[7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 15* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* rausayar da kai ABU yayi kafin yace, "ko ba da hakan na kiraka ba to babu abunda ze canja kai ɗan uwa na ne, karkayi saurin yanke min hukunci Khaalif ba nine maci amanar ba SO ne yaci amanar mu, ba tin yau ba tin tana ƴar ƙarama zuciyata ta gama daskarewa da sonta na tabbata a lokacin baka fara sonta ba ma, ka dena cewa naso abunda kake so ba haka labarin yake ba, dani da kai duk muna son abu ɗaya bana son tashin hankali a tsakanin mu, abunda na daɗe ina koka mana kenan bamu da mahaifiyar da zata iya yimana alƙalanci itace wadda zata iya kwantar mana da hankali a duk lokacin da hankalinmu yatashi, ka dena kiran hakan da cin amana, maslaha tafi komai daɗi mu fahimci juna Khaalif ba muyi ta rikici a tsakanin mu ba ita kanta wadda muke so hakan ze taɓa zuciyarta sosai muyi maslaha a ganina shine mafi sauƙi tin kafin abun yayi tsauri" Khaalif yayi saurin tarar sa da cewa, "indai da haske ne maslahar kake so to abu ɗaya ne ze kawo maslaha" ABU ya ɗan murmusa kafin yace, "menene Junior ????" Kai tsaye yace, "kabarmin Ayeeshah ta" Lumsassun idanunsa yaƙara lumshewa ya buɗe sannan yace, "ba lallai ka fahimci irin yadda nakeji ba ƙanina, ta yuwu soyayyar tsakanin ku ƙarfinta shaƙuwa ce kawai saboda kun taso tare, amma ni nayi DAKON SO na ɗauki nauyin sonta tin bansan kaina ba, ina tsaka da azabtuwa a gurin matar baba na amma hakan be sa na manta da ita ba, uhm.. kasan ma abunda nake tunawa ya sani farin ciki a lokacin?? idan na tuna wata rana Eeeshu xata girma, zuciya tana gaya min itace farin cikina sai naji na ƙagara lokacin yayi wanda zan kasance tareda ita, ASALIN SO nakewa Eeeshu Junior kai kaɗai ne gareni ciki da waje kaine dole na kai zan nuna nace kaine ƙani na ka tausayawa ɗan uwanka mana dan Allah ka barmin Eeeshu" Girgiza kai Khaalif yayi yace, "wannan labarin naka yayi fa Bro, sai dai be hau kan layi ba, bazan iya janyewa ba bana so ma naƙara ji ka kira soyayyar da nake mata da sunan shaƙuwa ko menene ma ina so kabarni da ita kamar yadda ka ganni tare da ita" ABU yace, "bazan iya ba, duk da in na faɗa ma ba yarda zakayi ba amma bazan iya barinta ba idan nayi haka naci AMANAR SO ka ɗangale min mana ɗan uwana, shi so ba'a yimasa shamaki, a lokacin da nafara sonta ban taɓa zaton ma wani namijin ze sota ba bayan ni bare nayi tunanin Ƙanina ze so ta, sai dai so makaho ne kuma kurma ne baya gani kuma bayajin kira haka baya ɗaukar shawara amma da yaso yimana adalci da be kaini kanta ba" Sosai ran Khaalif yaƙara ɓaci dan haka ya miƙe tareda cewa, "ni yanzu tafiya zanyi banida lokacin tsayawa naji wannan kalaman naka masu kama da wasan kwaikwayo, kamar yadda kace bazaka iya ba haka nima bazan iya ba, Ayeesha tawa ce adalcin da zakaiwa kanka nima kaimin kawai ka barni da ita dani tafi dacewa, idan ba haka ba kuma mu zuba ɗan halak ka fasa, dani da kai zan ga ɗan halak a cikin mu" ƙasa ABU yayi da kai ya Share ƙwallar da ta zubo kan kumatunsa cikin takaici yace, "Junior uwa ɗaya ce ta haife mu kuma a ƙasa ɗaya a iya sani na Mahaifiyar mu bata haifi ɗan da ba na halak ba, dani da kai duk ƴaƴan halak ne, kana da uba ina da uba banbancin kawai kai mahaifinka mutuwa yayi ni kuma rabuwa sukayi dan ƙaddara badan mugun halinta ba, Mahaifiyar mu Uwa ce tagari me son ganin dariyar ƴaƴanta idan kai baka santa ba to ni da hankali na ta mutu" takaici ya hana Khaalif magana ya fice fuuuuu yayi gaba kamar me shirin tashi sama. Zazzafar iska ABU ya furzar tareda zabga tagumi yana roƙon mafita a gurin Allah. Khaalif yana dawowa gida yayi sa'a Mama bata nan sai Aisha ita kaɗai tana kicin tana girki ya shigo, kai tsaye can ya nufa dan yasan a can ne ze same ta. Tana aikin tana ƴan waƙe waƙe tana juyowa babu zato tayi tozali dashi haka kawai taji gabanta ya faɗi, ta zaro ido tana kallonsa ganin yadda fuskar sa take ba annuri tsoro ne yafara kafa sansani gareta, da kyar ta haɗiyi yawu tana son tayi magana amma takasa sai ido. Takawa yayi har zuwa gabanta yana fuskantar ta cikin tsananin ɓacin rai yace, "rayuwar da kika zaɓa mana kenan??? bakya tunanin faruwar wani mummunan abu akan mu?? kuskure ne haɗa hamayya tsakani na da ɗan uwa na dan bazan iya janye masa ba kuma bazan saurarawa kowa ba, shin da gaske ne kina son sa ko kuma shima yaudarar sa kike kamar yadda kike yaudarata???" Kauda kai tayi daga kallonsa cikin ƙarfin hali tace, "eh ina son sa kamar yadda kakejin kana sona haka nakejin ina sonsa, abu wanda ba na zahiri ba shine wanda akeyin tambaya amma ai yanzu a zahiri ka gani ko?" a hasale yace, "haka ma kike gaya min, ya kike so nayi ne wai?? kinsan bazan iya jurar rashin ki ba bakya tsoron nayi abunda ze sa kowa ya rasa ko kuma nayi abunda dole sai na mallake ki???" Kai tsaye tace, "bana tsoron ko ɗaya idan kayi abunda ka mallake ni hakan zeyi min daɗi dan na samu wanda nake so idan kayi abunda kowa ze rasa shima zanji daɗin kasancewar ban auri ɗayan ku ba hakan ze fi wa kowa kwanciyar hankali, halama Khaalif ba kai bane na asalin Khaalif ɗina ka zama wani daban ba wanda na sani ba, kai me haƙura ne da komai ka barwa yayanka ko da ba ni ba amma kake irin haka" Hannun ta ya finciko har sai da tafaɗa jikinsa ya haɗe duka hannayen nata ya riƙe gamm cikin zafin rai yace, "bazanji komai ba ko me kika gaya min amma abunda nake so ki barwa kanki sani babu wani ɗan da aka haifa kuma zaki aure shi ki kasance cikin kwanciyar hankali bayan ni, daa nake me haƙuri da juriya amma yanzu ta ƙarfi kin canja ni ko me na koma kece sila kinsa na haukace, tabbas yanzu ba Khaalif ɗin daa bane na yanzu ba ya yafiya kuma baya ragawa duk wanda ya hau hanyarsa ko me na aikata kisa a ranki kece sila haka ko me na zama kece kika maidani hakan, ba ina faɗan komai bane da sunan wasa da gaske nake kuma zan aikata" kuka me ƙarfi ne ya ƙwace mata ta shiga rusa shi kamar tashin hankali, ta rasa wace irin masifa ce take damunta a rayuwa shin meye maganin matsalarta??? waye wanda ze kawo mata ɗauki a rayuwarta?? a cikin su waye ze zama katangar ƙarfe tsakanin ta da damuwar da ta taso da ita???, girgiza masa kai ta shigayi alamar "aa" tana son cewa wani abu amma ta gaza magana dole ta cigaba da kukan gami da kwantar da kanta akan ƙirjinsa saboda mugun riƙon da yayi mata. Ido ya zuba mata kamar wanda yake wani dogon nazari, sai a lokacin kukan nata yafara ratsa zuciyarsa tareda jefashi cikin wani yanayi, cikin sanyi yace, "Ayeeesha kiyi haƙuri ba laifi na bane sonki ne ya zautar dani na rasa makama abun sunyi min yawa har yasa nafara wasu banzayen tunani bana son rasa ki shiyasa nake tunanin yin komai domin na sameki, ki dena kukan nan bana so" Ɗagowa tayi da kyar ta kalleshi sannan taƙara maida kai ta kwantar, cikin ƙunar zuci tace, "ka rage son zuciya Khaalif, Allah ya jarrabe ni da son mutum uku kai kuma ni kaɗai kake so bana son ɓacin ran ku ku duka ina son saku farin ciki na taƙaitaccen lokacin da ya rage min kun sani zan auri Saif amma kai baka ta kowa son zuciyarka shine kan gaba komai sai dai ya kasance kaine, Khaalif ina son Yusuf Ina Son ABU kuma ina Sonka kuma zan auri Saif bazance komai ba dan ba ni nayiwa kaina wannan zaɓin ba Allah ne ya tsara haka a jikin Allon rubuta abu me afkuwa a rayuwata har ma da wanda be faru ba da wanda yafaru a baya duk daga Allah ne kuma gareshi nake roƙon sassauci kuma inaji a jikina a kwana a tashi dole wannan damuwar zata gushe nima zan zama mutum kamar kowa, zuciyata tana gaya min a cikin ku ɗaya ze zamo silar zamana mutum, amma bansan kowaye ba kayi min uzuri karka illata min rayuwa Khaalif" Taƙarasa maganar tana ƙara fashewa da wani sabon kukan. Dumm.. dummm. zuciyarsa ta shiga bugawa ɗaya bayan ɗaya, girgiza kai yayi gami da lumshe idanunsa har cikin ransa yakejin kukan nata kamar ya tarwatsa masa zuciya , jimmm yayi kafin ya buɗe idanun nasa da yanzu sun gama canja kamanni ya ɗora akanta, hannunsa yasa ya shiga share mata hawayen wasu suna ƙara zubowa, cikin wata rikitacciyar murya yace, "Ayeesha kukan ki barazana yake ga rayuwata, ki saurari bugun zuciyata shirin tarwatsewa take saboda kukan ki ki tausayawa Khaalif ɗinki ki dena kuka Ayeeshahh.." a hankali tafara sassauta kukan har tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya sai da tafara nutsuwa sannan tafara jin yadda zuciyarsa take tsalle fakare tayi tana saurara kafin ta ɗago idanunta ta jefa cikin nasa, a hankali ta zame daga jikinsa ta nufi ɗaki ta nemi guri ta zauna. da ido ya rakata har ta ɓacewa ganinsa sannan ya wuce yabar gidan. Tin tana sa ran jin wata magana ko wani alamu daga Saifu har ta dena sai dai tasa a ranta kawai yayi shiru ne badan ya tsorata ba sai dan yaƙara ɓullowa ta wani gurin da ze mata illa. Saif yaga canji da canje canje sosai a gurin Khaalif har ta kai ga ko maganar arziƙi baya yi masa kuma tin daga ranar da ya gaya masa maganar ABU dan haka ya yanke hukuncin tambayar sa dalili. Suna zaune Khaalif yana danne danne shi kuma yana cin abinci, kallonsa yayi ya kauda kai sannan yace, "Khaalif in ɗan tambaye ka mana" Yace, "inaji" Saif yace, "meke faruwa tsakanin mu ko kuma nace tsakaninka da Aisha tabbas akwai abunda ban sani ba ko kuma nace nagagara ganewa, na shiga ruɗani sosai" Murmushi Khaalif yayi kafin yace, "hmmm hakane kam abun kaico ne wannan wai yaya na ne wanda yake son Ayeeshah, inajin zafin abun sosai yanai min ƙuna " Da mamaki yace, "kana nufin wannan yayanka ne?" Yace, " na jini ma kuwa be min adalci ba ko kaɗan ina shi ina Ayeeesha banda sharrin zuci??" Jinjina kai Saifu yayi tareda cewa, "yayan ka ne????" Khaalif Mohammad ya gyaɗa masa kai. Murmushi me tarin manufofi ya saki kafin yace, "ka ja masa kunne akanta dan babu abunda bazan aikata ba, tsira da mutuncinsa shine fita harkar Aisha abarta da mijinta" Shima Khaalif murmushin yayi wanda babu wanda yasan asalin sa sai Allah, yace, "ko baka faɗa ba dama ni meyin ruwa da tsaki ne akan hakan don nima ta shafeni" maganar tayi masa bau shiyasa ya tambaye shi akan yayi masa fashin baƙi akan manufarta amma sai ya share zancen hakan yasa Saifu ya ƙudurewa kansa shiga da fita domin ja musu layi gaba ɗaya dan ya lura akwai wani abu a tattare da Khaalif. *INDO CE..* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 16* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* tin ƙarfe takwas na safiya Mama tace Sayid ya tashe ta amma taƙi tashi sai dai tayi juyi ta koma, misalin ƙarfe tara da rabi kuwa ya shigo da gudun sa a tsaye ya tsaya a kanta yafara kiran sunan ta a hankali dan idan yayi da ƙarfi yasan kwanan zancen zata iya jan ƙafarsa ma ta taɗe shi ya faɗi ta cigaba da baccinta, Juya masa baya tayi tana ƙifil ƙifil da ido, yasan ta farka dan haka yace, "ai kuwa ga babansu yaya Saifu nan sun zo kuma ranar aure za'a saka" Rasssss ƙirjinta ya buga a kwancen da take ko ƙoƙarin motsawa batayi ba sai zazzaro ido da tayi, a take jikinta yayi sanyi ƙalau, babu shakka wannan shine sakamakon da Saifu yake son yimata dama tasani ba wai wani abune yasa yayi shiru ba dan ya iya hannunsa ne" Sayid kuwa komawa yayi gefe yafara karkaɗa ƙugu yana zasu sha biki, sai da ta fashe da kuka sannan yayi saurin yin kanta yana tambayar lafiyarta sai dai ba amsa, jikinsa yayi sanyi ƙalau haka ya fice sakato sakato. Abba kuwa yana shigowa ya sanarwa Mama cewar ansa lokacin auren Aisha da Saifu kuma wata biyu aka saka dan haka yana da kyau duk abunda zatayi na shirye shirye tafara kar lokaci ya ƙure. Mama kuwa kawai cewa tayi, "Allah ya tabbatar da alkairi" Wani zazzafan zazzaɓi ne ya lulluɓe ta ta ƙundume a cikin bargo sai dai saurarar karakainar da suke kawai take dan kuwa ganin su ma takaici ze ƙara mata. Saif cikin gadara ya ɗaga wayarsa ya kira ABU yana ɗauka yace, "sannu fa dama kiran ka nayi na sanar da kai sa ranar aure na da Aisha ina fatan zaka halatta amma idan da lafiya" ABU ya murmusa sannan yace, " faɗar bikin ba bikin bane, na tayaka murna, halartar biki kuma cikin sauƙi zan halarta dan ta iya yuwuwa ma nine angon" maganar bata yiwa Saifu daɗi ba sam ya ɗauka zeji ya tashi hankalinsa ko kuma yaji ya karaya, a ƙufule yace, " wai kai me kake taƙama dashi ne?? ka fiye jin kai dan kana taƙamar tana sonka ai kuma ta riga tayi maka nisa" ABU yace, "nama fika kusanci da ita dan haka bar cewa taimin nisa, yadda kake ɗan uwanta haka nima nake ɗan uwanta banbancin shine a koda yaushe zukatanmu suna tareda juna ne kuma kai baka isa ka shiga tsakanin su ba ƙaryar ka ma ƙarya take ka gane?? kuma daga nan har numfashi na ƙarshe bazan cire rai daga gareta ba, hakan da kayi be sa naji zan fasa sonta ba yanzu ma na fara, kuma kasani koda ka aure ta bazaka taɓa samun nutsuwar ta ba, wannan shine tabbacin tayi maka tazara, Saifu kake ko wa?? kaje ka cigaba da shirin biki Allah ya nuna mana lokacin ya kuma sa alkairi" Yaƙara da cewar, "zan iya kashe wayata ko??" Saif ya dakatar dashi da cewa, "ka tsaya kaji abunda zance maka, kashedi ne kawai ya rage min ina ƙara jaddadada maka ka ajiye batun Aisha sunan ta ma banason ji a bakin ka, kallo da ido ma karka sa ran zaka ƙara kallonta da idanun ka sai nayi maka babban tsakani da ita ba kai kaɗai ba har maci amanar ƙanin naka yana zaune dani yana cin dunduniya ta to duk zaku gane waye Saifu wallahi sai kunyi nadamar sanin Aisha a rayuwarku" Daga haka yayi ƙilll da wayar, ABU ya zubawa wayar ido haka kawai hankalinsa yaƙi kwanciya bayan firgicin auren da za'a yiwa Aisha da Saif sai yaji duk hankalinsa yabar jikinsa. tana nan kwance kiran Khaalif ya shigo wayarta jikinta na rawa ta ɗauka tareda yin sallama cikin rawar baki. Da kaji muryarsa zata tabbatar maka ba a nutsuwarsa yake, da kyar yace, "Saif yayi min illa Aisha bazaki temake ni ba??? indai Saifu ya aureki to bazan iya zama ba gwara na shiga duniya da na zauna na mutu dan baƙin ciki, kuma duk laifin ki ne Ayeesha kina sona kina son yayana ga Jose meyesa bazaki gayawa Abba kinada zaɓi ba?? hakane fa ya cutar dani kin kasa ceton rayuwata daga gararin duniya meyesa bazaki manta da kowa ki aureni ba? meze hana ki jarraba hakan ko a yanzu??" Numfashi taja kafin tace, "Khaalif Moh... a cikin ku bansan WA NAKE SO ba nakasa banbancewa, bayan haka ma ban kasance bauɗaɗɗiya daga maganar iyayenta ba zaɓin mahaifina ne dan haka zan aureshi muyi haƙuri da duk yadda Allah ya ƙaddara mana mu karɓa hannu bibbiyu insha Allah wata rana zamu ga RIBAR HAƘURI rashinsa ba abunda yake amfana mana sai ɓacin rai mu jure har zuwa lokacin da ta Allah zata kasance" Khaaalif yace, "banso jin wannan maganganun daga bakin ki ba Ayeeshah dama idan bamu haƙura ba babu yadda zamuyi amma fa dole na nunawa Saif taƙadarancin da yayi mana nashi kaɗan ne" Cikin kuka tace, "Khaalif indai son gaskiya kake min bana so wata rigimar tsakanin ka da Saifu ka zuba masa ido kawai ina tsoron makircin sa, ka manta da batunsa kawai dan Allah" Yace, "zan jarraba hakan" Daga haka ya katse kiran yanajin kamar kansa zeyi tsawa saboda rugugin da yake. Gaba ɗaya ya tsani kowa bama kamar ɗan uwansa da yake ganin shine wanda yafi shige masa gaba. Wayarsa ya ɗauka ya kirashi suka yiwa juna tatasss kowa yaji a jikinsa, dan shima ABU idan aka taɓa shi ba haƙuri yau Khaalif ya kaishi ƙarshe dan haka sukayi kaca kaca. Cikin kwana biyu Aisha ta manta da Saifu ta cigaba da gudanar da rayuwarta ba tareda la'akari da ta kusa aurensa ba. hakan kuwa ba Ƙaramin zafafa Saif yaƙara yi ba yaso ace ta hukuntu da hakan da yayi mata sai yaga ko a jikinta, Hakan yasa yayi mugun ƙuduri kuma yafara shirin aiwatarwa. Jose. Tattare takardun da suke gabansa yayi ya watsar gefe ya ɗauki ƙafa ya ɗora akan ƙaramin tebur ɗin gabansa ajiyar zuciya ya sauke tareda lumshe ido. Muryar Umma ce ta katse masa tunanin sa, "Jose baka da lafiya fa" Da mamaki yace, "meke faruwa Umma?" Umma tace, "cikin aikin ka yanzu akwai kuskure da kuskunda an sanar dani cewa ka zama mashiririci baka abunda ya kamata " Yace, "Umma waye ya gaya miki wannan zancen??" Tace, " yaron ka Haruna shine ya sanar dani hakan kuma har anfara tunanin ɗaukar mataki akan ka, banason hakan fa Jose kai da na sani me ƙoƙari da maida hankali akan aiki ya akai yanzu ka koma haka??" Nazari ya ɗanyi kafin yace, "nima ina da irin wannan tambayoyin Umma akwai wanda yake bibiyar rayuwa ta akwai wanda yake son ganin na kasa kuma duk inda taje tazo an samu bara-gurbi a cikn yaran kusa dani, to waye Umma??" Umma ta taɓe baki kafin tace, "babu wasu ƴan zille zille da zakai min bansan waye ba dan a yaran naka ma mutum nawa kawai na sani ?? ba dai zakace Haruna bane Jose dan shi yaron kirki ne" Jinjina kai kawai yayi ba tareda yaƙara magana ba, amma abun yana ɗaure masa kai sosai duk ranar da ya haɗu da Aisha sai yaji ance wani abun, besan ya akai ma mutane suka san yafara soyayya ba mutanen ma kuma ba abokansa ko dangin sa ba gaba ɗaya abokan aikinsa sun san labarin komai yanzu duk motsin sa a idon duniya yake sai yaji ance ai yau kayi kaza to waye wannan da yake bambaɗar da sirrin sa kuwa??, Batun shiririta kuwa ya yarda dan kuwa yanzu duk wani aiki ma baya son jin ko labarin sa komai nashi yafi karkata ga Ashshah. Yau ya shirya tsaf ya nufi gidan su ABU sai dai zuwan beyi masa daɗi ba saboda ya tarar da abokin nasa ba'a yanayi me daɗi ba jikinsa ne yayi sanyi salam, yau babu surutu ko hirar ma babu, Matsawa yayi kusa dashi kafin yace, "meke faruwa ne wai??" ABU yace, "ba komai bane" Girgiza kai Jose yayi yace, " kuji wani bagwaren zance, ba haka kake ba fa, da an kalle ka za'a san baka cikin yanayi me daɗi da alamu ma kayi kuka amma ahakan kake cewa ba komai?? ai baze yuwu ba" ABU yace, "idan na faɗa ma babu abunda hakan ze amfana maka sai ɓacin rai" Jose yace, "na yarda komai yawan ɓacin ran da zanyi naji na kuma yarda, karka manta fa irin amintar dake tsakanin mu ABU babu wani abunda ze taso yasaka kuka kuma kayi tunanin be shafeni ba ka faɗa min duk da ni ba kowa bane amma ta yuwu ko akwai temakon da zan iya yi maka" ABU ya ɗanyi murmushin ƙarfin hali sannan yace, "Khaalif ya dena ganin mutunci na ya raina ni duk saboda soyayya ta haɗamu guri ɗaya, yakasa tausaya min nima nakasa tausaya masa saboda muna jin duk bazamu iya ba, ina tsoron rasa Eeeahu Jose bansan yadda zanyi ha, kuma Khaalif ya gaya min akwai wani da take so bayan mu kuma narasa ko waye, kayi haƙuri fa abokina tin farko nakasa gaya maka ina son Aishan Mama sai yanzu da komai yaƙare min " Wani mugun suman zaune Jose yayi sai ido da baki da ya buɗe yana kallon ABU wanda yake maganar sa da gaskiya kuma da yaƙini, zuciyarsa ta shiga tsalle a take zuffa tafara tsatstsafo masa jikinsa yayi sanyi ƙalau tin daga tsakiyar ka har tafin ƙafa Da mamaki gami da firgici ABU yace, "Abokina?? meke faruwa??? naga kamar abun yazo maka ba daɗi" Har yanzu Jose yakasa magana sai dai wasu zafafan hawaye da suka ciko idonsa suke ƙoƙarin samun damar gangarowa. ABU da zuwa yanzu ya gama diriricewa yace, "Jose kar dai kaima kana son Eeeshu?? kayi magana dan Allah ka faɗa min gaskiya abokina kar ka ɓoye min komai" a hankali ya gyaɗa masa kai alamar hakane, Zumbur ABU ya tashi daga zauna yafara zarya a cikin ɗakin da kyar da kyar yake jan numfashi yana saukewa saboda nauyin da zuciyarsa tayi kamar an ɗora masa dutse. Ƙasa Jose yayi da kai tareda lumshe ido hakan ya bawa hawayen damar zubowa, cikin sanyi da kuma sarewa yace, "ka yafe min saboda naso wadda kake so ABU tabbas da nasan kana son Aisha da na hani kaina daga sa rai gareta da na danni zuciyata da haƙura da tunanin ta, A RASHIN SANI son Aisha yayi min mugun kamu ABU kuma nima nakasa gaya maka, ka dena damuwa haka, babu amfanin amintar dake tsakanin mu indai har bazan iya haƙura da farin cikina na samar da naka ba, ina maka fatan nasara a cikin su, na bar maka Aisha abokina ina so ka haɗa da SOYAYYATA da taka guri ɗaya domin nema mata farin ciki, akwai ƙalu bale a rayuwarta ina so ka zamo mata katanga da duk wata damuwa abokina dan Allah kar kace min aa ka amince da buƙata ta ni nayi niyya kuma na janye maka domin a cikin mutane ukun da Aisha take so ina ɗaya daga cikin su" Dawowa ABU yayi kusa dashi ya zauna girgiza kai yayi gami da cewa, "aa karka jefa kanka cikin matsala saboda ni ni na haƙura Jose" Jose ya karyar da kai sannan yace, "uhmm dama nasan sai kayi gardama, daga yau ka rubuta ka ajiye babu ni babu Aisha nayi maka alƙawarin fita harkarta zan manta da ita nashimfiɗa sabuwar rayuwa, bayan haka ko meye yafaru dani kasa a ranka daga Allah ne ba daga kai ko ni ko Aisha ba, ina maka fatan nasara kuma ina so ya kasance kaine Gwarzon su iya haka zakai min shine abunda zanji daɗi, daga yau kuma anan gurin labarin ya sauya daga RINTSIN SO ya koma SADAUKARWAR SO na sadaukar da soyayyata gareka abokina" Kuka ne ya kufcewa ABU wanda yakasa banbance ko na mene, Jose beyi ƙoƙarin dakatar dashi ba dan kuwa shima hawaye yake, sai bayan ɗan wani lokaci sannan ABU yace, "nagode abokina bansan da wane baki zan iya gode maka ba Allah ne kawai ze baka ladan abunda kai min" Jose yace, "karka ƙara sa damuwa a lamarin ka dan damuwa tana kawo matsaltsalu gare mu kayi ƙoƙarin kare lafiyar ka" Be bari yayi wani zance ba yafara ƙoƙarin jansa da surutu, sun ɗan daɗe suna hira kafin Jose ya tashi tafiya gida, Allah ne kawai yasan iya raɗaɗi da azabar da yake ciki amma duk ya danne saboda ƙarfafawa abokinsa guiwa sai da yafara tafiya yaƙara tabbatarwa kansa a hargitse yake, azababben ciwon da kansa yake masa ƙara ƙaruwa yake ga jiri jiri da yake ɗibarsa ga tarin ƙuncin da yakeji a zuciyarsa, lokacin har yafara ganin duhu duhu, sauri sauri yake dan ya isa gida kamar daga sama yaga wani me mashin ya shiga gabansa, da sauri yayi gefe da motar shima me mashin ɗin yayi gefen da yayi, me mashin ɗin yafara yin wasa da hankalinsa har ya ida ruɗar dashi, garin ƙoƙarin kauce masa yana dawowa ɗaya hannun sukayi wata kyakkyawar arangama da wani me tifar ɗebo yashi, ji kake kantsam, Kafin mutane su farga tini me tifar ya gudu dan dama gefe yasa masa ya daka, asalin abunda ya haddasa hakan ma kuɗi aka biyasu daga shi har me mashin ɗin da yafara wasa da hankalinsa har ta kai ga haka. *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 17* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* waya direban tifar ya cira ya turawa Haruna yaron Jose kira ya sanar dashi ya aiwatar da abunda ya sa shi. Haruna ya murmusa cikin farin ciki da jindaɗi shima ya kira Saif basu wani magantu ba Haruna ya faɗa masa abunda yafaru duk shirin da sukayi yayi. Shima Saif Yaji daɗin hakan sosai lokaci guda yaji hankalinsa ya kwanta komai ya lafa ya rage wata matsalar. Haruna ya kira Ogansa bayan ya ɗaga yace, "Sai Oga kafi ƙarfin kayi sai dai ayi maka, kana daga gefe ka haɗa gwaramar da aka kawar maka da maƙiyin ka cikin sauƙi, Saifu yasa an haɗawa Jose haɗari a yanzu haka ba lallai yana raye ba ko ya rayu ba lallai yayi tsawon rai ba, shima ya kashe tashi matsalar muma ya kashe mana, na tsani ganin Jose shine ya hana ni zama babba kawai aka ɗorashi da tini fa nine ogan sa amma yayi min kaka gida dan haka ya wajabta akaina na kawar dashi na hau kan matsayi na" Oga yayi wata shegiyar dariya kafin yace, "bansan wane irin kyauta zan maka ba saboda wannan kyakkyawan albushir naka, yanzu na samu damar da zanyi komai kaima ka samu taka damar, amfanin Saif yaƙare garemu ina tunanin, dan haka ka fita harkarsa kawai tin kafin ya gano asalin karatun" Haruna yace, "Shikenan Oga yadda kace haka za ai babu me yi maka musu Oga" Da haka sukayi sallama dukansu suna farin cikin an kawar musu da Jose. Saif Murmushi ya saki na gayya kafin yace, "saura kai ABU na sallami Jose ɗin yanzu nasan dole yayi nakastuwar da da kanta ma zatace bata son sa, to irin wannan hukuncin ne ya dace da ABU Khaalif kuwa a haka zan cigaba da tafiyar dashi har zuwa lokacin da ze faɗa ramin" Aisha tana zaune suna ɗan hira da Mama jefi jefi dan kuwa nutsuwarta duk ta tafi gurin tunane tunane, kiran Rookha ne ya shigo ta tashi ta nufi ɗaki tana amsa sallamar da Rookha take mata, cikin sanyi suka gama gaisawa kafin Rookha tace, "Aisha na haƙura da soyayyar ABU na gaji da azabtuwar da nake na haƙura, ba ta ni yake ba hankalin sa baya kaina be damu da Tarin yawan son da nake masa ba, narasa ya zanyi dashi sai a yanzu na yanke hukuncin haƙura dashi dan ba ni yake so ba" Taƙarasa maganar tana kuka. Kan kujera Aisha ta zauna cikin kaɗuwa tace, "Rookha??" Katse ta tayi da cewa, "Aisha ABU ke yake so meyesa zaki tambaye ni bayan kin fini sanin halin da muke ciki gaba ɗaya koda na aureshi bazan samu kwanciyar hankali ba dan haka na haƙura, kawai abunda banji daɗi ba da kika ɓoye min tsakanin ku tin farko, ni kaina na sani ABU baya sona nice nafara son sa kuma be taɓa gaya min yana sona ba dan haka bana ganin laifin ki, kuma shima bashi da laifi nice babbar me laifin da nafara son sa ba tareda bincike ko nazari akan abunda ze je yazo ba, ina miki fatan alkairi a rayuwa Aisha nima ina yiwa kaina fatan samun mafi alkairi ga rayuwata" daga haka ta tsinke kiran, rintse ido Aisha tayi da ƙarfi gami da cije gefen leɓenta wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska, tabbas bata kyautawa kanta ba sai dai babu yadda ta iya dan ba yin kanta bane. Cikin tashin hankali mutane suka taru a wajen suka fara ƙoƙarin nema masa temakon gaggawa kai tsaye asibiti suka wuce dashi, baya motsi kamar babu rai a jikinsa kuma gashi babu inda yayi ko ƙwartane sai dai kamar gawa haka yake. Dandanan likitoci suka taru akansa suka fara ƙoƙarin bashi temako sai dai basu ga alamun ze tashi ba gashi dai zuciyar sa tana bugawa. Ƙoƙarin neman wani nasa da za'a sanarwa aka farayi cikin sa'a sukayi arangama da lambar Mu'Allim ƙaninsa kai tsaye suka kirashi suka sanar dashi, shi kuwa be sanarwa kowa ba ya nufi asibitin hankali tashe, karo yayi da Dr Muktar yace masa ya biyo shi ofishin sa dan haka ya bishi. Ruwa ya miƙa masa tareda cewa, "ga ruwa kasha Mu'Allim" "Nagode" kawai ya iya cewa sannan ya ɗan kurɓi ruwan yaƙara bin Dr Muktar da kallon tuhuma, cikin sanyi yace, "Dr yaya na fa?? meke faruwa dashi?" Dr Muktar yace, "aa karka fa wani damu yanzu lafiyarsa tana tareda shi insha Allah dan haka ina son sanar da kai ne ko kuma baka shawara akan cewa kar a sanarwa kowa rashin lafiyarsa kasancewar sa Jami'in sirri" Mu'allim yace, "hakane shiyasa nima ko iyayen mu ban sanarwa ba, ni yanzu ba wannan ne damuwata ba meye ya same shi????" Jinjina kai Dr Muktar yayi kafin yace, "to maganar gaskiya akwai wata ƙudura ta Allah a rayuwar Jose dan kuwa babu abunda ya same shi duk da irin wannan iftila in da ya faɗa amma sai dai ya samu buguwa sosai, yanzu firgicin da nake ciki kawai ace kansa yayi buguwar da ze manta da rayuwarsa ta baya ko kuma ya samu wata illar amma hakan ma Allah ze kiyaye babu abunda ze faru karka damu, amma fa har yanzu ya faɗa suma har yanzu be dawo ba muna nan dai muna ƙara bincike akai domin gano ina ne inda yafi buguwa dan magance matsalar dan haka ina so ka kwantar da hankalin ka" Numfashi Mu'Allim ya sauke sannan yace, "Nagode Dr to amma ya akai ya samu haɗarin ma wai??" Dr yace, "eh to gaskiya ina tunanin sai dai ka nemi yaransa ko kuma abokan aikinsa sai suyi maka bincike domin gano inda bakin zaren yake, amma yanzu karka sanarwa kowa idan ance ina yake ma kawai ka sanar dasu cewa yayi tafiyar gaggawa har dangin ku ma ina tunanin faɗa musu hakan shine mafita" Jinjina kai kawai Mu'Allim yayi yana godewa Allah. Dr yace, "wani hanzari ba gudu ba Mu'Allim maganar gaskiya akwai matsalar zuciya a tattare da ɗan uwan ka, da alamu ya shiga wani abu na firgici da damuwa kafin ya faɗa wannan yanayin yana da damuwa sosai wadda idan abun yazo da matsala ze iya zamo masa ciwon zuciya ma kuma me matuƙar illa, idan an samu lafiyar sa yanzu ƙoƙarin da zaka farayi kenan na yaƙi da damuwarsa " Sosai jikin Mu'allim yayi sanyi ko uffan kasa cewa Dr yayi sai tashi da yayi ya fice. sai washe gari Allah ya bashi ikon farkawa sai dai ba um ba um um sai bin mutane da ido da yakeyi. Mu'allim ne ya kalleshi cikin tausayawa yace, "Yaya Jose meke damunka haka dan Allah" Murmushin ƙarfin hali yayi da kyar yayi magana irin ta marasa lafiya yace, "Umma ta" Mu,allim yace, "zata zo nan ba da daɗewa ba amma ka faɗa min me yafaru da kai" Girgiza kai yayi alamar baze faɗa ba hakan yasa Mu,allim yaja bakinsa ya tsuke dan yasan halin kayan sa. Ba a wani ɓata lokaci me yawa ba Umma ta iso cikin sanyin jiki ta matsa kusa dashi kamar zatayi kuka tace, "ya jikin Jose??" ya gyaɗa kai tareda cewa, "da sauƙi Umma" Tace, "Jose meke damunka ne?? ƙanin ka ya gaya min kana da damuwa menene damuwar??" Girgiza kai yayi kafin yace, "Umma damuwar akan soyayya ne kuma ta wuce tinda na riga na sadaukar da ita wa abokina ABU kuma bana so ku gaya masa banida lafiya dan Allah" Zama Umma tayi a gefen sa da mamaki tace, "kana sane da abunda kake faɗa kuwa?? kana nufin ABU ma yana son Aisha??" Be bata amsa ba sai cewa da yayi , "Umma dan Allah ki kira Mama ki gaya mata banida lafiya" Umma tace, "to saboda me kuma? ka tayar mata da hankali haka kawai ko me??" Yace, "Umma ki gane dan Allah wallahi ina son ganin Aisha ne ganin ƙarshe nake so nayi mata nasan idan kika faɗawa Mama zata zo duba ni" Cikin tausayawa Umma tace, "shikenan Yusuf Allah ya baka lafiya " Yace, "Umma na ma warke fa kawai dama na bugu ne sosai shiyasa duk jikina yake min ciwo ina tunanin fa ƙugu na ya sauka daga kan layi magana ma da kyar nakeyi Umma amma fa duk hakan ba wani abun damuwa bane, ni banso ma na rayu ba naso ace na mutu na bawa wanda basa son ganina sararin duniyar, Allah ne kawai yasan me yake nufi dani da yasa na rayu amma ina ji a jikina na gama ingantacciyar rayuwa wadda zan shiga yanzu bazata kasance me kyau ba" Yaƙarasa maganar yana zubda ƙwalla, shafar kansa Umma tayi cikin sigar rarrashi tace, "be zama lallai abunda zuciya take saƙawa ba shine abunda ze faru ko yake faruwa a zahiriyya bana so ka dinga irin wannan furucin domin baki kaifi gareshi, kayi mana fatan Alkairi domin ko meye ya sameka mu ya shafa ba kai ba, ka dena kukan nan addu'a itace maganin duk wata damuwa da ta sako mu gaba mu fauwala wa Allah lamuran mu shine yafi kowa sanin halin da muke ciki kuma babu wani ɗan adam da ze dauwama cikin baƙim ciki ko ƙunci dole sauƙi ze zo daga Allah, ka cigaba da addu'a karka gaza da yinta domin ba'a gajiya idan kayi kana ganin batai maka amfani tanan ba to zaka ga tayi maka amfani ta inda baka taɓa zato ba bama lallai kasan tayi maka amfanin ba sai kayi dogon tunani, ka dena kuka domin shi kuka alamar rauni ce Kuma ni Yusuf ɗina jarumi ne ba rago ba" Hannunta ya riƙe gam tareda rintse idanunsa da suke masa zafi da kyar ya ƙwaƙulo murmushi ya ɗora akan fuskarsa sannan yace, "Umma na dena kema karki damu kanki kinji Ummata kisa a ranki komai yafaru dani Allah ne ya tsara hakan ga rayuwa ta" Sai a lokacin hawaye suka kwaranyo kan fuskarta tayi saurin zame hannunta ta tashi daga gurin ta juya masa baya cikin muryar da bata fita sosai tace, "ban damu ba Jose ina fatan alkairi gareka a duk inda kake" Daga haka ta fice daga ɗakin dan gudun yin kuka a gabansa. *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 18* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* suna zaune suna kallo itada Sayid suna rigima akan remote wayar Mama tafara ƙara, sakar masa tayi tana cewa, "maza ka cinye idan ka tashi, ni bari na kaiwa Mama waya Allah yasa ma muji ance Anti Zulaihat ce ta haihu" Kafin taƙarasa ya rigata saurin ɗauke wayar yana dariya yace, "da yardar Allah sai satin aurenki zata haihu ni kuma ni zan kai mata wayar kinga anfi ƙarfinki kenan dole ki zauna ki kalli Arewa" Kansa tayi da nufin ƙwatar wayar sai yatashi da gudu yayi waje itama ta taka masa baya, sai da ya riga ya miƙawa Mama sannan ta ƙaraso tana numfarfashi, harara kawai ta zuba masa sannan ta maida hankalinta kan Mama, jin ta zuba salati ne yasa ta zaro ido tana kallonta, tana sauke wayar ta jefa mata tambayar "me yake faruwa?" Mama tace, "oo ikon Allah kenan, kana taka Allah na tashi Yusuf Jose ne yayi haɗari yanzu ma haka suna asibiti abun kamar almara" rarassss zuciyarta ta buga firgitar da tayi tasa ta sarƙe da yawunta ta ƙware aikuwa tafara tari me tsananin zafi takawa tayi da nufin barin gurin amma takasa saboda wani irin tangaɗi da take can ta tsinci kanta a jikin bango lokacin har tafara ganin duhu gashi tarin ba dena shi tayi ba, dishi dishi take iya ji da ganin Sayid da Mama da suka taru akanta ruwa ma Mama ke miƙo mata amma azaba ta hana ta amsa, lokaci ɗaya ta jigata matuƙa ta fita daga hayyacinta idanunta sunyi jajir sun ƙara firfitowa indai kana da zuciyar imani kayi mata kallo ɗaya sai ka tausaya mata, su Mama duk sun ruɗe sun rasa yadda zasuyi gashi da alamu duk maganar ma da sukeyi bata jinsu, ta ɓata lokaci cikin wannan yanayin kafin ta fashe da wani azababben kuka me matuƙar zafi da raɗaɗi" cikin sanyi Mama tace, "Aisha sannu maza kisha ruwa ki dena kukan kinji ko??" Girgiza kai tayi alamar "aa" ƙoƙarin tashi tafarayi Mama ta temaka mata da bi bango ta isa ɗaki wayarta ta ɗauka tafara neman lambarsa amma taji a kashe, wani sabon kukan taƙara buɗewa tashin hankalin ta yaƙara ninkuwa a yanzu bata da buri ko muradin da ya wuce tayi tozali dashi taga halin da yake ciki hankalinta ze fi kwanciya, iya rarrashin duniya anyi amma taƙi dena kuka dan dole suka rabu da ita ta cigaba da yin kayanta har zuwa lokacin da ta gaji ta dena sai sauke huci da ajiyar zuciya, Bata dena kiran lambarsa ba amma duk da hakan taƙi tafiya. Khaalif yana shigowa Mama ta sanar masa zataje asibiti da daddare duba Jose. tinda Aisha taji haka ta fitar da rai da samun nutsuwa koda sunje da ita, daren kuwa yanayi Khaalif yace babu amfanin zuwa da yara asibiti dan haka ta zauna ta kula da gida ita kuwa Mama ta yarda, baƙin ciki kamar ya kasheta ji take inama zata iya ta rufeshi da duka sai dai hakan baze amfana mata komai ba dan abun takaici kuma yace baza a je da ita ba kuma an tafi da Sayid sai kace shi ba yaron bane, duk mutanen da suke wajen ba ta tasu yake ba ido kawai yake bazawa ko ze ganta amma ko me kama da ita be gani ba wata sabuwar damuwar ce taƙara harba masa mashi dandanan yayi ƙasa da ido magana ma ya dena yiwa kowa sai dai alama da kai" Sayid ne ya matso kusa dashi ya miƙa masa takarda tareda cewa, "saƙon Anti Aisha bata samu zuwa ba" cikin sauri ya Karɓa ya warware ta yafara karantawa, " kasancewar Mama baza ta zo da Shahid ba yasa ta barni a gida domin kula dashi amma karka damu gobe zan zo ko ta wane hali ne, idan ban ganka ba bazan iya shan iska me daɗi ba, ina fatan dai jikinka da sauƙi ba kamar yadda nake tunani ba na shiga firgici sosai gashi an hanani ganinka" murmushi ya saki tareda shafar kansa sai a lokacin yaji ɗan sanyi sanyi, "waye ze hanaki ganina ma idan Ba Khaalif ba??" ya jefawa kansa tambaya, wayar Mu'Allim dake kusa dashi ya ɗauka ya tura mata saƙo kamar haka, "tinda kin ɗorawa Mama laifin ba komai Allah ya kaimu goben ina fatan dai kar wani abu ya dameki ina lafiya naji sauƙi sosai koma nace komai yazo da sauƙi kar hakan yasa ki shiga damuwar da zata jawo min matsala kisa a ranki lafiyata ƙalau kuma zaki tabbatar da hakan idan kinzo gobe idan kinga na faɗa ba daidai ba to ina jiran ki hukuntani" Murmushi ta saki da taga saƙon ta mayar masa da amsa da cewa, "duk da ban tabbata ba amma naji daɗin jin hakan ko ba komai nasan saƙo na ya iso gareka Allah ya ƙara maka lafiya" a daren ranar da zazzaɓi ta kwana amma da gari ya waye sai tayi kamar ba ita ba saboda tana son fita kuma idan tabari Mama ta gane bata da lafiya babu yadda za ayi ta barta ta fita" Cikin baƙar doguwar riga ta shirya ta yafa baƙin mayafi batayi kwalliya ba dan dama ba damunta tayi ba kanta a ƙasa tace, "Mama zan tafi aiki Maman Nabia tace nazo" Ido Mama ta zuba mata tana nazartar yanayinta kafin tace, "kuma shine baki faɗa min da wuri ba??" Ƙara yin ƙasa tayi da kai kafin tace, "Mama ai yau ta sanar dani hakan kuma yana da kyau naje dan tace akwai aiki da yawa" Jinjina kai Mama tayi tace, "Allah ya tsare ki kula sosai fa" Ta amsa da "amin" ta fice cikin sauri sauri, tayi babbar sa'a batayi gamo da kowa ba, Lambar Mu'Allim ta nema dan ya sanar da ita inda zataje kai tsaye, ya sanar da ita sun koma gida ma ya rigime musu dole aka taitayeshi akai gida dashi, Ita hakan daɗi yayi mata dan haka ta nufi gidan nasu. cikin sakin fuska Umma ta tare ta bayan sun gaisa ta rakata ɗakin da yake, yana kishingiɗe bakin gado Kiarat tana zaune a ƙasa ƙoƙarin lallaɓa shi take yaci abinci amma yayi banza da ita ko kallonta ma yaƙi yi bare tasa ran ze saurari abincin. Da sallama ta shiga ɗakin kanta a ƙasa Kiyarat ta amsa cikin fara'a tace, "ga Anti ga Anti zo kisa baki ko ze ci abincin nan yanzu Yaya Jose yafi yara murɗewa wallahi yanzu baya son cin abinci" Fuskarta ɗauke da murmushi tace, "Kiyarat sannu da ƙoƙari ai kinyi ma idan da nice ni zan cinye abincin na cewa Umma yacinye tinda ba yaro bane" Kiarat tayi dariya tareda cewa, "ai kuwa wallahi kin kawo shawara da alamu sai yasha duka ma ze dawo dai-dai" Ido Aisha ta zaro tana cewa, "laa ila Kiarat nifa da wasa nake haba ke kam yanzu ai kamar jariri haka yake sai da rarrashi amma me yakawo zancen duka?? har kinsa ma na tsorata" Kiarat ta kwashe da dariya tayi hanyar waje tana cewa, "Anti Aisha kece fa kika fara kawo aidiyar" fitar da tayi ne ya bata damar ƙarasawa kusa dashi ido ta zuba masa cikin tausayawa tace, "Jose?? ya jikinka" Tattausan murmushi ya sakar mata tareda cewa, "naji sauƙi sosai ki zauna mana" Zaman tayi a gefensa tana ƙara binsa da ido zatayi magana yayi saurin katse ta da cewa, "ina tunanin ki sai ga ki kinzo da wuri ma ba kamar yadda nayi tunani ba yanzu Kiarat yar raini take cewa na ma dena tunanin ki ba zaki zo yanzu ba" Ƴar dariya tayi kafin tace, "ai Kiarat akwai ta da son wasa ooh kenan? abunda ta faɗa maka ne yasa ka ƙi cin abinci??" murmushi yayi yace, "ba ni kaɗai ne nake buƙatar abincin ba ai kema kina buƙatan dan nasan baki ci komai ba tinda kika tashi" Cikin zaro ido tace, "kaii? ya akai ka sani" Shiru ya ɗanyi yana kallonta sannan yace, "nasan hakan ƙaramin aiki ne gareki to yanzu bismillah zauna ki ci ko nayi miki ɗura" Turo baki tayi gaba kafin tace, "aa gaskiya nifa dubiya nazo kuma sai na ɓuge da cin abincin mara lafiya to ba dani ba, ka zauna ka ci naka kawai" Girgiza kai yayi yace, " nima kuwa bazanci ba" Miƙewa tayi ta zubo masa abincin ta dawo ta zauna ta wani haɗe fuska kamar gaske a dake tace, "idan bazaka iya ci da kanka ba buɗe bakin" "iyee?? zarra zaki min??" Tace, "eh ai naga alamun hakan" Murmusawa yayi gami da lumshe ido sannan yace, "tinda na ganki ma sai naji na ƙoshi" Zare masa ido tayi tareda cewa, "wai wasa nake maka?? maza ka karɓa ka ci ko kuma na tashi nai tafiyata" Da sauri yace, "aa zanci" Miƙa masa tayi ya karɓa yafara ci yana ɓata rai kamar me cin magani, ba wani da yawa ya ci ba ya ajiye ya janyo ruwa ya ɗan kurɓa sannan yayi wurgi da robar. Kallonsa tayi baki a sake ta buɗe baki zatayi magana yayi sauri ɗora hannunsa kan nata cikin wani irin salo me ɗauke wutar kai, hakan yasa ta haɗiye maganar ta ƙara warara masa ido, kallon ido cikin ido suka shiga yiwa juna har na tsawon lokaci be gaji ba sai da tafara neman nutsuwarta ta rasa sannan tayi saurin sauke kallonta ƙasa gami da lumshe ido ta sauke ƴar ajiyar zuciya" Cikin wata sanyayyar murya yace, "Ashshah nayi miki laifi fa, ba tareda na sanar dake ba na barwa amini na soyayyarki, kinsan alfarmar da nake so kiyi min??" Girgiza kai tayi cikin sanyin da jikinta yayi. ɗan cije leɓensa yayi saboda wani irin zugi da yaji zuciyarsa tanayi, dannewa yayi ta yadda bazata gane ba yace, "dani da ABU duk abu ɗaya ne ina so ki ninka masa son da kike masa ki haɗa da nawa hakan ne kawai ze sani farin ciki a koda yaushe, kar kiji babu daɗi ko kuma ki fahimci hakan abai-bai Abubakar ya fini buƙatar ki Ashshah yana sonki so me tsanani wannan ne karo na farko da yake son wani abu kuma yake sa ran samu ina son ganin farin cikinsa kuma kece wannan farin cikin nasa dan Allah kar kice min aa" Tinda yafara maganar take kallonsa har ya kai ƙarshe, murmushin da takasa gane na farin ciki ne ko baƙin ciki ya suɓuce mata, tace, "nayi farin ciki kasancewar ka jajirtaccen aboki kuma na ƙwarai, naji daɗi da kayi hakan domin farin cikin abokin ka bazan taɓa so matsala ta shiga tsakanin ku saboda ni ba ka tseratar dani daga wannan tafarkin ina maka godiya Jose, amma abunda yake damuna shine aurena da Saif lokaci koda yaushe ƙara zuwa yake kasan me ya rage yanzu? be wuce sati biyu ba ina cikin matuƙar damuwa Jo amma babu yadda na iya dole na na aureshi" Taƙarasa maganar tana kuka kashirɓan. Duk yadda yake daurewa yana cijewa sai da hawayensa suka samu damar zubowa, ya rasa ma ta ina ze fara rarrashinta gashi kukan take da gaske sai yaji zuciyarsa tana ƙara ƙonuwa dan kuwa ya tabbatar kukan nata yana da alaƙa da abubuwa da yawa ba iya maganar ce ta kawo shi ba tausayinta yaƙara ɗarsuwa a ransa zuciyarsa taƙara yin rauni, janyo ta yayi ya rungumeta tsam a jikinsa yana ɗan bubbugar bayanta alamun rarrashi. Cikin sanyi yace, "kiyi shiru Ashsha dan Allah kiyi haƙuri akan kuskuren da nayi miki bada son raina nayi hakan ba ba kuma dan bana sonki bane bazan iya so wa kaina abunda bazan iya so wa ɗan uwa na ba ni me haƙura da komai ne na barwa ABU koda hakan ze jawo silar mutuwata dan shi wani tsagi ne na rayuwata, kukan nan naki yana ƙona zuciyata sosai dan Allah ki dena" Tana so ta dena ɗin amma takasa saboda ya riga ya gama cin ƙarfinta sai da kyar ta samu ta rage ƙarfinsa amma duk da haka bata dena ba. share nasa hawayen yayi yana ƙoƙarin yin magana muryar Abi ta katse shi "wacece wannan kuma Jose??" Sunkuyar da kai yayi yana ɗan murmushi a shagwaɓe yace, "Abi harna ɗanji kunya" Abi yace, "na shigo ne da nufin ganinka amma na ganka tareda wata dole na dasa alamar tambaya amma kai komai sai ka saka shi da wasa da alama sunan kakannin ka gareni ko??" ƴar dariya yayi yace, "Aisha ce ƴar gidan Ɗan Gaske" Jinjina kai yayi yace, " to meye alaƙarka da ita kuma??" Yace, "ƙanwata ce fa Abi" zeyi magana Umma ta katse shi da cewa, "ƴar ƙanwata ce Aisha kenan bayan alaƙa ta jini ma akwai alaƙar soyayya tsakanin su" Da mamaki Abi yace, "amma meyesa baku sanar dani ba?? da kun faɗa min ai da abun bazeyi girma haka ba ma zanje na samu Ɗan Gasken muyi magana" *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 19* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Umma tace, "baka nan ne shiyasa baka sani ba amma ai yanzu komai ya wuce dan ya riga ya haƙura saboda ɗan uwansa yana sonta" Da kallo Abi ya bishi cikin mamaki da kuma tausayawa, ƙasa yayi da kai cikin dauriya yace, "Abi kasan waye Abubakar a wajen Yusuf, nayi hakan kawai dan samuwar farin cikinsa ni ɗan gata ne wanda ya taso tareda iyayensa shi kuwa ABU be san daɗin su ba ni me yin ƙoƙari ne dan samar masa da nutsuwa Abi zan ɗauki ko wace irin kasada ce akansa" Jinjina kai Abi yayi kafin yace, "barakallah Jose Allah yayi muku albarka baki ɗaya Allah ya ɗorar da kai akan kyakkyawar zuciyar nan taka" Umma ta amsa da "amin" Abi yace, "kukan me takeyi ne ko laifi kayi mata??" Girgiza kai yayi yana murmushi yace, "aa Abi kukan ne kamar wasa ta ɗauke shi ko Ashshah??" ya faɗa yana kallonta, cigaba yayi da cewa, "Ashshah ga mahaifina ku gaisa" Sai da tayi da gaske sannan ta iya tsayar da kukan da kyar ta gaishe shi ya amsa cikin fara'a da sakin fuska. Umma tace, "ka ci abincin kuwa??" Yace, "eh Umma naci da yawa ma kuwa ta zuba min" Murmusawa tayi tareda cewa, "bari na baku guri ko?" Kai kawai ya gyaɗa lokacin ma tini tayi nisa a hanyar fita daga ɗakin dama Abi suna gama gaisawa ya fice. Kallonta yayi kafin yace, "kuka fa baya maganin komai sai kawo ciwon kai bazanji daɗi ba idan hakan ta kasance" Murmushin ƙarfin hali tayi tace, "na dena karka damu" Miƙewa tayi tana cewa, "Jo zan tafi Allah ya ƙara lafiya" Ya "amsa da amin yana ƙoƙarin tashi" Mukullin mota ya bawa Mu'Allim yace ya kaita inda zataje ba musu ya karɓa yayi gaba su kuma suka jera tare har ya rakata ta shiga mota sai da suka tafi sannan ya koma cikin gida kai tsaye ɗaki ya nufa a ɗakin ma sai da ya rufe ƙofa sannan ya koma ya zauna, tafukan hannun sa duka biyun yasa ya rufe fuskarsa, nanfa damuwa tace gani nan wani irin raɗaɗi zuciyarsa takeyi wanda yakejin inama yayi kuka ko ze ji sauƙi amma kukan ya gagara ya rasa yadda zeyi yaji sanyi" Sai yamma sannan ta koma gida bata wani daɗe da dawowa ba wayarta tafara tsuwwa tana ɗauka taga kiran Saif ɗagawa tayi gami da yin sallama. ya amsa Cikin fara'a sai bayan sun gaisa yace, "ina kikaje ne yau??" Tace, "aiki mana" Yace, "ok da kyau me da me kika Ɗinka mana yau??" a ƙagauce tace, "aikin zanin gado ne dani amma ko abu ɗaya kasa Ɗinkawa nayi saboda banajin daɗi Sosai" yace, "kai haba to meyesa?" Tace, "da alamun an taɓa wani sashi na rayuwata ne" Ƴar dariya yayi kafin yace, "gaskiya ne dole kiji a jikinki wani sashi naka ai abu ne me girma, a adai-daita sahu kikaje??" Ɗan murmusawa tayi dan kuwa tasan kwanan zancen tambaya ɗaya ce amma ya tsaya kwalo kwalo, a gatsale tace, "kasan dai na iya tuƙa mota ai" dariya yayi yace, "ba fa cewa nayi ki gaya min magana ba, nasan baki iya ba ai amma kin biya ta wani gurin ko?" Kafin ya gama rufe baki tace, "ƙwarai kuwa Ya Jo ɗina ne ba lafiya shine naje duba shi akwai damuwa ne??" Yace, "oh wanda yayi haɗari ko?? Allah sarki be mutu ba?" Tace, "tukunna kwanakin basu ƙare ba lokacin shan iska beyi ba" Ganin kamar ta tsargu da wani abun yasa yace, "ai naga motar ta mammole ne da yawa idan mutum ya ganta ze zata na ciki baze rayuwa ba shiyasa" Ƙwafa tayi iya cikin bakinta sannan tace, "Allah yayi dai da sauran kwanansa Allah sarki dama wani zubin yadda muka so ba haka muke samu ba ai yama ji sauƙi dangargar abunsa" Takaici kamar ya kashe shi ganin zata ƙara ɗora masa wata jarfar yasa yayi saurin cewa sai anjima yayi maza ya kashe wayar. Ƙwafa tayi tareda cewa, "baƙin azzalumi ai Allah ya fika" ABU Kamar da wasa yarafara jin bacci sun gama waya kenan da Jose ya ajiyeta gefe ya kwanta, be daɗe yana baccin ba ya farka yana buɗe idonsa abun mamakin sai yaga baya ganin komai sai duhu, mutsika idon yayi sosai sannan yaƙara waro su dan ya tabbatar ya buɗe sun ko kuwa dama basu buɗu bane har yanzu dai duhun yake gani kuma ba duhun dare ba duhu na gaske tinda lokacin ma ba dare bane rana ce, "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" itace kalmar da ya furta tareda dafe ƙirjinsa saboda yadda gudun zuciyarsa ya ninku, Abul'Abbas ya fara ƙwalawa kira ya shigo da sauri yana amsawa tareda cewa, "yaya gani nan waye ya taba ka" Cikin lalube irin na makaho yafara neman inda Abul Abbas yake, ganin haka yasa Abul Abbas ya matso a fitgice yana cewa, "meke faruwa yaya??" ABU yace, "ba komai Abul kawai na dena gani ne bana ganinka" Wata kyakkyawar razana Abul Abbas yayi cikin tsananin firgici ya zuba masa ido a warwaje sai da yayi ƴan sakanni a haka kafin ya iya magana cikin kuka yace, "yaya Umman mu ce ko?? ta makanta ka taji daɗi yaya wallahi bazan yafe mata ba nasan ba kowa bane itace yaya" Fashewa yayi da kuka me zafi tareda kifa kansa akan kafaɗar ɗan uwan nasa. hannu ABU ya ɗora akansa yana hawaye cikin sigar rarrashi yace, "ba Umma bace ƙanina kar kayi saurin zarge ta ka dinga kyautata mata zato a koda yaushe" Cikin kuka yace, "me kayi musu?? baka shiga haƙƙin kowa ba yaya me ka tare musu da zasu nakasta ka??" cikin daurewa yace, "Abbas kowa ƙaddarar sa tana zane a tafin hannun sa da ita yake cin abinci yake shan ruwa yake komai ma duk da ita be zama lallai sai ka tarewa wani abu ba sannan Allah ze jarrabe ka karka yarda da cewar wani ne ya aika hakan gareni Allah ne ya ɗoramin ana jarabtar mumini ko dan a gwada imaninsa Abbas karka damu komai ze shuɗe kamar ba'a yi ba" Shiru Abul Abbas yayi yana sharar ƙwalla yakasa cewa komai. ABU yace, "bana son tayarwa Jose hankali Abul Abbas kar ka bari ya tsinkayi labarin a yanzu kabari sai nan gaba" Gyaɗa kai kawai ya iyayi dan kuwa bakinsa ma yayi nauyin da baze iya magana ba har yanzu be yarda ba Umman su ce ta mayar masa da ɗan uwa makaho ba" Jose duk yadda yake son yayewa kansa damuwa yakasa kullum ƙara ninkuwa take ga wani irin zafi da zuciyarsa takeyi koda yaushe a ƙuntace yake gaba ɗaya ya fita daga hayyacin sa, baze iya jurar zaman gidan su ba dan haka ya tattara ya koma gidan sa wanda shi kaɗai ne babu wanda ze dameshi dan yanzu gaba ɗaya baya sauraron kowa, Umma ce dama take ƙoƙarin sa shi magana ko tace zata tilasta masa ya ci abinci shi kuma duk wannan baya gabansa, haka ya tare shi kaɗai sai dai yayi ta ƴan make maken sa babu wanda yasan halin da yake ciki. Khaalif ne ya shigo cikin sanyin jiki ya zauna bayan sun gaisa da Mama yake gaya mata abunda ya faru da ABU Umma ta sa salati. Aisha kuwa zumbur tayi ta miƙe tafara baya baya tana kokawa da numfashin ta gaba ɗaya hankalinta yabar jikinta lokaci ɗaya kafin su farga ta zube a wajen a sume. Mama ta nufi kanta da gudu tana faɗin "Hasbunallahu wani imalwakil" Khaalif kuwa mamakin suman da tayi yasa shima ya daskare yakasa motsawa sai ido da ya zuba musu jikinsa har rawa yake ba gaira ba dalili. Mama tace, "Sayid kawo min ruwa da sauri" Ruwan ya ɗebo ya kawo mata ta karɓa ta yayyafa mata, fizgar numfashi tayi gami da firgita lokaci ɗaya jikinta ya hau kakkarwa tafara rawar sanyi, da kyar ta iya cewa, "Mama ki kaini ɗaki dan Allah" Mama da mamaki ya gama mamayarta da kyar ta miƙewa ta temaka mata ta kaita ɗakin, bayan ta zauna ta dafe kai ta zuba tagumi hannu bibbiyu Mama ta kalle ta cikin sanyi tace, "Aisha meke damun ki ne, Jose yayi haɗari kin ƙware ABU kuma ya makance kin sume nakasa gane alaƙar da ke tsakanin ku amma firgicin yayi yawa na daɗe ina ganin damuwa iri iri a tattare dake amma idan anyi magana sai kice ba komai to duk wannan me yake nufi" Ba tareda ta kalle ta ba tace, "Mama zazzaɓi nakeji" Rausayar da kai Mama tayi gami da cewa, "toh Allah ya baki lafiya ya kuma kawo ƙarshen abun, shi kuma ABU Allah ya kawo masa ɗauki" Bata ce komai dan kuwa bata san abunda zata furta ba... *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 21* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* ƴar ajiyar zuciya ya sauke kafin yace, "nagode da kuwalarki Eeeshu kuma ko a yanzu nagodewa Allah dan wani yana son matsayin da nake dashi a gurinki amma be samu ba ni kuma na same shi, bana so ki damu kanki kawai kisa a ranki Allah beyi ke matata bace dan a wannan halin da nake ciki bazan yarda na aureki ba koda na samu dama domin hakan cutarwa ne gareki bazan zalumce ki ba Eeeshu, duk da kwanakin auren ki kullum ƙara zuwa suke amma inaji a jikina auren ki da Saif kamar ba me yuwuwa bane, to dan Allah idan kina da dama Eeeshu ki auri Junior kiyi haƙuri da soyayyata ki ajiyeta a gefe" Share ƙwalla tayi kafin tace, "nasan dama zakayi wannan tunanin, to nima bana son hakan indai na samu wannan damar babu abunda ze hanani aurenka dan ka zama Makaho karkayi wannan tunanin da gaskiya nake son ba dan wani abun ba bazan iya yin hakan ba kayi haƙuri dan Allah" Yace, "Eeeshu Khaalif Mohammad fa ƙanina ne ina ganin dani dashi duk abu ɗaya ne ke fa yarinya ce Eeeshu so kike rayuwar ki ta lalace wajen kula dani?? ni hakan beyi min ba gaskiya a yanzu babban abunda zakiyi min shine ki aure ƙanina tin kafin ya fara barin kan hanya Eeeshu yanzu Khaalif ya gigita ba kamar daa ba ki amsa masa zaki aureshi ko ze nutsu, ba wani abu ne yasa nace hakan ba fa kawai saboda shi ne mu biyu ne kawai mahaifiyar mu ta haifa ina ganin na fishi haƙuri da jurewa zan iya jurar rasa ki amma shi gani nake baze iya ɗauka ba a yanzu ma rayuwa tareda ni ƙalu bale ne a gareki, kiyi haƙuri idan na takura miki" ... Jikinta yayi sanyi ƙalau tayi shiru tana tunani na ɗan wani lokaci kafin ta sauke numfashi sannan tace, "shikenan na amince da hakan kaima Allah ya baka lafiya" yayi murmushi ya amsa da "amin " ya cigaba da cewa, "bana son ki damu fa" Murmushin ƙarfin hali tayi kafin tace, "shikenan bazan damu ba ka kwantar da hankalin ka" ganin kamar tana shirin fara kuka yasa yayi mata sallama. tana ajiye wayar kuwa ta fashe da kuka. tin Mama tana tashin hankalinta saboda halin da ta ganta a ciki har ta dena dan abun ya fara ɓata mata rai shegiyar gardama tayi mata yawa tambayar duniya bazata faɗi abunda yake damunta ba. Abba kuwa yana dawowa da daddare ya tambaya yanzu baya ganin warginta ina take Mama ta gaya masa bata da lafiya, sai da yayiwa Mama faɗa akan rashin kula da lafiya sannan yace suje ganin likita. Bayan Dr ya gama dubata ya kalle ta cikin tausayawa yace, "kinsan kuwa abunda yake damunki??" Girgiza kai tayi alamar "aa" Yace, "kina da damuwar da take neman jaza miki ciwon zuciya duk da irin wannan ƙuruciyar taki" Da sauri tace, "nasan hakan amma banaso Abbana ya sani dan Allah" Da mamaki yace, "hakan kenan shine zaɓin ki?? kinfi so ki zauna da cuta?" Tace, "eh wannan hukuncin na yankewa kaina, ba'a son raina ma nazo ganin likita ba burina kawai ko me ze faru yafaru" Jinjina kai yayi yace, "gaskiya na daɗe banga mutum me tsauri irin haka ba, wani hanzari ba gudu ba Madam kamar nasanki" Tace, "ba ni bace gaskiya ni baka sanni ba" Ya ɗan murmusa kafin yace, "Yusuf Jose, wato Yusuf Usman Husain jami'in SS kinsan shi ba?" gyaɗa kai tayi tana kallonsa cikin mamaki, ɗan murmushi yayi yace, "shi Abokina ne ba mamaki dan na faɗi sunan sa haka kai tsaye naga kamar abun ya taɓa ki, to a gurinsa na sanki na saba ganin hoton ki akan wayarsa" lumshe ido tayi ta buɗe sannan tace, "ya lafiyarsa??" Yace, "bazan ɓoye miki ba domin shi kansa kece sirrin sa, maganar gaskiya Madam Jose baya cikin yanayi me daɗi, bayan rabuwar ku damuwa ta tilasta masa yin abunda ba halinsa ba kullum damuwar sa bata raguwa sai ƙaruwa da take har ya kasance yafara shan giya da nufin rage damuwa sai dai abunda ya kasa fahimta bazata amfane shi da komai ba gashi yanzu abin ya haɗe masa ga maye ga kuma damuwar hakan yasa duk ya fita daga hayyacinsa jiya aka bashi lasisin dakatarwa a aikinsa duk da cewar shi mutum ne me ƙoƙari haka suka rufe ido suka dakatar dashi" Ƙasa tayi da kai tana sharar ƙwalla gurin yayi shiru na wani lokaci kafin tace, "kenan?? yanzu babu yadda za'ayi Jo ya dawo dai-dai???" DR yace, "gaskiya kece kawai maganin damuwarsa banajin ze ɗau saiti hakan nan har sai idan yana jin ɗumin ki ina nufin idan kuna tare kullum ze ganki kuma zaki dinga tunasar dashi, to ina ganin wannan hanyarce kawai za'a bita Jose ya dawo hayyacinsa" Miƙewa tayi tareda cewa, "ka cewa Abba taifod ne yake damuna" yace, "to madam" duk da tana shan magungunan da Dr ya haɗa mata hakan besa ta dena damuwar ba sai ma abunda yayi gaba domin kuwa yanzu ƙiris ya rage a ɗaura mata aure da Saif. Umma ce zaune ta zuba tagumi hannu biyu Mu'Allim yana gefenta shima da kallo ɗaya zaka san yana cikin damuwa, ɗaya gefen kuwa Yaya Khalil ne tareda Abi sai Kiarat da ta zuba tagumi da alamu ma ita kuka tasha. Jin shirun yayi yawa yasa Abi yace, "gaskiya lamarin Yusuf ƙara girmama yake, zanje na samu Ɗan Gaske muyi maslaha gaskiya a maida maganar auren Aisha kan Yusuf" Umma tace, "shi mutum ne me tsatstsauran ra'ayi wanda ba'a sauya shi ko a sa shi yayi abunda ba shi yayi niyya ba, bana jin ze amince da buƙatar mu bare yanzu Yusuf ba mutumin kirki bane babu wanda ze so aurawa ƴarsa mashayin giya" Shigowarsa kenan gidan yaji suna zancen abunda Umma ta faɗa shine ya burgeshi dan haka ya fara dariya yana tangaɗi ya ƙarasa ya zauna kusa da Mu'allim cikin murya irin ta maye yace, "Umma ce kawai take iya fahimtar komai, Abi bana son ma maganar auren nan wallahi dan ni yanzu bana sonta kawai Abokina ne yake sonta kuma shi zakaje ka nemawa aurenta idan kace ni zaka aurawa ita ai kayi son kai, ni nabarwa abokina ita halak malak, nifa yanzu nazama ɗan iska itama Ashshah nasan yanzu ta tsane ni kamar yadda mutane suke min kallon banza" Shiru gurin yayi kafin Mu"allim yace, "Yaya Jose ya kamata kaje kayi bacci fa" Yace, "wayo zakai min ai na gano ka so kake na tafi sai Abi yaje yace a auramin Ashshah to bana so" Abi yayi murmushi me cike da tausayawa yace, "ai tinda baka so nima bana so babu me yimaka dole ka kwantar da hankalin ka" Yace, "yauwa Abi shiyasa nake sonka" Kowa ya kasa cewa cikal sai zancen zuci shi kuwa ya ɓalle sogar surutansa kuma baya kalami uku ƙwarara be sako Aisha a ciki ba. Saif ya lura akwai abunda Khaalif Mohammad yake shirin yi dan haka shima yayi nasa shirin ɗaurin auren a lisaafin da ake kai yazo a ranar talata hakan yasa ake tunanin ɗagawa zuwa wani satin shi kuwa yayi tsalle ya dire yace a ɗaura shi a ranar jumu'ar da zata zo yayi sa'a babu wanda yace aa. haka aka cigaba da shirye shiryen biki ba tareda sun san halinda da amarya take ciki ba duk da sunsan tana cikin damuwa kasancewar basu san meye ke ƙunshe a ranta ba yasa babu wanda ya damu da bin takanta. ABU kullum be fasa addu'a ba kuma ya sa ayi masa saukokin alƙur'ani me girma hakan yasa yakejin sauƙi cikin duk abunda yake damunsa sai dai har yanzu be samu lafiyar idon ba. Aisha tana zaune Aunty Maimuna ta kawo mata wani abu a kofi tareda cewa, " karɓi wannan ki shanye" Yadda tayi maganar ba tareda wasa ba sai da ya bawa Aisha dariya ta ɗan murmusa sannan tace ajiye min. Bata tsaya jayayya ba ta ajiye mata tayi nata guri. Kallon kofin tayi taƙara sakin murmushi a zahiri tace, "su kuma ana ta kai suna ta kaya sai kace ance musu zaman auren zanje yi, aikin banza yanzu mutane duk basu da tausayi wallahi, zaki ga na shanye ne wallahi zubar dashi zanyi" Bata gama surutan ba wayarta ta katseta, sai da zuciyarta ta buga ganin Kiran Khaalif Mohammad dan yanzu tsoronsa takeji, jiki na rawa ta amsa dan idan bata ɗauka ɗin ba ma wata rigimar ce, Cikin sanyi tace, "Assalamu alaikum Khaalif??" *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 20* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* tashi Mama tayi ta bar ɗakin cikin sanyin jiki abun yayi mata yawa ga ɗan da yanzu bashida kowa sai Allah sai su ya makance ga itama Aisha koda yaushe ƙara fita take daga hayyacin ta. ABU Umma ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama cikin rawar baki tace, "ɗan nan wannan wane irin baƙin labari ne??" Abul Abbas ne ya katse ta da cewa, "Umma ai kinfi kowa sani tinda ke kika aikata" Kafin ya gama rife baki tace, "na shiga uku na lalace Abul ni kuma?? to wallahi tallahi ban aikata ba wallahi ba ni bace" Rai ɓace Abul Abbas yace, "dama ai babu yadda za ayi ki amsa Umma bansan meye abunda bawan Allahn nan ya tare miki ba a rayuwa duk irin izayar da kikai masa hakan be isa ba sai kin nakasta shi wace irin mummunar zuciya ce wannan Umma?? tabbas badan kin haife ne ba da na ɗauki tsatstsauran mataki akanki wanda bama shi kaɗai ba babu wanda zaki iya cutarwa ko ba mutum bane, amma babu komai duniya ce yadda kika yiwa ɗan wani wata rana za a yiwa naki ko meye ya faru akanmu karkiyi tunanin ƙaddara ce kece kika jawo mana kuma Allah zeyi mana sakayya" Yaƙarasa maganar cikin kukan baƙin ciki. Fashewa tayi da kuka harda ɗora hannu aka tana jujjuya kai tareda cewa, "Wallahil azimu ban aikata ba Abubakari ka yafe min dan Allah wallahi nasan na cutar da kai amma nasan ba nice na makanta ka ba wallahi dan Allah karku ƙullace ni ƴaƴan nan amma ko meye ma baƙin halina shine ya jawo min gashi yau na taka sahun da ba nawa ba wayyo Allah ni Sakina yau naga ta kaina" cikin zafi Abul Abbas ya ɗago zeyi magana ABU yayi saurin dakatar dashi da cewa, "ya isa haka Abbasu, ka manta cewa ita ɗin mahaifiyar ka ce?? bance kar na ƙara jin wannan kalamin daga bakinka ba??" Cikin kuka yace, "yaya ina baƙin cikin kasancewa ta ɗa gareta dama na mutu tin kafin ta haife ni tabbas da na huta da takaicin duniya dani da kai da ƙannen mu fa duk ƴaƴa ne amma ta fifita mu akanka meye banbancin mu?? ta zalumce ka duk hakan be isa ba, badan kanada dogon kwana ba na tabbata da tini ta kashe ka amma ka tsalle duk wannan siraɗin rayuwar har ka girma ka zama wani hakan be sa ta ƙyale ka ba taga kafi ƙarfin ta shine ta maida kai haka ita ba abun yarda bace nasan zata aikata fin hakan ma" Da sauri tace, "Abubakar Abbas ku gafarce ni dan Allah wallahi kuskuren baya ne yake bibiya ta amma yanzu ban aikata masa haka ba Abbas wallahi ba ni bace amma nasan bazaku yarda ba saboda banida hali me kyau na zalumci kaina " Cikin dauriya ABU yace, "Umma zafin zuci ne yasa Abbas yake irin wannan maganar amma ba da gaske yake ba, karki damu kanki ni nasan bazaki aikata min hakan ba ki dena kuka dan Allah" Cikin hanzari tace, "nagode ɗan nan ko a yanzu kai min rana wallahi ni azzaluma ce na cuci kaina nima Ban taɓa tunani faruwar hakan ba abun ya girgizani wallahi bani bace ka yafe min Abubakar nasan duniya ma bazata barni ba bare lahira ka yafe min ɗan nan" Share hawayen sa yayi tareda jinjina kai yace, "Umma ki yarda na fa yafe miki kuma nasan ba kece ba banaso ki cigaba da damuwa koda Abbas ze ƙara cewa wani abun" Tace, "wallahi zan jure ko meye ze faɗa dan nasan nayi, wannan ne kawai ban aikata ba kuma nayi baƙin ciki nayi baƙar nadama ABU in Allah ya yarda nabar mugun halina yanzu zan gyara rayuwata na dena zalumtar ka" Aisha abun kamar da wasa tana jin zazzaɓi kamar ba na gaske ba sai ya zama na gasken kuka take na fitar hankali yayin da jikinta yake tsuma yayi zafi ɗau ga wani mugun ciwon kai da ya tirsaso ta yake mata barazana, har wunin ranar yafaru ya ƙare bata cewa kowa uffan ba sai aikin kuka Abinci kuwa ko tunaninsa batayi bare tasa ran zata yau Mama ta shirya zuwa dubashi dan taga halin da yake ciki babu yadda Aisha batayi ba akan su tafi tare amma taƙi Khaalif kuwa dama shine ɗan hannunta bata son laifinsa haka ko me yafaɗa hawa take ta zauna musamman idan akan Aisha ne dan haka ta murzawa idonta toka tace baza taje da ita ba dole ta haƙura. Tinda ta shiga ɗaki ta kulle ta nemi guri ta zauna ta haɗe kai da guiwa bata da aikin da ya wuce tayi kuka ta share ƙwallar sai tunane tunane da sukai mata yawa ga tarin damuwa, ita kanta a yanzu tasan bata da lafiya" Tana zaune ta ji sallamar Khaalif takaici ne yaƙara lulluɓe ta, kai tsaye ɗakin ya nufa har ya ya isa inda take bata ɗago ba da sunan tasan ya shigo, ƙare mata kallo yayi kafin ya murmusa sannan yace, "Ayeesha kiyi haƙuri fa nakasa jurar hakan ne shiyasa nace Mama kar taje dake" cikin ɓacin rai tace, "me kuma zaka gaya min?? bana son jin komai dan Allah kayi shiru da bakin ka" Karyar da kai yayi kafin yace, "meye na ɓacin rai kuma bayan kece kika jawo faruwar hakan, kin sani ina kishin ki sosai kuma ina sonki so mara misaltuwa amma baki damu dani ba kan yadda kika damu dasu mamakin suman da kikai saboda ABU ya makance sai da ya hanani bacci fa, dan na hanaki zuwa duba Jose shikenan sai da kowa ya ɗanɗana ɓacin rai saboda kema ranki ya ɓaci kuma duk da hakan sai da kikaje, duk meye hakan yake nufi?? bakya sona ko Ayeeshah??" Kuka ta shiga razgawa cike da tausayin kanta ji take inama zata iya ta rufeshi da duka ranta in yayi dubu ya gama ɓaci ta rasa meyesa baya tausayinta baya sassauta mata kodan mugun halin da take ciki" Ɗan murmushi yayi yace, "bana jindaɗin kukan nan naki amma ke kuma shine zaɓin ki, ki dena wahalar da kanki kawai kisa a ranki nine mijin da zaki aura bayan ni kuma ko waye to fa babu zaman lafiya bare kwanciyar hankali wannan kawai nake so ki dinga tunawa dan haka ki dena sa kanki a damuwa, tin yanzu gashi kin gani da idon ki nasan dai da hankalin ki bazaki auri makaho ba haka kuma bazaki auri mahaukaci kuma ɗan shaye-shaye ba" A matuƙar razane ta ɗago tana kallon sa da idanunta da suka gama fita daga hayyacin su cikin tsananin firgici take masa kallon neman ƙarin bayani. Gira ya ɗaga mata tareda cewa, "ƙwarai nasan zakiji abun a bauɗe, nasan kinsan dai Saif yana ta'ammali da ƙwayoyi to ba wannan ne abun damuwar ba domin nasan ba son Saif kike ba, wanda kika so ɗin kuma kike masa kallon me hankali shine yanzu ya zama mahaukaci kuma ya zama mashayin giya kinsan waye ?? Jose kenan yanzu hakan ma baya gidan su ya zama gantali daɗi aikinsa ma suna gab da korar sa saboda ya haukace ba'a hayyacinsa yake ba gashi kuma ɗayan ya makance yanzu kinga babu wanda ya rage miki sai Khaalif Moh... wanda bakyaso ɗin" lokaci ɗaya jikinta yaƙara rikicewa tsoro da razani suka bayyano, cikin rawar baki tace, "Jose ɗina ya haukace kake cewa?? kasan kuwa me kake faɗe Moh... anya kuwa ba kaine ka haukace ba?? a hayyacin ka kake kuwa??" ƙasa yayi da kai yana murmushi yace, "Ayeeesha Ayeesha wallahi kina burgeni ina dai kinji abunda na faɗa?? to ki tabbatar dan kinsan bazan miki ƙarya ba" da sauri tace, "indai hakane kuwa a yanzu banida zaɓin da ya wuce su biyun ka dena tunani dan sun zama haka zan guje su tausayin su yasa nake jin kamar nayi hauka tabbas da ana auren maza biyu da na auri Yusuf da Abubakar ban zamo irin matan da suke gudun masoyan su ba dan wata jarrabawa ta faɗa kansu, bazan taɓa dena son su ba idan kuwa kunyi wannan tunanin to kun yaudari kanku zan cigaba da neman zaɓin Allah kuma indai ya kasance ɗayan su ne mijina to zan aureshi ba tareda nayi duba da halin da suke ciki ba, nayiwa kaina tabbacin ABU ya makance ne ta dalilin soyayya ta a wannan tafarkin ne aka nakastar dashi kuma Allah zeyi mana sakayya duk wanda ya zalumce mu Allah baze barshi ba Khaalif ka bar bin son zuciyarka kaji tausayina ka tausayawa ɗan uwanka son zuciya baya kai mutum hanya me kyau bana son ka faɗa wani yanayi saboda son zuciyar ka Khaalif ka dena Khaalif ɗina karka zama mutumin banza dan Allah" Ta ƙarasa maganar tana ƙara fashewa da wani sabon kukan. Ido ya zuba mata har wani lokaci sannan ya tashi ya nufi hanyar fita har ya kusa ƙofa ya juyo yace, "ban zamo yadda kike tunani ba amma dama nayi miki kashedi karki bari na rikiɗa na zama wani daban ba Khaalif ɗinki ba Ayeeesha yanzu banajin tausayin kowa akanki maganar gaskiya idona ya rufe ina ganin ma nafi ɗan uwana makanta saboda sonki, kuma bazan karaya ba Allah shine yasan daidai tayuwu duk abunda kike tunani ba lallai ya yuwu ba kwatsam zaki iya wayar gari kiga na zama mijinki ni kuma wannan shine mafarki na kuma shine cikar muradin Khaalif Mohammad" Daga haka yayi waje yabarta da sakakken baki tana kallonsa maganganunsa suka shiga yimata yawo a tunanin ta, kamar mahaukaciya haka takejin ta saboda yadda duk tunanin ta ya wargatse zuciyarta take ƙuna da raɗaɗi, ga ƙululun baƙin ciki da yayi mata tsaye a maƙoshi, tabbas badan tasan hukuncin wanda ya kashe kansa ba kuma tana tsoron hukuncin da itama ta shiga sahun su ta kashe kanta ta huta da zafin duniya, yanzu ta tabbatar bata shigo duniyar a sa'a" Bata haƙura da tambayar Mama akan zataje duba ABU ba amma maganganun Khaalif sun sa Mama tayi kunnen ta shegu da ita. yau tana zaune bayan ta gama kuka ta gaji wayarta tafara ƙara, cikin sauri ta ɗauka gami da yin sallama, ABU ya amsa sannan ya cigaba da cewa, "kina lafiya dai ko?" Wani gwauron numfashi ta sauke sannan ta gyaɗa kai kamar yana ganinta takasa cewa uffan. Cigaba yayi da cewa, "Eeeshu kiyi magana mana dan Allah ABU ne ko baki ganeni bane?? na matsu naji lafiyarki dan bana cikin nutsuwata har yanzu" Sai da ta haɗiyi wani ƙullutu sannan tace, "Ya ABU lafiya ta ba itace abun damuwa ba kana cikin irin wannan halin karka damu kanka akaina dan Allah bana so ka sawa kanka wata damuwar bayan taka, ina lafiya kuma ina tareda kai a koda yaushe duk da an hanani ganinka amma addu'a ta nasan tana bibiyarka Allah yasan da kai kuma ze yaye maka karkayi tunanin a haka zaka dauwama duk me son ganin kukan ka in Allah ya yarda sai ka gagareshi" *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 22* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* murmushi yayi tareda cewa, "ya akai kike wani saurin kiran sunana??" Ƙasa tayi da kai sannan tace, "ba komai" Yace, "Amarya kenan, shikenan nima ba wani abu zance miki ba wata dama ce kawai zan baki shiyasa na kiraki idan kina so fa amma" Tace, "ina jinka Allah yasa zata amsu" Murmusawa yayi yace, "wannan kuma abunda ya shafe ki ne, kina sona ko??" Tace, "eh" Yace, "idan har da gaske ne to ki shirya gobe zamu bar gida, amma fa sai kin amince, babu amfanin ki zauna kina ɓata lokacin ki a banza kinsan ko maza sun ƙare bazaki zauna da Saif ba ko?? to ina ganin tin kafin a ɗaura auren kawai ki bi ni" Shiru tayi tana tunani kafin tace, "kayi haƙuri Khaalif Moh.. ina sonka amma bazan iya yin abunda kake so ba a wannan ƙadamin, bazan iya saɓawa iyaye na akan son zuciyar mu ba, shi Abba babu ruwansa ko me na aikata laifin ze ƙare ne akan Mama ta batasan irin wainar da muke soyawa ba batasan halin da muke ciki ba haka laifin da mukayi ze rataya a wuyanta bazan iya zalimtar ta ba Khaalif Moh.. ba wai dan bana sonka bane ya kamata ka fahimce ni dan Allah" Taƙarasa magana tana shirin fashewa da kuka. Jinjina kai yayi sannan yace, "zaɓi me kyau Ayeeshah kije kiyi auren ki keda Saif sai kuma ku jirayi abunda ze biyo baya" tace, "ko a yanzu jiran hukuncin ka nake Khaalif na yarda da ko menene amma bazanyi wannan kasadar ba zan auri Saif" Yace, "bance fa karki aureshi ba Allah ya sanya alkairi, kuma ki fito yanzun nan ina jiranki idan baki zo ba kuma kinsan kwanan zancen" Kafin ya gama magana ta miƙe jikinta har rawa yake cikin sauri tace, "gani nan zuwa"... Murmusawa yayi sannan ya ajiye wayar. Surar kofin da Anti Maimuna ta kawo mata tayi ta kundume a cikin hijab dinta sannan tayo waje dashi tana fakar idonsa ta zubar dashi tayi wurgi da kofin sannan ta cigaba da tafiya, tana fita ƙofar gidan tayi katari dashi ya tsira mata ido kamar me shirin haɗiye ta da sauri tayi ƙasa da kai tana wasa da yatsunta. Daf da ita ya matso sannan yace, "ga mota can je ki shiga salin alin" Bata tsaya gardama ba ta nufi inda motar take gidan gaba ya buɗe mata tayi masa banza ta shiga baya, murmusawa yayi sannan ya shiga yafara janta, tin batayi magana ba har tagaji tace, "wai ina zaka kaini Khaalif??" Yace, "kasshh irinku ne bakwa cin ribar zance baki bari kin gani ba ai kika fara tambaya, ba komai bane ba fa kawai irin yadda Jose yakeyi nima shi zanyi yau ko shi kaɗaine yake da matsayin ɗaukarki a mota? kodan shi ɗan masu dashi ne?? ni kuwa kinga iyaye na ma sun mutu" Cikin sanyi tace, "ba haka bane ba fa ka fahimce ni mana Khaalif ka rufamin asiri karka cutar dani ko kayi abunda zaka ƙuntaci iyaye na, ka mayar dani gida dan Allah" Kai tsaye yace, "Ayeeshah aurefa zakiyi zaki auri wani ta yaya ni kuma hankalina ze kwanta " Shiru tayi masa har sai da yaje inda yake son tsayawa sannan ya tsayar da motar ya fito ya koma baya, cikin zaro ido take kallonsa yayin da bugun zuciyarta yake ƙara ƙaruwa baki na rawa ta kira sunan sa "Khaalif!!!!!" Cikin wata narkakkiyar murya ya amsa mata da cewa, "Ayeesha nah!!!!" Saurin sauke kanta tayi zuwa ƙasa har cikin ranta tsoro ya dirar mata tayi shiru tana tsammanin abunda ze ce, Gefe guda kuwa wutar so gami da tausayinsa sai azalzalarta suke" Tana cikin tunani taji yasa hannu ya ɗago haɓarta yana cewa, "kin kasa haɗa ido dani fa Ayeeshah" Sai a lokacin ta ware idanunta a cikin nasa lokaci ɗaya taƙara lulawa duniyar tunani wanda ya jawo zubar hawayenta, lallai ta yarda duniyar abai-bai tazo mata dama haka rayuwa take idan Allah yaso sai ya wadataka da komai sai kuma ya tauyeka ta wani gurin ko kuma ka samu silar ƙuntata a dalilin da baka zata ba to ita tata ƙaddarar ɗa namiji ne bata da wani ciwo ko damuwar da ta wuce namiji shine yafara nakasta ta sannan basu haƙura ba kowa ya ɗora idonsa akanta farmaki yake kaiwa. Iskar da ya hura mata ne yasa taja numfashi tareda sauke kallonta ƙasa, cikin sanyi tace, "Khaalif bana so a neme ni a rasani dan Allah mu koma gida yanzu idon kowa akaina yake su kansu sun fara dasa alamar tambaya akaina yanzu basu yarda dani har yanzu hankalin Mamata be kwanta ba da bakinta tafaɗa bazata nutsu ba har sai ta kawar dani daga gabanta, ni kuwa wace irin ƴa ce haka" Ta ƙarasa maganar tana cije baki dan hana kukanta kufcewa. Khaalif ya tsira mata ido na wani lokaci kafin yace, "zamu koma mana" magiya ta shiga zuba masa amma yayi banza da ita daga baya ma sai ya ciri wayarsa ya shiga dannawa yayi banza da lamarinta. Zuwa yanzu tagama kaiwa maƙura musamman da ta duba lokaci taga yadda suka kwashi lokaci me yawa batasan lokacin da ta fashe da kuka ba. Murmusawa yayi gami da kashe wayar tasa ya saka a aljihu sannan ya matso kusa da ita, hannunsa ya jefa cikin tafin hannunta a hankali yace, "ki dena kuka fa Ayeeshah na wannan ba abun zafi bane fa" Ko ta kansa bata bi ba ta cigaba da kuka da iya ƙarfinta, janyota yayi cikin kulawa yayi mata masauki a ƙirjinsa cikin sigar rarrashi ya shiga bubbugar bayanta amma takasa dena kukan, abun yafara hawar masa kai cikin nutsuwa ya kai bakinsa saitin nata ya shiga sumbatar ta cikin wani irin yanayi da ya tsinci kansa a ciki yanayi yana lumshe gami da sauke sassanyar ajiyar zuciya, Aisha kuwa wata wahaltacciyar ajiyar zuciya ta sauke gami da rintse ido tin abun baya mata daɗi har ta saki jikin taƙara lafewa a jikinsa. Sun ɗebi lokaci cikin wannan yanayin kafin ya dakata kallon fuskarta yayi cikin sassanyar murya me sanya nutsuwa yace, "kiyi haƙuri Ayeesha yau nazo miki da baƙon lamari nima ba haka naso ba kawai na tsinci kaina ne cikin wannan halin, meyesa bazaki aureni ba Ayeeshah na???" tinda suka haɗa ido sau ɗaya ta rufe idonta dan in tanada kunya bazata iya ƙara haɗa ido dashi a wannan lokacin ba, ƙoƙarin zamewa tafarayi daga jikinsa amma yaƙi bata damar hakan sai ma cigaba yayi da cewa, "naso a ɗaura min aure dake a ranar jumu'ar nan kafin lokacin da aka sa aurenki da Saif amma ya riga ya tarwatsa duk shiri na da alamun ya gano me nake nufi, amma ba kome za'a haɗu wata rana ai, nidai abu ɗaya nake so kiyi min hankalinmu ya kwanta mu duka" Gyaɗa kai tayi alamar tana sauraronsa, yace, "karki bari Saif ya taɓa min komai a jikinki hakan ne ze sa mu fi nutsuwa bayan haka kuma kinsan hankalina baze iya ɗauka ba" Cikin tausayin kanta tayi saurin amsa masa da, "to amma dan Allah ka maidani gida" yace, "to shikenan ko?" Kai kawai ta iya gyaɗa masa dan lokacin bacci yafara fizgarta kafin yayi wani yunƙuri bacci ya saɓeta hakan yasa ya gyara mata zama don tafi jin daɗin baccin. bayan wasu mintuna kamar da wasa ta farka ta jita a jikin mutum tayi saurin buɗe ido sukayi ido huɗu dashi take duk abunda yafaru ta shiga dawo mata saurin rintse ido tana tana furta "Astagfirullah" cikin sauri ta zame jikinta ta matsa gefe, Shu'umin murmushin nasa yayi kafin yace, "kin tashi kenan??" Kamar zata fashe da kuka tace, "Khaalif meyesa baka maidani gida ba??" Yace, "kin danne ni tayaya zan iya jan motar kinsani dai ko a mafarki bazan iya tashinki a bacci ba" Bata ce masa komai ba dan ta lura neman zance da neman dalili kawai yake. Tin a ƙofar gida Sayid yake sanar da ita sai nemanta ake zuciyarta na dukan tara tara haka ta shiga gidan sai sauke ido ƙasa take gaba ɗaya ita kanta ta tsargu da kanta duk ta kasa sakin jiki musamman idan ta tuna ɓelesin da sukayi sai taji takaici yaƙara kamata, har mamakin yadda Khaalif yayi tasiri akanta take musamman kwanakin nan idan layi ya shata yace kar a tsallaka tofa ta barshi kenan" Aunty Zulaihat ce ta maka mata harara gami da watso mata tambayar "daga ina kike??" Ba tareda ta kallesu ba tace, "daga gidan su Surayya" Anti Maimuna tace, "a layin nan inane inda bamu tambaya ba kuma duk ance bakya nan har gidan su Surayyan" Sayid yayi saurin cewa, "amma dai Mamansu cewa tayi sun tafi wani guri itada Surayya amma bata faɗi inda sukaje ba" sai da ta sauke ajiyar zuciya saboda daɗin maganar Sayid da taji tayi gaba tana cewa, "na rakata haɗo kayan kwalliya ne" Maida hankali sukayi kan Sayid suna tambayarsa dalilin da yasa be gaya musu hakan tin wuri ba kawai yace ya manta ne dole suka ja baki suka tsuke. Tana zaune ta buga tagumi tana abunda ta saba wato tunani Sayid ya shigo ya zauna kusa da ita sai haɗe rai yake, cikin fushi yace, "yanzu Anti Aisha kin kyauta kenan?? kin tafi gantali keda Yaya Khaalif gashi sai nemanki ake ke bakya gudun ɓacin rai ne wai?? keda zaki auri wani ina ke ina wani banda neman fitinar ki" Cikin sanyi tace, "Sayid Khaalif!! ina tsoron fushinsa wallahi" Kai tsaye yace, "fushin nasa na banza? duk Tsananin fushin sa ya kai ya ɓacin ran iyayenki ne??" Tace, "kai Sayid so fa ba ƙarya bane do Allah karka takura min da zancen shashashan Saifun nan dan shi ban ɗauke shi namiji ba ka gane??" Yace, "na dai gaya miki ai kuma gaskiya ce idan kinji ilaiki idan bakiji ba ilaiki" Banza tayi masa sai ma harara da ta bishi da ita taja tsaki. yau ta kasance ranar ɗaurin auren Saif da Aisha gidan ya cika maƙil sai kai kawo akeyi. Tin safiyar Allah take kuka kamar wadda ta rasa iyayenta, Nuriya ce ta miƙo mata wayarta tana cewa, " gashi an kira ki" Karɓa tayi ta duba tana ganin ABU ne tayi saurin karawa a kunne. Cikin farin ciki yace, "Alhamdulillah Eeeshu na samu lafiya" murmushi ne ya buwayi fuskarta ta zaro ido tareda cewa, "Da gaske????" Yace, "da gaske ba da wasa ba haka kawai naga nafara gani nima kaina kamar a mafarki nakeji" saboda farin ciki bakinta yaƙi rufuwa ga murmushi ga hawayen farin ciki duk a lokaci ɗaya, share ƙwallar tayi kafin tace, "nagodewa Allah nikam nayi farin ciki mara misaltuwa tabbas naji daɗi Ya ABU Allah yaƙara maka lafiya ya kare ka da dukkan wani sharri" Ya amsa da "amin" sannan ya cigaba da cewa, "Eeeshu Khaalif Mohammad ya sanar dani yau ne ɗaurin aurenki ina miki fatan alkairi a duk inda kika shiga" Murmushi tayi tace, "nagode sosai" Yayi murmushin farin ciki kafin yace, "Rookha tazo kuwa??" Tace, "nima banji daɗin rashin zuwanta ba amma babu yadda na iya dan kuwa yanzu bata son ganina ko jin labari na ma saboda na rabata da abunda take so" Yace, "Allah sarki ai ba laifin ki bane" Aisha tace, "ka kirata kaji lafiyarta ka sanar mata yanzu ka samu lafiya nasan zatayi farin ciki sosai" Yace, "zanyi ƙoƙarin hakan" Murmushi tayi tace, "sai anjima ko?" Yace, "eh amma dai ina fatan duk abunda Khaalif yayi miki be sa kin dena son sa ba ko??" Lumshe ido tayi sannan tace, "koda kaɗan banji hakan ba" Yace, "nagode Eeeshu sai yanzu na gane wautar da nayi da na tauyewa ɗan uwa na farin cikin sa ban kyauta ba gaskiya banji daɗi ba gashi yanzu ya tsane ni nayi matuƙar dana sanin ƙin sakar masa da nayi tin farko, ko a yanzu gani yake duk nine na jawo ya rasa ki" Tace, "hmm dan dai be sani bane amma ko yanzun ma ba wai ya rasanin bane, amma fa karka damu kanka akan wannan indai Khaalif ne ze sakko ne dan fushin sa baya ɗorewa" Yace, "ina fatan hakan Allah yasa karya ƙullace ni har gaba gaba" Tace, "amin" Da haka sukayi sallama ta ajiye wayar sai fara'a take, Nuriya ce ta kalle ta tace, "Ya ABU ya samu lafiya na tayaki murna" Tace, "nagode Nuriya gaskiya zan kasance cikin farin ciki a wannan ranar samuwar lafiyarsa ta wanke duk wani ɓacin rai nawa" Nuriya tace, "to Khaalif fa dan yanzu shine abun ji" Murmushi tayi kafin tace, "Nuriya yau za'a kaini gidan Saifu amma gobe i warhaka ina gidan ubana" Cikin zaro ido Nuriya tace, "saboda me wai meye yake baki ƙwarin guiwa haka ne??? kashe shi zakiyi??" Tace, "rufani ki sayani ina ni ina kisan rai??? ke dai ki jira kawai zakiji" Da misalin ƙarfe ɗaya 01:00 na dare, Aisha cikin rashin sanin madafa take tafiya ga wani jiri da yake ɗibarta tana tafiya tana haɗa hanya, kamar daga sama taga mota ta tsaya a gabanta bata tsaya tunanin komai ba tayi gaba zata wuce, hannunta yaja ya tura ta a motar sannan ya jata da mugun gudu. Kai tsaye wani madai-dai-cin gida ya kaita har zuwa lokacin batasan ko Waye ba kawai dai tayi shiru ta zubawa sarautar Allah ido, Sai da ya kunna hasken ɗakin sannan ta gansa cikin zaro ido take kallonsa cikin rawar baki tace, "Dawood kaine?????" yace, "nine mana A'isha dama nasan hakan zata faru ne shiyasa na kasance a yankin ina jiran zuwan ki, gaskiya ƙanina yayi rashi kai tsaye zan iya kiran sa mutum mara sa'a" A tsorace tace, "meyesa zaka ƙara shigowa rayuwata kuma?? abunda kaine be ishe ka ba ko me?? meyesa?? me zakayi min???" Yayi dariya tareda cewa, "haba ƙanwata abun ba na zafi bane ba fa ki nutsu mana yanzu a daren nan ina zaki dosa?? ni bazan miki komai ba kawai zan kora miki wasu bayanai ne" *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 23* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* da Azhar aka ɗaura auren Saif da Aisha bayan anyi sallar Jumu'at kowa shagalinsa yakeyi amma banda ita da Nuriya dan kuwa Nuriya ta damu da damuwarta sosai hakan yasa itama bata farin ciki. shirun da tayi tana tunani ne yasa Nuriya cewa, "Aisha tunanin me kike ne haka??" Ta ɗan murmusa kafin tace, "Khaalif Mohh..." Murmushin takaici Nuriya tayi kafin tace, "zancen banza da wofi bayan an aura miki wancan shashashan kuma?? kodan bari nai miki uzuri dan SO BA ƘARYA BANE" tace, "hmm.. ai kin gama magana kuma, ba fa zan dena tunanin Khaalif ba Nuriya dan bansan halin da yake ciki ba tin jiya baya gida kuma lambarsa ma bata tafiya nikuma hankalina nema yake ya kasa jurar hakan dama sai dai kui min uzuri indai akan Khaalif ne na kasa sarrafa kaina gashi sai yanzu nakejin ina ƙara son sa wallahi" Nuriya tace, "Allah yayi miki maganin damuwar ki hakan kawai shi zan iya cewa" Ta amsa da "amin" tin yamma da sauran rana aka ɗauke ta aka kaita gidan Saif aka dangwarar tayi kukan tayi kukan har ta gaji, sai da akayi da gaske sannan aka ɓanɓare ta daga jikin Mama aka tafi da ita, Zuwa dare gidan ya ɗaɗe ba kowa sai ita kamar tsohuwar mayya. Tana zaune can ƙuryar gado ta haɗe kai da guiwa sai fizgar numfashi take tana saukewa saboda azababben kukan da tasha ga kanta da ya dasa ciwo kamar ya rabe biyu ga tunane tunane da fargaba sun yi mata cunkusss. Saif ne yayi sallama a ɗakin, ko motsawa batayi ba da sunan taji motsin mutum. ƙare mata kallo yayi tass sannan ya saki murmushi aransa yace, "shikenan fa ƙarya ta ƙare Aisha gaki kin shiga hannu" A zahiri kuwa cewa, "yayi sannu da gida Amarsu". Har lokacin bata motsa ba sai ma takaici da baƙin ciki da suka ƙara turnuƙo mata. be ƙara cewa uffan ba yayi waje bayan wani lokaci ya dawo tareda ledoji ya zube sannan ya kalleta yace, "wai har yanzu kina nan?? taso ki ci abinci, kuka baya magani sai dai ya kawo cuta ya zakiyi tinda Allah ya haɗa babu wanda ya isa ya raba, dan haka haƙuri ne ta kama ki dan nan gidan bautar aure ne" Sai a lokacin ta ɗago kai ta kalleshi ta kauda kai kafin tace, "bana buƙatar komai da zaka kwashe su ma da yafi, na riga na ci a gidan da ba na bautar aure ba" Yayi dariya yace, "Aisha kenan ƙarfin hali da tsaurin ido to ba komai baa tilasta mutum" Banza tayi kamar bata jishi ba, haka ya cigaba da ƴan surutansa duk tayi masa banza har abun yafara ɓata masa rai dan haka ya tattara ta ya watsar daga ƙarshe ma bar mata ɗakin yayi" tin tana zaune har tagaji ta zame ta kwanta saboda gajiyar Da tayi tana kwanciya bata ja lokaci me tsayi ba bacci ya sungume ta, kamar mara gata haka take baccin a wahalce. Saif kuwa sai da ya gama shaye shayen sa sannan ya nufo ɗakin kai tsaye kan gadon ya nufa ya zauna kusa da ita ya ƙare mata kallo kafin yayi murmushi, janyo ta yayi zuwa jikinsa saboda farin cikin da yake bakinsa ma yaƙi rufuwa, ba dan komai yake farin ciki ba sai dan ya sa mugunta a ransa ya ɗau aniyar nuna mata iyakatar ta tareda fansar duk wahalar da ya sha akanta. Cikin bacci tafara jin baƙon al'amari duk da tanada nauyin bacci amma indai za'a taɓa ta to fa zata tashi bare kuma anyi mata me dalilin, cikin matuƙar razani ta farka ido warwaje take kallonsa, zuciyarta ta buga cikin ranta tafara neman tsari dashi dan daga ganin yadda idanunsa suka canja tasan sai da yasha mugayen ƙwayoyi har da na ƙeta dan ta tabbata yayi ƙazamin shiri akanta, Cikin ɗan sauran ƙarfin da ya rage mata tafara ƙoƙarin ƙwatar kanta. da yake ƙarfin ba ɗaya bane takasa saboda yadda yaƙara yimata dabaibayi, Fashewa tayi da kuka kawai dan bata da abunyi wanda ya wuce shi cikin ranta kuwa ta dage wajen kai kukanta ga Allah tareda neman temakon sa. bayan wani lokaci ya ture ta daga jikinsa jikinsa har rawa yake saboda jaraba ga ɓacin rai ga kuma ƙwayoyin da ya bankaɗa suna masa aiki, a fasace yace, "dama abunda ake faɗa akanki duk gaskiya ne ko?? ashe dama da gaske bin maza kike munafuka?? bazaki gaya min gaskiya ba" Ita kuwa ganin ta tsira yasa tayi saurin direwa daga gadon tana murtsike idanunta da suka gaji da koke koken nata, cikin bushewar zuciya tace, "ba nice nake binsu ba su suke bina" Inda take yayi yana ƙara cewa, "ni zaki yiwa hauka ? bazaki gaya min inda kikai budurcin ki ba? dama an daɗe ana gaya min gaskiya naƙi yarda ashe duk da gaske ne, bazaki bani amsa ta ba sai na ɓallaki" Ba tareda ta kalleshi ba tace, "kai ni fa duk wannan maganganun banza ne ƙarya ce kawai" Wata kyakkyawar mangara ya bata har sai da bakinta yafara jini sai da ta ɗauki ɗan lokaci bata ƙara wani motsin kirki ba saboda azabar da ta ratsa ta, kafin tayi maganar ma ya shaƙe mata wuya cikin hargagi yake cewa, "bazaki faɗa min ba?? kuma ki sani sai na ɗau fansar duk abunda nayi wallahi kuma bazan zauna da ke ba na aureki kuma ban samu abunda nake so ba ai baze yuwu ba, ki gaya min waye ɗan iskan naki ko kuma na saɓawa tunanin ki yanzu" Kai kawai take iya girgiza masa takasa maganar saboda shaƙeta da yayi, sai da ya tabbatar ta jigata sannan ya sake ta sai da yayi mata tsala tsalan maruka guda uku a jere sannan yaƙara jefa mata tambayar" kuka take na fitar hayyaci da ƙyar ta iya cewa, "gaskiya nake gaya maka wallahi ni bana abunda kace, kawai dai da ina yarinya ne.." Yace, "akai uban me???" cikin azabar da take sha tace, "fyaɗe yayi min" Kukane yaƙara cin ƙarfinta hakan yasa sauran maganar ta maƙale, baji ba gani haka Saif yafara dukanta cikin rashin tausayi da rashin imani, sai da ya tabbatar yayi mata jan duka sannan ya kama hannunta ya jata kamar akuya yayi waje da ita ya watsa ta. Duk irin magiyar da roƙonsa da takeyi akan ya barta sai gobe yayi kunnen ta shegu, sai ma cewa da yayi "kije tsohon banzan da ya yaudare ni ya bani ke a haka ya tambaye ki ki bashi amsar inda kika barbaɗar da mutuncin ki, kuma na sakeki saki uku ki jira ma na kawo miki takarda dan ya tabbatar ni bazan zauna da mace irin ki ba" Yayi fuuu ya shiga cikin gidan ya fito ya miƙa mata takarda tareda cewa, "gashi nan na sake ki sai kije ki cigaba da yawon barbaɗin" Cikin kuka tace, "Saif ko ni ba ƴar uwarka bace ban cancanci wannan hukuncin ba da daddaren nan ina zan tafi? ka barni na kwana dan Allah in yaso gobe da wuri sai na tafi" Yace, "ki kwanar min a gida?? baki daku ba ko?? dan banyi miki lahani ba shine zaki dinga kawo min maganar banza" Girgiza kai tayi kafin tace, "ai Saif ka zama mutum, tin bakasan kanka ba tsohon nawa ya raine ka ya baka tarbiya amma saboda ba ɗan kirki bane kai duk ka watsar da ita, wai yau gashi kaine kake korar ƴarsa daga cikin gidan ka kamar kaga mugun abu saboda ya riga yayi maka komai, Saif duniya ce da kai da wadda ta kawo ku duniya da ƴan uwanka duk sai kunga sakaiya Allah baze barku ba Saif kuma na gode ko babu komai yanzu ka bani damar auren wanda nake so" Kafin yayi wata magana tafara tafiya, kawai yaja tsaki ya koma cikin gidan sa sai huci yake, a duk tunanin sa ba abunda yake yawo illa ta cuce shi tagama dashi. Tana cikin tafiyar ne mota ta tsaya a gabanta har zata wuce taji ya cukume ta ya tura a motar bata san ko waye ba batasan irin halin sa ba dan haka tayi shiru har suka isa inda yake son zuwa yace ta fito sannan ta fito. har lokacin bata yarda bazeyi mata komai ba sai dai bata da zaɓin da ya wuce yimasa ladabin kunama dan kuwa daga shi sai ita a gidan ko yankata yayi har ya soya ya cinye wani be sani ba. yana murmushi yace, "Aisha in faɗa miki gaskiya ?? ke ba macece wadda ake samu a gama gari ba, Kuma ke macece wadda duk wani lafiyayyen namiji in ya ɗora idonsa akanki sai yaji ya ƙyasa, ke ƴar baiwa ce fa" Murmushin ƙarfin hali tayi masa kafin tace, "nagode" Takowa yayi ya matso inda take ya zauna kusa da ita yana fuskantar ta idanu ya zuba mata kamar tsohon maye sai wani murmushi yake me manufofi da yawa. ita dai kanta yana ƙasa dan kuwa a tsorace take. Muryarsa ce ta katse mata tunanin ta, "idan na tuna daren farkon mu sai naji shauki ya ɗebe ni A'isha jinake dama za'a kuma" Cikin takaici tace, "ai za'a kuma ɗin amma ba da kai ba" Dariya yayi yace, "shikenan na yarda ba dani ɗin ba amma koma waye ai nine na nuna masa hanya" Takaici be barta tayi magana ba sai ɗan murmushi da takeyi wanda ita kaɗai tasan manufarsa sai Allah. Yace, "tashi kije kiyi wanka" kai tsaye tace, "bazanyi ba" Murmusawa yayi yace, "ohhh A'isha har yau baki canja ba, gardama ga tarin zurfin ciki gaskiya kina burgeni" Tace, "idan da na canja ai da tuni labarin ma ya canja" Yace, "kuma fa hakane amma dai kiyi abunda nace" Tace, "nifa bazanyi ba, akan me zanyi wanka a gida dagani sai kai??, kana ma hauka" be tsaya jin zancen ba ya sungume ta ya ɗorata a kafaɗa ya nufi ɗakin wanka da ita, mutsil mutsil ta shigayi tana ƙoƙarin ƙwacewa amma takasa har sai da ya kaita sannan ya direta, ya kalle ta a dake yace, "zaki cire kayan da kanki ko kuwa na cire da kaina??" Da sauri tace, "dan Allah kayi Yaya Dawood zanyi wankan ma da kaina" Wani shu'umin murmushi ne ya buwayi fuskarsa har cikin ransa maganar ta ratsa shi be taɓa tsammanin akwai ranar da zata zo Aisha taƙara kiransa da Yaya ba shiyasa yaji abun kamar a mafarki, gefe guda kuwa yana mamakin yadda har take iya yimasa murmushi yau bayan idan ta ganshi kamar taga shaiɗan amma yau gashi ta saki jiki dashi, beyi tunanin komai ba dan kuwa idonsa ya rufe haka kawai tinda ya ɗakko ta yakejin wani irin shauki har ma ya kasa yi mata kashedi ta hanyar azabtarwar da yace ze bi mata da farko. Muryarta wadda take ƙara bauɗar da tunaninsa ce ta sarƙaƙa cikin kunnen sa, da yake lallaɓa shi take cikin sigar rarrashi tace, "dan Allah ka fita zanyi wankan karka ƙara shigowa kuma" yace, "na yarda kuma kiyi sauri dan nasan kina tareda ni bazan juri zama ni kaɗai ba" Kai ta gyaɗa masa tana murmushi, yana juya baya ta doka masa harara me taken ZALLAR ƘIYAYYA. Sai da ta tabbatar ta garƙame ƙofa sannan tafara wankan tanayi tana kuka sauƙin ta ma dai da ruwan ɗumi yadda take shan jiki da ruwan sanyi ne da ta ɗanɗana ta" Yana nan zaune ta fito sai raɓe raɓe take cikin sanyi tace, "na fito" Kallonta yayi sama da ƙasa kafin yace, "kuma shine kika ɗauki kayan da kika cire kika mayar dan shirme??" Tace, "kaga malam bana son iskanci nan fa ba gidan ubana bane ina naga wasu kayan" Yana dariya yace, "A'isha nine ɗan iskan ko?? kodan yau banyi miki iskancin bane yasa kika samu bakin magana?" sai a lokacin ta tuno da irin halinsa na rashin imani gudun kar a kuma yasa tace "kayi haƙuri" sannan taja baki ta tsuke. bata ankara ba sai ganinsa tayi a gabanta yana binta da kallo yana murmushi yace, "A'isha makullin sirrina gaskiya naga ƙoƙarin ki da kika kasa gayawa kowa, to amma yanzu kinga Saif ya jawo mana dama abunda naso gaya miki tin farko shine bana son sunana ya fito duk gumurzun da za'ayi idan kikace nine kinsani ke zaki kwana a ciki dan idan nace banyi ba babu me cewa dole nayi" Ƙasa tayi da kai tana murmushi tace, "Dawood Yayan Saif gaskiya kun more wajen tarwatsa farin cikina da kai da ƙanin ka, to amma ba komai indai akan wannan ne karka wani tashi kanka tsaye, duk tsawon shekarun da aka ɗauka ko mahaifiyata bata san anyi ba bare wani kaga kuwa babu dalilin da ze sa yanzu na faɗa" Yace, "wow A'isha gaskiya kin iya riƙon amana irin ku wahala kuke a zamanin nan" *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 24* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* yaƙara da cewa, "har yanzu ƙara kyau kike amma kin ɗanyi baƙi ba kamar lokacin da kina yarinya ba da fa kamar a taɓa jini ya fito haka kike" Zamewa tayi zuwa gefe tana cewa, "zafin duniya ma kaɗai ya isheni bare kuma kasan wani idan yana girma kamannin sa suna ƙara fitowa sai kaga ya canja launi" Yace, "hakane kuma" Wasu kaya ya miƙo mata yana cewa, "maza ki canja kaya" Karɓa tayi tareda nufar hanyar ɗakin wanka, da ido ya rakata har ta ɓacewa ganinsa sannan ya saki murmushi tareda cewa, "A'isha manyan gari" yana nan zaune ta fito ta tsaya akansa ba tareda ta kalleshi ba tace, "gida zan tafi" Yayi kamar be ji ba sai da taƙara cewa, "nace ka kaini gida ko?" Ido ya zuba mata har tsawon wani lokaci kafin yace, "anan zaki kwana" A zabure tace, "me????" Sarawar da kanta yayi ne yasa tayi saurin sakin maganar ta rintse ido gami da cije leɓenta, sai da ya sassauta sannan tace, "Dan Allah Dawood karka ƙara cutar dani ka maidani gidan mu, ka fita daga rayuwata ko na samu sassauci, nayi maka alƙawarin bazan faɗawa kowa abunda yafaru ba ko a wane matsayi aka ɗaukeni zan yarda amma dan Allah karka ƙara cutar dani" wata ƴar dariya yayi sannan yace, "na yarda bazaki faɗawa kowa ba yakamata kema ki yarda bazanyi miki komai ba indai ba ke kika amince ba, amma fa anan zaki kwana bazan kaiki gida da daren ba" Sanin ba kaitan zeyi ba yasa ta koma ta zauna ta buga tagumi. sai da ya gama abunda zeyi sannan ya kalleta tace, "tashi muje ki kwanta" Bata tsaya yimasa gardama ba ta bi bayansa wani ɗan madai-daicin ɗaki me ɗauke da matsakaicin gado ya kaita sannan yace, "duk abunda zaki iya buƙata akwaishi a ɗakin, sai da safe ko??" Gyaɗa kai tayi idonta a ƙasa. yace, " bazaki ce min komai ba??" Shirun taƙarayi dan kuwa bata san abunda zatace masa ba hasalima ta ƙagu ya tafi yabata guri dan ba ƙaunar ganinsa take ba. Ɗan murmushi yayi kafin yace, "shikenan sai da safe naga kamar kina jin bacci sosai" be jira me zatace ba ya fice, sai da ta sauke ƴar ajiyar zuciya sannan taƙarasa kan gadon ta zauna a gefen sa ta shiga ƙarewa ɗakin kallo har wani lokaci kafin taja tsaki, tareda zullumi da adda'a a bakinta ta haura kan gadon ta kwanta gami da lumshe idonta tana jiran zuwan bacci, tin tana sa ran ze ɗauke ta har ra dena saboda tunane tunane da suka durfafeta ga idonta sun ƙeƙashe babu alamun bacci a tattare dasu sai zafi da zugi kawai suke, fargaba da tsoron abunda ze faru kuwa sunyi cunkuss a zuciyarta hakan ya haifar mata da buguwar zuciya akai akai wanda yasa jikinta ya ɗauko tsuma, ta daɗe cikin wannan yanayin tana shan azaba kafin zuciyarta tayi rauni har kuka ya samu damar kufce mata hawayenta suka zuba, sai a lokacin ta ɗanji damar zugin da takeji sai dai kanta da ya cigaba da tsala ciwo, ta daɗe tana kukan sannan bacci me cike da mafarkai munana yayi ɗaukar shaho da ita, batafi minti ashirin ba tafarka bayan wani lokaci taƙara komawa, haka tayi baccin guntu guntu sai ƴan mafarkai da tunani da take faman yi, sai gab da Assubhu sannan bacci me nauyi ya ɗauketa. lokacin Sallah yanayi kuwa Dawood yazo ya tashe ta a cewar sa tayi Sallah ko takansa bata bi ba ta nufi inda take tunanin ɗakin wanka ne ta ɗauro alwala ta fito lokacin shi kuma ya fita hakan kuwa ba ƙaramin daɗi yayi mata ba, tayi sallarta cikin nutsuwa tareda roƙon Allah sassauci. Sai da tayi addu'o'i sosai sannan ta koma bacci, ba ita ta farka ba sai tara da minti arba'in da biyu 09:42 sannan ta tashi a razane tana wuri wuri da ido ai kuwa idonta ya sauka akan Dawood da yake zaune a gefenta yana ƙare mata kallo kamar wanda yaga baƙuwar halitta, ashe dai mafarkin da tayi gaskiya ne banbancin kawai a iya kallonta ya tsaya be taɓa ta ba. Yadda ta zazzaro masa ido ya tabbatar masa a firgice ta tashi ya sakar mata murmushi sannsn yace, "Barka da safiya ƙanwata A'isha ina fatan lafiya kika tashi" da kai ta amsa masa da "e" cikin ranta kuwa cewa take azzalumi ko meye damuwarsa da lafiyata bayan ya rabani da ita?" Katse ta yayi da cewa, "na haɗa miki ruwan wanka kiyi ki fito kiyi kari" Bata tanka masa ba ta zame tayi ƙasa har ta fito daga wankan yana nan zaune, zama tayi a gefen gado tayi zugummm ba um ba um um,. Abincin karin ya ya dire mata sannan ya koma ya harɗe, da taƙi ci sai da taga yayi da gaske sannan ta ci saboda tsoron abunda ze biyo baya. Sai kusan Azhar sannan ya ɗakko mota yace ta shiga ya maida ita gida tayi kukan tayi magiyar har tagaji ta dena ta zuba masa ido. Da har ƙofar gida ze kaita sai da ta dage bata so sannan ya haƙura ya direta a bakin layinsu bayan ya ƙara jaddada mata kar yaji ta ambaci sunan sa a cikin labarinta, hakanan ta amsa masa sannan ya barta ta tafi, bugun zuciyarta ƙara gudu yake a duk takun da tayi da sunan ta nufi gidan. tana yin sallama sukayi ido huɗu da Mama ta bi ta da kallon mamaki da tambaya. Ƙasa tayi da kai a ciki ciki tace, "sannun ku" daga haka ta wuce ta nufi ɗakinta. Mama da ta daskare a zaune tace, "Aisha????? kina cikin hayyacin ki kuwa???" Aunty Maimuna ta jinjina kai tareda cewa, "tabɗi jam Aisha ya zamu ganki anan yanzu kuwa bayan kamata yayi ace kina gidan mijinki" Duk da ba kallonsu take ba amma tasan duk idanun su suna kanta kuma jiran amsarta suke, Rintse ido tayi da ƙarfi a ƙagauce tace, "ya sakeni saki uku". Mama kasa magana tayi sai sauran mutanen da suke gurin me salati tanayi me ƙara jefo wata tambayar tanayi. Aunty Zuhailat tace, "iskanci ne ko ƙuruciya yake damunki Aisha?? akan wane dalili zaki zo mana da irin wannan banzan zancen??" Tace, "Aunty Zulaihat wallahi Saifu ya sakeni ga takardar ma a hannu na" Inna lillahi wa inna ilaihirraji un shine kalmar da Anti Zulaihat ta faɗa cikin rawar jiki da firgici, Aisha kuwa wuce tayi ta nufi ɗaki har taje ƙofa Mama ta dawo da ita da cewa, "zo nan dan ubanki Aisha" Dawowa tayi idonta a ƙasa tayi tsaye tana sauraren su, Cikin kuka Mama tace, "yanzu Allah ya rufa miki asiri ya rufamin shine zaki kashe aurenki?? Saif dai nasan bashi da wata matsala ko meye yafaru daga ke ne, maza ki gaya min wace tsiyar kika shuka" Gyara tsayuwa tayi gami da cewa, "ku tambaye shi mana shi da yai sakin" Mama takasa cewa komai sai sharar Ƙwallah, Cikin ɓacin rai Anti Maimuna tace, "bazamu tambaye shi ba ke zamu tambaya" Tace, "aikuwa zaku mutu bakuji ba" Tana rufe baki Anti Zulaihart tayi kanta da duka sai da ƙyar mutane suka dakatar da ita aka bata baki sai kuma ta fashe da kuka. Aisha kuwa gefe ta koma ta cigaba da ƙasa ƙasa da ido yanzu kukan ma har ta kai matakin da takejin baza ta iyayinsa ba zuciyarta ta bushe. Mama tace, "ku ƙyaleta idan ubanta yazo sai ta gaya masa tinda shine maɗaurin auren nata" Bata tanka ba kawai ta wuce ta shige ɗaki, wata ƙanwar Abban su wadda suke Ɗan wa da ɗan ƙani ta tashi ta bi bayanta, da yake akwai tsugul da son nuna iyawa ta raɓa kusa da ita cikin sigar lallami tace, "Aisha kinga ran mahaifiyar ki ya ɓaci kije ki bata haƙuri koda bazaki gaya mata abunda yafaru ba, amma kinyi ƙememe da ido ko hawaye bakyayi ai dole ace kece da laifin kije ki bata haƙuri kinji ko?? kar ta gayawa Abban ku ya ɗauki tsatstsauran mataki fa" A faɗace Aisha tace, "yaaa isa hakaa!! har shekara nawa zan ɗiba inayiwa ɗa namiji kuka??? bazanyi ba ɗin haƙurin ma bazan bayar ba tinda idan na faɗa ma ba abunda ze ragu ko ya ƙaru dan haka kar a ƙara yimin zancen banza na ɗebi tsawon lokaci ina kokawa saboda namiji yau ɗaya dan na samu hutu shine za'a takura min?? ki fita tin ina ganin mutuncin ki ki bani guri" Kamar munafukar kaza haka ta summ summ jikinta har rawa yake ta bi iska ta fice daga ɗakin... Waya Mama tasa aka kira Abba aka sanar dashi ai kuwa sai gashi ya dawo shima tin kafin ya dawo ya zabaro Saifu bayan dawowarsa kaɗan sai ga Saif ɗin. Aisha kuwa tanajin su tayi kamar bataji ba, Abba ne ya fara yambayar Saif ba,asi ai kuwa ya zayyana masa abunda yafaru tin jiya" Shiru yayi yana nazari sannan yasa a nemo masa ita a gefe ta tsakure tana jiran abunda ze ce, sai da ya ɗanyi gyaran murya sannan yace, "kinji abunda ta faɗa ko??" ta gyaɗa kai, yace, "to hakane" tace, "eh amma fa karya ƙara cewa ina neman maza dan ba aikina kenan ba" Cikin fushi Abba yace, "bayan tin jiya ya sakeke kuma ina kika kwana?? wannan ma kaɗai ya isa shedar abunda yafaɗa, Subhanallahi Aisha wannan rayuwar kika zaɓawa kanki?? A uzu billah" Saif yace, "gata nan dai ana ganin kamar su kaɗai ne masu tarbiya duk dangi ashe kura ce a lulluɓe da fatar akuya, ku tambaye ta waye wanda take zuwa gurinsa dan ni an daɗe ana sanar dani akwai wani namiji da take zuwa gurinsa, kuma ko waye sai munyi shari'a dashi" Cikin ƙunar rai Mama tace, "ka tambaye ta Alhaji ni ta ɓatawa suna ta zibarwa da mutunci dan nice uwa mace, ko meye yafaru ni za"a fara hari dan haka ta gaya mana da yaushe ta zama haka da yaushe ta watsar da tarbiyar da muka bata?? ta gaya min waye wanda ya lalata ta wallahi sai dai duniya tarabani dashi dan ni ƴa ta nasan ba karuwa bace sai dai in wanine yaja ra'ayin ta" Cikin tsawa Abba yace, "zaki goyi bayan ta ko??? gashi ƙiri ƙiri kina ji kina gani zaki ce ba haka ba?? ta gaya min ma jiya gidan ubanwa ta kwana" Shiru tayi dan kuwa tana matuƙar tsoron Dawood babu yadda za"ayi tace a gidansa ta kwana. Abba yace, "zakiyi magana ko kuwa sai na fara dukanki??" Tace, "Abba wallahi kawai zargina ake amma ni bana haka wallahi kunji na rantse" Saif yace, "ƙarya fa take munafuka ai na firgita da lamarin yarinyar nan azzaluma ni ai ta gama cutata kuma bazan yafe ba duk ma abunda na kashe dan aurenta sai an biyani" Abba ya jinjina kai kafin yace, "daga nan zuwa gobe ki gaya min waye idan ba haka ba ranki ze ɓaci, ku kuma ku sa ido akanta karta ƙarayin wani gurin" Mama ta share ƙwallah gami da cewa, "to" Komawa tayi ɗaki ta zauna sai fici fici take da idanu. Nuriya da take ta kuka ta kalleta cike da damuwa tace, "Aisha wannan wane irin baƙin labari ne?? neman maza kike???" Murmusawa tayi kafin tace, "ba nice na nemeshi ba shine ya nemeni Nuriya, kasancewar ki amintacciya a gurina ke kaɗai zan iya gayawa, amma ki tashi mu zagaya inda babu mutane" Tashi Nuriya tayi suka zagaya gurin ba kowa duk suna ɗayan sashin suka nemi guri suka zauna, Aisha tace, "lokacin ina yarinya Mama ta taɓa yin wata rashin lafiya me tsananin da sai da aka kwantar da ita a asibiti tayi kwanaki, to a wannan datsin ne wata rana, su Sayid suna makaranta Anti Zulaihart ita aka bar mana a gida domin kulawa damu, a ranar tace min zataje asibiti gurin Mama ni kuma na zauna a gida sai na kulle kar nabar kowa ya shigo, nayi nacin duniya da magiya akan tabarni muje tare amma taƙi, haka tasa ƙafa tabar gidan nan tabarni duk da ƙananun shekaru na, ina zauna zaune sai naji ana ta bugun ƙofa............." (Littafai na, SIRRIN ƘETA A JINI ƊAYA TAJMAHAAL Paid BOOK IB ƊAN WANKA Tareda RINTSIN SO" *INDO CE* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 25* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* "....da nace bazan buɗe ba sai naji ba'a dena bugun ba dan haka nayi tambayar waye, nan yake ce min Dawood ne, nace Mama bata nan ya tafi idan ta dawo sai shima ya dawo, amma sai yaƙi sai ma cewa da yayi aiko shi akai ze ɗauki wani abu, ni kuma jin hakan yasa na buɗe masa da tunanin gaskyar abunda ya faɗa, sai bayan nan nagane ashe labarin ba haka yake ba, to a wannan lokacin ne ya samu dama dan kowa baya nan, da yake inada gardama da na bujire masa ma haka yasamin ƙarfi, bayan nan kuma ya bani kyakkyawan kashedi akan kar na faɗawa kowa yace idan na faɗawa wani to zeyi min abunda yafi wannan, to ni kuma ina tsoron hakan, mutumin da ya iya danne ƙaramar yarinya yayi mata fyaɗe menene baze iya aikawata ba? ko akaina ko akan wani nawa nasan ze iya cutar damu, ga yara nan su Aunty sun haifa banaso ta dalilina ya cutar da wani dan haka yanzu ma bazan faɗa ba zan cigaba da riƙe maganar har zuwa lokacin da Allah ze tona masa asiri" "Haka nasha wahala a lokacin nan kafin kowa yazo na kwanta ga zazzabi ya tara ni, shi dama Dawood babu wata alama da yabari wadda zata nuna wani abu yafaru sai dai azabar da nakesha kawai koda Anti Zulaihat ta dawo ta tarar ina zazzaɓi sai tace nasha magani bayan nasha taga abun ba sauƙi sai ta tsiri cewa aje asibiti ni kuma ina tsoron su gane wani abun dan haka na daure na dena nuna damuwata kuma na kafe akan bazanje ba, haka sukai ta yimin tambayoyi amma naƙi basu amsa me kyau, Anty Maimuna a lokacin taso gane kamar wani abun yafaru saboda yadda taga ina tafiya da kyar kawai sai nace musu ciwon ƙafa nake kuma na tubure ahakan har sai da nayi abunda ya ɓata musu rai sukai fushi suka ƙyaleni, dama idan Abban mu ya dawo gidan su suke tafiya yana dawowa kuwa sukai gaba shi kuma dama Abba yana ɗakinsa muna namu, ... Haka nayi ta haƙuri na danne duk wani raɗaɗin da nakeji na kwana cikin wannan baƙin ƙadamin, washe gari ma na ƙoƙarta ina ɗan zagayawa kar su ganni a kwance su kinkime ni sukaiwa likita kowa yayi maganar tafiyata sai nace ciwon ƙafa nake idan ka matsa kuwa duk zafin da nakeji akanka zan juyeshi dan kuwa DA INA YARINYA inada faɗa sosai" ..... Nuriya ta numfasa kafin tace, "lallai wannan ya cika mara mutunci kuma maci amana in Allah ya yarda sai ya gamu da abunda hankalinsa baze ɗauka ba sai ya gamu da ƙuncin duniya da na lahira baze taba ganin ƙarshe me kyau ba mugu, shine kuma dan rashin kunya har Saif ne za'a kaiki gidan sa ya koro ki saboda wannan dalilin? lallai bashi da ma hankali" tayi Murmushin takaici tace, "Nuriya Saif be san hakan ce tafaru ba amma ko ya sani ma hakan zeyi min dan kuwa suna da mummunar aƙida ta son zuciya, a koda yaushe neman tsari nake dasu da irin su" Haka sukaita jajantawa juna sannan suka koma ɗaki. Washe gari kamar yadda Abba yace ta sanar masa hakan yaƙara tambayarta amma ko alu bata ce musu ba haka akaita gumurzu da ita amma taƙi faɗe har dukanta sukai dik ta shanye, hakan ya tabbatar musu da gaskiyar Saif tin daga lokacin suka hau dokin zuciya suka dena saurarar ta ko abunda ya shafeta kowa fushi yake da ita daga kan Abba Mama Anti Zulaihat Anti Maimuna kowa fushi yake da ita gaba ɗaya rayuwar tayi mata ƙunci bata da aboki sai kuka duk mutanen gidan ƴan biki sun tafi Nuriya ma ta tafi sai Sayid ne kawai yake ɗan kulata shima Mama hanashi takeyi. yau tana zaune Sayid yazo ya miƙo mata wata takarda karɓa tayi ta warware kafin ta tashi da sauri cikin rawar jiki ta yafa mayafinta sannan ta nufi ɗaya sashin yana tsaye ya riƙe ƙugu idonsa yana kan guri ɗaya da alamun wani tunanin yake. Cikin sauri taƙarasa inda yake cikin fara'a tareda farin cikin ganinsa, ido ya zuba mata da yake itama shi take kallo yanayin kallon da yake mata sai taji ya sare mata guiwa, cikin daurewa tace, "Khaalif Moh.. meke faruwa ne?" Yace, "ba komai" Shiru ce ta biyo baya kowa da nasa tunanin tasan dai da kyar ace babu komai ɗinnan dan ko a yanzu taga canji, katse mata tunanin yayi da cewa, "Ayeesha kinsan abun hakane meyesa baki sanar dani tin wuri ba?" Cikin mamaki tace, "me kenan??" yace, "au baki gane ba??" Tace, "Khaalif wata magana kayi min wadda ban fahimta ba" Hannunta ya kama ya janyota jikinsa yana cewa, "to bari na ganar dake" Ido taƙara waro masa cikin alamar tsoro dan kuwa ta lura yau babu alamun soyayayya sai dai wani abun. Sake rungumeta yayi tsam sannan ya jefa idanunsa cikin nata, cikin wata kalar muryar da bata saba ji daga gareshi ba yace, "kinsan haka abun yake da arha amma kika hanani, ko ni ba namiji bane?? faɗa min mana?? da nufinki na aureki a haka?? to maganar gaskiya bazan iyaba na auri budurwa amma babu lasisin budurci kinga ya tashi abanza" Tsananin mamakin irin kalaman da suke fitowa daga bakinsa yasa ta kasa magana sai kallonsa da takeyi, murmushi ya sakar mata kafin yace, "wannan kallon na meye ne?? ya isa haka mana abunda bakiyi tunani ba kafinki faɗa sona shine yake faruwa baki taɓa tambayar kanki meyesa duk matan duniya ke kaɗai na maƙalewa ba duk da irin rashin mutuncin da kika shuka min a baya?? nifa dama ba komai nake yiwa ba, ba wai zuciyarki nake buƙata ba iya jikinki ma kaɗai ya isheni more rayuwa amma yanzu labarin ya sauya ni nafasa kije ki auri wanda ze iya aurenki a haka, amma fa raina ya ɓaci sosai da sosai nayi takaicin rasa abunda na daɗe ina muradi, Ayeesha ni ba namiji bane da bazaki yarda dani ba??" A'uzu billahi itace kalmar da take mai-mai-tawa akan leɓen ta jikinta har kakkarwa yake saboda razani da kiɗima, Yace, "Ayeesha yanzu nasan ai kin gane me nake nufi ko??" Jin yana neman wuce iyakarsa ta haryar taɓa inda be dace ba yasa ta shammace shi ta zame tayi gefe tana so tayi magana amma takasa saboda zuciyarta da take bugawa cikin sauri, wasu zafafan hawaye ne suka wanke mata fuska da kyar tace, "Khaalif wallahi ni ba mutuniyar banza bace ni ba ƴar iska bace fin ƙarfina akai duk yadda kake zato na ba haka nake ba wallahi ni bantaɓa iskanci da wani ba, kai ma Allah yayi min tsari da kai shaiɗani ashe dama duk soyayyar taka ta ƙarya da yaudara ce Khaalif?? meye ribarka dan ka cutar dani?? amma Allah yana kallon komai kuma ze saka min wallahi Alhakina baze barku ba Khaalif kun cutar dani kun zalumce ni" Gyara tsayuwar sa yayi kafin yace, "ban cutar dake ba fa ke kika cuci kanki kinga da kin bari na aureki komai kike so zaki samu amma kin yiwa kanki, gaskiya naji takaicin hakan sosai yanzu ni ba abunda zance miki sai dai nace Allah yabaki wanda ze karɓe ki dan nasan ko ABU ɗin baze iya aurenki a yanzu ba bare kuma Jose iyayen faɗin rai da girman kai, nima yanzu daidai dani zan nema ina nufin budurwa dan kinsan saurayi sai da budurwa" Kasa magana tayi kawai ta juya ta koma cikin gida kai tsaye ɗakinta ta wuce ta zube a ƙasa ta haɗe kai da guiwa kuka take me tsananin ƙuna, ji take kamar a wuta take saboda tsabar raɗaɗin da takejin zuciyarta tanayi. Sayid ne ya dafa ta cikin sanyi yace, "Anti Aisha me Ya Khaalif yayi miki??, ki faɗa min" ɗagowa tayi ta kalleshi sannan tace, "Sayid ko meye Khaalif yayi min nice na jawowa kaina Khaalif Macuci ne na haƙura da soyayyar sa tin farko amma yaƙara hura min ita yanzu kuma ya gujeni ya ƙara dasa min son sa amma yabarni Sayid ya suke so nayi da rayuwa ta?? shin an halicce ni ne saboda su dinga wulaƙanta ni??" Taƙarasa maganar tana kuka. Cikin tausayawa yace, " kar kiyi maganar da zakiyi saɓo Allah yasan da zaman kowa a cikin bayinsa kuma kema kina cikinsu dan haka kiyi haƙuri Allah ze kawo miki sauƙi, ki manta dashi tinda har ya iya mantawa da soyayyar ki kema ki manta dashi ki cire shi daga rayuwar ki" Tace, "wallahi Sayid ina sonsa so me tsanani kafin na manta dashi zan sha baƙar wahala" Yace, "haka nan zaki jure amma ina ganin da ki zauna kina ɓata lokaci a banza da kin faɗi gaskiyar abunda yafaru da yafi, kinga yanzu kowa fushi yake dake kuma ɗauka suke da gaske ne abunda Saifu ya faɗa meye amfanin ɓoye gaskiya bayan kinsan dole wata rana zata bayyana??" Murmushin yaro man kaza tayi kafi tace, "Sayid bazan iya ba duk wanda yakeji da taurin kai ni na fishi ko me za'ayi min wallahi bazan faɗi gaskiya ba sai dai a kashe ni ko kuma ƙarewar dena kula ni a rufe ni a jefa mukullin a ruwa" Jinjina kai kawai yayi domin kuwa ya lura gwagwarmayar yau da kullum tasa zuciyarta tafara ƙeƙashewa be ƙara wata magana ba ya tashi ya bata guri dan yaga kanta yafara wuta zata fara masifa. *INDO CE..* [7/5, 10:53 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 26* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* yau ma kamar kullum haka ta kwana da zazzaɓi kamar yadda ta saba dama ba ƙaunar magani take ba bare yanzu da babu me tilasta mata akan ta sha, tana zaune tayi tagumi wayarta tafara ƙara, ɗauka tayi ba tareda ta duba ba takara a kunne. Cikin muryarsa irin ta maye yace, "Ashsha? kina lafiya??" Numfashi taja tareda zaro ido cikin mamakin abunda batayi zato ba, cigaba yayi da cewa, "Jose ne, Aisha baki cancanci irin wannan rayuwar ba kwata kwata dan samun rangwame daga su Mama idan sun tambayeki waye wanda kike zuwa gurinsa kice nine duk ki ɗora laifin a kaina ni kuma zan ɗauka ki gaya musu ni ne na aikata komai ke baki da laifi, kuma abokina har yanzu yana sonki yace yana son kiranki dan tunatar dake amma ya kasa, dan Allah ki kirashi kar damuwa tayi masa yawa shi tsakani ga Allah yake sonki kuma ze aureki indai har kin amince, dan haka ni ki ɗora min laifin ki auri abokina kawai hakan shine farin cikina ki temaka min Aisha" Shiru tayi tana sharar ƙwalla saboda tsananin tausayinsa da ya lulluɓe ta, Jose ɗin da kowa yayi masa shedar mutunci wai yau shine ya zama haka kuma adalilin ta, idan ta tuna takanji kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu dan baƙin ciki. da ƙyar ta iya cewa, "Jose bazan iya ba laifin da baka aikata ba na ɗora maka shi aa, Saif mugu ne bansan me zeyi maka ba bayan kuma ba kaine da laifin ba, ka dena wannan tunanin bazan iya ɓata maka rayuwa ba" Yace, "Aisha ni nace miki haka fa dan Allah ki amince bana so ki cigaba da irin wannan rayuwar kuma ki sani ba wai fasa bibiyar ki zeyi ba mafi sauƙi shine kiyi aure kibar gidan nan" Numfashi taja ta sauke kafin tace, "shikenan na amince zanyi hakan" Da sauri yace, "nagode Aisha" Murmushin dole kawai ta iya yi, tagumi taƙara zabgawa ta cigaba da tunani a yanzu babu abunda yake damunta kamar Khaalif idan ta tuno da abunda yafaru sai taji zucyarta kamar ta tsage, da ace ta yiwa sauran masoyanta rashin mutunci saboda shi da taga baƙin yanayi Allah ya temake ta batayi hakan ba sai ta bi su a sannu amma da ta ɗauki wasu shawarwarin da tini ya rage daga ita sai ita babu wani masoyinta da ze saurare ta" Waya ta ɗauka ta kira Nuriya bayan sun gaisa tace, "meke faruwa??" Tace, "Nuriya Khaalif" Tace, "me yayi kuma?" Zayyana mata abunda yafaru tayi Nuriya tafara salati da sallallami dan kuwa abun yayi mata girma bata taɓa kawo wannan tunanin ba. Aisha ce ta katse ta da cewa, "Nuriya dole abun ya baki mamaki, fiye da kowa na yarda da Khaalif na fifitashi akan kowa na yarda dashi fiye da ko wane namiji a duniya ashe shi ba abun yarda bane, idan na tuna dan dole nakeyin kuka" Nuriya tace, "Allah ya iya mana Aisha da yardar Allah ƙarshen wahalarki yazo in Allah ya yarda hakan shine silar daidaituwar rayuwarki, ki kwantar da hankalin ki ki dena damuwa kina zaune Allah ze kawo miki ɗauki" Murmushi tayi cikin jin daɗin maganar tata, cigaba tayi da bata labarin yadda sukayi da Jose har zuwa wani lokaci sannan sukai sallama. Yawan damuwa da larure larure sunsa Jikin Aisha ya rikice yau tin safe bata fito ba tayi bulum cikin bargo sai rawar sanyi take saboda zazzaɓi, Sayid ne ya shigo cikin tausayawa yace, "Anti Aisha kitashi na raka ki asibiti" Girgiza kai tayi tace, "aa kar ace naje wani gurin" yace, "Anti baza a ce ba fa gaskiya bazaki zauna da ciwo ba" Badan ta so ba ta tashi ta shirya sannan tace yaje ya sanarwa Mama, koda ya faɗa mata cewa tayi bazasu iya zuwa su kaɗai ba dan haka a nemo Khaalif ya kaisu ta haɗa shi da mukullin mota da kuɗi, haka ya koma ɗakin cikin ƙunar rai ya sanarwa Aisha abinda tace bata da zaɓin da ya wuce hakan shiyasa tace yaje ya sanar masa. Bayan wani ɗan lokaci ya dawo yace, "yace kizo" Miƙewa tayi cikin rashin ƙwarin jiki tabi bayan sa, tinda suka fara tafiya bata cewa kowa ƙala ba har suka isa bayan ta ga likita ya sanar mata ta kamu da ciwon zuciya hakan ba ƙaramin kashe mata jiki yaƙara yi ba. Suna cikin tafiya Khaalif yace, "ina son biyawa wani guri ko zan iya zuwa??" Shiru tayi masa dan haka ya canja tafiyar, da kyar tace, "Khaalif ka bar Sayid a asibiti fa" Yace, "na sani ai amma kinsan dai yasan hanya ko??" Tace, "to dan yasan hanya ba tare muka tawo dashi ba, ina tsoron Mama tayi min faɗa fa" Murmushi kawai yayi ba tareda yace komai ba. A bakin wani layi ya ajiye motar sannan ya fita yayi wani gurin tin tana sa ran ganinsa a lokacin har ta dena sai da tayi kuka me isarta kafin bacci yayi gaba da ita, a cikin baccin kamar a mafarki taji ana taɓata ana sumbatar ta, ta farka a tsorace gami da fashewa da kuka jikinta na rawa take kallonsa, murmushi yayi kafin yace, "Ayeeshan Khaalif kin gaji da jirana ko??" Ita dai baya tayi ta tsakure acan gefe sai kuka take cikin matuƙar firgici, fita yayi ya zagaya mazaunin sa sannan ya cigaba da tafiya, har suka dawo kuka take, tana shiga gidan tayi gamo da Abba a tsakar gida yayi tsaye da bulala a hannunsa sai faɗa yake, Mama Sayid Shaheed kuwa kuka kawai sukeyi. kanta Abba yayi yana cewa, "ina kikaje??? nace ina kikaje??" Cikin kuka tace, "Abba wallahi asibiti mukaje" Yace, "ni zaki yiwa munafurci?? asibitin ne tin rana sai yanzu bayan magrib?" Kafin tayi magana ya hau dukanta da iya ƙarfinsa yana tambayarta suwaye da waye wanda take mu'amala dasu, sai da ya gaji da dukanta sannan ya saita mata hanya yace ta fice masa daga gida. Haƙuri ta shiga bashi tareda roƙon afuwarsa amma yace firr besan da hakan ba, taso gaya masa abunda Jose ya gaya mata sai dai be bata dama ba dole taja jiki ta fice, tana tafiya tana kuka ba tareda sanin ina zata dosa ba. ji tayi an riƙe hannunta nan fa taƙara firgicewa, ganin Dawood ne yasa yaji zuciyarta ta fara yaji, ƙoƙarin fizge hannunta tafarayi amma takasa. Yace, "A'isha ki tsaya ki saurare ni mana" a masife tace, "me zaka gaya min?? yanzu ma wani sharrin kazo min dashi?? meyesa kake son ganin bayana ne Dawood me nayi maka??" Be saurare ta ba sai jan hannunta da yayi ya tura a cikin motar sa yajata ganin yayi ƙofar gidan su da ita yasa ta sake fashewa da kuka tana roƙonsa akan ya barta ta tafi gidan ƙanin Abbanta dan kuwa tana matuƙar tsoron Abba idan ransa ya ɓaci bayaji baya gani. tsawa ya daka mata hakan yasa tayi saurin kama bakinta sai dai kukan ƙasa ƙasa, huci ya furzar kafin yace, "kiyi haƙuri nayi miki tsawa amma nima ba haka naso ba ki tashi mu shiga ciki" Girgiza kai tayi alamar "aa" bayan son jiranta ta ɓata masa lokaci dan haka ya saɓa ta a kafaɗa, da sallama ya shiga gidan har lokacin duk suna tsakar gida ya dire ta sannan ya riƙe hannunta tamau. Abba yace, "mene kuma hakan" Dawood yace, "Abba Aisha bata da laifi gaba ɗaya kuskuren nawa ne" Abba yace, "wani salon yaudarar ne kuma akazo min dashi?? kai meye laifinka a ciki??" Yace, "Abba asali nine na rabata da mutuncin ta kuma Wallahi Abba bayan ni bata san kowane namiji bata yawon banza ba ɗabi'arta bace, Abba nine na aikata kuma na haneta da sanarwa kowa, dan haka bata gaya muku ba, ranar da Saifu ya kore ta daga gidansa a gidana ta kwana ni na ɗauketa, tin tana yarinya nayi mata fyaɗe, kuma a cikin gidan nan lokacin Mama bata da lafiya tana asibiti,... Tiryan tiryan ya zayyana musu yadda akayi kamar yadda ta sanarwa Nuriya yana maganar yana kuka. Abba ma tini yafara kukan baƙin ciki gami da kunya, Mama kuwa murmushi tayi tace, "to Alhaji dangina sune tsinannu su suka lalata maka ƴa shima wannan inaga dangi na ne, ai Allah ba azzalumin sarki bane gashi tin kafin tafiya tayi nisa ya fitar dani ya wanke dangina daga mugun zargi dama dangin ka sunce Khaalif ne ya hure mata kunne ya lalata, kuma Allah zeyi min sakayya da ni da ita bamu da ƙarfi kuma bamu da ikon da zamu hukuntashi Alhaji amma tabbas Allah ya san yanda zeyi dashi, bamu yafe ba kuma bazamu yafe ba" Dawood ya share ƙwalla sannan ya kalli Aisha cikin sanyi yace, "tin bayan rabuwarmu a wannan ranar na nemi nutsuwa ta na rasa duk tunani na ya juya ya koma kanki, mafarkin ki da tunanin ki suka hanani bacci, A'isha ni namiji ne kuma nima na kamu da son ki so me tsananin da zan iya fansar da rayuwata akanki" *INDO CE..* [7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 27* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Cikin kuka tace, "Abbana shine kawai zeyi min zaɓi na karɓa bazan ƙara yarda naso wani ba har sai idan Abba na ne ya zaɓar min shi, indai har yace ya amince nima a shirye nake" Daga haka ta miƙe ta shige ɗaki, kan kujera ta zauna ta share hawayen sannan tafara dariya sai da tayi me isarta kafin tace, "Dawood kenan, yanzu ka shiga hannu" Mama ce ta katse ta da cewa, "Aisha meyesa zaki ɓoye min wannan abu? ba irinsa ake kira da sirri ba fa meyesa zaki ji tsoron wani bayan ubangijin ki?? da kin sanar tin a lokacin da ansan matakin da ya dace kinga yanzu ya riga ya cuceki yayi miki mugun tabo ya zubar miki da mutunci a idon duniya" Ƙasa tayi da kai kafin tace, "shima ze ga dai-dai nashi Mama" Mama tace, "da izinin Allah kuwa sai yayi nadama mafi muni a rayuwarsa, amma duk da haka ya cucemu wani idan ya yarda wani baze yarda ba yanzu duniya ta ɗauka ke ba ƴar arziki bace amma Allah zeyi maganin komai, Addu'a ta ta karɓu Allah ya bayyana mi damuwarki Aisha kuma ya tona asirin wanda ya zalumce ki" Murmushi tayi tareda cewa, "Mama dan Allah ki dena zubda hawayen ki komai ya wuce" Tace, "be wuce ba dan indai ina raye bazan bari ki auri wannan macucin ba" shiru tayi tana wasa da ƴan yatsunta. washe gari tin safe Abba ya neme ta a gefe ta zauna tana sauraren abunda ze ce, bayan yayi gyaran murya yace, "to Aisha ina neman Afuwarki baya ga haka kuma kince zaɓi na kike so to gaskiya bazan ƙara wannan kuskuren ba idan kinada wanda kike so ki sanar dani idan ma bakida shi ki jira har lokacin da Allah ze kawo" Shiru tayi takasa cewa komai sai zuciyarta da take bugawa yanzu wasa biyu ya rage mata ABU da Jose cikinsu wa zata zaɓa??? idan tace ABU shi ya warke yanzu bashida matsalar komai, mugun halin da Jose ya faɗa shi yake sawa taji duk duniya bata da burin da ya wuce ta aureshi kuma ta zauna dashi a duk halin da yake ciki, shi kuma yafi son ta auri ABU yanzu me zata cewa Abban????. sanin batada amsoshin wannan tambayoyin yasa tayi shiru kawai da yaƙara tambayarta ma sai ta fashe da kuka sai da ya lallaɓa ta ya rarrashe ta da ƙyar sannan yabar zancen, ya koma kan Dawood tambayarta yayi wane mataki take son a ɗauka akansa, kawai tace a ƙyaleshi karma a ɗaga maganar duniya taji kawai abunda take so Abba yace masa ze aura masa ita, koda ya tambaye ta dalilin hakan bata bashi ƙwaƙƙwarar hujja ba, da yake neman hanyar gyara kuskure yake sai ya amince kawai. Sosai take farin ciki, idan ta tuna Dawood kuwa koda yaushe cikin kiranta da turo saƙonni yake ita Kuwa tai ta karɓa tana fakawa nuna masa take idan ba shi ba sai rijiya, gefe ɗaya kuwa kullum cikin ƙara so da shaƙuwa suke itada ABU abunda yake damunta kawai Jose da batasan halinda yake ciki ba dan yanzu ya zama ɗan kaɗai idan ya furtse sai yafi sati ba'a san inda yake ba. Yau Mahaifin Jose yayi takakkiya zuwa wajen mahaifin ABU dan ya lura shi ba ta ɗan nasa yake ba har yanzu besan ciwon sa ba dan haka ya yanke shawarar zuwa ya nemeshi akan yaje ayi maganar aure, anyi sa'a beyi gardama ba ya amince suka sa ranar zuwa. Tana cikin goge tsakar gida Saifu yayi sallama, amsawa tayi tareda binsa da ido cikin mamaki, ƙerere ya tsaya kamar gawar sababi yana kallonta, wani shu'umin murmushi ta sakar masa kafin tace, "barka da warhaka yaya Saifu" Sai da ya haɗiye wani ƙululu da yayi masa tokarere a maƙoshi kafin ya amsa da kyar yace, "barka dai Abba ya tashi??" Tayi farrr da ido kafin tace, "inajin ya tashi gaskiya" a tsaye ya sume saboda wata duniyar da ya faɗa ita ba ta tunami ba ita ba duniyar mutane ba, sai da tace, "ka wuce mana" sannan ya sauke gwauron nishi ya wuce, da sallama ya shiga ɗakin, bayan wani lokaci Abba yayi kiranta, ai kuwa da sauri taje ta durƙusa gami da cewa, "Abba gani" Abba yace, "to kinji dai abunda Saifu yace yana so ki koma ɗakin ki yana bada haƙuri tareda neman yafiya sannan yace beyi saki uku ba gida kawai yace ki tafi ya sakeki, shin haka ne?? kuma zaki iya amincewa ki koma???" Girgiza kai tayi tace, "Abba bazan iya ba kuma bama haka bane yanzu zan ɗakko takardar da ya bani da hannun sa" Abba yace, "to kai Saifu kaji abunda tace kuma koda ta amince ni bazan amince ba baka cancanci zama mijinta ba, da farko ma kawai ka ɗauka ƙaddara ce ta kawo hakan amma yanzu anyi walƙiya bazan ƙara bada ƴata gareku ba ko ba wannan ba, kai kaci mutuncin ta kaci zarafinta yayanka ya keta mata haddi kodan kunji nayi shiru shine zaka ƙara dawowa??? to tabbas idan na ƙara ganin ka a gida na Saifu ranka ze ɓaci fiye da tunanin ka, na rabaka da hanyar ma da Aisha tabi ba kai ba ita ko hanya karka yarda ka ƙara haɗawa da ita" Cikin mamaki yace, "wane yayan nawa kuma?? me yai mata??" Aisha ta fashe da kuka tana cewa, "kaje ka tambayi yayanka Dawood shi yasan amsar da ze baka" Da sauri Abba ya shiga rarrashinta gami da kwantar mata da hankali yana haƙur-ƙurtar da ita. Saifu kuwa cikin ɓacin rai yabar gidan kamar me shirin dukan iska. itama ɗakinta ta koma ranta duk a ɓace gefe guda kuwa tayi farin ciki da irin hukuncin da Abba yayanke. Ranar asabar da wuri Abi da mahaifin ABU suka zo suka sami Abba da maganar auren ABU da Aisha, sai da ya tambayi ra'ayin ta tace ta amince sannan shima ya yarda bayan sun tsaida magana suka koma. Kiran Khaalif ne ya shigo ta amsa, bakinsa har harɗewa yake wajen cewa, "Ayeesha Yaya na zaki aura?" Da ɗan mamaki tace, "Khaalif? mene ruwanka to a ciki?? shi zan aura shine wanda na yarda dashi" Yace, "Aisha idan kin Auri ABU ni kuma fa??" tace, "wannan kuma ruwanka ne idan kaso ma zaka iya dauwama ba aure ni kam yanzu babu wasu ƴan barikin kalamai da zaka faɗa min su ratsa zuciya ta, kasan wani abu ma kuwa Khaalif?? na tsaneka na tsani duk namijin da besan mutuncin ƴa mace besan darajar so da ƙauna ba, yanzu hankalin Abba rabi yana gareni kayi ƙoƙarin fita shirgi na tin kafin nasashi ya shata maka layi, ai yanzu ko maza sun ƙare Khaalif ba abinda zanyi da irinka ma balle kai na wuce tsararka wallahi" Daga haka ta katse kiran gami da kashe wayar dan tasan shi da naci idan yafara kira kamar baze dena ba. wayar yabi da kallo cikin ƙunar rai yana mamakin ma ta yadda akai ya fallasa kansa ya kwafsa gashi yanzu a memakon yaji ya dena ta ta-ta to sai ma abunda yayi gaba. sati shida akasa lokacin bikin ABU da Aisha, har zuwa lokacin Saifu da Dawood duk basu san halinda ake ciki ba. Yanzu dukansu gwarama suke a tsakanin su biyun kowa ya zuba musu ido baban su ma Allah ya isa yayi musu dukansu yace be yafe ba. yau auren ya rage saura Sati ɗaya su kaɗai suke shirye shiryen su ba tareda kowa ba dan kuwa kowa kallon bazawara yake mata shiyasa ba'a wani damu kai ba, Abba kuwa duk motsin da zatayi hankalinsa yana kai kafkaff suke da ita, har tayi ƙiba tayi mul saboda kulawar da take samu. Wayar Mama ce tayi ƙara ta ɗauka tareda yin sallama a ɗaya gefen Umma tana kuka tace, "Hajiya Rabi Jose ya zama mahaukacin gaske yace ze zo nan gidan ki dan Allah ko me ze faɗa karki saurare shi ya haukace" Da mamaki Mama tace, "garin ya Yaya??" Tace, "ba wannan ne abun damuwar ba banaso yazo yayi muku hauka a gida dan Allah Karku saurare shi" Tace, "to shikenan Allah ya bashi lafiya" Aisha tace, "waye mara lafiya Mama??" Mama tace, "wai Jose ya haukace" Zumbur tayi ta miƙe da sauri ta shige ɗaki sai kuka, Mama ta saki baki tana kallonta kafin ta jinjina kai, Anti Maimuna tace, "nifa ina tunanin akwai wata alaƙa a tsakaninsu ta soyayya" Mama tace, "ai naga alamun hakan yanzu kuma lokaci ya ƙure mata" Sayid yace, "ai dama ya haƙura sanadin son nata ne ma ai ya zama haka" Cikin kaɗuwa Mama tace, "da gaske??" Yace, "wallahi kuwa" Sosai jikinsu yayi sanyi ƙalau. Tin Mama tana sa ran ganinsa har ta dena da alamu ƴar matsutsiyar ta kaɗa shi wani gurin. Dawood dawowarsa kenan gida yayi tuntuɓe da ƴarsa ƴar kimanin shekaru uku kwance shaƙe shaƙe babu alamun numfashi a tattareda ita, da sauri ya ɗauketa yayi cikin gidan da ita yana ƙwalawa mamanta kira ta fito suka shiga dubata jikinta yayi faca faca da jini, wata muguwar razana yayi saboda karo da yayi da mummunan gani yayi baya taga taga yana shirin faɗuwa. Da sauri matar tashi ta shiga tambayarsa lafiya, da kyar ya iya cewa, "fyaɗe sukai mata" Yaraff ta zube a wajen tareda fashewa da kuka ta shiga jera masa Allah ya isa bata yafe ba a cewarta shine ya ja mata komai. Be tsaya saurarenta ba ya nufi asibiti da ita,, bayan likitoci sun shawo kanta da kyar suka sanar masa ta kamu da ciwon ɓarin jiki rabin jikinta duk ya dena aiki, tashin hankali da masifa babu wanda be shiga ya zama kamar zautacce yace wancan yace wancan ya kasa zaune yakasa tsaye. *INDO CE..* [7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 28* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Dawood yana zaune ya haɗa kai da guiwa matarsa tazo ta tsaya akansa cikin masifa tace, "ban takardar sallama ta, nagaji da zama da kai da bala'in da yake tareda kai nan gaba ba iya ƴarka ba ni kaina shafa ta zeyi dan haka sakeni kaje ka riƙe ƴarka kayi jinyarta bana buƙatarku dukan ku" Cikin kame kame yace, "haba Wasila Ƴarki ce fa ba tawa ni kaɗai ba ki tausaya mata mana karki tafi ki barta" Saurin katse shi tayi da cewa, "yanzu ƴa taka ce duniya da lahira ka sakeni ko kuma kaga bala'i wallahi" Yace, "bazan sake ki ba duk matakin da zaki ɗauka ki ɗauka" Sufa tayi ta cikume shi da kokawa kicici kicici har ta samu ta cafki inda take hari, ihu ya zuba cikin ruɗu da tashin hankali yafara meman ɗauki, kafin mutane su ƙwaceshi tini ya sume a gurin, ita kuwa ta koma gefe sai huci take bayarwa. kai tsaye gurin likita akayi dashi da yake a asibitin ne abokin sa ne yayi duk cuku cukun da za'a dubashi lokacin. Bayan wani lokaci suka sanar da cewar yana lafiya sai dai jijiyar shaukinsa ta samu matsala. sosai Wasila tayi murna da hakan dan dama abunda take so kenan kuma tayi ƙudurin ko yana tafiya kansa yana fesar da wuta sai ya sake ta. Haka akayi Ƴa kwance uba kwance kowa yana fama da tashi larurar, mahaifiyarsa ce kawai take ƙoƙarin komai akansa sauran ƴan uwansa da mahaifinsa kuwa cewa sukayi abunda ya shuka shi yake girba dan haka ba abunda zasu tsinana masa" Ana kwana ana tashi har ranar asabar ta zamo saura kwana biyu, amarya Aisha a yanzu ne zaka tabbatar amaryar ce tayi kyau sosai tasha ado ko ta ina. Sayid ne ya shigo da gudu yace, "Mama wallahi ga Saifu can a ƙofar gida sai zazzaga masifa yake" Kafin ya rufe baki Nuriya tayi hanyar fita tana cewa, "da abamu labari gara mu bayar dan da alama ya haukace" Ita ma Aisha Mayafi taja tayi waje, kafin wani lokaci duk sun fito ganin ikon Allah, shi kuwa be fasa tijara ba, "anci amana ta an yaudare ni, to wallahi nafi ƙarfinki ko kin auri wani bazaki zauna lafiya ba sai na hanaki farin ciki a rayuwarki azzaluma, kuma nafi ƙarfin kowa duk wanda yace yana sonki ma nafi ƙarfinsa nine na makantar da ABU ɗin kuma kowaye ya shiga hanya ta sai na illata shi" maganganu yake kamar na marasa lafiya da iya ƙarfinsa kuma da son nuna gaskiyar abunda yake faɗa. Ƙamewa tayi a wajen jin yace shine ya makanta ABU, bama ita kaɗai ba duk wanda yake gurin ma sai da maganar ta girgiza shi musamman waƴanda basa zaton hakan daga gareshi wanda basu san halinsa ba. rasa abunyi tayi dan haka kawai ta fashe da kuka tashige cikin gida. Mama tafara tambayarta abunda yafaru, wanda suke biye da itane suka rattaba mata aikuwa ta shiga salati da sanarwa ubangiji gaba ɗaya jikinta yayi sanyi ƙalau sai yau taƙara tsorata da al'amarin su. Aisha kuwa zafin ƙiyayyar su ce ta ƙara ta'azzara tinda ta zauna tayi tagumi taƙi kula kowa abun ya bata mamaki sosai duk da tasan irin baƙin halin Saifu batayi zaton hakan ba, gefe guda kuwa tausayin ABU ɗinta yayi mata maƙil. Sai da kyar Nuriya ta samu ta lallaɓa ta. a daren ranar ɗaurin auren ne Mahaifin ABU da Mahaifin Jose suka sake kawowa Abba ziyara bayan sun gaisa Abi yace, "to dai kar a gaji damu kamar munyi magana biyu" Abba yace, "babu komai ai" Mahaifin ABU yace, "Alhaji ɗana ne yace ya barwa ɗan uwansa ya auri Aisha wato Yusuf shine nima naga hakan ya dace domin kuwa Yusuf ɗin shi yafi dacewa da ita fiyeda kowa, dan haka idan babu damuwa dan Allah a mayar da auren kansa shi kuma ABU sai a aura masa Ruƙayya mun gama magana da iyayenta za'a ɗaura auren tare yanzu kawai izinin ka muke jira idan hakan babu damuwa" Abba yace, "to Alhamdulillah duk ɗaya ne a wajena amma sai dai ina buƙatar jin ta bakin ta" Abi yace, "ai hakan yana da kyau babu komai" Abba yace, "to bari naje naji ko?" Suka amsa sannan ya nufi cikin gida. Koda Abba ya sanar mata abunda yafaru sai da takasa ɓoye farin cikinta haka kawai taji gaba ɗaya farin ciki ya lulluɓe ta. Iya haka ma ya tabbatarwa Abba tafi son Yusuf ɗin akan ABU dan haka ya amsa maganar shima yana farin ciki. Haka suka rabu cikin girmama juna da mutuntawa, yana shirin komawa ciki ne sai ga Dawood wujiga wujiga dashi, a gaban Abba ya zube a wahalce yace, "Abba ka temake ni karka aurar da Aisha ga wani ba ni ba wallahi mutuwa zanyi idan ban aureta ba, wallahi na tuba nayi nadama bazan kuma ba Abba wallahi na shiryu na faɗa masifa saboda Alhakin ta kaga Abba nima anyiwa ƴata fyaɗe har ta samu mutuwar rabin jiki matata ma ta gujeni ta gudu tabarni gashi yanzu banida shauki Abba ka temake ni karka ƙarasa rabani da farin ciki na nasan kanada tausayi nima ka tausaya min Abba" Ko da kaɗan Abba beji alamar tausayin Dawood ba sai ma ransa da yayi mugun ɓaci, baya son sake sauraron wasu banzayen maganganun nasa dan haka ya zame yayi cikin gida kawai. Saƙol Dawood ya tashi sanin baze saurare shi ba, yana tafiya yana kuka kamar ƙaramin yaro, haka ya koma ya tarar da ƴar tilon ƴarsa sai gunjin kuka take ita kaɗai a gida, tsugunnawa yayi a gabanta ya fashe da wani sabon kukan yana cewa, "na cuceki na cuci Aisha Allah baze barni ba, nasan ta dalilina akayi miki haka Bilkisu wallahi ni mugun mutum ne nayi nadamar haihuwa ta da akayi a duniya har narayu, tabbas da mutum yanada sani da be so zuwansa duniya ba indai yasan haka zata faru dashi" (ni kuwa nace ka sani🤷🏽‍♀️ tinda kowa yasan ƙarshen mugu baya kyau, Allah ka tsare mana zukatan mu ka karemu da bin son ranmu🙏) Khaalif saboda baƙin ciki da takaici ma barin gidan yayi ya koma dangin mahaifinsa dan baze iya jurar jin an shafa fatiha ba, sai yanzu ya gane me ake nufi da So lokacin da Allah ya jarrabe shi da sonta bayan tarwatsewar ƙudurin zuciyarsa, yanzu yasan me ake nufi damuwa da ya shige ta da gaske, sai yanzu ya gane me ake nufi da rasa Abunda kake so. Idan aka gansa sai an tausaya masa saboda yadda yayi ranƙol dashi koda yaushe cikin damuwa da tunani yake. Saif kuwa da alamun ya birkice ne dan hauka yakeyi sosai ko a gidan su ma be bari ba sai zazzaga bala'i yake ko gajiya bayayi kamar mahaukaci. Aisha yau kwanan farin ciki tayi har sai da ta ƙagara gari ya waye saboda ƙaguwa da taji an ɗaura mata aure da Jose, su Nuriya sai tsokanarta suke sai dai tayi dariya kawai. Washe gari da misalin goma da rabi na safiya aka ɗaura auren masu farin ciki sunayi masu baƙin sunayi. (nikam nace Alhamdulillah na taya murna team Jose) (Dan Allah kuyi haƙuri da wannan ba yawa, biki muke ina Aurar da ɗa😄 wannan ɗinma da kyar nayi kamar zanyi kuka😂) *sannan ina me farin cikin sanar daku cewa zan cigaba da Littafin da na Ajiye na ɗora RINTSIN SO, wato SIHIRIN ƘAUNA da yardar Allah* *INDO CE..* [7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 29* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* da kallo ɗaya za a gane irin farin cikin da Aisha take ciki sai fara'a da walwala take kamar ba ita ba. Da yamma aka ɗauke ta aka kaita gidan Umma, tarba ta mutunci ta samu daga kowane ɓangare dangin mahaifinsa da na mahaifiyar sa gaba ɗaya kowa murna yake da zuwan ta, Duk abunda ake Jose be sani ba shi dai kawai yaga taron mutane maganin kar su dameshi ma sai yabar musu gidan yasan inda dare yayi masa. zuwa dare ƴan kai amarya duk sun watse ya rage daga ita sai dangin Yusuf sauƙin ta ma dangin mahaifiyarsa duk ɗaya ne da na Mama sai dai Uba kawai suka haɗa amma duk da hakan tasan wasu daga cikin su, Ita yanzu duk ba ta tasu take ba burinta kawai ta sanya Jose a idanunta amma taji ko labarinsa ba'ayi itama kuma bata tambaye su ba, Tasha ƴan tayon kwana dan ƴan matan su Kiarat duk wajenta suka dawo suka tare sai da suka raba dare suna surutu kafin suyi bacci, ita dai sai murmushi take musu daga baya ma sai ta kwanta kamar tayi bacci sai dai ba baccin take ba har ma sai da suka rigata baccin. Sai da tayi kwana biyu a gidan Umma lokacin taro ya tashi sannan Umma ta shiryata tsaff duka gidan suka nufi gidan Yusuf da Abi ya tanadar masa, acan suka tarar da Jose da Abi sai sokana yakewa Abin shi dai sai lallaɓa shi yakeyi. Koda yaji sallamar su be bi takansu ba ya cigaba da ƴan surutunsa har sai da Kiara ta zauna kusa dashi tace masa Yaya Jose ga Ashshan ka mun kawo maka. Binta yayi da ido kafin yace, "ke bana son raini fa" Tace, " da gaske fa gata nan tareda Umma" Da sauri ya miƙe ya nufi inda Umma take tsaye tana kallonsa cike da tausayawa, idanunta sai zubda ƙwalla suke, gefe guda kuwa farin cikin samuwar farin cikin ɗan nata kamar ya kashe ta. Cikin rawar jiki ya ƙarasa ya tsaya a gabanta cikin son gazgatawa yace, "Umma?? da gaske KIARA take???" Umma ta gyaɗa masa kai, a hankali ya matsa gaban Aisha yana ƙare mata kallo kafin yasa hannu ya zame mayafin da aka rufe mata fuska dashi, dogon numfashi yaja tareda sake waro idonsa akan fuskarta, cikin nutsuwa ta ɗago kai cike da ɗokin ganinsa itama ta zuba masa ido, zazzafar ajiyar zuciya ya sauke lokacin da idanunsu suka hautsinu juna yaƙara sakin baki yana kallonta har yanzu gani yake kamar ba gaskiya bane. Hawayen da kai tsaye zata iya kiransu na farin ciki ne suka kwararo kan fuskarta tareda wani sassanyan murmushi. hannu yasa kan kumatunta ya shiga goge mata ƙwallar cikin wata rikitacciyar murya yace, "Ashshah!!!!! meyesa kike kuka????" Girgiza masa kai tayi alamar "aa" tana so tayi magana amma takasa sai ma kuka ne ya ƙwace mata, da saurin ya rungume ta cikin kiɗima ya shiga bubbugar bayanta alamun rarrashi tareda tambayar abunda akai mata. Mu'allim yace, "Yaya Jose naga kana harara ta bafa mune mukai mata laifi ba kaine da kanka" Yayi magana yana dariya. Murmushi Jose yayi gami da lumshe idonsa ya buɗe su sannan ya zubawa fuskarta ido lokaci ɗaya ya lula duniyar tunani, a hankali hawaye suka fara sintirin zubowa da sauri ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana shashshekar kuka a hankali. Sun ɗan kwashi lokaci a haka kafin Umma ta share ƙwallarta ta kamo hannunta tareda cewa, "bani ƴata nan da ba cewa kayi baka sonta ba. badan yaso ba ya bari ta janye ta daga jikinsa, ya durƙusa kan guiwoyin sa cikin muryar kuka yace, "Umma wallahi Ina Sonta bazan kuma cewa hakan ba" Umma tayi murmushi sannan tace, "na sani Yusuf shiyasa ma na kawota gareka a matsayin ta na matarka, yanzu amana ta dawo gareka Jose kayiwa Aisha adalci ka zauna da ita tsakani ga Allah ba cuta ba cutarwa" Mu'allim ya dafa kafaɗarsa tareda cewa, "haba Yaya Jose ka dena kuka dan Allah lokacin sa ya wuce yanzu farin ciki ya kamata kayi" Share ƙwallar yayi kafin ya miƙe, kusa da Abi ya zauna cikin farin ciki yace, "Abi nagode Allah yaƙara girma Allah ya jiƙan manyan ku" Cike da ƙauna Abi ya rungumeshi yana amsawa da "amin" Nasihohi sosai Umma da Abi harma da Mu'allim sukai musu kafin suka Rufe da Addu'o'i da fatan alkairi sannan suka barsu a gidan su biyu. Kusan a tare Yusuf da Aisha suka sauke ajiyar zuciya lokacin da motar su Mu'allim tafara tafiya, hannunta ya riƙo tareda cewa, "Ashsha???" Ɗago ido tayi ta kalleshi tareda sakar masa tattausan murmushi, shima murmushin yayi cikin sanyin murya yace, "Ashsha Allah yayi ke rabona ce, gashi kin dawo gareni" Murmushi me sauti tayi tace, "Kalamillah!!! (Cewar Allah) ɗa ɗaya tilo da babu kamarsa, ina farin cikin kasancewa ta matarka Kalamillah" Tinda ya zuba mata ido ko san ƙiftasu bayayi duk hankalinsa ya tafi akanta maganar da tayi ce tasashi sakin murmushi me sauti har sai da haƙoran sa suka bayyana ya lumshe ido tareda jan numfashi ya sauke" Jan hannunsa ta shigayi tareda cewa, "mu koma ciki ko?" Binta kawai yayi zoƙal zoƙal har sai da tace ya rufe gidan sannan ya rufe sukayi Addu'a sannan suka koma ciki, Tana shirin wucewa sashinta ya dakatar da ita da cewa, "gaskiya tareda ni zaki kwana Ashshah" Yadda yayi maganar a shagwaɓe sai sa ya bata dariya ta rausayar da kai tace, "to shikenan" Hannunta ya kama gami da cewa, "riƙe ki zanyi karki gudu ki barni" Tayi murmushi kafin tace, "Jose yanzu nifa mallakin ka ce har sai kace nagudu sannan zan gudu" yace, "ai kuwa bazance ba" Dariya kawai tayi bata sake magana ba har suka isa ɗakinsa, shi kuwa har yafara bata ƴan labarai" A bakin gado ta zauna tareda cewa, "zaka ɗakko min kaya na?" Shiru ya ɗanyi sannan yace, "aa bazanje ba sai dai ki raka ni" Tace, "to meyesa??" Yace, "wallahi kar naje zaki tafi ki bi Umma" yadda yake maganar ma kawai ya isa tabbatar da ba wata cikakkiyar nutsuwa ce dashi ba, murmushi me cike da tausayawa tayi tace, "Muje na raka ka " yace, "yauwa amma ki riƙe hannu na" Miƙewa tayi ta kama hannun nasa gamm sannan tace, "to muje ko??" suna tafiya yana bata labari har sukaje suka dawo, gurin shiga wanka ma sai da sukayi mujadala da kyar yabarta ta shiga ita kaɗai ya zauna a bakin ƙofa yana jiranta. bayan sun ɗauro alwala suka gudanar da sallah . Suna kammalawa ya janyo kwalba ze fara sha tayi saurin katse shi da cewa, "subhanallah Kalamillah me nake gani haka???! .. a ɗan kunyace yace, "ɗan kaɗan zansha fa" Matsowa tayi kusa dashi ta kwantar da kanta akan kafaɗarsa cikin nutsuwa tace, "ba irin wannan ne ya kamace ka ba, kaifa nasanka akwai sauƙin kai ga haƙuri haba Jose ɗina dan Allah kayi haƙuri da shan wannan abun nikam banaso, da fa ba haka kake ba meyesa yanzu kuma zaka koma haka?" yayi ƙasa da ido kafin yace, "gobe fa?" Tace, "idan bakasha yau ba kaga gobe ma zaka iya haƙura ai" A wani irin sangarce yace, "kaiii???? gaskiya ban yarda ba gara nasha yanzu kinga goben ma sai na sha" Sai yanzu ta fahimci hausar da tayi masa shine shi kuma ya baibaita abun, dariya tayi kafin tace, "ba haka nake nufi ba ina mufin goben ma zaka iya ƙin sha amma dai zakasha ƴar kaɗan" Murmushi yayi cike da jindaɗi yace, "to na yarda, amma dai kinci abinci ko?" da sauri tace, "na ci sosai kuwa" Ya murmusa sannan yace, "to ai da dafa miki zanyi" tace, "aa na ƙoshi bacci kawai zanyi" Kafin yayi magana har tafara ƙoƙarin kwanciya, shima kwanciyar yayi tareda yimata matashin kai da damtsen hannunsa sai shafar kanta yake yana murmushi farin ciki yana ƙara lulluɓe zuciyarsa. *INDO CE..* [7/5, 10:54 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 30* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* *shafi na ƙarshe* A gidan su ABU kuwa zaman lafiya suke sosai dukan su suna bawa juna kulawa dama Rookha a shirye take wa komai saboda shi dan haka ta shirya tsaf dan tarbarsa ta kowace siga ya zo mata, a nasa ɓangaren kuwa duk wata damuwarsa ya cireta ya ajiye a gefe sai ma roƙon Allah da yake da ya yaye masa Son Aisha, ana kwana ana tashi har nutsuwarsa tadawo dai-dai kuma hankalinsa ya koma kan Rookha. Khaalif ne zaune yayi tagumi duk duniya ya rasa abinda yake masa daɗi jiyake kamar baze iya yafewa kansa ba saboda amanar soyayya da yaci yanzu ya tabbatar Aisha ta me rabo ce kuma tafi ƙarfinsa gashi wata sabuwar fitinar ma gaba ɗaya ya zurmawa son Nuriya yana cike da fargaba da tunanin yadda za ayi ta so shi dan kuwa yasan abunda ya damu Aisha itama ya dameta babu yadda za ayi kai tsaye ta amince dashi. Saif kuwa gantalewar tasa kullum ƙara yawa take haka kawai ya zama wani mugun masifaffe shi kaɗai ma sai yayi ta zuba bala'i, rana tsaka kuwa aka wayi gari ya nemi ganinsa ya rasa dunɗum. sai a lokacin ya gane girman kuskurem da ya aikata na na cutar da ABU ta hanyar makantar dashi da kuma haɗin kai da ya bayar wajen tarwatsa nutsuwar Jose gashi yau duk abunda ya shuka ya dawo kansa. A fannin Haruna yaron Jose kuwa shima ya gama girba nashi makircin ya karɓi matsayin da yake hari na Jose kuma lamarin Allah lokaci guda aka gane ya haɗa hannu da Oga aka kamasu dukansu aka yankewa kowannen su hukunci daidai da abunda ya aikata. Dawood tsanani iya tsanani yana cikinsa ya rasa gaba ya rasa baya bashida matemaki sai Allah shi kaɗai yake jigila da ƴarsa yake jinyarta gashi duk ɗawainiyar da yake wajen nema mata magani Allah be karya dokar abun ba beyi nasarar samuwar lafiyarta ba, duk ya rame yayi kanjau kamar ba shi ba. Jose sai godiyar Allah Aisha tayi da gasken gasken wajen ganin ta shiga tsakaninsa da duk wata shiririta kuma tayi nasarar rabashi da shaye shayen da yakeyi kuma ya dawo Asalin Yusuf ɗinsa. Suna zaune a falo suna hira cikin farin ciki da nishaɗi Mu'allim yayi sallama, amsawa yayi tareda faɗaɗa fara'arsa yace, "ƙaraso mana ƙanina" Ƙarasawa yayi ya zauna kusa dashi bayan sun gaisa yace, "Yaya daman takardun komawarka aiki ne aka aiko ni dashi" Da mamaki yace, "kuma ni Yusuf ɗin ba wani ba??" Mu'allim yace, "ƙwarai Yaya" Girgiza kai yayi yace, "bazanyi ba banaso" maganin ma kar yaƙara wata maganar sai ya miƙe ze bar wajen Aisha tayi saurin dakatar dashi da cewa, "lokacin da kabar aikin kaine kasa kanka ne?? ko kuwa kasan hakan zata faru??" Yace, "Maman Twins bazaki gane bane banason..." Katse shi tayi da cewa, "basu kyauta ba kam, amma kai da kanka kasan dokar aikin ka, kayi haƙuri badan su ba dan Allah Ina son aikin" Komawa yayi ya zauna kafin yace, "Mu'allim waye ya aiko ka?" Yace, "waye kuwa idan ba iyayen mu ba? sune masu burin faranta mana a koda yaushe" Jinjina kai yayi yace, "kace zan koma" Cike da farin ciki Mu'allim yace, "Allah yayi maka jagora Yaya na" Ya murmusa sannan suka amsa da "amin" Khaalif bashi da zaɓin da ya wuce tinkarar Nuriya dan haka yayi kyakkyawar ɗamara yaje har gidan su, ai kuwa yasha ta sai da tayi masa wankin babban bargo sai da yayi kuka da idonsa amma hakan besa ta saurare shi ba. Aisha tana kwance tayi matashin kai da damtsen Yusuf tana danne danne kiran Sayid ya shigo da sauri ta amsa tana kiran sunansa, bayan sun gaisa yace, "Aunty Aisha wallahi Yaya Khaalif ya zama abun tausayi Nuriya yake so kuma tace bata son shi tayi masa rashin mutunci a yanzu haka bashida lafiya, dan Allah ki shiga maganar kisa baki ko zata amince dan Allah ku yafe masa tinda har ya gane kuskurensa" Shiru tayi tana tunani kafin tace, "Sayid sai anjima ko?" Daga haka ta katse kiran tareda ajiye wayar a gefe tana sauke gwauron numfashi, kallonta Yusuf yayi kafin yace, "meke faruwa da Khaalif ɗin?" Cikin sanyi tace, "ƙanwar nan tawa Nuriya yake so shine tayi masa rashin mutunci abun ya taɓani sosai gaskiya" Yusuf ya murmusa sannan yace, "karki damu Baiwar Allah har hauka nayi na dawo nai hankali saboda sonki kuma gashi Allah yayi na mallake ki kinga kuwa idan dai rabonsa ce to fa dolenta tasa ce, kinsan ya za'ayi??" ta Girgiza kai alamar "aa" Yace, "kira mana ita a waya mu bata baki nasan zata sakko, kuma kinsan ƙanin nawa ba baya bane tinda har yayi nasarar sace zuciyar Zinariyar kinga kuwa ai itama cikin sauƙi zata faɗa" Murmushi Aisha tayi sannan tace, "shikenan" Sai da tayi kira uku sannan ta ɗauka bayan ta kusan katsewa, Aisha tace, "haka duniyar ta zama?? wai muna ta taku amma ba ta tamu kuke ba meye rayuwar ne har zanyi kira uku manya manya ba'a ɗauka ba ko nima laifin Khaalif ne ya shafeni??" ɗan Murmushi tayi tace, "haba dai wallahi bana kusa ne ya gidan ya ɗan namu?" Aisha tace, "waye yace miki namiji zan haifa ne?? har kinsa uban ɗan yafara wani yashe baki kamar wani me tallan makilin to ƴan biyu zan haifa kuma duk mata ɗaya me sunan Mama ɗaya me sunan Umma kin gane ko???" dariya Yusuf yayi tareda cewa, "insha Allahu namiji zaki haifa min" Nuriya tace, "ato ina dalili haihuwar fari ta haifa maka mata wallahi karka yarda kwana kaɗan zakaji an fara kawo maka sirikai daga haka sai kaji ana Kaka Kaka" Dariya sukayi sosai kafin yace, "na ɗauki wannan zigar taki kuwa Nuriya?" Tace, "af zauna kallon ruwa kwaɗo yai maka ƙafa to Allah dai ya raba lafiya ni kam zanga me za'a haifa" Yayi saurin cewa, "ƴan biyu duk maza" Nuriya tace, "to Allah ya baka" Aisha tace, "kinga malama ba wannan ba tukunna ina dalilin ki na sassabawa Khaalif ɗina rashin mutunci" Murmushin takaici tayi tace, "kiji ƴar iska wani Khaalif ɗinki nayi masa ɗin bana son harkar rashin amana kinsani" Aisha tace, "to amma madam kinsani sarai yanzu Khaalif ya canja kinga kuwa da da yanzu ba ɗaya bane, yanzu kinga kinsa shi rashin lafiya" Zatayi magana Yusuf Jose ya dakatar da ita da cewa, "aaaa ba haka akeyi ba Nuriya itafa rayuwa tana son afuwa da masu afuwa idan mukayi haƙuri muka manta da baya mukai ƙoƙarin gyara gaba sai kiga Allah yayi mana temako rayuwar tayi mana daɗi, kiyi haƙuri komai ai ya wuce ki yafe masa" ta buɗi baki zatayi magana Aisha ma ta ƙara tarar numfashinta, sai da sukayi mata nasihu masu ratsa jiki sosai har suka tabbatar tayi sanyi sannan sukayi sallama. Suna gama wayar ta shiga turawa Khaalif kira, jikinsa har ɓari yake wajen ɗagawa amma sai yakasa magana. sai da taja shi da surutu sannan ya warware yana ɗan taya ta. Tin daga lokacin take kiransa da ya gane cewa ta dawo gareshi farin cikinsa kasa ɓoyuwa yayi yanzu bashida zancen da ya Wuce Nuriya kullum baitinsa kenan, Sunyi sabo da shaƙuwa sosai da sosai. ana kwana ana tashi har magana tayi ƙarfi komai ya kankama aka tsayarda lokacin auren Khaalif Mohammad da Nuriya. yau Aisha ta tashi ba lafiya har ta kaiga asibiti bayan wani lokaci ma'aikatan asibitin suka sanarwa Yusuf cewar an samu ƴan tagwaye mace da namiji amma sun koma dukansu macen bata zo da rai ba namijin kuma daga baya ya koma. Sosai jikinsa yayi sanyi liƙiss Allah kenan me yadda yaso gashi dai ya basu ƴan biyun da suke ta muradi kuma ya karɓi abunsa. Bayan wasu lokuta aka sallemata daga asibitin ta samu lafiya sosai tayi tangargar. Haka suka koma rayuwarsu cikin farin ciki da walwala bayan wasu watanni taƙara samun wani cikin, sai fatan Allah ya raba lafiya. Rookha ma ta samu ƴarta mace santaleliya taci sunan Aisha ana kiranta Humaira. Tana zaune ta miƙe ƙafa sai ciye ciye da gwaguye gwaguye take itace goruba itace gyaɗa itace aya. Yusuf ne yayi sallama ta amsa tana murmushi tace, "barka da dawowa" Yace, "yauwa, kina nan kina cin ko?" Tayi dariya gami da cewa, "kyautar da Allah ya baka ce ta kawo hakan" Dariya yayi yace, "to Allah ya raba lafiya kuma ya bamu masu albarka" Ta amsa da "amin" Bayan wani ɗan lokaci ta haihu lafiya ƙalau ta samu namiji shi kuma yaci sunan ABU Abubakar. Ansha murna da farin ciki ta ko ina ALHAMDULILLAH . *Alhamdulillah. anan na kawo ƙarshen littafi na me suna RINTSIN SO na godewa Allah da yabani ikon farashi lafiya kuma na gamashi lafiya kuma ina roƙon yafiyarsa a dukkan kuskure na a ciki.* *ina godiya sosai masoyana ina fatan ganin so da ƙaunar ku a littafina na gaba da nayi waja waja da basirata wajen tsara muku shi wato DOGON YARO* inkiya *(JANCY)* *Naira 300 Ne Kacal Ba Yawa, Sai Na Jiku.* *KU BIYO NI A CIKIN LITTAFIN (SIHIRIN ƘAUNA) DOMIN JIN MEKE ƘUNSHE A CIKIN WANNAN SALON SHI KUMA KYAUTA NE BA KO SISI KAWAI ƘAUNA CE TASA NA TSARA KUMA NA RUBUTA MUKU SHI* Sunayen littafai na. Sirrin Ƙeta A Jini Ɗaya Tajmahaal paid book Ib Ɗan Wanka Rintsin So tareda Sihirin Ƙauna da nake kan rubutawa sai Dogon Yaro. *Jinjina gareki Ummu Sulaim ina godiya da yabawa da irin ƙoƙarin ki Allah ya saka da Alkairi* *Waziriya ta wato Salmaaji kema taki dabance Allah yabar kyakkyawar ƙauna* *sauran masoyana musamman Group 1 abun alfaharina Allah ya ƙara zumunci, bazan iya zayyana sunayen ku ba amma tabbas kuna raina* *INDO CE..*