[30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA ƊAYA Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali. Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin. "Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka. "Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami." Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce. "Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta. "Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa." Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce. "Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana." "A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..." "Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri. "Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes. "Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya. "Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta. "Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gyaɗa kai tana murmushe. "Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta. CIKIN DARE A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada. "Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi..." "Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..." "Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje. Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa. "Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar garke da ke cin dusa, ya tattaro iya ƙarfinsa ya ɗago ta sai ji kake ɓaaaarrrrrrr wata uwar tusa ta ƙwace masa. Uwani da kawo kanta kenan ta saki murmushi ta ce. "Kai da jin wannan tusar ka san su uwar garke bacci ya yi daɗi." Har za ta gota sai ta leƙa garkensu, sai dai haskarwar da ta yi babu uwar garke babu alamunta. Da sauri ta juyo tana shirin fasa ihu ta hango Baba Isuhu rungume da uwar garke, ita kuma uwar garke jin matsar da Baba Isuhu ya yi mata ya sa ta ware baki ta ce. "Meeeeeeeeehhh." Cikin sauri Baba Isuhu ya miƙa wa Mai gari Talle, Mai gari na karɓa ya fara kici-kicin hawa mashin. Uwani na ganin Baba Isuhu ya miƙa uwar garke ta yi caraf ta kama katanga, sai dai tana gani Mai gari shi da wani da ba ta gane fuskarsa ba suka haye mashin suka fita da gudun gaske. A haukace Uwani ta diro daga kan katangar ta ɗora hannu a kanta cikin tashin hankali ta ce, "Wayyo Allah uwar garkena." Sai kuma ta yi sashen Dada a guje. Ganin haka ya sa Baba Isuhu da sauri ya nufi sashensa. A tsakar ɗaki ya sami Lami don haka tana ganinsa ta ce, "Ya dai Isuhullena an dace kuwa?" Baba Isuhu da ke faman haki ya ce, "Maza ki tafi ɗaki ki kwanta, ni ma lamfo zan yi shegiyar yarinyar nan ta kama mu ni da Talle." Zaro ido waje Lami ta yi ta ce, "Mun shige su Isuhuna ya za ka yi?" "Babu lokaci Lami ke dai ki je ki yi yadda na ce miki." Lami ta yi saurin ficewa shi kuma Baba Isuhu ya faɗa uwar ɗaki ya haye gado sannan ya fara sauke numfashi kamar wanda ya jima yana bacci. "Wayyo uwar garke." Uwani ta furta haɗe da ɓarkewa da matsanancin kuka. Ganin Dada na sakin bacci har da minshari ya sa Uwani ta buga tsalle haɗe da faɗin. "Wayyooo uwar garkena!" Sai a lokacin Dada ta ji ihun Uwani. "Kai ni kam Mamman ya cuce ni da ya haɗa Uwani da kiwo tun tana ƙanƙanuwarta. Yanzu ban da masifa a ce yarinya har cikin bacci tana ambatar tinkiya, wannan bala'in da me ya yi kama..." Dada ba ta ƙarasa magana ba ta ji Uwani ta faɗi a gefen ƙafarta tim! Ta fashe da wani irin matsanancin kuka. A razane ta tashi zaune sannan ta kai hannu ta kunna fitilar ɗakin, hannuwa biyu ta sa ta dafe ƙirji a firgice Dada ta furta. "Uwani ke ce nake gani a gabana ko buɗe mini ido aka yi?" Uwani ta ji tamkar Dada ta watsa mata ruwan zafi, don haka ta fyace majina da gefen zaninta cikin ihu ta ce. "Uwar garkeeeeeena! Baba Isuhu ne uwar garkenaaaa." Dada ta zaro ido waje. "Ke Uwani ko dai gamo kika yi ne? Shi Isuhun ne ya zama uwar garke? An ya lamarinki Uwani babu jifa a ciki?" Dada na gama magana ba ta ji daga bakin Uwani ba ta fashe da kuka tana faɗin. "A'ubikalimatillahi tamma min sharrin ma kalaƙa. Aniya bi aniya wallahi aniyar kowa ta bi shi, Allah Ya kai mu wayewar gari wallahi sai na je gidan Sarkin aska na karɓo miki ƙaiƙayi, ni za a kashe da ƙullutun baƙinciki..." Uwani ta katse Dada daga dogon jawabin da take yi. "Dada wallahi ganin idona Baba Isuhu ya ɗauke mini uwar garke ya miƙa wa Mai gari ta katanga." "Ke yarinyar nan ki ji tsoron Allah, shi Isuhun nawa ne kike jifa da sata? Isuhun da ko yatsa ba za a saka masa a baka ya tauna ba?" Ganin haka ya sa Uwani ta fice daga ɗakin tana faɗin, "Wallahi ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ka dawo mini da uwar garkena. Wayyo Allah garkeruruna!" Jikin Dada nan take ya ɗauki karkarwa don haka ta miƙe cikin sauri ta bi bayan Uwani. Kafin wani lokaci wasu daga cikin mutanen gidan suka fara fitowa, kowa ya tambayi Uwani amsa ɗaya take bayarwa 'Uwar garke, Baba Isuhu ya miƙa wa mai gari ta katanga.' Carko-carko suka yi domin ga dukkan alamu sun fara aminta da kalaman Uwani, sakamakon sun duba garken awakinta sun ga babu uwar garke. "Ina shi Isuhun ne?" Baba Idris ya tambaya. Kallon juna suka shiga yi don haka ya bayar da umarnin a je sashen shi a kira shi. Sahabi da Tasi'u ne suka nufi sashen Baba Isuhu, sun jima suna buguwa sannan ya buɗe ƙofa, yamutsa fuska ya hau yi tamkar wanda aka tasa yana bacci ya ce. "Kai waye a tsohon daren nan yake mana bugu haka?" "Baba Isuhu dama Baba ne ya ce a taso ko?" Suka amsa masa. "Ni kuma? A tsohon daren nan? Ko ciwon Yaya ne ya tashi?" Baba Isuhu ya jefa musu tambayoyi kamar bai san abin da yake faruwa ba. Girgiza masa kai suka yi, suka wuce gaba yana biye da su a baya. Yana zuwa ya samu mutane a tsaye carko-carko, tun daga nesa gabansa ke dukan uku-uku amma gudun tonuwar asirinsa sai ya yi hanzarin aro mayafin jarumta ya lulluɓa wa jikinsa. Ya sake aro fuskar mamaki ya ɗora a saman tashi, cikin mamaki ya furta. "Yaya lafiya na ganku haka a tsohon daren nan?" "Uwani ce ta zo mana da wata magana..." Duk abin da ya faru Baba Idris sai da ya zayyane masa sannan ya ɗora da cewar, "Ina Uwar garke take?" Duk da ƙirjinsa bugawa yake amma bai hana shi fututtukewa ba ya ce. "Haba Yaya yanzu duk faɗin gidan nan a rasa wanda za a laƙa wa sata sai ni? Me zan yi da wata uwar garke? Shekarar uwar garke nawa a gidan nan? Amma kawai don yarinyar nan ta shirya ƙaryarta sai a hau kai a zauna, shi kenan tun da ni ne ɓarawon da kuke zargi a faɗa mini nawa ne kuɗinta zan biya." Ganin yadda ran Baba Isuhu ya ɓaci ne ya sanyaya jikin ilahirin mutanen da ke wurin, Dada ta zauna daɓar haɗe da rushewa da matsanancin kuka. "Tsakanina da wannan ɓarawon ni kam sai na kai kukana gaban Ubangiji, ina zaman zamana zai haɗa mini husuma a cikin zuri'ata." Baba Mustafa ya ɗago Dada sannan ya ce, "Yanzu dai duka mu bar maganar nan ni nan zan sayo miki wata ƙatuwar tinkiyar da ta fi uwar garke girma kin ji Uwani." Jin haka ya sa Uwani ta rushe da kuka. "Wallahi ni uwar garke nake so, kuma ko kur'ani aka ba ni zan dafa ganin idona na ga Baba Isuhu da uwar garkena..." Baba Mustafa ya yi saurin katse ta don haka kawai ya ji ya yi na'am da kalaman Uwani, don haka ma ya ce. "To shi kenan ba tinkiya kaɗai zan saya miki ba, kina son ɗan maraƙin sa ko?" Ba don Uwani ta daina jin zafin rashin uwar garke ba ta amsa, sai don son da take wa ɗan maraƙin sa. Saboda haka ta gyaɗa masa kai tana goge hawaye, a gefe ɗaya tana kuma ƙudurtar irin fansar da za ta ɗauka a kan Baba Isuhu don ta yi rantsuwa da Allah jinin Uwar garke ba zai tafi a banza ba. Daga haka gabaɗaya kowa ya watse, Uwani da Dada suka yi sashensu sai dai buta ta sake ɗauka ta fito kamar za ta banɗaki kai tsaye ta wuce sashen Baba Isuhu cikin sanɗa, ta ci sa a bai rufe ƙofa ba don haka tana laɓe daga bakin ƙofar ɗakinsa ta ji Lami na faɗin. "Isuhullena ai ka birge ni da ka ƙaryata shegiya, haka kawai da tuni da tozarta ka a gaban mutane." Baba Isuhu ya saki dariya ya ce. "Ke zan cen da nake miki gobe warhaka mun riga da mun gama ɓarje dabgen kan uwar garke." A gefe ɗaya ta ji muryar Goggo Sala na cewa. "Yanzu dai tun da aikin gama ya gama ai sai ku ja baki ku yi shiru, amma dai Isuhu dole ka badda kama idan za ka shigo da uwar garke don ka san dole a saka maka idanu." Baba Isuhu ya fashe da dariya yana shirin yin magana daga can bayan ƙofa suka ji muryar uwar garke ta ce. "Meeeeeeeeh." A zabure suka kalli juna cikin tashin hankali. "Kukan uwar garke nake ji a tsakar gida Isuhu leƙa ka gani..." Lami ta faɗa da sauri. "Ba ki da hankali Lami, ya za a yi ganin idona Talle ya tafi da uwar garke kuma na ji muryarta ke ki leƙa mana..." Kalaman bakinsa suka katse sakamakon sake jin kukan Uwar garke ta ce, "Meeeeesuhuuuu." Wani abu ne ya tsargawa Baba Isuhu tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa. "Isuhu kamar sunanka na ji a cikin kukan uwar garke." Lami ta faɗa a tsorace. "Meeeeeesuuuhuuuu." Uwani da ke laɓe ta sake maƙale murya ta faɗa da yanayin kukan uwar garke, tana gama faɗa ta dokon ƙauren ɗakin da suke ciki. A zabure Lami, Isuhu da Goggo Sala suka faɗa uwar ɗaki, Goggo Sala da ke ɗaure da ɗaurin ƙirji tun a falo zanin jikinta ya faɗi ba tare da ta sani ba. Goggo Sala da baba Isuhu suka shige bayan ƙofar uwar ɗaki ita kuma Lami ta maƙale a gefen gado, shirun da suka ji ba a ƙara kukan tinkiyar ba ne ya sa suka fara dawowa hayyacinsu. Goggo Sala ta kai idonta jikinta sai a lokacin ta yi ido biyu da tsurar ɗan fatarin (Under wear) da ke ƙugunta, ga ƙirjinta zube a saman kan Baba Isuhu da ke tsugunne a ƙasa. Sai a lokacin ta lura da hannuwan baba Isuhu da ke riƙe da ɗan fatarinta. Cikin matsananciyar kunya ta ce. "Kai Isuhu wanne irin iskanci ne haka saboda Allah za ka nemi shigewa cikin fatarina, ni fa ƙanwar mahaifiyar matarka ce ." Cikin rashin sani Baba Isuhu ya miƙe tsaye sai jin ƙirjin Goggo Sala ya yi a saman fuskarsa, yana ɗagowa suka haɗa ido da ita. Ganin abin kunyar da aka tafka cike da borin kunya ta ce, "Amma dai Isuhu yadda ka kwaso mini ƙirji ina a matsayin sirikarka Allah Ya kwashe maka albarka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYU Uwani da ke laɓe tana jin su sai da ta saki murmushi sannan ta wuce ɗakin da Lami da Goggo Sala suke kwana, tana shiga ta samu mai sunan malam yana kwance yana bacci. A hankali ta ɗauko shi sai da ta zo tsakar gida, ta saka shi a cikin ƙatuwar tukunyar da ake dafa wa Lami ruwan wanka amma babu ruwa a ciki. Ta saka hannu ta ɗan jijjiga shi don ya tashi, saboda dama ta jima da sanin Baba Isuhu matsoraci ne na bugawa a jarida, don haka ta gano lagonsa. Baba Isuhu ba ƙaramin ɗacin kalaman Goggo Sala ya ji ba, ya saci kallonta rai a ɓace ya ce. "Allah Ya kwashe mana dai, ni allan-musuru ne na san ke ce a wurin? Wallahi ni da na ji na ɗebo abu a kaina na ɗauka hannuwan Lami ne." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar yana fitowa falo. Ya bar Goggo Sala a tsaye cike da takaicin abin ya faɗa. "Tsabar iskanci da wulaƙanci har ƙirjina ya yi lalacewar da za a ɗebo su aka a ɗauka hannuwa ne?" Goggo Sala ta ayyana a ranta. Yana zuwa ya ji mai sunan malam ya tsanyare da kuka. Kusan tare suka kalli juna shi da Lami, sai dai jin shiru babu kukan uwar garken ya sa suka ɗan saki jikinsu. Cikin sanɗa suka fara takawa a hankali har suka fita tsakar gida, suna yunƙurin tafiya ɗaki suka ji kukan mai sunan malam a cikin tukunya ga shi kuma tukunyar a rufe. Lami ce ta yi ƙarfin halin buɗewa nan take ta yi tozali da shi. "Isuhu akwai abin da yake shirin faruwa wallahi." Lami ta faɗa murya na rawa. "Lami ko dai a garin ɗaukar uwar garke ne na tako aljanu? Na shiga uku kada su taɓa mini mai sunan malam." Baba Isuhu ya ƙarasa maganar cikin kuka, Goggo Sala na ƙarasowa suka wassafa mata abin da yake faruwa. "An ya kuwa Isuhu uwar garken ka ɗauka ba aljanu ba kuwa? Gaskiya ruwa ba ya taɓa tsami banza." Cikin Baba Isuhu ya sake ɗurar ruwa, ya waiga a hankali yana kalle-kalle daga can kusurwar bango ya hango kamar mutum a tsaye, Uwani da ke raɓe ganin kar ya gano ta ya sa ta yi wata girgiza haɗe da cewa. "Meeeeesuuuuhuuuu zaaaaan cinyeeeeee idoooonnnnkaaaaa." Jin abin da aka faɗa ya sa Baba Isuhu da su Lami suka faɗa ɗakin da su Lami suke jego. Uwani ta samu ta saɗaɗa sannan ta wuce sashen Dada tana sakin murmushi, ko ba komai ta gano lagwansu da yadda za ta dafa su a ruwan sanyi. Su Baba Isuhu gabaɗayansu babu wanda ya samu sukunin rintsawa, don Baba Isuhu ko sallar asuba bai samu ya fita ba. Sai da gari ya yi haske tarwai sannan suka fito suka yi alwala suka yi sallah, Goggo Sala ta ɗora ruwan wankan mai jego. Ita ma Uwani idonta biyu har aka yi sallar asuba sannan bacci ya yi awon gaba da ita. Ko da gari ya waye babu wata damuwa a tattare da Uwani don ba ƙaramin jin daɗin mafitar da ta samu ta yi ba, ita kanta Dada ta yi mamakin ganin Uwani tana harkokinta. Sai dai a lokacin da ta ƙarasa garken awakinta sun ba ta tausayi musamman da ta ga tagwayen uwar garke sai koke-koke suke alamun suna neman ta, tana zuba musu abinci suka daina kuka sai tagwayen uwar garke da har lokacin ba su daina kuka ba. "Kai Talle asirinmu fa ya kusa tonuwa, kai Allah ne kaɗai ya tarfa wa garinmu nono." Baba Isuhu ya faɗa yana yin ƙasa da murya. "Ai na san za ka gyara komai, kai ma fa shaiɗanin kanka ne. Yanzu dai ya za a yi da kai da ƙafafuwan? Kuma cinyoyin baya ka san na ce maka ni zan ɗauke su." Mai gari Talle ya furta. "Ni yanzu kai da ƙafar 'yar akuya nake so ka samo mini, saboda zan kai wa Dada don na badda idonsu a kaina, cinyoyi dai gaskiya na gaba za ka ɗauka. Kuma sai yamma liƙis za ka aiko min, ka tabbatar an daddatsa komai don kada a fahimci naman babbar tinkiya ne." Mai gari Talle ya gyaɗa kai yana shirin magana ya hango Uwani a ɗan nesa da su tana haɗa tukwanen taɓo, idan ka ga yadda ta mayar da hankali tana wasa sai ka rantse da Allah ba ta san wainar da suke toyawa ba. Ganin ta ya sa Talle Mai gari ya ce. "Abokina ma yi magana anjima kawai, yanzu dai gaskiya sauri nake." Daga haka suka wuce, don shi kansa Baba Isuhu ya lura da Uwani duk da ta yi kamar ba ta san suna yi ba. Uwani na ganin Talle mai gari ya tafi gida ta watsar da kayan ƙasar hannunta, ta sake ɗaure ɗamarar da ta yi da ɗankwali wacce cike take da jelolin raguna da tumakai, da ta shiga kasuwar awaki ta samo. Tana daga jikin katangar ƙofar gidansa ta ga ya shiga soron gidan, da yake turakarsa a soro take don haka a kan idonta ya faɗa ɗakinsa. Tana nan tsaye ta ji ya sake fitowa a tsammaninta fitowa waje zai yi sai ta ji ya shiga cikin gida yana faɗin. "Amarsu ta ango mai daɗin tuwo da miya, wannan ɗan waken da kika shanana mini man ƙuli ai dole na bada tukwici." Da sauri Uwani ta faɗa ɗakin tana shiga ta samu sabuwar langar Zuwaira amaryar mai gari cike da ɗan wake, da sauri ta cakuɗa ta hau ci saboda tsabar ƙeta ta dinga haɗa uku-uku huɗu-huɗu tana ci, cikin ƙanƙanin lokaci ta cinye ɗan waken tas, sannan ta ɗauki ruwa ta sha, ta zaro jelar tumaki biyu ta saka a ciki. Tana shirin miƙewa ta ji alamar tahowar mai gari shi da Zuwaira yana faɗin. "Haba wane mutum ki dinga haɗa kanki da waccen ballagazar. Ke fa komai na ki na daban ne Zuwairatuna." Uwani da ke ɗakin cikin matsananciyar faɗuwar gaba ta shige uwar ɗakinsa, can bayan ƙofa ta ɓuya don ta tabbata matuƙar mai gari ya kamata sai ranta ya yi mummunan ɓaci. Zuwaira cikin kwarkwasa ta zauna tana fari da idanu, hannunta ɗauke da mufici tana yi masa firfita. Mai gari da ƙarfinsa ya ɗauko langa amma jin ta fayau ya sa shi mamaki don ɗan waken da ya gani cike da langa yake, yana ɗaga murfin ya ganshi fayau sai jelar tinkiyoyi a ciki. Wani abu ne ya tsarga masa tun daga tafin ƙafarsa har tsakiyar kansa, cikin faɗuwar gaba ya furta. "Zuwaira kina ganin abin da nake gani kuwa?" Zuwaira da mamaki ya sa ta hangame baki ta ce. "Mai gida me ye wannan kamar jelar tumaki? Ina ɗanwaken da na zuba maka?" Mai gari ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana shirin magana daga can uwar ɗakinsa ya ji an ce. "Taaaaalleeeeeeeeeh." Zuwaira ta waiga cike da tsoro ta ce, "Kamar kukan tinkiya kamar kuma cewa aka yi Talleh." Kafin ta gama magana tuni gumi ya gama wanke Mai gari, Zuwaira na shirin sake magana suka ji ƙarar buhu sai kuma Uwani ta sake maƙe murya ta ce. "Ga uwar garke ta dawo ba ta mutu ba, na zo tafiya da talleh a cikin buhun mutuwa." Zuwaira da mai gari nan take suka shiga rige-rigen guduwa, Uwani da ta saka kanta a cikin wani ƙaton buhun gero ta biyo su buguzum-buguzum da gudu tana fisgar malun-malun ɗin mai gari. Mai gari kafin ya shiga cikin gida ya kifa ya kai sau uku, da ya tashi malun-malun sai ta sake harɗe shi. Ladiyo da ke tsakar gida sai ganinsu ta yi a guje. Zuwaira ta shige ɗakinta ta banke ƙofa, yayin da Mai gari ya faɗa ɗakin Ladiyo, yana tafe fitsari da zawo na bin wandonsa. Waige-waige Ladiyo ta fara yi don ita ba ta san gudun da suke yi ba, ganin haka ya sa ta shiga ɗakinta, a can ƙasan gado ta hango Mai gari gumi na yanko masa ta ce. "Mai gida wai me yake faruwa ne?" Mai gari ya sake jan zanin gado don ya rife kansa ya ce. "Ladiyo gamo muka yi a ɗakina, wallahi aljanu ne a ciki." Wani wari ne ya ziyarci hancinta, ta kai kallonta wurin ƙafar wandonsa ta ce. "Mai gida me nake gani kamar zawayi?" "Idan zawayin ne akwai uban da ya yi mini shi? Ba abina ba ne ki bar ni mana Ladiyo." Mai gari ya faɗa yana muzurai. "Don Allah ka taso mu je ka sauya kaya kafin yara su dawo gida." Shiru mai gari ya yi sannan ya ce. "Amma za ki tsaya a ƙofar banɗaki ko?" Ladiyo ta gyaɗa masa kai cike da mamakin wai yau ita Mai gari yake ce wa ta yi masa rakiya banɗaki. Da ƙyar da suɗin goshi Ladiyo ta samu kan Mai gari ya fito, Uwani da ke ɗakin Mai gari har ta fito za ta tafi gida ta ji suna maganar shiga banɗaki. Da sauri ta saki murmushi ta ɗauko buhun ta zagaya ta bayan gidan Mai gari, zuciyarta fes don babu mutane sosai sai waɗansu ƙananan yara da ba su wuce shekara uku ba suna wasa. Kasancewar banɗakin karkara a buɗe yake ta sama ya sa duk abin da Mai gari yake faɗa tana ji, sai da ta tabbata da Mai gari ya tuɓe sannan ta tsugunna ta saitin rariyar ta ce. "Shi kenan ma Talle ya zo masarautarmu da ƙafafuwansa yana wanka, buhun mutuwa zo ka kai Telle inda ya kai shugabarmu wato Uwar garke." Uwani na gama maganar ta watsa masa jelar tumaki biyu ta saman banɗakin, sannan ta wurga ƙaton buhun geron da ta fito da shi. Tana daga nan wurin ta ji Mai gari ya zuba ihu ya fice a guje yana faɗin. "Wayyo Allah! Za su tafi dani, wayyo Ladiyo ki taimaka mini buhun mutuwa ya biyo ni." Garin gudun da Mai gari yake yi ne ta ga takalminsa wari ɗaya ya faɗo ta bayan katanga. Dariya Uwani take yi kamar mahaukaciya sabon kamu, sai da ta yi mai isarta sannan ta ɗauki takalmin mai gari wari ɗayan ta ɗaure shi a cikin ɗankwalin da ke ƙugunta kai tsaye ta wuce gida. Yamma ta yi liƙis a lokacin tana tafe tana waƙoƙinta, da mamaki take bin galleliyar motar da ke ƙofar gidansu. A gaban motar ta tsaya ta isa gaban mudubin motar tana kallon kanta tana yatsine-yatsine, ta mudubin ta hango Salele hannunsa ɗauke da tulu ya ɗebo ruwa. Uwani ta ƙwalla masa kira, nan take jikinsa ya fara rawa, "Yar ƙashin gwiwa don girman Allah ki bari na kai wa Innata ruwan nan." Uwani ta tsuke fuska sannan ta ce. "Don uwarka wani abin na ce maka ne, kawai ka zo na ce ko." Jikinsa a sanyaye ya ƙarasa idonsa na zubar da ƙwallah don ya san yau kwanan tulun Innarsa ya ƙare. Duk abin da yake faruwa Jafar na daga cikin motarsa yana kallonsu, kamar ya yi mata magana sai kuma ya ce bari ya tsaya ya ga iya gudun ruwanta. Don ko ba a ce masa Uwani ba ce, kamaninta da na mahaifinsa ya alamta masa. "Sauke ruwan tulun nan." Ta furta fuska a haɗe. Babu musu Salele ya sauke, Uwani ta fara ɗiban ƙasa tana ƙwaɓawa a saman gilashin motar Jafar, domin baƙin gilas ne kuma ba ta taɓa tsammanin da mutum a ciki ba. A hankali ta fara zuba ruwan tulun tana wanke ƙasar wani wurin ya yi jurwaye wani ya wanku, ta ɗora tulun a saman motar sannan ta ce. "Salele tulun Innarku yau shi zai tuƙa mu zuwa garin Kano, ka san fa sabuwar motata ce da Dada ta sayo mini jiya." Uwani na sakin tulu ya faɗo ƙasa tush! Salele ya wage baki ya saki ihu cikin ɗacin zuciya. A hankali Jafar ya fara zuge gilashin motarsa, Uwani da ke gefe ta yi mutuwar tsaye saboda tsoro don ba ta taɓa tsammanin da mutum a ciki ba. Sai kuma ta maze ta fara harare-harare don kar ya raina ta, ta kalli wurin da Salele yake ihu ta buga masa tsawa. "Za ka yi mini shiru ko sai na mayar da bakinka ƙeya." Tamkar an yi ruwa an ɗauke haka Salele ya yi tsit yana goge ƙwallah. "Uban wa ya ce ki jiƙa mini mota." Uwani ta ji saukar maganar Jafar a kunnenta, ƙirjinta ya buga da ƙarfi saboda tsoro amma don kada ya gano ta sai ta haɗe fuska ta ce. "Ka ga malam bar ganinka da wasu kayan 'yan sanda ka ɗauka za ka tsorata ni, babana ma babban ɗan sanda ne. Wallahi yanzu ihu ɗaya zan yi ya kai ka caji ofis ya sa a kulle ka." Uwani ta ƙarasa maganar tana murguɗa baki, sannan ta yamutsa fuska ganin Jafar ya kafe ta da ido yana kallo ya sa ta ci gaba. "Kai ni fa ban ma yarda da kai ba wallahi, an ya ma kai ba ɗan sandan bogi ba ne? Dubi yadda kake raba idanu kamar shege a rabon gado. Wai ma uban wa ya ce ka jiye mota a ƙofar gidanmu..." Uwani ta haɗiye ragowar kalamanta sakamakon ganin Jafar ya buɗe mota ya fito, ba Uwani ba hatta Salele sai da ya tsorata da yanayin da ya ga Jafar. Uwani a dole don kar ta kunyata kanta ya sa ta cigaba da tsaiwa ta ce. "Ka ga malam tun kashinka bai bushe a hannuna ba ka..." Ta sake haɗiye ragowar kalamanta sakamakon jin Jafar ya damƙi hannunta da ƙarfin gaske. "Yeeeh Uwani ta shiga hannun ɗan sanda." Salele ya faɗa da ƙarfi cikin murna yana tsalle, tuni cikin Uwani ya kaɗa. Salele ya ja baki ya rufe sakamakon ganin bindiga saƙale a gefen aljihun Jafar. Da ƙarfin gaske Jafar ya fisgi hannun Uwani kai tsaye ya wuce cikin gida da ita. Tamkar raƙumi da akala haka Uwani take bin Jafar ƙirjinta na bugawa, zuciyarta na shelar neman agajin gaggawa. Don duk iskancin Uwani tana tsoron bindiga ɗari bisa ɗari. Lokacin da Jafar ya shiga ɗakin Dada babu kowa a ciki, don haka ya wurgar da Uwani gefe fuska a haɗe ya ce. "Maza tashi ki fara tsallen kwaɗo." Uwani jiki na rawa ta fara tsallen kwaɗo sai dai ba ta kai ko ina ba, ta fara hawaye shaɓe-shaɓe. Belt ɗinsa ya ciro yake lafta mata idan ta tsaya, don haka lokaci ɗaya Uwani ta fara fita a hayyacinta. Bayan ta gama tsallen kwaɗo ya saka ta tuƙin babur, da kansa ya gwada mata yadda za ta yi, tana daga tsaye ban da numfarfashin kukan Uwani babu abin da yake ta shi. "Allah mai yau da gobe, wato yau kukan Uwani nake ji a gidan nan? Tabbas gaba da gabanta wai aljani ya taka wuta, Uwani yau wa kika taɓo wanda ya fi ƙarfinki haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon ganin Uwani a ƙobare da ƙafafuwa tana tuƙin mashin. Baki a sake Dada ta ce. "Ke Uwani wane sabon iskanci ne kuma haka? 'Ya mace da ke ki hau wani ƙobare ƙafafu kuma kina kuka." Uwani jin abin da Dada ta faɗa ya sa ta faɗi ƙasa ta sake fashe wa da kuka. "Wallahi idan na ƙirga uku ba ki tashi ba sai kin maimaita har da tsallen kwaɗo." Jafar da ke zaune a gadon ƙarfen Dada ya furta fuska a haɗe. A yatsine Dada take kallon wurin ta ce. "Waye haka kuma da baƙaƙen kaya? Na san dai na ba wa Mamman tarbiyya ba zai yi wannan rashin imanin ba, domin ni musulma ce kuma ina sallah a ɗakina amma dubi garsameman ƙato ya shigo mini da waɗannan takalman kalar na arnan Lagas har cikin ɗakina. Wai Jafaru za ka fito ka cire mini takalmi a waje ko sai na kira ubanka mamman ya fitar da kai?" "Dada kada ki sake ɓata mini rai!" Jafar ya furta a takaice. "Ran naka ya fi na ran ƙuda ɓaci, ke Uwani ta shi ki tafi wannan zalinci ba za a yi shi a ɗakina ba. Ni kam wallahi Sa'idu ya gama cutata da ya haɗa mini zuri'a da aikin kaki." Dada ta furta ƙwalla na zuba. Bindigar aljihunsa ya zaro yana juya ta, ganin bindigar ya sa daga Uwani har Dada suka zabura. Hawaye bibbiyu na bin fuskar Dada ta ce, "Yanzu harbe mu za ka yi Jafaru? Ni kam ko ana sauya muku zuciya daga ta musulmai zuwa ta kafirai a wurin tirenin ne?" Jafar ya sake haɗe fuska ya ce. "Ta kanki zan fara ma, Dada sai yau kika san ana sauya mana zuciya?" Ganin yadda ya sha kunu ya sa jikin Dada ya fara karkarwa, Jafar ya fara takowa a hankali kafin ya ƙarasa sai gani ya yi Dada ta zube ƙasa a sume. Murmushin gefen baki ya saki, Uwani na ganin haka ta wage baki ta ƙwalla ihu, a daidai lokacin Malam na madina ya kawo kai yana faɗin. "Wallahi Uwani sai Allah ya yi mana hisabin wannan ihun da kike yi mana babu ji babu gani." Jafar ya hango a tsaye ya mayar da bindigarsa aljihu, yana shirin magana ya hango Dada a yashe a ƙasa. "Na Madina wallahi Jafaru ne ya sa bindiga zai harbe mu shi ne Dada ta faɗi." Uwani ta faɗa fuska da hawaye shaɓe-shaɓe don ba ƙaramin tsorata ta yi ba. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya yi wani irin ihun da jaruman indiya suke yi, cikin kukan kura ya yi wata irin sufa ya cukumi wuya Jafar haɗe da maƙale shi yana faɗin. "Wiiiiihuuuuuuhuuuu gafara ga maza nan bisa kanka." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA UKU Ilahirin ƙarfinsa Malam na Madina ya ware yana cakumar Jafar, idan ya dunƙule hannu sai dai ka ji dum! Ya kai masa dundu a baya. Shi kansa Jafar ya yi mamakin ƙarfin dattijon duk da ba fin ƙarfinsa ya yi ba. Na Madina da ya ga ya ɗauki lokaci bai kai Jafar ƙasa ba, ya zuba wata uwar kabbara tamkar wanda yake tsakiyar yaƙin musulmai da arna yana faɗin. "Allahu Akbar." Da ya yi kabbara sai ya sauke wa Jafar wani dundu a baya. Uwani na ganin haka ta ɗebo ruwa a randa ta fara yayyafawa Dada, babu jimawa Dada ta fara sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe idonta. Jafar tun yana ganin dukan da Na Madina yake yi masa wasa ne har ya ga ya cukwikwiye masa wuya, har wani zullo yake yana kabbara yana kai masa duka tamkar mai jifan shaiɗan. Jafar ya haɗa hannuwan dattijon wuri ɗaya ya murɗe su sannan ya ce. "Wallahi Na Madina ko ka sauko daga kaina ko na bi yatsun hannunka ɗaya bayan ɗaya na tsike su kamar yadda ake tsinkar mangwaro." Jin matsar da Jafar ya yi masa da kuma furucinsa ya sa cikin Na Madina ya karta, yana shirin yin magana ya ji Dada na salati daga kwance. Tamkar ɗan biri sai ga na madina ya yi tsalle ya faɗo ƙasa, Jafar ya gyara wuyar rigarsa ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ya wuce ɗakinsa da Dada ta sa aka gyara masa. Malam na Madina ya tsugunna a daidai kan Dada ya ce. "Sannu da farkowa Kulu." Dada ta dube shi luuuu da idanu a shanye sai kawai ta ɗaga ɗan yatsa ɗaya ta ce. "Ashhadu anla'Ila'ha'illahu wa anna Muhammadur Rasulillah." Malam na Madina ya sake cewa. "Mun auna arziƙi Dada wannan yaron ashe harbe ku ya so yi?" Dada ta sake yin luuuu da idanu fuskar na Madina na yi mata gizo ta ce. "Ismi Hauwa kulu wa ana musulima." Jin haka ya sa Na madina ya fashe da kuka, kukan da Dada ta ji ne ya sa ta ɗan wartsake sai a lokacin komai ya fara dawo mata. Zumbur ta tashi zaune ta fara bin su Uwani da kallo. "Uwani kina jin maganata ko kuma da gaske Jafaru ya harbe ni na mutu?" Uwani ta saki dariya ta ce. "Ina jin ki mana Dada ga Na Madina ma a zaune." Dada ta kalli na Madina suna haɗa ido kamar haɗin baki suka fashe da kuka a tare. "Uwani maza ɗauko mini wayata."Dada ta furta cikin kuka. Da sauri Uwani ta ɗauko mata don ta san ba ya wuce ta ce a kira mata baba Mamman. "Maza kira mini Mamman." Uwani ta karɓi wayar ta gama dube-dubenta sannan ta ce, "Lambarsa ce mai hotan zuciya ko?" Da sauri Dada ta gyaɗa kai. Uwani ta kira tana jin an ɗauka ta miƙa wa Dada. "Assalamu Alaikum. Hajiya Dadata yau ke ce da kira da kanki..." "Dakata Mamman! Kiranka na yi ka gaya mini waye shugaban 'yan sanda na duk faɗin duniya?" Dada ta katse Baba Mamman a zafafe. "Shugaban 'yan sanda na duniya? Dada me ya faru kuma?" Ya tambaya a sanyaye. "Me ye ma bai faru ba Mamman? Ka gaya mini shugaban 'yan sanda na duniya da inda zan same shi, domin a yau ba sai gobe ba wallahi zan ce ya tube Jafaru daga wannan aikin kakin. Kai ni dai Sa'idu ya gama cutata, a ce 'ya'ya duka babu mai aiki ƙwaƙƙwara daga Soja, Rosafti sai Ɗan sabda. Wai kamar ni 'yar limamai jikar limamai ace duka 'ya'yana babu limami ko malamin makarantar allo." Sai da Dada ta fyace majina sannan ta cigaba. "Mamman ko ka sa a tube Jafaru ko kuma wallahi sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba..." "Don Allah Dada me yake faruwa?" Baba Mamman ya katse ta hankali a tashe. Nan take Dada ta zayyane masa duk abin da ya faru, ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba. Cikin kwantar da murya ya fara lallashinta har ya samu ta daina kukan sannan ta ce. "To yanzu Mamman yadda aiki yake wahala, idan aka tube Jafaru daga aikin nan wacce sana'a zai fara? Tsorona Allah tsorona kada ya fara ɗauke-ɗauke, ni dai na san Jafaru da tsoron Allah ko mage ba zai iya kashewa ba, to ko dai a Lagas ɗin nan ya fara 'yan zuƙe-zuƙe ne da ya zo zai harbe mu?" Murmushi baba Mamman ya yi ya furta. "Dada da ya kashe mana ke ai gara a tube shin kawai, amma dai ba na jin Jafar yana shaye-shaye ki bar ni da shi zan kira shi yanzu a waya wallahi ransa sai ya ɓaci." Dada ta ɗan yi jim sannan ta ce. "Ni fa Mamman ban ce ka kira shi ka yi masa tijara ba, ina zaman zamana Jafaru ya zo ya cika ni da nunkufurcin tsiya. Ni ban san ma lokacin da Saratu ta koya maka masifa ba, yara irinsu Jafaru sai addu'a da lallashi. Kai kanka Mamman ba don tsayuwar da na yi a Harami ba ai da ban san abin da za ka zama ba, Allah dai Ya shirya mana zuri'a." Baba Mamman ya yi murmushi ya amsa mata sannan suka yi sallama. Uwani sam ba haka ta so wayar ta kasance ba, don haka ta miƙe har za ta fita sai kuma ta wuce uwar ɗakin Dada tana sakin murmushi. A can ƙarƙashin gado ta ciro bankinta ta ƙwaƙulo kuɗaɗen da suke ciki, sai da ta ƙirga su kusan dubu ɗaya da ɗari biyar ne. Ta ɗaure su a ɗankwali haka kawai ta fara sakin murmushi, Dada ta bi ta da kallon mamaki baki a sake. Baba Mamman na kashe waya ya kira Jafar ya yi masa faɗa sosai, tare da nuna masa illar tsoratar da Dada da ya yi musamman da shekarunta suka tura. Jafar ya fahimci mahaifinsu sai dai shi tsokanar Dada yake da ya ce harbe ta zai yi. Can ƙasan akwatinsa ya je ya tura bindigar ya ajiye sannan ya shiga banɗaki ya watsa ruwa ya wuce ɗakin Dada. A nan ya shiga tsokanarta suka fara hira har Malam na Madina kamar ba shi ne ya gama kabbara yana naushinsa ba. Uwani na fita can kantin Ɗan bala ta wuce ta sayo alawa irin da raɗin suna leda biyu, sai ta ƙarasa wurin Ali mai dabino shi ma ta sayo gwangwani uku. Sai da ta tsaya a gefen hanya ta kunce kowacce leda ta zuba kofato biyu da ragowar jelar tumaki ɗai-ɗai sannan ta ɗaure. Tana tafe tana sakin murmushi har ta ƙarasa gida, kai tsaye sashen Baba Isuhu ta nufa za ta shiga kenan ta gan shi ya fito da alama masallaci za shi don an kira sallar Magriba. "Sakaryar banza ke ba kya ganin mutane ne?" Baba Isuhu ya furta yana wurga wa Uwani harara. "Ga shi wata mata ta ce na kawo maka." Uwani ta faɗa tana miƙa masa ledar hannunta. Da mamaki ya karɓa ya furta, "Wata mata kuma? Ba kuma Lami aka ce ki kai wa ba?" Uwani ta girgiza kai cikin alamun tsoro ta ce. "Kai ta ce a kawowa kuma ni fa idanun matar ya ban tsoro wallahi, Baba Isuhu dama mutane suna da kofato ne ban taɓa sani ba sai yau?" A firgice Baba Isuhu ya saki ledar alawar ya ce. "Kofato fa? A ina kika ga kofaton?" Uwani na ganin yadda ya firgice sai ta basar ta ce, "Bari dai na wuce wurin Dada..." "Don ubanki za ki tsaya ki mini bayani ko kuwa?" Baba Isuhu ya yi magana jiki na rawa, don bai jima da barin gidan Talle Mai gari ba, da yaje duba shi sakamakon yana kwance sharɓan. Kuma a dubiyar da ya je ne yake shaida masa abin da ya faru da shi a banɗaki da kuma ɗakinsa. "Eh matar ce na ga ƙafarta da kofato, sai ta miƙo mini ledar nan ta ce na ba ka. Kuma ta ce na faɗa maka idan ka wurgar da saƙon nan a kan mai sunan malam za ta fanshe."Da sauri Baba Isuhu ya tsugunna ya fara tattaro dabino da alawar, a nan idanunsa suka ci karo da kofato, tuno abin da Uwani ta faɗa ya sa jikinsa na rawa ya haɗa ledar ya sa a aljihu ya dubi Uwani ya ce. "Ina matar take yanzu." Uwani ta zuba hannu biyu ta yi tagumi ta ce. "Ni fa tana ba ni ledar nan da na waiga sai ban ganta ba, wallahi ina jin ɓacewa ta yi don kamar ƙiftawar ido haka na neme ta na rasa." Wani irin sanyi ƙafafun Baba Isuhu suka yi, Uwani ta yi kamar ba ta gane yanayin da yake ciki ba ta shige cikin gidansa. Baba Isuhu yana nan tsaye har zai fita ko me ya tuna da sauri ya faɗa cikin gida, yana tafe hawaye na zuba don jikinsa ya gama ba shi ta shi ta zo ƙarshe. Uwani na daga ɗakin Lami ta hango shi nan da nan ta ƙunshe dariyarta, yana shiga ɗakin ita kuma Goggo Sala na sirka ruwan wanka don aiki ne ya hana ba ta yi wanka da wuri ba. "Lami ni kam na shiga uku!" Da sauri Lami ta kalle shi, Uwani na jin haka ta muƙe ta fice. Da yake ta lura hankalinsu ba ya kanta kai tsaye ta bi hanyar banɗakin da Goggo Sala ta bi domin yin wanka. Lokacin da Uwani ta je wurin banɗakin Goggo Sala ta riga da ta tuɓe har ta fara wanka, a hankali ta saɗaɗa ta janye kayan da ta cire. Sannan ta fara wani irin gurnani tana kukan tinkiya. Goggo sala ta riga da ta saɓa sabulu a fuska da sauri ta dakata, jin ta daina wankan ya sa Uwani ta yi wani gurnani mai ɗan tsoratarwa sannan ta maƙe murya ta ce. "Gani gare ki Goggo Sala, ki nutsu ki saurari abin da zan faɗa miki domin zai yi miki amfani a matsayinki na jinsin bil'adam." Nan take jikin Goggo Sala ya ɗauki karkarwa kamar mazari, hannu biyu ta sa ta fara kiciniyar goge kumfan fuskarta amma yajin sabulu ya hanata buɗe ido. "Nan wurin da kike wanka masarautarmu ce, kuma kina tsaye ne akan karagar shugabarmu ga hadimanta nan sai zagaye ki suke yi. Wani abin haushi kin saka su kallon tsiraici, don ma Allah Ya taimake ki aljani Manu ɗan kwarto ba ya kusa da tuni ya haike miki." Jin haka ya sa Goggo Sala ta fashe da kuka, Uwani ta gimtse dariyarta ta cigaba da cewa. "Ni ce uwar garke wacce kika dafa namanta, to yanzu haka na dawo domin ni dama ba tinkiya ba ce. Kuma namana da kika dafa a tukunya na ɗauke shi na kai garkena, sannan zan kafa miki wani sharaɗi matuƙar kika saɓa masa zan ɗauke ki zuwa duniyarmu." Goggo Sala baki na rawa ta ce. "To Babata uwar garke faɗi kowanna sharaɗi ne ni mai biyayya ce a gare ki." Uwani ta sa hannu ta toshe dariyarta ta ci gaba da cewa. "Sharaɗin shi ne kullin za ki dinga goya Isuhu sau uku a rana, safe, rana da kuma dare. Idan kika zo goya shi ki dinga yi kina lasar baki, kuma idan kika kuskure koda na lokaci ɗaya ne ba ki yi ba take zan ɗauke ki ko kuma na tsotse romon kanki." "Wallahi zan yi ba dai goyo ba, ko har da Lami aka ce zan haɗa na goya su." Goggo Sala ta faɗa cikin kuka. "Kin taimaki kanki, yanzu kayan da kika cire zan kai shi garkena amma zan bar miki ɗankwali, kuma kada ki kuskura ki fito sai an kira sallar Isha'i domin anfara tattaunawar fadar aljanu da ke. Sannan ɗan autan shugabanmu ya ce da baya da baya za ki tafi ɗaki kina cewa nasara a kanku Isuhu da Lami." Goggo Sala ta amsa, a zuciyar tana da-na-sanin zuwanta zaman daɓaro gidan Lami. Uwani na gama maganar cikin sanɗa ta koma har lokacin baba Isuhu yana ɗakin don ta hango shi ta cikin labule, ta raɓe a gefen ƙofar ɗakin ta karkace murya ta fara kukan tinkiya. Shiru ta ji sun yi sannan ta yi wani gurnani tana yi tana buga ƙafa irin tsalle-tsallen da awaki suke yi. "Shi kenan Lami ta zo ina jin tafiya za ta yi da ni." Baba isuhu ya faɗa cikin kuka. "Ba zan tafi da kai yanzu ba. Ni uwar garke ni ce na aiko maka da saƙo ɗazu. Ku buɗe kunnenku da kyau, uwar garke ba mutum ba ce. Na zo na kafa muku sharuɗɗana idan kuka bi su zan yafe muku zunubin da kuka aikata mini, idan ba haka ba kuma a gabanku zan yi farfesun mai sunan malam na saka ku cinye shi kuma ku shanye romonsa." "Wallahi ko mene ne kika ce mu yi za mu yi miki biyayya." Lami ta faɗa a tsorace. "Kai Isuhu da farko taimakonka za mu fara yi kafin ka ji sharaɗinmu. Ƙanwar mahifiyar matarka babbar matsafiya ce a ɓoye, kuma dama da biyu ta zo zaman daɓaro gidanka. Idan kuma ka yi yunƙurin korarta za ta halakaka da iyalinka gaba ɗaya. Daga gobe ne wa'adin aikin da take yi a kanka zai fara, don haka yanzu ma za ku ga ta fito tana tafiya da baya-baya tana ambatar sunanku don haka kada wanda ya tanka mata. Kuma gobe za ta zo da sassafe ta ce maka za ta goya ka. Duk rintsi kada ka bari ta taɓa maka jikinka." A zabure Baba Isuhu ya ce. "Goyo fa? Ni Isuhu za a goya da giramana ban da iskanci?" Uwani ta katse shi. "Idan muna magana ba a tankawa. Sannan Sharaɗin da za mu kafa maka ya zama wajibi ka ɗauki rigunan mama na Lami guda uku ka kai wa mahaifiyarka Dada ka ce ta saka su..." "Dadar ce za ta saka bireziya..." Baba Isuhu ya furta cikin suɓutar baki. Uwani ta buga masa tsawa cikin gurnani ta ce. "Idan ka saɓa mana wallahi sai mun hallaka ka da kisa mafi muni." Nan take Baba Isuhu ya ce. "Duk abin da kika ce na bi Inna uwar garke." "Na dawo gare ki Lami. Ke kuma akwai dafin da Goggo Sala ta saka miki a ruwan wanka wanda wa'adinsa gobe zai cika, ko ba kya ganin irin maganin da take zuba miki a ruwan wanka kullin?" Da sauri Lami ta gyaɗa kai. "Idan kika sake shayar da ai sunan Malam daga gobe ke da shi mutuwa za ku yi, domin dodonta zai zuƙe jininku tas." Da yake Lami ta san Goggo Sala da shegen bin malamai nan take ta aminta da kalaman Uwani. "Sharaɗin da zan kafa miki ya zama dole daga gobe ki dinga ɗaukan mai suna Malam kina kai wa Jafar shi yana shayar da shi a sashen Dada." Cikin haɗin baki Lami da Baba Isuhu suka ce. "Jafaru kuma? Shi zai shayar da mai sunan Malam?" "To kada ku kai shi dama ɗan autan Goɗiya kwaɗayin romon jariri yake ji sai na dafe masa shi." Uwani ta faɗa cikin wata irin murya, don ita kanta dagewa take da tuni dariya ta kwace mata. "Wallahi za mu kai shi, Allah Ya kai mu gobe." Gabaɗaya suka amsa. "Kuma ya zama wajibi a gare ka, kai Isuhu ka saka ƙarfi ka danne Jafar domin a shayar da mai sunan malam idan ba haka ba komai zai iya biyo baya. Kuma sharaɗin da zan kafa muku na ƙarshe ko da wasa kuka faɗi abin da ya faru tsakanina da ku, sai na sa wuƙar aljanin mahauta ya yaɗe fatar jikinku sannan na ɗauke ku zuwa duniyarmu a azabtar da ku kamar yadda kuka azabtar da ni." Uwani na daga tsaye ta fara jiyo shasshekar kukan Baba Isuhu. Sai da ta lallaɓa ta ɗauke tukunyar naman da aka yi farfe su ta ajiye a soro sannan ta ce. "Tukunyar namana da kuka dafa ku same ta a wurin garkena, kada wanda ya fito har sai an kira sallar isha'i domin tuni an zauna zaman fadar aljanu da ku. Kuma idan kuka bari namana da kuka dafa ya kwana a garkena cikin dare zan gayyato tawagar jinsinmu su ɗauke mini ku." Uwani na gama maganar ta fara kukan tumaki tana wani irin dire-dire sannan ta ɗauki tukuyar ta tafi a hankali, kai tsaye ta wuce garken awakinta. Da yake duhu ya yi awakin Uwani duka sun kwanta, a hankali ta isa turken uwar garke ta ajiye tukunyar. Ta janyo igiyar uwar garke ta saƙale a jikin ƙafar tukunyar, zuciyarta fes ta wuce sashen Dada don ta yi sallar magriba tana tafe tana dariya kamar sabuwar kamu. Har alla-alla take gari ya waye ta ga irin diramar da za a tashi da ita. A lokacin da ta shiga ɗakin Dada Jafar na zaune ta kofin shayi a gefensa , ga laptop a gabansa yana dannawa, dawowarsa daga masallaci kenan. Uwani na ƙare masa kallo ta tuntsire da wata mahaukaciyar dariya, domin yanayin zaman da ta ga ya yi ne har ta hango yadda Baba Isuhu zai danne shi a shayar da mai sunan malam. Ɗagowa ya yi ya kalle ta sai kuma ya ci gaba da danna laptop ɗinsa, Uwani ta sake kallonsa ta ga yadda yake jin magani sai kawai ta tsugunna a wurin tana sheƙa uwar dariya. "Uban me kike yi wa dariya?" Jafar ya furta a daƙile. Tamkar wacce ya sake ingizawa, sai Uwani ta sake fashewa da dariya har da hawaye da ta tuna duk irin haɗe fuskar da yake yi wai shi za a danne a shayar da mai sunan malam. "Ba tambayarki nake yi ba?" Jafar ya buga mata tsawa. "Dama wani wasa ne muka fara bugawa ni da ƙawata Lantana shi ne na shirya mata yadda zan cinye ta gobe." Uwani ta yi maganar tana ɗan murguɗa baki. "Ba na son shashanci idan wannan iskanci za ki yi ki fice mini ba na son hayaniya." Uwani ba ta kula shi ba ta gimtse dariyarta ta shige uwar ɗakin Dada. Ku kawo wa Jafar ɗauki zai shayar da mai sunan malam🤭🏃🏼‍♀️😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA HUƊU Tun da Uwani ta fito daga gidan baba Isuhu daga shi har Lami babu wanda ya kuma motsin kirki, baba Isuhu ya sharɓe hawaye ya dubi Lami cikin kallon tsana da jin haushi ya ce. "Tsakanina da ke Allah Ya isa Lami, kin cuce ni kin cuci rayuwata. Ni ban san ƙaddarar da ta sa na auro ki ba, duk wannan ƙaton bakin na ki ko ina ya je da ban gan shi ba sai yanzu?" Lami ta wurga masa harara ta ce. "Mun dai cuci juna malam ka gyara maganarka. Ni kaina ban azal da kuma rabo me zan yi da kai? Ka san dai duk a samarina kai ne faƙiri matsiyaci." "Wallahi aurena da ke bai ƙare ni da komai ba sai masifa, ina zaman zamana kin jefa ni a jafa'i muguwa mai ƙashin tsiya..." "Dakata malam, kada ka raina mini hankali. An gaya maka ban san dama can kana 'yan sace-sacenka ba? Ko ka manta kajin Yaya Haladu da muka taɓa soyewa?" Shiru baba Isuhu ya yi yana nazari, shi kam ya ci alwashin daga uwar garke har abada ba zai ƙara taɓa kayan wani ba. Dama tun da yake 'yan ɗauke-daukensa ba a taɓa kama shi ba, don haka zai ajiye sata salin-alin ba tare da ta tona masa asiri ba. Suna nan zaune suka ji an rafka kiran sallar Isha'i, babu jimawa suka ji takun Goggo Sala tana tafe da baya-baya, taku ɗaya-biyu idan ta yi sai ta ci karo da kwanuka sannan ta furta. "Nasara dai a kanku Isuhu da Lami." Da hannu Lami ta yafito baba Isuhu ta cikin labule take nuna masa ita, cikin gasgata maganar da Uwani ta gaya musu suka saki baki suna kallonta, a ɓangare ɗaya kuma tsoron Goggo Sala ya kama su. Tana shiga ɗakin da suke kwana da Lami ta banko ƙofa, can ƙuryar bango ta zauna sai kawai ta rushe da wani irin kuka mai cin zuciya. "Kaico kwaɗayina bai amfane ni da komai ba, Allah ka fitar da ni daga wannan gidan annobar. Wallahi nan gaba idan duniya Lami za ta haifa har abada ni da gidanta." Ganin ta shige ɗaki ya sa baba Isuhu ya fita a hankali domin cika umarnin uwar garke, kai tsaye garken Uwani ya nufa yana haskawa kuwa ya yi ido biyu da tukunyar farfesun naman. Nan take ƙirjinsa ya buga, jikinsa ya fara karkarwa sai da ya yi ta maza ya ɗauko tukunyar ya nufi sashensa. WASHEGARI Baba Isuhu tun da ya yi sallar asuba ya gagara runtsawa saboda fargabar goyon da Goggo Sala za ta yi masa, yana zaune a gefen gado ya kallo Lami da ke kwance ita da mai sunan malam. Motsi ya ji a tsakar gida yana leƙawa ya hangi Goggo Sala tana kaiwa da kawowa, abin duniya ya dame ta saboda gari ya fara haske amma har kawo lokacin babu Isuhu babu motsinsa. Cikin sanɗa ta nufo ɗakin da suke ciki baba Isuhu ya leƙo ta windo ya ce. "Munafukar Allah ta'ala ina ankare da ke, wato fakona kike za ki hallaka ni ko?" Goggo Sala ta washe baki tana basarwa ta ce. "Isuhu barka da safiya." Baba Isuhu da ya tuna gargaɗin da aka masa, aka ce kar ya yi mata kora da hali shi ma sai ya yaƙe baki ya amsa. Amma a zuciyarsa ji yake tamkar ya fashe da kuka. Mai sunan malam ne ya motsa Lami ta yi fitgigit ta tashi zaune. "Maza tashi mu je ki kai shi wurin Jafaru." Ba musu Lami ta tashi ta saka hijabinta, baba Isuhu ya manta Goggo Sala da ke waje tana fakonsa ya sa hannu ya buɗe sakata suka fito. Har zai yi gaba ya tuna bai ɗebo rigunan maman Lami da aka ce ya kai wa Dada ba, dama tun a daren ya sa Lami ta ɗebo masa guda uku daga cikin na ta. Komawa ya yi ya ɗebo ya zuba a aljihu sannan ya fito. Yana fitowa Goggo Sala ta yi wata uwar sufa za ta cafko baba Isuhu, a firgice ya zuba a guje yana faɗin. "Wayyo Lami ki zo za ta cafke ni, wallahi tsaf za ta sa a tsotse romon kaina." Goggo Sala na ganin rana ta fara fitowa ga shi ba ta cika umarnin uwar garke ba, ya sa ta rufa wa baba Isuhu baya yana gudu tana bin sa. Da yake ya gama tsorata da ita har gani yake kamanin Goggo Sala kamar har rikiɗe masa suke yi, Goggo Sala irin dogayen matan nan ne, shi kuma baba Isuhu ba shi da tsayi kuma ba shi da jiki. Don haka Goggo Sala ta kusa kama shi amma Allah ya taimake shi ya fice daga gidan, Lami ta rufa masa baya da sauri ya tura ƙofar ya datse ta. Wata gwaruwar ajiyar zuciya ya sauke yana ayyana shi kenan da tuni an bayar da jininsa. Ɓangaren Dada a buɗe yake don haka ba su sha wata wahala ba suka nufi ɗakin da Jafar yake ciki, Lami ce ta fara ƙwanƙwasawa sun ɗan jima sannan Jafar ya buɗe da alama bacci yake yi. Daga shi sai singlet da gajeren wando ya buɗe ƙofar yana murza idanu. Da mamaki yake bin su Baba Isuhu da kallo ya furta. "Ina kwana baba." Baba Isuhu ya washe baki. "Jafaru an tashi lafiya?" Jafar ya amsa sai baba Isuhu ya ce. "Wurinka muka zo Jafaru amma ko za mu ƙarasa ɗakin Dada?" Zuciyar Jafar fes ya ce. "Ok to bari na saka kaya ga ni nan zuwa." Lami da baba Isuhu suka wuce ɗakin Dada a lokacin tana zaune tana jan carbi. Tana ganinsu ta shafa addu'ar, sai da ta cire hijabin ta ajiye carbin ta ce. "Isuhu lafiya na gan ku da farar safiyar nan?" Cikin haɗin baki suka gaishe ta. Baba Isuhu ya ciro rigunan maman hannunsa ya miƙa wa Dada ya ce. "Dada ga wannan a saka." Dada ta karɓa tana yamutsa fuska. "Kai kuwa Isuhu kamar wanda ya kwana da Uwani a rai, tun da farar safiya ka kawo mata wata rigar mama. Wannan dai rigunan ai na manyan mata ne, ina Uwani ina wannan lalacewar." Baba Isuhu ya ɗan sosa kai ya ce, "Ai dama ba na Uwani ba ne, ke na kawowa Dada..." Tun bai ƙarasa magana ba Dada ta katse shi, "Ni fa Isuhu? Ni kuwa me zan yi da rigar mama tsofai-tsafai? Amma dai ka ci mutumcina Isuhu, wai ko dai ka fara 'yan zuƙe-zuƙe ban sani ba?" Idanun baba Isuhu suka ciko da ƙwalla sai da ya share hawaye ya ce. "Don girman Allah Dada ki ɗiba ki shiga ɗaki ki saka." Baki sake Dada take kallonsa, ta rafka salati haɗe da faɗin, "Maza kwashe mini lalatattun kayan nan kafin ranka ya ɓaci. Ni Kulu uban me zan saka a ciki? An ya Isuhu shaɗanu ba su dafa maka kai a cikin bacci ba?" Uwani da ke uwar ɗaki ta sunne kai ƙasa tana dariya. "Haba Dada da farar safiya ki cika wa mutane kunne da ihu." Jafar ya faɗa yana sako kansa cikin ɗakin. Uwani da ke ɓoye a ɗaki ta yi ƙasa da murya ta ce, "Kai ma naka ihun yana tafe." "Ba dole ka ji ihuna ba Jafaru yanzu kamar ni tsofai-tsofai." Sai kuka ya ci ƙarfin Dada sai da ta share hawaye sannan ta watsa wa Jafar rigunan a fuska ta ci gaba. "Wai Isuhu ya rasa me zai kawo mini sai baraziya wai na saka. Yanzu saboda Allah Jafaru ko uwarka Saratu me za ta yi da baraziyya ballantana kuma ni?" Tun Dada ba ta gama magana ba Jafar ya watsar da rigunan sakamakon wani tsami da bashi-bashi da ya ji ya doko hancinsa. "Haba Dada me kike yi haka ne?" Jafar ya faɗa a ƙazance. Kafin Dada ta yi magana mai sunan Malam ya sake tsanyarewa da kuka, Lami ta dubi Jafar ta miƙa masa shi. Kamar Jafar zai yi magana sai kuma ya basar ya miƙa hannu ya karɓe shi, yana bin su da kallon mamaki. "Don Allah Jafaru ka taimaki yaron nan ka ba shi mama ya sha ko ya yi shiru." Lami ta faɗa a ɗan kunyace. Jafar ya kalli Lami cikin sauri ya ce. "Wane Jafarun?" Jafar ya tambaya a hargitse. "Kai mana Jafaru, don Allah ka yi ka ba shi kada ya shiɗe don tun ɗazu yake kuka." Baba Isuhu ya furta. Ran Jafar ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya haɗe fuska ya dubi baba Isuhu. "Baba wannan wacce irin magana ce babu tsari, yanzu idan na faɗa maka magana a ce na yi rashin kunya. Idan har ni zan iya shayar da shi me ya hana kai ba ka shayar da shi ba?" Dada ta saki baki da hanci tana kallon baba Isuhu a tsorace, don ita a yanzu ya fara ba ta tsoro shi da Lami. A hankali ya ajiye mai sunan malam a gefe sannan ya miƙe, yana shirin tafiya Lami ta ce. "Isuhu sai fa mun danne shi..." Tun Lami ba ta ƙarasa magana ba baba Isuhu ya sa ƙafa ya shatalo ƙafar Jafar sai ga Jafar a ƙasa. Dada na ganin haka ta fara tafiya da rarrafe don ta tabbata yau su Isuhu babu lafiya, shi ya sa ta nemi guduwa kafin ita ma su dawo kanta su danne ta su saka mata rigar mama. Jafar ya yi mamakin yadda ya gagara ƙwace kansa a hannun baba Isuhu, don haka jin baba Isuhu ya fara ɗaga masa riga sama ya fara kiciniyar kare kansa, garin yunƙurin danne rigarsa sai ga Jafar yana sakin tusa. Uwani kuwa me za ta yi ba dariya ba har hawaye saboda mugunta. Ganin haka ba zai kai Jafar ba ya sa ya fara ihu. "Wayyo Dada ki kawo mini ɗauki. Wayyo Allah! Mutanen gidan nan ku kawo min ɗauki su Lami za su haike mini." Uwani na daga ɗaki ban da dariya babu abin da take sheƙawa, saboda tsabar dariya har kwanciya ta yi ƙasa. Suna cikin haka sai jin muryar Goggo Sala suka yi a bakin ƙofa ta fara lashe baki tana faɗin, "Allah na gode maka da har yanzu lokaci bai ƙure mini ba." A zabure baba Isuhu ya ɗaga Jafar, take jikinsa ya fara karkarwa ta fara tunkaro shi yana ja da baya. "Wayyo Allah Dada ki zo Goggo Sala za ta sa a cinye ni." A madadin Jafar ya gudu tun da ya samu ya tsira sai ya bi baba Isuhu da kallo, saboda ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba. Dada da ke cikin ɗaki ta kai wa Uwani duka tana ce wa. "Dariyar me kike yi Uwani mu da ya kamata mu fara yunƙurin ƙwatar kanmu." Kafin Uwani ta yi magana suka ji baba Isuhu ya zuba ihu. "Wayyo ta shanye mini ƙafafu, Jafaru, Dada ku zo ku kawo mini ɗauki." Goggo Sala ba ta bi ta kan baba Isuhu ba ta shatalo ƙafafuwansa za ta sunkuta shi a baya sai ga baba Mustafa da baba Idris sun shigo. "Subhanallahi kai Isuhu lafiya kuwa?" Suka ƙarasa maganar suna ƙarasawa wurin Goggo Sala, baba Isuhu da yake ya gama tsorata sai ji suka yi sharaf ya faɗo jikinsu da alama ya suma. Suka kama shi suka kwantar a ƙasa sai kawai Goggo Sala ta fashe da kuka. "Yanzu shi kenan rayuwata ta zo ƙarshe." Da mamaki suke bin ta da kallo, Baba Mustafa ya dubi Jafar da ya yi laƙwas a gefe ya ce. "Kai Jafar wane sakarci ne haka ake yi kai kuma kana zaune?" Jafar ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Baba ni ma ta kaina nake da tuni sun haike mini, dube ni wai fa ni zan shayar da mai sunan Malam." "Gara da Allah Ya kawo ku Idirisa, wallahi Isuhu shi da matarsa sun haukace. Ashe ba su kaɗai ba har da Salamatu ita ma, an ya ba gamo suka yi a cikin gidan ba. Ban da haka wai ni Isuhu zai kawowa rigar mama ya ce na saka, sannan su dubi garjejen ƙato kamar Jafaru su ce ya shayar da me sunan malam." Baba Mustafa ya yi farat ya ce. "Shi Jafarun ne zai shayar da jariri?" Dada ta wara hannuwa ta furta. "Ta ya ni ji dai Muɗɗafa, ka ga dai a kan idona aka haifi Jafaru. Kai ƙarshe ma dai ni na yi jinyar shayin da aka yi masa ballantana na ce ko Jafaru ya koma mata-maza, Jafaru ko ka sauya daga baya zuwa mata-maza ne ban sani ba." A ƙufule Jafar ya ce, "Wallahi Dada kar ki ƙara ce mini mata-maza." Kukan da mai sunan malam yake tsanyarawa ne ya sa baba Idris ya yi wa Lami magana, sai da ta share ƙwallar idonta ta ce. "An ce daga jiya kada na ƙara shayar da shi." A daidai lokacin baba Isuhu ya farfaɗo sakamakon ruwan da aka yayyafa masa. "Waye ya hana ki shayar da shi?" Shiru gabaɗaya suka yi, baba Isuhu ya dubi Lami ita kuma ta kalli Goggo Sala sai kawai suka fashe da kuka lokaci ɗaya. Shiru ɗakin ya yi kowa yana bin su da kallon mamaki, ban da Uwani da ke sakin murmushi a fakaice. Sai da suka yi me isar su sannan aka samu da ƙyar Goggo Sala ta ce. "Ni kam na san wannan jawabin da zan yi ƙila shi ne na ƙarshe a rayuwata don na san kashe ni za su yi." Baba Isuhu ya yi tsammanin bayanin 'yan ƙungiyar asirin da take ciki za ta faɗa, don haka ya zuba mata ido sai ya ji ta ce. "Dama dai uwar garke ba..." Kamar haɗin ba ki Lami da Isuhu suka ta fi da gudu suka toshe mata baki, da mamaki mutanen ɗakin suka bi su da kallo. "Ƙarya take yi makira haɗa ni da 'yan uwana za ta yi." Baba Isuhu ya faɗa yana haki kamar wanda ya ci gasar tseren gudu. "Ba ma son shashancin banza da wofi Isuhu, sakar mata baki kada ranka ya yi mummunan ɓaci." Baba Mustafa ya faɗa a fusace. Babu yadda suka iya haka suka koma suka zauna jiki a sanyaye, baba Isuhu ya sunkuyar da kai ƙasa gabansa na faɗuwa. Goggo sala ta fara wassafo jawabi tiryen-tiryen tana hawaye. Tana gama jawabi gabaɗaya ɗakin suka ɗauki salati. "Kaico rayuwa ni Kulu me na haɗa da sata da Isuhu zai janyo mini mugun hali cikin zuri'ata." Dada ta furta tana zubar da ƙwallah. Malam na Madina da ke gefe ya ce. "An ya Isuhu yanzu rayuwar da ka ɗauko mana kenan? Wallahi ka yi gaggawar yin istigifari kuma ka nemi masu kaya ka mayar musu da abin su. Idan ba haka ba muna cikin Firdausi kana Hawiya, atoh faɗar Allah ce ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani." Shiru ɗakin ya yi kunyar duniya ta mamaye baba Isuhu shi da su Lami. Baba Idiris da baba Mustafa suka rufe shi da faɗa sosai, don haka ya nuna nadamarsa a fili. Sannan baba Mustafa ya juyo wurin Dada. "Dada ki gafarce ni a game da abin da zan faɗa amma tun farko ke ce kika ɓata Isuhu, saboda Isuhu yana ɗan autanki kika ɗauki son duniya kika ɗora masa. Hatta makaranta da Baba Sa'idu ya saka shi daina zuwa ya yi kuma kika goya masa baya, duk cikinmu shi kaɗai ne bai samu karatun arabi da boko mai zurfi ba. Ga shi nan sana'o'in ma wacce ce ba a nuna masa ba amma kullin a tsalle-tsalle yake ba shi da aiki sai kame-kame, tun wuri ka yi wa kanka faɗa domin kullin girma kake ƙara yi." Dada ta sharce ƙwallar da ke fuskarta ta ce. "Yanzu dama Muɗɗafa ka na da tarin nasihohin nan tutuni ba ka yi mini ba? Ni dai wannan maganar a rufe ta a nan kada Sa'idu ya ji don wallahi sai ya kusa cinye ni ɗanya." Gabaɗaya suka amsa mata. "Dama wannan abin kunyar ai ba za mu bari ya fita ba Dada, yanzu dai a tambayi Uwani tun da haƙƙinta ne ta yafe masa?" Uwani da ke gefe ta saki murmushin ƙeta ta yi saurin cewa, "Ni dai Baba na riga da na yafe musu baba Isuhu ai tamkar mahaifina na ɗauke shi." Da sauri Jafar ya dube ta don haka kawai ya ji bai yarda da kalaman Uwani ba. "Allah Ya yi miki albarka Uwani, dama ɗa ba sai wanda ka haifa ba kaico rayuwa Allah Ya gafarta wa Yaya Umaru." Baba Isuhu ya faɗa yana sharce ƙwallah. Uwani ta saki murmushin ƙeta a ranta ta ce, "Za ka ga ɗa ba sai ka haifa ba." Baba Idris ya yi musu nasiha sannan ya ce shi da kansa a ranar zai kira su Aramma na gangare su yi saukar Alƙur'ani a gidan gabaɗaya. "Baba ni fa gani nake wannan abin da aka yi musu kawai tsoratarwa ne wani ke yi musu, idan aljanun gasken ne ai da tuni sun ɗauki mataki. Kada a yi wasa da hankulan mutane a dai duba lamarin." Jafar ya yi maganar yana zuba wa Uwani kallon tuhuma, don yadda ya ga tana sakin murmushi ya ji sam bai yarda da ita ba. "Koma dai mene ne ai babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji Jafaru. Allah Ya yi mana maganin wannan masifa." Baba Mustafa ya faɗa, gabaɗaya suka amsa da Amin. Uwani na haɗa ido da Jafar ta sakar masa harara, haɗe da murguɗa masa baki. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHIDA Dada ta zuba musu ido ganin yanayin da Uwani take ciki ya sa ta aminta da kalaman ɗan'uwanta, ta san dai ba zai taɓa yi musu ƙarya ba. Runtse idonsa Jafar ya yi yana fesar da iska mai zafi, ya buɗe idanunsa da suka rine jawur kamar gauta ya sauke su a kan malam Na Madina. A fusace ya ƙarasa gabansa ya cukwikwiyo babbar rigarsa ya riƙe shi wuri ɗaya rai a ɓace ya furta. "Wallahi ba don ina duba tsufanka ba, da yau sai na bambamce maka tsakanin zuma da maɗaci." Jafar ya sake shi sannan ya wuce ɗakinsa, saboda tsoro tuni malam Na Madina ya yi mutuwar tsaye. Dada ta bi bayan Jafar da kallon tsoro baki a sake. "Yaya an ya Jafaruna ne ba aljanu ne a kansa ba..." Kuka ya katse maganar da Dada take yi. "Sharrin ƙwaya ce Kulu, na sha faɗa miki wannan aikin ɗamarar ba zai haifar da samun ɗa mai ido a cikin zuri'armu ba. Yanzu wa gari ya waya? A ce Jafaru bai san Kano garin Musulunci ba ne? Ya ɗauka rayuwar da yake yi a Legas ita zai yi a gidan nan. Kin ga dai abin da ya faru a gabanki. Da fa dukana zai yi, kaico rashin haihuwa ne ya ja mini haka." Na Madina ya fashe da kuka, Uwani da ke gefe ko a jikinta ta shige ɗaki ta ci gaba da sauya kaya. Don ita hakan da ya faru ma daɗi ta ji, ko ba komai ta san Jafar da zuciya ba lallai ya sake shiga sashen Dada ba sai bayan kwana biyu, ballantana ya hora ta a kan laifin da ta yi masa. Tana gama sauya kaya ta fice a nan harabar gidan ta ga Lawan da matarsa Fanteka, 'ya'yan ta ɗibo ta yi hanyar keji da su uwar ta rufa musu baya. Sai da ta dawo ta ga Lawan yana tsince-tsince a wurin akuyoyinta. "Kai dai Lawan ka cika ɗan kishiya riƙon mai haƙuri, wallahi da kiwon ka aka ba ni da ka ja mini zagi a ce na bar ka da yunwa." Uwani ta yi maganar tana ƙoƙarin kama shi, Lawan ya yi tsalle zai dira a kan katangar gidan Baba Isuhu da ƙyar ta kama shi tana sakin murmushi. Kai tsaye sashen Dada ta wuce tana shiga ta ci karo da Jafar ya fito ɗauke da jaka a kafaɗa.   "Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Yaya ka ga yaron nan saboda ya san tsiyar da ya shuka fita zai yi ya bar mu, ni dai wallahi Sa'idu ya cuce ni duk wannan abin da yake faruwa Sa'idu ne sila." Jafar bai bi ta kan su Dada ba ya fice daga gidan har yana hankaɗe Uwani. "Kulu Allah Ya ba mu alheri, wallahi Jafaru ba zai yi mana turun jeka ka mutu ba. Ya shuka bishiyar tsiya mu da ba mu ji ba, ba mu gani ba mu girbe masa." Malam na Madina ya sake jan jaka ganin haka ya sa Dada ta ce. "Ka jira ni yanzu zan kira Inusa dole ya tara mini 'yan'uwansa a gidan." Dada ta yi maganar tana faɗawa ɗaki domin ɗauko wayarta. "Inusa a yanzu ba sai gobe ba ka tara mini 'yan'uwanka, wallahi idan ba haka ba zan bar muku gidanku na shiga duniya. Kuma ku yi gaggawar kiran Jafaru ku ce ya dawo don zaman nasu ne, shi da Uwani ne suka ƙulla tsiyar da bakina ba zai iya furtawa ba." Daga haka Dada ba ta sake cewa uffan ba ta kashe wayarta, da kashe wayar babu jimawa Baba Yunusa ya sake kiranta, Dada na ɗauka ta ce. "Yunusa wai wa muke yi wa Sallah da azumi?" Daga can ɓangaren Baba Yunusa ya ce. "Allah." Dada ta sake haɗe fuska kamar yana ganinta ta ce. "Da ma saboda na fita haƙƙinka a matsayinka na babba shi ya sa na kira na sanar da kai, wallahi idan ba ka haɗo mini kan 'yan uwanka ba sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba." Dada za ta katse da sauri Baba Yunusa ya ce. "Shi kenan Dada ga mu nan zuwa yanzu In shaa Allah." Ta amsa masa sannan ta katse wayar, sai da ta lallami Na Madina sannan ya mayar sa akwatinsa. Falon tsit ya yi da ka kalli fuskokinsu ka san kowanne yana cikin damuwa, Baba Yunusa ne ya yi  ƙarfin halin cewa. "Dada gaba ɗaya ga mu mun hallara." Jafar tun da ya sunkuyar da kai ƙasa zuciyarsa ke tururi, Uwani na raɓe a gefe sai raba ido take kamar ƙosan sadaka. Ganin haka ya sa jikinsu ya sake yin sanyi, don sun tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa.   Sai da Na Madina ya kalli Jafar da Uwani sai ya sake fashewa da kuka, ganin haka ya sake raunata zuciyar Dada ta ja gefen mayafi ta fara sharce hawaye sannan ta fara magana. "Gabaɗayanku na tabbata idan za ku yi mini shaidar Allah da Annabi, za ku yarda da abin da zan faɗa." Suka amsa mata cikin haɗin baki. Dada ta ci gaba da ce wa. "Wallahi ƙanin mahaifinku Sa'idu ya cuce ni cutar ta har abada, amma ya je ba ni ya yi wa ba zumuncin Allah ya yi wa kuma ranar gobe ƙiyama sai igiyar zumunci ta zarge shi. Ni dai ba zan shiga tsakaninsa da Ubangiji ba amma sai mun tsaya a gaban Ubangiji ni da shi." Sororo gaba ɗaya suka yi hankali a tashe suna kallonta. Baba Yunusa ya ce. "Dada me yake faruwa haka ne Baba Sa'idu fa? Baba Sa'idu da ya zame mana bango madafa kuma majingina, mutumin da ya maye gurbin mahaifinmu..." "Inusa wa ya samar maka aikin Sojan nan? Kuma wa ya samarwa ɗan'uwanka Mamman aikin Ɗansanda, shi kuma wancan Rosofti?" Dada ta Katse shi. "Duka Baba Sa'idu ne ya samar mana Dada wani abu ne ya faru?" Ya tambaye ta a sanyaye. "Aikin ɗamarar ba shi ya kai Jafaru Lagas ba?" Duka suka amsa mata, jin furucin Dada ya sa Jafar ya ɗago a fusace. Dada ta cigaba da faɗin. "Silar haka ai ga shi muna shirin samun Iron Alto na biyu a cikin gidan nan." Jin kalaman Dada ya sa gaba ɗaya suka ɗauki salati hankali a tashe. Baba Isuhu ya wurga wa Jafaru wani mugun kallo cike da ƙyama, yana riƙe da haɓa hannunsa ɗaya kuma na riƙe da mai sunan Malam. Sai da ɗakin ya lafa da hayaniyar da ake yi sannan Na Madina ya ce, "Wallahi ba tun yau ba shi ya sa magana ta a kullin yaran nan a aurar da su, amma da yake nasara ya hure muku kunne sai ku ce yara sai sun yi karatu. Yanzu dubi garsamemen ƙato kamar Jafaru a ce bai yi auren fari ba, ni wallahi ina kamarsa da Allah Ya ba ni haihuwa da na yi 'ya'ya uku. To yanzu me ya fi wannan haushi? Wa ya sani ma a Lagas ɗin ko 'ya'yan ƙedarai ne suka suke buɗe masa idanu, yake wartar ɗaya bayan ɗaya yana sakayewa a gefe. Ga shi nan yanzu ai ya gagara haƙuri ya ja Uwani ɗakin Kulu suna watsa wa sunnar Ma'aiki ƙasa a ido." Kamar haɗin baki gabaɗaya mutanen ɗakin suka furta. "Innalillahi Wa'inna ilahirraji'un."   Duk budurin da ake yi ko a jikin Uwani ita babbar damuwarta ba ta wuce ta samu ta tsira daga horon Jafar ba, don ta san yadda ransa ya ɓaci idan ta shiga hannunsa sai Allah. Ran Jafar ya kai matuƙar ƙololuwar ɓaci don haka a zuciye ya buga tsaki haɗe da miƙewa zai fice daga ɗakin. "Wallahi matuƙar Jafaru ya fita daga ɗakin nan Mamman sai ka bi ɗanka, tun da ni da ɗan'uwana ba mu isa da shi ba." Dada ta yi furucin rai a ɓace. "Koma ka zauna Jafar." Mahaifinsa ya furta murya a dashe saboda ɓacin rai.   "Daddy wai ba ka ji me waɗannan mutanen suke faɗa ba ne? Wannan wanne irin abu ne. A ce a rasa ƙazafin da za a yi mini sai na zina, kuma na rasa da wa zan yi sai Uwani yarinyar da ƙazanta ta samu gurbin zama a ilahirin jikinta..." Na Madina ya katse Jafar sakamakon rarrafowar da ya yi, ya dafa ƙafarsa. Kwanciya na Madina ya yi a gabansa sannan ya fashe da kuka. "Don Allah kada wanda ya hana Jafaru ya rufe ni da duka, dama ɗazu ka so dukana to ka saka bindiga ka tashi kaina a kan waɗannan magangun da kake faɗa mana ni da 'yar uwata." Na madina ya furta ƙwallah na zuba, idan ka ga yadda yake rusar kuka sai ka rantse da Allah wani abin aka yi masa. "Ba na son sakarci ka koma ka zauna Jafar." Mahaifin Jafar ya buga masa tsawa. Sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya koma ya zauna yana wurga wa su Na Madina harara, ya sunkuyar da kai ƙasa cikin ɓacin rai. Baba Inusa da kansa ya ƙarasa ya tashi Na madina ya koma mazauninsa sannan shi ma ya koma ya zauna.    Baba Rufa'i ya gyara zama, sannan ya fara magana. "Dada duk mun ji abin abin da yake faruwa amma don Allah ku gafarce ni a maganar da zan faɗa." "Kayya Rufa'i muke wa Ubangiji laifi ma ya yafe mana, ballantana ɗan'adam abin banza." Cewar Dada. "A iya sanin tarbiyyar da yaran nan suke da ita ba mu taɓa tsammanin haka za ta taɓa faruwa ba, sai dai kuma ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba." Dada ta jinjina kai jin kalaman Baba Rufa'i yana shirin ci gaba da magana ta katse shi. "Ai albasa ce ba ta yi halin ruwa ba Rufa'i, wai a rasa wurin da za a yaye wa sunna labulen albarka sai a ɗakina. Kaico ni Kulu." Sai da Dada ta yi shiru sannan ya ɗora. "Kai Jafar ina maka kallon mai hankali ya aika yi haka ta faru?" Kai tsaye Jafar ya nuna su Dada murya a shaƙe ya ce. "Baba a tambaye su ni kaina sama ta ka na ji abin da suke faɗa." "Ba ni da ɗan uwana ka ƙaryata ba, uwarka Saro da ubanka Mamman su ka ƙaryata ka ji Jafaru." Dada ta furta tana wurgawa Jafar taƙuwa. "Ka shiga taitayinka Jafar? Idan na kuma jin magana mara daɗi daga bakinka sai ranka ya yi mummunan ɓaci, ke Uwani shin yau wannan abin ya taɓa shiga tsakaninki da Jafar ne?" Baba Rufa'i ya jefa mata tambaya. Zuciyar Uwani ɗaya ta share ƙwalla ta ce, "Wallahi ni kam azalce ta kai ni ɗakin Ya Jafar, ashe Lawan yana laɓe a bayana ban san ya biyo ni ɗakin ba." Cikin haɗin baki duka suka ce, "Waye Lawan? "Mijin Fanteka ne." Uwani ta faɗa cikin kuka. "Ashe ba ki da hankali Uwani? Ashe sakarcin na ki da ake faɗa gaskiya ne? A ina Lawan ɗin yake kuma ɗan gidan uban waye a ƙauyen nan? Da har zai shigo cikin gida ya bi ki ɗaki." Baba Yunusa ya yi maganar rai a ɓace. "Ban gan shi ba Baba, duk neman da na yi ban gan shi ba ma ɗazu, kuma wallahi ganin idona ya fito daga ɗakin ya Jafaru. Sororo suka yi suka gagara gane kan maganar Uwani. "Shi Lawan ɗin ne zai ɓata a gidan kamar wani zobe? Kin san me kike faɗa kuwa Uwani?" Cewar Baba Mamman. Ganin duka ba su fahimci inda maganarta ta dosa ba ya sa Dada ta ce. "Lawan ɗin da Uwani ke faɗa ba kowa ba ne fa face zakaran da take kiwo, ko ba Lawan mai wake-wake ba Uwani?" Da sauri Uwani ta gyaɗa kai.   "Ba maganar zakara muka yi miki ba, muna magana ne akan tsakaninki da jafar." Baba Yunusa faɗa. Jin haka ya sa Uwani ta kwashe duk abin da ya shiga tsakaninta da Jafar ta faɗa musu, shiru duka suka yi Dada ta dubi Na madina ta ce. "Yaya wai haka ne abin da ta faɗa? Don gaskiya shedar zir haramun ce kar Mamman ya fusata ya ce mun yi wa ɗansa ƙazafi ya kaimu kotu, alƙali ya yanke mana bulala tamanin mu shiga uku." Jikin Na Madina ya yi sanyi don shi kasan ya san zargin ne yake yi idanunsa ba su gani ba. "Ni dai Allah Ya sani ban kama Jafaru da Uwani turmi da taɓarya ba, amma na ji waɗansu kalamai da suke yi a cikin ɗakin Kulun. Don Allah me zai sa su keɓe idan ba warware mutumcin sunna suke ba?" Sai a lokacin iyalan wurin suka fahimci gabaɗaya inda maganar su ta dosa. "Amma dai Yaya ka ci zarafin zuri'ata, yanzu saboda Allah wacce ƙiyayya kake yi wa Jafaru da Uwani da za ka nemi  ka haɗa su da hali irin ta'adar Iron Alto, ni dai ku zama shaida ta daga yau ba zan sake haɗa inuwa ɗaya da Yaya Musa ba." Dada ta yi maganar cikin kuka, ta mayar da kallonta wurin su Jafar ta ci gaba da cewa. "Ban da ƙarfin alƙawari ma me zai haɗa Uwani da Jafaru? Yarinya kyakkyawa kamar Uwani a ba ta Ɗansanda, Ɗansandan ma kamar Jafar mai zuciyar masifa. Ni tsorona ma kada watarana Uwani ta yi masa laifi ya sa bakin bindiga ya bindige ta..." "Allah ya tsare ni, ni kuwa me zan yi da Uwani wallahi ko a ƙafa aka ɗaura mini ita ba zan ja ba, kai ko abokina ba zan yi wa hanyar aurenta ba, haka kawai a ce na yi sanadin auren ƙazama kamar Uwani." Jafar ya faɗa a ƙazance kamar zai yi amai. "Idan kai ba ka so ba ai tuni alƙwari ya ba ka aurenta Jafaru, shafa Fatiha kaɗai ya rage muku. Amma fa wallahi faɗi kanka tsaye Jafaru ƙazantar uwani tun da na zo duniya ban taɓa ganin ƙazama irinta ba."  Jin tonan asirin da Dada take mata ya sa Uwani tura ba ki gaba. "Rigar mama wannan Uwani ba ta san ta canza ba sai dai idan na tilastata ta sauya, ban da ma Allah Ya kawo mu zamani yaushe yarinya za ta fara saka rigar mama a gaban iyayenta? To haka take zama da tsamin hammata, rannan ina kwance a saman kaina na ji tsami ya cika min hanci wallahi ina dubawa na ga ashe ɗan diras da kanfanta ne a ajiye. Ni ina tsoron ma kar a aurar da Uwani ta shafa wa Jafaru kwarkwata, don wallahi ko gorin kwarkwata aka yi wa Uwani sai haka. Amma dai tun da Hajiya Saro (Mahaifiyar Jafar) ta daina ƙazanta Uwani ma za ta daina, don bara war haka sai da na roƙa wa Uwani addu'ar yayewar ƙazantar nan a Harami." Dada ta mayar da kallonta wurin su Baba Rufa'i sannan ta cigaba. "Yanzu dai ba za mu tashi daga wurin nan ba sai mun kammala maganar yaran nan. Kun dai ga yadda Uwani ta zama budurwa ni tsorona ma kada ta fara baƙon wata a gabana na shiga uku..." "Subhanallah wannan wanne irin mummunan fata ne haka Kulu? Yanzu saboda Nasara ya gama wanke wa su Mamman hannu a ka sai su bar yaran nan haka?" Jafar ya saki murmushin takaici don shi gani yake duk sokiburutsun tsofaffin ne. "Don Allah ku dubi fuskar Jafaru washar yadda yake sakin murmushi, ko wannan miskilancin da yake yi fa aure yake so, kuma yanzu ya samu an soso masa wurin da yake yi masa ƙaiƙayi." Na Madina ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi. Baba Rufa'i ya yi gyaran murya sannan ya furta. "Dada dama ba mu ƙi ta ku ba, amma gaskiya shekarun Uwani sun yi ƙanƙanta a aurar da ita yanzu Ina laifin ta gama sakandire ma..." "Sakandi me? Kana nufin zan zauna ina ganin Uwani a gabana har tsawon shekara biyar? Wallahi da kunci amanar zumunci, yanzu saboda kun ga ƙasa ta lulluɓe idon mahaifin yarinyar nan shi ne za ku watsa mata ƙasa a ido. Kaico mutuwa mai yankan ƙauna. Allah Ya jiƙanka Umaru, ni na san da Umaru ne ba zai taɓa yi wa bayanku haka ba." Shiru suka yi Baba Mamman na shirin magana Na madina ya katse shi, "Amfanin me karatun bokon zai yi mata? Aure fa shi ne sunnar Ma'aiki. Yanzu Dada ba ga su Safare nan ba kowacce tana ɗakinta da 'ya'yanta, ina ce firamare kawai suka yi. Ko kuma mu iyayenku da ba mu yi yi bokon ba sai a ce ba mu ji daɗin rayuwar aure ba?" Dada ta ware hannuwa cikin gamsuwa ta ce, "Gane mini hanya Yaya, so suke yadda fitsararrun yaran can suka rasa miji ita ma ta gandame mini a gabana." "Dada domin fa mu inganta rayuwar Uwani muke son mu tsaya mata ta yi karatu kamar yadda sauran yara suka yi, amma ba don wata manufa ba. Don Allah ku fahimce mu Uwani yarinya ce, har yanzu fa ba ta cika sha biyar a duniya ba duk fa girman jiki ne." "Ni dai Baba kawai a aura mini Ofisana, kar na je Furaira ta riga ni gabatar da kanta a wurinsa. Don wallahi Furaira masifar son shi take. Ka ga ni ma sai na dinga gayu irin nasa, Allah ko su Fanteke sai sun zama 'yan gayu..." Da sauri Jafar ya katse Uwani. "Ke ba na son shashanci da rashin hankali an gaya miki ni sa'anki ne? Tun wuri dama ki nemi mijinki don ni tuni akwai wacce zan aura a Lagos..." "Lagas? Yanzu Jafaru ka rasa wacce za ka auro sai ƙedarun Lagas, wallahi ni kam dole na je Zariya na samu Sa'idu." Dada ta faɗa cike da damuwa. "Jafar wannan daɗaɗɗan alƙawari ne da na ƙulla shi shi tun ranar da Uwani ta zo duniya, kamar yadda ka sani mahaifinta ya rasu tun tana ciki sakamkon hatsarin da ya yi. Ba ta taɓa sanin fuskar mahaifinta ba sai mahaifiyarta. Tausayinta ya sa na ɗauki alƙawarin aura maka ita matuƙar kuka kai munzalin aure, tun da a lokacin ba ka fi shekara goma sha uku zuwa sha biyar a duniya ba. Daga kai har ita mu muke da iko a kanku babu wanda ya isa ya bijire wa umarninmu." Baba Mamman ya yi wa Jafar jawabi fuska a haɗe. Dada ita da na Madina suka washe baki cikin farinciki ya ce, "Wallahi ka jima ba ka faranta mini rai irin na yau ba Mamman." "To yanzu dai duk ba wannan ba, abu ɗaya zan yarda da shi. Ba zan zuba wa Uwani ido ba a yi mata aure ba har nan da shekara biyar ba. Watan Maulidin nan me zuwa ne bikin su Shukra ko?" Baba Mamman ya gyaɗa mata kai. "Nan da watan maulidi nake son a ɗaura musu aure idan ya so nan da wani lokaci sai a yi maganar tariya. Ko dai mutuwa na yi kafin lokacin na sauke nauyin da muka ɗauka, ko ba haka ba Yaya?" Dada ta furta tana kallon Na Madina, cikin gamsuwa ya amsa mata. Duk yadda su Baba Mamman suka so shawo kan Dada don ɗaga maganar fir ta ƙi amincewa. Don haka suka haƙura suka tashi daga taron, Jafar tun ba su kai ga tashi ba ya fice fuuu daga ɗakin. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya saki murmushi ya furta. "Ja'irin yaro wannan doron da ya yi yana yin aure zai miƙe, na san yau kwanan farinciki zai yi yoo aure wasa ne." Dada ta bushe da dariya. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BIYAR Kasancewar sunan gidan baba Isuhu ya zo a lokacin hutun zangon karatu ya sa ilahirin zuri'ar gidan sun hallara, musamman da ya kasance baba Mamman ya dawo gida ne gabaɗaya domin lokacin ritayarsa ta kusa. Kuma a wannan kwanakin ne yake shirin tarewa a katafaren gidan da ya gina a nan cikin Unguwar rijiyar zaki da ke jihar Kano. Hajiya Saratu da iyalanta sai shan ƙamshi suke yi suna kallon mutane ɗaiɗai, don ko maganar arziƙi ba ta cika haɗa ta da sauran facalolinta ba. Sanin halinta na raini da wulaƙanci ya sa suma sauran mutanen gidan suke kama mutumcinsu ba tare da sun shiga sabgarta ba. Asalin Tarihinsu Malam Haruna mai shanu shi ne ainihin cikakken sun marigayi malam mahaifin su baba Isuhu. Asalinsa mutumin garin Rigana ne da ke cikin ƙauyen lambar ƙunci, ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da ke jihar Kanon Dabon Najeriya. Sunan mai shanu ya samo asali ne tun a wurin mahaifinsa kasancewarsa fitaccen bafulani a wannan ƙauyen, duk girman garin Rigana babu mai albarkar shanu da dabbobinsa. Yana da matar aure ɗaya da 'ya'ya biyu sakancewar duka maza, Malam Haruna shi ne babba sai ƙaninsa mai bin sa Sa'idu wanda bayan su mahaifinsu bai sake haihuwa ba. Bayan mahaifiyar su malam mahaifinsu ya auri mata biyu sai dai ko ɓatan wata babu wacce ta taɓa yi. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna samari yayin da mahaifinsu ya rasu bayan da kowannen su ya yi aure a lokacin Malam haihuwarsa biyu. Baffajo tun da ƙuruciyarsa yakan ɗebi shanu da awakinsa su tafi garuruwa kiwo bayan wani lokaci sai ya dawo gida, hakan yake yi har zuwa lokacin da su Malam suka zama samari suma yake nuna musu hanyar kiwon shanu. Sai dai tun suna yara ya fahimci sam ba su da ra'ayin kiwace-kiwacen shanun da yake yi, bayan da mahaifinsu ya rasu sai suka ɗora daga inda ya tsaya sai dai su ba kamar Baffajo ba. Don tun bayan da ya rasu bai fi sau uku zuwa huɗu suka fita da shanu zuwa wasu garuruwan ba. A wannan lokacin ne kuma watarana bayan malam ya fita da shanun su da suka gada a wurin mahaifinsu, ya yi nisa sosai da garinsu sai ya faɗa tarkon wasu 'yan fashin daji. Kasancewar kuma sarkin yawa ya fi sarƙin ƙarfi sai suka yi masa ƙwacen shanu da yawa, kaɗan ya rage ba su hallaka shi ba ya dawo gida da tsirarun shanun da ko goma ba su kai ba. Wannan yanayin da suka shiga wasu sun dasa zargin har da saka hannun mutanen garinsu, yayin da wasu kuma suka ce jarabta ce kawai daga wurin Ubangiji. Dalili kenan da ya sa bayan da malam ya warke suka haɗa kai shi da ɗan uwansa suka bar garin gabaɗaya tare da sayar da shanunsu, suka dawo wani ɗan ƙauye a nan garin Kura suka kafa kasuwancin su. Kuma cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya saka musu albarka. Hauwa kulu Ibrahim mai allo shi ne cikakken ainihin sunan Dada asalinta mutuniyar garin Bauchi ce, baƙar bafulatana ce tana da kyau daidai gwargwado. Mahifinta Malamijo ɗan gidan malamai ne domin a rigarsu gidan su Dada ba ɓoyayyan gida ba ne. Mahaifinta yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Musa shi ne ainihin sunan malam na Madina, kuma shi ne babban yayansu Dada uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Ya auri matarsa bayan zamansu mai tsawo Allah Ya yi mata rasuwa, sai dai bayan ita ya yi aure-aure da dama bai taɓa samun haihuwa ba. Dada ita take bin shi sai kuma Fatsime take bin Dada sai dai akwai tazara sosai tsakanin Dada da Fatsime. Fatsime ta rasu a wurin haihuwa, ta rasu ta bar 'yarta Abuwa dalilin da ya sa Dada ita da na Madina kaɗai suka rage waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya. A lokacin da mahaifiyar su Dada ta haifi Fatsime har ta cire rai da sake samun haihuwa. Hasiya, Safare, Sule da Gali sune sauran 'yan uwan Dada da suke Uba ɗaya. Malam ya haɗu da Dada ne a lokacin da suka tafi kiwo garin Bauchi tun mahaifinsu na raye, don haka ba a ɗauki lokaci ba aka tsayar da maganar aure bayan wani lokaci aka ɗaura musu aure. Da yake Dada nesa da garinsu za a kai ta sai mahaifinta ya haɗa ta da ƙanwarta Fatsime, a kan bayan wani lokaci idan Dada ta saba sai Fatsime ta dawo. Sai dai ko da Malamijo ya buƙaci Fatsime ta dawo malam da kanshi ya je har garin Bauchi ya roƙi arziƙin a bar musu Fatsime a wurin su. Ganin yadda malam ke kula da Dada da kuma girman da yake ba shi sai ya kawar da kai ya haƙura ya bar masa ita. Dada da malam sun haifi 'ya'ya tara bakwai maza sai biyu mata. Baba Yunusa (Soja ne), baba Mustafa (Road safety ne), baba Idris (Malamin makarantar secondry ne), baba Mamman (Ɗan sanda), baba Rufa'i (Likita), Atika, Halimatu, marigayi Umaru wato mahaifin Uwani sai kuma Baba Isuhu (Sayar da itace yake yi). Baba Sa'idu (Ƙanin malam) Yana da mata ɗaya da 'ya'ya biyar. Biyu maza sai uku mata. Ya auri matarsa ne tun a garin Rigana, kuma tin bayan komawarsu Kura da suka fara kasuwanci shi da ɗan'uwansa, sai ya fara tafiye-tafiye zuwa garuruwa. Sannu a hankali sai nemansa ya fi ƙarfi a garin Zaria, don haka ya ɗauki iyalinsa suka koma can da zama. Cikin ikon Allah kowannensu ya ci gaba da zama da iyalinsa. Da yake Dada kwanika ta dinga yi gabaɗaya 'ya'yanta tazarar su babu yawa, kuma a lokacin da take da cikin Baba Isuhu ne Allah ya yi wa malam rasuwa. Kafin rasuwarsa ne ya biya mata Makka, zuwan farko umara ta je ta yi sai zuwa na biyu da suka je tare suka yi aikin Hajji. Malam Sa'idu ya kaɗu da rashin ɗan uwansa domin ko mutuwar mahaifinsu ba ta bige shi haka ba, daga nan kuma ya riƙe dukiyar ɗan uwansa da amana yana juya musu. Kuma ya ci gaba da tallafa wa Dada ita da yaranta, ya tsaya musu kai da fata suka samu ilimin addini da na zamani kuma har Allah ya ci da su suka samu aikin yi. Sai dai ba da aikin Gwamnati kaɗai suka dogara ba domin suna harkar kasuwancin kayan robobi da harkar kayan abinci. Baba Mamman yana da matar aure ɗaya Hajiya Saratu da yara biyar. Jafar shi ne babba, Ibrahim, Shukra, Jidda, sai Mufida wacce suke kira da Auta. Hajiya Saratu 'yar aminiyar mahaifin baba Mamman ce, ba ta da son mutane ko kaɗan. Mace ce mai faɗin rai da taƙama uwa-uba tana da son kanta, ga ta da tsananin kishi sannan akwai ta son hulɗa da matan masu kuɗi. Wannan halin na ta ya sa ko kaɗan ba ta jituwa da Dada, kuma kusan halayenta ne su Shukra suka kwasa gabaɗaya. Jafar da Ibrahim ne ba su da irin halinta sai Auta don haka har sun fi su Shukra sabo da mutanen cikin gida. Gidan marigayi malam Haruna mai shanu gidan gandu ne da ya haɗa kakanni, iyaye, jikoki da kuma 'ya'yan jikoki. Baba Mamman da Baba Yunusa ne kaɗai ba sa zaune a cikin gidan, kasancewar yanayin aikinsu da sauye-sauyen garuruwan da ake yi musu a wurin aiki. Amma kowannensu yana da ɓangarensa a cikin gidan, idan suka zo hutu suna sauka da iyalansu a ciki. Marigayi Umaru Haruna Mai shanu shi ne mahaifin Uwani, ya rasu tun mahaifiyar Uwani na da cikinta wata bakwai sakamakon hatsarin mota. Maryama Shu'aibu shi ne ainihin sunan mahaifiyar Uwani, dalilin mutuwar mahaifin Uwani ya sa Dada da su Baba Mamman suka ci gaba da kula da ita. Bayan wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi jaririyarta, ta ci burin idan namiji ne ta mayar da sunan mijinta Umaru. Amma da ta haifi mace su Dada suka tambaye ta sunan da take son a raɗa wa jaririyar, da kanta ta ce a saka sunan Dada saboda irin karamcin da suka nuna mata, sai ake kiranta da suna Uwani. Bayan da aka yaye Uwani ne mahaifin Maryama ya nemi da ta dawo gabansa da zama, domin zawarawa suna ta zuwa kai masa gaisuwa da nuna ƙoƙon bararsu a kan aurenta. Ranar da za ta tafi ne Dada ta nemi da ta bar mata Uwani saboda soyayyar da take yi wa mahaifinta, idan tana ganinta za ta dinga jin daɗi. Bayan komawar mahaifiyar Uwani gidansu ko shekara ba ta rufa ba aka ɗaura mata aure da wani mutum, a lokacin yana da aure da mata ɗaya da yara huɗu. Maryama ta aure shi ne ba don tana son shi ba, sai don kawai ta yi wa mahaifinta biyayya amma har lokacin zuciyarta na ga mahaifin Uwani. Garin da take aure yana nesa da garin su Uwani sosai, kuma ta haifi yara biyu da malam Salihu mace da namiji, sai dai ko kaɗan ita da kishiyarta ba sa jin daɗin zama da shi sakamakon mugun halinsa. Uwani ta taso a hannun Dada cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, tun bayan tafiyar mahaifiyarta baba Mamman ya so a ba shi riƙon Uwani amma fir Dada ta hana shi, lokacin da Hajiya Saratu ta ji ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Shekarun Uwani goma sha huɗu a duniya kuma irin fitinannun yaran nan da suke fita zakka ko a cikin unguwa. Rashin ji, rashin tsoro, kafiya, naci, tsokana rashin yafiya sune halayen da suka mamaye Uwani har mutanen garin suka saka mata suna 'Uwani 'Yar Ƙashin Gwiwa' saboda hatsabibanci da rashin jin ta. Duk cikin gidan mai shanu Dada ce kaɗai ba ta ganin laifin Uwani, don haka ma duk wurin da ta shiga sai dai su bi ta da harara. Jafar ma'aikacin ɗan sanda ne mai ɗauke da muƙamin ASP, shekarunsa talatin da biyu cif a duniya. Ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa matakin degree a jami'ar Bayero University. Miskili ne bai cika surutu ba, sai dai wani lokacin bauɗaɗɗan hali gare shi. Yana da kirki ga wanda suka fahimci juna sai dai wani lokacin yana da saurin fushi. Ba ya son raini ko kaɗan kuma yana da kykkyawar mu'amala da abokan aikinsa. Lokacin da ya fara aiki jihar Kaduna aka tura shi bayan wani lokaci ne ya samu sauyin aiki zuwa garin Katsina daga baya aka mayar da shi garin Lagos, ya kwana biyu a Lagos don bai cika zuwa hutu sosai ba. Ko da ya zo ma a gurguje yake kawo wa Dada ziyara shi ya sa Uwani ba ta wani san shi farin sani ba. Tana yawan jin labarin irin kulawar da Jafar ɗin ya dinga ba ta a lokacin da take yarinya, sai dai a wannan karon sam ba ta ga kalar mutumci a tattare da shi ba. Wannan hutun da Jafar ya samu kusan wata guda zai yi kafin ya koma, kuma ya ji labarin zuwan mahaifansa hutu da tariyarsu don haka shi ma ya yada zango a nan sashen Dada. Mu Koma Labari Tamkar sabuwar munafuka ko ɓarawon da yake sanɗa a daidai gaɓar da yake ɗaukar abin da ba na shi ba, haka Uwani ta shiga cikin ɗakin saɗaf-saɗaf tana tafe tana waige. Sai da ta kai ga ƙuryar ɗakin sannan ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya. "Uban 'yan iyayi ashe ba ya cikin ɗakin, da tuni yana nan a naɗe a kan katifa kamar mai karyayyan ƙugu." Ta furta cikun salon kwaikwayon muryarsa. Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa ta yi mutuwar tsaye, zuciyarta ta fara harbawa tamkar za ta bijirewa zama a ƙirjinta, cikinta ya shiga juyawa yayin da zazzafan gumi ya shiga keto mata. Caran zakaran da ta ji a bayanta ne ya sa ta sake sauke ajiyar zuciya, ta saki murmushi a fili sannan ta furta. "Lawan wallahi ka cika binbinin tsiya, yanzu ɗakin Ofisa ma sai ka biyo ni. Idan kuwa ya kama mu wallahi sai ya kusa murɗe maka wuya." Tamkar zakaran ya san da shi take ya ci gaba da takawa yana tafe yana sakin kashi a tsaftataccan ɗakin da ya sha gyara ta ko ina sai zuba ƙamshi yake.   Kafin Uwani ta ƙarasa kan katifar ɗakin tuni zakaranta da take kira da Lawan ya yi mata jagora zuwa kan luntsumemiyar katifar da ta sha gyara, a ɗame take da zanin gado kamar gadon sabuwar amaryar da za a kai ɗakin miji. "Lawan ina ka baro Fanteka, uwar 'ya'ya na san tana cen tana yawo ita da 'ya'yan iya." Uwani ta yi maganar kamar da mutum ɗan'uwanta take yi. A saƙale ta hango uniform ɗinsa na kayan 'yan sanda masu bulun riga da baƙin wando. Da sauri ta janyo ta hau kwaɓe kayanta kafin wani lokaci tuni ta saka a jikinta, sai da ta gama soshe kanta da ya cukurkuɗe sannan ta kafa baƙar hularsa a kanta. Cikin ƙwambo ta fara taku ɗaiɗai sannan ta cake a wuri ɗaya. "Ba na son hayani matsa daga kaina, ƙazama mai kwarkwata." Ta yi maganar cikin kwaikwayar maganar Jafar, tana faɗin irin maganganun da yake faɗa mata.  Ta jima a tsaye tana surutanta sannan ta ƙarasa gaban mudubin da ke can gefenta, kamar a mafarki haka ta hange shi tsaye ƙyam kamar wanda ya haɗiyi falwaya. Fuska a haɗe kwatankwacin ta fusataccan bujumin sa. Nan take yawun bakinta ya ƙafe, ƙafafuwanta suka ɗauki rawa ƙirjinta ya shiga harbawa. Sai dai dakiya da ƙarfin zuciyar Uwani ya sa ta basar kamar ba ta gan shi ba. "Iya iya iya." Ta ji 'ya'yan kazarta na faɗa yayin da zakaran da ya gama kasaye ɗakin ya fara cara, da sauri kazar ta tunkaro ɗakin da niyyar shiga a fusace Jafar ya sa ƙafa ya yi ball da ita. Wata azababbiyar ƙara Uwani ta ƙwalla kamar da ita Jafar ya yi ball, ta fara tafiya wandon uniform ɗin yana zamo mata. "Innalillahi kashe mini fantake za ka yi..." Uwani ta yi maganar tana shirin fita daga ɗakin, yayin da Lawan (Zakaranta) ya firgice yana tsalle-tsalle a ɗakin, yana jefo masa kwalaben turare. "Gidan uban wa za ki?"Jafar ya wurga mata tambaya rai a ɓace. "Ina da gidan da ya wuce ɗakin Dada..." Jafar ya katse maganarta ta hanyar bige bakinta da ƙarfi. "Wallahi na ba ki nan da minti goma ki gyara mini ɗakin nan, sannan ki yi gaggawar cire mini uniform tun ranki bai ɓaci ba. Kuma idan kin gama zan gauraya da ke." "Sai ka fita na canza kaya." Sororo ya yi yana kallon Uwani don bai san lokacin da ta raina shi ba. Yana shirin sauke yatsunsa biyar a fuskarta wandon uniform ɗin ya zamo mata, gajeren wandon da ke jikinta ya bayyana. Fari ne amma dauɗa da jirwaye sun sa ya dafe saboda ƙazanta. A ƙazance ya kawar da kai gefe haɗe da tofar da yawu. "Ka san dai kallon tsiraici haramun ne, ka fita na sauya kaya. Kuma ni dai ba 'yar iska ba ce..." "Idan ba ki rufe mini baki ba wallahi sai na haɗa miki jini da majina a wurin nan. Sakarya fuska kamar ta aljanu, daga yau ko wani ne ya aiko ki ɗakin nan ba za ki ƙara marmarin shigowa ba." Tun da Jafar ya fara magana Uwani take kallonsa sheƙeƙe tun daga sama har zuwa yatsu biyar na ƙafarsa. Ba ta yi aune ba ta ji ya zuba mata rankwashin da ya sa ta gagara gane muhallin da take tsaye. Cikin sauri ta fisge hular kanta, ta zame dogon wandon uniform ɗinsa da ke jikinta. Jafar na nan tsaye ya ji tuuush! Lawan ya jefo sabuwar kwalbar turarensa, a firgice yake miƙa wuya yana cara haɗe da ci gaba da taka kayan da ke saman mudubin. A zuciye Jafara ya jefa masa takalmin kanbas ɗinsa. Firgitar da Lawan ya yi har cikin ran Uwani don haka cikin ɓacin rai ta ce, "Allah dai ba ya zalinci yana kallon baƙaƙen azzuluman duniya masu baƙaƙen kaya." A fusace Jafar ya yo kanta rai a ɓace, ganin haka ya sa Uwani ta zuba a guje kai tsaye ta wuce sashen Dada Jafar ya rufa mata baya. A daidai lokacin da Jafar ya nufi sashen Dada shi kuma malam na Madina ya kawo kai, cikin rashin sani Jafar ya bangaje shi kaɗan ya rage gemunsa ya taɓa ƙasa. "Jafaru! Kai Jafaru kana ji ka angije ni kamar ka angije dabba? Wallahi duk laifin Kulu ne ni take nunawa 'ya'ya da jikoki sun fi ɗan uwa." Ya ci gaba da tafiya har bakin ƙofar Dada yana kiran sunanta. "Kulu! Kulu kina ina ne..." Cikin sauri Malam na Madina ya datse ragowar kalaman bakinsa jin furucin da Jafar ke faɗa.   "Wallahi tun wuri ki wuce mu je ɗakina don har kan katifa..." Uwani ta yi farat ta katse shi. "Amma dai ai ka bari na saka kayana yaya Jafaru, wallahi na fita a haka ka san dai mutanen gidan nan kowa sai ya san abin da yake faruwa." Jafar ya yi ƙwafa yana shirin ba ta amsa daga can waje ya ji muryar Malam na Madina yana sallallami. "Yanzu Jafaru dama munafurcin da kuke aikatawa kenan? Shi ya sa saboda sauri har ka angije ni ko waige na ba ka yi ba. Ba da ni ba, wallahi ba zan zauna ana aikata alfasha ina kallo ba, lokaci ɗaya Ubangiji ya halakar da mu." Sai da Jafar ya fito daga ɗakin Dada ya samu Malam na Madina da ke bin shi da ƙazantaccan kallo. Ficewa ya yi daga sashen Dada ya faɗa ɗakinsa, akwatin kayansa ya janyo ƙiiiiii yana kokawar fito da ita Dada ta sako kai ciki. Jin motsin ya yi yawa ya sa ta fara mita. "Waɗannan dabbobi na Uwani yadda kasan tare aka shayar da su saboda duk hatsabibancinsu iri ɗaya ne..." Ganin Malam na Madina ya janyo akwatinsa ƙiiii ya sa Dada sakin baki, "Wai Muda ne a wurin nan ko Usumanu?" Ta wurga masa tambaya tana ɗan ƙanƙance ido. Sai da Malam na Madina ya fito sannan ya ce. "Ki yafe ni Kulu don kar na tafi da haƙƙin wani a kaina." Baki sake Dada ta ce, "Yaya wani abin aka yi maka ne?" Malam na Madina ya share ƙwallar idonsa, ta waiga wurin da Jafar yake tsaye a bakin ƙofa ya jefa masa mugun kallo sannan ya furta. "Ubangiji aka yi wa laifi, ni dai tsakanina da mutanen gidan idan na ce an yi mini wani abu na ɗauki haƙƙinsu. Amma ni kam ba zan zauna ina ji ina gani a dinga saɓon Allah ba, gara na mutu salin-alin da a tashi idanuwa su bada shaidar baɗala ranar Lahira." Malam na Madina na gama magana ya fara jan akwatinsa ƙiiiii, da sauri Dada ta sha gabansa don tuni hankalinta ya tashi idonta ya fara ciko da ƙwalla. A duniya idan akwai abin ta tsana shi ne a ɓata ran Malam na Madina. Jafar ya kafe Malam da kallo yana jin kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi ko ya rufe shi da duka. "A duniyar nan dai Yaya ka san mu biyu kaɗai muka rage, kuma kai ne uwata kai ne ubana kai nake gani na huce rashin su marigayi, (Iyayensu) don Allah ka faɗa mini abin da yake faruwa."Dada ta yi maganar tana share ƙwalla. "Waye wancan a tsaye?" Na Madina ya nuna Jafar a daidai lokacin Uwani ta leƙo don jin abin da yake faruwa daga ita sai gajeren wandon jikinta, ta tuɓe riga ta rufa hijabinta a saman ƙirjinta. Dada ta kai kallonta wurin ta ce, "Jafaru ne sai Uwani da ta fito." "Amma a rigar kwasam na san ba za ki manta Iron Alto ba?" A firgice Dada ta kalle shi, ba ita ba hatta Jafar ya san labarin Iron Alto a bakin Dada. Dada na shirin magana Malam na Madina ya katse ta. "To Ta'adar Iron Alto na ji waɗannan yaran suna aikatawa..." Tun bai rufe baki ba Dada ta saki butar hannunta wacce ta ɗauro alwala da ita jiki na rawa. Yau dai bari mu tsagaita dariyar na ga jiya har da masu shiɗewa 😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TAKWAS Uwani saboda dariya har kwanciya ta yi a ƙasa, Ba ka da nauyi ya ƙarasa wurinta tun bai yi magana ba ta miƙa masa ɗayar ƙullin gyaɗar. "Ba ki da nauyi ta yi malolo." Haka yara suka dinga yi wa Shukra waƙa suna tafi, ban da kuka babu abin da take yi saboda tsananin kunya da ɓacin rai. Da ƙyar wasu matasa suka kori yaran suka yi kama-kama suka tsamo ta a cikin kwata. Tana tafe ruwan kwata na ɗiga wasu daga cikin yaran suka fara yi mata wata waƙar. Ɗoyi, ɗoyi ɗoyi. Ɗoyi damalma kashi. Ɗoyi tukunyar kashi. A haka Shukra ta ƙarasa gida nan ma wasu daga cikin tsurarin yara suka bi ta Uwani na take musu baya, Shukra na shiga sashensu ta ɓarke wa Mami da wani irin kuka. "Yaya Shukra lafiya? Me ya same ki a goshi? Mene ne wannan yake wari a jikinki kamar kwata? Ina shi Yaya Salim ɗin?" Auta ta jero mata tambayoyi, sai dai babu ɗaya da ta iya amsawa ban da hawaye da ke shatata a fuskarta. Mami da Auta suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta faɗa musu abin da ya faru, suka shiga zagin Ba ka da nauyi suna mamakin in da Salim ya je bayan motarsa na ƙofar gida. Jin ihun Dada ya sa su Atika shiga sashenta da sauri, ganinta a daskare daga ita sai ɗan tofi ya ba su mamaki domin Dada ba ta taɓa sauya kaya a gaban mutane. "Dada lafiya?" Hannu na rawa ta nuna uwar ɗakin. "Wani tabbataccan kwarto ne ya fisge mini zani ya yi uwar ɗaki. Ni Kulu ban san uwar me zai laluma a jikin tsohuwa ba." Da sauri su Atika suka leƙa ɗakin, ba su iya hango komai ba sai 'yan idanun Salim da ke duƙe a ƙarƙashin gado. Fa'iza ce ta kira Baba Isuhu, da sauri ya ƙarasa hannunsa ɗauke da ƙatuwar gora ya fisgo Salim. Sai dai sororo ya yi yana bin yadda halitar fuskar Salim ta sauya. "Wa nake gani kamar Salim? Kai uban me ya kai zanin Dada hannunka?" Salim da gefen baki zuwa fuskarsa ya kumbure sundundun ya ce, "Baba wani mahaukaci ne zai sauke mini fuska don Allah ku ɓoye ni. Ya ɗauke Shukra a ka ma ya tafi da ita." Sai a lokacin suka fahimci wurin da maganar Salim ta dosa, Baba Isuhu ya miƙa wa Dada zaninta. Ya kama hannun Salim suka fice Salim sai tirjewa yake, a zuciye baba Isuhu ya waigo ya furta. "Me kake yi haka ne wai? Ka san Allah ka ci sa'a na gane kayan jikinka don mun gaisa ɗazu kana ƙofar gida, wallahi da don ta wannan sukunbiyar fuskar taka ne ba zan gane ka ba. Dubu fa yadda ka koma fuska kamar ta sumammiyar akuya. Mu je na raka ka ƙofar gida ka tafi don indai Ba ka da nauyi ne fiye da haka ma zai yi maka." Sai a lokacin Salim ya saki jiki suka ƙarasa, da sauri ya shige mota ya fusge ta da gudun gaske ko waige ba ya yi. Su Dada suna tsaye suna mayar da yanda aka yi wayar Dada ta fara ringing, da sallama ta ɗauka jin muryar Maryama mahaifiyar Uwani ya sa ta furta. "Ke kuwa Maryama da ƙuruciyarki amma waya ta nemi ba ki wuya, tun daren jiya nake kiranki na sanar da ke abin alheri amma waya a kashe." Maryama cikin shasshekar kuka ta ce. "Dada hankalina ne ba a kwance ba." "To Allah ya rufa asiri ai ni dama tun da na ga yanayinki na san Aramma na zalintarki, ki ci gaba da haƙuri Maryama komai ya yi don kansa." Maryama ta saki kukan da ke cinta, Dada na son Maryama shi ya sa duk lokacin da suka yi waya take tausarta. "Kin ga ki yi shiru 'yar nan su maza fa haka suke, ni tsorona ma kada Aramma ya zo ya ji kina mini kuka ya ce ko Umaru kika tuno. Yanzu dai ba wannan ba jiya da dare dai an cika alƙawarin da aka ɗauka, Uwani dai an ɗaura aure ita da Jafar. Abin ne ya zo a gaggauce, amma dai tariya sai nan da watan maulidi." Maryama ta ji daɗi don ta san waye Baba Mamman, amma har a ranta ta so a ce Uwani ta yi hankali kafin ɗaurin auren. Sai da ta kwararo addu'a sannan ta sanar da Dada dalilin kiranta. "Dada dama kiranki na yi na faɗa miki Me sunan Iya ce ta rasu (Babbar 'yarta ta gidan Aramma.)" Salati Dada ta rafka sannan ta yi mata gaisuwa ta kuma yi mata alƙawarin washegari za su shiryo su zo mata gaisuwa. Bayan sun gama waya Dada ta miƙa wa Uwani waya, suka gaisa sannan ta yi masa sallama. Kimanin ƙarfe goma na safe su Dada suka isa ƙauyen da mahaifiyar Uwani take aure, sun yi kara sosai don har su Baba Yunusa gabaɗaya suka je mata da matansu. Tun da suka faka motoci yara ke zuwa kallonsu, mazan suka zauna a tabarmar da ke ƙofar gida suka tambayi mijin Maryama aka ce musu ya shiga cikin gida. Su Dada kuma suka shiga ciki. "Gata nan da ran Allah ita ta san inda ta kai mini yarinya aka cinye ta, amma idan ta zauna ta ishi mutane da kukan munafurci. Daga zuwanta garinsu ta dawo da yarinya ba lafiya, wai muna zuwa aibitin gangare da suka tura mu babban asibiti a binni aka ce sikila ce, yo ban da ƙaryar likitoci lokacin iyaye da kakanni aka san wata sikili? Ta kai mini yarinyar dai mayu sun cinye kawai." Shigar su Dada gidan suka samu Aramma na zazzaga wa Maryama masifa yana kumfar baki, tana durƙushe a gefen yayan Aramma da ya zo yi mata gaisuwa. A lokacin Aramma ya zo wucewa ya shi ne yake yi mata sababi. Ganin su Dada da yanayin shigarsu ya sa ya hau yashe baki. "Barkanku da zuwa Hajiya." "Barka dai." Dada ta amsa a daƙile. Jin muryar Dada ya sa Maryama ta miƙe tana goge hawaye ta shiga yi musu sannu da zuwa. "Ai kuwa wannan mutumin sai na gyara maka zama." Uwani ta faɗa a ranta. Maryama jiki a sanyaye ta miƙe za ta wuce da su ɗaki. "Ke Maryama wanne irin rashin hankali ne haka kina ganin baƙi ba za ki kai su ɗaki ba." Aramma ya faɗa cikin faɗa shi a dole sai ya birge su Dada. Ɗaki ta kai su bayan sun gaisa suka yi mata gaisuwa cikin jimami, Dada har cikin ranta ba ta ji daɗin irin zaman da Maryama take yi da Aramma ba, domin mace ce mai sanyin hali da haƙuri. Duk wanda ya santa idan ya san Uwani dole zai ce albasa ba ta yi halin ruwa ba. Aramma jikinsa har rawa yake ya sa aka sayo musu ruwa, ba su jima sosai ba Dada ta kawo kuɗin sadaka dubu biyar ta bata. Sauran sirikan Dada kuma mai ɗari biyar mai dubu ɗaya duk suka haɗa mata, lokacin da za su tafi ne Dada ke ce wa Maryama Uwani za ta zauna har sai an yi sadakar uku za ta tafi. Har ƙofar gida Maryama ta raka su, su Baba Idris suka yi mata gaisuwa, suma suka kawo abin sadaka suka ba ta da shi ma Aramma. Har sun ɗauki hanya za su tafi Dada ta dawo ta ja Maryama gefe tana yi mata raɗa. "Dama kuɗin da aka ba ki ko da wasa kada ki ba wa wannan mijin naki kin ji Maryam!" Maryama ta gyaɗa kai jiki a sanyaye sannan ta raka Dada bakin mota tana ɗaga musu hannu. "Dada gaskiya zan yi kewarki kwana biyu an ya ba biyo ku zan yi ba?" Uwani ta faɗa tana tura ba ki gaba. Dada ta watsa mata harara sannan suka wuce. Tun da suka koma cikin gida Uwani ta lura da mahaifiyarta sam ba ta da nutsuwa, suna nan zaune sai ga Aramma ya shigo. "Ke Maryama kawo abin sadakar nan da aka ba ki zan haɗa a yi abincin rana." Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka Maryama ta miƙe jiki ba ƙwari ta kunto kuɗin wurin su Baba Idris ta miƙa masa. "Ke ba na son shashanci da rainin hankali, kina nufin su matan ba su ba ki komai ba? Wai Maryama me ya sa kin fiye baƙin halin tsiya ne." Ran Maryama ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ganin irin tozarcin da Aramma yake yi mata a gaban Uwani da kuma sauran mutanen da suka zo gaisuwa. Don haka rai a ɓace ta ce. "Wai Aramma ya kake so na yi ne? Me ya sa..." Tun ba ta gama magana ba Aramma ya ɗauke ta da mari, yana shirin kai mata duka Uwani ta shiga tsakaninsu ta furta. "Baba bari na miƙo maka kuɗin a cikin jakar can ta ajiye dama na ji ta ce za a auno garin masara a yi tuwo, amma bari na miƙo maka." Jin haka ya sa Aramma ya washe baki ya ce. "Ka ji yarinya mai hankali maza miƙo mini, ke dai kin yi asarar hali Maryama." Babu musu Uwani ta zuge jakar da ta ga mahaifiyarta ta zuba kuɗin a ciki, ta ɗebo su duka ta miƙa masa. "Kai Allah wadaran naka ya lalace wallahi Maryama kin ji kunya ace wai har 'yar cikinki ta fi ki hankali." Wasu daga cikin ƙannen Aramma suka bi mahaifiyar Uwani da baƙaƙen maganganu. Ba ta tanka musu ba sai ma ruwan hawaye da ke tsiyaya daga fuskarta. Uwani na daga gefe ta ci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kowanne tana zana gashin azabar da za ta yi musu daga baya. Sai da mutane suka ragu a ɗakin sosai daga Maryama sai 'yan uwanta ta dubi Uwani ta ce. "Me ya sa za ki ɗebi kudina ki ba shi." Ta ƙarasa maganar fuska a haɗe. "Gobe da safe zai dawo miki da su Inna rance na ba shi!" Uwani ta furta cikin rashin damuwa. "Rance fa? Ta ya ya zama rance bayan a kan idona kika ba shi?" "Allah Inna kada ki damu zai dawo miki da kuɗinki har ma ya ƙara miki wasu." Jin sokiburutsun Uwani ya sa Maryama ba ta sake bi ta kanta ba saboda takaici. "Maryama yaya aka yi kika bari har ya ga lokacin da aka ba ki kuɗin nan? Kin fa san halin mutumin nan sarai, ba shi da tausayi ko kaɗan." Indo kishiyar Maryama ta furta ƙasa-ƙasa. "Ai kin san tun da ya gan su ya san za su ba ni wani abu, kuma ragowar ma ba ni na ba shi ba yarinyar nan ce ta ba shi." Maryama ta furta. Suka gama jajantawa juna, don zaman da suke yi sam babu kishi a ciki saboda dukkansu ba wani daɗin zama da shi suke ji ba. Wuni ɗaya da Uwani ta yi a gidan ta fahimci irin zaman ƙuncin da mahaifiyarta da kishiyarta suke yi a cikin gidan, a kan idonta ta ga Aramma ya yo cefane har da nama ya ce a yi masa jar miya da shi. A yadda ta lura hatta abinci ma daban ake yi masa, su kuma duk kwamacalar da ya ga dama sai su dafa. Don abincin dare sai da ƙyar Uwani ta iya cin miyar kukar da aka kaɗa, saboda haka ta ci alwashin gyara masa zama kafin ta bar gidan. Tun da doshin magriba Uwani ta hangi wani ludayin silba a kwandon wanke-wanken mahaifiyarta, a fakaice ta ɗauke shi ta ɓoye sai da dare ya tsala kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki a hankali. Har za ta fita ta hangi wani zumbulelen farin hijabin Inna Suwaiba, wani tunani ne ya faɗo mata da sauri ta saki murmushi. Ta figi hijabin a hankali ɗayan hannunta ɗauke da ludayin sulba, can hanyar soro ta nufa da yake a baki-bakin ƙofa turakar Aramma take, daga ɗakinsa kuma sai ɗakin da suke ajiye kayan abinci. Toka ta ɗiba ta bursune fuskarta da ita sannan ta saka zumbulelen farin hijabin, ta leƙa ɗakin ta hango Aramma a kwance ya sharɓe sai sakin munshari yake yi daga shi sai gajeren wando. Da yake irin mutanen nan gajeru masu ƙiba ga uban tumbi. Tana shiga ɗakin ta tsaya a kansa, sai da ta gimtse dariyarta sannan ta daidaici gefen goshinsa ta ba shi raaaal da ludayin hannunta. A firgice Aramma ya miƙe yana dafe da goshi, "Wane ɗan iskan ne a tsohon daren." "Tawagar fatalwar 'yan iskan lahira ne!" Uwani ta faɗa da wata irin murya, ta sa hannu ta cikin hijabin ta buɗa shi, sai ta ƙara faɗi ta cikinsa. A razane Aramma ya ja da baya ganin hallitar da ke tunkaro shi. "Mu sababbin ƙawayen 'yarka da ta baƙunci lahira ne. A cikin fatale ma mu tawagar shaiɗanu ne domin fatattaka ɗan adam muke yi da kulkin lahira. Ita da bakinta ta gaya mana irin zalincin da kake yi wa iyalinka, don haka muka zo domin mu tsintsinka hanjin cikinka, ko kuma mu gayyato 'yan uwanmu mu yi daga-daga da kai." Uwani ta yi magana tana wani miƙa wuya gaba. Jin kalaman Uwani ya sa Aramma ya fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, cikin tashin hankali ya ce. "Ku dubi Allah ku yi haƙuri wallahi zan daina duk abin da nake yi..." Da sauri Uwani ta katse shi. "Zo nan maza-maza, matso nan." "Don Allah ku yi mini rai." Aramma ya faɗa fuska haɗe da hawaye da majina. "Za fa ka taka ɗan tsiti a bayanka, wallahi tawagarsa ta fi ta mu bala'i ka matso na ce maka." Da sauri Aramma ya matsa tiɓi-tiɓi sai haɗa gumi yake. Yana zuwa ya tsugunna a ƙasa, hannun Uwani mai ɗauke da ludayin da ke cikin hijabi ta ɗaga da sauri ta sake ba shi raaal a ƙeyarsa. A zabure Aramma ya miƙe sai da ya yi tsalle uku ya faɗi a can gefe cikin azaba. "Fatalwar 'yarka ta gaya mana duk abin da matanka suke samu karɓe musu kake yi, a jiya ma ka karɓe wa uwar marigayya kuɗaɗenta to ko ka mayar mata da abin ta ko kuma mu mayar da kai kuɗi. Domin muna cikin irin fatalwar da ke yi wa 'yan ƙungiyar asiri aiki, za ka zama kuɗi wayyo kuɗi, kuɗi masu daɗi." Uwani ta yi maganar tana wani tsalle tana ɗaga hannu ta cikin hijabi kamar mai shirin tashi sama. "Na rantse da Allah ko wasu aka ce na ƙara mata yanzu zan ƙara mata su." Uwani ba ta bi ta kansa ba ta ce. "Da ma ga hantarka da zuciyarka nan muna gani manya ne, ko su kaɗai muka tsaface za ta kawo mana miliyoyi." Da sauri Aramma ya dafe cikinsa da hannuwansa biyu, ya sake ɓarkewa da kuka. "Idan ka sake ka tona mana asiri wallahi a yanzu za mu hallaka ka." Jin haka ya sa Aramma ya haɗiye kukansa, ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa. Uwani ta sake jingina da bango ta furta. "Ganin yadda muka ga ka yi nadama za mu ɗaga maka ƙafa na kwana biyu mu ga idan za ka sauya halinka, kuma ka gaggauta mayarwa da mahaifiyar 'yar uwarmu kuɗinta. Sannan ita da kishiyarta dole ne ka ƙara musu dubu hamsin-hamsin. Kuma ya zama wajibi duk sati ka dinga ba su dubu uku-uku na kashewa." "Duka na ji kuma na yi alƙawari zan yi yadda kuka ce, na gode muku Allah Ya biya ku." Aramma ya yi maganar yana rissinawa. "Ba ma buƙatar godiya, yanzu dai za mu tafi da kai ka je ka ga makwancin 'yarka, sai mu baro ka a can bayan sadakar uku sai mu dawo..." Tun Uwani ba ta gama magana ba ya katse ta cikin kuka. "Wallahi na haƙura da ganin ta, Allah ba sai na ga halin da take ciki ba. Na san mai sunan Iya tana da halin na gari." "To kuwa ya zama wajibi ka zaɓi ɗaya, ko mu ɗauke ka ta ƙarfin tsiya mu tafi da kai. Ko kuma ka zo ka ku yi sallama da shugabar tawagar 'yan iskan fatale." Jin haka ya sa jiki na rawa ya matsa gaban Uwani ya ce. "Zan gaisa da ita..." Maganar bakinsa ta katse sakamakon jin saukar ludayin da ya yi a gaban kansa. Wannan karon kasa motsi ya yi ganin haka ya sa Uwani ta sake sauke masa na biyu aka sannan ta ɗora da cewa. "Yanzu haka za mu fita mu ba ka wuri, sauran tawagarmu na tsakar gidan nan. Kuma duk abin da ka ji ko kuma duk hukuncin da ka ji muna aikatawa matuƙar ka leƙo to zai dawo kanka. Sannan saura idan gari ya waye ka ce ga abin da ya faru da kai." Daga haka Uwani ta fice tana wani shagiɗewa gefe tana tura wuya gaba. Kusan duk abin da ya faru tsakanin Uwani da Aramma, Yaya ƙarama da su Rahane 'yan uwan Aramma sun ji, sakamakon ɗakin da suke kwance a jikin na Aramma yake. Da yake dama idan wani abin taro ya kama a gidan to duka danginsa a wannan ɗakin suke sauka. Kowannensu na daga kwance cikinsa ya ɗuri ruwa ko motsin kirki babu mai yi, babban abin da ya ɗaga hankalinsu yadda suka dinga jiyo kukan Aramma ƙasa-ƙasa, da ita kanta saƙon fatalwar da take faɗa. Suna nan kwance suka ji motsin Uwani a ƙofar ɗakinsu tana ɗan wani gurnani, take fitsari ya jiƙe zanin Yaya ƙarama. Uwani na ɗaga labulen ɗakin ta hango yadda aka jere yara a ƙasa, ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga jidar yaran tana kai wa tsakar gida. Yaya ƙarama na daga kwance ta ji Uwani ta dafa ƙafarta, jiki na rawa ta ce. "La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillah." "Ba za ki mutu yanzu ba sai mu fafe ƙwayar idonki." Uwani ta faɗa da wata irin murya, har ta juya za ta fita ta ce. "Su kuma waɗancan yaran zan ba wa ƙananan fatalenmu umarni su gama da su." Uwani na ƙarasa magana ta wuce wurin yaran da ke kwance a tsakar gida, idan ta ɗauko yaro ɗaya sai ta gasa masa mintsini ta tura shi cikin ɗaki. Ganin yadda yaran ke shigowa a firgice cikin kuka ga magagin bacci ga kuma zafin mintsini, ya sa su Yaya ƙarama suka banka uwar ɗaki a guje. Uwani ta yi wata irin sufa ta rufa musu baya tana faɗin. "Ya Ahalul fataleeee ku zo ga nama mun samu." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA BAKWAI Kamar Jafar zai tashi sama haka ya nufi sashen mahaifiyarsa saboda ɓacin rai ko gabansa ba ya gani sosai, da ƙarfi ya doka ƙofar falon Mami da su Shukra na zaune. A zabure duka suka miƙe Mami ta dube shi ta ce. "Hankalinka ɗaya kuwa Jafar? Saurin me kake yi haka?" Jafar bai tanka mata ba ya wuce kan kujera ya zauna yana furzar da iska mai zafi. Sai da ta ƙare masa kallo sannan ta ƙarasa kusa da shi ta furta. "A kullin ina gaya maka ka dinga rage wannan baƙar zuciyar taka. Me aka yi maka?" "Mami me ya sa Daddy ba ya son farin cikina ne?" Shi ma ya jefa mata tambaya. "Me ya sa ka faɗi haka?" "Yanzu Mami da girmana ni ba ƙaramin yaro ba a ce za a wani nemar mini matar aure, saboda Allah an yi mini adalci kenan? Atleast ko shawarata ai sai a nema." Nan take Mami ta haɗe fuska sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Ina tunanin dai wasa yake yi maka, amma kuma ban da abin ka Jafar ka sani ko 'yar manya ce ita ma. Duk da dai na san kun gama daidaitawa da Safna ai ita ma wannan sai mu ji waye ubanta." Tun da Mami ta fara magana wani ƙululun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi, "Mami ko 'yar gidan uban waye ni fa idan ba na sonta ba zan aure ta ba. Kuma Daddy ya rasa wa zai haɗa ni da ita sai waccen kucaka, sakarya kuma ƙazamar yarinyar can Uwani." A zabure Mami ta miƙe tsaye har ba ta san lokacin da wani ashar ya suɓuce mata ba. "Uban waye zai haɗa ka da wata Uwani? Yarinyar da ko a mai aiki ba zan ɗauke ta ba. Ba zai taɓa yuwu ba wallahi, wannan ma ai shiga haƙƙi ne ina kai ina wata jakar yarinya Uwani." Jin haka ya ƙarfafa gwiwar Jafar nan ya kwashe duk yadda aka yi ya sanar mata, tun ba ta gama jin jawabinsa ba ta dakatar da shi tare da faɗin. "Bari na je na samu Dada wallahi ba zai taɓa yuwu ba wankan kuturu da sabulu." Fuuuu Mami ta wuce su Shukra na daskare mamaki ya mamaye su. "Waye haka mai ƙirar samudawa ya yi mini gandandan a tsaye?" Dada ta furta tana ƙare wa Mami kallo da ta yi tsaye a bakin ƙofa. Mami ba ta amsa ba ta wuce ta zauna a kan hannun kujerar Dada, tana cika tana batsewa. "Sannu da gida Dada." Mami ta furta a daƙile. Dada ta bi ta da kallo sai da ta taɓe baki sannan ta ce. "Sannunmu dai." "Dada a gaskiya ba a yi mini adalci ba, saboda Allah wai a rasa da wa za a haɗa Jafar sai da wata Uwani. Yaron nan fa namiji ne ko mace ba za a yi wa dole ba, gaskiya a duba lamarin nan don ko kaɗan ba su dace ba. Wai Jafar ne da Uwani yarinyar da ko wanka ba ta yi, ga rashin nutsuwa yarinya kamar rainon gwaro, ko tashin gidan mahaukata." Mami ta yi maganar tana haki. Baki sake Dada ta bi Mami da kallo har ta gama jawabi sannan ta ce. "Uwata kin gama magana ko da saura? Ke Saro amma dai ba ki da kunya kuma ko kaɗan ba ki da mutumci, yanzu ni kike gaya wa haka?Maganar auren yaran nan tamkar yau kika san da ita? Ina ce tun ranar da Uwani ta zo duniya aka ajiye ta. Ki saurare ni da kunnen basira, wallahi ko mutuwa na yi ban amince su Mamman su aura wa Uwani wani mijin ba Jafaru ba. Ke har kya yi zancen ƙazanta Saratu? Kin manta lokacin da kike fama da tsamin kai da na hammata? Ko kin manta lokacin da Mamman yake tasa ki zuwa banɗaki da soso ya tilasta miki ki yi wanka?" Mami ranta ya yi ƙololuwar ɓaci, a fusace ta ce. "Koma dai mene ne ni na ɗauki cikin Jafar na haife abina, don haka babu wata ƙatuwa da ta isa ta yi mini iko da shi wallahi duk ƙarfin ikonta..." Cikin sauri Dada ta katse ta. "Iyeee rashin kunya za ki yi mini Saro? To ni kuma ni na haifi Mamman kuma zan nuna miki ƙaryar gadarar da kike yi. Wallahi idan har ni na ɗauki cikin Mamman wata tara na haife shi sai an ɗaura auren Jafar da Uwani a yau, idan kin isa ki sa Jafar ya warware shi a yau ɗin nan kema." Dada ta ƙarasa maganar cikin ɓacin rai. Mami ta miƙe tsaye jikinta har rawa yake saboda ɓacin rai ta ce. "Ke kin haifa kuma kin isa ki yi gadara da ɗanki to wallahi ni ma zan nuna miki Jafar ba rainonsa na yi ba, naƙudar abina ni ma na yi na haifa don haka mu zuba mu gani." Daga haka Mami da buga wa Dada cinya haɗe da tsaki ta fice daga ɗakin. Daidai lokacin da Mami za ta fita Uwani ta kawo kai, duk da Uwani ba wani shiga sabgar Mami take ba amma ganin ta ya sa ta ce. "Ina wuni Mami." Ko ƙurar da ta ajiye Uwani Mami ba ta kalla ba ta wuce sashenta, Uwani ta taɓe baki ta faɗa ɗakin Dada. Tana shirin yin magana Dada ta katse ta. "Ke Kulu maza je ki kira mini Mamman shi da 'yan uwansa." Jin yadda Dada ta kira sunanta da Kulu ya sa ta sha jinin jikinta don ta lura ran Dada ya ɓaci sosai. Kai tsaye Uwani ta wuce sashen su Mami da sallama ta shiga ɗakin sai dai gaba ɗayansu babu wanda ya tanka mata, sai ma wani kallon tsana da suke bin ta da shi. "Dada ta ce Baba Mamman ya zo." "Sai ki neme shi a ɗakin uwarki." Mami ta furta. "Uwata fa? Me na yi miki za ki zage ni?" "To ko za ki rama ne? Mami ta katse ta. "Ba zan rama ba amma wallahi kada ki sake zagina ban yi miki komai ba, don uwa ba ta fi uwa ba..." Kafin ta rufe baki Shukra ta sauke mata tagwayen mari biyu a fuska. "Rashin kunya za ki yi wa Mami don ubanki, shegiya ƙazama baƙa mai baƙar aniya." Uwani riƙe da kumatu ta ce. "Kan uba marina kika yi?" Uwani na cikin magana Shukra ta sake sauke mata wani marin a fuska. Jin zafin marin ya sa Uwani ta yi tsalle sai ji kake tass a fuskar Shukra Uwani ta rama. Cikin ɓacin rai Mami ta fisgo Uwani da ƙarfi, ita kuma Shukra ta yi mutuwar tsaye tana mamakin marin da Uwani ta yi mata. Kamar haɗin baki Mami da Shukra suka rufe Uwani da duka tun tana ihu tana kuka har ta ja bakinta ta yi shiru saboda galabaita, sai da suka gaji don kansu sannan Mami ta koma kujera tana haki. Shukra na kan Uwani Daddy ya shigo cikin gidan, ganin irin dukan da take yi wa Uwani ya sa Daddy ya ɗauke Shukra da mari. Da kansa ya ɗago Uwani lokaci ɗaya fuskarta har ta sauya saboda kukan da ta ci. Ya lallashe ta sosai sannan Uwani ta faɗa masa saƙon Dada, a haka ta fara dafa bango ta wuce wurin Dada. Shi ma Dadday bai tsaya bi ta kan su Mami ba ya rufa wa Uwani baya. Ganin a yanayin da Uwani ta koma ya sake ɓata ran Dada, nan take ta sa Baba Mammam ya kira mata sauran 'yan uwansa. Suna zama ta wassafa musu duk abin da ya shiga tsakaninta da Mami, ta kuma nuna musu Uwani da irin dukan da suka yi mata. Daga ƙarshe ta ɗora da jawabin ɗaurin auren su Uwani a ranar, duk yadda suka so shawo kan Dada a kan a bari zuwa nan da watan Maulidin ma fir ta ƙi yarda. Sai ma ta nuna musu ana idar da sallar Isha'i su tabbata da sun ɗaura wa Uwani da Jafar aure. Dada ta dubi Baba Mamman ta ce. "Kai Mamman tun da ka zama sakarai sai ka bari Jafaru ya saki Uwani tun da uwarsa ta yi rantsuwa ba zai aure ta ba, to ka sani matuƙar Jafaru ya saki Uwani wallahi sai dai ka nemi wata uwar ba ni ba. Kuma a take kai ma ka miƙa wa Saratu takardarta ta saki. Na gama magana ku tashi ku ba ni wuri." Babu wanda ya iya tankawa haka suka fice ɗaya bayan ɗaya kowa zuciya babu daɗi. Uwani tun da ta kwanta zazzaɓi mai zafi ya rufe ta har sai da Dada ta ba ta magani ta sha, don haka da dare ko fita wasan dare ba ta yi ba. A ɓangaren Jafar ma tun da ya tashi daga falon Mami ya biya wasu almajirai suka gyara masa ɗaki, tun da ya shiga ɗakinsa sallah ce kaɗai take fito da shi. Daddy kuwa ko da ya fito daga sashen Dada sun jima suna tattaunawa da 'yan uwansa sannan kowa ya kama gabansa. Lokacin da aka idar da sallar Isha'i a masallacin gidan marigayi Mai shanu har mutane za su fara watsewa, malam Liman ya yi shelar akwai ɗaurin aure da za a yi. Nan take aka gabatar da waliyai daga kowanne ɓangare, aka ajiye sadaki dubu ɗari da hamsin da alewar ɗaurin aure. Jafar da ke can kusurwar bango da mamaki yake bin malam Liman, a zuciyarsa yake ayyana wanne irin aure ne za a ce za a ɗaura shi da daddare? Ganin su Daddy a gaba-gaba ya sa gabansa ya yi mummunan faɗuwa, ya yi saurin kawar da tunanin da ya faɗo masa a rai har yana neman tsari da shi. Wayarsa ya ɗauko ya fara latsawa, saƙon Safna ya ci karo da shi yana shirin buɗewa ya ji Liman ya furta. "Ga waliyin Jafaru ga waliyin Hauwa kulu an kawo sadaki dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba. A bisa duka shaidun da ake buƙata sun kammala kowa ya shaida an ɗaura auren Jafar Mamman mai shanu da amaryarsa Hauwa kulu Umaru mai shanu, a kan sadaki naira dubu ɗari da hamsin lakadan ba ajalan ba." Daga haka ya fara rattabo addu'o'i ana ta saka albarka. Baba Isuhu ya ƙarasa yana yi wa Jafar Allah sanya alheri, ganin shi ne angon waɗanda ba su san shi ba suka ƙarasa suna masa fatan alheri. Tamkar butum-butumi haka Jafar ya ƙame a wuri ɗaya, ta cikin hayaniyar mutane ya sulale kai tsaye ya wuce gida. Na Madina sai ƙwala masa kira yake amma ya yi banza da shi, Jafar kai tsaye ɗakinsa ya shige ya datse yana kai wa da kawowa. "Ga alewa da dabinon ɗaurin auren ɗanki, ki saka albarka domin addu'arki na da muhimmanci a wurinsu. Bayan mun idar da sallah aka ɗaura auren Jafar da Uwani." Daddy ya furta wa Mami bayan ya shiga gida. A fusace Mami ta suri ledar dabinon ta yi wulli da ita, cikin ɓacin rai ta furta. "Daddyn Jafar yanzu tozarcin da za ka yi mini kenan? Wannan tsinannan auren zan saka wa albarka? Wallahi a daren nan sai Jafar ya saki Uwani." Murmushin takaici Daddy ya yi ya ce. "Na riga da na gama magana da Jafar, ki sani idan kika tilasta shi ya saki yarinyar nan wallahi sai na sauke miki igiyar aurenki uku daga kaina." Baki sake Mami ta bi Daddy da ya wuce ɗakinsa da kallo, saboda takaici sai kawai ta fashe da kuka. Su Shukra ne suka ƙarasa suka fara lallashinta. Cikin ƙanƙanin lokaci garin ya ɗauka 'Yar ƙashin gwiwa ta yi aure, wasu masu ƙarfin halin har gidan suka shiga yin tsegumi. Uwani duk wainar da ake toyawa ba ta sani ba sai daga baya Dada take sanar da ita, babu wani abu da ya ɗaga mata hankali abin da ya fi damunta ciwon jikin dukan da su Mami suka yi mata, wanda ta ci alwashin gabaɗaya za ta ladaftar da su ɗaya bayan ɗaya. Washegari ne ya kama sunan gidan Baba Isuhu sai dai tsamin jikin da Uwani take fama da shi ya hana ta walwala, don ta ci burin ko yaya ne ta tarwatsa 'yan taron suna. Yamma liƙis Uwani da ƙawarta Kubra na tafe suna hira Kubra ta ce. "Oh 'Yar ƙashin gwiwa yanzu dai aurenku da Ɗansandan nan ya tabbata, to kema 'yar sanda za ki zama?" Uwani ta yi jim sannan ta ce. "Da dai tuƙin jirgin sama nake son koya na dinga lulawa a jirgi ta cikin gajimare, an ce fa idan ka na jirgi har taɓo gajimare ana yi da hannu idan aka zira hannu. Amma dai yanzu tun da na auri Ɗansanda gaskiya ina jin ni ma 'yar sanda zan zama, ko ba komai Yaya Jafar ba zai mini baraza da bindiga ba tun da kar ta san kar..." Maganar Uwani ta maƙale sakamakon hango Shukra da saurayinta a ƙofar gida, suna jingine a jikin mota Shukra sai karairaiya take masa tana fari, a can gefen wata bishiya ta hango wani mahaukaci da ake yi masa laƙabi da 'Ba ka da nauyi.' Ɗabi'arsa ce ya ɗauki mace ko namiji ya dinga yawo da kai a gari yana ce wa ba ki da nauyi, kuma ba zai dire ka a ko ina ba sai tsakiyar kwata. A fili Uwani ta sheƙe da dariya Kubra ta ce. "Lafiya kike dariya 'Yar ƙashin gwiwa?" Gyaɗa marau ɗin hannunta ta kalla sannan ta ce. "Zo mu je wurin ba ka da nauyi." Kubra ta zaro ido, da sauri Uwani ta haɗe fuska. "Malama tsaya a nan wallahi kika ɓata mini shiri sai na sa shi ya ɗauki Baffanki gobe." Kubra ta ja baki ta tsuke don ta tabbata Uwani za ta aikata fiye da haka. "Baka da nauyi za ka ci gyaɗa marau?" Uwani ta faɗa tana kaɗa ledar gyaɗar a gaban mahaukacin. Washe baki ya yi cikin katuwar muryarsa ya ce. "Anci gyaɗa." "To bari kaji ina da gyaɗa marau soyayyiya da yawa, idan kana son na baka to ka ga waccen saurayi da budurwar ka je ka ɗauki budurwar ka zaga gari da ita, duk wanda ya zo cetonta ka haɗa masa jini da majina ni na sa ka. Na maka alƙawari zan ƙara maka wata, ƙila ma ba baka kwano guda..." Tun Uwani ba ta gama magana ba, Baka da nauyi ya fisgi ledar gyaɗar hannunta ya saka a aljihu, kai tsaya ya nufi wurin su Shukra ya tsaya a gabansu yana sakin shashashar dariya. A yatsine Shukra ta dube shi ganin yadda kayan jikinsa suke duƙun-duƙun ya sa Shukra ta tsartar da yawu sannan ta ce. "Malam mene ne haka ka zo ka saka mutane a gaba? Haka kawai ka saka mu tashin zuciya, dalla matsa daga nan." Ta yi maganar a yatsine ita a dole ta yi birga a gaban Salim. Salim ya kaɗa mukullin motarsa yana shirin yin magana sai gani ya yi Baka da nauyi ya suri Shukra yana dariya, da mamaki Salim ya dube shi fuska a haɗe ya ce. "Kai Malam wannan wane irin iskanci ne..." Tun Salim bai rufe baki ba Ba ka da nauyi ya sa gwiwar hannunsa, ya yi masa mahangurɓa a fuska ya kusa haɗa masa jini da majina. Wani haske Salim ya gani ya gifta masa kansa ya yi wani irin nauyi dum. Cikin gigita ya faɗa cikin gidan da gudu, da yake sashen Dada shi ne yake kallon ƙofa da sauri ya faɗa ciki a guje cikin fitar hayyaci, Dada na tsaye da ɗaurin ƙirji za ta sauya kaya sai ganin mutum ta yi ya shigo a guje yana wuri-wuri da wawure-wawure. "Hasbunallahu wa ni'imalwakeel kai wane gansamemen ƙaton ne haka..." Kalaman Dada suka maƙale sakamakon jin Salim na fisgar zanin jikinta ta ƙasa yana tura kai don shi maɓoya yake nema. "Kai don ubanka ba ka ganin ni tsohuwa ce, wai me kake nema a ciki ne?" Salim ya sake hankaɗe kansa yana shirin bankaɗe Dada ta faɗi a ƙasa, ganin haka ya sa Dada ta saka kuka tana faɗin. "Yau wane salon kwartanci ne haka ido biyu tun dare bai yi ba." Dada ta furta tana fisgar zanin shi ma Salim yana ja. Ganin Salim da gaske tura kansa yake yana yunƙurin sauke zanin Dada a ƙasa ya sa ta fasa ihu tana faɗin. "Jama'a ku kawo mini ɗauki ku ceci tsohuwa a hannun kwarto." "Don Allah ki ɓoye ni zai sauke mini fuskata daga jikin kaina." Salim ya faɗa cikin tashin hankali, yana sake fisgar zanin Dada yana tura kansa ciki. "Don Ubanka ka rasa a ina za ka ɓoye sai a cikin zanina, kai amma dai yau Allah Ya haɗa ni da lalatattun kwaratan zamani." Salim bai bi ta kan Dada ba ya sure zanin jikinta ya yi uwar ɗakinta a guje, sai ga Dada daga ita sai ɗan tofi shi ma ya zazzago ƙasa saboda kiciniyar da suka sha da Salim. Shukra ban da ihu da zille-zille babu abin da take yi, don Ba ka da nauyi ya sauke ta amma ya ƙi, yara kuwa sai bin su suke a guje suna masa waƙa da tafi. Wannan ya sake ingiza shi ya ci gaba da gudu da Shukra a saman kansa, ɗankwali da mayafinta tuni suka cire tun a ƙofar gida. Sai da ya gaji don kansa ya je wata ƙatuwar kwata ya tsoma ta a ciki. "Allah Ya isa tsakanina da kai." Shukra ta furta cikin kuka. Hannu ya zira a aljihu ya ciro wata ƙatuwar goruba ba ta yi aune ba sai ji ta yi ƙwal ya buga mata a goshi, ya juya ya ci gaba da tafiya. Azaba ta sa Shukra ta rushe da kuka, ga zurfin kwatar ya mata nisa ba za ta iya fitowa ba ga zafin dukan goruba a goshi. Kafin wani lokaci tuni goshinta ya yi wani malolo a daidai wurin da ya ƙwala mata. Cike da takaici Dada ta rushe da kuka sannan ta ce, "Jama'a ku zo ya ƙwace mini zanin jikina, ku kawo mini ɗauki kwarto har uwar ɗakin tsohuwa." 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA TARA Sai a lokacin Uwani ta fahimci ashe ba iya su Yaya Ƙarama ce kaɗai idonsu biyu ba, hatta mutanen da ke cikin uwar ɗakin lakur suka yi sai da suka ji Uwani ta yi sufa za ta faɗo uwar ɗakin suka fara ihun neman ceton rai. A daidai bakin ƙofar uwar ɗakin Uwani ta tsaya sai ta hango wata wuƙa a gefen randa, ta janyo ta ta fara wasawa. Naziru ɗan wurin Sa'a da a lokacin ya wartsake ya kafe Uwani da kallo, ganin haka ya sa Uwani ta kalle shi tana zare ido ta ce. "Ga wani ɗan ƙwage da shi za mu fara." Uwani ta ƙarasa maganar tana fusgar hannun Naziru da bai wuce shekara huɗu ba. "Wayyo Iyata! Wayyo Iyata." Ya fara ihu hankali a tashe don ƙiri-ƙiri ya ga wuƙar hannun Uwani. Sa'a na ganin haka ta fara jan hannun Naziru Uwani na jan ɗaya, Sa'a ta waiga wurin su Yaya ƙarama ta ce. "Ƙarama don Allah ku kawo mini ɗauki Naziri zai tafi." Yaya ƙarama da ke ƙuryar uwar ɗaki ta ce. "Sa'a ki haƙura da Naziru tun da ba wuce haihuwa kika yi ba, wallahi a yanzu ko Habibu (Shi kaɗai ne ɗanta) suka ja sai dai na bi shi da addu'a." Sa'a na shirin magana Uwani ranƙwala mata ludayi a ka, a guje ta saki hannun Naziru cikin kuka ta faɗa uwar ɗakin tana faɗin. "Wayyo Naziru." Shi ma Naziru sai tirjewa yake yana faɗin. "Iyata wayyo Iyata." Yaya ƙarama ce ta yi sauri ta banka ƙofar ɗakin ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya. "Idan kun rufe ƙofa za mu ɓullo ta ƙarƙashin ƙasa, mu dama ai daga kabari muke. A wannan lokacin babu buƙatar mu yi muku bayanin mu su waye, domin hukunta ku muka zo yi ɗaya bayan ɗaya, a kan cin zarafin da kuke yi wa mahaifiyar 'yar uwarmu da kishiyarta. Mu tawagar fatale sai mun saɓule fatar jikinku sannan mu tsotse romo da ɓargon jikinku. Amma za mu ɗaga muku ƙafa zuwa nan da ɗan wani lokaci, don mun lura kun fara nadama. Sai dai muna mai tabbatar muku babu wanda zai tafi gidansa sai an yi sadakar uku, idan kuma mutum ya yi kuskuren tafiya gida gobe, to a daren ranar sai dai ya kwana a ƙiyama." Uwani ta furta a lokacin da ta fita da Naziru tsakar gida da ke ƙwala ihu. A yadda ta lura kusan ilahirin mutanen gidan duka sun tashi, wata dabara ce ta faɗo mata don haka ta buga tsalle a tsakar gidan ta ce. "Waɗanda kuke leƙenmu muna gano ku, ke wato har da ke ko. Wallahi ɗaya bayan ɗaya za mu bi ku mu ƙwaƙwale idanunku idan ba ku koma kun kwanta ba." Ta saki hannun Naziru ai kuwa da gudu ya faɗa ɗaki yana ihu, sai ta tafi da gudu ta nufi ɗakin mahaifiyarta, a guje ta ji mutanen ɗakin suna shigewa uwar ɗaki wasu na hantsilawa. Nan ma ta nufi ɗakin kishiyar mahaifiyarta ta razana su, sai da ta tabbatar da sun gama tsorata kowa ya shige uwar ɗaki sannan ta lallaɓa ta isa banɗaki ta wanke fuskarta. Ta duƙunƙune hijabin Inna Suwaiba ta soke a hammata, sai da ta shirya sosai sannan ta nufi ɗakin mahaifiyarta da gudu tana faɗin. "Wayyo Allah! Ku taimaka mini za su ƙara janye ni." Tana shiga ɗakin ta tarar falon mahaifiyarta babu kowa an banke uwar ɗaki sai ƙananan yara da ke kuka suna buga ƙofa, saboda kada a gano Uwani ita ma ta fara bubbuga ƙofar tana ihu. Da ta lura ba za su buɗe mata ba sai ta janyo ƙofar falo ta datse. Har aka yi assalatu babu wanda ya yunƙurin fitowa daga ɗakin, duk da duka baƙin gidan a zuciyarsu kowa ya ayyana gari na wayewa tafiya zai yi. Amma da sun tuna kashedin da aka yi musu a kan kada wanda ya bar gidan har sai an yi sadakar uku sai jikin kowannensu ya yi sanyi. Sai da gari ya yi tangararan sannan Indo ta yi ƙarfin halin buɗe ƙofa, kamar sababin munafukai haka mutane suka dinga leƙowa ɗaya bayan ɗaya suna fitowa suna yin alwala suna sallah. Duk wannan abin da ya faru bayan da gari ya waye babu mutum ɗaya da ya jajantawa kowa, domin kowa a tsorace yake. Su Uwani suna zaune sai ga Aramma ya shiga ɗakin kansa ya yi waɗansu ƙulalai sun fi biyar, daidai tsakiyar hancinsa har wani ja ya yi yana maiƙo. Da mamaki suka bi shi da kallo, Aramma ya zauna daɓar jikinsa zafi zau da zazzabi. Gaishe shi mutanen ɗakin suka yi, suna son jin abin da ya faru da shi suna tsoro. Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin ya ce. "Ungo wannan Maryama, kuɗinki na jiya ne. Wannan kuma kyautar dubu hamsin ce na ba ki ita ma Indo zan miƙa mata nata." Baki sake Maryama ta bi shi da kallo, ta ce. "Malam dubu hamsin fa? An ya ba mantawa ka yi ba?" Aramma ya dube ta a fusace da ya tuna gargaɗin fatalwa sai ya wayance ya sassauta murya ya furta. "Maryama shaidar da za ki yi wa mijinki kenan? Kyautatawa ce kawai ta sa na ba ku." Maryama hannu na rawa ta sa ta karɓa tana zuba masa godiya, Aramma har ya miƙe zai fita Inna Suwaiba ta ce. "Aramma ungo shafa-shafa sai ka shafa a malolon nan na ka, Allah dai ya sawaƙe sanyi haka yake lokaci ɗaya ka ga wuri ya luluye. Ko kuma bige wa ka yi ne da dare?" Aramma da ba ya son a ja doguwar magana ya karɓa ya yi gaba ba tare da ya amsa mata ba, ɗakin Indo ya faɗa ita ma ya sallame ta ya koma ɗakinsa don ilahirin jikinsa ciwo yake masa. Aramma na shiga ɗaki sai ga Indo jiki na rawa ta shiga wurin Maryama suka fara tattaunawa cikin mamaki, ba su ƙara nutsa wa a tekun mamaki ba sai da suka ji Aramma ya ce a yi shinkafa da miyar dage-dage da rana. Wannan sabon sauyi da suka samu daga wurin Aramma ba ƙaramin daɗi ya yi musu. A na gobe Uwani za ta koma gida wurin ƙarfe goma sha biyu na dare ana zaune ana ɗan hira, ta hangi Aramma ya suri buta ya yi banɗaki. Sai da ta tabbatar da hankulan mutane ba ya kanta ta saci jiki ta nufi banɗaki, da yake banɗakin ya yi nesa da ɗakuna don haka ta laɓe a can kusurwar bango ta fara magana. "Baba ga tawagar 'ya'yanka sun dawo. Kada ka tsorata mune dai fatalen nan." Aramma da ke tsugunne a kan masai sai abin ya yi masa a daidai, saboda wata sabuwar gudawa ce ta tsarge shi. Gumi ya fara tsattsafo masa ya ce. "To 'ya'yana don Allah kada ku taɓa lafiyata, wallahi har yanzu ban warke ba." "Ba za mu sake cutar da kai ba, domin ƙawarmu wato matacciyar 'yarka ta ce ta ga irin kyautatawar da kake yi wa iyayenta da 'yan uwanta. Ki yi masa magana ya ji sabuwar muryarki ta cikin jinsin fatalwa." Uwani ta yi maganar tana wani fuffuka, sannan ta maƙale murya ta furta. "Baba ni zan tafi da kai na fi so na dinga ganinka." Tamkar an buɗe fanfo haka cikin Aramma ya birge, ya ci gaba da sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa. Cikin tashin hankali ya ce. "Na yafe don Allah ki je ki ɗauki mahaifiyarki." "Shi kenan Baba zan dai dinga kawo muku ziyara a ɓoye duk dare ina ganin rayuwar da kuke yi, idan na ga saɓanin abin da ka fara yi wallahi cikin tumbinka zan shiga, na kannaɗe hanjinka ita kuma kodarka na fansarwa shugaba." Uwani ta furta tana gimtse dariyarta. "Wallahi komai zan ci gaba da yi idan na saɓa ki mini duk abin da za ki yi mini." "Mu zamu tafi Baba sai mun sake zagayowa." Uwani na gama faɗar haka ta fara wata fuffuka tana gurnani sannan ta saɗaɗa ta bar wurin. Saboda yadda Aramma ya razana bayan da ya gama uzurinsa a duƙe ya dinga tafiya, saboda yadda ya ji ƙafafuwansa sun yi sanyi har sun gagara ɗaukar nauyin gangar jikinsa. Ranar da aka yi sadakar uku dai tun da safe wasu daga cikin 'yan gaisuwa suka fara watsewa, domin dama wasu tamkar a kan ƙaya suke. Ita ma Uwani sai da aka yi sallar la'asar sannan Aramma ya zo ya sanar da Maryama an zo ɗaukan Uwani, ta so Uwani ta ƙara kwanaki amma babu yadda ta iya haka ta danne. Wasu daga cikin 'yan uwan mahaifiyarta sai tsokanarta suke suna amarya sai sun zo biki. Kafin Uwani ta fita sai da Maryama ta sata a gaba ta yi mata nasiha sosai. Fakare Uwani ta yi tana sauraronta kamar nasihar na shigarta, sai gyaɗai kai take tana amsawa. Sai da ta gama sauraron mahaifiyarsa sannan ta ce. "Ni kam Inna don Allah zan faɗa miki wata magana amma don Allah kada ki faɗa wa kowa." Take gaban Maryama ya faɗi amma sai ta basar ta ce. "Ina jin ki babu wanda zai ji Uwanina." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita tana dariya, ita kanta Maryama dariya take sheƙawa sanna ta riƙe baki ta furta. "Allah Ya shirye ki Uwani ni dai wallahi ban san halin wa kika ɗauka ba, mahaifinki dai har ya fi ni sauƙin kai. Allah Ya shirya ki ko ba komai kin samar mana 'yanci." Suna cikin haka suka ji ƙarar horn da sauri Uwani ta sungumi jakar kayanta, ta ɗauko hijabinta ta saka. Sai da ta yi wa mutanen gidan sallama da Aramma sannan ta ƙarasa bakin motar cikin murna, don tun daga nesa ta hango motar baba Mamman. Don haka da saurinta ta buɗe motar tana faɗin. "Daddy wallahi na yi kewar Dada, ƙila ma ita tana can ko a jikin..." Kalamanta suka maƙale a maƙoshi sakamakon ido biyu da suka yi da Jafar. Wata uwar harara ya banka mata, ta yamutsa fuska tana ƙare masa kallo ta ce. "To kai kuma ina motarka ka ɗauko ta Daddy?" Jafar bai tanka mata ba ya fisgi motar da gudun gaske har sai da wasu yara suka matsa a guje. Suna cikin tafiya babu wanda ya tanka wa wani sai Uwani ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa, a fusace Jafar ya waigo ya zuba mata manyan idonsa. Sai kuwa Uwani ta sake kwashewa da dariya, gangara motar ya yi ya faka ya ɗauke kai gefe a daƙile ya ce. "Fice mini daga mota." Uwani ta gimtse dariyarta sannan ta ce. "Kamar ya na sauka ai ba motarka ba ce." "Uban me kike wa dariya?" Uwani ta yi murmushi ta ce, "Wallahi dariya ka ba ni, ni dai ba baƙuwa ba ce a wurinka atoh. Kuma dai komai na ka Dada ta ba ni labari tun kana jariri har fa tunbiɗin da ka dinga yi kana yaro. Sai kuma na ga ka fafaki mota kana yin wani irin tuƙin 'yan Kaduna-Zaria, to wai ni birgar me za ka yi mini?" Jafar ya haɗiyi wani yawu mai ɗaci haɗe da fusgar da iska mai zafi, jin irin maganganun da Uwani ta faɗa masa. Yana shirin yin magana Uwani ta sake sakin wata dariyar tana faɗin. "Kasan Allah yadda ka iya fafakar motar nan da Inuwan Toyota zai ganka tsaf zai ɗauke ka kwandasta, saboda wataran idan ya gaji ya ba ka ɗani..." "Fice mini a mota." Ya furta mata cikin tsawa. "Wallahi ba zan fita ba ai motar Daddy ce, malam kada ka yi mini gori ni nan gaba ma jirgin sama zan tuƙa." Kalamanta na ƙarshe suka kusa ba shi dariya. 'Yarinyar da cikakkun sentence na hausa ma ba ta iya haɗawa ba ita ce za ta tuƙa jirgin sama.' Ya raya a ransa. Ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya fisgi motar ya ci gaba da sharara gudu, har suka ƙarasa gida wani bai sake kula kowa ba. Tun Jafar bai gama faka motar ba Uwani ta suri jakar kayanta ta ɓalle murfin motar ta fice a guje ko rufe motar ba ta tsaya yi ba, tun daga soro ta fara ƙwalla wa Dada kira tana washe baki. Mami da ta rako aminiyarta Hajiya Falmata ganin Uwani ya sake tado mata da wani malolon baƙin ciki. "Ƙwata wannan abar ce fa aka aura wa Jafar, imagine a ce wannan ce sirikata." Hajiya Falmata ta ƙare wa Uwani kallo sannan ta saki wani malalacin murmushi ta furta. "Haba ƙawata wai da wannan 'yar abar ce ke barazana da aurenki? Tun da ƙuruciya ba ki yi yaji ba sai yanzu? Babu inda za ki, matuƙar kin bi duk tattaunawar da muka yi wallahi na faɗa miki da ƙafarta za ta kori kanta babu boka babu malam." Sai a lokacin Mami ta ƙara jin ƙwarin gwiwa, Hajiya Falmata ta ci gaba da biya mata miyagun shawarwari sannan suka yi sallama. Da murna Dada ta tarbi Uwani don ita kanta ba ƙaramin kewarta ta yi ba, dalilin da ya sa tun safe ta sa baba Mamman ya ɗauko ta. Shi kuma ya ce a bari zuwa bayan azahar sai Jafar ya ɗauko ta. Kuma ya yi haka ne domin so yake kafin lokacin tariyarsu su ƙara samun fahimtar juna. Sai da aka yi sallar Margriba kamar yadda Baba Yunusa ya ce za a zauna ya tara 'yan uwansa, Dada, na Madina, Uwani, Jafar da kuma Mami. Sai da ya buɗe taron da addu'a bayan kowa ga gama sannan ya fara magana. "Alhamdu Lillah! Na san wasu daga cikinku sun san dalilin wannan zaman yayin da wasu kuma ba su sani ba. Maƙasudin zamanmu a kan kai Jafar da kuma ke Uwani ne." Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa rai a bace. Tsabar takaici ya sa Mami yin ƙwafa a fili, Dada ta dube ta haɗe da taɓe fuska ta ce. "Aure dai Allah Ya haɗa duk mai hassada sai rabo ya kashe shi, yara su haihu kuma a mayar da sunansa." Mami ta shiga aika wa Dada harara a fakaice. "Jafar a yanzu wani nauyi ya hau kanka domin aure ba wasa ba ne, ka riƙe yarinyar mutane amana don a yanzu da kake gani komai nata ya dawo ƙarƙashin ikonka. Ke kuma Uwani wannan da kike gani aljannarki na ƙarƙashin ƙafarsa, ki bi mijinki sau da ƙafa yi na yi bari na bari. Duk abin da kika san zai faranta ran mijinki shi za ki yi, abin da ba ya so sai ki haƙura da shi don zaman aure ɗan haƙuri ne." Sai da Baba Yunusa ya numfasa sannan ya ci gaba. "Mun tattauna ni da 'yan uwana a kan za ku tare tare da Mahaifinku tun da an riga an ɗaura aure babu fa'idar a ce za a zauna har sai nan da wata biyu idan auren su Shukra ya zo. A don haka idan Allah Ya kai mu ranar Laraba mai zuwa ne mahaifinku Mamman ya ce za a ƙarasa gyara komai da saka komai na gidan, tun da akwai wadataccen wuri za ku zauna a ƙaramin part ɗin da ke gefen na Maminku." Wani irin tuƙuƙin zafi ne a zuciyar Mami har za ta ƙi amimcewa da hakan sai kuma ta tuna da huɗubar ƙawarta Hajiya Falmata. "Saboda haka muka yanke shawarar idan Allah Ya kai mu juma'a mai zuwa ne tariyarku, kuma bayan nan za a nema wa Uwani wata makarantar za ta ci gaba da karatunta. Idan ya so bayan sun yi hutu sai ka ɗauki matarka ku wuce wurin aiki." Jafar ya yi shiru ba tare da ya amsa ba. Wannan maganar ta ƙarshe ba ƙaramin daɗi ta yi wa Mami ba, don a wannan lokacin ne za ta ci karenta babu babbaka a kan Uwani. "Ni iya abin da zan iya ce wa kenan, Dada kafin mu zo kan ki ko akwai mai magana a cikin?" Gabaɗaya suka girgiza kai ban da Baba Mustafa da ya ce yana da abin cewa. "Sannu da ƙoƙari Yaya Allah Ya ƙara girma, duk bayananka a kan tsari suke. Amma abin da nake gani me zai hana a ɗaga tariyar ta su zuwa nan da kamar sati biyu zuwa uku, duba da yanayin ragowar shirye-shiryen da ya kamata a yi musu. Daga haɗa lefe har zuwa wani shirye-shirye na su na mata, sannan a wannan lokacin mahaifiyar yarinyar na cikin halin rashin 'yarta. Amma bayan wannan lokacin ita kanta za ta samu nutsuwar gudanar da bikin yadda ya kamata." Dada ta jinjina kai sannan ta furta. "Wallahi Mustafa ka yi kyan kai, saboda Allah kamar gajiya na yi da Uwanin da za a ce nan da kwana huɗu a kai ta ɗakin miji." Baba Yunusa ya yi murmushi ya furta. "Wannan haka ne, Dada me za kike ganin ya dace bayan haka." Dada ta yi jim sannan ta furta. "Ni dai kam nasiha ce zan yi wa Jafaru da ita Uwani, amma kam ba yanzu zan yi musu ba sai ranar da za su tare. Don ina gudun na tofar da yawun bakina a banza, su barbaɗar da nasihar da na yi musu tun kafin tariyarsu." Tambayar Mami aka yi ko tana da abin faɗa ta ce babu, don haka suka ƙarƙaren zaman tun ba a gama addu'a ba Mami ta sa ƙafarta ta fice rai a ɓace. 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA GOMA Tun daga wannan ranar su baba Yunusa suka shiga hada-hadar shirye-shiryen tariyar auren Uwani da Jafar, a ɓangaren baba Mamman sai abin ya haɗe masa biyu ga tariyar su Mami ga kuma ta shirin su Jafar. Babba Mamman da kansa ya kira Jafar ya nemi da ya bada wani abin domin ba don da auren ya zo a haka ba, ba shi da tsarin haɗa wa ɗa namiji lefe sai dai ya yi komai da kansa ko ya fi ganin darajar auren da aka ba shi. Amma fir Jafar ya ce ba shi da wasu wadatattun kuɗi, sai da ya ga ran mahaifinsa ya ɓaci sosai sannan ya iya bayar da dubu ɗari uku. Su ma sai da Baba Mamman ya yi masa barazanar zai ɗaga wani filinsa ya sayar a haɗa wa Uwani lefen da shi sannan ya bayar. Mami ban da 'yan uwanta babu wanda ta iya gaya wa sai kuma ƙawarta Hajiya Falmata da ta san da maganar, babban tashin hankalinta kada Hajiya Salima ta ji labari ta ce Safna ba za ta auri Jafar ba. Don haka ta kira Jafar a ɗaki ta gargaɗe shi a kan ko da wasa kada ya sake ya faɗa wa Safna maganar aurensa, don a yadda ta tsara auren ko wata biyu ba zai rufa ba Uwani za ta bar gidan da ƙafarta. Dada da ƙafarta ta je har garinsu mahaifiyar Maryama ta sanar da su duk halin da ake ciki, ba ƙaramin murna suka yi ba suka yi fatan alheri. Haka Dada ta sa aka dinga sanarwa da jama'a wunin bikin Uwani, shi kuwa Jafar har kawo lokacin kallon abin yake kamar a mafarki. Yana shiga ɗakin abokinsa Amir zama ya yi a gefen gado ya zuba uban tagumi, labule Amir ya ɗaga ya shiga hannunsa ɗauke da karan sigari yana zuƙa. Da mamaki ya dubi Jafar ya furta. "Abokina yaushe ka shigo? Kai fa daɗina da kai ka yi wa mutum zuwan bazata, yanzu kuma da ka zuƙi warin 'yar so sai ka hau ni da sababi." Jafar bai ɗago ba ya furta. "Miƙo mini kara ɗaya ka ba ni lighter zan zuƙa." Baki sake Amir ya ƙarasa bakin gadon ya ce. "Ko dai mafarki kake abokina?" "Na ce ka ba ni." Jafar ya faɗa a ɗan zafafe. Ba musu ya miƙa masa, Jafar ya hau kiciniyar kunnawa. Ganin ya kasa saboda rashin sabo ya sa Amir ya karɓa ya kunna masa, Jafar ya kai baki ya zuƙa da ƙarfi lokaci ɗaya ya ƙware ya hau tari. "Malam za ka kashe kanka a banza da wofi, wai me yake faruwa ne?" "Da zan mutu ɗin ma ai da ya fi mini komai sauƙi." Cikin zaro ido Amir ya ce. "Wa ya ɓata maka rai ne?" Jafar ya kauda kai gefe murya a dashe ya ce. "Aure aka yi mini." Amir ya shafa gemu yana sakin wani murmushi sannan ya furta. "Ɗan iskan ƙarya. Kai yanzu don an maka auren ne har kake wannan..." "Ka san wa aka aura mini? Uwani fa, wannan ƙanwar ta wa da ta taɓa sace maka tayar mashin." Jim Amir ya yi da sauri ya ce. "Wai wannan black beautyn? Amma fa kai shege ne, ka tsinci dami a kala ka zauna ka na sa kanka a damuwa?" Kalaman Amir suka ɓa ta ran Jafar bai tanka masa ba ya saka kai ya fice. Kafin ya ƙarasa fita Amir ya ce. "Billahillazi ni zan ɗauki nauyin kazar amarci idan muna raye." Jafar ya dawo da kansa a ƙufule ya ce. "Sai dai ka cinye abarka don ubanka." Amir ya bushe da dariya sannan ya bi bayan Jafar, sai da ya shawo kansa da ƙyar sannan ya labarta masa yadda auren na sa ya kasance. Sam Amir bai ga abin damuwa ba, don ce masa ya yi bayan auren Uwani babu jimawa kawai ya auri Safna tun da ita ce zaɓinsa. Kamar yadda baba Mamman ya tsara juma'ar da ta zo a ita ce su Mami suka tare a sabon gidansu, babban gida ne sosai don haka Mami ta ƙara jin kanta ya daɗa girma. Ta dinga kallon Facalolinta tana basarwa don ita a yadda ta so sam ba ta so sun kwaso jiki da gayyar 'ya'yansu sun zo mata ba. Yamma liƙis suka fara haramar tafiya a nan ne kuma baba Mamman ya ce Dada ba za ta tafi ba sai ta yi kwana biyu. Da yake a part ɗin su Mami har da ɗakin Dada da banɗakinta a ciki, fasalin gidan ba ƙaramin birge Uwani ya yi ba. Don haka da ta ji Dada ta ce ba a ranar za su tafi ba ko a jikinta. Mami ba ƙaramin haushi ta ji ba, don dai tana shakkar Daddy shi ya sa ba ta yi wa Dada kora da hali ba har suka gama kwanakinsu suka koma. Sannu a hankali kwanaki suka fara gangarowa har bikin su Uwani ya ƙaraso, shirye-shirye daga kowanne ɓangare ya yi nisa. Dangin mahaifiyar Uwani da mahaifiyarta ba ƙaramin ƙoƙari suka yi ba, haka su baba Yunusu su suka yi wa Uwanu komai har da su gara. Ƙawayen Uwani su Zulai, Hansatu, Furaira da Kubra sai rawar kai suke su a dole ga manyan ƙawayen amarya. Jafar kuwa ya yi wata irin rama ya ɗan yi duhu kamar shi ne macen, ita kuwa Uwani ko ajikinta sai ma warkajaminta take yi. Ranar juma'a ita ce ranar da aka yi kamun Uwani kuma a ranar ne za a kai ta, tun ranar alhamis aka rangaɗa wa Uwani lallen dungulmi hannu da ƙafa. Ranar Juma'a da sassafe Dada ta ja Uwani uwar ɗaki ta ce. "Uwani ni kam ina kunyar a kai ki ɗaki da wannan uwar kwarkwatar, kin san dai Jafaru da tsirfa tsiya. An ya ba aske miki kan nan zan yi baki alaikum, ba tare da wani ya sani ba." Ita kanta Uwani kan ya ishe ta ga yawa ba gyara ga kuma kwarkwata, don haka ba ta musa wa Dada ba. Da kanta ta karɓi kuɗi ta sayo reza, kamar masu yin wani ɓoyayyan sirri haka Dada da Uwani suka shige uwar ɗaki. Da farko almakashi Dada ta sa ta fara sauke mata kan tass sannan ta bi shi da reza ta yi mata ƙwal kwabo. Nan take Uwani ta ji wata ni'imtacciyar iska na shiga kanta, Dada ta bi ta banɗaki ta wanke mata kan tass sai ga kan Uwani ya fita ƙwal kamar bayan silba yana sheƙi. Bayan Uwani ta gama shiri ta kawo ɗankwali ta ɗaure kanta da shi, tun da ta ji iska na shigarta ta ci alwashin daga ranar idan kanta ya taru aski za ta dinga yi. A daren ranar ne kuma aka shirya Uwani domin kai ta ɗakin mijinta, saboda haka Baba Yunusu ya tara 'yan uwansa aka yi wa Jafar da Uwani nasiha. Uwani na daga cikin mayafinta sai satar kallon iyayen nata take, Jafar kuwa ya haɗe fuska ya sunkuyar da kai ƙasa abin duniya ya haɗe masa. Har an zo fita da Uwani sai Dada ta ja ta gefe ta fara yi mata raɗa a kunne, lokaci ɗaya sai ji aka yi Uwani da Dada sun bushe da dariya. Bayan Dada ta gama mata nasiha sai kuma ta rushe da kuka, sai da aka lallashi Uwani sannan suka wuce Dada ta riƙe hannun Jafar da Uwani suka shiga mota. Ragowar 'yan kai amarya kuma suka bi sauran motoci aka wuce da su gidan Mami. Sai da Dada ta kai Jafar da Uwani har sashen Mami domin ta yi musu nasiha, a yatsine ita da 'yan uwata suka tarbe su don yadda ta hangi Uwani tare da Jafar har ji ta yi kamar ta shaƙe ta. Su Dada na fitowa suka ci karo da su Amir shi da wasu abokan Jafar guda biyu. Dada ta wuce da Uwani sashenta shi kuma ya wuce wurin su Amir. "Ango ango!" Amir ya furta yana dariyar ƙeta. "Kai ba na son iskanci." Jafar ya faɗa a daƙile. "Wato wata miyar fa sai dai a maƙota, abokina ga fa alƙawarina na cika." Amir ya yi maganar cike da shaƙiyanci yana ɗago masa ledar kaji. Jafar duk tsiyar da suke yi masa shiru ya yi ya ƙyale su, ganin dare ya fara yi ne ya sa suka tilasta masa shiga cikin gidan. Har kan gado Dada ta kai Uwani, suna shiga ɗakin Uwani ta fisge mayafin tana kalle-kalle. Dada kuwa sai murmushi take tana sa wa su Baba Yunusa albarka. Sai da Dada ta zo tafiya a nan ne fa Uwani ta maƙele ta tana wani irin kuka mai ban tausayi, ita a dole sai Dada ta zauna. Sai da Inna Atika ta zare wa Uwani ido sannan ta koma laƙwas kan kado ta zauna. Gabaɗaya manya suka tafi daga Uwani sai ƙawayenta su Furaira. "Ke kam Uwani a duniya me za ki nema? Ga miji kin samu ga gidan miji kamar na kwamihina. To ke kuwa kukan me za ki yi?" Furaira ta faɗa, da yake duk cikinsu ta girme musu nesa ba kusa ba. Uwani ta goge ƙwalla nan take su Furaira suka dinga yi wa Uwani huɗuba kala-kala, wani su ƙyalƙyale da dariya wani kuma su tashi su gwada abin da suka ce Uwani ta yi. Suna cikin haka sai ga sallamar su Amir, Uwani da sauri ta ta ja mayafi ta rufe fuska tana murmushi, ita a dole irin kunyar nan ta amare. Tun da su Amir suka shigo Furaira take wata irin kwarkwasa, bayan sun gaisa a gefe ta hangi Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa. Furaira ta ƙarasa gabansa fuskarta cike da ɗige-ɗige ta saka mayafin a kafaɗa, ga wasu hannuwan jajayen rigar mama da suka leƙo ta kafaɗarta. Furaira yi farrr da ido ta ce. "Angonmu na ga kana cikin damuwa, idan ka yi haƙuri za mu ba ku wuri kai da amaryarka ku gwangwaje amarcinku, wannan tagumin ai ba naka ba..." Tun da Furaira ta fara magana Jafar ya kafe ta da ido yana kallon tsana, wani irin takaici ya mamaye shi. Jin abin da ta faɗa ya sa ya ɗago ya ɗauke fuskarta da mari. Sai ga Furaira daɓar a ƙasa, waɗansu manyan tagwayen taurari na yi mata yawo a fuska. Ganin abin da ya faru da Furaira ya sa su Zulai suka fita a guje har mayafai da ɗankwalayansu na faɗuwa ƙasa. Amir na shirin magana Uwani ta buɗe kai daga cikin mayafi ta furta. "Haba Ya Jafar yanzu a gaban abokanka za ka zubar mini da mutumci? Furaira fa ka mara gaskiya ba ka..." "Rufe mini ba ki." Jafar ya buga mata tsawa, sai da ta muguɗa masa baki sannan ta shiga wurga masa harara don a wannan karon Jafar ya ba ta haushi sosai. "To ango mu dai maƙasudin zuwanmu shi ne..." Da sauri Jafar ya katse Salis. "Ba na son hayaniya Salis sai da safe." Amir ya gimtse dariya yana miƙa masa ledar kajin hannunsa ya ce. "Au har korar mu kake, shegen gora mum muna kan hanya..." Gabaɗaya sauran abokan Jafar suka saka dariya, sai da suka yi wa Uwani sallama sannan suka fita. Uwani saboda ɓacin ran abin da ya yi wa su Furaira ko tanka musu ba ta yi ba. Jafar na raka su ya koma falo ya zaune, a gajiye ya tuɓe babbar rigar jikinsa ya faɗa kan kujera yana lumshe idanu. Wayarsa ce ta fara neman agaji, da sauri ya ɗago ya duba. Safna ce ke kiransa don haka ya yi rejecting sannan ya kira ta. "Baby wuni guda ka manta da ni." Daga can ɓangaren ta furta a shagwaɓe. "Ta ya ya zan manta da ke cutie?" Ya amsa mata. "Akwai wanda ya taɓa mini gwarzona ga dukkan alamu, baby me yake damunka? Kwana biyu na gagara gane kanka." Murmushi Jafar ya yi sannan ya furta. "Daddy ne ya saka ni wani aikin so na gaji sosai." "Ok, ka yi wanka ka huta da safe ma yi magana becouse akwai maganar da nake son yi da kai." Dam! Ƙirjin Jafar ya buga ba tare da ya san dalili ba, ya yi ƙarfin halin amsa mata sannan suka yi sallama. Tun bayan fitar su Jafar Uwani ta fisge mayafin kanta, ta shiga ɓuruntun duba ɗakin ta buɗe wannan ta leƙa wannan. Bayan ta gama dube-dubenta ta koma bakin gado ta zauna, tuno huɗubar su Furaira ta yi da wacce Dada ta yi mata sai kawai ta saki murmushi. Banɗaki ta faɗa ta yi wanka, sannan ta buɗe akwatin lefenta ta zaro wata doguwar riga. Sai da ta ɗaga wata riga ta ƙare mata kallo sannan ta furta. "Ashe shi ma ya Jafar ƙwallon ɗan iska ne a fakaice ban sani ba, dubi irin rigar fitsararrun indiya da ya sa aka sayo mini. Allah Ya sawaƙe ina zan yi wannan lalacewar Dada ta ga ya wa baba Mamman, haka kawai ya yi mini faɗa." Uwani ta cusa rigar cikin akwatin sannan ta zaro wasu riga da wando ta saka. Sabuwar hula ta farke ta saka a kan ƙwaryar molon kanta, sai kuma ta ciro wasu sababbin panties da rigar mama guda bibbiyu ta farke tana dariya. Can drower kayan Jafar ta buɗe ta jefa guda biyu sai kuma ta taka gado ta saƙale biyu a saman drower, ta koma tana bin ledar kajin da kallo ƙamshi na dukan hancinta. Ganin Jafar ba shi da niyyar dawowa ya sa ta ɗauko ledar kajin da sauran kayan shaye-shaye ta baje ta hau lodawa cikinta. Uwani na nan zaune Jafar ya shiga ko kallon ƙurarta bai yi ba ya nufi drower kayansa domin ya ɗauki towel zai shiga wanka, yana buɗe drower sai jin abu ya yi a kansa rigar mama ta faɗo. Dama Uwani su Furaira sun ce ta yi haka ne, wai yin hakan na jan hankali ango da ƙara danƙon ƙauna. Shi kuwa Jafar yana buɗewa da ya ji abu ya faɗo kansa yaraf da sauri ya buga uban tsalle yana faɗin. "Wayyo ɓera, wayyo Allah ɓera a kaina." Uwani na daga wurin da take zaune sai dariya take, a gefen kafaɗarsa ya hangi rigar a fusace ya fisge a yatsine ya furta. "Mene ne wannan." Uwani ta kanne dariyarta ta ɗan basar ta ce. "Me ka gani to? Ba kai ka saƙalo a jikinka ba? Wai dama duk wannan muzuran da kake yi tsoron ɓera kake?" Jafar ya fisge rigar ya wurga mata, ya ƙarasa ya bige bakinta haɗe da matse shi da hannunsa. "Idan ba ki daina mini rashin kunya ba sai na fasa bakinki." Towel ya ɗauka har zai shiga toilet ɗin da ke cikin ɗakin ko me ya tuna sai ya fice ta nufi public toilet, bayan ya yi wanka ya ɗauko filo ya dawo falo ya kwanta. A kan kujera ya kwanta ya ji kwanciyar babu daɗi ya miƙe kenan ya ji bugun ƙofa, kafin ya tambaya ya ji muryar Mami da sauri ya buɗe Mami ta shiga tana bin ɗakin da wulaƙantaccan kallo. "Ina kucakar nan take?" A sanyaye Jafar ya nuna ɗaki, kamar Uwani ta san da ita take sai ga ta ta leƙo falon hannunta ɗauke da cinyar kaza tana ci. "Ke don Ubanki ba a koya miki ladabin gaida manya ba ne?" Mami ta furta cike da tsana. "Mami na ce miki ki daina zagin iyayena musamman mahaifina da yake lahira..." Jafar ya katse Uwani cikin tsawa. "Ke ba ki da hankali ne? Idan Mami na magana na sake jin bakinki sai na yi ƙasa-ƙasa da ke." "Ka bar ta ba sai ta rama zagin da na mata ba, 'yar iskar yarinya marar mutumci. Ban da ƙaddara ko a mai aikin gidan Jafar za ki zo ne." Uwani ta kafe Mami da kallo, Mami ta mayar da kallonta wurin Jafar. "Kai kuma ka lura da kanka, atoh ka dai gane abin da nake nufi. Wallahi ko da wasa kada na ji ka tsaya sauraron yarinyar nan ballantana wani abu ya ratsa tsakaninku, don wannan tsinannan auren wallahi ko wata biyu ba na saka ran ya kai ba." Jafar ya ɗan tsuke fuska. "Me kike faɗa ne Mami don Allah? Yarinyar da ko kallonta ba na son yi." Zuciyar Mami fes ta ce. "Shi kenan Son Allah Ya yi maka albarka. Ke kuma da ma gobe kina yin sallar asuba ki zo sashena ina son ganinki, shegiyar yarinya da ido kamar na mujiya." Uwani na tsaye ta ji zuciyarta babu daɗi. Wannan shi ne karo na farko da wani ya taɓa yi mata abin da ya bugi zuciyarta, tana nan tsaye ta sake jin muryar Mami a kanta. "Don uwarki ba magana nake yi miki, 'yar iska yarinya tsohuwar kakarki ta sangarta ki kina iskanci kala-kala. Da ƙafarki sai kin bar gidan nan da ni kuke zancen." Uwani ta sauke ajiyar zuciya rai a ɓace ta furta. "Mami wannan ce magana ta ƙarshe da zan gaya miki a kan zagin iyayena, zan jure komai amma ban da zaginsu. Dada ta daban ce a wurina amma matuƙar kika ci gaba da zaginsu ni ma..." Maganar Uwani ta katse sakamakon marin da Jafar ya sauke mata. Take idonta ya ciko da ƙwalla ta dube shi za ta yi magana ya katse ta. "Uwata ba sa'arki ba ce..." "Kenan ni iyayena ne sa'anninta? Wallahi ba zan jura ba..." Tas tass Mami ta sake ɗauke fuskar Uwani da mari. "Na zagi Uwarki sai ki rama don ubanki." Ban da ruwan hawaye babu abin da Uwani take yi, Mami ta gama ci mata mutumci sannan ta fice daga ɗakin. Tsaki Jafar ya saki ya wuce ya ɗauko bargo ya koma falo ya shimfiɗa ya kwanta zuciyarsa na suya, ta koma ta ɗauko mayafinta ta yafa ta zo za ta fice. Da sauri Jafar ya fisgo ta fuska a haɗe ya ce. "Gidan uban wa za ki a tsohon daren nan?" "Gidan da na fito tun da nan ba gidan zinare ba ne." Uwani ta ba shi amsa a zafafe. Tana gama magana ta sake miƙewa za ta fita ya sha gabanta. "Wallahi ba don Daddy na gidan nan ba, da babu abin da zai sa na hana ki fita. Shashasha ƙazamar banza da wofi." Daga haka Jafar ya sa key ya rufe ƙofar. Uwani ta koma ciki rai a ɓace. A ƙasa ta zauna tana nazarin hanyar da za ta samarwa kanta mafita, don ta tabbata idan ta ce a haka za ta ci gaba da zama a gidan nan ba za ta sha ruwa ba. Kuma ita dai wannan ƙerarran gidan ba za ta so ta fita daga shi ba ko don ta dinga cin daɗi kuma ta gyara wa Mami zama. Ƙurajen da suka fara tsattsafo mata a kai ne suka fara yi mata raɗaɗi, don haka ta ɗauko jakarta ta ciro farar hoda ta bursune kanta, fuskarta har zuwa wuyanta. Hamma ta fara saki tana gyangyaɗi ba shiri ta ɗauki fulo ita ma ta nufi falo. A lokacin da ta shiga falon Jafar har ya kashe fitilar falon ya yi bacci, a gefe ta yarda filonta ta kwanta ita ma nan take bacci ya yi awon gaba da ita. Lokacin da dare ya tsala Jafar na cikin bacci juyin da zai yi sai jin mutum ya yi a kusa da shi, a tunaninsa Uwani ce don haka ya miƙa hannu sai ji ya yi ya shafo kan mutum da rantal da aski. A zabure ya tashi yana faɗin. "Kwarto ne zai shigo mana gida." Ya ɗaga hannu da ƙarfin gaske ya ɗaka wa Uwani duka a baya a tunaninsa kwarto ne. Tun da ya san ban da haka babu abin da zai kawo namiji ya kwanta a kusa da shi. A zabure Uwani ta tashi tana susar baya, sai a lokacin Jafar ya kunna fitilar ɗakin. Cikin tashin hankali ya fara ja da baya ganin baƙuwar fuskar da ya gani fururu da hoda, a hankali Uwani ta fara tunkaro shi. Jafar ya fara ja baya yana faɗin. "Don Allah waye kai?" Uwani ta ci gaba da matsowa ganin ta tunkaro shi gadan-gadan ya sa Jafar ya zuba a guje ya fice daga ɗakin yana faɗin. "Wayyo Allahna." Ita ma Uwani ta rufa wa Jafar baya a guje tana gudu tana wani irin gurnani. Daga yau zan tafi hutun sallah sai ranar Laraba (19/06/2024) zan ci gaba da posting In Shaa Allah. Littafin Uwani 500 ne amma daga yau zuwa ranar Laraba 19/06/2024 duk wacce ta za biya za ta turo 400 ta wannan Acc ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank Evidance ta wannan number 07062062624 na rage muku 100 for Happy Sallah. Mutanen Nijar su tuntuɓe ni. Ina fatan 'yan uwa za a bi nama saffa-saffa don gujewa rikicewar ciki.😂 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA ƊAYA Ilahirin jikin Jafar ban da karkarwa babu abin da yake yi, iya ƙarfinsa ya taƙarƙare yana gudu tun don tun da ya zo duniya bai taɓa cin karo da hallitar da ta ba shi tsoro lokaci ɗaya kamarta ba. Tashin hankalinsa ya ninku sakamakon jin ƙofar da za ta sada shi da gareji ta datse ƙam ta ƙi buɗuwa, ganin haka ya sa Jafar ya maƙale wani dogon ƙarfen da ke jikin rumfar harabar wurin. Cangala ƙafa Uwani ta fara yi ta fara wata shaƙuwa da ƙarfi tana zaro ido waje ta tunkare shi. Hannu ta sa ta fisgo ƙafarsa ɗaya sannan ta ce. "Sai mun fige wannan ƙafar taka kamar yadda ake figar kaji, sannan mu ɗauke ka mu tafi da kai dajin tsumbur. Tun da har muka buɗe maka idanu kana iya ganin mu sai mun tafi da kai." Jafar a ruɗe ya furta. "Wayyo Mami, wai Daddy ba kwa ji na ne? Ku taimaka mini kada su fige ni." Uwani ta fara wani juya idanu tana buɗe baki kamar mai shirin kai cizo, sai da ta sake zaro ido waje sannan ta kai baki ta gasa wa Jafar cizo a ƙafa. Ta sa hannunta na hagu ta yaƙuso ƙwaurinsa, ta ci gaba ta fisgar ƙafar tana faɗin. "Ɗan tsita yau balangu za ka ci, sai mun babbake maka wannan cinyar guda ɗaya mai kama da ta sauro ka cinye." Cikin azaba ya fisge a nan Allah Ya ba shi nasara ya buɗe ƙofar, ganin ɗakin Lado mai gadi ya fi kusa da shi ya sa ya nufi wurin a guje yana tafe yana waige. Abin da ya ƙara ɗaga masa hankali, bai wuce yadda idan ya waiga yake ganin Uwani na sake tunkaro shi tana zaro harshe waje. A wannan karon Uwani ta sauya salon tafiya a hankali take tafiya tana zaro harshe, ta sake karkatar da kai ƙasa kamar yadda zombie suke yi. Lado mai gadi da ke zaune a kan kujera cikin gyagyaɗi ya ji gudun Jafar, a zabure ya miƙe yana faɗin. "Ranka shi daɗe lafiya kuwa?" Jafar ko ta kan Lado bai bi ba ya banke shi ya faɗa ɗakinsa ji kake garam! Ya doko ƙofar ya rufe, dabass! Lado ya faɗi saboda bangazar da Jafar ya yi masa ya yunƙura yana kaɗe jikinsa ya furta. "Allah na tuba wane dare ne jemage bai gani ba? Ai sai daren mutuwarsa. Ni akwai wani aljani ko ɗan fashi da zai razana ni, ni da tun ban fi shekara biyar a duniya ba Baffa ya fara kwana da ni a wurin gadi..." Maganar Lado ta maƙale sakamakon hango Uwani da ya yi tana tafe tana ƙaƙƙanbare hannu, 'yar ƙaramar sandarsa ya ɗauka zai tunkari Uwani tsoro ya fara kama shi. Lado ya fara waige hankali a tashe ya cewa Jafar. "Yallaɓai! Wai mene ne ma ya karo ka daga cikin gidan ne." Muryar Jafar a can ƙuryar ɗaki ya ce. "Lado gamo na yi don Allah ka yi wani abu a kai." Lado ya fara tunkarar Uwani gabansa na faɗuwa, sai da ya tafi gadan-gadan kamar zai iya taɓuka wani abu sai kawai ya zuba a guje ya fara doka ƙofar ɗakinsa. Jafar na jin an fara doka ƙofar ɗakin Lado wani abu ya sake tsarga masa, jiki na karkarwa ya ce. "Lado ya ake ciki ne kar dai sun fi ƙarfinka kai ma?" Lado da ke cikin tashin hankali ganin Uwani ta zo daf da shi ya fara fitsare wandonsa ba tare da ya sani ba. Uwani ta fisgi sandar hannunsa tana wage baki, ta zuba masa tana caccaka masa tsinin sandar a baya. Cikin tashin hankali Lado ya fashe da kuka ya furta. "Yallaɓai don Allah ka taimaka mini, ni ma fa na shiga hannu." Jafar da ke cikin ɗakin jin Lado na kuka shi ma sai ya fashe da kuka don ya san tun da aka fi ƙarfin Lado shi ma yana nan ɗakin za su zo su cim masa. Daga can saman window Uwani ta hango Mami na ziro kai tana leƙen abin da yake faruwa, Uwani ta ɗaga kai tana wani gwale fuska ta nuno Mami da sandar hannunta ta ce. "Keeee me leƙen nan! Wallahi za mu mayar da fuskarki ƙeya, mu ɗebo ƙafafunki mu dawo da su ƙirjinki. Shi kuma ƙirjinki mu mayar da shi gadon bayanki." Tun Mami ba ta gama jin abin da Uwani ke faɗa ba ta yi saurin banke gilas ɗin window. Lado na ganin ya ɗan samu sarari ya zuba uban ihu ya nufi sashen su Mami a guje. Uwani ta rufa masa baya tana tafe tana ranƙwala masa sanda a baya, Lado ban da ihu babu abin da yake saki. Jafar da ke cikin ɗakin Lado ya yi sharkaɓa da gumi jikinsa ban da karkarwa babu abin da yake yi. Lokaci ɗaya ya ji zazzaɓi ya rufe masa jiki, a lokacin da ya ji Uwani ta bi Lado a guje da sauri Jafar ya ja zani ya tura kansa a ciki yana kalmar shahada. Lado na tura ƙofar sashen Mami ya tura ƙofar da datse da sakata jiki na rawa, da ƙarfi Uwani ta fara kartar ƙofar tana faɗin. "Za mu jijjige ƙauren gidan mu shigo, mu banka wa mutanen cikin gidan wuta. Ko kuma mu burtso ta ƙarƙashin ƙasa mu kwashe ku tass." A guje Lado ya shiga cikin gidan, da ɗakin Mami ya fara cin karo don haka ya banka da ƙarfin gaske ya faɗa ciki. Mami na kwance a kan gado cikin bargo ban da karkarwa babu abin da jikinta take yi, jin an yi sufa a kan gadon da take ciki an shige bargo ya sa ta yi tsammanin ko Daddy ne shi ma aka tsora ta yake neman ɗauki. Sai da Uwani ta tabbatar da Lado ya gama tsurewa sannan ta yarda sandar ta nufi sashenta, kayan jikinta cire ta saka wata doguwar riga har ƙasa sannan ta shiga banɗaki ya wanke fuskarta ta haye gado ta kwanta abin ta. Duk budurin da ake yi Daddy da su Shukra sam ba su sani ba, da yake Daddy ya tsaya nafilfulu bai kwanta da wuri ba. Kwanciyarsa babu jimawa bacci mai nauyi ya yi awon gaba da shi, da ma Mami ba ɗaki ɗaya suke kwana ba tun ranar da ya je mata da maganar auren Jafar ta yi masa yaji take kwana a ɗakinta. Don haka ko da suka tare a sabon gidan ma, ba ta sauya zani ba. Daga Mami har Lado babu wanda ya gane wanda yake kusa da shi, don haka sai da asuba ta yi Lado ya zuro kai a hankali. A daidai lokacin Mami ta ɗago kai karaf suka haɗa ido da shi, a zabure Mami ta ja da baya fuska a murtuke ta ce. "Lado! Uban me ya kawo ka ɗakina?" Sai a lokacin Lado yake bin ɗakin da kallo, don shi dai bai san lokacin da ya shiga ba. Hankali a tashe ya furta. "Hajiya wallahi sai dai idan kawo ni aka yi! Wallahi ba ni na kawo kaina ba. Aljanun da suka biyo Jafar ne suka kawo ni..." A zafafe Mami ta katse shi. "Fita don Ubanka Lado." Kamar sabon munafiki haka Lado ya fita yana waige-waige, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci yana cikin tashin hankali. Banɗaki Mami ta faɗa ta ɗauro alwala ta yi sallar asuba, da yake gari ya yi haske sosai fita ta yi ta nufi sashen Uwani. A lokacin da ta fara buga ƙofa Uwani tana kwance, ta fara magana. "Waye?" "Uwarki ce." Mami ta amsa a taƙaice. Babu musu Uwani ta buɗe ƙofar ta furta. "Ina kwana..." "Riƙe gaisuwarki, ina Jafar yake?" Uwani ta wara hannuwa ta ce. "Ni ma ban wayi gari na gan shi ba, yanzu nake shirin zuwa na tambaye ki." Rass gaban Mami ya faɗi, da sauri ta fice daga sashen Uwani ta nufi wurin Lado da ke zaune a kujera yana jin rediyo. "Lado ba ka ga fitar Jafar ba?" Mami ta tambaya. "Hajiya ai Jafar na cikin ɗakina tun daren jiya, yanzu haka na yi-na yi ya buɗe wallahi ya ƙi, ni tsorona ma kada mutanen ɓoyen nan su dawo su tarfa ni a wurin nan." Lado ya ƙarasa maganar wasu tagwayen ƙwalla na zuba. Mami ba ta ƙarasa jin maganar Lado ba ta nufi ɗakin tana bugawa. "Son buɗe mini ƙofa Maminka ce." Daga cikin ɗakin muryar Jafar can ƙasa ya furta. "Mami ku miƙo mini ruwan alwala, ba zan iya fitowa ba wallahi gwagwiye mini ƙafa za su yi." Duk yadda Mami ta so Jafar ya buɗe ƙofar fir ya ƙi buɗewa, Lado ya miƙa masa ruwa ta window da sauri Mami ta nufi sashensu kai tsaye ta wuce ɗakin Daddy. Da sallama Mami ta shiga, turus ta yi ganin Daddy na zaune a kan dadduma yana karatun Alƙur'ani. Ganin Daddy ba shi da niyyar sallame karatun ya sa Mami ta furta. "Daddy gidan nan fa babu lafiya. Domin ganin idona na ga aljanu a daren jiya, yanzu haka Jafar yana ɗakin Lado tun daren jiya ya ƙi fitowa. Ka ga dai yau kwananmu ashirin da biyu a gidan nan ko kunama ba ta taɓa tsoratar da mu ba, amma zuwan yarinyar nan ga shi aljanunta suna neman sabauta mini yaro." Daddy ya kafe Mami da kallo, a daƙile ya furta. "Allah Ya sawaƙe." Ran Mami a ɓace ta ce. "Iya abin da za ka iya faɗa kenan Daddyn yara? An ya kana ƙaunata ni da 'ya'yana yanzu kuwa?" Sai Mami ta fara zubar da ƙwalla. Daddy bai tanka mata ba ya rufe Kur'anin sannan ya naɗe dadduma ya fice daga ɗakin. Duk abin da yake faruwa Lado ya zayyana wa Daddy, Daddy ya isa bakin window ɗakin Lado ya leƙa. Ban da gumi babu abin da Jafar yake yi, da ƙyar Daddy ya shawo kan Jafar ya buɗe ƙofar. Lokaci ɗaya Jafar duk ya yi zuru-zuru, Mami ta ƙarasa ta ruƙo hannunsa tana faɗin. "Son amma babu abin da yake damunka ko?" Uwani da ta ƙarasa ta nuna kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ta ce. "Ya Jafar ina ka shiga da asuba na ga ba ka nan." Jafar ya bi Uwani da shanyayyun idanunsa da kallo, Mami ta wurga mata harara sannan ta ja hannunsa suka wuce sashenta. Uwani ta gimtse dariyarta ganin yadda Jafar yake tafe yana ɗimgisa ƙafa, sai ƙara wani shagwaɓe wa Mami yake. Daddy ne ya koma wurin Lado ya sake tambayarsa tsakaninsa da Allah a kan abin da ya faɗa masa, don shi bai yarda da abin da Mami ta faɗa ba. Gani yake kamar wani sabon shirin suka ɓullo da shi, sai da ya ji ta bakin Lado ya kuma nuna masa shatin bayansa wurin da Uwani ta caccaka masa sandar wurinsa sannan Daddy ya yarda. Shiru Daddy ya yi yana nazari, a iya zamansu dai a gidan ba su ga wani baƙon abu ba. Sai tunaninsa ya tsaya a kan ko Uwani tana da iska, ya fi aminta da wannan tunanin na shi a kan mutanen jikin Uwani ne suke yunƙurin tashi tun da dama wasu sai an yi aure suke nuna kansu. Jafar wanka ya yi Mami ta dafa masa tea ya sha sannan ya samu ya kwanta bacci ya yi awon gaba da shi, ita kuwa Uwani tana can zaune Daddy ya leƙa ya kira ta ya ce ta nufi sashen su Mami ta zaune akwai baƙin da zai kira za su yi saukar Alƙur'ani a cikin gidan. A rakaɓe Uwani ta zauna a falon, sai uwar harara da Mami take auna mata don ma Daddy yana gidan amma ta ci burin tun a ranar ta fara hora ta da aikin wahala. Sai kusan sha biyun rana ragowar 'yan uwan mahaifiyar Uwani da wasu tsirarun 'yan uwan Dada suka sake dawowa ganin gidan Uwani, sai a lokacin ne Uwani ta ɗan saki jiki suka dinga hira. Mami ba don ta so ba ta sa Inna mai aiki ta girka musu abinci, bayan sallar la'asar kuma kowa ya kama gabansa. Daren ranar da ƙyar Daddy ya shawo kan Jafar suka koma sashensu, don ita Uwani fir nunaawa ta yi ba ta gane abin da Jafar da su Mami suke faɗa ba. Dalilin haka ya sa Daddy ya sake tabbatar da ƙila mutanen jikin Uwani ne suka tsora ta su. Sai da suka ci abinci a ɓangaren su Mami sannan suka nufi na su, suna zaune a falo zaman kurame wayar Jafar ta fara ringing. Number Safna ya gani bai san dalili ba haka kawai ya ji gabansa ya faɗi, a hankali ya ɗauki wayar daga can ɓangaren aka furta. "Haba Baby wai ina ka shiga ɗazu na kira no respond." Jafar ya saki murmushi. "Cutie na gaya miki kwana biyu ba na zama but am very sorry, In shaa Allah haka ba za ta ƙara faruwa ba." "Beb dama fa Daddy ne na ji yana yunƙurin haɗa ni da wani cousin ɗina, ni kuma na ce masa ina da wanda nake so. So yanzu dai ya ce kawai ka fito..." Tun Safna ba ta gama magana ba Jafar ya miƙe a zabure, "Da gaske kike Cutie?" Jin yadda ya karɓi maganar ne ya sa Safna ta ce. "Da wani abu ne Baby?" Jafar ya ɗan wayance yana sosa ƙeya ya furta. "Am ba komai Dear kawai na yi mamaki ne, na ɗauka Dad ba zai bari a yi maganar aurenmu yanzu ba." Cikin jin daɗi Safna ta ce. "No ka san Daddy bai da matsala." Jafar ya ma manta Uwani na wurin shi da Safna suka ci gaba da hirar soyayya, ya tabbatar mata da zai sanar da mahaifinsa duk abin da ake ciki. Baki sake Uwani ke bin sa da kallo tana mamakin yadda yake sakin murmushi. "Ya Jafar dama kana dariya haka?" Uwani ta tambaya. "Sai ki hana ni, da waya ce ki zauna ki saka mini ido?" Uwani ta tura baki gaba. Suna nan zaune sai ga kiran Dada ya shigo wayarsa. Sai da ta kusa katsewa sannan ya ɗauka yana faɗin. "Tsohuwa mai ran ƙarfe." Dada ta saki murmushi ta furta. "Lallai Jafaru dare guda wai amarci ya ɓoye ka, ja'irin yaro da ana baka ka na ƙin karɓa..." "Kin san Allah Dada zan kashe wayata." Jafar ya furta a taƙaice. "Yoo kashe mana Jafaru, ai ubanka Mamman na nan. Ni ba zan aiki uwarka Saro ba saboda ba ganin mutumcina take ba. Amma wallahi ka kashe mini waya ban gaisa da Uwani ba sai na kira ubanka Mamman ya kawo mata waya." Jafar bai tanka ba ya miƙa wa Uwani waya. "Dada ni dai gaskiya wurinki zan dawo, gidan nan babu daɗi ko kaɗan." Dada ta washe baki ta furta. "Haba Uwanita ai dama gidan aure kowa a sannu yake sabawa, lokacin da aka kawo Saratu uwar Jafaru ta haura wata biyu tana guduwa gida. Amma ba ga shi yanzu Saro ta murje tana zuba mulki ba, ke dai duk shawarwarin da na baki na riƙe miji ki riƙe su gam, kin san dai halin Jafaru da baƙin halin tsiya. Kar dai ki ɓata masa ya sa bakin bindiga ya harbe mini ke." Gaban Uwani ya faɗi, da sauri ta ce. "Kuma sai ya harbe ni fa ko Dada?" Jafar da ke jin duk abin da suke faɗa ya kalli Uwani ganin lokaci ɗaya ta firgice. "Wallahi indai halin Jafaru da na sani ne tsaf zai harbe ki, yo ba Mamman ne ya haifo shi ba. Ai Allah kaɗai ya san haƙurin da Saro take yi da shi, ni ina zargin duk rashin mutumcin da take yi ma Mamman ne ya koya mata. Atoh kowa dai ya san mata na da alkunya, kuma idan kika ga mace ta canza daga mijinta ne. Ni dai yanzu duk wannan hirar da muke yi kada ki bari Jafaru ya ji, don sai ya sanar da Mamman. Ina zaman-zamana tun daga ƙuruciya ban taɓa sanin wurin Hukuma ba Mamman ya yi ƙarata. " Uwani ta ce. "Dada wai ina na Madina ko cigiyata ba ya yi ne? Ina su Lawan kina dai kula da su ko?" Lokaci ɗaya Dada ta bushe da dariya sannan ta ce. "Na Madina fa ya tafi wurin wata Goggon su Sabi'u, ni ban san na Madina neman aure yake ba sai jiya, ashe shi ya sa kullin a cikin sayen turaren binta sudan yake. Ni dama na jima ina yi wa na Madina addu'ar Allah Ya damƙa shi hannu mata ta gari..." "Dada zan yi amfani da wata na gaji da wannan hirar ta ku." Jafar Ya faɗa yana ƙoƙarin karɓar wayarsa. Daga can ɓangaren Dada ta ce. "Jafaruruna gaskiya na ji daɗin yadda na ji zamanku kai da Uwani, amma don Allah ka sayo mata waya ma dinga gaisawa idan kana gida." Jafar zai yi magana Dada ta katse shi. "Kai gaskiya kar ma ka saya wa Uwani waya ka yi asarar kuɗinka, haka kawai kuna zaune lafiya ta haɗa lamba ta kira maka mutanen duniya. Kwanki da ta ɗauki wayata sai ji na yi ta kira wani ɗan yuniyon..." "Shi kenan sai da safe Dada." Jafar ya katse ta yana karɓar wayar daga hannun Uwani. Dada ta saki murmushi ta ce. "Allah mai iko wai Jafaru ne yau yake zumuɗin kashe waya saboda ga mace a gefensa." Ɓacin ran kalaman Dada ya sa ya katse wayar ba tare da ya tanka mata ba. Dare ne ya fara yi don haka Uwani ta gaji da kallon da take yi, ɗaki ta shiga ta fara duba akwati domin ta ɗauko rigar bacci ta saka. Tsulum ta ga Jafar ya shigo da sauri sai wani wuri-wuri yake yi. "Malam ka fita zan sauya kaya." Uwani ta furta. Banza ya yi mata don a yadda ta lura da Jafar kamar a tsorace yake, don haka ta ɗauki wata doguwar riga ta shige banɗaki. Sai da ta sauya kayan sannan ta koma ɗakin, tana shirin hawa kan gado ta ga ya jefa mata filo ƙasa. "Ina zaki je?" "Kwanciya zan yi." Ta amsa masa a taƙaice. "Daga yau a nan ƙasa za ki dinga kwana idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci." Jafar ya yi maganar yana ɗaukan jallabiyarsa ya shiga banɗaki, sai da ya sauya kaya ya fito sannan ya haye gado ya kwanta. Uwani ta ɗauki filon ta koma can gefen gado tana shirin ajiye filo Jafar ya riƙo kunnenta da ƙarfi ya murɗe. "Kin raina abin da na faɗa miki ne? To ki kwanta Allah Ya ba ki sa'a." Ya ƙarasa maganar yana murɗe mata kunne har sai da Uwani ta ɗan ƙwalla ƙara. Babu yadda ta iya haka ta koma ƙasa ta yarda fulo ta kwanta, bayan wani lokaci gabaɗaya bacci ya yi awon gaba da su. Cikin dare Uwani ta ji sanyi ya dame ta ga bargon na su Jafar ya ɗauka ya rufa da shi, cikin sanɗa ta ɗauki filo ta koma can gefen gado ta janyo bargon ta rufa. A wannan karon ma Jafar yana juyowa cikin bacci ya ji ya sake shafo ƙwaryar molo, Uwani da ke bacci jin ana shafa ƙwaryar molon kanta ya sa ta buɗe ido. Da yake ƙeyarta ce ke kallon fuskar Jafar sai ta maƙe murya ta ce. "Kada ka motsa, idan ka yi yunƙurin guduwa sai na tsinke ƙafafuwanka." Jafar na jin haka sai kawai ya taƙarƙare ya rushe da kuka, ya fara biya duk wata addu'a da ke bakinsa. Sun ɗan jima a haka suka ji an fara kiran assalatu, Uwani ta fara wani gurnani tana wani bubbuga hannuwa sannan ta ce. "A yanzu za ka iya fita ka je ka yi sallah." Tun ba ta rufe baki ba Jafar ya buga tsalle ya fice a guje, yana fita ya ci karo da Daddy jikinsa na rawa ya furta. "Daddy wallahi gidan nan da aljanu Allah ba zan ƙara kwana a ciki ba." Ganin yadda jikin Jafar ke rawa ya sa Daddy ya riƙe shi gam a jikinsa, riƙe hannunsa ya yi suka fara tunkarar sashensu. Da sauri Jafar ya fara kiciniyar fisge hannunsa ya ce. "Daddy ina za mu shiga?" Daddy ya saki murmushi irin na manya ya ce. "Trust me son, ka san dai ba zan cutar da kai ba." Shiru Jafar ya yi suna tafe gabansa na faɗuwa har suka shiga, cikin shammata Uwani ba ta yi tsammani ba suka yi ido huɗu da Daddy. Cikin tashin hankali Uwani ta zaro ido, ta kai hannu ta dafe kanta. Na ce kin turo kuɗin littafinki kuwa? Yau promo ɗin zai ƙare💃🏻 faka-faka ki turo 400 Aisha Adam First bank shedar biya ta wannan lambar 07062062624 idan yau ta wuce za ki turo 500 maza hanzarta kada a yi babu ke🫠 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA BIYU Ganin yadda Uwani ta tsorata ya sa Daddy ɗan kawar da kansa, duk da a falo suka ci karo da ita za ta fito. A fili Uwani ta sauke ajiyar zuciya, ta sauke hannunta daga kanta don kaɗan ya rage asirinta bai tonu ba. Saboda ta ɗaura ɗan kwalinta a kanta kenan su Daddy suka shiga. "Barka da asuba Daddy." Uwani ta furta. "Barka dai Uwani me yake faruwa ne?" Daddy ya tambaye ta yana kallon yanayinta. Sai da ta saci kallon Jafar sannan ta ce. "Wallahi Daddy ban sani ba, ina cikin banɗaki na ji ihun Ya Jafar, fitowar da na yi kenan zan bi shi na ga abin da yake faruwa." Ganin yadda Uwani ta rattabo bayani kamar ba ta san abin da yake faruwa ba ya sa Daddy ya aminta da ita, don haka ya furta. "Ki ɗauko hijabinki ki taho sashen Maminku." Daga haka Daddy ya juya, Jafar ya yi saurin bin bayansa. "Ka sako kayanka mana Jafar." Daddy ya katse shi. Sai a lokacin Jafar ya lura daga shi sai singlet da gajeren wando. "Uwani miƙo mini kayana." Uwani ta wuce ɗakin tana ƙumshe dariyarta ganin yadda Jafar ya tsure lokaci ɗaya. Tana miƙa masa kayan ya yi sauri ya sa, yana cikin saka riga Uwani ta janyo hijabinta za ta fita da sauri Jafar ya fisgo hannunta ya ce. "Ina za ki tafi ki bar ni, ki jira ni mana na gama shiryawa. "A wannan karon sai da dariya ta ƙwacewa Uwani ta ce. "Wai don Allah a wurin training ba a fitar da masu tsoro da marasa tsoro ne a cikin aikinku ne?" Jafar ya wurga mata harara. Sai bayan da suka yi breakfast sannan Daddy ya kira Jafar, Uwani da Mami sannan ya fara magana. "Dalilin da ya sa na tara ku bisa wata matsala da ke faruwa daga jiya zuwa yau, a baya ban yi niyyar sanar da 'yan uwana ba amma yanzu..." "Daddyn yara babu fa buƙatar a tsaya ɓata lokaci, raba wannan auren shi ne mafi amfani a gare mu. Ina ji ina gani sheɗanu ba za su kashe mini ɗa ba, wannan yarinyar ba alkairi ba ce a wurinmu face annoba." Shiru Dadday ya yi yana sauraron Mami har ta gama. Sannan ya ɗora da cewa. "Ka buɗe kunenka da kyau ka saurari abin da zan sanar da kai Jafar." Daddy ya furta rai a ɓace. Jafar ya gyaɗa masa kai, Daddy ya ci gaba. "Ga Uwani nan ni da 'yan uwana da kuma mahaifiyarmu mun damƙa maka ita amana, wallahi ko bayan raina idan ka rabu da ita ban yafe maka ba." A hargitse Jafar ya ɗago, Mami na jin haka sai kawai ta rushe da kuka ta fice daga falon. "Dama Daddy cewa na yi zan koma Lagos, saboda gidan nan ba ni da nutsuwa da shi." Jafar ya yi magana yana satar kallon mahaifinsa. Daddy ya jinjina kai ya ce. "Hakan ma ya yi idan kana ganin ya fi a wurinka, amma ka sani a waɗannan kwanakin naka duk inda za ka saka ƙafa sai dai ka tafi da Uwani. Ba zai yiwu kwana biyu da yin aure ka tsallake yarinya ka bar ta a nan ba, sannan kuma wannan matsalar da ke faruwa zan nemar muku magani idan daga kai ne ko kuma daga ita ne." Wani malolon ɓacin rai ya tokare Jafar, ya haɗiyi yawu mai ɗaci ya furta. "Shi kenan Daddy." Daga haka Daddy ya sake yi musu nasiha sannan ya sallame su. Jafar na fita ya kira Amir a waya bayan sun gaisa yake ce masa ga shi nan zuwa, a lokacin da ya je Amir na zaune da Laptop a gabansa yana aikin tracking. Kamar mai ciwon haƙori haka Jafar ya yi sallama ciki-ciki ya zauna a bakin katifa. "Ango ka sha mai, kai ka ga yadda saman hancinka yake ƙyalli. Shegen kaya kana so kana kai wa kasuwa." Amir ya yi maganar yana dariyar shaƙiyanci. "Ba na son iskanci ni ba wannan ne ya kawo ni ba." Jafar ya furta rai a ɓace. Da ido Amir ya bi shi da kallo Jafar ya ci gaba da cewa. "Zuwa na yi ka ba ni aron ɗaki na kamar sati biyu." "Ni kuma na je ina? Ka san dai ai hutu muka dawo ko?" Jafar ya dage kai da hannuwa biyu cikin damuwa, Amir ya sanarwa yadda suka yi da Daddy sannan ya ɗora da cewa. "Allah Ya sani ba zan iya tafiya Lagos da Uwani ba, haba kawai sai na fara nuna ta na ce ga matata. Kuma ka san duk yadda zan ɓoye wa Safna na yi aure matuƙar na je da Uwani sai asirina ya tonu." Jafar ya sauke ajiyar zuciya ransa na ɗaci ya ci gaba da magana. "Ga Safna na shirin ɓallo mini ruwa ita ma." Nan ya kwashe hirar da suka yi da Safna, ya ɗora da cewa. "Abokina don Allah ka ba ni mafita komai ya cushe mini, al'amura duka sun kwaɓe mini." Shiru Amir ya yi yana nazari, da sauri ya ɗago ya ce. "Na samu mafita. Yanzu dai da farko ka ɗauki Uwani ka kama muku hotel, ba ka ce makaranta za a saka ta ba. Idan kuka cinye wannan hutun ka ga ai sai dai ka dinga zuwa ka na dawowa, ita kuma Safna idan har ba jagwal kake son haɗa wa kanka ba to ka yi mata dabara har zuwa nan da bayan kwana biyu, idan ya so kafin nan matsalar Uwani ta ragu sai ka ji da waccan matsalar." Jim Jafar ya yi jiki a sanyaye ya ce. "Sai kuma kawai na koma rayuwar hotel kamar wani ɗan iska." "Wa ya ce maka 'yan iska ne kaɗai ke rayuwar hotel? Masaukin baƙi ne fa. Kuma idan ma iskancin za ka yi ai matarka ka ɗauka ko?" Amir ya yi maganar cikin zolaya. Sun ɗan taɓa hira sannan Jafar ya yi masa sallama ya wuce gida. Daren wannan ranar a ɓangaren Mami suka kwana, Daddy ya sa aka buɗe musu ɗakin Dada suka shiga ciki. Fes yake babu ƙura a ciki, wannan karon Jafar bai kori Uwani daga kan gadon ba saboda a matuƙar tsorace yake. Kowannensu ya juya bayansa ya kwanta, bini-bini Uwani idan za ta gyara kwanciya sai ta ƙara tamke kai da ɗan kwali. Kimanin ƙarfe tara na safe Uwani da Jafar suka shirya kowannensa ɗauke da jaka, Uwani kayanta ta ɗiba ta saka a akwati kamar yadda ya gaya mata. Mami da ta je yi wa Jafar sallama sai jaddada masa take ya kula da kansa tamkar wani mace, shi maganar tata har kunya ma take ba shi. Daddy ne ya ɗauke su a mota ya nufi tashar sabon gari da su, Jafar yana gani bai faɗa masa cewar ya fasa zuwa Lagos ba don nauyi yake ji ya ce masa hotel zai kama musu. Sai da ya tabbatar da motar Daddy ta yi nisa da tasha ya dubi Uwani ya ce. "Sai ki ɗauko jakarki." Ba musu Uwani ta fara jan jaka har suka samu mai adaidaita sahu, Jafar ya ce masa ya kai su Light Hotel da ke Zoo road. "Ina kuma za mu?" Uwani ta watsa masa tambaya. "Sayar da ke zan yi. Wallahi idan muka je kika yi mini ƙauyanci sai jikinki ya faɗa miki." Uwani ta ja bakinta ta yi gum tana kalle-kallen titi. Har cikin harabar hotel ɗin ya shigar da su, nan Uwani ta saki baki tana kalle-kalle don wani lokacin sai Jafar ya yi gaba zai waiga ya ƙwalla mata kira, reception ya tsaya ya cike duk abin da ya dace. Aka ba shi key ya tasa Uwani a gaba da ta saki ba ki tana kallon wurin. "Don Allah ina ne nan ka kawo ni kamar Dubai da nake gani a TV?" Jin tambayar da Uwani ta yi masa ga kuma mutane na kallonsu ya sa ya ce. "Eh Dubai ce." Cikin lifter suka shiga Uwani ta ji wani irin zuuuuummmm A firgice ta ƙanƙame Jafar ta saki ihu, ƙirjinta sai bugawa yake. Sai da suka tsaya sannan Uwani ta ɗan ɗago da kanta amma har lokacin jikinta bai daina karkarwa ba. "Malama sake ni." Jafar ya faɗa yana yakice Uwani. Kamar sabuwar munafuka haka Uwani ta dinga raba idanu kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci a tsorace take. Buɗe ɗakin ya yi suka shiga, a gajiye ya zube a kujera Uwani ta tashi ta fara leƙa ɗakin. "Don Allah ina muka zo Ya Jafar?" "Light Hotel." Jafar ya amsa mata a taƙaice. A zabure Uwani ta miƙe tsaye jiki na rawa ta ce, "Wallahi ba zan kwana Otal ba salon haka kawai a dinga ce mini 'yar iska." Uwani ta dubi Jafar a yamutse ta ce. "Ya Jafar ina maka kallon mutumci ashe kai ma kana cikin sahun sababbin 'yan iska ashe ban sani ba..." Jafar ya bige wa Uwani baki, cikin jin zafi ta sa hannu ta dafe bakin ta furta. "Wallahi ban yafe ba..." Ba ta ƙarasa magana ya sake bige bakinta. Uwani ta zauna a gefen gado tana watsa masa harara. Wayarsa ya zaro ya fara dannawa, Uwani ta ci gaba da zama cikin gundura don ita tsarin wurin sam bai yi mata ba. "Ni fa yunwa nake ji." Uwani ta yi maganar, Jafar ya yi kamar bai ji ba. Sai da ta maimaita sau uku amma ko ƙurar ta bai kalla ba, ta tashi ta leƙa ta window a nan ta hango mutane na zirga-zirga a farfajiyar wurin. "Bawan Allah ka taimaka mini yunwa nake ji." Uwani ta ƙwalla wa wani mutum kira da ta gan shi ya wuce da take away a hannu. "Mai farar rigar nan don Allah ka taimaka mini..." Cikin zafin nama Jafar ya ƙarasa ya fisgo Uwani. Da ƙarfi ya wurga ta kan gado yana huci ya ce. "Ke wacce irin mahaukaciya ce ne? Wallahi kika nemi ki tara mini jama'a sai na zane miki jikinki." "Ba na gaya maka yunwa nake ji ba? Wallahi ka kiyayi hukuncin Ubangiji atoh, a kan mage ma wata ta shiga wutar jahannama, ka san ni ma ka kashe ni da yunwa duk gatanka babu mai hanaka shiga Hawiya." Jafar ya yi yunƙurin kai mata duka da sauri Uwani ta zille tana dariya, tana gani ya ɗauki waya ya kira ita dai ta ji yana turanci amma ba ta san abin da yake faɗa ba. Bayan awa ɗaya sai ji ta yi an ƙwanƙwaso musu ƙofa, Jafar ya karɓi abincin ya dire. Plate ɗinsa ya ɗauka bai tanka wa matai ba, ganin haka ya sa ita ma ta sauka ta ɗauka ta fara cin abinci. Bayan ta gama babu jimawa aka kira sallar Azahar, tana idarwa ta ɓingire a akan dadduma bacci ya yi gaba da ita. Tun da Jafar ya fita sallar Azahar bai dawo da wuri ba, kusan sallar La'asar Uwani ta farka shi ma sanyin AC ne ya dame ta. Banɗaki ta shiga yin alwala tana ta jinjina lamarin ƙayatuwar banɗakin da kuma nasu ɗakinsu, bayan ta idar da sallah atamfar jikinta ta sauya ta ɗauko wasu riga da wando baƙaƙe ta saka. Sai wata farar hula da ta ɗora a kanta, ta saka hijabinta ƙarami. Jin zaman ta yi ya gundure ta don haka ta buɗe ƙofar a hankali tana leƙe-leƙe. Sai a lokacin da lura da fasalin ɗakunan duk suna kallon juna sai dai kowacce ƙofa a datse take. Tafiya ta fara yi tana kalle-kalle ba ta yi aune ba sai ji ta yi garam ƙofar ɗakin ta datse, Uwani ba ta wani damu ba ta ci gaba da tafiya har ta fita wurin wata baranda ta hangi step ɗin bene. Takawa ta fara yi a hankali har ta sauka sai ganinta ta yi ta sauka can farfajiyar wurin da ta hango mutane na kai-kawo. A kan ɗaya daga cikin kujerun harabar wurin ta zauna, a gefe ɗaya kuma swimming fool ne tsirarun mutane sun zauna suna saka ƙafarsu a cikin. Abin ba ƙaramin birge Uwani ya yi ba, abu ɗaya ne ya takurata ganin yadda wani Alhaji da ke gefenta ya zuba mata idanu da sun haɗa ido sai ya sakar mata murmushi, ko ya kashe mata ido ɗaya. Kiransa ta ji an yi a waya ya ɗauka yana barin harabar wurin. Babu jimawa ita ma ta tashi ta nufi hanyar ƙafar benen da ta sauko, wata hanya ta bi wacce take ganin kamar hanyar ɗakinsu ce. Amma sai ta ga ta gagara gane ainihin ɗakinsu, wata ƙofa ta gani a buɗe. Ta ga yanayin wurin ya yi mata kama da ɗakinsu da sauri ta tura ƙofar, turus ta yi tana kallon mutumin. Mutumin ɗazu da ta ga an kira a waya ne, ya washe mata baki yana faɗin. "Ranki shi daɗe ke kaɗai ce?" Uwani ta yi saurin kawar da kai gefe don jibgegen mutumin daga shi sai gajeren wando, ya ɗora towel a kafaɗarsa da alama wanka zai shiga. "Eh ɗakina nake nema?" Kallon tsaf ya yi mata, nan take ya lura da Uwani farin shigar zuwa hotel ce. Ba ta yi aune ba ta ji ya janyo hannunta ciki ya datse ƙofar, ya fara shafa gemu ya ce. "Ranki shi daɗe ni fa dama tun ɗazu nake ɗago miki hannu ba ki fahimta ba ne." Uwani ta fisge hannunta da sauri ta ce. "Malam ni ba 'yar iska ba ce ka buɗe mini ƙofa." Alhajin mai tumbin kuɗi ya ajiye towel ɗin a gefen gado, ya sake tunkarar Uwani ya furta. "Yarinya kada ki cuci kanki, yayyafin kuɗi zan yi miki ko awa guda ba za ki yi ba za ki kama gabanki." Ya ƙarasa maganar yana sake riƙo hannun Uwani. Uwani ta fisge tana ja da baya, Alhaji mai tunbin kuɗi ya lashe baki yana faɗin. "Ni fa tun da na yi arba da ke yawuna ya tsinke, dama tunanina ɗaya na san yadda za a yi na yi arba da ke." Alhaji tumbin kuɗi na rufe baki Uwani ta sunkuyar da kai ƙasa tana ɗagowa sai ji ya yi ta fara ɓaɓɓaka dariya. Juya idanunta ta yi ta fara wani ƙobare hannuwa cikin wata irin murya ta fara magana. "A yau za ka mutu tun da har ka taɓo mana goɗiya 'yar sarkin mayun aljanu." Uwani ta fara tunkarar Alhaji tumbin kuɗi tana wani murɗe kai gefe. A can gefen gado ta hango belt ɗinsa sai ta buga wani uban tsalle ta suri belt ɗin, daidai wurin ƙarfen ta shammaci Alhaji ta zuba masa a baya. A zabure Alhaji ya ƙandare yana faɗin. "Wash! Bayana." Uwani ta dafa hannuwanta biyu a saman kanta, tana motsi da bakinta. Ganin haka ya sa Alhaji ya saki baki yana kallonta a tsorace. "Uwar ƙwaƙwido ki ɗauke gashin kaina a yanzu, saboda mummunan hukunci za mu zartar a yanzu. Ki mayar mini da kaina babu gashi irin na wannan tsinannan da yake gabana." Uwani na gama faɗin haka ta fisge hular kanta, nan take Alhaji tumbin kuɗi ya zaro ido cikin tashin hankali ganin kan Uwani babu gashi. Uwani ta fara wani gurnani tana tunkararsa, ganin haka ya sa Alhaji ya taƙarƙare ya zuba uban ihu yana faɗin. "Wayyo Allah maman Garzali ki taimaka mini za a hallaka ni." Uwani ta maƙe wuya tana zaro harshe ta ce. "Za mu kwashe wannan tumbin naka mu zuba maka duwatsu a ciki, domin kana cin amanar Maman Garzali matarka. Zan kuma fafe ƙoƙon ƙeyarka na dura maka ruwan tekun maliya a ciki." Da sauri Alhaji tumbin kuɗi ya dafe ƙeyarsa ya zuba a guje, hawaye haɗe da majina suka wanke masa fuska. "Matso ka hau saman silin ko ka hau kan fanka, idan ba haka ba zan sa a yi sama da kai ko a nutse ƙarƙashin ƙasa da kai." Jiki na karkarwa Alhaji ya hau saman gado ya fara tsalle zai hau saman silin, idan ya yi tsalle ɗaya sai ka ji ɗass! Uwani ta zuba masa duka da belt. A galabaice ya dubi Uwani ya ce, "Don Allah ku yi mini rai wallahi a yanzu jinina zai iya hawa, ko nawa kuke so zan ba ku amma ku ƙyale ni." Uwani ta yi wani farrr da idanu, sannan ta ce. "Mu ba matsiyata ba ne, ba ma buƙatar kuɗinka Dama mu yawo muke Otel-otel muna hukunta masu hali irin naku masu lalata 'ya'yan mutane." "Wallahi har abada na daina ba zan sake ba don Allah ku yi mini rai." Uwani ta wurƙila ƙafa tana kanne ido ɗaya ta ce, "Za mu ƙyale ka amma da sharaɗin sai ka cinye sabulun wankan da ke banɗakinka, ko kuma mu farke cikinka mu tura maka 'ya'yan aljanu bakwai..." Tun Uwani ba ta gama magana ba Alhaji ya faɗa banɗaki da gudu ya ɗauko ragowar sabulun wankansa ya tura baki, yana ci yana kuka haka ya cinye sabulun bakinsa sai kumfa yake. Uwani ta suri hularta a fakaici ta riƙe sannan ta sake ɓaɓɓaka wata irin dariya ta ce. "A zo a buɗewa Goɗiyar mayun aljanu ƙofa." Ba musu Alhaji tumbin kuɗi ya buɗe mata ƙofar, jikinsa banda karkarwa da gumi babu abin da yake yi. Sai da Uwani ta fita ta sauke ajiyar zuciya don ita kanta ilahirin jikinta karkarwa yake, duk abin da take yi ƙarfin hali ne don ta lura da ta nuna masa tsoronta a fili ba abin da zai hana bai ci galaba a kanta ba. Daga ɗaki mai kallon na Alhaji tumbin kuɗi ta ji wani mutum yana yi mata ɗan kira, a shekaru shi ma bai fi sa'an Alhajin ba. Yi ta yi kamar ba ta gan shi ba gabanta sai faɗuwa yake. Ta bayanta ta ji ya fara biyo ta yana faɗin. "Haba 'yan mata kada ki yi wasa da damarki, abin da abokina ya ba ki ni zan ninka miki shi." A tunanin mutumin tun da ya ga Uwani ta fito daga ɗakin abokinsa ita ma 'yar hannu ce. Ganin haka ya sa Uwani ta fara sauri mutumin na biye da ita har dai ta ga da gaske yake ta saka gudu, tana yunƙurin shan kwana sai ta ji ta yi karo mutum. Cikin tashin hankali ta furta. "Don Allah ku taimaka mini wallahi ɗan iska ne ya biyo ni." Mutumin da kawo kansa kenan ya furta. "Haba 'yan mata ni fa ko awa guda ba za ki yi mini ba, don Allah ki bari..." Maganarsa ta maƙale sakamakon arba da ya yi da Uwani riƙe da Jafar. "Kai yaro wannan fa ba kalar yara ba ce. Don 'yan shiloli kamar su sun wuce ajinku." Cikin ɓacin rai Jafar ya furta. "Amma dai Allah wadaran hali irin na lalatattun tsofaffi kamar ku." Jin muryar Jafar ya sa Uwani ta ɗago da sauri don ko kaɗan ba ta taɓa tsammanin shi ba ne, suna haɗa ido ta riƙe shi ƙam jikinta na rawa cikin kuka ta furta. "Ya Jafar." Sai kawai kuka ya sake cin ƙarfinta. Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 Free pages ɗinmu ya kusa ƙarewa🫠 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA HUƊU *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 A sanyaye Lado ya ɗebo agogo da links ɗin Salim ya dawo cikin gidan, sai dai yana shiga ga wutar harabar wajen ta ɗauke. Ga kuma ƙarar duka da ake yi wa Shukra tana ihu, zuwa can kuma sai ya ji an yi wurgi da bokiti an zuba cikin gida a guje. Gudun kada abin da ya same su, shi ma ya zo kansa ya sa Lado ya shige ɗakinsa ya danno ƙofa ya rufe don shi kansa bai manta abin da aka yi masa a tsakar dare ba. Da gudu Uwani ta bi bayan Shukra tana gurnani tana zabga mata igiyar a baya har Shukra ta fara kama ƙafar bene Uwani ba ta daina dukanta ba, tana hawa sai ga Shukra na rarrafe tana kuka saboda tashin hankali. Sai da ta ga Shukra ta shige sannan Uwani ta yi saurin ɗebe bokitan ta mayar da su wurin da suke, ta je ta ɗaga table ɗin ta mayar da ruwan jarkokin kai sannan ta koma ta kunna ƙwan fitilar harabar wurin ta wuce sashenta. A lokacin da ta shiga sashenta shiru babu motsin Jafar, ta zube a kan kujera kanta na matsanancin ciwo kamar zai tsage gida biyu. Uwar ɗakinta ta wuce don ta sauya kayan jikinta saboda rawar ɗarin da take yi, ɗrower kayanta ta buɗe tana shirin miƙa hannu ta yi ido biyu da Jafar tsugunne a cikin. Uwani ta basar kaman ba ta san abin da ya faru ba ta ce, "Kai kuma Ya Jafar mene ne haka?" Jafar ya fara wuri-wuri sannan ya ce. "Wai Uwani ke ce kika zama biyu ko ya aka yi?" Jafar ya wurga mata tambaya. "Wai me ka mayar da ni ne ya Jafar? Ni fa yanzu na gama yi wa saurayin Shukra wankin mota bayan na gama yi wa Mami wanki..." Cikin sauri ya katse ta. "Wankin me? Ke kika wanke wa Salim mota? To su waye na gani da bokiti a kansu suna ihu?" Uwani ta wara hannu ta ce. "Ni kam ban sani ba, ƙila dai mutanen gidan ne suke son buɗe maka ido." Jafar ya yi fakare yana nazari, abu ɗaya ne ya fi tsaye masa a rai wai Uwani ce ta wanke wa Salim mota. A fili ta ji ya furta, "Dole sai na ɗauki mataki a kanta." Uwani ta yi saurin tambayarsa. "Wace ce?" Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya furta. "Babu komai." Saboda tsabar gajiya Uwani na sauya kaya ta ɗauro alwalar Isha'i ta gabatar da sallah, a nan kan dadduma bacci ya yi awon gaba da ita. A yadda ya ga tana sauke numfashi sama-sama ba ƙaramin tausayi ta ba shi ba, ya ƙarasa ya cire mata hijabin ya ji jikinta ya ɗauki zafi zau! Cikin jakarsa ya duba ya ɗauko Paracetamol, ya jima yana tashinta sannan ta tashi ya ba ta magani. Duk yadda ya yi da ta tashi ta ci abinci ƙi ya yi, ya rabu da ita ya haye gado ya kwanta. Shukra da rarrafe ta ƙarasa falon Mami, babu ɗankwali ballantana mayafi ko takalmi, a razane Mami ta fara tambayar Shukra. "Ke Shukra lafiyarki kuwa?" "Mami ki ɓoye ni bokiti ne, wallahi bokiti ne ya danne mu ni da Salim." Da mamaki Mami ta ce, "Kamar ya bokiti ne Shukra? Shi bokiti mutum ne da zai iya motsi har ya danne ku. Wai ma ina ɗankwalinki?" Shukra fuska da ta gama jagulewa da makeup da hawaye ta zayyanewa Mami duk abin da ya faru, Cikin damuwa Mami ta ce. "Ni fa wallahi ina zargin yarinyar nan tana da Aljanu, mu dai tun da muka tare babu wani abin tashin hankali da muka taɓa gani. Amma tun ranar da yarinyar nan ta zo gidan nan masifar yau daban ta gobe daban, yanzu bala'in har ya kai kina hira ke da Salim ana razana ku? Gaskiya dole a san abin yi." Daga haka Mami ta shiga lallashin Shukra, da ƙyar a daren ranar Shukra ta yarda ta kwana a ɗakinsu. Da yake Daddy ba ya gari ya sa asubar fari Shukra ta koma ɗakin Mami bayan ta yi sallar asuba ta koma ta kwanta. Washgari Tun bayan sallar asuba Uwani da Jafar har sun koma bacci, suka ji bugun ƙofa. Jafar ne ya je ya buɗe da mamakin mai buga musu ƙofa da farar safiya. Karo ya kusa yi da Mami a ɗan duburburce ya ce. "Mami ke ce tun yanzu?" Mami ta ƙare masa kallo ta ce, "Eh ni ce, ina Uwani take?" Jafar ya ɗan sosa kai ya ce. "Tana ciki bacci take yi." "Ciki ina? Uwar ɗaki?" Jafar ya gyaɗa kai. Cikin sauri Mami ta ce, "To kai kuma a ina ka kwanta?" A ɗan kunyace Jafar ya ce, "Ni ma a ciki na kwanta..." "Laha'ilaha'illallahu Jafar tun ba a je ko ina ba?" Salatin Mami ya katse shi. A ɗan duburburce ya ce. "Am ai ita a ƙasa take kwana ni nake kwana a kan gado." A fili Mami ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi ta wuce cikin ɗakin. Yadda Jafar ya faɗa mata haka abin yake, bacci Uwani take sosai a ƙasa saboda gajiya. Mami ta ɗauki ruwan jarkar da ke kan mudubinta ta sheƙa mata, a zabure ta tashi tana waige Mami ta taɓe baki ta ce. "Ki zo ki wuce kitchen za ki taya Inna haɗa breakfast, kin saki baki kina bacci ai duk gidan nan babu bawanki da zai dafa miki ki dinga ci." Jafar kamar ya yi magana sai dai kuma ya yi shiru, tun da yake bai taɓa samun saɓanin da mahaifiyarsa da har za ta mare shi ba, don haka ya kawar da kai har Uwani da Mami suka fice daga ɗakin. Suna tafe Mami ban da masifa babu abin da take mata, kai tsaye kitchen suka wuce. A lokacin Inna har ta fara haɗa kayan breakfast, suna shiga Mami ta dubi Inna ta furta. "Inna daga yau Uwani za ta dinga zuwa tana ta ya ki haɗa kayan breakfast." Inna ta washe baki cikin jin daɗi ta ce. "Allah Ya taimaki Hajiya, ina matuƙar godiya. " Uwani da har lokacin bacci bai gama sakinta ba, ta fara murza ido. Ba ta yi aune ba sai jin ranƙwashin Mami ta yi a kanta ta furta. "Kin ga dai ta hanyar da na biyo da ke, wallahi kika kuskura kika bi ta ƙofar ciki daidai da rana ɗaya kika haɗa ni da Dadyn yara sai ranki ya yi mummunan ɓaci." Cikin damuwa Uwani ta amsa mata, Mami har za ta fita ta juyo ta ce. "Idan kuma kin gama ki same ni a falo." Mami na fita Uwani ta jingina kai da bango, lokaci ɗaya hawaye ya fara ziraro mata. "Yarinya a wannan lokacin kuka ba na ki ba ne, shi wannan aikin da kika ga Hajiya ta kawo ki mu dinga yi gata ne take yi miki. Saboda duk macen da ba ta iya girki ba wallahi ta faɗo a wurin miji, ki ci gaba da haƙuri watarana sai labari." Inna ta yi maganar ƙasa-ƙasa. Kukan da Uwani take yi ya yawaita jin kalaman Inna ya sa ta furta. "Wallahi ni kam na gaji Inna, gara na koma wurin Dada ni ban saba da wannan wahalar ba." Sai da Inna ta ɗan leƙa bakin ƙofa sannan ta sake ƙasa da murya ta ce. "Ita dama rayuwar aure ai takan zo wa bawa da al'amura mabanbanta. Ni na ɗauke ki tamkar jikata duk abin da yake damunki ki dinga samuna a fakaice kina gaya mini, amma kada ki bari kowa ya fahimci haka don gudun mu samu matsala ni da ke." Uwani ta ji daɗin yadda Inna ta amshe ta hannu bibbiyu, don haka ta share hawayenta ta fara taya ta duk abin da ya dace. A cikin aikin da suke yi ne Inna ta fahimci sam Uwani ba ta iya wani girki ba, hatta aikin ma wani abin sai ta koya mata. Sai kusan tara saura sannan suka kammala komai, don har wanke-wanke babu abin da ba su gama ba. Uwani ce ta bi Inna dianing tana ganin yadda take yin komai, lokaci ɗaya Uwani ta nemi duk ƙuncin da take ciki ta rasa. Suna gab da barin kitchen ɗin ne Mami ta dawo tana bin Uwani da harara, ta dubi Inna ta ce. "Idan kun ƙarasa aikin ki ɗebo mata gero kwano ɗaya ta surfa, ta niƙe mini shi yau furar daka nake sha'awa." A sanyaye Inna ta amsa, Mami ta wuce ta buɗe tukwanen wurin, ganin abincin da Inna ta rage kusan na mutum bibbiyu ne ya sa Mami ta furta. "An kai wa Lado abincinsa ne?" Da sauri Inna ta amsa. Mami ta sake haɗe fuska ta ce. "Wannan abincin ai ya yi miki yawa Inna zuba mini a wancan plate ɗin." "Dama ni da Uwani na rage mana..." Mami ta yi saurin katse Inna. "Uwani idan ta gama za mu rage mata abincinta a wurinmu." Inna babu yadda ta iya haka ta ɗauki plate ta zuzzuba kamar yadda Mami ta buƙata, kusan shekararsu Takwas tana yi wa Mami aiki ba ta taɓa ganin ta yi mata iyaka da abinci ba sai yau, a ranta ta jinjina ƙarfin ƙiyayyar da take yi wa Uwani. Uwani tana kuka haka ta karɓi geron ta nufi harabar gidan tana dakawa, tun ba a je ko ina ba hannunta ya fara kanta ga turmin dakan ba shi da girman kirki don a surfe ma sai da ta raba shi gida huɗu sannan ta gama dake shi. Tun Uwani na cikin inuwa har rana ta same ta don sha biyun rana a lokacin ta kusa, tana nan tana daka su Shukra suka fito cikin shirinsu gwanin birgewa. Auta ce ta ƙarasa wurinta da sauri ta ce. "Uwani me kike yi haka ne?" Uwani ta share hawayenta. Tausayin Uwani ya kama Auta, a sanyaye ta ce. "Ki yi haƙuri Uwani In shaa Allah Mami za ta gane abin da take ba ta kyautawa, unguwa za mu yanzu wallahi da na taya ki." Uwani ta gyaɗa mata kai sannan ta wuce wurin su Shukra da har sun fita bakin gate. Fitar su Shukra ba jimawa ita ma Inna ta zo ta yi wa Uwani sallamar za ta je kasuwar Garu, Mami ta aike ta yin cefane. Ita kanta Inna ta so taya Uwani sai dai tana tsoron kar ta je ta yi abin da za ta bar aikinta, don da kuɗin albashinta take samun na rufin asiri. Lokacin da Uwani ta gama ta gama galabaita, ga yunwa ga kuma gajiya. Can kitchen ta je ta ajiye wa Mami garin geron saboda ba ta san yadda za ta sarrafa shi ba, ta fito za ta shiga ta ƙofar falo ta hangi wani tafkeken jangwalagwada. Har a fili sai da Uwani ta saki murmushi, ta ɗauko tsumma a kitchen da sauri ta ƙarasa wurinsa ta yi A'uzubillahi sannan ta damƙe shi da hannunta, a wannan karon ta ci alwashin yadda Mami ta azabtar da ita to ita ma sai ta rama. Har ta gama tsara komai koda ta kwaɓe mata tana gamawa Kura za ta yi wurin Dada, kuma ko kashe ta za a yi ba za ta dawo gidan ba. Cikin sanɗa take tafiya har ta shiga falon babu motsin kowa daga can ɗakin Mami ta fara jiyo muryarta sama-sama da alama waya take yi. Ta matsa a hankali da niyyar ta buɗe ƙofar ta zura mata ƙadangaren ta ji Mami na faɗin. "Haba Hajiya Karima kin gan ni fa na tuɓe kaya yanzu haka wanka zan shiga, don Allah ku jira ni. Kin san yadda nake bala'in son haɗuwa da matar DC kuwa? Kin san fa duk in da harkar manya take ba ma sanya da ita." Uwani ta saki murmushi da ta tuna tsiyar da za ta ƙulla wa Mami. A kan kunnen ta Mami ta gama wayar ta faɗa banɗaki, sai da ta tabbatar da wankan Mami ya fara nisa sannan ta buɗe ƙofar ɗakin a hankali ta shiga. Ƙofar banɗakin ta nufa sai ta fara murɗa ƙofar da sauri-sauri, daga ciki Mami na saɓa sabulu a fuska ta ji ana murɗa ƙofar. Mamaki ne ya kamata don ta san su Shukra ba sa nan, kuma ko suna nan ba za su buɗe mata banɗaki tana ciki ba. "Waye a nan?"Mami ta tambaya a hassale. Uwani ta kausashe murya ta ce, "Sarki ne ya zo da kansa ba aike ba." Da mamaki Mami ta furta. "Sarki wane iri? Kai waye da har za ka tsallake ko ina ka shigo ɗakin matar aure, kuma har ka nemi buɗe ni a banɗaki." "Sarautar ce haka! Kuma na aure ki daga yau, tun da na samu sukunin mai gidanki ba ya nan. Dama tun ranar da aka yi maganar auren ɗanki Jafar ni ma na kai kuɗin aurenki, yanzu haka kuma na biyo ki ne domin na ɓarje amarci." Uwani ta ƙarasa maganar dariya na son ƙwace mata. A hargitse Mami ta ce. "Kai malam wai waye kai ne ma? Ba ka da hankali za ka ce ka na son matar aure?" Uwani ta sake kausashe murya ta ce. "Ni dai babban burina ki ba ni haɗin kai domin ni matashin saurayi ne dal, soyayya ce kawai ta sa na tsaya a kanki. Amma kada ki yi mamakin kasancewa ta wata halitar da ba irin taki ba." Uwani na gama faɗar haka ta buɗe ƙofar a hankali ta wurgar wa Mami Jangwalagwadan sannan ta janyo ƙofar da ƙarfi ta rufe, da yake da key a jikin ƙofar nan take Uwani ta murza key ɗin ta cire shi ta ajiye a gefen gadon Mami. Lokacin da Mami ta ji abu ya sauka a kafaɗarta da sauri ta hau kiciniyar wanke kumfar fuskarta. Hannunta ta kai ta shafo kafaɗarta bayan ta wanke fuskarta, wani irin ƙadabarbar ta ji take jikinta ya hau karkarwa. Ta yi ta maza ta yi wurgi da shi, sai a lokacin idonta ya sauka akan tafkeken ƙadangaren. Da yake shi ma ya galabaita nan take suka fara 'yar tsere da Mami a banɗaki, duk yadda Mami ta so buɗe ƙofar sai ta gagara. Cikin Kuka Mami ta ce. "Wayyo Allah Lado, Jafar kana ina ka kawo mini ɗauki." Uwani ta gimtse dariyarta, ta sake matsa wa jikin ƙofar ta ce. "A yanzu babu mai iya taimakonki domin amarci na zo ci. Kuma daga yanzu ni fa zan dinga rikiɗa har zuwa surar mutane ina kawo miki ziyara." Uwani na gama faɗar haka ta sulale ta fice daga ɗakin, cikin sauri ta zagaya ta wuce sashenta. Jafar ta gani ya yi ɗaiɗai a falo yana bacci, da alama kallo yake yi bacci ya yi awon gaba da shi don ga remote nan a gefensa. A hankali ta wuce cikin ɗakinta ta faɗa kan gado tana sauke ajiyar zuciya, ƙugin da cikinta ke yi ne ya sake ankarar da ita yunwar da ke cin ta. Kitchen ta faɗa ta fara duba tukwane, ta ci karo da guntuwar Indomie da Jafar ya ci ya rage. Tukunyar ta ɗauko ya zuba shayi ta koma falo ta zauna ta ci, sannan ta buɗe bokitin dubulan ɗin ta ta ɗebo alkaki da dubulan na gararta ta baje a ƙasa ta ci gaba da loda wa cikinta. Tana cikin ci suka ji bugun ƙofa kamar za a ɓalle ta. "Ranka ya daɗe! Ranka ya daɗe akwai abin da yake faruwa a sashen Hajiya." Jafar shi da Uwani kusan lokaci ɗaya suka miƙe a zabure, da sauri Jafar ya buɗe ƙofar ya ga Lado da Baba tsoho, a ɗimauce ya ce. "Lafiya Lado?" "Ranka ya daɗe bugun ƙofa nake ji a sashen hajiya kuma idan aka buga bayan wani lokaci sai na ji shiru, kuma sama-sama nake jiyo muryar Hajiya kamar tana kuka." Jafar tun bai gama jin kalaman Lado ba shi da Uwani suka zuba a guje suka yi sashe ta, ganin haka ya sa Lado da Baba tsoho suka rufa musu baya. Jafar na zuwa ɗakin Mami ya nufa, abin mamakin komai tsaf yake babu wata hayaniyar tashin hankali. Wani rin numfarfashi suka ji a cikin banɗaki, da sauri Jafar ya dinga buga ƙofar yana kiran sunanta. Bugun da Jafar yake yi ne ya sake farfaɗo da Mami daga suman da ta yi, wanda ta yi suma a cikin banɗakin babu adadi. "Jafar! Wayyo Jafar ka shigo ka taimaka mini, wallahi ƙadangare ne zai haike mini." Mami ta yi maganar a galabaice don saboda wahalar da ta sha ko motsin kirki ba ta yi. Da ƙarfi Jafar ya dinga buga ƙofar amma a ƙame take ƙyam ta ƙi buɗuwa, "Ranka shi daɗe wannan ba shi ne mabuɗin na?" Lado ya ɗago key ɗin da ke kan gadon Mami. Da sauri Jafar ya karɓa ya buɗe yana buɗewa ƙadangaren ya yo bakin ƙofar a guje, ganin haka ya sa daga Lado har Jafar suka ɗiba a guje. Sai da suka ga ya shige ƙarƙashin gado sannan suka fara leƙowa, Mami da rarrafe da jan ciki ta fara tahowa Baba tsoho ya tunkari ƙofar banɗakin da niyyar taimaka mata, yana leƙawa ya hangi Mami tumɓur da sauri ya juya da baya yana faɗin. "Kai a'uzubillahi wannan lamari da muni yake." Baba tsoho ya nufi bakin ƙofa su Jafar na ganin yadda ya dawo jiki a sanyaye Lado ya je zai shiga da sauri Baba tsoho ya girgiza kai ya furta. "Ummm-ummm ku dawo Lado abin babu kyawun gani." Lado na zuwa ya ci karo da Mami na jan ciki, Mami da take a yunwace da neman taimako ta fara jan ƙafar wandon Lado tana faɗin. "Ku fitar da ni daga gidan, idan ba haka ba za su kashe ni." Ganin yanayin da Mami take ciki ya sa Lado ya fisge a guje yana faɗin. "Subhanallahi wannan lamarin ya munana Baba tsoho me ya sa ba ka buɗan aiki ba? Haka kawai zan ƙone idanuna." Jafar ya nufi wurin banɗakin, kamar haɗin baki Lado da Baba tsoho suka yi wata uwar sufa suka dafe kafaɗun Jafar suna faɗin. "Wallahi al'amarin akwai muni Jafar kada ka shiga." A ƙufule Jafar ya fisge ya ce. "Ni da uwata ne za ku yi mini iyaka? Duk halin da take ciki ni ba zan guje ta." Jafar ya fisge da ƙarfi ya tunkari wurin da Mami take. Cikin hukunci Ubangiji gobe ne za mu kammala Free pages ɗinmu, idan kina buƙatar ci gaba za ki biya 500 ta wannan Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar ta wannan lambar 07062062624 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA UKU Jin yadda jikin Uwani yake karkarwa ya sa Jafar ya kwantar da ita a jikinsa ya sa hannu ya fara bubbuga bayanta, nan take idanunsa suka yi jawur saboda ɓacin rai. Ya dubi mutumin murya a dashe ya furta. "Ka san wa ka taɓa kuwa? Ka san wanne irin kuskure kake yunƙurin aikatawa. Wallahi sai na nuna maka bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Jafar ya ƙarasa maganar yana yunƙurin cire Uwani daga jikinsa, cikin kuka Uwani ta furta. "Tsoro nake ji Ya Jafar don Allah kada ka sake tafiya." Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya riƙe hannunta suka fara tafiya rai a ɓace, ganin haka ya sa Alhajin ya zuba a guje ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa. Ɗakinsu suka wuce sai da Jafar ya sa key ya buɗe suka shiga, ya kai ta kan kujera ya zaunar da ita sannan ya ce. "Ki jira ji yanzu zan dawo." Fuska da hawaye Uwani ta furta. "Ya Jafar kada ka tafi ya shigo mini." Sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya ɗan hura mata iska ya furta. "Ba abin da zai faru da ke yanzu zan dawo kin ji." A hankali Uwani ta gyaɗa masa kai sannan ya fice. Ɗakin Alhajin ya koma ya yi bugun duniya ya ƙi buɗewa, shi kuwa Alhaji tumbin kuɗi jin ana buga ƙofar ɗakin abokinsa da ƙarfi, ya sa ya ƙara wa tashi ƙofar key sannan ya wuce banɗaki a guje jiki na rawa ya ɓuya. Ganin ba shi da niyyar buɗewa ya sa Jafar ya zaro waya ya danna lambar DPO ɗin unguwar Zoo road, da yake abokinsa ne. Nan take ya sanar da shi abin da ya faru tsakanin Uwani da Alhajin. Sannan Jafar ya sauka ƙasa ya sanar da ma'aikatan reception abin da yake faruwa da kuma ɗakin da Alhajin yake ciki. Wata mata da ke gefe nan take ta furta. "Kai malam Allah Ya yi maka albarka. Wallahi ni ma jiya da dare na ɗan fita unguwa na dawo haka wani ya dinga mini ɗan kira, da na shiga ɗaki har buga mini ƙofa ya yi ƙila ma shi ne." Jafar ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Daga yau ai ba zai ƙara ba." "A toh ai wasu mutanen gani suke idan suka ga mutum ya kama hotel kowa ma ɗan iska ne, Allah Ya kyauta." Ba a ɗauki lokaci ba sai ga motar 'yan sanda ta ƙaraso, lokacin da suka je bakin ƙofar Alhaji sai da ƙyar ya buɗe musu ƙofa. Har ƙasa ya tsugunna yana ba wa Jafar haƙuri amma fir ya ƙi sauraronsa, yaran D.P.O bayan sun saka masa ankwa Jafar ya ce su wuce da shi zai zo daga baya. A wurin da ya bar Uwani a nan ya koma ya same ta, fuskarta ta kumbura saboda kuka. Tana ganinsa ta yi zumbur! Ta miƙe tsaye. Bai kula ta ba ya koma can gefen gado ya zauna ya dafe kansa, wani irin ɗaci yake ji a maƙoshinsa ya ɗago murya can ƙasa ya ce. "Ya aka yi mutumin nan ya biyo ki ke da na bar ki a ɗaki?" Zuciyar Uwani ɗaya ta fara masa jawabi. "Ni fa kasan ƙafata ba ta saba zaman wuri ɗaya ba, gajiya na yi da zama shi ne na fita can ƙasa na sha iska. Da na dawo sai na rasa ɗakin nan, bisa tsautsayi na faɗa ɗakin wani ɗan iska..." Uwani ta kwashe komai ta gaya masa amma ba ta gaya masa irin azabar da ta yi wa Alhaji tumbin kuɗi ba, ta dai ce masa Allah ne ya ƙwato ta bayan ta fito wannan Alhajin ya biyo ta. Tass! tass! Jafar ya sauke wa Uwani wasu tagwayen mari biyu a fuska, cikin ɓacin rai ya furta. "Uban waye ya ce ki fita? Ba ki da hankali za ki fita da waɗannan kayan?" Ganin yadda Jafar ya hargitse mata lokaci ya sa nan take jikinta ya fara karkarwa, ya rufe ta da faɗa tamkar zai rife ta da duka daga ƙarshe ya faɗa toilet ya bar ta a zaune. Bai jima ba ya fito har lokacin ransa a ɓace yake ya furta. "Ki shiga ki yi wanka za mu wuce gida yanzu." Zani uwani ta ɗauka ta faɗa ban ɗaki kafin ta fito har Jafar ya gama shiryawa, gefe da gefen fuskar Uwani har ya ɗan kumbura don har lokacin ba ta daina hawaye ba. Jafar na zaune a gefen gado ya hango Uwani ta fito don ita ta manta ko hula ma ba ta saka ba, a razane yake bin ta da kallo baki sake. Ganin irin kallon da Jafar yake bin ta da shi ya sa Uwata ta sha jinin jikinta, tana sake tunkaro shi Jafar ya zabura a guje ya nufi ƙofa yana faɗin. "Wayyo Allah! Jama'a ku taimaka mini sun biyo ni nan ma!" Da yake ya manta ya datse ƙofar haka ya yi ta murɗawa ta ƙi buɗuwa. Cikin rashin fahimta Uwani ta ɗan waiga ta ce. "Wai ya Jafar me yake faruwa ne?" Laƙwas Jafar ya yi ya zauna a ƙasa kamar mutum-mutumi yana kare mata kallon, tamkar ya ga sabuwar hallita. Uwani ta shiga goge kanta da towel ko a jikinta ta ce. "Malam ka fita zan shirya." Har lokacin Jafar mamakin Uwani yake, ya shiga tariyo abin da ya dinga faruwa a cikin dare. Uwani ta fahimci sarai in da Jafar ya dosa, ta fito da kayan da za ta saka ta sake furta. "Don Allah ka fita zan shirya." "Uwani ina gashinki?" Cikin halin ko in kula ta ce. "Dada ta aske mini tun rannan." Miƙewa ya yi ya tako gabanta sannan ya furta. "Wato iskanci ne ya sa kika dinga tsora ta ni ko? Wallahi za ki shiga hannuna da ni kike zancen." Take dariyar da Uwani ke gimtsewa ta suɓuce mata. Jafar ya saki wani malalacin murmushin mugunta yana ayyana irin azabar da zai yi mata cikin ruwan sanyi ba tare da Daddy ya gane ba. Daga haka Jafar ya fice daga ɗakin, Uwani ta saka kayanta sannan ta haɗa ragowar kayanta da ke warwatse ta saka a jaka. Ba su ɗauki lokaci ba suka shirya suka fito Jafar ya ƙarasa gaban ma'aikatan da ke reception ya biya duk abin da ya suka kashe, sannan ya yi musu sallama suka fita da yake akwai Manajan wurin da shi a ka kai Alhaji can police station. Domin a cewar Manajan Alhajin na ƙarƙashin kulawarsu dole ne su san halin da yake ciki. Lokacin da su Uwani suka ƙarasa gida mommy ta rako ƙawarta Hajiya Binta bakin gate, ganin su Uwani ya sa Mami ta yi turus tana faɗin. "Ya aka yi Jafar?" Jafar ya ɗan sosai, sannan ya gaida Hajiya Binta da ke bin sa da kallon tuhuma. "Ƙawata wai kar dai raɗe-raɗin da nake ji a kan auren Jafar haka ne?" Hajiya Binta ta tambaya tana satar kallon Uwani. Ras! Gaban Mami ya faɗi, ta ɗan basar tana ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce. "Haba Hajiya Binta kina ganin akwai yarinyar da Jafar zai aura a duniyar nan bayan Safna? Ai me aiki ce ya taho mini da ita daga Lagos, a bakin gada take kwana shi ne ta roƙe shi Allah-Annabi wai ta dinga yi masa aiki. Da ya sanar da ni na ce idan zai taho ya kawo mini ita, kin san ɗa na kowa ne ƙawata." Cikin gamsuwa Hajiya Binta ta bi Uwani da wulaƙantaccen kallo ta furta. "Ban da taɓarɓarewar zamani yanzu wannan yarinyar har ta isa kwanan gada, mtsww Allah Ya sawaƙe." Mami ta furta. "Amin dai, yo yaran da maza ke ba su ɗari biyar suna sa su a ɗaki ina za ki yi mamaki?" Kalaman Mami da ƙarshe da ta jefi Uwani da su ba ƙaramin zafi suka yi masa ba, don haka ko sallama bai yi wa Hajiya Binta ba ya wuce. Ita kanta Uwani kusan daskarewa ta yi a wurin jin irin munanan kalaman da Mami ta jefe ta da shi, tunanin da ta zurfafa ciki ne ya sa Jafar ya wuce ba tare da ta sani ba. A ɗan tsawace Mami ta ce. "Tsawar me kike yi a gabanmu ne?" Babu yadda ta iya haka Uwani ta ja jaka jiki a sanyaye ta wuce ciki, kai tsaye sashensu ta shiga idanunta cike da ƙwallah. Sanin Daddy ba ya gidan ya sa Mami kai tsaye ta wuce sashen su Jafar, a falo ta same su duka ta dubi Jafar ta ce. "Wai fasa tafiyar ka yi ne Jafar?" Bai ɗago ya kalle ya ba ya furta, "Eh Mami." Jim ta yi tana nazartarsa ta furta. "To haka za ka zauna ana tsorata ka har a sabauta mini kai?" Jafar ya furta. "Ai na biya ta Islama Islamic Center na karɓo magani, kuma ya ce mini za a dace In shaa Allah." Jafar shi kansa ya yi mamaki yadda ya tsara wa Mami wannan jawabin, Mami ta wurga wa Uwani mugun kallo ta ce. "Wuce mu je akwai aikin da za ki yi mini." Babu musu Uwani ta bi bayan Mami, Jafar ya kwanta a kan doguwar kujewa. Haka kawai ya ji yana kewar Safna, don haka ya zaro waya ya kira ta suka fara hira. Mami na shiga sashensu ta haɗo wa Uwani wanki duk da a lokacin magriba ta fara kawo kai, bayan gida ta zuba mata wankin ta yadda koda an yi a arashi Daddy ya dawo ba zai ganta ba ballanta ya yi mata faɗa. Kuma dama ta san ba ya gari, don haka za ta ci karenta babu babbaka akan Uwanin. Cikin wankin da Mami ta haɗo wa Uwani har da labulaye da zannuwan gado, tun Uwani na wankin cikin daɗin rai har ta fara galabaita tun da ko a wurin Dada ba ita take yin wankin kayanta ba. Lokacin da aka kira sallar magriba Uwani wucewa ta yi sashenta don ya gabatar da sallah, tafiyarta babu jimawa Mami ta zagaya ta ga wurin wayam. Sai tsirarin kayan da ta shanya ga waɗansu nan a cikin ruwa. Uwani na zaune tana zaman tahiya Jafar ya shiga ya zaune yana kallonta, a yadda ya lura da Uwani duk hatsabibanci da ƙiriniyarta ba ta wasa da sallah ko kaɗan. Hakan ba ƙaramin birge shi yake ba, yana nan zaune Mami ta shigo ko shi ba ta yi wa magana ba ta rufe Uwani da duka. Ganin dukan da take wa Uwani ba zai ƙare ba ya sa Jafar ya yi saurin shan gaban ta. "Lafiya kuwa Mami? Me ta yi miki haka?" Jafar ya furta hankali a tashe. "Lallai Jafar wannan abar har kake tarewa?" Mami ta faɗa tana sauke numfashi. Ban da kuka babu abin da Uwani take yi, ga gefen bakinta ya fashe jini na ɗiga. Saboda yadda ta galabaita kukan da take yi ko fita ba ya yi, Mami ta sake zuba mata ranƙwashi a ka tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Mami wai me ta yi miki?" "Wanki na saka ta don iskanci za ta zube mini ta zo ta saka miji a gaba, idan uwarki ce ta saka ki za ki ajiye mata." Mami ta yi maganar tana dungurin Uwani, cikin kuka Uwani ta ce. "Sallah aka kira shi ne na zo na yi..." Da sauri Mami ta sake doke Uwani nan take bakinta ya sake fashewa. "Haba Mami, ina ce Haladu ne yake yin wanki. Kuma sallah fa ta ce ta zo..." Tas! Mami ta ɗauke Jafar da mari, ba ta tanka masa ba ta figi hijabin Uwani ta fara janta a ƙasa, ba shiri Uwani ta miƙe ta bi Mami. Saboda ɓacin rai tun ba su gama fita ba Jafar ya gegare su ya fice daga gidan zuciyarsa na suya. "Iyeee Allah Jafar watsa mini ƙasa za ka yi a ido yaushe har ka san zafin mace. Wallahi dole kai ma na ɗauki mataki a kanka." Mami ta yi maganar a ɗan tsorace don ta yi tsammanin ko wuta za ta jefa Uwani sai dai Jafar ya taya ta ba dai ya hana ba. A cikin duhu ga sauro haka Uwani ta wanke ragowar kayan da ba ta ƙarasa ba, kanta ban da ciwo babu abin da yake yi. Bayan ta gama ne ta nufi sashen Mami har ƙasa ta zube ta furta. "Na gama wankin." A yamutse Mami ta dube ta tana shirin sallamarta Shukra ta shiga ɗakin tana taunar cingam ta ce. "Ke zan saka ki aiki yanzu saura ki yi mini hauka." Uwani ta ɗaga kai a galabaice ta amsa wa Shukra. Auta da ke zaune a gefe duk sai ta ji babu daɗi, tana son ta yi magana amma tana tsoron faɗan Mami. "Kina ji Shukra na yi miki magana ba za ki iya amsawa ba?" Mami ta yi maganar tana haurin Uwani. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta rarrafa gaban Shukra ta tsugunna. "Ga Salim nan ya faka motarsa a cikin gate, za ki je ki wanke masa kuma wallahi idan ba ta wanku ba sai kin sake." Da sauri Auta ta furta. "Aunty Shukra wankin mota fa?" Shukra ta sake shan kunu ta ce, "Waya na yi da shi zai kai wankin mota ya ce ba zai samu zuwa yau ba, so don haka na ce ya zo gida za a wanke masa saboda ina son magana da shi." Cikin tausaya Auta ta ce, "To shi kenan zan ta ya ki Uwani..." "Waye ya gayyace ki? Uwar iyayi da kankanba?" Mami ta katse Auta. Shukra ce ta yi gaba Uwani ta bi bayanta a lokacin zazzaɓi har ya fara rufe ta, lokacin da suka ƙarasa Salim na cikin mota. Da ya hango su ne ya fito yana sakarwa Shukra murmushi. "You are welcome dear." Shukra ta furta tana fari da ido. "Beb an ya zan iya jiran sati ukun nan masu zuwa kuwa? Kin ga yadda kika yi kyau." Salim ya furta cikin shauƙin soyayya, Shukra ba ƙaramin daɗi ta ji ba kin kissa ta ce. "Well mu je mu zauna, ga 'yar aikin Mami za ta wanke maka mota." "Za ta iya kuwa Baby? Na ga mata ba sa wankin mota." Salim ya faɗa yana bin Uwani da ke rakaɓe a gefe. Shukra ta dubi Uwani a tsawace ta ce. "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Jikin Uwani na rawa ta tsugunna ta gaishe da Salim, sannan Shukra ta ɗan yi murmushi ta furta. "Ai in gaya maka daga motar Daddy har ta ya Jafar ita take wankewa za ka sha mamaki." Shukra da Salim suka wuce wurin wasu fararen kujeru, daga wurin da suke zauna suna iya hango Uwani da duk abin da take yi. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta ɗauki bokiti ta fara ɗebo ruwa, da yake wurin ɗiban ruwan yana da ɗan nisa da wurin wankin motar a galabaice ta fara wankin motar har ta gama. Gaban Shukra Uwani ta je ta tsaya ta ce, "Na gama wankewa." Shukra ta bi ta da harara sannan ta ce. "Matso nan." Ba musu Uwani ta matsa gaban Shukra, da ƙarfin tsiya ta fisgo Uwani har sai da ta bugu da ɗan ƙaramin table ɗin da ke gabansu ta ce. "Don ubanki ke ba ki da ladabi ba za ki iya tsugunnawa ba?" Shukra ta ƙarasa maganar tana zuba wa Uwani ranƙwashi. "Haba Beb da kin ƙyale ta kin san irin yaran nan ba wani tarbiyya suke samu ba, so don sun yi haka ni ba zan yi mamaki ba." Salim ya faɗa a ɗan ƙyamace yana duban Uwani da ta gama jiƙe wa da ruwa sharkaf. "Dallah tashi ki ba ni wuri kina tafe da baƙi kamar na zunubi." Dariya sosai Salim ya yi jin abin da Shukra ta faɗa ya furta. "Wai yaushe kika koyi masifa ne love?" "Haba ka rabu da ni na tsani yarinyar nan wallahi." Uwani na laɓe a ta bayan fulawiyin da ke zagaye da harabar gidan, takaici ya mamaye zuciyarta. Wani tunani ne ya faɗo mata don haka da sauri ta zagaya can bayan gidan, ta ɗebo irin manyan bokitan fentin nan guda biyu waɗanda ta gama wanki da su. Sai da ta yagi wata igiya ta haɗa hannuwansu ta ɗaure, sannan ta saki murmushin mugunta. Cikin sanɗa ta fara tafiya ta cikin fulawoyi, a daidai bayan su Shukra ta tsaya ta ji Salim yana faɗin. "Haba ke dai Baby ba kya mantuwa, wannan fa mahaukacin ma shammatata kawai ya yi amma yadda nake ƙaunarki akwai abin da zan ga zai cutar da ke na gudu ban taimaki rayuwata ba, ke ce fa rayuwata ke ni fa idan za ki rayu da farinciki zan iya sadaukar da komai ciki kuwa har da numfashin da nake zuƙa." Shukra ta rangwaɗa kai cikin farinciki, tana shirin ba shi amsa Uwani ta saki murmushi duk da zazzaɓin da ke jikinta. Sai da ta daidaita saitin kansu sannan ta ɗaga bokitan fentin hannunta, ta kifa musu a kansu ta saka iya ƙarfinta ta danne saman ta yadda ba za su iya fisgewa ba. Salim da abin ya haɗe masa biyu ga zafin hula ga na bokiti ya ware murya cikin ihu ya ce. "Wayyo Allah wuyana!" "Wayyo kaina, Baby kana ina!" Shukra ta faɗa a ɗimauce. Daga Salim har ita sai ɗaga hannuwa suke cikin neman taimako. Sai da Uwani ta ga sun fara galabaita sannan ta fisgo hannun bokitin ta baya, da yake ƙafafuwansu na ƙasan table ɗin da ke gabansu faɗuwar da za su yi ta baya sai suka taho da table ɗin da ƙafafuwansu. Uwani na ganin za su kai ƙasa ta yi saurin matsawa a guje, sai ji kake rugugum! kacacar kofuna da ruwan jarkar duka sun watso kansu. Ga bokiti ya sarƙafe su ga kuma ƙafafuwasu sarƙafe a cikin table, Uwani ta laɓe a cikin shukoki tana dariya ƙasa-ƙasa don duk ƙwaƙwar mutum ba zai gano da mutum ɓoye a wurin ba. Da ƙyar Salim ya samu ya zaro ƙafarsa daga cikin Table, ya tashi zai zuba a guje Uwani da ke laɓe ta sake fisgo shi da yake igiyar tana hannunta. Daɓar Salim ya koma ya faɗi hankali a tashe ya ce. "Jama'a a taimaka mana wallahi jana ake yi." Shukra ce ta yunƙura ta tashi a guje saboda tashin hankali ko yunƙurin cire bokitin ba ta yi ba, ita da Salim suka zuba a guje a daidai lokacin Jafar ya shigo harabar gidan. Turus ya yi ya ɗan fara ja da baya ganin ƙafafuwan mace da namiji suna tafe da bokiti a kai, da yake ba sa ganin gabansu yana ganin sun tunkaro shi ya zube takalmansa shi ma ya shige a guje yana ihun. "Wayyo Allah! Lado kana ina?" Jin ihun Jafar ya sake ruɗa su Salim, a wannan lokacin Lado ya zagayo da buta a hannu shi ma turus ya yi yana kallon ikon Allah. Da ƙyar Salim ya samu ya cire bokitin kansa, hular ta faɗi can gefe. Dama takalminsa na cikin ƙasan table ya jima da fita, iya ƙarfinsa ya tattara ya fita a guje yana faɗin, "Jama'a ku duba mini kaina idan yana gangar jikina." Sai a lokacin Lado ya gane shi, ya bi bayansa yana faɗin. "Alhaji ka bar motarka." Lado na ƙarasawa bakin gate ko ƙurar Salim bai gani ba sai agogonsa da links ɗin hannun rigarsa da suka zube a wurin. Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki turo ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank sai shaidar biya ta wannan lambar 07062062624 idan littafi ya kammala za ki turo 800 Free pgs ɗinmu ya kusa ƙarewa🫠 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 [30/06, 19:35] Ameerah Adam🌚: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye. SHAFI NA SHA BIYAR *BOJUWA HERBAL'S & SCENTS* *Suna kawo Saiwowin da suke dagargaza sanyin mara da na jijiya.* *Haka nan suna kawo Saiwowi daban daban daga Chad da Sudan, kuma marasa illah* *Saiwowin tsumi* *Saiwowin dahuwar kaza/tattabaru* *Saiwowin matsi gangariya* *Original gadalin mata* *Ƴaƴan gadali na asali* *Original gumba* *Tsumin Saiwowi* *Tsumin kwakwa da Dabino* *Igiyar alkairi* *Zumar goran tula* *Hakkin daka na musamman na asali* *Bayan haka suna dafa kazar amare da masu jego da ma uwayen gida*. *Akwai bridal package* *Mai jego package* *Ƴar gata package*. *Dukkan kayan kuma available ne for pickup or immediate delivery.* *A Kano nake amma kuma nationwide delivery ne* *Ku tuntubi Surayya Halin yau a wannan lambar dan samun naku cikin musulmin farashi* *08032773332* *Iyah Basiru na gaisuwa*😅 Jafar na shiga da ya ga a halin da Mami take ciki turus ya yi, da sauri ya juya cikin damuwa ya dubi Uwani ya ce. "Maza ki shirya ta za mu wuce asibiti." Uwani da ke gimtse dariyarta ta wuce sumi-sumi kamar sabuwar munafuka ta ƙarasa wurin Mami da ke sharɓe a ƙasa. Baba tsoho shi da Lado dama tuni suka fito harabar gidan, suna nan tsaye Jafar ya fito abin duniya ya dame shi. "Kai Jafaru, wai ya aka yi ƙadangare ya shiga har banɗakin mahaifiyarka? Ko dai ture aka yi mata?" Jiki a sanyaye Jafar ya ce, "Wallahi Baba tsoho ban da masaniya, ka na gani dai kune kuka kira ni ina ɗaki." Daga haka gabaɗaya suka yi jigum-jigum. Abin ka da mai ƙiba Uwani da ta ɗago Mami sai dai ka ji ta sake komawa sharaf, kuma har lokacin idanun Mami a rufe suke. Da ƙyar Uwani ta samu ta ja Mami a ƙasa kamar rago, ta ƙarasa da ita bakin gado tana zaunar da ita a kai ta sake tafiya sharaf, kayan da ta gani a gefe wanda Mami ta ɗauko za ta sa su ta fara dubawa. Rigar maman Mami ta ɗauko ai kuwa Uwani tana ɗaga wa ta faɗi a wurin tana ƙyaƙyata dariya saboda girmanta, sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe ta fara kiciniyar saka wa Mami. Da ƙyar Uwani ta samu ta shirya Mami sannan ta leƙa waje ta kira Jafar, yana zuwa nan take ya kama Mami ita ma Uwani ta kama ta suka fita ita. A kujerar baya suka saka Mami, Jafar ya kunna motarsa suka wuce asibiti. Suna zuwa asibiti da sauri aka karɓi Mami aka shiga da ita, aka fara ba ta agajin gaggawa. Sai da Jafar ya ga Mami ta samu bacci sannan ya samu sukunin kiran Daddy ya sanar da shi halin da ake ciki, a nan take yake sanar da shi yana hanyarsa ta dawowa. Lokacin da Mami ta farka gabaɗaya iyalanta na wurin, Daddy ne ya matsa gaban gadon ya fara yi mata sannu. Da wani irin kallo take bin sa ta yunƙura ta cukumo wuyan rigarsa a zabure tana faɗin. "Wallahi ba zan aure ka ba, ni ina da aure har da 'ya'yana!" Da sauri Daddy ya riƙo ta, Mami ta ɗago kai tana ƙare masa kallo sai gani suka yi Mami ta sake tafiya luuuu a sume. Har rige-rigen fita kiran Likita suke yi, babu jimawa Dr Nura ya shiga cikin shigarsa ta likitoci. Sai da ya gama jin bayaninsu sannan ya ce gabaɗaya su fita, don yana son ba ta kulawa babu buƙatar hayaniya. Daddy ya so zama don ciwon na Mami ba ƙaramin tsoro ya ba shi ba amma Dr ya ce ya fita. Wata allura ya yi wa Mami ba ta fi minti ɗaya ba ta sake farfaɗowa, tana daga kwance ta ga Dr Nura tsaye a kanta cikin fararen kaya ga farin gilas maƙale a idonsa. "Wato wannan karon rikiɗe mini ka yi zuwa wannan surar kenan? Wannan fa idan ba da gaske na yi na ƙwaci kaina ba sai ya illata ni ya cuci iyalina." Duk waɗannan maganganun Mami na yin su a cikin zuciyarta ne, ta dai kafe Dr Nura da kallo ko ƙiftawa ba ta yi. Ta fara motsa baki a hankali tana biya Ayatulkursiyyu. "Sannu Hajiya! Yanzu yaya kike jin jikin na ki?" Dr Nura ya tambaye ta yana gyara tsayuwarsa. A hankali ta yunƙura ta tashi zaune tana ɗan dafe kanta, cikin shammata Mami ta suri dogon ƙarfen nan da ake maƙala ledar ƙarin ruwa a jiki ta shiga zungura masa tana kwaɗa masa. Idan Mami ta karanta Ayatulkursiyyu ta tofa masa sai ta ɗaga ƙarfen ta ba shi ƙwal. Hankali a tashe Dr Nura ya shige can kusurwar ɗakin yana faɗin. "Help! Help! Help!" Mami ta sake zungura masa ƙarfen tana faɗin. "Wato don ubanka har surar Nasara kake rikiɗewa ai wallahi yau ko ni ko kai." Dr Nura ganin neman agajin da yake yi da harshen turanci ba zai kai shi ba, ya sa ya taƙarƙare cikin ihun tashin hankali ya ce. "Wayyo Allah! Jama'a Patient ɗin nan za ta halaka ni." Su Daddy na daga waje suka jiyo ihun Dr Nura, da gudu suka taho za su buɗe ƙofar, sai dai da yake Mami na jingine da ƙofar tana jin alamun za a buɗe ta sake danna ƙofar da ƙarfi tana zungurin Dr. Ganin Mami na niyyar illata shi ya sa ya faɗa ƙarƙashin gadon asibitin, da ƙyar su Daddy suka turo ƙofar suna ganin ta da ƙarfen suka shiga kallon-kallo suma suna ja da baya. Daddy ne ya murɗe hannun Mami ya karɓe ƙarfen ya ajiye, sororo ta yi ta fara kallonsu ɗaya bayan ɗaya sannan ta ce. "Daddyn yara da gaske kune? Ina ne nan?" Kafin Daddy ya ba ta amsa tuni Dr Nura ya yi wata irin sufa irin ta jaruman indiya ya fice daga ɗakin, glass da takalmansa kusan lokaci ɗaya suka yi tsalle sama suka zube a tsakar ɗakin sai dai hakan bai sa ya tsaya ko waige ba ballana ya ɗebi abin sa. Kan gado Daddy ya zaunar da ita yana yi mata sannu, sai ji suka yi ta fashe da kuka tana faɗin. "Daddyn yara ni dai daga nan ka wuce Kura da ni, har abada ba zan sake kwana a gidan can ba." Kamar ƙaramar yarinya Daddy ya shiga lallashinta sai da ta yi shiru sannan ya tambaye ta ainihin abin da ya faru. Tiryan-tiryan Mami ta sanar da shi abin da ta ji da kuma shigowar ƙadangaren, don ita ko shigar su Jafar ba ta sani ba saboda ta yi suma ya fi bakwai a cikin banɗakin. A yanzu shi kansa Daddy ya fara yarda da cewar gidan ba su kaɗai ba ne, saboda ya sake kwantar mata da hankali ya ce ya amince za su koma can da zama. Uwani na rakuɓe a gefe ta yi zuru tana ƙarewa fuskar Mami kallo, tana mamakin yadda Mami ta zabge ta zuƙe a wuni guda, suna haɗa ido ta doko mata harara ba shiri Uwani ta janye idonta gefe. Daddy da kansa ya koma kiran likitan da zai sake duba Mami duk da ya lura ciwon ba na asibiti ba ne, da ƙyar ya samu Dr Samira ta je ta duba Mami ta saka mata ƙarin ruwa da allurai bayan wani lokaci aka sallame ta. Su Shukra ko kaɗan ba su so komawa Kura ba don dai babu yadda suka iya ne, ita kuwa Uwani murna fal ciki. Daddy ne ya kwashe su suka ɗebo kayan sakawarsu. Mami kuwa fir ta ƙi yarda ta shiga gidan sai a mota suka bar ta. Su Shukra sun ɗauki hanyar Kura babu jimawa Salim ya kira ta a kan zai je ya ɗauki motarsa, bai dai gaya mata ba amma a cikin ransa ya ƙissima ba zai sake zuwa gidansu ba har zuwa lokacin da za a ɗaura musu aure. Adaidaita sahu ne ya sauke shi a ƙofar gidan Daddy, gaban Salim ne ya fara faɗuwa a hankali ya yi ta maza ya ƙarasa jikin gate ɗin ya fara ƙwanƙwasawa. Daga cikin gidan Lado ya furta. "Waye nan?" "Lado ni ne." Zuro kai Lado ya yi yana ganin Salim ya washe baki ya ce, "Allah Ya taimake ka, yau kaine da rana tsaka." Salim ya miƙa masa mukullin motarsa ya ce. "Shiga ka tuƙo motata ka fito mini da ita." Sororo Lado ya yi ya furta. "Ranka ya daɗe ni da ko mashin ban iya tuƙawa ba, ina ni ina tuƙa mota?" "Lado amma gidan nan ba ku kaɗai ba ne a ciki, ka na gani dai rannan aka so tafiya da mu a bokiti ban da ƙarfin addu'armu da ta iyaye da tuni wani zancen ake ba wannan ba." Lado ya yi jim sannan ya ce. "Ranka shi daɗe naka ai mai sauƙi ne." To yau dai in faɗa maka tik da ka sani haka ƙadangare ya tarfa Hajiya tumɓur tana wanka. Kai yanzu haka ma suna can hanyar Kura don gabaɗaya Hajiya ta rikice, ban da sha'anin iska ina ka taɓa jin ƙadangare ya auri mutum? Wai ƙadangare ne fa yake ce mata amarci zai sha da ita, ina ka taɓa ganin ƙadangare na magana?To Kai kuwa ma a shekarun Hajiya ban da neman cika wa da imani me take nema a wurin namiji ballantana ƙadangare? To ɗazun nan sun zo ɗiban kaya za su wuce Kura Uwani ta kwashe komai ta faɗa mini." Take cikin Salim ya sake kaɗawa, ganin ya ɗan fara ja da baya Lado ya ce. "Ni ma fa Baffa nake jira ya zo a yi wacce za a yi, idan har ƙadangare zai auri Hajiya ni waye da ƙangaruwa ba za ta aure ni ba. Haka kawai ina zaune ta murƙushe ni cikin dare babu mai ceton rai." Salim ya zaro ido ciki a tsure ya ci gaba da ja baya. Lado ganin haka ya sa ya ce. "Ranka shi daɗe ina za ka je ne? Ka shigo ka ɗauki motarka mana." Salim ya zabura a razane ya furta. "Allah Ya tsare ni wallahi, zan aiko a ɗaukar mini ita daga baya don ita kanta motar kafin na fara hawa sai an yi mata sauka biyar." Daga haka Salim ya juya ko sallama bai yi wa Lado ba yana zuba sauri. Da zuwan su Mami Kura ba a ɗauki lokaci ba, labarin abin da ya faru da ita ya watsu cikin gidan gabaɗaya. Facalolinta sai zuwa suke duba ta, wanda yawanci zuwan da suke yi da biyu suke yi. Domin masu yi mata dariya a bayan fage sun fi yawa saboda irin habaicin da ta dinga yi musu a lokacin da za su tare. Sai daga baya Dada ta shiga a lokacin yawancin mutane sun watse daga Daddy sai su Jafar, Uwani kuwa dama tun da ta shiga gidan ta yi sashen Dada daga nan ta wuce wurin turken awakinta. Sannu a hankali jikin Mami yake ƙara samun sauƙi, ganin yadda Mami ta yi laushi ya sa Uwani ta yi tsammanin ko Mami sauya halinta ne. A haka sai da suka shafe kusan kwana goma a cikin gidan, kuma a wannan kwanakin kullin sai Daddy ya sa an yi saukar karatun Alƙur'ani. Wannan saken da Uwani ta samu ya sa hankalinta ya kwanta, ta manta da matsalar Mami gabaɗaya. Don tun da suka koma Kura sau biyu ta shiga duba Mami, kuma ba wata kyakkyawar fuska take samu ba. Su Mami ba su suka koma gidansu ba sai bai fi saura sati guda bikin Shukra ba, da ƙyar Mami ta yarda ta koma kuma kafin ta koma sai da suka yi musayar ɗaki da Daddy, ita ta koma ɗakin Daddy shi ya koma ɗakinta. A kwalemar fitar da kayan ne aka fitar da Jangwalagwadan da ya shiga ɗakinta, don shi kansa ya galabaita. A lokacin da za su tafi ne Uwani ta saka kuka don cewa ta yi fir ba za ta koma ba, sai da Dada ta lallaɓa ita da Daddy ta amince amma sai cewa ta yi sai dai idan da awakinta za ta koma. Ba musu Daddy ya amince ya ce zai yanki wani wuri a cikin farfajiyar gidan a yi wa awakinta wuri, amma sai bayan bikin su Shukra. Cikin farinciki Uwani ta bi Jafar suka wuce duk da shi ma ba wata fuska take samu a wurinsa ba, amma ba ya zagin ta ko cin zarafin ta. Shirye-shirye sun fara kankama a wurin su Mami da wurin iyayen Salim, da yake Mami na zirga-zirga sai tsangwama da takurar da take yi wa Uwani ta yi sauƙi. Haka kuma Uwani ta fara gogewa da aikin da suke yi da Inna, don wani lokacin ma idan Inna ta gaya mata yadda za ta sarrafa abu ita take yi. Tun ana gobe kamun bikin Shukra hankalin Mami yake a tashe sakamakon wayar da suka yi da mahaifiyar Safna, a kan cewar za su zo ranar Juma'a da safe su tafi ranar Lahadi bayan ɗaurin aure. Sakamakon biyo jirgin da za su yi daga Lagos zuwa Kano. Tun da suka gama wayar gumi yake keto wa Mami. Ganin ta rasa mafita ya sa ta kira Shukra ɗaki. "Shukra ina tsoron asirinmu ya tonu, ina gudun duk plan ɗin da na shirya ya wargatse. Kin san dai matuƙar Safna da mahaifiyarta suka zo gidan ko yaya ne za su iya fuskantar Jafar na da aure, alhalin ni kuma ban sanar da kowa ba bayan Hajiya Falmata." Shiru Shukra ta yi sannan ta ce. "Hanya ɗaya ce, mu nemo abin da zai sa Yaya ya sake ta kawai." "Ta wace hanya kenan?" Shukra ta zuba tagumi tana nazari, da sauri ta dafa Mami ta ce. "Na samo mafita, kin san me za a yi Mami?" Mami ta girgiza kai da sauri. "Sata kawai za mu laƙa mata, ba kin ce Daddy ya ba ki ajiyar wasu kuɗi masu yawa ba? To da su za mu yi amfani." Shukra ta yi ƙasa da murya tana tsara wa Mami yadda za su yi, lokaci ɗaya suka saki dariyar samun mafita. Suna gama tattaunawa Mami ta ɗebo damin kuɗin ta damƙa wa Shukra, Shukra ta ɓoye su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da ƙawarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan ɗin su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau ɗaya Shukra ta taɓa shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu. Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta rangaɗa daga cikin ɗaki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo ɓangarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta ɗan saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma ƙawata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana ɗaya da har Shukra ta sakar mata fuska, a sanyaye ta amsa mata sannan ta wuce kiran da aka ce Mami tana yi mata. Uwani na fita Shukra ta faɗa ɗakin Uwani bayan da Fatima ta fita yin alwala, ta janyo drowar madubin ta saka kuɗin a ciki ta mayar ta rufe. Ba su wani jima sosai ba suka fice daga ɗakin bayan Fatima ta idar da Sallah, a ɓangaren Shukra dama kuma buƙatar maje Hajji Sallah tun da buƙatarta ta biya ba ta ga amfanin zaman nasu ba. Uwani na zuwa ta samu Mami a falo ta tsugunna har ƙasa, a lokacin Mami zaune take da matan Baba Mustafa sai ƙawarta Hajiya Falmata. "Uwani ku je ke da Auta ki taimaka mata ku ciro mini wayata ta faɗa bayan gado." Babu musu Uwani ta yi wa Auta magana suka shiga ɗakin Mami, sun sha wahala sosai kafin su samu damar ɗauko wayar tun da can ƙarshen gado ta faɗa. Abu ɗaya ne ya tsaye wa Uwani a rai, a iya sanin ta tun ranar da ta zo gidan Mami ba ta taɓa saka ta aiki tare da Auta ba. Amma sai ta sa a ranta ko don ganin mutane ne ya sa Mami ta yi hakan, don kar a ce har yanzu ba ta ƙaunarta. Wurin sallar Azahar bayan Mami ta yi sallah ta fito falo ta fasa kukan an sace mata maƙudan kuɗin da Daddy ya ba ta ajiya har kimanin raina miliyan biyu da rabi, nan da nan hankulan mazauna gidan ya tashi. Dada na jin haka ta fara sababi rai a ɓace. "A gaskiya ni kam idan aka kwashe kuɗin nan an cuci Mamman, saboda Allah a tara mutane domin harkar arziƙi su ɓige da harkar tsiya? Shi dai ɓarawo bai ji daɗin halinsa ba, ba don sai Hajji zan je Saudiyya ba da babu abin da zai hana na kai ƙarar ɓarawon nan wurin Ubangiji a ɗakin Allah ba." Haka dai kowa da abin da ya dinga faɗa, daga ƙarshe aka ce su waye suka shiga ɗakin Mami a ranar su za a bincika, nan take aka bada shedar Uwani ce da Auta suka ɗauko waya. Kiransu aka yi aka tambaye su kowacce ta ce ba ta ga kuɗi ba, Mami ta bada shawarar a duba ɗakunan kowaccensu, haka aka kasu gida biyu wasu suka yi ɗakin Auta wasu suka wuce ɗakin Uwani. Falonta aka fara dubawa har da ƙasan kujeru, sannan suka wuce ɗakinta, masu duba drower saka kaya na yi, wasu kuma har da leƙa ƙarƙashin gado suke. Kwatsam ana duba drower madubi sai ga kuɗi, nan take mutane suka ɗauki salati. Aka wuce wurin Mami da kuɗi, saboda tashin hankali Uwani jikinta har karkarwa yake yi. Duk yadda Uwani ta so fitar da kanta abin sai ya gagara, ta yi kuka ta yi rantse-rantse babu wanda ya yarda da ita. Hatta Dada a wannan karon ba ta yarda da ita ba, Uwani ta rarrafa gaban Dada tana kuka cikin takaici Dada ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗa ta gefe. Daddy ne kaɗai da ya zo ya lallashi ta, a ransa yana wasu-wasin wannan abin da ya faru. Lokacin da Jafar ya dawo ya ji labari ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, nan take kuma Mami ta birkice a kan sai Jafar ya saki Uwani a cewarta ba za ta zauna a ɓata mata tarbiyyar yara ba. Shi kuma Daddy ya sake jaddada wa Jafar umarninsa na ko bayan ransa bai amince ya rabu da Uwani ba. Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Uwani don haka ta koma sashenta, ta faɗa kan gado ban da rusar kuka babu abin da take yi. Lokacin da Jafar ya shiga ya same ta kallon tsana ya wurga mata sannan ya ce. "Wallahi ni dai an gama cutata, a ce wai matata ta rasa wa za ta yi wa sata sai mahaifina, me aka rage ki da shi ci ko sha? Ƙanƙanuwar yarinya da ke ko a ina kika san kuɗi da har za ki sa hannu ki kwashe miliyan biyu da rabi. Ni kam na yi dana-sanin aurenki, ni dai aurenki wallahi bai amfane ni da komai ba sai tsiya. Ya zame mini dole na yi gaggauwar auren Safna, don ba zan zauna ɓacin rai da takaicinki ya kashe ni ba. Shashasha ɓarauniyar banza da wofi." Jafar ya yi tsaki ya fice daga ɗakin. Uwani ta ci kuka kamar babu gobe, tana nan ɗaki Auta ta je ta same ta. "Uwani Allah Ya sani har yanzu ba na jin ke kika ɗauki kuɗin nan, tare fa muka yi komai muka gama." Rai a ɓace Uwani ta ce. "Auta fice mini a ɗaki kada na sauke fushina a kanki." "Don Allah ki saurare ni kada ki yi mana jama'u..." Cikin tsawa Uwani ta katse ta. "Ki fice mini a ɗaki na ce." Auta ta tsorata sosai da yadda ta ga Uwani ta birkice lokaci ɗaya, bayan fitar Auta Uwani ta fara nazarin shigowar Shukra da kiran da Mami ta yi mata. Murmushi ta saki ta share hawayenta a fili ta furta. "Wallahi wannan ƙwallar da na zubar ba za ta tafi a banza ba. Ni Uwani za ku laƙa wa sharri, ai ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Daga haka Uwani ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta, ta koma can sashen su Mami. Yadda mutane ke bin ta da kallo ita ma Uwani sai ta murje idonta ta fara bin su da kallo, hatta Dada fushi take yi da ita don haka ita ma ta yi kamar ba ta san da Dada a wurin ba. Duk in da Uwani ta gifta sai dai ka ji ƙus-ƙus na tashi. Auta ta nema ta ba ta haƙurin abin da ta yi mata, ita ma dama Auta ba ta ga laifin Uwanin ba don idan ita ce ma za ta yi fiye da haka. A cikin dabara Uwani ta tambayi Auta Event ɗin da za a yi kamu, Auta ta nuna mata ai sai su tafi tare tun da ba ta san wurin ba. Yamma liƙi jama'ar gidan ana ta hada-hadar tafiya wurin kamu, Uwani ma atamfarta ta saka da mayafi sai dai tun rana Auta ta hana ta yin wannan ɗige-ɗigen kwalliyar. Ita ta biya musu kuɗin make up aka yi muku kwalliya sai ga Uwani ta fito shar kamar ba ita, lokacin da Uwani ta saka ƙafa a cikin hall ɗin ne ta saki murmushin ƙeta da mugunta. Ta zura hannu cikin aljihun doguwar rigarta ta ji fakitin sabuwar rezar da ta saya tana ciki a fili ta furta. "Uwani ce fa 'yar ƙashin gwiwa, ai yanzu za mu fara wasan da ku tun da haka kuka zaɓa." AlhamduLillah a nan free pages na wannan labarin ya ƙare🫠 idan kina buƙatar ci gaba za ki turo 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lamber 07062062624 Idan littafi ya kammala cmplt 800 ne. Sai mun haɗe a shafin gobe idan Allah Ya kai mu domin mu ji tsiyar da Uwani za ta shuka, Fakitin Reza a cikin Hall ɗin kamu na san akwai ƙura.😂 #Ummou Aslam Bint Adam🌚 *SHU'UMAR MASARAUTA* ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba. SHAFI NA ƊAYA Masarautar Zazzau (1953) Wani irin zafi take ji yana ratsa ta tun daga tafin ƙafarta har zuwa tsakiyar kwanyarta, dalilin haka ya sabbaba mata karkarwar jiki tamkar wacce ta ji kiɗan gangi. Wanda hakan ne ya haifar mata gumin da ke tsatssafowa daga kowacce kafar da ke cikin ilahirin jikinta. Ba yau ne karo na farko da haka ya taɓa faruwa da ita ba, sai dai a wannan ranar ji take tamkar an saka ta a tukunya ana dafa naman jikinta da ruwan zafi. A hankali ta cije baki tana yarfe hannu haɗe da lumshe idanu. Baiwa Maimuna da ke bayanta tana mata fifita cikin ƙwarewa a makirci ta fakaice ta, ta yanki ƙasan jelar gashin kanta ɗan ƙanƙani ta yadda ba za ta fahimci hakan ba. Da sauri ta soke shi a jikinta haɗe da sauke ajiyar zuciya don ko babu komai ta san ta tsira daga siraɗin Fulani Umaima. Ta ɗan numfasa a hankali. "Ki gafarce ni uwar ɗakina zan ƙarasa sashen Takawa na ce Jakadiya ta karɓo miki magani kamar yadda na ji kin ambata a baya, ranki shi daɗe lamarin ciwon nan na ki ƙara ƙamari yake yi amma tuba nake idan da kuskure a kalamaina uwar ɗakina." Ta so musa mata kamar yadda ta yi kafin zafin jikin ya fara galabaitar da ita, dalilinta na yin haka bai wuce yadda take gudun kada Bayin cikin masarautar su fuskanci zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Mai martaba ba. Gyaɗa mata kai ta yi haɗe da ruƙo hannunta ta furta, "Idan kin fita Maimuna ki turo mini Baiwa Zainaba." Cike da girmamawa ta russana, "Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima mai jiran gado cikin yalwar ariziƙi da ƙoshin lafiya." Da hanzari ta fice a gaggauce don ko kaɗan ba ta son wargaza shirin ɓoyayyar uwar ɗakinta. Sai da ta turo wa Fulani babba Zainaba sannan ta wuce sashen Fulani Umaima cike da firgici, tana tafe tana waige kamar sabuwar munafukar da ta yi gulma a fada. Da yake Fulani Umaima ta kwana da sanin shirinsu, tun da doshin magriba ta sallami bayinta suka wuce sashensu na bayi. Tamkar wacce aka jefo daga sama haka ta faɗa ɗakin Fulani Umaima da ke tsaye tana kai kawo don gudun samun matsala a shirinsu, duk da tana da yaƙinin Baiwa Maimuna ba za ta iya shallake wa umarninta ba. A ƙasa ta zube tana sauke numfashi ta furta, "Hutawarki lafiya Fulani mai magajin masarauta, zinariyar Mai martana haskenki bai tsaya iya shi kaɗai ba kin haske lungu da saƙon cikin Masarauta. Ina gwanar wani ga tawa? Kin yi taki kin yi ta kowa, garnaƙaƙin dutse kike kowa ya ja da ke shi zai faɗi..." Fulani Umaima ta katse ta da cewar, "Ina fatan komai ya tafi yadda ya kamata?" Baiwa Maimauna ta saki murmushi, dalilin haka ya sa Fulani Umaima ta sauke ajiyar zuciya duk da ba ta kai ga jin amsar Maimuna ba amma ta fahimci sun yi nasara domin kuwa labarin zuciya a tambayi fuska. "Ranki shi daɗe an gama aiwatar da komai, ga wannan." Maimuna ta ƙarasa maganar tana kunto gashin kan Fulani Babba ta miƙa wa Fulani Umaima. Wani yalwataccen murmushi Fulani ta saki, Baiwa Maimuna ta ci gaba. "Yanzu haka tana can magashiyan har ta umarce ni da na aika Jakadiya ta karɓo mata ragowar maganinta a wurin Mai martaba." Wata irin dariya ce ta suɓuce wa Fulani Umaima wacce ba ta tsammace ta ba, tuna wacce take gabanta ya sa ta tsuke fuska haɗe da furta. "Ki jira ni." Uwar ɗakinta ta shiga can ƙarƙashin gado ta zura hannunta, ta ɗauko wani ƙoƙon kan ƙwarangwal. Wani garin magani ta ɗebo a ciki ta kulle a cikin wata 'yar busasshiyar ƙaramar fata. Ta fito zuciyarta fes cike da takun isa da ƙasaita. Sai da ta koma kan ƙasaitacciyar kujerarta ta zauna sannan ta miƙa wa Maimuna. "Ki fara zuwa ki karɓo maganin wurin Mai martaba, amma ki tabbata wannan kika ba ta ta yi amfani da shi, za ki zuba mata a ruwa ko abinci kuma ki tabbatar da ta shafe jikinta da shi. Duk dare ina buƙatar ganinki domin akwai fitar sirrin da nake so mu yi." Cike da girmamawa Maimuna ta russuna. "An gama ranki shi daɗe, fansar kaina gare ki ya shugabata domin kai da kaya duka mallakar wuyane. Ki sa a ranki na aiwatar da duk abin kika buƙata na gama, Allah ya taimaki giwar Takawa ɗawusu mai yawan ado." Fulani Umaima ta gyaɗa kai sannan Baiwa Maimuna ta miƙe, har ta je bakin ƙofa Fulani ta furta. "Ki tabbata ba a samu matsala ba, idan aka samu matsala ki kuka da kanki." Baiwa Maimuna ta russuna. "Godiya nake uwar gijiyata." Sai da Maimuna ta ɗaure maganin wurin Fulani Umaima sannan ta nufi sashen Mai martaba, Jakadiya ta samu ta sanar da ita saƙon Fulani Babba. Kai tsaye Jakadiya ta tunkari turakar Takawa. Sai da rangaɗa sallama haɗe da kirarin girmamawa sannan ta isar da saƙon Fulani Babba. Kamar ba zai amsa mata sai kuma ya miƙe ya nufi wata jakar fata da ke saƙale a jikin bango ya zura hannunsa, wasu ƙullin magunguna biyu ya ciro ya miƙa wa Jakadiya, ta karɓa tana godiya. Har ta fara tafiya ya furta. "Daga yau a sanar da ita ta riƙa karɓar magani kafin almuru, ba a koyaushe muke da buƙatar hakan ba." Jakadiya ta amsa sannan ta fice ta damƙa wa Baiwa Maimuna tana jaddada mata saƙon Mai martaba. Maimuna na shiga sashen Fulani Babba ta same ta kamar yadda ta bar ta, Baiwa Zainaba na gefe tana matsa mata ƙafafuwanta da suka ɗan kumbura. Cike da girmamawa ta miƙa mata maganin da Fulani Umaima ta bata sannan ta furta, "Allah ya ƙara wa Fulani lafiya, Ubangiji ya shiga lamuranki uwar ɗakina. Mai martaba ya ce a jiƙa rabi, rabi kuma a shafe miki jiki da shi." Idanun Fulani jawur kamar sabon barkono ta buɗe su a hankali ta furta. "A yi yadda ya da ce Maimuna." Zuciyar Maimuna ƙal ta tashi jiki na rawa ta jiƙa maganin kamar yadda Fulani Umaima ta gaya mata, ta taimaka wa Fulani Babba ta tashi zaune haɗe da kai mata ƙoƙon bakinta. Tas ta shanye shi sannan Maimuna ta shiga shafe mata a jiki gabaɗaya, sannu a hankali ta ji wata sassanyar iska na ratsata. Ta koma ta kwanta sakamakon jin daɗin jikinta da ta fara yi. Ta dubi su Baiwa Maimuna. "Maimuna za ku iya tafiya, Zainaba a tabbata an gyara makwanci su Khadija." Cikin girmamawa suka zube ƙasa, "An gama ranki shi daɗe, Allah ya ƙara lafiya ya kawo mana Yarima lafiya." Ba ta iya amsa musu ba sai ma runtse ido da ta yi sakamakon jin wata irin hayaniya da ta yi a tsakar kanta, ga wani irin jiri da ke ɗaukanta. A ɓangare ɗaya kuma wani abu mai tsini ya fara fusgar can cikin ƙasanta. A gurguje Maimuna ta fice haɗe da sake ba wa Zainaba umarnin gyaran ɗakin su Khadija da yake ita ce gaba da ita, ta juya ta fice daga ɓangaren 'yayan Fulani Babba. A sanyaye Baiwa Zainaba ta bi Maimuna da kallo don haka kawai take jin zuciyarta na wasuwasi a kan Baiwa Maimuna tun da ta taɓa ganinta ta shiga sashen Fulani Umaima sau biyu. Kai tsaye sashen Fulani Umaima ta faɗa, kuma a wurin da ta tafi a nan ta koma ta same ta. Fulani Umaima na ganin Baiwa Maimuna ta faɗa uwar ɗaki, wani sirrintaccen akwatinta ta ɗauko ta buɗe cikinsa. Kamar kullin idan za ta ziyarce shi haka take saka wannan sihirtacciyar rigar da Boka Bamagujen dutse ya bata, a lokacin ma sai da ta tube kayanta gabaɗaya sannan ta zura rigar mai ɗauke da launin ja, baƙi, ruwan ɗorawa da launin ruwan ƙasa. Rigar ɗinke take da waɗansu ƙananan layu sai kuma wasu ƙananun rubutu da aka yi da larabci, wani ɗan ƙaho ta riƙe a hannunta sannan ta fito wurin da ta bar Baiwa Maimuna. Hannu ta miƙa wa Maimuna babu musu da yake ta san kwanan zancen ta ɗora tafin hannunta a saman na Fulani Umaima, wanda ta tabbata ba don wannan sirrintacciyar tafiyar da suke yi ba babu dalilin da zai kai hannunta jikin Fulani Umaima, musamman yadda take nuna ƙyamar bayi da talakawa ƙarara a fili. Saka hannun Maimuna cikin na Fulani babu jimawa, ta runtse idanunta ta ɗaga hannunta da ta ke riƙe da ƙahon ta busa sau uku sannan ta kira sunan Bamagujen dutse sau uku. Wata irin guguwa ce ta karaɗe cikin ɗakin kamar ƙiftawar ido sai ga su a bakin wani ƙaton farin dutse mai ɗaukar ido, wurin kamar rana tarwai babu abin da ba ka iya gani. Kamar yadda yake bisa al'ada a duk lokacin da suka ziyarce shi, sai da suka saka ƙafarsu ta hagu a tare a kan wani jini da ke malale a gabansu. Sun ɗan ɗauki kamar minti biyu a haka sannan suka ji an bushe da wata irin dariya wacce take alamta musu aikin da ya da ce su yi a gaba. Ƙafarsu suka sake ɗagawa suka ɗora a kan wani kabari da ke gaban wannan jinin sannan suka fara takawa suka haye can sama dutse. Zaune suka hango shi babu ko ɗigon sutura a jikinsa, Maimuna ta kawar da kanta gefe don har cikin zuciyarta ba ta son ziyartar wannan shu'umin bokon don dai ba ta da yadda za ta yi ne. Suna ƙarasawa wurin wata ƙaramar bishiyar kuka Maimuna ta russuna tana faɗin, "Fatan nasara a kodayaushe ya shugabata." Fulani Umaima ta ci gaba da tafiya don Maimuna ta san ko karen hauka ne ya cije ta ba ta isa ta ƙara koda taku ɗaya ba. Fulani na zuwa sai da ta fara ɗiban wani jan ruwa a cikin wani ƙoƙon kan ƙwarangwal ta wanke fuskarta, sannan ta nemi wuri ta zauna tana fuskantar Boka Bamagujen dutse. "Barka da aiki uban gidana." Jinjina kai ya yi ya furta. "Barkanki Fulanin Sarki Abdul'aziz." Shiru ne ya ratsa Fulani Umaima ta kawo ido ta sa wa Bamaguje, ya saki murmushi don ya san wace ce Umaima. Ga tsananin buƙata fal ƙirjinta ga kuma taƙama da izzar mulki, kallo ɗaya ya yi mata ya fahimci halin da take ciki. "Umaima kin yi ƙoƙari." "Sanin haka ya sa na kawo ziyara a ranar da ka buƙata." Ta amsa masa a taƙaice. "Kin aiwatar da komai yadda ya kamata, don haka kishiyarki ita da Sarki Abdul'aziz sai kallo sai hange daga nesa. Matuƙar ba asirin nan ne ya karye ba, ba na jin kishiyarki za ta sake ɗaukan ciki a doron ƙasar nan. Ke ba ma ciki ba ina mai tabbatar miki ita da sake yin wata mu'amala da Sarki Abdul'aziz sai dai a lahira idan ana yi. Ina ragowar kayan aikin?" Ya wurga mata tambaya. Jin haka ya sa Umaima ta saki malalacin murmushi ta ɗebo gashin Fulani babba da gashin Sarki Abdul-aziz, haɗe da ƙasar maƙabarta da ta gidan tururuwa ta miƙa masa ba tare da ta tanka masa ba. "Mun sakar mata lalurar fitsarin kwance, kuma mun saka mata lalurar mantuwa da warin jiki." Bamaguje ya faɗa yana jefa tarkacen da Fulani Umaima ta bashi a cikin wata tunkunya da ke cike da jini tana tafasa. Kusan duk abin da suke tattaunawa Maimuna tana jin su, haka kawai ta ji tausayin uwar ɗakinta ya ɗarsar mata. Musamman da ta tuna zallar cin amanar da take yi mata mai haɗe da zagon ƙasa. "Ina maganar cikin jikinta ya kwana?" Fulani ta tambaya cike da izza. Bamaguje ta ɗebi wani jini mai yauƙi ya watsa a jikin wani allon farin ƙarfe. Take waɗansu inuwoyi suka bayyana, yana fara nazartarsu sai gani ya yi ɗuff komai ya ɗauke. Cikin da damuna ya sake ɗiban jinin ya watsa har sai da ya yi haka sau uku sannan ya dubi Umaima cikin damuwa. "Kishiyarki a daren yau za ta haihu!" Dum! Fulani ta ji tsakiyar kanta ya sara kamar wacce aka buga wa guduma. Rai a ɓace ta dube shi. "Wanne irin mugun labari nake ji haka, zancen banza kenan ƙafa ta mutu ta bar takalmi. Cikin jikinta ya fi komai ɗaga mini hankali..." Da sauri ya katse ta. "Tun fil azal kundunsa rubuce yake da zanen ƙaddararsa, cikin kishiyarki shu'umin ciki ne lulluɓe yake da almara tamkar yadda masarautarku ta kasance SHU'UMAR MASARAUTA. Kamar yadda na gaya miki a yau za ta haihu..." Duk dakiya da ƙarfin zuciya irin ta Fulani Umaima sai da hawaye ya suɓuto mata, Bamaguje ya tsaya yana kallonta haɗe da jinjina kai. "Yau shekarata biyar kenan a cikin masarautar nan ko ɓatan wata ban taɓa yi ba, tun Fulani babba na da goyon fari Takawa ya auro ni. Bamaguje kana son na ƙare rayuwata cikin ƙasƙanci da rashin mamora?" Girgiza kai ya yi, ya sauke ajiyar zuciya. "Wa ya ce miki ba za ki haihu ba?" Fulani ta zuba masa idanu zuciyarta na bugawa. "Yanzu haka kina ɗauke da juna biyu na tsawon makwanni uku." Kamar a mafarki haka ta ji kalaman Bamaguje na ratsa majiyar sautinta. "Ki yi imani da ni Umaima matuƙar ina numfashi ba za ki tozarta ba." Sanyi ta ji har cikin ranta. "Da kai na dogara Bamaguje na yi imani da kai tun da ba ka kunyata mahaifiyata ba na tabbata ba za ka tozarta ni ba." Ta yi maganar a raunane. Wata ƙatuwar kunama ya ɗauko da hannunsa ya ce, "Ba ni hannunki." A firgice ta wurga masa kallon baka da hankali, ya saki murmushi don ya fahimce ta. "Umaima kenan kura kike ga tsoro ga ban tsoro." Umaima ta haɗe fuska kamar ba ita ba. "An ya kuwa? Kar fa ka manta ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka, dalilin haka ya sa masallacin kura ba a ba wa kare limanci." Murmushi Bamaguje ya yi. "Kwantar da hankalinki kamar kin faɗa rijiya. Matso kusa ki ji." Bamaguje ya furta. Tun bai rufe baki ba Umaima ta matsa kusa da shi, raɗa ya yi mata a cikin kunne lokaci ɗaya ta bushe da wata iriyar dariya cike da farinciki. Ta koma mazauninta na farko tana sauraronsa. "Ki tabbatar da kin aiwatar da abin da na umarce ki, don kuwa kowa rai ya yi wa daɗi ba ya mai shi ba." "Bamaguje kenan! Ai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba." Umaima ta furta cike da nishaɗi. Kashe mata ido ɗaya ya yi yana ƙare mata kallo, ganin haka ya sa ta fahimci inda ya dosa. "Tukwina fa?" "Ka sallame ni kenan?" Ita ma ta wurga masa tambaya. Gyaɗa mata kai ya yi Umaima ta miƙe babu ko kunya ta sauke rigar tsubbun jikinta, Maimuna ta sunne kai ƙasa zuciyarta na bugawa. A fakaice take ƙare wa tsohon kallo cike da ƙyanƙyami don ko ita da take baiwa gani take ba za ta iya haɗa jiki da shi ba. Bamaguje na shirin ɗora hannu a jikinta ta ɗan ja da baya haɗe da sakin murmushin mugunta. "Na sadaukar maka da kishiyata a wannan daren, shi ne tukwicin da zan iya yi maka." Ba ta jira cewarsa ba ta ɗora rigar a jikinta. Bamaguje ya gyaɗa mata sannan ya furta. "Za ku iya tafiya." Umaima ta yi masa jinjina da hannu sannan ta sake ɗiban ruwan da ta wanke fuska da shi ta nufi wurin da Maimuna ke zaune hannunta ɗauke da kunamar da Bamaguje ya damƙa mata. Abin da suka aiwata a farkon zuwansu yanzun ma haka ne ya faru, sai da suka koma daidai wurin da suka buɗe ido suka gan su tun farkon zuwansu sannan, Fulani Umaima ta ɗaga ƙahon ta runtse ido ta busa haɗe da kiran sunan Bamaguje. Ƙamshin ɗakin Fulani ne ya ankarar da Maimuna dawowarsu gida, cike da girmamawa ta zube ƙasa ta furta. "Allah huta gajiya uwar gijiyata." "A kullin ina sake jaddada miki bakinki ƙanin ƙafarki Maimuna, duk ranar da kika bari kwaɓarki ta yi ruwa na ji sirrina ya fita za ki bambamce mini tsakanin tsaba da tsakuwa." Fulani ta yi maganar cikin sigar gargaɗi. "Maimuna ta duƙa kai ƙasa. "Wace ni uwar gijiyata? Kada Allah ya nuna mini ranar da zan aikata miki wannan zunubin ranki shi daɗe." Fulani ta taɓe baki, "Za ki iya tafiya." Da sauri Maimuna ta fice ko waige ba ta yi. Har za ta nufi sashen su na bayi sai uwar ɗakinta Fulani babba ta faɗo mata. Haka kawai ta ji sam ba ta kyauta ba. Zuciyarta ta ci gaba da azalzalarta da ta je ta ga halin da take ciki. Cikin sanɗa ta nufi sashen Fulani babba gabanta na faɗuwa. A haka ta ci gaba da tafiya har cikin ɗakin, ras! Ƙirjinta ya buga jikinta ya ɗauki karkarwa sakamkon ganin Fulanin a yashe babu sutura a jikinta. Wani tafkeken maciji ta gani a tsakanin ƙafafuwanta ya kafa kansa a saitin ƙasanta, ga wani irin gurnani da macijin ke yi. Idanun Fulani a rufe amma sai mutsu-mutsu take yi, da alama ma bacci take yi. Daga bayanta ta ji an dafa kafaɗarta, wani abu ne ya tsarga mata ta yi mutuwar tsaye cikin sanyin jiki ta waiwayo. Karaf idanunta suka sauka a kan Fulani Umaima da ta haɗe girar sama da ta ƙasa. _Ummou Aslam Bint Adam_🌚 07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.    SHAFI NA BIYU     Ras! Ta ji gabanta ya yi mummunan faɗuwa, lokaci ɗaya ta nemi yawun bakinta ta rasa. Cikin firgici ta buɗe baki za ta yi magana Fulani Umaima ta katse ta. "Me kike yi a nan kuma uban me kike leƙe?" Maimuna ta zube a ƙasa jiki na rawa ta furta. "Ki yi mini aikin gafara uwar gijiyata, na zo na ji ko Fulani nada buƙatar wani abu kafin na tafi." Da hannu Fulani Umaima ta nuna mata hanya, sum sum sum Maimuna ta fice jiki na karkarwa. Fulani Umaima ta leƙa Fulani babba da ke kwance, ta saki murmushi mai ɗauke da ma'anoni a hankali ta furta. "Mu zuba mu gani idan tusa na hura wuta, in dai ni ce yanzu kika fara gani." Daga haka ta fice daga ɗakin.    Fulani babba ta jima a haka sannan ta farka, a hankali take sauke ajiyar zuciyata. Duk da a mafarki ta ga Mai martaba yana kusantarta abin ya yi mata daɗi, ta ji farinciki matuƙa saboda idan ba mantawa ta yi ba rabon da wani abu ya shiga tsakaninta da Takawa tun cikin jikinta bai fi wata biyu ba. Danshin da ta ji a jikinta ne ya sa ta kai hannunta, da mamaki take kallon makwancin nata. Da ƙyar ta yunƙura ta tashi nan take fitsarin da ke naɗe da zaninta ya fara ɗiga, da farko ta yi tsammanin ko faya ce ta fashe mata tun da a halin da take ciki tana iya haihuwa a kowane lokaci, musamman da take jin ciwon mara sama-sama. Sai dai zarni-zarnin da ta ji ne ya sa ta shinshina hancinta. A hankali ta furta. "Fitsari? Ni kuma? Kai ina jin dai faya ce ta fashe." Gudun wasu-wasi ya sa da kanta ta ɗebo ruwa ta sa a katifar ta sauya kayan jikinta amma har lokacin gani take faya ce ta fashe mata. Banɗaki ta shiga ta yi wanka ta fito sannan ta ɗan ci abinci, a hankali ta ji mararta na ci gaba tsikararta daga baya bacci ya sake yin awon gaba da ita.    Fulani Umaima kai tsaye sashenta ta wuce don a ranar ba ta jin sha'awar zuwa wurin Mai martaba. Da shigarta babu jimawa sai ga Jakadiya ta shiga ɓangarenta da saƙon Mai martaba na gayyatarta zuwa turakarsa, ba don ta so ba haka ta amsa mata. Jakadiya har za ta tafi Fulani ta dakatar da ita. "Jakadiya ba na son ki yi nisa da sashen Fulani babba." Jakadiya ta amsa mata sannan ta fice. Cike da kissa Fulani Umaima ta shirya kanta da sihirtattun turarrukan da Bamaguje yake haɗa mata, ta ƙarasa turakar Mai martaba. Zamanta babu jimawa suka ji wata ƙarar busar sarewa. Da sauri Fulani da leƙa kusurwar turakarsa idonta ya sauka a kan ƙaton shurin da gudajen turuwa suka zagaye da ke cikin ɗakin, gabanta ya yanke ya faɗi don ta san tun da ta ji wannan sarewar a yau mai afkuwa za ta afku. Mai martaba ya saci kallonta, haka kawai yake jin shakkarta a zuciyarsa. Amma ko shakka babu wannan busar sarewar da shuri ya saki na da alaƙa da cikin jikin Fulani babba wanda yana da yaƙini za ta iya haihuwa a cikin daren nan. Ya so ya tanka wa Fulani Umaima amma sai ya fasa, hakan ya sa ta saki murmushi cikin kissa. "Jikina yana ba ni Fulani babba na gab da kawo mana Yarima, wannan abin farinciki ne. Tun da shuri ya saki sarewa na tabbata a yau za mu iya samun ƙaruwa a gidan nan." Faɗaɗa murmushinsa ya yi, ya janyo Fulani Umaima jikinsa ya furta. "Wannan haka ne yanzu me kike ganin ya kamata a yi?" "Ina ganin zai fi kyau a yi dakan ɗaka shiƙar ɗaka... sai a kira Jakadiya ta zauna a wurinta koda ciwon zai tashi tana kusa da ita, a madadin a kira Ungozoma. Amma sai yadda kace ranka shi daɗe farin jakada." Fulani Umaima ta ƙarasa magana tana sunkuyar da kai ƙasa. Ajiyar zuciya Mai martaba ya yi, "Na baki wuƙa da nama mai farar zuciya Allah ya yi miki albarka." Fulani Umaima ta amsa sannan hirar tasu ta fara sauya salon faranta ran ma'aurata. Zuciyar Fulani Umaima ƙal ta je ta samu Jakadiya da zancan Takawa, Jakadiya na gama sauraronta ta yi ƙasa da murya tana ɗan waige sannan ta ce. "Wani ma ya yi rawa ma ballantana ɗan makaɗi? Ai wallahi sai mun ga abin da ya ture wa buzu naɗi. Ina mai yi miki albishi tauraruwar Mai martaba gobe war haka Fulani Babba na nan cunkushe da baƙin ciki fal ƙirjinta, idan an isa a yi Yarima ba a ɗakinki ba shegiya nake." Fulani Umaima ta saki dariyar ƙeta. "Jakadiya tamkar zuma haka kike ga zaƙi ga harbi. Na aminta da ke fiye da haka ma za ki iya aikatawa." "Ai shi abin kasuwa na mai ciniki ne, ni ta ki ce Fulani har abada ina bayanki. Fulani kin manta ɗayan kirarin nawa kaska rabi mai jini ki bar shi da gashi." Fulani Umaima ta jinjina kai alamun gamsuwa. Jakadiya ta sake ƙasa da murya. "Allah ya taimake ki ni zan ƙarasa zan biya na taso Baiwa Maimuna da zarar haihuwa ta taho gadan-gadan zan turo miki ita." Murmushi Fulani Umaima ta yi har Jakadiya ta yi gaba ta sha gabanta da sauri ta furta. "Jakadiya a kawo mini kayan Bayi sashena, sannan a tabbatar an bawa Maimuna ta kawo mini cikin hanzari." Shiru Jakadiya ta yi tana nazaratar Fulani. Cikin zuciyarta tana ayyana ƙwarewarta a mugun makirci da ƙuduri.   Da sauri Jakadiya ta wuce ɓangaren Fulani Babba a lokacin da ta ƙarasa dare ya tsala sosai, sai da ta yi sallama sannan ta shiga har cikin ɗakinta. Shigar Jakadiya ya yi daidai da farkawar Fulani babba, ƙarasawa ta yi gabanta ta ce. "Allah ya taimaki uwar ɗakina ya ƙarawa Fulani lafiya. Yanzu haka Mai martaba ne ya turo ni a kan na kwana da ke saboda yanayin da kike ciki, domin tuni shuri ya saki sarewa." Murmushi Fulani ta yi don ko ba komai ta ji daɗin yadda Takawa ya ba ta kulawa, hannu ta miƙa wa Jakadiya alamar ta taimaka mata. Wani abu ta ji ya tsira wa mararta haɗe da bayanta. Cije baki ta yi jin ciwon na ƙara tsanani gadan-gadan. A haka ta miƙe ta ƙarasa banɗaki da ƙyar don ta gyara jikinta, a lokacin da ta tashi ta sake lura da fitsarin da ya jiƙe makwancinta sharkaf, na wannan lokacin har ya fi na baya yawa da wari. Fulani na dawowa kafin ta shiga ɗakin ta ci karo da wata mata baƙiƙƙirin a tsaye a dokin ƙofa. Hannu ta miƙa mata cikin wata irin murya ta furta. "Ba ni cikin jikinki!" Da Mamaki Fulani ke kallonta har lokacin ciwo na cin ta, "Wace ce ke? Me ya sa zan baki cikin jikina?" Tana rufe baki  ta ga matar ta miƙa hannuwanta masu ɗauke da waɗansu irin baƙaƙen farata da zaƙwa-zaƙwan yatsu, ta miƙa hannun da niyyar shafa saman cikinta, Fulani da sauri ta ja baya haɗe da furta. "A'uzubillahi, Innalillahi..." Da gudu ta ga matar ta shige cikin sashenta, wata uwar ƙara ta ƙwalla nan take sai ga Jakadiya ta nufo wurin da gudu. Jiki na karkarwa Fulani ta ce, "Jakadiya baki ganta ba?" Jakadiya ta waiga hagu da dama ta ce, "Wa kenan ranki shi daɗe?" Dum! Fulani ta ji kanta ya yi  nauyi tana son tuna a kan abin da Jakadiya take tambayarta amma ta manta, gumin da ke tsattsafo mata ta share ta ce, "Ba komai mu je Jakadiya marata ciwo take. Wash! Bayana zai ɓalle." Jakadiya ta taimaka mata suka ƙarasa ciki, kafin fitowar Fulani daga banɗaki tuni Jakadiya ta gyara wurin ta haɗa gabaɗaya kayan karɓar haihuwa. Ganin zaƙi haɗe da jini ya fara bin ƙafar Fulani ya sa Jakadiya ta shimfiɗa mata ƙatuwar leɗa, Fulani da ƙyar ta yunƙura ta hau kai tana jin ƙasanta tamkar ɗa zai faɗo. Fulani Umaima ce ta yi sallama daga bayanta Baiwa Maimuna na biye da ita, yadda Fulani Umaima ta marairaice tana yi wa Fulani babba sannu sai ka rantse zuciyarta cike take fal da tsoron Allah. Wani jan ƙoƙo ta miƙa mata ta furta, "Mai martaba na cikin tsananin damuwa da jin halin da kike ciki, musamman da ya tuna da mutuwar Marigayya Fulani Samira. (Matar Sarki Abdul'aziz ta uku ce da ta rasu wurin haihuwa.) Ya umarci da a kawo miki wannan yanzu na karɓa a hannun Shamaki." Ɗago kan Fulani babba ta ga Fulani Umaima ta sauya mata a kammani, har take ganin kamar ta taɓa sanin kamannin, sai dai kuma ba ta jin za ta tuna kalar fuskar. Baiwa Maimuna da ke tsaye jikinta ya yi sanyi don ta san garin maganin ba ya wuce na wurin Bamaguje. Fulani Babba ta karɓe za ta kai baki ta ji wani irin nishi ya taso mata, cikin tsananin azaba ta wurgar da ƙwaryar gefe ta riƙe Jakadiya da ke gefenta, take jaririn ya faɗo ya fara mutsu-mutsu yana tsanyarewa da kuka. Wani irin baƙin ciki ya turniƙe ta Jakadiya ta waiga tana kallon Fulani don sanin irin hukuncin da za su yanke, da sauri Fulani Umaima ta fita sakamakon manta kunamar da Bamaguje ya bata. Jakadiya ta tsugunna ta sa reza ta yanke masa cibiya, a tunaninta ko Fulani Umaima ta zubda makamanta ne tun da jaririn ya riga da ya zo duniya. Ta gama yanke masa cibiya kenan Fulani Umaima ta faɗo ɗakin hannunta ɗauke da wata ƙatuwar kunama, a daidai lokacin Fulanin ta sake wani yunƙurin babu jimawa wani jaririn ya faɗo. Kusan mutuwar tsaye gabaɗaya suka yi, fuska babu walwala Fulani Umaima ta ƙarasa ta ɗora kunamar a kan jinin da ke zuba daga ƙasan Fulani Babba, kunamar na fara zuƙar jinin Fulani babba ta yanke jiki ta faɗi jikinta na wani irin karkarwa. Fulani Umaima ta saki shu'umin murmushi, sai dai kuma ganin jariran biyu ya sa ta samu shakkun wanda za ta aiwatar da mugun ƙudurin a kansa, na farkon da jakadiya ta yankewa cibi ta naɗe a zani ta ɗauka, take zuciyarta ta ƙwaɗaita mata wata shawara. Kiran Baiwa Maimuna ta yi ta damƙa mata shi, sannan ta ƙarasa gaban ɗayan jaririn da ko cibiya ba a yanke masa ba. Wutsul-wutsul yake yana kuka ta ɗauki kunamar da ke cikin jinin ta buɗe bakinsa da ƙarfin tsiya ta matse kunamar a cikin bakinsa. Take wani irin ruwa mai yauƙi haɗe da jini ya fara ɗiga a bakinsa. Kamar yadda yaro yake kama mama haka jaririn ya riƙa tsotsar jini da ruwa mai yauƙin. Ya jima yana sha sannan jaririn ya fara wani irin kakari wani farin ruwa mai haɗe da jini na fita daga hanci da bakinsa. Fulani ta waiga wurin Baiwa Maimuna ta furta, "Ina buƙatar ki fita ta ƙofar baya a sirrince, ki samu ƙaton kogi ki jefa shi ko kuma ki samu wani ƙaton ramin ki binne mini shi. Duk rintsi kada ki bar shi da sauran numfashi, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci."  Baiwa Maimuna da jikinta ya gama sanyi ta ce, "An gama ranki shi daɗe." Har Maimuna ta yi gaba Fulani Umaima ta katse ta,  "Iya ruwa fida kai. Kowa ya biya allonsa ya wanke. Ki tabbatar ba a samu matsala ba, wallahi matuƙar asiri ya tonu sai kin gayyaci mutuwarki da bakinki. Ni da kika ganni ba na ƙwaina sai da zakara don haka ki bi sannu, shawara ce na baki don kar ki bari kwaɓarki ta yi ruwa." Baiwa Maimuna ta russuna rungume da jaririn ta furta, "Tuba nake ragamar damisa a ja ki da nisa. Na yi tsammanin kin fahimci somu-somun hauka zubda yawu. Mai ƙafa ɗaya ma ya yi rawa ballantana mai biyu? Indai ni ce har gaban abadan ba zan taɓa baki matsala ba." Fulani Umaima ta saki malalacin murmushi ta furta, "Na aminta da ke Maimunatu, idan kin kammala komai ki samu Jakadiya akwai kyakkyawar kyauta. Amma ina buƙatar ganinki da zarar kin kammala." Cike da girmamawa Baiwa Maimuna ta ce. "Godiya nake giwar Takawa fara mai farar aniya, sikari baki yi farin banza..." "Ba mu da isasshen lokaci ki hanzarta ki fita." Fulani Umaima ta katse ta a taƙaice. Daga haka Baiwa Maimuna ta fita daga sashen Fulani ta ƙofar baya, cikin duhu haka ta ci gaba da tafiya tana ratsa bishiyoyi da ƙayoyi har ta samu ta fita ta can bayan Masarauta.    Ganin har lokacin jaririn bai daina kakarin da yake yi ba ya sa Jakadiya ta dubi Fulani Umaima. "Ranki shi daɗe me zai hana mu ƙarasa shi tun da har yanzu bai ƙarasa mutuwa ba?" Da ido Fulani ta kafe jaririn. "Bamaguje bai ba ni damar haka ba, ki tsaya kawai mu zura wa sarautar Allah ido. Kuma ni kaina ba na son ya mutu yanzu, na fi son na dasa wa Fulani Babba ɓacin ran da har ta mutu ba za ta manta da shi ba." Jakadiya ta jinjina kai a daidai lokacin da jaririn ya tsagaita da wannan kakarin, a lokacin Fulani Babba ta farfaɗo. Ta yunƙura a hankali da niyyar tashi da yake jikinta babu ƙwari sai Jakadiya da Fulani ne suka taimaka mata. "Sannu Yaya, barkanmu da arziƙi Allah dai ya kawo mana Yarima lafiya." Fulani Umaima ta furta tana sakar mata murmushi, wani irin yammm take ji a jikinta kamar tafiyar kiyashi, jiki babu ƙwari ta sakar wa Fulani Umaima murmushi. Idonta ne ya kai kan jaririn da ke kwance ta kafe shi da idanu, wani abu take son tunawa amma kanta ya yi nauyi ta gagara tunawa. Jakadiya ta saki guɗa da ƙarfi tana ɗaukan jaririn da ilahirin jikinsa ya haɗe da gumi, ga wani irin zafi zam a kan fatar jikinsa. Guɗar da Jakadiya ta yi ce ta alamta wa Dogaran da ke kewaye da sashen saukar Fulani babba, kafin wani lokaci tuni labari ya isa wurin Mai martaba. Fulani da Jakadiya tuni suka gyara jariri da mai jego, an turare ɗakin da turaren wuta ko ina sai buga ƙamshi yake yi. Sai dai Fulani babba tana ƙare wa yaron kallo ta fahimci kamar idanunsa ba daidai suke ba, ga yawu da yake ɗan ziraro masa ta gefen bakinsa hancinsa na yoyon majina. Ƙura masa ido ta yi tana son tuna wani abu da ya shafi lokacin da take naƙuda har zuwa haihuwarta, sai dai nauyin da kanta ya yi ne ya haddasa mata ciwon kai ɓari ɗaya take jin kamar zai tarwatse mata. A hankali ta kalli Fulani Umaima cike da murmushi, "Na gode sosai da kulawarki ƙanwata." Fulani Umaima ta saki murmushin yaƙe don saboda rufewar ido har gani take babu abin da maganin Bamaguje ya yi wa jaririn, amma saboda kissa sai ta furta. "Haba Fulani babba me ye abin godiya ina ce da kai da kaya duka mallakar wuya ne?" Fulani babba ta jinjina kai cike da jin daɗi ta ce. "Amma kuma yaba kyauta tukwici in ji masu iya magana." "Ai lamarin tuwona maina aka yi, ni dai bari na wuce Fulani na ji asuba ta fara ƙaratowa." Fulani Umaima na zuwa sashenta ta faɗa gado cike da tashin hankali. "Ya zame mini dole na ziyarci Bamaguje kuma a yau ba sai gobe ba sai ya hallaka mini Fulani da abin da ta haifa, idan ba haka ba zuciyata bugawa za ta yi." Ta ƙarasa maganar tana shiga cikin uwar ɗakinta.    Tafiya mai nisa Baiwa Maimuna ta yi har sai da ta yi nisa da masarauta, ta shiga cikin wani daji mai duhun bishiyoyi. Kuka jaririn ya fara yana wutsul-wutsul, bankaɗa zanin ta yi ta ji tausayinsa ya mamaye zuciyarta. Da yake asuba ta yi haske ya fara mamaye cikin dajin, wani ɗan rami ta hango da ke gefen wata murgujejiyar bishiyar kuka, kallon bishiyar kukar kaɗai ya isa ya tsoratar da gangar jikin mammallakiyar ƙwayar idon. Da sauri ta ƙarasa wurin ta tsugunna  sai a lokacin ta lura da zagayyan gidan tururuwar da ke wurin, taku ta fara jiyowa a ɗan nesa da ita da sauri ta saka shi a ciki ta bar wurin ta ɓoye a bayan wata bishiya, amma ga mamakinta sai ta ji shiru babu kowa. Gudun kada asirinta ya tonu ya sa ta fara zabga gudu ta nufi hanyar gida, a yadda take ji ba ta jin za ta iya kashe jaririn da bai ji ba bai gani ba, don rashin imaninta bai kai nan ba. Tana cikin gudun ta ji ta yi karo da wani abu garam! Har sai da ta faɗi ƙasa. Tsoro, firgici da matsanancin tashin hankali ya mamaye ta, take jikinta ya hau karkarwa sakamakon ganin bishiyar kukar da ta kwantar da jaririn a gabanta ta tsaya dass kamar yadda ta baro ta a baya. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ƙirƙirarran labari ne bai faru a gaske ba. Ban yi shi don cin zarafin kowacce ƙabila da Masarautunsu ba.   SHAFI NA UKU   Fulani Umaima har ta zura hannu za ta ɗauko ƙahon ta busa sai kuma ta ayyana ta bari idan Maimuna ta dawo ta ji yadda ta ƙarke idan ya so sai ta ziyarci Bamaguje, saman gadonta ta faɗa ta kwanta babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.   Sannu a hankali ta fara jin dariya sama-sama, sai dai kuma yanayin dariyar ya tababtar mata da dariyar ƙaramin yaro ce. Ba ta tsinke zaren tunaninta ba ta hango wani jariri tube tamkar a lokacin ya zo duniya, tunkaro ta yake yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya hannunsa da wata murtukekiyar igiya yana jan waɗansu murtuka-murtukan shanu, hannunsa ɗaya ɗauke da kwari da baka. A tsorace ta miƙe tana ja da baya ganin jaririn na saita ta da niyyar harba mata, jin bango ya tokare ta ta baya ya sa hankalinta ya sake kai wa matuƙar ƙololuwar tashi. Sai da yaron ya zo gabanta ya furta, "Ba yanzu ba! Zan ƙara miki lokaci." Yana gama maganar ta ga ya juya yana ci gaba da ƙyaƙyata dariya. Firgigit Fulani Umaima ta tashi daga nannauyan baccin da ya ɗauke ta har ya gayyato mata mafarkin da ke neman wargaza kwanyarta. Ajiyar zuciya take saukewa akai-akai sannan ta jingina da bango, da ta ga zaman ba zai kai ta ba ta faɗa banɗaki ta yi wanka ta ɗauro alwala ta gabatar da sallar asuba, a lokacin da tuni rana ta jima da fitowa.        Kamar a mafarki haka ta ga bishiyar na sake tunkaro ta, a yadda take a zaune a ƙasa ta fara ja baya ilahirin jikinta na karkarwa. Wata irin iska mai haɗe da guguwa ce ta taso, Baiwa Maimuna ta sa hannuwa biyu ta rufe idanunta jin ƙura na shigar mata ido. Kamar an yi ruwa an ɗauke haka Maimuna ta ji wurin shiru tana buɗe idanunta ta nemi bishiyar ta rasa, a zabure ta tashi ta ci gaba da gudu kamar wacce ake bi a baya za a zare ranta. Ta jima tana abu ɗaya sannan ta ƙarasa ta bayan masarautar, a lokacin tuni gari ya waye. Sai da ta fakaici idon Dogarawan da ke gefen hanya sannan ta yi sauri ta shiga cikin gidan, tafiya take kamar za ta tashi sama don kallo ɗaya za ka yi mata ka fahimci kwanciyar hankali ya yi ƙaura daga gangar jiki da ruhinta. A haka da samu ta ƙarasa sashen matan sarki tana gab da shiga sashen Fulani Umaima ta ci karo da Uwar bayi, ƙare mata kallo ta yi sama da ƙasa sannan ta ce. "Maimuna daga ina kike haka?" Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake, take Maimuna ta yi fiƙi-fiƙi baki na rawa ta furta. "Amm da ma... Yanzu..." Daga can baya Jakadiya ta katse ta, "Uwar Bayi tare muka kwana da ita a sashen Fulani babba yanzu haka gyare-gyare ta gama yi mana." Jinjina kai Uwar bayi ta yi sannan ta wuce, Jakadiya ta ƙarasa wurin Maimuna ta ce. "Ya kamata ki riƙa sara kina duban gatarinki, ki riƙa gayyato nutsu kina yafa wa a gangar jikinki. Kin san sarai wace ce Fulani Umaima." Ajiyar zuciya Maimuna ta sauke ta amsa wa Jakadiya sannan ta wuce sashen Fulani Umaima jiki a saɓule. Tun da ta doshi sashen take jin gabanta na faɗuwa ta rasa dalili, gani take kallo ɗaya idan Fulani ta yi mata asirinta zai iya tonuwa. A haka ta lulluɓa mayafin jarumta ta shiga cikin gidan tana karkaɗe jikinta da ya yi butu-butu da ƙasa.   "Barka da hutawa ranki shi daɗe." Ƙuri Fulani Umaima ta yi wa Maimuna tana karantar yanayinta. "Binne jariri tamkar wacce ta yi dambe da jarumai biyar, Maimuna me yake faruwa na ga jikinki kamar wacce aka tono daga rami?" Ras! Gaban Maimuna ya faɗi, murya na rawa ta ce. "Ranki... Shi daɗe... Dama... zuwa na yi na sanar da ke an aiwatar da komai... Cikin nasara." Shekararta kusan hudu da Maimuna, ta karanci halaye da ɗabi'unta sarai. Take ranta ya yi mummunan ɓaci don ta fahimci zallar ƙarya a saman harshenta. "Me ya sa na amince za ki iya yi mini komai ban aiwatar da kaina ba?" Fulani Umaima ta yi maganar cike da murmushin yaƙe. Ɗakinta ta faɗa ta ɗauko ƙaho cikin shigar ziyarar Boka Bamaguje, ba ta tanka wa Maimuna komai ba ta miƙa mata hannu, zaro idanu Maimuna ta yi ta ji wani abu yana tsarga mata. Babu yadda za ta yi ta ɗora hannunta a kan nata, ba su jima ba sai ga su a fadar Boka Bamaguje. A wurin da ta saba zama koyaushe yanzun ma a nan ta zaune, gumi ya jiƙe jikinta sharkaf zuciyarta na dakan lugude kamar za ta hudo ƙirjinta. Fulani Umaima ta ce, "Bamaguje ina zargin Maimuna da cin amanata." Bamaguje ya saki murmushi. "Ba zargi ba ne domin yanzu haka duka jariran Sarki Abdul'aziz suna raye a doron ƙasar nan. Ba ta kashe shi ba kamar yadda kika buƙata." Wani yawu mai ɗaci Fulani Umaima ta haɗiya, ta wurgawa Maimuna kallon tsana. A firgice Maimuna ta zube bisa gwiwoyinta hawaye bibbiyu na zuba, "Ki gafarce ni uwar ɗakina wallahi..." Daga wurin da Fulani take ta ɗaga mata hannu. "Kin wargaza mini shirina Maimuna. Na yi rantsuwa da abin da ya busa numfashina sai na shayar da ke ruwan uƙuba mai tsanani." "Faɗuwa ce ta yi daidai da zama." "Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje." "Ina nufi sarane za a yi a kan gaɓa. Kin san akwai muhimmin aikin da na alƙawarta miki kwanaki, zan sadaukar da shi a kan baiwarki. Idan kuma za ki samo wata sai a aiwatar a kanta." Jin kalaman Bamaguje ya sa Fulani Umaima dariya ta sauya fuska cikin damuwa. "Amma kafin aikin Bamaguje ya aka yi aka haihu a ragaya? Na yi tsammanin kunamar da ka ba ni za ta hallaka jaririn Fulani? Ina fa tsoron kada wankin hula ya kai ni dare." Wata baƙar mujiya Bamaguje ya ɗauka ya sa hannu ya fige fukafukanta da ranta, ta saki wani kuka cike da azaba sannan ya jefa ta cikin wani daskararran jini. Ya shiga gudanar da al'amuran tsubbunsa, yana cikin yi ya ga tukwanen gabansa sun rushe. A razane ya ɗago yana ɗan ja da baya, ya sake kai hannun da niyyar sake aiwatarwa kamar saukar aradu ya ga wata baƙar kwari da baka ta faɗo tsakiyar tukwanen. Tashin hankalinsa ne ya tsananta, ya ɗago yana sharce gumin fuskarsa da ke cike da gashi. Garin wata farar ƙasa mai walwali da ɗaukan ido ya ɗebo ya watsa, nan take wata narkekekiyar baƙar saniya ta bayyana jingine da kwari da bakar nan. Da bayyanarta babu jimawa duka wutar wurin ta ɗauke, ƙirjin Bamaguje ya buga ya ɗago ya dube ta. "Tabbas wanzuwarsa a doron ƙasa akwai sanadi, ban san wacce kalar baiwa da matsayi ruhinsa ke ɗauke da shi ba. Sai dai a duk bincikena na garara gano taƙamaimai wane ne shi? Abu ɗaya shafin ƙaddararsa ya buɗe mini shi mai nasara ne, sai kuma samun goyon baya da taimakon ruhi da ke lulluɓe da fatarsa..." Cikin rashin fahimta Fulani Umaima ta katse shi, "Ban fahimci gurbin da kalmanka suke neman samun zama ba, wane ne shi wanda kake magana a kansa?"   "Jinin Sarki Abdul'aziz wato jaririn da kika sa aka fitar da shi, tabbas akwai ɓoyayyan al'amari a tattare da wannan yaron. Babban kuskuren da kika tafka kenan, da kika sa aka fitar da shi daga masarautar ba tare da shawara da ni ba. Zancan da nake yi miki yanzu ruhinsa ya yi nisan kiwon da babu hallitar da ta isa ta kawar da shi daga doron ƙasa. Ba zan ɓoye miki ba, daga ni har sauran matsafan da ke doron ƙasa ba na jin akwai wanda zai iya bankaɗa miki labuben sirrinsa, ba ina miki magana a kan masakin ɗan'uwansa ba domin wannan da shi da gawa marabarsu sauka da hawan numfashi. A yadda kika gan shi a haka zai ƙare rayuwarsa a nannaɗe, hatta ruwa da abinci idan ba a ba shi ba sai dai ya dauwama da yunwa. Shi kuwa wance ingarma ne mai ɗauke da rikitattun al'amura, amma ba zan yi miki iyaka ba Umaima idan har kina ganin za ki jarraba wani masanin fiye da ni ga fili ga mai doki." Wata gwauruwar ajiyar zuciya ta sauke fuska ɗauke da damuwa ta ba shi amsa, "Ba zan ja da kai ba Bamaguje domin na tabbata zaɓenka da mahaifiyata ta yi a matsayin madogara ba za ta yi zaɓen tumun dare ba, a halin da nake ciki babban burina bai wuce masarautar Zazzau ɗin nan ta dawo ƙarƙashin ikon abin da zan haifa ba wala Takawa yana raye ko baya raye." Bamaguje na ƙarasa jin kalamanta ta ɗauko wani baƙin ƙaho ya kai shi saitin idonsa na hagu ya haske wani allon farin ƙarfe mai ɗauke da rubutun jini, ƙahon da ke hannunsa na fesar da wani tartsatsin jini a jikin kaskon. Ƙuri ya yi yana kallo yana sake fahimtar al'amuran da ke wanzuwa a kwarmin ƙwayar idonsa, kamar kazar da aka jefa da gishiri haka Bamaguje ya ajiye ƙahon ya dube ta. "Za ki haifi gawurtacce kuma ingarman matashin saurayi, mai cike da isa ƙasaita da izzar mulki. Kuma zai kasance sarki wato magajin karagar sarki Abdul'aziz..." Murmushi da murnar Fulani ya katse kalaman Bamaguje ta ce. "Tabbas da kuwa mun shimfiɗa mulkin da wani mai numfashi bai taɓa aiwatar da makamancinsa ba. Sai na shayar da Fulani babba ruwa mamaki domin sai na gasa mata tsakuwa a tsakiyar tafin hannunta." Bamaguje ya kafe ta da idanu yana faɗin, "Haba Umaima me kike ci na baka ma zuba, ai duk gaggawar ungozoma ta bari a haihu. Kuma duk gaggawar asara ta jira yi samu. Kamar yadda na gaya miki jininki zai kasance sarkin ƙasar Zazzau ne kaɗai bisa taimakon jini da ruhin wata hallita, ban san ya zan fasalta miki ita ba amma ta kasance mai ɗauke da rikitattun al'amura. Wanzuwarta a doron ƙasa sanadi ne, kuma ta kasance abar farautar al'umma da dama ciki kuwa har da mahaifina wanda ya shafe shekara da shekaru cikin halwar tsafinsa yana dakon zuwanta. Ban gama tabbatar da abin da nake zargi ba amma tabbas na ga walƙiyarta a cikin masarautar Sarki Abdul'aziz, wannan zai sauƙaƙa miki cim ma muradinki..." Da sauri Fulani ta katse shi cikin ƙagauta.   "Wacce irin hallita ce? Me ne ne alaƙarta da masarautar Zazzauna? Shin dole sai da taimakonta ne abin da zan haifa zai kasance Sarkin masarautar Zazzau?" "Akwai ɓoyayyun al'amura game da ita, a sura ta zahiri ta kasance bil'adam kamar kowa. A baɗini tana da ɗauke da al'amura masu hautsina kwanya. Halwar tsafina bai fayya ce mini komai ba, sai dai ina mai shawartar ki da ki tabbatar kin yi nasara a kanta. Ina daga nan zan ci gaba da dafa miki domin ni ba iya boka kaɗai nake a wurinki ba, akwai wata ɓoyayyar alaƙa mai ƙarfi a tsakaninmu. Ba don na yi wa mahaifiyarki alƙawarin binne wannan sirrin ba da tuni na fayyace miki shi, amma ko ga iya haka na dakata na yi miki jurwaye mai kamar wanka don haka dabara ta rage wa mai shiga rijiya." Da yake hankalin Fulani ba ya jikinta ya sa ba ta fahimci inda kalaman Bamaguje suka dosa ba, tana shirin yi masa magana ta ji ya ci gaba da ce wa. "Tana da matuƙar hatsarin gaske don haka dole ki yi takatsantsan, wannan shawarar ina baki ita ne ba a matsayina na bokanki ba ina ba ki ita ne a matsayina na makusancinki. Wani abin da ɓatattu da dama irina ba su sani ba wannan hallitar na da wata tawaya ɗaya wacce da a ce an santa da tuni an yi galaba a kanta..." "Wacce irin tawaya gare ta?" Bamaguje ya wara hannuwansa haɗe da faɗin, "Ni kaina ban santa ba, sai dai allon tsafina ne ya alamta mini haka. Ammma  zan baki wannan sirrintaccen littafin mai ɗauke da labarin abin da ya taɓa faruwa a masarautar Daura, wannan al'amarin ya faru a shekara ɗari da hamsin baya da suka shuɗe. Ƙa'idar littafin ba a karatunsa kowacce rana sai ranar Lahadi ko Laraba daga bayan la'asar zuwa sallar isha'i. Ki bi shi a sannu ki karanta zai taimaka miki matuƙa. Umaima!" Boka Bamaguje ya ambaci sunanta cikin wani irin yanayi. Fulani Umaima ta dube shi cike da ƙwarin gwiwa babu alamar karaya ko tsoro a tattare da ita. "Jarumta da dakakkiyar zuciyarki na matuƙar birge ni, tabbas kin cancanci shiga sahun mace mai kamar maza. Na yi imani da abin bautar da nake bauta tare da siddabarun da na gada a wurin iyayena da kakanni sai na ci gaba da dafa miki kin kasance mai nasara har ƙarshen rayuwarki." Fulani Umaima ta saki murmushi. "Ai dama duka ɗaya baya kada sadaukan jarumai, don haka na dulmiya kogin azaba na yayyafa wa ruhi da gangar jikina don kada wani hatsari ko firgici ya razana ƙwarin gwiwata." Umaima ta ɗora tafin hannunta a saman tukunyar tsafinsa ta runtse idanunta ta ci gaba da cewa, "Na yi imani da kai Bamaguje kuma na yi maka alƙawari wallahi sai jinina ya mulki ƙasa da masarautar Zazzau bakiɗaya." Bamaguje ya jinjina kai sannan ya ɗauko wani irin littafi mai ɗauke da bangon ƙarfe wanda yake ɗauke da launin ruwan zaiba. A tafin hannunta ya ɗora mata, wani irin zuuuu ta ji a tafin hannunta kafin ta ankara ta ji wani sauti na furta. "Hidayaaaa!" A razane ta buɗe idonta suna haɗa ido Bamaguje ya jinjina mata kai, "Kamar yadda majiyar sautinki ta jiye miki haka ne wato Hidaya ba zan ce miko komai ba, domin amsar tambayar ki na cikin kundin littafin." Fulani ta rungume littafin ƙam kamar wani zai ƙwace shi, sannan ta waiga wurin da Maimuna ke zaune kamar gunki ta gagara motsa koda yatsanta ne. "Bamaguje ka aiwatar mini da duk abin da ka yi niyya a kan waccan la'ananniyar." Bamaguje na jin haka ya bushe da dariya, Maimuna ta fara mutsu-mutsu tana son tashi ta gudu amma ta gagar tashi. Yana daga wurin da yake zaune ya turmutsa hannunsa a cikin wani kabari, ya ɗauko ƙoƙon kan mamacin da ke ciki ya fara takawa har ya isa wurin da take zaune. Ɗora mata kan ya yi a kanta na ɗan lokaci take jikinta ya fara karkarwa, ya jima a haka sannan ya saka wata ƙaramar tsafatacciyar wuƙa ya yanki tsokar jikinta. Wajen kabarin ya koma ya tura fatarta a cikin kabarin sannan ya furta. "Wannan da kike ganinta a zahiri ne take tamkar rayayya amma ba ta da amfanin komai kuma za ta zame miki tamkar raƙumi da akala. Yanzu ki tafi da ita zuwa turakar Sarki Abdul'aziz, kuma a wannan ranar nake son ki sa Sarki Abdul'aziz ya kusanceta ta gaba da baya." A firgice Fulani Umaima ta ɗago ta kalle shi cikin tashin hankali. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masarautar Zazzau ta sauya zuwa Masarautar Huddam.*   SHAFI NA HUƊU    Wani irin kallo Fulani Umaima ta watsa wa Bamaguje, shi ma ya yi ƙuri yana kallon ta da daƙwa-daƙwan idanunsa jawur kamar sabon barkono, ta katse shirun da ce wa. "Ka na nufin Baiwata Maimuna ce Takawa zai kusance ta? A saboda wanne dalili kuma ba ka ganin tamkar na miƙa kai a kan hanyar da asirina zai tonu?" Bamaguje ya girgiza mata kai. "Matuƙar ina numfashi kullin za ki kasance lulluɓe cikin bargon rufin asirin da babu wani mai numfashi ya isa ya yaye miki shi, dalilin da ya sa na ce ki aiwatar da wannan aikin matuƙar Sarki Abdul'aziz ya kusanci Maimuna ta gaba da baya za ki sha gaban kowa. Wane na mai faɗa a ji a cikin ƙasar Huddam?" "Sarki Abdul-aziz." Umaima ta amsa masa. "Ki saurare ni da kyau. Ba akwai wata baƙar rijiya mai baƙin murfi a turakar Mai martaba ba wacce suke kallon juna ita da tsohon shuri mai tsohon tarihi?" Umaima ta gyaɗa masa kai. "Mai martaba na gama mu'amala da ita ki tabbatar kin ɗebi najasar jikinsu sai ki shafa ta akan saman murfin take murfin zai buɗe, ki zura Maimuna cikin rijiya ki koma gefe su zuba ido zai koma ya rufe kamar yadda yake da farko. Maruƙar kika aiwatar da komai yadda ya kamata za ki sha gaban duk wata hallita da ke cikin ƙasar Huddam, kwarjini da tsoronki zai mamaye zuƙatansu ta yadda kina faɗar maganar za a aiwatar miki. Sai dai akwai sharaɗi duk ranar da aka fito da Maimuna daga cikin wannan rijiyar wannan asirin ya karye, amma kuma abu ne da kamar wuya gurguwa da auren nesa domin yanzu haka rabon da a buɗe rijiyar yau kimanin shekara ɗari da hamsin kenan." Umaima ta sauke ajiyar zuciya. " Duk wannan ban ɗauke shi abu mai wahala ba, shin ya za a yi na wuce da Maimuna har turakar Takawa ba tare da wani ya gan ni ba, kuma na sa shi ya yi mu'amala da ita?" "Umaima a kullin kin fi son a yi miki ciki a yi miki goyo, za ki saka hannu ki ƙwaƙwalo ƙwayar idonta ki jefa a cikin wancen sihirtaccan ruwan, yadda za ta makance ta daina gani haka za ki ci karenki babu babbaka ba tare da wani ya kawo miki cikas ba. Kuma daga wannan lokacin hatta uwar da ta kawo ta duniya ba za ta sake tambayarta ba, yadda matacce ke mantawa da rayuwar baya haka duk wanda ya santa zai manta da shafinta." Umaima ta yi masa jinjina da hannu. "Na gode sosai Bamaguje faɗi kowanne irin tukwici kake buƙata." Bamaguje ya saki murmushi, "Ki je Umaima zan fanshi aikina a cikin masarautarku." Umaima na gama sauraronsa ta miƙe ta ƙarasa gaban Maimuna da ke zaune kamar butum-butumi, ƙaramar wuƙa ta saka ta ƙwaƙwalo idanunta ta watsa cikin wani koren ruwa kamar yadda Bamaguje ya faɗa mata. Ta koma gabansa ta yi masa sallama da faɗin duk abin da ake ciki za ta sake ziyartarsa. Ta rungume littafin a jikinta hannunta ɗaya riƙe da Maimuna na biye da ita kamar raƙumi da akala. Duk wani abu da take gudanarwa na siddabaru sai da ta gudanar babu jimawa sai ga su a cikin ɗakinta a tsaye. Kai tsaye uwar ɗakinta ta wuce da Maimanuna ta buɗe wani akwatinta na ƙarfe da take ajiyar abubuwanta na sirri ta ajiye littafin, sannan ta koma falo ta zauna tana ta zuba murmushi don gani take ƙiris ya rage haƙonta ya kai ga cim ma ruwa.    Bayan fitar Fulani Umaima daga sashen Fulani babba, Jakadiya da kanta ta ɗan tattara wurin. Ta leƙa madafa tana tambayar su Baraka ko ruwan zafin ya tafasa, a daidai lokacin ta same su sun fara kwashe ruwan. Bayan an zuba aka kai banɗakin Fulani babba, shi kuma jaririn Jakadiya ta zauna ta sulle shi tas. Sai da gari ya waye tangararan sanna Jakadiya ta ɗauki Yarima ta wuce da shi turakar Mai martaba. Farinciki fal fuskarsa ya karɓi jaririn yana jin son shi a zuciyarsa don ya jima yana mafarkin samu ɗa namiji. Huɗuba ya yi masa da suna Abubakar sannan ya ba wa Jakadiya ta mayar da shi, Jakadiya na mayar da shi Fulani ta rungume jaririnta suka kwanta bacci. Jakadiya da kanta ta sanar da Baiwa Zainaba a kan duk wanda ya zo mata barka a ce masa tana hutawa. Sai a lokacin ita ma Jakadiya ta wuce can sashensu na Bayi ta samu ta yada haƙarƙarinta don ta yi ramuwar baccin daren da ba ta yi ba.   Fulani Umaima tun da ta dawo ta kasa zaune ta kasa tsaye don burinta bai wuce ta ga ta aiwatar da abin da Bamaguje ya umarce ta ba. A yadda ta jingine Baiwa Maimuna a haka ta same ta a bayan ƙofa, bayan ta idar da sallar asuba ta riƙo hannun Maimuna tana faɗin, "Wuce mu je sashen Mai martaba." Babu musu Maimuna ta fara tafiya tana biye da Fulani. Duk da ta aminta ɗari bisa ɗari da hatsabibancin Bamaguje, a lokacin da ta fita harabar da Bayi suke kai wa da kawowa sai da gabanta ya faɗi, jikinta ya ɗauki rawa tana tsoron kada su ankara da Maimuna wacce take tafe da ƙwaƙwulallun idanuwa asirinta ya tonu. Amma ga mamakinta duk wurin da ta gifta sai dai Bayi su riƙa zubewa ƙasa suna kwasar gaisuwa. Cike da izza, ɗagawa, faɗin rai da alfari Fulani Umaima ta ci gaba da taku ɗaiɗai tana kallonsu a banzace ba tare da ta amsa ba ta wuce. Ba su yi mamaki ba domin ba wannan ne karo na farko da ta saba yi musu haka, wulaƙanci da tozarta na ƙasa da ita kamar a jininta yake don haka kowannensu ya sake shiga taitayinsa. Lokacin da ta isa sashen Sarki Abdul-aziz shiru ta ji wanda hakan ya alamta mata baya nan, can gefen gadon sa ta zaunar da Maimuna sannan ta fara jiyo motsi daga jikin windonsa. Tana leƙawa ta hango Takawa a cikin lambun shaƙatawarsa zaune a kujera a gefensa ɗawisu ne da ƙananan tsuntsaye suke ta kaiwa da kawowa. Har ta nufi ƙofar da za ta sada ta da lambun ta tuna ba ta ɗauko sihirtaccen turarenta, da sauri ta fice don kar Sarki Abdul'aziz ya dawo ba tare da ta kammala shirinta ba. Da fitarta ba a ɗauki minti biyar ba Sarki Abdul'aziz ya taso kai tsaye ya nufo cikin turakarsa, gabansa ya ji ya yanke ya faɗi ƙwarin gwiwar da ke tattare da shi ta tarwatse. A razane yake bin kan gadonsa da kallo, sakamakon ƙwaɗayin idanunsa da suka hango masa abin da ba yi tsammani ba.   Fulani Umaima na zuwa ta wuce ta zaro akwatinta da ke ƙarƙashin gado, ta buɗe ta da niyyar ɗaukon turaren amma zuciyarta ta fara kwaɗaita mata son sanin abin da yake ƙunshe a cikin littafin da Bamaguje ya damƙa mata. Ta sake tuna matuƙar ta rasa karatunsa a wannan ranar sai dai ta bari zuwa wani makon mai zuwa. Ɗaukan littafin ta yi ta koma gefen gado ta zauna, za ta sa hannu ta buɗe ta tashi da sauri ta je ta saka kuba a ƙofarta ta rufe sannan ta sake komawa ta buɗe shafin farko daga cikin littafin, ƙwayar idonta ta sauka a kan jimlar farko da aka yi rubutunta da ajami.   BAN SAN KAINA BA    Da mamaki ta sake furtawa da bakinta, "Ban san kaina ba! Me hakan yake nufi?" Duk harsashen kwanyarta ta gagara lalubo mata amsar tambayarta don haka ta sake mayar da kanta ta ci gaba da karatun.   Ban san mizanin tubalin ginin da ya dace na jingine rayuwata ba, balle na san kaina da abin da rayuwata ta ƙunsa, abu ɗaya na sani ban san kaina ba. Ban san wace ce ni ba domin kuwa wata hallita ce ke sarrafa zuciya da ruhin gangar jikina. Ban san asalina ba ballantana na binciki dangina, hasali ma kusan duk wani Bawa ko Baiwa da za ka gani a cikin masararutar Kabbab kusan kowa akwai tushe da asalin yankin da ya fito, nawa asalin ya yi rauni dalilin da ya sa ko a cikin Bayi na kasance ƙasƙantacciyar baiwa. Wacce take fuskantar tsangwama, kyara da duk wani nau'in cin zarafi saboda babu mutum ɗaya da zan kalla da sunan dangina. Har ya zame mana jiki a kowacce rana idan rana ta take muna karkasuwa ɓangare-ɓangare domin gudanar da ayyuka daban-daban. Ni da su Dije muna ɓangaren bangon yamma muna sirfen geron da za a yi wa su Fulani fura da shi, a lokacin rana ta take sosai daga bayana na ji an saka hannu an dafa kafaɗata wacce na ke kai taɓarya ina yin surfe da ita. A hankali na waiga ƙwayar idona ta sauka a kansa, cike da fargaba da sake waro idanuna haɗe da tattaɓa gefen fuskarsa don tabbatar da ƙwayar idona ba yaudarata take ba. Tun ban fi shekara biyar a duniya ba nake mafarkinsa ba dare babu rana, domin a duk lokacin da zan yada haƙarƙarina gangar jikina ta samu hutu bacci ya yi awon gaba da ni sai na yi mafarki da wannan hallitar. "Ki taya ni murna da farinciki domin na samu 'yancina, na zama kamar kowa mai ɗauke da rayuwar gashin kai. Na yi miki alƙawarin sai na karɓo miki karagarki, a kullin Kaka na sake jadadda mini mu tabbatar da mun ba wa alƙawari muhimmanci kuma mun cika shi, wannan zai dawo da ƙima da martabar ahalinmu, wacce zuri'armu ta tarwatse silar cin amanar da aka yi mana." Kalamansa suka mamaye masarrafar jina, mamakina ya ninku dalilin ganin ƙwalla na zuba daga ƙwayar idonsa. "Ke Hidaya kar ki raina wa kanki hankali, kina nufin mu za mu ci gaba da surfen kina can kina kalle-kalle banza da wofi? Wallahi kika bari muka surfe na cikin turmin nan sai dai ki surfe wannan kwano ukun ke kaɗai." Kalaman Safare suka katse ni, da sauri na waiga wurinsu kowaccensu ta sakar mini harara kamar idanunsu zai faɗo. A zuciyata na furta. "Ko dai su Safare ba sa ganin wannan saurayin?" Daga bayana na ji ya sake taɓo ni. "Ba za su taɓa ganina ba, saboda wasu muhimman abubuwa. Ke ma akwai dalilin da ya sa kike rayuwa a cikin Masarautar nan har kike mu'amala da su. Ki ci gaba da haƙuri kin san idan aski ya zo gaban goshi ya fi zafi." Yana gama furta mini waɗannan kalaman na neme shi na rasa. Wata irin azaba ta riyarci ƙafata sakamakon wurgo mini taɓarya da su Safare suka yi, na sunkuya cike da azaba ina matsa ƙafata. "Ga shi nan ki yi ki surfa ragowar, kuma kin fi kowa sanin halin Uwar tuwo matuƙar aka gama surfen aka bar ki a baya za ki yaba wa aya zaƙinta." Idanuwana na kai kan ƙwaryar da ke cike da gero har kusan kwano uku, tausayin irin wuyar sirfen da zan sha ya mamaye ni. Dole ƙanwar na ƙi, na sunkuya na ɗauko taɓarya kafin na ɗago na ji saukar bulala a tsakiyar bayana, azaba ta sa na wurgar da taɓaryar ina ihu haɗe da soshe-soshe. Ragowar mutanen da ke wurin babu wanda ya motsa ballentana na saka ran wani daga cikinsu zai kawo mini ɗauki, sai da Uwar tuwo ta gaji da dukana don kanta sannan ta nuna ni da murtukekiyar dorina. "Ki yi gaggawar ƙarasa surfen gabanki idan ba haka ba wallahi sai na sa Balele ya kai ki ɗakin duhu, shegiyar yarinya da idanu kamar na ƙwanƙwamai." Tun ba ta ƙarasa zagina ba na suri taɓaryar da a tsaye ta kusan tsayina, jiki na karkarwa na fara daka cike da tashin hankali. Ganin haka ya sa Uwar tuwo ta yi gaba tana buga wa sauran Bayin da ke tsaitsaye tsawa, da tafiyarta babu jimawa waɗansu zaratan samari biyu suka kewaye ni. "Shugaba wannan ba aikinki ba ne." Mamaki ya lulluɓe ni domin ko a mafarki ban taɓa cin karo da su ba, haka kuma suturun jikinsu bai yi kama da kayanmu na bayi ba. Na sake mamakin kalamansu da suke kirana da shugaba. Tsaye na yi ina bin bayan Uwar tuwo da kallo samakon har lokacin ina hango ta sai da ta ɗan yi nisa da ni, takaicin dukan da ta yi mini ya mamaye ni na fara ayyana da ina da hali sai na karɓi doriyar hannunta na zane ta ita ma ta ji irin abin da muke ji. Ihun da na ji Uwar tuwo na yi ne ya dawo da ni hayyacina, na kai ƙwayar idona wurin cikin mamaki nake bin ta da kallo. Kamar yadda na ayyana haka Uwar tuwo ke tsalle tana ihu, hatta ni da nake nesa da ita haka na riƙa jiyo sautin saukar dukan da ake yi mata.Ta jima cikin wannan halin sannan ta faɗa gefe ɗaya tana sauke ajiyar zuciya, kamar wacce aka ce na waiga ina juyawa wurin turmin na yi tozali da abin da ya daskarar da ni. Gabaɗaya geron da ke wurin an surfe shi an dake mini tas, tsoro ya mamaye ni da ganin wannan lamarin. Duk da ba sabon abu bane a wurina na ji kalamai daga cikin zuciya, amma a wannan karon na razana, "Kada ki  tsoro ta Shugaba domin firgici ba hali ko ɗabi'ar ahalinku ba ne." Jin haka ya ƙara mini ƙwarin gwiwa na ɗauki ƙatuwar ƙwaryar na ɗora ta a kaina da ƙyar, kafin na ƙarasa wurin da Uwar tuwo ke kwance tuni Bayi suka taimaka mata aka kai ta can ɓangarenmu na Bayi. Kallo ɗaya za ka yi wa Bayin da ke wurin ka fahimci kowa ya sha jinin jikinsa, don babu hayani tsit wurin ya yi kamar an yi mutuwa.   Kamar kullin idan kowannenmu ya dawo daga sashen da yake yi wa hidima, mukan taru a sashenmu na Bayi. Zaune muke gabaɗaya a tsakar gida, wasu daga cikinmu na zaune kusa da yayyansu suna wasa. Waɗanda suke da ƙanƙarta shekaru kamar nawa da ba su wuce sha uku ba suna kwance a jikin iyayensu, idanuwana suka ciko da ƙwalla sakamakon ganin ni kaɗai ce wari ɗaya ba ni da makusanci. Ko da ba ni da iyaye ya kamata wasu su tausaya mini su ƙaunace ni kamar yadda na ga wasu Bayin da aka samo marasa iyaye ake kula da su, me ya sa na kasance mai baƙin jini kowa ba ya ƙaunata?" Ba zato daga gefen kunnuwana na ji an furta mini. "Ke kike da kowa Hidaya! Kada ki karaya domin lokacin na nan da za ki tabbatar da haka." Abin ka da mai shirin kuka an jefe shi da kashi awaki nan take hawaye ya fara kai-kawo a ƙwayar idona. Jiki a sanyaye na miƙa zuwa gaban Jakadiya na tsugunna, da mamaki gabaɗaya suka juyo suna kallona. Ban damu da irin ƙalubalen da zan fuskanta ba, babban burina bai wuce ni ma na san wace ce ba. "Lafiya kika zo kika saka ni a gaba kamar tsohuwar mayya?" Gabana na dakan lugude na tattaro kalaman bakina da na guntso na fesa mata. "Don Allah Jakadiya su waye iyayena?" Kamar haɗin baki haka na ji sun tuntsire da dariya, sai da suka yi mai isar su sannan Jakadiya ta nuna wurin da Uwar Bayi ke zaune. "Akwai tarin bayanai dangane da samuwarki, ki tafi wurin Uwar Bayi za ta warware miki zare da abawa." Cike da ƙwarin gwiwa na miƙe cikin sassarfa na isa gaban Uwar Bayi, na baje tagwayen kunnuwana ina sauraron makoma da tushena.   Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta kai hannu ta rufe shafin littafin ba don ta gaji da karatun wannan hargitsattsan labarin mai cike da rikitar da kwanyar mai karatu ba. Mayar da littafin ta yi cikin akwatinta sannan ta ɗauko turaren da take amfani da shi a duk lokacin da za su yi wata mu'amala da Mai martaba. A cikinta ta soke shi sannan ta rufe ɗakinta ta fice kai tsaye ta wuce sashen sarki Abdul'aziz, haka kawai ta ji gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili. Babban tashin hankalinta bai wuce kada laƙanin jikin Takawa ya wargaza mata shiryayyan shirin ta a kan Maimuna ba. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚    07062062624. *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.   SHAFI NA BIYAR       Cikin mugun yanayin ta kafe shi da ƙwalaƙwalan idanuwanta masu razana duk wanda ya yi tozali da ita, a hankali Sarki Abdul'aziz ya fara ja da baya jikinsa na karkarwa. Bai yi tsammani ba ya ji bayansa ya bugu da bangon ɗakin, cikin tsinkewar zuciya yake sauke ajiyar zuwa. Da wata irin sanɗa ta taso daga kan gadon tana durfafo wurin da yake tsaye, ganin tana gabda cin masa ya sa ya fice da sauri daga cikin ɗakin ya ƙarasa wurin dogaran da ke tsaron sashensa. Yanayinsa kaɗai ne ya tabbatar musu da tabbas Takawa yana cikin damuwa, tun bai ƙarasa wurinsu ba suka zube cikin girmamawa. "Allah ya taimake ka ya ƙara lafiya da nisan kwana, ɗawisu sarkin ado mai taƙama da ikon Allah..." "Ya aka yi kuka bar waccan hallitar ta shiga har cikin turakata?" Mai martaba ya katse su fuska a tamke babu ɗigon fara'a. "Tuba muke ranka shi daɗe, Allah ya huci zuciyar amale a gafarce mu wannan ne na farko na ƙarshe." A daidai lokacin Jakadiya ta ƙarasa ita da Baiwa Saro hannunsu ɗauke da kayan lambun da ake kai wa Sarki Abdul'aziz kamar wannan lokacin. Dogaran ta gani sun nufi turakar Takawa kafin su ƙarasa su ka ga wata baƙar mage ta fito daga cikin turakar idanuwanta jawur kamar gauta tana bin mutanen wurin da wani irin kallo. A zabure Jakadiya ta furta. "Ka gafarce ni uban gidana ka yi mini afuwa, amma ba ni da masaniya game da sakacin Dogaran ƙofa da har suka bar kyanwar nan ta shiga cikin turakarka." Jakadiya ta yi maganar jikinta na karkarwa don ta san a duniya babu abin da Takawa ya fi tsoro sama da mage, wannan ɓoyayyan sirri ne da ba kowa ne ya sani ba saboda gudun kada magauta su fahimci lagonsa. Ita ma Jakadiya abin da ya sa ta sani tun wani  lokacin da ta taɓa shiga sashen Mai babban ɗaki (Mahaifiyar Takawa.) wata mage ta shiga har suma ya yi a wurin, kuma ko da ta ga haka sai da Mai babban ɗaki ta tsawatar mata a kan wannan sirrin. "A kiyaye gaba, ba na buƙatar sake ganin kowacce hallita a sashena." Gabaɗaya suka amsa masa cikin girmamawa.  Jakadiya da kanta ta shiga ta jera kayan lambun kamar kullin sannan suka fice bayan ta tambayi Takawa ko akwai wani abin da yake da buƙata, ya ba ta amsa fuska babu walwala. Har bayan wani lokaci Sarki Abdul'aziz bai saki jikinsa ba, ganin bai sake jin motsin komai ba ya sa ya ɗan saki jikinsa. Cike da ƙwarin gwiwa Fulani Umaima ta ƙarasa cikin turakar Mai martaba, ganinsa zaune a gefen gado kusa da baiwa Maimuna ya sa ta zaro idanu cikin fargaba har sai da ya fahimci ruɗewar da take ciki. "Lafiyarki Umaima?" Cikin kissa ta daidaita nutsuwarta ta ce, "Dama na yi mamaki ne ganinka shiru, kar dai ka jima kana jirana." Murmushi ya sakar mata haɗe da girgiza kai. Ta ƙarasa wurinsa asirtaccan ƙamshinta ya ratse hancinsa, ya lumshe ido cike da jin daɗin ƙamshinta. "Ki tabbata kin sa shi ya shiga bayan gida kafin ki saka wa Maimuna turare a gabanta." Kalaman Boka Bamaguje ya dawo mata raɗau a cikin kunnuwanta. Miƙe wa ta yi ta furta. "Sarkina bari na haɗa mana ruwa mu ɗan watsa ko?" Ba ta jira cewarsa ba ta nufi banɗaki ta haɗa komai da kanta sannan ta zuba turaren da Bamaguje ya bata, bayan dawowarta ta taimaka masa ya rage kayan jikinsa sannan suka wuce banɗaki. Da kanta ta ɗebi ruwan ta watsa masa cikin sigar tsokana, sai kuma ta yi farat ta furta. "Na yi mantuwa." Kallon da ya yi mata ne ya alamta mata yana buƙatar ƙarin bayani daga gare ta. "Ina zuwa." Kawai ta furta ta fice a gaggauce. Sai da ta tabbatar da ta rufe ƙofar ta baya sannan ta koma turakarsa cikin sauri ta ɗaga doguwar rigar Maimuna ta kwara mata turaren a ƙasanta sannan ta shafa mata a fuskarta, ita ma ta murtsuke jikinta da shi ta rage kayan jikinta ta sake komawa cikin banɗakin. Tana shiga ƙamshinta ya daki hancinsa, take ya ji wani irin yanayi ya tsarga masa. Buƙatar ya kusance ta ta yunƙuro masa, ganin saƙwannin da yake aika mata ya tabbatar mata da haƙonta zai cim ma ruwa, don haka ta fara neman shawarar da za ta yanke wa kanta. A hankali ta yakice shi tana faɗin, "Sarkina a banɗaki muke mu ƙarasa turaka." Bai musa mata ba, ta ƙarasa sheƙa musu ragowar ruwan sannan suka fito hannunta na riƙe da shi, idanuwansa a rufe suka ƙarasa don haka ko da ta zaunar da shi a gefen gado ta ga ya rarumo Baiwa Maimuna da ke zaune kamar gawa. Fulani Umaima ta koma gefe ta zuba masa ido zuciyarta ƙal, tana nan tsaye Takawa ya gama mu'amalarsa da Maimuna ya koma gefe ɗaya sai gani ta yi numfashinsa ya ɗauke. Da sauri ta ƙarasa ta ɗebi najasar jikinsu ta isa bakin rijiyar da tun da take shiga cikin turakar ba ta taɓa taka wurin ba, wata irin kuɗa ta fara ji a cikin kunnuwanta ga wata 'yar juwa-juwa da take ji sama-sama. A haka ta samu ta zuba najasar a kan rijiyar take murfinta ya buɗe, wata baƙar ƙura ta turnuƙe ta. Sai daga baya komai ya washe, ganin haka ya sa Fulani Umaima ta koma ta janyo hannun Baiwa Maimuna sai da suka je bakin rijiyar Fulani Umaima ta furta. "Maza ki shiga rijiyar nan da ƙafar hagu." Ba musu Maimuna ta ɗaga ƙafarta ta zura cikin rijiyar ta zauna a kan wani mulmulallan baƙin dutse. Kamar yadda Bamaguje ya gaya mata Maimuna na gama shiga murfin ya taso da kansa ya rufe ruf. Ta koma can gefen Sarki Abdul'aziz ta kwanta tamkar da ita Takawa ya gama mu'amala. Bayan ɗan wani lokaci Mai martaba ya fara motsawa, jin haka ya sa Fulani Umaima ta fara sauke ajiyar zuciyata tana rarumo shi cikin kissa da kisisina. Wani irin nauyi dum! Kansa yake yi masa don haka ya gagara tunano abin da ya faru a baya, ganin yanayin da suke ciki ya sa ya sakar mata ajiyar zuciya ya yunƙura suka wuce banɗaki don tsaface jikinsu. Irin rawar jikin da yake yi a kanta ne ya sake tabbata mata da tabbas alƙaluman tsafin Bamaguje ba su zube a ƙasa banza ba, ta ci gaba da narke masa tana cin karenta babu babbaka. Daren ranar a sashen Sarki Abdul'aziz ta ƙarashe shi har zuwa wayewar gari. Cikin abin da bai fi wuni biyu ba, maganar haihuwar Fulani ta yaɗu cikin da wajen Masarautar Huddam, musamman da ya kasance an san Takawa ba shi da ɗa namiji sai a wannan lokacin. Manyan mutane da masu kuɗi haka suka dinga zuwa suna bada gaisuwa haɗe da yi masa barka da samun ƙaruwa, mafi yawa daga cikinsu har da sha tara ta arziƙi suke kawowa. Duk da Fulani Umaima ta san jaririn a nakashe yake hakan bai hana ta jin ƙyashi, baƙin ciki da ƙunci a kan kyaututtukan da Fulani Babba take samu ba. A lokacin sai ta tsiri kwanciya da tsirfar ciye-ciye wani lokacin har amai take ƙaƙalowa a turakar  Mai martaba, duk da cikin jikinta babu abin da yake saka ta. Ganin haka ya ɗaga hankalin Takawa har ya aikata sashen magunguna aka kira masa Ungozoma da jikar Baushe don su duba ta su ba ta magani. Tashin farko aka sanar wa da Sarki cikin da ke jikin Fulani Umaima, farin ciki kamar zai zuba ruwa a ƙasa ya sha. Ita kuwa Fulani Umaima ko kaɗan ba ta nuna wa Takawa ta san da cikin jikinta ba, nan ta shiga gwalangwaso da feleƙe wani lokaci hatta ƙamshin Turakarsa ce wa take ba ta so. Cikin wannan yanayin aka ɗebi kwanaki mai jego tana ɓangarenta tana jego ita kuma Fulani Umaima tana rainon cikinta, gabaɗaya gidan sarautar ya zagaye da ƙananan maganganu. Jin labarin cikin Fulani Umaima da Fulani Babba ta yi ba ƙaramin faranta ranta ya yi ba, kuma rashin ganinta kwana biyu a ɓangarenta ko kaɗan bai dame ta ba don ta san yadda laulayin ciki yake ba shi da daɗi. A ɓangare ɗaya Fulani Babba na cikin matsanancin tashin hankali sakamakon yadda fitsarin da yake zuba daga jikinta yake sake ta'azzara, tun tana ɓoyewa har ya zamana sai da Baiwa Zainaba ta fahimci halin da take ciki, ga shi abin kullin gaba yake yi da ta kwanta ko bacci minti biyar ba ta yi tana farkawa sai dai ta ji ta sharkaf da fitsari, ga kuma jinin biƙi duk shimfiɗarta ta haɗu ta dagule. Ana gobe suna da asuba bayan ta tashi ta sake ganin wurin ya yi sharkaf da wani irin zarnin da ke tashi har ya wuce misali. A wannan lokacin take zuciyarta ta karye ganin lalurar tata a kullin gaba take yi ba baya ba, a daidai lokacin yayarta da suka zo daga Masarautar Bassar ta shiga ɗakin, ganin ta a zaune ya sa ta ɗan yamutsa fuska. "Fatima wai mene ne yake wari ne?" Da yake mai shirin kuka ne aka jefe shi da kashi  awaki take Fulani Babba ta fashe da matsanancin kuka, da mamaki Halima ta furta, "Fatima me yake faruwa ne?" Sai da ta yi mai isarta sannan ta miƙe tana nuna wa yayarta ta ce. "Ki duba ki gani Yaya Halima wai ni ce yau nake malala fitsarin kwance. Ni dai na fi zargin tun ranar na haihu na haɗu da wannan iftila'in, duk yadda zan yi takatsantsan ina runtse idona duk gajarta bacci sai dai na tsinci kaina a cikin fitsari." Jakadiya da ta zuro kanta da niyyar sanar da Fulani Babba ruwan wankanta ya yi zafi ta yi fakare tana sauraronsu. Yaya Halima cike da damuwa ta jinjina kai. "Kin sanar da Mai martaba?" Girgiza mata kai kawai ta yi don ba ta son ta buɗe baki har ta iya sanar da danginta zaman doya da manjar da ke tsakaninta da Takawa. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta furta, "Ya zama wajibi na sanar da Yakumbo a nemar miki magani, domin wannan fitsarin ba na lafiya ba ne. Ni fa dama zuciyata da hankalina ba su taɓa aminta da wannan kishiyar taki ba..." Da sauri Fulani Babba ta katse ta. "Yaya kada ki zargi Umaima domin ban taɓa zarginta a kan wani mugun abu ba, zamana da ita babu wata matsala ni dai a yi mini magani amma Allah ya sani babu sa hannun Umaima a lalurata." Inuwar da Yaya Halima ta hango a wurin labule ya sa ta furta. "Waye a wurin nan?" Jikina na rawa Jakadiya ta faɗa ɗakin tana faɗin, "Allah ya taimaki Fulanin Takawa, uwar yariman gobe da yardar Allah. Dama ruwan wanka na kwashe na zo sanar da uwar gijiyata." Daga cikin ɗakin Fulani Babba ta furta. "Saƙonki ya isa Jakadiya." "Godiya nake zinariya fara mai farar aniya bangon talakawa da marasa gata, Allah ya raya mana yarima ya gaji karagar da babu kamarta a faɗin nahiyar nan." Yaya Halima ta amsa tana bin Jakadiya ta kallon tuhuma. Sai da ta ga Jakadiya ta fita sannan ta furta. "Da alama wannan farar zuciya taki na iya kai wankin hula ya kai ki dare, jikina yana ba ni idon masarautar nan yana kanki." "Yaya Halima shi zato zunubi ne! Don haka..." Da sauri ta katse ta. "Dama ki ajiye zurfin cikinki kin amayar mini da abin da yake cikinki domin abokin kuka ba a ɓoye masa mutuwa." Idanun Fulani Babba ya ciko da ƙwalla don ita kaɗai ta san zafin da zuciyarta take yi mata, amma sanin Yaya Halima na daga cikin irin marasa haƙuri ya sa ta danne damuwarta ta furta. "Babu wani abu da yake damuna Yaya Halima, idan ma akwai na fauwala wa Allah saboda saniyar da ba ta da jela Ubangiji ne ke kore mata ƙuda." Yaya Halima ta taɓe baki ta fice ba tare da tanka mata ba, Fulani Babba da ta yi shirin wanka tana kai idanunta kan jaririnta. A kullin ta kalle shi zuciyarta na wasu-wasi a kan ingancin lafiyarsa, sai dai babu yadda za ta yi tun da ba fada gare ta a wurin Takawa ba balle ta yi masa bayanin halin da jaririn yake ciki.   Kamar za ta tashi sama haka Jakadiya ta yi sashen Fulani Umaima a lokacin Fulani na shaƙar bacci ko sallar asuba ba ta yi ba duk da gari ya waye garau, da farko Bayin da ke kula da ita sun sanar da Jakadiya Fulani na bacci. Amma da yake bakinta cike yake fal da tsegumi a dole haka ta shiga tana ta rangaɗa sallama. Kamar a mafarki Fulani Umaima ta ji sallamar Jakadiya wanda hakan ne ya alamta mata akwai wani muhimmin abin da yake tafe da ita, tana daga kwance ta sa a yi wa Jakadiya iso har cikin turakarta. Jakadiya na shiga ta zube a ƙasa, "Hutawarki lafiya tauraruwar Mai martaba uwar yariman gobe da yardar Ubangiji. A yi mini aikin gafara na tashi uwar gijiyata a farar safiya..." Da hannu Fulani Umaima ta katse ta, kamar ba za ta yi magana ba sannan ta ce. "Akwai magana a bakinki Jakadiya don na tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa." Jakadiya ta yi mata jinjina da hannu. "Allah ya ƙara yawan rai wannan yarinyar da nake ganinta mai hankali ashe lumbu-lumbu ce wutar ƙaiƙayi?" "Jakadiya tafi kanki tsaye. Fulani Umaima ta faɗa a gajarce. "Halima yayar waccan ragowar fitsarin, ita na ji tana shirin ɓallo mana ruwa. Ni kuma na ce har gaban abada kwaɓarmu ba za ta yi ruwa tsululu ba, sai dai a mutu har liman kowa ya rasa sallah..." Jakadiya ta kwashe duk maganganun da ta ji Fulani Babba suna yi ita da Yaya Halima. Murmushi Fulani Umaima ta saki. "Daga kallon da na ga tana bi na da shi ya sa na fahimci ruwa ba zai taɓa tsami banza ba. Ta shi ki je Jakadiya idan hantsi ya fito ki dawo akwai kyautar samirar alkaki da nakiya, zan haɗa miki da fallan zani da gorar maɗi. Na rantse da Allah sai na tabbatar wa Halima ba a taka shuri kowanne iri a zauna lafiya." Jakadiya ta sake zubewa. "Godiya nake uwar ɗakina, godiya nake zinariyar Mai martaba uwar duka mazauna ƙasar Huddam da kewayenta. Allah ya buɗi ido lafiya ya kawo mana Yarima cikin ƙoshin lafiya." Fulani Umaima ba ta amsa ba, inkiya ta yi mata da ido. Ganin haka ya sa Jakadiya ta fice daga ɗakin don ta san ba za ta amsa mata ba.   Washegari ya kama suna jaririn Fulani Babba ya ci suna Abubukar Sadiq, haka kawai Sarki Abdul'aziz ya tsinci kansa cikin farin ciki duk ba ya iya nuna soyayyarsa  game da yaron, ya so a gayyaci masu wasannin al'adar bahaushe amma wata irin fargaba yake ji da tsoron Fulani Umaima a zuciyarsa. Da ya yi wani yunƙuri sai ya ji kamar idan ya aikata bai kyauta wa Fulani Umaima ba. A haka aka ci taron suna sai dai hatta Bayin da ke cikin masarautar ranar sai ta zame musu daban sakamakon walwala da suka samu ta hanyar sauya abinci da sakewa. Fulani Umaima ta saki jiki sosai a ranar da kanta ta gayyaci 'yan wasan tauri aka gudanar da wasanni, tamkar babu wani mugun ƙuduri a zuciyarta. Bayan suna da kwana biyu 'yan uwan Fulani Babba suka tattara kayansu suka koma masarautarsu, ko a ranar da za su tafi sai da Yaya Halima ta jaddada wa Fulani Babba suna komawa za a aiko mata da magungunan da suka da ce. Ita ma kuma Fulani Umaima a ranar da suka tafi a ranar ta dira wurin Bamaguje ta shimfiɗe masa bukatunta, kuma take ya zartar mata da su, haɗe da jinjina mata bisa aikin Baiwa Maimuna da ta aiwatar ba tare da an samu matsala ba. Sai dai abu ɗaya da ya sanar mata ne ya nemi hargitsa kwanyarta har ta koma gida ta gagara runtsawa tana tunanin makomar abin da zai biyo baya. *Masu ganin laifin Fulani Babba na rashin yin addu'a kada ku manta labarin an sanya ya faru a shekaru saba'in baya da suka wuce (1953) Kun ga a lokacin ilimin addini bai yawaita ba, ba kamar yanzu da ilimi ya zaman ruwan dare ba. A mafi yawan wancan lokacin, camfi da tsubbace-tsubbace sun fi ƙarfi a kan yawaitar addu'a, babu wayewar kan da idan abu ya same ka kace bari ka duƙufa ba dare ba rana ka kai wa Allah kukanka.* _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚 07062062624 *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.   SHAFI NA SHIDA     Ajiyar zuciya Fulani Umaima ta sauke ta zauna a gefen gado, wani irin gumi ya fara tsattsafo mata. "Binciken da nake kan yi dangane da abin da kike ɗauke da shi a cikin cikinki, na shafe tsawon kwanaki ina bincike har yau na gagara sanin mene ne a ciki. Kullin duhu nake mai ɗauke da rashin alkairi, duhu ne mai ɗauke da tururi da ke ƙone duk wani makusancinsa. Ba ke kaɗai ba ni kaina ina da burin sanin me za ki haifa domin amfanar gobena. Ina buƙatar Magaji a halwar tsafina Umaima." A razane ta ɗago tana kallonsa, "Ban gane kalamanka ba Bamaguje, me ye alaƙar abin da yake cikina da gadon halwar tsafinka?" Bamaguje ya saki murmushi. "Wannan sirrintaccan sirri ne tsakanina da mahaifiyarki, ba alaƙar abin cikinki ya kamata ki tamabaya ba. Amma mu jirayi lokacin kin san ko ba daɗe ko ba jima akwai lokacin da ya za ta ɗakin ƙanwa." Sallamar Baiwa Salame ta katse Fulani Umaima daga duniyar taunanin abin da suka tattauna da Boka Bamaguje. Ba ta amsa mata ba don haka Baiwar ta koma, Fulani Umaima ta miƙe ta ci gaba da kaiwa da kawowa damuwa cunkushe a zuciyarta. Kamar wacce aka tsokara haka ta miƙe ta ƙarasa ta ɗauko akwatin sirrinta, ta ɗauko littafin da Bamaguje ya bata. Sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta buɗe shafin da ta tsaya da karatu.   Na jima a tsugunne gaban Uwar Bayi ina tsammanin kalamanta har sai da na fara yanke ƙauna da samun abin da nake buƙata, ba zato na ji muryarta a tsakiyar kaina. "Hidaya labarinki cike yake da almara, al'ajabi da ban mamaki. A tsammanina ni ce mace ta farko da na fara tozali da ke a cikin masarautar nan, ban sani ba ke 'yar cikinta ce ko akasin haka. Abu ɗaya na sani watarana na tafi isar da saƙon Fulani Hauwa na gan ki tsaye a jikin bishiyar kukar da ke bayan ɗakunan Bayi kina rusa kuka, gudun kada na yi latti a aiken da aka yi mini ya sa sai da na kai na dawo har lokacin ba ki daina kuka ba. Da yake a ranar an shigo da sababbin Bayi sai na yi tsammanin 'yar ɗaya daga cikinsu ce yawo ya kawo ta nan take kuka ta gaza gane hanya wurin mahaifiyarta. Sai na riƙe miki hannu muka wuce sashen Bayi na ƙaraci cigiya babu wanda yace 'yarsa ce, to da yake a cikin Bayin da aka kawo akwai wasu mata biyu da suka rasu sai na yi tsammanin mahaifiyarki na ɗaya daga cikinsu. Amma daga baya sai na ga 'yan uwansu suna cewa sam ba tare da su aka kawo ki ba, wannan dalilin ya sa kika ci gaba da zama a sashen Bayi ba tare da iyaye ba." Kalama Uwar Bayi suka zo ƙarshe a daidai lokacin da ni kuma bakin ƙomar idaniyata ta ɓalle, sai da na yi kukana mai isata na dube ta. "Haka zan ƙare rayuwata ba tare da sanin makomata ba." Uwar Bayi ta wara hannuwa. "Abin da na sani kaɗai na sanar da ke, idan Allah ya sa akwai rabo sai ki gansu ko a nan gaba ne." Yau ita ce rana ta farko da na ji daddaɗan kalamai daga bakin wani daga cikin Bayin da nake mu'amala da su, don haka na ƙirƙiri murmushin da bai kai zuci ba na furta. "Shi kenan ina godiya Uwar Bayi da wannan bayanin naki." Babu wanda ya sake tanka mini haka na tashi jiki a sanyaye kamar kazar da aka jefa da wuƙa na koma mazaunina na farko na zauna ina jin zuciyata babu daɗi. Ina jin su suka ci gaba da hirarsu sai dai ko kaɗan ba na fuskantar koda kalma ɗaya, zuciyata ta yi nisan kiwo a fannin tunani da na gagara janyo ta balle ta gane in da hirarsu ta dosa.   Wani farin tsoho mai ɗauke da farin gemu na gani yana tunkaro ni, tsananin kammanin da muke yi da shi ya sa na tsaya cak ina kallonsa. Tun da na zo duniya ban taɓa ganin mai kamceceniya da ni ba, ban yi tsammanin ya kusance ni ba don haka na ji hannuwansa a cikin nawa. "Kada ki damu da sai kin san wace ce ke, kina da kowa kuma wannan masarautarki ce gadonki ce halak malak, sai dai ina mai ta'ajibin sanar da ke har duniya ta tashi ba za ki ga mahaifiyarki ba. Ni ne mahaifinki! Ni ne mahafinki!! Ni ne mahaifinki!!!" Firgigit na farka daga mafarkin da nake yi, na juya ina kallon yadda mutane ke baccinsu hankali kwance. Mamaki ya kama ni, cikin damuwa na furta. "Ya aka yi ka zama mahaifina? Kuma me ya sa kuka guje ni." Kamar alamara na ji an furta mini. "Ba mu guje ki ba, mun kawo ki karagarki ne don ki karɓi abarki." Waige-waige na fara yi don ganin mai tanka mini a cikin tsohon daren nan, har na yunƙura zan tashi sai na ji tsoro ya mamaye ni, ba shiri na koma na zauna bacci ya ƙaurace mini. A lokacin da bacci ya fara fisga ta na ji Uwar bayi tana tashinmu cikin hargowa da masifa kamar yadda ta saba duk asubar fari.    A haka na ci gaba da gudanar da rayuwa cikin rashin daɗi, rashin 'yanci da ƙangin bauta. Mu Bayi ba mu da wani gata ba musan ci mai kyau da sha mai kyau ba, ana cikin haka watarana saƙo ya iso gare mu ana san Uwar bayi ta sake zaɓen Bayi ta kai sashen Fulani Hauwa kulu, haka kawai na ji gabana yana tsananin faɗuwa. Aka saka mu muka yi layi cikin tsautsayi ƙaddara ta yarfo mini hannunta, Uwar Bayi ta zaɓa har da ni a cikin mutane ukun da Fulani Hauwa take buƙatar ƙari.Tun da nake rayuwa a cikin Masarautar ban taɓa shiga sashen Fulani ba, hasali ma ban taɓa tozali da ita ba, sakamakon rashin imanin da nake jin ana faɗa game da ita. Wannan ta sa nake takatsantsan a kan abin da zai sa na kai kaina sashenta. Tun da muka dumfari hanyar sashen Fulani nake jin jikina yana yi mini wani irin zafi, hayaniya na fara ji sama-sama a kaina ga wani kiɗan tambura da nake ji yana tashi a tsakiyar kunnuwana. Sai dai yadda na lura ni kaɗai nake jin waɗannan baƙin al'amuran da ke yi wa duniyana dirar mikiya. Take gumi ya fara keto mini sakamakon yadda nake jin zafin na ratsani kamar wacca aka tsire a tukubar tsire. A babban ƙofar rumfar (Falo) Fulani Hauwa na coge, sakamakon yadda nake jin ana fisgata. Hayaniyar da nake ji ta fara rikiɗa zuwa muryar da nake jin tamkar na taɓa sanin mamallakiyar muryar. "Barka da zuwa Sarauniya." Na ji an furta. Waige na fara yi amma ban ga kowa ba, na riƙa jin busar sarewa a tsakar kaina ba tare da na ga masu yi mini ba. Ina nan tsaye na ji Uwar Bayi na faɗin. "Ku yi hanzari kada ku fusata Fulani kuke tafe laƙai-laƙai kamar marasa laka a jiki." Da sauri na ci gaba da tafiya har muka ƙarasa babban rufar Fulani da ta ƙayatu da kayan alatu kala-kala. Kaina na ji ya yi girma wata irin ƙasaita, isa da tsantsar izzar mulki na ratsa ni, da ƙyar nake taku cikin ƙasaita. Uwar Bayi da sauran Bayin da muka taho tare suka tsaya cak a bakin wata mashinfiɗa wacce bayi suke tsayawa idan sun shiga wurin Fulani Hauwa kulu. Ban kalle su ba na zarce kan ƙasaitacciyar karagar da ke cikin falon, na zauna ina kallon su Uwar Bayi ɗaiɗai. Da zamana na ji wani abu ɗau! Yana zagaye ƙoƙon kaina. Uwar Bayi kusan mutuwar tsaye ta yi ganin ɗanyan aikin da na aikata, bakinta na rawa ta furta mini. "Hidaya...hankalinki ɗaya kuwa? Kin san a fadar wacce kike?" "Ya kamata ki gyara linzamin harshenki, idan ba haka ba sai na sa an datse shi nan take. Wannan fadata ce..." Ashar ɗin da Fulani Hauwa kulu ta saki ya katse kalamaina, na dube ta cikin tsadaddiyar shigarta ina ƙare mata kallo. "Uban waye ya halatta wa wannan ƙasƙantaciyyar zama a karagata?" Cikin isa da ƙasaita na ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, kamar ba zan amsa ba na ɗago ina kallonta a wulaƙance. "Wannan karagar iyaye da kakannina ce don haka ki gyara kalamanki." Na lura da razani a saman fuskarta, ɗan yatsanta na rawa ta nuna ni. "Ta tabbata ke ce Hidaya ko?" Na jingina da jikin kujerar na furta. "Ba tsammani ba ne ni ce Gimbiya Hidaya." Wata gwauruwar ajiyar zuciya na ji ta sauke. "Tabbas da alama tarihi zai kuma maimaita kansa. "Tarihi tuni ya sake maimaita kansa tun da gani na wanzu a gabanki." Fulani Umaima  ta rufe littafin tana jin kanta na sarawa don a kullin labarin Hidaya ƙara hargitsa kwanyarta yake. Ta wurga shi cikin akwatinta tana sakin tsaki a fili don ba ta jin za ta sake ci gaba da karanta wannan rikitaccan labarin.    Komawar su Yaya Halima Masarautarsu da kwana ɗaya labari ya dawo wa Fulani Babba na sabuwar lalurar da ta afka wa Yaya Halima na kurumcewa da makanta, hankalin Fulani Babba ba ƙaramim tashi ya yi ba. Da yake jego take yi babu damar ta tafi dubiya haka ta zauna ta ci kukanta a cikin ɗaki, ta sake ayyanawa zuciyarta ko da wasa ba za ta sanarwa da mahaifiyarta halin da take ciki ba don kar damuwa ta yi mata yawa. BAYAN SHEKARA GOMA      Tafe suke a cikin wani baƙin ƙasurgumin daji mai matuƙar hatsarin gaske, su kansu sukan yi takatsantsan wurin shiga irin waɗannan dajijjikan sakamakon miyagun hallitu da iskokin da ke cikinsa. "Mai gado wai ni kam kin taho mini da baƙar bakata?" Umaru ya faɗa yana sake leƙen wani koren maciji da ke saƙale da wata koriyar bishiya. "A'a Malam tsakani da Allah ni kam na manta ka san sai da na ce idan za mu fito ka tuna mini." Da sauri ya ciro wata ƙanƙanuwar kwari da baka daga cikin ƙugunsa, bai cika harbi da ita ba don haka ya so Mai gado ta taho mata da farar bakar wurinta.  Ya kalli macijin haɗe da matsa wata laya da ke saƙale a wuyansa, ya sakar wa macijin harbi nan take ya tsire shi wani koren ruwa mai kauri ya fara fita daga jikinsa. Yana shirin miƙa hannu ya ciro kibiyar daga can gefensu suka fara jiyo numfarfashi, Mai gado da sauri ta fara matsawa don tabbatar da zarginta. "Wash wayyo! Ku taimaka mini, ku kawo mini ɗauki tsafi zai taimake ku. Tsafi zai shiga lamarinku, ku taimaka mini kada na mutu idan na mutu tsafi zai yi fushi da ku." Gaban Mai gado ya faɗi ganin wata matashiyar mace mai tsohon ciki tsugunne babu kaya a jikinta, ƙugunta ne kaɗai ɗaure da ganye sai saman ƙirjinta. Kanta da wani irin cukurkuɗaɗɗan gashi ya zubo har ƙirjinta. "Malam zo ka ga." "Kada ki taɓa komai Mai gado, har yanzu ba ki gama sanin sharrin daji ba. Wannan ba kamar sauran dajijjika ba ne, ki yi takatsantsan." Yana ƙarasawa idanunsa suka yi tozali da matar, ta galabaita da alama naƙuda take duba da yadda jikinta ya ɓaci kace-kace. Mai gado ji ta yi ba za ta iya daurewa ba don haka ta ƙarasa ta ruƙo ta tana faɗin. "Baiwar Allah me ya kawo ki naƙuda cikin dokar dajin nan?" Wani irin nishi suka ji ta yi cikin galabaita da fita hayyaci tana faɗin. "Tsafi, tsafi ka dafa mini. Abin bauta ka tserar da jinina ko ɗon ta gagara magautana, tsafi ka taimaka mini." Rufe bakinta babu jimawa suka ji ta ƙwalla ƙara nan take ta haifo jaririyar 'yarta mai tsananin kama da ita. Mai gado na shirin taɓa jaririyar da sauri matar ta dakatar da ita, ta hanyar ture hannunta tana girgiza mata kai. "Zuri'ar RUMZU daban take da sauran al'umma, idan muka haihu tashin farko jinin wata al'umma ba ta isa ta taɓa mana 'ya'ya ba har sai mun gama da 'ya'yanmu ake taɓa mana su. Idan ba haka ba yanzu za ki mutu, abin bauta zai hallaka ki." Mai gado ta ɗan zaro idanu cikin tsananin mamaki. Umaru da ya juya bayansa ya jinjina kai yana taɓe baki. Hannu ta sa a ƙugunta ta ciro wata ƙaramar baƙar aska ta yanke wa jaririyar cibiya, ta sa wata siririyar fata ta ɗaure cibiyar tamau. Hannunta ta saka ta lakuto jinin da ke fita daga ƙasanta ta shafa a saman goshin jaririyar lokaci ɗaya jaririyar ta tsanyare da wani irin matsanancin kuka, jinin da ta lakata mata a goshi ya shiga wata irin tafarfasa a kan goshin jaririyar. Wani irin baƙin jini ya fara zuba daga cikin hancin jaririyar, kunnuwanta da ƙasanta. Mai gado tana tsaye tana kallon abin da matar take yi cikin al'ajabi da tsananin mamaki har sai da tsoro ya fara kamata. Ganin jinin ya zarce ƙa'ida ya sa matar ta saka bakinta ta zuƙo shi sannan ta fesar a gefe, take ciyawar wurin ta ƙone ƙurmus. Ta jima tana zuƙe jinin jikin jaririyar tana ɗiban jinin gabanta tana zubawa a goshinta, idan ya tafasa sai ya shige jikin jaririyar. Sai da matar ta gama ta ɗago ta dubi Mai gado cikin karyewar zuciyata tana faɗin, "Ban san ku su waye ba, amma na tabbata daga yanayinku ku masu karamci ne kuma tsafi zai shiga lamuranku ya dafa muku..." Da sauri Umaru ya waigo ya katse ta. "Baiwar Allah mu ba mu dogara da tsafi da sihiri ba, mun dai dogara da Ubangijin sammai da ƙassai." Jinjina kai ta yi tana murmushi ta furta. "Koma da wa kuka dogara ban damu da na sani ba, zan bar muku amanar 'yata domin na san dangina ba za su bar ni ba mutuwa zan yi, don na hangi tsinin mashin tsafin da Mahaifina ya wurgo min, idan ban damƙa muku ita ba tabbas har ita za su hallaka mu. Ba a nan doron ƙasa ba, ko ƙarƙashin ƙasa na nutse matuƙar ina numfashin na tabbata zuri'ata ta Rumzu ba za su bar ni ba." A firgice suke kallonta. "Wace ce ke? Mutum ce ko aljan?" Mai gado ta wurga mata tambaya a tsorace. "Sanin matsayin hallitata ba shi ne mafita ba, domin a yanzu ba lallai ya amfane ku da komai ba. Ga amana zan bar muku ku dubi darajar abin bautarku ku riƙe ta amana, na so a sanya mata suna HAIZAT amma dalilin mahaifinta ya nunke nawa don haka ya ce mini ya fi son a saka mata sunan JAWAHIR, ban san ma'anar sunan ba don ba ya daga cikin sunan zuri'ata. Sai dai na tabbata wannan sunan zai amfane ta zuwa nan gaba, idan ta isa zama budurwa ku ɗauke zuwa bakin kowacce irin bishiyar kuka akwai ajiyar da mahaifinta ya taɓa yi wanda ita za ta tono gadon da zai bayyanar da ita jininsa ce da hannunta.  Wannan jaririyar ita za ta sanar da ku asalin wace ce ni har zuwa zuri'ata ta Rumzu, tun daga zubin hallita har zuwa tushenta. Na san dangina da bibiya, kafiya da matsanancin ruƙo duk rintsi kada ku bayyana ba kune asalin iyayenta ba matuƙar za ku shiga baƙon wuri ko al'umma, wataƙila ta iya tsira da rayuwarta daga kaidinsu." Tana gama maganar ta ɗora jaririyar a kan saman wani ƙaton gidan tururuwa, ta damƙi ƙasar gidan tururuwar tana runtse idanunta haɗe da furta waɗansu irin kalaman tsafi da su Mai gado ba su taɓa ji ba, tana gamawa ta shafa a jikin jaririyar gabaɗaya, take jinin da ke saman goshin jaririyar ya ɓace ɓat. Ta sunkuya saitin kunnen jaririyar tana yi mata raɗa, lokaci ɗaya jaririyar ta yi shiru tamkar wacce take sauraron kalaman mahaifiyarta. Wani irin jini ne ya ɓalle wa mahaifiyarta amma duk da haka cike da ƙwarin gwiwa da dakiyar zuciya ta ɗauki jaririyar ta fara takawa har zuwa bakin ramin kwarmin bishiyar kukar da ke gefenta ta ɗora jaririya a ciki, ta saka hannu ta dafa saman goshinta nan take suka ga ta fara wata irin jijjiga, idanunta suka firfito numfashinta ya ɗauke rai ya yi halinsa. Daga Umaru har Mai gado kusan mutuwar tsaye suka yi saboda al'ajabi don tun da suke a duniya ba su taɓa ganin makamancin irin wannan lamarin ya faru a gabansu ba. Mai gado ce ta iya motsawa ta ƙarasa ta ɗauki jaririyar da mamaki ta kalli Umaru jin jikin jaririyar ya yi wani irin sanyi kamar ƙanƙara. "Malam yanzu ya zamu yi da wannan gawar?" Ajiyar zuciya ya sauke yana shirin yin magana suka ga gawar matar na matsawa haɗe da nutsewa cikin bishiyar kukar da take jigine a jikinta. Cikin tsoro suka ja da baya suna kallo, kafin wani lokaci babu gawar babu alamarta ta nutsa cikin bishiyar kukar sai shatin jinin da ke manne a jikin bishiyar. Jiki na karkarwa Mai gado ta ajiye jaririyar a ƙasa tana ja da baya ta furta. "Mai gida Allah ya sani ba zan iya riƙon wannan abin ba, domin ba na ko tantama mahaifiyar yarinyar aljana ce ita kanta yarinyar dubi irin siddabarun da mahaifiyarta ta yi mata kafin ta mutu." Cike da gamsuwa Umaru ya ɗago zai yi mata magana, gabansa ne ya yanke ya faɗi sakamakon mugun gamon da ƙwayar idonsa ta yi. Da sauri ya ja hannun Mai gado suka faɗi can gefe haɗe da kurma ihun neman taimako. _Ummou Aslam Bint Adam_ 🌚    07062062624 *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye.   SHAFI NA BAKWAI       Koren macijin da Umaru ya kashe tun kafin haihuwar matar nan suka hango ya sulalo ya kafe su da ido yana kallo tamkar zai far musu da sara, suna nan cikin tsinkewar zuciya suka ga ya ƙarasa wurin jaririyar ya kanannaɗe ta, suna daga wurin da suke a gefen Umaru ya ce. "Mai gado an ya yau mun shigo dawa a sa'a kuwa?" Da sauri ta girgiza masa kai. "Tun wuri mu kama hanyar gida." Cikin sanɗa suka miƙe da niyyar tafiya sai dai bisa ga mamakinsu babu macijin babu alamarsa, don haka suka nufi hanya da niyyar tafiya. Cak Mai gado ta tsaya tana waige. "Tsayawar me kika yi Mai gado?" "Mai gida zuciyata ta karaya, ba zan iya tafiya na bar yarinyar can ba. Ka dubi yadda mahaifiyarta ta aminta har ta damƙa mana amanarta. Ba mu sani ba wataƙila samunta babbar rahama ne a tattare da mu, ta wani fannin ma gani nake Allah ne ya azurta mu da samunta ka duba ka gani haihuwata huɗu duk yanzu babu rayayye, idan muka bar ta a wannan ƙungurmin dajin ba mu san wacce irin rayuwa za ta gudanar ba." Jikin Umaru ya yi sanyi ya waiga yana hango jaririyar da ke tsala matsanancin kuka. "Mu je na ɗauko ta In Shaa Allah, Allah zai kare mu tun da ya ga kyakkyawar niyyarmu." Da haka suka rankaya suka wuce har gaban jaririyar suka ɗaukota, Mai gado ta kunto ɗankwalinta ta nannaɗe ta a ciki sannan suka nufi hanyar da za ta sada su da gida. Sai da fargabar da Umaru yake ciki ba wuce irin tarbar da mutanen ƙauyensu za su yi musu ba, musamman idan aka samu akasi wani al'amarin almara ya faru kamar yadda suka gani daga wurin mahaifiyarta. Sai dai sun ɗaukar wa kansu alƙwari babu wanda za su furtawa silar samuwar yarinyar don kada ta taso cikin tsangwama da ƙyara. Masarautar Huddam     Ɗan matashin ne mai kimanin shekara goma zaune a cikin fadar Sarki Abdul'aziz a kan shimfiɗaɗɗiyar shimfiɗar alfarma yana sanye da rantsattsiyar alkyabba. Kallon mutane yake yi ɗaiɗai fuska a murtuke babu walwala, kallo ɗaya za ka yi masa ka tabbatar da mulkin gadarsa ya yi ba taka-haye ba. Gajiyar da ya yi da zaman cikin fadar ya sa ya miƙe cike da izza yana taku kamar ba zai taka ƙasar ba. "Takawarka lafiya Yariman masarauta, a huta lafiya sarkin gobe da yardar Allah." Fadawa suka ɗauka a lokacin da suka lura Muhsin ya miƙe da niyyar fita daga fadar, wasu daga ciki suka ƙarasa suna take masa ba. Hannu ya ɗaga haɗe da tsayawa wuri ɗaya cak, ya kusa minti ɗaya a haka sannan ya furta. "Ba na buƙatar rakiya." Lokaci ɗaya suka ja da baya sannan ya ci gaba da taku, duk hanyar da ya bi haka bayi da fadawa suke zubewa suna kwasar gaisuwa amma ko kallansu ba ya yi ballanta su saka ran zai tanka musu. Yana gab da shiga sashen mahaifiyarsa bisa tsautsayi wata baiwa ta fito da sauri don isar da saƙon Fulani Umaima, a rashin sani ta bangaje shi har sandar hannunsa ta faɗi ƙasa. Jiki na karkarwa ta zube ƙasa. "Tuba nake shugabana, a gafarce ni uban gidana ni mai laifi ce ba tare da..." Marin da ya ɗauke kuncinta da shi ya sa haƙoranta suka datse harshenta har sai da bakinta ya fashe, idanunta suka fara zubar da ƙwalla ta sake zube wa a ƙasa tana faɗin. "Godiya nake Sarkin gobe." Ɗaga kansa ya yi ya hango wani Bafade hannunsa ɗauke da murtukekiyar bulala ya furta, "A hora ta na tsawon wuni guda da alama ba ta gama sanin a gidan masarauta take rayuwa ba tun da ba ta san aikinta ba." Yana gama maganar ya wuce ba tare da ya jira cewarsu ba. A kishingiɗe ya tarar da mahaifiyarsa tana huatawa, wasu 'yan matan Bayi na tsugunne wurin ƙafarta suna yi mata tausa. Ganin yanayinsa ya sa ta tashi zaune haɗe da sallamarsu. "Wa ya ɓata ranka Muhsin?" Fulani Umaima ta tambaye shi. Bai tanka mata ba sai da ya zauna. "Wata baiwarki ce ta ɓata mini rai amma komai ya wuce." "Wace ce ita na sa a hukuntata?" Muhsin ya fara rage kayan jikinsa. "Na sa a hukuntata, ina Ruƙayya ban ganta ba?" Fulani Umaima ta yamutsa fuska, "Za ta wuce sashen Fulani babba ne, yarinya sai baƙin nacin tsiya kamar tsohuwar mayya." Take idanunsa suka yi jawur rai a matuƙar ɓace ya saki guntun tsaki, ba tare da furta komai ba.    Ihun da Ruƙayya ke ƙwallawa ne ya ja hankalin Fulani babba da sauran bayin da ke harabar gidan, turus bayin suka yi suna kallon juna duk da ba yau ce rana ta farko da suka ga Abubakar na kama gashin duk wani mutum da ya kusance shi ba ciki kuwa har da mahaifiyarsa. Ruƙayya ƙanwar Muhsin ce ita take binsa shekararta bakwai a duniya, Allah ya haɗa jininta da Abubakar ba ta iya wuni guda cir ba tare da je sashen Fulani babba ta shiga ɗakin Abubakar ta tsaya yana yi mata gwaranci tana mayar masa ba. Babbar matsalar da ke damun Fulani Babba bai wuce yadda Abubakar yake cizgar gashin kansa yana ci ba, idan na kansa ya ƙare kuma duk wanda yake da tsautsayi idan ya damƙe ka haka zai dinga cizga har sai an kwace ka. Abubakar ya shiga shekara ta goma sha ɗaya, sai dai har lokacin a zaune yake ko motsi ba ya iya yi komai sai an yi masa. Fari ne sol kamar mahafiyarsa sai dai kammaninsa sak da Sarki Abdul'aziz, tun da ya taso ba ya iya magana sai dai gwaranci kuma har kawo lokacin yawu na dalala daga bakinsa. Idanunwansa duka biyun a juye suke, hannuwa da ƙafafuwansa suma a shanye suke babu abin da yake iya aikatawa hatta wanka da tsarki yi masa ake yi.   Fulani Babba da sauri ta ƙarasa gaban Abubakar ta sa hannu cike da ƙunan rai ta ɗauke fuskarsa da mari, wannan ne karo na farko da ta taɓa sanya hannu a jikinsa da sunan duka. Zafin marin ya ratsa shi hakan ya sa ya ƙarasa cizge kitson kan Ruƙayya da ke bakinsa, sai kuma ya fashe da kuka yana gwara kansa da ƙasa. Cikin azaba ta sake ƙwalla ƙara take numfashinta ya ɗauke ta sume a wurin. Tamkar mayuwancin zakin da ya samu nama haka Abubakar ya tura sillin jelar kitson kan Ruƙayya da ya cizge cikin bakinsa ya fara tauna kafin wani lokaci ya haɗiye shi gabaɗaya. A firgice Fulani Babba ta shiga yayyafa wa Ruƙayya ruwa ta jima a kanta sannan ta sauke ajiyar zuciya a galabaice, ganin ta buɗe ido ya sa Fulani Babba ta ji farinciki har cikin ranta sai dai kuma wurin da ya ɗaye mata kitson tuni gefen kan ya kumbura suntum. Wani irin sara ta ji kan yana yi mata a daddafe ta iya miƙewa ganin haka ya sa Fulani ta ba wa Bayin da ke gefe umarnin su ɗauke ta zuwa cikin turakarta. Duk dauriya irin ta Ruƙayya sai da ta dinga zubda ƙwalla sakamakon yadda take jin kanta na sara mata kamar zai tsage gida biyu. Duk yadda Fulani babba ta so zaman Ruƙayya a ɗakin zuwa lokacin da zugin zai sarara mata fir ta ƙi yarda, don haka ta sake saka Bayi suka ɗauke ta tana gaba suna biye da ita a baya har cikin sashen Fulani Umaima. Ganin a halin da aka shiga da Ruƙayya ya sa Fulani Umaima miƙewa zumbur! Bakinta har rawa yake ta furta. "Me ya faru da ita?" "Laifi ne yayanta Sadik ya yi mata, wallahi tsatsayi ne Fulani don haka na zo da kaina ba saƙo ba..." "Dakata Fulani! Hawainiyarki ta kiyayi ramata. Ba tun yau ba na lura da take-takenki dangane da kiranyen da kika yi wa Ruƙayya. Lokaci ɗaya kin sa an lashe kurwar yarinya ba ta ƙaunar zaman wurin mahaifiyarta, wannan fa ba shi ne karo na farko na ji labarin wancen shagirigirbau ɗin ya maƙure ta yana yi mata ƙamshin mutuwa ba. Amma an yi ta yanke ta gille, wannan shi ne karo na farko kuma na ƙarshe da zai sake taɓa kowanne bil'adama a sashenki." Fulani Umaima ta ƙarasa maganar tana kai kallonta wurin bayin da ke riƙe da Ruƙƙaya. "A samu Jakadiya ta gaggauta sanar da Mai martaba ina buƙatar ƙwararrun masu magani, don ban san dafin da haƙoransa suke ɗauke da shi ba." Da sauri suka shimfiɗar da ita suka fice, Fulani Babba ta ƙarasa gabanta ido cike da ƙwalla ta furta. "Wallahi ko a mafarki ban taɓa jin Ruƙayya ba 'yata ba ce, tamkar yadda na ɗauki su Khadija haka nake jin ta, ta ya ina sane zan bari Abubakar ya illatata." Sai da Fulani Umaima ta saki murmushin takaici ta furta, "Me ya sa bai kama Khadija ko Sakina ya illata ba, saboda kina baƙincikin kin haifi sauna, wawa, shashasha shi ne ni ma kike burin ƙarfi da yaji na rasa waɗannan biyun da Allah ya ba ni." Tsoron hukuncin da Fulani Umaima za ta yanke ya sake mamaye Fulani babba, ta tsugunna bisa gwiwoyinta don ta san kome Fulani ta gaya wa Takawa hawa yake ya zauna ɗaram. Ba tun yanzu ba ta jima da dawowa daga rakiyarta, don ta lura sai abin da Fulani Umaima take so Takawa yake zartarwa. "Tabbas Abubakar bai kyauta ba amma ki dubi girman Allah ki yi haƙuri..." "Idan ba ki yi gaggawar fita daga sashena ba wallahi sai na shayar da ke ruwan mamaki." Fulani Umaima na gama magana ta yi ciki cike da zafin rai. Fulani babba ta sunkuyar da kanta ƙasa tana zubar da ƙwalla, dama ya ya lafiyar kura ballantana ta yi zawo. Gari banza ma Takawa ba ƙaunar Abubakar yake ba ina ga an ce ya taɓa 'ya'yan gaban goshi. Cike da zullimi ta fara yunƙurin tashi, daga bayanta ta hangi Muhsin na zaune yana aika mata da saƙon harara cikin kallon tsana. A haka ta ƙarasa sashenta gwiwoyinta a sanyaye, ta windo ta leƙa Abubukar da ke zaune yawu na dalala. Sai a lokacin ta samu damar fashe wa da matsanancin kuka duk da tana da tabbacin bayin da ke zagaye da ita suna sauraronta. "Ya Allah ba don ba ka so ko ƙaunata ka jarabce ni da wannan bawa Naka ba, Ya Ubangiji ina godiya bisa baiwa da wannan ni'imar da ka yi mini domin dubbunaina na buƙatar ko da makamancinsa ne. Ya Allah idan rayuwar wannan bawa naka mai tsayi ce Ubangiji ka yalwace shi da lafiyar ya zama kamar kowa, saɓanin halin da yake ciki. Idan kuma mai gajeren kwana ne Ubangiji ka gaggauta ɗaukar kwanakinsa ko na samu salama a rayuwata..." Kukan da ya ci ƙarfinta ne ya datse ragowar kalamanta. "Allah ya sanyaya zuciyar uwar ɗakina Ubangiji ya ƙara wa Yarima lafiya." Baiwa Zainaba ta furta jiki a sanyaye kamar kazar da tono wuƙa. "Zainaba na ɗauka ko kowa zai furta son ransa ke mai faɗa mini gaskiyar abin da ke cikin zuciyarki ne? A haka kike kiran Abubakar da Yarima kina ga ko a mafarki za a damƙa wa Abubakar karagar mulki ne." Tabbas kalaman Fulani Babba a turba suke domin kowa ya san halin da Abubakar yake ciki kuma ko a garin gaɓa-gaɓa babu wanda zai damƙa masa kujerar sarauta, ina ya san kansa ma balle ya san matsalolin talakawa? Sai da ta ƙara rissinawa ta furta. "Tuba nake ranki shi daɗe, In shaa Allahu Allah zai ba shi lafiya." Fulani babba ta amsa mata sannan ta wuce cikin sashenta.   Ganin har zuwa dare babu wani saƙo ya sa Fulani babba ta ɗan fara sakin zuciyarta, har ta zauna su Khadija na soko mata hira wani ta amsa musu wani kuma ta yi musu shiru. Suna cikin wannan yanayin Jakadiya ta iso da kiran da Maimartaba yake yi mata. Take ƙirjinta ya buga dum! Zuciyarta kamar za ta yi tsalle ta fito daga ƙirjinta, da ƙyar ta tattaro jarumtar haɗa kalmomin da ta iya furta wa Jakadiya. A gurguje ta watsa ruwa ta ɗan gyara jikinta, don saboda yadda lalurar fitsarin da yi mata kamun kazar kuku har ji take haka kawai kamar zarni na tashi a jikinta. Da kwalliyarta fes ta ƙarasa turakar Mai martaba ƙamshi na tashi, haka kawai wani lokacin yake jin kamar yana tauye haƙƙinta ko yana yi mata ba daidai ba, musamman yadda ya ga ta fige ta lalace kamar ba ita ba. "Barka da hutawa Sarkina." Kalamanta ya ji na sauka a kunnuwansa, wani ɗaci ya ziyarci zuciyarsa kamar wanda ya haɗiyi maɗaci. "Barka!" Daga haka shiru ya biyo baya, ganin yanayin tarbar da Mai martaba ya yi mata ya sa jikinta ya yi sanyi. Cikin sanyin murya ta furta. "Allah ya taimake ka na ji saƙon kana son ganina." "Wani hukunci muka yanke da muke ganin shi ne mafi alfanu babu cuta babu cutarwa." Mai martaba ya faɗa fuska a haɗe kamar dafaffan kwanannan kunun tsamiya. Ƙirjinta ya hau dakan lugude, gumi ya fara keto mata ta ko ina. "Don haka ba ma buƙatar jayayya. Abubakar Sadiq zai koma ɗaya daga cikin ɗakunan gidan ajiya da gyaran hali, na sa a ware masa ɗaki guda wanda zai zauna a ciki, idan ya so duk wani abu da yake buƙata a aiwatar masa a can. Mun yanke wannan hukuncin ne domin sama wa lafiyayyun gidan nan mafita, idan yau ya nemi nasaka wannan jibi wancan watarana ina tunanin kaina zai dawo." Kafin dirar kalaman  Takawa tuni hawaye ya gama wanke fuskarta. Cikin kuka ta zube a ƙasa hannuwanta biyu a saman cinyarsa ta furta. "Don Allah kada ka yi mini haka ranka shi daɗe, Allah ya sani Abubakar ba shi kaɗai na haifa ba akwai yayyansa Khadija da Zainab amma wallahi babu wanda na ke jin ƙaunarsa har a cikin jinina kamarsa. Wannan ƙasƙanci ne a ce jininka zai ƙare rayuwa a gidan ajiya da gyaran hali saboda ya kasance mai nakasa, in dai a kan Ruƙayya ne na yi maka alƙawari ko inuwarsa ba za ta ƙara gani ba ballanta shi. Don Allah ka..." Cikin tsawa ya katse ta. "Ba mu san lokacin da raini ya gifta a tsakaninmu ba Fulani, da har ake neman yin jayayya da mu. Mu ba ƙananan mutane ba ne sanin kanki ne ba tun yau ba; ba ma taɓa magana biyu. Tashi ki ba mu wuri, wannan hukuncin ba zai tɓa canzawa ba." Fulani babba duk yadda ta so dakatar da hawayenta abin ya gagara, don haka ta fice daga turakar zuciyarta na tuƙuƙin ɓacin rai. Tana shiga ɗaki ta fashe da wani irin matsanancin kuka, ganin kukan na ta ba na ƙare ba ne ya sa su Khadija rungume ta suka fashe da matsanancin kuka! Yau ita ce rana ta farko da ta ji zama a cikin gidan ya gama fita daga ranta, ta kuma ji wani abu ya tokare mata maƙoshi game da Fulani Umaima sai dai kuma a ɓangare ɗaya shakka da tsoronta ya hana zuciyarta sanar da ita gaskiyar abin da ke ranta. Sun jima ita da yaran a haka sannan ta miƙe ta nufi ɗakin Abubakar, ta same shi a kwance kamar yadda ta barci. Sai da ta share ƙwallah sannan fito daga ɗakin.   Washegari tun safe Dogarawa suka cika umarnin Mai martaba, tun lokacin da aka fara jidar kayan Abubakar Fulani Babba take share hawaye don dai ba ta da yadda za ta yi. "Idan kika matsa mana da magana wallahi ranki zai yi mummunan ɓacin da ba ki taɓa gani ba Fatima." A razane ta dubi Mai martaba, yanayinsa kaɗai ya tabbatar mata babu alamar wasa a tattare da shi. Dole ƙanwar na ƙi ta zubar da makamanta, ta rungumi ƙaddarar da ta afka musu babu sallama. Ajiyar zuciya ta sauke bayan ta tuna yadda suka kwashe da Takawa, a daren ranar da ta sake zuwa sashensa tana yi masa magiya a kan ya bar Abubakar ya ci gaba da zama a sashenta. Hawaye ya gangaro mata sakamakon ganin wata irin birgima da Abubakar ya fara yi a cikin jar ƙasar da ke ɗakin saboda ɗakunan kowannensu babu daɓe a ciki. Wata ƙasar ya ci wata kuma ya burtune jikinsa da ita, tana ji tana gani bayan ta gama kallonsa ta fice daga  ɗakin. Abin ka da gidan masarauta take labarin kai Abubakar gidan yari ya gama zagaye gidan kowa da abin da yake tofawa, sai dai mafi yawa daga cikin shakkun Fulani Umaima ya hana su faɗar gaskiyar abin da yake cikin zuciyoyinsu. "Allah ya taimake ki ni fa don kada a ce na saki linzamin harshena amma Allah ya sani na fara ɗora zargi a kan Fulani Umaima. Lamarin zamantakewar da ke tsakaninki da Takawa akwai fa ayar tambaya." Jakadiya ta yi wa Fulani babba maganar tana yin ƙasa da murya. "Jakadiya tafi kanki tsaye ba mu fahimce ki ba." Jakadiya ta sake yin ƙasa da murya. "Bari na fito miki a mutum Fulani, an ya kuwa Fulani Umaima ba ta bi ta ƙarƙashin ƙasa a kan Takawa ba, duba da yadda take cin karen ta babu babbaka a gidan nan kamar wacce ta wanke masa hannu aka. Yanzu musakin yaron nan Bukari me ya yi da zai fuskanci zama a sashen gidan ajiya da gyaran hali." Jin haka ya sa hawaye ya zubo wa Fulani Babba. A fakaice Jakadiya ta saki murmushin cin nasara, don babban burinta ita ma bai wuce ta samu sanadin dandalar arziƙin da su Fulani suke ci ba a matsayinsu na matan Sarki. "Jakadiya al'amurana a yanzu haka na miƙa su a wurin Ubangiji, duk ma wanda ya nemi ya ƙuntata wa rayuwata Allah ba ya bacci yana sane da abin da yake faruwa." Jakadiya ta taɓe baki a fakaice. "Amma ya kamata ke ma ki tashi tsaye domin kin san da sanyin safiya ake kama fara." Fulani babba ta ɗan sauya fuska don haka kawai ta ji ba ta aminta da waɗannan shawarwarin na Jakadiya ba. "Ni fa hatta ciwon yaron nan wallahi na jima da ɗora zargina a kan Umaima, saboda Allah yaro shi ba aljanu ba amma an mayar da shi wani iri. Kwanaki fa har barbaɗe na ga tana yi a turakar Mai martaba wai don ya daina jin ɗanɗanonki." A ɗan razane Fulani babba ta dubi Jakadiya sai kuma ta haɗe fuska. "Jakadiya muna buƙatar hutawa a ba mu wuri." Ganin babu fuska ya sa Jakadiya ta fice tana wurgawa Fulani babba mugun kallo. "Sakarai da ba ta gaji arziƙi ba kya ƙare a wahale cikin warin jiki da fitsari." Jadiya ta faɗa cikin jin haushin rashin samun nasara a kan Fulani Babba bayan ta fita waje. Wacce ta shirya biyan kuɗin karatun ci gaban littafin *SHU'UMAR MASARAUTA* Ƙofa  buɗe take, za ta iya turowa ta wannan Acc ɗin da ke ƙasa domin free pages na gab da ƙarewa. Waɗanda suka fara biya su min afuwa zuwa lokacin da zan buɗe group bayan na kammala free pages. *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624. cmplt doc 800 ne* *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*   SHAFI NA TAKWAS    RIGAR ARƊO    A gajiye tuɓus suka dawo gida sakamakon yawon kiwon da suka je cikin dokar daji, zamansu babu wuya wata farar dattijuwa ta ɗauko ƙorai guda biyu sai da ta fara zuba nono a cikinsu ta miƙa wa mai gidanta Baffajo. Ta jima a tsugunne tana jiran ya karɓa tana ɗagowa ta lura da yadda ya dulmiya cikin kogin tunani, a sanyaye ta kai hannu ta taɓa shi. "Yanzu Baffajo ba za ka daina wannan tunanin ba? Idan kai kana yi ni kuma sai ƙaƙa?" Ajiyar zuciya ya sauke. "Inna wuro aradun Allah lamarin yaron nan ƙara ci mini tuwo a ƙwarya yake, yanzu a ce ɗan mutum ba shi da abokan rayuwa sai gidan tururuwa da dokar daji? An ya Inna wuro ba za mu kai Kamalu wurin Malamijon farar riga ba?" Inna wuro ta yi jim cike da damuwa sanna ta furta, "Eh to hakan ma wani abu ne amma ni sai na ga kamar har da sabon shiga dawa..." "Kayya mu ba a dawa muka yi rayuwa tun daga ƙuruciya ba? Kin manta a lokacin baya tsakiyar dare nake tsintoshi a bayan rumfar can wurin shurin da ke gabas da shi." Kamalu ya ɗago fuska a haɗe don jin abin da Iyayensa suke furtawa, motsa baki yake kamar wanda zai yi magana, amma sai ya gimtse ya kawar da kai gefe. "Kamalu kai fa ba yaro ba ne a ƙalla shekarunka sun haure goma, mahaifinku girma ya kama shi ba ka ganin sauran 'yan uwanka ba haka suke ba." Kamalu ya sunkuyar da kai ƙasa ba tare da ya kalle su ba, A'iru da ke gefe ta furta. "Kwarankwasa dubu rannan har gani na yi yana ɗibar wani abu a kan gidan tururuwa yana sha, dubi wancan zobe." A'iru ta yi maganar tana nuna hannun Kamalu mai ɗauke da wani zoben azurfa mai ɗauke da wani irin zane. "Da bakinsa ya ce mini tsintarsa ya yi a kan shuri wai gadon Masarautarsu ne." A razane su Inna wuro suka dube shi, Baffajo ya ce. "Kamalu wa ya ba ka wannan zoben?" "Tsintarsa na yi." Kamalu ya furta kai tsaye ba tare da ɗago ya kalle su ba. Haushi ya fara kama Baffajo don haka ya ce, "Kai Kamalu hai ka shiga taitayinka, ba ka san dawa ba ko?" Kafin Kamalu ta ya ba shi amsa daga sama suka fara jin gudun dawakai da iface-ifacen mutane, kafin su yi wani yunƙuri tuni waɗansu Dogarai da sojojin masarauta suka farmusu cikin shammata suka riƙa taɗe su suna ɗaure su da  wasu murtuka-murtukan igiyoyi a jikin manyan itatuwa. Lokaci ɗaya garin ya hautsine ban da ƙura babu abin da yake tashi, waɗanda suke da rabon tsira tuni suka shuɗa daji. Waɗanda aka riga da aka rubuta zanen ƙaddararsu kuma tuni aka damƙe su, a cikin waɗanda suka tsira har da Salele ɗan gida Baffajo. Shi kuwa Kamalu ko da ya ga abin da yake faruwa ko gezau bai yi ba, yana nan zaune wani Dogari ya isa gare shi ya fisgo shi da niyyar taɗe shi, ɗayan hannun nasa ya sa ya bigi gefen hannun Dogari, wata irin azaba ya ji tamkar an zuba masa ruwan dalma. Da kansa ya ƙarasa wurin wasu Dogarawa da ke tsaitsaye suna ɗaure ragowar mutanen da aka kama wanda ko tantama babu sun riga da sun zama bayi. Sai da aka ɗaure Baffajo da waɗansu mutane biyu sannan aka ɗaure Kamalu, a ɓangaren mata kuma tuni aka ɗaure Inna wuro da sauran mutanen da ke cikin rigar. Kafin wani lokaci rigar ta yi fayau sai kukan dabbobi da ƙananan tsuntsaye da ke tashi.   ƘAUYEN GANGARE    Jiki a matuƙar sanyaye suka ƙarasa cikin ƙauyen gangare hannun Mai gado ɗauke da jaririya, tun daga ƙofar gari aka fara jefa musu tambayoyin inda suka samu jaririya sabuwar haihuwa. Sai dai amsa ɗaya suke bayarwa tsintarta suka yi a cikin gona, da haka suka samu suka ƙarasa gida. Da zuwansu babu jimawa gidansu ya cika maƙil da mutane, wasu na taya su murna ya yin da wasu suka fara tsegungumi da ƙananan maganganu. Wani tunani Umaru ya yi take ya sa Mai gado ta ɗauki jaririya har ta ɗora ruwan da za ta yi mata wanka ya dakatar da ita kai tsaye suka wuce gabaɗaya wurin Mai gari. Umaru yana zuwa fadar Mai gari ya zube ya kwashi gaisuwa sannan ya gabatar da jaririyar hannunsu da mahaifiyarta ta yi mata laƙabi da Jawahir, bayan ya tsahirta ya karɓe ta daga hannun Mai gado ya miƙa wa Mai gari, sanƙira yana raɓe a gefensa. Tun da aka ɗago jaririyar Malam Malmo ya zura mata idanu ko ƙiftawa ba ya ni, wannan ya haddasa fargaba da tashin hankali a zuciyoyin Mai gado da Umaru, sakamakon sanin Malam Malmo sarai da mugun aikinsa. A sakaye Umaru ya ɗan yi gyaran murya ya furta. "Allah shi ba ka yawan rai yanzu haka Mai gado ta ɗora mata ruwan wankan da za a yi mata wanka da shi." Mai gari ya jinjina kai tare da yi musu nasiha a kan su riƙe ta da riƙon amana. Su Umaru har sun miƙe bayan mutane sun watse yana waigawa ya ga Malam Malmo yana yi wa Mai gari raɗa a kunne, haka kawai ya ji zuciyarsa ba ta aminta da wannan raɗar da yake yi wa Mai gari ba. Tsawar da sanƙira ya yi masa ce ta sa shi zura takalman fatarsa ya yi gaba jiki a sanyaye kamar kazar da aka watsawa gishiri. "Mai gado ina tsoron Malam Malmo a kan yarinyar nan kada fa a ce ya gano wani al'amari game da ita." Umaru ya faɗa bayan Mai gado ta yi wa Jawahir wanka tana shafe mata jiki da mai. "Ni kaina ina tsoro amma In shaa Allah babu abin da zai faru sai alkhairi." Wannan ƙawarin gwiwar da ya samu daga wurin Mai gado ya sa ya tashi ya fita don tatso wa Jawahir nonon akuyar da za a shayar da ita. Sannu a hankali suka ci gaba da rainon ta, tun suna ɗari-ɗari da ita har suka saki jikinsu sakamakon babu wani abu da suke gani na ban tsoro a tattare da ita. A ɓangare ɗaya kuma wata irin soyayya suke nuna mata, ga shi sai ta wuni ba a ji kukanta ba idan ba yunwa take ji ba. Abu ɗaya ne ya fara damun Mai gado da yake faruwa da Jawahir cikin dare, duk lokacin da ta farka don ta ba ta nonon akuya da dare sai ta ga wani baƙin jini ya tsattsafo a goshinta, idan kamar bacci ya ɗauke ta har asuba ta yi, sai da ga goshin na ta ya yi ɗan duhu amma babu jinin a jiki, zuwa wayewar gari kuma sai ta nemi komai ta rasa jinin ya washe. Tun tana barin maganar a ranta har ta taɓa tashin Umaru ta sanar da shi, shi kansa ya yi mamaki amma gudun kada ƙilu ta ja bau! Ya ce su zuba wa sarautar Allan ido tun da ba ta kuka wataƙila abin ya mata ciwo. Kwanan Jawahir goma Mai gari ya aika a kira masa Umaru, tun da Umaru ya ji kiran Mai gari gabansa ya faɗi har sai da Mai gado ta ƙarfafa masa gwiwa sannan ya nufi gidan Mai gari cikin wasuwasi.   Yana zuwa aka yi masa iso har cikin shagonsa da yake hutawa a soro, ganin Malam Malmo ya sake tsinka zuciyarsa. Dole ƙanwar na ƙi ya zuba wa fuskarsa murmushin yaƙe cike da girmamawa ya gaishe su. "Umaru ka sani a gaban Mai gari kake don haka muke son duk maganar da muka tambaye ka ta zama gaskiyarka za ka faɗa. Wace ce yarinyar da ka zo da ita kuma a ina ka same ta?" Malam Malmo ya jefa masa tambaya. "Allah ya baka yawan rai wallahi tsintarta muka yi..." "Idan tsintarta kuka yi ina mahaifiyarta? Ko kuna nufin jaririya ɗanyar haihuwa za ta kawo kanta ne?" Mai gari ya katse Umaru. Shiru Umaru ya yi yana tsoron kada ya ba da kai bori ya hau, yana cikin nazari ya tsinci kalaman Malam Malmo. "Sanin kanka ne Umaru duk yankin nan babu wanda ya kai ni sanin sirrin tsafi da sihiri, na bincika kuma na gano waɗansu bayanai tun ranar da na ɗora ƙwayar idona a kan yarinyar nan. A zahiri ne kuke ganinta ƙanƙanuwa amma a baɗini basarakiya ce, shu'uma ce kuma tana ɗauke da rikitattun al'amura. Ita ba kamar kowa ba ce dalilin da ya sa mahafiyarta ta yo gudun fanfalaki da ita kenan daga cikin danginta, mukuma a ɓangarenmu na masu aikin tsubbace-tsubbace wannan yarinyar ta kasance tamkar taki ce da ke farfaɗo da shukar da ke cikin gona. Ya zama wajibi ka mallaka mana ita domin cikar muradinmu, a zahiri Mai gari zai karɓi riƙonta ta koma gidansa da zama. A baɗini kuma zan aiwatar da aikin da za ta kasance a ƙarƙashin ikona. Sharaɗi na biyu ya zama dole ka nuna mini daidai wurin da gawar mahaifiyar yarinyar nan take, idan ba haka ba wallahi sai na shayar da kai ruwan mamaki." Gumin da ya shiga keto wa Umaru ne ya bankaɗa sirrin da ke cikin zuciyarsa, cikin matsanancin tsoro ya ɗago jiki na rawa ya furta. "Duk abin da kuka buƙata haka za a yi ranka shi daɗe, da kai da kaya duka mallakar wuya ne." Malam Malmo ya saki murmushi cikin jin daɗi don ya ga tsoro malale a saman fuskar Umaru don haka ya furta. "Ba zan barka haka ba Umaru dole za mu aiwatar maka da naka tukwici mai tsoka." Umaru ya saki murmushin yaƙe yana godiya, sannan Mai gari ya sallame shi. Kamar zai tashi sama haka ya ƙarasa gidan yana alla-alla ya ɗauko Jawahir ya kai musu ko ya yarda ƙwallon magwaro ya huta da ƙuda.   Masarautar Huddam     A ranar da aka kai Abubakar ɗakin da ke ɓangaren gidan ajiya da gyaran hali ko runtse Fulani babba ba ta runtse ba, baƙinciki da ɓacin rai ya mamaye zuciyarta. Sai gabannin asuba sannan ta samu hawaye ya zubo mata, zuciyarta cunkushe da ɓacin rai. Wani abu da ya so ɗaure mata kai ganin ta wayi gari lafiya ƙamas babu fitsari a shimfiɗarta, ba ta ankara da haka ba sai da aka kira sallar asuba da za ta yi wanka kamar yadda ta saba duk asuba sai ta wanke fitsarin jikinta. Amma wannan ranar da ta kwana idonta biyu sai ta ga babu komai a jiki, mamaki cike da zuciyarta ta yi alwala bayan ta gabatar da sallah a gurguje ta nufi sashen da Abubakar yake kwance ɗauke da kayan sawar da za ta sake masa kamar yadda ta saba tsaftace shi. "Waye nan?" Aka furta mata cike da tsawa a lokacin da ta ƙarasa jikin babban ƙauren ƙofar. Baƙin ciki ya kama ta jin ƙasƙantaccan bawa na buga mata tsawa, da ace a sashen ta yake babu wanda ya... "Ina magana waye nan?" Kamalan Dogarin suka katse mata tunani. Sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta. "Fulani ce na zo wurin Abubakar." Cikin girmamawa Dogarawan suka zube. "A gafarce mu uwar gijiyarmu, muna neman afuwar saƙon da zai fito daga bakunanmu." Zuciyar Fulani ta fara azalzala kamar za ta hudo ƙirjinta, fargabarta ɗaya kada su ce mata wani abu game da Abubakar. "Allah ya taimake ki, ki yafe mu amma Takawa ya ja kunne da kada a sake buɗe ƙofar nan har sai hantsi ya ɗaga wurin ƙarfe tara." Da sauri ta dube su. "Yaushe ya bada wannan umarnin?" "Ranki shi daɗe jiya da dare." Sai da ta haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ta miƙa musu kayan hannunta da akushin abincin da ta taho da shi. "A gyara Abubakar da shi a tabbatar da an yi masa wanka, wannan abincinsa ne." Jim suka yi sannan ɗaya daga cikinsu ya furta. "Allah ya taimake ki koda mun karɓi kayan nan sai lokacin da Takawa ya zartar za mu buɗe ƙofar, amma a gafarce ni ranki shi daɗe." Wani irin kukan takaici ne ya taso mata, gudun kada ta bar abin faɗa ya sa ta juya da sauri ba tare da ta amsa musu ba. Fulani babba na zuwa sashenta ta fashe da matsanancin kuka, tana tsaka da kuka ta ji Khadija mai kimanin shekara goma sha shida ta dafa kafaɗarta. "Ummi me ya sa kullin cikin kuka kike? Ummi kin san idanun masarautar yana ko ina a lungu da saƙo don Allah kada ki bari a samu a bin faɗe, komai ya yi tsanani maganinsa Allah kamar yadda na ji kina faɗa. Wuya ba ta kisa na san a kan Sadiq kike wannan kukan don Allah ki kwantar da hankalinki na tabbata babu abin da zai faru da shi." Khadija yarinya ce mai nutsuwa da sanin ya kamata, idan tana magana kamar babbar mace, a hankali ta goge wa mahaifiyarta hawaye ta ci gaba da tausarta har damuwar da take ciki ta yaye. Haka ta haƙurƙurtar da zuciyarta har lokacin da ya dace, sannan ta ɗauki kayan da kanta ita da Khadija suka nufi wurin Abubakar. Tun tasowar Abubakar ko da wasa Fulani ba ta taɓa yunƙurin ba wa wata baiwa hidimarsa ba, haka ta sawa ranta har zuwar ƙarshen rayuwarta za ta ci gaba da kulawa da shi ba tare da ta sare ba. A lokacin da suka ƙarasa ɗakin duk da kasancar safiya ce ƙudaje ne suka fara yi musu maraba, a kwance suka same shi kamar yadda Fulani ta bar shi da dare sai dai ya fitsari da kasaye duka kayan jikinsa. Ƙudajen da ke kai-kawo a kansa yake ɗaga kai yana cafko duk wanda ya zo hannunsa ya kai bakinsa ya cinye. A fakaice Khadija ta share hawayenta, sannan suka gyara masa jikinsa. Khadija ta kira Baiwa Salamatu ta damƙa mata kayan Abubakar don a wanke su, sannu a hankali Fulani babba take ba shi abinci wani ya karɓa wani ya zubar bayan sun gama suka tashi suka rufo shi suka fito daga sashen zuciyoyinsu babu daɗi.    Tsaye take hannunta ɗauke da wata irin sharɓeɓen tsafaffiyar takobin da Boka Bamaguje ya bata don kare kanta da shi, ta hango ƙurar ɗan matashin yaron ya tunkaro ta da bai fi sa'an Muhsin ɗin ta a shekaru ba, duk yadda ta so hana shi shiga cikin ƙofar Masarautar Huddan sai abu ya gagara. Ganin haka ya sa ta zaburo da sauri kafin ta aiwatar da abin da yake ranta ya sa hannuwansa biyu ya mauje ta, ta faɗi ƙasa warwasa. Ɗagowar da za ta yi ta hangi Baiwa Maimuna a bayansa tana sakar mata murmushin mugunta, sai wata inuwa da ta gagara tantance wace ce ita. "Ban yafe miki abin da kika yi mini ba kuma sai na ɗauki fansa a kanki." Rufe bakin Baiwa Maimuna ta sa hannu ta fara jan Fulani Umaina a ƙasa kanta sai kurjewa yake jini na zuba, ko da ta hango Bamaguje yana tsaye a gefe yana kallonsu cikin magiya da tashin hankali ta fara roƙonsa. "Da kai kaɗai na dogara Bamaguje ka taimaka mini za su kashe ni." Wata irin mahaukaciyar dariya ta ga ya bushe da ita, ya juya mata baya ya fara tafiya yana faɗin. "Na riga na gaya miki kin yi sake wannan yaron ba kamar ɗan uwansa yake ba." Firgigit Fulani Umaima ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi, a 'yan kwanakin nan ta rasa dalilin waɗannan miyagun mafarkai nata. Kusan kullin sai ta yi mafarkin wannan yaron yana barazana da rayuwarta. "Waye wannan da yake ƙoƙarin kutsowa cikin rayuwata har yake neman dagula lissafina?" Ta tambayi kanta ba tare da ta san amsar tambayarta ba. Ƙirjinta ya buga a lokacin da ta tuna jaririn da baiwa Maimuna ta fitar da shi yana nan a doron ƙasa, "Ƙarya ne ba shi ba ne! Ba zai taɓa razanar da ni ba." Fulani Umaima ta furta tana kai wa da kawowa. *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga ɗaukan tsattsauran mataki don haka a kiyaye. *Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*   SHAFI NA TARA    Ayarin dakarun masarautar da ke tafe da su Baffajo tafe suke cikin gajiya sakamakon doguwar tafiyar da suka yi, a farfajiyar wata bishiya suka yada zango suna hutawa sai bayan sun huta sannan suka ci gaba da tafiya, cikin zuciyarsu kowa da abin da yake ayyanawa. Ganin magriba ta fara dosowa ya sa suka yanke shawarar kwana a cikin dajin washegari da asuba sai su ɗora daga inda suke tsaya. Ƙauyen Gangare   Ganin yanayin da Umaru ya koma gida da shi ya sa Mai gado shan jinin jikinta. "Mai gida ya kuka yi da Mai gari na ganka duk a sanyaye." Ƙasa ya yi da murya ya furta. "Ina yarinyar nan take? Zan kai ta gidan Mai gari" Kallon rashin yarda ta bi shi da shi ta sake gyara goyon Jawahir da ke bayanta. "Me za ta yi a gidan." Kamar zai yi kuka Umaru ya ce, "Malam Malmo Mai gado ban san ya za mu yi ba, sun buƙaci na mallaka wa Mai gari ita." Rass! Ta ji gabanta ya faɗi, sai da ta sauke ajiyar zuciya sannan ta yi ƙasa da murya. "Ba zan iya rabuwa da Jawahir ba Mai gida, na san Malam Malmo sarai ba zai wuce tsubace-tsubbace zai yi da ita ba." Umaru ya waiga kamar wanda ake kallo duk a tsorace ya ce. "Ya zamu yi yanzu? Mene ne mafita?" Masarautar Huddam     Wuni guda haka Fulani Umaima ta yi shi cikin rashin ƙwarin jiki, ba ta san dalili ba amma haka kawai za ta ji gabanta na faɗuwa. Har ta so dannewa ta ji zuciyarta na azalzala ba za ta iya jure rashin zuwa wurin Bamaguje ba.    Tsufansa ya sake fitowa sosai don jiki da hannuwansa har karkarwa suke yi. "Ta zo duniya da ƙarfin iko, shi kuma yana gab da dawowa gidansu na gado." Bamaguje ya furta bayan ya gama sauraron ƙorafin Fulani Umaima. Ta ɗago a hargitse bakinta na rawa, ƙirjinta na dakan lugude. "Su waye? Kuma daga ina suke." "Garaje ga dami, daɗina da ke gaggawa Umaima. Na ɗauka za ki tambayi alaƙar shi da masarauta da ita kanta yarinyar." Ajiyar zuciya ta sauke. "Tamkar tagwaye haka suka kasance tsakaninta da Hidaya, sai dai waccan ruwan sanyi ce salam a kan wannan. Ban san a wanne muhalli zan tirke ta ba, abu ɗaya na sani ita ta kasance daga cikin wata irin zuri'a masu matuƙar hatsarin gaske. Na ga takobi a cikin jininta sannan wuta na gewaye sashenta, takaicina ɗaya Mahaifiyarta ta riga da ta binne duk wani al'amari da sirrin da ke ƙunshe a cikin rayuwarta. Daga ni har sauran matsafan duniya duk wani bincike da za mu yi ba za mu tantance takamaiman ainihin tushenta ba. Sai dai kuskure guda  mahaifiyarta ta tafka wanda da shi kaɗai za mu iya cin galaba a kan wannan yarinyar." Cike da zumuɗi Fulani Umaima ta furta. "Mene ne shi? Duk wuya duk tsaninsa zan nemo shi..." "Bincike ya bayyana mini tana da matuƙar tasiri a rayuwarsa. Ina nufin jaririn da kika sa Maimuna ta fitar da shi shekara goma sha ɗaya baya, shi yake gab da shigowa gidan sarautarku. Sai dai kuma ita da shi za su kasance tamkar wuta da ruwa a fannin gaba, kowannensu ba zai ƙaunaci ɗan'uwansa ba. Shigarsa tamkar dasa nakiyar da ke tashin zamani da alƙaryarki ne, ba tun yau ba; na gaya miki shi ba kamar ɗan uwansa ba ne. Ruhinsa ɗauke yake da zaratan dakarun da ke sarrafa zuciya da tunaninsa, tun ranar haihuwarsa na fahimci zanen ƙaddararsa ya wanzu dalilin da ya sa na baki shawarar matse kunamar nan a cikin bakinsa, ashe tagwaye ne halwar tsafina ya gagara nuna mini. Tun yana jariri ya sauka a fadar Sarkin fararen aljanun doron ƙasa, da ke tsakiyar dajin Wuruju a daidai wurin da Baiwa Maimuna ta dire shi. Sun naɗa masa kambun da babu mai iya sauke shi sai mutum ɗaya wato wannan yarinyar." Bamaguje ya ƙarasa maganar yana haska wa Fulani Umaima inuwar wata yarinyar. Ta tsinci muryarsa ya ci gaba da faɗin. "Mu koma maganarmu ta baya na kuskuren da mahaifiyar Fargi ta tafka. Ta bar tauraron 'yarta a sake wanda duk wani matsafi kallo ɗaya ko bincike ɗaya idan ya yi a kanta zai fahimci muhimmancinta gare sa. Duk wanda ya mallaki ruhinta shi zai kasance mafi shahara a faɗin yankin nan a ɓangaren gawurtar tsafi da sihiri, runduna ce guda a tare da ita domin mahaifiyarta kafin ta mutu ta riga da ta juye mata nata jinin a jikinta." "Mene ne mafita, don ta ni gabaɗaya a mutu har liman a rasa mai jan sallah." Cewar Fulani Umaima da zuciyarta ta gama ƙeƙashewa. "A baya na fid da rai da samun wannan ɗaukakar, amma idan kin yadda me zai hana mu jefi tsuntau biyu da dutse ɗaya?" Mai Gado "Guduwa ita ce mafita, sai dai mu bar garin nan amma ka san muddin muna cikin ƙauyen nan Malmo ba zai bar mu da sauran numfashi ba." Shiru ya yi yana tunanin shawarar da ta kawo, ganin ya tsaya yana nazari ya sa Mai gado ta faɗa ɗaki ta ɗaura kayansu a cikin ɗankwali ta fito. "Allah ya sani na ɗauki aniyar kula da yarinyar nan, Malmo azzalumin mutum ne, na san halinsa sarai tun da ya ƙallafa rai a kan yarinyar nan ko mun damƙa musu ita sai sun hallaka mu don gudun tonuwar asirinsu." Mai gado ta faɗa tana miƙa wa Umaru ƙullin kayansu, sai da ya karɓa sannan ya furta. "Na gode wa Allah ya sa kika fahimtar da ni da tuni na sa mun yi tsalle mun afka cikin rijiya gaba dubu. Yanzu dai babu sauran lokaci mu bi ta ƙofar baya." Cikin sauri Mai gado da Umaru suka hankaɗe katangar karan da ke gewaye da gidan, kamar masu shirin tashi sama haka suka dinga sauri suna kutsawa ta ciki bishiyu duk da a lokacin magriba ta kawo kai. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka ƙarasa wani ƙaramin gari a lokacin dare ya tsala sosai babu haske sai na farin wata, a gajiye suka zube a gefen ganuwar garin suna sauke ajiyar zuciya. Cike da galabaita Jawahir ta fara mutsu-mutsu sai a lokacin suka shiga damuwar abin da za su sama mata ta sha. Gorar ruwa Mai gado ta kunto ta ba ta sannan suka yi jigum-jigum, har sun zauna da sunan hutawa Umaru ya furta. "Mai gado an ya wurin nan yana da kyau kuwa? Me zai hana mu ƙarasa cikin garin nan mu nemi alfarma?" Mai gado ta yi murmushin takaici, "Duk in da za mu je matuƙar za su fahimci ba na shayar da yarinyar nan dole za su harbo jirginmu, kuma su ɗora mana zargi da tambayoyi a kanmu. Abin da muke gudu kuma ya faru ka ga an ƙi cin biri an ci dila." Umaru ya yi jum sannan ya furta. "Ina ganin mu ƙarasa bakin kasuwa mu kwana asubar fari sai mu bar garin, mu ɗora daga inda muka tsaya." Ta gamsu da shawararsa don haka suka yi gaba suna tambayar kasuwar garin har Allah ya datar da su, suna gab da shiga kasuwa suka ga wata mai fura da nono suka siya nono sannan suka ƙarasa. A bayan rumfunan kasuwar suka yada zango bayan sun take wa Jawahir cikinta da nono, babu jimawa baccin gajiya mai nauyi ya yi awon gaba da su. Sanyin asuba ne ya bige su suka farka don haka kamar marasa gaskiya suka sake nufar doguwar hanyar suka ci gaba da tafiya. Ba su yi tafiya mai nisa ba suka tsaya suka gabatar da sallah sannan suka ɗora daga inda suka tsaya. Sai da suka yi tafiya mai nisan gaske sannan suka tarad da wani ayarin mutane, yara, manya, maza da mata. Sai kuma Dogarawan da ke kai kawo a kansu, kallo ɗaya Umaru ya yi musu ya fahimci bayi ne aka kama. Da yake suna ɗan nesa da su da sauri Umaru ya ja hannun Mai gado ya furta, "Maza zo mu gudu idan Dogaran nan suka gan mu na tabbata kashinmu ya bushe don mun zama Bayi na har abada." Yana rufe baki suka juya da sauri. Cak! Suka tsaya cikin faɗuwar gaba, Mai gado ta riƙo hannun Umaru jiki na karkarwa. "Gidan uban wa za ku gudu?" Kalaman Sojan masarautar mai ƙirar samudawa ya ratsa su, gabaɗayansu aka rasa mai bakin magana. Ganin haka ya sa Dogarin tsula wa Umaru bulala a baya, cikin azaba ya hau susar baya yana faɗin. "Tuba nake ranka shi daɗe ba guduwa za mu yi don Allah ku yi mana rai." Da hannu Dogarin ya nuna musu hanyar da sauran mutanen da ke zaune a ƙasa suke, babu musu Mai gado da Umaru suka bi hanyar ba tare da sun furta komai ba. Tun da suka tunkari wurin mutanen wurin suka zuba musu na mujiya suna kallonsu.   Bai san dalili ba haka kawai yake jin ƙirjinsa na bugawa, zuciyarsa kamar za ta yi tsalle ta hudo ƙirjinsa. Duk taku ɗaya da Mai gado take yi tana kusanto shi ji yake kamar ana ɗana wa zuciyarsa ruwan dalma, da wata irin ƙuda da wani surutai da ya gagare tantance harafi ɗaya ballantana ya yi wa kalaman nasu hisabi. Da yake hannunwansa biyu a ɗaure suke a jikin itace, kansa ya tura cikin ƙafafuwansa yana runtse ido. Bai yi aune ba ya fara jin sautin kukanta a tsakar kansa, yana yunƙurin buɗe idonsa kamar a mafarki ya ji an furta. "Ita daban ce don haka ta fito daga cikin wani irin ahali, tarayyarku alheri ce mai samar da taimakon juna a koyaushe. Sai dai zuciyoyinku za su gagara ba ku haɗin kan da za ku cimma manufarku ta alheri. " Firgigit ya ɗago kansa cikin mamaki, ba yau ce rana ta farko da ya fara jin waɗansu irin surutai a kansa ba. Amma na yau sun matuƙar dagula lissafinsa. "Wace ce ita?" Ya furta a fili. A daidai lokacin aka kama Umaru aka ɗaure ita kuma Mai gado aka kama ƙafarta ɗaya aka ɗaure, ta ci albarkacin jaririyar da ke bayanta. "Idan muka kama hanya a yanzu babu wani sauran hutu da za mu ƙara yi a hanya, domin mun kusa shiga cikin ƙasar Zazzau." Wani turɓunannan mutum ya furta fuskarsa a murtuke babu fara'a. A galabaice cikin yunwa, ƙishirwa da wahalar tafiya suka ɗauki hanyar da za ta sada su da ƙasar Huddam. Sai da suka yi tafiya ta kusan sa'o'i shida sannan suka ƙarasa cikin masarautar ta Huddam. A lokacin da suka je daidai ƙofar shiga Jawahir da ke a bayan Mai gado ta fara wata irin jijjiga idanuwanta suka fara yunƙurin kakkafewa, cike da tashin hankali Mai gado ta sauko ta, ganin halin da take ciki ya sa ta ƙwallah kururuwa cikin neman agaji. Da sauri Dogaran da ke wurin suka buga mata tsawa. "Hattara dai muna gab da shiga masarauta..." Ganin Jawahir na ci gaba da shiɗewa ga wani irin jini da ke tsiyaya daga hanci da kunnenta ya sa Mai gado ta furta. "Ku taimaka mini ɗiyata za ta mutu." A fusace wani Dogari ya ƙarasa da niyyar zubga mata bulalar da ke hannunsa, gannin halin da Jawahir ke ciki ya sanyaya jikinsa, yana shirin yayyafa mata ruwa suka ji gijif alamun faɗuwar abu. Suna waigawa suka hangi Kamalu ya faɗi ƙafarsa ɗaya na jijjiga, daga ƙugunsa zuwa tafin ƙafarsa take ya sauya launi zuwa jawur, jini ya fara zuba daga cikin kunnuwansa. Ganin haka ya sa Dogarawan suka sa aka ɗauke shi aka shiga da shi ciki, jiki a sanyaye Mai gado ta rufa musu baya hannunta rungume da Jawahir da har lokacin ba ta daina kakkafewa ba. Fulani Umaima   Da yanayin damuwa ta dube shi, "Ban fahimci kalamanka ba Bamaguje." Bamaguje ya tattara nutsuwarsa wuri ɗaya ya furta. "A lokacin da nake ƙarami burin mahaifina kenan ya mallaki ruhin wannan yarinyar, sai dai kash binciken farko da ya yi ya bayyana masa lokacin da yarinyar za ta zo duniya ba ya raye. Ni kaina na yi tsammanin a farkon rayuwata za ta wanzu, amma sai ga shi sai da tsufa ya make gangar jikina. Ina son ko ba yanzu ba idan kun haɗu da yarinyar nan ki ribace ta har zuwa wannan tsibirin nawa. Domin ba za mu iya kamata da alƙaluman tsafi da sihiri ba, idan kika yi haka tamkar kin kawo ƙarshen rayuwar yaron da kika sa aka fitar da shi daga cikin masarautar ne. Wannan kaɗai za ki aiwatar mini sauran bayanan zan yi miki su daga baya." Fuska ɗauke da damuwa ta furta. "Ban santa ba ban taɓa ganinta ba ta yaya kake tunanin zan gane ta har na ribace ta na kawo maka ita?" Murmushi Bamaguje ya yi ya furta. "Daga shi har ita ba su kasance kamar kowa ba, kuma shigarsu cikin masarautarku zai ƙara tayar da rikitattun al'amuran da ke cikinta. Masarautarku shu'umar masarauta ce da ke raye a ƙarƙashin ikon waɗansu ɓoyayyun hallitu. Ko ban faɗa miki ba shurin da ke cikin turakar Takawa akwai dalilin wanzuwarsa, tun da kin san banza ba ta kai zomo kasuwa. Zan sake bincike game da wasu al'amuran ko za mu da ce a wannan karon." Bamaguje yana rufe baki ya watsa wani baƙin jini a cikin wata tukunyar ƙasa take wuta ta fara ci gangan-ganga, shiru ya yi yana nazartar abin da yake faruwa zuwa can ya saki wata irin dariya. Shiru Fulani Umaima ta yi tana kallonsa cike da ƙosawa. "Wani abin farinciki da ban za ta ba, kusan gabaɗayansu ruhinsu na da kusanci da juna..." Kalamasa suka katse sakamakon ganin wutar gabansa ta ɗauke yo kansa kamar za ta ƙone shi sai kuna ta ɗauke ɗif, bai so haka ba amma ko babu komai ya tsinci waɗansu abubuwa da za su ba shi narasa a game da yarinyar. "Ki sa ido sosai a wurin da kika binne jariran da kika taɓa binnewa a bayan ɗakin Sarki Abdul'aziz. Matuƙar kika ga an tone ta ba kowa ba ne face jininsa, ina nufin jininsa da kika fitar da shi. Idan har kika ga kan tinkiyar da kika rataye a ɗakinki wanda a kullin jini yake ɗiga a kan zanin kishiyarki ya fara tsutsa ta tabbata gabaɗaya su biyun suna da kusanci da ke, wato suna rayuwa a cikin masarutarku. Idan ba ki manta binciken da na yi miki a baya na gaya miki akwai wanzuwar rayuwar waɗansu ruhi masu ɗauke da rikitattun al'amura a cikin masarautarku waɗanda suke yunƙurin shiga al'amuran masarautarku. Lokacin ganawata da sarkin baƙaƙen aljanin ƙarƙashin ƙasa ya yi, zan ba shi aikin matar wani attajiri akan kishiyarta, ki ba ni wuri sai wani lokacin idan kin sake dawowa." Fulani Umaima guntun tsaki ta saki cike da takaici, ta yi masa bankwana ta koma ɗakinta.   Lokacin da aka shigar da su Baffajo sashen Bayi aka wuce da su, kusan gabaɗaya jikinsu a sanyaye yake sakamakon ganin halin da Kamalu da Jawahir suke ciki don a tsammanin mutane da yawa mutuwa za su yi. A hankali Kamalu ya fara buɗe idanuwansa yana ganin mutane dishi-dishi, ajiyar zuciya ya sauke ya yunƙura da ƙyar; da sauri Baffajo ya ɗago shi yana zubda ƙwallah. Mutanen da ke wurin suke bi su da kallo cike da mamaki, Inna wuro ta share ƙwallah tana faɗin, "Na faɗa maka Kamalu ba zai mutu ba." Baffajo ya jinjina kai yana tallafo haɓarsa, "Amma har yanzu jikina yana ba ni za su iya halaka mini shi, wataƙila ba za su bar mana shi ba." Kamalu da ke zaune bai tanka musu komai ba sakamakon wata irin juwa da ke ɗibansa, waani dattijo tsoho ya gani a gabansa ya sakar masa murmushi tare da faɗin. "Muna ta ya ka murnar dawowa cikin ahalinka, ka tashi ka ƙarasa bakin rafin can ka ɗebi ruwan cikinsa ka ɗura a kunnenka, ka damƙi ƙasar cikinsa za mu yi maka iso har bayan turakar Mai martaba yanzu, aikin da za ka zartar sai kai domin abin salsala yake bi." Kamar wanda aka ƙara wa ƙarfi haka Kamalu ya miƙe daƙau, Dattijon ya kama hannunsa ya fara tafiya Baffajo da Inna wuro suna ƙwala masa kira, ko waiwayensu bai yi ballantana su saka ran zai tanka musu. *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624.* *SHU'UMAR MASARAUTA*        ©AMEERA ADAM *FIRST CLASS WRITER'S ASSO...* *Masu ƙorafe-ƙorafe ta pc da groups zan rage 100 daga yau zuwa ranar da zan gama free pages. Free pages za su ƙare a page a 10 daga yanzu zuwa ranar duk mai son karanta littafin za ta turo 400*    LAST FREE PAGES SHAFI NA GOMA *🤔WAI NA CE KINA DA WAƊANNAN MATSALOLIN AMMA KIKE ZAUNE DA TARUN TUNANI FAL KWANYA?* *MAMAN MEENAT COLLECTION, MAMAN MEENAT SUPPLEMENT/SKIN CARE* *SHIN YAR UWA KINADA LABARIN* *SHAHARARRIYAR MAI SAYAR  DA SUPPLEMENT DIN NAN KUWA?* *TO IDAN BA KI SANI BA KIYI MAZA KI GARZAYA DOMIN KEMA KI SAMU RABONKI DOMIN ZATA GYARAKI TSAF KI FITO KAMAR SABUWAR AMARYA, KEMA KI SHAGA CIKIN MATAN DA SUKE HASKAKAWA KAMAR TAURARO. SHIN ƘURAJE NE SUKE DAMUNKI, KO KUMA MATSALOLIN JIKINE KAMARSU RAMA BUSHEWAR FATA KARANCIN NI'IMA NE KO BUDEWA NE, KO KUMA INFECTION? KO KUMA SO KI KEYI FATARKI TAYI LAUSHI KIDIN GA SHEƘI KINA HASKAWA? TO MAZA KI GARZAYO WURIN MAMAN MEENAT DOMIN KI SAMUN MAFITA CIKIN SAUKI, ACIKIN FARASHI ME SAUKI* *SANNAN YAN UWA KUSANI DUK* *SUPPLEMENT DIN DAZAMU KAWO MUKU SAI MUNYI BUNCIKE AKANSHI DAN TABBATAR DA INGANCINSHI MUN TABBATAR DA CEWA BASHI DA WATA* *MATSALA GA LFY, AKWAI MASU CEWA SUNSHA SUPPLEMENT AMMA HAR YANZU SU BASUGA WANI CANJI BA, TO YAR UWA KODAI AN BAKI FAKE KO KUMA BA'A BAKI WANDA YA DACE DAKE BA, KO KUMA BAKISHA YADDA YA KAMATA BA, DOMIN KISANI YAR UWA KAFIN KI FARA SHAN* *SUPPLEMENT AKWAI WASU KA'IDOJI DAYA KAMATA ACE KIN KULA DASU KUMA KIN KIYAYE, MATUKAR KINASO SUYI MIKI AIKIN DA KIKESO CIKIN SAURI, WANNAN KA'IDODIN SAI KIN NEMENI ZAN SANAR MIKI, DOMIN BAZAN IYA KAWOSU ANAN BA SBD SUNA DA YAWA* *Yar uwa muna da duk wani supplement da kuke bukata masu kyau da inganci tested and trusted, sayen na gari mai da kudi gida, gaskiya da Amana shine takenmu 08039437158.* 👉 *Supplements suna da yawa amma ga kadan daga cikin su.* *1.  Supplements na gyaran jiki ciki da waje* *2.   Supplements na gyaran gashi da farce, dasa haske mekyau ba irin na bleaching ba* *3.  Supplements mai da tsohuwa yarinya anti aging wanda zaisa ki kullum ki koma kamar yarinya matashiya* *4.  Supplements na karawa fata kyau da sheki  glowing skin* *5.   Supplements na masu fama da ciwon jiki da stress da rashin samun isashshen bacci* *6.   Supplements na masu ciki, da masu shayarwa wanda zai kara miki lfy keda babynki* *7.   Supplements na gyaran jiki da gashi, kara hasken ido da sauransu* *8.  Supplements me kara lfy da karawa garkuwar jiki karfi.* *9.  Supplements na karin ni'ima da dandano da tightening ciki da waje* *10.  Supplements na magance cututtuka, kamar matsalar ido ulcer, infection, karawa garkuwar jiki karfi, etc* *11.  Supplements na gyaran nono da mazaunai breast/hips Enlargement* *12.  Supplements na gyaran HQ ciki da waje* *13.  Supplements na rage tumbi slimming capsule/flat tummy Lipton* *14.  Supplement na whitening/glowing skin* *15.  Supplement for Acne, dark spots remover* *Da duk wasu nau'in supplement da kuke bukata, sannan Maman Meenat collection ba anan kadai ta tsaya ba muna saida turaruka kowanne irin na wuta dana jiki, da Airfreshners, sayen daya ko sari ke dai kawai neme ni a wannan number call or chat 08039437158*       Ba iya su Baffajo ba hatta sauran Bayin da ke wurin sai da suka rufa musu baya, sakamakon ganin wurin da Kamalu yake ƙoƙarin kai kansa. A tarihin masarautar babban kuskure zuwa rafin tsamiya da doshin magriba, hasali ma a ranar juma'a akwai abubuwa biyu da suka haramta ga mazauna cikin masarautar. Na farko, duk ranar juma'a haramun ne shan nonon shanu, awaki ko na raƙumi. Duk wanda ya yi gangancin karya wannan ƙa'idar kuma zai iya tsintar talatarsa a laraba, domin a labarin da yake yawo a cikin masarautar an ce shekara sama da ɗari an taɓa samun turka-turka tsakanin Sarkin da ke mulki da Bafulatanar Aljana kafin daga baya aka sasanta, amma wannan labarin kusan na kunne ya girmi kaka ne don babu wanda kai tsaye zai ce maka ga daga wurin wanda  ainihin labarin ya fito. Shi kuma wannan rafin ana kiransa da rafin tsamiya sakamakon wata narkekiyar bishiyar tsamiya da ke girke a tsakiyar rafin, shi wannan rafin yana daga can gefen sashen bayi kuma rafi ne mai hatsarin gaske. Ba a taɓa ganin ya ci mutum ba, sai dai duk wanda ya yi gangancin shiga cikinsa ranar juma'a, zai fito lafiya ƙalau daga cikinsa amma a ranar za a neme shi sama ko ƙasa a rasa. Wasu daga cikin mutanen gidan masarautar sun ce faɗan Bafulatana ne ya shafi rafin yayin da wasu suka ce alƙwarin babban sarkin Aljanin ruwa ne yake cika dalilin wata yarjejeniya da ke tsakaninsa da Sarki Muhammad Safwan wato Kakan Sarki Abdul'aziz na uku. Sarki Muhammad Safwan ya yi mulki kafin hawan Sarki Abdul'aziz da shekara ɗari da biyar, har zuwa wannan lokacin babu tsayayyiyar wannan magana. Sai dai duk mazaunin cikin masarauta ya kwana da sanin masarautarsu ta sha bambam da sauran masarautun da ke wannan nahiyar musamman a kan al'amura masu rikitarwa da ban mamaki.   Da sauri Baffajo ya sha gaban Kamalu cike da damuwa ya furta, "Kamalu hai ina za ka je ne, can ba ka ganin kududdufi ne?" Tsohon da ke riƙe da hannun Kamalu ya sakar masa murmushi haɗe da faɗin. "Tabbas sun kasance iyaye masu baka kulawa amma ka sani dakatarwarsu tamkar komawar cigabanka baya ne." Jin Kamalu ya yi shiru ya sa Inna wuro ta furta, "Kamalu ko wani abu yana damunka ne?" Girgiza kansa ya yi ya furta, "Inna wani ne ya ce na je cikin ƙoramar can." Ras! Gaban Inna wuro ya faɗi, tana shirin yin magana daga bayansu suka ji an furta. "Tun wuri ku kama ɗanku idan ba haka ba wallahi matuƙar ya shiga cikin wancan rafin a yau sai dai nan gaba ki haifi wani." Uwar Bayi ta yi maganar cikin halin ko-in-kula. Take jikinsu ya ɗauki karkarwa, Kamalu na kai dubansa wurin tsohon ya ga ya tsuke fuska rai a ɓace ya furta. "Kai ba kamar kowa ba ne, jininka yana da bambamci da nasu don haka ba koma ne za ka riƙa bankaɗa musu sirrinka ba." Yana gama faɗar haka ya ɓace masa. A lokacin tuni Baffajo sun riƙe hannuwansa bibbiyu sun koma da shi cike da tsoro. Komawarsa babu jimawa Jawahir ta farfaɗo tana yin wata irin shaƙuwa mai ƙarfi, duk wanda yake wurin sai da jikinsa ya yi sanyi ganin halin da ƙanƙanuwar yarinya take ciki. A hankali take sauke numfashi, Mai gado ta sa ruwa da ɗankwalin kanta ta goge mata jinin fuskarta. Buɗe baki ta fara yi alamar tana buƙatar abinci, a nan ne kuma hankalin mai yankan kaba ya koma ga rina domin Mai gado ta manta sam da batun nonon da za ta bai wa Jawahir. Cikin damuwa ta kalli wata Dattijuwa. "Baba don Allah ku taimaka mini ko da nonon akuya ne yarinyar nan shi nake bata." Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna a firgice, Uwar soro ta ce. "Baiwar Allah sai dai kam ki bata wani abin ba nono ba domin yau juma'a kuma duk ranar juma'a ba a shan nono a gidan duk wanda ya sha ya dinga aman nono har a zare ransa." Mai gado na jin haka ta rushe da kuka, don ɗan kwanakin da ta yi da Jawahir ta shiga ranta sosai. "To ke me ya sa bakya ba ta nono?" Mai soron baƙi ta sake wurga mata tambaya." Mai gado har za ta fallasa alaƙar da ke tsakaninsu da Jawahir sai kuma ta tuna da kalaman mahaifiyarta a lokacin da ta haife ta. "Tun lokacin da na haife ta babu ruwan nono a jikina, kafin zuwanmu nan har magani mun nema amma a banza kare ya sha tsamiya." Waɗannan kalaman na Mai gado suka ƙara dasa tausayin Jawahir a zuciyoyin mutanen da ke wurin, "Bakin da Allah ya tsaga na tabbata ba zai hana shi abinci ba, akwai baiwa Zinaru da ke shayarwa mai zai hana a roƙi alfarmar yau ɗaya ta shayar da ita?" Uwar tuwo ta furta. Zuciyar Mai gado ta yi ƙal ta ƙarasa wurin Baiwa Zinaru da ke goyon ɗanta mai kimanin shekara guda. Take Zinaru ta amsa ba ta musa ba, sai dai tana ɗaukar Jawahir ɗanta da ke gefenta ya ƙanƙame mahaifiyarsa yana tsanyare wa da matsanancin kuka haɗe da cusa kansa cikin jikin mahaifiyarsa. A lokacin babu wanda ya kawo komai a ransa don a tunaninsu ma kishine irin na yara yake yi don ya ga an ɗauki wata yarinyar, kai tsaye Zinaru ta rungume Jawahir ta fara shayar da ita, wani irin zuuu! Zinaru ta ji tamkar wacce aka kafa wa shocking har tsakiyar kanta. Ga wata irin zuƙa da take ji Jawahir na yi kamar za ta fige maman jikinta, suna nan tsaitsaye ruwan nono ya fara dawo wa Jawahir ta hanci da kunnuwanta. Wannan yanayin da  ta shiga ya sake faɗar da gaban mutanen wurin, cikin masifa Jakadiya ta fara magana. "Wannan wacce irin masifa aka kawo mana saboda Allah, yarinyar tun da aka kawo ku sai faɗar mana da gaba kike yi." Mai gado jiki a sabule ta karɓi Jawahir ta fita zuwa bakin wata bishiya ta zauna cikin sarewa ta fara zubar da ƙwallah. Jawahir ta jima a haka sannan nonon da ke fita daga jikinta ya dakata da zuba, ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ta sake goge mata haɗe da saka ta a baya ta goya ta. A ranar kusan kwanan zaune mai gado ta yi cike da rashin sabo da zaman baƙunta, uwa-uba rashin kyakkayawan makwancin saɓanin wanda suka saɓa kwana a ciki.   Cikin Dare.      Wata doguwar hanyar ya bi samɓal yana tafiya wacce babu komai sai dogayan bishiyu, tsawo da girmansu ya haddasa wa wurin duhu mai ban tsoro. Daga bayansa ya ji kamar ana bibiyarsa don haka ya yi saurin waigawa cikin tsoro da tashin hankali, wata baƙar mage mai ratsin fari ya gani tana tafe tana shinshina sawunsa. Tun bai yi wayo ba yake ƙaunar kyanwa don haka ya tsugunna da niyyar kai hannu kanta, da sauri ya ji an fisge shi gefe waɗansu surutai na tashi sama-sama a cikin kunnuwansa. Waigawa ya yi bai sake ganinta ba, ya ci gaba da tafiya. A jikin wata murgujejiyar bishiyar kuka ya hangi wata rantsatstsiyar karaga, "Je ka ƙarasa kan karagarka." Ya ji an furta masa. Wani irin sanyi ya ji yana ratsa shi, jiki a sanyaye ya fara takawa da niyyar hawa kan shimfiɗar da ke ɗauke da karagar, ga mamakinsa sai ji ya yi wannan baƙar magen ta hankaɗa shi gefe ɗaya. Ta ɗora wani mulmulallan abu mai kama da ƙawai a kan karagar, sannan ta fara zagaye karagar cikin ƙasaita. A can ƙasa ya faɗi kansa ya bugu da wani farin dutse take jini ya fara ɗiga, dafa wurin ya yi cikin azaba sai gani ya yi magen ta ƙaraso tana lasar jinin da ke zuba daga goshinsa. Ta fara ɗaga kanta tana da alamar tana son kai wa kansa farmaki wurin da ragowar jinin yake ɗiga. Ganin ta dumfaro shi ya sa ya ci gaba da ja baya zuciyarsa na dakan luguje, ganin haka ya sa magen ta fara wata irin dariya fiƙoƙinta na zubowa ƙasa ɗaya bayan ɗaya. Duk wurin da fiƙar ta faɗa sai ƙasar wurin ta rufta har ta yi tsalle za ta damƙi saman goshinsa. Firgigit Kamalu ya tashi cikin matsanancin tsoro, firgici da tashin hankali. A lokacin dare ya tsala sosai, ban da munsharin mutanen ɗakin da kukan tsuntsaye babu abin da yake tashi. Jin abu na gangaro masa a goshi ya sa ya kai hannunsa ga mamakinsa ya ji ya taɓa abu, da sauri ya yunƙura zuwa wurin aci-balbal ɗin da ke kunne a gefen ɗakin ya haske. Rass! Gabansa ya faɗi, jikinsa ya ɗauki karkarwa kamar mazari. "Jini!" Ya furta a kiɗime. Yana shirin komawa ya tashi Baffajo ya sanar da shi abin da faru ya ji an dafa kafaɗarsa. "Wannan gidan ba irin kowanne gida ba ne, sai ka ɗaura ɗamarar juriya da jajircewa. Gadon gidanku ba a sansu da sarewa ba, ka zama jarumi mara tsoro a haka ne za ka ƙwaci kanka. Ka gode wa Allah da ba ta yi nasarar yagar naman jikinka ba, kuma kada ka ɗauka za ta haƙuri. Wannan daɗɗaɗiyar mummunar manufa ca tunkafin haihuwarka, zan yi takaici ƙwarai matuƙar ta yi nasara a kanka kamar yadda ta ci galaba a kan mahaifiyar..." Sam Kamalu baya fahimtar kalaman da farin dattijon ke gaya masa, cike da damuwa ya katse shi. "Don Allah wane ne kai? Ya aka yi ka san mafarkin da na yi?" Murmushi Dattijon ya yi, "Yaro man kaza! Da sannu za ka fahimci turbar da nake son ɗora ka, izza da ƙasaitar jinin Sarki Muhammad Safwan ba za ta tashi a banza ba. Ba ni zan bayyana wa duniya waye kai ba, izza da tasirin jinin sarautar da ke jikinka ne zai bayyana wane ne kai. Ni Aminin Kakankakanka ne, ina bibiyar al'amarinka saboda waɗansu muhimman abubuwa da tasirinsu. Ta so mu je ka wanke ciwonka a wancan rafin, idan gari ya waye kada ka sanar da kowa mummunan mafarkinka hatta Baffajo da Inna wuro, domin wannan gidan sarautar cike yake da idanu mabanbanta."   Tamkar raƙumi da akaɗa haka Kamalu ya bi bayan tsohon yana gaba shi kuma yana biye da shi, lokacin da suka ƙarasa bakin rafin wani irin sanyi ne ya fara ratsa shi har sai da jikinsa ya ɗauki rawar ɗari. Kaf kaf kaf haƙoransa suka fara rawa, ga wata irin juwa da take ƙoƙarin fisgar shi ko ta halin ƙaƙa, ɗagowa ya yi a wahalce ya furta. "Ba zan iya ba, ba zan iya zuwa ba sanyi nake ji." Rufe bakin Kamalu sai dajjijon ya sa hannunsa a tsakiyar goshinsa, a hankali ya ji sanyin da yake ji yana raguwa, "Ba na jin daɗi a duk lokacin da ga karaya a ƙwayar idonka, daga yau kada na sake jin ka furta kalmar gazawa. Tabbas za ka iya domin duk tsawon lokacin da muka ɗauka lokacinka muke jira, mu je ka aiwatar da abin da yake gabanka." Dattijon ya faɗa yana kama hannun Kamalu ya sanya ƙafarsa ta dama a cikin rafin, wani irin zuuu! Ya ji har cikin kwanyarsa. Gabansa na faɗuwa ya tsugunna a ɗebi ruwan ya wanke ciwonsa kamar yadda tsohon yake ba shi umarni, yana gamawa ya sake ba shi umarnin wanke fuskarsa ya ɗura masa ruwan a cikin kunnuwansa. Ruwan ya gani ya fara kaɗawa a hankali, daga baya kuma ya ga igiyar ruwan tana katantanwa da su. Yana shirin guduwa tsohon ya riƙe shi tsam a jikinsa, ganin a kowanne lokaci yana iya halaka ya sa Kamalu runtse idonsa. Sannu a hankali ya ji komai yana lafawa, hakan ya sa shi buɗe idonsa suka fara takowa suka fito daga ciki. Wani irin sauti yake ji cikin sigar kururuwa da neman ɗauki, lokaci ɗaya ya ji zuciyarsa na fisgar gangar jikinsa. Tafiya yake yi ba tare da ya san wurin da yake jefa ƙafafuwansa ba har ya zagaya wurin da yake jin ƙarajin sautin na kusantarsa a bayan ɗakin Mai martaba. A saitin kusurwar yamma ya hangi wani mulmulallan abu baƙi saboda duhu bai tantance takamaiman mene ne ba. Cikin dakiya da ƙarfin zucuya ya sa ka hannu da niyyar tonowa take zoben hannunsa ya mamaye wurin da haske, a nan ya yi tozali da wani abu mai tsananin wari da siffar jarirai har sai da ya ji tamkar ya amayar da kayan cikinsa. Tsaki ya yi cike da jin haushin abin da ya aikata, shi kansa bai san dalilin da ya sa shi aikata haka ba, ya dai ji ba za iya haƙura ba har sai ya taimaki abin da yake cikin ƙarƙashin ƙasar. Koda ya koma sama da ƙasa ya nemi Dattijon ya rasa, a bakin ƙofar ɗakinsu ya hangi Baffajo yana kai wa da kawowa yana ganin Kamalu ya ƙarasa yana tambayarsa inda ya je. "Baffajo fitsari ne ya tashe ni, na ga kana bacci shi ya sa ban tashe ka ba." Ya tsinci kansa da ƙin faɗa wa Baffajo gaskiyar abin da ya faru. Riƙo hannunsa Baffajo ya yi tsam kamar wani zai ƙwace shi suka ƙarasa cikin ɗakin, ƙwallah ce ta ciko idanun Baffajo ya furta. "A wannan farautar da aka yi mana mun rasa Salele Kamalu yanzu haka ban san duniyar da ya nufa ba, don Allah kada ka yi yunƙurin abin da zai raba ni da kai, ka ga wancan rafin dai an ce hallaka mutane yake don Allah koda wasa kada na ga gilmawarka a wurin." Kamalu ya jinjina kai sannan ya koma ya kwanta cike da tausayin mahaifinsa.   Tun da asubar fari aka tashi duka Bayin da ke sashen kamar yadda aka sunnanta musu, bayan sun idar da sallar asuba Uwar Bayi ta shiga raba wa sababbin Bayi aikin da za su gudanar, waɗanda suka san aikinsu kuwa suka ci gaba ɗorawa daga inda suka tsaya. Sai da rana ta fara fitowa sannan suka samu zarafin kai abinci cikin bakunansu, Mai gado ita da Inna wuro kusan ɗura suka yi wa kansu da sauran baƙin Bayin da aka kawo su rana ɗaya. Baiwa Fatsim na ganin yadda suke cin abinci ta saki shewa tana yi musu kallon sheƙeƙe ta furta. "Ahayye! Allah na dawo inji kishiyar mai yaji, duk wannan feleƙen da kuke yi gumi ce ba ta yi gumi ba. Amma da sannu za ku gane karatuna." Gabaɗaya babu wanda ya tanka musu, wata Dattijuwa da suka ji ana jira da Uwar tuwo ta ƙarasa wurin ta ce, "Tun wuri ku cire kawaici da kara ku fara ƙwatar wa kanku 'yanci idan ba haka ba kowa takaku zai yi kamar takalmin sawarsa. Wannan gidan yana da matuƙar bambamci da wuraren da kuka fito..." Sallamar Jakadiya ta katse ta, fuska a haɗe ta dube su ɗaya bayan ɗaya. "Zan ɗebi sababbin Bayi gabaɗayanku zan kai ku sashen Fulani Umaima tana son zaɓar waɗanda suka yi mata domin tana buƙatar ƙarin masu yi mata hidima." Jin babu wanda ya tanka mata ya sa ta buga musu tsawa, jiki na rawa duka suka miƙe sai Inna wuro da ke faman jera loma da sauri don ita idan tana cin abinci tana tashi duk daɗin abinci ba ta iya cinsa, ballantana a nan da abincin dare da suka ci ko kaɗan bai ishe su. Jakadiya ta leƙa ganin Inna wuro na zaune. "Ke ce shafaffiya da mai ba ki ji abin da na ce ba?" Baki na rawa Inna wuro ta sanar da ita uzurinta, ai kuwa lokaci ɗaya ta ji an kwashe mata da dariya. "Ke a tsammaninki tun da kika shigo masarautar nan kina da sauran ikon da kanki? Ko kin manta matsayinki na Baiwa ne? Idan ba ki sani ba ki sani a yadda kika a cikin gidan nan sai yadda aka yi da ke, idan aka so ki kwana a tsaye dole ki kwana, gara tun wuri ki yakicewa kanki ɗan guntun 'yancin da kike taƙama da shi." A sanyaye Inna wuro ta tashi, idanunta suka ciko da ƙwalla. A duniya babu abin da ta tsana sama da yarfi da tozartawa. Babu yadda suka iya haka suka bi bayan Jakadiya haka kawai Mai gado ta tsinci gabanta na matsanancin faɗuwa, tun da suka nufi sashen Fulani Umaima Jawahir ke wani irin mutsu-mutsu har zuwa lokacin da Jakadiya ta sa suka jeru ɗaya bayan ɗaya. A hankali ta fara bin Bayin tana duba su a wulaƙance cikin yarfi da ƙasƙantarwa. Tana zuwa daidai kan Mai gado gabanta ya yanke ya faɗi, ta dube ta a yamutse. "A sauko da wannan jaririyar." Ba musu Mai gado ta kunto Jawahir da jikinta ya yi wani irin sanyi kamar wacce aka ciro daga ƙanƙara. Sauke idanun Fulani Umaima a kan ƙwayar idon Jawahir ya haddasa mata matsananciyar faɗuwar gaba, kalaman Bamaguje suka faɗo mata. Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba sai da ta yi tozali da goshinta. 😁😁 Yanzu ne za a fara buga wasan, Shin me yake shirin faruwa tsakanin Fulani Umaima da Jawahir. Wai ma wace ce Jawahir ɗin nan kuma mutum ce ko Aljan? Ina Dattijon nan kuma me ye alaƙarsa da Shu'umar Masarauta, wai ma me ye silar wannan abubuwan da ke faruwa? Akwai ɓoyayyan sirri mai ƙarfi da Dattijon nan ya sani mai ya sa bai aiwatar da komai ba sai da Kamalu ya zo. Wai shin Bayin Masarautar da shi Kansa Sarki Abdul'aziz za su gane shi ɗin jinin masarauta ne? Idan Fulani Umaima ta fahimta me kuke tunanin za ta aiwatar? Ina labarin Abubakar zai warke a nan gaba ko a'a?😢 Fulani babba tana warkewa daga cutar fitsari ko bata warkewa? Maza hanzarta kada ki bari a yi babu ke, salon labarin daban yake. Namu ba irin nasu ba ne💃🏼💃🏼💃🏼 na san ba ku manta da BAƘAR DAULA ko AN YA BAIWA CE da ZAUJATU JINNUL-ASHIQ ba. Kar ki bari a yi babu ke wannan kafcan.🥳🥳🥳💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼 *Littafin kuɗi ne 500 idan kina buƙata za ki biya ta wannan Account ɗin Aisha Adam 3090957579 First bank ko katin MTN, ki turo da shedar biya ta wannan lambar 07062062624. Cmplt doc 800 ne*