*GIDAN MAGAJI YA* Oumyasmeen *BOOK 2* _Allah isa yadda na fara lafiya Allah isa na gama lafiya ina godiya masoyana bazan iya biyan ku ba har abada_ Episode 21-22 Da tasan wannan rana zata zo da ta yanke alakar'ta da ko wanne ɗan iska sai yanzu ta gane gaskiyar maganar da kahu yake faɗa mata kullum ki dena tara ya'yan Allah ya shirya mana ina jiye miki ranar da za su dauko miki abin da baki zata ba su goga miki kashin kaji daga kanta sama tayi ba abin da take iya gani saboda duhu lumshe idanuwanta tayi miƙewa tayi ta zauna amma ina ba damar haka ala dole ta koma ta kwanta iya tsinuwa Asif ya shata ba iyaka daman ita ta dade da sanin duk wani me aikin force bashi da imani.....ko dan uwanta ne ai ta rabu dashi abin tsorone *🤔tab* Gurin dinana kuwa da sauke dakin da aka sa shi cel ne yana da fadi kuma shi da rabi aka sa shi sunyi haka ne ko za su ƙara jin wani abu sosai dinana ke kuka yace "Rabi kin ga irin kaddarar da kaska ya samu ko...?, Rabi'u dai wanne irin rabi da sauri dinana ya ɗago tun da aka shigo da shi be shi yayi magana ba da badaki ɗaya aka sa su ba dariya ce ta kubce mai duk kuwa da halin da yake ciki kan rabi da yaci jal ya koma yadda yake bakin nan ko jambaki babu idonsa yayi ziri ziri me zai yi in banda dariya yace "wayyo Allah huya ta sauka ki rabi kin ga kuwa yadda kika koma sai hawaye ya zobo mai ya share ya ci gaba da cewa zan so ace wannan abin tare muke gabaki ɗayan mu muyi faɗa muyi wasa Allah sarki kahu ko za mu ƙara ganawa ko rabuwar kenan Allah ka duba mu ka fitar da mu Allah kasani abin da ake tuhumar mu da shi bamu aikata ba Allah wannan wata jarabawa ce da muna da rauni Allah ka bamu ikon cinye ta kai rabi ya jingina a jikin bango yace "Amin ko wanne hali magajiya take gwara mu an hada mu tare ita fa Allah ya tsinewa kaska...., Amin ya Allah daga nan sukai shiru duk hirar nan da suke Asif na ganin'su a cikin laptop ɗin'sa biron hannun'sa ya ajiye ya jingina da jikin kujerarsa wayarsa ce tayi ringing ganin me kiran ya ƙi da gawa har yanzu mamaki yake Aysha ce zata kashe mai waya saka yayi a meeting ya ajiye ta ya ci gaba da aikinsa... *Kano.....* yinin ranar haka kahu yayi shi ba dad'i kallon Sama'ila yayi da yake kuka yace "kai hakuri wallahi inhar sun yi bincike sun ga basa hannunsu kamar an sako sune su hukumar dss basa kama mutun ba tare da sunyi bincike ba in sun kama shi ma za su ƙara bincike nasan magajiya baza ta aikata haka ba kamar an yi an gama...., ci gaba yayi da kukansa domin daga ita sai kahu suka rage mai a duniya kahu baya haihuwa sau daya ya haihu a wannan fadan na boko haram a gabansa aka yanka ɗan da ya haifa me shekara goma sha biyar sa'an sama'ila wani zubin yana sane yake biyewa su dinana dan ya kawar da radadin zuciyar sa da damuwarsa kallon uwani yayi yace "kinga gobe bamu da abincin ci ke zaki fara sai da duk abin da magajiya ke yi kafin ta dawo dan murufawa kan mu a siri......ai kai kasan duk inda take karbo kaya ko....? Muci abinci mu ajiye mata sauran kuɗinta...., eh na sani Sama'ila ya basa amsa Ajiyar zuciya uwani ta sauke tace "To Allah ya kai mu yau da dare sai inyi...dan mu tashi da abin da za muci..., amin ya Allah sumayya ce ta shigo kallon gabas tayi ta shiƙe da dariya tace "kahu kaga ikon Allah ko aminai uku an tarkata su Allah ya sa ma su dawo ta faɗa tana jin wani dad'i aranta daman magajiya ta tokare mata a rai komai ita kowa ita ga uban ciniki da take...., kallon ta kahu yayi cike da mamaki saunawa magajiya ke ciyar da ita ko kamata akai ita ke zuwa bilinta dan adam kenan Allah ka rufa mana a Siri Ka bawa maƙiyan mu kunya wannan kadan daga cikin halin dan adam wani burin'sa yagan ka kullum a cikin huya yace "Hassada da me rabo take ce baka samin nasara ta cikin sauki kar kiyi mamakin wannan shine silar arzikin ta kar ki mamakin wannan abin shine silar daukakar ta da haka Ubangiji yake komai yana da sanadi....., Wani kallo tayi mai tace "Gyara bakin ka kahu gidan yari naje ba sau daya ba sau biyu ba Ni zan faɗa maka wani gidan yari Allah ya rufa maka asiri kar ta dawo da cikin shege domin wasu a cikin su ba mutanan kirki bane....., Bakin ki ya sari danyan kashi Allah ba zai jarabbe mu ta wannan fannin ba insha Allahu tana tare da Allah da mala'ikon'sa wallahi wannan abin kamar a kunnan'ta wata dariya tayi ta fita fitar ta ba dadewa su saudat suka shigo da dan a shararle sai manjagara kuka sosai suke haka suka hunarwa kahu bayan sallar la'asar suka bar gidan inda uwani tace musu za tayi abinci da waina suka ce sai sun dawo daman baka gane masoyin ka sai kaddara ta hauka *Allah Ka hadamu da masoyan mu na hakika* *NNDC quarters* Kabiru wallahi kashedi nayi maka kaga danka ASIF kai mai magana ya fito da matar aure dan kaf dangin mu ba juya ka tsaya ka zuba ido kai da shashashar matar ka.... ƙasa yayi da kansa yace "Insha Allahu zan masa magana..., goro ta ɓantara tace "karma kai masa na kusan zaɓo dalleliyar budurwa a cikin kannan'sa yarinya sharaf yadda waccen saunar zata ji haushi in aura mai badai ina da malam liman ba rana tsaka wallahi za kuji ana sanarwa danni har lefe na gama haɗawa..., da sauri ya kalleta gaskiya abin hajiyar tasu azimin ne yace "godiya muke Allah ya ja daranki...., banza tayi mai tana ci gaba da cin goron ta can ta dube'sa tace "zaman me kake kuma bayan mun gama magana....?, tashi yayi yace Allah hucu zuciyarsa ki na zata da wani abin ya sakai ya fita...., jidda ce ta shigo tare da inteesar suka zauna suna kallo ya akram ne ya shigo da ayman suna hira sallama sukai hajiya ta amsa bakin'ta a washe tace "a'a yan samari yau kune a gari...?, zama sukai ayman yace "eh wallahi Abuja tayi mana zafi haba aikin Company sai da hutu dan ma ogan namu be sani ba jibi za mu koma...., Innalillahi haka kuka baro mai dukiya kuka tawo ita waccan shashashar ta maƙale kafa ba iya kular mai da ita za tayi ba....to wallahi kamar akunnan sa danni ba'a munafurci dani wallahi Akram yace "Kasan halin hajiya faɗi ce ba a tambaye ta ba me isaka Kai Mata wannan zancen dazu na kirashi na faɗa mai ya fada yana kifta ido..., Karab a idon jidda sanin baya wasa da su bakamar ya ayman ba tayi shiru da bakin ta halin su daya da ya asif shima ba shi da kirki kai hajiya ta gyada yan masifar basa kusa tashi jidda tayi tace "Hajiya bacci zanyi..., wata harara hajiya ta watsa mai tace "zo ki kwanta akai na yau nake jin wani tsohon kinibibi da ba hucewa kike ki kwanta ba shine zaki wani ce bacci kike ji a'a suma kike yi huce ki tafi gidan ku yau bazaki kwanar min ba kibi ki daddanne ni.....salon ki karya min kashi...., kuka jidda ta kusan sawa ta killi hajiya ta zata huce dakin hajiya akram ya daka mata tsawa ya nuna mata hanya yace "zo ki huce me ta ce miki..., kamo jidda hajiya tayi tace "to me halin uban gidana ku dai sai addu'a da nake cewa zan baka jidda ashe wata ran kashi zan tarar.....tab da sake...., haɗa rai Akram yayi yace "Allah ya rufa a siri nii...hajiya karfa ki fara ai wannan salon raini ne...., Ubanka kai da rainin dan uwarka nawa ubanka ya auri uwarka nace ko da sauri ayman yace "haba hajiya da fa yara a gurin nan be dace ba...., Allah ya rufa a siri ta ja bakin'ta tayi shiru dakin shiru yayi a fakaice akram ke ƙarewa jidda kallo yarinyar bata da makusa inba Dan rainon hajiya bace sai addu'a kafin ya tafi chaina zai lallaɓa hajiya a tsaida magana ci gaba da kallo inteesar tayi ɗagowa tayi suka haɗa ido da ayman murmushi yayu mata yace "zo kiga wata sabuwar game da na ɗauko..., ba musu tazo haka jidda suka sa shi a tsakiya suna kallo tsawa akram ya dakawa jidda yace "Baccin ke nan gaskiyar hajiya da tace na kinibibi ne ke inteesar ku tashi kuje kuyi bacci gobe a kwai makaranta...., ba musu suka tashi jidda rannan a ɓace kamar za tayi kuka ta kusan fita tace "Ya Ayman Dan Allah gobe zaka bamu yi...., Eh zan baku to wayar fa yau she zaka siya mana sai babban yaya ya yarda tab kawai ka fito fili kace baza ka siya ba ko inteesar in ta babban yaya ne mu mutu bamu da waya tana faɗar haka ta fita Akram na'am hajiya Akram amsawa ya ƙarayi ta ƙara kiran sunan sa tace "Saunawa na kiraka..., Uku hajiya ya bata amsa tace "Wallahi kafita a sabgar jikokina in ba haka ba zan ɓatar maka..., To yace ya ci gaba da danna wayarsa haka ma ayman halin hajiya sai hakuri ba wanda ta kyale...... *Abuja osokoro* Cikin sauri yake haɗa komai da zai buƙata a gida ya saka a cikin brief case ɗin'sa ya zuge wayar'sa ce ta kawo haske dubawa yayi yaga wanda ya bawa receip ɗin nan ne yayi bincike ya ɗauka cikin girmamawa yake cemai I researched it and sent you a photo of the two people who touched him, and the numbers on his body are now not working ... ya ci gaba da cewa but no matter which number there is information about its location dad'i yaji ganin binciken bazai dau ki tsahon lokaci ba yace "I'll go home and check..., see you later ya kashe wayar'sa zura ta yayi a cikin aljihu ya dauki kyes dinsa ya fito har yanzu surayya na office din sai ya tafi zata tafi sai dai in jimawa zai yi yace ta tafi zaune take ita da wata da sauri nihila ta kama kanta tace "Barka da fitowa......, Kamar kullum ciki ciki ya amsa mu su ya fita daga tashi surayya tayi tace "kinga ko ai daman na faɗa miki wannan mutumin in ba malamai muka bi ba wallahi bazai san kina yi ba....., dafa kanta tayi tace "bazan ƙarar da kuɗina a banza ba kina tunanin irin mutanan nan wani abu nacin su wallahi ba a shiga dawa dan karya surayya zai fito ne be shirya ba mudai canza wata shawarar anya kuwa nima ba aikin nan zan sa daddy ya samamin ba wai ke surayya ya akai rana tsaka kika sami wannan damar.....?, dariya ta shiƙe da shi ta buɗe da jakarta dala ta fito da ita tayi ƙasa da murya tace "Ni yarinyar matemakin Asif ce nima da ban gane ba sai da na gane nayi mai magana ina so da kyar na samu wai baya son aiki da mace kinji fa karamin dan iska.....ai a duniyar nan kawata inhar zaki bada wannan to wallahi ba inda ba zaki ba abin da ya saka ma naga baki da mu da irin wa'yannan abun ba kin tashi cikin gata nifa yar malam shehu gwara in yagi abin da na yaga kafin ungulu ta koma gidan ta na tsamiya....., ajiyar zuciya nihila ta sauke tace "bawai ban damu bane a'a wannan ita ce daraja ta kimata...., tsaki surayya ta ja tace "yanzu fa technology ya yawaita likitoci kwararru sun bayyana tuni za su mai da ke yadda kike a da wallahi ke karya mutum yace anyi...., dariya nihila tayi tace "Ginin Allah daban ba ɗaya dana baturai ba...., zauna kiga zama ni kuwa makarantar ma na dena zuwa wallahi takardar bogi akai min na zo gurin nan ke nifa naga kin tsaya kallon ruwa wallahi Allah tuni zanyi wub da shi sai dai kiji ana buɗa in zama kishiyar Aysha in goga kafada da ita hura hancin da take min nima in hura mata matsayin mu ɗaya da ita hmmm kin ɗauki duniya da zafi tana kokarin daukar jakarta raya ta yawa tayi tace "Ni zan tafi sai mun haɗu gobe...., okay see you later handle din kofar ta murɗa ta fita kai tsaye wajan da ta ajiye motar ta ta nufa gaban tane ya waɗi ganin uban security ashe Asif be tafi ba kasa shiga motar ta tayi ta zuba mai ido Allah ya ɗora mata son sa taka fatan Allah ya mallaka mata shi mota wani daga cikin security ɗin ya buɗe mai ya shiga sauran ma suka shiga a guje ko wacce mota ta fita cikin tsari kai dole mutumin nan yaji kansa a sama duk wannan mutanan an tanade sune saboda da shi ba dole girman kansa ya ƙaru ba ajiyar zuciya tayi ta shiga cikin motar ta a hankali take tafiya tana dan sake sake a zuciyar ta har taje gida ko dai-dai ta parking bata tsaya yi ba ta fito key ta miƙawa me bawa shukoki ruwa ta bashi amsa yayi ya gane me take nufi kai tsaye shiga floor tayi ba kowa a floor gidan yayi shiru daman yau hajiyar ta aikin kwana take hanifa na gun nanny bene ta hau ta buɗe dakin'ta cin karo tayi da zee tana kokarin fita fusgota tayi tace "na kama ki daman ke kike min yan kana nan sace sace.... bani abin da kika ɗauka....?, jikin zee na rawa tace "Wallahi ai kafin ta karasa ta wanke ta da mari tace "ki bani nace miki bawai tsayawa dogon zance ba...., dan Allah ki yi hakuri Tanka ɗata tayi ta rufe kofar ajiye jakarta tayi akan gado cikin ɗaga murya tace "Zaki bani ko sai nayi miki abin da zaki nadama na har abada...., jikin zee na rawa ta ƙara matsai abin da ta ɗauka a bra ɗin'ta a fusace nihila ta fisgota ta yaga mata riga sai ga sakar gold a cikin bra salati nihila ta saki tace "daman ke kika daukar min waya ta to dole yau ki koma kauye wallahi ....., ɗur ƙusawa tayi tana kuka tana bata hakuri amma nihila ko a jikin'ta sai ma hutar da take ruruwa a zuciyar'ta daukan sarƙarta tayi cikin kuka zee tace "Wallahi Allah ba sata nayi ba photo zanyi da ita in dawo miki da ita...., Rufe min baki dole yau ki bar gidan nan ƙara gigicewa zee tayi dan bata shirya cin kariyar miya ba da baƙin tuwo dakyar nihila ta haƙura ta fita daga dakin...... *Gidan Asif........* Daidaita parking driver da ya kawo shi yayi ya buɗe mai kofa mamaki ne ya kama shi ganin motar Aysha daman kiran da take mai kenan dauke kansa yayi tare da ƙara karantar wayan nan sabbin masu gadi da aka kawo mai yayi wani kasaitatcan murmushi wanda shi ƙadai yasan ma'anar sa........ *ku yi following ɗina domin samin ci gaba da zarar na ɗora* GIDAN MAGAJIYA EPISODE 23-24 book 2 Kofar da zata sada shi da main floor ya shiga baƙin sa dauke da sallama tana zaune yar aikin ta na tsiyaya mata ruwa jin sallamar Asif da sauri ta ajiye ta ƙara risinawa tace "Barka da dawowa...., ɗauke kai yayi cikin takaici yace "yauwa sai mutum ya kasa kunnu tukun na zai ji abin da yace tashi tayi ta bar gurin sai a lokacin Aysha tace "yauwa gobe ina so in je gyaran gashi wallahi kai na baya min dad'i zaman asibitin da nayi ya ishe ni..., Ba tare da yayi magana ba ya huce ta yana mamakin halin aysha abin da ta saka gaba shine ci aikin ta buƙatun na rayuwar'ta ba ruwanta da damuwar'sa ita dai damuwar ta kuɗi ta wata yar karamar kofa ya bi ya shiga part ɗin'sa ajiye briefcase ɗin'sa yayi akan kujera ya zauna ji yayi an turo kofa tace "Sweet magana fa nake maka banji kace komai ba....?, juyowa yayi ya kalle'ta ya zuba mata idanuwan'sa wani irin kallo yake mata me hautsina ya'yan hanji dakewa tayi dan wallahi dole ta kwashi kuɗin da zata gina kanta ko bayan ba ransa tun da tasan wannan shegiyar tsohuwar dole tayi mai aure a tasa zuciyar kuwa mamakin.....halinta yake ya aureta ko primary bata yiba ba duk kan wani mataki da ta taka shine sanadi mahaifiyar ta daga makka aka koro su ita sadakar yalla ce sai yanzu yake ganin illar kin bin maganar iyayen'sa kyau ya ruɗesa sai bayan sunyi aure yake ganin abubuwa kala kala tashi yayi da sauri ta sha gabansa tace "Asif in ma aure zakai ba sai ka sha wahalar hulakanta Ni ba ka fito fili kace min za kayi amma ka tsaya kana yi min hulakancin kala kala daman na sani wannan tsohuwar baza ta barni in zauna gidan miji na lafiya ba...., mari ya zabga mata idonsa yayi ja cikin ɗacin rai yake cewa wanda yasan darajar tsoho shike girmama shi A'isha ban yi mamakin halinki ba nasan rashin ingantacciyar tarbiyya ke ɗawainiya da ke da rashin ilimin addini halinki ne bazai bari ki zauna lafiya a gidana ba ina ja miki kunne wallahi wallahi wallahi duk lokacin da kika ƙara faɗar wata ɓakar magana da ta shafi hajiya ranar zaki sha mamaki.... dafa kumatun ta tayi cikin ɗaga murya tace "Asif ai naga ma shan mamakin ka wallahi dan hakasan bani da gata shine kake hulakan'ta ni bani na zaɓawa kai na rayuwa ba Ubangiji ya zaɓa minhar ni zaka duba kace iyayena basu yi min tarbiyya ba amma in ka manta bari in tuna maka bani na ganka nace ina so ba a rashin tarbiyar ka ganni cikin tsumma kace kana sona ....., baya son cece kuce dan haka ya bata guri cikin daga murya tace "wallahi ka ban mamaki tun yanzu kafara fito min da ainiyin kalar ka in Ka gaji dani ka fito fili kace ka gaji ina da arzikin da zan iya ci da kai na in ci da mahaifiyata a yanzu na tsaya da kafafuwana Kar ka manta niɗin wace zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana muzuru ana shawo sai yayi....., cije lips ɗin'sa yayi ya hau sama zuciyarsa tamkar ta fasa kirjinsa ta fito zama yayi a bakin gado ya fara cire safar'sa sannan ya cire agogon'sa a takaice dai daga shi sai boxer ya zauna ya dafa kansa ya zura hannunsa cikin sumar kan'sa yana al'ajabi ko a mafarki aka ce mai Aysha zata aikata haka zai musa wayar sa ce tayi ringing sai a Lokacin ya tuna da yabar ta cikin aljihun wandon'sa janyo shi yayi ya ciro'ta muzabfar ne ke kira ɗaugawa yayi ya saita nutsuwar'sa domin baya son ya fahimci halin da yake cikin yace "wa'alaikassalam munatanan Germany....., dariya muzamfar yayi yace "Barka da wannan lokaci mutanan Arewa...., Kwanciya Asif yayi yace "bakai karya ba wannan shine a salina..., dariya muzamfar yayi yace "ba shiri ka baro chaina da fatan dai an ga wa'yanda sukai wannan abun....?, ajiyar zuciya ya sauke yace "Har yanzu bincike nake...., To Allah ya saka a gano ga yarka ta takura sai taji Muryar uncle sai dai uncle din'nata be fiye tunawa da ita ba ya bugo yaji lafiyar ta ba kullum busy work ya faɗa yana dariyar tsokana..... wallahi muzamfar ka kiyaye ni bani ita salon kasa ta dena ganin girmana kasan yanayin aikin mu da naka ba ɗaya ba kai dan kasuwane nifa zaɓin ka kabi ya faɗa yana miƙawa mufida wayar amsa tayi cikin maganar yara tace "uncle good night...., beautiful princess ya karatu dariya tayi ta kalli daddy ta tace "kullum sai nayi kuka bana son school...., zaro ido Asif yayi kamar tana gabansa yace "Maza tuba kinyi babban saƙo bakya so ki zama doctor.....?, uncle ina so mana to maza ki dinga karatu in bakya yi na dena kulaki uncle yayi fushi da ke kukan shagwaɓa ta saka mai tace "Please uncle kai hakuri na dena....., duk kan wata damuwar'sa ne matar yayi ya rasa ashe daman ya'ya rahama ne lumshe idanunsa yayi a yanzu ya ji sha'awar daman tare yake da yaran'sa sun zagaye shi suna shirme yana biye musu har muzabfar ya ƙarbi wayar be sani ba sai da ya kira sunan sa maxaiwa yayi yace "me i saka ka karɓa muna hira....?, cikin takaicin halin dan uwan nasa yana cikin damuwa ba zai iya faɗamai ba suyi maganar matsalar yace "Miƙo min tayi tace ka kashe wayar baka magana...., shiru Asif yayi muzabfar ya ci gaba da cewa Wallahi tu da na kiraka naji Muryar ka nasan ba gajiya bace Asif Kai wa kanka adalci mana inna rantsai ko kaffara bazan ba wannan damuwar da kake ciki Aysha ce sanadin shigar ka ka ƙara aure ba duka mata suka taru suka zama ɗaya ba mata nawa ne suke binka suna so ita ta samu tana wasarere da damarta uwa uba rashin haihuwa amma kullum kana jibgawa kanka aiki dan ya rage maka damuwa alhalin ba shine mafita ba ina jiye maka ranar da za awa gari A'isha ta saka maka ciwon zuciya kuma wallahi guduwa zatayi ta barka dan batayi kama da macan da za ta dauki responsible ɗin ka ba tun huri kafin kane mowa Kan ka mafita Ajiyar zuciya ya sauke yace "Ina jin ka ubana ci gaba...., cikin dariya muxabfar yake cewa"ai na gama ƙi faɗi....., Kashe wayar'sa yayi ganin muzabfar zai cika mai kunne shiga toilet yayi yayi wanka tare da ɗauro alwala da yake an fara kiran sallar magariba cikin sauri ya xura jallabiya be san lokaci yayi haka ba feshe jikinsa yayi da turare ya tsane kansa ya dauki carbi ya janyo kofar sa ya fito ganoj bedroom ɗin aysha yayi a buɗe kai da kai yayi ya fita abin mamaki motar ta bata nan kenan yaji tayi a zuciyarsa yace kyama dawo da kafafunki ya fita daga gidan masallaci ya jufa kamar ance ya juyi da sauri mutumin dake binsa ya laɓe tasbihi ya ci gaba dayi har ya isa masallaci zama yayi kafin a kira sallahi yana salati to har aka kira sallar Isha be fito ba sai bayan an idar yayi shafa'i da huturi ya fito again har yanzu binsa ake waya ya ɗauko ya fara danne danne ya tura saƙo ya zura a aljihu ya ci gaba da tafiya wata farar mota ce ta dallemai ido saka hannu yayi ya tare saboda hasken yana neman ya kashe mai ido ba zato ba tsammani yaji harbi..... Cikin ikon Allah be samesa ba fitowa sukai duk fuskokin su a rufe abin da basu sani ba abuja ba kamar local unguwa ce tuni ko wanne security ya fito da sauri suka shiga Mota suka fita a guje Allah ya temake ku ba a kama suba Asif kuwa ɓoyayi da yake ya yi wa jami'an tsaro waya sun tare ko wanne get ba za su iya fita ba shiga cikin gida yayi kai tsaye bedroom ɗin'sa ya shiga ya dafa kansa ya zauna ba wannan ne karon farko da aka fara akai mai hari ba amma wannan yafi muni Allah ne yayi da kwanan'sa a gaba da tuni yanzu wata maganar ake matsantawar abokanan gaba tana ƙara tsanani ya zama me mai dole ya bar wannan kujera yana son aiwatar da gaskiya amma hakan baza ta yuhuba.... ɗaukan wayar'sa yayi ya soma lalubo contact din abba Saboda tashin hankali kasa ganinsa yayi abin mamaki duk wannan karar harbin da security ɗin gidansa da suka ji ba wanda ya fito tamkar da haɗin baƙin su zamansa a cikin gidan matsala ne dan haka ya ajiye wayar akwatin sa ya dauko ya ɗauki duk wani abu me mahimmanci da briefcase ɗinsa ya fita ta cikin kofar sirri sai gashi a waje wata mota ya shiga ya tada ita...a guje ya fata ba tare da mutanan gidan sun sani ba kan titi ya miƙa bazai je hotel saboda duk kan wani motsinsa akan idon matane yake bazai iya basadar da ba za a iya ganesa ba dafa kansa yayi tunani yayi wa kwakwalwar'sa yawa a she daman taƙa wani matsayi kamar ka taka haɗarin rayuwar ka ne baka da kwanciyar hankali kowa ya matsoka ga ni kake cutar da kai zai yi ji yake daman ya dawo da agogo baya rayuwar sa ta da me cike da aminci....ba wanda ya damu da shi zai shiga cikin mutane ayi wasa da dare amma yanzu fa bazai iya ba... bashi da tsayayyan gidan kwana ko mai nisan dare haka zai fito ya koma wani gidan ya kwana bashi da hutu na kansa wani lokacin ma baccin baya yuhuwa meeting ɗin na dare ne dole ya fito..... *Washegari* da kyar ta iya tashi zaune shima hakan da dabara ta tashi bata san rana ce ko dare ba ga gurin shuro baka iya jin komai kamar ba gurin ba wanda yake shiga in ansa Mutum a saka shine ba futowa haka ta raya a zuciyar ta ba abinci ba ruwa a yanzu zuciyar'ta ta bushe kallon ko wanne dan adam take mara imani *Kano unguwar kofar mata* Alan guburo lafiya naga kana ta shiri yawa me barin ƙasar....uwani ta tambaye shi Gyara zaman malin malin ɗin'sa yayi yace "jiya na manta ban faɗa miki ba munyi shawara ni da manjagara da mahaifin dinana da na rabi za mu tafi Abuja ko za mu sami bilin wa'yannan yaran kinga yau kwanan su uku ba wani labari gwara mu bi sahun'su...., taya akai kuka san a Abuja aka ajiye su Malam hamisu ne ya faɗamin domin ya je headquarter su tanan an tabbatar mai basa nan saidai yaje Abuja To Allah ya kai ku lafiya amma Ni ina jeye muku arba da wayan nan mutanan kar fa su nan naɗe ku su tura cikin cel Ashsha kaji mugun baki jan bakinta tayi ta tsuke tana yi mai fatan dawowa lafiya ba tare da an cire mai kafa ba domin ita ta tsorata da ganin mutanan nan ko ɗigon rahama babu a fuskarsu yanzu tasan duk wannan jikin na magajiya ya zube babu shi domin tasan sace shi za suyi tas to ga yan ƙari nan yan zuwa shishshigi su kuma Allah ya fitar da su.... gama shirin'sa yayi tas ya gama yace "Bani dubu goma a cikin kuɗin cinikin ki...., ba musu ta ɗaga kwanon da take jefa kuɗin cinikin ta dauko mai kirgawa yayi ya tura a aljihu ya dauki yar jakar'sa yace "To mu mu tafi zaki iya ganin na dade domin dole inga Ak sardauna na bashi hakuri ya sakar min yarana....., abin dariya ya bata tace "Allah shugaban ƙasa ganin irin mutanan nan bafa ganin limamin unguwar ku bane...., be tsaya jinta ba ya saɓa jakarsa ya fita cikin addu'a a kofar gida yaga mahaifin rabi da na dinana sai manjagara saboda yayi zaman Abuja kai tsaye waha mota sukai a ka kai su tashar da zasu hau motar Abuja suka hau aka fara tafiya ƙara maƙale jakar'sa kahu yayi saboda ɓacin rana wata uwar tusa na kusa da shi ya yi da sauri kahu ya tushe hancinsa yace "Haba bawan Allah me maƙon kace a tsaya za kai uzuri wane be san uzuri ba sai kai mana tusa a mota salon cikin mu ya ɓaci....✍️ *GIDAN MAGAJI YA* masu tambayar complete kuyi hakuri typing dinsa nake har yanzu *EPISODE 25-26.....* Wannan ai bura'ubanci ne in banda kai dan kwal'ubane taya zaka dinga cika cikin ka dabubuwa kana cutar mu..... gyara zama wannan taton mutumin yayi yana aikawa da kahu harara kara karkace wa yayi ya saki wata tusar da sauri kawo yace "Wallahi malam hamisu sai yau na fahimci karin maganar da hausawa suke yi na cewa tafiya yankin azaba a she wannan abubuwan sune azabar tafiya wallahi yanzu daje likita ya dubani ba mamaki ya ce min na kamu da cutar da ke damin wannan jibgegen mutumin domin fa cuta ya ke fitar wa......., shiru malam hamisu yayi domin bazai iya magana ba saboda zamansa da wannan mutumi cikinsa ta ɓaci gashi yana tsoron magana kar ya naɗamai duka tunda gashi suffar karfi......ya tushe hancinsa maltina wannan mutumin ya ɗauko da biredi yana ci ga wasu kayan ciye ciyen da sauri kahu ya kwace yace "Wallahi har mu sauka ko gutsure ba zaka ƙara ci ba al'ummar motar nan kuyi magana mana kuma fa yana cutar da ku bani kaɗai ba wannan wane irin mutum ne tun da muka shigo motar nan take zubawa cikin sa abubuwa....., haɗa baki sukai suna cewa gaskiya fa wallahi Wartar abinsa yayi ya nuna kahu da danyatsai yace "Kai tsohu ka fita a idona na rufe ko wallahi in kakkaryaka in watsaka ta cikin window din motar nan cikin ka ko nawa ka ƙara wata magana kaga kin ban rugurugu da kashin ka....., komawa baya kahu yayi ya rufawa kan'sa a siri domin bisa alamu tsab zai iya aikata mai hakan wallahi.... Sai karfe biyu ɗaya da rabi suka isa birnin tarayya Abuja bayan sun sha huya a cikin motar nan ban da manjagara da shi kamar ma warin maye ya sashi kai shayeshaye mugun ciwo Allah ka kare zuri'ar mu da shi......... gyara zaman rigar'sa yayi ya fara tsayar abin hawa cikin sa'a suka samu suka kwatanta mai in da za akai su juyowa yayi ya kalle su yace "amma a dan nesa da gurin zan ajiye ku dan wallahi bazan ƙarasa gunnan ba...., Kahu ne yayi carab yace "Haba dan nan ka gan mu nan gaɓoɓin jikin mu yawa an kunce mana ita wallahi ka temaka kai mu...., Baba wallahi bazan ƙarasa yellow gidan nan ba ato kai ai ni ko a mafarki bana fatan in ganni a jikin gidan infa sukai huru huru suka ga me laifi bindiga za su dauko wallahi sai dai kaga kwakwalwar mutum tana yawo a ƙasa yawa tarwaɗa wani mugun yahu su kahu suka haɗiye manjagara ya saka kuka yace "to Allah i saka mu gani su ba su kashe su ba....., a fusace kahu ta buge mai baki yace "tufar da mugun yahu falmata kaɗai ta rage min insha Allahu sai na dauki ya'yanta ai wahala bata kisa inhar da kwana a gaba......, daga nesa ya tsaya suka sauka kahu ha bada kuɗi tafiya suka fara har suka isa get ɗin bisimilla kahu yayi ya fara bugawa yana ɗora hannunsa aka buɗe ja da baya yayi ganin wani katon mutum jikinsa duk a murɗa ga wata bindiga ta kusan rabin sa kallon su yayi sama da kasa cikin rawar murya kahu ya zunguru malam hamisu yace "Tun da muka tawo ni nake magana dan haka kai da mahaifin Rabiu a yanzu ku za kuyi...., Mahaifin rabi yace "Dan Allah kai hakuri kayi..., ganin kamar suna ce ce kuce ya fara rufe kofar da sauri kahu yace "Hallaɓai mun zo ganin yaran mune da aka kama a kano Kai wa Allah kai wa annabi ka barmu mu shiga..., kati ya miƙa musu ya basu hanya zare ido suka fara ganin kamar gurin ma'akata suna hada hada da sauri kahu yace "ku zo mu shiga nan binsa sukai me tsaron kofar ya kalla yace "barka da aiki....,kallonsa yayi sama da ƙasa yace "yauwa..., dan Allah alfarma muke ne ma ka temaka ka kai mu inda za mu ga yaran mu da aka kama a garin Kano maza biyu mace ɗaya ko za ka kai mu gunsu...?, Kallonsu yayi yace bani da alhakin nuna maka su ka tafi wani gurin kai kahu ya gyaɗa yace "mun gode ku zo mu tafi...., binsa sukai gaban wani haɗaddan wani gini suka tsaya iya tsaruwa ya tsaru kamar a ƙasar waje mutum suna kokarin tsallaka wani karfi wata tsawa wani jami'i yayi musu yace "Ina zaku ku suwa ye maza ku dawo baya kunsan nan gurin gurin waye.....?, da sauri kahu ya dawi baya suka isa gunsa tsugunawa kahu yayi domin ya gaji ga yunwa ga kumburin ciki yace "dan Allah yallaɓai ka temaka mana yaran da aka kama a garin kano su muka zo gani....., wani kallo yayi wa kahu ya ɗauke kai yace "Nan an faɗa maka kamar gidan yari ne ko ance maka ofishin yan sanda ne....baza ka iya ganin su ba tun huri ina maku shawara kafin kuma a jefa ku cikin su ku tafi in har basu da laifi aka gama bincike za ka gannu sun dawo....., Kuka kahu ya saka dai-dai fitowar Asif zai yi sallah lokacin salla yayi tare da habib da jabir suna magana da sauri manjagara yace "Lah hantsi zarto...., tun daga nesa daman sun gansu nunawa sukai kamar ba dasu suke ba maganar da suke kenan jabir ya nuna mai dattijon da yaƙe ƙasa yake kuka kahun falmata ne duk kan wani tarihin rayuwar su ba wanda ba su sani ba ba ƙaramin bincike suke ba tausayinsa ne ya kama Asif amma sai ya dauke kai ya ci gaba da tafiya cikin kuka kahu yace "dan Allah yallaɓai ka nuna min wanda yake da alhakin kama su da kuma inda wanda akaiwa kidnapping ɗin matar tasa wallahi zan je har gida na basu hakuri yarinyar nan ita kaɗai ta rage min ita da ɗan uwanta yanzu haka ɗan uwanta ba lafiya yana kwance sai dai a ɗaga a kwantar bamu da yan uwa duk sun ƙare a faɗan boko haram mahaifiyarta ma neman ta mu muka rasa wata kila sun bawa karnukan farautar su sun cinye namanta kai wa Allah da manzon sa ka temake Ni......... ganin Asif ya fito tare da su sir jabir da sauri ya sara musu tare da koma inda yake tsaro da sauran yan uwansa tunda ya faɗa mai be ji ba ya zai mai..... Liƙen su manjagara yake yace "Kahu kamar fa su hantsi nake gani..., buge hannnunsa yayi da yasa a kafaɗarsa yace "eh su ka gani saboda haka ta faɗa maka kwayar da kasha mutanan da suke yan daba ina su ina aiki anan....., wallahi kahu su na gani mahaifin rabi ne yace "to jeka kai musu magana su sake su tunda abokanan harkar kune ai malam bulama ba a ƙin ta mutum yaje...., wani yahu ya haɗiye ganin kallon da Asif yayi mai ya dauke kan'sa kiran salla akai tashi sukai suka fara neman gurin alwala suyi salla samin ruwa sukai suka ɗauro alwala a kofar masallaci kahu ya ajiye jakar'sa ganin wani ma'aikaci yayi mai alama da ya ɗauki abarsa ya saka zuciyarsa kuwa ce wa yake da alama wannan gurin kurame sunyi yawa ba magana sai dai nuni ya shiga Masallaci domin har su malam hamisu sun shiga tsayuwa yayi kamar ance ya ɗago ya juyo yaga wannan dattijon a bayansa shi yana sahun gaba kusa da liman tare da su jabir..... tada salla akai bayan an idar kahu ya dade yana kaiwa Allah kukansa kusan tare suka ɗago daga sujjada liman yayi salla kowa ya watsai tashi Asif yayi bayan ya gama lazumi kallon ida kahu yake yayi ya haɗa kai da gwuiwa su malam hamisu sunza gaur suna bashi hakuri.... kowanne ka dubi fuskarsa yana cikin mahuyacin hali Allah sarki iyaye Allah ka raya mu da su ya Ubangiji ka farantawa iyayen wa yanda iyayensu suka mutu Allah ya jikansu ya saka aljanna makomarsu wannan ita soyayya ta ɗa da mahaifi amma me i saka shi nasa iyayen basu damu da shi ba ko dan yana dan fari ne suke mai alkunya suna nuna kamar basu damu da shi ba hajiya ce rayuwar sa komai ita tayi mai har ya girma tafiya ya fara ya kalli jabir yace "zuwa dare ka saki yaran nan tunda munyi bincike basu da hannu aciki amma ka yi wa su baba magana su zauna su tafi da su sannan ka kawi su office ɗina ina son ganin su gaba ki ɗayan su har na tsaran...., Cikin girmamawa yace"to sir suka tafi da Habib jabir ya tsaya gurin sauran ma'aikatan suna tattaunawa turo wani jami'i yayi ya tafi da su baba aka basu gurin zama badai wanda ya kara ce musu wani abu suna zaune suna jiran ikon Allah Jabir da wani suka huce su dakin da aka kulle su dinana suka fara buɗewa suna zaune sun jigum jigum ba abinci ba ruwa yau kwana uku kenan jabir yace "Ku fito...., Jikinsu har rawa yake suka fito ku je da su office director okay sir dakin da magajiya take ya buɗe ina bata san an buɗe ba tana kwance sai numfar fashi take Monica monica da sauri wacce aka kira tazo tace "Gani sir...., Cikin tausayawa yake kallon magajiya tuni ya tuno da alkairin da tayi musu yace "Kamata ki kai ta office ɗin director..., to tace ta fito da magajiya cikin muhuyacin hali tana ƙarasowa kahu ya tashi da yake shi bebisuba yana jiran magajiya taya za a fito da su ba a fito da ita ba ƙamata yayi yace "Falmata buɗe idon ki nine kahun kine...., ina bata san me yake faɗa ba sai kirjinta da yake kaiwa yana kawowa innalillahi badai ta mutu ba ya dubi jabir yana fadar haka Kai jabir ya ɗauke yace "Maza kirasa da ita can...., kamata kahu yayi yace "Ina zaku kai min ya'bayan kun gama illata min rayuwar ta gashin kanta ya tattare da ya rufe mata fuska yace "magajiya buɗe idon ki....dan Allah kar ki mutu ki barni...., Kamata Monica tayi suka fita kahu yana share kwalla har office director da sauri surayya ta tashi tace "Ke dakata bana son rashin m ina zaki kai wannan abin..., tana nuna su kahu da magajiya banza monica tayi mata domin rainin hankalin surayya kullum ƙara yawa yake wato Ni zaki mayar yar iska ko ina magana kina ƙara gaba wallahi kike yaye ni kuna kokarin shiga aikina ganin Monica ta zaro waya kamar reporting ɗinta za tayi taja baya murmushi monica tayi tace mara kunyar karya da sai inga wanda ya tsaya miki banza surayya tayi mata tana ci gaba da cin cingum ɗin'ta...... Shiga sukai su dinana suna zaune sai zare ido suke ba bakin magana mamaki suke me ya kaho zarto nan gurin ko daman binciken su kazo yi ba me basu wannan amsar..... kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa cikin mamaki yake duban Habib yace "badai ba a basu abinci ba tsahon kwanakin nan....?, Ƙasa dakai habib yayi yace "Sorry sir baka ce abasu ba..., sai nace abasu ku baku da tunanin basu tasowa yayi ya ɗaga kan magajiya a lokacin kuwa Allah ya bata ikon buɗe idonta zabura tayi ganinta a jikinsa da sauri ta ja gefe ganin kahu ta saka kuka me cin rai ta kwantar da kanta a jikinsa tafiya su Monica sukai komawa kujerarsa yayi ya zauna dan gyaran murya Asif yayi domin su bashi hankalin suyace "Ina baku hakuri game da abin da ya faru munyi bincike mun ƙara tabbatar wa basu da hannu daman kamasu da mukai ko sun san inda shi kaska ɗin yake saidai kaf cikin su ba wanda ya sani sannan a yanzu kunga illa siyan tsohon Sim da illar siyan tsohuwar waya gwara mutum ya ɓare sabuwa wacce kana da tabbacin kai ka fara amfani da ita sannan kuyi kokari ku zama na gari domin duniya da iyayenku suyi alfahari da ku sau dadama muna samin irin wannan cases ɗin wani ya tabbata wani ba ya tabbata ba akwai lokacin da arar wayar wani akai akayi karbi kuɗin fansa da ita sai da bincike yayi bincike muka gano bashi akwai wanda kuɗin da akai kidnapping da su aka turo ta cikin account ɗinsa be sa hawa balle sauka aka kamashi watansa biyu sannan muka gano bashi bane ba duk wanda baku san saba yace aramin wayar ka zanyi kira gwara ko kati ne ka siya mai yayi da tasa duniya ta tallace yanzu ko wanda ka sani ne zai iya juyawa ya zama bana kwarai ba ku nemi sana'ar yiku dena zaman banza ke kuma kina..... Mace kina tara masu alaifi a gida ki ki nutsu wata rana ke uwace za ki jidadi ya'yan ki su taso zuji abin da da kikai....?, wannan babbar naƙasu ne ga rayuwar ki wallahi ko wanine yazo binciken auranki ya ga abin da ake a gidan ki bazai so hada zuri'a da keba.... ya faɗa yana kafe falmata da ido takaicine ya kamata da wasu manyan idanuwansa masu kama da muciya yana kallonta harara ta zabga mai ta dauke kanta shima dauke kanyayi ya ci gaba da cewa "A yau muka gama komai mun salla me ku kofa a buɗe take in kunji wani bayyanai ku kawo mana...., Da sauri rabi ya tashi yana cewa godiya muke Allah ja daran ka dariya Asif ya danne yace "Yana ga kana sauri za ka bar mu ko irin alhinin nan bakai ba ba zaka zauna da mu ba.., wani wallahi ko gadon ubana ne wannan gida na bar muku dan murmushi Asif yayi na gefen baki sai ka lura za kaga yayi yace "Dini kaifa zaka zauna damu...., wane mutum inji mutuwa niii tab ai wannan gida wallahi Allah ko shi kaɗai ne arziki na da zan samu in na zauna bazan zauna ba wallahi wato dai gudun mu kuke ya faɗa yana dan rubuce rubuce dinana yace "Wa...mu ai ba gudun ku muke ba wannan gida abin tsore ne..., Falmata kefa baza ki zauna da muba.....?, in ta ɗago ta kallesa to bango zai iya kallonsa ji tayi tamkar ta shaƙe sa kowa ya huta kaf duniya ba halittar da ta tsana sama da wannan mutumin na gaban'ta duk kyahunsa zamarata yake kumurcin muciji wallahi ko a hanya bata fatan gamuwa da shi da yake yanzu a gaban iyayensu ne ai gashi yana yi musu wasa dan rainin hankali ita wallahi haushin ma su rabi taji da suka biye masa..., Assalamu alaikum da sauri kahu ya amsa muzabfar ne cikin mamaki Asif yake kallon sa yace "Saukar yaushe.....?, wallahi yau na sauka sannun ku kallon magajiya ya ɗauke kansa kahu yace "Yauwa dan saurayi...., kallon su Asif yayi yace "baba yanzu na sallame ku...., To Allah ya ja da ranka godiya muke tashi magajiya tayi da kyar ko juyawa batayi ba ta fice tana Allah ya isa a zuciyar ta falmata kuɗin wayar taki ko kin bar mana Asif ya faɗa tsaki taja ta ƙasa fita tana cewa kai ne matsiyaci wallahi......✍️ *Fopa kodai ASIF yayi kamu ne* *Mu haɗo a gobe kar kumanta kuyi following ɗina domin samin ci gaba da zarar na ɗora* *GIDAB MAGAJIYA* *EPISODE 27-28* *BOOK 2* Wallahi indai kudi daga hannun wannan azzalumin ya fito bazan iya cin su ba sauran kaɗan idona ya dena aiki Allah ya isa buge surayya tayi bata sani ba da sauri surayya taja rigar'ta tace "Ke yar kidnapping wallahi duk tashan cikin nafi ki iyawa wallahi Ni zaki buge kina kaskantatciya wacce aka kamata da laifin satar mutane...., Mata rufe bakin ta ba magajiya ta zabga Mata mari hagu da dama muci muci tayi da idonta alamun ba mutunci tace "Ke dan uwar....ki nayi miki kama da wacce zaki gasawa wayan nan maganganun...? ke wallahi kalleni tun daga sama har ƙasa bani da mutunci ke a rashin mutunci na wannan ko sharar fage ba'a fara ba na iya akuyanci dan haka ki kiyaye bakin ki....., Cikin mamaki surayya take kallonta dafe da kunci tace "Ke wacce irin dabba ce a cikin dabbobi....? Wani ubanki a Abuja yau zaki bayani...., dabbar da uwarki tinkiya ta haifa magajiya ta bata amsa tana jijjiga jiki ya lafiyar kura balle ta girgiza jiki Allah yayi mata diri ba namijin da zai kalle'ta be sha'awar ta zama mallakin'sa ba su kahune suka fito kahu yace "Magajiya anan kike tashin hankali ki rufan a siri na gama kuka kar a ƙara garƙame ki...., da yake ba a hankali yake faɗa ba sai ga muzabfar da Asif sun fito hannun Asif ya sarƙe a kirji yana kallon ikon Allah kwata kwata yarinyar bata da tsoro maza ma suna tsoron wajan nan nasu amma ita har ta sami damar faɗa jikin surayya ne yayi sanyi tace "kai hakuri sir wallahi ba a son rai na hakan ta faru ba ganin irin kallon da yake jifanta da shi be magana ba sai a lokacin magajiya ta lura da shi kama hanna tayi zata fita kamar daga sama taji yace "Be dace ba ki fita a haka a matsayin ki namace..., zuciyar'ta ce ta tunzura ta juyi tayi mai wani irin kallo ta daukan ta me cike da tsantsar tsana harta shi da ake wa ya gani hasbullahu wani'imal wakil haka ya ambata a cikin zuciyar sa ya juya ya shiga office zama yayi akan kujerar'sa ya zura hannayen'sa a cikin gashin kan'sa me isaka ya bari ƙaramar yarinya na neman mai da shi wani iri cije lips ɗin'sa yayi ya furzar da wata iska me huci saboda me duk ya aikata wannan abin har muzabfar ya shigo be sani ba kamar an tsikare shi ya tashi daukar waya yayi cikin bada order yace "There are some people who will come out and stop them, don't let them come out and let someone buy a hijab and bring it to you...., Magana ɗayan yayi ba tare da anji me yace ba sai wanda yake wa maganar ASIF yace"okay ya kashe wayar...., zama yayi yana murza goshinsa me isaka yaƙi barinta tafi haka ne tambayar da shi kansa bashi da amsa can ya nisa yace "Muzabfar dole in faɗawa wa'yannan yaran inhar suka je kama mace to su bari ta suturta jikin'ta ai.., kafin ya ida magana muzabfar ya tuntsure da dariya yace "Continue Ai me.....?, ai uwar....ka wallahi muzabfar bar gani ka manyanta yanzu duka zan maka shafa gemunsa yayi yace "ai dole in manyanta nafa ajiye mace har biyu kaga nan da wani lokaci aure zan mata ya faɗa yana ɗaga gira...., banza Asif yayi masa dan ganin yau muzabfar dan sanyin da munar da ake ya taɓa mai kwanyar kansa ya ci gaba da aikin sa babban yaya yaushe za mu zance....?, buɗurwa kayi ne ya tambaye shi ɗan shi kwatakwata be kawo falmata a cikin zancen nasu ba kama haɓa yayi yace "buɗurwar ka mana yar dambe kai wannan yarinya ita ce maganin A'isha wallahi....., shiru yayi mai ganin yayi shiru shima yayi amma wallahi in ya rantsai bazai kaffara ba abokinsa ya kamu da son wannan yarinyar saboda tsabar kishi da ya rufe mai ido har baya so ta fita a haka can wata dabara ta waɗo mai yace "Uncle ɗin mufeeda wallahi kayi tunani da ka dakatar da yarinyar nan saboda kaga ga irin kirar da Allah yayi mata ni wallahi zan nemi yaranka su nanamin gidan su Allah tayi min sosai komai yaji fa baruwan ka faɗa da ƙashi kaga irin wa'yannan chocolate ɗin wallahi hmmm ba'a magana me gidana yadda suke a zahiri cikin su tafi haka kaga wa'yannan fararan tab lamarin sai addu'a musamman farar fata in mutum me ragaggen imani ne sai susa shi yabi mata amma irin wannan JININ BABGARA malam ina....., Wata uwar tsawa Asif ya bugawa muzabfar hatta files ɗin da suke kan table ɗin'sa sai da suka zobe jijiyoyin kansa sunyi raɗa raɗa idonsa yayi ja tsorata muzabfar yayi da wannan yanayi da ya canza lokaci ɗaya ajiyar zuciya ya sauke ya zauna yace "Muzabfar daman kawali ka zama ban sani....? innalillahi tab...to wallahi zo ka fita ba zaka haɗani cikin zunubin kaba haka kurum kaga mace kai ta lissafi na zahiri da na ɓaɗini...amma kai wallahi nayi dan iska....., dariya muzabfar yayi yace "Auranta fa zanyi...., Wani abune ya tukarewa Asif maƙogaro dan haka yaja bakinsa sa ya tsuke zuciyarsa na harbawa yawa ba zuciyar namijin duniya ba wayar sa ce tayi ƙara da sauri ya ɗaga dan shiru yayi alamar sauraro sannan yace "Taƙi karɓa kace mata baza ta fita ba in bata saka hijabi ba....., Cikin girmamawa yace "Wallahi tace baza ta saka ba tsakanin ta da hijabi sallah....., What sai kuma ya saita kansa yace "Saka Joseph ya kai su har gida kyaleta ya kashe wayar'sa cikin mamaki muzabfar yace "Driver Ka ne zai ɗauke su kai nifa hakan ma yayi min gwara ya je gidan su gobe ya kai ni aiyi magana da gemu da gemu dan bazan tsaya bin takanta ba ta shigo ciki ta koyi sona dan wannan yar'darun wallahi aure ba'a gabanta yake ba kuma baza ta farasa samari ba dan mazan yanzu wallahi irin wannan suke nema....., File ya saka ya kwaɗewa muzabfar baki yace "Wai kai yaushe kakoma haka.....?, Kai kai shiga abin da ba ruwanka wallahi Asif Ka canza inda ne yarinyar nan ko tsirara zata fita ba abin da ya shafe ka da ita rayuwar ka ce amma ga yarda kake tada jijiyar huya sai ta rufe jikin'ta ko ita wannan ɗin ta daban ce a cikin mata ina cewa A'isha matar ka haka take yawo ba mayafi saboda boko ta sha mata kai..... kai wallahi sai ka barnan haka kurum ka cika Ni da zance to wa'azi naji akan illar barin mata su fita ba kayan arziki tashi muzabfar yayi yace''good amsata ta fito sauran ta gaba da kafar ka zaka zo guna neman yarda za ayi....., ayi uwar ka nace ka fita dariya yayi ya fita yana cewa muna gayyatar ka cin abincin rana gauro..... murmushi yayi ya jingina da kujera wayarsa ce ta fara ringing ganin sunan mahaifiyar A'isha yayi banza da kiran har sai da ta kira sau uku tukunnan ya ɗaga yana ɗagawa ba ta saurari gaisuwar da yake mata ba ya rufe shi da faɗa tana cewa wannan wanne irin tsohon hulakanci ne ka marar min ya'ta duk zaman haƙurin da take da kai ba haihuwa to gaskiya fa Ni yanzu dole ka sake'ta ta dawo kenan ina so ya'ta ta aure me haihuwa ba irinka ba juya nemo mata mahaɗi zanyi wanda ya yi dai-dai da rayuwar'ta me sonta wallahi ka ban mamaki duk ka gama shanye wa ya'ta ma'adanan jiki yarinyar nan tun kirgar dangin'ta be tasa ba a aure'ta saboda tsabar jaraba irin'ta ka suka fito a satin farko yanzu su zama slippers bara ka sauya wata to gyara ba a binda ya bari...... ba ƙaramin mamaki maganar ta ta karshe tayi ba ko kunya bata jiba a lokacin da ya aure aysha shekarar ta ashirin da biyar da girman'ta amma saboda halin rayuwa ko primary batayi ba shi ya gina musu rayuwa da mahaifiyar'ta shine yanzu za suyi mai butulci ko daman zargin da yake gaskiya ne aysha tana soyayya da mazan waje tunani ya shiga kafin ya tafi China ta tafi tana wanka aka kira wayar ta har sau shidda be ɗaga ba ganin number ba suna sai wata zuciyar tace"mai ɗaga ringing din wayar nan ko ya barka kayi aikin ka....ɗagawa yayi kalmar farko da tadaki kunnan'sa hello baby za mu haɗu ne yau cikin mamaki yace mai wrong number mutumin yana ji ya kashe maganar mahaifiyar ta ce da ta kusan tsinka mai dodon kunne ta dawo dashi da ga dogon tunanin da ya tafi.....tace "wato dan iskanci ina magana kayi shiru saboda baka san darajata ba tana faɗar haka ta kashe wayar'ta ajiyewa yayi ya kauda wannan tunani a ransa ya ci gaba da aikin'sa....... ****** Kahu ne ya dubi magajiya yace "Billahillazi dole mu shiga motar nan ke wai wanne irin taurin kai kika ɗaɗo ne wallahi taurin kanki yafi na jinjirin jaki...., kyale ta kahu shiga ba fashi wannan wane irin taurin zuciya ne da kafiya rabi ya faɗa maganar'sa sak ba wannan lanƙwashe lanƙwashen Joseph ne ya zo ya daidaita parking din'sa shiga su kahu sukai da yake motar katuwace ta ɗauke su magajiya ta zauna a gaba tun da aka fara tafiya suke bada labari kahu na tausaya musu haka su malam hamisu magajiya kuwa tayi shiru zaro ido tayi sakamakon ganin banner ta Asif a jikin dan ƙaramin mudubin motar na ciki da sauri ta saka hannunta ta tsige ta kallon mamaki Joseph yayi mata yace "You are safe and it's a photo, please take it off and I will tell you...., ƙarasa yagawa tayi ta zubar ta gyara zamanta takaicine ya ishi Joseph yace "Dannn iska..., ka bari sai ka iya faɗi tukunna ka fada ai yanzu mahaukaci baka iya ba your name mahaukasiiiiii.....ya tambaye'ta bawai dan yasan me kalmar take nufi ba dariya abin ya bawa magajiya tace "You You yout name mahaukaci.., No,no my name is Joseph Samuel is my name not mahaukasi.... Banza tayi mai dan ta lura be san ma abin da ta faɗamai ba daman an faɗamai kano zai kasu sai da aka zo kano kahu yake nunamai inda zai je da yake wata ran suna zuwa kano da oganna sa a kofar gida ya sauke su da sauri magajiya ta buɗe ta fito haka su kahu tuni yan unguwa suka dinga leƙowa ana ganin ikon Allah ya dawo Tsawa tayi tana kallon su tace "To munafukai maƙiya Allah ba haka aka so ba ko sai gashi na dawo...adai gyara hali wallahi....., ta faɗa tana shigewa gida fitowa su manjagara sukai kowa ya kama gabansa kahu ya shiga gida bayan yayiwa Joseph godiya tare da jajjadamai yayiwa ubangidan'sa godiya...... tashi uwani tayi da sama'ila da gudu suka rungume'ta suna farin ciki ta dawo cikata uwani tayi tace "Bara in ɗora miki ruwan wanka sannu magajiya...., To tace ta shiga daki ta kwanta...... bayi kahu ya shiga bayab ya ajiye jakar'sa da gudu domin cikin'sa ya ɓaci uwani tace "Anyi ciye-ciye ciki ya ɓaci....., ashe ya jiyo ta yace "Wannne cije cije wani azzalumi muka haɗo dashi a mota ya dinga tusa ba kakkautawa...., Dariya Sama'ila da uwani sukai.... zuciyarsu kallal ba sauran damuwa..... *****N.N.D.C QUARTER'S* da kata kawata kice kawai in fito yau akwai raƙashewa ai ni haka nake so wallahi ban fa haifa ba dole inyi abin na ga dama ita waccar shegiyar bafulatanar da yake ta haifa ai saita kanta take kuma wallahi fita a gidan nan bamma fara ba Ai kuwa kina fita yau gi zarce gidan malam sunusi.... da sauri ta juyo ta zare wayar ta daga kunne jikin'ta yayi sanyi jin maganar Hajiya wata uwar harara hajiya ta watsai mata tace "Wai ke izzatu wacce irin macece yawa wata ma'aikaciya kullum ke kenan sai kin fita to wallahi bazan lamunta ba daga nan kina fita kar ki dawo min cikin gida., mayafin ta taci ɗamara dashi ta koma part ɗin'ta batare da tace komai ba laɓewa hajiya tayi da sanda domin tasan kafurar yarinyar nan ba hakura tayi ba gwara yau ta nuna mata tsohun kashi ta zauna ko na sati ɗaya ne.... sanɗa izzatu ta fito tanayi da mayafi a ɗaure a kugunta sai ta kalmi da ta riƙ a hannun'ta ji tayi saukar wani a bu a gadon bayan'ta ba zato ihu ta saka ta ɗurƙusa ƙasa.....✍️ *Tab Hajiya yau tayi aiiki....* SANARWA BOOK 2 A 50 ZAI ƘARE BOOK 3 MU ƊORA A 51 har zuwa mu gama domin fara biya kamallaki naka ba tare da jiran gwar shanu ba ku fara payment ɗin ku insha Allahu zan yi kokari in bawa kowa document tunda bakwa son buɗe group kullum ayi muku page ɗaya ko biyu yan VIP 3 500 kacal Account number 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay a turo da shedar biya ta wannan number 09061890481 yan nijar za ku iya turo da katin 300fcfah Yanzu wasan ya fara ba a fara ganin komai ba *GIDAN MAGAJIYA* *EPISODE 29-30* *Book 2* Wayyo Allah gadon bayana na shiga uku da sauri kowa ya fito ban da hajiya jamila da ta leƙe ta sama taja kwafa tace kaɗan kuka fara gani ni daman na dade da dawowa daga rakiyar wannan tsohuwar... Cikin mamaki umma ke tambayar izzatu hararar umma tayi ta miƙe tana karkaɗe rigarta dafe da kugu tace "ta Allah ba taki ba kinga na miƙe ba mamaki ke kika laɓe kika bugan sanda...., umma mace ce me hakuri dan haka ko a fuska bata nuna taji me izzatu tace ba ta juya zata tafi hajiya ta fito tace "To rasa kunya ina jin irin rashin arzikin da kike wa umman yaya ke wai izzatu wacce irin macece ai Asma'u dama da kika tarar da ita a kwance ki daddage ki dauki tsabga ki ruɗa mata jiki da duka da wallahi ko kallon banza aka ce tayi miki ba zatayi ba ki ruɗawa yar iska ba yadda zata kasa kwanciya ta tsawon sati biyu ba yawo....., sosai zancen hajiya ya bawa mamy dariya da take gefe ita kuwa umma bata tsaya jin wani zance ba tayi gaba inde hajiya ce yanzu zata iya dawowa kanta ba abin dad'i bane ta ci mutuncin dan uwanka kayi murna anjima naka zata ci salati hajiya ta saki ta kalli mamy tace "Hamziya ina magana kina dariya saboda ga yar iska ko....., girgiza kai tayi tace "Allah ya hucu zuciyar ki hajiya...., Au da keki Ka kunna min huta a zuciyar tawa shine yan zu kike so tayi sanyi anya kuwa hamziya kina so kika annabi salim alim ba tare da ankwashe miki fatar baya ba Ubangiji yayi miki azaba Sosai drama hajiya take bawa faisak dariya dan haka ba abarsa a baya ba ya tuntsure da dariya ganin hajiya ta jiyo dariyar'sa ya koma cikin daki kar faɗan ya shafe shi hajiya jamila ta maida hankali kan fadan nasu bata san hajiya ta juyo ba sai ji tayi tace "Muna fuka ƙaremin kallo to wallahi Ubangiji yace hutar munafukai daban take kina sama yawa jemage da fuska a jeme kina munafur wallahi har na gano an dilmiya wannan fuskar'taki a dalma ta kwakkwaɓo in banda tsabar kin kware a munafurci har na juyi baki sani ba kina dariya rai yayi fari tas anci mutuncin faccalolin'ki me zubin kafurawan farko shi yasa ka Asma'u ke birgeni wallahi ba ruwanta da wannan baƙin halin kai Asma'u yar aljanna ce..., juyawa Hajiya jamila tayi ba tare da tace ƙala ba faisal ta tarar a floor yana cin abinci a tsawaya tayi akansa tace "Kaga masifar da kaja min ko har ubanka ya dawo ba zata dena wannan maganar ba kai Allah ya kashe hajiya mu huta....., tare da ke da sauri ta ɗago tace "Faisal niii mahaifiyar ka..., Mom ai ita ma mahaifiyar wasu ce yanzu in Mala'iku suka amsa miki addu'ar ki har dake zasu haɗa wallahi dan naji wani wa'azi ɗazu a she akanki zai aiki ban'sani ba duk fatan da kaiwa ɗan uwanka wala na alkairi ko akasin haka akwai mala'ikan da zaice Allah ya yayi maka misali in kace Allah ya jikan wane sai yace kai ma Allah ya jikan'ka Da hallacan rufan baki shashasha kawai har wani karatun addini ka iya in banda shashanci Hajiya tana mutuwa gado mahaifinka zai ci me tsoka mu ware kan mu ban masifar tsohuwar nan ta ƙi bari kowa ya ware ya zauna ai bata ƙarasa ba hajiya ta shigo cikin ɗakin tace "Ya ware ubanki....jamila wallahi kikiyaye'ni tab Allah ya ragewa aya zaƙin ta jiya ba yau bace da ke bama zaki iya yimin wannan maganar ba ko da abayan idona ne ban gurce miki baki ba in saka Mustapha ya auro wata ya sake ki to daman mene amfanin auran ki ɗa ɗaya kwal kika haifa shima gashi nan ga shina ba tsiya ba arzƙi...., hajiya cikin sauri ta tari numfashin'ta tace "Rufemin baki bana son dogon turanci..., ƙasa tayi da kanta zuciyar'ta kamar ta fasa kirjin'ta ta fito to wallahi tun huri ki canza taku domin wannan na dade da gano shi har ina magana da yake ba tsohuwar ki bace ki tafi ki barni Dan girman Allah hajiya ki hakuri wallahi Ni nayi dariya ba ita ba faɗa take min shine na koma Please............ Faisal ya faɗa yana haɗa hannuwansa alamar ban haƙuri wallahi taci arzikin ka da yau kwanan gidan alhaji Nuhu za tayi aje can sai kin gyara hali kya dawo ta faɗa tana kokarin fita daga ɗakin zama Hajiya jamila tayi zuciyar'ta na mata suya a kullum kashe kuɗi take akan matar nan amma har yanzu bata tsira da mutuncin'ta ba Mom Dan Allah Kar ki damu da halin Hajiya harara ta watsai mai tace "Wallahi duk kai ka jamin wai yaushe zaka shiryu ne ko kishi baka yi jibi Ayman Akram muzabfar uwa uba Asif ha kamis amma kai har yau jiya i yau sai iskanci ka saka gaba ka ɗauki yan mata kuje club anya kuwa Faisal gashi ka ƙi bani haɗin kai da tuni mun kawar da Asif....., tashi yayi yace "Mom kiyi min addu'a nima bajin dad'i nake ba wallahi amma maganar nan dan Allah ki barta haba mom abin da yaya zai bawa umman yaya shi ke baki ya bawa kowa baya warewa ko cin zarafin mu wallahi be yarda wani yayi ba matar sa kuma akwai abin da ya hada mu itama tarata nake ina gab da fasa kwai danni nasan wace ita tayi haka ne dan nayi zuciya na bar gidan to gobe zan koma.... Abuja zanbi jirgin yamma...., da sauri ta ɗago tace "Dan Allah faisal bani labari me zaka tona...., Kinga tafiya ta in lokaci yayi za ki ji..... Kiransa ta shiga yi amma ina tafiya yayi ya barta cikin takaici.... *_* *_* _*_*......osokoro Abuja..... *_* *_* _*_*......osokoro Abuja..... Aysha inhar kika kashe auranki wallahi ba abin da bazan miki ba babban burina yau in baƙanta zuciyar Asif kamar yadda ya baƙanta min Alhaji munner sani jos ya faɗa cire glass ɗin ta tayi ta ɗora akan coffe table ɗin tace "Alhaji ke nan badan Allah kake sona ba dan ka kuntatawa Asif....rai zaka aure ni...., ajiyar zuciya ya sauke yace "Aysha kin sani cewa ina son ki faɗama ɓata baki ne in har kikau abin da nace to wallahi zaki shiga jerun manyan mata me yake dashi me yake baki mace kamar ke tana hawa ƙaramar mota wacce kuɗin'ta befi na miliyan talatin ba....., Kanta ne ya ƙara girma tace "Allah Alhaji wato dai nafi karfin wannan....?, baƙin ciki yake miki lokacin da nasaka aka baki ministan ilimi ai be goyi bayan ki ba saboda baya so ki ci gaba wallahi wannan maganar taka gaskiya ne amma ka bani lokaci in ƙara shirye shiryen da nake dan sai na tsiyata shi tas tukunna zance ya bani takarda ta yanzu ma haka bana gida jiya ya mare ni da sauri Alhaji ya ɗago yace "Mari kamar ke.... hmmm kai ma ka faɗa wallahi marina yayi tab ki ajiye duk wani hulakanci da yayi miki akwai ranar ramawa yanzu boom din da nake na haɗa mai shugaban ƙasa ya cire shi a kan matsayin'sa muga dame kuma zai yi kafafa ya faɗa yana buɗe wata a ƙwati Zaro ido aysha tayi tace "Alhaji wannan dalar fa...., ta kice ya faɗa yana tura mata rufewa tayi tana wani irin farin ciki burin'ta kuɗi kuma ta samu tace "Nagode sosai alhajina..., bana son godiya kinsan mu yan siyasa kudin nan abanza muke samu ya fada yana gyara babbar riga yace "Sai kin gama yanke shawara...sai ki kirani..., Ajiyar zuciya ta sauke tace "Babbar matsala'ta matar ka....., dariya yayi yace "Hajiya ni'ima ba ruwanta dake balle nihila ko Hanifah...., Allah ya sa ta faɗa tana gyara mayafinta a kafaɗa glass ɗinta ta dauka haɗe da jakar da ya bata ta fita ta baya shi ya fita ta gaba....... ********* Joseph, until you come back to the truth, hurry up Dariya Joseph yayi yace "By the way, I was also quick to come back, she said, is too mahaukasii she gave me trouble until you took a photo and she saw that I was stopping her from walking...., cikin mamaki Asif ya gyara zaman'sa akan kujerar da yake kashe tv yayi yace "who is mahaukaci among them but this woman did not say your name like that...., Domin yasan ita kaɗai zata iya aikata haka Cikin tabbatar'wa Joseph yace Yes, her name is crazy Kai Asif ya jinjina yace "You can go, but not her name, not her name....Falmata...., so this old man said to thank you Okay kawai Asif yace ya kunna labaransa ya ci gaba da gani amma abaɗini tunanin ne yayi mai yawa waya ya ɗauka ya kashe kallon ya nemo number umma har ta tsinke ba a ɗaga ba ƙara kira tayayi sai a wannan karon ta ɗaga ajiyar zuciya ya sauke yace "Assalamu alaiki umma Barka da dare.., wa'alaikassalam barka dai limahe ido yayi ji yayi duk wata damuwarsa ta yaye jin muryar umman'sa da yayi yace "ya kowa da kowa da fatan kuna lafiya Insha Allahu a cikin satin nan zan shigo aiki ne yayi min yawa..., Kowa lafiya Allah ya kawo ka lafiya Allah ya temaka ya naka iyalin Amin ya Allah Alhmdllh lafiya qalau ki cigaba da yimin addu'a kasar nan mara gaskiya ke tsira me gaskiya yana cikin wahala umma Kullum cikin addu'a muke maka Allah ya tsare ka ya ƙare ka daga sharrin abokan gaba Amin ya Allah Sallama sukai ya kashe wayar kiran muzabfar ne ya shigo ban za yayi dashi domin sai ya sashi ciwon kai be dena kira ba har sai da ya gaji ya ɗauka yace "Wai kai muzabfar naci bashin kane.....?, Asif Ka ganni nan naka cin abinci photo yarinyar nan nake gani tana yi min murmushi Joseph ya dawo ne zai gane gidan gobe fa zani zaka rakani Ba shiri ya kashe wayar zuciyarsa na tafasa wani irin gumi ne ya shiga yanko mai duk kuwa da AC da take aiki a floor ji yayi kamar an saka shi a huta to me ke damun sa ne daga wannan maganar ya juya lokaci ɗaya jin dafin maganar muzabfar yayi tamkar ɗigar dalma a kunnan sa zuciyar sa tamkar an zuba mata fetur an saka mata ashana an kunna...ta........✍️ Akwai cakwakiya fa kudai ku kasance dani a book 3 domin in warware muku ita an fara fa payment Ku hanzarta yi domin mallakar document zan yi sauri na gama tun da bakwa son paid group *GIDAN MAGAJIYA" EPISODE 31-32 Jefar da wayar yayi numfashin'sa na sama yana ƙasa da kyar ya dawo hayyacin'sa cije lips ɗin'sa yayi rasa me yake shirin faruwa da shine tashi yayi zaune ya ɗauki wayar'sa ya tashi bedroom ɗin'sa ya shiga kwanciya yayi a kan gado text message ne ya shigo mai amma sai yayi banza da shi can sai ga wani a jere har guda uku buɗe wayar yayi ya duba biyu na Aysha ne ɗaya na wata baƙuwar number ce zaɓar ya fara duba na aysha yayi buɗewa yayi kasa tantance anya kuwa idanuwan'sa gaskiya suke faɗa mai ko mai karantawa yayi a fili tamkar me koyar karatu ASIF tun kafin in kawo maka sammaci da kotu ka sakeni na gaji da auranka tunda har ka fara saka hannu ka dake ni wata ran duka za kai min wallahi Asif na gama auran Da sauri ya shiga ɗayan message din tun huri kafin in tozarta a idon duniya ka sakeni ......... kafin ya ƙara karantawa yayi sauri a fita zuciyar sa na tsananin bugawa tabbas zai nuna mata ya cika dan halak ashe daman haka halin dan Adam yake ya janyo'ta inuwa tana kokarin kai shi rana ta ɓata mai suna cije lips ɗin'sa yayi ya ɗauki wayar hannunsa na rawa ya fara rubuta mata saki kamar haka *NI ASIF KABIR SARDAUNA NA SAKI MATATA AYSHA SAKI UKU.... SAKAMAKON ITA TANE MA DA KANTA.....,* ajiye wayar yayi bayan ya tura mata kasa kiran mahaifinsa yayi ya sheda mai dan haka ya kwanta zuciyarsa na yi mai ɗaci daga nan bacci ɓarawo ya salallaɓo yayi awan gaba da shi ba tare da ya shiryawa hakan ba Washe gari da sassafe yayi booking ɗin jirgi saboda yana so ya je kano cikin Sa'a ya sami wanda zai tashi karfe ɗayan rana bayan ya gama ya ajiye wayar'sa ya ci gaba da aikin office a gida bayan ya gama misalin ƙarfe sha ɗaya ya shirya cikin ɗanyar shadda gezner ash colour an mai aiki monogram hula ya saka da agogo da suka dace da kalar kayan'sa sannan ya feshe jikinsa da turare me dadin kamshi da sanyaya zuciya ko breakfast be yi ba sai ruwan black tea da ya sha da wainar kwai sune har yanzu a cikin sa...... wayoyinsa ya dauka sai briefcase ɗinsa sannan ya saka baƙin glass fitowa yayi ya kulle part din nasa daman Joseph na jiransa yana fitowa buɗe mai mota yayi ya shiga jaridar da ya ajiye mai ya soma karantawa sosai aikin da wannan gwamnati keyi yake burge'sa shagala yayi da karatun jaridar har aka'zo Airport be sani ba sai da Joseph ya faɗamai ajiyewa yayi be jira Joseph ya buɗe mai ba ya buɗe da kansa ya fito rike mai briefcase dinsa yayi har suka isa reception Abin ka da babban mutum nan nan suka dinga yi dashi kowa kokari yake ya faranta mai kafin ya lokacin hawa jirgi yayi guri suka bashi ya zauna tare da drinks kala kala da snacks wayar'sa ya ɗauko kamar ance ya shiga gurin text message dafa kansa yayi lokacin da ya ci karo da text message din da ya yiwa Aysha be shiga ba be ƙara resending ba ya goge......be kamata ace ya sake'ta yanzu ba kamata yayi ya ƙaro aure taga be damu da ita ba tun da anata tunanin gani take bazai iya rayuwa in ba ita ba ci gaba yayi da operating wayar sa har lokaci ya cika tashi yayi be ci ko abu ɗaya da suka kawo mai ba da sauri Joseph ya tashi yabi bayan'sa karɓar jarakarsa yayi sukai sallama da Joseph ya fara taka matattakalar jirgin hawa yayi sai da Joseph ya dena ganin da ya juya ya tafi yana yiwa ubangidan nasa fatan nasara a special prevent seat ya zauna....... dauko wayarsa yayi ya saka a play mode ya ajiye ta magazine din da aka ajiye mai ita ya ɗauka labari mafi munu ya fara cin karo da shi.... Cire glass dinsa yayi ya ya ɗauki tissue ya goge idonsa ba raguwar zuciya gare shi ba amma musgunawa talaka da ake a ƙasar nan ya fara yawa sai yau she arewa zata zauna lafiya mutane basu da kwanciyar hankali a garuruwan su sosai ya kurawa gawarwakin da akai musu salla a jahar katsina wa yanda yan bindiga suka harbe ajiye wa yayi.......... ya shiga tunani wata kila wa yan nan da aka kashe akwai masu aure a cikin su kuma suna da ya'ya ya ya rayuwar ya'yan da suka bari zata kasance an hana matasa karatu babban burin su suyi wasa da kwakwalwar matasa lokacin zaɓe su fito su basu yan kuɗi kalilan su tada hankalin mutane wannan abin bazai yuhuba sai da rashin ilimi su basu kwaya hankalin su ya gushe su aikata abin da za su zo suna dana sani mara amfani rayuwar su ta ƙare a gidan yari ba batun cin ma muradin rayuwa..... yan zu a ƙasar nan ilimi na nema yafi karfin takala ga matsin rayuwa takai ta kawo yanzu zaka ji fara shi in anjima ya tashi ga man fetur din nan a ƙasar mu ake haƙoshi amma yana nema yafi karfin talakawa hutar lantarki daman ba'a maganar'ta......yan handama da baba kere sunyi oder sola suna so ta tafi in da tsayuwar huta ba batun siyan huta me amfani da hasken rana..... ganin wayan nan ire-iren tunanin za suyi mai yawa ya fara neman ɗauki gurin Ubangiji yana tasbihi belt ya saka sakamakon ji dayayi an sanar jirgi zai tashi a hali jirginsu ya fata tafiya har ya ɗaga sama......... Unguwar kofar mata* Ashe gida rahama ne tab ai sai yau na tabbatar da haka dinana da nayi bacci cikin kwanciyar hankali kai Allah ya sakama mana nifa ba fuskar da na tsana a duniya sama da wannan me kama da bishiya Dariya dinana yayi yace "Yanzu dai besan kina yi ba tawo muje in raka ki Abuja sai ki faɗa mai....., Banza tayi mai rabi ne ya sheƙe da dariya yace "Na'rantsai da Allah da kuwa in ta shiga ba zata fito ba sai sun ya galgala naman ta ai ni a gurin na gane Ni dan iskan karya ne ina washe garin mu ka kwana kana ga zuwa yayi cikin wannan cel din da ke kallo mu ya harbe wani...., zaro ido magajiya tayi tace "Kace har kisa yana yi haba shi yasaka Ubangiji ya ɗauke mai rahamar fuskarsa ba rahama a fuskar sa ko ɗaya nifa daman can baya burge Ni mutane suyi ta yaban'sa ai shi adalin shugabane....., Magajiya nifa nayi mafarki mun sha biki ya aure ki dinana ya faɗa yana danne dariyar'sa Wainar da ta zuba mai ita ta fara ƙoƙarin juyewa da sauri ya saka hannu ya ɗauka yace "Ya kyauta da zobe...?, harara ta watsai mai kahu da yake zaune yana jin su yace "Allah ne ya rufab asiri da tuni dani za a kama.., Allah ya rufa maka asiri kahu bulama da kaga baƙin tashin hankali wallahi baka da rabon fige kazar hawala da ka dauki darasi mai girma..... Hmmm Allah ne ya fidda a'e daga rogo Dariya dukkan su suka saka ban da magajiya da tun da abin da dinana ya faɗi ya ɗauke mata annurin fuskarta Radio ya ware kamar kullum domin jin labaran duniya ya tarar ma har an kusan gamawa sai karashe A wata majiya me karfi a yau ne shugaban hukumar Dass zai kawo ziyarar ba zata kano in zai taya gwamnan jihar Kano buɗe sababbin aikin da yayi..... Garin nan ya cika da masoyan sa domin tarbar'sa duk da be sanar da zuwan'sa ba a safiyar ranar Laraba ne aka kai mai hari gidansa da ke Abuja osokoro ya fito yayi kyakkyawan martani in da ya zargi manyan kasar nan da sahun'su akai mai hari duba da ce wa duk tsaron dake abuja har akawo mai hari ba tare da an kama ko da ɗaya daga cikin su ne... Inda ya kara da cewa indai akan yaƙi da masu mugun laifi ne saidai a kashe shi yasan ya tafi akan hanya me kyau da sauri magajiya ta kashe Radio tace "Haba kahu yanzu abin da mutumin nan yayi mana be baka baƙin ciki ba har ka tsaya jinsa daman sun fasa kan shege kowa ma ya huta...., karɓar Radio sa yayi yace "Yau nake ganin ikon Allah Ni nasaka su suyi maganar nan falmata.....? Baki ga mutuncin da mutumin nan yayi mana ba motar sa ya bayar a kawo mu..., Juyawa tayi ba tare da tace mai kala ba sajan bala ne ya shigo shi da kufur Musa washe baki magajiya tayi tace "Yau jami'an doka ne a gidan nawa...., Gujera suka samu suka zauna kufur musa yace "Munji kin dawo ai dole mu zo jaje kullum sajan bala kwana yake baya bacci masoyiyar sa na hannun wayan nan mutane...., da hallacan rufe min baki bindiga ce a hannun su bindiga ce a hannunku me saka da kuka ji haka baku zo ba kun karɓo mu ai wallahi sajan bala yanzu na gane ko na aure ka baza ka iya kwato min yanci ba me isaka ba zaka kai su kara ba ai naga kai ma kakine jikin ka duk kan ku matsayi ɗaya gare ku a son da nake maka yanzu ko rabi babu... Haba sweet a gaban wa'yannan yan hana ruwa gudu kike maganar nan ai sai suyi dariya kalle ki zukekiyar mace in narasa ki ai na shiga wani hali Wata uwar buɗa rabi ya saki yace "Chasss anayi muna jin dadi kai ashe zan ga wannan rana...., Sakar baki su kufur sukai sajan bala yace "Kai Wa kake wa wannan maganar..., kama ƙigiya yayi ya kauda kai yace "Da wanda ya tsargu....., lallai so kake kayi kwanan cel Dariya ya sheƙe da'ita yace "aini yanzu nafi karfin cel KO kaman ta inda naje dinana kora mai bayani ai wallahi yanzu bana kallon ku a matsayin wasu jami'an tsaro malam jeka Abuja kaga yadda ake jami'an tsaro....ba irin kuba yan kuci ku bamu...., Wata uwar buda aka saki da sauri suka bada attention domin ganin wazai shigo ɗaga labulan buhun da suka saka suka rufe kofar su ashe shagari ne yaci uban dauri ka kamar gwaggwaro baƙin nan yaci jambaki sai sheƙi yake..... Jar'uban can sweet rabi ke nake gani ko gizo idona ke min ta masar ya faɗa yana taɓe baki yawa yaga kashi ta uwar yan sa ido nice dai kema wallahi baki haɗu da gamon ki ba da duk wa'yan nan hannayen'ki da kike shanyawa yawa ganyen da ake so ya bushe tuni zaki dawo da shi dai-dai buga cinya yayi ya gyara ɗaurin zanin'sa yace "Allah ya rufa min asiri ba dani kukai harƙallar kuba da tuni dani za aci wannan kwakwar ta huya....., Dinana ne yace "Ai ta masar munga tashin hankali mabayyani ke cikina har wani karta min yake saboda tashin hankali....na rasa inda zan saka kaina..inji dadi..., Kama haɓa ta masar tayi tace "Kuce sunci ubanku la'ada waje...., ɗaya kenan magajiya ta bashi amsa kujera ya samu ya zauna nan fa labari ya barƙe tsakanin su kahu ma ya bada nasa labarin..... *Aminu kano international airport* A hankali yake taka matattakalar jirgin yake sauko wa yayin da akwai motoci wa'yanda suke jiran'sa tuni yan jaridu suka fara ɗaukan sa ƙara saukowa yayi tuni bodyguard suka rufa mai baya yana gaba suna binsa abaya da sauri jidda ta ƙwalawa hajiya kira tace "Hajiya yaya yazo kano zo ki gansa...., Ke bana son rashin arziki in nazo naga ba haka ba Alkur'an uwar'ki halima sai ta sani.... domin ba dama ku ga mutum a kwance sai kun kirkiri abin da zai saka ya tashi...✍️ *Kuyi hakuri da wannan ba yawa* *GIDAN MAGAJIYA* EPISODE 33-34 Tashi jidda tayi zata fita ganin hajiya na neman karyata ta bayan ta gani da idon'ta karo suka ci da ya akram da sauri ta ja baya tace "Kai hakuri ban kula ba..., Shigo wa yayi ya zauna cikin haɗe girar sama da ta ƙasa yace"yau she zaki kula tun da ba hakan kika saka a ranki ba..., Innalillahi ga mala'ikan yara na biyu yazo wato kai dai akram wallahi baka da kirki kai kenan kullum faɗa da yara to bazan lamin'ta ba tunda bakai ka haifar min ita ba ko uwar da ta haifi jidda naga ta saka mata ƙawon zuƙa irin na ka tun zan mata wankin babban bargo ko da yake kai fa dan gidan jummai Dubai in bakai ba ai Allah ya tambaye ka kaf cikin yan uwan mahaifiyar ku ita ka ɗai ce me sanyi sauran daga Attahiru sai hita jummai Dubai kuwa ai ita transformer CE ta fito tana gyara zanin ta tana faɗar haka ɗora kafa ɗaya kan ɗaya yayi yace "Hajiya duk wannan abin da kike basu san kina yi ba Bara in kira miki aunty jummai ita ce dai-dai dake wallahi...., Dun gurai mai kai tayi tace "ja'iri ce maka akai ina tsoron jummai Dubai ai wallahi yawon siyasa kaɗai zata nuna min amma ba dai iya faɗa ba kai wai fa a haka zamanin mu yayi sanyi da kai karya kake ka faɗa min zaka kirawo min jummai Dubai wace ita wace ita a siyasar Sardauna fa shugaban ƙasa ya riƙe irin nada ba na yanzu ba kuma a mulkin soja nan da kawai ɗorawa ake an zaɓa ko ba a zaɓa ba abin da sukai niya shi sukai na goga da manyan mutane Akram share hawaye tayi tace "Allah ya jikan Sardauna yasa can tafi nan kaga komai nasa Asif ya dauko har jan halinsa Asif na da shekaru goma sha biyar ya mutu muka baro Lagos muka dawo nan da zama kasan fa Asif ni na raine shi saboda mahaifiyar ku wallahi shashashar uwa ce tana fa jin naƙudar sa amma tana zaune ita da Maryam ita ma wata kashu in ba kashu ba tafa girmi Fatima ai zata iya fuskantar wannan hali take ciki...ko zama tayi domin ta ji daɗin bada labarin tuni daman jidda ta fita ta ci gaba da cewa ina baka labari dai suna zaune sai da ciwo yaci karfin'ta dariya ta sheƙe da ita tace To naƙuda kanwar uwar'ta ce harira fara share hawaye marayam tana ta zuba ni daman banyi tunain ma zata iya haihuwa da kan'ta ba domin har madarar yara na tanada tun da naga alamun cikin bafa ta ba ri ana ganin girman cikin kullum cikin hijabi kai abu yakai abu ta fara kuka haka maryam ta sanar dani da sauri na fito daman bacci naƙe da ido ɗaya..... Samin ta nayi a lokacin mafaya ma ta fashe kan ɗa yana kokarin tawowa da sauri na ɗagata nanuna Mata yadda za tayi yar banzan nan har da dogon wando a jikin'ta uban wace mata ciki in ya tsofa ana sa wando haka naci re mata shi cikin ikon Allah sai ga Asif a tafin hannuna ya duro Ni na saka mai ASIF nakuma hana a can za mai suna tunda Sunan Alhaji ya ɓata kowa sardauna shine ya maye gurbin sunan...... Kai in takaice maka dogon labari domin sai mu kwana munayi mahaifiyar ka tun da ta haifi Asif bata fiye bashi abinci ba da ya fara neman lalacewa tuni na dawo dashi gurina nake kula da shi har ya girma na saka shi a makarantar sai ta haife ka tare sukai haihu da matar kahun ka mamy kuke ce mata Kowa rana ɗaya kai da Ayman ita daman izzatu juya ce sai wayan nan sauran yaran suka biyo baya su inteesar jidda fa'iza basma mudai asalin mu yan kasar nijiyar ne buzaye ne daga ni har mahaifin ku zama ya kawo iyayen mu kano muka kafa tushe me girma mun taso da arzikin mu babban sojane sardauna Asif Hammad shine a salin sunan sardauna amma mutane da dama ko azamanin da yayi soja A sardauna ake ce mai.........mun yi rayuwa me dad'i ba faɗa ya rayu cikin iyalansa da ya'yan'sa ya ga wasu daga cikin jikokin'sa sannan Allah yayi mai rasuwa sanadiyar ciki me tsanani Allah ya jikansa da rahama kamar ance ta ɗago ashe duk surutun da take earphone ne a kunnan'sa pillow case ta ɗauko ta maka mai cikin faɗa tace "Zaka ci kaniyar'ka akram ni zaka maida Radio ka saka wa'yannan abubuwan ka toshe kunnan ka ina baka labarin rayuwar ku..., Cire earphone yayi yace "Haba hajiya ba ina jin kiba baki ji nace amin ba.., zo ka fitar min a gidan uwar...ka fatima kace amin ɗin yanzu ana tambayar tarihin rayuwar ka wallahi waɗuwa zakai domin baka sani ba dan nema zo ka fitar min duk ɗuwawun ku ya goge min yadin kujera ni'anya kuwa ba tusar da kuke min a kujera ba take koɗar min da yadi nidai ba arana sukai ba amma jiyar da suka koɗe to yau kaje ka siyomin wasu Turkiyya nake so kuma..... Assalamu alaika da sauri ta ɗago jin muryar da baza ta taɓa mantawa da ita ba komai shekarun da ta ɗauka bata ji muryar ba tace "Wa'alaikassalam Sardauna kai ne ashe gaskiyar jidda da tace ta ganna Ka a TV..... Sannu da zowa me gidana...?, Ƙara sowa yayi ya cire takalmin'sa ya zauna gaishe shi ta yayi zama tayi ta amsa yaya ina huni kazo lafiya Cikin mamaki ya kalli Akram yace "Lafiya qalau daman kana nan....?, Dan sosa ƙeya yayi yace "Eh wallahi sai yau zamu tafi nida Faisal da Ayman..., Kai ya gyaɗa yace "Yayi muku..kyau..., tashi yayi zai fita hajiya ta riƙo kafar'sa tace "Munafukan banza sai da nace zan fada maka suka ce ka sani shi kuwa daman wancan rasa kunyar ba'a magana da ashar ya shigo gidan nan an rufe mai gida yar gold ta hana shi shiga ya tafi guesthouse ya zauna....na kirata na ci mata mutunci shegiya yar gidan fakirai jikan nawa za tayi hawa haka kai ma ina ciki da kai ina maganar auran da nace kayi in baka samu ba zan wanke maka jidda na kawo maka..ita...., da sauri Akram ya jiyu zuciyar'sa na tsananin bugu haka Asif da har cire glass yayi yace "Jidda kuma hajiya....?, Wallahi tas zata zauna in da rabo ma saidai ka wayi gari ka ganta da ciki ai ita mace bata kaɗan ba'a raina'ta ta faɗa tana cika kafar Akram da kyar ya iya ɗaga ƙafa ya fita gyara zama Asif yayi yace "Maganar da ta kawo ni kenan na samu amma sai mun ɗan ƙara fahimtar juna gudun samin matsala sai in fada miki..., yayi haka ne domin ya kaucewa maganar hajiya me zai yi da jidda kanwar kanwar shi washe baki tayi tace "A ina take....?, tsintar baƙin'sa yayi ya furta Maiduguri bawai dan ya shirya faɗar haka ba tamkar sunan daga kasan zuciyarsa ya fito kamar daman yana kwance a zuciyarsa jiran maganar ya ke ya furta Masha Allah Masha Allah kace shuwa zaka ɗauko mana....?, kai ya gyaɗa haɗa rai tayi tace "To kaɗan gare ka fara gyaɗa kai magana nace kai min bance kai min zancen kurame ba...., shiru yayi mata be ce mata komai ba dauko wayarsa yayi yana danna wa kiran A'isha ne ya shigo be ɗaga ba haka ta dinga kira hajiya na zaune tana kallon ikon Allah can tace mai kana jii wayarka na ringing kaƙi dauka ashe daman kana sane kake ƙin dauka sai kace wai aiki ne yayi maka yawa sannu saƙago wanda baya hutawa.... tashi yayi ya ciro damin kuɗi ya ajiye mata a gaban'ta yace "Zan shiga ciki mu gaisa...., dauka tayi tana shi mai albarka ya fita wajan mamy ya fara shiga jidda yake zaune ta tashi tace "Yaya sannu da zuwa....?, yauwa yace ya zauna mamy ce ta fito tana washe baki matar uncle hamza tace "Yau babban mutum ne a gidan namu..., Murmushi yayi yace "Ina huni na same Ku lafiya...?, Zama taji a hannun kujera tace "Lafiya qalau alhmdllh ya A'ishah yi ce ko tana lafiya...qalau,, Alhmdllh lafiya qalau jidda ce ta dawo da tiry a hannun'ta ajiye mai tayi a gabansa ajiye kuɗi yayi yace sai an jima Da sauri mamy tace "badai tafiya zakai ba ba abin da ka saka a bakin ka...?, Eh wallahi Nagode ya faɗa yana miƙo mata kuɗi amsa tayi tayi mai godiya da fatan gamawa da duniya lafiya amsawa yayi da amin tun kafin ya shigo labari yajewa Hajiya jamila zuwansa dan haka tuni tafara ƙoƙarin aiwatar da shirinta saidai ta nemi maganin ta rasa sosai take neman inda ta saka amma ina nema take tana cikin nema taji sallamar sa duk A.C da take aiki a dakin nata amma ta jiƙe sharkaf da gumi fitowa tayi tana zare ido tace "a'a dan albarka ne a gidan namu...?, sam matar jinin'sa be haɗu da ita ba dan yaƙe yayi yace "Na same Ku lafiya..., Hhh eh wallahi lafiya qalau ya hanya Alhmdllh kuɗi ya miƙo mata amsa tayi tace "Badai tafiya zakai ba ko wani abu baka sha ba....?, tashi yayi yace "nagode ya saka kai ya huce....., dafe Kai tayi tana baƙin cikin rashin ganin wannan magani malamin ta yace shi ake kira da ƙare magana tana saka mai sai ya hauka ce...... *_Allah ka saka mufi karfin zuciyar mu_* `Amin ya Allah` Shashin izzatu ya nufa saidai tana kokarin fita kamar kullum dai waya take mayafin'ta na kafaɗa jin kamshin turarensa da baya ɓoya ta ɗago gyara annurin fuskarta tayi ta cire waya a kunne tace....... "A'a Asif kai ne a garin namu...?, takaici ne ya ishe shi me hali baya fasa hali daman abba zai gane ya sama mata aiki da yawon banzan nan da take tunda bazai iya hanata ba yace "Eh na same kula lafiya...., Lafiya qalau alhmdllh gashi ka same Ni zan tafi asibiti kanwar kawata aka kwantar a international wallahi ba abin da batayi min ba wannan kawar tawa shine ba wanda zai zaunar mata da rana sai Ni... Allah ya bata lafiya Amin tace tana kallon aljihun'sa da yake kokarin fito da ƙuɗi fito da su yayi ya miƙa mata da sauri ta amsa tana kirgawa tace "Hhh kace yau in fita jaka'ta da nauyi kasan yanzu mahaifin naka yayi ritaya sai kana dan temakawa saboda haka yanzu nake neman jari da zan dinga juyawa kafin pension dinsa ya fito abubuwan sai hakuri sun canza...., Okay zan duba ya faɗa yana shige ta gyara mayafin tayi tace "Kar ma ka duba me fuskar shanu...kawa nitsaya mutum tamkar bishiya kamar arzikin ka ace ka bani dubu hamsin wacce bata huce kwandala ba a gurin ka.., jaka ta rayata ya tafi tana mita yawa wanda yayi mata dole ta amsa... Da sallama ya shiga shashin mahaifiyar tasa da sauri inteesar ta fito daga kitchen tace "Wa'alaikassalam yaya sannu da zowa ina aunty Aisha...., Zama yayi a ɗaya daga cikin kujerun alfarmar dake floor yace "Yauwa ina umma...?, tana sama bara in kirawo ta kafin ta rufe baki sai ga umma ta fito cikin wani hadaddan swiss lace blue black da adon flower golding Sai zabga ƙamshi take abin ka da jikin fulani ba zaka ce ta haifi Asif ba hannayen'ta sunci jan kunshi ga sarƙar gold a huyanta da hannunta ƙarasa saukowa tayi da sauri ya sauko ƙasa yace "Ina huni...., Zama tayi tace "Lafiya lau kunzo lafiya..., da sauri ya ɗago yace "Lafiya qalau ni kaɗai nazo...., bata ce komai ba ta tashi ta shiga kitchen bata dade ba ta dawo jera kayan da ta dauko tayi akan dinning table tace "bisimallah kaci sa'a yanzun nan na gama abincin rana ...., ba musu ba ya tashi buɗe flask din Dan gidan voccum lafiyayyan alkubus ne buɗe na miyar yayi vegetable soup ce kamshine ya daki hancin'sa zubawa yayi daidai yadda yasan zai iya ci ya fara ci ƙarawa yayi ga kunun aya yaji kayan haɗi ga sanyi haka ya din ga cii......text ne ya shigo wayar sa buɗawa yayi na aysha ne tace "Asif kana daukan magana ta kamar wasa a da naso auran Ka amma a yanzu bana so ana dole ne ka sake Ni na wallahi na shirya tsab duk da a bin da kake taƙama na fika....juya kawai..zan je in auri me haihuwa irina gogewa yayi ya ajiye wayar'sa ajiyar zuciya ya sauke in aka ce mai A'isha zata aika ta mai haka tofa zai ƙaryata..... *Littafin nan A 50 zan gama book 2 domin payment din book 3 zaka iya biyan ta wannan account din* *8141785374 Amina Alhasan muhammand opay ₦500* *Ka turo da shaida ta nan 09061890481* *dan girman Allah in Baka shirya ba kar kayi min magana* *GIDAN MAGAJIYA* (Oum-yasmeen) *I'm not worried about insulting you the rooster that Allah intended to fight with, even if he is being bullied, he will do it......* https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k EPISODE 35-36 Book 2 Zai karyata hakan amma abin da ya lura kamar akwai wanda yake daga gefe yana zugata to waye....? bashi da me bashi amsa tissue ya dauka ya goge baƙin sa saki gyatsa tashi yayi dai-dai da fitowar umma huce shi za tayi yace "Na gama zan tafi..., Kallon'sa tayi tace "To Allah ya kiyaye hanya.., ba Abuja zan koma ba zan dan jima anan zan tafi dakina ne Shiru tayi tana nazari tukunna ta kalli ɗan'nata cikin tausayawa be yi sa'ar mata ba ko lokacin da yace zai aure Ita dai cewa tayi Allah ya sanya alkairi dan sautari tasha kama shi yana yiwa kansa Allura ta rage feeling ta hanashi ya koma shan magani irin su Asif ba'a so su jima ba tare da mace ba....dan akwai wani ciwon ciki da yayi yawa ya mutu ajiyar zuciya ta sauke tace "to... Allah ya kai mu lokacin tafiyar taka.., Amin yace fito da kudi yayi aljihunsa ya miƙa mata amsa tayi ta sanya masa albarka wani sanyiyaji ya ratsa fita samin hajiya yayi tana zaune tana kallo ga jidda a gefen'ta sannu da zuwa tayi mai hajiya tace "Ga abincin ka na saka jidda ta dafa maka danni yau banyi niyar cin abinci ba....., naci ya faɗa a takaice haɗa rai hajiya tayi tace "Wannan fa da nasaka aka girka maka...?, cikin gajiya da maganar da Hajiya ke saka shi yi tunda yazo yace "Hajiya nafa ƙoshi...., fita yayi yabi ta wata karamar kofa dake kallon wajan dining din turawa yayi ta buɗe corridor ne da yar baranda an ƙawata shi da flowers masu kyau har wani kamshi suke fiddawa ta cikin baranda ya shiga wani waje ga wata ƙatuwar glass door turata yayi tuni ta buɗe wani haddadan floor ne me kyau da tsaruwa dafa kansa yayi lokacin da ya tuna be fito da briefcase dinsa ba tana mota mutane sun gajiyar da shi tun da ya sauka ya huce government House sai da aka gama taron ya dawo haɗi da buɗe wani sabo. Aiki da gwamnar yayi na gina sabuwar gada wayar sa ya dauko ya kirawo Akram bugu ɗaya ya dauka cikin bada umarni yace "Akram kazo dakina ka karbi key ka ɗauko min briefcase dina a cikin mota..., Cikin girmamawa yace"to...., Kashe wayar yayi yana kallon ko ina na dakin yana tuna rayuwar'sa ta yarinta sallamar Akram ce ta dawo dashi da ga dogon tunanin da ya waɗa ɗagowa yayi ya amsa ya mi ƙamai mukullin amsa yayi ya juya be wani ɗauki dogon lokaci ba sai gashi ya kawo mai amsa yayi ya ajiye yace "Thanks..., kasa kasa yawa me ciwon baki indai halin yaya ne inda sabo sun saba shi haka yake tashi yayi ya kulle bedroom ya shiga sai kamshi yake zabgawa da sauri ya fito..... yace "Hajiya badai yaran nan ne ba suke gyara min ɗaki....?, Wannan yaron ne Ubanka ne kabiru ke gyarawa ta bashi amsa a gatsai domin dazu ya ɓata mata rai da yaƙi cin abinci..... komawa yayi ba tare da yace komai ba dan yasan yace zai biyewa Hajiya akwai matsala ita haka take so.. bedroom ya shiga ya fara cire kayan sa daga shi sai boxer ya shiga toilet cire boxer yayi sakarwa kansa shower limshe idanuwan'sa yayi da sauri ya buɗe sakamaƙon ganin fuskar falma'ta tanayi mai gizo...... Sauri yayi ya gama wankan Saboda ya tara gajiya yana fitowa kaya kawai ya ja blanket addu'a yayi sannan ya ƙarasa lulluɓa ya kwanta na dade'wa bacci yayi awan gaba da shi........ `Unguwar kofar mata` Ina magajiya take da sauri magajiya ta ɗago ta kalli kofa wata mata ce da dattijuwar mace kallo ɗaya tayi musu tasan bada arziki suka zo ba tace "Gani ko naci ban biya ba....?, Ƙarasa shugowa sukai matar tace mata ke saurara tsohuwar kilaki zuwa mukai in ja miki kunne akan mijina tashi magajiya tayi ta sheƙe da dariya tace "Baki ƙarya ba danni nan da kika ganni tatatciyar yar iska ce duk da abin da kike zo dashi tofa ki shafa fatiha kin'samu dai-dai da kugunki......, Ba shakka mama kinga ko ashe labarin da aka bamu zan zo na tarar da haka tafi magajiya tayi tace "Gaskiya tsohuwa sun cuce ku basu baku daidai ba...., Salati tsohuwar nan ta saki tace "Bilkisu bala ya dauko miki ruwan dafa kanki..., Sai yanzu ta ɗauki haske ashe matar sajan Bala ce bilkisu tace "Wallahi kika sake kika shigo gidana wallahi zaki ga bala'i da tashin hankali ganin idon ki....., to ai baki san nice bala'in ba da masifa har tashin hankalin duk nice ke je kijawa mijinki kunne ya fita harka ta inhar kin isa dashi ko da yake yace fa baki iya tarbiyya ba zai auro me mai wa ya'yansa tarbiyya ba irin ki ba tunda nima gashi nagani ba a sami tarbiyya tun daga gida inban da rashin tarbiya ace uwa ke rako ya' gurin budurwar siriikinta tir da halin ku ga hanya nan tun kafin in nuna muku irin nawa tashancin ku tattara yan'matan ƙafafuwan ku ku barmin gida ko in saka ayi ƙasa ƙasa daku ta faɗa tana muci muci da idon'ta Bilkisu zo mu tafi a'a mama wallahi yau sai naga wanda ya tsaya miki karuwa dariya magajiya tayi tace "Daga nan hotel hotel muke zuwa da mijin'ki yanzu waka ma ciki ne dani...., Mama kinji ko innalillahi yowa kanta zata dake ta ji tayi an riƙe hannun'ta da sauri ta ɗago dinana yace "Ke har wace zaki shigo har cikin gida ki ciwa uwar dakin mu mutunci wallahi kinci karya kin zo gidan da har gurin dass munje mu dawo balle ke matar ƙaramin alhaki dan sanda...., Kuka ta saka tace "Ta tabbata mama gidan karuwai muka zo...., Sakin'ta yayi yace "tantagarya kenan in kina neman gidan karuwai da ya amsa sunan'sa karuwai kika zo GIDAN MAGAJIYA sha fatiya da salatin annabi in da hali haɗa da kurhuwallahu three three in miki ta turawa...., Kama hannun'ta mahaifiyar ta tayi ta goge kwallah tace "Kema mace ce za ai miki abin da yafi wanda kikaiwa ya'ta...., Komawa magajiya tayi ta zauna tace "Da kar ku tafi wallahi in saka a karya muku ƙafafuwa...., basu ce mata kala ba suka tafi..... dariya dinana yayi yace "Magajiya magajiya magajiya tamu wanda besan ki ba ya shiga uku a yau she sajan Bala yayi miki ciki......?, juya wainar'ta tayi tace "Kaɗan ka gani sun zo da bala'i ne sai suka tarar da wanda ya fishi....ko kahu....?, zare ta gumin da yayi yace "Falmata Allah ya kawo miki miji na aurar dake na huta kwanaki kin jamin bala'in dass gaba kuma bansan name zami jamin ba....., Hada rai tayi tace "Alkur'an daman nasan zamu sha gori....gurin kahu..., Rabi ce ta fito da ga bayi riƙe wando zanin'sa kuma a ƙafaɗa yace "Magajiya anya kuwa da kafafuwa a jikina dan Allah ku duba min ko sun cire....kashi nayi me ciwo......., Innalillahi a'a ka gan'su nan a saƙale a kofar banɗaki kahu ya faɗa yana jifan shi da harara.... kallon kofar bayi yayi yace "Ban gan'ta ba..., kai karka raina mana hankali bana zaka fito ko sai na jefo ka...... ka dawo daga gidan yari dole ka dawo da iyashegen'ka dinana ya faɗa.... Aini kaga na rasa bakin magana deeni in banda tsohon iskanci yace a duba mai kafa a'a kai za a duba maka cewar magajiya..... Kyale dan kut..tumar uba jira nake ya ƙaraso na danfara Shi da ƙasa zai yi explainesha (explanation) dala dala nine har da tafiya Abuja cikina duk ya kunbura dama ba muje ba sun harbe maka kafa da hannu ka shanya su da hujja manjagara ya faɗa yana zare ido irin na tsofaffun yan daba aaa wannan kuma har damu kake manjagara kafi to fili kace mun ishe ka tsohon dan wiwiii....dinana ya faɗa zaman dirshan rabi yayi yace "Wayyo ƙuguna na shiga uku zan rasa kugun haihuwa....., Iccen hutar magajiya kahu ya ɗauka ganin kamar kahu gunsa yake yowa ya tashi ya fita a guje yabar zanin'sa kahu yace "Kun ga dan iskan karya ko da ya tsaya na babbaka mai kafafuwa sai ya faɗa mana tana jikin'sa ko kuma tana saƙale a kofar bandaƙi....., Gafaran ku dai masu gida ba'a rasa ku da tashin hankali asho ya faɗa yana shigowa harara magajiya tayi mai tace "To gama abin ka wallahi bazan bada bashi ba..., kuɗi ya zaro yan hamsin hamsin yace "Yau da gwarina nazo....., Dariya su sauda suka saka suka daka ta da cacar da suke to yan bani na iya kuji da abin da yake gaban ku.... kallon'sa ba suyi ba suka ci gaba da buga cacar da suke kujera ya ja ya zauna ya miƙa mata yace "Bani ta duka...., Kirgawa tayi tace "Naira dari biyu ce fa...., Kinga kina gallakaikai da kudin nan nasan darajar'su in ba zaki bani ba bani kuɗi na ina gangarawa Yakasai zanci ta hadiza uwar yan daba... dariya ta sheƙe da ita tace "Dinana jiye min wannan magana.....✍️ Ana ta payment fa me kuke jira zuwa 50 na gama book 2 *8141785374 Amina alhasan Muhammad opay* *Ku turo receipt kai tsaye ta wannan number 09061890481* 500 Yan nijar Cameroon Katin VTU ta wannan number 09061890481 yan nijar katin Airtel na 300fcfa ku ɗauke shi kuturo ta wannan number 09061890481 *Only WhatsApp* *Dan Allah in baku shirya ba kar kuyi min magana* *GIDAN MAGAJIYA* EPISODE 37-38 Kaf faɗin unguwar nan wacce waina ce me dadi sama da tawa....? Wallahi babu uwar ɗakina ko zaki temaka ki bani ko fefe ɗaya ce da shinkafa da taliya da miya har da bama in dan na samu kyamini total na biya.... turo ɗaurin'ta gaba tayi tace "Banji me kace ba mai mai'ta injiii...., ba sai ya maimaita ba kawai kice bazaki bayar ba sai zaman kashe wando ba sana'a wallahi ka cuci kanka mu da ake ganin mu gamu ga munan to mu ke sana'a har mu samu abin sakawa a maƙoshi bama maula Maza zuby tofar da mugun yahu da inyi wannan sana"ar taku ta karuwanci yasin gwara in mutu banci ba lallai yarinyar nan kin ma raina min hankali ai kuwa zanyi maganin'ki ya faɗa yana kokarin ciro reshen bishiya ihu ya saka sakamaƙon kaɗan gare da ya hau jikinsa ihu ya saka da sauri kowa ya fara neman hanyar gudu har magajiya duk son wainar'ta da take haka ta tsallake ta barta kawu da yake cikin bayi ya na ƙoƙarin rufe wa dinana yayo kansa ihu ya saki yana cewa na shiga uku karka sake ka.....shigo min be ida rufe bakinsa ba ya shigo fita kawu zai yi amma ina dinana ya riƙe shi yana kuka rasa yadda zai yi saboda tashin hankali.... cikin ikon Allah ya sauka daga jikin dinana yabi ta tarariyar banɗaki ya fita...... duk da haka dinana be saki kawu ba sai ma ƙara rukunkume shida yayi....tun ƙuɗashi kawu yayi ya waɗi..... taka wa shege ruwanci ki rabi ya faɗa daya shigo yanzu.... Tashi dinana yayi yace "To dan kumbura masifa zo kai ka taka min ruwan ciki kaga yadda ake bura....uba wallahi....., Rabi aini na rasa bakin magana me yahana Kai da ka shigo ka taka min huyan'sa so yayi ya rungume'ni mu mutu tare da yake Allah almusawweru ne kuma adalu sai ya ƙara ruƙunƙume shi ya kasa barin jikinsa..... Dariya rabi ya dinga yi harda riƙe ciki ya gyara daurin zanin'sa....yace "Allah ya temake ni bani da rabon huya kawu kawai harsaso yadda gudun ƙadangaran da kuke nake...., tsaki kawu yayi ya huce shi bin kawu yayi yace "Kawu dan Allah wai yau she zaku koma Maiduguri...., Lokacin da uwar... ka salamtu ta shirya dinana ya bashi amsa tsaki ya ja ya murguɗa baki yace "Bandai kasa da mutum ba balle ya dauki kaso shege dama director na DSS ya harbe maka kai kowa ya huta haka ya dinga damuna da kuka yana face majina...., Zama dinana yayi a kan farin botikin uwani zame shi uwani tayi tace "Sau nawa zan faɗa maka ka dena zaunar min a kan botiki kaƙi to wallahi haka zan dinga yi maka kana zama ba magana zan zame ka ko ka yi hankali....., tab har abada wannan dai bazai hankali ba to ma duwawun nasa nawa yake da har zai fasa miki botiki da kinyi hakuri ko ki saka kunama yana zama ta sheme dan iska........kowama ya huta yayi jinya ko ta kwana ɗaya ce ko ma sarara KAWU Ka lura ka gane duk inda ka saka sabga da dan daudo ana tare da rashin nasara Ubangiji ne fa yayi hani da daudo shikkenan KAWU munga ta kanmu baka bina bashin rantsuwa yanzu haka jarin da MAGAJIYA ke baka yana rushewa nima yar sana'ar da na fara abun yaƙi arzki ba mamaki Ubangiji so yake ya ganar damu illar abota da fasiƙi amma munƙi fahimta duk inda ƊAN DAUDO yake to aminin KARUWAI NE.... Karuwa tana gidan malam hamisu zubaida ta faɗa tana wani girgiza haɗi da taunar chingum tana yi mai kallon tara saura kwata.... Dariya Rabi yayi yace "Dadina da gobe saurin zuwa godiya nake zuby ta waje na...., mayafin'ta taja a igiya ta kalla mai harara tace "Da hallacan matsamin zan huce uban haɗa husuma wallahi rabi kaidai anyi munafiki...., Kai tab gaskiya na lura ba a cikin hayyacin ki kike ba kin dawo wacce ta fi karfin ki yar tasha zo ki huce.... fita tayi har taje soro ta leƙo tace "Inka isa ka biyoni..., banza yayi mata dariya dinana yayi yace "Anayi muna jin dadi a hayye rasss...chasss warrrr Sai kawulliya namu na gargajiya Kawu ne ya magantu yace "Dinana ina jin ka ƙarasa sai akai yaya daman ni na dade da sanin cewa mutanan nan da falmata ke haɗawa abin da suke zunubin har dani...., Au kawu baka da labari tab makaranta nakoma ta addinin Islama kaga muwadda maliki a koya mana sai wannan abin ko uhmm na manta nafi dai riƙe muwadda maliki din nan yauwa Riyadursahali magajiya yama ƙarashen....sa? kaga kar ka sake ka sani a cikin wannan shirmen naku gabaki ɗaya ba daidai ka faɗa ba ka tubarwa Ubangiji..... Hhhh chass wayyo dad'i kaga ulama'u magada annabawa KAWU ka fahimta ko inyi maka bayani dala dala tashi KAWU yayi ya shiga daki ba tare da yace ƙala ba sosai rabi ke dariya yana cewa ulama'u masu aiki domin Allah wa'azi bako sisi kwafaɗawa mutum Allah yace annabi yace...... abin dariya ya bawa magajiya ta taya shi suna ciwa DINANA mutunci..... kuwai wallahi me iya muku sai Allah baku da gwani wallahi Allah ya shirye ku UWANI ta faɗa tana tur da halin su UWANI dadina dake kwai faɗar TRUE wallahi yanzu dai tela musu suji yadda ake zaman duniya RABI ya faɗa sanin hali ba mutunci ne da su ba yanzu zasu haɗe mata kai su dawo kanta sai ta ja baƙin'ta ta tsuƙe tana yi musu fatan shiriya in suna da rabooo... ✷✷✷✷✷✷⁠✷⁠✷SOKOTO BIRNIN SHEHU Nabeela nabeela wani kallon hadarin kaji tayi mai tace "Na'am ina jinka....?, Kai ya gyaɗa yace "Na lura kullum rashin mutuncin ki ɗaga gaba yake nagane abinda kike nufi saidai har abada baza ki samu ba ....., dariya tayi har da tafi tace "Ai Allah kalle ni da kyau haladu nafi karfin ka na huce a jikin ka da ka amshi kuɗin ka da kar ka amsa duk uwar....su ɗaya ka saka a ranka kamar na auri ASIF ne na gama...., Haka kika ce....? Juyawa tayi ta fara tafiya komai ta tuna sai ta tsaya tace "Wannan shine kashe di na karshe da zan maka haladu kar ka sake in ƙara ganin wa yannan matattun ƙafafuwan naka sun zo kofar gidan mu in ba haka ba wallahi sai na saka yan iskan garin nan sunyi gunduwa gunduwa da naman ka ka kalle'ni celebrity dani kace ni zaka aura ni wallahi bansan hau din da ta hauni ba har na'amin ce da ka turo gidan mu......., gyara zaman hularsa yayi ya tsura mata ido har ta gama maganar'ta ta shiga cikin gida tana wata iriyar tafiya ajiyar zuciya ya sauke ya tafi yana mamakin nabeela Cikin gida kuwa inno ce tsaye a tsakar gida sai kai kawo take nabeela na shigowa tace "Ta gaban mota ya kukai kin kora mai bayani da manyan baƙi ko yaya....?, cire maya'fin'ta tayi tace "Inno wallahi sai mun haɗa da bokaye ayi mana farraƙu dashi har fa yanzu yana kan bakan'sa kinga kuwa a kwai gagarumar matsala...inno na aure ASIF wallahi bake ba har kaka sai ta huta kuɗine ba iya ka lokacin da naje Abuja fa inno kinga company sa .....hmmmm abin ba a magana makkan nan da take tsada inno ki ɗauka kinje'ta kin dawo....., Dan Allah nabeela.....? Hmmm babban fa mutum ne kedai kawai ki tayani da addu'a kwanaki da naje Abuja ban ganshi ba wallahi To Allah ya temaka Bazai taɓa temaƙon ku ba akan muguwar niyar'ku wallahi sha'awa kin ban mamaki me maƙon ki ɗorata akan turɓa ta gari kece me ƙara ingiza ta gurin aikata ɓarna ita ba duniyar nan dakike gani a yadda ka ɗauke ka haka zata ɗauke ki in ta tashi juyi dake ta faɗo dake a tsakiyar rana..... haɗa rai tayi nabeela kuwa tashi tayi ta bar gurin tana ƙunƙuniiii..... Sha'awa magana fa nake kinyi shiru ɗagowa tayi kamar wanda wani abu ya tsikare'ta tace "Uhmm malam me kace ban jikaba saboda abin duniya ya isheni.....?, ƙwafa yayi dajin wannan rainin hankali irin na sha'awa ya fita daga cikin gidan yana yi musu fatan shiriya Allah ya ganar dasu gaskiya da basu ikon bin'ta.......... OSOKORO ABUJA Gaskiya A'isha abin da kikai baki daidai ba wannan fa zunubi ne babba da auranki ki dinga soyayya da wani a waje har kuna kokarin kulla aure in hankali ya gushe tunani be kamata nima nawa ya gushe ba in bi son zuciyar ki mata wane ne suke neman damar ki basu samu ba mata nawa suke bin mijin ki...be basu dama ba saboda yardar dayayi miki amma gashi Saboda son abin duniya zaki watsa mai ƙasa a ido mene ASIF be miki a rayuwa ba wallahi kin ban mamaki inza ki fita daga harkar Alhaji manneru ki fita dan wallahi kai ki zai yi ya baro ki amfani yake dake a lokacin da kika gamemai aiki keda banza duk ɗaya...... Hafsah kin gama nace kin gama tashi tayi tsaye ta ɗaga hannun tace "Yi min shiru munafuka ban saka da ke ba inhar ba zaku faɗa mata gaskiya ba be kamata Ku zugata ba wallahi tunda nake banta ɓa ganin wannan tashin hankali ba ba mamaki bokan'sa ne ya sa shi ya nemi matar Aure ko da yake Alhaji shi kansa shu'umin kansa ne kina kuwa da hankali ki bincika ME YA SAKA ASIF YA KAKA ALHAJI MANNIRU SAI DA WANNAN GWAMNATIN TAZO TA FITAR DA SHI....., tana kaiwa nan ta dauki jakar ta kamar kububuwa ta fita a fusace gyara zama Aisha tayi tace "Wallahi bestie sai yau na gane halin Hafsah ashe maƙiyata ce ban sani ba tana yi min baƙin ciki dan nabar ASIF saime...shidin autan maza ne matan da suke son'sa Suma dan basu san waye shi bane da sun sani wallahi baza su so auran'sa ba A'a a'a bestie banda sharri ko munan fa muna sha'awar ki wallahi ba zaki gane mene rayuwar zawarciii sai kin fito zaki fahimta kingani ina da kudi dai-dai musali amma abin tashin hankalin shine kowa da irin kallon da zai maka wani ma tahin wulakanci zai maka musamman wannan mazan namu da muke aiki tare abin da hafsa take faɗa miki gaskiya ne.... wallahi hajiya ni'ima zata iyayin komai dan ganin ta sulwantar miki da rayuwa kin san kuwa bata barin kowa ya raɓi mijin'ta ko ni da nake matemakiyar'sa Hmmm kallon hadarin kaji take min Wallahi ta dade batayi ba kinga nifa ba gudu ba ja da baya suka tafa da wata ta kusa da ita Allah ya ganar dake wace rufaida shedaniyar mace ce in baki sani ba yau ki sani yanzu haka ba mamaki kan'ta take yiwa wannan faɗan daga ta kautar dake saidai kiji ana buɗa....rayuwar yanzu ba yadda kowa mugun kansa ne ƙalilan ne na Allah Da kata MUSEENA tunda kuka shigo cikin wannan gidan nawa kuke fadar duk abin da ranku ya ga dama amma wallahi bazan yarda da cin mutunci ba zo ki fitar min daga gida ba saikin ce in fita ba daman fitar zanyi ke kuma A'isha Allah ya ganar dake ke da mahaifiyar ki idon ku ya rufe kun kasa ganin gaskiya ASIF garzone ko a cikin mazaje tana kaiwa nan ta fita dariya suka sheƙe dashi suka tafa........ *KANO TA DABO TUMBIN GIWA* N.N.D.C quarters KARFE 9:30 na dare Dan Allah Asif, please give me the address of their house, if you do not accompany me, I will go alone..... tamkar MUZABFAR da dutsai yake domin ci gaba yayi da aikin da yake a cikin laptop a zahiri kenan amma a baɗini shi kaɗai yasan irin bugun da zuciyar sa yake yi yana danna keyboard ɗin laptop din ne amma besan me yake ba rubuta wa ba ji yayi kunuwansa sun toshe ba abin da yake iya ji sai maganar MUZABFAR ina zai saka kansa in hakan ta faru shi kawai ko wani ne ya aure'ta amma ban da MUZABFAR komene dalili wata zuciyar ta tambaye shi I dont no shima be sani ba Amma duk wani bugu da zuciyarsa keyi tare da tunaninta take yi mene dalili anya kuwa ba ɗaukar fansar abin da yayi mata ba za tayi............... Yan aljanna me ke shirin faruwa Domin samin amsoshin ku kudai ku ci-gaba da payment a yadda naso ina gamawa in dora book 3 hakan bazai yuhuba sai kun ci gaban da payment wasu jiran document suke Please zan da masu jiran document da masu pages Ku biya ba lallai ne ma in bude group ba wata kila kafin na gama book 2 zan kammala book 3 amma sai kuna karfafamin gwuiwa ta hanyar payment Zaku ga kwana biyu bana yi da yawa ace duk son da kukewa GIDAN MAGAJIYA MUTUM BIYAR NE SUKA FARA PAYMENT haba yan aljanna ku nuna min so na karshe mana daga wannan fa hutu zan tafi...... Shi yasa ka na tsaya nayi dogun tunani domin faran ta muku da wa'azantar da ku ta hanyar nishaɗantar'wa Ni Fatahiyyah Muhammad yakasai nake cewa mu huta lafiya 09061890481 Domin biya ta kai tsaye ku sakamin a wannan asusun 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay Ku turo da sheda ta wannan number 09061890481 Dan girman Allah in baki shirya ba kar kiyi min magana *GIDAN MAGAJIYA* PERFECTLY PEN'S ✊ https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k EPISODE 39-40 ASIF tunanin me kake yi.....?, kodai kana shawara ne ka rakani ko kar ka rakani dan girman Allah ka raka ni ka temaka min ka ceci rayuwata kasan kuwa saboda kai'ta na bar Abuja na tawo....? tashi ASIF yayi amma ina ji yayi baya ganin komai dafa bango yayi ya runtsai idanuwan'sa yace "Please MUZUBFAR ka fita hutawa nake so nayi maganar ka tana damuna..., ASIF kana son FALMATA amma kafiyar'ka ta hana ka gane inza ka farka ka farka wallahi ina guje maka randa zaka wayi gari ace maka tayi aure lokaci ya kure ba damar maida hannun agogo baya.... Fita yayi daga daƙin ya bar MUZUBFAR a tsaye da sakakken baki yana mamakin hali irin na ASIF ga gaskiya nan amma yana kokarin karyata zuciyar sa da hana'ta abin da take so... bin bayan'sa yayi samun'sa yayi a zaune akan kujera ya dafa kan'sa da hannuwan'sa biyu zama yayi a kusa dashi yace "ASIF...., a fusace ya tashi yace "Kai baza ka mai dani dan iska ba wacce budurwa ce za'a je mata karfe tara ta fito indai tana da makwaɓi.....?, ajiyar zuciya yayi ganin ya sauko be yi tunanin abin da zai fito daga bakin'sa ba kenan yace "Eh naji mu tafi in bata fito ba shikkenan sai mu bari gobe maje amma fa...., Saurin tarar numfashin'sa yayi yace "Wallahi kana magana na fasa..., Yi hakuri oga muje harara ya banga mai ya shiga bedroom ɗin'sa jiransa MUZABFAR yayi har ya ƙosa kamar ance ɗago kansa dai-dai da fitowar ASIF sanye da riga red colour da wando baki yan gidan TOM FORD haɗe da P-cap Black color ha saka face mark dariya abin yaso ya bawa MUZUBFAR amma sai ya mazai daukan keys yayi binsa a baya MUZABFAR yayi har suka isa gun ya ajiye motar'sa Allah ya temake su Hajiya bata ga fitar'su ba domin data gansu tsare su za tayi da zance.... Wajan driver MUZABFAR ya shiga ASIF ya zauna gurin me zaman banza kome ya tuna har ya shiga ya fito ya dawo gaba wayar'sa ya fito da ita yana dan-dan nawa da alamar wani abu me mahimmanci yake yi sai da suka fara hawa kan-titi tukunna MUZABFAR yace "Allah ya ja daran oga mun hau titi fa yanzu ina zamu....?, Ba tare da ya ɗago ba yace "kai daman baka sani ba....shine ka jawo'ni....?, daman da address ɗin da su HABIB suka turo maka dashi zamu ni ban sani ba ranka ya dade oga... okay muje Unguwar sai ka tambaya be cemai kala ba ya ci gaba da tafiya har suka iso asibitin MURTALA ci gaba yayi da tafiya har suka iso kofar mata be mai magana ba ya fito wasu mutane ne zaune masu saida mai abakin titi sallama amsawa sukai sannan yace "Dan Allah tambaya nake....., Wani da yake gyara jarkar mansa yace "Allah ya saka mun sani....?, Amin GIDAN MAGIJYA nake nema da sauri wani yace "Kaga wannan shagon to in kuka miƙe zaku ga wani gida kofar'sa a cire da mutane nan ne gidan..., Godiya yayi musu ya juya baya yana ji wani yana cewa tab yau magajiya ta ɗebo ruwan dafa kanta jar ubancan anya kuwa ba mutanan da suka kamata bane suka dawo....ba Juyawa yayi ya buɗe mota ya shiga suna ta ce-ce kuce ko kallon arziƙi be samu ba shi abin nasama dariya yake basa gudun samin matsala sai ya danne tada motar yayi suka shiga cikin layin ya gane gidan tun daga nesa a kusa da kofar gidan yayi parking yace "Oga Munzo fa....., Sai a lokacin ya ɗago yace "ka fita mana dole sai na raka'ka....?, ajiyar zuciya MUZABFAR ya sauke yace "ASIF kai fa na kawo...., da sauri ya ɗago dai-dai saukar MAGAJIYA daga kan mashin sanye take cikin doguwar riga me haɗe da mayafi amma mayafin bata rufa ba yana kafaɗar'ta sai hular chetili da tasaka ta rataya ta jirgita ta tazo mata har ciki shiga cikin gidan za tayi me mashin ɗin ya kashe mashin dinsa da sauri ya tare kofar da sauri MUZABFAR ya kalli inda ASIF yake kallo da yake unguwar da wadatar haske ko ina da kwan lantarki su kuma ba'a iya ganin'su saboda motar me tinted glasses ce ASIF yayi yace "Malam in baka da abinyi ni da shi...., ASIF kamar fa faɗa suke da me mashin ɗin nan a'a dambe suke da hallacan ka jamu mu bargun nan wallahi bana kaunar ganin mata marasa kamun kai jibe'ta ASIF shigar da tayi kabaƙi ɗaya ba shigar banza bace me tayi na rashin kamun kai hawa mashinɗin da tayi ko kuwa faɗan da suke dame mashin ɗin kasan me ya haɗa'su wata kila ita ce da gaskiya ko shine..... banza yayi mai ya balle murfin motar ya fita yana ƙarasawa ta ɗaga hannu ta mari me mashinɗin tace "Narantsai da Allah wannan ka ɗan nayi maka harni zaka kawowa maganar banza nayi maka kama da irin wa'yannan matan ne saboda tsabar rainin hankali nace ka kawo ne gida zan baka dubu ɗaya saboda karfe goma tayi an saka doka shine zakai amfani da wannan damar ka ce min 2500 kabi a hankali wallahi baƙaramin aikina bane ince bazan bayar ba....., Kika mareni....? Juyowa tayi ta kalli ASIF cikin tsuwa tace "Malam lafiya kazo ka tsaya mana wallahi kome zaka ce bazan bayar ba dubu ɗaya zan bashi tun daga zoo road ka dauko Ni kace sai na baka 2500 ban da uwar a sara da na tabka me ɗinkin be mini ba...., Wayyo Allah wai ita wannan wacce irin mace ce haka haka ya faɗa a zuciyarsa afili kuwa ciro kuɗi yayi a cikin aljihun'sa dubu uku ya miƙawa me mashin yace "Gashi tafii..., ba musu ya amsa yace "Wallahi kinci darajar wannan bawan Allah da yau zaki san ke mara kunyar karya ce....., bisimilla zo wallahi Allah in Ka fita da kafarka Ka godewa Allah domin sai na saka anyi maka dukan tsiya irin kune kuke kuntatawa talaka in kunsami dama Allah ne yasan manufar jaki dabe mai ƙawo ba yowa kanta yayi da sauri MUZABFAR ya riƙe shi yace "Dan Allah malam bafa girman ka bane ka tsaya kana faɗa da mace jeka...., Burga mashin ɗinsa yayi ya yafi ko sai yanzu take tunani inna tasan wannan kamshin turaran tsaki taja a zuciyar'ta tace"ko ina ruwana da su owo afili kowa tace "Nagode amma wallahi daba ku bashi ba maceci ne a zoo road fa ya dauko nii amma yace 2500......, murmushi MUZABFAR yayi yace "Ba komai...., juyawa tayi zata shiga gida KAWU ya sawo kai zai fito tsayawa tayi ya fito yace "FALMATA lafiya nake jin hayaniya tun ɗazu nake jiran dawowar ki amma shiru me kika tsaya yi harkika dade daga zaki amso ɗinki..?, KAWU me ɗinkin ne baya nan na tsaya jiransa da ya dawo kuma beyi ba dakyar na samu abin hawa.... To shige Allah ya shirya ki bana son wannan faɗan dakike yi da maza amma bakyaji FALMATA shiga tayi ba tare da tace ƙala ba kallon su MUZABFAR yayi Allah yayi mai gane mutane dan haka lokaci kalilan ta gane su cikin tashin hankali yace "Ranka ya dade badai ku tayiwa wannan diɓan albarkar ba dan girman Allah ku rufan asiri kar saka a kama'ta kuyi hakuri...., Runtsai ido ASIF yayi ganin babban mutum yana me wannan magiyar da sauri MUZABFAR yace "A'a baba wajan'ta muka zo a bokina na rako...., da sauri ASIF ya buɗa baƙi zai magana KAWU yace "Allah ya saka lafiya....ba kamasu kuka ƙara zowa kuyi ba...., Ji ASIF yayi yawa ya ɗora hannu aka ya kurma IHU ko yaji dad'i gashi kamar an kulle mai baki ya kasa magana be tsinke da lamarin MUZABFAR sai da yaji yana ce baba daman wani babban lamarine ya kawo mu baba alfarma muka zo kai mana tun lokacin da kuka bar Abuja muke so muzo amma aiyuka summana yawa ASIF yana son yar gurinka FALMATA mun zo tambaya Allah isa ba aimata miji ba suman tsaye ASIF yayi ya kasa tantance me kunnuwan'sa suke ji mai muryar KAWU yaji yace "Babbar magana yanzu dai ga wayata ku samin number ku zan neme ku inde na gama bincike..., da sauri MUZABFAR ya amsa ya saka mai sallam sukai mai suka shiga mota har a wannan lokaci ASIF yaka sa tantance me ke shirin faruwa me i saka be dakatar dashi ba....amsar da ya kasa bawa zuciyar'sa kenan har suka isa gida ba wanda ya ƙara magana fitowa yayi ya shiga shashin nasu kiciɓus yayi da HAJIYA a kofar shiga part ɗinsa tana zagaye da waya a hannu da sauri ta juyo tace "Kai kuwa ASIF ina kasamu gun shiga tun dazu hajiuya kattime me dalilin aure wannan wacce gidan tv suke tallan'ta ta kawomin zuƙa zuƙan mata ka zaɓa amma shine kake ƙoƙarin watsa min ƙasa a ido na kirawa wayar ka tana faɗa min wani shirman banza....., MUZABFAR da shigowar'sa kenan dariya zancan Hajiya ya basa yace "Hajiya Allah ya bar mana ke...., Amin inda gaske kake kai kuma na dawo kanka dan wallahi bazan laminci ka zauna da wacca juyar'ba ba tare da ka auri me kwan haihuwa ba.....ga kanan marabar ka da gauro kaɗan'ce kamata yayi lokacin da zaka tawo ka tawo da me zubin taliya yar murji amma ka tawo kai kaɗai ni shigo ka zaɓa ka darje.... dabara ce ta waɗo mai yace "Hajiya yanzu daga gunta nake...., washe baki tayi tace "Dan Allah nasan Baka karya da gaske....daga gun jikartawa kake hakane MUZABFAR...., Eh Hajiya Shiga Hajiya tayi ɗaki ba tare da ta ce musu komai ba shiga part ɗin'sa yayi shikuwa muzabfar sai ya gano karshen wannan chapter dan haka bin Hajiya yayi dariya ce ta kusan kuɓucce mai dannewa yayi ganin yan mata sunci ado sun fi su goma sha wayyo Allah rigimar Hajiya ko salla bata yi.., da sauri Hajiya kattime me dalilin aure tace "Zaɓi ka darje ko wacce da ka ganta nan kwalin degree ne da ita wannan ita kuma master's degree ne da ita ta nuna wata tasha fenti a fuskarta sai taunar chingum take a ƙa'idar ungiyar mu photo muke bayarwa a zaɓa so lokacin da tayi min magana ta dauki number ta ne a television ne daga cewa babban mutum ne kai shi ya saka ma na kwaso su muka tawo akwai zaurawa a cikin su amma wallahi zam zam suke ciki da waje yasha gyara baza ma kace anyi ba ga yar shela can sabuwa ce fil Ranar auranta mijinta ya mutu.... kurɓar lemon da Hajiya ta saka yar aikin'ta ta kawo mus da snacks ta gutsire cake ta ƙara korawa da lemo tayi fari da idon'ta tare da yarfe hannu awarwaron da ta saka suka bada wani sauti tace "Dan samari zaɓa ka darje wallahi zasu zame maka aljihu kai saboda tsabar biyayya zasu iya kwantawa kabi ta kansu domin sun horu ba ƙaramin training na yi musu ba danni ba yau na saba harkar nan ba na dade a cikin'ta.... Zaro ido MUZABFAR yake tabbas Hajiya ta ɗebo abin da yafi karfin masifar'ta koya zasu kaya da wannan yar duniyar tab...... Nima zan so inga yadda zasu kaya *akwai rikice fa hmmm kudai Ku ƙarasa payment domin jin yadda zata kaya yau na buɗe paid group WA yanda suka biya zasu gansu a ciki.....* Sauran page 5 na gama book 2 09061890481 Only WhatsApp Nainarh kid's:.captain Ayusherh Queen Kainat:.shiryayyiyar kaddara Oumyasmeen:.gidan magajiya *GIDAN MAGAJIYA* EPISODE 41-42 Ina me dalilin Aure ajiye kofin hannunta tayi tace "Ranki yadade gani..., Hajiya tayi tace "ina me baki hakuri yaron nan yace min yana da wacce yake so ...., Hajiya ban gane mekika ce ba haɗa rai Hajiya tayi tace "Abin da kunnuwanki suka ji miki shi nace...., tab wallahi baza ta saɓuba saida na kashe uban kuɗi ki zomin da maganar banza kar ki ganki uwar manyan mutane narantsai da Allah yanzun nan sai mu lakaɗa miki duka iya karkarinta ace an kai mu gidan yari wannan kuma ba yau muka saba shigar'sa ba ya zame mana tamkar ɗakin uwar mu in banda rainin hankali na tako tun daga Sokoto na tawo kice min wai kun fasa muna dura a garin na ko hutawa bamuyi ba muka yo nan.... Ke daka tamin amma ke dai anyi mara mutunci ki dubeni tsofe tsofe dani ki dinga faɗan wannan magana bakya tsoron Allah ya kwashe miki albarka Sannu uwata nace sannu uwantale wallahi ku daka ta nawa ne abin da kika kashe....? MUZANFAR ya faɗa kama kugu tayi tace "Dubu dari uku domin jirgi muka hau...., Okay bani account number din ki karanto mai tayi ya saka ba dadewa ta ga alert tashi sukai ba wanda yayi wa Hajiya sallama ƙasa tafiya nabeela tayi ji tayi baza ta iya barin gidan nan ba Hajiya kattime ta roƙo hannun ta domin tasan damuwar'ta tace "Mu tafi zaki gwada min son zuciyar ki...., ba yadda ta iya haka ta bisu tashi Hajiya tayi zata shiga bedroom dinta dariya ce ta kubbu cewa MUZABFAR ya dinga yi harda riƙe ciki leƙowa Hajiya tayi tace "Innalillahi MUZABFAR kardai kaima ka haɗu da wannan ciwo na zamani mental processing da naji a radio...., be cemata ƙala ba ya fita shashin'sa ya nufa tura kofa yayi kamar yadda yayi tsammani haka ce ta faru tana zaune ta ɗora kafa ɗaya kan ɗaya tana girgizawa ta na kallo agogo my juyowa tayi tace "Habibty 11:39 fa .....?, rungumeta yayi yace "Zance...?, Dariya tayi tace "Masha Allah ina picture kanwar'tawa nunamin...., Wayar'sa ya zaro ya shiga cikin gallery din'sa ya miƙa mata dariya tayi ta rankwashe shi aka tace "Wannan photo na ne ai na kanwar'tawa nake nufi....., amsar wayar'sa yayi yace "Tunda baki yarda ba shikkenan...., dariya tayi tace "Uhmm..., ABUJA OSOKORO Kamar an jefo'ta haka ta shigo cikin gidan tana haƙi sai zare ido take tana wai waye domin yau taga bala'i ganin idon'ta hurjanjan ta shigi cikin dakin mahaifiyar ta da sauri hajja ta tashi tace "A'isha lafiya tun dazu nake neman ki amma wayar ki a kashe kin ɗaga min hankali....., kasa magana tayi sai ruwa da take cewa miƙo mata tayi ta sha bude wardrobe tayi tana zuba kaya a akwati.. A'ishah lafiya kike haɗa kaya tamkar wacce za tayi hijira....? Hajja gidan mijina zan koma ni wallahi na fasa auran wannan shegen mutumin ɗazu kinga tujarar da matarsa ta aiko akai min har da cewa zata buga sunana a jarida da photo na ai kinga ta kunyata ni a idon duniya harfa barazana tayi min da rayuwata to shi yanzu Allah isaka be sakeki ba Hajja ko ya sakeni wallahi sai ya mai dani yanzu dai ki bari sai gobe kya tafi dare yayi 12:00 fa Hajja da zafi zafi ake bugar karfe gwara natafi tun da zafin abin Abuja ba kamar sauran garuruwan ce ba a kwai tsaro zan isa lafiya ina zuwa zan faɗa miki kar ki damu ta faɗa tana jan akwatin ta Allah ya tsare ki Amin hajja ta ɗaga labule tafita inda ta ajiye motar'ta ta nufa buɗe'ta tayi ta saka akwatin'ta ta rufe za gayawa tayi wajan driver ta shiga kye tayi mata ta tashi horn tayiwa me gadi ya buɗe mata get ta fita hawa kan titi tayi zuciyar'ta cike da tunani kala kala har ta isa gida horn tayiwa masu ɗaya daga cikin masu tsaron gidan ne ya fito riƙe da bindiga a hannunsa ganin ita ce sai ya koma ba dadewa sai gashi me gadi ya buɗe get ɗin.... shiga ciki tayi da gudu daidaita parking din'ta tayi ta fito ɗaya daga cikin ma'aikatan gidan ne ya zo ɗaukan akwatin'ta yayi har kofar da zata sada ta da floor'ta ya ajiye mata da yake yasan dokar ogan'nasa dauka tayi ta shiga ajiye akwatin tayi a floor ta zuba ta gumi....tana tunani KANO N.N.D.C QUARTER tunda ya shigo ya kasa zaune ya kasa tsaye ya rasa abin yi ko dan Hajiya ya yi AURE amma wannan ta dace da ta zama uwar ya'yansa.....?wacce irin tarbiyya za ta bawa ya'yansa anya kuwa ba auran yarjeniya zai yi da ita ba in Hajiya taga yayi auran hankalin'ta ya kwanta nan da wani lokaci ya sake'ta tunda bisa dukkan alamu zata yarda da wannan agreement ɗin da haka yayi shiga toilet ya yi wanka ya dauro alwala canza kaya yayi ya saka pyjamas farare tas da su shinfiɗa daduma yayi ya tada sallah bayan ya idar ya ɗauki Alkur'ani me gir ya suma karantawa sai wajan karfe biyu ya ajiye ya kwanta.... Kiran sallar farko a kunnan magajiya dan haka da sauri ta tashi ta kunna fitila da yake a kwai huta zama tayi ta zuba wata uwar miƙa tashi tayi ta fito kiciɓis tayi da kawu ya fito zai tafi masallaci kallon'ta yayi ya shige ya fita alwala ta ɗauro bayan ta gama ta koma daki salla aka tada binsu tayi har aka idar tana idarwa ta fito ta soma haɗa kayan sana'arta ruwan wanka ta ɗora tana jiran yayi zafi ta dauka tayi wanka kamar anjefo rabi ya shigo yana haƙi sai zare ido yake kallon sa tayi tace "Lafiya...?, Wallahi Allah magajiya ido huɗu muka haɗa da wannan na Abujan yanzu ya zoge glass ɗin motar sa shi da wani kardai dawowa sukai su kashe mu na shiga uku wayyo Allah baba tashin hankali ba'a saka maka rana jar uban'can mun shiga uku da gudu ta shiga bayi zaman dirshin rabi yayi ya zuba ta gumi yana cewa nima da zanyi kashi da nafi kowa murna sai ringing yake a ciki na dinana ne ya shigo da M.P a hannunsa sai tashin ƙiɗa take yi kai kace kana club ɗin lagos ko kallon inda rabi yake beba ya sami guri ya ajiye MP sa yana tiƙarrawa yana cikin rawa.... yaji rabi yace "bazan hanaka rawar'ka ba wata kila wannan ce ta karshe da za kayi idona idon'su wallahi mu suke nema kashe ƙidan yayi yace "Rabi me kake faɗa ne haka....?, Kuka ya rushe da shi ya fyece majina da zanin dake jikin'sa yace "wallahi in kaci bashin wani kaje ka bashi haƙuri ya yafe maka bilahillazi idona idon shugaban DASS... innalillahi ƙiyamar mu ta tsaya shikkenan kai Allah ka tsinewa KASKA banda asarar dubu biyun mu da mukai bamu da zaman lafiya ana yi mana bita da kulli ka duba fa ka gani wannan dubu biyu kudin abinci na kwana biyu kenan Amma kai dinana anyi mara hankali wallahi muna ta rayukan mu da lafiyar mu kana ta dubu biyu to ai kasan hanya jeka ka karɓo wallahi magajiya aini kinga na rasa bakin magana in banda tsabar rashin mutunci da rashin sanin ciwon kai muna ta lafiyar mu ina batun wasu kuɗi KAWU ne ya fito daga daki yace "Rabi'u deeni falmata lafiya kukai jigum jigum kamar wa'yanda a kaiwa mutuwa...?, Wallahi Allah KAWU da wannan tashin hankali gwara in mutuwar ce ayi munsan mutum ya mutu in ma Bata ƙarasa abinda tayi niya ba RABi ya goge hawayen'sa yace "Wallahi gyara zancan ki wanne irin gwara mutuwa saidai in kece zaki mutu amma ni wallahi bayan zuba yaushe nazo duniyar da har zaki dinga batun mutuwa ana zaune kalau......, Dan girman Allah rabi ka zauna kayi jiran duniya anya kuwa dinana ba ƙarya yazo ya faɗa mana ba muka hau kai muka zauna mutumin da har jiniya ake mai shi ya gani....? gaskiya kam nima sai yanzu nayi tunanin haka kallon su kawu ya tsaya yi ya rasa gane baƙin zarar gashi kuma sunƙi faɗa mai...... yanxu dai makaryaci kuka ɗauke niii.... duk abin da zuciyar ka ta baka shi muka ɗauke ka ɗan rainin hankali botiki ta dauko ta juya ruwan ta tace wa dinana ya wanke mata tukunya ya zuba mata ruwa ya ɗora rabi kuma ya fara feraye doya gama wankan tahi ta fito shiryawa tayi cikin doguwar riga ta atamfa ta chokalo dauri gaban goshi sai kamshi take zubawa fara haɗa kullin waina tayi wata uwar sallama suji anyi gaban rabine ya waɗi yace "Shikkenan aikin gama ya riga ya gama innalillahi tun huri nace mu gudu kuka ƙi ai ga irin'ta nan...., da hallacan yi mana shiru dinana liƙa kaga suwaye..? Kafa na fiki ke mana ki leƙa kika suwaye Ni kake faɗawa haka dinana kafin ta ida zancen ta tuni rabi yafara kokarin ɗanewa kan katanga da sauri dinana ya riƙo shi yace "Wallahi ba'inda zaka kuka ya fashe dashi yana cewa MAGAJIYA duk shi ya saka mu a wannan tashin hankalin son zuciyarsa ne yayi yawa shi yasa ka har ya kai mu muka siyi sofaffin layi shine da wasu ƙafafuwan'sa yawa kwarashi za ka gudu ka bar mu ai ba kafa ya fi mu ba ....., da sauri ta tashi ta ƙara riƙo ɗaya kafar ta rabi tace "Zaka sauko ko sai na karya maka ƙafafuwa...?, Ku dakata wannan abin fa ba dole nayi muku ba zaku cika ni kusai nayi muku rashin mutunci ya faɗa yana muci muci da ido alamun ba'arziki Assalamu alaikum wa'alaikas...kafin KAWU ya ƙarasa tuni sun cika RABI shima saukowa yayi suka rufe wa KAWU baki kasa ƙasa rabi yace "Mun shiga uku kawu wa ya aike ka amsa wannan sallamar da ba aminci a tattare da ita...., kallon su ya shiga yi yana tunanin anya kuwa lafiyar su ƙalau dinana ne ya gane haka yace "Wallahi kawu duk kallon da za kai mana saidai kayi mana dan kuwa yau muna cikin rashin nutsuwa da tashin hankali rabi ne yace yaga shugaban mala'ikun duniya..... asho ne ya shigo yana rangaɗa sallama da alama abuge yake nuna su yayi da danya tsa cikin maganar maye yace "Amma ku anyi kafurai kuna jina ina sallama ba me amsawa saboda baku ga uwar motar da na tawo da ita ba.., wata uwar ashar magajiya ta yi mai tana cewa amma kai anyi dan iska wallahi ashe daman kai kake wannan sallama ka saka mu a tashin hankali zo ka fita wallahi baza ka zauna min a gida ba yau tunda bada kuɗin ka nake haɗawa na biya haya ba yau nake jin wani sabon isanci akai kafuri sama dakai wallahi Allah sai ka tashi kabar gidan nan dan kwal uba...... wallahi ko baki rantsai ba sai ya bar gidan nan dan durin uwa daukan sa zanyi aka na fitar dashi kai Allah ya tsinewa shaye shaye ga yarda ya saka mu a halin ha'ula'i cewar rabi sosai kawu yake dariya sai yanzu ya fuskanci inda suka dosa ba wanda ya biya ta kan kawu sai uwar tujara suke zubawa asho zaman dirshan yayi yana cewa Wallahi bazan fita ba Chak dinana ya dauke sa a kafaɗa gantsara masa cizooo yayi a huya ba shiri ya sauke sa yace "rabi zo ka duba min ba allura ya caka mini ba a huya dan Allah zo ka duba mini... Kai rabi kar ka kula shi zo ka ɗauke shi ka fita da shi hannu kika fini kina gani dai abin da ya yiwa dinana ni kuma da yake gani mara hankali sai na kara ɗaukan sa kinga abin da yafi cizo zai mini yan shaye shaye ba'a raba su da makami haka kurum ki saka a kai ni lahira ban shirya ba rufe min baki ina ka taɓa ji sai mutum ya shirya ake kai shi ƙabari kar kayi mamakin yau kawayi gari ka ganka a tsakanin tukwane Haba uwani kina a matsayi na uwar mu kina cewa na mutu gaskiya hakan be dace ba Rabi'u kenna ita fa mutuwa bata sallama ya kamata Ku nutsu ku san abin yi kaga shigar matan nan da kake Allah ya hana ya kuma tsinewa duk me yi Allahu akbar uwani ashe kin iya tafsir ban sani ba anan dai baki da rabo tafi masallacin bola ko kya sami wanda zai iya ɗaukan wa'azin ki cewar ta masar da ya shigo rataye da haka a hammata da dankwali yana juya shi a hannu..... Ku dai ku cigaba da yin payment ₦500 lokaci yana ƙaratowa sauran pages 4 na book2 gama 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay Ku turo da shedar biya ta wannan number 09061899481 Dan Allah in ba siye zaki ba karki min magana masu yi min magana ace ASLM dan Allah ku tafi kai tsaye game da abin da ya kawo ku GIDAN MAGAJI YA EPISODE 43-44 TA'MASAR UWANI kike fadawa haka zoka fita ko na karya maka kashin muƙamuƙi.. ɗamara yaci yace "Billahillaziii ba inda zanfi'ta ita baki ga abin da take faɗa ba sai nawa zama daram yana me naƙuɗa....., tab gaskiya ya raina ki kina faɗa yana faɗa wallahi magajiya zan faɗa miki gaskiya ki koma magajiyar ki tada faɗan nan da kike yafi naɗa sannan dole na kai ki gurin malam me ishimawee ya duba miki ƙasa a ga ko akwai wanda yasa ka miki hannu domin wannan rainin da akai miki da walakin gora a miya ya faɗa yana buga cinya game da harfe hannu..... tab sannu macuta ni za ku kai a cinyewa kuɗi a banza tsaya kuji wallahi duk macan da take kai kuɗi domin amallake mata miji to wallahi sunan kwakwalwar'ta dooosa haƙuri da iya magana da kyautatawa datarairaya da son yan'uwansa shine babban magani banda ka rainani ka mai dani kidahuma shine kake min zancen wani malami kai ka kiyayeni Rabi tamasar kuzo mu ɗauke wannan mahaukacin dan wallahi tunda ya sani gudawa a wando saboda cizon da yayi min Wallahi maza sun ƙare a duniya shine mu muna mata kake'so mu mu tayaka ɗaukan sa haram wallahi haram da hallacan rufemin baki shegu kawai wa'yanda Ubangiji ya tsine musu..... be ƙarasa ba suka rufe shi da duka ku daka'ta wallahi bazan laminci wannan iya shegen ba kawu zo ka raba su ga doya'ta tana kokarin dauhuwa kar su naɗa musu duka su kasa yi min aiki..... wallahi ba zamu yadda ba kullum aibata mu yake kawu ba ruwanka ina ganin mutuncin ka a matsayin ka na uban mu na bariki icce magajiya ta ɗauka tayo kansu ɗoɗanawa ta masar tayi a ɗuwawu ihu ya saki tuni suka fita a guje harda dinana da ya garzatsawa rabi cizoo sun zata kunama ce ta ciji tamasar ya saki wannan razanan nan niyar ƙarar da ya zunduma haɗe da ihuuuu binsa sukai har asho ashe iskancik nasa na karya ne.... dariya magajiya tayi tana cewa kawu anya kuwa suna da hankali gyara zaman kur'anin dake hannunsa yayi ya ci gaba da karatu be kulata ba a zuciyarsa kuwa nema musu shiriya yake kai ta gyaɗa ta koma kan kullin wainar'ta gefe kuma wutar da ta dora doya tana ta ci tun dare daman aka yo mata markaɗe..... ***** haɗa kayan'sa ya cigaba dayi yau yake so ya koma Abuja gobe kuma ya koma baƙin aiki... Asif daman ba hutu kazo ba kwana biyu kawai za kai ka tafi zuge akwatin'sa yayi yace uhmmm sanin halin aminin'nasa amma dan haka ya ja baƙin'sa yayi shiru zama ya gyara yace "baka tambaye ni ya hajiya tayi da me dalilin aure ba....?, bani da business da'ita hmmm haka kace da fa ban kuɓutar da kai ba ta hanyar kaika gidan magajiya da tuni dole ka zaɓa a cikin yan matan da Hajiya ta kawo maka matsar da akwatin yayi ya riƙe mai huyan riga yace "bana so in gwada training akan ka da tun a jiya na zubar maka da haƙora ce maka nayi ina son'ta da zaka haɗani da baban'ta kasan ina ganin ƙimar'sa bazan iyayi mai musu ba bazan kuma ina karyata ka a gabansa saba da girmana ina zaune kai zaka nemo min matar aure...., cika shi yayi ya naushi iska yana cewa wallahi narasa dalilin da a lokacin ban tsayar da kai ba daga shirman da kake shirin aikata min aikin gama ya gari ya gama da wallahi wannan maganar ɗazu hajiya take sanarwa da su abba kafin mu gama breakfast yanaji yana cewa ma zai neme ka ka faɗamai inda yarinyar take domin basa so a dade Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un shine abin da ya shiga maimaita wa ya ci gaba da cewa kasan kuwa yarinyar nan bazata taɓa yarda da aurena ba ka duba ranar da suka bar Abuja ta kwayar idanuwanta ina iya hango tsana'ta a cikin idonuwanta tashi yayi yace "to Allah in alkairine auran Ka da ita Allah ya haɗa sai kaga an sami rabo...., banza yayi mai har ya gama shirinsa na tafiya Akram ne ya shigo ya dauki kayan nasa shi da ayman tare da zu huce gurin Hajiya ya fara shiga tana zaune tana lazimi macece me son ibada baka rabata da jan carbi sallama yayi amsawa tayi cikin sakin fuska tsugunawa yayi ya gaisheta yace "Hajiya zan koma...., to nima fa binga zanyi domin tuni na saka a haɗamin kayana na gaji da zaman garin nan gwara na tafi yawon buɗe ido da sauri ya ɗago salati ta saki tace"au bazan bika kake nufi ba ko yaya...? da kanka yana ƙasa yana wanda yayiwa sarki karya da yake kaji zan bika shine ka ɗago tafiya fa ba fashi nida yar jikalleta inga wanda ya haifeni a cikin ku ya hanani..... Hajiya kiyi hakuri zan aiko a tafi dake amma yanzu bazan iya tafiya dake ba jirgi zan hau ba mota ba ba ai miki booking ba kai muzabfar dauko min jakata na rataya ga akwatina can hansai ta faɗa maka inda ta ajiye min ita bata jira me zai ce ba ta ci gaba da cewa hansai hantsai fitowa matashiyar buɗurwar tayi ta ɗurƙusa wayi tace "Gani Hajiya.... Alhaji barka da zuwa...., yauwa yace mata kamar dai ko da yaushe kinga ba gaisuwa na kiraki ki mai ba bana son tsohon kinibibi gaisar da uwar miji a kasuwa buɗe kunnan ki kijini bana son a sami problems kwanaki nasaki ki haɗamin kaya zani Abuja na fasa to shi zaki dauko min su Hajiya kince na mai da su har abada ba zaki ƙara zuwa Abuja ba tunda annuna miki iyakar ki Salati ta shiga yi tana goge kwalla da mayafin'ta tace "wallahi muzabfar karyar wannan yarinyar tana bani tsoro karfa wata ran ayi sama damu in Ubangiji ya gaji da halinta kasan me kan uwa da habi yake sai anje can a tantance yau she na faɗi haka da badan na dauko amanar'ta daga kauye ba wallahi yau ba'a binda zai hanani na maida ita yarinya sai shegiyar karya yau she na faɗi haka muzabfar ka duba min wannan zance...? yanzu dai Hajiya kiyi hakuri mantawa tayi bakin gyelanta tasaka ta goge idanuwanta tace "ba dole nayi hakuri ba..., ke hansai bata hakuri Hajiya dan Allah kiyi hakuri jeki Allah ya yafe mana baki ɗaya amin ya Allah ASIF ya faɗi haka tashi tayi ta bar gurin ganin Hajiya ta manta da wannan zancan ya tashi yace "Hajiya Allah ya ƙaddara saduwar mu...., kai ta gyaɗa mai ba tare da tayi magana ba binsa muzabfar yayi suka shiga yayiwa kowa sallama sannan ya shiga mota muzabfar ya ja su har airport badadewa jirginsu ya tashi..... Abuja tun da safe take cikin zullimi dan bata san tarbar da ASIF zai mata ba zai yi murnar dawowar'ta ko zai nuna mata halin ko in kula tun tana irga mintinan fitowar'sa har ta koma kirga awannin zuwa yanzu tabbatar baya garin ko kuma baya ƙasar domin in dai yana gari zai fito musamman ma da safe in ya dawo daga massalaci zai zauna yaji damuwar ma'aikatan gidan yau gashi har karfe 12:30 ba alamun'sa cikin sauri ta tashi part ɗin'sa ta nufa tana zuwa ta dafe kan'sa tunawa da tayi bata san password ɗin kofar tasa ba.... baku ma key a hannun'ta sau tari saidai tayi knocking ya buɗe mata tsaki taja yafi cikin kwando tajuya kenna sukai kaciɓis dashi sam kunnanta be jiye mata jini'yar da ake mai ba ko bakowa ne yasan da tafiyar tasa ba ko ya tafi ne ba wani me tsaron'sa bata da me bata amsa hugging ɗin'sa za tayi ta faɗaɗa annurin fuskarta tace "Your welcome back sweetheart...., hannu ya ɗaga mata cikin i don't care yace "Excuse me madam..., saroro tayi tabbas ta aikata babban kuskure wanda sai tayi da gaske tukunna su koma irin zaman su nada cikin sanyin murya ta langwaɓar da kai tace "Please..., be bata damar ƙarasa abin da zata faɗi ba ya shige abinsa tare da rufo kofar'sa juyawa tayi jikin'ta a sanyaye ta koma ɓangaranta rasa inda zata saka kanta tayi taji dad'i..... Shi kuwa bayan ya shiga ajiye akwatin hannunsa yayi da briefcase ɗin'sa akan gado sosai yayi mamakin dawowarta matar da take neman saki me kuma ya dawo da ita ba me bashi amsa dan haka ya kawar da tunaninta a ransa bashi da amfani cire takalmi yayi tare da safa ya rage kayan jikinsa ya shiga toilet ya dauki tsawon lokaci sannan ya fito ɗaure da towel a jikinsa lokacin ana kokarin kiran sallar azahar sauri yayi ya saka jallabiya maroon colour tare da hula feshe jikinsa yayi da turare sannan ya saka slippers ya rufo kofarsa ya fita cikin nutsuwa yake tafiya har ya isa masallaci lokacin har liman yana ƙoƙarin tada raka'ar farko sauri yayi ya shiga..... bayan an idar sai da ya tsaya yayi addu'a tukunna ya fito da gudu wani yaro ya rungume shi yana uncle kaga ya Asad ko Allah yayi mai kaunar yara dan hak ya rage tsayin'sa yace "Waya ke shirin taɓa mini yaro na...., mahaifin yaron ne ya ƙaraso da wani matashi yace "Abdul wato baka ji ko...., da sauri Asif ya ɗago rasa inda yasan wannan fuskar yaron yayi kamar yasan me kama da yaron amma ya manta yace "Barka da rana...., hannu mahaifin yaron ya miƙo mai suka gaisa yace "Yauwa...., hannu ya miƙowa abdul ƙin zuwa yayi dariya Asif yayi yace "Kun mai laifi bazai zo gun ku ba..., Uncle sai sun bani hakuri ko kuma na bika nima na zama soja Good boy yaron akwai wayo haka ya raya a zuciyarsa afili sai kuma yace "saboda me kake son zama soja...?, Saboda kai ina ganin ka a TV Murmushi ASIF yayi ya shafa mai kai yace Allah ya cika maka burin ka Amin yace kallon ASIF mahaifin yaron yayi yace "Indai surutun Abdul ne ka gaji dashi zo mu tafi..., murmushi yayi yace"yaro me baki yana da shiga rai Allah yayi mai albarka...., amin suka amsa dashi da kyar ya bar jikin ASIF saida yayi mai alkawarin zai ziyar ce su domin umminsa ta gansa da haka akai mai wayo ya barsa tafiya yayi yana tunanin yaron har ya isa gida a corridor da ya raba shashin A'ishah da nasa ya ganta taci wasu arnan English gownt marabar ta da babu kaya kalilan ne cikin sauri tace "nayi Knocking Ashe baka nan abinci ya kammala a dining zaka ci ko dakin ka zan kawo maka....?, No barshi na ƙoshi... sororo tayi tana kallonsa sarai tasan halin kafiya da taurin zuciya irin nasa ga yadda ya nuna tamkar shi wani dutsai ya gani sarai tasan ya ga shigar dake jikin'ta amma menema baya fushi bari ta ƙara gwaɗa sa'arta ko za'a dace ya dena wannan fushin da ita tace "Wannan abinci kaci Please ka daure kaci daga office fa kadawo da kaina nayi maka girkin fa...., bako ɗigon annuri a fuskarsa yace "Nace miki na ƙoshi..., hawayen da take riƙewa a idon'ta suka sami nasarar zubowa rungume shi tayi ta baya tana cikin shashsheƙar kuka tace "me isaka abu baya wucewa a zuciyar'ka na baka haƙuri har text message sai dana yi maka amma ba reply nasan nayi kuskure na dawo nayi na dama Allah yana son me yafiya me yasa ka kai ba zaka iya yafe min akan ɗan laifin da nayi maka ba.....?, juyosa yayi idon'sa ya kaɗa yayi ja nunata yayi da yatsa yace "ɗan laifin da kikai okay karamin ne kenan be kai ya kawo ba ko Please tun kafin in faɗa miki a bin da ranki zai ɓaci ki fita daga sabga'ta wallahi kin ban mamaki A'ishah....ba saki kike nema ba saboda sheɗan ya buga miki ganga duniya tana miki ihu aka ko....? to kije na....., Na kusa fa gama littafin nan sauran 4pages ku ci gaba da payment ɗin ku ta wannan hanyar 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay Ku turo da sheda ta nan 09061890481 Dan girman Allah in baki shirya ba kar kimin magana GIDAN MAGAJIYA PERFECTLY PEN'S EPISODE 45-46 Toshe kunnuwanta tayi ta ɗurƙusa ƙasa tace "Dan girman Allah kai hakuri kar ka ƙarasa...., Dariya abin nata ya bashi duk kuwa da tsananin ɓacin ran da yake ciki juyawa yayi ya fara tafiya ba tare da yace mata komai ba ajiyar zuciya ta sauke ta juya tabar gurin zaman tayi a ɗaya daga cikin kujerun alfarma na floor tana ta tubka da warwara wayar tace tayi ringing da kamar ba zata ɗaga ba sai kuma ta ɗaga ta ƙara a kunne batare da tayi magana ba jin me magana gabanta ya yanke ya waɗi tashi tayi ta shiga bedroom ɗin'ta tace "a gaskiya na fasa saboda matar ka tana yi min bara zana da rayuwa'ta jiya sawa tayi aka ɗaukeni mutanan nan suka gana min a zaba yanzu ma haka ina gidana...., dafe kirji tayi da jin abin da yace innalillahi yanzu ina ta kama taya zata iya nemo wa'yannan maƙuɗan kuɗi dakyar ta iya cewa gaskiya bani da hanyar da zanne mo wa'yannan maƙuɗan kuɗin ba kyauta ka bani ba........ bani nace ka bani ba kuma ba rance naci ba Ƙara shiga cikin ruɗani tayi tace "na shiga uku ko ɓera bazan iya kashewa ba balle mijina wai dan girman Allah me yayi muku kuke son ganin bayan.....sa bata ƙarasa maganar'ta ba ya kashe wayar'sa ganin ya taso da sauri Hajiya ni'ima ta ɓoya a jikin labule sarai ta gane da wa yake magana amma in yasan wata besan wata ba fita yayi ransa a ɓace da sauri itama ta koma ɗakin'ta tana kai kawo me mijin nata yake shirin aikatawa ne tab a kwai gagarumar matsala fa a gabanta tunawa da tayi yau NIHILA tana da lecture amma taga bata da niyar zuwa da sauri ta shiga bedroom ɗin'ta kamar ko da yaushe tana kwance tana charting NIHILA da sauri ta miƙe tace "Na'am mommy..., yau babu makaranta ne tunfa karfe 7:38 ya kamata ace kin fita gaban tane ya waɗi ita bawai makarantar ce bata son zuwa ba a'a baso ta haɗu da wannan sheɗaniyar matar ta gwammace ta kwashi carry over na dukka course ɗin da take yi da ta aikata wannan mummunan aikin nan musamman ma ɗazu da ta shiga tiktok taji wani malami yana faɗar tsananin azabar da Ubangiji yake yiwa me wannan hali in har be tuba-ba har ya koma ga Allah yana aikata haka tsawa ta daga mata da sauri ta zaɓura tayi ta turo baki..... nihila kin mai dani wata mahaukaciya ina magana kin mini banza ko hi hakuri mommy yau bana jin dadi shi yasa ka bazan shiga school ba Okay na lura kwana biyun nan wasa kike da karatu wai me ke damun ki....? ƙasa ta yi da idanuwanta ta ya cika da kwalla tace"mommy bakomai..., kwafa tayi ta fita kai tsaye floor daddy ta koma yana zaune yana aiki a cikin laptop sallama tayi be ɗago ba ya amsa samin guri tayi ta zauna tace "Daddy nihila..., Ina jinki ya bata amsa cikin rashin nuna kulawa ɗaga ƙafaɗa tayi alamar ko a jikin'ta tunda ta riga ta kashe boss ɗin taci gaba da cewa karatun nihila yana tabarbarewa a gaskiya dole mu fita da ita daga ƙasar nan inta je can tafi karatu..... okay anan batayi ba tana gaban mu sai a can...?, Daddy Ka duba magana ta fa ya kamata ace yanzu nihila aiki take karatun Nigeria sai addu'a wannan makarantar kuɗi ce amma me taƙi tsayawa tayi a gaskiya fita da ita ƙasar waje shine mafita.... Okay zan duba tashi tayi ta gallamai harara ta juya ta bar dakin ji take kamar ta rufe shi da duka ko ta samu sauki a cikin zuciyar'ta Komawa bedroom ɗin'ta tayi ta fara shirya wa saboda da huri yau zata karɓi aiki ..... KANO.....unguwar kofar mata FALMATA ki nutsu muyi magana ta fahimta ni dake to ina jinka kawu ka faɗa da sauri saboda zan koma zooroad dan wallahi yau saina yi mai akuya har da su asho zan tafi su gwada mai cin kai ko ya nutsu ya bani kayana Allah ya kyauta amin ta faɗa tana goge takalmin ta be damu ba da rashin bawa maganar sa mahimmanci da tayi ya ci gaba da cewa a duk kwanan duniya cikin zullumi nake falmata ina so in cika alkawarin da na ɗaukar wa fatima ina so in cika shi babban tashin hankalin da kike ƙara jefani shine mutanan banza su suka zama abokanan ki sau tari mutane suna hukunci ne da abin da suke gani ba abin da yake baɗini ba...ba ɗan arziƙin da zai zo neman aure ki ba a hana shine ba saboda BAƘIN SHAFIN da mutanan unguwar nan saukai miki ( ina maso yana nace kuna ina ina me gabatar muku da sabon littafi na me suna BAƘIN SHAFI kuda gajin sunan kunsan fa lamarin babbane....) to yanzu KAWU daman wannan maganar kakeson faɗa min da sai ka bari sai na dawo sai kai min wa'azin amma kawu wallahi yanzu kasa jikina yayi sanyi da niya nayi yau zan bar maka kuɗin belina dan wallahi sai na kwaso magana Allah ya shirye ku Amin kawu ai magana kayi me kyau ka gama Ni zan tafi....? a'a ban gama ba to ci gaba ina jin ka cikin hukuncin Allah sai gashi Allah ya kawo mana mafita hanyar da za a nemo mahaifiyar ki ta cikin sauki ba tare da munci wahala ba mun bada kuɗin mu an cinye duniya da faɗi ina zamu mu ne mota....? da sauri ta ɗago ya bawa maganar'sa mahimmanci ta ajiye ta bawa maganar tasa mahimmanci tace "Dan Allah kawu...?, wallahi ina wannan mutumin da ya kama ku har akan anyi kidnapping ɗin matar'sa ku kuma son zuciya ya kwashe ku kuka siyi waya da sim eh kawu na gane ina jin ka shine yace yana son ki zai aure ki tashi tayi har tana kokarin tuntuɓe da dutsai tace" tab wallahi never ni ai kawu in Ka ganni a lahira kai ni ake wannan banzan mutumin wallahi bani bashi ya riƙe temaƙon sa bama so... kaga ko bazai abu dan Allah ba sai dan na aure shi shege dan iska duk kwanan duniya Allah ya isa nake mai daga yaga na waɗi har da zuwa ya taroni tanan kawu zaka fahimci sana'ar sa Ni sajan bala zan aura shi nake so zamma ce ya turo magabatan'sa sannan ya tanadi yan rabon faɗa dan wallahi wannan shegiyar matar tasa ta kawo min wargi sai na karya mata ƙafa Innalillahi auran fa nayarjejiniya za ayi mahaifiyarsa ce ta dage sai yayi aure to wato Ni gani babbar yar iska ko kawu a aure ni yan satittika a sake ni tab a dinga nunani da baki ana ga wacce aka aure ta sati biyu auran ya mutu na zama ƙaramar bazzawara ina ina kawu wallahi bazan yarda ba ko duniya da abin da ke cikin'ta zai bani baya gaba na... ban gama faɗa miki ba kin yanke hukunci zaune kiji mana Uhmm uhmm kawu fa ɗamini ina daga tsaye domin bana son na din ga westing time ba wanda zai san anyi zai kuma nemo inda fatima take ya kawo karshen ta'addan cin da ake yi a Maiduguri har mu koma garin mu komai ya zama tarihi kinga daman kina da burin haka to saidai nayi shawara na tafi ta saka talminta daman mayafinta na jikin'ta sauran page biyu book two ya ƙare ku hanzarta payment ɗin ku domin samin ci gaba ta wannan hanyar 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay Ku turo da sheda tanan 09061890481 to Allah ya kiyaye amma dan girman Allah ban da faɗa in yace be ba ki haƙura gobe sai ki dawo Uhmm amin fita tayi kofar gida gyara tsayuwar'ta tayi ganin su rabi sun karya ko kwanar lahin nasu ƙarasowa sukai cikin muryar rikakken yan daba yace " magajiya yane yanzu za mu yafi...ko sai anjima...?, dazafi zafi ake bugar ƙarfe yanzu mu tafi to tana gaba suna take mata baya duk inda ta gitta sai an kalle su masu tirrr da hanlinsu nayi masu yi musu addu'a nayi bakin titi suka tsaya magajiya ta fara tsarar a me napep kowa yaga zugar dake bayan'ta sai su ja abin su dakyar suka sami wani zai kai su ba musu suka hau.... me napep ɗin ne ya tsaya yace "Gaskiya bazan iya kai ku ba ku sauka wannan lodi har ina ni nataɓa ganin inda mace ta zauna a gaban a dai-dai'ta yawa wata na miji wannan in muka haɗa ido dashi yana cije baki yana zabgan harara bazan iya ba ku sauka...., Rabi ne ya talle mai ƙyeya yace..... GIDAN MAGAJIYA *Those who ask me the complete document is not on the ground, but I have already opened a group for those who bought the GIDAN MAGAJIYA* EPISODE 47-48 "Yi mana shiru ja'irin banza wallahi sai ka kawo mu kuma ka mai damu in banda iskanci sai da ka ɗauke mu kace ba zaka ba..., Kai barni dashi su yake in nannaɗe mai ya'yan hanji yanzu zaka kunna ko sai nayi maka baƙin aiki ASHO ya faɗa yana cije baki da zare ido da yaci uban kwalli yawa wani boka be ce musu kala ba ya tada mashin din nasa yana fatan Allah isa su rabu lafiya kwatance sukai mai har shagon ya kai su bashi kuɗinsa magajiya tayi Fakar idon su ya fita a guje basu biya ta kansa ba ku kutsa bana son hauka Ku tsaya anan in na shiga be bani kayana ba ya raina min hankali sai na kirawo ku da dai kin bari mun shi ga mun kaddamar mai ɗamara taci da mayafin'ta tace "gaskiya a'a bana son rashin hankali kuyi yadda nace mana sai kuma an sami matsala mu zo muna cuzon yatsai...., to sai kin fito in kuma be baki ba muna shiga mu rufe su da duka cewar rabi a'a rabi wannne duka ana zaune qalau ina hukar da nace zaku musu barazana da ita kunsan kuwa kukan zuciya da dukan zuciya yafi na zahiri ASHO ne ya fito da ita yace "ga ta nan..., yauwa to ku adana'ta Kofar glass ɗin ta tura tace " Assalamu alaikum...., yaran shagon ne suka amsa mata sallama ina ogan'ku yake....?, Wani da yake yanka shadda yace "Hajiya ya tafi sinigal kwana uku da suka wuce...., kai kar ka raina min hankali ko shekaran jiya na gansa a daran ranar ya tafi okay to ba matsala da masu ibar min kayan kuɗi.... basu kulata ba kwalamusu kira tayi tace "TA'MASAR ASHO RABI DINANA....., shigowa sukai wata zabgegiyar huka asho ya zaro da ita har kyalli take yace "Zaku faɗi inda yake ko sai mun haɗa ku da jinya....?, Cikin rawar murya wani yaro a cikin su yace "wallahi yana cikin waccan akwatin ta kayan dinki..., Kai dinana bude akwatin can in karya yake kuma yau kowa sai ya baƙunci lahira ba musu dinana ya buɗe akwati Ido hudu sukai da salmanu me dinki janyo rigarsa yayi yace "Fito munafikin Allah ta'ala.., jikii a sanyaye ya fito yana raba idanuwa yawa wanda yayi wa sarki karya huƙa Asho ya saka mai a huya yace "Ina dinkin ta in baka dinkaba bata a tamfarta...?, dan girman Allah kai min rai wallahi wata tsawa ya daka mai yace "kaya yana ka bani ba rantsuwa nace kai min ba..., jikin'sa na'rawa ya ɗur kusa ya fara neman atamfar ta duk da AC da take aiki a gurin amma gumi ne ke yanko mai ɗagowa yayi yana zare ido yawa za su waɗo sama Kai yane kar fa kace baka ganta ba wallahi yanzu zan aika ka can ka ci gaba da neman'ta cikin sane ya murɗa gudawa ce take neman kubɓuce mai baƙin'sa na rawa ya buɗe zai magana sai ga hawaye haɗe da majina ganin ogansu yana kuka yaran shagon suka fara yadda kuka san gidan mutuwa.... ASHO ya ɓatar min da kayana kawai ciro min hantar cikin sa yau muyi dabge Kuka ya ƙara rushewa da shi yana fyace majina yace "dan girman Allah kiyi hakuri roɗewa nayi kai Abbas duba drawer ka ko tana ciki...., da sauri ya ɗago idanuwansa jage Jage da hawaye yace "kar ka goga min kashin kaji oga a yau she ka bani ku su walid ya bani....?, rige rigen magana sukai kowa yana cewa Wallahi bamu sani ba tamasar ne yace "ka taso ka zauna anan wato kai dashi kuke haɗa baki kuna cinyewa mutane kaya ko..., kuka Abbas ya ƙara rushewa da shi ya matsa kusa da ogan nasa yana fyatar majina yace "Wallahi ka tambaye shi be bani ba..., Mari ya kwaɗa mai yace"kai dan uban ka nayi maka kama da namijine..., sai a lokacin ya kai idon sa kan kayan jikin ta masar jallabiya ce irin ta matan nan baka har da adon duwatsu baƙinsa sai kyalli yake yaci pink din jambaki ya daura dankwalin abayar akan sa baƙin sa na rawa yace "aunty ma'eesha...ina huni..., dariya ce ta kama dinana ya dinga yi kamar ba gobe shi kuwa ta masar dadine ya cika shi yayi fari da idanuwansa yace"lafiya lau koma cikin yan uwanka..., jikin abbas na rawa ya koma cikin su Walid....ya zauna Aunty maeesha dan Allah ki bashi hakuri zan nemo salmanu ya faɗa Harara tamasar ya gallamai yace "bana son baƙin munafurci da kasan da kayan kaki daukowa yazun zan tura yaran ka su faɗawa tsohuwa ta haifi wani...in tana son me kama da kai..., Wayyo Allah na shiga uku wallahi ku bani ko minti goma ne zan nemo ku temake Ni...ya faɗa yana hada hannayen'sa biyu Owkay da sauri ya fara laluban atamfa cikin ikon Allah ya ganta miƙa musu yayi ransa fari tass yawa gonar audiga miƙa musu yayi amsa ASHO yayi yace "Ka temaki rayuwar ka..., Turo kofar shagon akai kallon mamaki Hajiya jameela ke musu me ya haɗa salmanu da wayan nan yan barikin ke da hallacan ki kalli gaban ki ko nayi miki kwalli da hukar nan ASHO ya faɗa yana zare ido... Ikon Allah kai kuma SALMANU me yakai ka ma'amalla da irin wa'yannan mutanan a ina ka samu su a gidan uwar....kiii ke zooooki fita ko sena farke miki ciki....?, ASHO ku shege mu tafi tun da ya bamu kaya shikkenan Dakin kyale ni na koyawa wannan tsohuwar hankali tunda ita sana'ar ta tasa ido ce ASHO shege mu tafiii kalloon mamaki hajiya jameela ke mata mace har mace tana ma'amalla da irin wa'yannan mutanan daga ganin'ta karuwa ce.... Ratsa ta sukai suka fita abakin titi suka tsaya suna neman abin hawa da sauri muzabfar ya sauke glass ɗin motar'sa tabbas ita ce tsayawa yayi yaga ikon Allah cikin sa'a suka sami abin hawa amma wannan karon guda biyu ta tarar musu.... hawa sukai ta hau tare da su dinana da rabi ta masar da asho suka hau dayar jan su yayi waya muzabfar ya dauki ya soma laluban lahin ASIF har ta kasai be dauka ba tsaki ya ja ya ajiye wayar ya yiwa motarsa key ya tada ita ya kusan kaiwa gida sai ga kiran asif ya shigo wayar'sa da sauri ya ɗauka ya saka ta a speaker yace "Yanzun nan naga girlfriend ɗin ka, haɗa rai yayi yace"kai lafiyar ka qalau kuwa..?, wallahi ajiye maganar wasa yanzun nan ita da mutanan ta sun fito daga shagon salman yaron daka buɗe mai shago ajiye kofin hannunsa yayi yace "me taje yi....., wallahi ban sani ba amma kirawo salmanu ɗin kaji kasan fa ana yawan kawo min korafin'sa ya saka wasa cikin sana'arsa wata kila yi mata yayi ta yimai gayyar yan iska okay sai an jima yabe jira me zai ce ba ya kashe wayar kiran lahin salmanu yayi bugu ɗaya ya ɗauka cikin girmamawa ya gaishe shi amsawa yayi yaci gaba da cewa yanzu me ya faru a shagon ka...?, gumi ne ya wanke shi wato dai yana tare da munafukai a tare da shi labari yar ya je mai kenan bakin sa narawa yace "oga ba abin da ya faru...., kasan dai ba abin da na tsana sama da karya ka turo min duk a bin da ya faru tunda akwai CCTV camera yana kaiwa nan ya kashe wayar'sa "honey...., ɗagowa yayi ya zuba mata narkakkun idanuwan'sa gaban'ta ne ya waɗi amma sai ta dake tace"sweet har yanzu fushi kake dani...?, ɗauke kai yayi yace "me ne...?, kuka ta rushe dashi rungume tayi tana kuka be hanata ba haka kuma be rarrashe'ta ba har tayi me isarta ƙara gyara kwanciyar'ta tayi a jikin'sa a hankali ta fara magana muryar'ta a dashe tace "sweet ban sanka da riƙo ba amma a wannan karon ka juya mini baya baka cin abinci na inna yi maka magana a takaice kake amswa dan girman Allah ka yafe min...., baya son wasu kananun maganganu dan haka ya haɗe baƙin'su shima din a buƙace yake da ita cikin zafi zafi yake yin komai..... mantawa yayi da duk wani takaicin da ta kunsa mai.... Tsakin miji da mata sai Allah *Kano unguwar kofar mata* Kai tsaya tsaya tsaya anzo wallahi kana gota gidan nan sai ka dawo baya ina yi maka magana yawa wani kurma me mashin ɗin tsayawa yayi suka sauka kuɗin sa ta dauko ta bashi cikin hassala tace "karɓi mana ka tsaya kana kallona...., fitowa yayi yace"anya kuwa kina da hankali kuwa tun daga zooroad kika zuba min mutane sai tsami suke shine zaki dauko 500 ki bani...., tab lallai yau akwai tashin hankali kai ni kake faɗawa haka jar ubancan nawa mukai da kai zaka kawo mu... Ubanki mukai be ƙarasa maganar'sa ba ta wanke shi da mari hannu ya saka zai kwanka mata mari ASHO ya riƙe hannun'sa yace "wallahi kana kai hannu fuskar'ta sai na cire maka kafaɗa.., kai kuma wane kasan wannan yar iskar'nan me tayi min....? laifin dad'i karewa mu haɗu a page na karshe domin shiga paid group zaku yi payment ta wannan number 8141785374 Amina alhasan Muhammad opay 500 Ku turo da shedar biya ta wannan number 09061890481 only WhatsApp Dan girman Allah in baki shirya ba kar ki min magana GIDAN MAGAJIYA FATAHIYYA MUHAMMAD YAKASAI EPISODE 49-50 https://whatsapp.com/channel/0029VaLdFeg4SpkQ9xyW5c0k .........................END OF BOOK 2 Lallai kai dai anyi ɗan iska uwar dakin namu kake faɗawa haka zaka karfa ko sai na datsai maka maƙogaro ta tabbata dai duniya ta lalace na Allah sun ƙaranci Malam Murtala yau she ka fara yawo gari gari kana wa'azi bani da labari yan kajin mutane da in sun fito kakebi kana chabkewa yanzu kenan ka tuba magajiya ta faɗa tana zabga mai harara to magajiya ita shiriya ba sallama take ba Ubangiji ya nufa Allah na shiryu ko zaki dawo da hannun agogo bayane...?, ahayye rasss haɗe rai tayi yawa haɗari ya gangamo tace "zaka shige ko sai na lakaɗa maka duka...?, a'a abin bekai haka ba uwar shagalallu nayi nan insha'Allahu alkadarin ki ya kusan karyewa banza tayi mai tace "asho sake shi ka bashi kuɗin'sa in kuwa yaƙi to kaci tsire da kuɗin..., amsa yayi yana cewa Allah ya isa sauran kudina dabe isa ba yayo ka shege dari biyar fa mukai dashi sai da ya kawo ni shine yake wannan tujarar hhhh da yaga zai rasa ai gashi nan ya karɓa ASHO ya faɗi haka rabi yace "nifa wa'yannan kananun tsagerun wallahi baraza nar su bata bani tsoro magajiya mu da muka shiga kurkuku mene bamu gani ba....?, ae yanzu na gane me kake nufi duk inda aka haɗa hanya da shege sai ya nuna halinsa yanzu zan maganin ka Ku dakata kafin ku fara faɗa nan magajiya bamu kuɗin mu kunsan shege ba bakon mutum ɗaya bane nacin'ye bazan bayar ai ka bari mu shiga daga ciki tun anan za kai min zancan kuɗi to bazan bayar ba na cinye sai ku yan kani ku kwaɗan'ta namana ku cinye sai na bayar haka kika ce....?, gyara damarar kugunta tayi ta daure tamau ta kama kugu tace"dinana haka nace ku a kan kuɗi baku da sanayya yawa wacce zan gudu...., magajiya kinfa saba yanzu zaki ficiccike akan karya kice kin cinye ni kuwa wallahi kobo na bazai ciwon kai ba sai kin bani ta masar ya faɗa yana haɗe rai tab jar'uban can lallai na yarda duk wani dan bariki kunama ne yau Shekara nawa muke tare da ku na taɓa cinye muku hakkin ku bani nace ku rakani ba zan baku wallahi yanzu nace bazan biya ba ta zauna sai abin wani sarkin bani ba Kinga karki nuna mata tashanci har karkashin gada na kwana yau ko da aljanu kike yawa wallahi sai kin bamu kuɗin mu yar hau.. da hallacan kuyi shiru motar hisba naga na yowa nan auzubillahi kuskure bakin ka da hypo wannan ai jamana masifa ne rabi dan ku kun tafi kurkuku shine ba'aza wayi gari ba kuyi zancen jami'an tsaro to wallahi saidai a kama ku ASHO ya faɗa yana mai da hukar'sa shiga cikin gida sukai amma zuciyar magajiya ta kasa nutsuwa kuɗin su ta zaro ta basu tace "kai ASHO ciro hukarnan in ma zuwa sukai kama mu ba kayan laifi a jikin mu karkarinta wa'azi zasu yi mana in yayi hutar duniya to su bama aikin share masallaci da jin wa'azi., cire wa yayi yana cewa kuma fa haka ne ai su ba kamar wayancan marasa imanin ba nifa wani daki da aka kai ni wallahi bana gane dare balle rana wallahi shi ya saka nake yiwa kaska Allah ya isa Dinana ga babban wanda za kai wa Allah ya isa wancan me kama da Yahudawan farko dan anyi kidnapping ɗin matar ka ba bincike sai ya kama mu gamu ya'yan talakawa bamu da yancin kan mu... gabansu ne ya wadi jin sallama da kyar magajiya ta iya amsa sallamar tasu wasu matane su ka shigo da hijabi da tambarin hisba a jikin hijabin'ta sai a lokacin falmata ta fahimci uwani bata gidan haka ma kahu cikin karfin hali magajiya tace "sannun ku...uwanin bata nan..., a'a gurin ku muka zo jingina tayi a jikin bango ta harɗe kafa tace " da alama dai maƙiya sunyi aiki to ina jin ku..shaf shaf ku faɗi abin da ya kawo ku..., kallon kallo aka shiga tsakanin jami'an hisba Idcard ta ciro tace "sunana hauwa ali me allo ni jami'ar hisba ce an toro ni domin mu kai ku hisba.., daka daka waya aiko ki kin faɗamin abu a dubu gwara ki mini gwari gwari yadda zan gane ko ba haka ba dinana....? baiwar Allah ki tsaya mana ta karasa maganar mana ke ma matemakiyar tace ko kuma yar karere ai bake nayi wa magana ba ita nayi wa ganin yarinyar bata da kunya tayi shiru ci gaba da bayanin'ta tayi tace "mutanan unguwa sun kai ƙarar ku...., yanzu kuma na fahimta ina zancan ki ya dosa sunan wa dawa sukai muku list domin ni gidan nan cika yake maƙil fiye da tunanin ki sana'a nake nake rufawa kaina a siri yan baƙin ciki masu hassada sunkai muku karanta shine za kuzo ku yayi me mu yawa wasu kayan wanki ku zuba a mota yanzu dai ni zaku kama dan su wa'yannan ba ruwansu buƙata ke kawo su ai dukkan ku ake ce mu kama da yan daudu uku da dan ɗaba ɗaya sai ke lah ha'ilaha illallahu shikkenan dinana na shiga uku yanzu ina na kama hisba kaji banza gyara bakin ki ta masar mene bamu gani ba gurin Dass aka kai mu fa ABUJA BIRNIN TARAYYA kora masa dai ai mu an shamu mun warke billahilazi rabi ya faɗa yana turo dauri gaban goshi.... kunga mu tafi ai wannan harka bata gardama bace mu tafi magajiya ta faɗa tana yin gaba binta sukai har gaban motar su ashe da maza suka zo shiga motar sukai ta gumi magajiya tayi ta fara tunanin rayuwar'ta ta baya har a ka zo bata sani ba sai ji tayi tamasar ya taɓa'ta yace "munzo.., fitowa tayi suka mara mata baya har office ɗin oc akai kai su zama sukai suna jiran ikon Allah hankalin ta masar a tashe yake sai zare ido yake domin wannan ne karon'sa na farko shiga hannun hukuma shi kuma daman asho ai dan hannu ne yasha shiga basu an kare ba sai ji sukai tamasar ya fashe da kuka cikin mamaki kowa ke kallon sa ya ɓara baki yawa ƙaramin yaro har da bubbuga ƙafafuwa kai da kata wannan wane salo ne faɗa mana in da futa muma sai muyi dinana ya faɗa yana dafa kafaɗar'sa be kulasa ba ya ƙara runtumewa da kuka ta gumi magajiya ta zare tace "zakai shiru ko kuma wallahi mu naɗa maka duka wannan wanne irin iskanci ne...?, O.C ne ya shigo kujera ya ja ya zauna hannu ta masar ya shanye yawa irin lalurarrun mutanan nan wa'yanda suka sha ruwan mahaifa yana dalalar da yahu mamaki ne ya kusan kashe su magajiya tace "dinana kaga wani sabon barikanci....?, uhmm magajiya in kana da rai kashe kallo gyaran muryar da O.C yayi sai suka bashi nutsuwar'su da hankalinsu annu'ar buɗe taro yayi sannan ya ƙara da cewa al'ummar wannan ungowa ta kofar mata yakasai da zango sun kawo mana koken su akan ku musamman ma ke da kike tara yan iska wannan bashi ne karon farko da suka kawo mana karar ki ba mu nan gurin da kuka gani hukunci muke cikin tsarin addini in Allah ya temaka har shiryuwa mutum yake daman haka muke so mu zama sanadin shiryuwar al'umma kai Sheikh Ibrahim al Bashir ciro min dan kwalayan kan su da zanin su ya faɗa yana nuna su rabi Allah ya jada ranka kamar wannan bawan Allah bashi da lafiya maƙe murya ta masar yayi yace 'kar ka sake ka taɓa ni kana taɓa ni zan cire maka hanjin cikin ka...., salati su magajiya sukai dinana yace "innalillahi gani tsohon makirci wallahi lafiya yake...., kwantar da hankalin'ka ai munan da ka gan mu muna da maganin komai musamman ma masu cutar aljannu kamar yadda na faɗa muku kusan cewa hisba aikin Allah ce abin da Allah ya ce Annabi yace shi muke yi buga cinya rabi yayi yace "uhmm gaskiya fa domin abin da sani yayi ya kone min ruwan kaiii wallahi..., yanzu ya Sheikh kai shi gurin da ake ruƙiya kafin mu gama da wa'yannan wata ƙara ya kwalla tamkar zata fasa musu dodan kunne ya ƙara karkacewa yace "kuna ganin abin namu wasa ne kana takowa sai na cire maka jijiyar ƙwaƙwalwar ka...., ganin kamar zai raina musu hankali O.C ya tashi ransa a ɓace ya ɗauki wata zabgegiyar bulala ya zabgawa ta masar gantsarewa yayi cikin haɗe rai O.C yace "ya sunan ka...?, cire ɗan kwalinsa yayi yace"SANI BADAMAS HALLIRU..., zama O.C yayi yace"yanzu ku za a kirawo iyayen ku domin su san halin da kuke ciki ke kuma ki kawo saurayin ki a daura muku aure domin kyahun mace sittirar ta gidan mijinta... da sauri magajiya ta ɗago yau take ganin ikon Allah yawa wani uban'ta yana ginda ya mata sharadi abin da bata gane ba shine yan unguwar tasu cewa sukai tana zina ko me lallai ta koma zata ci uban dukkan wani munafiki da munafuka gyara zama tayi tace "Allah ya ja da ranka ni bani da saurayi kuma duk wanda ya kawo muku wannan karar to fa ɗan hassada ne ranka ya dade da wannan sana'a nake ci na ciyar da iyayena ni bana shaye shaye bana duk wata harkar banza ina kara mutuncin kai na ko ba haka ba deeni.....?, dinana da jikinsa ke tsuma yace "eh wallahi muma tayata aiki muke tana biyan mu kaf cikin mu ba wanda salla take huce shii wata ran ma mu muke share masallaci RABI'U da kake gani har janmu salla yake babban limami ne ASHIRU (ASHO) kuwa har koyar da ilimin addini yake SANI almajirin'sa ne shine me share majalisi O.C ɗagowa yayi tun da yake wannan hukuma yau shekara ashirin be taɓa cin karo da manyan yan iska irin wa'yannan ba ga kalami basa kama mutun sai sun yi kwakkwaran bincike tukunna suke kama mutum yau anfi wata ana kawo musu karar wannan shu'umin GIDA har mai gidan yanzu sai sun kirawo gama rubutunsa yayi ya miƙawa ya Sheikh yace "ka miƙa wa su liman sannan ka tsaya ko wanne a cikin su yabaka number ɗin mahaifinsa...., ba musu kowa ya karanto ci gaba da tagumi tayi gaban ta na dukan uku uku zama ai tashin hankali aka ce sai tayi aure ita yanzu ba aure a jerin abin da tasaka a gaba.... fita yayi bayan ya gama amsa UNGUWAR KOFAR MATA Malam surajo bansan ya zanyi da yarinyar nan ba akan auran nan a duk binciken da kayi nayi yaron nan bashi da aibu duk macen da ta same shi ta more ajiyar zuciya ya sauke ya gyara zama yace "yanzu dai ka kirawo su kace su turo duk wani sauran abu kabar min a hannu na ga wayon da kak mata na cewa auran hucin gadi ne kaga in ka ɗaura basai ya sake ta ba zan zauna na fahimtar da yaron wannan abin da yayi tamkar jahadi yayi sai uwani ta ci gaba da sana'ar tata..., ajiyar zuciya ya sauke yace "tom shikkenan yanzu bani da kuɗi a wayata aramin wayar ka....., bashi waya yayi kiran number MUZABFAR ya shiga yi har ta katsai ba a ɗaga ba kira uku yayi mai be dauka ba ya ajiye wayar yace "in ya gani zai biyo number idan ya kirawo sai kai mai bayani..., to Allah dai ya shirya mana yaran nan ka haife su ne baka haifi halin su ba kullum addu'a nake amma abin na ASHIRU tamkar tiri ka ci gaba da yi addu'a bata waɗuwa ƙasa banza abin nasa da sauki wallahi tunda baya ɗaukar kayan mutane lallai kam Assalamu alaikum gaban kawu ne ya waɗi ganin jami'an doka ya kuma tuna maganar da FALMATA tayi mai na zata bashi kudin belin'su da kyar ya iya amsa sallamar su gaisawa sukai ɗaya daga cikin su yace "sunana malam sulaiman Yusuf ni jami'in hukumar hisba ne...., Innalillahi malam surajo yaran nan sun sake jawo min wani tashin hankalin wallahi aurar da ita zanyi na huta wannan tashin hankali har ina tun da nake ko gurin yan bijilanti ban taɓa zuwa ba sai gani har nine da zuwa Abuja babbar headquarter D.A.S.S.......✍️ Bazan gaji da baku nishaɗi ba😂😂😂😂😂😂 Laifin dad'i..... ALHAMDULLAHI ayau na gama book 2 Domin ci gaba da karanta littafin nan ku ci gaba da payment ɗin ku gobe zan shiga BOOK 3 insha'Allah zaku iya biya ta wannan hanyar 8141785374 AMINA ALHASAN MUHAMMAD OPAY ₦500 KU TURO DA SHEDA TA WANNAN NUMBER 09061890481 yan niger zaku dauki katin AIRTEL 300fcfah ku toro ta wannan number 09061890481 Dan giram Allah in baki yi niya ba karki min magana