[10/15, 10:26 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 1⃣ -5⃣ 👑👑 Cikin nutswa drivers din suke tukin,gudun kar ran Amal ya baci,motoci ne guda biyar ajere,gabadayansu bakakene,motar tsakiya itace wadda Amal ke ciki,akwai biyu agaba biyu a baya wadanda duk body guards din Amal ne aciki. Haka suka cigaba da tafiya,tana faman basu umarnin yadda take son tukin yakasance cikin tsiwa,da kuma mulki,suna xuwa kofar gidan,mai gadin yayi xumbur ya mike ya bude gate din tacewa drivern kai tsaya cikin tsiwa,ta xuge glass ta kalli mai gadin a wulakance,tace,banace maka idan na dawo kadaina batamin lokaci wajen bude gate ba?? Ya tsugunna yace kiyi hakuri ranki ya dade,baxan sake ba,Amal tace idan ka bari na kara maka magana a karo na biyu a ranar xakabar gidannan.ta bada umarni drivern yaja motar xuwa harabar gidan. Motar da Amal ke ciki na tsayawa,bayin ta guda biyu suka fito,kowacce a gefen ta guda daya,suna ta faman gyara mata riga wadda ke jan kasa,suka shiga cikin gida. Bangaren momy ta nufa,tana shiga momy tace my Amal kindawo?,Amal ta karasa ta kwanta a cinyar momy tace ehh,momy ta shafa kanta,tace Amal meya faru ne? Naga duk ranki a bace,yau kuma waya taba min ke? idon Amal ya ciko da kwalla tace momy nifa vanason mai gadin nan wlh,duk sai ya batawa mutane lokaci kafin ya bude gate,momy tace akan wannan kawai kike nema kiyi kuka? So kike ki tayarmin hankali,kawai dan kuka baya miki wahala? Kinga kiyi shiru xansa mai martaba,ya canja masa aiki acikin gidannan.momy ta kalli jakadiya dake gefenta tace kawowa Amal ice cream,jakadiya tace to rankiya dade,ta fita cikin hanxari,,sannan momy ta mai da idanun ta kan Amal tace,nasa akawo miki abinda kike so,ki daina bata ranki kinji.Amal tayi shiru alamar ta gamsu da rarrashin da momy tayi mata. Amal kyakykyawace,farace tass, gashinta har gadon baya,hakoranta ajere suke wadanda suma farare tasss,tana da diri mai kyau,Amal akwai mulki dasan nuna ita 'yar sarki ce👑,babu dama mutum yayi wani abu ba dai-dai ba sai ta nuna masa isa,da nuna sai abinda take so,akwai son hutu da kuma shanawa,wannan kadan kenan daga cikin halayyar Amal. Amal tace momy bari naje na kwanta bacci nake nakeji,ta kaimin ice cream din daki,momy tace to,ki turomin haneefa,Amal tace to. Amal na shiga daki ta tarar da haneefa a xaune akan sallaya tana karatun Alkur'ani,tacewa haneefa kije inji momy,yadda Amal tayiwa haneefa maganar kamar bataso,haneefa na karasa shafin da take karantawa tasa alamar tsayawa,ta tashi dan xuwa kiran da momy tayi mata,saboda tasan tana kara mintina dayawa xata sha fada awajen momy. Tana xuwa momy tace da haneefa kije cikin abin kayan wankin dakina ki debo duk ilahirin inner wears din dake ciki maxa-maxa ki wanke min su,wannan kan bashine na farko ba,haneefa ta saba tunda ta taso ita take wa hajiya fateema wankin inner wears,haka ta wuce ta debo kayan. Tana fitowa falon Abdul ya jijjiga kai aransa yace ina matukar tausayin yarinyar nan,haneefa tace yaya Abdul ina wuni ya ansa,lfy kalau haneefa ya karatu tace lfy kalau,ta wuce toilet don wanke kayan da momy ta bata. 😭😭 By Maryam y.Ahmad Hauwa s.Ahmad📚✍ 😭😭 [10/16, 7:56 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺 'YAR MULKI🌺 6-10 📚✍✍ Yau kam haneefa da wuri ta shirya,taje bangaren momy ta wanke toilet,ta gyara daki da kuma falon momy, wannan aikin haneefa ne na kullum,dan kuwa uwar gidan maimartaba hajiya fati bata barin kowa ya gyara mata bangarenta sai haneefa,ko jakadiya, bangaren maimartaba ne kawai hajiya fati take gyarawa da kanta,bayan haneefa ta gama tsaf ta koma daki inda ta tarar da Amal a kwance bata da ko niyyar tashi,ta dan taba gefen kafarta,sannan tace Amal-Amal kitashi lokaci xai kure karki makara,Amal tayi wani irin juyi tayi tsaki sannan ta mai dakai tacigaba da bacci abinta,gudun karsu sami matsala a tsakanin su yasa haneefa bata kara tashin Amal ba. Haneefa ta bude wardrop dinta wadda banda kanshi ba abinda yake tashi aciki,ko wanne jinsin kaya bangarensa daban ne acikin wardrop din,kayan awanke suke a goge,komai na cikin wardrop din tsaf,haneefa tana da tsafta matuka bata taba barin wani abu nata da datti saita tabbatar yayi tassss.wajen tsaftar jiki kuwa tayi fice danni na dade banga mai tsafta irin ta haneefa ba,ta dakko wani pink din gyale,gyalen kam ya hadu,taje gaban mudubi ta gyara fuskarta sannan ta nannade gashin kanta mai tsayin gaske,dakyar ribbon din ya rike gashin haneefa saboda tsananin santsinsa,sannan tayi rolling mayafin dayake bakar doguwar riga tasa,wadda akayi mata kwalliya da pink stones a hannu da kuma wuyan rigar,ta sa pink takalmi da bakar jaka,ta dau key din motarta,tana fita taci karo da yaya Abdul a bolcony ya dora kafa daya kan daya, tace yaya Abdul ashe ka fito?? Da wuri haka?? Yace eh,na gaji da kwanciya shiyasa na fito nan,sannan yace yau morning lectures ne dake kenan?? Haneefa tace eh wlh gashi ma na makara Allah yasa ya barni na shiga,dan lecturer bashi da kirki,yaya Abdul ya ce ahh to kiyi sauri, sai kin dawo amma kiyi tuki fa a nutse,haneefa tace to yaya. Kuka kwai haneefa take😭😭 rike da stiring mota a hannun ta,xuciyarta sai xugi take,irin kuntatawar da ake mata tayi yawa,dan dai bayyada xatayi ne,amma ji take barin gidan shine kawai xai fi mata sauki,amma sai ta tuna cewar to idan ma tabar gidan ina xataje???.haka dai tayi ta kuka,tana shiga school tun amota ta goge hawayen dake idonta sannan ta wuce hall din daxasuyi lectures din,ta tarar already hidaya ta ajiye mata seat,ta xauna suka gaisa da hidaya,babbar kawar haneefa kenan,baifi minti biyar da shigar haneefa ajin ba lecturer ya shiga aka fara gudanar da lectures. Amal kuwa na tashi toilet ta fada,tayi wanka ta fito ta shirya tasa kaya,tayi tsananin haduwa,doguwar rigar shadda tasa golden colour anyi mata aiki wanda ya dace da ita sai mayafi data yafa aka,kana ganin shaddar ba sai an fada ba kasan mai tsadace,ta wuce falon momy ta tarar da momy a xaune tana hutawa,tace momy wai ba'a gama breakfast din bane haryanxu? Momy tace xo ki xauna,yanxu xa'a kawo miki,bari naji ko sun gama, Momy ta kwalla kiran jakadiya,da sauri jakadiya ta bayyana a falon,tace ranki ya dade gani,hajiya fatee tace kicewa ladi inason ganinta,nan da nan ta amsa kiran momyn Amal,ta kalle ta tace ladi wai meyasa bakwason gama abinci da wuri a gidannan,?kun sani sarai Amal tana fita makaranta da wuri,ladi tace rankiya dade saura kadan ya karasa,kinsan dankali akwai daukan lokaci,hajiya fatee tace koma dai menene daga yau bana so Amal ta sake kukan ba'a gama abinci da wuriba agidanna,cikin ladabi ladi tace to,angama ranki ya dade,momyn Amal tace ki hanxarta ki kawomata yaxunnan,ladi ta fita cikin sauri,agurguje,nan da nan ta kawo kamar yadda momyn Amal tace,ta jera su akan dining.Haneefa takarasa kan dining din taci abincin sannan tace momy xan wuce school,momyn Amal tace,to sai kindawo,Amal tayi kissing momyn ta,sannan ta fita. Tana fita,tasa key ta bude motar ta,sannan ta shiga ta xauna,ta bude handbag dinta ta dakko glass ta manna a idonta,ta jefa chewing gum abaki,ta kuma daura agogo a hannun ta,sannan taja mota ta nufi school. Amal na shiga school ta tarar har an fito daga first lecture amma,bata damu ba ko ajikinta,taje daidai inda su mufeeda da Afrah suke xaune tayi parking,Amal na fitowa daga mota suka taso da sauri tare da fadin oyoyo suka rungume Amal,Afrah tace kai u look gorgiou,Amal tace tnx,sannan ta xauna a tsakiyar su,tace kunyimin attendance? Mufeeda tace kawata idan bamuyi miki ba ashe baxa muyiwa kan mu ba kenan,Amal tayi murmushi tare da gyara glass din dake idon ta,tace kawai tambayar ku nayi,Afrah tace munyi miki mana.Dai dai lokacin da suke wannan maganar Amal ta hango wucewar Haneefa da hidaya,tacewa su Afrah kunga yarinyar can sai na koya mata hankali,bata da aiki sai munafur ci,da asuba haka xata hanani jin dadin bacci,tana karatu bayan ba dan Allah takeyi ba,Afra tace ai fada mata xakiyi idan xatayi ta koma falon ku mana,dole sai tayi a daki?,Amal tace hhmm bakusan abinda yafi damu na akanta ba,cikin yanayin xuga da munafurci mufeeda tace menene? shishahigin da takewa yaya Abdul mana, wallahi ni shi yafi damu na,shima kuma yaya Abdul din yayi ta biye mata,abin yana bani haushi,Afrah tace ai naga yayan naku is simple amma fa akwai sarauta,Amal tace akawai kam,ai bahaye bane gado ne. Bayan angama lectures haneefa da hidaya sukayi sallama,kowa ya tafi gida. Haneefa na komawa gida,tayi wanka bayan ta fito taci abinci,dama ko break fast batayi ba haka ta fita school,ta gabatar da sallar la'asar,bayan tayi sallar ne ta nufi wajen baba mareeya. Baba mareeya tana daya daga cikin masu aikin gidan mai martaba sarkin kano,Alhaji salahudden Adam,tun haneefa tana karama baba mareeya take kula da ita,tana tsananin tausayin haneefa saboda tasan yadda rayuwar ta ta kasance,haneefa ta shaku da baba mareeya sosai, ita take kallo amatsayin mahaifiyar ta a gidan ba momy ba,duk damuwar haneefa baba mareeya kawai take fadawa don ta sami sauki axuciyar ta. Yauma kamar kullum haneefa da baba mareeya suna tare,baba mareeya tace haneefa kin dawo? Haneefa ta eh baba mareeya,sannan tace naxo ne muyi wata magana,baba mareeya tace to haneefa ina jinki,idon haneefa ya ciko da hawaye😭😭 tace inasone nabar gidannan ba tare da kowa ya sani ba sai ke,nagaji da ganin wasu irin halayen da momy da Amal suke nuna min,gara naje wani wajen daban inda xanfi samun kwanciyar hankali,kullum ina cikin bacin rai,tun bansan komai ba ake nunamin banban ci a gidanna,harna kai lokacin daxan iya sa bacin rai a xuciyata😭😭kuka yaci karfin Haneefa tayi shiru idonta ya kada yayi ja.😭😭 Baba mareeya ta dafa kafadar haneefa tace baxa'ayi haka ba,yanxu idan kika tafi ina kika san xaki fara xuwa??,idan kikayi haka ai ran maimartaba xai baci,ko yananan bai kamata ki tafiba,ballantan yayi tafiya,idan ya dawo yaji cewar bakya gidannan baxaiji dadi ba,haneefa ki kara hakuri komai xai wuce insha Allahu,karki manta fa yau shekarar ki goma sha hudu agidannan kuma na tabbatar baxaki mai-mai taba,don haka kiyi hakuri kinji?? Haneefa ta kafa kai a cinyar baba mareeya sai kuka take,itama kanta baba mareeyan kukan take.😭😭.saboda tausayin haneefa,ganin cewar ta taso a gidan sarauta,kuma acikin daula amma batajin dadin dadin rayuwar ta ko kadan. Baba mareeya ta cigaba dacewa dan Allah haneefa ki cire wannan kudirin da kika sa aranki,kinga duk abinda da ake miki mai martaba bashi da masaniya,amma a sannu Allah xai fahimtar dashi,ta kara da cewa yanxu magriba tayi kije maxa kiyi sallah,haneefa tace to. Haneefa na shiga daki ta tarar da Amal nayin sallah,ta fada toilet tayi alola ta gabatar da sallah,bayan ta idar da addu'a,ta dakko handout dinta da sukayi lecture da safe ta fara dubawa,Amal tace haneefa banason irin abin da kike min,cikin masifa Amal takeyin maganar tace karki kara tashina ko xan wuni in kwana ina bacci,ba matsalar ki bace,wannan ai mugunta ce ke baki huta ba shine baxaki barni na huta ba ko?? To wallahi ya isheki,kin gane ai? Tunda Amal ta fara magana haneefa bata daga kai ta kalleta ba balle ta tanka mata,haka ta gama masifar ta ta hakura,ita dai haneefa karatunta kawai take,amma acikin xuciyar abin ya bala'in kona mata rai,aranta tace ai kuwa kinyi da 'yar halak dan kuwa ko da wasa baxan kara tashinki ba. 😭😭😭 By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad📚 [10/16, 7:57 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 11-15 📚✍✍ Amal da Afrah na tsaye a upstairs din makarantar su,fitowar su kenan daga lecture,suna jiran mufeeda ta karaso su sauka kasa,don suje su sami wajen xama su cigaba da sana'ar tasu ta yiwa mutane rashin mutunci a cikin school,Amal na rike da rubar swan a hannun ta,tasha ta rage ruwan sannan ta leka kasan benen ta kalli Afrah tace leka kiga wannan guy din mai shegen iyayi, yana wani kasaita,sai kace akansa aka fara namiji dan gayu,Afrah na lekawa kafin tayi magana Amal ta saki robar ruwan dake hannunta a dai dai saitin inda mujaheed yake zaune. Afrah kam batayi mamaki ba,tasan halin kawarta sarai,bata da kirki,ga neman tsokana da kuma nuna ita 'yar sarkice,Afrah tace yesssss 'yar mulki kinmin dai dai,Amal ta gyara glass din dake idon ta cikin wata shegiyar taunar chewing gum tace ai nice dai dai shi acikin makarantar nan. Mujaheed na jin xubowar ruwa ajikinshi yayi sauri ya kalli saman benen don ganin wanda yayi masa wannan aika aikar,habaaaa yana ganin Amal yace dama sai ita marar kunya,duk makaran tarnan kowa kuka yake da ita,daga yau baxata sake marmarin yiwa wani haka ba,ba tana fariya baban ta sarki ba??, yayi tsaki mtswwww,sannan yatafi fuuuu ya nufi matattakalar benen da xai kaishi wajen da su Amal suke tsaye. Mufeeda na karasawa wajen dasu Amal suke tace,'yar mulki kuxo mu wuce,nan fa suka nufi hanyar daxata kaisu kasan benan,suna wata tafiya cikin kasaita wadda take indicating su 'yayan wasune. Mujaheed yana hango sakkowar su ya tsaya a kafar benan dan jiran isowar su. Suna isowa wajen,mujaheed yasha gaban su dai dai saitin Amal ya tsaya,ya xura hannayensa duka biyu a aljihu ya bata rai sannan ya karkatar da kansan gefe daya. Ya daga girar sa sama,sannan ya nuna Amal da dan yatsa yace keee baki iya bawa mutane hakuri ba idan kika musu laifi?? Cikin rashin kunya Amal tace hakuri fa kace,Allah ya kiyaye😏 ninasa ka ka xauna a saitin wajen danakeso na jefarda ruwa?? malam kabamu waje mu wuce dan muna da abinyi. Majaheed yaji haushi sosai ji yake kamar ya tsinkawa Amal mari,yace ki shiga hankalin ki,kuma kisan dawa kike magana,ki bani hakuri idan ba haka na kwasheki da mari,ina ganin a gidan ku ba manya shiyasa kike behaving haka. Afrah tace dakata mujaheed ya isheka haka,kasan Amal wacece kake mata magana any how??? Mujaheed yasan cewar Amal 'yar sarkice amma sam ya nuna baisan hakan ba,yace koma wacece ita wannan ba damuwata bane,kuma ba abinda naxo na sani acikin makarantar nan ba kenan,kawai ta bani hakuri. Amal aranta tace amma wannan guy din ya rainamin hankali,yana nufin yace baimasan ko ni wacece ba??? A fusace Amal tace kaga ka matsa mu wuce dan ko mutuwa xakayi wallahi baxan taba baka hakuri ba. Mujaheed yace kinyi kuskuren shiga gonata,xaki bani hakuri ko ba yauba,put this at the back of ur mind,ya sake mai maitawa,saikin bani hakuri ko ba yauba,kinci sa'ar addinin musulunci wallahi da saina mareki.kawai ya juya ya tafi,kallo daya xakayi masa kasan ransa ya mugun baci. Amal da friends dinta suka sami waje suka xauna sai tattauna abin da ya faru suke. Amal tace dama acikin makarantar nan akwai wanda xai iya kallo na yafadamin irin kamalan da guy din can ya fadamin? dole nasa a daure shi,kuma kafin ni na bashi hakuri shi xai fara bani hakuri.xanga wanda yake gadara dashi. Mufeeda tace 'yar mulki ina ganin kiyi hakuri ki kyaleshi,kina sawa a daure mutane da dama,amma banga alamar xakiyi nasara akan mujaheed ba,Amal ta kalli mufeeda cike da mamaki tace waye shi?? Dabaxan iya sawa a daure shiba. Mufeeda tace ba dan kowa bane amma,gaskiya ina ganin daure shi xaiyi wuya. Afrah tace nima dai gani nake ta kyale shi,Amal kinga next week abbanki xai dawo,idan kikasa aka daure shi na tabbata xancen nan sai ya koma kunnen mai martaba,nan danan jikin Amal yayi sanyi saboda tasan totally Sarki Salahuddeen baisan tana wannan iskancin a gari ba,komai takeyi momyn ta ke goya mata baya,batason ganin bacin ran Amal ko kadan. Afrah ta dafa Amal tace kawata kirama da wani abu,amma karkisa a daure shi,Amal ta dan yatsine fuska,tace ba matsala,amma sai ya gane kuskurensa. Gobene xa'ayi birthday din Afrah dukkan su sun shirya cewar kowa xai kawo 200,000.Naira contribution,saboda sunaso birthday ya hadu yadda ya kamata. Amal na shiga dakin momyn ta direct akwatin kudi ta nufa ta xari 250,000Naira,ta fice abinta,ta dauki mota ta nufi wajen birthday din,riga da wando tasa,sun matseta sosai,amma fa tayi kyau to d core,rigar blue ce da kwalliyar baki,sai wando da takalmi bakake,tayi wani hadadden dauri,ta manna na gadon a idonta(glass),kanshin da take kuwa xakayi tunanin companyn turaren ne ajikin ta. Tana shiga wajen attention ya dawo kanta frinds an taru,da sauri sukaxo suka rungume Amal,sannan aka cigaba da casu. Ran momyn Amal ya baci sosai,tace jakadiya kiramin haneefa,cikin girmamawa jakadiya ta risina tace to ranki ya dade,ta fita cikin sauri. Haneefa na xuwa momy ta dauketa da mari,tace maxa maxa ki wuce ki dakkomin kudina da kika dauka,sata kuma kika koma ?? Hawayene kawai ke xubowa daga idon haneefa😭😭,ta rike kumatunta da hannu daya saitin inda momy ta mare ta,tace wallahi ban daukar miki kudi ba😭😭. Karya kike,rufemin baki munafuka,to baki isa ba,kudi har two fifty thousand naira?? nafada miki,nabaki nan da 15minutes ki fitomin da kudina,kuma bari mai martaba ya dawo dole kibar gidannan,wannan ai abin kunya ne agaremu ace a gidannan ake sata, Baba mareeya na dai dai window,a labe tana jin abin dake faruwa,banda kuka ba abin da take.😭 Haneefah tace,dan Allah momy ina rokonki karki bata sunana awajen mai martaba,😭wallahi ban dau kudinki ba,tsawon shekaru muna tare da ina sata da tuni kin dade da sani,momy ban dauka wallahi.😭 Momyn Amal tace na dai fadamiki,kifitomin da kudina, kuma gidannan dolene kibarshi,gobe-goben nan na fadamiki,Allah ya dawo da maimartaba lafiya. Haneefa kuka kawai take😭😭 aranta kuwa cewa take ya Allah kabani mafuta. Maryam y.Ahmad Hauwa s.Ahmad📚 😭😭😭 [10/16, 7:57 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 16-20 ✍✍ Kida ne kawai ke tashi awajen birthday din,Afrah tayi kyau sosai,haka sauran kawayenta,dukkansu english wears sukasa kowacce da irin kalar kyan da tayi,yau itace ranar da Afrah ta cika shekara goma sha bakwai a duniya,kamar yadda aka rubuta ajikin cake din,"SWEET SEVENTEN" Amal da mufeeda ne suka tsaya ta sides din Afrah sauran friends kuma suka tsaya daga baya suka dau hotuna,kana ganin su kaga manyan yara kuma 'yan gayu,kowacce ji take da kanta saboda naira ta gama ratsa su,haka suka gama budirin su,sannan kowa ya watse. Amal na kan hanyar komawa gida,tuki take amma kamar bataso saboda ta gaji sosai ji take dama ta fita da drivern ta,haka dai ta karasa gida ba cikakken kuxari. Tana shiga daki ta yar da jakar ta akan gado,ta juya ta kalli haneefa dake kan gadon ta a kwance sai shashshekar kuka take,Amal tayi tsaki ko ajikin ta kukan da haneefa take bai dameta ba,ta fita ta wuce falo,ta xauna,sannan ta sa bayinta guda biyu suka fara mata tausa. Tsawa ta daka musu,kaiiii nifa tausa nace kuyimin ba cewa nayi ku karyani ba,nan da nan jikin su ya fara bari saboda duk bayin gidan da masu aikin gidan tsoron Amal suke,atare sukace tuba muke ranki ya dade,nan fa sukaci gaba da lallaba jikin Amal kamar kwan da ba'ason fashewar sa. Jakadiya na shigowa falon ta gurfana a gaban Amal tace ran gimbiya ya dade hajiya nason ganinki, wanna shine sunan da kowa yake kiran Amal dashi a gidan kawayen ta kuma da 'yar mulki suke kiranta ko Amal,Amal ta dago ido ta kalli jakadiya,ok Amal kawai tace daganan bata sake magana ba,ta tashi ta nufi dakin momyn ta. Tana shiga dakin kan cinyar momy ta wuce ta kwanta,momy ta shafa kan Amal tace kin dauki kudine a brief case dina?? Amal ta juya kanta idon ta acikin na momynta tace ehhh,dana gama shiryawa na fito sai na tarar kina wanka ni kuma bana so na bata lokaci shiyasa na dauka kawai na tafi,nasan ko kina nan ma cewa xakiyi kawai na dauka,kadan daga cikin aikin Amal kenan,momy tace me xaki siya dasu?? Cikin shagwaba Amal tace kaiii dan Allah momy harsai kin,tambayeni abinda xanyi da kudi?? Sannan tace contribution na bayar na birthday din Afrah,momy kinsan mune manyan friends dole muyi wa Afrah gift mai kyau,ni gani nake ma yayi kadan. Momy tace ina bude brief case din naga an debi kudi, nasan ba wanda xai dauka sai ke,amma kinsan me nayi??Amal tace a'a,momy tace haneefa na kira nasa ta agaba nace sai ta fito min da kudina,kinga wannan itace hanya mafi sauki da xamu koreta daga gidannan,dankuwa idan mai martaba ya dawo yaji labari baxai yarda taci gaba da xama acikin gidannan ba,saboda ko kadan baya son abinda xai xubar da martabarsa da kuma ta gidannan. Amal tace yesssss momy kinyimin dai dai,gara ma tayi gaba,dan wallahi na tsani xaman ya rinyarnan agidannan,duk farin cikin danake ciki idan na ganta sai raina ya baci. Momy tace ai yarinyarce sai kace mai asiri,kowa sonta yake,ba abinda yake bani haushi irin yadda mai martaba yake sawa ku xabi abu tare idan xai sai muku. Amal tace basai ta xaba ba mugani yanxu,sai dai awani gidan,Allah ya kaimu goben ya dawo. [10/16, 7:57 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 21-25 ✍✍ Haneefah tayi kukan har ta gaji,bakin cikine kawai yake yawo a ranta,tunanin dawowar mai martaba kawai take,yadda yake ganin hankalinta ace ta saci waddan nan makudan kudin,daga tayi wannan tunanin sai ta fashe da kuka,sannan ta tuna asalin ita wacece nan ma hankalinta ya kara tashi,tun yamma haneefa take kuka har sai da lokacin sallar magrib yayi,dakyar ta tashi da shiga toilet yayi alola bayan ta fito tayi sallah,haneefa bata tashi daga kan sallaya ba ta fara mika kukan ta wajen ubangiji kamar yadda ta saba. Hannu biyu ta daga sama👏 ta fara addu'a kamar haka a fili. Ya Allah ina rokonka ka bani ikon cin wannan jarabawar,Allah kai kace mu roke ka bani da wanda xan roka bayan kai,ya Allah ka karamin hakuri da juriya,ka kuma kareni daga sharrin mutum da aljani,da masifar gabas da yamma kudu da arewa,ya Allah ka bani mafita,ka kawomin farin ciki na har abada. Ya Allah ka kareni daga sharrin dake cikin wannan ranar,nan fa kuka yaci karfin haneefa😭 ta cigaba da cewa Allah ka sadani da alkhairan dake cikin wannan ranar,Allah ka sakawa iyayena da alkhairi,Allah ka sakawa mai martaba da alkhairi. Banda kuka ba abin da haneefa take😪 ,momy da Amal kuwa suna can sai faman hada wa haneefa tuggu suke. Haneefah tana idar da addu'a ta wuce wajen baba mareeya,tana xuwa ko magana bata iyayiba ta xauna akusa da baba mareeya,sautin kukane kawai yake fita daga muryar ta,baba mareeya tayi sauri ta dago tare da matsar da kwanon da take kadi daga gabanta,haneefa kiyi hakuri insha Allahu wannan yanayin baxai taba dawwama ba watarana xaki sami canjin rayuwa insha Allah,shi kudi da sarauta da suke ji dashi mai karewa ne,gaskiyar ki kuwa baxa ta taba karewa. Har alokacin da baba mareeya take magana haneefa kuka kawai take,ta cigaba da cewa nasan cewa baxaki taba iya daukan ko da tsinke na mutum ba,balle makudan kudi haka,haka kuma duk ma'aikatan gidannan kowa yasan baki dauka ba dan dai bamu da iko ne ba yadda xamuyi. Haneefa tace baba mareeya mai martaba ya rikeni tamkar 'yar da ya haifa komai yana yimin,idan yaji ance na dauki kudi baxai taba jin dadiba ni dai kawai barin gidannan xanyi,baba mareeya tace a'a haneefa idan kika tafi nima ai baxanji dadi ba saboda bansan hannun wanda xaki fada ba kinga ba wanda kika sani,dan haka kiyi hakuri Allah ya kaimu goben muga abinda xai faru idan mai marta ban ya dawo. Suna cikin wannan tattaunawar ne sukaji ankira sallah,haneefa tace baba mareeya bari na shiga ciki nayi sallah baba mareeya tace to amma dan Allah ki kwantar da hankalinki insha Allahu ba abin da xai faru,haneefa tace toh tare da goge hawayen dake xubowa daga idon ta. Haneefa tana da hankali sosai gashi ta dace hankalin nata ya hadu da addini,ko kadan bata wasa da sallah,tana ganin girman naga ba da ita komai talaucinsa,bata da yawan magana barkatai sai ta kama,shiyasa ta shiga ran yaya Abdul sosai saboda baya son mutum mai rawar kai da yawa.Allah sarki haneefa baiwar Allah. Sukayi sallama da baba mareeya,haneefa ta shiga cikin gida,tayi sallar isha,ranar ko karatu bata iyayi ba,gashi da safe tana da test,danma akwai brain ko batayi karatu ba bata tunanin shiga test ko exam,haka ta kwanta dakyar bacci ya sace ta. Asuba nayi haneefa ta tashi tayi sallah,tana kallon Amal sai sharar baccinta take,har xata tasheta kawai sai ta fasa saboda tasan ba tashi xatayi ba,bayan haka kuma masifa ce kawai xata sha. Haneefa tayi kyau sosai,amma kana kallon fuskarta kasan akwai damuwa mai tarin yawa,ta nufi sashen momy don ta gyara kamar yadda ta saba. Tana shiga dakin momy ta daka mata tsawa,what are u doing here?? Muryar haneefa cike da tsoro tace momy dama xan gyara dakin ne,cikin masifa momy tace ok,to banason gyaran,yau kuma idan na barki kika shigomin daki brief case din gabadaya xaki sace ai,haneefa tayi shiruuuuu kamar ruwa ya cinye ta. Momy tace to bari kiji infada miki daga yau banaso ki kara shigomin daki,keee falo na ma haka,barauniyar banxa barauniyar wofi,ciki shouting tace "oya get out of my room stupid".... Haneefa kam sai hawaye,jikinta a sanyaye ta bar dakin. Tana fitowa ta nufi hanyar part dimsu,kanta akasa ta wuce ta gefen yaya Abdul dake kan dining yana break fast,saboda bacin rai bata ma san yanan ba. Yaya Abdul ya kira sunan ta,haneefa,tajuya slowly ta fara kokarin,seta kanta,gashi ya riga yaga hawayen dake fuskarta. Yace xo nan,ta karasa kusa dashi,yace haneefa what's wrong?? tayi shiru,ya sake cewa meya faru kike kukane haka?? Still batayi magana ba hasali ma hawane ke kara xubowa daga fuskar ta,cikin yana yin damuwa yaya Abdul yace ehhnn ina jinki,muryar ta na rawa tace ba komai,yaya Abdul yace,no no no no no,banyarda ba,haneefa tace mo"..momy ta katseta,tace dalla can rufawa mutane baki,Abdul yarin yar nan sata ta koma a gidannan,250,000,naira ta dauka jiya a brief case dina,a fili kamar baxata aikata ba. Abdul yace haba momy,me haneefa xata dau kudi tayi dashi?? Momy tace ok dama ka saba bin bayanta ai,yaya Abdul yace bahaka bane amma dai gaskiya momy kisake duba kudinnan da kyau,ko kinyi misplacing dinsu. Momy tace ba wani misplacing danayi,gatanan ka tambayeta inda ta kaimin kudina,momy ta juya ta shiga part dinta tare dayin murmushin mugunta aboye...😊😊. Tausayin haneefa ya kama yaya Abdul,yace take heart haneefa,kije school idan kin dawo sai muyi magana karki makara. Haneefa tace to ta shiga daki ta tauki jakarta da mayafi tasa takalmi ta wuce school... Luv yhuuuu ol💞 By Hauwa s.Ahmad& Maryam y.Ahmad📚 Luv yhuuu ol..💞 [10/16, 7:58 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 26-30 ✍✍ Tunda haneefa ta fita yaya Abdul yake tunanin ta,yana matukar tausayin ta,yadda momy take treating dinta a cikin gidan,kamar batasan ciwon haihuwa ba. yana cikin wannan tunanin yaga kiran mai martaba na shigowa wayar shi,yayi picking call din sannan yace Hello Abba,mai martaba yace Abdul ya gida ya su momy?? Abdul yace lafiya kalau Abba,maimartaba yace,yace karfe 4:00pm jirgin mu xaiyi landing,sannan yace,,Abdul na matsu nasaka a kwayar idona,Abdul yace Abba ni kaina ji nake kamar kayi shekara da tafiyar nan,sarki salahuddeen yace wannan ne karo na farko dana farayin tafiya babu kai,haka kuma itace tafiya ta farko da batayi min dadi ba. Mai marta ya kula cewar jikin abdul a sanyaye yake yace Abdul kodai baka da lafiya ne?? Naji muryar ka sabanin yadda nasabaji. Abdul yace a'a lafiya kalau Abba,mai martaba yace Abdul karka manta nifa mahaifin kane,nine komai naka arayuwa,dan haka idan kana da damuwa ni yakamata ka fara fadawa. Abdul yace daddy ba komai,mai martaba yacewa Abdul ka shirya idan na dawo inason nasan menene damuwar ka,Abdul yace to Allah ya dawo dakai lafiya.sukayi sallama. Yadda marmartaba yaji yanayin Abdul yasan cewa kwarai yana da damuwa,fadamasa ne kawai bayasonyi,yana son Abdul sosai shiyasa komai kankantar damuwa yake fahimtar ta daga gareshi. Ko kadan mai martaba bayason abin da xai batawa Abdul rai,ya dau son duniya ya dora masa,haryanajin idan Abdul baya tare dashi kamar babu wani babban sashene a jikinsa.Alokacin yaji kamar yayi tsuntsuwa ya dawo dan kasancewa tare da Abdul. Tuki kawai haneefa take amma hankalinta baya duba yanayin yadda xata seta motar akan titin,bata ankaraba sai gani tayi ta kade wata yarinya da mamanta. Da sauri haneefa ta fito a gigice,kafin kace meye wannan har mutane sun taru awajen,a rikece haneefa ta durkusa agaban wannan matar tana cewa sannu kinji ciwo?? Haneefa ta daga yarinyar,ganin hankalinta ya tashi sosai maman yarinyar tace yarinya karki damu banji ciwo ba,sai dai ni ta yarinyata nake,kalmar da matar ta fada ta tunawa haneefa inda yake mata ciwo,a ranta tace da ina da mahaifiya nima nasan xataji xafin duk wani abu daxai sameni. Yarinyar tayi xumbur ta mike tace mama nima fa banji ciwo ba,haneefa taji wani irin dadi ganin yarinyar ta ware,tacewa yarinyar sannu,sannan tace baba ina saurine wallahi ban kula ba,tabasu hakuri sannan ta dakko 5000 a jaka ta basu ganin cewar suna da karamin karfi. Motar da Naseer yake ciki na karasowa wajen driver'n shi ya yunkurin fita don yayima haneefa magana saboda tayi blocking hanyar,Naseer yace bari na fita da kaina,driver'n yace to. Naseer ya fito cikin wata bakar suit,ya daura red neck tight ne a wuyanshi,yayi kyau sosai,Naseer kyakykyawan saurayine maiji da kanshi,shine first born wajen mai girma governor'n kano Alhaji muhammad salees. Ya karasa kusa da haneefa ya nuna ta yace ke wannan wanne irin sakarci haka? Kinxo kinyi blocking hanya,ta sama kike so mutane subi ko yaya?? Haneefa ta watsawa naseer kallo da kyawawan idanun ta,tace malam kayi hakuri bawai nayi hakan intentionally bane,bata sake magana ba ta juya kawai ta shiga motar ta ta nufi makaranta. Naseer yayi mamakin yadda haneefa ta bashi ansa cikin masalaha,yadda yaga tsananin kyan halittar ta ya dauka xatayi girman kai,gwiwar sa tayi sanyi yaji kawai ta gama birgeshi,yayi wani shegen murmushi ya ciji gefen lebensa kadan ta gefe daya,sannan ya koma cikin mota. Haneefa na shiga school tayi roushing xuwa class,kowa yayi tsit sun fara test din wasu ma har sunfito,5ive minute ya rage ayi submitting gabadaya,lecturer'n bai hana haneefa shigaba,kawai cemata yayi tym na cika xai karba, he will not wait for her,haneefa ta yarda tayarda akan hakan. Haka tayi test din cikin minti biyar,kowa yayi sunmitting. Already hidaya ta fita dama,haneefa na fitowa daga hall din ta wuce wajen da suka saba xama ita da hidaya,tana tuwa ta xauna,hidaya ta jefo mata tambaya kamar haka. Haneefa ya akayi kika makara sosai haka?? Haneefa tace wallahi na dan bige wasune a hanya shiyasa,sai da na tabbatar da lafiyar su sannan na taho,hidaya tace eyyyahhh Allah ya rufa asiri,haneefa tace amin ya Allah.Daganan haneefa bata sake magana ba,tunani kawai ta tafi wanda har ya kaita ga immagination,harta hasko a idan xuciyarta mai mar taba yace ta kwashe nata ya nata ta bar masa gida,ita kuma sai kuka take. Ashe har a fili hawane ke xubowa daga idon ta. Hidaya ta xuba mata ido har tsawon 2minutes abin yana bata mamaki,amma inaaaaa haneefa batasan tanayi ba. Hidaya tace hanny me yake damunki?? Haneefa tayi firgigit ta dawo daga immagination din da take,tace ba komai. Hidaya tace haneefa wanne irin tarayya mukeyi?? Ace abu yana damunki amma inaji ina gani bani da matsayin daxaki fadamin,nasha ganin yanayin ki cikin damuwa idan na tambayeki sai ki nuna ba komai. Ni ina ganin bai kamata ba. Haneefa tace am sorry hidaya cikin kuka take maganar,tace it's a personal problem. Hidaya ta bata rai tace haba haneefa,gaskiya am highly disappointed,☹☹ banyi tunanin xaki iya boye min wani abuba,aganina munxama daya kuma ko ban miki maganin abinda yake damunki ba xan iya baki shawara kuma nayi miki addu'a,wallahi haneefa ba abinda xan iya boye miki atare dani. Jikin haneefa yayi sanyi,tace hakane hidaya. Haneefa tace,hidaya yaune ranar farko da xan fara bayyana sirri na ga wani mutum,ina nufin kece ta farko data fara saninin sirrina bayan 'yan gidan mu. Xan baki labarin da xaki dade kina mamaki,magana haneefa take amma ta kasa tsayar da hawayen da yake xubowa daga idonta. Hidaya tasa handkatchief ta gogewa haneefa hawayen dake fuskarta.tace dan Allah haneefa ki daina kuka ina jinki meyake faruwa??? Luv u more guys💞 By Maryam y.Ahmad Hauwa s Ahmad. For call 08033660286 08063495753. 💞💞💞 [10/16, 7:58 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 31-35 📚✍ Haneefa tace,hidaya ni da kike gani ba 'yar mai martaba salahuddeen Adam bace. hidaya da haneefa tare sukayi secondary school,shiyasa maganar da haneefa ta fada ta bawa hidaya mamaki,tace kina nufin ba Abban kune ya haifeki ba?? Haneefa tace hakane bashi ya haifeniba,ta fashe da kuka,😭idon ta yayi ja kamar barkono,haka fuskarta,saboda haneefa farace tasss ko yaya ranta ya baci sai fuskarta tayi ja balle idan tayi kuka. Hidaya tace ki daina kukan nan haka pleassssse kanki xaiyi ciwo,haneefa tace dolene nayi kuka hidaya😭😭. Saboda bansan ko daya daga cikin iyayena ba,tun ina da shekara biyu wani bawan Allah ya tsince ni a bakin titi rike da takarda a hannuna wadda take tauke da rubutu kamar haka. Don Allah ga 'yatanan amana duk wanda ya tsince ta ina mai rokonsa da yariketa amana,bansame ta ta hanyar fasikanci ba,dan Allah a taimakeni wajen bata tarbiyya mai kyau. Kamar yadda mahaifina ko mahaifita ta rubuta a jikin paper,inaji ajikina ni ba 'yar da akayi fasikanci aka samenibace,😭😭. Ina bakincikin yadda iyayena sukayi abondoning dina,kullum addu'a nake Allah ya bayyana munsu,ya ganar dasu dan su dawo gareni,tun bani da wayo amma har yanxu shiru ba labarin su.😭 Hidaya tace insha Allahu Allah xai bayyana su. Haneefa ta cigaba da cewa,hidaya anyi sanarwa gidan radio,television ba iya jaharnan ba har other states amma iyayena sunki bayyana kansu.Daga karshe mai martaba ya yanke shawarar rikeni a hannunsa,alokacin bani da wayo ko sunana bana iya fada idan aka tambayeni,alokacinne mai martaba ya samin sunan matarsa ta farko da Allah yayi mata rasuwa,hajiya maryam,ake kirana da haneefa agida,a school kuma da maryam salahuddeen Adam. Hajiya maryam itace matar mai martaba ta farko,danta daya wato yaya Abdul Allah yayi mata rasuwa,sannan Abba ya auro maman Amal. Lokacin da aka kaini gidan yaya Abdul yana da shekara bakwai,Amal kuma tana da shekara uku,tare aka samu a makaranta,komai tare mai martaba yake mana baya ban ban tamu ni da Amal,wanda momy ko kadan batason hakan,tun bani da wayon daxan gane har naxo na fahimta. A lokacin da ya wuce bakiga yadda muka shaku da Amal ba muna yara,Amal tana sona sosai amma momy ta hana mu wasa tare daganan ta cusawa Amal tsana ta kuma ta nuna mata cewar ni ba 'yar gidan bace. Momy ta mai dani kamar mai aiki haka kawai xata kirkiri aiki ta bani har wanda yafi karfina,burinta kawai nasha wahala.Bayan akwai wadatattun bayi da masu aiki agidan. Duk abin da momy take yimin maimartaba bai sani ba saboda yawancin lokaci yafi xama a fada,idan ya gama da fada kuma bangarensa yake komawa momy tasameshi acan. Haka muma idan muna da bukata ko xamuje wani waje can muke xuwa mu sanar dashi. Tun bansan bani da iyaye ba sai da momy tasa na sani,kulawar da maimartaba yake bani yasa duk inda naje sunansa nake kira. Wata rana ina waya da wata kawata sai take cemin banason xuwa gidan su,sai nace mata xan tambayi Abbana insha Allah xanxo.kawai sai ji nayi momy ta katseni. Abban ki a ina?? Kije dai can duniya ki nemi ubanki,maimartaba bai haifi shegiya ba kin gane ai?? Kike wani iyayi wai Abban ki mtswwww. Nasa kuka bata bari nayi magana ba ta wuce part dinta. Dama nasan ba momy ce mahaifiyata ba,amma duk a tunanina maimartaba mahaifine,na fita da sauri naje wajen mai martaba ina kuka nafada masa,yasa aka kirata yayi mata fada sannan yace damme xata fadamin a tym din,sannan yace idan lokacin daxata sani yayi ai xansa ki fadamata ko ni nafadamata da kaina. Momy harda kukan munafurci,ta fara bawa mai martaba hakuri. Ni kuma na kasa jurewa,na ringa kuka,nace dole sai mai martaba ya nunamin iyayena shine ya kwashe labari yabani. Da farko yaya Abdul ma bai fahimci momy tana yimin mugun riko ba sai kwananan,saboda ba akasarnan yayi karatuba,kuma tana kuntatamin ne ta hanyar da baxai fahimta ba. Ina primary six nasan cewa mai martaba ba mahaifina bane,Abba yace daga ranar bayaso yaji ankara tayar da maganar. Daga lokacin ba wanda ya sake,sai yau dana fada miki. Kuma na yanke shawarar guduwa na bar gidan,saboda tun ban isa yin saurayi ba ake xuwa kamun aurena sai momy ta xage tace ni 'yar cikin shegece,😭😭daganan baxa'a sake maganar auren ba. Jiya kuma cewa tayi na satar mata kudi a brief case dinta har 250,000 Naira. Fuskar hidaya ta gama jikewa da hawaye jin labarin da haneefa ta bata,tace a'a haneefa karkice xaki bar gidan,watarana gaskiya xatayi halinta dan Allah ki kara hakuri. Haneefa tace kiyi hakuri hidaya gaskiya baxan iya jure cigaba da xama a gidannan ba. Hakadai hidaya tai ta bawa haneefa hakuri,sai karfe 6:15pm suka bar makarantar. By Hauwa s.Ahmad& Maryam y.Ahmad💞 💞💞💞💞 [10/16, 7:59 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 36-40 📚✍ EMIR IS ON HIS WAY BACK...✈ Motoci goma shabiyu Abdul ya umarci sarkin gida da'a shirya don xuwa taro mai martaba. Kamar yadda Abdul ya fada hakan sukayi,sarkin gida yaxo ya gurfana a gaban Abdul wanda ke xaune fada kan kujerar mai martaba,ya dunkule hannu ya daga sama alamar jinjina,yace Allah ya taimaki magajin sarki angama shirya motocin. Abdul yace ina ganin xamu iya tafiya,fadawan dake tsaye a gefe suka xagaye Abdul ya mike kamar maimartaba,sai faman kirari suke a haka har suke raka Abdul jikin motar da xai shiga,aka bude masa kofar motar, sai da suka tabbatar ya shiga ya xauna sannan suma suka koma wata motar. A layi motocin suke tafiya,daya daga cikin motocin mai jiniya ce,sai faman yi take,nan danan jama'ar kano suka fahimci ranar ne mai martaba xai dawo,har wani farinciki suke da nishadi,kokadan basason suji mai martaba xaiyi tafiya,saboda suna tsananin jin dadin mulkinsa tamkar na mahaifinsa da yayi murabus ya bashi,saboda adalcinsu da tausayin talakawa. Haka sukayi parking motocin a airport suna jiran isowar mai martaba. Ba'a jima da yawa ba jirgin da mai martaba yake ciki ya sauka,mutane sai daga masa hannu ake,fadawansa kuwa da sauri suka karasa matattakalar jirgin. Abdul ya tafi da sauri ya rungume mai martaba,sarki salahudden ya shafa kan Abdul sannan ya rike hannunsa fadawa suka raka sarki da Abdul mota majesticallay,wanda har suka shiga motar hannun sarki da Abdul a rike yake. Hhhmm lallai akwai kauna mai tsanani da shakuwa tsakanin sarki salahudden da dansa Abdulrahman💞💞 Haka suka nufi gida drivers din sunayin tuki cikin nutsuwa,duk unguwar da suka wuce munane suke dagawa mai martaba hannu saboda tsananin kaunar da suke masa. Motocin na tsayawa a harabar gidan,fadawa suka xo suka baxa manyan rigunan su dan kare mai martaba kar aga fitowar sa,bayan ya fito suka rakashi fada,bayan ya xauna sukayi masa sannu da xuwa tare dayi masa fatan Allah ya bashi lafiya,yace amin,haka sauran bayi da ma'aikatan gidan suma suka gaisheshi tare da yimasa sannu da xuwa. Baifi minti goma a fada ba ya wuce part dinsa inda ya tarar already momy tana jiransa,da sauri tayi hugging dinsa tare da yimasa kisss🙈 tace sannu da xuwa maimartaba,sarki yace yawwa uwar gida sarautar mata,ta kama hannunsa suka karasa ciki,tacire masa glass din dake idonsa ta rage masa kayan dake jikinsa,sanna ta mika masa towel,ta kalle maimartaba cikin kissa da kisisina tace sweetheart kafarayin wanka sai kaci abinci ko? Yace hakane dama nagaji hakan will be more better. Kafin ya fito daga wanka hajiya fatee ta fito masa da kayan da xaisa da sauran abubuwa na amfani daxai bukata idan ya fito. Bayan ya fito hajiya fatee tayi wa maimartaba dumping ruwan jikinsa,ya shirya cikin wasu kaya na sarauta amma basu da nauyi ko kadan,hajiya fatee tayi masa jagora xuwa dining don cin favourite dinsa data tanadar masa,sakwarace miyar agushi da ganda with fish and meat,sai papper chicken,dambun naman xabi da drinks.mai martaba na xama kafin ya faracin abinci yace ina Amal da haneefa suka shigane?? Momyn Amal ta danyi murmushi hade da yatsine fuska kadan tace uhhmm suna school gaba dayansu. 🌺'YAR MULKI🌺 2016 41-45 📚✍ Haneefa na dawowa daga school,tasa kafarta a hanyar falo kenan dai dai corridow taji an jawota a hankali tare da rufe mata baki da hannu,da yake magriba tayi corridow din akwai dan duhu bata gane waye ba,sautin muryar baba mareeya taji,tace haneefa kinsan cikin gida bashine wajen aikina ba,shiyasa na labe anan nake jira kidawo,nasan watikil sai gobe xamu hadu,shiyasa najiraki anan,so nake nace miki mai martaba ya dawo kuma idan aka kiraki akan maganar kudi karkiyi nuku-nuku kicewa mai martaba ke baki dauki kudiba nasan xata iya tilastaki kice kin dauka karki sake ki ansa laifin da bakiba kinji? Cikin tsoro kar wani ya kamasu haneefa tace to baba mareeya,nagode xanyi hakan,ki wuce kar munafukai sukai karar mu,haka suka rabu a tsorace.baifi minti 3 da shigar haneefa gida ba Amal ta dawo. Bayan anyi sallar magrib,maimartaba da Abdul suka xauna a falo suna hira,sarki yanajin ra'ayin Abdul da kuma bukatunsa,sai ga hajiya fatee ta shigo ta xauna akusa da mai martaba,Amal ta shigo cikin shagwaba tace Abba sannu da xuwa,sarki yace yawwa ya karatu?? Tace lfy kalau mun kusa fara exam ma,maimartaba yace sai a dage sosai,Amal tace Abba ina tsarabata,Abdul yaji kamar ya bige Amal dan haushi,yace ke wallahi haryanxu bakisan inda yake miki ciwo ba,kinsan cewa Abba asibiti yaje amma kike wani maganar tsaraba,mai martaba yace she is still young,ka rabu da ita. Momyn Amal taji haushin Abdul sosai,dama ta tsaneshi bata nunawane sabida kar mai martaba yayi waje da ita a kansa. Mai martaba yace ina haneefa bai rufe baki ba sai gata ta shigo,ta tsugunna tace Abba sannu da xuwa ya ansa sannan ta gaishe,sannan yace ya shirin exams?? Amal tace kun kusa farawa,haneefa tace ehh,sannan tace Abba ya jikinka yace Alhamdulillah. Yadda momy taga mai martaba yana yiwa haneefa magana cike da annashu ya kona mata rai. Tace mai martaba dama su nake ka huta nayi maka magana akan haneefa,cikin yanayin munafurci,tace ta canja halinta mai kyau daka sani acikin gidannan,saboda ta rika kudi ta satar min. Mai martaba yace subuhanallah,cikin yanayin mamaki marar musal tuwa,yace haneefan??😳 Tace kwarai kuwa,dan haka baxan cigaba da xama da barauniya ba,sai dai ta koma gidan marayu. Mai martaba ya kalli haneefa wadda banda hawaye ba abinda yake fitowa daga idonta,yace haneefa mai ya kaiki aikata wannan mummunan aiki haka?? Haneefa tace,Abba xanyi amfani da hurufa rantsuwa da Allah ya yarda a rantse da su,tace,wallahi,tallahi,billahi Abba ban dau kudin momy ba.sannan ta fashe da kuka. Tsananin tausayin haneefa ya kama Abdul,yace Abba nifa na yarda haneefa bata dauki kudinnan ba. Mai martaba yace na gani a kwayar idonta nima,sannan yacewa hajiya fatee ki duba da kyau kokin manta inda kikasa,nan fa taji haushi tace maimartane yake goyawa haneefa baya. Sarki salahuddeen yace ta fada kudin nawane xai bata,tace 250,000 ne a rake yasa Abdul ya dakko aka bata. Sannan yace duk laifin da haneefa tayi agidannan banaso ki kara furta cewar xata bar gidannan,shin bakya tausayin tane?? Yarinyannan batasan kowa ba fa sai mu.sannan inaso wannan maganar taxama tamkar ba'ayi taba. Haushi fal cikin momyn Amal tace toh,daga gani kasan abin baiyi mata dadi ba. By Maryam y.Ahmad Hauwa s.Ahmad✍ For call 08063495753 08033660286 Tnx 4 d lv,u guys r showing,it's more appreciated to us. 💞💞💞💞 [10/16, 7:59 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 46-50 📚✍ GOVERNMENT HOUSE🏤 Naseer na kwance akan gado ba abinda yake sai tunanin inda xai sake ganin haneefa.yayi danasani tafi dubu,da bai tsaya ya tambayi sunanta da number ta. juyi kawai ya ke,sanyin AC na ratsashi ta ko ina,aransa yana cewa menene amfanin jiji da kaina?? Anya xan iya jure rashin samun yarin yar nan kuwa? Shi kadai yake tambayar kansa.Gaskiya akwai matsala,i luv her dat very much,so I hv to find her.Naseer ya sake tambayar kansa to yanxu ta ina xan fara? shi kansa bashi da amsar tambayar.Dan kuwa bai saniba.Ganin la'asar ta kusa ya tashi ya shiga wanka,yayi alola yana fitowa ya shirya cikin kananan kaya.Bakaramin kyau Naseer yayi ba. Naseer kyakykyawan saurayine,kyan halittar sa ya cika ta ko ina,duk wani namiji idan yaga Naseer sai ya kara kallonsa,balle mace,gashi ya dace halinsa yanada kyau,sai dai akwai class guy din,ga kuma ji da kai,musamman idan yaga mace. THE FOLLOWING DAY.. His excellency Alhaji muhammad salees na tare da uwar gidansa hajiya Aisha,tace ur excellency badan bakin da nake dasu ba ai da nabiku munje tare,yace hakane,xamuje da Naseer then later sai mu koma tare dake,ya tambayeta hakan yayi?,haj.Aisha tace it's in order ur excellency,his excellency yace queen kice Naseer ya fito muje shi kawai nake jira,ta mike cikin tafiyar matan masu mulki ta nufi part din Naseer. Tana bude dakin,Naseer taga akwance ya xubawa pop ido,tace daddyn ka ya shirya kai yake jira,inaaa Naseer baisan tanayi ba,duk wata dabara da tunanin yadda xa'ayi ya sake ganin haneefa shi yakeyi. Mum dinsa ta karasa gefen gadon,ta kira shi da karfi Naseer,meyake damunka?? Yayi firgigit ya dawo hayyacinsa,yayi pretending bakomai,tace hakadai,kwana biyu na kula baka hayyacika,dad dinka na jiranka to. Cikin sakalci Naseer yace daddy nayi kyau,his excellency yace sosaima dan daddy,mum tana gefe tace bakayi kyauba to,Naseer yasa dariya ya kalli his excellency yace daddy wai dan ban tambayeta ba,sukayi dariya gaba daya😃,momy ta rakasu mota,Already an shirya motocin regularly,body guards,da drivers din basu shiga mota ba saida suka tabbatar Naseer da dad dinshi sun shiga,basu xarce ko ina ba sai gidan sarki salahuddeen Adam. EMIRS HOUSE.. Ganin governor ne yasa masu gadin basuyi wata wata ba suka bude,sallama yayi sauri ya sanar da maimartaba xuwan mai girma governor,akayi musu jagora xuwa fadar sarki. Maimartaba da governor suka gaisa,hisexcellency yayiwa sarki ya jiki haka Naseer ma,sarki yaji dadin xuwan su sosai,Abdul ya shigo fada suka gaisa sannan yaja Naseer suka shiga cikin gida,dama abokaine. Abdul ya kira Amal awaya yace nayi bako offer something for him please,ina main falo. Amal batason aiki ko kadan ta sangarce,ta yatsine,tace ni baxan iyaba,ke haneefa yaya Abdul yayi bako,ki kai musu ruwa main falo. Haneefa ko uhmm batace ba,tayi banxa kamar bata ji,ta mike ta nufi kitchen. ROYAL BLUE doguwar riga tasa da akayi mata kwalliya da red stone,shape din rigar ya fita,tayiwa haneefa kyau sosai,lallausan gashin kanta a nannade yake,xakayi tunanin acuci tasa,tasa jan dankunne karami a kunnen ta,ta yafa karamin gyale,sannan tasa flat shoe ja.haba ai kyan ba'a magana. Tana shiga kitchen din ta bude bridge ta dakko ruwa da lemu tasa akan faranti,ta dakko hadadden glass container ta shiga store din dake kitchen din ta xubo danbun nama,tasa a gefen ruwan da lemu,ta kama farantin da hannu biyu sannan ta nufi falon da su Abdul suke xaune. Tayi sallama,suka ansan idon naseer nakan wayarshi ko kallonta baiyi ba,ta nufi wajen da suke gently takarasa gaban su,tatsugunna ta ajiye farantin a nutse,Naseer na kallon kafar haneefa ya rikice saboda kyan halittar ta,sannan ya kalli xaratan yatsun hannayen ta,in takai ce muku saida naseer ya kalleta from head to toe,ta gama bigeshi,ga saje da ya kwannata yayi luf luf a gaban goshinta da gefen fuskarta ya kara birgeshe,kaiii Allahu Akbar yace aransa,Allah yasa wannan kyan nata ya xama mallakina,haneefa ta katse shi da cewa ina wuni,dakyar naseer ya iya ansawa ji swt voice din da bai taba karo da itaba duk cikin matan da suke masa roushing,ya basar gudun kar a ganoshi,Abdul yace weldone haneefa,Naseer yace wawww nyc Name aransa,gaskiya she must be myn,i lv u hannyfa ya lumshe ido. Abdul Naseer bismillah,murmushi kawai yake,Abdul yace aboki I can c dat r smile increased,ya basar just lyk that. Bayan sun gama,suka sha hirar su batare da Naseer ya fadawa Abdul sirrin da ransa ba. [10/16, 8:00 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 51-55 📚✍ Mai martaba da sarki,suma falonsa suka koma,yasa aka kawowa his excellency kayan motsa baki suka sha hira,sannan suka koma gida shi da Naseer. Haneefa na komawa daki tace,Amal xan fada miki gaskiya yau kam ko xakiji haushina bai kamata kiringa fadawa yaya Abdul haka ba,ko da ba agaban idonsa bane. Cikin masifa Amal tace hehehehehe,look haneefa karki kara shiga tsakanina da yaya Abdul,kin fini kusanci dashine?? Banda munafurci ina ruwanki?? Dama ke kikayi munafurcin da bama jituwa ni da yaya Abdul,mtshwwww tayi tsaki,so maintain ur self. Haneefa tace aranta,da ina da freedom a gidannan da saina tsinkawa Amal Mari.hhmm.tace sannan ta ci gaba da harkokinta. NEXT DAY.....👑 Motoci ne guda biyar Amal tasa aka jerasu,ko wacce bata da number,'yar mulki ne a number motar gabadaya,ansa 'yar mulki-1,2,3,4 up to five.kowacce mota da number da take dauke dashi. Amal ta fito cikin kasaita,kuyangun ta biyu na daga gefenta,tana wata tafiyar Mulki,ga kuma guards dinta guda biyu,ta shiga motar ta xauna tare da masu yi mata hidima,driver motar 'yar mulki-1 ya fito ya risina agaban Amal yace ran gimbiya ya dade ina xamu?? ko magana Amal batayi ba ta kalli kuyan garta alamar ta bashi answer,jiki na rawa tace,banki gimbiya takeso taje xatayi thumb print. Haka suka nufi bank din motocin na tafiya serially. Motacin na tsayawa,guard dinta daya ya shiga bank din da sauri yace,kowa ya fita gimbiya Amal xata shigo,sanin rashin mutuncin Amal yasa kowa baiyi gardama ba ya fito. Mutane sai kunkuni suke,yadda baxa ta gane ba,kowa yasan halinta agarin,haka kuma kowa ya dauka sarkine yake ya shagwabata shiyasa akarasa mai kai karar Amal wajen maimartaba. Motar da take ciki mai tudu ce ta xuro kafafuwan a hankali ta fito,sannan tace kuyangun ta da body guards su jirata a kofar bank din. Amal taga wata kyakykyawar budurwa a tsaye suna hada ido,ta karasa kusa da ita,ta daga hannu da sirfa mata mari,sannan tace banason too much kallo daga yau,take note.yarinyar tasa kuka.kowa na wajen abin ya kona musu rai. Saida ta gama abinda xatayi ta fito sannan kowa ya koma cikin bank din. Naseer ya kira Abdul a waya yakai 6missed calls bai daga ba,Naseer yaji kamar ya fasa wayar dake hannunsa.sai ga kiran Abdul yana shigowa wayar sa. Haske kawai wayar tayi,bai bari ta fara ringing ba caraf yayi picking call din,yace hlo,Abdul yace sorry Naseer bana kusa da wayar ne. Naseer yace no bad,sannan Naseer yace nifa nayi mata a gidanku,Abdul yasa dariya😊 yace wakenan?? Abdul yace kanwar ka,Abdul yace kannen nawa ai biyune wacce daga ciki? Naseer yace karamar,yace Amal kenen,Naseer yace nooo haneefa naji ka kirata dashi ranar da mukaxo da his excellency,yace haneefa ce babba sannan Amal ai,sannan yace hahhh no wonder ashe kamuwa kayi shiyasa ranar naga smile yaki karewa,Naseer yayi dariya.😄 Abdul yace congrats aboki,dan kuwa kayi sa'ar mata,nasan dai kyau ne ya rude ka amma ka dace haneefa akwai kyan xuciya dana fili,Naseer yace ka tura min no dinta to yanxu, amma ka fara fada mata kafin na kirata,Abdul yace it's alright.Naseer yace bye sai naji yadda kukayi. Suna gama waya Abdul ya kira haneefa suka fara tattaunawa kamar haka. Ya fara lallaba haneefa saboda yasan kokadan bata da rawar kai akan maxa,yace kawanta,haneefa tace na'an yaya Abdul,yace akwai saurayin da kike tare dashine presently?? Tace a'a,baxan iya irga wanda suke sona ba amma nayi decline dinsu,tace,yaya Abdul ko kadan banason yin saurayi. Abdul yace koda ni na kawo shi? Haneefa tayi shiru kanta a kasa,saboda tanajin nauyin yaya Abdul. Friend dina da kika same mu a falo yester tym shine yake sonki,haneefa bashi da problem ko kadan. Yace Naseer mutumin kirkine kanwata kinsan baxan bari ki auri wanda bai kamata ba.pleasee kice kin amince. Haneefa baxata iya yiwa Abdul musu ba tace shikena ba damuwa.Abdul yace na bashi number ki at any giving tym xai iya kiranki.tace ok. Aranta take magana tace, bansan iyayena ba meyasa xan yarda nafara maganar auren?asan ko bayanxu ba sai anyimin gorin iyaye,gashi baxan iya embassing yaya Abdul ba.ni maryam (haneefa) inaxan sa kaina.Allah ka bani mafuta. Abdul kuwa shi mantawa ma yake haneefa ba 'yar gidan bace,saboda tun bata da wayo take gidan amma ita kullum abin yana ranta.tace ya Allah ka kawo sanadi daxan fita daga gidannan naje har wajen da iyayena suke.ta fashe da kuka😭. 2hours later.... Naseer ya kira haneefa a waya,ta daga hlo,muryar haneefa akwai xaki,Naseer ya lumshe ido,yace ya gida,haneefa ta amsa lafiya kalau. kina magana da Naseer mohd salees,frnd din yayan ki Abbdul,haneefa tace ok,yace naji dadi sosai da Allah ya hadani dake haneefa,i luv u morethan u anticipate. Salon yadda Naseer yakewa haneefa magana yasa ta gane lallai da alama Naseer ya iya soyayya. Taji har sonsa ya shigeta,har mamaki take,Naseer yace ina neman ixini bayan sallar isha naxo na ganki mai cikakken iko,haneefa tayi murmushi irin najin dadi😊,jin yadda naseer ya fasa mata kai. Haneefa tace ai kaine mai cikakken iko,haneefa taji dadin sunan,Naseer ya karya murya cikkn salon soyayya yace baby na are u free?? Tym din yayi miki? Haneefa ta sake murmushi,tace yayi,Allah ya kawo ka lafiya,Naseer yace,ok bye bye,take a very good care of ur self babynah,. Ta ansa I will try,bye.... Gaskiya inason Naseer,rana daya kawai ya canja min rayuwa,ji nake kamar ban taba damuwa ba. A kasan,xuciyar ta tace gara nasakk jiki muyi soyayyar mu,dan bansan lokacin daxan ga iyayena ba,inaji ajikina kamar naseer shine mijina. Ya Allah ka xabamin abinda yafi Alkhairi. Ashe Amal na tsaye akan haneefa,kallonta kawai take,ta gama fahimtar cewa haneefa sabon saurayi tayi,aranta tace ki gamashan soyayya ba mai auren shegiya a garinnan.tayi gaba part din mummy ta nufa. Naseer da haneefa na xaune,sai hira suke kamar ba ranar suka fara haduwa ba,gabadayan su sunyi mummunan falling,Naseer yace yau shine gani na uku danayi miki amma kamar tunda Allah ya haliccemu na sanki haka nake ji,hanny tayi dareeya hmm kamar dagaske, sannan tace kamanta yau shine ganinka na biyu dani. Naseer yace xaki iya tuna ranar da kika kade wasu a titin bypass,tace eh na tuna,nasan a rikice kike shiyasa baxaki ganeni ba,tundaga ranar naji ina sonki sai gashi Allah ya sake hadani dake.haneefa tayi murmushi. Tace dama kaine? Kuwa ranar naji haji haushi,naseer ya gwiwar sa akasa yace baby am on ma kneels kiyi hakuri,haneefa tace do u want me to be on ma kneels too?? Yace noooo tace to ka tashi it's over. I don't wanna miss u Naseer ya fada tare da watsawa haneefa kallo da sleeping eyes dinnan nasa,yace daddy najira na xamuyi wata magana ne. Hanny tace ok,tarakashi mota sannan ta dagamasa hannu tare da fadin I luv u Yaya Naseer. 1month later.... Shakuwa mai tsanani ta shiga tsakanin naseer da haneefa,basa iya komai idan basuji muryar juna ba,naseer yana yawan xuwa shiyasa sukaji kanar sun shekara dari da fara soyayya,idan kaga yadda suke caring juna abin xai birge mai karatu saboda nasan kowa yasan yadda kulawa,damuwa,da kuma tausayi suke tasiri axuciyar masoya. AMAL.... Amal batasan wanda yake xuwa wajen haneefa ba,ita dai kawai ta arawa haneefa lokaci,tana ta hada mugunta,wai sai sun gama shakuwa xata tona sirrin haneefa,cewar 'yar cikin shegece,tayi dariyar mugunta,tace soyayya manya😂😂. Tofah idan Naseer yaji hakan xaisa yafasa auren haneefa?? By Hauwa s.Ahmad& Maryam y.Ahmad📚 For comment 08063495753 08033660286 💞💞💖💞💞 [10/16, 8:01 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣1⃣ 📚✍ Su Amal na fitowa daga lecture,suka nufi wajen da suka saba xama ita da Afrah da mufeeda,guards dinta sukayi yunkurin take mata baya,Amal ta daga musu hannu alamar dakatar wa,tace nooo basai kun bini ba,daya nake so kawai daga cikin ku,akwai aikin daxan sa aimin,kawai ta juya suka cigaba da tafiya,haka daya daga cikin guards din yabi bayansu. Suna karasawa wajen suka xauna,guard din Amal kuwa na tsaye yana jira abashi umarni,Amal ta dora kafa daya kan daya,tace luqman aikin danake so na saka ba mai wahala bane amma,yace ok ur highness,ta bude jakarta ta dakko number motar mujaheed a takardar datayi writting down dinta ta mika wa lukman,yasa hannu ya karba cikin respect,tace motar da take dauke da wannan number tana cikin tana cikin makarantar nan,kayi going round ka tabbatar ka sameta,sannan inaso ka sace iskar tayoyin motar gaba daya,yadda ba xa'a iya gyarawa ba sai dai a sake tayoyin. Luqman ya karba yace done.Amal tace bafa naso asami matsala,make sure that u do as I mentioned,tafada cikin mulki da kuma jan kunne. Cikin girmamawa luqman yace,angama,sannan ya juya ya tafi. Afrah da mufeedah suka tafa atare,mufeeda ta ce nyc idea 'yar mulki gaskiya kin hadu,Afrah ma tace lallai kam yau ran mujaheed idan yayi dubu sai ya baci,suka kwashe da dareeya,Amal tace hah ai ba ayi masa komai ba yanxu,this is just d begining. Kamar yadda Amal ta umarci luqman haka yayi gabadaya saida ya sace tayoyin motar mujaheed tasss sannan yabar jikin motar. Amal tayi sallama da su Afrah,drivers dinta suka jera motoci cikin tsari,kuyangunta kuma suka rakata mota,sannan suka nufi hanyar gida. Mujaheed ya gama duk wani abinda xaiyi,so yake kawai yaje ya kwanta ya huta dan kuwa ya gaji,gashi har yanajin kansa yana sarawa. Da sauri mujaheed ya karasa wajen da yayi parking motar shi,ya bude ya shiga,banda kanshi ba abin da motar take,yasa key sannan ya fara kokarin tayar da motar,kawai sai gani yayi wani waje yana bashi signal na red danger ga kuma hoton tayar mota daga gefen da red danger'n ke blinking,yace to meyake faruwa? Ya tambayi kansa.ya fito daga mota dan duba lafiyar tayoyin.yanasa idon shi an tayoyin yagasu a sace gaba daya,ransa yayi bala'in baci. Shiruuuuu mujaheed yayi yana tunanin barnar da akayi masa,ya ja tsaki sannan yace wanne irin rashin mutunci ne haka? Wannan ai da niyya akayi,ya jingina ajikin motar tare da sakale hannayensa biyu a kirjinsa,ya sake yin shiruuuuu sannan yace duk cikin makarantar nan ba wanda xai min haka sai Amal.amma lallai yarinyar nan ya fada cike da takaici,sai ta gane kuskuren ta. Mujaheed ya fito da wayar sa,yayi dialing number qualified engineer'n shi,yace inason irin tayoyin motata gaba daya hudun,ka ara kudi ka siyo,kasameni a cikin school,idan kaxo sai mu biya ta ATM na baka kudin,seti yace to ba damuwa yanxu xaka ganni insha Allah. Haka seti yaxo akasa tayoyin gabadaya,sannan suka wuce ya bashi kudin. Mujaheed da yakeson fita daga school tun kafin magrib shine sai da ya kai har karfe tara na dare. Mujaheed ya gama tsara abinda xaiyi wa amal dan kuwa ya rantse sai ta gane kuskurenta. EMIR'S HOUSE.... Haneefa yau bata je school ba,tun safe tana daki a kwance,ba abinda take sai tunani kala kala,amma tunanin nata yafi rinjaye akan inda xataga iyayenta,aranta tace oh ni haneefa,yanxu idan iyayena xan fara nema ma bansan ta inda xan fara ba,ni dai daxaman gidannan gara naje na sami wani gidan ko shara da wanke-wanke ne na ringa yi,tana cikin wannan tunanin taga kiran Naseer na shigowa wayar ta. Ta saki wani murmushi,da har saida dimple dinta ya fito,ta daga wayar tare da fadin hello,Naseer yace mai cikakken iko I hope u r ok,wani irin dadi ya kama haneefa jin muryar naseer ya kirata da wannan sunnan,tace am fyn my dear,Naseer yace tun daxu ina office amma na kasa komai saboda rashin jin muryarki,totally banajin dadi idan banji ki ba,haneefa tayi murmushin da har saida ya fito fili tace,kamar yadda nima nakasayin komai kenan? Naseer yace haneefa kenan kina ganin kamar son danake miki wasa ne ko?,u wil never undrstnd hw am feeling,haneefa am sincerely deeply in luv wit u. Shiya sa xakiga bana iya komai idan banjiki ba,na riga nasanar da mom da dad dina komai,yanxu kawai jira nake ki bani dama aturo,dan banaso auren mu yakai da nisa. Gani nake kamar xa'a sami wanda xai kwacemin ke,dan kuwa ba wanda zaiga kyan surarki,da halayyar ki yaji baya son kasancewa tare dake a matsayi mata. Jikin haneefa yayi sanyi jin yadda taga Naseer yayi xurfi acikin sonta,tsoron ranar daxai san asalinta take,dan kuwa ba lallai ne yayi bearing da stuation din da take ciki ba,ta saki wata irin doguwar ajiyar xuciya,takasa cewa komai dan kuwa gabadaya ruwan kanta ya gama tsotsewa tunda Naseer ya sako maganar aure. Naseer yace hello,haneefa,tace inajinka yaya Naseer,yace naji kinyi shiru ne,haneefa tace bakomai.sannan tace yaya Naseer da cewa nayi mu bari idan nayi completing level 2 sai a fara maganar aure,kaga daga wannan semester'n mun gama level 1,aganin haneefa kafin nan Allah ya kawo mata solution. Naseer yace karki damu babynah,ko a gidana ai xakiyi karatu dan har tayaki xan ringa yi.ta dan yi murmushin yake. Sannan ta mai da numfashi tace to,bari dai mu gama wannan semester'n.Naseer yace no bad babyna. Suna cikin wayarne Naseer yaji ana knocking kofar office din,yace sorry baby I will call u back,haneefa tace ok bye,stay blessed. By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad📚 💞💞💞💞 [10/16, 8:02 PM] ‪+234 706 370 3994‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣2⃣ 📚✍ EMIR'S PALACE..... Sarki salahudden Adam na fada a xaune tare da fadawansa,suna tattaunawa kan yadda xai samarwa jama'ar kano jin dadi,dakuma neman shawarar su dan samar da cigaban al'umma. Abdul na daga gefen mai martaba,ko ina Abdul yana tare da sarki,sai dai idan wani jenue uxuri Abdul yake dashi. Wayar Abdul ce ta fara ringing,ya daga hello,Naseer yace yah Abdul kana gidane?? abdul yace ehh,Naseer yace please kacewa haneefa xanxo anjima,na kira wayarta is not going,yakamata na sanar da ita kafin naxo,Abdul yace ok,a takaice ganin cewar yana gaban maimartaba. Abdul ya shiga gida,ya nufi part din su haneefa,yayi knocking ,haneefa na bude kofar sukayi ido biyu da yaya Abdul,kawai tayi murmushi sannan tace ashe kaine yaya Abdul? Abdul yace ehh dolece ta tasoni,haneefa ta juya ido sama tace dole? Meya faru? Abdul yace Naseer ne dolen ai,haneefa tasa dareeya,Abdul yace ina tare da mai martaba amma saida ya tasoni,kaiii haneefa narasa wanne irin so naseer yake miki,yace na fada miki anjima xai shigo.Haneefa tace ok,mungode da kokari yaya Abdul,cikin tsokana yaya Abdul yace hmm wato naxama messenger'n ku ko? Hanny tasa dareeya,ta rufe baki🙊 tare da fadin a'a yayan mudai. Abdul ya juya ya tafi tare da fadin to nidai na isar da sako. 3hours later... Haneefa na kwance akan gado,tagama shiryawa tsaf,call din Naseer kawai take jira,dan kuwa duk wani nau'in abinci da xata sauki naseer dashi is ready. Tayi kyau to d extent,doguwar rigar bakin material tasa wanda akayi masa kwalliyar pink,rigar tayi fitting dinta sosai,sai pink din siririn mayafi da haneefa ta yafa aka,gaskiya baxan iya shiru ba sai na fada cewar haneefa kyakykyawace,farace tasss ga yalwar gashi,akwai diri mai kyau,ga skin dinta kamar auduga,xaratan yatsun hannun ta da kafar ta kuwa duk wanda idon sa yayi arba dasu sai yaji tamkar ya sace ta,gaskiya Allah yayi halitta,mai karatu pleasse yimin alfarma kadan ka hasko min tsananin kyan haneefa da farinta cikin bakin material dinnan.basai na wahalar da kaina ba nasan maikaratu ya gamsu da tsananin kyan haneefa. Haneefa taji dadin kwanciyar,ji take kamar tayi bacci,har idon ta ya fara lumshewa,kawai sai ganin call din naseer tayi yana shigowa,da sauri tayi picking,tare da fadin hello,yaya naseer,yace na'am,babynah,nashigo ina greenplantation ke kadai nake jira nasaki a kwayar idona,haneefa tayi murmushi irin najin dadi tace ok ganinan fitowa. Bata bata lokaci ba ta fita,don kuwa itama ta matsu taga Naseer din. Tunda Naseer ya hango haneefa ya kafa mata ido,har saida ta karaso wajen da yake xaune,tayi masa sallama ya ansa sannan ta xauna. Naseer yace such beauty,baby na kinyi kyau sosai,haneefa tace nagode,amma ai ban kaika yin kyau ba,kafin haneefa ta sakeyin magana taji wayar dake hannun ta ta fa 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣3⃣ 📚✍ Amal da mota daya kawai ta fita shopping,haka kuma ko driver'n ta bata fita dashi ba,tunanin naseer kawai take. Tace kaiii anya guy din nan dan akasar nan ne kuwa?,dan kyan nasa ya wuce misali,saikace balarabe,dole na mallakeshi dan kuwa baxan iya rayuwa ba tare dashi ba. Haka Amal ta ringa tunani har ta karasa bakin store din. Ta fito daga mota cikin tafiyar kasaita,ta shiga store din tasai duk wani abinda take bukata. Tana fitowa taga anyi parking wata mota a kusa da tata,gashi dai xata iya fitar da tata motar daga wajen,amma saboda isa da kuma tsokana tace sai ta jira taga wanda yayi parking motar akusa da tata. 5 minutes later.... Kawai sai ga wata mata ta fito daga store din itama,matar xatayi kimanin shekara 37,motar matar ce akusa da ta Amal. Matar ta xira key kenan xata bode motar kawai sai ji tayi Amal taja gefen mayafinta tare da fadin wanne irin rashin lissafi ne wannan? Cikin rashin kunya Amal take maganar,ya xa'ayi kawai kixo ki matse waje ta yadda motata baxata iya fita ba??,sai an goga muku mota kuma kuce ba'a ktauta ba. Matar dan mamaki kasa magana tayi,tsawon rayuwar ta ba wanda ya taba mata rashin kunya kamar yadda Amal tayi mata. Dakyar tace anya yarinya kinsan darajar iyayenki kuwa?to kiyi a hankali,duniya ce wanda baixo bama jiranshi take. Tsaki kawai Amal tayi mtswww tare da cewa malama ki janya kaxamar motarki dan ni sauri nake.ta juya ta shiga motar ta. Haka matar ta ja motar ta tayi gaba cike da mamakin Amal,aranta kuwa abin yayi mata kuna matuka. Ita kuwa Amal ko ajikinta,tukin ta kawai take cikin sauri,aranta tana cewa take Allah yasa Naseer bai tafi ba dan kuwa tanaso ta kara sashi a idon ta. Mtswwww Amal tayi tsaki saboda sauri take ta isa gida,gashi danger ta riga ta tsayar da su,baya 2minutes aka basu hannu,motar dake gaban Amal wani dattijo ne aciki,yayi-yayi motar ta tashi taki,hakan ne ya hana motar Amal ta motsa ko ina,Amal tafito a fusace,ta bude motar da dattijon yake ciki,ta jawo shi sannan ta fella masa mari,tace idan kasan motar ka a lalace take ai sai kafara gyarawa,kafin kace xaka nunuwa mutane kai mai motane,mtswww yanxu haka ma ta aro ce. Mutumin bai iya cewa komai ba,kawai hawayene ya gangaro daga idonsa,😭harya daga hannu xai mari Amal,sai kawai wata xuciyar tace kyaleta xata hadu da dai-dai ita.rayuwa ce. Amal ta juya ta koma mota,ta fisgi motar da karfi tayi gaba. Tana xuwa gida part din momy ta wuce,ta kwashe labarin wadanda tayiwa rashin kunya ta bawa momyn ta,batayi mata fada ba hasali ma cewa tayi good karki ragawa kowa,dan mutane xumane sai an cisu da wuta. Sannan ta kwashe labarin yadda take matukar son naseer ta fadamata,tace momy ya xanyi soyayyar sa ta dawo kaina?? Wallahi shi nake so. Momy tace it's simple ai sweet Amal,tace kawo kunnen ki,Amal tasa kunnen ta dai-dai saitin bakin momy,ta rada mata wani abu,wanda nikaina bansan menene ba,sai kuma naji momyn tace idan mai martaba yayi magana ni kuma xance yarintace.Amal tayi dariya tare da fadin yesssss momynah. 3 days later...... Yau Naseer da haneefa a pink pallow suka xana,hirar su kawai suke,Naseer nata tsara yadda bikin aurensu xai kasance,fuskarsa with ful of joy. Murmushin haneefa kuwa yaki karewa,saboda maganganun da naseer yake ba karamin sata jin dadi suke ba. Naseer yace ammafa kina cika shekara daya cif agidana xan karo mata daya,haba nan da nan haneefa ta hade rai,ta mike da nufin xata shiga gida,tace wa naseer sai anjima,Naseer ya riko hannun ta tare da fadin haba babyna wasa nake fa,haneefa tace sakemin hannu,wanda sai alokacin ne Naseer ya kula cewa hannunsa na rike da na haneefa. Naseer yace ohhhh sorry babynah,ke kika rikitani,dan ko kadan banaso naga ranki ya baci.hakadai ya lallaba babynshi har ta hakuri. Ashe duk abin da suke akan idon Amal,saboda kofar falon is transparent saboda ta glass ce. Kawai sai ji sukayi Amal ta bude kofar falon ta shigo,ta gaishe da Naseer,ya amsa cikin fara'a ganin cewa Amal sis din haneefa ce. Amal tace yaya sai dai bansan sunanka ba,yace suna na Naseer,haneefa bata fada miki ba kenan? Gaskiya bata kyauta ba kanwata. Amal tadan gyara xama tace,gaskiya da alama kai mutumin kirkine,dan haka baxan bari ka fada ga halaka ba, xan fada maka gaskiya. Haneefa ba 'yar gidan nan bace,'yar tsintuwar bakin titi ce,idan kuma karya nake gatanan ka tambayeta. Naseer yace,ba damuwa koma yaya take,inasonta,kuma a shirye nake dana aure ta cikin kowanne hali. Banda hawaye ba abinda yake xubowa daga idon haneefa. 😭😭😭 By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad📚 💞💞💞💞 [10/21, 8:47 PM] ‪+234 814 443 8844‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣4⃣ 📚✍ Amal tace yayi kyau,ammafa ka birgeni,kuma ka cika gwarxon namiji.sannan tayi murmushin mugunta.tace. Idan kana ganin xaka iya auren ta ai nasan family'n ka baxa su taba yadda ba,shiyasa tun yanxu na baka shawara,basai maganar taje kunnen su ba. Naseer ya daka wa Amal tsawa ganin tana neman ta wuce gona da iri,yace will u shutup? u bloody fool,get out stupid kawai. Amal ta juya ta fita,direct dakin momy ta nufa,tana kuka. Yanayin haneefa kuwa xai bawa mai karatu tausayi,bata iya cewa komaiba awajen,kuka kawai take,Naseer yace kiyi hakuri babynah,dan Allah kiyi shiru. Inaaaaaa batasan yanayi ba,yau kam hakuri na yaxo karshe,haneefa tace a xuciyar ta,kawai ta mike cikin sauri ta fice daga falon. Naseer kuwa cewa yake babynah,babynah,inahhhh bata saurare shi ba. Haneefa na shiga daki bata xauna ba,sai da ta gama hada kayan ta tsaf a akwati,ta dakko key din motar ta daga jaka ta dora akan gado,ta leka ta window ta tabbatar Naseer ya tafi,sannan taja akwatin ta fito harabar gidan. Gidan baya rasa mutane wajen xirga xirga,amma tayi sa'a lokacin duk suna cikin masallaci dayake lokacin sallar isha ne,saboda sarki yace bai yadda lokacin sallah yayi su xauna gadi ba,yace komenene suje su sami jam'i, idan sun dawo sa cigaba. Haka haneefa ta lallaba ta bude gate din ahankali,tana fita ta tari adaidaita sahu,mai adai-dai tan ya tambaya,hajiya ina za'a kaiki,haneefa tayi shiru saboda bata da kowa a duniya da zata nufi wajensa,da har wata xuciyar tace taje gidan su hidaya,sai tace nooo gara naje inda baxa'a sake samun labari na ba,tace kaini gwauron dutse,unguwar da taxo bakin haneefa kenan,yace kudin ki dari takwas tace ba damuwa muje yi sauri. Allah Allah take kar a fito agane xata gudu. Suna hanya naseer ya ringa kiran wayar haneefa amma sam taki dauka,daga karshe ma kashe wayar tayi gaba daya. Hankalin naseer ya tashi sosai,yaji kamar ya koma gidan,saboda jikinsa yana bashi ba dai-dai ba.kawai sai ya yanke shawarar early morning xai koma wajen haneefa gobe. Sun shiga unguwar da haneefa ta fada,har suna nema su fice,mai keke napep din yace hajiya mun kusa mu wuce inda kika fada fa,tace to sauke ni anan,ya tsaya ta sauka sannan ta mika masa kudinsa. Ta fara tafiya da kafa,gashi dare yayi kuma batasan inda xataje ba. Kofar wani gida ta samu,da alama gidan sabone dan ko tarewa ba'ayi acikiba haka ta yi alola,ta shinmfida dan kwalinta tayi sallar isha a kofar gidan,bayan ta idar tayi pillow da akwatinta banda kuka ba abinda take. The Following day... Chager'n abdul tun dare taki daukan chargi,da sasssafe yaje yayi knocking dakin su Haneefa. Dakyar Amal tace wai waye,cikin yanayin bacci,jin yace ke dalla Abdoul ne yasa tayi saurin tashi,saboda Amal tana bala'in tsoranshi,dan kuwa basa ga maciji,ta bude kofar. Yace ina haneefa? Da nufin xai ari charger awajenta. Amal tana murtsika ido tace,bata kwana agidannan ba ai,tun jiya batanan,Abdul yace ina taje,tace oho nidai naga ta kwashe kayanta. Abdul yayi tsaki mtswwww dalla rufe min baki,shine kika sami damar yin bacci?,meyasa baki fadawa Abba da momy ba,ko ni kifadamin?,Amal tayi shiru alamar rashin gaskiya.Abdul ya juya a fusace ya fita. Bai wuce ko ina ba sai wajen mai martaba,saboda yasan kawai haneefa guduwa tayi,dan bata taba xuwa wani waje ta kwana ba a iya saninsa,to ina xata dau akwati taje da ita? Ya sanar da maimartaba abinda yake faruwa. Amal kuwa dakin momy ta nufa,tana xuwa bakin kofar taji momy tana waya,ta bude kofar ta shiga,momy tayi sauri ta katse wayar,gashi dai AC na tsananin ratsa dakin amma banda gumi ba abinda yake keto mata,Amal ta gama gane akwai abinda momyn ta take kullawa amma sai ta share bata tanka ba,ta kwashe labarin yadda sukayi da Abdul ta fadawa momy,tace Alhamdulillah tunda ta gudu dan kanta waya gayamata borno gabas take? Kafin kace meye wannan sarki yasa kowa ya hallara agidan a fada har,hajiya fati da Amal,baba mareeya sai kuka take awajen. Sarki yace waye yaga fitar haneefa acikin ku? Kowa yace bai gani ba,sarki yace to me ya faru yarinyar nan ta gudu daga gidannan? Kowa yayi tsit amma bayi da ma'aikatan gidan sun san dalili fadane kawai baxa suyiba saboda tsoro. Ana cikin wannan alhinin sai ga naseer ya bayyana a fadar,yayin da ake alhinin batan haneefa.yace gaskiya Amal baki kyauta ba,Abdul ya kalli Naseer yace metayi? Naseer yace itace sanadin barin haneefa gidannan. Ya kwashe labarin yadda ta kuntatawa haneefa agaban shi ya fada,habaaaaaa nan danan Abdul ya kwasheta da mari,sarki salahuddeen bashi da fada amma sai da yacewa Abdul karamata duk son da sarki yake yiwa Amal,ya kara mata biyu kyawawa. Amal sai kuka take,momyn kuwa cewa take ai yarinta ce tasa ta aikata hakan,ta jata suka koma cikin gida tana ta rarrashinta. sai kiran war haneefa ake amma akashe,sun rasa me yake musu dadi. Naseer kuwa bai iya jurewa ba kuka kawai yake. Gaba daya kansu ya kulle sun rasa ta inda xasu fara neman haneefa agarin kano. By Maryam y.Ahmad Hauwa s.Ahmad📚✍ 💞💞💞💞 [10/21, 8:47 PM] ‪+234 814 443 8844‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣5⃣ 📚✍ KAUYEN GANO DAKE KARAMAR HUKUMAR KANO......... Rashin lafiyar malam jibrin tayi tsanani dan kuwa yawancin abubuwa ma matar sa lami ce take masa,kullum yana kwance a daki saida maraice ake dan fita dashi dan yayi exercising jikinsa. Yau malam jibrin yana daki a kwance,kawai sai yaji an sako cikiyar haneefa agidan radio. ya daga kansa sama,tunanin abubuwan da ya aikata abaya kawai yake,sai naga ya fashe da kuka,xuciyarsa cike da danasani,kana kallon idonsa kasan akwai nadama. Ya fara tambayar kansa,anya kuwa idan na bari yarinyarnan taxo duniya ta koma batasan iyayen ta ba zan sadu da rahmar Allah? Yasake cewa anya ba alhakintane dalilin kwanciyata jinya ba? Duk aransa yake wannan maganar. Gaskiya lokaci yayi dayakamata na ragewa kaina wani xunibin. ya kwalla kiran lami dake tsakargida tana tankade,ta amsa na'ammmm malam. Tashiga dakin tace malam karde jikin nakane,yace a'a. Sannan yace lami asamo shatar mota lokaci yayi daya kamata in cire maryam daga halin maraicin da take ciki,yanxu naji sanarwa agidan radio ta gudu daga gidan maimartaba. Lami ta xuba tagumi tace malam ka bari ka kara samun sauki,saboda nasan idan muka je tabbas sai sarki yasa an fille maka kai,tasa kuka😭 idan kuma bahaka xaisa a daure ka.xa'a ganta insha Allah. Malam jibrin yace lami lokaci ba a hannun mu yake ba,ashirye nake dana mutu,indai akan maryam ne,banaso na mutu ban nemi yafiya awajen ta da mahaifinta ba,dan Allah lami ki hanxarta a nemo shatar mota,mutafi.muryar ta a sanyaye tace to malam. 15mintues later.... Motar da aka dakko shatar taxo,malam jibrin ya kira kaninsa talle don su tafi tare,mai motar da talle ne agaba,sai lami da malam jibrin abaya.basu xarce ko ina ba sai gidan sarki salahudden Adam.(EMIR OF KANO). EMIR'S HOUSE..... Kowa hankalisa ya tashi,Naseer yace Abdul ina ganin ka fita da motar ka nima na dauki tawa sai kawai mushiga gari mu fara dubata ko Allah xai sa mu dace,Abdul yace ok,amma mu fara xuwa motor parks,tukunna nasan dai ajiya baxata bar kano ba dare yayi,sai dai yau.sarki yace Allah yayi muku albarka kuma yasa a dace,suka ansa ameen. Dai dai lokacin sallam ya gurfana agaban sarki,yace Allah ya kara maka imani,akwai bako daga gano yana neman ixinin ganawa dakai,sarki yace ka bashi hakuri ya dawo wani lokaci. Sallama ya koma ya sanar da su malam jibrin,cikin matsanaicin kuka malam jibrin yace maganar na da muhimmam ci matuka,kace masa akan maryam naxo muyi magana,yarinyar da yake rikewa,sallama yace haneefa? yace ehhh. Da sauri sallama yaje ya sanar da sarki,maimartaba yace a shigo dasu. Jin ance akan haneefa bakon yaxo,Abdul da Naseer suka fasa motsawa ko ina sun dauka labarin inda take aka kawo. Jakadiya kuwa uwar munafurci har taje ta fesawa Hajiya fati da Amal gawani bako yaxo wai anga haneefa,nan da na suma suka nifi fadar sarki. An ciki sosai,kowa na gidan ya hallara a fadar. Malam jibrin yace ina neman gafara awajen sarki,domin laifin danayi muninsa baxai musaltu ba,sharrin shedan ne amma dan Allah kayafemin,sarki yace inajinka ina haneefan? Ko kasheta kayi? Malam jibrin yazama confused,yace bana na tare da ita,ina kwance naji sanarwa a radio cewar maryam ta bata. Shiyasa naga gara na bayyana abin da yake gaskiya ne,kafin na koma ga ubangiji na. Ni ne mutumin dana kawo haneefa wajen ka tun tana karama,nace na tsinceta ,tare da takar da. Gaskiyar magana maimartaba haneefa 'YAR KACE, kowa sai da xuciyar sa ta buga awajen,dum,dum,dum ,dum.......!!! Malam jibrin yace ina nufin 'yar cikin ka da ka haifa,kamar yadda ka haifi sauran 'ya'yan ka guda biyu. To fah,sarki kansa ya shiga rudani,saboda a iya sanin sa Abdul ne da Amal kawai 'ya'yansa.amma ya kasa musa abinda malam jibrin ya fada,saboda,yanajin son haneefa a xuciyarsa fiye da sauran 'ya'yansa,yana boyewa ne saboda karya sanya fitina a tsakaninsu. Sarki yayi kokarin cewa ban fahimce ka ba??? Malam jibrin yace nasan baxaka fahimce niba kamar yadda kowa na wajen nan baxai taba fahimta ba,har sai na baku labarin abin da ya faru. Ya fara bada labarin kamar haka. DAN ALLAH KUYI HAKURI BANIDA ENOUGH CHARGE,MU HADU A NEXT PAGE,KUMA KARKUGA PAGES BASA TSAYI SOSAI,MU YIN SUMMARY NE TA YADDA MAI KARATU XAIJI SAUKIN KARANTAWA,MUN GODE SOSAI,FOR LOVE U PEOPLE ARE SHOWING.Thank u once again. By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad📚 08033660286 💞💞💞💞 [10/21, 8:47 PM] ‪+234 814 443 8844‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣6⃣ 📚✍ Malam jibrin ya sake fashewa da kuka,ya gurfana agaban mai martaba,yace dan Allah kayafe min,nasan na tafka babban kuskure. Duk mutanen dake fadar kowa xuba tagumi yayi suna jira suji yadda malam jibrin xai warware wannan al'amarin. Malam jibrin yace,ni dan garin gano ne dake karamar hukumar kano,tunda na taso bani da wadata,na shiga kunci mai tsanani,bani da cin yau balle na gobe,lokacin da ya wuce ina daya daga cikin mutanen da suke xuwa gidannan ake bamu sadakar danyen abinci tun lokacin da uwar gidan mai martaba hajiya maryam tana raye. Ina cikin wannan halin ne wani abokina usman ya shawararce ni da na fara harkar fashi wanda shi dama tuntuni ya dade a cikin harkar,shedan yaci galaba akaina na biye masa nafara fashi. Ban jima a cikin harkar fashin ba na kware sosai,duk gidan da xamu ina bada gudun muwa,haka kuma muna yin fashi akan titi. Watarana mun fito fashi,a hanyar kano xuwa yola,dai dai dajin kare kukanka,ranar mun tare motoci da dama,aciki harda wadda uwar gidan ka ke ciki,motar da take ciki tafi duk motocin da muka tare tsada,dan haka muka yashe kudin sauran mutane,ita kuma muka yanke shawarar kwace motar,duk wadanda muka tare suka watse,saura ita da driver'n ta dakuma juna biyu da take dauke dashi. A take oganmu ya dagargaxa kan driver'n ta da bullet,sakamakon haka uwar gidanka ta tsorata har ya kaita ga haihuwa awajen,naji tausayinta kwarai da gaske,tun daga lokacin imanina ya kara yawaita,dana kare mata kallo sai na gane cewar uwar gidan kace,saboda duk lokacin da ake rabon abinci agidannan tana xama awajen hakan ne ya bani damar ganeta. Tana haihuwa Allah yayi mata rasuwa,sai ogan mu ya bada umarni muka jefa ta cikin ciyawa,haka shima driver'n,jaririyar sai kuka take akusa da gawarta. Sai hikima taxomin nace sauran 'yan uwana suyi gaba nixan tafi mana da motar da muka kwace awajensu,gudun kar ayi saurin,gane fashinta mukayi.haka kuwa suka ansa,sukayi gaba da tamu motar cike da dukiyar mutane. Ni kuma nasanya mahaifyar haneefa da driver'n a mota muka karasa wani kauye dake kusa,nayi wa mutanen garin karya cewar 'yan fashine suka taremu suka kashe matata da driver na,kowa sai da ya nuna tausayawar sa agareni,ganin jariya da kuma gawa biyu dana shiga kauyen dasu,suka tambaya meyasa baxan kaisu gida,sai nace musu nayi waya gida ance nasami gari mafi kusa ayi musu sallah,Allah ya gafarta musu,saboda ganin ni kadaine. Haka kuwa Suka taimakamin wajen yi musu wanka muka sallace su sannan muka kaisu makabartar kauyen. Itama kuma haneefa akayi mata wanka,suka taimakamin da kaya aka sa mata.na boye haneefa a gidana wajan matata kuma ban boye mata komai ba,sannan na wuce na kaiwa abokan fashina motar. Washe gari naji sanarwa cewar an rasa uwar gidan ka da driver'n ta,a hanyar xuwa garin su yola dan yin ta'axiyar kanin mahaifin ta wato galadiman yola. Harxan kawo haneefa alokacin,sai naga cewar xa'a sa tsaro akaina har agano yadda akayi na tsince ta,sai na yanke shawarar idan ta jima awajena sai na dawo da ita gareka. Daganan nayi nadama na shiryu na daina fashi,haka kuma nayi alkawarin rike haneefa. Daga baya kuma danaga xata taso cikin kuncin talauci yasa na yanke shawarar dawo da ita gareka ta yadda baxaka fahimta ba,nayi takardar karya akan tsintar ta nayi. Lokaci lokaci ina bin diddigin halin da take ciki agidannan,tanan ne na gane tana samun kyakykyawar kulawa daga gareka. Daga bisani rashin lafiya mai tsanani ta kamani,wadda har yau ban warke ba. Yau ina kwance naji sanarwa haneefa ta gudu,shiyasa na yanke shawarar xuwa na bayyana abinda yake gaskiya ne,amma dan Allah ka gafartamin. By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad 💞💞💞💞 [10/21, 8:47 PM] ‪+234 814 443 8844‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣7⃣ 📚✍ Sarki salahuddeen yasa wani irin kuka da har sai da sautin sa ya fito,hawayene kawai ke kwarara daga idonsa,ya matso gaban malam jibrin a fusace,ya daga hannu ya kwada masa mari,bai tsaya a daya ba saida yayi masa guda biyar kyawawa.sannan yace ka cuceni da baka sanar dani haneefa 'yata bace tun farko. Tun batan da maman haneefa tayi mai martaba bai karayin kuka ba kamar yau ba,saboda kullum kukan xuci yake tare da fitar da hawaye,kuma yana jin kamar hajiya maryam ba rasuwa tayi ba,bata tayi,yau kam sosai sautin kukansa yake fita saboda yasan baxai kara ganin maman haneefa ba. Kowa na wajen saida yayi kwalla banda Amal da momyn ta,ba haka sukaso ba. Ni kuwa nace to ya xasuyi? Abdul da naseer ma kukan suke,da sauri Abdul ya karasa kusa da maimartaba ya rike shi,tare da fadin Abba kayi hakuri,yanxu abin da yakamata muyi shine mu nemi haneefa,kar lokaci ya kure.sarki yana kuka yace I can't resist. Fadawa kuwa basu taba ganin bacin ran mai martaba kamar ranar ba,cewa suke Allah ya huci xuciyar sarki mai adalci contineously....!!! Lami kuwa(matar jibrin) kuka take haka talle suka xube kasa suna bawa sarki hakuri. Sarki ya daka musu tsawa tare da fadin ku bace min daga gabana banason ganinku,sannan ya nuna sallama yace ka bisu har kauyen su kasan inda gidan su yake.ya ansa angama ranka ya dade. Already Abdul da Naseer sun fita duba haneefa cikin gari,duk inda ransu ya raya nan suke bi ko xasu ganta ko kadan inda take banan suka nufa ba,ita tayi gabas su sunyi yamma(hannun riga kenan). Kafin kace meye wannan har labari ya yadu cikin gari,within a very short period of tym.cewar Haneefa 'yar sarkice. Nan da nan 'yan jarida suka cika gidan,suka fara suburbudawa mai martaba tambayoyi,wanda suke bukatar amsa daga malam jibrin,hakan ne yasa aka tashi driver da sallama suka dawo da malam jibrin don ansa tambayoyin da suka kamaceshi. Abin ka da lamarin manya a ranar gabadaya 36 states na Nigeria labari ya yadu,sarkin kano da malam jibrin ake nunawa a kowanne gidan television ga kuma hoton haneefa. Ummiey matar sarkin yola kenan,na ganin wannan sanar wa ta sanar da mai martaba sarkin yola,nan da nan suma members na family'n kowa ya shiga rudani,basu iya jurewa ba,a lokacin kowa ya shirya suka tafi kano cike da alhinin yadda akayi lamarin ya kasance. HANEEFAH...... Tunda tayi pillow da akwatin ta ba abinda take sai kuka,mai gadin gidan ne ya fito yace lafiya kike kuka malama,me kike anan da wannan daren haka?tace dashi bakomai amma dan Allah so nake ka taimakamin na shiga gidannan ko xasu bani wajen kwana kafin gobe,mai gadin ya nisa yace masu gidannan basu cika zama ba,yanxu haka da muke magana basanan,jiya jiyan nan suka tafi abuja,acan uban gidana yake aiki,haneefa tace to dan Allah ko a harabar gidannan ne ka tai makamin na kwana,inyaso gobe da wuri sai in wuce,yace to ba damuwa,haka haneefa ta shiga da kayanta tayi shimfida akasa ta kwanta. Washegari..... Tayiwa mai gadin godiya tare da yi masa sallama,taja trouly'n ta ta tafi gently,shiruuuu unguwar ba mutane sosai,sai kayi awa bakaga mutum ya wulga ba ko da ranane balle yanxu da sassafe.haka taci gaba da tafiya har ta gaji,taja ta tsaya don jiran abin hawa. Haneefa tayi xurfi sosai cikin tunanin inda xata,but she did not find out,eyyyahh..! Kawai sai ji tayi mota ta tsaya a daidai saitin ta,bata ganin fuskar wanda ke cikin motar saboda glass din tinct ne,guy din dake cikin motar ya xuge glass slowly,ya risina kansa kadan ta yadda xai karewa haneefa kallo. Idon sa na sauka akan haneefa,xuciyar sa tayi shaking aransa yace wawwwww,such beauty,yace amm 'yan mata ina xuwa haka da wuri? Haneefa bata amsa masa ba sanin cewar batasan inda xata ba,ya sake cewa,idan baxaki damu ba muje na rage miki hanya mana, Haneefa tace nooo,thank u,yace kiyi hakuri mana idan na tafi baxan ji dadin rejecting kyautatawar danakeso nayi miki ba,please let's go Haneefa ta danyi murmushi kadan da kyanta ya sake bayyana,wanda ba har xuci ba,Adnan ya fito ya karbi akwatin dake hannun haneefa yasa a boot,ya bude mata gidan gaba,ta shiga,ya rufe ta sannan ya koma seat dinshi,ya fara driving slowly. By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad 💞💞💞💞 [10/21, 8:47 PM] ‪+234 814 443 8844‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣8⃣ 📚✍ Adnan ya juya ya kalli haneefa wadda ba karamin birgeshi tayi ba,aransa yace baxan taba bari wannan kyakykyawar yarinyar tayi escaping daga gare ni ba,har sai bukata ta ta biya.ya saki wani shu'umin murmushi,sannan yace amm menene sunan ki? Ta dan basar sannan tace sunana haneefa,Adnan yace,sunan akwai dadi,ni kuma sunana Adnan,amma yanxu dole na koma haneef just because of u haneefa. Ta danyi murmushin yake,sannan ta kawar da kanta,Adnan yace ina xakije haka da wuri? Nan da nan idon haneefa ya ciko da kwalla,tace ni kaina bansan inda xani ba,bani da kowa agarinnan dawowata kenan jiya daga makaran na tarar gidan mu ya kone har iyayena gaba daya,gashi bani da relatives. Adnan yace it's ok please,don't cry,kamar dagaske tausayin haneefa yake,nan kuwa,tsanananin pretending ne,aransa yace yessssss dole ki kasance tare dani. Yace karki damu haneefa,bari xan kaiki gidanmu,wajen mamana,nasan xakiji dadin kasancewa da ita,haneefa taji wani irin dadi,tace to na gode. Adnan yayi horn a kofar wani makeken gida,mai gadin yayi sauri ya bude,cikin gidan Adnan yashiga da motar yayi parking a harabar gidan,ya bude boot ya dakko akwatin haneefa,ita kuwa rike take da hand bag dinta,Adnan ne yayi mata jagora xuwa cikin gidan. Tunda haneefa take bata taba ganin gida mai kyau kamar wannan ba,haka ta wangale ido tana kalle kalle kamar ba a gidan sarki ta taso ba,baxan misalta kyau da kuma tsananin girman gidan ba. Suka haura saman gidan Adnan yacewa haneefa nan ne dakin ki akwai bandaki a ciki,haneefa tace ok,muje na gai da mama,then sai na dawo,Adnan yace nooo relax,xan je nadan yi wanka,kema nasan kina bukatar haka,idan na shirya xanzo na rakaki har part din mama ku gaisa.haneefa tace alright. Kowa acikinsu yayi wanka ya shirya,haneefa ash doguwar riga tasa,mai kwalliyar pink amma bai yawaita ba,tayi kyau sosai,ta xauna a gefen gado tana jira Adnan ya xo don rakata wajen maman shi su gaisa. Sai gashi kuwa yayi knocking,haneefa ta bude ita kanta ya mata kyau,ba karya adnan kyakykyawa ne kam. Ko ni na shaida...😂 ga kuma ji da Naira. Yace muje kici abinci kafin mama ta fito tana toilet,haneefa tace ok,dama wata muguwar yunwa take ji,saboda rabonta da abinci tun jiya da yamma. Haka suka sauka,ta xauna a dining taci abinci tsaf ta kora da ruwa,da lemu sannan ta dau tissue paper ta goge bakin ta. 2hours later..... Shiru shiru,haneefa bata ga maman Adnan ba balle su gaisa,sai tace amm Adnan ko mu karasa ciki mu gaisa da maman? Adnan yace bari na fito freely na fada miki gaskiya,ba kowa acikin gidan nan bayan ni sai masu yimin hidima,nan da nan cikin haneefa ya duri ruwa tayi sensing akwai abinda Adnan yake nufi da kaita wannan gidan,yace dan haka ki shirya xama dani,kuma bawai ina nufin xan aureki bane noooo,xaki xama kamar matata dai kuma duk lokacin da bukatata ta taso xaki biya min,danni aure baya gabana ko kadan. Haneefah tasa kuka tace,please karkamin haka Adnan ni marainiyace bani da kowa na gode da taimakonka,ta nufi saman benen da gudu ta janyo akwatin ta sannan ta nufi kofar fita,shikuwa Adnan tafa hannu ya shiga yi irin na mugayen basawan nan, Haneefa na murda kofar da nufin xata fita taji is locked,ta juyo cikin yanayin tausayi tace pleasee Adnan this is d first tym na sanka arayuwa ta,dan Allah ina rokon ka kayi hakuri kar ka cutar dani. Adnan ya ciji lebensa ta gefe daya,tare da yin murmushin mugun ta,yace relax,u can't leave this house haneefa, because every where is locked,so get ready to stay with me okay?. Cikin fushi,haneefa tace,Never no matter how,no matter what,i can't stay in this house any longer,ta ajiye akwatin ta a gefe daya ta shiga jijjiga kofar da nufin xata balle,Adnan yasa hannu ya riko hannun ta,sannan yace idan xaki shekara kina jijjiga kofarnan baxata taba budewa ba,so ina ganin da kin hakura kawai kinyi abin da nakeso. Haneefa tace leave my hand,har alokacin Adnan bashi da niyyar sakin ta,ta sake fada cikin tsawa "I said leave my hand"!!! Da taga dai bashi da niyyar sakin ta kawai ta ja hannun ta da kyau ta fisge daga cikin na Adnan. EMIRS HOUSE.... 6:00pm..... Naseer da Abdul suka dawo sunsha bakar wahala sosai wajen neman haneefa amma Allah baisa sun sameta ba tun safe.Hankalin mai martaba ya tashi sosai ya kasa tsayar da hawayensa. Haka mutanen yola(Dangin maman haneefa da Abdul) sun karaso,kowa yana cikin damuwa. Amal da hajiya fati kuwa dan bakin ciki sun rasa inda xasu sa kansu. Mukace sai dai su mutu.... IT IS MORE APPRECIATED U GUYS FOR UR PRAYER. THANKS...! By Maryam y.Ahmad Hauwa s.Ahmad 💞💞💞💞 [10/21, 8:47 PM] ‪+234 814 443 8844‬: 🌺'YAR MULKI🌺 2016 6⃣9⃣ 📚✍ Sarki salahuddeen yace wa hajiya fati,kinga irin sakarcin da yarinyar nan Amal tayi ga abinda ya jawo mana,cikin fushi sarkin yake magana. Hajiya fati ta ririta muryarta tace,Allah ya huci xuciyar mai martaba,sannan tace kasan d'a Amal tasan matsayin haneefa baxa ta taba goranta mata ba,ko ba komai ai itama ai 'yar uwartace.cikin sigar munafurci. Sarki ya hadiyi yawu irin na bacin rai yace ke kike goya mata baya kenan? Tayi duk abinda take so,ko ma haneefa ba 'yar uwarta bace ai wannan furicin bai kamata ba,akan koma waye. Amal dake gefe kuwa sai wuri-wuri take da ido irin na rashin gaskiya,saboda tana tsoron mai martaba,dakyar Amal ta iya bude baki dan bawa mai martaba hakuri,tace Abba dan Allah kayi haku-..anan maimartaba ya katseta,cikin tsawa yace dalla rufemin baki mutuniyar banxa! Ko menene bake kika jawo ba?? Amal ta fashe da kuka. Momy'n Amal tace dan Allah kayi hakuri yarinyar nan fa haryanxu akwai sauran kuruciya atare da ita. Sarki ya dagawa momy'n Amal hannu da nufin dakatar wa,yace ya isheni haka,nariga nasan cewa dake da Amal kuka takurawa haneefa acikin gidan nan. Jiya ba abinda ba'a fada min ba akan kuntatawar da kukayi mata,yayi kyau..!!! Momy'n Amal tace kayi hakuri duk akan rashin sanine,ni dai fatana Allah ya bayyana hanneefa,amma a karkashin xuciyar ta ba hakan take so ba. Jin addu'ar da tayi yasa mai martaba ya sakko kadan,ta sake cewa yakamata muje kaci abinci,tun jiya rabonka da abinci,mai martaba yace banajin yunwa,idan ina bukatar hakan xan sanar dake.suna cikin haka Abdul ya shigo cikin falon,mai martaba yayi xumbur ya mike tare da jefawa Abdul tambaya cewar ansameta?? Idon Abdul yayi ja sosai,ya jijjiga kai yace nooo Abba bamu sameta ba,sarki ya saki wata irin doguwar ajiyar xuciya.yace Allah ka bayyana mana haneefa ka kareta daga kowanne irin sharri a duk inda take.Abdul yace Amin ya rabbi. Sannan yace Abba ni abin ne ma yake bani mamaki,sanarwa ake ba kakkautawa amma shiru kake ji ba wani alamar samunta,ko a dan kawo labari ma ace an ganta a wani waje babu,is unfurtunate.Allah yasa haneefa is safe some where else. Sarki yace Amin Allah dai ya bayyanata. GOVERNMENT HOUSE.....🏤 Naseer ne a kwance ya rasa abinda yake masa dadi,banda hawaye ba abinda yake fita daga gefen idonsa masu xafin gaske,yasa hannu ya janyo wayar sa daga gefen bed side drawer,ya fara dialing number'n hanny,amma switched of,yasan cewa number'n akashe take amma ya kasa resisting dole sai yayi dialing sannan yake samun peace of mynd,yanajinta arufe sai ransa ya shiga tafarfasa.juyi kawai yake amma ya kasa jin dadin kwanciyar,yaji wani irin haushi ya kamashi kawai ya kashe wayar gaba daya,dan bayason ganin call din kowa idan ba na haneefa ba. His excellency yace da momy'n Naseer,let's go and pleaseee Naseer nasan yana cikin damuwa sosai dan na fahimci yana son yarinyannan sosai,Her excellency tace ni kaina abin ya dameni ba yadda banyi da Naseer ba yaci abinci amma totally yaki,let's go and c him,suka dunguma dakin. Ganin yanayin da naseer yake ciki yayi matukar basu tausayi,suka xauna kowanne daga gefen naseer sai faman bashi baki suke. Naseer shi kadaine dansu tilo,shiyasa suke bala'in ji dashi,ko kadan basason bacin ransa,haka suka ci gaba da rarrashinsa amma inaaaaaa shidai kawai ganin haneefa shine kwanciyar hankalinsa. ADNAN..... Yace haneefa ina ganin kiyi giving up,ki shirya xama dani,dan ko kin gudu daga gidannan sai na dawo dake na fada miki. Baxan ci gaba da takura miki akan bukatata ba,saboda inason amincewar ki,amma ki xauna kiyi naxari,ni dai baxan taba bari kibar gidan nan ba,ya rage naki,na baki nan da gobe,ina jiran amsarki. Haneefah ta fashe da wani irin kuka na ban tausayi,jiki ba kwari ta tsugunna,tafi awa hudu a bakin kofar nan amma ba alamar Adnan xaiyi releasing dinta,ganin ba sarki sai Allah ta hakura ta koma dakin da Adnan ya nuna mata a matsayin masaukinta ganin magrib ta yi don tayi sallah,ta jingine akwatin ta gefe daya sannan tayi locking dakin da mukulli gudun kar Adnan ya shigo,ta xauna agefen gado tana ta tunanin yadda xa'ayi ta gudu daga gidan. Ta nisa aranta tace kaico,ina tausayawa rayuwar Adnan,gashi kyakykyawa ga arxiki Allah ya bashi,kyau kamar shi yayi kansa? Amma halinsa baiyi ba ko kadan,ya Allah ka kare ni daga sharrin Adnan,ta tashi ta shiga toilet dan yin,Alola,tana shiga tace Alhamdulillah ganin ta fara fashin sallah,wani irin dadi taji,ganin ta sami babban uxiri da xata fakewa Adnan dashi,kafin nan kuma sai ta shirya wasu 'yan dabaru don barin gidan,wanka kawai tayi mai makon alolar ta fito ta shirya tsaff,amma har alokacin hankalin ta bai kwanta ba,sanin cewar lallai Adnan shu'umin kansa ne.zai iyayin komai don ganin burin sa ya cika. Mu kam mukace ai bai fi karfin Allah ba...! LUV U MORE 'YAN SAUYIE....! By Hauwa s.Ahmad Maryam y.Ahmad 💞💞💞💞