CHANJIN RAYUWA book 3 (1)hankalin isma'il yayi mutukar tashi lokacin da aka juyada motar domin gaba daya khalil yadagargaje har kwanyarsa tanzuba juyawa yayi yana salati kmar yadda sauran sukeyi bai iya sake kallon grinba har aka faito da mimi sai da aka zuba su amota sannan mahmud yazoya kama kafadun isma'il yana cewa karka damu isma'il mutafi asibiti sun nufi motar kenan mahmud ya hango wani daga cikin masu kawo daukin ya kunkuci dan akwatin mimi dajakar khalil ya gane akwatin mimi ne sbd a gabansa tafito lkacin dazata tafi dasauri mahmud yanufishi yana cewa kaiba ni kayan nan konakane? yace ammm dama inace za aje gurin yansadane mahmud yace nanne hanyarguri yansandana,a gurin sojoji zaaje ba yan sandaba irinku ne masu yin sada in anyi hadariko? mutumin ya miko akwatin tare da cewa bani kadi bane yanuna wani gawanda yadauki waya chan! mahmud ya kwada masa kira, kai zonan bani wayar hannunka shi ma babu kunya yamiko ta muhmud yace kuji tsoro allah batare da ya jira jin ta bakinsu yajuya ya nufi motar hamisu ya zuba kayan sannan ya shiga yana cewa "muje hamisu!" kuwwar motar yansanda itace ta tsaidasu,suka iso. sannan suka nufi asibitin tare. cikin sauri aka amshi su aka yi emergency dasu, musamman dayake angansu da yan sanda.isma'il yana tsaye cikin matsanancin hali.addu'o'in da isma'il yake yine sukasa jikinsa ya daina bari saidai kallo daya zakayi masa ka san cewa yana cikintashin hankali.daya daga cikin yansandan ya nufosu.ya kalli mahmud waiyaya abin yafarune? mahmud yakalli dan sandan gudu yakeyi sosai,dan sandan yace naji lokacin da mukazo gurin,wani yana cewa,koyasha wani abune?sai wani ne acikin motar yace,irin yaran masu kudin nan ne suke dauko mota suzo sunamugun godu atiti.mahmud yce,yarinyar da suke tare matar wannance, yanuna isma'il.jiya aka daura musu aure shne yazo ya dauketa zasu gudu, shine fawannan hadarin yafaru.dan sandan yakalli isma'il batason kane?isma'il yace,babanta ne yahada nida ita ranka yadade baxan iya saniba.kafin dan sandan yasakecewa wani abu,sai ga likitan da sauri.ya ce,kune yan uwan masu hadarin nanko? dasuri mahmud ya taso,mune likita.likitan yace kun san cewa namijin yarasu ko? duk da cewa dama suna tunanin cewa ya mutu,saida suka dauki kabbara.sannan suka ce,allh yajikansa da gafara.isma'il yakama hannun likitan yana fadin"doctoh itafa?"yace,kar kadamu,munayin iyak kokarinmu.ta samu karaya guda biyu a kafarta,da kuma guda daya a hannu.sannan munaso ne ta farfado don mu sani ko ta samu wata matsala awani guri daga cikin kanta, saboda ta zubar da jini sosai.yaba shi wata takarda,kaje gurin sai da magani,gashi can zasu baka wadannan,yanxun kakawo mana.isma'il yace to,sannan ya kalli mahmud,gashi kudin suna gida.mahmud yace,to muje kadauko mana.daga nan sai mutan gadan su san halinda ake ciki.kafin su wuce saida suka dauko jakar khalil da wayarsa suka ba wa yan sandan.don tasa aka gani ba agata mimi ba. hamisu yajasu,kai tsaye gidan suka Canjin rayuwa bk3 (2) koma,inda isma'il ya aje jakar mimi,sannan ya dauko kudinsa duka na aikinsa da alhaji ya bashi.ya kulle dakin ,sannan yashiga cikin gdan yasanar da su inna abin daya faru.bai tsaya amsa tambayoyin dasu innar sukeyi masa akan wai yaya akayi haka,ko unguwa suka fita?ya fita suka koma asibiti suka sai magungunan.lokacin ne ma dansandan yake fada musu cewa,yakira iyayan khalil.sunyi amfani da wayar khalil din ne. yakuma sanar dasu cewa,dansu yayi hatsari, kuma ya rasu.suzo su dauki gawarsa.isma'il ya girgiza kai don jinjina yadda mahaifan khalil zasuji wannan lamari.alhaji yakira hamisu don yaji ko ya kosa kaduna.zai sa shiya amsar masa sako gurin wani abokinsa na maganin diabetes ne na hausa da abokin nasa yace xaiba shi,don shima yaji dadinsa. hamisu yace,matsala aka samu alhaji,ko katsina ban baroba har yanxun.alhaji ya ce,meya faru kuma?hamisu ya sanar da shi komai. ran alhaji ya bace mutuka dajin cewa mimi tasake yankurin guduwa.cikin bacin rai yace ma hamisu,"kataho kawai!"yace,alhaji yarinyar nan tana (3)cikin mawuyacin hali sosai,don duk akakkarye taka.alhaji yace,hamisu kabarsu kawar.babu abin da zan iya yi mata,kaima bbu abin daxaka iyayi mata,don haka kayi abin da nace kawai.yace,shikenan,alhaji zan taho yanxun."yace,"to,kana kusa dashi malam isma'il din ne?yace, "eh ina kusa dashi.yace,toka bashi!"ya mikama isma'il wayar.sun gaisa,alhji yace,"ashe abinda yafaru kenan?"isma'il yace kwarai kuwa alhji.yace allh yakyauta."cikin tashin hankali isma'il y2e,alhji kayi mata duk abinda takeso,zata iya rasa ranta,domin shi khalil din ya rasuma."duk da alhajin ya jinjina batun mutuwar khalil a ransa,amma afili sai yace,"karka damu malam isma'il,tunda yanxun ta karye ai bazata sake yankurin guduwa ba.ka ba hamisu wayar."isma'il yace alhji kuzo ku taimaka mata."alhji yace,isma'il inayi maka jajen abin da yafaru da iyalinka,amma kayi hakuri ba zan iya taimaka mata ba.kaba hamisu wayar!"cikin rawar hannu,isma'il ya mika ma hamisu wayar. Canjin rayuwa 5⃣A sanyaye ya koma ya jingina da bango. Sai lokacinne ma ya tuna ya kamata ya sanar da hajiya sauda. Ya kalli mahmud, "ya kamata in sanar da mahaifiyar yarinyarnan ko? " Mahmud yace, "tabbas ya kamata ka sanar da ita" kan benci ya zauna, sannan ya soma kiran layinta. Bata jima ba ta daga. A sanyaye ya gaishe ta. Ita kam yanayin muryarsa tasa ta faduwar gaba. Tace, Ismail ta sake guduwa ne? Yace Eh hajiya, amma sunyi hatsari akan hanyar su ta guduwa. Yanxu haka muna asibiti. Tace, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Da sauqi dai ko? Yayi ajiyar zuciya, to da sauqin dai za'ace amma shi ya rasu... Ya rasu?? Ta katse shi. Yace tabbas, ita dai sunce suna jira ta farfado. In har ta farka a cikin hayyacinta, to suna ganin karayar data samu ce guda biyu a kafarta daya kuma a hannunta sune kawai matsalar, cikin kuka hajiya tace, wane asibitin kuke? Yace babbab asibiti, tace shikenan bari in Kira alhaji zanzo ynxu,. Kafin ya amsa da cewa Alhaji ya kirashi, har ta kashe wayar. Hajiya ta soma kuka. Su hasana suka fito da sauri suna tambayar ta lafiya? Tace musu mimi ce sukayi hadari. Nan suma suka shiga damuwa. Tace bari in kira Alhaji Muje mu ganta. Ta shiga kiran layin Alhajin, tana soma ringing ya daga, Tace cikin kuka Alhaji kaji abinda ya faru? Yace naji. Ko ba hadarin su mimi ba? Tace ashe ka sani. To dama zamu tafi da yara ne. Ga mamakin ta sai taji yace, ban amince ba, yaci gaba da cewa, ki Fadama duk sauran 'ya'yanki banyi wa kowa izinin zuwa duba ta ba, matsawar na isa. Mamaki ya cika hajiya sauda, tace sbd me Alhaji? Yace cikin fushi, ban isa ince ga abinda nakeso ba saina fadi dalilina kenan ko? Tace kayi haquri. Yace to na saka Allah ya isa! Daga kanki har sauran da suke qarqashi na matsawar kuka taka gurinta! Ya kashe wayarsa. [8/14, 15:02] A~PROF: 6⃣shi kansa Alhajin cikin damuwa yake, amma ya tsara ma kansa cewa, dole ya haqura don wani dalili nasa, sannan yasan cewa, abin Ya ta6a zuciyar hajiya sauda, sbd hk ya yanke Shawarar sake kiranta. Ta daga, har lokacin kuka take, a nata ganin bai dace abar mimi cikin wannan halin ba. Yace amma hajiya don Allah kiyi haquri, akwai dalilin da yasa dole sai nayi hakan. Zan yi miki bayani daga baya. Sannan ina mai jaddada miki ban haquri na, ki taimaka kuyimin wannan. Nasan zaki iya saka 'ya'yanki su dangana da zuwa gurin mimi. Kuma daga baya zaki daina jin zafi na in kinji dalilina. Kin fahimceni ? Tayi ajiyar zuciya, shikenan zanyi duk yadda kk so. Shima ya sauke tasa ajiyar zuciyar. Na gode, Allah yayi miki albarka, ya saka miki da aljannah. Sai nazo. Tace to Allah ya kawo ka lfy. Ta kalli su usaina tace, inaso kubar maganar nan anan, ko su yayanku abba, bana son su sani. Hasana tace sbd me hajiya? Tace sbd hk dadynku ya buqata. Kuma banison ku damu da cewa sai kun san dalili. Zamu dinga jinya lafiyarta daga bakin mijinta. Suka kalli juna da ido, suka mamakin zancen mahaifiyar su, sannan suka miqe suka shiga dakinsu. Ita kuma sai ta daga waya ta kira layin Ismail. Cikin sauri tare da yin sallama, ya amsa a sanyaye, yace kun iso ne? Tace a'a ba zan samu zuwa ba, in dai ta tashi kace ina gaisheta. [8/14, 15:24] A~PROF: 7⃣Yace hajiya kema baki samun damar zuwa kenan? Ta soma shesshekar kuka, mahaifinta yayi mana iyaka da zuwa gurin ta, cikin sauri yace sbd me? Don Allah ku yafe mata, sbd tana cikin wani hali, wanda ba dole bane ta tashi. Hajiya tace na yafe ma ta duk abinda tayi min, wanda na sani da wanda ban sani ba. Kuma nima bansan dalilin sa nayin hkn ba, amma idn ya fadamun zan sanar dakai. Sannan kuma malam Ismail zan sake baka amanar mimi, ka qadd ara batada kowa, sai kai kadai mijinta. Lokaci zuwa lokaci zan dinga jin yadda jiki nta yake, amma ta waya daga bakinka. Ismail yace shikenan nayi miki alkawarin zanyi iyakar iyawata, sai Anjima. Ya kalli Mahmud, bayan ya kashe wayar, wannan wace irin qaddara ce ta hau kaina? Alhaji ya hana su zuwa ma. Mahmoud yace wanna n abin da Mamaki, amma tunda kai iyalinka ce, nauyinta ya rataya ne a wuyan ka. Kai ya cancanta kaci gaba da kula da lfyr ta har zuwa lokaci n da zasu huce. Nawa zaton sunji zafin guduwar data sake yi ne. Amma in sun huce zasu zo. Ismail yace Allah ya sani, tunani na dama banida qarfin dazan iya kula da lafiyarta. Mahmud yace, kar ka damu Allah zai duba maka. A sanyaye Ismail yace Allah ya duba mana, suka hada baki gurin cewa Ameen! Saida lokacin sallah yayi sannan suka miqe suka nufi masallaci. Daga masallaci ne Mahmud ya nufi gd don sanar wa malam Aminu. Ismail yace kabi ta gdn yaya Amina ka fada mata don bata sani ba, Mahmud yace zanbi insha Allahu. Canjin rayuwa 8⃣kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai, tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani da Addu'a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya shige mana gaba. Yace Ameen. Bayan la'asar su malam suka zo tare da wasu malamai suka yi masa jaje, tare da addu'ar cewa, Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci. Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a'a yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda hakan, yace a'a ki riqesu a hannunki, sbd kema kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku abincin da wuri. Yace a'a kai ki yo abincinnan yau tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso suka shiga s Canjin rayuwa 8⃣kusan qarfe uku yaya Amina tazo tana kuka don tausaya ma dan tilon qanin nata. Yace kar ki damu yaya Amina, insha Allahu zata samu sauqi. Tace wai yaya abin ya faru ne? Nan ya sanar mata da komai, tace Allah mai iko, yanzun kaine zakayi jinyar ta, ko yaya zakayi kenan alhalin bata qaunarka? Yace yaya ai dole in kula da ita tunda nine mijinta. Kidai tayani da Addu'a. Allah ya bani yadda zanyi. Tace to Allah ya shige mana gaba. Yace Ameen. Bayan la'asar su malam suka zo tare da wasu malamai suka yi masa jaje, tare da addu'ar cewa, Allah ya bata lfy, sannan suka tafi. Itama yaya Amina sai alokacin ne tace bari ta tafi gd sbd batun abinci. Ta ciro kudi daga aljihun Jakarta naira dubu uku da dari takwas, tace gashi kadan kara. Ya kalle ta a'a yaya ki barsu, inada kudi. Sannan kinsan akwai batun abinci, kece zaki dinga kawo mana. Tace dukda hakan, yace a'a ki riqesu a hannunki, sbd kema kinada rauni. Tace to bari inje gida sbd inyo muku abincin da wuri. Yace a'a kai ki yo abincinnan yau tukunna, ki vari sai gobe, don bazan iya ci ba, bari dai muga yadda jikin zaiyi, tace shikenan baka buqatar komai? don bayan magriba zamu dawo da abbansu saddam.yace sai dai dardumar sallah, sbd basu riga sun bamu daki ba tukunna. Tace hk ne shikenan sai zuwa Anjima din. Bayan fitar yaya Amina, ya sake miqewa ya nufi qofar dakin da mimi take kwance yana hangenta, zuciyar sa cike da tausayinta, kamar da wasa, idanun sa suka nuna masa tana motsi, da sauri ya nufi gurin nurse da suke zaune, yace ina likita? Tana motsi. Nan take suka tafi kitan likitan. Da gudu-gudu likitan ya iso suka shiga s Canjin rayuwa 9⃣sun kai kusan minti goma, sannan wata nurse ta leqo, ta kalli Ismail, tace masa wanene khalil? Yace mata shine wanda sukai hadari tare ya mutu. Ta juya da sauri, Ismail dai yanata kai komo. Ya kai kusan rabi sa'a sannan likitan ya fito, ya kalli Ismail yace masa, zo muje! Ya bishi zuwa offishinsa, inda suka zauna, ya kalli Ismail, kai wanene dinta? Ismail yadan yi jim kadan don yana jinjina kalmar, duk lokacin da zai furta ta. Tsakanin jiya zuwa yau, ya lumshe ido, "ni mijinta ne" likitan yace ok to zamu kaita dakin jinya, domin ynxun ta farka, amma yanxu munyi mata allurar varci sakamakon tana ta kiran sunan marigayin. Ya ajiye biron daya dauka, sannan ya kalli Ismail yace, wazai zauna da ita? Ismail yace nine, likitan ya girgiza kai, babu dama ka zauna da ita, sbd kai namiji ne, kuma dakin akwai matan mutane, sai dai in zaka biya daki na musamm an, sannan za'a buqaci kudi sbd likitan da zai mata dorin zaizo ne da ga kano, kuma gashi dorin har guri uku ne, Ismail yace to likita kamar nawa ake nema? Yace kasan shi likita ne mai zaman kansa, dauko shi akeyi, qila yakai gurin dubu sittin, banda magani. Ismail yace insha Allahu za'a san yadda za'ayi, Amma likita bata samu matsalar da ake tunanin ta samu ba ko? Ya girgiza kai, bana zaton ta samu wata matsala, Ismail yace Allah yasa dai, zan biya kudin daki na musamman din. Likitan yayi masa kwatancen inda zai biy a kudin dakin. Har ya miqe sai likitan ya sake kallon sa, ba tada iyaye ne a garinnan? Eh, kawai yace, to ko cikin dangin ka ba wanda zai iya zama da ita? Cikin qosawa yace nima yayata ce guda daya, kuma tana da qananan yara. Baya son doguwar magana, shiyasa ya amsa a qagare, shikenan ka iya tfy, inji likitan, an kaita daki na musamman akan kudi naira dubu ashirin a sati biyu. Dakin akwai TV da dan fridge, sai na'urar sanyaya daki. Ismail yana tsaye yana kallon mimi, an manna mata bandeji a gurin da taji ciwo. Addu'o'i kawai yake yi mata, har lokacin da yaje yayi sallar magrib a bata farka ba. Canjin rayuwa 1�0⃣Yana shigowa yaci karo dasu yaya Amina, suna neman dakin da aka kaisu. Ya amshi kular hannunta sannan suka nufi dakin, suka gaisa da abbab saddam, yayi masa jaje. Basu jima ba suka ce zasu wuce. Yabi su don yadan taka musu, anan ne take tambayarsa ko 'yan gdansu sunzo? Yace kinsan dai koda zuwan ne, sai dai in mazan, amma matan ban sa rai ba, mazan ma daqyar in sunji, tunda lokacin da naje gdn basa nan, tace to ba komai Allah ya bata lfy, yace Ameen, tace tuwo ne fa akular da muka zo da ita, naga kana son tuwo, yace nifa yau ko karyawa banyi ba, dama zan samu ruwan zafi, tace vari to inje in dafa maka, sai abban su saddam ya kawo maka, tunda ga mashi n ahannunsa. Ismail yace to na gode. Suna fita, wayar Ismail ta soma ringing, ya daga ashe Mahmud ne ya kawo innarsu zata duba ta, suna cikin gaisawa da innar sai ga kiran hajiya sauda. Bayan sun gaisa take tambayarsa jikin mimi, yace da sauqi, amma tana varci, bata farka ba, tace to zata kira zuwa gobe, sannan ya turo mata account number dinsa, yace to insha Allahu, sannan yayi mata godiya. Kusan qarfe goman dare, mimi ta farka, lokacin Ismail yana zaune kan sallaya, ya idar da sallar shafa'i da wutiri. Sai yaji tana cewa, "daddy na, daddy na!" cikin wani irin sauti mai ban tausayi. Da sauri ya miqe ya nufi gadon da take, ya kama hannunta yana "khadija, sannu kinji. Kin tashi ne? Bari in kira likita" ya miqe ya nufi qasa da sauri domin kiran likita. Canjin rayuwa 1�1⃣Daidai da Na'ima ta shiga dakin Abbas, yana akan kujera yana shan 'ya'yan itatuwa. Tun daga qasa ya soma kallon Na'ima har sama, sannan ya dauke kansa gefe. Cikin jin kai yace lafiya? Duk da faduwar da gabanta keyi bata fasa yin abinda tayi niyya ba, kai tsaye kujerar da yake ta nufa ta zauna a hannun kujerar. Tasa hannunta akan kafadarsa, tare da fadin, "sweety ashe ka dawo, ka shigo lfy? Tsawa ya daka mata. Duk da ta firgita, amma bata tashi ba. Yace ke ni abokin wasan ki ne, ko na ta6a wasa dake? Kwanciya tayi akan cinyarsa, "baka wasa dani, amma yau zamu fara" ga mamakinta sai kawai taga ya hankadeta, ta fadi kan kafet. Ta dago rai 6ace, duk da aunties dinta suna fada mata cewa kar tayi zuciya da duk abinda zai fada mata, ta kalleshi, "A zato na masoyi ya dara maqiyi, menene laifi na don na soka? " Cikin daga murya yace "shine kuwa babban laifinki a guri na. Bana ra'ayinki, amma keda mahaifinki kun liqemin, sai da akayi wannan auren" Ta soma kuka, ni fa taimako nayi sbd kar aji kunya, yace aikuwa zakiyi da kin sanin wannan taimakon. Inaso kisan wani abu, ni mutum ne wanda in naga abu inaso, to so ne na gske, kuma ba zanyi wasa da son ba. Haka nan kuma qi, don bana yin qi da wasa, mimi na gani nace inaso, tunda tace bata yi ai sai abarni inji da ciwon rashin ta, ba wai akwaso min ke ba, baqi qirin! Ni farar mace itace ra'ayina, kin gane? Canjin rayuwa 1�2⃣Na'ima ta soma kuka wiwi, tana cewa, toni ynxun ka fatamin matsayi na, ya miqe tare da nufar dakin varcin sa. Gashi na fada miki kuwa, banda wannan matsayin wanne kk son ji? Don Allah tashi ki fita a daki na, Na'ima ta miqe jiki babu qwari, ta nufi dakinta cikin kunya da kuka, ta kira momy nafisa a waya, momy tace lfy da wannan daren? Na'ima cikin kuka tace "momy Abbas baya so na, ya fadamun " momy tace sakarya! Baki dai iya kissa ba kawai zaki ce. Har akawai namijin d zai raina mace? Bare ke da kyanki da komai, amma dai ki vari zamuyi magana dake zuwa da safe, na fada miki jikin dadynku ne ya motsa, gashi ma anyi masa waya mimi tayi hadari. Duk da ya nuna abin bai dameshi ba, amma jikin nasa ya qara rikicewa, ynxun dai ya samu varci, bayan likita ya gama dubashi. Na'ima cikin sauri tace "sis mimi din ce tayi hadari momy? " tace eh itace, sake guduwa wai tayi, ita d wanda takeso din, sunyi mummunan hatsari, shi wanda take so din ya mutu. Na'ima tace innalillahi wa inna ilaihi raji'un! To ynxun tana ina? Amma da sauqi ko? Momy tace, dalla can, duk kin wani rude, ni ina zan sani? Dadyn ku ya hana zuwa. Hamisu direban yara yace, tana jin jiki. Na'ima tace Allah sarki sis mimi! To shi daddy ya haqura mana, momy tace karma ya haqura, su qarata can, kedai ki samu kija ra'ayin mijinki, yadda zaki samu hanklin mahifinku ya dawo kanki. Ni araina ma cewa nayi dama itace ta mutu, Na'ima tace a'a momy kar ta mutu, tunda dai mun samu ta barmin abbas din ba shikenan ba. Ki tayani in shawo kansa, baki ga irin wulaqancin da yayi min ba, tace shikenan zanzo da safe. Na'ima tace Yauwa gara ma kizo kiyi masa magana, tace to shikenan sai nazo din, sukayi saida safe. Canjin rayuwa 1�3⃣Zainabu tana kwance akan gadonta, sai juyi takeyi, cikinta banda hautsinawa babu abinda yake yi, amai kawai take ji, amma ta kasa yi, ga zazza6i data kwana dashi. Da qyar tayi sallah. Budo qofarta da akayi ne yasa ta tashi a firgice, tasan Alhaji ne, kullum sai ya shigo dakinta daidai wannan lokacin, yayi buqatarsa da ita, kuma babu ruwansa ko da dakin wa yake cikinsu, ya cire rigarsa ya rataye, tace don Allah kayi haquri yau banida lfy, yace ruwa na da ciwonki? Nima yau sauri nake yi, ba ddewa zanyi ba. Ya fado kan gadon. Ji tayi aman da takeson yi tun jiya ya taho. Nan kuwa tayi ta sheqo masa shi a jiki har kan gadon, ji tayi turarensa dada hankado mata aman, da sauri ya tashi ya wanka mata wani wawan mari. Yana ta surfa mata ashariya. Ita dai amai take ta wankawa, har saida ta amayar da duk abinda taci, sannan ta kwanta tana maida numfashi. Shi kam da zage-zage ya fita har xuwa dakinsa, ya wanke ya fito ya nufi gurin wacce zainabu take bi mata don kai buqatarsa can tace, sai yau kasan dani? Tunda kayi amarya ka daina shigowa da safe, yace ai tsiyarki kenan mita. Ita wancan har mace ce da har zaki damu kanki? Yarinyar da kullum saina dake ta ko na zage ta sannan zan samu buqatata. Wai ahakan ne ta kama amaye amaye, in dai ciki ne zanci mutuncinta, sbd ban mori kudina ba. To bata sonka kai kuma ka nace, in bata sona ai tanason kudina ko? Ba sai a faranta min na kudina ba, sisina bazai yi ciwo ba.in ba zata zauna ta faranta min rai ba, to zasu bani 'yan kudina. Uwar ta ga roqon tsiya, ko jiya saida ta aiko wai in bata dubu goma. Kuma kabata? Ta katseshi. Yace dan iska ne ni, dari biyar na bada aka kai mata. Wane farin ciki nake samu gurin 'yarta da har zan dinga bata kudi? Tace inace ka bata ne,nima ince akai wa uwata. [8/17, 11:04 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�4⃣Yace ke har kinyi magana? Ko wata uku ba'ayi ba, tsohonki ya dage saida na sai masa mashin, tace eh amma kayimin gori yafi sau dari akan mashin dinnan, kai matsalar ka kenan gori duk wanda kaba abinka to ya tabbata zaisha gori, yace eh amma su kuma iyayen naku rokonsu yayi yawa. Ni muje kinji, sauri nake zan fita. Alhaji lawal kenan, sam bai damu dayin al'amuransa bisa tsarin addinnin musulunci ba bare bin doka. Rayuwar gdansa yana tafiyar da ita bisa son zuciya, shi ganinsa, kudi za suyi masa maganin komai, bai qara bi takan zainabu ba ya fito. Shirun da uwar gd maman bushira taji, yasa ta leqa dakin tana cewa, amai kkyi haka? Kai ta daga, alamun eh, maman bushira tace anxo gurin kenan. Ta kama ta, tashi in taimaka miki, ban daki takai ta tace ta wanke jikinta. Ita kuma ta koma tana kwashe kayan gadon, saida ta gyara ta, sannan tasa aka kawo mata abin kari. Da qyar ma tadan kur6i ruwan kunu. Ta kalli uwar gdn, maman bushira me yasa kk ce anzo gurin? Uwar gd tace alamu sun nuna cewa kinada ciki ko? Zainabu ta zaro ido, nima ban sani ba. Uwar gd tace gsky ina zaton ciki gareki. Yaushe rabonki da al'ada? Zainabu ta sunkuyar da kai, fashin sallah kuma? Eh, inji maman bushira. Tun ana saura kwana biyar bikina. Maman bushira tace tabbas ciki ne dake, abinda yasa nace haka, sbd Alhaji baya son haihuwa. Zaki fuskanci wulaqanci sosai. Canjin rayuwa [8/17, 11:10 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�5⃣Zainabu tace, banda wannan wulaqancin, har akwai wani kala da zai min? Maman bushira tace sosai ma kuwa! Amma Shawarar dazan baki, in ya tambayeki cewa kina da ciki ne? Kice masa a'a shawara ke damunki, Zainabu tace sbd me to? Tacesbd zai baki maganin zubar da ciki. Zainabu tace zaifi murna, in har cikin ya zube, maman bushira tace ai ba wannan ne matsalar ba. Matsalar zaije ya kawo miki magani, kuma ba wai zai kaiki asibiti bane. Akwai wata yarinya daya ta6a aure, haka akayi qarshe Yarinyar rasuwa tayi, sbd jini ne ya 6alle mata. Tace to in na 6oye masa, kuma yasa aka kaini asibiti aka gano cewa inada ciki fa? Maman bushira tace bazai gane ba. Don ba zai kaiki asibiti ba, don kuwa baya daga cikin mazajen da suka damu da lafiyar iyalinsu, don ko panadol sai dai ki saya. Zainabu ta soma kuka tana fadin dole zai sani, tunda cikin zaiyi girma, maman bushira tace kafin cikin naki yayi girma, da ace zaki iya sakin jiki dashi kema ki sauko, ki tarairaye shi, to da kin yagi na xuwa asibiti, dana kayan jariri. Zainabu tace, nayi ta qoqarin in kwatanta tun kwanaki da kk fadamun, amma na kasa sakin jiki dashi, don inada wanda nake so, kuma yake sona. Tace shikenan zako kiyi zaman wulaqanci, duk ranar daya gano akwai wannan cikin, sabulun wanka sai kin rasa. Zainabu tace zan kwatanta in gani ko zan iya. Maman bushira tace da dai yafi miki. Ranar Zainabu wuni tayi sheqa amai da kuka. Ta galabaita sosai, da magriba ya shigo ya ganta kwance. Ya dube ta a wulaqance, ke kuma kukan me kkyi? Tace shawara ce, dama ko a gd inayi, yace oho' to kina shan wani magani ne in ya tashi? Tace eh, amma banida kudi ban sayi na asibiti ba, sannan ina kuma shan na hausa. Yace to ina kumazaki samu kudin na siyen maganin, tunda ni dazan baki kin mai dani kamar wani dodo? [8/17, 11:10 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�6⃣Ta kalleshi, ai na bari, yace da gske? Ta sunkuyar da kai, sannan tace eh. Yace kinyi alqawari? Ta daga kai, alamun eh. Cikin yace to shikenan vari inzo in nemo miki magani. Ko ke fa? Ynxun zaki san kinyi aure. Amma zan vari yau ki huta tunda baki jin dadi, amma gobe da safe zanzo ko? Tace eh, yana fita ta nufi ban daki ta dinga kakarin amai, don gsky shi kansa wari kawai yake yi mata. Washe gari yana shigowa, haka tayi qoqarin yi masa duk abinda yake so, tare da maida masa martanin duk abinda yayi mata. Tasha wahala matuqa, amma haka ta jure ta nuna masa tana tare dashi, yaji dadi matuq a. Dazai fita ya kawo dubu biyar ya bata. Ya ce ki jirani da daddare, gabanta ya fadi, tace a ranta na shiga uku, a fili tace ai yau ba'a dakina kk ba, yace ina ruwana da wani inda nake, karki damu, abinda kawai na sani dukkanku matana ne, kuma zan shiga gurin duk wacce raina ya biyamin ko kina da ja? Cikin sauri tace, A'a haka ya fita ya barta tana mamaki, tare da tambayar kanta wai daman haka auren yake, ayi ta abu sai kace cin tuwo, kuma ba gajiya? Ita kam ta gaji wlh. Ta dinga juya kudin a hannunta, sannan ta bude akwati nta ta saka, tana yin wanka, sai kuma zazza6i ya rufe ta, ta qudundu ne akan gado cikin bargo. Bata san tsawon lokacin data dauka ba akan gadon nata. Can kamar daga sama sai taji muryar su innarta suna salalla ma. Da sauri ta tashi suka shigo, itace da aminiyarta inna yelwa. Suka iso bakin gadon suka zauna. Inna tace lafiya na ganki cikin bargo haka? Zainabu tace banida lfy ne inna, tace me kuma ke damunki? Ta sunkuyar dakai, tace wai uwar gdnsa ce tace ciki ne dani, shi kuma gashi baya son haihuwa, inna tace to ynxun daya ji kina da cikin me yace? Canjin rayuwa 1�7⃣Zainabu tace, bai sani ba. Uwar gdn tace, kar in fada masa, shine nace m asa shawara ce ke damuna kawai, kuma tun ina gd take damuna, shine ya siyo min magani. Inna yalwa ta ce, anya kuwa gsky wannan matar ta fada miki? Ance kar ki sake ki saurari maganar kishiya. Har wata soyayya ce zaki samu a gurin kishiya? Zainabu tace Allah kam tana sona da gske. Don tana fadamin gsky, kuma in tabani shawara in nabi ina ganin daidanta. Jiya ma saida ta matsa kan cewa in na saki jiki dashi zan samu kudi, wai anan ne zan samu nayi siyayyar kayan Jariri. Shine nadan daure na saki jiki dashi, shine ma har ya bani dubu biyar. Kuma dama ko yaushe tana fadamin cewa inyi hakan, don dai naqi yi ne. Inna tace kedai akwai sakarya, dama qin sakin jiki kkyi dashi don ubanki? Shiyasa ni kaina ya rage bani abinda yake bani, don jiya na aiko ya bani dubu goma, amma sai ga dari biyar, yadda kk san in yaga ta don haushi, amma na fasa, to tashi ki dauko min dubu biyar din, Zainabu ta turo baki, to zan tara ne fa inna, don fa an fadamun har in ya gano cikinnan, bazai bani komai ba, kuma kayan Jariri ma fa nice zan nema. Inna yalwa tace, jaririn banza, ke kk ta Jariri, waya ce miki za'a barshi? Yanxun nan zamu je a hado maganin da zaibi makwarara, ko yaya kk gani Aminiyata? Ta kai qarshen zancen da kallon innar Zainabu. Inna tace tace, yadda kk ce dinnan haka za'ayi. Zainabu ta soma kuka, don Allah inna kar ku bani maganin zabar da ciki, ance fa wata matarsa ta rasu sakamakon shan maganin zubar da ciki. Inna yalwa tace to shikenan don ta mutu sai aka fada miki cewa kema .mutuwar zakiyi ko? Inna taja tsaki, bar sakarya! Duk abinki cikinnan baza'a barshi ba. [8/17, 11:06 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 1�8⃣Inna yalwa tace, saurara kiji Zainabu. In an zabar da cikin, sai kinfi jin dadin kar6ar kudin a gurinsa. Duk lokacin daya zo gurinki, ki tarairaye shi. Zainabu tace shifa ko wane lokaci, sai yace zai shigo dakina, koda ba anan yake ba, inna yalwa tace saurare ni dakyau, in kullum zaizo gurinki, karki sake kice masa NO, inji ku 'yan boko, kuma kar ki nuna kin gajiya. Sannan zamuje a hado miki kayan da'a a gurin 'yar jibiya sbd aqara samun kansa. Kinga ya qara sakin miki baki n aljihu. Inna tace shikenan sai a shigar mata zubin adashi, ai kya san abinda kk tara ko? Ta kalli inna yalwa. Tace qwarai kuwa. Inna tace to yaya batun zuwa gdn malaminnan yalwa? Inna yalwa tace, abar batun zuwa gidan malamin nan, tunda shi ga inda yasa gaba, sai mubishi tana gurin. Tayi ta dirkar maganin da'a masu qarfi. Inna tace shikenan hakan yayi, inna ta miqe, ynxun dai tashi muje yalwa, zamu dawo zuwa Anjima. Zainabu ranta 6ace tace anjima kuma? Nidai zaku fa sa ace iyaye na suna ta sintiri a gidannan, ayi min gori. suka ce a daura miki goruba! Anjiman nan zamu zo. Ai da zafi-zafi akan bugi qarfe. Don haushi ko sallama bata yi musu ba, ta sake qudundunewa akan gado tana ta kuka. Canjin rayuwa 1�9⃣Ismail kusan kusan tare suka shigo da likitan, har lokacin daddyn ta take kira cikin sarqarqiyar murya wadda take a galabaice. Likitan ya isa gaban gadon ya dafa goshinta, sannu khadija ? Bude idanun ki in gani. Ta soma yunqurin budewa, dishi-dishi take gani. Yace kin sanni? Ta sake lumshe idanu. Ya waiwaya ya kalli Ismai l sannan ya yafito shi da hannu, Ismail ya matso. Likitan yace yi mata magana. Ismail yace bude idanunki ki ganni. Yakai hannu ya dafa goshinta. A wahalce ta bude idon ta numfashin ta sama sama, tace malam ina khalil di na? Yace yana nan yana varci acan dakin maza. Bai mutu ba? Yana samun sauqi, sannu kinji. Ta daga idanunta a wahalce, ta kalleshi, malam ka kaini gurin daddy na zan mutu ne kaji? Zan mutu. Hankalin Ismail yayi mugun tashi. Ya kama hannun likitan. Don Allah ka bata magani. Wlh Yarinyar nan amana ce a gurina likita. Likitan ya kama hannun Ismail zuwa bakin qofa, yace karka damu, tambaya daya zan maka, Ismail yace to. Sunan data ambata wanene? Ismail yace daddy mahaifinta ne, shi kuma khalil .shine wanda yasu, ina nufin wanda sukayi hadari tare. Likitan yace Alhmdlh. Ynxun ina ganin matsalarmu wannan karayar ce. Sai dai kafin zamu qara mata jini, don ta zubar da jini sosai, daga nan sai mu dora ta. Ismail yace babu matsalar jini, a gwada nawa, in zan iya bata, sai asa mata. Likita yace babu matsala, da safe zamu gwada jinin naka. In zaiyi sai mu ta ce asa mata. Sannan maganar dori, nayi maka batun mai dori, ban nemi shawararka ba, ko kuna son na gd, Ismail yace to ni dai likita, wanne kaga yafi? Domin wannan Yarinyar amana ce a gurina. [8/18, 6:18 AM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�0⃣Likitan ya dafa kafadarsa, kar ka samu damuwa. Mu dai a gurin mu wannan likitan, kamar yadda na fada maka zaizo ne daga kano, kuma yana yin dori sosai anan asibitin, kuma bamu ta6a ganin wata matsala ba. Amma kayi shawara da 'yan uwanka. Yace to shikenan zuwa da safe duk yadda muka yi zaka ji. Likitan yace, babu komai. Ni zan tafi dama na jira ne sbd inga farkawarta. Ismail yace, to yanxu ba zan iya bata wani abu ba ko da tea ne? Likitan yace kai ka damu, zaka dai iya bata ruwa ne in ta buqata. Nurse zasu zo su saka mata ruwa tare da yi mata allurai, domin ta samu varci da kuma sauqin radadin. Ismail yace, nagode likita, saida safe. Ya girgiza kafadar Ismail, kar ka damu. Insha Allahu zata samu sauqi, 'yar amanarka. Akwai likitan dare ma, wanda ina zaton ma yazo. Inda wata matsala sai ka fadawa nurses, zasuje su kira likitan. Ismail yace nagode sosai likita. Bayan fitar likitan ne Ismael ya sake dawowa ya tsaya akan mimi. Yana matu qar tausaya mata. Ji yake kamar ya kar6ar mata ciwon. Nunfashin ta dai-dai yake fita. Yasoma karanta addu'oi don nema mat a sauqi daga mahaliccinta. Bada jimawa ba Nurses guda biyu suka shigo suka sa mata ruwa tare da yi mata allurai. Suka ce, ka lura ko da cikin dare, kar ka bari ya goce. Yace musu, to suna fita ya zauna yana riqe da tattausan hannunta, wanda shine mai lafiyar, yana ta kallon fuskarta tare da tuno yadda abubuwan suke ta faruwa tamkar cikin mafarki. Alamun tayi varci yasa shi ajiye mata hannun a gurin da ba zata gotar ba. Sannan ya tashi ya koma kan dayan gadon ya kwanta yana fuskantar ta, har ynxun yana ci gaba da kallon abubuwan kamar almara ko kuma mafarki. Ina mabya farka ya ganshi a dakinsa na zauren su, ace ma shi baisan wata mimi ba. Amma da ya dan ciji yatsansa, sai ya tabbatar cewa ba mafarki yake yi ba, domin yaji zafi. Amma ya tattara komai ya barma Allah, da haka varci 6arawo yake ta fisgarsa sama-sama. Canjin rayuwa 2�1⃣Cikin dare ne yaji shigowar nurses din, sunzo ne su sake duba ta, yayi musu sannunsu da aiki, suka amsa suka tambaye shi ko kwai wata matsala? Yace musu babu komai suka ce to. Suna fita ya shiga bandaki yayo alwala yazo ya soma yin sallah, yana fada ma Allah matsalolinsa. Washe gari misalin qarfe bakwai na safe yana zaune kan sallaya yana tilawar qur'ani, sai aka turo qofar tare da yin sallama, Mahmud ne dauke da flask din shayi a hannunsa. Bayan sun gaisa ya tambayi mai jiki, Ismail yace, da sauqi, gata nan bata ma farka ba, tun jiya data farka suka yi mata allura, Mahmud yace, ta farka babu wata matsala ko? Ismail yace, babu matsala, don ta gane ni, tana ta kuma kiran daddyn ta da kuma khalil dinta. Ban san yaya zanyi mata ba. Da nace mata yaron yana raye. Kasan ni na tsani inyi qarya, amma hakanan na fada mata sbd kar ta qara tada hankalinta, Mahmud yace, to yaya za'ayi dama ka fada mata gsky? Gara dai in ta samu sauqi, sai a fada mata. Ismail yace, tunani na kenan. Sannan kuma likita ya tambaye ni wai anan za'ayi mata dori, ko kuma a gida,wai inyi shawara, shine nace bari dai kazo inji yadda za muyi. Mahmud yace gara dai ayi mata anan asibitin, kasan dalili? Ismail yace a'a, Mahmud yace, kasan masu kudinnan aje ayi mata na gida, Allah ya kyauta ba'a fata, a samu matsala suce an barta a gd babu kula. Ismail yace hakane, duk nayi wannan tunanin. Sannan ga matsalar gurin zama. Ina zan kaita in an dora ta? Ni mai daki daya a zaure, Mahmud yace, hakane koma dai yaya ne, mu roqi Allah yasa ayi a sa'a. Baki suka hada gurin cewa Ameen. Ismail ya kalli flask din yace, harda ruwan zafi kazo min? yace eh, inna ce tace in taho maka dashi, ynxun ma zanje in siyo maka bread, sbd lokacin dana fito duk masu shagunan basu fito ba. Ismail yace, ka bari sai kamar qarfe takwas, don ynxun zaiyi wuya ka same su. [8/18, 12:01 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�2⃣Mahmud yace, to shikenan dama kai nake tunani, qila ma jiya ba kaci komai ba. Ismail yace saida yaya Amina suka zo, sannan da suka zo da abinci nace nafi son, ruwan zafi, shine mijinta ya kawo min bayan sun koma. Mahmud zai sake magana kenan, sai yaga kamar mimi tana motsi. Da sauri yace Ismail kamar tana motsi. Cikin azama suka isa gaban gadon, Ismail yace mimi kin tashi? Ta lumshe idanunta, sannan ta sake budesu ta kallesu. Alamu sun nuna yau jikin da sauqi, Numfashinta ya daidaita. Hawaye suka soma zuba daga idanunta, Mahmud yace sannu ya jiki? Bata amsa ba, sai dai hawayen ne ka bin gefen kumatunta. Ismail ya dora hannunsa akan nata, cikin damuwa yace sannu kinji? Zaki sha ruwa? Taja wani numfashi, cikin muryar marasa lfy tace, ni daddy na zaka kai ni, ban son wannan asibitin. Mahmud ya daga ma Ismail kai alamun yace mata eh, zai kai ta, Ismail yace eh zan kai ki, amma sai kin samu sauqi, sbd kinsan ba za'a iya tafiya dake a haka ba ko? Ta lumshe ido, ina.. Ina hajiya ta? Da momy na? Yace duk zasu zo. Sunce inyi miki sannu. Tace malam kace suzo su tafi damu, ni da khalil, kirasu ynxun malam. Yace zan kira su, zaki sha ruwa? Ta sake juyar da kai, dai dai lokacin ne wayar Ismail ta soma ringing. Ya ciro ta daga aljihunsa, sannan ya kalli fuskar wayar, hajiya sauda ce, don haka sai ya fita waje, ya daga tare da sallama, suka gaisa. Tace masa, Ismail yaya mai jikin? Yace da sauqi, tace ta farka ne? Yace eh ta farka kuma Alhmdlh jikin da sauqi sosai. Tace to mungode ma Allah, kar ka manta ka turomin account number dinka. Yace insha Allahu. Tace nagode sosai. Canjin rayuwa 2�3⃣Bayan ya kashe wayar, zai juya kenan sai ya hango likitan ya nufo dakinsu don haka sai ya jira shi, likitan ya qaraso. Sun gaisa ta hanyar yin musabaha, sannan ya tambayi yadda ta kwana da jikin? Ismail yace jikin da sauqi yau, don ta daina wannan nishin. Likitan yayo ciki, Ismail ya biyo shi yana masa qorafin har ynxun bata ci wani abu ba. Daidai sunje kanta ne, likitan yake bashi amsa da cewa, kar ka damu da wannan, sbd ruwan da muka sa mata jiya da daddare yana dauke da sinadaran abinci, so, ko bata ci ba, ba zai zama matsala ba. Ynxun muje a debi jininka a gwada mu gani, in yayi sai muyi qoqarin saka mata a yau. In mun tabbatar da samun sauqin ta, sai mu saka ranar da za'a yi mata aiki, ina nufin dori. Ismail yace, na zaci yau za'ayi mata sbd kar qafar tayi tsami. Likitan yayi murmushi, kar ka damu zata samu sauqi, ba tare da wata matsala ba. Haka kuma babu abinda zai faru ko da takai sati daya ba'a dora ta ba. Ismail yace, shikenan Allah ya bata lfy. Ameen, inji likitan, tare da dafa kafadar Ismail ya jinjina. Sannan ya kalli mimi, sannu khadija. Ta dago, ta kalli likitan, ya kama hannunta mai lafiyar, inane yake yi miki ciwo ynxun? Tace duk jikina, amma qafafu na sunfi yimin ciwo da hannuna. Likitan yace, bayan nan fa? Ta soma kuka, nidai gidanmu nake son a kaini, can zanje gurin daddy na. Likitan yace, za'a kai ki da zaran kin samu sauqi, kinji ko? Tace ina khalil? Likitan yace, yana nan yana samun sauqi kinji? Cikin sigar lallashi yayi maganar. Kar ki damu kisha tea kinji ko? Tace ni banajin yunwa. Ina son in wanke baki na. Likitan yace, karki damu k8nji ko? Ya kalli Ismail, ka bini muje ko? Ismail ya dubi Mahmud, ina zuwa ynxun. Mahmud ya koma bakin daya gadon ya zauna tare da cewa to. [8/18, 9:31 PM] Inna👬 Habiba dr Sa'ad: 2�4⃣Ismail yabi bayan likitan, suna fitowa, sai gasu yaya Amina, yace su shiga bari ya dawo Yanxun. Likita ne ya nuna masa har sashen masu dibar jinin, sannan ya kalleshi, in sun gama, ka sameni a office dina, kar ka damu ko kaga mutane ga shigo kawai, Ismail yace to nagode. Bayan an diba ne, sai suka ce ya tafi zasu kaima likitan sakamakon in sun fitar. Yace to, nan ya nufi office din likitan, kamar yadda likitan ya fada masa haka yayi, ya shiga duk da wadanda ya samu suna ganin likitan. Ya samu yana ganin wani a ciki, har zai fita, sai likitan yace, dan jira mu kadan, ynxun zan sallameshi, yana fita, ya nuna ma Ismail kujera, zauna nan. Ya dora hannuwansa saman babban teburin dake gabansa, sannan ya kalli Ismail wace, shawara kuka yanke? Game da daurin dorin matarka. Ko baku riga kun yanke shawara ba? Ismail yace mun yanke, kawai ayi mata anan. Likitan yace, shikenan za'a kawo maka takardar biyan kudi, sai kaje ka biya, sannan su baka takardar shedar biyan kudi, Ismail yace to, na gode. Likita yace, amma shi wanda ya mutu yaya suke da ita? Ismail yace, shi take so, likitan ya aje biron dake hannunsa, ya tattara hankalinsa a gurin Ismail, kamar yaya shi take so, gaka mijinta? Ismail saida ya danyi shiru, don ya tsani bada labarin, sannan yaba likitan labarin aurensu a taqaice. Likitan ya danyi jim, sannan yace, kayi haquri, ka kuma riqeta, wata rana zakaji dadin haqurinka. Ya miqe tare da cewa na gode likita, kar ka damu zan taimaka iyakar iyawa ta, inji likitan, Ismail ya sake cewa nagode, yace ba komai kaje, in sun kawo sakamakon kazo. Canjin rayuwa 2�5⃣Lokacin daya dawo, ya samu mimi tana ta kuka, yaya Amina tana ta bata haquri, ya isa gurinsu, yaje cikin damuwa, daidai kunnenta ya rusuna yana cewa, yi haquri mimi, ki fadamin me kk so? Tace ni gurin daddy zanje, ka bani wayata in kira daddy na.Yasa dan yatsansa yana share mata Hawaye, wayarki ta 6ace a gurin da kukayi hadari, amma ki bari zan siya miki wata. In kinji sauqi, zan kaiki gurin daddyn ki. Sabon kuka ta saka, tana fizge-fizge, ya miqe ya koma kusa da Mahmud yace, nifa gsky zan kira mata shi suyi magana, Mahmud yace ka kira shi kawai don kada ta zarge ka. A handsfree ya saka wayarsa, sannan ya kira layin daddyn nata, tayi ta katsewa ba'a daga ba. Ya sake kira, gab da zata katse aka daga, tare da cewa hello! Ta gane muryar daddy, don haka cikin kuka tace, daddy kazo ka tafi dani. Zan mutu anan. Daddyn cikin zafin rai, a fusace yace kar ki sake kiran layina. Ni ba mahaifinki bane, baki daga cikin 'ya'ya na, da farko nayi niyyar in huce sbd kinyi min biyayya a karo na biyu, kinbi wanda na baki, ashe ke kina kan bakanki, to inaso ki sani, ko mahaifiyarki na samu labarin inda kk, sai na kada ta ta barmin gidana, bare wata nafisa da kk kira tazo, kisa a ranki bakida kowa sai wannan mijin naki. In kinga dama ki zauna. In kuma sake tafiyar za kiyi, duk ba damuwa ta bace. Nidai gargadina kar ki sake kirana, ko ke ko mijinki! Yakai qarshen zancen tare da kashe wayar sa. Ihu mimi ta saka, tare da fizge ruwan da aka sa mata a hannunta mai lafiyar. saboda tsananin kukan da takeyi, ya hana Ismail lallashinta, don bai san ta ina zai fara ba. Tayi kuka har muryarta ta dushe, babban takaicin ta, ba zata iya tashi ba, don da tuni ta fita titi, mota ta taka ta ta huta. [8/18, 10:13 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 2�6� Ganin abin bana qarewa bane, yasa Ismail kiran likitan. Yayi fada sosai, ganin halin da mimin ke ciki, yace bai dace mara lfy irin haka a sata cikin damuwa ba. Ya kalleta, khadija kiyi haquri dadyn ki zai huce insha Allahu, kinji ko? Tace ya daina so na, tunda ya iya hadani aure da talaka, nasan ya daina so na, kuma da gske yake yi, abinda yz fadamin, ya cire ni daga cikin 'ya'yan sa. Likita ka taimake ni, kayi min allurar guba in mutu, likita yaja kujera ya zauna, bai kamata ki nemi mutuwa ba bayan Allah ya raya ki, kun yi mugun hadari fa, da Allah ya ga dama, sai ya dauki ranki a lokacin. Ki natsu koda daddyn ki ya qi ki, ba ga mijinki ba? Tace bana sonshi! Malami ne fa? Ismail ya lumshe ido cikin takaici, kar ki damu, ki bari ki qara samun sauqi, muga yadda za'ayi, kinji? Ta dago ido ta dubeshi, zaka barni mu tafi tare da khalil? Ynxun bani da kowa sai shi, yace zaku tafi, da qyar suka lallashe ta tayi shiru Kwadayi madudin wahala na'im da mom Nafisa bakuga komaibama ai Canjin rayuwa 2�7⃣Ismail yace, ga ruwan da ta cire nan a maida mata. Likitan yace, babu damuwa, tunda ta dawo hayyacinta, zata iya cin komai ba sai an maida ba. Sannan jininka za'a iya ba kowa, don haka za'a zo a diba ynxu. Ismail yace, zanje can ne? A'a ba sai kaje can ba, inji likitan. Anan ma za'a zo a diba. Da qyar Mahmud ya matsa ma Ismael yasha ruwan tea. Shi kansa duk ya rame sbd tashin hankali. Tara da kusan rabi, Sai ga wata nurse ta shigo da wasu mata guda biyu, lokacin yaya Amina tana cewa bari ta tafi, shi kuma Ismail yana cewa Mahmud, ya kamata kaima ka tafi. Shi kuma yana cewa, bari dai in an dibi jininka din sai na wuce. Sallamar wasu matan ne, yasa su yin shiru daga zancen da suke yi don jin ko su waye. Dai dai lokacin mimi ta dangana daga kukan da takeyi har ma ta yanke hukuncin yadda zatayi. Nata ganin, abin da zai fissheta, in sun samu sauqi ita da khalil, zata bishi gidansut tunda shi hajiyarsa tana sonsu tare, sai ta zauna a gidansu, in ya kammala karatu sai ayi musu aure, Amma ta daukar ma kanta alqawarin yadda daddy yace ya barta, ita ma har abada ba zata sake nemansu ba. Dama hajiya bata sonta, shikenan zata yi Rayuwar ta da khalil, ta amince bata da kowa sai shi din. Sallamar matan ne ta katse mata tunani. Ta daga ido ta kalle su. Ko cikin mata dubu ba zata kasa sheda fuskar mahaifiyar khalil ba. Ba wai don kamar da sukayi dashi ba, domin tun kafin suje gidansu a kwanan baya ita da khalil din, ta mallaki hotunan mahaifiyar tasa masu dinbin yawan gske a wayar ta wadanda khalil din ke turo mata. A ranta tace shikenan ma tazo tafiya damu. Nasan khalil ya riga ya fada mata komai. Sai taji wani farin ciki ya darsu acikin zuciyar ta. [8/19, 11:13 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 2�8⃣Kukan da mahaifiyar khalil din ta fashe dashi ne ya katse tunaninta, tare da tattaro dukkan hankalinta zuwa gurin ta. Ji tayi tana fadin. Alahu Akhbar! Yarinyar nan babu rabon kuyi aure da khalil, ajalinsa ya jawo miki wahala. Ni dama nayi tunanin wannan zazzafar s soyayyar da khalil ya kamu da ita, da qyar in zai rayu, yaron nan bai ta6a min sata ba tunda ya taso, sai dalilin wannan soyayya. In da mahaifinsa ya bada hadin kai, kila da ynxun khalil yana raye. Allah ya baki lfy. Mimi ta zaro idanu tana kallonsu. Qwaqwalwarta ta kasa saita zantukansu. Wai suna nufin khalil ya mutu ne? Ismail kuwa ya rikice, yana ta yi wa nurse din alama da yatsansa a baki wai suyi shiru, amma sam basu lura ba. Saima fadi da nurse din take yi, wai iyayen wanda ya mutu dinne suka zo daukar gawarsa, shine suka ce a rakosu su duba ta. Daya matar kuwa wadda suka zo tare, fadi takeyi, kiyi haquri aunty Amina, Addu'a kawai zaki yi masa, kinyi dauriya a gida, baki masa kuka ba, sai anan? Cikin kuka mai tsanani mahaifiyar take cewa, ban gaskata mutuwarsa ba saida nazo naga gawar khalil. Ihun da mimi keyi ne ya katse mahaifiyar khalil. Wani yunquri da mimin tayi shine ya saka su nufar gadonta. Sai dai Ismail ya rigasu isa. Duk da haka kafin yakai ta riga ta kai qasa a sume. Ya dauke ta yana fadin, inata alamta muku cewa kuyi shiru. Sbd batasan komai game da mutuwarsa ba, amma sam baku kula ba, gashi kunsa itama za'a rasa ta. Ya dora ta akan gadon yana cewa, ku taimaka ku kiramin likita! Mahaifiyar khalil fadi take, Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un! Ai ban san bata sani ba, nurse kuwa tuni tayi qasa da gudu don kiran likita. Canjin rayuwa 2�9⃣Qarfe sha daya da mintina momy Nafisa ta shiga gidan 'yarta Na'ima. Aljannar duniya. Ha ta furta lokacin data iso cikin falon farko, Ta kalli 'yar tata, wadda tazo ta bude mata qofa. Na'ima kina cikin irin wannan gdn kk daga hankalinki? Na'ima ta turo baki, momy ni wannan gdn yayi mintg girma, abin haushi kuma ni hadai ke yini a cikin sa. Momy tace, a'a ina masu aikin da akace an kawo miki? Tace, suna gefensu. To ai su ba abokan hirana bane momy. Suje su raina ni? Momy tace, ba nufi na kenan ba, ba wai kuyi hira ba, ina nufin a qalla kina jin motsin wasu a cikin gdn. Na'ima ta turo baki, to momy shifa bashi da lokaci na. Momy tace, matsalarki dai mijinki ko? Na'ima tace eh. Momy nafisa tace, kije kice masa inason ganinsa, ko har ya fita? Na'ima tace, yananan banji fitar sa ba. Ta miqe ta nufi sama cikin zumudi. Tana bude qofar ta jiyo shi yana waya, yana zaune a kujerar computer. Daidai abinda kunnenta ya jiyo yana cewa, "tsaya mana kiji Jennifer. Kar kisa ma kanki damuwa, na fada miki ba wadda nakeso din na aura ba, ko da ita dince ma kinsan cewa ke ta musamman ce, kina tsammanin rayuwa ta zata tafi sak ne in babu ke? Cikin turanci yake magana. Yayi jim, alamun yana sauraron abinda take fada. Sannan yayi 'yar dariya, tare da cewa, na san dai zaki iya bada sheda ta kan fadar gsky komai dacinta. Ya sake yin jim, sannan yace, to zan tabbatar miki da cewa kinfi wadda aka kawomin a matsayin mata. Zan tabbatar miki yadda ke da kanki zaki gamsu da batun, ya sake saurawa. Sannan yace, fadamin me zan miki ki yarda tunda naga kina tantama, kamar kin manta ni waye. Dariya taji ya saki, tare da fadin, ai wannan mai sauqi ne, in dai kwana da nine, ina me yi miki albishir cewa, ni da ke yau a gida na zamu kwana. In nayi miki haka, zaki gamsu cewa ni dake mutu-ka-raba? [8/19, 5:55 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�0⃣Maganar ta maqale, bai qarasa ba, sakamakon jin muryar Na'ima da yayi cikin kuka tana cewa, dama mata kk nema? Ya saki murmushi, sannan ya maida wayarsa kunnensa. Baby zan kira ki zuwa Anjima. Ya kashe wayarsa, sannan ya juyo da kujerarsa gaba daya, don irin mai jujjuyawarnan ce, cikin fara'a yace, baki sani ba dama? Ta tsaya tana Numfashi, tare da mamaki, gami da zaro idanu. Yayi murmushi mai sauti, kina nufin dama bakuyi bincike ba? Ya girgiza kai ayya. Ni qasurgumin manemin mata ne. Sannan ina shan wiwi da giya kadan, akwai wata matsala ne? Ta rasa me zata ce, sai kuka. Cikin kuka take cewa, ba zan iya zama dakai ba. Mutumin da baya iya 6oye laifinsa. Yace, oho, dama kinzo kin la6e min ne? Kada ki zauna dani din mana, dama ni na kawoki? Ko na riqe ki ne? To kazo momy na tana jiran ka a falo, ya ta6e baki, wacece kuma momy? Tace, don wulaqanci, mahaifiyata dince baka sani ba? Ya kalli danqareren agogon bangon falon, me kuma tazo yi da wannan safiyar? Ya kalli computer dake gabansa. Ta jirani, aiki nakeyi, in zata iya, in kuma ba tada lokaci, taje ta dawo wani lokacin, in abinda tazo dashi ya dame ta. Na'ima tace, wadda ta haifeni ce fa? Yayi mata wani kallon banza, cike da izgili yace, don ta haifeki, ni ta haifa? Kuka ta fasa, sannan ta juya ta tafi ranta a 6ace, hankalinta kuma a tashe. Cikin kuka ta sami momy nafisa zaune a falo, tana zaune tana jiranta. Momy kinji abinda na sameshi yanayi? "me? " inji momy. Na'ima ta fada jikinta, tana kuka, na sameshi yana waya. Don nayi masa magana, kai tsaye yace min waishi yana neman mata. Kuma wai yana shan giya da wiwi. Momy nafisa ta zaro idanu, cikin faduwar gaba tace, da gske? Kai inajin wasa yakeyi, zalayarki kawai yake. Kin ta6a ganin mai aikata irin wadannan qazaman laifukan sannan ya fada ma matarsa kai tsaye? Dole zaiji shakka. Ki barshi bari yazo. Inna👬 Habiba Sa'ad:na ce Kwadayi madudin wahala na'im da mom Nafisa bakuga komaibama ai😂😂😂 Canjin rayuwa 3�1⃣Na'ima tace, ai yace, ba zaizo ba, shi yana aiki. Momy ta yi shiru tana ta kallon Na'ima cikin matuqar mamaki, sannan ta miqe. Muje gurin nasa, mara mutunci kawai. Na'ima ta kalleta. Da kin barshi kawai momy, tace muje kawai, bazan dauki raini ba, gara in taka masa birki. Ta tasa Na'ima suka nufi saman. Yana latse latsensa a computer, yaji shugowarsu, amma sai ya dauke kai, yayi kamar baiji shugowarsu ba. Saida momy tace, bakaji Sallamar mu bane? Sannan ya waiwayo, fuskarsa babu annuri, yace, naji. Ina jinku, aiki nikeyi, ina kwana? Duk da baice su zauna ba saida momy Nafisa ta zauna, sannan tace "lfy" shine wato Abbas nace kazo, amma kacemin kana aiki ko? Ya nuna computer da hannuwansa guda biyu, ba gashi ba kina gani? Ya juya yaci gaba da aikinsa. Tace, to zaka iya bani 'yan mintuna muyi magana? Ya hada tafukan hannuwansa wuri daya ya murza tamkar mai jin sanyi, sannan yace, kamar minti nawa? Ta zaro ido cikin mamaki. Abbas ni kk tambaya? Ashe baka da mutunci har haka? Da sauri ya juyar da kansa gefe yana kuma dannar zuciyarsa, don kar ya nuna mata ainihin kalarsa. Taci gaba da cewa, to zuwa nayi inji laifin da Na'ima tayi maka da har zaka soma wulaqanta ta daga kawo ta. Har na qaryata ta, sai kuma gashi nima ka gwadamin. Ya kalli Na'ima, me nayi miki harda zaki kai qara ta? Tace, ko Yanxun dana shigo ba na sameka kanayin magana da wata bane? Ya daga murya cikin zafin rai yace, me ya dameki don kin sameni ina waya da wata? Meye naki a ciki? Ya kalli momi, tunda taxo gidannan ban ta6a shiga harkarta ba sbd banason matsala. Tayi harkarta inyi tawa. [8/19, 11:16 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�2⃣Momy tace wannan kuwa ba zai yiwu ba kana mijinta. Sannan kace, kowa yayi harkarsa? Ko kuwa dama baka amince da auren bane? Ya miqe tsaye yana kallon momy tare da cewa, "au dama baku sani ba? Ya girgiza kai, ni gsky mimi na gani nace inaso. Momy tayi shiru tana kallon sa, gabanta ke faduwa, damuwa ta bayyana qarara akan fuskar ta. Ta sauke ajiyar zuciya, ta rasa me zata ce, sai ta kalleshi tare da aje fushinta, to ynxun me kace? ko ince me kk nufi? Ya kalleta, ban gane ba. Momy tace, matsayinta. Yayi murmushi, sannan ya koma ya zauna kan kujerar computer tare da yin juyi. Ban sani ba gsky. Momy ta miqe tsaye ta sake daga murya, to me ya hana ka cewa iyayenku baka sonta tun kafin a daura auren? Yace, momy karki kiji haushi na. Ko na fada musu ba zasu fahimceni ba a wannan lokacin tunda suna da burin kansu. Ya nuna Na'ima, ke kuma ki bani lokaci, in burikan iyayen mu sun cika, sai in sauwaqa miki. Da sauri momy ta katse shi da cewa, ha Abbas, ai ko mutuwa tana kunyar idon mahaifi, inji masu magana. A gabana kk fadin bakason 'yata? Yayi guntun murmushi, momy kenan. Don dai ni ba danki bane, saiki takura min? Ya kamata kusan cewa, shi so ba'a masa dole. Ni mimi na gani nace inaso. A tsari na farar mace nake so. Kinsan kowa da ra'ayinsa. Qila da fara ce da nayi manage. Momy ta miqe, shikenan na fahimce ka. Yace, Yauwa nagode da kk fahimceni, kuma naji dadin haka, don ni mutum ne mara son takura. Ta kalli Na'ima, tashi muje. [8/19, 11:16 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�3⃣Na'ima wadda ke ta faman kukan takaici, ta miqe tana cewa, nidai kawai momy ki tafi dani, bazan iya zama ba. Yace, kin kawo shawara, ku tafi tare kawai momy, ta dube shi a qufule. Babu inda zanje da ita, zan kuma sanar da mahaifiyar ka, daka-duka auren yau kwana biyu, sannan ace tana gida? Yace, umm, yadda kuka za6a haka zakuyi. Amma in da zakiji shawara ta, da sai ince kar ki kai qara ta gurin momy na, sbd itama irinki ce, tafi son 'ya'yanta akan na kowa. Ni dai kunji ra'ayina. Sannan don Allah a daina takura min, a kuma guji shiga harkata. Basu sake cewa komai ba suka fice. Shi kuma yaci gaba da aikinsa. Dakin Na'ima suka koma sukayi jugum-jugum. Na'ima tana ta faman kuka. Mommy ta kalleta cikin damuwa, sannan tace, share Hawayenki. Badai farar mace yakeso ba? Na'ima tabi ta da kallo. zamu duba mayukan cikin akwatinki, in babu wanda zaisa kiyi fari, saimu shiga kanti. Kafin da wata guda, sai kin koma tamkar baturiya. Daga nan sai ki dinga yin duk wani abu da zaki ja ra'ayinsa. Na'ima ta dan ta6e baki tallafe kanta sbd tsabar ciwon da yake yi, tace, hmm mu gwada mu gani, haka suka sauke kafatanin kayan shafan dake cikin lefen, amma basu fahimci komai ba, ma'ana basu gane ko mayukan zasu iya yi mata bilicin din ba. Momy ta dafa Na'ima, cikin sigar lallashi, karki damu Na'ima, zan nemi Shawarar Aminiyata hajiya nana, domin na ta6a jin suna zancen qwayoyin da suke saka fari. Na'ima tace, to kafin ta wuce saida ta tabbatar hankalin 'yar tata ya kwanta, ta nuna mata cewa ta zauna tayi haquri, ta zauna kada ta sake maganar tafiya. Ta kwantar da hankalinta, wata rana sai abin da tace masa zaiyi. Canjin rayuwa 3�4⃣V Momy dai ta tafi cikin takaici, ta bar Na'ima cikin damuwa. Ta jima sannan ta tashi ta shiga cikin kicin dinsu masu aikinta ssuna ciki. Dattijuwar tana zaune tana firar dankali. Yarinyar kuwa tana wanke-wanke. Daqyar ta amsa gaisuwar da suke mata, wai ita dole ga matar gida, ta kalli tsohuwar, me za'ayi da wannan dankalin? 'Yalla6ai ne yace ayi masa cips da shayi. Na'ima tayi sororo, cikin muzanta, domin itace ya dace tayi masa, ko kuma tazo tasa ayi masa, amma sai ta wayance da cewa, dama har ynxun baku kai masa ba? Dattijuwar tace, hajiya zuwansa kenan yazo yai magana. Na'ima tace, ni bance sai kinyi min lissafi ba. Inason ki gasa min bread da kifi, Na'ima kenan. Wannan kuma ai cimar mimi ce. Yinin ranar, Na'ima ta kasa sukuni. Domin ita gsky tana matuqar son Abbas. Tana jin lokacin da zai fita wuraren daya saura na rana, ta fita taje gurin window tana leqensa har ya dau motarsa ya fice. Qarfe goma da mintuna na dare, taji tsayuwar motarsa. Cikin sauri ta fito falonta wanda tasan nan ce kadai hanyar binsa don hawa samansa. Ta dau gayu cikin riga da wando matsattsu, kanta babu dan kwali, tayi wankan turaruka har maqaqi suke mata a wuya. Sai dai kash! Tayi dana sanin fitowa daga dakinta, don burge angonta, domin kuwa da wata budurwa ya shigo, bayan ya buga alarm ta bude, sororo tayi cikin tsananin kishi, ba tada wata power da zata iya ce musu wani abu. Kuka ta saka sannan ta juya ta nufi dakinta. Abbas ya kalli Jenifer, kin gani ko? Har ynxun babu kamarki, tayi murmushi suka nufi samansa bayan ta saqalo hannuwanta a qugunsa. Tana fadin, na yarda honey. [8/20, 10:57 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�5⃣Cikin matsanancin kuka, Na'ima ta kira layin momy, wadda shugowarsu kenan daga asibiti, ita da daddy. Jikinsa da dan sauqi, shine ya matsawa likitan ya sallamesu, don ya tsani zaman asibitin. Momy Nafisa bata son daddy yaji wannan matsalar, don haka taqi dagawa, saida ta shiga dakinta. Tana dagawa ta fara da cewa, meyasa bakida haquri ne? Na'ima ba nace zanyi shawara bane? Zan kiraki da kaina. Tsaya kiji momy, da karuwa fa ya shigomin gida. Karuwa?? Momy ta tambayi Na'ima. Ta rantse, sannan ta ci gaba da cewa, ni bansan yaya zanyi ba ynxun, Momy tace, ki barshi zuwa gobe zanje gurin uwarsa. Na'ima ta shiga daki, ta zauna bakin gado cike da nadamar auren Abbas. Kuka take sosai, amma babu mai lallashi. Qarfe shida na yamma, innar su Zainabu ta shigo tare da Aminiyata, inna yalwa, suka sake dawowa gidan Zainabu, ta danji dama, tana zaune kofar dakinta. Jin muryar innar tata yasa gabanta faduwa. Rai a dagule ta kallesu, sannan ta shiga dakin, suka bi ta ciki, Aminiyar inna ta kalli Zainabu, meye kika dagule rai? Zainabu ta sunkuyar da kai. Ni wallahi da baku dawo ba, za'a ce iyaye na suna ta sintiri. Da ma aikowa kawai kuka yi. Ni bana son abin gorin nan gidan. Inna tace a daura miki goruba, mu dai in burinmu ya cika ina ruwan mu dasu? Inna yalwa tace, anqi a turo wani din, basha zakiyi ba. Ta daga hijabinta, ta ciro wata gora mai dauke da maganin da suka hado. Tace, zauna kisha shi maza-maza. Zainabu ta soma kuka tana shan maganin. Tasha kusan rabi suka ce, ki ajiye Anjima sai ki shaki shanye sauran. Karki sake baki shashi ba. Tun fitarmu daga gidannan, muna can muna qoqarin hadoshi. Don haka ki maida hankali ki shanye. Canjin rayuwa 3�8⃣Alhaji lawal ya dawo gurin su Maman bushira yanata zage-zage, wai shi za'a kawo wa raini da rashin mutunci? To, shifa ba zai bada jininsa ba bare kuma kudinsa. Duka-Duka yaushe ne akayi auren ma? Ko wata daya ba'a yi ba za'a ce har tanada wani ciki? Uwar gidan tace, haba Alhaji yaya kake irin wannan maganar? Sbd Allah, dubi yadda mutane suke kallonka. In jiya kuka yi aure, ai ba abin Mamaki bane ku wayi gari da ciki. Kai dai kayi fatan samun sauqinta, ka kuma bada duk abinda ake nema. Ya kalleta a fusace, sisi na bazai ciwon kai ba. Zanje in fadawa uwarta, wadda ta kawo mata maganin zubar da ciki. Sai su zo suyi jinyar ta, da kuma kudin sun, tace haba Alhaji don Allah ka duba wannan al'amarin. Cikin tsawa yace, in zakije gida, kizo muje! In ba zakije ba, in tafi. Tace, abarta da wa? Tsaki yaja, sannan ya wuce abinsa. Nurse tazo ta kira maman bushira zuwa dakin da aka ajiye Zainabu. Sannan taba ta wata takarda, ta nuna mata wata qofa, ki shiga zakiga wasu nurses, anan ne zaku biya kudin gadon, sannan zasu rubuta muku takardar shaidar biya. Likita zai shigo ya rubuta magungunan daya kamata tasha. Maman bushira dai, to, kurum tace, tana tsaye da takarda bayan tafiyar nurse. Gashi ba tada ko sisi tunda fitar bana shiri bane. [8/20, 9:17 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 3�9⃣Shi kam Alhaji lawal, kamar yadda ya fada, gidan su Zainabun kuwa ya zarce. Kafin ya kai saida ya kira direbansa, dan korensa. Bayan ya daga, sannan yace, iroro kana ina ne ynxun? Yace, Alhaji naje gidan, ance kunje asibiti da amarya ba lfy. Alhaji yace, mu hadu gidan iyayenta ynxun nan. Ka hau aca6a. Yana isowa qofar gidan, ya hangi iroro har ya iso, suna tsaye da dan acha6an, iroro ya nufo Alhaji yana cewa, sannu da qarasowa Alhaji. Alhaji yace, har ka rigani, to me kuma dan acha6a ke jira? Iroro yace, banida ko kwabo Alhaji, daman kai nake jira in sallameshi. Tsaki Alhaji yaja, sannan ya ciro naira dari biyu ya miqa masa, iroro ya amsa tare da cewa, Yauwa. Ya biya dan acha6a, sannan ya zuba sauran aljihunsa. Ya kalli. Alhaji, "lafiya dai kazo nan? Alhaji yace, zuwa nayi in sanar da iyayen Yarinyar nan Zainabu suje suyi hidimarta a asibiti. Kaji ma wai har tanada ciki, Duka-Duka yaushe akayi bikin? Iroro yace, tafdijam! Ba don ma baka mori kudinka ba ai da sakinta kayi kawai, ka kawo wata. To, jinyar cikin takeyi a asibitin? Alhaji yace, sun dirka mata maganin zubar da ciki, jini ya 6alle mata. Ai shiyasa nace, suzo suyi jigilar, iroro yace, kayi gsky Alhaji. Kuma zan soma duba maka madadinta tun daga ynxun. Alhaji yace, shiyasa nake matuqar sonka iroro. Sau da yawa in kayi magana, kamar ka shiga raina. Da ace ta kwana biyu, zuwan nan da nayi, yadda take asibitin nan, da takardar ta zanba iyayen ta. Amma su gama jinyarsu, zan dawo da ita, ba zanyi asara ba, kuma ba zamuyi dogon Zango da ita ba, don daga gani ita irin masu jarabar haihuwarnan ce, sai kace 6era. Canjin rayuwa 4�2⃣Cikin fada likitan ya shigo, ya kalli Ismail, "kai kanaso ne sai zuciyar ta ta buga tukunna? Me zaisa ku fada mata mutuwarsa? Don Allah ku fita waje, banason ganin kowa anan sam. Bai saurari kowa ba, bare yasan ba laifin Ismail bane. Gaba dayansu sukayi waje,, Ismail yana cewa, kun gani ko? Nasan dama laifina zai gani. Cikin kuka mai tsanani, mahaifiyar khalil take cewa, kuyi haquri, nima ban sani bane, Mahmud yace, karki damu hajiya, babu komai, shidai Allah ya jiqansa. Tace Ameen, bari mu tafi, Allah ya bata lfy. Ameen ya rabbi, ina fata 'yan sandan sun baku jakarsa da wayarsa ko? Sai dai ban sani ba, tunda tare da mahaifinsa muka zo, qila sun bashi, Mahmud yace, 'yan sandan sunzo lokacin da mukazo. Tace bari zanyi musu magana in munje. Mahmoud yabi su da kallo, suka tafi cikin damuwa. Ismail kam tamkar zuciyar sa ta buga don damuwa. Ya qosa likitan ya fito don yasan halin da ake ciki. Ya kusan rabin sa'a tare da taimakon nurses, sannan ya fito, ya kalli Ismail, fuskarsa a daure, ku biyoni office. Sun sameshi a tsaye yana duba wani file. Suna shigowa bai zauna ba, kuma bai musu izinin su zauna ba. Sai ma fada da ya hau yi musu, tare da cewa, kasan meye? Kaje ka samo wacce zatayi jinyar ta, domin kaikam baza ka iya ba. Ismail yace, doctor ba laifina bane, nan ya sanar dashi komai, likitan yace, shikenan, daga yau zuwa gobe bamason ganin koea gurin ta. Ina nufin 'yan dubiya. Likitan ya sassauta murya, ka nutsu sosai, ka lallasheta, sbd kasan dole ne ta zamo ta farka cikin damuwa da tashin hankali. "Ismail yace, Insha Allah. Na gode likita. Ynxun ta farfado ne? Mun kuma yi mata allurar varci, bamu fito ba saida varcin ya dauke ta. Don haka saiku kula sosai. Tashi kuje, za'a zo a dabi jinin naka ynxun. Ismail yace, to nagode likita. [8/21, 4:10 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�3⃣Suna fitowa suka dawo gurin su Mahmud, yace vari ya wuce, sai zuwa anjima. Ismail yace, Allah ya kaimu. Bayan tafiyar su, Ismail, a hankali ya tura dakin ya shiga. Ya jima tsaye a kanta, yana kallon ta tana varci, ya juya ya koma kan kujera, zamansa keda wuya, sai aka turo qofar dakin. Ya dago ya kalli mai shigowar, Namiji ne da riga fara, irin wadda likita ke sawa, sai wasu kayan aiki dake hannunsa. Yace. Kaine Ismail bin Abdurrahaman? Ismael yace, Na'am, Mutumin yace, nazo ne in debi jininka. Ismail yace, to bismillah. Bayan an dauki jininsa ne, sai wata nurse ta kawo masa wani dan tea a kofi da wasu 'yan qwayoyin magani, yasha ya dan kishingida, kafin lokacin sallah. Bayan la'sar, sai ga babban wan su Ismail yazo, lokacin Ismail yana dawowa daga masallaci, suka shiga ya duba ta. Har lokacin bata farka ba, bayan sun fito yace masa, ance zata gudu ne tayi hadari. Ismail Yace, eh, yayan yace, in bata sonka dolene? In ta warke ka maida musu 'yarsu, Ismail bayason doguwar magana, don haka yace wa, to, sai ya sake cewa, ka fadama iyayen ta? Yace eh, da haka suka kai qofar asibitin, inda yayan ya hau mashin, shi kuma ya koma ciki. Duk fargaban Ismail, in ta farka baisan dame zata tashi ba, bai san wane qalubale zai fuskanta ba. Kuma shi gaba daya ma zaman asibitin ya gundure shi, sam ya qosa ya barshi. kiran hajiya sauda yake shigowa, sai lokacin ya tuna da zancen account number da tace ya tura mata. Suka gaisa, bayan ya daga, tace masa. Baka turo ba, gashi har yamma tayi. Yace, kiyi haquri hajiya, kaina ne yadau zafi. Ban tuna ba, kuma banida account nawa na kaina, sai namu na makaranta. Insha Allahu dana sanar da malam Aminu zan turo. Tace, zancen dorin fa? Yace, sai gobe. Ynxun dai jini za'a qara mata. Tace, an samu jinin ne? Yace, eh, nawa ne za'a sa mata. Tace, Allah ya bata lfy, sai naga number, yace, insha Allahu. Canjin rayuwa 4�4⃣Ismael ya shanyo kwanar da zata kaishi matakalar da zai koma dakinsu, sai kurum ya hango innarsu Zainabu, ita da aminiyarta hannunta riqe da wata takarda. Ya jira har saida suka iso gurinsa, sai dai da alamu innar bata lura dashi ba. Yaji tana cewa, wannan maganin shi kadai dubu daya da dari bakwai, su kuma sauran kudinsu ya zama nawa? Qawar tace dama nice ke, tunda ta samu dan qwarin jiki daukarta zanyi mu gudu, mu bar asibitin. Baiji mai innar tace ba, sbd lokacin sun dan gota shi, ya hau sama yana tunanin, to wa suka kawo asibiti? Sai dai babu mai bashi amsa. Ya samu har an sawa mimi jinin, har lokacin tana varci. Likitan ya tambayeshi inda yaje? Yace ya raka wansa ne. Ya tambayi likitan ko babu matsala a irin wannan varcin da takeyi? Likitan yace, babu komai karka damu. Fitar likitan da nurse dinnesai ya kira malam Aminu suka gaisa. Malam ya tambayi mai jikin, Ismail yace, da sauqi, sannan yace, dama mahaifiyar tace take son in tura mata account number na, nace mata banida shi, amma zan turo mata na makaranta. Shine nake neman izini. Malam Aminu yace, babu komai, ko baka fadamin ba zaka iya amfani dashi. Ismael yace, nagode malam, Allah ya saka da alkhairi. Malam yace, haba babu komai, Allah dai ya bata lfy. Ismail yace, Ameen. Suka yi sallama. A take ba tare da 6ata lokaci ba, Ismail ya turawa hajiya Account number din, bada jimawa ba ta kirashi tace masa zaiga saqo zuwa gobe. Yayi mata godia, sannan sukayi sallama. Lokacin da zai tafi sallar magriba, yanason sai yayi isha'i zai dawo don haka yaje ya fadama nurses din da suke kula da dakin na musamman dake sama cewa, zaije sallah koda za tayi motsi tunda suna daf da dakin ne sukace to, amma yayi sauri don sun kusa tashi, masu shifting din dare suke jira. Bayan an idar da sallar isha'i sai yadan kishingida, dan varci yana da fizgarshi don akwai bashin varcin akansa na tsawon lokaci. Tun ranar da ya rasa Zainabu baya varcin kirki, har zuwa shigowar wannan matsalar. [8/22, 11:47 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�5⃣Can sai yaji vibration din wayarsa don ya sa ta a silent, lokacin da ya shigo masallaci. Ya duba yaga ashe Mahmud ne. Don haka, sai ya tashi ya fita daga masallacin, sannan ya daga wayar. Mahmud yace, nazo baka nan, ina kaje? Gashi ma ta farka. Cikin sauri Ismail yace, ta farka? Cikin wane hali take? Mahmud yace, kana inane kai? Ismail yace, ganinan zuwa, sallah naje. Ya kai qarshen maganar tare da kashe wayar, take yaji varcin ya sakeshi. Cikin hanzari ya nufi saman. A bakin qofa ya samu Mahmud, ya miqa masa hannu sukayi musabaha. A maimakon gaisuwa, sai Ismail yace, ta farka fa kacemin Mahmud? Mahmud yace, eh ta farka sadda nazo. Ban ganka ba, sai na tambayi nurse tace, kaje sallah. Shine na tsaya jikin window. Can na leqa sai naga alamun tana motsi, shine na kira nurse din. Da sauri Ismail ya bude dakin ya shiga. Nurse daya ce a kanta tana lallashinta. A tsakiyar dakin Ismail ya tsaya yana tunanin ta inda zai fara lallashinta. Yana jinsu da nurse din tana ce mata ya isa mana, ki daina wannan kukan haka. Nurse dince ta waiwayo ta dubeshi. Yauwa kazo ka lallasheta. Yace, ko zaki kiramin likita? Tace, ya tafi, kuma mai shifting din dare baizo ba. Ya isa bakin gadon ya daura hannunsa saman goshinta, sannan ya rusuna saitin kunnenta. Mimi kiyi haquri da wannan kukan. Ba magani bane, khalil ynxu babu abinda yake buqata agareki sai Addu'a, ki roqa masa yafiyar Allah, yafi miki wannan kukan. Batayi magana ba, kuma bata daina kuka ba. Haka da Mahmud yana tayi mata sannu, sam bata san ma yanayi ba. Duk wani lallashi da ya kamata, Ismail yayi mata, amma sam bata ma san yana yi ba. Don haka ya miqe daga kusa da ita, ya nufi waje ya zauna akan benci tare da riqe kansa mai sarawa. Mahmud ya biyo shi ya dafa shi, sannan ya zauna kusa dashi. Canjin rayuwa 4�6⃣Ismail Yace, Mahmud yadda kasan in fasa kuka haka nakeji. Yarinya sai kace wata jaririya, bata jin lallashi. Nifa in ta qure ni, sai in tafi in barta. Domin yadda bata sona, nima bafa yimin tayi ba. Gashi sai wani uban kuka takeyi, ban san yaya zanyi mata ba. Mahmud ya dafa shi, kar ka damu Abokina, kayi haquri. Ka jure, ka jajirce, in ka tafi to ka barta da wa? Kada ka manta matarka ce, wadda take a matsayin ba tada kowa, sai kai. Kayi iyakar yinka, ka hada da Addu'a. Zamu taya ka, wata rana sai labari, ka jure, karka sare, Ismail ya sauke ajiyar zuciya, tare da cewa, abin ne ya fara isata. Mahmud yadan girgiza kafadarsa kadan, alamun lallashi, kar ka damu akwai Allah. Ya sake sauke ajiyar zuciya. Allah ya taimake mu. Mahmud yace, Ameen, sannan ya miqe, bari in tafi, gidansu rabi'a zanje. Insha Allahu gobe zamu zo da ita. Ismail ya kalle shi da dan murmushi, kace ina gaishe ta. Sai kunzo. Ya miqe ya taka masa zuwa gurin matattakalar benen. Har ya juya zai tafi, Mahmud yace, Ismail kaga na manta ko? Ismail ya waiwayo. Yaya akayi? Mahmud yace, na zo ne in fada maka anyi admission fa. Haba? Inji Ismail. Mahmud yace, sosai ma kuwa. Ya kamata muje mu duba. Ismail yace, bari mu gani ko zuwa gobe ne, in wannan rigimammiyar ta dangana, sai yaya Amina ta zauna da ita muje, Mahmud yace, shikenan Allah ya kaimu goben.! [8/22, 8:04 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�7⃣Yadda mimi taga rana haka taga dare, kuka kawai take, babu qaqqautawa har mutyarta ta dishe. Tun Ismail yana lallashin ta, har ya gaji ya fice yayi alwala don yin shafa'i da wutirinsa tare da da addu'o'insa daya saba. Haka suka kwana har asuba tayi ya tafi sallah. Gurin qarfe taran safe aka shigo aka soma yi mata shirin yin aiki, wato dori. Goma saura aka shiga da ita. Lokacin ne malam Aminu ya kira Ismail yana sanar dashi cewa, yaga alert. Ya duba yaga an turo kudi naira dubu dari(100,000). Kuma yaga sunan saudatu bashir. Ismail yace, eh, saqon da mahaifiyar ta ta turo din ne. Ynxun haka ma an shiga da ita gurin dori. Zan fito Anjima sai in amshi katin ATM din in yana gurin Mahmud. Dama kudin hannuna sun qare kaf. Yace, kar ka damu, ko nine sai inje in ciro maka tunda akwai mashin a gurina. Allah dai ya bata lfy. Ameen, inji Ismail. Sannan sukayi sallama. Ismail ya saukar da ajiyar zuciya, har ya danji dadi sbd samun wannan kudin, domin hannunsa babu kudi. Tagumi yayi yana tuna irin kukan da mimi tayi ta rerawa jiya. Ko sallolinsa yayi ne dai kawai, amma gunjin kukanta yana daukar hankalinsa. Cikin wannan tunanin ya hango yaya Amina. Yaji dadin zuwanta sosai, domin zamansa shiru ya isheshi. Ya tare ta, tare da amsar kular hannunta da kuma ledar ruwan pure water, suka shiga cikin dakin, tace ina mara lafiyar? Yace, an shiga da ita dakin da za'a yi mata dori. Ya bude kular, dame kk zo? Tace, alala ce don nasan kanaso. Yayi dan murmushi, a fili yace, naka sai naka. Yaya Amina nagode da hidima. Tace, haba Ismail wa gareni banda kai? Kaima kuma bakada wadda ta fini. In ban maka ba in ma wa? Donma Allah yasa ni ba mai hali bace. Yayi dariya, hakane yaya. Allah ya qara mana zumunci. Tace Ameen, yaci alalar sosai, yana ci suna hira, har take bashi labarin cewa, su inna dasu fatu sunce sunanan zuwa anjima. Canjin rayuwa 4�8⃣Yace, Allah ya kawosu qila ma ke zasu samu yaya. Sbd jiya Mahmud yace min anyi admission, zamuje mu gani ko Allah zaisa mu samu. Don kinsan qasarmu sai Allah. Qiri-qiri zaka ci jamb amma saika rasa admission. Sai ace baka ci post UTME ba. Mu dai munce zamuje mu gani. Sannan mahaifiyar mimi ta turo kudi a account din makaranta zanje in cire. In kuma malam ya ciro shikenan, don yace koshi sai yaje ya ciro tunda da mashin a gunsa. Sha daya saura aka fito da mimi daga dakin da aka yi mata dori, tamkar wadda akayi wa operation. Nurses suka kwantar da ita akan gadonta tare da maqale qafafunta da gadon. Bayan sun gama kintsa ta ne likitan shima ya shigo, tare da ainihin doctor salis, likitan dayake kula da ita. Sunyi ma Ismael bayanin babu matsala, insha Allahu zata samu lfy, cikin zolaya doctor salis yace ma Ismael, "yar amanarka zata warware. " Ismail yace, Allah yasa. Sannan suka rubuta magunguna suka ce ya siyo kafin ta farka. Yace musu zata iya cin abinci? Suka ce eh, zata ci komai in ta farka. Wannan varcin ma da takeyi anyi mata allura ne sbd ta wahala. Sai azahar Mahmud yazo, don haka nan yabar yaya Amina suka tafi. Sai dai iyakacinsu banki don bazai yiwu suje zariya yau ba, sai gobe, Daga nan yaje ya sai magungunan da likitan ya rubuta masa wadanda bai samu acikin asibiti ba. Sannan ya koma gida yayi wanka, ya shanza kayansa zuwa farar jallabiya qal da hula 'yar fakistan. Ya fesa turaruka, sannan ya fito. Ya rufe qofar zai fita saiga su inna zasu shigo. Ya tsaya suka gaisa, sannan yace, daga unguwa kuke ne? Suka ce, daga asibiti muke. Ai mun samu Amina. Yace to mun gode, Allah ya saka. Sukace Ameen. [8/23, 1:49 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 4�9⃣Fatu tace, umm. Wannan abu yaban mamaki Inna. Me ya janyo wannan hadarin? Inna ta kalleshi, "ina zan san abin da ya janyo. Kai sama'ila yaya abin ya faru ne? Yace, tsautsayi ne kurum. Fatu tayi murmushi. Zancen dake yawo a gari haka ne kenan. Guduwa zatayi sbd bata sonshi. Ta kalleshi, kaima kayi wauta Ismail. Dubi wannan Yarinyar, kallo daya zaka san ta saba da hutu, amma ka cusa kanka. Da ido kawai Ismail yake binsu. Kuma bai shirya ce musu komai ba. Yasa kai ya fita. Tsaki Inna taja "Mtsss" sannan tace, aishi tsiyar sa kenan. Qarya ne kaji cikinsa. Shidai ya sani. Inji rashida, daya matar wan nasa. Matar musa ce kurum bata ce, komai ba don bata cika shiga shirginsu ba. Sai da ya fita titi, sannan ya kira Mahmud yake fada masa cewa, gashi zai koma asibiti. Mahmud yace, to sai sun shigo Anjima shi da rabi'a. Ya tare dan acha6a zuwa asibiti. Suna cikin tafiya ne yana kalle-kallen sa, idanun sa suka sauka akan wani super market. Yace ma dan acha6an don Allah dan dakata in duba nan. Dan acha6an yace, amma ba dadewa zakayi ba ko? Daidai lokacin da ya tsaya, A'a insha Allahu bazan jima ba, Ismail ya bashi amsa bayan ya sauka daga mashin din. Ya shiga tafkeken super market din tunaninsa kawai ya sayi abinda mimi zata iya ci ko sha. Da makilin ya soma cin karo, gasu nan kala kala, ko wanne da kudinsa manne a jiki. Sai ya dauki mai tsadar ciki, ya sai brush da sabulun dettol na wanka. Sannan ya koma gurin kayan sha. Ya rasa wanne irin drink take sha. A qarshe sai ya dauki maltina a nasa tunanin kowa yanasha. Ya sai katan din ruwan gora guda biyu, sai kayan tea na manyan gwangwani. Suga na kwali. Ya sai flask din ruwan zafi. Daya fito wajen gurin ne kuma ya isa gurin masu saida kayan marmari, ya sayi Apple, lemon zaqi, sai kankana da abarba. Dan acha6a yace, gsky malam za fa kaimin qarin kudi. Ismail yace, babu komai, Allah dai ya kaimu lfy. Canjin rayuwa 5�0⃣Da kaya niqi-niqi ya hau samansu, gabansa har faduwa yake yi daya tunkaro asibiti. Haka dai ya nufi dakinsu, tunaninsa a wane hali zai samu mimin aciki? Don yasan zaiyi wuya in bata farka ba. Ya tura qofar cikin sallama, k idanunsa suna kan gadon. Yaya Amina ta amsa Sallamar tana kishingide a dayan gadon. Yace sannu yaya na barki ko? Ta sauko tana tana fadin, banyi zatonka a wannan lokacin ba, ko har kunje zariyan? Ya nufi gadon mimi yana cewa, mun bari sai gobe, sbd yau yamma tayi. Bata farka bane? Yaya Amina ta iso gaba gadon. Tace, ta farka, ko ido bata bude ba, kuka kawai take yi. Don nima nishin kukan ta yasa nasan ta farka. Tsaki yaja cikin damuwa yace, nidai Allah ya sani wannan kukan yana damuna. Yasa yatsansa ya debe mata gashin kanta daya watso kusa da idonta, ya maida mata shi bayan kunnenta. Ya tsura ma fuskarta ido, wadda tayi jajur don kuka. Idanunta kuwa sun kumbura sunyi luhu-luhu. Ya dora tafin hannunsa akan goshinta. A fusace ta bude idanunta, qwayoyin idon sunyi jajur. Ta zuba masa harara, sannan ta girgiza kanta, alamun ya cire mata hannunsa daga goshinta. Yace bakisan in dafa miki goshi ne? To na cire. Amma ynxun ki tashi kici wani abu. Ya rusuna ya soma ciro abubuwan daya siyo daga cikin ledar. Yaya Amina tace, Yauwa yanada kyau ta wanke baki kuwa, ga makilin da brush. Amma ka manta baka siyo roba 'yar mai fadi ba, da FO sbd fitsari, don kaga tana varcin nan duk ta fitsare kayan jikinta da na kwanciyr. Gashi Kaje gida amma baka dauko mata kayan sawa ba. Ismail yace, fitsari kuma? Ya dago ya kalli mimi, fitsarin lfy? Sabon kuka mimi ta saka. Domin farkawar da tayi taji ta sharkaf cikin fitsari ya tada mata hankali. Wai ita mimi ce haka? Mimin daddy mai shanawa. Sam bata son ta bude ido ta kalli asibitin bare malam Ismail, wanda ta tsana fiye da kowa. Ta tuna lokacin da tayi wani zazza6in mura, waje suka fita, can England aka duba lafiyarta. Tunda ta taso, duk bayan wata uku dad yake kaita a duba lafiyarta a qasar Misra. Amma yau gata a wani qazamin asibiti kwance cikin fitsari. Ina ma dai mutuwa tazo ta dauke ta. Da ma da sukayi hadarinnan itama ta mutu da yafi mata wannan Rayuwar. [8/23, 1:50 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�1⃣Ismail yace, ba zaki yi magana a saki ba mimi? Yaya Amina tace, haba Ismail, Kalli yadda take mana qafafu a sagale taya za'a sata tayi fitsari? Yace hakane. To ynxun sai dai ta dinga yi a kwance? Yaya Amina tace, dole a samu robar fitsari, amma mu nemi Shawarar likitan. Ismail yace, to zan sameshi. Amma ynxun ya kk ganin za'ayi gurin cire mata kayan? Ko inje in fara dauko mata wasu in dawo? Yaya Amina tace, to kayi sauri don inason inje gida sbd abincin dare. Insha Allahu yanxun zan dawo. Duk akwatunanta ya chaje su tsaf, babu riga da zani, mafi yawa daga cikin kayanta 'yan kanti ne, riga da wando, sai dogayen riguna. Na atamfan ma daga doguwar riga sai riga da siket. Tsaki yayi, cikin haushi ya bude qaramar Jakarta, wadda ta dauko zata gudu da ita. A ciki yaga Jakarta wadda ta zuba kudadenta data debo sbd guduwar su. Ya ciro jakar yaje ya daga can qasan katifarsa ya sata cikin tsohuwar malum-malum. Ya daga ledar tsakar daki, ta qasan katifar ya saka, sannan ya maida katifar. Yayi hakane sbd tsoron 6arayi, tunda shi ba wai yana kwana a gidan bane, kar a zo a bude dakin. Ya dawo ya bude akwatin da yaga kayanta na ciki. Aciki ya ciro siket da dan kanfenta, sai best. Baisan meyasa ya zuba ma rigar mamanta ido ba, qila kyau tayi masa, amma duk da haka bai dauka ba. Qamshin turarenta kayan sukeyi, sai ya dauki 'yan shirt guda uku, tunda babu zannuwa. Yace zaibi ta bakin kasuwa ya sai turmin zani ya tsaga su gida uku. Ya dauki bargon rufarsa da zanin gado, sannan ya nufi kasuwa, daga can ya wuce asibitin. Yauma ya hangi innar su Zainabu acan baya gurin wanki. Yauma haka ya hau sama yana tambayar kansa wai wa take jinya? Ya samu yaya Amina da taimakon nurse din dake aiki a wannan lokacin suna cire mata kaya. Ido hudu sukayi da ita, lokacin daya shiga an cire mata riga. Cak ya tsaya, domin idanunsa sun kalli abinda bai ta6a gani a fili ba Canjin rayuwa 5�2⃣Runtse idanunsa da yayi, sunzo daidai da ihun data yi. Yaya Amina tace, "mun yi miki fami ko? " Malam Ismail ku rufemin jikina. Tun farfadowarta, sai ynxun tayi magana. Ismail ya ajiye kayan hannunsa a gurin. Idanunsa a Runtse ya juya. Sannan ya bude idanun. Abin daya gani suna yi masa gizo. Ya fita kan benci, ya zauna tare da tura hular kansa baya. Sannan yasa hannunsa ya shafe fuskarsa. Wani yanayi ya samu kansa a ciki, wanda ba zai iya tantance shi ba. Wata zuciyar tace, ba fa haramun ka gani ba, duk ka rude haka, matar kace. A cikin dakin kuwa, yaya Amina ce ta zo ta dauki kayan da uwanta ya ajiye taje kan daya gadon ta zazzage su tana dubawa tare da cewa, shikenan tunda ya fita sai kiyi haquri. Nurse tace, wane haquri, ba kunce mijinta bane? Yayan tace ai bata ta re bane shiyasa. Nurse tace, to kuwa kina da aiki. Mimi dai sai kukanta takeyi, saboda baqin cikin qirjinta da malam Ismail ya gani, har suka gama kintsa ta bata daina kuka ba, sunce zasu sa mata robar fitsari, tace ita dai bata so, Nurse din ce taba yaya Amina Shawarar su sai mata pampers na manya. Shi sai dai kawai a cire a yar, ayi mata tsaki, yaya Amina tayi mata brush, taqi cin komai, sai ruwan data sha kusan rabin gora. Baiji fitowar nurse din ba, sai dai muryarta yaji tana cewa, kana zaune anan ne? Ya kalleta, kun gama? Tace eh, ya ce na gode. Tace ba komai, sai kaje kayi lallashi, don shagwa6ar matarnan taka tayi yawa. Hannu yasa ya shafa fuskarsa tare da yin guntun murmushi. Ta wuce gurin aamansu shi kam ya kasa shiga dakin.5�3⃣Yaya Amina ta fito, cikin jin nauyi ya kalleta. "tafiya zakiyi? "Tace, eh, kaga yamma tayi, ga girki. Ummi ba girki ta iyaba. Nasan dai zata share min gd tsaf, har ma ta hana su Saddam yimin wasa a cikin daki. In ba ayi sa'a ba sai yayi ta dukanta. Ismail yace, ai rigimar sako da sako na gurin saddam da Ummi, kamar masu ganin hanjin juna. Tayi dariya. Haka suke, amma in daya baiga daya ba, ayi ta damuna, mama ina take, ko ina yake? Ismail yace, haka suke fa. Cikin zaulaya yace to kisa abbansu saddam ya qaro aure mana. Kin ga kin huta, baki da tunanin yin wani girki. Tace oho, sakamakona kenan nayi maka jinyar mata? Cikin dariya yace, yaya laifi ne? Tace, ban sani ba, ni kaga tafiya ta, sai anjima. Yace yaya ki vari sai gobe mana. Tunda ma da kayan tea, sai in sha ruwan zafi. Tace shikenan sai goben. Yace, zaki zo da wuri ne, sbd inason zamuje zariyar nan. Tace, zanzo dai kamar qarfe goma. Yace, Allah ya kaimu. Har gurin matattakalar ya rakata sannan ya dawo. Tsaye yayi a bakin qofa yana tunanin yadda zai shiga dakin. Daga bisani yayi ta maza, ya tura qofar tare da yin sallama. Tana zaune akan gadon, an cire mata qafafun daga sagalewar da akayi musu. Sannan an dago gadonta, gurin kwanciyr, ta yadda zata iya kishingida. Ya kasa kallon fuskarta. Yace, meyasa bakici komai ba? Ya isa gurin fridge ya bude, ya ciro gwangwanin maltina. Kisha maltina mana? Tsakin da ta ja shine yasa shi kallon fuskarta. Harara take ta zabga masa da jajayen idanunta. Ya sauke idanunsa, yasan kan abin da ya kalla dazu ne. Sannan ya sake kallon fuskarta. "kiyi haquri, dazun bansan ana shiryaki bane. Kuma ni banga komai ba ma. Canjin rayuwa 5�4⃣Bata dai tanka shi ba. Yace, kisha maltina ko kadan ne kinji? Tace, ni bana sha. Yace to fadamin kk so kici? Ta soma kuka. Yace, kinga matsalarki. An ce miki kuka yana maganin matsala ne? Wannan kukan sai dai ya qara miki ciwon. Tace, ni da zan mutu sai nafi murna. Rayuwata ba tada amfani. Yace sbd me? Tace, khalil ya mutu. Shine kawai ya ragemin a duniya. Ismail yayi murmushin takaici. Ko zaki bishi ne? Ta Kalli Ismael a fusace, ai da ace inada izinin tashi, to da tuni na fada ta wannan windon. Ismail yace, in kuma Allah baiga dama ba, kk karye, kuma yaqi daukan ranki, kizo kiyi ta jinya ba. Wai shin ma in tambayeki, da kk ta burin mutuwa, me kk tanada na ibada ko na alheri, wanda zaki kare kanki, ko kuma ince wanda zaki amsa tambayoyi a gaban Allah? Mimi ta sunkuyar da kai. Yace, inaso kisan wani abu, fushin iyaye ba qaramin bala'i bane. Dakin mutu a hadarinnan, kin tafi da fushin iyaye a gudun da kk yi, kinsan illar dake cikin guduwar 'ya mace kuwa? Koda yake kece zaki bada labari tunda gaki a gadon asibiti. Sannan gudunki na farko ma nasan kin hadu da wani qalubalen, sai dai in ba zaki fada ba. Ta daga masa hannunta mai lafiyar, ni bance maka kaimin wa'azi ba. Da zama da kai a matsayin miji, gara min mutuwa. Yace sbd me? Tace ni ban son ka, na tsane ka. Ismail baya varin bashin magana. Don haka yace, ashe duk daya muke. Nima mimi bana sonki. Sam bakya cikin tsarin macen da nake so. A ra'ayina inason mace mai kyau, mai son addini, kuma maijin maganar mahaifanta. Kalamansa sunyi wa mimi zafi. Har ta kasa cewa komai, sai kai data sunkuyar ta soma kuka. yasa hannu ya daga fuskarta. Karki damu in kin samu sauqi, zamu san yaya za'ayi ,ta goce kanta da qarfi, kar hannunka ya sake ta6a ni. Yace, nifa damuwa ta kici wani abu, tace bazan ci ba, ni ka barni, ya koma bakin dayan gadon ya zauna. Ya soma shan maltina tare da cewa. Na barki. [8/23, 9:59 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�5⃣Har bayan isha'i tana kukan maganganun da Ismail ya danqara mata, lokacin kuma likita yazo. Bayan sun gaisa, ya tambayi jikin nata. Ismail yace, jikin da sauqi, amma taqi taci komai. Likitan ya kalleta, khadija! Ta dago ta dubeshi. Yace me zakici? Cikin wata murya mai ban tausayi tace, ba komai. Ismail ya ta6e baki, barta likita, cikinta ne zai fada mata. Sai kuma maganar pampers, dazun wata nurse ta ba yayata Shawarar mu sa mata pampers sbd fitsari, tunda taqi a sa mata roba. Likitan ya kalleta, ki bari mana a sa miki robar fitsari? Tace doctor bana so. Ta sunkuyar da kai tana tuna zuwansu katsina, ita da hajiya. Ta matsa wai sai an kai ziyara asibiti da gdn marayu. Daddy baiso zuwa ba yace zai bada abinda za'a kai, amma hajiya ta cije tace dashi za'aje. Aka tafi harda ita, a wani asibiti ne taga marasa lfy an daura musu ledar fitsari. Ta tambaya menene wannan? Aka ce mata ledar fitsari ce, saida tayi rashin lfy sanadin ganin marasa lafiyan. Sannan ace za'a sa mata. Shikenan ka sai mata pampers din, amma amma dai zaku sha kudi, in kuma zaka dinga sata a toilet din da kanka, da sai yafi muku. Da sauri mimi ta daga kai, Allah ya tsareni, ko hannuna karka sake ta6a min. Ba mijinki bane? Ko pampers din waye zaisa miki in ba shi ba? Duk wahalar da yake miki, yana kashe kudi akanki shine zaki dinga yi masa haka? Canjin rayuwa 5�6⃣Mimi tasoma kuka,"Ni bana son yasake tabani,na tsaneshi". Kuma ai kudina ya dauka yakemin magani.Ai bashida kudin dazai kashemin. "Likita kar ka damu da ita,nima inayi mata ne don Allah,da Lima tausayin halin da take ciki,amma rashin mutunci halintane ko tayi min bazae dameni back.Ita ikirarinta bata sona,nima kuma bnga abinso a gurinta ba". Likitan yayi murmushi ,don ya fahimci Isma'il yana maganar ne don son cusa haushi ga marar lafiyar. Yace "khadija wae bakya son shi?" Tace "eh". Saboda me? Tanuna isma'il da yatsanta,"saboda abubuwa da yawa. Ina zargin sa da shiga cikin rayuwata. Kuma ya taemaka gurin shigata wannan halin. Isma'il yazaro ido yana kallonta,a zuciarsa yace"sharri zatayi min?" Likitan yaja kujera, yazauna tare da tattara hankalinsa gareta. Sanar dani hujjoinki,kila inada taemakon dazanyi miki. Tasoma kula "Ranar wata asabar nasoma jin lavarinsa a wurin kannaina. Sunaji dashi a matsayin malaminsu. Ranar farko Dana dora idanuana a Kansa,ranar ya raena min wayau,tare dafada min maganganu na wulaqanci.Abinda baa taba yi min ba a rayuwa ta. Sannan shi ne mutum na farko da banyi nasarar rama abinda yaemin ba, duk da cewa yayi min abin da baa taba yimin ba. Sannan shine mutum na farko dana taba kae qaran shi wurin daddyna bae amshi korafina ba. Tundaga ranar asabar din daya dira gidanmu Abuja,van qara samun kwanciar hankali ba.A qarshe shine daddy ya daura min aure dashi a ranar asabar kuma. Kalli wannan abin doctor,ta yaya zan yafemasa wannan zunubin? [8/23, 10:28 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 5�7⃣Salis yayi qoqarin danne dariyar da ke qoqarin kufce masa,sannan cikin zolaya yacee "gaskia yayi babban zunubi". Ismail kam dariyarsa yayi harda qwalla.sannan yace, "Mimi kenan ,kiyi haquri,don nifa haka nake, duk inda nashiga sae nayi nasara akan duk mae ja dani, saboda na dogara ga Allah.kinsan duk Wanda ya mika lamuransa ga Allah,to fa Allah ya Isar masa.kinci sa'a ma wannan guntun labarin naki agaban likita kika fada,ba agaban alqali ba, da sae ya daureki.Domin babu abinda ya hada labarin nan da halin dakike ciki.ni na hanaki bin umurnin mahaefinki? Ni nace miki ki gudu? To, in baki sani ba kisani,bijirewa mahaifinki da kuma gudun dakikayi kika bar iyayenki sune silar shigarki wannan Hamlin. Likita have, wai-wai-wai kin gudu ne dama? Ta sunkuyar da kai, hawaye ne kawai ke zuba. Lallai kinyi babban laifi. Ko dani ba alqali bane. Kamar yadda Ismael yace, amma na yarda gudunki ne ya jawo miki wannan halin da kk tsinci kanki a ciki. Ta soma tuna yadda suka auna arziki a gudun farko. Ashe gargadi ne suka tsallake. Na biyu kuwa shine masoyinta ya mutu, ita kuma gashi ta kakkarye, Burinta in ta warke ta sake guduwa inda iyayenta da danginta ba zasu ta6a jin labarinta ba. To kenan mezai faru in ta sake guduwa? Duk zatonta a zuciya takai qarshen maganarta. Ashe a fili ne. Sai kurum taji yace, in kk sake guduwa na uku, qila qafafunki da hannayenki su gutsire, ki koma gundulmi, kinga kenan sai bara. "Bara? " ta zaro ido. Likita cikin son firgita ta yace, "bara kuwa" sabon kuka ta dora, tare da cewa, " Allah ya dauki raina in huta. " Canjin rayuwa. 5�8⃣Ismail yace kinata burin mutuwa, an fada miki sauqi zaki samu in kin mutu a haka? Na tambayeki guzurin da kkyi na zuwa lahira, amma baki ban amsa ba. Kk yarda kk mutu a haka, ai kwanciyr kabari ma kawai ya isheki. Ta Runtse ido cikin tsoro, tana tunanin kalmar likita. Wai tayi bara, Nan ta tuna wani English novel data karanta yadda Yarinyar cikin labarin 'yar sarauta, sakamakon son zuciya, ta qare da gutsurarrun qafafu kuma a gidan yari. A firgice ta dago ta Kalli likitan, sai taga ya yagi kwalin magani ya ciro biro a gaban aljihunsa ya soma rubutu. Ya gama, sannan ya miqa ma Ismael tare da cewa, duba ka gani, kasan wannan magani? Ismail ya kar6a tare da cewa to, Ya soma karantawa kamar haka. "Ismail inason ka sauke duk abinda ke ranka game da Yarinyar nan. Ynxun na san bata san tunanin da zatayi ba. Amma ni da kai in mun hadu zamu saita mata tunanin ta. Ismail ya dago kai, ya kalli likitan sannan ya kada kai, na san shi. Likita yace, to kasai mata shi a hada cikin magungunan. Ba damuwa, inji Ismail. Likitan ya sake kusantar gadon mimin, "yanxun, menene tunanin ki a gaba, ko ince burinki? Inason in taimakeki ne matuqa. Mimi cikin kuka tace, banda wani sauran tunani, tunda malam ya dage wai mutuwa ma ba hutu bace a gareni. Da farko na daura aniyar dana warke zan gudu, in nesanta kaina da mahaifana, yadda baza su sake samun labari na ba. Inason su manta sun haifi 'ya irina. Kai in mutu ma yadda zan nesanta dasu gaba daya. Amma ynxun kunce haka. Likita kai ka taimakeni ka nesanta ni dasu mana. 5�9⃣Doctor salis yace, "yi shiru daina kuka, in miki abinda kk so, ta tsagaita saidai ajiyar zuciya da takeyi. Yace, na tabbata in kin kwantar da hankalinki, Ismail dinnan zai nesanta ki dasu, kamar yadda kk so domin shi mijink... "Ta katse likitan da cewa, bana buqatar yaci gaba da zama mijina. Doctor salis yace, dukda haka zai iya, zaka iya ko? Ya kalli Ismail. Yace zan iya matsawar zatayi min alqawari guda daya, sannan zata kwantar da hankalinta tare da bani hadin kai, to zan nesanta ta da mahaifanta, sannan ba aanci gaba da zama mijin nata ba, in ta buqaci hakan. Tace, menene tabbacin, zaka bar gari dani ko qasar? Ya ce, kina cikin garin katsina amma ba dole ku hadu ba, ko susan inda kk. Ta danyi shiru, sannan tace, fadi alqawarin inji. Yace, zaki dauki alqawarin cewa, ba zaki gudu ba, duk wuya, duk runtsi. In kinyi haka, ni kuwa zan 6oyeki, tare da yi miki duk abinda kk so, iyakar iyawa ta. Haka kuma in bakya buqatar inci gaba da zama mijinki, sai in koma wanki. Likita yace, bakida wani za6i sama da wannan. Kuma asirinki rufe. Tace, in kuma hajiya ta kirashi fa ko Alhaji don jin inda nake? Yace daga yau zan kwafe duk numbers din dake wayata banda nasu, sai in baki sim din ki karya, ki zubar. Tace, to in akazo gidanku fa? Ai kafin mubar asibiti zan nemi haya a wata unguwa daban, kuma ko 'yan gidanmu ba zasu sani ba. Dama basu san gidanmu ba. Dama Hamisu direba ne kawai ya sani. Tayi shiru, domin qaramar kwanyarta ta yarda da abinda akace. Ta kalli Ismail, kenan daga ynxun kai ba mijina bane? Ismail yace, a'a wannan shine zai zama a qarshe, ko yaya kace likita? Likitan yace, wannan hakane. Canjin rayuwa : 6�0⃣Ta girgiza kai, tare da dan yatsina fuska, sbd dan radadin da ciwonta keyi mata. Tace ban fahimta ba. Likita yace, kinsan za'a bi abin daki-daki ne. Farko dai zamu fara ta lafiyarki. Zanso ki bada hadin kai gurin ganin anyi jinyar ki cikin sauqi. Ki dinga cin abincinki, kina shan magani har a sallameki. Kinga wannan ne farko. Sai mu koma kan abu na biyu, bayan an. Sallameki ki zauna dashi tamkar 'yar uwa, kiyi haquri da duk abinda ya samo ya baki na abinci, ko na sutura, ki kuma nutsu, babu batun guduwa, don kamar yadda yace, zai zamar miki wa. Ko ince kun riga da kun zama daya ma, domin jininsa ne aka zuba miki yake hade da naki. Ta dago ido ta Kalli Ismael, sannan ta Kalli hannunta mai lafiyar. Ta runtse tafin hannunta tana kallon tsintsiyar hannunta, kamar mai kallon jinin yana haduwa. Likitan shiru yayi, daya ga tayi hakan, don yasan zantukan nasa sun shigeta sosai. Ta katsewa likitan tunani da cewa, Doctor in nayi haka fa? Ina nufin sai menene a gaba? Yace, sai batun raba auren ku dashi. Ismail yace, kuma in kin samu wanda kk so, ba zai hana muyi miki aure dashi ba. [8/24, 10:56 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�1⃣Da sauri ta Kalli Ismael. "Ni bazan qara soyayya ba. Nayi ta na gama, don na haqa rami na binne ta. Zan rayu ne ni kadai. Ismail yace, duk wannan babu matsala, matsawar zaki cika alqawarinki na qin guduwa ko ina. Ni kuma zanyi miki duk abin da kk so. Ta soma qoqarin zamewa don ta kwanta. Sai dai amma ta kasa. Likitan yace, yayanki ya taimaka miki? Tace a'a likita, bana so ya dinga kai hannunsa jikina. Likita yace, wannan babu matsala. Ya miqe ya nufi waje, nurse ya kira yace tazo ta taimaka mata. Sannan ya kira Ismail, zo mana, mu danyi wata magana. Sun jera tamkar abokai. Likitan yace, Ismail banaso ka damu da duk abinda Yarinyar nan zatayi. Ka ceci Rayuwar ta ta hanyar kyautata mata don kar tace zata sake guduwa. Kabi da ita ta hanyar da muka sata akai. Sannan kayi mata qoqarin nesanta ta da mahaifanta na wani lokaci, sbd a samu ta nutsu, ta kuma saba daku. Ismail yace, Allah yasa ta iya. Domin in kaji labarin gatan da take ciki zaka sha mamaki. Allah dai ya shige mana gaba. Doctor salis yace, Ameen. Sannan inason duk lokacin da kk buqatar taimakona a game da wannan matsalar taku, ka kira number ta, sannan ya ciro katinsa ya miqa ma Ismael, "akwai numbers dina a jiki, ko da bana nan a asibiti. Ismail yace, nagode sosai Doctor. Canjin rayuwa 6�2⃣Na'ima kuwa, yadda taga rana, haka taga dare, sbd mijinta yana samanshi tare da wata mace, wadda ba halalinsa ba. Tayi kuka ta gaji, idanunta sun kukkumbura sunyi jajur. Maimakon Na'ima ta tashi cikin darennan ta miqa kukanta ga Allah, madadin kukan da takeyi. Saidai kash ba zata iya yi ba. Tasan ma anayin hakan. Allah ka ganar damu, Ameen. Bata qara tsurewa ba saida gari ya waye kusan goma da wani abu tayi wanka ta fito. A tunaninta sun bar Gidan. Ta nufi kicin ne don tasa masu yi mata aiki su hada mata abin kari. Cak ta tsaya sakamakon ganin karuwar tare da angon nata suna hada abin da zasu karya. Batasan sadda zuciya ta kwashe ta ba, ta qarasa kicin din cikin fushi ta daqumi wuyan 'yar best din da Jennifer ta saka, tana kuka tana cewa, "zo ki fita a gidana, shegiyar karuwa. Saukar marin da taji ne ya sata sakin Jennifer cikin sauri, ta tallabe kumatunta. Ta kalli Abbas, wanda yake cewa, kinsan dawa kk son yin fada? In baki sani ba, to tsaya in sanar dake. Sunanta Jennifer kuma itace ta musamman dina. Ko da ace mimin da nakeso ce na aura, dole ta barni da ta musamman dina, bare ke wadda baki cikin ra'ayina! Karki sake ki sake kai wannan baqin hannun naki jikinta. Sannan ya juya gurin Jennifer, wadda ta koma gefe, ta 6ata rai matuqa, ya janyo ta jikinsa. Kar ki damu da wannan 'yar wahalar kinji ko? Banida lokacinta. [8/24, 10:57 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�3⃣Na'ima tace, cikin kukan takaici, Akan wannan zaka mareni? Yace kadan na miki na gargadi. In kin sake kuma, zaki bada bayani. Sannan ki fita anan, in mun gama, mun fita kina iya shigowa kiyi abinda zakiyi, haka Na'ima ta fita, ta koma daki, cikin nadamar auren Abbas. Bakin gado ta zauna, tare da daukar waya ta soma kiran layin momi, tare da fadin cewa, ko momy bata zo ta tafi dani ba, yau na gama Rayuwar gidannan. Momy tana dagawa, kafin Na'ima tayi magana, ta katse ta da cewa "ga daddyn ku kiyi masa sannu da jiki, kafin mu gaisa sbd Jikinsa yayi zafi yau. Na'ima ta fahimci tayi hakane sbd ta sanar da ita tana tare da daddy. Sbd batason daddy yaji wannan matsalar. Muryar daddyn ce ta katseta da cewa, "Na'imatu. Tace, Na'am daddy ina kwana? Yace lafiya lau Na'imatu, yaya kuke da maigidan naki? Tace, lfy daddy yaya jikinka? To da sauqi kenan za'ace tunda ina gd. Amma sugar din yaqi sauka sam. Tace to Allah ya sauwaqe daddy, sai nazo duba ka. Yace a'a Na'imatu karki soma fitowa da wuri haka, in dai ba mijinki bane yace kuzo tare. Tace to daddy, Allah ya qara maka lfy. Yace Ameen. ga Momyn taku. Ta amshi wayar, sannan ta nufi fita. Alhajin yace, kizo ki bani maganin. Tace to Alhaji ina zuwa. Alhaji bashir ya kwanta shiru, yana tunanin yadda sukayi da likitansa daya fita ynxun. Bayan likitan ya auna shi ne yace, "Alhaji meyasa sugar dinka bata sauka? Alhaji yace kuma ina qoqari gurin shan magani da kuma kiyaye duk abinda aka hanani. Doctor yace, to kuwa kana tare da wata damuwa. Saboda shima sugar haka yake, kamar hawan jini 6acin rai yana tayar dashi. Canjin rayuwa 6�4⃣Alhaji yace, ni bana tare da 6acin ran komai likita. Likitan yace, to ynxu zanyi maka allurar da zata saukar da sugar din inqha Allah. Sannan kasha wannan maganin. Ya dago daya daga cikin magungunan ya nuna masa. Sannan yace, Allah ya qara sauqi. Kuma yana da kyau kadan qara samun varci. Momy Nafisa ce ta katse masa tunani da cewa, "Alhaji ga ruwan kasha maganin. Ta dauki kwalin maganin ta bude masa tare da cewa, likita fa yace, ka rage wannan tunanin. Wai tunanin me kkyi ne Alhaji? Saida ya afa sannan yace, ko na fada bakida maganinsa. Amma ni burina ynxun in dan samu sauqi inje katsina. Inason ganin sauda sosai, don tana buqatar lallashina. Na tabbata ban kyauta mata ba. Nafisa ta ta6e baki, ka 6ata mata rai, ko mimi ta 6ata mata rai? Shawarata dai a gareka Alhaji. Ka kauda kanka ga komai din lafiyar jikinka ta samu. A tunanina tunda Na'ima ta share maka Hawaye, bai dace ka tsaya tuna wata damuwa ba, wadda zata hana ciwonka sauka, "hannu ya daga mata, alamun tai shiru. Sannan yayi mata alamun cewa ta fita daga dakinsa kurum. Rigingine yayi, tare da dora qafafunsa wadanda sukeyi masa zafi tamkar ana hura musu wuta akan filon, ya kalli qafafun nasa wadanda ciwon sugar din yasa suke masa radadi, ya mai da kansa gefe, yana tuna sai zuwa yaushe kenan zai rabu da wannan ciwon? Domin kuwa damuwa agurinsa ta zama dole. Bai ta6a tunanin cewa, don ya yi wa mimi abin da yayi mata zai dameshi ba. Duk da qoqarin da yakeyi na tanqwasa kansa don fada da zuciyar sa. Mimi ce dai, har ynxun sonta a zuciyar sa bai canza ba. [8/25, 8:47 PM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�5⃣Harma wani sashen na zuciyar sa yana fada masa cewa, bai yi wa 'yar tashi adalci ba, domin yasan har ynxun mahaifiyar ta kawai yake yiwa tsantsar SO. Sai yaji tamkar ya daga waya ya kirata, ko kuma ya tashi yaje gurinta. Amma in ya tuna qudirinsa, sai ya fasa, ya lallashi zuciyar sa da cewa, lokaci baiyi ba da zan nemeta. A fili yace, ynxun sauda ce babbar damuwa ta. Yakama in je inyi mata bayani, yadda zata fahimci dalilina. Ya karkata kansa, ya kalli wayoyinsa dake saman durowar gefen gadon. Cikin qarfin hali irin nasa, ya kai hannu, ya dauko qaramar ciki, wadda itace ya tanada don iyalinsa kawai, mata da yara. Ya shiga Numbers, sannan ya danna, kai tsaye yayi qasa, ya latsa masoyiyata sauda. Sunan da duk cikin matansa ba wadda bata nuna kishinta tsantsa akanshi ba. Domin su ya rubuta musu matata wance dukkansu. Yayi guntun murmushi sbd tuna hakan, sannan ya latsa kira. A ringing na uku, ta daga tare da yin sallama. Yayi shiru na kamar qiftawar ido, sannan ya amsa. Sakamakon duk lokacin da yaji muryarta, sai yaji wata nutsuwa ta ratsashi. Yace "sauda." tace Na'am Alhaji. Mun tashi lfy, ya kuma jikinka? Yace da sauqi sauda, amma fa ciwo yananan. Koda yaushe likita ya gwadani sai yace sugar yana qara sama. Kila ma ciwon bana tashi bane. Ji tayi wani abu ta tokare mata qirji, sbd fargaba. Tace Alhaji bakaje asibiti bane? Yace na gaji da zaman asibiti. Kinsan bayan taron nan, na kai kaina asibiti an bani gado. Tace ynxun a gd kk a kwance? Yace eh. Likita yana zuwa dubani. Kar kijini shiru sauda, kina raina. Da naji 'yar dama zanzo in wanke kaina a gurinki Canjin rayuwa 6�6⃣Zugum tayi tunda suka gama wayar da Alhaji. Kalmarsa ta qila ciwon ba na tashi bane ta tsaya mata arai. Ta san cewa, mutuwa dole ce, amma gsky batason rabuwa da Alhajin ta. Bata san yaya zatayi ba, in har hakan ta kasance. Kurum sai taji Hawaye na zuba daga idanun ta. Hasina ce ta katse ta da cewa, menene hajiya? Cikin sauri ta share hawayen, tare da cewa, babu komai hasina. Ta zauna kusa da ita, shine kk kuka? Ba kuka nakeyi ba Hasina, tunanin rayuwa nakeyi mai cike da canje-canje. Yau fari, gobe tsumma. Hasina bata fahimci hausar ba, don haka sai tace, sis mimi ce? Eh, kawai hajiya tace, don kawai Hasina ta rabu da ita. Miqewa tayi ta nufi gefen masu aiki, sbd aiken da zatayi ayo mata niqan dan waken da muktar ko Abba zai tafi dashi Abuja Anjima. Momy nafisa kuma, lokacin da taje dakinta ta saurari koken Na'ima sai tace, ta jira, bari ta bawa dadyn su magani. Bayan yace, ta fita ne ta koma dakinta ta soma kiran Na'iman. Cikin sauri Na'ima ta daga har lokacin kuka takeyi. Na'ima wai kkce Abbas ya mareki? Tace eh momy marina yayi akan karuwar daya kawo suka kwana tare. Gsky momy zan dawo gida bazan jure ma wannan cin kashin ba Allah. Momy tace, kai wannan abu ya isheni. Aure ko sati daya baiyi ba, amma matsalarsa tafi ta shekara daya. Amma ba komai, ki qara haquri. Zan turo Aminiyata anjima, zatazo da mayukan da kuma qwayar da zakiyi amfani da ita. Munyi waya tun jiya. Ni kinga dadynku ba zai barni in fita ba sbd baijin dadi, amma kome kenan ki fadawa hajiya nana din kinji? Na'ima tace to. [8/26, 8:37 AM] Inna👬 Habiba Sa'ad: 6�7⃣Suna gama wayar, ta budo grp chat dinsu na wtsapp. Qawayen ta suna ganinta tayi musu hello, shikenan suka shiga shewa. Ga Amarya! Ina ango? Amarci ya 6oye ki. A turo mana sababbin hotunan da aka dauka cikin amarci. Kowa da kalar tambayar da yake mata. Kasa cewa uffan tayi a group din sbd hawayen da suke zubo mata. A fili tace, da ace kun halin da nake ciki, haqiqa da baku tambayi Amarci ba. Tana kashe data dinta ta jiyo qwanqwasa qofa. Tayi kamar ba taji ba, sbd tana zaton ko sune da suka fita suka dawo. Kusan minti uku ana buga qofar, sannan ta tashi ta nufi qofar da zummar taga ko waye. Tana budewa, sukayi ido hudu da surikarta Hajiya Bilkisu da qawayen ta. Ta hau raba ido tana kallon su. Sannan tace musu, "sannunku da zuwa. Ku yi haquri. Wlh bansan ku bane. Hajiya Bilkisu ta harareta, cikin 6acin rai tace, "au dama in kinji a ta6a qofar bazaki bude ba, sai kin san ko wanene? Hum kuzo mu shiga hajiya ladi. Suka shiga Na'ima ta zauna a gabansu tana cewa, kuyi haquri momy. Sannan ta miqe ta nufi kicin don kawo musu abin sha. Zuciyar ta cike da nadamar rashin bude qofar akan kari. Hajiya ladi ta kalli hajiya Bilkisu, Yarinyar nan tanada tarbiyya kuwa? Hajiya zuwaira tace, banga alama ba. Hajiya Bilkisu tace, ai kuwa ba zan dauki rashin tarbiyya ba. Kusan minti uku muna buga qofa kina ciki kina yauqi, sai kace gidanki. Canjin rayuwa 6�8⃣Har Na'ima ta kawo musu abin sha da cincin, su diblan, da alkaki, irin wanda amare ke ba ma baqinsu, amma basu daina maganar ba. Kai kurum Na'ima ta sunkuyar, suka yi mata tatass. Har kuka saida tayi tana bashi haquri, amma basu daina ba. Sunyi kusan minti talatin, sannan suka ce zasu tafi. Har gurin mota ta rakasu, sannan ta dawo cikin damuwa da takaici mara misaltuwa. Alamu sun nuna sam ba zata ji dadin dangin mijinnan nata ba. Tun kafin motarsu tabar harabar gdn, hajiya ladi tace, hajiya Bilkisu gsky bakiyi sa'ar sarakuwa ba, alamu sun nuna zatayi rowa. Kin tuna lokacin da muka raka hajiya mairo gdn danta mansur? Wace irin kyauta tayi mata harda mu? Hajiya Bilkisu tayi tsaki. Abinda ke raina kenan ladi. Mu kanmu surukar hajiya mairo ta bamu turaruka masu tsada, ita kuwa lesuka ta bata da atamfa. Hajiya zuwaira tace, ko qannensa da sukaje yini, sai da ta hado su da kayan shafa. Gsky hajiya Bilkisu ki taka birki tunda wuri. Domin in kk bari wannan rowar da rashin son jama'ar nata yayi nisa, to kuwa nan gaba shi kansa dan naki, kina ji kina gani, zai tsani danginsa, ya kuma qanqame abin hannunsa. Ran hajiya Bilkisu ya qara sosuwa, ta ce, ina zai yiwu! Gobe zan turo su Aisha da samira, har Azima da jamil, in gani suma rowar zatayi musu. Hajiya ladi ta saka dariya, kinji hajiya Bilkisu, kema tayi miki rowa ballantana wasu yaranki? Kawai danki zaki tasa a gaba ki nuna masa cewa, yayi mata tarbiyyar kyuta da son jama'a tunda an kasa yi mata gidansu. Hajiya zuwaira tace, zancen kenan. Tafdijam! Wannan shine gaba kura baya damisa. Na'imar da bata samu kwanciyr hankali daga Abbas ba, ta yaya zata san yadda zatayi abida ya kamata? Muje dai zuwa. 6�9⃣Haka kuwa washe gari sai Na'ima ta sake jin bugun qofa, guraren qarfe dayan rana. Bata yi qasa a gwiwa ba, ta tashi ta nufi budewa don kar ayi irin na jiya. Su Aisha ne da samira da kuma Azima harda auta jamil. Cikin 'yar fara'a mai kama da yaqe tayi musu sannu da zuwa. Suma suka amsa cikin isa, musamman samira da Azima. Sun zauna, ita kuma ta nufi kicin don kawo musu abin sha da dan na ta6awa sannan ta sanar da masu aiki cewa, ga baqi a dora musu abinci. Taje ta kawo musu hotunan biki. Sannan ta zauna. Jin basu gaisheta ba tace musu, ina yininku? Suka ce lfy. Aisha tace, ina bros Abbas fa? Na'ima tace, ya fita tun safe, don tana daki taji fitarsa. Samira tace, sis Aisha kin manta jiya bros daya zo yace, zai koma aiki? Aisha tace, haka ne, Na'ima tace, eh ya koma aiki yau. Ta fadi hakane kurum, sbd kar su fahimci irin zaman da sukeyi. Sun wuni cur, amma bataji dadinsu ba. Komai cikin isa da nuna mata iyakar ta sukeyi. Sannan Abbas ya shigo kusan shida na yamma. Tana dag cikin daki tana jiyosu yana ce musu, kunci kunsha duk abinda kk so, ko kuma anyi muku rowar? Samira, wadda tafi kowa rashin kunya, tace, an ma isa? Bros muzo gidanka ayi mana rowa? Za ma mu jira kenan. Kowa abida take so, shi tasa masu aiki suka dafa mata. Yace, kunyi daidai. Bari inyi wanka inzo in kaiku gida. Aisha ce ta shigo tana ce mata. Bros fa ya dawo. Tace to, sannan ta taso daga kan gadon, ta nufi samanshi, cikin fargaba, sbd kar qannensa su fahimci wani abu. Canjin rayuwa 7�0⃣Ta tura qofar falon ta bude. Na'ima ta shiga cikin fargaba. Yana zaune kan kujera yana ciro wasu takardu daga cikin jakarsa. Tace sannu da zuwa. Baiji shigowar ta ba, sai magana kawai yaji. Ya dago a fusace, "lafiya? " A tsorace kuma cikin faduwar gaba tace, dama Aisha ce tace min ka dawo, kuma su baqi ne dai, kada su gane cewa akwai wata matsala Tsakanin mu. Ya watso mata harara. Don Allah fitan min anan! An dade ba'a gane cewa, Tsakanin mu akwai matsala ba. Waton ma jiya da Momyn mu suka zo shine kkyi musu wulaqanci ko? Na'ima ta riqe kanta sbd wani sarawa da yakeyi. Tace, ai dai na basu haquri ban zaci sune suka zo ba. Na zaci wannan matar ce data biyo ka. Yace, in itace sai kiqi bude qofa tunda gidan babanki ne? To bari in sanar dake, in baki sani ba, ta fiki matsayi. Ke har iko ta fiki a gidannan. Sbd haka kibi a sannu. Sannan duk lokacin da 'yan uwana suka zo wani yayi kuka dake, na rantse miki sai na zane ki. Fita! Wawiya kawai! Na'ima ta dubeshi rai 6ace, kai bakasan darajar dan adam ba. Ka sake ni kawai, don ba zan iya da wannan wulaqancin ba. Yace, fita nace kiyi. Da kuka ta fito, sbd 6acin rai har ta manta da baqin da suke gidan. Gadonta ta fada tana kuka. Samira, suka kalli juna da Aisha, lokacin da ta wuce su a falo. Har suka shiga dakin, sallar magriba tana kwance tana kuka. Aisha ce ta tambaye ta ko lafiya? Sam Na'ima bata tanka ba har zuwa lokacin da suka gama shirinsu suka ce, mun wuce, Na'ima bata daina kuka ba bare ta amsa.7�1⃣Sun isa gida cike da dokin labarin kaiwa mahaifiyar su. Aisha tana jinsu tana kallon su, samira Tana sanar da mahaifiyar su cewa, Bros Abbas yasa Na'imar kuka. Qila ma dukanta yayi. Azima kuma tace, sannan munyi abinda muka ga dama a gdn. Aisha tace, ku dai bakuda hankali, ina ruwan ku da kukan ta?shiyajiya Bilkisu tace, yayi min daidai! Ai shiyasa jiya daya zo na fada masa abinda tayi, sbd ya kwa6a mata. Samira tace, mu ma da zamu taho ba tace mana komai ba. Aisha tace, ku dai kuna da matsala wlh, ba kuga tana ta kuka bane? Tayi tsaki, ta miqe ta nufi dakinta. Ita dai ko a cikin ranta, bata so Bros Abbas yaci zarafin matarsa ba. Domin ta ba ta tausayi lokacin da take ta kukan. Na'ima kuwa kiran layin momy nafisa tayi, amma bata daga ba. Don haka sai ta tura mata saqon waya kan cewa, ita fa ba zata iya wannan auren ba. Domin mimi ba qaramar sa'a tayi ba, da bata kasance matar Abbas ba. Don Allah ki ceci rayuwa ta. Sam ynxun na haqura da son Abbas. Saqon yaje sama da minti goma sannan kiran momy nafisa ya shigo. Na'ima ta tashi zaune, ta tallafe kanta mai matuqar sarawa, sannan ta daga wayar, momy tace, Na'ima yaya ne? Na'ima ta soma kuka. Momy tace kashh! Ke kullum Sallamar ki kenan kuka? Sake dukanki yayi? Na'ima ta sanar da momy zuwan mahaifiyar sa da qannensa. Momy tace, tirqashi! Abin harda danginsa? Na'ima tace, momy kizo ki daukeni don Allah. Momy tace gobe zamuzo da hajiya nana. Na'ima tace, don Allah mommy kuzo. Tace karki damu zamuzo. Canjin rayuwa 7�2⃣Kwanan Zainabu biyu a asibiti, amma babu labarin alhaji. Innar ta kuwa taci bashi yafi na dubu goma. Sawunta hudu a gidan Alhajin, amma bata samunsa. Don haka sukayi shawara da aminiyarta yalwa cewa, in an sallami Zainabu su wuce da ita gida kai tsaye, in yazo ya biya kudin saita koma. Baban su Zainabu kuwa yaje ya duba ta sau daya, bai kuma komawa ba. Zainabu kuwa kuka takeyi akan ba zata koma ba, domin kwanakin nan da bata gidan, duk da cewa a asibiti take yafi mata zaman gidansa. Hankalinta bai sake tashi ba, saida 'yan gidan su Ismail suka zo duba ta, taji wannan fatu din tana cewa innar su wai sunzo duba matar Ismail ne tayi hatsari. Innar su Zainabu tace, ai yayi aure ne? Nan su fatu da sauran matan gidan suka soma ba innar su Zainabu labari. Ai maigidansa ne ya bashi 'yarsa, ita kuma bataso, ta gudu shine tayi hatsari. Daga nan Zainabu bata iya ci gaba da saurarensu ba, ta shiga rera kuka. Daren ranar bata runtsa ba, kenan Ismail yananan asibitin yana jinyar matarsa. Ita dai zata so ta sake ganinsa a rayuwar ta ko da daga nesa ne. Ta san lallai ta rasa Ismail tunda har yayi aure. Ta yi ta tuno kalaman da yake fada mata na irin tsantsar son da yake mata. Washe gari da safe innar ta taje famfo inda zata wanko 'yan kayan Zainabun, ita kuma zainabu ta sauko a hankali, ta dauki zani guda daya daga cikin zannuwanta ta yafa ta nufi fita. Matar kusa da gadonsu tace, ina zakije Zainabu, ko bandaki zaki shiga? Tace a'a zan dann tattaka ne, sbd jikina duk ciwo yake sbd zaman guri daya. 7�3⃣Ta fito tana tunanin ina zata nufa. Tafe take sannu -sannu tana 'yan waige-waige. Daga baya ta yanke shawarar tambayar dakin 'yan hadari. Dan haka sai ta tun kari wata nurse. Tayi mata sannu, ta amsa. Sannan tace, don Allah inane dakin 'yan hadari? Nurse din tace, mata ko maza? Zainabun tace "mata." Nurse din ta nuna mata. Zainabu ta nufi gurin a cikin zullumi kala-kala. Shin zata gashi ko ba zata ganshi ba? Matar tashi ta fi ta ko bata kaita ba? Ta shiga, dogon falo ne kamar nasu, kwakkwance da marasa lfy gado-gado. Tabi tana yi musu sannu, tare da tambayar matar Ismail, amma har ta gama dubawa bata ganota ba. Ta fito ta tafi tana waigen dakin. Yinin ranar cikin damuwa tayi shi, don ko 'yar shinkafa da waken da innarta kan siyo mata taci, yau kam kasa ci tayi. Da magriba, innarta ta nufi dan lungun da sukan shinfida tabarma suyi sallah. Ita kuma zainabu ta fito ta sake zuwa dakinnan na 'yan hadari. Bata shiga ta qofa ba, window qarshe ta nufa, ta dafa windon tana leqen mara lafiyar dake kwance a gadon. Zuciyarta ce ke zargin cewa, lallai wadda ke kwance a Gadon nan ita ce matar masoyinta. Bisa dalilinta na ganin cewa, kaf dakin itace yarinya qarama. Sannan da safe da tazo babu mai jinyar ta a gurin gadon su, sannan da tace mata kece matar malam Ismail? Kai kurum ta girgiza alamun a'a. Ita kuma sai take qara dogara da cewa, batason sa shiyasa shine dalilin da yasa tace a'a. Fatanta ace Ismael yana gurin ta samu ta dan ganshi ko zataji sanyi. Sai dai tana leqawa taga wata gyatuma zaune kusa da Yarinyar. Tayi ta leqe-leqe kusan minti biyar. Ko mai kama da Ismail bata gani ba. Taja silifas dinta zata tafi dakin. Daidai kwanar da zata kaita babban daki, inda suke kwance, sai ta hango Mahmud shida rabi'a, budurwarsa, don ta san ta, itama 'yar islamiyyarsu ce, sai dai ita, 'yar babban aji ce, ajin da Ismail ke koyarwa. Canjin rayuwa 7�4⃣Da sauri ta shiga kwanarsu ta juya baya, sam su basu ganta ba suka wuce. Ta fito ta bisu da kallo, yana riqe d kula ita kuma da leda mai dauke da lemu da ayaba. Wata zuciyar tace, ki bisu mana, kinsan dai babu gurin wanda zasu, sai gurin masoyinki. Da sauri tabi bayansu, sai taga sun nufi wata matattakala. Itama sai ta bisu har suka hau saman. Wata qofa suka shiga, dan tsayawa tayi kamar mai tsoron binsu don batasan yaya cikin qofar da suka shiga take ba. Sai kuma taga ashe dogon guri ne mai dauke da dakuna. Can ta hango su sun kusa kai qarshen dakunan. Don haka ta shiga itama cikin azama. A tsorace take tafiya har takai gurin da Nurses masu kula da wannan sashen suke zama. Yadda take tafe tana waige-waige ne yasa wata nurse tace, ke ina zakije? Nan Zainabu ta daburce, ta soma inda-inda, "am zan..zanje can ne. Yin me? Nurse din ta katse ta. Duba mara lafiya zanyi. "ya sunan wadda zaki duba? Zainabu ta sake rudewa, ni ban..bansan sunanta ba. Nurse din tace, daga ina kk? ynxun bama yarda da mutane, sbd rashin gsky yayi yawa, don ko jiya an saci Jariri a dakin 'yan tiyata. Zainabu ta firgita. Nima nan nake, can dakin 'yan 6ari aka bani gado. Dan uwana ne matarsa take nan tayi hadari. Shi sunansa Ismail. Nurse tace, ok na gane shi, wani ustaz haka ko? Zainabu tace eh, shine. Ta nuna mata, ga dakin can na qarshe. Zainabu tace, nagode sannan ta sauke ajiyar zuciya.7�5⃣Cikin fargaba ta doshi dakin. Zuciyar ta tana tambayar ta me zata ce, in ta shiga? Ta kalli jikinta, dube ni sai kace wata tsohuwa. Gabanta yana tsananin faduwa, don haka sai ta fasa shiga, ta window taje ta leqa. Tana iya hango Mahmud da Ismail suna zaune bakin wani gado. Rabi'a kuma ta zauna kan kujera ta kare fuskar mara lafiyar. Sai dai tana ita kallon qafafun mara lafiyar akan gado. Zuciyar ta ta tsananta da bugu, sakamakon Ismail data gani, hawaye suka soma sharara akan kumatunta. Can kuma sai taga Ismail din ya bude kular da ta gani ahannun Mahmud ya zuba acikin plate. Bata dai san ko menene ba. Tana kallo, yazo ya dagata ya jingina. Tana ta son taga fuskarta, amma gashin kanta mai tsawo ya bazu ya tare. Rabi'a ta tashi, shi kuma ya zauna yana bata a baki kan bencin dake gurin. Ta koma ta zauna kuka sosai takeyi. Daga bisani ta miqe, ta tafi tana kuka. Bata damu da mutanen da suke kallonta ba. Wasu a zatonsu ko mutuwa akayi mata, sai suce, "Allah sarki! Allah ya jiqan rai. Tana saukowa taci karo da innarta tana nemanta. Tace ke ina kk shiga ne, inata nemanki? Zainabu bata kulata ba, ta wuce. Tsakiyar gadon ta zauna tare da dora kanta akan gwiwoyinta. Matar kusa dasu tace, wai Zainabu lafiya kk wannan kukan? Yau tun safe kk cikin damuwa. Innarsu ta qaraso. Wai Zainabu daga ina kk da kuka? Cikin kukan take cewa, an cuce ni an hadani da namijin da baisan darajata ba. Tunda nazo asibiti ko sau daya bai leqo ba. Canjin rayuwa 7�6⃣Innar taja tsaki, tare da ce mata, sai ki tona ma kanki asiri kowa yaji. Ai duk laifinki ne tun farko da kk qi nuna masa so. Zainabu tace, to ni bana sonshi, kuma bazan koma gidansa ba. Inna tace, sai kiyi tayi. Ga faten doya nan da mai wancan gadon ta sammiki. Cikin takaici tace, bana ci. Innar tace bari inci, dama ba qoshi nayi da tuwon da wannan ta kusa damu din ta bani ba. Zainabu ta zame ta kwanta, idanunta na qara hasko mata Ismail dinta ke baiwa matarsa abinci a baki. Ta tabbatar da irin son da Ismail yake yi mata, da ace ita ce, qila ma sai ya tauna a bakinsa zai bata. Tuno durowar da ake dora abubuwan ci na dakin dasu Ismail din suke tayi shaqe da abubuwan ci. Gashi a daki na musamman. Su kuwa abincin da zasu ci ma sun rasa mai kawo musu, sai dai maqotansu na kwanciya su sam musu. Da wannan takaici Zainabu tayi varci mai cike da mafarkan masoyinta Ismail. Mahmoud ya kalli rabi'a kinyi qoqari domin mara lafiyar nan bata ci komai ba tunda tazo asibitinnan sai yau da kika kawo mata. Azaton Mahmud Ismail baijishi ba yanayin jinjina ne ga masoyiyarsa. Sai kurum yaji Ismail ya cafe da cewa, ni kaina na jinjina miki rabi'a domin a tarihin mami abincinki ta fara ci. Sai dai abinda basu sani ba mimi mayyar kifin ruwa ce, kuma farfesunshi rabi'a tayo da alayyahu. Haka nan ta dai yo ne don batasan me zata yi ta kawo ba. Yayanta masunci ne, in yayo fatsa yana saida ma masu suyar kifi. Shine tace ya dan sam mata zata girkawa mara lafiya. Sai gashi ta kawo a daidai. Mimi dai tana jinsu bata ce komai ba, sai data qoshi sannan tace, ya bata ruwa. Tasha sannan tace zata kwanta. 7�7⃣Tun lokacin da likitan ya taimaka masa suka shawo kanta bata qara yi masa gaddama ba sai dai kuka. Sannan bata magana sai in tana da buqata. Ko da suka tafi zariya shi da Mahmud ya barta tare da yaya Amina da suka dawo ta fada masa cewa, batayi kuka ba hakanan ta yini shan ruwa, kuma sun saka mata pampers ita da wata nurse. Harma mimin tace, su sake canza mata rigarta. Yaji dadin sannan ya dawo da murna sun samu admission islamic ya nema. Mahmud kuma sai suka bashi English baiso ba amma hakanan ya haqura. Mahmud sun kai kusan qarfe goma sannan suka fito, Ismail ya rakosu, saida suka hau mashin din Mahmud sannan ya dawo. Sannu yayi ma wadannan Nurses din na gefensu da zai wuce, sai dayar take tambayarsa dazun wata 'yar uwarka ta gane gurin ku ko? Ismail yace, da yau she kenan? Tace dazun nan kuma nice nayi mata kwatancen dakinku. Ismail yayi shiru kodai rabi'a ta gani da Mahmud. Yace ita da Abokina dinnan ko? Nurse tace, a'a ita daya ce tace, tana nan asibitin ne dakin masu 6ari. Ismail ya girgiza kai. Gsky babu wanda yazo. Dayar nurse din tace, naga lokacin data dawo tana kuka, sai nayi zaton tana tausaya ma wadda ba lfy dinne. Ismail ya sake dawowa kusa dasu. Tace kuma mu take nema? Nurses din Sukace, sunanka ma ta kira. Yace to gsky bata zo ba. Suka ce. Shikenan. Mu dama munga har kwatancenka anyi mata tace kaine. Canjin rayuwa 7�8⃣Yace to bari inje qila bayan mun fita ne tazo. Shiru sukayi masa don sun kasa fahimtarsa, kamar yadda shima ya tafi ba tare da ya fahimcesu ba. Ya shiga dakinsu ya isa gadon mimi, ya leqa fuskarta har lokacin idonta biyu. Yace, mimi bayan fita ta anyi wata baquwa? Tace A'a sai dai ina neman wata alfarma guda daya. Ya zagayo saitin fuskarta."ina saauraronki" yadan rusuna sbd Mimi bayayin magana da qarfi dama ita. Tace, banason ka sake cemin mimi, sbd sunan yana tunamin da gidanmu. Idanunta sukayi narai-narai. Ya girgiza kai, a hankali yake magana tamkar rada wane suna kk fi son in kiraki dashi? Tace, khadija kadai ya isheni. Yayi murmushi. Nima zanfi so ince miki khadija. Sbd suna ne mai dadi da ma'ana. Allah yasa halayenki su rikide su koma irin nata. Ta kalleshi, idanunta sun nuna alamun son qarin bayani. Yace matar manzon Allah ta farko sunanta kenan, kuma itace mace ta farko data soma kar6ar musulunci a tarihi. Ta sadaukar da dukiyarta sbd addinin musulunci. Sa'annan itace ta haifawa ma'aiki 'ya'ya guda shida. Kinga ko anan aka tsaya ta kai daraja. Mimi ta lumshe ido, ta bude bata ce komai ba. Cikin zuciyar ta taji dadin jin asalin sunanta a takaice. Shi kuma ganin bata yaba ba, sai yace aransa, ashe wannan fa bata san kan musulunci ba. Allah yasa ta san wadanda nake magana a kansu. Ya dago ya dubeta. Kin fahimci wadanda nake magana akansu? Ta dubeshi da sauri, sai kace ba musulma ba? Duk wanda aka haifa a cikin musulunci, kai ko ba musulmi ba yasan mai tsira da Aminci. Canjin rayuwa 7�9⃣Ismail yayi murmushi mai sauti, sbd shi in har za'a yi hira akan addini yana Jindadi. Sannan yace, nasan kinsan shi mana. Na zata dai baki fahimceni bane. Kinsan tarihinsa ai? Tayi shiru don bata sani ba. Yace inada wani littafi da wani malamn sunna Mutumin kirki ya fassara shi zuwa hausa da turanci, zan kawo miki in naje gida. In kin karanta aciki zakiji tarihin Annabin Rahma, da iyalansa, da nasabarsa, zuwa jarumtarsa har zuwa mutuwarsa. Har lokacin bata ce masa qala ba. Ya sake cewa, in kin gama dashi zan sake baki wadansu littattafan ki karanta na Addini. Zasu taimaka miki wajen fahimtar me musulunci ke nufi. Tsaki taja, sannan tace, kana nufin can dama bansan komai a musulunci ba? Yace ba haka nake nufi ba. Tace shikenan, ni inason ka fadama doctor na gaji da qafafuna a haka ni kam a sauke min qafafuna daga wannan sagalewar na kasa varci. Yace, to zan fada masa. Amma ynxun kiyi varcinki. Shiru tayi masa. Bayan ya idar da sallar nafilolinsa cikin dare, sannan ya nufi gadon mimi yayi mata addu'o'i ya shafa mata, sbd yau ya manta bai mata ba har varcin farko ya daukesh. Sannan ya koma kan gadonsa ya kwanta yana tunanin rayuwa mai juyi da canji a kowane lokaci. Tunanin wadda akace tazo nemansu ya fado masa, to ko wacece? Ko kuma cikin 'yan uwanta ne? Haka yayi ta tambayar kansa amma babu amsa. Sai kuma yaya Amina ta fada masa cewa, dasu inna suka zo tare da matan yayyinsu sunce zasu je su duba Zainabu. Sai yake cewa, lallai kuwa yaga innarta da yalwa Aminiyarta anan asibitin, to me ya samu Zainabun? Yaya Amina tace, oho. Kai ina ruwanka ma da wata Zainabu tunda matar wani ce? Yace hakane. Daganan abubuwa sukayi yawa, bai sake tuno da batun ba sai yanxun. Sai dai duk da haka bai kawo ko a ransa cewa, Zainabu ce tazo nemansu ba.8�0⃣Yaya Amina ta shigo, lokacin likitan da yayi dori yazo, kuma yace, komai yana tafiya daidai. Sannan yasa an cire mata qafafun sai aka dora mata su kan filo. Sannan yace, bayan sati biyu in ya dawo sai ayi hoton qafar sbd a gani ko qashin ya hadu da kyau. Mimi tace, yaya don Allah za'a iya yimin wanka? Yaya Amina tace, ki qara haquri mim.. Ismail yace, "yaya ta ce batason mimi dinnan, a kirata da khadija. Yaya Amina tace, tanada gsky. To khadija kiyi haquri zuwa dan kwana biyu, kada muje wanka wanka muyi fami. Ba ga shi kullum inayi miki gugar jiki ba? A jikinki babu datti. Takai hannu ta ta6a gashin kanta ta sunsuna. Allah yaya, sai inji kamar ina wari, har ta gashin kaina. Yaya Amina tace, bakya warin komai khadija, don dai kina da son wanka ne. Mimi ta lumshe ido tana tuno gidansu da sasanta da dakinta. Ta tuno gatan ta. Sai kurum taji Hawaye suna bin kumatunta. Ismail ya dawo kusa ita yace, haba khadija. Menene na kuka kuma a batun wanka? Wannan fa duk anayi ne sbd lafiyar ki, garin wanka in aka turgude qafar ko hannun, kinga sabon dori ya samu kenan ko? "Don Allah malam ku barni inyi kukana, sbd in nayi ne nakejin sauqin abubuwa. Ba wai inayi don na raina qoqarinku bane, ina yi ne sbd ya zama dole inyi. Yaya Amina tace, ki dinga sassauta wa zuciyar ki dai domin wani ciwon zai shigar ki. Canjin rayuwa 8�1⃣Ismail ya miqe "yaya ni dai bari in barki da 'yar rigimar nan taki inje gd inyi wanka. Sannan zanje gurin malam Aminu. Su Mahmud dazun ya kira ni wai lallai yana nema na. Tace to sai ka dawo. Amma fa kar ka taushe hannu sbd yau waina nakeson yi, zan koma gida da wuri. Ismail yace, zan dawo da wuri insha Allah. Ya kalli mimi, khadija bari inje in dawo, ko kina son wani abu inzo miki dashi? Ta girgiza kai alamun a'a. Taci taci gaba da kukanta. Yace, shikenan sai na dawo. Yasa kai ya fice mimi ta qara sautin kuka. "yaya malam ya saba da ganin kukana, ya daina lallashi na ynxun. Yaya tace a'a bayason kukan ne, shiyasa. Kuma gashi inya lallasheki bakyayin shiru. Ai khadija a rayuwa in akace maka kayi haquri, to kayishi. Karka ce wai kai zakayi tayi, mai lallashinka sai ya gundira. Mimi tayi shiru. Can tace, Yaya wai kuma baku da 'yan uwa ne? Tace me kk gani? Tace naga ku kadai ne kuke zuwa. Yaya Amina tace, muna dasu khadija, amma dai basu damu damu ba. Ni da Ismail ne muke uwa daya. Nan ta ba ta labarinsu. Bata 6oye mata komai ba game dasu. Mamaki ya cik mimi, tace dama ana samun haka? Ni kam kishiyar mama na har tafi mamana sona. Ynxun haka nasan tanaa cikin damuwa. Yaya Aminu tace, bana zaton akwai wanda zaifi uwa son 'yarta. Khadija duk inda mahaifiyar ki take a ynxun tafi kowa tashin hankali, sai dai in qila ita mai kawaici ce. Soyayyar uwa da 'ya na daban ne kinji. Amma zaki gane haka nan gaba. Mimi tace, ko qawayena sunsha fadamun haka, amma har yau ban gamsu ba. Yaya Amina tace, to ke dame kk dogara wanda har yasa kk ganin mahaifiyar ki bata sonki? Mimi tace, zan baki labari, saina qara jin sauqi, amma ina da hujjoji masu yawa. Canjin rayuwa 8�2⃣Shi kam Ismail har ya Sauka samansu, ya dauki hanyar fita, sai ya fasa, ya dawo ya nufi gurin saida magani domin ya amshi canjinsa. Tun kafin ya qarasa dan windon da zai amshi canjin nasa, sai ya jiyo muryar innar Zainabu tana cewa, ni kudina sun qare banida sauran ko na mota. Wani yace, ina ruwanmu da qarewar kudinku. Kuma bamu damu ku sai mata magani ba. Mu dai ku bamu kudinmu, ynxun da wannan abokin aikin nawa bai ganku ba, da ynxun kun gudu. Ismail ya qarasa gurin su daidai lokacin da innar su Zainabu take cewa, nima ba laifi na bane, Alhaji ne baizo ba. Dayan yace, ku kirashi a waya mana babu inda zakuje. Ismail ya miqa wa Mutumin hannu tare dayi masa sallama suka gaisa, sannan ya kalli Inna wadda tunda ta ganshi taji kunya matuqa, kamar tace, qasa bude in shige. Yace, inna lfy kuwa? Tace lfy qalau. Dayan yace, kawai inna ki fada masa gsky. Kanaji ko malam. Wannan matar tun ranar da suka kawo 'yarsu aka bata gado, bata biya kudin gadon ba, sannan akwai cikon kudin magani, wanda zata bada ciko, amma taqi, kullum sai tace, sai alhaji yazo. Yau likita ya ba sallama kurum, sai dai wannan abokin aikin nawa ya ganta a bakin Gate zasu hau tasi. Kaga mu taja mana kenan, ace mu muka cinye kudin. Ismail yace, nawa ne kudin? Inna cikin kunya tace, umm ai da ma ka barshi kawai, Alhajin dama yayi tafiya ne shiyasa. Mutumin yace, inna ki bari kurum a biya muku. Ba wani Alhaji, kullum kina zaizo, amma shiru. Ya kalli Ismail, dubu biyar. In kuma za'a basu ragowar maganinsu, dubu shida da dari uku da saba'in. Ismail ya saka hannu cikin aljihun wandonsa ya ciro 'yan dubu dubu ya miqa musu dubu shida. Sannan ya ce, jiya canji na nawa na bari anan? Dayan yace dari bakwai da hamsin. Ismail yace, ku cire cikon ku bani sauran canjin. Kanta a qasa tace, an gode Ismail. Ta juya zata tafi, suka ce, ki tsaya mana ki amshi sauran magungunan da kuma takardar shedar biya. 8�3⃣Ismail ya amshi canjin sa, sannan ya kalli innar Zainabu, "Allah ya qara sauqi" bai jira amsarta ba, ya wuce. Ita kuwa dama kunya ta hana ta amsawa. Zainabu ta nufo gurin, sbd itama tasa baki, ko zasu yarda za'a kawo musu daga baya. Sam basuga juna ba, saida suka zo daf. Itace ta soma ganinsa. Tsayuwar da tayi ne yasa shi ganinta. Tayi sauri ta juya baya. Ismail ya runtse ido ya bude. Gabansa yaci gaba da faduwa. Shima yayi saurin dauke idanunsa daga kallon bayanta. Da qyar yace, "yaya jikinki? Tace, da sauqi, cikin rawar murya dake dauke da kuka tayi magana. Yaya taka mai jikin? Ya dubi inda take, a ransa yace, ashe taji. A fili yace ta samu sauqi. Yaja qafafunsa wadanda sukayi masa nauyi yace, sai anjima. Ta bishi da kallo bayan ya wuce. Sam ta kasa ko motsi, sai kuka har innarta ta iso tana tambayarta lafiya? Zainabu tace, an cuce ni. Dajin haka innar tasan Zainabu taga Ismail. Cikin borin kunya tace, "kina ta an cuce ki. Matar mutum ai kabarinsa ko? Ki barshi a qaddara. Zaizo ya sameni shi kuma Alhajin. Ya sanni, ni walki ce ina daidai da qugun kowa. Zainabu dai bata tanka ba, sai ta fita abinta. Tunda suka koma gida ko yaushe Zainabu tana cikin qunci da kuka. Musamman da innarta ta fada mata cewa, Ismail dinne ya biya kudin gado. Innarta tanason Alhajin yazo ya biya kudin da suka kashe, indai yanason zama da Zainabu. Ita kuwa Zainabu ba haka nata tunanin yake ba. Jiran Alhajin takeyi. Ko nawa zai kashe, batajin cewa, zata koma gidan Alhajin. Canjin rayuwa 8�4⃣Ismail ya jima zaune akan katifarsa kafin ya tashi ya dauki bokitinsa ya nufi cikin gidan, suna ta nasu harkoki. Yayi sallama suka amsa sannan ya gaidasu, ya nufi dakin Inna, tana ta gyangyadi, ya gaida ta. Ta tambayi mai jiki, yace, da sauqi, tace kai dama ashe Yarinyar nan ba sonka takeyi ba? Ismail yayi murmushi, tare da cewa ai wannan ya wuce Inna. Ya miqe ya nufi bandaki. Tace, haka dai kk kullum ba'ajin cikinka. Jeka can ka qarata. Bayan ya fito ne yaga wata yayarsu tazo ya gaida ita, zai wuce, fatu tace, kin masa jaje kuwa? Yaya shafa tace, meya faru dashi? Fatu ta tuntsire da dariya. "huce haushi akayi masa da mace. Ashe bata sonsa ta gudu, sai kuma tayi hadari a hanya. Shafa ta kalli Ismail wanda shi yana daf da zaure tace, to ashe haka akayi Ismail? To Allah ya kyauta. Yace, Ameen tare da shigewa zauren. Ya gama shirinsa tsaf cikin yadi mai kalar sararin samaniya marar nauyi. Ya saka hula sannan ya feshe jikinsa da turarukansa na musamman da yake hadawa a gurin masu saida turaruka sannan ya fita ya nufi gidansu Mahmud don amsa kiran malam Aminu. Da Mahmud ya soma haduwa, sai dai irin fara'ar da ya gani a fuskar Mahmud din ta bashi mamaki. Yace, malam ko anyi maka baiko da rabi'atu ne? Mahmud yace, qila da hakan ne zaiyi wuya ka gane a fuskata. Gara ma inda ranar daurin auren ce. Ismail ya dafashi, to sanar dani mana game da farin cikinnan naka? Mahmud ya kama hannun Ismail. "Zomuje kaji daga bakin malam. Tunda na iya jure daren jiya dana samu labarin, na jure safiyar yau, to kuwa zan jure ynxun muje kaji da kanka. Na yafe goron albishir din.8�5⃣Cike da fara'a suka gaisa da malam yace, malam Ismail yaya mai jiki? Jiki da sauqi Alhmdlh. Malam yace, masha Allahu. Ka samu labari daga bakin dan uwanka ko? Cikin zaquwa yace, bai fadamun ba malam. Yace, inji daga gareka. "malam ya fadada fara'arsa, sannan ya kalli Mahmud dake zaune gefe, yana murmushi, ya maido da kallonsa ga Ismail, "Scholarship dinku ya samu. Shekaran jiya malam mukktar yazo ya sameni da batun. Don haka sai ku soma shirye-shirye, nan da wata daya Matsalarmu kudin da zakuyi amfani dashi. Ismail yayi mutuwar zaune, jinsa yake tamkar a mafarki. Wai malam madina yake nufi ko zariya? Da darsuwar wannan zargin, sai ya kalli malam. "Malam wai madina dinne? Malam yayi dariya, ka samu nutsuwa Ismail, madina ce zaku tafi, kaida dan uwanka. Saiku soma shiri, tare kuma da neman kudin da zakuyi 'yan abubuwan daya kamata. Sam Ismael baisan lokacin daya rungume malam ba. Sunyi murna sosai harda sujjada don nuna godia ga ubangiji. Ismail ya soma tunanin wa zai soma fada mawa? Duk lokacin da wani abin farin ciki ko baqin ciki ya sameshi, sai ya tuna mahaifinsa, 'yar qwalla ta taru a cikin idanunsa, amma sai ya daure ya cije. Yace musu bari yaje ya fadawa yaya Amina da mutan gidansu. Mahmud yace, to sai ya shigo anjima, a gaida 'yar amana. Ismail yayi murmushi, "zata ji." Canjin rayuwa 8�6⃣Sam ya manta da Damuwar Zainabu daya baro asibiti da ita. Saida ya idar da sallar azahar sannan ya nufi cikin asibitin, zuciyar sa fal da murna. Yana shiga yaya Amina tana nunke sallaya, ta idar da sallah. Ismail yana shigowa sai ya rungume ta, ta tsorata sbd bata ta6a ganin haka ba. Ya sake ta yana dariya, "naga kin tsorata?" Tace ai dole Ismail ban ta6a ganin haka ba. Yace, zamu tafi karatu madina, nida Mahmud. Yaya Amina ta sake rungume shi, cikin tsananin murna tace, Allah da uwana? Allah mun gode maka. Sai kuma ga hawaye suna zubar mata. Ya ciro hankici yana share mata hawayen. Ba ason kuka a cikin murna yaya, cewa zakiyi "Alhmdlhi llazi bini'imatihi tatimmussalihat. Ta maimaita abinda ya fada, sannan sukayi murmushi. Ta kalli mimi. Wadda take kallonsu, kinji ko khadija? Mimi tace, Allah yasa alkhairi. Ismail yace, Ameen. Sannan suka zazzauna yaya tace, to ya batun karatunka na nan? Yace yaya ai kuma ba wannan zancen. Tunanina ina zamu samu kudi sbd tafiyata da kuma sauran hidimomi. Yaya tadan yi shiru, can tace "to ko daura zamuje wajen su kawu a saida gonarmu ta gurin mamarmu? Ismail a'a yaya gonar fa ba ta ni kadai bace, gaki kuma kema mai buqata ce. Yaya tace, ko ni na siya da kudina bazan sadaukar maka da ita ba, balle gadonta mukayi. Haba dan uwana abin duniya fa na duniya ne. Ya kama hannunta "nagode yaya, Allah ya kaini lokacin da zanga nayi miki fiye da abinda kikai min. Tace Ameen Ismail, in jikin khadija ya qara sauqi sai muje dauran ko? Yace to hakan za'a yi. Dama basu san komai game da auren nan nawa ba. Sai kuma sai kuma ya kalli mimi, tunda ba wai lallai auren ya dore ba, mubarsu kawai. Yaya ta gane yana fadin hakane don kar mimi taci gaba da rikicinta. Kafin kwana goma labarin tafiyar su Ismail ya zaga dukkan 'yan uwa da abokan arziki, sai murna akeyi wa Ismail da Mahmud. Mimi kuwa jiki ya soma sauqi, gashi tanacin abinci amma fa rabin abincinta kifi ne.8�7⃣Hajiya sauda ta shiga damuwa sakamakon rashin samun Ismail a wayarsa. Ynxun ma da take zaune saida ta dauko wayarta da zummar ta sake gwadawa, kamar wasa sai layin ya shiga. Cikin Jindadi tace, Alhmdlh. Lokacin Ismail yana zaune yana 6are wa mimi lemun zaqi, ya daga ne ya kalli mimi, wadda ta qosa tasha lemun. Yace, ina zuwa. Ya fita cikin sauri. Suka gaisa, sannan yace, hajiya kwana biyu? Tace layin ka baya shiga. Yaya mai jiki? Yace da sauqi sosai hajiya. Ina tsammanin matsalar ntwk ne, amma wayata a kunne take, kuma akwai charge. Tace sauqi na samuwa sosai ko? Ismail yace, tunda tana dai kar6ar abinci. Hajiya sauda tace, to mun gode Allah, sannan ina qara jaddada maka amanata, sannan ina qara baka haquri. Na sani zakaga abubuwa gurin mimi. Ismael yace, don wannan karki damu hajiya. Sannan ina godia kan kudin da aka turo. Tace, karka damu wannan ba wani abu bane. Zan sake turo ma wasu insha Allahu. Daganan sukayi sallama. Ya dawo ciki yaci gaba da 6are lemunsa. Sai da ya gama ne, ya kalli mimi tare da cewa,, qanwatah ga lemun. Fuskarta daure tace, bana sha. Sbd me? Ya tambayeta cikin sauri. Tace, saida ka gama yin wayar, sannan zaka 6are min, alhalin tun tuni nace zansha lemu. "cikin irin shagwa6arta data zame mata jiki tayi maganar. Sannan qasa qasa don ita mimi ko yaushe maganarta qasa-qasa ce. Ya matsa kusa da ita haba qanwatah waya nayi. Ta harareshi, bana son ana hada uzuri na dana wasu. Inka gama nawa sai kayi na kowa. Yayi 'yar dariya sbd yadda ya lura itafa iyakar gskyrta take magana. Yace, shikenan ranki ya dade. Ko wane lokaci uzurinki zansa a gaba. Tashi kisha lemun to. Tace ya fita raina. Barci nakeso inyi ynxun. Ya kalli lemun na hannunsa, sannan ya ajiye ya gyara mata kwanciya, tare da cewa, ayi bacci lfy. Canjin rayuwa 8�8⃣Ismail shida yaya Amina sun tafi Daura sbd maganar saida filin mahaifiyar su na gado. Hannun Ramatu Nurse Ismael ya bar mimi. Domin yace, komai dare aranar zai dawo ba zai kwana ba. Mimi kam ko amsa shi batayi ba, lokacin da yake yi mata saiya dawo. Ya gama karantar halin mimi tsaf, dan zaman da sukayi tare, shirunta na nuna taji haushin tafiyarsa. Bai damu ba, nasa ganin tafiyar itace zata kawo masa qarshen tunanin, ina zai samu kudin tafiya jami'atul madina. Sun samu tarbar mutunci da qauna, kamar yadda aka san dangin uwa. Sannan sunyi murna dajin batun tafiyar Ismail qasa mai tsarki don yin karatu. Haka nan sun jajanta masa batun hadarin matarsa da suka basu labari. Sannan sunsha alwashin zuwa su dubata. Kawunsu yace, shikenan nan ma in za'a zo sai a taho da kudin tunda yau za'a sata a kasuwa. Qarfe takwas da rabi Ismail ya iso katsina, yabar yaya Amina a can zatayi kwana biyu. Ya nufi gida kai tsaye, yayi wanka yasa jallabiya mai ruwan siminti, sannan ya nufi asibiti. Sai da yayi mata tsarabar kifi, sannan ya qarasa asibitin. Kuka sosai ya sameta tanayi idanunta jajur. A rude yake tambayarta abinda ya sameta. Bata tanka ba. Yace, to ga gasasshen kifi na siyo miki, nasan zaki ci. Ya duba cikin kular da yaya ta dafo mata abinci kafin su wuce, ashe faten wake ne da kifi, amma bata ci ba. Ya dawo ya zauna bakin gadon. "Kar dai duk yau bakici abinci ba? Ta kalleshi idanunta jajur, "yau na yarda banida kowa, muryarta tana rawa irin na wanda ya gaji da kuka. Yace me akayi miki khadija da bana nan? Fadamin. Kuma karki sake cewa, bakida kowa. Gaki da ni, ga yaya Amina, muma da mu biyu ne, amma ynxun kinga mun qara mun zama mu uku. Mun tafi da tunanin ki. Ya warwaro tissue ya soma share mata hawayen. Sannan ya dauko kifin ya soma bata a baki sala-sala tare da jajjagaggen kayan miya. Taci sosai, sannan ya debo ruwa ya kawo mata, ya taimaka mata ta wanke hannu da kuma baki. Sannan yace khadija tunda ynxu kina iya zama zaki iya yin sallah. Ta 6ata rai. Yace wai meyasa duk lokacin da nayi miki zancen sallah, sai ki 6ata rai? Tace to yaya zan iyayin sallah a haka? Yace, zaki iya mana. Shi addinin musulunci sauqi ne dashi, ya nuna mana yadda zakayi ibada matsawar kana cikin hankalinka. Ita kuwa sallah sbd muhimmancinta, ko a filin yaqi anayin ta. Tace, ni ynxun dai ka barni barci zanyi. Ya ce, kinada yaqinin daga varcinnan zaki farka? Tayi shiru, yace bakida yaqinin cewa, zaki farka, kuma zaki iya farkawa ki ganki a kabari. Tace, oh Allah na, don Allah kabar zantukannan. Yace assha! Assha! Ina tsoron kar zuciyarki ta kamu da mugun ciwo, wanda batason ko kadan taji an ambaci Allah ko manzonsa, ko wani abu na addini. In hakane kuwa lallai kin daura qawance da shaidan, kuma yaci galaba akanki. "Don Allah ka barni mana! Ga mamakinsa, sai yaga ta soma kuka, shiru yayi, ransa 6ace. Lallai akwai matsala babba, akan zancen addini mimi ke kuka. A fili yace "akwai aiki!. Canjin rayuwa 8�9⃣Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za'a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za'a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. "kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na'ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na'imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, "ke da Allah natsu! Na'ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.9�0⃣Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar 'yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba'in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na'ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. "Na'ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. 'yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na'ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na'ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Canjin rayuwa 8�9⃣Hajiya Nana tace, Nafisa in har zaki fitar da kudi gurin shawo kan yaronnan, ba zai zama matsala ba. Nafisa tace, haba Nana kamar baki sanni ba, in ta samu kan yaronnan koni sai na qara haskawa a idon babansu bare ita. Kin sani ban tausayin kudi a gurin kashewa, ynxun dai fada min me za'a yi? Hajiya Nana tace, tsabar katan qamshi za'a hada masu fizgar hankali. Sai yabi ta ko ba don Allah ba. Ba sai ta shafa wani man bilicin ba. Tashi muje gidan Hajiya Hauwa. Naje naga kayan, daga kaduna aka turo mata su jiya, lokacin ina gidan nata. Dandano ta bani na shafa, amma Alhaji, yadda kk san ya zauce. Surutai kuwa daya dinga zubowa, wane yayi kaza, wacce ma tayi kaza. Momy Nafisa ta sheqe da dariya. "kai Nana! Allah ya shiryeki. Tace, kin zata qarya ne? Zomuje in mun dawo kidan ta6a ki gani. Momy tace, ni mijina da bashi da lfy, yaushe zan sake zauta shi. Har suka kai gidan Hajiya Hauwa, Hajiya Nana tana bawa momy Nafisa labarin kyawun kayan. Da ido kurum momy nafisa ta kalli kayan, ta gamsu da batun Hajiya Hauwa. Ta basu kayan, inda daganan suka nufi gidan Na'ima. Cikin sauri ta bude falon lokacin da taji qaran alarm. Domin tana tsoron kar ta sake yin laifi. Rungume momy tayi tana kuka. Kayanta ta soma hadawa bayan sun zauna a bakin gadon Na'imar. Tana fadin momy qafata qafarki. Ba zan sake zama a gidannan ba. Hajiya Nana tace, "ke da Allah natsu! Na'ima ta tsaya tana share hawaye don tasan Hajiya Nana bata daukar raini, tace zonan ki zauna in karanta miki.9�0⃣Nan ta soma shiryo abinda suka zo dashi, tace kin zauna kinata faman wasu koke-koke. Duk matar da kk ganta gidan auren ta, karki tsaya tona irin qalubalen da take fuskanta, ko kuma wanda ta fuskanta a baya. Mu kanmu nan da kk gani munsha gwagwarmaya kafin mu kafu a cikin gidajenmu. Ta ciro mata wata kwalba, wannan ki lura dashi da kyau, don duk yafisu tsada kuma ya fisu aiki. Natsu sosai kiji yadda zakiyi amfani da ko wanne. Nan suka karanta mata, tare da bata shawarar yadda zata shanye duk wani wulaqncin da zai mata. Momy tace, kar in sake jin batun tafiya a bakinki, du-du-du, yaushe akayi auren da zakice kin gaji. Salon kija mana dariyar 'yan baqin ciki. Da ma gashi jikin dadynku yaqi, ki jure kawai, kuma kiyi aiki da abinda aka fada miki. Nan dai suka dan kwantar mata da hankali, suka fita, suka tafi. Sha biyu da kusan minti arba'in na dare lokacin ne Abokan Abbas suka sauke shi a gida a buge. Daga bugun qofar falon, zaka san baya cikin hayyacinsa. Na'ima, wadda ta soma barci sbd gajiya da tayi da jiranshi, ta miqe a tsorace ta nufi qofar inda yaketa kiranta. "Na'ima in na shigo sai na ci miki mutunci. Ba zaki budemin qofar ba? Tana budewa yabi ta da kallo tun daga qasa zuwa sama. 'yar mitsilar rigar varci ce a jikinta mai shara-shara. Yana kai idanunsa fuskarta, sai yaga ta rikide masa ta koma mimi. Cikin wata kidima ya rungume Na'ima a zaton ta abubuwan da tayi amfani dasu ne suka fizgeshi. Amma shi mayensa da yake ciki shine ya suranta mashi haka. Sai kurum taji yana cewa, Mimi kin dawo gurina ko? Dama nasan zaki dawo gareni. Samansa sukayi yanata ririta ta, tare da nuna qaunarsa tamkar zai cinyeta. Na'ima tana kukan takaicin yana tare da ita, amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. , amma yana ambatar sunan mimi, har lokacin da yayi buqatarsa da ita ya fadi gefe, yana sheqa varcinsa. Canjin rayuwa 9�1⃣Na'ima tayi kuka, iya kuka cikin daren kafin varci yayi gaba da ita. Qarfe takwas ya farka. Halin daya ganshi ciki ya sashi kallon gefensa. Na'ima ya gani kwance cikin irin yanayin daya samu kansa. Ya soma tunanin da yaushe har tazo masa daki akai hakan? Ya dai iya tuno jiya sun samu matsala da Jennifer. Yarinyar daya kawo ta Abuja da kansa ya kama mata gida tana zamansa, ynxun kuma sai ta dinga munafuntarsa. Jiya yaje mata zuwan bazata sai ya sameta ta kawo wani gidan. Yayi mata magana tana fada masa cewa, itafa ba matarsa bace bare ya dinga yi mata dokoki. Yayi mata duka kafin ya baro gurin ta ya nufi club dinsu inda suke hadewa da abokansa suna shaye-shayensu. Ya fada musu halin da yake ciki, nan suka bashi shawarar cewa, yasha mayensa ya manta da ita, ya daina zuwa ta gani in akwai wanda zai mata kwatankwacin abinda yake mata. Sha yayi sosai, don bai ta6a sha irin haka ba. Ko iyayensa basu san yana sha ba, domin baya sha da yawa. Ya kasa komai don haka suka kawoshi gida. Tuna hakan yasa shi gane cewa, maye ne ya suranta masa Na'ima a matsayin Mimi. Tsaki yaja sannan yasa hannu ya daddaka mata duka. Firgigit ta farka tana kallonsa, fuskarsa daure. Yace, tashi ki fita! Tace dama kai ka kawoni bani nazo ba. Ta soma kuka, yace ban tambayeki wani dogon zance ba. Nace dai ki fita. Na'ima ta saka rigar varcinta ta fita da kuka. Ya jima shiru yana takaicin faruwar hakan Tsakanin su, don bai tsara zaiyi hakan da ita ba. Amma sai ya miqe ya nufi bandakinsa.9�2⃣Na'ima ma bayan tayi wanka da sallah, ta koma ta zauna tanata tunanin yadda mijinta yake mutuwar son mimi. Kai ita da ta sani, da bata kawo kanta gurin son maso wani ba. Can ta miqe ta nufi kicin, yauma da kanta ta girka abinda zataci kifi ta gasa, irin gashin da Mimi kansa ayi mata. Na'ima ta dan iya girki, domin ko a gidansu tana shiga kicin gurin masu yi musu girki jefi-jefi. Ta gasa bread dinta, zata fito shi kuma zai shigo kicin din, ya kalli tiren hannunta, "bani kiyi wani! Bata musa ba, ta miqa masa don tanason su riqa 'yar hulda ko yaya. Ta koma ta hado wani abin karin. Bayan ta karya ne ta shiga turare gidan da turarukan da aka kawo mata. "Yayi qamshi. Ya fada, duk da ba cikin walwala yayi maganar ba. Taji dadi, kuma taji mamaki. Don haka bayan fitarsa, sai ta dauko sauran abubuwan ta kama amfani dasu. A waya Abbas ya kira Usman, yana bashi labarin abinda ya faru a jiya. Usman yace, kai sakarai me nace maka? Ai na fada maka kawai ka more quruciyar Yarinyar kace a'a, to ynxun don ja nuna ma Jennifer kurenta kawai, ka share ta kaci amarcinka. Abbas yace, banason Yarinyar tayi tunanin cewa, ina sonta ne. Usman yace, ai ba wai zaka sakar mata fuska bane sosai. Ka gane? Abbas yace, shikenan zan kwatanta. Tun daga ranar Na'ima tadan samu sauqin mijinta. Zai sata ta dafa masa abinci, kuma zai kirata shimfidarsa. Amma ba wata soyayya, ko kulawa, ko hira ko sakin fuska. Abin da ta lura amfaninta kenan tayi masa girki, sannan yayi buqatarsa. Wani dare ya kirata a waya taje samansa. Ta sameshi a falo tace gani. Yace ki shiga mana. Kin tsayamin akai, sai kace wani sa'anki. Ranta ya sosu, tace, wai kai kana bani mamaki. Kana nema a gurina amma kayi ta dauremin fuska, kana fadamin abinda kk so. Yace kar ki kawomin raini. Ki wuce muje. Tace, ni varci nakeji, ta juya. Nan take ya kamota, saida ya mammareta, sannan yayi abinda yake so anan falon, ya kuma koreta zuwa dakinta. Zahiri baya sonta, amma abubuwan da take sha, da wanda take qamsasa jikinta suke fizgarsa gareta. Irin Rayuwar da Na'ima ke ciki kenan. Gashi danginsa sun tsane ta, musamman uwarsa wadda tace, Na'ima ta bada ita a gaban Qawayen ta. 9�3⃣Zainabu kuwa tana can gidansu, saiga Alhaji ya diro da la'asar sakaliya. Yayi sallama dz innar su Zainabu. Yau kam fuska daure ta fita, da nufin bala'i tare da ita. Sai dai shima tana kallon sa tasan cewa da hakan yazo, kuma in ba sa'a bama shi ya dama ta ya shanye. Kafin tayi magana ya riga ta. Nazo daukar Zainabu ne. Ta lailayo ashar ta maka, sannan tace, Zainabu ba zata koma ba, sai ya sauke dubu ashirin da hudu na asibiti. Yace, tunda dai banyi muku qorafin cikina da kuka zubar ba, to ku bani matata kawai mu tafi. Inna tace, au tanan ka biyo? To ai inason ka sani, tuni muka samu labarin baka son haihuwa, bare kayi wata barazanar banza. Ba zata koma ko ina ba, sai ka canke kudin mutane. Yace, haka kk ce? To kuwa ku shirya cin wani bashin don zaku amsa sammaci, kotu zamu shiga. Ya ciro wayarsa, iroro dake gefe yace, Alhaji ai sai ka kira lauyannan naka tukun, domin duk wanda baisan mutunci ba, gara ayi masa abinda yafi sani. Wato rashin mutuncin ba. Inna tace, ku kira alqali, ba lauya ba. Kai kuma dan kanzagi makwadaici kabi a sannu. Kaje ka nemi sana'a ba maula ba. Iroro yace, ai indai wannan ne sunanmu daya dake, wato 'yan maula. Kwadayinki kuwa ya ninka nawa. Tunda kk miqa 'yarki ga wanda bashi ta za6a ba. Alhaji yace, ko ba haka bama Iroro, ai baka kaita roqo ba, kullum dan aike yana hanya. Tace, kodai me zaku fada, ku fada...... Canjin rayuwa 9�4⃣Lokacin ne layin ya shiga wanda yake nema. Alhaji yace, yauwa Barista audu kaji ko? Daga can suka ji murya tace, eh ina jinka Alhaji lawal. Iroro yace, Yauwa Alhaji ai gara kasashi a speaker taji. Alhaji game da zancen da mukayi ne na matata. Ynxun haka ina gidan uwarta ta hanani matata, don haka zanzo mu shigar da qara. Daga can sukaji muryar barista yace, qarar kisan kai zamu shigar, tunda basu da mutunci. Ina ga ko dan gidan da suka mallaka, sai sun daida ba tare da kuma sun kare kansu ba. Don haka kar ka damu. Alhaji yace, shikenan nagode. Ya kalli inna yayi murmushin mugunta, sai mun hadu a kotu. Iroro ya sheqe da dariya. Dana sani tanata bibiyarki. Har sun juya tace, Alhaji ya tsaya. Sannan ya waiwayo. Lafiya? Tace, bari in turo ta ku tafi. Kudin mutane dana aro kuma idan nayi maka Allah ya isa fa? Tare suka sheqe da dariya, Iroro da Alhaji. Iroro yace, shegiya wuya! Alhaji yace, inna ai dama Allah ishasshe ne. Cikin jin haushi, inna tace, ni ba innarka bace don na tabbata ni kaina ka girmeni. Ta juya cikin takaici, suna tayi mata dariya. Zainabu tana kuka, tana komai, ta fito tabi Alhaji, tabar innarta cikin takaici. Wani qarin abin haushi a lokacin suna isa gida, saida yayi buqatarsa ya fita, ya barta tana kuka. Kishiyoyin suka shigo sunayi mata sannu tare da bata haqurin rashin zuwansu. Ko kawo mata abinci sunce Alhaji ne ya hana. Haka Zainabu taci gaba da Rayuwar gidan Alhaji mai cike da matsi da takura, gami da wahala, duk ta qara kodewa, ta fige ta lalace. Kuma ya hana innarta zuwa, kamar yadda itama yace ta daina zuwa gidansu. Innar Zainabu tasha kuka tare da takaici da kuma da na sanin hada Zainabu da Alhaji lawal. 9�5⃣Alhaji bashir ya dauki wayarsa ya soma neman layin Abba. A ringing na biyu Abba ya dauka, ya kara a kunne yana fadin dad ina kwana? Bayan sun gaisa Alhajin yace, inason kazo yau ka tafi dani katsina. Abba yace, amma lfy dai ko dad? Alhaji yace, lfy lau, inason ganin mahaifiyarku ne, gashi har ynxun bana jin dadin jikina. Abba yace, shikenan daddy, sai nazo. Qarfe biyu Abba ya sauka garin Abuja. Tuni daddy ya turo direba yana jiransa. Suka nufi maitama. Momy Nafisa batasan da batun ba, saidai taga Abba. Ya gaisheta tare da tambayar jikin daddyn, tace da sauqi. Lokacin data shiga don sanarda Alhajin zuwan Abba, sai yace ta hada masa wasu kayansa na ciki da kuma wasu takardunsa. Tace, ina zaka Alhaji? Yace katsina, nine nace wa Abba yazo ya tafi dani. Tace, ba zaka bari kadan qara samun sauqi ba? Yace, karki damu, can ma zanci gaba da ganin likita. Shida daidai suka sauka a filin jirgin sama. Sun samu direba na jiransu, domin kafin su taso daga Abuja, Alhaji yasa Abba ya kira direban hajiya sauda, batasan da zuwan Alhajin ba tana zaune a falo tana ba Zainab magani, don yau kwananta uku babu lfy, kullum suna hanyar asibiti. Sai kurum taji Sallamar su. Bata zaci Alhaji bane, don muryar Abba irin ta Alhajin ce. Saida taji yaran suna Oyoyo daddy. Da sauri dago tace, sannu da zuwa Alhaji. Ta miqe cikin sauri bayan ta kwantar da Zainab, tace, Alhaji baka sanar dani cewa kana tafe ba. Yace karki damu tu tunda mun iso lfy. Sun gaisa da Abba sannan ya nufi gidansa. Canjin rayuwa 9�6⃣Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki. Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti. Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan sha. Tace, a'a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa. Ya tsura mata ido, "sauda nayi miki laifi ko? Ta kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi. Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai ta6a son wani cikin 'ya'yansa kamarta ba. Amma dole ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa. Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share hawayen sa, saida tace "na shiga ukuna! Alhaji kukan me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani babban al'amari.9�7⃣Ta kama hannunsa. "Na roqeka karka 6oyemin komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa hannunta, "sauda karki tada hankalinki ba wani abu bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan cewa, na sa6a miki da yawa. "qara firgita tayi, gani takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, "sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani. Tunda munyi sallar isha'i, sai inje in sallami yara na inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin plate, tasa a gabansa. "in baka a baki?" yadan karkatar da kai, "bana tuna shekaru na matsawar ina gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.9�8⃣Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam. Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano maganar Mimi ce damuwarsa. Batun 'yan uwanta ta dauko masa na auren 'ya'yan sa'ade 'yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu. Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai. "sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai yarda ba shiyasa na haqura. Ya qura mata ido na 'yan kakwanni. Ta shafi kumatunsa, "wai wannan kallon fa? Yace, karki tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. "wlh tsoron kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya. "sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a'a sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin 'ya'yanki su samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin samun tarbiyyarki. Ma'anar in na mutu kuyi farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane. Canjin rayuwa 9�6⃣Hajiya kuwa ta dauki jakarsa kuma ya bita zuwa daki. Sannan ta dawo kusa dashi. Ya kamata kayi wanka ko? Ya kalleta, zan yi wankannan kuwa? Barci nakeji kuma inajin sanyi, sai inga kamar in nayi wankannan zazza6i zai iya rufeni. Ta cire masa riga, sai singileti. Ya kwanta akan gado, ta zauna bakin gadon. Kasha magungunan ka kuwa? Yace, nasha, sai dai akwai na ynxun qarfe shida, amma sai zan kwanta sannan zan sha. Tace, a'a nidai kasha ynxun, yana da kyau kabi dokar likita. Ynxun tashi zakayi in taimaka maka kayi wanka, kasha magani kayi sallah don kaga magriba ta kusa. Ya tsura mata ido, "sauda nayi miki laifi ko? Ta kama hannunsa, ni baka min laifi ba, to muje kayi? Yace, to sauda muje. Kafin yayi sallah har ta shiga kicin da kanta tayi masa tuwon alkama miyar alayyaho. Yana zaune kan sallayarsa yana istigfari. Can qasan zuciyarsa kuwa tunanin mimi takeyi. Zuwa ynxun ya gama tabbatar ma kansa cewa, son da yake wa mimi ya zarta tunaninsa, kuma ba zai ta6a son wani cikin 'ya'yansa kamarta ba. Amma dole ya jure sbd ya samu ya ida nufinsa don ta samu canjin rayuwa. Wasu hawaye suka soma zubo masa. Sam baiji Sallamar Hajiya sauda ba, har saida ta dafa shi, sannan ta tsugunna tare da aje abincin dake hannunta dayan. Duk da saurin da yayi ya share hawayen sa, saida tace "na shiga ukuna! Alhaji kukan me kkyi? Cikin sarqaqqiyar murya yace, ba kuka nake ba. Sauda ta zauna dirshan akan sallayar, cikin tashin hankali tace, haba Alhaji. Shekarunmu nawa ban ta6a ganin hawayen ka ba sai yau. Dole akwai wani babban al'amari.9�7⃣Ta kama hannunsa. "Na roqeka karka 6oyemin komai. Idanunta suka cika da hawaye yadan matsa hannunta, "sauda karki tada hankalinki ba wani abu bane. Sannan inason don Allah ki yafe min nasan cewa, na sa6a miki da yawa. "qara firgita tayi, gani takeyi tamkar Alhajin mutuwa zaiyi ya barta. Sai ta soma kuka. Jikinsa ya janyo ta. Haba sauda, mene ne na kuka kuma? Tace Alhaji don Allah karka tafi ka barni. In kuma wata matsala ce tasa zubar hawayen, don Allah ka fadamin. Yace, sauda bazan 6oye miki ba, ina kuka ne sbd mimi. Saida na rabu da mimi nasan cewa, inayi mata mugun son da bansan adadinsa ba. Tunanin ta ne ya hana sugar na sauka, na sani. Ya dago fuskarta mai dauke da mamaki. Ta kalleshi cikin ido, "sbd mimi kk cikin wannan tashin hankali? Yace, eh sauda. Tace to me zai hana ka tashi muje gurinta ynxun a asibiti? Yace, lokaci baiyi ba. Sauda ynxun zan sanar dake dalilina na aura wa mimi talaka. In kince ban kyauta ba, to zanje gurinta ynxun, in kuma raba auren ta, sannan in fita da ita wajen qasarnan don nema mata lfy. Hajiya sauda tace, kafin nan bari in baka abinci da kuma magani. Tunda munyi sallar isha'i, sai inje in sallami yara na inzo in saurareka har zuwa asubahi. Yayi guntun murmushi. Ta janyo tiren, ta zuba tuwon a cikin plate, tasa a gabansa. "in baka a baki?" yadan karkatar da kai, "bana tuna shekaru na matsawar ina gabanki. Ki bani zanci da hannayenki masu albarka.9�8⃣Ta soma bashi tuwon, bayan yayi bissimillah. Bai iya tuna lokacin da yaci abinci kamar na yau ba sam. Tana bashi tana masa hira har yayi qat. Ta bashi magani, sannan ta jashi da wata hirar, tunda ta gano maganar Mimi ce damuwarsa. Batun 'yan uwanta ta dauko masa na auren 'ya'yan sa'ade 'yar uwarta, da irin gudummuwar da ta basu. Yace, nima zan bada tawa. Kullum inason in nazo inje in gaida ya Dikko sai abubuwa susha min kai. "sauda tace, har na gaji dayi mata qaryar cewa, kana gaida ta. Kwanaki tazo tayi sati hudu. Har yaya jabiru yazo suka tafi baka zo ba. Yace, wannan karan zan huta a gurinki sauda, zanje in ganta jabiru dai ya hanamu ita, da ynxun tana nan. Sauda tace, ai bazai yarda ba shiyasa na haqura. Ya qura mata ido na 'yan kakwanni. Ta shafi kumatunsa, "wai wannan kallon fa? Yace, karki tsorata sauda. Nasan tsoranki, kar in mutu in barki ko? Ta matsa hannunsa dake cikin nata. "wlh tsoron kenan Alhaji. Ko tuna hakan nayi ina zubar da Hawaye bare ace ta kasance. Ya sauke ajiyar zuciya. "sauda ni kaina banason in mutu ba tare da na cika burina ba. Burina in saku cikin farin ciki bayan mutuwa. Tace, wace irin mutuwa zakayi inyi farin ciki in ba ni na riga ka ba? Burina in rigaka. Yace, a'a sauda, ni ya dace in tafi in barki, domin 'ya'yanki su samu tarbiyyar ki. Ko mimi inayi mata takaicin rashin samun tarbiyyarki. Ma'anar in na mutu kuyi farin ciki shine, in daidaita tsakani na da Allah da kuma tsakani na da iyalina da sauran mutane. Canjin rayuwa 9�9⃣Hajiya sauda, cikin mamaki tace, kana da wani hali ne na daban? Domin in da za'a tambayeni halinka, zan bada shedar cewa, kai mutum ne na gari. Yace, "sauda kowane dan Adam ajizi ne, in dai ba ma'asumi bane. Harkoki na sunsa bana samun yin sallah akan lokacin ta. Harkokina sunsa 'ya'ya na basu samu soyayyata ba. Harkokina sunsa 'yan uwa maqota ban basu nasu haqqinba. Shawararki da nayi ta guje mawa ynxun na gano itace mafita. Zan aje tunani na na kullum, wato maida Naira ta zama Dala, ko ko taro ya zama sisi. Ta kamashi, tashi ka koma kan gado, bari in kwashe kwanukannan, in kuma tabbatar da yarana suna cikin makwancinsu. Ya miqe tare da komawa kan gadon. To karki jima maman yara. "Bayan fitowar ta ne ta tsaya bakin qofar, sannan ta daga hannunta sama, "Alhmdlh, ya Allah ka qara sa mijina akan hanya madaidaiciya. Kamar kullum daga dakin su Abdullahi ta soma har zuwa dakin su Zainab dasu Hasina. Nan ta dan 6ata lokaci don sai da taba Zainabu magani sannan ta fito. Zata shiga dakin su usaina saiga su sun fito. Tace, ina zakuje? Suka ce munason mu sake yiwa daddy sannu da zuwa, sannan muga jikinsa ne. Tace, to kuje yana ciki, ina zuwa nima. Dakinta ta shige don ta dan sake kintsawa cikin kayan varci. Su Hasana suka shiga dakin daddyn su bayan sunyi sallama, ya kuma basu izini. A hannun kujera suka zauna suka gaida gaida shi tare da sake tambayar jikin sa. Ya tashi zaune daga kishingidar da yayi. "kuzo nan yarana! Suka kalli juna cikin mamaki, sannan suka nufeshi. Ya ce, ku zauna bakin gado kyawawan 'yan biyu na. Suka zauna. Ya dora hannunsa akan kafadar ko waccensu. 'Yan biyu kuma fa kun girma, masha Allahu. Hajiyarku tace min zakuyi jamb da Waec ko? Suka sake kallon juna, sannan sukace "eh daddy mun kusa mu fara. Yace, to Allah ya baku sa'a. Suka ce Ameen. 1�0�0⃣Ya sake cewa, me kuke karantawa ne? Ina nufin Art ko science? Usaina ta kalleshi "'Hassana ce take science class, ni Art nike. Yace, Hassana zamu doctor kenan? Ta kalleshi cikin Jindadi tace, eh daddy inason in zama medical doctor. Yace, Usaina fa? Tace, daddy nikam 'yar jarida nakeso in zama, ina sha'awar haka, shiyasa mass com zan karanta. Cikin farin ciki yace, nagode ma Allah. Allah ya cika muku burinku yara na. Daidai lokacin Hajiya sauda ta turo ta shigo da sallama. Ta kallesu da fara'a " 'yan biyu azo aje ayi varci ko? Suka miqe, sannan suka sake cewa, daddy Allah ya baka lfy. Yace, Ameen nagode. Suka ce, Hajiya saida safe. Tace, mu kwana lfy karku manta da Addu'a. Suka ce, to. Ta zauna tana kallon fuskarsa, "sun dameka da surutunsu ko? Yace, inason su saki jikinsu dani. Tace, ya kamata kam. Yace, "ynxun wace shawara zaki bani? Ta kalleshi "tame? Maganar da nayi miki dazun, ta damqa harkoki na ahannun yara, kamar yadda kike ta bani shawara tuntuni. Tace, ynxun kwanta kasha magani fa, in ka samu varci, gobe idan Allah ya kaimu, sai muyi maganar ko? Ya kwanta tare da cewa, Allah ya kaimu. Itama ta kwanto masa, tare da kashe fitilar dakin. Alhaji Bashir ya jima bai samu varci kamar na yau ba. Yaji dadin jikinsa daya farka, har masallaci yaje. Sannan da gari ya dan yi haske, sai yace, ki fitomin da kayan motsa jikina, zan dan fita. Likita yace, in dinga motsa jiki sosai, zufar da zan fitar tana fita da cutar. Canjin rayuwa 1�0�1⃣Hajiya sauda tace, tunda yarannan suna hutu, to ka fita dasu Abdullahi mana da Sadiq da Ameen da Umar. Take ya yarda sbd ynxun kam burinsa bai dara kusantar duk 'ya'yan nasa ba. Suka fito cikin kayan motsa jiki. Yaran sun sa gajeran wando da riga mai gajeran hannu, yayin da uban yasa mai dogon hannu da kuma dogon wando. Yaran cikin murna, domin suna son fita motsa jiki sosai, Hajiya ce take hanasu, wai tace, batasan da wadanne irin abokai zasu hadu ba in sun tafi can gurin motsa jikin. Alhaji ya dube ta, "sai mun dawo." Cikin salon tsokana tace, "to Alhajina. "Ta kalli Abdullahi, "Yarana masu albarka, ku lura min da mijina. Gaba daya suka sa dariya. Tace, da gske nakeyi Abdullahi, kar yayi gudu, tafiya kawai zakuyi. Suka ce "To" suka jera suka fita, biyu nan, biyu nan, suka sa mahaifinsu a tsakiya. Kafin ya dawo tuni ta dama masa kunun alkama da qosai. Qarfe takwas suka dawo, duk yayi zufa, yaran suka nufi dakinsu don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka don yin wanka. Shi ko Alhaji har taimaka masa tayi tayi, yayi wanka don nuna kulawa. Bayan yaci abinci, yasha magani, sai yace, ki shirya zamu fita. Tsaf tayi kwalliya cikin koriyar super da hijabinta wanda kyansa ya nuna tsadarsa. Qamshi take yi, ta bar sallahun komai gurin masu aiki tare da sauran yaran, sannan suka fita. Direban shi ya taso, Alhaji yace, je ka huta. Nine zanja motar. Saida ta zauna a gidan gaba, sannan ta kalleshi da murmushi. "kai da baka da lfy?1�0�2⃣Yace, sauda kowane lokaci in muna tare bana son mu samu na uku. Sai inga tamkar mu kadai ne a duniyarmu. "Tasa dariya, daidai lokacin daya tada motar. Tace, to kaba ni in tuqa mu. Kaifa jiya kazo. Yace, baki lura ina ganinki na samu sauqi ba. Ynxun ma kinsan ina zamuje? Tace, a'a. Sai da ya hau titi sosai, sannan yace, gidan saukar baqina. Inason muyi hirar da muka dade bamu yi irin ta ba. Sannan mu tattauna muhimman zantuka. Murmushi tayi batace qala ba. Kwance suke a tsakiyar gadon na dakin baqin, suna fuskantar juna, yace sauda na buqaci muzo nan ne musamman don in baki haquri, sannan in fada miki dalilaina. Sauda nasan cewa, na sa6a miki lokacin dana rabaki da 'yarki na kaita ga wata, wanda harga Allah lokacin soyayyar Mimi ta rufemin ido har na aikata haka. Amma kika yi haquri. Sannan na biyu kece kadai zanyi wa 'yarki abinda nayi mata, wato aurar da ita ga talaka ba tare da kin dagamin hankali ba. Da wata ce, cikin sauran matan, na tabbata da ranar aurenmu da ita zai mutu. Sai na qarshe kece kadai 'yarki zata samu hadari, in hanata zuwa, kuma ta hanu. Sauda duk inda ake neman mace ta gari, kin kai. Ina roqon Allah yasa ki zama shugabar matana a gidan Aljannah. Cikin murmushin jin dadi tace, Ameen Alhaji. Ya tashi zaune. "sauda dalilina na aurar da Mimi ga malam Ismail, tare kuma da yanke duk wata alaqa da ita tare da cire ta cikin ahalina shi ne........ Kashhh! Mu hadu cikin littafi na hudu, kuma na qarshe. K. Mashinku ce, sai na jiku a 08081165107