KIN CUCE NI Gargadi Bamu yarda wani ko wata suyi amfani da shashi na littafin nan ba ko juya shi batare da izinin mu ba ko mai da shi document 📄📃 in kunne ya ji jiki ya tsira Ya Ubangiji kabamu iƙon rubuta dai dai ka hanamu rubuta ɓarna ya Allah ba bamu iƙon gamashi lafiya kamar yar da muka fara lafi Wannan labari kirkirarre ne duk wanda yaga yayi dai dai da rayuwar sa to ya ɗauka arashi ne *KIN CUCE NI* _Story And Writing_ _By_ * (Oum Yasmeen) And *_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_* (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k ```Duk kan yabo ya tabbata ga Ubangijin talikai ya Allah ka bamu ikon gama littafin nan lafiya, kamar yadda cikin amincewar ka zamu fara lafiya..``` *GARGADI!!!!!!* _Bamu yar da wani ko wata suyi amfani da wani shashi na littafin ba ko kuma mai da shi Document in kunne yaji jiki ya tsira_ *_Ep one_* Taƙu take ɗadɗai duk inda ta taka sai kaji yace ƙas tana taunar chewing gum wani ƙwai ta saki jikake yace tussh glass ɗin fusƙarta ta ɗaga sama ta saki dogon tsaki. Msssswww tace "Wallahi in har ba zaku dena kwaso matattun ƙafafuwan ku ku kawo min gidana wallahi ba zaku dena ganin hulaƙanci kala kala ba nace muku me gidan nan yafi ƙarfin ku kuƙi yarda taurin kai yayi muku yawa ni wallahi na tsani in dinga ganin ku baki duk goro , Cikin baƙin ciki naseeba tace "Yan zu fateesat hulaƙancin ki har ya kai haka Inna mai towo ƙanwar mama ba ce fa in kin manta in tuna miki?, Ƙara sa saukowa tayi daga stairs case ɗin ta sheƙe da wata uwar dariya ta tafa hannaye tace "Naseeba ce miki akai na kamu da cutar mantuwa nagane ko wace ce ita ƙanwar gyatumar ki ce domin ba zan ce mahaifiyar mijina ba domin tun ranar da ya auro ni na cire shi daga cikin dan gin ku tun huri ki faɗawa tsohuwa tayi gaggawar cire shi a sahun ƴa'ƴan ta domin ita ta haife shi amma yafi ƙarfin ta ?, Kuka mai tuwo ta saki tace "Amma fateesa kin cuce mu in Allah ya yarda sai kin ga ƙarshan ki naseeba ta shi mutafi kuma gida ba zamu fasa zuwa ba tun da ba na uban ki bane , Ƙaro sowa tayi cikin floor iya huɗuwa ya haɗu daga gani zaka san gidan me arziki ne ɗaya daga cikin luxury sofa ta zauna ta ɗora ƙafa ɗaya ƙan ɗaya tana gir giza kafa hannuwanta shaƙe da zoɓe daham da awarwaron daham tace "SALAMATU DAUDA ME ALLO wallahi wanda kike ta ƙama ɗan yayar kine zan kira shi ya ci miki mutunci , hy my sweetheart lafiya nake jin warin talauci duk ya cika floor nan Juyowa tayi tace "Baby hayaniyar su ta tayar da ke daga baccin da ya ɗauke ki jiya mun kwana muna cin juna , Daga ita sai sleeping dress wata me net shara shara ba abin da ya ɓoye a jikin ta komai ana gani tace "Ehwllh me ya kawo wan yanan old human ɗin ?, Tsaki taja ta kamo hannun abokiyar sheɗancin nata ta zaunar da ita kusa da ita hannunta ta ɗora akan breast ɗin ta tana shafawa tace "We wata aljanar ƴar ta ce ba lafiya shine tazo ya bata kuɗin magani , Ai kafin ta ƙarasa naseeba ta yo ƙan su hannunta me tuwo ta kama tace ''Naseeba barta kina ga sunana ta faɗa gatsal ba sakayawa zo mutafi Allah ya isa tsakanin mu da keee, Dariya suka saki baby tace "Yau nake jin wata jarabawa me kuma mukai miki ko talauci ne ya motsa kai wannan matar tana shan kebura, Wallahi kuwa zo mu shiga ciki tashi tayi suka shiga Tafiya suke yawa zasu faɗi ga yunwa ga zafin rana yawa zai fasa musu ƙwaƙwalwa tun daga tudun Yola har asibitin Murtala a ƙafa ɗakin da aka kwantar da ita ta shiga tana kwance rai a hannun Allah ba abin da a kai mata saboda ba ta siyi abin da aka rubuta mata ba wata nurser ce ta shigo tace "Umma ku ceci rayuwar yarinyar nan ko ba kuga halin da take ciki ba blood transfer za ai mata jinin ta ya ƙone dole juyan jini za ai mata O+ muke nema shini jinin sa zai mata , Mayafin ta tasa ta share hawayen fusƙarta tace "To, zan nemo , Juyawa tayi ta fita Naseeba tace "Inna bara in tafi gida ko mama ta ajiye muni abinci in kawo miki kici tun da kin ga bata san na tawo gun ki ba, A jiyar zuciya ta saki tace "To Nagode naseeba Allah yayi albarka , Ameen Inna Allah ya bawa ƙanwata lafiya Amin tace domin yanzu rayuwar duniyar ta fitar mata a rai yayan ta uwa ɗaya uba ɗaya yana gudun ta ɗan bata da shi ciwon ƙafar ta ta duba ya ƙara kumbura yan zu ta mutu ta bar ilham bata san wanne halin zata kasance ba ji tayi ta saki salati jini yana zuba a baƙin ta da sauri naseeba ta dawo ta yo kanta cikin kuka tace......... "Inna Inna Dan Allah inna ki tashi ?, Da ƙƴar ta iya buɗe baki tace "Naseeba ki tafi ƙar ane miki kar ki damu ba abin da zai same ni insha'Allah, A jiyar zuciya ta saki tace "Inna ba zan iya tafiya in barku ba , Murmushi tayi wanda ake kira da yafi kuka ciwo tace "Ƙar ki damu Allah zai kare mu , Tashi tayi tace "To inna natafi , Allah ya kiyaye hanya bayan tafiyar ta tashi tayi da ƙƴar ta zauna a kusa da gadon ilham ta ƙura mata ido kowa na ɗakin sai harƙar gaban sa yake zuba ta gumi tayi wata shawara ce ta waɗo mata da sauri ta tashi ta nufi wani gado kusa da su tace "Assalamu alaikum ya me jiki , Matar ce wacce ta ke jinyar yar ta ta amsa bata fuska a tsuke ganin haka yasa jikin inna ƙara sanyi tace "Dan Allah baiwar Allah ki temaka min ki bani aron wayar ki zan kira ɗana , Duban wayar hannunta tayi ta ƙara haɗe rai tace "Bani da chaji, Baiwar Allah ungo tawa da sauri ta fito da wata ta ƙarda a zanin ta duk taji jiki tace "Nagode dan Allah saka min ki kirami ita , Yarinyar ta dubi ta ƙardar tace "Baiwar wannan ai bata ƙasar nan ba ce, Gaban inna ne ya waɗi domin ba zata taɓa manta waba ganin ta na ƙarshe dashi hannun sa ya bata wannan number yace ko wani abu zai tashi tace iya sannin da tayimai baya karya dan Adam me canzawa amma duk Inda yake tasan zuciyar nan tasa da tsayawa a kan gaskiya tace "Yanzu kenan ba zata yi kira ba ?, Aa inna zata yi amma sai ansa kuɗi masu yawa kamar dubu biyu Dan Allah yarnan ko flashing ne ki yimai To Allah yasa ya kira a hand free ta sata har ta gama ƙarar ta ba aɗauka ba duban Inna tayi tace "Ba aɗauka ba , To yarnan Nagode ai kina asibitin nan insha Allahu zaikira Eh ina nan Allah yasa Amin tace ta koma ta zauna shiru shiru naseeba bata dawo ba ga wata yunwa da take ji ilham ko motsi bata yi kadan kadan take fusgar numfashi Wannan kenan Tun daga soro zaka fara cin karo da yara kowa na sabgar gaban sa daga bakin titin unguwar dan dago in kace a kai ka gidan yan adakawa har gidan za a kai ka gini ne na da ya kusan ruttawa wata ƙatuwar kwata ce a soron da ƙƴar na huce ciki gidan na shiga saboda jin alamun ana magana da karfi wani tsoho na zai kai shekara saba'in rigar sa duk a ƙode yace "wanne dan iskanne ya shigar min ɗaki ya dauke sabuluna ?, Ko wacce aikin gaban ta take ba wacce ta kula shi sauran yaran da suke cikin gidan sun yi tsuru tsuru ɗakin inna salamatu yaje domin ya ɗan ƙo ilham ya naɗa mata duka a cewar shi tun da aka haife ta ya dena Samu motar da yake ja ta ƙune ƙurmus ƙafa yasa ya tura ƙofar wayam ya gani juyowa yayi yace "Ke hansatu inna salamatu, tuƙunyar da ta wanke ta shinkafar siyarwar ta ta ɗora akan murhu sosai huta ke ci ga wata irin rana da ake yi gyara baƙin zaninta tace "Owo ka bani ajiyar ta ?, Wani yaro ya yake zaune ya goge majinar hancinsa yace ''ilham ce ba lafiya , Tuƙunyar kusa da shi ya ɗauka yayi cilli da iya yace "Wato raini ya shiga tsakani na da salamatu to wallahi kar ta dawomin da arjanar ƴarta gidana fuuuuuu ya fita , Wata dariya maryamu ta saki suka tafa da hansatu tace "Duniya juyi juyi tab salamatu ta taɓo sama da faɗi , Dan kwali ta gyara tace "Hansatu an faɗa miki ni din ta wasa ce , zani ta gyara tace "Dan Allah yar uwa me kikayi na lura shirinki yafi nawa, Ɗariya ta saki tace..... Ku tayani da addu'a Allah isa in gama jarabawata asa'a *KIN CUCE NI* _Story And Writing_ _By_ (Oum Yasmeen) And *_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_* (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k ```_-_Ita Rayuwar Haka Take Muddin Kace Ruwan Wani Bazai Tausa Ba. Tabbas Naka Ko D'umi Bazai Yi Ba. KOMAI YA YI FARKO ZAI YI K'ARSHE``` *Ep two.* "Hansatu ke nan an faɗa miki ni ɗin shashashar mace ce kamar ke?. Wannan zamanin kissa da kisisina sune kawai ke aiki ba boka balle Malam." Ta faɗa tana sheƙewa da dariya. "Uhum na lura bakya gane karatun bari ki gani na ci gaba da abin da ke gabana." Tayi maganar tana kallon Maryamu da ta saki baki tana kallon ta. *Asibiti Kuwa....* *Wuraren Ƙarfe Bakwai na Marece.* Bakinta ɗauke da sallama ta shigo Room ɗin. Inna Salame dake naɗe Sallaya ta dubeta ta ce. "Naseeba kin dawo ke nan nayi zaton ma sai da safe zaki dawo ya hanya ya mutanen gidan?." "Uhum Alhamdulillah Inna Salame ga abinci na kawo muku nasan bakici komai ba tun safe kiyi haƙuri kici abincin ki kwantar da hankalin ki in sha Allah komai mai wucewa ne a Rayuwa, Ilham zata warke garau Bi'iznillah." Shiru Inna Salame tayi domin ba abin da zata iya faɗa koda zatayi Maganar kuka ne, zuciyarta a karye take, ta dubi gadon da tilon Ɗiyar tata take kwance rai a hannun Allah Hawaye na ƙoƙarin zubo ma ta, tayi saurin sharewa tare da faɗin. "Bakomai Naseeba na gode da kulawa Allah ya miki albarka." "Ameen Inna Salame bakomai ke tamkar uwa ce a gareni." Tayi maganar tana miƙa ma ta Plate mai ɗauke da Jollot na Shinkafa da spoon a ciki ta yadda zata fi jin daɗin ci. "Naseeba a'ina kika sama wannan abincin haka in ce ba roƙo kikayi ba?." Naseeba tayi Murmushi. "Karki damu Inna Salame ba wanda na roƙa dama akwai wasu 'yan kuɗaɗe a jikina shi ne kawai nayi muku girki ko kin manta abin da na karanta ke nan fannin girke girke?." Inna Salame tayi Murmushi kaɗan. "Ban manta ba kam." Ta faɗa sannan ta karɓa plate ɗin abin cin ta fara ci. Naseeba ta miƙa ma ta Ruwan Pure Water da ta siya musu a hanya ta na faɗin. "Wai kuwa nace ya ake ciki maganar Yayah Aryaan ɗin, kin sama wayar da za'a kira lambar nasa ne?." Inna Salame tayi shiru zuciyarta cike da rauni, Naseeba ta famo ma ta inda ke ma ta ƙaiƙayi. "Ina fa har yanzu dai shiru na samu wata ta aramin wayarta ɗazu na kira lambar ba'a ɗauka ba da yake flashing ne, kuma mai wayar ta ce lambar bana nan ƙasar bane, kuma yana jan kati sosai wurin kira." "Bana nan ƙasar ba, ikon Allah no wonder tunda ya tafi shiru bai dawo ba har yanzu amma kam Fateesa da Mahaifiyarta har da kakarta sun cuceki sai dai Allah yana ji kuma yana gani talala ya yi musu da sannu zasu girba abin da suka shuka Azzalumai kawai." Naseeba ta faɗa cike da jimamin lamarin. Inna Salame kam shiru tayi tana kuma duban 'yar ta ta dake halin rai ko Rayuwa, sun daɗe basu sama haihuwa ba daga ƙarshe har sun cire rai da samu cikin ikon Allah da nufar sa sannan da yardar sa ta sama juna biyu duk da a lokacin sun fara manyan ta haka ta raina cikinta cike ta kulawa har Ubangiji ya nufa ta haihu, a tunaninta haihuwar nata zai canza gaba ɗaya Ƙaddarar da kallon da ake ma ta na juya, ashe abin ba haka yake ba a lokacin ne ta fara ganin jarabtar uƙubobi kala kala daga hannun mutane ba ita kaɗai ba harda 'yar nata da ta haifa kwayar idanunta ya banbanta dana sauran mutane da Sanadin hakan har uban 'yarta mahaifi ya tsaneta yake ganin ba 'yar sa ba ce, tun tasowar Yarinyar da girman ta bata san wani soyayya daga wuri ubanta ba sai kyara da hantara wasu lokutan har da duka da zargin ta yana kiranta da Aljanna mai shuɗayen idanu, ba daga garesa kaɗai take kwasan wannan uƙuba ba har ta wurin mutanen Gidan su bata tsira ba balle uwa uba mutanen gari haka Rayuwar Ilham ta taso cikin kyara da hantara daga kowa gani ake ita ɗin BA MUTUM BACE (By M Lumu) don kawai idanunta sun kasance shuɗaye. Inna Salame taja gauron numfashi tana sauke idanunta daga kallon Ilham tare da lulawa Duniyar tunanin Rayuwar ta a baya Asalin ta... *WAI WAYE.....* Tunda daga bakin titin unguwar ƙoƙi kace a kaika gidan Malam daudah mai allo za akai ka bama iya nan kadai ba har da sauran unguwoyi da yake babban malamine kuma masani mu hudune gun mahaifan mu yaya inusa ana kiransa da danjuma sai yayata marigaiya mahaifiyar aryan wato A'isha sai Ni salamatu sai dan autan mu Mahmud mun taso cikin so da kaunar juna kowa yasan cikin gari akwai karatu tamkar tagwaye muka tashi Ni da yaya indo komai iri daya mahaifin mu yake mana muna shekara goma sha biyar muka sauke Alkur'ani me girma mahaifin mu bashi da wani buri a lokacin sai na mun ci gaba to Allah be nufa ba kasancewar bashi da wani hali ko wayasan karatun yanzu sai da hali tun muna yarana ya Danjuma Allah yayi mai son kansa a rayuwa ga son kuɗi a na haka ranar nan mun fito zamu gidan kanwar mahaifiyar mu dake goron dutsai wato hajiya Ruqayya Allah yayi mana diri dan haka ko ina zamu da hijabi malam ya harya gashi da korar mutane kunsan dai da ba adamu da mota ba sai tafiyar kafa haka muna tafi muna hira ji mukai ansha ga ban mu wani kyakkyawan matashine alokacin zaiyi shekaru ashirin da takwas da haihuwa sanye da jamfa da wando kallo daya zakai mai kasan dan gidan manyane kuma buzu ga wani uban saje ya kwanta mai sai sheƙi yake ba wanda Zai yi zaton cewa ya iya Hausa shagala nayi da kallon sa yace "Bayin Allah dan Allah kuyi haƙuri na tare ku a hanya, Yaya indo ce ta dauke kanta taja hannuna zamu tafi nan fa ya karya lagwonmu yace "Dan girman Allah da Manzonsa ku tsaya, Cak muka tsaya saboda an hadamu da fiyayyan halitta murmushi yayi har dimple din sa ya lutsai yace "Dan Allah ina ne gidan ku da yake ba kamar lokacin yanzu ba waya bata karɓo ba sannan dan Allah ya sunan wannan ya nuna yaya indo, Kamar ya asurce ni nace "Sunan ta A'isha sannan mu yan gidan malam me allo ne, Limshe kyawawan idanuwansa yayi yace "Masha Allah nagode sunana abdulyasar turaki turba yana gama fadar haka ya juya ya hau mashin ɗinsa , Mamaki ne ya kusan karni nace "Yaya indo kinsan wannan zuri'ar ta turaki turba?, Shiru tayi sanan tace "Haba salamatu kaf kano wane beson wannan family ba ai sunyi suna , "Amma kuma anya hausawa ne ?, Dariya tayi tace "Da kin sani kafin ya tafi kin tambaye shi ko mu bishi mu tambaye shi, Nan muka rufe babin hirar muka dau wata har muka isa goron dutsai sosai Hajiya Ruqayyah tayi murna da ganin mu tace "Yau Asma'u ta tuna zumunci ta toroku sai de tazo ba dai kuzo ba, Dariya nayi da yake yaya indo bata da magana nace "A'a yauma dan dai bamu da makaranta ne shi yasa muka zo makaranta ke hana mu zuwa kuma kinsan malam baya son mu dinga fita, Haka ne yarnan ya'ya mata sai da sa ido da kafkaf da su Sai karfe hudu muka dawo gida shaf mun manta da maganar abdulyasar bayan mun gama cin abinci mun idar da sallar isha Muna zaune muna hira autan hajiya yana kusa da ita suna cin gyaɗa bamu da kuɗi amma bamu san me ce damuba wani yaro dan maƙotan mu yashi go yace "We inji wani yana sallama da A'isha, Hajiyar mu tace "Je ka kace tana zuwa da yake ita burin ta be huce ta aurar da mu ba, Yaya aisha tace "Hajiya ban son kowaye ba fa gashi bacci nake ji, Dan murmushi tayi irin nasu na manya tace "Ɗazu yazo ya tambayi izinin malam shi yasa ma nace kifita kuma malam ya bashi izini, Tashi tayi badan ta so ba ta zunduma hijabinta fita tayi kamar ance ta dago sukai ido hudu da abdulyasar......✍️ *KIN CUCE NI* _Story And Writing_ _By_ (Oum Yasmeen) And *_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_* (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k _Ep 3_ "Assalamu Alaikum WarahamatuLlahi Wabarakatuhu." Ta masa sallama da kyar mamaki bai kyaleta ba na Ganin sa. Yana sakar ma ta wadataccen murmushi ya ce. "Wa'alaiki Salam WarahamatuLlahi Wabarakatuhu Barka da ƙari sowa Gimbiya." Tayi Murmushi kaɗan ba tare da ta ce komai ba, domin ba tasan menene zatace ba. "Nasan zakiyi mamaki na ganina yanzu daidai wannan lokaci sai dai ba abin mamaki ba ne wannan duba da yadda lokaci guda da ganin farko kikayi Nasarar sace Zuciyata har nake tunanin ki zama mata a gareni uwar 'ya'ya na." Aisha ta zaro ido jin abin da ya ce. "Haba Bawan Allah daga ganin Sarkin fawa kawai sai miya tayi zaƙi." Ya yi Murmushi wanda ya zame masa ɗabi'a ko cikin wani yanayi yake bakya rasa murmushi saman Kyakykywar fuskarsa ya ce. "Gimbiya ta ke nan kin manta da zafi zafi akan daki ƙarfe. Yanzu dai ba wannan ya kawoni gareki ba kafin na kiraki nan sai da na nema iznin Hakan wurin Mahaifin ku kuma ya amince. Aisha wallahi tallahi tsakani da Allah nake ƙaunar ki kuma Indai kin amince a shirye nake dana turo magabata na domin maganar aure." Aisha tayi Shiru jikinta ya yi sanyi, Allah mai iko wai da gaske ɗaya daga cikin Dangin Turaki turba shi ne tsaye gaban ta da ƙoƙon bararsa na son aurenta. "Bakomai Allah Ubangiji ya shige mana gaba amma kayi haƙuri zan fara shawara da Mahaifiyata tukunna." Cikin sauri yana Murmushi ya amsa ma ta da faɗin. "To ai Shikenan babu damuwa Allah ya sa naji Alkhairi gobe zan dawo." "Ameen." Ta amsa tana yunƙurin barin wurin. "Bakiji ba." Ta juya ta kallesa ba tare da ta ce komai ba. "Ga wannan a kai ma 'yan ƙannina." Ya faɗa yana miƙa ma ta ledar hannunsa. "A'a wallahi da ka barshi Allah amfana." "Ki karɓa Kawai kinsan dai babu kyau mayar da hannun kyauta baya kuma ai ƙannina nace ki kai ma." Tayi Murmushi sannan ta karɓa ta ce. ''Sun gobe." Sallama suka yi sannan ya tafi ita kuma ta shiga gidan su da isarta ta sama Mahaifiyar su a ɗakinta tana zaune ita da Salamatu da alama fira suke yi nan bada ɓata lokaci ba ta sanar musu yadda suka yi da Abdulyasar. Hajiyarsu tayi Murmushi irin na manya ta ce. "A'isha ki tsaya ki nutsuwa idan wannan yaro ya yi miki falillahil hamdu haka ake so sai a girmama zancen idan kuma bai yi Miki ba Ubangiji ya haɗa kowa da rabon sa, sai dai ni aso samu na kuyi Aure gaba ɗayanku a wannan shekarar." Aisha tayi Shiru cike da nazarin Maganar Mahaifiyar tasu sai dai ba tace Komai ba sai da aka ɗan jima sannan ta amsa da faɗin. "To Mama In sha Allah." Hajiya tayi Murmushi. "Kuje ku kwanta dare nayi Allah ya bamu Alkhairi." Suka amsa ma ta sannan suka yi ma ta sallama suka wuce zuwa Ɗakin kwanarsu basu daɗe da fita ba ita ma ta fito kai tsaye ta wuce ɗakin Mijinta ta sanar da shi dukkanin yadda suka yi da Aisha. Washe gari koda Abdulyasar ya dawo ba tare da ɓata lokaci ba Aisha ta sanar masa da ta amince da ya turo magabatan sa. Ya yi farin ciki sosai domin kuwa tsakani da Allah yake ƙaunar Aisha da zuciya ɗaya. Aikuwa bai jira komai ba ko sati ɗaya ba'a cika ba ya turo magabatan sa domin tsaida Maganar auren bayan tataburza da aka sha tsakaninsa da su na cewa ba zasu taɓa yarda jininsu ya aure jinin talakawa ba wulaƙantattu sai dai babu yadda suka iya Abdulyasar shi ne jinin jikinsu ganin yadda ya rikice musu ne yasa ba don suna son auren ba suka je aka nemawa ɗan su Abdulyasar Auren A'isha, kuma cikin ikon Allah an basa Aisha nan dai aka tsayar da Rana Watanni uku masu gaba towa za'a ɗaura Aure, sosai Abdulyasar ya yi farin ciki da murna abin har mamaki yake bawa Aisha nan ta fahimci cewa lallai ba ƙaramin so yake ma ta ba, to amma danginsa fa shin suna sonta kwatankwacin yadda Abdulyasar yake son ta?. Wannan shi ne tambayar dake damun zuciyarta a koda yaushe. * * * Tabbas rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya, lokaci na wucewa sauri sauri yayin da sakanni mintoci awanni suke shuɗewa ranaku satikai watanni suma su shuɗe su wuce wucewa na har abada haka wannan lokutan da suka gabata gaba ɗaya cikin shirya shirye na bikin ake, da yake da Bikin Salamatu za'a haɗa ita da masoyinta Adamu da suka daɗe suna tare kuma an yi bincike kam ba laifi bashi da wata mummunar hali dai a zahiri wannan dalilin yasa aka haɗa auren nasu gaba ɗaya za'ayi lokaci guda. A Ranar wata Litini misalin ƙarfe biyu na Rana aka ɗaura Auren Abdulyasar Turaki Turba tare da Amaryarsa A'isha Dauda Mai Allo bisa sadaki mafi daraja da dacewa lakadan ba ajalan ba. Yayin da gefe guda ma aka ɗaura na Adamu Jibril tare da tasa Amaryar Salamatu Dauda Mai Allo. Wannan rana ita ce ta kasance Rana ta farin ciki ga kowa musamman Amare da angwaye kowa ka kalla fuskarsa wadataccen farin ciki ne kwance. *KIN CUCE NI* _Story And Writing_ _By_ (Oum Yasmeen) And *_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_* (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k *Tambas rayuwa komai na rayuwa me wuce wane ya Ubangiji ka bamu iƙon aikata dai dai arayuwar mu Allah ya jiƙan ki aneesa Allah yasa kin huta wannan page sadakar wace agare ki nayi rashin yar uwa bazan taɓa iya samin madadin ki ba anee wanda ya fimu sonki ya amshe ki Allah yasa Allah janna CE nakomar ki* *Tunatar wa* _Bawa ya taɓa tsairewa kaddararsa sai dai muyi addu'a Allah ya bamu me kyau in kuma ya jarabamu Allah ya bamu iƙon cinye jarabawar sa_ ```ina sanar da masoyana cewa zan sabon littafi me suna DESTINY OF LOVE wanda da ga shi zan tsaya da rubutu sai kuma lokacin da Allah ya bani iƙon dawowa``` _Ep 5_ *End of previous of last episode* Wannan rana ita ce ta kasance Rana ta farin ciki ga kowa musamman Amare da angwaye kowa ka kalla fuskarsa wadataccen farin ciki ne kwance. *Continue* Samalamtu aka fara kai wa gidan dake dandago indo sun rabu cikin kewar juna da ƙƴar aka raba su gidan salamatu dai dai na me rufin asiri ɗaki ciki da floor da toilet a cikin bedroom ɗin ga shareren tsakar gida ga wasu ciki da floor har guda biyu gidan ba matsatsi nan fa yan bani na iya suka fara cewa tab wata ran dole ya kara aure tun da har part biyu yayi ƙaton kitchen ne a tsakar gida kai kace shagon siyar da kayan kitchen malam yayi bajinta ko wacce yayi mata gara ta ban mamaki nan fa mutane ne suka ƙara ruƙe haɓa cewa malam yana da zuciyar yi tafiya akai aka barta ita daya da yake bata da kawaye ___________________gidan malam Shiru shiru ba azo daukar A'isha ba nan ba wasu da ga cikin yan gulma suka fara tsaigunmi daman sunyi mamaki da alhaji Junaid turaki turba har ya yarda ɗansa zai aure yar talaka ko wa yasan cewa wannan family turaki turba basa auran bare sai dan ɗangin su muzaye ne na asali mahaifiyar Alhaji Junaid kuwa baggara ce wato (shuwa arab ) shi yasa suke da kyau na bammamaki ba su yarda bare ya raɓe su ba yanzu fa Alhaji junaid shine chef accounter na Kano baki daya duk wani kudi da za'a fitar sai da sa hannunsa ƙanin sa kuwa Alhaji Zubair shine former governor yanzu haka gari guda duka kwasa a unguwar janbulo suka gina estate duk wani dan family ɗin sun mai gida aciki kama baki wata tsohuwa tayi tace "Tab ina tausayawa indo yanzu cikin wannan daular zata shiga ?, Wata ta taɓe baki tace "Ae kwaɗayi ya kai ta shi daman mabuɗin huya ne wace mata barno gabas ce duk irin samarin da suka dinga nunawa suna sonta amma ta bujire rabon huyane akanta, A fusace hajiya Ruqayyah ta fito tace "Sai de kiga huya a ya'yan ki me isa mutane baku da shedar kirki bakwai fadar alkhairi Insha Allahu indo da abdulyasar mutu ka raba banzaye ku tashi ku fitar mana daga gida , Sum sum suka fita har wannan tsohuwar girma yayi gardama ɗaki ta koma kai da gwiwa ta haɗa tana kuka yau sai de ta kwana a wanni gidan da ba nasu ba yau wata sabuwar rayuwar zata fara me cikin da kalubale kala kala tambas rayuwar aure ibada ce duk kuwa abin da aka ce ibada to sai anyi haƙuri Wasu irin baƙaƙen Benz ne suka iso nan fa wa yanda aka kora suka ce ba ayi basu ba suka shiga cikin mota ai kawa akai anzo daukar amarya tana kuka tana ruƙe inna aka shigar da ita cikin mota a jere motocin suka fara barin unguwar wata mata ce ta tsaya me mashin ya sauke ta kallo daya za kai mata kasan ba mutuniyar kirki ba ce tsayawa tayi tana bin motocin da kallo tace " jar ubancan tab aliko daman ya'yan malamin nan me ƙudi zasu aura aliko?, Gyara tsayuwar mashin ɗinsa yayi yace "To yar hau ko kin ƙƴasa ne dan nasan halinki duk gidan da yake da danshi nan kike zuwa lokacin da da danshin ya ƙare sai kiyi gaba dan ma kefa ba me haihuwa bace yasin da ƴa'ƴan ki sunfi goma shegu da ya'yan sunnah, Duka ta kai mai tace "Wa wacce haihuwa tab ai saide in alahira anayi inyi ai wani matsiyaci na samu ashe ba mutumin kirki bane ya kaini gidan sa muka gama sex ɗin mu ina haka ya shaƙamim hoda sai tsintar kaina nayi a sabiti wai ancire min mahaifa , Dariya yayi harda ruƙe ciki yace "Gaskiya tantiriya baki da rabon shiryuwa yanzu har haka ta faru a kanki baki dena bin maza ba ?, Riƙe hannunsa tayi tace "Hmmm aini ina tashi cewa nayi anragemin shan magani yanzu inzaka kwanta dani sau dari Zan dau ciki ne kai nifa wallahi gaba ta kaini kana ga huni nake a sabon gari ina kwalta, Dariya yayi yace "Tantiriya kifi karfin kaina yasin jakar ubancan nikam ina nan ina shirin barin harkar nan yasin, Mayafin ta ta gyara tace "Ai sai kayi ni yanzuma gobe zan tafi garin ogun state kauyen ilaro kasan fa su sun iya sari na tashin hankali kai wallahi daga su sai India kaga duk fadar asirin India dake to wallahi bokan yarabawa ya fisu zan je ariki tamin zuciyarsa malamin nan kai sufa tsafi suke yi ba asiri ba , Sakar baki aliko yayi yace "Tantiriya anya kuwa kina da imani nasan halinki yanzu zaki tarwatsa mai gida kefa sheɗaniya ce Please dan Allah kibi wani ba malam ba wallahi yana da kirki kullum sai yayi min addu'a abokin mahaifina ne , Daurin kanta ta gyara tace "Yasin sai de kayi Ni nayi nan tayi gaba abinta ________________*unguwar janbulo* Motocin tafiya suke cikin tsari ba wacce take kauce hanya har suka isa unguwar janbulo tun daga farƙon layin akai ɗan allo aka sa *turaki turba Street* wani irin shegun gine gine ne turawa ne sukai ginin yawa kana Dubai tsarin ginin Dubai akayi ga wasu irin shegun benaye masu tsayi a harabar estate ɗin suka tsaya hajiya Ruqayyah da yayar malam wato saratu suka ruƙota kai tsaye Bangaren Hajiya fa'iza aka kai ta domin ita ce mahaifiyar abdulyasar shiga sukai floor na alfarma tana zaune yawa kana afadar queen Elizabeth ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya hannunta shaƙe da dam wani irin swiss less ne ajikin ta colour army green da adon light purple a jikinta ta ci ɗauri ture kaga tsiya ta haɗa girar sama da kasa kai kace wata boss ce fara ce kal yawa balarabiya gaban Hajiya Ruqayyah ne ya waɗi amma sai ta dake sukai sallama Bata amsa ba me yimata tausace ta amsa tace "Wa'alaikumussalam barka kun da zowa ku shigo Ita kuwa gimbiyar ko nuna alamun tasan da shigowar mutane batayi ba sai ma ɗaukar remote tayi ta canza channel zuwa Bollywood ai kuwa tayi sa'a suna Film ɗin khafi kushi khafi gamman mai da hankalin ta tayi kan sa sai da Hajiya Ruqayyah tace "Barka da wannan lokaci uwar masu gida yau Allah yayi A'isha ta zama daya ga cikin ahalin ku ga amanarta nan , Ya tsuna fuskan tayi tace "Yauwa barka dai , Duban gefen ta tayi tace wa yar aikin ta "Jeki Sama ki kira min surayyah da kaltum, Sannan ta juyo tace "amma ban ɗau amanar k ........✍️ *KIN CUCE NI* _Story And Writing_ _By_ (Oum Yasmeen) And *_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_* (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k *EP 4_6.* Gaba ɗaya suka saki baki suna kallon ta cike da al'ajabi Hajiya Rukayya ta girgiza kai sosai take tausayawa Aisha da zata tsinta kanta cikin waɗan nan mutane waɗan da basu san dajara na 'yan uwan su mutane ba. Daidai lokacin kuma Surayyah da Kalthum suka sauko Down suna bin mutanen da kallon ƙasƙanci suka sama wuri suka zauna. Su Hajiya Rukayya basu ja zancen da nisa ba suka basu amanar amarya basu jira amsawar su ba suka fito Direct Apartment nata suka wuce da ita nan ma sai da suka kuma ma ta nasiha sosai kuma suka ja hankalinta sannan daga baya suka shishshiga mota domin komawa can gida dan kuwa sun ce ba zasu kwana ba. Sosai A'isha taci kuka kamar ranta zai fita kanta har ciwo ya fara tsaban kuka da ta sha. *_A TAƘAICE DAI_* A Ranar ango ya shiga Dakin masoyiyar sa A'isha kuma Matarsa cike da Tsantsar so ƙauna da tarairaya ya mantar da ita dukkan wani damuwa da take ciki da tsoron danginsa da ya fara ɗarsuwa a ranta duba da irin tarbar da ta samu wurin Mahaifiyarsa, sun raya daren nasu ne cike da ɗin bin kula ga junansu cike da so da kauna haka ma ɓangaren Salamatu da angonta sai fatan zama lafiya. _____ *_Marka Ba Tabbas _* Shi ne sunan ta kuma wanda aka fi sanin ta da shi tsahuwar kilaki ce aurenta babu a dadi tana fitowa Sanadin hakan ne ma ake kiranta da Marka Ba Tabbas domin kuwa bata da Tabbas Indai akan maza ne kamar riga haka ta ɗauke su tana sakawa da cirewa a duk lokacin da ta ga dama ita kanta ba ta san adadin Auren da tayi ba balle kuma yawan mazan da tayi tarayya da su ba ta hanyar Aure ba, Balan tana uwa uba adadin cikin da ta zubar. Wa'iyazubillah. Tana da Yarinya ɗaya da ita Kanta batasan Wane ne uban Yarinyar ba shin cikin mazajen da take Aura bata zama ne ko kuwa cikin shin mazajen da take mu'amula dasu a kan titi ne?. Tun ranar da ta kyalla idon ta akan Malam Dauda Mai Allo Ranar da yake aurar da Yaransa kuma taga Irin tanfatsa tanfatsan motocin da suka zo ɗaukar Aisha Ranar ɗaura auren ta raya a ranta ta ga Mijin aure domin kuwa a washe garin Ranar asubanci tayi wurin zuwa ogun state wurin bokan ta da mummunar ƙuduri a ranta. ____ _Amare kuwa_ Watannin Aisha uku a gidan Abdulyasar tsakaninta da Mijinta sai sam Barka suna zaune Lafiya Qlau abin su cike da so da kuma ƙaunar junansu mara adadi yayin da gefe guda take karɓar wulaƙanci da cin mutunci tozarci duk daga wurin dangin mijin nata ba daga 'yan uwansa ba haka ma ba daga mahaifiyar sa ba, ko ta ina dukan ruwa take kwasa a wannan 'yan tsakanin ne kuma ciki ya bayyana a wurin A'isha da sanadin hakan ne kaɗan daga cikin uƙubar da take kwasa wurin mahaifiyar Mijin nata ya fara raguwa tun lokacin da ta fahimci Aisha tana da cikin ɗan ta ma'ana dai zata sama jika duk da ba ƙaunar Aisha take ba amma tayi farin ciki da hakan ta kasance kuma ta fara tsawatar wa sauran mutanen Ahalin Turaki Turba masu uzzarawa Aisha ɗin. Ta ɓangaren Salamatu kuwa da fari lafiyar Allah suke zaune Qlau da Mijinta Adamu sai dai daga baya ya fara fito ma ta da mugayen halayensa da ya ɓoye ma ta a farko kaɗan daga ciki su ne Abu kaɗan zatayi ya hauta da faɗa wasu lokutan ma har da duka da zagi Sanadin hakan ma har gida tasha komawa yaci tun ba'aje ko'ina da auren ba amma haka zai zo yayi ta ma ta ƙaramar murya har ta haƙura ta koma kwanaki kaɗan su wuce ya ci gaba dama mai hali baya fasawa. Ta ɓangaren Marka kuwa tuni ta aikata dukkanin muna nan ƙuduranta lokaci Kawai take jira domin kuwa ta ɗa na ma Malam Mai allo tarkon ta babu mai iya fidda shi sai Ubangiji. ____________ **** "Dan Allah Hajiya ki Dena wannan kukan mana sai kace wata ƙaramar Yarinya fisabilillah kin tasa yara a gaba kina ta wani kuka." Hajiyarsu A'isha ta fyace majina tana gallawa Inusa harara cike da baƙin ciki da taƙaici ta ce. "Ɗan juma ka kiyaye ni wallahi tun kafin raina ya ɓaci nayi maka abin da ban yi niyya ba shashasha kawai." Gum Ɗan juma ya yi daga bisani ma ya fice daga gidan baki ɗaya ko kula matarsa dake zaune gefan Aisha da ta miƙar da ƙafafu ga cikinta da ya tsufa haihuwa Yau ko gobe bai yi ba. Salamatu dake gefe tayi Murmushi a ɓoye ta ce. "Hajiyarmu Dan Allah ki Dena wannan kukan ina ce dai idan Amaryar tazo ba'a kanki zata zauna ba kam nifa banga abin tayar da hankali ba anan wurin badai amarya ba ce Allah ya kawo ta lafiya." Hajiyarsu A'isha ta kuma fyace hanci ta ce. "Salamatu ba zaki gane bane wannan matar da uban ku zai Auro min ba kalar matan da kika sani ba ce tsahuwar kilaki ce fa fisabilillah da tsufan mu gaba ɗaya ni da shi ya rasa wacce zai Auro min sai tsohuwar kilaki." Ta kuma rushewa da kuka. Salamatu tayi ka saƙe tana Kallon ikon Allah. Yayin da Aisha taja ajiyar zuciya tana faɗin. "Allah Sarki Rayuwa tunda nake ban taɓa tunanin koda a mafarki ba ne wai Baba zai ƙara Aure saboda bai yi ba tun ƙuruciya sai yanzu ni kam babu abin da zan ce sai Allah ya bada zaman lafiya. Hajiyarmu ki kwantar da hankalin ki Dan Allah ki Dena damuwa ita Rayuwar ma gaba ɗayanta nawa take da zaki dame kanki akan wannan ƙaramin abin, wata ƙila ma jahadi zai yi wata ƙila hakan ya zama sanadin shiryuwarta tunda ance tsohuwar kilaki ce." Gaba ɗaya Shiru suka yi suna sauraren Aisha kuma tayi gaskiya a zancen ta Hajiya ta ja Ajiyar zuciya ta ce. "To shikenan A'ishata zan gwada Allah ya muku albarka." Suka amsa da Ameen gaba ɗaya. Fira suka ci gaba da sama sama domin ranar sun zo ma ta wuni ne basu suka koma gida ba sai dare Alhaji Abdulyasar Matashin mai Dukiya a wancan lokacin ya zo ya ɗauki Matarsa A'isha daga nan suka rage wa Salamatu hanya suka kaita har gida sannan suka wuce nasu Gidan. _____ A kwana a tashi babu wuya wurin mai duka. A Ranar wata Laraba ce misalin ƙarfe sha ɗaya na safe aka ɗaura auren Malam Dauda Mai Allo da Amaryarsa Marka lakadan ba ajalan ba. An yi shagali kamar ba gobe zuwa dare Amarya da tawagar ta waɗan da mafiya yawa 'yan bariki ne suka iso gidan Amarya ta tare lafiya tare da Yarinyar ta Iyami sai fatan zaman lafiya. Wata ɗaya da Bikin zuwa lokacin har cikin Aisha ya fita a watan haihuwa amma Shiru kakeji kamar malam yaci shirwa. A yammacin wata Ranar Juma'a ce Aisha ta haifo santalelan Yaron ta fari sol mai kama da uban sa a haske amma Komai na mahaifiyarsa ya ɗauko har Dogon hancin haske ne kawai na ubansa yaro ya zo duniya cikin ƙoshin lafiya haka ma A'isha lafiyar Allah ta haihu. Sai dai me??. Cikin dare ta fara zubar da jini sosai abin da ya ɗaurewa mutane kai tasha wahala sosai domin kuwa ba ƙaramin jini ta zubar ba ko kafin safiya Allah Ubangiji da ya fi mu son ta da ƙaunarta ya amsa abin sa A'isha ta tafi gidan gaskiya ta bar jaririnta. Wannan rasuwa na A'isha ba ƙaramin Girgiza al'umma ya yi ba musanman ma 'yar uwarta Salamatu da mahaifiyar su Hajiya ba ƙaramin bugun su mutuwar tayi ba balle kuma uwa uba Mijinta Abdulyasar kusan susucewa za'ace ya yi kusan ƙaramin hauka a lokacin domin kuwa har aka yi bakwai na Aisha bai dawo daidai ba har sai da aka yi arba'in ne ma sannan ya fara magana. Yayin da Salamatu ta ci gaba da kula da yaro da yaci suna Aryaan bayan tataburza aka kwasa tsakaninta da Dangin ubansa kafin yaron ya dawo hannunta....✍️ *KIN CUCE NI* _Story And Writing_ _By_ (Oum Yasmeen) And *_Khadeejarth Sabi'u Yahyah Kaduna_* (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k *Tambas rayuwa komai na rayuwa me wuce wane ya Ubangiji ka bamu iƙon aikata dai dai arayuwar mu Allah ya jiƙan ki aneesa Allah yasa kin huta wannan page sadakar wace agare ki nayi rashin yar uwa bazan taɓa iya samin madadin ki ba anee wanda ya fimu sonki ya amshe ki Allah yasa Allah janna CE nakomar ki* *Ep 7* Nanfa adamu mijin salamatu yayi tsalle ya dure yace "Be yarda ta dauki wani ɗaba inku wa ki ka yarda ki ka dauka shinkafa wannan silli ɗaya be yarda a bashi ba ke Ruwa maƙwarwa ɗaya banyar da ki bashi ya shaba in har nawa ne domin bani ne a hakku na in ciyar da shi ba , Kuka tasa ta fyece majina tace "Na yarda da duk abin da zaka shinfiɗamin inde zaka barni in ruƙe Aryan Zan yiwa yaru uwata halatci, Malin malin ya buɗa yace "Owo miki har yayi gaba ya dawo ya ce "Yauwa ƙarkiji a gari kice ban miki a dalciba gobe za a ɗauramin aure hhhh aikinsan shi aure kamar jahadi ne musamman ko ka auri kilaki ko mara gata tasana diyar haka sai Allah yayi maka gafara a'a bawe gajiya nayi da baki kina ci ba ba haihuwa sai dai aimin kashi a shatda (masai) inkira me yasa ya kwashe min yasa kafa ya fita , Kuka salmatu tasa ta rungume aryan ganin irin ruƙon da tayi mai yaron yasa kuka sausauta ruƙon tayi ta goyashi ta fita ta ɗeɓo ruwa a fanfon kusa da gidan ta ajiyewa tayi kuɗi ta ɗaga langarta ta ɗauko ta fita ta siyo icce lufuf aryan yayi a bayan ta hura huta tayi ta ɗora ruwan wankansa wan tayi mai haka rayuwa ta cigaba da tafiya adamu yayi sabon aure yanzu ba ko da yaushe yake bawa salamatu abinci ba duk dan aryan ya rayu ba sana'ar da batayi ba Jinsa take tamkar yaya indo bayan auran hansatu da wata daya Allah ya bata ciki kar kuzo kuga murna harta dangin mijinta sai su ɗinga ya da mata da habaici suke ko a fuska ba ta damu ba yau haka ta shirya bayan ta gama surfe zata gida shi kansa mahaifin aryan yawa an kaudamai da hankalinsa daga kan yaron baya zuwa gunsa yana dashi dai dai da sabulu be taɓa kawo mai ba tafiya take aƙafa har ta isa unguwar su a bakin ƙofar gida ta tarda yaya dan juma yana zaune yana al'wala da sauri ya tashi ya toƙare ƙofar gidan ya ɗauki wani sanda yace "Yasin kika matso nan sai na shemeki haka ƙurum ki ɗinga zuwa kina cinye mana abinci Ni kai na nida matata be wada cemu ba ke kizo keda shirgegen ɗanki me ƙaton kai kuci da idanuwansa yawa mujiya maza koma inda kika fito, Kuku salamatu ta tace "Yanzu yaya in duniya ta juyan baya bantaɓa tunanin kai zakai min haka ba yanzu yaron nan ɗafa marigaiyane fa, Tsaki yaja yace "A to yanzu dan marayane me yahana ubansa ruƙe shi ke wallahi fa ki kiyaye ni kar inyi ƙuliƙulin kubura da ke ?, juyawa tayi ta koma bata ce mai ƙala ba tafiya take kamar zata waɗi abubuwa summata yawa tana komawa gida ta tarar an kwashe mata kaya an mayar da shi ƙaramin ɗaki wai amarya yau za a kawo mai sosai ta shiga mamaki amma ganin hansatu tana ta shiga tana fita tana turo ciki bata kulata ba tasan neman magana take akanta malam ya dawo ya daketa akan hansatu sauko da aryan tayi yaron yayi wayo sosai jikin sa taji zafi da alama awon haƙuri ya fara kwanciya yayi a cinyar ta taɓa shi tayi taji jikinsa ya saki gaban tane ya waɗi ta ɗauke shi ta goya ko motsi bayayi asibiti ta kaici cikin gaggawa akan amsheshi wata allura aka rubuta mata me tsada ce zata kai dubu goma aikuwa bata da zaɓi sai ta tafi gidan su abdulyasar a kafa ta tafi tana kuka ba kuɗin hawa mota domin ance tayi sauri ta kawo ƙar jijjigar da yake ta taɓa mai ƙwaƙwalwa da ƙƴar me gadin ya barta sai da tayi zaman jiran abdulyasar can sai ga motarsa ta shigo cikin sauri ta tashi ta isa gunsa wata mace ce tafito kamar balarabiya ga uban ciki a ƙƴar take tafiya cikin sauri tace "Abdulyasar , Cikin sauri ya juyo sai da ya ƙura mata ido sannan ya gane ko wace huyanta tamkar zaka zura hannu ka ɗauko ƙashi saboda rama yace "Salamatu yakike?, miƙo mai ta ƙarda tayi tace "Lafiya lau abdulyasar aryan babu lafiya ance in maza in kawo ta ƙar ta taɓa mai ƙwaƙwalwa, Ƙansane ya sara masa da sauri ya dafe yace "Ki haƙuri Wallahi yanzu nan na dawo daga asibiti bani da shi na biya dubu dari Domin duba halin da ɗan cikin juwud yake ciki gwara shi ya zo duniya ta kuwa kin ga kuwa dole inbiya a dubata gobe ma zan koma dan haka bazan baki kuɗi ƙar muyi rashi biyune ga ita gashi to ina amfanin haka amma zaki iya zuwa gidan radiyo ki faɗa ko a samu me tausayi ya bayar......✍️ *KIN CUCE NI. 8* _Story And Writing_ _By_ * (Oum Yasmeen) And (Nainarh KD)_ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k _____ Zakaran da Allah ya nufa da cara, ko ana muzuru ana shaho sai ya yi. ____ Life is beautiful with full of badly destiny against the Unjustly.🔥 ___ Sam bata bari ya ƙari sa faɗan abin da yake niyyar faɗa ba cikin wani irin tsawa da tuƙuƙin baƙin ciki ta katsesa ta Hanyar ɗa ga masa hannu ta ce. "Naji Abdulyasar Tabbas ka bani mamaki ban taɓa tunanin zaka yiwa jinin Adda Indo haka ba kuma ɗan ka na cikinka sai dai ba laifin ka ba ne na gode da kulawa sannan ina maka fatan gaggawar dawowa cikin hayyacinka domin wannan mutumin dake gabana ba Abdulyasar mutumin kirki da na sani ba ne, wannan mugu ne mara imani da tausayi." Da gama faɗin hakan ta sa kai ta wuce abin ta zuciyarta cike fal da baƙin ciki da damuwa yayin da Abdulyasar ya yi tsaye yana bin ta da kallon mamaki sam ya gaza motsi ko kaɗan jikinsa ya yi sanyi ƙalau da maganganun ta. **** A taƙaice haka Rayuwar ta ci gaba da kasancewa Salamatu cikin wannan mummanar hali da ta tsinci kanta. Aryaan yana asibiti rai a hannun Allah gaba ɗaya hankalinta a mugun tashe yake bata da wani Buri da ya wuce samun lafiyar Aryaan wannan dalilin ya sa ba tare da wani dogon tunani ba ta kwashe gaba ɗaya kujerun ta tun na aure duk sun fara fita hayyacinsu ma sakamakon katakon da aka yi amfani da su wurin haɗawa ba masu inganci ba ne ta siyar gaba ɗaya. Da kuɗin ta samu ta biya aka yi ma Aryaan Allurar sannan aka haɗa su da magunguna suka dawo gida tana ci gaba da kula da shi ragowan kuɗin dake Hannunta ta tattala abin ta ta fara sana'a. A Rayuwar Salamatu babu kalar baƙar wahala da sana'a komai wuyanta da batayi ba domin ganin Aryaan bai kwana da yunwa ba haka da kuɗin sana'ar ta samu ta ƙuƙuta wuya da daɗi ta saka sa a makaranta ta arabi da boko bayan ya fara tasawa.... Ta ɓangaren Rayuwar aurenta da Adamu mijinta kuwa abin sam babu daɗi domin kuwa sam bai ɗauke ta da wani muhimmanci ba da ita da babu ma a wurin sa duk ɗaya dan shi har mantawa da ita yake musamman ma da ya sama mata 'yan Duniya Hansatu Tantiriyar mace da banda bin bokaye da malaman tsubbu domin mallakar miji babu abin da ta iya. Haka ma Maryamu sai dai ita ba boka balle Malam sai shegen kissa da kisisina Wurin ta shi ya sa gaba ɗaya suka susuta Adamu ko kallon Salamatu ma ba ya yi dama kuma can halinsa ne wulaƙanta mata suma su Hansatu ɗin ba tsira suka yi ba domin duk Ranar da abin nasa ya motso ko su ba ya bari.. Tohm haka dai Rayuwar ta ci gaba da tafiya Salamatu tana kula da ɗan ta mafi soyuwa a gare ta sama da komai na Duniyar ta wato Aryaan tana son sa sosai domin ita ce uwansa kuma ubansa bai san kowa da komai ba a Duniyar sa sai ita ɗaya.... Aryaan ya taso yaro ne shi mai matuƙar kaifin basira sosai wannan dalili ya sa ya kasance zagwagwurin jajirtaccen ɗalibi mafi hazaƙa cikin Makarantar su sam Aryaan ba shi da wani sake wa sosai da mutane domin ba mutum ne mai son yawan surutu ko hayaniya ba yana da sanyin hali da kyakyawar zuciya kyakyawa ne shi sosai domin komai sak mahaifinsa ya yo sai dogon hancin ne Kawai irin na Mahaifiyar sa. So da yawa idan ya tambaya Salamatu akan ainihin iyayensa sakamakon yawan gori da Adamu da matansa Hansatu da Maryamu suke ma sa akan shi ɗin agola ne cikin gidan ba kowa ba. Idan ya yi ma ta tambayar sai dai ta sha re hawaye Masu zafi ta faɗa masa kyawawan halaye irin na mahaifiyarsa Maragayya Aisha. Zuwa lokacin ya san cewa Mahaifiyarsa ta rasu sai dai bai san komai Dangane da Mahaifin sa ba duk da sanin da ya yi yana raye. A lokacin ne kuma wani babban abu ya kasance musu na alhini sakamakon hatsarin motar da Abdulyasar ya samu shi da matar da aka Aura masa juwud suka rasu sai dai 'yar su ɗaya tilo ta rayu mahaifiyar Abdulyasar ta ci gaba da kula da ita. Sosai Salamatu tayi kuka lokacin da ta sama labarin rasuwar Abdulyasar sai da ta ba uku lada ta bisa da addu'a shikenan kuma Aryaan ya zama cikakken Maraya. Sai dai ta ƙudirta a ranta ko wuya ko daɗi zata zame masa majingini na Rayuwa indai tana Raye bazai taɓa kukan rashin iyaye ba in sha Allah kuwa haka ta ƙudirta. Har zuwa lokacin kuma haihuwa Shiru daga Salamatu tun abin yana damunta tana kuka da damuwa har ta haƙura ta fawwalawa Allah komai domin yana sane da ita tabbas Allah maji roƙon bayin sa ne......✍️🌹 *KIN CUCE NI* Oum yasmeen And Nainarh KD https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k EP 9 _Previous_ Har zuwa lokacin kuma haihuwa Shiru daga Salamatu tun abin yana damunta tana kuka da damuwa har ta haƙura ta fawwalawa Allah komai domin yana sane da ita tabbas Allah maji roƙon bayin sa ne......✍️🌹 _Continue_ Yayin da adamu ya kara tsanan ta mata yanzu ya zare hannunsa akanta ficikarsa baya bata yau kam tana zaune tun safe take wankau ɗin da aka kawo mata wasu ma tayi a hanata kuɗin sallamar Aryan taji cikin sakin fuska farin ciki ya mamaye ta farin cikin ta ya dawo tace "Ɗan albarka andawo, Be fiye fara'a ba da sai murmushi da yasakar mata yace "Eh inna, Taƙarda ya miƙo mata goge hannun ta tayi sannan ta amsa yace "Taro ne na makaranta ance kowa abbansa yazo, Wani tashin hankali ta shiga gumi ya dinga yanko mata ƙoƙarin saita kanta tayi tace "Aryan Allah ya kai mu ai mace tana iya wakiltar namiji ni zanje, Be nuna da muwarshi ba sanin halinsa na zurfin ciki inna tace "Aryan, Ɗago kyawawan idanuwansa yayi ya dube ta yace "Na'am, Kuɗi ta ciro agefen zaninta ta miƙo mai tace "Inka cire kayan ka kasiyo karin kwaki ka sha kaji yau ban da kuɗin yin girki sannan ruwan da muke amfani da shi ya ƙare, Amsa yayi yace "TO, Malam Adamu ne ya shigo hannunsa riƙe da yaro amma aryan ya girme sa yana kuka wuf aryan yayi saurin shiga ɗaki baya kaunar ganin wannan mijin inna azalimine jama'a yana cire kaya yaji wani ashar da ya lailayo ya ɗannawa inna da sauri ya toshe kunne sa malam adamu yace "Wato dan rashin mutum ci shine kika yiwa musa faɗa to ke dan kutu mar uban ki kin haifa ne ko kinsan ciwon ƴa'ƴa da har zaki wa wani faɗa ke gaki yar gidan malam ko uwar iya?, Ajiye wankin da take ta ɗurƙusa ƙasa muryar ta na rawa tace "Malam kai haƙuri insha Allah bazan ƙara ba malam ganin su nayi shi da iliyasu almajinrin da ke yiwa hansatu tallah suna wasa da gaban su shine na ce mai babu kyau, Aguje hansatu ta fito daga banɗaki tace "To annamimiya ina gidan ban fita ba wato Ni za aiwa iya shege malam sai ta sa kuka ta shiga ɗaki ganin ran yar gold ya ɓaci ya tsinko igiyar da tayi shanya ya shiga labta mata yana ta sababi aguje aryan ya fito ya rungume inna yana kare mata Aikuwa haka ya haɗa su ya zane zuciyar inna ta ƙeƙashe dan haka ba kukan da tayi sai na zuciya gajiya yayi yana hura hanci ya bar gidan (Hattara iyaye yau duk wanda zai wa ya'yan ku faɗa to wallahi me ƙaunar ko ne musamman wannan yazu zamani yar da ake lalata ya'yan mu ba mazan ba ba matanba musamman masu ɗauko almajire ku ɗinga kula da irin wasannin da sukewa ya'yan ku yana gama ku bashi abin da zaku bashi ya tafi ƙar ku yarda wata alaƙa ta shiga tsakanin ku da ya'yan ku ya kama garuruwan da suke turo almajerai suji tsoron Allah baka san a ina ɗan ka ya ke kwana ba bakasan wake wa ya'yan ku tarbiyya ba wallahi ina jin ciwo in fito inga almajirai yara ƙanana a kawo su uwa duniya da sunan karatu abin mamakin shine har suna da kwanciyar hankali yaya su suna watan gaririya a gari Wallahi wani ma sai yayi sati malamin nasa be son baya nan ba me yasa Ubangiji yake jarabamu iri iri ai daman ya fadi in har aka kauracewa faɗar sa to zai jarrabemu su ya'ya amana ce a gare mu akwai ranar da Allah zai tambaye mu kiwon da ya bamu ) Haka rayuwa ta ci gaba da kasan a gidan dangin uban Aryan ba wanda yake zuwa ganin sa duk da cewa kamar su ɗaya da mahaifinsa ko hakan ya ja hankalinsu su soshi amma ba wannan shekarar Aryan goma sha huɗu yana gab da fita junior school Allah ya bawa salamatu ciki tun daga fitowar cikin nan abubuwa suka cakuɗe mata malam adamu motar sa ta ɗinga lalacewa nan fa ya dorawa cikin ta shi ya jamai domin shi har ya manta yau she rabun da wata ma'amallah ta aure ta haɗa su nan fa yace aljanune sukai mata ciki billahir lazi sai dai ta nemi uban ta acan duniyar aljanu haka ta ɗinga jurewa saboda matsaloli sun mata yawa gana matar ubanta ga nata ta daina zuwa gidan jikin ta yayi nauyi ana haka Aryan kungiyar tallafawa marayu da mara ƙarfi ta America ta ɗauki nauyin su a lokacin ya shiga senior yana aji biyu ganin kwazon sa yasa suka zaɓe sa duk da secondary ɗinsa a college of Qur'an yayi makarantar kusa da S.A.S ranar da yaci jarabawa ranar Allah ya sauki salamatu Ba tare da dugowar na ƙuda ba ranar kuma motar adamu ta kone ƙurmus shima sai zaro shi akai ga kuɗin mutane da kayan su yana dawowa aka shimfida mai tabarma ya zauna su maryamu da hansatu sai fifita akai mai ni kuwa ina ban ɗaki ina wanka fitowa nayi naga kafar shi duk akone sannu nayi mai da ƙƴar ya amsa shiga ɗaki nayi na ɗauko yarinyar da na haifa nace malam yau Allah ya sauke ni sa hannu yayi ya buɗe ta ihu ya saki ganin idanuwanta da kuma irin kyawun ta yace "Haba ashe yar aljanu aka haifar min shi yasa na gamu da wannan ifti'ila'in to ke da ita kutattara ku barmin gidan nan, Cikin kiss maryamu tace "Haba malam ai yanzu ka koreta sai su ƙona mu muna kwai ka ƙƴaleta ta amshi gashi, Dariya yayi yace "Kuma hakane fa , Girgiza kai salamtu tayi ta tashi Aryan da yake me jikin girma ne ya zama saurayi ya shigo bakin sa da sallama fuskarsa ta ƙasa ɓoye murnar da yake ciki tace "Inna na ci jarabawa ta nan da sati me zuwa zamu tafi kasar waje sun ɗauki nauyin karatuna........✍️ إِنَّ اللّهَ مَعَ الصَّابِرِينَ Tabbas Ubangiji yayi gaskiya me haƙuri yana tare da Allah Muslims will face all kinds of adversity, we will face all kinds of trials and bear all kinds of deprivation. This is why Allah in Surah Baqarah ayat 153 Allah says, surely he will be with the patient Allah is with those that are patient”. It emphasizes the Islamic concept of sabr meaning endurance, perseverance and persistence. For a Muslim, Sabr represents one of the two parts of faith 💔💔💔 *KIN CUCENI 10* 💔💔💔 BY OUM YASMEEN & Nainarh KD https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k _____ **** Duk da cewa sosai Salamatu tayi farin ciki da samun tallafawar gwamnati da Aryaan ya yi zai tafi zuwa ƙasar waje domin karatu amma bataso ta rabu da shi ko da kuwa na sakan guda ne sai dai babu yadda ta iya haka Allah ya nufa cikin wannan tazaran ne aka fara shirya shirye na tafiyar Aryaan zuwa ƙasar waje karatu ta hanyar tallafawar gwamnati. Yayin da gefe guda kuwa Salamatu take kula da Jaririyar ta Yarinya kyakyawar gaske fara tas ga hanci dogo ma daidaici komai nata daidai sai kwayar idanunta da suka kasance shuɗaye masu kyalli da kyau sannan suka janyo ma ta gagarumar tsana a wurin uban ta Adamu Jaririyar taci suna Aisha yayin da ake kiranta da Ilham. Ilham ta taso Yarinya ce Shiru Shiru bata fiye surutu ba Kuma tana da saurin kuka sosai sanadiyar tun tasowar ta bata da wani aiki sai kuka sakamakon yawan cizguna ma ta da Mutanen gidansu da unguwa suke yi suna kiranta da Aljana mai idanun mayu haka ma mahaifinta abin bai sauya zani ba daga garesa domin kuwa ba ƙaramar wahala da baƙar Azaba Ilham take kwasa a wurinsa ba, a cewar sa ita ɗin mai ƙashin tsiya ce kuma mai farar ƙafa domin tun da aka haifeta ya fara ganin Bala'i kala kala cikin Rayuwarsa da fari motarsa ce ta ƙone ƙurmus daga nan kuma sana'a ma gagarar sa take yi sai da kyar ake samun na cefane shi ne ya ɗauki karar tsana ya ɗaura ma Baiwar Allah Ilham a cewarsa ita ba jininsa ba ce saboda ita ɗin mai farar ƙafa ce ga kuma waɗan nan shuɗayen idanun nata na mayu. Tsaban tsanar da ya yi ma Ilham ya sa ko abincin gidan sa baya taɓa yarda a bata kuma ya ce duk wacce ta bata to a bakin Aurenta.... Waɗan nan duk suna daga cikin dalilan da suka saka Ilham ta taso a Rayuwarta bata da kowa sai mahaifiyarta dama tuntuni Aryaan yana ƙasar waje karatu bai dawo ba tsawon shekaru sai dai idan ya kira waya ta hannun wani sunusi ɗan unguwan ne suke samu su gaisa da Inna Salamatu... Hatta a makaranta bata sauya zani ba babu sunan da aka sakama Ilham kuma aka kiransa da shi fa ce Aljana mai idon Mayu wannan dalilin ya sa ko ƙawa Ilham bata da ita. Sai Naseeba da ta kasance ɗiyar Ɗan Juma ne Babban Yayansu Inna Salamatu ita kaɗai ce takeson Ilham har zuciyarta kuma take tausaya ma ta duk da cewa mahaifinta yana da rufin Asiri daidai gwargwado amma domin kuwa da daɗewa ma sun tashi daga unguwar talakawa sun koma unguwar masu da shi. Amma ko kaɗan baya tausayawa 'yan uwansa musamman ma Salamatu da take cikin halin buƙatar tallafi amma saboda rashin imani ko kallo ma bata ishesa ba, kuma ya hana matarsa ko 'ya'yansa tun karar inda Salamatu take balle su tallafa ma ta tsaban baƙar zuciya da rashin imani amma duk da hakan a ɓoye ba tare da kowa ya sani ba Naseeba take yawan kaiwa Gwaggon nata ziyara kuma tana tallafa ma ta da duk abin da bai fi ƙarfin ta ba.. **** _*Bayan wasu Shekara...*_ A yammacin wata Ranar Juma'a ce kuma Ranar da ta kasance ɗaya daga cikin ranakun da Salamatu ba zata taɓa mantawa da ita ba a rayuwarta. Ita ce Ranar da Ɗan Lelen ta Aryaan ya yi ma ta dawowar bazata domin bai sanar da kowa Dawowar tasa ba sai kawai ganinsa suka yi. A lokacin kamar kullum ita da ɗiyar ta Ilham da ta fara girma dan kuwa takai shekaru goma sha uku a Duniya suna daga can gefen tsakar gida Inna Salamatu tana fama da Sukola na aikatau da take yi yayin da Ilham take tayata duk da cewa ba wani iyawa tayi ba Kawai sai sallamar wata sassanyar Muryarsa mai cike da daɗin sauraro sukaji ya yi lokacin da ya shigo gidan Aikuwa gaba ɗayan su har da su Hansatu da Maryamu da suma suke nasu aikace aikace na gida da ma Adamu da yake daga kishingiɗe saman tabarma yana sauraren Radio gaba ɗaya suka juya suna kallon wani kyakkyawan matashin Saurayi dogo kuma fari mai faffaɗan ƙirji ma'aboci cikar zati da kamala sanye cikin wasu shegun Korean suit masu masifar tsada da kyau fuskarsa maƙale da wayfarer sun glasses da ganinsa kaga cikakken Bature ziryan bawai wanda ya yi haye ba domin daga ganin shigar nasa na Turawan zaka danganta shi da su.... Tsakanin ta da Allah da fari Inna Salamatu bata gane ko wane ne ba sai daga bayan ya cire Glasses dake rufe da manyan kyawawan idanunsa farare tar tar da su sannan cikin kamilalliyar Muryarsa ya ce. "Inna.! Inna ta Inna ni ne fa Ɗan Lelen ki Aryaan....!" Mutuwar zaune Inna Salamatu tayi baki wangame tsaban mamaki da kaɗuwa na jin kalaman sa da kuma tabbatar da cewa shi ɗin ne da gaske ba mafarki ba kamar yadda ta saba. Tsaban Farin ciki kawai sai ta saka masa kuka amma fa na farin cikin ganinsa da sauri cikin sassarfa ya saki Suitcase da yake janye da ita ya ƙari sa da sauri ya rungumo ta cike da farin ciki shima yana hawayen sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba tare da kowannen su ya iya sakin ɗan uwansa ba yayin da mutanen gidan suke binsu da kallo cike da mamaki... Farin ciki da murna na dawowar Ɗan Lelen ta ya mantar da ita duka wata wahalar da suka sha a baya ta miƙa dukkanin godiyan ta ga Allah lokacin da Aryaan yake bata labarin da daɗewa ya kammala karatun sa kuma ya sama aiki ne a can shi ya sa ya ɗiba waɗan nan shekaru ba tare da ya dawo ba a halin uma shi ɗin Pilot ne ma'ana dai Matukin jirgi.. Sosai tayi farin ciki da hakan sai dai ta nuna masa rashin jin daɗin ta na kwashe tsawon shekarun da ya yi ba tare da ya neme su ba nan dai ya bata da hakuri da kare kansa da faɗin can ɗin ne suka riƙe sa yanzu haka ma wata ɗaya kacal zai yi ya koma kuma ya tabbatar ma ta da zuwan sa gaba da zai yi in sha Allah tare zasu koma gaba ɗaya gefe guda kuwa mamakin girman Ilham yake yi Yarinyar da ya tafi ya barta ko wata ɗaya batayi ba a Duniya.... **** Kwanaki kaɗan da Dawowar Aryaan Inna Salamatu ta tilasta masa akan ya shirya ya zaga danginta ya sanar da su dawowarsa a so samunta ma har Dangin Mahaifin sa ya je amma tasan yadda Aryaan ya tsani dangin mahaifinsa ko giyar wake ya sha ba zai je ba. Sakawa ya tafi danginta domin kai musu ziyara shi ne wani babban kuskure da Salamatu ta tafka ba tare da ta san hakan ba domin kuwa Fateesat Jikar Gwaggo Marka matar Malam Mai Allo ta Biyu ita da Mahaifiyarta tun daga kallon farko da kuma samun labarin komai da suka yi akan Aryaan shikenan suka raya Fateesat ta sama miji ita kuma Mahaifiyar ta ta sama suruki domin a ganinsu banza ta faɗi Aikuwa ba tare da ɓata lokaci ba suka fara Aiwatar da mummunar ƙudurinsa akan Bawan Allah Aryaan da bai san suna yi ba. Watannin sa Uku da su Inna Salamatu zuwa lokacin ta murmure ta fara kumari ƙibanta ya fara dawowa haka ma Ilham. A lokacin ne ya yi musu sallama zai koma sannan kuma ya bawa Inna Salamatu lambar waya da zata dinga Kiransa sannan ya siya ma ta wayar ya tafi suna cike da kewarsa haka ma ita sai dai wayar nan da ya siya ma ta a Ranar da ya tafi ta nema ta rasa cikin gidan sama ko ƙasa. Daga wannan komawar da Aryan ya yi ne komai ya sauya komai ya lalace domin kuwa shekarar sa ɗaya da komawa sai da Mahaifiyar Fateesat ta tasan yadda tayi da Asiri ta aurawa Aryan ɗiyarta Fateesat suka bisa can ƙasar da yake kuma suka rufe bakin kowa babu wanda ya isa ya yi maganar. Sosai Inna Salamatu ta shiga matsanancin tashin hankali da damuwa lokacin da ta sama wannan Labarin sanadiyar hakan har ciwo sai da ta kwanta amma bai canza komai ba na daga mummanar ƙaddara dake tunkarar Rayuwar su shekarar Fateesat ɗaya da auren Aryaan ta hanyar mallake sa da Asiri suna zaune ƙasar da yake can zauna kwatsam ta kwazzaba masa akan zata dawo Nigeria ta zauna domin kuwa ba zata iya zaman can ba dama ta addabesa amma baya iya yi ma ta Komai haka ya nema ma ta tamfatsetsan gida katafaren gaske anan Nasarawa G.R.A Kano ta dawo ta ci gaba da sheƙe ayar ta tsawon shekara ɗaya ke nan. Yayin da ya kasance tsawon shekaru uku ke nan rabon sa Inna Salamatu ta kuma saka Aryaan a ido tun Dawowar da ya yi kuma tana nan maƙale da takardar da ya bata na lambar waya bata taɓa kiransa ba. A wannan taƙin ne kuma ciwon Ilham da take fama da shi ya tsananta har ya kai su ga kwanciya a asibiti likitoci suka tabbatar da aiki za'ayi ma ta sannan kuma kuɗaɗe ne masu yawa wannnan dalilin ne yasa hankali a tashe Inna Salamatu ta tafi gidan matar Aryan Fateesat a tunaninta yana ƙasar amma Fateesat tayi ma ta rashin mutunci marar daɗin faɗe a taƙaice dai wannan shi ne labarin Rayuwar Baiwar Allah Salamatu da ɗiyarta Innocent Ilham da take kwance a halin yanzu rai a hannun Allah...... _*Present*_ _Ci gaban Labari...._ *KIN CU CE NI* Story and writing By Oum yasmeen And Nainarh kd ___________________________________________________________________________________________________________________________ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k *EPISODE 11* Ajiyar zuciya me karfi ta saki kwallah na taruwa a idonta da sauri nasiba tace "Inna lafiya ?, Karfin halin ta aro tace "Nasiba lafiya qalau dare yayi ki tashi ki tafi kar aimiki fada , Zama nasiba tayi tace "A'a inna yaya bashi da niyar bugowa kinga mu tashi muje gida ko a cikin su musa Allah zai dube mu mu samu jini, Shiru tayi tana nazari bata so ranta ya ɓaci amma fa tilon yar ta tana gaɓar mutuwa ko rai ya kamata tayi wani abu duban nasiba tayi tace "Nasiba zauna ni zanje in nemo me jinin, Hannun Ilham ta kama inda taji sanyi qalau gashi ta ƙara yin fari tace "To inna Allah ya temaka mu samu, Amin tace ta fita tafiya take a hankali domin jikinta yayi mata nauyi ga ciwon kafar da take fama da shi jan kafar ta take har ta isa gidan su sallama tayi ba wanda ya amsa duk kuwa suna tsakar gidan ɗurkusawa tayi tace "Malam barka da yamma , Lomar shinkafa da miya ya kai bakin sa ta ji kifi zuƙu xuƙu ya haɗiye jikake yabada wani sauti kutt alamar ya abincin ya waɗa mai yace "Yauwa uwar gantali anya salamtu kina so ki shiga aljanna ?, Da sauri ta ɗago ta kalle sa tace "jikin ilham ya tashi yanzu ma jini ake buƙata me 0+ jininta ya ƙone za ai mata juyan jini to shine na dawo ko za'a dace a sami me irin jinin a gidan nan, Jin ta ambaci jini ya saki baki ya dakata da cin abincin furzar da na bakin sa yayi saboda duk daɗin abincin ji yayi yayi mai ɗaci yace "Maryamu hansatu jaƙar uban can kunga abin da nake so ku gane tun haihuwar yarinyar nan amma kukaƙi ganewa ko da kun barni na kore su amma ai gashi anxo kan gaɓa wallahi gidan sarkin ruwa yau zani na bashi ita ya aura dan shine dai dai da su ya nake jin wata masifa jini jini wato ta rasa na wanda zata sha shi ta bullo da wannan hanya ta shaye jinin ta tab yau akwai tashin balagar tsintsaye yasin ni za akawo wa rainin hankali ta zuke jini ance jini ya ƙone ai wannan tafi ƙaska, Hawaye ta share tace "Wallahi malam cuta ce ilham ba aljana bace mutum ce, Ƙwano ya ɗauka yayi jifa da shi aka ce sa'a be dira a ko ina ba sai a ƙasa ta kauce ya e "Kan uban can zanci bura'uban mutum ce ke salamatu ki nemo mahaifin yarinyar nan aljani ya amshi yarsa wallahi tashin hankalin nan har ina wallahi dole in nemo ma fita tab wani ta shanye jini tarasa yarda zatayi ban da jinin mu da take sha hakan be mata ba sai tayi me gabaki daya tashi yayi ya ɗaga malin malin ɗin sa yace "Hansatu daga be ni duk nabi na rame ashe shan jinin mu ake da bargon mu kai wallahi ba zata saɓu ba dole in nemo mafita satin da ya huce yar akuyar da na gada ta kasa sai mahauci nakira ya siya a she game ci a kusa kai wannan jarabar har ina gidan sarkin ruwa zani shine dai dai da su yasin ko ta nemo ubanta aljani ga yarda aka kawo yarinyar nan maryamu duk sai tabi ta fige yawa kazar matsiyata tun da aka haifi yarinyar nan dole indau mataki tun kafin ta sheƙani barzahu da sauran kwanana a gaba, Dadi hansatu taji tace "A'a me gida kawai ka aura mata sarkin ruwa shine dai dai amma yaushe zaka ce a nemo ubanta sai sun ƙara ƙona ka kamanta shekarun baya abin da sukai maka yanzu kuma kaga mekan uwa da wabi za suyi sarkin ruwan shine dai dai da su tunda har fito na fito yake yi da aljanu shi zai iya zama da ita Hula yaci re yace "Eh kuma hakane da zafi zafi ake bugar ƙarfe ya gyara babbar rigarsa wani yaro ne ya yace "Wai malam adamu yana nan inji idi tsohun direba, Washe baki yayi yace "Faɗuwa ta zo dai dai da zama muje ya rakani domin bilya hillazi yau sai na kawo karshen annobar nan, Tusa kan yaron yayi suka fita leƙawa hansatu tayi ganin yayi nisa tace "A hayye rass chass muna da shan biki rawa take tana juya ɗuwawu yawa lotsassiyar tasa, Tashi inna salamatu tayi bata nuna mata taji abin da ta ce ba ko ta gani sai da ta zo soro ta saki kuka ta rufe fuskar ta da mayafin ta yawa an kwato shi daga bakin kura tunani ta shiga yi wannan ne irin ubane yanzu yarinyar da shekarar ta goma sha shidda ita za aiwa aure da dan shekara 70 har ya'yan jikoki ya aurar tashi tayi ta bar soron ko gaban ta bata gani sosai ta nufi gidan mahaifin ta a kofar gida ta ganta gaishe dashi tayi Cikin kulawa ya amsa yana tambayar ta lafiya Bakin mayafinta ta sa ta share hawaye muryar ta na rawa ta bashi labari Shiru yayi yana tunani ya saki ajiyar zuciya yace ''insha Allah zan kawo karshen matsalar nan kije zan toro miki mudadssir ko jinin sa zeyi, Godiya taimai ta tashi dan ko gidan ba zata iya shiga ba isa asibitin tayi ta shiga ɗakin su nurse din ce ta dawo tace "An samo likitan da zaitai mata ta kusan zuwa tunda ta safe ta tafi baku samo ba, Inna da ƙƴer ta buɗe baki tace "Yanzu zai zo, To tace mata ta juya ta fita da sauri a wata matashiya ta shigo ta miƙa wa inna wayar tace "Gashi ankira, Hannunta na rawa ta amsa sai dai me ta katsai bata lura ba ta kara tana hell hello jin shiru ta sauke wayar nasiba tace "Ta katsai bara in ƙara kira, Tashi tayi tace "Nasiba bara inyi salla magariba ankira, To tace mata domin ita bata yi fita tayi ta ɗauro alwala ta da sallah ƙara kira yayi da sauri nasiba ta ɗaga ta fashe da kuka tace "Yaya katafi kabar inna da ilham ba lafiya tana nan rai a hannun Allah ga ciwon inna yaya me inna tayi maka ta can can ci rashin kulawa ƙarfin ta ya ƙare ko aikaton da take yi take samawa kanta abincin ci ta daina tallan da ilham keyi ba lafiya ta daina ba makaranta karatu ya tsaya yaya, Shiru yayi yana sauraren ta ji yayi kansa na juya mai anya kuwa ya kyauta ga irin halatcin da inna tayi mai anya kuwa lafiyar sa qalau ina kuɗin da yabawa fateesat ta bawa inna anya kuwa ma taje har ta bata ransa a mutuƙar ɓace yace "Fateesat ta baku kuɗi ?, Kuka nasiba ta saki domin ta tuno cin mutuncin da tayi musu Tsawa ya daka mata domin shi baya ɗaukar nonsense yace "Magana nace kimin ba kuka ba , Sanin halinsa tace "A'a munje sai zagin mu ma da tayi, Tsai kiran yayi ransa ya ɓaci wato da takira shi sun zo basu da lafiya har ya turo mata dubu dari biyu ta basu bata basu ba me fateesat take son zama Ita kuwa kallon wayar ta shiga yi kira tayi amma ba a ɗauka ba me yake nufi inna ce ta zo tace "Me yace miki ina lazumi naji kina magana?, Hawayen da tun ɗazu suke maƙale suka sami nasarar zubowa tace "Inna ya tsai ba abin da yace, Shiru inna tayi budurwar da ta saba su waya ce tazo ta amshi a barta Ganin tunanin zai zautar da ita ta sami gu ta zauna akan takalman ta tana karatun kur'ani da yake mahaddaciya ce ko zata sami sauƙi a zuciyar ta *********✍️💅****** 12&15 Last Of Free Page's 🙌 ✨💖 KIN CUCENI 💖✨ BY OUM YASMEEN AND NAINARH KD _____ Wannan littafin na kuɗi ne zaku iya biya ta wannan account ɗin har kati muna amsa MTN 8141785374 Zaku iya turo sheda ta nan 07067953066 Ko 09061890481 _____ Anan Asibitin suka kwana ita da Naseeba da sassafiya kuma Naseebar ta koma gida domin taho musu da abin karin kumallo yayin da Inna Salamatu ta tsaya tana ci gaba da kula da Ɗiyar tana, ko zuwa sha ɗaya na safe Naseeba ta dawo tare da abin da zasuyi karin kumallon sai dai daga gani ranta a ɓace yake. "Wani abu ne ya faru acan Gidan naga kamar bakya cikin walwala?." Inna Salamatu ta tambaya cikin kulawa.... Sai da Naseeba ta ja qwafa cike da takaici kamar ba zatayi magana ba sai kuma ta ce. "Babu komai Inna Salamatu kawai mamaki nakeyi wannan zamanin da mutanen cikinsa ace son Kai yayi yawa uwa ɗaya uba ɗaya ma bai ji tausayin ƙanwarsa ba ina ga mutanen gari kuma wannan abu yana bani mamaki da tsoro." Inna Salamatu tayi Murmushi mai ciwo da jin abin da Naseeba ta faɗa ko bata ma ta bayani ba ma tasan kwanan zancen. Buɗe baki tayi da niyyar magana sai dai shigowar da wata Nurse tayi da sauri ne ya sa ta dakata gaba ɗaya suka mayar da kallon su gareta. "Yallaɓai zaka iya shigowa nan ne ɗakin." Nurse ta faɗa cike da girmamawa tana kallon ƙofar Room ɗin yayin da Inna Salamatu da Naseeba da suka mimmiƙe tsaye suka zuba ido domin ganin mai shigowar. Cikin nutsuwarsa yake taku na burgewa ya ƙari sa shigowa Room ɗin gaba ɗaya ƙamshin sa ya cika ko'ina. Dogo ne kuma fari tas tas mai cikar kamala haiba ga kwarjini sanye cikin wata arniyar Korean suit maroon color ƙafafuwan sa sanye cikin wasu Oxford Shoes coffee Brown color hannunsa agogo ne na Rolex expensive kansa babu hula gashin kansa baƙi siɗiq wanda da gani ba ƙaramin kuɗi ake kashe masa ba a washe sai walwali yake gunin ban sha'awa gaba ɗayansa dai ya haɗu haɗuwa ba ƙarama ba. Sallama ɗauke a bakinsa ya ƙari sa shiga ciki yayin da Nurse ɗin tayi waje abin ta. Cikin Naseeba da Inna Salamatu har shi kansa uban gayyan rasa mai iya furta komai aka yi. Sai da kyar Naseeba ta samo kalamai ta haɗa a Bakinta ta ce. "Wa'alaika Salam kamar wannan dai kamar Yah Aryaan?..." Daga yarda tayi maganar zaka fahimci zallar mamaki al'ajabi a tare da ita. Zura hannunsa yayi cikin pocket trouser nasa ba tare da yace komai ba ya yi ma ta nodding kai alamar haka ne. Inna Salamatu kuwa rasa mene ne abin da ya kamata ta yi a wannan taƙin tayi shin farin ciki ko aka sin hakan, a hankali dai idanunta suka fara lumshewa alamar zata suma yayin da tayi baya zata yi ƙasa. Cikin wani irin zafin nama duk da ɗan Interval dake tsakaninsu Aryaan ya isa gareta tare da tallafota kam yana faman kiran sunanta. Buɗe idanun nata tayi ta zuba masa yayin da Bakinta yake motsi kaɗan alamar magana kafin ta iya cewa. "Ɗa na kai ne kuwa kai ne a gabana Ɗa na Aryaan ashe da rabon zamu sake ganin juna ashe da rabon zamu sake haɗuwa da kai bayan shafe waɗan nan shekaru." Wannan shi ne first time da ta kira sunansa tun bayan girmansa hakan ya sa cikin sauri tare da nadama bayan ya taimaka ma ta ta zauna saman wata Plastic Chair na wurin ya tsuguna da duka gwiwowin sa a ƙasa gabanta tare da haɗe hannunsa ya fara magana kamar dai haka. "Ni ne Inna ta ban san da wani ido ba, ban san da wasu kalamai zanyi amfani wurin neman afuwarki ba Tabbas nasan nayi butulci a gareki sai dai bayin kaina ba ne kamar a mafarki nake ganin komai Dan Allah Inna ta kiyi haƙuri ki yafemin da duka abubuwan da suka faru a baya..." Gefe tayi da kanta tana sha re kwalla na tausayin kanta da shi kansa ta ce. "Aryaan ai bakayimin komai ba rayuwace sai dai Tabbas naji zafi da kayi aure ba tare dana sani ba kuma ka rasa wacca zaka aura sai Fateesat ko ka manta mene ne abin da yake Tsakanina da mahaifiyarta ce uhum Aryaan?." Ta ƙarishe maganar tana kallon sa. Sunkuyar da kansa ya yi ya ce. "Ni dai ina mai bada haƙuri." "Karka damu in sha Allah komai ya wuce." "Na gode sosai Inna ta Allah yaji kan Iyaye gaskiya ke ta dabance." Duk abin da yake gudana tsakaninsu Naseeba tana daga gefe bata saka musu baki ba. "Ilham ce ta zama haka kodai ba ita ce Ilham dana sani ba?." Ya tambaya mamaki ƙarara yana nuni da saman gadon da Ilham ɗin take kwance rai a hannun Allah da alama Bacci ma take yi, mamaki Biyu ne a tare da shi na farko dai ta girma ba kamar yadda ya barta ba ta fara zama budurwa na biyu kuma yadda ya lura ba ƙaramin ciwo take fama da ba. Ko kafin ta basa amsa ya nufa hanyar fita yana faɗin. "Bari nazo Inna wurin Doctor zanje muyi magana akan rashin lafiyar nata." Da kallo ta bisa har ya fita. Da sauri Naseeba ta ƙari so tare da kama hannunta tana Murmushi ita ma Inna Salamatu ɗin Murmushi Kawai take yi Yaron ta ya dawo gare ta. Ƙoƙari sosai Aryaan ya yi a ɗan wannan taƙin ya biya kuɗin komai da za'a buƙata nan da nan aka shirya komai aka fara kici kicin shiga theater Room da ilham domin Aryaan ya yi kokari an samo komai har maƙudan kuɗaɗe ya biya a taƙin aka samo jinin da ake buƙata kuma an tabbatar da ingancin jinin sannan aka shiga da ita ɗakin aiki sai fatan fitowa lafiya. Kuɗaɗe maƙudai ya bawa Inna Salamatu da duk take cikin fargaba da fatan waraka ga ɗiyar nata sannan ya yi ma ta sallama da faɗin dama saukarsa a ƙasar ke nan ya yo hospital ɗin direct yanzu tun da komai ya saisaita zai wuce gida ya shirya sannan suka taho da Matarsa. Badan Inna Salamatu taso ba ta bari ya tafi domin fargaba take yi sosai na abin da zai biyo baya..... Shi kuwa ta ɓangaren Malam Adamu Mahaifin Ilham a Ranar sai da yace ya sama mutumin da Maganar Aurar masa da 'yar sa Ilham kuma a sadaka cikin washe baki kuwa Mutumin mai shekaru 70 a duniya ya amince suka gama magana suka a je akan gobe za'a ɗaura Auren a masallacin juma'a bayan an idar da sallar juma'a daga wurin mutumin gida ya koma ya fara sanarda da jama'a ɗaurin Auren da zai yi gobe wasu na tayasa murna tare da mamaki wacece kuma zai aurar sanin da sukayi da bashi da wata Budurwar 'ya a halin yanzu duk an musu Aure da ya koma gida ya faɗa ma su Hansatu da Maryamu sun yi farin ciki sosai burin su zai cika Salamatu da ɗiyarta zasu wulakanta nan dai suka ƙara zigasa. Washe gari da ya kasance juma'a kuma ranar ɗaurin Auren Direct Malam Adamu gidansu Salamatu ya wuce ya sama Malam Mai Allo kamar kullum yana zaune ƙofar gidan an shimfiɗa tabarmu dai ai kuwa ko gaisawa bai bari sun yi ba ya faɗa masa abin da yake tafe da shi wai na Aurar da Ilham da zai yi a yau. a cewarsa ma saboda ya kasance uban matarsa Salamatu ne ma shi ya sa ya faɗa masa da sai dai suji a gari bai bari Malam Mai Allo da Mamaki ya cika sa ya ce komai ha ya karkaɗe Babbar riga ya yi gaba abin sa. Cikin wannan hali na tashin hankali da ruɗu tare da Mamaki da ɗunbin al'ajabi Aryaan ya ƙari so ya sama Malam Mai Allo domin bayan barinsa daga asibiti Direct gidansa dake Nasarawa G.r.a ya wuce ya yi wanka ya shirya kuma matar gidan bata nan sannan bai san ina ne take ba har ya shirya ya yi waya company aka kawo masa mota ya kuma fitowa bata ma san ya dawo ba shi kuwa Direct Gidan kakansa Malam Mai Allo yayo shi ne ya sama sa a wannan hali koda ya tambaye sa abin da yake faruwa nan dai Malam Mai Allo ya faɗa masa komai. Aryaan sam bai yi mamaki ba domin kuwa yasan Wanene uban Ilham wato Malam Adamu mara mutunci da yake a lokacin ana gab da shiga sallar juma'a dan haka shiryawa Kawai Malam Mai Allo ya yi Aryan ya ɗauke sa a mota suka wuce can Masallacin juma'a ɗin da za'a ɗaura Auren. Bayan an idar da sallar juma'a duk an tsayar da su da cewar za'a ɗaura Aure. Malam Adamu baki a washe a ganin sa zai yarda kwallon margwaro ne ya huta da ƙuda zai rabu da mayyar gidansa duka an nutsu ana jiran Ango sai dai mene ne zai faru shiru Shiru babu ango babu Labarin sa sai can ɗan aike yazo musu wai an ce a faɗa ma uban amarya an fasa Auren 'yar sa saboda mayya ce ba za su iya da Dangin Mayu ba. Turƙashi.......!!! Wannan abu da ya faru ba ƙaramin mamaki ya bawa Kowa ba shi kuwa Malam Adamu sai zarar ido yake yana muzurai bai taɓa ji ya tozartu ba kalan yau kuma bai ɗaura laifin akan kowa ba sai Salamatu da ɗiyarta. Ana shirin watse wa ne sukaji sanarwar za'a ɗaura auren da wani kowa ya tsaya da Mamakin wani mai ƙarar kwanan ne zai aura Yarinyar da ake kira da mayya. Shi kuwa Aryaan Ransa a matuƙar ɓace yake da wannan lamarin dama koda Angon bai fasa ba bazai taɓa bari a gabansa a tozarta Ilham jinin Innarsa Salamatu ba saboda haka koda Angon ya sanar ya fasa abin ya yi masa daɗi nan take ya fitar da kuɗaɗe da bai san adadin su ba, ya yi ma Malam Mai Allo magana akan a ɗaura Auren da shi ai kuwa cike da farin ciki Malam Mai Allo ya amince ya sa ka aka yi sanarwar. Nan dai Malam Adamu yanaji yana gani aka ɗaura Auren A'ishatu Adamu da Aryaan Abdulyasar, Malam Mai Allo shi ne ya yi ma Aryaan wakilci yayin da Malam Liman aminin malam Mai allo ya yi ma Ilham domin kuwa Malam Adamu ƙin saka baki ya yi a zancen an ɗaura Aure tare da shaidawar dubban jama'a Ilham ta zama matar Aryaan..... ______ *_Turƙashi...!!! Akwai ƙura fa. Wai shin Mene ne kuke tunanin zai faru ne. Aryaan dai ya aura Ilham Ɗiyar Innarsa Salamatu Yarinyar da take cikin halin rai ko Rayuwa sannan kuna tunanin Malam Adamu da matansa zasu amince su bar Ilham ta zauna a tare da Aryaan koda ta sama lafiya. Wai shin Ilham zata warke kuwa. Ina labarin Fateesat wani irin mataki zata ɗauka idan ta sama labarin auren da Mijinta Aryaan ya yi. Wai shin ina labarin Dangin Mahaifin Aryaan ne._* *To dai ba zaku sama amsoshin waɗan nan tambayoyi ba sai kun kasance cikin wannan tafiyar a labarin _KIN CUCENI_ Wacece zayi cutar????.....* *In sha Allah an kammala free page's zamu ci da posting on Paid Grp ga waɗan da suka yi payment don't Miss It Dearest Sister's 🙌💖* ____ Wannan littafin na kuɗi ne zaku iya biya ta wannan account ɗin har kati muna amsa MTN 8141785374 Zaku iya turo sheda ta nan 07067953066 Ko 09061890481