaƙin muryar, ganin bai juyo ba hakan yasa na zaga gabansa cike da zumuɗin son ganin fuskarsa. Annashuwar farinciki na ƙara bayyana a saman fuskata na zube a gabansa, haƙorana duk a waje saboda na kasa ɓoye jin daɗina, sai dai yanayin da idona ya hau kansa komai nawa ya tsaya cak, hankalina yay ƙololuwar tashi, a jere na jefa masa tambayoyi baki na karkarwa a yayinda da ruwan hawaye ya cika min ido suna zuba. "Yayana mene haka nake gani a jikinka? Wannan bandage ɗin na mene? Aina ka sami ciwuka masu yawa haka? garin ya ya hakan ya faru da kai? wane yay maka hakan?". Nayi maganar gefen zuciyata na harbawa da tsananin zafi, a yayinda tsananin tausayinsa ya kanainaye ilahirin jinin jikina, na miƙa hannuna dake rawa zan kamo fuskarsa ya janye kansa. a hankali laɓensa na sama dana ƙasa suka tale suka buɗe wajen faɗin. "ina kika tafi watanni da yawa? me yasa kika daina zuwa inda nake? me yasa na daina ganinki? a haka kika fito da fuskarki waje jama'ar duniya suna kallonki? Ina niƙab ɗinki? Me yasa ba ki saka ba?". A wani irin yanayi tambayoyin nasa suka jefani, yanayin dana kasa gane mishi, na kasa jurewa kallon da yake min na sadda kaina ƙasa, nafi buƙatar daya amsa min nawa, ina ɗagowa naga ya kauda fuskarsa gefe, idonsa a lumshe, yana ƙoƙarin tashi ya bar wurin nayi saurin kamo hannunsa na maido shi ya zauna. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(22)* harufan bakina na fita a kakkarye nace da shi,"Don Allah Yayana". kalaman bakin suka fito acikin siga ta roƙo ina mai ƙare damƙe hannunsa. Cak ya tsaya ya dawo ya zauna, yana ta so ya ƙwace hannunsa daga riƙon dana masa amma na hana, kansa na kallon ƙasa yay shiru bai magana ba, damuwa na ƙara bijiro min na datsi shirun da cewan,"Yaya zuciyata matsewa takeyi, dan Allah ka faɗa min wannan ciwon fa?". ya ɗago ya sareni da ido, sannan ya buɗi baki yace,"ni me yasa ba za ki amsa min nawa ba?". "to aini na fara tambayanka". Yace, "idan har aka ɗora duka tambayoyin a bisa mizanin ma'auni, nawa ita tafi muhimmanci da cancantar amsawa sama da taki, duk da cewan tambayanki yafi yawa amma girman tawa zata rinjayeta. Na rantse miki idan har ba ki bani amsar dalilin da yasa kika fito babu niƙab ba, zan tashi na tafi, tafiyar da har abada ba za ki kuma ganina ba". Ban san lokacin dana haɗa yatsuna da nashi wuri ɗaya ba ina wasa da su, na fara magana ina cewa,"kamin mu bar gari nazo har sau huɗu bana samunka, har a ƙarshe na bar maka saƙo wanda idan ka gani zaka neme ni. ba haka kawai na daina zuwa inda kake ba, mun koma Abuja da zama ne sai yau na sami daman zuwa, kuma na bar niƙab ɗina a can shisa, ita kuma Hajiya bata da shi bare na amsa na saka. Yayana tunda na tafi kowanne rana a cikin tunanin halin da kake nake, haka zalika a cikin kowanne daƙiƙa na bugawan agogo jiran tsammanin kiran wayarka nake amma shiru. Yayana ina ka tafi a wancan lokaci? Me yasa na dawo na sameka a wannan halin?". idonsa na kallon gefe guda yace,"abubuwan da yawa...na farko anyiwa wata yarinya fyaɗe hr ta mutu shine aka ɗora alhakin hakan akaina, na jima kamin gaskiya ta bayyana, ashe Baban Yarinyar yana harkar ƙwayoyi sai suka sami matsala da yaransa shine suka ɗau fansar abunda yay musu akan yarinyar. bayan na fito da ƴan kwanaki aka sace yara anan anguwar, mutane suka ɗora min laifin da banji ba ban gani ba akan cewan ni na sacesu, bisa wannan zargin nasu yasa ƴan sanda suka kamani, nasha wuya sosai a wurinsu har naji inama na mutu na bar wannan rayuwar ƙuncin, a ranar da zamu wuce kotu ranar akaga yaran, sati ɗaya kenan da aka sakeni, na dawo duk inda naje na zauna domin samun mafaka sai an koreni, babu wanda ya tsauyawa halin buƙatar taimakon da nake ciki sai limamin wannan masallacin, shine ya kaini chemist aka bani kulawa". Tunda ya fara maganar nake kuka sosai, har ta kai ga na daina sauraron abinda yake cewa, hannu yasa ya dafa goshina ya ɗago fuskata da tayi shaɓe-shaɓe da ruwan hawaye. Ina kallo ya yagi ƙasan rigarsa yay min tsumman goge hawayena "kina so a kuma kamani ne?". Ya faɗa a yayin da yake gogen gefen idona wanda nake tunanin kwalli ne ya zazzago. Na shiga girgiza masa kai da sauri alamar a'a. "to ki bar kuka, kar mutane su ganki ace nayi miki wani abun, a ƙara kamani ayi min ɗaurin rai da rai". Babu shiri na tsayar da kukana, ina faɗin,"wallahi ba zan taɓa yafewa wanda yay maka wannan sharrin ba, wallahi ba zan taɓa yafewa wanda ya wahalar da kai ba, Allah ya bi maka hakkinka. Me yasa daka dawo baka kirani ba?". "ta ina zan kiraki?". "nafa aje maka letter da zan tafi, na san kuma har zuwa lokacin yana nan tunda babu wanda ke shiga sai kai, kuma nayi yanda ko da iska ba zai iya figansa ba bare ruwa ya lalata shi". Yay wani murmushi mai ciwo, damuwa na daɗa bayyana a tare da shi. "tunda na sanyo ƙafata cikin anguwar nan ake min ruwan duwatsu akan saina koma, da ƙyar wasu bayin Allah suka taimakeni. Ba daban ina da yaƙinin idanuwana zasu ƙara ganinki ba, da ba ki zo kin kuma samuna anan ba". Hannunsa dake cikin nawa ya daɗa matsewa ya damƙe, idanunsa a runtse ya shiga juyi da kansa yana faɗin. "tunda suka kamani, tunda suka sanya ƙafafuna a sasari, tunda suka jefani a ɗakin duhu, a kowanne bugun azabtarwa, a kowanne nau'in horo mai wahala, a duk wani bugu na zuciyata kece a raina, bana jin daɗin duniyar, har saina rufe idona na hasko ki aciki sannan nake samun sassauci. Don Allah kice min kina da alaƙa da ni, ki ce ke ɗin jinina ce, ki ce kin shigo rayuwata ne domin ki share min hawayena". Ya gama faɗin hakan yana mai jinginar da kansa jikin bishiya, ya kuma ƙara damƙe hannuna wanda har sai da jikina ya amsa, yana ƙara rumtse idonsa sosai. Nace da shi,"Yayana ba zan iya barinka a wannan halin ba, yau ɗin nazo tafiya da kai ne. Ba zan kuma barinka a cikin ƙangin rayuwa ba...daga yau insha'Allahu ka bar wannan gararin, dan zanyi maka gata a yayin da zan sanyaka cikin ahalina, zan tabbata ƙanwa a gareka a yayin da zaka tabbata Yaya a gareni ka kuma tabbata ɗa a wurin Babana, a inda zaka tabbata jika a wurin Gwaggona. Insha'Allahu lokacin yayewar baƙin cikinka yayi, haka kuma lokacin dawwamarka a farinciki yayi, ba zan kuma bari ka shiga damuwa ba har abada". Sai yanzu ne ya buɗe kyawawan idanunsa ya zuba su a cikin nawa. Ido cikin ido muke kallon juna, har sai da kwarjininsa ya kashe min ido tukunna nayi saurin kawar da idanuwana daga kallonsa. Na miƙe ina jan hannunsa akan ya tashi mu tafi. murya a ƙasan maƙoshi yace,"nan shi yafi dacewa da ni, idan kika tafi da ni ina za ki kaini?". "nan ba shine ya dace da kai ba. Kyakykyawan mazauni shi ya dace da kai, kaifa mutumin kirki ne, don girman Allah Yaya ka tashi mu tafi gidanmu, na rantse maka idan bamu tafi tare ba, ba zan bar cikin layin nan ba zakaji saƙon mutuwata, na tafi inda ba zaka kuma ganina ba sai a aljannah". Zumbur naga ya miƙe, ina riƙe da hannunsa muke tafiya kaman wani yarona, wanda nayi hakanne gudun kar ya tsere min, har sai da muka fito bakin layi na tari me napep kana na sake shi lokacin da muka shiga ciki. Muna tafe ina tunanin yanda zanyi da Yayana, Hajiya ba zata taɓa fuskantar wani zance da zan mata ba, don haka ya zame min dole na koma gida a yau. Na ɗauko waya na kira Baba yana ɗagawa nace,"Baba kana so na?". "Sabina babu sallama babu gaisuwa sai tambayar dake kin san amsarta". Na lumshe ido ina ƙara narke fuska nace,"Baba ni dai ka amsa min". Murmushi mai sauti yayi yace, "ina sonki sosai Sabina, duk cikin ƴaƴana bayan Abba nafi sonki na kuma fi ji dake". Maganan Babana yay min daɗi, na ƙara ce masa,"to Baba indai da gaske kana sona kayi min buking jirgi yanzu, zuwa anjima zan dawo gida". "ki dawo kuma? Wani abu ya faru ne?". Nace da shi,"a'a Baba babu abinda ya faru, kawai zan dawo ne na gaji da zaman". "a'a ban yarda dake ba ki dai faɗa min gaskiya, ko Hajiya tayi miki wani abu ne?". "ko ɗaya Baba, mun gama gaisawa da Hajiya kuma dama ai ita nazo gani, don Allah Baba ni dai a biya min kuɗin jirgi yanzu kujeran mutum biyu, yau nake son dawowa". "tom shikenan, Allah ya dawo min dake lapia". Kai tsaye wani private hospital muka wuce, ƙwararren likita na nema, aka ƙara treating ciwukan Yayana sosai, dan sai da aka sauya masa bandage, aka kuma lodo mana magunguna kamar me, banda allurorin daya sha. Bayan fitowanmu muka nufi resturant, ordering lafiyayyan abinci na sa aka mani wanda nasan Yayana zai san ehh yaci abincin daya amsa sunansa abinci. Gaba ya saka abinci ya kasa ci sai ido daya ƙura min, dana kalla baida niyyan ci na ɗauka spoon na kai bakinsa ina cewa, "oya haaa". Bai buɗe bakin ba sai neman sauke hannuna da yayi. Na ɗan tsuke fuska nace, "Yayana zafa kasha magani naka ne, ko baka so ciwonka ya warke da wuri?, to idan kai baka so ni ina so, plsss kaci abinci idan ba so kake nasa maka kuka ba ka rasa yanda zaka yi da ni, yanzu mutane suzo su tafi da kai a kuma sanyaka a cell". Na faɗi hakan ina kuma kai abincin bakinsa, ya dafa hannuna yana tayani kai cokalin bakinsa, haka naita bashi abincin har sai dana tabbata ya ƙoshi kana na ƙyale shi, na sauke kaina ƙasa ina ɓallo magani cike da jin nauyin kallon da yake min, na bashi magungunan duk daya dace yasha yanzu, sannan muka bar wurin muka wuce wani boutique na kayan maza. Kayan maza nake ta ɗauka sama da kala nawa, duka ƴan kanti ne kowanne haɗe da takalminsa, duk wanda na ɗauka saina kara ajikinsa don tabbatar da cewan zai masa, kuma duk wanda zan gwada mashi sai ya dace da shi, hakan yasa na ƙara jin ƙananan kaya sun kuma shiga raina, domin ni ina son naga namiji nasa ƙanan kaya amma na mutumci. Shi dai bina da ido kawai yake har na kammala na kuma riƙo hannunsa muka fito, kansa na kalla wanda gashinsa ke buƙatar aski, amma saboda ciwon dake goshinsa babu damar yi. Ina kallon Hajiya nata kirana naƙi ɗagawa, na kuma taran mota muka wuce kasuwan kwari, nan ma manyan shaddojiji na saya, yadi da boyel da huluna. Muna fitowa daga kasuwan naga kiran Baba, ina ɗagawa yace da ni yasa abokinsa ya kammala komai, bakwai na dare jirgi zai tashi, ina murna nayi masa godiya, dama cikin tunanin inda zamu wuce yanzu nake. Ko rabin awa bamu yi ba a airpot jirginmu ya tashi, cikin ƙanƙanen lokaci sai gamu mun sauka a abuja, minti biyu da isowanmu Yaya Abba yazo ɗaukana. Sai yanzu ƙirjina ya hau bugu, to waima mene zance idan na kai masu shi? ta ina zan fara bayani? lallai fa nayi wawta da yawa, ko Gwaggo da nake sa ran zata fahimce ni to zan sha gwagwarmaya kamin ta aminta da buƙatar da zani da ita. Tsaye nayi na kasa ƙarasawa gaban motar, na ɗago na kalla Yayana, hannunsa da nake riƙe da shi na saki, maganganun bakina na neman rasasu nake. "Karfa naja maki matsala a gida". Nace, "babu wani matsala ka jirani anan bari na dawo". ko dana isa wurin Yaya Abba da ƙyar nasha kansa ya fahimceni, shima don yana da tausayi ne kuma mutum ne mai son yin taimako, ba komai na faɗa masa ba, hasalima ce masa nayi a yaune na fara ganinsa. Baya Yayana ya shiga ni kuma na shiga gaba, su kaima juna musabaha, naji daɗin hakan, muna shiga gida muka tarar da Yaya Haidar shima ya dawo, kallo kawai ya bimu da shi ya amsa key ɗin part nasu wurin Yaya Abba ya wuce. Na kalla Yaya Abba nace masa, "ga wannan kayan na saya masa, ka ajiye a wurinka kamin Allah yasa muji amincewan su Baba". Ya amsa ya wuce ciki bayan yacewa Yayana yaji tsoron Allah ya faɗi asalin tarihin rayuwarsa karya ɓoye komai. A parlo nayi masa masauki, na wuce ɗakin Gwaggo domin kiranta, sai na tarar bata nan, na fito zan duba kitchen saina kalleta tsaye tayi turus tana kallon Yayana dake zaune kan kujera kansa na ƙasa baima san da zuwan nata ba. Zuwa nayi na rungumeta tare da fashewa da kuka, nan ta ke hankalinta ya tashi maganar dake bakinta ta mutu. A ruɗe ta hau tambayana mene ya faru, ni dai shiru na mata ina ci gaba da kukana, sai da ta tsawatar min kana na ɗago ina kama hannayenta na shiga roƙonta. "Gwaggo nah kene kika ce min duk wanda ya taimaki wani shima Allah zai taimake shi, kika ce mana mu taimakin mutumin da yake cikin tsaka mai wuya domin Allah yana son masu taimako...". "ke ni naji duk, ban son kuma wani bayanin, idan har ba za ki mani shiru da wannan kukan naki ba, kukan zan saurara ko kuma bayanin". Nai shiru ina goge fuskana. Tace, "to mene dama?". Na kama hannunta zuwa kujera ta zauna ni kuma na durƙusa a gabanta nace. "Gwaggo baya da gatan kowa sai na Allah, ko iyayensa bai taɓa sa ni ba, shine wanda na ba ki labari kika ce na fita sha'aninsa ko ki saɓa min, wallahi wallahi Gwaggo ki yarda dani shi ɗin mutumin kirki ne, jarrabar rayuwa ce ta jefa shi cikin wannan mummunar rayuwar ta shaye-shaye, Sai dai nasan ba za ki taɓa yarda dani ba sai idan kinji daga bakinsa, don Allah Gwaggo kiji tausayinsa ki taimaka masa kamar yanda muma Allah ya taimakemu ya daɗa rufa mana asiri, ina so naga ya fita daga wannan halin kuma kema nasan za ki so hakan". ta sauke ajiyar zuciya, ta kalle shi wanda tuni ya sauko daga kan kujera ya durƙusa a ƙasa. "tashi ka koma ka zauna". tace da shi tana dubansa da tausayawa, don jikinta yay sanyi da kallon yanayinsa da tayi. ta kalle ni tace, "Sabina ba wai ina ƙin ta taki bane, a'a ina tsoron yanda halin wannan rayuwar ta koma. za ki kalla mutum abin tausayi har kiyi masa kuka ki taimaka masa amma ƙarshe yazo ya cuceka, yaci amanarka, kuma kinga ke macece ina tsoron abinda zaije ya biyo baya, ba kowa ne kake yarda da shi ba yanzu. Kar muzo mu taimake shi yaci amanarmu daga baya". Sannan ta kalle shi tace, "bawan Allah tsakanin ka da Allah har zuciyarka baka da wata mummunar manufa, baka da wani ƙuduri na cutar da wannan yarinya dake tausayinka?". "Gwaggo zuciyata tsarkakkiya ce, bani da fatan cutar da wani a rayuwata". "to shikenan Allah yasa da gaske kake, ina son dukkan abinda Sabina ke so, dan haka zamu taimaka maka da iya abinda ta buƙata, sai dai bazan fasa ce maka kaji tsoron Allah ba. Bari mahaifinta yazo". "na gode Gwaggo Allah ya saka da alkhairi". Wayyo Allah nah wani sanyin daɗi naji ya baibaye ni. tace da ni, "kinje kin gudo ko. Bamu jima da gama waya da Hajiya ba tace za ki sani karki kuma zuwar mata gida. Kuma kayanki bayar da su zata yi, karta soma ganin koɗaɗɗiyar ƙafarki da sunan ɗaukan kaya". Dariya kawai nayi bance komai ba, tace naje na zubowa Yayana abinci, na miƙe naje na kawo masa abin sanyawa a baki, ina duƙawa zan aje masa yace,"na gode amma ki koma da shi, a ƙoshe nake da wanda kika ciyar dani ɗazu". Zuwan Baba Gwaggo ta zayyane masa komai. Baba ya numfasa yace da shi, "bawan Allah ka duba girman Allah ka faɗa mana wane kai". Ina kallon Yayana yay saurin rufe ido, kuma da alama tambayar ta Baba ta jefasa a wani yanayi na baƙinciki, ya buɗi baki muryar na fita da ainihin damuwar dake ransa yace,"wanene ni? Da ace nasan wanene ni da ban kasance a cikin wannan rayuwar ba, wallahi Baba ban san asalina ba. Abinda kawai na sa ni shine na taso a hannun wasu bayin Allah har na tsawon shekara biyu, suma kuma sun tsince ni ne a bola lokacin ba zan wuce shekaru huɗu ba a duniya a cewarsu. Amma mene asalina? daga ina nake? wanne gari? mene asalin sunana dana iyayena? ina zan bi in neme su? ina zan dosa? duk ban sa ni ba. Wallah summa tallahi bani da masaniyar komai a ga me da tarihin rayuwata". Ya faɗi hakan yana kuka. Baba Yace, "to su ina waɗanda suka tsinceka ɗin?". "sun gaji da riƙona shi yasa suka koreni daga garesu saboda mutane na zargin cewar ƴarsu ce tayi cikin shege. tun ban gama wayo ba nake yawo kwararo², idan na samu abinci naci idan ban samu ba hakan zan kwana da yunwa, banda matsuguni da makwanci sai kanguna, sai dai ina zuwa makarantar almajirai a duk garin dana tsinci kaina a haka har nayi sauka, sai dai duk inda na shiga jama'a ƙyamata suke suna hantarata. sigari na fara shanta ne saboda samun sauƙin abunda ke damuna, amma ni ɗin ba mutumin banza ba ne". Yanzu na ƙara jin tausayinsa ya kamani, su Gwaggo ma hakan take a gare su, Baba yace,"haƙiƙa duk wanda yaji labarinka dole ya taimaka maka in har yana da damar hakan. To ka kwantar da hankalinka, munyi maka alƙawarin zamu taimake ka mu share maka hawaye ka fita daga rayuwar ƙuncin da kake ciki, zan kuma maidaka tamkar ɗan dana haifa da cikina. Ina fatan ba zaka taɓa cin amanarmu ba". Furucin Baba ya sa ni shauƙi a ruhina ba kaɗan ba, ta yanda fuskata ta gaza ɓoye farincikin da nake ciki. "Allah yay miki albarka Sabina, lallai ke ɗin kina zuciya mai kyau tunda har kika yi tunanin taimako irin haka, tabbas nayi dacen ƴa ta gari. Kina da halin kirki da mutunci kamar mahaifiyarki". nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsun ƙafata ina jin daɗin adu'ar Baba da kuma yabona. Yayana na zubar hawaye yake yiwa Baba godiya, nima kuma yake ƙara gode min. Da wannan ya samu kyakykyawan matsuguni a cikin gidanmu, kamar yanda aka bawa Yaya Abba part nasa haka shima aka mallaka masa nasa part ɗin wanda dama shi ɗaya ne ya rage a gidan, da har su Umma na zargin Baba da munafurtarsu yake aure ne zai ƙara, to yanzu da aka bashi sai hankalinsu ya kwanta. Kowa na gidanmu Yaya yake ce masa har Baba da Gwaggo, kuma naci sa'ar ƙannena akansa. Sun zama kamar tagwaye shi da Yaya Abba, kuma duk sanda Baba zai fita office da shi yake fita, haka duk saturday and sunday yana zuwa makaranta mai suna Comprehensive collage, har mota Baba ya bashi, haka ma duk dare su kanyi zaman karatu shi da Yaya Abba don babu girman kai a tare da shi. Bayan kwana biyu na fito ɗauke da flask ɗin abinci zan kaima Yayana ɗakinsa, Ina shiga parlonsa na lumshe idanuwana ina shaƙar daddaɗan ƙamshin turaren dake tashi aciki, na lura Yayana dai ma'abocin son ƙamshi ne. Kamin na kai ga gama shaƙar ƙamshin tuni wani mugun warin taba ya dakar min hanci, nayi saurin buɗe idona nasa hannu ina toshe hancina dan ƙiris na kwara amai. Raina a ɓace na wuce cikin ɗakinsa, zaune na hangeshi daga can ƙuryan gado yana zuƙar abarsa hankali kwance. idan da abinda ke sa zuciyata ɗaci na tsince shi a irin wannan yanayi, nafi minti biyu tsaye ina masa wani duba, baima san da zuwan nawa ba, zuciyata naji tayi zafi. plastic chair na ɗauka naje gabansa na ajiye, sannan na ɗauko kwalin sigarin daya ajiye saman table na ɗauka guda biyu, tukunna na dawo kan kujeran na zauna, ƙafa na ɗora ɗaya kan ɗaya ina girgizawa, ashana na kunnawa sigarin, duk wannan abin da nake ina kallonsa ta gefen ido yana kallona, irin kallon kissima abubuwa da dama a rai. Zuciyata na lugude na rufe idona na kai sigarin bakina ina ƙoƙarin zuƙa, da mugun hanzari ya miƙe daga zaunen da yake ya warceta a hannuna. tsawa ya doka min wadda tasa ni firgita, yana huci yake cewa, "ke ba ki da hankali ne, kinsan me kike ƙoƙarin aikatawa kuwa?". Ya faɗi hakan ransa a ɓace yana kafe ni da jajayen idanunsa da suka yi jawur. tuni idona ya ciko da ruwan hawaye har yay nasarar gangarowa saman fuskata, na zube gwiwoyina gabansa hawayena na ƙara tsananta gudu. "don Allah Yayana ka bani nasha ko nima na samu sauƙin abinda nake ji a zuciyata. Please ka bani abata nasha damuwata ta yaye, wallahi ina jin zuciyata na min zafi ne". "tashi ki bar ɗakin nan bana son rigima". Ba tare dana miƙe ba nace,"ba zan fita har sai ka bani maganin damuwata nasha, please ka bani a bata, ko kai dana zo na sameka kana sha na hanaka ne? to kuma sai kaine zaka min baƙincikin maganin matsalata".Na faɗi hakan ina ɗaga sanyayyiyar muryata. Shima gwiwoyinsa ya zube a gabana, ya runtse ido yana ajiyar zuciya, sannan ya miƙo min sigarin still idonsa a rufe kansa kuma a ƙasa a sunkuye. nasa hannu na amsa, ina karɓa ne ya buɗe idonsa, ganin da gaske shan zanyi yay saurin miƙo hannu zai kuma ƙwacewa, da sauri na ɓoyeta a bayana ina turo baki gaba. *Gwarimpa, Abuja.* ƙarfe tara da rabi na safe, kamar yanda tsarin gidan yake gaba ɗayansu ake haɗuwa a parlo idan za'aci abinci, amma idan Daddy na gari kenan. yanzu ma hakan ta ke, ba ki ɗayansu a dining, Mami da iyalanta, haka ma Mom da nata iyalin sai Anie dake zaune itama, Muhsin ne kawai babu. Daddy yay gyaran murya kamin yace, "lafiya Muhsin bai fito ba har yanzu? ko bai tashi bane?". "ya tashi, na barshi yana wanka ne, ban sa ni ba ko ya fito yanzu". cewar Muhsina. Daddy ya tashi ya wuce zuwa ɗakinsa, yana shiga ya gansa yana kokawan ciro riga a wadrobe, ya ƙarasa da sauri ya riƙe shi dan yana gab da faɗowa daga kekensa, rigar ya ciro masa ya saka masa, yana shafa fuskarsa yace,"me yasa baka kira wani ba?". da damuwa fal tare da shi yace,"Daddy ina so na fara sabarwa kaina da irin wannan ɗawainiyar, Muhsina zata yi aure soon idan Allah ya bata miji...". sai kuma yay shiru bai kuma cewa komai ba. Daddy ya sauke ajiyar zuciya cike da tausayin ɗan nasa, shima bai ce komai ba ya tura shi suka fita a ɗakin. kowa abincinsa yake ci baka jin ƙaran komi saina spoons, ana cikin ci ne Mami taja tsaki ta miƙe ta bar wurin, Abid ya mara ma ta baya, babu wanda yay magana bayan bin bayansu da kallo sai kuma girgirza kai. Khaleesat gaba ɗaya ta fara rikicewa domin wannan tashin da Mami tayi idan har bata bisu ba tasan sauran, ga shi jazaman ta miƙe sai Daddy yay ma ta magana, kuma zaice itama ta fara ɗaukan mugun halinsu ne. abincin ta dakata da ci, sai juya spoon ɗin ta ke, duk abinda ta ke Mom na lura da ita, bayan ta sauke numfashi tace, "Khaleesat". _innalillahi wa'inna ilaihi waji'un._ shine abinda Khaleesat ta ambata a ranta tare da jin faɗuwar gaba. tun ɗazu ta ke adu'ar Allah yasa kar Mom tayi ma ta magana, Mom ta kuma kiran sunanta amma bata amsa ba sai sunkuyar da kanta da tayi, ta rasa wannan wacce iriyar rayuwa ce da mahaifiyarsu ta ɗaukar ma kanta, ita kam wannan dokar da ta kafa ma ta tayi mata tsauri, Mom ta wuce gban komai, saboda macece mai mutunci. doka tsawar Daddy yay dai-dai da kiran sunanta da Mom ta kuma yi a karo na uku. cikin faɗa Daddy ke cewa, "ke dan ubaki ba ki ji Mom ɗinku na maki magana bane kika ma ta banza, ko kema kin fara bin sahun uwar ta ki ne. to ni ba zan ɗauki wannan shirmen acikin gidana ba kinjini ko. idan kina so mu shirya kiyi abunda nake so idan kuma ba haka ba babu ruwana dake". muryarta a sarƙe tace, "kayi haƙuri Daddy". shine abinda tace da shi hawaye na sakko ma ta. "ba ni za ki bawa haƙuri ba". jin abinda yace sai ta juya saitin Mom sai dai ta kasa yi ma ta magana haka kuma ta kasa kallonta sai hawaye da take saukarwa. hakan yasa Mom ta fara fahimtar wani abu, dan haka ta dafata tana faɗin, "Maminki ta hanaki yimin magana ko?". ta ƙara yin ƙasa da kanta, duk tabi ta dabarbarce ta rasa abin cewa. "kar ki damu Khaleesat kinji, ki taiwa mahaifiyarki adu'a domin abunda ta ke buƙata kenan". kai kawai ta iya jijjigawa ba tare da tace komai ba. Anie na gefe tace, "Allah dai ya kyauta halin wannan Mata, ni na rasa randa zata yi hankali wallahi". ran Daddy a ɓace ya miƙe ya bar wurin yana cewa Khaleesat ta biyo shi. Khaleesat na gaba yana biye da ita a bayansa, tana kuwa yin sallama parlo Mami ta damƙo wuyanta ta fara sauke ma ta ruwan bala'i. "saketa". Daddy daya shigo ya ce da ita a tsawace. sakinta tayi ta kama ƙugu tana faman cika tana batsewa sai hure huren hanci ta ke. shi kuma yaci gaba da magana a zafafe,"wai ke Na'ima me yasa a rayuwarki sam ba ki son zaman lafiya ne. yanzu abu da kika aikata a tunaninki dacewa ne?...". ai bat bari ya ƙarasa ba cikin hargowa yace,"to me nayi kuma ni ƴar gidan laifi, ni da aka tsana ake ɗora min laifi ko da yaushe". yay ƙaramin tsaki yace, "kinji matsalar taki ai, babu wanda ya tsaneki a gidan nan sai dai kowa ya tsani halinki, wannan ban zan halin naki shine ba'a so...yanzu kawai ki kama sakin tsaki a gaban babbar mace, fisabillahi wannan ɗabi'a ce mai kyau?". ta taɓe baki ta juya masa baya tana harare harare. "to ita ɗin uwa tace da ba zanyi tsaki a gabanta ba. kaga ni fa Alhaji na gaji da wannan takurawarka akan waccan baƙar matar taka, akan abinda bai kai ya kawo ba bini-bini sai kazo ka kama sauke min buhun masifa, to ni na gaji, na gaji gaskiya". ido kawai ya bita da shi yana kallonta kamin yace, "to ita kuma Khaleesat da kika hanata kula Mom ɗin nasu mene dalili?". "saboda ba ita ta haifeta ba, ba kuma ta tayani naƙudarta ba". "amma aini ubanta ne ko, kuma na isa da ƴata ko". ya kalla Khaleesat yace, "ke kije ki tattaro duk kayanki ki koma wurin Fa'iƙa da zama har sai randa na ba ki umarnin barin wajenta kinji ko". Ta ke kuwa Mami ta lailayo wata ashar ta yarfa sannan tace, "wallahi ba zai yiwu ba. ba'a isa an maida ni ɓora ba acikin wannan gida. a rasa inda za'a kai min ƴa sai wurin kishiya saboda ba'a sona ba'a ƙaunata. tun wuri Alhaji ka sauya shawara ko kuma wallahi na ɗaga hankalin kowa a cikin gidan nan". yay guntun murmushi da takaici sannan yace,"kije gidanku sai ki ɗaga hankalin kowa acan...ai tunda har yanzu kika gagara hankali to tabbas baki da ranar da hankali, kin girma amma sam baki san abunda ya dace ba. to ki bar min gida na ba ki hutu". "mtswww". taja tsaki da ƙarfin daya doki kunnuwansu. "to sai me da hutunka dama. ko baka faɗa ba dama zan tafi, abunda kawai nake so ka sa ni shine baka isa ka kaimin ƴata wurin kishiya ba, ehh wallahi kayi kaɗan". Daddy yay mata wani kallon banza kamin yace,"ba ina nufin na ba ki hutu bane. kije na sake ki saki guda". ya kalla Khaleesat yace, "wuce muje". ya bar Mami anan da ife-ife tana zage-zage kamar mahaukaciya sabuwar kamu. _😅Masu cewa maganar Gwaggo yayi yawa hakana zakuyi haƙuri, dan Kakata nake tunawa in akazo babin Gwaggo, mu ma tamu Kakar idan ta fara sababi sai mun matseta Babban Yaya ya juye mata coflin a maƙoshi tukunna muke samun salama😅, so ku barni nake tunawa da Marigayiyata._ [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(23)* cikin ɗagin murya yace da ni. "ba za ki bani ba?". nima na cukule ina kauda fuska nace, "ehh ai kaima ga taka can kaje ka ɗauka ka ƙarasa sha, idan kuma ka ƙoshi da itane sai ka ɗauka wani sabo a kwali ai akwai da yawa". Na faɗi hakan ina fito da ita zan kuma kaiwa bakina, cikin amon muryarsa nan mai dadi ya dakatar dani. "don girman Allah karda kiyi gangancin sha, wallahi Allah bata dace dake ba, babu abinda takeyi fa ce ƙara damuwa amma bata maganin komai...". na saki wani yalwataccen murmushi da sautinsa ya amsa acikin ɗakin. sai ya ɗago yana kallona da kallo irin na mamaki. na ɗaga masa gira nace,"Yayana wai ni zaka ma wayo ko, saboda karna sha zaka ce min haka, to naƙi wayon sai nasha nima naji irin daɗin da kake ji acikinta har yasa kake min rowa". Kasaƙe yay yana dubana yayinda yake jin wani abu ga me dani na ƙara ɗarsuwa a zuciyarsa. sai ya kulle idonsa ya wani fizgi numfashi. "na rantse ba wayo ne nake miki ba. Da gaske nake miki bata maganin komai kuma wallahi bata dace...". Bai ƙarasa ba nayi saurin sanya yatsana a leɓensa alaman yay shiru. "Yayana". Na kira sunansa kiran daya ji har ƙwaƙwalwarsa, ya zuba min ido kamar yanda na zuba masa idanuna da suka taru da ruwa. "Yayana idan har wannan abar bata dace da ni ba to na rantse da Allah kaima bata dace da kai ba, saboda mutumin kirki baya shanta, mutumin da yake jin tsoron Allah baya shanta. idan har kana son lafiyarka ba zaka shata ba, idan har kana so damuwarka ta yaye ba zaka sha ba sai dai ka ɗauka maganin damuwa kankat Al-qur'ani me girma ka karanta, wannan shine hanyar da ma'aiki ya koyar damu, ba wai mu ɗauka abinda mun san zai cutar damu ba don magance damuwarmu, ita ɗin fa haramun ce na faɗa maka haramunce mene yasa ba zaka haƙura da ita ba?". Bayan na numfasa naci gaba da cewa,"haƙiƙa ba zan hanaka damuwa ba amma ba zan bar damuwa ta dameka ba Yayana, amma ina so ka fahimci cewar ƙaddararka ce a haka domin tuni Allah ya rubuta hakan zai faru da kai, dole ne kayi imani da ƙaddararka muddin kana son cika mumini na ƙwarai. A baya na faɗa maka bayan imani da ƙaddara akwai haƙuri, Yayana kayi haƙuri da yanda ka sami rayuwa, Allah da kansa yake cewa ana cikawa masu haƙuri ladansu ba tare da ƙididdiga ba. Yayana shaye-shaye babban zunubi ne mai girma ya kamata ka nisance shi, musamman abinda zai kawar da hankali ko kuma yasa maye, Allah ya mana umarnin mu guji kayan maye zamu rabauta, da kansa acikin littafinsa mai girma ya ambaci kayan maye da aikin shaiɗan. Ka sani lallai fa aikata saɓo yana hana arziƙi ya kuma gusar da ni'ima da albarkar dukiya. Don girman Allah Yayana kayi haƙuri da ƙaddarar da ta sameka, ka bar shan abinda yake haramun". Na faɗa hawaye na sakko min. Ganin yanda nake hawaye gaba ɗaya sai yaji ya ƙara shiga damuwa, ya rumtse idonsa ya buɗe sau uku a lokaci guda. "don Allah ki bar kuka bana son zubar hawayenki". Muryana na rawa nace,"wallahi Yayana wannan hawayen ba zasu taɓa daina zuba ba har sai randa ka rabu da wannan haramtacciyar abar. Na rantse maka idan har zaka dinga shanta to ko da yaushe hawayena zai dinƙa zuba a ƙasa ne. ka faɗa min a yanzu mene ka nema ka rasa da har ba zaka iya rabuwa da ita ba? Ka faɗa min ko mene shi na maka alƙawarin samar maka shi ko don ka bar cutar da kanka in har baifi ƙarfina ba. ko kuma Baba ya gaza yi maka ne?, Adu'a fa itace maganin damuwarka ba wannan muguwar abar ba". na numfasa na goge hawayena sannan nace," *ALLAHUMMA INNI ABDUKA, IBN ABDUKA, WABNI AMATIKA, NASIYATI BIYADIKA, MADIN FIHA HUKMUKA, ADLUN FIHA ƘADA'UK. AS'ALUKA BI KULLI MIN HUWA LAKA, SAMMAITA BIHI NAFSAK, AU ALLAMTAHU AHDAN MIN KAL'IK, AU ANZALTAHU FI KITABIK, AU ISTA'ASARTA BIHI FIL ILMI GAIBI INDAK, AN TAJA'ALIL QUR'ANA AZIMA RABI'A ƘULUBINA, WA NURA SUDURINA, WAJALA'A AHZANINA, WA ZAHABA HUMIMINA WARMUMINA*, wannan adu'ar itace Annabi ya koyar damu, kuma yace in har ka karanta Allah zai tafiyar maka da damuwarka ya kuma musanya maka da farinciki a maimakon damuwar. Don Allah Yayana kafi ƙarfin zuciyarka ta hanyar hanata abinda take so in har na saɓon Allah ne". abunda nake gani a ƙwayar idonsa dabanne, wani abu dake haskawa yana motsawa tare da zuciyata. motsin yatsunsa kawai nake iya gani a wannan lokacin, kuma kamin ƙifatawar idanuwana sai ganinsa nai ajikina, ya rungumeta tsam, kuma duk jarumtar namiji, duk yanda yaso ya hana wannan ruwan hawayen zuba ya kasa, sai kawai ya fashe da kuka yana daɗa matseni a sanda yake cewa. "haƙiƙa ke ɗin kina da baiwar da ba ki san kina da ita ba, iliminki da kyawun halinki sun dace dake, ki godema Allah da wannan baiwar da yayi miki. na rantse miki daga yau na barta, na rantse ba zan kuma sha ba tunda ba kya so. na barta har abada. Nima ban san lokacin da nake sha ba, baƙincikin ta yanda aka sa me ni shi yake jefani cikin wannan hali, iyayena basu kyauta min ba, Amma wallahi nayi miki alƙawarin daga yau ba za ki kuma ganina da ita ba har mutuwa, kin riga kin gama yi min gatan da duk abinda kika ce a gareni zanbi umarninsa". Jikina na rawa na raba shi da jikina. "Yayana ba don ni nake so ka daina ba, nafi so ka daina don Allah". Murmushin daya ƙawata fuskarsa ya sa ki yace, "zan daina don Allah kuma zan daina don ke". Ya faɗi hakan yana bani hanky na goge hawayena. Ina kallo ya tattara sigarin ya zuba a baƙar leda, yana cewa da ni,"kin gani ma na kwashe su duka, Yanzu zanje na zubar a shara". Ni dai tsaye na miƙe ina kallonsa, yellow t-shirt da black jeans ɗin daya sa sun masa matuƙar kyau, ya juyowa muka haɗa ido nayi saurin rufe idona. Dab dani naji ya tsaya, yasa hannu yana shafa kumatuna yace, "ƙanwar Yayanta bayan wannan akwai wani abun da kike so na daina?". Na buɗe lumsassun idanuna ina kallonsa, ya ɗaga gira yana waro min ido yace, "ehen yi magana mana". ina murmushi na buɗe masa tafin hannuna, ya kalla ya kalleni, na ɗaga masa gira kaɗan ina cewa, "duk dana yarda da kai amma ina so ka mani alƙawari, saboda idan harna kuma ka maka kana shan sigari wallahi nima sai na sha". Ya ɗora nasa tafin hannun kan nawa yana cewa, "na maki alƙawari". Na sauke numfashi nace,"to ka bari ka fara cin abinci tukunna kamin ka fita yarda wancan abun. abincin yana parlo na ajiye maka, Gwaggo tace idan ka gama tana nemanka". Fita nayi na barsa yana zuba abinci, zan shiga side ɗinmu Yaya Haidar ya kirani. Na ƙarasa wurinsa nace gani, fuskarsa a murtuke yace,"me ya kai ki side ɗin wancan ɗan tsintuwar?". Na ɗago da nuna rashin fahimtar maganar tasa. Cikin ɗagin murya ya kuma ce min, "ba ina miki magana bane". Ya miƙo hannu zai buge min baki yana cewa, "za ki maida bakin ko saina fasa shi". "to aini ban gane wa kake nufi ba". "ni za ki rainawa wayo. Ba ki san wanda nake nufi bane, tunda yazo gidan nan na fahimci kanki na rawa, kina wani shishshige masa. Shi sarki ne da ba zai iya zuwa ya ɗauka abincin da kansa ba kamar yanda mukeyi? sai kin wani ɗibi jiki kin kai masa". Na ɓata rai nace, "to ai naga shima Yayana ne tunda ya zama ɗan gidan nan". Bai kuma cewa da ni komai ba naji yaja dogon tsaki ya bar wurin a fusace, nabi bayansa da harara. *** Gwaggo ce ta fito daga ɗakinta, wanda sai yanzunne ta fito tun tashinta, ganin Haidar da Abba akan dining yasa taja ta tsaya daga shiga kitchen. ƙugu ta kama ta riƙe tana ƙare musu kallo, wannan abu nasu na bata takaici. Iklima dake aikin goge-goge ta durƙusa ta gaisheta. "lafiya lau Iklima, sannu da aiki kinji". "yauwa Gwaggo, ga abincin naki can bari na kai miki ɗaki". tace da ita, "a'a barshi tukunna ba yanzu ba. tun yaushe waɗancan Ƴaƴan suka shigo nan?". tace, "ehh sun ɗan jima". tsaki Gwaggo taja ta hau sababi,"wannan ai shine nayi banyi ba rufe ƙofa da ɓarayi, sam na rasa irin wannan abu, sai a kama zuwar maka wuri tun sassafe ko tashi baka yi ba, a shigar maka kitchen babu izininka, banda uban ci babu abinda aka saka a gaba, sai shegen kashi kamar ɓerayen daji, ina jin Auwalu rannan yana maganar sokawai ɗin gidan nan na neman cika, na rufa muku asiri nace matansa ne. to tsakani da Allah haka akeyi, gaskiya ku rage ci, ni ba zai yiwu ayita zuwar min waje ana aikin turawa ciki ba kuma babu taimakon da za'ai min, ko shara wannan ba'a iya min ba sai dai a ɓatan wuri a zunguri ƙatunan kai kamar randa a ƙara gaba. to gaskiya ni nama gaji da dafawa ƙarti abinci, Auwalu yazo ya shiga tsakanina daku, duba fa don Allah inata magana amma kun min shiru kun cika min kunne da ƙaran cokali kamar ba daku nake magana ba, saboda ni bakwa ganin girmana...to daɗin abin dai ni na haifi iyayenku, idan ku ba ku yimin biyayya ba su sa yi min ai". duk cikinsu babu wanda ya saurareta, sai abincinsu da suka ci gaba da ci, Abba yana kai cokali bakinsa ya ɗago ido ya kalleta, kamar jira take ta zabga mishi harara. Haidar na gamawa ya tashi daga dining ɗin, ta gabanta yazo ya wuce yana rataya earpiece a kunne yaje ya kunna tv, da ido ta bishi, sai daya koma kan kujera ya zauna tukunna tace da Iklima. "ke kashe min kayan kallona kinji, idan kin kammala aikinki na kunna idan zan kalla tunda kayan nawa ne ba na wani ba, kuma Auwalu ya saya min ba uban wani ba da za'a dinga yimin gadara da su, duk sanda aka tashi sai azo a kunna min ɗan iskan yaren da ni ba fuskantarsa nake ba". sai kuma ta juya kan Abba da har yanzu yake kan cin abinci, tayi ƙasa da murya tace,"yanzu kai Abba wannan dacewa ne fisabilillahi, abinda kuka yimin kun kyauta kenan?, inata magana kun min shiru kamar da dutse nake magana kun barni sai zuba nake babu mai tarar numfashi na, a haka na raineka? tarbiyar da na baka kenan? idan shi bai san dai-dai ba ai kai ka sani, kuma ni dai ban koya maka rashin kyautawa ba, duk da kaima halinka sai kai amma tunda ka ƙara ɗinkewa da wancan yaron iskancinka ya ƙara hawa sama, shi yasa na ƙagu ya gama abinda ya kawo shi ya koma gidan ubansa, tun kamin ya ruguza min tarbiyar dana shekara 27 ina baka ita". Yaya Abba yace, "amma dai Gwaggo kin san ba kyau ana cin abinci ana magana, kuma ma meye ne kike so muce miki?". tace, "au ku baku da hankalin sanin abinda ya kamata kuce min, idan babu haƙuri ai akwai lallashi. amma babu komai kowa yay na gari kansa, ni dai daga yau na bar ciyar daku. yazo yay min katangar ƙarfe daku, idan ba zai haɗaku da matansa ba to kuma yay muku ɗakin girki idan yaso kuyi ta kwaɓarku kuna ci. amma ni dai na bar girki da gardawa, atou magana ta gaskiya kenan ina dalili, Ƴaƴana basu saka min hawan jini ba Ƴaƴan wasu su saka min". tana gama faɗin hakan ta shigo ɗakin Sabina. har lokacin bata tashi ba, tana zuwa ta kashe ac, zafin da naji shi ya tashe ni, ina buɗe ido naji tana cewa da Iklima. "ki fito da kayan wankinta gaba ɗaya kamin ta tashi, naji tana batun wankesu kuma ni ba ƙaunar wankin injin nan nake ba sai naga kamar yana yaga kaya, ita kuma ba ganewa take ba saboda ba kuɗinta ne ke ciwo ba wajen saya". na miƙe zaune ina ɓata fuska nace, "Gwaggo ke kika kashe min Ac?". a hasale tace, "ban sa ni ba, mutum sai shegen lalacin banza da wofi, kiyita bacci kamar kasa ko gajiya ba kya yi, to ki tashi haka". "ni fa ban gama baccin ba, kuma ma yaushe ne rabon da nayi bacci irin haka. don Allah Gwaggo ki barni da zaran an koma makaranta fa shikenan". tace, "sai ki koma ai kiyi tayi kar ki tashi har a busa ƙaho, kuma ita dai wannan na'urar sanyi da baki da aiki sai warewa jikinki ita, to billahillazi kibi a hankali don ba gata ne kike wa kanki ba, mijinki za ki cuta, atou gaskiya nake faɗa miki ni babu ruwana". ƙunshe dariyata nayi har sai da ta fita na sa ki, na miƙe naje na kashe AC'n saboda Gwaggo gaskiya take faɗa min, na shiga toilet domin yin wanka. sai dana shirya na fito yin break, Yaya Abba da Yaya Haidar na zaune kan kujera, na gaida su kana na wuce dining, ina zama sai ga Baba ya shigo, gaishe shi muka yi, yake tambayarmu ina Gwaggo bata tashi ba ne?, a tare muka haɗa baki wurin ce masa ta tashi tana ɗaki ne. yana shiga ya tarar tana sallar walha, zama yay ya jira idarwarta, suka gaisa da Baba yace,"Gwaggo tun yanzu kika yi sallar, ai da kin bari sai anjima". tace, "walla kaga Auwalu kwana biyun nan da hadari ke haɗowa sai dai naji kiran azahar kawai, shi yasa nake yinta da wuri na huta". Baba yace, "ina agogon ɗakin ko ya lalace ne?". ya faɗa yana ɗaga kansa ya kalla bango. tace, "a'a yanayi, ai ɗan albarkar yaron nan Haidar shi ya koya min ma yanda ake gane lokacin, ranar yini mukai muna abu guda har sai dana iya. to kuma yanzu kasan idon sai a hankali ni ba kallon komai nake daga nesa ba, ita kuma waccen ƴar bata tashi sai azahar". Baba ya saita mata alerm ɗin landline ɗinta, yace duk sanda taji ya buga to lokaci ne yayi. idan kuma da daddare ne ya buga asuba ce tayi. sallama yay mata akan zai fita aiki, ya ɗauko kuɗi ya bata, ta amsa tana tasa masa albarka tana masa adu'a. ta fito masa rakiya ta kalla Yayana daya shigo babu jimawa, ta dakatar da Baba da cewan. "yauwa Auwalu ni namanta inata so na maka magana. kaga dai magana ta gaskiya bana jin daɗin abinda wannan yaron yake min, wai ba zai tashi cin abincin safe ba sai rana ta take zaka gansa ya shigo zagalo-zagalo ya wuce kitchen, kuma idan ya tashi du-du ɗan abinda zaici bai wuce cokali biyar ba zai ambatar min baƙar kalmar da bana so a gare shi yace wai ya ƙoshi, kuma daga wannan ƙoshin in Allah ya yarda ba zai kuma cin komi ba sai dare. to dan Allah irin haka ba sai yaja min zagi da tsinuwa ba ace bana bashi abinci, ina zaluntar maraya bayan ba halina bane. idan ciwon yunwa ya kama shi fa tsakani da Allah, idan shi baya son lafiyarsa aini ina so, haka kawai yaja min tashin hankali ya hanani natsuwa, na koma zaman jinya. to gaskiya kayi masa magana tun kamin ya kassara kansa". Baba yace,"wa kike magana akai ne?". tana cuna Yaya da baki tace,"gashi nan wannan yaron da Sabina ta kawo. ni fa ka ganni duka su ukun ba jin daɗin zama nake yi dasu ba, ina haƙuri ne kawai da halin kowa acikinsu. kuma duk maraicinsu nake tausayawa, bare shi wannan zagalon da babu uwa babu uba, duk cikinsu yafi ɗagan hankali, amma shi baya tausayin kansa, ni kuma abin yana ci min tuwo a ƙwarya. to gaskiya idan ba zaka yi musu faɗa su sauya hali ba ni zan cewa tsohon bazawarina ya fito muyi aure kawai na huta, banda Sahibina ma ya rasu ai da basu ganni a gabansu in tattalinsu haka ba, har suji daɗin min iya shege. dan haka ni dai don Allah kaja masa kunne ya bar zama da yunwa kar yaja min tashin hankali, na kasa tsaye na kasa zaune na ƙare a zaryar neman magani". Baba yay ƴar ƙaramar dariyar rikicin Gwaggo, yana duban Yayana yace,"to kai Yaya me yasa baka son cin abinci? ya kamata ka dinga ci kaji ko, kaga ulcer dai yanzu ta zama ciwon zamani Allah ya rabamu da ita. a dinga yin abinda Gwaggo take so kunji ni gaba ɗayanku, idan ba haka ba mu daina shiri da mutum". gaba ɗayansu suka ce "to". kamin nan Yayana yace, "Baba nifa ina son cin abinci, itace sai tace dole da safe shayi ne za'a sha, ni kuma ba sha nake ba. shi yasa nake haƙura sai da rana". caraf Gwaggo tace, "to nufinka zama zan dinga yi ina dafa maka abinda kake so, to wannan sai ka bari sai kayi aure shine kake da iko akan matarka". tace da Baba, "kaga Auwalu tafiyarka Allah ya bada sa'a. ni zanma tufkar hanci". Baba na murmushi ya fita, yana fita tace da Yayana,"to yanzu daka zo min wuri ƙarfe tara mene ya kawoka?". bai bata amsa ba saboda idonsa na kaina yana kallona, haushi ya isheta ta daki cinya tace. "kanka ka walaƙanta ba ni ba". ta faɗa tana wucewarta ɗaki. *5hours letter.* da Yayana da Yaya Haidar na zaune kan kujera kowa da abinda yakeyi, Yaya Abba ma ya shigo daga baya, gaba ɗaya basa iya zama a ɓangarensu. ni ina zaune an saka min lallai duk na gaji da shi, gashi ko 1hr ma bai yi ba, na kishingiɗe a wurin ina bacci, muryan Gwaggo ce ta farkar da ni. "har yanzu wannan lallan bai yi bane?". tace dani tana zama a kujera. "umm baiyi ba, kuma ni walla duk na gaji". tace, "ke daɗina dake kenan kin cika raki, to kuwa karki cire shi har sai naje na dawo, dan ba za ki sani asarar kuɗi ba. ina kuɗin dana ba ki ki ajiye min ɗazu?"."yana ɗakinki cikin ƙaramar drower". "nawa ne dama da kika ƙirga?". nace, "sha biyar ne". tace,"kai Allah dai ya yiwa Auwalu albarka ya ƙara masa arziƙi...ke Iklima". ta ƙwala mata kira, tazo cikin gaggawa ta durƙusa tana cewa gata,"kije inda nace ki ɗaukon goro ranan, za ki ga kuɗi ki ɗauko min". ta tashi ta tafi ta kawo mata, ta karɓa tana dubansu, sabbin ƴan dubu-dubu ne wanda aka cira a rapa. Yaya Abba na gani ya taso ya dawo kusa da ita yana yin ƴar murya akan ta bashi nasa kason. kamar ba zata bashi ba sai kuma ta cira dubu biyu ta bashi, ta bawa Yaya Haidar ma biyu, sannan tace da Yayana kai Zagalo kaima ga naka, ya taso ya amsa yana cewa,"na gode Matar". "uhmm kaji da shi dai, ai ka kusa bani takarda ta matsawar ba zaka sauya halin cin abinci ba. haka kawai ciwon yunwa ya kamaka ka mutu ka barni da zawarci ina budurwata ɗanya shagab". ta faɗa tana miƙewa, kamin kuma tace da shi yazo ya kaita unguwa zata dubo mijin ƙawarta babu lafiya, tunda yazo dama ta daina yarda Yaya Abba ko Yaya Haidar wani ya kaita anguwa, acewarta su tuƙin sai da rai sukeyi, ita kam bata shirya tafiya yanzu bata kaini ɗaki ba. na shagwaɓe fuska nace,"to Gwaggo nifa ba ki bani nawa kuɗin ba". ta waigo daga tafiyar da take tana cewa,"ayyah ke fa muna tare, waɗan nan da kika gani asu zan cira na saya kayan dubiya, sauran kuma nemawa Yayanki maganin cin abinci zanyi, akwai wata Mata ƙawata Hajiya Me Riga zata min kwatace, ko yaye yaro za'ayi can ake kaishi a bashi maganin cin abinci. ki bari idan aka kuma bani wasu gaba ɗaya ma naki ne, aike ƴar lele ce". nayi murmushi ina jin daɗi, nayi mata adu'ar a dawo lafiya, tana amsawa da amin, tana kuma cewa su Yaya Abba duk wanda ya kuma taɓani bata yafe ba, tunda ita sai bata nan su dinƙa sani aiki kamar jaka, to yau ko banzan kallo akayi min ta bar mutum da Allah, gani nan amana ce, wanda yaci amana kuma ya san sauran a lahira. Yayana yazo ya wuce ta kusa da ƙafata har yana tankwaɓe min lalle, wanda nasan kuma yana sane, ni ban san me nayi masa ba yake jin haushina kwana biyu, ko magana nayi masa sai yaga damar amsa min.[4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(24)* nabi bayansa da kallo ina hararsa kamar zanyi kuka, banda ina tausayinsa da saina faɗawa Gwaggo yanzun nan ta rama min. ***Ƙwiiiiii kake ji a sanda Alhussain yay wani mugun take burkin motar, Allah ya rufa asiri baibi ta kan matar da ta ɗauke yaronta ba daya fito daga cikin shop, Alhussain ya kifa kansa akan sitiyarin motar idanuwansa a rumtse. a wannan lokacin da wasu hawayen da bai san sanda suke saukowa ba, a wannan lokacin Gwaggo dake gaban motar ta sauke wata nauyayyiyar ajiyar zuciyar data amsa gaba ɗaya acikin motar. ta buɗe baki tana ta fitar da numfashi, gefe ɗaya ƙirjinta sai lugude yake kamar allon ƙirjinta zai faso waje. a yanda take ji inda za'ace zuciyarta ce ta fito tayoyin motar tasu tabi ta kan zuciyar ta mitstsike ba zata musa ba, tsawon wucewar wasu daƙiƙu kamin ta dawo hayyacinta, sannan ta dubi gefenta inda Alhussain yake wanda har sannan goshinsa ke akan sitiyarin. sautin muryarta ya fito da wannan fargabar da bata gama barinta ba. "Yaya kasheni zaka yi?, saura kaɗan fa kabi ta kan ɗan mutane ina hankalinka ya tafi?". magana take tayi amma sam bai ɗago ba kuma babu alamar zai ɗago ɗin. hakanne ya ɗarsa tsoro a ranta ta miƙa hannu ta ɗago shi, sai ta ganshi ruwan hawaye duk ya wanke masa fuska, yayinda da idonsa dake buɗe ke kallon waje, inda wannan matar da ɗanta ke tsaye tana rungume da shi tsam ajikinta. "kai lafiya? menene? kai ka juyo ka faɗamin halin da ake ciki, kukan namiji ko tashin hankali". yasa hannu ya goge hawayensa, sannan muryarsa ta fito cikin wani irin rauni me tsinka zuciya yace,"Gwaggo wasu iyayen Mata suna tsananin son ƴaƴansu, irin soyayyar da zasu iya jefa kansu a kowanne irin hatsari". sai yay shiru wani hawayen na ƙara sauko masa, kuma har wannan lokacin ƙwayar idonsa bata ɗauke daga kan wannan matar ba da yake jin wani abu akanta na tsarga masa ba. Gwaggo da tai kasaƙe tana dubansa tace,"hakane. amma maganar daga ina haka?". a wannan lokacin da ya shiga magana muryarsa na fita ne da karyewar kowanne harafi, kuma a yanzu kuka yake sosai. "Gwaggo me yasa tawa mahaifiyar bata kasance irin sauran ba? me yasa tata zuciyar babu wannan ƙaunar dake tsakanin ɗa da uwa?...Gwaggo ni ba ƙaramin yaro bane, na girma, na zama cikakken namiji, amma me yasa kullum nake jin ina buƙatar mahaifiyata a kusa da ni? ina tsananin buƙatar na jita a kusa dani...in da tasan ba zata so ni ba me yasa ta zaɓi ta samar dani ta hanyar da bata dace ba?, ta samar dani ta gurɓatacciyar hanya, dalilin da yasa ta jefar dani kenan a bola...ina sonta, duk da haka ina sonta Gwaggo, kuma na yafe mata ba, kuma zanso tazo gareni ko da na second ɗaya ne, nima na samu naji wannan ɗumin jikin na uwa da kowanne ɗan sunnah yake samu, wallahi ina sonta Gwaggo, ko kaɗan bana fushi da ita". ya ƙarasa furucin da wani irin murmushi me ciwo dake fita a saman fuskarsa, yana mai saka hannu ya goge hawayen fuskarsa sannan yaywa motar key suci gaba da tafi. "ka tuna me likita yace maka?". Gwaggo ke cewa da shi, kuma ba tare da ta jira cewarsa taci gaba da faɗin,"yace damuwar dake danƙare a zuciyarsa zata iya haifar maka da matsala nan da lokaci kaɗan...ka daina damuwar haka, ajikina ina jin akwai wani ɓoyayyan lamari tare da kai". tai shiru tana saka yatsa ta dungure masa kai. "kaje dan kanka tunda ni baka ƙaunar kasancewa tare da ni". sai kawai fuskarsa ta washe da wani murmushi, yasa hannu a kafaɗar Gwaggo, haka yaci gaba da driving ɗin har ya kaita inda take son zuwa. basu dawo ba sai bayan la'asar, tana shigowa ko zama batayi ba Zainab tazo tace mata Umma babu lafiya, ta zabari ƙafa ta fice a kiɗime sai salati ta ke zabgawa kamar ance mata ta mutu ne. yanzu ma da Yayana zai wuce da gayya ya kuma sa ƙafa ya shafe min tafin ƙafata, ya kuma yi wucewarsa kamar bai san abinda ya aikata ba, baƙinciki ya isheni kawai na fashe da kuka, Yaya Abba dake bacci ya farka ya doka min tsawa akan nai musu shiru, ni dai ban kula shi ba naci gaba da kukana ina kiran Gwaggo. "wai ke me yasa kuka baya miki wahala?". Yayana dake durƙusawa kusa dani ya faɗa. na ɗago na kalle shi na ɗauke kaina, na maida kaina ƙasa naci gaba da kukana. ina kallonsa ta gefen ido yana murmusa fuska saboda walaƙanci, na ɗago ina miƙa masa hannuna nace,"ni dai kunce min na cire shi haka nan kamin ka ƙarasa dagule minshi ya koma dungulmi". na faɗi hakan bana kallonsa saboda ina jin haushinsa. murmushin mungunta yayi, yay ƙwafa kaɗan kamin yasa hannunsa ya kuma dame min na hannun gaba ɗaya, ai ban san lokacin da na kuma fashewa da kuka ba ina dire diren ƙafa, cikin tsawa Yaya Haidar yace. "dilla Malama wannan wane irin rashin hankali ne?". ina sheƙar kuka nace, "don Allah Yaya Haidar kazo ka kunce min na hannu ɗaya na cire sauran, duk an dagule min shi karya zama na tsofaffi". harara ya zabga min yace,"uban wani ya sa ki yin ƙunshin? idan ba ki shiga hankalinki kin cire shi kin tashi kin wuce ciki ba sai na tashi na ɓarar dake anan wurin. kuma karki rufe mana baki ki kalla yanda zanyi dake". ina kallon yanda ya kafeni da ido yana min wani mugun kallo. ni kam ina zumɓura baki nace,"to ni ya kake so nayi, ba zan iya cirewa da kaina ba, kuma Iklima ta tafi islamiya. kawai dan anga Gwaggo bata nan sai a dinga cin zalina, da ace ma ina da Yaya mace babu me min irin hakan". can shima Yaya Abba ya hauni da masifa,"na rantse da Allah kika katse min bacci gaba ɗaya saina taso nazo nan na faffale ki da mari, shashasha kawai, har yanzu ke ba za ki girma da kuka ba". ba shiri naja bakina na gimtse, saboda ko kowa ba zai iya aikata abinda yace ba shi zai iya, dan ya tashi yasa waya ya tafasan jiki ba komai bane a wurinsa, ganina yake kamar ƴar shekara biyar. ni ban san me nayi musu ba suka tsaneni haka, babu mai tattalina acikinsu matsayina na ƙanwarsu, abu kaɗan zanyi su hayayyaƙo min, dama ga abinda ke ƙara basu haushi shagwaɓa ni da Gwaggo ke yi, ina sheƙar kuka naketa ƙunƙuni, Yaya Haidar ya taso a harzuƙe zai bige ni. Yayana ya riga shi isowa, ya tankwashe ƙafarsa tare da kamo hannuna yana kunce min lallan. "Malami kai kuma miye hakan?". Yaya Haidar ya faɗa yana mai jifansa da harara cike da jin haushinsa. Yayana yayi masa shiru, yana sa cokali ya kankare min lallen, dama tunda yazo sam basa shiri da juna, ko magana basa yi, idan kuwa ta kama dole to a rigima za'ayita. sai can ne kuma yay maganar a fizge yace,"kai yanzu idan aka barka sai ka daketa?, Haidar kana abu kamar ba wayayye ba". Yaya Haidar ya mayar masa da cewar,"to kai abinda kayi a wurinka wayewa ne? ka kama hannun yarinyar da ba muharramarka ba da sunan kai mai ilimi". na kalla Yayana naga yana murmushi, a tunanina hannu ɗaya zai cire min sai naga ya kamo ɗayan ma ya shiga cire min, yana gamawa da hannaye ya shiga cire min na ƙafata ma. Haka Yaya Haidar ya gama kwasar haushinsa anan tsaye ya fice ya bar parlon a fusace. ni kuwa yana gama cire min na miƙe ina cewa,"kuma ban gode ba". na faɗa ina murguɗa masa baki. kamin na bar wurin ya damƙo hannuna, shima ya miƙe tsaye, dab dani ya tsaya yana cewa,"ina jin haushinki shine za ki ƙara ɓata min rai ko". ashe lallen daya cire min ya kwaso a hannunsa, ban sani ba naji ya mulke min shi a fuska, sannan ya cika ni yay ficewarsa. cike da takaici na ɗauka wayana dake ringing nayi ɗaki, ina tunanin abinda zan masa na huce, haka kawai ni ban san me nayi masa ba yana cewa yana jin haushina, na shiga toilet na wanko fuskana inata jera ƙwafa. ina karkaɗa kai na ɗaga kiran wayar daya kuma shigowa, sallamar muryar dana jine yasa ni rufe ido ina jin faɗuwar gaba, ban san me yasa ba a duk lokacin da naji muryan Proff sai gabana ya faɗi, kuma duk da cewan muryansa iri guda ne dana Yayana amma shi akan Yayana bana jin hakan, sai dai kaina yana ɗaurewa akan wasu al'amuransu. "Beauty nah". ya katse min tunanin dana tafi. "na'am sir". ko taya akai ya gane, sai ji nayi ya jefo min tambayar,"lalala wa ya taɓa min Beauty, wa ya ɓata miki rai umm Beauty nah?". cikin sanyin shagwaɓata nace,"Yaya ne, kuma ba abinda na masa". na faɗi hakan ina turo baki kamar ina gabansa. "Ya Salam shi Yayan da kansa, gaskiya bai kyauta min ba. amma kiyi haƙuri kinji, Yaya ne babu yanda na iya da shi da na ɗau mataki yanzun nan. yanzu kiyi haƙuri kinji, oya yi dariya naji". ya faɗa kamar yana magana da wata ƴar yarinya, ban kuwa san lokacin da dariyar ta subce min ba nace,"ai ka rabu da shi zan rama ne". Yay siririyar dariyar da sai dana furgita da jinta da kuma sautinta, na rantse da Allah irin dariyar Yayana sak, kalle-kalle na farayi a ɗakin naga ko dai shine ya shigo, sai naga babu kowa, na buɗe baki nace, "Proff...". ban ƙarasa ba naji an fizge wayata an jefar a ƙasa, ina ɗaga kai naga Yaya Haidar a kaina. da muryar ɓacin rai yake nuna ni da yatsa yana cewa. "ke ba ki da mutunci ba ki da hankali ba ki da tunani ba kya aiki da iliminki ko. kin maida kanki ballagaza kowane kare ɗora idonsa yake ajikinki, ki kalla a yanda kike fita parlo bayan duk kin san maza ne a wajen, amma saboda shashanci yay miki yawa an gama sangartaki ke ba ki san abinda ya kamata ba. to ki jini da kyau, duk randa kika kuma bari wancan ɗan tsintuwar ya kuma kusanto inda kike ma sai ranki yayi mummunan ɓaci, bare ki bari ya taɓa miki hannu, za ki kalla yanda zan dake". na buɗi baki zanyi magana naga har ya fice ya barni da takaici, ni yau kam gaba ɗaya sun gama ƙona min rai duk su ukun, shi ko meye ruwansa dani oho. Gwaggo kuwa tunda ta isa ɓangaren Umma taga yanayin da take ciki hankalinta ya tashi, ta fashe da kuka tana cewa,"Allah sarki Hajara sannu kinji. Allah ya ba ki lafiya ya yaye miki. wai dama shi ciwon tun yaushe ne?". ta ke tambayar Yaran. Amina tace,"tunfa jiya ne, ɗazu ma Baba ya turo Dr yazo yasa mata drip da allura. harta samu tayi bacci sai yanzu kuma da ta tashi jikin ya kuma dawowa". Gwaggo ta matsi ƙwalla tana ƙoƙarin kamo Umma ta sanyota jikinta tana cewa,"Allah sarki Sannu Hajara insha'Allahu yanzu za ki samu sauƙi, ba wai-wai za kiyi ba adu'a za ki dinga yi". tana gyara yafen mayafinta kuma take cewa,"yanzu ke gaki aba rusheshiya da na miƙar dake zaune ko kya ɗanji daɗi, jiki sai kace buhun masara. ke Amina zo ki taimakan mu ɗagata zaune, wannan kwanciyar ita zata ƙara kashe mata jiki". haka Gwaggo ta zauna a wurin Umma, sai nan da nan take da ita, bata baro wajenta ba sai da ta ga jikinta yayi sauƙi tukunna. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(26)* shigarmu parlo muka zube kan kujera tare da fashewa da dariya. Gwaggo ce zaune kan carpet tasa Yayana a gaba tana barbaɗa magani a abinci, gefenta kuma wasu ɗaurin magunguna ne na daban suma iri-iri. faɗi take tana cewa,"yanzu kaga idan Allah ya taimaka sai kaga cikin kwanaki kaɗan kayi kuɓulɓul da kai, saboda maganin matar nan akwai kyau sosai, so nake na gama da kai saina koma kan Abba". Yaya Abba yace,"to ni kuma Maganin me za'a samo min?". "shegen cinka da yake damuna shi zan shiga fafutukar neman maganinsa, domin wannan babbar lalura ce kake fama da ita, yawan cinka har tsoro yake bani Abba". ta faɗa tana kuma kunce wani ɗaurin ta ɗibi garin maganin ta barbaɗa acikin abincin. sai da ta gama tas tukunna tasa cokali ta juya, sannan ta tura ma Yaya plate ɗin abincin gabansa tana cewa,"gashi nan maza kaci, kaga sau uku a rana akace, kuma kai da ba ƙaunar abinci kake ba gashi har yamma tayi ko ci ɗaya baka yi ba. gaba ɗaya ni na rasa wanna irin ciki ne da kai wallahi, naso ace ma an haɗa maka da ɗurar ƙwai yanda za ka dinƙa ci babu ƙaƙƙautawa, to matsalar ba bina za ka yi ba Yaya, tunda kai ba sanin ciwon kanka kayi ba". shirun da taji ya mata ne yasa ta tsaya tana masa wani duba tace,"wai ba da mutum nake magana bane?". gaba ɗaya hankalinsa na kan waya, ba wai jinta ne baiyi ba, sarai yana jinta ya shareta, kofi ta raruma ta wurga masa ya sauka a goshinsa, ya ɗago cikin sauri yana sosa wurin yana kallonta. "Gwaggo me nayi miki? da kin fasan goshi fa". harara ta zabga mishi tace,"kai dama baka da mutunci, yanzu duk maganar nan da nake ashe ba saurarena kake ba, ka barni sai zuba nake kamar tsohuwar kanya, su kuma waɗancan mahaukatan suna min dariya. to ni duk wanda yay min dariya kansa ya cuta saboda rage imani ta ke. yanzu da ka ɗago aika fahimci ina magana da kai ko, zaka ɗauka abincin kaci ko ƙaƙa?". yace,"kai Gwaggo, wai fisabilillahi taya za'ayi da girmana na kama cin abinci da wani maganin ƴan yaye, nifa ba yaro bane. gaskiya ni bazan sha wannan magungunan ba da ban san daga ina aka samo su ba". tayi galala tana kallonsa cikin jin haushi tace,"to kana so kace min kasheka zanyi kenan, to ka sani ni ba azzaluma bace, dan ko kishiyoyina ban cutar dasu ba bare kai da kake jikana. kuma dan ubanka Auwalu banda ma ina ƙaunarka kai har kaga na damu da kaci ne, amma saboda baka yo gadon arziƙi irin na Sahibina ba shine kake faɗa min son ranka. kasan irin wahalar da nasha wajen neman gidan mai maganin nan kuwa? da ace kana da imani wallahi sai ka tausaya min, ka duba ƙafafuna tun yammacin jiya da na dawo suke min ciwo har yanzu kuma, amma sam bai dame ni ba saboda nafi so na ganku kullum acikin ƙoshin lafiya". Ya tankwashe ƙafa ya matso kusa da ita, sai daya rungumeta yace,"Hajiya Gwaggo tah ina so ki fahimci su kansu masu maganin hausan nan ba lallai sun san abinda suke badawa ba. da maganin bature ne zan sha, amma wannan da babu Nafdac taya zan aikawa cikina shi, garin neman gira a rasa ido". ta juyo ta kalle ni tace,"ke meye Nauduk ɗin daya faɗa?". irin kallon da take min yasa na gimtse dariyata nace,"kai Gwaggo ba Nauduk ba Nafdac, hukuma ce ta tace magunguna da kayan abinci, duk wani magani ko abinci ko nasha idan babu nafdac ajiki ba'a so ayi amfani da shi". "hmm". tace tana taɓe baki, ta ture Yaya daga jikinta, ta yunƙura tana tattara magungunan tana cewa,"naudok mata shegiyo dan uwar ubanta, da ma'aikatar, da masu aikinta da masu bin umarninta na haɗasu na kankantsa musu mari. shegen tsirfar banza da wofi, kai wannan bature anyi ɗan jaraba billahillazi. daga yau ɗin nan indai ni ɗin masoyiyar Sahibina ce, babu ɗan banzan da zan kuma cewa yasha magani acikinku, ku rayu ko karku rayu ba damuwata bace, ana tausaya muku amma ba kwa gani. to ni daga yau babu ruwana na fita a sha'anin kowa. masu shegen ci idan sun mutu ta dalilin haka Allah ya jiƙan rai, suma marasa ci idan ciwon yunwa ya kwantar dasu a asibiti iyakata nabi su da Allah ya kyauta amma babu mai sa ni zaman jinya, nima kunga tattalin arziƙina ya ƙaru, dama wannan ma jiya dubu uku haka nasa na karɓo maganin nan, to ajiye shi zanyi idan Hajara ta haihu na bata in ta tashi yaye, an huta da kuma ɓarnatar da kuɗi". har ta nufa hanyar ɗakinta ta juyo a ƙufule, tana cuna Yaya da baki tace masa,"kai Zagalo daga yau idan kaga dama abincin ma ka daina ci gaba ɗaya, shine zaka burgeni. kuma ka sa ni na bar saka kwano da kai, kaje wurin Hajara ko Zara'u wani ya dinga baka, in kuwa har na kuma ganin ƙafarka tazo karɓar abinci saina bika da muciya". ta kalla Yaya Abba dake dariya tace,"kaje kai da Allah, tunda na faɗa maka bana son dariya, kuma kaima karka kuma zuwar min karɓar kwanon abinci dan ba zaka dinga sa ni almubazzaranci ba, ci sama da sau biyar a rana, ɗan ƙaramin buhun shinkafata ya dinga ƙarewa a kwana uku yo ina dalili haka kawai. amma in kuka daina zuwa nima na huta, kaga ubanka Auwalu sai ya gane ba ni nake cinye masa kayan abinci ba". tayi shigewarta ɗaki ta barmu da dariya, muka haɗa ido da Yayana munawa juna wani irin kallo muna murmushi, yanda kallon ya fara shiga jikina ne yasa nai saurin ɗauke idona. Kaina a ƙasa ina ƴar dariya nace,"ni dai gaskiya ba'a kyautawa Gwaggota, kullum a cikin tattalinmu take amma har ta taƙarƙare taje ta karɓowa mutum maganin ƴan yaye yace bazai sha ba". yace da ni,"to ke me ya hana ki karɓa ki sha?". nace,"aini na tsaya a yanda take so, bana shegen ci kuma bana ƙin ci". Yaya Abba ya haɗe rai yace,"tashi ki bar wurin nan tunda babu sa'anki". na ɓata fuska na tashi na bar wurin, aikinsa kenan idan ana zaune yace na tashi na bar cikin manya. da Magriba Uncle Sulaiman yazo Babansu Yaya Haidar, wanda shine Babba a ƴaƴan Gwaggo sai Baba da yake auta, dama su bakwai ne kuma duk sun rasu sai su biyu yanzu. tunda yazo Gwaggo ke masa faɗa akan rashin sada zumuncinsa, shi kuma yana bata haƙuri. ta dubeni tace,"ke je ki kirawo masa ɗansa yazo, dan nasan dai shi yazo gani ba ni ba". Uncle yace, "Gwaggo wallahi ba haka bane, kin san namu aikin sai a hankali ba ko da yaushe muke samun lokaci ba, amma don Allah kiyi haƙuri zan dinga yakicewa duk weekend na dinga zuwa". tayi dariyar manyace tace,"haba ɗan nan, karka damu wayarma da muke kullum ta isa, ai nasan yanayin aikin naku shi yasa ma nake maka uzuri nake kuma tausaya maka. ni dai fatana yace ko baka karɓar cin hanci? dan ƴan sanda halinku ɗaya ne". Uncle ya murmusa yace,"a'a Mama, ai a kullum ina tunawa da nasiharki da kuma faɗanki. kuma na tabbata hakan shi yasa nake samun ci gaba". taji daɗi ta kuma ƙara yi masa adu'a. ta kuma ɗora masa compalin da cewar,"ka ɗau matakin hana Junaidu zuwa gidan nan, sam bashi da kirki baiyi halin ƙwarai ba, yaran nan daga nayi masa tsiyar idan zai zo gaisheni bai iya kawo abin arziƙi ba kamar Haidar, sai dai yazo ya sa ni gaba da surutun banza, shine shekaranjiya daya tashi zuwa ya ɗuro ruwa da gishiri a kwalbar lemu ya kawo min. wallahi Sulaimanu na zaci lemun gaske ne nayita masa godiya nace yasa min a freezer sai ansha ruwa, ana shan ruwa na hau kwankwaɗa harshena ya ɗaure, ai ɗan nan ya shiga da hakkina. ni dai inaga a duniya ni kaɗai ce banyi sa'ar jikoki na arziƙi ba, Sabina ce kaɗai ƴar albarka, dama-dama ma Aliya da Husnah sai Muklas, duk da shima bai cika halin ƙwarai ba wataran, amma dai yafi su Abba a haka, dama su Aisha ba'a magana. saboda haka ni dai ka hana Junaid zuwa dan gaba zai iya jiƙa min barkono ya karni. kaga yanzu shi Haidar yau kwata-kwata ma ban sa shi a idona ba, ko gaisuwar safe wannan babu, dama sa'anni yake ganina da shi, to ban damu ba tunda gaisuwarsa ba zata ƙare ni da komai ba haka kuma ba zata rageni da komai. ni dama gaba ɗayansu maraicinsu nake tausayawa to amma sun maidani abar banza. ina faɗa maka fa Haidar har gaba ya ɗora dani a gidan nan, daga nacewa Auwalu yana shigowa da sassafe yay min sata a kitchen, shikenan ya daina zuwa inda nake sai dai yaje waje ya siyo abinci yaci". sai kuma ta fara matsar ƙwalla tana cewa,"hakan da yayi ya kyauta min kenan Sulaimanu, idan na tuna basu da uwa hankalina tashi yake, wallahi duk sanda ban saka yaran nan uku a raina ba bana samun kwanciyar hankali. to shi gaba ɗaya ya ɗauke ƙafa da shigo min, Abba da Yaya ne kawai masu zuwa na gansu naji daɗi, shi kuwa sai dai ya barni da tunanin halin da yake ci, tsakani da Allah idan na kamu da ciwon zuciya fa". Uncle ransa ya ɓaci, ya hau bata haƙuri ni kuma yace, "Sabina je ki kirawo min Haidar". ko da naje na ɗau 2minutes ina buga ƙofan ɗakinsa amma shiru, ina murɗa handle ya buɗe, nayi tsakin ɓata lokacin da nayi ina aikin bugu, ina shiga na ganshi kwance kan gado yana kallon sama, ko vest babu jikinsa sai towel dake ɗaure a ƙugunsa, na ɗauke kai da sauri ina kallon gefe. nace,"Yaya Haidar Uncle yazo yana kiranka, ya kira wayanka duk baka ɗauka ba, kuma Gwaggo ma tun safe take nemanka". nayi magana a ƙalla ta kai huɗu bai amsa min, ganin yaƙi motsawa kuma bai amsa min ba yasa na matso ina cewa,"Yaya Haidar Uncle yana kiranka". na faɗa ina ɗan taɓashi dan a tunani na ko bacci yake. nan ma bai motsa ba, ina leƙa fuskarsa nake ƙara ɗan bugun hannunsa ina ƙara kiran sunansa, abinda ya bani mamaki ya kuma bani haushi idonsa biyu kawai ganin damar amsawa ne bai yi ba. naja tsaki a ƙasan maƙoshina nace,"Yaya Haidar magana fa nake maka, ai dai nasan ka jini ma, idan kaga dama karka zo". na faɗa cikin jin haushi, na juya zanyi tafiyata sai kuma naji tsoro ya kamani, dan idonsa ne kawai a buɗe amma baya motsi, anya lafiya kuwa? duk walaƙancinsa da mikilancinsa dai ba zanyi wannan maganar ba ya shareni ba. tsoro ya kuma kamani sosai na dawo hankalina a tashe, ina ɗan bugun hannunsa nake kiran sunansa. naji shiru babu alaman ma yana numfashi, ina kallon fuskarsa idona ya ciko da ruwa, saboda yanayinsa zam na matattu, idonsa a buɗe yake ya juye sama. tuni na fara hawaye na kama hannunsa ina cewa, "don Allah Yaya Haidar ka tashi". sai kuma na fara ƙwala kira, "Gwaggo, Yaya Abba, Baba". ina jijjiga shi. zubar hawayenta a ƙirjinsa yasa shi fizgota ta faɗo jikinsa. a tsaroace na shiga kallonsa, shi kuma ya tsareni da kallo da numsassun idanunsa waɗanda suka tara ruwa, gashi sun sauya kala zuwa ja kuma shimfiɗe da damuwa a cikinsu, sai zallar ɓacin rai da yake kwance a saman fuskarsa. yanayin Sabina matuƙa yana burge shi, dukkan abunda yake buƙata a wajen ƴa mace ta tara, kama daga ilimi har zuwa kyawun halittar jikinta, ga irin shagwaɓar da yake biɗa a wurin ƴa mace, haka kuma yana son mace mai saurin kuka yanda zai dinga saurin sakata kuka, ba shi da wani buri da wuce na ya mallaketa, to amma kuma baya so yarinyar ta raina shi, zai ƙwammaci sonta ya zama ajalinsa akan dai ya bayyanar mata da abinda ke ransa, a ganinsa ma ya aureta to ajinsa ya matuƙar faɗuwa. shi yanzu ma bai san dalilin da yasa abun ɗazu ya dame shi ba, so yake ya yakice soyayyarta ya watsar a gefe bare har kishinta ya dame shi amma ya gagara. kamo tafin hannuna yay ya haɗa da nasa ya damƙe kamar zai ɓallani, na sa ki ƴar ƙara ina ƙoƙarin sauka ajikinsa,"Yaya Haidar Leave me". nayi maganar cikin rawar murya. bai kulani ba sai rufe ido da yayi ya buɗe, wannan karon kallon da yake min saina tsorata da shi, anya kuwa lafiyar mutumin nan ɗaya, ya gaza controlling abinda yake ji, hakan yasa ya shiga zura hannusa a rigarta yana yawo da shi a bayanta, na haɗiyi wani yawu mai wuya na ture hannunsa, murya a ɗage nace. "Yaya Haidar wai mene hakan, babu fa kyau ni ka sake...". ban ƙarasa ba naji bakinsa a nawa, duk ƙoƙarin da nayi wajen ganin na ƙwaci kaina abin ya faskara, ya kama leɓena na ƙasa sai tsotsa yake kamar mai shan alawa, yana kuma ta yawo da hannunsa a bayana zuwa cikina, tuni jikina ya fara amsawa, idanuna suka rage girma ina kallansa cikin wani yanayi. nan da nan hawaye ya shiga reto a fuskata, ganin hakan ya sakar min baki yana goge min hawaye, jikina banda kyarma babu abinda yake, na buɗe baki zanyi magana ya ƙara sa bakinshi cikin nawa, yanzu kam harshena ya kamo, ido na lumshe sai samun kaina nayi da maida masa da martani, sumbatar juna muke sosai acikin wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa. jin ina aikin kuka yasa ya rabu dani, a hankali ya ɗago fuskata yana kallona da idanunsa da sukai jaaa, na ƙara rumtse ido ina ci gaba da kukana, a hankali cikin magana mai kamar ta raɗa muryarsa a ɗan disashe kuma cike da ɓacin rai yake ce min. "me yasa ke ba ki san abinda ya dace ba, mene yasa....?". Yay maganar raunin zuciyarsa na neman rinjayar furucinsa. bai ƙarasa tambayar ba ya ture ni daga jikinsa ya hankaɗa ni na faɗo ƙasa. ya sauko ya wuce toilet ya barni duƙe ina kuka, har ya fito yazo yasa kaya ina nan yanda ya barni ina aikin kuka, dama na tara abuna, gaba ɗaya takaicin abinda ya faru nake, ni dai Allah yayi wadaran halin wannan mutum. tunda ya gama sanya kaya yay tsaye yana mata wani mugun kallo, har cikin ransa yake jin kukan nata, sai da tayi mai isarta tana yin shashsheƙa sannan yazo inda take, ya kamo hannunta ya miƙar da ita tsaye, tare da janyota jikinsa ya rungumeta, yana aikin shafa kanta cikin sigar lallashi. ni dai shimfiɗar da kaina kawai nayi a ƙijinsa ina fizgar numfashi. "ki min shiru". ya faɗa a cikin ɗaurewar murya. ya ɗago kaina yana duban fuskata yace,"ke wai ba'a ce miki ki bar abu ki bari ne". ni dai ban kalle shi ba sai ƙarfi da nasa zan ƙwace daga jikinsa, ya kuma matsoni yana ɗaga min kai yace, "kinji na rantse ba zan sake ki ba har sai kin bar kuka. miye ma akai miki da za ki sa ni gaba kina min ɗan banzan halinki". "ni Yaya Haidar bana son irin wannan abun da kake min, wallahi Allah babu kyau, kaima fa kasan irin haramcin da yake ciki, duk da ni ina ƙanwarka amma ai ba muharramarka bace ni. dan darajan Allah ka daina wallahi bana jin daɗi kuma bana so a rubuta maka laifin zunubi". na faɗa hawaye na gangaro min, shi kuma fuska a tamke yace. "naji, ba zan kuma ba. amma kema k...". sai kuma yayi shiru ya kama hannuna muka fita yana cewa nai masa shiru na goge hawayena. muna shiga parlo Gwaggo ta taso hankalinta a tashe ta shiga tambayata lafiya duba da yanayin da ta ganni, ya saki hannuna yana faɗin. "aljanu ta tayar, ki daina barinta fita da daddare". ya faɗi hakan yana kama hannunta ya damƙa mata magani a kwalba, na kalleshi naga ya haɗe rai kuma yana maganar kamar da gaske, muna haɗa ido na murguɗa masa baki nace,"Allah ya isa". na faɗa a yanda kowa ba zai jini ba sai shi daya ganni. Gwaggo kuwa kuka ta saka sosai, tana faɗawa Uncle lalurar dake damuna, yace insha'Allahu za'ai min maganin da zasu rabu dani. "ita fa ɗaya tilo nake da ita Sulaimanu. baka ga yanda suke takura mata". ta kuma faɗa tana kuka. irin yanda take zuzuta abin kamar kullu yaumin nake tayar da su, ni harta bani haushi ma na miƙe na bar wurin, shi kuwa Uncle cewa yake. "ki bar kuka Mama, adu'a za'ayi Allah ya yaye mata, sai kuma magani da zamu durfafa wajen nemansa". tace,"to Sulaimanu dan Allah kayi taimakon daka za'a dace saboda shi ubanta ba damuwa yay da wannan ciwon nata ba, sam ko a jikinsa, don da na gaya masa ma ko razana bai yi ba. yanzu ka duba banda Aliyu yana gidan nan yanda suka tashi da wannan daren ya zanyi?, ai ni dai wannan yaro babu abinda zance da shi sai dai Allah yayi masa albarka yasa ya gama da duniya lafiya, ya kuma haɗa shi da matar ƙwarai. walla a kaf jikokina babu mai ƙaunata kamar Aliyu". ta ƙarasa maganar tana sa gefen zanenta ta goge hawaye. tace,"Aliyu Haidar". suna gaisawa da Mahaifinsa ya ɗago ya kalleta baiyi magana ba tace,"na gode maka ƙwarai kaji". "ki godewa Allah". ta miƙe zuwa ɗakin Sabina inda ta shiga ta sameta tana aikin kuka. duk yanda tayi dani akan nayi shiru ƙememe naƙi sauraronta, har saida tace zata kira Yaya Haidar yazo ayi min turare ko sune basu tafi. nai saurin cewa da ita,"a'a dan Allah Gwaggo, wallah naji sauƙi". muna haka Yayana ya shigo, kallo ɗaya zaka yiwa fuskarsa ka hangi damuwa acikinta. yazo ya zauna gefen gado yana min sannu, na tsaya ina kallonsa, kenan shima ya yarda da maganarsu aljanu na tayar, jikinsa na faɗa na kuma sakin kuka ina cewa. "Allah ni Yaya ban tada aljanuna ba, ni bani ma dasu wallahi Sharrin Gwaggo da Yaya Haidar ne kawai". yasa hannu yana shafa gashin kaina, muryansa mai sanyin daɗi yace, "na san Cutie nah bata da wani aljanu, ki rabu dasu kinji. idan ma sune Allah zai rabaki dasu, amma ki share hawayen bana son jin kukanki". ya ɗagoni a jikinsa ya kama haɓata yana goge min hawayena da hanky ɗinsa mai ƙamshin daɗi, ni kuma ina ta sheƙar kukana ina kuma ɓata fuska cike da shagwaɓa. ya haɗe goshina da nasa, ya kashe min ido guda tare da raɗa min wata magana a kunne, muka haɗa ido na ƙyalƙyale da dariya wanda tuni hakan ya wanke ɓacin ran da nake ciki. Gwaggo dake jiƙa magunguna zata bani ta juyo tana kallonmu, tana kallon Yaya da suka yi faɗa tayi ƙwafa tace,"Allah yasa su ƙara tashi suyi maka ɗan banzan dukan da zaka kasa motsawa, tunda ka zama mai ɗaurewa ƙarya gindi, wato rikicin tsufana ne yasa nace tana da aljanu ko?, saboda an faɗa maka bana ƙaunarta, to Allah yasa su bayyana yanzu su gwada maka ko ta hanyar shaƙe maka wuyana sai ka ƙaryatamu da kyau". [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(27)* Gaban mirrow nake ina drying gashina, wayana maƙale a kafaɗana muna waya da Farhana, har yau bata bar fushi dani ba akan zuwan da nayi naje na dawo banje gidansu ba, bayan nace mata a gidansu zan sauka. ina dariyar masifar da take aikin yi nake bata haƙuri ina cewa ita dai ta cika mita, nace mata inan zuwa ai, taja tsaki ta kashe wayan. ban kai ga kammalawa ba wayana ya kuma ƙara, na miƙa hannu na ɗauka, sunan Proff na gani a jikin screen na yawo ta hanyar vedio calling, na cuno baki haɗe da yin ƙaramin tsaki na ajiye, na rasa me yasa kwana biyu yake takura min da kira, shima kiran dole sai yace vedio call, idan ban ɗaga ba kuma ya addabeni da message, har saina fusata na ɗaga zan masa tsiwa sai karsashin muryarsa ya hanani aiwatar da komai, ta hakan zargina akan Yayana ya ƙara yawaita, na kuma ɗora ayar tambaya akansa akan abinda zuciyata ke saƙa min a game da shi. inata mita a zuciyata kiran ya kuma shigowa a karo na kusan biyar, dai-dai da lokacin da nake ɗaure jelar gashina, garin kai hannu na katse kiran saina danna answer ba tare dana sa ni ba naci gaba da abinda nake. sai bayan dana kammala na ɗau wayan zan fita kawai naga mutum ya tallabi fuskarsa yana aikin kallona, kallonsa nayi ya sakar min murmushi yana faɗin,"gyaran gashin yayi kyau, sai ya ƙara fito da beauty nah, kin kalla kanki a madubi kuwa ko kuma kin bar min gari na faɗa?". na samu bakin gado na zauna ina zumɓura baki, nayi ƙasa da kaina ina cewa,"to wa yace ka kalle ni?". wani siririn murmushi ya saki yace,"yanzu ni har sai an bani izinin kallon Beauty? kallonki fa shine abincin idanuna". na ɗago ina kallonsa, nayi shiru bance komai ba saboda wata magana da ta haska acikin kaina, wannan furucin nasa yayi salo dana Yayana da ya taɓa cewa Kallon Cutie nah abincin idanuwana. kamar yanda Proff yay ƙuri yana kallona haka nima na ƙura masa ido, don so nake na ga aina yake a zaune, idan har naga wani abu mai kama da gidan nan to tabbas zargin Yaya da nake na shine Proff to ya tabbata, sai dai banga wani alamu na shaidan hakan ba. yace da ni, "Beauty please ki bani aron hankalinki yau muyi magana kinji". "ina jinka". nace ina daɗa haɗe fuska. "ki fito gani a ƙofar gidanku". nai saurin ɗagowa ina dubansa da mamaki,"gidanmu kuma?". yace,"kar ki ɗauka wasa, am serious". ina daɗa dubansa nace,"taya akai ka san gidanmu, ni fa ban yarda da kai ba". Yay murmushi mai sauti kamin yace,"Beauty me nayi kuma na rashin yarda, kin kalla nan". ya faɗa yana nuna min wata ƙatuwar waya dake ɗaya hannunsa. map naga yana aiki, lallaima mutumin nan wato wayo yay min kenan ya kirani ya biyo sahun kiran, kamar ya san tunanin da nake yace,"nayi miki wayo ko. kiyi haƙuri nazo ba tare da izininki ba, yanzu dai ki fito waje muyi maganan da ya kamata". nace,"ai bani nace kazo ba, don haka sai ka koma". "aikuwa to yanzu zan shigo da kaina, dama yau weekend nasan Baba na gida kinga saina sanar masa da abinda ke tafe dani". nayi zumbur na miƙe ina faɗin, "ni ban saka ba, gani nan". ƙaramin gyalena na ɗauka na yafa na fita, na ce da Gwaggo nayi baƙo ina zuwa, ta bina da kallo baki a sake wato abin ya bata mamaki, ina buɗe ƙofan parlo naji tana cewa,"wayyo ni Hannatu daɗi barni da raina, yau Sabina taga zaɓin ranta, yau zanyi kwanan farinciki, dama zuwan wannan rana nake ta jira, Allah yasa dai ku daidaita, fargabata Allah yasa kar jami'an tsaron kanki su sauya miki ra'ayi, domin nima a yanzu banda burin da ya wuce naga na kaiki gida mafi girma da daraja a wurin ƴa mace". tana ta murna take faɗin haka don harda ƴar rawarta, ni dai ban kulata ba nayi ficewata. gaban gate ɗin gidanmu kaɗan yay parking motan nasa, na ƙarasa wurin da sallama, da jikin motar na jingina sai haɗe rai nake, ni har ga Allah banso wannan zuwan nasa ba, wayana yay ringing, ina kallo naga sunansa ne, na ɗaga ina cewa,"to mene kuma na kirana bayan gani nazo, ai nasan ka ganni ka fito mana". na faɗa cike da tsiwa a lokacin dana ɗaga, da murya mai ban tausayi yace,"Beauty da ace ina da ƙafafun da zan taka, da kamin fitowanki zan iso tarbanki, ki tayani da adu'a na samu lafiya naci gaba da takawa kamar yanda nake lokacin da ina ɗan shekara uku, na rantse miki Beauty daga wannan lokacin za ki zama sarauniya ta gaske, domin ni zan zame miki bafadanki a duk wani taku na tafiya naki". gaba ɗaya sai naji wani nauyi ya kamani tare da yin da nasanin furucina, dan sosai ya bani tausayi har naji dama ban faɗa masa hakan ba, driver ne ya zagayo ya buɗe min murfin motar, na leƙa kaina ciki nace da shi, "ba zan iya shigowa ba saboda Gwaggo ta hanani shiga motan kowa, ka faɗi ko mine daga nan ina jinka". yace da driver ya fito masa da wheel chair nasa, jin hakan nace. "a'a barshi kawai, bari na shigo ɗin amma sai dai ka hanzarta". kuma nima dama na faɗa masa ne don na gwada shi, saboda in har ya damu da maganar da ta kawo shi to zai fito da ƙafafunsa, ashe dai da gaske bayada ƙafan ba wasan kwaikwayo ne yake ba, tabbas shi ɗin ba Yayana bane. bayan na zauna na ɗan dube shi kaɗan naga mood na fuskansa ya sauya, raina naji babu dadi domin nasan magana ne silar hakan, nayi ƙasa da kaina ina wasa da yatsuna nace," kayi haƙuri don Allah, nasan baka ji daɗin furucina ba". kwantar da kansa yayi a jikin kujera, hakama idonsa a lumshe suke, da raunin murya ya fara magana yana cewa. "wannan shine rashin yarda da kika yi da ni? Beauty miye ribana idan na ɗorawa kaina cutar ƙarya, don kawai na samu shiga a wurin mutane? to me na rasa? ban rasa komai ba na jin daɗin rayuwar ba, ki yarda dani Beauty wallahi babu yaudara a tare dani, dukkan abinda kike gani tare dani gaskiya ne, wannan ƙafafun da ki ke gani shekaru 27 kenan rabon da su taka, anyi maganin amma shiru, kullu yaumin a zaune suke basa iya sarrafa kansu sai da taimakon wani". yay shiru tare sauke wani nauyayyan numfashi, na goge ƙwallar dake neman sauko min nace,"Allah ya baka lafiya". har lokacin idonsa a rufe ya amsa min da amin kamin ya ɗora da cewa,"tun da nake a rayuwata ban taɓa jin wata mace ta shiga raina ba sai dana fara ganinki Beauty, duk da nasan ke ɗin kinfi ƙarfina amma ina da yaƙinin za ki iya kasancewa tare dani a cikin kowanne irin hali, domin ke din kina da zuciya mai kyau, halinki mai kyau, ko mai naki me kyau... ko da nace miki kin min sata ba satar komai nake nufi ba fa ce zuciyata da kika sace, Beauty na rantse miki labarinki yasa mahaifiyata acikin farinciki, yasa ƴan'uwana a farinciki, Daddyna kaɗai ya rage ya sanki kuma shima ina jiran dawowansa ne, Beauty shin za ki iya yimin alfarma? ki aminta dani ki zama matar aurena?". na wani ɗago a zabure ina kallonsa, da gaske ne dama sona yake? me yasa na bashi fuskar da har ya iya furtamin wannan maganar? cikin tsiwata nace,"dama wannan maganar ce ta kawo ka wurina?, dana san ita ce da ban fito na ɓata lokacina ba anan, idan kai kana sona to ni bana sonka domin ina da mijin aure". mtswwww naja tsaki na fito daga motan na wuce gida raina a ɓace, ba tare dana tsaya sauraron me yake cewa ba. abinda na gani a parlo ne ya razani, har ban san lokacin dana jefar da wayana a ƙasa ba na ruƙunƙume Gwaggo, sosai ganin Yaya ya furgita ni, idan nace muku shine Proff karku musa min, abinda ya bani mamaki taya akai ya rigani shigowa cikin gidan nan? na rumtse ido sosai jikina ya hau mazari, idan Yayana ba aljani bane to shi wane? adu'oi na shiga karantowa cikin raina ina ƙara damƙe hannun Gwaggo wadda ta zubawa sarautar Allah ido, har ina neman tasar hankalinta. gaba ɗaya su ma kuma saina basu tsoro saboda yanda nake yi, ina buɗe idona naga yana kusanto inda nake wanda shima ya cika da mamaki gami da tsoron abinda ya sameni, na shiga nuna shi da hannu ina karkaɗawa nake cewa,"karka zo inda nake, karka kusanto ni tunda kai ɗin mayaudari ne". yanda nake kamar wata wadda ta tada iska, ni kuwa tsabar baƙin cikin yaudararmu da yay shi ya tsayan a rai, lallai yayi wasa da hankalina, naji Gwaggo ta doka wani uban tsaki ta yarfar da hannuna. domin itama ta fahimci abinda ke tsakanina da Yaya, sai dai tunda ta gane soyayya muke ta nuna min bata so domin ba abune da zai ɗore ba. ta wuce tana faɗin,"aikin wofi, to da yake sonki sai akace miki da ke kaɗai zai zauna? to ko ni da kike ganina duk wannan uban kyan nawa Sahibina bai zauna dani ɗaya ba, haka ya ringizani da ɗai ɗai har ɓiyu, atoh tun wuri ma ki bar damun kanki akan ɗa namiji". wani takaicinta ya kamani, ni ga abinda ke damuna ita kuma tana wani zance na daban. Yayana yana zuwa ya damƙi kafaɗuna yana girgiza ni da tambayar mene, nayi watsi da hannayensa, kallonsa nake da takaici ina zubda hawaye, sam bama zan iya kwatanta haushinsa da nake ji ba a raina. cikin muryar da ta jiƙu da ɓacin rai nace. "a tunaninka mu kayiwa,? to ka yi babban kuskuren tunani domin kuwa kanka ka cuta, Allah ma ba zai barka ba domin kaci amanarmu, musamman ma ni kaci amanata kuma bazan yafe maka ba, mayaudari munafuki kawai". ai ban kai ga rufe baki ba tass naji an ɗauke ni da mari, ina kallonsa yake nuna kansa yana cewa,"me nayi miki da har za ki dinga dangantani da waɗanan maganganun?". cikin ƙunar rai nake kallonsa, cikin baƙin ciki da takaici na ɗaga hannu nima na yarfa masa maruka har guda biyu, domin nima a hasale nake kamar yanda yake. na ɗaga muryar da ta karaɗe duka parlon nace,"an gaya maka ɗin, idan da kalaman da suka fi wannan you deserve them, me kake nema a rayuwarmu da ka biyo mana ta wannan siga? who are you?". wani irin kallo yake min na rashin fahimtar inda maganarki ta dosa, na cakumi kwalar rigarsa ina daɗa ɗaga siririyan muryana nake cewa,"Ka faɗa min waye kai? kuma mene dalilinka na shigowa rayuwata?". yay watsi da hannayena, shima ransa a ɓace kuma murya a ɗage yace,"na shigo rayuwarki ko kuma kika shigo da ni rayuwarki? idan ke zan miki ƙarya tunaninki zan zauna nayiwa manyan mutane ƙarya ne, wallahi inda na san nufinki wulaƙantani ne da cin zarafi ne da ban jinginu dake ba...me tasa za ki saka min da hakan a lokacin da na riga na gama sakankanewa?". na juya na kalla Gwaggo nace,"Gwaggo shi ɗin azzalumi ne kuma mayaudari, kice ya faɗa miki gaskiyar shi wane, ni ban yarda da shi ba, wallahi idan ba mugun mutum bane to aljani ne, ki tambaye shi Gwaggo kiji". kamar bada ita nayi magana ba tayi min shiru, Ya juya zai fice ransa a dagule. nac,"idan kana da gaskiya ka tsaya mana". tsayawa yay ba tare daya juyo ba, naje gaban Gwaggo ina daɗa ce mata,"Gwaggo ki tambayeshi shi ɗin wane? waya aiko shi? kuma me yazo yi mana?". tana sauya channel tace,"yo dama ki tsinci mutum a bola kiyi tunanin bil'adama ne, a wannan yafi kama da aljan". na turo baki ina mata wani duba saboda gaba ɗaya ita ɗaukan abin wasa take, na kuma ce mata,"Gwaggo ki bar batun wasa Alah shi ɗin dama na jima ina zarginsa, yau kuma na ƙara tabbatar da zargina akansa, yaudararmu kawai yake da sunan shi ɗin ba kowa bane, yana wasa da hankalinmu, Gwaggo ki kore shi kice ya bar mana gida kar ya cutar min daku". sai yanzu dai taga da gaske ne nake maganar, babu batun wasa, ta dube shi dake tsaye hannayensa zube cikin wandon aljihu kamar yanda ya saba, sai idonsa dake rumtse gam. a hankali yake magana. "Dama bada niyyar taimakona kika shigo rayuwata ba?, me kike zargi akaina da har kike min kallon macuci?". "na shiga uku". na faɗa ina ɗora hannu akaina. "Gwaggo ke faɗin ni dai daka zo gidan nan tsakani da Allah na ɗauke ka, ina jinka kuma tamkar jikina, bana taɓa banbantaka dasu Abba ba, shin Yaya maganganun da take gaskiya ne?". gabanta yazo ya durƙushe ƙafafunsa. "Gwaggo kamar yanda na faɗa miki a baya yanzu ma haka zan maimaita miki, na rantse da Allah bani da niyyar cutar da kowa a rayuwata, bare ku da kuka gama yimin gatan komai. ni kaina da Sabina tai yunƙurin taimakona nayi mamaki saboda babu wanda zai so haɗa alaƙa da mutumin da baya da asali, mutumin da baka san shi ba, ki yafe min Gwaggo, ban cuce ku ba kuma ban yaudareku ba, ina matuƙar godiya da kyautatawar da kuka yi min a rayuwa". ya faɗin hakan yana miƙewa, jikina yay sanyi nai saurin kamo hannunsa na miƙe tsaye, nauyinsa ya kamani sai dai wani gefe na zuciyata na rasa me nake ji, wani abune ya tokare wurin. shi kuma ya ɗauke kai daga kallona yay kauda fuska, yana kuma kiciniyar ƙwace hannunsa dana damƙe, murya a hankali nace,"to amma Yaya idan ba kai bane to shi ɗin daya zo wane?. kayi haƙuri na maka bahaguwar fahimta, Yaya ko kaina ka tsinci kanka a irin yanayin dana tsinci kaina za kayi mamaki." "waike maganar me kike ne?". Gwaggo tace dani, ina riƙe da hannunsa na juyo gareta ina cewa,"na rantse da Allah Gwaggo su biyu ne. surarsu iri guda ce, maganar iri guda ce, yanzu haka dana fita wajensa irin kalar kayan nan dake jikin Yaya shima sune a jikinsa, kuma shima ɗin baƙin glass ya saka saɓanin fari daya saba sanyawa, kamar yanda na dawo na tarar da Yaya zaune shima haka na tarar da shi a mota. Gwaggo dole na tsorata nayi tunanin shi ɗin ba mutum bane". na kama hannunsa ina ja nace," idan baku gasgata ni ba kazo muje na nuna maka shi nasan har yanzu yana nan domin na barshi da abinda ba zai iya tafiya lokaci ɗaya ba". ko da muka je gate babu motarsa bare ƙyallinsa, kaina ya kuma ɗaurewa, abin ya kuma ɗaure min kai da kuma tsoro, anya kuwa?. dariyar Yaya tasa ni juyowa ina dubansa, sosai yake dariya wadda har haƙonsa suka bayyana gaba ɗaya,"yarinya ta gama sa ni a ranta tazo wurin saurayinta tana masa kallon ni ne". shine abinda yake faɗa yana kuma dariya har da tafawa. "Yaya kana ɗaukan maganata wasa ko". naji haushi na bar masa wurin. abinda ya ƙunsa min shi na dawo Gwaggo ma ta kuma ƙunsa min, takaici ya isheni na shige ɗaki. cikin kwana biyu gaba ɗaya sai suka koma cewa wai aljanun kaina ne ke buɗe min ido, haka ina ji ina gani da lafiyata amma kullum a cikin yimin hayaƙi ake. na rasa ta yanda zanyi su gasgata ni amma ni dai yanzu ina da yaƙinin Yaya na da alaƙa mai ƙarfi da Proff idan har da gaske ba mutum ɗaya bane kamar yanda na fi zargi, a yanzu jira kawai nake a koma makaranta kamar yanda Farhana ta bani shawara. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(25)* "oak see u letter". na faɗa cikin wayar dake maƙale a kunnena, kuma daidai lokacin da nayi perking motana a parking lot. Hidaya tace,"yauwa karki manta in zaki shigo ki taho min da Arable crop handout ɗin nan". na amsa mata,"ba zan mata ba insha'Allah, bye". na kashe wayan ina jefawa cikin jaka, yayin da Aisha wacce muka fita tare ta buɗe murfin motar ta fita. tana tsaye daga bakin ƙofar tana cewa,"na tafi zaki shigo da kayan ko na ɗauka?". nace da ita a sanda nake fitowa,"ɗauki ki tafi da su, ba zan shiga part ɗinku ba zanyi karatu ne". "oak". ta faɗa tana buɗe bayan motar ta ɗauki kayan da muka amso a office ɗin Baba. ko sanda na shiga ma Gwaggo bata san na dawo ba, ɗakina kawai na shiga nai wanka na sanyo english wears na fito, naci alelen da na tabbatar Gwaggo ce tayi shi saboda yanda yay daɗi. ina gamawa kuma na suri maltina a fridge nayo waje. cikin rumfar bunun dake garden ɗin gidanmu na nufa, na zauna kan deck chair ɗin dake wurin. hannuna riƙe da waya wanda na gaza ɗauke ƙwayar idona akanta tun ɗazu, abar ta batun littafin dana ɗauko zan karanta, dan tuni nayi watsi da shi gefe. kallon screen ɗin wayar nake fuskata sai fitar da yalwataccen murmushi take me cike da annashuwar jin daɗi, hoton Yayana ne na shagala a kallonsa wanda yayi matuƙar kyau, gaskiya shi ɗin kyakykyawa ne, a duk wani kallo biyu da zanma hoton sai na lumshe ido. kuma ban sani ba kawai ta bayana naji an rufe min ido, ban tsorota ba saboda ƙamshin turaren daya daki hancina kaɗai ya riga ya bayyanar min da kowa ne. na ɗora hannuna saman nasa ina ƙoƙarin cirewa, sai ya zuro kansa ta gefen wuyana yana leƙen abinda nake kallo, ina jin hakan nayi saurin kifa fuskar wayan saman cinyata don karya gani. "ni bazan gani ba?". Ya tambayeni cikin zazzaƙar muryarsa me sanyaya ilahirin jiki. ban buɗe baki na ba shi amsa ba, sai ɗaga masa kai da nayi alamar ehh, kuma har zuwa yanzu idona a rufe yake da hannunsa, ni kuwa sai aikin murmushi nake ina jin wani abu me sanyi na tsarga min. "ƙanwar Yaya ki barni na kalla abinda ya ɗauke miki hankali har na jima tsaye anan ba ki san da zuwana ba". gabana ya faɗi, wato ma ya daɗe da zuwa ban sa ni ba. _wayyo Allah yasa bai san abinda nake kallo ba._ na faɗi hakan a zuciyata ina rumtse idona dake cikin hannunsa. ajikina naji ya ƙura min ido yana kallona, duk na jin wani iri a tare dani saboda rigar jikina mara hannu ce, ga saman ƙirjina duk a waje kasancewarsa dukiyar fulanina acike take kuma a sama, abinda ma yasa na fito a haka saboda babu mai zuwa wajen idan ba ni ba, saima Aisha dana gani ranar nan tazo tana karatu zasu fara exams. na yunƙura zan miƙe ya maidani na zauna yana me zagayowa ya zauna kusa dani, yana jana da wasa Alallai saina bashi ya kalla. ina samun damar ƙwace hannuna daga nasa na miƙe da sauri ina ja da baya ina dariyar dake daɗa ƙawata kyawun halittar fuskata, haɓa ya riƙe yana kallona, ni kam sai dariya nake masa. na ɗan tsaya ina cewa,"ka gama ƙiyasce ƙiyascenka amma ni kam bazan baka ka gani ba". nace da shi ina yi masa gwalo. tasowa yay ya biyoni muka fara guje-guje, gaba ɗayanmu ƙyalƙyala dariya muke, banyi aune ba caraf naji ya damƙo hannuna ta baya, muka tsaya muna aikin sauke numfarfashi, ina ƙara ƙanƙame wayata saboda bana so yaga hotonsa da nake kallo. dab dani ya matso kamar zai mannu da jikina, yana zuro kansa ta kafaɗata yace,"wa na kama?". ina maida numfashi na lumshe ido, jikina yay sanyi ina jin wani iri a tare dani saboda yanda tsigar jikina ta tashi sakamakon ɗumin iskar bakinsa dake sauka ajikina adalilin numfashin daya ke saukewa shima. na turo ɗan ƙaramin bakina gaba ina cewa,"to wai miye ruwanka da abinda nake kallo, ni Allah ba zan baka wayana ba". na ƙarasa faɗa cike da shagwaɓata mai narkar da zuciya. juyo dani yay muna facing juna, fuskarsa lulluɓe da murmushi mai kyau, ya kafeni da ido ko ƙiftawa babu, nima hakan take agareni domin tunda na fara kallonsa na gaza ɗauke idona ko da na second. sautin murmushinsa ya fito har haƙoransa farare na bayyana, ya ɗan zoro min ido kaɗan yana ɗaga gira duka biyun. da sauri na sauke idona ƙasa cike da wata muguwar kunya, na fizge hannuna zan gudu ya kuma kamoni yana faɗin,"zo nan sai kin faɗa min mene kike yi da hotona?". gabana ya faɗi na ɗago na kallesa, ya sake ɗaga min gira yana cewa,"uhmm tell me, ai ina ganinki tun ɗazu, me yasa kike kalle min hotona? idan ba haka ba yanzu na shigar da ƙararki kotun Gwaggo". na hankaɗo baki gaba ina ɗan tirtirjewa nace,"wane yace maka hotonka nake kalla, to ni mene zanyi da hotonka da zan zauna ina aikin kallonsa bayan gaka a gida. na ma gane wayo ne kake son yi mani kuma naƙi wayon bazan dai nuna maka abinda nake kallo ba". na ƙarasa faɗa ina siririyar dariya me bayyanar da haƙora. shima dariyar waskewar da nake neman yi yayi, ban aune ba kawai naji ya fizgi wayar hannu, nan da nan kuwa na hau dukan ƙafafu kamar zanyi kuka ina cewa ya bani wayata kar ya buɗe min. na murguda baki ina cewa,"to ai dai ma baka san password ɗin ba, ni ka bani kayata bincike babu kyau". na faɗi hakan ina miƙa hannu zan amshe shi kuma yana kaucewa. kallona yay kawai yayi dariya kaɗan kana yace,"ki ƙaddara ban san password ɗin ba, amma idan na buɗe kyautar me za ki bani?". na ɗaga kaina sama ina nazari, tsawon daƙiƙa ɗaya nace,"shikenan naji in har ka buɗe ni kuma duk abinda kake so ka faɗa zan baka ko menene shi". na faɗi hakan saboda ina da tabbacin ba zai iya buɗewa ba, kusa da shi na tsaya ina kallon yanda zai buɗe ina masa dariya ƙasa-ƙasa. gani nayi yana rubuta Yayana, abinda ya matuƙar bani mamaki, taya akayi yasan password ɗina? bayan wayata bata taɓa zuwa hannunsa ba, kuma ban taɓa buɗewa agabansa ba tunda fingerprint nake amfani. muka haɗa ido ina masa kallo mai alamar tambaya da kuma tuhuma. na tsuke fuska na kama ƙugu ina cewa,"taya akayi kasan passowrd ena? wato ka jima kana ɗaukar mani phone kayi min bincike ban sa ni ba ko?". yanayin irin yanda yara ke rantsuwa yayi yace,"ni wallahi Allah ban taɓa ɗaukar maki waya na buɗe ba, kawai fa nayi guessing ne....to ni dai bama wannan ba tunda na buɗe saiki ba ni kyautar da kika ɗau alƙawari". ya faɗa yana sarƙe hannayensa ta baya. zanyi magana ya tari numfashina da cewa,"tsaya tsaya! tukunna ma kika ce mene za kiyi da hotona?, to yanzu mene wannan, gashi nan a wallpeper kuma gashi a screensaver. shikenan ma gano ki yarinya, wato kina kallona kowanne lokaci don ki cinye min kyawuna ya dawo kanki, saboda na fiki kyau, shine ma idan mun fita kike jin haushi idan ƴan mata na bina, to kuwa wannan kyan ƙwalelenki, ba za ki taɓa ƙwace min shi ba ki kashe min kasuwa". na kalleshi ina hararansa, na ɓata fuska na juyar da kai gefe ina cewa,"su ƴan matansu sune basu san kyau ba da har suke maka kallon me kyau, ni kam dana ke wise ai ban taɓa ganin kyan ba bare har ya burgeni...yanzuma Malaminmu ne yace mu zana mutumin da yafi kowa muni a duniya za'a buga shi a kafa hoton a gidan zoo, ni kuma ina shawara da zuciyata tace nayi drowing ɗinka, kaga ma na taimaka maka tunda kana jin daɗi ƴan mata na kallonka, kaga idan ka fita yanzu sai ake biyan naira biyar naira goma ƴan wahala suyita zuwa can suna ganinka". dariyar da ya bushe da itane yasa na juyo ina kallonsa cike da jin wani abu a raina da na kasa tantance menene, ya dage sai sheƙa dariyar yake babu ƙaƙƙautawa harda su tafa hannu yana kifawa, sai ya ɗago ya nuna ni da yatsa ya kuma kifawa ya tuntsire da wata dariyar. kamar na fashe da kuka don haushi, na juya zan tafiyata ya biyoni yana dakatar dani da cewar,"Malama dakata mana. kin manta da kyautata fa. ki tsaya ki bani sai kiyi tafiyar kije kici gaba da aikin zane na tunda na zama celebriry". "sai ka faɗi abinda kake so ai". ina faɗa ina murguda masa baki don duk haushinsa nake ji, na rufe ido ina ƙara tamke fuska ina hura hanci, kawai kuma sai kuka ya taho min lokaci ɗaya hawaye ya shiga sauko min. jinsa nayi ya kama haɓata yana ja yana haɗa ƴar waƙarsa wai nayi shiru sai kace yaga wata ƙaramar yarinya. "ki taimake ni ki bar kukan nan, ki rufan asiri a wurin Gwaggo kar na shigesu yau a wurinta". na bige hannunsa ina cewa,"ai duk saina faɗa mata ka sa ni kuka, dama tace zata rama min kwaɓe min lallan da kayi. ni ka faɗi abinda zan baka nayi tafiyata, kuma daga yau na bar kulaka". hannuna ya kamo ya jawoni kusa da shi sosai, wanda tazaran dake tsakaninmu ko 1inch bai kai ba. tukunna ya juyar dani ya ɗora haɓarsa bisa kafaɗa yana kewaye cikina da duka hannayensa, ban nuna masa haramcin hakan ba saboda ni kallon matsayi guda da Yaya Abba nake masa, ga kuma wani yanayi da na shiga wanda nasan dole ba zan iya hana shi ba. "Cutie". a hankali ya faɗi sunan daya ke kirana da shi yanzu, yana kuma manne gefen fuskarsa da tawa. na daɗa lumshe ido ina haɗiyar wani yawu kamin na amsa. "ummm". a kasalance sakamakon iskar numfashinsa dake sauka cikin ƙirjina. hannunsa ya ɗago ya nuna ƙirjina saitin ɓangaren zuciyata da manuniyar yatsansa, da wata iriyar murya ya furta, "Cutie nah, Cutien Yayanta, abinda ke cikin nan, abunda ke cikin nan nake so, shi nake so ki mani kyautarsa...kinji dan Allah". da rashin fahimtar abinda yake nufi nace,"ban gane ba. miye ne dama acikin nan ɗin banda ƙashi, indai ba kaina zan baka gaba ɗaya ba ka kaiwa Gwaggo ta dafa maka ka cinye". yay wani murmushi, yana kuma yin ƙasa da murya yake cewa. "nima nafi so ki mallaka min kan naki gaba ɗaya amma bazan cinyeki ba saboda ina buƙatarki". yana juyo dani na fuskance shi yake ƙarasa cewa,"sai dai na tsaga ƙirjina na adanaki a ciki ta yanda babu wanda zai ke kalle min wannan cute face ɗin sai idan ni naso". yana faɗin hakan yana shafa kumatuna da babban yatsansa. tsintar kaina nayi sakin murmushi, iskar bakinsa daya hura min a ido ita ta dawo dani daga duniyar tunanin dana tafi cikin ƙanƙanen lokaci, nai saurin sanya tafukan hannuna ina rufe fuskata. hannunsa yasa ya ɗauke hannun nawa, shima murmushin yake amma mai ɗauke da wata ma'ana, tun daga tsintsiyar hannuna ya kama har zuwa yatsuna yana mai tsugunawa agabana ya dire gwiwansa ɗaya a ƙasa, ya kamo yatsana na kusa dana tsakiya yana cewa dani,"please close your eyes". na rufe idona, zuwa wani lokaci naji ya saki hannuna yana cewa na buɗe idona, ina buɗewa na gansa ya miƙe tsaye, ya kalleni ya lumshe ido, sannan yay min nuni dana kalla yatsuna. ina duba hannuna na furta,"wow". da ƙarfi tare da yin tsalle, ina matuƙar nuna jin daɗina. kallon zoben nake ina jin wani farinciki a raina don ba ƙaramin kyau yayi ba, tsanin jin daɗi yasa na faɗa jikinsa tare na rungume shi. "thanku so Much Yayana, gaskiya naji daɗin ring ɗin nan ya mani kyau kamar ni. na gode, na gode Allah ya ƙara maka kuɗi da yawa". na sake shi ina cewa, "Yayana taya kasan ina son zobe matuƙa". kallona kawai yake da numsassun idanunsa ba tare daya furta komai ba, ina kallonsa na ɗaga masa kai alaman mene, duba da yanda mood nasa ya sauya zuwa damuwa saɓanin ɗazu da yake cikin nishaɗi. kai ya girgiza min alaman babu komai, na zunɓuro baki ina cewa,"to kai kurma ne, kayi magana mana". ya rumfe ido ya buɗe, har yanzu kuma bai ce min komai ba, ina wasa da zoben daya samin nayi ƙasa da kaina ina cewa,"Yayana to ka faɗa min kyautan dana maka alƙawari, ɗazun ban gane me kake cewa ba". murmushi naga yayi, ya lakuce min hanci yana cewa,"zama ki gane ne yarinya mai wayo". yana faɗin hakan ya kamo fuskata yay min kiss a goshi, tukunna ya zuba hannayensa a aljihu ya juya ya tafi, ya barni tsaye ina aikin juya zoben dake hannuna wanda har yanzu jin daɗi ya hanani rufe bakina. dukkan abinda ke faruwa tsakanin Sabina da Alhussain akan idon Haidar dake window a tsaye, be saki labule ba sai daya ga barin Alhussain a wurin, samun zuciyarsa yayi da babu daɗi, ya jingina kansa da bango tare da rumtse idanuwansa. lokaci ɗaya kansa ya hau ciwo, ya dafe ɓari ɗaya daya fi masa azaba, idanuwansa suka fara tara zafin baƙin ciki, zuciyarsa kuwa ta canza takun bugunta, gaba ɗaya duk wasu sassa da gaɓoɓin dake jikinsa sun fara shiga wani yanayi na azaba. jiri ne ke ɗibarsa sosai dan haka ya faɗa kan gado yana fuskantar sama, yana sauke nauyayyiyar ajiyar zuciya. idonsa na rufe yake hasko abubuwan da suka wakana tsakaninsu, mai kama da zallar soyayya, abunda yafi tsaya masa arai yanda Alhussain yasa hannunsa acikinta da kuma haɗa fuskarsu, gashi har yana da damar yi mata kiss kuma yasa mata zobe, Wata bahaguwar ajiyar zuciya ya ƙara yi, hannunsa dafe da saitin zuciarsa. tunda yake bai taɓa shiga tashin hankali irin haka ba, sai yanzu ne Yake mamaki ƙwarai matuƙa da yanda yake jin Sabina a ransa, me yasa tun farko ya kasa ɗaukan hakan a matsayin *SO* ?, mai yasa ya kasa barin yarinyar ta saba da shi ko da ace bada sanin yana sonta bane, shi kansa ya san babu kowa a zuciyar Sabina amma yanzu gashi farat ɗaya wani daban yazo ya shige zuciyarta, wani irin ƙullutun baƙin ciki ne ya tsaya masa a maƙogaro. da ƙarfi yasa hannu ya daki goshinsa, jin zuciyarsa yake na neman fitowa, ƙululun abinda daya tokare masa zuciya SO ne ko kuma KISHI? idan duka biyun suka haɗe suka tabbata ya zaiyi? dan ba zai taɓa iya furtawa yarinyar cewar yana sonta ba, kuma gashi ba zai iya jurar ganinta da wani ba. zuwana compound nayi kiciɓis da Umma, na rissina ina cewa,"Umma ina yini, ya sauƙin jiki? Allah ya ƙara lafiya". na haɗe maganta duka don na san ba lallai ta amsa min ba. ina kallo ta taɓe baki bayan ta kalleni, na duƙa ƙasa zan cire abu a takalmina naji tana cewa. "ahaka dai za'a lalace, anƙi ai aure sai aikin jera kafaɗu da manya saboda babu kunya, anje an ɗauko mutum da niyyar taimakonsa an ɓige da iskancin banza a bayan idon mutane, to bari Baban naki ya dawo zan zayyane masa komai saboda baza aci amanata da shi ba, tun wuri yasan irin matakin da zai ɗauka kamin kija mana abin magana". na ɗago na danƙara mata harara kamar idanuwana zasu zazzago nace,"A kaf duniya inda mai yimin mugun baki kece ta farko, Umma ya kamata ki lura ki gane ni ba sa'arki bace, kija girmanki ki kama shi ki riƙe, ni ɗin fa da kike haukar kishinki akaina ba nice kishiyarki ba, amma duk kinbi kin ɗora min karan tsana saboda kawai soyayyar da mahaifina yake min, to hala idan bai so ni ba ke zai so? karki manta kefa matarsa ce da zai iya sauyaki duk sanda yaso, ni kuma ƴarsa ce abadan abadina, so babu yanda kika iya da ganina, da za ki haƙura ma da kin hutawa kanki da cutar hawan jini, idan ba haka ba soon za ki kamu da ciwon zuciya saboda a kullum soyayyata ƙara ninkuwa take a zuciyar Babana, atoh, saboda haka please ki fita a rayuwata. Lalacewa kuma da kike magana ki gani akan Ƴaƴanki, kuma idan Baba ya dawo kika fasa karanta masa komai ke ɗin ba ki amsa sunanki ba". na nufi side ɗinmu zan shige tace,"Sabina" Cak na tsaya na juyo ina kallonta ina kuma jifanta da harara da murguɗa baki. tana nuna kanta take cewa,"Sabina ni kike gayawa waɗannan maganganun saboda ba ki da mutunci ba ki da tarbiyya, ni ɗinfa matar ubanki ce". na taɓe baki nace,"so what, dan kina matar ubana ai ba yana nufin ke ɗin uwata bace, kuma ko mene na gaya miki aike kika jawo tunda ba kya kama girmanki, ke kullum burinki kija tashin hankali acikin gidan nan, to duk wata masifa taki ta ƙare miki ke ɗaya". Yaya Abbane ya iso wurin, ya tambayeni meke faruwa, na zayyane masa komai. ya dubeta cike da jin haushi yace,"wallahi ke dai Umma anyi girman banza, ki zauna ki dinga jan ƴar cikinki da rigima. kuma a haka kike so a dinga yi miki biyayya, to ki fara kama kanki kamin nan aganki da gashin ido, ni dai ina gargaɗinki kar ki ƙara yiwa ƙanwata mugun baki, don gaba abin ba zai mana kyau ba". Umma ta ƙufulu tana huci tace,"to Abba ko dukana zaka yi ne sai nasan da gaske mataki zaka ɗauka". yace,"to wuyar dukan za kiyi ne, ki ƙara taɓa min ƙanwa ki gani".ya faɗi hakan yana cewa da ni,"mu tafi". [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(28)* bakin wani tangamemen gate motar tasu ta tsaya ƙirar lexus, kallo ɗaga zaka yiwa gidan kasan ba ƙanan mutane ke rayuwa cikinsa ba, dan tun daga farkon estate ɗin zaka san its not possible ma talaka ya shigo shi, iyakan tsaruwa gidan ya tsaru kamar a ƙasar turai, ƙaryar baki yace zai fasalta haɗuwar ginin, gaba ɗaya wajensa kewaye yake da wasu irin flowers masu ƙawata kyawun wuri. a yayin da mutanen dake cikin motar fuskokinsu ke cike da annashuwa. driver ya danna horn da sauri gate man yazo ya buɗe, suna shiga kai tsaye wajen entrans shiga main part na gidan driver yay parking motan, ƙasan wajen gaba ɗaya shimfiɗe yake da grass carpet sai hasken fitilu multi colour dake haska wurin sai kace hotel, driver ya fito cikin sauri ya buɗe booth ya ɗauko wheel chair, sannan yazo ya buɗe ma Muhsin murfin motar, sai dai bai fito ba yana zaune ya ɗauko waya a aljihunsa yana dialling number. daga cikin kantamemen parlon gidan irin 100 by 100 ɗin nan, parlon ya gaji da haɗuwa kamar ba za'a mutu ba, kewaye yake da wasu lumtsatstsun cushions na alfarma, a cikin ɗaya daga cikin cushions ɗin mai zaman mutum guda, farar dattijuwar Mata ce kyakykyawa daka ganta kaga shuwa arab, ta dubi agogon gwal ɗin dake hannunta, ta sauke numfashi, damuwa a tattare da ita tace,"Muhsina do you look up the time? your brother is still not yet back, duba ki ga har da additional five minutes on his return time". Muhsina na zaune kan ɗaya daga kujeran dining tana cin fruit tace,"Mom, thats what am thinking, but he might be on his way back ko kuma ya tsaya wurin seminer da Daddy yace zaije". Mom tace,"I don't think so, he could have informed me if that was the case. wayansa ma fa not recherble gaba ɗaya, fatana Allah ubangiji yasa lafiya". she spoke in anxiety way har tana jin ƙirjinta na beating faster. "ni fa am worried da rashin dawowan yaron nan har yanzu, is everything alright? haba he's a determined boy, banda haka me ne zaisa shi fita aiki? ya zauna wuri guda tunda ubansa ya tara dukiyar nan ya ajiye musu. anyway to ya dawo yau ɗin ya sameni". Tsohuwar Matar dake sakkowa daga stairs ke wannan maganar cikin faɗa, sanye take da lapaya orange colour fuskarta kuma ɗauke da glass me yanayin na fashions amma kuma medical ne, kana kallonta kaga mahaifiyar Mom saboda tsananin kamansu, Mom da Muhsina suka maida dubansu gareta. ta kuma cewa,"Fa'iƙa zaman me kike da ba za ki tashi muje dubo shi ba? yaran da ba cikakkiyar lafiya gare shi ba". Mom tace da mahaifiyartata, "Anie we are sitting here driver went to pick him up. ni ba wannan ba ma, not knowing the reason for their returning early shine yafi damuna, since he had never reached such a time. ga wayoyinsa duka basa tafiya". Anie sighed and said,"shi drivern babu waya hannunsa ne da aka gagara tuntuɓarsa aji halin da suke ciki?". dukansu basu kai ga kuma furta ko wacce kalma ba wayar Muhsina ta fara ringing, ta ɗauka da sauri tana cewa,"yauwa Mom gashi ma ya kira". daga ɓangaren Muhsin yace,"Sister am back". yana faɗin hakan ya kashe wayan. dukansu suka sauke ajiyan zuciya, sai yanzu nutsuwa ta samu a garesu hankalinsu ya kwanta, lallai ba ƙaramin ji da shi ake a wannan gida ba, minti biyar kawai ya ƙara akan lokacin dawowansa amma hankalin kowa ya tashi, ana tunanin ko ba lafiya ba, tabbas shi ɗin ɗan gata ne gaba da baya. Anie tace, "lamarin Hassan sai shi, wato har yanzu idan ya dawo dole dai sai Muhsina taje tarbo shi tukunna zai shigo". Mom tace,"ai haƙurinsa ɗaya idan bata nan, amma anan kuma dole ni ce zan fita. yace damuwa yake shiga indai yagansa shi ɗaya yana tafiya a keken nan, kuma baya so yake saka ma'aikata turo shi". Muhsina na isowa entrance ta iske Mami na balbalin masifa, ita dai wannan mata kwai jarababba, ko da yaushe acikin masifa ta ke muddin wani abu zai shiga tsakanin ƴaƴanta dana kishiyarta, Muhsina tayi tsaki taja ta tsaya cike da takaici, ta tsaya ne kawai saboda Mom ta hanasu saurarenta idan tana wannan haushin karen, amma da bata isa ta tsaya kan Brother tana masa wannan hargowan ba. Khaleesat ita dai ƙuri tayi ta rakuɓe daga bayan keken Muhsin, ita kanta yarinyar bata son wannan halin na uwarta, sai noƙewa takeyi gudun karta kawo mata duka, muryarta a hankali tace,"Mami kiyi haƙuri please". aiko kamar ta watsa mata petrol ta damƙo kafaɗarta tana cewa,"kin rufe min baki ko saina zubar miki da haƙora anan wurin, shashasha wadda bata da kishin uwarta, to dama kin zama ma'akaciyar jinya ne da kika zo kinibibin taimako?, ke ga ƴar neman suna, ko kuma dama ke kike taimaka masa tun asali?. Abid ne ya rasa ƙafa da za ki tashi hankalinki akansa? keken nasa ai da inji yake aiki me ya hana ya kunna ya gurgura da kansa?, a'a ke ga ƴar neman gindi ya zama dole kiyi aikin da babu lada, ni dai wannan ƴa banda a hayyacina na haifeki wallah da zance ba jinina bace ke, tunda na haifeki ba ki taɓa faranta min rai ba kullu yaumin acikin baƙanta min kike, anya Khaleesa kina so ki gama da duniya lafiya kuwa? ni fa uwarki ce wata goma cif haka na ɗau cikinki. na kuma sha baƙar wuya kamin ki fito saboda an riga an min asiri ba'aso na haihu dan baƙin ciki da zalunci, haka aka jefeni da ciwon nono saina waccan shegiyar matar ubanki yasa aka dinga ɗirka miki kina zuƙa, to banda Allah yasa ma na tashi tsaye na nemi maganin tsari a gareki ai wallahi da babu abinda zai hanaki ɗauko baƙin halinta gaba ɗaya tunda kin sha a ruwan nono. banza kawai kin wani taho da rawar jiki kamar ƙanin uwarki ne ba lafiya, ana gudun nakasassu amma ke tusa kanki cikinsu kike saboda hankali bai gama isarki ba, haka kawai ina zaman zamana ki jawo min masifa kema ki shafi ciwon gurgunta a haɗa biyu, dama ana min baƙinciki da ku, yanzu ace akanki tattalin arziƙin ubanki yake ƙarewa, dan shi Ubanki ko duka arziƙinsa zai ƙare wurin ɓarnatarwa wannan gurgun ba zai taɓa gani ba tunda tsatson waccen ne, ta riga ta gama da shi, amma ke kuwa daga ke harni wuya zamu sha". ita dai Khaleesa shiru tayi ta rasa abin cewa, yanzu tana buɗar baki Mami zata aikata abinda tace, ita kuwa bata shirya rasa haƙoranta ba, yanzunma sai dai Allah ya kiyayeta idan sun koma part nasu, dan Mami ba dai mita da jaraba ba. Mami ta maka ma ta wani shegen kallo tare da kamo kunnenta ta murɗe har saida Khaleesa tayi ƙara. "yau ya zama rana na ƙarshe da zan faɗa miki bana so kike kula wannan gadon tsiyar, idan kuma kinƙi ji wallahi saina tsine miki tunda ke kunnen ƙashi gareki, ke ko uwarsu kika gani kika gaisheta ban yafe miki ba, sau nawa zan faɗa miki bana sonsu kamar yanda bana son uwarsu, sam-sam kin gagara gane cewar uwarsu maƙiyita ce saboda ƙwaƙwalwar kifi gareki, to kici gaba da kulasu ki kalla yanda zanyi raga-raga dake a gidan nan, sokuwar banza mara wayo, su ba ki ga duk abinda uwarsu tace ba basa ƙetare shi, amma ke saboda ban isa ba ke maƙiyana su kike so, da ace ke kaɗai Allah ya bani da tuni baƙin cikinki ya kasheni, kina kallo ubanki bai ɗaukeni komai acikin gidan nan ba, sai abinda waccan shegiyar matar tace shi zai hau ya zauna akai, ke wannan bai isheki aya ba ki gane ba'a ƙaunar taki uwar?, Abid kaɗai ke goya min baya kamar shi kaɗai na haifa...to dan uwar ubanki ɓace a wurin nan". ta faɗa tana hankaɗata, sannan ta koma kan su Muhsin tana cewa,"ku kuma daga yau karku ƙara kula Ƴaƴana tunda ba Fa'iƙa ce ta haifa min su ba, idan kuma kunƙi ji da ku da shegiyar uwar taku...". Cikin fushi Muhsin ya katseta da cewa,"saboda muna yi miki shiru hakan baya na nufin muna tsoronki bane, kina cin darajar masu daraja ne, karki ƙara sako mahaifiyata a cikin haukarki, ki tsaya a iya kanmu domin akan mahaifiyata zan mance da darajar Daddy da kike ci naci muntuncinki iya gwargwadon ikona, dan haka ki kula ki kuma kiyaye". yana faɗa ya kunna kekensa ya bar wurin. Muhsina tayi wani murmushi tana nunata da hannu sama da ƙasa tace,"ki ji, ki kuma kiyaye, domin idan kika gama hassala Brother nah da wannan haukar naki da baida ranar ƙarewa, abin ba zai miki kyau ba. dama darajar Daddy da Mom yasa muke ɗaga miki ƙafa, su kuma ƴaƴanki da kike magana akai sai ki jira wanda ya isa damu yazo ya bamu wannan umarnin tukunna, dama Khaleesat ce kaɗai tamu ba wannan ɗan daban yaron ba". tana faɗa taja tsaki ta bangajeta ta wuce. tunda ya shigo Mom ta kalla yanayinsa tasan anyi ta faru, kasancewarsa mutum mara fushi, da wuya kaga ransa ya ɓaci, ya kanyi duk yanda zaiyi wajen ɓoye ɓacin ransa. cikin hanzari ta bar abinda takeyi ta ƙaraso inda yake, tayi swith ɗin machin nasa off ta ƙarasa tura shi, ta kamashi ta zaunar da shi kan kujera, da duka tafukan hannunta ta tallabi fuskarsa tana cewa,"whats happened to my one and only son? what made him sad? after knowing Ɗana baya fushi me yasa zanga hakan yau?". Muhsina dake shigowa tace,"wace banda waccan akuyar matar, don Allah Mom allow us to teach her lesson since she will never be smart. kawai sai ta dinga haukarta tana sakoki ciki tana zaginki, we know your worth, please Mom ki bamu go ahead ɗin gyara ma ta zama". Mom tai ma ta wani kallo tace,"idan baku gyara ma ta zama ba kwa kashe mahaifinku ai, you know him very well he does'nt like any commotions, yanzun nan sai jininsa ya hau. him self knows muna haƙuri ne da ita that is why he use to praises us. so ni ban baku goyan bayan biye mata ba, duk abinda zata yi muku kuyi banza da ita, babu ruwanki da shiga sha'anin haukarta, idan kuma kun shirya rasa mahaifinku to ni ban shirya rasa mijina ba. duk wanda ya kuma saurarenta cikinku i will be angry with him". Muhsina ta zauna tana fushi bayan ta kauda keken Muhsin zuwa ma'ajinsa. Anie tazo ta rungume Muhsin tana masa welcome, dake wannan itace al'adarsu. tana cewa da Mom,"wai Fa'iƙa har yanzu Na'ima bata sauya zane ba dama?". da yake 2days kenan da zuwanta daga Mali. Mom tayi murmushin takaici tace,"tana nan a yanda kika santa, sai abunda ma yake ƙaruwa. ba dan ma Daddynsu tsayayyen namiji bane ai saita fi haka". "To Allah ya shiryeta ya ganar da ita. ke kuma Muhsina Allah ya fiddo miki mijin aure ki tafi naki gidan kema ki huta da takaicin matar uba". "tab ai Anie ai hankalina ba zai kwanta ba, saboda Mom sanyi-sanyi zata dinƙa ma ta, ƙwamma na zauna kusa da Mom yanda duk randa na kasa haɗiye fushina zan kwarfe ƴar banza ta zube a ƙasa". Mom ta dawo ɗauke da tray na abinci tana cewa,"a wani hadisi manzon Allah S.A.W yana cewa ba mai ƙarfi ne yake buga mutane da ƙasa ba, mai ƙarfi shine yake mallakar zuciyarsa yayin fushi. ni ba komai yasa nake daɗa tausar zuciyoyinku ba sai dan tunawa da wannan hadisi da nake saboda hadisi ne da yake nuni da muhimmancin haƙuri. so kiyi ma ta abinda yafi kwarfewa ma in kin tashi, ni dai duk wanda ya kashe min miji ba yarda zanyi ba, dan mijina zaman lafiya yake so...kuma akan mijina zan iya kai ƙarar mutum kotu". Muhsina tayi ƴar dariya tace,"Mom nima fa ina son Daddy, inaga ma na fiki sonsa". Mom tace,"banga alama ba kam". ta zauna tana feeding Muhsin kamar ƙaramin yaro, shi kam cike da jin daɗi yake amsar abincin yana kallonta, sai hira ta ke masa duk don ta kawar masa da ɓacin ran da abokiyar zamanta ta haifar masa. ta duba Muhsina dake aikin ɓata rai tace,"am sorry daughter". tayi knooding kanta kawai bata ce komai ba. bayan Mom ta gama bashi abinci ta ɗauko magani ta shafa masa a ƙafafunsa tana massaging a hankali. tace da shi,"when will your Daddy going to return?". yace,"tomorrow by now insha'Allahu". "Allah ya dawo mana da shi lafiya". tace tana ɗaga ƙafafunsa ta ɗora kan tumtum. Anie tace,"to ke dama ba ki san lokacin dawowan mijin naki ba sai kin tambayi nawa mijin". Tana murmushi tace,"Anie ai ya fini kusanci da shi ta wannan ɓangaren, da lokacin tafiyansa dana dawowansa duk a wurinsa nake ji. ina so ya dawo ne mu koma wurin mai maganin nan tunda yana jin daɗinsa, yanzu fa har motsa ƙafan nasa ya kanyi kuma ba ta cika yi masa ciwo ba". Anie tace,"to ai dama kune da kuka liƙewa na asibiti, tunda naga irin kuɗaɗen da ake kashewa daga wannan ƙasa zuwa wannan ƙasa an gagara gane taƙamemen me yake damun ƙafar jikina ya fara tsinkewa da lamarin ciwonsa, tun a baya na faɗa miki a haɗa da wurin Malam ƙwarai a nemi ayoyin waraka za'a dace tunda lamarin yafi kama dana jinnu". Mom tace,"Anie it's not my fault. Daddy ne ba zai yarda ba sai yace dole sai asibiti. yanzu kinga shi wannan Malamin garin habba yace a kwaɓa da man zaitun Allah idan na shafa mishi ba ki ga daɗin da yake ji ba. amma asibiti sai muje a haɗo mu da maganin sama da 50k in za'ayi kwana nawa ana amfani da shi ba wani sauƙi da za ki gani". "to Allah ya bashi lafiya. itama kuma Muhsina ya kamata a nemar ma ta magani gaskiya. dan na fara tsorata da al'amarinta. ace shekara 30 mace taƙi auruwa duk wanda yazo sai an gama magana al'amari ya lalace. dole itama akwai ayar tambaya akanta, idan zaku koma ɗin har ita za'a tafi". Mom ta kalla Mushina taga yanda ta shiga damuwa, sai tayi saurin kawar da zancen da suke da Anie, don bata son ganin yarinyar a damuwa. a ɓangaren Mami kuwa rufe Khaleesat tayi da duka, sai da ta tabbatar jikinta ya gaya ma ta sannan tace ma ta,"kuma kinji na rantse miki ko, kallon arziƙi wannan kika kuma yiwa Uwar nakasashshen yaron can sai kinci uwar ubanki, bare ta kai ga har kin buɗi baki kin mata magana. matsawar ba zaginta za kiyi ba to wallahi ban yarda da kiyi ma ta magana ba ko da kuwa a gaban ubanki ne". Khaleesat na kuka sosai tace, "Amma Mami...". cikin tsawa ta dakatar da ita da faɗin,"idan kika min magana sai na miki abinda yafi haka, ke kinga irin cin zarafin da wannan figaggiyar kazar tayi min yanzu kuwa?(Muhsina), amma ke shegiya sam ba ki lura da irin walaƙanta ni da ubanki ke yi akan uwarsu sai kike liƙe ma ta kamar itace tayi naƙudarki". "to Mami ai shi Daddy ba sonki ne ba yayi ba halinki ne baya so". a fusace Mami ta gwabje ma ta baki,"ni kike gayawa haka saboda ba ki da mutunci, uwarki ce fa ni, Khaleesat anya ban taɓa yi miki baki ba kuwa saboda na fara tsorata da lamuranki". kuka sosai Khaleesat ke yi, suna haka sai ga ƴar aikinsu ta shigo, ta duƙa ta gaida Mami amma ko amsa ma ta bata yi ba, sanin hali yasa ba ta damu ba, ta miƙawa Khaleesat baƙar leda tana cewa,"Anty gashi mai gadi ne ya kawo yace a ba ki inji Malaminku". ta amsa ba tare da tace komai ba, ta miƙe cikin sauri zata wuce ɗaki gudun kar Mami ta tambayeta menene, aikuwa bata ida zance zuci ba Mami tace,"wait, weting be inside the leather?". shiru tayi tana tunanin abin cewa, ta doka ma ta tsawa da sake faɗin,""am i not asking you? bani nan na gani". ta faɗa tana miƙa hannu zata amsa ita kuma duk da haka taƙi bata, gashi har yanzu ta gagara sharto ƙarya da zata faɗa tunda bata saba ba. Mami ta kama ƙugu tana kallonta, kamin tayi kanta tana cewa,"ke dan ubanki what are you hiding from me da ba kya so na sa ni? mene aciki nace?". ganin zata duketa tace,"Mami magani ne". "Magani!". Mami ta faɗa da mamaki, kamin ta ƙara cewa,"wanne irin magani? ciki kika yi da Malamin makaranta zai kawo miki maganin zubarwa?, maganin mene? ko kuma da gasken ciki ki kai kamar yanda tunanina ke bani". ta tambayeta a tsawace, jikinta na kyarma ta hau girgiza kai tana cewa,"Mami ba ciki nayi ba. Maganin Brother Muhsin ne, na faɗawa Malaminmu matsalan ciwon ƙafarsa ne shine yace zai ke taimaka mana da tofi na adu'a a dinga bashi insha'Allahu zai warke". Mami ta hau jijjiga kai tace,"Allah zabiya, kice kin shahara da yawa. to shi dama Hassan ɗin ce miki yay yana biɗar taimako daga gareki? a'a ko dama duk cusa kan naki ne ya shura haka?". tana girgiza ma ta kai tace,"a'a kawai dai nce nasa ake masa". "to dama kin kai tsawon yaushe kina karɓar masa maganin?". "an kwana biyu, shine ma har yaji daɗi yanzu yana iya motsa ƙafan kaɗan...". ai bata ƙarasa ba Mami ta kunce ledar ruwan tofin adu'ar ta watsa ma ta shi tas a fuska. "shegiya uwar cusa kai da neman gindin zama. ina tambaya kuma kina bani amsa ko kunya, ke alallai sai kinyi suna a wurin ubanki ko, saboda kinga babu abinda yake ƙauna sama da ɗansa. to kije kici gaba da wahalar da kanki kina karɓo masa magani, wannan ɗa dai yanda kika taso ki ganshi a haka har abadan abadina ba zai taɓa takawa ba, a haka zai ƙare a wannan keken. kin ma ji na gaya miki, insha'Allahu ba zai warke ba, ni da ace ma ina da damar da zan ƙarasa ƙafafun ai saina ƙarasa su ko da kuwa da bin bokaye ne, dan haka sai kiyi ta wahalarki mu gani da adu'arku da tawa wacce amsashshiya". ta shige ɗaki ta barta anan, ita kuma ta durƙushe tana kuka cike da takaicin wannan hali na uwarta. Abid ya shigo ya sameta ahaka, ya nemi kujera ya zauna a hakimce yana ma ta wani mugun kallo, ƙafa ɗaya akan ɗaya yana girgizawa. "kin bar kukan nan ko saina tashi na zane miki jiki". yace da ita murya a ɗage. ta dube shi tace,"Bross dan Allah ka cewa Mami ta sauya halinta wannan ba hali ne mai kyau ba". shima murya a fusace yace,"ke ai jaka ce, ba ki san inda yake miki ciwo ba sam. taya za'a Mami ta ƙaunaci mutanen da suke sa ubanmu ya muzguna mana. tunda kike kin taɓa ganin Daddy ya ɗorani akan wani harkar business ɗinsa?, ya ɗau komai ya bawa wancan Muhsin ɗin, shege Allah ne ma yasan manufar jaki da bai bashi ƙaho ba, shi yasa aka riƙe masa ƙafafu". ta tashi zata wuce ɗaki tace,"ai mai gaskiya ake ɗorawa akan komai ba maha'inci ba. da kayo kyawun hali irin nasa da babu ta yanda Daddy zai nuna banbanci tsakaninku". tana ganin ya biyota tai hanyar ɗakinta ta gudu, tana faɗawa ciki tasa key ta rufe tana sauke nauyayyar ajiyar zuciya, dan da ace ya kamata sai taci ɗanyen kashinta yau. washe gari ƙarfe biyu na rana Daddy ya dawo daga Italy daya tafi. Muhsin na zaune kujera ɗaya da Daddy a kusa da shi, suna magana ƙasa-ƙasa da alama zancen sirrinsu ne, suma gefe ɗaya su Mom ke tasu hiran. Daddy ya lura tun ɗazun idon Muhsina na kansu, so kawai ta ke taji me suke cewa, yay murmushi cike da tsokanar ƴar tasa ya kuma yin ƙasa da kansa suna ci gaba da mgana. da ƙarfi Muhsin yace,"a'a Daddy ba ita ya kamata a bawa sabon company ba, Muhsina ai tayi yarinya da yawa, macece fa ita ba zata iya aiwatar da ayyukan company ba, a barta kawai da lecturing nata idan yaso sai a bawa Abid, shi zai iya lura da komai". ai kuwa tana jin haka ta miƙe ta fara dukan ƙafa tana kukan shagwaɓa har saida ya koma na gaske, tana cewa da Mom,"Mom kinji abinda Brother yake cewa ko, shi dama duk abinda yaga za'ayi min sai yace a'a, shi Abid ɗin ba ni ke gaba da shi ba. haka fa aka yimin wancan karon ma, ni dai gaskiya Daddy ban yarda ba". Daddy yana dariyar manyance yace,"to kwantar da hankalinki Daughter nah, we're just kidding you". sai ta fara dariya itama ta dawo kusa da Daddy ta zauna, yasa hannu ya kwanto da ita jikinsa yana faɗin, "wato dai sirikina zai sha fama, har yanzu kinƙi girma". kunya ya bata tai saurin rufe fuskarta. Muhsin na duban Mahaifiyarsa yace,"Mom kin manta ba ki faɗawa Daddy saƙona ba ko?". tana masa wani duba tace,"O'O! ba mantawa nayi ba, ina jira ne ya gama hutawa sai na sanar masa". Daddy yace,"hutun mene dama zan kuma yi?, good 3hours da dawowa na fa, hutawana yafi saƙon ɗana ne?". yay maganar da sigar faɗa. tace,"kayi haƙuri, dama cewa yay na sanar maka aure yake so domin ya samu mata, sauran bayani kuma kaji daga gare shi". Daddy ya dubi ɗansa cike da farinciki a fuskarsa yace,"are you serious? da gaske ne ka samu wadda ta yarda da aurenka a haka?". Ya ajiye file ɗin hannunsa gefe guda ya kamo hannun Muhsin yana daɗa kallonsa yace,"ina jinka son, ka sakani a farinciki, wace kake so kuma take sonka?". Shafa ƙeya Muhsin yay yana sunkuyar da kai ƙasa yace,"Daddy da gaske ne, Yarinyar ta aminta da ni". sai kuma ya marairaice fuska yace,"amma Daddy kar ayi westing time saboda ina gudun mahaifinta ya bawa wani ita, ba zan iya jurewa ba". Murmushi Dad yayi, ya shafa kan ɗan nasa shima kuma ya shafa gemunsa kafin yace, "Okay Son, Anything for you, ba zanyi sanya ba zaka sameta insha'Allahu. Uncle naka baya nan yana Cairo, but ending of this week zai dawo, so as soon daya dawo za muje mu gana da mahaifinta". Muhsin ji yake kamar zai mutu dan murna, ya kusa mallakar Beauty tasa, duk da ya yarda bata sonsa amma ya yarda zata so shi yayin daya mallaketa. Daddy yace,"Anan garin ta ke ko a wani state ɗin ka samo ta?". yace,"anan Abuja ta ke sai dai ban sa ni ba ko ƴan asalin ina ne". "Okay son, it shall be well, za muje ayi komai, worry not kaji. but can i get some information about her? like part of her education and her parents". yace,"Yeah Dad why not, her name is Sabina Auwla, she is one of my students yanzu haka L1 ta ke, she is well educated both arabic and boko, her father is the MD of PHCN. I recently went to their house, kuma da ganin gidansu gidan mutunci da karramawa ne duk da ban samu ganawa da wani a gidan ba, amma naga hakan daga wurin gate man nasu". "Okay Son, kamar an gama ne, karka wani damu kaji, kasa a ranka kama gama samunta". Cike da jin daɗi Muhsin ya rungume mahaifinsa, ya kuma buɗewa Mom hannu itama, ta taso daga inda take tazo ta rungume shi, Wadda kallo ɗaya za kai ma ta kasan tana farinciki da wannan maganar. Muhsin yace da Anie,"Anie ke ɗaya ne ba za ki tayani murna ba?". tana shafa makekiyar wayarta tace,"to Alhaji Hassan murnar me zan tayaka alhalin kana ƙoƙarin yimin kishiya. ai sai dai kawai na bika da adu'a Allah yasa yarinyar ƙwarai ce". Muhsina ta amsheta da cewa,"wallah kamar kin sa ni Anie, ga kyan hali gana fuska. wallahi duk kyauna dana ganta sai dana raina kaina, ai Brother nah yay dace, har na hangosu a lokacin biki". Daddy yana riƙe da hannunta yace,"kema Daughter ina roƙon Allah ya fito miki da miji kamin zuwan lokacin, na haɗaku gaba ɗayanku. ba ƙaramin farinciki zanyi da wannan rana ba". Haka dai suka ci gaba da harkokin su, Anie na cewa ta fasa tafiya har sai kishiyarta tazo ta gaisheta. da daddare kuwa Daddy ya shiga ɗakin Mom, ya sameta zaune a tsakiyar gado hannunta riƙe da wani medium enlargement tana kallo tana kuka. cikin hanzari ya ƙaraso gareta, ya amsa hoton daga hannunta ya ajiye sannan ya kwantar da kanta bisa kafaɗarsa yana lallashinta, sai da ƙyar ya samu ta tsagaita da kukan. yace,"yanzu Sweetheart har sai yaushe ne za ki bar wannan kukan umm? Mutasim fa ya tafi inda ba'a dawowa ya kamata ki haƙura ki fawwala Allah". tace,"Daddy a kullum ina ji ajikina wataran Mutasim zai dawo. ko a jiya nayi mafarki da shi, nafi tunanin yana raye bai mutu ba, kawai dai yana cikin wata rayuwar ne". Daddy ya sauke ajiyan zuciya yace,"but you know that dreams are not real. How can a person who has been missing for 27 years be back?, think of yourself. If he were alive ai da mun ganshi, dan Allah ki daina yawan sa shi a ranki kar wani ciwon ya kamaki". ta ɗago ta dube shi tana cewa,"Daddy karna ƙwallafa abinda na haifa a raina kenan? ni fa rashin ganin gawarsa ita tafi damuna, naso ace naga gawarsa nayi masa adu'a, yaron da bai jima da gama shan nono ba, rashin ganin gawarsa yasa har yanzu na kasa yarɗa da cewan ya mutu, Allah kaɗai yasan a wacce rayuwa yake ciki yanzu". kuka ta fashe da shi sosai, Daddy yaji tausayin matar tasa a ransa matuƙa, yana shafa bayanta yake bata haƙuri da lallashi har ta samu nutsuwa. daga nan ya kashe musu fitila suka kwanta yana manne da ita a jikinsa. ɓangaren Muhsin kuwa tunda ya shiga ɗaki yake a fargaba, yanzu idan su Daddy suka je gidan su Beauty suma tace musu bata sonsa ya zaiyi? ya riga ya kamu da sonta wanda zai iya shiga wani hali a dalilin rashinta. wayarsa ya ɗauko yay dialling numba nata, domin ko kaɗan shi bai yi fushi da ita ba da abinda tayi masa, ya ma ta uzuri ne kasancewarta yarinya. haka wayan ya ƙaraci ringing nasa amma ba ta ɗaga ba, sai dai ya kwana da tunanin dole sai ya kama ƙafa da Yayanta da ta ke yawan masa zancensa, tunda ya lura tana sonsa tana kuma jin maganarsa, wataƙila idan yabi ta hanyarsa ta amincewa ƙudurinsa. [4/1, 3:34 PM] Oum Ramadan: *AL-HUSSAIN* _By Oum Ramadhan✍🏼_ *(29)* "ka cire soyayyarta daga zuciyarka, ka cire burin aurenta a ranka...ka barta a wannan matsayin da kuka fara bawa juna tun farko". "saboda me?". "saboda ba zaka sameta ba, Hussain ba zaka aureta ba muddin ina numfashi a doron ƙasar nan". wannan furucin shi yasaka Alhussain saurin zuro ƙafafunsa ya sauko daga kan gadon, ya miƙe tsaye akan ƙafafunsa yana ƙarewa bayan matar da baya iya kallon fuskarta kallo, kallonta yake da saƙawar mabanbanta abubuwa acikin ransa. sai dai a duk abunda ya saƙa ɗin baya iya warware shi, saboda haka yayi tattaki zuwa inda ta ke a tsaye jikinta naɗe da lafaya brown colour, tana fuskantar kusurwar ɗakin nasa ta ɓarin hagu, daga tazarar da ba zata wuce inchi 2 ba a tsakaninsu ya dakata. sannan ya tattaro yawun bakinsa da yaji kamar yana neman ƙafewa yace da ita,"wace ke?". shiru tayi masa bata bashi amsa ba, ya rufe ido ya zuƙi numfashi, gami da sanya hannu ya shafo sumar kansa yana kaiwa cinyarsa duka. "Wace ke? kuma me yasa kike min waɗannan maganganun?". ya ƙara tambayarta amon muryarsa na cika ɗakin gaba ɗaya. maimakon amsar daya tsammaci ji daga gareta sai yaji sautin murmushinta ya fita a hankali, wanda ya tabbata murmushin ya tsaya mata iyaka leɓe ne kawai duk da cewar bai ga fuskarta ba. zuciyarsa tayi wani zafi dan haka bai san lokacin daya ɗora hannu a saman kafaɗar matar ba dan juyo da ita, amma abu biyu ya hana hakan, farko wani azababben shock daya ji ya ratsa gaba ɗaya jininsa har yay saurin ɗauke hannunsa yana yarfewa, sai na biyu kuma da matar taƙi juyowa tana me ƙara sunkuyar da kanta ƙasa tare da matsawa, kuma bakinta na furta masa,"ba yanzu ba Hussain, ba yanzu zaka sami waɗannan amsoshin ba, da sauran lokaci". tsaye yayi yana tsare bayanta da ido, dan ya tabbata in har ya ƙara taku ɗaya to zsta iya guduwa. "ban sanki ba, kuma kema nasan baki sanni ba, dan haka ki fita acikin rayuwata da kike ƙoƙarin shiga...ba ruwanki da lamarin soyayyata balle aurena". wannan karon a zafafe yake maganar, yana mai yin ƙoƙari wajen ganin ya wata dabarar da zata sa matar ta juyo yaga fuskarta. "tukunnama! me kike nema a wurina?". kai tsaye kuma ya ji muryarta fa fito da cewa,"kai nake nema Hussain, kai nake nema na faɗa maka muddin baka cire soyayyar yarinyar nan tunda wuri a ranka ba to la shakka zata zame maka guba, Hussain karka Ƙwalla soyayyarka akanta domin hakan zai illataka...kuma abu na ƙarshe da nake so na faɗa maka shine, Alƙalamin ƙaddara bai rubuta abunda ku ka tsarawa kanku ba Hussain". da gama faɗar hakan ɓat sai matar ta ɓace. wanda hakan ya zama dalilin farkawar Alhussain a gigice yana ambaton sunan Allah. ya shiga murza idanuwansa yana daɗa ƙarewa ɗakin nasa kallo dan tabbatar da mafarkin da yay ba gaskiya bane. ya sauke ajiyar zuciya yana mai duban agogo dake saƙale ajikin bango. "10:00am". ƙarfe goma na safe haka agogon ya nuna, sai ya mayar da kansa ya jingina ajikin gado yana me haɗe murfayen idonsa ya rufe. lokaci ɗaya mafarkin da yake yi tsawon kwanaki uku a jere ya shiga tariyo masa acikin kansa, kwana uku kenan wannan matar tana zuwar masa da magana ɗaya. _"wace ita?, kuma me yasa take waɗannan maganganun?, wanne irin saƙo take so ta bar masa? me alƙalamin ƙaddarar ya rubuta? sunan Hussain da ta ke kiransa da shi daga ina ya samo asali?"._ sai kawai ya shiga sauke nunfashi da sauri-sauri. _"ba zaka aureta ba, ka cireta a ranka muddin ina nunfashi."_ wannan maganar ta kuma haskawa acikin idonsa, a wani zabure ya buɗe idonsa yana fitar da huci yayin da yake damƙar zanen gadon da kyau yana jin kamar zai jijjige ɗakin baki ɗaya. ** yau sati guda kenan ina fama da ciwo, zazzaɓi yay min wani irin kamu duk na rame na fita a hayyacina. yaune kawai na samu ɗan dama-dama na fito parlo, shima a kujera na kwanta dan bana iya zama saboda rashin ƙwarin jikina, ko school ban je ba tunda aka koma yau sati biyu kenan. kuma ba komai ya haifar min da wannan ciwon ba sai mafarkin da nayi, mafarkin wani dattijo da nayi yana min nuni da wani mutum dake zaune kan kujera kamar wani sarki, yayin da yake faɗa min cewa wannan mutumin shine mafarin ƙaddarata, kuma akansa ne alƙalamin ƙaddarata yay rubutu. a yayin da ƙaddara ta ɗauremu ni da shi a wannan lokacin zan tsunduma a duniyar farinciki, sai dai kuma abu biyu zai haɗe min a lokacin, wannan lokaci gudan da nake cikin farinciki zai haɗe min da kuka mara iyaka. a duk lokacin da nai ƙoƙarin ganin naga fuskar na kan kujerar sai na gagara, a jiya ne dana tunkare shi ina taɓa kafaɗarsa sai naga ya faɗo daga kan kujerar, kuma ta ke iska ta ɗauko wani farin ƙyalle wanda yayi kama da linkafani ta rufeshi gaba ɗaya, ban san ta yanda zan kwatanta tashin hankalin da na shiga ba, amma dai nayi dakiyar tsugunawa gaban gawar na kai hannu zan buɗe fuskar dan ganin waye, kuma a daidai lokacin dana kama likafanin zan ɗaga lokacinne Gwaggo ta shigo ta tasheni daga barci. dalilin daya sa gabana yake ta faɗuwa kenan har zuwa yanzu, na kuma gagara gane fassarar mafarkin, tashin hankalina ɗaya kar ace silar taɓa shi ne na zama ajalinsa, gashi ban san ta inda zan yiwa Gwaggo bayani ba tunda ance ba'a faɗar mummunan mafarki. "ya jikin naki". muryar Anty ta faɗa a sanda ta ke shigowa parlon, na ɗaga kai na kalleta ina amsa sallamarta har ta ƙaraso inda nake ta zauna. masu karatu kunji abun kamar almara ko, haka dai muka wayi gari Allah ya shiryar da Anty, hakan kuma yay ma kowa daɗi musamman ma ni, dan yanda ta ke lura dani babu ha'inci sai nake jin kamar ƙanwar uwata. "kinci abinci?". ta tambaye ni cike da kulawa, na girgiza ma ta kai ina cewa,"komai naci ɗaci Anty, bakina ba daɗi". ta kamani tana miƙar dani zaune ta ke cewa,"to haka za'ayi mutum dan Allah babu cin abinci babu shan magani, Sabina sauƙi fa muke nema dole sai kinyi haƙuri". ta taɓa kaina taji zafi rau, pillow'n kujera ta samun ta bayana ta jinginar dani, ta miƙe ta shiga ɗakin Gwaggo, tana sallah ta sameta, sanin sallar Gwaggo ba mai ƙarewa bace da wuri yasa ta tambayeta ina maganina, tayi ma ta nuni da drower, ta ɗauko ta fito. curstard ta dama, duk sona da shi kasa sha nayi, har Gwaggo ma ta fito suna ta fama da ni amma naƙi shan ko da spoon ɗaya bare nasha maganin, kowa sai roƙona yake akan na daure nasha maganin amma naƙi sai ƙara narkewa nake inawa Gwaggo kuka. ita dai duk hankalinta tashe yake, sam bata so ta rasani, ana haka Yayana ya dawo daga school, shima duk yanda ya lallaɓa ni ƙememe naƙi shan maganin, Yaya Abba kuwa dama shi ko ta kaina baya bi, ga jikina ƙara tsananta yake zafi rau kamar wuta, ga uban amai da nake kyalawa. Gwaggo kuka ta saka tana cewa,"wannan yarinya kwai muguwa, kawai dan kinga ke ɗaya Allah ya jarabceni da mahaukacin sonki shikenan sai ki dinga yi min baƙincikin rayuwarki, yanzu idan ba ki sha maganin ba taya za'ai ki samu sauƙi, an san dai sauƙi na wurin ubangiji amma don Allah dan Annabi Sabina ki daure kisha maganin nan ko kema kyaji ƙwarin jikinki, tun safe ake fama dake akan abu guda". na miƙe zaune ina cewa Anty ta bani curstard ɗin na sha, ina kai cokali ɗaya bakina nayo amansa, na fashe da kuka domin nima Allah ɗaya yasan irin wuyar da nake ci. Yaya Haidar ne ya shigo, kowa ya maida hankalinsa ga sallamar da yake. "a'a Haidar an sauka?". da yake yaje ganin gida kusan satinsa uku. "ehh Anty". ya faɗa yana zama a kujerar kusa damu. ya miƙawa su Yaya Abba hannu suka gaisa, kallon ball ɗinsu suke hankali kwance, Yayana da Yaya Abba sai uban musu sukeyi akan ball ɗin. Gwaggo ta miƙe tana masifa taje ta kashe TV ɗin, ta fuskancesu tana cewa,"ku kam dukanku baku da imani, kuna ganin yarinya babu lafiya amma kunzo kun saka ƙwallo a gaba kuna kallo, me makon ku zauna kuyi ma ta adu'ar samun sauƙi". tana rufe baki Yaya Abba ya miƙe ya raɓawa ta gefenta yaje ya sake kunna tv ɗin, bai kai ga ɗago kai ba yaji saukar ranƙwashi zazzafa akansa. "haba dan Allah Gwaggo, kin san kuwa yanda wasan nan yake da zafi". ya faɗa yana sosa wurin yana kuma ɓata rai. "matsamin". ta faɗa tana bangaje shi a wurin ta kuma kashe tv. "wallahi idan kun kuma ganin kayan kallon nan a kunne to yarinyar nan ce ta samu lafiya. wai ku ina naku ma yake da baku da aiki sai zuwa ku addabi nawa salon ku lalata min, to wallah kar yaron daya kuma kunna min kayan kallo tunda kuma duk ansa muku naku. ni kar a ƙara kunna min ko socket ne tunda jikata babu lafiya, wanda ba zai jura ba sai ya daina shigo min ɓangarena". "mtswww". Yaya Haidar yaja tsaki, ta waigo gare shi tana masa wani duba. "ka dawo zaka fara ɗan iskan halin naka ko Aliyu. ni dai ka kuma yimin tsaki kaje kai da Allah tunda ni ba tsaka bace". ya ɗago ya kalleta ta wurga masa harara. "kai dama sam baka yo gadon arziƙi ba, mutumci sam bai gama ratsa ka ba da alama baka tsotsa ba. banda haka ka shigo ka kallemu da mara lafiya amma ko sannu baka mata ba kasa kai ka wuce, saboda zuciyarka sam babu tausayi bare imani". "to idan na tsaya ni zan bata lafiyar, ke fa Gwaggo akan waccen yarinyar kina da matsala Allah". bata kuma magana ba ta jiyoni ina wayyo Allah nah, ta iyo kaina da sauri tana zabga salati, Amina da Zainab sun riƙeni ina aikin kyala amai kore shar, sai Anty dake zuba min ruwa a fuska. shi kuwa Yayana gaba ɗaya hankalinsa baya jikinsa, tun ɗazu idonsa na kaina ganin idon Anty a wurin ya kasa zuwa inda nake, sai na ɗago ido sai naga yana ta kallona da tausayawa, yanzuma ina maida numfashi muka haɗa ido, ya haɗa hannu yana roƙona akan na daure naci abinci na sha magani. yanzu kam Allah ya taimaka na shanye curstard ɗin duka sai dai na kasa shan maganin. "Anty kawo maganin". Yaya Haidar yace da ita a lokacin daya iso wurinmu, ta miƙa mishi yace su Zainab su bashi wuri. ya ɗaure fuska tamau yace min buɗe bakin, zanyi gaddama ya ɗaga min hannu yana min wani mugun kallo, ya kalla Gwaggo yaja tsaki kaɗan yace. "don Allah tsohuwa ki mana shiru, duk kin cika mana kunne. kukan naki ne zai sanya ta samu lafiya". aikuwa cikin masifa tace masa,"ba zanyi ba, ba zanyi ba, nace bazanyi ba ɗin idan ka isa kuma ka hanani. mara mutunci kawai". ta kuma rungumeni tana ci gaba da kukanta. a hankali yace,"dama ta mutu kowa ma ya huta". "ɗan banza mai mugun jafa'i kaga mutuwa akanka. dalla Malami ka tashi anan wurin uban wa ma ya kawoka". bai kulata ba ya kama bakina ya matse ya zuba min maganin, tukunna ya zuba ruwa ya matsen hanci yace idan na dawo da shi sai raina ya ɓaci, haka babu yanda na iya dole na shanye inata kakarin amai. "ina da ina ke miki ciwo dama?". ko kallonsa banyi ba na nuna masa kaina kawai, ya kama kan yay min adu'a tukunna ya tashi ya fita. ba jimawa kuwa bacci ya ɗaukeni dan naji daɗi sosai dama ciwon kan ne ya addabeni. washegari da safe ina zaune ni ɗaya a parlo na ɗan ji daɗin jikina, Yaya Haidar ne ya shigo, nai saurin miƙewa zan wuce ɗaki saboda irin rigar dake jikina, ya kalleni ya taɓe baki, na harare shi ta ƙasan ido nima na murguɗa masa baki na wuce ɗaki. a dining na dawo na sa me shi yana zuba tea a cup, na wuce na kwanta kan kujera ina ci gaba da kallon cartoon ɗina, ya dawo ya zauna a kujeran dake facing ɗina. ya ɗau remote ya sauya channel yana kurɓan ruwan tea, ina marairaicewa nace,"Yaya Haidar dan Allah ka mayar min". ta gefen ido yay min kallo ɗaya, kamar ba zai mayar ba sai kuma ya maida ya aje remote ɗin, ya ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yana cigaba da kurɓan tea ɗinsa. "tashi zaune". nayi kamar ban jisa ba, sai daya kuma ɗaga murya yace,"ba za ki tashi zaune ba. ke ko gajiya ba kya yi da kwanciya, a haka za ki ji ƙwarin jikinkin naki". nan ma shiru na masa sai murguɗa baki da nayi ta gefe. "idan ba ki miƙe zaune ba babu abinda zai hanani juye miki ruwan tea ɗin nan idan na iso nan wurin". ya faɗi hakan yana ƙoƙarin miƙewa, aiko nai saurin tashi zaune ina aikin zumɓura baki, dan nasan kaɗan daga cikin aikinsa. Gwaggo ta fito tana cewa,"kai dai wannan yaro anyi mugun mutum. to ni dai karka ƙara ɗaga ma ta murya bata da lafiya. ka barta taji da jikinta". "ina kwana Gwaggo". yace da ita. "lafiya". ta amsa masa a daƙila kafin ta kuma cewa,"na ganka da sassafe haka". ya ɗaure fuska dan yasan yanzu zata yi halin nata, yace, "breakfast nazo yi". "to baka da labari na daina ciyar da ƙatti ne, to gaskiya anjima karka dawo saboda ni yanzu bana girki da ku. Zara'u ce ta ke dafa muku saboda Allah ya shiryeta, yanzu ma idan kaje ƴan'uwanka suna can suna kwasa, da mai cin da mara cin duk acan suke yanzu. jiya ma naji batun katan ɗin taliyarta ya ƙare, nace ai sai dai haƙuri kuma". yace,"to ni gaskiya anan nake son cin abincina kuma anan zan dinga ci". "tabɗi aikuwa dai baka isa ba, wannan na baka trki hanyar neman zaman lafiya ba. sam ba zan iya ci gaba da ciyar da ƙaton gardi kamar ka ba, kalla fa yanzu daga dawowarka ka yashe min rabin madara, dama kai anan kafi kauri. ni fa na gaya maka zancen gaskiya ma banji daɗin dawowar nan taka nai ba...irin kune abun gudu, lokacin da muna tsohon gidanmu ai baka zuwa, amma da ike mun dawo gidan aljannar duniya shine ka gagara zama a naku gidan". shi dai bai sake ce mata komai ba, ita kuma ta kwashe kayan tea ta wuce da su kitchen tana mitar yashe mata madara da yayi. na gyara zan kuma kwanciya saboda ganin idon Gwaggo ya kuma doka min tsawa, babu shiri na saita hankalina, kamar an jefo Gwaggo sai gata ta fito tana cewa. "kaga Aliyu ni dai idan ba zaka iya zama haka kawai ba dan girman Allah ka bar min ɗaki, ba fa ni na gayyatoka ba, haka kawai ba zaka zo ka dinga firgita min Ƴa ba na rasa yanda zanyi da daddare, dama ya aka cika da wannan zafin zazzaɓin nata, ni kaina idan ka ɗaga murya furgita nake yi da wannan ƙatuwar muryar taka". ya ɗaure fuska yace,"dama meye ne yake damunta?". sai kuma tayi ƙasa da murya tana cewa,"wallah tun tafiyarka take fama da zazzaɓi mai zafi, gaba ɗaga fa sai yaune ta samu kanta". "kunje asibiti?". "ehh to likita dai yazo har nan ya dubata. ni kuma kasan ba son takura ma ta nake ba tunda naga bata son asibitin nace a ƙyaleta". "saboda anga Baba baya nan ko, da yanan ai ko gwal ce ita sai taje asibiti". ya dubeni yace,"tashi kije ki shirya muje ai miki test". nai saurin ɗagowa ina dubansa, ya haɗe rai yana min wani wawan kallo, na shagwaɓe fuska na kalla Gwaggo ina shirin fashewa da kuka. "Gwaggo ni fa naji sauƙi". nace da ita ina karayar da kai. tace da Yaya Haidar, "shi abunda ka faɗa idan anyi ma ta zata samu sauƙi ne?". "me zai hana, ai kawai ki rufe ido ki barni da ita. haka za'a zuba ma ta ido ciwo na cinta. idan kuma kinƙi sai na ƙyaleta zazzaɓin yanzu ne kashe mutane yake". babu shiri ta juyo tana ce min. "kinga miƙe dan Allah bana son tashin hankali". na miƙe ina dukan ƙafa nayi ɗaki, ba dan naso ba shirya na fito, na samu Yayana ya shigo ma Gwaggo sallaman zai tafi makaranta, na taho tagal tagal kamar zan faɗi, ya riƙoni zuwa jikinsa yana tambayana sauƙin jikin. "da sauƙi". nace da shi ina kuma kwacewa a jikinsa. "me zan taho miki da shi idan zan dawo?". yace dani yana sunkuyo da fuskarsa saitin tawa. "pure bliss wafer". nace ina ɗago ido na kalle shi. murmushi yayi ya ɗan ja hancina yace,"Cutie nah wai sai yaushe za ki girma ne? pure bliss pure bliss dai". na karyar da wuya bance koma ba, ya kama hannuna ya zagaya dani na zauna a kujera, yace "Gwaggo zan tafi". "to ɗan albarka a dawo lafiya Allah ya bada sa'a. duk cikin jikokina kai ɗaya ne mai tausayi, cikin Abba da Haidar babu mai yiwa yarinyar nan magana a hankali sai kai". Ya murmusa kawai, sannan yay hanyar fita ina cewa,"Yaya a dawo lafiya". sai daya kalleni ya sakar min wani ƙayataccen murmushi tukunna ya fita. shi kuwa Yaya Haidar tunda na fito ko kallona bai kuma yi ba, har Yaya ya fice, sai daya gama jan ajinsa da miskilancinsa tukunna ya miƙe yace na biyo shi. muna isa hospital ɗin ya samu wani likita abokinsa, yay min tambayoyin abunda yake damuna, duk na faɗa masa, yace ba kya iya cin abinci ko? na gyaɗa masa kai alaman ehh, yay rubuce rubuvensa ya dubi Yaya Haidar yace ga wannan, ni dai tunda naji batun test hankalina ya tashi, dan naƙi jinin allura, tuni na fara kuka a hankali, na ruƙo hannunsa na damƙe ina roƙonsa, yay banza da ni kamar bada shi nake ba. test har uku haka likitan ya rubuta, ya miƙo masa takardar ya amsa, ya kalle ni fuska a haɗe kamar hadari yace,"tashi muje". na miƙe har lokacin ina riƙe da hannunsa har muka isa lab ɗin, suka masa bayanin wurin biyan kuɗin, yace dani na zauna anan na jira shi, bai jima ba ya dawo da reciept hannunsa, ya miƙawa mutumin, nan yace na taso dan ma a hakan ya roƙi alfarma ne amma da mutane da yawa kan layin. muryana a dashe nace,"dan Allah Yaya Haidar kar a min allura wallahi bana so, ka tambayi Gwaggo kaji ba'a min allura magani nake sha". yay min wani kallo yace,"to ni Gwaggo ne, dilla Malama tsaya kiyi abinda aka ce miki". na runtse ido kawai nayi surrender, Nurse ɗin yace dani na ɗaga hannun rigata, ina jinsa nai masa banza dan har shi nake jin haushi, Yaya Haidar yaja tsaki ya kama hannuna ya yaye hannun rigar tawa, sai dai lokaci ɗaya yaji tausayinta ya kama shi yanda yaji jikinta yayi zafi rau. yay ƙasa da Murya ya kira sunana, na amsa da umm, yace,"kiyi haƙuri ki daure ba za'a miki da zafi ba". ina sheƙar kuka nace ni fa ko da zafi ko babu bana so a ɓula min jikina. shiru yay ya jawo kujerar da yake zaune kusa da ni, ya kwantar da kaina saman cikinsa, a hankali yaji zafin jikinta yana ratsa kayansa ya shiga jikinsa, ya rumtse ido ya furta"Ya Salam, dama haka jikinki yay wannan zafin shine za kice wani ba za'a maki allura ba". ina jinsa ni dai bance masa komai ba, Mutumin ya kama hannuna ya tsira min allurar da har ta sa ni zillo ina sakin ihu. "dalla can tsaya".yace dani murya a ɗage. na maida kaina jikinsa ina sheƙar kuka. _wannan zafin jikin is worst, to me ya sameta haka?_ ya yiwa kansa tambayar da bashi da mai bashi amsa sai likita. haka aka kuma yin sauran test aka gama duk ban motsa ba, sai bayan da aka gama yaga ashe ma nayi bacci, kamar ya zareni daga jikinsa sai ya yatsinci kansa da kasa aikata hakan, dan haka da sanyin jiki ya gyara mata kwanciyar kanta, ya zauna jiran amsar result ɗin test ɗin. yana zaman jira sai ga wani abokinsa ya kawo matarsa shima, sun jima basu haɗu ba nan suka shiga musabaha, matarsa ma ta gaida Haidar kafin ta nemi wuri ta zauna itama. "a'a kace kaima Madam ka kawo". cewar Mustapha dake kallon Haidar. Yay masa wani kallo yace,"who told you she is my beb, rigimammiyar ƙanwata ce na kawo babu lafiya. kasan ranon Kaka sai a hankali". "ehh gaskiya kam, rainon Kaka ai akwai rigima". suna hira nurse ya kawowa Haidar result ɗin, ya shiga tashinta a hankali har ta buɗe idon, ni kaina nai mamaki dan ba ƙaramin bacci nayi ba, yana riƙe da hannuna muka koma office ɗin wancan likitan, ya amsa result ɗin yay masa bayanin typhoid da maleria suka haɗar min, nan ya rubuta mana magunguna muka fito muka wuce pharmacy, ni dai duk na gaji da tafiyar hakan yasa naja na tsaya ina hutawa, sai da yayi gaba ya juyo ya ganni na jingina da bango. "mene kuma?". "Allah Yaya Haidar na gaji da tafiyan, kamar zan faɗi nake ji". tsaki yaja ya harare ni kamin ya dawo ya kama hannuna ya kaini mota yace na jira dawowansa. ya jima kamin ya dawo, a hanya ya tambayeni ko da abinda nake son ci, ina kallonsa nace,"Pure bliss wafer da choculate". sai kawai yay min kallo mai kama da harara ya ɗauke tare da cewar,"ba zan saya ba". har muka iso gida kuma bai kuma ce min komai ba, yau dai ƴan mutunci yake ji dasu dan sai nan da nan yake dani, yanzu ma daya ga zan faɗi kamani yay ya jingina ni da jikinsa. muna shiga parlo yace na nemi wuri na zauna, zan kwanta yace,"karki sake ki kwanta". na langaɓar da kai ina yamutsa fuska yace,"ke abu kaɗan kuka ko gajiyaba kya yi, mtsww". yaja tsaki ya wuce friedge, roban faro ya ɗauko ya buɗe ya haɗa min ɗaya daga cikin maganin da akace da mun dawo na sha. ya haɗa ya miƙo min yace nasha, ban samu fuskar gaddama ba na amsa na sha, Iklima tazo tana min sannu. nace ma ta ina Gwaggo tace taje wajen Anty. na tashi zan tafi wajenta naji muryarsa yana dawo ki zauna, na koma na zauna ina kumbura fuska. "kalla yanda kika bi kika wani rame". yana maganar yana hararata, ni dai na tashi na bar masa wurin nai wucewata ɗaki dan ban shiryawa bala'insa ba. ban fito ba sai dana jiyo muryan Gwaggo, na sameta ta riƙe ledar magungunan da ya bata tana ta masa godiya tana faɗi,"ai kaf cikin jikokina babu mai halin kirki irinka Haidar, shi yasa kake burgeni a ko da yaushe, yanzu ka duba waɗancan yaran, daga zagalon har lagwanin duk cikin kwanakin nan babu wanda yay tunanin kaita asibiti, kai dai Allah yayi maka albarka yasa ka gama da duniya lafiya". "ameen". yace da ita. Yaya Abba kuwa yace,"daga baya kenan". ta harare shi bata ce masa komai ba. Haidar yace ma ta,"idan da gaske kina son ta samu sauƙi da wuri saiki sa ta dinƙa shan magani, idan kuma kin biye ma ta sai kiyi ta zaman jinya". "insha'Allahu Haidar". ni ko alluran da aka mani har naji daɗin jikina sosai, har na ɗau wayana na kunna data muka hau hira da ƴan school namu ina tambayansu game da lectures. har yamma Yaya bai dawo ba, na ɗau waya na kira shi ina tambayansa Pure bliss dan Gwaggo ta hana a siyo min wai na fiya cin zaƙi. ina jinsa ya sa ki murmushi yace,"go slow ne yay tsaida ni amma saura ƙiris na ƙaraso, ki haƙuri Cutien Yaya". kamar ina gabansa nayi knooding kaina nace,"Allah ya dawo da kai lafiya". yace, "amin Cutie nah".