[7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 1* Alƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* (my Fans😂😂 mabiyan littafin 💖💖SIHIRIN ƘAUNA💖💖, Dan Allah kuyi min uzuri kuyi min afuwa sannan ku gafarce ni🙏🏻 nasan zaku so jin ya zata kaya tsakanin Yaaye da Annur da kuma Minoji da Yaa-ya, sai gashi lamarin Allah ya gifto, na ajiye SIHIRIN ƘAUNA na ɗora RINTSIN SO inkiya (WA NAKE SO) Shima labarin soyayya ne me sarƙaƙiya, ina fatan zakuyi min kyakkyawar Fahimta sannan ku cigaba da bibiyata a cikin wannan SALON me taken RINTSIN SO dan jin meke ƙunshe a cikin wannan littafin wanda har ya samu nasarar sani nayi abunda ban taɓayi ba, wato ajiye wani littafi da nafara rubutawa na ɗora wani, ban taɓayi ba tinda nafara rubutu sai akan wannan, kuyi haƙuri ku cigaba da bi na💞💞 INA SONKU KAMAR YADDA KUKE SO NA💖) [26/5/ 2022. Kamar yadda nafarashi lafiya ina rokon ALLAH yabani ikon gamashi lafiya] "Anti Aisha kiyo gudu kiran ze tsinke" Yaron yafaɗa cikin ɗaga murya. gudun tayi ta ƙaraso ɗakin ta karɓi wayar tana kallonta dan ganin wanda yake kiran, wani dogon tsaki ta zuƙa kafin tace, "aikin banza aikin wofi wannan kiran ba wani me ma'ana bane amma kake min wannan mugun kiran shashasha kawai, daga yau se yau idan KHAALIF MOH.. yaƙara kirana ka gaya min ma sai na dauje maka baki bare ma kana yimin ihun nan aka, da na zame na faɗi Fa? kaga ni na cutu shi kuma bashi da asara" Yaron ya turo baki, ƙasa ƙasa yana cewa "shine ma yana fama da girkeken kai ko me zaki masa ma oho" Zaram tayi dan kuwa ya sosa mata inda ke mata ƙaiƙayi cikin sauri tace, "wallahi kuwa kaifa kasan me ze min, ina jiran kira me muhimmanci shine ze wani kira ni, da yasan baƙin cikin da nakeji idan ya kirani wani lokacin da be fara kirana ba" shi dai Sayyid abun dariya yabashi dan haka ya dara sosai, daga baya faɗan ya koma kanshi da gudu ya fice yana dariya dan gudun kar ta lode shi . da sallama ya shigo gidan, fuska a haɗe ta amsa ƙasa ƙasa, Cikin fara'a yace, "ƙanwata barka da yamma" Kallonsa tayi ta kauda kai kafin tace, "naga kiranka ɗazu lokacin ina aiki ne" Ya murmusa gami da cewa, "shikenan dama ba komai bane, ina Mama?" Haka kawai ta saki murmushin da bata shiryawa zuwansa ba sannan tace, "tana ɗakinta" Kasancewar ba'a rabashi da fara'a yasa be dena washe baki ba sai ma ƙara buɗe haƙora da yayi dan kuwa murmushinta ko bakai niyya ba idan tayi maka shi sai naka murmushin ya kwance indai ka cika namiji" Khaalif Mohammad kenan. juyawa tayi tana wani tattausan murmushi harda lumshe ido, dai-dai lokacin aka ƙara yin sallama, lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɗauke ta koma kadaran kadahan ba yabo ba fallasa, ko kallonsa batayi ba ta cigaba da abunda takeyi, da ido ya bita yana murmushi. A fizge tace, "Ina wuni" "Ya amsa da lafiya lau yagidan?" "Lafiya" Kawai tace daga haka yayi gaba itama ta cigaba da aikinta. Saifu kenan. har Khaalif ya fita ya kuma dawowa cikin yanayinsa na sanyi yace, "ƙanwata temaka ki zuba min abinci dan Allah" Wata shegiyar harara ta zuba masa sama da ƙasa sannan tace, "banida lokacin hakan aiki nake" sai da ya haɗiye wani ƙululu sannan yace, "shikenan" Yayi waje ta rakashi da harara sannan ta kora masa tsaki. runtse idonsa yayi da ƙarfin gaske yanajin wani mugun ɗaci yana turnuƙo masa, ya cije gefen leɓensa yana girgiza kai har wani lokaci sannan ya furzar da huci, a hankali ya furta "kina Azabtar dani Ayeeshahh!!!" A cikin gida kuwa Sayid ta kalla tace, "kaji fa wannan ɗan rainin hankalin wai na zuba masa abinci, naƙi zuba masa ɗin, banida asara idan ya kwana da yunwa, yana Faman jan jiki kamar maciji" Mama ce ta ƙwala mata kira ta amsa tareda nufar inda take cikin sauri. Mama tace, "meyesa bakida Kunya ne Aisha?? ke kowa ma baki raga masa ba?" keɓe fuska tayi tana cewa, "ni bana son iyayin tsiya ne Mama, kuma ai zan bayar a kai masa Dama dan banaso yaje yai ta ƙunci a banza" Mama tace, "Allah ya shirye ki Aisha halinki akwai gyara amma da ba haka kuke da Khaakif Muhammad ba" Shiru ta ɗanyi kafin tace, "ko me nayi masa shine ya jawa kansa, sai dai har yanzu wani lokacin sai naji duk duniya tausayinsa nakeji" Mama ta taɓe baki tace, "to Allah ya shirya ku kuwa" Ta amsa da amin tana dariya. Har tayi shirin kwanciya taji wayarta tana ruri ɗauka tayi ganin kiran Saifu ne harda murmushinta, ta Kara a kunne ba tareda tayi magana ba. Cikin lumana yayi mata sallama ta amsa sannan ya cigaba da cewa, "kina lafiya My Baby?" Ɗan taɓe baki tayi sannan tace, "lafiya Lau" Yace, "har kinyi bacci ne? fatan dai ban takura miki ba" Ta murmusa tareda sauke ajiyar zuciya tace , "tayaya kuwa zaka takura min bayan koda yaushe begen ka nake" Murmushi me sauti yayi yace, "kyakkyawata kenan naji daɗi, nasan bakyason takurawa ne bari na barki kiyi bacci ko? sai da safe" Ta amsa da, "Allah ya tashemu lafiya. Da haka sukai sallama ta gyara kwanciyarta tana murmushi har cikin ranta tanajin farin ciki, take zancen aurensu ya dawo mata yanda ƴan uwa da abokan arziki suke lissafawa kuma suke ɗokin bikin nasu wasu ma sukance baze wuce watanni biyar ba, ita dai jinsu kawai take dan kuwa ba'a sa rana ba an dai kawo kuɗi, kuma bataji ana zancen sa ranar ba ma bare ta tabbatar" Yau kwana biyu kenan Aisha bata saka Khaalif Mohammad a idanunta ba haka kawai duk sai ta shiga damuwa. Mama tana zaune ta lallaɓo ta raɓe a kusa da ita, cikin sanyi tace, "Umma ta, ina ɗanki yayi ne?" Mama tace, "meye kuma abun tambayata? Meke faruwa?" Cike da damuwa tace, " Mama Khaalif fa baya nan ne kawai babu komai tambaya dai kawai nayi dan kwana biyu ban ganshi ba" Tace, "oho shirmen banza idan ya dawo ma banda rashin kunya me zaki bashi?" Ƙasa tayi da kai dan kuwa batada ta cewa haka ta tashi jiki ba ƙwari saɓalo saɓalo tayi ɗaki. Khaalif yana zaune kusa da Yayansa ABU suna hira Khaalif yace, "Bro wai in tambaye ka" ABU Yace, "Ina jinka ƙani na, Allah yasa dai ba zancen aure zakai min ba, dan na lura ka girma da yawa har kana neman zama Muzuru" yayi maganar cike da zolaya. Dariya sosai Khaalif Mohammad yayi kafin yace, "Bro kai ko bakayi aure ba dan tsaurin ido ni sai na ɗebo zancen aure?, ba yanzu ba tukunna dan ni banida ma wata a ƙasa, kawai inason tambayarka ne akan baka zuwa gidan mu, kodai akwai wani laifin da sukayi maka har kayi fushi?" Shiru yayi yana ɗan tunani kafin yace, "Khaalif se yanzu wannan ya faɗo cikin tunaninka?, ba komai babu wani abunda za'a yimin a gidan ku wanda ya wuce alkairi, kai tsaye ma dai zan iya cewa babu wani ƙwaƙƙwaran dalili" Cikin ransa kuwa yana tunanin dalilin nasa, tabbas ba kowa bane dalili face ƙanwar tasu wadda Khaalif yake tutiyar ƙanwarsa ce, tabbas itace sila a duk lokacin da ya ɗora idonsa a kanta yakanji kamar kar ya sauke, idan yaje gidan ji yake kamar ya ɗauke ta ya tawo da ita gidansu, Tin tana yarinya indai ya ganta haka Zuciya zatai ta raya masa abubuwa da dama, dan gudun ɓacin rana yasa ya ƙauracewa gidan da duk abunda ze haɗashi da ita, sai dai a koda yaushe be fasa tunaninta ba yana sane da ita sarai kawai jiran ranar da ze bayyana gareta yake.. Marai-rai-cewa Khaalif yayi yace, "haba Bro shiyasa fa duk ƙanne na basu sanka ba gaskiya ya kamata kaje, idan akace waye yasan Abu yayan Khaalif dan abun kaico har Ayeeshah cewa take bata san ka ba" . Murmushi yayi yace, "zata sanni indai Eeeshu ce kabari kawai Zanzo muku ka faɗawa Mama ta shirya ɗanta da baya zumunci ze zo" Sosai Khaalif Mohammad yayi farin ciki dan kuwa yana so yaga ɗan uwan nasa a gidan. Kwana biyar yayi sannan ya dawo, lokacin tini Aisha tafara koma danja da an taɓota sai masifa haka kawai batasan meke damunta ba, randa ya dawo kuwa dan farin ciki kasa dena murmushi tayi, sai dai ko da wasa bata bari ya gane tsantsar farin cikin da take ba. jikinsa duk yayi sanyi damuwa da ƙunci suka ƙara kafa sansani a cikin zuciyarsa, lallai yanzu ya tabbatar Ayeeshan sa tayi masa nisa, ya kasa gane wane laifin ya aikata mata da ta zaɓi hukuntashi ta wannan hanyar, yau gashi an wayi gari bata damu da ganinsa ba har yayi kwanaki a wani gurin amma ko a wasa bata nuna tasan ma ya dawo ba bare yaga farin cikinta. *INDO CE..* [7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 2* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Haka ya kwana cikin tunaninta sai juye juye kawai yake baccin ya gaza yimasa daɗi. Washegari yana Shigowa yayi karo da ita, lallausan Murmushi tayi gami da cewa,"yaushe ka dawo?" Shima murmushin yayi yace, "jiya" Tace, "inace ma bazaka dawo ba, to sannu da dawowa" Murmushi me ciwo yayi kafin yace, "ya zame min tamkar wajibi ne dawowa gidanku Ayeeshah dan ni maraya ne banida uwa banida uba, uhm, to ya za'ayi dama ai ɗan riƙo sai haƙuri, haka nan zan dawo dolena har zuwa lokacin da Allah ya ƙa'ide min" Murmushin gefen baki tayi tace, "haƙƙun zancen ka yana kan hanya sai dai kai ka bauɗe, meye naka na wannan zancen? ka fiye neman fitina Khaalif Mohh... ka fita idona in rufe banason haɗin faɗa, yanzu da Mama tana kusa ko zan shiga kogin rantsuwa bazata yarda ba wani abun nayi maka ba, dan haka ka tarkata kayi gaba, ni gaba ɗaya ka ɓatan rai" Cikin sanyi yace, "kiyi haƙuri dan Allah ba'a son raina na faɗa ba kinsan wani zubin baki ba'ai masa shamaki, banso ranki ya ɓaci ba ƙanwati, kiyi haƙuri dan Allah" Ƙasa tayi da kai tana murmushi kafin ta ɗago murya ƙasa ƙasa tace, "nayi kewarka Mohammad" Murmushin sa ne yaƙara faɗaɗa, har cikin rai yaji daɗin maganar sai dai baze iya gazgata gaskiyarta ba, kamar bazeyi magana ba sai kuma yace, " da gaske?" Taɓe baki tayi tace, "banda lokacin ɓatawa, ina fatan ka fahimta" Ya jinjina kai tareda cewa, " na fahimta" Haka lokaci yake tafiya rayuwa tana cuɗawa, tsakanin Khaalif da Ayeeshan sa, wataran suyi faɗa wata suyi daɗi, ita da Saifu kuwa kullum soyayya suke sha ba kama hannun yaro. Yau tinda ya tashi yake farin ciki dan kuwa ɗan uwansa yace masa ze zo ranar, Ta lura da yadda yake murna amma da yake ba damuwa tayi da abunda ya dameshi ba yasa bata bi ta kansa ba. Sai kusan yamma yazo, Khaalif Mohammad sai rawar jiki yake, tana dawowa ta shiga ɗakinta da nufin sutale kayan jikinta sukai ido huɗu dashi, ko ba'a faɗa ba tasan duk inda taje tazo wannan jinin Khaalif Mohammad ne dan haka ba sai tayi tambaya ba. Da sauri tayi baya tana zaro ido tareda cewa, "Auzubillah, meyesa basu gayamin ba na shigo sangam sangam haka? laifin Khaalif Moh.. ne ba wani ba, mutum idan akace ƙwaƙwalwar kifi gareshi sai dai addu'a" Muryar ABU ce ta dawo da ita hayyacin ta, "A I INDO" Saurin shiga ɗakin tayi tace, "ba haka ba Aisha zalla ba wani kwalo kwalo" kafin yayi magana Mama tace, "to arasai, shima bazaki raga masa ba? duk ba sunanki bane? daga dawowa zaki fara tijara ko gaisawa bakuyi ba?, memakon kifara tambaya daga ina ya fito dan kuwa ni kaina ban ganeshi ba" Ta ƙarasa maganar tana dariya. ɗan rissinawa tayi tace, "ina wuni?" Ya amsa da "lafiya lau ya karatu?" Tace, "Alhamdulillah" Yace, "Eeeshu kin sanni kuwa?" Tana dariya tace, "ta sanadin Khaalif Mohammad dan kuwa kana kama dashi, kuma naji labarin cewar yana da yaya hakanne ma yasa da na ganka ban gudu ba" Dariya sosai yayi yace, "lallai ne wai da gaske muna kama kenan?" Kafin tayi magana Mama tace, "ke do Allah maza kizo ki kawo masa abun taɓawa" Gaba Maman tayi ita kuma tanabinta a baya, duk ta harhaɗa mata a tire sannan ta ɗakko, da sallama ta shigo ɗakin ya amsa cikin sakin fuska, dire masa tayi tana cewa, "gashi nan saura kayi mana fulatanci" Yayi dariya kafin yace, "zauna ki tayani" Keɓe baki tayi tace, "nifa yanzu na dawo yana da kyau naje na huta" Yace, "Eeeshu ban zata zaki manta ni ba kuma ban zata zaki gane ni da wuri haka ba" Murmusawa kawai tayi kanta a ƙasa, sai a lokacin taji gaba ɗaya yayi mata kwarjini ko motsin kirki takasayi. Cigaba yayi da cewa, "lallai ƙanwata ta girma kice na fara shirye shirye" Ko ɗagowa tayi ta kalleshi batai ba sai murmushin da batasan usulin sa ba da takeyi. Shigowar Khaalif ce ta katse masa hanzari sai da ya amsa sallamar tasa sannan yace, "ƙanina kaga yadda A i ta girma?" . Khaalif yace, to ya zamuyi Bro haka ake haifar yara ƙannen mu sai su zo su girme mu dan ko yanzu Ayeeesha tamin tazara" ABU be ɗauki maganar a komai ba sai maganar da sukeyi, ita kuwa Ayeeshah haka kawai taji maganar tasa tafi mata kama da harshen damo, ABU yace, "Eeeshu kije ki huta naga kamar kin gaji" Tace, "to Allah dai ya shiryi wanda basa zumunci, sai anjima" yana dariya yace, "zo nan Eeeshu da wa kike?" Dawowa tayi tana murmushi kanta a ƙasa tace, "da wanda basa ziyara nake" Yace, "ohh ai bana cikin su, shiyasa naso tawowa da aboki na JOSE nasan shima ba lallai kinsan shi ba, dan nasan halin kayana ba zumuncin yake ba shima" Tunani ta ɗanyi kafin tace, "ohh Jose dai ƙanin Khalil? to ai shi ya fika zumuncin ma, nasanshi dan muma muna zuwa gidan su kaɗan kaɗan ba da yawa ba, be fi sau biyu naje ba" Dariya yayi yace, "lallai Jose ya ciri tuta, kice ya fini zumunci gaskiya nima zan dage" Tace, "gwara dai, amma fa bana magana da Jose ɗin kawai daga gaisuwa shikenan" yace, "subhana to Allah ya shiryaku kuwa, shi Jose miskilanci... Khaalif ya katse shi da cewa, "ƙanwata kuma girman kai" Kallon sama da ƙasa tayi masa bata tanka masa ba ta maida hankali kan ABU tace, "karkaji wani ya faɗa fa ka yarda ni banida girman kai ko kaɗan, ni an ɓata min rai ma sai anjima" Daga haka ta fice ta basu guri. Sosai jikin Khaalif Mohammad yayi sanyi, duk wani farin cikin da yake ya gushe, ya rasa meyesa Ayeeshah take masa haka. ABU ya lura da canjin yanayin Khaalif haka kawai yaji gabansa ya yanke ya faɗi, ido ya zuba masa yayin da shi kuma kansa yake ƙasa yana tunanin ta, Duk yadda ABU yaso karantar wani abu daga Khaalif yakasa dan haka ya canja musu hira. tuƙa motar yake amma tunanin sa da hankalinsa nutsuwar sa duk basa gareshi suna ga Eeeshu tabbas idan yayi kwance kwance za'ayi masa kwance kwance dan haka yake jin gwara ya bayyyanawa Eeeshu irin soyayyar da ya daɗe yana tanadar mata tin bata san kanta ba. haka ya koma gida cike da tunane tunane da sallama ya shiga gidan Umma ta amsa tanabbinsa da ido, ya gaishe ta ta amsa a ciki ciki, bayan ta gama ƙare masa kallo tace, "ina kuma kaje?, ana ta neman ka amma an rasa ka" cike da rashin kulawa yace, "gidan yayar mahaifiyata naje dan itama tana da haƙƙi a kaina" . A hasale tace, "ni zaka gayawa wani haƙƙi lallai ABU wuyanka ya isa yanka" Murmusawa yayi yace, "ba haka bane Umma yana da kyau ne ziyarta, kyautatawa dangin ka ɓangare biyun nan dangi mahaifi da na mahaifiya koyarwa ce ta addinin mu muslinci duka sun rataya a wuyanka, da dai banyi ba amma yanzu zan fara" Daga haka yayi waje be tsaya sauraron abunda zata faɗa ba. Baki buɗe ta raka bayan sa da ido....... *INDO CE..* [7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 3* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* (yau fa mura nakeyi taimin mugun kamu😥😥 sai dai kuyi haƙuri da abunda kuka samu😞 ban sani ba ma ko zan iya read more 1😂INA GAISUWA GAREKU🙏🏻😊) Har sai da ya ɓacewa ganinta sannan ta jinjina kai tace, "lallai ABU ka cika ai, har ni yaron nan ze gayawa magana?? dan yana ganin ya girma? hehe!! ta yaro kyau take bata ƙarko, zaka gane a hannu na ka taso ni na raine ka" ABU ganin tana neman ɗora masa hawan ruwa yasa yabar gidan ma baki ɗaya, tunane tunane sunyi masa cunkusss zuciyarsa cike take tafff da tsoro da fargaba wanda ya kasu gida biyu,na farko yana tsoron rasa Eeeshu na biyu kuwa shine abu mafi girma da ya ɗaga masa hankali, yanayin da ya gani a tareda ɗan uwansa haka kawai yaji yana matuƙar kishi Yana matuƙar tsoron gazgatuwar abunda zuciyarsa ke raya masa, wata rana a wayi gari ɗan uwansa ya kamu da son Eeeshu tabbas da yaga baƙar rana mafi muni, dan bayajin ze iya barwa Mohammad Khaalif ita. Haka ya cigaba da tunaninta gaba ɗaya bashida sukuni da kallo ɗaya zaka gane yana cikin damuwa irin sosai ɗinnan yanzu abunda yafi tsaya masa arai shine INA MAFITA?????" Yau Aisha tana zaune ta harɗe ƙafa tana danne danne, sallama yayi a ɗakin ta amsa ƙasa ƙasa. Nemarwa kansa masauki yayi ya zauna dan bayajin yanada matsayin da za'a bashi masauki. Cikin sanyi yace, "barka da yammaci ƙanwati" A fizge tace, "barka dai" Murmusawa yayi yace, "ƙanwata kowa yanada matsayi a gurinta kowa tana iya saurarar sa amma banda Mohh... ko wani laifi yayi me girma haka??" ƙare masa kallo tayi sama da ƙasa sannan ta cigaba da abunda takeyi, cike da rashin kulawa tace, "ohh tambaya ma kake??" Yace, " ƙanwata kinada matsaltsalu sai dai ke bakya jin magana ba kuma kya ɗaukar shawara, Ayeeshah meye rayuwar ne??, komai na maslaha fa yafi daɗi, komai idan kayi haƙuri sai kaga watan watarana komai ya wuce kamar ba'ayi ba, amma jure Iyayi da kwainanen yayan naki ya gagareki Ayeeshah" cike da takaici tace, "Khaalif Mohammad baka da laifi, dan ance muni tudu ne ka take naka ka hangi na wani, Bana son jin irin wannan kalaman daga bakin ka Moh Khaalif, raina yana ɓaci zuciyata tana tafasa ina fusata fiye da tunaninka, hmm.. kai matsala ma idan kaji ana nemanta akazo kanka ai an tashi, bana son tsirfa ze fi kyau ka Rufe min bakinka ka tattara ka koma inda ka fito dan kafara takura min" "KIYI HAƘURI" jin kalmar da ta fito daga bakinsa kai tsaye yasa ta ɗago kai tana kallonsa, zatayi magana ya katseta da cewa, " me laifi Ayeeshah ina shi ina tsayawa sanya? neman afuwa shine abu mafi dacewa dashi, amma dan Allah idan babu damuwa ki amsa min wannan tambayar, Meyesa mukeyin faɗa a koda yaushe " Tace, "laifin waye in ba kai ba? ko kanada abun cewa" . . Yace, "banida abun cewa Ayeeshah wanda ya wuce neman mafita daga Allah, yasan da zamana kuma inaga a hakan yake son gani na, kinsan Ƙaddara kowa da irin tasa kuma babu me iya tsallake mata, ni da tatashi sai ta rabani da Mahaifiya ta haka Mahaifina a yanzu abunda yake sani fargaba shine tsoron ta rabani da wani sashi na rayuwata" Da ido ta bi shi har yakai alama, ta buɗi baki zatayi magana yace, " na ƙara dasa wani surutun bari nayi waje" Daga haka ya fice yabata guri, wani tattausan murmushi ne ya kufce mata wanda bata shiryawa zuwansa ba hasalima batasan na meye ba, Haka kawai Takejin bata gaji da ganinsa ba, tuno diramar da sukayi ne yasa taƙara sakin murmushi tana lumshe ido, take wasu tunani suka fara kelo mata, lallai anyi kutse cikin rayuwarta amma duk da hakan bata da abin cewa wanda ya wuce takai kukanta gurin Allah. shigowar kiran Saifu ne ya katse mata tunanin tabi wayar da kallo har ta kusa katsewa sannan ta ɗauka, ba wani daɗewa sukai suna waya ba sukayi sallama tayi katantanwa da wayar zuwa gefe, ta sauke nannauyar ajiyar zuciya, a zahiri tace, "kowa da kalar tasa ƙaddarar amma ni nasan tawa ba me kyau bace" Muryar Sayid ce ta katse mata maganar "Anti Aisha naji Mama tana cewa za'a saka ranar auren ku keda yaya Saifu, kai wallahi zamusha biki ai ranar kaya kala talatin zansa, kowa burin ganin wannan ranar yake Anti" Katse shi tayi da cewa, "yayinda ni kuma nake fargabar zuwanta ba" da mamaki yace, "fargaba kuma???" Murmushi tayi tace, "kai yaro ne ba lallai ka fahimci me nake nufi ba, manyan mu ma bazasu fahimci irin ciwon da yake damun zuciyata ba bare kai, tashi kawai kaje Allah yayi min zaɓin alkairi kawai shine abunda zan iya cewa, amma yanzu ni kwata kwata auren Saifu baya gabana" sosai maganganun ta suka ɗaure masa kai yakasa gane meke damunta sarai kuwa kamar yadda ta faɗa ɗin be fahimci komai ba dan haka yatashi yabata guri" Haka rayuwa ta cigaba da garawa lokaci yana ƙara tafiya, kiran Mama ta ƙwala mata har sai da ta rintse ido da ƙarfi dan a rayuwa ta tsani kira me kamar tsawa sai taji tsikar jikinta har tashi take kanta yana sarawa, da sauri ta fita ta nufi inda Mama da Sayid harma da Shahid suke zaune kowa bakinsa har kunne, tsoro da fargabar abunda zataji ne ya kamata taƙarasa ta zauna tareda cewa "gani" Mama tace, "Saura ƴan kwanaki bikin uwarku, bayan ƙaramar sallah" Tace, "wa kenan?" Mama tace, "Anti Laila mana" Sai a lokacin ta washe haƙora cike da murna tace, "Mama zakije amma ko?" Tace, "bikin autar guda ai dole naje banda abunki nida ƙanwata ?" Dariya tayi tace, "to amma zaki kwana?" Tace, "eh idan Allah ya yarda" Ai murna a gurin Aisha ba kama hannun yaro a lokacin tafara lissafin abunda zatayi a bikin. ana kwana ana tashi yau aka wayi gari da azumi. rana ta goma da daddare kamar daga sama taga ABU tayi mamaki sosai Har sai da ta kasa ɓoyewa. Khaalif ma ba ƙaramin mamaki yayi ba dan be sanar masa ze zo ba zuwan bazata yayi masa, koda ya tambayi dalili yace masa gaisuwar azumi yazowa Mama. Mama kam tayi farin ciki sosai da sosai. Sunyi hira sosai daga baya Maman ta fita Shahid yana shirin bin bayanta ABU ya dakatar dashi da cewa, "ƙanin ƙanwata kiramin Eeeshu kaji?" Shahid yace, "to" Da tsallen sa yaje ya gaya mata, ido a waje take kallonsa zuciyarta na tsalle, kardai mugun mafarkin da ta daɗe tanayi ya tabbata, taɓe baki tayi tace, "to me zanyi masa kuma?" Shahid yace, "sai kinje zakiji" Badan taso ba ta nufi ɗakin sai murguɗe murguɗe take, daga hanyar ƙofa ta zauna tace, " gani Ya ABU" Fuskarsa ɗauke da murmushi yace, "Eeeshu badai har kin gaji dani ba daga zuwa biyu har anfara gajiya da gani na?" Tana dariya tace, "aa" Ya sauke ɓoyayyar ajiyar zuciya kafin yace, "naga daga gaisuwa ko takaina baki ƙara bi ba kodai nima na zama Jose ne??" Tace, "wallahi aa ai naga kuna hira ne da Mama kuma kaga bazanzo na saku gaba ba dan hirar yaushe gamo kukeyi" jinjina kai yayi yace, "lallai ƙanwata akwai hankali, nima yanzu tafiya zanyi ai" Tace, "wai tin yanzu ka bari sai anjima" Yace, "ƙauyen mu da nisa Eeeshu kuma dare yayi" Tace, "to Allah ya tsare" yace, "amin" Shiru ce ta biyo baya har wani lokaci sannan ya ɗan saci kallonta ya murmusa sannan yace, "Eeeshu?" Kallonsa tayi alamun ta amsa. Ya cigaba da cewa, "Eeeshu yaushe ne zaki cika min alƙawarin da kika ɗaukar min??" Zaro ido tayi tareda cewa, "wane alƙawari kuma ni ƴarnan??" Ƴar dariya yayi yace, "ba wani abun tashin hankali bane fa, alƙawarin da kikayi na zama dani idan zanyi aure" Ido ta ƙara gwalala masa arazane bakinta har motsi yake saboda son tayi magana amma kallonda ya yake mata yasa takasa furta komai, girgiza kai ta shigayi dan kuwa kwata kwata bata fahimci inda jirginsa ya sauka ba..... (🙄😏🙄 na rasa ma kalar hararar da zan muku😂😂 wallahi nasha wuya gurin rubuta fejin nan sau uku inayi yana gogewa😥 ga murar da nakeyi😿 kuma ƙarshe ma ko sannu bazaku iya yimin ba bare comment dan naji daɗi😒, wallahi in kunga typing error ma sai dai kuyi haƙuri🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️) *INDO CE..* [7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 4* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* murmushi ya sakar mata kafin yace, "ina nufin lokacin da kina yarinya kinyi min alƙawarin zama a gidana idan nayi aure" Ƙasa tayi da kai tace, "Laah ya ABU ai kuma yanzu na girma" Yace, "hakan ne ma yasa nayi ƙoƙarin tuna miki, nasan baki manta ba ai ko?" Tace, "ai kuwa na manta" Murmushi yayi ya tashi yana cewa, "zan wuce Eeeshu sai wani lokaci ko??" Kai kawai ta gyaɗa masa dan kuwa ya barta cikin ruɗani, a inda yatafi yabarta anan ta zauna tai ta tufka da warwara. Koda ya koma gida shirin kwanciya yayi amma baccin ya gagara, tunani ne fall cikin zuciyarsa a duniyar nan wa yake dashi wanda ze fara sanin sirrin zuciyarsa?, bashida mahaifiya mahaifinsa be damu dashi ba, waye ze jiɓanci lamarinsa? tabbas yanason zayyana abunda yake zuciyarsa ga mutum mafi kusanci dashi sai dai ya rasa wa ze tinkara, a duniya ɗan uwa ɗaya gareshi Khaalif sai dai bayajin ze iya furta masa wannan babbar maganar yana matuƙar tsoron abunda da Khaalif ze faɗa a lokacin da ya sanar masa haka kawai yakeji kamar ɗan uwansa ma ya faɗa RINTSIN SO kamar yadda shima ya kasance, sai yanzu yake ƙara tabbatarwa kansa shi maraya ne wanda yayi rashin wani babban jigo na rayuwarsa, ya rasa mahaifiya wadda itace wadda ko be faɗa ba zata gane halin da ya faɗa, a yanzu waye zeyi Alƙalanci tsakaninsa da ɗan uwansa? mahaifiyarsu ta rasu gashi ba mahaifinsu ɗaya ba babu wani wanda ze iya tausasa ɗayansu idan hakane kuwa tabbas sun faɗa garari dashi da Khaalif ɗinsa, ya tabbata da mahaifiyarsu tana na wani abun ze zo musu da sauƙi. kuka me tsanani ne ya ƙwace masa ya shiga mazgar abunsa kamar ƙaramin yaro lallai rayuwa duniya me yayi bayan irin wahalar da yasha ta rayuwa har ya girma ga wata baƙar ƙaddarar ta ƙara riskarsa. Haka yai ta kuka babu me rarrashinsa babu wanda yasan ma yanayi bare ya kawo masa ɗauki. tana zaune tana karatun Alƙur'ani wayarta tafara ƙara ɗauka tayi ta zuba mata ido ganin ko wace yasa tafara murmushi ta kara a kunne gami da cewa, "Hello Rookha!" A ɗaya ɓangaren Rookha tace, "yagarin ne Ayeeshan Yaya Khaalif" Murmushi Aisha tayi tace, "lafiya wallahi" Rookha tace, "ke shegiya saura kaɗan bikin Anti laila na kusa zuwa kano, wayyo Allah idan na tuna jinake kamar na mutu dan daɗi" Aisha dai dariya ta shigayi sannan tace, "to ƙafar yawo asha biki dai" Rookha ta ɗanyi sanyi da murnar da take sannan tace, "ba wasa fa Ayeeshah wallahi farin ciki nakeji kuma karki zata fa dan bikin nake murna, kawai dan zan haɗu da Ya ABU shine kawai farin ciki na, ina son nuna masa soyayyar da babu wata ɗiyar da zata iya yimasa ita a duniyar nan" Laƙwas Aisha tayi jikinta yayi sanyi sosai, tausayin Rookha ya danne duk wani karsashin ta. Jin shiru yasa Rookha tace, "lafiya kike kuwa??" Cikin ƙarfin hali tayi murmushi me sauti tareda cewa, "lafiya mana Rookha kibari kawai ai nasan bikin zeyi daɗi Allah dai ya kaimu lokacin" Tace, "amin ƴar uwa sai munyi waya" Da haka sukayi sallama, Aisha tabi wayar da kallo cikin sanyin jiki. itama Rookha mamakin sanyin da taji Aisha tayi take dan kuwa ta saba ƙwarara mata guiwa akan ABU amma yau duk ba wannan. Khaalif Mohammad. yana zaune ya haɗa kai da guiwa zuciyarsa tana masa wani irin tuƙuƙi da ɗaci, ya ɗan kwashi lokaci a haka kafin ya ɗago idanunsa da suka canja kala suka koma jaa ya zuba a guri ɗaya da alamu tunanin wani abu yake, ko motsawa bayayi sosai sai dai jefi jefi yakan haɗiyi wani mugun yawu, girgiza kai ya shigayi tareda cewa, "Ayeeshah ina cikin ƙuncin rayuwa ta dalilin ki meyesa kika dena SO na a lokacin da Sonki yayi min mugun harbi?, meyesa zaki nesanta dani a lokacin da nakejin kece bugun numfashi na?, Ayeeshah baki san ina sonki ba amma ni nasan ina sonki so na haƙiƙa son da ze iya tarwatsa rayuwata, zuciyata a ƙuntace take takasa bayyanar miki da abunda ke cikinta Ayeeshah nakasa faɗa miki ina sonki gashi har lokaci na yaƙare inama zan iya gaya miki ko zanji sanyi sanyi, watan wata rana zaki auri wani ba ni ba Ayeeshah ta bazan iya jura ba ya zamo wajibi gareni na nesanta gani na dake bazan iya jurar ganin ranar da zaki auri wani ba Ayeeshah. Kasa ƙarasa maganar yayi saboda zazzafar ƙwallar da ta shiga zubo masa, Allah sarki Ummi na na rasaki narasa mahaifina yau gashi Ayeeshah zata gagareni na zama banida wani amfani dan babu wani jigo a gareni, nasan da kinanan rayuwar zatayi min sauƙi koda yaushe cikin tsanani nake Ummi nakasa sanin yaushe zan dena kukan rashi" Wannan shine abunda zuciyarsa take gaya masa yayinda yake ƙoƙarin tsaida ƙwallarsa amma taƙi tsayawa. Jose. jin motsin Umma ne yasa yayi saurin soke wayar a Aljihunsa yafara zare ido da kallo ɗaya zaka gane bashi da wata cikakkiyar gaskiya. Murmushi tayi irin na manyance sannan tace, "wayata dama na shigo ɗauka ko ka ganta??" Shafa kai zuwa ƙeya ya shigayi yafara inda inda. hannu ta miƙa Masa tareda cewa, "bani idan ka ganta" Cikin in-ina yace, "ai tanaaa, gata ma a aljihu na ai" ya faɗa tareda saurim zarowa ya miƙa mata. Ta kalli wayar ta kalleshi kafin tace, "me kake min da waya??" Yace, "Umma hotuna nake kalla" Ta murmusa tareda cewa, "hotuna kake kalla ko kuma hoto??, ba yau ne farko ba fa, hala babu hotuna a wayarka?" Ƙasa yayi da kai yana mui mui da baki da alamu magana ce me ƙarfi a bakin nasa wadda besan tayaya ze furta ba. Zama tayi a gefen gadonta sannan tace, "Aisha ƴar ƙanwata!! yanayin tsayuwar hoton ne ya burgeka??" Zaram yayi ya kalleta dan kuwa ta sosa masa inda ke masa ƙaiƙayi, da sauri ya zauna gefenta sannan yace, "Umma ta maganar gaskiya bana iya ɓoye miki sirrin zuciyata wallahi na daɗe ina son ƴar nan taki sai dai banajin zata So ni dan naga kamar ta fiye girman kai, wallahi Umma Mahaukacin so nake mata tabbas zan susuce idan Ashsha bata sona" Da ido Umma ta bishi har wani lokaci sannan ta sauke ajiyar zuciya tareda ambaton sunan Allah buwayi, sai da ta lumshe ido ta buɗe sannan tace, "Jose Aisha bata da girman kai miskilanci ne ya gamu da miskilanci shiyasa karon yaƙi yin kyau, amma bata da girman kai sai dai tana da nauyin baki, baka taɓa janta da magana ba baka bata fuskar da zakaga rashin girman kanta ba shine zaka yanke hukunci? abunda zuciyarka take gaya maka ba gaskiya bane banyarda ba" Kafin taƙarasa abunda take son faɗa ya katse ta, Da sauri ya riƙo hannunta gami da ɗorashi kan ƙirjinsa daidai ƙahon zuciyarsa cikin wata sabautacciyar murya yace, "Umma ke mahaifiyata ce bazan taɓa yafewa kaina ba idan na faɗi maganar da kece wadda zaki fara ƙaryatawa, Umma na rantse da Ubangijin da ya dasa zuciyar da take bugawa a ƙirjina ina son Ashsha fiye da kaina, Umma idan kin ƙaryata zance na ta yaya Aisha zata yarda cewa ina sonta?? ki yarda dani ki gazgata gaskiyata dama kawai nakeso wadda zan gwadawa duniya irin son da nakewa Aisha" Rungumeshi tayi ta shiga bubbugar bayansa ganin yadda ya burkice lokaci ɗaya, sai da yayi sanyi sannan tace, "Jose bazan taɓa ƙaryata ƙaunar ka ga Aisha ba domin nima sheda ce, ba wannan ne naƙi yarda ba ban yarda tana da girman kai ba amma tabbas na gazgata Kana sonta kuma koda yaushe ina maka add'ar samun farin ciki a rayuwar ka tareda Alkairi akan komai, ka dawo nutsuwarka Jose, Aisha bata shiga sabgar wanda be shiga tata ba haka tana jan mutuncinta dan gudun wulaƙanci, amma tana da mutunci ga duk wanda yake mutunci da ita, kaima ka jaraba ka gani kuma zakace mahaifiyarka ta gaya maka wannan, kuma hakan sirri ne wanda ba kowane yake samu ba" (Allah sarki me uwa ɗan gata.. Allah ka rabamu da iyayen mu lafiya ka sakanya musu da mafificin alkairi ka kare su daga dukkan wani sharri ka sanya su cikin entattun bayinka, ba dan mu ba badan wayon mu ko iyawarmu ba dan Albarkacin shugaban mu Annabi Muhammad (SAW) ya Allah kayi musu jagora ka wanzar da haske a tattare dasu a duk inda suke, wanda muka rasa Allah ka jiƙansu ka wadata su da rahmarka ya Allah, (Ameen) wannan addu'a ba ni kaɗai ba har ku masoyana dan Allah kuce AMIN. ALLAH YABAMU IKON KYAUTATA MUSU) Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "nagode sosai Umma Allah ya jiƙan mahaifanki" Ta amsa da amin tareda ture shi daga jikin ta tana cewa, "do Allah ɗaga ni kana neman karya min kafaɗa, wai Jose duk ina wannan kunyar taka??" Da sauri ya ƙara rungumeta yana cewa, "Umma dan Allah kiyi shiru"... Ta murmusa gami da cewa, "fatan nasara YUSUFU Allah yai mana jagora" Sosai Jose yaji daɗin ƙwarin guiwar da ya samu daga mahaifiyarsa dan haka yasha ɗamba ya gyara ɗamarar tinkarar guguwar dake gabansa. ABU. Yanzu bashida ishashshen lokacin da ze ware yaje gidansu Aisha gashi da ko wace Sa'a tunaninta da kewarta ƙara yawa suke gareshi dan haka ya yanke shawarar neman lambarta. a yanzu tunaninsa ɗaya waye ze bashi lambar?? a gurin wa ze same ta??? ko dai ya nemi Rookha ta bashi?? anya kuwa idan yayi haka yayi adalci?? shin idan ya tambayi Khaalif Mohammad ta wace fuskar ze fahimce shi???. (KU BASHI SHAWARA FANS ƊINSA😂) *INDO CE..* [7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 5* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Ya daɗe yana neman lambar amma be samu ba duk wanda yake tunanin ze samu a gurinsa sai yaji babu har ƴar rama sai da yayi, sai daga baya ya sallama, wayarsa ya ɗauka ya turawa Khaalif Mohammad kira sai da ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, a tare sukayi sallama kafin Khaalif Mohammad ya amsa, ABU yace, "yagida?" murya a cunkushe yace, "lafiya lau Bro" Shiru ce ta biyo baya, ya shiga tunanin ta yadda ze shawo kansa cikin sauƙi haka kawai ya tsinci kansa da lafta masa ƙarya yace, "Hajja ce dama takeson yin magana da Mama kuma na nemeta ban samu ba ka turo min lambar Eeeshu" Shiru Khaalif Mohammad ya ɗanyi sannan yace, "ok bari kawai idan na koma gida zan kira ka" Cikin ƙarfin hali ABU yace, "idan kuma sauri ake kenan sai an jira ka??, ka turo min kawai ai nasan da hakan nace ka turo min ko??" Badan ransa yaso ba yace, "to shikenan zan turo maka bata son a dinga rabawa mutane lambarta ne shiyasa, naji kamar ranka ya ɓaci kayi haƙuri" Ɓoyayyar ajiyar zuciya ABU ya sauke tareda rintse idonsa har ga Allah yana tausayin ɗan uwansa sai dai shima abun a tausaya masa ne, "ina jira" kawai ya iya cewa ya kashe wayar. Khaalif mohammad ya raka wayar da ido yana mamakin abunda ya faru haka kawai yakejin kamar be gamsu da maganar ABU ba amma yasa a ransa koma menene Allah ya fishi sani dan haka ya fauwalawa Allah.. Ba wani ɓata lokaci lambar ta shigo murmushin farin ciki ne ya ziyarce shi, har ya tura kira ya fasa saboda idan ya kira ta a yanzu ma bashi da abun cewa. koda Khaalif ya dawo gida suna Hira da Mama yace, "kunyi waya da Hajja ɗazu ko??" Da ɗan mamaki tace, "Hajja kuma yaushe kenan?" Cikin sauri yace, "Mama Hajja fa ɗazu ABU yace na bashi lambar Ayeeshah zakuyi magana da Hajja" Mama tana shirin tayi magana Aisha ta fito ciki hanzari tace, "ya kira ni kuma lokacin bacci nake nace ni bazan tashi ba kuma kowa ma yasan ba son bada wayata nake ba ato" Taƙarasa maganar cikin sigar ko in kula. Ba Khaalif kaɗai ba Mama kanta sai da tayi mamakin hakan da Aisha tayi kuma tana gama maganar ta shige ɗaki duk suka rakata da ido. Tana shiga ɗakin ta jingina da bango tana rintse idanunta da ƙarfin gaske, wayyo Allah na wai ni kaɗaice mace a duniya da kowane namiji yake ƙoƙarin fakewa dani??, shi yazo ya tirke ni da maganar aurensa, kai kuma ka damu dani a lokacin da na cire sa rai na da kai, ga ɗan uwanka yana neman jefa kansa cikin wani ƙangin duk a dalilina, ina tsoron Yaya ABU ya zama silar tarwatsewar ZUMUNCI DA AMINTAR dake tsakani na da Rookha, ina cikin firgici ina cikin wata rayuwa Allah ka kawo min mafita" Zamewa tayi tai zaman daɓaro a wajen tareda fashewa da kuka. Sayid tareda Khaalif har gware suke wajen shigowa ɗakin yayin da Mama take bayansu. A matuƙar gigice Khaalif mohammad yake tambayarta abunda ya faru. Ganin sun shiga ruɗani yasa ta dena kukan ta share ƙwallar tareda danne duk wani ƙuncin da takeji tafara ƴar dariya. Sororo suka tsaya suna binta da ido, a marai-rai-ce Khaalif mohammad yace, "Ayeeshah meke faruwa??" A shagwaɓe tace, "wallahi Mama tiles ɗin ɗakin nan mugu ne kawai daga shigowata ɗaki ya zameni na faɗi kuma sai da na buge kaina a bango" Ɗan murmushi khaalif mohammad yayi tareda cewa, "Ayyaa Allah sarki ƙanwata sannu banji daɗi ba gaskiya be kyauta ba, dama ni ya kayar ba ke ba amma karki damu ki dena yi masa kuka kar ya raina ki" Mama kuwa tsaki ta ja ta taɓe baki sannan tace, "to kuwa Allah ya shirya ku dukan ku kaima da taya ɓera ɓari, bata bugun bane da har ta samu bakin yiwa mutane ihu kamar wata yarinya ko mahaukaciya" Da sauri tace, "Mama ina ganin fa kin faɗi gaskiya dan wani lokacin ji naje kamar na haukace ya kamata ku kaini asibiti naga likitan ƙwaƙwalwa tunani sun sa na fara zaucewa Mama" Zuwa yanzu Mama riƙe haɓa tayi saboda abun yafara girman kanta. Khaalif kuwa da yake akwai ƙarfin hali da juriya sai da ya dara sannan yace, "shikenan tashi muje dama na daɗe ina tunanin hakan ashe da gaske ne kina buƙatar likitan hankali" Yayi maganar cikin sigar zolaya. Harara ta buga masa taja tsaki kafin tace, "kaga wa kake da suna? Khaalif ko? idan kana neman mahaukaci kaje can ka duba amma ba'a gidan nan ba, bana son dattin ƙwaƙwalwa" Harara Mama ta zuba mata hakan yasa tayi gim da bakinta ta miƙe tana karkaɗe karkaɗe ta koma gado ta kwanta. Khaalif ya murmusa tareda cewa, "haka dai aci a ƙoshi a kwanta ba aikin fari ba na baƙi" Ta murguɗe baki tace, "daɗin ta dai ba wani ne yake yin abincin da kuke ci ba, kuma lokacin da zanyi aikin ba gayyato ka zanyi ko nace dole sai ka sani ba dan haka karka samin ciwon kai ka fitarwa mutane daga ɗaki ko kuma ni na tashi na fita" sim simm yayi ya fita dan baya son abun yayi tsauri yanzu sai ta ƙare masa rashin mutunci tinda tsakiyar kai har tafin ƙafa. ABU yana zaune sai saƙi da warwara yake har wani ɗan lokaci sannan ya ciri waya ya tura mata kira. Tana cikin jin waƙa ta saka iyafis kiran ya shigo bata tsaya dubawa ta ɗauka tareda yin fakare dan taji waye me nemanta. sassanyar muryarsa ce tayi tafiyar mashi da ita lokacin da ya rangaɗa mata sallama, sai da numfashinta ya ɗan tsaya kafin ta sauke ajiyar zuciya ƙirjinta na bugawa, sai da ya kuma yin sallamar sannan ta amsa a sanyaye. Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace, "ina gaisuwa Queen Eeeshu barka da wannan lokaci" A daburce tace, "barka dai yagida?" Yace, "gida lafiya lau sai godiyar Allah ya Mama? ya jiki jikin nata??" Tace, "taji sauƙi sosai bari na kai mata wayar" Da sauri ya dakatar da ita da cewa, "Eeeshu ke nake nema dama kice ina gaisheta cewa nayi tinda bakya nema na ni bari na nemeki" tattausan Murmushi me sauti ta saki sannan tace, "Ya ABU!! to amma dai bazance komai ba dan kuwa ka fini gaskiya nagode da tunawa dani" jin tana ƙoƙarin kashewa yasa yayi saurin dakatar da ita, yace, "idan na manta dake tamkar fa na manta kaina ne kinga kuwa daga lokacin na fita daga sahun masu hankali, Eeeshu har yanzu kin kasa sakin jiki dani kamar baki sanni ba? amma nasan ba haka kikewa Khaalif mohammad ba ai" ƴar dariya tayi tace, "to ai nafi sanin Khaalif ɗin ne shiyasa kaifa sai yanzu nasanka amma daa labarin ka kawai nakeji"... murmusawa yayi har sai da haƙoransa suka bayyana sannan yace, "tab gaskiya ba haka yakamata ayi ba, ni na riga khaalif Mohammad zuwa duniya dan haka ni yakamata kifara sani kafin shi" Dariya tayi tareda cewa, "gaskiya kana da abun dariya, ga wanda nafara buɗar ido na gani ga kuma wanda zan fara sani, beyi maka kama da tatsuniya ba kuwa???" yanayin yadda take maganar yafi komai ɗaukar hankalinsa ba shiri shima yafara dariya kamar yadda takeyi, jin tayi shiru yasa ya sauke numfashi sannan yace, "ko ɗaya yafi min kama da wasa amma, ni nasan Khaalif ya riga ya mamaye duk inda nake tunanin za'a tsakura ni nasan kinfi shaƙuwa dashi har cikin rai" .. da sauri tace, "a'a a'a rufamin asiri Khaalif ɗin da baya son ganin farin ciki na??"" Ido huɗun da sukayi dashi ne yasa tayi saurin haɗiye sauran maganar tana ƙwalala masa ido. kallon mage da ɓera suka shiga yiwa juna kafin ya matso tareda miƙo mata hannu yace, "mugani keda waye???" Kallon wayar tayi taga har zuwa lokacin ABU be katse ba da sauri ta katse ta bankaɗa cinyarta ta jefa wayar sannan tasauke ɓoyayyar ajiyar zuciya a dake tace, "ai ba taka bace tawa ce" Yace, "na sani kawai gani zanyi naji ana ambaton sunan marayan Allah bansan laifin da na aikata ba" Murmushin gefen baki tayi tace, "cewa tayi Ayeeshan yaya Khaalif shine na faɗa mata gaskiya ko ƙarya nayi??? gaskiya ce ba son ganin farin cikina kake ba idan kuma kanada hujjar kare kanka to??" Durƙusawa yayi kan guiwarsa yana fuskantar ta, kamar ze fashe da kuka yace, "Ayeeshah wallahi ban taɓa yin wani abu da gayya dan ɓata miki rai ba kuma bana fatan nayi wannan daga yanzu har zuwa lokacin da raina ze bar gangar jikina, ina son farin cikin ki sai dai bansan meyesa kika zaɓa mana irin wannan rayuwa ba, ina amfanin na ƙuntata miki kin ƙuntata min kenan rayuwata batada wani amfani Ayeeshah ko meye nayi banayi miki dai-dai abunda nake sa ran ya saki farin cikin sai naga ya saki ɓacin rai ƙanwata wai shin ni kaɗai ne mutum mara sa'a da ya kasance haka a duniya?? bana iya yiwa mutum abunda ze faranta masa kenan?? shiyasa wani lokacin nakanji inama ni ba rayayyen mutum me tsawon rai bane inama na mutu tin kafin na sanki Ayeesha, bana jin daɗin ɓata miki rai da nakeyi sai naji bazan iya yafewa kaina ba" Ido ta zuba masa jikinta yayi matuƙar sanyi takasa furta masa ko uffan sai hawaye da suka cika idanunta. Jin shirun nata yayi yawa yasa yace, "Ayeesha hakan ma ya ɓata miki rai ko?? kice wani abu dan Allah" Murmushi me ɗauke da wani Sirri ne ya wanzu akan fuskarta ta kauda kai tareda cije gefen leɓenta ta girgiza kai tareda cewa, "a'ah banida abun cewa ne indai kaji nayi shiru kasan dai baki na sai kace Reza haka yake idan kaji be furta ba to be samu abunda ze faɗa bane, karka wani damu kanka idan natashi magana wata ma ko ni kaina sai na faɗa nake ganewa" Murmushi ta sakeyi kafin tace, "ya akai yau ka dawo da wuri??" ƙululun da ya tsaye masa a maƙoshi ya haɗiye da kyar sannan yace, "nima kaina ban zata haka ba kawai canjin yanayi ne, ni bari naje waje dama Mama ce tace na tambaye ki ina kika ajiye mana mukullin ɗakin mu" Tace, "uhm bansani ba, sai dai ka tambayi Sayid " Miƙewa yayi tareda cewa, "shikenan" a daddafe ya fita sai faman cizon leɓensa yake yana rintse ido, duniya rawar ƴan mata wannan tayi gaba wannan tayi baya to shima misalin haka rayuwar ta gara masa, zuwa yanzu ya yarda babu yadda za'ai Ayeeshah ta yarda da duk wata hujjar da ze faɗa mata da sunan ba dan gayya yake mata wani abun ba, be ƙi ba ko ranar da ya furta mata asalin abunda ke ƙunshe a zuciyarsa sai dai bayajin ranar zata zo, bata bashi damar da ze iya bayyanar mata da hakan. ABU. Murmushi me haɗi da ƙwallane ya suɓuce masa cikin ransa yana cewa, "Khaalif Mohammad sai dai muyiwa juna uzuri SO yayi tafiyar ruwa da yayanka na riga na sabauta da Son Eeeshu ina kuma matuƙar kishinta". Jose. da ABU suna zaune suna hirarsu irin ta abokai Jose yace, "ABU....... (banson gulma😒 kun wani buɗe kunnuwa kuji zance to sai a shafin gaba🤭🤭🤭😂) Share da Sharhi pls Takun Nan Dai… MARUBUCIYAR✍🏿✍🏿✍🏿... SIRRIN ƘETA A JINI ƊAYA TAJMAHAAL paid book. IB ƊAN WANKA😂 tareda... RINTSIN SO. *INDO CE* [7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 6* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Yace, "ABU bani lambar Ayshan Mama mana" Kafeshi yayi da ido yana masa kallon tuhuma ba tareda ya nuna masa komai ba yace, "kayi me da ita?" Ƙasa ƙasa ya sakeyi da ido kafin yace, "kai me kake da ita?? banson iskanci fa ko ka fini kusanci da ita ne?? yadda kakejin kai ɗan uwanta ne haka nima nakejin kaina dan haka idan zaka bani bani idan bazaka bani ba ka faɗa da manyan baƙi". ABU yace, "daɗi na da kai fa saurin hawa daga tambaya sai zarar zance? ta jina ban fika kusanci da itaba amma a zahirance nafika tinda kai ko lambarta bakada yanzun ma be zama lallai idan amfani kanka bane, to bazan bayar ba idan zaka nema da kanka ruwa ya rage naka, har ɗan wuya nayi saboda neman lambar nan dan haka bazan bayar ba" Jose yace, "haka kace ko??" ABU yana dariya yace, "eh idan kana shakka ma ka dena inason ganin wane lokaci zaka ɗauka kafin ka samu dan na lura lambarta ba gama gari bace, Hala ma su Salma ke neman ta??" Shiru Jose yayi yana ɗan tunanin ko dai ya faɗawa Aminin nasa gaskiya?? wata zuciyar tace a'a kabari kafara samun kanta tukunna sai kaji daɗin faɗe, lumshe ido yayi sannan yace, "eh tinda su kaɗai ne mutane ba?" ABU yace, "dama na sani ai, tashi mu fita mana nagaji da zama" Jose yace, "to tafida ni kuma banajin zuwa ko ina doka ta hanani yawo dan haka sai ka dawo" Komawa yayi ya zauna tareda cewa, "saboda nine gantali daɗi ko abi doka a zauna lafiya??" Dariya Jose yayi yace, "bari kawai ABU Ni ke tausayin doka amma ita bata tausayi na, jiya ma nasha wahala a aiki wallahi sai ka tausaya min wani bincike suka bani me ɗaure kai ba shiri na sambaɗa musu ƙaryar rashin lafiya nayo nan sai litinin nake tunanin komawa aiki ka'in da na"in" ABU yace, "Allah sarki abokina Allah ya bada nasara" Jose ya amsa da "amin" Haka suka cigaba da hira cikin nishaɗi batareda ɗayan su ya gane cewar ɗan uwansa yana son abunda yake so ba, kasancewar babu wanda ya taɓa zaton ko da wasa hakan zata faru yasa ko tunanin abun ma be zo musu ba dukansu, shi dama ABU idon hangensa yafi sauka akan Khaalif, shi kuwa Jose ji yake tamkar shi kaɗai ne mutum da yake sonta duk duniya dan yana jinta ne tamkar itace rayuwarsa hankalinsa da tunanin sa kuma yasa a ransa babu wani mutum da zeyi mata irin son da yake mata har abada, shiyasa baya ma tunanin komai idan ba nata ba. Yau sosai Azumin yake wahalar da ita tayi shawal da ida ko tafiya ma da ƙyar takeyi sai bin katifa idan kuwa a tsaye take to tana jikin bango, Khaalif Mohammad yana shigowa yayi tozali da ita yafara yimata dariya, ko kallonsa batai ba dan kuwa ƙara mata ɓacin rai yake dama haushin kowa takeji, bayan sun gaisa da Mama ya ɗakko kujera musamman ya zauna harda tagumi ya zuba mata ido abun yayi masa matuƙar daɗi yadda take zumɓure zumɓure da murguɗe murguɗe shi yafi tafiya da imaninsa, shi sai yaga ma ta ƙara kyau hancin nan nata yayi wani zuwait dashi idon sunyi firi firi duk da ba ƙaunar buɗe su wanwar take ba. Ita kuwa kallon nata ma da yake jitake ina wuta kusa ta jefashi ko zata huta da takaici, batada bakin yimasa magana dan haka ta fashe da kuka tana cewa, "wallahi Mama kiyi masa magana Allah idan nayi masa abunda ze zo yana kuka kar kiji haushina, wallahi badan ina tausayinsa ba da sai na hanashi shaƙar iska me daɗi a duniyar nan" Taƙara ɓarje baki ta cigaba da kukanta ido rufe. Mama tace, "tofa? a dalilin me?? har wane laifin yayi miki da zakice haka bana hanaki maganganun banzar nan ba wai???" Tace, "kina gani fa dariya yake min kuma sai nayi masa abu yaje yai ta ƙunci ko?? badan ina tausayin ka ba Khaalif da ka ɗanɗaba kuɗar ka wallahi" Cike da tausayin kansa yace, "Ayeeshah kiyi haƙuri iya hakama ya isheni badan ina da tsawon rai ba fa da tuni na haɗiyi zuciya na mutu Ayeeshah, dama bakyason gani na ai karki damu wata rana sai labari bazaki ganni ba Ayeeshah, amma ki dena kukan nan dan Allah banaso kina kuka saboda ni, wasa kawai nake miki amma ina neman afuwarki" Share ƙwallar ta shigayi tana ƙara turo baki gaba. Mama tace, "Allah wahidun, kai jama'a ke ba'a isa ace bari ki bari ba ko?? zan ɓata miki rai fa Aisha meyesa bakida kunya ne??" Murmushi me ciwo Khaalif Mohammad yayi kamar wanda akaiwa dole yayi magana yace, "Mama ki ƙyaleta dan Allah, hakan shine farin cikinta ki ƙyaleta ko menene zatai min tayi min indai hakan ze sa taji daɗi ni me iya jure mata ne tinda ita takasa jurar nawa kwainanen" Rausayar da kai Mama tayi tareda cewa, "toh Allah ya sauwaƙe ya kuma shirya ni dai iya haka zance" dariyar ƙarfin hali yayi yace, "amin Mamanmu" Lokacin Aisha tini ta shige ɗakinta tana cigaba da sharar ƙwallah dama ƙiris take jira dan kuwa abubuwa da dama sun tare mata ta rasa mafita. Jose haka shima ya shiga laluben inda ze samu lambarta sai da ya gama shan tashi wuyar sannan ya sameta a wajen ƙanwarsu ƴar ƙanin Umman sa, sai da ya samu sannan hankalinsa ya kwanta sai dai har ila yau ya kasa kiranta. Tsakanin shida ABU kuwa babu wanda yaƙara tayarda zancen. Azumi ashirin da tara akayi watan sallah ya kama washe gari aka tashi da sallah. Farin ciki a wajen Aisha biyu ya haɗe ga murnar an kusa auren Anti Laila ga farin cikin sallah, ansha kwalliya kamar ba gobe. tsakaminta da Khaalif kuwa sai kallon kallo dan kuwa babu me cewa ɗan uwansa cikal saboda faɗan da suka sha ta shata masa rashin mutunci, tin lokacin yakejin shakkar yimata magana ba dan baya so ba sai dan gudun abunda ze je yazo ta yuwu idan ya faɗi magana ɗaya ta faɗa masa biyu masu zafi dan haka ya janye bakinsa ya kulle, maganin kar ayi kar a fara. Ranar biyu ga sallah ma bar mata gidan yayi gaba ɗaya ya koma gidan kakarsa wadda ta haifi mahaifinsa. Rana ta biyar ne kamar daga sama taji sallamar ABU da Jose bata wani yi mamaki ba dan kuwa ya gaya mata zasu zo ko takansu bata bi ba ta cigaba da sabgoginta, tana zaune Mama ta shigo ɗakin da fara'ar ta tace, "Aisha ku shirya su Jose zasuje gidan kawun ku sai kuje kuma kunga kun huta dama su Khadija sunata tambayar yaushe zakuje musu" Da sauri ta miƙe tana cewa, "bari ki gani yanzu kuwa zan shirya ɗazu kuwa nida Sayid muke lissafin zuwa" Nuriya tace, "kai amma Allah ya tsindima su a Aljannah dama yawo nakeso amma wannan matar tace yau bazata ko ina ba" Aisha tace, "da ƙafata kike yawon?? banson ruɗanin zuci kuji iskanci fa dole sai zan fita zaki fita??" Dariya Nuriya tayi tana cewa, "zauna sababi su gudu su barmu kinaji Mama tana sauri suke" Murguɗe baki tayi tace, "su fi ruwa gudu dallah" Nuriya tace, "temaka dai kiyi saurin" Bata saurare ta ba ta cigaba da shirya. Ba ɓata lokaci ta shirya cikin wata atamfa riga da siket ta murza ture ka ga tsiya ba wata kwalliya tayi ba daga hoda ba ƙari ko kwalli bata sa ba sai man leɓe. Dai-dai lokacin da suka fito su ma su ABU sun fito ido ya zuba mata dan kuwa baze iya yiwa kansa shamaki da kallonta ba. Jose kuwa sai dai satar kallonta da yake dan baya so su haɗa ido. Kasa shiru ABU yayi yana murmushi yace, "Eeeshu irin wannan shan kyau haka?" Yalwataccen murmushi ta saki tareda kauda kanta gefe tace, "kai Ya ABU harda zagi?" Ido ya zaro yana dariya yace, "kaii Eeeshu ni waye da zan zageki?" Murmusawa kawai tayi takasa magana dan kuwa ɗagowar da zatayi sukai ido huɗu da Jose kowannen su ya basar shi gaba ma yayi ita kuma sai da ta jira ABU yayi gaba sannan ta rufa masa baya ita da Nuriya da Sayid da Shaheed. Sai da suka tsaya jayayya wajen tuƙa motar sai da ƙyar ABU ya karɓa dan kuwa Jose ya tirje baze ja ba a cewarsa shine ya kawo su dan haka dole yanzu ABU ne ze ja. tinda suka fara tafiya batace ƙala ba sai su Nuriya da suke surutu tareda Sayid ABU da JOSE ma suna hira kaɗan kaɗan dan dukansu hankalinsu ba a jikinsu yake ba yafi karkata ga Aisha, ita kuwa tunanin yau da goben rayuwarta ya sakota gaba dan haka duk ta manta dasu sai aikin tunani take. Daga baya ma ABU ya kunna sauti a motar dan haka kowa yayi shiru wanda be iya bin waƙar ba ma ya saurara. har sukaje suka dawo babu wanda ta kula a ciknsu, dama Jose kasancewar ba wata magana suke ba yasa bata ce masa ƙala ba, shima be tinkari yimata magana ba dan be ga fuska ba. har zata shige gida ABU ya katse ta da cewa, "yau ba surutu ko Eeeshu?" Gyaɗa kai tayi alamar "eh" Ya murmusa sannan yace, "shikenan sai wani lokacin ko?" Yanzu ma gyaɗa kanta taƙarayi har abun yaso bashi dariya sai dai ya danne. Ze ƙara magana Jose da takaicin yadda take saurarar ABU shi kuma ko kallo be isheta ba ya ishe shi yace, "sauri fa muke ka sani zaka tsaya surutu" Dariya yayi kafin yace, "to naji" bata tsaya sunyi sallama ba tayi cikin gida sosai taji daɗin dakatar dashi da surutun da Jose yayi. bayan ta idar da sallar isha tana zaune wayarta ta ɗauka ta tsira mata ido, tunanin Saifu ne ya faɗo mata idan bata manta ba rabonsa da kiranta haka siddan wai dan suyi wata magana tin farkon Azumi, lumshe ido tayi tareda sakin murmushi me ɗauke da ma'anoni, aranta tana tunanin "anya kuwa ze iya kiran kansa masoyi? idan ma aka kirashi da sunan sai ya amsa?? kwata kwata beyi mata kama da masoyi ba, ya riga da ya gama cutar ta ya danne duk wata damar da take da ita gashi yanzu yasa ta shiga ruɗanin SO ta kasa banbance wa take so iya abunda ta sani kawai yanzu ko sunan Saifu bata cika son taji an ambata ba, idan kuwa ta tuna labarin aurensu sai zuciyarta tafara bugawa, tana matuƙar tsoro da fargaba gami da tunanin Anya kuwa ze iya riƙe ta ya bata kulawa?? batajin ze iya hakan gareta amma dan karambani ya nemi aurenta to me yake nufi da hakan?? ko dama yayi ne kawai dan cutar da ita?? zata iya zaman aure da mutum koda bata taɓa son shi ba amma banda wanda baze iya bata kulawa ba. Langaɓar da kai tayi tareda sakin murmushin gefen baki tace, "bazan iya bujirewa iyaye na ba Saifu ta nan ne kawai ka samu tasiri a kaina, amma indai har ba da gaske kake ba watan watarana dole zaka karaya gaskiya tayi halinta a lokacin dolen ka kuma ka barni na auri wanda nake so. Saifu kuwa shi harkokinsa kawai yake baya tunanin ma kiranta kwata kwata yafi maida hankali akan harkar kasuwancin sa shine abunda yafi bawa muhimmanci be damu da kulata ba koda ta Whatsapp ne mafi yawanci ma itace take fara yi masa magana a hakan ma wani lokacin sai yaji kamar ta takura masa. *INDO CE..* [7/5, 10:51 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 7* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* kwanci tashi ba wuya gashi har lokacin bikin Anti Laila yayi Aisha sai rawar kai take tin saura kwana biyu su tafi taje ƙunshi da kitso washe gari akai mata baƙi tayi rangaɗau yayi mata kyau sosai. Washe gari kuwa tin safe ta riga kowa shiryawa ta zauna ta cancara kwalliya kamar ba ita ba. Suna zuwa da ABU tafara yin tozali amma sai ta ɗauke kai tayi kamar bata ganshi ba tayi gaba, Rookha ce ta katse mata tunanin ta da cewa, "barka da zuwa ƴar halak yanzu nake maganar ki wallahi!, irin wannan shan kwalliya haka gashi Yaya Mohammad Khaalif baya kusa da ya gani ya biyamu kuɗinta " Taƙarasa maganar tana dariya. Itama dariya tayi tareda jan hannunta suka shiga ciki dan kuwa bata son abunda ze jawo ɓacin rai tsakaninsu kuma ta lura shirye shiryen da ABU yakeyi kenan" Da yake gwanar surutu ce Rookha ga Nuriya a gefe sai abun yayi rabajau tinda suka zo basu huta ba faɗi wancan faɗi wancan gasu duka gwanayen rawar kai ne. Miƙewa Aisha tayi tareda cewa, "Rookha kuzo mu zagaya mana wallahi nagaji da zaman surutun nan" fitowa sukayi suka shiga zagaye a gidan suna gaisawa da wanda basu gaisa ba, Nuriya tace, "dan Allah kuzo muyi waje mana" Kafin ma ta rufe baki tini Aisha tayi gaba tana cewa, "sai kun tawo" Rookha tayi saurin zuwa kusa da ita tana cewa, "wallahi jirani, wai wacece wannan ban santa ba fa" Aisha ta murmusa tace, "dama taya zaki santa bayan zuwan ki Kano ɗaya" Harara ta zumbuɗa mata tana cewa, "banson iskanci fa wallahi ba zuwana ɗaya ba kema kin sani" Dariya tayi tareda cewa, "Nuriya kenan ƴar ƙanwar Baba na ce gata nan itama sahun ku ɗaya tarkacen surutu" Nuriya tace, "kice ke bakyayi mana, a'ahh yau naji" Rookha tace, "barta kawai iya takunta tayi, shegiya zata gayawa mutane magana" Dukansu kawai tafiyar suke amma hankalinsu ba'a jikinsu yake ba, bama kamar Aisha da gaba ɗaya hankalinta baya kusa tunanin ta inda zata ga Khaalif Mohammad ya ɓullo kawai take. Ba zato sai ji tayi ta bangaji mutum tayi baya taga taga zata faɗi, a zabure yace, "Ashshah!!! tareda riƙo hannun ta idanunsa a warwaje zuciyarsa tsalle kawai take dan ya gama bayarwa Taje ƙasa" Ganin yadda ya firgice yasa ta ƙame ƙyam sai taga nata tsoron me sauƙi ne akan nasa bilhaƙƙi a gigice yake, ido ta zuba masa har wani lokaci yayinda shima itan yake kallo. zazzafar iska ya furzar tareda lumshe ido sannan ya saki hannunta da yake cikin tafin hannunsa, a sanyaye yace, "ki dinga bi a hankali dan Allah, idan kika faɗi a tiles ɗinnan zakiji zafi sosai" Kallon hannunta da ya riƙe tayi haka kawai ta tsinci kanta da sakar masa murmushi idonta a ƙasa ƙasa a ɗan kunyace tace, "zan kula" Jinjina kai yayi tareda maida kallonsa ga Nuriya da Rookha a marai-rai-ce yace, "ku dinga kula da ita dan Allah" Rookha tace, "to" kallon Aisha tayi tace, "to ƴar yaye muje sai mu dinga kula dake ko ƴar gol? tinda mu ba mutane bane" Murmusawa yayi yana shafa kai yace, "kai hajiyar gigi ba haka nake nufi ba naga kamar bata san mutane bane shiyasa kar taje ta ɓata ta barmu da sallallami" Dariya suka sa ita kuwa tayi ƙasa da kai takasa ce masa uffan dan ba ƙaramin kwarjini yake mata ba. Nuriya ta gaisheshi bayan sun gama dariyar, ya amsa cikin sakin fuska tareda tambayarta yaushe suka zo ta gaya masa, jinjina kai yai sannan yayi gaba yana cewa, " ku kula fa" Suna fita Rookha tace, "bari naje na dawo yanzu ba daɗewa zanyi ba ku jirani fa" suka amsa da "to" Zatayi magana muryar ABU ta katse ta, " sannun ta da zuwa Autar Mata jinjina ta ban girma, naga yau shareni ake ma an samu ƴan uwa da yawa ko??" Dariya tayi gami da rausayar da kai tace, "ba haka bane Ya ABU kawai ina sauri ne kar Mama ta ɓace min narasa inda tayi" Murmusawa yayi gami da cewa, "da wasa nake miki fa naga kinsha kyau sosai kamar yau itace ranar" yayi maganar tareda kashe mata ido ɗaya. juyawa tayi tana dariya tace, "tab ni dai ka dena ma cewa haka dan Allah" Yace, "to na dena dan nasan ma idan ranarce kwalliyar sai tafi haka" Nuriya tayi tsaram tace, "wallahi kuwa ai ranar dole ma na tsikari rayuwata da tsinke" Yace, "kema dai kya faɗa" Gaba tayi tana cewa, "Ya Allahu shikenan kuma kema biye masa zakiyi nifa ban isa irin wannan maganganun ba, sai kin tawo bazan jira ki gama zubar ba " dariya ABU yayi yana cewa, "shikenan tinda kin tsorata nima bari nayi ciki sai kun dawo" Nuriya ce kawai ta amsa masa da "Allah yasa" huci Aisha ta furzar tareda jingina jikin bango tana rintse ido abubuwan da suka faru ne a yanzu suka shiga dawo mata, jikinta yayi sanyi ƙalau. Nuriya ta kalleta ta murmusa kafin tace, "a dai bi a hankali kar a kasa mana Yaya Saifu dan na lura Ya ABU da ƙaninsa da abokinsa duk sonki suke" Da sauri ta waro ido tana kallon Nuriya kallon tuhuma batasan lokacin da tace, "ƙarya kikeyi yarinya wallahi banason irin abunnan da kuke min Nuriya wannan ai rashin albarka ne ance miki kuma ni kaɗaice mace a duniya da dukansu zasu taru a kaina hala kin fara haukane???" Nuriya tace, "kull!! wallahi karki sake ki ƙara gayamin kalmar hauka akan gaskiyata, ke yanzu tsakaninki ga Allah Aisha sai kice Ya Khaalif baya sonki idan kince sauran baki sani ba??, kiji tsoron Allah ki faɗi gaskiya" Laƙwas tayi ko kallon Nuriyar taƙiyi dan kuwa ta fita gaskiya. Nuriya kuwa ganin haka yasa ta murmusa tareda cewa, "ƙaryar banza ni zakiyiwa molanka idan baki sani ba in gaya miki ke kanki kina son Ya Khaalif kuma dukansu babu wanda zaki bugi ƙirji kice bakya son sa sai dai in ba gaskiyar zaki faɗa ba" ajiyar zuciya ta sauke kafin tace, "dawo kan hanya mana ya kike da suna Nura kike ko Nuriya?? eh to kin faɗi gaskiya tabbas inason Ya Khalif Moh.. amma a yanzu yayi min tazara kuma shima nasan yana sona, abunda yake firgita ni kuma ina ganin yayansa ma yana so na Ya ABU ina jin tsoron hakan sosai, amma ko zaki haɗiyi zuciya ki mutu bazan taɓa yarda Ya Jose ma sona yake ba wannan ƙarya ne" Nuriya tace, "haka kikace ko?? haka kikace ko?? to wallahi daga yanzu har zuwa lokacin da zaki gane ki rubuta wannan ki aje wallahi yana sonki, kuma idan bakiyi da gaske ba zaki faɗa rijiyar masoya me wuyar fita, dan na lura cikinsu duk bakida gwani, gaskiya ina tausaya musu ma wallahi duk fa basu san akwai kuɗin auren Yaya Saifu akanki ba ko?? gaskiya suna ruwa kawai sai dai suji abu bagatatan sun kama ganye sun saki reshe shi Ya ABU dama Rookha ɗinsa ya ɗauka yabar dakon so abanza" Lumshe ido tayi kafin tace, "Ya ABU kam banajin ya sani amma dai Khaalif Moh.. ai ya sani tinda Ya Saifun abokinsa ne, sai dai kinsan idan mutum ya riga ya zurmawa abu nasan ya riga yayi nitso sosai, babu yadda zamuyi sai dai haƙuri dan banajin ze iya cire sona daga rayuwarsa" Nuriya tace, "wallahi kam shiyasa nake bala'in tausaya masa yana shan azaba a dalilinki Aisha kina son sa amma kike azabtar dashi meyesa haka??" Ƴar dariya tayi wadda da ka gani kasan ta yaƙe ce kafin tace, " bazaki gane ba fa Nuriya kimin shiru kawai, kuma daga yau har ranar da zan auri Saifu indai baki tabbatar min da gaskiyar ki ba duk abunda nayi miki ke kika siya karki manta akwai wannan yarjejeniyar a tsakanin mu kinji ko??" Nuriya tace, "na yarda ko menene kiyi, ke nifa tin ba yau ba nake ganin tsantsar sonki a idon bawan Allahn nan amma tinda baki yarda ba shikenan wata rana zaki gazgata" Da harara kawai ta rakata a cewarta bata da lokacin da zata ɓata wajen jayayya akan abunda baze yuwu ba. Da daddare. sauri sauri take dan ta cimma su Rookha da suka haɗa tawaga suna tafiya suna hira suna raha. duk ta gama gajiya dan batada wani lokacin zama sai kace itace uwar bikin itada su Nuriya Rookha Naseera da sauransu ba zama daga can sai can su zolayi wancan su fitini wancan aikinsu kenan. Har ta gifta ta kusa da motar dake ajiye a gefe taji ya kira sunanta cikin ƙwarewa kamar a bakinsa aka samu Ashshah duk da dama mafi yawanci shi kaɗai ne yake kiranta da sunan. Cakkk ta tsaya takasa juyowa har sai da yace, "ina zuwa haka naga anata sauri??" Juyowa tayi sannan tace, "inason zuwa gurinsu Nuriya ne" takowa yayi har zuwa gabanta sannan ya tsaya yana fuskantar ta kafin yace, "baki gaji ba??" ɗan murmushi tayi tace, "eh mana sai lokacin bacci tukunna" Yace, "bakya tsoron ki tashi da ciwon jiki??" Dariya tayi gami da cewa, "kai to ko nice amaryar dai ai sai haka, ni kam da nayi bacci shikenan banida wata gajiya" Murmush yayi gami da lumshe ido tareda cewa, "Gaskiya ke ƴar baiwa ce kin ganni nan gajiyar da nayi Allah ne kaɗai yasan iyakarta, bacci nakeji so nake naje na kwanta idan kinji ana nema na ma karki ce kin ganni" Tace, "a'a?? bacci kuma yanzu?? ai kuwa nasan dole ma Ya Abu ze neme ka ni kuma zan faɗa masa gaskiya ta" ya marai-raice a wani irin shagwaɓe yace, "Ashshah bakiji tausayina ba dan Allah?? tinda aka fara bikinnan ban huta ba bakyaso na huta ko??" Da sauri tace, "o'o gaskiya bance haka ba kaje ka huta abunka, nima neman inda zan huta nake amma idan ina tareda su Nuriya ai ba hutu" Yace, "to tinda hakane na ɓoyeki kiyi baccin ki hankali kwance ki ƙyalesu ranar da suka gama nasu sai su kwanta" Dariya ya bata dan haka ta dara sannan tace, "lallai kam kai da kakejin bacci ina kai ina ɓoyeni nayi bacci?? ai kuma nima indai zanji motsinsu bazan iya baccin ba, ka samu kaje ka kwanta kawai" Rausayar da kai yayi yana ƙarayin ƙasa ƙasa da murya yace, "anya kuwa?? zan iya bacci bayan ke baki rintsa ba anya kuwa son kan beyi yawa ba?" Girgiza kai tayi tace, "a'ah babu komai wallahi ko ɗaya kar kayi laka'ari dani dan zaka iya kwana bakayi bacci ba kuwa " Cikin wata narkakkiyar murya yace, "Ashsha bazan iya ba, tinda kika riga kika gayamin kinason yin bacci nima bazanyi ba har sai naga kin nutsu ba iya kwana ɗaya ba koma kwana nawa ne zan iya jura ko bazan kai ba dole na in jarraba" numfashi taja ta sauke tana kallon gefe a take tunanin yadda sukayi da Nuriya ya dawo mata hakan yasa tayi sauri ɗagowa tana kallonsa ganin yayi mata rumfa aka yasa taƙara zaro ido sai a lokacin ta lura da wayo da wayo ya dawo da ita baya har ta dangana da jikin motarsa kuma yayi mata kaka gida ta yadda bazata iya sillewa ba" Ɗan murmushi ya saki tareda shafar ƙeyarsa yana lumshe ido ya lura mamakin ta yadda akai yayi mata hakan take duba da yadda take kallonsa ta kalli gefe da gefe, yasan halinta sarai bata son tsayawa ta saurari mutum kanayi mata magana tanayin gaba musumman idan ta zumuɗanta da wani abun dan haka yayi mata wannan dabarar kuma ta rufta cikin sauƙi" Buɗe idonsa yayi akanta gami da cewa, "zaki rakani??" ƙasa tayi da kai tace, "ina kenan?" Kai tsaye yace, "bakin titi zaki rakani amma fa idan ba damuwa" Shiru ta ɗanyi kafin tace, "to zanje naga ma sun gudu sun barni nima kuwa bazan zauna ba" Murmushi ya saki a ransa yace, "iyayen son yawo ba" buɗe mata gidan gaba yayi ta shiga sannan ya zagaya mazaunin direba (Team Khaalif Mohammad How Market😂😂😂😂😂😂😂🤣) *INDO CE* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 8* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Ajiyar zuciya ta sauke saboda daddaɗan ƙamshin da ya risketa ta lumshe ido tareda jan numfashi ta sauke. Ta gefen ido yake kallonta ya lura hakan yayi mata daɗi dan haka ya murmusa. cikin nutsuwa yake jan motar har sukayi ƴar tafiya babu wanda yaƙara magana, Har ga Allah ta manta ma a inda take dan kuwa neman inda zata faɗi ta mutu take tayi matuƙar gajiya dan haka takejin kamar ya tsindima ta a Aljanna, bata farga ba sai buɗe ido tayi ta ga har sun wuce bakin titin sun ɗau hanya. Zaro ido tayi tareda cewa, "Kalamillah ya haka?? kace titi zamuje kuma naga kana tafiya harda gudu ko dai siyardani zakayi??" Sassauta gudun yayi saboda wata muguwar dariya da ta antayo Masa ba zato ba tsammani, abun ya haɗe masa biyu ga sauran kalamanta ga kuma sunan da ta laƙa masa wai Khalamillah. Yanayin yadda yake dariyar yasa murmushinta suɓucewa murys ƙasa ƙasa tace, "dariyarka abun dariya wallahi" Ɗan tsahirtawa yayi kafin yace, "ai kece kika bawa dariyar tawa dariya, yaushe na zama Kalamillah kuma ban sani ba?" Ɗan turo baki tayi tace, "to ai naga baka son magana ne Salihi da kai" Kallonta yayi kafin ya maida hankalinsa kan titi cikin murya me matuƙar jan hankali da sanya nutsuwa yace, "Ashshah? kin tabbatar kuwa?? ina ganin nafiki surutu fa, dan baki taɓa bani damar da zaki gane hakan bane" Kai tsaye tace, "haba Ya Jose anya kuwa akwai wanda ze fini surutu a diniyar nan??" yana Dariya yace, "shikenan Ashshah tinda kin rama" murmushi tayi tareda lumshe ido sannan tace, "to wai ina zamuje ne haka?" A nutse yace, "kinsan meyesa na ɗakko ki?? nasan kina son yawo a mota da daddare, ko ban faɗa dai-dai ba??" Da mamakin yadda akayi ya iya gane hakan ta zuba masa ido har wani lokaci sannan ta rausayar da kai tace, "shikenan amma kasan dai bana fita tareda kowa idan na ƴan gidanmu ba ko?? kuma idan Mama ta neme ni fa me zance mata?? ka rufa min asiri ka maidani gida kaji Kalamillah?" Ta ƙarasa maganar cikin sigar rarrashi. Murmusawa yayi yace, "Mama kikeji ko??" Gyaɗa masa kai tayi tana ƙara binsa da ido. wayarsa ya kara a kunne duk da batajin me ake cewa sai dai kawai taji yace, "Umma dan Allah idan Mama ta nemi Ashsha ki gaya mata muna tare" Shiru yayi kafin yaƙara cewa, "Umma cewa tayi na rakata fa" Yayi maganar yana dariya tareda kasheta da idanunsa masu matuƙar yimata kwarjini. Da sauri tace, laa? hakama zakace??" Girgiza kai yayi sannan yace, "Umma tinda baki yarda ba sai mun dawo kawai zamuje taga gari ne su Rookayya sunƙi barinta ta huta" Daga haka ya ajiye wayar yana cewa, "to yanzu ai ba matsala ko??" Tace, "eh da sauƙi tinda bata yarda nice zaka raka ba" . murmusawa yayi yace, "yace bakya buƙatar wani abun kuma??" Gyaɗa kai tayi a hankali tace, "eh" Shiru ce ta biyo baya shikuwa sai tafiya yake, iskar dake kaɗawa ba ƙaramin tafiya da hankalinta take ba shiyasa ma batasan tafiyar tasu tayi nisa ba bare tasan lokaci ya tafi. Buɗe idon da zatayi taga ya zaro bindiga ƴar ƙarama piston daga jikinsa yana ƙoƙari saƙalata a wani guri na motar. dakatar dashi tayi da cewa, "dama kai ɗan ta,adda ne??" Idanunsa ne suka ƙara girma ya waresu tasss akanta yana kallonta har na ɗan wani lokaci, shi a tunaninsa tayi bacci ashe lumbu lumbu ce, dariya yayi yace, "Ashshah rigima tayaya me yaƙi da ta,addanci ze zama ɗan ta,adda??" Zumɓuro baki gaba tayi tace, "to ko kasheni zakayi??" Ƙasan titi yayi da motar ya tsayar da ita cakk sannan ya kunna fitilat cikin motar ya kalleta sosai kafin ya murmusa gami da lumshe idanunsa, murya ƙasa ƙasa yace, "Ashshahh!!! idan na kashe ki ni kuma sai na rayu?? idan bakya duniya kenan ni miye amfanin rayuwata??, sai naji kamar na fashe da kuka Ashshah muna zaman lafiya me yakawo zancen mutuwa?" Ɗan murmushi tayi a ranta tana mamakin yadda yake kashe murya yanai mata magana har wani lallaɓawa yake, ga irin maganganun da yake mata masu kama da jirwaye sai dai har yanzu bata gazgata faɗar Nuriya ba bata yarda sonta yake ba sai dai haɗuwar jini. Jin shirun tayi yawa yasa yace, "mamaki kike ko??, bazaki mutu yanzu ba insha Allah" Girgiza kai tayi da sauri tace, "a'a banyi mamaki ba, tab ni wacece da bazan mutu ba idan lokacina yayi?, ai ko yanzu ma a shirye nake" Yace, "da gaske??" Tace, "eh mana" Murmushi me sauti yayi kafin yace, "da kuwa abun yayi armashi kinga idan na mutu gani ga ke labarin ze fi daɗin faɗa ko?? na shirya mutuwa tareda ke dan haka yanzu abunda za'ayi zamu fara tafiya a motar nan muna cikin gudu sai mu tari gaban manyan motocin nan da suke tafiya a titin ko?? kinga gobe da labari kenan" Ƙyalƙyalewa tayi da dariya harda ƙwallah shi kuwa aikinsa ido ne tinda tafara ya zuba mata su sai dai murmushi yake wanda yake ƙara tabbatar da irin farin ciki da shaukin da yake ciki. Sai da tayi me isarta sannan tace, "wallahi Ya Jose a gaisheka nidai kar naje tsautsayi ne yake nemana ko ajali wallahi mu koma gida". Sai a lokacin ya ɗauke ido daga kanta tareda sauke sassanyar ajiyar zuciya sannan yace, "nifa nakasa gajiya da tafiya amma zan koma saboda ke" Murmushi kawai tayi batareda tayi magana ba. lokacin surutun nata ya wuce har suka dawo batayi masa surutun ba maganar ma sai jefi jefi. Ƙoƙarin buɗe motar ta shigayi amma taji a kulle, marai-raicewa tayi tace, "Ya Jose dan Allah buɗe min mana??" Langaɓar da kai yayi shima da yake gwanin shagwaɓar ne kamar yadda tayi magana haka ya mayar mata da martani da cewa, " to Ya Ashshah jirani mu fita tare mana" Sake langwaɓewa tayi ta kwantar da kai a jikin kujerar tana ɗage gira ɗaya tareda cewa, "ohhh dan Allah kai sauri mana!!" Ya gyara zama kafin yace, "to ko da kaina zan kaiki ne??" Da sauri tace, "aa rufan asiri mana bawan Allah" Fitowa yayi yana dariya cikin ransa yana jinjina mata akwai iya rigima ya daɗe da shaidar hakan, zagayawa yayi ya buɗe inda take zauna, dama jira take tayi zumbur ta fito amma ya tare mata hanya dole tafasa tafiya ta jingina a jikin motar tana jiransa. Haka kawai yakejin kamar kar su rabu bayason barinta ta ƙara sille masa dan bayajin zasu ƙara irin wannan kasancewar. Yana shirin yayi magana muryar Mama Hasiya da tazo wucewa ta katseshi , "au ɗana kaine anan?? wacece wannan ko sirikar tawa ce??" Da sauri Aisha tace, "aa Mama Hasiya nice wallahi" dariya Mama Hasiya tayi tana cewa, "ohh ashe ta Khaalif Mohammad ce kaima yakamata ka fito mana da taka" Lokacin da tagama maganar tini ta wuce dan kuwa sauri take. Suman tsaye Jose yayi yayinda zuciyarsa ta shiga harbawa da sauri sauri lokaci ɗaya zuffa tafara keto masa ya ɗebi lokaci ba tareda yayi wani motsi ba sannan ya shafa kansa ya yarfar da hannu, takawa yayi sau uku yaƙara riƙe ƙugu sannan ya juyo yana kallon Aisha wadda mamakin yadda taga ya burkice ya hanata motsawa. Matsowa yayi dafff da ita cikin razani da ruɗani yace, "Ashshah da gaske ne?? nasan ko yanzu ko anjima ko an daɗe da yawa da ƙaunarki zan mutu amma ban taɓa zaton itace ajalina ba, Ashshah idan kina soyayya da ƙanina Khaalif ni kuma ya zanyi da sonki da ya gama mamaye jini da tsoka ta?? " Tsananin firgicin da ta shiga yasa takasa furta komai illa jikinta da yake wata irin kakkarwa kamar me jin sanyi kanta ya shiga juyawa zuciyarta tafara tsalle kamar me shirin ɓalle ƙirjinta ta fito. Ƙara matsawa yayi daf da ita yayi mata rumfa, cikin rufewar da idanunsa sukayi yace, " kar kiyi mamaki da gaske nake karkiji kamar a mafarki tabbas rashin samun soyayyarki tartsatsin azabane ga rayuwata rasaki yafi komai haɗari gareni rayuwar zatayi min tsanani, na riga na haukace na ɗimauta da sonki tabbas idan narasaki zan haukace kiji tausayina ki tallafi rayuwata karki barni na shiga gararin duniya, ASHSHAH kece nutsuwa ta tabbas idan bana tare dake ni mahaukacine kuma mutum mara amfani, na faɗa wata rayuwa a yau saboda jin kina son Khaalif, bazan hanaki abunda kike so ba kuma bazanƙi haƙuri na rungumi ƙaddarata ba, abunda nake so kisa a ranki kawai shine zan mutu da tsananin so da ƙaunarki kuma zan rayuwa a cikin RINTSIN SONKI wanda ya zama babbar illa gareni, bazan iya dena sonki ba har sai bayan raina kuma idan bakya sona zan ɗauki haƙuri na barki da wanda kike so bazan shiga rayuwarki na tauye miki haƙƙi ba, amma INA SONKI Aishatul,Humaira" shiru ya Ɗanyi sannan ya cigaba da cewa, "Gobe da wuri zan tafi saboda yanayin aikina ina fatan sake ganinki ko ganin ƙarshe ne zuciyata zata ɗanyi sanyi, zanje nayi jinyar zuciyata Ashshah"... Daga haka yayi gaba yana haɗa hanya yabarta a wajen, idanunta da suke mata zafi kamar an watsa barkono ta zuba masa har ya ɓacewa ganinta, takawa tayi da nufin tafiya amma takasa jitayi ƙafafunta bazasu iya ɗaukarta idanunta suka dena gani sai duhu da ya mamaye su ga wani shu'umin jiri da ya ɗebeta tayi luuuuuu zata faɗi. Da sauri Khaalif ya tareta tafaɗa kan ƙirjinsa, liff tayi kawai duk da batasan jikin me tafaɗa ba amma tasan tasamu madafa sai da tafara dawowa dai-dai sannan tagane a jikin mutum take, a hankali ta buɗe idonta ta zuba akansa. cikin rawar baki yace, "Ayeesha meke faruwa haka?? wani abun akai miki??? menene gaya min" Da ƙyar ta iya girgiza masa kai alamar ba komai ta ƙaƙalo murmushin gaibu ta ɗora akan fuskarta. Ba tareda ya gamsu da abunda tafaɗa ba yace, "daga ina kike ke kaɗai haka? tin ɗazu nake nemanki ban ganki ba Ayeesha hankalina yaƙi kwanciya ina kika shiga, meye wannan da har yake miki irin wannan barazanar, hankalina baze iya jura ba Ayeeshah!" Zamewa tayi daga jikinsa cikin rarrabewar kalma tace, "ba-cci na-ke-ji" yace, "shikenan muje kisha ruwa amma naga kamar kinajin ƙishi, halama bakida lafiya kike ɓoye min"… Kasa magana tayi sai lumshe ido kawai ga zuffar da tafara yimata wanka. Jan hannunta yayi zuwa ciki can wani ɗaki da babu kowa ya nufa da ita sai da ya zaunar da ita a bakin ɗan madai-dai-cin gadon ɗakin sanna ya ɗakko mata ruwa ya miƙa mata, ta karɓa batareda ta jira komai ba ta shanye ta miƙa masa kofin, ta sauke wani gwauron numfashi sannan tace, "nagode" tattausan Murmushi ya sakar mata tareda jinjina kai sannan yace, "inada damuwa fa Ayeesha kuma kece silar komai kuma kece maganin damuwar, Amma bazan gaya miki ba ki ki kwanta ki huta kawai" *INDO CE..* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/IMbPeZwcVmK8hZ9UIJluKW *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 9* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* rintse ido tayi da ƙarfi tana girgiza kanta da ya kamu da wani azababben ciwo lokaci ɗaya, da ƙyar tace, "Khaalif nagaji da jura yau dai ka gaɗamin meye damuwarka da kake ikirarin nice silarta?? bazan iya bacci ba idan baka sanar dani ba dan hankalina yaƙi kwanciya" Zama yayi a gefenta sannan yace, "kin shirya saurara??" Da kai ta bashi amsa. Ya cigaba da cewa, "damuwata ba komai bace face yawan rashin jiton dake tsakaninmu bayan daa, ba haka muke ba, meyesa kika sauya min Ayeeshah?? kin zaɓi ƙuntatamin hakan shine ke saki farin ciki wane laifin nayi miki me girman haka?" Daurewa kawai take tana sauraronsa a yanzu batada burin da ya wuce ta samu gurin da zata raɓe tayi kuka saboda abubuwa iri iri da suke mata turnuƙu, kamar me koyon magana tace, "nima ba'a son raina hakan take faruwa ba amma ko menene ma laifinka ne" Yace, "bazan musanta ba, iyakar abunda zance shine ta wace hanya zamu samu dai-daito?? meyesa kike wulaƙantani Ayeesha?" Kamar zata fashe da kuka tace, "banaso kake irin wannan maganar banajindaɗi nifa ba wulaƙanta ka nake ba" Yace, "nasani amma ba lallai kina tunanin yadda kike jefani cikin tsanani da hakan ba, kuka ya zamo abokin rayuwata a dalilinki damuwa itace al'ada da duk wasu ɗabi'u na a yanzu tunani shine abincin da nafi amfani dashi kafin komai, da tini fa wata rana sai dai ki wayi gari kiga babu Khaalif a dalilinki, nasha yin tunanin tafiya wata duniyar na nesanta dake amma idan na tuna hakan rashin adalci ne ga iyayen mu sai na fasa, saboda ke har banason idan na fita na koma gida saboda ke nakan tsiri tafiyar da zatayi tazara tsakanin mu, amma duk da hakan zuciyata takasayin sanyi koda yaushe ƙuna take amma hakan baya sawa ki tausayamin Ayeeshah kuma daa, ba haka kike min ba" Shiru tayi saboda duniyar tunanin da ta luƙaƙa tausayinsa yasa zuciyarta taƙara yin rauni kasa ɗago ido ta kalleshi tayi saboda bazata iya haɗa ido dashi ba. murmushi me ƙuna yayi kafin ya cigaba da cewa, "meyesa hakan take faruwa?? nasan daa, kina sona Ayeeshah meyesa yanzu kika tsaneni?? bakyason ganina kullum wulaƙancin da kike min kalarsa daban kamar ba nine wanda idan banci abinci ba hankalinki baya kwanciya amma yau kece me cewa bakida asara dan na kwana da yunwa daa, zato nake ko wani ke tunzura ki amma yanzu na gane karatun, a baya kin soni nikuma lokacin nakasa nuna miki irin son da nake miki a tunani na wannan dalilin ne ya kawo haka" .... katse shi tayi da cewa, "ka ma dena wannan tunanin ba shine dalili ba" Gyara zama yayi yana fuskantar ta sannan yace, "zaki gaya min??" Girgiza kai tai alamar "aa" Ya ƙara da cewa, "Ayeesha wallahi ban taɓa ƙinki ba ƙaddarace tasa nakasa saurarar soyayyarki har lokacina yaƙare, lokacin akwai wadda nakeso ita ko sani ma batayi ba inason sanar mata amma nakasa har sai da lokaci yayi tsawo kuma abun kaico Ayeeshah tace bata sona, kai tsaye na ɗauki hakan a matsayin hukunci na na yin wasarere da soyayyarki Ayeeshah daga lokacin hankali da mutsuwata ya dawo kanki sai a lokacin na tabbatar da ke nakeso ba ita ba kuma lokacin kin fara sarewa daga gareni ƙaddara tasa a lokacin da nake ƙoƙarin tinkararki a lokacin aka tsayarda maganar aurenki da abokina Saifu a lokacin ne nasan me ake nufi da tashin hankali a lokacin na tabbatar na faɗa cikin ƙuncin rayuwa a lokacin nasan nashiga RINTSIN SO me wuyar war-wa-ruwa ban gama shiga gararin rayuwa ba sai da naga kin dena saurarar duk lamura na abunda ya shafeni ma bakyason ganinsa ko jinsa na yankewa kaina hukuncin haƙura ko dan abotar tsakanina da Saifu nayi tunanin sonki ze iya raguwa gareni amma sai naga kullum ƙaruwa yake har ya kaini matsayin da a yanzu bazan ita ɓoye miki ba fuskata ma tana iya nunawa nasan daa, bakisan ina Sonki ba amma yanzu nasan kin fahimci hakan dan yagama mamayata, abunda baki taɓaji a bakin Mohammad ba Ayeeshah yau kiji INA SONKI kuma zan faɗa na mai-mai-ta ko a gaba waye, kiyi haƙuri babu yadda na iya ne idan ban faɗa ba ni kaina bansan irin ruɗun da zan ƙara shiga ba bayan wannan, gashi yanzu kinyimin nisa yanzu bakyasona Saif kike so na rasaki na saki damata ta guje min ni mutum ne mara sa'a da nakasa karɓar soyayyar mace mafi kyau da daraja komai ya kwarkance min Ayeesha na" Ko motsin kirki Ayeeshah takasayi illa baza kunnawa da tayi tana sauraron sa, babu shakka kalamansa sun ratsa ta kuma sunyi bala'in tasiri akanta sosai kalmar INA SONKI ta ɗarsu a cikin zuciyarta kuma taji tayi na'am da ita sai dai akwai ƙalu bale me girma a rayuwrta wanda shi kansa Khaalif ɗin tasan ba lallai ya iya jura ba, Babu shakka tasani yana shan baƙar azabarta yakamata lokacin wannan yaƙare, shin duk ina Soyayyar da tayi masa a baya?? ina tsananin tausayawar da take masa??? ko waye yace tana son Saif kuwa besan Asalin Barbela ba duk da tasan kowa tunanin da yake kenan sai dai abun ba haka bane" Tunane tunane harda marasa hujja sukai mata rubdugu, muryarsa ce ta katseta cikin sanyi yace, "Ayeeshah baki ce komai ba indai har wulaƙantani da muzguna min yana saki farin ciki dan Allah ki cigaba karki dena zan iya jurewa wata rana sai labari"... Wasu zafafan hawaye ne suka yararo kan fuskarta sai da ta ɗanyi gyaran murya saboda cunkushewar da zuciyarta tayi sannan tayi magana, "ka dena fa, dan Allah ka dena cewa ina wulaƙanta ka Ya Khaalif zuciyata tartsatsi take min kuma ka dena tunanin bana sonka har gobe har kullum ma INA SONKA sai dai nasan bazan aure ka ba shiyasa nake nesanta da duk wani farin cikin tsakanin mu bana saurararka ina janye jikina daga gareka domin ina tsoron muyi shaƙuwar da bamuyi a baya ba sai yanzu kuma azo a shiga tsakanin mu ina tsoron hakan shiyasa ko ganinka bana son yi ni tawa ƙaddarar kenan a lokacin da na soka ba ni kake so ba a lokacin da muke son juna kuma wani ya shiga tsakanin mu" a sanyaye yace, " ba kina son Saif ba?? karki damu dani kiyi farin cikin ki nima abunda kikeso shi nakeso ina abu da dama dan naga Saif ya saki farin ciki ina son ganin farin cikin ki shiyasa nai ta haƙur-ƙurtar da kaina dan gudun ɓacin ranki, ni me iya jurewa ko wane ƙalu bale ne akanki ki manta dani kawai". Murmushi me ɗaci tayi kafin tace, "kake iya faɗe da bakinka?? waye yagaya maka ina son Saif? shi ba komai bane face ZAƁIN IYAYE NA har yau nakasa yarda ina son shi a iya wannan matsayin kawai na ajiyeshi" Murmushin yaƙe yayi yace, "babu yadda muka iya sai haƙuri farin cikin iyayenmu shine namu iyayenki iyayena ne bazanso mu mayar dasu ƙananun yara ba, ki ɗauki Saif wani abu me daraja gareki hakan ze sa ki samu salama daga iyayenmu mu kasance masu haƙura da farin cikin mu domin wanzuwar farin cikin iyayenmu" Jan numfashi tayi sannan tace, "hakan ne ma yasa nayi haƙuri na danne na karɓe shi a matsayin wanda zan aura badan haka ba da tini nayiwa kaina iyaka dashi, be bi takaina ba kawai sai jinayi ance shi zan aura" Murmushin baƙin ciki tayi ta cigaba da cewa, "dole na haƙura dan mahaifina amma idan ni ba rabonsa bace??? uhmm... akwai lokacinda asalin masoyina na gaskiya ze bayyana har yanzu lalube muke a duhu bamusan waye ze ɗauke wasan ba, shima akwai lokacinda ze zo dole ya ƙyaleni indai ba shine Me Rabon ba kuma inajin hakan a jikina tabbas akwai wannan ranar, ranar da za'ayi tankaɗe da rairaya da yardar Allah" Jinjina kai yayi yace, "hakane Allah yasa mu dace Ayeeahah, amma da kin faɗamin bakyason sa tin farko ai da na ɗauke ki mun gudu ko??" Yaƙarasa Maganar yana dariya. Itama dariya tayi sosai kafin tace, "sai kace ba namiji ba??" Yana dariya yace, "gaskiya da kuwa son zuciya da ɓatan hanya me kyau yayi yawa" Lumshe ido kawai tayi ba tareda tace koma ba. Zeyi magana Rookha ta shigo da sallama tace, "Mama na nemanki Aisha" Gyaɗa kai tayi cikin sanyin jiki. Kallonta yayi cike da kulawa yace, "Ayeeshah tashi kije" gyaɗa kai kawai ta sakeyi Tana son tashin amma jikinta yayi nauyi gashi bata gaji da ganinsa ba, sai da yaƙara magana tareda miƙewa tsaye sannan itama ta tashi. Tafiya take tana haɗa hanya saboda ɗan jiri da takeji gashi idanunta kamar an watsa yaji sun wani ƙeƙashe. Hannunta Rookha taja tana cewa, "wallahi ba ruwan Mama mu muke nemanki ina cewa ina kika shiga ashe kina can kina kashe Love" Bata iya cewa, ƙala ba sai murmushin da baya wuce kan leɓe" Kallo ɗaya Nuriya tai mata tagane tana cikin matsanancin yanayi dan haka tace, " yakamata muje mu kwanta wallahi" Rookha tace, "wallahi nima nagaji dama ga wadda muke nema nan kuma mun samu dan haka mu kama mu tafi" .... Ita lokacin ma har tayi gaba, Sai da tasha ruwa kaɗan saboda bushewar da maƙoshinta yayi sannan ta kwanta. Har suka gama surutunsu kowa yayi bacci ita baccin ya gagareta tunane tunane sin addabeta, har gari ya waye batayi wani bacci me daɗi ba sai juye juye da take da ƴan ƙananun mafarkai, abun ya tsaye mata a rai ainun, ta kasa babbance tsakanin Jose da Khaalif abun tambayarma menene dalilinda yasa kowa yake sonta? shin dama ana samun mace irinta a duniya wadda da namiji ya ƙyalla ido akanta shikenan? anya ma kuwa son gaskiya suke mata ba na wani abu ba??, so da yawa takanyi wannan tunanin amma idan ta tuna kalaman Jose sai taƙara jin takaraya batajin ko da wasa akwai kalmar da ya faɗa mata wadda ba gaskiya ba ta lura da gasken gaske yake har yafi Khaalif Mohammad zurmawa dan ahi a lokaci ɗaya ya bayyana mata abunda bata taɓa zata ba amma ga wanda taso tin asali Khaalif shi kuma yakasa wani motsi har saida lokacin ya wuce. Tin safe ta tashi tayi wanka ta haɗe cikin wani lesi kalar marun me ratsin bulu kwalliyar ta-ta ba wata bace daga hoda sai man baki ko kwalli ba son sakawa take ba, Amma duk da hakan be hana asalin kyawunta bayyana ba. Duk wannan kwalliyar da tasha taƙi sakin jiki da kowa sai ƙasa ƙasa take da ido har yanzu jikinta a sanyaye yake ko abincin kirki bataci ba a hakan ma sai da suka haɗa ta da Mama sannan ta nutsu. Safiyya ce ta kalleta cike da kulawa tace, "amaryar Yaya Khaalif ku zo ku rakani can mana" Nuriya ce tafara tashi tana cewa, "muje idan kika biyewa ta Yaya Khaalif ɗinnan bazakiyi wani abun kirki ba munyi wanka munyi kwalliya me muke jira??" Miƙewa Aysha tayi tana murmushi tace, "muje nima nagaji da zama gara naje nasha iska" Sanye yake cikin ƙananun kaya riga fara tassss da wando baƙi sai gilashi baƙi wanda ya hana ganin ƙwayar idonsa, kansa a ƙasa yake tafiya, yayinda mahaifiyarsa take gaba yana take mata baya tafiya suke cikin nutsuwa Umma tanayi masa magana kaɗan kaɗan amma yayi banza ko ɗaya be ɗauka ba dan hankalinsa ba a kanta yake ba. tin daga nesa ta hangosu taji gabanta ya faɗi har ƙasa rage saurin tafiyar tayi saboda fargabar isa inda suke sai dai ya zama dole dan kuwa tawowa suke suna nufo su, ganin ta zuba musu ido yasa Umma ta sakar mata tattausan murmushi tareda yimata alamar tayi kyau. Ƙasa tayi da kai tana murmushi wata ƴar ƙaramar kunya ta kamata. Kasa motsawa tayi har suka ƙaraso wajen Umma ta tsaya tana tambayarsu inda zasuje, sai da suka gama gaisawa da kowa sannan ta durƙusa har ƙasa ta gaisheta, ta amsa cikin fara'a da kulawa gami da sa musu albarka gaba ɗaya. ganin sunyi gaba yasa tafara sauri dan ta cimmusu, caraf taji ya riƙo hannunta, tsayawa tayi cakk ba tareda ta juyo ba, cikin nutsuwa ya juyo inda take bayan ya zare tabarau ɗin nasa ya zuba mata ido, cikin wata kasalalliyar murya yace, "juyo na ganki mana Ashshahhh!!!" juyowa tayi kamar yadda yace amma kanta a ƙasa takasa haɗa ido dashi. Sassanyar ajiyar zuciya ya sauke gami da ƙara yin ƙasa da murya sannan yace, "Murmushin ki yakan sani cikin farin ciki rashin sa kuwa shi yake nasarar tarwatsa farin cikina ya rabani da nutsuwa ta, Kintashi lafiya??" bata san lokacin da ta ɗago idanunta ta zuba masa ba takasa magana sai dai kallo, hakan ya bashi damar jefa ƙwayar idonsa cikin nata, lallausan murmushin sa me ƙara kashe mata jiki da jefa ta cikin wani yanayi yasaki sannan yace, "nakasa yin bacci me daɗi saboda fargaba da rashin sanin a wane hali kika kwana na saki damuwa ko??" Ɗan riƙe kunnen sa yayi tareda cewa, "Afuwan bazan ƙara ba, na kasa sarrafa kaina ne babu yadda na iya sai na faɗa miki banida mafitar da ta wuce wannan dan idan baki sani ba ma zuciyata zata hukuntani yana da kyau na gwada miki koda kwatan-kwacin irin ƙaunar da nake miki Ashshah ko zan samu wannan damar?" Wani dogon numfashi taja tareda sauke kallonta zuwa ƙasa a hankali tace, "......................................." (😜🙄baza kuji ba to🤭) *INDO CE..* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 10* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Tace, "Umma tana jiranka kaje ka rakata gida" Gyara tsayuwarsa yayi yana murmushi yace, "tayi tafiyarta saboda itama tanason kasancewa ta tareda ke" Ƙara yin ƙasa tayi da kai tana wasa da zoben azurfar dake hannunta idanunta sun kawo ruwa kamar wadda take jiran ƙiris ta fashe da kuka" Cikin nutsuwa yace, "bazaki cemin komai ba Ashsha? shikenan zan wuce sai mun sake haɗuwa ko??" Gyaɗa masa kai tayi alamar "eh" Yace, "kije ƙawayen ki suna jiranki" Batace ƙala ba tayi gaba yana tsaye har ta isa inda su Nuriya suka tsaya jiranta sai da ya tabbatar ta isa gurin sannan ya furzar da huci ya juya ya cigaba da tafiya. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tareda goge ƙwallar da tafara zubo mata dan gudun kar su ankara. Rookha tace, "ke kuma daga gaisawa sai zama?? ko ance miki lokacin jiranki garemu??" Murmushim ƙarfiin hali tayi tace, "na sani ko kuna dashi? kodan idan baku dashi ma taya zaku tsaya kuma??" Safiyya tace, "wallahi kuwa ai Ya Jose ɗinne akwai mutunci akwai rashinsa amma ke naga taku tazo ɗaya ya fiye shan ƙamshi da yawa" Gaba tayi tana cewa, "idan kun gama muhawarar nayi gaba, cikin ranta kuwa godewa Allah take da suka kasa gane asalin tsakaninta dashi. Su Jose suna tafiya babu daɗewa Aisha ta dawo gurin Mama ta maƙale sai shagwaɓa a tashi a tafi gida daga baya ma fasa kuka tayi, Sosai Mama tayi mamakin faruwar hakan kuma tambayar duniya taƙi bata amsa, dan haka ta sauke alamar tambayarta akan Khaalif Mohammad dan tasan shine kaɗai wanda ze iya ɓata mata rai har tace a tafi gida. Ba shiri Mama ta harhaɗa i nata i nata Sayid sai faɗa yake dan kuwa ba haka yaso ba kuma babu yadda ya Iya dolensa tafiya ta kamashi. Aisha kuwa da ta tabbatar tafiyar za'ayi sai tayi murƙisisi ta dena kukan, tana shirin fita ne tayi karo da Khaalif da kallo ɗaya ta gane ba a wani nutsuwa yake ba dan haka ko kallon inda yake batayi ba, dan tasan ƙarshen zancen meyesa takeson tafiya" Kamar yadda tayi tunani kuma hakanne tambayar da yafara jifanta da ita kenan, "meyesa zaki tafi yanzu??" Ba tareda ta kalleshi ba tace, "inason komawa gida ne" Yace, "na sani ai amma nan ma ai ba'a daji kike ba ko??? kodan saboda Jose ya tafi ne kema zaki tafi????" Ido ta ware akansa tana masa kallon mamaki ya gyaɗa mata kai domin tabbatar mata da abunda ya faɗa" Gaba tayi tana cewa, "duk daɗin gidan wasu kuwa be kai ya gidan ubana ba dan haka inason komawa can, sai ka tawo kawai" Da ido ya rakata yana mamakin yadda ta juye lokaci ɗaya, kar dai Jose ya rushe duk wani tubalin ƙaunarsa a cikin zuciyarta" Tunanin da yafara ɗarsuwa a zuciyarsa kenan lokaci ɗaya yaji ko sunan Jose baya so yaji an ambata wani masifaffen kishi yayi masa rumfa. Har suka isa babu wanda ta saurara suna sauka ma ɗaki ta wuce ta kwanta. sai bayan sati ɗaya da yin bikin sannan tafara dawowa hayyacinta shima ba warewa tayi fess ba duk ta rame tayi duhu saboda tunane tunanen da tasa wa ranta duk tambayar da Mama zatayi mata amsar ɗaya ce "ba komai" Yau suna zaune daga ita sai Nuriya suna taɓa hira kaɗan kaɗan Nuriya tace, "nifa gaskiya yau sai kinyi min fashin baƙi, kuma kinsan akwai yarjejeniya a tsakanin mu to nabar wannan ma dan nasan yanzu kin gazgata ko kuma nace Yaya Jose ya gazgata miki yanzu abunda kawai nakeson ganewa tunanin da kike yake ƙarar dake a tsaye haka" Tambayar tazo mata a bazata kuma tayi mata girma aka. Shiru tayi tana wani tunanin lokaci ɗaya jikinta yayi sanyi idanunta suka ciko da ƙwallah. Kamar baza tai magana ba sai kuma tace, "tunamin makoma ta nake Nuriya ni abun tausayi ce tabbas ina tausayin kaina kuma ina tausayin wanda suke so na ina shiga tashin hankali a duk lokacin da na tuna ƙalu balen dake gabana inaga ƙarshen rayuwata ne yayi wa'adi na yaƙare shiyasa wannan wahalar ta kunno min kai, banason Saifu Nuriya kuma shi zan aura, Jose ya riga ya haukace da sona ina tsoron rayuwarsa ta ɓalɓalce saboda ni alhakinsa baze barni na rayu cikin salama ba, Khaalif ya daɗe yana azabtuwa duk saboda ni, wane hali zasu faɗa shida ɗan uwansa??, jinake inama zan mutu da na raba gardama, Meyesa wai sai ni Nuriya?? ba ni kaɗaice mace ba meyesa suke min so me tsanani ni kaɗai?? na shiga RINTSIN SO Nuriya cikinsu nakasa gane WA NAKE SO kuma wa yakamata naso?? zuciyata takasa samun nutsuwa da ɓangare ɗaya meyesa nakejin babu wanda zan iya juyawa baya a cikinsu?? " Nuriya da ta saki baki ido da hanci tana binta da kallon mamaki da al,ajabi sai a lokacin ta samu damar cewa, "ke Aisha?? bakyason Saif dama nufinki?? kin haukace ne da kike cewa kina son mutum uku a lokaci ɗaya?? kodai kin zauce ne Aisha??" Wasu zafafan hawaye ne suka samu nasarar Wanke mata fuska ta girgiza kai cike da tausayin kanta tace, "Wallahil azim kinji nayi miki babbar rantsuwa gaskiya na gaya miki bance ina son su ba amma jinake kowa yanada babban matsayi a zuciyata bansan so ba Nuriya saboda ni mahaukaciya ce ni ba mutumce kamar kowa ba tabbas na zauce indai yadda nakejinsu har cikin raina shi ke nufin ina son su to tabbas nagama haukacewa, bansan ina zan sa kaina naji daɗi ba dole ne ciwon tunane tunane ya kamani nan gaba ma nasan zuciyata ce zatayi tsawa ta tarwatse na mutu, be zama lallai ni me tsawon kwana bace dan ruhi na baze iya ɗaukar wannan masifar ba, Saif beyi min adalci ba beyi nazari akaina ba kawai da son zuciyarsa yayi amfani ni ban taɓa sonsa ba koda sunan wasa ban kawo a raina ba, kawai na wayi gari naji duniya ta ɗauka Saif yana sona nima ina sonsa, meyesa ze min haka?? kuma hakan be wadatar dashi ba babu zato ya kai maganar gurin mahaifina shi kuma ya amince musu ya basu ni, kawai sai naji labarin ya sauya daga batun soyayya zuwa ga aure, tin a lokacin raina ya ɓaci na gaya masa bana son sa amma yaƙi ya amince haka ya haɗani da su Antin mu sukai min faɗa nikuma wacece da zan bi ZAƁIN IYAYE NA ba?? na ajiyeshi a wannan matsayin kuma nake binsa sahu da ƙafa a matsayinsa na wanda zan aura duk hakan be burgeshi ba sai ya banzatar dani tukunna, banajin ze iya kulawa dani koda ya aureni ko a waya ba dai Saif yace bari na tuna da waccan ba sai nayi magana yace I love u na tsani kalmar nan kamar yadda na tsani Saif dalilinsa yasa naji banason jinta kuma banason auren Saif ki faɗawa wanda ranki yake so bana son sa kuma bazan so shi ba hasalima na tsaneshi na tsani auren nasa, rashin sani ne yasa Babana ya yarda cewa ina son Saif kuma xan aureshi ne kawai saboda Babana bayan haka kuwa da ya gane ni ba tsarar sa bace" Sallallami Nuriya ta shigayi tana tafa hannuwa, jinjina kai tayi gami da cewa, "tabb lallai ma Saifu sai yanzu na yarda bashida tausayi da imani, tabbas ya shiga haƙƙin ki ya jefa ki cikin Tara ba Uku ba, ya haneki da wanda kike so sannan ya sallama ki sai kace ance masa ke ba mutum bace??? amma ba komai akwai Allah kuma zeyi miki sakayya ko ba daɗe ko bajima, wallahi raina ya ɓaci Aisha gaskiya an zalumce ki amma sai dai kiyi haƙuri shine mafita dan bazaki tayarwa iyayenki hankali ba, amma yakamata maza su dinga tunani kuma su dinga yimana adalci dan akwai irinsa da yawa a duniya wannan ba kyautawa bace zalunci ne kuma duk wanda ya zalunci wani Allah ze sakawa mutum ƙarshe kuma abun yaƙi yimusu kyau, rayuwar aure fa ba zaman ayi a tashi bane taya yake tunanin da haka ze iya rayuwa da mace ta har abada ko ba ke ba?? dan dai kina da haƙuri ne amma in wata ce da tuni anyi an gama" Share ƙwalla tayi kafin tace, "badan ina haƙurin ba ai da tuni anyi walle walle komai yaƙare, mutumin da yake sa ran rayuwa ta har abada dani kuma yake banzatar dani kamar abu mara amfani banajin son gaskiya ne wannan,, hmm... indai nice akwai lokacin da gaskiya zatayi halinta bazan damu kaina ba yayi kawai lokacinsa ne wata rana da kuɗi akace yayi bazeyi ba" Nuriya tace, "Allah ya kawo muku mafita amma kuna cikin yanayi wallahi bama dai kamar Khaalif ni shi nafi tausayawa" Murmushin takaici kawai tayi batareda tace uffan ba. Tana zaune tana tufka da warwara kiran ABU ya shigo bin wayar tayi da ido har wani lokaci sannan ta ɗauka tareda yin sallama, amsawa yayi sannan ya cigaba da cewa, "barka da wannan lokaci kina lafiya?" Ɗan murmusawa tayi tana cewa, "lafiya lau" Yace, "masha Allah jiya muna magana naga kin gudu a online ina fatan dai lafiya" Tace, "wallahi lafiya kawai dai na sauka ne" Yace, "kenan bakyaso kiji abunda zan faɗa miki ne yasa kika gudu?" Shiru ta ɗanyi tana tunani tabbas zata iya cewa hakan ne duba da yadda ya ɗakko zancen tasan baze wuce hakan ba shiyasa ta gudu dan batada amsar da zata bashi, a zahiri kuwa cewa tayi, "aa ai zaka ganni idan anjima kawai lokacine ban samu ba" Da sauri yace, "ahh ba sai kin wahalar da kanki ba ba wani abun dama zance miki ba dan magana ɗaya ce zuwa biyu, nazo da ƙoƙon barata ne kuma ina fatan zan samu karɓuwa" Shiru tayi tana sauraren sa jin tayi tsitt ne yasa ya cigaba da cewa, "Eeeshu haƙiƙa Allah ya dasa min tsananin sonki a zuciyata tin kina ƴar ƙarama har zuwa yanzu babu abunda ya canja sai ma wanda yayi gaba, na kasa ɓoye miki saboda inaso nayi rayuwa ta har abada tareda ke dan Allah kiyi tunani kafin ki yanke min hukunci zanyi farin ciki idan ya kasance na sameki a matsayin matata Eeeshu zanji kaina tamkar wanda yafi kowa sa'a aduniya nasha gwagwarmayar rayuwa tin daga lokacin da mahaifiyata ta rabu da mahaifina narasa asalin farin ciki na narasa gata da kulawa yanzu rayuwata tana buƙatar ki Eeeshu domin kece sirrin farin cikina" Tinda tayi ƙasa da kai ko cikall takasa furtawa sai wani kurman kuka da take mara sauti sai cin zuciya da azabtarwa, babu shakka taji labarin irin mugun halin da yafaɗa a baya yayi rashi a yanzu kuwa yanada kyau ace ya samu farin ciki ita kanta zata so ta zama silar wannan farin cikin nasa tinda dai ita ya zaɓa kuma ya damƙawa kyautar zuciyarsa tareda ɗora sa rai gareta. Katse kiran tayi ta saki wayar ta rufe fuskarta da tafukan hannunta tana cigaba da kuka. ABU. da kallo yabi wayar yana mamakin yadda akayi ta tsinke ta baya son takura mata dan haka be ƙara kiranta ba ya cigaba da tsammanin warabbuka tareda saran watarana zata amince idan Allah yaso. *INDO CE* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 12* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* "Ban damu da damuwa ta ba Ashsha damuwarki kawai itace damuwa ta koda ni nayi farin ciki nasan ke bazakiyi ba dan haka nima babu amfanin nawa farin cikin" Rausayar da kai tayi kafin tace, "ni kam banda wata damuwa" Ɗan murmushi yayi yace, "idan nace ki rantse zaki iya rantsewa??" Ƙasa tayi da kai tafara wasa da ƴan yatsun ta dan kuwa bata rantsuwa akan gaibu. Ganin tayi shiru yasa ya rausayar da kai sannan yace, "nasan kina cikin damuwa kuma ina ɗaya daga cikin wanda suka haddasa miki damuwar shiyasa gaba ɗaya banida walwala, mutane da yawa sunce na canja kuma kece kika kawo wannan canjin da ana ƙorafin bana magana yanzu kuma kowa cewa yake Jose ya canja kamar ba shi ba to wai ya ake son ganina ne?? faɗawa soyayya dama yana sa mutum ya zama wani daban ne? kodan ni mahaukacin so nake shiyasa kowa yake iya gane na susuce" Rasa abun cewa tayi sai dai ta kalleshi ta sunkuyar da kai. Hakan yasa ya cigaba da cewa, "Ashshah dan Allah ki amsa min tambayar nan kina so sona ko bakya sona??, Na ƙagauta da son jin wannan amsar ki faɗa min gaskiya dan Allah karki ɓoye min" Dogon numfashi taja kafin tace, "lokaci yana tafiya fa" lumshe idanunsa yayi gami da haɗiye mugun yawu sannan yace, "hakan yana nufin bakya sona kenan?? idan na kira ki bakya ɗauka bakya sauraron duk wani abunda ya shafeni, idan na tuna hakan zuciya takan gaya min bakya sona amma nakasa yarda bakya sona har sai na samu tabbaci daga gareki, inada damuwa sosai Ashsha ba iya Khaalif Mohammad ne yake buƙatar kulawarki ba nima ina buƙatar samun farin ciki daga gareki amma matsayina be kai nan ba, da gaske rayuwata zata ƙare a gantale da gaske mafarkin samun ki a matsayin matata da nake baze tabbata ba kenan nida farin ciki mun bawa juna baya?? da gaske bakya sona haukana kawai nake?? "hasbunallahu'wani'imal'wakil" itace kalmar da ta shiga mai-maitawa a cikin zuciyarta sabida turnuƙun zafin da take mata, da kyar ta iya dannewa tace, "kenan?? idan nace bana sonka kaima zaka yarda?? bana fatan ranar da zata zo na iya gazgata maka bana sonka" Ɗan gyara zama yayi sannan yace, "banga alamun kina so na bane amma fa kiyi haƙuri nayi miki shigar sauri bana iya sarrafa kaina ne akanki ko abunda ya shafeki, komai yanada mahaɗin rayuwarsa shukoki da tsirrai mafi yawanci ruwa ne abokin rayuwarsu ko ga mu mutane rayuwa tana tsanani idan ba'a samun ruwa sosai kiyi tunani idan ya kasance babu shi duka fa?? rayuwar zata yuwu kuwa?? misalin hakane nakejin zata faru dani kinada muhimmanci gareni na riga nayi zurfi nayi nisa banajin kira akan sonki, so yana buƙatar tausayi da kulawa Ashshah amma ni bana samun ko ɗaya daga gareki, kin kasa yarda da irin tsananin ƙaunar da nake miki me kike so nayi wanda ze sa ki gazgata cewa na mutu akan sonki?? ki faɗa min ko mene zanyi indai be kaucewa hanya me kyau ba na shiryawa fuskantar duniya saboda ke amma narasa duk wannan damar kin kasa yarda dani kin kasa yarda ina sonki" Tinda yafara magana kanta yana ƙasa tunanin kalamansa take wanda suke mata kamance-ce-niya da na Khaalif Moh.. ɗinta, shima yakance bata son sa bata tausayin sa ina suke son ta tsoma ranta ne taji daɗi?? ya zatayi da soyayyar mutum uku da take ƙara ruruwa a cikin zuciyarta da kowane lokaci?? shin bazasu iya tausaya mata ba suyi mata uzuri?? sai da ya gama sannan ta dago ta zuba masa idanunta da suka fara canja kamanni cikin rawar murya tace, "banajin daɗin hakan da kake faɗa Jo kenan yanzu babu wanda zan faɗawa magana ya yarda?? bazance ina sonka ka yarda ba kenan Ya Jose??, bazan ɓoye maka ba ina son Ya Khaalif kuma kaima ina sonka Murmushi yayi yace, " amma baki taɓa faɗamin ba ko so kike zuciyata ta tarwatse?, duk da nasan Khaalif ya fini matsayi Amma ke allurar cikin ruwa ce me rabo ka ɗauka idan ba rabonka bace ko ka ɗauka sai ta sille, amma duk da haka inason ji daga gareki domin na tabbatar, yau ɗaya kuma ni kaɗai kice kina so na badan ni ba dan Allah" tafukan hannunta tasa ta rufe fuskarta tana murmushi tareda sauke ajiyar zuciya, tace, "yanzu idan na faɗa zaka yarda??" Yace, "da gudu ma kuwa" Tace, " to shikenan ina sonka" kukan da yaci ƙarfinta ne yaƙarasa kufce mata ta shiga rero shi ba ji ba gani. Sosai hankalinsa ya tashi ya shiga tambayarta abunda ya faru amma tayi banza, da sauri ya riƙo hannunta cikin sigar rarrashi yace, " Ashsha kiyi shiru dan Allah ki dena kukan nan idan nine na ɓata miki rai ki gafarceni ba'a son raina hajan ta faru ba bazan iya yin abunda ze zamo ɓacin rai gareki ba, ki tausayawa masoyin nan naki ki dena kuka har kisa zuciyata ta buga kukan ki barazana yakewa rayuwata banaso na mutu batareda na mallakeki ba ki huce dan Allah" ƙoƙarin dakatar da kukan ta shigayi amma takasa sai ma ƙoƙarin buɗe motar ta fita da tafarayi.. Shi kam kansa yafara kullewa yarasa meye musabbabin kukan nata, baze iya barinta ta tafi tana kukan ba dan hakan yaɗora motar kan titi ya sau tafiya. Kai tsaye wani ɗan madai-dai-cin gida ya shiga sannan ya tsayar da motar ya zagaya ya buɗe mata, ba musu ta fito hannunta yakama yayi ciki da ita, gidan ba kowa da alamu shi kaɗaine yake karakaina a cikinsa a falon yayi mata mazauni wanda yaji ado dai dai gwargwado shima mazauni yayiwa kansa a gefenta cikin sanyi yace, "zan fi jin kwanciyar hankali kasancewarki anan bazan iya juya baya na tafi na barki kina kuka ba bansan halinda kike ciki ba zan iya rasa tunani na" ƙasa tayi da kai cikin mamakin yadda akai ta janwowa kanta wata rundunar yanzu ba fata ba ace wani yaga lokacin da suka zo ai ta gama yawo kowa da kalar matsayin da ze ɗauki abun" ruwa ya ɗakko ya kawo mata yace, "kisha ruwa ko zakiji daɗi" karɓa tayi tareda yimasa godiya. A waje kuwa yaron sa Haruna murmushin da yafi kama da na mugunta ya saki kafin ya ɗauki wayarsa ya tura kira, jimm kaɗan aka ɗauka yayi saurin cewa, "barka da wannan lokaci Oga ka gagari kowa" A ɗayan ɓangaren wanda aka kira Oga ya saki wani murmushi tareda gyara zamansa sannan yace, "ina jinka meke faruwa??" Haruna yace, "to Oga dai maganar gaskiya giwa tafaɗa tarko dan Ogana gaba ɗaya yanzu yafara rasa makamar aikinsa saboda yafaɗa soyayya da wata yarinya yanzu duk baya wani abun arziki a yanzun haka yana cikin gidan sa tareda ita waye ma yasan abunda sukeyi? amma babu dama mutum yayi farin ciki sai yace dan me ashe dama kowa ɗan iska ne sai dai ta wani tafi ta wani zafi" Oga yayi dariyar sheƙeƙe ta yaro mankaza sannan yace, "zan turo maka kuɗi kaje kayi bincike ka gane ko ƴar waye sannan ina so ka sa ido akan abunda sukeyi ina buƙatar abunda idan na watsawa duniya uwarsa ma zataji kunyar fita daga gida shi kuwa idan ya fito mutane da kansu zasu gama min dashi" Haruna yace, "Allah yaja zamanin Oga ka gagara Allah yayi maka jagora Oga" Oga yayi dariya hehehehe yace, "Haruna kenan to ai ni akan YUSUF JOSE babu abunda bazan iya yi ba" "Wannan haka yake Oga" Faɗar Haruna kenan. Da haka sukayi sallama Haruna ya cigaba da kiwon su yana lelewa a wajen dan sanin adadin lokacin da suka ɗiba atare. Kallonsa tayi kafin tace, "JO ina son tafiya fa" "kenan sai na bari ki tafi cikin damuwa bayan kuma nine na tsindima ki ciki??" ya faɗa yana kafe ta da ido. Murmushi tayi tace, "nifa na dena damuwar banaso ne Mama ta tambaya ace ban je ba" yace, "shikenan muje na raka ki amma fa sai kin maimaita min abunda kika faɗa ɗazu" Ido ta waro tareda cewa, "menene???" Ɗan ƙasa ƙasa yayi saitin fuskarta yana kallonta, itama shi ta shiga kallo tin tana kallon cikin idonsa taga bazata iya jura ba hakan yasa ta sauke kallonta ƙasa laɓɓansa ta zubawa ido tareda lulawa duniyar tunani, Babu tsammani taji yace, "INA SONKI" Numshi ta ja tareda ƙara girman idanunta tsikar jikinta ta yarrfa yarrrr har cikin rai maganar tazo mata a bazata kuma ta firgita dan yanzu tsakani ga Allah tsoro irin wannan kalmar take. ƴar Dariya ya shigayi ƙasa ƙasa tareda cewa, "matsoraciya ta zata haɗiye ta zanyi" ta sauke Ajiyar zuciya murmushi ya suɓuce mata har sai da fararen haƙoranta suka bayyana. Yace, "to ita nake so ki faɗamin amma ka zakice ba ki ba" Miƙewa tayi tana dariya idonta a lumshe tace, "Ina sonka" Murmushin farin ciki ne ya wanzu a tattare dashi ya miƙe tareda surar mukullin motar sa yayi gaba tana bin bayan sa. Sai da ya tabbatar ya direta a inda zataje sannan yayi nasa guri. Ba ita ta dawo ba sai yamma tana tafiya tana murmushi har ta isa gidan, a haraba ta tarar da Khaalid da Shahid suna hira irin ta yaro da babba, sallama tayi Khaalif ya amsa yana sakin murmushi harda ƴar ajiyar zuciya, gaishe shi tayi tana shirin wucewa yace, "jimana matar aboki na" Dawowa tayi tana turo baki gaba. Yace, "dama ba komai bane kawai naga kina murmushi ke kaɗai ne hala yau kinyi katari da wanda kike so Jose dan shi kaɗai naga ana yiwa irin wannan tsadadden murmushin" Yanzu ma murmusawa tayi sannan tace, "kamar ka sani" Sosai magana ta daki zuciyarsa a ransa yace, "shegen bakina ne ya jawomin dama ance kaza garin tone tonenta take tono wuƙar yanka ta to shima hakance tafaru, kawai shaci faɗi yayi dan murmushi a gurinta baya wahala sai dai kowanne manufarsa daban matsayinsa daban amma neman zance yasa shi ya burkitowa kansa kaifaffar magana" Jinsa shiru yasa tace, "Kishi kake ko???" Da sauri yace, "ina ko ɗaya ni banida kishi ai ba kamar su Ayeesha da Ashsha ba" Murguɗa baki tayi tace, "idan bamuyi ba waye zeyi? kaifa neman rigimar ka yayi maka yawa ana cikin kwanciyar hankali ka dinga kawo wani ƙauli da ba adi" .. Yace, "Ayeeshah wasa fa nake miki amma kin ɗauka da gaske" Tace, "ni kuma da gaske nake yau na haɗu da Jose" ya Shafa kai, kawai yace, "wuce gida Ayeeshah bazan iya ji ba" Dariya tayi tace, "ko me nace bazaka ji ba??"… yace, "eh bana buƙata" Tace, "idan nace ina sonka ma baka buƙata??" Ido ya ware akanta tareda cewa, "kaii?? yaya zance bana buƙata kawai baki faɗa ɗin bane, ina sauraren ki" Wucewa tayi tana dariya tace, "nafasa" Shima dariyar yayi dan kuwa ko yanzu yaji daɗi amma ya sha wa kansa alwashin sai ta mai-maita. Mama da taga ta shigo tana dariya bata tambayi dalili ba dan tasan baze wuce tace ɗanki ba. Suna gaisawa ta shige ɗaki tafara cire kayan jikinta da nufin shiga wanka hankalinta ne yakai kan wayarta ta ɗauka tana dubawa taga kiran ABU har guda biyar wanda da alama tana hanya yayi mata su, da sauri ta bi kiran tana murmushi har ta kusa tsinkewa sannan ya ɗauka, Sun kwashi lokaci suna wayar kafin sukayi sallama sannan ta nufi ɗakin wanka sai yauƙi take tana murmushi takunta ma kansa ya canja. Mama dai ta ƙare mata kallo ta riƙe haɓa tareda cewa, "oo yau naga abunda na gani Aisha Indo kin koma macijiya ne?????" *INDO CE..* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 11* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Sai da tayi kuka sosai sannan ta tashi badan ya isheta ko ta gajiya da yinsa ba sanin bazeyi mata maganin komai bane yasa ta barshi ta tashi. Cikin sanyin jiki ta ƙarasa gurin Mama ta lafe a bayanta jefi jefi takan sauke ajiyar ziciya, Mama tace, "ya rasulullah Aisha meke damuwarki ne haka kin ɗai-ɗaice a tsaye amma kina cewa ba abunda ke damunki idan baki faɗa min ba wa zaki gayawa damuwarki??, yanzu ma fa da alamun kuka kikai" Lumshe ido tayi tana murmushin ƙarfin hali tace, "Mama cikina ne yake ciwo fa shiyasa duk na yamutse". Da yake ba me jan zance bace sai kawai tace, "to Allah ya sauwaƙe kece bakyason shan magani sai kinfara ciwon cikin kuma ki ta mita" Ƙara kwantar da kai tayi Kafin tace, "gobe idan Allah ya kaimu zam koma aiki insha Allah" Mama tace, "Allah ya yarda". da amin ta amsa sannan tayi shiru tafara tunane tunane ABU shine yake mata yawo a cikin tunaninta tabbas ze ga rashin kyautawarta da ta katse masa kira kuma bata ƙara bin takansa ba batasan halin da yake ciki ba anya kuwa ta kyauta masa??. zumbur tayi ta tashi kamar wadda aka tsikara tayi ɗaki Mama ta rakata da ido cikin ranta tanayi mata add'ar samun sauƙi da rangwame daga duk wani abunda ya tsananta mata har ta koma kamar susutacciya haka" Wayar ta ɗauka hannunta har kakkarwa yake ta lalubo lambarsa amma sai ta kasa kiransa sai da ta ɗebi lokaci a haka sannan ta canja shawara ta koma wajen tura saƙo tafara rubutu kamar haka, "Amincin Allah ya tabbata gareka ma'abocin murmushi ina fatan kana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, naji ba daɗi sosai kasancewar na katse maka kira ina neman afuwa gareka mutum me daraja da girma a gareni inaso ka sani ko ba yau ba kana da babban matsayi ga Eeeshu kuma ƙaunarka ta samu rinjaye akaina zuciyata ta alaƙantu da kai kuma ina barar sama maka farin ciki a koda yaushe, ina so ka kwantar da hankalinka banaso kayi damuwa hakan ze sa naji kamar bazan iya yafewa kaina ba" Ta karanta ta mai-maita yakai sau huɗu share ƙwallar da take zirya a kumatunta tayi sannan ta tura shi, tana turawa ta ajiye wayar tareda jan dogon numfashi. har ABU ya fitar da rai zata saurare shi a lokacin sai kuma yaji wayarsa ta motsa ya ɗauka ya duba, karo yaci da saƙon ya shiga karantawa jiki na tsuma a gefe guda kuwa yana cike da fargabar yaji tace be samu shiga ba, ƙafafunsa ne suka gagara ɗaukarsa har sai da ya durƙusa kan guiwoyin sa yana ƙara karantawa, rungume wayar yayi tareda lumshe idanunsa da suke masa zafi wasu sanyayan hawaye suka samu nasarar gangarowa, "Alhamdulillah" yafaɗa sannan ya cigaba da cewa, "ina godewa Allah a bisa ni'imomins gareni, banyi zaton haka daga gareki ba Eeeshu kuma insha Allahu zan cigaba da sonki fiye da kaina zan shimfiɗa rayuwata domin taki rayuwar" Ya daɗe a gurin yana murmushi shi kaɗai kafin ya mayar mata da martani. Bata kusa dan haka bata sani ba har sai dare ta ɗakko tana dubawa ta ganshi buɗe saƙon tayi tana binsa da ido "ina godiya gareki ƴar Aljannah kin sani farin ciki fiye da yadda nake tunani, na daɗe ban shiga cikin farin ciki irin na yau ba saboda jin tausasan kalamai akaina daga gareki Hayati ki huta lafiya" idanunta ne suka ƙara girma yayinda take tambayar kanta wai me tace masa?? sai da taƙara karantawa ta gani sannan ta saki murmushi shaf ta ma manta me tace masa dan kuwa a lokacin idonta arufe yake ta shagala da son taga ta faranta masa, " kuma da gaskene har cikin rai abunda ta faɗa??" lallausan Murmushi ta saki tareda gyaɗa kai ta bawa kanta amsa, "tabbas hakane ba gaibu bane kin faɗa masa gaskiya a hakan ma baki baze iya furta iya matsayinsa gareki ba" Kasancewar Nuriya ta koma gidansu yasa takejin duk ba daɗi dan haka kamar yadda ta faɗa tin da wuri ta shirya tsaff domin tafiya aikin, ta fito sai sauke rumfar ido take a hanyar fita tayi katari da Khaalif ido ya zuba mata kafin yace, "barka da warhaka ƙanwata" A ɗan fizge tace, "ina kwana??" Ya amsa da "lafiya lau ina zakije haka" Amsa ta bashi sannan ya kuma cewa, "badan ina sauri zan fita ba da na kaiki da kaina amma ki kulamin da kanki dan Allah, da da yadda zanyi na hana kowane namiji ganinki da nayi dan ke macece me daraja ba kowane ido ne ya kamata ya sauka akanki ba" Murmushi tayi tareda cewa, "insha Allah zan kula" Har tayi gaba da nufin fita ya katse ta, murya ƙasa ƙasa yace, "dama ni kaɗai ne masoyinki duk faɗin duniya da nazama tamkar sarki" Lumshe ido tareda cewa, sai munyi waya ko??" Gyaɗa kai yayi sannan yace, "karkiyi nesa da ita har na kira ban samu ba" Tace, "to" Daga haka tai gaba ba tareda ta tsaya sauraron abunda ze ƙara faɗe ba. tana fita titi ta samu adai-dai'ta sahu ta hau. Aikin tunani kawai take tayi zugum, muryar direban ce ta katse ta, "dan Allah ranki ya daɗe zan ɗan shiga gidan mai idan ba damuwa" Batareda ta kalleshi ba tace, "ba komai" Kutsa kai yayi zuwa gidan man yana shiga wata baƙar mota me baƙin gilashi ta tare masa hanya dan haka ya tsaya yana shirin yayi magana Jose ya fito hakan yasa ya janye bakinsa yayi tsitt. Bata ankara dashi ba har ya ƙaraso sai muryarsa taji yana cewa me adai-dai-tar "sannu fa" maza Rayyan a mayar min da ɗaya motar gida zan ƙarasar da ita da kaina" Wanda aka kira da Rayyan yace, "angama yallaɓai" Da mamaki ta kalleshi ta kalli me adai-daitar kenan ma shine ya turoshi?? ta jefawa kanta tambaya" Hannu ya miƙi mata tareda binta da kallon da yasa taji jikinta ya mutu lokaci ɗaya, yau duk bashi da wata walwala ko da can da basa magana zata iya cewa bata taɓa ganinsa cikin irin wannan yanayin ba shi mutum ne me yawan fara'a maganar ce dai sai anga dama" Kallon ido cikin ido suka shiga korawa juna ganin takasa motsi yasa yace, "a hanya muke mun tare mutane" Hannun nasa ta bi da kallo kafin ta ɗora nata hannun, riƙeta yayi gam sannan ta sakko sai faman kallonsa take batada burin da ya wuce jin dumuwarsa dan ganinshi hakan beyi mata daɗi ba. gidan gaba yace ta shiga sannnan ya zagaya yafara jan motar, shiru ce ta biyu baya har wani lokacin kafin yace, "narasa hankali da nutsuwa ta saboda rashin sanin laifin da na aikata kike hukuntani ta wannan hanyar" .... Ɗago idanunta tayi ta zuba masa har ƙasan zuciyarta tana jin ba daɗi sai dai abunne yai mata yawa dan haka ta ajiyeshi gefe, tin da suka dawo daga biki sau ɗaya ya kirata ta amsa bayan haka kuma bata ƙara amsawa ba bata saurareshi ba".. A hankali ta shiga motsa laɓɓanta tafara magana cikin muryar da bata fita sosai, "babu abunda kayi min, tayaya kasan cewa zan fita yau??" Kai tsaye yace, "laifi ne dan nasan duk wani motsin matata?? tinda ke kin kasa gayamin kinga ai yanada kyau na gane da kaina??" Ƙasa tayi da kai har suka isa takasa cewa uffan shima be ƙara magana ba. Kallonta yayi a tausashe yace, "munzo ".. Taune gefen leɓenta tayi tareda rintse ido ta haɗiye ƙululun da ya tsaye mata a maƙoshi, cikin sanyi tace, "Jo meyesa ka dena murmushi?? rashin fara'a ba ɗabi'ar ka bace, dan Allah ka dinga farin ciki mana " taƙarasa maganar cikin marai-rai-cewa. *INDO CE.."* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 13* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* tintsirewa tayi da dariya tana cewa, "Mama nice na zama macijiya kuma??" Mama ta rausayar da kai kafin tace, "tohh Aisha naga tafiya kike kina lanƙwashewa kamar almara me kika koma ne?? meke damunki duk kika susuce??" Turo Leɓen ta na ƙasa tayi a shagwaɓe tace, "Mama nifa babu komai fa" "to Allah ya kyauta" kawai Mama tace ta cigaba da abunda takeyi. Haka rayuwa take tafiya koda yaushe babu canji sai ma abunda yayi gaba, da tagama magana da wancan zatayi da wancan. Indai har zata fita to tabbas zata ga Jose kwatsam tin tana mamakin ganin sa har ta dena ta kuma saba da hakan har tsammatar ganinsa take, A ɓangaren ABU ma kullum shaƙuwar su ƙara gaba take, idan akace Khaalif kuwa ba'a magana, yanzu ba faɗa sai ɗagwarmashi iri da kala kasancewar ba tsirr yake wuni a waje ba in ya fita yasa suke samun damar zama su sha hira sai dai har yau basu bari Mama ta gane akwai wani abu a tsakanin su ba. Yau kam tuburewa tayi akan sai taje gidan su Nuriya da MaMA ta hana Sai da Khaalif Mohammad yasa baki sannan ta amince, bayan ta gama ɗaskwara kwalliya ta fito tana yalƙi tace, "Mama sai na dawo" Mama tace, "Allah ya tsare ki kula fa banason sakarci" Ta amsa da "amin insha Allah" Tana fitowa kai tsaye inda yake da mashin ta nufa da kyar ta hau baya saboda ba iyawa tayi ba shi dai aikinsa dariya ce yanda kasan zatayi wani babban yaƙi. Sai da suka fara tafiya sannan tace, "gaskiya hawa mashin akwai wahala Ya Khaslif da yamma idan zaka zo ɗakko ni kawai ka ɗakko motar Mama dan Allah" Yace, "shikenan???" Tace, "akwai wani abu ne bayan hakan" Yace, "ai nima tambayar da zanyi kenan to amma dai ba komai Allah ya kaimu" Murmusawa tayi tace, "neman magana dai??" Yace, "Ayeeshah kece kika sabar min da hakan idan ban tsokane ki ba banajin daɗi kin riga kin shagwaɓani da hakan" Dariya tayi sosai kafin tace, "ka yarda in dai-daita ka??" Da sauri yace, "aaa ban shirya mutuwa ba kiyi shiru kawai kar kunnuwa na su kurumce dan sun san jan gashi zan ɗauka kafin na dawo dai-dai" Tace, "oh da kace eh kawai da sai na maidaka ajin farko na fara baka horo" Yana dariya yace, "wallahi banaso iya horon da nasha a baya ma ya isheni baki san sauran mutuwa bane ni ko?? ƙiris nake jira, kuma ina so mu mutu tare mu rayu tare" shiru ta ɗanyi kafin tace, "ta yuwu zamu mutu tare amma rayuwa tare ina jin kamar baze yuwu ba aure na da Saif lokaci kawai ya rage kuma banajin ze fasa, ko bama wannan ba inada wata matsala a rayuwa wadda ko kai ba lallai ka iya aure na ba, Khaalif Moh.. kawai ka ganni ka barni a yadda ka ganni amma ina da damuwa wadda takasance sirrin zuciyata ne babu wanda zan gayawa yayi min maganinta Na riga na cutu Khaalif" Taƙarasa maganar tana sharar ƙwallah. jikinsa yayi sanyi lokaci guda duk wani farin ciki da walwalarsa suka gushe, ya kasa gane inda kalamanta suka dosa shin me take nufi da hakan?? wannan wace irin damuwa ce?? wace matsala gareta wadda har take tunanin baze iya aurenta ba saboda wannan matsalar???. Tambayoyin da suke masa yawo a tunaninsa kenan, muryarta ce ta katse shi cikin muryar da take ƙara tabbatar da irin tsananin damuwar da take ciki tace, "Ya Khaslif indai har kana sona da gaske Karka sa wannan tunanin a ranka damuwa ce wadda ta shafeni ni kaɗai ko iyayena ma na ɓoye musu ita dan gudun ransu ya ɓaci kabarni na cigaba da dakon abata ni kaɗai kamar yadda na taso da ita har na girma, A gaskiyance babu wanda ya dace da aure na kamar Saif bayanshi cikin ku duk wanda na aura na cuceshi ne dan ba kowane hankalinsa ze iya ɗauka ba" Saboda tsabar ruɗanin da ya shiga kasa magana yayi sai mai-maita zancen nata yake a cikin ransa, har sukaje basu ƙara magana ba, bayan ya temaka mata ta sakko daga mashin ɗin kasa tafiya tayi saboda bata son rabuwa dashi sai faman kallonsa take cikin sanyi tace, "Khaalif Moh.. a rayuwa kowa da kalar tasa ƙaddarar kuma babu me iya tsallake ta kai nice ƙaddarar ka amma ni nawa ƙaddarorin da yawa ba iya soyayya ce damuwa ta ba, gaba ɗaya tubalin rayuwata ya gino ne akan damuwa ƙaddarata mummunar ƙaddara ce wata rana ma nasan dole zaku gujeni, ina sonka Khaalif har cikin ƙoƙon raina" Daga haka ta shige cikin gidan su Nuriya tana sharɓar kuka ta barshi a tsaye da sakakken baki, har yanzu ko da wasa tunanin sa ya kasa bashi ma'anar maganganunta amma yasa a ransa tabbas akwai wani gagarumin abu a rayuwarta sai dai baze damu da hakan ba tinda har tace bata so ya damu amma koda yaushe ze kasance cikin tunani da jefawa kansa tambayoyin da yasan bashi da amsar su. ya ɓata lokaci a wajen yana tunani sannan ya ɗau hanya. A cikin gida kuwa Umman Nuriya tana zaune tana wanki Aisha tayi sallama cikin rawar murya, amsawa tayi tana binta da kallon tuhuma. Nuriya ta bugo tsalle daga ɗaki tana murna, ganin tana kuka yasa tayi turusss tana tambayar lafiyarta. Umman Nuriya ma tambayar da tafara yimata kenan, bata amsa ba sai share hawayen da tayi tana murmushin ƙarfin hali tace, "sannun ku da gida Umma" Umma ta amsa da "yauwa" Sai da ta zauna sannan suka gaisa Nuriya ta ja ta zuwa ɗaki suka zauna, kallonta tayi da mamaki tace, "meye na kuka kuma??" murmushi me ciwo tayi tace, "Nuriya bari kawai ni kuka ya kama a rayuwa ta akwai tangarɗa akwai ƙalu bale da tarin yawa a rayuwata" Gyara zama Nuriya tayi sannan tace, "haka kawai ina tausayin ki Aisha nima nasan akwai damuwa sosai gareki amma kinada kafiya juyin duniya kin ƙi gayawa kowa abunda yake saki kuka tin daga ytintar ki har zuwa yanzu" Tace, "ai daga lokacin ƙuruciyar ne labarin yafara ban kuma san yaushe ne ƙarshen sa ze zo ba" Nuriya tace, "ki tuna fa koda yaushe lokaci tafiya yake tabbas ƙarshensa ze zo sai dai fatan yazo mana da kyau dan har yanzu bamu san mene labarin ba" Tace, "nima a koda yaushe fatana kenan yazo min a ƙarshe me kyau" Nuriya tace, "wallahi Aisha idan labarin ki naji a garari bazan taɓa yarda gaske ba sai gashi ina gani a kusa dani, son gaske ba na wasa ba kuma mutum har uku" Aisha tace, "shiyasa nake tuhumar kaina ko nayi wani saɓon da Allah ya jarrabe ni da wannan mugayen iftila'in Nakanji kamar ni ba mace bace ko kuma ni ba mutum bace" Numfashi Nuriya ta ja sannan tace, "kuma kin kasa faɗa musu gaskiyar akwai wanda ze aureki kin kasa faɗa musu su uku kike so" "Nuriya so fa ba ƙarya bane, kinsan waye Khaalif kuwa?? kinsan wace irin zuciya gareshi?? da bakina nace masa inason ɗan uwansa kina ganin baza'a samu matsala ba?? Jose yasan ina son Khaalif kamar yadda Khaslif yasan ina son Jose, sannan duka su biyun sun san inada Saif kuma sun san ze aure ni, Jose yace be ɗauki Saif a matsayin mutum ba dan haka ba komai bane a gurinsa, to ya kike so nayi dashi??, Khaalif ya fini sanin waye Saifu amma be fasa sona ba ya zanyi?? yasan ina son Jose amma be fasa ƙoƙarin samun soyayyata ba yace me nema baya gajiyawa shima kinaso na gaya masa abunda hankalinsa ze dugunzuma na jefashi cikin wani hali bazan iya hakan ba, Aminta ba abota ba itace tsakanin YUSUF da ABU na gayawa ABU ɗan uwansa yana sona abokinsa yana sona?? na gayawa Jose amininsa yana sona abun bazeyi kyau ba fa Nuriya, Komai yanada sila wata rana da sannu Allah ze kawo silar da zasu gane da kansu abun zefi zuwa da sauƙi, wani makauniyar zuciya gareshi wani baya iya jurar rashin nasara wani bashi da haƙuri kenan na tarwatsa duk wannan?? idan wani mummunan abu ya samu ɗayansu nima fa ya shafeni dan Allah kiyi nazari akan rayuwar mu" Nuriya ta numfasa tana nazari kafin tace, "kinada gaskiya wallahi Allah ya kawo me sauƙi" Sunsha hira sosai har yamma liƙis, duk yadda suka so ɓoyewa Umma abunda yake faruwa sun kasa dole sai da suka sanar da ita, sosai ta tausayawa Aysha kuma tayi Alƙawarin taya ta da addu'a" Da yamma Khaalif yana zuwa shima Jose yazo ya tsikara fakin, motar tasa Khaalif ya bi da kallo yana mamakin ko waye wannan da yake goga layi dashi?. yana cikin wannan tunanin Jose ya fito, yasha baƙin gilashin nashi na gado kai tsaye inda motar take ya nufa har sai da ya ƙwanƙwasa gilashin motar sannan Khaalif ya katse tunaninsa ya fito. Hannu Jose ya miƙa masa tareda cewa, "barka da wannan lokaci ƙanina" Da baze saurare shi ba amma sai ya danne ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan yace, "nayi mamakin ganinka fa daga ina zuwa ina haka??" Gyara tsayuwa yayi tareda zare gilashin sannan yace, "gurin matata nazo zan maida ita gida" Ƴar dariya Khaalif yayi yace, "bakaji kunyar faɗen haka ba?? matarka fa" Jose ya murmusa sannan yace, "ehh ina mafarkin faruwar hakan kuma mafarkina yakan zama gaskiya idan Allah yaso" Khaalif yace, "a wannan kam be zama lallai ba gara ma tin yanzu kasan me ake nufi da ɗaukar ƙaddara, amma kasan ai da wanda zata aura dan haka ka dena wannan jin kan kasa a ranka kawai ba taka bace" Jose yayi murmushin yaro man kaza kafin yace, "na gode da tunatarwa ɗan uwa" Suna cikin haka ta fito tareda Nuriya suna tafe suna dariya har suka ƙaraso wajen, ganin Jose yasa ta dena dariyar mamaki ya hanata cewa ƙala sai dai ta bishi da ido" Kallonta yayi kafin yace, "ina fatan dai banyi laifi ba dan nazo maidake gida" Murmushi tayi tana kallon gefe tace, "aa bakayi laifi ba kuma naji daɗin hakan amma dan Allah kayi haƙuri zan tafi ne tareda Ya Khaalif shi nace yazo ya tafi dani kuma dama shine ya kawo ni" Duk da irin ɗacin da yakeji tinda yaga Khaalif ɗin amma sai ya danne yace, "shikenan zan wuce sai munyi waya ko??" ta gyaɗa masa kai tana murmushi. sai da ya buɗe mata gidan gaba ta shiga sannan yayi gaba yana cewa, "ƙanina ka kulamin da ita fa" Ko takansu be bi ba ya zauna a mazaunin direba ya ɗorawa motar wuta cikin gaggawa ya fige ta a sukwane. Sai da sukayi ƴar tafiya sanan ya samu damar cewa, "har wani murmushi kike masa kina kallo yana cin mutunci na dama kinsan hakane shiyasa kika ce nazo ko?? ashe dan ki tozartani ne ko?? meyesa bakida tausayi Aisha kin dage sai kinga bayan raina sannan zakiji daɗi bakyason farin ciki na" ƙasa tayi da kai cikin ranta tana kuka da halin Khaalif yanzu ko zata mutu baze taɓa yarda ba itace tace su zo su duka ba ita kuwa bata da dalilin ɓatawa ɗayansu rai dan haka bazatayi abunda ransu ze ɓaci ba. Cikin sanyi tace, "Khaalif Moh... kasan dai bazanyi hakan ba akan me zan tozartaka" Kafin taƙarasa abunda take son faɗa ya katseta da cewa, "babu abunda zaki gaya min na yarda kinaji kina gani har wani cewa yake na kula masa dake inda na sani to tin kafin ki girma na kashe ki sai ya huta nima na huta sai kace ba tare ya ganmu ba, duk kusancin ki dashi dai nasan bekai ya ni ba kodan kinga inayin shiru kawai banajin daɗin hakan kawai ƙyalewa nake dan babu yanda zanyi dake amma tabbas da inada yadda zanyi na sauya labarin nan da na canja shi ko ta wace fuska, a gabana kike yiwa wani murmushi kina nuna masa so Ayeeshah meyesa???" Tinda yafara magana ta rintse idonta da ƙarfi tana mai-maita a,uzubillahi sai da ya gama sannan ta buɗe idonta hawaye suka fara zuba sharrrr, kasa yi masa magana tayi sai zancen zuciya inaga ta faɗa masa gaskiyar abunda yake ranta inaga da a ranar ze aiwatar da abunda bakinsa ya furta, subhanallah Allah ka rabamu da sharrin zuciya, tsoro da firgici ne yaƙara ɗarsuwa a cikin ranta baki shike yanka wuya tabbas tinda har ya furta wata rana ze kamanta zeyi abunda bazeyi kyau ba, meyesa Khaalif yake da son zuciya ne?????" Tambayar da ta ƙara watsawa kanta kenan har zuwa lokaci batace masa ƙala ba. *INDO CE..* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 14* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* Yana shirin cigaba da magana ta dakatar dashi da cewa, " ni kuma ba abun a tausayawa bace ko?? meyesa kake da son zuciyarka Khaalif?? uzurin wani ba uzuri bane naka ne kawai uzuri hakan shine tausayawa??" Cikin ƙuna da raɗaɗin da zuciyarsa takeyi yace, "haka ma zakice? meyesa tinda kinsan bakya sona tin asali baki sanar dani ba?? har wancan shashashan yana rainamin hankali yana gaya min maganar da yaga dama kuma duk kinaji" Haɗiye ƙululun baƙin cikin da ya tsaya mata a maƙoshi tayi kafin tace, " banji wata maganar banza da Jose yayi maka ba kawai daui ka tsargu da kanka ne shiyasa, yanzu fa shikenan bazaka yarda bansan da zuwansa ba ko??" Taƙarasa maganar tana shirin fashewa da kuka. Rai ɓace yace, "banga alamu da zasu nuna min ba ke bace kuma ya cigaba da shiga gonata wata rana baze fita lafiya ba" Zuwa yanzu dole hawayen da take ta hanasu zubowa suka zubo, kuka ta shigayi me cin rai da kyar ta iya cewa, "Khaalif kamar ba ɗan uwanka bane Jose meyesa ka zama wani daban ne?? banaso komai ya samu wani saboda ni nima ka tausaya min Khaalif da wanne zanji? har da bakin ka kace cewa dama kasheni kayi ka huta duk saboda sharrin zuciya kayi tunani fa, kodan ni bansan kaina ba da nafara sonka tin ina ƴar ƙarama amma ka banzatar dani sai da ka rasa wadda kake so sannan zaka dawo kaina hakan ba son zuciya bane ko bazaka iya tausayina ba??, bazan dena mai-maita maka ba bansan Jose ze zo ba duk da nasan ba yarda zakayi ba amma har yanzu ban zama matar wani ba kuma ina roƙon Allah zaɓin alkairi kuma zeyi min" Huci ya furzar kafin yace, "Ayeesha ki fahimta fa wallahi sam abunda kike tunani ba haka bane na riga na kiɗime ne narasa makama ya ɓata min rai amma dan naso wata daa ba yana nufin bana sonki bane na riga na kamu kuma nayi zurfi shiyasa nakejin takaicin ganin wani ya raɓeki, ni kaɗai yakamata na soki ba tareda kowa ba" Katseshi tayi da cewa, "daga yau ka dena sona Khaalif tinda bakasan tausayi ba, bazan taɓa ce maka ga yadda akai ka yarda ba saboda kafiya da taurin kai, bana son wannan halayen naka Khaalif Moh.. bana son jin komai daga gareka dan Allah ka rufe mun baki kawai" Ransa in yakai dubu ya gama ɓaci dan haka ya tarkata yayi mata banza tana fita tayi cikin gida, akayi sa'a Mama tana ɗaki bata tsakar gida tayi saurin shigewa ɗakinta, zubewa tayi gefen gado tana ƙara fashewa da wani sabon kukan, ta kasa gane yadda akai Khaalif ya kasance wani irin mutum a bai-baice. Ranar saboda baƙin ciki da ɓacin rai ƙin kwanan gidan yayi, da ƙyar ya samu idonsa ya rintsa da sunan bacci hakan ma sai juye juye yake ya rasa inda ke masa ciwo. sai da suka kwashi tsawon kwanaki baya ce mata ko uffan ko gaidashi tayi ciki ciki yake amsawa, hakan yasa ta shiga damuwa sosai duk taƙara figewa ta zuƙe duk ba nutsuwa a tattare da ita tafaɗa mugun yanayi, dole ta sauke duk wani jin kanta tabashi haƙuri sannan suka dawo dai-dai. yau tin safe Aunty Maimuna ta kirata ta sanar da ita tana nemanta Dan haka ta shirya ta nufi gidan ta, a can ta tarar da Anti Bilkisu itama taje sai shan hira suke, bayan sunyi sallar azhar ne Anti Maimuna take cewa, "Aisha Mama tace akwai abunda yake damunki amma kin ƙi faɗa mata to yana da kyau mu ki sanar damu saboda barin damuwa a cikin rai bashida wani amfani, mu ki faɗa mana idan ita nauyinta kikeji" "ba komai" itace amsar da ta basu, juyin duniya sunyi akan tafaɗa musu koda kaɗan amma taƙi gashi abun yana cinta a rai amma taƙi gaya musu sai aikin kuka wanda daka gani zaka ƙara tabbatar da akwai damuwa jingim a cikin ranta, babu yadda suka iya dole suka haƙura suka ƙyaleta. Yau tana zaune gaban furji tana gyarawa abubuwan ciki zama Sayid ya shigo yana dariya cike da shikiyyanci yace, "a'ah kaga Amaryar Yaya Saif abar mana furji haka tinda ba'a can bane, wallahi sai naga kamar ziyara nazo" Ko kallon iskarsa batayi ba bare ya cigaba da tara mata takaici, ganin bata rarumo madoki ba yasa ya cigaba da cewa, "to shikenan dai tinda ban samu shiga ba, dama Yaya Saifu ne yace dan Allah ki ara masa wayarki" Sai a lokacin ta kalleshi tareda maka masa harara cikin gatse tace masa, "sai ka ɗauka ka kai masa ai shashashan banza" Dariya yayi yace, "aikuwa kai masa zanyi" Bata kulashi ba dan kuwa bata son duk wani zancen da ya shafi Saifu ɗin, ta dogara da cewar wayar ta akwai key sai dai abunda ta manta dashi sai tayi minti talatin sannan take shiga key ɗin kuma ta manta ta ajiye ta a haka ba tareda ta sata da kanta ba, shi kuwa jiki na tsuma ya ɗauka yayi waje ba tareda ta sani ba. Sai da tagama tazo nemanta taga bata gani ba gabanta ya yanke yafaɗi har ƙasa zaman daɓaro kawai tayi takasa cewa komai, tana cikin wannan yanayin Sayid ya dawo mata da wayar yace wai ya gode" Ta ɗora hannu aka tareda zazzaro ido tace, "meke faruwa dani Sayid wayata ka kaiwa Saifu?? meyesa?? da gaske kake ko tsokanata kakeyi" Yace, "wallahi da gaske nake ba dai shi zaki aura ba ai babu komai dan yaga wayarki, kin ajiyeta babu key ni kuwa da kikai min gatse na ɗauka na kai masa". dafe ƙirjinta da yafara tafarfasa tayi cikin muryarta da take sarƙewa saboda shiga ruɗu da tashin hankali tace, "na shiga uku ka jefani a tara Sayid meyesa zakai min haka?? shikenan ka jefani cikin matsala" Da mamaki Sayid yace, "wai wani abu ne a ciki wanda bakyaso a gani??" Da sauri tace, "a cikin wayata akwai zaman lafiya da kwanciyar hankali na akwai sirrina a ciki amma yanzu duk ka bankaɗe min shi ka tayar min da masifa daga bacci ina zaune lafiya kasan adadin fitinar da ka jawo kuwa??" Har yanzu ya kasa fahimtar komai amma duk da haka jikinsa yayi sanyi ganin yadda ta kiɗime dan haka yace, "Allah ya baki haƙuri ban zata haka ba" Kasa cewa, "komai tayi sai tagumi da ta zabga tana jiran tsammani, abun mamakin shiru babu wani motsi, Haka ta kwana tana zullumi da fargabar abunda ze je yazo" ba wani mamaki abun ya bawa Saif ba sai dai be zata abun nata haka yake ba ansha kiransa ace masa tana kula samari tin yana ƙin yarda har yafara yarda dan kuwa a lokacin da za ace an ganta da wani to insha Allahu idan ya kirata lokacin bata gida hakan ne yasa yaji yafara yarda amma dan neman tabbaci ya buƙaci ganin wayarta kuma yayi sa'a sai dai be zata haka abun yake ba saƙonni da kira na ABU da su yafara karo abun ya bashi mamaki sosai dan be zata ma ta iya soyayya ba ashe yaudarar sa take tanayi ta bayan fage da wani ba shi ba, a lokaci ɗaya yaji tsanar ABU ta ɗarsu a zuciyarsa lambarsa ya cira ya saka a tasa wayar sannan ya aiko mata da ta ta. Tin a ranar ya kira ABU akayi sa'a ya amsa tareda yin sallama, be amsa ba sai cewa da yayi, "ABU kake ko waye??" ABU yace, "eh nine lafiya dai ko???" Jinjina kai yayi sannan yace, "eh yanzu lafiya amma rashin lafiyar ze iya wanzuwa nan gaba, naga lambarka ne a cikin wayar matar da zan aura kuma naga kana soyayya da ita gaskiya kayi ƙoƙari, to amma inaso a tsahi wasan daga haka dan bana so nayi abunda ze zo ya ɓatawa kowa rai ka janye ka ajiye makamanka ita ɗin tawace aure kawai ya rage a ɗaura" .... ABU ya ɗan murmusa kafin yace, "akaramakallah naji duk wannan bayanan naka sai dai basu da wata fa,ida aure ya rage a ɗaura tsakanin ku kace kuma ba,a riga an ɗaura ba ba dan haka ka dena cewa takace ta me rabo ce, kuma me nema yana tareda samu babu wata barazana da zaka yimin akan Eeeshu yadda na riga nayi zurfi a cikin sonta banajin zaka iya firgita ni koda da duniya kake tafe a bayanka, lallai ka saita harshenka ka gyara kalamanka ba matarka ba matar me rabo ka gane??" Cikin ƙunar rai Saifu yace, "kaga malam mu bama haka bansan wannan zancen jahilci da rashin ilimin naka ba, kashedi kawai zanyi maka bana son harkar ƙaramta ka fita shirgin ta tin kafin lokacin da ganinta ma ze gagare ka nasan kai ɗan uwanta ne to amma kaci darajar masu daraja amma da sai ka raina kanka, bana so abun yayi tsawo nace maka ka janye karka ƙara kiramin mata karka ƙara magana da ita tin kafin nayi abunda be dace ba zan yanke ɗanyen hukunci akanka da duk wanda yaƙara gigin son Aisha" ABU yace, "masha Allah wannan batu naka sunyi kuma sun zauna dai-dai, amma bazan fasa ba kurarin ka yayi kaɗan yasa na janye, son Aisha ban fara ba ma tukunna ina jiranka daga yau har yaumattanad zanga abunda zakayi" Daga haka ya katse kiran tareda furzar da wata zazzafar iska yana girgiza kansa da yake masa wani rin sarawa, da yayi musu amma yanzu ya tabbatar Aisha takusa zama matar wani, kai kawo ya shigayi a ɗakin hannunsa goye a bayansa, yanzu tunaninsa ɗaya ta yaya ze karya lagon Saif da yake wasu banzayen zantuka akansa?? haka kawai yaji be kwanta masa ba a take yasa a ransa da Saifu ya aure ta gwara kowa ya rasa shi ya rasa ƙaninsa ya rasa shima Saif ɗin ya saɓa. Saif kuwa kallon wayar yayi cikin takaici da baƙin ciki ya sake tura kiran amma sai yaji wayar a kashe taƙi tafiya juyin duniya taƙi tafiya hakan yasa jininsa yaƙara tafasa gashi akwai maganganun da yake son faɗa amma yarasa damar yin hakan zuciyar sa sai raɗaɗi take, miƙawa Khaalif wayar yayi yace, "kaga wannan lambar nake nema amma taƙi zuwa takaici yasa nakejin kamar na fasa wayar" Da mamaki Khaalif yace, "wace lamba ce ka matsu da kiran har kake huci haka??" Saifu yace, "wai yarinyar nan soyayya take da wani har binsa take yana ɗaukarta a mota" Kai tsaye zuciyar Khaalif ta gaya masa ba kowa bane yake ɗaukarta a mota face Jose, dan haka yaja tsaki kafin yace, "bari na gani ko zata shiga a tawa" Saif yace, "ka kwafa a cikin wayata to karka kira wani bana so a samu matsala dashi nake son yin magana, har ni ze faɗawa maganar banza ya kashe waya me akai akayi shi?? me yake dashi da ze takale ni akan wadda nake so??" jikin Khaalif har rawa yake wajen duba lambar idanun sa ne suka ƙara girma saboda tozali da yayi da lambar yayansa ABU, ya kalli Saif ya kalli wayar sannan yace, " a ina ka same ta lambar kuma?" Ɗaya bayan ɗaya ya gaya masa yadda abun yake, a take yanayinsa ya canja idanunsa suka sauya kamanni jikinsa yafara tsuma zuciyarsa tafara harbin iska, kasa cewa komai yayi sai tashi da yayi yabar wajen. Saif ya bishi da kallo yana mamakin faruwar Hakan ko dai Shima Khaslif sonta yake??tambayar da jefawa kansa kenan ganin babu amsa yasa ya cigaba da neman lambar ABU amma yakasa samu. Khaalif ma yana fita kira yafara sheƙa masa amma taƙi tafiya, yarasa inda ze zauna bashida tsugun sai kai mari yake yana kai gwauro lallai ABU ya cika mara mutunci kuma maci amana. Washegari tin sassafe yayi diren mikiya a gidan su ABU da fara ar sa da komai ya tareshi faran faran amma Khaalif sai shan kunu yake, ganin abun nasa ba na ƙare ba yasa ABU yace, " lafiya na ganka a haka Junior???" rai ɓace Khaalif yace, "da wannan banzar tambayar zaka tari zancen?? ai kasan abunda ka aikata banda girma yayi gardama ina kai ina son abunda nake so??? duk dangin mu sun shaida ina son Aisha wasu ma Aishan Khaalif suke ce mata amma saboda cin amana shine kake soyayya da ita??? ita fa ba hankali ne da ita ba duk inda ka jata nan zatayi amma dan ka rabani da farin ciki na shine ka shiga rayuwa ta ina gina tubalin ƙaunata kana rushe min a hakan kake son ka kirani ɗan uwan ka???" (DAN ALLAH INA SON KU NUTSU KUYIWA LABARIN FAHIMTA ME KYAU, ABUNDA KE FARUWA AN SAMU RARRABEWA TSAKANIN MASOYAN MUTUM UKUN NAN DABAN DABAN KOWA YAFI SON NASHI, TO SAI DAI KUYI HAƘURI DANI FA DAN YADDA NA TSARA LABARIN HAKA ZAN RUBUTA DAN ALLAH KUYI HAƘURI DA ABUNDA YAFARU A BAYA DA KUMA WANDA ZE FARU🥰🥰🥰 *NAGODE* ) *INDO CE..* [7/5, 10:52 PM] INDO CE..: *💖💖💖RINTSIN SO💖💖💖* (Wa nake SO???) *Shafi na 15* Aƙalamin *INDO CE..* ELEGANT ONLINE WRITER'S *Bismillahirrahmanirrahim* rausayar da kai ABU yayi kafin yace, "ko ba da hakan na kiraka ba to babu abunda ze canja kai ɗan uwa na ne, karkayi saurin yanke min hukunci Khaalif ba nine maci amanar ba SO ne yaci amanar mu, ba tin yau ba tin tana ƴar ƙarama zuciyata ta gama daskarewa da sonta na tabbata a lokacin baka fara sonta ba ma, ka dena cewa naso abunda kake so ba haka labarin yake ba, dani da kai duk muna son abu ɗaya bana son tashin hankali a tsakanin mu, abunda na daɗe ina koka mana kenan bamu da mahaifiyar da zata iya yimana alƙalanci itace wadda zata iya kwantar mana da hankali a duk lokacin da hankalinmu yatashi, ka dena kiran hakan da cin amana, maslaha tafi komai daɗi mu fahimci juna Khaalif ba muyi ta rikici a tsakanin mu ba ita kanta wadda muke so hakan ze taɓa zuciyarta sosai muyi maslaha a ganina shine mafi sauƙi tin kafin abun yayi tsauri" Khaalif yayi saurin tarar sa da cewa, "indai da haske ne maslahar kake so to abu ɗaya ne ze kawo maslaha" ABU ya ɗan murmusa kafin yace, "menene Junior ????" Kai tsaye yace, "kabarmin Ayeeshah ta" Lumsassun idanunsa yaƙara lumshewa ya buɗe sannan yace, "ba lallai ka fahimci irin yadda nakeji ba ƙanina, ta yuwu soyayyar tsakanin ku ƙarfinta shaƙuwa ce kawai saboda kun taso tare, amma ni nayi DAKON SO na ɗauki nauyin sonta tin bansan kaina ba, ina tsaka da azabtuwa a gurin matar baba na amma hakan be sa na manta da ita ba, uhm.. kasan ma abunda nake tunawa ya sani farin ciki a lokacin?? idan na tuna wata rana Eeeshu xata girma, zuciya tana gaya min itace farin cikina sai naji na ƙagara lokacin yayi wanda zan kasance tareda ita, ASALIN SO nakewa Eeeshu Junior kai kaɗai ne gareni ciki da waje kaine dole na kai zan nuna nace kaine ƙani na ka tausayawa ɗan uwanka mana dan Allah ka barmin Eeeshu" Girgiza kai Khaalif yayi yace, "wannan labarin naka yayi fa Bro, sai dai be hau kan layi ba, bazan iya janyewa ba bana so ma naƙara ji ka kira soyayyar da nake mata da sunan shaƙuwa ko menene ma ina so kabarni da ita kamar yadda ka ganni tare da ita" ABU yace, "bazan iya ba, duk da in na faɗa ma ba yarda zakayi ba amma bazan iya barinta ba idan nayi haka naci AMANAR SO ka ɗangale min mana ɗan uwana, shi so ba'a yimasa shamaki, a lokacin da nafara sonta ban taɓa zaton ma wani namijin ze sota ba bayan ni bare nayi tunanin Ƙanina ze so ta, sai dai so makaho ne kuma kurma ne baya gani kuma bayajin kira haka baya ɗaukar shawara amma da yaso yimana adalci da be kaini kanta ba" Sosai ran Khaalif yaƙara ɓaci dan haka ya miƙe tareda cewa, "ni yanzu tafiya zanyi banida lokacin tsayawa naji wannan kalaman naka masu kama da wasan kwaikwayo, kamar yadda kace bazaka iya ba haka nima bazan iya ba, Ayeesha tawa ce adalcin da zakaiwa kanka nima kaimin kawai ka barni da ita dani tafi dacewa, idan ba haka ba kuma mu zuba ɗan halak ka fasa, dani da kai zan ga ɗan halak a cikin mu" ƙasa ABU yayi da kai ya Share ƙwallar da ta zubo kan kumatunsa cikin takaici yace, "Junior uwa ɗaya ce ta haife mu kuma a ƙasa ɗaya a iya sani na Mahaifiyar mu bata haifi ɗan da ba na halak ba, dani da kai duk ƴaƴan halak ne, kana da uba ina da uba banbancin kawai kai mahaifinka mutuwa yayi ni kuma rabuwa sukayi dan ƙaddara badan mugun halinta ba, Mahaifiyar mu Uwa ce tagari me son ganin dariyar ƴaƴanta idan kai baka santa ba to ni da hankali na ta mutu" takaici ya hana Khaalif magana ya fice fuuuuu yayi gaba kamar me shirin tashi sama. Zazzafar iska ABU ya furzar tareda zabga tagumi yana roƙon mafita a gurin Allah. Khaalif yana dawowa gida yayi sa'a Mama bata nan sai Aisha ita kaɗai tana kicin tana girki ya shigo, kai tsaye can ya nufa dan yasan a can ne ze same ta. Tana aikin tana ƴan waƙe waƙe tana juyowa babu zato tayi tozali dashi haka kawai taji gabanta ya faɗi, ta zaro ido tana kallonsa ganin yadda fuskar sa take ba annuri tsoro ne yafara kafa sansani gareta, da kyar ta haɗiyi yawu tana son tayi magana amma takasa sai ido. Takawa yayi har zuwa gabanta yana fuskantar ta cikin tsananin ɓacin rai yace, "rayuwar da kika zaɓa mana kenan??? bakya tunanin faruwar wani mummunan abu akan mu?? kuskure ne haɗa hamayya tsakani na da ɗan uwa na dan bazan iya janye masa ba kuma bazan saurarawa kowa ba, shin da gaske ne kina son sa ko kuma shima yaudarar sa kike kamar yadda kike yaudarata???" Kauda kai tayi daga kallonsa cikin ƙarfin hali tace, "eh ina son sa kamar yadda kakejin kana sona haka nakejin ina sonsa, abu wanda ba na zahiri ba shine wanda akeyin tambaya amma ai yanzu a zahiri ka gani ko?" a hasale yace, "haka ma kike gaya min, ya kike so nayi ne wai?? kinsan bazan iya jurar rashin ki ba bakya tsoron nayi abunda ze sa kowa ya rasa ko kuma nayi abunda dole sai na mallake ki???" Kai tsaye tace, "bana tsoron ko ɗaya idan kayi abunda ka mallake ni hakan zeyi min daɗi dan na samu wanda nake so idan kayi abunda kowa ze rasa shima zanji daɗin kasancewar ban auri ɗayan ku ba hakan ze fi wa kowa kwanciyar hankali, halama Khaalif ba kai bane na asalin Khaalif ɗina ka zama wani daban ba wanda na sani ba, kai me haƙura ne da komai ka barwa yayanka ko da ba ni ba amma kake irin haka" Hannun ta ya finciko har sai da tafaɗa jikinsa ya haɗe duka hannayen nata ya riƙe gamm cikin zafin rai yace, "bazanji komai ba ko me kika gaya min amma abunda nake so ki barwa kanki sani babu wani ɗan da aka haifa kuma zaki aure shi ki kasance cikin kwanciyar hankali bayan ni, daa nake me haƙuri da juriya amma yanzu ta ƙarfi kin canja ni ko me na koma kece sila kinsa na haukace, tabbas yanzu ba Khaalif ɗin daa bane na yanzu ba ya yafiya kuma baya ragawa duk wanda ya hau hanyarsa ko me na aikata kisa a ranki kece sila haka ko me na zama kece kika maidani hakan, ba ina faɗan komai bane da sunan wasa da gaske nake kuma zan aikata" kuka me ƙarfi ne ya ƙwace mata ta shiga rusa shi kamar tashin hankali, ta rasa wace irin masifa ce take damunta a rayuwa shin meye maganin matsalarta??? waye wanda ze kawo mata ɗauki a rayuwarta?? a cikin su waye ze zama katangar ƙarfe tsakanin ta da damuwar da ta taso da ita???, girgiza masa kai ta shigayi alamar "aa" tana son cewa wani abu amma ta gaza magana dole ta cigaba da kukan gami da kwantar da kanta akan ƙirjinsa saboda mugun riƙon da yayi mata. Ido ya zuba mata kamar wanda yake wani dogon nazari, sai a lokacin kukan nata yafara ratsa zuciyarsa tareda jefashi cikin wani yanayi, cikin sanyi yace, "Ayeeesha kiyi haƙuri ba laifi na bane sonki ne ya zautar dani na rasa makama abun sunyi min yawa har yasa nafara wasu banzayen tunani bana son rasa ki shiyasa nake tunanin yin komai domin na sameki, ki dena kukan nan bana so" Ɗagowa tayi da kyar ta kalleshi sannan taƙara maida kai ta kwantar, cikin ƙunar zuci tace, "ka rage son zuciya Khaalif, Allah ya jarrabe ni da son mutum uku kai kuma ni kaɗai kake so bana son ɓacin ran ku ku duka ina son saku farin ciki na taƙaitaccen lokacin da ya rage min kun sani zan auri Saif amma kai baka ta kowa son zuciyarka shine kan gaba komai sai dai ya kasance kaine, Khaalif ina son Yusuf Ina Son ABU kuma ina Sonka kuma zan auri Saif bazance komai ba dan ba ni nayiwa kaina wannan zaɓin ba Allah ne ya tsara haka a jikin Allon rubuta abu me afkuwa a rayuwata har ma da wanda be faru ba da wanda yafaru a baya duk daga Allah ne kuma gareshi nake roƙon sassauci kuma inaji a jikina a kwana a tashi dole wannan damuwar zata gushe nima zan zama mutum kamar kowa, zuciyata tana gaya min a cikin ku ɗaya ze zamo silar zamana mutum, amma bansan kowaye ba kayi min uzuri karka illata min rayuwa Khaalif" Taƙarasa maganar tana ƙara fashewa da wani sabon kukan. Dumm.. dummm. zuciyarsa ta shiga bugawa ɗaya bayan ɗaya, girgiza kai yayi gami da lumshe idanunsa har cikin ransa yakejin kukan nata kamar ya tarwatsa masa zuciya , jimmm yayi kafin ya buɗe idanun nasa da yanzu sun gama canja kamanni ya ɗora akanta, hannunsa yasa ya shiga share mata hawayen wasu suna ƙara zubowa, cikin wata rikitacciyar murya yace, "Ayeesha kukan ki barazana yake ga rayuwata, ki saurari bugun zuciyata shirin tarwatsewa take saboda kukan ki ki tausayawa Khaalif ɗinki ki dena kuka Ayeeshahh.." a hankali tafara sassauta kukan har tayi shiru tana sauke ajiyar zuciya sai da tafara nutsuwa sannan tafara jin yadda zuciyarsa take tsalle fakare tayi tana saurara kafin ta ɗago idanunta ta jefa cikin nasa, a hankali ta zame daga jikinsa ta nufi ɗaki ta nemi guri ta zauna. da ido ya rakata har ta ɓacewa ganinsa sannan ya wuce yabar gidan. Tin tana sa ran jin wata magana ko wani alamu daga Saifu har ta dena sai dai tasa a ranta kawai yayi shiru ne badan ya tsorata ba sai dan yaƙara ɓullowa ta wani gurin da ze mata illa. Saif yaga canji da canje canje sosai a gurin Khaalif har ta kai ga ko maganar arziƙi baya yi masa kuma tin daga ranar da ya gaya masa maganar ABU dan haka ya yanke hukuncin tambayar sa dalili. Suna zaune Khaalif yana danne danne shi kuma yana cin abinci, kallonsa yayi ya kauda kai sannan yace, "Khaalif in ɗan tambaye ka mana" Yace, "inaji" Saif yace, "meke faruwa tsakanin mu ko kuma nace tsakaninka da Aisha tabbas akwai abunda ban sani ba ko kuma nace nagagara ganewa, na shiga ruɗani sosai" Murmushi Khaalif yayi kafin yace, "hmmm hakane kam abun kaico ne wannan wai yaya na ne wanda yake son Ayeeshah, inajin zafin abun sosai yanai min ƙuna " Da mamaki yace, "kana nufin wannan yayanka ne?" Yace, " na jini ma kuwa be min adalci ba ko kaɗan ina shi ina Ayeeesha banda sharrin zuci??" Jinjina kai Saifu yayi tareda cewa, "yayan ka ne????" Khaalif Mohammad ya gyaɗa masa kai. Murmushi me tarin manufofi ya saki kafin yace, "ka ja masa kunne akanta dan babu abunda bazan aikata ba, tsira da mutuncinsa shine fita harkar Aisha abarta da mijinta" Shima Khaalif murmushin yayi wanda babu wanda yasan asalin sa sai Allah, yace, "ko baka faɗa ba dama ni meyin ruwa da tsaki ne akan hakan don nima ta shafeni" maganar tayi masa bau shiyasa ya tambaye shi akan yayi masa fashin baƙi akan manufarta amma sai ya share zancen hakan yasa Saifu ya ƙudurewa kansa shiga da fita domin ja musu layi gaba ɗaya dan ya lura akwai wani abu a tattare da Khaalif. *INDO CE..*