DARAJAR 'YA'YANA1-01 Posted by ANaM Dorayi on 11:41 PM, 08-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Cikin sauri sadiya take yin komai dan bata son mai gidanta ya dawo ya sameta ba yanda idonsa yake bukata ba.Tuwon (semo) tayi mashi miyar kubewa danya, sai farfesun kafar sa, sanan ta tanadifura da nono, tasa a cikin fridge don tana bukatar yayi sanyi.Ta share ko ina na gidan fes ta wada tashi da kamshi turare, taje ta fesa wanka sanan ta bata lokaci a gun kwalliya.Kankwasa kofar da taji ne ta tuna da 'yan yaranta, da sauri taje ta bude musu, kai tsaye ban daki tace su nufa.Wanka ta sake yi musu sanan ta shirya su cikin sababin kayansu masu kyau ta feshesu da turaruka.Ta dawo dakinta inda ta rasa wane kayane ma zata saka, a karshe ta yanke shawarar saka wani jan material riga da siket.Ta dubi kitsonta kanana da ta yarfa a madubi, sanan ta kashe daurin dan kwali. Tasan yau zata burge mijinta, musanaman da ta kalli lallen hannunta na fulawa da aka zana mata.Ta kalli agogo karfe shida da kwata, wayarta wadda ta dauke saboda rashin chaji, ta jonata chaji.Ashe garin sauri bata sa dai dai ba, don haka bata samu chajin ba har aka dauke wuta. banda haka da taji yanzu mijinta yana dai dai ina?Kwnkwasa kofar ne ya dawo da ita daga haushin rashin cajin da wayarta bata da shi, ita da yaranta suka diba da gudu don taryo mijinta.Tana bude kofar shine tsaye, sanye cikin kayan yansanda, daga ka ganshi kasan babban jami'ine, ta fada jikinshi tare da rumgume shi, amma me?Sai taga ya sabule tare da cewa sannu da gida.Cikin mamaki ta amshi ledar hannunsa tare da jakarshi, ya tsugunna yana sha kan yayan sa cikin jin dadi da kewa, sadiya ta tsaya cike da mamakin saboda al'amari da take gani a gurin me gidan nata.Abin da tasani a duk lokacin da ya dawo yakan iso ne a marmatse cike da kewarta, da ya shigo burinsa kawai ya rungumeta tsam a jikinsa kafin yaran, amma yau sai taga ita ce ta rumgume shi har yana sabulewa, lallai wanan sabon al'amarine a gurinta.To ko dai gajiya ce take damunsa?Kokuma fushi yayi ya gaji da kiranta bai samu ba?Ta dubi kanta, kokuma kwaliyarta ce batayi ba?Ta sake wai wayawa ta kale su inda yake rungumarsu daya bayan daya.Da kausar ya soma, sanan Al'amen, sai mama ta tuno yanda yake mata a duk juma'ar da yazo, ya kamata ya fi dokinta a wanan karon da ya hada saty biyu bai zoba.Abin duk ya dameta, tana tsoron kada wata masifa ko annoba ta ratso cikin kyakkawan zaman nasu, tana tuna da yadda take makale a gefen damansa sannan ya dauki mama da hannun hagunsa har cikin falonsu.Yanxu dai ba zatace ganin yara bane, domintasan yaransu sun taso sun samesu cikin wata rayuwa da suka shinfida ta shakuwa da kaunar juna.Sun saba ganinsu rungume da juna, sun saba ita da yaran suyi ta kokuwa a jikinshi, basa yin wani abu da zai kawo matsala ga tarbiyar yaransu, amma sukan rungumi junako yin falo da junan ana hira.Sun rigata shiga falo, ta shigo nan ma ta sake kallonshi, mamaki ganin ya zauna shi da ke zarcewa dakinsa, can suke zuwa ya basu tsarabarsu. Sanan ya basu ta iya ya ce su kai mata, sanan kada kudawo in na huta zanzo in gaidata, sai mu dawo tare.Su ce to Abba, su tafi suna tsallensu.Shi kuwa suna fita wata ran ko wanka baya yi zai rungumota ya ce Dear my choice a matse nake.Ya wancin lokacin sai ya samu natsuwa kafin ya ci abincin ba yan yayi wanka.Dan Aliyu mutum ne mai matsanan ciyar bukata.Cikin damuwa ta isa kusa dashi.Yaya Ali yau kagaji sosai ko?Ya dubeta me kika gani?Ta ce, baka saba zama cikin falo ba.Ya miko hannu bani ledar nan in sallami yaran nan.Ya fada ba tare da ya bata waccen amsar ba.Ta miko masa kanta daure ta nufi dakinsa da jakarsa, ya ba yaran tsarabarsu, kayan ciye ciye ne da na wasa, sanan ya mike ya nufi dakin sa.Kausar tace, abba yau ina tsarabar iya?Sadiya daga cikin dakinta ta kaso kunne taji amsar da zai ba da.Ba tare da ya waiwayo ya dubi kausar ba, yace kinga magariba ta kusa, bari in anyi sallah sai muje ko?Ya shiga daidai lokacin ta shiga ban daki dan hada masa ruwan wanka.Ta fito yana zaune bakin gado yana kwance igiyar takalminsa ta iso gurin.Da sauri ta tsugunna tare da cewa abba kausar yau kuma harda aikina zaka shigar min?Ta ci gaba da kwance takalmi tana cewa, yau duk na ganka wani iri daban, ko duk gajiyar ce?Ya ce gajiya saikace ba jami'in tsaro ba?Ta soma balle masa maballen riga, to baka jin dadin jikinka ne ko? Yaja tsaki, dan Allah ki bar ni da tambayoyinnan naki please, gabanta ya fadi, ta dubeshi da gaske yake yi fuskarshi daure.Jikinta yayi sanyi, ta gama balle botiran, ya mike ya nufi ban daki ta mike zata taimaka mashi kamar yadda ta saba, ya shiga sai ya banko kofar zata tura sai taji karar makulli yana kulle kofar.Cike da tsoro taje dakin tana kallon kanta a madubi, ko dai batayi kyau ba ne yau?Ta duba ba wata makusa, ta kara jan baki da turare sanan ta fito ta same shi yana shafa mai,ta isa gurinshi, ta ciro masa kaftani da wando na shadda mai ruwan sararin samaniya, ta ciro hular da zata dace da kayan ta ajeye masa, amma sai taga ya janyo jallabiya mai dogon hannu fara sol ya saka.Daga nan sai ta koma ta jingina da bango dan jiran ganin sarautar Allah.Ya fita, ta bishi ganin zai fita waje ta ce, tabban kausar abincin fa?A sanyaye tayi maganar.Ba tare da ya waiwayo ba ya ce, sallah zan yi tukunna.Kausar ta ce,Abba ina kayi sallar ka dawo kaje damu gidan iya, kada kaje daga can.Ya dubi yaran da murmushi zan zo muje kunji?Suka ce to Abban mu, bari muyi muma sallar.Ko da tayi sallar sake zama tayi gaban madubi tayi sabuwar kwalliya sanan tayi canjin kaya daga jan yadin zuwa leshin ruwan dorawa mara nauyi .Ba kamar ko yaushe da yake kashe waya baina zasu ci abinci wayarshi kunne kuma jifa jifa yana amsa kira.Guri daya taji dadi ya zage ya kwashi abinci kamar yanda yake yi ko yaushe, haka nan haka nan 'ya'yan shi yana ta surutu da su.Amma ita ya dauke wuta da lamarinta har ta kasa cin abincin ma, so take ta tuno kurun laifin da tayi masa dan kawai ta bashi hakuri.Bata saba da wanan yanayin da suke ciki ba, zuciyarta ta ce ko ya ta kiran wayarki ne ba a ji?Da sauri ta dube shi.Abban kausar nasan kayi ta nema na layi naa kashe ko?Ya dubeta ban nemi layinki ba, ba wuta ne ta ce eh ba wuta.Kutashi muje gidan iya,suka mike cikin murna,Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kausar ta ce,Abba, momi bata dauko hijabinta ba.Ya ce, bata son zuwa ne, tayi aiki ta gaji.Wanan ya nuna mata ba a son zuwa da ita tunda ba a tambayeta ba bare a ce ita ce tace ba za ta je ba.Sun barta cikin tunani da jimami, ta gyare gidan musanman gurin da suka ci abinci, tayi ta jiransu tana zaune a falo tana kalon TV amma inda zaka tambayeta abinda ake yi a TV din ba zata fada maka ba.Ita burinta kawai ta san laifinta, amma ina ta tuna da cewa anjima da yazo dole zai sauke ko mai dan tasan cewa ba zasu taba kasancewa gado daya da shi ba ya iya kauda kai daga gare ta.Itama zata ja aji lokacin har sai taji dalilinsa, ganin sun kai har sha daya sai kurum ta cire tayi shirin bacci, kayan baccin bakake masu matukar daukar hankali, ta dora hijabi saboda da yara zai shigo.Kausar ce kurun batayi bacci ba, Al-Amin yana sabe a kafadar dama, mama a ta hagu, kausar din tana biye dashi suka shigo.Kai tsaye dakinsu ya nufa da su, tabi bayan su yana kwantar da su, ya fita ita kuma ta gyara su, sanan tayi musu adu'a taja musu kofa.Dai dai lokacin kausar tana cewa momi sai da safe, sadiya tace, Allah ya kaimu kausar.Dakinta ta nufa ta sake fesa turare, sanan tanufi fridge don ta dauki furarshi wadda ta riga ta dama.Shiru ta tsaya dan ya riga ya dauka, ta nufi dakin shi.Yana zaune bakin gadonshi sanye da kayan bacci, laptop ce a gabanshi kan dan tebirin da ake ajeye mai fura.Kofin yana hannunshi yana kurbar furar, idonsa sanye cikin farin gilashi ta ce, tace ashe har ka dauko furar ka?Ba tare da ya dubeta ba ya ce eh.Ta zauna kusa da shi wai abban kausar nayi laifi ne da ake ta share ni? Ban gane na neke ta share ki ba?Ta ce na gane yau duk ka canza ko na ce abubuwa sun canza kamar ba mijina ba maita rairayata?Ya dago ya dubeta baki min komai ba.Ta dora hannunta a kan cinyarsa, abba kausar to naganka ne ni yau irin kamar banyi kyauba din nan.Ya kalleta Dan Allah ki barni ina yin abu mai muhimmanci ne.Ta ce, amma dai da aka saurare ni bai fi abin da ka ke yi muhimmanci ba?Ga mamakinta sai kawai taji ya daka ma tsawa,kin san me kike fada kuwa dan Allah tashi ki bani guri a nan,ta zaro ido, mikewa tayi ta nufi kan gado ta kwanta a ranta tana cewa ka gama kazo ka same ni ina nan kwance.Abin ta'ajibi ranar dai haka ya raba dare yana harkokinshi a internet sabon abu ga Sadiya mutumin da in yazo satin karshen mako hatta wayoyin shi kashewa yake suna manne da juna har sai ya tafi yana cike da kewarsu.Ko da ya kashe laptop ya kwanta juya mata baya yayi,don Allah babban kausar me yake faruwa ne?Dan Allah in wani abu ya faru ne ka sanar dani zan baka hakuri, ban saba da wanan rayuwar ba.Cikin zafin rai wanda banta ba ga ni ba ya ce, nace bakiyi mini komai ba, kina son dole sai nayi maki karya ne?Dan Allah ki bar ni in huta ki barni na ce.Ta rike kai to banyi maka laifiba me yasa ka canza min?Nasanka kai mutun ne mai bukata a marmatse ka ke zuwa in kayi saty daya, wanan satyn har saty biyu kayi amma sai naga kazo bana gabanka.Ya zoro ido to yau ban da bukata ko dole ne?Ya ja tsaki, tashi dan Allah taf dakinki bana son jaraba kada ki dameni.Kuka ne ya subuce mata, ta fita a dakin tunda aka kawota gidan yau ce rana ta farko da zata kwana a dakinta ita daya.Dan ko haihuwa tayi basa raba makwanci, ta fito falo ga mamakinta sai taga kausar tsaye a falo tayi saurin dai daita fuskarta tare da share hawayenta ta nufi kausar.Me kika fito yi?Kausar me kike so?Ta ce, mome naji abba ne yana fada ne, me kika yi masa?Ta kama hannun yariyanyar suka nufi dakin yara.Kan katifarsu ta kwantar da ita ta kuma ta kwanta a bayanta tare da rungumeta, kausar ta sake tambayarta momi kinyi laifi ne Abba ya ce ki fita? kasa magana tayi don al'ajabi ne ke dankare cikin ranta, ta danne hawayenta ta ce kausar laifi nayi masa.Kausar ta ce, momi ki bashi hakuri mana,'to' Sadiya ta ce zan bashi sai da safe in ya huce kinji?Kausar tace, eh.Sadiya ta ce ki daina tashi cikin dare kin ji, tadinga shafa kan yarinyar tana lallashinta hartayi bacci ita kuma ta koma duniyar tunani tuno farkonsu.Iya mahaifiyar Aliyu ya ce ga mahaifiyata, uwarsu daya ubansu daya,su 'yan asalin jahar jigawa ne, a karamar hukumar Hadeja.Mahaifiyarsu ta rasu ta barsu su hudu mazabiyu mata biyu, kawu Adamu da kawu Dauda duk iya ce babbar su.Lokacin da mahaifiyata ta na budurwa, dan haka iya ta dauketa lokacin suna zaune a Dutse da mai gidanta da yaranta hudu.Yaya sulaiman yayazakari, yaya sani, sai cikin yaya Aliyu.Mijinta ma'aikacine a ma'aikatar gona ta jahar Jigawa, daga baya yayi ritaya inda ya dawo kaduna da zama sana din dan uwansa dake noma.A unguwar mu'azu ya sai gida madaidaici a ciki aka haifi Aliyu kuma a nan aka aurar da mahaifiyata inda ta auri mahaifina wanda yakasance ma'aikacin gidan Raidio kaduna.Amma dan zariya ne kuma zariyar aka kaita,yana da mata biyu da yara kusan goma, ko a lokacin.Maimuna mahaifiyarta ta kasance mai hakuri da juriya, duk da cewa bai kasance mutum mai cika hakkokin iyalansa ba.Amma bata taba kawo kararshi gurin iya ba,don tasan iya tana da fada sam bata da wasa.Shekarar da yaya sulaiman yayi aure shekarar ce mujin iya Allah yayi mai rasuwa,sunji mutuwar ta farat daya yana cikin sallah yayi sujjada a masallaci har aka idar bai dago ba.An dago shi sai gawa, ashe mutuwar kenan.Yaya sulaiman koyarwa yake yi a makarantar yan mata dake Tudun wadan wada wato Sai yaya zakari kasuwanci a babbar kasuwar kaduna, duk da cewa ba wani babban dan kasuwa bane,Sani kuma da ya gama secondary sai kurum ya shiga wurin gyaran motoci dan a lokacin babu halin ci gaba saboda yanda karatu ya zama a kasarmu sai yayan masu shi.Talaka yana so yake hakura.Ya Aliyu karamin su kuma suna tallafa mashi don ganin ya samu karatunshi, kwanci tashi suma duk suka yiyyi auransu.Lokacin da mahaifiyata tana dauke da da tsohon cikina don ta jima bata haihu ba, har lokacin iya bata gane yar uwarta tana cikin matsala ba, sai bayan ta haife ni.Lokacin da taga komai babu, abin ci a gidan gashi ya sake yin aure ya ciko mace ta hudu,iya ta same shi ta ce, yanzu tsakanika da Allah Abubakar hakan da kake yi dai dai ne?A ce ka ajiye mata babu kulawa ba abinci badai baka da shi ba sai don zalunci?Ya ce ai za a siyo.Tace, gara ma ka siyo don ba zan dauki zama da yunwa ba, in an ganka a waje kwas kwas har da mshin din hawa gareka amma a gidanka da yunwa.A daddafe akayi suna inda aka rangada min Halimatu Sadiya, iya ta tasa mahaifiyata ta tafi da ita, tace ba za a bartaba haihuwar fari ba kulawa ba,Ita kenan gareni dan wadan can yan uwan namu sai munyi tafiya mai tsawo kan mu gansu.Sai da mahaifiyata tayi kusan wata shida lokacin ni da ita munyi bulbul tamkar kada iya ta bari mutafi, amma yanda mahaifina ke ta suntirin zuwa yana kuma turo mutane don baiwa iya hakuri sai ta hakura tace mu koma.Amma ta ja masa kunne sosai, to dan saukin yanzun ba kamar da ba, hakan yasa ki shiyoyin jin haushinta suna ganin ya fifitata shi ko tsoron karr a dauke ta ne don iya ta tabbatar masa in tazo taga ba daidai ba to zata tafi damu.Shakarata biyu ta sake samun wani cikin tun yana karami take fama da laulayi iya tana zuwa tare da yayanta akai akai suna duba mahaifiyata tare da kawo mata abubuwa.Iya taso ta tafi dani amma lokacin an ce inna da kalafucin uwa, kulafaci gareni sosai ta hakuraKu ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Gurin haihuwarta kuma taji jiki da kyar ta haifi yar bubu rai.Sanan itama jini ya balle mata ya dinga zuba kafin aje Asibiti rai yayi halinsa, ance iya taji mutuwar nan kaman me.Bayan anyi bakwai aka raba dan abinda ta bari sanan iya tace ba zata barni ba dani zata tafi da kyar mahaifina ya yarda don shima yaji mutuwar yayi kuka tamkar ranshizai fita , to mafarin zamana a gun iya kenan.Na taso cikin gata da tarbiya duk da irin son da iya take yi min, bai sa ta kasa bani tarbiya ba.Lokacin da aka kawoni gidan yaya Aliyu yana shekararshi ta karshe a makarantar kwana ta barewa kwaleji dake zariya.Sam yaya Aliyu halinsa ba iri daya bane da yayyansa, don su suna da sakin fuska da fara'a, amma shi kullun rai a hade ta bakin iya in tana masa tsiya takan ce na rasa inda ka gado wanan halin naka na shegen miskilanci, kullun cikin bacin rai sai kace jakadan yan wuta. Tunda nake gidan bai taba yi mun wasa ko hira ba, magana in ta hada mu to bata wuce yazo bai ga iya ba, yace Sadiya ina iya?Tare da haka ba shi dai raini ko rashin kunya, sai dai kafi ya ga saurin fushi gami da zafin zuciya. Yanada matsananciyar tsafta da ibada Iya na yaba masa a nan, tunda na taso Allah baitaba nuna mun bacci iya na dare ba, sai dai na rana, bayan azahar. Duk lokacin da na farka zan ganta tana yin nafilfilu. Yaya Aliyu akwai iya saka kaya, bani manta kawayena in sun biyo mini makaranta suka ganshi sai kiji suna cewa, sadiya yayan nan naki dan kwambo ne, ya cika yanga gashi baya fara'a.Nakan ce kurufa mini asiri kada yaji.Burin yaya Aliyu aduniya bai wuce ya zama police ba, kalmar da Iya ta tsana duk lokacinda ya ce mata shifa in ya gama karatunshi zai shiga makarantar horar da yansanda.Sai ta ce masa ya daina wanan tunanin don ita bata son dan sanda, wai a nata ganin sharri kullun ake koya musu, kullin suna kan titi suna karbar cin hanci.Wani lokacin tace, dan sanda da aka ce ko ya mutu gawarsa tana fita da ban, dan baki take to ban amince ba.Shi kuma sai yace, iya kiyi min adu'a buri na kenan zancen zancen ace kaza kaza duk sharri ne babu ma'aikatan da babu na gari, kuma babu inda ba battace.Kimin adu'a in zama mai kawo gyara a cikinsu kuma in na zama dan sanda in sha Allahu sai kinyi alfahari dani.Takan tabe baki ta ce, uhm ni rabu dani da wanan zancen, ni dai insuna yi sauraransu kurun nake yi, don sam in yaya Aliyu yana fira da iya bana sa baki, domin tsawa zai daka min ko ya harareni, haka nake rayawa a raina ba wai dan haka ta taba faruwa ba.Iya tana yin wainar saidawa a cikin gida, muna yin ciniki sosai, wani lokacin har da sha'anin buki suna ko walima duk muna yi da sana'ar ta take yi mana dawainiyar karatu ni da yaya Aliyu, sai dan abin da sauran yara suka kawo mata.Dan suma yanzu ko wanensu yana nan da dawainiyar iyalansa, karatun ya Aliyu shine mai cin kudi, dan Alokacin yana karatun digree sa ne a jami'ar Ahamadu bello dake zariya.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Yana karantar (Engineering) ban san yanda zan kwatanta muku ra'ayinsa ba, amma shi mutum ne mai babbancin hali da ra'ayi.Bayan ya kammala karatun sa ne ya dagewa iya yayyinsa shifa sai yaje police Acadamy, wato makarantar horar da manyan yansanda dake wudil jahar kano, dakyar ya sha kansu.Ko da yake har sai da kawunsu kannan iya dake Hadeja,Kawu Adamu ne yaje har gida ya lallashi iya.Bayan ta yarda tace, to ita fa bata da kudi,yaranta kuma suna fama da iyalansu, dan haka yaje ya nemi kudi.Aliyu ya ce, iya ai na fada miki asaida gona ta, ta gadonmu da aka raba mana.Nan ma da kyar ta yarda kawu Adamu shineya saida gonar Aliyu yaje ya amsa, haka yayita zirga zirga tsakanin kano da kaduna har sai da yayi nasarar shiga police Acadamy.Ranar farko da yaxo ni kadaice ina cikin wanke kayan waina bayan mun tashi, iya bata nan taje kai kudin kayan miyan wainar gobe, sai kurum naji sallamar sai naga mutum tsaye kyam da kayan dan sanda riga blue mai haske wando baki, ga wanan takalmin na su da hula.Nikuwa dama gani da tsoron Dansanda, sai naji cikina yana kugi, fuskarshi daure yace, bakinki yana ciwo ne, bakya iya amsa sallama ko? Cikin in-ina nace, wa...alai...kassalam.Ya zuba min harara, yau ne kika fara ganina ne da har zaki tsareni da idanu ko na can za maki ne?Na sunkuyar da kai, a'a ya nufi dakin nace bata nan ta je wurin Isa mai kayan miya, ya ciji ya tsa to dauko min makullin dakina najena duba inda na san iya tana ajewa na dauko masa da zan bashi sai da na dan rusuna.Ya amsa ya nufi dakinshi nazo na karasa wanke wanken na gyara gurin ya fito cikin gajera wando da yar T-shirt irin ta yansanda,Ina cikin kicin zan dora tafashen kashin waina, yace baki san mutun yazo kiyi mai tayin abinci ba, kenan ina ganin rowa zakiyi?Nace nayi zaton ko kana azumi ne, na ga kullun kana yin azumi,yace, oh, dama kina samun ido ne har kika san cewa kullum ina Azumi?To yau ban yi.Nace, duk abincin ya kare sai sauran tuwo kuma baka cin dumame, sai dai in ko na dafa maka wani abu.Yace barshi nasha cornfilakes,ya juya ya nufi dakin sa.Na sauke ajiyar zuciya ban san meyasa ba yaya Aliyu in yana guri bana so in tsaya a gurin sai in ga duk ya cika gurin,gashi tsananin tsoransa nake bai dai taba duka na ba watarana ne dai da yake iya gadanga take ce masa sai tace in kira mata shi, ni kuma naje nace iya ta ce kazo gadanga.Wata tsawa da yayi min kadan ya rage in saki fitsari, ya dora yatsinsa a dan manuni a goshi na.In kika sake ce min gadanga sai na zaneki tas kinji ko?Jikina yana bari nace, kayi hakuri.Don tsoro lokacin har fitsari nayi a wando.Lokacin da iya ta dawo tai murna da ganin autanta, nan suka zauna suna yin fira, cikin hirar ne naji tana yi masa zancen aure, inda ta ce gadanga dan Allah ka nemi matar aure kasan shekarunka nawa yanzu?Yayi dan murmushi ni kwan nasan shekaruna, muke nan kullum cikin rubuta date of birth ba dole in rike shekaruna ba?Talatin da uku ne kacal. Iya tayi dariya talatin da uku shine kacal?Ai dai cikin sa'anninka ina tsammanin kai kadai ka rage ba kai aure ba.Ya ce iya ba ni kadai na rage ba, kin manta da usman?Ta ce, usman bikin shi kafin Azumi ba kuyi waya bane?Aliyu ya zaro ido, iya da gaske?Tace, ko jiya na kira shi na fada masa yau zan shigo shi ne zai ki sanar dani?Iya ta ce kila sai kazo din za ka ji zancen.Ya ce, iya kiyi adu'a kawai amma ayanzu ba mata a ga bana, kokari na in hada wanan course din nawa.Ta ce, Allah ya taimaka.Ya ce sauran mu wata shida.Ta ce, to Allah yasa a gama cikin nasara, ni dai fata na ka zama mai gaskiya da amana, kayi aiki a kasarka da kishi.Ya ce in sha Allahu, na gode.Duk ina jin su har suka gama ya dube ni ita waccen sunyi jarabawar J S. C.E din?Iya ta ce, tin yau she har sun amso yan zu kici kicin shiga SS din ta muke yi, ya ce zo ki bani saka makon na ki in gani, dan nasan bawata kwanya ce da ke ba.Iya ta ce, in ji wa?Sadiya boko da islamiya tana da kokari.Na dauko gaba na yana faduwa na bashi ya duba sanan ya kalleni babu laifi, amma kina jin turanci?Na sunkuyar da kai, amma ban iya bada amsa ba.Ya ce shirmen yaran hausawanmu kenan, kuna jin tsoro ne kada kuyi ba dai dai ba ayi muku dariya, to ai gara ayi muku dariyar sanan a gyara muku.To ni dai daga yau kada ki kara mun hausa.Har in koma duk kuma zuwan da zanyi in baturanci zakiyi mun ba bana son jin maganar ki.Iya ta ce, kuji mun fin karfin hali gurin gadan ga, wanan ai mugun horo ne.Yare ba na uwarka ba, ba na ubanka ba kace dole sai tayi maka magana da si.Ya ce, in ba haka ba yau she zata iya ga yanda zamanin namu ya zama sai da karatu, ko da ta gama scondary zaki mata aure? Iya ta ce, tana samun miji zan sallamata, don haka kar ka takura mata.Ni dai nayi ciki na barsu nan suna ta jayayya, yana cewa ilimi ko dan tarbiyar yara ai ko ni ba zan auri matar da bata ta shiga jami'a ba.Iya ta ce Allah ya taimaka ni tawa tana samun miji zan turata can gidan mijinta shi ne babbar jami'ar ta.Ku dai yan zamani baku da magana sai dai in kun tashi aure kun fi son yan boko sabo da tarbiyan yayan ku.To amma kada ka manta ni banyi boko ba, amma duk in da kuka shiga yabon ku akeyi ana sha awarku.Aliyu yayi dariya, to iya in kin lura ai baban mu yayi boko, kefa kika ce mun lokacin su yaya sulaiman suna yara sun zo da home work shi yake musu.Nima lokacin da na taso sune suke yi mun ba, tace to wanan ce tarbiyar?Ban ce ilimi baya cikin tarbiyya ba, amma bashi ne gundarinta ba.Gun darin tarbiya shi ne ka dora dan ka kan hanyar Allah da monzo (S. A. W) su rinjayi komai a kan mazaunin shi.Sanan ka cusa musu Tauhidi su iya rike Amana,Cika Alkawari,Tausayin na kasa da taimakonshi, Girmama na sama, in dan ka ya san wanan sai ka hada masa da ilimin zamani da na adini shi ne tarbiyya.Kai in dan ka ya san wadancan ya rike ko bai je boko ba zai yi rayuwa ingantacciya.Aliyu ya ce, haka ne zancen ki Iya, Allah ya sa muma muyi tarbiyar yayan mu kamar yanda kuka yi mana.Ta ce ameen.Ina da ga ciki ina jin su na ce, in dai Iya ce duk musun ka da gardama tana yi maka baya ni sai ka fahimta.Abin da ya bani al'ajabi da mama ki, da dare na je kai masa abinci dama fakon sa na yi tayi dan ba zan yar da wata magana ta hada mu da shi ba, tunda ya ce sai da turanci, niko dan tsinta tsinta na iya.Dan haka ina ganin shigarsa ban daki na dauki abincin na nufi dakin sa na ajiye zan fita sai na hangi wata mujalla can kan katifar sa, ni kuma da shegen son kalon hotunan yan film.Na zata irin tasu ce yan fin din India, sai na koma na dauko na bude jiki na ya dauki tsuma ganin mata tsirara.Da sauri na rufe wato dai mujallar ta tsiraici ce, na sake bude wani shafin da sauri na rufe, ina fitowa yana isowa kofar dakin.Ya ce cikin harshen turanci me kike so na cecikin hausa, dama abinci ne na kawo maka.Ya matso ya damki kunne natamkar zai cire shi.Ba na ce kada ki kara yi mun hausa ba?Nayi shiru dan ina tsoron yi masa turanci ya ji ba dai dai ba ya ci uba na.Ya sake matse kunnan, cikin turancin da zaniya na ce yayi hakuri.Ya saki kin ci sa'a daga yanzu ba hausa tsakanina da ke.Duk cikin turanci yake maganar.Ni dai nayi daki ina Al'ajabinshi, mutum kamar na Allah ashe dan iska ne, ya tasa hotunan batsa yana kallo.Shi kuma da ya shiga dakin sai yaga kamar an jawo mujarlar daga inda ya ajiyeta, a ranshi yace wato dai yarinyar nan ta bude mujallar nan kenan,In ko haka ne ban ji dadi ba, amma sai wata zuciyar ta ce, kada ka zargeta, domin bata da rawar kai, tsoranka ma takeji ba zata taba maka komai ba, sai kurun ya samu natsuwa tare da gaskata hakan.Kwana biyu yaya Aliyu yayi ya tafi, niko cikinkwana biyun nan binshi nake da kallon mamaki.Bayan tafiyar shine na samu ci gaba da karatu na a makarantarmu ta maimuna gwarzo.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Kwanci tashi su yaya Aliyu an kammala wanan karatun, buki sosai akayi ko na ce walima dan su yaya Sulaiman su har can suka je nan gidan mu kuwa mun aikatu.Anyi wainar shinkafa, da su zobo da kunun zaki, daga can suka turoshi kaduna (headquarter) a matsayin A. S. P Aliyu Tukur.Ranar da ya zo gida na jima a uwar daki ina tunanin fitowa saboda tsoron maganar da zan masa da turanci, gashi a fallon iya suna fira.Na zauna ina bitan abin da zan fada masa da turan ci, can iya ta kwalo mini kira na amsa, ta ce me kike yi?Na fito, ya kalleni dama tana ciki, kin wani kunshe kamar wani munafiki?Na ce, sannu da zuwa. Cikin turanci na yi maganar, shi sai lokacin na tuna mai da batun wani turanci.Ya kalli iya sanan ya kalle ni ya amsa, na ce ina taya ka murna, ya ce ya gode.Ya tambayi nawa karatun na ce lfy lau.Da sauri nayi waje ina tsoron kada ya daukowani zancen da va zan iya amsawa ba, a rai na na ce, baka sanan wannan ba na fi sati ina haddar su.Bayan na fita ya cewa iya, to kin ga dai yarkita soma zama baturiya, iya ta ce, eh, ai hakan yana da kyau.Tunda ya dawo kullun zancen shi da iya ba ya wuce kayi aure gadanga, ka fito da mata sai dai in bai zo gidan ba, kokuma bai zo mata fira ba.Har ta kare ta ce yaje gidan hajiya talatu ya nemi diyarta Jamila, yace iya kiyi hakuri har inga wacce ta yi mun da idona, bana son cushe cushe.Ta ce, duk fadin unguwar Mu'azu har yau baka ga wacce kake so ba?Sai ya ce, ina nan dai ina binkitawa, har dai ta hakura ta zura mashi ido.Daga baya naji suna hira da yaya sulaiman wai ta sama mashi magani tana ganin kamar bashi da lafiya, niko da naji wanan xancen lokacin cewa nayi a raina, ras yake kila ma neman matan shi yake yi a waje tunda mai ya hada mara lafiya da hotunan tsiraici?Kuma bayan nan ina zaton yana kalon fina finan tsiraici, don lokuta da yawa in yana kallon in nayi sallama dakin zai kai abinci ko wani abu sai yayi sauri ya kashe, sanan ya ce in shigo.In kaset din arziki ne menene na kashewa?Amma na sa a raina wata rana sai na kama shi. Haka kuwa watara na xan kai masa abinci darana lokacin aikin dare yayi da safe ya dawo,Iya kurun ya gaisar muna aikin waina ya shige daki ya kwanta.Sai kusan sha biyu sanan ya farka, lokacin Iya ta tafi gurin sabo mai shikafar waina, ta ce in ya farka in kai masa ruwan zafin shida waina in kuma bredi zaya ci to in kai masa.Ya fito ya shiga wanka, da sauri na dauki dan flask din sa na ruwan zafi na nufi dakin, ko mai a kashe yake amma na san zan kunna in gani tunda wanka ya shiga saboda shi mutum ne mai dadewa a wanka.In dai ya shiga tamkar zai canza fata, don haka ina lokacin sallah ya katato xai shiga ban daki iya kance bari muyi alwala dan in ka shiga sai lokacin salla ya fita baka fito ba.Na jona komai ya kawo na ce oji bulumme can kasa dan muna funci aikuwa CD yana gama login sai ga mata da maza tsirara suna aikata masha'a.Da sauri na kashe na fita naje na ci gaba da aikina abin da na gani ya girgiza ni kuma naji haushin kaina da karan bani na.Na fito na dauki waina da bredi naje nayi sallama ya ce in shigo na shiga na ajiye xan fita ya ce tsaya, me kika shigo yi nan dakin?Gaba na ya fadi na ce ni flask na kawo, ya ce daga nan sai kika yiyi me?Cikin in ina na ce, banyi komai ba ya Ali.Ya tsareni da idanu, bashi da tabbacin nayi wani abu amma yana shigowa yasan an shigo.Ya kalleni, jiki.Na fita sanan na harari dakin na tafi.A raina na ce dan iska, amma wani lokaci sai ya kure wa'azi sai kace na Allah. Kwanci tashi ba wuya, muna cinye kwanakinmu har mun kammala (SS3) mun zana jarabawa kuma lokacin ya zo dai dai da saukar karatun mu na alkur'ani.Munyi komai cikin nasara, kuma nayi walimata a gidan mu inda iya ta matsawa ya Aliyu sai ya buga mun memo wanda zan rabawa kawaye na.Sauran yayyansa ma sun taimako, baba na kuwa da naje zaria na fada masa dubu biyarya bani wai inyi hakuri da yake ina zuwa danhutu can wani sa'in iya tace inyi sabon dinki da kudi na.Dangi kam sun xo babu laifi, har yan uwa na na zariya, babanmu ya zo da su komai na yayi babu laifi.Da yamma ni da kawata Aisha muna kwashe kujerun da muka zauna akai mukayi walima a waje da kawaye na.Mun hada su guri daya sai naga guda biyu wanda ya Aliyu da wani abokin sa suka zauna su na hira.Ta ce, kije ki amso wadancan cikin zolaya tayi maganar, don tasan ina jin tsoron shi.Na ce, ke kije ki amso.Tayi yar dariya bari inje.Tayi tamkar zata nufi gurin sai ta fasa.Muyarshi ta katse maganata da zanyi lokaci daya kuma gaba na ya fadi, Ke! Na wai waya, zo nan.Naje na rusuna na gaida su cikin in ina ya ce, ke daga jin maganar ki baki da gaskiya ko?Na ce, a a.Ya ce, to me nene nayin in ina din?Nayi shiru, ya kalli abokinsa ga ta.Abokin ya ce, ina yi muki murna da yin saukar alkur'ani mai girma, Allah yasa anyi na tsoron Allah.Na ce, amin.Ya Aliyu ya ce, jeki dama murnar zaiyi maki.Ina tafiya ya kalli Aliyu ya ce, kanwar nan taka tayi fa.Ya Ali ya ce, ok, iskancin naka har agida ma zaka yi?Auwal ya ce bada wani abu na ce ba, cewa nayi tana da kyau.Kai da ma ka shiga kayi yar gida tunda duk matan dake sonka baka kallon su.Ali ya ce don me zan tsaya kallon yayan mutane, alhalin na san cewa ba auran su zanyi ba?Auwal ya dan yi masa dukan wasa a kafada tare da cewa, ko jiya munyi gulmarka da Sajen Bello, wai ina ma shine mata keyiwa wanan shishshigin, da sai ya more kuriciyarshi son ranshi, amma kai kullun cikin Azumin dole, in kaga mata sai kace kaga Abokanan gaba.Aliyu ya ce, ban ga anfanin zina ba, koda ba haramun bace mutum ya gujeta, ya kyamace ta, dan kare kansa daga cututukan zamani.Ina fada maka ina da kyama ba zan iya hada jiki da wayan can ba, kuma dole in naga mata in hada rai tun da ba halali na bane, kuma ba muharramai na bane.Kullun dai ina adu'a Allah ya bani mace ta gari mai kamun kai, kuma da kuke bin matan Allah ya shiryeku, kai gashi kayi auran ma amma ba ka daina ba.Kayi hattara duk abin da ka shuka shi zaka girba, kana kallo wani can zai bata rayuwar yayan ka yadda ka fada ta yayan wasu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Auwal ya ce , ka samu cikin adu'a abin ne dawahalar bari, mata ne nishadin rayuwa, hira da su ma a kwai dadi ne.Tsaki Aliyu ya ce in kaso kaji dadin ba?Ni kuwa bana fatan in ji dadin fira da mace wadda ba tawa ba, ina nufin halalina.Auwal ya mike, bari ni in tafi kai dama malami ya kamata ka zama ba dan sanda ba.Sam Aliyu be mike dan raka shi ba, daga nan suka yi sallama.Shi kam tunani ya shiga, shima yana sabo wajen kallon fina finan batsa da karantar mujallan batsa, duk da cewa bai taba aikata zina ba ya san wanan laifi ne babba.Kuma in mutum bai daina ba wata rana zai kai ga aikata zinar, kuma tunda Allah ya rufamini asiri tsawon lokaci yana yi ba wanda yataba ganinshi, ya kamata ya daina.Ya tuna lokacin da ya fara, wata rana yaje dakin su Auwal da rana lokacin suna jami'ar Ahmad Bello ta Zaria, ya ga wani novel a dakin ya dauka ya karanta, ashe na batsa ne.Daga lokacin sai yaji yana so ya gani, ya ko je wani shago a kasuwa ya siyo kaset din tare da mujallar tun daga nan lokaci zuwa lokaci sai ya siya ya kalla, sanan ya kona su ya sake siyan wani.Shi da kanshi ya sha fada wa kanshi cewa, yanda yayi Imani zai tsaya gaban Allah haka yayi imani za a tambaye shi yanda yayi ya sami kudi da kuma hanyar da yabi gurin kashe su.Me zai ce game da wanan kudin da yake sawa yana siyan batsa?San nan baya karanshi da komai sai karata da masu hankali?Lallai wanan abune da ya kamata yayi makansa tun kafin ya mutu.Ya mike tare da kudircewa daga yau ya tuba,ba zai kara ba. Dai dai gwargwado ba xa a ce bani da kyau ba tunda Allah bai halicci mumuna ba matsawar mutum yana da kyan hali, balantana a ce mutum musulmine.Aina ya ga kyau sai dai kuma in ba tsafta, ni fara ce sol amma bani da dogon hanci.Wanan baisa fuskata muni ba, haka idanuwa na matsakaita ne, ni mutum ce mai tsananin kwalliya ko alwala nayi sai na sake sabuwar kwalliya.Haka nan iya bata gajiya da siyan mun kayan kwalliya, sanan bata ganin bekena duk lokacin da zan bata gurin kwalliya.A cewarta ya mace doki ce sai da kwalliya, abinda kawai bata yarda da shi ba shi ne, ayimini dinkin da zai nuna surata, nan ne zata ce ba zata bada kwamasho ba gurin yada zina.Ta ce, shigar da yawancin mata keyi ita ce ke haifar da zinace zinace sannan zata zuba ko nawa ne ta yankan mini yadin hijabi amma mayafi dai sai dai inyi asusu in siya. Shima din ban isa in siya karami ba sai babba, kuma mai kauri ban taba jin haushinta ba dan nasan tana kare nine daga afkawa cikin shaidan.Dai dai misali ina da farin jinin samari masu sona, dan ma iya bata bari in fara fita zance da wuri ba sai da na kai SS2 duk masu zuwa gurina da aure suke sona.Sai dai ni cikinsu banga wanda yayi mini ba irin injishi kane kane cikin raina din nan ba, fada haka iya take cewa maza ki tsaya ruwan ido daga karshe kowa ya gudu kizo kina nema.Ai yanxu lokacin ya mace mai hankali ake dubawa wanda yake da hali mai kyau sanan ba jahili ba kuma ya kasance yanada yar sana'ar da zai rikeki, to ki kamashi.Allah shine mai azurtawa, in da rabo sai kuyi arzikin tare, ke in ma baku samu anan ba to ya baku na gobe kiyama.Yawan yi mun wanan nasihar yasa nake ganin zan iya tsaida Idris kuma zan iya auransa amman sai mun zauna da kawata aminiyata Aisha.Mun zauna da ita ita ma tace, gaskiya duk cikin masu sona babu kamar Idris a hankali.Mun yanke shawarar in tsaida shi ita kuma dama akwai makocinsu Bello dake sonta.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Wata safiya Iya tana kwance ba lafiya dole na fasa zuwa makaranta tunda mun riga mun hada kullun waina, sai kuma ciwon cikin dare.Ya Ali ya shigo da shirin fita, don bai san bata da lafiya ba sai da ya shigo dakin, ya girgiza da ganinta kwance cikin bargo dakyar take magana.Arude ya ce, ya babu lafiya ne?Tace, eh, yace meyasa ba a tashe ni ba a gida fa na kwana?Ita wacen sakaryar ba sai ta fada min ba.Iya ta ce ni na hanata ta ce bari ta taso ka, ya cire hula, bari muje Asibiti, bari in samo mota, ta ce, a a naji sauki.Fita yayi sai gashi da likita wani dan nan unguwar ya duba ta sai gashi hadda ruwa a dora mata.Ranar dai bai fita bahar rana, bai taba birgeni ba irin ranar, duk wani abu sai yayi, hatta bata magani a baki da abinci sai gurin la'asar sannan ya fita.Su yaya Sulaiman,Zakari da Sani duk sun zo da matan su, sanan makota na ta zuwa.Da yaje gurin aiki ya bada uzirin shi sai ya dawo kusan shabiyun dare, jikinta yayi sauki.Ina jiyo hirarsu,rokonshi take yayi aure ta ce Aliyu bani da wani burin da ya wuce inga auranka, kai na fuskanci kafi son sai na mutu sanan zakayi aure.Jikinshi yayi sanyi, dan ya kasa tuna ranar da ta kira shi da Aliyu, cikin tautasar murya da lallashi ya ce, zan yi iya, in sha Allahu kina raye.Ta ce, kayya, gadanga kullun haka kake cewa, ni dai ai tuni na cire rai ka tashi katafi na yafe maka Allah yayi muku albarka kai dasauran yan uwanka.Yarinyar nan sadiya dan Allah ko ban tashi ba kada ku bari ta koma zaria ta zauna gurin wannan yaron hardai ta sami miji kuyi mata aure.Ya ce, iya ke ce da kanki zaki aurar da ita insha Allahu, ta ce shi kenan tashi kaje ka kwanta.Hankali tashe ya fita bayan ya tai maka mata ya kawota cikin daki, na tashi idona naxubar da hawaye, na taimaka mata muka kwanta.Ina kuka kasa-kasa ta ce,Sadiya lafiya? Tace iya bana so inji kina cewa zaki mutu ki barni, ta ce in fada ko kar in fada sadiya ba zan kara lokaci ba sai dai in ajalina bai zo ba.Da kyar bacci ya daukeni, lokacin iya tayi nisa da bacci.Shima Aliyu tun da ya koma dakin shi fa ya kasa ko zama, lallai dole ne ya nemi mata, sai dai matsalar shi ta ina zai fara?Bai taba yin budurwa ba, bai taba soyayya ba, shi kuma yana ganin kamar raini zai ja masa in yaje kofar gidan su yarinya.Amma bari gari ya waye yaje wajen usman amininshi.Kafin ya wuce masallaci sai da ya fara lekowa dakin mu ni da iya duk muna sallah, sanan ya wuce,dan Allah ya kawo mata sauki a cikin daren daga masallaci gidan Usman ya wuce, ta wya ya kira shi cewa gashi a kofar gida,Usman ya ce, lafiya?Aliyu ya ce, lafiya ba lau ba, fito kaji.Da sauri usman ya bude gida ya fito, sama sama suka gaisa.Usman ya ce, aboki lafiya? Aliyu ya ce ina fa lfy, jiya tsohuwa ba lafiya, ta fara bar mun wasiya, sannan tayita jaddada min burinta kawai nan duniyar shine inyi aure.Usman yace aboki ba ita kadai ba, ni kaina buri na kenan, to tunda kaga tsohuwa ta tsananta gara kayi ko kwa rabu lafiya.Aliyu ya ce, ai baka sani ba, tunani na yanzu ina zanje nemo mata?Na rantse maka banda budurwa... Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 DARAJAR YAYANA1-02 Posted by ANaM Dorayi on 08:55 PM, 09-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA ___________________NA ___________HALIMA K/MASHI Usman yayi yar dariya sanan ya ce, ni da zakaji shawarata wanan sadiya ta gidanku?Aliyu yace, ah haba?Usman yace, naga yanda ake yabon hankalin yarinyar, ko a gida tana da matsalane? Aliyu ya ce, sam ko a gida bata da matsala gaskiya, amma ban taba jin koda alamar sonta ba, to wanan yarinyar ma ina ganin ta tsaida wanda take so, in ma ba ta tsayar ba sai inga ta yi mun yarinya.Shekarunta sha bakwai fa yanzu in ban cika ma ba, usman ya ce, dai dai.Nafi son wacce ta shiga makarantar gaba da scondary a kalla ta mallaki hankalinta, ta san yadda zata kula dani sai nine zan koma in kula da ita.Usman ya ce, ba yaran yanzu ba, tunda kaga bata yiba in kaga wata da tayi maka ko a unguwarku ko a kafatanin unguwar mu'azu ka fada min yanxu anjima sai muje, kaga yanxu sai kaje wa iya da kwarin gwiwa.Aliyu yayi shiru yana tunani can ya ce, aboki kasan Allah?Nifa ba wai ina kallon mata bane, na layinmu ma ban sansuba balle na unguwa.Usman ya ce, to aboki ka tsaya a Sadiyar mai hankalice,Sadiya tayi.Aliyu yace inda ta kaicin yake sai kuma in kirata ince ina sonta?Usman ya ce in baka iyawa bi ta sama mana ka samu iya ka fada mata kana son Sadiya, nasan zatayi murna.Aliyu ya ce, aboki daina cewa ina sonta, zadai ayi aure amma ba wai ina sonta ba, Aliyu yace kuma ba zanyi karya ba tunda banji cewa ina sonta ba,har Aliyu yaxo gida tunani yake anya kuwa zai amince cewa yana son auren sadiya? Lokacin da ya shigo dai dai na bare magani na mikawa iya, ta afa tare da kora ruwa, ya tsaya ya rike kugu yana kallon mu, tunaninshi a wanan lokacin lallai babu wanda ya dace ya auri irina, bisa hujjarshi tacewa ba zai sami matsala ba wace take tsakanin iya da matan yayanshi ba.Iya tana kuka cewa cikinsu matar yaya Sulaimance kawai ta san darajarta, kuma tabbas hakane domin sai suyi wata uku basu zo sun gaida ta ba.Ita ba wai tana kwadayin abin hannunsu ba ne, a a ko ba komai taga yan jikokinta yayi, amma Sadiya bata da uwar da ta wuce iya.Dan haka yana nan ko baya nan zata zamo a karkashin kulawarshi, burinshi yaga ya daukewa iya duk wani matsalarta, su kuma yayinshi suji da iyalinsu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tunaninsa ya katse lokacin da iya ta ce, gadanga ka shigo ne?Yayi firgigit, na shigo iya.Na gaida shi na fita, shima a ranar bai iya yi mata zancen ba, karshe ma tunani yayi ya samu yaya sulaiman suyi shawara.Haka kuma bayan sallar isha'i ya nufi gidan yayan nasa bayan sun gaisa sai ya sanar dashi abinda ke tafe dashi.Yaya sulaiman yaji dadin zancen da Aliyu yazo dashi, sanan yace sai ka samu yarinyar ku daidaita, Aliyu ya ce, ina ga ba sai na sameta ba, indai iya ta amince shi kenan.Yaya Sulaiman ya ce, iya ba zata ki ba, yarinyar ce abinji, in ta ce bata sonka fa?Aliyu ya ce, ai nima ba wai ina sonta bane, dacewar auren kurum nake dubawa, shi yasa.Ya Sulaiman ya ce, shirme kenan, to kai in kaje wajen iyar ce mata zakayi ba sonta kake ba?Aliyu yayi murmushi ce mata kurum zanyi ina so na auri Sadiya, Sulaiman ya ce, Allah yayi mana zabi na alkairi.Ka bari zanje gurin iyar, duk yanda mukayi zakaji.Aliyu ya ce to.Yayi godiya yayi masa sallama ya tafi..Sulaiman ya sami iya cike da karfin gwiwa, ganinshi babu wanda zaikai iya murna kai yasan har goron albishir zata bashi.Amma ga mamakinshi yana gama labarta mata dalilin xuwansa sai yaga tayi kicin kicinda fuska ta ce kaine kaga sun dace ka bashishawara koko shine ya sameka da zancen?Yace, a a dazu ya zo mun da zancen sai kuma naga dacewar haka.Ta ce, to ka koma ka fada mashi ban amince ba, kace mashi ya nemo matarshi can itama ta nemo nata mijin.Jikin Sulaiman yayi sanyi ya sake tausasa murya ya ce, iya ban san dalilinki ba, kokuma akwai abinda kika hango wanda ba na Alkairi ba?Ta ce, na farko dai kasan halin gadanga, zuciya ce dashi ga saurin fushi, ga miskilanci tsiya, ga shegen jin kai.Sanan na sha ji ko in ce ya sha fada min cewa shi yar jami'a yake son aura.Niko tawa ko secondary din bata gama ba.Sulaiman ya ce, iya in kin duba tunda shi din ya ce ta mashi ai ina ganin ba za a sami wata matsala ba.Fir iya ta ki zancen, duk ta inda sulaiman ya bullo sai iya tabi ta wata hanyar, haka nan yaya sulaiman ya hakura ya fita rai babu dadi.Aliyu ya sunkuyar da kai yana sauraron sakonshi a gurin yaya sulaiman, sam bai zaci jin haka ba, amma sai ya ce, ba komai Allah yasa haka shine mafi alkairi, na shi ganin ba zai damu ba, tunda dama ba wai yana sonta bane.Sai dai kuma yanda ya tsammaci abun yafi haka, samun kanshi yayi da shiga damuwa, ko ba ya son yarinyar hakika ya tsananta dason aurenta.Ya samu iya da kan shi wata safiya yaxo gaida ta bayan yayi shirin fita cikin dakin sa.Ya ce, iya me yasa ba zaki bani auren sadiyaba? Ta lissafo mashi dalilinta kamar yanda ta lissafawa yaya Sulaiman takuma fada masayaje ya nemo mata can.Ranshi ya baci amma bai nuna ba, sai dai cikin sanyin murya ya ce, to shikenan iya na hakura, amma ba zan taba xuwa ko ina neman aure ba saboda ina da munmunan halayen da ban can canta a bani mataba,tace, ni ban ce ba,ya ce to iya tunda ba a bani a gida ba in naje nema a wani gida suka bani na cutar dasu tunda ba su san hali na ba,yana kai aya ya mike tare da cewa, sai na dawo.Ita kuma lafuzan nashi suka hanata magana.Ita zahiri ba wai bata son auren ya Aliyu da sadiya bane, na farko ta san halinsa, sanan tana tsoron ta tursasa min.Kullun Aliyu sai yayiwa iya naci amma taki ko ta ga zai dauko zancen sai ta hade fuska.Wata safiya ina kwance kangado ina fama da matsananciyar ciwon mara, dama mun rabu da yin waina tunda iya tayi rashin lafiya.Ya Aliyu ya ce, a daina yin wainar duk wata nake wanan ciwon marar.Yaya Aliyu ne ya shigo gaida iya, bayan sun gaisa ta ce, har ka shirya fita kenan?Ya ce mata eh, akwai wani case a hannunsane yana son ya kammala dashi kafin fitowar(AC) ta ce, to Allah ya taimaka, a can zaka karya?Ya ce, eh.Sanan yayi shiru ta ce, da magana ne?Ta sani in har yayi haka to da magana a bakin sa, ko da yake ta san zancen na sa daya ne, bai wuce na sadiya ba.Kuma tana son Sadiyar ta ji ma kunnenta in ta amince ruwanta don haka ta ce yaya autana?Yace iya dai maganar Sadiya, Allah iya ba maganar yabon kai ba, ina da kamalar da za'a bani mata, ya ko ta gidan waye 'yar taki ai ba kyau tafini ba,ya fada cikin sigar wasa, ta ce,duk da haka ba zan baka ba, kai ita fa tarigata fidda mijinta.Yace dan Allah iya ki fada mata kinji?Ta ce, au, nice ma zan fada mata?Lallai ba ma son auran nata kake ba.Ya ce, ni iya in na fada mata sai naga tamkar zata rainani ne.Iya ta ce, kun ji girman kan ba?Don Allah kayi hakuri nifa ka tayar dani,ba zan yarda ba.Aliyu da ya gaji ya fita.Tun daga lokacin da naji ya Aliyu ya ambaci sunana na mike zumbur hankalina atashe,ni Sadiya yaya Aliyu yake nufi ko wata?Kai in ko nice na more, dan gaskiya yaya ba irin mijin da zance bana so bane, tab!Wanan shine tsintar dami akala.A a iya kada kyi min bakin ciki, ina jin fitarshina fito da sauri ina kallon iya, ko zata ce wani abu, amma sai ta shareni, na ta nufintadaga yanda na dauki al'amarin tunda ta tabbatar naji.Ko daga irin fitowar da nayi, ganin iya ba zatayi magana ba sai na ce iya ta dubeni, wai ya Aliyu wa yake so? Ta tabe baki dan Allah rabu da shi, wai ke, na dafa kirji da karfi na furta da gaske?Ta ce, zan maki karya ne?Na ce to iya shine zaki ce mashi ina da wanda nake so?tace, au.Sharri nayi maki kenan?Ina ce ke naji kina cewa kin tsaida Idris? Na ce, ai ban fada mashi ba.Ta ce, meye nufinki yanzu?Kina so ki ce min kina son Gadanga?Nayi shiru tare da hade fuska, mamaki ya cikata, ta ce, Sadiya dama can kina son Gadangan ne?Na ce, nifa ban ce ina sonshi ba, amma ke meye dalilin da kika ca baki yarda ba?Iya ta shiga tafa hannu tana salati.Kin tirke nine lallai sai kinji?To ba wani dalili bane sai na kare mutuncinki, gadanga yana da zuciya, gadanga yana da fushi, sanan ga miskilanci,ina tsoron ki shiga matsala, gaki karamar yarinya, shi kuma shekaru sun dan soma ja.Da sauri na ce iya in dai dan wanan ne na yarda kinji?Ta ce, wai me ya burgekine a dan sanda duk jikinki ya hau bari? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce, to iya gaskiya ya Aliyu ba irin mutumin da za a ce ba a so bane .Ta ce, ni dai na ce a a ban yarda ba.Na mike cikin fushi na fita tsakar gida, da kallo iya ta bini, matuka ta ji mamaki musanman ta sanni bani da rawar kai.Ni kuma kicin na shiga na zauna banyi aune ba sai kurum naga hawaye suna zuba a ido na, ni kaina har naji mamakin kaina.To da bai ce yana sona ba fa?Ranar haka na yini har dare, kusan mutum uku suka aiko kirana naki fita, iya duk tana lura dani tana kallona ranar bai dawo gida ba sai sha biyun dare, sanan tunda a subahi ya fita.Yau sam na kasa sukuni, iya sai kallona takeyi tana salla, can bayan ta idar ta ce sadiya!Nayi shiru, ta ce, nasan kina jina ta shi kawaiki tashi, na tashi zaune ta ce, sadiya ina ganin baki gane nufina ba game da zancenkike da gadanga shi yasa har kike fushi dani.Gadanga bahogon mutum ne, ni na haifeshi na sanshi tun yana dan karamin shi, gadanga bashi da dadin lamari, amma in kinji Allah ya baki sa'a.Sai dai ina so ki sani in da wanda zaiyi farin cikin aurenki da gadanga to ya biyo baya na,sai dai duk da haka ba zan kasa fada maki gaskiya ba.Shawarar da zan baki kuma ki rage rawar kai in ya fahimci kina doki kimarki ta zube.A zaton iya zan hakura amma sai taji na ce, in sha Allahu ba zan sami matsala ba.Ta tsura mini ido haka kika ce? Nayi shiru ta ce shi kenan, to da sharadi ba zuwa kawo kara.Da sauri na ce, to,da kallo tayi ta bina ni dai na tashi na koma makwancina ina murna.Na zaci da safe zata neme shi ne ta fada mashi ayi sai kurum ta share, ko da dai ya fita da wuri, wasa wasa sam taki zancen inaji lokaci da yawa da ya dauko zancen zata ce don Allah ya rabu da ita.Sai dai abinda ke bani mamaki, kullum yanda yaya Aliyu bai can za min yanda yakemin ba , amma nakanyi uziri cewa kila sai iya ta amince sanan za mu soma yin tadi.Cikin haka ne har aka dauki tsawon lokaci muka shiga shirin zana jarabawa (SSCE) duk na kori samari na babu wani mai zuwa tunda na fada musu na tsaida miji.Shikam ya Aliyu bai san na sani ba, kullum ya zo gurin iya sai yayi mata nacin shi fa yana nan yana jira ita kuma takan ce mishi kar ya dame ta, ba ya ce ya fi son yar jami'a ba?Ya je ya nema.Ni kuma in ya tafi wani sa'in in ce iya don Allah ba kince kin hakura ba, tunda na yarda?Sai ta ce min sakarya, dubi fa ko kallo baki isheshi ba, amma duk kin tsamgwami kanki don fitina, ni dan kare mutuncinki nake kin abin nan. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Usman abokinsa yaji shiru batun maganar Aliyu da sadiya, sai ya zo gurinshi musanman don zancen , dama ya kirashi a waya yaji cewa yana nan.Bayan sun gaisa usman ya ce, aboki wai haryanxu ban sake jin batunka da yarinyar nan sadiya ba, in mun hadu baka yimin zancen ba, ni kuma ban tambaye ka ba.Aliyu ya gyara zama yayi sanan ya lumshe ido don haushi ya ce, kabari kawai abokina, haushin maganar nake ji, shiyasa ban taba yi maka zance ba.Ya miko hannu ya dafa gyiwar usman abokina ban taba samun abinda ya bani matsala ba kamar maganar yarinyar, ni abin haushi duk lokacin da nayi kudirin hakura dazancen sai na kasa.Kullum adu'a ta Allah ya yaye min ita daga raina, amma abin ya faskara.Ko son yarinyar ne ya kamani? Usman yayi murmushi lallai sonta kake yi, Allah yasa ita ma ta soka hakan.Aliyu yace ina ruwana da ita?Iyace kurum damuwata, in da ta amince shi kenan, amma baiwar Allah nan wai zan cuci yarinyar ita ba zata bani yarinya karama ba.Ranar harda cewa na tsufa.Usman yace zanje in sameta aboki, kada kadamu.Aliyu ya ce, ko kaje matarnan ba zata yarda ba, na dai fada mata ni na hakura da yin auren. .Usman yayi ta dariya tare da zolayar Aliyu da cewa, aboki ka dai shiga da yawa, to da ka ajiye duk wani girman kai ka dinga kiran yarinya hira in taga haka zata fi yarda cewa da gaske kake yi.Aliyu ya ce ka yarda ni ba zan taba iya kiran yarinyar ba, ko ba Sadiya ba, kuma sanin kanka ne ban taba ba, so bansan ta ina zan fara ba.Ba ta ita fa nake ba, in iya ta yarda tayi hakuri ta aureni dan da cewa auren sai kuma ya ja tsaki kada ma ta hakura.Tama ji dadin zancen ta samu miji irina, Usman ya ce, yabon kai?Aliyu yayi dariya aboki ka fadi gaskiya, ni da ita wa yafi kyau?Bai jira amsa ba ya ci gaba na farko dai kaga ita fari ne kurum ya ceceta..... Usman ya katsishi au, wai dama haryanzu akwai mummuna?Ni dai yanzu na daina ganin mummunaai tunda naga alamun kai ya waye, ba a zama da kazanta, Aliyu ya ce, haka ne, amma wani wan wani ne a kyau.Usman ya ce, duk da ka fi ta kyau dai ita zuciyarka ta zaba, zanyi maka kokari, zanje in samu iya.Aliyu yace tunda ka dage jeka din, duk yanda kukayi zamuji. Kamar yanda Usman ya alkawarta yazo ya samu iya wajen la'asar ina yi mana tuwo, itakuma tana zaune a kofar dakinta.Na gaida shi sannan na dauko masa tabarma ya zauna, na kawo masa ruwa sanan naje na ci gaba da aiki na.Daga inda nike ina jiyosu suka gaisa sanan ya fara yi mata zancen da ya kawoshi.Iya dama akan batun abokina ne da yar uwarsa sadiya, iya dukkan su naki ne, a ganina wanan abin farinciki ne.Iya ta tsuke fuska,Usman ina ganin kimarka, zaifi kyau ka bar zancen nan bana jin cewa zan amince.Usman yayi shiru yana tunanin yanda zai bullo mata.Can ya ce, to shi kenan, amma na so ki amince domin yana cikin wani hali na son yarinyar nan, nasan halinshi kin san halinshi,baya daga cikin mutane ma su magana biyu.Yayi mun rantsuwar ba zai taba aure ba in ba Sadiya ba, duk duniya ita yake so.Zaman shi haka nasan yana damunki.Ta ce in duk duniya Sadiya yake so ita Sadiyar ya tambayeta ta ce tana sonshi? Nifa ba zanyiwa yata auren dole ba, don in faranta masa.Daga inda nake a kicin na da ga hannu ko nace ya tsa tamkar mai bada amsa a cikin ajinmakaranta, sanan na kwalawa iya kira!!Ta kalleni tare da yi mun da kuwa, shi dai baisan dalilin dakuwar ba, tunda ya bani baya, ita kila ya zaci laifin nayi mata. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Usman ya fahimci nufin iya, shi yasa ya ce mata Aliyu ya dinga kiran yarinyar suna fira.Ya dubi iya, to in sha Allahu za mu tuntubi yarinyar, idan bata amince ba shike nan.Yana fita ya dauko waya ya kira Aliyu, bugu uku ya dauka. Usman ya ce, Aboki da farko fara bani goron albishir.Cikin sauri Aliyu ya ce kada dai ka ce mun tasaurareka? Usman ya ce, in sha Allahu munyi nasara Aliyu ya ce shi kenan sai na xo aboki, gidanka zan sauka kaitsaye daga office yanxu ina kan wani aiki.Suna cin abinci a falonsu Usman yana koro mashi bayani duk yanda sukayi a karshe yace yanzu kaga tana nufin ta yarda sai dai amma tana so ka kira yarinyar ka nemi amincewar ta.Aliyu ya tsirawa Usman ido, sanan ya ce, ai wanan shine mai wahalar, gaskiya a boki ba zan iya kiranta ba.Usman ya ce, tsoronta kake jine?Raini ne bana so, yanxu dai kai kaje ka sameta kuyi magana.Usman ya ce, nima ke nan zan yi maka yakin neman sonta?Aliyu ya ce, duk yanda ka ce amma ni in na kira tafa ba ra'ayinta zanjira ba, umurni xan bata.Usman ya ce, shi kenan ka bari xanje.Bayan sallar isha'i muna zaune ni da iya muna cin abinci tare kamar yanda muka saba, yaya usman yayi sallama shi da matarshi Anty Abida da yaran shi guda biyu,tsam na mike daga cin tuwon ina yi musu sannu da zuwa, suka zauna na kawo musu abinci da ruwa, sukace yanxu suka tashi daga kan cin abinci.Na koma tsakar gida bayan na dauki yarinya wato Ummulkhairi, yarinyar tana da wayo yar mai kyau taji kitso, na ce Ummulkhairi kina makaranta? ta ce eh mana, kuma Abban mu yake kaini har ma da Abulkhairi, nace, iye, to koya mun karatu.Ta ce, na islamiya ko na boko?Na ce, a a islamiya dai.Ta gyara zamanta a cinyata ta ce, in miki sunayen Allah kyawawa?Na ce, eh,ta fara kenan babanta ya fito, ya kallemu karatu kuke yi? Na ce, eh, tana koya mun ne.Yayi dan murmushi ya ce ummu jeki wajen umman ki, ki ce mata ta jira ni ina zuwa.Ta na shiga daki ya ce, kanwata zo mana.Na mike na bishi zuwa kofar gida, nasake gaisheshi nayi , bayan mun tsaya ya ce,Sadiya nasan ba zakiji mamakin kiran da nayi maki ba ko?Na ce ba wani mamaki, kila zaka aikeni ne. Yyace bahakabane na kiraki ne dan in sanardake wani abun alkairi, ko da yake ban san yanda zaki amshi abun ba.Na gane zan cen ya Aliyu, ya duba duk cikin matan da ke garin nan yaga babu wadda tayi masa sai ke, tamkar bai san zancen ba na furta da karfi so!!!Usman ya ce ba wani abun mamaki bane, dami ne kika tsinta a kala.A raina na ce lallai ma yaya usman din nan, to bari in latsa shi.Na ce, ya Usman ka ce masa yayi hakuri kawai dan na riga na tsaida mijin aure wanda nike so.Ya Usman ya ce, kin kai shi gida ne?Na ce, gobe ne iyayan sa zasu shigo gidan mu.Usman ya ce, in har zan baki shawara ki yarda zan so ki dakatar da su domin kowa zaki aura na tabbata bai kai Aliyu ba, samunsa sai an tona, ko na ce irinsa.In kika sameshi a matsayin miji tabbas zakiyi alfahari samun muji kamarshi, mata da yawa suna sonsa, kila sun fahimci nagartarsa, amma ba matsi in baki sonshi zan koma in fada masa cewa baki sonshi da aure.Na kalleshi bance bana sonshi ba, saboda duk abinda iya ta haifa dole ne in soshi, kai ko wani ne can ba danta ba in dai ya mutunta ta to zan soshi bare dan cikinta, na riga na zabi wani ne.Usman yayi shiru, ya zaci da yayi mun magana zan amsa da murna, can ya ce, to yanxu mai zanje in ce masa? Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce, ka fada masa zanyi tunani zuwa gobe. Ya ce, shi kenan, zan kiraki amma kiyi shawara da kawarki wadda ta sanshi, na san zata fada maki qualitie din Aliyu. Na ce, ba damuwa. Ya ce, shi kenan gobe zanzo naji. In kin shiga kicewa Abida su fito mu tafi daman na sallami iya. Na ce, to. Bayan tafiyar su iya tashiga yi mun fada wai ai gashi nan saboda bai daukeni da muhimmanci ba abokinsa ya turo min, ta san jikina yana bari na ce na yarda. Na vata fuska tamkar zan saki kuka na ce, ni fa iya banyi fa rawar jiki ba, ce masa kawai nayi zanyi shawara zuwa gobe. Ta ce, ato in kin kimanta kanki yaga darajarki in kuma kinki ni dai na fada maki babu zuwa a kawo mun kara. A waya Aliyu yaji duk yanda mukayi, mamaki ya dinga yi wai wanan yarinyar ce zata ce sai tayi shawara, dawa zata yi? Kuma ita ce wa? Usman ya ce ita ce mace. Aliyu ya ce, shi yasa kaga ba zan iya kai kaina ba ga wata ya in ce ina son ta ba, bare tayi mun yauki, nidan oya-oya ne. Usman ya ce ka barni da itakawai na san jan ajine zamuyi nasara cikin jin haushi Aliyu ya ce, in taki ka kyaleta kawai, yarinya sai kace wata ta gold sai ga ruwa nake yi a kanta. Ya ja tsaki nan ya kashe wayar ba tare da ya sake jin mai Usman zai ce ba. Kwana Aliyu yayi da zullumin halin da zai tsinci kanshi, in yarinya taki amincewa da shi. Da safe ina shara ya fito daga dakinsa ban san me ke sani faduwar gaba a duk lokacin da na ganshi ba.Na gaida shi ya amsa cikin isa, kuma a ta kaice kamar yanda ya saba. Sanan bai ko kalleni ba sai dai nice na bishi da kallo. Namiji ne sosai ko tafiyarshi ta shaida haka, daga ganinshi baka ga rago ba, dama abin da ya dace dashi kenan jami'in dan sanda. Iya daga daki ashe tana kallona ta ce, in kin gama kallonshi sai ki ci gaba da sharar ko? Cikin kunya da shauki na ci gaba da sharata. Da rana naje gidansu Aisha kawata nake bata labari duk yanda muke ciki, tace, tabbas! Sadiya idan zan fada maki gaskiya ki amince kawai, kada ma ki tsaya wani jan aji,sau nawa nake fada maki Aliyunku unique ne?Allah in kika yi sake kin tsaya yauki kya zo kina na dama, kin san shi da zuciya ya ce yafasa.Kash!Ina ma nice ya ce yana so?Jin haka yasa na kagu dare yayi.Har na debe tsammanin xuwansa dan tara ta kusa, duk na tsure kar dai ya Aliyu ya hakura da gaske.Can sai na tsinkayi muryar wani yaro yana sallama ni ina cikin daki a kwance kan kujera.Iya ce ta amsa salamar don tana tsakar gidan, ya ce an ce sadiya ta zo inji wani a waje.Ka fin ya rufe baki na mike, zaraf na suri mayafi na fita.Iya ta ce, kai jama'a!Kai jama'a!!Ni wanan yarinya ko dai zaki kai kanki ne?Na ce ban fa san ko wane ne ba, ma ai iya.Cikin gatse iya ta ce, ina zaki sani, shiyasa kike ta sintiri tun daxu kin kosa ko wanene maya zo?Na ce, sai na dawo.Ta ce, kada ma ki dawo ki kwana can.Usman yana tseye a gurin da muka tsaya jiya, na sameshi da sallama, muka gaisa ya ce to kanwata nazo jin me kika yanke?Na danyi shiru kamar mai nazari, ya ce, kada ki damu in har baki sonshi ya ce babu komai.Na ce, ai ba zan iya cewa bana sonshi ba ko dan iya, don haka ka ce masa na amince.Usman ya ce, Alhamdulillah, sai kin ji mu.Ranar nayi farinciki har nafila nayi don godiya ga Allah, iya ta ce yau kuma ibadar ce ta motsa har da nafilar dare?Ni dai ban tanka mata ba, ta ci gaba, Allah ya sa a dore, ina ta samun gadanga ce akayina san daga yau shi kenan. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Washe gari yaje ya samu yaya zakari da yaya Sulaiman yayi musu bayani, su kuma suka sami dan uwan mahaifinsu dake nan layin kasuwa, a nan unguwar mu'azu.Nan dai suka sa ranar zuwa zariya gurin mahaifina don jin zance, Aliyu da zasu tafi ya bada dubu hamsin ya ce har sadaki duk yanda ta kaya shi kenan.Mahaifina yayi murna har yana cewa wannan abu ai da ba sai anxo ba, ita iya Sadiya tata ce, Aliyu ma nata ne, da ba shi kenan ba sai dai muzo a yan gayyata.Kawu ya ce, a a kun wuce haka, kuma dole abaku hakkinku.Baba yayi ta godiya kafin daga bisani ya ce bari ya kira dan uwansa.Sun yanke sadaki dubu talatin sanan aka basu na gaisuwa goma, sai dai suna dawowa suka fadawa iya duk yanda akayi.Iya ta ce sam yarta tafi talatin, su kawo goman nan hamsin ne sadakin yarta, sanan gadanga ya ciko goma kudin gaisuwa.Da kyar suka shawo kanta ta amshi goman, sadaki arba'in kenan.Aliyu dai yana zaune yana jin su yana kallonsu amma bai ce ko mai ba.Suka ce an tsaida rana watan tara sha biyar da shi, lokacin kuma ana watan shida.Aliyu ya ce yaya Sulaiman lokacin nan bai yi tsawo ba kuwa?Anawa ra'ayin nafi son wata biyu, iya ta ce, har ka gama shiri ne zaka ce wata uku yayi maka kadan?Aliyu ya ce, wane shiri ne mai zafi?Ba lefe bane ko meye ne kuke cewa ya rage ba?Ta ce, kana da gurin zama kenan ko nan zaka gyara mu zauna?Ya ce, a haba dai, zan nemi gurin zama duk a cikin wanan lokacin.Ta kalli Sulaiman ni fa in nayi auran nan zataci gaba da karatunta ku shaida wanan, in ya ce a a za a jimu.Aliyu ya ce, na sani iya, nima ina son ta ci gaba da karatun.Ta ce, to batun aure a barshi wata ukun, sai kaga lokacin ya zama ba ka kammala da wani abun ba har kake raina lokacin.Ya ce Allah ya kaimu.Ina zaune cikin ajinmu bayan mun gama zana paper din mu ta karshe, ina kallon yanda yaran ajinmu suke ta jin dadi da murna tun da muka baro hall din.Ta gumi na zabga ina mamakin irin halin ya Aliyu, yau kusan sati hudu da sa muna rana amma ko sau daya bai taba kirana ba, haka nan kuma ko cikin gida ya shigo ban isheshi kallo ba.Nima fa yanxu na soma sarewa, anya kuwa mutumin nan yana sona? Kullum iya sai tayi min gori, yau kam zanje in nemi ya Usman.Bayan nan na cewa Anty Abida in yadawo tace ya zo, ina son magana da shi, ta ce to zata fada masa na ce ina su Ummulkhairi?Ta ce suna makaranta.Da daddare kuwa sai gashi ana sallama dani, na mike har ina tum tube.Iya ta ce, sai karaftu kike sai kace a dakin Ajantina, na san dai ba wanda kike son gani bane, dan nasan shi ya fi karfin ya kiraki. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Nace, iya to ai ina so ne na ga ko wanene.Ta ce, oho ke dai kika sani.Ina fita yaya Usman ne kamar yanda nayi tsamani bayan mun gaisa ya ce, Abida ta ce kin zo nema na.Na ce, eh.Na sunkuyar da kaina ina wasa da yatsuna, na ce dama nazo ne a kan maganar mu ne da ya Aliyu, in abin ba zai yuwu ba gara mu hakura tun yanzu.Ya gyara tsayuwa wani abu ne ya faru?Na ce to ya Usman a haka ne za mu fahimci juna in san abinda baya so yasan abinda bana so?Na ci ga ba, bai taba kirana da sunan muyi zance dashi ba, ko gida ya shigo ban ko isheshi kallo ba, shi bashi da wani lokaci ne sai na aikin shi?Usman yace ba wai zan goyi bayan shi bane amma ninasan kina ranshi,ki fahimce shi, shi mutum ne mai kishin kasarsa da aikin sa, shi yasa baya samun lokacin kansa.Amma da zarar kin zama a gidansa na san dole ya baki dukan lokacinki.Nayi shiru kamar maganar ta shigeni, ammada na tuna ko kallo na bayayi na ce, yaya Usman ka san Allah ba dan aikin shi bane, ko kallo fa ban isheshi ba.Usman ya ce, to bari zanyi mashi magana.Na ce, don Allah kada ka ce nayi maka magana, kada yayi tsammanin na damu da shi ne.Usman ya ce, zanyi masa maga na da ma ai, ba zan ce kece kika sani ba.Kusan sha dayan dare Usman ya daga wayar Aliyu tare da yin sallama, bayan sun gaisa Usman ya ce aboki dazun ina ta kira baka daga ba.Aliyu ya ce, bari kawai aboki, lokacin ina tsakiyar wani case ne abin nan yana matukar daga hankalina tare da bani mamaki.Ka san wani mutum dan kimanin shekara arba'in aka kama yayi wa yar shekara hudu fyade.Usman ya zabga salati tare da cewa, wai aboki wanan wace irin masifa ce?Ko dai wani tsafi ne?Aliyu ya ce, wa ya sani?Wannan fyaden na kananan yara yayi yawa.Kullum sai mun sami wanan case din wlh yanda abin nan ke mun zafi a raina zan iya kashe irin wadannan mutanen, don mugaye ne.Idan mata ne su je mana ga karuwai nan,Usman ya ce, to Allah ya shirye su, ya tsare mana daukacin musulmi.Aliyu ya ce, amin aboki to kaji halin da nake ciki, lokacin da ka kirani lafiya lau dai ko?Lafiya lau dama zance ne ya kamata mu shirya muje muyi hira da yarinyar nan ko?Aliyu ya ce, wace yarinya ke nan?Usman ya ce, sai karinka yi kamar baka san da zancen ba bayan nasan tana ranka.Aliyu ya ce, tsakani da Allah sai ka tuna min.Usman ya ce, ok, tunda yanxu iya ta yarda dole ka manta.Aliyu ya ce subuhanalla? Dama wai Sadiya kake magana?To wacce hira kuma zamuyi tun da na rigaya an gama magana, sai jiran lokaci.Usman ya ce, ai duk da haka za aje ayi hira ta san abinda baka so don a samu zaman lafiya.Aliyu yayi yar dariya.To ni ba haka tsarina ya ke ba, ina zaton in har zanje gurin budurwa zan jene don ina tallata kaina in in samu shiga,tonina riga na samu shiga babu dalilin da zan matsawa kaina.Usman ya ja tsaki kai dai bahago ne wlh, to sai ka sai mata waya ko ta waya kunyi magana.Aliyu ya ce, to yan zu dai kaine sarkin yakinta ko?Suka sa dariya.Usman ya ce, da gaske nikeyi, akwai wata waya da ake saidawa mai kyau nan kusa daoffice din mu (MTN OFFICE) ya ke aiki.Aliyu ya ce, ka suyo mata in kazo sai na baka kudin, sanan kai zaka bata don har karshen satin nan ban san lokacin dawowata, kafin ita ta tashi na fita.Usman ya ce shi kenan.Washegari da daddare ya usman yazo ya kawo mun waya wai iji yaya Aliyu, inyi hakuriza mu rinka waya aikine yayi masa yawa.Bani da zabi dole na hakura tunda ga waya har da layin (MTN) ko da na nuwa wa iya baki ta tabe sanan ta ce Allah ya sa alheri.Tun da na karbi wayar ko flashing ba a taba yi mun ba, ga dai lambarshi a ciki ya usman ya samun duk da cewa har da kudi a layin nawa nima cewa nayi ba zan kira shi ba.Sai dai in ta kiran kawaye da yan uwa wadanda nake da number su. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Wata rana da dadare naji Iya tana yi masa fada cewa yana zaton haka za ayi auren ba lefe, biki saura wata daya da kwanaki, amma ba a ga yana motsi ba.Ya ce, abin ne ya shige masa, amma gobe zai je ya sami matar ya sulaiman.Ita da matar Usman Anty Abida sukai ta zaryar zuwa kasuwa, saura sati biyu lefe ya kammala da dinki da komai.Iya ta ce ya Aliyu ya bada kudin mota a kaisu zariya, ni kuma nan kawaye na sun matsa da batun anko, lokaci yana tafiya gashi ba zan iya yi mashi magana ba.Aisha ta ce, kiyi wa iya magana.Na ce, iya kwana biyu bata sana'a , bata da kudin anko?Tab! Ba zai yuwu ba.Wayata na dauka inyi kamar zan kira shi in fasa, Aisha ta amsa na ce kada ki kira shi dan bai taba kira na ba, ba wani kiranshi da nima zanyi Allah aisha ni auren nan tuni ya fitan min daga rai.Ace kai kafi karfin kazo sai dai abokinka?Aisha ta ce, Allah sai na rubuta masa tex.Ina kallonta ta rubuta masa.SALAM.INA FATAN KANA LAFIYA?KAYI HAKURI KILA YANXU KANA CIKIN AIKI NA TSAIDA KA, DA MA NAYI MAKA WANAN MESSAGE DIN NE DON NA TAMBAYEKA A KAN MAGANAR ANKO, DONKAWAYENA SUN DAMU SABODA LOKACI YANA KAREWA.NA GODE, KA HUTA LAFIYA.Tana gama rubutawa ta tura masa, maji amsa-maji amsa shiru, nace kin gani ko?Ke ayi biki haka bani kara masa batun anko.Aisha ta ce, niko yanda yake nashi salon birge ni yake, na ce, au!Wulakancin da yake min din ne yake burgeki?Tayi dariya, ai ba wulakanci bane rayuwar sa ce haka. Lokacin yana office din commissiner ya je a kan nemansa da yayi tsam ya kame kamar yanda yake al'adar yan sanda, sanan ya soma magana cikin natsuwa ranka ya dade an ce kana nema na.Commissioner ya dube shi cikin natsuwa sanan ya ce da ma na kira ka ne a kan maganar barawon shanu din nan da aka ce kaki yarda a bada belinshi.Aliyu ya sunkuyar da kai don girmamawa, yace ranka ya dade haka ne, naki bada belinshine saboda bincike ya nuna shi din ba karamin mai laifi bane.Daji suke shiga da motoci suna kora shanayen fulani suna kwashewa su kai kudu su saida, wanan kamawar ita ce ta goma sha uku amma ba a taba mikashi kotu ba, azzalumine na gaske,Commisioner yayi dan murmushi sannan yazo ya dafa kafadar Aliyu ya bubbuga alamun jinjina, san nan ya ce, Dan Sanda mai kishi, lallai kasan aikin ka da ka tsaya binciko wannan files din, ka tattarosu ka miko min nan, ni nasan yanda zan kawo karshen lamarinsa.Zan shigo gurinku anjima kaje.Aliyu ya sara masa, sanan ya fito.Gaskiya in son samu ne case din nan ya tsaya a hannunsa dan kam zaiyi gogaiya da zalunci.Shigarshi office din sa kenan sako ya shigo wayarsa, sai da ya zauna sanan ya duba.Murmushi yayi bayan ya karanta, a fili kumaya ce, ko me nene anko?(hahaha,kunjifa dan rainin hankali inji,shin kuna ganin zai yuwu ace baisan Ankoba,ai dai kayan yansanama Ankone,kuma kala biyu, wasu su sa baki kawai,wasu kuma baki da light blue ko? Cewar ANaM Dorayi) Ya kira layin Usman bayan sun gaisa ya tambaye shi ko menene Anko? Usman yayi murmushi wato kai dai in kaje ka shige caji ofis dinku shi ke nan baka tuna meye a cikin garin.Aliyu ya ce, aboki mu kuwa dake wanan ofishin mu muke da labarin abunda ke cikin garin, amma ba wanda ya shafi biki ba.Usman ya ce zaka bata kudi ne kurum ta shiga kasuwa da kawayenta su zabo, haka su ke yi.Aliyu ya ce, gashi ni kuma bana son yawo bare kuma xuwa kasuwa, in dai zani ne in zan je gidan zan tsaya nan wani super market in sayan masu, guda nawa ake siya?Usman ya ce, da ka basu kudin.Aliyu ya ce, ba zata kasuwa ba, wanan shine ra'ayi na, zan siyo musu zani.Usman ya ce shi kenan, sai ka suyo musu mai kyau.Aliyu ya ce ina ruwa na da zabe, ni dai kawai in dau zani.Don haushi Usman ko sallama babu ya kashe wayar.Aliyu ko da wuri ya bar office din ya bi ta kasuwa ya sai zaunnuwa kala uku ko wanneguda bibbiyu ya nufi gida.Iya tana zaune tana yankan kubewa ni kuma ina daga kicin ina kwashe tuwo ina mulmulawa a leda ina sakawa a kula ya Aliyu ya shigo da sallama. Kusan kwana hudu ban sashi a ido na ba , da ya zauna yana gaisheta.Ta amsa ya ce, ga zaunnuwa anko ne suka ce ko menene ma?Ta dauki ledar tana cirowa ta re da fadin kaine ka siyo ankon gadanda da kanka?Ya ce, to duk ba zani bane, shi nan sai su zaba.Ina kallo daga ciki kuma ina jin su, tun kafin in fito zaunuwan suka tafi dani.Ya ce, naki ne da nata.Iya ta ce, to mun gode, da ma ina so inyi maka zancen gidan ne, a ina kasamu?Ya ce, to ni dai nafi so a can kasan layinku, gefen makabarta din nan, to ba a samu ba sai na dawo neman na siyarwa, kudina dakekasa yanxu za su iya semin gida, amma albashin wanan watan da na wancan watan hada mana za ayi.To ganin kurewar lokacin sai kurum na barshi yanxun anjima zamuje mu ga wani gida da yaya Sani da Usman wai ciki da falo sai kichin da ban daki dubu dari da hamsin.Iya tayi shiru tana nazari, can ta ce ina nufin kasan gidan su babba ne?Ya ce ciki uku ne da kicin da ban daki sanan ga filin da mutum zai iya fakin din mota har biyu.Iya ta ce kuma nawa?Da sauri ya ce wai miliyan daya da dari takwas.Ta ce, ina ganin zaifi ka siya gidan in yaso sai a daga bikin.Ya dubi iya, ai saboda bana son dagawar shiyasa na hakura da siyan gidan.Iya ta ce siyan xai fi maka sauki ka huta da biyan haya, auran kurum za a daga ba.Ya ce ba dagawa za'ayi ba, abinda ya sa in an daga za ayi asara da yawa.Abokaina sun kashe kudi gurin kati mai tsada tare da wasu abubuwan abokan aikina suma sun kashe kudi gurin shirya bukin.Iya ta ce to, kana ji ko, yanda za ayi kawai a daura auren da buki, sai ta zauna gida kafin a gama gyara tunda dai nan a gida ne ba a dawa ba, bana so ka rasa gidan nan ne muhalli a bariki ba karamin rufin asari bane Aliyu ya ce, shi ke nan sai ayi haka din bari zan kira yaya Sani sai muje dake ki ga gidan sai a biya.Lumshe ido nayi cikin jin dadin an fasa daga bikin, kai naso in tare a gida na ranar amma baji, buri na dai a daura auren, amma da iya ta so kwafsawa wai a daga.Ya mike ya juya da nufin fita ida nunsa sukasauka a kichin a inda nake, da sauri na ce ina yini?Sai da ya dauke kai sanan ya ce, lafiya.Har ya fita ina kallonshi.Iya ta katse ni da cewa, wata rana sai kin gaji da kallon shi.Na sunkuyar da kai kunya ta rufe ni, ban santana kallona ba sa karya, in dai gadanga ne gaki ga shi nan. Pink din muka zaba ni da Aisha, sai dai muna zuwa kasuwa aka ce dubu uku ce gashi kudin aisha bai kai ba.Sai muka dawo gida da kyar mamanta ta cika mata muka koma muka siyo.Muka roki mai shagon ya ajiye mana da mu siya da yawa.Yamma tai mana a kasuwa gashi ana wahalar mota.Muna tsaye a kan titin kano Road, na ce bana son magariba tayi mana tun daya muka fito gashi iya ba ta san mun koma unguwar mu'azu mun dawo kasuwa ba.Aisha ta ce, sai dai muje mushiga dambancen ko za mu samu, na ce zamuje.Ta kan legas street wani lokacin ba a wahalar mota.Muna tafe wai wani mai mota ya tsaya, 'yan mata kuzo mana.Na ja tsaki tare da kara sauri, Aisha ta ce, lafiya?Ya ce rage muku hanya zanyi.Na ce Aisha, kema kika tsaya tambayarshi.Haka mutumin nan ya ci gaba da bin mu yana magiya, duhun magariba ya shigo na ce Aisha ko dai mu tsayar da mutumin nan ya kai mu gida?Don ina tsoron fadan iya. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tace, nima hakan zan ce,dai dai lokacin ya sake cewa ku kuwa tunda na ce Allah ya kamata ku saurare ni, dan kun san mugu dai ba zai yi muku sallama ba.Aisha ta ce unguwar Mu'axu muke.Ya ce, ai hanya ta ce ni kuma Nasarawa zanje.Cikin far gaba muka shiga motar ya ce mun a'a ke dawo gaba dai ki nuna mun hanya , na koma ga ba.Ya tam bayi sunayen mu, ina shirin xollo masa karya sai naji Aisha daga bayana ta ce, ita Sadiya ni kuma Aisha .Ya ce, masha Allah , sunaye masu ma'ana.Ya dube ni, Sadiya dan ke fa nake ta wanan bibikon sai aka ci sa'a kina da sunan matata, ni sunana Auwal.Hakika jin sunanki ya kara samun sonki Halimatu duk wace ta amsa wanan sunan takan zama mai hakuri da hange, bata rani bata daukar raini, macen rufin asiri zan so na sake samun ki.Na ce matar taka ta hada duk wanan halin shine zaka yi mata kishiya?Ya ce jin dadin halinta yasa zan kara.Aisha ta ce bakai mata adalci ba, au, ke fa sunan uwata ne ke da zaki tayani yakin neman shiga?Aisha ta ce, nan da sati biyu ita ma tana dakin angonta.Da sauri ya ce, da gaske?Ta rantse mashi tare da fada mashi ashobe muka zo siya.Daga nan nayi shiru bai sake magana ba harya shigar damu layin kasuwa, na ce sauke mu a nan ma mun gode.Sai mu karasa.Ya tsaya muka fito, ya ce marya ba godiya?Na dawo dai dai saitin shi na ce, mun gode, na ce kayi hakuri muna sauri ne dare yayi.Ya ce shi kenan, Allah ya baki zaman lafiya.Juyawar da zanyi in tafi tare da cewa amin, sai maganar ta tsaya, sa kamakon ya Aliyu da nagani tsaye yana kallon mu. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana 1-03 Posted by ANaM Dorayi on 10:51 PM, 14-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA __________________NA ___________HALIMA K/MASHI Duk da kasan cewar duhun magariba ba zai sa in kasa gane bacin ran sa ba.Gaba na ya fadi, irin wanda ban taba yi ba.A fili na furta na shiga uku!Aisha ta ce, me nene?Bakinta yayi shiru sakamakon ganindatayiwa abin da nagani.Kusan minti biyu yana kallo na, ko da banga fuskarshi sosai ba na san a daure take .Sai yaja tsaki sanan yayi babban titi abin shi.Muka kwashi sauri ni da Aisha inayi ina waiwaya shi, a zuciyata ina cewa yau na kade, Aisha ta ce muyi wa ni kin ga da sauki tunda mama ta san mun xo mun koma ne.Munyi sallama iya tana tsaye tsakar gida tana cewa, kai ni wadan nan yara ko ina suka shige ne?Kai Sadiya bata da hankali, ki fita tunda hantsi har magariba, to ko kasuwar kwari ta kano suka je?Ko jiran mu gama sallamar bata yi ba bare ta amsa ta hau fada, Aisha ta shiga jero mata dalilan mu, ta ce ku refa mun baki, ko kasuwar kano kuka je ya ci a ce kun dawo tadubi Aisha ta ce uwaki ta ganki hankalinta ya kwanta, masu shegen rawar kai.Ta bini ke kuma, sai ki jira xuwan gadanga don tun yamma yake shige da fice bai ganki ba, har dai ya kare ya ce ita wanan yarinyar ina tayi ne?Ina son ta hada mun abin shan ruwa ina azumi, na dafa kirji na ce, to me kika ce masa?Ta harare ni karya zan masa?Ce masa nayi kinje kasuwa sayan anko, yayita fada me yasa na barki don baya son xuwanki kasuwar ne yasa shi siyo ankon dakansa.Na ce, na kade.Na dauki buta dan yin auwala, a xuciyata inatuno yanda ya ganmu muna fitowa a motar, da nayi salla nayi addu'a Allah ya yayyafawa abin ruwan sanyi.Da a zamar sa ya shigo da sallama ga ba naya fadi da sauri, don haka ma ban iya amsa sallamar ba, dakinsa ya shiga bayan wasu mintina ya fito tsaf tsaf cikin shirin fita.Ban taba ganin dansanda da kaki yake masa kyau matuka ba irin ya Aliyu, kan cinya ta na dora fiskata ganin ya nufo dakin Iya.Ga zato na da ya karaso zai zabga min mari,ina jiyoshi yana cewa iya ya tafi sai da safe, ta ce, can zaka kwana?Ya ce eh, ta ce, Allah ya tsare mun kai, ya kuma bada sa'a ka yawaita adu'a.Ya ce to ina yi iya, zan kara kulawa.Ya sake wuce ni ya nufi fita, da kallo na bishia raina na ce, zaki na maza sarkin jin kai.Nan ya tafi ya barni da kamshin sa sai dai da dukkan alamu yana fushi dani.Da dare ina cikin daki kwance kan gado, juyi kawai nake zuciyata tana mun nazari a kan kallon da ya Aliyu zai mun, ganin da yayi mun a motar wani kamar in kira shi in bashi hakuri, sai na fasa.Na rubuta sako kamar haka:YA ALI DON ALLAH KAYI HAKURI IN NA BATA MAKA RAI. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ban jira amsa ba don nasan ba samu zanyi ba, amma ga mamaki na sai naji sautin shigar sako.Da sauri na bude na soma karantawa.KUL! BANA DAYA DAGA CIKIN MUTANEN DA SUKE DAUKAR LOKACIN AIKINSU, SUNA HADA SU CIKIN LAMURANSU NA DABAM.SAI KI RIKE WANAN DAN GABA.Na lumshe ido ina son yin nazari a kan kalaman nasa, na san dai kul! Dan gargadi ne ya yi mun kenan ba ya bukatar a shigar masa lokacin aikin sa.Nayi juyi ina mai yiwa kaina jajen auran ya Aliyu, yanxu auren ya fi ban tsoro fiye da birgeni.Washegari sukuku na tashi,Iya ta ce jiya kuna can kuna gararin yawon ku mahaifinki ya zo yayi ta jiranki har ya tafi.,na ce kash!Ko da yake na san dole ya dawo kafin bikin.Ta ce ba dole ne ba , kudi ne ya kawo sadakin ki da akayi, sai gudumawar su dubu hamsin.Na ce hamsin iya?Yaushe hamsin zatayi mun kayan daki?Ta ce, ina laifi, mahaifinki fa yanxu ba aiki yake yi ba, tunda yayi ritaya sai dai dan noma.Shi ko noma a kasarnan yanxu dai ba a dauki maiyinsa da mutunci ba, shine koma baya a gurin gwamna ti.Su ba ga taki ba ba ga tallafi ba, dan gurarenda suke nomawan ma kwanaki yakecemun gwamnati ta ce zata amshi wurin.Na ce iya gurin da ma ba nasu bane?Ta ce, Sadiya kenan, dama talaka yana da guri ne a a wanan karnin?Sai wanda Allah ya taimaka ya kuma tsaga da rabonsa.Gurinka da takardu da komai za a amshe maka,dubu hamsin ai yayi kokari.Na ce haka ne Allah ya rufa asiri, duk abindaza ayi dai dai karfinmu za muyi.Iya ta ce, in sha Allahu sai kin zaba yata.Jugun nayi ina kallon Iya, baiwar Allah nan tana sona fiye da yayan da ta haifa, abin da take min ko ita ce ta haifeni sai haka.Kusan duk dare sai bacci na ya katse, in yi kiri kiri ni kadai cikin xullumi irin zaman da zanyi gidan ya Aliyu.Na gama duk hashashen da zanyi ban hango jin dadi ko kulawa a cikin auren ba, sai yanxu na gane nufin iya ta guje mun wahala ne, gashi lokaci ya kure mun bani da damar in ce bana so.Kusan karfe uku na rana ina zaune ina yankan farce na tare da gyarawa, sautin shigowar sako naji, sharewa nayi amma naki dubawa don nasn MTN ne.Sai kuma wata zuciyar ta ce mun in duba, gaba na ya fadi ganin sunan ya Ali, na duba cewa yayi.KI SAMENI A DAKI NA YANXUN.Duk da cewa ina fargaba sai da na dan sakemurza hoda tare da man lebe, sanan na fesaturare.Iya ta kalle ni tana zaune gefe tana gyaran goron ta da yayi tsutsa Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Ta ce, to mai aljanun kwaliya don a sarar turare ana zaune kin hau feshe feshe.Na ce, iya yaya Aliyu ne yake kira na, ta ce ya shigo ne?Na ce ina zato, amma ta waya ya turo min.Na suri hijabi na na nufi dakin gabana na matukar faduwa.Nayi sallama ya amsa, na shiga kallo daya nayi mashi yana sanye da gajeren wando da(t-shirt) fara sol na sunkuyar da kai sanan na tsugunna tare da cewa gani yaya.Sam bai ko kalleni ba, hasalima danna wayarsa yake abinsa, nayi kusan minti uku sanan ya ce (ba tare da ya kalli inda nake ba).Ya sunan saurayinki da na ganku jiya ya sauke ku a mota?Ban san lokacin da na zauna ba don tsabar tsoro.Sanan na ce, ba saurayi na bane.Lokacin ne ya dubeni cikin wata irin harara da murya ta isa ya ce, ba karamin zunibi ba ne wajen dan sanda mai laifi yaki amsa laifinsa.Kar ki raina hankalina kokaryata ni, sunansa kurum na tambaya.Murya ta ta soma rawa alamun kuka zai kubuce min, ya dora yatsansa dan manuni akan leben shi ta re da cewa, shhhhhi!Kul!Kika min kuka, ko rawar muryar nan bani son ji.Ya ci ga ba duk da dadewarku da shi baki san sunan shi ba?Nayi kokari na kalaci miyau na hadiye shi tare da kukan da ke son kwace min.Na ce, yau ne na soma ganin shi, yana ta binmu yana rokon mu wai mu tsaya muka ki, toda muka ga duhun dare muka yarda ya kawo mu, don ana wahalar mota kuma kudin mu ba zai ishe mu mu hau achaba ba.Ya maida kanshi ya kwanta rigingine, ya kuma ci gaba da danna wayarshi.Kusan minti biyu sanan ya ce, wa yake so cikin ku da yake ta binku?Da dama yana ta binku ne kawai ya rage muku hanya duk da dimbin jama'ar da ke jiran mota a gurin?Tsoro ne da faduwar gaba suka karu gareni, cikin in-ina na ce, am.. Em.. Haka ya ce wai ni yake so.Da sau ri ya tashi zaune, cikin daga murya ya ce, menene?Da sadakin nawa a gurinki?Da sauri na ce, ai Aisha ta ce mashi aure za ai min.Ya zuro kafafunsa kasa, oh, da ke baki fada mashi ba?Na ce, ta rigani yin mga na ne shine dalilin da ya tsareni da idanunsa.To me yace da ta fada masa?Haka ya ce Allah ya sa alkairi.Ya sake komawa ya kwanta.Jeki zan bincika, in na samu zantukanki ba gaskiya sai kin sani.Zaraf!Na mikexan fita sai ya sake cewa, me ya fada miki lokacin da zaki tafi ya kiraki?Na ce, ya ce ne ba godiya?Shine na ce mun gode.Tamkar ba shi na bawa amsa ba, don bai komotsa ba bare ya dubeni.Ina ta tsaye har lokacin da ya kula dan kansa, sanan ya ce, kina da wata maganar ne?Na ce, a a.Ya ce, to kin tsaya min a kai.Na tabe baki a raina na ce, masiffafen ikon ka zan dauke shi kuwa?Tsuntsun dayaja ruwa......ANaM)Na fice, duk da ba lokacin zafi bane jikina sharkaf da zufa, kan kujera na zauna ina maida numfashi.Iya ta ce, me ya ce miki ne?Ko abinci zai ci?Na ce a'a mun dai yi hira ne.Ta ce, shine kika yi wujiga wujiga sai ka ce kunyi dambe?Sakon da ya kara shigowa wayata shi ne ya hana ni baiwa iya amsa, ko da yake dama bani da amsar.Sunan shi na kara gani na bude sakon, cewayayi.NA MANTA BAN GARGADEKI BA, DOMIN KE TAWA CE TUN KAFIN NA BADA SADAKI, BARE NA BIYA KUDINKI.Naaje wayar a gefena, na zari buta zuwa ban daki ba don zanyi wani abu ba sai dan inkaucewa tam bayoyin iya.Sauran sati daya biki iya ta zauna da duk yayanta, sun shirya yanda za su gabatar da komai cikin tsari.Ina tsakar gida ina jiyo su, iya ta kwala min kira sadiya!Na amsa, zo kije gidan Hajiya Umma Rimaye matar Likita Hassan ki ce mata tayi wa maiyin alkaki magana?In sunyi maganar nawa ne kudin?Na ce to.Na shiga dakin, kaina sunkuye dan harda ya Aliyu a gurin, ta ce maza-maza ki dawo, dukkwanakin nan na kula baki son aike.Ina shiga uwar daki na tura mashi sakon cewa iya ta aikeni, ya bude ya gani amma sai ya ajiye wayarsa, sanan bai ce mun kala ba.Neko sai nayi zamana gefen gado, jin shiru ban fito na ta fi ba iya ta ce, kin tsaya kwalliyarki ta jaraba ko?Na ce, a a.Ya san shi nake jira, sai ya ce ba aikenki akayi ba kina jiran menene?Na fito na tafi.,ya Usman ne ya kawo mun katinan bukin a ranar da dare.Lallai su na kula biki zasuyi na sosai.Farko zasuyi walima bayan daurin aure, sai kuma dinner, sanan akwai police day, shi kuma washe garin daurin aure zasuyi shi, damisalin karfe uku.Ni da Aisha da Fatiman ya Sulaiman muka shiga rabon kati.Ana saura kwana hudu biki, Anty Abida matar Usman ta kirani ta waya naje, bayan mun gaisa ta ce, kina dan gyaran jikinki ko?Na ce da me?Ta ce dan shirye shiryen mu na mata.Na ce, a a ni bani da kudi anty.Anty ta ce, baki tambayi ango ba?Na ce anty, ni ba zan iya tambayarshi ba.Nan take ta kira wayarshi ta sa handsfree, ya daga tare da amsa sallamarta, ya ce madam ya akayi ne?Ta ce ango, ango ka sha kamshi.Ya ce bansha ba tukunna.Suka yi yar dariya, ta ce dama maganar gyaran jikin amarya ne, ka san anayi.Ya ce ban sani ba gaskiya wane irin gyara kenan?Ta ce dogon bayani ne yanzu dai kudi muke bukata.Ya ce nawa ne?Ta ce talatin ne kacal ba yawa.Ya ce madan kuna so sai kun tsotse ni tas! Ya fadi? Ta ce tashi muje gidan Hajiya Umma Rimaye.Na ce, a a, ita ce mai gyaran jikin?Ta ce, eh.Nace na ga iya gurinta ta aikeni in kai kudin alkaki.Ta ce, eh, ai kawarta ke yin kayan buki, ita dai ke gyaran jiki.Na ce gaskiya tana da kirki.An hada kayan dilka masu kyau an lailaye ni da su, duk da kasantuwata fara ba karamin kyau nayi ba, kwana uku zanyi ina zuwa.Kuma ran na uku za ayi mun lalle.Iya da kanta tayi ta yabon kyan da nayi, haka naita zuwa ranar da na cika kwana uku ta kira mai zanen lalle inda aka zuba min fulawa.Abinka da fara, kowa sai tanka ni yake ta ce,tunda gidan su yana da girma kawaye na suzo nan a yi masu na su lallan na ce, to na gode.Abida ce ta amso kudin ta bada, Usman shine ya bamu kudin walimar mu.Wani abun da ban gane ba duk dare sai iya ta dama mun wata fura wace ita ta hada kayan hadin da kanta, sanan ta va inno yar sokoto ta daka mata.Furar tana da danko, furar sai kace magani gashi duk yawanta in ta dama sai ta tsare nina shanye.Sanan da safe ta xuba gero a turmi ta surfe shi, wai zata tara na dama kunun safe saboda yan buki, amma tana gamawa zata wanke shi ruwan farko ta tsareni sai na shanye ina kuka ina komai.Tun ana jibi daurin aure wasu suka soma sintirin taya aiki, makota dangi duk sun cika gidan, yan gefen su iya da na baba na. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 An yi mini kamu inda aka feshe mu da turareni da kawaye na kamar yanda muke yi a nan Kaduna.(Ina yan kadunan,yakukeyi kubamu Labari,ANaM) Gidan matar yaya sani mukakwana. Zariya za a daura aure amma an ce ni ba saina je can ba, tunda ba tarewa zan yi ba.Na nufo gida dan kwasan kayan da zanyi anfani da su in nayi wanka.Su ya Aliyu na ta shirin tafiya gurin daurin aure, an kawo motoci.Ya Aliyu ba ya gurin sai abokanan sa sun taru a kofar gidan mu, kunya ta kamani, na ja gefen hijabina na rufe fuskata.Ina jin wani cikin su amaryarmu ki bude idonki kada ki fadi mana.Sai naji muryar Usman yana cewa, sarkin kunya kenan.Zan shiga soro (zaure) naji mun zabga karo da wani, da sauri na bude fuskata, gaba na ya fadi.Ya Alyu ne har wayarsa da ya na magana tafadi.Da saurina tsugunna dan dauke, tare muka hada hannu zamu dauki wayar. Hannunshi ya taba nawa.Ba ni kadai ba, na kula harshi yaji abin da naji, tamkar wutar lantarki ta jamu.Shi ne ya janye hannunsa, na dauki wayar na mika masa tare da furta kayi hakuri.Kala bai ce ba, sai amsar wayar da yayi ya tafi, na bishi da kallo yayi matukar kyau cikintsaleliyar shadda mai ruwan suminti, tana tamaiko.Kamshinsa ya cika zauren, a fila na ce na more muji, na juya na nufi ciki.Sai tsiya ake min Amarya-amarya. Munyi walimama inda nai ta canjin kaya, kusan karfe hudu Aisha ta miko min wayata, sa ko ya shigo na bude kamar yanda na zata ya Aliyu ne, in da ya ce, "Alhamdulilla" na kalli Aisha dubi abin da ya ce, ta karanta da murmushi ta dube ni, kin zama tashi dole yayi hamdala ga Allah.Nace, Allah ya sa haka yake nufi, wanan danjin kan?Sakon shi ya sake shigowa musalin karfe bakwai na safe, na idar da sallah ke nan, ya ce kije gidan Usman da ga can za a dauke mu ni da ke dan zuwa dinner, kawayenki kuma su xama cikin shiri su tsaya a kofar gidan mu, please, banda marasa hankali, bayan sallar isha'i za a tafi.Na ce, Aisha kinji mutuminki ko?Ta da fani, me ya ce?Na mika mata wayar ta karanta ta dube ni.Ki dauki kayanki da zaki sa ki tafi can ki shirya, ni kuma zan kula da sauran kawayenmu a nan dan mu shirya cikin tsari.Kinsan su ya Aliyu masu aji ne ba irin tarkacen nan suke so ba.A gidan Abida nayi salar isha'i sanan na shirya da taimakon abida da yake ita ma in dai kwalliya ne, matirial ne na saka riga da siket ruwan madara da ratsin kore.Sai nesa kore takalmi da jaka duk koraye, sarka kuma ja sai muka yi anfani da ja a kwalliyar fiska ta gashi ya sha gyara, da ta shiga fesa mun turare sai da na soma atishawa, kaloli ta samun masu kamshi.Da na kalli kaina a madubi sai na ce Alhamdulillah ni ce haka?Ita ma sai yaba ni take yi, ta shirya, sun zo daukarmu Usman ya ja motar suna gaba shida Abida ni kuma a ka bude mun baya ashe ya Aliyu na cikin motar.Sanye yake cikin lallausan yadi ruwan madara, kalar kayana ke nan hular kube ce kai yayi kyau matuka, sam bai kalleni ba.Waya ma yake yi motar tana tashi wutar motar motar ta dauke dai dai lokacin kuma ya gama wayar.A hankali motar ke tafiya motar shiru sai sanyin (AC) da wani dan sauti dake tashi a raidiyon motar mai sanyaya rai, ban san ko wacce zabiya bace mai wakar ba, tunda ba sauraran wakar turanci nake ba.Sai dai wakar tamasoya ce, kalamar zabiyarsun haddasa min shiga wani irin yanayi, na lumshe ido tare da jingina baya na a kujerar motar.Kamar daga sama naji saukar tafin hannunsa a saman nawa, da sauri na ware idona, a zatona bayanan zabiyar ne suka sani dan karamin mafarki.hhhhh,kujita da shiririta.. Amma sai naji yatsunsa suna ratsa tsakiyar nawa, lokaci guda kuma ya matsatse su tsam.Na dube shi da sauri sam ba zaka ce shi bane.Don har yanxu yana fuskantar inda dama yake fuskanta, na kalli hannuwa na ma duk da cewa a kwai karancin haske bai hana ni ganin sarkakun hanuwan namu ba.Na sake mai da baya na jikin kujerar tare dasauke yar karamar ajiyar zuciya.Lumashe ido nayi ina tuno karon da mukayi dashi da zun, goshi na da hanci na suka dakikirjinsa.Na tuna hanuna da nasa suka hadu wajen daukar wayar.Hannuwa na farare sun sha lalle, na lura da yanda ya tsurawa hannuna ido na yan sakwanni a lokacin. A raina ina ta mamaki da tam bayar kaina, shi wanan ya canza daga jin kan ne?Koko isa ce tasa shi yin haka?Wata zuciya ta ce koma me nene mijinki ne a yanzu.Tsayuwar motar ne yasa ni bude ida nuna.A zatona in zai fita dole ya sakar min hannu,amma har muka fito hannuwan mu sarke, a haka yayi ta daga waya na kalli gurin da muka zo, an rubuta Cristal Garden da wani rubutu mai yi kala kala na wuta.Usman ya shiga ciki ya fito sanan muka shiga tare.Dam gurin ya cika da mutane an wadata ko ina da kayan ciye ciye da na shaye shaye, naga muta ne manyan mutane da banyi tsammani ba. Anci ansha kuma anyi wasa da kudi, sai dai duk yanda abokan ya Aliyu suka so muyirawa yaki ko mikewa tsaye.Dan haka duk wanda ya matsu da ya yi mana liki sai dai ya ishe mu a kan kujerar mu, abokan shi da kawaye na sun sha rawa.Sai kusan sha daya a ka tashi, mu kam sai sha biyu sanan muka tafi don sai da aka kwashe kowa.A kofar gidan mu motar ta tsaya, na yunkura zan fita, sai naji ya dafa hannuna, wato ya dora hannunshi a kan nawa.Na kalleshi shima ya kalle ni, dai dai lokacin Usman ya fita, da ma mun sauke Abida a gida.Aliyu ya ciro wayarshi ya haska fiska ta, ya cire hannunshi da ke kan nawa, ya dora a kan kuma tuna ya shafa har zuwa dokin wuya na.Sannan ya juya bayan hannunshi ya shafi haba ta, dole na lumshe idanuna abin sai kace a mafarki.Ya tsansa dan manuni ya saka ya gewaye lebuna na, na bude ido ina kallonshi, murya kasa kasa ya ce, ki bar wayarki a kunne zan kira ki.A jiyar zuciya na sauke, sanan na amsa a kasalance to.Tsakar gidan mu cike da mutane duk sunyi shinfida sun kwanta, kasancewar lokacin damina ne amma anyi kwana biyu ba ayi ruwa ba.Don haka gari duk ya dauki zafi.Na nufi uwar daka, nanma duk jama'a ne kwance, gado na dai ba kowa.Na cire kayan jikina nai daurin kirji sanan na fada kan gado.Iya can na varo ta a falo tana yin sallar nafila, a rai na na ce iya koda biki ba a daga kafa.Filo na dauka na rumgume ina tuno abubuwan da suka faru yau, tamkar almara ji nake yau na zama mace sosai.Karar ringing din waya ta shi ne ya dawo dani cikin hankali na, na dauka cikin faduwargaba na ce salamu a laikum.Muryarshi can kasa kasa ya amsa sanan yace ke da waye ne a nan?Na runtse ido dan yanda muyarshi take ratsa dodon kunnena, na ce ni da mutane amman sunyi bacci sunyi shinfida ne a kasani a gado nike, ya ce ok, kin san me yasa na kira ki?Na ce a a ya ce, saboda mu fahimci juna... Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347. A raina na ce abin da ya kamata a ce shine a farko ya koma karshe.Tamkar ya shiga raina.Ya ce kila kiga abun babu tsari ko?Kafin na bashi amsa ya ci gaba.Ni irin nawa tsarin kenan, kina jina?Na ce eh.Yace to yanxu sai ki fada mun dokokinki kafin kiji nawa.Da sauri na ce ya Aliyu ai bani da wata doka sama da ta Allah da manzonsa, wada suka tsara ita ce abin bina doka ta ni kadai in bika.Gud to me kike so me bakya so?Zan so in soma jin naka yaya, tunda kaine babba.Ya ce, to da farko dai bana son kazanta, duk inda zan shiga a gidan bana so in shaki wani wari.Kuma bana so in ganki babu tsafta ko in shaki wani wari daga jikinki, sannan ina son komai a kan lokaci.Na san kin fi kowa sanin ni dan oya oya ne, komai cikin hanzari bani son kasala, bana son musu ko gaddama.Abu na kusa da karshe bana son duk wani abu da zai shiga lokacin aiki na, ina fata kin fahimta?Na ce eh.Ya ce yan zu sai inji naki.Na ce, ni dai bai wuce uku ba, duka da zagi ne bana so.Sai nayi shiru.Ya ce, ina jinki, saura daya.Na ce imm.... Bashi kawai ma.Ya ce a a, ki fada in nayi maki cikin rashin sani fa?Bana son mu munafunci juna,fadamin duk abinda ke ranki da xuciya daya.nace amm...dama kishiya ce bana so dai,kuma bamuyi sabo daxan fada maka ba.shi kanshi shiru yayi,nasan yana mamaki ne don bai zaci jin haka ba,a zuciyarshi shi kamshiru yayi saidai bai ji wani mamaki ba saboda yasha samun case din mata akan kishiya.ganin kishiya ce abu na karshe da mata suka tsana.nima shiru nayi gabana yana ta faduwa,tsai din dana ji araina na raya cewa magana xai dankaramin mara dadi,can yace ba xan yi miki alkawari ba in na duba cewa komai na rayuwata rubutaccene tun fil'axal kamar yanda yake ga kowa.kifahimta,baxan taba yi miki karya ba,don kawai kiji dadi.sai dai shawara daya xan baki,kiyi kokarin tsare duk hakkokina,ta yiwu in kinyi hakan bazaki rage gurbin wata ba Kuma kila baxan ji sha'awar karawa ba.(Lallai yaya kazama abokona,muna da ra'ayi daya dakai, dan haka me sona nima namiki nasiha makamanciyar ta Yaya Aliyyu,kiyi kokarin kyautatawa,tayanda zaki rufe idanuna daga ganin dukkanin wata mace da matsayi irin na soyayya bayan ke. ANaM Dorayi) Nayishiru tabbas nasan gsky yafada,amma kishi ne daninasan wanan tundaga ranar da kunnena yaji ya Aliyu ya furta yana son aurena.can kasan xuciyata tunani ne kada wata rana yace xai so wata har ma ya aureta.duk sauran samarina da duk wanda yaxo da niyyar aurena nakan fada mishi koda na aure ka banason kishiya fa.Toh shi xakin nawa ina naha fuskar fada masa,shine sai yanxun...ya katse tunanina da cewa,nasan baki fahimce ni ba akan batun kishiya,don haka a aje zancan gefe muyi mai amfani.nima naji abinda bakiso zan kuma kiyaye insha Allahu.kiyi baccinki sai dasafe kar ki manta gobe akwai ranar yan sanda.bikin da suka shirya mana,ina fatan zakiyi shiri?muryata sarke nace Allah yakaimu goben. shine ya katse wayar sannan nakashe tawa na kwanta,kalamansa ne ke yawo cikin kaina na damu da bai min alkawari cewa baxai min kishaya ba har bacci yayi gaba dani.(kabwata duk lokacin da saurayi yace bazaimiki kishiyaba to kisani hakan mafificiyar karyace a hasashena,pls kabwata karkisa saurayin yayimiki wannan alkawari kawai dan gudun bacin ranki,ANaM) Ya aliyu ya iya magana cikin natsuwa,kai inason gayen sosai. Dasafe kin fitowa nayi ina yin sallah asuba dama komawa nayi nacigaba da bacci. da Iya ta tashe ni sai na langabe nace mata kaina ciwo yake yi nan ko banason tashine in ta aiki ga mutane. sai kusan sha biyu sannan na tashi nayi wanka na karya.Aisha taxo muka sha hira anan ma muka xabi kawayanmu da zamu je bikin anjima dasu.yau kam shigar Green da Golding nayi nawani leshi mai kyan gaske,abinka da farar mace kayan sun dauke ni duk da cewa wai farin ne yacece injiwasu Duk yau ban sa shi a idona ba sai yanzun da za mu tafi., yau kam gadanga kusar yaki kakinsa yasha na yansanda, ya iya aje hularsa a kai tamkar sai da ya yi course din sata,wani dan sanda ne ya jamu zuwa wajen, guri yayi guri,Usman shi ya taho da sauran kawayena, Police band sai tashi take ga wasu yan sanda suna ta bin kida fareti. gurin zamanmu na musamman muka nufa înda masu kidan suka dafo bazanmu da kida. ya Ali da abokansa da fareti suka yi tafiyar har zuwa gurin zaman har wani yana cewa yakamata matar dan dan sanda ta îya fareti itama . sun yi wasa kala kala har wani wasan su wai lokacin suna makaranta suna cin garin kwaki,anci ansha anyi rabon abubuwa.sai bayan magriba muka dawo gida.karfe sha biyun dare dai dai wayata ta soma ruri da sauri natashi nadaga yace xo mana natashi xaune na kalli shashin da Iya take, tadan rumtsa kafin lokacin sallarta ya karato,Na tashi sadaf-sadaf tamakar munafuka nafita, a kofar daki nayi sallama, ya amsa na shiga.Kwance rigingine na same shi yana danna wayarshi, jikinsa sanye da farar singileti tareda gajeran wandonta.Nayi saurin dauke kaina don kunnyar ganinshi a haka.Na rusuna kaina a kasa ga ni yaya ba tare da ya dube ni ba ya ce, tun cake din da kika bani a baki dazu gurin party nan ne a ciki na,yun wa nake ji.Na dube shi me zaka ci? Shima sai lokacin ya dube ni, me kika ga ya dace in ci?Na ce, ko za ka fara shan ruwan zafi tun da ka jima baka ci abinci ba, saboda cikin ka yawarware?Ya ce to yaya za ayi, na samu ruwan zafin?Na ce sai na dafa maka, na mike tare da ajiye wayata a gefe na nufi kicin, ina kunna risho naji takun tafiya, sai ga iya tsaye a kaina ta ce, na farka ban ganki ba lfy kika kunna risho?Na ce, yaya ne ya kirani a waya wai yana jin yunwa shi ne zan dafa mashi ruwan zafi , ta ce, hum!Ki dai kiyayi kanki, kuma ri rage wanan barin jikin, sanan kiyi maza ki dawo daki na ce, to.Ina komawa dakin dauke da dan flaks dinsa na ruwan zafin na same shi yana danne danne cikin waya ta, na juyo na jawo kofi zan zuba masa ya dube ni baki da numbata a she?Na ce ina da ita mana.Ya ce in gani.Ya ciro number ya miko min wayar, na amsa na danno sunansa inda na sa ya Ali, ya ce ok, bani ruwan zafin, na zuba a kofi na hada masa sanan na mika masa.Sai da ya amsa ya kurba sanan ya ce, amma na zaci cewa na wuce wanan matsayin na yaya.Na kalle shi eh haka ne.Ya dauko wayarshi ya danna ya nunu min numbata a wayarshi.Yayi saving dinta da suna my choice, a fili nafurta my choice, ya ce nima sai a canja min suna ko?Muka kalli juna cikin ido sannan na soma danna wayata, ya ce zauna sosai mana, sai kace ba dakin mijinki ba? Na zauna sannan na soma rubutawa na sa honey, sai na goge na sa darling, shima na goge sai kuma na rubuta sweet Aly.Zan goge yayi zaraf ya amshe wayar ta re da cewa in gani me kike rubutawa kina gogewa?A fili ya ce sweet Aly.Yayi dadi ki barshi haka.Ni kuma tuni na sunne kaina cikin cinya ta don kunya. Ya ce ai babu wani sauran kunya tsakanin mu, kinyi alkawarin za ki rinka kirana sweet dinki har gaban kowa?Na dubeshi cikin kunya sanan na sunkuyar da kai ina wasa da gefen hijabina na ce ba dai ga ban muta ne ba, yace to ni gaban kowa zan ce maki my choice, sunan ya da ce?Na saka yatsa a bakina ina dan wasa da shi,na ce me yasa ka zabi ka sanya min zabin ka?Ya dan kara matsowa, dan duk duniya ke kurum zuciyata ta zaba har mamakin ki tai lokacin da muka taya wai saida kikaimana yanga kafin ki amsa.Na yunkura bari inje in kwanta, ya ajeye kofi bakya jin dadin firar tamu ko?Ya ci gaba, kiyi hakuri dani ban taba fira da mace ba shi yasa, na dube shi tare da dan zare ido ya ce baki yarda ba ko? Nace naga kana dan sanda ka ce baka taba fira da mace ba?Amma ba wai ban yarda bane yayi dariya gaskiya bana yi, tsakanina da mace sai dai in matsalar da ta shafi aikina ne ta hada ko har yanzu baki yarda ba?Na ce na yarda na mike tsaye ya ce, firata ba dadi ko?Na ce, da dadi mana.Ya ce to shi yasa kike so ki gudu? Iya ta ce kar na dade,yace ta manta ni mijinki ne ya ce ok sai da safe?Na ce tam, har na kai bakin kofa yace, gaki dai baki son kishiya sai ina ganin ba zaki iya kula dani ba.Ina tsoron kada hakan ya ja maki kiashiya. Cak!Na tsaya cikin wata murya wacce ban san ina da ita ba na ce, sweet Aly, Allah zan iya kula da kai fa ka ji?Kasa amsa ni yayi don jin irin muryar da nayi anfani da ita.Na ruga da gudu cikin kunya shi kam shiru yayi yana mama kin mata.Lallai mata abokan nishadi ne, dubi yar hirar nan da yayi da yarinyar nan ya shagaltar dashi ya koma kamar sakarai, yayi murmushi sanan ya kwanta.Nima kwanciya nayi ina tuno abin da ya faru tsakaninmu duk da kallon da Iya ta bini da shi, da na shigo sai dai yi nayi kamar ban lura ta ji haushin dadewar da nayi a wurin yayan ba.Washegari ban tashi da wuri ba sai wajen tara lokacin baki suna ta shirin tafiya gida jen su.Sha biyu kowa ya kama gaban shi, sai mu munata aikin gyaran gida ni da iya.Kusan karfe uku na yamma ya kirani wai a kwai fura ko?Don anzowa iya da fura da nono lokacin biki, na ce masa nono yayi tsami, sai dai in ya siyo yogot ya shigo da shi ya ce to. Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Tunda na idar da la'asar na zauna zaman zabar kayan da zan saka iya dai tana kallo na na sauke akwatuna na zabo atamfa cikin kayan aure na.Da na idar da sallar isha'i kuwa na shiga zabga kwalliya ina ta feshe jikina da turaruka.Iya ta shigo ta zauna bakin gado ta tsareni da idanunta ko da bata fada ba nasan abinda kallon nata yake nufi.,don haka nakoma nima bakin gado na zauna tare da ajiye dan kwalin da na dauko zan daura.Ta ce sadiya ni ba wai ina hanaki ki lura da mijinki bane ko ki shige masa a ana fi so ki bari sai kin tare, shi fa namiji babu ruwan sa da zancen kunya, in baki ji nauyi na a matsayin mahaifiyar Aliyu ba ai kyaji kunya na a matsayina na uwarki.Saboda iya shege ko watsewa yan biki basu tafi ba kin tafi dakin miji kin raba dare saboda rashin kunya?Na sunkuyar da kaina rai bace a zuciya ta na ce, har ga Allah shi yasa na so in tare a daki na, ta ce daina bata rai, daraja nike nemamaki da kima in kin tsare kanki har sai kin tare kifi kima a idonsa, ga dai misali a gidan ku.Kiji tsoron abinda ya faru da yar uwarki ta zariya Harira ya faru dake, kan ta tare tayi ciki a gidan mijin nata ya shiga yi mata wulakanci.Kin manta banda ubanku tsayaye ne ai cewa zaiyi cikin ba nasa bane, shi yasa in andaura aure ba a tare ba mace ta mika kanta ba karamin so mijin keyi mata ba za ya daraja ta.Wani dama sha'awa ce ta kawosa gurin mace da ya biya zaiji baya sonta, amma in tana gidansa fa?Ai yasan da kunya ya ce yayi aure sati daya ya kori matar.Jikina yayi sanyi, tabbas babu ja a batun iya,kuma haka ne batun Harira, tayi goyon ciki a gida ta haihu a gida ba ta tare ba.Kuma ya saketa da kyar ya amshi cikin amma har yanzu dan yana hannun uwarta agidan mu ita kuma tayi aure a Hunkuyi.Na saka kaya a sanyaye na zauna ina kara nazarin abubuwa.Har dakin iya ya shigo suka gaisa ya ce, ina yarinyar nan?Ta ce, tana ciki.Kamar daga sama sai naji ya ce, my choice.Na fito da sauri tare da amsawa, duk da nasan iya bata san me yake nufi ba.Amma tana da saurin dago abu, zata san cewa suna ne na musanman ya sa min, na amsa sannu tare da gaishe shi.Ya miko min yoghot din in kin gama ki kawo min.Na ce to,ya dubi iya bari nayi wanka. .Na shiga da sallama, yana zaune kan sallaya da alama salla ya idar, na ce baka sami jam'i bane? Yace, shafa'i da wutiri nayi.Zan tsugunna ya ce zauna a bakin katifa mana.Kina yi ya ce, sai kace ba dakin mijinki ba.Ya gyara zama kan sallayar, sanan ya dauko wata laide dake gefe ya bude ya ciro kunshin takarda ya warware yana fadin.Kin ganni da son kilishi shi yasa na saimuku Balango.Ya dauki daya ya saka a bakin shi, zo in baki a baki. Nace na koshi ni na ci abinci tun dazu.Yace wanda kika ci da ban nawa nama ne, matso kiji.Na dan sunkuyo ban sauka daga kan katifarba, shima ya matso ya miko nannu ya sa min abaki, na amsa tare da rufe fuskata cikin tafukan hannaye na.Ya ce fada min gaskiyarki, ni dake yanzu ba wani batun jin kunya. Kin kosa ko? Na daga kai alamun eh, yayi yar dariya kinyi kyau da wanan kwalliyar ta wace?Nasake makale kaina cikin cinyoyi na, na ce eh. Ya matso sai kurum naji ya kama ka fada ta, ya saka dan yatsansa yana bin zanen fulawar, jikina ya dauki bari don ji nake tamkar susa yake min.Shima nasan yaji abin da naji don naji muryarshi ta dan sarke.Ya ce wata gwana ce ta zana maki wanan fulawar?Na ce wata yarinya ce.Ya ce, yayi kyau.Ina son farar mace na dan ware ido ina duban shi.Me yasa?Ya saki kafada ta Ra'ayi nane kawai ba dan komai ba, ke fa?Na sun kuyar da ka, kalar ka nafi so a cikin maza.Yayi yar dariya, wace iri ce kala ta?Na ce, wankan tar wada baka cikin farare kuma fara cikin bakake.Ya tashi daga mazaunin shi ya dawo kusa dani kan katifar.Kina nufin duk mun dace da zabin mu?Ban iya amsawa ba saboda yanda ya kusance ni, jiki na da na shi har suna haduwa.Ya saka hannun shi a kafada ta ya manno nijikin sa, fada mini gaskiya can dama kina sona?Duk da halin da nake ciki na faduwar ga ba sabo da irin yanda ya makale ni, bai hana ni tunanin wanan mutimin ya cika tam baya.Ko yana zaton nima mai laifin ce?Ya dago fuska ta, kalli cikin ido na ki fada mun. Zan gane in kinyi karya kwa yar idonki xata nuna mun.Naji mamakina lokacin da nake furta can dama ina son ka kai fa kana sona?Cikin wata ma yaudariyar murya nayi maganar.Kurum sai na fuskanci le bunan shi a kan nawa yana yi mun sumba, lamarin ya zo min sabo, ko na ce bako.Ya dinga yi mun wasu abubuwa masu firgitani har na zama bani da karfi.Tsoro na daya kada ya gota daga haka, saboda ina tsoron Iya.....zandakata Anan,muhadu a lokaci nagaba Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100 Darajar Yayana1-04 Posted by ANaM Dorayi on 10:48 PM, 16-Mar-16 Under: DARAJAR 'YA'YANA _______________NA _____HALIMA K MASHI Nayi karfin halin zame jiki na daga na shi, yakwanta rigingine na mike sai da safe.Ya miko hannu ya riko nawa hannun, cikin wata rikitaciyar murya ya ce, ki zo nan mu kwana.Da sau ri na ce, tab Iya ba zata yarda ba.Ya ce, ina ruwanta, ni ba mijinki bane?Na ce to ai ban tare ba.Ya saki hannu na.Da sauri na fice.Na tabbata in na shiga daki haka iya zata fahimci wani abu, don duk kwalliyar fiskata ya goge min.Don haka sai na bige da sabar buta na nufi bandaki, na zo nayi alawala.Ina shiga uwar daki ta bini da kallo tana kwance kan gadonta.Na cire kayan jiki na dauko rigar sallata nayi shafa'i da wutiri.Ta tabe baki bata dai ce min komai ba ko takula duk na tsargune?Oho.Da kyar na samu bacci ya soma dauka ta sabo da tunanin abubuwan da suka faru tsakani na da shi.Shigowar sakonshi dan sautin ya farkar dani, na bude na duba cewa yayi, kin hanani bacci my choice kixo ki taima ka min please.A raina na ce mai zanyi maka sweey Aly, ka dan bani lokaci mu tare, kiranshi ne ya katse tunanina,sa sauri na farka dan ina tsoron kada ringing din ya farkar da iya, duk da cewa na san tana jina don bata da nauyin bacci.Can kasan makoshi na nayi sallama ya amsa muryarsa a raunane, har mamakinsa nake ina girman kan? Ina isa da jin kan?A she dai mace dai ita ce namiji.In ba mace rayuwar namiji ragaggiya ce.Ya katse mamaki na da cewa, kizo kinji?Ba zan iya bacci ba ki taimake ni.Nace iya fa tana jinmu ka bari sai tayi bacci.Ya ce dagaske zakixo in jira ki? Na ce eh.Sai ya yanke niko gaba daya ma sai na kashewayar, na amsa masa cewa zan xo ne kurum amma ba dan zan je din ba, sai don ya barni.Kuma ko ba dan iya ba ina tsoro, tunda ban san yanda abubuwan suke ba.Na makele fulo ina tunanin ko a wane hali yake ciki yanzun, na jima kafin bacci ya tafi dani.Nayi mafarki kala kala masu dadi wai muna ta shawagi a cikin wata duniya ni da ya Ali.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Da safe kuwa fuskarshi a murtike, don ko amsa gaisuwata baiyi ba, lokacin da yazo gaida Iya ina gai da shi,hakan bai yi min dadi ba, na kunna waya ta na tura masa sakon ban hakuri tare da ce masa jiya naso inzo Iya ce bata bari na fito ba.Ko ya gani ko bai gani ba oho, bai dai bani amsa ba, na dafa ruwan tea na kai mai na same shi ya gama shirin fita yana daura ta kalmi.Na shiga da sallama ciki ciki ya amsa, ina shiga ya dubeni fuska daure ya ce, lfy?Cikin wata murya irin ta a salin jarumin maza.Jiki na ya dauki bari na ce, dama....dama tea ne.Ya ce fitan min da shi ina azumi, fargaba na ya karu, iya ce jiya ta fash....Ke!Ya katse ni, fita a nan dan Allah.Na fita da sauri, zugun na zauna ina tunanin yanda ya Ali yake canza launi tamkar hawainiya... Kimanin kwanaki uku kenan yayi mun dif, inna gaida shi baya amsawa, haka nan in abinci na kai mai ko yaushe sai ya ce yana azumi.In iya tayi mashi magana ke nan, in nice ma na kai mishi ni abu sai ya koro ni, ina girki a kicin iya ta fita lokacin sai ga Aisha kawata.Naji dadin zuwanta ta tayani,muna fira na bata lbr duk halin da nike ciki na kara da cewa, ya Aliyu gaba yake dani, iya ta sa ido sosai dan ganin ban bada kai ga miji na ba, ba tare da mun tare ba.Don Allah Aisha ki bani shawara, ta ce, ni dainawa ganin in har zan fada maki gaskiya kibi mijinki, daga lokacin da aka daura muku aure da shi dukkannin hakkokin shi sun hau kanki.Nayi ajiyar zuciya tace, nasan kin san komai ma kina yi ne kamar baki sani ba nace Aisha nasani,Iya fa idonta yana kanmu.Ko daki na shiga sai kiga tana kai kawo, in na fito kuma tayi ta yi mun kallon tuhuma, to ki bashi shawarar ku fita wani wurin mana.Nace tap nice ma zan bashi shawarar?To an ce maki iya za ta barni in fita ne?Aisha ta ce, yanda kika gani, amma in nice zan bi miji nane.Rayuwar nan ta yanxu mata suna bin maza har inda suke, balantana mijinki dan kwas irin wanda basu da yawa a cikin jama'a?Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na ce nima ina tuna haka, shiyasa wlh ban so ba da ban tare ba, kamar yarda ko wace Amarya take tarewa a dakinta. Ki tayani da adu'a don sun sani a tsakiya ita tana kallo na a mai rawar kai na shige masa,shi yana kallo na mara biyayya.Aisha ta ce, abu ne fa mai sauki ke ce kika dauke shi da zafi, in kin bi mijinki kinga dole ta barku.Na dubi Aisha ta ce, fa ba zai dubi mutuncina ba, Aisha ta ce, in bai sameki a mutuncenba ba?Kin bi maza ne?Na kai mata duka, kinji ki da wani zance, in na bi tare muka bi kenan.Ta ce ke ce da wani shirme, in kin ga namiji yaga rashin mutuncinki ya sameki kin bi wasu....(Biri fa kuma yayi kama da mutum,watakila irin haka tafaru da yar uwarki da Zaria,shiyasa mijin yayi inkarin kasancewarvcinkin a matsayin nasa,hartakai ga saki ANaM Dorayi) Kalu bale ga masu saida mutuncinsu a banxa. Aliyu tukur ya tsaya a gaban shugaban shashin su na binciken manyan laifuka, mataimakin Commissioner.Ya ce ASP Aliyu zanfi so idan kana tsayawa a kan aikinka, ina nufin ka rinka dakatawa a madakatarka.Sanan ka rage kishin ka, domin kasar mu a yau in kace haka zakayi lallai ba zaka kai ko ina ba.Ina yi maka magana ne a kan barawon shanu din nan, mutumin mai girma commissioner ne, na tabbata da yana gari baza ka kamashi ba bare tsarewa.Inma kayi nasara ka kama shi, ba zaiyi minti talatin a tsare ba kai ba a taba kama shi ba, yaranshi kurum ake kamawa.Da sunyi waya da commissioner zaisa a sake su, nayi mamakin ma da commissioner bai tsawatar maka ba, ya ce kawai ka bar case din a hannunsa.Ran Aliyu ya baci, shi da ya shiga aikin dan sanda kishin kasarshi da kawo gyara, sai kuma su rinka ganin barna suna kauda kai?Ya ce, yallabai ina rantsuwar da mukayi da alkur'ni cewa zamuyi aiki tukuru bisa amana da gaskiya, idan dannanda bai zama mai kishi da gaskiya me za a kirashi?Idan dan sanda zai rinka amsar cin hanci yana hulda da manyan azzalumai yana daurewa barayi gindi suna zalunci, za a kirashi mai tsaron lafiya al'umma.AC ya dagawa aliyu hannu, dakata ASP, wannan tambayoyin zasu fi dacewa kayiwa CP su, ni shawara na baka.Da akwai mutane irinka da yawa wadanda suka nuna kishi, wasu anyi musu canjin gurin aiki zuwa wasu garuruwan da ba zasu sami irin wanan barnar ba bare suyi gyara.Wasu anyi musu sharri an koresu, kai wasu sun mutu yayin da wasu da yawa suka ajiye hularsu.Ban hanaka yin kishi da gaskiya tare da kin karbar cin hanci ba, sai dai ina mai baka shawara ka dinga tsayawa ga kananan masu laifi, jeka abinka. Aliyu yana zaune a office din shi, kansa ya dauki zafi yana tuno sa'insa da sukayi da Barawon shanun, inda barawon yace, kai yaro wanan ba wani bakon abu bane satar shanun da muke yi.Haka nan mu nan Headquarter gidan mu ne kaine mutum na farko da na taba bawa cin hanci ya maido mini.Nafi tunanin kana daga cikin mutanen da basu da rabo, amma kai bako ne ko?Aliyu ya ce, ba jin tarihi ko maganar cin hanci na xo ba, nazo nan ne dan in kama ka,a matsayinka na mai laifi, ni kuma na hukuma.Duk wadan nan baya nan zasu biyo baya in munje office, yaranka muka kama kuma suka ja sunanka.Barawon ya zaro ido tare da daga murya ya ce, kai bako ne shiyasa baka sanni ba amma muje.Aliyu ya ce nasan ko ban sanka ba, bako ne ni bako ne wannan ba damuwata ba ce.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Sun san Aliyu bai san wanene wanan barawon ba, shi kanshi barawon cewa yayi zakayi da nasanin kamani.Aliyu bai ce kala ba, ya nufi Office din sa zuciyarshi cike da son nunawa wanan baron cewa hukuma bai bar kowaba.Amma me? daidai lokacin da yake bada ummarnin ashigar da kara ne shugaban shashin su AC ya ce, kajira tukunna sai an sami ummurni daga commissioner.Dafawar da akayi mashi itace ta dawo dashi daga dogon tunaninsa.Ya dago kai.Insperctor kamal kaita ne ya ce Sir, ka daina damuwa da irin wadan nan matsalolin, sanan ka ci gaba da yanda kake, Allah zai kawo maka dauki dan yana tare da irinku.Sai dai dama baku cika farin jini ba a cikin yan sanda, saboda kowa yana ganin cewa zaku toshe masa kafar samu.Shawarata ka bar batun Barawon nan ko ba komai kayi namiji tunda ka kamo shi, ka kuma tsare shi.Sanan Allah ya doraka a kan CP bai dauki zafi a kanka ba.Aliyu ya mike tsaye, na shigo aikin dansanda cike da kishi da buri, gami da kwazo.Manufata insamu waddanda zasu fahimci niyyata don mu kawo gyara cikin hukumar yan sanda.Na tabbata ko cikin headquarter din nan akwai masu kishi da yawa wadanda suke jin irin abinda nake ji yanxu a zuciyata. Inspector ya ce, hada dani, sai dai ina mai bakin cikin sanar da kai cewa ba zamu kai labari ba, tunda daga sama a ake tadiye mana kafa.Aliyu yace inko haka ne zaya ci gaba da faruwa, watarana zan iya ajiye hulana.Inspector ya ce, ranka ya dade kada kasaka haka a ranka tun yanxun, kaji a cikin xuciyarka cewa burinka ya cika, Allah yana tare da mai gaskiya.Ranka ya dade ka duba tashin farko bin diddiginka yasa sashinmu na bincike suke shakkarka, ina son mutum irinka.Aliyu ya lumshe ido tare da cewa zantukanka sunyi mun allura inspector, zan kara kaimi.Da wanan ya cigaba da aikin sa.Daf da zai tashine aka shigo da wani da ake zargi, ya kalle gobjejen mutumin sanan ya dubi yan sandan.Me yayi shi kuma wanan? Sajan Ado ya ce, ranka ya dade, kato kamar wanan aka kama yayiwa yar shekara takwas fyde,ran Aliyu ya tunxura, ya runtse ido cikin takaici, ya ware ido ya kalli mutumin cikin tsana ya ce, wai wane irin zaluncine wanan kuke yiwa jikokinku?Cikin rawar murya mutumin ya ce ranka ya dade na rantse maka ba ni bane, sharri sukayi min, na rantse maka.Aliyu ya harareshi, ba kowa bane yake amsa laifinsa da sauri.Ya kalli yan sandan suwaye suka kama shi?Sajan ya ce ranka ya dade ga mutanen da suka kawoshi can, sune suka kamashi da yarinyar a shagon shi tana ihu.Yace ina yarinyar yanxu?Sukace an tafi kaita Asibiti.Ya kalli mutumin yaja tsaki ya ce, ya ce ku rufe shi, yanxu ba wani sausauci ga irin mutanen nan masu cutar da kananan yara ta ta hanyar fyade Ya koma office din sa cikin ta kaicin fyadan nan, kullum sai sun samu irin wanan case din da yar da jarirai yafi yawa, amma yanzun yanaga zasu xo daidai.Ya kira sajan ya ce, ya kawo masa takardar tuhumar (statement) da ya duba tsaki yaja, ya dubi sajan.Kullum dai abin iri daya ne.Ya tabe baki, sanan ya dubi a gogonsa, yau shida zan bar nan, duk wanda ya nemeni saidasafe.Sajan ya sake kamewa tare da fadin yes sir!Sai kuma wanan mutumin yaya za ayi da shi?Aliyu ya ce, ba maganar beli ko wani ya zo zuwa gobe za a hada bincike a turashi kotu.Sajan ya sara masa sanan ya fito.Da dunbin wanan damuwar ya iso gida, daga ganinshi kasan akwai abin da yake damun shi, kan katifarshi ya zube rigingine bata re da ya cire koda ta kalmi ba.Lokacin da ya shigo ina zaune a kan kujera a kofar daki ina karatun wani littafi (SIRRIN BOYE) na Anty Bilkisu.Ga al'adarshi in ya shigo dakin Iya yake fara shiga kafin ya dawo dakinsa, ya cire kaya in sun gaisa.Ya shiga wanka.Amma yanxu tunda ya shigo shiru, iya ta fitodaga bayi (ban daki) na dubeta na ce, yaya fa?Ya dawo yanayin shi kamar na mara lafiya, ko baya jin dadi ne?Ta ce, ba wani ke dai kina sonzuwa gurin mijinki ne, kuma ba zan hanaki ba.Na hade fuska, Allah iya nifa ba wai zanje bane fa.Ta ce, kije ki duba ko lfy,naki tashi, dan dama ina tsoron inje yayi mun wulakancin shi, ya ce nafita shiyasa naki zuwa.Ganin da iya tayi tabbas ba zan shiga ba kuma tabbas bai fito ba sai ta shiga dakin. Yan da ta ganshi warwas a katifa batare da ya cire ko takalmi ba, sai abin ya bata tsoro.Cikin saurin muyar ta ce, Gadanga!Ya dago kai da kyar ya dubeta, wani matsanancin ciwon kai ke damun sa.Ya ce na'am Iya sannu.Ya tashi zaune, ciwonkai ne ya hanani shigowa ciki.Ta ce, matarka nema ni take ce mun ka shigo cikin wani yanayi, bari a kawo maka magani ka sha.Yace zanje Asibiti in anjima bayan magariba.Duk kwanakin nan da haka nake ta yawo da ciwon kan nan. Ta ce, to kasha maganin yan xu sai kayi sallar da dan karfin jikinka, kaje asibitin da dan kwari.Ya ce, to.Ta kwala min kira Sadiya.Na amsa ta ce, dauko min magani panadol kizo da ruwa.Naje har gabanshi na ajiye da ruwan ina yi mashi sannu yaya, ya jikin?Ko kallo na baiyi ba bare ya amsa, mamakin yanda naga iya tan gutsi gutsi da maganin, ta dubeni dauko mun cokali.Na dauko ta jika ta bashi a baki tare da fadin, shiyasa nake fargaban ciwonka gadanga.Duk da dai ba yawan ciwon kake ba, amma kin maganinka shi ke wahalar da kai a ciwo dai dai yake da na yaron goye.Shi yasa duk lokacin da katashi ciwo bama jita dadi.Ya sha ya koma ya kwanta, dai dai lokacin aka kwada kiran magariba.Ta dube ni, bari inje inyi sallah, nima na biyo bayanta.Ta dakatar dani da cewa, jira tukunna muga yanda jikin zaiyi.A raina na raya cewa dan ta ga ina fashin sallah, shi kuma bashi da lfy.Shi kam yana kwance, na isa gurinsa gabana yana ta faduwa, duk da ina zaton zai daka min tsawa ban fasa yin abin da nayi niyya ba.Gabansa na tsugunna ina kwance masa takalmi, na cire su na aje gyafe, sanan na kwashi kafafunsa na zubasu a kan katifar.Har lokacin idanunsa biyu amma suna lumshe, haka nan hannunsa yana dafe da kai.Kusan minti shabyar ina zaune can gefe, ya tashi zaune yana kici kicin cire rigarsa, na taso na balle masa boturan, sanan na sabule rigar sai farar singiletin, ita ma ya kama ya cire.Na kalli kirjinshi gashi ne kwance na kauda kai don sai da naji wani iri.Ya sabule wandonshi, sai gajere na ciki, shima na kwashe su na zaba su a cikin kwandon da yake zubawa.Naga yana kokarin tashi nace mai zaka dauko in dauko maka?Ka zauna kawai.Ya ce, bani jallabiyata.Na bashi fara kal mai dogon hannu, ya mike zai fita, na ce ina zaka je?Ya ce masallaci.Yana fita na shiga gyaran dakin, ban taba yi masa gyaran daki ba sai yau.Ko yaushe da kansa yake yin gyaran dakinsa, nayi zaton zanga mujallun da na taba gani da, sai kuma ban gani ba, har na gama.Iya ta idar da sallah, ta sake lekowa ko ya tashi, na ce ya je yin sallah, shiru shiru ashe daga can ya tafi asibiti.Har kusan tara gashi bai fita da waya ba.Iya da kanta ta fita har masallaci layin mu, wanda suke sallah tana nemanshi.Duk wanda ta tambaya sai su ce mata tare dai suka idar da sallar isha'i.Da ta dawo sai na ce mata ko dai yatafi Asibintin da ya ambata ne?Ta ce zata iya yuwuwa ya tafin, tun da ya ambata.Nan dai muka zauna zaman jiran tsammani,mun kasa ko cin abinci.Sai sha dayan dare da yan mintuna dan acaba ya sauke shi, ni da iya har rige rigen fita muka yi, shi ne muka yi masa sannu ya amsa, iya ta ce, muna ta neman ka.Ya ce, natafi Asibiti ne shi yasa ciwon kai ya matsa min da yawa.Amma na sami allura da magunguna, kuma na kwanta canne kamar yanda likitan ya ce in dan huta, Alhamdulillahi kai yayi sauki.Ta ce to me zakaci yanzun?Ya ce, nasha tea a can kafin ayi min allura, muka shiga dakin shi ya zauna bakin gado.Iya ta fita nima na mike zan fita, sai ta ce ki dan tsaya ke saboda dare ko?Na koma na zauna ya kwanta tare da lumshe ido. Wayarshi tayi ringign, ya daga ya kalla sannan yaja tsaki, bari na kashe wayar nan ina so in dan huta.Har zai kashe sai ga ma bari yayi anfani da wanan damar ya nunawa sadiya anafa ribibin shi har da take masa yan ga.Don haka sai ya daga ni dai naji yana fadin yaya mati na me ya faru ne? Ban zaci jin muryarta ba, ashe ya saka hanfree.Sai kurum naji ta ce, lafiya lau sir, ban gankaba ne an ce ka tashi tun six, ya ce akwai wata matsala ne matina?Ta ce babu, naso in ganka kawai, kayi hakuri kasan ganinka kawai yana cire min damuwa dayawa, dayawa, amma sir sai kanayi kamar baka san haka ba.Yace matina yanzu bani da lafiya ne, ban dade da dawowa daga Asibiti ba in nafito da safe zamuyi maganar.Ta ce to Sir, nagode Allah ya kawo sauki.Raina yayi mugun baci, a gabana yake magana da wata arniya har take ce masa ganin shi yana sata sukunni da kwanciyar hankali?Yana ajiye wayar ya kalleni, na hada rai matuka na mike ya ce, ina zaki?Nace zanje in ci abinci ne, da kyar nake magana.Ya ce, au dama baki ci abinci ba?Kamar in kai masa duka don ta kaici.Mutumin da yayi nasa guri bai fada muna ba muka yi tsuru tsuru cikin damuwa.Shine zai ce dama ban ci abinci, ya mai maita tambayar nace um, ya ce kina ciwon baki ne?Nayi shiru yace in kin ci ki dawo, tunda Allah yasa yau naji da kunnena ba iya ce take hanaki zuwa wurina ba, karya kike yi mata.Ban tanka shi ba na wuce, a raina na ce ba zan dawo baCan kusan daya saura ina ta tubka da warwara na kasa bacci, ni nasan kaina ina da mugun kishi, sai ga sako ya shigo cikin wayata cewa ba zaki dawo bane?Na tura masa amsa da cewa eh, ka kira Matina.Yana ganin haka yayi ta dariya, sakonshi ya kai ke nan, don haka shima kurum sai ya kashe wayarsa ya kwnta.Da Asubahi iya taje dubashi ta sake shiga dan duba shi, sai ta samu jiki yayi sauki, har ma ya tafi masallaci.Don ya Aliyu ba rago bane namiji ne, ga juriya da izza, matsalarsa daya in yana ciwo kin magani,yayi tawa iya shagwaba sai kace karamin yaro, shi a dole auta.Nikam har gari yayi haske ban tashi daga makwanci na ba, tunda ina fashin Sallah ba wai ina bacci bane kurum takaici ne ya hanani tashi.Jiya ko baccin kirki banyi ba, saboda takaicin ya Aliyu.Iya ta shigo, ke ba zaki tashi kije ki gano mijinki ba?Ko da nafito kin xuwa nayi na debi ruwa na shiga wanka.Ina fitowa nayi zaman shafa mai duk ina jan lokaci ne don yayi abinda zaiyi ya kama gabanshi.Bana ma ko son ganinshi, lokacin da na shirya na nufi kicin a tsammanina ya fita.Ina tsakiyar kunna risho sai naga mutum a kofar kicin tsaye.Na rasa dalili in zan ga ya Aliyu sai gabana ya fadi.Na kalli fuskarshi, gaskiya har ya dan rame na ce ina yini?Ya ce ban yini ba, ni yanxu zafiya ce, sanan ba zan amsa ba tunda baki san hanyar daki na da bazakije ki gaida ni ba.A raina na ce ina matina?Ita batazo ta duba ka ba?Ya katse tunanin da cewa,ruwan zafi nake so zanyi wanka.Na kalleshi, ban taba ganin yayi wanka da ruwan zafi ba, nace to bari in dora yanzun, bai ce, kala ba ya koma daki.Da yayi zafi na sirka na kai masa ban daki, sai naje na ce masa ga ruwa can.Lokacin yana waya, da hannu yayi min alamar cewa in je yaji.Na tsargu da wa yake waya, don haka da nasaki labule sai na tsaya.Ji nayi yana cewa, kada ki damu, yanzu zanfito.Jikina yayi sauki, ai da tunaninki na kwana araina.Na girgiza kai tare da yin kwafa.Tabbas da matina yake yin waya, nayi kicin ina yin magana ni kadai, na ce to ita wanan shegiyar matinar me ke tsakaninsu?Nemanta yake yi ko me?Wata zuciyar ta katseni da cewa, ba kina gudunsa ba? Ai ga Matina zata maye gurbinki. Jikina ya sake mutuwa, na shiga tambayar kaina mafita.Wunin ranar sukuku nayi shi, na kasa tuna yanda zan bullowa abin.Duk jin su iya nake ko da can da suke cewa ba ruwanshi da mata, ni nasan da ruwanshi tunda ni naga mujallun batsa a dakin shi.Wanda baruwanshi da da mata me ya ruwanshi da irin kallon tsiraici?Dole ke nan inyi yakin rabashi da matan banza.Wata zuciyar tace haka ba zata yuwu ba, sai in zakiyi aikinki a matsayin matarsa, lallai saikin mika kanki a fili na ce ya na iya?Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Muna zaune a falo da iya washe gari da safe, yazo yiwa iya sallama zai fita, nima na bude baki da nufin ce masa sai ka dawo.Amma da yake matina ce a raina sai kurum naji na ce masa ka gaishe mun da matina.Har ya juya sai naga ya tsaya cak, sanan ya waiwayo fiskarsa dauke da murmushi ya furta cewa zataji in sha Allahu.Ya juya ya tafi, ni kam kamewa nayi tamkar gunki, a zuciyata tambayar kaina nake dama mutun na iya kuskuren magana ya furta abinda ke son zuciyarshi ya bar na saman leben shi?Kash!Ban so nayi zarar bunun nan ba, abin takaici harda murmushi na ambaci sunan masoyiyarshi. Kwana uku suka shude ina cikin damuwa,na san Iya ta lura banza kawai tayi mun,narasa abinda ke yi min dadi, ni ba fita nake ko ina ba, ba TV Garemu ba bare nayi kallo, ta lalace ni kuma ba ma abociyar radiyo ba.Wani kayan haushi ko littafi na dauka da sunan karantawa sai in kasa fahimtar komai.Na san kaina ina da shegen kishi na ban mamaki, ko saurayina naga suna yawan gaisawa da wata budurwa hankalina kan tashi, bare a ce miji na.Tabbas da Ya Aliyu ya skar min fuska da tuni na same shi munyi ta, amma ya Aliyu ya wuce haka.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Cikin sauri sauri ya Aliyu ya shiga shashin su, ya kalli sajan Ado ina barawon?Suka kaishi ya shiga.Ya tsura mutumin ido, aransshi ya ya ce kai wanan mutumin baiyi kama da barawo ba.Ya kalli Sajan, kawo abin zama, sai da ya zauna sanan ya kalli mutumin.Kaine barawon fili ko?Hawaye suka soma kwarara daga idanun tsohon, don bakin cikin sunan da aka kirashi.Ya ce cikin rawar murya, ranka ya dade ni ba barawo bane, ban taba sata ba.Aliyu ya juya kulkin dake hannunshi ya dan jefashi, sanan ya cafke.To baba ya akayi har ka mallaki filin da kake gini?Ya ce, ran ka ya dade filin nan na gajeshi ne a gurin mahaifiyata, don mahaifinta manomine.To ina zaune a gidan haya ga iyali, ina da mace daya ga yaya takwas.Yan samarin yara na a makota na roka sunakwana, ganin kullum nauyi na karuwa, sai nayake shawarar gina fili na ko da daki biyu ne rak.Na soma gini ni da yaya na, dan sana'ar mu ke nan ta leburanci da yaran.Mun soma ginin kawai sai ganin yan sanda nayi sun xo kamani, ban san abinda nayi ba.Aliyu ya ce, to baba naga takardar bayanin laifinka, naga cewa ana zarginka da laifin yingini a filin da ba naka ba, filin tsohon jami'in dan sanda ne.Tsoho ya ce, dana wlh wanan filin nawa ne, kowa ya sani a unguwar mu ina da takarduna ina da sheduna.Kuma ni da aka kawoni nan ba a tambayeni ankawoni nan aka jehoni ne kawai.Babu wanda yaji ta bakina.Aliyu ya ce ka tabbata kana da takardu da shedu?Tsoho ya ce ina dasu ranka ya dade.Aliyu yace zamu mikaka kotu kuma in sha Allah zan tsaya maka sai kayi nasara.Cikin izza ya nufi wajensu Sajan Ado, yace sajan, yace Sir, bayan ya kame.Aliyu yace waye ya kawo wanan mutumin?Sajan ya ce, barawon fili?Aliyu ya ce, eh shi.Sajan ya ce CP ne yasa a kamo shi.CP da kanshi?Ya tambaya cikin mamaki.Yace shi, amma AC ne ya tura.Kan Aliyu ya daure, ina takardar bayanan da kuka bani dazu?Sajan ya sake daukota, Aliyu ya kalla ya sake karantawa, wanan rubutun kofur bala ne ai, sajan ya ce, eh, Aliyu ya ce kira min shi.Ya juyya ya koma office din shi.Ya tsare kofur da idanun shi waddanda basadaukar raini, kainne ka rubuta wanan takardar ko?Ya kame, eh, nine Sir, ya juyya mishi baya, amma ai baka tambaye shi ba ka rubuta da yawun shi.Ko menene dalilinka?Kofur cikin daburcewa ya ce,Sir ai nima AC ne ya ce na rubuta haka, sabo da raini mutumin yake so ya kawo wa tsohon mataimakin IG.Aliyu ya daga hannu da nufin dakatar dashi, tsaya min kowa ya cuta sai a ari bakinsa a ci mai albasa?Ya ninke takardar ya zura cikin aljuhunsa, yace dauko wata kazo muje ka sake rubuta ainihin bayanin da yake daga bakinsa, mu masu kare Al'umma ne da rayukansu ba masu danne masu hakkin ba ne da kuma kashe su.Kofur dake biye dashi ya ce, sir, wanan tsohon mataimakin IG yana yawan kawo mana matsalolinshi a nan, kullum maganarshi bata wuce an cuceshi.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Aliyu ya ce dan ya taba zama jami'in dan sanda bazaiyi anfani da wanan damar ba, sanan yayi anfani da mu.Alkawari na daukarwa kaina ba zan bar zalunci ba, matsawar naganshi zanyi yaki dashi.Aliyu ya tsananta bincike kuma cikin kwanaki kadan yagano cutar tsoho wanan jami'in ke son yi, don hakka ya tattara dukkan bayanai ya turasu zuwa kotu.Gobe da safe ya tabbata in anje can tsohon zai sami hakkinsa, saboda bayanai da hujjojin da Aliyu ya hada.Yana tsaye a bakin titi zai hau a caba zuwa gida Inspector Kamal ya sameshi a gurin, ya ce ranka ya dade zuwa yanzu yakamata a ce ka mallaki abin hawa ko da mashin, amma in san samu ne a ce kana da mota.Aliyu yayi murmushi, kada kadamu, ko mai lokaci ne, ya ce in dauko maka na aiki mana ba sai ka sha mai ba?Aliyu ya ce, a a na aiki anyi shi ne dan aiki kawai.Ispector ya ce, kana birgeni Sir, komai kana barinsa a muhallinsa.Lokacin da aka raba mana mashina baka zoba.Aliyu ya ce, ko ina nan ba zan amsa ba, don bana son bashi.Ya karasa zancen tare da tare dan acaba.Wayyarshi ta dauki tsiwa, ya cirota cikin hanzari ya daga saboda ganin sunan AC, hakuri ya baiwa dan acaban, sanan ya komaciki kamar yanda AC ya bukata a cikin officeya same shi, kai kawo yake ransa a bace ya dubi Aliyu.Me yasa ba bada damar a kai barawon filin nan kotu?Aliyu ya ce, angama bincike ne sir, sanan doka ta hana a tsare mutum tsawan lokaci ba tare da an kaishi kotu ba.AC ya ce, na san dai na rigaka sa kaki ko?Bai jira amsa ba ya ci gaba da cewa, don haka kasan na rigaka sanin doka.Ya koma kujerarshi ya zauna.Wanene ya hada binciken? Kai kasan ma da wa yake rigimar?Kasan filin wayake son kwacewa?Aliyu ya ce, nine da kaina nayi binciken sanan nasan rigimarsu shi da tsohon IG ne, kuma CP ne ya sa a kawoshi.AC ya ce, gud, to zan sake mai maita maka, in an kawo mai laifi da umurnin CP dan Allah ba ruwanka da shi, in zaya shekara.Ran Aliyu ya baci, ya ce, Sir, amma ba akan haka mukayi rantsuwa ba.AC ya daga masa hannu ban ce maka inason tunatarwa ba, sai dai ina son kasani ka kusan kai CP bango, dan kana son shiga cikin lamarinsa.Sanan kayi hanzarin cire kanka daga cikin lamarin tsohon, ka barsa yayi nashi binciken.Shiru Aliyu yayi, amma ji yake tamkar ya kama da wuta don zuciya.AC ya ce, ka iya tafiya.Aliyu ya fice da kunan rai.Matina ta hangoshi cikin sauri ta bishi, yana tsayawa a bakin titi tana tsayawa, ta ce barka da warhaka yallabai.Ya furzar da wani huci mai zafi, sanan ya ce barka dai.Tace ina tuni yallabai ya runtse ido don yanason saita zafin da zuciyarshi ke yi.Baya so ta fahimci yana cikin damuwa, sanan ya budesu sun kada sunyi ja, sanan ya ce matina zanfiso mu zauna a matsayin abokai, na fada maki bani da sha'awar auran mata biyu.Ina yi maki adu'ar samun mijin da ya fini.Ta ce, samun kamarka ne yallabai sai an tona, kunyi karanci a cikin al'umma.Ba duka namiji mace kamata zata bashi kanta ya kauda kai, har yanxu ina tuna ranar, ranar da na fada maka ni da kai muyi soyayya koda bamuyi aure ba.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Na fada maka cewa wata gara basa da zan maka shi ne, zaka iya yin duk yadda kake sodani na mallaka maka kaina, amma sai kayi mun nasiha ka kuma nuna min cewa addininka ya yi hani da hakan.Na sami kaina da sonka tare da son addininka, sanan cikin aikinka kowa yasan kana kwatanta gaskiya da amana.Ina tsoron in auri wani cikin masu addininku ya sake ni, dan ku hausawa ance kuna da sakin aure amma kai nasan ba zakayi haka ba.Aliyu ya kasa kallonta dan ta daureshi da jijiyoyin jikinsa.Ya ce, Matina ki amshi addinina da zuciya daya, sanan kisa a ranki zaki sami mijin da ya fini, nima zan tayaki da adu'a.Ta gyara tsayuwa kada ka damu, ni zan ci gaba da zaman samun irinka, alfarma daya nake roko in zaiyuwu, in na kiraka ka daga wayata.Sanan in kazo nan muke rinka gaisawa.Ya ce dan mun hadu mun gaisa ba damuwa,abin da zaiyi dan wuya ki rinka kirana ina da mata, nasan bazata so hakan ba.Ta rausayar da kai gefe, cikin raunaniyar murya ta ce, na gode,ka fadiwa matarka cewa ta rikeka da kyau, dan tana cikin matan da sukayi sa'ar zuwa duniya.Murmushi yayi duk lokacin da kuka hadu saiki fada mata da kanki, na barki lfy.Yana kan mashin yana tunani ko me yasa yake samun irin wanan matsalar?Mata suyi ta sonshi suna binshi, amma shi bai damu da su ba.Matina yana kulata ne saboda musulantar da take sha'awar yi, ya san in yazama sanadiyya zai sami ladan hakan.Daga nan tunanin sa ya koma kan matsalarshi ta office, in dai da irinsu AC da PC anya kasar nan zata gyaru?Lallai kasarsa Nageria tana cikin wani hali, kullum burin nasama ya danne na kasa, sam ba a son gaskiya.In ka tsayawa halas dinka sai mutane su rinka yi maka kallon dan kauye.Ya girgiza kai sakamakon tuno tsohon nan da yayi, shi da gaskiyarshi da filin sa da komai ba a tausaya masa ba, kasancewarshi mai rauni ana neman a zalunce shi.Mai dama yana anfani da damarsa gurin cutar mai rauni, yasan in ba wani ikon Allah ba tsohon nan ya rasa filinsa kenan, in yasamu ya fita da ransa kenan.Duk lokacin da irin wanan ta faru sai yaji tamkar ya bar aikin dansanda, amma da ya tuna kudirinshi na kawo canji da gyara, sai ya hakura, da wanan sake saken ya isa gida. Niko tun lokacin da na furta masa cewa ka gaishe da matina cikin kuskure, ban sake yarda mun hadu dashi ba.Kusan kwana uku wasan buya muke yi har iya ta fahimci cewa na guje masa, amma bata nemi jin ba'asi ba, yi tayi ma kamar bata san me ni ke yi ba.Sam ban zaci dawowarshi a wanan lokacin ba, domin cikin kwanakin nan sai dare yake dawowa.Ni kadaice a gidan,Iya tun bayan la'asar sun tafi Asibitin dutse duba wata makociyarmu da bata da lafiya.Sun tafine da ma da sauran makotanmu.Na wanke hijabaina da na Iya ina shanyawa,daga ni sai best, zanina kuma iyarshi kugu.Ina shanya ina mitar cewa iya sunje sunyi zamansu, nasansu da son tafiyar kafa, yanzu haka ma da kafa suka tako.Banji sallamarshi ba sai dai naji ya ce ina suka tafi?Na waywaya na kalle shi, da gudu na shige daki dan kirji na duk a waje yake.Dan murmushi yayi sanan ya shige dakinsa.Ina zaune bakin gado ina kallon jikina sai ganin shi nayi tsaye a gaba na har uwar daki.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Naja hijabina, ya ce ina tambayar iya kina gudu? Ya hade fuska tamkar bai taba dariya ba.Tsoro ya darsu a raina, cikin in ina na ce,Asibiti suka tafi.Ya ce, dan kada ki bani amsa shine kika kwasa da gudu?Nayi shiru, ya ce kin min banza.Nace yi hakuri dama zan dauko dan kwali nein daura.Ya ce, ok, ni zaki boye min gashin kanki?To ajiye hijabin in ga gashin tunda halas dina ne.Gabana ya soma faduwa, na zame Hijabina ya ce ashe ma ba wani gashi kike dashi ba, cire hijabin daga jikinki in gani.Na kalleshi da sauri ya kauda fuska yana yatsina baki, sai kace zai ga abin kyama.Na cire hijabin na ajiye cikin sauri kuma na sa hannuna na rufe kirjina.Ya ce cire hannunki.Na cire tare da runtse idanuna.Sai kurum naji yasa hannu ya turani baya, na fadi rigingine na bude idanuna da sauri ina tsoro, yasa hannu ya janyo best din sai ta yage, kirjina ya bayyana.Tsayawa yayi yana kare mun kallo, ya tabe baki, dama best din taki rubabiya ce? Sallamar iya ta tsakar gida ce ta sani tashi zumbur, na dauki hijabi saka.Cikin tsoro mai tsanani na ce ga iya nan.Shi kam ko a jikinshi.Ya tabe baki tare da daga gira sai me?A zato na bai fahimci nufina ba, don haka sai nayi nufin fahimtar da shi katafi da sauri kada ta ganka a nan tayi zaton ko wani abu ne.Sai naga kurum ya zauna bakin gado, na zaro ido dai dai lokacin da ta shigo falo tana cewa Sadiya ina kika shige ne?Kin ganmu sai ynzu?Da sauri na fito cikin in ina na ce gani nan, kun...kun dawo?Eh, lafiya na ganki a hargitse?Ta ce ba ko mai.Na yi waje.Ita kuma ta nufi uwar daki, gabana yana faduwa.Tana shiga ta ganshi zaune bakin gado yanawaya, ta ce au, ka dawo?Ya ce, eh, na dawo tun dazu, waye babu lafiya kika tafi asibiti?Tace matar mai besfa ce a asibiti mukaje duba ta.Ya ce, Allah ya bata lafiya.Ya mike bari in karasa masallaci.Sai tin kunne na naji maganar shi, a hankali yace sarkin tsoro. Sam ya kasa bacci abin da ya kalla daga yarinyar kurum yake tunanowa, juyi yayi har gari ya waye sai ya dauki waya da nufin kiranta dan yana togon cewa ita din halas dinsa ce.Sai kuma ya tuna cewa yarinyar ba zatazoba, sanan ga iya, kai!Shi fa ba zai iya jira sai sun tare ba.Da safe naje kai masa abin kari, lokacin ya gama shirin fita kawai zaiyi, ya amshi kofin daga hannuna ya kurba.Sanan ya kalleni kin kawo a latti, kin san da wuri nake fita. Na ce, a shanarmu ce ta jike shi yasa, sai da masu shago suka bude iya ta fita ta siyo.Ya ce my choice.Na kalleshi zan sunkuyar da kai, ya ce a a kada ki sunkuyar da kai, kalli cikin idona, bana son wanan sunkuyar taki tana cutar dani.Na kalli idon shi, ya ce yau ina bukatarki, na gaji ina da mata kullum nine cikin azumi.Nayi kwalkwal zan soma kuka, ya tsareni da idonshi, ya kuma hanani sukuyar da kai.Cikin raunaniyar murya na ce, kasan dai iya ba zata bari ba.Ya ce daina karya da iya, na gano ma ba ita take hana ki ba tun da ranar nan in an ji ta ce ki zauna da ni, lokacin bani da lafiya.Ya mika min kofin tare da cewa, zan fada mata, jeki abinki.Na tafi ina mamakin shi, musanman da naji ya ce zai fadawa iya zanso inji ko me zai ce mata na kasa karyawa don zullumi, ina ta juya biredin dake gaba na, kamshin turarenshi ne yasa gabana faduwa. Ya ce, iya na tafi.Ta ce to auta na, Allah ya tsare.Ya ce, amin.Yana wucewa na sauke a jiyar zuciya.Cikin jin dadi na gutsire biredi, na dago kofin shayi na kurba sai naji takun sawunsa ya dawo, take naji shayin ya sane.Ya ce au, na manta iya.Ta ce, na'am iya za a zo a dauketa taje ta gaida matar oga, ko bani ba wani zaizo daukarta. Na kalli iya, shi dama vai jira amsaba ya tafi, ganin kallon da take min sai na tsargu, na taihashashen baki muka hada.Don haka na ce, iya ke ce masa ba zanje ba,Allah ni bana son xuwa.Ta harareni, bakya son zuwa ne kika bari ya tafi baki ce ba zaki ba, sai nice zance karki je? Bayan kun kitsa abinku?Ta taba baki haba yayan nan, na fa rigaku zuwa duniyar har da kuke son maidani wata sakara. Na ce iyya Allah ba haka bane, ba mu kitsa komai ba, ni bansan ko mai akai ba, ban san da wata magana ba sai da yayi yanxun. Ta ce kwaji da shi, nifa bance kada kije ba, ke da mijinki zan hana ki?Ta fada cikin gatse sanan tayi tsakar gida tabarni zaune cikin damuwa.Da naga har la'asar babu wanda yazo nemana, kuma shi bai dawo ba, sai naji dadi kuma na dan saki jikina. Cikin haka wayata ta fara ruri, na daga a raina ina adu'ar Allah yasa ya ce an fasa.Sai naji ya ce ki shirya Usman zaizo ku taho.Sai da na daga murya yanda iya zata jiyo, sanan na ce, yaya, Allah iya ta ce bazanje ba. Iya daga inda take ta ce, a a ba ruwa na ni Sa'adatu, ban hanaki ba ni ko baku hada baki ba ni yar bada shawara ce.Yace to najiyo abinda iya ta fada, don haka na baki minti talatin ki shirya.Sai ya kashe wayarshi.Na ce na bani yanxu yaya zanyi?Don Allah ku bani shawara, inbi mijina ko in nunawa iya harshashenta ba haka bane? Taku Halima K/Mashi kemuku godiya. Awanna gabarma Kanwarku Sadiya tana neman shawarar ku, Saimun hadu a cikin littafi na biyu.Ku ziyarci blog dinmu domin karanta Littatafai masu nishadantarwa Anamdorayi.mywapblog.com Kokuma ku kasance taredamu a facebook https://mbasic.facebook.com/HAUSA- Novels-389304544597988/?_e_pi_=7%2CPAGE_ ID10%2C737012347 Zaharaddeen Shomar Whatsapp 08168575100