MASARAUTAR MU!1 to 4 Compiler: Suleiman Kurya Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR SADAUKARWA Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. SHIMFIDA Rana ta tasamma faduwa, misalin karfe biyar na yamma. Lahadi ce, wadda ta kasance ranar kasuwar kauyen. Tsanyawa, karamar hukuma ce a cikin birnin Kano. A dai-dai wannan lokacin kasuwar garin ta fara watsewa, kowa na kokarin komawa gida cikin iyalin sa domin lokacin magariba ta kawo kai. Malam Hashimu, daya daga cikin dattijan garin Tsanyawa, dattijo ne mai kamala dan kimanin shekaru sittin da biyar, ya baro kasuwar akan keken sa, wani tsohon keke wanda da kyar tayoyin sa ke juyawa sabida tsatsa da tsufa. A hankali yake tafe a gefen hanya kikiki-kikiki....bayan keken sa dauke da tsarabar kasuwa ta kayan miya (kayan gwari) wadanda yake sayarwa da tsarabar yalo, dafaffen rogo da rake dasu agwaluma cike taf a katuwar leda. Tun daga bayan darnin gidan sa ya ke jiyo tashin kukan diyar sa SA'ADE. Zuciyar sa ta tsinke...kamar koyaushe ya ji kukan yarinyar tasa. Ya kara gudun keken sa ya iso gida jikin sa yana rawa, da hanzari ya jinginar dashi a jikin jinka ba tare da ya bi ta kan ledar tsarabar sa ba, ya fada gidan da dan banzan sauri, babbar rigar sa tana harde shi saura kadan ya fadi, da kyar ya samu ya dafa katangar dakin sa ya shigo gidan kamar an jefo shi. Abinda ya zata shi ya gani, wato mai dakin sa ce Inna Laure ke jibgar Sa'ade, da wani murtukeken iccen darbejiya tun karfin ta, yarinyar tana ta ihu da neman taimako kamar kullum. Hannu ya mika ya daga yarinyar wadda ke kuka kamar ranta zai fita tana fadin..... "Baba ka cece ni Inna zata kashe ni....". Inna Laure ta yarda iccen tana masifa tana fadin. "Gobe ki sake dawo min da sauran gasara baki sayar ba, ki ga yadda zanyi da ke a gidan nan. Haka kawai ki dinga jaza min asara, ai ba uban naki ya bani jarin ba, in baza ki yi min talla ba, to ya dauke ki ya yi miki aure. Ba zan zauna ina ciyar daku ga banza ba, kartin banza kartin wofi da basu san komai ba sai ci da juyewa a masai, dole ki fita ki nemo min tunda kun zame min jaraba daga ke har sullutun uban naki da bai ko iya ciyar da gidan sa". Malam Hashimu bai ce komi ba, amma ba kalmar data fi bakanta mai rai cikin maganganun ta irin "sullutu", ya tada yarinyar ya kama hannun ta suka nufi dakin sa. Har zuwa lokacin Sa'ade kuka take yi jikin ta yayi birdin-birdin yana ta rawa. A gefen wata tsohuwar kujera kwalli daya da ke dakin mahaifin nata ta zauna, ta takure jikin ta tana sheshsheka hadi da hadiyar zuciya. Malam Hashimu ya ce "bar kukan ki gaya min kin ci abinci?" Sa'ade ta girgiza kai hawaye na sakko mata. "Baba tun kokon safe, ban kara cin komai ba". Tashi yayi ya koma inda ya jingine kekensa ya dauko kullin ledar da ya dawo da ita, ya dawo ya zauna a gaban 'yar tasa. Kwancewa yayi ya fiddo daurin awara mai zafi a cikin leda ya tura mata gaban ta ya ce "maza cinye". Sa'ade ta shiga tunkuda awara a bakinta hannu baka hannu kwarya, daidai lokacin aka bankado labulen dakin aka shigo. Laure tasa hannu ta dauke kullin awarar gabadaya tana fadin "eh lallai! Gata mugun abu, in baki dambu ki ci ki koshi, ki cewa ubanki ban baki abinci ba ko? To daga ke har shi kun yi kadan ku nuna min iyakata a gidan nan, idan bazaki ci abinda na dafa da kaina ba, sai dai ki kwana da yunwar ki". Ta fice kamar kububuwa tana maganganu da fadace-fadace kamar sabon kamu. Malam Hashimu ya sunkuyar da kai, Allah kadai ya san abinda ya ke tunani, zuwa can ya dago ya ce "Sa'ade!" Cike da haushin baban nata wanda ba ya iya tabuka komai a gidan sa, Laure ta gama raina shi sabida sanyin halin sa. Sa'ade ta daga kai ta sauke manyan idanun ta akan mahaifin ta. Ya ce "me yasa data baki dambun baki ci ba?" Ta bude baki cikin murya ta wanda ya ci kuka ya koshi ta ce "Baba ni bata bani ba, babu dambun data bani, bana gidan ma, tun safe ta dora min tallan gasara. Ni kuma sai na tafi makarantar su Hanne na tsaya a bakin taga ina jin yadda ake koya musu karatu, sai da aka tashe su na tafi tallan gasarar, kuma har yamma tayi ban sayar gabadaya ba, na dawo mata da saura shine take duka na". Girgiza kai yayi ya ce "ki yi ta hakuri kin ji Sa'ade? Watarana sai labari. Insha Allahu sai Laure ta amfana da ke watarana, ina raye ko bana raye kullum ina gaya mata wannan. Ni Allah bai dora min iya fada da masifa ba, bana son su, ban kuma iya su ba. Shi yasa na barta da halin ta. Ki cigaba da yi mata biyayya, ita din duk yadda take uwa ce a gare ki. Da dadi ba dadi ta rike ki har kika kawo munzalin da kike yau. Shi yasa nake kauda kai akan duk muzgunawar data ke miki kada ta ce don ba ita ta haife ki ba........". Sa'ade ta katse Baban ta da sauri da tambayar data dade tana cin ta a zuci. "To Baba ni wacece uwata? A ina take? Ka ce tana raye, amma meyasa ban taba ganin ta ba ko a hoto?" Fuskar Malam Hashimu nan da nan ta tattare ta koma kamar jikakken tsumma, ba ya son tuno ta.....ba ya son tuno duk abinda zai tuna masa da ita...... ta bar masa tabon da har abada bazai taba bacewa daga zuciyar sa ba! Ba kuma zai taba gayawa Sa'ade inda take ba har sai ita din ta nemeta da kanta, wanda ya san mawuyaci ne tayi hakan; a matsayin da take kai a yanzu, da kuma shi data gujewa. Da Sa'aden data haifa bada son ran ta ba! Ya riga yayi amanna da cewa....... ko bajima ko ba dade zata nemi Sa'ade, a lokacin da zai nuna mata shine ubanta duk talaucin sa. Mulkin ta bai yi isar da zai kwatar mata 'yar ta daga hannun sa ba. Idanun sa suka kada suka yi jazur da ya tuno kiyayyar uwar ta gare shi, mummunar kiyayyar da ko a hikaya bai taba jin irin ta ba, ba don komai ba sai don shi talaka ne? Idan yayi la'akari da inda take aure ta kuma yi zaman ta yanzu? Daga ita sai shi, sai Ubangijin ta suka san dalilin kiyayyar ta gare shi. Murya a sanyaye ya ce. "Ga Yalo da dafaffen rogo yi maza ki ci ki debi ruwa a randa ki sha, ni zan je na yi alwallah". Ya fada yana mai kaucewa kaifin manyan idon Sa'ade, wadanda a lokuta da dama suke firgita shi ya ganta ta rikide ta koma masa kamar BILKISU! Sa'ade bata dauke idanun nata daga kansa ba har ya bar dakin, sannan ta ci dafaffen rogon ta koshi, bayan ta ture yalon gefe, ba ra'ayin ta bane. Ta kora da ruwan randar baban dake gefe mai sanyi da gardi. Ta mike ta fito tana leken Inna Laure a madafi, da ta ga hankalin ta ya dauku ga tukin tuwon data ke yi sai ta kwashi takalmanta a hannu ta danna a guje ta fice daga gidan. Gida biyar ne a tsakanin gidan su da wanda ta shiga, ta maqe murya tana fadin "Hanne tana nan? Ta zo inji Iliyasu!" Hanne wadda ke alwala a gindin rijiya tayi murmushi ba tare da ta juyo ba ta ce "Sa'aden Baba, Sa'aden Hanne, Naziru na kira a dandali!". Suka kwashe da dariya a tare. Sannan Sa'ade ta shigo tana fadin "ai ban baki labari ba, jiya da ya zo waje na Inna Laure ta dage sai na fita, ina zuwa mun fara gaisawa ya saki wata tusa kamar mushen jaki, don wari ba shiri na gudu gida, gara mun dukan Inna akan tusar Naziru. Kuma lazim ne kullum ya zo sai ya yi ta. Ni me yayi min zafi da Naziru? Ga saurin tusa sannan ga shegen surutu". Hanne sai dariya take yi harda hawaye. "Inna Laure ke son sa sabida yana kawo mata dankalin da yake sayarwa kuma yana bata 'yar murtala idan ya zo". Innar Hanne ta fito daga bayan gida rike da buta da alama alwala zata yi, duk abinda suke fadi tana jin su, a ranta amincin su yana bata sha'awa, ta ce "Ho! Sa'aden Hanne, ba'a fita da manghariba fa, na hana ki amma bakya ji, zo ga abinci na ajiye miki na san ba ki ci ba" Sa'ade ta tsugunna ta gaida Innar Hanne, ta wuce madafi kanta tsaye don ta dauki abincin data ce ta dauka. Kusan kullum sai Innar Hanne ta ajiye mata abinci. Sai da suka yi sallah sannan suka ci abincin ita da Hanne a kwano guda, suna ci suna hirar samarin su suna kwasar dariya, Hanne ta roki Innar ta zata raka Sa'ade gida kada Inna Laure ta doke ta. Har dakin Inna Laure Hanne ta raka Sa'ade, wadda ke rabe-rabe a jikin bango irin na wanda ya san yayi laifi, da Hanne ta fita ji tayi kamar ta bita a guje. Hanne na bada baya Inna Laure ta shaqo Sa'ade ta makure ta a jikin bango ta ce. "Shine don kar ki kwashe min tuwo kika faki ido na kika tafi gantali ko? To kin yiwa kwanon tuwon ki, ko loma daya bazan baki ba, ki kwana da yunwar ki, 'yar banza mai mugun hali irin na uwar ta". Sa'ade dai bata tanka ba, don inda sabo ta saba ji a bakin Inna Laure uwartamai mugun hali ce. Kuma dai a koshe take, don haka bata damu ba data ce bazata ci tuwon dare ba. ****** Washegari ma da Inna Laure ta dora mata gasara maimakon tabi gida-gida kamar yadda ta ke yi sai ta karkata hanya ta tafi makarantar su Hanne, yau ma a bakin taga ta tsaya daidai saitin da Hanne ta ke farantin gasarar ta yasar da shi a gefe. Malamin yana cikin bada darasi ya hangota tana leke. Zagayowa yayi ba da sanin ta ba sai ganinsa tayi a bayan ta, ta zabura zata gudu ya tare hanya. "Shiga aji ki zauna, zan sa Dagaci ya yiwa baban ki magana, kullum ina ganin ki kina leken kawayen ki, wanda ke nuna kina sha'awar karatun da muke yi". Bakin Sa'ade ya ki rufuwa don dadi, sai dai ta sani Inna Laure bazata taba bari ba, shi kuwa Baba sai abinda tace sabida tsoron masifar ta. Hankalin ta ya dauku ga abinda ake koya musu A BA CA DA Ee FA GA HA.....! Sa'ade ta bude murya tafi kowa yi... abinda ya dauki hankalin malamin a kanta ya gane da gaske take son karatun. Don haka kamar yadda yayi alkawari har kasuwa ya bi Malam Hashimu bayan sun tashi, cikin nutsuwa ya neme shi ya bar Sa'ade ta dinga zuwa makaranta a daina dora mata talla. Malam Hashimu yayi shiru, daga bisani ya ce a sanyaye, "uwar rikon ta bata so, kada ka sa ni a tashin hankali ina zama na lafiya". Sa'ade data zo washegari malam yace tayi zamanta, ana tashi yaje ya gayawa Dagachin Tsanyawa, shi kuma ya tura aka kira masa Malam Hashimu da Laure, a gabanta ya ce yayi umarni ga Malam Hashimu ya saka 'yar sa a makaranta a daina dora mata talla lokacin zuwa makaranta, idan kuma sun ki to su tattara su bar Tsanyawa dama dukkan su ba haifaffun garin bane, gara Laure wadda ta zo da ita Tsanyawa daga kauyen Kiyawa 'yar asalin garin ce. Shi kuwa Malam Hashimu Dagaci ya ce har gobe bai san daga ina ya zo ba. Mafari kenan da Sa'ade ta samu 'yancin zuwa makarantar boko har da ta allo, wannan bai hana Laure cigaba da dora mata talla ba a duk lokacin da ta dawo. Tana aiki tana mita tana tsinewa Dagacin Tsanyawa. A wannan lokacin ne makerin budurci ya soma kera Sa'ade, ta fara kirgan dangi har da jinin al'ada a shekarun ta goma sha biyu kacal. Hanne ce ta koya mata kunzugu, da wankan sallah da tuni Innar ta ta koya mata don ta riga Sa'ade farawa. Manema suka yiwa Sa'ade Caaaa! Manya da yara. Kai ka ce wata budurwar kirki ce, bayan Naziru mai dankali harda dan Dagachi dake karatu a birni, da wani Alhaji Talle mai mata uku amma yana da sukuni sosai. Kyawun fuskar ta shine abinda ya ke fara jan hankalin maza a kanta, wani irin sassanyan kyau ne da ita na mutanen wani yanki daga BORNO da ake yiwa laqabi da shuwa-arab wanda ake rasa gane daga inda ta samo shi don kwata-kwata bata yi kama da mahaifin ta ba, wanda yake baki, tittirna, mai gajeren hanci. Mutane da yawa a garin na fadin Sa'ade ba 'yar sa bace, tsintota yayi, don babu wanda ya san shi da uwar ta, kawai an wayi gari ne an ganshi a garin tare da yarinyar 'yar shekaru uku yana rainon ta. Daga baya ya nemi auren Laure, ba bata lokaci aka bashi ba tareda binciken asalin sa ba don ta buwayi marikanta kuma ta rasa mijin aure duk fadin kauyen. A tsakankanin wannan lokacin ciwon da aka rasa gane kansa ya kama Malam Hashimu, tun yana yi a tsaitsaye har ya gagara fita kasuwa, kullum abu kara gaba yake yi, banda jike-jike ba abinda yake sha don Laure ta ce sisin kwabon ta ba zai yi ciwon kai ba wajen kai shi asibiti, ita ba haihuwa ba a barta da asara. Sa'ade ko makaranta daina zuwa tayi sabida jinyar baban ta, kullum ce mata yake ciwon sa ba na tashi bane, bai damu ba don ya mutu a wannan lokacin, ita Sa'ade ce damuwar sa. Wa zai rike masa ita? Ina za ta je idan bai tashi ba? Ya sani Laure ko a kafa aka daura mata Sa'ade sai ta kwance ta yar. Sabida tsanar data yi mata. Damuwa ta karu akan ciwon Malam Hashimu ta yi sanadin da ko idonsa baya iya budewa. Sa'ade na ji Laure na gayawa mutanen da ke zuwa duba shi wai ciwon daji ke damun sa. Baban Hanne shine ya tausayawa Sa'ade ganin halin da take ciki na fita hayyaci sabida ciwon Baban ta, duk da shima ba wani karfi gareshi ba haka ya kukkuta ya samo motar akori -kura ya tafi dashi asibiti a cikin Kano. Ba yadda Sa'ade bata yi ba zata bisu amma Malam Sale yace ta zauna a ranar zasu dawo. Har kwana uku basu dawo ba, a kwanakin nan uku Sa'ade ta gama karewa a tsaye, bata ci bata sha. A rana ta hudu kuwa tana gindin murhu tana hurawa Laure wutar tuwo taji ana fadin. "Ku shigo da shi daga ciki, a kawo tabarmi.......". Sai ihu da kururuwar Laure. Tana fadin "Malam ashe sa'i ya yi? Ashe rabuwar kenan?" Fitowar Sa'ade a guje daga madafi yayi dadidai da shimfide gawar da aka yi a tsakar gidan su. Da gudu ta karasa ta bude fuskar ta tabbatar Baban ta ne..... Ya rasu! Tafiya ta har abada wadda babu dawowa........ Ji kake yiff! Ta fada kan gawar a sume bata kara sanin inda kanta yake ba. ***** Ta farfado ne ta ganta a gidan su Hanne, Hanne na kuka Innarta na mata firfita. A lokacin ne abinda ya faru ya dawo cikin kwanyar ta. Ta rushe da kuka tana fadin "Hanne da gaske ne Babana ya rasu?" Innar Hanne ta rungumota jikin ta tana ta lallashinta tare da bata kalamai masu dadi. Sai da aka kwana bakwai Sa'ade bata daina kuka ba, kulawa da kauna ta duniya babu wadda iyayen Hanne basu gwada mata ba don dai su samu ta kwantar da hankalin ta ta karbi reality na rasuwar Malam Hashimu. Washegarin sadakar bakwai malam Saleh Baban Hanne ya kirata dakin sa, ya ce ta je ta kwaso kayanta gabadaya, ta kuma yi sallama da Laure ta dawo. Zai cika wasiyyar da marigayi ya bar masa suna hanyar zuwa asibiti. Zai dangana ta da mahaifiyar ta hannu da hannu.... A razane Sa'ade ta dago ta dube shi manyan idanun ta kamar sa fado kasa. Ya gyada mata kai da murmushi a fatar bakin sa ya ce "maza je ki ki dawo, daga yau zuwa gobe, zan sadaki da Innar ki da ta haife ki". **** Tunda suka iso tasha Sa'ade ke rarraba idanu, wannan ne karo na farko da zata fita daga garin Tsanyawa tun tasowar ta. Ita da Hanne rabuwar su mai taba zuciya ce. Tunda suka taso basu taba rabuwa na kwana biyu ba, kullum suna tare dare da rana, yau an ce Jihar Kano zata bari bakidaya ba garin Tsanyawa kadai ba. Zuwa inda bata sani ba, bata taba mafarki ba. Zuwa wajen uwar da bata sani ba, bata taba gani ba. Ko mahaifiyar tata ya zata karbe ta? Ko zata bata matsayin 'ya? Duba da cewa bata taba sanin ta ba? Sai yau a dalilin mutuwa.... mai tonon asiri! Tunaninnikan da Sa'ade ke ta yi kenan a lokacin da suka bar garin Tsanyawa cikin motar Rake Akori-Kura, suka hau titi dodar! Wanda zai sada su da birnin Kano. Hanyar garin ba kwalta a wancan lokacin don haka kura ta turnike idanun su a bayan akori-kurar, sai rufe fuskokin su suka yi da mayafan su. A tashar unguwa uku aka sauke su, inda direbobin suka ce yamma ta yi, zasu yi dare, su nemi waje su kwana in ya so washegari su yi asubanci su samu motar farko. A rumfar wata mai tuwo malam Saleh ya roka mata ta kwana, shi kuma ya kwana a masallacin tashar. Da asubah suna idar da sallah sune pasinjan farko a fasinjojin da zasu tafi garin MAIDUGURI.... ***** "Tafiya yankin azaba". Sa'ade ta fada a zuciyar ta. Sabida yadda ta wahala a motar. Kafin su isa Maiduguri sai yamma lis, duk sun yi wujiga-wujiga daga ita har Baba Saleh. Sau biyu yana saya mata gurasar masu balangu da pure water tana ci a hanya. Shi kam bawan Allah bata tunanin ko loma daya ya saka a bakin sa. Aka sauke su a tashar BAMA, anan ma a tashar suka kwana, da Asuba suka bi mass transiet wadda zata tafi kai tsaye zuwa garin ASKIRA. Sa'ade ba zata manta da garuruwan da suka wuce ba, saboda akwai wani mutum mai yawan surutu a motar tasu, duk garin da aka zo sai ya fadi sunan sa, sun wuce Damboa, sannan suka bulla ta Chibok, sannan Uba, a karshe sai garin da ta ji an kira ASKIRA. (A wancan lokacin ba insurgency, garuruwan Borno lafiya kalau suke). Sa'ade ta daga kai tana kallon garin Askira, garin da aka ce wai anan ne zata ga mahaifiyar ta, wadda ta haife ta, anan take raye. Babban gari ne wanda ya samu cigaban zamani kala-kala a yankin Borno. Koda aka sauke su a tasha tana ji Baba Saleh na tambayar ta ina zai bi ya je gidan Sarki? Sa'ade ta tambayi kanta. Me ya hada mahaifiyar tata da gidan sarki? Bata samu mai bata amsa ba. Da tambaya da kwatance aka kawo su har kofar tankareriyar masarautar Askira. ***** ASKIRA EMIRATE Gidan sarkin Askira koko in ce masarutar Askira babban gini ne a tsakiyar gari, a unguwar da ake kira "unguwar gabas". Tafkeken gida ne mai ginin sama da kasa. Dogarawa ne tun daga zauren farko har zuwa ciki rukuni-rukuni, wasu a zazzaune wasu a tsaitsaye. Daga soron farko za'a cire takalmi duk mai shiga gidan mace ko namiji, ginin farko dake tsakiyar gidan wani irin gidan sama ne wanda ke dauke da kayataccen falo na sarauta wanda anan sarki ke ganawa da bakin sa na nesa. Balcony din dake gefen wajen shine wajen zaman sa tare da mahukunta (king-makers) in ana wani muhimmin sha'ani kamar hawan sallah, nadin sarauta, bikin aure da sauran su. Akwai wata doguwar baranda a kasa wadda anan ya kan zauna a kowanne yammaci ya gana da jama'ar gari yayi musu maganin kukan su, alkalanci da zaman fada. Daga hannun dama na tsakiyar ginin akwai wata babbar kofar katako wadda in ka bi ta zai kai ka barga (ma'ajiyar Dawakai). A kowanne yammaci kyakwawan Dawisu (Peacock) ne a gaban gidan bila-adadin masu ado da ban sha'awa suna baza dogon bindin su cikin nuna baiwar ado da kyau da Allah yayi musu wanda bai yi wa wani tsuntsu ko wata dabba a duniya ba. Akwai fili fetal daga get din farko zuwa ginin farko na shiga ainihin zauren farko na masarautar. Akalla zaka wuce zauruka shida kafin ka tarar da wajen zaman sarki na farko da jama'ar sa na nesa, kafin ka isa wajen zamansa da mahukuntan sa, sannan ka yi tafiya mai tsayi kafin ka shigo ainihin cikin gidan mazaunin iyalin sa. Tsakanin inda sarki ke zama da 'barga' dakunan samarin gidan ne da yara maza da ake riko a gidan, sannan kayi tafiya mai tsayi wadda zata kawo ka get din cikin gida. Bangaren sarki zaka fara taddawa wanda ya hadu da get din cikin gida, kuma akwai kofofi da ke hade da bangaren kowacce matar sa ta aure. Daga gaban ginin akwai baranda mai kama da balcony a gaban kayatacciyar shigifar sarki inda anan ne ya ke ganawa da 'ya'yan sa, matan sa da 'yan uwan sa mata. An fi yin wannan ganawa da yamma ko da daddare. A wannan shiyyar babu mutane da yawa, kowa yana bangaren sa, sai bayi mata wadanda suma suke shige da fice babu yawan surutu, kowacce tana bangaren data ke hidima suna kuma shige da fice daga wannan sassa zuwa wancan na matan Sarki. Sarki kan zauna a kofar shigifar sa da yamma, don gabatar da sallahr la'asar, maza in na jiki ne suna iya shigowa nan, idan 'ya'ya ko jikoki suka shigo a daidai wannan lokacin saidai su rike takalman su a hannu su sunkuyar da kai su wuce in har ba shine ya ce a kira su ba. Amma in a barandar data raba shigifar sa data matan sa yake zaune, da 'ya'yan ko jikokin sun karaso zasu zube gaban shi su kwashi gaisuwa..... "Alanguburo" (Allah ya kara maka yawan rai) shine abinda ake cewa. Ba'a gaida sarkin Askira da "ina wuni? Ko ina kwana?" Shi kuma ya amsa da "Allah Kawun jo" wato kamar ace (Allah yayi albarka). Akasari a wannan shiyyyar babu dogarai babu bayi, in ya ga dama ya kan ja 'ya'yansa da jikokin sa da wasa, yayi musu tambayoyi akan rayuwar su a irin wadannan lokutan. In ka wuce wannan shiyyar ne zaka hadu da bangaren matan gidan. Wato matan Sarki na aure. Kowacce da bangaren ta wadatacce ginin zamani mai manyan shigifu, wanda aka yiwa ado da royal furnishing, babu abinda babu a ciki na jin dadin rayuwa, domin masarautar a zamanance take sannan ilmi ya wadaci al'ummar masarautar, ba abinda zai hada kowacce da 'yar uwar ta in har ba ita ta neme ta ba. Daga bayan nasu bangaren ne na kwarkwarorin sarki ya ke. Ana kiran bangaren kowacce matar sarki da sunanta.....Unguwar Ya Gumsu (Fulani Babba), Unguwar Ya Kirjinoma (Fulani Halima), Unguwar Fulani Hibbani (matar sarki ta uku) sai unguwar Fulani BILKISU (amaryar sarki). 'Ya'yan gidan duk sun girma, mazan na wajen ayyukan su da masu karatu a garuruwa daban daban, matan duk an yi musu aure a masarautu daban daban na jihar Borno, 'ya'yan Hibbani ne kawai 'yan kasa da shekaru sha takwas. 'Yammata ne guda biyu: Naja'atu, da Humaira. Sune kuma kadai ba'a yiwa aure ba a 'ya'ya mata. Kowacce cikin matan sarki tana da manyan 'ya'ya maza da mata, in ka dauke amarya Fulani Bilkisu, wadda har yau take haihuwa suna mutuwa tun suna jarirai wato (wabi). Wannan a takaice shine description na gidan sarkin Askira mai ci a yanzu, da bayanin tsarin masarautar gabadaya. Masarauta ce mai farin jini da tarin arziki wadda aka yiwa shaidar adalci da kyautayi ga talakawanta. Daidai gwargwado 'ya'yan sarki maza da mata sun wadatu da ingantacciyar tarbiyya da ilmin addini da na zamani, duk da ba'a rasa masu fitina ba musamman samarin maza. Kishin da ke tsakanin iyayensu mata bai hana su hadin kai a junan su ba, suna matukar kaunar junan su. Sarki na da 'ya 'ya goma sha biyar, maza da mata da jikoki sama da goma. **** Baba Saleh ya koma gefe ya daga kai yana kallon wannan babbar masarauta da bai taba mafarkin gani a zahiri ba, tun suna yara ya ke jin labarin masarautar Askira, irin tarin arzikin ta da karfin mulkin ta, hannun sa cikin na Sa'ade, sun yi zuru-zuru sabida yunwa da gajiya. Tunanin sa shine wa zai dosa ya ce yana son ganin BILKISU? Wadda marigayi Malam Hashimu ya ce tana daga cikin matan gidan??? Bar ta wadannan dogayen dogaran dake shige da fice suna muzurai kamar sa ci babu, wasu a tsaye kyam kamar an kafe su. Kai sai ka dauka babu bargo a cikin jikin su. Babban abinda ya fi razana shi shine shirgegiyar kofar masarautar, irin kofar nan ce ta jan karfe da ake kira mahdi-ka-ture. Ya ajiye kunshin kayan Sa'ade dake hannun sa a kasa yace da Sa'ade ta hau kai ta zauna, shikuma ya zare sidadden silifan sa ya zauna akai ya kurawa kofar shiga masarautar ido yana tunanin ta inda zai bullo. Kafin ya farga sai ya ga Sa'ade na gyangyadi akan kunshin kayan ta sabida wahala da gajiya. Sai ji yayi wani Dogari ya buga musu gigitacciyar tsawa, "Kai tsoho! Me kuke nema anan?" **** Baba Sale ya mike yana kakkabe kurar jikin sa Sa'ade ma ta yi firgigit ta farka daga gyangyadinta, sai rarraba ido take gabadaya ta firgice. Cikin raunin murya Baba Saleh ya dubi dogarin ya ce. "Mu baki ne tun daga Tsanyawa ta jihar Kano, bawan Allah na zo garin nan ne takanas don in ga Sarkin Askira, don Allah don Annabi ka taimaka mana". Wani wulakantaccen kallo dogarin yayi musu sannan ya ce "ka san wa ka ke nufi kuwa? Tsoho anya lafiya kalau kake?" Baba Sale yayi murmushi mai ciwo irin wanda dan adam ke yi in yana son boye bacin ran sa, ya ce "bani da alaqa da shi, kuma ban zo neman komai wajen sa ba, sakon dana ke dauke da shi na matar sa ne, kaga kuwa bai yi daidai ba in nemi ganin matar sa ba tare da na fara neman alfarmar sa da yardar sa ba. Ka taimaka mana ko don yarinyar nan da ke jin yunwa, marainiya ce". Dai-dai lokacin wani gajeren dogarin ya taso don ganin abinda ya tsayar da dan uwansa wajen wadannan mutanen masu kama da korarrun jeji, "Buba me suke nema ne?" A raine ya dube su sannan ya nuna su da bakin sa "wai maimartaba suke son gani" "amma shine zaka bar su a tsaye ko wurin zama bazaka basu ba?" Ga dukkan alamu shi wannan din mai kirki ne, ya ce da dan uwan sa "maimartaba ya bada damar duk mai son ganin sa ya ganshi cikin kasar sa, cikin aminci da girmamawa, don haka barkan ku da zuwa Masarautar Askira, amma baza ku samu ganin maimartaba ba sai washegarin gobe in Allah ya kaimu idan an fito fada". Baba Saleh yayi godiya sannan ya ce "don Allah ko zan samawa yarinyar nan wajen kwana? Ba mu san kowa a garin nan ba, ni bani da matsala ko a nan wajen zan iya kwana". Wanda aka kira da Adamu wato mai kirkin dogarin, ya ce "ta zo muje in kaita wajen matata ta kwana, kai kuma ka biyo ni". Matar Adamu itama baiwa ce a gidan, bangaren su yana daga can karshen masarautar, unguwa ce guda duk bayi ne da iyalan su, amma yawanci basa wuni anan kowacce tana sassan data ke aiki cikin masarauta, sai dare can suke komawa gidajen su. Ta zubawa Sa'ade tuwo da miyar yauki ta kawo mata ruwa a kofin silba, Sa'ade ta tasar ma tuwon nan kamar Allah ya aiko ta. Sai da ta ci ta koshi matar ta zuba mata ruwa a buta ta nuna mata bayi, taje ta kama ruwa ta fito tayi alwallah ta shimfida mata tabarma anan dan tsakar gidan ta, ta shiga rama sallolin da ke kanta. Ana idar da sallahr isha kuwa barci ya dauke ta akan tabarmar data yi sallar, matar tayi mata shimfida a dakin ta ta tashe ta ta koma daki, ita kuma ta cigaba da ayyukan ta. Washegari ta bata koko da kosai ta karya kumallo, ta sa ta tayi wanka ta canza kaya cikin nata dake kulle, Adamu bai shigo ba sai karfe goma na safe ya ce ta biyo shi. Tayi wa matar da ta ji ya kira Kubra godiya sosai, tabi bayansa, anan waje suka hadu da Baba Saleh ya ji dadin ganin ta cikin kyakkyawar kama, ya karbi kullin kayan ta suka bi bayan Dogari Adamu zuwa fadar sarki. Wuce wannan shigifa, tsallake wannan soro, wuce wannan falo har suka dangana da inda Sarki ke ganawa da jama'ar gari a kowacce rana. Dogarin ya ce su tsaya daga waje, ya shiga ya fadi yayi gaisuwa, sannan ya fadi sakon Baba Saleh, Wazirin sarkin Askira yayi masa tambayoyi a kan su kafin aka amince masa kan ya shigo da su. Baba Sale ya shigo rike da hannun Sa'ade, ya fadi yayi gaisuwa yadda ya ga ana yi, dogarawa suka ce "Sarki ya gaishe ka, ka yi gaggawar fadin abinda ke tafe da kai". Baba Sale ya muskuta sannan ya soma koro bayanin sa cikin nutsuwa, wasiyyar da abokin sa marigayi Malam Hashimu ya bashi a lokacin da yake cikin tsananin ciwo akan gargarar mutuwa, na cewa ya kawo yarinya Sa'ade hannun BILKISU a masarautar Askira idan ta Allah ta kasance da shi. Ya gaya mata cewa diyar ta ce da ta haifa tare da shi a garin Tsanyawa. Sarki Yusufu Bin AbdulHakimu (mai Askira), ya dan zamo daga cikin kujerar mulkin sa ya tsurawa yarinyar ido, wadda ke sanye cikin ragga, 'yar kauye futuk, ya shiga tunanin ta inda ta fito daga jikin matar sa mafi soyuwa a gare shi, ya san ta taba aure kafin ya aureta, amma bai taba sanin tana da 'ya ba, bata taba gaya masa ba.... Sai dai ido, hanci da baki kadai sun nuna zahirin kamannin Fulani Bilkisu a tare da yarinyar. Jini baya taba buya. Har lange-langen jikin. Musamman data dago manyan idanunta tana kallon sarkin, sai ya ga kamar Bilkisun ce ke duban sa da manyan fararen idanun ta. Magana yayi kadan da Wazirinsa, shi kuma ya yiwa bafaden dake gefensa magana, sai bafaden yace da Baba Saleh su biyo shi. Wani hamshakin falo ya kai su can hanyar shiga cikin gidan, falon bai cika girma ba, amma ya sha adon kayan fata na sarauta dasu tum-tum, dogarin ya ce su zauna anan, su jira rabin awa. Daga Sa'ade har Baba Sale ba mai magana, sai kalle - kalle suke mai nuna kauyancin su tifikal, zuwa can Baba Sale ya nisa ya ce. "Sa'ade! Ko me kika ga ya faru da bawa haka Allah ya ga damar ya kasance a gare shi, idan mahaifiyar ki ta karbe ki shikenan, idan bata karbe ki ba, ni zan rike ki tare da Hanne a cikin iyali na har iyakar nawa numfashin". Daga yadda yake magana zaka gane ya karaya, bai san girman masarautar da kasaitar ta ya kai haka ba! Bai san sarautar babba ce irin wannan ba! Ya dauka normal sarkin kauye ne irin wanda ya sani. Masarautar Askira kuwa tana cikin manyan masarutun jihar Borno masu tsohon tarihi da yalwar arziki wadanda ke sahu na biyu a jihar ta Borno bakidaya. Sa'ade cikin rawar murya ta ce "Baba Sale ni dai mu koma Tsanyawa.... ko ta karbe ni bazan iya zama a gidan nan ba tsoro nake ji....wallahi bazan zauna ba". Baba Sale cikin lallashi ya ce "ki kwantar da hankalin ki Sa'ade, idan ta karbe kin shine babban gatan ki, kin ga ni na tsufa, ko zan rike ki na dan lokaci ne nima wa'adina zai cika, baki da kowa a Tsanyawa bayan ni da Innar Hanne, aure zai yi miki wuya don kuwa babu wanda ya san asalin iyayen ki". Yana rufe baki suka ji ana "gyara kimtsi mai Askira......taka lafiya Giwan Askira.....". Sarki ya shigo falon shi kadai, dogarawan suka tsaya daga waje. Kujerar sa wadda ita kadai ce kujera a falon ya je ya zauna. Baba Sale ya fadi kamar zai yi sujjadah yadda ya ga ana yi ya kara gaida sarki, sarki yai masa murmushi ya amsa da wata irin hamshakiyar kamilalliyar murya. Ya mika hannu ya yafito Sa'ade, "zo nan kusa gare ni diya ta". Sa'ade ta rarrafa ta isa gaban shi, ya dora hannu a kanta ya ce "yaya sunanki?" Murya na rawa ta ce "Sa'ade!" Yayi murmushi ya ce "Sa'adatu dai ko? Sannu da zuwa Askira kin ji Sa'adatu?". Sannan ya maida hankalin sa ga Baba Saleh yace ya bashi labarin rayuwar Sa'ade a hannun mahaifin ta tun daga sanda mahaifiyarta ta bar ta. Baba Sale ya gaya masa duk irin abinda ya sani cikin nutsuwa akan Sa'ade da Baban ta, da irin yadda yadda ya raine ta cikin tsananin kulawa, ya gaya masa malam Hashimu ya gaya masa ba don rayuwa da yake zaton ta kare masa ba bazai taba baiwa Bilkisu 'yar sa ba, sabida bai taba jin dadin zama da ita ba har auren shekara biyu ya shiga tsakanin su ya kare a shekaru biyu kacal. Ya gaya masa wahalar da yarinyar ta sha a hannun matar uban ta, da yadda ta kare rayuwar ta a talle. Sarki Yusufu ya kara jan Sa'ade jikin sa yana tunani cikin ransa "anya Bilkisu ce da ya sani? Zata haifi Da ta tafi ba waiwaye shekaru goma sha biyu? Kuma bata taba gaya masa ba daidai da kuskure, ya san dai a bazawara ya aureta amma bai san komai ba bayan wannan akan auren nata na baya. Bata son zancen ko kadan. Shi kuma nan duniya sai ya samu zuciyar sa da matsananciyar kaunar Sa'ade, wadda tausayi da soyayyar uwar ta shine sila. Ya tambayi Baba Sale asalin malam Hashimu, Baba Sale yace "kowa ya san Malam Hashimu bakon haure ne a Tsanyawa babu wanda ya san asalin sa, amma a sanda yake bashi wasiyyar kawo Sa'ade wajen Innar ta ya gaya masa shi dan asalin garin Damaturu ne. Daidai lokacin da aka daga labulen falon, ta shigo cikin taku na kasaita, sanye cikin farar alkyabba da hular alkyabbar a kan ta. A kasan alkyabbar wani kasurgumin bakin leshi ne mai matukar nauyi. Doguwa sambaleliya, fara sol, kamar da ka taba ta jini zai yi tsartuwa. Fatar jikin ta a murje, ga tsayi ga zati, sannan ga kira ta matan Shuwa-Arab tattare da ita. Akwai barima ta danyen gold makale a gefen hancin ta. Manyan fararen idanun ta sun sha 'kohl' sai walainiya suke suna fidda wani sheki na musamman. A hankali take taku har ta isa gefen mijin ta ta zauna. Kuyangin ta suka tsaya daga waje. Ta bi mutanen dake sunkuye a gabansa da kallon mamaki, don sun fi kama da normal talakawan gari, amma a falon ganawar sarki da iyalin sa? Kuma saboda su ne aka kirawo ta? Idanunta suka kai ga birkitacciyar bakauyiyar yarinyar dake zaune gefen sarki, ya rike ta cikin jikin sa. Ta tsurawa yarinyar manyan idanun ta tana kallon ta, idanunta a hankali suke kara girma suna fidda mamaki da al'ajabi. Da gaske ne da aka ce duk inda uwa ta ga dan da ta haifa cikin kowanne hali sai jikin ta ya bata. Babu wanda ya ce mata uffan tsakanin sarki da Baba Saleh, har saida ta dauke idon ta daga kan yarinyar ta sunkuyar. Wani abu yammmm! Na bin jikin ta. Tsigar jikin ta na tashi. Ta kifa fuskar ta cikin tafukanta, cikin zuciyar ta take fadin...... "dama na san ko bajima ko ba dade zata zo ne da kafafun ta, muddin ni na haife ta. Amma ban zaci a wadannan kananan shekarun ba, na dauka dai sai ta mallaki hankalin kanta zata kawo kanta". Sarki Yusufu ya kama hannun Sa'ade ya sanya cikin nata. Expression na fuskarta kadai ya gaya masa duk abinda Baba Saleh ya fada gaskiya ne. "Jeki ga mahaifiyar ki Sa'adatu, ki ji dumin jikin ta, kamar yadda kowanne da yake jin dumin jikin uwar sa". Sa'ade ta kasa yin hakan, ganin yadda matar ta cire hannu daga fuskar ta ta bubbude mata ido, kamr tana gargadin ta da yin hakan. Ta dubi Baba Saleh da kakkausar murya tace. "Kai dan aiken Hashimu! Ka koma ka gaya masa yadda Bilkisu bata taba son sa ba, haka bata son abinda ya fito daga jikin sa, bana bukatar 'yar sa ya cigaba da rikon abar sa shi kadai". Sa'ade ta fashe da kuka, Baba Saleh kuma ya sunkuyar da kai. Sarki Yusufu ya daga ido cikin firgici ya dube ta, anya Bilkisun sa ce wannan? Wadda ko barorin ta bata dagawa murya tsakanin ta da kowa kyautayi ne da mutuntawa? Balle dan da ta haifa? Dan da kullum take adduar Allah ya bar mata ko guda daya? "Ko da Hashimun ya mutu bazaki rike 'yar da kika haifa ba?" Muryar sarki akwai fushi da fusata mai tsanani a cikin ta a lokacin da ya jefe ta da wannan kalami, mikewa tayi tana shirin barin falon ko kadan zuciyar ta bata russuna ba, "idan ya mutu yana da dan uwa a garin Damaturu, a kai ta can ya rike masa". Har ta kai bakin kofa sarki ya kira ta da kakkausar murya... "FULANI BILKISU!" Ta dakata, amma ba tare da ta juyo ba. "Zo ki kama hannun 'yar ki ki tafi da ita sassan ki, ki bata duk kulawar da uwa zata baiwa danta, tana karkashin amana ta, zamana zata yi a gidannan daga nan har karshen rayuwar ta, a bisa kulawa da kiyayewa ta". Yana fadin hakan ya mike tsaye, ya dubi Sa'ade da ke kuka wurjanjan, "daina kuka Sa'adatu, mahaifiyar ki ce bazata cutar da ke ba, dauki kayan ki ki bi bayan ta". Sa'ade ta share hawayen ta da bayan hannun ta, ita in aka ce wannan galleliyar matar mahaifiyar ta ce ma wani iri take ji, tsigar jikin ta har tashi take, tsoron ta take ji sosai, gata da manyan ido da wani irin kwarjini, ita gara ta bi Baba Sale su koma Tsanyawa, abinda ta fada cikin kuka kenan, amma Baba Saleh ya girgiza mata kai ya ce. "Bi ta Sa'ade, kiyi mata biyayya a bisa dukkan umarnin ta, aljannar ki na tare da ita". Ta dauki tsummokaranta tana waiwayen Baba Saleh, shikuma yana yi mata murmushi, tuni Fulani Bilkisu ta fice, kuyangin ta sun mara mata baya, sai da ta hada da gudu-gudu ta cimmasu, Sarki Yusufu yace da Baba Saleh za'azo a kai shi masauki ya huta har zuwa iya kwanakin da ya ke so, sannan zai sa a maida shi har Tsanyawa a motar gida, zai bada sallama a bashi, Allah ya kai shi gida lafiya, yana yi masa fatan hutu mai dadi cikin masarautar sa. Baba Saleh ya zube yayi ta godiya, a take dogarawa suka kai shi masaukin bakin sarki, aka wadata shi da abinciccika da ababen sha na alfarma, sittiru da duk abinda zai bukata. Amma duk wannan bai dame shi ba, tunanin sa na ga halin da Sa'ade zata kasance a hannun mahaifiyar ta. Wadda ta nuna a fili bata bukatar ta cikin rayuwar ta. Bai san laifin da Malam Hashimu yayi mata ba, amma ya lura kiyayyarsa ce ta shafi 'yar sa. Abu daya yake da yakini yake kuma dan kwantar masa da hankali idan ya tuna ita ta haifeta da gaske, duk kin ta da ita bazata cutar da ita ba, sai dai ta kasa nuna mata soyayya. Yana tausayin Sa'ade sabida bata taba dandana kaunar UWA ba, bata taba jin dumin uwa ba, ga wahalar data sha hannun Laure, sannan yanzu ga ta ga uwar amma bata kaunar ta. Zuciyar sa tayi maza ta ce masa "ba ita ce bata so ba uban ta ne bata so, da sannu in sun zauna tare Allah zai musanya zuciyar ta zuwa alkhairi akan 'yar ta".. Da kyar ya samu ya runtsa a wannan dare sabida tunanin Sa'ade, hutun da aka ce ya zauna yayi ya ga bazai iya ba, washegari ya gayawa mai kula da shi ya gayawa maimartaba yau zai koma garin su. Sarki yasa aka yi masa goma ta arziki, aka cika masa bayan mota hilux, sannan ya damka mishi kyautar kudi da sittiru masu yawa. Suka kama hanyar zuwa Tsanyawa a mota hilux zuciyar Baba Saleh cike da alhini na tausayin Sa'ade. **** Sa'ade na bin kuyangin Fulani a baya, fada nan fada can har suka dangana da wani babban gini, kamar gida guda bangare guda haka, aka bude kofar Fulani ta sanya kafar ta kamar wata Dawisu sabida yadda take taku su kuma suna biye da ita, kyawu da kayatuwar ginin yasa Sa'ade sakin baki da hanci tana kallo, har tana tuntube saura kadan ta fadi. Manyan faluka suka rika wucewa har suka tadda wanda daga shi kuyangin suke da shamaki, sai guda daya daga cikin su ce ta bi bayan Fulani, bata jima ba ta fito tace da Sa'ade wadda ta tsaya a inda ta ga kowa ya tsaya itama, ta biyo ta ta kai ta dakin da zata zauna. Inda Fulanin ta shiga nan ta ga sun shiga, wani (english parlour) ne komai fari sol har labulaye da kujeru, kilishin falon ne kawai launin makuba shima da adon fari da baki a jiki, kofofi ne wajen guda hudu a falon bata san a wanne Fulani ke ciki ba, kuyangar ta bude daki daya suka shiga. Sa'ade ji tayi numfashin ta ya tsaya a wuyanta sabida kyawun dakin da tsaruwar sa, komai dake cikin dakin kalar blue and light pink ne, ga wani shimfidadden gado na sarauta (royal bed) da ya ji shimfidu na alfarma. Kuyangar ta shiga bandaki ta hada mata ruwan wanka, tazo ta kama hannnun ta ta kaita har gaban kwamin wankan, ta nuna mata yadda ake amfani da komai don ba sai da bayani ba kallo daya za'ayi wa Sa'ade a fahimci bata taba alaqa da irin wannan muhallin ba a rayuwar ta. Ta kasa boye firgici da razanar data ke ciki. Kuyangar tace zata cuda mata baya. Sa'ade ta zaro ido tace "bana so". Ta fita ta barta bayan ta tattare tsummokaran data tube ta hada da kullin kayan ta ta fita dasu ta zubar kamar yadda Fulani ta bata umarni. Kafin Sa'ade ta fito ta ajiye mata dogayen riguna daidai tsayin ta guda biyu a gefen gado, sannan ta shigo mata da abinci lafiyayye kala kala akan tray. Ta zauna har ta fito daga wankan daure da tawul din data nuna mata sannan ta gaya mata nan ne dakin ta, ba koyaushe zata ga Fulani ba, in tana son ganin ta zata nemeta da kanta, ba'a yarda taje ko'ina bayan dakin nan ba, duk abinda take so ita kuyangar zata dinga shigowa tana yi mata, ta gaya mata cewa itace amintacciyar Fulani, kuma ita kadai ke shigowa wannan sashen, sunan ta "Fanna". Sa'ade ta gyada mata kai alamar ta gane, sannan ta ce da ita "ga hijab nan da darduma kiyi sallah". Bayan fitar Fanna Sa'ade zama tayi a bakin gadon a dofane tana ta kallon dakin, sai ta ji duk alatun dake cikin sa bai burgeta ba, ta ji duniya tayi mata kunci, kewar Baban ta mai son ta, ta zo ta lullube ta. Soyayyarsa ta fi mata duka wannan alatun da babu soyayya a cikin sa sai kiyayya zallah. Amma duk da wannan damuwar dake cin ranta, ba abinda zuciyar ta ke hango mata sai fuskar Fulani Bilkisu ma'abociyar zati da kamala, da wani irin feelings mai fizgar zuciya tamkar maganadisu (maternal love). Wata irin soyayya da bata taba ji akan kowa a duniya ba bayan Babanta, wannan soyayyar har ta zarta wadda take ji akan Baban ta. Shine abinda ta ke ji akan Fulani Bilkisu! Ta lumshe ido tana hasaso yadda ta zazzaro mata ido kada ta zo kusa da ita, a kuruciyar Sa'ade ba don komai bane sai don ita 'yar kauye ce. Tana kyankyamin ta ne kawai. Tasa a ranta daga yau kullum zata dinga wanka, don Fulani ta daina tsantsamin ta. Ta mike ta sanya hijab ta tada birkitacciyar sallarta, wadda ko kadan ba daidai take yin ta ba, sannan babu wani karatun sallah na azo a gani, karewa ma "BA-SIM-MI'ARA" take karantawa a cikin sallahr. Data idar da azahar da la'asar sai ta ja farantin abincin da Fanna ta ajiye mata, ta ci iya cinta kunnenta kamar ya gutsure don dadin naman tolo-tolo, data gama ta je ta wanke hannu ta dawo ta kwanta a gadon da tun dazu take son ta ji yaya yake? Wane irin laushi gareshi haka da tun dazu ya ke fizgar idanun ta? Wani barawon barci yazo yayi awon gaba da ita, sau biyu Fanna tana shigowa, ta fidda farantin ta kunna mata iyakwandishan wanda ni'imar ta ya kara armasa mata barcin. **** Sai safah da marwa take a dakin barcinta, ta kasa barci, ta rasa abinda ke mata dadi. It's very unusual maimartaba ya shigo sassan matan sa. Amma yau sai kawai ta ganshi ya shigo har dakin barcin nata, ba zaton ta ba tsammani. "Zuwa nayi ki gaya min abinda matsayi na bai kai na sani ba, wanda ya faru cikin rayuwar ki ta baya". Ya fada yana mai zama a gefen hamshakin gadon ta. Gabadaya ta zama upset, daga rana zuwa dare, fuskarta kamar jikakkiyar takarda, ta zama yellow, kasancewar ta jazur, damuwa kwance baro-baro, ga wani tsohon kwantaccen bacin rai da ya dawo mata sabo. "Allah ya huci zuciyar ku, Allah ya huci zuciyar Askirama!". (Askirama na nufin 'mai Askira' da harshen Kanuri). Ta cigaba da fadin "Al'amarin bashi da muhimmancin da zaku san shi, shi yasa baku san shin ba. Sabida ban taba daukar sa da muhimmanci ba, ban kuma taba zaton wannan 'yar zata biyo ni ba, don nasan uban ta ko za'a dora masa wuka a makoshi, akan ya bani ita, ba zai taba bayarwa ba". "Sai kuma mutuwa ta yanke muku dukkan kudirin ku ke da shi, akan baiwar Allah, wannan ya isa ya nuna muku cewa karfin kudura da irada naShi ne, bawa bai isa ya tsarawa kansa rayuwa ba, face abinda Ubangiji ya tsara masa". Mai martaba ya fada mata a tsanake. Ta sunkuyar da kanta, tana wasa da yatsun hannun ta, bata ce komai ba. "Ki gaya mini duk abinda yakamata na sani akan yarinyar nan, tunda dai kin yarda sunnah ki kai kika haifeta, kada ki zama azzalumar Uwa, wallahi Allah bazai bar ki ba". Fuskarta tayi jajawur kafin hawaye su cicciko idon ta. "Ran ka ya dade bana son tuna labarin nan, bana so. Ba abun fade a cikin sa, me kake so ka ji? Yes, aure na yi na haife ta, amma ban taba son uban ta ba! Sau daya ya taba kwanciya da ni bisa fin karfi har na samu cikin ta. Kana so ka ji cewa Babana biyan bashi yayi wa ubanta da ni? Ya aura masa ni a matsayin filin sa da yake bin sa bashi?" Maimartaba ya nuna abin bai bashi mamaki ba, a fuska da muryar sa babu komai, yace "to ita yarinya meye laifin ta? Bata zo duniyar ba lokacin, balle ta san laifin da babanta ko baban ki yayi miki da zaki rama a kanta. Ki yi a hankali, 'ya'ya amanar Allah ne a hannun mu, bar ganin ke kika haifeta, wallahi hakkin ta zai iya kai ki wuta. Ba kya tunanin hakkin ta ne yake hana wadanda kike ta haifa rayuwa? Tunda itama baki ji kanta ba a lokacin da Allah ya baki ita?" Bata ce komai ba amma tabbas kalaman sa sun shige ta, daga zaunen da yake ya kamo hannun ta. "Bilkisu ki karbi amanar da Allah ya baki da hannu bibbiyu, na yafe jin labarin auren ki da mahaifin ta tunda na lura yana tono miki bacin rai ne, wanda kika riga kika manta. Abu daya nake so ki rike a ranki shine wannan yarinya dolen ki ce, bata da sauran gata sai ke, wani dan uwan baban ta da kika ce akwai a Damaturu ba shi shari'ah ta bawa rikon ta ba kasacewar ta mace, kuma kina raye, sannan kina da halin rike ta. Ni na karbi yarinyar nan kamar sauran 'ya'ya na..... idan ni da nake kishin Baban ta ya riga ni samun ki, na karbi 'yar sa zan rike da amana, ke mai zai hana ki kwatanta tausayi da adalci irin na UWA ki karbi marainiyar Allah???" Sai ta fada jikin sa tana kuka sosai, jikin ta yana tsuma, ya rike ta sosai a jikin sa yana cigaba da lallashin ta, Fulani Bilkisu ta san maimartaba yana son ta, amma bata zaci son ya kai har haka ba, duk da bata taba haife masa rayayyen Da ba. Shi gashi yau ya karbi nata da hannu bibbiyu, wanda bai taba sanin da wanzuwar sa ba. Idan bata yi masa biyayya ba kuwa, hakika ta cika butulu, wadda bata godewa ni'imomin Ubangiji gareta ba. "Zaki kula da ita ko Bilkisu? Zaki bata kaunar duk da ya kamata ki bata?" Ta gyada masa kai, ba tare da ta ce komai ba. Sai rungume shi data yi sosai a jikin ta. "Ka yi min alfarma Askirama kar ka gayawa kowa cewa 'ya ta ce, don Allah, kace 'yar kanwata ce na karbo, ina gudun gorin kishiyoyi, tunda cikin su babu wadda ta san na taba aure kafin na zo gidannan". "In don wannan ne kada ki damu, amma akwai wadanda sun riga sun ji a fada, zan gargadesu don duk na san su". "Nagode.... Nagode Askirama. Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai)". **** Duk da haka sai da ta kwashe kwanaki uku bata nemi Sa'ade ba, bata shiga dakin ta ba, bata nemi sanin halin data ke ciki ba. Fanna dai ta gaya mata tana nan lafiya kuma tana kokarin koyar da ita tsafta da sauran abubuwa. Sarki Yusufu ya san halin kafiya irin na Bilkisu, don haka bai gushe ba yana cigaba da lallashin ta akan Sa'ade. Tana nuna masa komai lafiya, alhalin bata kara sanya yarinyar ma a idon ta ba. A rana ta hudu sai gashi ya kara dawowa da kansa da safe kafin ya fita zuwa zaman fada. Tana karya kumallo ita kadai a 'dining table' din falon cin abincin ta. Ta mike cikin girmamawa ta same shi a kujerun da suka kawata falon, suka gaisa kamar yadda suka saba cike da kewar juna kasancewar ba ita tayi girki ba, kwana biyu kenan basu hadu ba, cikin hikima irin ta manya ya ce, "Yaya kike cin abincin ke kadai babu 'yar tayin hira? Maza kirawo min ita mu gaisa, sabida ita na shigo". Fuska a turbune tace "bata tashi daga barci ba" "A taso ta" Ba yadda ta iya dole ta juya cikin kasaitaccen takunta ta nufi dakin da ta san ta ce a ajiye mata Sa'aden kamar wani kayan wanki. Ta murda kofar ta shiga a hankali ba tare da ta bari sauti ya fita ba, akan darduma ta same ta tana sallah, tana wani karatu a fili "basim-mi'ara, alu ambaki wau-zal, wa'aluba ilallan haakuri"..... sannan ta tafi sujjadah ba tare da ta yi ruku'u ba. Fulani ta mutu a tsaye, sujjadar ma guda daya tayi ta sallame sallahr. Kamar jikin ta ya bata da mutum a dakin, da sauri ta juyo, suka hada ido da matar data ke kwana tana wuni da ita a ran ta. Da kyar Fulani ta hada sautin muryar ta waje daya, ta ce "sallahr me kike yi?" "Asubah ce Inna" "Asubah? Wa ya ce miki yanzu ne lokacin sallar asubah karfe goma na safe har ta wuce?" "Ai i yanzu nake yin ta kullum, wataran ma sai na dawo daga talla ma nake hadawa da azahar inyi kafin Baba ya barni na fara zuwa makarantar A-BA-CA-DA". Takaici ya hanata magana kawai ta juya a fusace tare da cewa "biyo ni". Suna shigowa falon taga maimartaba a zaune cikin rawanin sa da jabba, da sauri ta tafi gareshi ta zube a gaban sa, ta lura shi mai kirki ne ba irin matar sa ba mai kama da mala'ikun daukar rai. "Baba ina kwana" yayi murmushi yana kallon ta da tausayi "Anan ba'a cewa Baba diyata. "Alanguburo" ake cewa. Tayi kokarin maimaita kalmar amma ta kasa. Yayi dariya kadan cikin tausayi yace "kina son makaranta?" "Sosai Alan...." sai ta yi shiru. Ya karasa mata "......guburo" ta maimaita a hankali "Alanguburo" "masha Allah! Makaranta wacce kike so? Ta kwana ko ta jeka ka dawo?" Ta saci kallon Fulani Bilkisu ta ga yadda take hararar ta, sai ta ga ai gara mata ta zabi makarantar kwana akan zama ita kadai cikin daki da idanun Innarta masu razanata. A hankali ta ce. "Na fi son makarantar kwana Alanguburo" "To shikenan tashi jeki abun ki, nan da sati biyu za'a kai ki, amma bazakiyi nisa da gari ba, nan cikin garin Maiduguri zan sa a nema miki mai kyau, ince ko kina kunna talbijin kina kallo?" "Menene talbijin Alanguburo?" Ya nuna mata ita da hannu, ta ce "ai babu a dakin dana ke" ya ce "Innar ki bata kyauta ba, yau zan sa a kawo miki taki a jona miki a dakin ki". Ta hau murna sosai ta ce "Nagode Alanguburo" Yace "Allah Kawun jo". **** Duk yadda ta so ta wuni cikin sukuni a ranar ta kasa, sallahr Sa'ade da karatun sallahrta kawai take tunowa. Hankalin ta ba karamin tashi yayi ba, wai dan musulmi ne yake irin wannan ibadar, me ake da rayuwar jahilci. Ta so ta share, don a ganinta tunda Askirama ya ce zai kaita makaranta ta san zata koya a can, amma sati biyun da zata cigaba tana irin wannnan sallahr zuwa lokacin da zata koya din shin idan ta bari Allah ba zai tambaye ta ba? Tunda har ya nufe ta da gani, tamkar umarni ne ya bata kan ta yi mata gyara tana so ko bata so, ita ba jahila bace ta san muhimmancin sallah ga dan musulmi, balle wanda ka haifa a cikin ka. Ta kira Fanna da zata wuce kai mata abincin dare, tace "kira min yarinyar can ta same ni a dakina yanzun nan". Fanna ta yi matukar mamaki don banda ita Fannan ba mai shiga dakin Fulani Bilkisu, itama gyara ne kawai yake kai ta shima ba kullum ba, sai lokacin da Fulanin ta bukata. Har dakin ta kawo Sa'ade, sannan tayi bankwana ta juya, don ta gama aikin ta na daren sai kuma gobe. A wannan lokacin ne Fulani ta yi mata kallo na sosai, tana durkushe gabanta kamar yadda ta ga Fanna na yi, da can a fizge take kallon ta, a 'yan kwanaki hudun kacal data yi cikin gidan har ta fara washewa, kamannin ta da ita sun gigitata, kallo daya zaka yiwa yarinyar ka san ita ta haifi abar ta, kamar ta yi kaki ta tofar. Anya akwai wanda zai yarda in aka ce ba 'yar ta bace? Ko dai ta bari Askirama ya fadi gaskiya ne? Amma in ta tuna gorin da zata sha wajen Ya Gumsu (most senior wife ta sarki) kuma wadda suke buga mugun kishi da ita fiye da sauran matan sarki sabida yadda take jin kanta matsayin uwar manyan 'ya'yan sa, amma ya zo yana fifita Bilkisu akan ta, wanda hakan ya haifar da zazzafan kishi a tsakanin su, sai ta ga gara ta bar ta a 'yar kanwar ta ce, ai is normal dan dan uwanka yayi kama da kai. Ta yi ajiyar zuciya tareda dauke kanta daga kallon yarinyar tana jin kirjin ta na wani irin bugawa, inta kalli yarinyar sai ta tuno sanda Hashimu ya daure ta a jikin karfen gado ya haike mata, ko ta so ta ji tauayin ta abinda take tunawa kenan ta ganta bakikkirin a idanun ta, duk da an ce ya mutu, bata jin nan kusa zata yafe masa, ta hadiye wani kullutu daya tokare ta a kahon zucci, tana mai kautar da kanta ta ce mata. "Kin yi sallahr Isha?" "A'ah Inna, bari nayi sai can dare, an ce sallah cikin dare tafi lada" Ta galla mata harara tace "inji uban wa? Ni kar ki sake ce min Inna". Sa'ade ta yi shiru tana kikkifta ido. Ta nuna mata hanyar toilet da hannun ta "muje ki yi wankan sallah da alwalah akan idona na gani" Sa'ade ta zaro ido. "Kina nufin a gaban ki zan yi timbir?" Ta sake galla mata harara cikin tsawa tace, "Rufe min baki! Ko kin ga ana yi min musu a gidannan? Zaki wuce ko sai na hankada ki?" Sum-sum-sum Sa'ade ta wuce ita kuma ta bi bayanta. Da kyar Sa'ade ta iya cire riga a gaban Fulani, tana yi tana kare kirjin ta, tace tayi wankan tsarki tana gani. Ai yadda ake normal wanka da soso da sabulu haka Sa'ade ta yi, alwala kuwa ba'a zancen ta. Fulani Bilkisu ta ji kwalla ta tarammata, ba na tausayin yarinyar bane na tunanin wai gudan jinin ta a duniya ne wannan ba arabi ba boko. Zama tayi akan masai ta dinga gaya mata yadda zatayi wankan tsarki don ta tambayeta cewa ko ta fara ganin jinin al'ada ta tabbatar mata ta fara, sannan ta koya mata alwala, suka fito ta bata mayafi tace ta tsaya ta lura sosai da yadda take sallah. Sannan tasa ta tayi tana kallo. Akwai improvement sosai duk da haka wani abun sai kyalewa ta yi, ta san a hankali zata kara gyarawa. Sannan ta zaunar da ita a gaban ta ta koyar da ita fatiha, falaki da nasi da ikhlas, cikin 'yan mintuna Sa'ade ta karanta mata su tiryan-tiryan, daga nan ta gane tana da saurin daukar abu muddin zata samu kulawa. Sai karfe goma na dare ta sallameta. Bayan ta gaya mata wannan karatun data koya mata yanzu ta karanta ta tofa a hannayen ta ta shafe jikin ta da shi. Daga ranar kuma bata kara nemanta ba, sai bayan sati guda, shi din ma kayane akwati uku maimartaba ya aiko mata dasu, atamfofi, lesuka da shaddoji na alfarma, ta sa telar ta tazo har sassan ta ta gwada yarinyar a gabanta, don har zuwa ranar ko kofar falo na biyu bata bari ta fita ba, Allah Allah take ma satin ya zagayo a kaita makarantar kwanan ta huta. Ta manta cewa magana bata buya a gidan sarauta, abinda bata sani ba kuyangi suna magana a junan su cewa yarinyar nan da aka kawo daga kauye tun ranar da ta zo basu kara ganin ko inuwarta ba kuma basu san daga ina aka kawo ta ba ko aikin me ta zo yi. Har tsakanin kuyangin sauran matan sarki suna zancen har zance ya kai kunnen su Ya Gumsu, Ya Kirjinoma da Fulani Hibbani cewa Fulani Bilkisu ta dauko rikon 'ya daga kauye. Ya Gumsu tace "matar so an gaji da zaman kadaici an buge da tsinto 'ya'ya". Ita kuwa Hibbani cikin hila ta tambayi Askirama ko ya san da batun 'yar da Bilkisu ta dauko riko? Ba tareda ya bata hankalin sa ba ya ce 'yar kanwarta ce, kanwar tata ta mutu". Haka ta je ta fesawa Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma dama bata shiga sha'anin su, daga ita sai 'ya'yan ta take harkokin ta, tana da kamun girma sosai. A cikin sati biyun kafin tafiyar Sa'ade makaranta akwai cigaba sosai a tare da ita, sallahrta ta gyaru, ga wanka ya kama jikin ta, Fanna ta koya mata yin Brush sau biyu a rana, safe da dare, ta zama kamar Yayarta. Har hira suke yi sosai in Fulani ta tafi girki Turakar Sarki. Tana kara gyara mata kome ta ga ta yi ba daidai ba, har dige-digen data ke yi a fuskarta da kwalli Fanna ta hana ta. Sannan ta kiyaye umarnin uwargijiyarta da gaskiya na cewa kada ta bari kowacce kuyanga ta zo inda Sa'ade ta ke, bata yarda tayi alaqa da kowa cikin sassan ba bayan ita Fannar. Ana i gobe sati biyun da Sarki yayi alkawari ya sake shigowa sassan nasu, wannan karon da daddare. Ya samu Fulani da kuyanginta kusan su duka goman ana bata labarai tana murmusawa. Yana shigowa duk suka mike, fadi suke in chorused "...zauna daidai mai Askira... takawar ka lafiya Askirama!" Suka fice akan layi, shikuma ya zauna sannan ya soma yiwa Fulani fada. "Haka kawai kin kama yarinya kin kulle a daki don mugunta, kin hanata ko zama cikin kuyangin ki, to wadanda kike gudun su san da zamanta sun riga sun sani, gara ma ki sakarwa yarinya mara ta yi fitsari". Ita dai bata ce komai ba sai "Allah ya huci zuciyar Askirama (mai Askira). Bai amsa ta ba ya ce "kira wo min Sa'adatu". Ta tashi tana tafiyarta cikin yauki na halitta ta nufi dakin Sa'ade. "Ke ki zo ana kiran ki". Ta ce da Sa'ade wadda ke luntsume tsakiyar gado ta kafawa talabijin ido tana kallon diramar larabawa. Irin yadda ta saki baki da hanci tana kallon ba karamin haushi ya baiwa Fulani ba. Kamar tayi fiffike ta shige cikin akwatun talbijin din a yi da ita. Ko maganar Fulani bata ji ba, sai da ta taka ta kashe soket din talbijin din, tayi firgigit tace "haba don Allah Inna ya zaki kashe mini.....?" Sauran maganar ta makale mata a makoshi sabida mugun kallon da Fulani ta jefe ta da shi. "Na ce ki zo, ko ke kurma ce ne?" Sa'ade ta sauko daga gadon ta bi bayan ta don tuni har ta fice, tana shigowa falon ta yi arba da Sarki, ai tuni ta washe ta daina fushin kashe mata talbijin da Fulani ta yi ta nufi wajen sa cikin tsananin murna. "Alan....ina wuni?" Yayi murmushi ya yafito ta da hannun sa. "Zo nan kusa gare ni Sa'adatu" ta rarrafa gabansa ta zauna ya ce "Ah! Masha Allah, da alama Fulani tana kula da ke, gashinan kin yi haske kin yi kumatu" ta saci kallon Fulanin, hararar data ke mata yasa ta kasa fada masa abinda ta yi niyya, cewa ita bata wani kula da ita, Fanna ce take kula da ita, ita sai tayi kwanaki bata ko ga inuwar ta ba. Aka soma shigo da kwalaye da katon katon na kayan masarufi ana jibgewa a gefe. Daga ita har Fulani Bilkisu bin kayan suka yi da kallo don basu san ko na menene ba. "An samo makarantar Sa'adatu, an gama komai, gobe za'a kaita, ita da zuwa gida sai karshen kowanne zangon karatu, sai kuyi sallama yau, don gobe da sassafe za'a kai su ita da Humaira". Fuskar Fulani ta tattare cikin rashin jin dadi, bata son a alaqanta komai na Sa'ade da 'ya'yan gidannan, ba don komai ba sai don gudarwa kanta gori. Balle 'ya'yan Hibbani sarakan surutu, ita kuma Hibbanin uwar tsugudidi, in taji abu to tabbata Ya Gumsu ta ji ta gama. Amma ai da kunya tace masa bata so ya hada 'yar ta da 'yar sa, shi da yayi wannan kara ta mutuntawa in ba'a gode masa ba akalla baza'a kalubalance shi ba. "Allah ya kaimu" Kawai ta ce. Sa'ade ta dago cikin farin ciki ta ce "Alan....amma inna tafi sai bayan shekara zan dawo ko?" Cikin mamaki yace "ba kya marmarin ganin Innar ki zaki yiwa kanki fatan yin shekara a makaranta?" Ta sunkuyar da kai a ranta tana so ta gaya masa ita Innar ce bata son gani kusa da ita da wadannan muzuran idanun nata masu karkada mata 'ya'yan hanji, sannan kadaici yana damun ta, banda yanzu da aka jona mata talbiin take debe mata kewa. "Wata uku zaku yi ku dawo hutu, na hada ki da 'yar uwarki Humairah don ki ji dadin zama kina ganin na gida a kusa da ke. Ki maida hankali kiyi karatu, ki kawo min sakamakon da zan yi alfahari da ke, kin ji Sa'adatu?" Ta gyada masa kai "insha Allah zan yi kokari Alan....guburo, nagode, Allah yayi maka fin abinda kayi min". Shi da Fulanin duka suka kalle ta jin abinda ta ce, don basu yi zaton tana da hankalin sanin an yi mata alkhairi ta bi da kyakkayawar addua irin haka ba. Cikin daren Fulani ta kasa barci, ba kewar Sa'ade ta ke ba, damuwar ta na hada Humaira da Sa'ade da za'ayi ne waje daya, ta san Humaira da shegen kinibibi kamar na uwar ta zata iya jan Sa'ade a jiki ta ji sirrin su ta fesawa uwarta. Don haka ta mike daga kwanciyar ta ta sanya hijab kan rigar barcin ta ta nufi dakin Sa'ade. Ta yi dai-dai sai sharar barci take abinta, santala-santalan fararen cinyoyin ta a waje, rigar barcin ta yaye can sama, gashin kanta da Fanna ta wanke mata dazu da shampoo sai sheki yake ga santsi, sai ta ganta exactly like herself when she was twelve years of age, a perfect replica of Bilkisu! Bata taba yi mata cikakken kallo irin na yau ba, kauyancin duk ya fara barin jikin ta, a maganarta kawai zaka ji shi. Ta daddage ta daka mata duka a cinya, Sa'ade ta zabura ta tashi tana sosa wajen tana mutstsikar ido. "Haka kike kwana tsakiyar kwan lantarki sabida baki da hankali ko? Me yasa baki kashe ba?" Sa'ade ta zumburo baki "ni ban san ana kashewa ba" "daga yau duk sanda zaki kwanta ki kashe fitila mai haske ki bar dim, na ga alama ke kidahuma ce" Sa'ade ta kumburo kumatu bata amsa ba. Ta dora kafarta daya bisa gadon ta tsaya akan daya, sannan ta kama kunnenta na dama da kyau ta murde, Sa'ade ta saki tsuwwa don zafi, Fulani tace "idan kika gayawa wani a makarantar ku ko wadda zaku tafi tare ke 'ya ta ce sai na kabari ya fi ki jin dadi a gidannan, kowa ya tambayeki wacece ni a wurin ki ki ce ke 'yar kanwata ce, babar ki ta mutu, kin ji ni ko baki ji ni ba?" Hawaye na fitowa daga idon Sa'ade ta ce "na ji!". Fulani ta sakar mata kunnen, ta juya zata bar dakin. Sai ta tsinkayo muryar Sa'ade cikin rishin kuka. "Amma me yasa kika tsaneni haka? Da har ba kya so a ce ni 'yar ki ce? Kawai saboda ni Babana talakane ba sarki bane?" Wuta ta daukewa Fulani Bilkisu, ta kasa gaba, ta kasa baya. Bata taba zaton yarinyar zata iya yi mata wannan tambayar ba. Sa'ade tayi murmushi mai ciwo ta share hawayen ta da bayan hannun ta..... "Ki nemo min dan uwan mahaifina na Damaturu, tunda kinsan inda ya ke, insha Allahu zan nesanta kaina dake kamar yadda kike so, zan koma wajen sa". Bata bata amsa ba ta fita daga dakin, jikin ta yai matukar sanyi, bata zaci yarinyar nada hankalin gane abubuwa har haka ba, a shekarun ta goma sha biyu, ko ta yi mata bayani bazata gane ba, bata kin mahaifin ta don talaucinsa sai don rashin SO da zafin AUREN DOLE. Tunda itama 'yar talakawa ce futuk! Gaba da baya, inda halacci ashe kuwa bazata manta talauci sabida arzikin gidan aure ba. Da maganganun da Sa'ade ta gasa mata ta kwana a ranar suna gasa mata zuciya. Shi yasa da safe ta ki fitowa balle ta ga tafiyar ta, bata so ta karasa karya mata zuciya, bata shirya karbar ta matsayin 'ya anan kusa ba kuma har abada bata jin zata iya idan ta tuna Hashimu ne Baban ta. Fanna ce ta zo ta tashi Sa'ade ta taimaka mata tayi wanka, ta bata kayan makarantarta ta sanya, tuni an fidda kayan ta zuwa mota. Tun shigar ta gidan kwana ashirin da daya sai yau ta fito ta shaqi fresh air, daga iskar fanka sai ta A/C. Ta na ta wurga ido ko zata ga Fulani, amma ko motsin ta bata ji ba, ta san kuma bata isa ta shigar mata daki ba bisa umarni ba. Duk ta ji ba dadi da abinda bacin rai ya kwashe ta ta gaya mata jiya. Ta san a matsayin ta na uwa, ko me zata yi mata bata cancanci wadannan kalaman daga gare ta ba. Kawai sai ta kama kuka. Jikin ta a sanyaye ta bi bayan Fanna suka fita daga shiyyar Fulani, kuyangin Fulani na ta kallon ta don su har sun manta tana cikin gidan. Da yake safiya ce basu hadu da mutane sosai a hanya ba sai bayi jefi-jefi amma matan gidan da 'ya'yan su ko jikokin su babu ko daya, kowa yana sashen sa. Har suka shiga dalleliyar motar da direba da dogarai biyu ke ciki, daya na tuki, daya na gefen sa. Sa'ade bata bar kuka ba. A jikin motar an rubuta da ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". Gefen hagu dogarawa suka bude mata ta shiga, kafin su rufe kofar ta kamo hannun Fanna, idanunta narai-narai da hawaye tace. "ki ce ma Fulani don Allah don Annabi ta yi hakuri". Fanna bata san akan me ake aiken ta bada hakurin ba, ta dai lura akwai wani babban al'amari tsakanin uwargijiyarta da wannan bakauyiyar yarinyar. An raineta ne kawai a bisa bin umarni, babu tambaya, don haka tace "insha Allahu zan gayawa Fulani sakon ki". Fanna na barin wajen ba da jimawa ba Sa'ade ta hango wata kyakkyawar budurwa na tahowa karkashin rakiyar bayi 'yammata tsararrakin ta, tafiyar ta kawai data banbanta da tasu ya sa ta gane itace Humaira da Alanguburo yace zasu tafi tare wato 'yar autar sarki. Duk da kayan makaranta ne a jikin ta irin wadanda ke jikin ta amma an dora farar alkyabba wadda ta sha aiki da zare ruwan gold mai matukar walwali akai. Tun kafin ta karaso dogarawan nan suka bude kofar da azama suna yi mata kirari irin wanda 'ya'yan gidan kawai ake yi wa. Ta shiga barin dama, yayin da Sa'ade ke barin hagu. Da ta zo bakin motar sai kuyangar dake bayanta ta zare mata alkyabbar ta shiga daga ita sai kayan makaranta. Daga haka aka ja sullubebiyar motar a hankali suka soma tafiya, kuyangin nata basu bar wajen ba har motar su Sa'ade ta hau kwalta. Tunda suka mika hanya sosai yarinyar take ma Sa'ade kallo na kurilla, ita kuwa tun gaisuwar farko data yi mata bata kara ce mata komai ba. Ta maida hankalin ta ga kallon hanya suna wuce bishiyu da dazuzzuka kamar walkiya. Sanda suka cimma garin Chibok ta ce da Sa'ade cikin ginshira. "Me ye hadin ki da Fulani?" Sa'ade ta tuna gargadin Fulani don haka nan da nan tace "ni 'yar kanwar ta ce, mahaifiyata ta mutu". Gimbiya Humaira ta yi mata kallon shakka don ita dai bata taba ganin irin wannan kamar ta kwabo da kwabo ba irin wadda ke tsakanin Fulani Bilkisu da yarinyar da ke gefen ta. Kamar kamannin sun zarta na matsayin data ambata din na kasancewar ta 'yar kanwa a gareta. To amma wace hujja gareta na karyatawa? Tunda ta san bata haifi 'yar a gidan su ba? Sai ta dauke kai itama ta koma kallon gefen titi. A ranta tana fadin ita sam bazata yi mu'amala da 'yar kalen dangi ba mai maganar kauyawa. **** EL-KANEMI COLLEGE OF ISLAMIC THEOLOGY Makarantar kwalejin kimiyya ce ta addinin muslunci wadda Larabawan Yemen dana Sudan suka bude a Maiduguri da hadin gwiwar manyan masu kudin jihar Borno. Itace makarantar da sarki Yusufu ke kai 'ya'yan sa maza da mata, tun daga kan babbar 'yar sa (Ya Maira) sunan sarautar ta kenan a matsayin ta na babbar 'ya, har zuwa kan auta Humairah. A tsarin makarantar daga Lahadi zuwa Alhamis sune renakun karatu, Juma'ah da Asabar renakun hutu. Malamin maths na fita na Qur'an na shiga, na English na fita na Nahawu ko Fiqh zai shiga, na chemistry na fita na Adab ko Tarikh ko Mutala'a zai shiga haka dai tsarin karantarwar su yake. Wato kimiyya cakude da ilmin addini tsantsa. Sannan ana gama lessons karfe uku ake fara Islamiyya ga mai son haddan Qur'an zalla ake yi har zuwa biyar na yamma. Malaman makarantar kuma yawanci larabawan Sudan da Yemen ne, sai kuma Yarabawa Maza da mata basa haduwa sam, dan katanga ce makekiya a tsakanin su sannan kowane bangare da gate din shi. Tunda aka kai Sa'ade da Humairah dormitory dalibai 'yan uwan su ke kallon su, ba don komai ba sai don irin tsadaddun kayan abincin da ake shigo dasu katan-katan ana loda musu a lokokin su, a karshe lokokin nasu ma sun yi kadan su kwashe kayan, sai Humaira ta ce da metron da masu jerawar su je da sauran ta bar musu. Ko kallon Sa'ade bata yi kada a ce tare suke, amma kayan abincin su ba banbanci haka takalmi da jakar makarantar su, wanda ya tabbatarwa 'yan dakin cewa tare suke din. Gadon Humaira na gefen na Sa'ade, don haka ta yi amfani da wannan damar ta maida ita baiwar ta, komai tana daga kwance take sa ta ta yi mata, dauko wannan miko wancan, ko kofi zata yi amfani da shi sai ta sa Sa'ade ta wanke mata shi, kuma da yake Sa'aden ta iya kitso ita ke yi mata duk sati, basa yin wanki iyayensu ke biya a wanke musu shiyasa Sa'ade ta samu sauki, da har wanki da guga ita zata ce ta yi mata. Girman kai irin na Humaira ya hanata alaqa da mutanen dakin, ita kadai take rayuwar ta ko a class don bata ga wanda ya isa tayi mu'amala da shi ba duk da cewa duk 'ya'yan masu kudi ne a makarantar amma a wurin Humaira in ba ka da jinin sarauta cikin jikin ka to baka isa mutum ba. Kuma duk makarantar ita kadai ce 'yar Sarki. Sabanin Sa'ade wadda ta maida kanta abokiyar kowa a dakin nasu, in har bata hidimar Humaira to zaka sameta cikin jama'ar dakin suna hira da harkar arziki, ga ta da kyauta, haka take ta rabar da kayan abincin nata musamman ga wanda ta lura yana da bukata, cakuduwar ta da dalibai 'yan uwan ta wadanda suka fita experience da exposure ya sa ta fara samun wayewar kai. A aji kuwa duk ita ce koma baya a kowane darasi daga na boko har na addini, amma bata barin hakan ya kashe mata gwiwa, ya cire mata hope na cewa da sannu zata iya idan ta sanya jajircewa da bada himma. Haka monitar ajin nasu Raheema Kyari ke yawan gaya mata, wadda tasu ta zo daya, sakamakon yawan tambayar ta abubuwa da Sa'ade ke yi idan bata gane ba ba tareda nuna jin kunya ko girman kai ba. Ba ajin su daya da Humairah ba ita 'yar JSS 3 ce yayin da Sa'ade ke JS 1. Don haka tafi jin dadin rayuwa a class fiye da a dormitory (dakin barcin dalibai) sabida babu Humaira mai takura mata, a nitse take karatun ta tare da likewa monita Raheema tana daukar ilmi daga wajen ta. Malaman ko sun so yin korafi akan rashin kokarin Sa'ade sai su fahimci abin nata daga tushe ne wato bata samu foundation a makaranta mai kyau ba kamar sauran daliban makarantar, don in sun tambayeta wace makaranta tayi tana gaya musu a kauyen Tsanyawa ne, makarantar da maigari yasa aka bude, don a koyawa yara A BA CA DA sai su daga mata kafa musamman in suka lura da yadda take da kishin abun a zuciyarta, in aka koya abu bata gane ba har kuka take yi. Duk kokarin Raheemah na koyar da ita ba komai take ganewa din ba musamman darasin lissafi, da yawa a makarantar sun dauka Sa'ade baiwar Humairah ce, irin 'ya'yan bayi da ake hado 'ya'yan sarakai dasu su zo makaranta tare don su dinga hidimta musu, sabida haka Humairan ke nunawa. Sannu-sannu bata hana zuwa, saidai a dade ba'a je ba, a hankali Kwakwalwar Sa'ade ta soma budewa, musamman a haddar Al'qurani da Ingilishi. Raheema ta taka rawar gani akan hakan don fisabilillah take kaunar Sa'ade sabida saukin kanta, baban Raheema babban dan kasuwa ne a jihar Maiduguri wanda sunan sa yayi fice akan sana'arsa ta fata. Watarana Raheema ta kawo wa Sa'ade ziyara dakin su, sai ta same ta durkushe gaban Humaira ta sunkuyar da kai tana hawaye, Humairan na ta zazzzaga mata fada har tana fadin dama 'yan kalen dangi basu iya cin arziki ba, banda haka tun safe ta sa ta gyaran sittirunta amma tasa kafa ta fice yawon neman suna bata gyara mata ba, su ko Fulani Bilkisu ba wata tsiya bace a wurin su tunda sun san asalin ta balle su ya-ku-bayin data kawo musu gida suna cinye arzikin Babansu. Ba fadan data ke mata ne yasa ta kuka ba, domin in da sabo ta saba, ambaton sunan Fulani data yi ta zaga ne ya tsaya mata a zucci. Ya kona mata zuciya. Fulanin da has never been nice to her in any way amma zuciyar ta na mata wani irin so, da bata taba jin sa akan kowa ba including Baban ta. Rahima ta kama hannun ta ta cira ta tsaye suka bar dakin, Humaira ta sakar musu tsaki tana fadin "ya'yan mutsiyata, gayyar tsiya". Can bayan dormitory suka zaga suka zauna akan duwarwatsun da ke wajen, Raheema ta ce "wai don Allah Humaira ke baiwar ta ce? Ko iyayen ki bayi ne a gidan su?" Bata san me yasa ta yarda da Raheema ba, tun sanda ta fahimci Raheemar na tausaya mata tsakani da Allah. Ta girgiza kai tare da share hawayen idon ta "ni ba baiwar ta bace, ana riko na ne a gidan su, kishiyar mamanta ce yar mahaifiyata a hannun ta nake". Raheema tace "tabdi! Amma shine kike mata bauta tana miki wannan wulakancin? Ke ba baiwar ta ba iyayenki ba bayin su ba? To wallahi ki kama kan ki, ki nuna mata zaman kan ki ke yi ba zaman ta ba in ba haka ba watarana sai ta kai ga taba lafiyar jikin ki" da sauri Sa'ade ta girgiza kai. "Zan yi mata komai saboda Baban ta!". Raheema ta rasa abinda zata ce, sabida a amon muryar ta kadai ta fahimci akwai wani girmamawa da kauna na musamman data ke yi wa Baban Humaira, abinda ta fada har zuciyar ta ya ke. Wannan ya tabbatar mata Sa'adatu irin mutanen nan ne da basa manta alkhairin da wani yayi musu komai kankantar sa. **** An yi jarrabawar karshen zango, as expected Sa'ade ta dauko na biyun karshe, ta yi kuka har ta gode Allah, amma a islamiyya ta yi dan kokari ba laifi musamman a hadda. Damuwar ta yadda zata dauki wannan mummunan sakamako ta kaiwa Alanguburo, bayan ta yi masa alkawarin yin kokari iyakar iyawar ta. Raheema ta ce ta bata lambar wayar wani a gidan su zata kira ta in ta koma gida, Sa'ade tace banda Fulani babu mai waya a sassan su, ita kuma bata san lambar ta ba, ko ta sani bazata yi karambanin bayarwa ba Fulani ta tsinke mata kunne haka kawai. A daren ta hada musu kayan su da zasu tafi dasu gida a kananan trollies din su, sauran kayan abincin da suka rage Humaira tace ta fitar duka ta kaiwa metrons. Ta yi sallama da 'yan dakin su cike da kewa suna fadi a ransu ai gara ta je gida ta huta da wannan bautar data sha ta gimbiya Humaira, wasu kuma suka ce a ran su watakila har a gidan ma irin bautar data ke mata kenan. Kusan su ne na farko da aka zo dauka a washegari. Suna tsaye ita da Raheema a jikin bishiya suna hira, Humaira na daga zaune a gefe akan jijiyar bishiya tana ta harare-harare irin wanda ta saba da kallon kowa a wulakance. Zungureriyar mota kirar 4matic baka wuluk ta yi parking a gefe, da rubutu baro-baro cikin ruwan gwal "ASKIRA EMIRATE". "Ma'assalam Raheema, an zo daukar mu" Ta fada tana jan trollies din biyu dake gaban ta, nata da na Humairah, Raheemah ta daga ido tana kallon inda ta nufa, tun kafin ta karasa dogarawa biyu suka yi wuf suka fito daga motar suka karbi kayan hannun ta. Ta karanta rubutun ta sake karantawa "ASKIRA EMIRATE" Ashe daga masarautar Askira suke, no wonder Humairah take mulkin data ga dama. Baban ta ya sha basu labarin masarautar Askira da irin dimbin arzikin ta da shaharar ta a yankin Borno. Ta karasa da gudu ta cimma Sa'ade, ta rike hanayen ta, tana murmushi ta ce "ki gaida mun Fulani, i will give you a giant surprise insha Allah" Sa'ade ta yi dariya ta ce "Fulani zata ji, ki gaida Mama dasu Sarina (kannen ta)". Raheema na juyawa ta kusa karo da Humairah, da sauri ta bata hanya sabida mugun kallon data sakar mata. Ta shiga gefen dama data saba zama dogarin ya rufe kofar. Ya zaga mazaunin sa ya zauna suka ja motar zuwa get, inda suka cike takardun daukar dalibai sannan aka basu dama suka wuce daga get din makarantar. Tun daga kofar gida kuyangin Humaira na tsaye suna jiran isowar ta. Cikin rakiyar su suka wuce cikin gida kowacce ta doshi bangaren su. Fanna ta fara cin karo da a bakin kofar shiga unguwar Fulani Bilkisu da alama jiran karasowar ta take, tana mata murmushi tace "sannu da zuwa 'yar gida na, yaya hanya kuma yaya karatu?" Tare da karbar jakar kayan ta wadda Humaira ta hana kuyangin ta su daukar mata. Suka wuce zuwa ciki, tsakanin ta da sauran bayin Fulani sai ido, don ba'a basu damar alaqa da juna ba, only Fanna. Ta kaita har dakin ta, ta hada mata ruwan wanka a bathtube sannan ta fita don ta kawo mata abinci. Sa'ade tayi wanka ta ji dadin jikin ta, ta sauya kayan makaranta zuwa doguwar rigar atamfa exclusive mai hasken sararin samaniya, sosai tayi kyau, farar fatar ta ta yi tas, wanka da tsafta sun kama jikin ta, ita kanta data tsaya a jikin mudubin dogon yaro ta kalli kanta sai da ta razana, don gani tayi kuruciya kadai ce zai sa ta kasa cewa Fulani Bilkisu ce a cikin mudubin. Ta ga ta kara tsayi, hancin ta da idon ta sun kara fitowa dara-dara, tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta. Sai data ci abinci ta koshi tayi sallar data kufce mata sannan ta hau gado sai barci. Cikin barcin ta ji an dala mata duka a cinya, ta zabura ta mike zaune, Fulani ce tsaye a kanta ta ci gayu kamar mai shirin gasar sarauniyar kyau. "Wa ya ce da ke ana barci bayan la'asar? Kidahuma kawai". Ta zumburo baki tana mutstsikar ido. "Amma ko sannu da zuwa baki mun ba kin rufe ni da fada, don Allah Fulani me na yi miki ba kya so na?" Ta saki kuka har da na shagwabar ganin uwa, ba wai na zafin fadan da ta yi matan ba. She just felt relaxed by seeing her......after missing her for over ninety days. Fulani ta saki baki tana kallon ta don bata ga abun kuka ba don kawai tace ta daina barci bayan La'asar. Tsaki tayi tace "ba'a son naki, an ki a so ki din, ubanki ya ja miki, banda alfarmar Askirama wallahi bazaki zauna mun a gida ba, Damaturu zan kai ki". Sa'ade ta ida rushewa da kuka, it's painful uwar data haife ka ta bude baki tace bata son ka sabida mahaifin ka komai kazantar laifin uban naka ai mutuwa ma na kunyar idon Da. Balle in ta tuna Uban nata da akewa kiyayyar ba ya duniyar ma. Ita Fulani wace irin zuciya gareta? "Duk talaucin sa dai bazaki kankare cewa shi kika fara aure ba, tun da ga ni.....", sai bayan ta furta kalaman wadanda a zahiri a zuciyar ta tayi niyyar fadar su, ta yi maza ta toshe bakin ta da ta fahimci sun fito fili, amma ina! Already Bilkisu ta ji su. Har ta kai bakin kofa gabadaya ta juyo, ta kankance idanu ta kai mata wani wawan mari, Sa'ade ta kauce amma saida ta samu bayan kunnen ta, dan kunnen ta ya fice ya karce gefen kunnen ta sosai jini ya kwanta a wurin tare da yatsun Fulani Bilkisu. "Wannan ya zamo rana ta karshe da zan kara yin magana ki maida mun, mara kunyar banza! Mai mugun hali irin na uban ta!" Sa'ade na kuka wurjanjan Fulani ta bude kofar dakin ta fice. Tana zuwa falon ta ja ta yi turus! Ganin Askirama a zaune yana jiran fitowar ta. Ya sauke nagartattun idanun sa akanta, ma'abotan kamala da ilhama, a hankali ya ce. "Koma ki kirawo min ita, na jiyo kukan ta". Bata da damar yin musu, haka ta koma jiki a sanyaye tace daga bakin kofa. "Ki zo Askirama na kiran ki". Without giving her a second look ta fice ta bar dakin. Sa'ade saida taje toilet ta wanke idon ta don dai ta boyewa Alanguburo cewa kuka take, amma tana fitowa ta zauna a gaban sa idon sa bai sauka a ko'ina ba sai a bayan kunnen ta. Ya kamo fuskar Sa'ade ya kalli ciwon sosai, yace "Sa'adatu ki yi hakuri kin ji? Ni na gaya miki watarana in wani daban yayi miki haka, sai inda karfin ta ya kare". Sa'ade tayi murmushi duk da idanun ta sun kumbura, a ranta tana tantamar zuwan wannan ranar. Yau ta yarda da gaske Fulani ke kin Baban ta wanda shine mujazar nata kiyayyar. Amma bata ga laifin ta ba, laifin kanta ta gani, da ta ke kasa tankwara zuciyar ta ta mayar mata da magana. Wanda ko kusa bata cancanci hakan daga gareta ba. "Alanguburo ka taya ni bata hakuri don Allah, ni na bata mata rai". Ya yi murmushi ya ce "babu komai ta hakura, amma nan gaba ko me zata yi miki kada ki ji haushin ta, sannan kada ki tanka mata. Uwa ta wuce duk inda kike tsammani. Matsayin ta da darajar ta daban yake dana kowa a wajen ubangiji. Sai da Ya ce abi ta.....a bi ta.....a bita... sau uku kafin ya ce abi Uba. Ina fata kin fahimce ni?" Hawayen nadama na zuba a idanun ta ta gyada masa kai, ta dago ta dubi Fulani da appealing look, amma sai Fulanin ta kauda kai idanun ta jazur, ko kusa bata yi nadamar ciwon data ji mata ba da jinin data fitar mata, ta ma so ya fi haka, tunda ita bata da kunya. Amma can a karkashin zuciyarta ta ji wani sashe daban ya darsa mata tausayin yarinyar. Sanin cewa bata da kowa da zata raba a rayuwar ta sai ita, amma duk kokarin ta ta kasa sanya ta a ranta. Watakila sai ranar da Sa'aden da kanta ta yarda cewa ba laifin ta bane duk abinda take yi mata akan baban nata. Ko kuma ranar da zuciyar ta ta gaji ta russuna ta karbi Sa'aden don kan ta. "Je ki ki huta zan sa a kawo miki magani ki sha". In ji Alanguburo. Har ta mike sai kuma ta dawo gaban sa ta durkusa. "Ka yi hakuri Alan....ban cika alkawarin dana yi maka ba, ban yi kokari a makaranta ba, na yi duk iya kokarin da zan iya amma na kasa kamo kowa....a karshe nice ta biyun karshe". Yana murmushi ya ce "to ai babu komai tunda kin kada mutum daya, a ta gaba na tabbata goma zaki kayar, a ta can gaba ashirin, a ta gabanta talatin, daga haka har ya zamo kece a saman kowa. Kada hakan ya karya miki gwiwa kin ji? Ba wanda aka haifa da iyawa, kowa a hankali yake zama gwani, je ki kwanta ki huta sosai kafin a kawo maganin, ko talbijin ban yarda ki kunna ba sai gobe". Cikin jin dadi ta amsa tareda yi masa godiya, ta saci kallon Fulani ta ga harara kawai take zabga mata, ta wuce su zuwa daki kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki. Barcin da ya ce ta yi, ta so ta yi amma ta kasa, duk tunanin ta na yadda zata dinga yiwa Fulani biyayya ne, insha Allahu daga yau bazata sake bata mata rai da gangan ba. ***** "Me ya kai ki? Me ya kai ki dora hannu a jikin marainiyar Allah Bilkisu? In da ya zo da tsautsayi kin kurunta ta fa? Wallahi bar ganin ke kika haife ta, akwai hisabi tsakanin 'ya'ya da iyayen su". "Ku yi hakuri Askirama!". Abinda ta iya furtawa kawai kenan, ya mike cikin bacin rai mai tsanani ya ce "ni kam ba abinda kika yimin sai kyautatawa, balle ki bani hakuri, tunatarwa ce kawai nake miki domin tana amfanar da muminai. Amma tunatarwar da kullum sai an maimaita maka ita, ban ga amfanin ta ba. Daga yau bazan kara yi miki magana akan 'yar ki ba, na tabbata kin fi ni son ta. Saidai bana bayan zulunci, ni shugaba ne mai adalci wanda Allah ya damkawa amanar duk wani talaka da ke cikin garin Askira babba da yaro, balle wanda ke cikin gida na karkashin iyali na don haka bazan lamunci duka ba, in kin so ko dakin ta ki daina shiga wannan ya rage naki, amma duk ranar da kika sake kai hannu a jikin ta zaki ga bacin rai na Bilkisu". Ta tabbatar yau ta kure hakurin mai Askira, dole ta kwantar da kai tayi ta bada hakuri. Tsakanin mace da miji sai Allah balle Bilkisu da Sarki Yusufu mai Askira. Soyayyar su wata ajiya ce daga Allah. Wadda babu irin ta a wannan zamanin, soyayyar mazan jiya masu dattako da sanin yakamata. Fanna ta kawo mata magani ta sha, arashin sanin ta har da maganin barci a ciki. Haka tayi ta barci kuma Fanna bata tashe ta ba saida lokacin sallah yayi. **** Kwanansu bakwai da dawowa hutu, Sarki Yusufu da Fulani Bilkisu da Fulani Hibbani suka tashi zuwa kasa mai tsarki domin gabatar da aikin Hajji na wannan shekarar kamar yadda suka saba duk shekara, yana daukan mata biyu ne cikin matan sa su tafi da kwarkwarori biyu. Harkokin gidan suka cigaba da gudana kamar yadda suke gudana in sarki baya gari karkashin kulawar Wazirin gari Ibrahim. Kadaici ya kara yi wa Sa'ade sallama, bata ganin kowa sai Fanna, bata zuwa koina daga dakin ta sai falon Fulani na karshe wanda babu mai shigar shi in ka dauke Fanna. Ta kagu a koma makaranta ko ta hadu da Raheemar ta su yi ta karatun su ya fiye mata wannan jin dadin mara 'yanci. Domin kafin Fulani ta tafi ta ja kunnen ta sosai akan kowa na gidan koda kuwa bayi ne, bata yarda ko magana ta hada ta da kowa ba sannan bata yarda ko kofar unguwar ta ta fita ba. Ko me take so ta gayawa Fanna zata yi mata. Satin su Fulani biyu a kasa mai tsarki, rannan da Fanna ta kawo mata abincin rana ta hado mata da wata wasika da aka rubuta da fensir, tace "sakon ki ne daga kawar ki". Tun kafin ta bude takardar ta gane rubutun Raheema wadda ta rubuta sunanta a bayan takardar. Raheema Kyari. Jikin ta har rawa yake wajen warware takardar. Ga abinda Rahima ta rubuta. "Hi Sa'adatu, Ni ce Raheema, na zo tun daga Maiduguri as i promised to surprised you, an hana ni ganin ki, don an ce ba'a bada umarnin ki ga kowa ba, sannan Fulani bata gari balle a nemi izninta. Ina fatan ba za kiyi ta kallon talbijin ba, zaki yi ta bitar littatafanki ne kina koyar da kanki kafin mu koma hutu, na so in kwana uku tare da ke don muyi karatu sosai in koya miki mathematics, Allah bai yi ba, musamman Abba ya bada mota aka kawo ni, dana gaya masa masarautar Askira ne bai hana ba. Na so mu hadu, na so in ga Fulani, na so in gan ki, but some other time insha Allah. Mama da Sarina suna gaishe ki. Yours sincerily, Raheemah Kyari. Har hawaye ta yi na bakin cikin rashin ganin Raheema, ta yarda Raheema mai son ta ce, mai kaunar ta ce. Tunda har ta iya biyo ta tun daga Maiduguri har Askira. A karshe ta dauki shawarwarin Raheema, ta daina kunna talbijin, ta mayar da littafanta da darussanta na baya ababen debe mata kewa kuma abokan hirar ta. Sosai take tsintar abubuwa masu muhimmanci, sannan ta dinga tisa haddar ta, Fanna ta kawo mata 'yar radio tana sauraren karatun Abdurrahman Sudaith a ciki. Cikin haka har Allah yayi wa Fulani da maimartaba dawowa daga aikin hajji ana saura kwana biyu su koma makaranta. Suna dawowa shirin komawar su aka fara, aka yo musu provision har fiye dana wancan hutun, babu wanda Fulani bata yiwa tsaraba ba cikin unguwarta (sassan ta). Banda Sa'ade. Ko tsinke bata sayo mata ba. Ita Sa'ade bata san ma an yi rabon tsarabar ba tunda tana cikin daki kullum, ta dai daidaici sanda Fulani take zaman falo ita kadai ta je ta yi mata sannu da zuwa. Tare da tambayar ta "an dawo lafiya?" "Lafiya kalau, alhamdulillahi" Kawai ta ce, ba tare da ta tambayeta komai ba, kamar lafiyar ta ko yadda ta sameta, wannan abu ya sosa ran Sa'ade, ta wuce daki tana share hawaye da bayan hannun ta. Kamar Maimartaba ya san za'ayi haka, da daddare sai ga kyawawan akwatuna manya guda biyu Fanna ta shigo mata dasu, tace tsarabarta ce inji Alanguburo. Ta ce Fanna ta bude mata. Tsala-tsalan dogayen riguna na 'yammatan larabawa ne a ciki kala-kala harda masu ado na sarauta a jikin su, takalma da jakunkuna na yammata masu karshen tsada a daya akwatun kalar kowacce daga cikin dogayen rigunan. Ta cire biyu a ciki ta bawa Fanna, amma sai Fanna tace bazata karba ba Fulani ta basu irin nasu. Wadannan 'ya'yan gidan kawai suke sanya su. Don haka sai ta dauki guda uku a ciki tasa a kayan ta na tafiya makaranta da zummar zata kaiwa Raheemah a matsayin nata tsaraban. Tunda suka dawo hutu wajen kwana arba'in bata kara sa gimbiya Humairah a idanun ta ba, sai yau a cikin mota da zasu koma makaranta. Da ta gaisheta ko amsawa bata yi ba don Fulani Hibbani ta kara ja mata kunne akan mu'amala da ita, ta gaya mata duk abinda Alanguburo ya sayo mata a Saudiyyah irin wanda ya saya mata ne ko banbancin kala babu. Wannan ya kara rura wutar kishin Sa'ade a zuciyar Humairah, ta kudiri aniyar kuntata mata wannan zangon fiye da na baya. **** Da Allah ya tashi taimakon Sa'ade, satin su biyu da komawa aka yiwa dalibai canjin dakunan kwana, inda aka dauke ta daga dakin su Humaira kuma cikin ikon Allah ba'a kaita kowanne hostel ba sai na su Raheema. Murna wajen su abin ba'a cewa komai, a daren ne ta samu ta baiwa Raheema tsarabar data ajiye mata, ita kuma ta bata labarin zuwan ta Askira, tace ta damu baban ta da labarin ta ne ta yi ta rokon sa kan ya sa a kaita, shi kuma ya amince, amma cikin rashin sa'a sai bata samu ganin ta ba. Nan aminci ya kara kulluwa, suka hade kai suka zama kamar 'yan biyu, gasu dama tsayin su daya, sai dai Raheema baka ce sosai cikakkiyar Kanuri, yayin da Sa'ade take jajawur kamar Fulani Bilkisu. Kawancen Sa'ade da Raheema ba karatun Sa'ade kadai ya taimaka ba, ya taimaka mata a sauran fannoni na rayuwar diya mace, tsafta, kwalliya, da iya magana, hatta tafiyar ta Raheema gyara mata take don tace tana tafiya gaba-gadi babu tsanaki. Ta koya mata magana a hankali cikin nutsuwa da yadda zata dinga gyara da kula da sassalkan gashin kanta na Shuwan usli. Rayuwar Sa'ade ta yi ta samun cigaba islamically, educationally, socially and morally a makarantar EL-KANEMI COLLLEGE OF ISLAMIC THEOLOGY. Balle yanzun da bata da tension din Humairah, kowa son ta yake a dakin su, kowa so yake ace shi abokin ta ne. Ga hannun ta a bude, kyauta gare ta kamar 'yar siyasa. Kwakwalwar ta ta bude a lokaci daya kamar kiftawar ido, take grasping ilmi na kowanne bangare wanda nan da nan ya kara canza ta. Dama Alanguburo ya ce mata tunda ta kayar da mutum daya, to nan gaba zata kayar da goma ne, to ba goman kadai ta kayar ba talatin ta kayar, ita ce ta dauki na goma a ajin su, Raheema ta dauki na farko. Don haka da karfin gwiwarta ta dawo gida wannan hutun. Amma har ta kwana ta wuni, bata ga Fulani ba haka bata ji shigowar Alanguburo sassan su ba. Ta gaji da kallon kofar dakin Fulani ta tambayi Fanna, sai Fanna tayi murmushi ta ce. "Fulani ta tafi kasar India zata haihu". Ta rasa a wane yanayi ta karbi zancen, haihuwa? Daman ciki gare ta? Tana farin ciki da jin zata samu karin mutum a kusa da ita, amma wani gefen na zuciyarta yana kishi. Idan ta tuno dama fa Fulani ba wai tana son ta bane, inaga ta samu dan kanta da ta haifa a gidan sarauta? Ai wulakanci gareta zai koma mode activated. Ta kyabe baki tareda cewa "Allah ya sauke ta lafiya". Hutun nasu dama ba mai yawa bane, na sati biyu ne, har sati biyun ta cika Fulani bata sauka ba balle ta dawo, suka koma makaranta zuciyar ta cike da kewar ta, bata san tana son ta har haka ba, sai yau da ta nemi ganin ko inuwar ta cikin gidan ta rasa. Shima Alanguburo Fanna tace yayi tafiya zuwa kasar Amsterdam (Neitherlands) shi da Ya Gumsu kaiwa babban dan Ya Gumsu dake karatu a can ziyara. Rayuwa ta mikawa Sa'adatu Hashim a makarantar EL-KANEMI da budi da nasara da cigaba ta kowanne bangare. Wani sihirtaccen kyau ke bayyanarwa Sa'adatu wadda zuwa yanzu Sa'ade ya bace bat da taimakon Raheema, dama itace in an tambayeta sunanta sai ta ce Sa'ade Hashimu, bayan ba haka yake a rubuce a rijista ba. Raheema ta tsaya tsayin daka wajen tabbatar da ta mantar da ita rayuwar ta ta kauye, ta yi adopting rayuwa mai cike da cigaba, wayewa da aji daidai na shekarun su, kaunar su da juna abin akwai sha'awa da burgewa a ciki. Ranar wani visiting ne Raheema ta kira ta don ta gaisa da 'yan gidan su, fuska fal far'a take gaida Abban Raheema da mamanta, Bakin Babarbare mai zanen bare-bari akan fuskar shi ya sha manyan kaya na kamala, bayan sun gaisa ya sa musu albarka sai ya kasa dauke ido akan Sa'ade yana tunanin inda ya san wannan fuskar. Tabbas ya san fuskar amma ya rasa ta inda ya santan. Yana ta kokari ya tuna amma ya kasa. Har Sa'ade ta yi musu sallama ta koma cikin dalibai 'yan uwan ta. Su dama ba'a zuwa musu visiting daga ita har Humairah, aiken kayan abinci kawai ake musu daga gida a kowanne visiting. Amma yau tana tsaye cikin daliban da ba'a zo musu ba ta hango shigowar motar data bata mamaki, bakar 'Land Cruiser' ce mai tsayi dauke da rubutun 'Biu Emirate'. Ba ta tafi wajen motar ba ta tsaya a inda take tana kallon su, don ta san ba wajen ta aka zo ba sai dai ko Humairah. Wasu hamshaqan 'young ladies' ke fitowa daga motar tare da kyawawan 'ya'yan su kanana maza da mata, matan su hudu ne, daga inda take tsaye ta hango Humaira ta nufo su, duk jan ajin ta yau sai da ta hada da gudu-gudu ta rungume babbar cikin su. "Yaa Maira! Ashe da gaske zaku zo?" Ya Maira itace babbar 'yar sarki Yusufu, sunan sarautar ta kenan 'YaMaira' a matsayin ta na babbar 'ya. Sai mai bi mata a dakin Ya Kirjinoma wato Mairam Murjanatu, sai kanwar Murjanatun Mairam Naja'atu 'yar Hibbani, wadda Humaira ke bi a haihuwa. Ya Maira tana aure ne a masarautar Biu yayin da Murjanatu ke auren Ambasadan Najeriya a Turkiya, ta zo ganin gida ne tareda 'ya'yan ta ta tadda Ya Maira ta zo daukar Naja'atu su zo wa auta ziyara kamar yadda ta alqawarta mata, sai ta biyo su, don itama ta jima bata ga Humairan ba. Wani kilishi mai taushi baiwar da suke tare ta shimfida musu, ta koma motar ta soma fiddo sundukan abinci na alfarma da picnic coolers masu dauke da ababen sha masu sanyi. Nan suka baje suna ta hira, kai bazaka ce 'ya'yan kishiyoyi bane sabida shaquwa da kaunar da ke tsakanin su sabanin iyayen su da ke zaman kishin kwatar kai. Naja'atu ta juya idanun ta kan Humaira, "Hummy ina yarinyar da ake kawo ku tare ne 'yar kalen dangin da kike cewa? Kin ji uwar rikon nata ta haihu ko?" Humaira tace "wai wannan 'yar mutsiyatan nan, ni rabon da insa ta a idona tun ranar da muka dawo hutu, da yake an raba mana daki". "Wace yarinya kuke magana ne? Menene kuma kalen dangi?" Inji Mairam Murjanatu. (Mairam title ne na kowacce 'yar sarki). Humaira ta ce "yarinyar da Fulani Bilkisu ta dauko riko, da fari cin uban ta nake yi as if na samu baiwa, sai kuma aka zo aka raba mana daki aka barni da cizon yatsa". Murjanatu tace "dadi na da ke Humaira baki da kirki, albarkacin zaman tare ai ko gaisawa kya dinga yi da ita, ni na rasa inda kika dauko wannan fadin ran naki, na san dai ba daga Fulani Hibbani ba haka ba daga Alanguburo ba". Dama can Murjanatu tafi kowa saukin kai cikin 'ya'yan sarki kai bazaka ce ita 'yar gidan bace. An raine su akan yiwa wanda ke sama da su biyayya! Wannan ne ya sa Humaira ta kira wata junior din ta tace ta je ta zo mata da Sa'adatu Hashim. Ya Maira bata ce musu komai ba. Sai dai itama tana son ganin 'yar da Fulani Bilkisu ke rikon. Suna tsaye itada wata 'yar ajin su Falmata wadda itama ba'azo mata ba, yarinyar da aka aiko ta zo ta same su, tayi mata nuni da inda suke zaune tace "ki je in ji Princess Humaira". Saida ta ji gabanta ya fadi don ita har ta manta da matsalar Humaira, tace da Falmata "ina zuwa" sannan a hankali ta soma taku cikin nutsuwa zuwa inda suke zaune. Tunda ta doso su taji gabanta na faduwa, duka fuskokin bata san su a gidan ba banda Humaira amma ta gane iyalin Sarki ne. Haka suma suka zubo mata ido cikin tsananin mamaki a fuskokin su, hatta gait (takun tafiyar ta) irin na Bilkisun Askirama ne. Is it possible dan kanwarka yayi irin wannan kamar da kai har fiye da dan da za'a ce kai ka haifa? Har ta tsugunna ta soma gaishe su an rasa mai magana a cikin su, sai kallon ta suke with astonishment, duk sun mata kwarjini irin na su na 'ya'yan Saraki ta kasa ko duban fuskokin su. Ya Maira....ji tayi zuciyar ta na bugawa, tana da wata baiwa ta sunsunar kaddara. Haka kawai jikin ta ya bata akwai wani babban al'amari da zai zo ya kasance tsakanin su da yarinyar nan wanda bazata ce menene ko na menene ba. So she became mute, kamar an dinke mata baki, ko gaisuwar Sa'ade bata iya ta amsa ba. Murjanatu ce ta kawar da mamakin ta ta amsa mata gaisuwa, sannan ta ce Yaya karatu? Ina fatan kina kokari? Kuma kina jin dadin makarantar taku?" Sa'ade tayi murmushin da ya fidda beauty point a barin hagu tace "ina yi ranki ya dade, kuma ina jin dadin makaranta" tana ta kallon yaransu cikin sha'awa kasancewar Allah ya sanya mata son yara kamar me, Murjanatu ta nunawa baiwar da suke tare daya daga kulolin abincin da suka zo da su tace ta dauka ta bita da shi har kofar hostel. Sa'ade tayi ta godiya, ba don yunwa take ji ba sai don karamcin Mairam Murjanatu, a ranta tana fadin ashe akwai mai kirki irin Askirama cikin 'ya'yan sa, at the same time tana ta karbar sakon harara mai zafi daga Humaira. Har ta kule basu daina kallon bayan ta ba, Murja ta ce "Allah mai iko, dole Fulani Bilkisu ta dauko yarinyar nan daga cikin dangin ta, ku dubi kama don Allah har zuba take" Humaira ta kyabe baki ta ce "Ya Murja yanzu ne ta kile fa, da in kin gan ta ko kin ji maganar ta ko kin ga yadda take tafiya sai kin kusa yin amai. Kawaye take bi kamar mayya suna kilar da ita, banda haka bazaki so ki ganta sanda aka kawo ta makarantar nan ba". Murjanatu tace "to ai sun taimaketa, yanzu wannan yarinyar ina ne baza'a shiga da ita ba ko wanene ba za'a iya aurawa ba? Kin ce Alanguburo na son ta, ki zuba ido ki ga irin mijin da zai zabo mata, kin san shi dai da so wa 'ya'yan sa da 'ya'yan rikon sa babban gida". Kishi ya kara turnike Humaira tace "insha Allahu tsohon hakimi zai bata gidan kishiyoyi goma taci uban ta". Ya Maira tace "ka so wa dan uwanka abinda kake so wa kan ka". Haka suka maida Sa'ade da uwar ta topic of discussion har lokacin tafiyar su. A cikin hirar tasu naji Murjantu na gayawa Humaira Fulani Bilkisu ta haihu 'ya mace, amma bakwaini, 'yar tana cikin incubator har yanzu acan kasar India basu dawo ba. Ya Maira tace "dama Alanguburo ya daina asarar kudin sa, sunan wannan din ma matacciya, wadanda ta haifa lafiya ma basu zauna ba balle bakwaini mai cutar sikila. Raheema ta shigo da nata kabakin abincin, nan ta ga abincin alfarmar dake gaban Sa'adatu, tace "yanzu dama 'yan gidanku sun zo shine baki kira ni ba?" Sa'ade ta girgiza kai "ba waje na suka zo ba, ni ban san su bama, arzikin Humaira na ci suka bani wannan din". Nan suka zauna suka soma dibar garar dadin su. Yau kam sun wuni cikin farin ciki marar misaltuwa. A haka zangon karatun ya kare, akayi hutu suka dawo gida. Wannan karon ma bata tadda Fulani a gida ba, Fanna dai ta ce mata ta haihu, bata dawo bane don 'yar bata isa haihuwa ba aka haifeta sai ta yi kwari tukunna a asibiti. Ta kasance cike da farin cikin jin labarin haihuwar nan, ashe itama zata samu dan uwa a duniya, wanda zata kira "kanin ta". Babban abun farin cikin ma diya mace. Sai dai damuwa ta biyo bayan farin cikin da Fanna tace 'yar mawuyaci ne ta rayu. Sai ta ji tausayin Fulani, yadda ta lura Alanguburo na son ta, sai take musu fatan samun rayayyen Da a tsakanin su. Da tayi sallah sai ta samu kanta da daga hannu tana addu'a. "Ya Allah ka raya abinda Fulani ta haifa". Haka tayi wannan hutun ma cikin kadaici da kewar Fulani, amma da yake yanzu ta auri littafan ta sai komai ya zo mata da sauki. Tana son karanta littafan hikaya na turanci, duk da turancin nata baida karfin fahimtar kowacce kalma, sai take yi tana duba kamus na hausa da turanci, haka ta karbo su kala-kala daga library ta taho dasu gida musamman na ZAYNAB ALKALI da ABUBAKAR GIMBA. A wannan hutun saida Sa'ade ta maida kanta 'yar karamar Farfesa a Ingilishi sabida karatu da duba dictionary. Kullum Fanna ta shigo kawo mata abinci abinda zata tarar tana yi kenan. Har ce mata take "ki dinga ajiyewa kina hutawa kada kan ki yayi ciwo". Sai tace da Fanna "da haka ne zan kayar da kowa Fanna, idan na iya turanci, idan ka iya shi kowanne darasi zai zo maka da sauki". Fanna sai tace "to ALLAH ya bada sa'a". Har suka koma makaranta Fulani bata dawo ba. In ka lissafa zaka ga cewa watanni masu yawa kenan basu ga juna ba, wanda hakan ya sanya matukar kewar junan su a zukatan su. Ga Fulani, ba damuwa tayi ta ganta ba don ta san tana lafiya amma somehow tana jin kewar ta a can kasan zuciyar ta. Saidai hankalin ta ya dauku ga son rayuwar abinda ta haifa wadda ke tsakanin rayuwa da mutuwa, don haka bata cikin kwanciyar hankali ko kankani. Shi kam Alanguburo ya gama fidda rai da rayuwar yarinyar kamar sauran wadanda suka gabata. Amma bai fasa karfafawa Fulani gwiwa ba kan tayi hakuri ta barwa Allah ikon sa. Da sun haihu ko basu haihu ba, soyayyar da yake yi mata bazata taba raguwa ba, sannan ba ga Sa'adatu Allah ya basu ba?" Bata cewa komai idan ya fadi hakan, amma a ranta cewa take "yar Hashimu ce ba tawa ba, da sannu Allah zai bar min tawa". A sannu kuma sai Allah ya soma baiwa 'yar koshin lafiya sabida tsananin kulawar data ke samu daga likitoci da adduar uwa, tayi bul-bul kamar ba bakwaini ba, amma still sikila ce. Sun dawo gida ranar wata Lahadi, sati biyu da komawar Sa'ade makaranta. Nan aka yi ta shigowa Fulani barka kamar za'a tsaga sassanta don yawan al'umma, kishiyoyin ta dake jiran gumbar sadaka dole suma suka yi lullubi suka zo barka don ganewa idon su abinda ta haifo ba don barkar ta Allah da annabi bace, "yarinya kamar Murjanatu" inji Ya Kirjinoma cikin al'ajabi. Hibbani tace "wannan dan gajeren hancin ai na Ya Maira ne, Murjanatu mai dogon hanci zaki hada da wannan burtuntunar, ai komai nata na Ya Maira ne" Ya Kirjinoma tace "in zaki tsoraci Allah, Murjanatu ce sak wannan". Fulani tayi murmushi bata ce komai ba, amma burtuntuna da aka kira 'yar ta ya sosa mata rai. Ta san kadan da aikin Hibbani, in ta kwabo maka magana ko zaka mutu ita babu ruwan ta. Amma abin mamaki Ya Gumsu bata shigo ba, tana can bakin ciki na neman kashe ta, don bata taba zaton 'yar zata rayu ba. Haka 'ya'yan gidan maza da mata na nesa dana kusa suka yi ta tururuwar zuwa barka har wajen kwanaki talatin mutane basu tsagaita ba. Daki guda sai da ya cika taf da kayan barka na uwar dana 'yar mai suna "Zarah" Cikin kuyangin Fulani aka warewa Zarah masu kula da ita su biyu, dattijuwa da budurwa, dakin Zarah yana jikin na Fulani, yayin da na Sa'ade ke kallon nasu. Suka cigaba da rainon ta cikin tsananin kulawa. ***** Kayan su suke hadawa itada Raheema kasancewar gobe hutu, suna yi suna hira, Sa'adatu tace "wannan hutun ina duban hanyar ki, na san daga Fulani har Alanguburo in suna gida, baza'a hanaki shigowa ba". "To Allah yasa Abba ya barni, ya ce min ma shi kallon sani yake miki" Sa'ade tayi dariya, "ba dole yayimin kallon sani ba tunda nima 'yar sa ce?" Haka suka yi ta hira har suka kammala hada duk abinda suke bukatar zuwa dashi gida. **** Yarinyar dake tsaye yau a gaban ta wata siririyar budurwa ce, cikin shekaru na tashen balagar diya mace. In bata manta ba tana kamar girman ta aka yi mata auren fari, auren dolen da ya zamo silar zuwan ta duniya. Tana tsaye daga bakin kofa sanye cikin uniform din ta na makarantar sakandire, kyakkyawar fuskar ta kunshe da sassanyan murmushi, wanda kai tsaye ta fassara shi da murmushin farin cikin abinda yarinyar ta shigo ta tarar tana yi (breastfeeding her baby). Ta tako a hankali cikin tafiyar data banbanta da ta SA'ADEN da ta sani watannin baya, mai tafiya tana hada hanya, wannan Sa'adatun a nitse take tafiya. Her gait, her serene smiles duka suna kara tabbatar mata da cewa, ta fito ne daga cikin mahaifar ta kwatankwacin diyar dake rungume a hannun ta a yanzu, wato Zarah. Banbancin dake a tsakani shine; wannan soyayyah ce ta kaita ga haifar ta, yayin da waccan kiyayya ce silar nata zuwan duniya. Ta yi nisa a wannan tunanin har bata san lokacin da Sa'ade ta karaso gareta ba, kokari take ta karbi 'yar daga hannun ta wadda ta saki nono tana kallon Sa'aden da kyawawan idanun ta. Sa'ade blushing ta ke from ear to ear, ta dauka Fulani zata hana ta daukar diyar ta, amma ga madaukakin mamakin ta sai ta ga ta sakar mata. Ta dauki kanwar tata tana ta murmushi. "Beautiful!" Ta fada cike da kauna. Fulani ta cigaba da bin ta da kallo ba tare da ta sani ba, duk wani kankanin canji dake tare da Sa'aden a watannin data kwashe bata ganta ba saida ta zaqulo shi cikin idanun ta. "Ashe kilewar diya mace ba wuya muddin zata je makaranta!" Fulani Bilkisu ta fada a zuciyar ta. Tana son comparing soyayyar data ke ji akan Sa'ade da Zarah. Sai ta ga cewa ratar dake a tsakani mai tsananin fadi da girma ce, ta haifi Sa'ade ne kawai amma babu ko digon soyayyar ta a zuciyar ta, sai tausayi da kyautayi irin na zuciyar musulunci. Yanzu ne ta san kaunar uwa akan dan ta, da ta haifi 'ya da wanda take so. Can wani lungu na zuciyarta kuwa kururuwa yake yana objecting: idan soyayyar Sa'ade da ta Zarah, bata zo daidai da juna ba, sai dai ace ta Zarah ta rinjayi ta Sa'ade, amma ba wai ace babu burbushin ta ko kankani a zuciyar ta ba. Bata ankara ba sai ganin 'yar ta tayi a bayan Sa'ade, tasa tawul din da aka nannade ta a ciki tagoye ta tsam ajikin ta, ta soma dan jijjigata sabida dan rikici data ke yi irin na jarirai. Sai tasamu kanta da kasa cewa ta sauko mata 'yar ta, ta mike ta shige turakarta ba tare da ta ce da ita komai ba. Dama kuma tana so ta huta din, gashi ta sallami kowa tace bata son ganin kowacce baiwa a bangaren ta sai gobe da safe in Allah ya kai mu. Sai ganin tsayuwar Sa'ade ta yi a gaban ta ba zaton ta ba tsammani. Sa'ade saboda jin dadin Fulani ta bar mata Zarah sai ta nufi dakin ta goye da ita, roba ta samu ta hada ruwan dumi ta saukota ta soma yi mata wanka, ta gama ta nade ta cikin shawul ta fito kan gadon ta ta dauki basilin din ta tana shafa mata. A lokacin Fulani ta shigo, ta bude baki da zummar yin fadan don me ta yi mata wanka bayan ba'a jima da yi mata wanka ba? Amma sai ta ga yarinyar na ta bangala dariya Sa'ade kuma ta himmatu wajen yi mata wasa a cute kumatunta. Sai suka bata sha'awa, ta juya silently ta fita. Ta dauko set din kayan baby na sanyi ta dawo ta watsawa Sa'aden ta sake juyawa ta koma. Shikenan daga wannan ranar Sa'ade ta kwace rainon Zarah daga hannun Fulani da masu rainon ta, kayan yarinyar ma saida ta san yadda tayi suka dawo dakin ta. Tsakanin ta da Fulani shine kawai idan ta bukaci nono. Hausawa suka ce wai "Mai Da wawa ne", wannan kyautatawa da kauna ta Sa'ade ga Zarah a hankali yake hakurkurtar da zuciyar Fulani Bilkisu, daga mummunan kullacin Mal. Hashimu dake cikin ta, wanda ya hanata ganin farin Sa'ade har ta kaunace ta matsayin 'ya 100%. A hankali ta soma rage fada, da tsawa da hantarar da take yawan yi mata, ta soma yi mata magana jefe-jefi cikin sanyin rai. Satin ta uku a gida sai ga Raheema Kyari, wannan karon ba'a hanata shigowa ba, Kuyangar data rako ta sai ta hada ta da Fanna, ita kuma Fanna tace ta jira daga waje, ta nemo izni tukunna. "Kawa kuma daga Maiduguri?" Fulani ta fada cikin mamaki. "Haka ne ranki ya dade, sannan ta tabbatar min ita aminiya ce ga Sa'adatu sannan ta san da zuwan ta". Fulani ta hadiye fushin ta wanda tayi aniyar saukewa akan Sa'ade bayan tafiyar bakuwar, ta ce Fanna ta shigo mata da yarinyar. Cikin sallama da shiga ta mutunci da kamala Raheemah ta shigo, tunda ta shigo Fulani ta kura mata ido. She looks so much like her father wanda ta yi wa farin sani. Mikewa tsaye tayi ba tareda ta san lokacin da ta yi hakan ba, hatta tsagin fuskarsa biyu-biyu dogaye gasu nan kwance a fuskar Raheema. Da ta gaisheta da kyar tayi controlling razanar ta ta amsa, "yaya sunanki?" "Raheema Kyari Babagana" "Kyari?!" Ta fada da amon muryar da ya baiwa Raheema mamaki, "eh, sunan Babana kenan" "daga wane gari kike?" "Daga Maiduguri na zo, acan muke zaune, amma mu 'yan asalin Damaturu ne". "Shikenan dangin ubanta sun biyo ta, a lokacin da na fara sanyata a raina". Fulani ta ayyana a zuciyar ta, ta kuma kudiri aniyar kin gayawa Sa'ade kowacece Raheema a gareta. "Shiga nan dakin, tana ciki" Ta fada tare da nuna mata dakin, ta kuma tashi ta bar musu area din gabadaya zuwa turakar ta. Sa'ade sai ganin Raheema ta yi ta shigo da sallama, zo ki ga gudu da murna wajen Sa'ade, saura kadan ta kada Raheema. Ita kuwa sai dariya take. Ta dauki Zarah dake tsakiyar gadon ta tana fadin "masha Allah, beautiful baby". Hira kamar ta kashe su. Fanna ta shigo wa da Raheema abinci na musamman suka ci tare cike da farin ciki. Can da yamma Raheema ta ce "Sa'adatu ki zagaya da ni mana in ga masarautar taku in samu abun baiwa su Sarina labari". Sa'ade tayi dan jimm! Kafin tace "ni bana zuwa ko'ina, daga daki sai daki, Fulani bata bari na". "Amma meyasa?" Inji Raheema. Ta dan kyabe baki "i don't know. May be sabida kishiyoyin ta". Daga haka suka bar hirar. Washegari Fulani ta sa aka yiwa Raheema sallama ta girma, aka maida ita har Maiduguri. **** Ya Gumsu ta shiga turakar mai Askira cikin kwalliya ta kasaita a matsayin ta na mai girki ranar, abinci yake ci tana gefen sa tana masa firfita, cikin hila irin ta matan da suka san kan mazan su ta yi durkuso a gaban sarki, ta ce "Alanguburo (Allah ya kara yawan rai) Yarima na rokon alfarmar a bar shi ya zo gida, ko da na sati daya ne, shekaru goma kenan rabon sa da gida, yayi digiri yayi masta ya jima yana aiki har ya fara digiri na uku, yana cikin damuwar rashin sanin halin da 'yan uwan sa ke ciki, yayi alkawarin baza'a sake samun sa da laifi makamancin na baya ba". Nan da nan wani kwantaccen bacin rai ya bayyana a fuskar sarki, ya dago idanun sa da suka kada ya dube ta, sai da hantar cikin ta ta kada. Ta yi azamar sunkuyar da kai amma a ranta zata jure komai in har zai bar dan ta ya zo gare ta, haka kawai ai ba shikadai ne fitinannen Da ba, fitinannun nawa ya haifa? Amma bai daukewa Ya Kirjinoma nata ba sai shi kadai bayan ba fin su fitinar yayi ba. Yana kusa da su ma suna masa fada ai zai fi gyarawa fiye da hannun aminin nasa. Sarki Yusufu AbdulHakimu mai Askira, ya dubi uwargidan sa Ya Gumsu da idanun bacin rai kamar koyaushe ta sako zancen YARIMA SAGEER a gaban sa, idan da abunda ya ke bata masa rai a rayuwar sa to al'amarin Yarima Sageer ne, babban Da, kuma zakka a cikin 'ya'ya mazan da Allah ya bashi, yet mafi madaukakiyar soyayya a zuciyar sa. Dama an ce wai fitinannun 'ya'ya sun fi shiga zuciyar iyaye. Kusan wannan magana haka take. Duk cikin 'ya'yan sa maza da mata ba wanda yake so irin Muhammad Sageer, sai kuma ya zamo mafi munin jarraba da Allah ya taba yi masa. Ubangiji yayi gaskiya da ya ce "ya'ya da dukiya fitina ne......". "A takaice dai kina rokawa dan ki alfarmar ya dawo cikin gidan nan ya cigaba da turmushe 'ya'yan mutane, ya cigaba da wulakantani tare da tozartani a idanun Bayi na da hadimai na dake tsananin ganin girma na, ta hanyar turmushe musu 'ya'ya dake hidimta masa?". Fulani ta runtse ido cikin jin zafin kalaman sa, "Alanguburo, wannan abu ne na kuruciya, kai kan ka da ka ga Yarima ka ga nutsuwa da hankali a tattare da shi, abinda yayi yana yaro ba zai taba maimaitashi cikin hankalin sa ba, balle da 'ya'yan bayi makaskanta a gare shi. Wallahi don an ki yarda da nine, amma Yarima makiya ne suke jifan sa a baya, ba yin kansa bane. Kai shaida ne akan tsantsani da tsafta irin na Yarima, amma a ce ya rasa matan da zai bi sai 'ya'yan bayi, ai daga nan zaka gane akwai lauje cikin nadi a al'amarin sa. Bayan haka kuma na dukufa da yi masa addu'a tun tafiyar sa, Allah kuma baya juya addu'ar Uwa, inada kyakkyawan yaqinin cewa ya daina, mu taru mu kyautata masa zato, mu bashi dama ya rayu cikin gidan su kamar kowanne Da cikin gidannan, idan aka sake samun sa da wani laifi makamancin wannan, na amince ayi masa duk hukuncin da ya kamata da shi". Maganganunta ga dukkan alamu sun dan shigi Askirama. Ya dade cikin halin shiru, ya kasa cigaba da cin abincin sa. A karshe yace da Ya Gumsu wadda ke jiran amsar sa kamar ta shiga zuciyarsa taga abinda yake yankewa. "Zan yi shawara da Waziri". "Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai nagode matuka, kuma insha Allahu Waziri zai amince da abinda na zo da shi, don shima na tabbata yana son ganin Awaisu)". "Ina bukatar kadaicewa". Ya ce da ita. Ta mike cikin azama ta soma tattare akusan abincin dake gaban sa. "In ma kwana zaka yi kai kadai ka yi, ni dai a bar Da na ya dawo gida". Ya Gumsu ta fada cikin ranta, a fili kuwa dukawa ta yi a gaban sa tana fadin. "Na bar ku lafiya gatan Askira". Fitar ta ke da wuya ya kishingida ya lula cikin tunani. Tunani mai zurfi na shekarun da suka gabata. **** SHEKARUN CAN BAYA (A Masarautar Askira) Lokacin da Ya Gumsu ta samu cikin babbar 'yar sa 'Yaa Maira' duk burin sa da dokin sa shine a haife masa Da namiji domin ya samu magaji, kamar yadda kowanne sarki ke burin samu. Amma sai aka haifi Ya Maira, ciki na biyu ma yayi ta fata da addu'ar samun da namiji, amma sai ta kara haihuwar diya mace. Dalilin sa kenan na kara auren Ya Kirjinoma a daidai lokacin domin yana ganin 'ya'ya mata kawai Ya Gumsu zata yi ta haifar masa. Kamar Allah ya san cewa bai yi farin ciki da haihuwar Mairam Lubabatu ba, bata fi shekaru uku ba Allah ya karbi abinsa. Ya Kirjinoman ma da ta tashi haihuwar ta ta fari, sai ta haifo masa Mairam Murjanatu. Wannan ya kara mayar da shi desperate ga son haihuwar da namiji. Ba ruwan sa da 'ya'yan sa mata, duk kulawar su da hidimar su da tarbiyyar su tana wuyan iyayen su mata. A kullum ya tuna wancan lokacin ya kan ce "wannan shine deadly mistake da ya taba yi a rayuwar sa". Ba shikadai ba, masu sarauta da yawa hakane tunanin su akan haihuwar fari, idanunsu rufewa yake ga son haihuwar da namiji ba tare da baiwa Allah zabi ba. Ciki na uku da Ya Gumsu ta samu kusan a tare suka sameshi itada Ya Kirjinoma. Ita ta haifi MUHAMMAD SAGHEER, Ya Kirjinoma ta haifi MUHAMMAD ASHGAR tsiran watanni biyu kacal ne a tsakanin su. Ashgar sai ya zo da rashin lafiya ta Autism wadda aka fi sani da (autism spectrum disorder). Baya magana (in a meaningful way) tun yana karami saidai ya maimaita abinda aka fada masa sannan kamar kwakwalwarsa ba daidai take ba. Wannan yasa sarki Yusufu ya dauki soyayyar duniya da tattali da kulawa ta duniya bakidaya ya dora akan lafiyayye Yarima Sageer, wanda hakan ya ruruta wutar mummunan kishi tsakanin Ya Kirjinoma da Ya Gumsu, ya kuma sa Ya Gumsu daukar girman kan duniya ta dorawa kanta, da jin tafi kowa, tunda kuwa ita ta haifarwa sarki Yarima. Koma waye zai biyo baya saidai ya zo a matsayin kanin sa ba Yayansa ba. Soyayyar data sa tun yana yaro daga uwar har uban suka sangarta shi, basa iya kwabar sa, gata na duniya babu irin wanda basa gwada masa. Hakan bai hana shi yiwa Sageer addu'a ba a duk sallahr farillar sa kan Allah ya kare masa shi a duk inda ya shiga. Musamman da ya bayyana ga kowa cewa yaron fitinanne ne na kin karawa. Ya addabi 'ya'yan jama'ar gari da mugunta da tsokana, baya zama cikin masarauta saidai cikin 'ya'yan talakawan gari, sune abokan sa abokan mu'amalar sa, don Sageer ya tare yaro a lungu ya targadashi ya fasa masa hanci babu gaira babu dalili ba wani abu bane sabo a wajen jama'ar gari, suna dauke ido ne sabida mutuncin mahaifin sa da farin jinin yaron. Yaro ne mai shiga rai matuka, sabida kwarjini da kyawun suffar da Allah ya bashi. Yana girma fitinar sa na karuwa a ciki da wajen masarauta. Kullum Sageer ya fita makaranta da yaron da zai targada ko ya fasawa hanci ba'a kuma isa a kawo kara ba sabida tsoron Ya Gumsu, saidai Awaisu ya gani ya zo ya fada a gida. Waziri ya aika a bada hakuri. Don ba'a bari ma Sarki ya ji. (Awaisu dan Waziri ne kuma sa'an Sageer don haka tare aka raine su), har ta kai ga Awaisu ya kwaso kayan sa duka ya dawo dakin Sageer kwatakwata, sai dai hali kowa nasa daban. Don kuwa Awaisu babu ruwan shi yaron kirki ne, amma duk inda Sageer yasa kafa nan zai mayar da tasa. Darajar Sarki yasa jama'ar gari suka yi ta hakuri da Sageer tun yana yaro har ya shiga sakandire anan Askira. Kafin ya gama sakandire ne kuma yayi dan hankali ya daina taba 'ya'yan kowa, sabida yawan addua'ar Alanguburo akan sa. Har yake dan shigowa fada a zauna zaman fada tare da shi kamar yadda Sarki ke so ya dinga yi kullum amma ya ki. Lokacin da Sageer ya soma balaga, sai abubuwan gabadaya suka canza, 'yar nutsuwar da yake da ita tabi ruwa. Ya koma neman bayin sa mata. Lokacin da wannan mummunan labari ya kai kunnnen sarki Yusufu mai Askira sai ya kira Wazirin sa cikin sirri. "Na yanke shawarar in aura masa mata hudu a rana daya, ina ganin hakan ne kawai mafita ga al'amarin sa". Waziri Ibrahim ya girgiza kai yana kallon maimartaba sarkin Askira cikin tausayi, ganin yadda ya zabge ya birkice a kwanaki uku kacal da samun wannan labari da yayi. Lallai 'ya'ya da dukiya fitina ne. Kamar yadda mulkin kansa fitina ne da rashin kwanciyar hankali ga bawa. Yace. "Baza'a yi haka ba Askirama. Baza'a yi haka ba gatan Askira, aure ba laifi bane a shekaru goma sha tara amma karatu za'a kai shi, zamani ya canza, auren mata hudu a rana daya ba zai zamo solution ba, don kuwa zai hanashi maida kai ya yi karatu musamman idan ya soma tara iyali. Ka manta da komai ka kwantar da hankalin ka ka barshi yayi karatun da zai amfane shi muma watarana ya amfane mu. Zan hada shi da Awaisu zuwa duk inda zaka kai shi zan kuma san yadda zan yi Awaisu ya zame masa jagora a komai nasa. Mafi a'ala shine mu bisu da addua". Ya sani duk duniya babu mai kaunarsa cikin 'yan uwan sa na jini irin Waziri Ibrahim, wanda ya kasance Da ga wan mahaifin sa marigayi sarki AbdulHakimu mai Askira. Bai taba bashi shawarar da in ya bi ta baya ganin mafita da yaqini a cikin ta. Don haka yayi na'am da shawarar Waziri ba tareda shawara da Ya Gumsu ba. Kafin ya zama sarki shi Ambasada ne na kasar Egypt, saida mahaifinsa Sarki Abdulhakim ya rasu ne aka dawo dashi gida aka bashi sarauta, don haka yana da kyakkyawar alaqa da ambasadan Egypt mai ci a lokacin kamar amini yake a gare shi, sannan yana da connections mai yawa da kasar ta Misra domin yayi sama da shekaru goma yana aikin jakada a cikin ta. Don haka ya yanke shawarar kai shi kasar muslunci bai kai shi kasar turai ba don ya kara hankali, a Egypt din ma hannun Aminin sa Amb. Hassan Labaran ya damka shi bai yarda ya zauna a hostel ba. Amb. Hasan bai taba haihuwa ba shida matarsa Hajiya Laila, suka karbi amanar Sageer da Awaisu a gidan su wadanda aka samarwa gurbi a jami'ar Al. Azhar. Saidai ba fanni daya suke karanta ba. Daga wannan lokacin ne kuma haihuwar 'ya'ya maza ta budewa Sarki Yusufu daga duka matan nashi biyu, a lokacin ne ya hadu da Hibbani ya aure ta, daga baya ya auri Bilkisu, haihuwar ta biyar suna mutuwa. Amb. Hassan zazzafan da boko ne mai zafi da sanya ido akan iyalin sa, tashin farko ya gano dabi'ar da Sageer ya zo masa gida da ita ta shan sigari, kuma ba jimawa yayi fata-fata da ita, ya cigaba da dora shi a hanya ta hanyar tsawatarwa da jan sa a jiki, yana nuna masa illar smoking ga lafiyar sa ta dan adam. Wani abu da bai samu daga iyayen sa ba sabida kawaici na masu sarauta ga 'ya'yan su. Gara ma Maimartaba akan Ya Gumsu wadda babu wani kusanci ko kankani tsakanin ta da dan nata, bata san me yake ciki ba, bata taba bincikar halayyar sa ba, ita dai burin ta ya kasance cikin gata ya samu duk abinda yake so, ya girma ya gaje sarauta. Cikin dan lokaci kankani Amb. Hassan ya canza da yawa daga baragurbin halayen Sageer sai abinda ba'a rasa ba. Shima Awaisu a nasa bangaren yana iya nasa kokarin wurin ganin Sageer ya canza munanan dabi'un sa zuwa na cikakken dalibin da ya san ciwon kansa. A karshe Awaisu ya fahimci wani abu, zai iya nasarar raba Sageer da komai, amma ba zai iya raba shi da 'yammata ba. Mahaukatan kudin da sarki ke turo masa don yayi hidimar karatu, da wadanda Amb. Ke basu lokaci-lokaci duk a hidimar 'yammatan sa yake karar dasu. Yana kuma da masaniyar cewa yana branching da 'yammata a hotel ba da sanin Amb. Hassan ba. Al'amarin ya kara kazanta ne lokacin da aka yiwa Amb. Hassan sauyin kasa, daga Egypt zuwa Amsterdam akan aikin jakadancin sa. Suka tattara suka bar Egypt suka koma can. Inda suka fara karatun doctorate degree dinsu a fannin da kowanne yake a babbar jami'ar Amsterdam. Awaisu na karantar (Social Work) yayinda Sageer ke karantar (Pure and Applied Chemistry). A duka wadannan shekarun bai kara ganin kowa nasa ba, wadanda aka haifa baya nan bai san su ba. Haka wadda aka aura a bayan sa wato Fulani Bilkisu. Bayan su akwai kwarkwarori da yawa. Sannan elder sisters dinsa biyu duk sunyi aure sun hayayyafa: Ya Maira da Mairam Murjanatu. Bayan su an haifi maza biyar, biyu Ya Gumsu, uku Ya Kirjinoma, sannan Hibbani na da Humaira da Najaatu. Bayan kammala M. Sc din su dukkan su sun samu aiki a kasar Amsterdam, Awaisu aikin asibiti yake yi yayin da Yarima Sageer ke aiki da wani mashahurin kamfanin sarrafa kayan abincin gongoni na kasar. Tuni sun manta daga gidan sarauta suka fito, sun karbi rayuwar gidan Amb. Hassan wanda bazaka taba sanin ba shi ya haife su ba. Rayuwar kasar Amstedam ta karbe su sosai, sun tara arziki nasu na kansu, ga aiki ga muhalli ga ababen hawa. Amma duk da haka a gidan Amb. Suke zaune. Tun barin sa gida sai a shekarar baya ne maimartaba da Ya Gumsu suka kai masa ziyara, bisa tsananin rokon Amb. Hassan don maimartaba yace shi har abada Sageer bazai dawo masa gida ba, ya barwa Amb. Hassan shi duniya da lahira sabida gamsuwa da irin rikon da yake musu shi da Awaisu, shi kansa Waziri bai taba bada shawarar su dawo gida ba. Sai kuma ga abinda Ya Gumsu ta zo da shi yau, na nema masa alfarmar zuwa gida yayi ko sati daya ne. Ya sake lumshe idon sa ya bude a hankali. A fili ya furta "nima ina kewar ka Muhammad Sageer, tsoron abinda zai je ya zo nake. Ina tattalin mutuncin ka a idon al'ummarka. Duk da Baban ka ya tabbatar min baka da matsala yanzu". **** A shawarar da suka yi da Waziri ya karfafe shi akan ya bar Yarima ya zo gida, koda sati dayan ne, tunda dai bazai dawwama a kasar da ba tasa ba, dole watarana zai zo gida, sannan Amb. Hassan ya tabbatar musu komai lafiya a tareda Yarima. Awaisu ne dai da yafi kowa kusanci da shi ya ce da Babansa Waziri da saura. Wazirin kuma bai gayawa sarki hakan ba don ya samu nutsuwar barin dan sa ya shiga cikin 'yan uwan sa ko yaya ne. A gefe ya saka limamin Askira da sauran malaman fada yin addu'a ta musamman akan zuwan Yarima Sageer, Allah ya kintsawa mahafin sa shi a matsayin sa na magajin sa. Da wannan sarki ya yiwa Yarima umarnin zuwa gida don yayi sati daya. A wannan lokacin Amb. Hassan ya gama tenure dinsa na aikin jakadanci yana shirin dawowa gida gabadaya, don haka tare suka soma shirin tahowa shi da 'ya'yan nasa Sageer da Awaisu, inda Amb. Hassan zai sauka a kasar shi ta haihuwa Kanon Dabo, kafun ya koma Birnin Tarayya da zama. ***** "Na ga sai wani zumudi kake zaka je gida, kamar wani special abu ne zamu je mu taras banda zafin Maiduguri, ni banda Ya Gumsu ta dage sai naje ai har abada na bar Askira kenan, tunda Alanguburo baya son gani na". Awaisu yayi murmushi yana ninke kayan Yarima yana jera masa cikin tsadaddiyar trolley din sa. Bai yi niyyar bashi amsa ba sai da ya ji Yarima ya sake yin kwafa, "ni ko satin ma bazan cika ba zan dawo, ka san nextweek akwai birthday din da na hadawa (Rose), kawai sai jin zancen tafiyar nan na yi, da na san da ita da tun satin da ya wuce mun yi mun gama, she will be 26 by next week". (Rose, yarinyar Yarima ce da yake ji da ita, 'yar asalin kasar Korea ta kudu), Awaisu ya tamke fuska kamar bai ji shi ba, ya cigaba da jera masa kaya. Daga baya kuma ya ce "ayya! Ai kawai ka tafi da ita Askira ka hada mata birthday din acan zai fi bada ma'ana" Yarima yayi miskilin murmushin sa, ya ce "me kake ci na baka na zuba? Ka zuba ido zuwa shekaru biyu zan kaita Askiran ne, amma a matsayin matata ba budurwa ta ba". Awaisu ya dauka ya fada ne kawai don ya ji dadin bakin sa, ya manta da wani hali na Yarima Sageer Yusuf Askira, duk abinda ya furta yana nufin sa ne har zuciyar sa. Amma akan zancen Rose bayahudiya bai taba kawowa Yarima da gaske aurenta yake da niyyar yi ba. A halayen Yarima in ka dauke son matan sa, sauran duka ababen sha'awa ne, Awaisu ba zai daina kiran sa (his role model) ba. Mutum ne mai muhimmanta sallah da kiyaye lokutanta, mai kirki mai kyauta, abun hannun sa bai taba rufe mai ido ba. Ga jin kan na kasa da shi, ga girmama iyaye, sannan ga kokari wajen neman na kai kamar ba dan sarki ba. Bayan kamfanin da yake yiwa aiki yana kasuwancin automobile daga Amurka zuwa Amsterdam. Duk da haka maimartaba bai taba fasa turo masa kudi duk karshen wata ba, shi Awaisun shine akan komai na kasuwancin nasa kuma kyautatawar da Yarima yake masa a ciki sai ka rantse su biyu suka mallaki jarin kasuwancin. Babban abunda ke burge Awaisu a halayen Yarima Sageer shine submissiveness, ya san shi mai laifi ne a gurin Ubangiji, amma yana yawan ce da Awaisu ya kasa dainawa, kuma yana so ya daina din, mata sun zame masa barin rayuwa da baya iya rayuwa daidai sai tare da su, don haka kullum cikin istigfari yake yana fadin yana rokon Allah yasa kada ya mutu yana aikata laifin da yake aikatawa. Ko Awaisu ya soma wa'azi, baya arguing da shi, cewa ya ke ya sani babu kyau ya taya shi addu'a. Sai Awaisu ya koma yi masa yakin karkashin kasa, don kuwa yarima tausayi yake bashi, kana sabo ka san kana yi amma ka ce ba zaka iya dainawa ba, duk yarinyar da ya gani tare da shi zai bi ta bayan idon sa ya ci mutuncin ta ya razanata akan tarayya da Sageer, wani zubin har ya ce Sageer nada cuta, ga turawa da shegen tsoro, saidai Sageer ya nemi yarinyar sa sama ko kasa ya rasa, a karshe saidai ya nemo wata, shi kuma Awaisu baya gajiya da lalatawa, kamar yadda shima baya gajiya da sake nemowa. Wannan itace rayuwar Yarima Sageer da dan uwan sa Awaisu a kasar Amsterdam. Tamkar ciki daya suka fito, sha'awar su akan komai daya ce ra'ayin su daya, sannan zuciyar su tsayayya ce akan junan su, saidai hali kowa nasa daban. Jirgin su ya sauka a filin jirgin saman Maiduguri da asubahin safiyar Litinin, zaratan matasan suka soma saukowa daga matattakalar jirgin 'AZMAN' cikin shiga ta barebarin usli, wadanda fatar jikin su ta jiku da boko da kasar sanyi, kai da ganin su ka san sun fito ne daga sarauta ta ainahi ko daga irin takun su da kasaitar su. Suna sauka motar 'Askira Emirate' na jiran su. Tun a Abuja suka rabu da Amb. Hassan da Mama Laila wadanda suka hau jirgin Kano, su kuma suka hawo na Maiduguri. Dogarawa bila- adadin duk daga motocin masarautar Askira, suka bude musu kofar motar BMW wadda maimartaba kadai ke hawan ta a gidan. Daga nan basu bata lokaci ba suka kama hanyar Askira da motar civilian mai dauke da wasu fadawan cike fal a cikin ta. Yau tun safe masarautar Askira ta tashi da bushe-bushen algaita da kalankuwa da goge irin na masarautar, baka jin komai sai tashin kirarin gidan sarautar Askira, maroka da makada daga kowane bangare na garin sun barko sun cika kofar fada, haka tun jiya 'ya'yan sarki maza da mata na nesa dana kusa sun hallara a gida dakunan iyayen su mata ba don komai ba sai don marabtar Yarima Sageer wanda ya kwashe shekaru goma baya cikin masarautar gabadaya. Mairam Murjanatu ce kawai bata samu halarta ba saboda ta yi nisa tana kasar Turkiya. Naja'atu da Humaira kusan sun fi kowa zaquwa da murnar ganin Yariman domin sune basu san shi ba, suna kanana sosai ya tafi, sai kuma jikokin gidan wato 'ya'yan Ya Maira su wajen takwas. Lokacin da motocin su suka iso fada, sai kade'kaden da bushe-bushen ya karu. Wani abu ne da Sa'ade bata saba ji a cikin masarautar ba in ba wani muhimmin abu ake ba, kamar nadin sarauta ko bikin aure. Duka-duka ma dai tun zuwan ta Askira bai fi sau biyu ta ji irin wannan ba, don haka ta gane akwai muhimmin abin da ke faruwa yau a masarautar. Tana so ta san me ake yi, amma ta rasa wanda zata tambaya, don Fulani ma tun safe tasa aka shirya Zarah suka wuce babban falon ganawar sarki da iyalin sa, inda sauran iyalin gidan suka hallara, ko ta kanta bata bi ba. Fanna ma dai ta lura yau dukkan su busy suke a cikin gida da girke-girken da iyalin gidan zasu ci da wanda za'a tarbi Yarima Sageer da shi. Don haka itama tun safe bata sa ta a idanun ta ba. Sa'ade duk ta zama curious ga son sanin me ake yi haka cikin gidan, a ranta tace yau dai zata yiwa Fulani laifi sau daya, dole taje ta baiwa idon ta abinci, iyakaci Fulani in ta kamata ta murde mata kunne ko ta mare ta. Da wannan tunanin ta dau mayafin ta, sadaf-sadaf ta fita daga sassansu, a falon daya raba sassan Fulani da inda sauran bayinta ke shige da fice ta ci karo da wasu duk suka zubo mata ido, bata ko kallesu ba ta daga kafa ta fice daga unguwar Fulani Bilkisu. Mayafin ta ta janyo ta rufe rabin fuskarta, idanun ta kawai ake gani. Ta rasa ina zata dosa? Dan ba sanin kan gidan tayi ba, daga bisani ta lura da inda bayi ke karakaina da manyan farantai, kanta tsaye ta doshi wajen. Wani babban falo ne ta ga bayin suna shiga da sundukan abinci da katon katon na lemukan gongoni, ta bi bayan su a hankali har zuwa kofar falon, sai ta zagaya ta bayan tangamemeiyar tagar gilashi ta falon ta leka a hankali. Ba zata iya shaida fuskokin data gani ba don tagar ta baya ce duk sun juya bayan su, ta dai hango Alanguburo akan kujerar mulkin sa, zagaye da shi kananan yara maza da mata har da matasan 'yammata kamar ta, a gefensa daura da shi bisa kujerar da bata kai tasa ado ba wani zankadeden matashi ne, duk da bata yi nasarar ganin fuskar sa gabadaya ba ta ga gefen fuskarsa, da dogon karan hancin sa, kalar bakar fatar sa kamar ta mutanen kasar Morocco, hular sa ta nitse a cikin tarin sumar kansa sannan fararen kayan dake jikin sa babu ado irin na sarauta a jikin su. Normal tsadadden yadi ne (filtex London) mai taushi a idon mai kallon sa, sauran mata da mazan dake zagaye dasu duk bata ganin fuskar su, amma ta shaida bayan uwarta Fulani da kalar tufafin dake jikin ta kasancewar ta san ta da kayan. Wata zuciyar ta ce "yi ta kanki Sa'ade, idan Fulani ta kama ki a gaban kowa sai ta yi miki dan banzan duka. Tunda dai kin gani taro ne suke yi nasu su-ya-su (family get together)". Wata kyakkyawar mata ta juyo tana magana da wata dattijuwa, sai ta gane fuskar ta, tana daga cikin wadanda suka je wa Humaira visiting har suka kira ta (Ya Maira). Salin-alin ta soma ja da baya, sawun ta a likkafa, sannan ta juya da sassarfa akan kafafun ta ta koma inda ta fito. Ko ba komai ta ba idon ta hakkin sa. Da Fanna ta fara cin karo ta saka bayin dake sassan a gaba tana ta yi musu fada don me suka barta ta fita, sai gata ta shigo kamar an koro ta, da sauri Fanna ta doshe ta tana hamdala. "Daga ina kike Sa'adatu?" "Kai Fanna, sai kace wata karamar yarinya zan bata a cikin gidannan ne da wayo na da idanuna da komai?" "Ba cewa na yi zaki bata ba ranki ya dade, inda Fulani ta shigo ta nemeki bata gan ki ba me kike so mu ce mata?" Sa'ade ta murguda baki tayi shigewar ta ciki tana kunkuni. "Haka kawai ayi ta kulle mutum a daki sai ka ce wani daddawa, su suna can suna jin dadin su cikin jama'a, bata so a ganni don me ta haifo ni?" Wunin ranar zungur bata ga Fulani ba, sai washegari da safe ta fito don ta gaisheta kamar yadda ta saba duk safiya in dai tana garin, ta same ta ta hargitsa bayi suna ta gyare-gyare a sassan wai Yarima zai shigo ganin Zarah, yau zai shiga kowanne sassa na gidan. Sama-sama Fulani ta amsa gaisuwar ta sannan ta cigaba da bada umarni, ta juya cikin jin haushi, ta tsani wannan rashin bata muhimmancin da Fulani take yi amma ba yadda zata yi. Bakon da ake ta shirye-shiryen domin sa bai shigo sassan nasu ba sai bayan sallar la'asar. Tana jin wani irin kirari yana tashi daga bakin bayi (Gyara kimtsi da kyau... Lafiya dan zakin duniya. Lafiya dan malafar duniya. Lafiya dan mai fada da cikawa. Lafiya dan masha-sha. Lafiyar ka dama da hauni mai nasara. Zauna dai-dai dan bawan Allah. Zauna dai-dai dan waliyin Allah. Aminchinka rike linzamin ka dan bawan Allah....zauna dai-dai dan masu Alheri...) daga bisani ta ji muryoyin mutane da alama ba shi kadai bane, mazane sun kai su biyar, bayan Yarima Sageer akwai Awaisun sa, kannen sa maza su hudu tareda Ashgar duk da ba lafiya ce da shi ba hannun sa na cikin na Yarima kamar zai maida shi cikin sa. Tana so ta yi leke tana tsoron Fulani, sai ta zo bakin kofar dakin ta ta kasa kunne ita a dole sai taji me ake yi kuma su wanene? Lol. "Yarima in a hanya na ganka ai bazan taba gane ka ba, sabida a hoto kawai nake ganin ku wajen Askirama, gara kai kana nan a bakin ka, amma Awaisu ya koma bature sak!" Inji Fulani. Awaisu yayi murmushi ya ce "duk da haka gara ni ban manta Kanuri ba, amma wannan ko Hausa da kyar yake yin ta, su sanya alkyabba kuwa tuni ya manta yadda ake yin su balle yadda zai wara kafafu ya hau doki". Yarima ya harareshi a lokaci guda yana jijjiga Zarah dake hannun sa, wadda tun ganin sa da ita jiya Allah ya sanya matsananciyar kaunar ta a zuciyar sa musamman da ya ji cewa sikila ce, yayi kissing kumatun ta yace. "Ranki ya dade da fatan zaki bani Zarah in tafi da ita Amsterdam in kin yaye ta in sa ta a makaranta?" Fulani ta ce "in ka yi aure ba? Kuma matar 'yar gida ka aura wadda bazata ji kyashin rike maka diyar ba" Awaisu ya fashe da dariya da ya tuna wadda Yarima yake shirin aure, dan kuikuiwo ne pet din ta dake biye da ita duk inda zata, ya ga yadda zata rike dan mutum sukutum ko sallah bata yi. Ta kasan ido Yarima ke kallon sa, shi kadai ya gane me yake nufi da kallon da yayi masan, don haka ya ja bakin sa yayi shiru yana cigaba da dariya. Yarima ya dago manyan idanun sa farare kal, ya sauke su a kan maridin dan uwan sa wato Ashgar, ya ce. "Ashgar, ina labari?" Murmushi Ashgar din yayi, sannan ya maimaita abinda Yarima ya ce, ba tare da ya san me ya fada ba, Awaisu yace "ya kamata ace Ashgar yana karbar rehabilitation therapy, da an samu cigaba sosai a rayuwar sa, a can kasashen da muka fito ana bawa irin wadannan lalurorin muhimmanci sosai su yi rayuwa mai ma'ana kamar kowa". Suhail dan Ya Kirjinoma yayi tsaki ya ce "da dai Ya Kirjinoma zata yarda cewa ciwo ne daga Allah mai zaman kansa, amma ita kullum zancen ta bakaken aljanu ne aka tura masa" haka hirar ta koma a kan Ashgar, Yarima da Awaisu na fadin ba wani aljanu, in maimartaba zai amince da Ashgar zasu koma Amsterdam su kai shi rehabilitation center na masu lalurar sa. Yarima ya ki ajiye Zarah a tsayin zaman su a falon, tana rungume a hannun sa, baya gajiya da kallon ta yana mata wasa jefi-jefi. Aka gabatar musu da kabakin da Fulani ta shiryawa Yarima na barka da zuwa, sosai suka ci abincin suna hira a tsakanin su cike da kaunar juna, duk cikin matan maimartaba sai yaji Fulani Bilkisu tafi kowacce samun matsayi a zuciyar sa akan dalilin da bai sani ba. Koda yake a fili yake; Fulani na da matukar kirki sannan tana kaunar 'ya'yan Askirama da zuciya daya kamar yadda yake kaunar ta. Hassada ce kawai da kishi irin na mata zasu sa ka kushe Fulani Bilkisu ko wani hali na ta, domin ita din ta yi ta kowanne bangare. Basu bar sassan ba sai ana gab da kiran sallahr magriba, shima din sai da Ya Maira ta biyo bayan su don ganin uwar da suke kullawa a unguwar Fulani Bilkisu wajen awanni biyu, tana shigowa ta ce in ya gama yaje Ya Gumsu da bakin ta na jiran sa, dole suka yi haramar tafiyar yana gayawa Fulani gobe in ya dawo daga hawan kilisar da zasu yi zai dawo ya ga Zarah. Tayi murmushi tace "Zarah na murna da dawowar wannan babban Yaya nata, mai ji da ita, bakon Amsterdam!". Yayi murmushin da ya kara masa kyau da ilhama ya sunkuyar da kai sannan ya fita, ya bar kamshin turarensa INVICTUS (by Paco Rabbanne) a sassan Fulani bakidaya. Zata wuce daki ta hango Sa'ade na leke ta tsakanin kofa, murmushi tayi tace "uwar gulma". Sa'ade bata ankara ba sai ganin Fulani tayi agabanta, sosai ta razana ta ja da baya, Fulani tace "uban me kike lekawa?" Ta zumburi baki. "Ni ba abinda nake lekawa, maganar maza na ji, nikuma na san maza basa shigowa sassan nan". Fulani tace "to ina ruwan ki da ko su waye? Ko maza na soma kawowa? Wallahi ki kiyaye ni bana son gulma, ba ruwan ki da duk abinda bai shafeki ba a gidannan don kuwa ba gidan ubanki bane, kara ki Uban su yayi". Hawaye suka ciko idon Sa'ade, ba yau Fulani ta soma cin mutuncin ta ba akan kankanin abu, amma sai ta ji na yau ya fi na kullum kona mata rai, ta yi alkawarin ta daina mayarwa Fulani magana amma tsabar bacin rai bata san sanda ta ce cikin hawaye. "Tunda kin ce inada dan uwan uba ki kaini wajen sa mana!" Fulani tace "an ki a kaiki, anan zaki zauna zaman AGOLANCI. Zaman da ubanki yake guje maki, gashi ya same ki bayan ran sa. Enjoy!". Ta fice ta rufo mata kofar da karfi. **** Ya Gumsu ta dubi Yarima yana shigowa babban falon ta, bayan dawowar su daga masallaci sallahr isha. Hararar sa ta yi cike da kauna da jin haushi, ba karamin haushi ya bata ba da ya ja kannen sa suka tafi sassan Bilkisu suka shantake bata san uwar da suke yi ba, abinda bazata taba lamunta bane wata alaqa ta shiga tsakanin Yarima da Fulani Bilkisu shima a sammace mata shi yadda aka sammace uban sa. Yana zama ta soma fada Ya Maira na taya ta "ka san tsakanina da ita ne da zaka je ka rashe a unguwar ta har ta baka abinci ka ci? Meye hadin ka da ita? Gara kowa da ita, ita ce annamimiyar gidan nan bakidaya, kai bako ne baka san komai ba don haka ka tsaya a matsayin ka na bako. Ka kama 'yan uwan ka da na haifa kadai, ban yarda da wani hadin kai na munafunci ba kowa ya zauna da wanda uwar sa ta haifa". In da sabo ya saba da halin mahaifiyar sa na kishi da korafi akan abokan zamanta, don haka bai wani damu ba har tayi iya fadan da zata iya ta bari, ta koma hirar arziki. Duk abubuwan da ke faruwa a gidan sai da ta labarta masa wanda ya shafe shi da wanda bai shafe shi ba. Har labarin Bilkisu ta dauko 'ya daga inda basu sani ba tana boyewa a sassan ta saida ta bashi "sabida ada haihuwa ta ki tsaya mata. Ka ga 'yar? Don an ce suna kama sosai" "ni ban ga kowa ba" ya fada (sounding uninterested). Sannan ya mike ya ce da ita zai je ya kwanta don a gajiye yake sosai, yau sun sha yawo. A matsayin ta na mai girki ita ke da turakar maimartaba yau. Lokacin shigar ta na yi ta bar Ya Maira da yaranta ta tafi kasancewar anan zasu kwana sai gobe zasu koma Biu. Da sallama ta shiga ta samu Alanguburo yana addua ya fuskanci alkibla. Saida ya gama ya shafa sannan ya ankara da shigowar ta dakin. Ya dube ta daga inda yake zaune ya soma magana cikin yanayin data kasa fassarawa. "A tabbatar duk bayin da aka zubawa Yarima babu mata a ciki, maza kadai na yarda suyi masa hidima har ya koma". Yanayin fuskar Ya Gumsu ya nuna bacin rai tsantsa, har sai yaushe Mai Askira zai daina yiwa Sageer kallon tsohon laifin sa? Abu an yi shi tun kuruciya amma har gobe dan ta mai laifi ne dan kowa tsarkakakke. Dubi Yarima don Allah wanke hannu ka taba me zai yi da wasu matan bayi? Ya Gumsu ta juya kai cikin takaici tace "to ayi masa aure mana! Wannan irin takunkumi haka!" Sarki ya karanto tarin bacin ran da ke cikin kalamanta, kuma ta yi maganar ne da alama ta dade ta na cin ta a zucci. An kai mata Da wata uwa duniya an yasar ba wanda ya damu da halin da yake ciki, kuma a yanzu ma ana nufin ya koma babu aure ko me? Ta san duk laifin Waziri ne, don sai abinda ya ce Askirama ke amfani da shi, idan kuwa bai ce lokacin Auren Yarima yayi ba Mai Askira ba zai taba zancen auren nasa da kansa ba sabida kawaici irin nasa. "Me kike ci na baka na zuba Fulani! Akwai abinda nake jira ne, zuwa wani dan lokaci da zai dawo gida bakidaya". Nan da nan fuskar Ya Gumsu ta washe, wani farin ciki ya bayyana akan kyakkyawar fuskar ta. Ta gyara zama tace "Alanguburo sai a san daga masarautar da ya kamata a dauko masa mata tun yanzu, ni in son samu ne na fi son masaurautun wajen Borno, kamar Kano da Bauchi, su ne kawai zan ce masarautun su sun fi namu, kuma auratayyar mu da su zai karawa masaurautar Askira kima a sauran masarautu tsararrakin ta". Sarki Yausufu sauraron ta yake absent-mindedly a daidai lokacin da wani bakon tunani ya bakunce shi. Ya Gumsu sai gani ta yi ya miki zuruf! Kamar an tsikare shi ya nufi hanyar waje. Sai kawai ta biyo shi don abu ne da bai taba yi ba fitowa a lokacin da ya riga ya shiga barci. Sai gani tayi kai tsaye ya doshi sassan Yarima Sageer cikin takun shi na alfarma. Yana so ya tabbatar da idanun sa. Yarima lafiya yake zaune ko yau ma ya kama 'ya'yan mutane ya danne. Dogarawan da ke gadin bangaren Yarima tuni suka wangale kofofin suna bawa Sarki da Ya Gumsu hanya, da suka doso dakin barcin Yarima sai maimartaba ya dauke karar sawunsa, sadaf-sadaf yake takawa yayin da Ya Gumsu tashin hankalin bata san me Yarima yake ciki ba ya dugunzuma zuciyar ta. Sarki na zuwa ya danna kai dakin da ya tabbatar yana ciki, sai ya same shi bisa darduma yana sallah. Ya Gumsu na iya jin nannnauyar ajiyar zuciyar da Alanguburo ya sauke, ya yarda ko Yarima bai daina halin sa gabadaya ba akwai improvement kashi 70% cikin halayen sa na yanzu, wanda ya kara masa karfin gwiwa akan sabon tunanin da ya bakunce shi a daren yau ba tareda ya taba kimsawa zuciyar sa ba. Ya kudure kafin ya gabatar da kudirin sa ga kowa zai yi istikhara ya nemi zabin Allah. Juyawa yayi ba tare da ya ce komai ba, itama Ya Gumsu ta bi bayan sa. Da sa'an maganarta ne cewa zata yi "a dai dinga kyautatawa dan adam zato". Da ba sa'an maganarta bane sai ta kumshe abarta a cikin ta tana kunkuni cikin ranta "haka kawai kamar shi kadai ne fitinannen da a gidannan". Ta manta cewa adadin soyayyar ka akan mutum, adadin damuwar ka gareshi. Sannan 'ya'ya ababen kiwo ne ga iyayen su wannan umarnin Ubangiji ne. Mai Askira bai kwanta ba a ranar sai da ya gabatar da sallahr istikhara akan kudirin dake zuciyar sa. Ita kuma Ya Gumsu ta kwana zuciyarta kal, a kalla dai daga yau zai sassauta zargin Yarima a ransa. **** Kwana biyu kenan Sa'ade da Fulani basu hadu ba, kowacce fushi ta ke da 'yar uwarta. A jiya Yarima ya kara shigowa kamar yadda yayi alkawari amma bai dade ba Ya Gumsu ta ishe shi da aiken kira dole yayi sallama da Fulani ya tafi. Yau dai Sa'ade ta yiwa kanta fada bata yi musu labe ko leke ba, amma tana jiyo tashin sautin muryar Yarima mai kauri da zurfi (husky) a lokacin da yake magana da Fulani. Ta fahimci ko ma wanene bakon nan mai matsayi ne sosai a gidannan, tunda har yake shiga ko'ina ba shamaki. "Idan ka kara shiga unguwar ta Allah ya isa ban yafe maka ba!" Ya Gumsu ta fada a zafafe tana numfarfashi, munafukar baiwar ta ta gaya mata abinci Bilkisu ke bashi yana ci wanda basu san me aka zuba a ciki ba. A firgice ya dago ya dubi Ya Gumsu. "Me yayi zafi haka Ya Gumsu?" Ta harareshi kamar idanun ta zasu fado, ai har gara ya likewa Hibbani akan Bilkisu, itace ta dauketa mutum take kuma bata girmanta na Gumsun gari, ba wannan mai yiwa kowa kallon bai isa ba, bayan bata aje musu komai ba sai katon kashi da 'yar da ita da babu duk daya. "Ubanka ne yayi zafin, nace Ubanka ne yayi zafin Yarima!". Ba shiri ya sadda kansa, amma hakika ya firgita da kalamanta, ya kuma tabbatar kishin ta da Bilkisu ba dan kadan bane don sauran matan ma ai ya shiga unguwar su amma ko sau daya bata yi magana a kai ba. "Allah ya huci zuciyar ku Ya Gumsu, in kun yi hakuri ni da ba mazauni ba tafiya zan yi babu mai sake gani na nan kusa". Ya juya ya fita ba tare da ya bi ta kan abincin data shirya masa ba. Koda ya koma bangaren sa ransa a bace yake, baya son wannan halin na Ya Gumsu tun yana karami, balle yanzu da ya girma ya mallaki hankalin kansa. A ganin sa a matsayin ta na babba kuma Gumsun gari kamata yayi ta kama girman ta ta rungume kowa dake karkashin sarki, tunda shi ya dauko da kansa ya kawo ya hada cikin iyalin sa to tabbas yana so ne. Ya samu sako daga jakadiyar sarki cewa maimartaba yana son ganin sa gobe kafin ya shiga fada. Wanka ya shiga sannan ya fito ya sauya zuwa pajamas, Awaisu ya kira a waya yana daga tsaye jikin taga "kana ina ne?" Awaisu yace "gani nan tare da Ba'ana (mahaifiyar sa) tana min hira, amma yanzu zan taho, hirar tata dai duk guda daya ce tun isowar mu bata wuce ta aure, wai har matar ta zaba mini" murmushi Sageer yayi, ya ce "ai gara a taimakeka a lullube a kaiwa wata mai tsautsayin, in ba hakan ba a haka zaka tsufa baka taba morar kuruciyar ka ba". Awaisu ya ce "gara in tsufa a hakan dai, Allah ya gani ban taba 'yar kowa ba balle in na haifa a taba min tawa". Sageer ya san magana ya gaya masa don haka ya cillar da wayar bayan ya ce da Awaisu "don't show me your ugly face, sai na neme ka".. Washegari bayan ya shirya cikin sababbin dinkunan da maimartaba ya aiko masa dasu, sai kamshin invictus ke tashi a dakin, ya fuskanci alqiblah ya sallaci sallahr Dhuha. Idan akwai wata dabi'a mafi kyau cikin dabi'un Yarima Sageer to sallahr farillah ce akan lokaci da kokarin yin nafilfili babu gajiyawa. Ba ya yin sallahr farillah kadai ba tareda ya hada ta da nafila ba. Sannan sallahr "Dhuha" bata wuce shi komin busyn da yake ciki. Karfe tara daidai ya tasamma turakar mahaifin sa, inda duk ya gifta sai ya bar kamshin turaren sa Invictus (Paco Rabbanne). Inda duk bayi suka ci karo da shi sai sun fadi sun yi gaisuwa sun yi masa kirarin da suka saba yi masa, a haka cikin takunsa na kasaita da sassarfa har ya isa falon da sarki ke ganawar sirri da iyalin shi. Tare da Ya Gumsu ya same shi yana karya kumallo, ta sha ado cikin koriyar laffayan matan Kanuri, bai taba ganin Ya Gumsu da wata suttura da ba laffaya ba, da alama yau maimartaba cikin nishadi yake, nishadin nasa baya rasa nasaba da kyakkyawan sauyin da ya gani a tare da Sageer tun zuwan sa, da kuma na kyakkyawan kudirin dake zuciyar sa. Yarima Sageer ya zube yana kwasar gaisuwa wajen iyayen sa, su kuma suna amsawa with so much affection wanda ya bayyana karara akan fuskokin su, maimartaba ya zuba masa ido cikin murmushi ya ce. "Kamar ba Sageeru na ba, Sageer wanda ya tafi ya barni dan firit da shi kamar a bushe, wannan dake gabana ai babban mutum ne wanda ya kamata ace zuwa yanzu ya ajiye mata hudu da kwarkwarori a gefen sa". Murmushi mai kayatarwa Yarima yayi, wanda ba kasafai ya ke yin sa ba, ya sake sunkuyar da kansa. Sarki Yusufu ya dan tsura masa ido kafin ya kira sunan sa cikin sigar son ya bashi hankalin sa. "Muhammad Sageer. Kafin mu yi kowacce magana ta aure ce kan gaba, yanzu babu abinda nasa a gaba banda burin auren ka. Duk wani kyakkyawan kudurin mu akan ka ya cika. Ina fatan zuwa yanzu ka samu nutsuwar da kake ganin zaka iya zama da iyali?" Yarima ya muskuta cikin jin nauyi, kansa a kasa bai ce komi ba, aure baya gaban sa ko kadan, don a ganin sa yanzu ne yake cikin twentieth din sa, ya ke cin kuruciyar sa da duk irin macen da yake so, aure zai zamo tamkar takura ne da takunkumi a gare shi, amma what if Maimartaba zai yarda ya auri zabin ran sa, Rose? In ita ya aura bazata takura masa ba, zata bar shi ne yayi rayuwar sa yadda yake so. Ya ga cewa wannan itace damar sa ta karshe da zai samu ya gabatar da zancen ta. Idan wannan damar ta wuce mawuyaci ne ta sake zuwa. Don haka ya tattaro dukkan courage din sa, ya ce. Ya gyara zama ya fuskanci Baban sa. "Alanguburo (Allah ya kara maka yawan rai) akwai yarinyar da na yi wa alkawarin aure a can Amsterdam, kusan shekara guda muna tare". Sarki Yusufu ya ji gwiwar sa ta yi sanyi, kuzarin jikin shi ya kare. Me yasa ya fara tambayar sa kafin ya fada masa na sa kyakkyawan kudurin akan sa? Yanzu duk abinda zai ce bayan wannan da Yarima ya fada zai zamo tamkar yayi imposing dinsa ne ga auren da baya so, tunda ya ce yana da zabin sa tuntuni, zai zama auren force....wanda baya cikin tsarin sa, bai taba yi wa 'ya'yan sa auren dole ba daga matan har mazan. Kenan dole a matsayin sa na Uba mai muhimmanta hakkin farin cikin 'ya'yan sa da ya rataya a wuyansa kuma shugaba mai adalci ya bawa Yarima dama ya auri zabin ransa. Kamar yadda nasa iyayen suka yi masa. "Kana da damar auren zabin ranka Yarima, Allah yayi albarka". Ya Gumsu ta tattare gira tace "haba Mai Askira? Haba Askirama? Haba gatan Askira? Yaya ba'a binciki gidan da ya nemo auren ba za'a amince masa da gaggawa haka???" "Ko a ina ya nemo in dai yana son ta shike nan" Yarima ji yayi kamar ya rungume Baban sa, saidai duk da haka yana cike da fargaba, shin mai Askira zai amince ya bashi goyon baya idan ya ji cewa Rose bayahudiya ce wadda bata da addini koda na kiristanci ne? Ya Gumsu ta kasa hakuri, ta ce a kagare "sai ka fada mana su waye iyayen ta, 'yan wace masaruta ne? Sannan daga wace kabila ta fito?" Jin Alanguburo bai ce komai ba ya fahimci shima yana son jin amsar. Mu karasa a littafi na biyu. Tare suke. Taku har abada: Takori MASARAUTAR MU! 2 Littafin SUMAYYAH ABDULKADIR SADAUKARWA Ga Bilkisu Askira, (Billie Askira), Maiduguri, sabida gudummuwar ki yayin rubuta wannan littafi. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. You are my source of inspiration. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. MASARAUTAR MU 2 Ya kara tattaro dan sauran karfin gwiwar da ya rage masa, yace cikin kwantar da murya, kodayake kodayaushe muryarsa a kwance take. "Baturiyar Asia ce, Jew (bayahudiya), ta yarda zata karbi addinin muslunci in dai zan aure ta". Daga sarki har Ya Gumsu a razane suka dube shi. Mai martaba ya kasa cewa komai kamar an dinke masa baki. Ya mutu a zaune cikin kujerar sa. Ya Gumsu ta mike tsaye tana nuna shi da dan yatsa "....ka yi kadan Yarima, karya kake ka tozarta ni a idon duniya da idon kishiyoyi na masu son ganin faduwa ta!. Ko mata sun kare ban yarje maka auren nan ba, da yawun baki na bazan taba saka albarka ta ba!!!". Sarki Yusufu ya ce "kana iya tafiya Yareema zamu yi shawara, duk abinda muka yanke Waziri zai kira ka". Ya Gumsu ta zaro ido tana kallon Mai Askira tamkar idanun ta zasu fado. Tunda har ya amince zai tattauna zancen nan da Waziri ta san karshen alewa kasa.....ba ya kai zance ga Waziri sai ya fara yin na'am da shi a karan - kansa. Ta fashe da kuka ta tashi ta bar falon. Yarima ya mike zai bi bayan ta. Sarki ya ce ya kyaleta sai ta huce yanzu bazata taba sauraron sa ba. Ya koma ya zauna jikin sa a sanyaye, da wannan damar Sarki Yusufu yayi amfani ya dinga tambayarsa abubuwa akan Rose din, da yadda suka hadu, shi kuma ya gaya masa duk abinda ya kamata ya sani banda wanda bai kamata ba. Ya kare zancen sa da cewa yana mata kwadayin musulunci ta hannun sa don jihadi, sabida kyawawan halayen ta, sannan ita din ma tana sha'awar addinin muslunci a karan - kanta. Ta zabi ta bar kowa nata in dai za'a bar shi ya aure ta. Alanguburo ya fahimce shi sabida saukin kansa, a lokaci guda yana kokawar ture nasa BURIN akan Yarima Sageer can gefe daga zuciyar sa, yana fadawa zuciyar sa ya bar shi yayi jihadin; wani ya shiryu ta hannun ka yafi a baka jajayen Rakuma tunda Allah bai haramta ba. Ba duk abinda muka yi burin tabbatuwar sa ne yake tabbata ba. Wasu mafarkan a mafarkai kawai suke tsayawa, ba sa zama REALITY yadda muke burin su. Wasu kuma Allah kan jinkirtawa bawa zuwa lokaci mafi dacewa. Ya sallame shi da cewa ya saurari kiran Waziri idan sun tattauna gobe. **** Sarki Yusufu da Wazirin sa Ibrahim suna tattaunawa akan al'amarin Yarima bayan sun kadaice a falon ganawar sirrin su, Waziri yace su bar Yarima yayi auren su samu ladan muslunci, amma bisa sharuddan cewa zata biyo shi gida su zauna tare dasu cikin MASARAUTA a matsayin sa na Yarima mai jiran gado. Dole ya dawo gida gabadaya ya zauna cikin ahalin sa. Lokacin da Waziri ya kira Yarima ya gaya masa hukuncin da suka yanke, Yarima Sageer yayi dan jim! Domin nan kusa bai shirya dawowa gida ba, ba zai iya rayuwar karamin gari kamar Askira ba, zai takura, ba zai shana yadda ya saba ba, sannan Rose ma zata takura, ga zafin Maiduguri, bata taba zuwa Africa ba haifaffiyar South - Korea ce. Aiki ya kai iyayenta Amsterdam. Ba abinda ya tsana irin ace shine 'mai jiran gado', bayan ba shikadai ne namiji ba, shi sarauta sam bata cikin tsarin sa, Yarima Sageer bakin bature ne kawai wanda ya rungumi affluent western lifestyle ya manta da asalin sa tsayin shekaru masu yawa, wannan kuma ya faru ne da laifin su iyayen sa da suke ganin yin nisa da gida fintinkau shine abinda zai nutsar musu da shi; don nutsuwa ya nutsu irin wanda tarin shekaru ke haifarwa da namiji, amma ba nutsuwa irin wadda su suke zato ba. Karewa ma, ya goge ne yayi mastering akan harkar neman mata, har wadanda ba addinin su daya ba. Amma in ka gan shi a fuska tsammani zakayi wani saint ne shi din (waliyyi) sabida tsabar iya badda-kama a gaban iyaye. Abu daya Allah ya tserar da Yarima akan sa shine shan giya, ko sha'awar ta bai taba yi ba. Yana matukar kyamar ta. A cewar sa ai sai da hankali ake sallah dai-dai, kuma a yi ta akan lokaci. Hatta sigari tun lokacin tashen samartakar sa ya bar ta. Amma da ya duba wannan alfarma da iyayen sa suka yi masa wadda bai taba zaton zata zo masa da sauki haka ba, sun bar shi ya auri zabin sa dai-dai da ra'ayin sa, sannan sun toshe kunnuwan su daga duk abinda zasu ji akan auren nasa, auren da a tarihin masarautar su ba'a taba yin irin sa ba, sai ya ga cewa ya zama dole shima ya amince da tasu bukatar na dawowa Askira tare da matar sa. Kafin nan zai roke su su bashi lokaci, ya kammala phd din sa, ya tattaro kasuwancin sa zuwa Nigeria ya kuma nemi aikin da zai rike shi in ya dawo, ba zai zo ya dogara da mahaifin sa ba kamar yadda akasarin 'ya'yan sarauta ke yi. Koda ya yiwa Waziri wannan bayanin take ya amince, ya kuma ce sun bashi shekaru biyu ya kammala komai, ya dawo tare da matar a musuluntar da ita a daura auren su. Awaisu was shocked lokacin da yaji labarin nan domin bai taba zaton iyayen su zasu amince da zancen Rose ba, haka bai taba zaton Yarima is serious akan maganar Rose ba, ya dauka yana fada ne kawai for fun irin nasa. Shikam tuni Ba'ana ta zaba masa mata 'yar kanwar ta mai suna Asiya suna dawowa za'a hada auren nasu lokaci guda shi da Yarima, don yarinyar bata kare sakandire ba ma. Kwanan su bakwai suka koma Amsterdam with nostalgia (cike da begen gida) a yadda suka tsammaci masarautar ta su sai suka tarar akwai cigaba na zamani sosai fiye da yadda suka tafi suka bar ta. Suka kuma fara tunanin hanyoyin da zasu kara kawo mata daukaka da cigaba na zamani ta kara zama zakaran gwajin dafi a masarautun jihar Borno tsararrakin ta. Tuni Yarima ya tsara sababbin gine-gine da za'a kara cikin masarautar, da yadda za'ayi renovating din ta daga kamfanin gine-gine da tsare-tsaren gidaje na COSIMCO na kasar Amsterdam (Neitherlands). Yana komawa abinda ya maida hankali akai kenan, wato project da cosimco akan masarautar su. Daga can suka taho suka fara ayyukan su a masarautar Askira. Gininnika na zamani masu tsayi da nagarta suka kara fiddo da martabar masarautar Askira. "Lallai dan zaki an girma" Sarki ya fadawa Waziri cikin murmushi a lokacin da suke zagaye cikin masarautar da wajen ta, suna kallon renovation din da Yarima ya tsara da kansa ya kuma turo COSIMCO construction company suka yi. Waziri da sauran 'king-makers' sai albarka suke sanyawa Yarima, fatan su bada jimawa ba ya dawo ya karbi sarautar mahaifin sa tun yana raye. Wanda basu sani ba wannan baya cikin tsarin Yarima Sageer ko kadan. Bar shi dai a gogaggen dan bokon sa. Awaisu ne kawai ya san hakan. **** Hutun su Sa'ade na karewa suka koma makaranta, ashe wani abin alhini ke can yana jiran ta, shiru-shiru tana zuba idon ganin dawowar Raheema amma har ta share sati biyu da komawa Raheema bata dawo ba. Sa'ade ta kasa sukuni, ta kasa walwala ta kuma kasa cigaba da harkokin karatun ta yadda ta saba a dalilin babu Rahima, ta kuma rasa wanda zata tambaya ko ya san abinda ya hana Rahima dowowa don kowa ita yake tambaya. Ga wani kuskure data yi bata taba karbar adireshin Raheema ba, sabida tana ganin ko ta karba babu wanda zai kaita, Fulani bazata taba barin ta ta je ba. Da abin ya isheta sai ta tafi ofishin principal, tayi gaisuwa ga principal sannan ta soma share hawaye. Principal tace "what's wrong Sa'adatu Hashim?" Sa'ade ta idasa fashewa da kuka a gabanta sannan ta gaya mata yau sati uku kenan Raheema Kyari bata dawo ba. Principal tasa aka yi bincike akan rashin dawowar Raheema, nan malamin dake kula da dawowar dalibai ya sanar da ita sakon da mahaifin Raheema ya aiko na cewa sun bar kasar Najeriya. Wanda ke nufin Raheema ta bar makarantar gabadaya. Damuwar Sa'ade sai ta nunku akan ta da, me ya sa Raheema za ta bar kasar ba tare da ta yi mata sallama ba? Laifin me ta yi mata? Amincin dake tsakanin su ya fi gaban haka. Bata san ta yi mugun shaquwa da Raheema ba sai yau data wayi gari babu ita cikin kwalejin El-Kanemi. Rayuwar Sa'ade gabadaya sai ta sauya a makaranta ta zama ba umh ba umh-umh. Haka ta dukufa yi wa Raheema addu'a ba dare ba rana kan Allah yasa tana lafiya, tana kuma rokon Allah ya sake hada su cikin gaggawa. Sannan a fannin karatu ta kara dagewa, don yanzun shi kadai ne abinda ke debe mata kewa. Tana yawan tunanin Zarah da Fulani, amma kullum tana sawa a ranta Fulani bata son ta don haka is a waste of time yawan tunanin ta data ke yi, har addu'a take yi a kowacce sallahr farillarta Allah ya rage mata son da ta ke yi wa mahaifiyar ta Fulani Bilkisu! **** BAYAN SHEKARA BIYU! Abubuwa da yawa sun faru cikin shekaru biyun nan, wadanda yawanci rigingimu ne na kishi a cikin gida tsakanin Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Sun ki zama lafiya da juna, amma kashi 80% na rigingimun in ka bincika zaka tarar laifin Ya Gumsu ne, tana kishi da Fulani Bilkisu ba dan kadan ba, a bisa abubuwa da dama; muhimmi shine son da Askirama ke mata wanda ya zarce na kowacce cikin matan auren sa, kuma ba ya iya boyewa. Yayin da ita Ya Gumsu a wurin ta ita ta cancanci wannan fifitawar a matsayin ta na uwar Yarima kuma uwar manyan 'ya'yan sa. A haka dai ake rayuwar, da dadi ba dadi a gidan sarkin Askira, kamar kowanne gidan sarauta, duk wani babban gida ko ba na sarauta ba ya gaji haka, girma na kara kama kowaccen su, kamar kuma suna girma ana kara rura wutar kishi a tsakanin su. A yau Litinin, gidan sarautar Askira an tashi da hidimar shirin tarbar Yarima Sageer wanda zai sauka a yammacin yau tareda matar da zai aura, 'Rose Hathaway'. Labari ya gama baza cikin gida na inda Yarima ya nemo aure. Surutu ba irin wanda ba'ayi a sassan kowacce daga cikin matan gidan in ka dauke unguwar Fulani Bilkisu, ita kadaice ta goyawa Yarima baya akan auren da yake so kuma bata yi Allah wadai da zabin nasa ba, ko dama kusan koyaushe ra'ayinta na zuwa daidai dana maimartaba ne. Yamma lis Yarima Sageer da dan uwansa Awaisu da Rose wadda ta sha doguwar riga har kasa da mayafinta kamar balarabiya suka iso masarautar Askira karkashin rakiyar dogarawan fada masu yawa, wadanda suka dauko su daga filin jirgi daga Maiduguri a mota civilian ta Askira Emirate. A wannan lokacin Sa'ade na makaranta tana zana jarrabawar shiga aji biyar SS 2. Ya Gumsu ta yi tsalle ta dire tace ba dai baturiyar Yarima a sassanta ba, babu ita babu wannan auren koda za'a sa mata wuka a makoshi. Don haka Mai Askira ya ce a kaita unguwar Fulani Bilkisu ta zauna karkashin kulawar ta. Dakin Sa'ade ta sa Fanna ta gyarawa matar Yareema, duk abinda zata bukata Fulani ta tanadar mata, to saidai hira ta gagara tsakanin su don Fulani bata iya turanci ba, saidai ta yi magana da Yarima a waya shikuma ya kira Fulani ya gaya mata abinda ta ce. Kwanan su biyu da dawowa aka musuluntar da Rose a masauratar Askira aka daura auren ta da Yarima Sagir, babu wata gayya ta kunya da sarki yayi iya jama'ar gari ne kawai da king-makers suka shaida auren Yarima Sagir, bai gayyato 'yan uwan sa sarakuna ba, shi kansa bai san meyasa a can kasan ran sa baya farin ciki ko kadan da auren ba, duk da cewa bisa amincewar sa da yardar sa ne. Ya dauka Rose zata zo tare da wani nata, sai ya ganta zikau daga ita sai jakar kayan ta... sai ya soma tambayar kansa ranar da 'ya'yan Yarima suka tambayi dangin mahaifiyar su me zai ce musu??? Ko dai uwar Yareema, Ya Gumsu, ta fi shi gaskiya ne??? **** Babu wani shagalin biki kamar ba auren Yarima guda ba, haka aka dauki amaryar aka kaita gidan da Maimartaba ya ginawa Yarima wanda ke gefen masarauta. Gida ne tankarere ginin sarauta kuma ginin zamani, wanda ya lashe miliyoyin kudi har ya zarta ginin masarauta tsari sabida an yi amfani da hikimar kamfanin cosimco. In ka ji ana aljannar duniya to gidan Yareema Sageer ne. Auren Awaisu sai bayan shekara biyu don matar da aka bashi bata gama makarantar sakandire ba. Rayuwar Yareema da amaryar sa Rose wadda ta karbi suna (Aisha - Sultana), sun dora ta ne daga inda suka tsaya a Amsterdam, wato rayuwar nasara zallah, don su kan manta cikin masarautar Askira su ke, Yareema na matukar son Sultana yayin da ita kuma ta karbi muslunci ne don son data ke wa Yareema ba don tana ra'ayi ba, don ya ce mata shine kadai hanyar da iyayen sa zasu yarje mishi auren ta. Don haka kusan zamu iya cewa addinin ta karbe shi ne kawai a baka, amma daga sanda suka bar cikin gida zuwa nasu gidan ta jinginar da sallahr data fara a sassan Fulani Bilkisu, ta gayawa Yareema ita bazata iya kullum ba, akwai wahala sai ta saba tukunna, yayin da Yareema ya nuna ba zai lamunci hakan ba sai take yi a gaban sa, in baya nan kuwa a hadu a gaba. Sati hudu ana barzar amarci, an cika musu gida da bayi da hadimai, Sultana sai a lokacin take lakantar ko wanene Yareema Sageer Yusuf Askira? Ashe a baya bata san komai a kan shi ba? Banda kasancewar shi abokin shashancin ta, ta fahimci a yanzun tana sahun gaba na mata masu sa'a a rayuwa, domin Sageer daya ne cikin dubu, wanda irin sa ta fannin nunawa matan su soyayya tsiraru ne a cikin al'umma. He's genius a halayya da dabi'a, superb a rayuwar auratayya, splendid a tafiyar da matar sa.... Ko don ta cigaba da rayuwa da Yareema zata cigaba da zama cikin rigar addinin sa mai wahala, amma ba don ya dadata da kasa ba. Watanni ukku Yareema ba ya komai sai neman aiki ta yanar gizo ba da sanin maimartaba ba, sai amarci da mai jan kunnen sa, Fulani Bilkisu ta zama uwar dakin Sultana ita ke kula da komai da ya shafe ta don Ya Gumsu ko gaisheta tayi bata amsawa, haka Ya Maira bata taba takowa gidan ta ba sai Humaira da Naja'atu, mazan kam suna zuwa sosai wajen Yareema musamman Ashgar wanda ya maida gidan wajen hirar sa sabida yadda Yarima ke jan sa a jiki, don yana tsananin tausaya masa, kuma yana samun sauki sosai daga rehabilitation din da Yarima yasa shi ya samu a kasar Amsterdam. Ayyuka har biyu Yareema ya samu a lokaci daya, NTNU (Nigerian Turkish Nile University) dake Abuja sun bashi aikin koyarwa (lecturing) kamar yadda ya zaba a tsangayar (Pure and Applied Chemistry), haka OAU (Obafemi Awolawo University, Ile-Ife) suma sun dauke shi da gaggawa, tun kafin dawowar sa ya yanke shawarar komawa academia wani professsion da 'ya'yan sarauta basu fiya karba ba. Kamar yadda komai nasa yake daban da na sauran mutane, haka tunanin sa ma ya ke. Ba ya danganta kansa da sarauta ko kadan kamar yadda mahaifin sa ke so, a ganin sa tana hana 'yanci, sannan takura ce. Gashi shikuma mutum ne mai tsananin son rayuwar da babu takura, kuma babu matsantawa a cikin ta. Mutum ne mai (tsinkaye) da tsantseni a cikin dukkan mu'amalolin rayuwar sa, mai son dogaro da kai, mai zafin nema, mai zafin nama, sannan mai nasara a kan duk abinda yasa a gaba. Bar shi dai da son matan sa (his only shortcoming) abinda zamu iya kira nature a jikin maza jinin sarauta, wanda zamu iya cewa tun bayan auren nan wata irin nutsuwa ta saukarwa Yareema Sageer Askira; Mata suka rage burge shi banda matarsa Aisha-Sultana. Haka ya zauna yana deleting numbobin mata kala-kala yare daban daban dake kan wayar sa, ya na fadawa kansa da kansa; yadda ya bar Amsterdam gabadaya, haka ya baro ta tareda dukkan matan da ya baro cikin ta. Kasuwancin automobile din sa ma ya maido shi gida Nigeria ya dora Awaisu akan komai. Yanzu kuma da ya dawo sai ya hada da biyu daga cikin kannen sa wadanda suke gab da kammala karatun digiri akan kasuwanci, Suhail dan wajen Ya Kirjinoma da Ahmad kanin sa a dakin su. An kai ruwa rana kafin Maimartaba ya yarjewa Yarima komawa Abuja da iyalin sa, don a tunanin sa da farko ya dawo Askira kenan don har ya fara shirin yi masa nadin sarautar Chiroma, amma sai Yarima ya zo da batun samun aikin sa da NTNU yana rokon Maimartaba alfarmar ya bar shi ya tafi, sai da Fulani Bilkisu ta sa baki sannan maimartaba ya amince don baya iya hanata kowacce alfarma ta nema, kuma Yarima ya zama dan gidan ta yanzu tun lokacin da Maimartaba ya damka mata amanar Sultana. Ya bar shi ya tafi da alkawarin duk bayan wata uku a gida zasu yi hutun kowanne karshen zangon karatu na jami'a. Ranar wata Lahadi Yarima Sagir da maidakinsa Aisha-Sultana suka tattara suka koma Birnin tarayyah. Humaira da Naja'atu da sauran kannen sa maza ne suka yi masu rakiya, basu dawo ba sai da suka taya su suka shirya gidan su tsaf wanda Jami'ar NTNU ta baiwa Yareema Sagir cikin jerin gidajen malaman Jami'ar. Jami'ar NTNU mallakar Turkawa ce (Turkish University) da suka bude a kasar Nigeria, suna biyan malamansu sosai a matsayin ta na (private international university) ko kusa ba daya take da jami'o'in Arewacin Nigeria ba wajen biyan malamai. Haka gidajen malaman jami'ar dole tsarin su ya burge ka. Flat ne hawa daya mara girma sosai, dakuna ciki hudu, kitchen da bandaki a kowanne dakin barci, tafkeken falo da bangaren cin abinci (dining) sannan akwai garden daga bayan kowanne gida, daga gaban gidajen kuma balcony ne domin shan iska da yamma, akwai rumfar gargajiya (hut) a cikin gate din kowanne gida wadda aka zuba kujerun roba da gadon shan iska na Turkawa, gabadaya ginin daga na jami'ar har na gidajen malaman an dauko tsarinsa da sample dinsa daga Istanbul ne, duka gidajen iri daya ne sun kai guda 100 a cikin jami'ar. Su Humaira suka dawo gida suna ta santin gidan Yayan su Yarima (Dr. Sagir Yusuf Askira) sunan da Jami'ar ta mayar masa, da alwashin zuwa hutu duk sanda suka samu hutu domin ba laifi Aisha - Sultana tana da kirki ga kowa nasa, daga auren zuwa yanzu ta saba da daukacin kannen Yarima na sauran dakunan matan sarki, banda 'yan dakin Ya Gumsu. Tun bata fahimta ba sabida rashin jin yaren hausa dana kanuri har zuwa yanzu ta fahimci Ya Gumsu bata yi na'am da ita a matsayin surukarta ba. Da suka je mata sallama ma zasu taho abuja ko kallon ta bata yi ba, haka tace da Yarima cikin fushi "tattara wannan danyen naman ku bar min sassa tun ranka bai baci ba". Ba wai ta ji me Ya Gumsu ta ce bane amma ta fahimci ba maganar arziki bace duk da Yarima bai nuna komai akan kyakkyawar fuskarsa a lokacin da ta yi maganar ba, baya ga cewa da yayi da ita ta tashi su koma gida dare yayi. Satin su guda itama ta fara neman aiki da (Insurance Brokers) kasancewar tattalin arziki ta karanta, Yarima ya samar masu kuku da mai gyaran gida duka kabilu, ba'a jima ba kuwa suka dauke ta, sai ya zamo daga shi har ita ba mazaunin gida, a lokacin ne Yarima yayi wani aboki dan kasar Turkey wanda yana cikin masu ruwa da tsaki na jami'ar sunan sa Dr. Ziyad, zasu yi shekaru daya kuma a tsangaya daya suke koyarwa. Tun haduwar Sageer da Dr. Ziyad abubuwa suka kara canzawa Yarima, domin Dr. Ziyad fitinanne ne na karshe kuma shi ba shi da mata, gidan sa babu nisa da gidan Yarima don haka lokuta da dama suna tare, suyi yawo cikin gari ko su debo 'yammata gidan Dr. Ziyad, A haka suke rayuwar shi da Sultana kowa yana sha'anin gaban sa, don so suna son juna har gobe amma rashin albarkar uwa ya hana auren gamsar da kowannen su ba tareda sun san hakan ba. Itama tunda ta waye da rayuwar Abuja shikenan ta koma harkokin ta na baya, bata kara tuna wani abu wai shi musuluncin data karba ba, shaye-shaye take na fitar hankali, data gane inda ake sayar da giya a Abuja kuwa shikenan kakarta ta yanke saka. Ta san halin Yarima akan 'giya' don haka bata taba gigin shigowa da ita gidan ba, kullum ta taso aiki sai ta tsaya a Bar ta sha mai isar ta, ta yo guzurin kayan mayen ta kala-kala sannan zata dawo gida, tana riga shi dawowa sau tari domin Dr. Sagir yafi fixing laccar yamma ga daliban sa, tana shigowa kai tsaye dakin barcin ta take nufa ta zube a kasa ko a gado tayi ta barci, har sai ya dawo ya tasheta da kan sa ya ce ta yi sallah. Wannan itace kalar rayuwar Yarima da matarsa Aisha Sultana a birnin tarayyah, Abuja. Rayuwar da kowanne ya zabawa kansa. A haka lokaci ya cigaba da mikawa. Abinda Yarima bai sani ba tun dawowarsu Abuja da sati daya, Aisha-Sultana ta je an juya mata mahaifa. ***** BAYAN SHEKARA BIYU! Yau ne daliban El-Kanemi College of Islamic Theology suka kammala rubuta final paper din su ta barin makarantar sakandire wato SSCE wadda ta kasance darasin addinin muslunci (islamic studies). Farin cikin dake zukatan su ba zai bayyanu ba, fuskar Sa'adatu Hashim tafi ta kowa yalwar far'a, ta yi dakacen wannan rana inama da Rahima Kyari! Sun yi hotuna na tarihi kala-kala da kawayen ta da abokan arziki da suka yi zaman aminci tare. Babban farin cikin SA'ADE shine Alanguburo yayi mata alkawarin karatu a jami'ar Turkawa dake Najeriya (Nigerian Turkish Nile University) muddin ta fiddo da 9 credits, kuma daga yadda ta rubuta kowacce paper tana da kyakkyawan zato akan kokarin ta. Humaira ta gama makaranta shekaru biyu baya, yanzu haka tana jami'ar Maiduguri. Da suka iso gida yau ta yi abinda bata taba yi ba a tsayin rayuwar ta (without minding the consequence); a guje ta shiga sassan su tana kwalawa Fulani kira, Fulani bata san hawa ba bata san sauka ba tana tsaye tana yi wa little Zarah fada taji anyi wuf! Da ita an kankameta a tsakar dakin. Dama ga ta babu kiba ko kadan. Saura kadan ta sha kasa "I have finally graduated Fulani, i've really -really made it!". Kokarin banbare Sa'ade take daga jikin ta kada wani ya shigo ya gansu a haka, yayin da Little Zarah ke ta kyalkyala dariya cike da murnan ganin Sa'aden, ta tafi itama ta rungume su, Sa'ade ta saki Fulani da ke ta banbamin fadan so take ta karya ta? Ta russuna ta dauki Zarah tana rada mata cikin kunnen ta "na taho miki da choculates mai dadi" Zarah ta ce "bazamu san wa Fulani ba tunda tana yi miki fada" a haka suka shige dakin Sa'aden wanda Fanna ta gyare tsaf. Ta sanya turaren wuta irin nasu. Don tana da masaniyar yau ne graduation din Sa'adatun. Sa'adatu Hashim dalibar El-Kenemi, doguwa ce sosai, mai kirar jiki na bare-barin usli, wadanda suka hadu da shuwa suka haifeta, suka bata colour din fata mai kyau da daukar ido. Doguwa sambaleliya tamkar kirar matan Saliyon, a yanzu ne take cikin shekaru goma sha takwas komai nata ya kai ya kawo, cikakkiyar budurwa mai wani irin class na daukar hankali. Duka wadannan Fulani Bilkisu ta nazarce su ne a lokacin da Sa'ade ta dauki Zarah suka bata baya zuwa dakin Sa'aden, ta bisu da kallo cike da kauna tana jin wata irin soyayyarsu su a zuciyar ta, a yanzu kam ta saduda, ta tabbata ta kuma haqqaqe tana son 'yar ta, kwatankwacin ko ma fiyecda yadda ta ke son Fatima-Zarah. Ta koma cikin hamshakiyar kujerar falon ta ta zauna, ta lumshe idon ta a hankali, yayin da tunanin shekaru goma sha tara a baya na yadda ta samu 'yar, ya soma rewinding filla-filla a cikin kanta..... **** SHEKARU GOMA SHA TARA A BAYA! Mu 'yan kabilar "Baggara" ne wadanda aka fi sani da "Shuwa-Arabs", asalin mu makiyaya ne masu yawo da dabbobin su a kasashen Africa, mun fito daga kasar Chadi wadda take daga yammacin Ifriqiyyah, yawanci zaki samu yan kabilar Baggara sun watsu a kasashe irin Sudan, Cameroon, Niger, Chad, Nigeria, da kuma Central African Republic. Baggara musulmi ne na haqiqa masu rikon addini tun karni na goma sha uku, harshen mu shine "Chadian Arabic" wanda muke yin shi da shuwa-dialect, Allah ya zubawa Baggara kyawun surah na kirar jiki data fuska, da wata irin kalar fata mai sheki da kyau, wanda ya samo asali daga cakuduwar su da larabawan Sudan. Mahaifina Malam Soumana ya baro kasar Chadi tare da mahaifiyata a lokacin tana da cikina tare da 'yan uwan su Baggara zuwa Nigeria inda suka yada zango a yankin Borno, daga baya suka koma Damaturu bayan an haifeni da shekaru hudu, inda mahaifina yake sana'ar kiwo, shanu yake kiwo da tumaki ya sayar a karshen kowacce shekara ya sayi wasu ya sake sabon kiwo. Mahaifiyata Roumana tunda ta haife ni bata sake haihuwa ba, inada shekaru biyar Allah yayi mata rasuwa. Babana shi ya cigaba da raino na, yasa ni a makarantar firamare, daga baya jarin kiwon nasa duk ya balbalce, wani abokin sa ya yaudare shi ya saye su da zummar washegari zai kawo masa kudin gabadaya, cikin dare ya bar Damaturu da dabbobin gabadaya, wanda hakan yayi silar talaucewar mahaifi na, muka koma rayuwa cikin kaka-ni-kayi, abinda zamu ci kansa ba kullum muke samu ba, mahaifina ya koma yin dako a kasuwa duk don mu samu abinci baya ko zancen aure don tsoron matan borno wadanda ba kabilar sa ba. A haka na rayu hannun mahaifina cikin kwanciyar hankali don talaucin mu bai hana mana kwanciyar hankali ba, duk wata buga-buga da dan adam zai yi don ya samu abinci mahaifi na yayi ta har na gama makarantar firamare, inada shekaru goma sha uku watarana mahaifina ya zo da dabbobi masu yawa, ya dinga yi musu turke yana daure su daya bayan daya, na tambayeshi inda ya samo su sai ya ce ya karbe su ne yayiwa wani kiwon su zai dinga bashi ladan kiwo duk karshen wata. Sabida zai yi tafiya Kano ci-rani bashi da wanda zai dinga kula masa da su. Watarana muka wayi gari dabbobinnan babu ko daya, an biyo dare an sace su. Mahaifina ya shiga tsananin tashin hankali, domin mai dabbobi ya kusa zuwa gida, duk bayan wata uku yake zuwa, sabida tashin hankali mahaifina har kwanciya yayi ciwo don bai san bayanin da zai yiwa mai dabbobi ba. Bansan yaya suka kare ba, illa a wani dare mahaifina yana kuka ya gayamin gobe zai daura min aure, bashi da abinda zai biya mai dabbobi, shikuma ya ce sai ya biya shi, ko ya bashi aure na madadin dabbobin sa. Na rasa a wane yanayi na karbi wannan zance na mahaifina. "Auren biyan bashi" zai yi dani, sai kace ni din ba mutum bace mai darajah. Ban taba yiwa mahaifina musu ba amma wannan karon na ce a'ah, bazan auri mutumin da ban sani ba ban taba gani ba, sannan kuma tafiya zai yi dani can wajen ci-ranin sa ya rabani da mahaifina wanda shi kadai nake da shi a duniya. Amma rashin yardar tawa bata kara komai ba, washegari mahaifina ya daura min aure. Bayan gama daurin auren yana kokarin shiga gida ya fadi, faduwar da ta zamo numfashin sa na karshe. Kwana uku da rasuwar mahaifina makota sun tayani zaman makoki, kowa ya tausaya mun, na zama abun tausayi, hankalina ba ya kara tashi sai na tuna auren da mahaifina ya daura min. Na tsani auren na tsani mai dabbobin tunda bashi da zuciyar musulunci da ba zai iya yafewa mahaifina asarar data same shi ba, zai ce ayi masa biyan bashi dani sabida rashin sanin darajar dan adam. Washegari sai ga mata uku sun zo wai sun zo tafiya da ni, daya tace sunan ta Yagana matar Yayan mijin nawa ce, sai matan abokinsa guda biyu. Ina kuka ina komai haka suka fidda ni daga gidan mu ko wanka babu, a gidan Yayan sa Malam Kyari aka bamu daki wai zuwa sati mai zuwa zamu wuce Kano inda yake ci-ranin sa. Ban ga mijin ba sai da daddare. Ya manyanta sosai, ga shi bakikkirin ga rashin kyawun gani, ni duk ba wannan ne damuwata ba yadda zan zauna daki daya da shi. Ga dakin ciki daya falle daya. Ya cire babbar rigar sa ya rataye ya jawo ledar da ya shigo da ita yana ta far'a yace "Amarya Bilkisu taho ki ci, ki kwantar da hankalin ki ni mai kaunar ki ne, na dade ina son ki, kuma na gayawa Babanki yace shi bazai aurawa kowa ke ba sabida baki da kowa a kasar nan, burin sa shine ku koma Chadi cikin dangin ku. Nayi duk iya kokari na ba abinda ban bashi ba amma ya ki karba. Sabida haka ne na bashi ajiyar dabbobi na kuma biyo dare na kwashe abina don in samu hanyar mallakar ki. Gashi dabara ta tayi min amfani, saidai ban ji dadi ba da ya rasu ban nemi gafarar sa ba. Na so bayan auren mu in gaya masa cewa ni na kwashe dabbobin". Na daga rinannun idanuna ina kallon mutumin nan da wata irin tsana...tsanar da ban taba yiwa wani dan adam a duniya ba, kawai sai na sa kuka mai cin rai. Ya kawo hannu wai zai lallashe ni na kai masa mahangurbar data sa dole ya ja da baya. Ya sake kokarin kamo ni na buga tsalle na bar dakin da gudu. A ranar a dakin Yagana na kwana. A gabadaya kwana bakwai din da aka ce zamu yi a garin Damaturu ban kara yarda na shiga wancan dakin ba, nasiha da lallashin duniya matar Kyari ta yi da shi kanshi Yaya Kyarin, amma bana ce musu komai sai kuka. Tunanin makomar rayuwata nake da ba uwa, ba uba, babu dangi sannan bansan asali na ba, abinda na sani kawai shine daga Western Chad muke. Bayan wannan bansan komai akan iyayena da asalin su ba. Sannan ga auren wannan azzalumin mutumin! Yo azzalumi mana! Wanda ya sanya mahaifina cikin kaka-ni-kayi don biyan bukatar zuciyar sa. Ya raba mu, rabuwa ta har abada. Don na tabbatar bakin cikin irin auren da yayi min ne ya sa ya fadi, faduwar da ta zamo ajalin sa. Kwana bakwai ta cika, Yaya Kyari ya sameni shi da matarsa, ya fara da yimin nasiha da nuna min girman hakkin aure a wurin Ubangiji, sannan ya kuma tabbatar min kanin sa mutumin kirki ne zai kula dani, in kwantar da hankali na in bi shi, duk abinda yayi min wanda bai kwanta min ba yayi alkawarin tsaya mini, yace daga yau shi uba ne a gare ni ba suruki ba, in na yarda da hakan to in bi Hashimu mu tafi garin Kano. Haka ina kuka ina komai muka shiga motar da zata kai mu Kano, ko fuskarsa ban yarda na kalla ba, don yadda na tsani Hashimu da za'a bani wuka ace kisa halal ne da na caka masa na huta. Duk wata kulawa da tarairaya yayi min a mota, komai ya gani sai ya saya mani duk da bana yarda in karba balle in ci. A haka muka iso Kano, daganan muka hau motar unguwar da yake zaune. Gidan karami ne sosai, sana'ar kayan gwari yake yi (kayan miya) a kasuwar 'yan Kaba, idan ya fita tun goma na safe sai magariba yake dawowa, kafin ya dawo kuwa na gama duka abinda zanyi na dau abinci na na shige daki na sanya sakata. Bana kara budewa sai washegari inna tabbata ya fita kasuwa. Mun dauki watanni a haka, a wani dare da bazan iya tantancewa ba, cikin barci na ji kamar ana kokarin balla kofar daki na, kafin a yi haka na ganshi a kaina. Na soma kurma ihu ya toshe min baki ya sa igiya ba tausayi ba imani ya daure ni jikin karfen gado. A wannan bakin daren ne na samu cikin SA'ADATU. Kuma daga ranar bai kara kusantata ba, domin ya tausaya min azabar da ya gana mini. Washegari ba irin kyautatawar da Hashimu bai yi min ba, amma ba abinda hakan ya kara min banda tsanar sa. Ban taba sanin alamun shigar ciki ba, sabida ban tashi tare da mace ba, koda naga cikin ma yana turowa ban taba kawowa a raina cikin bane, don bansan me ake a samu cikin ba. Balle in yi tunanin na samu. A haka ciki na yayi ta girma, sai da na soma jin motsi da wutsilniya na tabbatar cikin Hashimu ne a jiki na. To dama haka ake samun cikin kamar kiftawar ido? Kamar azal? Fadin tashin hankalin da na samu kaina abu ne da bazai fadu ba, nayi kuka nayi kuka har na ji babu dadi. A karshe dole na dangana, ina ji ina gani na haifewa Hashimu 'ya. Tunda na samu kaina na ce saidai ya sake ni ko in kai karar sa. Shikuma a lokacin ba abinda yake so a duniya irin rayuwar jaririyar sa, na fice mai a ka, sabida duk iya kyautatawar da namiji zai yiwa mace a duniya domin ta so shi yayimin, amma na kasa kallon shi da kauna komai kankantar ta. Ba don komai ba sai don abinda yayi wa mahaifi na, da hanyar da ya bi ya samu aure na. Sai yace "mu yi jinga, na yarda zan sake ki, amma bayan kin shayar min da yarinyar nan na tsayin shekara daya kacal, ni kuma zan sawwaka miki kije duk inda kike son zuwa". Da wannan yarjejeniyar na yarda na shayar da Sa'adatu na tsayin shekara daya. A ranar da ta cika shekara daya ya cika alkawarin sa ya sake ni saki daya. Yace ga gida nan ya mallaka mini albarkacin haihuwar Sa'adatu, ya san bani da kowa, ya san bani da inda zani, amma tunda haka na zabawa kaina shi ya bar min gidan, ya dauki 'yar sa yace kauye zai koma ya raine ta. Wannan ba damuwa ta bace tunda na samu 'yancin kaina. Ba wadda zata san zafin kiyayyar namiji sai wadda aka yiwa irin auren da aka yi min. Auren dole is a challenge da ba duka mata ne zasu iya jure shi ba. Kwana bakwai a tsakani na sayarwa da makocinmu gidan, na kulle kudi na sai tasha, na hau motar Maiduguri, don na kudurce a raina ni da Damaturu har duniya ta nade. **** Aka sauke mu a tashar Bama, daga nan na rasa ina zan nufa. Ga yunwa ga gajiya. Haka na hau tafiya a gefen titi dauke da kullin kaya na. Tunani yayi min yawa har bansan na hau bisa titi ba, a yayin da zungureriyar motar ta shararo a guje, duk kokarin da direban yayi bai yi nasarar kauce min ba sai da ya kwashe ni ya watsar bisa titi. Jini kuwa ya balle ko ta ina, baka jin komai sai salatin mutane. Sauran motocin dake biye dasu in convoy duk suka dakata a gefen titi. Fadawa suka fito bisa umarni suka ciccibe ni suka saka a mota sai asibiti. Ban samu kai na ba sai bayan awanni uku. Na farka na ganni a wani hamshakin asibiti. Likitoci farar fata fal a kaina, ga karin ruwa ga karin jini, juyawar nan da zan yi sai na yi tozali da wani babarbaren mutum ma'abocin zati da kamala, mai yawan murmushi, yasha nadin rawanin da ya tabbatar min yana da alaqa da babbar sarauta. Baza'a kira shi tsoho ba, amma kuma ba yaro bane ko kusa. A bayan sa Fadawa ne guda biyu a tsaye sai muzurai suke. Ya fara da bani hakuri, sannan ya gaya min an dauko shi ne daga Airport zasu wuce garin su direbansa yayi duk kokarin da zai yi ya kauce min Allah ya rubuta sai sun kade ni. Ya tambaye ni sunana na gaya masa. Ya ce in bada kwatancen gidan mu aje azo dasu sabida na samu karaya a kafa da hannu bazai yiwu a sallame ni a yau ba. "Bani da uwa bani da uba, bani da 'yan uwa, nikadai ce. Ban da kowa, kuma bani da inda zani". Na bashi amsa cikin kuka na zafin ciwo. Maimartaba Sarki Yusufu mai Askira, ya dade yana kallo na kafin ya ce "Kin yarda ki bini masarautar Askira cikin amana in zame miki uwa da uba sannan MIJI abokin rayuwa?" Haka naji furucin sa tamkar cikin mafarki, na kasa yarda da abinda kunnuwa na suka jiye min, na kasa amincewa ido na biyu it was just in a dream..... (and that was how I became a QUEEN) wannan ne silar zamowata Sarauniyar amaryar sarkin Askira, wanda daga kallo na farko na ji ya kwantamin a rai, da wani irin exceptional feelings..., wata irin kwantacciyar soyayya da kauna, da ban taba ji a rayuwa ta ba. Komai ka ga ya faru da bawa to dama can rubutacce ne a lauhul-mahfuz, na yarda rabon Sa'adatu ne ya sabbaba aure na da mahaifin ta, ban taba jin son sa ba, domin soyayya ta Allah ce. Shi yake kimsa ta a zuciyar bayin sa. Haka itama kiyayya. Amma a ganina da ba ta hanyar da Hashimu ya bi ya aure ni ba kenan zan iya hakurin cigaba da zama da shi ko don maraici na dacrashin gata na. Bayan na gama iddah a gidan Liman inda aka yi min masauki, Limamin Askira shi ya zama waliyyi na, Wazirin gari Ibrahim ya zama waliyyin Sarki Yusufu suka daura mana aure, auren da ya jawo cece-kuce mai yawa a masarautar Askira domin Sarki Yusufu bai taba auren diyar talaka ba balle mara asali mara dangi. Duka matansa 'ya'yan sarakuna ne daga masarautu daban-daban na jihar Borno. Gorin kishiyoyi da damuwar rashin dangi dana shiga shi yasa maimartaba maida hankali ya binciko min dangin mahaifana, wadanda suka zo kasar Nigeria tare, ta hanyar su ne aka bi aka cimma sauran a Chadi duk da cewa da yawa sun watsu cikin duniya wasu kuma sun murmutu. Kusan mutum biyar aka samu masu alaqar jini da iyaye na a kasar Chadi. Sannan ne na samu kaina daga gorin rashin asali dana dangi daga wajen kishiyoyi na. Aka maida gorin kan ('yar talakawa). Rayuwar gidan sarauta rayuwa ce mai wahala, musamman ga ni da ban ta so cikin sarauta ba, na sha wahala ba 'yar kadan ba a hannun Ya Gumsu, ita Ya Kirjinoma bata da matsala sosai, ita kuwa Hibbani sai munafurci da tsugudidi da daukar zance. Sa'a ta guda daya ce; matsanancin son da miji na ke yi mun, wanda yayi maganin kowacce damuwa da kowanne kalubale dake cikin babban gidan sarautar Askira. Sarki Yusufu bai kyale ni haka ba cikakken ilmin addini dana boko ba, malama ya dauka mai digiri take zuwa har gida tana koyar dani karatu da rubutu na zamani, sannan ya daukar min malamar karatun addini, don haka daidai gwargwado inada sani a duka fannonin har fiye da kishiyoyi na wadanda girman kai ya hana su zama daukar karatu wurin kowa. A cewar su wanda suka yo a gidan iyayen su ya ishe su. A haka nayi haihuwa har biyar 'ya'yan basa sati a duniya suke komawa. A cewar maimartaba alhakin SA'ADEN dana baro a lokacin da tafi bukatata ne, ko hakan ne ko ba hakan bane a halin yanzu na yarda na amince akwai hakkin Sa'ade a kaina, wanda ya zama dole in nemi yafiyar ta, ban taba ganin yarinya mai hakuri da son mahaifiya irin Sa'adatu ba. Mahaifiyar da ko sau daya bata taba kyautata mata ba!!! Amma kullum ta zo gaba na sai annurin fuskarta ya canza. Walwalar ta ta karu. Sai ta nuna kaunar da ta ke mun cikin fararen kwayan idanun ta. Meye laifin ta akan tsakanina da mahaifin ta? Bata san komai ba, bata san an yi ba. Don haka cikin mu'amalar mu ta Uwa da Da na amince akwai daukar hakki...... A hankali Fulani Bilkisu ta sake lumshe idanun ta. Ta bi kofar dakin Sa'ade da kallo, inda take jiyo karadin su ita da Zarah. Ko in ta baiwa Sa'adatu labarin nan zata yi mata uzuri ta yafe mata?? Domin hakika ta cuzguna mata ba dan kadan ba. Wannan tunanin ne ya sa ta mikewa tsaye, ta doshi dakin Sa'ade cikin sanyin jiki da mutuwar zuciya...... **** "Bude bakin.....haa...in sa miki choculate" ta ji Sa'ade na fadi a lokacin ta tura kofar dakin, ta same su bisa gado itada Zarah, har sun sake wanka sun sake kayan jikin su kasancewar akwai wasu kayan Zarah a dakin Sa'ade sabida yawan yi mata wanka data ke yi idan tazo hutu. Murmushi Fulani tayi ta karasa gare su ta zauna a gefen gadon. Sa'ade ta saki baki tana kallon ta don abu ne da bata taba gani ba; Fulani a zaune gefen gadonta tana mata murmushi irin na UWA....murmushin Fulani, da zama akan gadon ta ya dugunzuma zuciyar Sa'ade. Kullum ta shigo tana tsayawa ne daga bakin kofa ta fadi sakon da ya kawo ta ta juya. Yau kuwa kyakkyawar fuskarta a sake, dauke da murmushi mai taushi. Ta lura da kallon tsoron da Sa'ade ke mata sai ta kara kashe ta da lallausar murmushi. "Ki daina dura mata chocolate baki ga hakobranta duk sun cinye da zuma ba?" "Tana so ne Fulani, kuma da ta fara fanfara duk ficewa zasuyi masu kyau su fito". Ta sake yin murmushi, "an gama makaranta sai aure ko? Ko baki da saurayi ne?" Nan da nan Sa'ade tayi kicin-kicin da fuska kamar Fulani ta aiko mata da sakon mutuwa. Kamar zata yi kuka tace a shagwabe "to ni ina nake zuwa balle inyi saurayin? Daga makaranta sai daki na, ko tsakar gidannnan ba bari na kike in je ba, sabida bakya so a gane ni 'yar ki ce. Kuma Alanguburo yayi min alkawarin tafiya Jami'a a Abuja idan na ci SSCE dina, ke kuma kina zancen aure". Fulani ta dora hannayenta biyu akan kafadun Sa'ade duka biyun tana murmushi tace "karatu ai ba ya hana aure Sa'adatu. Sanda ina kamar ki haihuwata uku don dai basu rayu bane, kuma shi Alanguburo ai ra'ayin ki yake bi amma ni da shi duka mun fi so mu yi muki aure....." da sauri ta tare Fulani "to sai ku bari sai Allah ya kawo mijin, ni 'yar mitsitsiyata dani....." ta fada tana zumburo baki. Fulani tayi dariya ta dalle mata siririyar fatar bakin nata "zaki je makaranta kamar yadda kike so, amma bazamu bari ki zauna a hostel ba, saidai gidan Yarima, tunda shi malami ne a makarantar zai taimaka miki, sannan gidan sa cikin jami'ar yake, zaki samu saukin zirga-zirga". Fuskar Sa'ade ta nuna ba haka ta so ba, campus life take sha'awa, ta ganta a jami'a tana rayuwa a cikin dalibai 'yan uwan ta, rayuwa ta 'yanci ba irin ta EL-KANEMI ba. Sa'ade ta ga cewa zuwa jami'ar ma da aka barta dama ce, domin babu wadda ta samu irin wannan alfarmar a 'ya'yan gidan, da sun gama sakandire Askirama ke aurar dasu, itama ya duba maraicin ta ne da kuma tunanin karatun shine gatan da zai yi mata a rayuwa ranar da baya doron kasa. Ta tambayi Fulani ko wanene Yarima? Da ta ce a gidan sa zata zauna a Abuja? Fulani tayi mata bayani yadda zata gane cewa babban dan maimartaba ne a maza, shine Yarima mai jiran gado, Chiroman Askira, wanda ya dawo daga kasar Amsterdam shekarun baya yayi aure. Sa'ade ta kwantar da ido tana kallon Fulani, ganin yau akwai rahma tattare da ita, watakila in tayi sa'a ta gaya mata abinda ta dade tana son ji daga gareta....an ce Dama tana zuwar wa dan adam sau dayane a rayuwa....watakila daga yau din bazata sake ganin murmushin mahaifiyar ta ba, bazata sake ganin ta cikin wannan maternal mood din ba...don haka ta tambayeta abinda ta dade yana cin ta a zucci.... "Don Allah Fulani me yasa ba kya so na? Me babana yayi miki kika tsane shi? Meyasa kike bakin cikin kasancewata diyar ki? Fulani ko don ni babana talaka ne shine dalilin da......." ta kasa karasawa sai kuka ya kufce mata, tana tuno bad memories na tun zuwanta hannun mahaifiyar ta..... Ga dukkan madaukakin mamakin ta, sai jin hannun Fulani tayi ya zagayeta cikin runguma kyakkyawa, ".....Ban taba kin sa don yana talaka ba, hasalima ni a mai arzikin sa na san shi. Ban taba neman komai a hannun sa na rasa ba, ya ciyar da ni ya tufatar da ni a tsayin zamana da shi. Laifin sa gare ni daya ne....hanyar da ya bi ya aure ni.....". Tiryan-tiryan ta soma bata labarin ta, labarin da ya dauki hankalin Sa'ade har bata san lokacin da tace. "Lallai Baba bai kyauta ba. Amma ki dubi Allah Fulani ki yafe masa albarkacin ni da nake tsakanin ku, da kuma kasancewar a halin yanzu ba ya duniyar". Ta fada tana share hawaye. Fulani ta kara jawota jikin ta, ta sanya fuskarta cikin tafukanta "daga yau kin daina zargi na akan babanki? Kin daina ganin beke na a kan sa?" A hanakali Sa'ade ta gyada kai. Ta ce "to na yafe masa duniya da lahira, kema ki yafe mini deprivation dina a gareki da yadda na tafiyar da ke a zaman mu tare. Nayi kokari in tanqwara zuciyata na kasa....amma alhamdulillahi yanzu na samu sauki daga duk wani duhu da kullaci dake cikin raina". Ranar sai ta zama ranar reunion ta soyayyar uwa da 'yar ta. Kusan kwanan zaune suka yi a dakin Sa'ade, tana bata labarin rayuwar data yi tare da mahaifin ta a garin Tsanyawa tun tana karama har girmanta, da rayuwar wahalar data yi a hannun inna Laure da kuma yadda mutuwar mahaifinta ta kasance, har zuwa yadda suka yi suka zo Askira ita da Baba Saleh. Sai ga Fulani Bilkisu tana share hawaye, "nikuma na zo na yi shekaru shidda ina cuzguna miki, a matsayi na na mahaifiyar data haife ki. Bayan a lokacin ne ya kamata ki ji dadi kamar kowanne da a hannun uwarsa...don Allah Sa'adatu ki yafe mini". "Na yafe miki Fulani ban taba rike ki ba, kullum ina gayawa raina ne kina da hujjar ki, haka kawai uwa bazata ki dan ta ba, Allah ya yafe mana bakidaya". Tun daga ranar, mu'amalar Fulani Bilkisu da diyar ta Sa'ade ya canza, ta cire mata takunkumin fita, ta bata damar shiga ko'ina take so cikin masarauta, bata ki ba don gaskiya ta fito gaban kishiyoyin ta a yanzu cewa Sa'ade 'yar ta ce, tunda ta san ba shegiya bace da uban ta. Ta ja ta a jiki har fiye da kima, idan zata shirya abincin mai Askira kasancewar da kansu suke masa abinci sai ta kirata sun shiga kicin tare, tana yi tana mata bayanin yadda ake komai, anan Sa'ade ta koyi girkin sarauta iri-iri dana zamani, kasancewar Fulani Bilkisu kwararriyar kuku. Ta kuma dinga koyawa Sa'adatu tsaftar jiki data muhalli da amfani da turarukan Borno a jiki da tufafin ta. Duk da ta bawa Sa'ade damar shiga koina cikin masarauta Sa'ade bata yawon, kullum tana sassan su ko dakin Fulani, ko kuma suna kicin suna girkin Askirama idan ita ce da girki. Hatta gashin kan Sa'ade Fulani da kanta ke zama ta gyara mata yanzu, gyara na masu kwarewa akan kula da gashi, wata irin shaquwa suke yi cikin 'yan watannin nan wadda basu taba yin ta a shekara shidda da suka yi tare ba, ta yadda har Fulani ta soma zullumin zuwan ranar tafiyar Sa'ade makaranta Abuja. Maimartaba ya fi kowa jin dadin wannan sauyi da ya ke gani a tattare da Bilkisu da 'yar ta Sa'adatu, 'yar da yake jin kamar shi ya haifeta saboda son da yake wa mahaifiyar ta. Jin dadin hakan yasa ya hada musu tafiya umrah karshen wannan watan don dai su kara shaquwa da juna ba idon kowa tare dasu, amma dole tareda Fanna zasu tafi sabida kula da hidimar Fulani. A saudiyyah ba abinda Fulani Bilkisu ke roko a wurin Ubangiji sai miji nagari ga Sa'adatun ta, wanda zai rike mata ita amana ya rike maraicin ta, wanda ba zai taba duban asalin ta ya wulakantata a kan sa ba. Wanda zai zame mata miji kuma uba sannan Yayan da bata da shi a kafatanin rayuwarta. Ta kuma sakankance cewa an amshi rokon ta, don wannan shine ladabin addu'a. Ba son tafiyar Sa'ade jamia'ar Turkawa take ba, amma ta yarda da hujjojin Maimartaba, na cewa gara Sa'ade tayi karatu kafin Allah ya zaba mata mijin aure. Karatun zai zamo gata kuma majingina a agareta ranar da babu su. Suna dawowa suka tarar da sakamakon su Sa'ade ya fito, Mai Askira da kansa ya kira Yarima ya gaya masa kowacece Sa'ade, gaskiyar ya gaya masa cewa 'yar Bilkisu ce. Ya damka masa komai na alhakin nemo mata makaranta da daura masa dukkan nauyin hidimar karatun ta. Ya kuma gaya masa a gidansa zata zauna ba a hostel ba. Wata irin zufa ce ta soma ketowa Yarima ko mu ce Chiroman Askira. A tsarin rayuwar su shi da matar sa, ko kuda basa so ya gifta a tsakanin su balle dan mutum ya zauna a cikin su. An tarbiyyance su da rashin yin musu ga magabatan su, an raine su a bisa bin umarnin na gaba, balle Mai Askira gabadaya. Don haka amsar sa ita ce kawai "toh" amma a ransa ya ce kora da hali kawai zai sa yarinyar ta bar masa gidan sa. To amma kuma Maimartaba ya ce 'yar Fulani Bilkisu ce ta cikin ta, matar da duk fadin gidan su in ka dauke mahaifiyarsa ba wadda yake gani da mutunci kamar ta, ba wadda ke kula da al'amarin sa dana matar sa kamar ta. Anya zai iya wulakanta jinin ta? Babbar damuwarsa Sultana bazata taba amincewa ba musamman sabida yadda take shaye-shayen ta babu takura, ta dauka bai sani ba, amma kallon ta kawai yake, duk abinda take ciki ya sani, baya magana ne don ya san shima da nasa guntun kashin a katara. Aka ce wai in ka ji ma'aurata masu ha'intar juna suna zaman lafiya to tabbata daya na ha'intar daya, babu yadda dayan zai yi ya hana, kada nashi asirin ya tonu. Wannan shine tsakanin Yarima Sageer da matar sa Aisha-Sultana. **** Babu yadda zai yi, haka yasa neman admission din Sa'ade a gaba a washegari a matsayin first thing da ya shiga ofis ya zauna, takardun ta duk sun yi kyau. Ya tsurawa sunan ido.... SA'ADATU HASHIM ASKIRA. Hatta course din ma nasa ta dauka......Pure and Applied Chemistry. "Does she know me?" Ya tambayi kansa cikin mamaki. Salon karatun ma mai Askira ya ce ni zan koya mata??? Tsaki yayi ya ture takardun gefe ya janyo na wasu, a lokacin da Dr. Ziyad ya turo kofar ya shigo dauke da sallama a bakin sa. "Wata hot baby na samo yanzunnan daga zuwa na Millenium Park, akwai abubuwa, kayi maza ka gama mu bar ofis dinnan". Tsaki yayi ya ce "kai baka san halin da nake ciki ba, wata yarinya za'a kawomin riko daga gida, Allah ya sa ba spy mai martaba zai kawo min ba, ko wani ya kai gulmata ban sani ba, ka san a ko'ina yana da jama'a musamman nan Abuja" ya fada kyakkyawar fuskarsa dauke da damuwa tsantsa. Dr. Ziyad yace "i don't think so. How old is she?" "JAMBITE ce fa" "whao!" Inji Dr. Ziyad. Kace sweet 16 za'a kawo mana kawai, yo meye abin damuwa banda mu dinga kwasar rabon mu kawai muna saya mata pizza muna cika mata aljihu? Gida na is very quite and secret ko Sultana bazata san muna kwasar gara ba". Wata muguwar harara Yarima Sageer ya zabga masa, ya tsartar da miyau da sauri. "Allah ya sawwake Allah ya tsare ni, ni ba dan akuya bane, ina dai neman matan bisa titi amma ban da na mutunci balle wadda ta fito daga gidan mu, daga gidan mun ma daga hannun mahaifi na, 'yar matar mahaifi na mai yawan karamci a gareni. Allah ya kiyaye! Iskancin nawa mai limit ne, and i'm hoping watarana in bari gabadaya". Dr. Ziyad ya kyabe baki tareda mikewa tsaye yana dariya yace "kai din? Na yarda bazaka iya neman ta gidan ku ba, ko don kada asirin ka ya tonu, amma bazaka iya barin mata ba i swear ...." Yarima ya dauki mukullan dake bisa teburin sa ya jefe shi dasu, Dr. Ziyad ya dafe keya ya fice da gudu yana masa dariyar data kara masa takaici kan wanda yake ciki, na yarinyar da za'a turo masa babu gaira babu dalili. Cikin sati daya ya gamawa Sa'ade duk shirye-shiryen ta, an dauke ta a NTNU a tsangayar da yake koyarwa (B. Sc Pure and Applied Chemistry). Ya aikawa Askirama admission letter din ta ta email. Abinda ke gabansa yanzu shine ta yadda zai tunkari Sulatana da maganar. Amma abin mamaki da ya koma gida da yamma, ya tarar ta riga shi dawowa, ta shawo ta yi mankas tana kwance dai-dai a tsakiyar falo. Haka ya tsallake ta yana tsaki ya wuce dakin sa ya sunce ya shiga wanka. Yana fitowa ya shiga kitchen don neman abinda zai ci, ya bude firji, abin takaici babu komai sai Giya nau'i nau'i, yanzu Sultana ta daina shakkar ya san shaye-shayen ta, kai tsaye take komai don ta ga baya daga ido balle ya nuna ya san tana yi. Wani mugun tsaki ya saki ya rufe firinjin da karfi, yanzu in yarinyar nan ta zo ta gani fa? Mai Askira yace rana ita yau za'a kawo ta tare da kayan ta su gyara mata daki. Ji yayi yunwar da yake ji ta kama gaban ta, da sauri ya fito ya sa kafa ya shuri Sultana da karfi. Ta bude idanu jazur dasu, ta sauke su a kan shi, dama gasu tun asali kamar na mage (brown eyes). A fusace yace "ki tashi ki kwashe abubuwan da kika cika min firji dasu, we're having a guest from Askira, and she's going to stay with us for years, so mind yourself else.....duk abinda ya biyo baya ba ruwa na". Sultana tayi mici-mici da ido "bakuwa? A gidannan? Daga Askira? To ban yarda ba" ya galla mata harara yana hango wani irin muni a tare da ita da bai taba gani ba wanda yake bayyana in ta sha giya "sai ki kira maimartaba ki gaya masa" ya jefa mata wayar hannun sa. Har dare suna fafatawa, ta dage sai ya kira Babansa ya ce bata yarda ba, shi kuma yace ba tarbiyyar da aka yi musu kenan ba but she's free to call him herself. "To ko dai aure suka yi maka shine za'a fake da karatu don nasan mamanka bata so na!" Sultana ta fada cikin kuka. Shi don mamakin kalamanta ma dariya yayi, wai aure! Wa ya isa yayi masa aure ba da yardarsa ba? Besides, su gidan su ba'a auren dole. Sannan ya gama aure a rayuwar sa ba zai taba yin mata biyu ba duk da kasancewarsa basarake. Tashi yayi ya dau motar sa ya bar gidan zuwa inda ya tabbatar za'a faranta masa rai, yau ranar kwata-kwata a birkice ta zo masa. He's upset, sannan wannan mahaukaciyar Sultanar ta kara masa bacin rai. Ai kuwa ya samu Dr. Ziyad ya dauko musu baby din da ya gaya masa sun hadu a millenium park, nan ya manta da zancen Sa'ade da Maimartaba ya shantake acan har karfe daya na dare. Sanda ya shigo gida ya tadda Sultana ta baje kwalabe sun fi biyar duk tayi emptying din su. Ta koma zukar marijiuana cikin tsumma, gashin kanta a birkice, gabadaya sai ta zame masa kamar motsatsiyar tsohuwa, ya dinga tambayar kansa tun farko me ya gani a tare da ita ya yarda ya daukota har kasar sa ya aureta??? Tsaki yayi ya tsallake ta ya wuce dakin sa. Wanka ya fara yi ya tsaftace kansa, yana jin wani abu na tsirga masa a zuci da gangar jiki, wanda yafi kama da jin kunyar Ubangiji. Wankan janabar da bata aure ba alhalin ga matar sunnar ya tsallake tana nata sabon Allahn. Wannan wace irin rayuwa ce??? Idanun sa a rufe ya hau gadon sa ya kwanta. Addu'a yake cikin ransa in yana da rabon dainawa kafin ya mutu, Allah yasa ya daina......!!! **** Tunda Askirama da kansa ya shigo ya ce da Fulani gobe ne tafiyar Sa'ade gidan Yarima jikin ta yake a sanyaye, don bata san wane irin riko da karba Sultana zata yi mata ba, tunda ita ba jinin gidan bace, duk da su Humaira suna fadin bata da matsala. Amma ga Sa'aden sai murna take, very enthusiastic ga tafiya makaranta, bata tunanin komai da ya danganci abinda zata ta tarar banda kasancewa dalibar Turkish University. Don a daren Fulani ta zaunar da ita a gabanta. Don ta ga murnar tata har ta so ta yi yawa, tun azahar ta kammala daure kayanta tsaf. Kadan ta bari wadanda bata cika amfani dasu ba. Allah-Allah take garin Allah ya waye ta kama hanyar birnin tarayyah. "Sa'adatu bani hankalin ki nan" inji Fulani. Ta dago fararen idanun ta ta dubeta, wadanda a lokuta da dama suke wani irin sheki da walainiya (sparkling eyes) wanda shine babban sirrin kyawun Sa'adatun. Fulani tace. "Na ga sai rawar kai kike, ki kama kan ki, gidan Yarima zaki je, sannan matarsa asali ba musulma bace, sannan ba bahaushiya bace, don haka dole ki kula da tarbiyyar kan ki da kan ki, ki maida hankali akan abinda ya kai ki kawai, ba ruwan ki da rayuwar su, ban da sa-ido, banda daukar zance, banda shiga shirgin da ba'a sanya ki ba. Tsakanin ki da su yi na yi bari na bari. Ki dinga taimaka mata da girki da ayyukan gida tunda ita ma'aikaciya ce. Na hore ki da kama mutuncin kanki, ko ya kike da namiji kada ki yarda ki kebe da shi, Ko hannun ki namiji ya taba cikin shege zaki yi, kin ji na gaya miki?" Sa'ade ta gyada kai cikin fahimta, sannan ta dan zaro ido ta ce "to ai gidan ba maza ko?" Fulani ta hana kan ta yin dariya sabida yadda muryar Sa'ade ta koma razana zallah. Tace "shi mai gidan ma ai namiji ne, kuma ba muharramin ki bane ba, don haka matsayin uba yake a gare ki, ki kama kan ki, ki rike mutuncin ki. Allah yayi miki albarka ya saka albarka a neman ilmin ki. Ga waya karama na saya miki duk halin da kike ciki ni zaki kira ki gaya min, ban yarda ki bawa kowa lambar ki ba". Sa'ade ta gyada kai cikin murna a lokaci guda tana mika hannu don karbar karamar wayar siemens da Fulani ke mika mata. Kawai sai ta ji Fulani ta hada da hannun ta ta janyota jikin ta ta rungumeta... "Ki yafe min Sa'adatu don Allah ki yafe mini..." "ni baki yi min komai ba Fulani, na yafe miki abinda na sani da wanda ban sani ba. Nima ki yafe mini!" Sallamar tasu is very emotional da ta fiddo hawaye daga idanun kowaccen su. Washegari daya daga cikin direbobin gidan karkashin rakiyar kuyangin Fulani Bilkisu mata guda biyu maimartaba yasa suka dauki Sa'ade zuwa Abuja a daya daga cikin motocin 'Askira Emirate'. Tun asussuba suka kama hanya basu isa Abuja ba sai karfe takwas na dare. Inda Allah ya taimake su shine sun yo guzurin abinci da abin sha wadatacce wanda har suka iso Abuja sallah ce kawai take tsayar dasu a gidajen mai na gefen hanya. Suna fitowa daga mota Sa'ade tayi mika....ta ware ido tana kallon kyawawan gidajen estate din malamai na NTNU kamar kana kasar Istanbul. Ashe ba ginin masarauta kadai ne gini mai kyau ba, ginin Turkawa ma abu ne mai matukar kyau da daukar hankali. Ita dai tunda take bata taba ganin kananan gidaje masu tsari da kyawun zubin wadannan ba, ko ya mutanen cikin gidan suke? Koda yake Fulani ta ce turawa ne, ai sai turawan.... "wannan gida wanke hannu ka taba". Sa'ade ta ce cikin ranta. Daidai lokacin da daya daga cikin kuyangin da suka zo tare ta yi mata magana ganin ta shagala a kallon gidan "ranki ya dade mu karasa daga ciki ko?" Suka isa ga entrance na gidan suka hau danna kararrawa, suka yi har suka gaji ba'a bude ba, a lokacin Sultana na kwance a falo ta sha ta kai mata karo, tun misalin karfe 6 na yamma take kwance har a lokacin bata san inda kanta yake ba. Allah ya kawo Uche (kukun gidan) zai shiga da cefane, kasancewar yana da mukullin gidan ta kofar kicin ta baya. "Hey! What do you want here?" Ya tambaye su. Aka rasa mai amsawa don 'yan rakiyar Sa'aden basa jin turanci, sai itace ta gayamasa daga Askira suke, sun zo wajen masu gidan ne. Ya tambayeta ko Dr. Sageer ya san da zuwan su? Ta ce "ya sani" a takaice, domin bata da tabbacin hakan, Allah-Allah take ta sanya hakarkarinta akan shimfida sabida gajiyar zaman mota data kwaso. Wayar sa ya dauko ya kira wata lamba yayi magana cikin harshen turanci, ya kalle su, sannan ya maida wayar aljihun sa ya ce su biyo shi. Ta baya suka shiga ta kofar kitchen suka kurda zuwa falon gidan. Nan Sa'ade taga mace jajawur kwance magashiyyan a dandaryar tayals, gashin kanta ya baje ya rufe fuskarta, Uche bai ko dubi inda take ba ya bude wani daki yace su shiga nan ne dakin bakuwar. Sannan ya ce su bashi minti 15 zai kawo musu abinci. Kafinnan ga ruwa da lemo su sha. Tsaruwar dakin ya burge Sa'ade, duk da bai kai dakin ta na Askira ba amma daki ne mai tsari irin na turawa babu tarkace sam a cikin sa. Gado ta fada tana ce da Fariha daya daga cikin 'yan rakiyar ta in an kawo abincin ta tashe ta tunda ita tana fashin sallah, in taci abinci sannan tayi wanka. Uche ya kawo musu abinci mai rai da motsi suka ci suka koshi, sannan Sa'ade ta fara yin wanka, ta shirya cikin kayan barci tabi lafiyar gado bayan ta kure iyakwandishan, sukuma kuyangin suka kwanta daga kasa. Ba wanda ya nemesu har washegari. Da asubah suka kama hanyar Maiduguri lokacin Sa'ade tayi sallah ta koma barci. **** Sai karfe takwas na safe Sa'ade ta tashi, ta duba babu 'yan rakiyarta, sai ta tuna sun ce da asubah zasu kama hanya, tsaki tayi tana mitar shine ko su tashe ta su yi sallama. Wanka ta fara yi, kafin ta ji cikin ta yana kiran chiroma, a gurguje ta shirya tana fadin bari in bi su kitchen din tunda sun manta da mutum a gidan. Tana kokarin fita bayan ta murda kofar dakin taji ta yi karo da mutum....Wani irin sassanyar kamshi mai huda zuciya, coupled with his gait and geniusness, beautiful elegant face wadda babu far'a sam a cikin ta. A kiyasce yadda ta kimanta shekarunsa zasu kai talatin da biyar zuwa da shidda. Alamu sun gama nuna ya gama samun duk wasu achievements na rayuwar dan adam. Kama daga ilmi na addini dana zamani, sannan ya zauna da kafafun sa ya gama kama kasa. Da farko ta dauka Askirama ne a gabanta (mai martaba) sabida tsabar kamannin su, saidai data lura sosai sai ta fahimci wannan akwai tarin kuruciya da hasken boko a tare da shi, bi ma'ana yaro ne mai jini a jika, babu ko tsillin furfura a kwantaccen sajensa zuwa gashin kansa, wanda ya kwanta luf a gefen fuskarsa. A duniya bata taba katari da mutum mai cikar kamala da kyawun suffa kamar sa ba, ga wani irin kwarjini da ya banbanta shi da sauran maza. Sarauta ta gama bayyana kanta a komai nasa. His lips are so luscious kamar ana basu extra kulawa, fatar jikin sa fresh kamar haifafen kasar Morocco. Sai ta ga kamar ta taba ganin sa, somewhere else da bazata iya tunawa ba. Yadda ta saki ido, hanci da baki tana kallonsa shi ya fi komai bashi haushi, amma da yayi kokarin yin magana sai ya samu halshen sa da kasa motsawa. Suka dubi juna directly cikin ido yayin da wani gravity mai karfi ya fizgi ido da zuciyar kowannen su. Alal hakikah a rayuwar Dr. Sageer Yusuf Askira, bai taba ganin macen da ta tabo wani sashe na kololuwar zuciyar sa irin wannan da ke gaban sa ba. As professional as he is akan sha'anin mata, ya fada a zuciyar sa cikin 'yan dakikan da suke tsaye..... "ta mallaki komai da yake mafarki a diya mace". Amma kuma nan da nan mulkin sa da izzarsa ta Yariman Askira ta zo ta shafe komai, daga ganin yarinya baka san komai akan ta ba, sannan wadda ta fito daga gidan ku? Tuni ya mallaki kansa, fuska a daure ya ce da ita "come for breakfast". Ya juya ya fita, ba tareda ya kara wata kalma ba. Komawa ta yi ta dauko mayafin ta ta yane kanta akan doguwar abayar dake jikinta ruwan hanta, da sallama ta shigo falon, can bisa dining ta hange su shida matar sa. Gaskiyar Fulani ashe...baturiya tsantsa. Ai kuwa sun dace duk da shi baki ne kamar Askirama. Sa'ade ta fada a zuciyar ta. Sultana ta daga ido tana kallon Sa'ade, kallo daya Yarima yayi mata ya maida kai ga cin abincin sa. A take ta ji wani irin kishi ya soke ta, wannan kyakkyawar yarinyar za'a dauko a ajiye mata a gida? Ai da sake wai an bawa mai kaza kai. Ta dauke kai daga kallon Sa'ade ta mayar kan abincin ta. Har kasa ta tsugunnan tana gaishe su, daga matar har mijin babu wanda ya amsa mata. Wannan abu ya sosa mata rai. Daga bisani Yarima ya mike yana goge bakinsa da tissue. "If you finish meet me outside" ya ce da Sa'ade. Matar ta tambayeshi inda zai kai ta? Yace tare zasu dinga shiga makaranta. Har zata yi magana, sai kuma ta ja bakin ta tayi shiru, itama ta mike ta bi bayan sa. Haka jiki ba kwari ta ja jiki zuwa tebir din cin abincin, ta zuba abinda zata iya ci, duk yunwar data ke ji sai taji ta rasa appetite din ta, sabida irin tarbar da masu gidan suka yi mata. A can kofar gida rigima ake tsakanin Sultana da Yarima, ta ce ita sam bata yarda su dinga tafiya tare ba, ko dai ya daukar mata direba ko ta dinga tafiya da kanta tunda babu nisa zuwa cikin makaranta. Ya san halin nacin Sultana in bai yi mata abinda take so ba bazata barshi ya fita ba, don haka yace zai daukar mata direba amma for the mean time zasu dinga tafiya tare kafin a samu direban kuma ta gama registration dinta. Daga bisani ya sassauta murya "you want to me into trouble with my father? Do you know how much he loves this girl?" Sultana tayi narai - narai da ido, sai ya sunkuya ya sumbaci bakin ta cikin lallashi. "Ki kwantar da hankalin ki ni babu wata bakar mace a gabana, look at you me zan nema a wurin sauran mata? I just want to live in peace with my father shiyasa na karbi yarinyar kuma da an yi hutu zan maida ita Askira sai an koma makaranta". Dai-dai lokacin da Sa'ade ta fito ta gansu a haka kamar zasu manne cikin jikin juna, sai ta samu kanta da jin kunya tayi maza ta juya don bata taba ganin namiji da mace so close hakan ba. Sultana ta harareta sannan ta ja da baya ta budewa Yarima kofa shikuma ya budewa Sa'ade kofar gefensa ya ce ta shigo. Don haushi bata iya ta tsaya ta ga fitar su ba ta juya ta dauki tata motar don tafiya nata wajen aikin. Tana tafe tana tunanin irin takurawar da zaman Sa'ade zai yi mata don tun shekaranjiya Yarima ya kwashe duk wata kwalbar giya dake cikin gidan ya zubar. Jiya sai Bar ta je ta sha abinda ta dade rabon ta da yi. Suna shiga cikin makaranta Sa'ade ta bude ido tana shan kallon NTNU (Nigerian Turkish Nile University). Its various faculties and administrative offices...the equisite lecture halls and different departments. Wani shauki na diban ta idan ta tuna ta zama cikakkiyar dalibar NTNU yanzu. Haduwar ofis din YARIMA Sageer Yusuf Askira ya tafi da ita, ko'ina sai raba da sanyi da kamshi mai sanyi. Sai da ta jira ya gama abinda zaiyi sannan ya hadata da assistant dinsa ya taimaka mata ta fara registration. Cikin kwana na uku ta gama, ta zama cikakkiyar dalibar tsangayar (Pure and Appplied Chemistry). Ranar litinin zata fara daukar lacca. **** Yau asabar, daga matar har mijin duk suna gida, Sa'ade in ta gansu a falo bata fitowa tayi ta zama a dakin ta kenan, ko abinci bata yarda ta zauna ci tare dasu sai ta jira sun gama sun tashi, sannan zata zo ta zuba ta ci ta kwashe kayan ta kai kicin, Uche ya karba ya wanke ya dora wani. Saidai ita sam ba jin dadin abincin gidan take ba sabida abincin turawa ne ake yi kullum, wani ma bata san da me aka sarrafashi ba ko sunan sa, ga kaguwa (shrimps) da ake zubawa a kowanne girki, don haka yau da bazasu je cikin makaranta ba kasancewar hutun karshen mako ne sai tace da Uche kada ya sanya abincin su da ita, she want to cook for herself (tana so ta dafa da kanta). Uche ya bata duk abinda zata bukata don ta ce tuwon acca zata yi miyar egusi. Nan da nan ta hau girkin ta cikin kula da takatsan-tsan da kuma kwarewa. A can falo Sultana ke tambayar Yarima yaya zacen direvan da ya ce zai daukarwa Sa'adatu? "Ana nan ana bincikawa", yace da ita, a lokaci guda yana cigaba da marking takardun dalibansa ba tareda ya bata hankalin sa ba. Ya rasa me yarinyar ta tare mata, bata da zance sai na Sa'adatu a tsayin satinnan bakidaya. Shikuma a yadda ya lura sam yarinyar bata da matsala, sannan bata takura musu, bata sa musu ido kamar yadda suka yi tsammani, tana da tsananin kamun kai da gudun zuciya. Sannan rayuwar ta is very simple. Wani unique kamshin girki da bai saba ji ba ya bakunci hancin sa, dama kuma yunwa yake ji, ya kwalawa Uche kira. Ya fito da sauri har yana tuntube. Daidai lokacin da Sa'ade ta zo ta wuce su da food flask biyu a hannun ta na tuwo da miya da plate da cokali tayi dakin ta. Ya dan kalle ta ta gefen ido yadda bazaka taba zaton ya kalletan ba yace "Uche, me kake girkawa haka?" "Ba ni bane Oga, Sa'adu ne" yayi murmushi jin sunan da ya kira Sa'ade dashi yace "me ta girka?" "Tuwo ne Oga, with egusi soup" "ok idan da saura debo ka kawo min" "ya kwashe duka ya tafi daki" "saboda rowa ko saboda me?" Uche yayi dariya, "Oga akwai wanda ta diba min, lemme bring it" "thank you Uche". Uche yaje ya kawo abincin a kyakkyawan flasks a rufe ya aza bisa dining. Sultana na daga kwance tana kallon Yarima yana cin tuwon nan zuciyarta na tafasa, bata isa kuma tayi magana ba yace zai bar gidan, don yace duk renakun weekends baya son korafi, in ta yi masa complain ko guda daya ne zai bar mata gidan ya tafi gun Dr. Ziyad. Ita kuma sam bata son alaqarsa da Ziyad don bashi da aure kuma kullum tana ganin shi yana kwashe-kwashen mata a motar sa zuwa gidan sa. Shiyasa take making sure bata yi abinda baya so ba a kowanne weekend don dai su zauna tare. Bai san yayi missing cimar gida ba sai yau, sosai ya ji dadin tuwon, da izzar shi zata barshi ai da yace da daddare ma ta kara yi masa, musamman mai miyar ganyen Ugu, yana son ganyen sosai. Shikuma Uche tunda ya lura Ogan sa na son tuwo sai yake kokarin yi masa, amma sam baya kyau da dandano kamar na Sa'ade don bai kware ba, a wurin Sa'ade ya koya don ya ce mata ta koya masa ya dinga yiwa Ogansa. To amma kullum yayi haka yake dauko shi Oga ya yi loma daya ya ajiye, ko yace ya dafa masa wani abun. Don haka Uche yake mata wayo, kullum zata dora girki sai ya ce ta dora da dan yawa, shima yana so, tana bada baya zai shirya abincin ya kaiwa Yarima, ya gaya masa Sa'adu ne ya girka, ya rasa ya aka yi Uche ya dago shi kan yana son cin girkin Sa'adatu. Duk ranar da bata yi girkin ba ta wuni a makaranta ne yake cin na Uche. Sultana ta shigo gida yau da sabon bed-side fridge wanda babu a dakin ta. Washegari kuma data dawo aiki ta dawo da manya-manyan kwalaye. Tana kokarin fito dasu daga mota direban da Yarima ya dauka ya sauke Sa'ade. Ganin tana kiciniyar ciccibar kwalayen Sa'ade ta karasa da sauri ta ce. "Can i help you aunty?" "No, thank you" In ji Sultana. Ta ciccibi manyan kwalayen ta daya kan daya tayi cikin gida. **** Tun daga ranar Sultana ta daina zuwa Bar ta koma shaye-shayen ta a dakin ta, a zuciyar ta tana tsinewa Sa'adatu, ita da gidanta an zo an takura ta. Bata sha a weekend sabida Yarima yana gida, da yamma kuma sanda ta dawo shima ya dawo, don haka sai ta tsiri kulle kanta da zarar ta dawo aiki bata kara fitowa sai lokacin barcin su. Dr. Sageer yana lura da sabon sauyin nata, ya rasa me take kulle kanta tayi a daki, bugun duniya in zai yi bazata bude ba sai ta ga damar fitowa wajen sha biyun dare. Tuni ya harbo jirgin ta. Rannan ya faki idon ta ya dauke safayan mukullin. Tana tsaka da shan whisky ya bude kofar dakin ya shigo ya mayar ya rufe. Kayan barci ne na RALPH LAUREN farare sol a jikin sa. He never looked so handsome in her eyes like today. Ya tsaya a kanta ya harde hannayensa a kirji yana kallon ta with furious eyes... "Sultana why? Ba na hana ki shan giya ba? Ko syrup ban hana ki sha ba? Ban gaya miki haramun ne a muslunci ba? Idan da kin yi na kyale ki yanzu kin sani ba mu kadai bane a gidannan, a slight mistake will probably go to my father, har yanzu jiki na na bani spy ce ya sanya mun. Ki yi a hankali idan ba kina son janyo min bala'i ba". Ta daga rinannun idanun ta ta dube shi, cikin maye tace "I....i cannot live without beer, a haka ka ganni ka aure ni, kai ma ka sani bazan taba iya barin giya ba". "Sai ki zaba ko aure na ko giya, tunda na sanar dake addinina ya haramta kika ce kin amince zaki daina, tunda kika fara aiki na san kin koma shan beer, sallah kin dade da daina ta, na sa miki ido ne don in ga iya gudun ruwan ki, and now na lura duk musluncin ki ba na gaskiya bane kin dade da daina sallah. Ni kuma bazan zauna da kafira ba". Ya fadi yana watso kwalaben dake jere cikin firji, ya hada su da bango ji kake taratsatsa! "Kika sake shigo min da wannan kazantar gida, zaki ga yadda zamu kwashe, i'm not that fool and i respect my religion......". Wani wulakantaccen kallo Sultana tayi masa....tace "addini! Kai nan har kana da bakin cewa ka san addini? Addinin naka ne ya baka damar yin adultery? Tunda na san ka na san you are an adultrer wanda baya iya rayuwa sai da mata. Na dauka in mun yi aure shikenan zaka bari, gara ni giya da kayan maye kawai nake sha amma bana zina, balle da aure na". Tamkar ta watsa masa garwashin wuta haka fuskarsa ta koma, bai taba sanin ta san wannan side din nashi ba, abinda bai sani ba shine tana bibiyar wayar sa. Sultana ta lura da efffect din kalamanta akan sa, sai ta yi wani miskilin murmushi "tunda na barka kana zina, ban taba takura maka ba, sai ka bar ni in sha giya, ko wannan yarinyar ta bar min gida......" ta mike tana layi tayi toilet ta bar shi a wajen. **** Kwana biyu basa magana da juna, abinda basu taba yi ba a rayuwar auren su, wani abu da Sultana ta tsiro da shi don ta baiwa Yarima haushi shine ta daina boye shan giyar da kayan mayen ta, nan falo take zama ta baje tana abin ta. A ranta ta kudure duk ranar da ya gayawa iyayensa tana shan giya itama tace musu yana neman mata. Gara ma yayi hakuri su ci gaba da zaman su yadda suke yin sa, wata figigiyar yarinya bakauyiya bata isa ta canza mata rayuwa ba. Sa'ade ta shigo falon da sallama, misalin karfe shidda na yamma, direbanta Salis ya riko mata manyan littafan chemistry har zuwa kofar shiga falo, ya mika mata tayi masa godiya. Tana kokarin shiga Yarima na parking. Ta juya suka hada ido ta cikin gilashin motar sa, sai ya yafito ta, yace "Sa'adatu help me with these files" ta karasa cikin nutsuwa ta karba, shi kuma ya dauko daurin answer sheets na daliban sa ya bi bayan ta suka shiga falon tare. Nan idanun sa suka yi kyakkyawan gani. Kamewa yayi a inda yake tsaye, a lokacin ta kai bottle na whisky bakin ta, ta gefen idon sa ya saci kallon Sa'ade don ganin reaction din ta, sai ya ga babu wani sauyi a tare da ita, ga dukkan alamu bata san menene a hannun Sultana ba, ta dauka just lemo ne. Sannu da gida kawai ta yiwa Sultana ta ajiye masa takardunsa bisa centre table, daga nan bata kara kallon su ba tayi shigewar ta daki. Yayi catching breadth din sa da karfi tana bada baya ya wankawa Sultana mari, ya sake wanka mata, sai da ta nemi jin ta da ganin ta na wucin gadi ta rasa. Tana farfadowa ta kai hannu zata rama ya kama hannun ya murde shi. Ta saki karar data kai kunnen Sa'ade. Har zata fito da gudu ta tuna hudubar Fulani (ba ruwan ki da shiga shirgin da ba'a sanya ki ba) tunda dai ta san su biyu ta bar su. Kwanan tashin hankali aka yi tsakanin ma'auratan, irin wanda bai taba faruwa tsakanin su ba, zagi ta uwa ta uba babu irin wanda Sultana bata yi wa Dr. Sageer ba, har tace duk da kasancewarta kafira kamar yadda yake kiranta bata taba zina ba shi ya koya mata, shi yayi disvirgining din ta, musluncin sa bai kare shi da komai ba, fasiqi mara tsoron Allah. Gara ita giya kawai take sha. Duka wannan a kunnen Sa'ade, wadda hayaniyar su ta hanata barci, ta tsaya jikin kofar dakin ta sai shivering take (karkarwa). Bata taba jin abinda ya kada ta ya gigitata irin wannan ba, gidan masu zina da shan giya aka kawo ta! Uncle Yarima da take gani da matukar girma da kima shine mai yin zinar? Ko dai Sultana karya take yi? Abinda ta gani tana sha dazu shine giyar kenan kuma shi ya hada fadan? Tana jiyo kukan Sultana da alama marin ta ya kara yi, jikin ta na rawa ta dauki waya ta kira Fulani, hawayena zuba mata tace "Fulani! Ni dai gobe a zo a dauke ni bazan iya zama a gidannan ba, zan koma hostel" cikin muryar kwantar da hankali Fulani tace "take it easy....gaya min me ya faru? Ana miki wani abu da ba kya so ne?" Cikin kuka tace "no, Uncle Yarima is very nice to me....amma yana dukan matar sa....gata can sai ihu take.....kuma ta ce shi mazinaci ne...." ba shiri Fulani ta dauke wayar daga kunnen ta ta juya, sai idon ta cikin na Askirama da ke gefen ta da alama shima sauraron wayar yake yi don ta manta a (hands-free) take. Yanayin da ta ga fuskar sa a ciki yasa ta jin kamar ta shiga cikin wayar ta shaqe Sa'ade har sai ta daina numfashi. "Wallahi maganar Sa'ade shirme ce ni na tabbata....". Fulani ta fada muryar ta na rawa, kwalla cike da idon ta. Daga taimako Sa'ade zata baro musu tashin hankali da yake ita butulu ce, ina ruwan ta da abinda ke faruwa tsakanin Yarima da matar sa? Bayan ta gargadeta? Sai ta tuna Sa'aden bata san tana turakar Askirama ba, kuma ita ta bata damar duk halin da take ciki ko karfe nawa ne ta kira ta ta gaya mata. "Ba shirme bace Bilkisu..... he has this taboo since childhoood". Ya fada muryar sa abin tausayi. Har yaran bayi yake raping...na dauka ya bari, na dauka girma ya sa ya nutsu, na dauka aure ya canza shi...ashe i'm mistaken. To aikin zai bari ya dawo gida kusa da ni kawai ya karbi sarautar gidan su, in cika masa gida da mata da kwarkwara tunda hakan yake so.....da raina da lafiya ta bazan bar shi ya karasa rayuwar sa a haka ba........". The way Mai Askira ke magana ya taba zuciyar Bilkisu, bata taba ganin sa cikin wannan sad mood din ba. A muryarsa da fuskarsa bakin ciki ne zallah. Ya kare zancen sa da cewa "zan raba Sa'adatu da gidan sa, tsoro na Allah yanzu tsoro na kada itama ya taba ta......" "Haba-haba Askirama! Kada bacin rai ya kai ku ga yi masa mugun fata, ni na tabbata ko Yarima na neman mata bazai nemi na cikin gida ba balle Sa'adatu kanwar sa, don Allah a kyautata masa zato, kada a raba shi da aikin sa he is very young da karbar sarauta yanzu, sannan kaima in ka zauna a gida me zaka yi? Da cikar lafiyar ka da shekarun da basu kai 70 ba. A yi masa hakuri ayi masa addu'a, ita ce kawai mafita. Kuma daga Sa'ade ta fadi abu ai bai kamata mu yarda ba tunda bamu gani da idon mu ba". Mai Askira yayi murmushi mai ciwo "baki san Yarima ba!" Da kyar, da lallashi da ban baki Fulani ta ciwo fushin maimartaba ya fasa cewa Yarima Sageer ya dawo gida, amma ya ce dole zai dauki mataki. Shi ya gama amincewa Sa'ade ba karya take ba, ta fadi abinda ta gani ne da abinda ta ji tabbas. Koda ya tura Sa'ade gidan Yarima yana da dalilin sa, gashi tun ba'a je koina ba zuwan ta ya sa yanzu ya san halin da Yarima yake ciki. **** Da asubah Fulani ta koma daki ta kira Sa'ade, wadda ta kwana zungurgur a bakin kofa, ta dade bata ji ma'auratan sun gama fadan nasu ba, ta ji abubuwa da yawa da suka razanata, Sultana ta dage in ya takura mata akan shan giya to zata koma addinin ta na Jew (ridda). Shikuma ya ce ta koma din, amma ta sani muddin ta bar muslunci a bakin auren ta. Zina kuma yanzu ya fara in ita uwarsa ce ta hana shi. Sa'ade bata taba fadawa tashin hankali irin na yau ba, ta ji ta tsani Yarima da matar sa bata ko marmarin sake ganin munanan fuskokin su. Kuma sai gwada wayar Fulani take ta tubure mata azo a dauketa ta kasa samun ta, sai goshin asubahi sannan ta samu kiranta. Jiki na rawa ta amsa wayar, cikin kuka tace "Don Allah Fulani....don Annabi ki aiko a dauke ni, bazan kuma kwana a gidan nan ba, ko na minti daya ban yi barci ba, they are fighting....." Fulani tace "Ki nutsu Sa'adatu ki saurareni, babu inda zaki, ba ruwanki da fadan su tunda basu sanya ki a ciki ba, kiyi kamar baki ji komai ba ki cigaba da harkokin karatun ki. You are not there for Yarima or matar sa, you are here to study. Kada ki kara sauraron maganganun su kin ji na gaya miki. Yanzu baki san abinda wayar ki ta jawo ba. Askirama ya ji duk abinda kika fada kuma ya ce sai ya dau mataki akan dan sa, duk akan surutun ki, ina ruwan ki?" Cikin kuka Sa'ade tace "wallahi ba sauraron su nake ba, ba labe nake musu ba, da karfi suke magana, ni ina daki na ma" Fulani tace "na fahimta, amma ki kwantar da hankalin ki kin ji? Kiyi pretending as if baki ji komai ba, fadan mata da miji sai Allah, kwana biyu zaki ga sun shirya. Tunda dai ba takura miki suke ba to ba ruwan ki dasu" da haka Fulani ta samu ta lallasheta ta daina kukan, tace tayi alwallah tayi sallah tayi azkar tayi shirin tafiya makaranta. Yadda Fulani tace ta yi haka ta yi, da misalin karfe 8:30 ta fito rataye da jakarta, tayi shirinta tsaf. Hannun ta rungume da manyan littafan ta na chemistry. Da Yarima ta fara tozali yana sipping shayi akan dining, gabadaya ya birkice kamar bashi ba smart guy mai tafiya da imanin mai kallon sa, gashin kansa ya cukurkude kuma ga dukkan alamu ko wanka bai yi ba. Ta gefen idon ta ta saci kallon sa, a ranta tana fadin how comes this perfect and handsome gentleman is adulterer? Ga goshin sa har da tabon sujjadah. Watakila matar sa ta dai fada ne don ta bata masa rai tunda shima ya ce tana shan giya. Ta dan russuna daga bakin kofar dakin ta ta ce ciki-ciki "barka da asubah". Ya dago lumsassun idanun shi ya dube ta wadanda suka canza kala zuwa brownish sabida rashin barci. Ta ki yarda su hada ido ta sunkuyar da kanta wanda hakan ya bashi damar ganin yadda idanun ta suka tasa, kada dai kuka tayi? Kada dai ta ji fadan su shi da Sultana? Tabbas da ya shiga uku ya lalace. Murya a cunkushe ya ce "come take your tea" cikin rawar murya ta ce "i'm ok" tasa kai zata wuce ya daka mata tsawar data firgitata "kina nufin haka za ki fita baki ci komai ba? Me ya samu idanun ki haka? Have you slept yesterday night?" Jikin Sa'ade ya soma rawa sabida bai taba yi mata magana cikin tsawa ba. Ta tuna Fulani ta gargadeta akan ta nuna bata ji komai ba. Sai tayi narai-narai da ido gab take da sakin kuka ta ce "na tashi da ciwon ciki ne" Yarima ya ji wani irin relief ya sauko masa, ya nuna mata kujerar dake gefen sa "zauna ki sha tea ko kadan ne, bai kamata ki fita haka ba, sai in baki magani" ta bi umarnin sa kan ba yadda zata yi, amma kwarai take so ta bar gidan ko ta samu sa'ida. Da kansa ya hada mata tea din, wanda shi ya dafa shi da kansa. Uche ya masa waya cewa ya tafi garin su Ogun mahaifiyar shi ta rasu a safiyar yau. Ta karbi tea din da yake mika mata ba don ranta ya so ba, amma kaifin idanun sa da ya tsare ta dasu ya sa ta kasa kurbar shayin. Yarima ya mike ya bar dining din zuwa dakin sa don ya bata dama ta sha shayin, ya lura yau wani tsoro-tsoron shi take ji, jiya kuwa har labarin karatunsu ta bashi. Yana tashi tayi maza ta kurbe shayin, saura kadan ta kware, ya fito a daidai lokacin da ta mike tana daukar handbag dinta, hannunsa rike da kwalbar gestid. Ya jijjiga ya zuba a murfin ya mika mata. Hannu na rawa ta karba daidai lokacin da Sultana ta fito daga daki cikin nata shirin na tafiya ofis. Wani kallon banza tayi musu sannan ta dauke kai ta wuce su fuuuu! Sa'ade na fadin "good morning aunty" ko kula ta bata yi ba. Salis ya soma horn don ta gane ya iso yana jiranta. Kallon Yarima tayi ta kasa-kasan ido tana jiran ya bata umarnin tafiya sai ta samu idanun sa a kanta suke. Da sauri ta kara sadda kanta. Ya ce "in kin dawo kin yi abinci ki sa da ni, Uche ya tafi garin su Maman sa ta rasu" kai kawai ta gyada tana mamaki a cikin ranta. Ita wacece da zata yi abincin da Uncle Yarima zai iya ci? Har suka isa makaranta tana kakabin abin cikin ranta, in matarsa ta ce ta yi mata shishshigi fa? In Uche baya nan meye amfanin matar sa? Koda yake wannan mai jan kunnen bata taba ganin ta tana dafa ko da ruwan zafi ba. Gara dai ta fara tambayar Fulani, kada ta yi abinda ba dai-dai ba. Data gama lectures din yau zata fito ne ta tadda Salis a parking lot ta kira Fulani tana cigaba da tafiya a gefen hanya, bayan sun gaisa tace "Fulani wai uncle Yarima ne yace yau in zan yi abinci na in sa da shi, sabida Uche yayi tafiya, ina tsoron kada in yi abinda ba shikenan ba" Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce "meye gamin ki da Yariman da har kuke hira?" "Ba hira muke ba, dazu ne da safe da zan fito ya gaya mini" Fulani ta yi ajiyar zuciya ta ce "Sa'adatu! Ki kula da kan ki kin ji? Ba zan hana ki bashi abinci ba tunda Yayanki ne, amma bana son wata mu'amala mai zurfi a tsakanin ku bayan kasancewar shi guardian din ki. Maza duka ba abin yarda bane you have to be careful!" "To Fulani in ce bazan bayar ba mana? Wani abu ne?" "A'ah kar ki ce hakan, just cook and keep it on dining ki shige dakin ki, ban yarda da hira mai tsayi tsakanin ku ba" da haka suka yi sallama. Tana shiga gida ta ajiye littafanta tasa apron ta shiga kicin. Girki na nutsuwa ta yi, wanda ta inganta da kayan kamshi na gargajiya, lallausan tuwon semovita miyar danyar kubewa data ji ganda da busashshen kifi. Sannan ta markada abarba ta hada da zobo da pinapple flavour. Sai tayi farfesun kayan ciki mai rai da motsi. Sugar kadan ta sanya. Tana gamawa ta shirya masa a dining ta shige dakin ta ta kulle ta hau yin assignment din da aka bata yau daga laptop dinta. Yarima ya riga Sultana dawowa domin data tashi aiki Bar ta wuce ko don ta sauke bacin ran data kwana ta kuma wuni da shi, domin hakika tana shakkar sake shan giyar a gaban sa don yadda ta ga ya rikide mata jiya ta san komai zai iya faruwa da auren ta, one thing shine tana son Yarima bazata iya rabuwa da shi ba. Yana shigowa falon, falmaran din black Italian suit din jikin sa ya fara cirewa, yayi loosen tie din wuyan sa, kai tsaye dining ya nufa, a yunwace yake sosai, rabonsa da abinci tun tea din safe. Yana budewa ya ja kujera ya zauna ya soma ci cikin nutsuwa irin tasa, kunnen sa har wani irin motsi yake yi. "She's blessed in cooking!" Ya fada a hankali. Yana so ya kira ta, bai san in ta zo mai zai ce mata ba, he just want to check she is well, don haka yasa murya a tausashe ya kira ta. "Sa'adah!" Ta ji kiran nasa amma sai ta kasa yarda kiran nata yake yi, it sound so weird, don bai taba kiranta da wannan sunan ba, sannan amon muryar ya taimaka wajen sawa taji kiran kamar ba nata bane, don haka ta cigaba da aikin ta, hankalin ta ya rabu biyu, ya kan kirata Sa'adatu ne in full. Da ya ji shiru kai tsaye ya mike zuwa dakin nata, bayan ya wanke hannun sa a sink din dake manne a gefen dining din, ya tsane da karamin tawul. Kanta a sunkuye tana sarrafa na'ura mai kwakwalwar ta, riga da wando ne na pakistan a jikin ta ruwan goro turarre, ta yane mayafin su a kanta. Bata ji karar bude kofar sa ba sabida yadda hankalin ta yayi nisa kan abinda take yi. Sai sassanyan kamshin INVICTUS (By Paco Rabbanne) ya ziyarci hancin ta, ya kuma sauya atmosphere na dakin bakidaya wanda ke cakude da rabar iya kwandishan. Har gabanta Yarima ya zo ya tsaya hannayen sa biyu zube cikin aljihu, a hankali Sa'ade ta dago ido sai idon ta cikin na Yarima.....wani abu mai karfi tamkar magnet ya manne idanun su wuri guda. Yarima Sageer ya tuna wannan kanwar sa ce a gaban sa (step-sister) kuma amanar mahaifin sa.... amma akwai wasu abubuwa cikin idanun yarinyar da ke da matukar tasiri akan sa, wadanda yake kasa controlling din su, wadanda bai san yadda zai fassara su ba. Watakila kyawun idanun ta ne ko hasken da ke cikin su? Juyawa ya yi ya bata baya don kaucewa kaifin idanun ta. Murya cunkushe ya ce "I just want to check on you. Have you eaten?" Kai ta gyada duk da ba kallon ta yake ba "zan ci in na gama" ta fada da sassanyan sauti. Taku daya, biyu yayi kamar zai fita, sai kuma ya juyo gabadayan sa. "Sa'adatu will you help me with your food har Uche ya dawo?" Ba tare da ta dago ba tana cigaba da typing din ta ta motsa dan bakin ta a hankali "sai na tambayi Fulani" yadda tayi maganar innocently ya burgeshi, ta nuna bata da wani ra'ayi kai tsaye sai na uwar ta. "Fulani bazata hana ki sammin abinci ba, nima uwata ce har fiye da ke" murmushi tayi wanda ya kara fiddo kyawun karan hancin ta. "Har fiye da ni? Ai daga ni sai Zarah ta haifa. Ka ga kuwa bata da kamar mu" ya dubeta straight cikin idon ta duk da ba shi take kallo ba "ni ta fara haifa kafin ta haife ku" murmushin ta ya zarce zuwa dariya "ai watakila ma ka girmeta Uncle Yarima" "sabida kin ganni da furfura?" "Ni ban gani ba, amma ko baka girme ta ba zakuyi age mates" ya juya ya fita yana murmushi cikin fadin "i look forward to my dinner Sa'adah. Na bar ki lafiya". Bin sa ta yi da kallo har ya fice, amma dakin ta bai bar INVICTUS perfume ba. Abinda ta ji jiya ya fado mata a rai. A fili ta ce "ba kama....". Sannan tayi ajiyar zuciya ta cigaba da aikin ta. Wannan baturiyar ta yi sa'ar zankadeden miji wanke hannu ka taba, amma don asara ko abinci bata bashi... tadin Sa'ade kenan ita da zuciyar ta. Ta kira Fulani ta gaya mata yadda sukai da Yarima, Fulani ta shiga dan rudani, ta ce "Sa'adatu ya ce da ke wani abu bayn wannan?" "Wallahi iya abinda ya fada kawai kenan, sai cewa kema uwar sa ce har fiye da ni" Fulani ta yi murmushi ta ce "bakomai ki dinga dafa masan in har kina gida, kinsan turawa basu daukarwa kansu irin wannan wahalar, shikuma watakila yana marmarin abincin mace ne". Da wannan Sa'ade ta cigaba da dafawa Yarima Sageer abinci har tsayin kwana uku, wanda ya haifar da wata 'yar kwarya-kwaryar shakuwa a tsakanin su, duk da Yarima ba sakar mata fuska yake ba itama kuma hakan, amma yana nuna concern akan al'amarin karatun ta. Da tabbatar da ta ci abinci akan lokaci don in tasa kwamfuta a gaba mantawa take da cikin ta. Aisha Sultana bata san me suke ciki ba, ta dai lura yanzu tana bashi abincin ta tun tafiyar Uche, hakan kuma bai dadata da kasa ba don ta san ita bazata iya ba. Ga yarinyar da shegen zafin nama cikin 'yan mintuna ta sarrafa abinci mai wahala. Ko suna shiri a tsakanin su ko basa yi ita dai Sa'ade bata sani ba. Yau da Sultana ta dawo hatta firjin kicin sai da ta cika shi taf da kwalaben giya bana dakin ta kadai ba. Sabida za'a shiga weekend bazata samu zuwa bar ba ta san Yarima bai barin ta fita koina a karshen mako. Yarima ya fito falo misalin karfe na goma na safe yayi wanka yayi fresh da shi cikin kananan kaya DKNY ash colour, tsammani zakayi saurayi ne dan shekaru ashirin da biyar ba magidancin dake neman talatin da biyar ba. Maganar da maimartaba yayi masa a daren jiya a waya da ita ya wayi gari tana cin zuciyar sa, ya kuma yanke tunkarar Sultana da maganar. "Kai da matar ka sai yaushe zaku kawo min jika? Ko sai na mutu ban ga kwan ka a duniya ba? Aure shekara biyar ana neman ta shidda babu ko labarin bari a gidan ka Yarima? A matsayin ka na mai jiran gado?" Wannan magana ce da maimartaba bai taba yi masa ba sai wannan lokacin, don haka sai yaji tamkar an yi masa tuni ne akan abinda ya manta. Sultana ta fito sanye cikin wando 3 quater da yar karamar rigar shan iska armless ta nemi waje ta zauna a nesa da shi duk don ta nuna masa har yanzu fushi take. Ya hadiye wani abu da ya tsaya masa a makogaro sakamakon kallon zara-zaran kafafun ta da suka sha adon jan farce purple abinda ya hanata sawa sabida ya gaya mata baya sallah amma ta ki daina shafawa. "Ki shirya mu tafi asibiti yanzu, a bincika a ga shin ni da ke waye baya haihuwa?" Ba karamin duka maganarsa ta yiwa Aisha -Sultana ba, amma bata bari fuskarta ta nuna ba. Mikewa yayi tareda daukar mukullin mota yayi waje yace yana jiran ta a mota. Ta bata lokaci kafin ta fito cikin shigar atampa hiterget, suka tafi zuwa Nizamiye Hospital inda suke da file. Da tana da yadda zata hana zuwa asibitinnan da ta yi, amma yadda ta ga fuskar Yarima ta san babu wani excuse da zai karba, fargabar dake ranta kadai ta isheta don bata taba zaton watarana Yarima zai taba sha'awar haihuwa ba. Ita kuma duk son da take masa bata shirya haihuwa da bakar fata ba, ta aure shi ne domin ya dinga satisfying soyayyar da take masa ba don su tara 'ya 'ya ba. A gaban sa likita ya duba ta, tayi fuska kamar bata san abinda ta aikata ba, ya kuma tabbatarwa Yarima Sageer babu mahaifa ma a jikin matar sa, an cire ta gabadaya. Yarima ya daga kai yana kallon Sultana wadda ta sunkuyar da kai, girar idon sa har wani irin tattarewa take yi sabida bacin rai, har suka zo gida bai iya ya ce mata komai ba. Suna shigowa gida kowa ya nufi dakin sa rai a bace. Har zai wuce daki yayi tozali da abincin da Sa'ade ta shirya masa akan dining, ya kuma jiyo kamar jan majina irin na kuka da sheshsheka daga dakin nata. Sai ya ji bazai iya wucewa ba tareda ya dubata ba, haka yau bacin rai bazai bar shi ya iya cin abincin ta ba. Knocking yayi mata har sau biyu, daga ciki ta amsa cikin dusashshiyar muryar data ci kuka. "Waye anan?" "Sunana Sagir" Murmushi tayi sabida yadda ya fadi sunan cikin lallashi? Ta taso ta bude kofar, tareda dan ja da baya don ta bashi damar shigowa. Cikin idanunta ya kalla, wadanda suka kada zuwa brown, "kukan me kike yi?" Akwai alamun hankalin sa ya tashi da ganin halin da take ciki, ai kamar jira take ya tambaya sai ta idasa rushewa da kuka. Da kyar Yarima ya samu tayi shiru, sannan ta rufe ido ta gaya masa ta fadi kwas din Physiology shine dalilin kukan ta. Ajiyar zuciya ta kwacewa Yarima, ya dauka wani abu ne terrible. Kai Sa'adatu 'yar maman ta. "Do you have issue with some of your courses baki taba gaya mun ba?" "Ai Fulani ce ta ce kada mu dinga hira" dariya ta kama shi sabida wautar ta data fito fili a yayin maganar. Ya tako zuwa gaban ta, gab da ita ya tsaya duk invictus ya mamaye ta. She can feels him breathing softly.... "gaya min abinda yasa Fulani ta ce kada mu dinga hira" gabadaya ta daburce ta kuma ga wautar kanta data fada masa hakan. Sannan bai bada space a tsakanin su wanda zata yi masa musu ba. Da sauri ta ja baya, amma sai taji bayan ta ya hadu da kofar dakin "umh...umh nima ban sani ba Uncle Sageer" "ni na sani, in kin amince in gaya miki....." da sauri Sa'ade ta girgiza kai "don Allah kada ka gaya min ni ba son sani nake ba" ta fada, her voice trembling. Kai gabadaya tsokar zuciyar ta ma rawa take sabida closeness din dake tsakanin su da kamshin Paco Rabbanne da yake hargitsa ta. A hankali ya ja da baya yana murmushi yace "ki ce ma Fulani, ai mutum baya cutar da abinda yake so ya zama nasa gabadaya. Ta bar ki kiyi hira da Yayanki. Fi-amanallah, har zuwa lokacin da zai dau ajiyar da ya bata". Bata gane zaurancen sa ba amma ta ce "toh" da sauri don ta samu ya bar ta haka, tayi jinyar sababbin abubuwan da ke ziyartar ta, a zuciya, ruhi da gangar jiki gabadaya. "Gobe zamu fara karatu ni da ke, physiology will never fail you again. Na bar ki lafiya". Har ya fita bata san meyasa ta kasa dauke ido akan sa ba, al'amuran sa na yau masu ban mamaki ne data kasa gane inda yasa gaba. A hankali tabi lafiyar gadon ta, ta lumshe ido tana tariyo maganganun Yarima Sageer daya bayan daya. In wani yace mata yana magana haka zata karyata. To me ya canza shi haka? Me ya kawo canjin? Sai dai kuma ga mamakin ta ta kasa kiran Fulani ta gaya mata abinda yace din duk da bata iya boye mata komai. Amma wannan karon sai ta ji ta kasa. Kamar tana jin kunya.... Kamar yadda barci ma ya gagare ta. Sai scenes din Uncle Yareema ke mata gifcin gizon makauniya. **** Washegari da safe basu hadu ba, kowa ya kama gaban sa, cikin daren an tafka rigima tsakanin Yarima da maidakin sa Aisha-Sultana, yace tunda ta yaudareshi ta cire mahaifarta ba da sanin sa ba tasa a ranta ta bashi lasisin auren wadda zata haifa masa 'ya'ya. Sultana ta dauki kalaman nasa a matsayin abinda ake kira 'shifcin gizo', watakila ya fada ne out of frustration na ta cire mahaifa, amma in ma mafarki yake na zai hada ta da wata diya mace a duniya su yi sharing din sa ya dade bai farka ba. Lokuta da dama in a buge take bata mayar masa da magana, tana bin shi da ido ne kawai. Wadanda basa ko buduwa sosai. To yau ma hakan ta bishi da rinannun idanun ta har ya shige turakar sa. Zaune take akan irin kujerun sumintin nan na cikin makaranta karkashin wata bishiyar lemon tsami mai duhun ganyayyaki, fitowarta kenan daga lacca ta zauna tana kara nazarin abinda tayi jotting cikin littafinta. Sallama ta ji a kanta da wata lallausar murya kamar ba ta namiji ba, da sauri ta dago ta kalli wanda ke tsaye a kanta, kallo daya tayi masa ta gane shi, coursemate dinta ne amma bata san sunan shi ba. Ta amsa sallamar sa tare da maida kanta kan littafin ta, yaron ya cika kyau kamar aljani, da ganin sa ruwa biyu ne ko kuma bafillace. Cikin lallausar turancin sa ya ce "Ma'am, ki taimaka min da laccar da kika rubuta inyi photocopying, i missed alot from it" Sa'ade ta zumburo baki "bana bada aron littafi na" murmushi yayi ba tareda ya ji haushin abinda tace ba, kawai sai ya sa hannu ya dau littafin daga cinyarta ya juya ya soma tafiya. Sa'ade ta mike da sauri ta bi bayan shi tana fadin "Malam...malam" "sunana Mr. Sa'id ba malam ba" "to ni ina ruwa na da sunan ka? Ka bani littafi na" yayi kamar bai ji ta ba, ya nufi wani shago da suke photocopying, Sa'ade bata yi kasa a gwiwa ba wajen binsa tana ta mita "haka kawai sai ka daukar mun abu ba izni babu yardata? Don baka san wanene Yayana a jami'ar nan ba wallahi sai na sa an baka carry-over" bai san sanda dariya ta kubuce masa ba data fiddo fararen hakoransa, yarinyar akwai wauta kamar diyar fari ga magana cikin shagwaba. Ya hadiye dariyarsa ya mika wa mai hoton takarda littafin ya fada masa yayi masa photocopy sannan ya juyo ya dubeta da wani irin kallo. "A'a spill-over zaki sa a bani ba carry-over ba. Sa'adatu Hashim I loved to be your friend" zaro ido tayi na mamakin inda ya san sunan ta, sai ta tuna a jikin littafin ya gani, ta kyabe baki tace. "Allah ya sawake in yi abota da namiji, matan ma sun ishe ni kallo ne balle kai sungumemen kato?" Yayi dariya yace "ko sai na yi kamun kafa da Yayanki mai jami'a?" Wani kallo tayi masa na sannu sarkin tsautsayi, sannan ta juya tana cewa. "In ka so ka kwada littafin ka cinye na bar maka". Ta kama hanyar komawa hall. Tana zama laccara na shigowa suka fara karatu, sai ga wanda ya kira kansa Mr. Sa'idu ya zo ya zauna a gefenta, a hankali ya ajiye mata littafin ta yana murmushi, a ranta tace sai shegen murmushi kamar gonar auduga, jan aji da class sai Uncle Yariman Askira, kafin yayi murmushi ma za'a dade. Amma shi wannan sai faman murmushi yake kamar mace. Wata zuciyar tace Sa'ade! Me kike cewa? Da sauri ta ce "ba abinda nace kenan ba, nufi na Uncle Yarima yafi kowa jan aji a duniya" ta kara ankara da kalar tunanin da take yi tayi saurin toshe bakin ta tare da dafe kanta tana fadin "Yaa Ilaahy! Na tuba ya Allah!" Bata san cewa a fili ta fada ba. Kowa a ajin sai da ya juyo ya dube ta, kasancewar an yi tsit ne ana sauraron malamin. Tayi maza ta sunkuyar da kanta tana fadin meke damu na ne? Ni Sa'aden Tsanyawa? Ba komai bane sai tunanin Yarima Sageer Yusuf Askira. Wanda ya dusar da hasken sauran maza daga idanun ta, ya dasa wani dan kankanin tsiro a zuciyarta daga lokacin da bazata iya tantancewa ba. Sa'id bai bar Sa'ade ba, tun daga ranar ya like mata, inda duk tasa kafa cikin NTNU nan yake mayar da tasa. Ba da sanin ta ba ma ya bi bayansu a mota itada Salis bayan sun tashi karatun ranar ya ga gidansu cikin quaters ne, nan ya tabbatar 'yar wani babban Dr. Din ce kamar yadda tayi masa barazana. Kodayake ta ce Yayanta. Tun tana basar da shi amma yawan hakurin sa da yawan murmushin sa yasa dole ta soma kula shi suke harkar karatun su tare. Dama tana neman abokin karatu kuma ajin nasu maza sunfi yawa, tsirarun matan dake ajin kabilu ne. Tun ranar da Yarima yace zai fara koya mata karatu kuma tafiya ta kama shi zuwa Lagos (Lagos State University) zai halarci annual conference. Basu kara haduwa ba sai yau da ya dawo, kuma Uche ma ya dawo daga Osun, tayi masa ta'aziyar mahaifiyar sa ta shige dakin ta a ranta tana fadin "shikenan na huta da girkau, wahalar da ba'a ce min an gode". Uche yana tsaye yana girki ta shigo kitchen din, ruwa take so ta sha, na firjin dakin ta duk sun kare. Ta bude firij din kitchen din tana fadin "Uche what are you cooking for your Oga?" Uche ya ce "Basmati Rice and salad nake yi masa, ban sani ba ko zai so" tace "kada kasa spices din can da kake using, kayi amfani da rosemary, coriander da oregano, basu da karfi, he really likes their aroma". Uche yayi godiya da gyaran data yi masa. Ta bude firji babu ruwan gora sai wasu manyan kwalabe, an cire takardun jiki babu rubutun komai, Uche ya bata baya yana yankan albasa bai lura da abinda take ba, ta dauka tana juyawa a hannun ta sannan ta bincire murfin zata kai bakin ta. Sai ji tayi an yi wurgi da kwalbar daga hannun ta, ita kanta saura kadan ta fadi sabida yadda Yarima ya angije hannun ta da karfi. Kwalbar ta fashe, ruwan ciki ya malala a kasa, wani ruwa mai wani irin tsami da hamami, Yarima bai tsaya ba ya finciki hannun ta suka bar kitchen din yana ce da Uche ya gyara wurin ya fitarda duka whisky daga firinjin ya zuba a bola. Bai tsaya da ita koina ba sai a falo ya jefata jikin Aisha-Sultana, wadda ke zaune tana danna ipad din ta. Ta dago a fusace sai idon ta cikin na Yarima, yadda ta ga idanun sa kamar na mayunwacin zaki ya kada mata 'ya'yan hanji. Muryarsa har sarkewa take ya ce "Sultana! Ban hanaki shigomin da giya gida ba? Ko kin san saura kadan yarinyar nan ta sha giyar ki? Me kike so in cewa iyayenta da ace ta sha da suka damka min amanar ta? Kuma har a firinjin kichin sabida kin raina ni?" Sultana tayi mici-mici da brownish idanunta, "cewa nake mun yi da kai sai ka daina shiga gidan Ziyad yin zina nima zan daina shan beer?" Da sauri Yarima ya nunawa Sa'ade hanya yace ta bace a wurin kafin ya kifta idon sa. Ai kuwa kafin ya kifta din ta kai kofar dakin ta tana jin karar marin da ya kaiwa Sultana. Ta dafe kunci ta ce "you slapped me?" Bai tsaya a wurin ba ya danna kai dakin ta ya watso su duk daga firinjin ta, ya kwalawa Uche wani mahaukacin kira, ya fito da gudu daga kitchen yana amsawa, ya nuna masa dakin Sultana yace ya kwashe whisky ya je ya zubar gabadaya. Yau Sa'ade ta ga tashin hankali don har dare ya tsala tana jiyo fadan Yarima da matar sa har tissue tasa ta toshe kunnuwan ta tana kuka, marin da ya yiwa Sultana ya daga mata hankali ba kadan ba, ita bata san giya bace kuma ba sha zata yi ba sunsunawa zata yi taji menene? Sai Allah ya kawo shi. Tana so ta kira Fulani ta gaya mata ta tuna abinda Fulani ta gaya mata wancan karon cewa maimartaba ya ji wayar su, har yace zai dau mataki akan Yarima. Ina ga in ya ji ana shan giya kamar ruwa a gidan sa? Wa'iyazu billah. Ko isashshen barci bata samu ba yau, don haka washegari ko karin kumallo bata tsaya yi ba ta riga kowa ficewa a gidan ko Salis bata jira ba, duk nisan dake tsakanin gidan su da cikin makaranta ta gwammace ta taka a kasa data kara ganin fuskar Yarima mai zuwa yin zina ko matarsa mai shan giya kamar yadda suke cewa. Sa'idu ya ganta duk a birkice, ya bata wuri ta zauna, "hi friendy, me ya sameki haka?" Kawai sai ta saka kuka tace "don Allah ka san inda ake shiga motar Askira?" Ya ce "ni ko sunan garin ban taba ji ba" ta sake rushewa da kuka, yayi-yayi ta gaya masa abinda aka yi mata ta ki, har malamin su ya shigo suka fara darasi, dole ta tsagaita da kukan ta bashi hankalin ta, don inda abinda ta ki jini a duniya to carryover ne. Da wuri suka gama lacca yau, tace da Sa'idu gida zata koma, da in sun gama lacca da wuri maimakon su tafi gida lab suke zuwa suyi research da ya shafi karatun su, yace ina direban ta tace ba shi ya kawo ta ba da kafarta ta taho, kuma ta baro wayarta gida balle ta kira shi ta gaya masa inda take. Sa'idu yace "do me a favour to drop you at home, tunda naji kina zancen zuwa Askira bazan barki ki tafi ke kadai ba". Ya dage da nacin sai ya kaita, ta san Sa'idu zuwa yanzu yaron kirki ne mai kokari da son taimakon ta, don haka ta amince ta shiga motar sa kirar civic suka karasa gida. Sa'idu na yin parking daidai Yarima ya zura mukulli jikin motar sa zai bude, yayi mugun hadewa cikin danyar shaddah ruwan madara samfurin excelcior (London). Wadda ta sha aiki da zare ruwan kasa irin na sarauta. Gilashin idonsa ya zare a hankali don tabbatar da Sa'ade ce yake gani a motar wani ko wacece? Fasa bude motar yayi ya kafa musu manyan lumsassun idon sa har Sa'idu ya kashe motar Sa'ade ta bude ta fito tana masa godiya. Sa'idu ya so ya fito ya gaida Yayan Sa'ade amma yadda yaga fuskarsa kamar hadarin da ya nausa yayi gabas dole ya kama kansa, ya ja motar sa da gudu ya bar harabar gidan don kwarjinin Yarima da haibar sa da cikar kamalar sa kadai ya tabbatar masa ba karamin mutum bane, kada yaje ya gane shi ma wani abu ya samu karatun sa, duk da ya so ya fito ya gaisheshi ya gaya masa taimaka mata kawai yayi shi dan ajin su ne, amma ina! Tsoro ya hana shi. Makarantar ma bai koma ba ya gudu gidan su a unguwar Maitama. Ta gaban sa Sa'ade ta zo ta wuce amma ga mamakin sa ko kallon sa bata yi ba ta wuce ciki. Mamaki ya kusan kayar da shi, bin bayan ta yayi cikin takunsa na kasaita. Tana saka kafa a dakinta ta turo kofar yasa hannu ya dafe kofar. Sai ta sakar masa, ta juya ciki ta na kokarin sauke jakar dake goye a bayan ta wadda ta lamushe dukkan komatsanta harda laptop. Muryar Yarima har tsakar kanta, babu alamun wasa ko kadan a tattare da shi. Zata iya rantsewa bata taba jin sa yayi magana da irin wannan muryar ba. So furious, angry and jeolous.....! "Sa'adatu who is this boy?" Bata san yaya aka yi ba, bata san wa ya kitsa mata ba, kawai sai ta samu bakin ta da cewa "saurayi na ne" bayan ita kanta bata gama sanin ma'anar kalmar saurayin ba. Kawai ta san ta tsani Uncle Yarima ne yanzu, tunda dukan matar sa yake yi, in ta sha giya ai shi ya bata dama. Idanunsa sun rikide sun juye zuwa wani yanayi da bazata iya fassarawa ba. "Look into my eyes...and tell me he's your boy friend" kokarin ja da baya take. Data rasa mafita, ga zuciyarta na wani irin azalzala da mixed feelings; haushi, tsana, da zazzafar soyayyah duka a lokaci daya, kawai sai ta saka kuka. "Ni dai a maida ni Askira, wallahi na gama zaman gidan ku" Yarima ya ja da baya sabida da karfi ta fasa kukan. "Da mu kayi miki mene?" Ya fada yana hararar ta, in wani yaji irin kukan da ta fasa tsammani zai yi wani abun yayi mata. Ba ta ce komai ba sai cigaba da kukanta. Da zata iya da ta ce dashi sabida dukkanku fasikai ne marasa tsoron Allah. Amma ta san ko giyar wake tasha bazata iya dubar tsabar idon Dr. Sageer ta gaya masa haka ba. Apart from all these she respects him so much. Yana da wata irin kima a idanun ta da bata san yaushe ta samu matsugunni a zuciyarta ba. Tafi danganta hakan da kulawar sa da kyautatawar sa gareta. Yarima ya dubeta a fusace, ya rasa yanayin da yake ciki yau, amma ya tabbata bai taba ganin abinda ya bata masa rai a duniya irin Sa'adatu da saurayin ta a mota ba, yaga yadda hawaye ke gudu akan kundukukinta kai ka ce wani mugun abin aka yi mata. Ya nunata da dan yatsa ba tare da ya bari hawayen da take zubarwa sun yi tasiri akan sa ba "Yau ta zama rana ta karshe da zai kuma tako min gida, ba shi kadai ba kowanne rubabben saurayin ki ma, in ba haka ba in gayawa Fulani da maimartaba su cireki a makarantar su yi miki aure tunda hakan kike so". Sa'ade ta zaro ido abin dariya abin tausayi "Uncle Yarima wasa nake ba saurayi na bane ba, wallahi, dan ajin mu ne" ya juya ya fice bai saurareta ba, damuwar duniya Sa'adatu ta shigeta, ba abinda take tsoro, taki jini take kuma gudu a rayuwar ta irin AURE! Saida yayi kwana uku bai kara kula ta ba, bai kara nemanta ba, he's really suffering a ruhi da zuciyar sa akan ganin Sa'ade da saurayi akan dalilin da bai sani ba. A haka su Sa'ade suka fara jarrabawar karshen zango babu shiri ko kankani tsakanin ta da Yayan nata Yarima. Ranar da sukayi takardar karshe ta kira Fulani ta gaya mata, Fulani ta gayawa maimartaba, shikuma ya kira Yarima yace yasa direba ya kawo Sa'ade gida tayi hutu. Yarima yace dama shima zai shigo Askiran jibi, zai taho da ita da kansa. Sa'adatu na kwance a gadon ta tana karanta mujallar turanci ta 'Thrills and Boom' taji knocking a kofar ta. Ta gyara kwanciyarta da dankwalin ta daya cire sannan tace "yes". Yarima ya sanyo kai a dakin, t/shirt ce a jikin sa fara kal an rubuta Marks&Spencer da bakin rubutu, sai bakin wandon jeans mai kauri. Hararar ta Yarima yayi sannan ya jingina da kofar, a hankali ya ce. "Sabida na hanaki kula samari, shine kika daina gaishe ni ko?" Sa'ade ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, amma sosai taji kunya, wai wa yace ma Uncle Yarima Sa'idu saurayin ta ne? Bata cika son magana tayi tsayi a tsakanin su ba, karatun ma da yace zai koya mata bayan dawowarsa daga tafiyar da yayi saida ta san yadda tayi ta kaucewa hakan ta roki Sa'idu ya koya mata lokacin jarrabawar kwas din, yana da effect mai karfi kanta wanda shi bai sani ba itama bata sani ba, abinda ta sani kawai shine bata son mu'amala mai zurfi a tsakanin su. "Ki shirya gobe da asubah zamu kama hanyar Askira, maimartaba yace a kai ki kiyi hutu" bata san lokacin da ta dago zaune ba tana ta faman blushing, bai tsaya kallon ta ba yasa kai ya fita. Tun a daren ta hada duk abinda take bukatar tafiya da shi. Baccin ta ma ragagge ne sabida doki. Tayi kewar Fulani da Zarah.....Shi kansa Askirama ta yi kewarsa. Washegari data yi sallahr asubah bata koma barci ba, wanka tayi, tayi ssaukar shiga ta bakar abaya mai santsi da adon stones sosai a jikin ta. Bata shafa komai a fuskarta ba sai wet-lips ta kuma fesa sassanyan turare. Ta zauna bakin gadonta da trolley dinta a gaba tana jiran Yarima. Bai fito ba sai wajen karfe shidda na safe, kallo daya tayi masa da ya murda kofar dakin ya shigo bayan tayi masa izni, taji bazata iya jure kallon ba, kwayar idanunta ta zamo mai rauni sabida yau ya fito Prince dinsa. Ta taba ganin maimartaba da irin kayan jikin sa, yakan saka kayan in zai zauna cikin iyalinsa, kaya ne kufta da wando na sarautar Askira wadanda basu cika nauyi ba. Amma kuma sun sha aikin zare na silver da hula zanna bukar a kansa. Kasancewar kusan kullum cikin shigar suit take ganin sa yau sai ya zamo mata wani daban, classique and elegant kai kace Askirama ne ya zama yaro. "Lets go!" Inji Yarima, ganin ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, bayan a badini kirjinta ne ke wani irin harbawa da sabbabin emotions da bata san daga ina suke fitowa daga karkashin zuciyarta ba. Hannu yasa ya ja trolley dinta. Ya fita ta bishi a baya bayan ta dau handbag dinta tana mamaki a cikin ranta; Yarima ya dau kayanta da kansa. Sai taji har tsigar jikin ta na tashi da wani irin feelings mai sanyi a zuciyar ta. Hakan kuma bai janye bakin fentin data ke kallon shi dashi ba. A falo suka ci karo da Aisha - Sultana, kayan barci ne a jikin ta, ta tsaya jingine da kofar dakin ta tana kallon su, ta gabanta Yarima ya wuce dauke da jakar Sa'ade, Sa'aden na gaisheta da safiya, wata harara ta zabga mata ba tareda ta amsa ba. "Mun tafi Askira Aunty, sai na dawo" jin bata amsa mata ba ta wuce ta, ta tadda Yarima a mota, Salis ne ya ja su. Ta dauka a motar zasu tafi har Askira amma sai ta gansu a filin jirgin saman Abuja. For the first time Sa'ade a jirgi, in ka gansu itada Yarima tsammani zakayi sababbin couples ne sabon aure duk da babu hira a tsakanin su. A cikin jirgin Azman ne mai zuwa Maiduguri a first-class seats, ga kujerar ta ga ta Yarima, Lokacin da waitress ta kawo abin motsa baki kasa cin komai tayi sabida uneasiness din da take ciki na zama a gefen Yarima. Ga kamshin Paco Rabbanne dinsa dake kara hargitsa ta. Shikuwa yayi amfani da wannan damar wajen kare mata kallo, kallon da bai taba yi mata ba, har ya zarta ka'idar muslunci domin kallo ne na kurullah. A zuciyar sa ba abinda bai fada ba, wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani, a zahirin sa kamar ba ita yake kallo ba. Bai fi minti goma ya rage suyi landing ba Sa'adatu ta soma jin amai na taso mata sakamakon wani Igbo da ya gifta ta gabanta yana warin qashi irin na maza, ai kuwa tana yunkurawa domin ta tashi sai amai ya kelayo a jikin Yarima Sageer, basu da yawa a first class seats din don haka hankalin sauran mutanen ya dawo gare su, Sa'ade ta hau zazzare ido cike da tsoro bakin ta na rawa tana son furta ban hakuri kalaman sun ki fitowa. Amma ga mamakin ta ko a fuska bai nuna kyama ba, wani irin kallo yayi mata yace "sai kin goge min shi tas!" Tayi narai-narai da ido kamar zata yi kuka don damuwar abinda tayi masa "...don Allah kayi hakuri Uncle Yarima....ban yi da sani ba" a ginshire ya ce "na ce kin yi da sani ne?" "To kayi hakuri don Allah bazan iya goge maka ba" suna wannan jayayyar sai ga waitress tazo don ta gyara wajen tana ta yiwa Sa'ade sannu don a zaton ta ciki gareta. Kasancewar kayan rubi biyu ne ta saman kamar jabba take mara nauyi akwai jamfa daga ciki yasa ya cire ta saman. Sa'ade tayi maza ta dauko turarenta a jakarta ta mika masa. Karba yayi yana jujjuya shi a hannun sa 'sapphire' itama Fulani ce ta bata, a tunanin ta zai bukaci turare tunda tayi masa kayan karni. "Me zan yi da turaren mata?" "Ka fesa saboda karni" Ta fada kamar zata saki kuka don damuwa, ta rasa da bakin da zata bashi hakuri. Mika mata turarenta yayi yana dubanta ta kasan ido yace a hankali "idan matata taji kamshin turaren ki a jiki na what do you expect?" Sa'ade ta runtse ido tace "ni fa ban bayar da wata manufa ba, don ya kashe smell din aman ne" "idan kuma ni son smell din aman nake fa?" Kallon sa tayi da budaddun idanuwa.... mamakin ta ya bayyana karara cikin idanun ta Ba jimawa jirgin su yayi landing a Maiduguri. Motocin ASKIRA EMIRATE har guda biyar manya da kanana suka zo tafiya dasu, da fadawa da dogarai cikin uniform din su na bayin masarautar. Mota guda suka yi amfani amma da yake babba ce sosai kirar (4matic) mai kujeru takwas ba kujera daya suka zauna ba, Sa'ade na daga kujerar baya Yarima na owner side. Suka dauki hanya. Ji take kamar tayi fiffike ta ganta a dakin mahaifiyar ta. Har suka zo Askira barci take wanda a jirgi takuruwar zama kusa da Yarima bai barta ta yi ba. Ana bude musu motar ta fice da azama bata jira fitowar Yarima ba, wanda tun shigowar su Askira taga kamar komai nasa ya canza, simplicity din da annurin ya tafi, ya juye ya rikide ya zama cikakken Prince din sa. Da gudu ta karasa unguwar Fulani Bilkisu ko jakarta bata dauko ba sai biyota aka yi da ita. Da Zarah ta fara tozali, suka ruga da gudu suka makalkale juna. Zarah na tambayar me ta taho mata dashi daga Abuja? Tace "everything, sweetheart". Fulani ta fito daga shigifarta cikin wata irin kyakkyawar shiga ta alfarma, ta tsaya daga bakin kofa tana kallon su da murmushi, kamshin ta ne yasa Sa'ade ta lura da ita, ta ajiye Zarah ta kwasa da gudu ta rungume Fulani, kawai kuma sai ta fara hawaye. Fulani tace "yau nake ganin sakarci, me aka yi na kuka? Ko suna miki wani abu ne?" Ta girgiza kai "babu komai, kukan farin cikin sake ganin ki nake yi, watanni shidda ba kwana shidda ba". Fulani ta hau tureta daga jikin ta jin takun ana shigowa, Fanna ce ta taho dauke da abinci a makeken tray ta ajiye a dining. Tana murmushi tace da Fulani "Allah ya taimakeki yau tare na hada muku abinci da uwar daki na, don Allah ku ci tare" Sa'ade ta sa dariya cikin dadi tana kallon uwartata. Fulani ta gimtse fuska tace "Fanna yaushe na koma abokiyar wasan ki?" Fanna tayi nara-narai da ido tana murmushi tace "Allah ya ja da ranki Alfarma ce muke nema, wata shidda cif bamu ganki ba". Babu wanda ya gayawa Fanna Sa'ade 'yar Fulani ce ta cikin ta amma ta dade da fahimtar hakan. Yadda aka yi ta samu 'yar ne bata sani ba. Tana gama fadin hakan ta juya ta fita, Sa'ade tayi wata irin super ta dane jikin Fulani saura kadan ta kada ita, Zarah sai dariya take yi. A haka suka ci abincin cike da begen juna su uku. Tana gamawa tayi wanka ta sauya kayan jikin ta zuwa marasa nauyi ta dauko waya ta kira Sa'id. Yace "Sa'adatu, yaya kwana biyu kuma ya hutu? Ina fatan kina bitar Physiology textbook dinnan?" Sa'ade tace "ni yanzu ina garin mu bana Abuja ka kyale ni in huta da wani karatu, ina tare da uwata rabin raina" Sa'id yayi murmushi yace "sai na zo Askira kawo gaisuwar neman iri" Sa'ade tayi tsaki tace "Allah ya sawwake inyi saurayi da classmate dina, wani dan yaro da kai, ni dinnan da kake gani matar manya ce inji Fanna" dariya sosai Sa'id yayi, ya ce "me yafi ka auri yaro sabon jini kamar ka? Ya sa ka dariya kaima ka saka shi? In yaga dama ya goyaki ya yi ta zagaye gida dake?" Sai ganin Fulani tayi tsaye a kanta. Ba karamin firgita tayi ba ganin expression na fuskarta. Tayi maza ta kashe wayar ba tareda ta yiwa Sa'idu sallama ba. Tana zazzare ido na rashin gaskiya. "Keda wa kike waya?" Fulani ta tambaya fuskarta babu annuri. A tsorace tace "dan ajin mu ne kawai" Fulani ta juya bata ce komai ba. Saidai kwarai ta so ta magantu din, but she don't want to be too strict har Sa'ade ta koyi boye mata sirrikan ta. Saida ta kai bakin kofa sannan tace mata ta tafi wajen Askirama kada ta nemeta..... **** Rami ne mai tsananin zurfi, wanda har baya iya hango karshen sa sabida zurfin sa, ya leka ciki sabida ya ji kamar muryar Yarima yana kuka yana neman taimako. Bai ga ta inda ta bullo ba kawai ya ganta ne a bakin ramin, tana rike da igiya mai tsayi, tana zuwa bakin ramin ta jefa masa igiyar tace "Kama ka fito da iznin Ubangiji". Bai ga fuskarta ba sabida ta sunkuya ne akan ramin, gashin kanta ya sakko ya rufe fuskar tata gabadaya, saida tayi magana sannan ya shaida muryar ta. Ba jimawa ya ga ta kama igiyar nan tana janyo wanda ke ciki har ta fiddo shi tsaf, yana fitowa suka rungume juna suna hawaye. A lokacin ne ya samu damar ganin fuskokin su gabadaya; Sa'adatu ce da dan lelen sa YARIMA SAGEER. Tamkar an warware masa dukkan baccin da ke kansa ya farka firgigit misalin karfe biyu na sulusin dare, lokaci ne da aka tabbatar mafarki yana iya zama reality. To ko me wannan mafarkin da yayi yake nufi? Sa'adatu as saviour of Sageer? Ba don babu kyau bayyana mafarki ga wani ba, da ya nemi Limamin Askira ya gaya masa mafarkin da yayi. Duk da haka a nasa hankalin, ya fahimci tamkar wani hannun ka mai sanda ne Ubangiji yayi masa, mai nufin akwai wani babban al'amari tsakanin Sageer da Sa'adatu kamar yadda ya so hakan ta kasance a baya. Bai san sanda ya sa hannu ya soma tashin Fulani Bilkisu wadda ke barci sadidan a gefen sa. Ta tashi tana yamutsa fuska tana mutstsikar ido. Ya ce "Bilkisu bude idon ki ki dube ni". A yanayin da Askirama yayi maganar cikin rauni yasa ta dole watstsakewa. "Lafiya Askirama? Lafiya gatan mara gata? Lafiya giwan ASKIRA?" Ta fada cikin tausasa murya, mai Askira ya kama hannayenta duka biyu ya rike cikin nasa. "Alfarma nake nema wajen ki irin wadda ban taba nema ba...... ki bani Sa'adatu in aurawa Yarima a gobe". Fulani Bilkisu ta ji maganar ne tamkar saukar aradu a kunnen ta, kwakwalwarta ta kasa digesting maganar yadda ya kamata sabida wani abu ne da bata tsammani ba a rayuwar ta. Bata kin Yarima don tamkar dan cikin ta ta dauke shi. To amma neman matan da ake cewa yana yi fa tun bai san kansa ba har girman sa har ita Sa'adatun ma ta shaida da bakin ta? Shin Sa'ade ta cancanci hada rayuwa da wayayyen mutum irin Yarima? Ina Sa'aden ta ina hada kishi da Aisha-Sultana? Don haka Fulani ta rasa amsar da zata baiwa mijinta mai Askira, sai bin shi da ido, a zaton ta makuwa yayi cikin barcin sa. Amma da ya girgiza kafadun ta ya sake maimaitawa sai ta tabbatarwa kanta mai Askira yana nufin abinda yake fada ne. "Kin amince ko Bilkisu? Hankalina bazai kara kwanciya ba batare da na tabbatar da sunnah tsakanin Sageer da Sa'adatu ba, jikina na bani itace zata zamo maganin dukkan matsalolin sa, don ban taba yin mafarkin da bai zama gaskiya ba". Ya kwashe mafarkin da yayi duka yanzun nan ya fada mata. Fulani Bilkisu ta rasa abinda zata ce, she's mute for some minutes, tana mai tariyo tarin alkhairin Sarki Yusufu ga Sa'ade tun zuwanta Askira, shin bazata manta da komi ba ta bisu da addu'a ta zama mai rama khairan da khairan? Ta lumshe idon ta cikin na Askirama, wanda ke tabbatar masa da ta karbi alfarmar sa, bata da abin cewa. Itada Sa'adatu duka abin ikon sa ne sai abinda ya hukunta a gare su. **** Koda ta koma dakin ta a washegari bata ce da Sa'adatu komai ba, cikin dimuwa da zullumi take, sabida Mai Askira ya ce kafin su koma hutun nan da suka zo sai da igiyar aure a tsakanin su. Sa'ade ta lura a wunin ranar bakidaya Fulani ta zama sukuku! Bata umh bata umh umh. Abinci wannan a wunin yau bata ci shi ba kuma tace ba azumi take ba. Ta lura tunda ta dawo daga turakar maigidanta take cikin wannan halin, to ko ita da Mai Askira ne suka samu sabani? Saidai hakan mawuyaci ne don bata taba ganin ma'aurata masu fahimtar juna kamar su ba. Sai itama ta shiga damuwa, damuwar uwarka ai yana nufin taka damuwar. Damuwar Fulani shine bata san ta ina zata farawa Sa'ade zancen aure ba, she's too young and innocent, auren ma kuma da Yarima Sageer, wanda ta riga ta gama sanin sirrin su shi da matar sa, ta kuma dauke shi matsayin guardian dinta. Sama da komai bata taba tunanin yiwa Sa'ade aure nan kusa ba, ta so sai ta gama karatun ta, to kana naka Allah na nasa kuma nasan shine gaskiya. Sa'ade sai zarya take tsakanin dakin ta dana Fulani very disturbed, ko Fulani zata kira ta tace zo kiji damuwata, amma Fulani ko kallon ta ta kasa yi, ji take kamar ta yi ba daidai ba ta kuma yi mata laifi data karba mata zancen aure bada sanin ta ba. Ba jimawa jikin ta ya dau dumi, data tuno me ake yi a gidan Yarima Sageer "Zina da Shan giya". Ba ga matar ba ba ga mijin ba kowanne shegen kansa ne, ta dauki innocent 'yar ta ta kai musu, matar ta sha giya ta rotsa mata kai, ko mijin yayo zinarsa ya goga mata cuta? Amma kuma wanene Yarima? Dan Askirama mafi soyuwa a gare shi. Askiraman da ya maida Sa'aden mutum a lokacin da ita ta kasa karbar ta. Wannan damuwa a take ta kwantar da Fulani Bilkisu, amma sai ta mike tana rangaji ta sawa kofar ta mukulli kada Sa'ade ko Fanna su zo su dameta. **** Ya Gumsu na tareda mai Askira a washegari, itace tayi turaka kuma itace zata wuni tare da shi a wunin yau da baya fita fada, duk ranar Jumaah daga ya dawo masallaci sallahr jumaah baya kara fita, yana zama ne ya ribaci yammacin da ibada musamman karatun Suratul-Kahfi da suratul Mulk, Yaasin da Waqi'ah. Sannan yana karanta Suratul Nouh kafa 41 a kowanne yammacin Juma'ah. Tana hada masa shayi a cikin kofi (mug) ya dubeta da murmushi. Ya ce "Gumsun Askira, Uwargidan mai Askira....inada wani kyakkyawan albishir dauke a bakin nan nawa". Ya Gumsu ta karkace ta gyara zama bisa tattausar dardumar da maimartaba ke zaune har da tattara dukkan nutsuwar ta ta bashi, a zaton ta albishir zai mata da tafiyar su wata kasar su huta. Amma abinda mai Askira ya fada bata taba jin abinda ya girgiza zuciyarta da rayuwarta bakidaya irin sa ba. Ya jirkita kwanyarta, ya gusar da annurin fuskarta nan take ya mayeshi da wani mummunan bacin rai da Askirama ko wani mahaluki bai taba gani a kan fuskarta ba. "Kwanaki uku masu zuwa zan daura auren Yarima da Sa'adatu!" Amma Ya Gumsu sai ran ta ya bata gara ta tambayeshi don ya tantance mata wace Sa'adatun yake nufi? Don haka ta hadiye komai cikin laluma ta tambayeshi. "Allah ya taimaki Giwan Askira, ko zan iya sanin wacece Sa'adatun?" "'Yar ku Sa'adatu wadda yake riko a gidan sa ta wajen Fulani Bilkisu......". Ai bai karasa ba sai ganin Ya Gumsu yayi tsaye a kansa, idanun ta a warwaje tana huci, yau da ba shi ne sarkin Askira ba, da ba shine uban 'ya'yan ta ba, furfurarsa ko wannan himilin rawanin nasa bai hanawa ta kwashe shi da mari. "Idan wasa kuke..... Allah ya taimake ku ku bari, bana son irin wannan wasan....." cikin mamaki Askirama ke kallon ta baki a bude, ya dauka wannan karon farin ciki zata yi da zabin da yayiwa Yarima, shi da take fushin ya auri mai jajayen kunnuwa mara addini, ga wadda suka san asalin ta suka san addinin ta suka bata tarbiyya cikin gidan amma tana neman kawo masa zancen banza. "Ni ne nake miki wasan? Zaki ga wasa kuwa ganin idon ki". Mikewa yayi zai bar wajen Ya Gumsu ta sha gabansa idanunta tamkar an gumbuda musu barkono "Allah ya taimake ka ashe kuwa zaka bani takardar saki na.......kafin ranar da zaka aurawa Da na aure da tsintacciyar magen da har yau bamu san asalin ta ba, da 'yar data fito daga hannun makiyiyata don su hada kai su cuce ni su ga baya na nida zuri'ata a gidannan.....na tabbata ita ta kitsa maka wannan sharrin to insha Allahu a kanta zai kare! Ba dai Yarima ba! Ba irin tsiya irin talauci ba, irin da babu cikakken asali don ni ban yarda ma BAGGARA ne su ba sun fi kama da bororon daji......". Mai Askira ya hadiye tsananin bacin ransa bai nuna ba ko a fuska, babu wata mace data taba yi masa irin wannan tsaurin idon a rayuwar sa....amma Gumsun Askira zata ci albarka da yawa....albarkar 'ya'yan ta...albarkar kasancewar ta uwar 'ya'yan sa. Da albarkacin kasancewarta UWA ga duk wani mahaluki dake cikin Askira. Kawai sai ya zagayeta zai wuce, bai taba sa'in sa da kowa ba, tsakanin sa da kowa dake karkashin sa biyayya ne ana so ko ba'a so. Shiyasa ba karamin yaki yayi da zuciyar sa yau akan Ya Gumsu ba, sabida babu saki a tarihin sarautar su, babu kaskanci ga uwar iyali. Ya Gumsu bata daddara ba ta sake jawo Alkyabbar sa..."wallahi sai ka bani amsar inda kuka samo yarinyar nan....ba tun yanzu ba nasan watarana sai ta zame min jidali, na san sai an kakabawa 'ya'yana, yadda naga uwarta ta ci buri a kanta, dama dalilin kawota gidan kenan don ta samu ta auri dan sarki.....kamar yadda ta samu tsuntsu daga sama gasashshe....to ai ba ni kadai na haifi maza ba......don haka in har inada hakki akan Yarima na haihuwa da shayarwa to ban yarda ba ban amince ba.....". Mai Askira yayi murmushi yace "sai kace dan wani na arziki ne da kike tada haqarqari akan sa ke mai da! Dan da tun yana karamin sa ya san dadin zina......girma da aure da martabar gidan su bata sa ya daina ya kama kansa ba. Zan rufa masa asiri da 'yar mutunci don ta taimaka mana ya kintsu shine kike wannan zubar da kimar? Gumsu ina jiye miki ranar jin kunyar ki.....ranar da duniya zata san dan da kike tinkahon dashi har yanzu bai bar zina ba, matar sa shan giya take, rayuwa suke kamar ta dabbobi, musuluncin nasu duka ba maraba.....gara ita nata babu tushe amma wanda bai ji tsoron Ubangiji ba kuma girman aure bai hana shi yin zina ba ba abun tutiya da shi a matsayin Da bane.... A da, na sanya kwanaki uku auren Yarima da Sa'adatu, don in samu inyi gayyata, to na fasa yanzu, nida Waziri zamu daura auren yau Juma'ah bayan sakkowa masallaci. Don in nuna miki ni ke da iko daku daga ke har dan naki. Gara ke na baki hakkin ki na uwa na sanar miki... shikuwa saidai ya ji labari......". Yana gama fadin haka yasa kai ya fice fadar da bai yi niyyar fita yau ba. Waziri sai ganin maimartaba yayi yana shigowa fada a matukar fusace, shikadai yake iya gane fushin mai Askira. Kyawun fuskarsa da kamalarsa kan boye fushin sa a yawancin lokuta. Yana zama fadawa suka yi kirari suka kuma basu wuri, don sun lura ya shigo fada ne kawai sabida Wazirin sa Ibrahim. "Ka fadawa 'King-makers' akwai daurin auren Yarima bayan sakkowa daga masallaci yau". Waziri yayi kabbara a fili, don ya dade yana jiran ranar da Askirama zai zo masa da zancen karin auren Yarima, yana daga wasu daga cikin labaran halin da rayuwar auren Yarima ke ciki daga abakin Awaisu, hatta zancen cire mahaifa da Aisha -Sultana ta yi ya sani, bai gayawa mai Askira bane don ya san in rashin jikoki ya ishe shi da kan shi zai magantu. "Amma Allah ya taimakeka baka ganin gara a hada masa guda uku a wanke su rana daya a kai masa? Hakan taimako ne babba gare shi a bisa nazari na na halin da yake ciki, kamar guda daya ta yi masa kadan". Askirama yayi murmushi ya dubi Waziri Ibrahim, "wannan daya ce tamkar da goma! Kuma itace maganin matsalolin Yarima insha Allahu. Tun farko ita naso ya aura ya kawo min zancen baturiyar nan, idan har ta fito daga cikin Bilkisu ina tabbatar maka karamar Bilkisu ce.....da ace Bilkisu na fara aure a rayuwata babu macen da zan kara aure". Waziri Ibrahim bai san sanda yayi dariya ba, yau mai Askira ya saki layi sabida soyayyar Fulani Bilkisu, ya manta ko da wa yake magana.... A take ya dau waya ya fara aiwatar da umarnin sarki. Kafin karfe 2 na rana duk wani da ya kwana ya tashi a garin Askira mace ko namiji ya samu gayyatar daurin auren Yarima Sageer da Sa'adatu, banda Sa'aden da uwarta dake kule kowacce a dakin ta zuciya babu dadi, ita Sa'ade halin da ta ga Fulani a ciki ne ya hanata kwanciyar hankali, tun jiya data shige daki ta rufe bata kara fitowa ba, sannnan daga ita har Fanna da Zarah tace bata bukatar ganin kowa. Abinci ma tace bata bukata tanada cake da friuts a firjin gefen gadon ta. Duk tunanin Sa'ade yafi bata matsala suka samu tsakanin ta da Askirama. Wajejen karfe daya Fanna ta shigo ta samu Sa'ade dake kwance a gado tun safe, waya take da Sa'id yana gaya mata yadda garin Abuja ya zame masa boring saboda rashin ta, maimakon tayi dariya ta bashi amsa cikin raha yadda suka saba sai tace "Sa'id, ina cikin damuwa, mamana ta shige daki ta kulle tun jiya tace kada wani daga cikinmu ya je inda take" Sa'id yace "manya kanyi irin wannan a lokacin da suke so su kebe don su samu suyi tunani ko neman mafita kan wani mhimmin al'amari da ya shafe su, so karki damu tunda kinsan lafiyar ta kalau, ita da kanta in ta samu saukin al'amuranta zata neme ku......." Fanna ta ce "ranki ya dade....ranki ya dade!" Ta cire wayar daga kunnen ta ta dubi Fanna, Fanna ta ce "lokacin sallah ya yi, ga kuma abincin ki". Sa'ade ta yamutsa fuska ta ce "maida abincin nan" "me yasa bazaki ci ba?" Inji Fanna cikin damuwa, uwa ta ki ci, 'yar ma tun safe ta ki cin komai duk sun sa ta a damuwa....Lokacin yayi daidai da bugawar dakikar agogo karfe biyu da rabi na rana, ya tafi tare da bugun zuciyar SA'ADE.... ba tareda ta sani ba, ta zama karkashin igiyoyin Yareema Sageer har guda uku. "An daura auren Yarima Sageer Yusuf Askira da Sa'adatu Hashim Askira akan sadaki lakadan ba ajalan ba.....". Abinda Fanna ta ji kenan data sako kafarta a kitchen don dawo da kayan abincin da Sa'ade ta ki ci, amma bata yarda tasu Sa'adatun bace don wani abu makamancin wannan bai taba zuwa mata a rai ba, Yarima mijin baturiya wacece zata yi gigin shiga gidan sa? Ai sai mai tsautsayi, matar da aka ce har kwalba take dagawa. Don haka ta tausayawa koma wacece wannan Sa'adatun da aka aurawa Yarima. Don daula zata samu zata shigeta iya shiga....amma tabbas ta hadu da gamon ta. Abinda Fanna ke ta fada a ranta kenan tana cigaba da ayyukan ta a kicin. Yarima yana dakin Awaisu na gidan Waziri a wannan lokacin, shima Awaisun ya zo sakamakon kiran gaggawa da Waziri yayi masa. Ya kuma gaya masa ko me kenan amma yace kada ya bari Yarima ya sani har sai an gama daurin aure, mai martaba zai gaya masa da kansa. Awaisu, kamar zai suma don dadi da farin cikin jin wadda aka zabawa Yarima, once or twice, Yarima ya taba yi masa maganar Sa'ade, yace ta iya girki sannan ga ta da hankali. Daga wannan bai kara cewa komai akan ta ba. Ya tabbata ko baya son ta zai karbeta tunda har yana yabon ta, sannan uwarta mutuniyar sa ce (Fulani Bilkisu). Bazai bada mata kasa a ido ya ce baya son 'yar data fito daga hannun ta ba. Yarinyar kawai yake tausayawa zama da Sultana amma zai nemi Yarima da ya raba musu gida don a zauna lafiya. Shi dai Yarima ya ga Awaisu sai shiri yake cikin farar shadda excelcior, yana yi yana bin waka a radio da alama cikin nishadi yake, ya ce Asiya tana jirana a cikin gida don haka na sallameka inada daurin aure a fada inna gama da ita". Yarima ya kulu da wannan kora da Awaisu yayi masa yace "ni kake kora? Daurin auren wa?" ALLAH ya taimaki Yarima wane ni in kore ku! Amma don Allah ka kara gaba ko in bar maka mukullin dakin in ka gama hirar ka rufe, inada daurin aure muhimmi". Daga haka ya sanya hularsa da takalmi ya fesa turare, ya dubi Yarima yana murmushi ganin kallon takaicin da yake masa.... dariya yayi a rans yace ka kuma zama namiji malam, a da muna maza ne tunda mai jan kunne kake aure, yanzu ne zaka san ka yi aure da matan usli da suka amsa sunan mata.... Yayi ficewar sa ya barshi kwance a gadon sa da baki sake, yana mamakin Awaisu ne yau yayi masa wannan wulakancin? Daurin auren da zai je ya fi shi Sageer muhimmanci??? **** Bayan daurin aure aka zarce da bushe-bushen algaita da kalankuwa, masu goge da masu ganguna kowa na baje kolin nasa. Gabadaya garin ya rude da hayaniya anata labarin Yarima ne aka daurawa aure da 'yar da kishiyar mahaifiyar sa ke riko, wasu na fadin 'yar ta ce data yi shegen ta kafin tayi aure (wa'iyazu billah) Allah ka kare harshenmu daga fadin gaibu, da abinda bamu da tabbas a kan shi. Wannan zance ya kai kunnen Ya Gumsu ta hanyar 'yan kanzagin ta da 'yan hana ruwa gudu, cewa ashe Sa'aden 'yar Bilkisu ce data yi shegenta kafin tayi aure aka kuma biyota da ita har gidan auren ta. Saura kadan Ya Gumsu ta haukace, ga Askirama yana fada bazai shigo ba sai bayan isha balle taje ta huce akansa. Me ya dace ta yi? Ban da ta je su yi wacce zasu yi itada Fulani Bilkisu? Shegiya a cikin iyalinta! Ai gara mata mara addinin! Yau babu ko mayafi haka ta ratsa ta tafi unguwar Fulani Bilkisu, ta wuce bayin ta da hadimai fuuuuuu! Ko gaisuwar da suke mata bata karba ba.... yau ko ita ko Bilkisu, koda hakan shine zaiyi sanadin igiyar aurenta. Fanna na kokarin fitowa da tsintsiya a hannun ta Ya Gumsu tayi ciki da ita, saura kadan ta fadi, sai wara ido take tana neman Fulani amma bata ganta ba, ta daga murya kamar zata tsaga gidan tace. "Bilkisu! Fito wajen ki na zo!" Wannan kira har cikin kwanyar Fulani Bilkisu, gabanta ya fadi ta dafe kirjin ta, Ya Gumsu ta soma dukan kofar dakin ta tun karfin ta, tana cewa "Da na ya fi karfin auren SHEGIYA kurwar mu kurr. Yadda kika lashe mai Askira shine kika kawo shegiya ta lashe Yarima? Wallahi sai bayan raina wannan auren zai tabbata...." dukan kofar take kamar zata ballata. Bilkisu jikin ta sai rawa yake hawaye na zubo mata, tana so ta fito ta fuskanci Gumsu ta fada mata 'yar ta ba shegiya bace da ubanta kuma itama bada son ranta bane amma ta san halin Ya Gumsu, zata tara mata mutanene aka, ta wulakantata gaban bayin ta, su taru su zubar da mutuncin mai Askira don ta tabbata Gumsu dambe take so su yi ba wani abu ba, ta samu hanyar lalata maganar auren, to ko za'a lalata zancen auren nan ba daga gareta ba, da Gumsu ta san halin da ta ke ciki akan auren da ta tausaya mata, itama bata so, ko kadan bata so. Saidai ta zabi farin cikin Askirama akan nata da na Sa'ade. Don haka ta daure ta cije bata fito ba, ta bar Ya Gumsu ita kadai tana ta zage-zage, bakaken maganganu ba irin wadanda bata fada akan Bilkisu ba, har da cewa da ganin ta dama an ga tsohuwar karuwa ta zo ta hargitsa musu miji bakidaya ya daina ganin kowa da gashi sai ita, duk wannan bai isheta ba ta zo ta hada auren masifa da bala'i a cikin zuri'arta, to ko zata yi yawo tsirara sai Yarima ya sakar mata 'yar ta. Kuyangi da bayin Fulani duk sun sunkuyar da kai ko motsi sun kasa, sai yanzu suka fahimci dawa aka daurawa Yarima aure, jikin su yayi matukar sanyi musamman Fanna, hawaye ta soma na tausayin Sa'ade don bata cancanci aure na rashin kwanciyar hankali irin wannan ba ko shekaru ashirin bata yi ba. Saida Ya Gumsu ta tabbatar ta gayawa Bilkisu maganganun da har ta mutu bazata manta ba, in kuma tana da zuciya to zata karbi 'yar ta daga auren Yarima sannan ta bar falon, duk wannan bai isheta ba ta so ne Bilkisu ta fito tayi mata dukan da Askirama zai kasa ganeta. Ita kuwa Sa'ade tana daki a kwance, tun shigowar Ya Gumsu data soma dukan kofar Fulani ta taka aguje ta shige toilet ta rufe kanta, a zaton ta Ya Gumsu ta samu tabin hankali ne, so yawancin duk abubuwan da take fada bata ji su ba kasancewar kofar sound proof ce. Bayan fitar Ya Gumsu data ji shirun yayi yawa sai ta fito, a guje ta nufi kofar Fulani tana kuka tana rokon ta ta bude. Kome Fulani tayi tunani? Sai kawai ta taso ta bude kofar. Halin da Sa'ade ta ganta a ciki ya matukar tada hankalinta, fuskarta ta kumbura tayi jazur idanun ta sun yi luhu-luhu. Sa'ade ta fada jikin Fulani ta wani irin rungumeta tana tambayarta "dukan ki ta yi? Is she lunatic?" Duk da halin da Fulani ke ciki sai da Sa'ade ta sanyata murmushi. Ta ja ta suka shige ciki bayan tasa mukulli ta rufe kofar. Suka zauna a tare a gefen gadon ta. "Ba duka na tayi ba, zagi na dai kawai tayi saboda an aurawa dan ta 'ya ta". Innocently Sa'ade tace "to ke ina ruwanki don an yiwa dan ta aure? Ko ke kika ce ayi masa?" Fulani tayi murmushi ta murza tausasan hannun Sa'ade cikin nata sannan tace. "Laifi na gareta shine ni na haifi 'yar da Askirama ya aurawa dan nata, bayan wannan bani da hannu a ciki". Sa'ade ta yamutse fuska tace "ban gane ba? Zarah ta isa aure ne?" Kwatakwata ta manta itama 'yar Fulani ce tsabar rudun da kalaman Fulani suka jefa ta". "Zarah kadai na haifa? Kafun in samu Zarah wa na fara samu?" Sa'ade ta luluka a duniyar a tunani, ita lallai so take ta canko wa Fulani ta haifa wanda ya isa aure amma tunanin ta ya kasa bata, domin bata ga marabarta da Zarah ba. Murmushi Fulani ta sake yi sannan ta rungume Sa'ade, "ki yi hakuri Sa'adatu kin ji? Mun yi miki laifi daga ni har Askirama, ya nemi alfarmar in bashi ke ya aurawa Yarima nikuma kinsan bazan iya juya masa baya ba. Tunda daga ni har ke zamansa muke yi cikin gidannan mu abin ikon sa ne, sannan in da halarci ko mahaukaci Askirama ya kawo yace ki aura daga ni har ke mun isa mu ce a'ah? Balle dan cikin sa mafi soyuwa a gareshi?" Sa'ade sauraron ta take absent-mindedly tana hada daya da biyu domin ya bata ma'ana. Aure.... ita da Yarima......Yarima wanne? YARIMA! Yarima!! Yarima!!! Shikadai ne mai wannan sunan duk masarautar Askira. "Don Allah Fulani ki fiddani duhun da kalamanki suka sanya ni.." ta fada cikin karkarwar jiki data murya. Ta kama hannuwan Fulani biyu ta rike tamau a cikin nata. Fulani ta ga wannan shine lokaci mafi dacewa da zata gayawa Sa'adatu komai, tunda bakin alkalami ya riga ya bushe. Tiryan- tiryan ta gaya mata mafarkin da Askirama yayi akan ta da yadda ya roketa ta bashi aurenta....da kuma auren da aka daura dazu....."Shine fa Ya Gumsu ta zo tana wannan jidalin". Ita dai Fulani ta san Sa'ade na sauraron ta amma bata san lokacin da ta fado jikin ta yarab! Cikin hali na unconsciousness......kamar suma, kamar fita hayyaci, cikin biyun bata san wanne Sa'aden ta ke ciki ba. Sai ta rungumeta tana kuka abin tausayi ta rasa wane irin taimako ya kamata ta bata.... MASARAUTARMU! Ba ta taba jin tausayin Saade da soyayyarta ba irin yau, yau din da ta tabbatar sun kusa rabuwa, rabuwa ba ta aje a dawo ba, aah rabuwa irin ta kowacce diya mace da iyayenta idan munzalin aure ya riske ta. Fulani ta rasa taimakon da za ta bai wa Saade da ke kwance a jikinta numfashinta na shirin barin gangar jikinta. Ta san Saade za ta razana in ta ji zancen nan, amma ba ta zaci har haka ba. Abin da ba ta sani ba shi ne, Saade ta san sirrin Yarima, ta san na matarsa Aisha-Sultana, tana kyamar dabiunsu na sabon Allah fiye da yadda ba a zato. Hakan kuma bai hana ta ganin wani irin girman Yareema Sageer ba, da kimarsa cikin idanunta, saboda iyakar kyautatawa a zamanta tare da su Yareemah ya yi mata. Amma kalmar AURE a tsakaninsu, ai is underestimated. Wani abu ne da hankalinta da tunaninta ba zai dauka ba. Kullum kallon kanta ta ke yarinya karama tamkar Zarah. A aura mata Uncle Yareema ta kai shi ina? Matarshi ta sha giya ta yi mata shegen duka ko kuwa za ta iya manta kalmar zina' da Sultana ta ce yana yi? Duk da ba ta gama sanin mene ne ainihin maanar kalmar zina ba, amma ta fahimci wani abu ne mummuna, abin kyamata a addini da alada, kuma da shi za ta ke kallon Uncle Yareema in har ba ta samu tabbacin ya tuba ya bi Allah ba daga bakinsa. Ba ta taba kawo wa ranta aure a nan kusa ba, karatu ta ke so, shi ne kuma burinta, sannan tana matukar jin dadin abunta, yau da ba Askirama ne da kansa ya yi mata wannan yankan kaunar ba, cewa za ta yi ba ya kaunarta don ba shi ya haife ta ba. Amma ta sani, ta kuma amince kaunar da Mai Askira ke mata daga Allah ne. ba zai taba yin wani abu da niyyar cutar da ita ba, amma har abada zuciyarta ba za ta yi amanna da auren Uncle Yareema ba. Kamar yadda ba za ta iya karbarsa a matsayin miji ba. Ba gara mata auren Saidu ba in ma auren ya zama dole? Shi ne tsaran aurenta. Fulani robar ruwan faro ta dauka ta yi ta shafa mata a fuska, wuya zuwa kirjinta. Ba ta fasa ba sai da ta ji Saade ta saki nannauyar ajiyar zuciya. Ta kara langwabewa a kafadar Fulani ba ta kara dagowa ba. Duk suka yi shiru cikin wannan yanayin, kowanne da abin da yake sakawa a zuciyarsa. Zuwa can Saade ta yi magana a hankali. Ni bana son Uncle Yareema Fulani, kamar yadda Mamanshi ba ta sonki. Ki ba wa Maimartaba hakuri, ba zan iya ba. Ta soma wani irin kuka a hankali mai girgiza zuciyar mai sauraro, balle kuma zuciyar UWA! Sosai kukan na Saade yake motsa zuciyarta. Ta shafa kwantaccen gashin kan Saade da hannun damanta ta ce. Saadatu, me zan yi in faranta miki? Ki fadi ko mene ne, amma ban da cewa ba za ki yi auren nan ba. Bakin alkalami ya riga ya bushe. Laifi kan laifi mun yi miki ni da Askirama, ina rokonki ki dubi Allah da darajar da Allah ya bai wa iyaye a kan yayansu, ki dubi karamcin mai Askira gare ki ki yi hakuri ki yi hakuri ki yi hakuri ki bar wa Allah komai. Saade ta ce, Ta ya ya zan zauna da shi mahaifiyarshi ba ta sonki? Ni ma bana sonshi, matarsa ba ta sona. Komai na rayuwarsu daban yake da tawa. Fulani yadda ake shan ruwa a firji haka ake shan giya a gidan nan kuma kuma Ta kasa cewa ZINA don sai ta ji kalmar ta yi gundumemiya a bakinta ta alakanta ta da Uncle Yareema, saboda cikar kamalarsa da cikar zatinsa kadai yana hanawa ka alakanta shi da kowanne irin aibi Kin taba jin kishiya ta so kishiya ne Saade? Don haka ki cire wa kanki damuwar wai Gumsu ba ta sona. Yanzu matsayin uwar miji ta ke a gare ki, ki yi duk iya yadda za ki iya wajen kyautata mata. Sauran lamarin sai ki bar wa Allah. “But I dont love him Fulani, ina da saurayi na dan ajinmu da na ke so, sunansa Saidu Ki san abin da za ki dinga fada, don ke matar aure ce yanzu. Mace kuma addini bai bata damar ta so kowa ba ko da kuwa da fatar baki ne sai mijin aurenta. Ki gaya min me ki ke so in yi miki in faranta miki ki saki ranki ki manta da komai? Ki sa a ranki babu wani bambanci tsakanin rayuwarki ta da da ta yanzu. As if normally makaranta za ki koma ki ci gaba da karatu, ni kuma zan tsaya in ga cewa Yareema bai hada ki gida daya da Aisha-Sultana ba, kin san yana jin maganata. Sannan zan roke shi ya daga miki kafa har ki kare karatu, in ba zai iya hakan ba ya kara mata ta uku. Saade kamar ta fashe da kuka saboda ita yanzu ko sunan Yareema ba ta son ji. Ya shigo rayuwarta unexpectedly ya rusa ta. Duk burinta na yin karatu mai zurfi ba a yi shawara da ita ba an kakaba mata aurensa. Yariman da ta tabbata yana neman mata. Laifin me ta yi wa Fulani da Askirama da zasu rasa wanda zasu aura mata sai Yarima Sageer? Ta mike za ta bar dakin idon ta fal hawaye Fulani ta sake riko ta tana murmushi. Ba ki gaya min me zan yi miki ba a matsayin gift dina na aurenki. Saade ta ce, Fulani ni me ye nawa a ciki da har sai an ba ni gift? Ai ba'a nemi yardata ba kafin a daura don haka bana bukatar kowanne gift din ki Fulani ta danne dariyarta duk wani tension da ta ke ciki shirmen Saade ya sa ya tafi, ta ce, matsayinki na babbar kanwar ango. Saade ta kyabe baki ta ce, Yana da kannensa su Humaira yan gayu, ni in kina so ki faranta min kawai ki sa a kai ni Tsanyawa in ga Hanne da Innarta, Baba Saleh da Inna Laure. Ta yi ficewarta zuwa nata dakin, ta bar Fulani cikin tunani. Hakika ta yi kuskure da ba ta kara kai Saade Tsanyawa ba, wajen bayin Allahn da suka sada ta da ita. Da kuma matar babanta, duk da Saade ta ce ba zaman dadi suka yi ba, amma dai ai ta rike ta komai lalacewar riko a lokacin da ita ta yasar da ita. Ta kudire a ranta za ta faranta wa Saade da wannan kuma za ta nemo mata wan mahaifinta Kyari da yarsa Rahima kawarta duk da ba ta da tabbacin da gaske Rahima yar Kyari ce ko ko kamanni ne kawai da suna ya zo daya. A take ta kira Askirama a waya kasancewar ba girkinta ba ne. Ta gaya masa tunanin da ta yi, ya ce shi kuma ba zai kai Saade gidan Yarima ba sai ya nemo Babagana Kyari, sai ya aika an dauko Baba Saleh da iyalinsa don ya tabbatar wa Ya Gumsu cewa, Saade da asalinta. Ba don ya sassauta kiyayyarta ga auren ko ga Saade ba, sai don ya cika farin cikin Bilkisu da yarta. A koina Mai Askira yana da mutane, daga bayanin unguwar da Kyari ya zauna a Damaturu daga bakin Fulani ya bi ya dinga tracing labarin Babagana Kyari. Mutanen unguwar suka tabbatar masa Kyari da iyalinsa sun dade da barin Damaturu zuwa garin Maiduguri inda Babagana Kyari ke kasuwancinsa na fata, har gidansa na Maiduguri sai da aka binciko, inda makwabtansa suka tabbatar da cewa Kyari da iyalinsa suna kasar Italy kwata-kwata inda yake sanaar kai fatu. Mai Askira bai gushe da ci gaba da tracing Kyari ba har sai da wani abokinsa ya bada lambar wayarsa ta kasar Italy, kuma a daren shi da fulani suka yi zaman kiran Kyari Babagana inda suka yi magana a handsfree baki da baki shi da Bilkisu. Ta cikin wayar Kyari yake kuka da ya ji mutuwar dan uwansa Hashimu, ya ce Ba yadda ban yi da shi ba ya dawo gida ya ki, wai tunda kin guje shi ba shi ba Damaturu. Na ce ya ba ni yar in rika, Hashimu ya ce mai raba shi da yarki sai mutuwa. Ashe kuwa ita din ce za ta raba su, daga baya na bi bayansa har Kano inda ku ka zauna ban tadda shi ba, aka ce bayan kun rabu ya koma wani kauye da yarshi, kauyen da har yau nake bincike Allah bai ba ni ikon sani ba. Ina fatan yar tawa tana lafiya, kuma ya ya sunanta? Fulani ta gaya masa sunanta Saadatu, sannan cikin jin kunya ta ce, Mai Askira ya daura mata aure jiya, da Dan wajensa Yareema Sageer. Askirama ya karbi maganar da cewa, Ka yi hakuri na yi maka shisshigi, ya kamata a ce ni na fara nemo ka kafin daurin auren hikimar hakan ba ta zo min ba har sai da Fulani ta ankarar da ni. Ka yi hakuri, ka yi hakuri, na yi gaggawa ga sadakinta nan na damka wa Bilkisu na warawaran danyar gwal guda shida. Alhaji Kyari Babagana ya yi murmushi, ya ce, Its a pleasure meeting you your Royal Highness the Emir of Askira. A yi min alfarmar kara sati daya kafin a yi bikin yata Saadatu, don ni da uwarta da yan uwanta mu samu halarta. Da sauri Askirama ya ce, An yi wannan alfarmar, na sanya har sati biyu biki da tarewa, don bikin da ban yi a auren Yarima na farko ba shi zan yi a yanzu, tunda yanzu ne na san Yarima ya yi aure irin wanda hankalina ya kwanta da shi, kuma na yarda da shi. Matarshi ta farko daga Asia ya kawo ta. Sun dade suna tsara abubuwa na yadda bikin Saadatu da Yarima Sageer zai kasance kafin su yi sallama. Maimartaba ya dubi Fulani tana hamma, ya ce, me ya hada ki da Gumsun gari? An gaya min wasu maganganu marasa dadi wadanda ban yi zato daga gare ku ba. Fulani ta tabbatar ba wanda zai kawo wannan gulmar sai Fulani Hibbani uwar tsugudidi, Allah kadai ya san iya abin da ta gaya masa. Ta yi kwafa sannan ta ce, Ni da idanuna ban ga Ya Gumsu ba, kusan watanni shidda kenan. Amma na ji an ce ta zo nemana ina barci. Bayan wannan ban san wani ba kuma. Maimartaba ya jinjina kai, amma bai ce komai ba. Ya san Bilkisu ba za ta yi masa karya ba, amma maganganun da Hibbani ta gaya masa sun tayar masa da hankali. Cewa ta yi, Ya Gumsu da Bilkisu sun yi dambe a gaban bayinsu da kuyangi. Bai yi wa Gumsu maganar ba don tun artabunsu akan maganar auren rabonta da sake tako kafarta turakarsa. Yanzu abin da ya sa a gaba shi ne, ta yadda zai fuskanci Yarima da maganar, ya hana Awaisu gaya masa, ya ce shi da bakinsa zai gaya masa ta hanyar da za ya fahimta. Yarima bai san wainar da ake toyawa ba, domin bayan rabuwarsu da Awaisu a ranar Maiduguri ya tafi, akwai wani project da yake rubutawa zai yi bincike a UNIMAID, wanda zai dauke shi har tsayin kwanaki uku. Bincike ne da yake bukatar nutsuwa (applied research) a fanninsa don haka ya kashe wayarsa. A daren ranar aka yi ta tura masa text na taya murna da fatan alkhairi ba tare da ya sani ba, don duk wayoyinsa ya kashe su. Ya tattara hankalinsa kan abin da yake yi, yana gidan saukar baki na jamiar Maiduguri. Awaisu ne kadai ya san inda yake. Kwanansa biyu kawai sai ga Awaisu. Har masaukinsa ya je, Yarima zaune cikin tattausar kujerar leather ta falon masaukinsa yana kurbar lemun Don Simon a cikin tambulan, ya dubi Awaisu wanda bakinsa ke ta motsi yana yan mutsu-mutsu wadanda Yarima ya riga ya gama gane su. Akwai abin da ke faruwa wanda ba ya son gaya masa idan yana irin wannan mutsu-mutsun. “You better be comfortable, wannan mutsu-mutsun naka da magana Dariya Awaisu ya yi ya ce, Me ya samu wayoyinka na kasa samunka? Shi ya sa fa na zo da kaina. Tunda na zo ban kunna su ba, ina da muhimmin project a gabana, amma dama yanzu zan dan kunna in ji lafiyar Saadatu. Tunda muka zo ba mu kara haduwa ba, kuma ni nan da kwana uku zan koma Abuja, ina so in ji yaushe za ta koma sai in dawo in dauke ta. Awaisu ya tsura masa ido yana son karantar wani abu game da shi a kan Saaden, bai fahimci komai ba, ban da seriousness irin na Sageer da wuya ka iya karantar abin da ke zuciyarshi. Maimartaba ya ce, in zo mu taho ni da kai yanzun nan. Cikin mamaki Yarima ya ce, Lafiya? Sai dumbin alkhairi. In ji Awaisu, Amma a yammacin nan mu kama hanyar Askira is too late, ka yi hakuri ka kwana zuwa gobe, sai in tattara hankalina waje daya in kammala aikina a daren nan da safe mu kama hanya. Awaisu ya ce, Zan bi shawararka ne only in ka amince za ka jinkirta kiran Saadatu har sai ka fara ganawa da Maimartaba ko in ce ka yi hakuri da kunna wayar zuwa goben after encounter dinku da Maimartaba Kokari yake ya fahimci me Awaisu ke son boye masa ta hanyar kura masa ido, kuma sai kawai ya ji gabansa ya fadi. Wani abu ne ya faru da ita? Ya tambaya in subdued (cikin karayar murya). Awaisu ya gyara kwalar rigarshi yana murmushi, ya ce, Ita wa ke nan? Ita Saadatun da ka ce kada in kira. Ya fada cikin daure fuska don ya kasa gane inda Awaisu ya dosa. Awaisu ya sake sakin murmushi, in dai wannan damuwar da ya gani kwance a kan fuskar Yarima a kan Saadatu ne, to insha Allahu komai zai zo wa Maimartaba da sauki, Yarima ba ya taba damuwa da lamarin wanda ba ya so, ko da kuwa ba so ne na soyayya ba, to akwai alamun shakuwa da aminci. Babu abin da ya faru da ita, tana dakin uwarta. You better call your wife not Saadatu, bana tunanin tunda ka zo ka kira ta. A hakan ake mana ikirarin duk duniya ba wadda ake so sai ita. Ita ma ko za ka kira ta, to fa sai gobe, in ka fito daga turakar Maimartaba Ya fada yana dariya, tare da kwashe wayoyin Yarima guda uku da ke bisa center table din gabansa, ya zuba a aljihun jamfarsa. Ya zabi daki daya cikin 3 bedrooms din da ke falon ya shige yana ce da Yarima, Lemme take a shower, ko na samu saukin gajiya ta. Yarima ya bi shi da kallo, ya kasa cewa komai, lamarin Awaisu sai shi. Sai ya dauki kan telephone ya yi dialling lambobin da yake bada umarnin a kawo masa abinci, ya yi wa Awaisu odar abin da zai ci. Daga haka ya maida hankalinsa kan macbook dinsa yana ci gaba da abin da ke gabansa. Sai dai kuma duk hankalinsa ya rabu biyu, jikinsa ya ba shi akwai muhimmin abin da ke faruwa a cikin gida da Awaisu ba ya son gaya masa, ya fi so ya ji kai tsaye daga bakin Maimartaba. Kuma da kyar in alamarin bai shafi Saadah ba, in ba haka ba don me Awaisu zai ce kada ya kira ta? Yana aiki yana ta tunane-tunane, duk a kan Saadatu da alamarinta da ya yi wa zuciyarsa karan tsaye, ya hana shi sukuni ya kuma hana shi enjoying komai da yake yi sabida rashin ganinta cikin kwanakin nan, sai dai ya kudire a ransa suna isa Askira da ya ga Maimartaba zai je har unguwar Fulani Bilkisu don kawai ya ga Saadatu. ****** Suna kwance a bayan mota 4-matic mai dauke da rubutun ASKIRA EMIRATE, direba na ta sharara gudu don su isa Askira cikin lokaci, ta garin Damaturu suka bi, duk da ta fi nisa amma ta fi lafiya sabida insurgency da ya fara kafuwa a daidai lokacin a jihar Borno. Zuwa Askira ta Chibok bai yiwuwa dole sai an bi ta Damaturu. Duk hirarrakin da Awaisu yake masa don ya dauke masa tunani ya ki kulawa, jikinsa ke ba shi kawai, theres something fishy going on akan Saadatu da har ya sa Maimartaba ya yi masa kiran gaggawa. Ana kiran sallar magriba suka shiga Askira. Inda Awaisu ya ji dadi shi ne kafatanin fadawa da dogarai da duk wanda ke wajen ya shiga masallaci sallah lokacin da suka iso, ba don haka ba da tun fitowarsu mota za a fara tarar Yarima da Allah ya sanya alkhairi. Yan tsirarun da suka hadu da su a hanya mata ne bayi suke wucewa. Gaishe su kawai suka yi suka wuce. Suna shiga sassan Yarima da ke cikin gidan alwallah suka yi suka tada sallah, kafin su idar hadiman Yarima sun gama jera musu abinci. Awaisu ne kawai ya zauna yana ci, Yarima sai magiya yake masa ya ba shi wayoyinsa yana cewa, sai ya fito daga ganawa da Maimartaba. Kawai sai jin sallamar Ya Gumsu suka yi a kansu, karkashin rakiyar kuyanginta. Daga bakin kofa suka tsaya ita kadai ta shigo sai huci ta ke kamar mesa. Yarima da Awaisu suka mike tsaye a tare har suna hada baki a tare wajen cewa, Ya Gumsu lafiya?? Kawai sai ta zauna a kujera ta sa fuska cikin tafuka ta fashe da kuka. Yarima da Awaisu suka tsugunna a gabanta suka kasa magana, suna nan durkushe gaban Ya Gumsu tana kuka suka jiyo takun tafiyar Askirama. Daga kirarin da ake masa daga waje suka gane shi ne yake tahowa. Ya karaso har dakin Yarima bakinsa dauke da sallama. Idonsa ya sauka a kan Ya Gumsu, ransa ya yi mummunan baci, da kyar in ba ta lalata komai ba. Biyo ni Yarima. Abin da ya ce kawai kenan ya juya ya fita. Yarima ya kasa tashi daga gurin ya bar Ya Gumsu da ke kuka har sai da ta dago idanunta jage-jage da hawaye, ta ce, In ka karbi auren nan da ya yi maka sai na dauke maka albarka. A razane Yarima ya cira kai ya dubi mahaifiyarsa, kafin ya samu zarafin ce mata komai ta tashi ta fice kamar kububuwa. Yarima ya shiga cikin halin rudu mara misaltuwa. Kawai sai ya bi bayan maimartaba ya bar Awaisu a wajen. Awaisu ya jinjina kai cike da taraddadin wannan alamari, bai yi zaton ya Gumsu ba za ta so auren nan ba in ya yi laakari da yadda ta ke adawa da auren Yarima na farko. Da ya tuna kishin da ke tsakanin matan gidan sai mamakinsa ya ragu, don Saadatu ta fito daga dakin Bilkisu ne wadda suke kishi da ita fiye da kowacce matar sarki. Yarima bai zauna ba sai da Askirama ya fara zama a kujerar mulkinsa. Ransa a tsananin bace don a zatonsa Ya Gumsu ta riga ta yi masa riga-malam-masallaci. Ya yi kokarin boye bacin ransa sabida ba ya taba bari a gane fushinsa, ya dubi Yareema Sageer da ya samu wuri ya zauna daga kasan kafafunsa. Kafin in ce komai Yareema idan na yi maka umarni, uwarka ma ta yi maka, na wa za ka bi a cikinmu? Yarima ya kara rudewa, gabadaya sun rikita shi, ya kasa gane komai. Kawai sai ya yi shiru ya sunkuyar da kai. Mai Askira ya yi murmushi ya ce, Aure na yi maka shi ne ta ke adawa, aure na mutunci da rufin asiri, auren da na tabbatar zai dauke dukkan kwadayi da shaawarka daga kan sauran mata kamar yadda ya dauke nawa daga kan Bilkisu ko kwarkwarorina na hakura da su daga ranar da na mallaki Bilkisu, domin matan BAGGARA daban ne. Don haka ne nake da kyakkyawan zaton cewa abin da ta haifa ma zai zamo irinta ga Sarki mai jiran gadon Askira. Na aura maka diyar Bilkisu, wato SAADATU don in raba ka da kusantar zina da matan haramun. Ya rage naka ka bi umarnina ko na mahaifiyarka. Ka tashi na sallame ka, ka je ka yi tunani kan abin da ya fi dacewa da kai. Rana ita yau za a fara biki, biki irin wanda ba a yi a aurenka na fari ba, bikin aladar gargajiya na masarautar Askira. Na kai shi zuwa rana ita yau ne don kawunta da ke kasar Italiya ya samu halarta shi da iyalinsa. A nan Maimartaba ya gaya wa Yarima labarin asalin Saade, tun daga auren mahaifiyarta da Malam Hashimu zuwa rabuwarsu. Rayuwar Saade a kauye da ranar da abokin Babanta Malam Saleh ya kawo ta Askira ya karbe ta, wahalar da ta sha a hannun fulani kafin ta amshe ta matsayin ya, da nagartattun halayen Saade da ya dade yana fahimta. A karshe ya gaya masa tun farko ya yi niyyar aura masa Saade a matsayin matarsa ta farko sai ya kawo zancen Aisha-Sultana, shi kuma ya ba shi dama don ya fita hakkinsa. Yanzu ne yake so ya yi masa biyayya da auren Saade, duk abin da suke ciki shi da matarsa ya sani, kuma wannan shi ne matakin da zai iya dauka. Ga mamakin Mai Askira tunda Yareema ya dukar da kai bai dago ba sai da ya kai aya, da ya dago idanunsa sun kada sun yi jazur kamar an gumbuda musu borkono, labarin Saade da ya ji daga bakin mahaifinsa ya gama kashe zuciyarsa, ya luguiguitata. Tun asali kuma ya dade da wani irin feelings a kan Saadatu wanda daga shi sai Ubangijinsa suka sani. Feelings din da shi kansa bai san ma'anar sa ba, bai san a muhallin da ya sanya shi ba. Yau da ya samu wannan labarin na zamowar Saadatu halalinsa, matar auren sa ta sunnah daga bakin da ba zai taba yi masa karya ba, zuciyarsa ta ki tsugunnuwa a waje daya, sai dawurwura ta ke a cikin kirjinsa kamar za ta fito ta bakinsa tsabar contentment din da ya cika zuciyar sa da wani sabon yanayi da ya samu kansa a ciki irin wanda biro ko yawun baki ba zai iya bayyanawa ba. Lokacin da Yarima ya dago ido don ya baiwa mahaifinsa Askirama amsa, Askirama couldn't believe cewa hawaye ya gani a idon Yarima...... Hawayen da bai san na menene ba, tsakanin.... bakin cikin abin da ya yi masa, tausayin labarin Sa'ade, ko ko na farin - ciki ne kai tsaye? Ba zai iya cewa ba!!! Mu karasa a littafi na 3. Na yi muku alkawarin cigaban ba zai jima ba, insha Allahu. Taku har abada; Sumayyah Abdulkadir Takori. 27th August, 2021 MASARAUTAR MU!. 3 SUMAYYAH ABDULKADIR takorikabara@gmail.com babbangoro2015@yahoo.com SADAUKARWA Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare.Muna son ki Hasna. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. MASARAUTAR MU 3 Cikin raunin murya marar amo da rashin karsashi kamar ta wanda ya sha duka sabida yadda tayi kasa sosai, Yarima Sageer ya duka gaban mahaifin sa Askirama tamkar zai shige cikin sa, ya soma magana cikin sanyin murya da hardewar harshe. Allah Kawun jo (Allah ya baka yawan rai) amma me ya sa tun lokacin da na dawo daga Amsterdam din, na kuma zo da bukatar auren Sultana baa tambayi raayi na a kan Saadatun ba? Allah ya ja da ran ku da a ce kun bayyana min kudirin ku akan mu tun farko, tun a wancan lokacin, a kan zabin da ku ka yi min, zan hakura ne da nawa zabin duk son da nake masa in karbi zabin ku. Saboda na san duk wani hukunci da za ku yi a kaina alkhairi ne wanda ni duk yawan shekaru na ba zan taba iya hangowa kaina ba!!!. Sai hawaye suka fito sharr! Daga idanun Yareema Sageer, wadanda a yanzu Askirama ya tabbatar na farin-ciki ne ba na komai ba; hawayen wani irin contentment da Dr. Sageer bai taba ji a rayuwarsa ba. Sai ya ji rayuwarsa a yau ta cika, ta zama cikakkiya, duk wani gibi dake cikin ta ya cika, amma a baya incomplete yake jin ta somehow shattered. duk da tarin dimbin achievements din da ke cikin ta. kamar akwai wani wawakeken gurbi a can kasan zuciyar sa da a da can, yake jira a cike, gurbin da bai san ko na menene, ko kuma na wanene ba, ya samu aka cike masashi yau unexpectedly. A yanzu ya gane cewa ya jima yana jiran shigowar Sa’adatu cikin rayuwar sa, he'spatiently waiting for her to come to his life ba tare da ya sani ba, sai a yau ya gane hakan. A can baya kafin zuwan wannan ranar jin sa yake tamkar bashi da komai tamkar bai taba mallakar komai a rayuwar sa ba, duk da ba abinda bai mallaka din ba a rayuwar tasa including ASIAN WIFE. Amma a yanzu da yake durkushe gaban Mai Askira yana yi masa wannan bushara sai yaji tamkar Askirama ya mallaka masa dukkan mulkin matan duniya, da mulkin dake cikin duniyar, mulkin da ya fi na garin Askira girma da ilahirin El-Kanem Borno Empire, da duk wani nau'in farin cikin dake cikin duniya da dan adam ke burin samu da ya mallaka masa Saadatu diyar Bilkisu da Mallam Hashimu. Na gode da wannan gatan Mai Askira, Nagode ZAKIN Askira, ina mai rokon Ubangiji da ya fi ni godewa, na kuma karba da hannu bibbiyu. Ina rokon Allah Ya sa daga yau ba za ku sake jin wani abu a kaina wanda ya jibinci laifuffukana na baya ba. Hakika na sani Askirama ni Sageer mai yawan laifi ne, mai saba muku ne, mai ketare tarbiyyar da kuka yi masa, amma hakan bai sa kun yi fushi da ni ba, kullum burin ku da fatan ku shine in dawo hanya madaidaiciya, wanda hakan yasa a kullum nake cikin tuba da neman gafarar Ubangiji. Ina rokon Allah ya fidda ni kunyar ku, Ya ba ni ikon rike muku yar ku da amana. A yi min godiya wurin Fulanin Sarki (yana nufin Fulani Bilkisu), kodayake bari in je in same ta da kaina. Askirama sai gani ya yi Yarima Sageer ya mike cikin wata irin azama, jikin sa har bari yake, gabadaya ya zama ba cikin nutsuwar sa ba, ya rude saboda excitement din da ya samu kan sa a ciki. Wanda Mai Askira zai iya rantsewa bai taba ganin sa cikin kwatankwacin irin wannan farin-cikin ba. Sai Askirama ya mika hannu ya kamo hannun sa, kada ya je ya yi abun kunya a gaban bayi da kuyangin Fulani Bilkisu, kuma dai Fulanin ta gaya masa Saade ta dau fushi tun jiya ta kulle kanta a daki. Wanda ke nuna ita bata murna da auren ko kadan. Kamar yadda nasa dan ke neman shidewa sabida farin-cikin hakan. Zo zauna in kirawo Fulanin ka yi mata godiyar nan a gabana, kada ka je sassan ta yanzu har sai bayan biki. Baa zuwa. Zuwa lokacin Saadatu ta huce daga laifin da muka taru muka yi mata. Yareema ya yi murmushi yana sosa kai, laifi? Auren sa ne ya zamo laifi ga Saade? Kodayake bai kamata hakan ya zamo abin mamaki ba a gare shi duba da cewa daga shi har ita respect ne a tsakanin su, babu wata magana bayan wannan, koda ace akwai din ita a gareta babu komai tunda bai taba furta mata ba, ko nuna wata alama da zata gane cewa he sincerely admires her tun farkon rayuwar ta a gidan sa. A lokacin suka hada ido da mahaifin sa wanda ya kura masa ido kawai yana murmushi, yana karanto duk abinda yake son karanta. Yareema Sageer yayi hanzarin dawowa daga duniyar tunanin da ya fada cikin jin nauyin kaifafan idanun Askirama. Kada dai ya zamanto cewa Mai Askira ya gane a rude yake gabadayan sa? Kuma already a rijiya yake? A rayuwar shi babu farin cikin da ya taba ruda shi irin na yau, kai mawuyaci ne wani abu yasa ya kasa mallakar kan sa amma yau? Saadatu a matsayin matar sa! Wani al'amari ne da bai zata ba. It comes abruptly. And it touches him more than he can imagine. Wani abu ne da bai taba kawowa zai samu da sauki haka ba, duk da zuciyar sa ta dade tana buri, kwakwalwar sa na kiyasta masa, ruhin sa na kwadayi da mafarkin kasancewar hakan. Ba don bashi da gatan samun ta ba, sai don yana ganin hes not worth enough ga mallakar ta matsayin mata, in yayi laakari da tarin aibubbukan sa. Maimartaba ya kira Fulani ta wayar hannun sa, suka yi magana ya aje, ya dubi Yarima wanda jikin sa ke ta (tsuma) ya kasa nutsuwa a waje daya, ya zama very upset, bai taba ganin dan sa Sageer cikin kwatankwacin irin wannan halin ba.. daga haihuwar sa har girman sa. Wanda ke nufin....(already Sageer na son Sa'adatu)!!! Ba abin da ya furta a zuciyar sa sai godiya ga Ubangijin talikai, ya ce da Sageer a hankali cikin muryar sa ta girma da sanyawa dan adam nutsuwa, yana murmushin kasaita irin nasa ta kyakkyawan gashin bakin sa da farin gemu ya zagaye; Be a Prince!". (Wato ya koma Yariman sa). Yareema ya dafe goshin sa yana yar dariya da jerarrun hakoran sa bakidaya a waje, wannan ma wani abu ne da Mai Askira bai taba gani ba, iyakacin sa murmushi ga duk abinda yayi impressing din sa, sannan ya kuma koma cikakken Yariman sa ta hanyar kokarin sarrafa kan sa da komawa cikin nutsuwar sa. Sai ga sallamar Sarauniya Fulani Bilkisun Askirama cikin kwalliyar ta ta kasaita, ta shigo ta kofar da suka saba shigowa bangaren Askirama ita da sauran matan sa, kowacce akwai kofar da ta bulla unguwar ta, zuwa turakan Mai Askira. Takun ta kadai abin kallo ne ga mijin ta. Yarima na ganin shigowar ta ya dukar da kai kamar tsohon da ya yi wa sarki karya. Surukuta sosai yake nunawa yau ga Bilkisu. Bai taba jin kunyar ta matsananciya ba irin yau. Kafin zuwan wannan ranar, jin ta yake kamar Yayar sa Yaa Maira, ba matar mahaifin sa ba. Alal hakika yana son matar nan ba tun yau ba, sau-tari, mantawa yake kishiyar Ya Gumsu ce sabida kirkin ta, mantawa yake da duk wani sabani da ke tsakanin ta da mahaifiyar sa sabida son da yake mata da kulawar da itama take bashi. Ashe Allah ya rubuta Kakar yayan sa ce masu zuwa nan gaba cikin kudurar Ubangiji. Jinin su ne zai zo ya cakude wuri guda ya kara binding din su together. A can gaba. Ya kara dunkule su matsayin iyalin Sarki Yusufu Mai Askira. Ya kara nutsuwa a wurin da yake tankwashe zaman Rakuma akan kafafun sa, sannan ya gaishe ta da sassanyar murya, bayan ta zauna kusa da Mai Askira tana zolayar sa. Ango! Ango ka sha kamshi. In ji Fulani cikin murmushi. Maimartaba ya juya gare ta yana tambayar ta, “Fulanin Askira Me ku ke shiryawa ne game da biki? Fulani Bilkisu ta gyara zama,sannan ta kaskanta murya cikin yanayin ladabin da Askirama kadai take yiwa magana da shi ta ce. Alanguburo, ai ni rabon da in ga Saade tun jiya da na gaya mata. Ta shige daka ta kulle kofarta, watakila idan ta ji mutanen Tsanyawa sun zo ta bude, kuma dai dama bukukuwan gidan nan Ya Gumsu ce ta ke tsara su ga shi kuma tana fushi da ni a kan laifin da babu ruwa na. Maimartaba ya ce, Zan turo Yaa Maira (babbar yarsa) ku tsara komai, Murjanatu ma tana kan hanya za su zo su same ki. Wannan kiran kuma na Yarima ne ba nawa ba, shi yake son ganinki, zai bi ki unguwarki na ce ya bari in kirawo ki nan, na ga yana ta bare-baren jiki kada ya je ya yi abin kunya a gaban bayi. Dariya Fulani ta yi, shi kuma Yarima ya kara dukar da kai, murya a raunane ya ce. Fulanin Maimartaba, Allah ya baki yawan rai, na gode. Allah ya jikan magabata, insha Allahu ba zan ba ku kunya ba. Na karbi auren Saadatu da hannu bibbiyu. Allah ya ba ni ikon yin adalci a tsakaninsu. Sosai Fulani ta ji dadin kalaman Yarima Sageer, suka wanke damuwarta kaso hamsin cikin dari na tunanin Yarimazai wulakanta mata Saade tunda yar talaka ce kuma yana da mata Baturiya, damuwar hakanta ragu daga ranta, don ba ta zaci haka zai karbi maganar ba with due respect, tunda uwar shi ma ba ta so. Ta ce, Da kai da Saade duk daya ne a wurina Yarima, kamar yadda Askirama bai taba bambantata da ku yayan da ya haifa ba. Rokona daya gare ka Yarima ina so ka raba musu gida, sabida Saade ba za ta iya zama waje daya da Aisha - Sultana ba, shekarun su, tunanin su, akidunsu da halayyar su ba zai taba zuwa daya ba. Ka ga kuwa zama da juna zai musu wahala. Ya saci kallon Askirama ta kasan idanun sa,sabida tsoron ko ya ji abin da Baggarar matar san nan ta ke fadi? Sai ya ga hankalin shi ba ya kan su sam, waya yake yi ma da yar sa Yaa Maira lokacin, wadda ke aure a masarautar Biu. Tana gaya masa cewa sun taso suna hanya har sun wuce Maiduguri. Wani sigh of relief Yarima ya sauke da ya fahimci Askirama bai ji ta ba. A ran sa fadi ya ke na tabbata sanda aka yi miki aure da Baban Saade baki yi girman ta ba kuma kin haifeta lafiya. A fili kuma ya ce, Insha Allah zan nema mata nata muhallin, daya bukatar kuma zan duba insha Allahu ran ki ya dade. Ai ba abinda zai gagara. Da wannan ya yi musu sallama ya mike zai fita. Sai Askirama ya sake yafito shi. Be a man also, after being a Prince (ka zama namiji bayan zama Yarima) wanda ba mai iya juya raayin sa, wanda ya san cewa mata da karkataccen haqarqari aka halicce su tunanin su ba kamar na maza bane, ka san yadda za ka lallaba mahaifiyarka har ta sauko daga dokin fushinta, ta karbi Saadatu matsayin diyar ta, ta sanyawa auren ku albarka. Tashi ka je ku tsara komai kai da Awaisu. Allah ya yi wa rayuwarku ku duka albarka. ***** Yaa Maira ta iso daga masarautar Biu kamar yadda mahaifinta ya kira ta don ta zo su yi shirye-shiryen bikin dan uwansu. Haka Murjanatu ta taso dagaIstanbul tun jiya ta sauka Abuja. Zata biyo connecting flight zuwa Maiduguri yau. Kamar yadda Maimartaba ya yi mata umarni cewa, idan ta iso kafin ta shiga koina ta fara ganinsa tukunna. Yaa Maira, ta bi wannan umarnin na mahaifin ta, ta yi saa babu kowa tare da Mai Askira lokacin da ta shiga falon ganawarsa da iyalinsa. Ta same shi yana cin abinci. Ita dai ta ji an daura wa kanin ta Yareema aure, amma ba ta san da wa Askirama ya daura ba. Yanzu da ta ke durkushe a gabansa suna magana ta Da da mahaifi, bayan ya kare cin abincin sa sun gaisa, ta fahimci ko wace ce Maimartaba ya zaba wa kanin ta Yareema Sageer. Ba kowa bace face Saadatun Fulani Bilkisu!!! Yaa Maira, wadda sunan ta na sarauta kenan, tana da wata baiwa ta daban kamar yadda na fada a baya ta sunsunar kaddara. Tun ganinta da Saadatu na farko jikinta ya ba ta wannan yarinyar will some day become part of them, za kuma ta zamo wani jigo a rayuwarsu. Zubin halitta da komai nata na Fulani Bilkisu ne, Bilkisun da ke juya zuciyar Maimartaba a halin yanzu. Bilkisun da babu tauraruwa mai hasken ta a idanun Mai Askira. Sai ba ta yi mamaki ba ko kadan da wannan zabin na mahaifin su domin BAGGARA matan manya ne. Abu daya ta ke so ta tantance yanzu shi ne hakikanin alakar dake tsakanin Bilkisu da Saadatu. Mai Askira sai bai boye mata ba, ya gaya mata hakikanin alakar da ta hada Bilkisu da Saadatu. Yar ta ce ta cikin ta! Mamaki, alajabi da tuajjibi kamar ya zauta Yaa Maira, kodayake dama ta dade tana kiyasta hakan, kawai sai ta ji ta karbi Saade da dukkan zuciyar ta matsayin suruka. Duk da aibanta ta da Humaira ke yi duk sanda suka taru bata taba fadin wani mugun hali a tare da ita ba, in ka fahimci duka kushen Humaira akan Saade to kishi ne na son da Askirama ke mata da daidaita musu matsayi da yake yi lokacin suna makaranta. Sai ko taya uwar ta Yaa Hibbani kishi da Fulani Bilkisu. Sai kuma kyawun Saaden da take cewa irin na shegu ne. Ita ta sani uwar Saade mai nagarta ce, cikin matan gidan kaf babu mai kirkin ta, saidai kishi ya hana aga hakan a kare da fadin aibun ta. Maimartaba ya sa mata albarka domin ta ce ta karbi amanar Saadatu a dakin su, ita ce uwardakinta daga yau, za kuma ta yi duk irin kokarin da za ta iya wajen ganin cewa mahaifiyarsu (Ya Gumsu) ta sauko ta sanya wa alamarin albarka. Da wannan ta bar falon Askirama zuwa unguwar Ya Gumsu. Tana tafe tana saka irin lallashin da zata yi mata. ***** Yaa Gumsu ta yi mamakin ganin Yaa Maira a daidai wannan lokacin, don dai ita da kanta ba ta gaya ko dayan su zancen auren Yarima da Saade ba saboda tsananin kiyayyarta ga auren. Yaa Maira ta kwaso gabadaya yayanta maza da mata sun taho, kallo daya ta yi wa Ya Gumsu, ta tabbatar da abin da Askirama ya gaya mata na cewa tana matukar adawa da auren, ba kuma don komai ba sai don kishinta da Fulani Bilkisu. Ya Gumsu hakimce cikin royal chair ta babban falon ta, kuyangi na yi mata firfita da maficin gashin dawisu. Wasu na tausa mata kafafu, wasu na zubo kirari amma duka basu ishe ta kallo ba sai kumburi take kamar zata fashe. Ta daga ido tana kallon Yaa Maira da ke warware lafiyayyar laffayar jikinta don ta ji dadin hutawa, sun sha zaman mota daga Biu zuwa Askira. Take gayawa Yaa Gumsu. Ya Gumsu ta harare ta sosai, sannan a hassale ta ce. To da ki ka kwaso bataliyar yayanki ku ka zo kuka cika min gida me ku ka zo yi? Wa ya gayyato ku? Na ayya gayyar sodi?” Dariya Yaa Maira ta yi, ta ce, Allah ya taimaki Gumsun Gari, mu ai ba sai an gayyace mu ba. Su Murjanatu ma duk suna hanya. Ya Gumsu ta kara shaka sosai, amma ta ja bakinta ta yi shiru sabida kuyangin da ke zazzaune wasu a tsaitsaye, zuciyar ta na tafasa. Ta kara ganewa Mai Askira bai dauki auren nan da ya daura da sauki ba tunda har da kan sa yake gayyatar yayan sa abinda bai taba yi ba. Allah kadai yasan iya gayyatar da yayi da irin hamshaqan sarakunan da ya gayyato akan auren nan. Bata kara magana ba sabida kunar zuci. Kallo daya Yaa Maira ta yi wa kuyangin da ke wurin duk suka mike suka bar falon, suna masu yi mata kirari irin wanda suke yi wa diyan Ya Gumsu. A tashi lafiya Yaa Mairar gida, A gana lafiya uwar marayun Askira, A fito lafiya cikin alheri Yaa Maira uwar diyan Yaa Gumsun Askira bakidaya.. Daidai kafafun ta Yaa Maira ta zauna suke kara gaisawa a nitse, gaisuwa irin ta Da da mahaifi, Yaa Gumsu na kokarin hadiye fushin ta, yaran duk sun bazama cikin gida, kowa ya tafi wurin saanninsa yadda suka saba in sun zo gidan. Yaa Maira ta ce da mahaifiyar ta cikin sanyin murya. Sai muka ji abin alheri Yaa Gumsu, da ma zaman Yarima da mace daya ai ba yi ba ne, Yarima fa, Yariman Askira Mai jiran gado! Balle wadda ba ta fito daga jinsinmu ba balle addinin mu. Na yi farin ciki kwarai da gaske don dama ni auren nan na farko na Yarima bai kwanta min ba ko kadan, babu wani biki na alaadunmu da muka yi sabida abin kunya ne ma mu fito mu fadi ga wadda ya aura a cikin masarautun da ke zagaye da mu. Sai kuma ku yo gayya a auren shegiya mara asali? Tukunna ma kin san da wa ya daura masa auren da kike wannan giringidishin? Subhanallah, Yaa Gumsu tofar da miyan bakinki tun kafin malaiku su rubuta. Saadatu ba shegiya ba ce, diyar Bilkisu ce ta cikinta Tayi aure ta haife ta da mijin ta na fari kafin ta auri Askirama..!. A razane Yaa Gumsu ta dago ta dubi diyar ta Yaa Maira. Sai Yaa Maira ta yi amfani da wannan damar data samu wajen luguiguita zuciyar ta. Tiryan-tiryan ta soma bai wa Ya Gumsu labarin Bilkisu da yadda ta haifi Saade, sak yadda mahaifin su ya bata labari, ta kare da labarta mata Bilkisu ta boye musu Saade yarta ce sabida ba ta son gori musamman daga ita Yaa Gumsu in ta ji cewa ba a budurwa Mai Askira ya aure ta ba ta kade har ganyen ta da gori. Karshen maganar da Ya Maira ta fada shi ya kara sanyayar da jikin Ya Gumsu. Dangin mahaifinta na hanya, wan mahaifinta uwa daya uba daya Alhaji Kyari Babagana, na tabbata kin san wannan sunan, don kuwa shi ne yake bai wa Bulama fatun da yake kai wa kasar Italiya. (Bulama kani ne ga ya Gumsu, wanda suke sanaa daya da Alhaji Kyari). Ita ma Ya Maira Askirama ne ya gaya mata hakan. A binciken da yasa aka yi masa akan asalin mahaifin Saade. Ya Gumsu da ke ba ta son nuna karayarta, sai ta hau mitar rashin dalili. Ban da munafurci me ye na boye mana cewa yarta ce? Ina ruwanmu don ta taba aure? Gori yana tsiro a goshi ne? Duk wata harka ta kishiya sai kin samu dunkulallen munafurci a ciki. Ashe ma a bazawara ta zo shi ne ta bi ta juye kan tsoho, kinibabbiya, haba! Ni fa in ce wannan so da Askirama ke wa yarinyar nan da walakin, ashe agola diyar mowa ce, to muna jira mu ga wan baban yarinyar da idanunmu don mu tabbatar ba shegiyar bace. Kuma shi Yareema shi ke nan ba zai auri yar sarauta ba, auren misali sai dai ya gani a wurin tsararrakin sa? Alhalin ba gata aka fi shi ba? Daga jinsin yahudawa da masu kanan ido sai jinin talakka agola a matsayinsa na Yarima mai jiran gadon Askira? Ya Maira ta yi kasa da murya ta ce. Yaa Gumsu, gara talaka, agola tushen musulunci tashin musulunci a kan tubabben da aka ce daga kwalba ta ke yi a bar, sallar ma ta daina. Ki gode wa rahmar Allah Ya Gumsu alheri Askirama ke nufinmu da shi. Yariman ai ba wankakke ba ne kin fi kowa sani. 'Yar Bilkisu aka cutada auren Yarima ba Yarima ba. Ni tun ganina da yarinyar na farko na san za ta zame mana wani jigo cikin zuriar mu. Tana da charisma mai yawa. Tana da wisdom bayyananne. Allah ne bai taba kai hankali na kan Yarima ba, musamman da ya zo ya yi auren sa daga baya. Amma na yi zaton Ashgar zaa bai wa, sai dai lalurar sa ba za ta bari ya yi aure ba, Jiki na ya dade da bani hakan cewa bazata wuce mazan gidan nan ba koda ba daga dakin nan ba. Yaa Gumsu Ta kyabe baki tace Mairam ki fita ido na in rufe, na bi wisdom da gudu na tattake babu takalmi a kafata me yasa baa baiwa dakin Yaa Kirjiloma ba? Uban wa yace miki Ashgar bazai iya aure ba? Sai Yarima na dana dora dukkan buri akan sa da yayan da zai haifa? Kawai sai kuka ya kwace mata. Yaa Maira ta rasa yadda zata yi da Yaa Gumsu, duk dabarar ta ta kare. Haka ta yi ta tausar Ya Gumsu tana nuna mata muhimmancin wannan aure ga mutuncin Yarima da rayuwarsa, da alkhairin da ta ke hangowa a cikinsa na kimtsuwar Yarima. Yaa Gumsu baki da masaniyar cewa har yanzu Yarima Sageer bai bar bin mata a garin Abuja ba? In baki sani ba ki sani, in kuma kin sani ki tuna. Ko jikin ta ya yi sanyi dai ba ta nuna ba, Ya Gumsu akwai Ki-Fadi, ko ma me ye ba za ta so hada jini da Bilkisu ba gara dan kowa a kan nata. Da ta rasa hujjar kamawa sai ta ce da Yaa Maira. Shi ke nan kuma shi ba zai yi aure irin na gidansu ba? Ba zai yi auren martaba (auren sarauta) ba sabida ubansa na auren uwarta? Yaa Maira ta sake kwantar da murya, Allah ya taimaki Gumsun Askira, ai akwai sauran damarmaki. Yarima na da gurbin wasu matan biyu bayan Saadatu, ki ka sani ko duka ya auri yayan masarautu a sauran guraben yadda kike masa shaawa? A nan ne Ya Gumsu ta yi ajiyar zuciya, don shaf bacin rai ya sa ta manta da hakan, yayi zabin sa ya yi zabin mahaifin sa dole nan gaba kadan ya yi nata zabin. Ta ce, Yanzu ki ka yi magana Mairam, daga yau zan fara binciken yayan babban gida wa Yarima. Ba zai yiwu a ce duka aurarrakinsa babu zabina a ciki ba. Yaa Maira ta ce, Oh ni ya su. Amma Ya Gumsu ki bari ki ga kamun ludayin zaman nasu tukunna, kafin ki nema masa sabon aure. Yarima kodayake basarake to bature ne na gani kashe ni. Ba zai so da kuruciyarsa a cika masa gida da mata ba. Ki yi hakuri ki daga masa kafa zuwa wani lokacin. Haka ta yi ta lallashin Ya Gumsu cikin kwantar da kai da lalama, kodayake da ma cikin yayanta kakaf Yaa Maira ce kadai ta iya tafiyar da ita cikin hikima duk taurin kanta. Ko dai ba ta sauko duka ba, to Yaa Maira ta yi nasarar dakushe kiyayyarta da auren kashi talatin cikin dari. Tunda ta ji Saade ba shegiya ba ce sannan yar Fulani ce ta cikinta ba yar riko ba kamar yadda suke tsammani. Kuma ta ji cewa dangin ubanta za su bayyana kansu. Wannan ne kadai ya sassauta zuciyar Ya Gumsu har ta yarda ta amince musu su je su shirya biki nasu na aladar masarautar Askira. Amma ita tana nan sassan ta ko waje bazata leka ba. Don farin ciki Ya Maira a take ta hau buga wa kannenta mata da maza waya ta ce duk su hadu yau a Unguwar Fulani Bilkisu kan shirin bikin Yareema bayan sallar isha’. Kafin lokacin Mairam-Murjanatu ta iso. Ko hutawa ba ta yi ba suka dinga firfitowa daga sassan iyayensu mata zuwa na Fulani Bilkisu. Da ma kuma tun da yamma Yaa Maira ta aika wa da Fanna sakon zuwan nasu. Fanna kuma ta gaya wa uwargijiyarta. Don haka ba su zauna ba tun lokacin suke dafe-dafen abinci na alfarma domin saukar su Yaa Maira da sauran yayan Askirama maza. Humaira ce kadai ta ki zuwa don ta shiga matukar damuwa da wannan auren da aka daura. Fulani Hibbani kuma ta ce ta raba kanta da wahala, fadan da ya fi karfin ka ka maida shi wasa, ta fita batun Fulani Bilkisu da yarta, don sun gama da ubanta saidai wani sarkin ba shi ba, in kuma ta ki ji ita ce a wahale. Saade da ma ba ta yarda ta bar dakinta a bude tun daga lokacin da suka yi magana da Fulani a kan aurenta da Yareema, ita kanta Fulanin haushi take bata yanzu don ta lura ta gama mika wuya ga auren sabida son da take wa mijin ta Askirama, kuma bata dauki shirin sa da wasa ba, ko don bata san waye Dr. Sageer ba? Ko kuma bata dauki hakan da muhimmanci ba? Aisha Sultana bazata yi masa karya ba da ta ce hes committing adultery kuma SAI YA BARI ITAMA ZATA BAR GIYA, wannan ne gidan da Fulani ta amince a kai ta kuma cikin mutanen da take mata fatan rayuwa ta har abada? Ita kuma Fulanin kamar ta san tunanin da take yi sai ta fita sabgarta, shirye-shiryenta ta ke kain da nain, ta ce cikin ran ta, Allah shine mai shirya bawa bani da tsumi banida dabara sai abinda Allah ya shiryawa rayuwar ki Sa'ade. In kun tafi Abujar ku karata can, ni biki ne a gaba na. dama ai tare kuka zo, don kun koma tare matsayin miji da mata yanzu babu laifi. To yau ma tana jin su suna maganar kabakin abincin da za a shirya wa su Yaa Maira ita da kuyangin ta wadanda a nan za su ci abincin dare, bata dai ji hakikanin me zai kawo su ba amma taji ana maganar abinci na gani na fada zaayi yayan Askirama gabadayan su, da gudu ta kara murza key din kofar ta duk da dama a kulle ta ke. Kada ma wani ya shigo in da take. A bar ta ta ji da damuwar ta ita kadai tunda babu mai taya ta bakin cikin kaddarar da ta same ta. Karewa ma kowa harkar gaban sa yake yi, dan tausayin ta da Fulani ke ji a farko ta zubar. Abinci wannan Saade ta daina cinsa sai fruits kawai ta ke sha a firjinta, sai ko fresh milk din oldenburger gora-gora idan yunwa ta matsa mata. Yau kwanaki biyu kenan rabon da ta sa Fulani a idonta. Wayarta ta kashe ta don ta san dole Saidu zai kira ta, ba ta san da wanne baki za ta fara masa bayanin ita matar aure ba ce yanzu, ta san babu kyau mace ta dinga muamala da wani kuma. Ta ce ita matar Uncle Yarima ce ma ai yanzu ai abun kunya ne bayan ta gama yi masa homar Yayan ta ne. Saidu-Saidun ta hakika zata yi kewar sa. Babban tsoron nata shi ne kada Yarima ya kira ta a waya. Tuna sunansa kadai fadar mata da gaba yake yi. Duk wata kyakkyawar alaka da ke tsakaninsu a baya daga yanzu ta yanke ta. Karatun ma in dai ba hostel zaa maida ita ba ta hakura ta yafe shi har abada. Tana nan kusa da uwarta da kanwarta, a rayuwa wannan shi ne babban kwanciyar hankalinta wato ta gan ta tsakanin Fulani da Zarah. Bayan ita ma Zaran ko za ta wuni tana buga mata kofa ba za ta bude ba sai Fulani ta zo ta kore ta a wurin. Wajejen karfe takwas suka fara shigowa mazansu da matansu iyalin Mai Askira. Yaa Maira ce karshen shigowa har da bawan Allah Ashgar wanda bai san me ake yi ba shi dai an kira shi kuma ya zo. Babban falon saukar bakin Fulani na musamman aka bude musu, kuyangin Fulani sai shige da fice suke suna shirya abinci na alfarma. Sai hirarrakinsu ke tashi cikin kasaita da taushin murya kamar ba magana ke tashi a falon ba sabida yadda suke yin ta cikin nutsuwa da salama. Sassan Fulani Bilkisu ya game da kamshin turaruka na alfarma, wannan na wane wannan. Ya kuma cakude da na wuta irin nasu na barebarin usli, ga sanyi da rabar iya kwandishan na ratsa su. Ba jimawa Fulanin Askirama ta shigo cikin falon, as usual cikin kwalliya ta alfarma, ta fi kowacce iya tsara kwalliya cikin matan Mai Askira kamar yadda duk ta fi su kuruciya da daukar ido. Da faraa sosai wadda ta fiddo hakoran Makkanta na danyen gold guda biyu ta ke musu barka da zuwa. Ta dubi Mairam-Murjanatu cikin jin dadi ta ce, Har da mutanen Istanbul? Lallai kuna ji da wannan yar kanwa taku, ga shi ta shige daki ta rufe balle ku gaisa. Ya Maira ta ce, Kyale Saadatu kin ji? Kunya ce irin ta Baggara, me ake da amaryar da babu kunya? We really appreciate, muna nan tare har abada ai. Mairam Murjanatu ta muskuta cikin lallausar royal chair three seater da take zaune a kai, ta ce, Shin wane shiri ki ka yi Fulani game da biki ki gaya mana mu ji? Fulani ta yi dan murmushi ta ce, Ban shirya komai ba. Na bar muku wuka da nama, ku ne Yayyenta kuma surukanta. Ni ina gefe yar kallo ce. Yaa Maira ta ce, To madallah da wannan girma da anka ba mu, mu kuma za mu shirya mashahurin biki na alada, wanda za a dade baa manta a masarautar nan ba. Za mu huce na auren farko da ba mu samu yi ba. Daga nan Fulani ta yi umarni a zo a yi serving dinsu abinci. Sun dade suna tsare-tsare da shirye-shiryen yadda abubuwa za su gudana a junansu, bayan sun gama cin abinci. Fulani ba ta saka musu baki sai dai ta raka da eh ko aah. Yaa Maira ta dubi kannenta su Murjanatu ta ce. “Kamar yadda kuka riga kuka sani a aladar bikin gidan nan za mu fara da sakun lalle ranar laraba, alhamis za mu yi nakiya, jumaa wushe-wushe, ranar asabar ake daurin aure, to tunda an riga an daura ba shiri, to a ranar ne za mu yi kelatul (wanke kai da kitso na amarya), sannan mu yi Biji Ginata (ana shimfida tabarmi ne a ranar a ajiye amarya ana kida ana wakoki bayan an yi mata kwalliyar masarauta. Ranar lahadi za mu yi kaulu na amarya da ango da safe (kaulu shi ne, zaa ajiye miyar yauki a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya, Baaba za su goyo amarya (sisters din Maimartaba su ne Baaba) su kai ta wajen Kaulu, yan uwa da iyaye su dinga dibar wannan miyar yaukin suna shafa mata. Da daya da daya kowa zai zo yana shafa mata yana ajiye wa amarya kyauta, wasu har gold suke badawa, wasu iphone ko mota ya danganta da mukamin mutum a masarautar, wasu kuma kyautar kudade suke yi, kaulu kenan. Da yammacin lahadi kuma za mu yi ‘dubdo’, wato wunin biki a gidan amarya bayan an kai ta ranar asabar da daddare (a wannan ranar yan uwa da iyaye za a wuni ana shige da fice a gidan amarya. Ke kuma Fulanin Maimartaba ke ce da alhakin yin Miskero (abincin da ake kai wa gidan amarya ranar wunin) wanda jamaa da ke shiga da fita a gidan za su ci. Sannan a satin bikin gabadaya har ila yau ke za ki dinga ciyar da amarya da ango abinci mai kyau. Har zuwa ranar da za a kai amarya, wato asabar. Idan asabar ta zagayo kuma ana ‘tulur’, wato sati daya da kai amarya, ranar ne ke da kawayenki (Fulani Bilkisu) da yan uwan amarya za ku je gidan amarya, mu kuma za mu yi mata kwalliya, sai a saka mata muciya a hannu, a ranar za ta fara girki kenan, ana wakoki da raye-raye, a ci a sha, to daga nan biki ya kare. Ranar asabar kuma za mu kawo lefe. Fulani ta ce, Turkashi, wani aiki sai Amale, bikin Kanuri sai Askira! Allah ya sa muna da rabon gani. Aka yi adduoi aka shafa, bayan mazan ma sun yi nasu tsare tsaren, sannan duk suka fara watsewa. Amma sai da daya daga cikin kannen Yarima da ake kira Houdda yar dakin Yakirjinoma ta je har kofar dakin Saade ta yi magana ta hudar kofar dakin tamkar mai yin waka cikin harshen Kanuri. Ki gama boyon amarya, kin riga kin zo hannu, da sannu za mu yi miki kaulu, kelatul, biji ginata da tulur, sannan mu damka wa Yarima ke. Murjanatu ta zuba mata duka a baya [dundu], ta ce, Houdda kar da ki tsoratata ta kara kunshewa a daki duk zafin nan da ake yi, in kika firgita masa amarya ke da shi ne, kin fi kowa sanin halin sa. Saade da ke cikin daki duk tana jinsu ba ta san sanda ta fashe da kuka ba.. Da gaske dai ya tabbata an yi mata auren kenan, this is the reality da take ta kokawa da zuciyar ta wajen yarda da shi. Take yaudarar kanta da kanta da cewa mafarki ne. Iyalin Askirama bazasu bata lokacin su su zo har da na wata kasa ba idan ba gaskiya bane. [They are very serious people] a sanin data yi musu. Auren kuma ba da kowa ba sai UNCLE YAREEMA! Yariman da ta yi wa farin sani, uban dakinta mijin Aisha-Sultana. Yanzu ya tashi daga mijin Sultana ita kadai, ya koma mijinsu su biyu. Da wane karfin zuciya za ta iya karbar wannan sauyin rayuwar na bagatatan da ya zo mata rana daya? Ta tura kanta karkashin filo tana ta kuka, wani irin kuka wanda tun lokacin da Fulani ta sanar da ita zancen auren ba ta yi shi ba sai yanzu. Yanzu data ji ana shirye-shiryen biki kain da nain daga kowanne bangare. Daga bakin kofa ta ji ana sallama da wata irin murya cike da doki da zakuwa ga son ta bude. Muryar da ba za ta taba mantawa ba. Ko mutuwa ta yi ta dawo bazata kasa shaida muryar Hanne ba, Hannenta, Hannen Tsanyawa! Diyar Innar Hanne da Baba Saleh. Ai ba ta san lokacin da ta isa ga kofa ta bude ta da sauri ba. Hanne da Saade aka tsaya ana kallon-kallo, kafin su runtuma da gudu su rungume juna tsam tsam. Cikin yan kallon sakanni da suka yi wa juna, kowacce ta karanto irin sauyin rayuwar da ke tare da yar uwarta. Bi maana, Hanne ta gano tarin sauyi na ci gaba da nasarar rayuwa a tare da Saadenta, domin inda a hanya ta ganta ba za ta gane ta ba, to dadin abun mahaifiyarta Fulani ce da kanta ta tabbatar mata Saade na cikin dakin nan a kwance, in ta yi magana ta ji ita ce za ta bude mata. A yayin da Saade ta hango tarin nakasu da koma baya a rayuwar Hannenta, ta zama kamar mai shekaru arbain bayan ko ashirin ba su rufa ba. Ta yi baki; ta rame; ga goyon wani katon yaro a bayanta wanda da gani ka san ya wuce goyo domin har rinjayarta yake. Saade ta soma kokarin kwanto dan daga bayanta don Hanne ta ji dadin zama, suka karasa bakin gado suka zauna suna hawaye. Ina Baba Saleh? Abin da Saade ta fara tambayar Hanne kenan. Hanne ta idasa rushewa da kuka, ta ce, Baba ya jima da rasuwa Saade. Baba ya dade a kushewar sa. Mu kuma ba mu san garin da ki ke ba da tuni mun zo, shekara da shekaru muna kewarki. An yi min aure shekaru hudu baya da saurayinki Naziru, tunda na samu ciki ya gudu birni ya bar ni yau shekaru hudu ba mu kara jin labarinsa ba, kin ga dan da na haifa masa nan, Inna ta sa masa sunansa Naziru. Jiya kawai muna alwala a gindin rijiya sai ga sako daga gidan Maigari wai mu zo an zo daukarmu za a kawo mu inda ki ke. Inna Laure ta ce ba zaa zo da mu ba, ita kadai zaa dauko, sai da direban ya ce an ce masa iyalin Baba Saleh da Inna Laure, sannan ta yarda aka taho da mu. Saade ta rungume dan Hanne a jikinta tana tuno Naziru don kamar su daya, ta ce, Yanzu ina Innarmu da Inna Lauren? Aka bude kofar dakin aka shigo, Fulani ce, sai tsofaffin guda biyu biye da ita. Duk sun tsufa sun yamutse a idon Saade. Tana kuka ta ke rungumarsu daya bayan daya, ta ce, Inna, ku yafe min. Na dade ban neme ku ba, ajizanci ya tabbata gare ni, wallahi karatu ne ya sha kaina sam bana samun hutu. Inna Laure da Innar Hanne suka rike ta suka zaunar a tsakiyarsu suna fadin, Babu komai Saade kin ji? Allah ne ya nufa sai yanzu za mu sake haduwa, komai kana da niyya sai Allah ya nufa. Innar Hanne ta ce, Shi ma Babanku yana ta wakar zai dawo ya sake duba lafiyarki, sai cuta ta sarke shi, bai jima yana jinya ba mutuwa ta raba mu. Mu kuma ba mu san garin ba, mun dai san masarauta ce a Borno. Sai yau da ki ka sa aka tura har Tsanyawa aka dauko mu cikin mutunci a mota. Ashe Saade aure ya zo? To Allah ya sa an yi ke nan, Ya ba ku zaman lafiya. Saade kamar jira take sai ta rushe da kuka, ta ce, Innar Hanne ku roki Fulani, don Allah ta bai wa Maimartaba hakuri, bana son auren. Inna Laure ta ce, Kul Saade! Aure sunnar Annabi ne, wanda ba ya son sunnar Manzon sallallahu alaihi wasallam hakika Manzon rahma ya ce ba ya tare da shi. Ni dai rokonki zan yi ki yafe mini, na ga babbar ishara a kanki, duk abin da na yi miki kin manta ki ka ce a je a dauko miki ni har Tsanyawa. Ta saka kuka sosai. Saade ta ce, Inna Laure, ni ba ki yi mini komai ba sai alheri, rike ni da ki ka yi tun ina karama shi ne babban alherinki gare ni, don haka ni komai ya wuce a wurina. Daga nan hirar ta koma kan yadda auren Hanne da Naziru ya kasance, Innar Hanne ta ba ta labarin Naziru ya sha kuka bayan tafiyarta Askira, A karshe da ya tabbatar ba za ki dawo ba ya like wa Hanne, Baba Saleh ya cire ta daga makaranta ya ba shi aurenta cikin mutunci. Amma tunda Hanne ta samu ciki aka neme shi aka rasa a Tsanyawa sanadin kamuwar Babanku da hawan jini ke nan. Hanne ta haihu a gida, ba ta jima da haihuwa ba Babanku ya cika, ni na yi ta dawainiya da su da sanaoin hannu iri-iri har kawo yau. Fulani ta ce, tunda ya shekara hudu bai dawo ba kuna da damar kai kara kotun muslunchi a ba ta yancinta, ko ta samu ta yi wani auren. Shi kuma in da gangan ya gudu ya barta Allah zai saka mata, in kuma wani uzurin ne ya rike shi, Allah ya sada su da alkhairi. Zan yi magana da Maimartaba ya shige muku gaba Hanne ta samu yancinta. Hanne ta ce, Burina kenan, ban san ina da wannan damar ba da tuni na yi amfani da ita. Ina matukar son in koma makaranta in raini Naziru shi ma in sa shi makaranta. Fulani ta ce, Kada ki damu Hannatu, insha Allahu komai zai yi daidai bari mu kare bikin Saade. Sai da suka raba dare suna hirar yaushe gamo, a dakin Saade duk suka sauka don saboda zuwansu ta manta da damuwar ta, ta cire wa ranta kunci, ta ware suna ta hira da Hannenta. Washegari Fulani ta raka su suka yi gaisuwa wajen Askirama, ya ji mutuwar Baba Saleh sosai, Fulani kuma ta gaya masa maganar Hanne, Askirama ya ce zai shiga maganar bayan biki insha Allahu. Tun zuwansu Hanne, Saade ta samu walwala, amma ta ki kunna wayarta. Tabbas da ta ga sakonnin Yarima Sageer har guda uku. Sako na farko ga abinda Yarima Sageer yace. “Thank you for being the PRINCESS Im waiting for.Thank you for coming to my life when my heart is desperate to have you..(Madallah da zamowar ki GIMBIYAR dana ke jira tuntuni, madallah da zuwan ki cikin rayuwa ta a lokacin da zuciyata ta dimauce ga son mallakar ki). - Sageer. Na biyu kuma yace. “Saadatu save a soul by picking my call(Saadatu ki cece ni ki daga kira na). - Sageer. Sakon Yarima na karshe ga Saade cikin harshen hausa ne, ga abinda Yareema ya rubuta ma Saade. Kin ki bude waya saboda ni ko Saadahtouh? Bonono kenan rufe kofa da barawo. Bari in tuna miki wani abu guda daya da baki sani ba ko kika manta; daga rana irin ta yau mun zama abu guda,tare zamu kare rayuwar bakidayan ta,daga nan har gaban abada, ko makwanci bazamu kara rabawa ba sai bisa unvoidable reason.. Duka wannan bidirin da Yarima ke yi shikadai yake yin abinsa Saade bata san yana yi ba don kememe ta ki kunna wayar ta kamar ta san tashin hankalin dake jiran ta cikin ta daga zafafan kalaman sa [ba raba makwanci har karshen rayuwa]. Da ga karshe Yarima ya kasa hakuri, Saade ta kure dukkan hakurin sa, idan ba ganin ta yayi ba ba zai samu nutsuwar fuskantar bikin nan dake gaban su ba, ba zai koma nitatstsen Sagirun sa ba, matukar son ganin Saade yake anyhow ko jin muryar ta, don ya ga da fuskar da ta karbe shi matsayin miji ne ko akasin sa? Ko har yanzu kallon Uncle take masa? Ya aiko a gaya wa Fulani ta yi ma Saadatu magana ta kunna wayar hannunta su yi magana, mai muhimmanci. Da Fulani ta sa Fanna ta gayawa Saade, sai Saade ta ce ma Fanna ta ce da Fulani ta kunna har sun yi maganar, bayan kuma ko taba wayar daga inda ta yi mata kyakkawar maboya ba ta yi ba. To me Uncle Yarima zai ce mata? Na ji auren da aka yi mana bagatatan ni ma bana so ko me? Ko ki kama kanki ni ina da mata ta da nake matukar so? Ba ta bukatar wata sabuwar muamala a tsakanin su bayan official one irin wadda ke tsakanin su a baya, cuta ce an gama yi mata tunda an hada ta da shi, don haka ta yi kememe ta yi kemadagas ta ki kunna waya. Kulawa ma yabawa ce inji 'yan magana. Ya gaji da trying wayar Saade a daren yau, ana cewa a kashe, sosai yake son ya gan ta don ya ga da fuskar da ta karbi wannan babban alkhairin da ya same su. Yes shi a wajen sa alkhairi ne, GIANT (katoton) alkhairi ma kuwa, da bashi da yadda zai iya bayyana farin cikin sa da muhimmancin sa gare shi! An bashi abinda ya dade yana so yana kwadayi batare da ya cancanta ba, ba kuma tare da ya furta ba kuma ba tare da ya sha wahala ba sannan cikin girma da daukaka. A ganin sa hes not worth enough (bashi da darajar da zai mallaki Sa'ade) innocent soul kaman Saade, in yayi laakari ga tarin nakasun sa da laifuffukan sa na baya. Ya dade yana sunsunar takalmin, bai san ta yadda zai yi ya dauka ba. Sabida ganin cewa Sa'ade tafi karfin sa. Sai Askirama-Mai Askira cikin dimbin alfarmominsa da karamcinsa da ba su taba karewa a gare shi ya sunkuya ya hutar da shi, ya dauko takalmin nan ya miko masa har inda yake. Me zai ce da Mai Askira? Me zai ce da Fulani Bilkisu banda Allah ya ja kwanan su? Sun yi masa gatan da ya kasa yiwa kansa. Ba zai gushe yana rokon Allah Ya kara soyayya a tsakaninsu, ya ba shi soyayyar Saadatu kwatankwacin ta mahaifiyar ta Fulani ga Askirama! Da ya gaji da trying wayar Saadatu ta ki kunnawa sai ya kira Yaa Maira. Ya san Yaa Maira ce kadai zata yi masa wannan taimakon, sabida yadda take son sa da tausayin sa, in ba haka ba shi da ganin Saadatu sai an gama biki. Yaa Maira na dagawa ta ce, Angon Saadatu ka sha kamshi. Murmushi Yarima ya yi, cikin jin wani irin karin nutsuwa a zuciyar sa da ruhin sa wanda bai taba ji a baya ba, da wannan daddadan suna da inkiya da Yaa Maira ta kira shi da shi, ya ce, ni bana kamshi Yaa Maira tunda amaryar ba ta son ganina ko kadan balle ta san min kamshin, ko murya ta bata son ji Yaa Maira. Ko kai na ya fara furfura ne ban sani ba? Kin san yammata basa son mai furfura, rabo na da ita tun ranar da muka zo, ko waya ta ki kunnawa don kar in kira ta in ji muryar ta in samu nutsuwa. Dariya Yaa Maira ta yi, in wani ne yace Yarima ne wannan zata musa, Yariman da magana a gare shi sai dole, fitar kalma wannan tsada gareta daga bakin sa, amma yau shine yake joking, lallai Saadatu ta ciri tuta kaman uwarta, wane irin sirri gare su haka? Da suke juya zukatan sarakuna? Bata tantama in nan gaba kadan Saade bata juye kan Yarima ba kamar yadda mahaifiyarta ta juye na Askirama. Ita dai in auren Saa zai raba Yarima da bin mata ba ta da damuwa a kan hakan, ta tabbata dama ranar da ya auri matar da yakewa hakikanin so zai bari, musamman idan halittar su ta zo daya, tunda Mai Askira ya hakura da kwarkwarori tun zuwan Baggara Bilkisu,ta ce, Amma Saadatu ba ta kyauta ba, an gaya mata miji wasa ne? Bari in je in samu Fulani zuwa anjima a shirya muku ganawa ta musamman, don in anka shiga hidimar bikin nan ba za ku samu ko ganin juna ba. Tana kashe wayar ta nufi unguwar Fulani Bilkisu. A falon ta tadda ta tare da mutane, nan ta nemi kebewa da Fulani, suka dan yi magana kuskus, Fulani ta kama baki cikin mamaki. Ashe Saade ba ta kunna wayar ba? Na rasa me ke damun yarinyar nan??? Yaa Maira ta ce, Ki bi ta a hankali dai, Saadatu na bukatar lallashi har zuciyarta ta samu nutsuwa da auren, kada ki manta baku nemi shawarar ta ko amincewar ta ba, don haka lallashi ne naku ba tursasawa ba, shi ma Yarima gajen hakuri ne irin nasa, ina ce tare za su koma Abujan? Fulani ba ta saurari Yaa Maira ba ta nufi dakin Saade cikin fushi. Ita da Hanne ta same su tana ware sitturunta masu kyau kala-kala daga wardrove tana bai wa Hanne. Suna yi suna hira. Gabadaya ta manta da damuwar da take ciki sabida zuwan Hanne. Ashe ba ki kunna wayarki ba Saa? Fulani ta fada daga bakin kofa. Tana kokarin hadiyefushin ta. Saade ta turo baki gaba irin na shagwababbun yaya, Babu caji ne, amma yanzu zan saka daman. Ya yi kyau!. In ji Fulani, sannan ta juya ta bar dakin cikin fushi. Dakinta ta koma ta dauko wani dandatsetsen leshi cotton mara nauyi kalar maroon da ratsin golden, an yi masa dinkin riga da zani fitted, ta saka Fanna ta saka shi a kabbasa ya turaru tukun ta feshe su da turarukanta na musamman, ta kuma zabo mayafin da ya dace da su kalar golden sannan ta dawo dakin Saade, Hanne ta mika wa kayan, Taimaka mata ta shirya Hanne, tana da baki daga Abuja. Tana gama fadin haka ta juya. Mamaki ya kama Saade, ita yaushe ta yi kawa a Abuja? Kawarta daya Saidu ne, kuma Fulani ba za ta ce ta yi kwalliya saboda shi ba, watakila ya gaji da nemanta a waya ne ya taho har Askira, amma ta ya ya Fulani za ta ce ta yi masa kwalliya irin wannan? Sai ta mikawa Hanne kayan. Bar kayan nan Hanne, Fulani ba ta san wanene ne ya zo ba. Hanne ta ce, Tunda dai ta ce ki saka, to ki saka kawai, baki ganin kin bata mata rai ne?. Ta mika mata zanin, daya bayan daya ta sanya, sai ga Fanna ta shigo tare da wata mata, wadda Saade ta san ta mai kwalliyar Fulani ce during occassions, ta ce, Fulani ce ta turo ta ta yi mata kwalliya. Haka matar nan ta zaunar da ita kan stool ta yi mata wani irin light serene make up, karo na farko da cute fuskar Saade ta ga sassanyan fentin bature, tana kunci tana komai matar bata biye mata ba tunda bisa umarnin Fulani take, a ganin ta ma fushin da Saade ke yi ya kara ma fuskar ta annuri, classique and gentle amaryar Yareema, [inji mai kwalliya cikin ran ta], bada jimawa ba tuni Saade ta fito a beautiful Princess dinta. Matar wadda babarbariya ce ta feshe ta da tsadaddun turarukan humra, sannan Fanna ta kamo hannunta suka fito, Saade ta kasa magana bin Fanna kawai ta ke, Fanna ba ta tsaya da ita a koina ba sai falon saukar bakin Fulani na musamman. Falon shimfide yake da kilisai na alfarma da tumtum a koina, da hoton Mai Askira cikin nadi da amawali windowsize a gabas maso kudu na dakin, sannan zagaye da golden din kujeru na zamani. Har bisa royal chairs na falon ta kaita ta zaunar da ita, ta gyara mata lullubi, sannan ta juya tana fadin, A fito lafiya uwargijiya ta, takawar ki lafiya Gimbiya Saadatu. Fanna ta fita da kamar minti biyu, angon na Saadatu ya bayyana gabadayan sa cikin falon. Yana takun sa na kasaita tamkar mai tafiya akan gajimare. Shalelen Askirama da Ya Gumsu. Kanin Ya Maira da Mairam Murjanatu. Mijin Aisha Sultana. A yanzu kuma angon Saadatu saar mata. Wato [Dr]Yareema Sageer Yusuf Askira. Kamar dama yana falon dake bin wannan tun dazu yana jira. A yau sanye yake cikin royal attire dinsa, shudiyar alkyabba da jamfa na wani rantsattsen yadin filtex, hular kan sa Dara ce baka gashin jikinta na reto daga gefen damana fuskar sa ba karamin kyau tayi masa ba. Tunda Saadatu ta ke a tsayin rayuwar ta ba ta taba ganin mutum maabocin cikar zati, ilhama da kwarjinin Yareema Sageer da ke tsaye nan a gabanta a yau ba. Gabadaya ya canza mata, daga wayayyen dan bokon nan da ta sani mai tsukewa cikin suit da necktayil zuwa hakikanin BASARAKE na gasken-gaske, sarautar ma ta Askira wadda duk yankin Borno babu kamarta. Ji ta yi kamar ta narke a wurin lokacin da Yareema ya tako ya tsaya a gabanta, kamshinsa na Invictus (Paco Rabbanne) da ke hargitsa ta ya mamayi hancinta. Ta sunkuyar da kai ta kasa ko kwakkwaran motsi.Dr. Sageer ya yi taku daya, biyu, ya tsaya a gaban Saadatu, kwalliyar da aka yi mata bai taba ganin ta da ita ba haka kalar kayan jikin ta ya matukar karbar lafiyayyar fatar jikin ta, ya kara fiddo zahirin kyawun ta da kwarjinin ta na Shuwa Arab, duk wani fushi da ya zo da shi da niyyar sauke mata a kan rashin kunna waya tunda aka daura aure, sai ya ji yana melting yana bin rariya, yayin da wata matsiyaciyar soyayya ke maye gurbin sa. Ya zuba hannuwansa duka a cikin aljihun sa, lumsassun idanun sa a kan ta, murya a sanyaye kamar ba Uncle Yareeman da ta sani ba, ya ce, Saadatu laifin me na yi miki ki ka ki kunna wayarki? Atleast mu gaisa ko? Rabo na da ke tun zuwan mu garin nan. Kin san yadda na azabtu a kan hakan? This is sheer punishment! Ba don Yaa Maira ba kenan har mu koma Abuja ba zan ganki ko na ji muryarki ba Saadatu, me yasa? Do you know how difficult and tortured is this to me? Maimakon ta ba shi amsa sai hawaye suka zubo. Ganewa da ta yi cewa Yarima Sageer bai cikin irin bacin ran da damuwar da ita take ciki akan auren bazatan da aka yi musu. Karewa ma ya karbi alamarin da hannu bibbiyu. Har yana fadin rashin ganin ta tun zuwan su gidan ya azabtar da shi. To dama can yana jiran hakan ne ko yaya ne? Ko dama akwai wani abu makamancin so a ran sa da bai taba nuna mata ba sabida girman kan sa? Aka dauke ta a bagas aka bashi don shi dan gatan Askira ne? Hawayen da suka sa Yarima saurin durkusawa a gaban Saadatu ba tare da ya san lokacin da ya yi hakan ba. Ya dora tafin hannun sa akan kafar ta. Zuciyar sa cike da fargabar kada dai Saadatu bata farin-ciki da kasancewa cikin iyalin sa? Kada dai hawayen ta na nufin..bata yi naam da zamantowa matar sa wani bangare na rayuwar sa ba? Idan hakan ne a ran ta shi yaya zai yi da rayuwar sa yanzu? Ya riga ya afka a rijiyar da zurfin ta ya fi na gaba dubu. Babu mai iya fito da shi sai Saadatu. Already Saadatu ta dade da mamaye shi, ta mamaye kowanne gurbi da kowanne sako na zuciyar sa ba tareda ya san lokacin da hakan ya fara ba… Ya wayi gari ne ya gan shi dumu dumu a soyayyar Saade. A wannan lokacin hes helpless idan Saade ta ce bata auren sa yaya zai yi? Bai iya sakin ta! Baa saki a gidan su, ko ana yi bai taba sakin Saadatu. Ba kuma ya so ya nuna mata weakness din sa. Ya daga hannu zai rike natafor the first time a tarihin rayuwar su don ya korewa kan sa shakkun kasancewar ta mallakin sa a yanzu, ta yi saurin ja da baya cikin matukar razana! As if lantarki ya jona mata. Tare da maida hannayen ta duka baya ta sarke su a bayan ta. Yareema Sageer Ya daga lumsassun idanunshi yana kallon Saade, a galabaice, a susuce cikin wani yanayi na damuwa da rashin sanin abin cewa. A lokacin ne Saade ta soma shesshekar kuka a hankali, kukan da ya ratsa har cikin kwanya, ruhi da zuciyar Yareema ya hargitsa shi, ya sake kai hannu zai rike ta, ta yi maza ta sake ja da baya. Kada ka kuskura ka taba ni, ni ba zan auri mai yin ZINA ba, Allah ya tsare ni, kuma ba zan kuma bin ka Abuja ba!. Cikin wata irin razana Yarima Sageer ya wara manyan idon sa ya dubi Saadatu, da iyakacin girman su, a ina ta ji wannan maganar? Ya bude baki zai yi magana, ga dukkan mamakin sa maganar ta makale ta kasa fita, kafin ya ankara Saadatu ta mike ta nufi kofa da zummar ficewa. Da wani irin zafin nama Yarima ya sha gabanta, ya kama duka kafadunta biyu ya girgiza ta da karfi. Sai da kashin kafadar ta ya amsa. Bata san sanda tace, zaka balla ni!. A kausashe Dr. Sageer yace. “Kin san da wa ki ke magana Saadatu? Are you scolding me? Hawayen da ke tare cikin idanunta suka idasa gangarowa akan kuncin ta, ta ce cikin karyayyar murya marar amo da rashin karsashi. Im not scolding you. Kawai ina gaya maka abinda na dade da sani ne a kan ka. Na san da wa na ke magana mana; Yarima ne, Yariman Askira, Yarima Sageer mai jiran gadon Askira, amma ba mai halin real Askirama ba Shi Askirama ba ya zina, matan sa ba sa shan giya, ba sa zuwa Bar, sannan suna yin sallah”. Ta bude dukkan idanun ta dake jike da hawaye ta cigaba da cewa A gidan Yarima duk ana yin wadannan abubuwan dana lissafa, don haka babu ni a wannan gidan. Matattarar shaidanu da sabon Allah. In kuma aka takura min sai na bi ka, wallahi zan gudu! Ba za ku kara ganina ba, da ma ba ku san daga ina na zo barana daya kawai kuka ganni a gidan ku, don bani da gata ubana talakane kuma ya mutu, ni sai a yi min aure ba izini na. Saadatu ba ta yi aune ba idanun ta bakidaya a rufe, tana ta zubda rashin kunyar ta ta hanyar fadin duk abinda ya zo bakinta wa Yarima, ta hakan ne kawai zata amayar da kuncin dake zuciyar ta, tunda in ba shi din ba wa zata iya gayawa wannan? Burin ta ya ji haushi ya bar musu sassan su, in yaso kada ya kara dawowa. Ba zaton ta ba tsammani ta ji Sageer ya janyota jikin sa gabagadi da wata irin azama da zafin nama, jikin sa na shaking [tsuma] kamar kamar bai taba rike mace ba a tsayin rayuwar sa sai wannan karon. Har kuma ran sa da zuciyar sa abinda yake ji kenan a zahiri. Kafin ta yi kokarin zamewa ko kwacewa sai jin taushin bakin Yarima Sageer ta yi ya sauka a kan nata ya sima sumbatar ta in an abrupt manner, wanda hakan ya rufe sauran bakar maganar da ta ke so ta furta. Cewa ita a rasa wanda zaa aura mata sai mai yin zina? Ba gara Saidu ba? Kafin ta tantance what is going to happen next? Dr. Sageer ya soma hawaye, bai taba nadama ba akan rayuwar sa irin yau, gabadaya jikin sa yayi sanyi da kalaman Sa'adatu, ba tare da yayi shawara da zuciyar sa ba ya fara sumbatar ta gently, expertedly, and then by dragging her closer, sai ya cigaba da kissing dinta softly, then a urunce wato [da sauri da sauri]. Tun daga karkashin zuciyar sa sautin sumbar take fitowa tana bada sauti. Duk kokarinta na kwatar kanta hannun Yareema ta kasa sai da ya yi sumbar mai isar sa tukunna, ya sanyata cikin jikin sa a hankali ya rungumeta tsam-tsam ta hanyar hada bugun zuciyoyin dake cikin kirjin su wuri guda, inama zata iya jin tari nadamar dake cin ran sa daga bugun kirjin sa? Yana yi yana sauke kakkarfar ajiyar zuciya. Sai kuma ya bi hawayen fuskarta yana dauke su tsaf da lips din sa. Ya dago fuskar ta da hawaye kadai ke zuba tana kakabin abinda ke faruwa a mafarki ne ko ido biyu? Dr. Sageer ya sanya fuskar ta cikin tafukan sa, sannan ya sake ta ya ja da baya kadan yana jifanta da wani irin sassanyar kallo, wanda Saadatu ba ta taba gani a tare da shi ba. Gabadaya ya rikide mata ya koma tamkar ba shi ba. Ga dai nadama ce fal da tsoron rasa Sa'ade a ran sa tunda ta san ko wanene shi, amma abinda ya furta ba lallashi bane ba kuma nadamar dake baibaye da shi bane. Yarima Sageer is always bold, baya yarda ya nuna weakness din sa a komai. Kin fara da kissing mai yin zina Saadatu, kafin ku sha giyar tare ke da matar sa. Daga nan ku zarce BAR din ke da ita ku sha ku yi mankas ku dawo gida ina jiran ku. Na bar ki lafiya sai mun hadu a kauyen naku na Tsanyawa in kin gudu, amma ina rokonki don Allah in kin tashi gudun, ki fi ruwa gudu. Ya zuba hannuwa cikin aljihu yana kara jifarta da killing smile dinsa wanda shi kadai ya iya abunsa, ya kuma san maanarsa. Bai tsaya sauraron amsarta ba ya juya cikin sassarfa da takunsa na haiba da mulki ya bar falon. Ya bar Saadatu a tsaye kamar an kafe ta a wurin. Ta kai hannu ta shafo kasan lips dinta a hankali. Damshin yana nan. Haka kamshin mouth freshner din bakin sa yana nan. Shin abin da ya faru yanzun da gaske ne ko a mafarki ne? Ta yi kissing da mijin auren tafor the first time a rayuwar ta? Kuma ba kowa bane Uncle Yareema ne, guardian din ta na NTNU Dr. Sageer Yusuf Askira? Ta fi karfin minti goma a tsaye, ta kasa maida nutsuwarta, ta kasa yardar wa kanta abin da ya faru ba mafarki bane, ta dauki everything as an illusion. Kafin ta ja matattun kafafunta ta zauna. Me wannan ke nufi tsakaninta da Yareema Sageer? Ba dai wannan shi ne rayuwar kusancin da ake nufi yanzu zasu yi tare har abada ba, maimakon tasu ta Guardian da step sister irin ta baya? Koda take yarinya karama ta san me aure yake nufi a darasin biology. Kawai sai ta ji kuka ya kwace mata. Shikenan ita tata ta kare. Ta zauna a dandaryar kafet ta yi kukanta mai isarta. Kanta cikin cinyoyinta, kan ta har sarawa ya shiga yi. Fanna da ke jiran fitowarta daga daya falon, ta ga fitar Yarima da sassarfa da jimawa, da ta ji shiru-shiru Saadatu ba ta fito ba, sai ta biyo bayanta ta same ta a zaune tsakiyar kilishin falon tana ta kuka. A zuciyarta ta ce, Dole ki koka Saadatu, wannan mutumin ya fi karfinki ta koina. Da dai sun barshi da bayahudiyar matarshi ita kadai zata iya dashi, amma ina innocent yarinya irin Saade ina fitinannen Yariman Askira? Tun suna yara suke da labarin sa cikin gidan nan, wa ya san irin rayuwar da yake yi a Abujar? Fanna ta tsugunna da gwiwa bibbiyu a gaban Saade, cikin lallashi da ladabi ta ce, Ranki ya dade ki yi hakuri ki tashi mu koma daga ciki. Tana so ta gaya wa Fanna damuwar ta. Don ta san ita kadai ce a yanzu zata saurareta har ta fahimce ta. Ko ta fada mata abin da Yarima ya yi a gare ta yanzun nan, da abin da ya ce da ita, amma sai ta ji ta kasa. Maganar ta yi mata nauyin da ba za ta iya furtata ga kowa ba koda kuwa Fulani ce. Ta mike cikin mutuwar jiki, Fanna ta kama hannunta suka koma ciki. Ta gaban Fulani da su Inna Laure da ke zaune suna raba kayan daFulani ta diddinka musu suka wuce zuwa dakin Saaden. Fulani ta daga kai ta dube su. Idanun Saade jawur da alama ta ci kuka ta koshi. Ko me aka yi mata kuma? Fulani ta fada a ran ta. Suka wuce zuwa dakin Saade inda suka tadda Hanne tana gyara dinkunan Saaden da aka kawo daga wajen dinki. Fanna ta koma bayan shigar Saade daki. Bisa gadonta ta haye ta ja duvet ta rufa har saman kanta. Ba ta son magana da kowa, don ko Hanne ba ta jin za ta iya gayawa abin da Yarima ya yi mata wanda ya kara tsoratata da auren. Ita ma Hanne har ta gama abin da ta ke ta yi wa danta shirin kwanciya ba ta tambaye ta komai ba. Fulani ta so ta kira ta don ta ji dalilin kukan da ta fahimci ta yi, wata zuciyar ta hane ta. Gara ta bar Saade ta koyi rike sirrin auren ta yanzu girma ya hau kanta. In dai ba matsala ce wadda ta zama dole su sani ba. Washegari duka gidan ya rikice da hayaniya ana shirye-shirye. Kowa da ke cikin masarautar nan ya ci wa bikin nan na Yarima buri da alwashi don huce haushin wanda ba a yi ba a aurensa na farko. Maimartaba ya aika da goron gayyata zuwa dukkan masarautun Borno guda bakwai, (Bama, Borno, Dikwa, Gwoza, Shani, Uba sai kuma Askira wadanda su suka hadu suka bada Borno Empire. Hakan nan ya aika da sakon gayyata har fadar Shehun Borno don haka Mai Askira ba karamin shiri yake wa wannan auren ba. Duk wani gyara da ake wa amare na kayan mata Fulani ba ta yi wa Saade, banda Su dilke su halawa da dukhan kafin a mata lalle, (mai gyaran jikin Fulani daga maiduguri ta zo ta mata gyaran jiki), a cewarta Saade yarinya ce sai nan gaba in ta kara shekaru koda zata bata kayan mata, duk da tana tantama idan Yarima zai daga kafar yadda ya alkawarta. Kodayake fa bai bata cikakkiyar amsa ba akan hakan in zata iya tunawa cewa yayi zai duba. Ta yi ajiyar zuciya cike da tausayin Saade, ta san duk ranar data shiga hannun Yareema sai Allah. Tunda dan Askirama ne. Ranar talata, wato ana i-gobe sakun lalle Saade ta fito wanka tana busar da lallausar gashin kanta da dryer don ta cire wa kanta damuwar Yareema ko aurensa yanzu, ta hada su su duka ta zuba a kwandon shara, ta sa a ranta ba inda za ta yarda a kai ta, ko dai a barta nan a gaban uwarta ya koma gidan sa shi kadai yayi ta auren, ko ta bi su Innar Hanne su koma Tsanyawa ta yi zamanta a gidan su Hanne. Karatun ta hakura ta yafe in dai sai ta amsa sunan matar Yareema Sageer. Ina ita ina zama da yar giya matsayin kishiya? Ta je bar din ta ta dawo ta rotsa mata kai? A hakan ma kowa yana zaman kan shi ya suka kare balle suna zaman auren sa su duka? Wannan shine tunanin Saade. Wata siririyar muryar budurwa ta yi sallama daga bakin kofa, da yakeSaade ta bada baya ne tana fuskantar mudubi, amma jin wannan murya ba ta san lokacin da ta yi azamar juyowa ba, muryar sounds so familiar a kunnenta. Murya ce da ko mutuwa ta yi ta dawo ba za ta manta mai ita ba. Tana tsaye jikin kofa, harde da hannayenta a kirji, yar gaye da ita kyakkyawa sai murmushi ta ke. Ta kara tsayi da haske, ta murje sumul fiye da sanin da Saade ta yi mata. Idanun Saade suka bubbude gabadaya, ta saki dryer din hannunta kasa, kafin ta tafi da mugun gudu ta rungume RAHEEMAH. Fulani ta shigo, a bayanta wata mata ce da akalla za ta girme ta. Kyakkyawa da ita, da ganinsu ka ga mazauna kasar sanyi, sai kannen Rahima su biyu Sarina da Jamila. Kallo daya Saade ta yi wa matar ta gane mahaifiyar Rahima ce sabida tsabar kamannin su, wadda Rahima kullum ke kira da “Mama”. Ta saki Raheema ta tafi ga Mama za ta tsugunna, Mama ta yi saurin riko ta a jikinta, sannan ta rungume ta. Cewa ta ke, Masha Allahu, yau ga ni ga Saar Raheema, Saadatu Saar Mata! Ta kama su ita da Raheema ta rike a jikinta, Sarina da Jamila sai murmushi suke mata. Ta tafi gare su suka rungume juna don dai ita duk wani ahalin Raheema tana sonsa a kan dalilin da zuciyarta har yau ba ta sani ba. Raheema shi ne ki ka gudu daga El-Kanemi babu ko sallama, babu notice? Na shiga damuwa Raheema, zaman makarantar ya fice min a ka saboda rashinki. Na dade kafin na saba da rashinki Raheema, nayi kewar ki yadda harshe na ba zai iya bayyanawa ba, don Allah kada ki sake tafiya ki barni Raheemah. Sai kuka. Raheema tana share mata hawaye da tafukanta, ta ce, har yanzu kina nan da kukan wofin kin nan ko? Is o.k Saadatu. Im here now, da ni za a sha shagalin biki, ba zan tafi ba sai na raka ki dakinki. Ni ma ba da son raina muka koma Italy ba, kuma ban samu damar dawowa El-Kanemi don in miki sallama ba. Ki yi hakuri. Sannan ne suka zazzauna a kasa, iyayen na daga gefen gado suna kallon su withaffection. Nan Fulani ta gaya wa Saade labarin da ya girgiza zuciyarta, cewa ita da Raheema yan uwa ne na jini, da mahaifinta da mahaifin Raheema uwarsu daya ubansu daya. na dade da gane hakan ban dai gaya miki bane tuntuni, don in Baban Rahimah ya san ke ce ba zai bar ki hannu na ba. Saade sai ta ji duk wata damuwar duniya ta yaye mata. Feeling din da mutum ke ji idan ya san cewa yana da dangi na jini kuma na halali. Lallai da ake cewa wani farin cikin ya fi gaban kuka, sai dariya. Ta zama kamar wata karamar zararriya don murna. Ta rungume Raheema, ta saki ta rungume Sarina, ta saki ta kamo Jamila ta rasa inda za ta sa su don kauna, su kuma sai dariya suke mata, don sun riga ta jin labarin tun suna Italy. Maimartaba ya kira Fulani a waya ya gaya mata ta sa a rako Saade da Rahima falon saukar bakinsa ta gaisa da Babanta, wato Alhaji Kyari Babagana. Tare da Fulani suka tafi har falon ganawa ta musamman da bakin Maimartaba Sarkin Askira. Kallo daya ta yi mishi ta hango kamanninshi da mahaifin ta Malam Hashimu, saboda jini ba ya buya. Har kasan kafafunshi ta je ta zauna ta gaishe shi a ladabce. Shi kuma ban da kallonta da tasbihi ba abin da yake a fili, tamkar Bilkisu ta yi kaki ta tofar, ko kadan ba ta debo dan uwansa Hashimu ba ko da da kalar fata ne. Sai yanzu ya tuna kallon sanin da yayi mata a ganin sa na farko da ita a El-kanemi. Ashe fuskar Bilkisu ya hango cikin idanun ta. Alhaji Kyari ya ce, Madallah da yata mai albarka, Allah ya sanya alkhairi da albarka cikin aurenki. Allah ya hada hankulanku, Ya bada zaman lafiya. Ba ta iya ta amsa wannan adduar ba, saboda nauyin da ta yi mata a zuciya da kwakwalwa. Idan ta ce, ameen, Allah ya amsa adduar fa? Aurenta da Yarima ya zama tabbatacce ba mafarki ba kamar yadda ta ke kallonsa? Duk da Yareema Sageer ya tabbatar mata cewa, reality ne, ta hanyar da bata taba zato ba, kuma ba shi da alamun ja da baya daga hukuncin iyayensu? Don haka ya rage nata ta cigaba da yaudarar kanta da kanta, da cewa mafarki ne. Sun dade yana mata tambayoyi tana ba shi amsa a kan marigayi da rayuwarsu a Tsanyawa, karatun da ta ke yi a yanzu a NTNU da kuma burin ta na yanzu wato barin karatun ta zauna a gida. Daga shi har Askirama suka hada baki wajen tambayarta, Saboda mene za ki bar karatunki Saadatu? Ko shi Yareeman ne ya ce ba ya so? In ji Maimartaba, sounding worried da hukuncin Saaden, duk da ya san hakan mawuyaci ne a matsayin Yareema Sageer na malamin jamia cikakke ya ce ya hana matar sa karatu. Saade ta bude baki a hankali kamar mai ciwon makogaro, ta ce, Saboda na fi son in ci gaba da zama a Askira, bana son komawa Abuja Alanguburo. Fulani ta ce, Babbar magana, mijinki yana wani gari ke kina wani gari, a dalilin me? Maimartaba ya yi saurin cewa, Ya isa Fulani, Saadatu za ki zauna a gidan Yarima na Askira har ki kare hutunki? Inyaso daga baya sai mu raka ki Abuja da kanmu ni da Fulani ki koma makaranta, kin amince? Askirama ya yi maganar cikin lallashina uba mai tsananin kulawa. Kaunar da Mai Askira ke nuna mata da yawan alkhairinsa gare ta ya fi gaban ya yi hukunci ta ce, aah. Sauran zai kasance ne tsakaninta da Yarima, tunda shine bai ce shima baya son auren ba, yayi uwa ya yi makarbiya ya amshe auren, ita ta fada a ce ta yi rashin biyayya, da kyar in Fulani bata bubbuge mata baki in ta fada hakan a gaban Askirama ba, amma tsakaninta da Askirama babu jayayya. A hankali ta gyada kai alamar ta amince, idonta kuma ya cicciko da kwalla. Amma ta yi kokarin maida su sabida Askirama. Ko yayan da ya haifa ba ta taba jin ya raka gidan miji ba ko ya je gidajen auren su. Amma ita ya ce shi da kansa zai kaita. What an honour! Wannan ba karamin girma ne da kulawa ya ba ta ba. A wannan daren daga Raheema har Saade sai goshin asubahi suka kwanta. Labarin juna suke bai wa juna. Inda Raheema ita ma ta sanar da ita ta samu miji a Damaturu suna karatu tare a jamiar Heartfordshire, U.K. sunansa Usman Bello Jajere. (Jajere garin fulanin Damaturu ne suna da kyau farare ne kuma suna karatu sosai yan garuruwan Jajere da Kollere. Yan Jajere kan yiwa kan su kirari da Jajere garin jajaye in ka ga baki to bako ne), amma aure sai ta gama karatu, shi kuma ya dawo gida ya yi service. Ba abin da Saade ta tuna a lokacin sai Saidu, da yanzu ita ma yaro dan makaranta kamarta za ta aura, ina ma ta bawa Saidu damar da yake nema tuntuni tana gwasale shi? Yanzu gashi girman kanta ya sa an dauki mijin wata an ba ta wanda a haihuwar kauyensu Tsanyawa ya haife ta. Allah kadai ya san irin farin cikin da Usman zai sa Raheema, ita kam yanzu sai dai ta je ta yi ta fama da yar giya Wannan tunanin ya fiddo hawaye daga idon Saade, wanda Raheema ta nace sai ta ji dalilin saukarsu. Don bata ga dalili ba. Saade ta tuna cewa, wannan Raheema ce, mai kaunarta da zuciya daya tun tana bakauyiyar ta, kuma yar uwar da ba ta da kamarta a yanzu. Babu wanda ya dace da sanin halin da zuciyar ta ke ciki a halin yanzu ya kuma fahimceta ya bata shawarar data dace kamar Rahimah. Don haka Saade ta gyara zama, ta warwarewa Rahimah komai a kan rayuwarta gidan Yareema Sageer, da halin da matarsa ke ciki, irin kyautatawar da yake mata, girmansa da ta ke gani, har da labarin Said sai da ta bata. Amma ta rasa dalilin da ya sa ta kasa ce da Raheemah Aunty Sultana na yawan cewa Sageer yana neman mata. Maganar ta yi nauyi sosai a bakinta tunda ba ta taba gani da idonta ba, shaidar zina kuwa sai ka kwana a ciki in ba ka yi taka-tsan-tsan ba. Ta gaya wa Raheema damuwarta shi ne ba ta taba jin wani abu a zuciyar ta a kan Yareema ba, bayan na kasancewarsa guardian dinta a Abuja. Ita a wurin ta Uncle Yarima Yayanta ne mai kula da alamuran karatun ta. Rana daya ta ji labarin aurensu daga bakin Fulani bagatatan kamar saukar aradu, ita ta fi son in auren ne ma a aura mata Saidu ba za ta damu ba, shine tsaran auren ta daidai da rayuwar ta ta yar talaka. Amma ina zata kai YARIMAN ASKIRA??? Raheemah Kyari, ta yi wani irin lallausar murmushi. Ta kama hannayen Saade ta rike cikin nata. “inda kowacce mace take kai mijin ta Saadatu! Ina ma ni ce ke Saade! Ki yarda ba tun yau ba cewa you are among the luckiest. Auren matured men shi ne aure, wadanda suka san ciwon kansu, ki rabu da samarin nan yan rawar kai ki kama mijinki da iyayen ki suka zaba miki kin ji? What is your own business da rayuwar matar sa? Kuma tunda Fulani ta ce ya raba muku gida, kuma ya amince, ina ruwanki da matarsa? Wannan rayuwar su ce shi da ita bai shafe ki ba.” Saade ta zumburo baki, Raheemah ba za ki gane ba. I have no feelings a kan Yareema Sageer, na dauka zaman auren sai da feelings din soyayya yake yiwuwa??? Raheema ta girgiza kai, ta ce, inji wa? Saadatu, ki gode wa Allah kawai, ki kuma hada da addua, ki roki Allah ya sanya miki soyayyar mijinki, kuma zabin iyayenki. Soyayya da kike ambato shirme ce, cike take da unbearable challenges, aure daban soyayya daban, sai kin yi auren soyayyar in gishiri ya sauka daga kan kaza za ki gane shayi ruwa ne. Above all kin ce kina ganin girman Yareema, to magana ta kare. Along the way soyayyar za ta zo, irinki in ku ka tashi soyayyar ma mahaukaciya ku ke yi, kuma makauniya, tunda kin ce ba ki ga alamun shi yana kin auren ba. Muryar Saade abin tausayi ta ce, Sai ma kin ji bakar maganar da ya gaya min da na ce ba zan koma Abuja ba zan gudu kauyenmu he was like (in yi ta gudu, in fi ruwa gudu, giya in shirya sha tare da matarsa) meaning bai dauki maganganun nawa da wani muhimmanci ba. Raheema ta yi dariya sosai, ta ce. I would like to see Yarima Sageer. Sister you are blessed for having him as a husband, ina son brave men, wadanda suka yarda da kansu, cika baki ko rikicin mace ba ya razana su su ja da baya a kan soyayyar su. Ni ma sai in ce, Sai kin dawo, a gaida mutanen Tsanyawa. Saade ta kai mata bugu ta goce tana mata dariya. Muryar ta abin tausayi tace. Wato dai Raheema kema kina bayan in auri mai mata ko? Ta je bar ta dawo ta yi min dan karen duka? Dariya sosai Raheema ta sake yi, ta ce, Tunda ki ka ce ga inda ya auro ta kuma ga asalinta me ye abun mamaki don ta sha giya? Su fa yadda muke shan soft drinks, haka suke shanta don baki taba fita ketare bane, canjin addininta ba zai sa ta iya dainawa farat daya ba, tunda dai ba shi yake sha ba shi kenan falillahil hamdu, ki yi mata addua Allah ya sa tana da rabon dainawa. Sai kiran sallar asuba suka ji a kunnuwan su, dole suka mike don bada farali. Daga nan kuma suka kwanta, Hanne sai barcinta ta ke hankali kwance bisa katuwar katifa ita da danta Naziru. ***** Washegari aka tashi da event na farko, wato sakun lalle. Masarautar ta cika ta batse da yan uwa da abokan arziki da baki da aka gayyato daga masarautu daban-daban, ga kuma alummar garin Askira wadanda ma ba a gayyata ba. Da ma in dai biki na gidan sarki ne ba sai an gayyace su ba, kwansu da kwarkwatarsu suke tahowa daga gidajensu zuwa gidan Sarki. To balle auren Yareema Sageer kuma wanda Maimartaba da kanshi ya shelanta gayyatar ga kowa da ke Askira, bayan saukowa sallar jumaa a babban masallacin jumaa. Don haka ba a taba ganin taron bikin da ya hada jamaa irin na yau ba a masarautar gabadaya. Tun daga kan auren su Yaa Maira har zuwa kan na yar sarki ta karshe da aka aurar Najaatu. An saka amarya a lalle lafiya, Raheema da Hanne da kanwar Raheema Sarina sune kawayen amarya. Washegari alhamis aka yi NIYA wato ranar yin royal snacks su nakiya, alkali, dubulan, bakilawa da sauransu daro-daro don raba wa mutane. Ranar jumaa aka yi WUSHE-WUSHE. A babban filin dake cikin fada aka kira decorators suka tsara shi yayi kyau sosai. Wushe-wushe shine wuri daya da Yareema da Sa'ade Zasu hadu a duk tsawon bikin su, makada ne aka gaiyyato daban daban daga garuruwa daban-daban ciki har da HajjaGumsu da yaran ta da suka zo daga Maiduguri. Sai da aka taru ana kade-kade ango ya zo cikin manyan kaya da abokan shi karkashin rakiyar Awaisu Ibrahim Waziri da kuma sisters din shi mata su Mairam Murjanatu, Yaa Maira and co.zagaye da shi cikin laffaya mai hasken sararin samaniya suna rike da kaskon turaren wuta suna turara shi, makadan fada na biye da su,suna kide-kide da bushe-bushe suna wake Yarima da amarya Saadatu har su ka kai shi mazaunin da aka tanadar musu shi da Saadatun. Abokanen shi kuma aka yi musu shimfidun kilishi na alfarma daga gefen sa, sannan su yan uwan shi mata su kuma suna zaune inda aka tanadar musu. Sai aka cigaba da wasa da kide-kiden cikin zakuwar fitowar amarya, wanda yawanci sai an dan ja lokaci sosai kawai dan a ja wa ango rai, haka aladar bikin masarautar Askira ke gudana a kowanne bikin dan sarki. Saade an shirya ta cikin laffaya an rufe ta ruf har kai. Sannan kawayen ta su Rahimah da Hanne sun saka ankon dongasho da su murjani sun rike kaskon turarukan wuta suka sako ta a tsakiya kamar yadda aka koyar dasu.Maman Rahimah da Innar Hanne na rike da ita cikin rakiyar kide-kide har aka kai ta aka zaunar a gefen Yarima Sageer, wanda a lokacin da Saade ta zauna a gefen sa sai da ya dauke numfashin sa na wucin-gadi. Kawayen ta kuma by her side akan shimfidundake kallon na abokan ango. Daga nan sai aka cigaba da kide-kide da wasanni.Saade bata yarda sun hada ido da Yarima ba duk kokarin sa ga son faruwar hakan, bata ma bude fuskarta daga cikin laffaya ba, duk kokarin Yarima Sageer na son gano halin da kwayar idon ta ke ciki a wannan lokacin hakan bai yiwu ba. Tana jin sanda Uncle Sageer da yan uwan sa mata da maza da abokai suka yi ta yi mataruwan liki. Har tsakar dare ana wannan shagalin kafin taron wushe-wushe ya tashi. Kuma Yarima bai samu damar ganin Saadeprivately ba har su Maman Rahimah suka kama ta suka koma cikin gida. Ranar asabar kuma aka yi KELATUL wato aka wanke wa amarya gashi aka yarfa mata kitson bare-bari kanana-kanana sun kai guda dari uku. Da yammacin ranar kuma aka yi biji-ginata inda aka shimfida manyan tabarmi aka ajiye amarya a tsakiya ana kida ana wakoki irin na barebarin Askira. Bayan an yi mata kwalliyar masarauta. Ranar lahadi aka yi kaulu na amarya da na ango da safe. Kaulu shi ne za a ajiye miyar yauki a gaban amarya bayan an mata kitso da kwalliya. Baaba suka goya amarya suka kai ta filin da ake yin kaulu. Yan uwan Yareema na ciki daya da na sauran dakunan suka dinga dibar wannan miyar yaukin suna shafa mata, sannan daya bayan daya suka zo suna ajiye mata kyaututtuka na bajinta haka sauran matan Maimartaba. Da yammacin ranar aka yi dubdo, wato wunin biki a harshen Hausa. Biki ya yi biki ba ka jin komai a masarautar Askira sai kade-kade da bushe-bushen algaita. Duk wadannan events din da ake yi ango bai ga fuskar amarya ba, kuma Fulani Bilkisu ita ke da alhakin yin miskero, wato abincin da ake kai wa gidan amarya. Kuma ita ke ciyar da ango da amarya dadadan girke-girke masu kara lafiya da kuzari. In ta girka sai kuyanginta su kai sassan Yareema su ci shi da Awaisu. Korafi kam Awaisu ya sha shi gurin Yareema, kan cewa shi fa bikin nan ya ishe shi hayaniya ta yi masa yawa. A ba shi amaryarshi kawai su kama hanya. Shi ba auren fari ba to wadannan aladun duk na menene? Awaisu sai dai ya yi murmushi don ya gama gane Yareema Sageer ya karbi auren nan da hannu bibbiyu. Har fiye da auren sa da baturiyar sa mai kananan ido. Auren da yake kira na soyayya kuma babu ya shi. Abin da bai sani ba, kuma yake matukar son sani shi ne, da ma can Yareema yana son Saade ne ko sai da aka ce an aura masa ita ya fara son ta?? Sai da Baaba (kannen Maimartaba mata) da kannen Ya Gumsu suka shigo tafiya da amarya ne idonta ya karasa raina fata. Domin a baya kallon komai take matsayin almara ko mafarki. Saadatu ta kankame Fulani tana ihu sosai ita ba inda za ta je ta bar Fulani. Sai yanzu ne ta tabbatar da gaske an yi mata aure, kuma ba da kowa ba da Yariman Askira, Uncle Yareeman da ta ke girmamawa fiye da kowa in ka dauke iyayenta, Dr. Sageer a NTNU, kuma mijin Aisha-Sultana. A karshe Baaba sai goya amarya suka yi tana kuka tana komai, kannen Yareema mata su Houdda sai tsiya suke mata, ko irin nasihar nan ta uwa Fulani ba ta samu damar yi mata ba sabida kukan da ta ke tun safe ya daga mata hankali. Su Mama (Babar Raheema) da su Raheeman suna gidan amarya tun safe inda ake aikin jere da kafi. Duk wasu furnitures da aka zuba a sassan Saade dake gidan Yarima Alhaji Kyari ne ya taho da su tafiyayyu daga kasar Italiya, wadanda Maimartaba ya yi mata an wuce mata da su Abuja. ****** SAADE A GIDAN YAREEMAN ASKIRA Daga ita sai Hanne da Raheema a bedroom din da aka zaba aka shigar da ita, wanda shi yafi kowanne kayatuwa, sai kuyangi da bayin Fulani da ke ta kintsa duk inda aka bata. Fadin dukiyar da Askirama ya dankara a gidan Yareema Sageer bata baki ne, ki sa a ranki gidan Yariman Askira mai jiran gado, shi ke nan zance ya kare. Gida ne ginin sarauta (royal mansion) wanda aka yiwa zubi na zamani,turawa suka zana shi suka kuma zo suka gina daga Amsterdam, da aka yi wa sassan matan aure har hudu, komai da ke cikin wannan sashe shi ne a wancan sai bambancin kalar fenti. A sashen kowacce mace manyan faluka ne bi-da-bi har guda Uku da dakunan barci Uku. Babun ce kawai babu a gidan Yarima Sageer Yusuf Askira. Sassan Aisha Sultana shi ne na farko, sai na Saade sannan wasu guda biyu a rufe. An ware bangaren bayi da hadimai daga can karshen gidan. Sassan Yarima kuma yana upstairs wanda girmansa ya yi a hada sassan matan nasa guda biyu. Komai da ke cikin sassan Yarima ya zo da shi ne daga Amsterdam kuma duk bayan shekaru biyu ake fidda komai na gidan a sake, a yo odar wasu. A raba wa talakawan gari, ko bayi da hadimai. A can gidan Wazirin gari Ibrahim a dakin Awaisu Yarima Sageer ne tsaye jikin mudubin dogon yaro yana sanya links din hannun farar shadda kal da ya saka, sai tashin kamshin invictus dakin Awaisu ke yi. Awaisu ya kasa danne dariyarsa ganin irin kwalliyar da Yareema ke yi wadda ko ranar da zai raka shi dakin Aisha-Sultana bai yi irinta ba, ya karkata hula ya sake karkatawa yafi sau biyar, ya ga bata yi kyau ba ya cire ya sake canza wata, [to wancan aure ne da aka riga aka kwashe albarkarsa tun a waje]. A ransa Awaisu godiya yake wa Allah yana kuma adduar Allah ya sa auren nan ya zamo karshen duk wasu matsaloli na dan uwansa Sageer. Amma dai sai gobe za mu je sayen baki ko? Ka ga yanzu dare ya yi sosai, na san duk sun yi barci bai kamata mu tada amarya ba tana barcin gajiyar biki irin wannan. Inji Awaisu cikin seriousness. Wata harara da Yarima ya juyo ya zuba masa sai da ta sa Awaisu durkushewa a inda yake yana dariya. Kafin ya dago daga dariyarsa Yarima ya gama saka takalmansa ya fice yana fadin. In ka ga dama kada ka je, da ma ba ni na gayyace ka ba, aure dai ka sani ba yau na fara ba balle ka ce rawar kafa na ke yi. Awaisu bai bar dariya ba da ma gwanin ta ne, ya saka takalmansa ya bi bayan Yareema Sageer yana cewa, Ko don in bata maka lokaci kafin ka shiga dakin Sa'adatu dole in bi ka. Yarima ya girgiza kai jin abinda Awaisu ya ce, ya ce, Awaisu! Mind your language. Saadatu is my step-sister rainon ta na yi wa uwarta alkawarin zan yi, kuma shi zan yi din. Zan ba ka mamaki, jibi-jibin nan zan koma wurin mata ta. Awaisu don dariya har da hawaye, ya ce, Aah Yarima, kada wata tara ta cika kuma mu zo bikin radin suna, wannan rainon in dai kai za ka yi shi Saadatu ba za ta taba girma ba. Suna ta barkwancinsu na aminai har suka karaso gidan sarki, don Yareema ya ce sai ya je ya yi wa Ya Gumsu sai da safe, ya kuma nemi albarka kafin ya karasa wajen Saadatu. [Da ya san abinda zai tarar, da ya yi wucewar sa kai tsaye dakin amaryar sa, in ya so da safe ya zo tasani]. Dazu da yamma Yaa Maira ta kira shi cikin sirri sun yi magana, inda ta ce ya bi Ya Gumsu a hankali da duk abin da ta ke so, don ba karamin yaki ta yi da ita kafin ta amince a yi bikinnan cikin dadin rai ba. Yarima ya yi sallama a hamshakiyar turakar mahaifiyarsa Ya Gumsu, Awaisu bai biyo shi ba ya zauna a mota don ya ba shi dama ya gana da Ya Gumsu. Tana hakimce bisa kujerar mulkinta sai karkada kafa take yi cikin izza lokacin da Yarima ya yi sallama. Ta hadiye wani malolon abu da ya tokare ta a makoshi ganin irin kwalliyar da ya caba da bata taba ganin sa cikin irin ta ba, wanda ke nuna yana farin ciki da auren diyar Fulani Bilkisu. Har kasan kafafunta ya isa ya gurfana yadda suke gaida iyayensu, ya yi gaisuwa ta amsa cikin dacin rai. Daga nan duk suka yi shiru. Yarima ya kasa ce mata ya zo neman albarkarta ne zai shiga dakin amaryarsa, aka ce wargi ma wuri shika samu. Ita kuma tana ta kitsa abubuwan da ta shirya fada masa ba tare da tunanin me zai je ya zo ba. Ya Gumsu ta dubi dan ta Dr. Sageer wanda kansa ke sunkuye a gabanta. Ji yake kamar ya yi fiffike ya fice ya tadda Saadatu. Shi kansa ya rasa ko wane irin excitement yake ciki mai neman karar da numfashinsa. Zuciyarsa har wani irin bugawa ta ke yi in ya tuna Saadatu zai je ya tadda a matsayin matarsa yau, ba yar amanar da yake riko a gidansa ba kullum yana fama da zuciyarsa a kanta. Sai jin muryar Ya Gumsu ya yi a tsakiyar kansa. An yi aure na gani, kuma na sa albarka kamar yadda Yaa Maira ke so. Maimartaba ma yake so, amma Yareema ban yarda ka taba yar Bilkisu ba. Ina nufin ban yarda ka hada shimfida da ita ba, don kuwa jinina ba zai gogi jinin Bilkisun Askirama ba. Balle in hada zuria da ita. Na ba ka watanni uku ka zo ka kara aure, aure na mutunci na gidan mutunci, duk wadannan matan naka tarkace ne, tunda babu jinin sarauta ko daya a cikinsu. Na samo maka mata yar Sarkin Bauchi, sunanta Hajjaju, mun gama magana da mahaifiyarta ta ce kana iya zuwa ku fara fahimtar juna, in dai da gaske ni na haife ka Yarima wannan shi ne umarnina. Ta mike ta shige turakar barcinta ta rufo kofa ta bar Yarima sai tsiyayar zufa yake daga tsugunne, ya rasa inda zai sa kansa. Don kwata-kwata bai fahimci inda zancen Ya Gumsu ya dosa ba, ko kuma ya ce ya fahimta, kwakwalwarsa ce ta kasa fassarawa. Ya Gumsu na da masaniyar cewa weakness dinsa shi ne Mace. Macen ma ta aurensa wadda zuciya da ruhinsa ya dade yana so da kwadaituwa akan ta, to in ta ce ba zai tabbatar da aurensa da Saade ba, neman matan ta ke so ya koma wanda ya yi wa Maimartaba alkawarin ya daina? Ya yi wa Ubangijinsa alkawarin daga ranar da ya mallaki Saadatu ya daina? Wane irin aure sai ka ce namamajo, aure wata uku ya zo ya kara aure wai Hajjaju? Yo shi ko sunanta Makkah ina zai kai ta duk son matansa? Guda biyun sun ishe shi sabida shi ba wai mata yake so ya tara ba, in ya samu abunda yake bukata a guda daya zai iya kama kan sa. Abin da ya rasa daga matarsa Aisha-Sultana (sai jar fata da yalolon gashi) wanda ya kai shi ga bin son zuciyarsa da zugar aboki Ziyad maimakon ya nemi karin aure. Rana daya Mai Askira ya hutar da shi da yake shi uba ne mai tsinkaye, mai son gyara rayuwar yayansa ba ya dagula ta ba irin Ya Gumsu. Shi bai dauki wannan auren da ta ke son yi masa gata ba, sai hanyar huce haushinta a kan auren diyar kishiyarta Fulani Bilkisun Askirama. Amma ya sani a yadda Ya Gumsu ta ke kan dokin zuciya irin wannan, ba wasu kalaman lallashi da zai yi amfani da su da za su sa ta saurare shi. Mafi aala ya nisance ta har sai ta huce, tunda dama ga alfarmar da ita ma Fulani Bilkisun ta nema daga gare shi, na cewa zai bar Saadatu ta gama makaranta kafin ya dora mata nauyin aure. Jiki a salube Yareema Sageer ya baro turakar Ya Gumsu, ya tadda Awaisu a mota, bayan dogarai sun bude masa ya shiga, Awaisu ya ja motar ta kofar shiga gidan Yareema ta baya suka bi, duk da cewa ba wata tafiya ce mai nisa ba, trackable distance ne daga masarautar. Hanne, Raheema da Saadatu ne kadai a dakin, Hanne da Raheema hirar tsaruwar gidan Saadatu suke yi da komai da ke cikinsa. Yayin da Saadatu ke ta kuka har zuwa lokacin, tun suna lallashinta har sun gaji sun kama hira sun koma yi mata dariya. Hanne ta ce, Sai ki yi ai, dadi ne ya yi miki yawa. Ni mijin nake so ya gudu ya bar ni, ke Allah ya kashe Ya ba ki kina so ki yi butulci, kukan dadi ki ke yi, ki ci gaba Saade. Raheema ta ce, Ni in ni ce na samu wannan gidan na Saa ai bude ido zan yi in sha kallon abuna mu more niimar da Allah ya ba mu. Sai jin gyaran muryar Awaisu suka yi daga bakin kofa. Ya yi sallama suka amsa, sannan ya dan shigo ya dube su ya ce, Me kuke jira ba ku kama gabanku ba?. Hanne ta ce, Kudin sayen baki mana!. Ya yi dariya don daga jin maganarta ya san yar kauye ce futuk, ya ce, Ai ke ce sayen bakin amma fadi me ki ke so a ba ki ki fito ki bar Yarima da Sa'adatun sa? Sai ga Yariman ya iso kofar dakin ya ce cikin kasaitarsa da muryar da ke gigita Saade har cikin kwanyarta. Ba jimawa kuwa jikin ta ya hau tsuma. Awaisu please drop them at home, na gaji da yawa. Awaisu ya ce, Sun ce kudin sayen baki suke jira. Ya ce, ka ba su ko me suke so, amma ku kama gabanku dukkanku, har kai. Ai kuwa Saade ta sake rushewa da kuka ta kama hannun Raheema ta kankame. Yanzu tafiya za ku yi da gaske ku bar ni ni kadai Raheemah? Yareema ya jiyo abinda Saade ta ce, da kukan da ta ke yi mai ratsa zuciya, zuciyar sa ta motsu, ba zai iya jure jin sautin kukanta ba, daga Awaisu har su Raheema ba su ankara da sanda ya shigo dakin ba, sai sunkuyawarsa da daukar Saadatu kacokam a hannayensa biyu kamar ya dauki karamin yaro, ya juya ya fice yana ce da su. please....Mun sallame ku, mu kwana lafiya. Saade wadda kanta ke rufe ruf cikin laffaya tana aikin kuka, bata gane me ke faruwa ba, har sai da Yareema ya soma hawa matattakala da ita a hannun sa,wadda zata sada su da turakar sa, sannan ne ta gane a hannun Uncle Yareema ta ke dungurugum, ta hanyar jin kamshin invictus paco rabbanne da taushin hannayen sa da ya mamaye ta. Ta kuma ji an raba ta da kasa kacokam. Kukan ya makale don kansa ta koma salati tana wutsil-wutsil da kafafunta. Su Raheema me za su yi ba dariya ba? Yarima bai sake bi ta kansu ba ya bi matattakala da Saade a hannunsa zuwa upstairs dinsa. Bai dire ta a koina ba sai a kan sofa. Yana ajiye ta tana zabura tana mikewa suka tsaya a tsaye kamar zakaru suna kallon-kallo, idanunta jazur wadanda suka sha kuka suka koshi. Idanunsa a lumshe, wadan suka jiku da soyayya. Ba ta ankara ba ta ga Dr. Sageer ya juya cikin tafiyar sa ta kasaita, ta dauka daya dakin zai shiga don rage manyan kayan dake jikin sa, don a sanin data yi masa bai iya zama da kaya masu nauyi na tsayin lokaci, ta samu damar da ita kuma zata fice ta koma kasa. Maimakon hakan data yi hasashe, sai gani ta yi ya isa ga kofa ya murzawa dakin keydin dake jikin kofar, ya kuma zare mukullin ya jefa a aljihun gaban rigarsa. Ya koma can jikin gado yana rage nauyin kayan alfarmar dake jikinsa, ya cire babbar rigar ya ajiye a gefe, sannan ya zauna a bakin gado ya dauki wayarsa yana daddannawa ya baiwa banza ajiyar ta. Har zuwa lokacin Saade na tsaye inda ya barta kamar mutum-mutuma. Ta kasa motsawa ko nan da can. A yadda Yarima ya ganta ya san ba karamar rigima ta ke ji ba, sai motsi take da baki amma ta kasa magana. A yadda yake ji shikuma ya shirya wa kowacce irin rigima da za ta zo da ita, koda zasu babbaka kan su a dakin, tunda finally ya mallake ta shi ke da nasara cikin kudura da iradar Ubangiji, ba don ya isa ba, babu tsumi ba dabararsa. So duk wani protest da zai zo daga gareta zai iya shanye shi. Tunda iya wuya ita aka kwara. Matsalar sa daya sarautar sa bazata barshi ya iya lallashin mace ba, ko ya nuna weakness. Ta ya ya zai yi wasa da wannan kyautar bazata mai daraja da mahaifinsa ya yi masa? Bai kara bi ta kan Saade ba yana ta latsa wayarsa. Da Awaisu yake magana kasa-kasa, inda Awaisu ya tabbatar masa ya maida su Raheema wajen Fulani, ya kare da cewa, Ka tausaya wa yarinyar mutane please Yareema. Ka rike ta amana. Ka san dai a cancanta baka cancanci auren ta ba Allah ne ya dube ka da rahmar sa. Dubi yadda ta ke ta kuka kamar ranta zai fita, wallahi ta matukar bani tausayi. Very young da aure. Ya san Awaisu gaskiya ya fada. Amma a ki-fadi irin nasa. A kufule ya amsa. Ina ruwanka da matar mutane da har ka kalle ta ka san kuka ta ke yi? Awaisu ka fita idona in rufe, ka fiya shiga sabgata da yawa, ko kukan jini ta ke bai shafe ka ba, tunda dai ba Asiya ba ce. Wannan maganar da kake yi ba hurumin ka bace. Awaisu sai dariya yake har Yarima ya kashe wayarsa. Malama, in kin gama kukan ki yi mana light-off, zan kwanta. Saadatu ta sake bare baki tana kuka da sauti kamar karamar yarinya, wane irin light-off ita da namiji a daki daya? Kukan nata sai ya koma bai wa Yarima dariya, amma da yake ba gwanin yinta ba ne, sai bai yi ba. Ga tension din da Ya Gumsu ta saka shi a ciki. Ga maganar Awaisu ta taba shi. Ya mike zuwa closet din jikin bango yana canzawa zuwa pajamas. Ta gefen ido Saadatu ta sato kallonshi, ai kuwa riga yake kokarin sa wa ta hango ingarmanphysique chest din Yareema Sageer Yusuf Askira da manyan damatsansa wanda ke lullube cikin muscles da ba shiri ya sanya ta kauda idonta. Jikin ta ya hau tsuma. Ta kuma durkushe a kan kafafunta ta bude shafin sabon kuka wanda ya ratsa har cikin kwakwalwar Yareema Sageer. Zuciyarsa ta karaya, ko kusa bai yi niyyar rarrashinta ba a yau, so yayi su yi duk irin rigimar da zasu yi ya nuna mata ba gudu ba ja da baya a auren su duk rashin son ta da auren. Auren su mutu-ka-raba ne. Amma kukan nata ya karya lagonsa, ya ji ba abin da yake so irin ya san hakikanin damuwarta a kan aurensa. In dai har za ta yi hakuri ta zauna da shi cikin kowane hali, shikuma zai yi duk abinda take so komai tsaurin sa. Gefen gadon ya koma ya zauna, ya dunkule hannayensa cikin junansuya dora habar sa akan su, ya rasa abinda yake masa dadi. A yanzu ko bata furta ba ya gama gane Saade bata farin-ciki ko kadan da zamowar shi barin rayuwar ta. Wannan kukan data ke yi ya wuce na amarci, kuka ne mai nuna an zalince ta, an katse mata rayuwa. A hankali ya kira sunanta da wata irin lallausar murya da shi kansa yake tababar kasancewar tasa ce. Saadatu! Ba ta amsa ba, haka nan ba ta fasa kukanta ba, kukan da ke cin ran sa, sannan ba ta dago ta dube shi ba. Tana nan durkushe a inda ta ke kamar an kafe ta a wurin, nannade cikin jar sassalkar laffaya ta bare-barin usli. Yarima ya mike daga zaunen da yake a gefen gado, a hankali ya soma takawa zuwa gaban Saade, kafarsa na nitsewa cikin tattausar kilishin tsakiyar dakin.Pajamas ce ruwan toka kawai a jikin sa iya gwiwar sa samfurin Marks and Spencer, ya daure tsakiyar da igiyar ta. Yana zuwa hanayenta da ta rufe fuska da su ya kama, ya tsuke su tsakiyar tafukan tausasan hannayen sa, ya bude fuskarta wadda ta yi kaca-kaca da hawaye ta yi jazur, da ka ganta a wannan lokacin za ka san BAGGARA ce. Kamar uwa da uba duka shuwa-arab suka haife ta. Hannayenta da ya kama ya ja ta a hankali zuwa jikinsa daga tsayen da suke. Bata kai shi tsayi ba iyakacinta kirjin sa.Slowly yake rungume ta tightly, ta yadda kowacce gaba ta jikinsu sai da ta hadu da yar uwar ta. Haduwar fatar jikin su wuri guda tamkar jan wutar lantarki ya haifar ga kowannen su. Da wata irin azama Saade ta soma kokarin janye jikinta daga na Yarima Sageer, saboda wani alamari ne da bai taba faruwa da ita ba (physical contact) da kowanne Da namiji, balle wanda ta ke wa ganin matsayin babban Yayanta. Tsatstsauran rikon da Yarima ya yi mata ya sa ta kasa kwacewa, tun tana kokawar da mutsu-mutsun kwatar kanta har ta gaji tubus! Ta bari, hawayen fuskarta Yareema ya soma wiping da lips dinsa, wanda hakan ya jefa Saade cikin wani hali da ta kasa ganewa. Wani ignition ne tamkar electrical shocking ke yawo a cikin gangar jikinta a duk lokacin da lips din Yarima ya sauka a kan fatar fuskarta. Duk da haka kokari ta ke ta kwace jikinta amma bai bata damar hakan ba. Kina so in cika ki Saadahtouh? Muryar Yareema Sageer tamkar ba tashi ba. Ta zama very pale idan aka kwatanta ta da ta dazu da yake magana cikin izza da sarauta. Kai ta daga, domin kwarai ta ke so ya cika tan ko ta shaki numfashi yadda ya kamata, sabida ba ta saba da hakan ba. The feeling is awesome, and their closeness is so intoxicating. (Kusancin ta da shi mai bugarwa ne). Kai za ta iya rantsewa babu namijin da ya taba rike mata hannu in this manner ta ji irin abinda ta ji yanzun tun tasowarta, don haka komai da Yarima yake yi a yau is so strange to her, zuciya da gangar jikin ta sun kasa karbar sa. Maimakon ya cika ta kamar yadda take fata, sai ya kwantar da kai gabadaya a kafadun ta ya kanainaye cikin jikin ta. Har tsayuwa ta soma gagarar ta domin ya saki duka nauyin sa a jikin ta, amma yasa hannu daga bayan ta ya tare ta. Yareema ya soma magana da murya mai kassara zuciyar diya mace, mai nuna karbar laifi da shirya repenting, zaka rantse ba shine Dr. Sageer din da ka sani a NTNU ba. Kuma Yariman Askira mai jiran gado. Mafi soyuwa a zuciyar Mai Askira. “Na ji kuma na yarda da korafin ki na cewa an miki laifi an aura miki mai yin zina. Ba tare da an nemi yardar ki ba. Ba zan iya cewa kin yi karya ba. Sai dai kada ki manta su din iyayen mu ne bamu da kamar su, nima baa nemi yarda ta ba, da an nema da na gaya musu ban cancanci mallakar pure soul irin ki ba Saadah!. Tunda bakin alkalami ya riga ya bushe ni da ke duka bamu da abin yi banda fuskantar reality na rayuwar da ke jiran mu a gaba, mu manta da ta baya. Ko me ki ke so zan miki Saadah, in har za ki amince ki zauna da ni. Duk sharuddan da za ki kafa min a zamanmu zan bi su, in dai za ki ci gaba da amsa sunan matar Sageer Askira. Saadatu this is not the right time to discuss anything sensitive like this, dukkan mu hutu muke bukata, don haka so nake ki kwanta ki huta na gaji Saadahtouh, bikin Askira mai wahala ne, hutu kawai nake bukata yanzu, ke ma kin gaji da hidimar bukukuwan mu na aladah, ki yi hakuri da kukan nan haka mu kwanta mu yi barci. Mu bar wa gobe tattaunawar, komai dacinta zan saurare ki! Na yi alkawarin canza komai na rayuwata zuwa mai kyau daga ranar dana mallake ki Sa'adah na yi alkawarin nan. Ka bude min kofa in fita to. Karo na farko da ta yi magana tun shigowarsu dakin. Domin kalamansa sun sanyaya mata zuciya. Saadahtouh, ke matar aure ce yanzu, kuma macen arziki ba ta raba makwanci da mijinta sai bisa lalura. Muryar Saade bata fita sosai sabida kukan da ta sha. Ta ce. Don Allah Uncle Yarima ka bar ni in koma wancan dakin, ni ba zan iya kwana daki daya da kai ba. Ta fadi da iyakar gaskiyarta. Me ki ke tsoro? In kin kwana gado daya da mijin ki Malaiku ne za su yi ta sa miki albarka har garin Allah ya idasa wayewa, musamman if you act as my messeuse (idan kika zama mai min tausa) duk jikina ciwo yake mun saboda zirga-zirga da hayaniya. Please Saadah help me... Ya fada yana kara makalkale ta ta yadda suka dunkule wuri guda kamar curin alkaki, ba tare da Saade ta san yaushe hakan ta faru ba Saboda gabadaya muryar Dr. Sageer ta gama kashe duk wani kuzarinta. Ta saukar mata da wata irin kasala. Ita ma ba ta san me ta ke tsoro a kwanansu daki guda bisa gado guda babut shes really-really afraid, wani abu ne STRANGE a gare ta, don bata taba ganin inda akai hakan ba. Duk da ta san a yanzu an daura musu aure amma zuciyar ta ta kasa karbar wannan sabon dingimemen sauyin da sauki. Tana wannan tunanin mai matukar dagula zuciya, ba ta yi aune ba sannan bata tantance komai ba ta ji Uncle Sageer ya soma warware laffayar jikin ta tun daga sama cikin nutsuwa har ya sauketa kasa tsaf, ya saura daga ita sai underwear din dake jikin ta, kallo daya Dr. Sageer ya yiwa Saadatu cikin fararen under wear ya ji komai na duniya ya tsaya masa; including numfashin sa. Daga hakan ya sunkuce ta ba tareda ya tsaya sake kallon ta ba, bai dire ta a koina ba sai a royal bed din su, ya ja wani lallausar duvet ya lullube su, tare da latsa makunnin lantarki daga nan inda ya ke kwance. Fitilu shudaye suka maye gurbin masu haske (dim light). A dirowar jikin gadonsa ya bude ya fiddo turarensa Invictus (Paco Rabbanne) ya soma feshe su dukkan su, ya ce. Bana son wadannan turarukan matan barebarin da aka gumbuda miki, daga yau kada ki sake shafa su, we will be using the same scent, wadannan sun cika karfi da yawa hawa min kai suke yi. Daga yau za mu dinga using nawa tare (Paco Rabbanne), you can use it too ba shi da karfi. Saade ta zumburo baki kamar yana ganinta, ai kuwa ya gani ta cikin dan hasken dim din wanda hakan ya sa shi yin abin da bai shirya ba. A hankali ya soma sumbatar Saade tun daga yatsar kafarta At first hes doing it gentle kafin gabadaya ya koma hungrily, da gani za ka san abu ne da ya dade yana fatan kasancewar sa. Ya dauki Saadatu diyar Fulani Bilkisu ya kai ta wata kololuwar duniyar soyayya da ba ta taba tsintar kanta a ciki ba. A yadda Saade ta yi amanna ta mika wuya ko me Yarima ya nema a lokacin tabbas zai samu, domin ba ta san inda Yarima Sageer ya dauke ta ya kai ta ba. Amma sai me? Kalaman Ya Gumsu ne suka fado cikin kwakwalwarsa suka katse duk wani hanzari nasa. Ban yarda ka taba yar Bilkisu ba, ban yarda ka hada shimfida da ita ba. Sai kuma na Fulani Bilkisun Ina neman alfarmar ka daga mata kafa har ta kare makaranta. Yarima ya rasa inda zai sa kansa a wannan lokacin. Ji ya ke tamkar ransa zai bar gangar jikin sa. A hankali ya mirgina ya koma can karshen gado ya runtse idanunsa yana ambaton sunan Allah. Saade na jin shi, amma ba ta san dalilin sa na janyewar ba. Da nutsuwa ta soma dawo mata sai ta ji wata matsananciyar kunya ta kama ta. What happened like this? Wannan wane irin abu ne mai tsauri da nauyi yake faruwa tsakaninta da Uncle Yarima haka? Kanta ta tusa cikin pillow kamar ta roki gadon ya tsage ta shige. Tana jin saukar numfashin Yareema a hankali har daga baya ta gane ya yi barci. Ta yunkura da zummar ta nemi mukulli ta fice, amma sai ta ji caraf! Hannuwan Yarima sun maida ta kwanciyar, ya kuma sake mirginowa ya rungume ta sosai a jikinsa. Bai kuma kara attempting komai ba, tun tana fargabar faruwar wani abu makamancin na dazu har ta gane barcin sa ya yi nisa sosai. Akai-akai Saade ke sauke ajiyar zuciya tana tambayar kanta, wannan shi ake nufi da auren ke nan? Su dunkule su zama abu guda in every aspect kuma marufar sirrin juna? Sirrin da yafi karfin kwatance ko fadar sa ga wani. As a university student ba za ta ce kwata-kwata ba ta san manufar aure ba duk da babu wanda ya taba zaunar da ita ya gaya mata, duk sakewar da ke tsakaninta da Fulani magana irin wannan ba ta taba hada su ba. Baggara akwai kunya tamkar Fulani suke, sai dai kuma sun fi Fulani ilmin addini. Sai goshin asubahi ta samu barci, kuma ko na minti daya Yarima bai yarda ya raba ta da jikinsa ba. In ma ta yi kokarin zamewa tsaf cikin barcin zai kara kanainaye ta. Tun tana jin kunya har ta gaji ta yi barcin ta a jikin sa. Ko don wannan turaren nasa mai dadin kamshi da sanyaya zuciya za ta so su wayi gari a haka. Daren yau bakidayansa wani yanayi ne da ba za ta taba mantawa ba a tarihin rayuwarta. Ba ta maraba da auren Yareema Sageer, ba ta kuma taba mafarkin faruwarsa ba, amma daga daren jiya zuwa yau sai ta ji dama su dauwama a haka! Ba tareda wani dan adam ya kara ratsa tsakanin su ba. The moment is awesome because its strange but pleasant ga Saade, don haka image din ya tsaya a kwakwalwarta. Hoton ta makalkale cikin jikin Yarima Sagir, ya kasa bacewa dagascreen na zuciyarta. A haka aka yi kiran assalatu. Da yake ba ta dade da samun barcin ba, ko motsi ba ta yi ba. Har Yarima ya mike ya je toilet din da ke makale da dakin ya kammala abin da zai yi ya fito Saade ba ta da alamar farkawa. Duk da bahagon halin Ya Gumsu, a baya na gaya muku cewa yayanta akwai sallah. Sai ya tsaya a daidai fuskar Saade yana taje jikakkiyar sumar kanshi. Yarfin ruwan a fuskarta ya sa ta bude ido kadan, sai idonta cikin na Yarima. Da fari ta dauka a dakinta ta ke na Abuja, amma ta san Uncle Yarima bai taba shigar mata daki a irin wannan lokacin ba. Ta sha ganinshi da pajamas ko a gidanshi, amma ya kan daure tsakiyarta da igiyar jikinta, amma yau bai daure ba, physique chest dinsa dauke yake da suma a kwance luf, wanda hakan ya sa ta saurin kauda kanta. Sai kuma ta tuna wai fa ashe su din yanzu miji da mata ne. Ajiyar zuciya ta kwace wa Saade daga kwancen da ta ke. Har sai yaushe kwakwalwarta da zuciyarta zasu karbi reality na kasancewar ta matar Yarima Sagir ne? Yareema ya mika mata hannu da nufin ta kama ya taimaka mata ta tashi, amma sai ta juya daya barin ta rabu da shi. Ya ce, Tashi Saadahtou mu yi jamin sallah kina makarar da ni. Saadatu ta yi shiru, ta ya ya za ta iya gaya masa cewa, period ta ke yi? Ba za ki tashi ba? Ya fada for the second time yana mamakin abin da zai hana ta yin sallah, sai kuma ya tuna mace ce, don haka ya juya ya tada sallarsa. Har gari ya soma haske Yarima na sallah, ita kuma ta kasa komawa barci. Tunanin rayuwar da za ta riske ta a gaba ta ke yi. Tunda yanzu rayuwarta ta zama dependent upon Yareema. Sai yadda yayi da ita. A baya shi din guardian ne, amma a yanzu matsayinsa ya zarta na kowa kenan including iyayenta. Wannan ba karamin nauyi ba ne aka dora mata, wanda ba ta san ya ya za ta yi da shi ba. Ta duba ta laluba cikin tsokar zuciyarta ko za ta ga SO ko akasin sa a kan Yareema Sageer? Amma sai ba ta samu ko guda dayan su ba, babu soyayya haka babu kiyayya tsakanin ta da Yarima, sannan daga daren jiya zuwa yau alamuran Yareema Sageer masu ban mamaki ne da suka soma rikita hankali da nutsuwarta. Tana nan kwance har Yareema ya gama sallolinsa, ya sunce ya shiga wanka. Da ya fito ya tambayi Saade, Manyan kaya zan sa ko kanana? Ta yi masa shiru. Ya ce, Alright. Bari kawai in sa kanana, ban sani ba ko saboda tsufana ne ba kya so na. Ta juya masa baya bata ba shi amsa ba. Ya gama sanya kayansa riga da wandon BALANCIAGA ruwan goro masu ratsin black. Sai ya fito a Georgeous Prince dinsa. Kai bazaka ce ya taba aure ba. Ya hawo bisa gadon daidai inda ta juya fuskarta yau zaki sha tea irin wanda baki taba shan irin sa ba. Sai ta rufe idanun ta gabadaya daga barin kallon sa, don ji ta yi zuciyar ta na racing. A cikin dakinsa akwai karamar butar dafa shayi, ya jona kettle din bayan ya yi hade-haden shayinsa na naa-naa da girfa, yadda Saadatu ta juya masa baya ta ki juyowa yana taba ransa, sabida shi dai ba haka matarshi ta sabar mishi ba. Da sun wayi gari da ta soma haba-haba da shi har sai ya ce ta dame shi. Ya zuba kakkamsan shayinsa a dan karamin farin kofin shayi na karau, ya zauna a gefen gadon daga daidai kafafunta yana sipping a hankali. Kamshin shayin da yake sha duk ya cika ta, ya kuma tayar mata da appetite na abinci, sai lokacin ta tuna rabonta da abinci. Tun na safiyar jiya da Hanne ta matsa mata ta ci lomar sinasir guda biyu. Akuyar cikinta har wani irin kugi ta ke yi cikinta na murdawa da yake tana da ulcer kadan tun a El-Kanemi. Dole ta mike ta nufi toilet ta yi brush, ta yi wanka ta kuma nemi pad din da za ta canza ta rasa. Kayan jikinta ta maida, wato doguwar riga mai bin jiki ta roba wadda ake sa wa a kasan laffaya (underwear), ba ta nada laffayar ba ta fito gashin kanta da ya sha kitson nan jelunan sun kwanta lambam a wuyanta. Kai tsaye ta nufi kofa don ta tuna Raheema ta gaya mata ta sa mata pad din a lokar jikin gadon dakinta da suka kai ta jiya. Amma me? Kofar a kulle gam, kuma ya zare mukullin jiki. Ta juya a sanyaye ta dube shi suka hada ido yana kurbar shayi, ya ga damuwa karara a tare da ita. Ya ajiye kofin hannunsa a kan lokar gadon ya taso a hankali ya iso gabanta. Hannayensa duka biyu ya zuba a cikin aljihun wandonsa, ya dube ta keenly, murya raunane ya ce, Me ya sa ki ke guduna ne Saadatu? Ta sadda kanta kasa. Ya ce, Ki kwantar da hankalinki kin ji, za mu zauna mu yi magana ta fahimta kafin mu tafi Abuja, yanzu nan da awa guda za ki ga gidan nan ya cika, don haka ki yi hakuri ki ba ni one hour in yi ta tare da ke, kada ki bar ni ni kadai. Murya can kasa kamar an shake ta ta ce, Zan dawo, abu zan dauko. Gaya min ko mene ne in dauko miki, amma ba za ki bar dakin nan ba sai na miki umarni. Kamar ta fashe da kuka, ta ce, Ba ka san inda yake ba, besides abin na mata ne. Yarima ya ce, Okey. I can relate. To mu je tare, kada ki yi min wayo ki shige daki ki rufe. Ta turo baki, ta ce, Na yarda. Sannan ya bude kofar suka sauka zuwa downstairs. Bayin da aka ba su suna ta hidimar tsaftace gidan suka wuce su bayan sun gurfana sun yi gaisuwa, yana kallo ta bude lokar ta dauko ledar sanitary pad ya sa ta a gaba suka koma upstairs dinsa. Suna shiga dakin ta wuce toilet, kafin ta fito Yarima ya zuba mata shayin da ya sha yana firfita mata between two cups. Ta fito tana taku a hankali kamar mara gaskiya ta zauna a kan sofa bed can nesa da shi ta zuba uban tagumi da hannaye bibbiyu. Yareema ya taso zuwa inda ta ke, ya rusuna ya mika mata shayin, sannan ya zauna daidai kafafunta, kai ka ce ita ce Yariman ba shi ba. Ta sa hannu ta karbi shayin don ba ta yi wa yunwa fulako. Ganin yadda ta ke shan shayin da sauri duk da zafinsa ya sa shi tambayarta. Tun yaushe rabonki da abinci? Saade ba ta ce komai ba, sai shan shayinta ta ke yi, kan ka ce me ye wannan ta zuke shi. Da gaskiyar sa bata taba shan shayi mai dadin nasa ba da wartsake makoshi. Ya mike zuwa ga bed side fridge dinsa, ya dauko danyar madarar oldenburger mara sanyi, ya zo ya bude ya tsiyaya mata a tambulan ya zauna dab da ita ya kai kofin bakinta. Da farko kunya ta ji, amma kuma an ce mata suna son kulawa irin wannan daga mazajensu, kulawar da ba duk maza ke iyawa ba sabida girman kan su. Sai ta ji ta kasa tankwabe wannan kulawartasa, ta bude baki tana shan madarar sosai daga hannun Yareema, sai da ta shanye madarar tas, zai kara mata ta ce a hankali, Ya isa. Sai ya ajiye kofin ya juya ya kwantar da kai a cinyoyinta. Hannayensa zagaye da kugun ta. Now, tell me Saadatu, why dont you love Sageer? Ta rasa inda za ta sa kanta, sabida Uncle Sageer ya yi kwanciyarsa akan cinyoyinta, ya mike kafafunsa bisa sofa din. Uncle Ta fada a hankali very upset and unease. So take ta ce ya daga ta kada wani ya shigo, amma kunya ta hana ta. Kada ki kara ce min Uncle, ban san ta ina na zama Uncle dinki ba. Ni ba kanin Fulani ba, ni ba kanin Baban ki ba... Ni, (ya nuna kan sa) ni ne SAGEER kawai, Sageer Askira, ba ni da wani lakabi bayan wannan. Ya sa tafukan hannunsa a fuskarta. Very smooth and supple. In ji dai ba shafe-shafen zamani ki ke ba? I love natural skin shi ya sa nake son Sultana. Ai ba ta san lokacin da ta ture kansa daga cinyarta ba ta mike. Allah ya so ta bai cire mukullin daga jiki ba, ta bude kofar ta yi ficewarta. An ce ko babu SOYAYYA kishin cikin AURE daban yake. Haka ta wuni ranta a bacea kan yar maganar da Dr. Sageer ya fada akan Sultana, yayin da Dr. Sageer ya wuni cikin matsanancin nishadi da bai taba tsintar kansa a ciki ba. A yadda ya fahimta insha Allahu ba zai sha wahalar samun soyayyar Saadatu ba, tunda har ta fara kishin matarsa. Dama ya fada ne don ya ga reaction din ta. Ya canza kayan jikinsa zuwa Jabba da hular data dace da kalar kayan wato deep-brown, ya fesa turarensa ya fito. Tuni bayi sun cika tebir da abinci naui-naui. wanda aka kawo daga unguwar Fulani Bilkisu. A cikin bayin da Maimartaba ya ba su akwai wata kuyanga Sadiya, burinta kawai Yarima ya yi kwarkwara da ita ba tun yau ba, don haka ba karamin dadi ta ji ba da aka hado da ita cikin hadiman gidansa. Yanzun ma yana fitowa ta fadi gabansa, Gyara kimtsi da kyau, lafiya dan zakin Duniya lafiya dan malafar duniya, lafiya dan mai fada da cikawa lafiya dan mashasha lafiyarka dama da hauni mai nasara zauna daidai dan bawan Allah zauna daidai dan masu alheri. Yana zama bisa dining table ba tare da ya dago ido ya dube ta ba, ta hau yi masa firfita da maficin gashin Dawisu tana ci gaba da zubo kirarin. Daidai lokacin da Saade ta bude kofar dakin ta fito cikin wata irin sassaukar kwalliya ta riga da zane dark blue na yadin karen miski wanda ba a samunshi koina sai gidan sarauta. Wani kallo da ta sakar wa Sadiya ya sa ba shiri ta juya tana mata nata kirarin. An fito lafiya uwar masu gida, zauna daidai uwar alheri taka lafiya matar Zakin duniya. Saade ta kira sunanta a hankali kafin ta wuce ta ce, Sadiya! Kada ku kara zuwa nan in ba ni na kira ku ba. Lokacin aikinku daga karfe shidda ne zuwa bakwai na safe, da kun gama jera abincin karin kumallo shi ke nan na sallame ku. Sadiya ta amsa a matukar ladabce, sannan ta fice. A ranta tana fadin, Ta Allah ba taki ba. Insha Allahu ni ce Sa-dakarsa ta farko duk boyon da za ki yi masa, me ya kai ki auren Basarake in kin san kishi gare ki? Yarima yana jinsu kansa a duke yana danna wayarsa, sai ya ji murmushi ya kwace masa. Ya dauka zuba masa abincin ta fito ta yi, amma tunda ta kori Sadiya sai ta juya ta koma daki abinta ta barshi a nan zaune. Sai ya ji ya kasa ci. Ya zuba abincin daidai misali a kan plate, ya dauka ya bi bayanta. Ta zauna kenan a bakin gado ta yi tagumi, wadannan yammata da aka cika mata gida da su kullum suna sintiri a gaban Yareema yaya zata yi da su? Ta isa ta ce zata zauna babu kuyanga? Ko cewa zata yi a kwashe su a kawo mata tsoffi? Kowa ya ji hakan a take zai fassara ta da kishi. Ita kuma ta san ba kishi take ba tsoro ta ke ji, tunda ta san wa aka aura mata. Tana wannan sake-saken sai gani ta yi tattausan hannun Yarima mai daure da agogon ‘Swatch Blustery’ ya miko mata plate cike da soyayyen dankali da sauce din koda da hanta. Saade ta dago ido a hankali ta dube shi. Ya daga mata gira, ya ce, Karbi. Sai ta kasa tankwabe wannan kulawar a karo na biyu. Ta sa hannu ta karba cike da jin nauyi, ita ba ta ba shi ba shi ya dauko da kansa ya kawo mata, ta tuna wane ne Yareema Sageer a masarautar Askira gabadaya da yadda kannensa da yayyensa duka ke sonshi da girmama shi. In ta ce ba ta ji wani iri a ranta ba kan rashin kyautawar ta ta yi karya, sai ta ji somehowkamar abin da ta ke yi ba daidai ba ne. Don haka ta motsa dan bakinta a hankali yana shirin ficewa daga dakin tace. Uncle kai ba za ka ci ba? Ya juyo gabadaya ya fuskance ta sabida ya tsani wannan Uncle din da ta ke ce masa. Ya ce, This will be the last time da za ki sake kirana Uncle tunda dai ni ba kanin Fulani ba ne, idan ba za ki fadi sunana ba ki sa ma min wani. Amma ki ka sake ce min Uncle Allah zan cire hijabin da ke tsakaninmu Saadatu, wanda ke sa ki yi min kallon kanin Babanki. Maganar ta bata dariya amma bata yi ba. Ya juya ya fice yana cewa, Mun tafi Ta-Sani ni da Awaisu. Murmushi ya subuce wa Saade, kowanne irin hijabi ne tsakanin nasu? Oho! Ta maida hankali ga cin abincinta, kunnenta har motsi yake sabida yunwa da dadin abincin wanda daga jin kamshin sa ta san daga unguwar Fulani Bilkisu yake. Yareema da Awaisu sun je sun gaida Alhaji Kyari, bayan sun gaida Maimartaba, sannan suka wuce cikin gida, unguwar Ya Gumsu suka fara zuwa suka kwashi gaisuwa, ta amsa musu kadaran-kadahan sai kallon Yareema ta ke da wutsiyar idanu kamar mai son gane cewa ya bi umarnin ta ne ko aah? Ya maida Saadatu cikakkiyar matar sa? Tsoronta Allah tsoronta ranar da Sageer zai hada shimfida da Saadatu, don ta san daga ranar ba za ta sake gane kansa ba,kamar yadda ba ta kara gane na ubansa ba tunda ya auri uwarta, kai ba ita kadai mahaifiyarsa ba, har waccan baturiyar tata ta kare. Ita ta san sirrin matan BAGGARA, ta san ta inda Fulani Bilkisu ta bi ta birkice musu kan miji kenan. Allah kadai ya san iya abubuwan da ta koya wa yarta, da sirrin mallakar da ta dankara wa Saaden(Allah Sarki ZATO. Mu kasance masu kyautata zato ga yan uwanmu musulmi, in ba haka ba za mu kare ne da daukar nauyin zunubansu. TAKORI). Daga wajen Ya Gumsu suka nufi unguwar Yaakirjiloma, Mairam Murjanatu na shirin tafiya tare da yayanta, tana ganin Yarima faraarta ta fadada, ta ce, Ka ga ango sha kamshi. Angon Saa da Aisha-Sultana. In ce ko an rago min kazar amarci? Dariya Yareema Sageer ya yi, don yana son Yayarsa Murjanatu sosai, tana da son zumunci da hadin kansu, shi sai yanzu ma ya tuna wai ana kai wa amarya kaza, shi haka ya tafi hannun sa na dukan cinya, dan banzan Awaisun nan kuma bai tuna masa ba, amma babu komai bari lokacin ya zo su koma Abuja, zai yi komai don Saadatu. Ko dawisu ne zai sa a gasa mata ba kaza ba. Ya ce, Mairam Murja, ba dai shirin tafiya ake ba? Na dauka za ku zauna har ku raka amarya Abuja? Murjanatu ta ce, Na so hakan, amma Ambassador ya yi waya maza-maza in koma sabida yara sun koma makaranta, kada ka damu za mu zo suna next year in Allah ya yarda. Yarima ya ji kamar ya nutse kasa don kunya, amma a zuciyarsa ya ji dadin wannan fatan nata, fata na gari lamiri in ji masu iya magana, kuma babu wanda zai so ta haifa masa Da a duniya irin Saadatu. Wani disappointment din is a blessing (Aisha Sultana da ta cire mahaifa) don an ce yaya suna tsotso dabiu da halaye na mahaifan su. Ya ce, Wa zai kai ku Maiduguri (airport)? Ta ce, Maimartaba ya bada mota da dogarai su kai mu, Humaira da Najaatu za su raka mu har su ga tashinmu sai su dawo. Ya fiddo wayarsa daga aljihun gabansa yana fadin, Bari in kira Suhail da Ahmad duk su raka ku, tafiya da maza za ta fi dadi. Ya yi magana da Ahmad da Suhail, sannan suka yi sallama da Murjanatu, suka karasa falon Yakirjinoma suka yi gaisuwa ta sa musu albarka. Ta kawo turaruka ta ce a kai wa Saadatu. Daga nan sai Unguwar Fulani Hibbani. Najaatu da Humaira suka gaida yayyun nasu, Sageer da Awaisu. Humaira sai faman dauke kai ta ke don tsananin haushinsa da ta ke ji, ya rasa wadda zai aura sai yar Fulani Bilkisu don kawai a wulakanta iyayensu? Ita tun filazal ta tsani Saadatu sabida son da Askirama ke mata, balle yanzu da ta zama surukarsa kuma matar Yarima dungurugum. Shi bai kula Humaira na ciccin magani da shi ba, ya dube ta da kulawa, ya ce, Auta, sai yaushe za a shigo mana? Ta yi wani dan murmushi na dole, ta ce, Matarka Yaya Yareema Junior ta ce fa, ya za a yi ni in je gaishe ta? Ai sai dai in ta zo nan mu gaisa. Cikin mamaki ya ce, Junior? Don sam bai gane me ta ke nufi ba. Ta ce, Kwarai, tare aka kai mu makaranta a El-Kanemi, ina aji uku tana aji daya, she has been washing my pants and undies, kai har gugar kaushi ta ke min, everything. Yareema ya kufula iya kufula saura kadan ya kai mata mari Awaisu ya rike shi. Ya ce, Saadatun? Wa ya ce miki baiwar gidanku ce? To yadda ki ke ya a gidan nan haka ita ma ta ke, idan watarana na ga kafarki a gidana sai na kakkarya ki, sakarai kawai. Ya Hibbani ta fito daga dakinta tana daura dankwali, ta ce, Yareema mene ne? Ina barci na ke jin tashin fadanka. Nan ya gaya mata a gajarce. Hibbani ta kyabe baki, ta ce, Kada ka ga laifin kanwarka Yareema, saboda da farko mu ba mu san yarta ba ce, boye mana ta yi. Cewa ta yi yar riko ce ta karbo, so don Humaira ta sa ta aikatau a makaranta ba ta yi laifi ba. Kada ka manta Humaira yar sarki ce, jikar Sarki. Wannan kuwa ko asalin ubanta ba mu sani ba. Idanun Yarima suka kada kamar gauta, ya bude dukkan idanunsa yana duban kishiyar mahaifiyarsa Fulani Hibbani, zai yi magana ya ce ita ma sun san nata asalin ba yar kowan ba ce, sadakarta aka kawo wa Askirama, Awaisu ya toshe masa baki, ya ja shi suka bar sassan gabadaya. Humaira ta ce, Humm! Aka ce auren hadi ne na Askirama, ashe da ma can yana sonta, dubi yadda yake neman dukana. Hibbani ta ce, Tabdijan! Ya Gumsu ta ga ta kanta, ai zama bai gan ni ba, bari in je in gaya mata Yareema ya gama afkawa har fiye da ubansa sai ta yi da gaske, kin ga yadda jijiyar kansa da ta wuyansa ke tashi? Humaira ta ce, Ni tunda nake ban taba ganin makiran mutane irin wadannan Baggaran ba, kyawunsu ke rudarSarakuna, amma wallahi kyawun da babu asali aikin banza ne. Hibbani ba ta saurare ta ba ta figi mayafi ta nufi Unguwar Ya Gumsu. Karya da gaskiya duk ta gaya mata, Ya Gumsu mai neman kuka an jefe ta da kashin awaki ba ta san sanda ta fashe da kuka ba tana fadin, Tawa ta same ni, ni Gumsu. To ba inda za ta bi shi a nan za ta zauna a Askira, ya je can wajen baturiyar ya zauna, ko ba komai su ba sa mugun abu, zuciyarsu ba muguwa ba ce. Bangaren Fulani suka nufa, Awaisu na ta cooling dinsa yana cewa ya yi hakuri, mata ne haka suke, sun gaji kananan maganganu wadanda bai kamata a biye musu ba. Sabida yadda ransa ke bace, duk tsokanar da Fulani Bilkisu ke masa ya kasa tankawa sai murmushi kawai yake. A karshe ta yi musu addua da fatan alkhairi. Ya sunkuyar da kai da ganinshi ka ga wanda ke gaban surukar da yake matukar girmamawa, ya ce, Allah ya taimaki Fulani, ina ganin fa gobe za mu wuce Abuja, nan hayaniya ta yi yawa ba ta barin mutum ya huta. Fulani ta ce, Haba Yareema, ka yi hakuri ku cika sati daya a gama miskero sai ku tafin. Ba da son ransa ba ya amince, don ba zai iya yi mata musu ba, amma kwarai maganganun Hibbani da yarta sun sa so yake ya dauke Saade su bar Askira. Ba zai lamunci kowa nasa ya taba mutuncinta ko na mahaifiyarta ba. Daga nan sai gidan su Awaisu wato gidan Wazirin gari Ibrahim, nan ma suka kai gaisuwa, sai gidan Galadima, Zanna, Shettima, Wali da dukkan king makers daya bayan daya sai da suka bi su suka kai gaisuwa, suka kuma yi musu godiya da ban gajiya. Sai goshin magriba ya dawo gida, Awaisu da ya sauke shi bai tsaya ba ya wuce gidansa. Awaisu na da matarsa Asiya har da albarkar yara biyu. Sanda Yarima Sageer ya shigo gidansa koina tsaf-tsaf sai tashin kamshin turaren wuta yake kuma koina shiru. Kuyangi da hadimai sun kulle koina sun wuce bangarensu. Saadatu ta gaya musu daga karfe shidda na yamma ta sallami kowa. Ita da za a raba ta da wannan tarin yammatan masu jini a jika daga gidanta da sai ta fi jin dadi, to ta san ba ta isa ta zauna babu kuyangi ba a matsayinta na matar Yariman Askira mai jiran gado, ba ta isa ta karya aladar masarauta ba. Zai wuce ke nan zuwa upstairsdin sa da zummar yayi wanka sannan ya zo ya duba Saade, sai ya ji motsin mutum, da sauri ya juya, wata siririyar kuyanga ce ta sha hoda da jambaki ta zube a gabansa. Allah ya taimake ka dan zakin duniya, sunana Sadiya ko da ana bukatar kwarkwara (sa-daka). Kamar daga sama sai ga Saadatu ta bullo daga kitchen din falon za ta wuce, ta yi wannan kyakkyawan gani ta kuma ji abin da Sadiya ta ce. Kofin tangaran na (mug) da ta hado zazzafan shayi mai kauri ta saki ya fadi kasa ba da saninta ba, ji-ka ke tush! Kofin ya tarwatse, gilashin da ruwan zafin duka a kan kafarta. Da sauri ta durkushe ta kama kafar wadda har ta soma fidda jini. Sadiya da Yarima suka yi kanta a tare. Wata irin tsawa da ta daka wa Sadiya sai da hantar cikinta ta kada, Dont touch me, get out! Ki hada kayanki duka ki koma cikin gida, kada in kara ganinki a sassana. Da gudu Sadiya ta fice ta san yau kashinta ya bushe, ta yi shuka a idon makwarwa. Babu bayani ga sauran bayi yan uwanta ta hada kayanta ta koma gidan Sarki a daren. Yarima ya sunkuya ya kama kafar, ta ture hannun sa tana kokarin janye kafarta. Azaba ba yar kadan ta ke ji a cikin tsokarta ba amma ta fi jin zafin tayin da Sadiya ta yiwa Yareema fiye da ciwon, kawai sai ya sunkuce ta ya yi saman benen da ita, duk inda suka wuce sai jini ya disa. Shi ba likita ba, amma ba ya rabo da first aid box a gidansa, toilet ya kai ta cikin jacuzzi ya wanke jinin ya cire kwalbar da ta makale tana kuka tana kankame shi, sannan ya sa mata iodine don azaba ba ta san sanda ta rungume shi ba. Ya dauko ta suka dawo daki bisa sofa ya shimfidar da ita yana ta faman jera mata sannu. He looked worried and disturbed kamar a jikinsa ciwon yake. Ya dauko pain reliever da gorar ruwan Faro ya ba ta ta sha. Ya kwantar da kanta bisa cinyoyinsa yana shafa kanta hankali. Saade sai ajiyar zuciya ta ke, amma bacin ran Sadiya bai gushe daga zuciyarta ba. Kamar Yareema ya fahimci hakan sai ya ce, Me ya sa ki ka kori yarinyar can? Da jajayen idanunta ta harare shi. Ba ka ji me ta ce ba ne? She wantto be your concubine bayan na ce kada in kara ganinsu daga karfe shidda, amma shi ne don ta raina ni ta dawo da ta ji dawowarka. Wani murmushi ya subuce wa Yareema, mace ba ta kishi sai a kan mijin da ta ke so, ko ta fara so. Ya ce, To me ye abun damuwa anan? Za ta taimaka miki ne ta dauke dukkan lalurorina har zuwa lokacin da za ki karbe ni a matsayin miji, tunda ba ki sona Saadatu ba laifi ba ne don sauran mata sun so ni, beside ba haramci ta fada ba. A hankali Saade ta janye kanta daga jikin Yareema Sageer, ta kwanta daya barin akan pillow, sabida yadda zuciyarta ke tafarfasa. A wannan lokacin ta tabbata da za ta ga Sadiya sai ta yi mata mummunan lahani. Yareema Sageer ya je ya kwanta a barin da ta maida fuskarta, ya yi mamaki da ya ga cewa kuka ta ke yi. Im sorry idan maganata ta bata ranki Saadatu. Gaskiyar magana ita ce, ba kya sona, ban san dai wa ki ke so din ba. Amma jikina yana ba ni wannan siririn yaron fari da na ke yawan ganinku tare nemai wuya uwa marikin lema. Ni na gaya maka? Ta tambaya cikin rishin kuka. Ban taba ce maka bana sonka ba Yaya Sageer, kuma ni ban taba son kowa ba. Karatu kawai nake so in yi. Auren ya yi min wuri, ka ga fa duka shekaruna sha tara, level 2 nake. Akwai sauran shekaru biyu a gaba kafin in yi nutsuwar da zan iya daukan marriage responsiblities, sannan baa nemi amincewa ta ba aka daura mana aure, ba mu fahimci juna ba in this aspect ta ya ya ka ke tunanin hankalina zai karbi wannan auren? Sosai Yareema ya fahimce ta, ya sanya hannu cikin jelunan kitsonta yana murzawa a hankali, ya ce, Na fahimce ki Saadatu. Ni kuma na ba ki dama ki ci gaba da yin rayuwarki yadda ki ka saba gudanar da ita a Abuja banda kula wannan yaron. Ni bazan takura miki ba. Insha Allahu ba abin da zai canza har sai lokacin da ki ka ji cewa you are ready to accept me as a husband, kafin nan ina so ki ba ni dama in zama malamin ki kuma aminin ki, mai koya miki karatu kuma abokin shawarar ki mai kula da dukkan alamuranki. Alfarma daya za ki yi mun, duk lokacin da zan sumbace ki kada ki ce min aa, ina matukar son in sumbace ki, na yi miki alkawarin ba zan wuce hakan ba. Da sauri Saade ta wara ido cikin jin kunya ta dube shi. A hankali ta ce, Yaya Sageer ina jin kunya!. Ya janyo ta gabadaya zuwa jikinsa, ya ce, I will take care of that daga yau, a hankali zan cire kunyar dukkanta har watarana da kanki za ki zo ki ce, Yareema Sageer.. Saade ta yi maza ta rufe idon ta. Ta cusa kai kasan filo. Shikuma ya yi amfani da wannan damar ya dauke filon ya kuma hade bakinsu wuri guda yana kissing din nata gently, softly, affectionately. Tun Saade na kokarin janyewa har ta soma lumshe yan idanunta. A zuciyarta tambayar kanta ta ke, wato bayan kissing din akwai abin da ya fi shi kenan anan gaba,tunda gashi Yareema yana cewa, ba zai wuce sumbar ba? To ko mene ne? Ko wace rana ce Yarima zai nemi hakan? Wannan din kadai sai ta rufe ido ta kuma kai zuciya nesa sabida nauyin sa..Idan akwai abin da ya fi shi a nan gaba ba ta san ya ya za ta yi da ranta ba. Sauran kwanakin su a Askira sai suka zamo na jinyar kafa da sassanyar soyayya, wadda Yareema Sageer yake matukar kokari wajen ganin bai wuce gona da iri ba. He is not going far beyond what he begged for. He is only kissing her, sumba mai sunan sumba in dai ga Saadatu ne ba ya taba gajiya, baya taba koshi. Rannan ya ce mata, “theres charisma in kissing You. Kwanansu shidda a gidan su na Askira kafarta ta kame, ya ce ta hada duk abin da ta ke bukata gobe za su bi jirgi tare da Maimartaba da Fulani zuwa Abuja. Alkawarin da Askirama ya yi na kaita Abuja gidan mijinta da kan sa ya ce zai cika shi da yardar Ubangiji. Washegari tunda asubahi an shirya motocin da za su kai su Maiduguri (filin jirgi) sannan an zabi wadanda za su yi wa Maimartaba da Fulani rakiya, cikin masu rakiyar Fulani har da Fanna wanda hakan ya faranta ran Saadatu sosai, fargabarta ta komawa Abuja ta ragu kashi sabain cikin dari ganin irin wannan rakiyar gata da zaa yi mata. ****** Jirgin Azman ya sauke su a Abuja da yamma lis. Direban Dr. Sageer da na abokinsa Dr. Ziyad su suka zo suka kwashe su a manyan motoci zuwa gidajen malamai na NTNU. Tunda suka sauko daga jirgi yake ta gwada kiran lambar Sultana tana ta ringing amma ba ta dauka ba. Ya san duk inda ta ke zuwa yanzu ta dawo gida. So yake ya gaya mata tahowarsu tare da su Maimartaba don ta sa Uche ya tanadi abinci na musamman, amma ga wayar tana ta ringing ba ta daga ba. Ya yi tsaki, sannan ya kira Uche, wanda ke Baskwata a lokacin yana wanka, ita ya kamata ta bai wa Uche umarni ba shi ba, amma da bai same ta ba dole ya kira shi. Uche, Im already on the way with his Royal Highness, cook to your best, deliciously. Madam ta dawo? Uche ya yi shiru da waya a kunne, ta ya ya zai ce masa ta dawo, amma tun shigowarta tana main falo tana drinking kada ya zo da iyayensa yanzu? Kafin ya hada amsar da zai bai wa ogan nasa Sageer ya kashe wayarsa. Da sauri Uche ya hau sake kiran shi a waya amma rashin kyawunnetworkyasa yakasa samun shi. Kuma kafin ya sanya suttura a jikin shi ya wanke kumfar jikin shi ya baro baskwata (boys quarters) zuwa cikin gidan ya ji saukar dirin motocinsu suna shigowa get din gidan. Duk da yake arne ya san drinking alcohol is very bad to Muslims more especially women in marital homes, its against their religion, tradition and culture. Sai ya ji tausayin ubangidansa ya kama shi, don yana son Sultana. Allah ya sa kada father din ya ce ya sake ta. Yana daga kitchen wanda ya bi ya shigo ta kofar baya cikin mutuwar jiki yana lekensu ta window suna ta shigowa cikin nadi da amawali da kaya na sarauta a jikin kowannensu. Ga wata mace kuma an lullube a cikin alkyabba wata baiwa ta riko ta. Yarima ya bude kofar falon wadda sakayota kawai aka yi. Maimartaba shi ne farkon shiga don Yareema ya dan ja baya ya bashi hanya cikin girmamawa sannan Fulani ta mara masa baya. Suka kuwa yi kyakkyawan gani, wanda ba su jin za su taba mantawa a rayuwar su. Aisha-Sultana ce daga ita sai half vest da wando three quarter baki, tana kwance magashiyyan cikin manya-manyan kwalaben whiskey. Ba barci ta ke ba, kuma tana jin shigowarsu amma ko yatsarta ba ta iya motsawa, idanunta a lumshe. Ba su taba ganin GIYA a fili ba, amma kallo daya suka yi wa kwalaben da kuma yanayin da ta ke ciki suka gane komai. Ko da ma can suna da labari. Kunya! A wurin Yareema kamar ya ce da kasar ta tsage ya shige. Allah ya so shi yan rakiyar sun tsaya daga waje, yau da ya gama tozarta a rayuwarshi. Maimartaba sai kawai ya juya ya ce da Fulani, Bana zama a inda ake saba wa Allah, sannan yata ma ba za ta zauna ba. Ku juya mu tafi. Yareema ya sha gabansa yana roko. Alaguburo, Allah Kawun jo na tuba, na bi Allah na bi ku. Zan dauki mataki a ba ni dama ta karshe. Nan shi ne gidan Saadatu sabida cikin makarantar su ne. Ita na riga na kama mata wani gidan a Maitama, kusa da wajen aikinta. Maimartaba ya yi tsaki ya fice, amma Fulani ba ta fita ba. Ya ce da dogarawan da ke bakin kofa a nema masa hotel din da zai sauka gobe da asubah zai juya inda ya fito. Fulani ta ce da Yarima wanda ya zauna ya dafe kansa da dukkan hannayensa.Bai taba wulakanta irin yau ba. (Don ma ba shi aka kama a gidan Dr. Ziyad ba ke nan!) Kunyar duniya kenan da tozarcinta kafin a je lahira. Me ye riba a kin bin umarnin Allah kowanne iri ne? Bai san ya zai yi da Sultana ba, ya yi fadan ya yi nasihar, ya yi barazanar duka a banza. Har duka ya yi duk da ba girman sa ba ne. Nadamar nashi laifuffukan suka kara lullube shi. Mai yiwuwa ta nan Allah yake kama shi kan nasa laifin. Don kuwa duk da halin ta yana son kayar sa. A fili yake fadin, Astagfirullah! Astagfirullah!!. Ya kuma alkawarta ma ransa daga wannan ranar duk wani sabon Allah ya bar shi. Sultana kuma zai dauki mataki na karshe a kanta. Fulani ta dafa kafadarsa, Ka kwantar da hankalinka Yareema, zan ba shi magana. Amma tunda ya ce ba zai zauna ba, to da gaske ba zai zauna din ba. Ka yi hakuri ka tashi mu je ka nema mana masauki, ita Saa zata zauna tare dasu Fanna zan bashi hakuri. Tuni Fanna ta janye Saadatu zuwa dakinta wadda ke rufe cikin alkyabba ba ta san a kan me ake cece-kuce ba. Yareema ya mike yana hararar Aisha-Sultana wadda ke sakar masa murmushi cikin maye. “Darling you.you are back? Bai ce mata komai ba ya bi bayan Fulani suka fita. Hotel din TRANSCORP HILTON ya kai su, ya kama musu daki na musamman kwana daya. Saadatu ba ta san su Fulani sun juya ba, ita da Fanna kawai aka bari a dakin, ta dauka tare da su za su kwana cikin gidan suna wani dakin ne. Fanna kuma sai dauke mata hankali ta ke da hira don kar ta gane abin da ake ciki. Haka ki ka tsara dakinki ranki ya dade gwanin shaawa? In mun tafi gobe sai ki kara tsara komai na gidan yadda ki ke so tunda ke kadai za ki zauna a cikin sa. Na ji maigirmaYarima ya ce Uche ya hada kayan uwargida ya sa a mota. Ki kula da cikin mijinki ta fannin girki bana jinki, na san Yareema ya gama morewa. Haka ta yi ta hilatarta da daddadar hira har Yareema ya je ya dawo daga kai su Askirama Hilton. Ya leko kadan ya ce da Fanna, In kin gama direba yana jiranku a waje zai kai ku inda za ku kwana. Fanna ta gurfana tana godiya hadi da kirarin da suke yi masa, sannan ta dau jakarta tare da cewa da Saadatu. Sai mun zo suna. Idon Saade ya yi rau-rau kiris ta ke jira ta fashe da kuka. Ta ce, Fanna Fulani fa? Au, ta ce a yi miki sallama sun tafi masauki ita da Askirama, gobe kafin mu wuce za ta leko ku yi sallama. Saade sarkin kuka nan da nan ta fara. Ya tabbata kenan ta shigo kwaryar sauran mata. Aure yau ya raba ta da Fulani, rabuwa ta har abada sai dai a je ziyara. Ta yi kuka, ta yi kuka bayan fitar Fanna da ta gaji ta shiga bayinta ta daura alwala, tana jin Yareema yana ta yi wa Uche fada da harshen turanci kamar Charles Dickens ya diro Nigeria, kan don me sanda ya bugo masa waya bai gaya msa Sultana tana falo drunkard ba? Uche ya rasa kalaman kare kansa sai cewa ya ke, “Im very-sorry Sir.. Yana so ya yi masa bayanin cewa wanka yake yi a baskwata lokacin, kuma kafin ya harhada bayanin da zai masa akan harshen sa ya kashe waya, ya bi bayan kiran network ya hana shi samun sa, ko kumfar jikin sa bai tsaya wankewa ba yasa wando ya fito kawai sai ganin motocin su yayi har sun shigo harabar gidan amma Yarima bai bashi damar yin wannan dogon bayanin ba sabida yadda ransa ya yi mugun baci. Wata muguwar tsawa ya buga masa ya ce ya bace masa da gani. Saade ta kyabe baki ta tada sallah. Ai gara da Askiraman ya gani da idonsa, watakila shi in ya hana ta ta daina, tunda mijin nata ba shi da fuss a kanta, har nema yake a rufa mata asiri. Ba ta san ya ya suka kare ba shi da matarsa. Ta fito ta shiga kitchen don ta sama wa cikinta abin da za ta ci ba ta gansu a falo ba, ba ta ga kwalaben giya ba. Ta dan tsaya tana nazarin falon ta ji tashin motar Yareema, ta daga labule ta leka ta waje sai ta hango shi ya yi ribas ya nufi get zai fita, Sultana tana gefensa kanta a kwance jikin kujera. Tsaki ta yi cikin jin kishi, ta ce a ranta, Da kyar in ba shi ya dauke ta ya sa ta a motar ba, don in ta sha ta yi tatil din nan ko yatsanta ba ta iya motsawa, da ma ta gama gane shi gwani ne wajen daukar matarsa a hannu. Ta zubo abinci iya wanda za ta iya cinyewa da Uche ya girka yanzun nan, ta zauna a dining tana ci. Shiru-shiru har ta gama ta koma daki babu Yareema. Tun tana duba agogo har barci ya ci karfinta, ta kishingide a kan gadonta, gadon yammatancinta a NTNU. A yau ya rikide ya koma na gidan aure! Kudurar Ubangiji ta fi ga haka. Duk da bacci ta ke, amma zuciyar ta cike ta ke da damuwa, Yarima ya manta da ita cikin gidan ne ko kuwa? Ya dau matarsa sun fice. Ba ita ta bude idanunta ba sai da masallacin gidajen Malamai na NTNU suka tada sallar asubahi. Ko da ta tashin ma da Yareema a ranta ta tashi. Ta yi zaton ganinsa a gefenta yana barci ko sallah, don ta gane shi maabocin sallah ne a zaman su na Askira kwanaki bakwai tare, kuma ya gaya mata muddin suna tare ba su ba raba makwanci, tun tana jin nauyi da kunya har ta saba da hakan cikin kwanaki bakwai da suka yi tare matsayin maaurata. Itama in ba sa manne cikin duvet bata jin dadin barcin. Amma ga mamakinta har zuwa lokacin Yareema bai dawo ba. Tana alwallah tana hawaye, hawayen da ba ta san dalilinsu ba. ***** Har karfe sha biyun dare yana tare da Aisha-Sultana a sabon flat din da ya kama mata a Maitama, jira yake giya ta sake ta, ta wartsake sannan su yi magana. Tunda suka zo ta ke barci, maigadin da ya daukar mata shi ya fiddo duk kayan sanyawarta jaka-jaka daga bayan motar Yareema ya shiga da su ciki, wadanda ya sa Uche ya kwaso mata. Da ya kashe motarshi ya dauke ta a kafadunsa zuwa cikin apartment din, ya kwantar da ita bisa gado kasancewar ya yi order already an zuba komai na bukata a gidan. Haka ya zauna zaman jiranta ta wartsake, ya tashi ya yi alwala ya yi sallar isha, sannan ya zauna kiraye-kirayen waya, ya gabatar da dukkan uzurorinsa ta waya. Amma duk abin nan da yake Saadatu na makale cikin ransa. Allah-Allah yake Sultana ta farka su yi maganar da yake so su yi, ya tafi wajen Saadatu. Sulatana ba ita ta farka ba sai karfe sha biyu na dare. Ta yi mika sannan ta hau bude idonta a hankali, sai ta ganta a bakon wuri. Ganin Sageer a gefe yana sallah, sai tsoronta ya ragu. Ta sani ko ma ina ne shi ya kawo ta kenan a lokacin da ta ke cikin maye. Darling ina ne nan? Ta tambaya tana hamma. When did you get back? I missed you!. Hararar ta ya yi, sannan ya dauke kansa. Can kuma ya dago ya dube ta cikin ido. “My father saw you drunk!. Sultana ta zaro ido, Oh dear! Me ya sa ba ka gaya min kun taho ba? Ya galla mata harara, ya ce, sau nawa zan ce miki in kina son zamanmu ya dore sai kin bar shan giya? Ta zumburo baki, sannan ta mike ta yi kan Sageer ya soma ja da baya ya kuma kira sunanta da karfi, Sultana! Ba ta fasa abin da ta ke ba, ta ce, Ai ni ma na gama magana, ranar da ka daina branching da yammatan bisa titi ni ma zan daina shan giya tell your Dad Im sorry. Ya ce, Sultana na dade da bari, har na kara aure. Don Allah ki daina in ba haka ba rabuwarmu ita ce mafi alkhairi. Sauran maganar makalewa ta yi a makoshinsa sakamakon cewa, Aisha Sultana ba ta ba shi damar karasawa ba. And then she seduce him. Da ma ya dade cikin kishirwa, sai ya kasa tankwabe tayinta da kaunar da ta ke kokarin nuna masa. Ga dukkan alamu ba ta ji cewa da ya yi ya kara aure ba, idan kuma ta jin, to ba ta fahimta ba. Yareema Sageer bai tashi dawowa Sageer dinsa ba sai karfe hudu na sulusin dare. Lokacin da kuma ba zai iya tafiya gida ba. Ya tuno Saadensa, da kadaicin da ya barta ciki ranarta ta farko a gidan mijinta. Amma a addinance bai aikata haramun ba sabida girkin Sultana ne, ya yi mata kwana bakwai dinta da addini ya bata babu kwange. Ya duba agogo ya kuma dubi Sultana da ke ta sharar barci. Ta inganta masa daren jiya kamar ba gobe, iyaka iyawarta. Don dai ta mantar da shi laifinta amma duk da haka ya kasa mantawa, abu in ya hada da Maimartaba ba ya daukansa da sauki. Ya yi wanka ya tsarkake kansa ya dauro alwalla. Bai jima yana nafilfili ba ladani ya kira sallar asubah a masallacin da ke kusa da su sai ya ga bara kawai ya shiga masallacin tunda ba su da nisa daga can ya wuce gidan Saadatu, sai ya hukunta Sultana. Ya hau dukan bayan Sultana ya ce ta tashi ta yi sallah shi zai wuce masallaci daga can ya wuce gida. Ta ce, Wane gidan kuma? Na dauka mun yi parking zuwa nan ne? Ya ce, Kin yi parking dai, amma mu muna can, ke da gani na sai ranar da ki ka bar GIYA Sultana. Da haka ya fice tana ba shi hakuri, amma ko juyowa bai yi ba. Ita ma ta yi shirin ofis ranta a bace. Ba abin da ta ke so a duniya irin Yareema Sageer. Shi kadai ne daidai da rayuwarta haka babu mai wahalar da ita a duniya irinsa. Amma me ya sa ya kasa gane cewa alcoholism is an addiction? Tana tuki cikin hawaye har ta isa wajen aikinta da ke kan titin Aguiyi Ironsi. Ya karya kan motar ya shiga gidan sa. Yayi horn maigadi ya taso da azama ya bude masa kofa, misalin karfe shidda na safe, yana shigar da hancin motar maadanin ta yana harhada kalaman da zai yi amfani da su wajen lallashin Saade bisa wannan babban laifi da yayi mata da bai san yadda zai yi ya wanke kansa ba. ****** MU KARASA A LITTAFI NA 4. KADA KU DAMU TARE SUKE. TAKU HAR ABADA; SUMAYYAH ABDULQADIR (TAKORI). 26|11|2021 NA HUCE.. LITTAFIN SUMAYYAH ABDULKADIR Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji ta yi zuciyar ta na son karyewa (rauni irin na diya mace na son mamayar ta) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta. Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya. Shi kuma ya sa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa ba zai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwarsa ba. Ko da bayan cikar burin ta, na zama cikakkar otorhinolaryngologist. **** Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo with so much adoration, hawaye na sauka a kan fararen kundukukin ta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare? Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba a kan kulawar da yaron zai samu ba ne domin hakika tana da tabbacin HABIBUNAHUCHEzai kula da dansa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigaraure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafarsa bai kama ba, ko da kuwaya fi shi komai na rayuwa. Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayinsa na yanzun ba (mamallakin NAHUCHE HOTELS) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashinsa na rayuwa tun daga ranar da ya raba ta da Dan su. Dalilin bibiyar ne ba ta sani ba har yau, tunda ita ta ce bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai ba ta ba, kuma burin Dada shine ta yi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza daga shi sai dan mutanen NAHUCHE. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah ya yi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwarsu. Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar ba za ta daina zubar da su ba har zuwa karshen rayuwarta. Idan har rayuwa ba ta koma yadda take a baya ba; with him aside. "Auren Wucin Gadi". "Auren kwanaki bakwai kacal". Wadanda abubuwan da suka wakana cikinsu sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwansa duniya ne ya yi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar da ta samu kanta. -Takori MASARAUTAR MU! 4. SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI SADAUKARWA Ga 'yar uwar da muka rasa a TAKORITES. Allah ya jikan ki da rahma HASNA'U yasa aljannah ce makomar ki. Ya bamu guzurin tadda ke. Takorites bazamu taba mantawa da ke ba. Da zaman amincin da muka yi tare. Muna son ki Hasna. JINJINA Har kullum jinjinar taku ce dukkan members na TAKORI'S ONLINE FORUM whtspp, littafin MASARAUTAR MU jinjina ne a gare ku, nagode da kauna da kwarin gwiwa, ni da ku hadin Allah ne. Allah ya bar mana zumunci har gidan aljannah. GARGADI Ban yarda a karanta wannan littafi a kowacce kafa ta sadarwa ba batare da iznina ba, tun daga radio, youtube, facebook, whtsp idan har ban yi izni ba, yin hakan karya doka ne kuma abin tuhuma ne daga lawyer na Barrister Sadiq Rufa'i Wali. MASARAUTAR MU 4 S aadatu na gyangyadi bisa dardumar da ta yi sallahr asubahi, kamshin turaren Yarima ya ziyarci hancinta wanda ya durkusa a gabanta kamar ita ce Yareemar shi subordinate. A hankali ta bude idanunta sai suka sauka cikin na Yareema. Wanda ke kallonta da dukkan kauna da soyayyar duniya cikin idanunsa. Sannan kwayar idanun sa sun nuna submissiveness wato karbar laifin da ya san ya yi. Ta maida idanunta ta lumshe don ba ta san me za ta ce masa ba, ya bata mata rai da yawa, har ba ta son ganinsa. Don jikin ta ya bata ko daga ina yake, to tare yake da Aisha-Sultana tunda ta ga fitar su tare. Ranar ta ta farko a gidan sa, ranar alfaharin kowacce amarya, ita nata angon ya tafi da matarsa hotel ne ko wane waje bata sani ba ko sallama bai yi mata ba, idan ta ce ba ta ji ciwon hakan ba hakika ta yi karya. Ita bazata ce kishi take ba amma taji ciwon abun a can kasan zuciyarta yadda bazata iya kwatantawa ba. Im sorry Princess!. Dr. Sageer ya fada cikin lallashi. Da karyayyar murya mara amo. Ba shi da kalaman kare kansa, so he admit kawai cewa ya yi laifi. Ya sake cewa, Im so sorry Saadahtouh, yanzu taso mu je mu yi sallama da su Fulani mu raka su filin jirgi sai mu dawo a yi min bulala goma sha biyar. Ai da jin haka ta yi maza ta mike ta nufi kofa batare da ta kalle shi ba, da ma da hijabinta jikinta. Yareema bai mike ba, ya ci gaba da durkuso a inda ta barshi. Sai ta ja ta tsaya daga bakin kofa tana kallonsa questionably. Ya lumshe mata shanyayyun idanunsa ya ce, Saadatuh, not even a good morning kiss? Saade ta juya masa baya cikin jin haushi, zuciyarta na tafasa, ita wane kiss ta iya? Meyasa bai samo can a wajen tubabbiyar baturiyar sa da ya dauka suka tafi hotel suka bar ta ba? Tana mai tambayar kanta wai dama ashe haka Uncle Yareema yake tana masa kallon salihi duk da abinda matar sa ke fade a kansa mafi muni? Daga sanda ya taso ya tako zuwa gaban ta, zuwa sanda ta ji saukar hannunsa ya zagaye bayan ta gabadaya ya rungume ta tsam-tsam, ba ta tantance ba. Im sorry Saadah, very sorry. Ban yi da niyya ba, uzuri ne mai karfi ya rike ni. Amma ko ina nake, cikin kowanne hali kina rai na Saadahtuh. Saade bata san yaya aka yi ba ta sunne kai cikin kirjin Yareema, zuciyar ta tayi wani irin sanyi da yadda Yareema ke lallashin ta, daga can kasan makoshin ta ta ce, Ni ai ban ce komai ba Yaya Yareema, ko ka ji na yi complaining? Na riga na san mijin wata aka aura min, don haka I should expect things like this. Don Allah mu bar zancen nan mu je wajen su Fulani. Sai hawaye. Wadanda tuntuni suke son samun damar zubowa, bata basu dama ba, sai yanzu da weakeness din ta na kishi ya nuna a cikin sautin furucin ta. Ya ce, Don zuwa za mu je, amma kafin nan he began to kiss her passionately, wani irin zazzafan kiss wanda ya sa Saadatu gigicewa da ficewa a hayyacin ta. Har yanzu ta kasa sabawa da sumbar Yareema Sageer mai tsirgawa har cikin ruhin ta, she always feels it strange a tare da ita. Sai da ya yi mai isarsa amma ko taya shi bata yi ba, sannan ya kama hannunta suka fito. Ya rasa kuma ta hanyar da zai bi ya goge laifin sa. A hotel din hilton sun samu Fulani da Maimartaba sun shirya, direban Yareema kuma ya debo su Fanna, don haka ba su bata lokaci ba kuma bata samu damar yin wata magana da Fulani ba sabida Askirama yana wajen, da ta yi mata korafin abinda Yareema yayi mata jiya; ya tafi ya bar ta ita kadai ranar ta ta farko a gidan sa (the first challenge), don haka basu bata lokaci ba suka wuce filin jirgin saman Nnamadi Azikwe. Ta hadiye bacin ran ta ita kadai. Da kyar Saadatu ta saki Fulani lokacin da jirginsu zai tashi, tana kuka Fanna na yi. Sai da suka ga tashin su Yareema ya kama hannunta suka koma gida, jikinsa a sanyaye don har zuwa lokacin Maimartaba ya ki sakar masa fuska. Kuma bai yarda sun yi musayar kowacce kalma ba har jirgin su ya tashi. Sannan Saade ma ta ki sakar masa fuska har yanzu fushi take. Suna shigowa gida ya janyo daya daga cikin jakunkunanta da ta dawo da su ya soma fidda mata kaya da kansa. Sai da ya fidda kala bakwai ya ce ta dauki duk abin da ta san za ta bukata na kwanaki bakwai, yana rike da kafadun ta bayan sun shiga dakin ya ce, Za a yi refurbishing gidan nan kafin ki fara zama a cikin sa. Zaa fidda komai dake ciki a kawo wanda Maimartaba ya yi miki ki tsara shi yadda ki ke so. Ita dai ba ta ce komai ba, ta gane so yake ya wanke laifinsa. Ko ina zai kai su kuma? Oho! Bai jira amsarta ba ya tafi nasa dakin don ya hada nasa kayan. Har ya janyo madaidaiciyar trolley ya fito zuwa dakinta Saadatu ba ta motsa daga inda ta ke ba. Da alama wanka ya kara yi ya canza kaya zuwa wani danyen yadin boyel fari kal mai shara-shara har tana iya hango singlet dinsa. Ya tsaida trolley din a kan tayoyinta ya karaso cikin dakin, cikin sanyin murya ya ce, Saadatuh mu je ko? Ta sunkuyar da kai hawaye na son zubowa, kewar Fulani, Fanna da Zarah ke damun ta. Yanzu kuma Dr. Sageer na cewa zai kwashe ta su yi wani wurin har tsayin kwana bakwai. Ni ba inda za ni, jibi za mu koma makaranta. Dr. Sageer ya harare ta, ya ce, Ko yanzu za ku koma ke ba za ki koma ba, gara tun wuri ki sani, da da yanzu ba daya ba ne, lokacin da babu nauyin kowa a kanki. So ki bi ni a hankali in na ga dama sai in soke karatun gabadaya. Hawayen da ta ke ta tattali kada su zubo suka zubo din. Ta mike cikin fushi ta dauki handbag dinta. Ba abin da ta dauka bayan ita, shi ya ja mata tata jakar suka fito. A cikin motar Yareema 4Maticsuke tafe, babu mai magana daga shi har Saade, tuki kawai yake cikin nutsuwa da kwarewa. Tun tana tsammanin cikin Abuja ne inda za su je din har ta ga ya kama hanyar barin gari. Mikakkiyar tafiya sosai suke yi akan titin Jos, uffan ba ta ce masa ba. In ma sayar da ita zai yi ya sayar, Fulani da Maimartaba su suka jawo mata. Sai wajejen azahar suka shiga garin Jos, ya nemi wajen sallar matafiya a gefen hanya wanda mata za su iya amfani da shi ya yi parking. Kwarai ta ke son shiga toilet don haka har ta riga shi fitowa. Sai da suka yi sallar azhar (kasaru) sannan suka sake daukar hanya. What do you want to eat? (Me ki ke so ki ci). Yareema ya tambayi Saade. Shiru ta yi masa kamar ba da ita yake magana ba. Ya yi kwafa ya ci gaba da tuki. Ya rasa gane inda ta sa gaba, in laifin da ya yi mata jiya ne ai ya ba ta hakuri, ya kuma karbi laifin sa. Yayi duk irin lallashin da ya kamata. Wannan shirun da ta ke masa yana ci masa rai. Ya ci gaba da tukinsa yana tunanin ta inda zai billo mata. A hanyar fita garin Jos ya tsaya ya saya musu gasasshen nama mai laushi, kuma mai yawa, ya hada musu da gorar ruwan swan mai sanyi, sannan suka sake daukar hanya. Ya bude naman ya ajiye a gefenta, kamshinsa ne ya tado mata da tsohuwar yunwa kuma da ma dai akan abinci ba ta iya filako. Don haka ta yi fuska abinta ta hau cin nama cikin yanga. Ta gefen ido Dr. Sageer ke kallonta yana murmushi, komai na Saade burge shi yake ba tun yau ba. Suna cikin tafiya wayarsa ta yi kara, da ya duba sunan Ya Gumsu ne. Sai da ya ji gabansa ya fadi, har fargaba yake magana ta sake hada su. In dai alkawarin da ya yi mata ne ai ya cika. Saade ido kawai ya zuba mata sai dan abin da baa rasa ba, wanda dan Adam ba shi da iko a kansa. Tsoro yake kada ta yi masa maganar Hajjaju shi ya sa da ya je mata sallama bai gaya mata tare da Saade zai taho ba. Amma ya san bai isa ya ki daga kiran mahaifiyarsa ba. Duk irin rigimar ta, wadda ta diga masa jinin haihuwa ta dauki cikin sa watanni tara ta haife shi cikin wani hali na kaka-ni-kayi ba tareda taimakon kowa ba. Don haka ya rage gudun motar ya amsa kiran Ya Gumsu da sallama cikin tsantsar ladabi. Ko amsawa ba ta yi ba ta jefo masa tambaya. Da gaske da yarinyar nan ka tafi Abuja? Yareema Sageer ya yi shiru cikin rashin sanin abin cewa. Ya Gumsu ta yi kwafa, cikin tsananin hushi ta ce, Watanni uku na ba ka ka zo a yi maganar auren ka da yar Sarkin Bauchi (Hajjaju) kuma watanni uku na ba ka ka sako mata yarta, idan ba haka ba ALLAH YA ISA haihuwarka da na yi, na sallama ka ga Bilkisu da yarta. Tana gama fadin hakan ta kashe wayarta. Yarima ya ja wani irin birki a tsakiyar titi, ji ka ke kuuuu! Saura kadan ya buga wa motar gabansa. Daga shi har Saade suka jirkito sannan suka koma mazauninsu daidai kasancewar duk da belt a jikinsu. Da sauri ya sa wa motocin bayansa signal, sannan a hankali ya sauka gefen titi, ya danna wani abu gilassai bakake (tinted) suka maye gurbin masu haske. Saadatu ba ta yi aune ba sai ji ta yi Yareema Sageer ya jawo ta jikinsa da karfi ya rungume ta, cikin kunnuwanta yake rada mata. Cikin kowanne hali kada ki rabu da ni Saadatuh! Shiru ta yi, bugun zuciyoyinsu na bugun kirjin juna. wani irin moment ne mai wuyar fassarawa ga Saade komai na Yareema ratsa ta yake har cikin kwakwalwa his gentle touches, his sexy voice, and everything da yake yi a yanzun. Kasa magana ta yi, domin gabadaya Yareema ya gama rikirkita duniyarta da zuciyarta cikin dan lokaci kalilan. Ta ga ba shi da niyyar ci gaba da tukin motar ga yamma na yi musu, ga shi ba ta san iya inda za su je ba, don haka ta janye gefe tana regaining consciousness. Lokacin ne ya ja motar suka ci gaba da tafiya. Amma sabanin lokacin tahowarsu ta lura wannan karon akwai babban abin da ke damunsa tun wayar da ya amsa. A hankali kuma barci ya dauke ta. Ba ta farka ba sai da suka shiga garin Bauchin Yakubu. Nan ma ta dauka masauki zai nema musu musamman tunda dare ya yi, amma sai ta ga ya kara nikar hanya. Ba ta so Yareema ya ji muryarta balle ya yi tunanin ko ta huce daga fushinta (sunan littafin Takori mai zuwa, NAHUCHE), shi ya sa ta yi masa shiru. Ba su dade suna tafiya ba ya karya kan motar suka hau titin da ta ga sign board dinsa zai kai mutum ne YANKARI GAME RESERVE. ****** Yankari game Reserve and Resort na nan a Wikki Camp. Yankari na daya daga cikin Nigerias Foremost Tourist attractions, ana kuma kiransa (home of wild life) saboda wadatar manyan namun jejin da ke cikinsa. A ciki akwai hotel domin maziyarta wato Marshall Suit a nan Yareema ya kama musu daki V.I.P Room. Kwarai attraction na Yankari ya dauke hankalinta har ta manta fushi ta ke da Yareema, duk da cewa dare ya yi musu amma koina haske yake da fitilu kamar rana. Ba ta san lokacin da ta dora hannunta a kan na Yareema ba, wanda ke bisa birkin mota. Uncle au? (ta toshe baki da ta tuna ya hana ta kiran sa Uncle) Prince, kwana za mu yi? Kwana nawa za mu yi a nan?The place is quite attractive and I like it. Mutane da yawa na kiransa Prince, musamman abokai, amma bai taba jin wanda ya fada with correct accentdawankakken harshe da makogaroirin Saade ba. Bai san sanda ya yi murmushi ba don ya ji dadin sunan da ta canza masan. Ya dube ta da gajiyayyun idanunsa irin na wanda ya sha tukin mota ya gaji, In kin yarda za ki yi min tausar tukin nan da na sha, kuma za ki ba ni baby in sa masa suna Dan Yankari, ko kwana nawa ki ke so mu yi sai mu yi abinmu, tunda babu mai jiran mu ko neman mu. Da sauri Saade ta kai tafukanta ta rufe fuskarta, kunya kamar ta yi ya ya, da ta san abin da zai fada kenan da ko kusa ba ta nuna shaawar wajen ba har ya gane ya nemi reward. Reward din da duka cikin biyun da ya ambata babu wanda ta ke jin za ta iya, don sosai ta ke ganin girman Yareema Sageer, ta kasa accepting reality na kasancewarsa miji a gare ta har zuwa yanzu. Har gobe kallon matsayinsa na baya ta ke masa (Uncle/Guardian) duk da he seldom kisses hera duk lokacin da ya bukaci hakan a kwanaki bakwan su tare, cikin siga mai nuna tsananin bukatuwar miji zuwa ga matarsa (physical urge). Suna shiga dakin nasu ko zama ba su kai ga yi ba Saade na ajiye handbag dinta akan kujera wayar Sultana ta shigo wayarsa. Bai ki amsawa ba, amma da ya daga wayar bai ce komai ba, sauraron ta yake yi. Sultana ta ce cikin fushi. Sageer ina ka shiga ne har yanzu ban ganka ba? Na dawo aiki tun dazu ga Uche baya gidan Ina inda ki ka aike ni tare da amaryata. Ke da ganina sai ranar da ki ka karbi addinin musuluci da gasken-gaske, sai kin tuba kin bar giya gabadaya, if not ki kama hanyar Korea ba ni da ranar dawowa. Wani ihu Aisha-Sultana ta saki a cikin wayar, You are lying you cant do this to me Sageer remember Im your Rose, wadda ta bar kasarta da addininta ta shigo wani saboda kai. Ya ce, sabida jiki na dai. Notbecauseofme, in sabida ni ne you can sacrifice everything for my sake, you will give me children. Abu daya nake dubawa da ya sa ban sake ki ba a jiya; mahaifi na baya barin saki. You hurt my father ko gaisuwa ta ya daina amsawa. Sultana ina yi miki sallama, na gaya miki in bazaki iya barin giya ba zaman mu ba zai taba dorewa ba, kin cire mahaifa ba da sanina ba, kin dauke ni kawai a matsayinsex slave ban yarda da wannan soyayyar taki ba. Na ba ki zabi, ko barin GIYA ko komawa Korea ne ko Amsterdam ke ki ka sani.... Yana gama fadin haka ya kashe wayar gabadaya ya ajiye ta gefen bed side-lamp. Saadatu tuni ta shige toilet da ta fahimci sensitive magana yake yi da matarsa. Ta yi wanka ta gasa jikinta sosai daga gajiyar zaman mota. Ba ta san me ya sa ya zabi su taho a mota ba tun daga Abuja har Bauchi. Daga baya ta lura cewa tukin mota is his hobby. Ko ba komai yana jinsa a privacy da Saade, ba tare da wani ya gifta a tsakaninsu ba, ko da kuwa ba za ta yi masa magana ba. Kafin ta fito ya yi musu odar abinci na alfarma, kayan da ta shiga da su da su ta fito a jikinta, sai tawul da ta rufo a kansu. Yareema ya shiga wanka wannan ya ba ta damar shiryawa a nutse. Amma maimakon ta sanya kayan barci sai ta dauko wata kakkaurar laffaya ta nannada ta dora a kai. Kai ka ce unguwa za ta tafi, ba ta yi wa fuskarta kwalliyar komai ba banda wet-lips da ta shafa kadan, amma ba karamin kyau ta yi ba. Ta daga ido ta dubi Yareema Sageer yana fitowa daga toilet ruwa yana yarari daga cikin gashin kansa. Bakin kyakkyawan Babarbare mai kama da Mai Askira. Tawul kawai ya daura zuwa gwiwoyinsa, ta hango wani ingarman physique chestna manyan maza wanda ya sanya ta ba shiri ta sunkuyar da kanta. Lokaci guda jikinta ya dauki rawa da makyarkyata lokacin da Yareema ya tako zuwa gabanta. Kamshin bathrobb din da ya yi amfani da shi na desire dunhill ya bakunci hancinta. Saadatu Hashim, tayi saurin sunkuyar da kan ta cikin neman taimakon Allah ganin irin kallon da Yarima ke mata. Kallo ne mai aika sakon kiran miji zuwa ga matar sa. Ya kira sunanta da wata siga da bai taba kiran ta da ita ba wanda hakan ya sa ta dago ido a hankali ta dube shi, idanun ta na ragaita, ya kama dukkan hannayenta ya mikar da ita tsaye, hannayensa sarke cikin nata. Ya ce, Saadatu hakurina ya gaza, na yi alkawarin da ba zan iya saukewa ba, Im so sorry Saadatu. Na daga kafar iya yadda zan iya, kuma na tabbatar kin samu tsarki, ki yarda ba zan cutar da ke ba, kuma ba zan hana ki karatunki ba, sannan zan bi hanyar da ba za ki samu ciki yanzu ba. Ki yi hakuri Saadatu, hakkina nake so na aure a daren yau ba sai gobe ba Saadatu, I promised you it will only be sweet, not hurting akwai barazanar da nake fuskanta wadda tasa dole zan tabbatar da aurena a yau. Saadatu ta soma kuka, Yaya Yareema ni ban shirya ba, na karanta a biology (reproduction) yana faruwa ne sanadin haka in na zo haihuwa mutuwa zan yi. Im only 19 years. Daga yadda jikin Yareema ke kyarma ta tabbatar yau ba ta da maceci sai Allah. Kalaman fatar bakin ta sun yi kadan su sa Yarima fasa abinda yayi niyya. Cikin wata sassanyar murya ya ce, Saadatu hakuri za ki yi, ni ma ban shirya hakan a yau ba, amma ba zan bari a raba ni da ke ba, dole in tabbatar da ke matsayin matata a daren yau. Iyayenmu har shekaru sha hudu ana musu aure, kuma suna haihuwa lafiya tambayi Fulani shekararta nawa sanda ta haife ki.. and he began from there... with very hot and irresistible kisses..Saadatu roko ta ke tana magiya, amma kamar tana kara zuga Yareema Sageer ne. To ka bari in ci abinci? Ta fada cikin ragaitacciyar murya jikin ta na kara karkarwa. Kafin kukan ya kwace mata gabadaya. Ya soma warware mata laffayar idanunsa ko buduwa ba sa yi, Abinci? Abinci fa ki ka ce Saadatu? Im sorry ki ba ni only two hours in ba haka ba zan cutu Saadatu. Da ta ga ba sarki sai Allah, sai ta mika lamarinta ga Allah. Hawaye na bilbila, in wuya ta yi wuya ta kira sunan Fulani, yau har Hanne da Raheema sun sha kira da neman taimako daga bakin Saade. So it was with every woman. Cikin awanni biyun da Yareema Sageer ya ambata, ya mayar da Saade cikakkiyar matarsa, wadda ko mutuwa ya yi sai ta yi masa idda. Bayan samun nutsuwarsa bai juya mata baya ba, rungume ta ya yi with utmost devotion and affection wanda baki ba zai iya fassarawa ba. Tunda yake biye-biyen matansa, farare, jajaye da bakake, da aure da ya yi na shekara da shekaru bai taba zama sexually satisfied irin yau ba. Rayuwarsa daga ranar ya tabbatar ta juya zuwa anotherdirection, zuwa sabuwar rayuwa wadda babu sauran sabon Allah a cikinta. Saade na kuka, Yareema na lallashi, ta rantse cikin daren nan sai ya maida ita Askira, bazata kuma zuwa gidan sa ba, ashe haka auren yake bata sani ba? Kuma ya rasa da wa zai yi sai ita kanwar sa da aka bashi amana don kawai ita ba Askirama ne ya haife ta ba? Kuma ta rantse sai ta gayawa Fulani komai. Wani abun in ta fada dariya Sageer yake amma a cikinsa, yadda ta ke a fusace din nan daren yau za ta iya kai duka, tunda cizo da yakushi ya sha su har ya gode Allah. Na ji duk abinda kika ce Saadatu, na ji ni dan ne, amma na Saadatu da Aisha-Sultana kadai, na amshi laifina ki yi hakuri ki yafe min, rayuwar will not besmooth ba tare da wannan din ba, baki ji ba yanzu duk wani tension da ke kaina ya fita, duk wata damuwa ta gushe, babu komai a rai da zuciya ta sai SAADATOUH,and I want to use this mediumin gaya miki tun daga karkashin zuciya ta cewa;I love you very- very muchhh!. Yadda ya furta kalaman na karshe har cikin ruhin Saade, ta ci gaba da kuka ba ta ce komai ba. Har ya je ya hada ruwa ya dawo ya dauke ta ya sanya a jacuzzi idanun Saade a rufe suke suna bulbular da hawaye. Idan wannan ita ce rayuwar diya mace hakika ta jinjina wa mata. Duk wani taimako da ya kamata miji maabocin kulawa ya nuna wa matarsa, Yareema Sageer ya nuna wa Saade daren yau. Abincin kuma da ya ce ta ci bayan sun kimtsa, cewa ta yi ba za ta ci ba, sanda ta ce zata ci ai bai saurare ta ba. Ya yi juyin duniya ta ki, sai kuka. A haka suka kwana, washegari ko waya bai kunna ba, tunda ya yi wanka ya tafi falo ya barta a dakin, ya kunna talabijin domin ya gaji da lallashin. Ko yaron goye nan ya ga Saa ya barta wajen kukan banza. SAADATU SAAR MATA!!! Yareema Sageer ya fada a fili, yana tuno kalaman Mai Askira. Za ta dauke kwadayinka a kan sauran mata tunda Bilkisu ce ta haife ta matan Baggara ne don manya aka halicce su. Murmushi ya yi yana jin kaunar mahaifinsa na kara ratsa shi. Sai kawai ya dauki wayarsa a gefe ya kira Maimartaba. Da kyar ya daga wayar tashi, sabida a ganinsa Sultana ta ci gaba da kafirci ne da sakacin Yareema. Ga shi an ce Da na kowa ne ba zai so ya sa shi sakinta ba. Amma Allah ya gani auren Aisha da Yareema ya fice masa a ka. Damuwarsa ita ce irin tarbiyyar da za a bai wa yaya idan Allah ya kawo. Ciki-ciki Mai Askira ya amsa gaisuwar Yarima, shi kuma excitedly yake bayyana masa dalilin kiransa da ya yi Godiya marar adadi da ba shi auren Saadatu, ya kuma yi alkawarin rike aurenta da daraja da amana har karshen rayuwarsa. A karshe ya dora da bada hakuri a kan Sultana, ya ce, ya dauki matakin kaurace mata har sai ta daina shan giya. Idan ba za ta iya dainawa ba ya ce ta tafi garinsu. Wannan hukunci ya sanyaya ran Askirama har ya sanya musu albarka, ya kuma ce ya saya wa Saadatu waya mahaifiyarta na cikin kewarta, ga shi ta bar wayarta a nan dakinta na Unguwar Fulani Bilkisu. Yareema ya ce, A nan inda muke ba za a samu waya ba, amma in mun koma Abujan zan saya mata. Mai Askira ya ce cikin tsokana. An bar kasar ke nan zuwa shahar asal (honeymoon)? Yareema ya yi murmushi cikin jin kunya yana shafa kai, ya ce, Aah Alanguburo muna cikin Nigeria. Na kawo ta ta ga dabbobi ne, a nan Yankari Game Reserve. Askirama ya yi dariya, idan yana magana da Sageer mantawa yake shi Sarki ne. He so much love him, zai iya komai don ya faranta masa ko da kuwa kara masa wata mace ne bayan Saade in dai har zai nutsu ya tsaya a kan matansa na aure. To a ga dabbobi da kyau. Ina gaida Giwayen Yankari. Dariya Yareema ya yi, sannan suka yi sallama cike da begen juna. Ya koma dakin, Saade na kwance har yanzu yadda ya barta abincin da aka kawo musu ko tabawa ba ta yi ba. Da ya duba sai ya ga bacci ne ya dauke ta, ga busasshen hawaye a fuskarta, ya tsugunna ya sumbaci goshinta, sannan ya hau kintsa kayansu da ya yi watsi da su a dakin daren jiya. Jinya sosai har ta kwanaki uku cif! Yareema ya yi ba shiga ba fita, ko kofar falo ta ki fitowa sai a rana ta uku ne ta yarda ta ci abinci ta koshi, amma a tsayin kwana uku oldenburger fresh milk kawai ta ke sha a Yankari. Ranar da ta dan soma walwala, Yareema bai yi kasa a gwiwa ba ya sake kalallame ta ya maimaita laifinsa. Sai dai wannan karon ita kanta ta san da bambanci. So sweet, so gentle. Kafin su bar Yankari cikin kwanaki bakwai Saade an zama manyan mata. Ta iya dauke wa mijinta Yareema Sageer Yusuf Askira lalurar da mata hudu ba za su iya dauke masa ba. Sun dinke sun zama miji da mata na haqiqa mafiya kusanci da juna, maabota soyayyar da biro ya yi kadan ya bayyana ta. Sai a na i-gobe za su tafi ne suka zaga wild life na cikin Yankari Resort, Saadatu ta ga dabbobi iri-iri a fili, wadanda sai a talabijin ta ke ganinsu. Ta baro Yankari with nostalgia, ta sanya zamanta na amarci na dan lokaci a Yankari cikin kundin tarihinta as the beginning of the beginning na kafuwar rayuwarta da maigidanta Yareema Sageer Yusuf Askira. ****** ABUJA Sun dawo Abuja ranar lahadi da yamma. Saade ta saki baki tana kallon yadda aka canza komai na gidan da ROYAL ONE. Duk abin da ke cikin gidan zubin na sarauta ne, sarauta ta zamani mai tafiya da boko. Ta karaso cikin main parlour tana latsa cushion din Royal Chairs din da suka yi wa dakin kawanya. Komai ya burge ta beyond her taste, beyond her expectation. Da Yareema ya ce za a yi refurbishing gidan ne shi ya sa suka tafi Yankari ba ta taba zaton gyaran zai kai kayatuwar haka ba. Once again, she simply fall in love with her humble abode (ta fada a matsananciyar soyayyar gidanta). Tunanin me ya kamata ta fara gyarawa ta tsaya yi. First of all zata gyara zaman kujerun. Su kalli juna madadin yadda aka ajiye su. Ta daga kai tana kallon hoton kyakkyawa Fulani Bilkisu cikin alkyabba da aka kafa mata a bangon gabas maso kudu na falon, ta saki murmushi ita kadai murmushin farin ciki. Ta matsa a hankali zuwa ga hoton, ta kai hannu ta shafi fuskar Fulani a hankali tana murmushi, lebbanta suka furta, Ina kewarki Fulani ba dan kadan ba. Ba ta san Yareema ya shigo jaye da trollies dinsu ba, yana tsaye daga bayan ta, ya ce, Me ki ka ce? Ta juya ta yi masa wani kallo na kasa-kasan ido, sannan ta zumburo dan bakinta gaba ta ce, Na ce ne Im missing her Prince, don Allah yaushe za mu je Askira? Dariya ya yi tare da mika mata kwalin wayar da ya sayo a hanya yana fadin, Ke da Askira sai na ga kina daga kafa da kyar, kina tafiya da kyar, sannan kina tashi da kyar. Ya karaso ya kama hannayenta ya sanya mata kwalin wayar, ya ce, Call your Mum, anytime. Har da dan tsallenta don farin ciki, ta makale a gefen kafadun Dr. Sageer ta na fadin, Na gode Prince. Dakin barcin Sultana na da nan ya kai mata kayan. Ya ja hannunta suka shiga dakin. Saade sai da ta rike numfashinta sakamakon ganin irin dankara-dankaran Royal furnitures da Maimartaba ya zuba mata. Wanda sai yayan sa su Ya Maira kadai zai iya yi wa. Hawayen farin ciki suka zubo mata, ba ta san sanda ta juya ta rungume Yareema Sageer ba. Ka taya ni godiya ga Alanguburo, Allah ya kara yawan rai, ya kara nisan kwana mai albarka. Ya gama yi min duk wani gata a rayuwa. Yareema ya rike ta sosai a cikin hannayensa, sannan ya ba ta kyakkyawar sumba saman idanunta. Yace. Nima ya gama min kowanne gata a rayuwa, tunda ya bani ke a lokaci mafi dacewa. When my heart was bewildered. Na kasa tunkarar ki in ce ina son ki, haka na kasa tunkarar kowa don ina ganin Im not good enough to have you. Bansan ni da ke wa Askirama ya fi so ba. Dariya ta yi ta zame daga cikin rikon sa, cikin jin dadin kalaman sa, aah Prince. Blood is thicker than water, ni ce ma yakamata in ce Im not good enough to haveyou, ni da ba yar kowa ba, ba yar sarau!. Yarima yayi saurin toshe mata baki da nasa in such a waythat hakan ya sa ta hadiye abinda ta yi niyyar fada cikin cikin ta, ya kuma kalubalance ta da cewa; watarana ruwan yana fin jinin kauri Saadatu. A daren ranar suna cin abinci yake cewa, Saadatu in na tafi na barki ke kadai a gidannan sai maaikata, babu matsala? Zan sake yin tafiya ta tsayin kwanaki uku. Da sauri Saade ta sake cokalin hannun ta, damuwa ta bayyana karara a kan kyakkyawar fuskarta. A dan zaman da suka yi tare a Yankari game reserve ta saba da Yareema Sageer fiye da tsammani, ya shiga zuciyar ta fiye da kintace. Tace tana son shi ma bata baki ne and is not enough to express the feelings Zuwa ina kuma Prince? Muryarta ta nuna tsantsar damuwar data fada.Yareema Sageer ya kamo hannunta ya dunkule cikin nasa, suka zauna a tare a gefen katafaren gadon Saaden, ya sassauta murya cikin lallashi, Its a promise ba zan wuce kwana ukun ba, zan kai Aisha-Sultana ganin gida ne. Wani abu ya zo ya tokare a kirjin Saade, wanda a nata sanin yafi komai zafi a zuciyar diya mace, a hankali ta janye jiki daga gare shi,sannan cikin karayar murya ta ce, A dawo lafiya!. Yareema ya sanya fuskarta cikin tafukansa, yana kallon fararen kwayar idanunta, ga mamakinsa idanunta sun cika taf! Da kwallah, kada dai Saadatu ta fara kishinsa? Babban burinsa kenan ta so shi irin yadda shi yake sonta. “Look at me Saadatu, na yi tafiya da ke mun yi kwanaki bakwai, ita ma tana da hakki a kaina, so ki yi hakuri in je in rakata, na yi miki alkawarin ba zan wuce. A hargitseSaadatu ta mike. Ka ji na ce wani abu ne Prince? Ko na ce Aunty Sultana ba ta da hakki a kanka? Ko me ye damuwata a ciki don ka dauki matarka kun tafi kun bar ni jiran gida? Ta juya masa baya a kokarin ta na boye hawayen ta. Yareema Sageer yana daga zaune yana kallonta ban da murmushi ba abin da yake yi. She never talked to him in this manner (cikin tsiwa). Saade ba ta ankara ba ta ji Dr. Sageer ya sure ta yana juyi da ita a tsakiyar dakin, kafin ya dire ta a tsakiyar gadon su ya koma samanta, ya dora mata dukkan nauyinsa gabadaya. Say it againba ki da damuwa don na dauki matata mun tafi Korea, to su wadannan hawayen kuma na mene ne, ya ya sunansu? Zan so kwarai in san maanar su. Saade ta runtse idonta hawayen na ci gaba da bulbula. Kamshin INVICTUS da ya riga ya kama Yareema ya soma hargitsa ta. Yana tada tsigogin jikin ta. A hankali Yareema ya soma kissing dinta from head to toe, lungu-lungu, sako-sako, kusfa-kusfa, kafin dan lokaci Saadatu ta fice a hayyacinta. Abin da ya biyo baya mai nauyi da girma ne da ya shallake tunaninsu. It was kind of gentle romance da ya gudana da hobbasar Yareema shi kadai, yayin da Saade ta sakar masa komai, gangar jiki, zuciya da ruhi, sai yadda ya ga damar sarrafa ta. Daren ya zamo cikin dararen tarihi a rayuwar amarcin ta, dare ne da daga Sageer har Saadatu, bazasu taba mantawa ba. Washegari suka yi shirin shiga makaranta. Saade ta yi tsaf cikin doguwar rigar atamfar chiganvy kalar pusher pink, ta yi lullubi da mayafi kalar kayanta wanda ya ciza sosai. Kallo daya Dr. Sageer ya yi mata yana shigowa dakin nata yana daura agogon hannunsa na danyar zurfa samfurin (Gucci) na maza, ya girgiza kai ya ce, Ai da sake. Ba ke ba fita da irin wadannan mayafan Saadatu, ko dai ki sa hijab ko ki koma gado ki nade ki kwanta. Saadatu ba ta kula shi ba, don ba wai ta huce daga fushin tafiyar da ya ce zai yi da matarsa ba ne, duk da duniyar soyayyar da ya dauke ta ya luluka ta daren jiya, yayi shawagi da ita a sararin samaniyar soyayya sky-blue mai haskaka zuciya da ruhi,still kishin hakan na makale a kasan zuciyar ta. Ya ce, reporting kawai zai je ya yi a ofis ya je gidanta ya dauke ta su wuce airport. Hijabin sallarta ta dauka ta saka akan atamfar jikin ta sannan ta biyo bayansa suka fito. Suna tafe a shimfidadden titin da zai shigar da kai cikin jamiar NTNU, a hankali Yareema ke jan motar tamkar ba ya so. Kwanakin nan da ya yi da Saade cikin rayuwarsa su ne kwanaki mafiya daraja da farin ciki da zai iya tunawa. Kwanaki ne da ba zai taba mantawa da su ba. Sannan kwanaki ne da suka bude sabon shafin tsaftatacciyar rayuwa da bai taba samun kansa a ciki ba. Sannan wadannan kwana ukun da zai yi ba tare da ita ba suna nufin komai. In ya ce komai yana nufin komai. Amma su kadai ne za su ba shi madauwamin kwanciyar hankali tare da Saade, ba zai iya hada rayuwarsa da ta kowace mace a yanzu bayan ita ba.(ASKIRAMA ya yi gaskiya). Aurensa da Sultana aure ne da bai san a rukunin da zai sanya shi ba. A yanzu ya gane kwanciyar hankalinsa da na Maimartaba shi ne kawai rabuwa da Sultana duk da Askirama bai furta hakan ba sabida principles din gidan sarautar Askira ya san abinda yafi so kenan. Don ya tabbata ba za ta taba yarda ta bar alcoholism ba. Ta fannin sa abubuwa sun dade da canzawa, ko yace suna kan canzawa, tun kafin shigowar Saade cikin rayuwar sa ya dade da nisantar zunuban sa. Abinda ba shi da tabbas a kai shine abinda gobe zata haifar. Amma ya dade yana tuba akan laifuffukan sa na baya. Tuban da Ubangiji yayi alkawarin karbar sa wato tuban da aka yi da niyyar bazaa sake komawa izuwa zunubin ba. Cikin matakan da ya dauka don kare kansa har da nesanta kansa da Dr. Ziyad. Ko Maimartaba bai gayawa ba, don ya san zai dakatar da shi ne daga hukuncin da ya yanke a kan Sultana, zai ce zai yarda da kowanne irin hukunci amma ban da rabuwar aure, sabida ba ya cikin aladar sarautar Askira. Shi kuma ya yi laakari da fadar Ubangiji (S.W.T) ne da ya ce, Na hore ku da auren abin da ya yi muku dadi daga daya-daya, biyu-biyu, uku-uku ko hurhudu. Amma in kun san ba za ku yi adalci ba, to ku zauna da guda daya. Shi kam ya tabbata bai iya yin kowanne adalci tsakanin Saadatu da Aisha-Sultana. Musuluncin da ta karba a yanzu ya gane don ya ba ta lasisin aurensa ne kawai, daga sanda ta same shi kuwa ta nade shi cikin tabarma ta jingine a gefe. Don haka ya amince wa ransa rabuwarsu ita ce mafi alkhairi. Har gaban department din su Saade ya shiga da motar, inda babu mai wucewa sai staff only. Yana tsayawa ta bude kofar za ta fice, cike da dokin shiga aji, ta yi kewar karatunta sosai, ta san abubuwa da yawa sun wuce ta, amma ta tabbata Said zai dora mata komai. Yarima ya rike hannunta tana shirin fita. Haah! Saadatu har murna ki ke zan tafi in ba ki fili ko? Ya fada da marainiyar murya, har cikin ransa yake jin rabuwar nan da zai yi da Saade har tsayin kwanaki uku. Kwarai bai yi karya ba tana murna da tafiyar sa ta wani fannin ko don kwarzaba irin tasa, ta san za ta samu hutu da nutsuwa na dan lokaci ta yi karatu sosai na abin da aka wuce ta. Amma in ta tuna da matarsa zai tafi sai ta ji gara ya zauna ya yi tumurmusar nata da ya tafi wajen mai jan kunnen tasa. Amma ko kashe ta zaa yi ba za ta iya gaya wa Yareema tunaninta ba. Ta san kuma da gaske ne kamar yadda ya ce matarsa ma na da hakki a kansa, ba don ita kadai aka halicce shi ba. Ba ta ankara ba ta ji hawaye sun zubo mata. A hankali ta ce, Ni ba murna nake ba, hasali ma I will really miss you. Cikin jin dadin kalaman ta Yareema ya mika mata hanky dinsa ya ce, To share hawayen, ki bar wayarki a kunne, zuwa asubahi in mun sauka zan kira ki. Me zan sayo miki? Kasar Korea ta Kudu za mu je ni da Sultana. Ta kasa sabawa da ambaton Sultana da yake yi, don ji ta ke kamar ya fi kowa iya fadar sunan. Wasu hawaye suka sake zubowa, wadanda ba ta san dalilinsu ba. Yareema ya sa hannunsa yana shafe mata hawayen da tafukansa sai a idanun Said da ke fitowa daga lecture hall. Dr. sageer ya gan shi ta karshen idon sa amma ita Saade bata lura da shi ba, da gayya ya kara rungumo Saade yana mata magana cikin kunnen ta. Zan iya tafiya? Ta tambaye shi bayan ya gama dauke mata hawayen fuskarta da tafukan hannun sa. ...Only if you give me a farewell kiss (za ki tafi ne only in kin ba ni sumbar bankwana). Wani irin murmushi ne ya subuce a siraran lebbanta, wanda Said bai taba gani a tare da ita ba. Ji ya yi kafafunsa na neman kasa daukarsa ya juya ya koma cikin aji da mugun sauri. Har yana cin tuntube a bakin kofa saura kadan ya kifa. Prince ka bar ni in tafi aji, ka ga malam ya shiga. Kuma nan kan hanya ne, mutane suna iya hango mu ko daga lecture hallne. Kin yi alkawarin in na dawo komai zai canza Saadatu? Za ki daina fushi da ni, za ki dinga gaya min duka bacin ranki? Zamu shimfida sabuwar rayuwa ta amana, soyayya da fahimtar juna? Da sauri Saade ta gyada kai. Yareema ya ratsa yatsunshi biyu cikin nata ya matse su sosai sannan ya sake su a hankali. Ta kasa dago ido ta dube shi, domin wata irin soyayyar Sageer da ta ji tana shigarta tana mamayeta a hankali. Ta bude kofar motar ta fice rungume da folder dinta. Ba ta waiwayo ba sai da ta kai kofar lecture hall dinsu. Har yanzu yana nan a inda ta bar shi, kanshi kwance bisa sitiyari, bai dauke ido a kanta ba. Ta sakar masa lallausar murmushi, sannan ta juya ta shige aji. Yau sai ta ji ta kasa zuwa ta zauna kusa da Said yadda suka saba, wanda ya tattara hankalinsa duka ya dora a kanta tana shigowa. Ta dauke kai ta nemi gefen wata kabila mace ta zauna. Mai miji kamar Yareema Sageer, ji ta yi ta daina son ganin kowanne namiji a duniya sai shi. Tafiyar da ya yi kuma tamkar ya tafi tare da ruhin ta ne. Gabadaya ta rasa kuzarinta da walwalarta. Malamin Baireshe ne, yana ta bayani a kan applied chemistry, Saadatu ba ta jin muryar kowa sai ta mijinta Yareema Sageer cikin kunnuwanta yana rada mata tausasan kalamansa. Har ya yi awanni biyunsa ya gama ko alifun ba ta rubuta ba. Said daga inda yake zaune ban da satar kallonta ba abin da yake yi, yana yi yana rubutu, ta yi wani mugun kyau, ta yi fresh da ita. Yana ta mamakin abin da idanunsa suka gane masa yana faruwa cikin motar Dr. Sageer Askira da kanwar tasa Saadatu. Ba ta taba yin kama da mutanen banza ba, yarinya ce mai tarbiyyar babban gida, amma anya abin da ya gani cikin idanunsu ita da Yayanta Dr. Askira bai yi kama da mashahuriyar soyayya ba? Soyayyar ma irin wadda ba ta taba faruwa sai da physical relationship a tsakani. Bayan fitar Malamin, Saade dole ta taso ta cimma Said a mazauninsa don ya ba ta notes din da ya wuce ta. Ta yi masa sallama, ta ce, Said kwana biyu? Ya daga ido ya dube ta a hankali, sai kuma ya dauke kai. Mamaki ya kama Saade. Said ba ka gane ni ba ne? Kawai sai ya tattara takardunsa ya bar gurin. Saade mamaki ya kashe ta a tsaye, ta bi bayansa yana fita daga theater din. Said! Said!! Ta daga murya tana kwala masa kira. Juyowa ya yi ya jefe ta da wani mugun kallo, sannan ya dakata har ta cimmasa. Suka yi kallon-kallo na yan sakanni kafin Saade ta tuna cewa ita yanzu matar aure ce, ta yi saurin kawar da idonta. What happened Said? Ina magana kamar ba ka san ni ba? Said ya rasa me zai ce mata, idanunsa sun kada sun yi jazir don kishi. Saade ta soma shaka, don ta tsani wulakanci. Ta kankance ido ta ce, In dai don notes dinka ne, ka rike abunka kada Allah ya sa ka ba ni, kada ka manta kanwar Dr. Sageer ce ni, zai karba min a hannun kowanne malami. Said ya yi murmushi mai ciwo, ya ce, Kwarai, na shaida hakan tunda kuwa kina ba shi reward a cikin mota, abin da ya fi notes ma zai karba miki. Kan Saade ya kulle, ta ce, Me ka ke nufi? Ya yi mata wani irin kallo zuciyarsa na zabalbala, ya ce. Kin ba ni mamaki Saadatu, ina miki kallon yarinyar kirki, mai hankali da tarbiyya, yar manyan mutane, yar babban gida, amma ashe kallon kitse nake wa rogo, duk abin da ya faru cikin motar da ta kawo ki tsakanin ki da wanda ki ka kira Yayanki na gani. Abin da ban sani ba shi ne, da gaske biological brother dinki ne ku ke aikata wannan assha? Saade ta kai yatsu ta toshe kunnuwanta ta juya da sauri ta bar wurin. Ba ta san me za ta ce masa ba, tunda ashe duk amincin da ke tsakaninsu ba zai iya shaidarta ba, zai iya yi mata mummunan zargi irin wannan. Ranta ya yi mugun baci, har ta ji ba ta bukatar fayyace masa gaskiyar ko wane ne Dr. Sageer a gare ta a yanzu. Ya je ya yi ta yi mata kallon yar shan minti a mota, damuwarsa ce. Daga yau ba za ta kuma shiga shirginsa ba. Ba su gama lectures ba sai yamma lis. Direbanta ya zo ya kai ta gida bisa umarnin Yareema. Ta fito daga motar goye da jakarta irinta yan sakandire (school bag), ta gaya masa gobe karfe takwas zai zo ya shiga da ita. Uche ta taras ya yo cefane himili guda yana shiga da su kitchen. Ta yi masa sannu, sannan ta ce daga yau ta hutashe shi girkin gidan, aikinsa ya koma share-share da goge-goge kafin ta dawo makaranta ya yi duk abin da zai yi ya gama ya wuce baskwata. Sai kuma cefane da aike da zai dinga yo wa lokaci zuwa lokaci. A ransa Uche ya ce, Tunda dai ba za ki sa a kore ni ba ai shi ke nan. A fili kuma ya ce, Yes Ma!. Don haka yana gama jera mata komai a firji da store ya bi ta kofar baya ya koma baskwata ya ci gaba da aikin fulawoyin gidan. Wanka ta yi, sannan tayi sallar magriba ta yi lazimi zuwa isha. Ta kawo sallar isha da shafaI da wutiri, sannan ta roki Allah ya sauki Yareema lafiya, Ya kuma dawo mata da shi lafiya. Ta koma kitchen ta hau aiki, ta gyara komai zuwa yadda ta ke so, ta ke buri tuntuni kitchen din ya kasance (da a ce nata ne). To shi Allah buwayi ne, gagara misali. Abin da ba ka taba zato ba ko tsammani ya riga ya rubuta shi cikin littafin kaddarorinka. Noodles kawai ta dafa guda daya ta shige daki, ta ci ta koshi sannan ta yi shirin kwanciya. Da asubah tana idar da sallah ta janyo wayarta da ta saka a caji ta kunna. Wayar ta cika taf da caji. Tana kunnawa kamar jira yake, sai ga kira daga international number. Saade na amsawa, tana jin muryar Yareema sai ta saka masa kuka. Prince yaushe za ka dawo? Jiya da kyar na yi barci, tsoro nake ji. Hankalinsa gabadaya ya tattara ya mika mata, ya ce, Ki yi hakuri Saadatu, mun sauka lafiya on transit a Amsterdam, yanzu za mu jau jirgin South Korea, insha Allahu jibi i-yanzu muna tare. Mun fara shirin tarbar mai sunan Maimartaba, da ni ki ke so ya yi kama ko da ke? Ba ta san sanda ta yi murmushi ba, ga hawaye shabe-shabe a idon ta. Ina gaida Aunty Sultana, ka gaya mata ni ban ce ina son mijinta ba aka aura min, ta daina fushi da ni. Yareema ya yi ajiyar zuciya, ya ce, In ki ka ce haka ba ki yi min adalci ba Saadatu, dukkanmu mun dade muna son juna, ba mu gane hakan ba ne har sai da Maimartaba ya ankarar da mu. In kuma da gaske ba ki sona din ne Saadatu, to gata ki gaya mata da bakinki. Ta girgiza kai da sauri kamar yana gabanta, ta ce, Yaya Yareema!!! (In exclamation). Ya ce, Yes, ki gaya mata da bakinki, sannan ne zan yarda cewa ba kya son nawa. Murmushi ya subuce mata, ta kawar da zancen da cewa. Karatu ya wuce ni da yawa, an yi min fintinkau, in ka dawo za ka koya min? Ya ce, Karatun namu ai kala-kala ne, wanne daga ciki? Ba ta gane hausarsa ba don haka ta ce, Courses din Applied Chemistry, inorganic, organic and petrochemistry. Tunda kai ka jawo aka wuce ni. Ta fada cikin shagwabar da ba ta san ta yi ba. Dr. Sageer ya yi ajiyar zuciya. Anya Saadatu za ki bar ni in yi kwanaki biyun nan? Gabadaya kin rikita min lissafi, na kasa zama lafiya cikin nutsuwa tun barowata makarantarku. Ke kawai nake son gani, ke kawai nake son ji a jikina. Ta kai tafin hannunta ta rufe ido kamar Yareema na ganinta, sannan ta ce, Kada in shiga lokacin Aunty Sultana. Prince sai ka dawo. Ta yi maza ta kashe wayar ta koma ta jingina bayanta jikin allon gado, ta lumshe idanunta. Ba abin da ta ke son gani a daidai wannan lokacin sai Yareema Sageer. Wayewar gari ke da wuya ta soma shirin shiga makaranta. Ba ta dade da zama a mazauninta ba, Said ma ya shigo suka hada ido, ta dauke kai. Yau fuskarsa a sake ba kamar jiya ba. Ya zo har gaban kujerarta ya ajiye mata tulin wasu takardu. Gabadaya notes din da ya shige ta ne ya je ya yo mata photocopying dinsu. Ba tare da ya ce komai ba ya koma mazauninsa. A kwanakin biyu gaba daya ba sa magana da juna, ya kasa cire abin da idanunsa suka gane masa daga kwakwalwarsa, ita kuma ta kasa yi masa bayanin da ya kamata ta yi masa. Kunya ta ke ji a ce ita yanzu matar aure ce. Kwarai ta ji dadin photocopies din da ya yi mata, amma wata zuciyar na cewa ta dauka ta bishi har mazaunin sa ta watsa masa tsiyar sa, zuciya mafi adalci na cewa ta yafe masa muggan maganganun sa ya fada ne a bisa rashin sani. A kwanaki biyun in ta koma gida ba ta komai cikin kwanaki biyun sai bitar karatun da ya wuce ta. Abin da ba ta gane ba ta kira Dr. Sageer ta gaya masa ta waya ya yi mata bayani yadda za ta gane. Yana yi yana kashe ta da kalaman soyayyarsa masu ratsa zuciya da ruhinta. Yau kwanansa uku da tafiya kuma ya sauka a Abuja, amma bai kira ta ba. Ta wuce makaranta har yamma tana fama da assignments din da ta kasa solving gabadaya. Ta daga agogon hannunta ta ga karfe shidda, ko me ya hana direbanta zuwa har yanzu? Ta dauki wayarta don ta kira shi sai ta samu cajin wayar ya mutu gabadaya, don jiya kusan kwana suka yi a kan waya ita da Yareema, kuma da asubah ta manta ba ta sanya cajin ba. Gabadaya Dr. Sageer ya gama kwance kan Saade da soyayyah ba abin da ta ke jira sai dawowarsa a kashe wutar da ake rurawa a waya. Da ta tuna yau zai dawo, sai ta ga ba za ta iya zaman jiran direbanta ba, sabida tana son yi masa girki na musamman, gara ta gangara da kafarta zuwa cikin quarters dai ba nisa, ban da Yarima da ba ya so tana tahowa ita kadai da yamma da da kanta za ta dinga komawa gida ko don ta motsa jikinta. Ba ta jima tana tafiya a gefen hanya ba, motar Said ta yi parking a gabanta. Shigo in karasa da ke. Aah na gode, ka je kawai. Ki yi hakuri ki shiga, ba zan barki ki bi jejin nan ke kadai ba daf da magriba. Sai ta ji tausayinsa ya kamata, ya kasa cireta a ran sa, ta fi kowa sanin yadda yake sonta. Ko ya zai ji in ya ji ta yi aure? Sai ta ga gara ta shiga motar yau ta gaya masa gaskiya ko don ya daina kishi a kan abin da ba nasa ba, kuma ba zai taba zama nasan ba. Sannan babu yaudara a tsakaninsu har abada sai mutunta juna. Ba za ta taba mantawa da dimbin kirkinsa gare ta ba. Don haka ta bude gaban motar ta shige, ya soma tafiya a hankali, Saade ta ce, Da dai ka yi sauri maigidana yana hanyar dawowa. Ka yi hakuri ban samu damar gaya maka ba kana ta fushi, an yi min AURE! Said ya taka wani wawan birki sai da suka jirkito dukkansu, Saade ta yi maza ta rike hannun kofar motar, ta ce, Yaa Salam! Said ya dube ta a sanyaye, ya rasa abun cewa. Sai ya ja motar suka karasa kofar gidanta. Har cikin get ya shiga da ita, tana kokarin fitowa motar su Yarima na shigowa shi da Dr. Ziyad ne da ya yi wa waya ya je ya dauko shi a filin jirgi. Bakuwar motar samfurin henessyta dauki hankalinsa, kuma ba jimawa ya gane yaron, ya taba sauke Saade, kuma ya yi warning dinta tun a wancan lokacin amma shi ne shi ne bakin ciki, kishi da bacin rai sun hana Sageer tunanin abin da ya dace. Dr. Ziyad bai gama tsayar da motar ba ya bude ya fito. Cikin takunsa na Yariman Askira ya taka ya isa gaban Said, sannan ya nuna shi da dan yatsa. Wannan ya zama lokaci na karshe da za ka kara daukar min mata a mota, ko da da niyyar taimako ne. bana so, nagode. Ko kallonta ka sake yi ba taimako ba, kotu ce za ta raba ni da kai, na gaya maka, na kara gaya maka wannan. Da sauri Dr. Ziyad ya karaso ya kama shi yana fadin, Haba Dr. he is your student, ba girmanka ba ne. Saade tuni ta shige gida jikinta na rawa. Dr. Ziyad ya bi ta da kallo yana hadiyar miyau. Said tuni ya tsugunna yana bada hakuri, ya gaya musu direbanta ne bai zo ba, ya ganta tana dawowa da kafa, kuma sawu ya dauke shi ya sa ya ce ta shigo ya karaso da ita. Dr. Ziyad ya ce, Is o.k, kana iya tafiya, mun gode. Bayan wucewar Said ya kwace hannunsa daga na Ziyad ya ce, Da ka bar ni na dan sassaba masa kamanni, gobe ko da kudi aka hada shi bai kara daukar matar mutane a akwalar motarsa. Cikin mamaki Dr. Ziyad ya ce, Daga zuwa na Istanbul da dawowata kana nufin ka kara aure? Is she this girl da ta wuce ciki yanzun nan? Dr. Sageer ya harare shi sosai da ya tuna waye Ziyad a kan mata, ya ce. Babana ya aura min yarinyar da na ke riko ce tun da jimawa. And now ina Sultana? Mun rabu. Na mayar da ita kasarsu. “This is serious, ashe za ka iya rabuwa da Rose? What a lucky girl, amma ta ciri tuta, ya ya sunanta? Sageer ya zabga masa harara ya ce, Don Allah malam kama gabanka, ina ruwanka da sunan mata ta? Dariya Ziyad ya yi, ya ce, Ina nan ina jiran ka, in ka gama kwasar amarci za ka zo neman new catch. Da sauri Dr. Sageer ya ce, Waiyazu billah, sai dai wani Sageer din ba ni ba, kai ma ina maka fatan shiriya, kuma ina mai ba ka shawarar ka dauko iyalinka daga Istanbul ka dawo da su kusa da kai ya fiye maka wannan kazamtacciyar rayuwar. Ziyad sai dariya yake yana mamaki, in wani ya ce masa Sageer zai bar mata saboda mace daya ba zai taba yarda ba, amma a sanin da ya yi masa shi kaifi daya ne, sannan ba ya taba fadin abin da ba haka yake a zuciyarsa ba. Ko sallama Dr. Sageer bai bari sun yi ba ya shige falon gidansa ya kullo kofa ta ciki. Ya bar Dr. Ziyad a tsaye ya kasa tafiya. Ba abin da idanunsa ke hango masa sai kyakkyawar surar BAGGARA-SAADATU diyar Fulani Bilkisu, a lokacin data juya baya tana shigewa cikin gida. ****** A yadda ta hango bacin ran da ke kunshe fuskar Yareema ta san ba za su kwashe ta dadi ba. Tana shiga dakinta ta aje jakarta ta sunce ta daura tawul ta shiga wanka, tana tsakiyar wanka a shower sai ganin Yareema ta yi ya bude kofar toilet din ya shigo. Idanunsa sun kada, amma ganinta cikin wannan yanayin tuni ya birkita shi. Ko a Yankari bai taba samun damar ganinta yadda ya ganta a zahirin yau ba cikin hasken farin lantarki. Da kayan jikinsa da komai ya tafi zuwa gare ta. Da sauri Saade ta ja da baya ta ce cikin karkarwar murya, na tuba Prince Duka jikinsu rawa ya hau yi cikin wani yanayi, ita nata rawar jikin na tsoron abin da zai yi mata don huce bacin ransa ne akan Said, yayin da shi kuma nashi na tasowar wata irin soyayya ne da bai taba ji ba a rayuwar sa a kan kowacce diya mace. Ka yi hakuri don Allah ba zan sake ba. Saade ta fadi cikin karkarwar murya, amma daga irin rikon da Yareema Sageer ya yi mata, ruwan yana sauka a kansu su biyu, tun daga sumar kansu har zuwa yatsun kafarsu, da yadda ya soma sumbatarta fiercely ya tabbatar mata ta hanyar da zai huce fushin nasa kenan. All of a suddenga Saade,komai ya faru cikin shower.. gently, romantically yet abruptly(in an abrupt manner). Abin nufi, bata zaci abinda ya kawo shi shower din kenan ba, ta zaci ya zone don ya gaggaura mata mari a yadda ta gaidanun sa lokacin da ya gan ta a motar Saidu. Sai ta ga alamarin ya juye zuwa zazzafar soyayya mara misaltuwa. Dukkansu sai da suka yiwani irin kuka(for emotion and satisfaction), wanda soyayyar juna, kewar juna da tsananin kauna suka kawo shi. Wata sabuwar rayuwa ce mai gardi da Saadatu da bata taba tsintar kanta a ciki ba. Wani sabon yanayi ne a gangar jiki da ruhin Yareema Sageer, ya ji nan duniya bai iya kara sake hada jiki da kowacce diya mace bayan Saadatu diyar Mallam Hashimu da Fulani Bilkisu. Kalaman mahaifinsa suka sake dawo masa a ranar da ya mallaka masa SAADE. Za ta dauke dukkan kwadayinka daga kan sauran mata, in dai Bilkisu ce ta haife ta. Allah ya saka da alkhairi Alanguburo. Allah ya kara yawan rai, Allah ya ba ni ikon rike amanar da ka damka min da gaskiya da amana, har zuwa ranar da muka daina numfashi. Kalaman da Yareema ke yi a fili kenan, yana kankame da matar sa Saade, ruwa na sauka a jikkunansu daga saman shower. Ba ta san adduar me yake yi ba har da sunan ASKIRAMA a ciki, daga baya ta fahimci gode masa yake da ya mallaka masa ita ta zama cikon farin cikin sa. Ko ita a yau tana gode masa da ya mallaka mata gwarzon dansa mafi soyuwa a gare shi, wato Dr. SAGEER YUSUF ASKIRA,Basaraken Askira daya cikin dubu, sadauki kuma jarumi a fanninnunawa matar sa kauna da soyayya. A baya gani ta ke Mai Askira ya katse mata rayuwa, yayi mata aure ba a lokacin da ta shirya ba. Yanzu kuwa ta gane Askirama ya cika rayuwar ta ne, ya ingantata.Ya suturtata cikin alfarmar aure. Aure suttura ne, cikar mutunci ne, garkuwa ne kuma rufin asiri ga diya mace, sannan gata ne da ba kowacce mace Allah yake yi wa Rahmar sa ba. Don haka godiyar ta ga Allah madaukakin sarki da kuma godiyar ta ga Mai Askirainfinite ce. Kaunar ta mijinta ta gama ratsa koina na sassan jiki da zuciyarta. Ta fara tantamar ya ya rayuwa za ta ci gaba da kasancewa ranar da babu wannanmuhimmiyar soyayyar ta Yareema Sageer a cikinta??? ***** DR. ZIYAD SAHEEB Ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakin barcinsa, ya rasa inda zai sa kansa. Shaidaniyar zuciyarsa na ci gaba da kawata masa surar sullubebiyar matar abokinsa, yarinya danya sharaf! Irin Africans din da kalar fatar jikin su ke da wuyar samu a cikin matan Nigeria. Ka kasa gane half-caste ne ko kuwa shuwa-arab ne? Dr. Ziyad ya kudire a ransa, ko ta tsiya ko ta arziki sai ya samu rabonsa a tare da matar Dr. Sageer, da ma ai sun saba sharing yammata, ya san Sageer bai taba neman matar aure ba, amma shi kam zai gwada saarsa a kan tasa, zina ai duk sunanta zina, kuma su ma wadanda yake neman a baya ai wani za su aura watarana. Don haka don an yi masa abin da shi ma yake yi ba laifi ba ne.Dole ya juyawa harkar su baya yana da wannan precious gem din a cikin dakin sa. Ya san ba zai sha wahalar samun kan yarinyar ba, yadda yake farin balaraben Turkish. Ya fi Sageer kyau nesa ba kusa ba, ya kuma san yadda matan Nigeria ke son fararen fata. Karfe takwas na dare ya kira Sageer a waya. Dr. Sageer na makale da Saade a lokacin suna karatun Organic Chemistry ana yi ana soyayya tamkar sun cinye juna wayar Dr. Ziyad ta shigo masa. Kamar ba zai dauka ba, sai kuma ya dauka. Akwai abinci ne a gidanka in shigo in ci? Cook dina ya yi tafiya. Sageer ya ce, Za mu bai wa Uche ya kawo maka yanzu, ka daina zuwar min gida, ba gidan Sultana ba ne yanzu, gidan Saadatu ne. Saadatu! Dr. Ziyad ya fada a hankali, wane irin suna ne mai tafiyar da ruhi haka? Duk wayonka sai na dandana abin da ka ke dandanawa. O.K no problem, a kawo. Da haka suka ajiye wayar. Yareema ya yi tsaki, sannan ya dubi Saade da ke kalmashe cikin jikinsa. Da ya sani bai daga wayar bama balle ya bata masa mood din sa. Kin yi ragowar abinci ne? Ta ce, Eh. Ba ta son abin da zai tada ita daga jikin Yarima sam a daidai wannan lokacin, tana cikin amarcinta, suna yi suna karatun su. Karatun ma ya fi shiga a haka (inji Saade). Ta ji wayarsu da abokinsa, kuma ta tabbatar dole sai ta tashin. Daure ki hada masa abinci a basket ki ajiye a kitchen, zan kira Uche ya kai wa Dr. Ziyad. Tana cuno baki ta mike tana fadin, Ba shi da mata shi? Ya yi dariya, ya ce, Yana da ita. Me ya sa ba ta ba shi abincin ba? Ba ta nan ne, tana Istanbul har yayan sa, ki taimaka. Ta sake turo baki gaba, sannan ta mike zuwa kitchen din, wandon three quarter ne a jikin ta da yar farar shimi (armless) ta je ta yi yadda Yareema ya bata umarni ta dawo. Shi kuma ya kira Uche a waya ya gaya masa abin da zai yi. Da safe Dr. Ziyad ya sake kiransa, Karfe nawa za ka shiga ofis yau kuma karfe nawa za ka dawo? Wannan wata tambaya ce da Ziyad bai taba yi masa ba. Nan da nan ya sha jinin jikinsa.Hausawa suka ce wai Shege shi ya san makwantar shege. “Why are you asking? Zan zo mu yi lunch ne tare. Yareema ya daure fuska sosai, ya ce, Look Dr. Ziyad, gidana gidan aure ne, ko da can ni nake zuwa gidanka ba kai ka ke zuwa gidana ba. Sabida ba matar aure a gidan ka. Ni ba zan hana a ba ka abincin gidana ba, amma na gaya maka gara ka dawo da Guneet Nigeria ya fiye maka wannan rayuwar. Maganar gaskiya matar da nake so nake kishi nake aure yanzu, don haka ba zan kai abokai gidana ba. In waccan rayuwar ce ni na bari, na gaya maka na kara gaya maka na bari. Don haka muamalarmu yanzu za ta koma ne strictly official, (ta tsaya a ta ofis kadai). Wani maketacin murmushi Dr. Ziyad ya yi, ko dama shi ya sake dulmiyar da Yareema a harkar neman mata bayan aurensa da Aisha-Sultana kuma ba karamin shaidani ba ne. Ya riga ya rantse sai ya kwanta da matar abokinsa ko da hakan zai kawo karshen abotarsu. Ya gani kuma ya yaba. Ko ana ha-maza-ha-mata kuma sai ya yagi rabon sa. Tun daga ranar yake studying shige da ficen Dr. Sageer da Saadatu zuwa cikin makaranta da lokutan dawowarsu ta tagar dakin barcin sa. Tsayin sati biyu yana hankalce da duk wani motsinsu, ya fahimci duk ranar alhamis yana dawo da Saade da wuri wajen karfe biyu na rana, shi kuma ya koma ofis ba ya sake dawowa sai shidda na yamma. Ranar wata alhamis wadda Saadatu ta kira fateful day, watanninsu ukku kenan da aure, a duka wadannan watannin ba su je Askira ba amma kusan kullum suna waya da kowa nasu. Yareema ya dawo da ita gida, ya ci abinci sannan ya dau keys dinsa ya fice yana ce da ita zai rufe gidan ta waje, ko an buga kada ta bude, shi in ya dawo zai bude da kansa. Uche zai kawo mata cefane ta kofar baya zai shigo, in ya gama shigar da su zai rufe ya koma baskwata. Bayan fitarsa Saade ta shiga wanka, wankan ma a gurguje ta yi shi don hankalinta na kan karatun paper din da za ta zana gobe, wadda ta kasance last paper ta kammala aji biyu (level 2). Ta fito wanka kenan daure da towel iya gwiwarta, ta shiga dakin barcinsu ta zauna a kan stool din mudubi ta janyo lotion dinta na Makari ta soma shafawa, kanta cikin shower cap. Tana yi tana bin wakar balarabiya Nancy Agram cikin wayarta da ke gefe, ta ji an murda kofar dakinta an shigo. Tana juyawa da sauri don a zatonta Yarima ne ya yi mantuwa ya dawo, sai ta ga wani balaraben mutum. Ya ma fi larabawa kyau. Ba ta taba ganinsa ba, yana sanye da jallabiyya, kawai sai ta sa a ranta aljani ne. Wata kara da Saade ta tsandara sai da Uche ya jiyo ta daga baskwata, ihu ta ke tana neman a kawo mata dauki da dukkan karfin muryarta. Dr. Ziyad ya karasa da sauri ya toshe mata baki, ya buga kanta da bango, sannan ya sa kafa ya tadiye ta ta fadi kasa. Duk da ta ji azaba ba yar kadan ba har cikin kwakwalwarta hakan bai sa ta kasa hobbasar ceton kanta ba. Bedside lamp da ke kusa da hannunta ta dauka ta kantara masa a ka. Fitilar ta fashe a kan Dr. Ziyad jini ya wanke masa fuska, shi kuwa Uche tuni ya kira Ogansa a waya tun karar farko da ya ji Saade ta kwallara. Rapist, at your home Oga!. Abinda kawai ya gaya wa Sageer ke nan. Ya na so ya shiga ya taimaki Saade yana tsoron ko Ziyad na dauke da makami. Shi kam Uche matsoraci ne na karshe. Duk da raunin da ta ji masa da fitila bai dame shi ba, ya dafe wajen da fitilar ta huda masa wanda tulin gashin kansa ya rufe shi. Sai jini da ke bulbulowa ta wajen, ya mike da mugun zafin nama ya dauke ta da mari haggu da dama. Saade ta nemi jinta da ganinta na wucin gadi ta rasa. Dr. Ziyad ya yi amfani da wannan damar ya fincike tawul din da ke jikinta Saade ta sake yunkurawa tana ihu, ya sake sanya kafa ya tadiye ta, Uche yana daga bayan tagar dakin yana ta jera wa Yarima kira, ga shi ba shi da lambar police ko security din makarantar cikin wayar sa, wata zuciyar ta ce ya dauki dutse ya shiga ya kwada wa Dr. Ziyad, wata zuciyar ta hana shi, in ya zo da tsautsayi ya mutu shi ma kashe shi za a yi, a kan matar da ba tasa ba ai ya san shima maigidan nasa yana danawa a gidan Ziyad din, abinda suke yi ne tare yau aka yi masa har cikin dakin auren sa.. Yana wannan sake-saken jikin sa yana bari sai ganin hancin motar Yarima ferrariya yi ya shigo gidan da wani irin mugun gudu, kasa tsayar da motar ya yi sai da ta daki daya dalleliyar motar da ke fake a gefe, sannan ta tsaya cikin kudurar Ubangiji, bayan ya take birkin tsayar da mota. Da gudu ya fito, jikinsa ba inda ba ya tsuma, hatta jijiyoyin kansa da makwallatonsa sun mimmike. Tsabar rudewa ya rasa ina ya jefa mukullin gidan, ga shi ya kulle ta ta waje. SaiUche yayi masa nuni da kofar kitchen ta baya. A lokacin Uche ya zargi ta kofar kitchen Dr. Ziyad ya shigo. A guje Yareema Sageer ya danna kai gidansa, don tun daga Kitchen za ka fara jiyo ihun da Saade ke ta kurmawatana ambaton sunan Sageer da neman taimakon Allah. A falo ya tsaya cikin gigita mara misaltuwa, yana son tantance daga inda ihun Saade ke fitowa. Daga karshe ya gane dakin barcin su ne. Tuni Ziyad ya kai ta kasa, yana ta kicin-kicin cire jallabiyyar jikinsa zai haike mata.. domin ya gama galabaitata da duka karfin kokawar ta ya kare, sai ambaton sunan Allah take hawaye masu zafi na kwaranya, ya yi nasarar cirewar kenan ya ji an ba shi (one blow one die) daga keyarsa. Da ma ga shi jiki ba jiki ba, siriri ne sai tsayi kamar falwaya, sai da ya tuntsira daga kutufo dayada Dr. Sageer ya yi masa, Yareema ya bi shi ya dinga buga kansa da bango yana naushin hancinsa da bakinsa. Saade ta yi amfani da wannan damar ta ja jiki da rarrafe ta shige toilet dinta ta rufe. Ta kifa kai jikin jacuzzi tana girza wani irin kuka jikinta yana ta rawa da kakkarwa, wanda sautin sa yake fitowa tun daga karkashin zuciyarta. Me wannan mutumin ko aljanin zata ce ya zo ya yi mata? Kisa ko me?? O.k tunda ta ganshi ya tube wando ya kuma tsiraitata to raping dinta ya zo yi. Rape, rape, rape dai da ta ke jin labari!!! Wani mugun tsoro ya shige ta, ta ji ba abin da ta ke so a halin yanzu ban da ta bude ido ta ganta a gaban uwarta. Ba ta san ya suka kare ba. Ta kasa fitowa daga toilet. Banda tsuma ba abinda jikin ta ke yi ta dunkule a wuri guda a gefen kwamin wanka. Sanyi yana kada ta. Ta dai ji karar shigowar motar security din Nigerian Turkish Nile University. Gabadaya kuma suka shiga motoci suka tafi har Yareema domin su yi report karkashin hukuma. Har Uche aka tafi, don shi ne zai bada shaidar komai. Uche ya fada wa kwamishinan yan sanda duk abin da ya sani, cewa yana shigar da cefane ya kai wasu ya koma don ya debo wasu, sai ya tuna wayar sa ya barota a baskwata tana caji ya je don ya dauko, da wannan damar Dr. Ziyad ya yi amfani ya shigo gidan ta kofar kitchen. Ihun Saade da ya jiyo da lekawa da ya yi ta taga ya gansu suna dauki ba dadi. Kiran Yarima da ya yi da daya makwabcinsu Dr. Wole da ya kira universitysecurity bayan shigowar Yarima. Lokacin da hukuma ta matsawa Dr. Ziyad kan ya amsa laifinsa kada ya wahalar da hukuma, budar bakin sa sai ya ce shi ma Yarima yana neman mata, komai suke yi ai tare suke yi, don haka bai kamata ya kawo zancen nan ga hukuma ba tunda abin da yake yi wa matan wasu ne shi ma aka yi wa tasa..kuma sharing matan suke yi. Yarima bai taba jin nadamar aikata zina a tsayin rayuwar sa irin ta yau ba. Lallai Ubangiji ya yi gaskiya, ita zina bashi ce, kuma bibiyar mai ita take yi, in dai ka yi ta a rayuwarka ko ba a yi da dan ka ba zaa yi da matarka ko kanwarka. Kuka riris Yareema Sageer ke yi akan bencin kwamishinan yan sanda, ya kuma yarda gaskiya Ziyad ya fada. Amma shi tunda yake bai taba neman matar kowa ba sai watsattsun bisa titi, to why matar sa? Amma da gaske ya taba raping yar wani duk da baiwa ce tun a shekarun tashen balagarsa. Amma ai an yi masa hukuncin addini, me ya sa tun bayan nan bai daina ba? Sai ma hakan ya bude shafin rayuwar kaico a gare shi? Sai ya ji koma me Ziyad ya yi masa kamun Allah ne. Ubangiji Subhana yayi gaskiya da yace (in kayi zina da yar wani to hakika zaa yi da yar ka ko kanwar ka ko matar ka.). Ubangiji Yana kyale mu mu yi ta saba masa, ranar da zai yi mana talala sai ya yi mana ita a kan abin da muka fi so fiye da komai a rayuwarmu. Yana son Saade, yana kishinta yadda harshe ba zai iya bayyanawa ba. Dr. Ziyad ya keta mata haddi, amma abin nan da Ziyad ya fada sai ya ji ba shi da sauran guts na neman hakki a kansa. In har ya yarda da fadar Ubangiji a kan zina. To ya yarda kawai kamun Allah ne tun a gidan duniya. Wani kamun sai an je lahira. Ya yi kukansa mai isar sa a gaban Ziyad da kwamishinan yan sanda, sannan ya share hawayen sa ya mike yace a sake shi, ya janye karar sa, amma yana so hukuma tayi masa iyaka da Dr. Ziyad ba shi ba shi har abada! Kuma daga yau ya ajiye aiki a jamiarsu ta Turkawa (Nigerian Turkish Nile University). Yana tuki a kan hanyarsa ta komawa gida yana hawaye. Hawayen nadamar duk abin da ya aikata a baya. Shi kansa ya san talala ce Allah ya yi masa da soyayyar Saade, soyayyar da ko a labarun hikaya bai taba jin wadda ta yi daidai da wadda yake yi wa Saadatu yar Bilkisu ba. Yau aibunsa ya janyo an shiga gonarsa an keta haddin sa. Ya shigar da motar maadanarta, sannan cikin sanyin jiki ya kashe ta ya fito, kayan jikinsa duk sun baci da jinin hancin Dr. Ziyad, da sanyin jikin dai ya bude kofar falon don bai san a halin da zai riski Saadatu ba. Falon yana nan yadda yake tun safe, kofar dakin barcinsu inda abun ya faru har yanzu a bude, ya leka can bai ganta ba sai ya fito zuwa nata dakin. Tana kwance a kan gadonta tana kallon ceiling hawaye na bi ta gefen idonta. Fuskarta duk ta kumbura ta yi jazur. Ba ta taba shiga tashin hankali a rayuwarta irin yau ba. Ba ta taba ganin abin da ya tsorata ya firgitata tsananin firgitawa irin yau ba da aka yi attempting raping dinta da tsakar rana har dakin aurenta. Dr. Sageer Yusuf, ya nufi Saadatu da sassarfa, ya dago ta daga kwanciyar da ta yi ya rungume a kirjinsa. Ga mamakin Saade shi ma kukan yake yi. Cikin wata kassararriyar murya tamkar ba tasa ba yake magana. Saadatu did hedid he succeed??? Ya kasa karasawa sabida tsoron abin da zai fada din. Ta runtse idonta ta kankame Sageer jikinta yana rawa. No he didnt. Wata irin kakkarfar ajiyar zuciya Yareema Sageer ya saki, wadda bai taba yin irinta a tsayin rayuwarsa ba. Ko an yi ko ba a yi ba, ya ji abin da miji ko uba yake ji in an yi zina da yarsa ko matarsa. A fili ya ke furta, ASTAGFIRULLAH WAATUBU ILAIHI. Saadatu ta fashe da kuka tana rokon Yareema ya maida ta Askira, ita ta hakura da karatun. Yareema ya ja lallausan duvet ya lullube su, ya kwantar da Saade saman kirjinsa. Ki kwantar da hankalinki don Allah Saadatu. Aikin ma gabadaya na aje. Alfarma daya nake nema kada ki fadawa Fulani ko Maimartaba wannan kaddarar da ta faru, ni kuma duk abin da ki ke so zan yi miki, I promised. Saade ta ce, In ban fada ba za ka maida ni Askira gobe? Ya ce, Insha Allahu za mu koma gabadayan mu, amma sai na mika resignation letter, ki ba ni kwanaki uku. Da wannan ya samu ya lallashe ta. Amma shi kansa Yareeman tsoronsa ta ke ji, ta daku a hannun Ziyad koina na jikinta ciwo yake yi, ba ta gaya wa Yareema ba ne don kada ta kara daga masa hankali, ganin mawuyacin halin da yake ciki, amma kanta ciwo yake sosai sabida yadda Ziyad ya buga shi da bango. Duk yadda ya so ya samu yadda yake so a daren yau, Saadatu ta ki, shi kuma yana so ne ya yi amfani da soyayya ya gusar da tsananin tsoron da ya dankare mata a zuciya, amma ta ki bada damar hakan. Ya gaji da kokawa da ita, ya mike ya kunna fitilar dakin. Sai kuka ta ke mai ban tausayi. Ya ce, For Gods sake Saadatu, ni ma rapist din ne? Kukanta ya karu, ta ce, Yau daya dai ai sai ka kyale ni in ji da abin da ya dame ni, I cantdo it, gida nake son tafiya. Yareema ya dawo ya zauna daidai kafafun ta, ya debi kafafun ya aza bisa cinyoyinsa, ai kuwa ta saki wata kara don azaba, wannan ya tabbatar masa akwai targade a yatsar kafarta. Sosai ya ci gaba da jan yatsun kafarta a hankali har ya gane mai targaden. Ba tun yau ba ya iya gyaran targade, tana kuka tana komai haka ya gyara mata. Sai lokacin ya lura cewa, goshinta ma ya kumbura sosai. Hawaye suka ciko idonsa, ya ce, Im sorry Saadatu, ni na jawo miki, one is responsible for the consequences of what he have done. Amma ke kam ba ki da laifi, tsarkakakkiya ce aka wanke aka bani cikin girma da daraja. Dole gobe mu je asibiti a binciki lafiyarki, in ma yayi kika boye min ayi miki wankin ciki. Ni ba inda za ni, kuma na gaya maka bai yi ba. Ta fada cikin kuka, ciwo har cikin kokon kanta. Kawai ka sa ni a jirgi in tafi Maiduguri, daga can sai a dauke ni a filin jirgi, bazan iya kara kwanaki uku a gidan nan ba. Ya kara sassauta murya mai nuna ya fi ta damuwa da abin da ya same ta. Na rage kwanakin ki ba ni kwana biyu mu tafi tare, in ma kin ce kada mu sake zuwa garin Abuja ba za mu sake ba!. Da wannan ya samu ya lallashe ta ta hakura ta yi barci. Washegari da asubah a firgice ta tashi tana tambayarsa aljanin nan ya sake dawowa? Ya kankame ta yana gaya mata, Relax Saadatu ba fa aljani ba ne, abokina ne Dr. Ziyad wanda yake karbar abinci a wajenmu. Mamaki da tsoro ya kashe Saade a kwance, ta kasa cewa komai, har duniya ta yi lalacewar haka? Aboki kuma makwabci mafi kusanci ya nemi raping matar amininsa? Wannan wace irin rayuwa ce? Tsoronta ya nunku fiye da tunanin ta na cewa Ziyad aljani ne. Abuja ta kara fice mata a ka, ba abin da ta ke so irin ta bude ido ta ganta a dakin ta na unguwar Fulani Bilkisu. Da gari ya waye ya yi wanka ya shirya, sannan ya rubuta resignationletterdaga NTNU. Da ya zo fita ne Saade ta ce, bai barinta ita kadai sai dai su tafi tare, tana da paper din karfe takwas. Duk da ba ta karanta komai ba, a matsayinta na matar Dr. Sageer wadda ko a kwance suke ba ya rabo da tisa mata karatun fannin su na Pure and Applied Chemistry, ta san ba za ta kasa rubuta wannan takardar ta Inorganic Chemistry ba. Shi ma ya fi so su tafi taren, don haka ya taimaka mata ta yi wanka. Tana fitowa daga paper ta same shi a mota yana jiranta, dukkansu ba mai walwala, suka nufo gida. A daren ba ta bari sai gobe ba ta hade kayanta tsaf ta daure. Lamarinta har da na shagwaba kuma, ya yi - ya yi su je asibiti a duba ta ta ki. Washegari ya shiga don ya gama cike sauran takardun ajiye aiki, ya ce mata insha Allahu ba zai wuce awanni biyu ba. Da kyar ya lallabata ta yarda bayan ya ba ta mukullan kofar kitchen da na kofar shigowa duka a hannunta. ****** Yareema Sageer bai dade da fita ba Ya Gumsu da kanwarta Aunty Daja wadda ke aure a nan Abuja tana auren wani ministan yada labarai, suka zo gidan cikin wata zabgegiyar mota. Ya Gumsu ta zo auren babbar yar Aunty Daja ne Abuja tun shekaranjiya. Tun da ta iso ta ke ce da Daja a kai ta gidan Yareema, Daja na ba ta hakuri kan ta bari a kai amarya ko me za su yi sai su yi, ita ma ba ta bayan hada zuria da yar annamimiya Fulanin Askirama. Suna sauka daga mota suka karaso kofar shiga falo, suka soma yi mata wani irin mahaukacin bugu, wanda ya karasa razana razananniya Saade, wadda da ma ta ke zaune a darare tana jiran dawowar Yareema da trollies dinta uku a gabanta. Ta gama sa wa a ranta yau komai dadin bakinsa a Askira za ta kwana. Sai kuma ga wannan mahaukacin bugun, ba abin da ta kawo a ranta sai Ziyad ne ya dawo. Idanunta suka raina fata, hawaye ya soma malalowa. Ba ta so ta yi ihu ma kada ya san tana cikin gidan, sai mazari jikinta yake daga tsayen da ta ke, wani fitsari ya kwace mata. Amma me? Sai ta jiyo murya kamar ta mata suna kiran sunanta. Ba ta yi wa Ya Gumsu farin sanin da za ta dau muryarta ba, amma sai ta ji tana fadin, Ni da gidan Dana aka bar ni ina buga kofa da mutuncina na Gumsun gari da komai? Da sauri Saade ta karasa ta bude kofar da mukullan da dama suke rike a hannunta. Ta gane Ya Gumsu, dayar ce ba ta sani ba. Tana kokarin yi musu barka da zuwa ta ji wani lafiyayyen mari ya sauka a kan kuncinta, Aunty Daja ma ta kai mata nata. Shegiya karuwa yar karuwa, tsintattun bisa titi. Idan ba Bilkisun ce ta haifa min Yareema ba, ba kuma ita ta ajiye ki a gidan nan ba, to sawunki a likkafa ki kama hanyar gidan ubanki, tunda an ce kina da shi. Idan na ganki a masarautar Askira sai na sa an nakasta ki yadda ba Yareema ba babu wani namiji da zai kwashe ki. Fice mana a gida ki san inda dare ya yi miki kafin in sassaba miki kamanni. Ta hankado ta waje, Daja kuma ta dauki hijab dinta ta jefo mata suka dinga hankada ta har kofar fita gidan, bayan Daja ta kara zazzabga mata mari. Farar fuskar nan ta yi jawur tayi kitumur kamar gauta. Marukan da ta sha sun kai goma. Yatsunsu ya kwanta lambam a kan farar fatar fuskar Saade. Kuka ma wani lokacin rahma ne ga dan Adam, a lokacin da zuciyarsa ta rasa abin yi. To Saade ta kasa ko da fidda hawaye, tana nadamar yarda da aure da soyayyar Yareema Sageer alhalin tana da masaniya kan cewa, mahaifiyarsa ba ta kaunar tata kamar ajalinta. Ya yi amfani da dukkan dabarunsa na wayayyen Da namiji ya sanya soyayyarsa a zuciyarta, ya ribace ta ya kassara zuciyarta. Yau mahaifiyarsa ta yi mata wulakancin da ko ita mayya ce dole ta hakura da Yareema Sageer sai a wannan lokacin ne ta ji hawaye masu dumi sun zubo mata. Ya ya za ta yi ta je Askira? Duk da Ya Gumsu ta ce kada ta je din, amma ba ta da inda ya fi can, tunda uwarta tana can, za ta bar masarautar Askira ne only ranar da babu Fulani a can ko ranar da ita ma Askirama ya kore ta. Ko kudin mota babu a tare da ita, daga ita sai hijabin sallarta. Amma ta tabbata za ta iya kai kanta Askira, idan ta ganta a Maiduguri. Ko da da rarrafe da jan ciki ne. Tana wannan tunanin tana kuka, ba ta san cewa ta hau bisa titi ba ta bar tafiya a gefen hanya. Daidai lokacin da shi kuma ya fito daga NTNU yana sharara gudu don tafiya gida, ya hango wata mace na tafiya tsakiyar titi kamar bata ji ba ta gani, motoci na ta kauce mata, wasu su bi ta da zagi, wasu su kunna mata fitilar zagi, amma ba ta ko san suna yi ba. Ya sakar mata kakkarfan horn don ta sha gabansa, ta juya a firgice sai ya ga Saade. A hankali ya sauka a gefen titi, ya fito da sauri ya bi bayanta yana kiran sunanta. Saadatu Hashim, Saadatu Askira ina za ki je haka? Muryar Said abokinta, Saidu-Saidunta. Yau da shi ta aura wa zai yi mata wannan wulakancin da cin zarafin? Wani hawayen ya sake zubo mata, ta sa fuska cikin hijabinta tana kuka. Said ya hau waiwaye cikin tsoro. Har zai ce ta shiga motarsa ya kai ta inda za ta je ya tuna gargadin Yareema Sageer. Kada ka kara daukar matata a motarka ko da da niyyar taimako ne. Said ya naushi hannun damansa da hannun hagu, ga shi kuma ba zai iya tafiya ya barta a kan titi ba, ko da kuwa supreme court Dr. Sageer Askira zai kai shi a dalilin hakan. Da ganin halin da ta ke ciki tana tsananin bukatar taimako, ba zai barta ta ragaita a babban birni irin Abuja ba. Wane irin taimako zan iya ba ki? Said ya fada cikin tsoro, yana tsaye nesa-nesa da Saade yana kuma waiwayawa dama da hauni kada Dr. Sageer ya zo ya same shi. Kudin mota. Ba ta san lokacin da ta furta ba. Ina za ki je? Ya tambaya da sauri. A hankali ta ce, Garinmu Askira. In aka sauke ki a Maiduguri za ki iya zuwa har can Askiran? Da sauri ta gyada kai. Said ya ce, Zan sa ki a tasi zuwa airport, sai in bi bayanku, sai mu je in yankar miki ticket din Maiduguri. Saade ta hau godiya, tana yi masa addua. Ji ta ke kamar ma ga ta ga Fulani a gabanta. Hakan kuwa aka yi, Said bai bar airport din ba sai da ya tabbata jirgin Maiduguri ya daga da Saade. Ya kuma damka mata naira dubu goma, ya bar filin jirgin cike da tausayinta. A ganinsa iyayensu sun cutar da ita da suka aura mata babban mutum kamar Dr. Sageer, ba zai ba ta kulawar da in shi ya aure ta zai ba ta ba, ban da kishin balaI bai san komai ba (a ganinsa). Tunda jirgin Azman ya lulluka sararin samaniya ya doshi arewacin Nigeria, Saade ta kankame jikinta wuri guda tana kuka, ba ta san ya ya za ta iya rayuwa babu Sageer ba. Amma ta tabbata Ya Gumsu ta raba su kenan, ba za ta kara bari su rayu inuwa guda ba. Ya taba cewa yana fuskantar barazana akan auren su, wanda ya sanya shi tabbatar da auren su a lokacin da bai shiryawa hakan ba, yanzu ta tabbatar ba komai bace barazanar, Ya Gumsu ce. Har gobe bata yi naam da zaman su tare ba. Wannan tunanin kadai na matukar tayar da hankalin Saade, ta rasa inda za ta tsoma zuciyarta ta ji dadi. Wani irin sanyi ta ji yana shiga har cikin bargonta. Ba jimawa hakoranta suka soma karo da juna, kafin a yi haka zazzabi mai zafi da ciwon kan da ta kwana a ciki sun hadu sun rufe ta ruf. Ta sauka a filin jirgin saman Maiduguri cikin mawuyacin hali. Ba ta gaya wa kowa tana tafe ba balle a san da zuwanta a zo a dauke ta, sannan ba wayarta a hannunta ta baro ta a kan gadonta. Duk da cewa ta haddace lambar Fulani, amma ta ga gara ta bi motar kasuwa ta karasa Askira, tunda akwai kudi isassu a hannunta. A nan airport ta samu wani mai taxi yana faman binta da nacin tambayar ina zaa kai ta? Ta ga cewa, zuwa tasha da neman motar Askira karin wahala ne a gare ta, ga shi da ma ta yi matukar jigata, sai ta juya ta ce da shi, Nawa zan ba ka ka kai ni har Askira? Mai taxi ya yanko kudin da a tunaninsa ko rabinsu ba za ta biya ba. Amma sai ya ga babu musu ta amince. Ya bude mata kofa ta shiga ya rufe, ya ja mota suka naushi hanya. ****** ASKIRA EMIRATE Lokacin da suka shiga garin Askira magriba ta kawo kai. Ita ta dinga nuna masa hanya har kofar fada. Ya ajiye ta ta mika masa duka dubu goman, sannan ba tare da ta kara cewa uffan ba bayan godiya, ta durfafi cikin gida. Amma me? Tana saka kafa a soro na farko hajijiya ta soma dibarta, ga yunwa ga wahalar zaman mota. Ga wani irin masifaffen ciwon kai da ke sakadarta, taku biyu ta yi a soron farko Fadawa na zazzaune sai gani suka yi mace ta fadi a wajen, sakamakon kafafunta da suka kasa daukarta, duhun yunwa da na hajijiya kuma suka mamayi ganinta. Taimakon Allah ne kadai ya kawo ta Askira lafiya. Fadawa biyu sun shaida ko wace ce, kasancewar cikinsu akwai direban fada da ya ke kai su El-Kanemi. Cikin kidima suka kira bayi mata, su uku suka dauke ta ranga-ranga sai Unguwar Fulani Bilkisu. Ba aladar Askirama ba ce bin dakunan matansa, amma Fulani Hibbani wadda ita ce mai girki, sarkin gulma da daukar zance ta shigo yanzun nan ta same shi yana cin abinci, kamar ta manta shi din ne ta ke magana da shi, tsabar gulma da ke cinta. Mai Askira ashe abin da Yareema ya yi ke nan? Ya sako yar Bilkisu bayan ya yi mata shegen duka? Ta dawo rai a hannun Allah Anya shi ma ba giyar yake sha ba kamar matar. Sauran maganar makalewa ta yi a bakinta ganin wata irin zabura da Askirama ya yi. Kafin ta ankara kuma ta tsinto shi a bakin kofa bayan ya saka takalminsa na gashin dawisu. Fanna tare da dukkan kuyangin Fulani suna kan Saade, sai firfita suke mata bayan an samu ta farfado, tana kwance shame-shame bisa cinyar Fulani, tambayar duniyar nan Fulani ta yi mata, amma ta ki cewa komai. Fulani ta soma fusata, amma ta yi kokarin hadiye fushinta. Ba za ki gaya min ina Yareeman ba? Ya san kin taho? Ke da wa ki ka zo? In sakinki ya yi ki yi mana bayani. Kallo daya Fanna ta yi wa sauran kuyangin suka hau darewa suna barin falon, ta yi hakan ne ganin irin rikicewar da Fulani ta yi har ta manta cewa suna tsaye. Ko sakin Saade aka yi ba za su so a ji ba, a wannan gidan na gulma da jiran kiris a kan duk wani abu da ya shafi uwargijyarta. Gyara kimtsi kimtsi gyara Zakin Askira. Suka jiyo kuyangi na fadi daga waje, tabbacin Alanguburo ya durfafo unguwar da kansa. Kamar kiftawar ido kuma sai ga shi a kansu, sabida saurin da ya shigo da shi ba irin tafiyar sarauta da yake yi ba. Lafiya Bilkisu? Me ya faru? Ya tambaya cikin matukar kidima yana kallon kumburarriyar fuskar Saade da ta hade ta cakude ta yi jajir. Wa ya kawo ta? Ina Yareeman? Dukanta ya yi? Muryarsa ta karye gabadaya cikin debe tsammanin abin da Hibbani ta gaya masa. Fulani Bilkisu ta yarfar da hannu, ta ce, Wallahi Allah ban san komai ba. Yadda ka ganta ni ma haka na ganta. Na kuma yi tambayar duniya ta ki ce min komai. Jikinsa har rawa yake ya ce, Bari in kira shi a waya, amma in ya tabbata abin da aka gaya min ne zan sa kafar wando daya da Yareema. Yana kokarin kiransa ne sai ga kiran Yareeman ya shigo. Ya amsa wayar ba tare da ya ce uffan ba. Daga can bangaren Yareema ya ce cikin wata irin murya da Askirama ya kasa gaskatawa ta Sagirunsa ce. Alanguburo, Allah Kawun jo (Allah ya kara maka yawan rai) a taimake ni a gaya min ko Saadatu ta zo Askira??? Kamar ba zai yi magana ba, amma tabbas yana son amsa guda daya kwakkwara daga bakin Yareema. Ka fara gaya min abin da nake son sani, sakinta ka yi? Yareema ya wani irin girgiza kai, tamkar Askirama na ganinsa, gumi ya wanke masa fuska, muryarsa na hardewa ya ce, Babu saki tsakani na da Saadatu har abada! Babu wulakanci tsakanina da amanarka har abada. Sai kauna da soyayya mara yankewa domin na samu fiye da abin da ka kwadaita min samu cikin aurena da Saadatu Na je in kai resignation letter ga V.C in cike takardu in dawo mu taho tare sabida wata yar matsala da na samu wajen aikin nawa, kafin in dawo sai sai sai. Ya kasa karasawa. Ambatar sunan mahaifiyarsa a wannan gabar ya san daidai yake da raurawar igiyar aurenta kamar yadda ya tabbata nasa auren yana rawa a halin yanzu, in har komawar Saade gida ya tabbata kuma ya je kunnen Askirama. Wata tsawa da Maimartaba ya daka masa sai da ta hautsina gabadaya kayan cikinsa, Ba za ka gaya min abin da nake son sani ba? Sakinta ka yi ko aah? Yareema ya kifa kai jikin kujera ya saka kuka kamar Mai Askira na gabansa. Ban sake ta ba wallahi ban sake ta ba Ya Gumsu ce ta kore ta, kuma Uche ya gaya min har dukanta sun yi. Im on my way nowto Askiratunda alhamdulillahi ta iso gida. Waye ya gaya maka ta iso gidan? Ka fada wa Babarka ta share dakin Saadatu ta zauna, don nata dakin na rufe shi daga yau. Kai kuma bana bukatar ganinka gabana ka je ta aura maka duk yar uban da ta ke so. Yareema kadan ya rage ya zauce, bai iya sauraron bakaken maganganun Askirama ba ya ji sallamar Ya Gumsu da Aunty Daja. Ya Gumsu ta dube shi ta kyabe baki, ta ce, Yanzu sabida na raba ka da wannan jarabar shi ne ka ke yanka wannan uban gumin? Sannu tattabara sarkin soyayya. Ai da ma waadin watanni uku muka yi da kai za ka mayar wa uwarta yarta yadda ka karbe ta. To na ji shiru, shi ne na zo ni da kaina na sake ta, ka gaya min hadisin da ya ce ba ta saku ba. Aunty Daja ta karbe, Ban da abinka Yareema, uwarka gata ta ke maka, yanzu aure na neman ci gaba ake yi ba na komawa baya ba. Kamar ka Yareeman Askira mai jiran gado ka rasa matar aure sai agolar gidanku? Ban da uwarka tsayayya ce ai da yanzu labari ya sha bambam. Bai san sanda ya kai mata kutufo ba, ta yi maza ta kauce ya naushi iska. Ya daga ragaitattun idanunsa ya dube ta. Aunty Daja ki ke ko wa? In uwata za ta shiga hurumina in kyale ta ban da ke wallahi. Na auri agolar tunda ke kin auri Minista ina ruwanki? Agolar na ga ta fi dacewa da rayuwata, sai ki zuba ruwa a kasa ki sha kun kore ta kamar yadda Askirama ya kori uwata. Bai ankara ba ya ji hawaye na son zubo masa, don haka ya tashi ya bar wajen. Ko a jikin Ya Gumsu, ta ce, Ya dade bai kore ni ba, tunda ya auri uwarta na kara gane kansa? Sau dubu gara min tubabbiyar nan a kan diyar Bilkisu. Dadin abun ina da inda zan zauna ko ba gidanka ba. Kuma ba zan bar gidan nan ba sai ka rubuta takardarta ka ba ni Yareema bai tsaya ba ya nufi motarsa. Yana ji Aunty Daja na lallashin Ya Gumsu, ta yi hakuri tunda dai sun kore ta ba sai ya yi saki ba, ko ba komai sun kunsawa Bilkisu bakin ciki, kuma in tana son yarta ba za ta barta ta dawo ba a yadda suka ci zarafinta. Yanzu abin da ya kamata ki maida hankali a kai shi ne, nema masa auren Hajjaju. Ya Gumsu ta balla mata harara tana zama cikin royal chairs din Saade, ta ce, Ke ma kina wasa ne, wa zai karba masa auren a halin yanzu na taba yar mowa? Da na sani ma ban kore ta ba, dagewa na fara yi aka auri Hajjajun, bayan ta shigo sannan mu san yadda zamu yi da ta gidan, amma yanzu na tabbata na bata goma ne daya ba ta gyaru ba. Tunda ki ka ji ya ce ubansa ya kore ni. Ya Gumsu ta fada cikin damuwa, wadda ba ta karasa har kasan ranta ba. Aunty Daja ta yi tsaki, ta ce, Haba Gumsun Askira, ke ce fa uwar Yareema, uwar Ya Maira, masarautar Askira taki ce ke da yayanki, kin taba jin an saki Gumsun gari uwar iyali? Ai sai dai ya yi fushinsa ya gama ya sauka, amma ba sa saki, shi ya sa na tabbatar miki yaron nan ba zai saki yar Bilkisu ba, mu dai yi kokari ya yi aure na shiga tsara ki manta da wata yar Bilkisu. Kishiya kadai ta ishe ta. Hum! In ji Ya Gumsu. Ba ta san irin bayanin da za ta yi wa yar uwarta ba, ta gane cewa, kishi da BAGGARA ba abu ne mai sauki ba, sai dai ita kishiyar ta yi ta jin jiki tana kunsar bakin ciki har karshen rayuwar ta. Ta yadda Mai Askira zai yarda ya karba wa Yarima auren yar sarkin Bauchi yanzu shi ne ba ta sani ba. Babu ubansa Sarkin Askira kuma wa zai bashi auren? Ko ita za ta je ta nemo masa waliccin auren yar sarkin Bauchin da kan ta? Ta fahimci ta lalata chance dinta ne kawai na kara auren Yarima da korar Saade da dukan ta. Da ta sani ma kafewa ta yi the other way kan cewa, tunda ta bada dama ya auri zabin ransa da zabin ran mahaifinsa, to ita ma ya auri zabinta. Amma yanzu ta tabbata kwabarta ta gama yin ruwa. Don haka ta kasa zama gidan Yarima kamar yadda ta yi niyya, ta bi Aunty Daja gidanta tunda shi ma ya fice ya bar musu gidan, ta kuma tabbata Askira ya nufa. Uche dake shigowa a lokacin yana ganin fitar su ya je ya kulle koina na gidan. Tana kallon kiran Maimartaba yana ta shigowa wayar ta, amma ta yi funfurus ta ki dagawa sabida tsoro. Ta san ba zai taba sakinta ba, amma in ka tabo shi hukuncinsa ba shi da dadi. Suna tafe a hanyarsu ta komawa gidan Daja, ta gaya mata Maimartaba yana ta kiranta, Daja ta ce, Ki dauka a yi ta ta kare. Ta kuwa daga ta hanyar cewa, Allah Kawun jo (Allah ya kara maka yawan rai). Ina kan layi. Muryar Askirama mai zurfi da kauri (husky) ta bakunci kunnuwanta. Bana zaton Yareema ya gaya miki sakona. Cewa na yi ki share dakin Saadatu ki zauna, don ba ki da daki yanzu a gidana. Cikin gatsali ta ce, Allah ya kara yawan rai wani abu aka ce na yi? Ziyara fa kawai na kawo musu. Ta fashe da kuka, kukan da daga ji za ka san bana gaskiya ba ne. Don takaici Mai Askira sai ya kashe wayarsa, kada ya yi abin da zai zo daga baya yana nadama. Ya Gumsu ta shiga bandaki a washegarin ranar za ta yi wanka. Ta sa kafa a cikin bahon wanka ba ta lura da jikakken sabulun da ke ciki ba, kafarta ta sauka a kan sabulun ta zame ta tafi gabadaya ta yi wata irin mummunar faduwa. Faduwar da sai daukanta aka yi ranga-ranga zuwa asibiti baki ya karkace yana ta fidda kumfa. Idan Ubangiji ya nufi alamari, bawa ya nuna ja da hukuncin Ubangiji, sai Ubangiji ya barshi da dabararsa, amma idan Ya ga dama talalar da zai maka ta dare daya ce. Wani rabon sai ya kawar da kai dagadoron duniya gabadaya. A ci gaba da rayuwar babu kai, babu mai tuna ka da kyakkyawar zuciya balle ya yi maka addua. Don haka Gumsun Askirais lucky that shes alive a daidai lokacin da Saade ke jikin mahaifiyarta tana ta kelaya amai kamar da bakin kwarya. Tunda ta iso ta ke zazzabi da ciwon kai, kafin wayewar gari kuma sai haraswa, ta kasa cin komai, gabadaya ta fige ta yi zuru-zuru. Fulani da Fanna suna tsaye a kanta tun jiya. Shi ma Maimartaba ba ya rufa awa guda bai kira Fulani ya ji me Saade ta ke ciki ba. A karshe ya turo likitar matan gidan don ta zo ta duba ta a san takamaimai me ke damunta. Ita dai Fulani tuni ta sha jinin jikinta. Tun daga sanda Saade ta ce ba ta son warin turarenta. Amma kuwa Yarima bai kyauta ba, ya saba alkawarin da ya yi mata. Saade is too young da haihuwa wani matsanancin tausayi ya kama ta. Amma da ta tuna ba haramci suka aikata ba sai ta rage wa kanta damuwa. Wannan rabo na kurkusa da kofar daki ina Ya Gumsu za ta kai shi? Ko kusa abin da Ya Gumsu ta yi wa Saade bai sa ta ji tana so a raba auren ba, ko don ganin halin bacin ran da Askirama ke ciki, wanda ko ita da ta haifi Saaden abin bai tabata har haka ba. Ta sa a ranta Ya Gumsu za ta yi fiye da wannan in dai a kanta ne. Kuma a washegarin ranar bayan fitar Dr. Zainab da ta duba Saade ta tabbatar wa Fulani akwai ciki na sati Shidda, ta shiga don ta yi wa Askirama wannan albishir ta ji yana amsa waya. Sai kuma ta ji ya ce, Stroke? Cikin tsananin mamaki. Gumsun da ko jiya na yi magana da ita a waya lafiya lau? Aka yi magana daga daya bangaren wanda ita ba ta ji ba, sai ta ji ya ce, Ai shi ke nan, Allah ya ba ta lafiya. Yayanta sai su je Abujar su yi jinyarta, amma Allah ya gani ni ba zan zo ba Daja, yar uwarki ta girma ba ta san ta girma ba. Na dade ina hakuri da halayenta ta kasa gane gata na yi wa rayuwar Yareema da shi bakidaya da na aura masa Saadatu. Babu yadda ban yi da ita ba ta karbi hukuncin Ubangiji, ta nuna min ta hakura har za ta kai musu ziyara, shi ne ta yi tattaki har dakin yarinya, ta ci zarafin marainiyar Allah ta koro ta tun daga Abuja har Maiduguri da Askira ita kadai a wannan marrar ta satar dan mutum kamar satar takalmi. Don haka ina nan a kan bakana, Gumsu ta ci gaba da maye gurbin Saadatu wajen Yareema Sageer. Babu Saadatu babu danta, sai ranar da ta yo tattaki har dakin Bilkisu ta ba ta hakuri a kan cin zarafin da ta yi wa yarta. Ta kuma furta da bakinta cewa ta amince su ci gaba da zaman aure da bakinta. In ba haka ba shi ma Yariman kada ya sake ya tako min gida. Yana gama fadin haka ya kashe wayarsa yana maida numfashi cikin bacin rai. Fulani Bilkisu ta karasa ta gurfana a gabansa, tafukan hannunta bisa tafin kafarsa. Cikin muryar lallashi da son kwantar masa da hankali ta yi masa albishir din da ke bakinta. Da gaske? In ji Askirama. Cikin excitement din da ba zai misaltu ba. Ta kashe shi da lallausar murmushi, ta ce, Da gaske Dr. Zainab ta tabbatar da ciki na sati shidda a jikin Saade. Sabida haka Askirama ka yi hakuri da duk wani bacin rai, tunda Ubangiji ya nuna mana ayarsa. Idan ta warware kwana biyu a manta da komai a mayar wa da Yarima matarsa. Mai Askira ya girgiza kai ya ce, Ayoyi kam ai muna ta ganinsu. Yanzu kanwarta ta kira ni ta shaida min cewa, suna asibiti da Gumsun Gari, ta fadi a bayan gida ta samu stroke. Innalillahi wainna ilaihi rajiun. In ji Fulani. An gaya wa Yarima da su Yaa Maira? Cikin damuwa ya ce, Yarima ya taho tun jiya ta mota, babu jirgi, amma Awaisu ya gayaminya samu minor accidentahanya, bai ji ciwo ba amma ya bugu, kuma motar sa ta jikkata, ya iso Askira tun jiya, ni na ce da Awaisu ya gaya masa kada ya sake in ganshi gabana ko bangarenki. Ya Maira kuma sun kama hanyar Abujan. Cikin dimbin alhini Fulani ta ce, innalillahi wainna ilaihi rajioun. Zama bai ganmu ba, ya kamata a shirya mana tafiya mu uku, ni da Yakirjinoma da Hibbani. Yareema na tabbata Awaisu zai bashi duk kulawar data dace, amma don Allah Askirama ka bar shi ya dawo gidan nan. Ya yi ajiyar zuciya, wannan karon cikin muryar sa akwai sassauci, ya ce, Su za su je, amma ban da ke. In kin tafi wa zai kula min da Saadatu da Chiroman Gari? Ta yi murmushi kadan, jin har ya bai wa dan cikin Saade Sarauta tun kan ya iso duniya. Ta ce, Fanna za ta kula da su sosai. Bai kamata a ce su sun tafi ni na zauna ba, sai ta dauka sabida abin da ta yi wa Saade ne wanda ni sam bai shafe ni ba. Ta kare zancen ta da cewa. Ai Saade yarta ce! Koda bata auren Yarima. Askirama ya kura wa matarsa Bilkisu ido, yana mamakin kyawawan halayenta. Matansa sun kasa fahimtarta ne, amma duk ta fi su kyan hali, ba ta taba dauko zancen wata cikinsu ta kawo masa. Su kuwa basu da aiki sai fadin aibunta. Sun dauki kishin duniya su duka sun dora a kanta. Sun kasa gane ba kyawun halitta kadai ke rudarsa a kan Fulani Bilkisu ba, har da kyawawan halayenta. Amma duk yadda ta so Askirama ya barta zuwa Abuja duba Ya Gumsu ya ki amincewa da hakan. Yaa Maira ce ta zo ta hada kan sauran kannenta mata da maza aka ba su motoci da dogarai suka kama hanyar Abuja. Cikin tashin hankali. Hibbani da Yakirjinoma jirgi daya suka bi tare da Ahmad da Suhail wadanda za su kula da su. Fulani ta kira Yareema a waya bayan ta koma dakinta. Muryar Yareema har ba ta fita sosai, kamar ta wanda ke fama da mura, shi kadai ya san halin da yake ciki. Ciwon da jikin sa ke masa sakamakon buguwar mota bai dame shi ba kamar hukuncin da Askirama ya yanke akan sa na nesanta shi da Saade. Yana gidansa tun isowarsa ko falo bai leko ba tunda Askirama ya aiko Awaisu ya gaya masa sakon kada ya sake ya ganshi a fada ko shigifar sa, kuma kada ya sake ya je inda Saade ta ke. Har sai mahaifiyarsa ta bada hakurin cin zarafin da ta yi mata har dakin auren ta. Ta kuma yi alkawarin karbar Saadatu matsayin suruka sannan ne shima zai janye nasa takunkumin. Shi ya san wannan decision ba mai sauki ba ne ga Ya Gumsu, a yadda ya san kafaffiyar zuciya irin tata in tana kin abu. Kuma bai fita daga wannan zullumi da tashin hankalin ba a daren jiya Aunty Daja ta kira shi tana kuka, wai Ya Gumsun ta fadi a toilet ta samu stroke. Ya kwana cikin wani hali na kaka-ni-ka-yi, and he is speachless.Wordless. Moodless. Ko magana ba ya iya yi. Awaisu ya so ya taya shi hira a daren ranar bayan ya bashi magani ya kira likita ya duba shi ya tabbatar babu mummunan rauni a jikin sa, ya ce ya tafi kawai ba ya bukata, sai kuma yanzu da wayewar garin yau ya samu wayar Fulani Bilkisu. Yareemah, kana lafiya? Ta fada cikin tausayawa. Ji ya yi idanunsa sun cicciko da kwalla, bai zaci wannan rahmar daga gare ta ba. Abin da bai sani ba shi ne, ita halinta ya bambanta da na sauran mata. Mace ce mai hangen nesa da tsananin kawaici da maida dan kowa nata. Im sorry Fulani, Im sorry. Ya furta in a subdued voice. Ta yi murmushi, ta ce, Ba zancen Saade ya sa na kira ka ba. Na kira ka ne in jajanta abin da ya faru da Ya Gumsu. Da accident da aka samu, Allah ya tsayar haka, Ya sa kaffara, Allah ya ba ta lafiya. Na so in bi su Yaa Kirjinoma Abujan, Askirama ya hana ni, sabida ita ma Saade kwance ta ke babu lafiya tun isowarta. Tamkar zuciyarsa za ta fito ta bakinsa sabida zullumi, ya ce cikin wata marainiyar murya, Me ke damunta? Fulani ta yi dan jimm! Kafin ta ce, Na dauka ka sani ai. Gabansa ya yi mugun faduwa, kada dai Saade ta gaya musu maganar Dr. Ziyad ne? Yau da ya shiga uku in Askirama ya ji zancen nan ya san aurensa da Saade ya kare. Hawaye suka fito daga idanun Yareema Sageer ba tare da ya shirya ba. Amma sai Fulani ta fadi abin da ya gigita shi, ya wanke zuciyarsa daga duk wani rudani da dimauta da ta ke ciki. Ciki ne tare da ita na kusan watanni biyu. Yareema sai da ya cire wayar daga kunnensa, don ya tabbatar da wanda yake magana, My inlaw ba gizo kunnuwansa ke masa ba. Ya wani irin lumshe idanunsa yana karbar wani irin excitement a cikin kirjinsa. Don haka ka kwantar da hankalinka ka koma Abuja ka kula da lafiyar mahaifiyarka. Saade tana karkashin kulawarmu insha Allah. Kafin sannan zuciyar Askirama ta huce sai a ba shi hakuri. Abin da nake so yanzu shi ne ka koma Abuja ka yi jinyar mahaifiyarka. Insha Allah, I will. Ya fada cikin girmamawa. Har sun yi sallama ya kasa jurewa. Cikin jin nauyi ya ce, Fulanin Sarki zan iya magana da Saadatu? Fulani ta ce, Ta samu barci, in ka koma Abuja ka samu nutsuwa ka kira ni, zan ba ta wayar insha Allahu. Da wannan suka yi sallama. A washegarin ranar ya tattara ya koma Abuja. ***** Yau asibitin national hospital Abuja ya ga iyalin masarautar Askira, ko ina ka wulga motoci ne cike da dogarai masu rubutun Askira Emirate. Tabbacin mara lafiyar na da alaka da hamshakiyar masarautar Askira. Lokacin da Yareema ya iso an kai Ya Gumsu daki na musamman (V.I.P room) an ba ta kwanciya. Sanda suka shiga shi da Awaisu Ya Gumsu barci ta ke yi. Amma jin muryar Yareema na magana da likita sai ta hau kokarin bude idonta. Duk da barcin da ya ci karfinta kokarin magana ta ke yi da bakinta da ya karkace, amma ta kasa. Yareema ya matsa daidai kanta yana hawaye yana fadin, Ki yafe ni ya Gumsu, na kasa cika alkawarin da na yi miki, amma na alakanta hakan da rabon gaggawar da ya rantse a tsakaninmu. Ya Gumsu Saadatu ciki gare ta, na kasa cika alkawarin ki Ya Gumsu na kasa. Ya saka kuka tare da kifa kansa a kan cikinta. Da hannunta mai lafiyar ta mika tana shafa sumar kansa, tana ci gaba da kokarin furta magana abu ya gagara, sai hawaye ke bi ta gefen idonta. Amma daga yadda ta kama shi da hannu daya ta kankame tana hawaye ya san alheri ta ke son fada. “Is ok Ya Gumsu, ki yi barci. Ni dai fatana ki fahimci cewa Saadatu alkhairi ce a gare mu kamar yadda Alanguburo ya hango. Ya Gumsu ki kwantar da hankalinki a kan Fulani Bilkisu da ahalinta, wallahi ba ta nufinki da sharri. Idan Askirama ya fi sonta ba ya nufin ke uwar yayansa ba ya sonki. Yana son ta ne saboda kyautatawar ta gareshi tafi taku. Amma kowa da gurbinta, kuma kowa da matsayinta. Sai ki duba ki tace ki ga shin me take yi wanda Askirama ke so? Kema sai ki kwaikwaya. Shaidan ne ya ke kambama miki soyayyar Askirama ga Fulani Bilkisu, amma ita in ya sa ta tana yi, in ya hana ta tana hanuwa. Ke kuwa fa Ya Gumsu? Abin da ki ka ga dama shi ki ke masa, yana hakuri saboda mu, Ya Gumsu lokaci bai yi ba da girma zai bayyana a halayenki? Hawayenta ya dadu, sai gyada masa kai ta ke akai-akai kamar kadangaruwa. Yarima ya ci gaba da cewa. Ya Gumsu ki yafe mini ban cika alkawarin da na yi miki ba, musamman da na ji kin ce bayan watanni uku za ki raba mu. Na kasa Ya Gumsu, na kasa Saadatu ciki ne da ita, zan yi azumin kaffara ki yafe mini. Tana so ta ce masa babu kaffara a kanka, tunda ba fadar Ubangiji ba ce, sannan baka sabi Allah ba, amma ta kasa. Yarima ya rungume ta yana ci gaba da rokonta rangwame da afuwa a kan aurensa da Saadatu wanda ya kara karya zuciyar Ya Gumsu, ta amince soyayyar danta ga yar Fulanin Askirama wani hadi ne daga Allah, domin ya dinke barakar da ke tsakaninsu. Ya kawo maslaha da fahimtar juna ga iyalan Maimartaba Sarkin Askira. Kwanan Ya Gumsu da iyalanta uku a National Hospital, sauki na samuwa a hankali. Ya Maira ta kira Yareema gefe ta ce tunda jikin da sauki, kuma an ce gashi ya rage za a dinga yi mata, ko zai nema musu sallama su koma gida? Sai a yi hiring professional din da za ta dinga yi mata gashin a gida? Sun yi yawa a asibiti, kuma ba wanda zai yarda a ce ya koma gida. Don wani hotel suka kama a nan kusa da asibitin mazansu da matansu. Yareema ya amince da shawarar Yaa Maira, ya nema musu sallama a washegari. Daga asibitin koyarwa na Maiduguri aka dauko physiotherapist din da za ta dinga kula da Ya Gumsu a gida ana biyanta. Yareema bai samu nutsuwa ba tun saukarsa Abuja, don haka bai kira Fulani Bilkisu ba. Amma ko me yake yi Saadatu na manne cikin ransa. Minti bayan minti, sakan bayan sakan son Saadatu karuwa yake a zuciyarsa. Tamkar nisa da suka yi da juna wani medium ne na linking zuciyoyinsu wuri guda. Haka kuma yake ga Saade, wadda ke can tana fama da kanta, amma kullum hankalinta yana kan mijinta Yareema Sageer. Ko yana cin abinci? Ko yana cikin irin damuwar da ta ke ciki? Ko shi ma Ya Gumsu ta mare shi a kan ta? Tambayoyin da ta ke yawan yi wa kanta ke nan ba ta da mai amsa mata. Domin Fulani ta lafiyarta ta ke ba ta mata zancen Yarima sam-sam. Sun dukufa ita da Fanna wajen kula da ita da dafa mata duk abin da suka san za ta iya ci ko da loma daya za ta yi masa. Dr. Zainab ma na kokari a kanta matuka, ta taimaka aman ya tsaya, amma kullum cikin tashin zuciya ta ke, don haka Fanna ta samo mata goro tana taunawa. Ta rame ta yi duhu, da ganinta za ka san a satin nan ta yi jinya ta sosai. Tana kwance a dakinta suna labari da Zarah Fulani ta shigo ta same su. Ta ce, Saade su Yareema sun dawo fa, an sallamo Ya Gumsu, don haka ki daure, ki kwarara jikinki yanzun nan ki je ki duba ta, ko da kuwa ba za ta amsa ba. Saadatu ta fiddo ido cikin razana, Fulani ta lumshe mata ido tare da girgiza mata kai, ta ce, Do as I said, sai Fanna ta raka ki. A sanyaye ta mike ta soma daura laffaya a jikinta. Fanna ce ta yi mata jagora suka tafi unguwar Ya Gumsu. Wata kuyangarta ta shiga ta yi musu iso, sannan ta fito ta shiga da su har tankareren falon da Ya Gumsu ta ke kwance. Gabadaya yayanta maza da mata suna zaune a falon tun daga kan Yaa Maira har zuwa auta Ahmad. Yareema Sageer na zaune a gefen Ya Maira daga kan tattausan kilishi, ya mike santala-santalan kafafunsa da waya a hannunsa yana latsawa. Sanye yake da alkyabba ruwan zuma wadda ta sha aiki da zare ruwan gwal. Duk hirarrakin da suke yi ba ya sanya musu baki domin gabadaya hankalinsa yana ga son ganin Saadatu, da sabon matsayin da zai kalle ta da shi na mother of his children. Lokacin da wata baiwa ta shigo ta isar da sakon cewa ga matar Yarima nan za ta shigo duba Ya Gumsu ko kadan bai ji su ba. Text messages yake rubutawa yana aikawa wayar Saade mai dauke da alkawurruka na soyayya da kauna masu wuyar samuwa daga bakin mazan aure a wannan zamanin. Duk da ya san cewa ba ta tare da wayar tata ta baro ta Abuja. Kamar cikin mafarki, kamar daga sama ya tsinkayi sassanyar muryar Saaden na sallama a falon. Ya riga kowa dagowa a rikice, a mamakance, sannan excitedly yake dubanta. Da shi ta fara hada ido, ta yi saurin sunkuyar da kanta. Idanuwan yayye da kannen Yareema suka yi mata caaa wanda hakan ya sa kafafunta hardewa kamar za ta fadi. Kafin Fanna ta riko ta Yareema ya riga ta. Babu wanda ya ga sanda ya mike cikin zafin nama ya taro Saade, ya ruko ta har gaban Ya Gumsu, ya zaunar da ita daidai kafafunta yana fadin, Ya Gumsu ga Saadatu ta zo duba ki!. Kunya a wurin Saade kamar ta ce kasar ta tsage ta shige. Amma da yake dukkaninsu wayayyu ne ko a jikinsu, murmushin kauna suke mata dukkansu. Yaa Maira ta ce, Barta ta zo nan kusa da ni ta zauna Yarima, dawo nan gefe na Saadatu. Cikin jin nauyi ta zame daga hannun Yarima ta tsugunna har kasa ta ce, Ya Gumsu sannu da jiki, Allah ya kara afuwa. Ya Gumsu ta daga mata kai alamar ta amsa, sannan ta rike hannunta cikin nata. Tana ta motsin maganarta wanda da alama so ta ke ta bai wa Saade hakuri. Saade ta girgiza mata kai tana hawaye, Allah ya ba ki lafiya Ya Gumsu, da yardar Allah za ki fadi duk abin da ki ke son fada. Mun yi laifi a yafe mana. Sai kuka, Yaa Maira ta zo ta kamata ta tayar da ita daga gaban Ya Gumsu, ta ja ta suka zauna tare, ta ce, Ba ki mata laifin komai ba Saadatu kin ji, kuma ta yafe muku duniya da lahira, Allah ya yi muku albarka. Kowannensu da kalar kulawar da yake nuna mata a falon, duk suka yi mata sannu da jiki. Awaisu ya yi sallama ya shigo, ya duba Ya Gumsu da jiki sannan ya dubi Yareema da ke gefe kusa da Yaa Maira yana hagunta Saade na damanta (babbar Ya, UWA). Tana ta tsokanar su; Princess Saa Allah ya sa ki haifo min mai kama da ni ba mai irin hancin Yareema ba (pointed noise), kin san in hanci ya cika tsayi muni yake komawa. Ahmad ya ce, Kai Yaa Maira! A dinga yi ana tsoron Allah, ko makaho ya shafa ya san Yaya Yareema ya fi ki kyau nesa ba kusa ba. Awaisu ya katse hirar tasu da cewa, Yareema bakinka na Neitherland sun iso airport din Maiduguri, zan je in taho da su. Gidanka zan sauke su ko guest house din Maimartaba? Yareema ya harare shi, ya ce, Awaisu! Kana shiga lokacina fa, this is family time, ka je ka ji da customers dinka kai kadai. Duk inda ka ga ya dace, ka kai su. Family ba za su ji dadi ba sai da kudi. A nemi kudi a bai wa family Malam, ina zan sauke su? Gabadaya aka yi dariya ban da Yareema da Saade wadda ke satar kallon Yareema ta kasan idonta, tana mai alhinin muguwar ramar da ya yi cikin sati guda kacal. Duk da haka kyawunsa da kwarjininsa suna nan, sai ma abin da ya karu. Sai lokacin Awaisu ya lura da Saade a falon tana daga gefen Yaa Maira, ya ce, Aah! Madame, are you here? Dole idanun Yareema su rufe, ga masoyiya a kusa me zaa yi da kudi? Don Allah ki yi masa magana ya gaya min inda zan kai bakin turawanshi. Saade ta yi dan murmushi ba ta ce komai ba, sai ma kara kasa da ta yi da kanta, gabadaya ta takura domin duk motsin da ta yi sai ta ji kaifafan idanun Yareema a kanta. Maganar Turawa da Awaisu ya yi ita ta sa Yaa Maira tunawa da Aisha-Sultana. Da sauri ta ce, Yareema, ina Sultana? Ban ganta ta zo duba Ya Gumsu a Abuja ba? Ai kuwa duk suka tattaro hankalinsu a kanshi, sai yanzu duk suka tuna ba su ganta din ba, including Saade ta dau ido ta dora masa, ita dai ta san sun yi tafiya tare, kuma ya dawo shi kadai bai kara yin zancenta ba. Yareema ya dubi Yayar sa Yaa Maira sannan sauran kannensa maza da mata, sannan matar sa Saadatu da aminin sa Awaisu, ya ce, Dukkanku ba bare a nan. Ba wanda zan boye wa sirrin gidana, muddin wanda ya dace ku ji ne. Aisha-Sultana (Rose) mun rabu. Na maida ita kasarsu. Gabadaya suka sa salati domin babban zunubi ne saki a masarautar, tun daga iyaye da kakanni. A kan wane dalili? Askirama ya sani? In ji Yaa Maira. Yareema ya yi ajiyar zuciya, calmly ya shiga ba su labarin halin da yake ciki da Sultana tun komawarsu Abuja da ta sarki shan giya ta kuma cire mahaifa ba da izininsa ba. Ya ce, Na yi ta hakuri ne da shan giyarta saboda nobody is perfect. Dukkanmu masu sabo ne in one way or the other. Sabida ni ma kaina din Im not perfect either. Amma sallah fa? Ba zan iya jure rayuwar aure da wadda ba ta sallah ba, sabida yayana da lahira ta. Ya ci gaba da gaya musu yadda Askirama da kansa ya zo har gidansu ya same ta drunkard, ya ce, bai ce in sake ta ba, amma bacin ran da na gani cikin idanunsa da gaisuwata da ya daina amsawa ya sa na ga duk son da nake mata gara in hakura da ita. (Ya boye musu abu guda daya, cewa ba zai iya adalci tsakanin kowacce mace da Saadatu ba, don ya sirranta soyayyar da yake wa matarsa ga yan uwansa, wanda hakan shi ya kamata ga duk namijin da ya san ciwon kansa). Yaa Maira ta fahimce shi, amma sai ta ce, Wani hanzari ba gudu ba, Sultana ba ta ce ta yi RIDDA ba, sakin da ka yi mata saboda shan giyarta zai sa ta kullaci musulmi, ta ga cewa, tukuicin soyayyarta gare ka kenan, ta baro kowa nata da addininta ta biyo ka a karshe ga abin da ka saka mata da shi. Ban sake ta saboda giya kadai ba. Na gaya miki ta karbi musulunci, amma ba ta sallah, mene ne marabarta da addininta na baya? Addinin ma da babu shi sam domin kuwa ba kirista ba ce, bayahudiyya ce (Jew). To cut it short, na yi nadamar aurenta tun farko, ban taba zaton Alanguburo zai amince ba, amma tashi guda ina fada bai turza ba, sai ya amince. Had I know akwai Saade, kamar yadda ya ce tun farko ita ya so na aura ba zan taba yin wani aure ba. Saade ba ta san lokacin da ta mike ta yi kofar fita ba, inda ta baro Fanna, kunya kamar ta yi ya ya. Tana ji Yaa Maira na fadin, Ka kore ta ka ji dadi. Saadatu dawo kin ji, yanzu zan sa Awaisu ya tattara shi su tai su ba mu wuri. Ina! Saade ta kai kofa. Cewa ta ke, Yaa Maira zan dawo ne, idan na kara jin sauki. Yareema ya daga murya yadda za ta jiyo shi ya ce, In zo zance anjima bayan isha? Ai saade kadan ya rage ta zura da gudu, suka dinga yi mata dariya. Tana komawa unguwar su ta tadda Fulani ta dafa mata lafiyayyen faten acca da ya ji ganyen alayyahu da kabewa, ta zuba a faranti tana firfitawa da kanta tana jiran shigowarsu. Tana shigowa ta nufe ta da sauri. Allah Sarki UWA! Saade ta fada a ranta, ta karbi cokali tana shan faten Fulani na tambayarta jikin Ya Gumsu, ta ce, ita ma tana jira Askirama ya shigo gida ne su shiga tare su dubo ta. Saade ta tambayi Fulani, Ya ya aka kare ne da zancen auren Hanne? Ta ce, An kai zancen kotun musulunci an yi mata gaiba, mun rabu a kan cikin watannin in ta gama iddah za ta dawo nan gabana, yaron a kai wa iyayen mijin. Plan dina akan ta shi ne a kai ta El-Kanemi, ta samu kwalin kammala sakandire sai a sama mata UNIMAID. Ta zauna hostel in sun yi hutu ta zo nan wajena ta yi hutun, har Allah ya ba ta mijin aure. Saade ta gode wa Fulani, godiya maras adadi, tsarin da ta yi a kan rayuwar Hanne ya yi mata. Ta ce, Su Raheema ko waya? Ta ce, Kusan kullum muna magana da Maman, Raheema ta koma makaranta (university of Heartfordshire) wannan watan za ta kammala daga nan ku sha biki. Zan tambayi Maman lambarta na UK tunda yanzu akwai waya a hannunki. Ta kyabe baki ta ce, Ni da na ji zafin maruka ina na tuna da wata waya? (Tana nufin marin da su Ya Gumsu suka yi mata). Fulani ta ce, Mari? Nan ta gaya mata duk yadda aka yi, amma ba ta manta rokon da Yareema ya yi mata ba na ta boye zancen Dr. Ziyad ga iyayen su, it will create a serious problem idan suka ji, tunda dai mun bar NTNU din gabadaya shi ke nan. In ji yareema Sageer. Sai dai tana tantama idan hukuncin da Yareema ya yanke musu is geniune, da gaske Abuja ta fice mata a ka, shi ma kuma Yareema haka, Dr. Ziyad yayi shattering zuciyar sa into pieces ya karya masa zuciya, ita kuma ya jefa tsoron rayuwar Abuja mai tsanani a tata zuciyar. To amma makomar karatunta ta ke hangowa, shekaru ukun da ta kwashe cikin wahala da fadi-tashi sun tashi a banza ke nan? Above all aka ce sabo turken wawa. Ta saba da NTNU. Babu wata jamia da za ta bi bayan Nigerian Turkish Nile University a wurinta. Fulani da ta ji duk abin da ya faru tsakanin Saade da su Ya Gumsu, sai ta jinjina kudirar Ubangiji. Ya Gumsu mai ja da ikon Allah dare daya yau gata ta zama sai dai a kwantar a tayar. Shin wannan bai ishi dan Adam ishara ba ya yarda cewa shi ba a bakin komai yake ba? Duk mulkinsa da izzarsa bai wuce talalar Ubangiji ba a duk lokacin da ya so? Bai isa ya sa, bai sa ya hana abinda Ubangiji ya hukunta ba? Matar nan ta jima tana cutar da ita, da harshenta, da bakin ta, da hannunta, da komai nata. Don ma dai kowa ya tabbatar cewa ba ta yin asiri ta tabbata da in akwai abin da ya fi shi sai ya Gumsu ta yi mata. Wannan sai Hibbani, shi ya sa ita din ba ta wasa da addua da tsayuwa gaban Sarki Allah a tsakiyar kowanne talatainin dare. Ta nisa ta dubi yarta Saade, ta ce, Saadatu marriage is not a bed of roses. Babu wani aure da ba shi da kalubale, ki sa a ranki Gumsu ita ce kalubalen aurenki, kuma ga yadda abubuwa ke tafiya na fahimci tsoron Allah ya kama ta. Ki cire ta a ran ki ki yi wa mijinki mai sonki biyayyah, komai za ta yi miki ta yi kadan ta raba wannan auren tunda har ga zuria a tsakani. So ni da Ya Gumsu yanzu mun zama JINI DAYA. Kun riga kun yi tiding wannan barakar da ke a tsakani. Ni kuma ko me ta yi mun a baya na yafe mata. Allah ni ma ya yafe mini, ina kuma rokonsa ya ba ta lafiya ta koma taka kafafunta a doron kasa. Kuma tunda kin warware ki soma shirin komawa dakinki tun kafin Yareema ya zubar da kawaici da kunyar da ke tsakanina da shi. Dazu ya roke ni Fanna ta raka ki dakinsa na gidan nan yana son gaisawa da babynsa tunda Askirama ya hana shi shigowa nan. Ni kuma bazan yi abunda in Askirama ya ji zai yi fushi da ni ba. Tunda har ya cire kunya ya fadi gaisawa da baby kin ga daga hakan wata rana abin da zai gaya min sai ya fi haka. Saade ta soma tirjiya, har da buga kafa na shagwababbun yaya, Ni wallahi ba yanzu zan koma ba, abin da jinyar Ya Gumsu suke yi? Ko na koma ba shi da lokacina. Fulani ta ce, Duk inda yake in dare ya yi ai zai dawo gidansa ne Saadatu. Dare mahutar bawa, don haka na gaya miki ki soma shiri, ba za ki kara kwana uku a sassan nan ba. Yau din nan zan bai ma Askirama baki, har ga Allah Yareema tausayi yake bani don ba shi da laifi. Saade har da hawayenta ita ba za ta koma yanzu ba sai Ya Gumsu ta warke. Warkewar da babu wanda ya san ranarta sai Allah? In ji Fulani cikin lallashi. Kamar yadda ta alkawarta da yake yau ita ke da Mai Askira, tare suka je suka duba Ya Gumsu. Da lokacin kwanciyarsu ya yi ta yi ta ba shi hakuri kan ya sassauta wa Yareema, cikin alamarin nan ba ta ga laifinsa ba, tunda shi bai ma san Ya Gumsu za ta je Abuja ba, kuma sanda ta je din Saadatu ta tabbatar mata shi ba ya gidan, sannan abin da ya faru da Ya Gumsu kadai ishara ce babba, Allah ya nuna musu su dukkansu a daina jayayya, a bar wa Allah ikonsa. Zuciyar Maimartaba ta tausasa, shi ya sa yake son Bilkisu amma matansa sai su ce wai kyawunta ne. Me ake da kyau in ba hali? Ai ga Hibbani nan kyau har kyau, amma ban da gulma, tsugudidi da daukar zance ba ta iya komai ba. Ya ce ya yarda a je a gyara musu gidansu kafin su koma. Ya kuma kira Yareema don ya ji yaushe za su koma Abuja. Yareema bai boye ba, ya ce da Askirama ya ajiye aikinsa da NTNU, wani zai nema. Cikin mamaki Mai Askira ya ce, A kan me? Yareema ya runtse ido, tuno cewa Ziyad ya ga tsiraicin Saade kadai yana kona zuciyarsa yana tafasa ta ba dan kadan ba. Ya ce, Allah ya kara maka yawan rai a taya mu addua Allah ya sa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu bakidaya. Zan yi mata transfer zuwa babban reshen jamiar tasu da ke Ankara (capital of Turkey) ta karasa shekara biyunta. Ni ma zan yi wasuprojects (applied research) da jamiar na tsawon shekara daya. In mun gama sai mu dawo Askira da zama gabadaya, bazan kumazama a garin da ba Askira ba, ina so in bude jamia tawa ta kaina (private university) tunda ni da ita duka fanni daya muke karanta sai mu hadu mu tafiyar da jamiar. Kafin in samu lasisin budewar (licence) shi ne abu mai wahala,domin a nan Askira nake so in bude jamiar ba a maraya ba. Askirama mutum ne mai ilmi kuma wayayye, sosai ya fahimce shi, yana alfahari da haihuwarsa a kullum. Da daya ne tamkar da goma wanda yake barranta kansa da sarauta when it comes to neman ilmi, duk ya fi yan uwansa maza talent da jajircewa a kan harkar ilmi. Ya yi addua ya sa musu albarka, ya ce, gobe insha Allah za su je Abuja su mika neman visa da neman tranfer din shi da Saade, in sun gama komai zuwa sati daya za su tashi zuwa Turkiya daga Abuja ba za su dawo Askira ba sai bayan shekara daya. Askirama ya ce bai yarda ba, idan watan haihuwa ya kama wa zai kula da ita? Yareema ya yi alkawarin zai kula da Saadatu kamar yadda zai kula da kansa. In watan haihuwar ya kama zai daukar mata Fanna, in kuma ta kammala karatun kafin nan tunda semester biyu ne kawai zai dawo da ita ta haihu a gabansu. All he need is to be isolated shi da Saadatunsa. Shi kadai ya san irin ragaitar da ya shiga a wadannan kwanakin da suka yi nesa da juna. Ba ya son hayaniyar gidan Sarauta ko kadan. Da kyar Maimartaba ya amince da wannan tsarin na Yareema, amma yana adduar ta gama karatun kafin watan haihuwar ta ya tsaya ta zo ta haihu a gaban su. Yana da jikoki kusan guda 20 amma na Yarima isspecial domin babu kamar sa cikin duka jikokin da zai haifa ko ya haifa a baya. Yana masa adduarsamun nasara akan duk abinda ya sa gaba kuma ya gama rubuce-rubucen da zai je ya yi na tsawon shekara guda a ANKARA UNIVERSITY wanda zai bashi damar hawa Professorial Chair. ***** Kin faya nawa, kin faya yanga Saade, don kin ga Askirama na biye miki, shin sau nawa zan aiko Fanna ta gaya miki Yareema na cikin mota tun dazu yana jiran ki zaku wuce ne? Duk wani shiri da za ki yi meyasa tun jiya baki yi shi ba? Saade ta cuno baki hadi da marairaice murya Fulani gashi na fa nake gyarawa kawai, ya ce baya son ganin sa a cukurkude, nikuma bana so kowa ya taba min kai, shine nake tajewa da kaina. Fulani ta karbi katon matajin dake hannun ta tace bari ni in taje miki, in ba haka ba zaki yi awa guda kina abu daya. Ta taje mata, ta tufke mata shi da murtukekiyar kalbaa tsakiyar ka. Ta kawo katon hair-bound kalar kayan jikin ta wato sky-blue ta zagaye mata shi. Fuskar Saade ta fito tsam, tayi cute da ita. Fulani ta taimaka mata ta nannada laffayar. Sannan suka fito. Ko kusa bata gaya mata kasar zasu bari ba don ta san halin shagwabar Saade da rigimar ta, cewa zata yi bazata iya shekara babu Fulani ba. Sun bata lokaci suna sallama, kamar kada su rabu,finally suka rabun. Saade na kwallah Zarah na kukan sai ta bi ta, da kyar Fulani ta rarrasheta da cewa asibiti zata je ta dawo, kafin Fanna ta raka ta wajen Ya Gumsu. An jinginar ta jikin pillow bakin da ya karkace ya sha gashi ya koma daidai. Amma har yanzu bata motsa daya hannun yadda ya kamata amma kana iya gane abinda take cewa. Sauki dai yana ta samuwa cikin yardar Ubangiji da kulawar yayan ta. Idan Allah ya baka yaya masu jin kan ka ya baka komai na duniya. Kishiyoyin ta ma baa bar su a baya ba wajen nuna kulawar su akan iftilain da ya same ta. Ya Gumsu na ganin shigowar su ita da Fanna ta mika mata hannun ta mai lafiya, da sauri Saade ta karasa ta zube gaban Ya Gumsu. Hannu ya Gumsu ta dora a kanta tana shi mata albarka tare da cewa cikin harshen barbarci. Wa gafurne kla awodune nyiro dikkuna samma so ro, Nadimtikna.(Ki yafe min na yi nadama a akan duka abinda na aikata, na yi nadama). Saade tace baki yimin komai ba sai alkhairi Ya Gumsu, Allah ya baki lafiya. Ta mika hannun ta mai lafiya kasan filon ta ta dauko warwaron zinare guda uku ta zura a hannun Saadatu. Saade ta rike hannun Ya Gumsu tana godiya. Daga nan Fanna ta rakata unguwar Yaa Kirjiloma da unguwar Yaa Hibbani duk tayi musu sallama, kowacce da dan abin arzikin ta na sallama don tun faduwar Ya Gumsu jikin kowacce yayi lakwas, musamman Hibbani ta rage daukan zancen kowa ta kaiwa Askirama. Impatientlykuma admiringlyYareema Sageer ya dubi Saadeda hanzari, lokacin da aka bude mata motar da yake ciki mai duhun glassai ta yadda baka iya hango wanda ke ciki. Zaquwar son ganin ta na tsayin wannan lokacin da ya dauka ba tare da ita ba yasa ya hadiye fushin sa na jiran data bar shi yana yi a mota. Data shigo ma aka rufe kofar motar jikin kofa ta koma ta makure ta juya masa keya. Da ta san yadda zuciyar sa ke racing a cikin kirjin sa sabida excitement din ganin ta finally by his side da bata juya masa keyarnan ba. Yarima ya girgiza kai yace ki yi lokacin ki ne Maman Chiroma, ko ba haka Askirama yace sunan Baby ba? Ba ta san ya san da wannan maganar ba don haka ba shiri ta sunne kanta cikin cinyoyintadireba na barin kofar masarautar sai taji sanyin hannun Yarima a gadon bayanta a janyo ta sosai barin jikin sa sannan hannun sa ya kurda kasan marar ta yana shafawa cikin a hankali, ya sunkuyo daidai saitin cikin nata yace. Stay blessed Chiroma. A ranta tace shin in kuma ya mace ta haifa fa? Yarima da Baban sa zasu yi farin ciki? Yadda Mai askira da Yarima suke ta ambaton haihuwar da namiji? Zata so ta yi wa Yarima wannan tambayar, amma jin nauyi bazai bar ta ba. Kamar ta yi azarbabi in tayi maganar nan tun yanzu amma curiousity na cewa ta daure ta tambayi Yarima tun yanzu. A dan zamanta gidan sarautar ta fahimci burin kowacce mace a gidan shine ta haifi da namiji har murna suke da Fulani Bilkisu ta haifi Zarah. Kuma a karan kanta gani take Askirama bai damu da Zarah ba kamar sauran yayan sa. Bata ji yana fadin a kawo ta fada ba. A ganin taHaihuwar dai ta janyewa Fulani Bilkisu gorin rashin haihuwa ne kawai a gidan amma da ita da babu sammakal. Direba ya ja mota suka dauki hanyar Abuja. Inda zasu yi visa su tashi zuwa Ankara. Basu tsaya ba sai lokacin sallahr Azahar a gidan mai. A motar ma Yarima bai bar ta sakat ba da nauikan soyayyar sa mai tsayawa a zuci wato (sumba). Ta amince shi din expert ne a wannan fannin, ta yarda yayi missing din ta fiye da yadda zai iya bayyanawa, ta ga hakan cikin emotions dinsa da rawar da jikin sa ke yi a kan ta, tun da shi mai karancin magana ne sai dai actions da shaukin dake cikin zuciyar sa su fadi halin da yake ciki. Sai dare suka shiga Abuja, kuma ba gidan su suka nufa ba kai tsaye hotel din (Fraser Suites)Yarima ya baiwa direban umarnin shiga. Tuni ya sa an kwashe komai na su daga gidan malamai na NTNU dama gidan mallakar jamiar ne. Suna shiga dakin da suka kama Yarima ya maida kofar ya yi azamar rungume Saadeverytightly, this seems like eternity! Ya Allah! Na roke ka, kada ka hora laifuka na ta hanyar nesanta ni da abinda na fi son kasancewa da shi a rayuwata. I missed you Saadatu!. Ta kara narkewa a jikin Yarima sai yanzu ta san itama tayi kewar wannan kulawar ta Yareema Sageer, zaman ta tare da jamaa ne yasa bata gane hakan ba, ajiyar zuciya take saukewa a jejjere, tace Prince, ina cikin damuwa, an ce ina da ciki, kuma na ji kuna ta kiran sa Chiroma tun ban haifa an ga me na haifa ba.. Ina cikin damuwar idan mace kuma na haifa fa? Wata zaka auro ta haifa maka namiji? Ko kuwa ita din bazaka so ta ba tunda bazata yi sarauta ba? Yadda ta karasa maganar cikin karaya sai da ta sanya Yarima Sageer dariya. Ya dago fuskarta bisa tafukan sa. Ya ce Saadatu in kin so ki jero min dozen na yaya mata, ki gani in zan so su ko ba zan so su ba, ki gani in zan kara auren wata matar don ta haifo min namiji. Namiji baya alkawari akan aure musamman Basarake wanda ya gaji aure-aure amma ni Sageer! A yau ina mai tabbatar miki da cewa idan harba kaddara ce ta bi raayin kan ta ta aura min wata ba, na gama aure a rayuwa ta. Abin da baki sa ni ba niSageer shaanin sarauta ba ya gaba na, Maimartaba na so in haifi namiji ne don ya tabbatar ba zan yarda in karbi sarauta ba. Amma ba don in kin haifi mace ba zamu so ta ba, ko hakan ne zai sa a kara yi min aure. Mun dade da gane illar hakan cikin gidan mu wato fifita haihuwar maza akan ta mata don haka in kina tunanin hakan, to ki dai na. Ajiyar zuciya Saade ta yi, a kalla yanzu ta samu peace of mind don ta san Yarima ba ya fadin abinda ba haka yake a zuciyar shi ba. Daga nanwanka su kayi kasancewar sun yi duka sallolin su a hanya. Suna idarwa ya yi musu odar abinci mai rai da motsi, amma kallo daya Saade ta yi wa abincin tace bazata ci ba, dan wake take so mai manja da yaji. Dan wake Saadatu? Yarima ya fada cikin damuwa. To yanzu ina zamu nemo shi a daren nan? Ta yarfarda kai ta ce mu je mu zazzzaga na san bazaa rasa mai dan wake ba. A take Yarima ya mike ya dau mukullin mota, Bukari ya kwanta yanzu (direban da ya kawo su) mu je mu nema. Ko dama so take ta fita din ta shaki freshair, ta gan ta Yariman Askira na tuka ta a mota da kan sa, wannan priviliged yana sanyata nishadi, shiyasa ta kakalo dan wake, in tace haka kawai su fita cewa zai yi ya gaji kuma dare yayi, yanzu kuwa ko don dan sa ya samu abinda yake son ci ta san ba shi da zabi banda su fita din. Shiga wannan titi fita wancan suna tafe suna hira har ya samo mata danwaken a wani karamin eatry. Basu dawo ba sai 11 na dare, tun daga bakin kofa Saade ta soma tausayin kanta, domin Yarima bai yi duka wannan wahalar neman danwaken ba sai da ya fanshe ta. A hakan ma yana tausayin ta sabida cikin jikin ta amma ta biya duka basussukan sa da ta ci tun kafin barin ta Abuja zuwa yau da kyakkyawan reward. Washegari suka nufi Turkish Embassy suka shigar da neman visa. A kwanaki bakwai da suka yi suna jiran fitowar visar su ta tafiya Ankara sai suka zama kamar renakun honeymoon cikin hotel din Fraser Suites. Abin ki da mace mai yaron ciki, komai na jikin ta ya canza, don haka mannewar da Yarima yake mata har tsoro yake bata tamkar bai taba aure ko kusantar mata a rayuwar sa ba. Auren sunnah daban yake, kuma macen alfarma daban Allah ke halittawa mijin ta ita. Shikansa ji yake kuruciyar sa na karuwa, lafiya da kuzari na kara shigar shi. Auren kananan yara ga maiyawan shekaru yana da wannan advantage din. Yayi amfani da zaman hotel din ya nema mata transfer ta yanar gizo daga NTNU zuwa ANKARA UNIVERSITY. A ranar da visar su ta fito transferdin Saade ma ya samu. Washegari suka bi Turkish Airlines zuwa kasar Turkiya. Duk wasu memories na zaman ta a kauyen Tsanyawa tare da Baban ta, zuwan ta Askira wajen mahaifiyar ta, zuwa Abuja zaman gidan Dr. Sageer da yayi sanadin auren ta da Yarima Sageer din,ta kasa manta ko daya. Ta yi musu kundi (littafi na musamman). Wato shi bawa tun haihuwar sa an rubuta masa dukkan kaddarorin sa. A hankali zaici karo da kowanne.Ta debo duka memories dinta taho dasu Ankara cikin kundin adana tarihin ta. Kuma bata san shirin Yarima ba sai bayan saukar su a babbanfilin jirgin saman birnin Istanbul wato HavalimanıİşletmesiA.Ş. Istanbul Airport.Cewa ita da gida sai ta gama karatun digirin ta, ko ta haihu ko kafin ta haihu. Zai aika a dauko mata Fanna. A lokacin da Yarima ya gaya mata hakan a filin jirgin ne suna tafiya zuwa terminal, hannayen su sarke cikin na juna. To ko taji damuwa ba kamar yadda ya zata ba, sabida a halin yanzu shakuwar da suka kara yi a dan tsukin ta zarce ta baya, a dan takaitaccenzaman su na kwanaki bakwai a Hotel dinFraser Suites, a halin yanzu tafi son kasancewa da shi har fiye da kowa a rayuwar ta. Daga Istanbul suka bi jirgin kasa (Turkish Railways) daga Halkali wanda zai kai su zuwa Ankara (capital of Turkey). ****** ANKARA Basu bar Ankara ba sai da Saade ta shiga watan haihuwar ta bayan bikin yaye su (convocation) na kammala digiri akan (Pure&Applied Chemistry) inda Saadatu Hashim Askira ta fiddo kwalin ta mai daraja ta farko. In aka duba kuma da idon basira duka nasarar karatun Saade sai ace hobbasar Yarima Sageer ne, miji mai cin tudu ukku a rayuwar Saade; malami kuma masoyi, ta wani fannin Yayan da bata da shi, kuma wanda babu kamar sa a rayuwar ta. Alkawarin da ya daukar wa Mai Askira ya cika shi, ya rike Saade da dukkan amana, ya rike ta da dukkan kauna da soyayya haka ya zama mijin marainiya. Ya gama appliedresearches din da ya je yi, yayi nasarar rubuta littafai muhimmai akan fannin sa. Wadanda suka bashi damar zama Farfesa, domin bayan dawowar su Askira da dan lokaci kalilan ya kama aiki da jamiar Maiduguri (UNIMAID) wannan ne dalilin komawar rayuwar su garin su Askira bakidaya, ko ya je Maiduguri baya wuce kwanaki biyu ko uku zai shigo Askira. Har gobe yana nan akan burin sa na kafa privateuniversity a garin Askira kuma yana cigaba da fafatukar hakan. Saade da ta tashi haihuwa sai ga kyautar Allah ta yaya mata har guda biyu. Wadanda suka ci sunan Ya Gumsu da Fulani Bilkisu. Soyayya ta karshe yan biyu (amaren Askirama) yadda ake kiran su cikin gidan sun gan ta wajen Mai Askira. Dr. Sagir kuwamaida Sahlah da Suhailah ciki ne kawai ba ya yi sabida soyayya. Ya Gumsu ta dade da samun lafiya kuma tuni ta kama girman ta ta kuma daina adawa da Fulani Bilkisu. Ta yarda da duk abinda Askirama ke fada a kan ta. Sun hada kai sun samarwa Mai Askira madauwamin kwanciyar hankali a shekarun tsufan sa. Yayin da Sahlah da Suhailah suka zamo masu debe masa kewa don kullum sai ya fita da su fada ya ajiye a hagu da daman sasuna kiriniyar su yana gudanar da alamuran mulkin sa. Ko kusa babu wanda ya yi mummunan furuci akan haihuwar yaya mata da Saade tayi a masarautar bakidaya, sabida yara ne masu shiga rai, da ko baka yi niyyar daukar su ba sai sun ja hankalin ka ka dauke su. Jinin BAGGARA ne dana BABARBARE ya hadu ya bada wadannan twins masu tsananin kyau da shiga zuci. In har ba UNIMAID zai tafi ba zaka same shi tare da yan biyun sa a cinyar sa ko a gefen sa ko a hannun sa. Prof. Sageer Yusuf Askira. ****** MURFI Nakuda take tamkar bazata tashi ba, nakuda ce da ko haihuwar yan biyu bata yi mai zafin ta ba. Ta riga ta fidda rai da rayuwa, tana kwance ne a cinyoyin Yarima Sageer ta hada gumi kashirban, gashin kanta ya watsu bisa jikin sa. Idan na taba cutar da kai a tsayin zaman mu ka yafe min Baban Suhailah, ta fanni na baka yi min komai ba sai alheri da soyayya Yaya Yareema. Idan na mutu,kada ka kara aure zan yi ta jiran ka aljannah har ka iso, ka ji? Ka cewa Fulani ta yafe min its not easy being a mother! Na kara daraja ta fiye da baya, na kara son ta fiye da wanda nake mata, na kara ganin kimar ta da martabar ta.. na so in yi tsawon rai in biya mata Hajji Allah bai yi ba.. Sai ga wani uban nishi ya biyo baya, Sageer ya dauka tafiyar kenan! Sabida haka numfashin sa ya soma kokarin barin kirjin saamma sai me? Kafin ya bude ido sai ya ji nurse Aisha na cewa cikin farin ciki. HERE COMES OUR PRINCE! Sai kuma baby data taro ya callara kuka wanda ba kwanyar Yarima kadai ya shiga ba har da ta unconscious Saade, kuma kukan ne ya maido ta a hayyacin ta. Nurse Aisha ta nade jaririn a tawul bayan ta goge masa jiki daman zaitun (olive oil) ta zo ta dora shi a ruwan cikin Saade wadda ke kwance kane-kane a jikin Yarima tana mai kallon komai kamar cikin mafarki. Yau itace da haihuwar namijin finally. Bayan ta fidda rai, domin kuwa bayan Twins sai da ta kara wasu setin twins din again duka mata, wadanda suka ci suna Rahimah da Hannatu. Sai yau haihuwa ta uku taji ana kiran Prince. A hankali ta lumshe idon ta da wahala tasa duk suka zurma ciki suka kankance, ta bude su akan kaykkyawan Babyn ta wanda bata ga fuskar kowa a kan fuskar sa ba sai Ahmad autan su Yarima, wato dai daYa Gumsu yake kama. Hakika La taqnadou min rahmatullah. Allah yana jinkirta maka abunda kake so zuwa lokacin da ya ga yafidacewa ya baka, abin so shine ka kasance cikin yin tagociya a adduaarka, wato idan kaza alkhairi ne a gare ni Allah ka bani, idan ba alkhairi bane Allah ka musanya min da mafi alkhairin sa. Not Allah ka bani kaza anyhow. Yarimah ya dauki babyn yana kallowith affection sannan ya lakuce masa hanci. kai Chiroma shine ka wahalar min da mata ko? Kasa har ta fara bada wasiyyar hana ni aure idan ta zarce? Daidai lokacin da Askirama da Fulani da Ya Gumsu suka shigo fuskar su fal fara don tuni albishir din isowar Chiroma ya je musu. Nan nurse Aisha take basu labarin wasiyyar Saade ga Fulani da Yareema. Suka ce me zasu yi ba dariya ba. Fulani ta ce yanzu ma bata baci ba a bani kujerar makkah na in je in yi azumi acan ni da takwarata, ban daukar takwarar Ya Gumsu tunda bata zuwa kwana waje na. Askirama yace to kai an ce kada ka kara aure ka jira sai an hade a aljannah, nikuwa da har na shirya maka kwarkwarori uku tunda Saadatu jego zata fara. Yaa Gumsu tace lala-lala Askirama in wasa nea bari, kaima ka haramtawa kan ka naka, a na me shi zaa takura shi a kai Alanguburo? Cewa yayi bai iya jiran matar sa ta gama biki? Kunya ta lullube Saade amma ta ji dadin yadda Ya Gumsu ta dage ta hana a baiwa Yarima concubones, ta san da watakila shikenan ta bar shakar numfashi daidai a duniyar subhanah.yammata hudu rus! Ga Yarima Sageer? Ai karshen ta a barrow zaa kwasheta zuwa asibitin masu dan karamin tabin hankali. Shima Askirama jin baki ne irin nasa, don ya san ba abinda Yarima ya ki jini irin ace ya kara aure. Da an fadi hakan zai jawo ayar Allah ya ce sai zaku iya adalci, shikuma bai iya adalcin tsakanin Saadatu da wata diya mace, da muguwar rawa gwamma kin tashi. Shiyasa Askirama yake so ya dauki kwarkwarori duk adadin da yake so, amma wani zubin har zuciyar sa yana ganin Yarima ya hada da concubines zai kara fiddo da kimar sarautar sa. A yanzu dai Yareema Sageer ya ce baya da bukata bai sani ba dai ko can gaba in ya fara tsufa. Baby ya ci sunan Askirama YUSUF. Ana kiran sa Chiroma. Tsakanin Mai Askira daYa Gumsu ban san wa ya fi son jikokin nan ba. Ya Gumsu kullum ta dubi yaran sai ta kara nadama ta yi dana sanin ja da hukuncin Ubangiji, lalle ne ko rabon wadannan yaya biyar ya isa ya kayar da ita kwanan ta bai kare ba. A halin yanzu ta fi kowa alfahari da auren Yarima da Saade ta kuma yardada abinda Askirama ke fadi cewa Saadatu diyar Bilkisu,rufin asiri ce, suttura ce ga dan su Yareema Sageer Yusuf Askira. Masha Allahu laquwwata illa billah. Nan na kawo karshen littafin MASARAUTARMU 3&4. Kurakuran dake ciki ku tayani rokon Allah ya yafe mini. Abin alfanun da ke ciki Allah ya hada mu a ladan nida ku bakidaya. Sumayyah Abdulkadir 18/11|2021. Ina mukualbishirda sabonlittafinamaisuna NA HUCE!Wanda zaizo a matsayingoronsabuwarshekarainsha Allah. TUNA SUNAN SA; NAHUCHE (DagaFushina) NA HUCE.. LITTAFIN SUMAYYAH ABDULKADIR Hawayen da yake ta rikewa ne suka kwace masa, ya juya kadan ya dubi Rahinah wadda ke kallon bayansa a lokacin, suka kuma hada ido, ji ta yi zuciyar ta na son karyewa (rauni irin na diya mace na son mamayar ta) amma ta amince wannan shine decision mai kyau ga rayuwar ta. Sai ta maida idanunta ta lumshe su a hankali. Tana sauke ajiyar zuciya. Shi kuma ya sa kai ya fita daga dakin, babu ko waiwaye. Kamar yadda yake ji a ransa ba zai kara waiwayar RAHINAH OMAR a rayuwarsa ba. Ko da bayan cikar burin ta, na zama cikakkar otorhinolaryngologist. **** Ta dauki hoton karamin kyakkyawan yaron mai kama da ubansa a komai tana kallo with so much adoration, hawaye na sauka a kan fararen kundukukin ta. Ta san yanzu ya girma, watakila aji hudu na firamare? Cikin kowanne hali dai ta san zai kula da shi. Damuwar ta ba a kan kulawar da yaron zai samu ba ne domin hakika tana da tabbacin HABIBUNAHUCHEzai kula da dansa har fiye da yadda yake kula da Hotels din sa. Damuwar ta akan yadda har gobe ta kasa kallon kowanne namiji da idanun sigaraure, kowa ya zo sai ta ga bai kai shi ba, ko farcen kafarsa bai kama ba, ko da kuwaya fi shi komai na rayuwa. Duk da cewa ta san shi ne kawai a matsayin dalibin jami'ar Cologne ba'a matsayinsa na yanzun ba (mamallakin NAHUCHE HOTELS) amma tana bibiye da duk wani fadi-tashinsa na rayuwa tun daga ranar da ya raba ta da Dan su. Dalilin bibiyar ne ba ta sani ba har yau, tunda ita ta ce bata son sa. Farin jini kam har bata san irin nata ba, manema ba irin wadanda Allah bai ba ta ba, kuma burin Dada shine ta yi aure tun kafin Allah ya dau ranta, amma har gobe ta kasa kallon kan sauran maza daga shi sai dan mutanen NAHUCHE. The one that took away her pride na diya mace. Wanda ta tabbatar zuwa yanzu ya manta da ita, a irin shuhurar da Allah ya yi masa cikin shekaru goma kacal da rabuwarsu. Bata san hawaye take ba. Sai da ta ji dandanon gishiri a bakin ta. Hawayen da ta tabbatar ba za ta daina zubar da su ba har zuwa karshen rayuwarta. Idan har rayuwa ba ta koma yadda take a baya ba; with him aside. "Auren Wucin Gadi". "Auren kwanaki bakwai kacal". Wadanda abubuwan da suka wakana cikinsu sun fi tsayin na shekaru bakwai. Wanda ya samar da kaddarar Dan da ke a tsakani, Dan da silar zuwansa duniya ne ya yi connecting komai, ya hada zukata ya kuma raba su cikin kwanaki bakwai. Jami'ar Cologne din Jamus ita ce tushe, mafari, ginshiki na dukkan walagigin rayuwar da ta samu kanta. -Takori