*💋KURKUKUN ƘADDARA💋* *Boss Bature ✍️* _Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_ Gargarɗi _Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_ *E1* Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfin gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, jikinsa na sanye da singlet da gajeran wando fari, aƙalla ya kai shekaru 40 a duniya. A launin fata kuwa wankan tarwaɗa ne, da ƙyar yake iya ware manyan idanuwansa a kan katafaren gadonsa kafin a hankali ya mayar da ƙwayar idonsa kan agogon bangon, tafin hannunsa ya kai tare da shafa fuskarsa cikin sanyin murya ya ambaci sunanta, "Angel!" Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar, cike da mamakin wane ne yake kiran shi a irin wannan lokaci? Anya kuwa Lafiya? Lokacin da ya kalli screen ɗin wayar sunan Aminina ne ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da ɗaga kiran ya manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare." A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?" "Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse. A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call. Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi. Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon ya zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan. Yana cikin wannan halin ha'ula'in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, "Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku." Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel. A matuƙar ruɗe ya miƙe, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key ɗin motarsa ya ɗauko saboda tsabar ruɗu wardrobe ya dosa zai buɗe a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin ƙofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiɗime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko'ina ba sai ɗakin Angel, bugu ɗaya ya yi ma ƙofar ta buɗe, ko'ina duhu, kunna hasken ɗakin ya yi, nan take haske ya gauraye ko'ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke ƙunshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, "Angel, Angle my daughter!Azeezaty!" Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaɗarsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar Range Rover, back seat ya buɗe ya kwantar da Angel tukunna ya buɗe driver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci kusan su shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka da gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror ɗin motar, hakan yasa shi ƙara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheƙar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba. A ruɗe take furta,"Daddy...What's happening, where are u going in this darkness night?" Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali. "Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba." Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheƙar kuka ta kuma cewa, "Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daɗi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata. Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruɗe ya yi parking ɗin motar ya fito ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya ɗauko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yayi cikin dajin da ita yayin da take sa6e a saman kafaɗarshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare da ya ankara ba, ya ɗaura kafarsa saman wani ƙarfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin ƙasa, kaifinsa tamkar na wuƙa, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin ƙafar ya 6ulo ta sama, wani irin raɗaɗin azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke ƙafarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, "Innalallahi wa'inna ilaihir raji'un." Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, "Dad let's go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?" Ta yi tambayar still tana shassheƙar kuka. Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, "Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji." Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji, A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin da ya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan da ta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta. Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa. Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi a mace. A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito. Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi. Guntun tsaki ɗaya daga cikinsu ya ja, "Mala'ika ya riga mu ɗaukar ransa, ba haka na so ba." Na gefensa ya ce, "Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir." Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, "Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter." A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu. "Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abu ne mai sauƙi." Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi. Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu. Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus *Boss Bature ✍️* dedicated to Aunty kubra😘 *E2* _Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_ Gargarɗi _Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube, ba tare da an nemi izni a wurina ba. Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_ The Begining Of The Story,(Farkon Labari) ƙasa ƙasa Cikin baccinsa ya soma Jin sautin kukan Jariri acikin kunnuwan shi, tun abun bai damun shi har kukan Ya fara addabar shi, ya hana shi sakat wanda Hakan Yayi silar farkawar shi daga bacci, a hankali ya ɗan ware manyan idanuwan shi masu ɗauke da Bacci don da alama bai gaji da baccin ba, Ceilling Ya ƙurawa ido kamar mai karanto wani abu, a ƙoƙarin shi naya tariyo abunda kunnuwanshi ke jiyo mashi wanda Yayi silar farkawar sa daga Bacci, Yana ƙoƙarin tunanowa Kwatsam Yaji kukan Jaririn Inya inya, mai sautin gaske, Zumbur ya ƙarasa Janye Blacket ɗin daya Lullu6a dashi Yayi wurgi dashi gefe ɗaya, kayan Bacci ne Ajikinshi Brown Colour Riga da wando, yayi mamakin ganin babu ita asaman gadon, ko ina taje ne? sauko da ƙafafun shi ya yi ƙasa ya yi, Cike da fargaba Ya miƙe yana mai tunanin Inda aka samu Kukan Jariri Acikin Gidansa, Shi dai A iya sanin shi Matar shi bata haihu ba,duk da cikinta nata yakai wata tara, Gaba ɗaya ya ruɗe Yama rasa Ta ina zai ga Jinjirin dake kuka, Domin kuwa sautin ya karaɗe Ɗakin nashi,zukunnawa Ya yi tare da leƙa ƙarƙashin gado, wayam baiga komai ba miƙe wa ya yi da sauri ya nufi wardrobe Ya buɗe ya zazzago da kayan dake acikinta, duk a ƙoƙarin shi naya gano inda aka samu kukan Jariri aɗakinsa, Tuni ya haɗa uban gumi ajikinshi, aran shi harya fara tunanin kodai Aljanune!? abu kamar wasa idan jaririn yayi kuka sai ya lafa ƙasa ƙasa,wannan karan Yanayin kukan tamkar Ana zare Ranshi ne, har wani jan kukan akeyi inyaaaaaaa, "Ka duba toilet"?zuciyar shi ce tayi mashi tambayar, shiru ya ɗanyi kamar me tunanin wani abu,tun da yake arayuwar shi wani abu bai ta6a tsorata shi ba irin na yau, kukan jaririn duk ya firgitar da shi,har wani gumi ya haɗa, Ja da baya da baya yayi a hanzar ce Ya juya gaban Faskeken Madubin ɗakin, Wayar shi ya ɗauko yana dannawa Call logs Ya shiga, missed calls Ya tarar Na Uzair, babban amininsa Calling Layin yayi tana fara ringing, uzair ya ɗaga kiran ko sallama baiyi ba ya soma magana"Uzair Akwai matsala Cikin gidan nan fa!" muryarshi na kerma yayi maganar, On the other hand Uzair yace"Wata irin matsala kenan?   "Kukan jariri ne Ya tashe ni daga bacci,Bansan a ina aka samo kukan ba, kuma na tashi banga benazir ba" "Ka kwantar da hankalin ka, Gani nan zuwa"   "Yawwa,dan Allah kayi sauri" rejecting call ɗin yayi kafin Ya ajiye wayar saman bedside drawer, Walking Slowly Ya nufi hanyar toilet ɗin Cike da fargabar abunda zai taras, cikin sanɗa yake yin tafiyar, jikinshi na kerma,a hankali ya ruƙe Handle ɗin ƙopar ya buɗeta   Haɗadɗen toilet ne Ko'ina Na Cikinshi Fari ƙal atsaftace ba ƙazanta, kamar ance Ya kalli ƙasan tiles,Ba zato ba tsammani Yaga ɗigon jini, Gaban shi ne Yayi wani irin mugun bugu ji kake daram! a firgice Ya ɗago da idanuwan shi yana kallon Cikin toilet ɗin,Wani irin tsoro ne Ya kama shi lokacin daya hango Jikin Bathtub(kwamin wanka) jaga jaga da Jini kamar an yanka ɗan akuya, a ruɗe ya soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un, kamkar a mafarki yake kallon Lamarin, Cike da fargaba ya ƙarasa shiga cikin toilet ɗin don ya gane wa idanuwanshi, a dai dai bakin kwamin wankan Ya tsara turus, Yana Kallon Jinjirin dake Acikinsa kwance,duk jini Ya wanke jikinshi Sai tsanyara kuka Yake yi,    Lokaci guda gabanshi Ya faɗi rass tunawa da wasu maganganu da suka tsaya mashi aranshi tun shekaran jiya     Tuni ya karaya hakan na nufin a daren Jiya ta haihu acikin toilet, saboda ƙarfin hali irin nata har ta iya haihuwa da kanta ta kuma Gudu duk da irin Jinin da ta Zubar, abun yayi mugun ɗaure mashi kai, ga wani irin ƙunci da yake Ji acan ƙasan Zuciyarshi, Tuni hawaye sun wanke fuskarshi, sam bazai juri ganin jaririn shi a cikin mawuyacin hali ba, sosai ya fashe da kuka tare da kai hannayenshi cikin bathtub ɗin Ya ɗauko Jaririn, bai damu da kayanshi su 6ace ba ahaka ya ƙanƙameshi ajikinshi yana shar6ar hawaye, "Taj!taj!! muryar amininsa ce da alama sun shigo cikin gidan, Atare suka faɗo Cikin ɗakin nashi a fujajen, Su Biyu ne shida Matarshi wadda ke sanye Cikin Jallabiya baƙa, Ta yafa mayafi akanta, farace tass doguwa,Shi kuma Uxair din, Jallabiyace ajikinshi brown color Shigarsu keda Wuya Sai gashi Ya fito rungume da jaririn a ƙirjinshi, Aruɗe suke kallonshi, murya na kerma Aneelarh tace"Ta haihu ne"? Tunkafin ta rufe baki Uzair ya kar6e da cewa"Meya ke faruwane taj?wannan Jaririn fa?Kodai ta sauka ne"?   Daƙyar ya iya daidaita natsuwarshi ya soma magana"Ita ce tabar mun shi, nima bansan meya faru ba, kawai naji kukan jariri, shine ma Ya tashe ni daga bacci,a toilet na sameshi cikin bathtub"   Atare suka haɗa baki suna salati, Kafin Aneelarh ta kar6i Jinjirin Tabi ta gefenshi ta nufi toilet don ta gyara mashi jikinshi, Uzair kuma Yaja Hannun Taj suka fito falo, tsayawa Sukayi suna fuskantar Juna, ran kowannan su a6ace,   "Amma dai matar nan anyi ƴar akuya, dama can Ni bata kwantamun araina ba, In banda daƙiƙanci taya laifin ka zai shafi abunda ke cikinta"? tun kafin yakai ƙarshen maganar taj ya katseshi da cewa"Laifin me nayi mata Uzair!? meyasa wasu mutanan basu da tunani ne?sun ɗauki duniya wurin zama,Suna manta cewa wata rana dole su koma Ga Allah, kuma zasu yi bayanin duk wani abu da suka aikata mai kyau ko mara kyau," dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yaja numfashi kafin yaci gaba da magana,.     "Benazir Ta ƙona mun rai, bazan ta6a yafe mata ba, Allah ya isa tsakanina da ita,Ta nuna mun rashin imaninta ƙarara akan Jariri na, In sha Allah Zata ga Sakayyar hakan......"kafin Uzair Ya kuma Furta wani abu, Sae ga Aneelarh Ta fito hannunta ɗauke da jaririn cikin lallausan towel fari, wani irin farin Cikine akan fuskarta,tunkafin ta ƙaraso wurinsu ta soma ambaton"Tabarakallahu Ahsanul kaliqin, Tunda nake amsar haihuwa a asibitin mu ban ta6a Cin karo da kyakkyawar Jinjira ba, Irin wannan Hurul ainin dake a hannuna ba.... A sukwane Uzair da Taj suka kalli juna kafin suka mayar da idanuwansu kanta,   "Am just Speechless wlh, Ka gode ma Allah, Da Benazir bata yi tunanin kashe maka itaba, da kuwa munyi Babbar asara,"takai ƙarshen maganar adai dai lokacin ta ƙaraso gabansu,.   Slowly Taj da Uzair suka ɗaura Idanuwan su kan Jaririyar, Saboda tsabar Kyanta har Razana saida Suka ɗanyi, Babu wanda yayi tsammanin ganin jaririyar haka, farko ma sun yi tunanin Namiji ne saboda hankalinsu ba'a kwance yake ba, ashe ta maca ce, Fara ce Sol har wani shining skin ɗinta take yi saboda tsabar haske, Natural Beauty ce, Bakomai yafi jan hankalin su ba, face Ƙwayar idonta (vivi gray) mai launin ruwan Toka ash Colour, ta ciza har ƙyalli take Yi, Sumar kanta Brown Colour ce Curly mai nannaɗa, har saman goshinta wani kwantaccen gashi ne, kuma kan nata acike yake da yalwataccen gashi, ga dogon hanci Allah ya bata, ga kuma Ƙaramin baki, mai ɗauke da siraran la66a Pink colour kamar an shafa mata jan baki, Saboda tsabar farin Ciki,taj Ya kalli gabas Yay sujjada Yana kuka Yana Gode ma Allah. "Ka fara tsarka ke jikinka mana,"Uzair ne yayi mgnr. Murmushi suka saki gaba ɗayansu a ya yin da suke Kallon shi,   "Ina taya mu farin Ciki sosai, Aneelarh Wannan kyautar Allah ce agaremu, Naji dadi da Benazir batayi tunanin kashe jaririyar ba,   Murmushi aneelerh ta ɗanyi"Ji nake kamar nafi mahaifin Yarinyar Farin Ciki, yau Rana ce me cike da tarihi, Ranar da Taj Ya zama Uba,   Murmushi suka kuma saki atare,A lokacin Taj ya ɗago daga sujjadar, hawaye sharkaf akan fuskarshi, Bazai iya misalta irin farin cikin da yake Ciki ba, Miƙewa Yayi tsaye Ya koma gabansu, hannu ya miƙa ma aneelerh ta bashi babyn, maƙe mashi kafaɗa tayi, tare da yi mashi nuni da idanuwanta, sai lokacin ya tuna da yadda jikinshi ya ke, duk ya 6ace da jinin babyn sa daya ɗauke ta ɗa zu, Mirmishi ya sa ki da sauri Ya kama hanya zuwa bedroom ɗin sa, within mins sai gashi ya dawo jikinshi sanye da jallabiya, ya gyara jikinshi miƙa mata hannu ya yi batare da musu ba ta miƙa mashi ƴarshi, Yasa hannu biyu ya kar6e abunshi, sosai ya ƙanƙameta, Ya tsare ta da idanuwashi yana kallonta, Sae faman mutsu mutsu take Yi, ta tura yatsanta ɗaya acikin baki sai tsotsa take Yi, Ba komai ya fi ɗaure ma shi kai ba a game da yarinyar face kwayar idonta, kaf dangin su babu mai irin launin ƙwayar idonta, sai dai ko acikin dangin mahaifiyarta, Cikin sanyin murya ya soma magana Yana kallonta"ke kyautace agare Ni, Inasonki Sosai, Allah ya raya mun ke bisa tafarkin addinin islama, Allah Ya bani ikon kula dake Alfarmar annabi muhammad (SAW) Allah ya tsare mun ke, Allah kuma yasa ki xama silar farin Cikinmu," haka ya dinga Jero addu'o'i, Suna uxair suna amsa mashi Ameen ameen *SHIN WANENE ZAHEER TAJUDDEEN?* Tajuddeen ɗan asalin Wani ƙauye ne da ake kira Buzaye wanda ke a ƙarƙashin ƙaramar hukuman ɗanja dake a jahar katsina, Haifaffen ɗan garin ne, nan ne tushen shi, anan dangin su suke,mahaifin shi da mahaifiyarshi Auran Zumunci ne, Ƴa'ƴan wa da ƙanine, Malam Zahiru shine sunan mahaifinshi, Mahaifiyar shi kuma Yahanasu, tun da su ka yi auren Allah bai ba su haihuwa ba, abun tun bai damun su harya fara damunsu, mutanan garin har sun fara yi masu surutu kan rashin haihuwa, haka dangin su ma, sun fara tanka masu akan Haihuwa, musamman Deeje Mahaifiyar malam zahiru, kullum mitar rashin haihuwar matarshi take yi, Ita dai burin ta a haifa mata Jikoki, sun shiga mawuyacin hali,Har shirin zuwa asibiti su ka yi don a duba lafiyar su a gano inda matsalar take, A wannan Lokacin basu da babban asibiti A yankin sai da su ka yi tafiya zuwa cikin jihar katsina, Suka sauka agidan balaraba ƙanwar Yahanasu da ke aure anan Cikin garin, sun samu kyakkyawar tarba a wurinta,haka mijinta ma, ya yi farin Ciki da zuwansu, domin kuwa malam zahiru Abokin shi ne ta silar shi Ya haɗu da balaraba, Kwanan su ɗaya a gidan ta, a washe garin ranar Suka je asibiti aka duba su, A ƙarshe dai Likita ya tabbatar masu da cewa Lafiyarsu qalou Lokacin haihuwarsu ne baiyi ba, Su Cigaba da addu'a kawai in dai suna da rabon haihuwa aduniya to zasu ga jininsu duk mun daren da ɗewa, kwanansu Uku a katsina suka dawo nan buzaye, Koba komai hankalin su Ya ɗan kwanta,tunda an tabbatar masu da cewa basu da matsalar Haihuwa, Bayan tsawon Lokaci Da yin aurensu, Kusan shekera ashirin da biyar kenan, A wannan Lokacin Allah Ya kawo ƙarshen koken rashin haihuwarsu, wato Yahanasu ta samu Ciki, saboda tsabar farin Ciki har ƴar ƙwarya ƙwaryar walima suka shirya aka kira masu kiɗan kwarya, Aka ci aka sha, A kwana a tashi, yahanasu ta haifi kyakkyawan jaririnta wanda yaci sunan shi Tajuddeen sunan Mahaifin Malam Zahiru, Tun yana yaro suka ƙwallafa rai akanshi, Kowa son shi yake yi, kuma tun daga shi Allah bai ƙara basu haihuwa ba har suka tsufa, a lokacin da taj ya fara girma, kawun shi ƙanin mahaifinshi Ya kwallafa rai akan subar mashi Yaron tunda basu da hali, Yanaso ya ɗauki nauyin karatunshi, acan inda yake aiki Jihar Jos, a lokacin ƙin yadda su ka yi saboda shi kaɗai ne ɗansu wanda suke kallo suji daɗi a duniyar nan, sunfi son ko da yaushe Ya kasance atare dasu, Babu yadda Uncle ɗin nashi ya iya dole yabar masu abunsu, Amma duk da haka sai da ya taimaka masu da abunda zasu kula dashi, don kafin tafiyarshi,Sai da ya tabbatar sun sanya shi makarantar Boko da islamiyya, tukunna Ya tafi, Tajudeen tunda ya taso Yaro ne mai hankali da natsuwa akwai na annabawa wato haƙuri mutun ne maison Jama'a, ga son Ibada,ga tsafta sam baida wata damuwa a rayuwarshi, ga kyautata ma iyayen shi, tun yana ɗan shekara Goma shabiyar aduniya yake ƙoƙarin ɗaukar nauyin iyayen shi,Wasu aiyukan na mata duk ya iya su, Share share wanke wanke,wankin kayan su da guga, Ɗebo ruwa a rijiya,Hatta girki Mafi yawan lokutta indai ba makaranta, shi yake zama ya girka masu abinci, shiyasa a kullum iyayen shi suke ƙara sonshi, kullum Cikin sanya mashi albarka su ke yi. Bayan Tajudden Ya kammala Secondry school, Wannan uncle ɗin nashi dake a Jos Ya ƙara kawo masu ziyara, Ai tunda Yayi arba da tajuddeen yaga Yadda ya sauya, Ɗan kyakkyawan matashi, nan fa ya ƙara sa naci akan subar mashi yaron Ya tafi dashi Can Ya sanya shi Jami'a dama yana da ɗa ɗaya Tilo mai suna Uzair burin shi ya haɗasu Wuri ɗaya su yi karatu atare, Nan ma suka ƙi amince mashi, haka shima Tahujudeen ya kafe akan baison zuwa yafi son zama da iyayenshi, Babu yadda Uncle ɗin bai yi dasu ba, Amma suka ƙi yadda,a karshe Ya yanke shawarar zuwa wurin mahaifiyarsu deeje, Lokacin daya je wurinta, Sosai ya Tunzurata, Ya nuna mata irin Albarkar da zasu samu da yaron idan ya tafi dashi birni,A ƙarshe dai hada Cin hanci Yaba uwar tasu, da yake tsohuwa deeje akwai shegen son kuɗi, Shiyasa Ko tsakaninshi da malam zahiru, tafi ji da shi saboda duk in zaizo Buzaye sai ya haɗo mata sha tara na arziƙi, haka idan zai tafi ma, Babu Yadda Yahanasu da malam zahiru suka Iya, Ba da son ran su ba, A wannan lokacin suka rabu da tajuddeen, Suna kuka yana kuka, gwanin ban tausayi duk da Uncle ɗin ya yi masu alƙawarin duk In suka samu hutun makaranta zai turo masu shi, hada mai aiki ya ajiye masu agidan wadda za ta ci gaba da kula dasu kamar yadda tajuddeen yake yi masu, hatta Ginin gidansu sai daya sabunta masu shi, Bayan tafiyarsu Jos, Rayuwar Tajuddeen ta canza sosai, Yana samun kyakkyawar kulawa a wurin Uncle ɗinshi da kuma matarshi Hajiya Adama, ga kuma aboki daya samu ɗan uwan shi Uzair, wata irin shaƙuwace a tsakaninsu, kullum suna atare, dare da rana a tare Uncle abdallah ya sanyasu A university kuma Course ɗaya suke karanta 6angaren jarida, da yake ra'ayinsu yazo ɗaya, duk in lokacin hutu ya yi Sukan shirya shi da Uzair su tafi Buzaye wurin danginsu, Har hutunsu ya ƙare tunkunna suke dawowa gida, Bayan Wani Lokaci, Tajuddeen da Uzair Su ka kammala degree ɗinsu, dama kuma tunkafin Su yi graduation, kowannan su yana da budurwar shi wadda yake da burin aure, Taj dai Wata ɗiyar hamshaƙin mai kuɗice ɗan siyasa Allah Ya haɗa shi da ita, Kyakkyawar gaske Asalinta ma half cast ce,mahaifiyarta balarabiyar Egyp ce, mahaifinta kuma Bahaushe ne gaba da baya, Sunanta Benazir Sam bata da sauƙin kai, maca ce mai matuƙar Ji da kanta, Sam bata mu'amala Da mutun idan har mahaifin shi ba shahararren mai kuɗi bane kamar mahaifinta, kuma ba'a ta6a ta a zauna Lafiya, shiyasa kowa ke shakkar shiga gonarta, ƙawarta ɗaya kwallin kwal wadda Jinin su ya haɗu da ita, amma kuma halinsu yasha banban, Aneelerh maca ce mai sauƙin kai, ita kanta ƴar masu kuɗi ce amma bata ɗauki duniya da zafi ba, Tana bin komai asannu, Ga tarin ilmin addini da take dashi, Dukkanninsu kowa da Course ɗin da ya karanta,Ita Benazir Business administration ta karanta, Aneerlerh kuwa Medicine ta karanta, tunkafin ma ta kammala karatu mahaifinta Ya gina mata Privet hospital mallakin ta, atare su ka yi karatunsu ƙasar germany ita da aneelerh, farkon haduwar su A cikin jirgi ne suka fara sanin juna, A lokacin zasu tafi Germany ƙaro karatu, sun zauna a seat ɗaya cikin jirgin, kasancewar aneelerh bata cika shariya ba, ko batasan mutun ba, takan gaida shi harma taja shi da fira, ita ta fara yi ma benazir magana suka fara fira sama sama, tana ta shan ƙamshi, sai ga shi daga baya da suka isa ƙasar germany sun kuma haduwa a University ɗaya, Sunyi mamaki daganan kuma suka ƙulla zumunci, Bayan sunyi degree suka dawo Nigeria, Sati ɗaya da dawowar su suka shirya zuwa Shopping Mall domin yin siyayya, anan Allah ya haɗa su da Su tajuddeen suma ranar sunje yin siyayya, basu sha wahala ba, wurin samun amincewa daga wurinsu, In a short time soyayya mai ƙarfi ta kullu atsakaninsu, har takaisu ga yin aure, Wannan shine farkon haɗuwarsu, Taj bai tashi sanin wacece Benazir ba, Sai bayan da aka shafa fatihar auransu, Aka kaita Gidanshi, ta hana abokan ango shugowa Siyen baki, dama Ko time ɗin da aka kaita gidan, Family ɗinta ne zalla babu ƙawaye don bata Hulɗa da mutane, Aneelerh ce kawai Aminiyarta da akayi masu aure rana ɗaya, Sati ɗaya su ka yi suna shan soyayya, Ta iya tarairayar miji da bashi hakkin shi akan lokaci, sai dai bata Iya girki ba, kuma bata iya Gyaran gida ba, dai dai da gyaran gado wannan batasan Ya zata yi shi ba, saboda tsabar sangartata da akayi, ranar da ya yi mata complain kan cewa Tayi mashi girki sai cewa tayi, ba'a halicci Hannayen ta donsu girka ma ƙato abinci ba, tsabar 6acin rai kamar Ya rufeta da bugu bata iya komai ba, sai danne dannen waya ko salla sai taga dama take yinta don wani lokacin Sai dare take hada sallar Azahar da isha'e da magrib duk tayi su a lokaci ɗaya.Salatul fajr kuwa, Sai ƙarfe goma na safe take Yinta, idan ya yi mata nasiha sai tace "Ae ba a ƙabari ɗaya za'a binne mu ba, mommy ta sanar dani cewa in yi sharholiya ta son raina Aljanna tamai rabo ce," Bawan Allah taj, da yake yana sonta, haka yaci gaba da zaman haƙuri da ita, kullum shi ne Zarya zuwa restaurant Cin abin, daga bisani ne da abun ya dameshi, ya samu Uxair Ya kwashe komai game da zamanshi da Benazir Ya sanar mashi, Ba ƙaramin tausayin shi Yaji ba, a ƙarshe Yace mashi Ya daina zuwa restaurant Cin abinci, Ya dinga zuwa gidanshi suna ci, idan ma bai iya zuwa kullum zai dinga kawo mashi, Tun daga ranar duk in Aneelerh zata Yi girki hada Taj take haɗawa, daga baya kuma Aneelerh ta fara zuwa aiki, hakan yasa suka nemi ƴar aikin da zata dinga yi masu aikin cikin gida kada abun yayi mata yawa, koda uzair ya sanarma Mahaifiyarshi hajiya adama game da neman masu aikin da zasu dinga yi masu aiki a gidanshi dana Tajuddeen, Cikin sa'a Hajiya adama tayi ma mai aikinta Esther magana akan ta nemo masu masu aiki mutun biyu, Batare da 6ata lokaci ba, Esther ta samo masu ƙannanta dake cikin buƙatar aikin yi, dama su ukune Kuma marayu, suna a Cikin buƙatar abunda zasu tallafi rayuwarsu dashi, Sai gashi Allah ya kawo masu aikin yi, Sunan ƙannan nata Ana da Janet Ana itace take aiki agidan Uzair janet kuma agidan tajuddeen, Rayuwar Janet a gidan Tajuddeen,Ta aikatu kamar jaka a wurin benazir, Gashi abu kaɗan saita rufeta da bugu saboda tsabar Zalunci, haka ta jure zama da ita, kodan saboda albashin da take samu mai tsoka awurin Taj, Yana ji da ita mutunne mai kirkin gaske, Tun bayan auransu da Sati biyu dai dai da rana ɗaya Taj bai ta6a jin dadin zama da benazir ba saboda baƙin halinta mahaifinta kanshi kuka yake da ita, duk Cikin ya'yanshi babu mai irin halinta, ga shegen yawon tsiya,da auranshi haka take fita Night club kuma ba yadda zaiyi da ita kusan kullum sai sunyi sa'insa da ita, hatta Cikinshi data ɗauka, ba irin maganin da bata shaba don ta zubar dashi amma Abun ya faskara, Allah ya riga daya ƙaddara zuwanshi duniya, ita fa duk duniya ba wanda ya isa yayi mata faɗa taji, wata irin bauɗaɗɗiyar macace, mai wuyar sha'ani hatta Aneelerh ta sha yi mata nasiha akan tagyara rayuwarta a karshe ma saita yaki ce aneelerh daga rayuwarta, ta ɗauki gaba da ita ko magana bata haɗa su, lokacin da Cikinta ya soma Girma kamar tayi hauka saboda ba ta san Ganin shi ajikinta, kamar ta sanya hannu ta danna shi ya baje haka take ji, Taj yasha kamata tana kokarin shan maganin don ta zubar dashi,Wanda hakan yayi silar da har su ka yi faɗa da ita kaca kaca, kuma Tace mashi koda ta haihu kada yayi tunanin zata shayar mashi da abunda ke acikinta, ashe dama jira take ta haihu tabar gidan, Shine ta tafi tabar mashi jaririya cikin kwamin wanka, dama kuma tunkafin tafiyarta, Ta kori mai aikin gidansu Janet, Batare da saninshi ba wannan kenan......... *Boss Bature* Cigaban Labari Bayan sun samu natsuwa, Aneelerh ta basu shawarar su ta fi asibiti don ta duba lafiyar babyn, Ta kuma Yi mata injections ɗin da ake yiwa kowani yaro da zarar an haifeshi, domin bashi kariya Atare suka tafi asibitin wanda Ya kasance Mallakin Aneelerh ne, Ƙaramin privet hospital acan aka duba Lafiyar babyn, tana da ƙoshin Lafiya bayan dawowarsu gida Aneelarh taso ta shayar da babyn Amma Taj ya hana saboda gudun kada Ya haramtawa ƴarshi auren ɗansu,wanda burinsu ne shi da Uzair, su haɗa Ya'yan su aure, duk da ita aneelerhn har yanzu shiru, A ƙarshe sai dai ƙanwar maigadin gidansa ce Inna kuluwa Take shayar da ita, dama Tana Cikin shayar da jikanta da mahaifiyarshi ta rasu tabar mata, watan shi shida a duniya shima yabi mahaifiyarshi, baba maigadi ne ya bashi shawarar ya bata Babyn ta shayar da ita, baiyi gaddama ba ya amince, a ranar tazo daga ƙauyen su, Sai da aneelarh taje da ita asibitin su aka duba lafiyar jikinta tukunna aka bata Rainon Babyn, Acikin gidan taj ya ware mata haɗaɗɗen bedroon ɗin da zata zauna, Ranar suna Yarinya taci sunanta *UNAISAH* shine sunan da mahaifinta ya naɗa mata Amma Yana kiranta da *ANGEL* a matsayin Nickname dinta, Bayan kammala sallar juma'a akayi naɗin sunan, Tun ana saura kwana Biyu suna, Mutanan Buzaye suka zo, daga Ciki hada Mahaifiyar tajuddeen Yahanasu ta tsufa tukuf tare da mahaifinshi malam zahiru, hada kakarsu deeeje suka zo, tare da wasu daga Cikin danginshi, a daren ranar da suka ƙaraso, kowa Ya soma tunanin ina Uwar yarinyar take ne, sai a lokacin yake sanar dasu game da guduwar benazir da ta tafi tabarshi da yarinyar, Ran danginshi ba ƙaramin 6aci yayi ba, sunji haushin Abunda Matarshi tayi, dama tun fil azal basu so ya auri bare ba, sun so ace cikin dangi ya samu mata ya aura, don ba yadda zasuyi ne ƙaddara ta riga fata, A 6angaren Taj kuwa yaso ace uncle abdallah ƙanin mahaifinshi, yana nan a ka yi sunan sai dai kash, tunda jimawa sukayi tafiya zuwa South korea, da ya ke acen kasuwancinshi yafi ƙarfi, duk da haka Sunyi waya dashi, Har video call suka kira shi don ya nuna masu babynsu, aikuwa sunsha ruwan mamakin ganin kyakkyawar ɗiyar tajuddeen, Don ita Hajiya Adama matar Uncle din, cewa tayi da zarar sun dawo nigeria zata ɗauke ɗiyarta, saboda ta raineta ko alokacin Taj bai sanar da su game da Abunda ya faru tsakaninshi da benazir ba, don baiso ya tashi hankalinsu ya bari ne sai Sun dawo tukunna Suji komai, Alhamdulillah An kammala taron suna Lafiya, ƴan uwa da abokanan arziki sunci sun sha sun shaida Zuwan *UNAISA* duniya, aranar Tajuddeen kamar yayi hauka saboda tsabar farin ciki, domin kuwa ya samu alheri sosai awurin abokananshi, da kuma masoyanshi don hada key ɗin mota ya samu, ga kuma kayayyakin da suka dinga haɗawa ƴarsa, manya manyan akwatina na kayan baby, shi kanshi ya samu kyautar shaddoji a daren ranar sunan Tare da Uzair suka shiga ɗakinshi suna ƙirga kyaututtukan daya samu, A kalla ya samu kuɗi Sama da 3m, baya ga kayayyakin da ya samu har hawaye saida taj ya zubar, dama shanun da aka yanka ranar sunan bai ƙarasa biyan kuɗinshi ba, bashinsa yaci har uzair na gargaɗin shi akan karya ɗauki abunda yafi ƙarfinshi Ya siya masu rago kawai ya wadatar, Amma yace ina ƴar shi tafi ƙarfin rago sai dai sa.sai gashi Allah Ya rufa mashi asiri, Sai da su Deeje sukayi Wata ɗaya Cuf tukunna suka shirya komawa Buzaye, Sunyi tunanin taj zai bar masu yarinyar ne su tafi da ita can ƙauyansu buzaye kafin Ya samu matar aure, Amma ina koda Su ka zo mashi da maganar tafiya da babynshi, Sai ya juya masu ƙeya, alamar bazai bayar ba,don dole suka haƙura, dama deejen ce ta matsa su tafi da ita,amma mahaifiyarshi Yahanasu sam bata ayyana hakan aranta ba, musamman da ta ga yadda Inna kuluwa ƙanwar baba maigadi take kula da ita Sai hankalinta ya kwanta, Ba ƙaramin alheri taj yayi masu ba lokacin da zasu tafi, kusan abunda ya samu ya kasa uku, ya basu kashi ɗaya,Kashi ɗaya kuma yaba Uzair amininsa, Amma yaƙi kar6a saima ya ƙara mashi sunyi rabuwar arziƙi da iyayenshi Sunata sanya mashi albarka har kwalla saidaya zubar bayan tafiyarsu Allah sarki rayuwa kenan A 6angaren inna kuluwa kuwa babyn Tana samun kyakkyawan kulawa a wurinta, duk da ba'a tare suke yini ba kuma ba a tare suke kwana ba, saboda taj da kullum yana manne da ita, sai dai fa duk lokacin da tafara tsala kukan yunwa, dakan shi yake daukar ta yakai ma inna kulu aɗakinta, Yaƙi yarda yabar mata Yarinyar Saboda ya mutu akan sonta, kona seconds baisan rabuwa da ita zuwa aikine kawai yayi mashi cikas, ba ƙaramin abu ke rabashi da babynshi ba, ko aiki yaje yana dawowa jiki na rawa ya ke zuwa ɗakin inna kuluwa ya ɗauketa, idan dare yayi kuwa dama atare da ita yake kwana, Saman kirjinshi yake kwantar da ita Su sha baccinsu, A daren ranar wata Alhamis ne Yana zaune saman Sofa Yana danne danne acikin Laptop ɗinshi, Ya jiyo sautin dirar motoci a lokacin angel tana a hannun inna kulu, bai kaiga zuwa ya ɗaukota ba, Yana jira ya kammala aikinsa ne kafin ya Amsota don su kwanta, Zugudum yayi yana jiran ganin wanene Ya kawo mashi ziyara a irin wannan Lokacin Kusan ƙarfe 9 na dare, Daga wajen Falon yaji anyi mashi sallama, muryar babban mutum, Da sauri ya kalli agogon dake manne a bango, kusan ƙarfe tara na dare, duk a tunaninshi uzairne don bai ɗauki murya ba, hakan yasa shi ɗan ɗaga murya tare da cewa"Come In" Turo ƙopar akayi, a hankali Ya shigo bakin shi ɗauke da sallama, Da mamaki akan fuskar taj yake kallonshi, Babban mutunne yana sanye Cikin kaya na mutunci na hausawa, Shadda tare da malun malun mutun mai cikar kamala, fuskarshi ɗauke da murmushi, Bakowa bane face Alhaji Ubaid Mahaifin Benazir Kaka Ga Angel, Fuskar taj ɗauke da murmushi ya miƙe tsaye Yana kallonshi, kowannan su da abunda yake saƙawa aranshi, "Taj nasan ban kyauta ba, wlh naji kunyar haɗa ido dakai," cikin sanyin murya yayi maganar, da sauri uzair ya qarasa inda yake a tsaye, ya miƙa mashi hannnu don su gaisa,girgiza kai yayi tare da cewa, "Bana jin zan iya haɗa hannu dakai don bancancanta ba" Tausayinshi ne ya kama Uzair, cikin sanyin murya yace"kada ka sanya damuwa aranka komai ya wuce," Damuwace ƙarara akan fuskarshi"ɗane ka haifeshi baka haifi halinshi ba," Murmushi taj ya ɗan saki, kafin ya ruƙo hannunshi zuwa cikin Falon, Suka zauna saman Sofa suna fuskantar Juna, "Baba yaushe kuka dawo ƙasar bansani ba? ya kuma Jikin naku"? "Jiya muka dawo, Jiki yayi kyau Alhamdulillah,wlh taj naso nazo tun lokacin da ka kirani waya ka sanar dani rashin Hankalin da benazir tayi maka, Naji takaicin abun nan ƙiris Ya rage in kwashe mata albarka" yakai ƙarshen maganar fuskarshi duk a hautsine, bawan Allah da alama Yaji jiki, tun lokacin da Taj ya haɗu da benazir kafin auransu mahaifinta baya qasar saboda lalurar da ya ke fama da ita, Na ciwon ƙafa mai raɗaɗin gaske, Alhaji ubaid tsohon gomna ne, bai jima da hawa mulkin ba, Shekara ɗaya kacal Lalurar ta sameshi,Ba ƙaramar wahala yaci ba, Don kowa yayi tunanin bazai rayu ba kullum Ciwon nashi ba sauƙi,ƙara gaba yakeyi,Gashi mutane suna matuƙar sonshi,Yana da farin Jini sosai, adalin shugaba ne mutumin kirki Mai son talakawa, Ga kyautata masu dayawa suna tunanin Abokan hamayyarsa ne suka Yi mashi Asiri, wanda hakan yasa shi ajiye shugabancin, kuma tun daga lokacin zama Nigeria ya gagares hi,da zarar yabar ƙasar Sai yaji sauƙi, da zarar ya dawo sai ciwon nashi ya dawo sabo,tun daga nan ne yabar ƙasar gaba ɗaya tare da Iyalinshi ya koma Dubai da zama, benazir kaɗai Ya bari anan saboda auran da tayi, "Allah ya ƙara Lafiya, Allah kuma ya kare ku daga sharrin makiya da mahassada," "Ameen ameen tajo, ae ina ganin saƙon gaisuwarka da kake turamun kullum ta waya, Inajin dadi sosai," shiru suka ɗanyi kafin Alhaji ubaid yaci gaba da magana"Abu biyu ya kawoni wurinka, Na farko ina mai baka hakuri game da abunda Benazir ta aikata mata, yanzu haka maganar da nake yi maka, Na yafeta acikin zuri'ata Saboda bata jin maganata, tafi karfina......"tunkan yakai ƙarshen maganar, taj yayi saurin katse mashi hanzarinshi"kada ayi haka baba, Ayi mata uziri, dukkan mu nan babu wanda yasan dalilin dayasa benazir ta gudu tabar jaririyar ta, Kowa yasan tsakanin Uwa da ɗanta akwai soyayya mai karfi, Ni nasan ba hakanan benazir ta tafi ba, Dole akwai wani abu da yayi silar tafiyarta, Girgiza kai Alhaji ubaid yayi"bakasan halinta ba ne, ni da na haifeta ni nasan halin kayana, Tagagari kowa, halinta sak dana jatumarta,dama ƙaddara ce tasa na aurota, Murmushi taj ya ɗan saki"Adaiyi hakuri baba,". "Bazan bari ayi 6arna ina kallo ba, Benazir so take tajamun zagi a idon jama'a, tana so ta zubarmun da mutuncina da kuma ƙimata,sai kace ita ta haifi kanta? Babban abunda yafi damuna, bansan a ina take rayuwa ba,Gaba ɗaya ta kashe layinkan wayarta, nasa A binciko mun ita amma an nemeta ƙasa ko sama babu, Ita kaɗai tasan uwa duniyar data shiga,"dakatawa ya ɗanyi da yin maganar yana mayar da numfashi, Mu haɗu a Next Page, yanzu wasan ya fara gaba ɗaya book one Introduction ne wannan story ɗin cakwakiyar dake acikin shi, is hardly to make a prediction about what wll happen next😂 ................... *Boss Bature ✍️ Taj kuwa tuni jikin shi yayi san yi, duk da ba su yi zaman lafiya da benazir ba, hakan bai sauya komai ba na daga son da yake Yi mata, Yana jinta sosai acikin ranshi, kusan tun ranar da ta gudu, kullum sai ya jaraba kira layin ta da daddare ko Allah zaisa ta buɗe shi, Amma kullum a kashe yake samun shi, Muryar Alhaji ubaid ce ta katse mashi tunaninshi"Ka sawwaƙe mata kawai, da ta je tayi ta aikata zunubi da auran ka akanta, don nasan ba dawowa zata yi ba," Girgiza kai taj yayi "baba bazan Iya ba, zan jira ta ne har ranar da Allah zai dawo mun da ita nasan zata dawo ne duk mun daran daɗewa" Gyaɗa kai Alhaji ubaid yayi"Abunda nake fata kenan Yanzu ina jikar tawa take ne? Inaso na ganta,' "Tana hannun Inna kulu, Ƙanwar matar maigadina ce, itace ke shayar da ita" "Allah sarki Amma naji daɗi sosai, ka ɗauko mun Jikata na ganta kafin na tafi da yake bani kadai nazo ba akwai escorts dina dake awaje suna jirana" Amsa ma shi ya yi da toh, kafin ya miƙe da sauri Ya nufi corridor ɗin da zata sada shi da ɗakin inna kuluwa Lokacin daya ƙarasa a kwance ya samu inna kuluwa tana bacci angel kuma na kwance gefen ta an sanya mata kayan sanyi ajikinta, sai faman tsotar yatsanta take yi, Murmu shi ya saki tare da kai hannu ya ɗauketa Ya fito da ita, Ƙarasa wa yayi tare da miƙa ma alhaji ubaid ita Wani irin farin Ciki ne akan fuskar shi "Tabarakallahu ahsanul khalikin Taj kaga ikon Allah, Yarinya ƴar kyakkyawa sai kace rainon turai wannan idan ta girma ae zata iya ciyo mana gasar miss world, Murmushi taj ya saki yana kallonshi addu'o'i ya shiga karanto wa yana tofa mata Taj na amsa ma shi da ameen ameen har ya kammala yi mata addu'ar, Fira sosai su ka yi da surukin nashi, har lokacin Angel na a hannunshi Sai da ya ta shi tafiya ne tukunna ya miƙa ma Taj ita "In sha Allah zan dinga zuwa akai akai ina duba jikata, Yanzu ka tura mun account number dinka In sha Allah zakaga saƙona" "Ngde ssae Allah ya kiyaye hanya, idan Anji wani labari game da benazir dan Allah a sanar min" "Kada ka damu suriki na, duk inda take nasan tana sane da ƴarta da ta bari, kodan saboda ita zata dawo ne" Har wajen da su ka yi parking na motocin su guda uku, Taj ya rako shi da sauri wani bodyguard Ya buɗe mashi mota ya shiga A jere motocin suka fuce, Fitar su ke da Wuya, ba zato ba tsammani Sai ga alert na Miliyan 20 ya shigo wayarshi, Ya yi farin Ciki sosai da kuɗinnan dama yana ta tunanin yadda zai tafiyar da rayuwar shi da kuma rayuwar ƴar shi, ga kuma Iyayen shi da yake taimakama wa ga kuma albashin baba mai gadi, Salary ɗin shi basu isa ya dunga ɗaukar duk wani responsibilities nasu, A ranar yayi kwanan farin Ciki, Bayan Wani Lokaci Alamu sun nuna cewa Angel ba ƙaramar fitinanniya bace, don tun bayan wata ɗaya da aka haifeta, Taj ya yi ban kwana da yin Bacci cikin kwanciyar hankali, Saboda tsabar kukan ta, da ya ke a ɗaki ɗaya ya ke kwana da ita saboda tsabar son da ya ke yi mata, Kona seconds baison rabuwa da ita,sai suna bacci Idan ta tsala ihu tamkar wadda za'a zare ranta, har asibiti ya mayar da ita don aduba Lafiyarta, Still binci ke ya nuna tana da ƙoshin Lafiya, Inna kuluwa kuwa da ke shayar da ita lokacin da ta fara Haƙora biyu agaba, Ba ƙaramar azaba take sha ba gartsa mata Cizo take Yi,baiwar Allah Ba ta ta6a sanar da taj halin da ake ciki ba, kullum sai tayi zazza6i duk da tana samun kulawa a wurinshi, Duk wani nauyi nasu ya ɗauke masu shi, Hatta Abincin da take ci wanda ke gina lafiyar jikinta Aneelarh ce ta rubuta masu komai, taj ya siya mata Lokacin da baby ta fara rarrafe A wata na shida, Tayi 6arna kamar zata haukata masu gidan, da rarrafe take 6aro da kaya su zube kasa ta kacaccalasu akwai ranar da Ta samu wasu mahimman takaddu na Taj, Ta kekketasu into pieces, Ranar Har zazza6i yayi saboda muhimmancinsu kuma idan tayi 6arna taga ya zabga tagumi Yana kallonta Sai ta 6a6aka dariya kamar babban mutun haka sautin dariyarta yake, a lokacin da takai shekara ɗaya da rabi, Da kanta ta daina shan nono, hakan yasa inna kuluwa ta yaye ta, a washe garin ranar da ta yaye ta, ta sanar da taj maganar komawarta ƙauyen su, ya yi mamakin jin zata tafi duk da irin rayuwar hutun da take yi agidan, Ba don yaso ba ya sallameta, kuma Yayi mata alheri sosai baiwar Allah ita kanta ba don taso ba, tabar gidan sai don zargin wani abu da take yi, Game da Ƴarshi to fah Bayan tafiyarta kamar an ƙarama yarinyar rashin ji, har tsoro take ba taj saboda ƙarfin halinta, a kwai wani lokaci da ta addabe shi da 6arna, Sai ya dinga ɗaurata Saman Freezer dake ajiye A falo, sam ba ta so Yana ɗaura ta a sama, tun tana mashi kuka a karshe Sai gashi Idan ya daura ta da zarar Ya bar wurin sai ta faɗo kasa, Taci gaba da 6arna Abun Ya ɗaure mashi kai Yarinya sai kace aljana ranar da ta ƙure shi Keji yasa akayi mashi mai girma hada mukullin rufewa Ya sakata acikin kejin Yasa mukulli Ya rufe A tsakar falo ya ajiyeta, shi kuma Ya koma saman Sofa ya kwanta yana kallonta ranta Ya 6aci sosai tun tana gwarancin ta har takai ga fashe mashi da kuka, tausayinta Ya kamashi har baisan lokacin daya fiddo da ita daga cikin kejin ba, Ya rungumeta yana lallashin ta har ya samu tayi bacci, A daren ranar daga zuwa Yin sallar isha'e, Ya dawo ya taras Ta 6alla mashi Laptop dinshi da yake aiki da ita, idanuwan shi sukayi jawur ga shi bai iya koda yi mata tsawa ne balle aje ga bugu, A fusace ya ɗauke ta ya nufi gidan su aneelerh da ita ya kai ma Su, Yace ya basu kyauta su ruƙe ta awurin su,ba ƙaramin farin Ciki su ka yi ba, hannu biyu suka kar6eta ashe xaune bata ƙare ba A tunanin shi Ya samu hutu Daren Ranar bayan yayi wanka ya zura kayan baccin shi Ya kwanta cike da farin Cikin Yau zaiyi bacci hada minshari, Wuraren ƙarfe 12:30 na dare, Can Cikin bacci Ya dinga Jin mutsu mutsun mutun ajikinshi, hakan yasa shi farkawa daga bacci, Yakai hannu ya kunna fitilar gefen gadon, Kamar ance Ya dago karaf idanuwan shi suka sauka akan baby Angel dake kwance ajikin shi ta ƙanƙameshi, wani irin tsoro ne Ya ziyarci zuciyarshi, a firgice Yake kallonta Har wani murmu shi take sakar mashi, yarinyar da bazata wuce shekara 3 aduniya ba, Abun yayi mugun ɗaure mashi kai taya akai har ta yi wayon da zata iya Kamo hanya daga gidan Taj dake a jikin gidan shi ta dawo gida ƙarfe 12 da rabi na dare batare da jin tsoro ba, Jiki a sanyaye Ya shiga yi mata addu'a yana tofa mata asaman kanta, Wai koda shaidanun aljanune suka shafe ta, sae faman lumshe ido takeyi alamar bacci zata Yi, Babu yadda ya iya haka ya ƙanƙame ta a kirjinshi Yana shafa sumar kanta, Sae gashi bacci Ya ɗauketa bada jima wa ba shima bacci Yayi awon gaba dashi. Wuraren Sallar asuba, Uzair da aneelarh suka buga uban sammako, Hankalinsu atashe Yarinya ta 6ace, Duk sun ruɗe Suna shiga falon Gidan Suka ci karo da Taj tare da Angel zaune saman Dining Chairs Hannun shi ruƙe da Kofin tea yana bata abaki tana sha, A ruɗe suka kalli Juna, saboda tsabar mamaki kafin ma Taj yayi masu bayani Uxair Ya rufe shi da faɗa yana cewa 'Don me zaije Ya ɗauki yarinya batare daya faɗa masu ba, Yasa duk sun tashi hankalinsu,'sai da ya Kammala zazzaga mashi masifa,   Tukunna Taj yace"Wlh bani na daukota ba,dakanta ta dawo, A sukwane Aneelarh tace"Wai dagske ita tadawo da kanta"? Kafin taj ya basu amsa angel tariga shi cewa"Eh da ƙafafuna na dawo, kuma ma baba maigadi bashi ya buɗe mun ƙopa ba, ni na buɗe dakaina" tana magana tana cije le6e kamar ƴar daba, Tashin hankalin da ba'a sama shi date! cike da tsantsar mamaki suke kallonta, Taya akai har ta iya buɗe ƙopar da ake rufewa da key?   Girgiza kai Taj yay "Lamarin Baby sai addu'a, Ina kwance jiya wuraren karfe sha biyu da rabi na dare naji motsin mutun ajikina a she itace ta dawo Ba ƙaramin tsorata Nayi ba" Tabbas sun fara zargin Yarinyar tana da aljanu shiru kawai sukayi batare da sun sanar ma Taj abunda suke hasashe ba, A daren Ranar Alhaji Ubaid Ya ƙara kawo masu ziraya, Kamar yadda ya saba duk in yana ƙasar sai ya zo, kuma duk in yazo sai ya kashe ma angel kuɗi kamar hauka kafin ya tafi, A washe garin ranar da safe Ba zato ba tsammani Sai ga text message an tura mashi da baƙuwar Number, Benazir ce tayi saƙon Bakomai ta rubuta ba face Tana neman Saki a wurin Taj, kuma kada yayi tunanin zata dawo ta tafi kenan har abada abunda yasa ya yi farin Ciki da saƙon sanin cewa tana araye, Hakan ba ƙaramin kwantar mashi da hankali yayi ba, Har bibiyar Number da ta tura saƙon yayi amma a kashe ya sameta, Yaji takaici sosai tun yana sa ran dawowar benazir cikin rayuwar shi harya fidda rai, ba don yaso ba ya tura mata da text ta number yasan wata rana dole ta buɗe ta gani, Saki ɗaya yayi mata acikin saƙon daya rubuta mata....,...... A ranar Uncle abdallah ya dawo Nigeria, Uzair ne da kan shi ya ɗaukosu a Airport zuwa gidansu, tsabar farin Ciki a wurinsu bakinsu kasa rufuwa ya yi musamman Taj, hajiya adama tayi murnar ganin su Cikin ƙoshin lafiya Ranar yini tayi da angel awurinta, tun dawowar su Angel awurun su take kwana, Bakomai yafi ba Taj mamaki ba face irin yadda yarinyar take natsuwa agaban mutane, Amma idan shi da itane tadinga 6arna kenan kamar 6eran gida, ****Boss Bature****** A kwana atashi. Yau angel Takai shekara 5 cuf aduniya, a wannan Lokacin Uncle Abdalla Ya kuma tafiya zuwa South Korea, Hajiya adama taso yabar masu Angel su tafi da ita can tayi karatunta amma Taj yaƙiya, duk irin alkunyarshi amma ya gaza jure rabuwa da ita, Babu yadda suka Iya haka su ka tafi suka bar mashi ƴarshi, Aneelerh kuwa Shiru har wannan Lokacin ba Ciki, ko 6ari bata ta6a yi ba a bun ya dame ta sosai, Shi kan shi Uzair ya shiga matsananciyar damuwa, har dai suka yanke shawarar Zuwa asibiti don a bincika lafiyarsu, Amma wani abun mamaki Lafiyarsu ƙalau daga ita har shi, Lokacine baiyi ba ganin sun damune yasa taj zaunar dasu Yana kwantar masu da hankalin su harya basu Labarin Iyayen shi da suka ɗauki shekaru da yin aure kafin Allah yabasu haihuwa, Tunda suka ji hakan sai hankalinsu ya kwanta har suka daina sa damuwa aransu, A 6agaren baby angel kuwa A tunaninsu idan ta fara Girma zata rage 6anna da rashin Ji, Ashe Yanzu wasan Ya fara, Tun tana da shekara Uku Ya sanyata nursery, hada islamiyya saboda Bakin da Allah yai mata, rana ta farko da ta fara zuwa makaranta, ta samu ƴa'ƴan mutane ta dinga gartsa masu Cizo, Itafa Ko kallonta kayi to ka Shiga huruminta, saboda jarabarta kusan makaranta Biyar ana sallamarta Saboda baza su Iya Control ɗinta ba, ga shi ya hana a dukar mashi ƴa ko tsawa Baiso Ayi mata sai dai bayan idonshi. Daƙyar aka samu Angel Ta daina Cizon ƴa'ƴan mutane, tun da yayi mata faɗa abunda bai ta6a Yi mata ba a ranar har fushi tayi taƙi cin abinci, daƙyar Ya lallashe ta ya samu suka shirya da ita, Wata rana zai tafi Wurin aiki da marece, tana bacci Ya tafi yabarta saman Gado, a tunaninshi Harya dawo bata tashi daga Bacci ba, bayan fitarshi Da rabin awa ta farka tana Jin yunwa gashi Sam bata da juriyar Yunwa, Kaitsaye Ta Nufi kitchen Tana kiciniyar Ɗaura girki, Ta sanya kujera agaban gass Ta samu ta haye sama har takai yadda zata Iya ganin saman gass cooker din, Dama tasan Yadda yake kunneshi Saboda wasu lokuttan a tare da ita Yake shiga kitchen Yayi girki, To yau dai ga angel zata Yi practicing abunda Ubanta ke Yi agabanta. Yana Wurin aiki Aka kira shi awaya ana sanar dashi cewa Gobara Ta kama agidanshi, Hankali amatuƙar tashe Ya shiga Mota Ya nufi gidan. Yana zuwa unguwar ya hango motar ƴan kwana kwana a ƙofar gidanshi, Duk yabi ya ruɗe babban tashin hankalin shi Ina angel ɗinshi kada ace wuta taci ta, da gudun gaske Ya fada Ciki gidan, Su uzair suka bi bayan shi dama sunzo hada aneelarh, A rude ya shiga kwalamata Kira Angel Angel!!kamar makoshinshi xai 6allo, Tunda suka Ji cewa Yarinyar tana agidan wutar ta kama nan fa hankalin kowa Ya tashi, Sai da suka gama shan wahalar nemanta, Ba zato ba tsammani suka same ta a cikin bedroom dinshi, tsakiyar Gado hannunta ruke da robar yogurt me sanyi tanasha. Da gudu suka nufe ta gaba ɗaya suka rungumeta, kowa ya na faman sauke ajiyar Zuciya, Abunda Ya faru a she bayan ta kunna gass, ta sauko daga saman Chair ɗin, Sai ta tuna akwai yogurt da ice cream acikin frigde shine taje ta dauko Ta shige daki tana sha, Sam ta manta da tabar gass a kunne, duk wannan budurin da akeyi na gobara ta kama ita ba ta ji ba, Baba maigadi ne Ya ga hayaki na fitowa ta cikin gidan,a hanzarce Ya shigo Ciki don yaga me ke faruwa, koda ganin Hayaƙin ta kitchen yake fitowa Jiki na rawa Ya nufe shi, Nan yaga wuta ta kama Jawur tana Ci,jiki na rawa Ya watso da gudu waje Yana neman a gaji, Angel tasha fada awurin Taj kuma duk da laifin da tayi ma shi ko dungurin ta bai yi ba, kadan daga Cikin munanan halin angel shine, Bata barinbshi yayi bacci muddin ta farka, to shima dole ya farka baccinshi Ya qare, Idan suka fita Yawan shakatawa komai ta gani tana so, koda a hannun wani yake to dole A mallaka mata shi idan ba haka ba hmmm xa'aga tashin Hankali, Bayan wannan Ta iya jan faɗa idan suka Je anguwa, komai ta gani saita dauka ta jefar, Ayita nema tana ji bata faɗin ita ta dauka. duk duniya babu wanda bata Jin tausayin shi Irin mahaifinta, azabtar da shi take Yi, Shi kuma Ya mutu akan sonta Bai iya rabuwa da ita ga shi ta tsani taga yana karatul Alqur'ani, da zarar Ya fara saita 6allo mashi aikin da zaisa ya ajiye karatun, kuma bai isa Yayi salla acikin gidan ba idan uziri ya hana shi zuwa masallaci, Kamar shaiɗaniya haka take, har malami aka dauko yayi mata addu'a Don a fidda aljanun da ake hasashen tana dasu, tun malamin na cikin yi mata rukiya ya dafa kanta, ta dinga buge mashi hannu tana faɗin dama ya daina wahalar dakanshi, Ita lafiyarta qalou Bayan malamin ya kammala Yi mata ruƙiya, Ta sace takalmanshi ƴan madina, sai da ya tashi tafiya aka nemi takalma wayam an ɗauke su, su ka yi ta nema kasa ko sama babu su, bayan tafiyarshi ta fiddo takalman da ta 6oye a ƙarƙashin gadonsu taba Taj, wai gashi A maida mata su na yara daidai kafarta, haushi kamar Ya rufeta da bugu, yaji kunyar abun nan haka ya kwashi takalman yaje har gidan malamin Ya mayar mashi da abun sa, Babban abunda zai baka mamaki da ita sam bata da tsoro, yasha farkawa tsakar dare Ya sameta zaune a falo tana kallon cartoon har ta Iya kunna kallo, tun abun na damunshi harya hakura ya kyaleta, Akwai ranar da zaije gabatar da wani programme agidan radion su, Sai daya kammala shiri Yaji ƙopa a rufe, Tasa key ta rufeshi, dalilin da ya sa Ta yi ma shi haka shi ne, Kullum In zai tafi Evening duty, a mota yake ɗaukarta yakaita Gidan Amininsa Uzair, Ita kuma bata son zuwa gidan tafi son duk inda zai je ya tafi da ita, Wannan ne yasa a ranar Ta saci keyi din ɗakin shi bayan ya shiga wanka, Ta ɗauko kujera ta sanya Yadda tsawonta zai kai, Ta murɗa mashi key ta datse ɗakin Ƙarfin Hali, Tun yana lallashinta ta buɗe ma shi ƙopa har yakai ga danƙara mata zagi kamar mai yin magana da babban mutun, Ya zazzageta Da masifa duk wannan baisa ta buɗe mashi ƙopa ba, har saida ya kira Uzair A waya ya sanar dashi cewa Angel Ta rufe shi a ɗaki, ya kawo mashi taimakon gaggawa batare da 6ata lokaci ba sai ga uzair Yazo gidan, A zaune Ya same ta saman Sofa tana kallo, aikuwa ya kar6e key din a hannunta Ya je ya buɗe ma shi ƙofa, koda ya fito baibi ta kanta ba Ya fuce daga falon yana huci, Uzair dai yaci dariya, shi ya ruƙo hannunta adole suka tafi da ita wurin aikin nasu, Saboda bala'in angel Saida yakai ga kullum sai Taj Ya zubar mata da hawaye don ta dinga Jin tausayin shi, bawan Allah duk yayi duhu ya rame, ita kuwa Babyn tashi har kumatu ta yi saboda rayuwar Jin daɗi, yarinya fa kamar rainon turai fara sol da ita, gashi duk wanda yaji Labarin Halayyarta bai yarda, saboda kowa Mamakin shekarunta ya ke yi Just 5 years fa, Duk irin ɗawainiyar da yake Yi mata sam bata Gani Shine girka mata abinci Yayi mata wanka ya wanke mata gashi Yayi mata kitson kalaba, har ƙunshi na jan lalle yake ƙunsa mata da kanshi, Amma yarinyar nan Idonta sun makance idan kana son Ganin Dariyar ta to ka tabbata ta ƙuntata ma Mahaifinta ne, Lokacin da takai Shekara 7 a duniya, Ranar wata friday Ya shiryata zasu fita Gidan ɗaya daga Cikin abokanan aikinshi, mai suna Muhsin lokacin da suka je ba ƙaramin farin Ciki muhsin da matarshi sukayi ba, musamman da yazo masu da angel, yarinyar da kowa yake kwaɗayin Yin tozali da ita saboda kyanta, Allah yayita da farin Jini, Tunda suka je gidan aka kawo masu kayan makwalashe, Taƙi ci da suka tambaye ta meyasa baza ta ci ba sai cewa tayi Daddynta ne Ya hanata cin abincin gidan mutane, a lokacim kasa magana taj yayi saboda baisan amsar da zai basu ba, ƙiri ƙiri ta yi mashi ƙarya, Muhsin ya roke shi akan yayi mata magana taci abincin, Sai taj ya sanya baki yana lallashinta akan taci, da buɗar bakin ta sai cewa tayi "Ai ko yace inci idan muka je gida buguna yake yi," Gaba ɗaya Angel ta kashe mashi baki, Muhsin kuwa ya nuna rashin jin daɗin shi akan maganar angel, har suka ta shi tafiya Bata Ci komai ba, tun lokacin yaci alwashin saiya yi mata fada in suka je gida, Ashe da zasu Baro gidan, Ta sace warin Takalmin matar gidan mai tsadar gaske, Babu wanda Ya lura sai bayan Da sukayi nisa da tafiya saman titi, Ta ɗago takalmin tana nuna mashi Wai yakai amayar mata dasu Na yara, Sun burgeta, hankali atashe Yayi parking ɗin motar, dama a ƙule Yake da ita wuyanta Ya shaƙo Ya jijjigata Ya hauta da masifa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, a karshe yace"Bana sonki kin fita araina, Ke ni ba mahaifin ki bane, bansanki ba ki fita arayuwata" Yayi waɗannan kalaman ne Cikin fushi, buɗe motar yayi tare da fitar da ita waje"Kije ki nemi wani uban" Yayi tunanin zata saduda ta bashi haƙuri, Amma sai yaga ta watsa da gudu Ta nufi Cikin wata ƴar kasuwa mai tarin jama'a, fitowa yayi daga Cikin motar yabi bayanta, yana faman ƙwala mata kira Koda Ta lura yana binta saita Ƙwala Ihu tana faɗin "Wayyo Allah taimako wani mutun zai sace ta, ɗan yankar kaine ataimaka A mayar da ita wurin iyayenta, kafin kace me Tuni mutane sunyi dandazo akansu, Ganin mutane sun taru hada ƴan ƙato da gora, Aikuwa Ta fashe da kuka ta faki idon mutane ta sanya hannu ta daki hancinta batare da kowa Ya ankara ba, Ya soma bleeding duk don mutane su ɗauki abun serious sosai tadinga kuka tana Faɗa masu cewa"Ba mahaifinta bane sace ta ya yi yana gana mata azaba, Yanzu ma gudowa tayi tana neman iyayenta, dan Allah Hukuma su dauki mataki akanshi, Jin wannan maganar yasa ran mutane Ya 6aci, Musamman ƴan ƙato da gorar nan sun fusata sosai, Kamar jira su ke yi dama a harzuƙe suke, Gaba ɗaya suka rufar mashi da bugu kamar sun samu jaki ita kuwa ko ajikinta, har rantsuwa ya dinga yi masu akan cewa Ƴarsa ce ba satarta yayi ba, Amma suka ƙi yadda saboda bata yi masu kama da jinsin baƙar fata ba, tafi kama da ƴa'yan larabawa da turawa, shi kuma yana da ɗan duhun fata ga kuma Launin idonta ba kalar nashi ba Ba don Allah yasa an samu wani bawan Allah ya kira ƴan sanda ba, da tuni ƴan ƙato da goran nan sun jima da halaka Tajuddeen, daƙyar suka ƙwace shi a hannunsu, Sunyi ma shi jina jina, rashin sani yafi dare duhu dayawa mutanan da suka rufar mashi da bugu sun san shi, saboda sanannan Ɗan jaridane a garin, babbar matsalar da aka samu, mafi akasarin su Fuskarshice dayawa basu sani ba muryar shi kawai suka sani, A wannan lokacin kuma ba wanda ya an kara kuma ba su ba shi damar da zai yi masu bayani ba. Police station suka wuce dashi, A cikin Cell suka tura shi, tare da garƙame shi, Sam baya acikin hayyacinshi, Ya galabaita sosai, A Yayin da Taj ke acikin Cell kulle cikin mawuyacin Hali, Angel tana Office ɗin Dpo tana shan A.c ta ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Ganin yarinyar tana da wayau yasa dpo ya soma tambayarta Ya sunanta, Tace mashi sunanta Angel, ya kuma tambayarta ko zata Iya tuna wani abu game da mai satar Yaran da aka kama ya sace ta? da budar bakinta sai cewa tayi ae bashi kaɗai bane mai satar Yaran ba, Akwai abokin aikin shi Uzairu, atare suke sace ya'yan mutane, A lokacin taj ya dawo hayyacinshi, Suna magana da wani inspector Ya nemi alfarmar su taimaka su ba shi waya Ya kira aminin shi da matar sa zasu bada shaida akan shi,Babu musu inspector ɗin ya bashi damar Yin waya, Nan ya kira uzair Ya kwashe duk abunda Ya faru ya sanar mashi, Bawan Allah uzair ashe da rabon Yaci na jaki, Saboda tsabar sauri Ko aneelerh bai jira ba, yaja mota Ya nufi station din da taj ya yi mashi kwatance. Bayan yayi parking ɗin motar, Ya fito ya shiga Ciki da azama, Kamar jira suke Uzairu Ya ƙaraso suka Tallabi ƙeyar shi zuwa cell ɗin da aka rufe Taj, Suka Hankaɗa shi ciki Lokacin daya Kalli tajuddeen dake ta faman Nishi Fuskar shi duk Sahun naushin mutane, bakinshi da hancinshi duk sun fashe, baisan Lokacin daya fashe da kuka ba kamar ƙaramin yaro, rungumeshi yayi ajikinshi, sosai, Gwanin ban tausayi, Har kiran Angel a kayi daga office din Dpo, Aka nuna mata uzair suka tambayeta shi ne, Tace Eh shi ne. Sun sha wahala a hannun ƴan sandan, Yinin ranar har dare ya yi ana Bincike a kan su, Daƙyar suka samu a kayi masu alfarmar su kira wani da zai bada shaida akansu, Anan ne Uzair Ya kira Aneelerh, Ya bata address ɗin Ps din da zata same su, Ba'a ɗauki Lokaci ba Motar Aneelerh Ta ƙaraso Cikin harabar station ɗin, hankalin ta duk Yabi ya tashi Jin suna a hannun police, bayan Tayi parking ɗin motar, Ta fito sanye Cikin doguwar riga ta yafa mayafi akanta a hanzar ce ta nufi cikin station ɗin, Lokacin da ta shiga Ciki, ƴan sandan suka Yi mata jagwaro zuwa cell din da aka rufe su, bata san lokacin da ta fashe da kuka ba Ganin Yadda aka raunata Taj, duk ya fita hayyacin shi kamar wanda yayi hatsarin mota, Saboda jigatar da yayi. Cikin shessheƙar Kuka Ta kalli ƴan sandan tana faɗin "Why why!why pls? Laifin me suka aika ta da za ku yanke masu irin wannan ɗanyen hukuncin," Copral ne Ya bata amsa da cewa"Ana zargin su da sace Ƴa'ƴan mutane suna amfani da su" Waro ido waje aneelerh Tayi tana kallon su, har bata san lokacin da tace "Amma baka da hankali Officer, Ka iya bakin ka, Shin kuna da hujja akan a bunda kuke zargin su ne? waye ke baisan Taj da uzair ba....."bata kai ƙarshen maganarta ba muryar dpo ta katse ta"Muke da ƙwaƙƙwara Hujja akansu," Idanuwanta jawur ta ɗago tana kallon Dpo ɗin, Cikin sanyin murya ta furta"where's the evidence"? Kafin dpo ya bata amsa sai ga Angel tana fitowa daga Office ɗin shi A ruɗe Aneelerh take kallonta Cike da son Jin ƙarin bayani, Da kulkin hannunshi Ya nuna Angel, itace ƙwaƙƙwarar Hujjar da muke da ita, Wannan yarinyar An same ta cikin kasuwa tana gudu tana kuka a kan Wannan bawan Allahn daya sace ta, Ya raba ta da iyayen ta don baƙin zalunci," yakai ƙarshen maganar Yana nuna Tajuddeen, Hankali amatuƙar tashe Aneelerh ta daura hannu akai tana sallallami"You ave made a big mistake officer wannan fa Ƴarshi ce," muryarta a disashe takai ƙarshen maganar, "Amma ae ita Yarinyar da kanta ta faɗa mana cewa shi ɗin ba mahaifinta bane satarta Yayi," acewar dpo, Tuni hawaye sun kuma wanke fuskar aneelerh, Girgiza kai tashi ga yi tana kallon angel, "Wlh officer Ƴarshi ce sharri take yi mashi, Yarinyar bata da cikakken hankali ne," Da buɗe bakin angel sai cewa"Ni ƙarya take yi mun officer itama hada ita suke yi ae" Curo handcuff Inspector yayi tare da cewa"You are under arrest" ya ambaci hakan yana ƙoƙarin sanya mata ankwa Ganin dagaske Kamata za su yi ne yasa tayi saurin cewa"Ku dakata kada kuyi abunda zakuyi danasani Officer, akwai hotunan yarinyar da videos ɗinta a wayar Mahaifinta zaku Iya bincika wayar shi ku gani. Girgiza kai Dpo yayi"Wannan ba hujja bace duk shirin ku ne" Jinjina kai tayi to shikenan me zai hana Muje asibiti ayi masu DNA test, this is the Only solution" Jinjina kai dpo "Good idea Copral"Dpo ne ya kira sunan shi "Yes sir" ya amsa mashi. "Ku tafi da Mutumin da yarinyar a yi masu gwajin DNA, ku tabbatar anyi komai agaban ku," "Consider it done sir" Ya ambaci hakan tare da sara ma shi,Kafin Ya fiddo dasu Taj daga Cell ɗin, Bawan Allah kamar lagwanin fitila duk ya rasa ƙwarin Jikinshi, sai da uzair Ya taimaka mashi tukunna ya iya tafiya da ƙafafun shi, wani abun mamaki ko kadan Angel bata ji tausayin shi ba, ko son kallon shi ma ba ta yi, A cikin mota suka sanya su, Aneelerh kuma Ta shiga motarta tare da angel, Bayan zuwan su asibiti, Akan idon Police men ɗin akayi komai, Bayan Bincike da likita Yayi result Ya nuna cewa Jininshi ce ita, Hankalin ƴan sandan ba ƙaramin tashi yayi ba, Lokacin da suka kalli result ɗin da likita ya basu Sun sha mamaki, Lamarin Yayi matuƙar girgizasu, Tun anan Inspector Ya kira Dpo ya sanar dashi sakamakon Gwajin da akayi masu, dpo yafi kowa girgiza, har sai da ya tako yazo asibitin Don Ya basu taj haƙurin akan zargin su da suka yi Anan aka kwantar da Tajuddeen, Sam ya fita hayyacin shi,hada drip suka sanya mashi, Atare ƴan sandan suka ba su Aneelerh da Uzair hakuri akan kuskuren da su ka yi na ɗaukar mataki batare da sun fara Bincikar ainihin tsakanin shi da yarinyar ba, A ƙarshe dpo ya ba aneelarh shawarar a haɗa ta da manyan malamai su cire shaiɗanun dake ajikinta, ko kuma a kaita Psychiatric Hospital koda tana da matsalar kwakwalwa ne, Bin shi da kallo kawai aneelerh tayi don ita tasan Wacece Angel, Lafiyarta ƙalou itace aljanar kanta da kanta, yarinyar da ana yi mata ruƙiya tana cewa malamin Yadaina wahalar da kanshi Lafiyarta qalou " Kwananshi uku a gadon asibitin saboda jikin shi da yaƙi sauƙi, cikin kwanakin Aneerlerh ce da Uzair suke ɗawainiya da shi Ko uncle abdalla basu Sanar mashi da halin da ake ciki ba, da yake suna waya dashi kusan kullum ne sai sun kira su kosu su kirasu, A ƙarshe suka koma gida da yin jinya, Har hutu Aka ba Taj wurin aikinsu jin Abunda ya faru da shi, Uzair ne ya sanar dasu amma bai fada masu ainihin abunda Ya faru ba, kawai ya sanar dasu cewa Sun yi hatsarin motane, ya yi hakan ne saboda sanin halin su na ƴan jarida, yanzu ka ji labari a social media, Bawan Allah Taj kullum yana kwance saman gado, Wanka da sallah ne kaɗai suke tada shi Wani sa'in yana ɗangya shi haka zai samu ya lalla6a Ya shige toilet, Ko sannu angel bata ta6a furta mashi ba sai in tana jin yunwa ne zata addabe shi wai ya tashi yayi masu girki, in ba haka ba zata je ta daura da kanta, In ta gaya mashi hakan Jiki na rawa Yake kiran Uzair a waya Ya sanar dashi, dama Cikin ƴan kwanakin nan mai aikin su Uzair hada Su taj take girka ma abinci duk in za ta yi, bisa umarnin Uzair ɗin, Ana haka Yau kwana Biyar kenan bai zuwa ko'ina Yana gida, Wuraren ƙarfe biyar na marece, ya fitowa daga wanka jikin shi sanye da short baƙi, saman Gado ya haye bacci mai daɗi ya ɗauke shi Yayi nisa acikin Baccin shi, Yadinga Jin Hayaniya acikin gidan jiki a mace Ya miƙe daga saman gadon ya nufi ƙopar ɗakin, Leƙawa yayi don yaga su wanene Waro ido waje ya yi ganin mutane maƙil Cike da falon, Kasa kunne ya yi yana sauraran me suke cewa "Allah ya jiƙan shi, Taj mutumin kirki halinshi na gari Ya bishi," Can kuma yaji wani yace"A ina ne za'ayi jana'izar ta shi"? Wani ya ba shi amsa da cewa"Mu jira Mutanan gidan su fito sai muji," Shiru yayi la6e bakin ƙopar Ya kasa fitowa, Jikin shi duk yayi sanyi, tunani ya shiga yi wai wanene Ya mutu? dama akwai wani taj ne bayan shi"? sam bai da mu da rashin ganin angel ba yasan bata wuce Gidan su Uzair. Komawa Cikin ɗakin yayi Jikin shi duk ya mutu, Wayarshi Ya ɗauka da ke a jiye saman gadon Yana kunnata Ya shiga call logs, Nan yaga missed Calls sunyi ɗari uku na mutune, abun ya ɗaure mashi kai, Number uzair yayi dialing Ya danna mashi kira, Tana fara ringing uzair Ya ɗaga, "Assalamu alaikum" batare daya amsa sallamar ba Yayi saurin cewa"Uzair kana ina ne"? On the other hand Uzair yace"Gida mana" Cike da damuwa yace"Uzair na shiga Uku, Yanzu kawai na farka daga bacci Naga dandazon mutane a falon gidana, Na kuma taras da missed calls a wayata Ya yi ɗari uku na mutane wai meke faruwa ne"? Muryar uzair da ɗan ruɗi yace"Kodai angel tayi wani abu ne? bata jima da shigowa Gidan mu ba, Take sanar dani cewa Ta ɗauki wayarka kana bacci, Ta sanya yatsan ka ta buɗe ta "tunkafin Uzair yakai ƙarshen maganar ta shi, Taj Yayi rejecting call ɗin, Ya shiga laluban wayar shi, Sai ga Notification na facebook on the top of the screen yayi appearing, Likes ya dinga gani na mutane da kuma Comment da ake tayi, A hanzarce Ya shiga facebook dinshi, a nan Yaga hoton shi dana angel ta ɗauka yana bacci tayi share ɗinshi a facebook, a ƙasa ta rubuta RIJF, Su kuma Mutane da suka Ga posting din dayawan su sunyi tunanin ko matarshi ce Tayi amfani da wayar shi donta sanar masu mutuwar shi, Shine suka kwaso ƙafafuwansu zuwa Gidan don a yi jana'ixa da su. jiri ne Ya soma ƙoƙarin kwasar shi, lalla6awa ya yi tare da samu wuri gefen gadon ya zauna yana ambaton Allahumma Ajirni fil musibati wa aklifli khairan Minha, Na jima ina tunanin Ranar mutuwa ta, da kuma abunda zai yi silar bari na duniya ashe ƴar Cikina ce, Laifin me nayi mata ne da ta tsane ni? sai ka ce ba mahaifin ta ba,ƴar ƙarama da ita sai Iya mugunta wayyo Allah na, sai daga bisani Ya tuna inda tasan kalmar RIJF, a tv ne wani ya rasu ana sanar da ta'aziyar shi, daga ƙasan hoton shi aka Sanya RIJF, Rest In jannatul firdaus, shine take tambayar shi wai me yake nufi, da yake ta iya tambaya kamar yar jarida, Bai yi tunanin komai ba ya sanar da ita ma'anar hakan, Shine tayi mashi aika aika. Kiran Uzair Ne ya shigo wayar shi, A sukwane ya ɗaga Kiran a nan yake sanar da shi abunda ta aikata mashi, Uzair yasha ruwan mamaki A ƙarshe dai,Uzair da aneerlerh ne suka shigo gidan suna bama mutune hakuri akan cewa Taj bai mutu ba, Yana a raye mistake aka samu wurin Yin posting din, ƙin tafiya sukayi Har sai da suka ga Taj da ƙafafun shi tukunna suka bar gidan suna yi mashi Allah ya kyauta, A falo suka zauna gaba ɗayan su, Uzair da Aneelerh suna zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, Taj kuma yana zaune a saman 2 seater,fuskarshi duk a hautsine, "Yanzu menene mafita"? taj ne ya yi maganar yana kallonsu, "Lamarin Angel Yafi ƙarfin mutun sai dai Allah, ae ni tun ranar da aka kira malami yayi mata ruƙiya ta sace takalman shi, tun daga nan Jikina Yayi sanyi," acewar Uxair, "Benazir ta tafi tabarmun bala'e" tamkar taj zai fashe da kuka Yayi maganar,. "Me zai hana ka jaraba Bugunta"? a ɗan firgice ya kalli Aneelerh da tayi maganar, Cigaba da magana tayi"Idan har ba za ka iya bugunta ba shawarar da zan bada shine, Kasan mafi a kasarin ƙananun yara akwai abunda suke tsoro, Ni ina ganin a jaraba samo Mage ko kare ko kuma ƙadangare, Idan aka samu wanda take tsoro acikinsu, Sai adinga Yi mata Baraza na da shi, Koya kuka Gani"? tayi tambayar tana kallon Taj, wanda ya yi zugudum yana kallonta, yarinyar da take kallon Zombie tsakar dare, Taya zata Ji tsoron waɗannan halittun, Acikin zuciyarshi ne yayi maganar, Jinjina kai Uxair yayi"Good idea idan na fita Yanzu xansa Almajirai su ɗauko mun ƙadangare a fara jarabata dashi, inyaso gobe sai a kawo karen Nasan dole asamu wanda take matuƙar tsoro acikinsu," "Allah yasa dana fi kowa Farin Ciki" acewar Taj, Sun jima suna tattaunawa kafin Su ka yi ma shi Sallama, Atare suka bar gidan, Duk dabbobin da aka kawo gidan don angel ta tsorata amma abun ya ba su mamaki bata tsoron su, illa ma ita dabbar da aka kawo taji tsoronta, yarinyar ta zarce tunanin mai tunanin ga karfi Allah Ya yi mata, Ranar da taj yasa aka kawo mage agidan Sai da ya yi dana sani, A lokacin Yana kwance yana bacci Ya barta a falo ita da magen da ta sanya ma suna Chu chu, suka soma kokawa tana kiciniyar kamata, magen ta watsa aguje tana kuka, tabi bayanta da gudu suka shiga zagaye palourn, Sune har cikin kitchen, Magen ta haye saman Dish racks, inda Jerin Plates na tangaran suke, Angel takai hannu da niyar ta cafkota aikuwa gaba ɗaya Ta 6aro da Kwanukan tangaran din, Suka tarwatse kasa duk suka faffashe, Tsalle magen tayi ta ruƙo jikin Cupboard wasu hadaddun Glass Cups ne dana tangaran, Ruƙo ƙafar magen Angel ta yi, Gaba ɗaya Cups din suka Rikito ƙasa duk suka tarwatse, Kubce mata magen tayi da gudu ta sauko ta nufi Store da kopar shigar shi ke anan cikin kitchen ɗin, Aguje angel tabi bayanta, Suka shiga yin yar tseral, Wasu jerin Crates din kwai Ne Magen Ta hau saman su, A ƙalla sunyi crates goma sha biyu, Gaba ɗaya suka kife kasa eggs ɗin suka faffashe, hayewa sama magen ta yi inda aka jera Sunƙi sunƙin bready, Ganin tsawonta bai kaiwa yasa ta janyo jarkar Manja, Ta haye samanta Ta cakumo wuyan magen, jarkar da ta hau saman kanta ce ta Karkace da ita da magen Da jarkar man, Da Ledojin breadin sunkutukum Suka Kife ƙasa, Nan take murfin jarkar ya buɗe Manjan Ya shiga gangarowa ƙasa, bari in takaice maku zance sai da Angel ta canzama Kitchen din halittarshi, tamkar Bola, uk Ta hargitsa komai ba, Da ta ga Ta yi 6arna sosai, saita Saki Cucu, Ta ruga da gudu ta nufi gate, A lokacin baba mai gadi Yana Cikin yin alwalar sallar magrib, Ya hangota ta nufo shi, Tunkafin ta ƙaraso Take nuna mashi gate ya buɗe mata, Sanin Tsiwarta yasa Ya buɗe mata ƙopar jikin gate ɗin ta fuce, Sai gidansu Aneerlerh lokacin da ta shiga Gidan, A bedroom ta samu aneerlerh ta kabbara Sallah, Saman Gadonsu ta haye Taja bargo ta kuɗunɗu ne, Bayan aneelerh ta kammala Yin sallar,t ana daga zaune saman darduma ta kalleta"Angel Lafiyar ki kuwa" Kasa ƙasa da murya tace"Zazza6i nake yi" "kin sha magani" "Eh nasha, daddy ne yace inzo wurin ki kiyi mun wanka,i n ya dawo daga masallaci zaizo ya dauke ni" Mikewa aneerlah tayi, bayan ta cire hijabin ta tura a wardrobe, "Tashi muje nayi maki wankan" Yaye bargon tayi ta sauko daga saman Gadon, rigar jikinta duk ta cukuikuye, hada manjan daya gogu agaban rigar, "A haka kika hau mun gadona? Ina kika samu manja ajikinki" Ashagwa6e tace" nace maki bana lafiya, Ni bana iya magana sosai" Sam aneelerh ba ta yarda da ita ba ta ƙyale ta ne kawai, Within minutes ta yo mata wankan, suka fito daga cikin toilet, ta shafe ma ta jikinta da mai, canza mata kaya tayi, dama Saboda Ita ta sayi kayan Yara dai dai Size dinta, saboda sun ɗauke ta tamkar ɗiyarsu, pink gown ta sanya mata,ta kuma ɗaure mata sumar kanta da ribbom,ba ƙaramin kyau tayi ba, hada light make up aneelerh tayi mata, "Aunty aneelerh,Z an koma saman gadon in kwanta, dan Allah ki hadamun fura, A sanya kwakwa da yogurt aciki da ƙanƙara" Jinjina kai aneerlah tayi fuskarta dauke da murmushi tace"Okey My daughter in law, je ki kwanta,"da gudu taje ta haye saman gadon, Bayan Aneerlerh ta hado mata furar a cikin Cup ta kawo mata Nan ta zauna tasha ta ƙoshi, kafin ta koma ta kwanta tuni bacci yayi awon gaba da ita, A 6angaren Taj kuwa, Lokacin daya tashi toilet ya shiga, ya dauro alwala ya dawo Cikin ɗakin Ya dauko Jallabiya Cikin Closet din shi Ya zura ajikinshi, Fitowa ya yi daga ɗakin yana ta faman sauri Ya fuce zuwa masallaci, Bai tashi sanin aika aikar da Angel tayi mashi ba, Sai daya Dawo daga masallaci, wata irin yunwa ta farmasa, ba arxiƙi Ya nufi kitchen shigar shi keda Wuya Tun abakin ƙopar yaci karo da Fasassun kwanukan da angel ta 6aro, A razane ya dago yana kallon cikin kitchen ɗin, har wani haya ki yake ganin cikin idon shi saboda tsabar 6acin rai, ashe bai ga komai ba sai daya Shiga Cikin store, Hannu ya ɗaura akai yana ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Nashiga Uku! Na bani! Ya Allah laifin me nayi aka jarrabceni da Angel? wani zunubi na aikata, dafe baki yayi da sauri jin sabon da ya yi yana mai fadin astagfurullah....." yana cikin sambatun nan yaji kukan Mage, Aikuwa a harzuƙe ya juya ya kalli magen dake a bakin kopar store ɗin, Shaƙo wuyanta yayi tare da jijjigata Yace"Ke da ubanwa ku ka yi wannan"? Ƙura mashi ido magen tayi tana Cigaba da yin kukan Yunwar da take yi, wurgi yayi da ita, tare da naɗe hannun rigar shi Ya fuce daga gidan, kaitsaye Ya shiga Gidan Uxair, tun a bakin gate mai gadin Gidan Ya soma tambayar shi"Yalla6ai Lafiya" Baiko tanka mashi ba Idonshi Ya rufe, Angel kawai Yake nema Ko sallama bai tsaya Yi ba Ya faɗa Cikin Falon Gidan, Ganin bakowa Yasa shi fara kwala mata Kira"Angel!Angel!Angel!!' tamkar makoshin shi zai 6allo, Da gudun gaske Aneelerh ta fito daga bedroom ɗinta Jin muryar Taj Cikin tashin hankali, "Me ya faru ne"?tayi tambayar tana kallon shi, "Where is Angel"? "Ɗazu ta shigo bata Jin dadin jikinta, yanzu haka bacci take yi adakin"bata kai ƙarshen maganar ta ba, Ya wuce ta a fusace Ya faɗa dakin, Can ya hangota saman gado a kudundune tana ta sharar bacci," Hannu biyu yasa ya Cakumeta, da sauri aneerlerh ta biyo bayan shi Tana tambayar shi Meya faru ne, Da budar bakinshi sai cewa yayi"kashe ta zanyi," Yana faɗin hakan ya nufi hanyar fita da ita, gida Ya koma da ita a dakin su Ya jefar da ita saman gado, sai lokacin ta farka tana kallon shi da manyan idanuwanta, "Daddy what"? "Zaki Ci ubanki ne" ya faɗi hakan tare da Janyo pillow Ya hau saman gadon Ya turmushi fuskarta dashi, Mutsu mutsu ta shiga yi, tana kokawar fitar da numfashinta, sae faman harba ƙafafunta take Yi, tana neman Ceto,Amma Taj sam Babu alamar zai sarara Mata, Saboda Baya acikin Hayyacinshi Dagasken kasheta Zai yi, Faɗowa ɗakin aneelerh tayi ko takalma babu a ƙafafuwanta, Anan ta same shi Saman Gadon Ya danne angel Da pillow, A gigice ta fasa ƙara, Tare da yin kukan kura Ta haye saman Gadon, Da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta cakumi wuyan jallabiyar jikin Taj tare da Yin Wurgi dashi gefe guda Ya faɗa saman mattress din, Cikin shessheƙar kuka take fadin"Taj ban sanka da haka ba, meyasa zaka yanke hukunci Cikin fushi ne? Meye ribar ka idan ka kashe Angel?yarinyar da ba ta wuci 7years ba, idan ka yi hakuri Wata rana zata daina ne, "Wlh bazan ƙyaleta ba Kafin ta kashe ni, Ni zan fara kashe ta," ya ambaci hakan tare da yunƙurawa Ya miƙe Yana ƙoƙarin Cakumar Wuyan angel da ta sume, da sauri Aneelerh Ta sanya hannu ta ɗauketa, tana ƙokarin sauko wa da ita daga saman gadon, A ƙokarin Ya damƙo angel Ya janyo wuyan rigar Aneelerh gaba ɗaya aneelerh tayi baya ta faɗa saman faffaɗan kirjinshi, Angel kuma ta yi gefe ɗaya saman gadon, Karo na farko da jikinta ya fara ta6a namijin da ba muharraminta ba, shi kan shi bai yi tsammani hakan zata faru ba, saboda ba ita yayi niyar Janyo ba, Angel da ke a hannunta Yaso Ya damƙo, hatta mayafin da aneelerh ta rufe kanta dashi ya warware sumar kanta mai tarin yawa ta sauka har saman kafadarta, wani irin yanayi mara misaltuwa ne ya ziyarci kowan nan su, ƙoƙarin miƙewa aneelerh ta yi sai dai ina wani magnet ne ya ruketa, Runtse idanuwanta tayi da karfi ta soma ambaton a'uzubillahi minasshaiɗanirrajim, tun da ta ambaci hakan sai ga shi ta samu ƙwarin guiwar Raba jikinta daga Na taj, aikuwa A gaggauce ta hanzarta sauka daga saman gadon, ko mayafin ta bata tsaya ɗauka ba ta watsa da gudu tabar ɗakin, A hankali taj ya lumshe idanuwan shi, ya yin da hancin shi ke shaƙar mashi ƙamshin turaren Jikin aneelerh daya gauraye Jikinshi, bakomai Ya tuna ba face Matarshi da ta gudu tabar shi, maca ce mai matuƙar son ƙamshi, shima kuma ma'abocinsa ne, baisan Ya akai ba Ya tsinci kanshi da tariyo yarda Aneelerh ta faɗo saman ƙirjinshi, da kuma yadda yalwataccen gashin kanta Ya zubo har a jikinshi,da kuma daddaɗan ƙamshin turaren ta, Ganin Zuciyar shi na ƙokarin Zayyana irin kyawun surarta ne yasa shi saurin Ambaton A uzu billahi minasshaiɗanirrajim, Astagfurullah Ya Allah, Miƙe wa Ya yi zaune Duk kasala Ta rufe shi, saukowa yayi daga saman gadon ya fito palour, babu kowa Hakan ya tabbatar mashi da cewa Neelerh ta gudu, frigde ya buɗe ya dauko Swan Mai sanyi ya dawo bedroom din shi, daga gefen gadon Ya zauna, buɗe murfin yayi ya tarfa ruwan a hannunshi Ya watsa ma angel asaman fuskarta, nan take Taja dogon numshi, Slowly ta buɗe idanuwanta akan fuskar shi, Suna hada ido ta fashe da matsanancin kuka, Natsuwa yayi yana kallonta ko kusa baiji tausayin kukan nata ba, tun da ya lura Ba son shi take Yi ba, Cikin shessheƙar kuka tace "You want to kill me because you don't love me, yanzu da na mutu Allah zai kamani, so kake in shiga wuta ko? ta yi tambayar tana kallonshi, har lokacin idanuwanshi na akanta baice uffan ba, "Kana Jina ka share ni ko" Gyaran murya ya ɗanyi can kasan makoshin shi ya furta"Dama kina tsoran Mutuwa"! A tsiwace tace "Eh mana,malamin mu ya karanta mana wani hadithi wanda ke magana akan mai munana ma iyayensa ba zai shiga aljanna ba, A wuta za'a babbaka shi......" Ƙiris Ya rage taj ya ɗan murmusa"So you know that but u keep hurting me ko"? Fashewa ta kuma yi da wani sabon kukan, Ganin tasha Jinin jikinta sosai yasa shi kwantowa Yayi mata rumfa da faffadan kirjinshi, cikin sanyin murya ya soma magana Yayin da idanuwan su ke kallon Cikin na Juna, "Angel, zan sanar dake wani abun da baki sani ba ba ki da wanda yafi ni a duniyar nan, ba ki ta6a tambayata mahaifiyarki ba, Bansani ba ko kina tunanin Namiji yana iya haihuwa ne, Shiyasa kike ganin kamar ni na haife ki, Baki da abun wulaƙantawa Irin mahaifin ki," shiru ya ɗanyi yana nazarin wani abu, ita kuwa ta kasa kunne tana sauraronshi, Cigaba da magana yayi"Angel, mahaifiyarki a wulakance ta haife ki, Cikin bathtub tabar min ke, Cikin Jini kina ta kuka, Ni ina bacci kukan ki ne Ya tashe ni haka naje na sameki, Na ɗauke ki na rungume ki ajikina, duk da jinin da ke ajikin ki, Ni ban gudu nabar ki ba, kuma ban bari kin wulaƙanta ba, Sai da na tsaya akan ki angel da taimakon Allah har kika kai wannan lokacin, Tun da ki ke ƙuntatamun dai dai da na rana ɗaya ban ta6a Tunanin na tafi nabarki ba, kuma ban ta6a tunanin in sanya hannuna wurin ta6a lafiyar jikin ba amma angel......"kasa ƙarasa maganar Ya yi jin yadda ta rushe da kuka kamar ranta zai fita, ɗagowa Ya yi zaune yana kallonta. Hannu ta ɗaura akai tana faɗin "Wayyo Allah na nashiga Uku,Na bani Na lalace!" hankalin shi ba ƙaramin tashi yayi ba,njin yadda babyn shi take Kuka, Lallashinta ya soma ƙokarin"Am really sorry daughter, I don't mean to hurt u darling, Na faɗa maki ne don ki ɗauke ni da muhimmanci, don ki san cewa Ina sonki, kuma ina buƙatar tausayawa daga gare ki," bata tsaya sauraronshi ba, Ta sauko daga saman Gadon da gudu ta nufi toilet ta shige taja ƙopar ta rufe, A hanzarce Ya sauko daga saman godon cike da fargabar karta kashe kanta, tura ƙopar yayi ya ji tayi Locking dinta, Bubbuga ƙopar ya shiga yi yana ambaton sunanta"My angel am sorry, kada hakan Ya ta6a zuciyarki, kinsan ina sonki, banason zubar hawayen ki" Daga Cikin toilet ɗin yajiyo muryarta Cikin shesshekar kuka tana faɗin"I hate my self daddy, cikin toilet aka haife ni, kuma ta gudu tabar ni saboda bata sona......" Runtse idanuwan shi Yayi tare da ɗan Cizon lips ɗinshi Calmly ya kira sunanta"Angel pls forget about it, Tunda kina da ni don me zaki damu kanki? Ni ne mom dinki kuma daddyn ki, Zuƙunnawa Yayi agaban ƙopar, yana ji aran shi cewa tana zaune a gaban ƙopar, tsit ya ji ta daina kukan "Pls say something to me, ko naji sanyi acikin zuciyata" Shiru bata tanka mashi ba, "Ki buɗa mun ƙopar" Sai Lokacin yajiyo muryarta can ƙasa ƙasa"daddy inaso na mutu, kodan saboda nadaina 6ata maka rai" Cikin matsananciyar damuwa Yace"idan kika mutu angel shi ne zan shiga Damuwa wadda zatayi silar mutuwata nima, saboda kece Oxygen ɗin da nake shaƙa," Yakai ƙarshen maganar tare da kwantar da kanshi jikin door ɗin, don Yaji daɗin Jin muryarta "I made a mistake daddy, I won't hurt you anymore," Saboda tsabar Mamakin Jin abunda tace har saida Ya ɗan dago da kanshi, yana kwalkwale kunnanshi wai koda Ya samu matsalar hearing ne, "I love u daddy" ya kuma Jin ta furta mashi aruɗe yace"Repeat it pls" "I love u daddy" "sake maimaita mun naji"fuskar shi ɗauke da murmushi Ya yi maganar, Sake maimaitawa ta yi kamar yarda ya nuna yana son ta yi ma shi, "I love U daddy, Bani da tamkarka a duniyar nan" Wani irin ihu ya saki, Irin wanda Ƴan kwallo ke yi idan sunci nasara akan wasan su, A ƙagare Yace"Come out pls, ina so naji ɗumin ki a jikina" Yana jiyo alamun tana buɗe ƙopar kamar jira yake yi, tana ƙarasa buɗe wa Ya janyo ta Jikin shi yayi hugging ɗinta very tight, hannun shi na acikin sumarta, Wani irin farin Ciki ne Ya lullu6e shi kamar wanda a ka yi ma Albishir da gidan Aljanna,' dole Taj ya yi farin ciki cos this is the first time da angel Ta fara furta mashi kalmar tana son shi a mtsayina mahaifinta, Ya ji tausayinta sosai, bai ta6a tunanin akwai lagwanta ba sai yau, da ta ji cewa mahaifiyar ta ta gudu ta barta, Jikinta ya yi sanyi, da yasan da haka da tuni ya faɗa mata, da duk wannan abun bai faru ba, daukarta Yayi asaman bayanshi, yakaita Cikin motarshi, atare da ita suka je masallaci, Ya barta acikin mota, Bayan ya kammala sallar, ya dawo Ya shiga motar yayi driving ɗinsu zuwa Restaurant, komai take so shiyasa aka kawo masu, sai da suka ci suka ƙoshi, sannan Suka dawo gida, A palour suka zauna saman Sofa tana rungume ajikin shi, Suna kallon tashar Mbs 3, dama best channel ɗinta ce saboda suna sanya Cartoon, tafi sha'awar kallon Cartoon da kuma zombie, Tuni bacci ya dauketa ajikinshi, asaman kafaɗar shi ya ɗauke ta Ya nufi bedroom dinsu, don ya kwantar da ita, a hankali Ya tura kopar ɗakin Ya shige, A saman gado Ya kwantar da ita, Sai da ya fara daukar wayar shi dake ajiye agaban mirror, Tukunna Ya haye saman gadon ya janyo ta a jikinshi, Yana shafa sumar kanta, cikin magagin bacci ya ji tana fadin"I luv u daddy" murmushi ya ɗan saki, Tare da manna mata kiss a gefen fuskarta "Luv u too My own daughter" Number Uzair Ya kira, tana fara ringing Uzair ya ɗauka, "Aminina Yanzu nake shirin zuwa duba jikin ka" "Na hutasshe ka ba sai kazo ba, Jiki ya yi sauƙi Alhamdulillah" "Naji labarin abun kunyar da kaso ka aikata na kashe ƴarka, Ae ni har na yi shirin zuwa ɗaukar rahoto" Fashewa Taj yayi da dariya"Ta 6atamin raine, ni kaina bansan nayi wannan yunkurin ba," "Yanzu Ina virus ɗin taka take"?a cewar uzair, don tun ranar da ta Sa ƴan sanda su ka kama su akan ƙazafin da ta yi masu na cewa su ƴan yankar kai ne, tun daga ranar Yake kiran ta da Virus, Murmushi Taj yayi, tare da kai hannu ya shafa sumar kan angel, Virus ta yi bacci, Mutumina ka ta ya ni farin Ciki," Uzair yace"Meya faru"? Nan Taj ya kwashe duk abunda Ya faru tsakanin shi da angel ya sanar mashi," Yana jiyo sautin dariyar farin cikin da uzair Yake yi, "Ja'irar taji ƙamshin mutuwa, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ce tazo, Amma fa nayi farin Ciki, "Ameen mutumina" Shiru suka ɗanyi,yana so ya tambaye shi aneelerh amma ya kasa, "Muyi video call mana"acewar uzair, Batare da musu ba suka canza Kiran zuwa Video call, A kwance uzair yake saman katafaren gadonsu, ya dan tada kan shi saman pillow, jikin shi na sanye da kayan Bacci, "Show me her face" murmushi taj ya yi tare da haska mashi fuskar angel, ta sa ki baki da hanci tana ta sharar bacci, Dariya uzair yayi"waya ga mashasha, wannan ae itace Laca sera jibi yadda ta saki la66a, a haka zata zama surukar mu," Fuskar Uzair ɗauke da murmu shi yace"cin mutuncin ya isa haka aminina, kai ka sani Wlh angel koda kuɗin mutun saida rabon shi, koda rabon shi sai in Allah ya nufa" Jinjina kai Uzair Yayi tare da ɗan yatsina fuska yace"Virus ɗin"? Taj na ƙoƙarin buɗe baki ya mayar mashi da martani, adai dai Lokacin Aneelerh ta fito daga Cikin toilet, Chest ɗinta ɗaure da farin towel iya guiwarta ya tsaya, Ta cikin Screen ɗin wayar uzair, Taj Ya hangota yanayin kwanciyar da uzair yayi ya juya ma Toilet ɗin ɗakin shi baya, wanda hakan yasa har Taj ya iya hango fitowarta, Baisan ya a kai ba Ya tsinci kanshi da satar kallonta, Ya bar uzair sai faman zuba yake yi kamar kanyar da bata da daɗi, gaban mirror ta tsaya tana tsane sumar kanta da towel, "Me kake tunani ne"? a firgice taj Ya mayar da hankalinshi kan Uzair, muryar shi na inda inda yace"Bakomai zan kwanta mutumina, Sae Allah yakaimu," da sauri ya yi rejecting kiran tunkafin ma uzair ya yi mashi sallama, Lumshe idanuwan shi ya yi zuciyar shi a cunkushe, duk yadda yaso Ya hana kan shi tunanin abunda ya faru tsakanin shi da aneelerh abun ya faskara, daƙyar ya samu bacci yayi awon gaba da shi, Tun daga wannan Ranar Angel bata ƙara 6ata mashi rai ba, koda yaushe suna manne da juna wata irin shaƙuwace a tsakanin su, mutu ka raba takalmin kaza, tabbas Angel taba kowa mamaki, irin yadda take son mahaifinta, tarairayarshi take yi, biyayya take yi mashi sau da ƙafa, Xaman Lafiya ya wanzu a tsakanin su. A hankali ya tura ƙopar falon ya shigo Ciki, dawowar shi ke nan daga masallaci, ya ɗan tsaya sauraron wa'azi, jikin shi na a sanye da jallabiya ash colour, da sauri ya nufi bedroom ɗinsa, Da sallama a bakin shi ya shiga, tunkafin ya ƙarasa shiga ya same ta a kwance tsakiyar gado tana ta sharar baccin ta hada minshari, Agogo ya kalla shida ta kusa, ƙarasa shiga Cikin bedroom ɗin ya yi a gefen gadon ya zauna, tare da ɗan juyo wa yana kallonta, tayi ɗai ɗai a saman gadon, Kayan baccin da ya sanya mata jiya sune a jikinta riga da wando blue sky, curly hair ɗinta duk ya cukurkuɗe ya nannaɗe, a Hankali ya sanya hannu tare da jan hancin ta, yatsina fuska tayi tare da juyar da kanta gefe batare data farka ba, "Wake up My lovely daughter" Cikin kunne yayi mata raɗa, Buɗe gray eyes ɗinta ta ɗanyi slowly tana kallon fuskar shi biji biji, "Nauyin bacci ko? Oya wake up, kada muyi late, ki tashi inyi maki wanka, in girka maki abinci mu ci mu ƙoshi, kafin na sauke ki a school ni kuma na wuce wurin aikina Jin tayi shiru ba ta ce komai ba, yasa shi fara Yi mata cakulkulo, lokaci guda ta 6a66ake da dariya, white teeth ɗinta kamar gonar auduga, saboda tsabar kyau, kai kace wani abinci bai ta6a giftawa ta cikinsu ba saboda hasken su, Sosai ya sanya ta nishaɗi, a ƙarshe Ya ɗauke ta saman kafadar shi Ya nufi toilet da ita, almost 15 mins Ya fito da ita Goye saman bayan shi, Ya ɗaura mata towel ajikinta, A saman mirror chair ya zaunar da ita, Hair dryer Ya ɗauko acikin drawern dake ɗauke da madubin, Ya jonata ajikin Socket,Nan take Iska ta soma busowa buuuuu, runtse ido tayi tana dariya mirmishi ya saki ganin yadda ta ɗan zabura, zura hannun shi ɗaya yayi acikin sumar kanta yana cakuɗata sosai ya busar mata da gashin, Bayan Ya kammala ya kashe dryer din, ya mayar da ita inda ya ɗaukota, ya kuma ɗauko Comb,Ya shiga sharce mata gashin, Sai faman sakin murmushi take yi, A duk lokacin da taga daddynta yana yi mata hidima kamar sarauniya ba ƙaramin daɗi ta ke ji ba, har tunani take yi anya kuwa akwai yaron daya fita samun gatanci? ta cikin mirror taj ke kallonta, ganin ta ƙurawa madubin ido da alama wani abu ta ke tunani, Man gashin ta Ya ɗauko Ya shiga shafa mata, Bayan ya kammala Ya ɗauki ribbom ɗinta da ke a jiye gaban mirror din, Hannu yasa yana ƙokarin tattara gashin kanta, Abun mamaki daga ya haɗa zai ɗaure saiya watse, Yawan gashi ne da ita ga tsayi, don a yanzu gashin ta ya kai mid back ɗinta, sai da taj yayi da gaske tukunna Ya samu ya ɗaure mata shi, "Daddy ni da kai wa ya fi kyau" ta yi tambayar tana sakar ma mirmishi Dungurin kanta yayi"Kinfi kowa sani ae" ya yi maganar tare da juyawa ya nufi closet ɗinsu, Hannu yasa ya buɗe murfin, Jerin kayan sawan shi ne da kayanta, Uniform ɗinta Ya ɗauko mata riga fara sai mini skirt red colour, Abaya fara ƴar short, a yanzu angel tana a class 5 saboda ƙoƙarinta, ga wayau da Allah ya yi mata uwa dila agari, bayan ya kammala sanya mata uniform ɗin Ya feshe mata Jikinta da turare, Ya zaunar da ita gefen gado"Am coming now" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya fuce daga ɗakin, jim kaɗan Ya dawo hannunshi ɗauke da Food basket ɗinta, madara ce me sanyi Acikin roba, tare da slide bread ya sanya mata aciki,Sai ƙaramar kula mai ɗauke da chips, Ajiye mata yayi a gefen gadon, Shaf shaf ya shige toilet Yayi wanka, Ya fito sanye da short, zuba mashi ido ta yi tana kallon shi,. Harara ya ɗan jefa mata"Zansa kaya" ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya tayi, tamkar bata ji me yace ba, Gyaran murya yayi mata"Can't u hear me? Ki koma Falo inaso zan shirya". Maƙe mashi kafaɗa tayi cikin shagwa6a tace"Amma ae ni har wanka ka ke yi mun, kuma kana ganina ba kaya, Amma ni kullum sai ka kore ni in zaka sanya kaya' Tashin Sense, zaro ido waje ya yi yana kallon ta Cike da mamaki, Ya ma rasa gane wai me take nufi, sai lokacin ya gane kuskuran sa na rashin ɗaukar mai aikin da zata dinga kular ma shi da ita da wankan da yake mata har wannan lokacin, "Angel don't waste my time, Oya hold ur basket, ki jira ni a falo," Ganin ya ɗaure fuska ba wasa Yasa ta sauko daga saman gadon tana tur6une fuska takai hannu ta sungumi basket ɗinta ta fuce falo, Saman sofa ta zauna tana Cika tana batsewa, Bayan ya kammala shiryawa cikin suit, Ya fito daga ɗakin Ya nufe ta, Hannunta ya kama suka fito daga falon, Baba maigadi ya samu, A harabar ajiye motocinshi, Yana goge ma shi motar da zai fita da ita, Tunkafin su ƙarasa baba maigadi ke ta faman washe ma angel baki, ita kuwa ta tsuke fuska, Dama aduk lokacin data ɗauki wanka ta san ta yi kyau, Daƙyar ta ke ma mutane magana, Suna ƙarasowa bakin motar, Baba maigadi Ya miƙa mashi hannu suka soma gaisawa, kafin Ya kalli angel"Ƴan mata makaranta za'a tafi"? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh" "Allah ya bada sa'a Angelata"maƙe mashi kafaɗa ta yi"Ni ta daddy ce"dariya su ka yi gaba ɗayansu, Taj yace"Bari mu wuce kada mu makara" baba maigadi yace "Allah ya tsare adawo lpy" ya amsa ma shi da ameen kafin ya buɗe mata motar ta shiga ciki, ya zagaya ta left hand, ya buɗe ya zauna a driver seat, A tsanake Yayi ma motar key, tare da karya kwana Ya nufi gate ɗin, da sauri baba mai gadi Ya riga shi ƙarasawa Ya buɗe mashi gate ɗin, Ya fuce daga gidan, A hankali yake driving, Ta wutsiyar idonshi ya kalleta, Ta natsu ta kame kanta, "Karfa kiyi mun bacci mun kusa ƙarasawa" "Ba bacci nake ba,Ina tunani ne" "Daddy wlh ni banaso mu rabu, dama ka dinga tafiya dani wurin aikin ku" Murmushi ya ɗan saki"Karatun naki fa"?y ayi mgnr yayin da yake ƙokarin juya sitiyarin moyar don ya kwarya kwana, Shiru bata amsa mashi ba, "Ni inaso ki yi karatu angel, sai da ilmi ita kanta rayuwa ta ke yin kyau, ko bakyason nan gaba ki zama wani abu da mutane za su yi alfahari dake"? "Inaso" ta amshi amsa a takaice, "To faɗamun me kikeso ki zama"? Da buɗar bakin ta sai cewa tayi"house wife" ae baisan lokacin daya tuntsire da dariya ba, zuba ma shi ido ta yi tana kallonshi, fuskarta babu alamun wasa don ita dagaske ta yi maganar, "Daddy why are u laughing? did i say something wrong"? Girgiza kai yayi"a'a,May be u did'nt understand my question, Ina nufin wani aiki ki ke son Yi idan kika girma, a aikin gomnati? ya yi tambayar adai dai lokacin daya ƙaraso bakin gate ɗin makarantar, Ya danna hon Mai gadi Ya buɗe mashi gate Ya shiga da motar Cikin school ɗin, A parking space ɗinsu Ya tsayar da motar, Fitowa yayi tare da zagayawa Ya buɗe mata murfin motar "baki amsa mun tambayata ba"? Ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi "Daddy my answer is the same, I wanna be a house wife" Sakin baki yayi galala yana kallonta, Ya rasa taya ya akai tafara tunanin zama house wife, dududu fa primary school ta ke, Gudun kada ya makarar da ita,Yasa shi yin shiru bai ƙara tanka mata ba, Ɗauko mata food basket ɗinta ya yi kafin ya ruƙe hannunta suka nufi Cikin makarantar, kamar kullum har Cikin class ɗin su Ya kai ta, English teacher ɗinsu ya taras a jin Mrs favour,Cikin harshen turanci suka gaisa da shi, ya damƙa mata angel kafin Ya fito daga class ɗinsu Ya nufi motar shi, Zuciyar shi a cunkushe duk ya rasa sukuni, tunani ya shiga yi taya za'ae ya canza mata ra'ayinta na zama matar aure? don wannan ba ƙaramar matsala bace agare shi, ƴar ƙaramar yarinya tana tunanin zama matar aure, Karasa shige wa Cikin motar yayi a tsanake Yayi mata key, Ya nufi gate ɗin makarantar mai gadi ya buɗe mashi ya fuce, Harya haura saman titi, Hankalin shi na akan Kalaman angel, shi da yake da burin ta zama babbar ma'aikaciyar gomnati, ashe ita sam Ba wannan bane agaban ta, A ƙarshe dai ya yanke shawarar idan ya ta shi daga aiki ya ɗaukota suka koma gida, Zai zaunar da ita ya yi mata karatun ta natsu, Ko ya samu ya canza mata ra'ayinta, Wuraren ƙarfe biyu na rana, Ya tashi daga aiki,Sai daya fara zuwa masallaci Yayi sallah cikin jam'i, tukunna Ya nufi school ɗinsu, Lokacin daya karasa makarantar, tunkafin ya fito daga cikin motar, maigadi ya sanar dashi cewa Dr tazo ta dauketa, Ba ƙaramin daɗi yaji ba, kaitsaye 6atare da 6ata lokaci ba, yaci gaba da da driving, har ya ƙarasa Gida Tun a bakin gate ya tambayi baba maigadi ko aneelerh ta kawo angel, Yace mashi a'a, hakan na nufin tana a gidan su, Bayan ya ajiye motar Ya nufi Cikin gidan, Bedroom ɗinsa ya shiga, Shaf shaf Ya rage kayan Jikin shi Ya fada toilet don ya yi wanka, ko yaji daɗin jikin shi, Adai dai wannan Lokacin Aneelerh ta shigo Cikin gidan, ɗauke da angel da alama ta yi bacci, lokacin da ta shigo falo tana ta kwala sallama ba'a amsa mata ba, kawai sai ranta ya bata cewar ko bai kaiga dawowa gidan bane, don bata lura da motar shi da ke ajiye ba, hakan yasa ta nufi bedroom ɗin shi kai tsaye, ta tura ƙopar kafin tasa kai Cikin ɗakin, Asaman gadon shi ta kwantar da angel, short gown ce ajikinta daga gani hada wanka aneelerh tayi mata ta kuma canza mata kayanta,ranƙwafawa ta ɗanyi daga tsaye tana shafa sumar kanta, Jin motsin ƙopa yasa Aneelerh tayi saurin ɗagowa tare da juyawa bayanta don taga wanene, ba zato ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Taj dake fitowa daga Cikin toilet,daga shi sai short a jikin shi, Burki yaci lokacin da yayi arba da ita, duk tabi ta ruɗe a gigice ta watsa da gudu zata fuce daga ɗakin, Unfortunately ta take rigarta dake jan ƙasa, gaba ɗaya ta tafi zata kife kasa da hanzari Taj Yayi ƙwaƙƙwaran Taku Ya ruƙota, ta dawo jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya, taji tsoran faɗuwa ƙasa don ba ƙaramin buguwa za ta yi ba. Sam ta manta Jikin wa take, ta ƙaƙameshi sosai, har sai da ya ɗanyi gyaran murya tukunna ta dawo hayyacinta, ta yi saurin raba jikinta daga na shi, duk kunya ta rufe kowannan su, Daƙyar ya iya buɗe baki yayi mata magana "Sai ka ce kin ga dodo, kawai daga gani na kin zabura zaki gudu, yanzu da kinji ciwo fa? so kike uzair Yasa a ɗaure ni ko"? Murmushi ta ɗan saki ba tare da ta ce uffan ba, idanuwanta na akan yatsun hannunta, "Thank u so much aneelerh, kina ɗawainiya da angel ɗina, tamkar mahaifiyarta, naso ace benazir tana da kyakkyawan hali irin naki sai dai kash ni ban yi sa'ar mata ba," Juyawa ta ɗanyi jiki a sanyaye ta soma tafiya tana tunkarar ƙopar ɗakin sai da takusa fita tukunna ta ɗan dakata da yin tafiyar, A tsanake ta soma magana, "Zan ta ya ka addu'a Allah ya baka mace ta gari wadda ta fini" tana kai ƙarshen maganarta, da sauri ta fuce daga ɗakin, Murmushi taj ya ɗan saki, tare dakai hannu ya shafa sumar kanshi, juyawa ya yi tare da koma wa gaban mirror, lokaci guda kasala ta baibaye shi, ƙamshin turaren aneelerh ne, Ya cika mashi hancin shi, ita koda yaushe Cikin ƙamshi take, Zama ya yi a saman chair din gaban mirror, Ya kura ido yana kallon fuskar shi ta cikin mirror, A 6angaren aneelerh kuwa, Da sauri ta fuce daga Cikin gidan, Tana shiga falon gidanta, A saman sofa ta zauna tana faman mayar da nunfashi kamar wadda tasha gudu, tarasa dalilin dayasa a ƴan kwanakin nan take jin faduwar gaba aduk lokacin da ta ci karo da taj, A tsanake Ya kammala Shirya kanshi Cikin farar t shirt,tare da jeans ya feshe jikinsa da turare mai kamshi, Yasan aneelerh bazata bar angel da yunwa ba, Shiyasa ma baiyi tunanin shiga kitchen ba, Wayarshi ce ta soma ringing, da sauri yakai hannu ya dauke ta daga saman drawer, Kallon screen ɗin wayar yayi sunan Aminina ne ya bayyana akai, murmu shi ya ɗan saki tare da yin picking call ɗin ya manna wayar a kunnanshi"Assalamu alaikum, ɗan uwana rabin raina" On the other hand Uzair yace"Ka koma gida lafiya"? "Lafiya lou, Yanzu na fito daga wanka ma" "Ka ci abinci"? Dariya taj yayi sosai, jin irin tambayoyin da yake yi mashi sai kace wani ƙaramin yaro, "Meyasa ka ke mun dariya? yau nafara tambayarka hakan"? Tamkar yana agaban shi Ya girgiza kanshi"Nop, just naji abun wani irine, kana tunamun rayuwar mu agidan Uncle" Muryar shi ya jiyo da sautin murmushi "Unforgettable momeries, Allah Yabar ƙauna aminina, Zan shiga stadio Sai mun haɗe anjima" Taj yace"Okey, take care of ur self for me pls" Uzair yace"U too" fuskarshi ɗauke da murmushi ya yi rejecting call ɗin, Yana ajiya wayar saman drawer, Yajiyo muryar baba maigadi daga Can cikin falo, Yana kwala sallama, A hanzarce Ya nufi hanyar fita daga bedroom ɗin, Yayin da yake amsa mashi sallamar"Wa'alaikum Salam" Cikin falon Ya nufa, A bakin entry ɗin ya same shi a tsaye, ƙarasawa Ya yi yana kallon shi, "Barka yalla6ai"ya amsa mashi da "yawwa barka" "Dama baƙo ne ka yi" Da ɗan mamaki akan fuskar taj yace"baƙo kuma"? yayi tambayar ne don shi a iya sanin shi, ba su yi da kowa zai zo gidansa ba, "yalla6ai, Wannan malamin ne daya ta6a zuwa yi ma angel ruƙiya?' cike da son fahimtar da shi baba maigadi ya yi maganar, "Kana nufin maisalati"? Da sauri baba mai gadi yace"kwarai kuwa shi ne" "Okey, Ka ce ma shi ya shigo" "To yalla6ai," Yakai ƙarshen maganar tare da juyawa yabar falon, Tajo na atsaye Yana jiran ƙarasowar malamin Ya ji sallamar shi, Fuskar nan dauke da murmushi, Jikin shi na sanye da jallabiya wadda tsayinta bai kai idon ƙafar shi ba, Hannunshi na ruke da cazbaha Kanshi yasha uban rawani, Wani irin ƙamshine ke fita ajikinshi, Sakar ma shi fuska taj ya yi tare da miƙa mashi hannu cikin girmamawa suka soma gaisawa "Allah ya gafarta malam, barka da rana Ya iyali ya jama'a ya ƙoƙari, Allah yataimaka, Allah Ya kara ɗaukaka" "Ameen ameen tajo, Fatan na sameka lafiya ya aiki, ya kuma ɗiyar mu" Taj yace"Alhamdulillah, Duk muna lafiya Mu shiga daga Ciki," ya ruƙo hannunshi, suka nufi sofa ɗin falon, maisalati ya zauna asaman 2 seater, Sae faman sakin murmushi yake yi, Dama shi haka yake kullum fuskar nan a washe, Da wuya kaga bakin shi a ƙulle. "Bari na kawo maka ruwa" da sauri Malam maisalati ya dakatar dashi"samu wuri ka zauna tajo, Magana ce mai mahimmanci ce ta kawo ni," Tunda Taj yaji hakan, Sai ya zauna saman 1 seater ya tattara kwandon hankalin shi a kan maisalati yana sauraron shi' "Game da ƴarka injila" da sauri taj yace"Angel sunan ya ke" "Oh toh, eh ita ɗin dai" shiru ya ɗanyi yana tunanin ta yadda zai fara yi ma shi jawabi. Taj kuwa ya tsare shi da ido, Jikin shi har tsuma yake yi, don a ƙagare ya ke ya ji me angel ɗin ta yi, Gyaran murya malam maisalati Ya yi kafin ya soma magana a tsanake, "ranar da aka kirani Inyi mata ruƙiya, nayi wani laifi laifin kuwa shine bansanar dakai wani abu da nake hasashe akan yarinyar ka ba, bama hasashe bane inanda tabbaci kan shi," Tunda taj yaji hakan,nGabannshi ya faɗi rass aruɗe yace"malam wani abu kenan"? Numfashi ya ɗanja kafin yaci gaba da kora mashi jawabi tiryan tiryan "Akwai abunda na gani a tattare da yar wurin ka, A lokacin da nake yi mata ruƙiya, Sai dai tsoro da firgici ya hana in faɗa maka, gaskia yana da matuƙar daure kai saboda ba ƙaramar sarqaqiya bace a cikin lamarin kuma ni kaina na kasa tantance sihiri ne a jikinta ko kuwa saboda gaskiya abunda nagani a jikinta babbar al'amari, Tuni jikin taj ya soma kakarwa, muryar shi na kerma yace"Malam dan Allah ka yi mun bayani, hankalina a tashe Yake wlh" Cigaba da magana malamin ya yi"Kaitsaye bazan Iya ce maka ga abunda nagani atattare da ita ba, Amma ina da tabbacin akwai wani abu dake faruwa da ita a jikinta .......", Muryarshi na ɗan rawa yace"am..amma malam ni inaga kamar lafiyarta ƙalau, yanzu haka da nake maka magana mun samu sasanci a tsakanina da ita, Tana sona ina sonta ba kamar lokacin baya ba" Murmushi maisalati ya yi dama yasan zaiyi wuya taj ya fahimce shi, jinjina kai yayi tare da cewa"Shin ka ta6a tunanin ka zauna da ita ka tambaye ta game da abubuwan da take yi maka a baya gamon kanta ne ko kuwa? kuma bata ƴan gane gane haka"? Shiru taj ya ɗanyi, Shi kaɗai yasan halin da zuciyar shi ta ke aciki, duk da yana kokwanto akan kalaman malamin amma kuma yana tsoron Zancen shi ya zama gaskiya," girgiza kai yayi alamar aah, gyara zama ya yi to gaskia abinda ya kamata kayi kenan dan musan Mike faru da ita ta hakane xamu samo bakin zaren" "Shikenan malam in sha Allah zan tambayeta," Maisalati yace"Yawwa ko kaifa, Sannan kuma shawarar da nake so na baka, Ka tabbatar kana Yi mata addu'o'i akai akai, idan bata iya ba ka koya mata, hada azhkar na safe dana marece, ka kuma koya mata addu'ar shiga toilet, idan zata kwanta da dare ka yi mata addu'oi'in neman tsari, kuma a koda yaushe ta kasance kanta akwai ɗankwali, ka lullu6e mata gashin kanta, Hatta kaya idan zaka sanya mata ka yi mata addu'o'a, Daso samu ne ma duk in zaka kwanta bacci ka kunna maku karatun al'qur'ani mai girma ku kwana da shi," sosai malam maisalati ya ba shi shawarwari a ƙarshe yace"Idan Allah yasa ƙarshen wahalar ta kenan sai kaga Allah ya yaye mata, Amma dai ina ƙara gargaɗinka kada kayi sakaci wurin Yi mata addu'a akoda yaushe, na manta ma ban tambayeka ba, Tana zuwa islamiyya"? Dakyar ya iya buɗe baki yace"Eh amma ta jima ba ta je ba, Girgiza kai maisalati yayi"Banso haka ba tajo, kanaso ka yi mana buƙulin samun Hafizar al'qur'ani, wadda zata yiwa addini hidima nan gaba, kamar yadda nake fata, Allah ya baka yarinya mai wayo tubarkalla, ga hali kamar na manyan mutane, bai kamata kayi wasa da wannan damar ba, Gaskiya ina mai baka shawara ka hanzarta mayar da ita makaranta, idan da hali harma tahfeez ka sanyata," Ajiyar zuciya taj ya dan sauke"in sha Allah zanyi hakan, Nagode sosai malam, Bansan da wasu kalmomi zanyi amfani ba wurin gode maka, Allah ne kaɗai zai iya biyanka, Allah dai yasa ka maku da alkhairi," sosai taj ya yi ma shi godiya, Koda ya miƙe zai tafi saibda taj ya ƙara tambayar shi ya kawo mashi ruwan sha, Yace a'a, Shi dai burin shi ya yi ƙokari wurin ceto rayuwar ƴar shi, Shi ma kuma zai taimaka mata da addu'o'i shida ɗalibansa,daga haka su ka yi sallama dashi Yabar gidan, Tofa, Bayan tafiyar malam maisalati, kasa zama taj ya yi saboda ruɗanin da zuciyar shi ta shiga, Zarya ya shiga yi a falon, Zuciyarnshi a cunku she take, wani irin faduwar gaba yake ji, tabbas yanyi kuskure sosai akan angle wurin rashin maida hankali ya yi bincike sosai lokacin da take cikin wannan halin" A hanzarce Ya juya ya nufi bedroom ɗinnshi, tunkafin Ya ƙarasa shiga Ya hango angel zaune saman gadon Ta jingina bayanta jikin headboard(kan gadon) Ƙura mata ido ya yi yana kallonta, ganin ta lumshe i danuwanta, tamkar mai tunanin wani abu, Shiga cikin ɗakin yayi tare da samun wuri daga gefen gadon ya zauna yana fuskantar ta, "My daugher" da buɗar bakin ta sai cewa tayi"Daddy, Malam mai dogon gemu yazo ya cika ka da surutu kamar radiyo mai jini ko" idanuwan ta a rufe ta yi maganar, Da mamaki akan fuskarshi yace"Taya akai kikasan yazo ke da kinke acikin ɗaki"? Bude idanuwanta ta yi a hankali, "Tun dazu nafarka daddy, har leƙa ku nayi," "Kinji me muka tattauna dashi" girgiza kai tayi"ae ka hanani yi maka la6e, shiyasa ban tsaya ba, nadawo na zauna" Ajiyar zuciya ya ɗan sauke, Kafin ya kuma cewa wani abu ta riga shi cewa"aunty aneelerh ce ta kawoni gida"? ɗaga mata kai ya yi alamar eh, "ta kawomin uniform ɗina da kuma bag dina"?ta kuma jefa mashi tambaya, "A'a,zanje na kar6o maki su anjima" Jinjina mashi kai kawai tayi, Shiru sukayi na dan wani lokaci,kafin ya ruƙo hannunta cikin na shi, "My daughter"! Ware ma shi manyan idanuwanta tayi"na'am daddy" Murmushi ya ɗanbsaki, ya rasa ta ina zai taro zancen, kamar maijin tsoron ta, Can dai ya daure Ya soma yi mata magana antsanake"Nasan kina sona sosai,bkuma kina kyautatamun, koba haka ba? Da sauri tace"Hakane daddy" Jinjina kai yayi"um..Yanzu kina sona,nba kamar lokacin baya ba da kika ɗauramun karan tsana tamkar ni ba daddyn ki ba ne, Pls inaso na tambaye ki, a wannan lokacin ke ki ke ƙuntata mun da kan ki ko kuwa akwai wani ɗan mutun mutumi dake sanya ki kina yi mun"? Cikin rashin fahimta tace"daddy i don't understand me ka ke nufi"? "Ina nufin, A time ɗin da kike 6ata mun rai, Wake sanya ki kina yi mun,i know there must be a reason, babu yadda za'ae ki tsani mahaifinki lokaci ɗaya," Wurga eye balls ɗinta sama ta yi tana kallon ceilling, ganin ta ɗauki tsawon lokaci tana kallon ceilling ɗin yasa shima ya ɗaga kai yana kallon shi, wai ko zaiga abunda take gani, Ganin bata da niyar daina kallon ceilling ɗin yasa shi dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"Pls explain to me kin ji babyna" Mayar da idanuwanta kan shi ta yi taɗan turo baki irin na shagwa6a66u, "Nidai bansani ba, Amma bani nake yi ba, kamar ana ce mun inyi kaza ni kuma sai inyi" takai ƙarshen maganar tana ƙyafƙyafta mashi ido, "Magana a ke yi maki acikin kan ki ko kuwa"? ya kuma tambayarta, "Daddy nifa bana ganewa" "Angel kina mafarki"? ya kuma tambayarta, bubbuga hannuwanta ta yi saman Mattress ɗin"Wlh daddy ni ka yi disturbing ɗina, kana rikita ni" Lallashinta ya shiga yi"Am sorry, wannan ce tambaya ta karshe, idan ki ka bani amsa, Zan ba ki wayata, kiyi game," yasanta mayyar wayace, aikuwa da sauri ta soma kora ma shi jawabi "Daddy, ko yanzu dana kwanta,na yi mafarki kuma kullum ina yin mafarki," "Faɗamun meke faruwa acikin mafarkin"?a ƙagare ya yi maganar, Angel tace"Ina ganina a cikin wani ƙurmin daji mai duhun gaske mai ban tsoro, kuma idan nayi mafarkin ina ganina Acikin wasu mutane masu sanye da baƙaken kaya, Bana iya ganin fuskar su, hannunsu zako zako da akaifa, Ni kuma Ina sanye Cikin jajayen kaya, riga da wando,kuma bani kadai bace hada wasu ƴan yara, Kuma suma red uniform ne a jikinsu,Daddy akwai tsorofa mafarkin Kuma babu alkairi a cikinsa" Tunda ta soma magana zuciyar taj tashiga harbawa da ƙarfi da karfi, tamkar zata faso daga kirjinshi, "Amma kinsan kina irin wannan bad dream ɗin shi ne baki ta6a sanar mun ba"? "Banaso na tayar maka da hankaline, Aunty aneelerh tace in dinga faranta maka rai, kada na 6ata maka rai, Zaka Iya mutuwa ni kuma banso na rasa ka, sometimes ma in nayi yinqurin fada maka sai wani abu ya daukemin hankali na manta" fashewa tayi da matsanancin kuka, Da sauri Ya janyota jikinshi sosai ya rungumeta, baisan lokacin da hawaye suka soma sauka akan fuskar shi ba, yana jin kukanta har cikin zuciyarsa "In sha Allah zanyi iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin na ceci rayuwarki, Bi'iznillahi duk wani mai nufinki da sharri zai koma masa ne, Tabbas akwai wani maison shiga tsakanina dake, akwai wanda yake Yi mun maƙarƙashiya, Bansan wanene ba!!Amma Allah ya sani, Kuma zai bayyanar mun dashi ne, duk mun daren daɗewa"! Yayi maganar ne don yasan Yana da maƙiya a wurin aikin shi, masu yi mashi hassada saboda ɗaukakar daya samu, kuma har akan idon shi suna nuna mashi ƙiyayya, shiyasa ya yi zargin kodai wanine keson ya 6ullo mashi ta bayan fage, shine a kayi amfani da ita wurin cutar dashi, Sun jima a wannan yanayin manne da juna shi da ita, sai da aka fara kire kirayen sallar la'asar, tukunna Ya ɗago da ita daga Jikin shi, Ganin ta fara bacci Ya dan jijjigata, firgit ta farka"time din sallah yayi daga yanzu bana so kina wasa da sallah, kinji ko'? Ɗaga mashi kai tayi alamar eh,ya kuma cewa"Addu'ar shiga toilet kin iya"?ɗaga mashi kai tayi"Eh"yace to karantamun, nan ta shiga karanto mashi, ya kuma tambayarta addu'ar kafin a kwanta bacci da kuma in an ta shi daga bacci duk ta karanto mashi Yace"masha Allah, haka nake son ji My daughter, Sannan kuma zan koya maki azhkar da zaki dinga yi na safe dana marece, pls ki bani haɗin kai, ki dage kin ji indai bakyaso a rabani dake"da sauri tace" zanyi daddy,"yace that's good, yanzu tashi ki shiga toilet kiyi alwala ina jiranki" Amsa mashi tayi"toh" da sauri ta sauko daga saman gadon ta nufi toilet ɗin, harta kusa shiga ya dakatar da ita"wait" ta tsaya tare da waiwayowa tana kallon shi, saukowa daga saman gadon ya yi ya nufi can cikin ɗakin wurin closet ɗinsu, buɗewa yayi tare da kai hannu ya ɗauko hijabi da mayafi, asaman gadon ya ajiye mata hijabin shi kuma mayafin ya taka zuwa inda take ya ɗaura mata shi a kanta, sosai ya lullu6e mata gashinta"yawwa daga yanzu haka nake so gashin kanki ya kasance a lullu6e, sannan kuma idan kin kammala sallah, ki dinga karanta surorin da nake koya maki" amsa mashi tayi"toh"kafin ta bude toilet ɗin ta shige ciki," Tsayawa ya yi har saida ta fito tukunna ya sanya mata hijabin,kafin ya wuce cikin toilet, lokacin daya fito salla ya same ta tana yi, baisan lokacin daya saki murmushi ba,yaji daɗi har acikin ran shi, Da sauri ya fuce zuwa masallaci, a bakin gate suka ci karo da Uzair yana ƙoƙorin shigowa ciki, dama biyo ma shi yayi don su tafi masallaci atare, Bayan tafiyarshi, Angel ta kammala sallah ta zauna tana karanta surorin daya koya mata irin su falaki da nasi, su ta yi ta biyawa, duk don saboda yace tadinga yi indai bataso a rabasu, Tana cikin yin ƙira'ar, Wayar shi daya manta saman gadon su ta soma ringing, Zumbur ta miƙe takai hannu ta ɗauke ta, Sunan Uncle ne Ya bayyana, Kafin ta ɗaga kiran ya katse, ganin wayar babu finger print din daya ke sanya mata, dama tun lokacin da suka shirya da ita ya cire security din wayar shi, Zama saman gadon ta yi ta dinga buga game na spider man, Sai da ta yi mai i sarta tukunna ta shiga contact dinshi, Numbobi ta haɗa daga cikin kanta ta buga kira, wani bayerabe ya ɗaga yanata gwaranci ta dinga tikar dariya, Har ya katse kiran, ta kuma haɗa wasu numbobin ba'a ɗaga ba, kusan number waya biyar ta kira ma shi wasu ba'a ɗaga ba, Sai na ƙarshene a ka ɗaga kiran, Shiru tayi taƙi magana,tana jiran jin wanene zaiyi mata magana, shiru taji ba'ace mata uffan ba, kusan mintuna kafin wata sanyayyiyar murya so sexy ta karaɗe kunnuwanta"who is on the line"? Ƙunshe dariya tayi yayin da take karkaɗe kafarta tace"Angel ce," Mutumin dake akan layin ya kuma tambayarta"kinsan dawa kike magana"? Girgiza kai ta yi tamkar tana agaban mutumin da take waya dashi tace"a'a," "Ur age"? ya tambayi shekarunta,da alama ya gane yarinya ce ƙarama, "7yrs" voice ɗin shi da alamun mamaki ya maimaita"7yrs? ina mai wayar yake'? "Daddyna ne, ya tafi masallaci ni kaɗai ce agidan, shine na hada numbobi na kira don in gaisa da mutanan duniya" "Can i call u video"? Da sauri tace eh, Nan take ya mayar da kiran Video call, ɗago da wayar angel tayi tana kallon screen din wayar bayan ta yi picking, Bata ga komai ba a screen ɗin sai duhu sosai, Amma shi wanda take wayar dashi da alama yana kallonta, "I can't see u" ta yi maganar tana faman gwale ido, Shiru ta ji baya magana, saukowa ta yi daga saman gadon, a tunaninta rashin network ne, yasa bata ganin shi a video din, Tana Cikin zagaye palour Tajiyo Sallamar daddyn ta, A gigice ta katse kiran,ta shiga goge numbers ɗin data kira, tana gamawa ta cillar da wayar saman gadon,ta haye itama ta kwanta tamkar maiyin bacci, Atare da uzair suka shigo falon, saman sofa suka zauna suna fuskantar juna, "Ban fada maka bane kawai, Amma nida aneelerh mun jima muna hasashen tana da aljanu, zai fa iyayiyuwa acikin toilet ta same su tunda a nan Benazir ta haifeta, kuma kaga shi toilet madaddalar su ce,"acewar uzair, Jinjina kai Taj ya yi"Yanzu menene mafita"? Uzair yace"Mu tayata da addu'a, Sannan Muyi ƙoƙarin ganin mun bi duk wasu sharuɗɗa na bata kariya da malam mai salati ya faɗa maka, in Allah ya yarda za'a dace ne," Taj yace"Allah Ya yarda, duk na damu wlh," Uzair yace"ka kwantar da hankalin ka, da yardar Allah zamu San abun yi, Sun ɗauki tsawon lokaci suna tattaunawa tare da uzair kafin ya yi mashi sallama ya tafi gida, Tundaga wannan Lokacin, bai ƙara yin sakaci wurin kula da ita ba har tahfeez ya sanya ta, ya ci wahala kafin ya samu tafara zama Makarantar islamiyyar, da yake a kusa dasu makarantar take, idan ya kai ta yana barin makarantar take kamo hanya ta dawo gida, Kowa ya yi mamakin yadda a kai ta ke guduwa daga makaranta, dakyar ya samu tafara zama, tun tana yi ma shi kukan ba ta so harta haƙura ta zauna, bai ta6a bari ta zauna tana shiririta ba, Kullum sai ya tasa ta gaba tana maimaita karatun haddar da aka bata, babu abunda bai siya mata ba, Wanda ya danganci karatun addini, Cikin ikon Allah sai ga shi tafara sanya naci tana yin karatun tunkafin ma yace mata ta yi take yi, wani lokacin ko bacci take yi ta dinga sambatu kenan tana Bitar karatun da a ka koya mata, Hakan ba ƙaramin daɗi ya ke yi mashi ba, Uzair da aneelerh ba ƙaramar rawa suka taka ba, wurin taimaka ma taj akan angel, dama sun ɗauketa tamkar ƴar su, Allah ya bata kaifin basira,wani irin ƙoƙari gare ne ita duka boko da islamiyya ko'ina yabon ta su ke yi, Kowa sonta yake yi, duk wani Competition da za'ayi Tsakanin makarantu, ita ke ciyo ma school ɗinsu, shiyasa su kansu malaman Ji su ke da ita, duk in tayi fashi bata zo school ba, Sai sun kira taj a waya sunji dalili, sometimes har gidan suke zuwa ganinta, A kwana a tashi ba wuya wurin Allah Angel ta shiga Cikin shekarata Goma, a wannan Lokacin suka Shirya Mata Party na taya murnar zagayowar ranar haihuwar ta, tun ana saura kwana biyu, Aneelerh ta kai ta wurin Saloon, gyaran gashi akayi mata mai kyan gaske, tare da ƙunshi na jan lalle, da ya rage saura kwana ɗaya birthday ɗin nata, gaba ɗaya suka shirya don zuwa yi mata siyayya A shopping Mall, Kaya sosai suka siya mata a kasuwar, sai da suka gama kashe mata kuɗi, Tasa masu rigima akan Tana son a siya mata Piano da kuma drawing materials, A lokacin sunyi ƙarƙaf, sun gama kashe ƴan canjin da suka rage masu, Lallashinta su ka soma yi akan tayi haƙuri next time idan suka ta shi dawowa zasu siya mata, Ƙin yadda ta yi a ƙarshe ma ta rushe masu da kuka tana fadin ita dai su siya mata su take so, ko kuma amaida sauran kayan da aka siya mata don kuɗin su isa a siya mata Piano, sosai Angel ta sanya masu rigima, tun mutane basu lura ba, har hankalin kowa ya dawo kansu, Ganin Yadda yarinyar take ta ruskar kuka, Aneelerh taso ta siya mata, Taj ne ya hanata saboda yasan ba isassun kuɗi gareta ba. A haka suka koma gida, Sosai ya yi mata faɗa akan ta daina yi ma shi rigima Cikin mutane, tunda yace mata ba shi da kuɗi meyasa zata takura shi, so take ta kunya ta shi a idon jama'a, daga ƙarshe yace mata ta yi hakuri idan ya samu kuɗi zai siya mata komai take so, shi kan shi baiji dadin yadda ya gaza siya mata Abubuwan da takeso ba, Don ta ƙwallafa rai a kan su sosai, A washe garin ranar ya kasance Juma'a, ranar birthday ɗin ta, Gagarumin party suka haɗa mata, tun bayan sallar asuba aka soma shagali don a wannan lokacin ne Angel tazo duniya, Ƴan uwa da a bokan arziƙi duk sun hallara don tayata murnar birthday ɗinta, Kaya kala Uku ta sanya aranar, aneelerh ce ta shiryata ta yi mata kwalliya, Musamman aka ɗauko photographers, Su ka yi masu hotuna, taro yayi albarka Anyi kulu washrabu hani'an, Kowa ya shaida ya nishanɗantu Angel ta samu Kyaututtuka masu yawan gaske daga wurin a bokanan aikin shi, Wasu gifts ɗinma baisan su wanene suka aiko mata dasu ba, baba mai gadi ake aikowa daga waje,ya kawo mata su cikin gidan, bakomai ya fi Ba shi mamaki ba, face wata kyuatar bazata da a kayi ma angel, Abun ya ɗaure mashi kai, Abunda angel ta kwallafa rai akan shi ne Aka samu wani ya siya mata su, piano da kuma kayan zane da ta sa masu rigima a shopping mall, Ya yi mamaki sosai har baba mai gadi ya tambaya waye ya aiko mata da gift ɗin don shi ya miƙo su Cikin gidan, Baba maigadi yace ma shi bazai Iya shaida fuskar wanda ya kawo ba, Matashin saurayi ne dai kuma ya sanya facemask a fuskar shi, Sannan kuma Acikin mota ya zo, har tambayar baba maigadi ya yi kobya lura da kofato a ƙafar mutumin daya kawo su? Baba gadi ya yi dariya Tare da cewa Bazai iya tantance ƙafafune ko kofato ba,tunda ya sanya takalma, jikin taj dai yayi sanyi sosai, ko angel bai bari taga kayan ba, Ya 6oye su a ɗaya daga Cikin ɗakunnan gidan, Kafin a kammala shagalin sun ke6e da Uxair ya sanar da shi game da kayan da aka siya ma angel, shima ya yi mamakin jin hakan, Amma sai yace mashi Ya kwantar da hankalin shi, Shi yafi tunanin Cikin mutanan dake kallonsu A mall ɗinne lokacin da angel tasa rigima akan su siya mata kayan, Shine aka samu wani na Allah ya siya mata su, don haka ya cire damuwa aranshi Ya bata kayanta, kada ya hanata yin amfani da su, Iya ka ci dai kafin tafara amfani da su, Ya tofe su da addu'a, kuma kada Ya dinga barinta tana yawan yin kiɗa, ko ƴan zane zane sai ya dinga lura, Sosai Uzair ya ba shi shawara, Har saida yaga hankalin shi Ya kwanta, Bayan kwana ɗaya da yin Birthday ɗin nata, Sai ga ɗan saƙo an aiko daga wurin Alhaji ubaid, Gift ne Ya aikoma jikarshi, danƙareriyar waya ƙirar i phone tare da Laptop, Bayan ya kar6esu daga hannun ɗan saƙon,Yakaisu ɗakinshi ba zato ba tsammani Sai ga alert na 1.5m ya shigo wayarshi, again daga alhaji ubaid, Ba ƙaramin farin Ciki ya yi ba, Yana ƙara Jin ƙaunar mutumin kodan saboda kyautatawar da yake yi ma ƴar shi, shi kaɗai ya damu da ita duk cikin family ɗin benazir babu wanda ya ta6a tuntu6ar shi koda a waya ne ya tambayi ya angel ta kwana, duk da yasan halin su ko lokacin auran shi da benazir dayawansu basu so ya aure ta ba, saboda arziƙin shi bai kai ya mallake ta ba, shiyasa sam babu ruwansu da abun da ya shafi tajudden, Alhaji ubaid ɗin kaɗai ne ya damu da su, kusan kullum sai ya kira don yaji ya lafiyar jikar shi, har uzair ya tuntu6a Don su yi shawara da shi game da Kuɗin da alhaji ubaid Ya turo mashi,Yace mashi Yayi amfani da su,Wurin Gyara mata bedroom ɗinta, Inda zata koma da kwana, ya sanya mata kayan wasanni da zasu dinga ɗebe mata kewa, Sauran kuɗin Kuma Akwai hidindimu masu Zuwa, ya ajiye mata su, Duk yadda taj yaso ya ɗauki wani a bu daga Cikin kuɗin yaƙi kar6a, Sai da ƙyar ya samu ya kar6i dubu ɗari, a tare da aneelerh suka tsara mata komai na bedroom dinta, Wani haɗaɗɗen gado suka sanya mata, Headboard ɗinshi Sak Jikin butterfly ne, Komai na bedroom ɗinta Pink Colour ne, Ba abunda ba'a sanya mata ba, Yaci wahala kafin ya samu angel ta koma kwana dakinta,Saboda sabon da su ka yi da juna, sai ya bari bacci ya ɗauketa tukunna yake kaita ɗakin ta, idan tafarka ko ƙarfe nawa ne na dare saita sauko daga Upstairs ta dawo ɗakinshi da yake ya dawo downstairs bayan sun raba daki, Sai dai kawai yaji ta Kwance ajikin shi, sai da yabi komai asannu tukunna ya samu Tafara sabawa da kwana a ɗakinta, yanzu da kanta take yin wanka ta sanya kaya har ma tayi kwalliya, har lokacin angel batasan an bata gift din piano da Kayan zane ba, Saboda ya 6oyesu Laptop kaɗai ya bata, wayar kuma da aka bata shi yaci gaba da amfani da ita, don bazai bari ta ruƙe waya ba, Saboda wayon dake gareta, kuma zata iya ɗauke mata hankalinta daga yin karatu, Acikin waɗannan kwanakin taj yaso yaje buzaye wurin Dangin shi, Amma Uzair ya dakatar da shi, Akan ya bari Su uncle su dawo Nigeria, in ya so sai su ɗunguma su tafi a tare, ba don yaso ba Ya amince ma shi, Tuni angel ta kammala primary school ɗinta a yanzu haka tana a Jss 3 Sunyi Exam na first term, tunda suka samu hutu ba inda take zuwa Kullum tana gida bata zuwa ko'ina, taj Ya damƙa mata Piano ɗinta, Idan ta zauna ta soma yi masu kiɗa ko gajiya ba ta yi, Sai in Lokacin Karatunta ya yi ko sallah take tashi, sam ya hanata Yin kallo In ba cartoon ba, Shima cartoon ɗin Sai ya tabbatar Baida wani abu da zai 6ata mashi yarinya tukunna yake barinta ta kalla, Ya sanya mata ido sosai, duk wani motsinta a tafin hannun shi, idan zai tafi wurin aiki, Gidan su Aneelerh yake turata, koda basa nan mai aikin gidansu Ana tana nan, A wurinta take zama kafin su dawo Wannan kenan, a gajiye ya ke driving a daidai bakin gate, ya soma dannawa mai gadi hon, Da hanzari baba mai gadi Ya fito daga ɗakinsa, ya buɗe ma shi gate ya shigo da motar Jikin gidan, Fitowa daga Cikin motar ya yi, Jikin shi na sanye da Shadda green Colour ba ƙaramin kyau tayi ma shi ba, Sai daya fara tsayawa suka gaisa da baba maigadi tukunna Ya nufi Cikin gidan, Tunda yayi sallama a palour Yaji shiru ba'a amsa mashi ba, ran shi ya ba shi cewar Ko bata dawo gida bane, yanke shawarar zuwa bedroom ɗinta Yayi, walking slowly Ya nufi stairs ɗin ya haye, a tsanake ya ke tattaka steps ɗin benan harya samu Ya haye sama, Kaitsaye Ya nufi inda ɗakinta yake, Da sallama a bakin shi ya tura ƙopar ɗakin, Yana shiga idanuwanshi suka sauka akan gadon, wayam baiganta ba, Hakan na nufin bata dawo ba, tana agidansu aneelerh, Ajiyar zuciya ya ɗan sauke tare da juyawa zai bar ɗakin, Karaf idanuwan shi suka sauka akan Zanen fuskar shi da angel ta yi a jikin bangon ɗakinta, Cike da mamaki Yaci burki tare da nufar Bangon yana kallon Zanunnukan da ta yi, da kuma rubuce rubucen da ta yi duk a jikin bangon, Motsa lips ɗinsa ya soma yi yana karanta abunda ta rubuta a jikin bangon _To my biggest hero_ _There's no better role model than you,_ _There's no one I'd rather look up to than you._ _I'm so proud to be your daughter_ _You're my one and only dad, and you'll always have a special place in my heart._ _Dad, you've made all my favorite memories._ _Dad, you've always been my hero._ _I'm so lucky to have your love and guidance in my life_ ya ma rasa mi zai ce lokacin daya kammala karanta Rubuce rubucen da ta yi ma shi, Wani irin tsantsar farin Cikine Ya bayyana akan Fuskar shi, Tuni hawaye su ka wanke ma shi fuskar shi, slowly ya zube saman gwiwowinsa, a yayin da hawayen ke cigaba da bin kuncin shi, kalamanta ba ƙaramin faranta ma shi rai su ka yi ba, maimakon Ya ji haushin 6ata bangon ɗakin da tayi sai ma yaji ya ƙara sonta a cikin zuciyar shi, Haƙiƙa angel ta ba shi mamaki, ta san ya shi farin Cikin da bazai ta6a mantawa ba, Da sauri Ya juya ya kalli ƙopar ɗakin Jin motsin mutun, Bakowa bace face angel Jikinta na sanye da jallabiya, daidai tsayinta, Tayi rolling mayafi akanta, "Daddy sannu da dawowa Nayi missing ɗinka sosai" ta ambaci hakan fuskarta ɗauke da murmu shi, buɗe mata hannayen shi ya yi alamar tazo gare shi, da gudu ta ƙarasa ta faɗa saman faffaɗan kirjin shi, Ya sanya dukkan hannayenshi Ya rungumeta sosai, Yana faɗin"kin sani farin Cikin da bazan ta6a mantawa ba angel, I luv u so much, bansan da wasu kalmomi zanyi amfani wurin bayyana maki irin ƙaunar da nake yi maki, Allah yabarnmin ke angel, Allah ya kare mun ke daga sharrin maƙiya da mahassada, Allah ya yi maki albarka" Amsa ma shi tadinga yi da ameen daddy, kusan mintuna goma suna manne da juna, batare daya raba jikin shi daga nata ba, wani irin yanayi yake ji attare da shi, sam baya son yana tuna mutuwa, Saboda yasan ita kaɗaice zata Iya raba shi da angel, ko yana so ko bai so, dolene bayan ita kuma sai wata ƙaddarar rayuwar wadda baya fata, Ɗagowa tayi daga Jikin shi ta sanya hannu tana goge mashi tears ɗin dake sauka akan fuskar shi"daddy kadaina pls, banason ganin hawayen ka na zuba" Kallonta ya yi da runannun idanuwan shi waɗanda su ka yi jawur da su, sam ya kasa furta mata komai, Huggin ɗinshi ta ƙarayi tana shafa sumar kanshi, bacci ya soma Ji hakan yasa shi miƙewa Ya lalla6a ya haye saman gadonta, ya kwanta duk da ya yi mashi ƙanƙanta, Gefen gadon ta zauna tana kallon shi, jikinta duk ya yi sanyi tace"daddy baka lafiya"? Eyes ɗinshi arufe yace"kinci abinci"? "Naci a wurin aunty aneelerh, Ko inje in kar6o maka naka" girgiza mata kai yayi"a'a,Bana jin yunwa, kizo mu kwanta muyi bacci" Ƙarasa hawa saman gadon ta yi a gefen shi ta kwanta, Ya sanya hannu ya janyo ta jikin shi, Cikin ƙankanin lokaci bacci yayi awon gaba da su, Wuraren ƙarfe 4 ya farka daga Baccin, Lokacin a nata kiraye kirayen sallar la'asar, saukowa daga saman gadon yai tare da nufar toilet ɗin ɗakin ta Ya shiga ciki, After some minutes ya fito yana share ruwan alwalar dake a fuskarshi, Kafin ya nufi inda angel take a kwance tana bacci, Cikin sanyin murya ya soma kiran sunanta"My angel!"shiru bata motsa ba, hannu yasa tare da ɗan bubbuga ƙafarta, nan take ta farka tana mutsu mutsun bude idanuwanta, "Lokacin Sallah yayi, Ki ta shi kije ki yi alwala, ni zan tafi masallaci" Muryarta a disashe tace mashi"a dawo lpy daddy," Bayan tafiyar shi, ta sauko daga saman gadon ta shiga toilet, Jim kaɗan tafito ɗaure da alwala, ta ɗauko carpet ta shimfiɗa, Ta zura hijab ajikinta a tsanake ta soma Yin sallah, Lokacin data idar da sallar zama tayi saman dardumar tana karatun alqur'ani mai girma daga cikin kanta, Tana cikin yin qira'ar, Ya dawo daga masallaci, murmushi yasaki Yayin da ya ke shigowa Cikin ɗakin, Ba ƙaramin daɗi yake ji ba aduk lokacin daya sameta, Saman darduma tana Yin sallah ko tana yin karatun al'qur'ani mai girma, Sai da takai ƙarshen ayar da ta janyo tukunna ta juyo ta kalleshi"daddy sannu da dawowo" "Yawwa daughter, Kin daiyi mana addu'a ko"? jinjina mashi kai tayi"eh,Ae kullum sai nayi" "Haka nakeson ji, My daughter" Shiru ya ɗanyi kafin Yace"Zamu fita tare da daddy uzair ɗinki, Zaki zauna a gida ko In kai ki wurin aneelerh"? "Daddy bazaka tafi dani ba" aɗan shagwa6e tayi maganar, "Am sorry, Ba cikin gari bane bazan iya yin tafiya mai nisa dake ba," Tuni idonta sun Ciko tab da kwalla sam bataso yana tafiya yana barinta a gida, musamman yanzu da babu school, islamiyace kaɗai yau kuma Alhamis ne basa zuwa da juma'a, "Dan Allah daddy......."tunkafin ta ƙarasa yayi saurin katse mata hanzarinta"yi mun shiru nace maki ba cikin gari bane," Shiru tayi Ƴar kwallar da take 6oyewa ta soma gangarowa akan fuskarta, Ƙarasawa Yayi tare da sanya hannayen shi gaba ɗaya ya ɗauketa, yana ɗan bubbuga bayanta"Idan kikayi mun kuka Allah zan fasa zuwa buzaye dake ne" Cikin shessheƙar tace"bazanyi ba" "Haka nakeson ji my angel" Sauke ta ƙasa ya yi tare da ruƙo hanunta, suka fito daga ɗakin ya ja ƙofar ta rufe, Kaitsaye suka nufi gidansu aneelerh, lokacin da suka shiga falon gidan a tsaye suka gansu shida Aneelerh, Ya kammala shirin shi cikin boyel, aneelerh kuma na sanye cikin Turkish dress, Riga da wando blue, ta ɗaure kanta da mayafin kayan. Gaisawa suka fara yi da aneelerh kafin Ya damƙa mata angel, Batare da 6ata lokaci ba, su ka yi mata sallama atare a cikin motar Uzair suka tafi, Saman Sofa suka zauna ita da aneeleerh, "Kina jin yunwa"? ɗaga mata kai tayi alamar eh, "Hawayen menene akan fuskarki"?tayi tambayar tana kallon fuskarta, "Daddy inata roƙon shi ya tafi dani amma ya ƙiya" Murmushi aneelerh tayi"Shine kike kuka? idan ki ka yi haƙuri ae ba kwana zasuyi ba," ta ambaci hakan tare da miƙewa ta nufi kitchen, Kishingiɗawa angel tayi tana jiran dawowarta, fitowa aneelerh tayi daga Cikin kitchen ɗin hannunta ɗauke da plate, mai ɗauke da farfesun naman Kaza, da alama ba'ajima da kammalashi ba, don sai huci ke tashi ga ƙamshi, A saman table ta ɗaura plate ɗin,tare da samun wuri gefen angel ta zauna, Jin ƙamshi Yasa angel mikewa ta gyara zamanta, "Aunty aneelerh,duk ke kikayi wannan"? "A'a bani nayi ba, Ana ce ta yi shi" Yatsina fuska angel tayi"wannan matar kamar munafuka,Ni ban yadda da ita ba Allah, Kullum tana aɗaki kunshe, Ita bata fitowa sai zata yi girki ko gyaran gida, Dariya sosai Aneelerh tayi"Zaki fara tsegumin naki ko"? Ta6e baki ta ɗanyi, tare da zura hannu cikin plate din tana ɗan tsakurar naman, Har wani jinjina kai take yi saboda daɗin da ya kai mata karo, zuba mata ido aneelerh tayi tana kallonta, "Aunty aneelerh," "Menene"? "Mutane dayawa suna cewa Ni matar Manyace, irin matan masu kuɗinnan, Allah idan na girma mai kuɗi zan aura, inda zanje in huta, Bani aikin komai sai dai Ƴan aiki suyi mun ina daga kwance," Tunda ta soma zuba, Aneelerh ta ƙura mata ido tana kallonta,Wato Zuzuta kyanta da mutane suke yi suna cewa ita matar manya ce, Shine ta haddace maganarsu acikin kanta, har tafara sawa ranta aure inda zata huta, "Bakya son talaka"baneelerh ce ta jefa mata tambayar, Yatsina fuskata tayi"ae annabima yace mu nemi tsari da talauci," Murmushi Aneelerh tasaki, tasan halin angel da gaddama, shiyasa bata ja zancen da tsayi ba, "kinga daddy yaƙi yin aure, Da a lama sai na fara haifa mashi ƴan jikoki" takai karshen maganar tana sakin ƴar dariya, Murmushi aneelerh tasa ki a ranta tana mamakin yadda take maganar aure har da haihuwa ko kunya babu halin angle sai ita kafin tace"mai zai hana kisa ma shi matar aure" ɗan zaro ido tayi bakinta cunkushe da naman data tura, ahaka tace"Tab, salon tazo ta mallake mun daddyna, Ƙwara yayi ta zaman shi a haka babu auran,"dariya sosai aneelerh tayi"Angel kenan mai abun ban mamaki" ta ambaci hakan tare da mikewa tace"zan shiga daga ciki inaso na kwanta, Idan kin kammala ci, Ki kai plate ɗin a kitchen, kizo ki same ni a ɗaki muyi karatun haddar da aka baki islamiyya" Ta amsa mata da toh"sai da angel ta kammala shan farfesun tukunna ta miƙe ta nufi kitchen, Bayan ta ajiye plate din,ta fito ta nufi ɗakin aneelerh *** *** *** *** *** ** A 6angaransu taj kuwa, gidan wani abokinsu suka fara zuwa kai mashi ziyara, sun jima a gidan bayan sun baro gidan abokin nasu, Suka Nufi gidan Gonar uncle abdallah, da niyar suje su duba yadda komai ke tafiya, Kafin su dawo gida, Gidan Gonar acan bayan gari yake cikin daji, lokacin da motar su ta ƙarasa Cikin dajin, Adai dai bakin Gidan gonar uzair ya yi parking ɗin motar, Wani tsohone daga waje saman benci yana sauraron radio da a lama shine ke kula da gidan Gonar, Tunkafin Suyi parking ɗin motar, Ya miƙe yana ta faman washe baki don ya gane motar uzair ce, At same time suka fito daga Cikin motar, A hanzar ce suka ƙarasa inda yake a tsaye, Jikin shi na sanye da riga da wando na yadi, Zariyar wandon har kasa kamar wani ta6a66e, Gashin kanshi duk hurhurace, Fari ne sol kanshi da rawani irin na buzaye, "A'a wa nake gani kamar Tajo?' cike da mamaki ya yi maganar yana kallon tajuddeen, miƙa mashi hannu taj yayi fuskar shi ɗauke da fara'a yace"Nine mana, baba buzu ashe kana a raye" ya yi maganar da zolaya, "Amana batace haka ba tajo,Yaushe rabon da in sanyaka a idanuwana tun kana ɗan matashi," "Yau dai gani nazo, kuma bada wuri zamu tafi ba, har sai ka gaji da gani na," yakai ƙarshen maganar yana dariya, shima dariyar ya yi"wuni kuka zo mun kenan aikuwa har masara zan gasa mana muci muna fira, Kafin taj ya yi magana uzair yace "Fatan mun same ku cikin koshin lafiya, Ya komai ke tafiya" Tsohon yace"alhamdulillah, Ku ƙaraso mu zagaya cikin gonakin mana," Gaba ya yi su ka bi bayan shi, suna ɗan tattauna fira atsakaninsu" Sunjima suna kewaye gonakin har cikin gidan gonar suka shiga, koda aka fara kiran sallar Magrib, atare da baba buzu su ka yi sallar Acikin gidan gonar, ba su tashi tafiya ba, sai bayan da akayi sallar Isha'e, tukunna su ka yi sallama da shi, Taj ne ya kar6i driving ɗin, Uzair na gefen shi, motar su na haurawa saman titi, wasu dankara dankaran motoci masu black tinted suka shararo da gudun gaske kusan su shida, A jere suka Kurɗaɗa cikin dajin, Duk akan idonsu tajuddeen, Da mamaki akan fuskar Uzair yace"kosu wanene a cikin motocin can? Kuma ina zasu dosa ne? Ni dai a iya sanina babu wani gida dake acikin dajin nan," Taj yace"May be ko wani party ne za su yi, ba abun mamaki bane" "That's impossible, Party kuma arasa inda za'ayi shi duk faɗin garin mu sai cikin dajin nan, Gaskiya ni ban yadda ba Allah, tabbas inaso nasan me zasu yi a cikin dajin can, Ka juya motar mubi bayan su"acewar uzair, Taj yace"Ni bazan bi su ba, kawai daga ganin motoci sun shiga daji sai kace mubi su, for what reason? "Nidai kawai kayi a bunda nace maka, Kada ka manta mu fa ƴan jarida ne, rai a ɗan 6ace taj yace"Mu ƴan jarida ne, Ba jami'an sirri ba, Don haka ni bazan bisu ba, Gida zamu koma" Yana ƙoƙarin juya sitiyarin Uzair ya damƙi hannun shi, juyowa yayi suka haɗa ido, "Ka yi abunda nace maka, In ba so ka ke in sauka daga Cikin motar nan ba, in bayansu da ƙafafuna" Sanin kafiyar Uzair ne, Yasa Taj Juya motar Ya nufi Cikin dajin, Zuciyar shi duk a jagule don ba ƙaramin takura shi uzair yayi ba, "Ka rage gudun motar" acewar uzair, a takure taj ya rage gudun motar, yayin da yake kurɗaɗawa cikin dajin har Allah ya kawo shi wurin da waɗannan danƙara danƙaran motocin su ka yi parking, A jere su shida a bakin wata ƙorama, Daga nesa dasu taj yayi parking ɗin motarsu, tare da kashe hasken motar su, don kada su gansu, Amma su suna iya hangensu saboda sunbar nasu hasken motocin su a kunne, Natsuwa su ka yi suna jiran ganin Su wanene zasu fito daga Cikin motocin, Kusan ƴan mintuna, kafin a buɗe motocin, kamar a shirin film suka fito a tare, Kowannansu Na sanye da suits ajikin shi black colour, fuskokinsu na sanye da mask, daga ganin bodyguards ne, At same suka buɗe murfin Back seat na motocin, Wasu Manyan mutanene suka soma saukowa daga Cikin motocin, kowannan su na sanye Cikin shigar hausawa, Daga ganinsu dattawane sun kwan biyu aduniya, Kallon juna taj da uzair sukayi a lokaci ɗaya kafin suka mayar da hankalinsu kan abunda suke kallo, Bayan Alhazawan sun kammala fitowa daga Cikin motar, Ɗaya daga Cikin bodyguards ɗin Ya zagaya bayan motar ƙarshe, Ya buɗe boot ɗinta, Hannu ya sanya ciki tare da danƙo rigar Wani bawan Allah dake naɗe cikin boot ɗin, Ya wurgo shi waje, Gaba ɗaya mutumin ya kife ƙasa, Rawanin dake naɗe a kan shi Ya warware, Jikin shi sai kerma yake yi, kamar wanda sanyi ya kama, daga ganin shi dai Malami ne, duba da irin shigar shi,Jallabiyace ga kuma rawanin shi, hada cazbaha a hannun shi lokacin daya ɗago, La66an shi nata kerma Yana ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'in, La'ila ha'illah anta subhanaka Inni kuntu minazzalimin,'duk yabi ya susuce, Cike da taku irin na majiya karfi, Bodyguard ɗin ya kuma takawa Zuwa mota ta biyun ƙarshe Ya buɗeta, Wasu ƙananun Yara ne guda biyu, Gwanin ban tausa yi sun ƙankame junansu mace da namiji, Sun cunkushe acikin boot ɗin,Yadda kasan irin kifin gwangwanin nan, Damƙo wuyan rigunan jikinsu yayi tare da ɗago dasu Ya wurgo dasu ƙasa, Gaba ɗaya suka kife saman Ciyayin dake a wurin,Sautin kukansu ya ƙarade wurin, Miƙewa Yaran su ka yi da gudun gaske suka nufi wannan malamin daga gani ubansu ne, Rungumesu ya yi a jikinshi sunata kuka, A ƙalla macen bazata wuce shekara Takwas ba, Namijin kuma goma, Tsananin tsoro ne Bayyane akan fuskokin su, Hankalinsu amatuƙar tashe yake, Daga gani bada shiri aka ɗaukosu ba, Saboda kayan dake a jikin yaran duk na bacci ne, Ita macen ko kalli babu a kanta, ɗan kitson Shukkun da akayi matane, ƙafafuwansu ko takalma babu, Ƙawanya waɗannan Alhazawan Sukayi masu, Suka sanya su a tsakiya, Yayin da bodyguard ɗin ke a bayansu, Wani irin kallo suke binsu dashi, kafin daga bisani wani dattijo daga cikin alhazawan Ya soma magana"Malam wa kake da suna"?muryar na kerma Malamin yace"Jazuli" Jinjina kai dattijon yayi"sau nawa ina jan kunnanka"? "Sau biyu" cikin shessheƙar kuka ya yi maganar, "Okey,Saboda kafiya da taurin kai irin naka Baka daddaraba ka sake shiga hurumina ko? Meyasa ka tsananta bincike akaina? Ka sanni ne? ko ina da wata alaƙa dakai ne?ya yi tambayar idonshi akan malamin Shiru Malam Jazuli yayi, yana ta faman mazurai, Hannunshi bibbiyu ya tallabe ƴa'ƴan shi, "Koda zaku cutar dani, Ina roƙan alfarma ɗaya a wurinku, dan Allah kada ku ta6a ƴa'ƴana," Tuntsirewa su ka yi da dariya gaba ɗayan su, mai sautin gaske, Taj da uzair dake la6e acikin mota suna kallonsu, Tuni sunsha jinin jikinsu, buɗe murfin motar su uzair ya yi da niyar ya fita, da sauri taj ya ruƙo Hannnunshi murya ƙasa ƙasa yace"baka da hankali ne, Idan suka kama mu fa" Uzair yace"bana jin abunda suke cewa, dole na fita" ya zame hannunshi daga ruƙon da taj yayi mashi, yasa kai ya fuce daga Cikin motar, kasa zama Cikin motar ya yi ya ƙwammace yabi bayan uzair komai zai faru ya faru, Buɗe motar ya yi tare da fitowa Yabi bayan Uzair Cikin sanɗa suke tafiya har suka ƙaraso gab da su, a bayan wata gabjejiyar bishiya, suka la6e suna kallon su,ɗan Jarida da kasada, "Nifa inaga,Yakamata mu tafi uzair"acewar Taj, Girgiza kai uzair yayi"Kaɗan jira muga Mai zasuyi ma shi, bari ma na ɗauki video,"yana ƙokarin zaro waya, Taj ya buge hannunshi"ashe baka da hankali, So kake hasken camera ya tona mana asiri, ba don yaso ba Ya haƙura da ɗaukar video ɗin, Suna Cikin yin Maganar nan, Su ka ji wani irin gurnani mai matuƙar tsoratarwa, A ruɗe suka ɗago suna kallon su, Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take yazama wata irin halitta mai matuƙar tsoratarwa,Ya shiga girgiza jikinshi Yana wani irin gurnani, *💋KURKUKUN ƘADDARA💋* *_daga alƙalamin Boss Bature ✍️*_ dedicated to Aunty kubra❤ قصة حزينة جدا عن السجناء🥺💔 *E7* Su na Cikin Maganar nan, Su ka ji yo wani irin gurnani, A ruɗe su ka ɗago suna kallon su, Wannan dattijon ne Ya rikiɗa nan take ya zama wata halitta mai matuƙar tsoratarwa, Ya shiga girgiza jikin shi Yana wani irin gurnani, Tashin hankalin da ba'a sama shi date, Wani irin tsoro ne ya bayyana a kan fuskokin su, Tuni zufa ta wanke su sharkaf, Don tunda Allah ya halicce su basu ta6a ganin mutun ya rikiɗa ya koma dabba ba, duk da suna Jin labarin Matsafan dake rikiɗa suna canza halittar su, Ja da baya halittar nan tayi, Kafin Ya daka suka, Kaitsaye Ya faɗa kan Ƴa'ƴan malamin nan, Ya shiga yagar Naman Jikin su Yana ci, malamin na kuka yana ƙoƙarin ceton ran ƴa'ƴan shi da jini Ya wanke fuskokin su, Aikuwa nan take sauran Alhazawan guda biyar dake a kewaye da su, suka rikiɗa, gaba ɗayan su ka canza halittar su, Cikin lokaci ƙanƙani su ka handame malamin nan da ya'yan shi, In taƙaice maku zance, Sai da Suka cinye namansu tass, Ko ƙashi basu bari ba, Tukunna Suka rikiɗa a lokaci ɗaya suka koma Mutane, Bakin kowannan su, Da6a da6a da jini, A hanzarce bodyguards ɗinnan suka zura hannayen su Cikin aljihunan wandunansu kowannansu ya zaro Hanky mai girma. suka shiga goge masu jinin da ya 6ata bakunan su, Bayan sun kammala suka jefar da hanky ɗin Cikin ƙoramar dake a gabansu, Batare da 6ata lokaci ba, suka koma Cikin motocin su, a guje suka bar cikin dajin 6aaat suka 6ace, Jikin Taj na kerma Ya kalli Uzair wanda tuni ya jima da ƙamewa a tsaye kamar saƙago, Idanuwanshi sun firfito waje tamkar zasu faɗo ƙasa,Wani irin matsanancin tsoro ne ya ziyar shi zuciyoyin su, hankalin su ya tashi matuƙa, A ruɗe Taj ya fisgi hannun Uzair suka Koma Cikin motar su, Aka rasa wanda zaiyi driving ɗin su, tsakanin su biyu, jikinsu duk yayi sanyi ga wata uwar zufa dake tsatstsafo masu, tamkar waɗanda aka tsamo su daga cikin ruwa sun haɗa uban gumi, daƙyar Taj ya iya tada motar, ya samu ya karya kwana da wani irin speed ya fusgi motar tamkar zasu tashi sama, Duk tsoro ya kama su ga tausayin malamin nan da ƴa'ƴanshi, abun ya yi matuƙar girgiza su, A can gida kuwa, Sam bacci ya ƙaurace wa idanuwansu, Daga angel ɗin har aneelerh, Sun yi zugudum saman Gado, kowa da abunda yake ayyanawa a ran shi, Ganin har ƙarfe 12 ta buga amma ba su dawo ba, "Aunty aneelerh, ni tsoro nake ji kada a ce wani abu ya faru da su daddy" Janyo ta Jikinta aneelerh ta yi Tare da shafa sumar kanta tace"in sha Allah ba a bunda zai faru da su, zasu dawo ne nan bada jimawa ba, ni inaji a raina" "Allah bazan ƙara bari ya tafi ya barni ba, duk inda zai je ƙafata ƙafar shi, idan ba haka ba zan sa ce tayar motor shi kowa ya rasa" aɗan shagawa6e tayi maganar, tamkar zata fashe da kuka, Fashewa aneelerh tayi da dariya daƙyar ta tsagaita da yin dariyar tace"Idan ki ka sa ce tayar motar shi ae yana da ƙafafu ko suma zaki guntule su ne? Kuma in banda abun ki, idan kika sa ce tayar motar shi, ae a kwai ta Uzair zasu fita a cikin ta shi ne," Tur6une fuska tayi, ba halin tace zata sa ce tayar motar uzair, Suna Cikin tattaunawar nan, Suka jiyo hon ɗin motar su, Da gudu Angel ta zabura Zata sauko daga saman gadon, Aneelerh ta ruƙo hannunta"ki bari su ƙaraso Ciki mana" Komawa tayi ta zauna jikinta har wani rawa yake yi duk ta ƙagara taga daddynta, Baba maigadi na buɗe masu ƙopar, A tsiyace suka shigo da motar bayan sunyi parking ɗinta Taj ya kashe motar, Uzair ya kalli shi ganin yadda zufa keta tsatstsafo mashi ya haɗa uban gumi"banaso su gane wani abu ya faru pls, Ka daidaita natsuwar ka" Kallon shi taj ya yi "natsuwa fa ka ce?tayaya kenan? akan idona fa mutane suka rikiɗa suka canza halittarsu, kuma akan idona suka handame mutun da ya'yan shi, wlh ko a film naga hakan saina girgiza ballantana kuma a zahiri, ni wlh ka cuce ni, danasani tunfarko ban biye maka ba, da duk banga wannan tashin hankalin ba" ranshi duk ajagule ya yi maganar, "Amma ae koba komai, mun ƙaru ko?tun da kaga yanzu mun samu a bunda zamu taimaki al'umma,"uzair ne yayi maganar, Wani kallo Taj ya jefa mashi"mu taimaki al'umma, ka yi hauka ne"? Bai ba shi amsa ba, sai ma ya fito daga motar, ya nufi cikin gidan, Jiki a sanyaye taj ya fito daga motar yabi bayan Uzair suka nufi cikin palourn, Kusan atare suka haɗa baki wurin yin sallama, jin muryoyin su yasa Angel da aneeleeh suka fito daga ɗakin, da gudu angel taje ta faɗa ma daddynta, "Nayi fushi sai yanzu zaka dawo,duk ka tayar mun da hankali, ko bacci na kasa yi" Zuƙunnawa yayi saman gwiwowin sa, yadda tsawon shi zaizo dai dai da nata, Sosai yayi hugginta ɗinta"Am sorry angel, Nasan nayi laifi, ayi mun afwa,"aɗan shagwa6e tace"shikenan amma kada ka ƙara," amsa mata ya yi da toh batare daya rabata da jikin shi ba, sam baiso ta gane halin da yake ciki, hawaye ne cike tab da idanuwan shi, tamkar ya rushe da kuka haka yake ji bakomai yafi tsaya ma shi a raiba fa ce yacce waɗannan Mutannan marasa imani suka fatattaki malamin nan da kuma ƴa'ƴan shi, Yanzu shikenan sun kashe su, Babu su a doran duniya, tabbas waɗannan mutanan sun san me suka taka, Aneelerh da uzair tuni sun shige ɗaki, "Sannu da dawowa" batare da ya kalle ta ba, ya nufi toilet zai shiga, "Wai meke faruwa ne? Nayi maka magana baka amsa min ba," Juyo wa ya ɗanyi Yana kallonta a lokacin ya ruƙe handle ɗin ƙopar toilet zai shiga, "To matar ɗan jarida, ba za ki bari na samu natsuwa ba" cikin zolaya ya yi mata maganar, Murmu shi taɗan saki, shima ya mayar mata da martanin murmushin kafin ya shige cikin toilet ɗin. Tunawa da taj yasa Aneelerh miƙe wa Ta fito falon, Bata same su a nan ba hakan na nufin ya ɗauki angel sun tafi gida. Ta so ace tayi ma shi sannu dawowa, ga shi kuma Ya tafi, Ta wani 6angaren kuma ji take kamar wani abu Ya faru ba daidai ba, Tun daga kan yanayin Uzair, da kuma shi taj ɗin. Hakanan taji hankalin ta bai kwanta dasu ba, sam babu natsuwa a tattare da su, Juyawa ta yi zuwa cikin ɗakin a lokacin uzair Ya fito daga toilet ɗin, da alama Ruwa yaɗan watsa ma jikin shi, short ne kawai ya bari ajikin shi, "Sannu da fitowa" ta faɗi tana kallon shi, "Yawwa madam," "Bari na kawo maka dinner ɗin ka, nasan ka kwaso yunwa," Da sauri ya dakatar da ita "No bana jin yunwa, bacci nake ji" yakai ƙarshen maganar tare da nufar Cikin ɗakin wurin Closet ɗin shi, Ya buɗe cikin jerin jallabiyoyinshi ya ɗauko ɗaya Ya zurata ajikin shi, Juyawa yai Still aneelerh tana a tsaye tana kallon shi, Ta gefenta yabi ya wuce ya kwanta, "Nayi tunanin zaka yi missing ɗina," tayi maganar tare da takawa Ta koma gefen gadon, "Kodai wani abu ya faru ne? naga duk ka sauyamun, Shima taj ko sallama banyi ma shi ba, Ya ɗauki angel sun tafi gida" Ganin zata takura mashi da surutu ne yasa shi yin saurin janyota jikin shi, wata irin runguma yayi mata, sai ga shi tayi tsit bata ƙara cewa uffan ba, Taj kuwa bayan Sun koma gidan, Upstairs Ya wuce da angel, Yakaita bedroom ɗinta, Yasan aneelerh bazata barta da yunwa ba, Dawowa down Yayi a hanzar ce ya shiga bedroom ɗin shi Ya faɗa toilet, shaf shaf yayi wanka ya fito, wuri ya samu saman kujerar gaban mirror ya xauna, wasu zafafan hawaye ne su ka soma yin zarya akan fuskar shi, Uban tagumi ya zabga tamkar marayan da ba shi da ma fadi aduniya, "Daddy"muryar angel ce ta katse shi, ta cikin madubin yake hangenta, tana a tsaye bakin ƙopar, Da sauri ya share hawayen dake a kan fuskashi cikin sanyin murya yace"Ba ki yi bacci ba? Ƙarasa shiga cikin ɗakin tayi"daddyna ba ka da lafiya ne? "Lafiyata ƙalou me kika gani ne"?yayi tambayar tare da ɗan juyawa yana kallon ta, a lokacin ta ƙaraso in da yake zaune, "Ni dai inaji araina, baka da lafiya," daƙyar ya ƙaƙaro murmushi yace "Waya faɗa maki bani da lafiya? "Naji a jikina" ta yi maganar tana ƙare mashi kallo, "Bana hana ki yawo da daddare ba kallabi ba"? da biyu ya yi mata maganar don ya mantar da ita wancen zancen, "Mantawa nayi," Nuna mata hanyar fita yayi da hannun shi"Oya go back to ur room ki ɗaure kanki da kallabi, before ki kwanta" Maƙe mashi kafaɗa tayi"Ni dai zan kwana anan, muyi bacci a tare" Ɗaure mata fuska ya yi"Za ki wuce ko sai nayi ball dake" a faɗa ce ya yi mata maganar,nan da nan yanayin fuskarta ya canza, ƙwalla ta ciko tab a cikin idanuwanta, cikin shessheƙar kuka tace "Dan Allah daddy ka bari in kwana anan yau kawai" ta ƙarasa maganar tana matsar ƙwalla, Gyaɗa kai yayi"Shikenan Ki fita waje Ki jirani zan kira ki" juyawa tayi da sauri ta koma daga waje, ta jingina bayanta jikin wall, Miƙewa ya yi jiki ba ƙwari ya nufi wardrobe ya ɗauko kayan baccin shi, ya soma sanya su a jikin shi, "Daddy in shigo" jin muryarta ya sa shi yin murmushi tare da cewa"ban kammala ba" Sai daya ƙarasa zura kayan a jikin shi, tukunna Ya kira Sunanta Angel, Shigo wa tayi cikin ɗakin A kwance ta same shi saman gado, Ƙarasawa tayi ta haye saman gadon, Can kusa da shi ta kwanta, Addu'a ya shiga jerowa yana tofa masu, Kafin Ya janyo ta jikin shi, a daren ranar da ƙyar ya samu bacci Ya ɗauke shi, ****Boss Bature**** A washe garin Ranar, Angel ta farka bata same shi a saman gadon su ba, Tunda ya tafi sallar a suba bai dawowa ba. Ita kaɗai acikin gidan, Ga yunwa tana ji, fito wa ta yi daga bedroom ta sauko down kaitsaye ta nufi cikin falo, Fridge ta buɗe ta ɗauko Fura a cikin roba, Ta koma saman sofa Tana sha, duk in taji kamar motsin mutun saita kalli ƙopar taga idan shi ne Ya shigo, Wuraren ƙarfe tara na safe Ya shigo Cikin falon, A kwance ya sameta, Tana ta bacci, ga robar furar data sha a jiye saman table, Ƙarasawa yayi a gabanta ya zuƙunna tare dakai hannu yana shafa gefen fuskarta, Yasan tayi neman shi har ta gaji, Shi kan shi baisan ya akai bacci ya ɗauke shi a masallaci ba, Kodan jiya bai samu isasshen bacci ba ne, Kasa janye eye ɗinshi ya yi daga kan fuskarta, hakanan ya dinga jin bugun zuciyarshi na ƙaruwa, sallamar uzair ce ta katse mashi kallon nata da ya ke yi, Miƙewa taj ya yi tare da juyawa Yana kallon shi, Gaisawa suka fara yi, kafin suka rungume juna kamar yadda suka saba, "Inason magana dakai" acewar uzair," Nuna mashi wuri yayi saman sofa"bismillah" Zama Yayi saman 2 seater, taj kuma ya zauna a saman 1 seater, kallon kallo su kayi ma junansu na tsawon mintuna biyar batare da wani daga cikin su yace ƙala ba, Sai da taj ya gaji da zaman tukunna yace "Ina sauraronka"? A tsanake uzair ya soma magana"game da waɗannan mutanan da muka gani jiya" "Suwa kenan"? yadda yayi tambayar tamkar baisan komai ba, "Ina nufin waɗannan Miyagun da suka Kashe malamin nan da ƴa'ƴan shi, Wani irin kallo Taj ya yi ma shi"Wai dama ba mafarki bane"? Harara uzair ya ɗan jefa ma shi"take it serious pls, Banason wasa so nake muyi magana a kansu,' Girgiza kai taj yayi"badani ba wlh, Na riga da nabar komai a matsayin mafarki, Bana so kasa ke tunamun a bunda ya faru jiya," "Kana nufin xamu ƙyalesu ne suna aikata 6arna acikin ƙasarmu"?acewar uzair ,A harzuƙe taj yace"ƙwarai kuwa, tunda bamu da yadda zamu yi da su, sunfi ƙarfin mu, mubar su da Allah shi kaɗai ne zai yi mana maganin su, Uzair yace"Ba haka na sanka ba taj, Nayi tunanin zamu haɗa hannu a matsayin mu na ƴan jarida wurin ganin mun fallasa su, don a ɗauki mataki a kansu," Taj yace"Allah ya taimaka, Amma ni dai babu hannuna a ciki, kaima kuma ina gargaɗin ka akan ka manta da su, tamkar baka ta6a sanin su ba, In ba haka ba zaka jefa kanka cikin matsala ne , domin kuwa waɗannan mutanan da kake gani Shaiɗanu ne, sunfi ƙarfin hukuma ita kanta ballantana kuma mu da muke ƴan jarida" Abu kamar wasa, suka soma gaya ma juna magana, Shi uzair yasa kafiya a kan saiya bi ƙwaƙƙwafinsu don ya tona masu asiri, Shi kuma taj yana ƙoƙarin fahimtar da shi irin haɗarin da zasu jefa kan su, a ƙarshe dai Uzair Ya miƙe rai a6ace yace"idan har ban tona masu asiri ba,tabbas zan ajiye aikina na ɗan jarida ne, domin ban cancance shi ba" yana kai ƙarshen maganar shi ya fuce, Taj dai yana a tsaye ya yi kasaƙe yana kallon bayan shi, har ya 6ace ma ganin shi, Duk wannan surutun da su ke yi akan kunnan angel tun ɗazu ta farka daga bacci, duk da bata fahimci me suka tattaunawa ba, "Daddy faɗa kuke da Daddy uzair?" a ɗan ruɗe Ya kalleta, da sauri yace"a'a, muna tattaunawa ne, game da zuwan Uncle abdallah, na faɗa mashi cewa Ya bari mu fara zuwa buzaye shi kuma yace dole mu jira su dawo Sai mu tafi atare" Murmushi tasa ki"Nima nafi so mu tafi tare da su mommy adama" "Me zaki Ci in kawo maki"? "Komai zaka ci nima zanci" miƙewa ya yi tare da juyawa Ya nufi kitchen, don yau ba aikin safe gare shi, Sai wurin mare ce zai fita. Zama tayi tana Jiran dawowar shi, almost 15 mins Ya fito hannun shi ɗauke da plate, indomie ce daga sama Kuma wainar ƙwaice, Asaman table ya ajiye masu,Kafin Ya koma kitchen ɗin Ya haɗo masu tea a cup biyu,Yazo ya ajiye gefen plate din tare suka zauna Suna ci, still zuciyarshi a cunkushe take, Yana so ya taimaka ma uzair wurin fallasa asirin waɗannan mutanan ta wani 6angaren kuma Yana jin tsoran su jefa kan su Cikin masifa, tunda mutanannan sunfi karfinsu nesa ba kusa ba, Allah ne kaɗai zai Iya dasu, ga kuma angle din shi bayaso wani abu ya faru da ita ta sanadiyar shi gaskia yana cikin tsaka mai wuya Ya yi zurfi cikin tunani, muryar Angel ce ta katse shi, "Daddy!" Firgigit ya yi tare da kallon ta, "Na'am!" Fuskarta da alamun damuwa ta ce, "Tun ɗazu ina ta kiran ka amma ba ka amsa mini ba. Daddy kamar kana cikin damuwa." Girgiza mata kai ya yi, "Am ok, ba wani abu. Kawai ina tunanin rayuwar duniya ne mai ban al'ajabi, rashin tsoron Allah ya yi ƙaranci a zukatan wasu mutanen. ban sani ba neman duniya ne koko mene ne yake jan hankalin su har su manta cewa wata rana za su mutu? Kuma za su koma ga Allah, sannan duk wani abu da suka mallaka ba za a ta6a binne su da shi ba, a gidan duniya za su bar shi." Tun da ya fara magana Angel ta ƙura masa ido tana kallon shi, sam ba ta fahimtar kan me yake magana. Shi kansa ya manta da wa yake magana? Abin ne ya dame shi yasa yake ta sambatu ko ya samu ya rage raɗaɗin dake cikin zuciyarsa. Haɗa ido sukayi da ita, lokaci ɗaya yaja bakin shi ya yi shiru, da mamaki akan fuskarta take kallonshi, can dai tace"Daddy, Meya faru"? Ƙaƙaro murmu shi ya yi"halan kinji inata zuba ko? wani programme ne da zamu gabatar a gidan radion mu shine nake tsara yadda zanyi shi" Murmushi tasa ki"Allah ya taimaka daddy, I wish u all the best' ya amsa mata da ameen, *ANEELER* A zaune su ke ita da uzair saman dining chairs suna fuskantar Juna, gaba ɗaya hankalinta na akan fuskar Uxair tunda ya ruƙe spoon yake ta jujjuyashi Cikin abincin da ta zuba ma shi a plate sam ya kasa cin shi sai kacaccala shi yake yi kamar ƙaramin yaro, ta lura da canzawar da yayi daga daren jiya zuwa yau kamar wani abu na damun shi bama kama bace tabbas akwai abinda ke damun shi. Gyaran murya ta ɗanyi ma shi, Ya ɗago suka haɗa ido tace"My man, kaƙi faɗamun abunda ke damunka, tun ɗazu nake kallon ka, sam ka kasa Cin abinci why pls"? Daƙyar ya iya bude baki yace"don't worry ur self am ok, just bana jin daɗin zuciyata ne," "daka daure ka faɗamun may be in sama mana solution" Murmu shi ya ɗansaki cikin zolaya yace"Matsalar bata asibiti bace balle kice za ki yi mun allura inji sauƙi" Ta6e baki ta ɗanyi tare da mayar mashi da martanin murmushin "kana nufin matsalar data shafi asibiti kaɗai zan iya magani"? Girgiza kai yayi"karfa ki dauka da zafi, It was a joke" Kallon shi kawai tayi kafin ta mayar da eyes ɗinta akan abincin dake gabanta, Wuraren ƙarfe shida na marece, taj, Yana daga kishingiɗe saman Sofa, jikin shi na sanye Cikin jeans da white shirt, a lokacin angel tana can cikin ɗakinta, Ƙwanƙwasa ƙopar falon shi a kayi daga waje, A hakanlali ya ɗan buɗe i danuwans hi tare da tambayar wanene, Ba abashi amsa ba aka turo kopar ɗakin, uzair ya gani a tsaye Sanye da jallabiya, fuskar shi babu walwala, miƙewa zaune taj yayi yana kallonshi yace"Shigo ciki mana" Ƙarasa shigowa Cikin falon yae tare da samun wuri saman Sofa ya zauna, batare da ya furta mashi komai ba, "Meke damun ka ne aminina? naga sauyi sosai akan fuskarka" harara ya dan jefa mashi tare da cewa"Kaine damuwata Taj, saboda kaƙi bani haɗin kai akan abunda nakeson Cimmawa" Murmushin takaici taj yayi"cos You wanna get yourself into trouble shiyasa naƙi goya maka baya, Idan suka kama mu munayi masu leƙen asiri what do you think will happen next? They will kill us as soon as they find out that we are investigating them," Jinjina kai Uzair yayi"Yanzu haka zamu zuba ido ana aikata 6arna batare da Mun hana ba"? "Ƙwarai kuwa, Saboda bamu da yadda zamuyi,illa iyaka Muyi addu'ar Allah ya kawo mana ƙarshen su, that's the only solution" Jiki a sanyaye Uzair ya miƙe ya soma tafiya har yakai bakin fita daga Falon ya ɗan dakata "Ka manta alƙawarin da mu ka yi ma juna tun kafin mu fara aiki'? shiru taj ya yi yana kallon bayansa, Cigaba da magana uzair yayi" duk runtsi duk wuya zamu ƙarfafa ma juna gwiwa wurin ganin mun taimaki ƙasar mu, amma sai gashi kaine na farko daka fara sare mun gwiwata, Narasa goyon baya daga gareka, ji nake tamkar narasa wani sashe na jikina," Miƙewa tsaye taj yayi tare da nufar inda Uzair yake atsaye Ya soma magana"Ina jiye mana tsoron abunda zai biyo baya ne, akan idon mu suka kashe mutun da ƴa'ƴansa, a haka kuma ka ke so Mu yi bincike akansu?wannan fa ba aikin mu bane, shin wai kai baka tsoron asirin mu ya tonu su gane cewa muna bibiyar su?ko ba don saboda mu ba, ka tuna kana da mata ni kuma inada ƴa, So ka ke Mu jefa su cikin masifa ne? Yana kai ƙarshen maganar shi uzair yace"In sha Allah hakan bazata ta6a faruwa ba, Nidai inaso ka bani haɗin kai kawai" Duk yadda Taj yaso ya fahimtar dashi amma Yaƙi ya gane, ba don yaso ba, Ya amince mashi akan suyi Bincike akansu, don su samu hujjojin da zasu fallasa su, har hukuma ta ɗauki mataki a kansu, Tun daga wannan Lokacin Suka soma tunanin ta ina zasu fara neman su, A ƙarshe Uzair ne ya ba shi shawarar su koma inda suka fara ganinsu acikin dajin nan, Cikin sa'a ranar da suka je again suka sake ganin miyagun mutanan nan sun kamo wani mutumin, kamar yadda suka kamo malamin nan, da alama Leƙen asiri shima Yayi masu, Akan idonsu suka koneshi, ranar Taj hankalin shi ya tashi matuƙa har yace ma Uzair shidai zai Cire hannun shi, kusan faɗa sukayi da uzair akan hakan, daƙyar suka sasanta kansu, kuma suka Cigaba da bibiyan Alhazawan nan, Sai dai duk wannan tsawon lokacin da suka ɗauka suna Bibiyarsu Allah bai basu damar sanin kosu wanene su ba, daidai da fuskokin su ba su sani ba, Abu ɗaya kawai suka sani inda suke yankewa mutum hukunci wato Cikin dajin nan a bakin ƙorama, Abunda su taj basu sani ba, duk wani motsinsu akan idanuwansu suke yin shi, Sunsan komai game da bibiyar su da su ke yi zuba masu ido kawai su kayi, yayin da su basu san da hakan ba, Lalube kawai su ke yi acikin duhu............ Ganin babu Riba a bindiddingin su da sukeyi ne yasa Taj ya cire hannun shi, uzair kuma yasa naci Akan binciken shi, duk yadda taj ya gargaɗeshi amma Ya sanya kafiya, ashe ajaline ke kiran shi. ************************* A daren Ranar Alhamis ne Wannan mummunan ƙaddarar ta riskesu wadda tayi silar rasa rayukan su, Wuraren ƙarfe 9 na dare, Taj na zaune tsakiyar gadon shi, ya tasa laptop ɗinshi agaba yana ta ƴan danne danne acikin, har ma ya yi shirin kwanciya singlet ce ajikin shi tare da short, wani aiki ne ya tsayar da shi, Allah Allah ya ke yi ya gama aikin ya je ya kwanta, sai hamma yake yi, ba zato ba tsammani yajiyo bugun ƙopar falo, Agogo ya kalle, Cike da mamaki Ya sauko daga saman Gadon ya fito ɗakin ya nufi cikin falon, a baƙin ƙopar ɗakin ya tsaya tare da tambayar wanene? Daga waje yajiyo muryar aneeleerh,ka bude mun kopa nice" muryarta Cikin shessheƙar yaji sautinta, jiki na rawa ya buɗe mata ƙopar har saida gaban shi ya faɗi ganin Yadda fuskar ta tayi jawur saboda kukan da ta sha, kayan Bacci ne ajikinta riga da wando sai mayafin data yafa akanta, gefen goshinta kwantaccen gashin kanta, Aruɗe yace"Aneelerh? Lafiya? me meya faru ne? Ya akai naganki acikin daren nan'? Daƙyar take iya kallonshi, da runannun idanuwanta wadanda suka yi jawur da su, "Uzair ya fita bansan inda yaje ba Cikin daren nan, na farka bangan shi ba, hankalina bai kwanta ba, na je wurin baba mai gadi don in tambaye shi ko sun yi magana da uzair kafin fitar shi, yace mun eh sunyi magana da shi kafin ya fita amma bai faɗa ma shi inda zaije ba,......" tunda ta soma magana hankalin taj ya ɗungunzuma, jikin shi ya soma kakarwa, fargabar shi kada ace uzair ya tafi Wurin mutanan nan, dama yace mashi bazai fasa bindiddiginsu ba, idan kuwa hakane to kuwa tabbas yaje yi masu leƙen asiri ne, Jin yayi shiru bai ce mata komai ba yasa tace"ko kasan inda ya tafi ne"? girgiza mata kai yayi alamar a'a, saboda bai son ya tayar mata da hankalinta, "Kin kira layin shi"? ya yi tambayar yana kallonta, "Na kira shi har bansan adadi ba, Amma bai ɗaga ba, kuma kiran yana shiga"jinjina kai yayi" Bari na jaraba kiranshi, ki shigo Ciki ki zauna" yakai ƙarshen maganar yana nuna mata sofa, Cikin sanyin murya tace"bazan Iya zama ba," tausayinta duk ya kamashi, bedroom dinshi ya koma a hanzarce Ya kai hannu ya ɗauki wayar shi dake a jiye gefen laptop ɗin shi, Ya shiga call logs, ya danna ma uzair kira, tana fara ringing, uzair yayi picking call ɗin, Rufe shi da faɗa yayi ta inda ya ke shiga bata nan yake fita ba, "Duk inda kake ka dawo gida yanzu yanzu, kasa baiwar Allah sai kuka take yi, Saboda rashin hankali, Ka kama hanya ƙarfe tara na dare ka tafi ka barta batare da ka sanar da ita inda kaje ba, Anya kuwa kasan me ka ke yi? wai shin ina kaje ne ma.......? duk wannan suratan da taj ke yi uzair baice mashi uffan ba, A ƙarshe ma saiya yan ke kiran gaba ɗaya, jikin taj ba ƙaramin sanyi ba, tunani ya shiga yi wai shin dawa ma yake waya? idan uzair ne meyasa bai yi ma shi magana ba? kuma ya ɗaga kiran Anya kuwa ba'a samu matsala ba, sake kiran Layin ya yi a switched off ya samu wayar, Nan fa jikin shi ya mutu, hankalinshi Ya tashi Saman bedside drawer Ya ɗaura wayar, ya fito daga ɗakin ya koma falon, Cike da zullumin amsar da zai ba aneelerh, Lokacin da ya shigo falon ya ƙaraso inda take tsaye, sai ya shiga Yin ƴan kame kame, "Bai ɗaga kiran ba ko" ta yi tambayar a ƙagare, Muryarshi na inda inda yace"Am..um..kingane..eh..muyi waya dashi, ki kwantar da hankalin ki, Yana kan hanyar dawowa gida, yanzu ki koma ki kwanta, kada ki takura kan ki," Wani irin kallo yaga tana yi ma shi kallon ban yadda dakai ba, da sauri yace"kiyi hakuri ki koma gida, nan badajimawa ba zai dawo" Jiki asanyaye Ta juya ta fuce daga falon, Ko bayan tafiyarta saida ya kuma kiranta awaya, Ya ƙara kwantar mata da hankalinta, Kasa zama ya yi, zarya ya shiga yi tsakanin ɗakin shi zuwa palour, ya rasa meke yi ma shi daɗi duniyar nan, duk bayan ƴan mintuna sai ya jaraba kiran Layin Uzair don yaji in ya bude wayar amma a kashe yake samun ta, Bawan Allah ya rasa ta zama, duk ya shiga damuwar rashin amininsa, juyawa ya yi da sauri Ya haye upstairs ɗakin angel, ya tura ƙopar ɗakin a hankali, ko'ina duhu, ya lalauba jikin bangon ya kunna switch, tare dakai idanuwanshi kanta, Sai bacci take yi, ta ƙudundune Cikin bargo, murmushi ya ɗan saki kafin ya ɗauke i danuwan shi daga kanta, ya mayar dasu kan wall ɗin dakinta, Zanunnukan da tayi ne tare da kalaman da ta rubuta ma shi, a kullum ya kallesu sai yaji farin Ciki acikin zuciyar shi, duk mun baƙin Cikin da yake ciki, A hankali Yake tafiya cikin ɗakin nata, ta 6angaren hagu ya zagaya saitin inda take kwance saman gadon, Kneel down Yayi tare dakai hannu Ya yaye blanket ɗin data rufa da shi, rigar bacci ce ajikinta, Kyakkyawar fuskarta Ya ƙurawa ido yana kallonta, Hakanan ya dinga jin bugun zuciyar shi na ƙaruwa, wani irin matsanancin faduwar gaba, a cikin zuciyarshi ya shiga ambaton Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un" ya ambaci hakan ba iyaka, "Daddy" muryar ta ce ta katse shi, kallonta yayi ganin ta buɗe manyan idanuwanta a kan fuskar shi, "Dama bakiyi bacci ba"? murmushi ta sakar mashi tare cewa"Nayi mana, yanzu na farka" hands ɗinshi ya sanya ya tallabo fuskarta"ƴar kyakkyawata, Allah yabar mun ke," "Ameen daddy, gobe uncle da aunty zasu dawo ko sai mu tafi buzaye ? tayi tambayar tana ƙoƙarin mikewa zaune, Girgiza mata kai yayi"Till next week nake tsammani" Ta6e baki ta ɗanyi"daddy ka kwana ɗakina yau"yatsina fuska yayi"Gadonki yayi mun ƙanƙanta" cikin zolaya ya yi mata maganar, Turo mashi baki tayi"To muje ɗakin ka mu kwana" maƙe mata kafaɗa yayi"A'a, kowa ya kwana a ɗakinsa," shagwa6a ta soma yi mashi, sosai ta ba shi dariya, suna Cikin Yin fira, Ya tuna da uzair, Rass yaji gaban shi Ya faɗi, Da sauri ya kali agogo, Ƙarge goma da rabi mayar da idanuwanshi kan angel yayi" ki koma ki kwanta, Sai da safe" yana ƙoƙarin mikewa tayi saurin ruƙo hannunshi da sauri kallonta ya yi idanuwanshi sun taunta sosai, ƙaƙaro murmushi ya yi don ya gane me take nufi, Kiss ya mannata mata a saman forehead ɗinta, Yasa hannu ya kwantar da ita tare da lullu6e mata jikinta da bargo, addu'a ya yi mata, kafin ya kashe hasken ɗakin, Lokacin daya fuce daga ɗakin yana jiyo sautin muryata tana faɗin"I love u so much daddy, Allah yabar mun kai, ina matuƙar ƙaunar ka habibi" murmushi yasaki A hanzarce Ya sauko down stairs, ya faɗa ɗakin shi, daga gefen gadon shi Ya zauna tare da ɗaukar wayar shi, ya ci gaba da jaraba layin Uzair, still a kashe yake samun ta, Zuciyar shi tajima da karaya, A sukwane ya ɗaura wayar saman bedside drawer, a wannan yanayin ne Bacci ya yi awon gaba da shi, sama sama yake yin baccin na shi, 🥺🥺🥺 Sannu a hankali agogon bangon ke harbawa, yana ba da sauti tik-tik-tik. Sakamakon dare da ya tsala don time din karfe ɗaya da rabi na dare, wayar da ke ajiye saman bed side drawer ƙirar Samsung Galaxy ta soma ruri da ƙarfi gaske. A lokacin ya yi nisa a cikin barcin nasa, kusan sau uku kiran na shigowa yana katsewa. A kira na huɗu ne, sautin ya daki dodon kunnansa, a firgice ya farka yana faman ambaton sunan Allah, Kafin ya zame hannunsa daga kan fuskarsa wani kiran ya sake shigowa wayarsa a hanzarce ya mika hannu saman drawer ɗin ya ɗauki wayar, Lokacin daya kalli screen ɗin wayar Sunan Aminina ne Ya bayyana, ajiyar zuciya ya ɗan sauke dama jiran kiran shi ya ke yi, A tunanin shi ya dawo gida ne, Shiyasa ya kira shi dan ya sanar ma shi game da dawowar shi, picking call ɗin yayi tare da manna wayar a kunnansa tun kafin ya yi sallama, kunnuwansa suka jiyo masa sautin harbin bindugu. A gigice ya furta, "Aminina!" Kafin Ya ƙarasa rufe bakinsa, muryar Aminin nasa ta katse masa hanzari, a ruɗe yake faɗin,"Na ba ni na lalace, shikenan tawa ta ƙare." A firgice ya dakatar da shi, "Ka nutsu ka yi mini bayanin me yake faruwa ne?" "Sun kama ni ina yi musu leƙen asiri, yanzu haka sun biyo motata, na san kashe ni za su yi, kai ma kuma ba za su ƙyale ka ba. ba zan so ka yi irin mutuwar wulakancin da zan yi ba, don Allah na roke ka, ka gudu kai da Angel, ba na fatan laifina ya shafe ka Abokina. Bayanan sirrin da na ɗauka a wurinsu, yana a cikin memory ɗina, ita kaɗai ce hujjar da asirinsu zai tonu..." Bai kai ƙarshen maganar ba, ɗif ya ji kiran ya katse. A gigice yake kwaɗa masa kira na fitar hayyaci sam ya manta da cewar wayar ta katse, sake kiran layin nasa ya yi cikin sa'a aka ɗaga kiran, abin da bai ta6a tsammani ba, sautin kururuwa ya ji a cikin kunnansa mai matuƙar razanarwa, wata kausasshiyar murya ya jiyo tana magana ta cikin wayar, "Idan kana son sanin meke faruwa, ka kalli screen din wayarka." Jiki na rawa ya ɗago da wayar yana kallon screen ɗin yayin da suka canza kiran zuwa Video Call. Saboda tsabar firgita, a ruɗe ya diro daga saman gadon, Idanuwansa sun firfiro waje tamkar ƙwayar idon za ta faɗo kasa. Ba komai ne yasa shi firgita ba, face motar Amininsa dake ci da wuta, akan idonsa suka zazzaga wa motar fetur, yana hango yatsun hannun amininsa ta tagar motar, wuta sai cin naman jikinsa take yi. Wata irin zufa ce ta wanke masa fuskarsa, a kiɗime ya shiga furta, "No, no!" Duk ya firgice, rejecting call din suka yi. Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far masa, ba arziƙi ya zube gefen gadon a zaune yayin da jikinsa ke kyarma sosai, ku san minti goma shabiyar baya a cikin hayyacinsa, ya rasa ma me yake yi masa daɗi duniyar nan. Yana cikin wannan halin ha'ula'in, muryar amininsa ta soma dawo masa a cikin kunnansa, "Ka gudu kai da Angel ba na so laifina ya shafe ku." Tabbas kuwa za su dawo kansa ne, domin su kashe shi kamar yarda suka kashe amininsa, ba komai ya fi ji ba face ƴarsa ɗaya tilo da ya mallaka wato Angel. A matuƙar ruɗe ya miƙe, ko jallabiya bai zura a jikinsa ba, iya key ɗin motarsa ya ɗauko saboda tsabar ruɗu wardrobe ya dosa zai buɗe a matsayin kofar dakin, har sai da kansa ya bugu tukunna ya ankare, ya nufi ainihin ƙofar, da sauri-sauri ya fito daga bedroom ɗinsa da ke a downstairs ya nufi cikin babban falon, kai tsaye Upstairs Ya haye. A kiɗime yake tattaka staircases din benen, bai nufi ko'ina ba sai ɗakin Angel, bugu ɗaya ya yi ma ƙofar ta buɗe, ko'ina duhu, kunna hasken ɗakin ya yi, nan take haske ya gauraye ko'ina, wurga kwayar idonsa ya yi kan Angel da ke ƙunshe cikin lallausan bargo, a hanzarce ya ƙarasa shiga ɗakin, tare da hawa saman gadon yana kwala mata kira, "Angel, Angle my daughter!Azeezaty!" Babu alamun za ta farka, a hautsine ya cakume ta ya saba ta saman kafaɗarsa. Da sauri ya fito daga bedroom din nata, ya sauko downstairs, Sam baya a cikin hayyacin shi, balle ya iya tunawa da aneelerh dake a cikin mawuyacin halin na rashin dawowar mijin ta gida, kai tsaye ya fito waje wurin da motocinsu suke, ɗaya daga cikinsu ya buɗe ƙirar Range Rover, back seat ya buɗe ya kwantar da Angel tukunna ya buɗe diver seat ya shige ciki, a gaggauce ya yi wa motar key, a daidai bakin gate ya tsayar da motar, a hanzarce ya fito ya buɗe gate ɗin, kafin ya koma cikin motar ya fusgeta da gudun gaske. Fitar motarsa ke da wuya, wasu danƙara-danƙaran motoci gudan shida suka nufo shantalelen titin da zai sada ka daga gidansa da alama sun hango motarsa hakan yasa suka bi bayan motar da wani irin matsiyacin gudu. Hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba, saboda ya hangi motocin da ke biye da motarsa ta cikin mirror ɗin motar, hakan yasa shi ƙara gudun motar. La66ansa na kyarma yake ambaton La'ila'ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! Shi kansa bai san inda zai dosa ba, driving kawai yake yi a makance, shessheƙar kukan Angel ce ta fara dawo dashi cikin hayyacinshi, da alama ta farka sakamakon gudun ceton ran da yake yi da su, yasa kanta ya dinga buguwa jikin motar, har hancinta ya fashe jini ya soma zuba. A ruɗe take furta,"Daddy...What's happening, where are u going in this darkness night?" Karamar yarinya ce da ba za ta wuce 11 years a duniya ba, maganarta ma daƙyar take fita saboda halin da take ciki, hawaye ne suka wanke masa fuska yana mai dana-sanin yin aikin jarida fiye da tunanin mai tunanin, saboda shi ne silar shigar shi cikin wannan tashin hankali. "Angel am really sorry! Na cuci rayuwarki, a yau daddynki ba zai iya ceton ki ba, Angel ba zan jure rashin ki ba, ba zan so laifina ya shafe ki ba." Yana magana cikin kuka, tafin hannunta ta sanya ta dafe hancinta dake bleeding, jini duk ya 6ata fuskarta, cikin shassheƙar kuka ta kuma cewa, "Dad! My nose is bleeding, zan mutu, gabaɗaya ya rikice ya rasa inda zai tsoma rayuwarsa ya ji daɗi. Bai san amsar da zai ba ta ba, iya sorry kawai yake iya furta mata. Har yanzu motocin nan na biye da motarsu, lokacin da ya fara jin saukar alburushin bindiga a bayan motar a gigice ya karya kwana ya faɗa wani kurmin daji, mai duhun gaske, shi kansa bai san ina zai dosa ba, ga manya-manyan bishiyoyi da suka cunkushe hanyar, a ruɗe ya yi parking ɗin motar ya zagaya ta back seat din motar jiki na kyarma ya zura hannu ya ɗauko Angel, daga ita sai rigar barci a jikinta, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, da gudun gaske yavyi cikin dajin da ita yayin da take sa6e avsaman kafaɗarshi. Hasken motarsa ne da ya bari a kunne yake haskaka masa gabansa, yana cikin gudun nan ba tare davya ankara ba, ya ɗaura kafarsa saman wani ƙarfe mai tsatsa, wanda ke a tsire cikin ƙasa, kaifinsa tamkar na wuƙa, zuruf karfen ya shiga ta cikin tafin ƙafar ya 6ulo ta sama, wani irin raɗaɗin azaba ne ya kai masa ziyara, tsikar jikinsa duk ta tashi, tuni jini ya wanke ƙafarsa, sam ya kasa motsawa daga tsayen da yake a hankali ya shiga furta, "Innalallahi wa'inna ilaihir raji'un." Cikin kyarma yake ambaton hakan, muryar Angel ce ta katse shi, "Dad let's go home, nan fa daji ne, akwai kura da zagi za su cinye mu. Daddy ko dai mafarki muke yi ne?" Ta yi tambayar still tana shassheƙar kuka. Cikin sanyin murya ya ba ta amsa, "Mafarki ne Angel, ba gaskiya ba ne." Hannayenta ta sanya tare da zagayo da su ta wuyansa, ta manna masa kiss a gefen fuskarsa, "Daddy, to mu tashi daga mafarkin, Angel tsoro take ji." Tamkar ya fashe mata da kuka haka yake ji, A tsiyace suka kwararo da gudu cikin dajin da ya shigo da motar, ai ko da jin sautin shigowarsu, bai san lokacin davya fisgi ƙafarsa ba, ya ɗago da ita daga jikin ƙarfen, jini ya dinga kwaranya. A haka ya dinga jan ƙafar har ya karaso daidai wani uban rami mai zurfi wanda kasansa tafkeken ruwa ne ke gudana, tsayawa ya yi zuciyarsa na raya masa cewar ya jefar da Angel cikin ruwan, ya ƙwammace ta mutu a cikin ruwan dacta yi mutuwar wulakanta a hannun mutanen da suka biyo su, don babu ɗigon imani a kansu, in suka kama mutun fetur suke zazzaga masa su ƙona shi har lahira. Ya yi zurfi a cikin tunanin Angel sai kuka take yi, sautin motocin miyagun da suka biyo shi ne yasa shi dawowa cikin hayyacinsa, Allah Sarki yana ji yana gani haka ya ɗaga Angel sama ya yi wurgi da ita, tsulundum ta faɗa cikin tafkeken ruwan mai zurfin gaske yana jiyo sautin kururuwarta. Ba ƙaramin tashin hankali ba ne zai sa uba ya yi silar mutuwar ɗiyarsa. Saboda tsabar kuka jikinsa har jijjiga yake yi, duk ya ji ya tsani kansa. Don tuni ya fitar da rai da rayuwa a cikin duniyar nan, domin kuwa Angel tamkar numfashi take a gare shi, jiki a mace ya zube saman guiwowinsa a gaban ramin wani irin jiri ne ya soma kwasar shi, nan take ya yanke jiki ya faɗi a mace. A daidai lokacin suka ƙaraso da motocinsu, bayan sun yi parking sun kewaye shi, wasu gabza-gabzan samari ne suka fito, ƙirar Samudawa, baƙake wulik! Babu ɗigon imani a kan fuskokinsu, sun yi shigar bakaken kaya da alama bodyguards ne, a tare suka buɗe wa iyayen gidan nasu murfin motocin don su fito. Abin ban mamaki, manyan mutanane dattawa, suna sanye cikin shiga ta mutunci wato shigar Hausawa, shadda har da malun-malun kai ka ce mutanen arziƙi ne. Koda fitowar su, ba su dora idonsu a kan komai ba sai a kan gawar Taj dake yashe cikin ciyayi. Guntun tsaki ɗaya daga cikinsu ya ja, "Mala'ika ya riga mu ɗaukar ransa, ba haka na so ba." Na gefensa ya ce, "Ban so ya yi salahar mutuwa irin wannan ba, amma duk da haka ba mu makaro ba, tun a nan za mu fara azabtar da shi kafin mu mika shi hannun Munkar da Nakir." Tuntsirewa suka yi da wata irin mahaukaciyar dariya, lokaci guda kuma suka ɗaure fuskokinsu. Ɗaya daga cikin manyan mutanen ne ya juya tare da kallan ɗaya daga cikin miyagun da suka zo da su, cike da ba da umarni ya ce, "Miƙo mini galon ɗin fetur tare da lighter." A hanzarce wanda ya yi wa magana ya nufi motocinsu. "Maganin masu kunnen kashi ke nan, an gaya musu shiga gonarmu abuvne mai sauƙi." Bai kai ƙarshen maganar ba, aka miƙo masa galon din fetur yasa hannu ya kar6a, cire murfin ya yi tare da zazzage masa fetur ɗin a jikin rigarsa, sharkaf suka wanke shi. Dalilin da yasa za mu ƙona shi, saboda gudun mu bar wata hujja da zai sa a zarge mu. Ba su ƙyasta lighter ɗin ba, har sai da suka kusa shiga motocinsu tukunna ya ƙyasta ya jefe saman ciyayin dake a kewaye da shi. Da gudu wutar ta shiga cinye ciyayin har ta hau saman jikinsa. A lokacin sun shige cikin motocinsu, da gudu suka fisge su tare da barin cikin dajin. Cikin ƙanƙanin lokaci, wutar tacinye shi ƙurmus. *To Jama'a Zaku ga nasanya Farkon labarin nayi hakan ne don in tariyo maku daga inda zamu tashi fatan an waye ni* *waɗan da su ka shirya yin payment zasu iya farawa, 08103884440 cikin wata mai zuwa free pages book one zai ƙare, Ina yi ma kowa fatan alkhairi, sai mun haɗu a next page in Allah yakai mu da rai da lafiya* *💋Boss Bature✍️💋**💋KURKUKUN ƘADDARA💋* _daga alƙalamin Boss Bature✍️_ *Dedicated To Aunty Kubra❤* *E8* Hasken rana ne ya haske fuskarta, sakamakon windown bedroom ɗinta da ta bari a buɗe, dogon numfashi ta ja tare da buɗe kumburarrun idanuwanta waɗanda suka yi luhu-luhu da su sun ƙanƙance saboda kukan da ta sha a daren Jiya. Kwance take a saman gadonsu, jikinta duk ya yi nauyi sam ta kasa motsawa, gefe da gefe na gadon ta kalla don ta ga ko Uzair ya dawo. Ras ta ji gabanta ya faɗi ganin still bai dawo gidan ba, hankali a tashe ta yunƙura ta miƙe zaune tare da wurga idanuwanta kan agogon bangon, ƙarfe tara na safe ko sallar Asubahi ba ta samu ta yi ba, saboda nauyin barcin da ya ɗauke ta. Siraran hawaye ne suka gangaro daga cikin kwarmin idanuwanta har izuwa saman kuncinta, masu ɗumi, harshenta ta sanya ta ɗan lashi gefen bakinta inda ruwan hawayen ya gifta. Daƙyar ta samu ta lalla6a ta sauko daga saman gadon, still riga da wandon jiya ne a jikinta, kanta babu mayafi, sumar kanta ce da ta zubo mata ta ko'ina ta yamutse. A hankali take tafiya harta shige toilet, after some minutes ta fito daga cikin toilet ɗinta, da alama alwala ta yi, lemar ruwa ce a fuskarta da hannayenta. Cikin wani irin yanayi na jin faduwar gaba, da tsinkewar zuciya, ta nufi closet ɗin kayan su, buɗewa ta yi tare da zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta, ta sanya a jikinta. Saman dardumar dake shimfiɗe ta tsaya, a tsanake ta kabbara sallah, cikin nutsuwa ta soma yin ibadarta. Bayan ta kammala, zama tayi saman dardumar tare da ɗaga hannayenta Cikin harshen larabci ta soma yin addu'o'inta daga ƙarshe ta rushe da matsanancin kuka tana faɗin. "Ya Allah Ka dawo mun da mijina lafiya,Ya Allah ka karemun shi aduk inda yake! inaji araina kamar wani mummunan abu ne ya faru da shi, Uzair bai ta6a tafiya batare da sanina ba. Amma jiya ya tafi ya barni in the midnight without my knowledge," Sosai take yin kukan ta jima, kafin ta yanke shawarar zuwa Wurin taj donta tambaye shi idan Sunyi waya da Uzair." Miƙewa tayi da sauri, ta fito daga Cikin bedroom ɗinta, ta nufi hanyar fita daga falon, a bakin gate ta samu maigadin gidanta zaune saman benci yana sauraron radio. Tunda ya hango ta ya yi saurin ajiye radio ɗin saman bencin ya mike ya tunkare ta, "Barka da safiya hajiya, kun tashi lafiya."Ba ta amsa mashi sallamarshi ba, saboda ba ta acikin natsuwarta, "Inaso zanje wurin taj ne, may be sunyi waya da uzair, wlh nadamu sosai nakasa samun natsuwa baba, inaji kamar wani abu ya faru da shi," Tana magana hawaye na fita daga cikin idanuwanta. Tsananin tausayinta ya kama baba maigadi, tunda yake bai ta6a ganin hawayen Aneelerh ba, sai a daren jiya da kuma yau, ya lura da tashin hankalin dake akan fuskarta. Cikin sanyin murya yace"Kiyi haƙuri ki kwantar da hankalinki, in sha Allah uzair yana cikin ƙoshin lafiya, babu abin da zai faru da shi." Gyaɗa mashi kai ta yi tare da wuce shi ta nufi gate ɗin, Hannu tasa ta buɗe ƙopar jikin shi ta fuce daga cikin gidan. Girgiza kai maigadi ya yi ji yake da a ce yana da halin da zai iya taimakon Aneelerh a yau daya taimaketa, abin da ciwo ka ga mutumin daya saba kyautata maka a cikin wani ƙunci na rayuwa kuma baka da yadda za ka iya taimakon shi, komawa yayi jiki asanyaye ya zauna saman bencin. Bayan fitar Aneelerh, kai tsaye ta nufi gidan Taj dake a jikin gidansu, tun abakin gate ta hango maigadin gidanshi a tsaye ya jingina bayan shi jikin gate ɗin, fuskar shi duk a harmutse da alamun damuwa atattare da shi, hakanan taji gabanta yayi wani irin mugun bugu ras! Ƙarasawa inda yake tsaye tayi muryarta da fargaba atattare da ita ta ce, "Assalamu alaikum" Tunkan takai ƙarshen maganar taga ya ɗan firgita, sai daya kalleta tukunna Yaɗan saki fuskarshi yace"wa'alaikum salam, malama Aneelerh, in ce ko lafiya?'' Hawaye ne suka sake wanke fuskarta, cikin shessheƙar kuka ta ce, "Har yanzu uzair bai dawo ba, yanzu ma zuwa nayi wurin taj, don inji idan ya kira shi awaya," Tana kai ƙarshen maganarta baba maigadi ya ce, "Innallahi Wa'inna Ilaihir raji'un!" A ruɗe ta ce, "Baba lafiya?" Cikin tashin hankali ya ce, "ƴar nan tun jiya na gaza samun kwanciya hankali, ko runtsawa ban yi ba, saboda damuwa, jiya bayan kin zo neman Taj, kin tafi na shiga daga Cikin ɗakina na kwanta, har bacci na fara bacci sama sama, can cikin dare wuraren ƙarfe ɗaya da rabi, ina kwance na ji fitar mota daga cikin gidan nan. A firgice na farka na fito daga ɗakina, koda na fito naga gate a wangale, na leƙe banga komai ba, na dawo na duba naga babu motar taj da yake yawan fita da ita, a nan na gane cewa shine ya fita cikin motarshi." Tunda ya soma magana Aneelerh ta dafe ƙirjinta da tafin hannunta, ta zazzare ido tana kallon shi, "Na yi mamakin ina Taj ya tafi batare daya sanar dani ba! domin kuwa tunda nake aiki a ƙarkashin shi bai ta6a lekawa koda ƙofar gida batare da sanina ba, amma sai gashi jiya tsakar dare ya fuce, kuma abun da ya ɗaure mun kai, ba shi kaɗai ya tafi ba. Hada ANGEL!" A gigice Aneelerh ta shiga ambaton Innallahi Wa'inna Ilahir raji'in! Na shiga Uku! Wai meke faruwa ne? Wayyo Allahna!" Gabaɗaya ta bi ta ruɗe, shi kan shi baba maigadi da ya sanar mata, sai da yayi danasani ganin yadda ta daura hannayenta a saman kanta tana zabga salati. Juyawa tayi da gudun gaske Ta koma Cikin gidanta, A lokacin malam Garba maigadinta Yana zaune saman bencin yaga shigowarta a guje, har yana tambayarta lafiya, amma bata saurare shi ba. Hankalinshi ya ƙi kwanciya, Miƙewa ya yi da nufin yaje su yi magana da tajo,yana ƙokarin fita daga cikin gidan, baba maigadin gidan Tajo, ya tura kofar gate ɗin, suka yi kicibus da juna. "Wai meke faruwane ɗan ladi"malam garbane yayi mashi tambayar fuskarshi a yamutse. Baba maigadi ya ce, "Tun ɗazu naso in zo mu yi magana. Amma damuwa ta hana ni, lamarin dai babu daɗin ji." Nan ya kwashe duk abin da ya faru na tafiyar Tajo tsakar dare ya sanar da shi." Malam Garba ya hauyin sallallami, hankalinshi duk ya tashi a rude ya ce, "Indai kuwa haka ne akwai matsala. Ya kamata a sanar ma Ƴan sanda don a san abin yi tun kafin lokaci ya ƙure mana"!! Jinjina kai baba maigadi ya yi" ni ma abun da nake tunani kenan, amma mu ɗan ƙara jira kaɗan zuwa anjima" "Shikenan zan koma bakin aikina, zuwa anjima idan ba wani labari game dasu sai muje police station ɗin" a cewar ɗan ladi, daga haka suka yi sallama da juna. Ya koma gidan da sauri don ya barshi a buɗe bakowa Aneelerh kuwa bayan shigarta Cikin gidan. Afujajen ta nufi bedroom ɗinta ta shige, jikinta na kerma ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer, Call logs ta shiga ta dannawa numbar da tayi saving da Abie kira,Tana fara Ringing, Aka ɗaga wayar, muryar babban mutuncine mai cike da kamala Ta karade kunnuwanta, "Assslamu Alaikum daughter..." Tun kafin ya kai ƙarshen maganar, Aneelerh ta rushe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita..." Muryar Abie a ruɗe ya shiga kwala mata kira." Aneelerh lafiya kike kuka meya faru? Waya ta6a mun ke? ki buɗe baki ki yi mun magana!" Sai da ta yi kukan mai isarta, sannan ta soma magana cikin shessheƙar kuka"a...Abie..Uzair da Taj.." katse ta ya yi da cewa."me ya faru dasu? Wani ya rasu ne' "A'a, tun daren jiya Uzair ya bar gida wuraren ƙarfe tara, shi kuma Taj ya bar gidansa karfe ɗaya da rabi na dare, kuma ya tafi tare da Angel. Babu wanda yasan meya faru dasu, kuma dukansu layinkan wayoyinsu akashe, Abie ina cikin matsanancin tashin hankali." Lamarin ya girgiza abie sosai," Muryarshi cikin sigar lallashi ya ce, "ki kwantar da hankalin ki aneelerh, In sha Allah babu abun da ya faru da su, yanzu zan yi waya da uncle ɗinki, ki ɗan ƙara haƙuri." Cikin shessheƙar kuka ta ce"To Daddy, saina jika "ya ce" ki daure ki ci abinci, na san ba ki ci komai ba" Amsa mashi ta yi da to kafin suka yi sallama ta kashe wayar. Saman gado ta koma ta zauna zugudun cikin zullumi, salla kadai ke tada ta. Wuraren ƙarfe huɗu na marece, tana kwance magashiyan fuskarta ta kumbura tayi suntum, tunda tayi sallar la'asar bata cire hijabin jikinta ba, jiniyar motor ƴan sanda tajiyo daga waje Wii! wiii! ras! taji gabanta ya faɗi, fargabarta kada ace gawar Uzair kota taj suka kawo Cikin gidan, A hanzarce ta miƙe, da gudu ta fito daga cikin bedroom tana sauko ƙafarta cikin falon, adai dai wannan Lokacin mahaifinta Alhaji Muhammad falgore ya doko sallama, Yana sanye Cikin shiga ta alfarma, Shaddace fara tass taji guga, tare da malun malun, kanshi Na sanye Cikin hula, Bayan shi kuma Ƴan sanda ne su huɗu sanye cikin kakin su, ɗaya daga Cikinsu Uncle dinta ne kaninta mahaifinta me ruƙe da muƙamin dco(Divisional Crime Officer),Atare dashi akwai Ic (inspector crime) sai kuma Ipo(Investigation Police Officers) Su biyu ne ɗaya mace ɗaya Namiji masu tsayi da jiki ba laifi a launin fata baƙake ne, Zuba masu ido aneelerh tayi tana kallonsu batare da kiftawa ba, tasan aikin mahaifinta ne, mutunne mai ɗaukar abu da mahimmanci babu wasa a lamarinshi, Sam ba ta yi tsammanin zai yi report din case din wurin ƴan sanda ba, Sai gashi ɗungurugum ya taho dasu Gidan, Ganin ta yi tsaye tana kallonsu yasa Shi yi mata gyaran murya yace"Daughter Kece kika koma haka"? jin haka yasa ta nufe shi da sauri, tunkafin ta ƙaraso ya buɗe mata hannayen shi ta faɗa a kirjin shi, ta fashe ma shi da kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Hannu yasa yana shafa bayanta cikin sigar lallashi, kafin ya kalli uncle din nata yace dashi Bismillah su zauna"wuri suka samu kowa ya zauna saman sofa, Bayan ya raba jikinshi daga na aneelerh yace itama ta zauna, atare dashi suka zauna, Uncle Bash ƙusa yace"Aneelerh Why tun daren jiya daya fita baki sanar damu ba"? Cikin shessheƙar tace"Ae nayi tunanin zai dawo kafin da safe" Jinjina kai yayi"okey, yanzu ki natsu ki faɗa mana taya akai yabar gidan without your knowledge"? Ƙoƙarin buɗe baki tayi donta kora masu jawabi kamar yadda suka buƙata, nan take Wani irin yunƙurin amai yazo mata, da sauri ta miƙe daga saman sofa din ta watsa aguje zuwa bedroom ɗinta, Dco ya kalli Ramlat Jami'ar binciken da suka zo da ita yace da ita tabi bayan aneelerh, amsa mashi tayi da Okey sir, Kafin ta miƙe ta bi bayan aneelerh cikin bedroom ɗinta, Tana shiga tajiyo Sautin ƙaƙarin aman da aneelerh keyi acikin toilet, kaitsaye ta taka izuwa cikin toilet ɗin, Agaban Sink ta samu aneelerh tana ta kwara amai tamkar ƴar hanjin cikinta zasu fito waje, Ƙarasawa tayi har zuwa bayanta, ta sanya hannunta tana ɗan bubbuga bayanta, Tana yi mata sannu, Bayan ta kammala yin aman, Ramlat ta kunna mata fanfo, ta wanke bakinta tass, Takai hannu jikin tissue holder ta yago kaɗan ta miƙa ma aneelerh ta goge mouth ɗinta, daga haka ta ruƙo hannunta suka fito daga Cikin toilet ɗinta "Sorry dear ki kwantar da hankalinki, in sha Allah we will try our very best wurin ganin mun gano inda mijinki ya ke,"acewar Jami'ar binciken, Aneelerh dake ta faman fitar da numfashi mai ɗumi tace"Bana jin daɗin jikina, tun jiya banci komai ba, kuma bana jin zan iya cin wani abu," Ramlat tace"Ki daure kici, lafiyar ki muke buƙata, domin kuwa idan ba lafiya atare dake taya zamu iya samun haɗin kanki wurin yin investigation ɗinmu"? Takai ƙarshen maganar a lokacin sun dawo Cikin falon, Hankalin Dco da na sauran jami'an ya dawo kansu, mahaifinta kuwa jikinshi ba ƙaramin sanyi yayi ba, ganin yadda ɗiyar shi ta rame, tamkar ba neelerh ɗinsa ba, A gefen abie ta zauna tare da kwantar da kanta saman kafaɗar shi, Ramlat Ta kalli dco tace"Sir, bata da koshin lpy, kuma ta sanar dani cewa tun jiya bata Ci komai ba," Uncle bash yace"Idan har bata ci abinci ba, ba zamu iya samun bayanan da muke bukata ba awurinta," Yayi maganar eyes dinshi akan Abie, kafin ya mayar dasu kan Ramlat yace"ki duba frigde nasan baza a rasa abunsha ba, Ki ɗauko mata tare da ruwa me sanyi"Amsa mashi tayi"okey sir" kafin ta juya ta nufi fridge ɗin dake A falon" Hanmu tasa ta buɗe frigde din, Lemuka ne a jere masu sanyi, hada fura da youghurt, fresh milk ta dauko mata tare da ruwa"ta ruƙo bottles din a hannunta ta dawo ta ɗaura su asaman C table din dake agaban sofa din da aneelerh take, Uncle bash yace"Aneelerh ta shi kisha,"batare da musu ba, Aneelerh ta mike zaune, Takai hannu ta ɗauki milk ɗin ta buɗe ta kwafa abakinta, ta shiga ɗaɗɗakarta, makoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat!! Abie yace"Ki sha a hankali, kada ki shaƙe" janye bottle din tayi daga bakinta tana faman sauke ajiyar zuciya, lallai ba ƙaramar yunwa take ji ba, bayan ta ajiye milk din Abie ya dauki bottle water me sanyi ya mika mata, hannunta na kerma ta buɗe mufin ta kwafa abakinta, A hankali take shan ruwan harta kammala, Sai gashi ta ɗan samu natsuwa, Uncle bash yace"Aneelerh kiyi mana bayanin yadda komai ya faru a daren jiya, muna sauraronki" Ganin yadda zufa ke keto mata, abie yace ta cire hijabinta"hannu tasa ta ɗebe hijabin, dama akwai Kallabin data ɗaure kanta da shi, A tsanake ta soma Yi masu Bayani tiryan tiryan "Ji wuraren ƙarfe tara, nafarka ban samu uzair a saman gado ba, nayi tsammanin ko ya shiga toilet ne amma ko da na duba baya a ciki, na yanke shawarar zuwa na tambayi megadi,koda naje wurinshi yace mun Yaga lokacin da Uzair ya fita acikin motarshi, kuma har magana sunyi da shi kafin tafiyar shi, koda jin haka na dawo cikin gida na ɗauki wayata na kira layin uzair tana ringing amma uzair bai ɗaga ba, a ruɗe na ajiye wayar na fito na nufi gidan taj, ina zuwa na shiga gidan, A falo nayi mashi sallama, ya fito daga ɗakin shi, harma yayi shirin kwaciya, nake faɗa mashi Game da tafiyar uzair ƙarfe 9 na dare na farka banganshi ba, Nayi tunanin ko ya kirashi awaya, saboda kusancinsu dana sani, Uzair zai iya 6oye mun abun amma bazai iya 6oyema Taj ba, Shiyasa na tambaye shi,A wannan lokacin taj yace na jirashi ,Zaije room dinshi ya kira shi awaya, na tsaya ina jiranshi, koda ya dawo na tambaye shi ya kirashi,yace mun in kwantar da hankalina duk inda yake ayanzu yasan yana akan hanyar dawowa ne, ba don na yadda da kalamanshi ba, na dawo gida zuciyata duk a harmutse na kwanta, Ko a daren sai da taj ya kira layina, ya ƙara kwantar mun da hankalina, a wannan yanayin bacci yayi awon gaba dani, Shiru ta ɗanyi tana mayar da numfashi, kafin taci gaba da cewa"da safe na farka wuraren ƙarfe tara, still uzair bai dawo ba, Nan ma hankalina ya ƙara tashi, Na yanke shawarar zuwa Wurin taj don inji idan sunyi waya da uzair, koda ace ya kirashi tsakar daren jiya, Ina fita daga gida na nufi gidan taj, tunkafin ma naƙarasa naga baba maigadin gidan atsaye ya jingina bayanshi jikin Gate din gidan fuskarshi da alamun damuwa atattare da ita..............."Komai daya faru saida aneelerh ta sanar dasu, lokacin da aneelerh ta kammala zayyana masu komai, Lamarin yayi matuƙar girgizasu, ipo Yace"akwai matsala, Uzair ya fita gida ƙarfe 9 na dare, Shi kuma taj ya fita tare da ƴarshi ƙarfe ɗaya da rabi nadare? tabbas wani Babban al'amarine ya afku" Ramlat tace"Kuma dukansu atare da wayoyinsu suka fita"? Aneelerh tace"Shi uzair da wayarshi ya fita, Amma shi Taj banda masaniya akan hakan" Dco yace"Aneelerh zaki yi mana jagora zuwa gidan Taj don mu fara gudanar da binciken mu"Amsa mashi tayi"toh" kafin suka miƙe gaba ɗayansu suka ɗunguma zuwa gidan Tajuddeen, A bakin gate Dco Yace ma malam Garba yabi bayansu, Don shima zasu buƙaci jin ƙarin bayani awurin shi, Lokacin da suka ƙaraso bakin gate ɗin gidan Tajo, Baba maigadi Na zaune saman benci cikin zullumi, Dco yace shima Yabiyosu Cikin gidan,Ya miƙe yabi bayansu, A falon Gida Taj, Abie ya zauna, baba maigadi da malam garba suka zauna saman Carpet suna jiran tambayoyin da za'ayi masu, Aneelerh ce ta yi masu jagora zuwa bedroom ɗin taj, A bude suka samu ɗakin, Da sallama tashiga ciki, Dco da ic da ipo suka mara mata baya, A tsakiyar Dakin suka tsaya suna bin ko'ina da kallo, Karaf idanuwan Aneeleeh suka sauka akan wayar Taj dake yashe ƙasan tiles, A ruɗe tace"Uncle ga wayar shi anan" A tare police men din suka kai idanuwansu kan abunda aneelerh ke nuna masu, Hanky Ic ya curo daga cikin aljihun shi, a hankali ya taka zuwa inda wayar take a ƙasan tiles,ya zuƙunna tare da ɗaukota,Ya dago da ita ya juyo da ita, Screeen ɗin wayar ya fashe, sakamakon Bugun tiles da Tayi, Juyowa Yayi tare da kallon Dco yace"Sir, A hasashe na, Jiya Bayan aneelerh tabar gidan nan, Tajo Ya dawo Ya kwanta har bacci ya ɗauko shi, Wuraren ƙarfe ɗaya da rabi na dare, An kira wayar shi, kuma ya ɗaga kiran, tabbas an gaya mashi wani abu daya ɗaga mashi hankali, wanda yayi matuƙar razanar da shi, har baisan lokacin da yayi wurgi da wayarshi ba, Ya fito daga ɗakinshi Yaje ya ɗauki ɗiyarshi ya gudu da ita,tabbas anyi mashi barazanane, kuma zai iyayiyuwa anyi amfani da uzair wajen razanar da shi" Jinjina kai dco yayi"tabbas akwai wani 6oyayyen Al'amari, daya faru a daren Jiya, taya za'ae mu gano ainihin meya faru? Ipo yace"Abu na farko daya kamata muyi shine, mu fara tambayar masu gadin gidajensu A wani yanayi sukayi rabuwar ƙarshe dasu, sannan Wayar taj, Yakamata A gyarata, kodan mu samu damar bincikar last Call da yayi recieving awannan daren! Sannan zamu duba messages ɗin wayarshi, koda ace sun tattauna game da wani sirri dake atsakaninsu shida uzair" Gaba ɗaya sunyi amanna da maganar ipo, aneelerh dae Jikin ta ƙaura yayi la'asar,Tunda taji hasashen Ic gabanta Ya dinga faɗuwa rass rasss! Daurewa kawai take yi, Cikin falon suka dawo Kowa ya zauna, Ipo Ya kalli ɗan ladi baba maigadi na gidan tajo, yace"lokacin da taj zai fita A daren Jiya! Kaine ka buɗe mashi gate"Da sauri baba maigadi ya girgiza kai"a'a yalla6ai, Wlh ni bansan ma Ya fita ba, Kwatsam Ina Cikin Bacci sama sama Naji alamun buɗe gate, kafin inyi wani yunƙuri in miƙe inzo in duba,Tuni Ya fuce, Babu shi babu alamar shi, har waje na leƙa banga komai ba, na dawo cikin don in duba wurin ajiye motocin shi anan naga ya fita da ɗaya daga cikin su, Bayan haka kuma na shiga cikin gidan don inga ko ƴar shi angela na nan, sai naga babu ita, nan na gane cewa da ita ya tafi, Wannan shine iya abunda nasani, Jinjina kai Ipo ya yi kafin Ya mayar da idanuwanshi kan Malam garba me gadin gidan Uzairu,Yace"kaifa?Me ka sani game da tafiyar Uzair"? Malam Garba yace"Naga lokacin da uzair ya fita, har magana mun yi da shi, Abunda ya faru ina zaune saman benci ina sauraron radio, Sai ga Uzair ya fito daga Cikin gidan, Sai faman sauri yake yi, Ya buɗe mota ya shiga yayi mata key,Ya ƙaraso da motar Yana yi mun hon in buɗe mashi gate, Na taso Na buɗe mashi, har ina tambayarshi ko lafiya, naga zai fita a lokacin da bansaba ganin ya fita ba, ya ce mun babu komai, bazai jimaba yanzu zai dawo, Nayi ma shi Allah ya kiyaye hanya, wannan shine maganarmu ta ƙarshe da shi,' Jinjina kai ipo yayi"bayan wannan ko akwai Wani wanda ke yawan zuwa gidajensu? Har suna haɗa baki wurin cewa a'a, Dco yace"Yanzu Idan munason ganawa da iyayen kowannansu taya zamu same su"? ya yi tambayar yana kallon aneelerh, Cikin sanyin murya tace"surukaina basa ƙasar nan tun da jimawa suka tafi suwa south korea amma kwanan nan zasu dawo, Shi kuma taj Iyayen shi Suna zaune a Buzaye, Sun tsufa sosai, Ni aganina baikamata asanar dasu ba, Hankalin su zai tashi sosai,' "Bazamu sanar dasu ba, Amma Shi taj ina matar shi? Ipo ne yayi mata tambayar, Abie yace"ae shi Taj tunda matarshi ta haifi ƴarshi ta fari, ta gudu tabar gidan, Kamar yadda aneelerh ta sanar dani, Acikin bathtub tabar mashi jinjirar,Itace ANGEL yarinyarshi," Dco yace"Okey, Shine Yake auran ƴar gidan tsohon gomna, Alhaji Ubaid Sani wadata" Jinjina kai abie yayi eh shine, Ipo yace"Abunda za'ae yanzu, zamu fara bincikar wayar taj, wata'ƙil asamu wata shaida, Sannan zuwa gobe in Allah yakai mu, Zamu Kira Surukanki, don yakamata asanar dasu halin da ake Ciki, Shima Alhaji ubaid Zamu tuntu6e shi, Sannan Zamu Je gidan Radion da suke aiki, Dole mu binciki kowa dake atare dasu, idan Akayi sati ɗaya ba'aji ɗuriyarsu ba,Za'a Yaɗa labarin 6acewar su ta kafafan sada zumunta, Wata'ƙil adace" Sun jima suna tattaunawa Da ƴan sandan kafin su tashi tafiya, Sai da suka ƙara kwantarma Aneelerh hankalinta, Sukayi mata alkawarin zasuyi iyakar bakin ƙoƙarinsu, sosai suka bata baki, kafin Ƴan sandan suka tafi, Ya rage gidan daga ita sai Abie sai su baba maigadi, Umarni abie Ya basu dasu Cigaba da kula da gidajen, Kafin a ƙare Binciken, Ita kuma aneelerh yace Ta tashi su tafi gida, don bazai barta ita kaɗai agidan ba, ba don taso ba tabi bayanshi, A motarshi suka tafi,drivern gidansu ne ke tukasu, Tsawon One Week Ƴan sanda suna Bincike akan case ɗin, Basu samu komai ba,Har gidan radion su taj sukaje,Ɗaya bayan ɗaya Aka fiddo da ma'aikatan gidan radion suka yi masu tambayoyi, A Ƙarshen Satin Cikin Weekend Uncle abdallah Ya dawo ƙasar tare da Hajiya adama, duk arana ɗaya Suka shigo garin tare da Alhaji ubaid, Sun girgiza da jin abunda ya faru na 6acewar Su tajudeen Hajiya adama tasha kuka tamkar ranta zaifita, Haka Alhaji ubaid ya shiga matsananciyar damuwa Musamma da ya ji cewa tare da jikar shi Taj ya tafi adaren Ranar, yarinyar da yake gani tamkar ƴarsa benazir data gudu tabarshi tsawon shekaru, kasancewar shi babban mutun Wanda yasan mutane da dama, tun ranar daya shigo ƙasar Ya kira Cp(Commisioner Of Police)Sukayi zama na musamman Akan case ɗin 6acewar Su tajo, Gaba ɗaya Cp ya tattara Jami'an da suke akan aikin Binciken case ɗin, don yaji bayani daga garesu, Bakomai yafi ɗaure ma kowa kaiba, face Yadda aka rasa samun wata hujja da zata tona asirin abunda ya faru dasu adaren ranar, Wayar Taj da suke tunanin zasu samu Wata shaida atare da ita, koda Akaba me gyaran waya ya canza screen ɗin, Cikin rashin sa'a suka samu komai na wayar Ya goge, Duk zurfin binciken da Jami'an sukayi, Basu samu koda motocinsu ba, Saƙo da lungu na garin da bayan garin dare da rana haka sukayi binciken amma basu samu wata shaida ba, A ƙarshe binciken ya koma CID, Labarin 6acewar Su taj ya karaɗe social media, Ta ko'ina zancen 6acewarsu a keyi, Mafi rinjayen mutane sunfi tunanin An kashesu ne a 6oye, Tunda kowa yasan su da son fiddo da gaskiya, kota halin ƙaƙa, Wannan yasa mutane su ke Hasashen kodai an kashesu a 6oye ne Allah shine mafi sanin dai dai!!! Rayuwar Aneelerh gwanin ban tausayi baiwar Allah, Ta jigata sosai, ta shiga mawuyacin hali na rayuwa, ta rame sosai ta ƙanjame hatta aiki Abie ya hanata zuwa tunda ba ƙoshin lafiya gareta ba, Rashin Uzair da taj da kuma ANGEL ba ƙaramin nakasa rayuwarta yayi ba,Tayi kewarsu sosai,a kullum addu'arta Allah ya bayyanar dasu aduk inda suke, saboda su takan tashi tsakar dare tayi nafilfili, tayi masu addu'a Tana kuka,Haka rayuwarta taci gaba da kasancewa, Abinci kanshi sai abie da mami sun tasata gaba tukunna take Cinshi, a karshe da ciwon nata yayi yawa, Dr ya duba ta, Ashe hada laulayin Ciki, Allahu akhbar Abunda suka jima suna rokon Allah ya basu ita da uzair, Ga shi Yau Allah ya kar6i addu'arsu a lokacin da shi uzair ɗin Bayanan, Allah sarki rayuwa kenan. A 6angarensu Hajiya adama kuwa, basu koma south korea ba, Anan suka Ci gaba da zama, saboda halin da ake Ciki na 6atan Ya'yansu ,kullum Cikin zullumi suke, Akwana Atashi Yau wata ɗaya cuff da 6atansu tajuddeen, A lokacin Kowa ya fara sarewa, Tuni ƴan sanda sun sallami su baba maigadi, makullan gidajensu Yana a hannun jami'an CID, sun ruƙe su har zuwa lokacin da zasu kammala bincikensu, Tun Uncle abdallah Yana 6oye wa Mutanan Buzaye game da 6atansu Tajo, harya yanke shawarar zuwa buzaye don ya sanar dasu halin da ake Ciki, A ranar da suka shirya tafiya tare da hajiya adama suka Bi jirgin asubahi zuwa katsina state, A hotel suka sauka, A washe gari su ka wuce zuwa buzaye, Lokacin da suka isa garin da safe, a ƙopar gidansu Malam zahiru suka risƙi mutane zazzaune saman tabarma, nan fa hankalinsu ya tashi, Sunzo da mummunan labari Sun riski labarin dayafi nasu ɗaga hankali . Mutanan da suka samu a ƙopar gidan, Ƴan zaman makoki ne, Allah ya yi ma iyayen tajuddeen rasuwa su duka Biyun, Malam Zahiru ne Ya fara Rasuwa sakamakon Hatsarin Da yayi, Yana Cikin tafiya gefen titi ya dawo daga gona zashi gida, Wata mota ƙirar dab,Ta biyo ta titin da gudun gaske kaitsaye tabi takanshi, Ashe burkin motar ne Ya samu matsala, Duk yadda drivern dake tuƙa ta yaso Ya yi control ɗinta abun Yaci tura,Gaba ɗayansu suka mutu a wannan lokacin, Tunda labarin mutuwar shi ta riski Yahanasu mahaifiyar tajuddeen taji mummunar mutuwar da Mijinta yayi,nan take Zuciyarta ta buga ko shurawa batayi ba, innalallahi'wa'inna ilahirraji'un!!!Uncle abdallah yaji mutuwar ɗan uwansa,duk yadda yaso ya jure hakan ya faskara tamkar ƙaramin yaro haka ya dinga kuka,mutane suna lallashinshi, Hajiya adama saboda tsabar kiɗima har suma saida tayi, Ciwo gadan gadan Ya taso mata, A nan gidan deeje suka xauna mahaifiyarsu Uncle abdallah, ita kanta deeje batasan inda kanta yake ba Tun bayan rasuwar malam Zahiru Ta kamu da ciwon paralyse, Laraba ƙanwar yahana su Ce ke yin jinyarta, da wasu daga cikin ƴan uwansu na nan buzayen, Kafin Barin su uncle abdallah buzaye, Itama deeje Allah yayi mata rasu wa, Wa'iyazubillah Babu wanda bai tausaya ma Uncle abdallah ba, lokaci ɗaya ya rasa ya'yan shi da suka 6ace,Ya rasa ya'yan shi da matar sa yanzu kuma Yayi babban rashi na mahaifiyarsu deeje, Lamarin dai babu daɗin ji! Kusan wata ɗaya su ka yi A buzaye kafin suka tattara yanasu yanasu suka koma Jos, Zaman ƙasar gaba ɗaya ya gagaresu, Babu wani Labari me daɗi, a ƙarshe suka tattara suka koma south korea, Cike da zullumin Me zai biyo baya, Don sunyi magana da Ipo, ya yi masu alƙwarin duk halin da ake Ciki game da bincikensu taj zai kira su awaya ya sanar dasu, Shima Alhaji Ubaid, Sun ƙare magana da Jami'an dake bincike a kan case ɗinsu Tajuddeen, sun yi mashi alƙwarin zasu yi iyakar bakin ƙoƙarinsu,wurin Bincikar ainihin abunda ya faru da su,kuma zasu binciko su aduk inda suke muddin suna a doron duniyar nan!,kuma duk halin da ake aciki zasu dunga tuntu6arshi akai kai, A 6angaren Aneelerh kuwa,Komai Ya hargitse mata baiwar Allah, Ga rashin da ta yi Ga kuma Laulayin Ciki da take fama dashi, kullum cikin yin kuka take, tsananin tausayinta ya kama su Abie, Kowa lallashinta yake yi, Akan tayi hakuri tabarma Allah komai, tun daga wannan lokacin ta hana idonta bacci,Takan tashi tsakar dare tayi nafilfili duk don saboda su Angel,idan tafara nafilfili har sai kafafunta sun fara yi mata zogi tukunna take dakatawa, idan kaga aneelerh tayi bacci to da rana ne, domin kuwa ta maida dare lokacin yin ibadarta, kullum rana ta Allah sai ta yi masu sadaka, bayan haka ta yi magana da abie akan A nemo manyan malamai su taya su da addu'a kuma ayi masu sauka, batare da 6ata lokaci ba, Abie Ya aiwatar da duk wani abu da Aneelerh ta bashi shawara akai, Ƴan sanda Sun Dage damtse wurin Yin Bincike,Yayin da malamai suka Bada himma Wurin taya su addu'a da kuma yi masu sauka, Haka zalika su aneelerh Sun taka rawa wurin Yi masu addu'a, da sadaka, akan Allah ya bayyanar dasu,wannan kenan.. Shin ya rayuwar Angel ta ƙare a cikin ruwan da mahaifinta ya jefa ta? Ta rayu ko ta mutu? Bayan wasu ƴan kwanaki da Tajuddeen ya jefa ta a cikin ruwa, hadari ne Ya haɗu bakikkirin a sararin samaniya, kafin wani lokaci yayyafi Ya soma sauka a doran ƙasa. Daji ne mai manya manyan bishiyoyi da tsirrai, kowane ganye ka kalla yayi kore shar da shi, gwanin ban sha'awa, musamman ciyayin da ke cikin dajin masu tsayi da cukowa, a daidai wannan lokacin garken shanu suka shigo cikin dajin. Aƙalla sun kai talatin da biyar, suna tafe suna Cin ciyawa. Wucewarsu keda wuya cikin dajin,Wata kyakkyawar bafullatanar daji, fara tass Jawur da ita, sanye cikin kayansu na al'ada, Ta bayyana hannunta ruƙe da sanda, siririyace Bata da ƙiba ko misƙala zarratin gata doguwa sam6al, Amma akwai dukiyar fulani cike tab da ƙirjinta, ga yalwataccen gashin kai dake gareta mai tsayin gaske, anyi mata kitson kalaba,Wanda yasha ado da duwatsu,wutsiyoyin gashin sun sauka har tsakiyar bayanta, ga wasu da suka zubo ta gefe da gefe na fuskarta, Tabarakallahu ahsanul khaliqin,Wasu dara daran idanuwa gareta Farare Ƙal kamar fatar farin Cikin kwai, Launin Idon nata Brown Colour ce, tana da kwarin ido sosai,Ga ziraran Eyelashes, Jagirarta tamkar anzanata saboda tsaruwarta, Ga wani dogon hanci da Allah yayi mata, siraran la66anta jawur dasu, Akwai kwalliyar ɗige ɗige asaman fuskarta har goshinta, Wuyanta na sanye da sarkoki, Haka hannunta ma akwai awarwaro,Tana da hujen hanci mai shegen kyau, idan tayi dariya kuwa wayyo Allah madarar kyau, Kai kace gonar audugace, Saboda kyan fararen hakoranta masu tsari, wani ƙarin kyan dimple biyu gareta wanda ko magana take yi, sai sun lotsa,A ƙalla Bazata Wuce shekara Goma sha Shida ba, Tafiya take Yi a bayan shanayen tana Korasu da sandar hannunta, Wani Lokacin Har rawa take Yi tana jujjuya Jikinta, Da alama ba ƙaramin daɗin yanayin garin take ji ba, ko kusa bata jin Sanyi, Burinta A ruwan sama ya sauka sosai don tayi rawa acikinsa, kamar yadda ta saba, Fararen kafafuwanta na sanye Cikin takalma, Cikin harshen fulatanci ta soma raira waƙa, Tana cikin yin waƙar ruwan sama ya soma sauka tamkar da bakin kwarya, Wani irin farin Cikine Ya lullu6eta, Cikin harshen fulatanci tace"Ni ɗin Jinin nasara ce, Mai nema mai samu,Mai nasara mai sa'a, Daga Yin magana Gashi ruwa ya sauka wuhuhu Sai ni DANEJO" Rawa Tashiga Yi acikin ruwan Yayin da shayenta suka duƙufa Cikin dajin suna kiwo, Juyi ta dinga yi tana karkaɗa qugu, ruwan saman duk ya jiƙe kayan jikinta sharkaf, sun manne mata,Ƴar rigar jikinta bata rufe Cibinta ba, Sai ɗan zanin data ɗaura, kallabin kuma taci ɗamara dashi, Tana Cikin Yin rawar nan Cikin rashin sa'a ta ɗaura ƙafarta saman wani dutse dake a bakin Ramin da wannan tafkeken ruwan yake, Gaba ɗaya Dutse ya jirkice, A gigice Ta fasa Uwar ƙara, duk yadda taso Ta hana kanta faɗawa Cikin ramin amma hakan ya faskara, Domin kuwa gaba ɗaya Ta rufza Cikin Ramin, Tsulum Ta nutse Cikin ruwan, Within Seconds Ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman haki kamar wadda tasha gudu, Gaba ɗaya gangar jikinta tana acikin ruwan, Iya kafaɗarta Ya tsaya, Idanuwanta sunyi luhu luhu dasu, Ƴan hanjin cikinta sun kaɗa, Hankalinta ya ɗunguzuma, Ba ruwan bane damuwarta, don tun tana ƴar ƙarama Baffanta Ya koya mata Ruwa, Babbar damuwarta shine taya za'ae Ta fito daga Cikin Ramin? Rushewa tayi da kuka cikin harshen fulatanci ta soma Kiraye Kirayen Sunayen Ƴan uwanta donsu kawo mata ɗauki,   "Inna wuro,Adda!Nanne!bawuro!Wayyo Allah Na babu wani akusa da zai kawo mun ɗauki"? tana Cikin wannan yanayin Shanayen ta Suka Leƙo Cikin Ramin Kamar sunji abunda take cewa, sun kewaye ramin suna ta kuka Emmoh !emmoh!   Nuna su Tayi da yatsan hannunta"Banga amfaninku ba, Ciyawa kaɗai kuka Iyaci,"cike da takaici tayi maganar,Tana Cikin sambatun nan, Aka kwatsa Tsawa mai sautin gaske a gigice Ta nutsar da kanta Cikin ruwan don ba ƙaramin tsorata tayi ba sosai ruwan saman Ke safka da ƙarfinshi, Lokacin da danejo ta nutsa kanta Cikin ruwan a tsorace sakamakon Tsawar da aka kwatsa, Ba zato Ba tsammani idanuwanta suka sauka akan Kyakkyawar Yarinyar dake kwance saman dutsen dake a ƙasan ruwan mai girma da faɗi, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, rigar Jikinta duk ta nannaɗe ta manne mata, biji biji take iya hangenta saboda ƙasan Ruwane Waro ido waje daneju tayi a matuƙar tsorace take kallon Yarinyar, Shin mutunce ko aljan, Abunda ta fara sakawa aranta kenan, tunawa da wata tatsuniya da Nannensu ke basu, Akan macen kifi, nan da nan tsoro ya ɗarsu acikin zuciyarta, A gaggauce ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan Tana faman Mayar da numfashi, Waswasi ta shiga yi acikin zuciyarta,Anya Yarinyar data gani Acikin Ruwan Mutunce? kodai ta macen kifi ce ko ɗan ruwa? ta jima tana wannan zancen Zucin Kafin Ta kuma nutsa kanta Cikin ruwan, Cike da fargaba ta nufi inda Yarinyar take saman dutse har Allah ya kawota Saitin Inda yarinyar take, Hannu biyu tasa Ta ɗaukota, Sama tadinga yi Har ta fiddo da kanta daga Cikin ruwan, Natsuwa tayi tana kallon kyakkyawar yarinyar, Daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba, Allah kaɗai yasan Tun wani lokaci take kwance a ƙasan ruwan, Cikinta yayi 6ul6ul dashi,Da alama Ta shaƙi ruwa sosai, Mu haɗu a next Page don jin yadda zata kaya, Jama'a an rasa shaidar da zata bayyana abunda ya faru? taya kenan za'a san meya faru dasu Taj?Su wanene waɗannan Mutanan masu haɗarin gaske? shin danejo zata taimaki angel? Idan ta taimake ta kuna tunanin angel yarinya mai ƙiriniya zata juri zama a hannun fulanin daji? ya zata rayu batare da mahaifinta ba? Duk dai acikin littafin kurkukun ƙaddara zaku samu amsoshin tambayoyinku, Tafiyar ta dabance salon ma na daban ne, a kullun burina in kawo sabon salo wanda ba'a ta6a ganin irin shi ba, Allah dai ya taimaka, Waɗanda suka shirya yin payment na kurkukun ƙaddara 500 ne, Suyi mun magana ta layi na 08103884440.*💋KURKUKUN ƘADDARA💋* *dedicated to Aunty kubra❤* _Daga alƙalamin Boss Bature✍️_ *E9* At first sight da Danejo ta kalli fuskar yarinyar, sai taji tsananin tausayinta, Kuma nan take taji tana son ta taimaki rayuwarta. Tunda ta ayyana hakan azuciyarta sai taji ta daina Jin tsoron tafkeken ramin Ramin, kodan saboda Yarinyar zata yi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin ganin ta ceci rayuwarta. Dabarace ta fado mata aranta, Da sauri ta sanya hannu ɗaya, ta Kwance kallabinta data ɗaura ɗamara dashi, Ɗayan hannun kuma na dafe da yarinyar, a saman bayanta ta goyata, kafin a hankali ta cigaba da matsawa cikin ruwan harta ƙaraso jikin gwamagwaman duwatsunan dake kewaye da wurin, jikinsu akwai hudoji, tsaf mutun zai iya daddafawa ya haura sama, Sai dai yana da matuƙar hatsari idan Duwatsunan Jiki suka 6allo, mutun zai iya jin mummunan rauni ga shi ita harda goyo. Cike da fargaba danejo ta sanya hannayenta, ta dafa jikin dutsen A haka tadin ta tafiya tana bin jikinsu, Har Allah ya taimaketa ta hauro sama, tana faman Mayar da numfashi, da sauri ta sanya hannayen ta tare da warware goyon da tayi mata, ta sauko da ita a hankali ta kwantar da ita saman ciyayin, ɗagowa tayi tare da kallon shanayenta dake ta kuka, Ta wurga masu harara don ba ƙaramin haushin su take ji, daga gani dai akwai ƙuruciya atattare da ita. Mayar da idanuwanta ta yi akan fuskar yarinyar, ta sanya hannu tana yaye sumar kanta data rufe fuskarta. Tayi wani irin haske, ƙananun la66anta sunyi pink sosai suka ciza, duk irin kyan danejo saida tayi mamakin Tsantsar kyawun yarinyar data tsinto acikin ruwa. Hannayenta ta ɗaura Asaman ƙirjinta tashiga dannashi, Nan take ruwa ya sona fesowa Ta bakinta da hancinta, cigaba da dannawa tayi har saida ruwa Ya daina zubowa, natsuwa Tayi tana kallonta, ta yi tunanin zata farka amma sai taga ko motsi ba ta yi ba, Da sauri ta jogana kunnanta saitin Zuciyarta don taji, idan tana harbawa a razane ta ɗago, ranta duk ajagule fargabarta kada ace yarinyar tarasa ranta. Tunawa tayi da saman dutsen da ta ganta akwance, hannu tasa ta juyo da bayanta, ta cusa yatsun hannunta acikin sumar kanta data cukurkuɗe, har saida ta taddo fatar kanta fara sol, Anan taga Raunin data ji, ashe kantane ya ɗan fashe daga baya, sakamakon buguwa da kanta yayi jikin dutsen, A ruɗe danejo ta miƙe tare da daukarta, ta sa6eta saman kafadarta, Sam ta manta da shanayensu, hankalinta na akan Yarinyar dake Cikin mawuyacin Hali, Watsawa Tayi da gudun gaske tamkar zata tashi sama, Tana Cikin gudun nan, wani bafullatanin Sanye cikin kayan fulani, da ƴar hularshi, Hannunshi ruƙe da sanda zai gifta, Karaf idanuwan shi sauka sauka a kan danejo dake ta tsala gudu, Mamaki ne ya kama shi, ɗaga murya ya yi tare da kwala mata kira, har cikin kanta tajiyo kiran da ya yi mata, Batare da ta juyo ta kalleshi ba ta amsa mashi da na'am, Cikin harshen fulatanci Yace inata baro masu shanayen su kuma menene ta dauko a hannunta, tace ma shi suna can suna kiwo, Yaje ya cigaba da kula dasu,"daga haka bata ƙara cewa uffan ba, Girgiza kai Bawuro yayi a ranshi yace bazata ta6a canzawa ba, daga haka ya nufi Cikin dajin inda shanayen su suke, Danejo kuwa bata nufi ko'ina ba, Sai wuraren wasu Bukkoki rukuni rukuni a ƙalla sunyi Shida, A gefen ɗaya daga Cikin bukkokin wani tsohone tukuf zaune cikin kayan fulani, daga gefe kuma Wasu Manyan matane, Sun kwan biyu aduniya, Sai sussukar gero sukeyi, ga wasu kuma Ƴan mata su biyu matasa Suna 6arar masara, Tundaga nesa Tsohon Ya hangota, da ƙarfi ya ambaci sunanta DANEJO, lokaci ɗaya sauran Mutanan suka ɗago suna kallonta, Ganin yadda take ta gudu yasa duk sukayi tunanin ko wani mugun abunne yabiyo ta, aikuwa aguje Suka nufi Cikin bukkokinsu kowa ya ɗauko makaminshi, Shima tsohon ya miƙe yana ɗangyale ƙafa ya shige cikin bukkar gefen shi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da Ma shi, (to fa yaƙi ya ta shi) Ƙarasowa tayi tana ta faman haki, lokacin da suka lura da abinda ke ruke a hannunta sai kowa ya ajiye makaman yaƙinsa, suka tattara hankulansu akan yarinyar data ɗauko, A saman Shimfiɗar kakansu ta sauke yarinyar, tare da ɗagowa ta kalli kakansu cikin harshen fulatanci tayi mashi bayanin inda ta tsinceta, koda jin hakan Jiki Na rawa Ya koma Cikin bukkarshi, Sai ga shi ya fito hannun shi ruƙe da ƴar jakkar fata, a gefen shimfiɗar ya sauke jakkar, Yace ma danejo ta nuna mashi inda taji ciwon, rubda ciki ta kwantar da ita, tasa hannu ta yaye sumar kanta, nan suka ga raunin da taji, Bude jakar yayi ya curo wasu magunguna nasu na gargajiya, wanda suke Yi ma mutun treatment dasu idan yaji ciwo, Matsowa sauran Fulanin sukayi Gaba daya sukayi masu Danejo ƙawanya, Duk sun baza idanuwansu akan yarinyar, Cikin ƙanƙanin Lokaci ya kammala Yi mata treatment ɗin Raunin nata, Sannan Ya kalli Danejo yace ta dauketa takaita Cikin bukkarsu, ta kar6o bargunan da suke lullu6a dasu, A rufa mata ajikinta, sannan a hado garwashin wuta, A sanya mata a cikin ɗakin don ya ɗumama. Bayan danejo ta dauketa, takaita Cikin bukkar su Saman shimfidar da suke kwana ta kwantar da ita, ta fita zuwa sauran bukkokin ta kar6o bargunansu, da zannuwa duka Ta haɗosu a hannunta, ta shigo cikin bukkar ta lullu6a mata su, kamar yadda kakansu yace ta yi mata, tana Cikin nannaɗeta cikin bargunan, Adda ta shigo hannunta ruƙe da murfi na karfe, Garwashin wutane jawur a saman shi, A gefe ɗaya ta ajiye garwashin wutar, Kafin ta samu wuri ta zauna gefen danejo, magana suka soma Yi cikin fulatancinsu, "Tausayinta nake ji, ƙaramar yarinya da ita, ko ya akai ta faɗa Cikin ruwa? Shin ina iyayenta suke ne? taya akai ta shigo Cikin kurmin dajin nan"? danejo ce ta yi maganar fuskarta da alamun tausayinta, Adda tace"Nikaina nakamu da tausayinta, Allah kaɗai yasan daga wata uwa duniyar take, har na ƙosa tafarka, duk da nasan zaiyi wuya ace tana jin yarenmu, baiwar Allah gata kyakkyawa da ita kamar ta macen aljanna da kaka yake bamu labarinta" Murmushi danejo ta ɗanyi kafin tace"Tunkafin ma tafarka Na ji nakamu da sonta sosai, kamar ni na haifeta" wani irin kallo Adda tayi mata"Ke da ko aure baki da shi," danejo tace"Ae ba laifi bane don na kirata da ƴata, balle kuma ni dana Tsinceta cikin ruwa kinga kuwa, a yanzu bata da wani makusanci daya wuce ni jinjina kai adda tayi "bazan biye maki ba, sarkin surutu" ta miƙe tare da fucewa daga Cikin bukkar. _Taƙaitaccen tarihin danejo, Fulanin dajine, Masu yaɗa zango acikin daji wurin da ke da yalwataccen Abincin da dabbobin su zasu ci, kuma Su yi kiwo su yi noma, fulanine dake rayuwa acikin daji, babu wayewa attare dasu, kuma suna da ƙarancin ilmin addini, a wannan Lokacin saboda su kadai suke rayuwar su a daji,_ Family din danejo basu dayawa, Saboda yawancinsu ba'a wuri ɗaya suke ba, Kowa Ya kama gabansa, Kaɗan ne suka rage, Ita dai takasance marainiyace, Iyayenta sun rasu tun kafin ta mallaki hankalinta, kuma ita kaɗai suka haifa, ta taso A hannun ƙanwar mahaifiyarta wadda suke kira da inna wuro, ƴa'ƴanta huɗu bawuro shine babban ɗanta,Yana da mata Ɗaya Haulatu, ɗansu ɗaya wanda suke kira da cubaɗo, bayan shi sai Adda itace ta biyu, sai gidaɗo sai kuma ƙanwarsu hasiya, Kakanninsu duk sun rasu, Ɗaya kaɗai ya rage masu na 6angaren Mahaifiyarsu, sukaɗai suke rayuwarsu a wuri ɗaya. Yinin ranar Danejo bata motsa ba, ta kasa ta tsare sai Yarinyar ta farka, saboda ta ƙwallafa rai akanta sosai, tunkafin ma tafarka tasan wacece ita, Allah ya jarabceta da son yarinyar, Tun tana sa ran zata farka, har dare ya yi bata farka ba, har sun fara fidda rai, Su uku ne acikin bukkar, Danejo da kuma Hasiya, suna ta zaman jiran tafarka har bacci ya yi awon gaba da su. Tsakar dare lokacin kowa Yayi bacci Cikin ƴar bukkarsa, ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta, ƙoƙarin motsa Jikinta tayi sai dai ina sam takasa,tamkar an ɗaureta da igiyoyi haka take ji, ga wani irin zafi da take ji ajikinta, sautin muryarta sam baya fita, Can ƙasan maƙo shi take sambatu, "Daddy mu koma gida, tsoro nake ji,"tun sautin baya fita harya fara fita da ƙarfi, da iya ƙarfinta na ƙarshe Ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, buɗe idanuwanta tayi sosai tana kallon Bukkar, Wasu jerin kwaryoyi tagani a jere, da wani akwatin karfe da sauran tarkacensu na fulanin daji, Wurga eyes dinta tayi akan Fitilar kwan dake Ajiye a ƙasa wadda ta haskaka Cikin bukkar, kafin takai idanuwanta kansu Danejo dake ta bacci daga zauna suna gadinta, Wani irin tsorone Ya ziyarci zuciyarta, hankalinta ya tashi matuƙa, ganin baƙin fuskoki, Ga kuma wani wuri mai kama da A kurkukin kaji, rushewa tayi da matsanacin kuka, a firgice Danejo da hasiya suka farka jin sautin kukan Mutun, Tsareta da ido su ka yi suna kallonta kamar yadda take kallon su, Cikin harshen fulatanci suka soma ƙoƙarin rarrashinta, Ta wawware masu gray eyes ɗinta, jin suna yi mata gwaranci, Cigaba da kuka tayi tana faɗi"Daddy! wayyo Allah na!! Ina daddyna ya ke!! Su wanene ku! A ina nake ne!!" miƙewa Ta yi da ƙyar saboda ba isasshiyar lafiya gare ta ba, Jikinta sai kerma yake yi, Ga uwar zufa data wanke mata jikin nata, ganin tana ƙokarin neman hanyar fita daga Cikin bukkar yasa suka miƙe da sauri Suka nufe ta zasu ruƙeta, watsawa ta yi da gudu tana bin jikin bukkar a ƙokarinta nata gano hanyar da zata fuce, su kuwa sun dage sai haƙuri suke bata"kiyi hakuri ki zauna baki da lafiya, muma mutane ne kamar ke kada kiji tsoron mu baza mu cutar dake ba" tunda suka soma magana take ta faman zazzare masu idanuwanta, saboda bata fahimtar yaren da su ke yi mata magana da shi, ballantana kuma harta fahimci cewa lallashin da suke Yi mata, "Wayyo Allah daddyna, Ni ku maida ni wurin daddyna, Inaso nagan shi," sosai take Yi masu kuka, mai tsiwar gaske, gaba daya sautin kukan nata ya karaɗe kunnuwan duk wani mai yin Bacci acikin bukkokin, Kukanta Ya ishesu, ɗaya bayan ɗaya suka soma fitowa daga cikin bukkokinsu, kowa yana ta faman Yin hamma, A haka suka nufi bukkarsu danejo, inda suke Ji yo sautin kukan nata. Inna wuro ce ta shigo ciki, tare da su haulatu, gaba daya suka ɗaura idanuwansu Kan ANGEL, dake ta kuka, tambayar su Danejo su ka yi meke faruwa?Suma su ka ce basu sani ba, ta tashi tana ta kuka, kuma su basu san harshen da take yi masu magana da shi ba" adaren ranar babu wanda ya runtsa Cikinsu, taruwa sukayi akanta sunata aikin lallashi, ta burkuce masu sam bata fahimtarsu, kamar yadda suma basu fahimtarta, sunan Daddynta kawai take kira, Koya rayuwar Angel zata kasance acikin fulanin daji? Yarinyar da ta taso Cikin kulawa da soyayyar mahaifinta, batasan rashi ba, batasan maraici ba, Ta saba da rayuwar gatanci sai abunda takeso daddynta yake yi mata, Yau gata a ƙurmin daji, Cikin fulanin daji mutanan da basu Jin harshen hausa Sai fulatanci, ita kuma bata Jin fulatanci daga hausa sai turanci, Sai kuma larabcin data koya a makarantar islamiyar da take zuwa, Taya zata Iya jure zama dasu? Abincinsu yanayin rayuwarsu sam ta banbanta da ta mutanan dake rayuwa Cikin gari, Kafin safiya tayi Angel ta galabaita sosai, Idanuwanta sun kunbura saboda rashin bacci da kuma kukan data sha, sun ƙanƙance, jijiyoyin wuyanta duk sun firfito rudu ruɗu jikin fatarta, le6enta ya faffashe hada busasshen jini, ga wani irin zazza6i na tashin hankali daya rufarmata, a ƙarshe yanke jiki tayi ta faɗi asume, Jinya ta koma sabuwa, magunguna suka shiga haɗa mata nagargajiya ƴan dabarunsu da ba'a rasa ba, Hada wasu ganyayyaki suka jiƙa mata acikin gora, suna bata tasha, Allah ya haɗa jininsu da ita, musamman Danejo kullum A tare da ita take kwana, Ba ƙaramin tausayinta suke Ji ba, Saboda ko magana bata Iya furtawa, Jikinta yayi tsauri sosai, Babu sauƙi tamkar zata rasa ranta, ga shi ko a bincinsu bata Iya ci, Furace kaɗai itama ɗin sai sun ɗura mata abaki tukunna take wucewa ta makoshinta daƙyar, angel ta wahala sosai, ta rame ta bushe ta ƙanjame tayi duhu tamkar ba yarinyar nan mai ƙiriniya ba, Kusan Wata Uku ta yi Acikin wannan mawuyacin halin, kafin Allah ya kawo mata sauƙi, tafara buɗe baki tayi magana, Sai dai subi ta da ido don basu fahimtar me take cewa, kullum saita yi masu sambatu akan su nemo mata daddynta, daga baya da ta fahimci basu gane yaren da take yi masu, Saita Zuƙunna ta sanya yatsanta a kasar wurin da ruwa ya jiƙa,ta soma Zana fuskar mutun Asaman ƙasar, data kammala zanen ta kirasu tana nuna masu zanen, Suka zuba ido suna kallon jagwalgwalon zanan fuskar da ta zana, Kallon juna su ka yi Alamar basu fahimta ba, fashewa tayi da matsanancin ku ka, Ta watsa da gudu Tabar wurin bukkokinsu, Suma suka bi bayanta a guje, suna ƙokarin kamota gudun kada wata muguwar dabbar daji ta halakar da ita, Cikin ƙurmin dajin ta nutsa, har tazo inda wannan ruwan Yake inda Taj ya jefa ta ciki, Juyo wa Tayi tare da kallonsu, sai faman haki suke yi sun sha uban gudu, da hannu ta dinga nuna masu cikin ruwan Saboda ta gane cewa a nan ne inda daddyn ta Yazo da ita Ya wurgata ciki, Duk yadda taso ta fahimtar dasu, Sam sun gaza fahimta, dunƙule hannayenta tayi tare da murzasu, tana kwatanta masu a cikin mota suka zo dajin, Nan ma still basu gane me take nufi ba, Zuƙunnawa tayi agaban ruwan, ta rushe da matsanancin kuka, duk jikinsu yayi sanyi, Babu yadda angel ta iya adole ta haƙura taci gaba da rayuwa acikin fulanin daji, tun bata saba ba da su ba, har ta fara sakin jiki da su, Bata da abincin daya wuce fura da nono, da kuma Gasassar masara, Sai kuma nama idan sunyi farauta, shigarta ta koma ta fulanin daji, Danejo ce tayi mata kyautar kayanta, Wanda tun tana yarinya kayan suke ajiye cikin akwatin ƙarfenta, Zuwan Angel Cikin rayuwarsu Ta fiddo da kayan, Ta bata su ta sanya, Duk rana ta Allah sai angel da danejo sunje Bakin ruwan nan, Kullum ne wani lokacin har dare suke kaiwa abakin ruwan, atare suke fita kiwon shanu, hatta tatsar nono sai da danejo ta koya mata, da wasu abubuwan nasu na fulanin dajin, baiwar Allah ba yadda za ta yi don dole take rayuwa a cikinsu, Allah ne kaɗai yasan halin da Zuciyarta take aciki, a kullum idan suka kwanta suna Bacci, tare da su danejo da hasiya, bata iya runtsawa, Zama take yi tsakar dare, tadinga kukan zuci tana roƙon Allah yasa daddynta yana A raye, ta karaya sosai, wani sashe na zuciyarta yana raya mata cewar Waɗannan mutanan da suka Biyo su suna harbin motarsu sun kashe mata daddynta, amma kuma har cikin ranta tana jin cewa Yana A raye, taya zata tabbar da hakan? Ita dai bata ga gawar mahaifinta ba, balle tashai da yabar duniya, A ƙalla Angel tayi shekara Biyu A hannun fulanin dajin nan, A lokacin Tafara Jin fulatanci sama sama saboda xama da tayi da su, duk da sabon da tayi da su hakan bai sa ta fasa ƙudirinta na guduwa daga Cikin dajin ba, duk don saboda taje neman Mahaifinta, abunka ga Yaro ga kuruciya, zuciyarta saita dinga raya mata cewa ta gudu taje gidan su, zata samu mahaifinta agida. A ranar data shirya guduwa daga Cikin dajin, Sai da tabari kowa Ya yi bacci, batare da jin tsoro ba ta fito daga Cikin bukkar, Ko'ina duhu kasancewar darene sosai, Cikin sanɗa take tafiya Tana nufar cikin dajin, duk in taji kukan shanayensu saita firgita, gani take kamar zasu farka daga bacci ne su hana ta guduwa Ganin tayi nisa daga inda bukkokinsu suke, ta soma tunanin wace hanya zata bi don ta fita daga cikin dajin, ga duhu ko'ina, sai ɗan hasken farin watan da ba'a rasa ba, tana cikin wannan tunanin ta jiyo muryar mutun a bayanta, A firgice ta juya don taga wanene, Hasken fitila tagani amma ba ta iya tantance wanda ya biyota ba, duk da taso ta ɗauki murya, Tattare zanin jikinta tayi na kayan fulanin da suka bata sune sanye ajikinta, ta watsa aguje cikin dajin tamkar zata tashi sama, tana gudu tana tuntu6e wani lokacin har faɗuwa kasa take yi a haka za ta daure ta miƙe taciga ba da gudu tana waiwayan mutumin daya biyo ta, ganin shi ma yana gudu, nan fa ta ƙara gudun nata, tsawon lokaci suna wannan ƴar guje-gujen cikin dajin ita da mutumin daya biyo ta har Allah Ya kawo ta bakin titi a galabaice ta haye saman titin, wani irin jirine ya soma ɗibar ta. Ta fara tangal tangal za ta faɗi ƙasa, a haka ta jure taciga ba da gudu, ba zato ba tsammani sai ga wata zungureriyar mota baka ta yi parking a inda take a tsaye, A slow murfin motar ya zuge, Zuro Hannu aka yi daga cikin motar aka ɗauke ta, murfin motar ya koma ya zuge da kanshi, da gudu motar ta miƙi titin. A daidai wannan lokacin Danejo ta faɗo saman titin a galabaice hannunta riƙe da ƴar filita. Ashe ita ce ta biyo Angel, don ta ga lokacin da za ta gudu daga Cikin bukkarsu. Waro ido waje ta yi ganin dankareriyar motar da ta ɗauki Angel, tunda take a rayuwarta wannan ne karo na farko da ta fara yin tozali Mota, Tsoro duk ya cika ta, hankalinta ya yi matuƙar tashi, ganin an raba ta da Angel. A gefen titin ta tsugunna tana kuka tamkar ranta zai fita. Wannan shi ne silar rabuwar Angel da Fulanin Daji. A nan gefen titin Danejo ta yanke jiki ta faɗi a sume, a washe garin ranar ƴan uwanta suka farka daga barci, ba su ga Angel da Danejo ba, hankalinsu ya tashi gabaɗaya suka bazama cikin dajin neman su. Har Allah Ya sa Su Bawuro suka tarar da ita a gefen titi ita kadai a kwance ba numfashi, lamarin ya yi matuƙar girgiza su, tunda suke da Danejo ba ta ta6a yin nisan kiwo irin na yau ba, sun yi mamakin ganin ta ita kaɗai ba tare da Angel ba. Bayan komawarsu cikin rigarsu, Suka yayyafa ma danejo ruwa ta farfaɗo, fashewa ta yi da matsanancin kuka tana faɗa masu yadda suka rabu da Angel. Duk jikinsu ya yi mugun sanyi, kowa bai ji daɗin lamarin ba, sai dai ba su da yadda za su yi. Da ma tsintacciya ce duk da sun yi sabo da ita, zuwan Angel cikinsu ba ƙaramin farinciki ta samar masu ba. Sun ji takaici da baƙin cikin ɗauke tan da aka yi, to ya za su yi? Allah Ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan. Da daɗi da ba daɗi haka Danejo ta ci gaba da rayuwa cikin ƙunci da takaicin rashin Angel, ta rame ta ƙanjame tamkar ba Bafullatanar nan ba mai yawan fara'a mai son yin rawa, yanzu ta koma salihar ƙarfi da yaji. Kullum cikin yin zazza6i take, kuma kullum tana akan hanyar zuwa bakin ruwan nan inda suke yawan zuwa ita da Angel su zauna. Kafin tafiyar Angel ta ba su labarin mahaifinta daya gudo da ita cikin daji, a lokacin ta fara jin Harshensu na Fulatanci, ta kwashe duk abin da ya faru ta sanar da su. *ANEELERH* Kwance take saman haɗaɗɗen gadonta na gidan su, A gefenta ƙaramin yaronta ne wanda bai wuci shekara ɗaya da ƴan watanni, Jikin shi na a sanye da overall pink colour, Kyakkyawan yaro rainon madara, fari tass kamannin shi sak na mahaifiyar shi, tamkar ta yi kakin shi, kan shi a cike yake da kwantacciyar suma mai laushin gaske, mommyn ta shi dake kwance gefen shi tana ta sharar bacci Rigar bacci ce a jikinta launin sky blue, Wata irin zufa ce ta soma wanke mata fuskarta, ta ko'ina zufar take tsastsafo mata, rurruƙe bedsheet ɗin tayi da hannayenta da ke ta kerma, sambatu ta soma yi tana ambaton sunan ANGEL, still idanuwanta suna a rufe da alama mafarki take yi, Cikin shesshekar kuka take faɗin"Angel meyasa nake ganin cikin mawuyacin hali? Waya ta6amun ke? Angel kiyi magana meyasa ki ke kuka? Dan Allah ki faɗamun angel," Ciccije lips ɗinta take yi sosai take ƙara sautin kukan nata, A dai dai lokacin mami ta fito daga ɗakinsu, itama kayan baccin ne a jikinta doguwar riga, sai hamma take yi da alama daga bacci ta farka, ɗakin Aneelerh ta nufa tunkafin ta shiga ta soma jiyo sautin muryarta, ta cikin ɗakin tana kuka, Da sauri mami ta faɗa cikin ɗakin babu wadataccen haske sun kashe Kwan ɗakin kafin su kwanta, bedside lamp ce kaɗai take a kunne ta ɗan haskaka ɗakin, Ƙarasawa tayi daga gefen gadonta, takai hannu tana ɗan bubbuga shoulder ɗinta"Aneelerh! Aneelerh! Lafiyar ki kuwa? Kike ta ku ka"? Muryar mami ce ta farkar da ita, lokaci ɗaya ta zabura zata sauko daga saman gadon, damƙo damtsen hannunta mami tayi'ke lafiya? Bakya ji ina magana"? "Mami ki barni in tafi, tana buƙatar taimako na," la66anta na kerma tayi maganar, Fuskar mami da alamun ruɗi tace"wai wacece kike magana akai"? Juyowa tayi suna kallon juna, idanuwanta sunyi jawur tace"ANGEL " Sakin hannunta mami ta yi ta dafa kafaɗunta, cikin natsuwa ta soma magana" ki kwantar da hankalin ki, ki faɗamun meya faru da angel, kinyi mafarki ne akanta"? Jinjina kai tayi cikin shessheƙar kuka tace"Mommy, I had a really scary nightmare about angel, tana a cikin mawuyacin hali, yanayin da nake ganin angel abun ya ta6a zuciyata......" takai ƙarshen maganar hawaye na bin fuskarta Shiru mami ta yi idonta akan fuskar aneelerh, Kafin tace"addu'a yakamata ki yi," Cikin disasshiyar miryarta, ta ambaci "أَعُوذُ بِاللَّهِ مِنَ الشَّيْطَانِ الرَّجِيمِ وَمِنْ شَرِّ هَذِهِ الرُّؤْيَا" Kusa sau uku tana ambaton addu'ar, "Aneelerh mafarki ba gaskiya bane, Shaiɗan ne kawai yake son rikitar dake" girgixa kai aneelerh tayi"mami wannan mafarkin ya wuce a ce shaiɗan ne, ba yau ne rana ta farko da nafara yin shi ba mami, kuma a duk lokacin da zanyi shi, angel nake gani ita kaɗai tana kuka jikinta sanye da yagaggun kaya kamar Almajira," "A kowani lokaci, ki ka yi mummunan mafarki akan angel, you should pray for her, alama ce da ke nuna cewa tana buƙatar addu'ar ki, duk da ki nayi saiki ninka akan wadda kike yi masu, muma kuma in sha Allah zamu dage" miryar abie ce, sam basu ji alamar shigowar shi ba, a tare suka Kai idanuwansu kan shi, A tsaye yake bakin ƙopar ɗakin jallabiya ce a jikin shi, yayi shirin zuwa masallacin domin yin sallar asubahi da ake ta kira, Tafiya yaci gaba da yi cikin ɗakin yana nufar su, "Wipe ur tears aneelerh, bana so na sake ganin hawayen ki, " cikin sanyin murya ta amsa mashi da "toh" "That's good, Jiya munyi waya da uncle abdallah" ya dakata da maganar, a ƙagare suke kallon shi, sun ƙosa su ji mai zaice, "Yayi mun magana akan BABY JUNAID, nasan aneelerh bazata ji daɗin maganar ba, shiyasa tun jiya ban sanar maki ba," tunkafin ma yakai ƙarshen maganar aneelerh ta ɗaure fuskarta walwalarta gaba ɗaya ta ɗauke, Ita kanta mami yanayinta ya canza, don tunkafin ma ya ƙarasa sunsan inda zancen nashi ya dosa, "Suna so A basu shi, ya koma hannun su da zama, da zarar kin yaye shi,.....' girgiza kai aneelerh ta shiga yi tana faɗin"Haba abie, idan aka raba ni da shi ya ake so inyi da raina? Yaron nan fa shi nake gani inji daɗi araina, ina kallon shi amatsayin kyautar Allah, inaji araina Allah yabani shi ne saboda rashin da na....." ƙasa ƙarasa maganar tayi saboda kukan da ya ciyota, da sauri ta kifa kanta saman pillow, Dariya sosai abie ya yi, ganin yadda ta harzuƙa jin za'a rabata da gudan jininta, Kallon juna su kayi shi da mami, "meyasa? Kana ganin halin da take ciki, kuma ka ke son ƙara tayar mata da hankali, dagaske ka ke ko wasa? Nasan ka da son zolaya" Bai bata amsa ba, Ya juya ya nufi ƙopar fita yana faɗin"Idan na dawo daga masallaci zamu yi magana" daga haka ya fuce daga cikin ɗakin, Shafa bayan aneeleeh mami tayi"ke ki kwantar da hankalin ki, ae wlh ba wanda ya isa ya raba ki da ɗanki, Sai Allah nasan aikin hajiya adama ne, ita zata tunzura shi akan su ɗauko yaro, in banda ma abunsu ae yaron bai kai shekarun da zasu ɗauke shi ba, koda kuwa an yaye shi, nifa ko ya cika shekarun da zasu ɗauke shi bazan bari su rabaki da shi ba, idan suna son ɗa su haifi wani mana, wannan dai naki ne ke kaɗai........" Jin kalaman mami yasa aneelerh ta tsagaita da yin kukan, ba ƙaramin daɗi taji ba, ɗagowa tayi daga kan pillow ta kwantar da kanta saman kafaɗar mami, "Mami karki bari araba ni da baby junaid ɗina, wlh zuciyata zata iya bugawa" shafa sumar kanta mami tayi"ae me raba ki da shi sai ya shirya, Idan ma suka matsa number zanyi wa lawyer na magana," murmushi aneelerh ta saki saboda jin daɗin maganar, tasan mami tana son farin cikin ta, bazata so a bunda zai6a ta mata ranta ba "Kada mu makara, ta shi kije kiyi sallah, shime babyn naki ki tada shi yaje ya yi sallah," dariya aneelerh tayi tare da saukowa daga saman gadon ta nufi toilet, mami nata kallonta har ta shige ta rufe ƙofar, ajiyar zuciya taɗan sauke dama ta faɗi hakan ne donta kwantar mata da hankalinta, Juyawa ta yi tana kallon Junaid dake kwance sai sharar baccinsa yake yi, hannu takai ta shafa sumar kanshi" Grandson, Allah yabar mana kai," bargo taja ta lullu6e mashi jikin shi, yaron ba ruwanshi sam baida damuwa, ga nauyin bacci da Allah ya yi mashi, shifa ba ƙaramin abu ke tada shi daga bacci ba, Saukowa mami ta yi daga saman gadon ta fuce daga ɗakin zuwa nata ɗakin domin tayi sallah, Fitarta keda wuya aneelerh ta fito daga toilet, shaf shaf ta canza rigar baccin jikinta zuwa Jallabiya, ta ɗauko hijabi ta zura a jikinta, ta koma saman darduma ta kabbara sallah a tsanake ta shiga yin ibadarta, Bayan ta kammala yin sallar saman darduma ta zauna tana yin tasbihi, hannunta ɗaya ruƙe da cazbaha, bayan ta kammala tayi azkhar, kafin ta ɗaga hannayenta sama ta soma yi masu Angel addu'a, Yayin da hawaye ke bin fuskarta, "Ya Allah kafi kowa sanin a wani hali waɗannan bayin naka suke ciki, ya Allah ka tsare su da tsarewarka, Ya Allah ka kare su daga sharrin mutun sharrin aljan da sharrin duk wani abin cutarwa, Ya Allah idan har suna araye ya Allah ka bayyanar mana da su, idan kuma......kasa ƙarasa addu'ar ta yi, sam bata so ta ambaci mutuwa, tuni idanuwanta sun cicciko tab da kwalla, lumshe idanuwa ta ɗanyi yayin da kwakwalwarta ke tariyo mata fuskokinsu, Uzair taj da kuma Angel, Ta yi nisa acikin tunaninta, Sautin kukan Junaid ya farkar da ita, ajiye cazbahar tayi saman dardumar ta miƙe da sauri ta nufi saman gadon, yana ganinta ya dakata da yin kukan ya tsareta da manyan idanuwanshi, murmushi tasakar mashi sai gashi shima ya sakar mata murmushi, Cire hijabin jikinta tayi tare da ninketa ta ɗaura saman mattress ɗin, hawa saman gadon tayi tare da kai hannu ta ɗauke shi jan hancin shi tayi"i know u are not hungry rigima ce kawai ko"? ta6e tausasa la66ansa yayi alamar zaiyi kuka, dariya tasaki tare da cewa"stop crying my baby boy, shagwa6a66an yaro na" a gefen gado ta zauna tana shayar da shi, bayan ta kammala ta zaunar da shi, takai hannu ta ɗauko hoton su angel dake ajiye saman drawer, Su haɗu ne a haton ranar birthday ɗin Angel a kayi masu hoton, sunyi matuƙar yin kukan, kowannansu fuskar shi ɗauke da dariya ga cake duk ya 6ata fuskarsu, yatsun hannunta ta ɗaura saman hoton tana shafa fuskokin su, tun daga face ɗin Uzair zuwa ta taj, kafin ta tsayar da hannunta a kan hoton Angel, murmushin takaici ta ɗan saki, ta ɗago ta kalli junaid, ya tsareta da ido yana kallonta ko ƙyaftawa baiyi, gefen shi ta matsa ta zauna, ta saita hoton saitin fuskarshi, magana ta soma yi mashi saitin kunnanshi, "Ka ga wannan shi ne daddyn ka, sunanshi Uzair, wannan kuma Taj, shi aminine kuma ɗan uwa ga mahaifinka, ita kuma wannan she's ur elder sister Sunanta ANGEL" tana rufe baki taji ya maimaita sunan Angel, murmushi tasaki dama wani lokacin duk in tayi magana saiya maimaita, "Da ace tana nan, da yanzu ita zata dinga goya mun kai abayanta, Allah sarki Angel tayi jiran zuwanka na tsawon lokaci kullum tana tambaya aunty aneelerh wai ke bazaki haifa mun ƙani ba, ni na ƙosa naga ɗan yaron ki, sai ga shi na same ka a lokacin da angel bata nan, tana a raye kota mutu bani da masaniya akan hakan," duk wannan surutun da Aneelerh ke yi, Ya natsu yana sauraronta kamar yana fahimtar me take cewa" "KANA NAKA ALLAH NA NA SHI wa ya yi tunanin ma za'a wayi gari babu su a lokaci ɗaya? Ban ta6a kawo hakan araina ba, kaima kuma ban sanya ran zan same ka ba, sai gashi Allah ya bani kai, ina matuƙar sonka my baby boy," takai ƙarshen maganar tare da manna mashi kiss saman forehead ɗinsa, kafin ta ɗaura hoton saman side drawer, Rungumoshi ta yi a jikinta, wani baccin ne ya kuma ɗaukarsu, Wuraren ƙarfe tara na safe, Mami ta shigo ɗakin nata, har ta kimtsa kanta Cikin Atampa, Ganinsu rungume da juna ita da junaid, yasa ta saki murmushi, baƙaramin ƙaunar yaron take ji ba, ita kanta mamin saboda sunan yaron yaci Sunan marigayi mahaifinta Alhaji Junaid Shuwa, tun lokacin da mami ta auri Mahaifin Aneelerh Alhaji Muhammad falgore ta ƙwallafa rai akan ta samu ɗa namiji don ta sanya ma shi sunan mahaifinta, Allah bai nufa ba, ƴa ta samu mace kuma daga ita bata ƙara haihuwa ba, Aneelerh tasan da wannan burin na mahaifiyarta, shiyasa ta sanyawa yaron Suna Junaid, kuma aka amince mata da sunan, ko lokacin da su Uncle abdallah suka zo Nigeria don su ga jikan su, basu yi gaddama ba da aka faɗa masu sunan yaron, saima farin Ciki da su kayi An haifa masu ɗan kyakkyawan Saurayi. Ƙarasawa gaban gadon tayi ta kira sunanta"Aneelerh wake up, lokacin yin breakfast ya yi, abie na son magana dake," Buɗe ido aneelerh tayi akan mami, biji biji take ganinta kafin idon ya washe, "Mami," ta ambaci sunanta muryarta da alamun bacci, "Muna jiran ki a dining area," mami ce ta yi maganar, tare da juyawa ta fuce daga ɗakin, A lalace Aneelerh ta miƙe ta sauko daga saman gadon, toilet ta nufe ta shige, bayan ta fito daga wankan, bata canza jallabiyar jikinta ba, mayafi kaɗai ta dauko cikin closet, tayi rolling ɗin shi a saman kanta, Fitowa daga ɗakin tayi ta nufi dining area, A saman dining chairs ta iske su zaune su biyu, sai Ana mai aikin gidan Aneelerh dake tsaye tana yin serving ɗinsu, Tana ƙarasowa Ana ta soma gaishe da ita cikin girmamawa"good morning madam, how was ur night" murmushi Aneelerh ta sakar mata"Alhamdulillah, ina fata kema haka," jinjina mata kai ta yi alamar eh, Mayar da idanuwanta tayi kan iyayen nata, gaba ɗaya ita suke kallo, da sauri ta gaishe da su, su ka amsa mata fuskokin su a sake, Kujera taja ta zauna, Ana tace" me zan zuba maki"? "Cup of tea, ki haɗa mun da noodles," amsa mata tayi da toh, ta ɗauki serving spoon da plate ta soma zuba mata noodles ɗin, bayan ta gama haɗa mata ta tura mata gabanta, tare da kofin tea, Har ta ɗauki fork zata fara cin abincin ta ɗago ta saci kallon iyayen nata, da yake suna fuskantar juna, Ganin suna kallonta yasa ta sunnar dakai ƙasa, murmushi su ka sakar mata, mami tace" Ina kika baro mana baby junaid ɗin mu"? "Bacci yake yi," "Ya cika bacci anya kuwa lafiya"? Abie yace"lafiyar ce ta kawo haka ae, yaron fa ɗan hutu ne, " da zolaya ya yi maganar, murmushin gefen fuska aneelerh tasaki"mami ae ya farka ɗazu, daga baya ne ya koma bacci" mami tace"Okey, ki ci abincin ki, yana huce wa" kallon abie ta yi tare da cewa"abie da gaske ne uncel abdallah ya kira akan zasu kar6i baby junaid"? yanayin yadda tayi maganar a ɗan tsorace take da jin amsar da zai bata, "Dagaske na, Amma ki kwantar da hankalin ki, bawan da zai raba ki da babynki, mutu ka raba takalmin kaza" dariyar farin ciki ta saki, hatta Ana dake a tsaye saida ta murmusa, "Ci ki ƙoshi daughter, farin cikinki ae shi ne namu," yakai karshen maganar tare da kallon Ana dake a tsaye"Nayi magana da drivern da zai kai ki garin ku, ki kasance a cikin shiri a kowani lokaci zai iya zuwa ku tafi" jin wannan maganar yasa yanayin fuskarta ya canza ta shiga yarfa hannu, cike da mamaki suke kallonta, tattara skirt ɗin jikinta tayi tare da zuƙunnawa saman guiwowinta, tana faɗin "Allaji ayi haƙuri abarni anan tunda har nakai wannan lokacin, wlh kona koma ƙauyanmu wahala zanci, Noman doya za'a sanya ni, dan Allah Alaji a taimaka, ƴan uwana duk suna a cikin garin nan suna aiki, dama mu uku ne marayu iyayen mu sun rasu," tuni hawaye sun wanke fuskarta, kallon aneelerh tayi a marairaice tace"madan ki taimaka, abarni anan wlh noman doya da wahala", duk wannan ƙibar da nayi idan har na kuskura na koma ƙauyan mu, Cikin kwana uku zan sace," mami dai dariya ce ke son kufce mata, amma ta gumtse ta cikin baki, shi kanshi abie taso ta ba shi dariya, musamman hausarta da bata fita sosai, "Abie, tunda tana taimaka ma Inna hauwa wurin yin girki, da aikace aikacen gida ni ina ganin barta kawai," Mami ma tace"Nima na goyi bayan haka, saboda ta nuna bata son noman doya....."takai ƙarshen maganar tana ƴar dariya, "Yanzu ina ƴan uwan naki"? Abie ne yae mata tambatar, Hannu tasa tana matse ƙwallar dake akan fuskarta, "Esther tana aiki a restaurant itace take aiki gidan Iyayen Sir uzair, Tun bayan barin su ƙasar ta koma restaurant da aiki, ita kuma janet, tun lokacin da madam Benazir ta koreta, ta samu aiki a hotel," Ajiyar zuciya abie ya sauke, kafin yace"Shikenan zaki zauna anan, amma fa zan sa maki ido, duk ranar da kika aikata badaidai ba, zan turo ki ƙauyan ku, aje can ayi noman doya," Gaba ɗaya suka saki dariya, miƙewa tayi muryar na rawa ta shiga faɗin"thank u sir, thank u madam ngde ngde," tsantsar farin ciki ne akan fuskarta, "Ki koma wurin Inna hauwa, ku yi breakfast ɗin ku," mami ce ta yi mata maganar, da sauri ta juya ta nufi part ɗinsu, A tsanake suka cigaba da yin breakfast ɗinsu, sai da suka kusa kammalawa, aneelerh ta mike mami tace ina zuwa, "Inaji araina kamar Junaid ya farka, bari naje na duba shi," da sauri ta wuce ɗakinta, Kallon Juna abie da mami su kayi, "Namanta ban faɗa maki ba, Munyi waya da ɗan Iya, wai yana so Aneelerh ta koma hannun shi da zama, Zai sama mata aiki a Asibitin *CHIEF OBINNA* " rass Mami taji gabanta ya faɗi, can kuma ta ɗan saki murmushi, "Ka daina yarda da maganar ɗan Iya, kasan halin shi, Ya iya shirga ƙarya in banda abunka taya za'ae ya iya sama mata aiki A wannan katafaren asibitin wanda ma'aikatan cikinsa ma fa, ɗai ɗai ku ne ƴan ƙasar nan, amma fa in ta samu aiki acan zan fi kowa mafarin ciki, don naji ance ƙaramin ma'aikaci na asibitin just cleaner kawai albashin shi yakai Dubu ɗari da hamsin, Abie yace"nima nayi mamaki da yace haka amma kuma kinsan shi, mutunne na jama'a, duk wani politician daya shahara yasan shi, to ba abun mamaki bane don yace zai iya sama mata aiki acan, Ni abunda yasa ma na yi mata sha'awarar zama can abujan, zata fi samun kwanciya hankali akan nan, yau fa tsawon shekara biyu da watanni, rabon aneelerh da taje aiki, badan Dr Aisha ta kar6i ragamar kula da asibitin ba, da yanzu komai ya durƙushe" Shiru mami tayi na wani lokaci, aranta ta ayyana cewa in kuwa har Aneelerh ta samu aiki a asibitin *CHIEF OBINNA* tabbas cikin ƙankanin Lokaci zata zama hamshaƙiyar mai kuɗi, kuma zata ji daɗin rayuwa agidan ɗan Iya, saboda barkwancin shi dana matar shi, ƴan sharholiya ne ana shan drama a gidansu, sai dai kafin Ashawo kan Aneeelerh ta zauna acan ɗin shine abu mai wuya, kuma suma kansu baza su so tayi nesa da su ba, duk da shima abie Suna hasashen zai samu ƙarin matsayi a wurin aikin shi, nan badajimawa ba za'ayi mashi transfer zuwa Ministry of finance dake abuja, Sun jima suna tattaunawa da abie kafin Yayi mata sallama, Ya tafi zuwa wurin aikin shi, ita kuma Mami ta koma falo, a lokacin aneelerh ta dawo falon hannunta ɗauke da juanid, fira suka zauna sunayi yayin da plasma tv ke a kunne suna kallon tashar arewa 24, *To fa😳Su Angel An yi gudun gara An faɗo gidan zago, ko ina ne Wurin nan? Lamarin ya ɗaure mun kaina, To dai mu haɗu a next page gobe in Allah yakainu da rai da lafiya, don jin yadda zata kaya, kada ku manta friday da weekend ba posting, Amma zanyi ƙoƙari in dinga yi maku Long pages, Ga waɗan da suka shirya yin payment ƙopa a buɗe take su yi mun magana (08103884440)**💋KURKUKUN ƘADDARA💋* *Boss Bature ✍️* dedicated to Aunty kubra❤ *E10* _Kamar yadda na fara littafin nan ina rokon Allah Subhanahu wata'ala da ya ba ni ikon kammala shi lafiya, alfarmar Annabi Muhammad(SAW). Allah Ya ba ni ikon faɗakarwa da kuma ilmantarwa harma da nishaɗantarwa, Ubangiji Allah ya kare ni daga rubutu abin da ba zai amfani al'ummar Annabi ba.✍️_ Gargarɗi _Ban amince wani ko wata ya yi amfani da wani sashe na book din nan ba ta kowace siga, ko a karanta mini shi a Youtube don already na siyar da littafin, Ko a haɗa mini document, idan kunne ya ji jiki ya tsira, ko da Allah na bar mutun zai bi mini haƙƙina!👌_ *South Korea* Seoul City-Gangnam-Gu Hamshaƙiyar Unguwace ta Attajiran masu kuɗi dake zaune a Seoul, Babban birnin korea ta kudu, babban birni ne mai manyan-manyan gine-ginen gargajiya dana zama ni masu matuƙar ƙayatarwa, ga manyan hanyoyin jiragen karkashin kasa da kuma Wuraren shaƙatawa, masu matuƙar jan hankali, A ɗaya daga Cikin jerin Modern apartments din dake a Gangnam-Gu Haɗaɗɗen masaukin Uncle abdallah ya ke, inda suke sauka duk in suka zo ƙasar. tafi ƙarfin awa ɗaya a tsaye Tana Kallon hotonsu dake a manne Jikin bangon bedroom ɗinsu, Idanuwanta Sun Cicciko tab da ƙwalla, Har yau she ne wannan baƙin Cikin zai gushe acikin zuciyarta? taya zata Iya sakin jiki tayi rayuwa acikin duniyar nan batare da Ya'yanta ba? tabbas ta yi babban rashin, A kullum ta kali hoton su, sai ta zubar masu da hawaye, Almost 2 years kenan babu su babu labarin su, itace kullum Cikin zullumi da zarar wayarta tayi ringing, jikinta har 6ari ya ke yi don ta ɗauka taga ko Jami'an dake bincike kan case ɗin su tajuddeen ne suka kirata don su sanar da ita ko an gano inda suke, Tun lokacin da suka dawo Seoul hajiya adama Bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, Gangar jikinta gaba ɗaya tana a nigeria, Sunan tana zaune a korea ne, duk irin Sabon da tayi da ƙasar hakan baisa ta gundure ta ba, duk don saboda Abunda ya faru na 6acewarsu tajudden, Ita fa a ayanzu Tafi sha'awar su koma nigeria, Hankalinta sai yafi kwanciya koba komai Zata dinga ganin ƴan uwanta, Tsadadden leshi ne a jikinta, launin silver yabi shape ɗin jikinta, Ta kashe ɗaurin ɗan kwali, Yayin da ta goya hannayenta a saman ƙirjinta, Sam ta kasa janye idanuwanta daga Kallon hoton nasu da take yi, bakowa tafi ji ba, face Angle ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalinta ba, taso ace tuntuni rainon yarinyar ya dawo hanninta da yanzu suna atare, Sai dai kash Ƙaddara ta riga fata, Ziraran hawaye ne suka soma saukowa kan kuncinta, Muryar me aikinta ce Ajumma ta katse mata Tunanin nata Cikin harshen su na korea take sanar da ita cewa Saƙon ta ya iso, Share hawayen fuskarta ta yi, kafin tace"A shigo mun da su ciki," itama da harshen nasu take magana, don tana ji ba laifi, Turo ƙopar ɗakin ajumma tayi, Babbar macace ta kwana biyu aduniya tsufa ya fara kamata, fara ce sol gashin kanta iya kafaɗarta ya tsaya, Jikinta na sanye da ƴar riga da gajeran skirt, Faffaɗan tray ne a hannunta, Saman shi kwalaban Soju ne (Giya) sun kusa Uku, tare da glass cup guda ɗaya, A saman Round table ɗin dake a kusa da gadon hajiya adama, ta ɗaura tray ɗin, Ta juya zata fita, har ta kusa kaiwa bakin ƙopar fita muryar hajiya adama ta katse ta"Idan mutun yana so ya bugu sosai, har ya manta wanene shi, kamar yaya ya kamata yasha" shiru ajumma tayi tana tuna gargaɗin da Abdallah ya yi mata akan karta kuskura ta ƙara ba matar shi soju tasha, idan ba haka sai ya kore ta daga aiki, Yau ɗunma don Abdalla baya a gari ne, Shiyasa ta kawo mata soju ɗin, "Kin yi shiru baki amsa mun ba"? Muryar na kerma tace"Kwalba ɗaya, Amma ran ki shidaɗe ina jin tsoro, kada yalla6ai ya ritsa ki a lokacin da kika sha kika bugu, Zai iya korata daga aiki" "Kada ki damu, Bazan faɗa ma shi cewa ke kika kawo mun giyar ba, Zance ni na fita na siyo ta, hakan yayi maki" jinjina kai ajumma tayi kafin ta ruƙe handle ɗin ƙopar ta fuce, Zama Hajiya adama tayi a gefen katafaren gadonta, takai hannu ta Ɗauki kwalbar Soju Ta cire mufin, Abaki ta kwafata Cikin ƙanƙanin Lokaci ta shanye duka, wani irin biji biji tafara gani a cikin idanuwanta, Ajiye kwalbar tayi, tare da kai hannu ta ƙara ɗaukar wata kwalbar ta shanye duka, sauke kwalbar tayi saman table, Ta yunƙura zata miƙe duniyar ta soma juya mata, sha tara sha takwas ta dinga gani acikin idanuwanta, wani irin nauyi Jikinta yayi mata, Tangal tangal ta soma yi tana tafiya ta nufi hoton dake manne jikin bangon ɗakinsu, Ta curo hoton ta ƙura mashi ido tana kallon shi, har wani girgiza kai take yi, Can dai ta rushe da wata irin mahaukaciyar dariya tamkar zararra, muryarta ashaƙe ta soma magana"Duniya juyi juyi, wohoho Kai ya ɗau zafi, In ban da ta6ara da ɗamsil basira Ta ya za'ace mutun ya 6ace tun 1960 Amma An gaza gano inda yake? Ƴan sandan nan basu san ciwon kansu ba, Gashin Hammata ma yafi su Amfani, Nayi fushi Allah Ni da kaina zan nemo abuna ahe, Ku zuba ido ku gani yanzun nan zan gano su,' takai ƙarshen maganar tare da ajiye hoton ƙasa, tattare Zanin leshin jikinta tayi, ta zuƙunna ƙasa tana rarrafe, Saƙo da lungu na ɗakin ta shiga Bi tana sambatu Tana faɗin"Gasu Can sun 6oye, kamo su nan kamaso Sunan, Zo nan ɗan ɗana Uzairu Yaron mamansa, kaima zo Tajuddeen ɗina, Kai na manta da Angela ta Yarinyata zonan in raira maki waƙa, Wacece Kumatu Angel ce kumatu, kumatutu kumatu, kumatutun mama, kumatutun baba......" tana raira waƙar tana kuka, zama tayi tare da cewa"Yauwa, Ga abinci Nan Shekaran jiya na girka maku shi, nasan kuna jin yunwa, banda wawaso, duk wanda ka samu rabon ka ne,," gaba ɗaya ta haukace ita kaɗai take ta sambatu, giya takai mata karo, ita fa ala dole su take gani acikin idanuwanta, tana magana tana sakin gyatsa, Yunƙurawa tayi ta miƙe tsaye tana faɗin"Zan Binciko ku duk inda kuka 6oye ja'iran yaran, harni zan girka maku abinci ku ƙi ci? Kai tajo hada cewa ba daɗi? Ni da ku ne" hannu tasa ta zuge zip ɗin rigarta, Ta cire rigar tare da yin wurgi da ita ƙasa, Ta warware zanin shima ta jefar da shi ƙasa, ya rage daga ita sai undy, Ƴar duma duma da ita, ga uban tumbi, wurgi tayi da kallabi leshin kanta, Ta koma mahaukaciyar ƙarfi da yaji, dambe ta shiga yi ita kaɗai, sai da ta Tarwatsa komai na ɗakin, da sunan tana neman Su Uzairu, itace har cikin toilet, gaban toilet seat taje tana leƙawa, Hankali Ya gushe, A karshe ta zube ƙasa tana birgima tana faɗin"Ya Allah kota sama ne, A jeho mini su, Nasan kasan inda su ke, tunda kai kana ganin komai, ko karkashin ƙasa mutun ya 6oye......." Ta jima tana sambatu, kafin Allah ya kawo bacci ya yi awon gaba da ita, Lokacin da Uncle abdallah ya shigo Cikin gidan, Jikinshi sanye Cikin Suit sun zauna ma shi, Tun a palour suka yi kici6us da Ajumma, Sam ba ta yi tsammanin Aranar zasu dawo ba, A tsorace ta gaishe dashi muryarta na kerma, Kota kanta bai bi, kaitsaye ya nufi bedroom ɗinsu Ya tura ƙopar ya shiga, tun daga kan Kayan Hajiya adama data tube ya fara Cin karo da su yashe a ƙasan tiles, Ko'ina na ɗakin ta hargitsa shi, tsayar da idanuwan shi yayi akan hajiya adama da ke kwance ƙasa ta baje sai sharar bacci take yi hada minshari, Ga kwalaban Soju ɗin da tasha nan Ajiye saman table, "YA SALAM" rai a6ace ya ambaci hakan, kutsa kai yae cikin ɗakin A ƙasa yayi toxali da hotonsu Uzair, wanda hajiya adama ta jefar ƙasa, zuƙunnawa yayi tare dakai hannu ya ɗauki hoton nasu yana kallo, Nan take ya gane dalilin shan giyar nata, in har zata cigaba da kallon hotonsu uzair, to kuwa bazata ta6a daina shaye shaye ba, ba irin faɗan da baiyi mata ba akan tadaina amma taƙiya, Takawa yayi zuwa jikin bangon ya liƙa hoton, kafin Ya nufi inda take a kwance ya zuƙunna, ya jima yana kallonta, hannu yakai saman ƙafarta yaɗan bubbuga, Shiru bata farka ba, Sai da yayi dagaske Sannan Ta buɗe idanuwanta waɗanda sukayi jawur dasu, Tana kallon shi, "Get up, Ina son magana da ke" da alama har yanzu wine ɗin bata sake ta ba, daƙyar ta lalla6a ta miƙe zaune tana faman yin hamma, "Waya kawo wannan abun Cikin gidan nan"? Ya yi tambayar yana nuna kwalaban Soju ɗin da ta sha, fuskar shi a murtuke, "Ni na kawo su, don su ɗebe mini kewa," "Narasa gane meke damunki? Meyasa kullum burinki ki 6atamun rai? Kin manta sharuɗɗan da dr park ya gindaya maki akan lafiyarki? Kina tunanin shan wine ɗin da kike yi shi ne mafita agare ki? Yakai ƙarshen maganar yana kallonta, Sai faman lumshe ido take yi,"magana fa nake yi maki? Harara ta wurga mashi"To Ubana Alhaji Adamu, Zaka fara faɗan naka ko? nasan bai wuci kace haramin bane shan giya, Zan illata lafiyata, bayan shi sai kuma me"? A harzuƙe tayi maganar tana kallon shi, har saida gabanshi ya faɗi ras! Saboda yadda ta rufe ido tana gaya mashi magana, lallai har yanzu bata dawo Cikin hayyacin ta ba, Sassauta muryarshi yae, Cikin sigar lallashi yace"Allah ya huci zuciyarki, ni ba faɗa nace zanyi maki ba, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan baida amfani, idan damuwa ce tayi maki yawa Ki ɗauko qur'ani ki karanta mana" "Ka yanke shawara game da komawarmu nigeria? nifa na lura kamar baka damu da 6acewarsu ba, harkokin kasuwancinka kawai kasa agaba, Nikaɗai ce nasanya damuwa akansu, almost 2 years ban ta6a ganin ka tashi tsakar dare kayi Nafila a kansu ba, Jinjina kanshi yae"Adama kenan, Ae duk cikakken musulmi wanda yayi imani da Allah, ya kuma yi imani da ƙaddara mai kyau ko mara kyau, Bazai ta6a zama ya ƙuntata kan shi ba don Allah ya jarabce shi, Nasan cewa aduk inda suke Allah yana atare dasu, Kuma inayi masu addu'a, wannan ma ya wadatar ba dole saina tashi tsakar dare ba, bansani ba ko so kike in ajiye harkokin kasuwancina, In sanya damuwa araina a ƙarshe Nima in koma ɗan giya,' hannu tasa ta dafe gefen kanta, hawaye masu ɗumi suka soma shararowa mata, Ruƙo hannayenta ya yi Cikin nashi"Ki faɗamun kome kike so zanyi maki, Amma dan Allah kidaina shaye shayen nan kodan saboda lafiyarki, bana so kema in rasa ki kamar yadda narasa iyaye na, da kuma ya'yana," cikin shessheƙar kuka tace"Mu koma Nigeri, Nagaji da zama a ƙasar nan, ƙwara idan ina acan zanfi samun kwanciyar hankali," "Shikenan, Zanyi abunda kike so amma ki ɗan bani lokaci, In kammala wani aiki da nake yi, da zarar na gama zamu koma can ɗin kamar yadda kikeso," Gyaɗa kai tayi"wannan karan idan har baka Cika min alƙawarina ba, sai dai kawai kaji labarin Na tafi," "In sha Allah hakan bazata faruwa," sosai ya kwantar mata da hankalinta, Har ya samu Ta shiga toilet tayi wanka ta canza kaya, Da kanshi ya gyara masu ɗakin, ya tattara kwalaban Soju ɗin ya fita yaje ya jefar dasu, Sannan hankalin shi ya kwanta, *UAE* Haɗaɗdiyar Daular Larabawa Abu dhabi, Alhaji Ubaid ne zaune A cikin Hamshaƙin falon gidansa, Wanda yaji Hadaddun furniture tsadaddun gaske, ga wani sanyin A.c dake ratsa sassan Jikin mutun, Ya ɗau wankan Shadda, Ya hakimce saman 3 seater, Hannun shi na ruƙe da jarida, A gaban shi table ne mai ɗauke da mug na coffee, Ya natsu yana Karanta Jaridar, kamar daga sama yaji An fisgeta, kafin ya ɗago ya kalli wanda ya kwaci jaridar daga hannun shi, tuni tayi tearing ɗinta into pieces, Bakowa bace face Laila, Mahaifiyar Benazir, doguwar balarabiya tasha wankan Abaya launin royal blue, yalwataccen gashin kanta har tsakiyar bayanta, Ƙafafunta na sanye da High heels, Zuba mata ido yayi batare daya ce mata ƙala ba, "Idan har zaka cigaba da kallon waɗannan gantalallun Ni kuma bazan gaji da yage duk wata jarida da zaka kawo A cikin gidan nan ba, tunda na lura bakasan ciwon kanka ba, Menene alaƙarka da su? Ga ƴarka ta cikin ka da ta 6ata shekara da shekaru Baka damu da ita ba, sai wasu can rainon talauci," rai a6ace takai ƙarshen maganar, tare da juyawa ta nufi bedroom ɗinta, Sai gata ta dawo hannunta ruƙe da newspaper me ɗauke da sunan khaleej times, ta wurga mashi saman fuskar shi"Ita ce jaridar dana amince maka ka karanta, tun da karantun jaridar ya zamar maka dole" Hannu yasa ya janye jaridar daga saman fuskar shi, still idonshi na akan fuskarta, "Mutanan da kika kira da gantalallu, Sunfi ki daraja da ƙima a idona, dake da ƴar taki, Saboda bakusan ciwon kanku ba, in banda rashin ɗa'a, da rashin sanin darajar miji har kin isa Ina karanta abu kinzo ki fisge ki yayyaga, Haka aka koya maki tarbiya a gidan ku,"? Wuri ta samu saman Sofa ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, batare da tace mashi ƙala ba, Sai da ta mula tasha iska tukunna tace"bansan meke damunka, duk kabi ka sanya damuwa kan wasu kucakai, ga wadda take jinin ka, Amma sam Baka damu da ita ba," Murmushin takaici yasaki kafin yace" Benzir don son ranta ta gudu kuma tana a raye tunda har ta iya ta turo mun saƙo a duk lokacin da taga dama, Su kuwa waɗannan bayin Allahn, Rana ɗaya aka neme su aka rasa, Har yau babu labari a kansu, taya bazan damu da su ba? Jikata ɗaya da nake da ita kwallin kwal, Narasa ta, ƙaramar yarinyar da bata mallaki hankalin ta ba, Wayasan a wani hali suke ciki"? Ta6e baki Laila tayi"Laifinsu ne ae, kasan ƴan jarida da kafiya, ga shegen naci da bin ƙwaƙƙwafi, acan wurin neman labari suka tsokano abunda yafi ƙarfinsu gayanan ae yanzu wa gari ya waya,"? Yadda tayi maganar ko ajikinta, Girgiza kai Alhaji ubaid yayi yayin da yake kallonta"Hada jikarki fa a cikinsu," "Jikarka dai, Ni ban haɗa komai da su ba, Auran benzir da yaron nan ƙaddara ce, kai ka sani nesa ba kusa ba, benazir tafi ƙarfin shi, Ni nayi tunanin ma ɗan Abdallan ne shima ashe ɗan wani faƙirin mutunne dake zaune a karkara....." rai a6ace Alhaji ubaid ya dakatar da ita"Cin mutuncin ya isa haka, Kuma ki iya bakin ki, mutumin da kike kira fakiri a yanzu haka baya a raye ya riga mu gidan gaskiya, ke wai baki tsoron Allah? Mace har mace ba kyan hali, silar ki ga shi nan duk narasa ya'yana saboda gur6ata masu tarbiyar da kike yi," Murmushi tasaki tana kallon shi,"Nifa komai zaka faɗi akaina bazan ta6a jin haushi ba, Ga Coffee ɗinka nan Yana huce wa yakamata ka sha" tayi maganar tana nuna mashi Mug ɗin dake ajiye saman table, Banza yayi da ita batare daya furta mata komai ba, Kashe murya tayi tare da cewa"Habibi fushi ka ke da Nooril ƙalbin taka"? Dariya taga ya saki kamar wani zautacce, mamaki ya kamata, ta ƙura mashi ido tana kallon shi, Wayar shi dake ajiye saman sofa hand ta soma ringing, Hannu ya miƙa ya ɗauki wayar tare da miƙe wa, still da dariya akan fuskarshi ya fuce daga Cikin gidan, Girgiza kai lailah tayi"ɗan siyasa kenan, Jibi yadda ya mayar dani shashasha, Ina tunanin na harzuƙa shi ga shi nan ya fuce yana yi mun dariya wato nice mahaukaciyar, Allah ya kyauta, Ni ya dawo ma muyi magana ta fahimta, Tunda ciwon ƙafar ta shi yayi sauƙi, zan tunzura shi ya nemi takarar shugaban ƙasa, Wannan shi ne burin da nake da shi,' takai ƙarshen maganar tare da kwalawa mai aikinta Zainab kira, da sauri ta fito daga Cikin kitchen ta nufe ta, Balarabiya ce a ƙalla takai shekara arba'en, jikinta na sanye da kayan aiki, Cikin harshen labaraci tace"ki sanar ma Sauran maids ɗin Gobe A shirya Abinci kala kala na gargajiya dana zamani, Dr Shureim zai kawo mana ziyara daga egypt" Jinjina kai zainab tayi cikin ladabi ta amsa mata da"Toh, in sha Allah za'a shirya komai, Allah ya kawo shi lafiya," Laila ta amsa mata "ameen" Bayan fitar Alhaji Ubaid, A entry hall na gidan ya tsaya ya amsa Kiran da akayi ma shi daga gida Nigeria, Yana waya idonshi na akan Masu aikin gidanshi, dake ta aikace aikacansu, "Ka kwantar da hankalin ka, Lokaci kawai nake jira, Ina nan ina shirye shirye dawowa Nigeria, Siyasa fa yanzu muka sanya ƙafa ba gudu baja da baya, Namiji da jarumta aka sanshi bada ragwanci ba, Wannan karan babbar kujera nake hari, Zanyi duk iyakar bakin ƙoƙarina wurin ganin Na siye zuciyar Dattijon nan, Kona samu ya sanya mun albarka Cikin lamurrana," On the other hand muryar Babban mutumin Da yake waya da shi ce ta soma bayyana" Da kamar wuya fa, kasan halin shi Kaifi ɗaya ne, wani irin bauɗaɗɗan mutunne abunda ya yi niya shi yake aiwatarwa, Amma zamu yi kokarin shawo kanshi, Ko dan muyi nasara akan abunda muke son Cimmawa, yanzu dai dawowarka Nigeria shiya fi komai mahimmanci," "zan dawo In sha Allah, Kodan saboda Yaran nan da suka 6ace, Sunan ina zaune ne a Ƙasar nan amma tunanina gaba ɗaya yana a nigeria, nadamu da su," fuskarshi ɗauke da matsananciyar damuwa yakai ƙarshen maganar, abokin nashi da suke waya yace"Wai har yansu babu labarin su? Ae ni da naji shiru nayi tunanin an same su ne," muryarshi da alamun mamaki "kusan shekara biyu fa kenan babu su babu alamarsu, Ni tsorona ma kada ace abokan hamayyata ne suka Farmake su, kasan mutanan nan ba imani ne da su ba, Komai zasu iya aikatawa indai akan siyasar su ce," Jajanta ma shi abokin na shi ya yi, da ga haka su kayi ma Juna Sallama, Har ya juya zai koma Cikin falon, Yaji ƙarar shigowar mota, juyawa yayi yana kallon Motar da ta shigo, Danƙareriya mota mai numfashi, da alama Baki ya yi, Bodyguard ne Ya fita daga Driver seat na motar, Ya zagaya ya buɗe mashi mota, Wata irin dariya Alhaji ubaid ya saki lokacin da yayi tozali da Alhaji badamasi, Mataimakinsa Lokacin da yana gomna a jihar jos, da sauri ya nufe shi yana faɗin"Marhaban bika Mutumina, Irin wannan zuwan bazata haka, Yaushe ka shigo ƙasar" Alhaji badamasi sai faman washe baki yake yi, yayi shigar larabawa, Ga wani ƙamshi dake fita a jikinshi, Rungume juna su kayi kamar zasu haɗiye juna, A tsaitsaye suka fara gaisawa kafin Suka Nufi Cikin garden ɗin gidan, A waya ya kira lailah yace Ayi ma mai aiki magana ta kawo masu kayan marmari su sha, A garden a kayi masu Shimfiɗa Saman Lallausar darduma suka zauna domin tattaunawa a tsakanin su, Shin Ya rayuwar Angel ta kasance bayan An sace ta Cikin Mota? Sambatu take ta faman yi, Cikin fitar hayyaci, tarasa gane inda take, Ko'ina duhu, babu haske ko misƙala Zarratin, jikinta yayi mata wani irin nauyi tamkar an ɗaura mata dutse a samanta, Ko yatsan ta ta gaza ɗagawa, Wani baƙon yanayi da bata ta6a jin kanta acikin shi ba, ga zafi ta ko'ina, numfashin ta kanshi daƙyar take fitar dashi, atakure take jin kanta, tun tana kukan a bayyana har ta koma tanayin na zuci, Cikin disasshiyar muryarta ta soma ambaton duk wata addu'a da tazo bakin ta, Tsawon mintuna talatin kenan, tana acikin wannan yanayin ta haɗa uban gumi, duk ta cicci je la66an ta sun faffashe, Saboda ƙuncin da take Ciki, takaici ya isheta, ta kuma rushewa da kuka tana faɗin"Wai ba kowa ne a kusa, Ku faɗamun ina ne nan! Wayyo Allah na! Danejo! daddy Can you hear me! its me ur angel, pls if u are hearing my voice, Answer me, Am really scared of being alone in this darkness......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, Wani irin raɗaɗi maƙoshin keyi mata hada ƙaiƙayi,Tana Cikin buƙatar ruwa, throat ɗinta ya bushe ƙamas, Ƙoƙin motsa lips ɗinta tayi da niyar ta ƙara magana, Ba zato ba tsammani, haske ya soma bayyana Acikin wurin da take, nan take ta dakata da yin kuka biji biji ta fara gani kafin idanuwan nata su ka washe ta ƙura ido tana Kallon Ceiling ɗin da take fuskanta, Dogon Ginin dutse ne mai matuƙar Girma da faɗi da tsayi, Ceilling ɗin Yayi uban soro daga inda take daƙyar ta ke iya hango ƙarshen shi, wasu fitilu ne jere can saman ceilling ɗin, hasken su ne ya gauraye Cikin ɗakin da ta ke, sauke idanuwanta tayi tare da yin ƙoƙarin miƙewa zaune, don ta samu damar ƙarewa baƙon wurin kallo, tamkar hostel na kwanan ɗalibai haka wurin ya ke, daga 6angaren da take kwance 6angaren yamma ne tana fuskantar gabas akwai jerin gada je da a ka yi su da Metal(ƙarfe) A ƙalla sun kai goma sha biyar, single bed ne na mutun ɗaya kowane gado yana da lallausar mattress a saman shi, tare da matashin kai (pillow) da kuma duvet, launin farare, a ɗaya daga Cikin gadajen ANGEL take a zaune, tana bin kowace kusurwa ta ɗakin da kallo, akwai wasu kujeru da a kayi su da Katako zubin armchairs guda biyu dake ajiye, agaban kujerun there's a table an ɗaura wasu fitilun kusan uku a saman shi, daga tsakiyar ɗakin akwai shimfiɗaɗɗen red carpet, Saukowa Tayi daga saman gadon Cike da fargaba take kallon baƙon wurin da ta tsinci kanta a cikin shi, juyawa tayi tana kallon bayanta bene ne madaidaici, da alama akwai ƙopa a can saman stairs ɗin, Amma daga inda take tsaye bata iya hangen ƙopar ta yi lungu, Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su akan ƙopar dake a rufe, saman ƙopar taga an rubuta "Toilet" nan take ta gane makewayi ne, ɗakin yana da tagogi both left and right na jikin bango amma an garƙame su, ginin da alama tsohon gini ne aka sabunta shi, A ruɗe take zazzare gray eyes ɗinta da suka jiƙe sharkaf da ruwan hawaye, long eye lashes ɗinta duk sun cukurkuɗe, dogon hancinta yayi jawur da shi saboda matsar da ya sha lokacin da take ku ka, heart shaped lips ɗinta sunyi light pink sun bushe ƙamas, gaba ɗaya ta rikice musamman da ta shafa jikin ta, a hautsine ta kalli uniform ɗin da aka sanya mata, launin baƙaƙe zaro ido tayi ganin an canza mata kaya ita a iya saninta kayan fulani ne ajikin ta lokacin da ta gudo daga hannun fulanin daji, hatta kanta kitson kalaba ne da danejo ta yi mata amma yanzu an warware mata kitson an sakar mata gashin ga shi nan a haukace har kusan waist ɗinta ya yi mata tamkar hijabi, uniform ɗin jikinta riga ce me dogon hannu takai mata har guiwarta, sai dogon wando har kasa, a bayan rigar an rubuta no 1, Juyawa ta yi da gudun gaske ta nufi benan nan, a zafafe take tattaka matattakalar har takai bakin ƙopar sai dai a garƙame take an rufe ta, Hankali a matuƙar tashe ta dunga bubbuga ƙopar tuntana yi a hankali tana tambayar bakowa ne anan har takai ga kai ma ƙopar naushi ta ƙafa ta hannu, tamkar ƴar dambe duk ta raunata jikin ta, Saboda ƙopar ta metal ce, Jiri ta fara gani acikin idanuwanta ba arziƙi ta dakata tana fama mayar da numfashi, zufa ta ko'ina a kan fuskarta, Jingina bayanta ta yi a jikin hand rail ɗin benan a galabaice, ga uwar yunwa tana ji kamar tacin ye ƴan hanjin cikinta, Tana cikin wannan yanayin ta jiyo motsin tafiyar mutane can kuma taji alamun ana buɗe ƙopar ɗakin da take ciki, a hanzarce ta wurga eye balls ɗin ta kan ƙopar tana jira taga wata ja'irar ce ko wani ja'irin ne xai shigo, domin kuwa ta ɗaura ɗamarar yin yaƙi da duk wanda ya yi silar ɗauko ta daga saman titi ya kawota wannan wurin mai kama da prison. Cikin ƙanƙanin lokaci aka buɗe ƙopar tare da turo ta, awani slow angel ke kallon ƙafar mutanan da suke ƙoƙarin shigowa ciki, wasu gabza gabza Mutanene masu tsayi da faffaɗan ƙirji, Wata kalar ƙira gare su mai ban tsoro kowannan su na a cikin Shiga ta baƙaƙen kaya long coat har guiwa sai dogon wando, sunyi 6adda kama ta yadda ko akaifar hannunsu baka iya gani, sun sanya mask a fuskokin su, Sun 6oye ainihin halittar su, ƙafafuwansu kuwa Army boots ne suka sanya, kawunansu na sanye da cowboy hat, dai dai da ziririn gashin kansu baka iya gani ko'ina arufe ya ke, motsa lips ɗinta ta soma yi da niyar ta yi magana sai dai kafin ta yi yunƙurin furta wani a bu, idanuwanta suka sauka akan ƙafar matashin saurayin da ke ƙoƙarin shigowa, kalar uniform ɗinta ne ajikinshi baƙaƙe masu ɗauke da No 1 A halitta dogo ne fari sol da shi, kyakkyawan gaske, Droopy eyes ɗin shi farare ƙyal da su, Yana da dogon hanci, full lip ɗinsa red colour ne, yana da dimple ɗaya a gefen fuskar shi wanda ko motsa lips ɗinsa ya yi sai ya lotsa, Yana da yalwatacciyar sumar kai, ta kwanta luf har mid back ɗinsa dark brown saboda tsabar kyanshi sai ka rantse da Allah maca ce ba namiji ba, ta yi tunanin shi kaɗai ne wuce warshi ke da wuya, sai ga wata matashiyar budurwa me sanye da black uniform no 2, itama fara ce sosai doguwa kamar angel tana da manyan idanuwa ga dogon hanci, soft lips ɗinta brownish colour ne, tana da yawan gashi ya cika kanta kamar an kifa mata kwando, tsayin shi ya haura kafadarta, Tana ƙarasa saukowa sai ga wasu matasan ƴan mata masu sanye da red uniform kowanne da numbers a bayan rigar shi, gasu nan kala kala wasu baƙake wasu farare wasu wankan tarwaɗa, kamar yadda angel ke kallonsu haka suma suke binta dana mujiya, A kalla mata sunkai goma acikinsu maxa kuma biyar, sai da suka kammala shigowa tukunna waɗannan GIANTS ɗin su ka fuce daga ɗakin bayan sunyi locking ƙopar, Cikin tashin hankali angel ke bin kowannan su da kallo, can dai tace"wai uban wanene ya kawo ni wannan wurin! Menene alaƙata da ku!"nuna matasan ƴan matan ta yi da yatsan hannunta "ku faɗamun su wanene ku?kuma ina ne wurin nan? kun wani tsare ni da ido kuna kallo na" a harzuƙe ta yi maganar, ɗaya daga cikinsu ce wannan me black uniform no 3 ta soma magana cikin harshen turanci"kamar yadda kika tsinci kanki a cikinsa batare da sanin ki ba, mu ma haka muka tsinci kan mu, abu ɗaya na sani shi ne, kurkukun ƙaddara gida ne na marayu wanda basu da gata,' girgiza kai angel ta yi'ae ni ba marainiya ba ce, iyaye na suna araye wlh bazan zauna acikin kurkukun nan ba, i must find away to leave........" kafin takai ƙarshen xancen nata wata matashiya me ɗauke da uniform jajaye no 4 baƙa siririya tace"ba gidan cutarwa bane, gidan taimakon marayu ne zasu tallafi rayuwarki, dayawa ma anan aka rainesu tunkafin su mallaki hankalinsu, xamu samu kulawa tunda bamu da kowa kurkukun ƙaddara shi ne gidanmu" Uwar harara angel ta wurga mata"prison will neve be a home for me, ba zan ta6a lamunta ba, taya za'a sato mutun akawo shi wani baƙon wuri sannan ace gidan marayu ne? Ta gidan ubanwa aka gaya masu cewa ni marainiya ce, da uwata da ubana kuma da dangina, ba daga sama na faɗo ba," yadda take magana rai a6ace har wani huci ke fita daga cikin bakinta, Takun tafiya suka jiyo daga cikin ɗakin muryar wata tsohuwa tukuf suka jiyo tana faɗin"Ina Magana"da hanzari dukansu suka sauka daga saman benan xuwa cikin ɗakin hada angel, Tsayawa su kayi idanuwansu akan tsohuwar, a tsaye take jikinta na sanye da doguwar riga mai gashi gashi ajikinta, launin ja hannunta na ruƙe da sanda fara ce tass ta tsufa tukuf idanuwanta duk sun zurma, fuskarta ta yi uban tamoji tamoji, kanta babu gashi ko ɗaya da yake baƙi, gaba ɗaya uwar hurhurace hatta jagirarta hurhura duk ta kamata, hada gemu gare ta fari fatt yadda kasan namiji, ga wani katon hanci dake gare ta, uban gi6in dake abakinta yadda kasan ƙogon dutse, haƙora huɗu kaɗai suka rage abakinta na sama dana ƙasa, can cikin kursurwar bakinta, dogayen haƙora ne ko ta rufe baki sai na saman sun leƙo waje, hannayenta kuwa xaƙo zaƙon akaifu ne haka ƙafafuwanta wasu tsoffin takalma ne launi rigarta jajaye, kunnuwanta falo falo an manna masu bari ma, Mamaki ne ƙarara akan fuskan angel, ta ya akai tsohuwar ta shigo cikin ɗakin batare da ta biyo ta ainihin ƙopar shigowa cikinsa ba? To kodai ta saman rufi ta duro ne ?ko kuwa bango ta tsaga ta shigo? Kamar daga sama angel ta ji tsohuwar tace"ko ɗaya! ta ƙopa na shigo ciki" ta yi maganar tare da juyawa tana nuna mata wata ƙopa dake a ɗaya daga cikin kusurwowin ɗakin, "Nan ɗaki na ya ke, Ni tamkar uwa nake awurin ku, dayawa sunsan wacece ni saboda na shayar da wasun ku, wasu kuma na rainesu kamar DANISH da BATOOL!" ta kai ƙarshen maganar tana nuna wannan mai kyakkyawar matashin nan da sandar hannunta tare da wannan matashiyar mai kama da larabawan, sunayen su ne ta faɗi, masu kalar uniform ɗin angel," Angel dai wani irin kallo take binta da shi, mamakin ta ke taya akai tsohuwar take karantar abunda mutun ke saƙawa acikin zuciyarshi"? "Ni duk ba wannan ba! Meyasa aka kawo ni gidan nan? Nifa ba marainiya bace, Ko da ace ni marainiya ce taya za'a sato mutun akawo shi cikin wannan munafukin ginin ace wai gidan marayu ne? Taya akai ku ka san cewa ni marainiya ce? That means ku ne ku ka kashe mun mahaifina kenan? Sannan ku ka raba ni da mahaifiyata itama ku ka kashe ta ko? Dama can kuna bibiyar rayuwata in ba haka ba ta ya akai ku ka san ina a hannun fulanin daji? Har ku ka tura aka ɗauko ni? wai menene manufar ku tayin hakan huh? "Gidan kurkukun ƙaddara Gidan Marayu ne wanda suka rasa gatansu, duk yaron da ki ka gani acikin prison ɗin nan to ba shi da iyaye! Zai iyayiyuwa iyayenki sun mutu batare da sanin ki ba, sa'annan duk wanda ki ka gani acikin kurkun nan na jininsa ne ya sadaukar dashi zuwa gare mu don mu gatanta shi har zuwa lokacin da zai mallaki hankalin shi" tsohuwa ce ta kora mata wannan jawabin, Still angel ta gaza fahimtar inda zancen ta ya dosa cikin ɗaga murya tace"If it's an orphanage, then why is it called a prison? You just wanna mislead me with your lies, I won't believe you, idan har kuna son zaman lafiya ku mayar dani inda ku ka ɗauko ni cikin salama in ba haka ba zan addabi rayuwar ku" takai ƙarshen maganar tana haki ta harzuƙa sosai, Sauran prisoners ɗin duk suna a tsaitsaye cirko cirko suna sauraran tattaunawar baƙuwar yarinyar da su kayi tare da tsohuwa, tun da suke a gidan prison ɗin ba'a ta6a samun yarinyar me taurin kai da kafiya ba irin baƙuwar da suka tsinta yau acikin su, "Bansan wacece ke ba, amma na lura kamar kina son wuce gona da iri, yakamata ki kiyaye harshen ki, wannan tsohuwar da ki ke gani tamkar uwa take agare mu, tun da mu ke da ita bata ta6a cutar damu ba, muna samun kyakkyawar kulawa daga gare ta, don haka bazamu bari zuwan ki ya zama silar tarwatsewar farin cikin mu ba hope u understand me!" A wani slow angel ta juya don taga wani isasshe ne ya yi mata magana, sauke idanuwanta ta yi akan kyakkyawar fuskarshi sai ka rantse da Allah bashi bane ya yi maganar, daga ganin shi akwai izza atattare da shi," "Sannu isasshen me walkin sa! Kai kuma a suwa ɗan wake a hotel? am talking you are talking? duk wanda ke son zaman lafiya acikin ku, kada ya kuskura ya shiga gona ta, domin ni ba irin ku bace! Wlh uban mutun zanci kuma a zauna lafiya!" Tana huci takai ƙarshen maganar tare da ɗauke idanuwanta daga kan shi ta mayar dasu kan tsohuwar" ke kuma tsohuwa na dawo gare ki! Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, Kuma a faɗa mun uban wanene ya sadaukar dani xuwa gidan nan! Saboda idan na samu damar fita daga cikin sa inje in naƙasa rayuwar shi" Lallai angel ba sauƙi a zafafe take magana tana huci yadda kasan mayunwaciyar zakanya, Sassauta murya ta yi"idan kun saba rainawa mutane hankali kuna ɗaukosu ku kawo su cikin gidan nan da sunan zaku gatanta su, to ni ba kalar su bace, ni ba marainiya bace kuma ni bana buƙatar gatanci daga wurin ku, Gata na shi ne Allah koda kuwa bani da kowa a duniyar nan ina da Allah," Murmushi tsohuwar tasa ki yayin da take kallonta tace"buri ya yi kama da mutun, da ace baki yi wannan haukan ba, da bazan tabbatar da cewa ke ɗiya ce ga Zaheer tajuddeen ba, hatsabibiyar yarinyar da ta addabi mahaifinta ina da labarin ki tunkafin zuwan ki duniya" Ruƙe qugu angel ta yi yayin da take kallonta, jin wani soki burutsi da tsohuwar ta yi mata, "Bazan yi jayayya dake ba, saboda nasan wacece ke! abu ɗaya nake so in tunasar maki shi ne, ke marainiya ce mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan mahaifiyar ki ma ta rasu babu ita, danginki kuma su ne suka damƙa mana ke don mu raine ki wannan dalilin ne yasa kika kasance acikin Gidan kurkuku saboda mu ne gatan ki, kuma muke da alhaƙin ɗaukar responsibilities na rayuwarki, kama daga cin ki shan ki da sauransu....idan ki kayi biyayya mu kuma zamu sama maki farin ciki," Hawaye ne suka wanke fuskar angel jin cewa mahaifinta ya rasu duk da bata gasgata maganar dattijuwar ba cikin shessheƙar kuka tace"kiji tsoron Allah ki fada mun gaskiya daddy na bai mutu ba! Kuma ƙarya ki ke yi mun na cewa dangina ne suka kawo ni cikin wannan kurkukun," Matsawa tsohuwar ta yi zuwa inda angel take atsaye, ta tausasa murya tare da cewa"ƴar nan ki kalle ni tsofe tsofe dani da ace na ta6a aure da yanzu nayi tatta6a kunne dake, amma har kika iya buɗe baki ki kace mun ƙarya nake yi? Lallai babu tarbiya atare dake shiyasa ƴan uwanki suka kawo ki prison don mu koya maku ladubban rayuwa, sa'annan ina mai ƙara tabbatar maki da cewa mahaifin ki ya rasu babu shi a doron duniyar nan, nasan ke bakisan da hakan ba saboda ya jefa ki acikin ruwa shiyasa baki ga lokacin da ya rasu ba, idan har kina son sanin komai game da mutuwar mahaifin ki, zan fada maki hatta wanda su kayi silar mutuwar shi, amma fa ba yanzu ba sai naga hankalin ki" Tana kai ƙarshen maganarta, bata jira angel ta bata amsa ba, ta juya tana dogara sandarta a daddafe ta nufi ƙopar shiga ɗan ɗakinta, Zubewa angel ta yi saman guiwowinta tare da fashewa da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, gaba ɗaya ta ji ta tsani kanta, komai ya sire mata zuciyarta ta karaya dama saida ranta ya bata cewar kodai daddynta ya mutu ne, dama yasan mutuwa zai yi shiyasa ya jefa ta acikin ruwa shi kuma ya tsaya waɗannan mutanan da suka biyo su da mota suna harbinsu suka kashe mata daddynta, Ƙara sautin kukan nata ta yi tana ambaton"Innallahi wa'inna ilahirraji'un! Wayyo Allah na daddy na! Sun kashe mun daddyna shikenan sun raba ni da farin ciki na, sun raba ni da Mahaifina sun naqasa mun rayuwata, ya Allah ka ɗauki raina nima in huta........."sosai take kuka fuskarta ta yi jawur jaga jaga da hawaye hada majina, Duk suna tsaye suna kallonta, an rasa wanda zai lallashe ta, saboda basu saba da ita ba, wasu kuma shakkar ta suke ji yayin da wasu kuma suke jin haushinta saboda ta zagi tsohuwa wadda suka ruƙa amatsayin mahaifiyarsu, Tuntana yin kukan nata da sauti har takai ga kakarewa muryarta ta dissashe ta, anan ta yanke jiki ta faɗi a sume. Guntun tsoki matashin saurayin nan yaja, tare da ta6e lips ɗinsa ya yi gaba abun shi ya nufi gadon shi me ɗauke da no 2 haka kowani gado yake da number, Suma sauran matasan suka wuce zuwa saman gadajen su, mutun ɗaya ce ta kasa tafiya saboda tsananin tausayinta da take ji, kuma ita har ga Allah yarinyar ta kwanta mata aranta, Hannayenta bibbiyu ta sanya tare da tallabo kan angel dake a ƙasa ta ɗaura shi saman cinyarta, juyawa ta ɗanyi tare da kallon kowannan su dake kishingiɗe saman gadonshi, tsayar da ƙwayar idonta ta yi akan Hannah ta ɗan ɗaga murya tare da cewa"abunda ku kayi ba ku kyauta ba, kuna ganin halin da take aciki na rashin mahaifinta amma kowa ya yi shiru ya wuce ta babu me lallashinta? Ta6e baki hanna ta yi"rashin mahaifi akanta aka fara rashi? tafi mu gata fa dayawan mu nan tun muna jarirai aka kawo mu kurkukun nan, mun ta shi ba mu san kowa namu ba, bamu da wanda ya damu damu tsohuwace kaɗai gatan mu, kuma agaban mu ta zageta tass ba ta ga girman gemun ta ba, saboda rashin kunya irin ta ta," Hanna na rufe baki, wani saurayi dake a cikinsu tuttu6e6e me suna haris yace"nifa bata kwanta mun araina ba, kyau kamar aljanna, kuma daga gani ma duk mun girme ta, "yana rufe baki mubeen ya kar6e da cewa"bazata wuce shekara takwas ba wannan jibi yadda take raira mana kuka kamar ba'a gama rainon ta ba," Gaba ɗaya suka sanya dariya, ran batool ya 6aci, "Is enough, kunsan bana son hayani ya" wannan kyakkyawar saurayin ne da tsohuwa ta kira da sunan DANISH ya yi maganar tare da lumshe idanuwanshi ya kwantar da kanshi saman pillow, Jinjina kai batool tayi, jiki asanyaye ta sauke kan angel a ƙasa, ta miƙe da hanzari ta nufi toilet ɗinsu, jim kadan ta fito hannunta ɗauke da ruwa sai sauri take yi saboda zubar da yake yi, adai dai saitin fuskar angel ta yarfar da ruwan, nan take taja dogon numfashi batare da ta buɗe idanuwanta ba, yatsun hannunta ne kaɗai suke kerma, miryarta adisashe take faɗin daddyna bai mutu ba, he is still alive ina ji araina sai sambatu take yi, ga wani irin matsanancin ciwon kai daya far mata ga yunwa da ƙishir ruwa duk ita kaɗai, Cikin sanyin murya batool ta yi mata magana"SISTER" har cikin kunnanta taji sautin kiran yadda kasan wadda aka tsokano a hargitse ta buɗe idanuwanta da suka kada su kayi jawur da su, yunkurawa ta yi da hanzari ta ɗauke kanta daga kan cinyar batool, ta jefa mata uwar harara tare da cewa"bana son ganin kowa a kusa dani, bana son kowa," ❤dedicated to Aunty kubra❤ *Daga alƙalamin Boss Bature✍️* *E11 Tuntsirewa su hanna su kayi da dariya jin yadda ta gwasale Batool, "Bai kamata ki yi mun haka ba, kowa yaƙi kula ki a lokacin da ki ka suma ni ce kaɗai na damu da ke amma shi ne kika watsa mun ƙasa a ido"? Cigaba da kuka angel ta yi ba tare da tace mata uffan ba, ita kaɗai tasan raɗaɗin da take ji, Zuba mata ido Batool ta yi batare da ƙyaftawa ba, Adai dai wannan lokacin suka soma jiyo motsin buɗe ƙopa, gaba ɗaya suka kai idanuwansu bakin benan Turo ƙopar a kayi waɗannan Giants ɗin ne su uku masu sanye da baƙaken kaya su ka shigo hannayen su ɗauke da Faffaɗan wooden trays masu ɗauke da kayan abincin su, kowanne na a ruƙe da faranti ɗaya, Bayan sun ƙarasa sauko wa kai tsaye su ka nufi jan carpet din nan, a saman shi su ka sauke farantan, kafin suka ja gefe ɗaya suka goya hannayen su asaman ƙirjinsu, dama ƙa'idar aikin su ce idan suka kawo masu abinci ba su tafiya tsayawa suke yi har sai sun kammala tukunna su kwashe kayan abincin su tafi, kuma basa magana sai in ta kama dole, one by one su ka soma saukowa daga saman gadajen su, izuwa gaban kayan abincin kowa ya samu wuri ya zauna, ruƙo hannun angel batool ta yi tare da cewa"ki taso muje mu ci abinci," fusge hannu angel ta yi" bazan ci ba, ni kawai a mayar dani inda aka ɗauko ni," "This is the only chance u ave to eat, we get food once a day, if u don't eat it now, u will lose ur food," cikin sigar lallashi batool ke yi mata magana, ita kuwa ta kangare akan baza taje taci abincin ba. Miƙewa batool ta yi duk bata ji daɗi ba, taso ace yarinyar ta saki jiki da ita amma ta nuna kafiya, wuri ta samu saman carpet ɗin ta zauna, faranti na farko Grilled Chicken wraps ne guda goma sha biyar a jere, iya adadin su, faranti na biyu kayan marmari ne nunannu an yayyanka su, a faranti na uku wooden cups ne guda goma sha ɗaya, sai jugs guda biyu ɗaya na ruwa me sanye ɗaya kuma na Lemu ne da aka hada da nau'ikan kayan marmari, A tsanake kowa yakai hannu ya ɗauki chicken wraps ɗinsa, suna Ci suna satar kallon angel, batool dai bata ji daɗi ba, ganin taƙi tasowa taci, ga nata nan ajiye shi kaɗai, idan wani ya cinye tayi asara, in kuma ba'a samu wanda yaci ba, zasu tafi da shi ne. baiwar Allah ta galabaita sosai, ga jaraba nacin ta ga yunwa ga kuma abinci amma taƙi ta shi taje ta xauna cikin su ta ci, wani irin ƙululun baƙin ciki ne acan ƙasan zuciyarta, eyes ɗinta a rufe hawaye ke gangarowa saman kuncinta, Ƙasa ƙasa da murya batool ke yi mata magana"ki taso ko ci," maƙe kafaɗa angel ta yi, alamar baza ta zo ba, A ƙarshe ma sai ta miƙe tana tangal tangal zata faɗi amma ta jure a haka ta taka izuwa gaban waɗannan Giants ɗin ta ci burki ta tsaya, "Ku maida ni inda ku ka ɗauko ni, bansan zunubin dana aikata ba, da har za'a sato ni izuwa cikin wannan kurkukun," magana take yi masu amma ko uffan basu ce mata ba, domin kuwa a tsarin aikinsu basa magana da prisoners, "Dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa waɗannan da kike gani basa ji basa gani, idan kuma kika ce xaki matsa masu jikin ki ne zai gaya maki" Juyawa angel ta yi da sauri don taga wani ja'irin ne ya tsoma mata baki, ɗaya daga cikin matasan ne me suna naufal, Nuna shi ta yi da yatsan hannunta"karka kuskura ka ƙara shiga hurumina, ba ruwan kowa da rayuwata," juyawa ta kuma yi kansu cikin xafin rai tace"magana nake yi maku, ku faɗamun wanene ya bada umarnin a kawo ni wurin nan? Shiru basu tanka mata ba ga shi bata iya ganin koda ƙwayar idonsu ce balle tasan ko suna kallon ta, Zubewa tayi saman guiwowinta tana raira masu kuka tamkar ranta zai fita, tana ji tana gani suka kammala cin abincin, Giants ɗin nan suka tattara kayan abincin suka kama hanyar fita daga ɗakin, ranta ya 6aci ta dunga ɗura masu ashar kamar ɗiyar maguzawa, Da gudu tabi bayansu tana kuka tana zagin su, ƙopa suka buɗe suka fuce, ƙopar ta datse, ta dinga bugun ƙopar tana kuka, silalewa tayi bakin kopar ta kwantar da kanta, tako ina babu sauƙi, "Idan kina jin bacci, gadon ki shi ne no 1 zaki iya zuwa kije ki kwanta" batool ce ta yi mata maganar, tana a tsaye saman matattakalar benan, buɗe idanuwanta tayi waɗanda suka kaɗa su kayi jawur, ta watsa mata harara muryarta a disashe tace"wai ke mayyace? Ki rabu dani mana kamar yadda sauran ƴan uwanki suka yi," jinjina kai batool ta yi," I worry about you but you don't worry about yourself, i won't disturb u again tun da kin buƙaci hakan, just whenever u change ur mind, za ki iya yi mun magana,' jiki a sanyaye batool ta juya ta koma cikin ɗakin, Tuni kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, wasu suka kama bacci wasu kuma suna zaune suna fira, Yinin ranar angel a galabaice ta yi shi, sai da takai ga bata gane komai idanuwanta sun rufe saboda tsabar jin yunwa, ga raɗaɗin da zuciyarta ke yi mata, wani irin matsanancin ciwon kai ne ya far mata, a nan saman benan ta zube rai hannun Allah, lokacin da dare ya yi, hasken ɗakin da kan shi ya ɗauke, dama ƙa'ida ne idan dare ya yi gaba ɗaya hasken wurin yake kashe kan shi, sai dai mutun in yana buƙatar haske ya yi amfani da fitilun da ke ajiye saman table, Duhu ya mamaye idanuwanta, ta ƙuntata sosai ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu, wannan wata irin rayuwa ce me cike da ruɗa ni? taya zata ci gaba da rayuwa acikin kurkukun nan? ta gaza gane sarƙaƙiyar da ke acikin rayuwarta, shin wanene a cikin danginta ya kawo ta cikin gidan kurkuku da sunan araine ta? Anya kuwa wannan ba ƙanzon kurege bane? tabbas akwai mata maƙarƙashi a cikin gidan kurkukun nan, A cikin zuciyarta take wannan tunane tunanen, Saboda tsabar yunwa ko yatsanta, bata iya ɗagawa, Batool sam ta kasa runtsawa saboda halin da yarinyar take ciki, ta damu da ita sosai ga shi ita kuma bata so ta kusanto ta, kowa ya yi bacci ban da ita, Saukowa ta yi daga saman gadonta cikin duhu ta shiga laluban inda fitilun suke, har Allah yasa ta gano table ɗin takai hannu ta ruƙe handle ɗin fitilar bayan ta kunnata, tafiya ta soma yi Cikin ɗakin har zuwa saman benan anan ta samu angel cikin mawuyacin hali, zuƙunnawa ta yi agabanta, muryarta ƙasa ƙasa tace"Yar uwa" angel bata iya amsa mata ba, domin kuwa takai mataki na ƙarshe wanda ko la66anta bata iya motsawa, a lokacin jikinta ya yi mugun yin sanyi ta fidda rai da rayuwa, cikin zuciya ta dinga yi furta kalmar"ruwa! ƙishi nake ji! A taimaka mun," batool batasan me take cewa ba, saboda a cikin zuciya ta yi maganar, Allah dai ne kawai ya taimake ta, batool ta yi tunanin ko tana buƙatar ruwa, dama ɗazu ta 6oye mata chicken wraps ɗinta, tun ɗazu taso ta bata taci sai dai taƙi bata fuska, shiyasa ta ajiye mata zuwa lokacin da zata neme ta, Miƙewa ta yi da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta inda take ajiyar ruwa acikin bottle water, ta zuƙunna tana haskawa da fitilar hannunta, kwando ne ajiye a karkashin gadon, a cikin shi take 6oye abinci idan ta rage saboda gudun yunwa, zura hannu tayi ciki ta ɗauko Chicken wrap ɗin, Ta tura cikin aljihunta, sannan ta ɗauki robar ruwan ta ruƙo a hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma yana a ruƙe da fitila, da sauri ta koma saman benan saitin inda angel take ta zuƙunna, ta sauke fitilar ƙasa, tare da bottle ɗin, hannu tasa ta tallabo kan angel ta jingina shi gefen shoulder ɗinta, Sannan ta ɗauki bottle din ta buɗe murfin ta kafa mata bakin robar, yadda kasan mafaraucin da yayi rashin ruwan sha na tsawon sati ɗaya haka angel ta shiga ɗaɗɗakar ruwan, maƙoshinta har wani sauti yake badawa, kwat kwat! Murmushi batool ta saki ba ƙaramin daɗi taji ba ganin yadda take shan ruwan,, Yarinya taji ƙamshin mutuwa, Sai da ta shanye ruwan nan tass tamkar xata haɗa da robar ruwan duka ta shanye, Janye bottle ɗin ruwan ta yi daga bakinta, ta ajiye ta saman matakalar, ta mayar da murfin a mazauninsa, Hannu ta zura cikin aljihun ta, ta ciro chicken wrap ɗin duk ta rugurguje, a haka ta dinga tura mata abaki, la66anta har kerma suke yi wurin ci, kuma har lokacin kanta yana asaman ƙirjin batool, sai da ta cinye tass ta soma jin wani irin tashin zuciya, yunƙurin amai ta soma yi, a ruɗe batool ta shiga bubbuga bayanta tana faɗin"Sorry sis, bari na raka ki toilet" kafin batool ta miƙe ta yi yunkurin tallabota, tuni Ta saki aman anan saman benan, ta dinga kwararo shi gaba ɗaya ya 6ata hada jikin rigarta, baiwar Allah taji jiki, saboda tsabar tausayinta da batool take ji, batasan lokacin da ta fashe da kuka ba, duka chicken wrap ɗin da taci sai da ta amayar da ita, tun ruwa na fita abakin ta, har yakai ga babu komai sai dai kawai kakarin aman da take yi, Ganin mawuyacin halin da ta shiga ne yasa batool ta miƙe tare da ɗaukar fitilar, ta ruga da gudu zuwa ƙopar ɗakin tsohuwa, knocking ƙopar ta soma yi tamkar zata 6alleta, Mutun uku dake bacci saida su ka farka, Danish da ya kasance baisan hayaniya ko misƙala zarratin, Sai hanna da kuma Haris, Har suna haɗa baki wurin tambayar Batool lafiya take neman tsohuwa, ko ta kansu bata bi ba, har saida tsohuwa ta buɗe ƙopar, Hannunta ruƙe da sanda ta fito, batool na kokarin buɗe baki ta yi mata jawabi, tariga ta cewa"Kada ki damu, ki koma wurinta zata dawo dai dai, nayi mata addu'a daga cikin ɗaki," tana faɗin hakan ta juya ta koma cikin ɗakinta, tare da jan ƙopa ta rufe, Jikinta asanyaye ta juya sam ba haka taso ba, taso ace tsohuwa tazo ta duba jikinta, saboda halin da yarinyar take ciki, muryar Haris ce ta ratsa kunnanta"Just because her duk kin damu kanki, kin hana idonki bacci, meye alaƙarki da ita"? Hanna tace"tambayar da nake so na yi mata kenan, shi dai danish baice komai ba, bacci ne dai an hana shi yi, ya takure saman gadon shi, sai faman lumshe ido yake yi, Batool ku wa Ko kallo basu ishe ta ba, lokacin da ta koma wurin angel, wani abun mamaki a zaune ta same ta, ta jingina kanta jikin bango, shanyayyun idanuwanta a buɗe sun kaɗa sunyi jawur, Sumar kanta duk ta barbazo mata har saman fuskarta, la66anta na kerma take ambaton"rabbi yassir wala tu'asir watammim bil khairi" wani irin farin ciki ne ya lullu6e batool, har batasan lokacin da ta saki murmushi ba, maganar tsohuwa ta tabbata ga shi ta farka har tana magana, duk da batasan me take cewa ba, "Yar uwa" ta ambaci sunanta, idanuwanta Jiƙe sharkaf da hawaye ta ɗago ta kalle ta, wato duk irin korar da take yi mata hakan baisa ta guje taba, lallai ba ƙaramin so take yi mata ba, batool ba tayi tsammanin zatayi mata magana ba, sai ji tayi tace"Ina so in wanke jiki na, bana jin daɗi," Miƙa mata hannu batool tayi"ki taso na raka ki toilet" miƙa mata hannu angel tayi, ta ruƙo nata daƙyar ta samu ta miƙe, ita kanta ta yi mamakin yadda ta rayu don ba ƙaramar azaba tasha ba, taji jiki sosai, amma yanzu ko yunwa bata ji, jikinta ba wani ciwo, sai dai ciwon dake a cikin zuciyarta dake tafarfasa, Har toilet batool ta rakata, da yake babu wadataccen haske bata iya kallace shi da kyau, A bakin fanfo suka tsaya ta wanke mata gaban rigarta daya 6aci da kuma wandonta, wani irin sanyi jikinta, tuni ta soma kerma, Fitowa su ka yi daga Cikin toilet ɗin hannunsu cikin na juna, batool ta kai ta har saman gadonta mai ɗauke da no 1 kusa dana danish na shi no 2 ne, sai na batool no 3, hawa saman gadon ta yi batool ta lullu6a mata bargo asaman jikinta, sosai ta ƙudundune, Komawa batool tayi ta gyara inda angel ta 6ata da aman, ta goge ko'ina duk ita kadai baiwar Allah, bayan ta kammala ta dawo Cikin ɗakin ta ajiye fitilar saman table ɗin, ta kukkuna sauran fitilun ɗakin ya yi haske, danish da bai koma bacci ba ya lafe saman mattress ɗinshi, yana fuskantar angel dake ƙudundune cikin bargo, babu tazara tsakanin gadajensu gab su ke da juna, idan har mutun zai iya miƙa hannu to xai iya ta6o gadon dake a kusa da nashi, shi dai hakanan sam yarinyar bata kwanta ma shi ba, ji yake kamar an kawo masu monster acikin ɗakin su, bargo yasa ya lullu6e fuskarshi, Dawowa batool ta yi wurin angel don taji idan ta yi bacci, a gefen gadonta ta zauna, Cikin sanyin murya tace"sister kinyi bacci" Hannu angel tasa ta yaye bargon da ta lullu6e kanta da shi, fuskar nan tayi jawur ta kumbura, daƙyar take iya kallon fuskar batool, Hannu batool takai tare da shafa fuskarta, Cikin sanyin murya ta soma magana" i know we don't know each other that well, but i'm still worried about you, nasan irin raɗaɗin da kike ji acikin zuciyar ki, bazan iya yaye maki shi ba, amma abu ɗaya nake so in tunasar da ke, duk abunda haƙuri bai baka ba, to rashin haƙuri bazai ta6a baka shi ba, tsohuwa ce ta ta6a faɗa mana haka," shiru ta ɗanyi na wani lokaci, angel na sauraronta kafin taci gaba da cewa" yau kika tsinci kanki acikin kurkukun nan ni kuwa tun ban mallaki hankali na ba nake acikinsa, bansan kowa nawa ba abun da nasani kawai tsohuwa ce ta raine mu........" bata kai ƙarshen maganar ba, cikin shessheƙar kuka angel tace"bazan iya jure zama acikinsa ba, cewa fa ta yi daddy na ya mutu, yanzu ni marainiya ce amma ae ina da dangi masu ƙaunata aunty aneelerh tana so, mommyna adama tana so na, don me za'a kawo ni gidan marayu"? daƙyar take magana saboda yanayin da take ciki, "bazan iya amsa tambayarki ba, amma shawarar da zan ba ki shi ne ki bi komai a sannu, idan kika ce zaki bi ta ƙarfi da yaji don ki bar cikinsa to kuwa kece a wuya domin kuwa ni tun da na taso a cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA yau tsawon shekara da shekaru banta6a ganin hanyar fita daga cikinsa ba, babu wanda yasan ta hanyar da aka shigo da shi, balle kuma yasan hanyar da zai fita daga cikin sa, sa'annan duk wani motsin mu a tafin hannunsu yake suna kallon mu, kewaye ne kaɗai idan kika shiga basa iya ganin ki........" Cikin rashin fahimta angel tace"Idan har dagaske orphanage home ne meyasa xasu ƙuntata rayuwar mutun babu shige babu fuce kenan ko makaranta mutun baida ikon zuwa? Gaskiya bazan ta6a yarda da gidan nan ba......." Batool tace"bana son muja zancan nan da tsayi, kamar yadda ba zaki fahimce ni ba, nima bazan iya fahimtar ki ba, saboda dukkan mu cikin ruɗani mu ke, abu ɗaya zan sanar dake GIDAN KURKUKUN ƘADDARA ba gidan cutarwa bane, saboda ni tunda na taso a cikinsa ba'a ta6a cutar dani ba kuma banga an cutar da wani ba, sai dai abu ɗaya ne da ya ke ci mun tuwo a kwarya shi ne kullan da a ke yi mana, ba ko'ina bane muke da ikon taka ƙafarmu ba acikinsa, najima ina tunanin ya wajen sa yake? Saboda ni ban ta6a fita daga cikinsa ba," Shiru angel ta yi batare da ta kuma cewa wani abu ba, saboda har yanzu tana ɗan jin jikinta ba daɗi, amma tabbas tana da tambayoyi dayawa da suka cunkushe zuciyarta, Dama gidan marayu bibiyar rayuwar mutun suke yi idan suka ga iyayen shi sun mutu sai su sato shi zuwa cikinsu? Meyasa batool tace sau ɗaya ake basu abinci a rana kamar yadda ta faɗa mata ɗazu! Meyasa za'a haɗa maza da mata a ɗaki ɗaya? Meyasa mutanan dake kawo masu abinci su ka yi 6adda kama!? Meyasa ba'a shige da fuce acikinsa? saboda me a ka yi masu iyaka da komai na cikinsa? Tabbas kuwa akwai wata maƙarƙashiya da ake shiryawa acikinsa, kodan saboda wannan tambayoyin da suka toshe kwakwalwarta, dole ta sanya nutsuwa don ta gano komai dake wakana, "Zanje na kwanta, Amma kafin nan i naso ki faɗa mun sunan ki, duk da naji ɗazu kamar tsohuwa ta ambace shi, sai dai ban ruƙe ba," muryar batool ce ta katse mata zancen zucin nata, Ajiyar zuciya angel ta sauke kafin tace"Sunana ANGEL ke fa?" batool ta bata amsa da cewa"Ni sunana BATOOL inaso ki ɗauke ni tamkar ƴar uwarki, kuma ina so ki saki jikin ki acikin mu, ta hakanne zaki samu duk abunda ki ke so," "Kin wahaltu sosai yau, ki samu ki yi bacci, takai ƙarshen maganar tare da jan bargo ta lullu6e fuskar angel da shi, "Sleep well my lovely sister" ƙasa ƙasa da murya angel ta furta mata"thank u, Sister" murmu shi batool tasaki ba ƙaramin daɗi taji ba, da angel ta kira sunanta da sister, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta kwanta, kamar daga sama ta jiyo muryar hannah"kin gama kula da jinjirar ta ki? Tsoki batool taja" mind ur own business" tana faɗin hakan bata ƙara tanka mata ba, Kowa ya runtsa a daren ranar banda mutun ɗaya! Dama taya zata iya bacci? ya yin da zuciyarta ke a cunkushe a ƙuntace da rashin mahaifinta, duk da har yanzu bata gasgata kalaman dattijuwar nan ba, ita dai tana ji aranta daddyn ta he's still alive! kuma taci alwashin duk runtsi duk wuya sai ta nemi hanyar guduwa daga cikin kurkukun ƙaddara, ni dai nace Allah ya ba mai rabo sa'a, Ataƙaice cikin ƴan kwanakin nan ba irin haukan da angel ba ta yi masu ba akan su fitar da ita daga cikin kurkukun amma duk a banza, babu mai saurarenta acikinsu batool ce kaɗai ke lallashinta, duk ta bushe ta rame dama ba ƙiba gare ta ba, yadda kasan ɗiyar roba haka ta koma cikin sati ɗaya kawai, duk ta fita hayyaci kuma taƙi sakin jiki da su, musamman mazan haushin su take ji, saboda wannan Danish ɗin da basa jituwa da shi, ta tsane shi kamar mutuwarta shima haka ya tsaneta ko kallon arziƙi bai haɗa ta da shi, ko fira suke yi ta sanya masu baki to ya gama magana, ita kallan ɗan iska ta ke yi ma shi saboda doguwar sumar dake akan shi ita a ganinta ta ya yana namiji xai tara suma? tsayin sumar shi har ya kusa taddo nata, gaba ɗaya dai haushin mazan take ji saboda an haɗa su rayuwa a wuri ɗaya sam bata so ko kallonta su na yi ae ita a wurinta iskanci ne hakan, abunda bata sani kwata kwata basu da feelings a tare da su, suna ɗaukar kansu tamkar jinsi ɗaya da matan, ita ce kawai ta sanyawa ranta hakan, bakomai ya ƙara ɗaure mata kai ba fa ce rashin barin su yin ibada, batool ta sanar da ita cewa basu da addini, duk wanda ke rayuwa acikin kurkukun ƙaddara baida addini, rayuwa kawai suke yi tamkar arnaku ko sunan Allah basu ambato acikin maganar su, ba sallah ba sallati, bama su san yadda akeyin ta ba, dokar prison ɗin ce ba'a ibada acikinsa, wani irin kurman kurkuku ne, baka sanin lokaci dare ne kaɗai idan ya yi suke ankara saboda hasken ɗakinsu da ake ɗaukewa sai kuma idan safiya ta yi sun ta shi daga bacci, ita kanta angel ɗin ta ta6a gigin yin sallah, duk da basu da hijabi, ranar da tayi alwala ta yafa bargon lullu6arta da sunan za ta yi sallah, zagaye ta su ka yi suna kallonta da mamaki don basu san menene take yi ba, da zarar ta ɗaura niyya zata kabbara, sai ta dinga jin kukan mahaifinta, idanuwanta su dinga nuna mata fuskar tajuddeen wuta na ƙone jikin shi, gaba ɗaya take rikicewa ta gigice ta dinga kuka ire iren irin wannan gane gane da take yi yasa ta daina yunƙurin yin sallar, abun yana affecting ɗin ta Yanzu dai ta zubawa sarautar Allah ido, ta daina haukan guduwa daga cikinsa tun da ta ga babu hanya, amma fa bawai hakan yana nufin ta haƙura ba, tana nan akan bakanta! ta lura cewa idan har zata cigaba da borin haukan da take yi masu tofa bazata ta6a samun nasara ba, wannan dalilin ne yasa ta nema ma kanta maslaha, tayin rayuwa cikin salama don ta samu damar yin bincike ta gano ainihin sarƙaƙiyar dake acikin Kurkukun ƙaddara, don tun daga kan ma'anar Sunan kurkukun fassara ce me zaman kanta, Kuma kullum tana cikin yin azhkar na safe dana mare ce, wanda daddynta ya koya mata, har tsakar dare bata runtsawa xama take yi tsakiyar gadonta, ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i akan Allah ya kawo mata mafita acikin rayuwarta, *Boss Bature✍️💋* *After some weeks* Zaune take a tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, idanuwanta suna arufe fuskar nan ta yi jawur idanuwan sun kumbura, ga busassun hawaye duk akan fuskarta, Kasancewar safiya ce ba su jima da farkawa daga bacci ba, Sautin dariya taji ƙasa ƙasa taji muryoyinsu suna yin gulmarta "Wari take yi, tun da tazo bata yi wanka ba daga gani dai ƙazama ce," can ta ji muryar wani ya kuma cewa"idan muka ƙyale ta mu zamu cutu, jiya fa daƙyar nayi bacci saboda warin jikinta gaba ɗaya ya cika ɗakin nan," tuntsure wa su ka yi da dariyar shaƙiyanci, "Ku ta shi muje muyi mata magana, ta je ta yi wanka, in ba haka ba mu zamu yi mata da kan mu," haris ne ya bada wannan shawarar, Angel dai ta natsu tana sauraronsu, dama mugun haushin su take ji, tana jiyo sautin tafiyar su a bakin gadonta suka tsaya kusan su shida, Gyaran murya ɗaya daga cikin su yai mata"ke tashi ki je ki yi wanka" a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗan kalle su, wanda ya yi magana shi ne Haris, a halitta baƙi ne yana da jiki, "Ba zamu zuba maki ido kina cutar damu ba, jiya nan daƙyar mu ka yi bacci saboda warin jikin ki, don haka ki tashi kije ki yi wanka ko mu yi maki da kanmu" cike da ƙwarin gwiwa javed ya yi maganar, dogo ne launin fatarsa chocolate, Jin ta yi banxa ta ƙyale su yasa Mubeen jinjina kai ya kalli naufal dake a gefen shi yace "je ka cika mana bokiti da ruwa," ya yi maganar yana naɗe hannun rigar shi, Danish da ke a kishingiɗe saman gadon shi bai tanka masu ba, yasan suna yi duk don su ƙuntata mata ne saboda tsanarshi da ta yi, ƴan matan dake a tare da su Deeja da yasmeen, sun ruqe qugu suna sakin murmushin mugunta, Da alama dai hada ƙuruciya ke damun su, don dukan su gaba ɗayan su baza su wuce shekara shabiyar ba, mazan cikinsu ne ke akwai ƴan shekara sha bakwai, kamar danish dasu haris, "Bakya ji ana maki magana"? muryarta na kerma tace" duk wanda ya yi gigin ta6a ni, zanyi mashi illah, babu ruwanku da rayuwata," tamkar xata fashe da kuka ta yi maganar, "Sarkin yawa yafi sarkin ƙarfi, zamu gani mu dake wazai ma wani illah," haris ne ya yi maganar, tare da naɗe hannun rigarshi yace dasu Naufal su ɗauko mashi ita, akaita toilet su yi mata wankan tsarki, Jin haka yasa ta durowa daga saman gadon, Duk da jikinta ba ƙwari daure wa kawai take yi, hannu haris yakai zai ruƙo kwalar rigarta, aikuwa ta daddage ta ɗaga kafarta tare da kai mashi naushi tsakiyar cikin shi, azabar zafi yasa ya yi saurin dafe cikin shi, rai a6ace javed ya kai mata bugu aikuwa ta damƙi ƙafar shi ta hagu ta dinga janta har saida ta yarfar dashi ƙasa, faɗa ne ya kaure a tsakaninsu, bugu tadinga kai masu da naushi, dama ta ƙware wurin iya cixo da yaku shi, duk sai da ta raunata su, sai faman nishi suke yi, da taga ta gama da mazan ta koma kan matan, Haɗe kawunan su tayi, ta ruƙo gashin kansu, tadinga ja tamkar xata tsunka su, kuka hada majina suka dinga yi, koken koken da suke yi ne ya farkar da su Batool da sauran ƴan uwan nasu dake bacci, ganin yadda Angel take Mazgarsu yasa suka sauko daga saman gadon suka nufeta suna ƙoƙarin rabata da su, daƙyar suka samu nasarar janye Angel gefe ɗaya, sai huci take yi kamar kuranya, Su deeja da yasmin suna zuƙunne ƙasa, dafe da kawunansu sai kuka suke yi, Duk wannan abun dake faruwa tsohuwa tana a tsaye baƙin ƙopar ɗakinta, hannunta ruƙe da sanda, ta yi tsaye tana kallon sabuwar ƴar wasan damben da suka samu, Danish kuwa dake kishingiɗe saman gadon shi, hankalin shi kwance dama yasan za'a rina, shiyasa bai shiga cikinsu ba, koda suke xancan zasu je suyi mata magana akan wanka, don ya lura ƙarfi ne da ita, gashi duk cikinsu itace ƙarama amma tafi su ƙarfi, Gyaran murya tsohuwa ta yi, da sauri angel ta ɗago tana haki, suka haɗa ido da ita, "Aikin ki ya yi kyau, tsanar da ki ka yi masu har takai ga bugunsu so ki ke ki kashe su?" Rai amatuƙar 6ace tace" bugun su yanzu na fara idan har ba su daina shiga gona ta ba, kuma wlh idan har baku fitar dani daga cikin kurkukun nan ba, zan addabi rayuwar kowa ne, nace banaso ku ƙyale ni inyi rayuwata na tsani gidan nan, Natsani kowa dake acikinsa, kince nan gidan marayu ne kuma za'a gatanta mu but why kuka killace mu sai ka ce dabbobi? haka ne gatancin Abinci sau ɗaya a rana? Kun hana mun yin ibada, uwa uba kun haɗa mu rayuwa da maza a ɗaki ɗaya? Me hakan yake nufi iye"? Idanuwanta azazzare ta yi maganar, tamkar ta sanya hannu ta shaƙo wuyan tsohuwar hake take ji, Maimakon tsohuwar ta bata amsoshin tambayoyinta sai ta kece da wata irin mahaukaciyar dariya, Runtse ido angel ta yi cikin jin zafin dariyar tsohuwar, cije lips ɗinta ta ɗanyi kafin ta buɗe eyes ɗin nata, "Wlh ban yadda dake ba, saboda gaba ɗaya babu gaskiya acikin kurkukun nan, idan kun 6oye mana manufarku ta killace mu anan baku isa ku 6oyewa Allah ba, yana ganinku kuma asannu Allah zai warware mana komai, ni nasani zuwana gidan kurkukun nan jarabawa ce ta ubangiji........."daƙyar takai ƙarshen maganar saboda hawayen da suka cika mata idanuwanta, "Dabbar dake yawo a daji, tafi mu gata tafi mu ƴan ci, idan su basu damu ba, zai iyayiyuwa don sun taso rayuwarsu acikin kurkukun ne, kuma sunsan basu da kowa, amma nifa ina da dangina masu sona, hakanan anje an sato ni an kawo ni cikin wannan munafukin ƙaddararran kurkukun mara kan gado," "Angel" muryar batool ce ta ambaci sunanta, a harzuƙe angel ta juya baya tana kallon batool tace, "Nasan bai wuci ki ce xaki bani hakuri ba, akan inja bakina inyi shiru, Batool bazan Iya ba, narasa gane meyasa bakwa fahimtata ne, iya cutuwa an cutar da rayuwata, tun ina jinjirata mahaifiyata ta gudu tabarni a wulaƙance cikin kwamin wanka, nata so cikin so da ƙauna na mahaifina, An raba ni da shi, An kashe mun shi duk da har yanzu ban gasgata hakan ba, sannan na faɗa hannun fulanin daji, na rayu acikin daji tare dasu a matsayin tsintacciya, wai ni Angel ƴar gidan daddynta, na shiga mawuyacin hali na rashin mahaifina atare dani, na saba dashi mun shaƙu sosai, komai shi yake yi mun wanka, ya gyara mun gashin kaina mu kwana rungume da juna, dama haka rayuwa take? Lokaci ɗaya narasa gatancin nan, na dawo ina kwana a saman tabar ma cikin bukka, bani da abinci daya wuce gasassar masara da fura, yanzu kuma gashi na tsinci kaina acikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, ya a ke so inyi da raina? Wlh da rayuwa acikin kurkukun nan kwara na ƙare rayuwata a hannun fulani daji, koba komai zan sha iskar duniya, in yawata inda nakeso, inyi rayuwar ƴan ci, Amma nan fa? Ta karfi ta tsiya aka kawo ni cikin shi banma san ta ina aka shigo dani cikin gidan kurkukun nan ba, don kuwa sai da aka fara gusar mini da hankalina tukunna, in banda munafurci taya xa'ace gidan marayu ne? Meyasa da za'a kawo ni cikinsa ba'a barni cikin hayyaci na ba? Meyasa za'a hana mu shige da fice, An tauye mana haƙkin mu na rayuwa an hana mu sakat wai da sunan za'a gatanta mu......................' (SHIN ME KU KE TUNANI AGAME DA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA? MU HAƊU A NEXT PAGE IN ALLAH YAKAI MU DA RAI DA LAFIYA, HAR YANZU FREE PAGES NE WANDA YA SHIRYA BIYA ZAI IYA YI MUN MAGANA 08103884440, WASAN FA YANZU AKA SOMA BUGA SHI, DOMIN KUWA BAMU NUTSA CIKIN LABARIN BA, YANZU AKA FARA)*💋KURKUKUN ƘADDARA💋* Daga alƙalamin Boss Bature✍️ Cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, hawaye ta ko'ina akan fuskarta, tabbas jikin kowannan su ya yi sanyi, banda mutun biyu, danish dake kwance saman gadon shi sai Haris dake zaune ƙasa ya dafe cikin shi, Saukowa batool ta yi tare nufar inda angel take tsaye agaban tsohuwa, ta dafa shoulder ɗinta"I feel ur pain angel, abun da ciwo labarin ki akwai ta6a zuciya, dole kiji ɗaci aran ki, kuma dole ki ƙuntata acikin kurkukun nan, abunda yasa kika ga mu ba mu damu ba saboda bamu da wanda zai yi kukan rashin mu! Mu matattu ne a idon jama'a kamar yadda tsohuwa ta faɗa mana, a gidan nan aka raine mu agidan nan muka taso, tunda mu ke bamu ta6a yin tozali da hasken daya fito daga wajen kurkukun nan ba, ina yawan tambayar kaina koya wajen kurkukun nan zai kasance? Ya mutanan dake rayuwa a wajen sa su ke? Bani da amsar tambayata amma ina fata wata rana nima wata rana in fita daga cikin sa, sai dai nasan abune mai wuya......" cikin sanyin murya takai ƙarshen maganarta, "Zan iya zuƙunnawa saman gwiwowina in roƙe ki akan ku fitar dani daga cikin kurkukun nan, inaso na rayu cikin ƴan uwana" angel ce ta yi maganar muryarta a rauna ce, Jinjina kai tsohuwa ta yi a yayin da take binsu da kallo da waɗannan kwarkwararrun idanuwan nata, tsawon mintuna kafin tace"koda ace kin zuƙunna saman gwiwowin ki don ki roƙe ni akan in fitar dake daga cikin prison ɗin nan, hakan bazaiyi aiki ba idan ku ka yi haƙuri a sannu zaku fahimci manufar wannan kurkukun na tara ku acikinsa, Amma a yanzu shawarar da zan baku shi ne, ku so junan ku tun da baku da kowa ku xama naku ku kaɗai, ku kasance masu faranta ma juna" daga haka bata ƙare cewa komai ba, ta dogara sandarta tare da juyawa tana ɗangyala ƙafa ta nufi cikin ɗakinta, tana shiga taja ƙopa ta datse, Zubewa angel ta yi saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsancin kuka mai cin rai tamkar ranta zai fita, Rankwafawa batool ta yi tare da ruƙo hannayen angel cikin nata, ta miƙar da ita tsaye, ta rungumeta ajikinta tana lallashin ta, sun ɗauki tsawon mintuna, kafin ta raba jikinsu, Kallon sauran ƴan uwan nasu ta yi, kowa yana a tsaye banda Danish dake kwance Ɗaya bayan ɗaya ta shiga kiran sunayen su"Hannah, Hibba, deeja parveen, Eve, yasmin, rubina, Aziza" kowa ya kasa kunne yana sauraron abunda zata ce masu, juyawa tayi kan mazan dake acikinsu ta ambaci sunayen su one by one"Danish, javed Haris, mubeen, naufal" sai faman huci haris yake yi saboda haushin bugun da angel ta yi masu, Calmly ta soma magana cikin sanyin murya"kamar yadda tsohuwa tace mu so junan mu, Let's consider ourselves as blood relatives, inaso mu yi ma juna alƙawarin duk runtsi duk wuya zamu kasance a tare, Sa'annan bana jin daɗin yadda ku ke ware angel acikin mu, i thought we are all the same, bamu da banbanci jinsi ɗaya ne mu da ita duk abu ɗaya ne, idan ba mu so juna ba, wa zamu so? Nasan kuna jin haushin angel ne saboda abubuwan da take yi wanda bakomai ya jawo hakan ba face ƙuntata rayuwarta da a ka yi, taya mutumin da ya saba rayuwar shi a sake rana ɗaya a tsamo shi daga cikin danginshi a kawo cikin GIDAN KURKUKUN ƘADDARA! taya bazai ƙuntata ba"? dakatawa ta ɗanyi da yin maganar tana bin fuskokin su da kallo, "Batool ni dai inason Angel, kuma bazan ta6a faɗa da ita ba, zan ɗauke ta tamkar yadda na ɗauki kowannan ku," bakowa bace ta yi maganar fa ce AZIZA, yarinya ce me ƙarami jiki fara ce sosai duk cikin su babu me gajartar ta, ɗaƙyar angel ta iya buɗe idanuwanta da suka kumbura ta ɗaura su akan fuskar aziza da ta yi maganar, ba ƙaramin son yarinyar ta ji ba, saboda ita kullum a cikin fara take baka ta6a ganin fuskarta a ɗaure, "batool, nima xan ɗauke ta tamkar yar uwata," kallon wadda ta kuma yi magana angel ta yi, hibba ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushi, Lumshe ido angel ta ɗanyi tare da buɗe su tana ci gaba da kallon su, "Nima na goyi bayan Batool, angel tamkar ƴar uwa take acikin mu" acewar Parveen Murmushi batool ta ɗan saki, har cikin zuciyarta ba ƙaramin daɗi taji ba, Miƙa hannunta na dama tayi saman iska tare da kallonsu tace"ina so muyi wa juna alƙwarin kasancewa atare, zamu so juna kuma zamu taimaki juna, sannan babu faɗa atsakaninmu kuma babu nuna wariya, duk wanda ya amince ya ɗaure tafin hannun shi a saman nawa," Angel ce ta fara ɗaura tafin hannunta saman na batool, matsawa aziza ta yi itama ta ɗaura nata hannun, Hibba ta ɗaura nata parveen ma ta ɗaura nata, kallon sauran Batool ta yi ganin sun ƙi matsowa su ɗaura nasu hannuwan, "Duk wanda bazai so zaman lafiya a cikin mu ba, babu ruwan mu da shi domin kuwa baya atare da mu" Jin wannan maganar da batool ta yi yasa Eve ta matsa ta ɗaura nata hannun, rubina ma ta sanya nata, mutun biyu suka rage Cikin mata basu sanya hannayensu ba, deeja da yasmin Sai kuma mazan su, don shi danish har yanzu bai motsa daga saman gadon shi ba, Zuba masu ido batool ta yi tana bin sauran da su ka rage da kallo, Masu girman kan Cikin su, "Idan har baku ɗaura hannayen ku ba, kada ku yi tsammanin idan wani abu ya faru da ɗaya daga cikin ku, xamu share mashi hawayen shi," Gyaɗa kai Javed ya yi tare da kallon su haris, kafin ya wuce su zuwa inda su batool su ke A tsaye shima ya ɗaura hannun shi fuskar shi ɗauke da murmushi ya ce"Nima ina goyon bayan ki batool, kuma ina ba angel haƙuri akan irin wariyar da muka nuna mata" yakai ƙarshen maganar idanuwan shi akan fuskar angel, itama kallon nashi ta ke yi, har cikin ranta taji daɗin waɗanda suka nuna suna sonta, Matsowa kusa Yasmin ta yi, "idan muka yarda da junanmu, muka so junanmu tabbas xamu cimma nasara, nima ina goyon bayan batool," takai ƙarshen maganarta tare da ɗaura hannunta saman nasu, Kallon deeja su ka yi dake a tsaye ta toge saboda haushin angel take ji, Matsawa mubeen ya yi da sauri haris ya ruƙo hannun shi"badai zuwa zaka yi ba"? Jinjina mashi kai ya yi"zuwa zanyi, saboda inason mu samu maslaha a tsakaninmu," ya janye hannun shi daga ruƙo da ya yi mashi, ya wuce wurin su shima ya ɗaura hannun shi, murmushi batool ta saki tana kallon shi, Kallon haris naufal ya yi tare da cewa" am sorry bro but am not supporting, also am advising u, ka aje makaman yaƙin ka kazo mu rungumi junanmu," yana kai ƙarshen maganar shi yaje wurin su, sai da ya fara kallon angel ya sakar mata murmushi kafin ya sanya nashi hannun, kallon kallon aka koma yi a tsakanin Deeja da haris da kuma mr arrogant dake kwance saman gadon shi, ganin suna kallon shi yasa shi rufe eyes ɗinshi tamkar mai yin bacci, tasan indai ba sanya hannun shi yayi ba, haris bazai ta6a supporting ɗinsu ba, gyaɗa kai ta yi tare da kallon deeja tace"ke baza ki goyi bayan mu ba? Bana so ki yi abunda zaki yi danasani, duk wanda bai sanya hannun shi ba, to baya a tare mu" Kallon harris tayi ganin yana maƙe mata wuya alamar karta shiga cikin ku, ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kan fuskar batool, ganin ba ta da mafita yasa ta shiga cikin su, itama ta sanya nata hannun Murmushi batool ta saki, kafin ta ce su maimaita duk abunda tace, suka amsa mata da toh, alƙawari ne suka ɗaukarwa juna, Banda mutun biyu Haris da Danish, bayan sun kammala yi ma juna alƙawari gaba ɗaga suka shiga rungume junansu, a yau suna jin kansu tamkar ciki ɗaya suka fito, Bayan kowannan su ya samu natsuwa, Batool da angel su ka kalli juna, lokaci ɗaya suka sakar ma juna murmushi, "Idan zaki shiga toilet, muje tare nima ina so zanyi wanka," Gaba ta yi angel tabi bayan ta, har zuwa ƙopar shiga toilet ɗinsu hannu batool ta sanya tare da tura ƙopar suka shiga daga ciki, ƙofofi ne kusan guda uku kowanne a rufe ya ke, ɗaya daga ciki angel ta shiga, itama batool ta buɗe ɗayan toilet ɗin ta shige ciki, Sai yau ta samu damar ƙarewa toilet ɗin kallo na ƙurulla, ko'ina a tsaftace ya ke, sai dai babu wadatattu kayan amfani, akwai dai toilet seat, sai shower ta tsaye wani ajiyayye bucket, kwandon wanka me ɗauke da soap and sponge, a kwai cabinet dake ɗauke da sabulai da hada ledar detergent da kuma Shampoo ɗaya, saman ceilling ta wurga idonta, wasu munafukan tagogi ne kusan uku, masu murfin ƙarfe an garƙame su da kwaɗo jikin su har ya yi tsatsa, mayar da idanuwanta ta yi akan tagar jigin bango guda ɗaya jikinta wani tsohon glass ne duk yayi ƙura, tunani ta shiga yi idan har zata iya samun makamin da zata iya fasa glass ɗin jikin glass ɗin da shi tabbas zata iya kutsawa ta cikin tagar ta dira ta baya, daga nan zata samu damar shiga cikin kurkukun taga me ke wakana, jinjina kai ta yi tare da cewa"I will try", sauke idanuwanta ta yi akan tukunyar fular dake ajiye daga ƙasa jikin bango tana da girma, fulawar cikinta duk ta yagalgale saboda rashin kulawa, ta6e bakinta ta yi kafin ta mayar da idonta kan igiyar da ke a ciki da a lama ta sagala kaya ce, tafiya ta soma yi tana bin kowace kusurwa ta makewayin da kallo, bakin magudajin da ruwa ke bi ta tsaya wasu ƙananun hudoji ne da basu fi shida ba, tanan ruwa yake bi ya wuce, akwai wasu fanfuna guda biyu da su ke a kashe, Sai da ta kammala bin ko'ina da kallo tukunna ta sanya hannayenta ta kamo ƙasan rigarta, ta cireta tare da rataya ta saman igiyar, "Ko madubi babu da mutun zai kalli fuskarsa, ta ya zan gane ina ƙara kyau ko muni nake yi"? tayi maganar acikin zuciyarta, Bokitin nan ta janyo tare da tara shi gaban fanfon ta kunna, ruwa ya soma bulbulowa daga cikinsa, tafi sha'awar ta yi da bokin akan ta kunna shower, Zuƙunnawa ta yi tana jiran ruwan ya cika, kamar daga sama taji an banko ƙopar toilet ɗin da ta ke ciki, A gigice ta ɗago tare da wurga idonta kan door ɗin don taga wanene ya shigo, *DANISH* ne a tsaye hannun shi ruƙe da rigar shi, tun daga ƙasa har sama take kallon shi, kamar wani bugagge sai faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, shafaffan cikin shi tamkar wanda bai ta6a cin abinci ba, ranta a matuƙar 6ace ta miƙe saboda tsabar fusata bata ɗauki rigarta ta sanya ba, ta rufe shi da faɗa" kai wani irin jaki ne ba ka da hankali za ka faɗo cikin kewaye batare da ka nemi izni ba? saboda daƙikanci da dabbanci dama da biyu ka shigo don ka ganni babu kaya ko? Tunda ta soma balbale shi da masifa bai yi yunƙirin tanka mata ba, kuma bai motsa ba ya dai yi kasaƙe yana kallonta, sai da takai ƙarshen maganar tana haƙi cikin sanyin murya yace"Duk kin wani ta shi hankalin ki, to me zan gani a jikin na ki? Ƙirjin naki ma ashafe ya ke kamar bangon ɗakin mu, kwarama tsohuwa tafi ki abun kir......."kafin ya kai ƙarshen maganar, ta sunkucin bokitin ruwan da ta tarba, gaba ɗaya ta sheƙa mashi ruwan a jikin shi, sharkaf ta jiƙa shi, Runtse idanuwan shi ya ɗanyi saboda ruwan daya shiga ciki, long eye lashes ɗinshi sun jiƙe sharkaf, hannu ya sanya tare da share ruwan dake akan fuskarshi, kafin ya buɗe idanuwan shi, ta yi saurin ɗaukar rigarta da ke a saman igiyar ta zurata a jikinta, Tana huci ta ci gaba da kallon shi tana fadin"Zaka fita ko saina ƙara watsa maka wani ruwan? Ƙaton banza kawai matsalar ace mutun baida addini kenan, ko dabba tafi shi kan gado," A lokacin ya ƙarasa buɗe idanuwan shi, jinjina kan shi ya yi still bai tanka mata ba, ya juya ya fita daga cikin toilet ɗin, Lamarin ya ɗaure mata kai, har ta soma tunanin kodai yana da ta6in hankali ne? In ba haka ba taya zai faɗo mata bagatatan Cikin toilet batare da ya tambayi ko akwai mutun aciki ba, idan ma ya yi tunanin babu kowa ne why bazai yi knocking ba? Guntun tsoki taja, aranta tace"Amma dai wannan anyi sullu6iyo, Shashasha sauna, next time idan ya kuskura ya ƙara faɗo mun irin haka, saina koya ma shi hankali," takai ƙarshen maganar tare da nufar ƙopar toilet ɗin da nufin ta rufe, hannunta ta ɗaura saman handle ɗin ƙopar, shiru ta ɗanyi jin alamun bai tafi ba, zurfi tunani ta shiga lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin ta manta bata yi locking ɗinta ba, kodai ya yi tunanin babu mutun ne shiyasa ya faɗo ciki? Don ta lura Haka suke yi idan suka ga ƙopa ba a datse ba, shi ne babu mutun a ciki, idan kuma suka ganta a datse to shi ne ke da akwai mutun, kenan itace ta yi ba dai dai ba? Da ace ta rufe ƙopar danish bazai iya shigowa ciki ba, Ta6e baki ta yi, ta tura ƙopar ta rufe, ta koma ciki domin yin wanka, Cikin ƙanƙanin lokaci ta kammala yin wankan, ta mayar da kayan jikinta, ita kanta ba ƙaramin daɗin jikinta taji ba, tana buɗe ƙopar ta same shi a tsaye ya jingina bayan shi jikin bangon toilet ɗin, da alama jira yake ta fito ya shiga, Wuce shi tayi zuwa cikin ɗakin, A tsaitsaye ta same su, banda mutun biyu Batool da Aziza, "angel" hannah ce ta kira sunanta, ƙarasawa ta yi kusa da ita ta tsaya, Fuskarta ɗauke da murmushi tace"kin fito kenan, nima wankan nake so inyi ina jira su batool su fito sai in shiga," "Idan ku kayi wanka babu wani abu da ku ke shafa ma jikin ku"? Angel ce ta yi mata tambayar, girgiza mata kai ta yi tare da cewa babu, mu ma haka muke zama duk in mu ka yi wanka, "Comb fa? Ina so in taje gashin kaina", "Guda ɗaya ne muke da shi, kuma yana a wurin danish, da shi muke amfani in kina so sai in aro maki," da sauri tace"a'a na fasa" aranta kuma tace komai danish danish sai na koya mashi hankali, sullu6uyo kawai, Tafiya ta yi zuwa gefen gadonta, ta zauna tana bin kowannan su da kallo, Motsi buɗe ƙopa su ka jiyo daga can kusurwar da benan ya ke, Nan fa su Hannah suka fara murna sunsan abinci ne za'a kawo masu, Takun tafiyarsu tamkar na dawakai, saukowa su kayi daga saman matattakalar benan, Giants ne Hannayen su ɗauke da farantai, shiga ciki su ka yi a dai dai saitin carpet ɗin nan suka ɗaura sauke tray ɗin, Kafin su ka ja baya tare da goya hannayen su saman ƙirjin su, Fuska a ɗaure angel ke kallonsu, ko gunki bazai nuna masu iya tsayuwa ba, abun na ci mata tuwo a kwarya, wai su waɗannan mutanan su wanene? Basa ji basa magana, kullum kuma cikin shiga iri ɗaya kuma sun 6oye ainihin suffar su, Jin jina kai ta ɗan yi aranta tace"A sannu zan gano ko su wanene ku," "Angel ki taso mu ci" Hibba ce ta kirata ganin ta yi zugudum saman gadon, Saukowa ta yi tare da tunkarar inda suke zaune itama ta zauna gaban farantan, ta lanƙwashe ƙafafunta, mutun uku suka rage basu ƙaraso ba, Javed yace"wai ina danish ya ke ne? da su batool, wani yaje ya yi masu magana su zo mu ci," yunƙurawa haris ya yi da niyar yaje ya kirasu sai gasu sun fito daga cikin ƙopar shiga toilet ɗin a tare, komawa ya yi ya zauna, gefen angel batool da aziza su ka zauna, danish kuma ya zauna gefen javed, yana fuskantar angel tun da suka haɗa ido, ta wurga mashi harara tare da murguɗa ma shi small mouth ɗinta, Bin ta ido kawai ya yi, don baima san menene ta ke yi ba, haushin shi take ji ta ƙara jin tsanar shi saboda sharrin da yayi mata, da ya ce ƙirjinta kamar bangon ɗakin su, tsohuwa ma tafi ta abun kirki, kalaman nan sun baƙanta mata rai, kuma taci alwashin sai ya ɗanɗani kuɗar shi, Batool ce ta ya ye jan ƙyallen da aka rufe saman trays ɗin, Hamburger suka samu tare da chicken legs na ƙosassun kaji anyi masu jar suya har wani maiƙo suke yi, kowa zai samu burger ɗaya da kuma Chicken leg ɗaya, a tray na biyu Tea pot ne sai jerin wooden Cups, faranti na ƙarshe basket ne mai ɗauke da kayan marmari, a gefe ɗaya kuma bottle waters ne' fuskar kowannan su awashe, baƙaramin daɗi suka ji ba, duk da sau ɗaya ake a basu abinci arana, Amma suna Ci su ƙoshi wani lokacin ne ba'a basu abun da zai ƙosar dasu, amma yau kam ba laifi, kowannan su Tunanin wanda zai rage yaci da anjima yake yi, Batool ce ta zuzzuba masu kakkauran tea a kowani Cup, ta miƙa masu ɗaya bayan ɗaya, kusan atare suka kai baki suna sha, Idonta idon danish Sun hana juna sakat, gani take kamar wani abun yake ayyanawa aranshi tun da ya ganta babu riga a jikinta, nan take ta murtuƙe fuska, a ƙule tace"Stop looking at me" "Ae bani ke kallon ki ba, ke kike kallona," amsar daya bata kenan, daga haka ya ɗauke idonshi daga kanta, ya kai hannu ya ɗauki burger ɗinshi yana ci, Yunƙurawa tayi tare da miƙewa, kowa yabi ta ido, batool tace"Har kin ƙoshi"? Fuskarta a hautsine tace"Zan ajiye ne da anjima inci" takai ƙarshen maganar tare da kai hannu ta ɗauki Chiken leg ɗinta, ta ɗibi fruits, ta kuma ɗaukar bottle water ɗaya,' duk fa don saboda danish tabar wurin, Saman gadonta ta koma ta zauna, kuma still bata daina kallon shi ba, lamarin ya ɗaure ma shi kai, shi dai baisan zunubin daya aikata mata ba, sam ta tsani ganin shi, abunda bata sani ba danish mugun shakkarta yake ji, shifa har yanzu kallon monster yake yi mata, bai yarda cewa itama mutun ce kamar su, saukowa ta yi daga saman gadon ta nufi gadon batool, ta zuƙunna bakin gadon ta zura hannu a ƙarƙashi ta janyo kwandon da batool ke ajiye ragowar abincin ta, a ciki itama ta ajiye Fruits ɗinta, apple uku sai ayaba guda biyu, ta raba cinyar kazar biyu ta tura rabi aciki, rabin kuma anan zuƙunne ta cinye ta, tana kammala ci ta buɗe murfin robar ruwan tasha rabi, bayan ta gama ta rufe kwandon, ta tura shi Ciki, kafin ta miƙe hannunta ruƙe da bottle water ɗinta, ta koma saman gadonta, daga ƙasa ta ajiye bottle ɗin, a lokacin suma sun kammala cin nasu abincin, wasu sun rage cinyar kazarsu, wasu kayan marmari suka rage, kowa dai ya ɗauki robar ruwanshi don ya ajiye zuwa anjima, Tattara kayan abincin giants su kayi, A jere suka fuce daga cikin ɗakin, prisoners kowa Ya koma saman gadon shi, Anci an ƙoshi saura bacci, aikin su kenan Abun ba ƙaramin ɗaure wa angel kai yake yi ba, wai su kwata-kwata basa gajiya da rayuwar kulle? Daga ɗaki sai toilet, daga anci abinci kuma sai hawa gado ayi bacci, anya kuwa suna da lafiyar kwakwalwa? Ganin da gaske bacci za suyi yasa tayi saurin cewa""Wai ku baku tunanin fita daga cikin kurkukun nan? Ko baku da ra'ayin yin rayuwar ƴan ci ne, Cikin mutane? "Ta ya zamu sanyawa ranmu fita daga cikinsa, bayan tsohuwa ta faɗa mana cewa mutanan dake awajen kurkukun nan baza su ta6a ƙaunar mu ba, wahala zamu sha tunda bamu da kowa a ƙarshe ma akashe mu da ranmu," yasmin ce ta bata amsa, Rubina tace" bamu da kowa tsohuwa itace gatan mu, taya zamu yi tunanin barin kurkuku bayan babu ƙofar fita daga cikin shi? idan mun fita wurin wa zamu je"? Guntun tsoki angel taja"daga anyi magana sai kuce tsohuwa, bansan me ta jiƙa ta baku kuka sha ba, wanda har ya gusar maku da tunanin ku, Amma ni inada tabbacin ba hakanan aka ƙyale ku ba, saboda babu mutumin da zai juri a kulle shi, tamkar yadda ake kulle dabba," Harara danish ya jefa mata, dama haushin ta yake ji, bai dai ce komai ba haris ne yace"yanzu kina so mu yadda dake mubar 6angaren tsohuwa? Wai ke da me kike taƙama ne? idan bakisan wacece tsohuwa ba, bari in ƙara tunasar dake, itace ta raine mu ta kuma gatanta mu, bamu da tamkarta a duniyar nan,' Cike da takaici angel tace"dukkan ku baku da tunani, bakusan ciwon kan ku ba, Ni bansan taya zan fahimtar daku ba, gidan kurkukun nan ba alkhairi bane, gatan da kuke faɗin tsohuwa ta baku, ba gata bane gata shine abar mutun ya yi rayuwar ƴanci, amma ku an killace ku, an hana ku ganin hasken rana, acikin kurkukun ma an yi maku iyaka da shiga ko'ina, a rana sau ɗaya kuke samun abinci, an haɗa maza da mata ɗaki ɗaya suna kwana shin wannan gata ne? Kullin mu ne yawo cikin uniform kala ɗaya, wai ku baku gajiya da rayuwa a kulle ne? Kuyi tunani mana babu alkhairi atattare da kurkukun nan" Murmushi Batool ta ɗan saki, kafin tace"angel, dama kin daina wahalar da kanki, domin kuwa indai akan tsohuwa za ki yi magana babu wanda zai ta6a fahimtar ki, its better ki yi shiru da bakin ki, yadda kika ganmu kibar mu kawai mu haka ƙaddarar tamu rayuwar take a cikin kurkuku" Shiru angel ta ɗanyi, sai lokacin ta ƙara tabbatarwa kanta cewa An gama dasu tabbas ba hakanan tsohuwa ta ƙyale su ba, batasan wata irin huɗu ba ta yi masu ba, da har suka gaza fahimtar dai dai, taso ace sun yarda da maganarta ta hakan ne zasu haɗa hannu wurin nema ma kansu mafita, sai dai kash sunƙi bata haɗin kai, "Ina son fita daga cikin kurkukun nan, amma bansan meyasa ba, bana jin zan iya rayuwa awajensa, a duk lokacin da nayi tunanin fita daga cikinsa sai inji ƙunci da raɗadi suna taso mun acikin zuciyata" javed ne ya yi maganar, "Nikaina ina sha'awar wata rana in ganni awajen kurkukun nan, but i don't know why bana jin zan iya fita daga cikinsa koda na samu damar yin hakan" Kasa kunne angel ta yi tana sauraron su kowa yana tofa albarkacin bakinsa, banda Danish, da ya lumshe idanuwan shi tamkar mai yin bacci, "Tsohuwa ba gaskiya take faɗa maku ba, nasan zaiyi wuya ku fahimce ni, amma kuyi tunani mana, Kowani ɗan adam Da Allah ya halitta A duniyar nan, ba daga sama ya faɗo ba, shin kun ta6a tunanin Ina iyayen ku su ke? Meyasa kuka kasance marayu? Idan iyayen ku sun rasu ina danginku su ke? Idan na baku labarin rayuwata ina da tabbacin zaku fara kwaɗayin yin rayuwa a wajen kurkukun nan, kuma zakuyi tunanin Ina iyayen ku da dangin ku su ke......." muryar Deeja ce ta katse mata xancen nata da cewa, "Kince kowani ɗan adam da Allah ya halitta? Waye ɗan adam ɗin kuma wanene Allahn da kike magana akai" Mamaki ƙarara akan fuskar angel ta ɗago tana kallon deeja dake zaune can saman gadonta, fuskarta babu alamun wasa ta yi tambayar, Speechless sam ta kashe mata baki, tsabar mamakin tambayar da Deeja ta yi mata, har wani shock taji, sai lokacin ma ta tuna dasu wa take magana, ta jima tana mamakin wannan ikon Allahn, Gaskiya yaran nan an cuci rayuwar su, basu san komai ba game da wanda ya halicce su, wato su kawai rayuwa suke yi kara zube, "Kinyi shiru baki ce komai ba"? Deeja ce ta yi maganar, jin tayi shiru bata ce komai ba, buɗe baki angel ta yi da niyar ta bata amsar tambayarta, ba zato ba tsammani taji an daki kokwan kanta, wani irin duhu cikin idanuwanta, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta dake yi mata raɗaɗi muryarta na kerma ta shiga ambaton"LA'ILA HA'ILLA ANTA SUBHANAKA INNI KUNTU MINAZZALIMIN!!" gaba ɗaya suka tsareta da ido ganin ta runtse idanuwanta, Jikinta na kerma, da sauri batool da su hanna suka sauko daga saman gadajensu suke nufi gadon angel, Suna tambayarta lafiya meya faru, bata basu amsa ba, jiki ba ƙwari ta sulale saman mattress ɗinta ta kwanta, Kallon juna su ka yi cike da tsantsar mamaki, Hanna tace"Anya kuwa lafiya? Kodai bata jin daɗin jikin ta ne" miƙa hannu batool ta yi saman wuyan angel ta shafa shi, Sanyi taji sosai " kallon su tayi"lafiyarta qalou, bacci ta ke yi," Sautin dariyar Haris suka ji, a tare suka juya suna kallon shi, hannun shi rungume da pillow, "Dama karta farka, kowa ya huta" Hararar shi batool ta yi, tare da kawar dakanta, Cigaba da magana Haris ya yi"Saboda ita duk kun ta shi hankalin ku, yarinyar nan fa ba son mu take yi ba, saboda bata son tsohuwa....." kafin yakai ƙarshen maganar shi, Danish yace"haris, pls stop talking about her,' shiru haris ya yi saboda Danish ya nuna baya son yana maganarta, A gefen gadon angel su batool suka zazzauna suna jiran ta farka, hankalansu sam bai kwanta da irin baccin da angel ta yi ba, shiyasa suka gaza komawa saman beds ɗinsu, Lamarin ya ɗaure masu kai, tsawon awanni tana bacci, Tun suna sanya ran zata farka har suka fara fidda rai, "Kodai inje in faɗa ma Tsohuwa ne? Acewar Hibba, Batool tace"Mu ɗan ƙara jira mu gani, wata'ƙil kafin dare ta farka,' Azeeza duk tafi shiga yanayi saboda ita tausayi gareta ga tsoro, muryata a sanyaye tace"Ni bana so wani abu ya samu angel, saboda ina sonta,' Haris dake sauraron su, kamar ya miƙe yaje ya rufe su da bugu haka yake ji, don shi ya tsani ya ji suna damuwa da ita, Saukowa javed yai daga saman gadon shi, hannyen shi Cikin Aljihun wandonshi ya nufi gadon angel, inda suke a zazzaune, a tsaye ya tsaya yana kallon su"ku kwantar da hankalin ku, zata farka ne, zaman ku anan yana ƙara takura mata" "To kai meye ruwanka da ita'? Haris ne yai maganar, Kallon shi javed yai tare da cewa"Cos she's my sis, i must worry about her, " yakai ƙarshen maganar shi, tare da janye idon shi daga kan haris Ya mayar da shi kan su batool da har yanzu basu matsa daga saman gadonta ba, Dogon tsoki Haris Yaja rai aɗan 6ace yace"daga zuwanta har ta fara canza maku tunanin ku," Mubeen yace"Ka fa iya bakin ka, halan ka manta bugun da muka sha a hannunta ɗazu da safe, kodan kaga tana bacci ne"? Cike da zolaya yakai ƙarshen maganar yana dariya, Janyo pillow haris Yayi tare wurga ma mubeen saman fuskar shi, Cafke pillown mubeen ya yi a hannun shi still da dariya akan fuskar shi yace"Yarinyar fa akwai ƙarfi, Na lura gaba ɗaya tsoranta ku ke ji, duk masu nuna basu sonta sunfi kowa jin shakkarta,' wannan maganar da mubeen ya yi ce tasa Danish satar kallon shi ta wutsiyar idonshi, yadda mubeen ya yi maganar kamar ya karanci abunda ke a cikin zuciyoyonsu, shifa a halin yanzu bai ƙi angel taƙi farkawa ba, saboda ko motsi ta yi sai yaji gaban shi ya faɗi, Ya tsani mutun mai tsiwa ita kuma taci ka kwakwazo, ɗazu a cikin toilet ɗinnan da ta rufe shi da faɗa har zazza6i ya ji a jikin shi, dauriya kawai ya yi wurin mayar mata da martani, don baiso ta gane yana jin shakkarta, "Zan koya mata hankali ne, ai ba ƙyale ta nayi ba," haris ne yayi maganar fuska a ɗaure, Javed yace"Zaka koya mata hankali ko zata koya maka hankali? Nakasa fahimta,' shiru haris yae bai tanka ma shi ba, "Yarinyar nan fa duk cikin mu babu tsaranta, saboda ƙarama ce, amma sai shegen wayau ga ƙarfi, Ni har tsoro take bani in tana magana, ƙwayar idonta ma tsoro take bani, Ita sam bata jin shakkar kowa" Deeja ce ta yi maganar, Naufal yace"Ni kuma ba ƙaramin burgeni take yi ba, yanayin rayuwarta ya banbanta da namu, tana da ƙwarin gwiwa sosai, babu tsoro acikin lamuranta," Naufal nakai ƙarshen maganar shi, Batool tace"Ni ina ji araina zuwanta cikin rayuwar mu, tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, idan har zamu zauna da ita cikin lalama zata koya mana abubuwa da dama waɗanda bamu sani ba, saboda ita ta yi rayuwa A wajen kurkukun nan, muna buƙatar neman ƙarin haske dangane da rayuwar mutanan dake a wajensa" Jinjina kai eve ta yi tare da cewa"Kalamanta na ɗazu sun tsaya mun araina, har na fara tunanin Ina iyayen mu su ke waɗanda suka haife mu? Ina dangin mu? Nafara doubting akan wani abu, Amma kafin nan, inaso angel ta farka ta bamu labarin rayuwarta, Inaso inji, kuma inaso ta faɗa mana wanene Ya halicci kowa, kuma wanene ɗan adam da ta take magana akai," Maganganun da su ke yi ba ƙaramin ƙona ma haris rai su ke yi ba, ganin Yarinyar ta fara cin galaba akansu, taya wata can baƙuwa zata shigo cikinsu, ta soma kokarin canza masu tunanin su' A harzuƙe ya daka masu tsawa, har saida Danish ya firgita, don baisan Tsawa ko kaɗan, Jikin shi har kerma yake yi, idon shi akan Haris dake ta faman huci, Nuna su ya yi da yatsan hannun shi "kada wanda ya kuskura ya ƙara magana makamanciyar wannan acikin ku, ban ta6a sanin baku da hankali ba, sai yau, taya zaku fara ɗaukar maganganun ƙaryar da take faɗa maku? Yarinyar na fa bata da cikakken hankali, batasan me take yi ba......" muryar shi a disashe yakai ƙarshen maganar idon shi akan danish daya daddafe kanshi da hannayenshi biyu, jikinshi nata kerma Gaba ɗaya hankalinsu Ya koma akan Danish, Sun san lalurar shi ta rashin son hayaniya, idan abun ya motsa kusan burkice masu yake yi, Sassauta murya haris Yayi"danish am really sorry, raina ne ya 6aci sam na shafa'a," ya yi maganar yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, ya nufi gadon danish ya zauna daga gefe yana lallashin shi, "Pls kada wanda ya ƙara magana a cikin ku, kowa ya koma gadon shi ya kwanta" acewar javed, Miƙewa su batool su kayi kowa ya nufi gadonshi, Ya zauna, Shima javed ɗin Ya koma nashi gadon Ya zauna, ya rage saura haris dake aikin lallashin Danish, daƙyar ya samu ya shawo kanshi, ya saki kanshi daya tallabe da hannayen shi, bai ta shi daga wurin shi ba har saida yaga ya kwanta tukunna ya miƙe ya koma nashi gadon, Lokacin da dare Ya tsala, hasken ɗakinsu ya ɗauke gaba ɗaya, kowannansu Ya nutsa Cikin bacci, a wannan lokacin ne ta soma mutsu mutsun buɗe idanuwanta da su ka yi mata nauyi, jikinta duk ba da daɗi ga zufa, Ambaton sunan Allah ta cigaba da yi har ta samu ta buɗe idanuwanta, duhu ko'ina saboda basu kunna fitilun ɗakin ba kafin su kwanta, Lalla6awa ta yi ta miƙe zaune tare da jingina bayanta jikin bango, Sam ta manta abunda ya faru da ita, hatta maganganun da su ka yi kafin ta kwanta baccin duk ta manta su, Wata irin matsiyacin yunwa ta soma ji, ga ƙishin ruwa, tunawa da ragowar naman kazarta da ta jiye yasa ta saurin saukowa daga saman gadon, cikin duhu ta dinga laluban hanya, har Allah ya kawo ta saitin inda table ɗinsu yake, hannu takai ta ruƙo handle ɗin fitila, ta kunnata tare da ɗago da ita, da sauri ta tunkari wurin gadajen su, ɗaya bayan ɗaya ta shiga haska fuskokinsu, wasu sun ƙudundune cikin bargo wasu kuma basu lullu6e jikin su ba, adai dai bakin gadon Batool ta tsaya tare da zuƙunnawa daga gefen gadon, ta zura hannu ta janyo kwandon, tana hamma ta buɗe shi, shiru ta ɗanyi tana kallon Ikon Allah, An samu wani ya gwaigwaye tsokar jikin naman sai ya bar mata ƙashin kaɗai, Apples ɗinta guda uku anciye biyu, sai ɗaya aka bar mata shima ɗayan saida aka Cinye kusan rabin shi, sam bata yarda da abunda idanuwanta suka nuna mata ba, hannu ɗaya ta sanya tana murza idanuwanta, don ta ƙara tabbatar da abunda suke gane mata, Dagaske dai an cinye mata Abincin da ta ajiye, a ruɗe ta ruƙo hannun kwandon, tare da jijjiga shi taga dai ba komai sai wannan guntun apple ɗin da aka rage mata, Ranta yayi bugun 6aci har wani jiri take gani acikin idanuwanta, tsabar takaici tuni idanuwanta sun cicciko da kwalla, Ta rasa wa zata zarga acikinsu, tasan dai batool bazata iya cinye mata abinci ba, sai dai Cikin sauran ƴan uwan nasu, Cikin shessheƙar kuka tace"Wlh tun da aka cinye mun Cinyar kaza ta saina hana kowa bacci a adaren yau," Runtse ido tayi tare da kwatsa wata irin gigitacciyar ƙara mai matuƙar tsiwar gaske, Har Cikin kokwan kansu, kusan atare Suka farka Sai faman zare ido suke yi, kowa yana tambayar lafiya wanene? Duk sun bi sun ruɗe, batool ce ta lura da angel dake atsaye, yaye bargon jikinta tayi tare da saukowa daga saman gadonta, ta nufi angel tana faɗin"Sister kin farka, Meya faru? Lafiyarki kuwa? a jere ta jefa mata tambayoyin, Su hanna ma duk suka shiga tambayarta lafiya meya faru, Zuciyarta na tafarfasa tace"Uban wanene ya cinye mun tsokar namana yabar mun ƙashi? Wlh kodai ku faɗa mun ko kuma in hana kowa runtsawa acikin daren nan,' A ruɗe Batool tace"A ina kika a jiye ne"? "Cikin kwandon da kike ajiye ragowar abinci, anan ciki nasaka, an samu wani mara imanin ya cinye mun kaya na" Parveen tace"Zai iyayiyuwa 6era ne ya cinye shi," "Dama kuna da 6eraye"? Jinjina kai parveen tayi alamar eh,"Muna dasu kuma duk in muka ajiye abinci, suna bi su cinye" Wata irin dariya angel tasaki"wannan dai ba 6era bane ya ci shi ba, Sai dai 6eranya, ku faɗa mun wanene ya cinye mun abuna idan har kuna saman lafiya" Guntun tsoki Haris Yaja"Wannan wani irin rainin wayau ne? Munyi maki kama da 6arayi ne? Saboda kin raina ma mutane wayau, " yana rufe baki deeja tace"wama ya sani, ko ke ce kika cinye abunki cikin magagin bacci shi ne xaki zo ki ishi mutane da tsiwa, muna yin baccin mu mai daɗi kin katse mana shi," Jinjina kai angel tayi"Shikenan tun da bazaku faɗi mini wanene ya cinye mun tsokar kaza ta ba, da apple ɗina guda biyu, Zaku ga abunda zai biyo baya, Bakusan wacece ni ba, Kafin zuwana kurkukun nan, Duk wanda ya 6ata mun rai, idan har na karanta mashi Carman dudu, Bai ƙara kwana ɗaya yake mutuwa, Cikin shi zai kumbura, ya fashe daga nan shikenan tashi ta ƙare" In a serious matter ta yi maganar, da yake ta raina musu wayau, Ta riga ta gane cewa basu san komai ba, Shiyasa tace musu haka, Kallon kallo suka soma yi a tsakaninsu, kowa da abunda yake saƙawa acikin ranshi, ruƙo hannunta batool tayi"Pls Angel kada ki karanta mana wannan abun, daga ji wani mugun abunne, nidai nasan bani naci ba, amma ina tsoro ace wani ne yaci acikin ƴan uwanmu kinga zai cutu," Ta6e baki angel ta yi"nidai nace a faɗamun wanene yaci mun abuna, in ba haka ba zan karanta ne" Fashewa da kuka azeeza tayi tana faɗin" Wai bazaku faɗa mata wanene ya cinye mata abinci ba," Shidai haris yayi zuru da ido yana jira yaga me zata yi musu, "Angel, kiyi haƙuri kada ki karanta mana, kinga mu nan duk ƴan uwanki ne. Ke kanki ba zaki so wani ya cutu ba" acewar javed, Girgiza kai angel ta yi"Ba kunce akwai 6eraye ba? To ai su zan karantamawa, tun da su suka cinye mun Abuna, meye naku na damuwa ne"? Shiru su kayi suna kallonta kowa yasha jinin jikin shi, Zuƙunnawa tayi a ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, kafin ta runtse idanuwanta, motsa lips ɗinta ta soma yi tana karanta Carman dudu, batare da sautin yana fita ba, Cikin shessheƙar kuka Parveen tace"ba ni kaɗai na ci ba," angel bata buɗe idanuwanta ba, taci gaba da karantawa, a gigice parveen ta duro daga saman gadonta, Ta zube agaban angel tana kuka, ta ruƙe kafafunta, gaba ɗaya ido ya dawo kan parveen, Dariya ƙunshe abakin angel ta buɗe idonta, "An samu 6eran kenan"? Murya na kerma parveen tace"Eh ni ce," ɗagowa ta yi da idanuwanta waɗanda suka kaɗa su kayi jawur tace "Bani kaɗai bace, Hada yasmin da deeja, Su suka cinye maki apples, ni kuma naci naman, ki yafe mana bazamu ƙara ba" Jinjina angel tayi"tun da ke kin bani haƙuri, Na yafe maki, amma su kuwa zasu Gane kuren su," tana kai ƙarshen maganar, ta rufe idanuwanta kamar wata bokanya ta ɗaga hannanyenta sama, taci gaba da sambatu, Kallon Juna deeja da yasmin su kayi, idanuwan su cike tab da kwalla, Batool tace"ku bazaku je ku bata haƙuri ba? So ku ke Cikin ku ya kumbura," Saukowa su kayi daga saman gadajensu, da rarrafe suka ƙarasa inda angel take zaune, Har suna haɗa baki wurin bata haƙuri, batare da ta buɗe ido ba, tace"Kun yi jinkirin tuba, Don haka zaku yi tsallan kwaɗi, duk idan ku kayi tsalle ɗaya zaku ce Aunty angel kiyi haƙuri bazamu ƙara ba, bayan haka kuma gobe idan aka kawo mana abinci, Zaku raba shi biyu kuban rabi, kun amince? Murya na kerma suka ce Eh, Fuska a ɗaure ta buɗe idanuwanta, tana kallon su"nan gaba idan kuka ƙara satar mun abinci na, kada kuyi tsammanin zan yafe maku, " atare suka ce bazamu ƙara ba, Gyaɗa kai tayi tare dakai hannu ta ɗauki filitar data ajiye a ƙasa, ta yunkura ta miƙe tsaye"Oya ku fara tsallan kwaɗi, " "Ae bamu san yadda ake yi ba" deeja ce ta yi maganar, kallon su tayi ganin yadda jikinsu keta kerma, sai taji tausayinsu ya kamata, Ta6e baki ta ɗanyi"Kada ku ƙara na yafe maku, Abunda kuka aikata baida kyau, domin kuwa sata ce, kuma haramun ne mutun ya ɗauki abunda ba na shi ba, babu daɗi ni yanzu baku kyauta mun ba, yunwa nake ji sosai, banci haƙƙin wani ba, nawa ne na ajiye saboda gudun yunwa amma kunbi kun cinye mun kaya ne, wannan ba adalci bane, idan naku aka ɗauka zaku ji daɗi" girgiza mata kai su kayi alamar a'a, "Kada ku ƙara, ko ba nawa ba kada ku ƙara ɗaukar abunda ba naku ba," amsa mata su kayi da toh, "Ina danish ya ke"? Haris ne ya yi tambayar ganin gadon shi wayam babu kowa" sai lokacin su ka lura da babu danish A cikin shi, Nan fa hankulansu suka ta shi, "Wai dama tun ɗazu Danish baya acikin mu? Amma kafin mu kwanta danish yana atare damu" Rubina ce ta yi maganar fuskarta da alamun ruɗu, Da sauri Javed Ya sauko daga saman gadon shi, yaje saman table ya ɗauki fitila ɗaya, batool ma ta ɗauki ɗayar fitilar duk suka kunna su don ɗakin ya yi haske, "Ku duba ko'ina, Allah yasa dai ba wani abunne ya faru da shi ba," haris ne yai maganar, gaba ɗaya sauran dake asaman gadajen su duk sun sauko, sai zagaye cikin ɗakin suke yi suna neman Danish, Saƙo da lungu ko'ina suka shiga dubawa amma babu shi, lamarin yayi matuƙar ɗaure masu kai, "Yakamata mu sanar ma tsohuwa halin da ake ciku" Acewar Mubeen, Deeja tace"bari naje na kirata," tana kokarin zuwa taje ta sanar da ita, Batool tayi saurin cewa"ku dakata" gaba ɗaya suka Juyo suna kallonta, Haris yace"kin gano inda ya ke ne? Girgiza kai tayi"a'a, " kafin ta kalli angel da ke a tsaye tace"lokacin da kika saki ƙarar nan, baki ga gifcin mutun ba"? Shiru angel tayi tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru, "Gaskiya ni banga gifcin kowa ba, amma meyasa kika tambaye ni"? "Saboda danish baya son tsawa, zai iyayiyuwa lokacin da kika saki ƙarar nan. Har muka farka daga bacci, a wannan lokacin danish ya rikice ya sauko daga saman gadon shi ya faɗa wani wurin" Sakin baki angel tayi galala tana kallon batool, da mamaki akan fuskarta tace"saboda kawai nayi ihu sai ya 6ace a neme shi arasa, ko dai yana da ta6in hankali ne"? Tayi tambayar tana kallon batool, Kafin batool ta bata amsa, Haris yace "yanzu ba lokacin yin magana bane, bamusan awani hali ɗan uwanmu yake ciki ba, yamakata muyi hanzarin nemo shi" Ya kai ƙarshen maganar, tare da kai hannu ya kar6e fitilar dake a hannun batool, ya yi gaba suma suka bi bayan shi, Ko'ina kaf sai da suka duba, Basu ga danish ba, a gajiye suka koma saman gadajensu, kowa ya zauna cike da jimamin rashin ganin danish, Deeja tace"ni dai bari naje na kira tsohuwa," haris ya dakatar da ita" dare yayi sosai, kada mu takura mata, mu jira zuwa gobe da safe, nasan kafin lokacin duk inda yaje zai dawo ne" Angel dai duk ta rasa sukuni, aranta tace No wonder dama ni nasani, ba cikakken hankali gare shi ba, " Bacci ne ya fara ɗaukar wasu daga Cikin su, Mutun uku ne suka gaza runtsawa, Haris da Batool sai Angel, kuma dukansu idanuwansu acike suke da bacci, Fitsari ne ya matse ta, da sauri ta sauko daga saman gadonta, hannunta ruƙe da fitila, ta nufi first door ta toilets ɗinsu, Bayan ta buɗe ƙopar ta shiga ɗaya daga cikin toilet ɗin, ajiye fitilar ta yi a ƙasa, ta sanya hannu ta tu6e wandon jikinta ta zuƙunna tana fitsari, har wani lumshe ido take yi, saboda daɗin da taji, sai da ta kammala yin fitsarin tayi tsarki, tana ƙoƙarin mayar da wandonta, taji mutsu mutsun mutun, Hankalin ta yayi matuƙar ta shi, Kasa juyawa tayi la66anta sai kerma su ke yi, tsananin tsoro ne bayyane acikin idanuwanta, Ta wutsiyar idonta take hangen shi biji biji, koma wanene dai a zaune yake, ya jingina bayan shi jikin bango, Gefen tukunyar fulawar dake ajiye cikin toilet ɗin su, Tafi ƙarfin minti goma a tsaye batare da ta juya ba, zuciyarta a cunkushe da tunanin wanene Acikin toilet ɗin? Mutun ko Aljan? Kenan koma wanene ya gama ganin budurcin ta," ta ambaci hakan acikin zuciyarta, tunma kafin taga wanene Ranta ya 6aci ta harzuƙa sosai, ko aljani ne wannan ɗan tahalikin sai ya ɗanɗani kuɗarsa, Daurewa ta yi ta cije, a wani slow ta ɗan juya tana kallon wurin, Har saida ta zabura lokacin da tayi arba da Danish, a matuƙar ruɗe take kallon shi, Ya ƙanƙame Jikin shi da ke ta kerma, ya saki dogayen ƙafafuwanshi ƙasa, ya jingina bayan shi jikin bango, Gaba ɗaya sumar kanshi ta rufe mashi fuskarshi, Runtse ido ta ɗanyi tare da biting lower lip ɗinta, Har ta kai hannu zata rarumi bucket ta kwaɗa ma shi akai, sai kuma ta fasa ganin da alama bai ganin ta, saboda sumar kanshi data lullu6e eyes ɗinshi, cikin sanɗa ta soma tafiya tana tunkararshi, a saitin inda yake zaune ta zuƙunna, tana kallon shi, Abunda ya faru lokacin da angel takwatsa ƙarar nan, ya farka a firgice ya duro daga saman gadonshi tamkar walƙiya yabar cikin ɗakin saboda tsabar rikitar da ya yi ashe cikin toilet ya faɗo, Tagumi ta zabga tana kallon ikon Allah, ta sauke ajiyar zuciya yafi sau uku, da ace yau ta kama shi yana kallonta lokacin da take Cikin yin fitsarin nan, da kuwa ya gane kuransa, Allah ne ya taimake shi saboda sam baya a hayyacinsa, baisan ma ta shigo cikin toilet ɗin ba, Miƙa hannu tayi da niyar ta janye sumar dake akan fuskarshi, sai kuma ta fasa ta miƙe, taje ta ɗauki fitilarta, kafin ta kama hanyar fita daga cikin toilet ɗin, Bayan ta fito ta nufi cikin ɗakin kamar yadda ta tafi tabar batool da haris xaune saman beds ɗinsu a haka ta same su, Gefen gadon batool ta tsaya tare da ɗan ranƙwafawa saitin kunnanta tace"Danish yana a toilet, ki faɗa ma haris kuje ku ɗauko shi, Amma kada ki ce ni na faɗa maki" Buɗe ido batool tayi jin maganar Angel a cikin kunnanta"are u serious danish yana acikin toilet" "Eh, yanzu na ganshi aciki, amma kamar baya a hayyacinsa" Jiki na rawa Batool ta sauko daga saman gadonta, Sai da tafara gaya ma Haris cewa Danish Yana acikin toilet, tukunna tayi gaba shima yabi bayanta, Ajiyar zuciya angel ta sauke, tare da ajiye fitilar ƙasan gadonta, Ta haura daman gadon ta kwanta, tana jiran taga sun shigo da shi, Zuciyarta a cike take da tunanin meke damun shi? yanayin abubuwan da yake yi kamar akwai wani abu dake damun shi, ' can kuma saita ja guntun tsoki aranta tace"Ko ina ruwana da shi, matsalar shi ce," Jin takun tafiyarsu yasa ta ɗan saci kallonsu, Batool ce da haris sun ruƙoshi daƙyar yake tafiya, A saman gadonshi suka sake shi, ya haye saman mattress ɗinshi ya kwanta, Haris ya janyo mashi duvet ɗinsa ya lullu6a mashi har zuwa chest ɗinsa, Kafin suka koma saman beds ɗinsu domin yin bacci, Juyowa tayi da niyar ta saci kallon shi, karaf suka haɗa ido da shi, Harara ta jefa mashi, tare da juya ma shi baya ta kalli 6angaren hagu, Tunani ta shiga yi acikin zuciyarta, anya kuwa ɗazu bai kalle ta ba, lokacin da take yin fitsarin nan ba? Idan kuwa haka ne tabbas ya gama da ita, shikenan Ya gama ganin tsiraicinta, ranta ne ya bata cewa ta ƙara juya taga idan ya yi bacci, a hankali ta sake waiwayowa, karaf suka haɗa ido da shi, Ɗaure mashi fuska tayi tare da zare ma shi gray eyes ɗinta"Kallon ya isa, Ka juya ka kalli can mana, bakasan ba'a son ana bacci ta 6angaren Hagu ba," Yadda kasan tayi magana da gunki, Ko motsa lips ɗinsa, baiyi ba balle ma tayi tunanin zai tanka mata, "Can't u hear me"? a ɗan tsawace tayi ma shi maganar, jin yaƙi tanka mata kuma yaƙi daina kallon nata, yasa ta ruƙo pillownta, Ta daddage ta jefa ma shi saman fuskarshi, Salon Jan faɗa, A hankali ya ɗaura dogayen yatsun hannunshi saman pillown ya janye shi daga kan fuskarshi, Ya ɗaura shi saman nashi pillow ɗin ya haɗa biyu kenan, ya ɗaura kan shi asama, Rai a6ace tace"ka dawo mun da pillow ɗina, ko ranka ya 6aci," banza ya yi mata, "Magana fa nake maka" Sai lokacin ya ɗan buɗe baki yace"Zo ki ɗauka, ae bani na kawo shi nan ba" shiru ta yi tana cigaba da kallon shi, ganin ta tsare shi da ido, yasa shi juya mata ƙeya, Cike da takaici ta koma ta kwanta, tare da jan bargo ta lullu6e fuskarta, sai da tayi addu'a tukunna ta samu bacci ya yi awon gaba da ita, In the morning, Kasancewar Jiya basu samu isasshen bacci ba, Babu wanda ya farka, Cikin bacci angel ta yi Kakkauran Juyi da niyar ta gyara kwanciyarta, kwatsam idanuwanta suka sauka akan fuskar tsohuwa dake a tsaye bakin gadon ta, hannunta na ruƙe da sanda, mamaki ne ya kamata har ta soma tunanin kodai mafarki take yi, ƙura mata ta yi tana kallonta, itama kuma tsohuwar ita take kallon, Ƙasa ƙasa da murya angel ta ambaci"A'uzu billahi minasshaiɗanin Rajim" Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Ni ce shaiɗanin"? Bata amsa mata tambayarta ba, har saida ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta jikin bango, tukunna tace "Ai kin wuce nan, idan akwai na gaba da shaiɗan to ke ce tsohuwa" Baki asake tsohuwa ke kallonta, "Meyasa kika zo kika tsaya a bakin gado na"? Ta yi tambayar fuska a ɗaure take kallonta, "Zuwa nayi don in tashe ku daga bacci, naga har gari ya waye baku farka ba......" tunkan takai ƙarshen maganarta, Angel ta katse ta da cewa"Ƙarya kike yi, Idan tashin mu kika zo yi daga bacci why baki bi kowani gado ba, Sai kika zo kan gadona kika tsaya kina kallo na, wlh kiji tsoron Allah, tsofe tsofe dake kina ƙarya," ta ƙarasa maganar tana sakar mata harara, Jinjina kai tsohuwa tayi"Ke wai baki jin tsoro na? Meyasa baki jin shakkar yi mini magana ne? "Inji tsorin ki akan me? Ni da nake neman hanyar da zan tarwatsa shirin ku taya kike tunanin zan ji tsorin ki? Idan ma kina tunanin hakan acikin ranki to ki daina, suma waɗanda suke jin shakkar taki don kin juya masu tunaninsu ne, Amma asannu zan dawo da su Cikin hayyacin su, " Shiru tsohuwa tayi tana kallonta batare data ce komai ba. Angel taci gaba da cewa" ina zargin jiya ke ce kika kwaɗe mun kaina da sandar hannun ki, Saboda kinga ina ƙoƙarin kwance shirinki, wato so ki kayi nima ki ɗaure mun kaina ta yadda zan manta da komai, tabbas kinso ki yi nasara sai dai Allah bai baki ikon yin hakan ba, farkawar dana yi daga bacci komai dana manta sai da ya dawo cikin kaina, Kuma bazan fasa faɗa masu Allah ba, har sai na fargar da su, "Taya kenan zaki iya aiwatar da hakan? Ko kina tunanin zaki iya sarrafa tunaninsu ne? Yaran da ni na raine su da hannu na, na gatanta su, tun da suke basu ta6a shan wahalar rayuwa ba, komai suna samu ba'a abunda ban yi masu ba, matsayin uwa nake a wurinsu, a haka kike tunanin zasu ji maganarki fiye da tawa"? Tsohuce ta yi maganar yayin da take sakin wani irin bazawarin murmushi, Wani irin kallon rainin wayau angel tayi mata"Wlh tun da nake arayuwata ban ta6a ganin Muguwar maca ba, Azzaluma kuma macuciya irin ki ba!" Yadda tayi magana batare da jin ɗar ba, ya yi matuƙar girgiza tsohuwa, "Wai ke baki jin tsoron Allah? Ki tuna fa komai kike yi Allah yana kallon ki, har kina da bakin da zakice kin basu gata? Kin raine su? Kuma har kike kiran kanki a matsayin uwarsu? Tirr wlh ji nake kamar inyi kakin majina in watsa maki akan fuskarki saboda natsane ki, Wlh nafi son mutuwa ta so dubu dake!" Zuba mata ido tsohuwa tayi tana kallon Ikon Allah, Sassauta murya angel tayi Idanuwanta cike tab da ƙwalla tace"Kin cuci rayuwarsu, kin gama dasu, ni banmasan ya zan kwatanta irin cin zalinsu da ki kayi ba, kuma ga dukkan alamu kin sani kike take sani, dan baki yi kama da jahila ba, Kawai salon tsabar mugunta ne, Yaran nan ko nonon raƙuma suka sha iya abunda zasu yi kenan, Ga sunan Wasu kala da su they don't even know anything about the one who created them because you never told them, cos of your wickedness Kin barsu a cikin duhu, sun zo duniya a wahalce kuma zasu koma a wahalce, Idan yau ɗayansu ya faɗi ya mutu menene makomarshi dan Allah meyasa ki ka yi musu haka? Meyasa?.........." kasa ƙarasa maganar angel tayi saboda wani irin ƙuntataccen kuka daya kubce mata, kuka sosai ta fashe da shi, Tsohuwa kuwa ta kafe ta da waɗannan Kwala kwalan idanuwanta nata, masu kama dana ƴan ƙwaya, Cigaba da magana ta yi"Idan wani zunubi suka aikata maki, bai kamata ki ɗauki fansa ta wannan hanyar ba, balle ma nasan basu aikata maki komai ba, To kodai cikin danginsu wani ya yi maki badaidai ba, shiyasa kike ɗaukar fansa akansu" ta yi tambayar idanuwanta jawur hawaye duk sun wanke fuskarta, Tun da suka soma magana babu wanda ya farka daga cikin masu yin baccin, tamkar wasu matattu, Jinjina kai angel tayi"dama nasani bazaki bani amsar tambayata ba, sai dai ki kafe ni da ido kina kallo," ta yi maganar cikin sanyin murya tare da sanya hannunta da dama tana share hawayen dake silalowa, Kafin ta ɗaura da cewa"Allah ba azzalimin bawansa bane, Allah zai bi masu haƙƙinsu, inda na gode ma Allah, Mutuwa tana akan kowa, Walau mutun walau aljan, akwai kwanciyar ƙabari akwai kuma hisabi, Ina fata duk kin shirya ma wannan........" Muryar Batool ce ta katse ta ta hanyar kiran sunanta"ANGEL" koda tsohuwa taji muryar batool, Sai ta juya da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar shiga ɗakinta, Har ta kusa shiga ciki muryar angel ta sake katse ta da cewa"Baki san Su ji me muke tattaunawa ne shiyasa kika nemi hanyar guduwa? Allah dai yana a madakata yana jiranmu, kuma inaso ki sani Zanyi amfani da ilmin da nake da shi, da kaifin basirar da nake da shi wurin Sarrafa tunaninsu, Kuma zansa su kar6i addinin musulunci, after that I will fight for our freedom, because no one deserves to live a locked up life! Tsawon mintuna tsohuwa bata motsa ba, kuma bata juyo ta kalli inda angel take ba, can dai taci gaba da dogara sandar, har samu ta shige cikin ɗakinta taja ƙopa ta rufe, Fashewa da wani sabon kukan angel ta yi, da sauri batool ta sauko daga saman gadonta, tazo gaban gadon angel ta zauna daga gefenta, Muryarta aruɗe take faɗin"Sister what's wrong with u? and why are u crying"? Kallonta angel tayi da idanuwanta da suka rune, muryarta a karye tace"Batool ina kuka ne saboda ku" "But why"? "it will be hard for you to understand me, even if i tell you, so just forget about it," cikin shessheƙar kuka ta yi maganar, Dafa shoulder ɗinta batool tayi"Pls ki faɗa mun meyasa kike kuka sabo da mu"? "Baki ga tsohuwa ba"? Angel ce ta yi mata tambayar, girgixa kai batool ta yi"Banganta ba, tazo ne? Ita ce ta saki kuka"? Girgiza kai tayi"A'a, Mubar maganar, inaso zan shiga toilet," daga haka ta zuro da ƙafarta daga saman gadon ta sauko, ta nufi toilet ɗinsu, Ta tafi tabar batool da tunanin dalilin kukanta, meyasa ta ke yin kuka saboda mu? ta yi ma kanta tambayar da bata da amsarta, Tunda ta shiga Cikin toilet ɗin taci burki ta tsaya Idonta na akan Window nan dake a jikin bango, wadda ta ƙwallafa ma rai akan son Fasa glass ɗin jikinta, don ta samu damar dura wa Cikin kurkukun. Hannu tasa ta share hawayen dake akan fuskarta, Cikin zuciyarta ta soma yin magana"rana ta farko dana tsinci kaina cikin gidan kurkukun nan, A ƙagare nake dana nemi hanyar da zan fita daga Cikinsa, Amma Ayanzu bana sha'awar Barinsa batare da waɗannan bayin Allahn ba, Kuma batare da ƙwaƙƙwarar hujja da zan yin amfani ba, wurin ganin na tarwatsa duk wani shirinsu, Zanbi komai asannu domin Cimma nasara, Bi'iznillahi,' Angel yarinya ce mai kaifin basira Fiye da tunanin mai tunani, wayan dake gare ta yafi ƙarfin shekarunta, wasu ɗabi'un nata da halayanta sam ba irin na yara bane, she's genius" Lokacin da ta fito daga wankan, A tsaye ta samu Batool tana jiran na ciki ya fito ta samu ta shiga itama tayi wankan" Kallon juna su ka yi, Murmushi Batool ta sakar mata tare da cewa"tun ɗazu nake jira na ciki ya fito in samu nima in shiga in yi wanka, Angel tace"Wani ya shiga sauran toilets ɗinne"? Jinjina kai batool tayi"Eh, Hanna ce ta shiga ɗaya, ɗayan kuma Danish ne da deeja suka shiga Ciki," Har wata zabura angel ta yi jin abunda batool tace"What! danish da deeja ne suka shiga atare? Saboda me"? Fuskar batool asake tace"Dama idan babu wuri kuma uziri ya kama mu, mutun biyu suna amfani da toilet ɗaya......." tunkafin Batool takai ƙarshen maganarta, Angel ta yi gaba zuwa ƙopar sauran makewayin, Rai a matuƙar 6ace takai hannu tana Bubbuga ƙofofin tamkar zata Fasa su, "zaku fito ko saina 6alle ƙopar"? Tana huci ta yi maganar, Bama tasan wanne suke a ciki ba, Kusan atare suka buɗe ƙofofin toilets ɗin, na biyun Hanna ce ta leƙo kai, Na ƙarshen ne Deeja da danish suka fito, wani matsiyacin kallo Angel ta shiga binsu da shi from head to toe, hannun shi na a ruƙe da rigarshi, ita kuma iya rigarce har guiwarta, wandonta na hannunta, "lafiya kike bubbuga mana ƙopa"? Fuska aɗaure deeja ta yi mata tambayar" Dakuwa angel ta sakar mata"Ungo nan, Ku dukanku ku kar6a ku raba," Kallon juna su ka yi don basu fahimci me take nufi ba, Runtse ido tayi zuciyarta na tafarfasa ta ambaci"Allahu ajirni fil musibati...... Batool sai faman tamyarta take yi lafiya? Meya faru"? Ware idanuwanta ta yi akan fuskar deeja da ta danish, sae faman lumshe eyes ɗin shi yake yi, da alama bacci bai ishe shi ba, Sam tarasa ta ina zata fara, wato su awurinsu ba laifi bane idan mace da namiji sun shiga toilet ɗaya, tun zuwanta bata ta6a sanin suna yin hakan ba, Sai yau da take ji awurin batool ta kuma gani da idanuwanta, Cizon lips ɗinta tayi tamkar zata fasa su, Cikin fusata ta nuna Deeja da hannu"Zoki wuce, Ki jira idan ya gama ki shiga" maƙe kafaɗa deeja tayi"babu inda zanja, meye naki aciki? Wata irin gigitacciyar tsawa angel ta daka mata, Saboda tsabar ruɗi a firgice danish Ya koma Cikin toilet din," Da gudu Sauran Ƴan uwansu dake acikin ɗakin suka faɗo Toilet area ɗin, Haris da su aziza, "Meke faruwa ne"? Javed ne yae tambayar, Batool tace"Nima bansani ba, ranta ya 6aci ne saboda na faɗa mata cewa idan uziri ya kama mu kuma babu wuri mutun biyu suna shiga toilet ɗaya shine take fushi," Harara haris ya watsa mata tare da cewa"To ke meye naki aciki da har zaki nuna 6acin ranki akai"? Matsawa angel tayi Saitin inda haris yake a tsaye, Kafin ta soma magana atsanake, "Saboda hakan bai dace ba, Koda kuwa Namiji da namiji ne su shiga toilet ɗaya balle kuma Mace da namiji, bazan bari ana aikata 6arna batare dana hana ba, don haka daga rana irin ta yau, idan har na ƙara kama mutun biyu acikin toilet ɗaya, Saina Karanta ma shi charman dudu Cikin shi ya kumbura ya mutu kowa ya huta" Jin wannan maganar ta angel yasa hankalin kowannansu ya tashi, musamman deeeja tuni idanuwanta sun cicciko tan da ƙwalla, "Ya kike so muyi idan uziri ya kama mu, a lokaci ɗaya"? Hanna ce tayi mata tambayar, "Sai ku matse koma menene ku ke ji, idan na ciki suka kammala suka fito sai mutun ya shiga" "Ammaaaa......."kasa ƙarasa maganar haris yayi ganin tana nannaɗe hannun rigarta alamar za ta yi dambe, "Abi Umarni na azauna lafiya, Shine kawai idan kuma mutun yace zaiyi mun gardama, yasan me zai biyo baya," Gaba ɗaya duk suka sha jinin jikinsu, juyawa tayi tare da kallon deeja"Ke kuma Munafuka, zoki wuce ki jira idan ya kammala ki shiga, ni dama sam ban yarda dake ba, da wasu idanuwanki tubarkalla kamar na kwartan mazuru, idan shi yana da ta6in hankali ai ke da hankalinki, Sullu6iyo kawai, zaki wuce kosaina Zubar maki da haƙoran gaba"? Jiki na rawa deeja ta ƙarasa fitowa daga cikin toilet ɗin Taja ƙopar ta rufe, Kallon sauran ta yi"Kowa Ya kama harkar gabansa, kuma Allah yasa wani yayi gulmata acikin ku, Aljanata kamila zata faɗa mun ne, daga nan ni kuma zan tofa ma mutun charman dudu" takai ƙarshen maganarta tare da sa kai ta wuce su tamkar damisa, Ta nufi Cikin ɗakin sai da ta shiga ta zauna gefen gadonta, Taci gaba da tiƙar dariya, can kuma ta dakata da yin dariyar hawaye suka soma shararowa daga cikin idanuwanta, Hannu biyu tasa ta dafe kanta, wani irin tsananin tausayinsu take ji, har cikin ranta take jin tsananin sonsu da ƙaunarsu, a halin yanzu babu wanda bata so acikinsu, saboda tausayinsu da take ji, ashirye take data taimaka masu wurin gyara rayuwarsu, Jin motsin shigowar su Cikin ɗakin Yasa ta yi saurin share hawayen dake akan fuskarta, ta kishingiɗa saman gadonta, A jere suka shigo kowa sai satar kallon Angel yake yi, cike da jin tsoronta, Ko zama ba suyi ba, Giants suka turo ƙopa suka shigo Hannunsu ruƙe da kayan breakfast ɗinsu, ba ƙaramin daɗi angel taji ba dama daren Jiya da wata irin matsiyaciyar yunwa ta kwana, Bayan sun ajiye Masu farantan, kamar kullum Jiki na rawa suka Nufi saman Carpet ɗin kowa yayi zaman Cin tuwo, Suka zagaye trays ɗin, Sai da duk suka hallara, Hada danish wanda tunda ya zauna Jikin shi keta kerma sam babu natsuwa attare da shi, Gaba ɗaya tsawar da angel ta daka masu ɗazu ta gama gigita shi, Tun da suka fara Cin abinci, Wurin ya yi tsit baka jin sautin komai saina taunar abincin da suke yi, ganin nata ya kusa ƙarewa yasa ta fara tsantsani, can data lura danish ba wani cin abuncin yake yi ba, tsakurarsa kawai yake yi kamar baisan ci, da yake suna Fuskantar Juna, ta faki idon sauran ƴan uwan nasu, tayi musayar plate dana danish, ko da taga yana kallonta, saita zazzare mashi ido don kar yace zai anshe kayan shi,' lamarin yayi matuƙar ɗaure ma shi kai, yana ji yana gani tayi mashi musayar plate, ta ajiye ma shi nata data kusa Cunye, na shi kuwa a cike yake da abinci, bai dai ce komai ba, Yaci gaba da cin nata abincin data tura mashi, Bayan sun kammala, Giants suka tafi da kayan abincin, Ganin Kowa ya nufi gado zai kwanta yasa tayi saurin cewa"Ku dakata" Tsayawa su ka yi tare da juyowa suna kallonta, "From now on, when you finish eating food, no one will lie down and sleep, you have to exercise, doka ta ce duk wanda yaƙi bi kuma yasan me zai biyo baya,' Natsuwa su kayi suna sauraronta, Haris ne yai kokarin cewa"Saboda me"? "Saboda lalacin ku yayi yawa, idan kuna motsa Jiki zaku yi ƙarfi, " "So kike kiyi iko damu"? Kafin ta bashi amsa aziza tayi saurin cewa"pls haris kayi shiru, kada ta karanta mana charman dudu, nidai zanyi abunda kike so angel," Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da kallon su batool tace"what about u guys? Zaku yi ko kuwa"? Har suna haɗa baki wurin cewa"eh zamuyi komai kikeso" Kallon haris tayi"kaima dole kayi idan har kana son zaman lafiya, idan ba hakan ba ta kanka zan fara aiwatar da aikina, tare da aljanata kamila," Haɗe girarsa yai fuska a tur6une yace"Ae bance bazan yi ba" Ƙumshe dariya tayi abakinta, daƙyar ta samu ta basar da dariyar, ta ɗaure fuska tana hura hanci, "Sister ya ake yi toh baki faɗa mana yadda zamu motsa jikin ba" "U will start running from wall to wall, untill i command you to stop, Idan aka kammala sai ayi Jumping," Amsa mata su ka yi da toh, jikin bango suka koma suka tsaya a jere, Kowa ya naɗe hannun rigarshi, Komawa tayi daga bakin gadonta, ta zauna tare da ɗaura ƙafa ɗaya bisa ɗaya, Cike da bada Umarni Tace"Idan Na ƙirga uku Sai ku fara" su ka amsa mata"Toh" "1,2,3, Oya start" Da gudun gaske suka tafi Bayin Allah, Idan suka kai karshen bango sai su dawo sai su koma, har saida su ka yi kusan sau talatin tukunna ta basu hutu, zuƙunnawa su kayi a ƙasa, zufa ta ko'ina ajikinsu, Musamman danish kamar an tsamo shi daga Cikin ruwa, sae nishi suke yi, "Lokacin yin jumping ya yi, Maza kowa ya miƙe afara tsalle sau talatin kowa zaiyi duk wanda ya kammala sai yaje toilet ya watsa ruwa," amsa mata su ka yi da toh, ta tsaresu da ido har saida kowa ya kammala tsallan nashi, sannan ta ƙyale su tace kowa ya watsa ruwa azo ayi fira, Anan ta zauna tana jiransu, Bayan sun kammala, Jiki amace suka dawo cikin ɗakin Kowa Ya zauna saman gadon shi, "Yau kin bamu wahala sister, amma naji daɗin Jiki na" batool ce ta yi maganar, Haris da deeeja sunfi kowa Jin haushin angel, saboda ta sanyasu aikin wahala, danish kuwa tuni bacci ya yi awon gaba da shi, sam basu saba da wahala ba, Kallon su ta yi ɗaya bayan ɗaya tun daga kan danish dake bacci har zuwa sauran dake ta faman yin gyangyaɗi, Gyaran murya ta yi masu gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanta, " Jiya kamar Kunyi mun wata tambaya ko'? har suna haɗa baki wurin cewa"tambaya akan me kanan"? Ta gefe ta kalle su "Kun manta? Ku tuna kun tambaye ni wani abu jiya," "Eh, muna so Ki bamu labarin rayuwarki," azeeza ce ta yi maganar, "Gobe zan baku labarin rayuwata, Yau inaso Mu tattauna dangane da addini ne, Kallon juna su ka yi kafin suka dawo da hankalinsu kanta, "Addini kuma? Menene ma'anar hakan"? Da ruɗi akan fuskar hibba ta yi mata tambayar, Tana kokarin buɗe baki taci gaba da magana, Danish dake bacci ya kwatsa wata irin razananniyar Ƙara mai firgitarwa, " gaba ɗaya Hankalinsu Ya koma kanshi, A zubure ya miƙe zaune Ya sanya hannayenshi Biyu ya daddafe kanshi, yaci gaba da fasa gigitacciyar ƙara, Da gudun gaske su haris suka sauko daga saman gadajensu. suka nufi gadon danish, Kowa ya shiga Lallashin shi suna bashi baki, Angel kuwa sakin baki tayi tana kallon ikon Allah. lokaci ɗaya ranta ya bata cewar tabbas Danish ba shi kaɗai bane, Meyasa sai lokacin da take ƙoƙarin yin magana kan addini zai farka yana fasa masu ƙara? Da alama anyi hakan ne don a ɗauke masu hankalinsu daga kanta, gashi yanzu gaba ɗaya sun rasa samun natsuwa sun duƙufa suna lallashin shi, Wani irin wahalallan murmushi angel tasaki tana kallon ikon Allah, wato da tsiya dai sai an dakatar da ita, jiya an kwaɗe mata kai da sanda yau kuma ta 6angaren danish aka biyo mata, "Danish Pls can u talk to me? kana ganin fuskokin mu? Meya faru dakai? Atare suke jefa mashi tambayoyin nan, Angel ta kasa kunne tana sauraronsu, "Danish ka yi mun magana meke damunka? haris ne yae tambayar yana shafa dogon wuyanshi, Sae faman kerma jikin shi yake yi, ga wata irin zufa dake tsastsafowa daga Cikin sumar kanshi, ya runtse idanuwanshi sosai, duk ya ciccije lips ɗinsa, Zurfin tunani ta shiga yi, shin wata hanya zata 6ullo masu, tun da nan an toshe ta, sai yanzu ta ƙara yarda cewa akwai wata maƙarƙashiya, bakomai take tunawa ba face Wani American film da ta ta6a kallo na Magicians, a gidan aunty aneelerh, A cikin Film ɗin matsafa ne suke canza ma mutun tunaninshi su sarrafa shi, ko su sanya mashi tsafi a jikin shi, ko kuma suyi amfani da shi,' Jiya daga za ta yi magana an kwaɗe mata kai, kuma bata ga kowa ba, hakanan ta ke zargin tsohuwace kuma ga dukkan alamu zarginta ya tabbata tsohuwarce, sanan meyasa Basa son duk wani abu daya shafi Addini? A lokacin da ta kalli film ɗin ta ɗan shiga ruɗu harta tambayi aneelerh, "Su matsafan ba'a iya yin maganinsu"? aneelerh tace"Allah shi ne maganinsu, idan yaso duk wannan 6acewar da suke yi sai kiga an kama su har an ɗauki mataki kansu, shiyasa ake so mutun ya kiyaye kuma ya dage da neman tsari awurin Allah, saboda su mutanene masu hatsarin gaske, ta kowace hanya zasu iya 6ullo maka," aneelerh tayi mata bayani akansu sosai, Natsuwa tayi tana bin ko'ina na ɗakinsu da kallo, tana ji acan ƙasan Zuciyarta kamar ta manta da wani abu, wanda ta gaza tunawa acikin kwakwalwarta, Aranta tana ji kamar ta ta6a kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara, tsayar da idanuwanta ta yi akan red carpet ɗin da suke zama Su ci abinci kanshi, tunawa tayi da maganar aneelerh a inda tace"ɗaya daga Cikin alamomin matsafa, shi ne launin Ja, suna sanya jajayen kaya ko kuma A gidansu suna yawan amfani da jan abu kamar labule haka da sauransu, Jinjina kai angel tayi tare da cewa"Tsohuwa tana sanya jajayen kayan, Kuma carpet ɗin ɗakin mu Shima ja ne, kuma duk in aka kawo mana abinci, a saman trays ɗin ana sanya janƙyalle a rufe shi, Menene ma'anar launin jan nan na gidan kurkukun ƙaddara? su Giants suna sanya Baƙaƙen kaya shima launin baƙi bako da yaushe yake kasancewa abu mai kyau ba, dole nayi kokari wurin gano ma'anar waɗannan kalolin guda biyu Black and Red, kuma dole Nayi bincike akan lalurar dake damun danish domin kuwa wannan ciwon nashi Ba Misophonia bace, Kirkirarta a ka yi domin shi kawai, Hankalin angel fa yaƙi kwanciya, Saima ƙara ta shi da yake yi, Babban abunda take ji ma tsoro, Abunda take hasashe ya zamo gaskiya, saboda taji ance matsafa idan suka ɗauki mutun suna amfani da shi ne, Ko su cire sassan jikinshi, Ko su ɗibi jinin jikin shi, idan kuwa har hakane, To kuwa bata ga ta zama ba, duk da tana kokwanto akan hakan saboda su Batool sun faɗa mata cewa ba'a ta6a cutar da su ba, Kuma suna samun abinci, Matsafa ina suka ga lokacin ba mutun abinci, da zarar sun kamo shi kashe shi suke yi bayan sun gama kwashe amfanin jikin shi, Duk ba wannan ba, tambayoyi da yawa da take neman amsarsu WACECE TSOHUWA? SU WANENE GIANTS DAKE ZUWA KAWO MA SU ABINCI? A INA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA YAKE? TA FARA HASASHEN GIDAN KURKUKUN BA'A CIKIN NIGERIA YAKE BA, ZAIYI WUYA MA ACE ACIKIN GARI YAKE, SHIN SU KAƊAI NE ACIKIN GIDAN KURKUKUN KO KUWA AKWAI WASU MUTANAN? MEYASA AKA HANASU SHIGA CIKIN SHI"? ta yi zurfi a cikin tunaninta muryar batool ta katse ta da cewa"Angel har yanzu baki yi bacci ba"! Firgigit tayi tare da kallon batool dake a zaune gefen gadonta hannun ruƙe da fitila, tsananin mamaki ne ya kamata, ganin duk sunyi bacci, ita kaɗaice zaune saman gadonta, batasan tsawon lokacin da ta ɗauka ba, Sai da batool ta fargar da ita, ashe dare ya yi har sun kwanta, ita a yadda tabarsu suna akan danish dake ta fasa ƙara, Yanzu ga danish ɗin nan kwance cikin bargonshi sai bacci yake yi, su azeeza ma duk sun kwanta, "Yansu na farka zan shiga toilet shine na hango ki a zaune, nayi mamaki" murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa"Bana jin bacci ne, ya jikin danish"? "Ya ji sauƙi, baki ga ma har yayi bacci ba" tayi maganar tana haska gadon danish , Gyaɗa kai angel tayi"Nima yanzu zan kwanta, kije ki shiga toilet ɗin," Batool tace"ae har na shiga na fito, zan wuce ne na lura dake a zaune" Shiru angel ta ɗanyi, ganin kamar tana acikin damuwa yasa batool tace,"Baki da lafiya ne? Ko wani abu na damunki"? da sauri angel tace"bakomai, kawai ina tunanin rayuwar duniya ne" "Yau da kika samu motsa jiki, ga6o6in jikina sai ciwo suke yi mun, amma yanzu dana ta shi daga bacci sai naji daɗin jiki na," Angel tace"idan kuka saba kullum zaku ji dadin jikin ku, zai saki sosai ba'a son mutun daga yaci abinci ya kwanta, anfi son kadan motsa jikinka, "bayani tayi mata dangane da amfanin motsa jiki, batool tace"Daga yanzu duk in muka ci, abinci zamu dinga yi, bari naje na kwanta" tana kokarin miƙewa angel ta yi saurin ruƙo hannunta, kallonta batool tayi tare da cewa"Lafiya"? "So nake na tambaye ki, A gidan kurkukun nan Ana kiwon kaji ne"? Cikin rashin fahimtar zancanta, batool tace"Kiwon Kaji kuma? Meye ma'anar hakan" Dafe kai angel tayi"Ina Nufin kaji da ake kawo mana muna ci kusan kullum, Ana kiwonsu ne a gidan nan ne? Still batool bata fahimci zancenta ba, ta dai san kaza da ake kawo masu a soye suci, amma batasan ma'anar kiwon ba, "Shikenan tunda baki sani, Amma kin ta6a shiga cikin kurkukun nan? Naga ranar da aka kawo ni, Ni kaɗai nafarka acikin ɗakin nan, Ku kuma daga waje kuka shigo Ciki, Ina kuka je ne"? Ta yi tambayar tana kallonta" "Bazan iya tuna komai ba," cike da takaici angel tace"Komai baki sani ba ke, to faɗa mun a gidan kurkukun nan ku kaɗai ne kuke rayuwa a cikinsa"? Girgiza kai tayi"A'a bamu kaɗai bane, Kinga wannan numbobin na bayan rigunan mu, akwai me 400," waro ido waje angel tayi muryarta har shaƙewa take yi wurun cewa"Are u serious"? Ɗaga mata kai batool tayi alamar Eh, taci gaba da cewa"idan zan iya tunawa kafin zuwanki, Munyi rayuwa acikin wasu Prisoners ɗin waɗanda Ke rayuwa a killace cikin kurkukun nan, bamu kaɗai bane, muna da yawa," mamaki ƙarara akan fuskar angel ta kuma cewa"Amma ku meyasa aka ware ku daga Cikinsu"? Batool tace"nima bansani ba," "Yanzu faɗa mun, duk wani abu da kika sani game da kurkukun nan," "Bansan komai ba" "Ke dai ki tuna" shiru batool tayi tana kokarin tunano abunda ta sani, tsawon lokaci kafin ta soma magana "Idan aka ɗauki mutun ba'a dawo wa da shi, idan muka tambayi tsohuwa ina ƴan uwanmu suke waɗanda aka ɗauka daga Cikinmu, sai tace mana mu kwantar da hankalin mu, Suna nan cikin ƙoshin lafiya wata rana zasu da....." bata kai karshen maganarba, ta miƙe da sauri ta dauki fitilarta, ko kallon angel ba ta yi ba ta wuce saman gadonta ta kwanta, Zuba mata ido angel tayi Cike da mamakin yadda ta miƙe zumbur ta tafi batare da ta ƙarasa maganarta ba, kodai itama an zungureta ne? Ta yi tambayar a cikin Zuciyarta, Kafin ta yi Shirin kwanciya, kamar kullum ta ɗaga hannayenta sama tana yi masu addu'o'i, Hada daddynta kullum ne bata mantawa da shi, Yana acikin ranta..........🥺 *ANEELERH* Mami ce zaune gefen gadonta har ta yi shirin kwanciya, jikinta na sanye da Sleeping gown, ta ƙura wa screen ɗin wayarta ido, fitowa abie Yayi daga Cikin toilet yana gyara wuyan jallabiyar jikin shi, gyaran murya yayi mata ta ɗago tana kallon shi, fuskarta da alamun damuwa tace"Ina ta kiran aneelerh bata ɗaga ba, " "Bansan meyasa kika tashi hankalin ki ba, sai kace wadda ta tafi wata uwa duniya," "Dole na damuwa, saboda ni bata faɗamun cewa a can xata kwana ba, kuma na kira layin Uncle bash ɗin tana ta ringing bai ɗaga ba, itama dr Aisha na kira layinta bata ɗaga ba, idan acan zata kwana ae yakamata su kira su sanar dani," Murmushi abie ya saki"Na lura ba ƙaramin ji kike da ƴar nan taki ba, Ko da yake nasan saboda wa kika hana idonki bacci," "Bai wuci kace saboda baby junaid ba, ae dole na damu da jika na, shi kaɗai fa nake da shi kwallin kwal an tafin mu da shi, sai da nace tabarmun shi a wurina, amma ta kafe akan saita je can da shi," "In banda abunki, taya zata tafi tabar maki shi, bayan ba'a yaye shi ba, idan ya yi kuka ya zakiyi da shi"? "Nima ae macace, Kaima kasan ina da abunda zan bashi" Dariya abie yayi a lokacin ya dawo gefenta ya zauna, "Yanzu dai ki kwanta kiyi bacci, zuwa gobe da safe, zasu dawo kiga jikanki," Ba don taso ba, ta ajiye wayar Suka kwanta bacci atare, A 6angaren Aneelerh Kuwa, tun Bayan magbrib suka baro gidan Uncle bash, Drivern gidansu Musa ne ke yin driving ɗinta, Tana a zaune Cikin back seat na motar, Jikinta na sanye da Arab gown ta yafa mayafi akanta, Baby junaid na rungume saman kirjinta, Yasha kayan sanyi ajikin shi, "Ba gida zamuje ba, Gidana nake so ka kaini akwai wasu kaya da zan ɗauka"musa dake driving yace"Amma Ba mu yi da Alhaji cewa zan kaiki gidanki ba," "Eh na manta ban faɗa ma shi ba, ka kaini ba matsala," acewar aneelerh, Shi dai hankalin shi bai kwanta da su je gidan nan ba, ganin dare yayi kuma gidan yana a karkashin Binciken ƴan sanda bai son wani abu ya faru, "Amm hajiya naga dare yayi yanzu, me xai hana mu bari sai gobe da safe in kaiki gidan'? ɗaure fuska aneelerh tayi sam batasan gaddama"meyasa ka ke yi mun magana sai kace wata ƙaramar yarinya? Bani nace ka kaini ba? Ae ba jimawa zanyi ba, akwai abunda nake so in dauko ne Ko minti biyar bazan yi acikin gidan ba,' Muryar shi na inda inda yace"Zan kai ki mana kawai dai naga dare yayi ga kuma yaro ahannunki,' "Muje kawai nidai" Amsa mata yayi da toh, ya juya sitiyarin motar ya haura saman titin da zai sada shi da unguwarsu Uzair, Lokacin da suka ƙaraso unguwar tsit babu hayaniya ko gifcin mutun baka gani, kowa ya shige gidanshi, akwai hasken street light ta ko'ina, A bakin gate ɗin Gidan, Musa yayi parking ɗin motar, ya fito da sauri ya buɗe ma aneelerh murfin motar, Fitowa tayi hannunta rungume da junaid, Key ɗin gidan yana a hannunta, Dama biyu gare su ɗaya na uzair ɗaya nata, wanda ke a hannun jami'an dake bincike na Uzair ne, "Madam kodai in bi ki mu shiga Ciki"? Kallon shi tayi ganin duk ya tsorata"Motar fa wa zaka barma gadinta"? Muryarshi a sanyaye yace"hakane kuma bari na koma Ciki na jira ki, dan Allah Aunty kiyi sauri" murmushi tasaki jin ya canza mata suna, ya kirata da madam ya kuma kirata da aunty, Maimakon sunan da yake kiranta da shi Hajiya, Wuce wa ta yi zuwa bakin ƙopar dake a jikin gate ɗin gidan, ta sanya key ta buɗe ta, ta shiga daga Ciki, duk akan idon musa dake a tsaye ya jingina bayan shi jikin motar, A tsanake take tafiya Cikin Gidan wani irin yanayi take ji atattare da ita, Ko'ina ta shiga bi da kallo, tun daga kan inda suke ajiye motocinsu har zuwa ƙopar shiga falonsu, Bakomai take tunawa ba face rayuwarsu da Uzair, tuni taji hawaye sun wanke mata fuskarta, yau tsawon shekara biyu da watanni kenan, babu su babu alamarsu, Hasken electric bulbs ne Ya gauraye gidan, tamkar da rana, Lokacin da tazo bakin ƙopar falon, ta sanya key ta buɗe ƙopar ta shiga daga Ciki, Ko'ina a gyare yadda kasan mutane na rayuwa acikin gidan, A saman Sofa ta kwantar da baby junaid dake ta bacci, ita kuma ta shige Cikin bedroom ɗinsu, tsayawa tayi tana bin ɗakin nasu da kallo, sai ta dinga ganin kamar fuskar uzair yana sakar mata murmushi, Girgiza kai kawai ta yi yayin da hawaye ke cigaba da sauka saman fuskarta, Hotonsu na aure dake manne jikin bango ta ƙurawa ido, Sunyi matuƙar yin kyau, kusan minti biyar kafin ta Hau saman gadonsu ta kwanta tana shessheƙar kuka, Dama babu abunda ya kawota Cikin gidan tazo ne kawai don ta ƙare mashi kallo saboda kewar Mijinta da tayi,, Bubbuga mattress din ta dinga yi da hannunta tana kuka tana faɗin Wai ina kaje uzair? Meyasa ka tafi kabarni cikin maraicin rashinka, bayan kasan bana iya rayuwa da wani ɗa namiji idan ba kai ba, dan Allah mijina ka dawo gareni wlh ban gaji dakai ba, ina matuƙar ƙaunarka, kazo kaga Babynmu kyakkyawa da shi, so kake ya taso amatsayin maraya wanda bai da uba? Why uzair? Wata amsa kake so na bashi idan ya tambaye ni dangane da Mahaifinsa? Sai sambatu take yi ita kaɗai tana kuka, sam ta manta da Musa driver dake jiranta, ga kuma Yaro da ta bari a palour shi kadai saman Sofa yana bacci, Kusan awa ɗaya aneeelerh bata motsa ba, wani irin yanayi mara misaltuwa take jin kanta a ciki, sai faman shessheƙar kuka take yi, Lokaci ɗaya taji mummunar faɗuwar gaba ras! Tamkar ƙirjinta zai dare biyu, bugun zuciyarta ya ƙaru, Jiki na rawa ta sauko daga Saman gadon muryarta na kerma take ambaton sunan Junaid, Da gudun gaske Ta faɗo Cikin Falon, Tana ɗaura kanta saman Sofa ɗin data kwantar da junaid, taga wayam babu shi sai dai towel ɗin data nannaɗe shi aciki, A ƙasa aka jefar da shi, Kamar afarmaki take ganin lamarin, Tsabar ruɗi tarasa me zatayi, Tsananin tsoro ne bayyane akan fuskarta, Ƙarasawa tayi gaban sofa ɗin ta sanya hannu tana shafa Saman kujerarar, ta tabbatar cewa an ɗauke Mata Yaronta, tunani tayi kodai Musa ya shigo ya ɗauke shi ne? da gudu ta zabura Ta fito daga cikin falon, Har ta kusa kaiwa Bakin gate ta juyo kukan baby junaid ɗinta, a matuƙar gigice ta juya ta koma Cikin gidan, duk inda ta nufa sai taga babu shi, Rushewa tayi da matsanancin kuka tana faɗin"Innallalahi wa'innna ilaihirraji'un! Wayyo Allah na! dan Allah wanene ya shigo? kada ku cutar mun da yarona na roƙe ku, ku ƙyale mun shi, ' tana Cikin maganar nan tajiyo takun tafiyar mutun a firgice ta juya bayanta, gifcin shi ta gani koma wanene yana a sanye Cikin bakaken Kaya, Fuskar shi tana sanye da face mask, Hannunshi na ruƙe da Baby Junaid, Da gudun gaske Aneeelerh tabi bayanshi, sai dai kafin ta ƙarasa tuni ya 6ace ma ganinta, Gaba ɗaya ta haukace Jikinta sai tsuma yake yi ga wata uwar zufa data tsastsafo mata, ita ba kanta take ji mawa ba, Ɗanta take jimawa ba, shida bai mallaki hankalin shi ba, "Dan Allah na roƙe ka ka dawo mun da ɗana, Kome kakeso zan baka, Amma kada ka cutar mun shi, idan ma ni kakeso ka dauke ni ka ƙyale mun shi pls," cikin shessheƙar kuka tayi maganar, Motsi ta kuma Ji daga can saman stairs ɗin gidan, A hautsine ta ɗaga ido tana kallon mutun dake atsaye, Hannun shi ruƙe da baby junaid, ƙarfin hali hada ɗaura shi saman kafadarshi, yana shafa bayanshi, kuma yaron yayi shiru, Zuba ma shi ido tayi tana kallon shi batare da ƙyaftawar ido ba, Koma wanene wannan mutumin ba ƙaramin karkarfa bane, Yana da tsayi da kuma faffaɗan Ƙirji, ta ko'ina ya rufe jikin shi, ta yadda mutun bazai iya shaida shi ba, Muryarta na kerma tace"Dan Allah kada ka cutar mun da shi, kome kakeso zan baka," ta yi maganar tana kallon shi, zufa ta ko'ina saman fuskarta, Gani take kamar zai jefo shi ta saman bene ne ya faɗo kasa kanshi ya fashe, Fashewa ta kuma yi da wani sabon Kukan, Tunawa tayi da musa driver da gudu ta juya ta nufi hanyar fita don taje ta sanar da shi abunda ke faru, Harta ruƙe handle ɗin ƙopar, Muryar mutumin ta ratsa kunnnuwanta, Cikin harshen Turanci yace"idan kika kuskura kika fita, zan wurgo da shi ƙasa," Ras Taji gabanta ya faɗi, Kamar gunƙi haka ta ƙame, zuciyarta a cunkushe Ta juyo tana kallon shi, Har lokacin Yana a can sama, Muryarta na kerma tace"Na fasa bazanje ba, wlh bazanje ba, dan Allah ka bani ɗana, wlh nayi maka alƙawari bazan ƙara zuwa gidan ba," Dawowa cikin Falon Ta yi, A bakin stairs ɗin ta tsaya, fuskarta jaga jaga da hawaye, Bata ta6a ganin tashin hankali ba irin na yau, Ko wanene wannan mutumin? Taya akai ya shigo Cikin gidan? Bayan makullan gidan Suna a hannun jami'an ƴan sanda? Anya kuwa mutunne kodai ta bango ya ratsa Ya shigo? "Ka faɗamun ko nawa kakeso zan baka ina da kuɗi, Ni dai kawai burina ka bani Yarona," Tana magana tana taka staircases ɗin, a kokarin ta nata haura inda yake, "Hajiya" Muryar Musa driver ce, A firgice aneelerh ta juya tana kallon musa, Ai koda musa yayi arba da mutumin dake A can saman stairs sanye da bakaken kaya, Nan take jikin shi ya hau yin kerma, Ya shiga ambaton"Ƙalu Innallahi wa'inna ilaihirraji'un hajiya wannan kuma daga ina"? Cikin muryar kuka aneelerh tace"Nima bansani ba, Daga shiga Cikin ɗaki na dawo na taras ya dauke mun baby junaid ɗina, dan Allah kataimaka ka sanya baki mu bashi haƙuri ya bamu junaid mu tafi mubar masa gidan," Kallon shi musa Ya kuma yi"Bawan Allah, Don son da kake ma iyayenka Ka taimaka ka bamu yaron nan, Wlh tsautsayi da ƙaddara ne ya kawo mu Cikin gidan nan, dama saida na gargaɗi hajiya nace mata kada mu zo, Amma ta sanya naci akan sai mun zo yanzu ga irinta nan" Roƙonshi suka dinga yi ko tanka masu baiyi ba, tamkar baijin me suke cewa, Ya ƙanƙame Yaro a hannunshi sai shafa sumar kanshi yake yi, "Hajiya wannan mutumin fa, ba bamu yaron nan zaiyi ba, Kizo muyi ta kanmu kawai, Allah zai baki wani ɗan, idan ba haka ba mu duka zamu rasa ranmu," "Wlh ba inda Zanje sai ya bani yarona, saboda bakasan ciwon haihuwa ba shiyasa zaka ce mu tafi mubar ma shi yaro a hannu, " rai a6ace takai ƙarshen maganar, Duk yana atsaye yana sauraron su, Suna Cikin yin maganar nan, gaba ɗaya hasken gidan ya ɗauke, duhu ya mamaye ko'ina, Aneelerh ta shiga matsanancin tashin hankali, Cikin duhu taci gaba da tattaka matattakalar benan, Tana jiyo muryar musa yana kwala mata kira, amma ina kota kanshi bata bi ba, lokacin da ta ƙarasa hawa benan, Muryarta na rawa take faɗin"Bawan Allah, ka bani yaro na in tafi, nasan kana jina, dan Allah kada ka cutar mun shi," tana magana tana lalube Cikin duhu, Motsin shi ta dinga Ji acikin kunnuwanta, alamun yana a kusa da ita, Kamar ma zagayeta yake yi, Jikinta sai kerma yake yi, ga wata uwar zufa dake tsastsafo mata, mugun tsoro take ji, amma saboda soyayyar dake a tsakanin uwa da ɗa, ta kasa guduwa ta kwammace komai zai faru ya faru, koda zata rasa ɗanta ne, Wani irin daddaɗan ƙamshin turare ta soma shaƙa Cikin hancinta, koma wanene wannan Ba 6arawo bane, Kuma ba da niyar mugunta yazo ba, Lamarin ya rikitar da ita, Cikin sanyin murya tace"Dan Allah ka bani shi in tafi, wlh bazan faɗi ma kowa naga mutun acikin gidan ba," Hannunta taji ya ruƙo, ras taji gabanta ya faɗi, ɗaura mata baby junaid yayi asaman ƙirjinta, da sauri ta tallebe shi, ta rungume abunta ajikinta, Natsuwa tayi tana jiran jin ya furta wata magana sai dai baice komai ba, Lokacin da ta daina jin motsinshi a kusa da ita, a dai dai wannan lokacin hasken Gidan Ya dawo gaba ɗaya ya gauraye ko'ina, Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, tare da ɗaura idanuwanta kan baby junaid dake ta sharar bacci, saman ƙirjinta, Ƙara ƙanƙame shi tayi ajikinta, kamar zata mayar dashi Cikin cikinta, Yau da ace ɗan tahalinkin nan ya kashe mata shi, da kuwa har ranta zata iya rasawa, "Hajiya zamu iya tafiya yanzu"? Musa ne yayi maganar jikinshi sai kerma yake yi, yana daga can down stairs, Harara ta wurga mashi, "Ka bani key ɗin motar, ka kama gabanka, Sakaran Namiji kawai, hada cewa in bar mashi yarona in Zo mu tafi, ban ta6a ganin ragwon namiji irin ka ba, duk macan da ta aure ka tayi asara, " zuru musa yayi mata da ido," Saukowa down stairs tayi tare da miƙa mashi hannu"bani key ɗin motar" Cikin sanyin murya yace"ayi haƙuri hajiya ruɗu ne ya jawo hakan" A fadace tace"dalla ni bani key," Zaro key ɗin motar yayi daga Cikin aljihun shi ya miƙa mata, tasa hannu ta fusge shi, Cikin fushi ta fuce daga cikin falon, Da gudu musa yabi bayanta yana lallashinta. Bayan ta rufe gidan da key ta buɗe mota zata shiga driver seat, da sauri musa Yayi hanzarin cewa"Dan Allah aunty aneelerh kiyi hakuri wlh bana Cikin hayyacina ne, su6ul da baka nayi wurin furta maganar, ban kaiga tace ta ba," Daƙyar musa ya samu aneelerh ta haƙura ta miƙa mashi key din motar, ta shiga passenger front seat ta zauna shi kuma ya zauna a driver seat," Da gudun gaske ya fusgi motar, kafin su ƙarasa gida saida ta gargaɗe shi akan karya kuskura ya faɗa ma su abie dangane da mutumin da suka gani Cikin gidan, yaja bakin shi yayi shiru tun da bai cutar dasu ba, su ɗauka tamkar mafarki su kayi, Yace mata toh, Lokacin da suka ƙaraso Cikin gidan, A parking space Musa ya yi parking ɗin motar, ya fito ya zagaya ta other side ɗin ya buɗe ma Aneelerh mota, Fitowa tayi hannunta rungume da baby junaid, Har lokacin Jikinta kerma yake yi, ta tsorata sosai da wannan tahalikin da ya kai masu farmaki, Kallon musa tayi shima kallon nata yake yi, harara ta jefa mashi ya sunnar da kan shi ƙasa, Ni zan wuce ciki, " "To hajiya sai Allah yakaimu, Allah ya kyauta gaba," bata amsa ma shi ba ta nufi Cikin gidan, Da alama duk sunyi bacci, bata nufi ko'ina ba, Sai Cikin Bedroom ɗinta, a saman gado ta kwantar da junaid, sai baccin shi yake yi hankali kwance, Rage kayan jikinta ta yi, ta shiga toilet domin yin wanka, after 15 mins ta fito waist ɗinta ɗaure da towel fari, Walking slowly ta nufi Saman mirror chair ta zauna, tare da ɗaura gwiwar hannunta gaban madubin, ta zabga uban ta gumi, Zuciyarta a cike take da tunanin mutumin nan, ko wanene shi? Taya akai ya samu damar shiga Cikin gidan dake a garƙame? Kodai bayan shigarsu ciki shima Ya samu damar shiga Cikin gidan? Shin me yaje yi acikin gidan, gaba ɗaya ta burkita ma kanta lissafi, kusan raba dare ta yi azaune tana tunani akan shi, bata iya gano komai ba, a ƙarshe ta miƙe taje gaban closet, ta buɗe ta curo kayan baccinta, Ta sanya su ajikinta, Komawa saman gadon tayi, ta kwanta tare da janyo junaid ta rungume shi ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci yae awon gaba da ita, Ko da gari ya waye Aneelerh bata sanar da kowa game da mutumin da suka gani acikin gidan Uzair ba, ita kanta tarasa gane dalilin dayasa ta kasa buɗe baki ta faɗa masu cewa wani ya shiga gidan, wata'ƙil ta hanyar hakan asamu wata evidence da zata bayyana ainihin meya faru da su tajo, kuma tun daga ranar bata ƙara gigin zuwa gidan ba, gani take kamar mutumin yana bibiyar rayuwarta, kodan kada ta tona ma shi asiri dole ya bibiyeta, shiyasa take tsoran fallasawa, Back To prison🌷 A kwana a tashi ba wuya wurin Allah A yau angel ta cika shekara 1 da rabi A gidan KURKUKUN ƘADDARA, tun daga ranar da tayi ma batool tambayoyin nan bata ƙara tambayarta wani abu dangane da gidan kurkukun ba, dalili kuwa shine a duk lokacin da zata tambayi batool game da prison ɗin, Sai wani abu ya faru, wanda zai ɗauke masu hankali, Haka xalika a duk lokacin da ta yi yunƙurin sanar dasu wani abu game da addinin musulunci sai wani abu ya faru wanda zai dakatar da ita, ta ko'ina an toshe mata hanya, Abu ɗaya ne take kokarin Koyar da su shine yawan ambaton sunan Allah acikin maganarsu, saboda kwata kwata basa furta sunan Allah, zuwan angel cikin rayuwarsu sun fara koyan wasu abubuwan wanda basu iya ba, salon maganarsu ya fara komawa irin na angel, ta zama tamkar malama acikinsu, Idan suka kammala Cin abinci, bata bari su koma bacci, motsa jiki take sanya su suna yi, Ko kuma suyi wasa a tsakaninsu, bakomai yasa suke jin shakkarta ba, face rashin tsoranta, da kuma wannan kalmar ta charman dudu da take yi masu barazana da ita, shiyasa a kullum take Cin galaba a kansu, duk wannan tsawon lokacin da angel ta ɗauka acikin gidan kurkukun ƙaddara, har yau babu jituwa tsakaninta da Haris da kuma mr sound hater wato DANISH, su biyun nan sunƙi yarda da ita, duk da sunfi kowa jin shakkarta, kuma in ta bada umarni dole kowa yabi hada su ɗin, Zaune suke gaba ɗayansu sun kewaye Kayan abincin da aka kawo masu, giants suna a tsaye sun kasa sun tsare suna jiran su kammala Ci su kwashe Kayan su tafi, Hanna ce ta ya ye jan kyallen da aka rufe saman trays ɗin, tray na farko fried meat ne, sai faffadan plate me ɗauke da Snacks a tray na ƙarshe kuma jug ɗin ruwa ne, sai kofuna Bayan su kuma sai kwandon dake ɗauke da kayan marmari da ƴar ƙaramar wuƙa, wadda zasu yi amfani da ita su yanka fruits ɗin, Kowa yakai hannu ya dauki fried meat yana Ci, Gaba ɗaya hankalin angel na akan wuƙar da aka sako Cikin kwandon kayan marmarinsu Cin naman take yi kamar zata shaƙe, so take ta sace wuƙar batare da sun gani ba, ɗagowa ta ɗanyi tana kallon Su Giants dake a tsaye, abinci ma baza a bar mutun yaci a tsanake ba sai an tsare mutun da ido, a cikin zuciyarta ta yi maganar don tasan suna kallon su, Cikin ƙankanin lokaci ta cinye nata abincin, miƙa hannu ta yi tana nuna jerin Cups ɗin dake a jiye Javed yace"ruwa zaki sha"? Ta ɗaga mashi kai alamar eh, Da kanshi ya zuba mata ruwan ya miƙa mata, ta kar6a tana yi mashi godiya, bayan ta shanye ruwan ta ajiye kofin, xama ta yi tana jira sauran su kammala cinye nasu, ko ta samu a zo kan fruit ɗin yadda zata ji daɗin sace wuƙar, Sun ɗauki tsawon mintuna kafin suka kammala, kowa ya sha ruwa Kafin suka kai hannu suna ɗaukar kayan marmarin, ganin basu yi amfani da wuƙar ba, yasa tace ma batool" ba zasu yanka ba" batool tace mata"A jiyewa zamuyi sai anjima mu sha," yatsina fuska angel ta yi ganin zata rasa damar da take da ita, ta ɗaukar wukar, Dabara ce ta faɗo mata aranta, miƙewa ta yi tsaye tamkar zata bar wuri, ta ɗan ɗaga kafarta alamar za ta yi tafiya, gaba ɗaya ta yanke jiki ta faɗa saman kayan abincin, aruɗe su hannah suka kewaye ta suna jijjiga jikinta, hankalinsu a tashe suke ambaton sunanta, Ganin sunyi mata rumfa ta yadda waɗannan Giants ɗin bazasu iya ganin meke wakana ba, a hanzarce ta yi wuf ta zura hannu ta ɗauke wuƙar tare da saƙe ta gefen qugunta, mutun ɗaya ne ya ga lokacin da ta ɗauki wuqar don ta fakaici idon su ne, Miƙewa ta yi tana faman haki tace su bata ruwa tasha, jiri ne ya kwashe ta, Da sauri Hibba ta cika mata kofi da ruwa ta miƙa mata, kaɗan tasha ruwan don bata jin ƙishir ruwa duk cikin plan ne, Ganin sun kammala cin abincin yasa Giants matsowa suka tattara komai da suka yi amfani da shi, har fa sun Kama hanyar fita, danish ya ɗaga murya tare da cewa"She took a knife" tashin sense a razane angel ke kallon shi, kafin ta ɗaura idonta akan giants gani ta yi sunja burki sun tsaya cak, ɗaya daga cikin ne ya jiyo tare da nufar inda suke, tamkar zaki Saboda tsabar ruɗi tunkafin ya ƙaraso angel ta curo wuƙar ta miƙa mashi yasa hannu ya kar6a, ƙiris ya rage ta fashe da kuka kamar jira take su fita, ta yi wani irin kukan kura ta daka tsalle ta faɗama danish, kokawa ta 6arke a tsakaninsu bugu ta shiga kai mashi, ta yakushe shi da akaifun hannunta, hada cizo ta gartsa mashi gefen wuyan shi, Su batool suna ta ƙoƙarin rabata da jikin shi, amma ina duk wanda ya yi gigin ta6a ta wurgi take yi da shi, daƙyar haris ya cakumota, rai a 6ace ya yi wurgi da ita gaba ɗaya ta kife ƙasa kanta ya bugu sosai, Zuƙunnawa su kayi agaban danish dake yashe ƙasa yana fitar da numfashi sama sama, farar fatar wuyan shi tayi jawur ga sahun haƙoran angen nan tamkar an zana su, duk ta 6ata ma shi wuya da yakushi red marks ta ko'ina, Ran kowannan su sai da ya 6aci, musamman haris, rai a 6ace ya ke faɗin "Dama ae ba sonshi ki ke yi ba, shiyasa ki ke son kashe mana shi, na rasa me danish ya yi maki, bafa shi bane ya yi silar zuwanki prison ɗin nan ba, ballanta na kice xaki ɗauki fansa a kanshi, ki bar ganin ana jin tsoronki, Allah daga yau idan kika kuskura kika ƙara ta6a fatar jikinshi saina karairayaki, ɗagowa angel tayi idanuwanta sunyi jawur, batool da aziza suna a 6angarenta, Cikin shessheƙar kuka tace"Idan ka ta shi ka kashe ni dan Allah, kada ka barni da rai na, meyasa zai ce na ɗauki wuƙa? Ina ruwan shi? Idan har bai shiga hurumina ba ni zan shiga nashi ne"? Ta yi tambayar a ƙule, Batool tace"ban goyi bayan wani a cikin ku ba, Amma laifin danish nafi gani, meyasa za ka tona mata asiri don ta ɗauki wuƙa? Menene naka aciki? Juyawa ta yi kan angel'ke kuma angel baki kyauta ba, kalli yadda kika raunta shi, sai kace ba ɗan uwanki ba...."tunkafin takai ƙarshen maganar angel tace"danish bazai ta6a zama ɗan uwana ba, bana son shi bana ƙaunar ganin shi," Jinjina kai batool ta yi"its okey, daga yanzu zan shiga tsakanin ku, kada wanda ya ƙara shiga hurumin wani ina fata hakan ya yi," Javed yace"idan ma suka ƙara ni da kaina zan sanar ma tsohuwa a ɗauki mataki akansu," daga haka Haris da su mubeen suka kama hannun danish su kayi mashi jagora zuwa saman gadonshi, kwanciya saman gadon ya yi bawan Allah har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi, shifa bakomai yasa ya tona ma angel a sirin ta ɗauki wuƙa ba, face sanin irin tsanar da tayi mashi, tsoron shi kada ace shi zata yanka da wuƙar wannan dalilin ne yasa shi tona mata asiri, ashe da rabon yaci na jaki a hannunta, Miƙa mata hannu azeeza ta yi"ki tashi muke ki kwanta, ki huta" sai da ta ɗanyi jim kafin ta ruƙo hannun azeeza ta miƙe, saman gado ta koma ta zauna, hawaye sha6a sha6a akan fuskarta, danish ya tarwatsa mata plan ɗinta, taji takaici kamar ta sanya pillow ta taushe ma shi fuska haka take ji, "Angel me zaki yi da wuƙa"? batool ce ta yi mata tambayar, ɗagowa angel ta yi tare da kallonta, tana a tsaye gefen gadonta, Girgiza kai ta ɗanyi"babu komai, kawai inaso na mallake ta ne," ɗan zaro ido batool ta yi"karfa ace wani kike harin kashewa a cikin mu" cikin zolaya ta yi mata maganar, Cikin sanyin murya angel tace"a'a batool bazan iya kisan kai ba, ni kawai naso ace na mallaki wuƙar," "Da ace kina shiri da danish, da ya aro maki wuƙar shi," da mamaki angel ta kalle ta tare da cewa"yana da wuƙa"? Jinjina mata kai ta yi eh, akwai wata ƙaramar wuƙa da yake amfani da ita wurin datse gashin kan shi, tsohuwa ce ta bashi wuƙar lokacin da ya ta6a tambayarta yana so ya rage tsayin sumar kanshi, shi ne ta ba shi wuƙar to bai mayar mata da ita ba, har yau tana nan a wurin shi," Dafe kai angel ta yi tare da satar kallon danish dake a kwance saman gadonshi, da alama bacci ya yi awon gaba dashi, yadai sha wahala, "Ga samu ga rashi" ta ambaci hakan acikin azuciyarta, tasan koda me take yawo danish bazai ta6a ara mata wuƙar shi ba Kallon batool ta yi"kinsan inda yake 6oye wuƙar" kallon sama batool ta ɗanyi da alama tunani take yi, can tace"a ƙarƙashin katifar gadonshi naga yana 6oye ta, Angel tace"ki taimaka kice ya ara maki ita a matsayin ke zakiyi amfani da ita, Ɗan zaro ido batool ta yi"ae bai yadda ya fiddo da wuƙar nan, kaifi ne da ita tana da haɗarin gaske, kona tambaye shi bazai bani ba, saboda yasan ba abun da zan yi da ita," Jinjina kai angel ta yi"shikenan na haƙura" daga haka bata kuma cewa komai ba, ta koma ta kwanta amma fa bawai ta haƙura bane, a can cikin zuciyarta tana shirya yadda zata sace wuƙar danish batare da sanin shi ba, da wannan tunanin ta yini da shi kuma ta kwana, A daren yau ta kammala shirya yadda zata ɗauke wuƙar, kowa ya yi bacci saman gadonshi, duk sun lullu6e da bargunansu, angel ce kaɗai idonta biyu tana kwance idonta na fuskantar ceilling duk da duhu babu wadataccen haske saina fitilun ɗakinsu da suka kunna, "Lokaci ya yi da zan tashi inje saman gadon danish in ɗauke wuƙar sa," acikin zuciyarta ta yi maganar, tana ƙoƙarin miƙewa tajiyo takun tafiyar mutun acikin ɗakin nasu, da sauri ta koma ta kwanta cike da fargabar wanene a dai dai wannan lokacin ya faɗo masu ɗaki, Ƙyalla ido ta yi daga kwancen da take tana satar kallon inda take jiyo sautin tafiyar, kaskon turaren wuta ta hango a hannun mutumin dake zarya cikin ɗakin nasu, wani irin baƙin hayaki ke tashi daga cikin kaskon, kamar ana turara turaren wuta, Mutumin dake ruƙe da kaskon turaren wutar, jikin shi na a sanye cikin doguwar riga me hula launin ja, rigar har ja take ƙasa, Kasa kunne angel tayi tana sauraron muryar mutumin dake magana, kamar muryar tsohuwa sai dai bata iya tantance da wani yare ake magana ba, wani irin gu6ataccem yare mara daɗin ji, Nan fa hankalin angel ya ɗan tashi, xufa ta wanke fuskarta, duk ta sha jinin jikinta, tsoro take ji kada ace wani mugun ne yazo cutar da su, Bata kai ƙarshen zancem zucin nata ba, ta hango mutun yana tafiya a bakin gadajen su Hannah, yana tafiya yana hura masu hayaƙin zuwa saman jikin su, Da sauri angel taja bargo ta lullu6e fuskarta, acikin zuciyarta tana ambaton la'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalamin," lokacin da mutumin yazo saitin gadonta, da sauri ta sanya tafin hannayenta duka biyun ta toshe bakinta da hancinta, duk don saboda kada hayaƙin ya samu damar shiga jikin ta, Tana jiyo takun tafiyar mutumin yadda kasan takun tafiyar jaki, Lokaci ɗaya tadaina jin takun tafiyar da kuma surutan da mutumin ya ke yi, da sauri ta ya ye bargonta, tabi ko'ina da kallo bata ga kowa ba, alamar mutumin ya tafi, sai dai hayaƙin daya turara masu har yanzu bai gushe ba, Saukowa angel tayi daga saman gadonta, Zuciyarta cike da ruɗani, ko wanene mutun nan daya zo masu a tsakiyar dare, sanye da jajayen kaya? Turaren menene yake hayaƙa masu a cikin ɗakinsu da kuma saman jikin su? sam bata yadda da hayaƙin nan ba, tafi tunanin wani mugun abunne aka turara masu, Tunawa ta yi da surori da kuma addu'o'in da malaminsu na makatantar islamiyya ya ta6a koya masu yace su yawaita karansu domin neman kariya daga sharrin mutun sharrin aljan da duk wani abun cutarwa, "Zan tai taimaka masu, saboda basu da maiyi masu addu'a, a kullum in na kwanta ina bacci, daddyna yana yi mun addu'a, su kuwa basu da iyayen da zasu yi masu addu'a" acikin ranta tayi maganar Kamar yadda mutumin nan yabi ko'ina na ɗakin yana turara Masu baƙin hayaƙin nan, itama haka ta soma bin kowace kusurwa ta ɗakin nasu tana karanta Ayatul kursiyyu, da amanar rasuli, Suratul mulk, Suratul kafiroon, Suratul ikhlas, falaqi da nasi, duk in ta karanta kowannan su Saita maimaita, daga bisani tabi kowani gado tana tottofa masu addu'oin saman bargunan da suka lullu6a da shi, daga kan gadon hanna ta faro xuwa gadon mubeen har zuwa gadajen su batool, tana zuwa kan gadon danish taja guntun tsoki zata wuce, sai kuma taji aranta kamar bata kyauta ba, don me zata yi ma kowannan su addu'a amma shi ta kasa yi ma shi saboda me? Lafin me ya yi mata? shiru ta yi tana tunani, menene ribar ta idan taƙi yi mashi addu'a, Har ta kusa wuce gadon shi taja da baya ta koma tare da shiga daga gefen gadon, ranƙwafawa ta ɗanyi saitin fuskarshi ta soma karanto addu'o'in bayan ta kamalla ta tottofa mashi saman fuskarshi, kamar daga sama taji an damƙi hannunta, a razane ta kalle shi ashe ya farka, muryar shi a disashe yace"tsanar takai har ki zo kan gadona kina tofa mun miyau asaman fuskata"? Zuba ma shi ido angel ta yi batare da tace Furta komai ba, tama rasa bakin magana, yadda ya yi mata maganar ita kanta ta yi mamaki sai kace ba wannan mai jin shakkartata ba, bakomai yake jima tsoro ba, face wannan kalmar da take faɗi na cewa zata tofa ma mutun charman dudu Cikin shi ya kumbura, tuna wannan yasa shi ƙara tsorata, shi kanshi baisan yana da ƙwarin gwiwar yi mata magana irin haka ba, tsawa ya ɗanyi mata tare da cewa"Ba ki ji ina magana ba"? Still ta yi ma shi shiru saboda bata jin zata iya faɗa mashi cewa addu'a take yi mashi, don ma kada yaji kamar tana ƙaunarsa ne, Ganin ta yi mashi shiru ya ƙara har zuƙa, A tsananin tsorace Ya damƙo ƙasan rigarta da ƙarfi da niyar ya goge abunda ta tofa ma shi asaman fuskar shi, Cikin rashin sa'a ya janyota gaba ɗaya ta faɗa saman jikin shi..................🥱 *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* dukkan ilahirin jikin shi rawa yake yi, kusan suman kwance ya yi saboda tsabar tsoratar da ya yi jin Angel saman jikin shi ɗungurugum, zuciyarta har wani tafarfasa take yi saboda tsabar fusata, a rayuwarta ta tsani jikinta ya haɗu dana ɗa namijin da ba daddynta ba, kamar ta haɗiyi zuciya take ji, tayi Niyar idan ta ɗago ta kwashe shi da zazzafan mari, Sai dai wani yanayi da ta tsinkaye shi a ciki ya yi silar dakatar da ita, lokacin da jikinta ya haɗe da nashi wani irin zafi taji rau tamkar hucin garwashin wuta, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, ta fahimci cewa baida ƙoshin lafiya, da alamun zazza6i attare dashi numfashinsa kanshi da hucin zafi yake fita, gaba ɗaya jikin nashi a raunace yake, Ga fargabar angel dake a kwance saman shi, yasha jinin jikinshi a tsorace yake da tsiwatarwa, baiso ta tayar mashi da lalurarshi daddagewa tayi tare da yunƙurawa ta ɗago daga jikin shi, tarwatsastsiyar sumar kanta ta sauka har saman wuyan shi, a raunace ta kalli kyakkyawar fuskarshi, sama sama yake numfashi ya lumshe sexy eyes ɗin shi bai kai ga datse su ba, shima ɗin ita yake kallo, farar fatar wuyan shi tabi da kallo, ta ko'ina Jan tabon yakushin da ta yi ma shi ne, Sun ɗauki tsawon lokaci A saman gadon Batare da wani ya furta wata kalma ba, idanuwansu acikin na juna, Jira yake ya ga wani Irin hukunci zata yanke mashi don yasan ba ƙyale shi za ta yi ba, tana iya cewa xata karanta mashi charman dudu, Cikin shi ya kumbura, saukowa ta yi daga saman gadon nashi jikin ta duk ba daɗi, Sai yanzu ta lura da irin illar da ta yi ma shi, tana zargin kanta da alhakin Ciwon nashi, Ji take kamar taje ta faɗa ma tsohuwa cewa baida lafiya, amma ta kasa sam ba ta so yasan ta damu dashi, kuma ba ta son taje wurin tsohuwa saboda tsanar matar da ta yi, zuciyarta a karaye ta koma saman gadonta ta kwanta, Ita kanta tasan bazata Iya runtsawa ba, Saboda zullumin rashin lafiyar danish, gani take kamar idon ta rufe idanuwanta zata farka ta taras da gawarshi ne, tana da hanyoyin da zata iya taimaka mashi sai dai bazata iya ba, saboda batason Raini ya fara shiga a tsakaninsu, "I don't know why I'm worried about him," ta ambaci hakan acikin zuciyarta tare da juyawa don ta saci kallon shi, a kwance yake kanshi saman fillow, idon shi biyu ya yi lamo yana kallonta, Gyara kwanciya tayi Ita ma ta fuskance shi, don yau taci alwashin bazata bari ya runtsa ba, kodan kada yayi bacci daga nan ya zarce zuwa barzahu, zullumin da take yi kenan, Ganin yaƙi daina kallonta yasa ta ɗan ɗaure mashi fuska tare da cije lower lip ɗinta, ƙasa ƙasa da murya tace"Stop looking at me or else i will poke ur eyes" ta yi maganar tana kwatanta mashi yadda zata zungure ma shi idonshi da yatsan hannunta, har wani lumshe ido ya yi, tamkar yaji saukar yatsan nata acikinsu, Slowly ya kuma ware manyan idanuwan nashi akan fuskarta, Ƙura ma juna ido su kayi kallo na ƙurulla, ta jima tana mamakin wani abu atattare da prisoners ɗin da take atare dasu, gaba ɗayansu babu mummuna acikinsu, sam ba su yi kama da ƴa'ƴan malam shehu ba, sunfi kama da rainon madara, ƴan gidan Mommy da daddy, Expecially danish da Batool da Azeeza Hasken fatarsu sam bana baƙar fata bane, Kamar dai ita da take half cast, Launin fatar Su Hanna da su javed Dukansu irin na ya'yan Hutun nan ne, Ko'ina Aka samu kyawawan yaran nan? Zaiyi wuya su kasance ya'yan talakawa ne , Sai dai irin ƴa'ƴan hamshaƙan masu kuɗin nan, wannan ɗan shilan da take kallo, Yanayin shi tamkar akwai jinin sarauta atattare da shi, Baisan magana baisan hayaniya, kullum yana naɗe saman gado yadda kasan ɗan wani basarake, idan ka kalli soft skin ɗinshi ko tabo babu, fari ne sol, ga kyan ido ga kuma kyan sumar kai, Anya wannan ba ɗan wani shegen bane, ta yi tambayar acikin zuciyarta, Bawan Allah, duk ya tsargu da irin kallon da angel ke yi mashi, Ga bacci yana ji amma yaƙi yarda baccin ya ɗauke shi saboda gudun kada ta yi ma shi wani abu, yasan dole ta hukunta shi, kallon juna suka cigaba da yi da zarar taga ya fara lumshe ido zai yi bacci sai ta Ambaci kalmar charman dudu, a firgice yake ware idanuwanshi , ta hana shi runtsawa gashi in bai samu isasshen bacci ba, yana samun matsala, kusan raba dare su ka yi ita da danish, sai da Allah ya taimake shi bacci ya fara ɗaukarta tukunna ya samu shima ya runtsa_ In the morning🌹 Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta soma yi, a cikin zuciyarta tana karanto addu'ar ta shi daga bacci, tunawa da danish yasa tayi hanzarin buɗe idanuwanta A hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana kallon shimfiɗarshi, babu kowa asaman mattaress ɗin sai Bargonsa da pillow dinsa, hankalin ta ya yi matuƙar tashi, ta shiga tambayar kanta Ina danish ya shiga? Meyasa kowa yana a kwance saman gadon shi, sai shi kaɗai ke babu? Ko dai ya shiga toilet ne? Ta ƙarasa zancen zucin a lokacin da take sauko daga saman gadonta, cikin takun sauri ta nufi ƙofar shige toilets ɗinsu, hannu tasa ta tura ƙofar ta shiga daga Ciki, sai da tabi kowani toilet ta bincika amma babu danish, Dawowa tayi da sauri taje gaban gadon batool, Bubbuga ƙafarta tayi tare da Kiran sunanta"Batool! Sister!" saboda tsiwar muryar angel hatta su Azeeza sai da su ka farka, "Meya faru sister" muryar batool a disasashe tayi mata maganar, tashin ta kenan daga bacci, idanuwanta sun ɗanyi ja saboda bacci, "Na duba ko'ina banga danish ba, Jiya ya kwana da zazza6i yanzu kuma na farka ban same shi ba," "What? Danish bai da lafiya"? Haris ne ya yi maganar tashin shi kenan shima daga bacci, Fuskarshi da alamun ruɗi don ba ƙaramin Jin danish yake ba acikin zuciyarshi, Jinjina kai angel tayi alamar eh kafin tace"Bansan inda ya shiga ba, tun ɗazu nake neman shi" Ta shi xaune batool ta yi, idonta akan angel tace"meya faru da danish ɗin mu"? Ina ya shiga"? Ta yi tambayar tana faman yin hamma, Javed yace"Ni dama tun jiya na lura bai da ƙoshin lafiya, kunsan halin shi idan baya da lafiya yana da juriya baya bari mu sani kodan kada mu tashi hankalin mu akanshi, Amma nasan yanzu duk inda yake yana a tare da GIANTS, zai iya yiyuwa sune suka so su ka ɗauke shi" Batool tace"taya zamu iya tabbatar da hakan"? Hibba tace"Idan mu ka tambayi tsohuwa zata faɗa mana inda ɗan uwan mu yake, Bari naje na sanar mata," Ta karasa maganar tare da saukowa daga saman gadon nata, da azama ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa, Kowa yayi zugudum yana jiran tsammani, Knocking ƙopar Hibba ta yi, Almost 3 times, suka soma jin mutsu mutsun buɗe ƙopa ta cikin ɗakin, Fitowa tsohuwa ta yi hannunta ruƙe da sanda kamar kullum dai Cikin shigar nan tata, ta gado, wato doguwar riga launin Ja, Haɗa ido su ka yi da hibba, Cikin girmamawa hibba ta gaishe da ita, ta amsa mata gaisuwar ta ta, tare da cewa"Zan iya sanin meke faru"? "Dama danish ne, Angel tace jiya taji zazza6i a jikin shi, yanzu kuma mun farka bamu ga ɗan uwan mu acikin mu ba, bamu san inda ya tafi ba" Hibba ce ke magana amma idon tsohuwa yana akan angel dake daga can cikin ɗakin tsaye ta ruƙe qugu a bakin gadon batool, wani irin kallo take yi mata, murguɗa mata baki angel tayi tare da galla mata harara, Ƙayataccen murmushi tsohuwa ta saki wanda bai kai zuci ba, ta ɗauke idonta daga kan angel ta mayar dasu kan Hibba, "Giant ne yazo ya ɗauke shi, yanzu haka danish yana a treatment room, da zarar yaji sauƙi za'a dawo maku da ɗan uwanku," tana kai ƙarshen maganarta, ta juyawa ta koma cikin ɗakin nata, taja ƙopa ta rufe, Kowa ya ji Amsar da tsohuwa ta ba hibba, hankalin su duk bai kwanta ba, Mamaki ƙarara akan fuskar angel tace"dama har treatment room ke akwai a Cikin prison ɗin nan" Batool ce ta bata amsa da cewa"Eh, amma bakowa ne idan baida lafiya, ake kai shi can ba, Tsohuwa ce take duba lafiyar jikin mu,' Yau tsawon shekara ɗaya da rabi, bata ta6a jin Zancan wani treatment room ba, sai yau, kuma tun da take da su, da wuya wani acikin su ya yi koda Ciwon kai ne, wani iko na Allah, Lafiyarsu ta banbanta dana sauran Jinsin bil'adaman da ta sani, ita dai hankalin bai kwanta da Treatment room ɗin nan ba, saboda me za'a ɗauke shi daga Cikin su, maimakon tsohuwa ta bincika lafiyar jikin, Shi ne sai an wani ɗauke shi daga cikin su, Zuciyarta duk ta karaya, Batasan a wani hali yake ciki ba, juyawa tayi tare da nufar toilet ɗinsu, Tana ƙoƙarin shiga ta jiyo muryar haris yana cewa"Ke ce silar Ciwon Danish, saboda jahilin bugun da ki kayi ma shi jiya, idan har muka rasa ɗan uwanmu, kema ki fidda rai da rayuwa" Kasa buɗe ƙopar toilet ɗin tayi Kamar wadda aka dasa ma aya Muryar batool ta kuma ji tana cewa"Haris dan Allah kadaina wannan maganar, Angel ba ita bace silar rashin lafiyar shi ba, lafiya lou muka wuni da danish, daga baya ne Ciwon ya same shi" Tsawa haris ya daka mata"Shut up! Dama ae kina bayanta, wa kika fara sani acikinsu? Danish tun kafin ki mallaki hankalin ki kike a tare da shi, amma saboda wata can wadda bamusan da zamanta ba, gaba ɗaya kin kwaye mana baya," yana huci yakai ƙarshen maganar, "Dama ba ƙaunarsa take yi ba, shiyasa take son raunata shi," acewar deeja, Ta yi niyar ta juya taje ta nakaɗa masu bugu, amma saita fasa, saboda a halin yanzu ita kanta zuciyarta ta karaya, Buɗe ƙopar ta yi tare da shigewa Ciki, Ta jingina bayanta Jikin bango, siraran hawaye masu ɗumi suka soma gangarowa saman kuncinta, Ta ɗauki tsawon lokaci bata motsa ba, har saida Taji motsin shigowar mutun a toilet area ɗin, Firgit ta ɗanyi tare da kai idonta kan wanda ya shiga, Batool ce a tsaye tana kallonta, "Angel meyasa kike kuka? Ko dan saboda abunda suka ce? Bafa laifin ki bane," Cikin sanyin murya tace"Ba saboda su nake zubar da hawaye na ba, idan naso zanje in bubbuge su ne, Kawai ina jin ba daɗi, saboda bugun da nayi ma danish jiya, baki ji jikin shi ba jiya yayi zafi sosai, yana a cikin wani hali, kuma nasan Nice silah," Dafa kafadarta batool tayi"Dan Allah ki kwantar da hankalin, ki daina zubar da hawayenki, danish fa zai dawo cikin ƙoshin lafiya, tsautsayi ne kuma ya riga da ya faru,' Murmushin takaici angel ta yi withouth sayin anything, Saukar tafin hannun batool taji a saman fuskarta, tears ɗin da take zubarwa ta shiga goge mata, "Ina da saurin kuka, abu kaɗan yake harzuƙa ni," angel ce ta yi maganar cikin ƙunar rai, "Koda ace kowa zai juya maki baya, Ki sani Ina atare dake, a koda yaushe zan kasance a hannun damanki," da ƙwarin gwiwa batool tayi maganar, Wani irin kallo angel ta ke yi mata mai nuna tsantsar so da ƙauna, "Da ace mu tagwaye ne Iyaye na suka haifa da sai ince ke ce twin sister ɗina, saboda yadda kika damu dani, kika mayar da damuwarki tawa, Idan ina farin ciki kema kina farin Ciki, haka zalika idan ina baƙin ciki kema kina baƙin ciki, Batool you're so special, Ina roƙon Allah ya bani damar taimaka ma rayuwarku,' Ƙayataccen murmushi batool ta ɗan saki, Kafin tace"Muje muyi wanka, idan muka fito, zan gyara maki gashin kanki, naga duk ya hargitse," tayi maganar tana ruƙo doguwar sumar kanta, Gashin yayi tsayi sosai har ya zarce waist ɗinta ga uban yawa, yayi datti babu gyara har tashi yake yi, ita fa mantawa take yi da wani gashi akanta, Tun zuwanta kurkukun sau biyar ta ta6a wanke shi, Cikin shessheƙar kuka tace "Na saba daddyna yake wanke mun kaina, shiyasa nake jin wahalar wanke shi da kaina, ya saba mun da komai, yanzu gashi bamu atare da shi," zuƙunnawa ƙasa tayi tare da fashewa da matsanancin kuka, da sauri batool ta zuƙunna agabanta, tana lallashinta "Ashe dama haka rayuwar duniyar take? ni ban ta6a tunanin akwai wani lokaci da zaizo ba, wanda zanyi rayuwa ni kaɗai batare da daddy na ba, kuma ba'a cikin gidan mu ba, sai gashi yau na tsinci kaina a wata sabuwar rayuwa Cikin mutanan da banta6a yin tozali ba, duk yadda naso in jure nakasa, ina kewarka daddyna, inason naganka, nasan bada son ranka ka jefa ni cikin ruwa ba, kayi hakan ne donka ceci rayuwata, meyasa baka bini cikin ruwan ba? Ka tsaya har saida suka kashe ka'? Natsuwa batool ta yi tana sauraron sambatun da angel take yi, da alama tafara fita hayyacinta, Mahaifina shine sanyin idaniyata, shine komai nawa, ya gatanta ni tamkar sarauniya, Ya Allah duk wanda yayi silar tarwatsa ƙaunar dake a tsakanin zuciyoyin nan guda biyu, Ya Allah ka ƙasƙantar da rayuwarshi, ka haɗa shi da bala'e da masifa, wanda zasu hana shi runtsawa,' Duk da batool batasan kan zancen ba, hakan bai hana zuciyarta yin sanyi ba, hawaye suka soma sintiri saman fuskarta, Girgixa kai ta shiga yi, idanuwanta cike tab da kwalla, fuskarta tayi jawur da ita, Kallon batool tayi Jin shessheƙar kukanta, ƙaƙaro murmushi angel tayi"meyasa kike kuka"? Cikin muryar kuka batool tace"Saboda ke angel, ina tausayin rayuwarki" Itama Cikin muryar kuka tace"Bani bace abun tausayi ba, kune abun tausayi, Nifa na taso ta tare da iyaye na, nasan dangina, Naje makaranta, kuma nayi rayuwar ƴan ci, Ina sanya sutura mai tsada, Inci abinci fiye da sau uku arana, Daddyna yana ɗaukata a cikin motarsa yakaini duk inda nake so, Amma kufa?....daƙyar takai ƙarshen maganar saboda kukan daya ciyota, "Ba...tool, An cuci rayuwarku, An ƙuntata ku, an hana ku duk wani jin daɗi na duniyar nan, tun kuna yara kuka tsinci kanku acikin gidan kurkukun nan, Bakusan komai game da rayuwar duniyar nan ba, bakusan su wanene Iyayen ku ba, ku kanku bakusan suwaye ku ba, rayuwar kawai kuke yi a kurmance, mutumin da baisan mahaliccinshi ba, idan ya faɗi ya mutu yau, ya farka ya same shi acikin ƙabari Ya zaiyi? A lokacin da yasan gaskiya bayan lokaci ya qure masa, Wlh an cuci rayuwarku, ni kuma indai ina araye duk runtsu duk wuya bazan ta6a bari rayuwarku ta qare ahaka ba, koda kuwa zan rasa raina ne wurin ceton rayuwarku, xan roƙi Allah ya bani tsawon rai saboda ku............' tana kai ƙarshen maganarta, ta kifa kanta saman gwiwowin ta, taci gaba da yin kuka kamar ranta xai fita, itama batool ɗin kukan take yi har yanzu hawayenta basu daina zuba ba Ƙara matsawa tayi tare da ɗaura kanta saman bayan angel, su ka cigaba da yin kukan atare, sun ɗauki tsawon lokaci, kafin batool ta ɗago da kanta daga saman bayan angel, Calmy ta furta Sunanta"Angel" a hankali ta ɗago tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta da suka raunata sosai saboda kukan da ta sha,_ "Batool kinsan komai game da gidan kurkukun nan saboda acikin shi aka raine ki, meyasa ba zaki iya yi mun bayani yadda zan fahimta ba"? Muryarta a sanyaye tayi maganar, Girgiza kai Batool tayi tare da cewa"Angel bansan komai ba, da ace na sani, bazan iya 6oye maki ba, Ni dai tunda na taso acikinsa, a killace nake bama zuwa ko'ina, bamu san komai ba" Jinjina kai angel ta ɗanyi tana faman matse hancinta da ya yi jawur, "Yanzu duk acikin ku, babu wanda yasan wani abu dangane da prison ɗin nan duk irin tsawon shekarun da ku kayi acikin shi"? Zurfin tunani batool ta shiga, ƙasa ƙasa da murya ta furta sunan"DANISH" A ruɗe angel ta maimaita sunan"Danish? Ya san wani abu? Ki yi mun bayani pls......' Cigaba da magana batool ta yi" Idan ma akwai wanda yasan wani abu, To shi ne, danish ne, duk da bani da tabbaci, " a matuƙar ruɗe angel ke kallonta, "Sai dai danish bazai ta6a baki haɗin kai ba, saboda yana da wuyar sha'ani fiye da tunaninki, baida yarda, tun fil'azal balle kuma yanzu daya samu lalurar rashin son hayaniya, sai ya ƙara burkicewa,' "Kina nufin lokacin baya Danish ba haka yake ba'? Jinjina kai batool ta yi"Eh, daga baya ne ya koma haka, lokaci ɗaya muka rasa gane kan shi, ko bacci yake yi ya dinga furgita kenan yana sambatu, yanzu ne abun ma ya ɗanyi sauƙi, Dafe kai angel tayi"Ni nasan koda me nake yawo danish bazai ta6a sakewa dani ba saboda ya tsane ni," "yana da sauƙin kai angel, sai dai yarda ce baida ita, bai yarda da kowa ba a cikin mu, tsohuwace kaɗai ya yarda da ita," Wani wahalallan Murmushi angel ta saki wanda bai kai zuci ba, dafa kafadar batool ta yi"ngde ssai batool, muje mu shiga wankan, idan muka fito sai ki gyara mun gashin kaina," amsa mata tayi da toh, Atare suka miƙe kowa ya shige cikin toilet,' Bayan wasu ƴan mintuna kusan atare suka fito daga Cikin toilet ɗin lemar ruwa kwance saman sumar kansu da suka wanke, Lokacin da suka shigo cikin ɗakin a zaune suka samu kowannan su Saman Red Carpet ga kayan breakfast ɗinsu nan an kawo masu, Giants Suna a tsaye Sun goya hannayensu saman ƙirjinsu, Yau fa ta 6aci saboda rashin danish, Sun gaza sakin Jiki su ci abinci, Ji su ke kamar ɗan uwansu bazai dawo Cikin su ba, sanin cewa a lokacin baya duk wanda aka ɗauka zaiyi wuya adawo da shi, babu irin lallashin da Batool batayi masu ba akan suci abinci amma sunƙi Ci, kowa sai dai ya tsakuri kaɗan kamar anyi ma su dole, ganin zasu wulaƙanta abincin yasa ta ɗauko kwandon da take ajiye abinci a cikin shi, ta kwashe rabi da kwata aciki, Ta ajiye masu shi tasan da anjima dole su 6uƙaci cin abinci, idan yunwa ta addabe su, Bayan tafiyar su Giants, Batool ta ɗauko Comb, ta zauna saman gadonta daga gefe, tace ma angel ta zo ta zauna ta gyara mata gashin kanta, Angel kaɗai tayi niyar gyarawa gashi, sai gasu rubina dasu Hanna, Sun jera layi suna jira ta kammala gyara mata ga shi, Suma ta gyara masu nasu gashin, Baƙamar wahala batool tasha ba, Wurin taje masu sumar kawunan su, kowa cikinsu tubarkallah Yawan gashi gare su ga tsayi, In ka cire deeja ita kaɗaice keda gajeran gashi, amma yana da yawa cike da kanta, Mutum biyar ta yi mawa, ta miƙa ma angel comb ɗin tace Ta gyara ma sauran Huɗun gashi idan ta kammala itama ta gyara mata nata gashin, yinin ranar abunda su ka yi ta yi kenan, hada mazan suma duk saida suka sharce sumar kawunansu, su kansu ba ƙaramin daɗi su kaji ba, da su ka gyara Sumar kawunansu. *Boss Bature🌷✍️* Wasa wasa Har dare ya yi ba'a dawo da danish ba, duk sun damu, kowa yana zaune saman gadon shi, ita kanta angel da bata shiri da shi saida ta damu da son sanin a wani hali ya ke ciki, kallon kowannan su ta yi"me zai hana ku kwanta ku yi bacci nasan cikin dare zasu dawo maku da ɗan uwanku," Batool tace"angel bazamu iya runtsawa ba, mun saba kwana atare idan har danish bai dawo ba, a zaune zamu kwana" Ba haka angel taso taji daga gare su ba, taso ace sun kwanta bacci ya ɗauke su, ko dan ta samu damar Bincikar inda danish ya 6oye wuƙar shi, Takun tafiya suka jiyo da sauri suka kai idanuwansu kan mutumin dake fitowa, tsohuwace ta shigo cikin ɗakin hannunta ruƙe da sanda, ta tsaya tana binsu da kallo, Da sauri haris dasu Hannah suka sauko daga saman gadajensu su ka nufi wurinta har suna haɗa baki wurin gaishe ta, ta amsa masu fuskarta asake, kafin tace"me ya hana ku yin bacci ne"? Atare suka haɗa baki wurin furta sunanshi" Danish, har yanzu ba'a dawo mana da shi ba, muna ta jira" ta lura da irin halin da suka shiga, "Kamar yadda kuke kewarshi shima haka yake kewarku, kuna aranshi," "Amma jikin na shi da sauƙi"? Haris ne ya yi tambayar a ƙagare, Kafin tsohuwa ta basu amsa angel ta sauko daga saman gadonta, ta nufi inda suke a tsaye ido cikin ido suke kallon kallo tsakaninta da tsohuwa, "Muna so mu gan shi, mu kuma yi mashi ya jiki," Acewar angel "Kada ku damu kanku, zuwa gobe danish zai dawo cikin ku," acewar tsohuwa "Me zai hana akai mu treatment room ɗin mu duba lafiyar jikin shi"? cike da tuhuma angel ta kuma yi mata tambayar, "Ba'a bada iznin zuwa inda danish yake ba, saboda ciwon nashi baya son hayaniya" "Idan muka je ba zamu yi surutu ba, kawai muna so mu ganshi ne" angel ta kuma tambayarta, Hannah tace"pls tsohuwa kibari muje mu duba shi, we really missed our brother" Girgixa kai ta kuma yi"dare yayi yanzu zuwa gobe zai dawo" "A yanzu muke son ganin shi, kibar mu muje mana ko akwai wani dalili dayasa baki so muje ne" "Ke da baki jituwa da shi, meyasa kika damu dashi ne"? Tsohuwace ta jefa mata tambayar, fuskarta ɗauke da wani shu'umin murmushi, Tur6une fuska angel tayi tare da haɗe rai tace"wannan bai shafe ki ba, wai taya ma akai kikasan cewa bana jituwa da danish? Bayan wannan taya akai kikasan Halin da danish yake ciki, ta wace ƙopa kike bi ki fita daga Cikin ɗakin nan ne? Don ni bana ganin gifcinki, bansani ba ko bangon ɗakinki, kike ratsawa ki wuce, ko kuma layar zane kike yi ki 6ace, Matashin murmushi tsohuwa ta saki, Yayin da idonta ke akan angel tace"duk yadda kika ɗauka haka ne," ta6e baki angel ta yi, su haris duk suna sauraronsu batare da wani ya sanya baki ba, "Danish zai dawo zuwa gobe, iya amsar da zan iya baku kenan, kowa yaje ya kwanta" tana kar ƙarshen maganarta, ta juya tana dogara sanda ta shige ɗakinta tare da jan ƙopa ta datse, "Wannan munafukin ɗakin ko menene acikinsa, wata rana saina san yadda nayi na kutsa kai cikinsa," angel ce ta yi maganar acikin zuciyarta, kafin ta kalli su hanna tace"har yanzu kun yadda da matar nan"? Jinjina kai su kayi alamar eh, harish yace"Tsohuwa bazata ta6a yi mana ƙarya ba, danish yana kar6ar treatment ne, Idan ma akwai wanda ya kamata mu ga laifin shi to ke ce Angel, jiya kamar xaki kashe shi duk Kika yakushe wuyan shi hada cizo saboda tsanar da ki ka yi ma shi" rai a6ace haris ya yi maganar tare da jefa mata harara, Ya yi tunanin zata mayar mashi da martani, amma sai yaga tana nannaɗe hannun rigarta, tuni yasha jinin jikin shi "Wlh duk wanda ya kuskura ya ƙara ɗauramun alhakin ciwon danish, Sai na yi mashi jahilin Bugun da zai gaza ta shi" A harzuƙe ta yi maganar, nan da nan kowa yasha jinin jikin shi, Murya na kerma azeeza tace"dan Allah kowa ya yi haƙuri, nidai bana son tashin hankali, tun da tsohuwa tace mana gobe zai dawo to mu haƙura muje mu kwanta mana" Sai da batool ta lalla6a kowannan su kafin ta samu, Suka nufi gadajensu kowa ya haye sama ya kwanta Ya rage saura angel kaɗai a tsaye tana binsu da kallo, Yayin da tunaninta gaba ɗaya yana akan Danish, Gyaɗa kai tayi tare da juyawa ta koma saman gadonta, har dare ya tsala bata runtsa ba, Allah na gani ta damu da rashin danish acikin su, tana ji aranta kamar wani abun ne zai faru da shi, ko a wani hali yake a yanzu oho Allah wa'alamu, Lokacin da kowannan su ya yi bacci, tana cikin saƙe saƙe acikin zuciyarta, tajiyo motsin mutun, da sauri ta ƙyalla idonta don taga wanene Wannan mutumin ne me jajayen kaya har ƙasa, hannun shi ruƙe da kaskon turaren wuta, sai yawo yake yi acikin ɗakin su, yana tafiya yana karanto wasu ɗalasimai, hannun shi ɗaya ruƙe da kaskon turaren wutar ɗayan hannun kuma yana amfani da shi wurin kora hayaƙin zuwa kowani sashe na cikin ɗakin, Mamaki ne ƙarara akan fuskar angel ga tsoro tana ji, da sauri ta ƙudundune cikin bargonta, ta sanya tafin hannayenta ta toshe hancinta da bakinta kamar yadda ta yi jiya. Aranta tace"Yau ma ya dawo kenan" Ya jima acikin ɗakin nasu yana turara masu hayaƙin, kafin taji tsit alamar ya tafi, da sauri ta yaye bargon tana faman sauke ajiyar zuciya, Saukowa ta yi daga saman gadon jikinta na kerma, hasken fitilun nan guda uku ne ya ɗan haskaka Cikin ɗakin, fitila ta ruƙo a hannunta tana haska wurin gadajensu, Kamar yadda tabi kowanansu jiya har gadon shi ta tottofe shi da addu'a, haka yau ma tabi gadajen su ta yi masu addu'o'i, A daidai bakin gadon danish ta tsaya tana kallon shimfiɗarshi, bakomai ya faɗo mata aranta ba face jiya da tazo yi ma shi addu'a, ya damƙo hannunta yayi tunanin wani mugun abunne take yi mashi, ɗan abunda ya faru jiya atsakaninsu ya tsaya mata arai, matsawa tayi zuwa gefen gadon ta tsugunna tare da leƙa ƙarƙashin gadon tana haskawa da fitila, ganin babu wuƙar anan, yasa tayi tunanin ɗaga katifarshi, koda ta ɗaga ƙarƙashin Katifar bata samu wuƙar anan ba, ba ƙaramin takaici taji ba, taso ace Ta gano inda wuƙar take kota samu ta lalata glass ɗin dake ajikin windon toilet ɗinsu, Allah kaɗai yasan inda ya jefa wuƙar, wata'ƙil ma, ya maida ma tsohowa ita, guntun tsoki taja, yanzu shikenan narasa damar da nake ita? Babu wani makami da zan iya yin amfani dashi wurin rotsa gilashin, kodai naje toilet ɗin In ƙara dubawa? tana yin wannan tunanin ta miƙe da sauri ta nufi Cikin toilet ɗin, Ta tura ƙopar ta shiga daga Ciki, tana haska ko'ina da fitilar hannunta, Abu biyu ne Yazo mata aranta, na farko Bokitin da ke acikin toilet ɗinsu Na ƙarfe ne, Na biyu kuma wannan tukunyar fulawar dake ajiye Jikin bango, waswasi ta shiga yi kodai tayi amfani da bokitin? ƙwara shi akan tukunyar fulawar, saboda Zata Iya rugujewa azo kuma buƙata bata biya ba, Anyi asara kenan, Bata kaiga yanke shawarar dame zata yi amfani ba, ba zato ba tsammani Taji saukar hannun Mutun saman kafadarta, awani irin Firgice tayi kwakkwaran juyi Ta daddage ta ɗaga fitilar hannunta zata kwaɗawa mutun daya dafa kafaɗarta, wani irin ihu batool tasaki a tsorace take faɗin"wayyo! Ke ni ce fa, batool ce,' Nauyayoyar ajiyar zuciya angel ta sauke, Tare da janye fitilar, ta daidai ta natsuwarta, ba ƙaramin dariya batool ta bata ba, ganin yadda ta gigice, "Allah ya taimake yau, da kin kwanta jinya," Dariya batool tayi"Kin ban tsoro me kike yi acikin toilet ne"? "Ke zan tambaya, dama baki yi bacci ba,? Taya akai kika faɗo mun Cikin toilet batare da neman izni ba, yanzu da ace wani uzirin nake yi fa? Hannu batool ta sanya tana sosa kai, tace"raina ya bani cewa ba abunda kike yi ne, shiyasa na shigo Ciki, Kuma na ganki Ɗazu zuƙunne agaban gadon Danish bansan me kikeyi ba, Amma ina hasashen wuƙar shi kika je nema halan" Yatsina fuska angel tayi"I don't know why kin sa mun ido, " ta yi maganar da zolaya, Batool tace"saboda na damu dake" Ruƙo hannunta angel tayi tare da janta suka fito daga Cikin toilet ɗin, a bakin ƙopar fita daga area ɗin suka ɗan tsaya suna magana, "Na duba ko'ina batool banga wuƙar ba, kodai ya maida ma tsohuwa ne?" Girgiza kai batool ta yi "I don't think so, nafi tunanin yayi mata wani mugun 6oyan ne, shiyasa na baki shawarar ki shirya dashi, Ku samu kusanci sosai, ta hakanne zaki samu damar sanin inda ya ajiye wuƙar,' Tur6une fuska angel tayi"Anya zan samu yardar danish, Kin fa ce yana da wuyar yarda da mutane, balle ni kuma daya ɗaurawa karan tsana," "Ki jaraba ke dai, Danish yana da sauƙin kai sosai, ya danganta da yarda kika tafiyar dashi, amma wani hanzari ba gudu ba, har yau baki faɗa mini me zaki yi da wuƙar Ba!? I ave to know,' Ta tsareta da ido tana jiran jin amsar da zata bata, ƴan kame kame angel ta shiga yi don batasan batool ta gane ainihin abunda zata aikata, tasan bazata bari ba, zata yi kokarin dakatar da ita ne Ganin tana ƙoƙarin ƙara tambayarta yasa tayin saurin katse mata hanzarinta da cewa "Ko kinsan akwai wani mutumi da ke zuwa ɗakin mu tsakar dare yana yawo da kaskon turaren wuta a hannunshi? Tayi maganar a kokarin ta nata gusar mata da zancen wuƙa, "Yaushe kika ganshi"? Angel tace"ko yau yazo, jiya ma na ganshi, idan yazo Sai yaita yin magana cikin wani irin yare mara daɗin ji, sannan yana bin kowani gado yana kora hayaƙin zuwa kowani sashe na ɗakin mu," Maimakon taga mamaki akan fuskar Batool, sai taga ta saki murmushi tare da cewa" kada ki damu kanki angel, tsohuwace ae kullum idan dare ya tsala sai ta shigo ɗakin mu, ta turara mana hayaƙin Kariya," Maimaitawa angel tayi'hayaƙin kariya kuma? Jinjina kai batool tayi eh, mun ta6a tambayarta hayaƙin menene tace mana hayaƙin kariya ne daga sharrin baƙaƙen aljanu domin kuwa akwai su acikin kurkukun nan, kuma hayaƙin yana da waraka acikin shi, shiyasa zaki ga ko ciwo bamu cika yi ba" Angel tace"Ni a iya sani na, idan har za'a ba mutun kariya ba hayaƙi yakamata ayi mashi ba, addu'a ya kamata ayi ma shi, sam ni ban yarda cewa hayaƙin kariya bane, dole akwai wani 6oyayyan sirrin a tattare da shi," Kafin batool ta kuma cewa wani abu, suka jiyo sautin shessheƙar kuka daga can cikin ɗakin su, "Wanene ke kuka"? Angel ce tayi tambayar tana kallon batool, Batool tace "Muje mu duba, ina tunanin Aziza ce, " da sauri suka fito daga area ɗin toilet, suka faɗo cikin ɗakin, haskata Angel ta yi da fitilar hannunta, a tsaye suka ganta tsakiyar ɗakin sai kuka take yi tana laluban hanya saboda lalurar da take fama da ita, ta makantar dare (nyctalopia) bata iya gani idan dare yayi, ko kuma idan babu wadataccen haske, haka suke fama da ita, in ta farka zata shiga Cikin toilet, sai ta dinga kuka tana ambaton sunayensu har sai wani ya farka acikinsu ya rakata, Tun lokacin da angel tayi noticing lalurar yarinyar, sai da tayi ma batool magana ta tambayeta tun yaushe take fama da ita? Batool ta bata amsa da cewa"tsohuwa tace haka aka halicce ta, da zarar dare yayi ganin ta ya ke ɗauke wa, koda an kunna hasken fitila biji biji take gani" tun daga wannan lokacin angel take jin tsananin tausayinta, tana matuƙar jin yarinyar acikin zuciyarta, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Ƙarasawa suka yi inda aziza taka a tsaye Angel ta ruƙo hannunta, "Its ok stop crying muna atare dake, Ina zaki je ne"? Cikin shessheƙar kuka tace"Fitsari nake ji ya matse ni," Bari naje na rakata, takai ƙarshen maganar tare da ruƙo hannun azeeza, suka nufi toilet, gefen gado batool ta koma ta zauna tana jiran fitowarsu, badajimawa ba Angel ta fito hannunta ruƙe dana azeeza, har saman gadonta takaita sai da taga ta kwanta, ta janyo mata duvet ɗinta ta lullu6a mata shi saman jikinta, tana jiyo muryar azeeza ta cikin bargon tana faɗin"I luv u so much angel," murmushi angel ta saki tare da cewa"Luv u too my sister, Allah ya kare mun ke, ki amsa da ameen" tana jiyo muryarta tana faɗin"Amen" ba ƙaramin daɗi taji ba, wuce wa tayi zuwa nata gadon ta haye ta zauna tare da jingina bayanta, "Ba zaki kwanta ki yi bacci ba"? Batool ce ta yi mata tambayar, "Zan kwanta, Ina yin addu'a ne ko baki gani ba" kallonta batool tayi ganin ta ɗaga hannayenta biyu sama tana magana cikin harshen da bata sani ba, da larabci take yin addu'ar, "Nima kiyi mun addu'ar, inaso," Angel tace"Toh, ki kwanta kiyi bacci, zanyi maki addu'a," amsa mata tayi da toh , kafin ta kwanta, Bayan angel ta kammala yin addu'ar ta ta sauko daga saman gadonta, tabi kowani gado ta tottofe su da addu'a, bayan ta kammala ta koma saman nata bed ɗin ta kwanta, Daƙyar ta samu bacci ya yi awon gaba da ita, har mafarkin danish sai da ta yi saboda ta sanya wa ranta shi sosai, Slowly ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta, dishi dishi ta dinga ganin mutane kewaye da gadonta, sanya cikin baƙaƙen kaya hannunsu zaƙo zaƙo da dogayen akaifu, Kowanne ya ɗaga gudumar dake hannunshi da niyar rotsa mata kanta, A gigice angel ta zabura tana faɗin"Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un" sautin dariya taji ta ko'ina acikin kunnanta, hannu tasa ta murza idanuwanta, tare da ware su akan mutanan da take gani, Su batool ne a jere, Sun nannaɗe hannayen rigunansu, Sai faman haki suke yi suna nishi kamar waɗanda suka sha gudu "angel tun ɗazu muke jira ki bamu wani training ɗin, duk mun iya wanda kika koya mana" rubina ce tayi maganar, Nauyayyiyar ajiyar Zuciya angel ta sauke, Ashe idanuwanta badai dai suke nuna mata ba, tayi tunanin wasu shaiɗanun aljanune suka kawo mata ziyara, "Ki tashi Muje mu motsa jikin mu atare" Acewar batool, Muryarta a disashe tace"Kun takuramun, ba haka ake ta shin mutun daga bacci ba, duk kun tsoratar dani" taƙarasa maganar tana jifarsu da harara hada murguɗa masu baki, gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Muryar javed taji yana faɗin"Zata taso ko sai munzo mun cuccu6eta"? ya yi maganar yana naɗe hannun rigarshi, ɗaya bayan ɗaya take kallon fuskokinsu, zufa sai tsastsafowa take yi daga jikin su, Ba ƙaramin burgeta su kayi ba, fuskarta ɗauke da murmushi tace"me yayi zafi javed, yanzu zan taso amma fa saina fara shiga toilet, " Har suna haɗa baki wurin cewa"To kiyi sauri ki fito, muna jiran ki," ƙarasa janye bargon Jikinta tayi tare da saukowa daga saman gadon, Suka matsa mata hanya tabi ta wuce, Walking slowly ta nufi ƙopar shiga makewayinsu, Harta ruƙe handle ɗin ƙopar da niyar ta buɗe sai kuma ta ɗan dakata tare da juyawa tana kallon Haris dake kwance daman gadonshi, idanuwanshi na fuskantar ceilling, da alamun damu atattare dashi, tasan bakomai ya jawo hakan ba, face rashin ɗan uwanshi danish don ta lura ba ƙaramin ƙaunarsa yake yi ba, Yau ce rana ta farka da tafara Jin tausayin haris, duk yabi ya ƙuntata kan shi saboda rashin danish, Allah sarki danish kowa Jikin nashi yake"? Janye idanuwanta tayi daga kan haris ta mayar dasu kansu Parveen dake a tsastsaye, Tace"Har yanzu ba wani labari game da dawowar danish"? Jinjina kai su kayi"eh, mu ma munyi expecting ɗin idan muka farka daga bacci zamu same shi kwance a cikin mu, ashe ba'a dawo mana da shi ba" In brittle voice Azeeza tace"nadamu da rashin ɗan uwanmu, Jiya har mafarkin danish nayi, Allah yasa su dawo mana da shi, idan ba haka ba ni ko abinci bazan Iya ci ba" muryarta tamkar zata fashe da kuka, Mubeen yace"nikaina daurewa kawai nake yi amma gaba ɗaya zuciyata a raunace take da rashin danish" yana rufe baki, Naufal yace"idan har jikin danish baiyi sauƙi ba, Zaiyi wuya su dawo mana da shi yau" zuciyarshi a karaye yae maganar, "Ni abunda nake jima tsoro ma, kada a ƙi dawo mana dashi, kamar yarda ake yi mana a lokacin baya" Da sauri angel ta kalli fuskar batool da ta yi maganar, a yanayi na jin farga ba, tunawa tayi da tattaunawarsu da ita jiya a cikin toilet area, Inda batool take faɗa mata cewa"A lokacin baya duk wanda aka ɗauko acikinsu ba'a dawo dashi, He has gone forever," da sauri ta shiga girgiza kai tana faɗin"that's impossible, danish must be back, ku kwantar da hankalinku, babu abunda zai same shi, bana so inji kuna xancen cewa ba lallai danish ya dawo cikin mu ba, ' a harzuƙe takai ƙarshen maganar tare da buɗe ƙopar ta shige ciki, Koda ta shiga cikin toilet ɗin a jikin bango ta jingina bayanta, Idonta akan windown nan data kwallafawa ran son fasa ta, "Da ace xan iya samun damar rotsa gilashin nan, dana yi ƙoƙarin binciko inda treatment room ɗin nan yake, kodan saboda inga danish, bawan Allah, ni tsorona ma kada ya rasa ranshi batare da ya kar6i kalmatusshahada ba, banaso ɗaya daga cikin su ya rasa ranshi batare da na musuluntar da shi ba, idan har hakan ta faru i won't forgive my self, tabbas zanyi asarar jinkirin da nayi,' cikin shessheƙar ku ka tayi maganar tuni hawaye sun soma sintiri akan fuskarta, ta ɗauki tsawn lokaci a tsaye batare da ta ta6uka komai ba, Har sai da tajiyo muryar Batul daga waje tana kwala mata kira"Angel! Angel! Kixo mu yi breakfast giants sun zo, ke kaɗai muke jira" Daƙyar ta iya ɗaga murya tace"Kada ku jira ni, ku fara kawai," Takai ƙarshen maganar tare da sanya hannayenta biyu Ta tu6e kayan jikinta asaman igiya ta ɗaura su, wanka ta samu tayi bayan takammmala ta mayar da kayan Jikinta, Lokacin da ta fito daga Cikin toilet ɗin, A zazzaune ta same su saman red Carpet, a tsakiyarsu wooden trays ne na kayan abincinsu, kowa ya hallara banda mutun biyu ita da kuma Haris dake kwance yana kallon ceilling, yadda tabarshi haka ta same shi, Ba irin lallashin da batool ba tayi mashi ba akan ya taso yaci abinci amma ya kafe akan sai an dawo mashi da ɗan uwanshi, a dole suka ƙyale shi, A hankali angel ta ɗaura idanuwanta akan su giants dake a tsaye kamar gumaka sun goya hannayensu saman ƙirjinsu, Maimakon taje ta zauna taci abincin, sai gani su kayi ta nufi Inda su giants suke a tsaye, A ruɗe batool ta shiga kiran sunanta tana faɗin"Angel where are u goinig? Ki zo muyi breakfast" ko kallon inda batool take ba tayi ba, Tana ƙarasawa gaban giants, taci burki ta tsaya tana ƙare masu kallo, ga tsoronsu tana ji haka nan ta daure ta cije, ganin kanta take yi wata ƴar ƙaramar halitta agabansu, saboda a Halittar jikinsu, Gabza gabza ne ga ƙirar jiki mai matuƙar razanarwa, "Pls angel kada kija mana muna zaman lpy, ki dawo ki zauna acikin mu muci abinci" hanna ce tayi maganar, Yasmin ma tace"Angel, giants basa ji basa gani, Kada ki ce zaki tanka masu, suna iya yi maki illa" Kowa yasha Jinin Jikin shi, duk tana sauraron magiyar da suke Yi mata, amma taƙi koda juyawa ta kalle su, hatta haris dake acan kwance saman gadonshi, Ganin angel agaban giants Yasa shi yin zumbur ya miƙe zaune yana kallon Ikon Allah, Azeeza har ta fara kuka saboda tsabar tsoron kada su cutar da angel, Sai da angel ta gama kalle su daga ƙasa har sama, Kafin tace"Ko dabba idan a ka yi mata magana tana responding ballanta kuma ku da kuke Jinsin bil'adama, Meyasa a koda yaushe Kuke yin 6adda kama idan zaku zo wurin mu? Why? u can't even talk to us? Saboda rashin gaskiya wato kuna tsoron muga fuskokin ku saboda gudun kada mu tona maku asiri nan gaba idan Allah ya ku6utar damu ko? Tayi tambayar cike da tuhuma tana kallon su, Ko motsi wannan ba suyi ba, Balle ma ta gane cewa suna sauraronta, "Ko gunki bazai nuna maku yadda ake tsayuwa ba, agoya hannu saman ƙirji, ku dai ga ku nan wasu hamagawa da ku, to kodai ba mutane bane ku? Nafi zargin cewa ku ɗin Robot ne, wato sarrafa ku akeyi daga Can sama, ta yadda baku iya furta komai sai an baku izni koba haka ba"? Tayi tambayar a harzuƙe tana kallonsu, Su batool sai faman lalla6a angel suke yi akan ta daina yi masu magana tazo suci abinci, amma ƴar tahalikar nan ko kallon inda su ke ba ta yi ba, sai ma cewa tayi"Su rabu da ita, Suci abincin su, Yau sai taga abunda ya turewa buzu naɗi, a tsakanin da giants dole suyi mata magana, Atsiwace tace"Ba zakuyi mun magana ba? wlh duk ranar da wani ya kuskura acikin ku, Ya furta koda kalmar A ce, zan gano ko wanene shi koda bansan shi ba, idan har naji muryarshi awani wuri zan shaida shi ne, saboda Allah yayi mun baiwar tantance muryar mutane," A zafafe takai karshen maganar, ga yunwa tana ji amma taƙi zuwa taje taci abinci, Ruƙe qugu tayi"meyasa baku dawo mana da danish ɗin mu ba? ina kuka kai mana ɗan uwan mu? Tsohuwa tace kune kuka zo kuka ɗauke shi"? Tayi maganar tana faman haɗiyar yawu, Aiki fa ya ga angel , ita kaɗai sai sambatu take yi kamar wata zautacciya, Ganin taƙi zuwa taci abinci Yasa batool taje ƙarƙashin gadonta, ta ɗauko kwandonta, ta kwashe ragowar sauran abincin da suka Ci, da niyar ta ajiye ma angel da haris, "Giants we are done," Javed ne ya sanar dasu, yayi hakan ne don su samu su tafi, kafin angel takaiga ƙure su, don in suka fusata, komai zasu iya aikatawa, Ta gefen angel suka bi suka wuce, Tattara kayan Abincin su kayi a jera suka nufi benan, Ganin zasu tafi basu bata amsar tambayarta ba, yasa ta watsa da gudu ta riga su hayewa saman benen, a jikin ƙofar ta jingina bayanta tare da ware hannyenta, wato ta toshe masu hanyar sa zasu bi su fuce, Tsayawa su ka yi a tsaye saman matattakalar benan, tunda suke aiki a prison ɗin, basu ta6a ganin hatsabibiyar yarinya irin wannan da take agabansu ba, da ace tasan irin hatsarin dake gare su da bata yi gigin shiga huruminsu ba, Kallon kallon aka soma Yi atsakaninta angel dasu giants, Hankalin su Batool yayi matuƙar tashi, duk suna a tsaye bakin benan sai roƙon angel su ke yi akan ta matsa ta basu hanya su wuce, ba iri magiyar da basuyi mata ba, amma angel ta maƙe kafaɗa akan bazata matsa ta basu hanya ba, Ita so take taga ikon Allah Shin giants zasu Yi mata magana akan ta basu hanya su wuce ko kuwa"? Cikin muryar fushi haris Yace"wai ke baki da hankali ne? Ba zaki matsa ki basu wuri su wuce ba? an faɗa maki basa magana, idan ma abunda kike ma hari kenan," rai a6ace tace"babu ruwan kowa dani, ku kama harkar gaban......." bata kai ƙarshen maganar ba, Taga ɗaya daga Cikin giants ɗin ya miƙa ma na gefenshi Kayan abincin dake a hannunshi, Ya kar6a ya haɗa dana hannunshi, Zuba ido tayi tana jira taga me zasu Yi mata, wani irin zazzafan taku giant ɗin yayi yadda kasan Zaki Ya nufi abun harinsa, tuni jikin angel ya soma kerma, ta ƙanƙame jikinta tana girgiza mashi kai, muryarta na kerme ta shiga faɗin"wlh kada ka kuskura ka ta6a....."bata kai ƙarshen maganar ba, Taji ya damƙi qugunta ya ɗaga ta sama, yadda kasan ƴar tsana, ta dinga ihu tana kuka tamkar ranta zai fita, saukowa da iya yayi daga saman benan, Su batool duk sunyi tsuru tsuru suna kallon shi, Daga inda yake yayi wurgi da angel Wani iko na Allah, Saboda tsabar iya saitinsu, bata faɗa ko'ina ba sai saman gadonta, gaba ɗaya ta kife sumar kanta duk ta tarwatse saman mattress ɗin, Juyawa Giant ɗin Yayi ya koma inda sauran ƴan uwan nashi suke, buɗe ƙopar su kayi suka fuce tare da datseta, Kusan atare su Azeeza suka sauke ajiyar zuciya, jiki na rawa suka nufi angel, wadda tunda giant ya wurgar da ita saman gado bata ƙara motsi ba, Jikinta gaba ɗaya ya mutu, tamkar wadda aka zarewa laka, Ta furgita sosai lokacin Daya jefar da ita, har wasu baƙaƙem turari masu wutsiya ta dinga gani acikin idanuwanta, Hayewa saman gadonta, Batool hanna da azeeza sukayi, Sai kokari suke yi wurin ɗago da ita, Su javed mubeen da Su Deeja duk suna a kewaye da gadon, "Angel,angel.pls wake up! dan Allah ki tashi angel, Muna atare dake Kinji? Suna magana suna jijiga jikinta, Haris yace"laifinta ne, tun farko saida muka gargaɗeta amma saboda taurin kai irin nata taƙijin maganarmu, yanzu wa gari ya waya " yayi maganar Cikin halin ko'in kula, Eve tace"bari naje na fada ma tsohuwa, azo a duba lafiyar jikinta" da hanzari ta juya ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa, Kafin ta kwankwasa ƙopar ɗakin sai ga tsohuwa ta buɗe ta fito hannunta ruƙe da sanda, "Meke faru wa ne yara"? Her voice was shaking tace"an...gel...ce .....bata motsi...' "Keep calm and tell me what's wrong, with her? is she not feeling well? Jinjina kai Eve tayi"Giant ne ya wurgar da ita, Tun ɗazu muke akanta, bata farka ba, ko motsi ba ta yi" Gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kan tsohuwa suna jira suji amsar da zata basu, Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tare da cewa"Yarinyar ce taci ka kafiya, sam bata jin magana, shiyasa bana so kuna yin koyi da ita, domin kuwa zata 6ata maku tarbiya ne, tun tana yarinya ba ƙaramar hatsabibiya bace......." gaba ɗaya tsohuwa ta takwashe tarihin rayuwar angel ta sanar dasu, hatta bugun da tasa ƴan ƙato da gora su kayi ma Mahaifinta, kuma a ƙarshe tace masu itace silar da mahaifinta ya rasa ranshi,' da alama tsohuwa tana ƙoƙarin dasa masu kiyayyar angel acikin zuciyoyinsu ne, gaba ɗaya sun saki baki galala suna kallonta, Batool ce tayi kokarin cewa"Amma angel ta faɗa mun cewa daddynta wasu ne suka kashe shi, kuma shine ya jefa ta Cikin ruwa, " bazawarin murmushi tsohuwa tasaki tare da girgiza kai tace"Ƙarya take yi maku, muguwar makirace, Ta faɗa maku hakanne don ku tausaya mata ba" Aruɗe azeeza tace"amma angel bazata ta6a yi mana ƙarya ba, saboda tana son mu dagaske, Kuma idan bazan manta ba, lokacin da aka kawo ta kurkukun nan, kefa da kanki kika ce zaki faɗa mata waɗanda suka kashe mahaifinta, meyasa yanzu kuma zaki ce mana itace tayi silar mutuwar shi!"? Cike da tuhuma azeeza ta jefa mata tambayar, sam tsohuwa batayi tsammani wani daga Cikinsu zai iya yi mata gaddama ba, tabbas an fara samun matsala, "Kinyi shiru baki bamu amsa ba tsohuwa? Kodai azeeza tayi gaskiya ne? Lamarin yayi matuƙar ɗaurewa tsohuwa kai, Javed yace"Nima idan zan Iya tunawa keda kanki tsohuwa kika ce Iyayenta sun rasu, hakan na nufin ita kanta angel ɗin batasan cewa iyayen nata sun rasu ba, sai a bakin ki taji hakan, But why kike kokarin ɗaura mata laifin kashe Daddynta? anya kuwa tsohuwa?ya kai ƙarshen maganar da alamun kokwanto, Haris dai ya rasa bakin magana ba, hatta sauran duk sun natsu suna jiran amsar da tsohuwa zata basu, Rai amatuƙar 6ace, tsohuwa ta buga sandar hannunta kasa, Nan take kowannan su ya toshe kunnuwanshi, sakamakon sautin buga sandar daya doki dodon kunnuwansu, Da kakkausar murya tace"Zan sake maimaita maku, Kudaina yarda da maganarta, Ni kaɗai ce na isa da ku, Babu wani mahaluƙin daya isa ya sarrafa tunaninku, Ina fata an fahimce ni" Da sauri suka amsa mata da toh, Cigaba da magana tayi"Angel ba sonku take yi ba, sam bata ƙaunarku, tana so ta shiga tsakanina daku ne, Ni kuma bazan bari hakan ta faru ba, saboda bana so ta gur6ata ku kamar yadda take gur6atacciya" A ladabce suke amsa mata da toh, deeja tace"Amma idan muka ce zamu ƙi bin Umarninta, Zata karanta mana charman dudu ne Cikinmu ya kumbura, shiyasa muke jin shakkarta", Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta saki aranta tace"Yarinya sai ɗan banzan wayau uwa dila agari" a fili kuma tace masu"Charman dudu ba wani mummunan abu ne, Angel tayi maku wayau ne don ta tsoratar daku, Saboda ta lura bakusan ainihin ma'anar kalmar ba" cike da mamaki suke kallon Juna, Jin abunda tace, Batool tace"zamu iya sanin ma'anar Kalmar"? Jinjina kai tsohuwa tayi, Cikun hikma ta fayyace masu komai game da asalin kalmar charman dudu, har waƙar ta raira masu, ' ransu ya 6aci sosai, irin yadda angel ta azabtar dasu da kalmar ashe ma waƙa ce ba abun cutarwa ba, sunji haushi sunji takaici, musaman haris da Deeja, "Daga yanzu, Ku daina yarda da duk wani abu da zata faɗa maku, saboda wayau ne da ita, so take ta burkita maku lissafi" acewar tsohuwa, Parveen tace"Amma tsohuwa menene ma'anar Sunan Allah dakuma Bil'adama? Angel tace mana Allah shine Ya halicce mu dagaske ne"? Har saida tsohuwa ta zabura jin tambayar da parveen tayi mata, Lokaci ɗaya kuma ta murtuƙa fuskarta tare da cewa"Shima duk ƙarya take Yi maku, babu wani Allah, idan harta ƙara matsa maku akan Ku yarda cewa akwai Allah, Ku sanar da ita cewa Ta kira maku shi ku ganshi da idonku, Kafin Ku yarda dashi anan zaku tabbatar da cewa ita ɗin babbar maƙaryaciya ce," takai ƙarshen maganar fuskarta ɗauke da wani irin munafukin shu'umin murmushi, irin na tantiran ƴan duniyar nan waɗanda suka ga jiya suka ga yau, Aka ce rashin sani yafi dare duhu, gaba ɗaya sunyi amanna da maganar tsohuwa, Ganin taci galaba akansu yasa ta Juya tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, Tare da jan ƙopa ta datse, Abunda ya faru tun lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, gaba ɗaya Tunaninsu ya canza, daga gardamar da suke yi mata zuwa bin umarninta, yanzu gaba ɗaya sun ɗauki maganarta, aransu duk sunji sun tsani angel saboda ta kashe mahaifinta, tsoronta ma suke Ji yanzu kada suma ta kashe su, ga haushin ƙaryar da tayi masu na Kalmar Charman dudu da take yi masu barazana da ita, jira suke tafarka suci ubanta, Bayan wannan kuma tayi masu ƙaryar cewa akwai wanda ya halicce su, lallai angel tana a tsaka mai wuya fidda ta sai ALLAH, Ta yi matuƙar karya masu zuciya, Jikin su duk yayi lakwas tamkar an zare masu laka, tafiya suke yi kamar mashayan giya, Idon kowa na akan gadon angel dake kwance magashiyan rai hannun Allah, Ji suke kamar su rufe ta da bugu har saita gaza tashi, Komawa su kayi saman gadajensu Zuciyoyinsu sai tafarfasa suke yi saboda tsabar 6acin rai, Kowa ya shiga faɗin Laifin da angel ta aikata mashi da kuma irin fansar da zasu ɗauka akanta idan ta farfaɗo, don sunci alwashin sai sun raunata Sassan Jikinta, Tsawon awanni angel ta ɗauka, Ba ita ta ta shi farkawa ba, Sai Wuraren marece, Da wani irin yunƙurin amai ta farka, da gudun gaske ta duro daga saman gadonta, idanuwansu akanta babu wanda yayi yunkurin zuwa ya taimaka mata, Toilet ta shige a galabaice Ta zuƙunna gaban tap tana kwarara amai, bakomai ke fitowa daga Cikin bakinta ba, face xallar ruwa, Cikinta sai tuƙuƙun azaba yake yi mata, har wani jiri take Gani, Cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan Batool don tazo ta taimaka mata, Batool tana jin muryar angel cikin mawuyacin hali amma zuciyarta ta hanata zuwa inda take, Kowa haushinta yake ji, An canza masu tunaninsu, hatta azeeza da tafin kowa jin tausayi ayau itama ta juya ma angel baya, Koda taji batool bata amsa mata ba, sai ta shiga kiran sunayensu ɗaya bayan ɗaya, suna jinta amma su kayi kunnan uwar shegu da ita, Numfashinta sama sama yake fita da hucin zafi, bugun zuciyarta ya ƙaru sosai, hakanan ta dinga jin kamar wani abu zai faru da ita, dakyar ta samu aman ya dakata da zubowa, ta kunna tap ruwa ya shiga kwararowa, Ta tarba tafin hannayenta, ruwa ya taru acikinsu, ta kuskure bakinta tare da wanke fuskarta, Sam takasa ta6uka komai, saboda tashin zuciyar da take ji, Ga jiri da take gani acikin idanuwanta, temperature ɗin Jikinta yayi zafi sosai da alama zazza6i ne ke shirin yi mata mugun kamu, tana ƙoƙarin miƙewa amma ta kasa cos she's feeling dizzy idan ta yi attempting miƙewa tsaye, Bata fasa neman ɗauki daga wurinsu ba, Taci gaba da ambaton sunayensu"Batool! Azeeza! hibba" muryarta a disashe take maganar daƙyar ma take ƙoƙarin ɗaga muryarta, Jin basu amsa mata ba, yasa ta soma kiran sunayen mazan dake acikinsu "Javed! Mubeen! Naufal!' nan ma taji shiru basu amsa mata ba, lumshe runannun idanuwanta tayi tare da cizon lower lip ɗinta, Daga Can Cikin ɗakin kuwa, Hankalin batool yaƙi kwanciyar, tana so taje ta taimaka mata amma zuciyarta taƙi bata haɗin kai, Idan ma tayi motsi kamar zata sauko daga saman gadonta, sai haris ya dakatar da ita tare da cewa"duk wanda ya kuskura yaje da niyar taimakata, babu ruwan mu da shi," tunzurasu yake yi duk don saboda kada suje su taimaki angel In taƙaice maku zance, A gajarcanshi Har dare yayi babu wanda ya motsa daga Cikin su, Sun bar angel acikin toilet ita kaɗai, tun tana kiran sunayensu har tagaji tadaina, baiwar Allah ta shiga mawuyacin hali, anan cikin cikin toilet ɗin ta kwanta saman floor ɗin, abu uku suka haɗe mata a lokaci ɗaya, Ciwon kai, raɗaɗi da Cikinta ke yi mata da kuma matsiyaciyar yunwar data addabe ta, yinin ranar ko ruwa bata kora ma maƙoshinta ba, ya bushe ƙamas har wani ƙaiƙayin azaba yake yi mata, Kafin su kwanta bacci, sai da suka cinye abincin angel da batool ta ajiye masu ita da haris, Koda su ka kammala cin abincin, Zaman jiran dawowar Danish Suka tsaya yi, har saida tsohuwa ta fito daga Cikin ɗakinta ta same su a zazzaune saman gadajensu, ganin damuwa akan fuskokinsu yasa tace"Akan danish ne"? Har suna haɗa baki wurin amsa mata da eh, Shiru ta ɗanyi tana kallonsu kafin tace"ku ƙara haƙuri, danish bazai samu damar dawowa yau ba, jikin nashi yayi tsauri sakamon Illar da ƴar uwarku angel tayi mashi, akwai wani dafi a hannunta wanda ku baku sani ba, idan har ta yakushi mutun kota gartsa mashi cizo, ya ɗauki tsawon lokaci ba'a bashi emmergency treatment ba, Dafin yana Illata sassan jikin shi ne, kuskuren da mu kayi shi ne, da bamu yi gaggawar miƙa dashi zuwa treatment room ba, lokacim da Angel tayi mashi wannan jahilin bugun, Shiyasa har Dafin yayi mashi illa ajikinshi........." dakatawa ta yi da yin maganar fuskarta duk a harmutse duk don su yarda da abunda take faɗa masu, Cikin jin ƙunar rai haris yace " idan har ɗan uwanmu ya rasa ranshi saboda ita, bazamu ƙyale ta ba, ita ma sai mun kashe ta" yana rufe baki deeja tace"Ae dama ba son shi take yi ba, muguwa kawai, tun da tazo gidan kurkukun nan, ta ɗaura mashi karan tsana ni bansan me danish ya tsare mata ba, " takai kai karshen maganar tana huci, Haris Yace" Yadda tayi ma danish Jahilin bugu, muma sai mun rama mashi, In yaso suyi jinyar atare" Yasmin tace"ƙwarai kuwa, Muje mu same ta har inda take, mu nakaɗa mata bugu har sai ta kasa tashi," Tsohuwa ta fakaici idonsu ta saki wani irin kafin murmushi, hanya mafi sauƙi da zata koya ma angel hankali, saboda rashin kunyar da take yi mata, Cikin sanyin murya batool tace"Bai kamata mu ce zamu bugeta ba, wannan ba dai dai bane, saboda ita ɗin yarinya ce duk mun girmeta, bugu bashi zaisa ta gane kuskurenta ba, idan muka daina shiga sabgarta ma ya wadatar, daga yanzu babu ruwanmu da ita, har sai danish yaji sauƙi ya dawo cikinmu tukunna zamu waiwayeta," Azeeza tace"na goyi bayan shawarar da batool ta bada," suma sauran su ka ce duk sun goyi bayanta, banda haris da deeja, "Tsohuwa yanzu Sai yaushe kenan zamu sake ganin ɗan uwanmi? Idanuwanmu sun yi maraicin rashin ganin shi" javed ne yayi maganar muryarshi a sanyaye, Tsohuwa tace" A yadda mu ka tattauna da giant, Ya sanar dani cewa"Danish zai ɗauki Tsawon kwana Biyar Kafin ya dawo cikin ku," Ransu ya ƙara 6aci jin cewa sai ya ɗauki tsawon kwana biyar kafin ya samu sauƙi, Kamar su ɗaura hannayensu saman kawunansu su fasa ihu, haka suke ji saboda tsabar takaici, tsanar da su kayi ma angel ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarsu, "Kowa ya je ya kwanta, Mu kwana lafiya Yara na" takai ƙarshen maganar tare da juyawa tana dogara sanda Ta nufi ɗakinta, ta shige tare da jan ƙopa ta datse, Kallonsu batool tayi"Mu yi haƙuri muje mu kwanta," gyaɗa kai su kayi kowa Ya wuce zuwa saman gadon shi Ya kwanta, Gaba ɗaya duk tattaunawar da su batool su kayi tare da tsohuwa akan kunnan angel, baiwar Allah da rarrafe ta fito daga Cikin toilet, ɗin abakin ƙopar shiga ɗakinsu, Ta zauna tare da jingina bayanta, saboda takasa ƙarasa tafiya cikin ɗakin, Kaf taji irin ƙalin sharrin da tsohuwa tayi mata, sai yanzu ta gane dalilin dayasa suka juya mata ba, Lokacin ta take ta kiransu acikin toilet don su kawo mata agaji, ashe sun jita suka ƙi zuwa, saboda tuggun da tsohuwa ta ƙulla mata, Jikinta duk yayi sanyi, zuciyarta ta karaya, Don sun ɗauki gaba da ita wannan ba damuwarta bace, ta yi masu uziri saboda jahilcin dake ɗawainiya dasu, ita tausayinsu ma take ji, yadda ake ta juya masu tunaninsu, wanda da ace suna da wayau babu wanda ya isa yayi masu haka, Abu uku ne yafi tsaya mata arai, na farko shine Batool, bata ta6a tsammanin batool zata Juya mata baya ba, Tunanowa tayi da maganarsu ta jiya da kanta take faɗa mata cewa"Koda ace kowa zai juya mata, Ita tana atare da ita, kuma a koda yaushe zata kasance a hannun damanta, amma sai gashi yau ba irin kiran sunan batool da batayi ba aka tazo ta taimake ta amma taƙi zuwa, Abu na Biyu kuwa meyasa tsohuwa take Yi masu ƘARYA? da girmanta tsofe tsofe da ita? ƙaryafa alamace dake nuna cewa mutun baida gaskiya, lallai wannan matar ba ƙaramar makira bace, abu na ƙarshe daya tsaya mata aranta shi ne DANISH! A wani hali yake ciki? Meke faruwa da shi? meyasa baza'a dawo da shi cikinsu ba? Jiyafa tsohuwa da kanta tace masu yau zai dawo, amma kuma yau sai gashi ta canza magana, meyasa❓❓❓ Ta jefa ma kanta tambayar da bata da amsarta, A hankali ta kifa kanta saman gwiwowinta, yalwatacciyar sumar kanta ta yi mata rumfa tamkar hijabi, shessheƙar kuka taci gaba da yi ita kanɗai a cikin toilet area, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, gaba ɗaya ta tsani Gidan Kurkukun ƙaddara, A yanzu bata ƙi ta samu hanyar da zata gudu daga Cikin shi ba koda kuwa ita kaɗai ce, tunda ta lura Yaran da take son taimaka ma rayuwarsu, Zaiyi wuya taci galaba akansu, saboda already an juye masu tunaninsu, Dare yayi sosai, duhu ya mamaye Cikin idanuwanta, ƙasa ƙasa da murya take ambaton sunan daddynta, wata magana ce ta faɗo mata acikin ranta wanda daddynta ne ya ta6a faɗa mata ita _Ki sama ranki cewa ko babu ni zaki iya rayuwa, nasan cewa ƴata jaruma ce, mutane suna yabonki saboda ƙwarin gwiwar dake gare ki, Angel bana so rashina yayi silar canzawarki_ a lokacin da taj yayi mata wannan maganar saita fashe da kuka tana faɗin"Nidai daddy kada kayi mun maganar mutuwa bana so," murmushi taj yayi idanuwanshi cike tab da kwalla yace"daughter mutuwa dole ce, ni dai kawai alƙawarin da nake so kiyi mini, shi ne, ki kasance a yadda kike ko bayan raina, kada ki bari wani abu ya canzaki, kada kiyi tunanin idan kika rasa ni xaki rasa gatanki, Domin kuwa Allah yana atare dake, kuma shine gatan kowani bawa, idan kika shiga hali na ƙunci Allah zaki kaima kukanki, In sha Allah zaki samu mafita_ Sosai angel ta fashe da kuka tunawa da wannan maganar ta mahaifinta, wani irin yanayi ta shiga mara misaltuwa, kusan raba dare Tayi acikin toilet area ɗinsu, batare da ta motsa ba Jikinta duk yayi tsami babu daɗi, ga kaɗaici dake damunta, ga yunwa da ciwon da take fama dashi duk ita kaɗai, Ɗagowa ta yi da fuskarta wadda ta kumbura suntum tayi jawur, Tsinin hancinta yayi Ja, saboda matsar daya sha, Idanuwanta sun kumbura sun ƙanƙance, daƙyar take iya buɗe su, dogayen yatsun Hannayenta sai kerma suke Yi, wani irin matsanancin sanyi ne ya mamaye Jikinta, ta ko'ina babu sauƙi, Daƙyar ta samu ta lalla6a Jikinta, Ta buɗe kofar da rarrafe Ta shiga Cikin ɗakin, tana tafiya tana kallon gadajensu duk sun kwanta sun lullu6e da bargo, hankalinsu kwance sai sharar bacci suke yi, adai dai bakin gadonta, Ta yunƙura ta miƙe ta haye sama ta kwanta, ta janyo bargo ta ƙudundune jikinta, Acikin Ƴan kwanakin Nan angel ta fuskanci Mawuyacin Hali, saboda juya mata bayan da su kayi, Haris Ya samu damar fanshe haushin shi akanta saboda sunga bata da ƙoshin lafiya, wani sabon wulaƙancin, Sai haris yaga tana bacci, Ya je toilet ya Ciko bokiti da ruwa ya sheƙa mata ajikinta, Idan aka kawo masu abinci tana bacci, babu me tashinta daga Bacci, Haɗuwa suke su cinye mata abincinta, Sai da ta jera kwana Uku bata Ci abinci ba, Ta rame ta ƙanjame, Ta zama abun tausayi, ko magana daƙyar take iya furtata, yanzu takai ga ita ke ji shakkarsu, saboda Rashin lafiyar da take ɗawainiya da ita, bata son abunda suke Yi mata, duk Cikinsu mutun uku ne basu ta6a yi mata wulakanci ba, Batool Azeeza da Javed, basu atare da ita amma kuma ko kallon banza bai ta6a haɗa su da ita ba, kawai dai sun janye jikinsu daga nata ne, ita kanta angel ta lura da wani abu agame dasu, Sam wani abun bada son ransu suke yi ba, kamar ana tunzurasu ne, Shiyasa take Yi masu uziri, Duk wani plan ɗinta a yanzu ya tarwatse, Saboda juya mata bayan da su ka yi, Yanzu takaiga Ko sunan Allah da suke fadi sun daina, taya zata fahimtar dasu Cewa Akwai wanda ya halicce su, Bayan Sun ƙureta akan sai ta Kira masu Allah yazo sun ganshi tukunna zasuyi Imani dashi? Wa'iyazubillahi, Tsohuwa ta gama da rayuwar bayin Allahn nan, suna A cikin duhun jahilci, zaiyi wuya ta shawo kansu Cikin sauƙi, Saboda tsanarta da su kayi ayanzu tafi sha'awar zama Cikin toilet, akan ta zauna Cikin ɗakinsu suna yi mata gal6anci da rashin wayau ba, Sun kasa banbance tsakanin gaskiya da ƙarya, Duk da ba laifin su bane, *Boss Bature🌷✍️* Runtse idanuwanta ta ɗanyi tare da buɗe su, ita kaɗai zaune Cikin duhu, Ta gaza runtsawa, Shessheƙar Kukan Azeeza Taji, Tasan bai wuci fitsari take Ji ba, ganin ita kaɗaice idonta biyu Yasa ta sauko daga saman gadon, Ta je inda fitilun ɗakinsu suke tabi kowacce ta kunna ta, kafin ta ɗauko ɗaya tana haska Cikin ɗakin, A tsaye ta hango azeeza ta matse idanuwanta, hawaye sharkaf, ƙarasawa tayi da sauri ta ruƙo hannunta, Ta rakata Cikin Toilet, Tayi fitsarin A bakin fita daga Cikin toilet area ɗinsu, Angel ta tsaya tana haska fuskar azeeza, "Angel" taji ta ambaci sunanta, ba ta yi tsammanin zata Shaida ta ba, "Taya akai kika gane ni ce"? tayi tambayar tana kallonta, "Naji ajikina cewa ke ce, " shiru angel tayi na ɗan wani lokaci suna fuskantar juna kafin tace"Azeeza kema kin tsane ni ko? Baki son ganina ? Shiyasa ko magana ba kuyi mun,' idanuwanta acike tab da kwalla tayi maganar, Girgiza kai azeeza tayi fuskarta da alamun rauni attare da ita tace"ba haka bane angel, dai dai da rana ɗaya ban ta6a jin tsanarki acikin zuciyata ba, kawai ba yadda zamuyi ne, sai kina yi mana uziri, mu kanmu bamu jin daɗin abunda ke faru atsakaninmu, " takai ƙarshen maganarta, tare da rungume angel a jikinta, kusan atare suka fashe da kuka, Cikin shessheƙar kuka azeeza take faɗin"ni nasan cewa angel ba cutar mu kike yi ba, kamar yadda tsohuwa take faɗa mana, ke mai son mu ce, kina ƙaunar mu, kamar yadda kikayi niyar taimakon mu, kada ki fasa angel," Kalaman azeeza ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sosai ta ƙara huggin dinta tightly a jikinta, Suna Cikin wannan yanayin su ka ji sautin shessheƙar kukan mutun, da sauri angel ta saki azeeza, ta wurga idonta kan mutumin dake tsaye abakin ƙopa, Da fitilar hannunta ta yi amfani wurin haska fuskarta, bakowa bace face batool, fuskarta sharkaf da hawaye Allah kaɗai yasan tun lokacin da take atsaye tana sauraronsu, Muryarta adisashe tace "Ki yafe mun angel, nayi kuskuran juya maki baya dana yi, bada son raina hakan ta faru ba, Na zauna nayi tunani duk irin ƙuntata maki da su haris su kayi dai dai da rana ɗaya baki fasa tashi tsakar dare Kinyi mana addu'a ba, saboda ƙaunar mu da kike Yi........" dakatawa tayi da yin maganar tana sauke ajiyar zuciya, kafin taci gaba da cewa"Bana so kiyi kokwanto akaina angel, nasan abunda ya faru cikin ƴan kwanakin nan zaisa Kiji aranki kamar bana ƙaunarki ne, ko kusa angel, har yanzu kina nan yadda kike acikin zuciyata,' Saboda Jin daɗin maganar Batool batasan Lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, Matsawa batool tayi inda suke Ta janyo Angel ajikinta ta rungumeta sosai, Ta mika hannu ta ruƙo azeeza itama ta rungumota, atare suka cigaba da yin kukan, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Muryar Javed su ka ji yo daga bayansu "Nima ina neman yafiyarki angel, duk da bana ɗaya daga cikin masu ƙuntata maki" raba jikinsu su ka yi daga cikin na juna, kowannansu idanuwanshi ya kaɗa yayi ja saboda kukan da suka sha, still hawayen basu daina sintiri saman faces ɗinsu ba, Kallon javed su ka yi dake a tsaye, Shima da alamun nadama atattare da shi, cikin sanyin murya angel tace"basai kun nemi yafiya ta ba, saboda ba laifinku bane, nayi maku uziri tuntuni' Ƙarasa shigowa Cikin toilet area ɗin yayi ya tsaya a kusa da su, sannan yace"Angel, muna so mu tabbatar da gaskiya, a tsakanin ki da tsohuwa, sai dai babu wata ƙwaƙƙwarar hujja da zamu shaida hakan," yakai ƙarshen maganar idon shi akan fuskarta, "Ku bani lokaci, bi'iznillahi Zan kawo maku ƙwaƙƙwarar hujjar da zan wanke kaina, ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA GIDAN KURKUKUN ƘADDARA BA GIDAN MARAYU BANE, SANNAN ZAN TABBATAR MAKU DA CEWA AKWAI ALLAH WANDA YA HALICCE KU, BA DAGA SAMA KUKA FAƊO BA," Baƙaramin daɗin maganarta su ka ji ba, batool ta ruƙo hannayen angel biyu acikin nata, cikin natsuwa ta soma magana"Ina yi maki fatan nasara Angel, muna atare dake," Angel tace"Bana so ku nuna mun shirya agaban tsohuwa, Ku cigaba da pretending cewa Kuna goyan bayanta baku atare dani, ta hakanne zan samu damar bayyanar maku da gaskiya,' Atare suka haɗa baki wurin amsa mata da toh, Kallon azeeza ta yi wadda ke atsaye tana jinsu amma bata iya ganinsu, "Mu koma Ciki mu kwanta, Azeeza ta gaji da tsayuwa" ta ruƙo hannun azeeza, Batool da javed su ka yi gaba a cikin ɗakin suka yi ma juna sallama, Kowa ya wuce gadonshi, sai da tafara kai azeeza saman gadonta ta kwanta ta lullu6eta da bargo, kafin Ta koma nata gadon, daga ƙasa ta ajiye fitilar hannunta, ta haye saman mattress ɗin taja bargo ta lullu6e jikinta zuwa saitin neck ɗinta, kasa runtsawa tayi, ɗan juyawa ta ɗanyi tare dakai idanuwanta saman shimfiɗar Danish, why Har yanzu ba a dawo da shi ba? Allah yasa dai ba jikin nashi bane yayi tsauri sosai ba, duk da babu sabo a tsakanin mu, naji na yi kewarsa sosai, inaso na sake ganin danish, Fatana Allah yasa adawo dashi, kada maganar batool ta tabbata na cewa duk wanda aka ɗauka ba'a dawowa da shi ya tafi kenan har abada! To wai ina ake kai su? Idan suna araye meyasa ba a ta6a dawo da su ba? Ni dai a iya sanina mutuwa ce kaɗai idan akayi ta ba'a dawowa!!!!! Ɗaura hannunta na dama tayi asaman goshin ta zagoyo da shi, idanuwanta na fuskantar ceilling, "Menene ma'anar Gidan Kurkukun ƙaddara? A iya sanina Gidan Kurkuku Yana nufin Gidan Gyara hali, Amma wannan kurkukun meyasa last name ɗinshi Ya ƙare da ƙaddara! Dole ya kasance ɗaya Cikin biyu, Kodai kyakkyawar ƙaddara ko kuma mummuna, ' lumshe idanuwanta ta yi a hankali ta ware su, Zuciyarta Cike fal da tunani, Tun lokacin da daddynta ya gudo da ita daga Gidansu, Take lissafin kwanaki, bata ta6a bari lissafi ya kwace mata ba, ko babu calender tana iya hasashen Yau nawa ga wata, ku ma ta canka dai dai, Tana Cikin Yin tufka da warwara, Tajiyo Takun Tafiyar Mutun, Tunkafin ma takai idonta kan wanda ya shigo ɗakin nasu, Ta yi hasashen tsohuwa ce, daga kwance ta wurga eye balls dinta kan tsohuwa dake shigowa Cikin ɗakin, Sanye cikin shigarta, ta gado jar doguwar riga me hula, hannunta ruƙe da kaskon turaren wuta, zagaye ɗakin ta soma Yi tana kora hayaƙin ta ko'ina, murmushin takaici angel ta saki, yau ta ƙudiri aniyar sai tayi mata magana ga da ga, batare da jin tsoro ba, ta mike tare da saukowa daga saman gadonta, Cikin sanɗa take tafiya har ta ƙaraso bayan tsohuwa ta Cigaba da binta suna tafiya atare, batare da tsohuwa ta ankara ba, kasa kunne angel tayi tana sauraran ɗalasiman da take karantawa, kai daga jin yadda take Karanto su zaka shaida cewa ba abun arziƙi bane, wani mugun abunne take ƙulla masu, "ƴar nan Kina tunanin bansan Kina bin bayana bane"? Tsohuwace tayi maganar, batare da ta juyo ta kalli bayanta, Koda angel taji maganarta, bata ji wani fargaba ba, saima ƙwarin gwiwa da ta samu na cewa" nasan kinsan ina bin bayanki mana, Taya ki aiki nake yi, naga kina ta wahala ke kaɗai, Me zai hana yau Ki bani Kaskon turaren wutar In rage maki aiki"? juyowa tsohuwa tayi suka fuskanci juna ita da angel, Wani irin balagaggen murmushi ne ɗauke akan fuskarta tsohuwa, Ɗaure fuska angel tayi tamau ba fara'a ko misƙala zarratin, "Bibiyata kike Yi kenan? Da alama har yanzu baki daddara ba, Ina mai baki shawarar Ki ajiye makaman yaƙin ki, Ki yi rayuwarki tamkar salihar dabba, ki ajiye wannan Girman kan naki, da taurin kan nan da kafiya, Muyi rayuwa Cikin salama,' takai ƙarshen maganar tana washe wawulan bakinta, Still angel bata tanka mata ba, Jira take ta kammala Suratan nata marasa kan gado, "Ƴata faɗa da aljani ba riba, Ko har yanzu Kina tunanin zaki Ci galaba akaina ne eye? Tsabar takaici Ji take kamar ta shaƙo wuyan matar, mummunar banxa kawai, ta ambaci hakan acikim zuciyarta, a fili kuma tace"tun yaushe kuma? Cin galaba akanki tuni na fara, bari na faɗa maki abunda kike tunanin bansani ba,' ƙura mata kwarkwararrun idanuwanta tsohuwa tayi tana jiran jin me zata ce, "Kafin na faɗa maki irin nasarar dana fara samu akanki, zan fara faɗa maki babban kuskuran da kuka tabka," fuskarta ɗauke da murmushi takai ƙarshen maganar, Tsohuwa dai tayi kasaƙe tana kallonta, A tsanake angel taci gaba da cewa"Kuskuren kuwa shine, ɗauko ni da ku kayi zuwa Cikin gidan Kurkukun nan, ganganci ne mutun ya ɗauko ajalinsa ya raine shi da hannunsa, ada ina tunanin meyasa na kasance acikin gidan kurkukun ƙaddara? Amma yanzu na samu amsar tambayata, inaji araina Ba hakanan Allah ya ƙaddara mun rayuwa acikin gidan kurkukun nan ba, babu shakka Nice zanyi silar tarwatsewar........" bata kai ƙarshen maganar ba, Sakamakon wata ƴar iskar dariya da tsohuwa ta fashe da ita, Ta wage wawake bakinta, Haƙoran nan jawur dasu, kasancewar angel na a kusa da ita, Da sauri ta kawar da kanta gefe Jin ƙarnin Jini na fita daga cikin bakin tsohuwa, lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai zuciyarta ta shiga ruɗani, gaba ɗaya ta rikice tana zare ido, fuskarta ɗauke da tsantsar mamaki da aljabi ta ɗago tana kallon tsohuwa a lokacin ta dakata da yin dariyar, Da shaƙaƙƙiyar Miryarta ta tsoffi tace"Your dream will neva come true angel, Wasiƙar jaki ce kike saƙawa aranki, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, har yanzu akwai sauran kuruciya atattare dake, shiyasa nake yi maki uziri, bakisan komai game da gidan kurkukun ƙaddara ba, ki kalli ginin da kyau, Tsohon ginine wanda tun kafin zuwana duniya aka ƙirƙire shi," Angel fa ta shiga ruɗani, Idanuwanta azazzare take kallon tsohuwa, sama sama take fahimtar zancenta, wata irin narkakkiyar zufa ce ta shiga tsastsafo mata ta ko'ina ajikinta, saman goshinta duk ya jiƙe da zufa, bakomai ya tsara mata arai ba, face wannan ƙarnin Jinin da taji abakin tsohuwa, "Gidan Kurkukun ƙaddara, Baida ƙopa a lokacin da aka Ginasa, Kurman ginine, Ke Ko mutuwa bata isa ta fidda gawar mutun daga Cikinsa ba idan har ya shiga Cikinsa, Duk wanda muka ƙaddara ma rayuwa acikinsa, Anan zai rayu Anan kuma zai mutu, Ƴar nan ta ina kike tunanin zaki iya tarwatsa Gidan kurkukun ƙaddara? Ta yi mata tambayar tana sakin shu'umin murmushi, Tuntsirewa Angel tayi da dariyar yaƙe, tana girgiza kai, hada dafe Ciki, tsohuwa ta zuba mata ido Itama da murmushi akan fuskarta, "Halan wani shaƙiyancin ne zaki yi mun shine kike dariya" ? Tayi tambayar tana kallon angel, Dakatawa tayi da yin dariyar, Tare da sanya hannu tana kore hayaƙin kaskon turaren wutar dake a hannun tsohuwa daya takura mata, Sai da ta daidaita natsuwarta tukunna tace"Ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala, mamallakin Komai da kowa, mahaliccin Maginin gidan kurkukun ƙaddara da kuma tsohuwa ita kanta dake agabana, da iznin shi komai ke wakana, wanda idan yaso a yanzu haka da muke atsaye sai ki fadi ki mace shikenan, An shafe babinki rayuwarki, duk wani ƙarfin iko da kike taƙama dashi kinga ya qare, Zaki je ki fuskanci reality, Allah kenan da shi na dogara, Kuma shi zai bani Ikon tarwatsa ku, wai ke har kina da bakin cewa duk wanda kuka kaddara ma rayuwa acikinsa Bai isa ya fita ba? Anan zaiyi rayuwa anan zai mutu? Ke wacece? Kin manta ta ƙofar da kika bi kika zo duniya? Kin manta yadda aka halicce ki tun daga ɗigon maniya har zuwa gudan jini? Ke kanki fa baiwace ta Allah ƙasƙantacciya butulu, waɗanda ma suka fiki hatsabibanci irinsu fir'auna Yanzu suna Ina? Jin wannan tambayar ta angel yasa Walwalar dake akan fuskar tsohuwa ta gushe zuwa tsananin fushi da 6acin rai, "Dama nasan bazaki bani amsa ba, ƙarya ta ƙare, Idan Allah yaso arana ɗaya dake da kurkukun duka zai shafe babinku, Shi kaɗai yake da iko akan komai, Bansan A ina kika samu kwarin gwiwar Yin magana a gadarance ba, akwai fa ranar da wannan sihirin naki bazai ta6a taimakon ki ba, Zaro ido tsohuwa ta yi tana kallonta, Cike da mamakin Jin ta ambaci cewa tana da sihiri taya akai tasan hakan? Bata kai karshen zancen zucin nata ba Angel tace"Kina mamaki ne? Ta yi tambayar fuskarta ɗauke da murmushi, Kafin taci gaba da cewa"Ɗaya daga Cikin nasarorin da na fara samu kenan, Kina amfani da sihiri wurin sarrafa Tunanin waɗannan bayin Allah, Kun Hana ayi ibada acikin gidan kurkukun ƙaddara saboda Itace Lagwanku, wannan dalilin yasa Duk wani prisoner dake rayuwa acikinsa, kuka hana shi yin addini, Hakan na nufin ku kanku Kuna tsoron Allah saboda kunsan cewa shi kaɗaine zai Iya kawo ƙarshen ku, shiyasa kuke gudun dun wani abu daya shafi addini musulunci, sai dai kunyi abanza, domin kuwa kome kuke Yi Allah yana kallonku, dama ce na ɗan lokaci ƙanƙani, " Ajiyar zuciya ta sauke kafin taci gaba da cewa"Ke kanki kin fara Jin shakkata, dalilin dayasa kuwa nace haka, Saboda kinga addu'ar da nake Yi masu tafara tasiri ajikinsu, Har sun fara gaddama dake, Wannan dalilin ne yasa Kika Koma Yi masu hayaƙin sihiri domin juye tunaninsu, sai dai kash aduk Lokacin da ki ka turara masu hayaƙin sihiri ni kuma ina bin kowani gado In tottofe su da addu'a, wannan yasa kike jin haushina saboda ina ruguza maki shiri, sabo tsabar makirci kikayi ƙokarin cusa masu tsanata acikin zuciyoyinsu, duk don saboda kisa in karaya, shima kinyi abanza," yadda take magana babu tsoro tamkar zata shaƙo wuyan tsohuwa, daurewa kawai take yi tana yin magana da ita, saboda munin fuskar matar, Ƙyamarta take Ji, fuska duk ta lalace ta ta6ar6are, "I ave alot to say, Amma bazan Iya jure Yin magana mai tsayi dake ba, saboda 6ata lokacine yin magana da matacciyar zuciya," fuskar tsohuwa babu annuri take kallon angel, Kaskon turaren wutar dake a hannunta tuni garwashin ya mutu, hayaƙin ya daina wanzuwa Dogon tsoki Angel taja, tare da juyawa zata je ta kwanta, har ta kusa kaiwa bakin gadonta, ta ɗan dakata da yin tafiyar ta waiwayo ta kalli tsohuwa dake a tsaye ƙiƙam uwa saƙago, ta kafe ta da waɗannan kwartayen idanuwan nata, "A'uzubillahi minasshaiɗanirra'jim, Aniyarki ta biki, Kuma ina nan ina zuba ido, Gobe adawo mana da ɗan uwan mu danish, idan ba haka ba komai zan iya aikatawa wlh, zan nuna maki hatsabibanci na, zan addabi rayuwarki, "takai ƙarshen maganar tare da jefa mata harara ta murguɗa mata baki, gyaɗa kai tsohuwa tayi Batare da ta furta wata kalma ba, ta dogara sandarta zuwa kopar ɗakinta, ta buɗe ta shige tare da jan ƙopa, tafiyarta keda wuya angel tabi kowani sashe na ɗakin ta tottofe shi da addu'o'in neman tsari kamar yadda ta saba, ta kuma bi kowani gado tun daga kan gadon su Hanna duk ta wanke su da addu'a, bayan ta kammata ta koma saman gadonta, A tsakiyar gadon ta zauna tare da ɗaga hannayenta tana addu'a, akan Allah yabata Ikon yin nasara akan miyagun mutanan nan, Allah kuma Ya tsare mata daddynta aduk inda yake, idan kuma Ya mutu Allah ya kai rahama ƙabarinshi, Hatta danish sai da ta yi ma shi addu'a, Ta kuma roƙi Allah daya kawo masu ɗaukin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Ta jima tana yin addu'o'i kafin daga ƙarshen ta janyo bargonta, ta lullu6a ma Jikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci Yayi awon gaba da ita, can cikin dare wata irin zufa ta soma wanke fuskarta, wani irin matsanancin zafi ta ko'ina ajikinta, mutsu mutsu ta dinga yi tana matse idanuwanta, yayin da ta dunƙule hannayenta, tamkar ƴar dabbe, duk ta hargitsa shimfiɗarta, da alama mafarki take yi, ciccije la66anta tayi har sai da ta fasa su, ƙasa ƙasa take karanta duk wata addu'a da tazo mata a cikin kanta, a daren ranar bata yi bacci mai daɗi ba, Tun daga saman gado Ta mirgino ta ƙundumo ƙasa ta daki floor ɗin sosai, har cikin kanta taji zafin buguwar da ta yi, Lokaci ɗaya ta farka kamar wadda Aka tsakura ta ware manyan gray eyes ɗinta tana kallon ceilling, Sai faman haki take yi kamar wadda ta yi gudun famfalaƙi, Ƙoƙarin tariyo abunda tayi mafarki akanshi tayi, A cikin mafarkinta wasu baƙaƙen Maguna Guda uku sun farmake ta asaman gadonta, Faɗa ya kaure a tsakaninsu, Ta dinga yakushinsu tana kai masu cizo suma suna kokarin yakushinta sai dai Allah bai basu nasara ba, a ƙarshen itace taci galaba akansu ta yi masu jina jina sukai ta kuka, har suka sauko daga saman gadonta suka watsa aguje, Nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke, wani irin sanyi ya ratsa zuciyarta, lokaci ɗaya ta saki murmushi har dimples ɗinta suka lotsa, da alama taji daɗin damben da tayi acikin mafarkinta, bata motsa daga kwancen da take a ƙasa ba, hada bargonta da pillow ɗinta duka suna rungume a hannuwanta, Suma hadasu akayi artabun, "Gidan kurkukun ƙaddara Ba gidan marayu bane Gidan Matsafa ne" yanzu ta ƙara tabbatar da zarginta akan cewa Gidan Mallakin Matsafa ne, Sai dai batasan wasu kalar matsafa bane, masu shan Jini, ko kuwa masu Cin naman mutun, akwai sauran rina akaba, dole sai ta bi asannu tukunna zata gano ainihin me waɗannan matsafan suke aiwatarwa da mutane , Ta yi zurfin acikin tunaninta muryar batool ta katse ta"Sister lafiya? Me kike yi a ƙasa"? Wurga idonta tayi akan batool dake A zuƙunne gabanta, ba tasan Lokacin da tazo wurinta ba, "Sai faman sakin murmushi kike Yi kamar wadda akayiwa albishir da mukullin fita daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara" fashewa angel tayi da dariya Jin abunda batool tace, haƙiƙa maganarta ba ƙaramin daɗi tayi mata ba, wannan babban albishiri ne kuwa mutun ya mallaki mukullin fita daga kurkukun ƙaddara, Har tafara ayyana irin shagalin da zatayi aranar da tabar gidan kurkukun nan, zatayi farin Cikin da bazata Iya misalta shi ba, "Faɗamun me kike ma dariya? Wata'ƙil nima ya sanya ni farin Ciki"acewar batool fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar, Mikewa zaune angel tayi still pillown ta na rungume a hannunta, sumar kanta duk ta tarwatse saman bayanta, hada side by side na fuskarta, hannu batool takai tare da ruƙo gashin kanta tana fadin"yakamata In rage maki sumar kannan naki, idan ba haka ba nan gaba idan kina tafiya sumar zata dinga taɗiyo ƙafarki ne," dariya suka saki atare, Angel tace"baki lura gashin ki yafi nawa yawa ba? Kalli Fa yadda sumar kanki ta Cika ko'ina kamar kin kifa kwando asaman kan naki, Gashin duk ya nannaɗe kamar taliyar indomie," Ta6e Baki batool tayi ta ɗan kai idonta kan sumar kannata, ita kanta tsoron kallon yawan sumar ta take Yi, saboda yadda take ha66aka, "Kwanan nan zan samu abunda zan datse ta, Don ni banga amfani gashin kaina ba," acewar batool, Angel tace"da ace a waje kike rayuwa da baki faɗi hakan ba, saboda gashi abun ado ne ga ƴa mace, yana ƙara ƙawata kyan mace sosai, kuma yana jan hankali mutane, idan Allah yasa muna da rabon fita daga Cikin kurkukun nan, ke da kanki zaki shaida abunda nake faɗa maki, mutane ma rububinki zasu dinga yi saboda kyanki," Duk wannan maganganun da angel ke yi batool fa bata fahimtarta, domin kuwa batasan Ya kyan fuskarta ya ke ba, tun da Allah ya halicce ta Bata ta6a kallon madubi ba, tadai san kyau a fuskar danish da kuma fuskokin su Azeeza, Amma Ita batasan Ya kamanninta suke ba, kamar yarda suma su Azeezan basu ta6a kallon madubi ba, Basusan Ya suffarsu take ba, Sai an kwatanta masu, "Angel nifa bansan Ya ake ganin kyau na ba, Saboda bansan ta wace hanya zan ga fuska ta ba," tayi maganar tana kallon angel, Tuntsirewa angel tayi da dariya Hada dafe Ciki, Batool ta daure fuska"stop laughing at me bana son wasa fa " daƙyar angel ta samu ta dakata da yin dariyar, A tsanake Ta kalli batool tana zayyana mata kyawun fuskarta, "Farko dai ke doguwace, fara sol son kowa ƙin wanda ya rasa, idanuwanki Dara dara dasu manya farare ƙyal launin su brown colour, ga dogon hanci, tausasan la66anki brownish colour ne yadda kasan yankan tumatur saboda tsabar kyansu, ke fa ɗin kyakkyawa ce ajin farko, tun da angel ta soma magana batool ta saki baki galala tana kallonta, Tsabar farin Ciki ya hana ta furta komai, Daɗi take Ji ana zayyana mata irin kyanta, Wani abu da angel bata sani ba, tun lokacin da Ta soma zayyana kyan fuskar Batool, Gaba ɗaya su Hanna dasu azeeza, rubina Hibba, eve, yasmin, da deeja da parveen Kaf ɗinsu Suna a zuƙunna kewaye dasu, Jira suke ta kammala Zayyana ma Batool kyawun fuskarta suma ta faɗa masu Ya nasu Kyan yake, Tofa angel ta zama Mirror, Baƙaramin wahalar da ita su ka yi ba, Sai da tagama da matan sai ga Javed da mubeen, hada naufal suma suka tasa ta gaba sai ta faɗa masu Ya kyawun fuskarsu yake, har wani jiri take gani acikin idanuwanta saboda tsabar gajiya, Ga gunwa tana ji sunƙi bari ko toilet ta shiga ta watsa ruwa ajikinta, sai daɗi suke ji an faɗa masu cewa su kyawawane, Sai da ta kammala Javed Yace"Yanzu ki faɗa mana waye yafi kowa kyau acikin mu"? Suka tsareta da ido suna jira su ji amsar da zata basu, Kowa sai gyara sumar kanshi yake yi don ta ce shine yafi kyau, "Zan fada maku tsakani da Allah, wanda yafi kowa kyau acikin ku, Baya atare daku yanzu haka," gaba ɗaya taga sun kwashe da dariya, Da mamaki akan fuskarta tace"meya baku dariya" Mubeen yace"saboda Kin canka dai dai, Wannan wanda baya atare damu shine yafi kowa kyau acikin mu," Murmushin gefen fuska angel tasaki tare da ɗaura idonta kan batool tace"Amma duk da kyanshi, Batool itace zata zo na ɗaya saboda Ita macace, bayan batool kuma sai Azeeza kodan saboda wannan kyakkyawan murmushin nata, Daga azeeza kuma sai Javed...." duk wanda ta ambaci sunanshi sai taga yanata washe baki "To ki faɗa mana wanene Yafi kowa muni Acikin mu"? Batare data yanke shawara da zuciyarta ta basu amsa da cewa"Haris ne, Cikin mata Kuma deeja ce" Deeja dake atsaye Ta ruƙe qugu tuni ta tur6une fuska, jin an kirata da mummuna, dama a ƙule take da angel ganin yadda sauran Ƴan uwanta duk suka Saki jiki da ita, bayan irin Ƙarairakin da tayi masu, ita kanta angel tayi mamakin zuwan da su ka yi wurinta, bayan Irin juya mata bayan da su kayi amma yau sai gashi sun sake da ita, duk da tasan Zaiyi wuya ayanzu su yarda da ita, kamar yadda suka yarda da ita a lokacin Baya, Duk wannan abun dake faruwa Haris Baya acikin ɗakin bai jima da farkawa ba, Ya wuce Toilet, baisan wainar da suke toyawa ba, "Kowa ya ta shi yaje ya shiga wanka, ya tsarkake jikin shi, kafin giants su kawo mana breakfast ɗin mu," batool ce tayi masu magana, ɗaya bayan ɗaya kowa ya mike Ya nufi Toilet, Lokacin da suka kammala Yin wanka, bada jimawa ba, Giants Suka kawo masu Abinci, Yau Hada Chocolate Cake aka kawo masu Kowa ɗaya, ba ƙaramin dadi suka ji ba, Saboda suna matuƙar son cake, Yanzu sun saba da zarar Sun kammala Cin abinci, Sai a haɗu a motsa Jiki, Bayan sun gama, Kowa zai zauna ya huta ne, Yau fa tun da aka ta shi basu ga walwalar haris ba, Hatta angel tayi mamakin halin daya shiga yau, ya saba kullum sai ya ƙunsa mata baƙin Ciki, amma Yau kota kanta baibi ba, ko abincin shi bai ci ba, kamar wanda ɗan kanoma Ya kama haka ya dinga yi masu safa da marwa acikin ɗakin, idan ya gaji da yin zarya ƙafafuwanshi suka soma yi ma shi raɗaɗi sai ya koma saman gadonshi ya kwanta ya kalli ceilling, damuwace ta ishe shi ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, Ya gaza samun kwanciyar hankali, kowa ya kasa gane kanshi, A lokacin suna zazzaune Saman gadajen su suna hutawa, Haris Ya sauko daga saman nashi gadon, Buguzun buguzun yake tafiya har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa yaci burki ya tsaya tare da kai hannu ya kwankwasa ƙopar, Duk suka zuba mashi ido suna kallon shi, kusan sau uku yana buga kopar kafin, Ya soma jin alamun ana buɗe kopar ta Ciki, Tsohuwa Ce ta fito hannu ruƙe da sanda, tun daga kan yanayin yadda ta ganshi ta tabbatar da cewar ba a hayyacin shi yake ba, ya haɗe rai zuciyarshi har wani tafarfasa take Yi, "Harisu Lafiya ka ke buga mun ƙopa"? Yana huci yace"Nagaji da jiran dawowar danish, So nake naganshi, ko bai warke ba adawo mana shi cikin mu mu cigaba da yin jinyarshi, hankalin mu sai yafi kwanciya," tunkan haris yakai ƙarshen maganarshi, Sauran ƴan uwan nashi duk suka sauko daga sama beds ɗinsu suka nufi inda tsohuwa da haris suke atsaye, banda angel dake hakimce saman gadonta, tana kallonsu, Marairaice mata fuska Azeeza ta yi, Cikin sanyin murya ta wanda ya karaya tace"Idan har dagaske Kina son Mu, adawo mana da danish ɗinmu mu cigaba da yin jinyarshi acikin mu, mun yi maraicin rashin shi acikin mu," Ɗaya bayan ɗaya suka shiga Yi mata magiya akan adawo masu da danish ɗinsu, Su suke Yi mata magana amma idonta na akan angel, dake kallonta fuskarta ɗauke da kayataccen murmushi, aranta tace"nasan yanzu zata ƙara jin haushina saboda sun fara tuhumarta akan bazata dawo masu da ɗan uwansu ba, Yanzu ya rage naki tsohuwa kodai ki dawo da danish ko kuwa sufara zarginki," Gyaɗa kai tsohuwa tayi fuskarta a tur6une tace"Ku kwantar da hankalin ku, Yau danish zai dawo Cikin ku, Kuje ku xauna," Takai ƙarshen Maganar tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta, A bakin ƙopar ɗakinta, suka Zazzauna don yau sunci alwashin indai Danish bai dawo ba anan zasu kwana, angel dai na can kwance daman gadonta bata motsa ba, ta zuba ido tana jira taga ta wace ƙopa za'a shigo masu da danish, Dagaske zai dawo yau ko kuwa? Lumshe idanuwanta ta ɗanyi tana jin bacci sama sama, Har wuraren marece ba'a dawo masu da ɗan uwansu danish ba, sai da kowa ya fidda rai da dawowarshi aranar Kwatsam Ba zato ba tsammani, suna zazaune a bakin kopar ɗakin tsohuwa wasu har sun fara gyangyaɗin Bacci, Suka soma Jin motsi buɗe ƙopa, zumbur kowan nan su Ya miƙe Cike da sa ran Ganin danish, sun tabbatar shi ne saboda yanzu ba lokacin kawo masu abinci bane sun riga sunci tun ɗazu da safe, takun Tafiyar Giant suka Jiyo daga Can kusurwar Benan, Jiki na Rawa suka Watsa da gudu Xuwa bakin stairs ɗin Kowa Ya ci burki yana faman Baza Idanuwanshi, Tuni Giant ɗin daya kawo shi Ya juya ya fuce Ya datse door, Tun daga ƙasa suka soma Kallon shi, doguwar ƙafarshi sai kerma take yatsun ƙafar duk sun manne ma juna, jikin shi sai rawa yake yi idanuwanshi sun zazzaro tamkar ƙwayar idonshi zata faɗo ƙasa, jijiyoyin wuyanshi duk sun fito ruɗu ruɗu saman farar fatarshi, Kayan jikinshi duk sunyi uban squeezing, sumar kanshi ta hargitse duk ta cukuikuiye Lamarin ya yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Duk sun gaza yi mashi magana, haris ne ya yi ƙoƙarin furta sunan shi"DANISH lafiyarka kuwa? Ko har yanzu jikin ne"? Ya yi tambayar yana ƙoƙarin matsawa kusa danish, Dafe kai suka ga yayi da hannuwanshi, Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda ta razanar dasu, Angel dake niyar nutsawa Cikin baccin ta, Sautin ƙarar danish ya farkar da ita, a firgice ta ware idanuwanta tare da kallon inda suke a tsaitsaye Cirko cirko abakin Benan, Da sauri ta sauko daga saman gadon Jikinta har 6ari yake yi, ta cikinsu ta ratsa ta tsaya Dab dashi tana kallon shi, Ya ƙanƙame Jikinshi yana Girgiza masu kai, la66anshi na kerma ya soma faɗin kada su matso kusa da shi, baison ganin kowa, ya tsani kowa" yana kai ƙarshe maganar shi, da gudun gaske ya bi ta tsakiyarsu ya bangaje su bai nufi ko'ina ba sai Cikin toilet area ɗinsu Ya shige ɗaya daga Cikin toilet ɗin Yaja ƙopa ya datse yadda baza su iya shiga ba, Fashewa da kuka Aziza tayi saboda tsoran da taji, Da gudu suka ɗunguma zuwa bakin ƙopar ta farko, Haris ne ya shiga bin ƙofofin toilets ɗin yana kwala mashi kira"Danish! danish! Baka ji ina kiran ka? Wai meke faru ne? Pls ka buɗe mana ƙopa, Munyi kewarka sosai," a ƙopar toilet na ƙarshe yaje ya bubbuga ta yaji ta a garƙame alamar Nan ciki danish ya shiga, A ruɗe rubina tace"Bari naje na faɗa ma tsohuwa tazo taga halin da ɗan uwanmu yake ciki, kada mu rasa shi" ta yi maganar tare da juyawa da gudu ta fuce, Cikin shessheƙar kuka aziza tace"Wayyo Allah danish meya ke faru dakai ne? Dan Allah ka buɗe ƙopar," Hawaye ne acike da idanuwansu Javed, Eve tace"Ban ta6a ganin shi cikin wannan mawuyacin halin ba, sam danish baya a hayyacin shi," tana rufe baki deeja tace"Ai duk laifin Angel ne, itace sila da ace bata ta6a lafiyar jikin shi ba, da duk hakanbata faru ba," Cike da takaici Angel tace"Nifa bani ce silar shigar shi cikin halin nan ba, koda ace ni ce amma ae an kai shi treatment room ko? meyasa daya dawo babu sauƙi ajikin shi? Kenan ba duba lafiyar jikin shi akayi ba, Wani abunne daban su ka yi mashi........"tsawa Haris ya daka mata"Idan har Danish ya rasa ranshi, ke ma ki shirya binshi, ƙafarshi kafarki, muguwa kawai," Fashewa angel tayi da matsanancin kuka tana faɗin ita ba ita bace sila, Faɗo wa cikin wurin rubina tayi har suna haɗa baki wurin tambayarta ina tsohuwar take, idonta cike tab da kwalla tace"Na kwankwasa ƙofar ɗakinta, bata buɗe ba" Guntun tsoki Haris yaja, Yaci gaba da bugun ƙopar yana kiran sunan danish amma shiru bai amsa masu ba, Gaba ɗaya sun taru agaban toilet ɗin Sai faman ƙwala mashi kira suke yi ya yi shiru babu magana, "Me zai hana mu sanya ƙarfi mu buge ƙopar wata'ƙil ta buɗe," batool ce ta kawo wannan shawarar, gaba ɗaya suka shiga bugun ƙopar, idan wannan yayi ya gaji sai wannan ya jaraba, duk anan ƙarfinsu ya ƙare dama ya lafiyar gwiwa, abinci sau ɗaya arana, Gaba ɗaya sun fidda rai da fitowar danish, duk jikin su ya yi sanyi, ransu yana basu cewar danish ya mutu acikin kewayan, Ransu duk a jagule suka fito daga wurin toilet din, suka koma cikin ɗakinsu a ƙasa kowa ya zauna, angel tana a tsaye bakin ƙofar farko ta shiga toilets ɗinsu, Idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla, zuciyarta acike take fal da tunanin Meya faru da danish? Yau 5 days kenan Yana a treatment room meyasa baiji sauƙi ba? Anya kuwa duba lafiyar jikin shi akayi ko kuwa ƙara mashi ciwon akayi? Duk yadda ta ƙagara ta yi toxali da danish sai da taji ƙuncin halin da ta ganshi aciki, kwata kwata Baya a hayyacinshi tamkar an canza shi, runtse idanuwanta tayi tana tuna Yanayin da tayi arba dashi, gwanin ban tsauyi kamar wanda aka zaƙulo daga bakin kura, "Yanzu ya zamuyi? Munbar shi acan ciki, Allah kaɗai yasan halin da yake Ciki" mubeen ne ya yi maganar fuskarshi jaga jaga da hawaye, Naufal yace"muna ji muna gani zamu rasa ɗan uwanmu, Wai meke faruwa da danish? tsohuwa tace an kaishi treatment room, ana duba lafiyar jikin shi but why danish baiji sauƙi ba"? Ya yi ma kanshi tambayar da baida amsarta, hibba tace" ga shi tsohuwa bata nan, nasan da ita zata ceto rayuwarshi" daga inda angel take tana iya juyo maganganun su, ta tsani taji sun ambaci sunan tsohuwa, kuma har suna da yaƙinin itace kaɗai zata iya ceton rayuwarshi, Aziza sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, shi haris Yama rasa ta cewa saboda tsabar ƙululun baƙin Cikin daya tokare mashi maƙoshin shi, zuciyoyinsu sun karaya, ba haka su kayi tsammanin zasu ga ɗan uwansu ba, ba ƙaramin sage masu gwiwa akayi ba, sun rasa yadda zasu yi danish Ya buɗe masu ƙopa, Ko magana baiyi balle ma su sanya ran yana araye, Gaza jurewa angel tayi, Juyawa tayi tare da komawa cikin toilet area ɗin, A bakin ƙopar toilet ɗin da yake aciki ta tsaya tare da kai hannu ta ruƙe handle ɗinta, Zurfin tunani ta shiga yi akan yadda zata samu Ta 6alle ƙopar, sam babu wani makami dazata yi amfani da shi, ƴan dabaru ta shiga yi na yadda zata 6alle ƙopar, Allah ne ya taimake Cikin sa'a, Sakatar ta saki, Ƙopar ta buɗe batare da tasha wahala ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da tura ƙopa ta shiga ciki tana faman wurwurga idanuwanta, tun abakin kopar tayi arba da wandonshi yashe a ƙasa, ras! Taji gabanta ya faɗi, cigaba da tafiya tayi tana bin ƙasan da kallo, rigarshi ta gani a ƙasa itama ya yi wurgi da shi, tsayawa tayi a tsaye cike da fargabar halin da zata yi tozali dashi, Yana acan Gefen tukunyar fulawar nan, anan ya zauna, daga inda take tana iya hangen fuskarshi, wuyanshi har zuwa ƙirjin shi, sai kuma ƙafafuwanshi daya zuro dasu ta ƙasa, Ya lumshe idanuwanshi sai nishi yake yi tamkar wanda yasha gudu, Muryarta na kerma ta ambaci sunanshi"DANISH" buɗe idanuwanshi ya ɗanyi Sunyi jawur dasu daga gani yana acikin mawuyacin hali, jikin shi duk zufa ta wanke shi kamar wanda aka tsamo daga cikin kogon ruwa Ta wutsiyar idonshi yake kallonta, juyawa tayi da sauri ta ɗauko mashi rigarshi da wandonshi, Matsawa ta ɗanyi nesa da shi, yadda bazata iya ganin tsiraicin shi ba Cikin sanyi murya tace"bansan me yake damunka ba, amma ina zargin kaina akan halin da ka ke ciki, dan Allah ka yafe mun ka yi haƙuri," har lokacin bai motsa lips ɗinsa ba, balle ta yi tsammanin zaiyi magana magana, Miƙa mashi kayan shi tayi"dan Allah ka mayar da kayan ka, bazan so ƴan uwanka su ganka a haka ba, hankalin su ba a kwance ya ke ba, duk sun damu dakai" Wurga mashi kayan tayi a saman fuskarshi suka sauka, "Dan Allah ka sanya kayan ka," ta kuma maimaita mashi, cikin sigar lallashi, Gani tayi ya runtse idanuwan shi sosai, ya ciccije soft lips ɗinshi duk ya fasa su, wata irin gigitacciyar ƙara ya saki, Afirgice angel ke kallonshi, Su Batool dake acan cikin ɗakin Jin sautin ƙarar Danish Yasa suka Watso a guje, kafin su ƙaraso angel ta yi saurin juyawa zuwa bakin ƙopar ta datse ta, Tana jiyo sautin bugun ƙopar da suke yi suna ambaton Sunan danish, tayi masu hakanne don bazata so sugan shi tsirara babu kaya ba, Kafin ta dawo inda yake, tuni Yayi watsi da kayanshi data wurgo mashi, kwance ƙasa ta hangoshi sai burgima yake yi wannan karan hada hawaye akan fuskar shi lamarin ya yi matuƙar ɗaure mata kai, tana so ta taimaka mashi amma tana jin tsoron kallon tsiraicin shi Rufe idanuwanta ta yi, amma bata rufe su sosai ba, tana gani biji biji a ahaka ta lalla6awa ta cigaba da tafiya zuwa inda yake kwance ta lalubo Wandonshi, ta soma kiciniyar mayar mashi a jikin shi, daƙyar ta samu ta zura mashi, Ajiyar zuciya ta saki tare da buɗe idanuwanta akan fuskarshi, Sai faman nishi yake yi, idanuwanshi suna arufe, long eye lashes ɗin shi duk sun jiƙe, calmly ta furta sunanshi"Danish are u ok" Jin muryar angel acikin kewayan yasa suka gane cewa tana a ciki, sunyi mamaki yadda akai ta buɗe kopar, nan fa suka shiga kwala mata kira suna fadin ta bude masu ƙopa Ɗaga murya ta yi tare da ce Masu Bazata buɗe ƙofar ba, saboda sun ƙala mata sharrin cewa itace silar jefa shi cikin halin da yake Ciki, don haka idan har sunga ta buɗe masu ƙopa, danish ya samu sauƙi ne" Bugun ƙopar haris yake yi tamkar zai 6alleta" Bazaki zo ki buɗe mana ƙopar ba? a harzuƙe tace"Bazan buɗe ba," Sassauta murya haris ya yi"pls angel ki buɗe mana ƙopa, nasan bakya son danish kada kice zaki ƙarasa shi," Girgiza kai ta ɗanyi cike da jin takaicin maganar haris, Tafin hannunta takai saman fuskar Danish ta shafa a hankali tare da ambaton sunanshi"Danish" Dogon numfashi taga yaja gami dasauke ajiyar zuciya, yana so ya buɗe idanuwanshi amma ya kasa, sai lumshewa eyes ɗin nashi suke, "Danish pls try to open ur eyes," Sama sama numfashinsa ke fita da hucin zafi, hannayenta ta sanya tare da tallabo kanshi ta ɗaura saman laps ɗinta, Shafa gefen fuskarshi taci gaba dayi, yayin da ta soma karanto addu'o'i acikin zuciyarta, tana ɗan tottofa mashi saman fuskarshi, Ba'a ɗauki tsawon lokaci ba, ya fara dawowa cikin hayyacin shi, Lokacin dare ya fara yi, su biyu acikin toilet, ya yin da su batool ke zazzaune bakin ƙopar shiga toilet ɗin, sun galabaita har sun gaji da bugun ƙopar suna yi mata magiya akan ta bude masu, suga a wani hali ɗan uwansu yake ciki, wasu har sun fara gyangyaɗin bacci, Itama angel ɗin baccin ta soma ji a cikin idanuwanta, A lokacin da bata yi tsammani ba, taji ya ruƙo hannunta a cikin nashi sosai ya damƙe mata hannu, firgigit tayi tana kallon shi, Lumshe idanuwanshi suke bai kaiga ƙarasa rufe su ba, He was calmly looking at her face without blinking his eyes, Furta sunanshi tayi"danish" muryar shi so cool ya ambaci sunanta "angel" for the first time da danish ya ta6a ambaton sunanta, "Are u ok,"? Ta kuma tambayarshi, bai amsa mata ba, ƙoƙarin miƙewa zaune yayi amma jikin nashi yaƙi bashi haɗin kai, da sauri ta taimaka mashi wurin tallabo shi ya miƙe zaune, tare da kwantar da kanshi saman kafadarta, still numfashin shi da huci yake fita, tana jin shi saman fatar wuyanta, saitin inda dogon hancin ya shafa, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Sam bata ji komai ba, daya kwantar da kanshi saman kafadarta, sai taji tamkar ɗan uwanta ne na jini, ƙurawa sumar kanshi ido tayi, doguwa har saman bayan shi, kamar ta sanya hannu ta shafa sumar haka zuciyarta ke raya mata, 'Pls angel open the door for us, mun ƙagara mu ga ɗan uwanmu," muryar hannah ce take yi mata magiya, Hannu tasa ta dafa kafaɗar shi"danish suna son ganin ka, mu koma ɗaki," kusan minti biyar da yin maganar, ya ɗan dago da kan shi, still jikin shi ba kwari kerma yake yi, Rarrafawa tayi ta ruƙo rigarshi ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ya zurata ajikin shi, Sai da ta taimaka ma shi wurin ruƙo shi tukunna ya samu ya miƙe, a haka suka soma tafiya har suka ƙaraso bakin ƙofar ta buɗe ta fito da shi, gaba ɗaya suka miƙe tsaye zasu rungumo shi, Da sauri batool ta ware hannayenta wurin kare shi"Jikin shi ba ƙwari, danish yana buƙatar hutu," A jiyar zuciya kowa ya sauke, wuce wa angel ta yi Cikin ɗakin, Su Batool suka Bi bayan su, ya rurruƙeta ji yake kamar zai faɗi ƙasa, wani irin jiri jiri yake gani a Cikin idanuwanshi, a saman gadonshi ta tsaya tare da taimaka mashi ya kwanta sama, "Sannu danish, Allah ya baka lafiya," batool ce ta yi maganar, su haris ma duk su kayi mashi ya jiki, sam ya kasa amsa masu amma duk yana jinsu, Sunyi tsaitsaye cirko ciko a gefen da gefen gadonshi, hasken ɗakin ya yi duhu, alamar dare yayi lokacin bacci ne, da sauri Javed yaje gaban table ya kunna masu sauran fitilun, ɗakin yayi haske ya ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ya ajiye ta daga gefen gadon Danish, Motsin buɗe ƙofa suka jiyo, da sauri kowannan su Ya juyo yana jiran ganin wanene zai 6ullo daga saman benan Biyu ne daga Cikin Giants dake kawo masu abinci, Abun mamaki ɗaya daga Cikin su hannun shi na ɗauke da wooden tray, samanshi an rufe da jan ƙyalle, da alama kayan abinci ne, ɗayan Giant ɗin kuma Syringe ne a hannun shi, already an zuba ruwan allurar a ciki, Me ruƙe da syringe ɗin ne ya yi masu nuni da hannunshi su matsa su basu wuri, da sauri suka ja baya, me ruƙe da tray ɗin ya sauke shi ƙasa gefen gadon danish, Kafin ya matsa zuwa saman gadon, wata irin zabura danish ya yi, ya daddafe kanshi yana faɗin baya so kada su matso kusa da shi, ya dinga ambaton sunayen su haris yana faɗin ba zasu taimake shi ba? Suna ganin za'a cutar da shi, Tsananin tsauyin shi ne ya kama su batool, idanuwan kowannan su ya ciko tab da kwalla, Ruƙe shi sosai Giant ɗin ya yi, shi kuma ɗayan Ya daddage ya caka mashi allurar a wuyanshi, nan take jikin shi ya saki, ya sulale saman katifar idanuwanshi a rufe, Sakin shi su ka yi, a tare suka juya cikin takun nan nasu, suka fuce daga cikin ɗakin, Fitar su keda wuya Su hannah suka yi mashi rumfa suna ambaton Sunanshi, danish danish Haris yace subar shi ya huta zai ji sauƙi tunda anyi mashi allura, Angel tace"Wai kun yadda allurar magani ce su kayi ma shi? Meyasa danish yake kuka yana faɗin bayaso sai kace ƙaramin yaro? Kuma har yana faɗin mu taimake shi, u ave to think about it, ni sam ban yarda da waɗannam mutanan ba, Allah kaɗai yasan me su kayi ma shi" Yatsina fuska deeja tayi cike da jin haushin angel ta soma magana"babu abunda su ka yi ma shi, tun da muke dasu basu ta6a cutar da wani daga cikin mu, koma meye kece kike da alhakin ciwon da.......' Bata kai ƙarshen maganarta ba, sakamakon naushin da angel ta sakar mata a saman fuskarta, tsabar raɗadi yasa Deeja ta dafe kuncinta, "Ni kika buga"? Harara angel ta jefa mata"kaɗan kika gani, in har kika ci gaba da faɗin cewa ni ce silar da danish yake a wannan halin saina zubar maki da haƙoran gaba, wawuya kawai, don kinga kwanakin nan nayi sanyi shiyasa har kika samu damar gaya mun magana" Ganin sun harzuƙa yasa javed yin saurin shiga tsakaninsu, cikin sanyin mirya yace" kodan saboda danish, kuyi haƙuri kuyi shiru," jinjina kai deeja ta yi"na ƙyale ki a yanzu, amma wlh saina rama naushin da ki kayi mun" Tsoki angel taja"duk lokacin da kika shirya nima a shirye nake, mai rabon shan duka," Daga haka su ka yi shiru, Can Haris ya hango parveen zuƙunne gaban Kayan abincin da aka kawo, sai faman shinshina su take yi, hannu yakai tare da ruƙo wuyan rigarta, ya ɗago da ita tsaye ta maƙe wuya "Abincin Mara lafiya ne, Kada ma mutun ya sanya rai," harara parveen ta ɗan jafe mashi"Amma ae muna jin yunwa sosai, wannan dama ce a gare mu, kuzo kawai mu zauna muci mu ƙoshi, in yaso sai mu rage mashi kaɗan, bama lallai ya iya cin abincin ba" Wani kallo Hannah tayi mata" ke fa dama indai kan abinci ne, Ba imani kika cika ba, Kinsan dai sau ɗaya ake kawo mana abinci, wannan kuma da kika ga an kawo na danish ne, ina ma laifin kice idan yaci ya ƙoshi ya rage sai muci kingin"? Murmushin yaƙe parveen ta saki"Ae naga bacci yake yi, zamuyi ta jiran shi ne har saiya farka yaci ya rage tukunna muci"? ta yi tambayar tana ƙyafƙyafta ido, yadda tayi ba ƙaramin dariya ya basu ba, Mubeen yace"Ni kaina yunwa nake ji, Don ba yadda zanyi ne Allah," yana rufe baki naufal yace"ae ba kai kaɗai ba, ina ɗazu ɗinnan da muka dinga bugun ƙopa, to anan duka abincin da muka ci ya zube," Murmushi haris ya ɗan saki tare da cewa"duk bala'in ku dai bazaku ta6a abincin ɗan uwana ba, har saiya ci ya rage" dariya su kayi gaba ɗayansu, da alama suna farin cikin dawowar ɗan uwansu, Dare fa ya yi sosai, yakamata kowa yaje ya kwanta, acewar yasmin, juyawa su kayi kowa ya nufi gadonshi, Banda mutun ɗaya Parveen ta yi tsaye agaban gadon danish Dawowa Haris ya yi tare da kai hannu ya ruƙo wuyan rigarta" muje ki kwanta" bubbuga ƙafa ta yi tare da cewa"Mara lafiya ne fa shi, taya zamu barshi shi kaɗai, Ni inaso Inyi jinyarshi ne", "Saboda shi kaɗai ne a ɗakin ko"? Ya yi tambayar yana kallonta, shiru tayi tana faman tur6une fuska, "Oya muje ki kwanta, sarkin wayau" ya ambaci hakan tare da janta, sai da yakai ta har saman gadonta, tukunna shima ya wuce nashi gadon ya kwanta, Gaba ɗaya sun kasa runtsawa, bakomai suke jira ba, face farfaɗowar Danish, "Kinyi bacci"? Muryar haris ce, yana daga kwance yayi maganar yana kallon Parveen dake a kwance saman gadon ta dake a kusa da nashi "Taya zan iya bacci da ƙamshin abinci a hanci na," dariya haris yayi, "Amma Haris baka ganin abincin zai iya lalace wa, tunda shi danish ba'asan lokacin da zai farka ba," "Calm down ur mind, tun da ki ka ga sun ajiye abincin nan, sunsan zai farka ne, Giants ne fa Sunsan me suke yi," sun jima suna tattaunawa, da haris before bacci yayi awon gaba da parveen, Tsakiyar dare lokacin rabi da kwatarsu sunyi bacci, banda mutun ukun, Angel data ɗaurawa kanta alhakin ciwon danish, sai kuma Haris da yake na hannun damarshi, bayan su sai Batool, kowannansu yana kwance sunyi likimo tamkar masu yin bacci, Ashe zuƙunne bata ƙare ba Kamar daga sama su ka ji danish ya fasa gigitacciyar ƙara mai matuƙar firgitarwa, farfaɗowarshi kenan, ya ta shi da wani sabon Ciwon, a matuƙar gigice angel ta yaye bargonta haris da batool duk suka cire bargunansu, hatta masu bacci sai da suka farka sakamakon Ƙarar danish data karaɗe Cikin ɗakin, Gaba ɗaya hankalin su yae matuƙar tashi, ganin Danish Zaune saman gadonshi sai ƙara yake saki, ya daddafe kanshi da dukkan hannayenshi, tamkar wanda ake cikin zare ranshi saboda tsabar yarda yake fitar da sautin ƙarar har wani jijjiga muscles ɗin Jikin shi ke yi, Durowa su ka yi daga saman gadajensu, jikinsu har kerma yake yi wurin tunkarar shi, Haris ne ya hau saman gadon, Javed da Mubeen hada naufal da sauran Ƴan matan duk Suna a tsaitsaye fuskokinsu da alamun ruɗu, "Danish meya faru? meke damunka? dan Allah kayi mana bayani, " magana suke yi mashi amma sam baya sauraronsu ihu kawai yake yi, shi kaɗai yasan Raɗaɗin da yake ji bawan Allah, "Bari naje na kira tsohuwa" Acewar Batool, juyawa ta yi da niyar taje ƙopar ɗakin tsohuwa, Angel tayi wuff ta ruƙo hannunta, tsayawa tayi tare da waigo wa ta kalli hannun angel da ta ruƙe ta, suka haɗa ido da juna"Ki jira akwai abunda nake so, in jaraba yi mashi idan bai ji sauƙi ba sai kije ki faɗa mata,". Rai a6ace haris yace"don me zaki hana ta zuwa ta kira ta? So kike mu rasa ɗan uwanmu? Baki ga halin da yake Ciki bane? Yana rufe baki Deeja tace"Da alama so take ta ƙarasa kashe shi, dama ni ban yarda da ita ba, ko me take da shi da zata iya taimakon shi? angel bata tsaya sauraronsu ba. Kota kansu bata bi ba, batool ta kuma kallo tare da cewa"Ku bani dama," jinjina kai batool ta yi tare da kallon su haris tace"Tun da ta nemi alfarma, mu barta ta jaraba, amma kuma komai ya biyo baya, ke kija tun da kin hana a kira tsohuwa" gyaɗa kai angel ta yi, tare da matsawa ta haye saman gadon danish, ya kakkame Jikinshi sai kerma yake yi, yana sakin ihu ga zufa duk ta wanke jikin shi, duk da weather ɗin prison mai sanyi ce, Miƙa hannu ta yi da niyar ta ruƙo shi, Ya buge hannun nata alamar baiso, duk yabi ya birkice masu, Ganin yaƙi bata damar ruƙe shi yasa haris jan dogon tsoki tare da cewa"U just wanna waste our time, pls batool go and call her" tafiya batool ta soma yi ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa, Rufe ido angel tayi, Cikin sanyin murya mai tattare da natsuwa da cikar kamala, ta soma raira qira'ar karatun alqur'ani mai girma, Gaba ɗaya suka bita da kallo, sam basu san me take karantawa ba, amma tunda suke basu ta6a jin sautin abu mai daɗi ba, irin wanda angel take Rairawa ba, hatta batool dake ƙokarin kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa, tana fara jiyo sautin karatun da angel keyi nan take ta dakata, tamkar an dasa mata aya, da matuƙar mamaki ta juyo tana kallon inda suke. Bakomai yafi ɗaure masu kai ba, Fa ce yadda danish ya yi shiru, yadaina ihun da yake yi, kuma jikin shi ya daina yin kerma, A hankali angel ta buɗe idanuwanta, ta ɗaurasu akan fuskar Danish still bai buɗe idanuwanshi ba, matasawa ta ƙarayi kusa dashi sosai, ta sanya hannayenta biyu tare da ruƙo doguwar sumar kanshi, ta tattare ta zuwa bayanshi, moving lips ɗinta ta yi xuwa saitin kunnanshi na dama, sosai taci gaba da raira mashi karatun har cikin kanshi yake jin wani irin baƙon yanayi mara misaltuwa, zuciyarshi tayi sanyi, kasala ta baibaye shi, , Haƙiƙa Angel tabar ƴan kallo, Su haris sun saki baki kamar lehen sakarai sai kallonta suke yi, ta kawo masu wani baƙon abu da basu ta6a ji ba, He slowly wrapped his arms around her waist and squeezed her tightly tamkar zai shige cikinta, sai faman nishi yake yi yana fitar da numfashi da sauri da sauri, tana jin zafin jikin shi sosai ajikin nata, saboda matsewar da suka yi ajikin juna, tana jin yadda heart ɗinsa ke beating very fast, ƙasa ƙasa da murya yake furta mata, kada tadaina, taci gaba yi mashi yana samun sauƙi," kamar yadda ya buƙata haka taci gaba dayi mashi karatun, har sai da taji tempreture ɗin jikin shi ya dawo normal, numfashinsa da natsuwarshi sun daidaita tukunna ta dakata da yi mashi karatun acikin kunnuwanshi, zame jikinta ta yi daga nashi, tare da sanya hannayenta ta dafa shoulders ɗinshi, eyes ɗinta na kallon Fuskarshi, idanuwanshi tamkar na mashayin giya, "Danish can u see my face" tayi maganar tana nuna mashi fuskarta, jinjina mata kai yayi alamar eh, ɗagowa ta yi tare da kallon su Haris dake a tsaitaye, Yadda kasan ƙerarrun gumaka, tsabar mamaki yasa sun kasa rufe bakunansu, Kowa zuciyarshi acike take fal da tunanin menene angel ta karantawa ɗan uwansu danish harya dawo cikin hayyacin shi, "Angel kinyi matuƙar bamu mamaki" batool ce tayi maganar a lokacin ta dawo inda suke. "Duk da bamusan menene kika karanta ma danish a kunnanshi ba, amma nayi matuƙar jin wani irin sanyi da daɗi acikin zuciyata, sai naji dama baki daina ba, kin cigaba da yi," Batool nakai ƙarshen maganarta, Javed yace"Nikaina naji wani irin daɗi mara misaltuwa, nayi mamaki kuma ganin yadda danish ya samu natsuwa yadaina haukan da yake yi," yakai ƙarshen maganar idonshi akan danish, Hanna tace"i feel the same, zanso nasan menene angel kika karanta mashi me daɗi," tayi maganar fuskarta ɗauke da murmushi, "Zanyi maku bayani, amma yanzu danish yana buƙatar kulawarmu," tayi maganar tana kallonsu, Haris dai yayi shiru shi da deeja kowa na tofa albarkacin bakinsa kan irin dadin da suka ji amma banda su, saboda tsabar kunyar da suka ji, "Ga abincinsa kar ya lalace, aba shi yaci" parveen ce tayi maganar, tare da rankwafawa ta ɗauko tray din ta miƙa ma Angel, hannu biyu angel tasa ta ruƙe handle ɗin tray ɗin a tsakiyarsu ta sanya tray din, ta cire jan ƙyallen, waro ido parveen tayi ganin Roasted Chicken guda ɗaya sai maiƙo take yi ga wani irin ƙamshi, gefe kuma Milk ce a cikin bottle me sanyi, sai wooden bowl mai ɗauke da Fruits salad,' "Zaka iya ci"? Ta yi tambayar tana kallon danish, wata irin narkakkiyar zufa ta gani tana gangarowa ta cikin yalwatacciyar suman kanshi, bai iya bata amsa ba, sai dai kallon ta da yake yi, Sai lokacin harisun tsohuwa ya samu damar buɗe baki yace"Bari na taimaka ma shi ya watsa ruwa ajikin shi," yakai ƙarshen maganar, Tare da ruƙo danish, Javed ya taimaka shi suka yi mashi jagora zuwa Cikin toilet ɗinsu, Bayan tafiyarsu batool ta kalli sauran ƴan uwan nasu"tun da jikin nashi da sauƙi, ku je ku kwanta," Yadda kasan ƴan gudun hijra haka suka tafi sharaf sharaf kowa Ya hau saman gadonshi Ya kwanta, Ganin parveen taƙi tafiya yasa tace"ke fa" Hannu tasa tana ɗan sosa keyarta "Jira nake Su haris su dawo da danish yaci abincin shi, idan ya rage nima in samu in ɗan ci....." wani kallon rainin wayau batool tayi mata wanda yasa ta kasa ƙarasa maganar, "Sai kace kinfi kowa Jin yunwa, Allah yasa idan ya fito ya cinye abincin duka sai muga ya za ki yi" angel dake zaune saman gadon danish ta yi zurfi Cikin tunaninta, bakomai ya ɗaure mata kai ba, face yadda ta iya yin karatun qur'ani tiryan tiryan tun zuwanta gidan kurkukun tasha Yin attempting karatun qur'ani tana gazawa, sai ta dinga jin raɗaɗi a maƙoshinta, A yau dai kamar umarni aka bata tayi karatun haka tadinga ji, Kuma taji kwarin guiwar yin qira'ar, kenan nan gaba zata Iya samun damar yin ibada, mamaki take yi ya akai take samun nasara akan wasu abubuwan? Tabbas Allah yana atare da ita saboda kyakkyawar niyar dake gareta, kuma tana ji aranta cewa Akwai masu yi mata addu'a, fatanta Allah yasa dadynta idan yana araye ya kasance ɗaya daga Cikin masu Yi mata addu'a, Saboda ita addu'ar Iyaye kar6a66iyace akan ƴa'ƴansu kamar yadda hadisa ya tabbatar da hakan, Shigowarsu haris Cikin ɗakin ne ya katse mata zancen zucin nata, ta ɗago tana kallonsu, Hannayensu ruƙe dana danish, jikin shi duk lemar ruwa, Hada sumar kanshi suka wanke mashi, duk ta manne mashi saman fatar wuyanshi, Lokacin da suka ƙaraso, Saman gadon ya haye ya ɗan kishingiɗa kan shi saman pillow, jikin shi duk ya saki babu ƙwari, idanuwanshi na a lumshe, "Abincin fa"? Angel ce tayi ma shi maganar, slowly ya dan buɗe idonshi akan fuskarta, in a throaty voice ya furta mata"I can't eat anything now, u can share it," voice ɗinshi yayi low sosai, daƙyar ta iya jin me yake cewa,' Cikin rashin jin ɗaɗin maganar shi haris yace"Ko madarar ce ka ɗaure ka sha, nasan kana jin yunwa," girgiza ma shi kai ya yi"bazan iya ba, kada ku damu kanku am ok," Babu wanda yaji daɗi Acikinsu, Sun so koda milk ɗin ce yasha, amma ya nuna masu cewa babu yunwa attare dashi, Su parveen abun nema ya samu, zama su kayi a kasa Kowa Ya shiga kai hannu yana yagar naman kazar yana Ci, Komai saida suka Bi suka lamushe, bayan sun kammala, Haris Ya zauna gefen gadon Danish, sauran suka wuce saman beds ɗinsu suka kwanta, Angel ma tuni ta koma nata gadon, hankalinta ba ƙaramin kwanciya yayi ba, danish ya dawo Cikin su, sai da dare ya nutsa, tukunna haris yabar gefen gadon danish ya koma nashi gadon ya kwanta, Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan ta juya ta saci kallon shimfiɗarshi, yayi bacci ko baiyi bacci ba?, kasa jurewa tayi a hankali ta dan mirgina ta juya ta 6angaren da yake fuskanta, bayan shi kaɗai take iya gani, jikinshi na lulu6e da bargon da haris ya rufa mashi har zuwa kafaɗarshi, tana kokari rufe idanuwanta, taga yana mutsu mutsu, ƙoƙarin juyowa ya yi, da sauri ta rufe idanuwanta, don kar ya gane shi take kallo, natsuwa ya yi a yayin da yake kallonta, zuciyarshi cike fal da mamakin canza mashi da tayi, yafi tunanin taji tausayin shi ne saboda halin daya shiga, wata zuciyar kuma tana saƙa mashi cewa kada ka yarda da ita, so take ka saki jiki da ita, ta samu damar kashe ka cikin sauƙi, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin sanyi yaji ba, tun da ta karanta mashi wannan abun da baisan menene ba, Sai yaji duk duniya babu abunda yake kwaɗayin ya kasance yana sauraro acikin kunnanshi idan ba shi ba, Tunani tayi ko yayi bacci yanzu, tana mutsu mutsun buɗe idanuwanta, yayi saurin rufe nashi eyes, shima baiso ta gane cewa Ita yake Kallo, ta jima tana kallon shi, da zarar taga xai buɗe ido sai ta rufe nata idon, shima haka idon yaga zata buɗe idonta sai yayi saurin rufe nashi, Sai da suka raba da dare suna wannan wasan, Kafin Allah ya kawo bacci 6arawo yayi awon gaba dasu *ANEELERH* A tsaye Take saman darduma ta kabbara sallah, Jikinta sanye da dogon Hijabi maroon colour har ƙasa ta sauko, tana ƙoƙarin yin sujjada Taji mutun saman bayanta Ya haye, Kasa ɗagowa tayi saboda gudun kada ya faɗo tasan bai wuci junaid bane, ba yau ya saba yi mata haka ba, a bedroom ɗin Mami ya kwana, har yasan ya tako daga ɗakin mami zuwa ɗakinta, a duk inda ya kwanta bacci ya ɗauke shi ko mun tsakiyar dare ne idan ya farka sai ya nemota duk inda ta shiga, Yadda kasan malamin duba, Bubbuga bayanta taji yana yi tare da ambaton "Doki sukuta sukuta, doki sukuta sukuta!, yana magana yana sukuwa hada cewa Mommy, Ki tashi mu tafi yawo,' a hankali ta miƙa hannu ta ruƙo shi tare da janye shi daga saman bayanta, Ya faɗo daga gefe saman dardumar, bubbuga ƙafafunshi ya shiga yi, yana raira mata kuka, daurewa kawai take yi sam bata so taji yaron yana kuka, Tsananin tausayin shi taje ji, Hannu ya miƙa ya ruko cazbaharta dake ajiye saman darduman, Ya miƙe zaune ya zura cazbahar saman wuyanshi, Allah Allah take ta kammala sallar kafin yayi tunanin ɗaukar qur'aninta da ta ajiye wurin daya ɗauki cazbahar, kura mata ido yayi jin taƙi tanka mashi ashagwa6e yake kiran sunanta"mommy! Ni ki tashi muyi wasan doki" yayi maganar da hausarshi da bata ƙarasa nuna ba, ya hanata sakat, daƙyar ta samu ta kammala yin sallar ta zauna zaman tahiya, Ya ɗaura kanshi saman laps ɗinta, Yana cigaba da yi mata shagwa6a, bayan sallame sallar ne ta samu damar kallon shi, "Bansan meyasa kake yi mini haka ba junaid why? Bakaga sallah nake yi ba, bana hanaka in ina sallah kana hawar min bayana ba"? Wani kallo taga yana binta dashi, kamar wani mai hankali, a yanzu fa shekararshi biyu da rabi, Sai daga baya ma ta lura da rigar dake ajikinshi, Singlet ce ta abie ya sanya, ta yi mashi yawa har ƙasan ƙafafun shi takai, cike da mamaki tace"kai! Waya sanya maka rigar abie"? Fuskarshi a tur6une yace"Ni na ta" hararar shi tayi"you're lying, ina kaga wayan da zaka iya ɗauko rigarshi ka sanya? tayi maganar tare da kai hannu tana jan kumatun shi, "Faɗa mun gaskiya My baby boy, ko mamie ce ta sanya maka ita"? Girgiza mata kai yayi"kintan Allah wlh ni nata, in na miki ƙarya Allah ya ƙona......" bata bari yakai ƙarshen maganr ba, ta ɗan hambare bakinshi" Bana haka irin wannan rantsuwar ba?ba'ajin magana ta ko"? ashagwa6e yace"Ae ae nima musha naji yana yi," tsoki taja, shiyasa batason Junaid Yana zuwa wurin shi, duk a wurin shi yake koyan wannan rantse rantsen marasa kan gado, dole sai ta ja mashi kunne, Ya daina Yi agaban ɗanta, tun da yaron wayau ne dashi komai ɗauka yake yi acikin kanshi, "Kadaina kaji babu kyau," amsa mata yae"Toh, in na daina zaki kai ni wurin Angela"? Murmushi tasaki tare da cewa"Da alama kana son ƴar uwar nan taka junaid, sai dai bansan ya za'ae in kaika wurinta ba, Nima nemanta nake yi...." cikin sanyin murya takai ƙarshen maganar, duk inta tuna su sai taji zuciyarta ta karaya, Almost 4 years kenan babu su babu labarinsu, ' Ɗaukar Junaid ta yi a hannunta ta miƙe ta ɗaura shi saman gadonsu, tana fadin"ka koma bacci dan Allah my baby boy, bana so kayi ta 6arna pls," amsa mata yayi"to" ya lumshe idanuwanshi alamar bacci zaiyi, ƙura mashi ido tayi tana kallonshi batare da ƙyaftawa ba, Shafa fuskarshi tayi da hannunta, kafin ta zauna daga gefen gadon, takai hannu ta ɗauki wayarta dake ajiye saman bedside drawer, Gallery ta shiga, ta lalubo tsoffin hotunansu tana kallo, Wani hoto ta buɗo wanda suka yi su uku, Ranar graduation ɗinsu akayi masu hoton a University of Hagen, dake a ƙasar germany, su uku su kayi hoton kowannasu yana asanye Cikin Graduation gown sunyi matuƙar yin kyau, Allah yayi halitta ta farko Aneelerh ce, A tsakiyarsu Benazir ce kyakkyawar balarabiya, Ta ƙarshe kuma wata aminiyarsu ce masha Allah, Matar akwai diri kamar ita ta ƙera kanta, kowacce da irin baiwar kyan da Allah yayi masu, sai dai kash gaba ɗayansu a halin yanzu ƙaddarar rayuwa tayi silar tarwatsewarsu, A tsanake take kallon hotunan nasu, tayi matuƙar yin kewar aminnanta, bazata ta6a manta irin shaƙuwar da su kayi da juna ba, runtse idanuwanta tayi tana tuna wasu maganganun da suka jima suna yi mata yawo acikin kanta, ɗaya daga Cikin aminnan nata ne ta furta su a cikin text message da ta ta6a tura mata lokacin da take Cikin tashin hankali tace"Aneelerh bazan Iya jurewa ba, ko gaisuwata bai amsawa, bansan shi wani irin uba bane, ni dai banyi dacen iyaye ba, Yanzu haka da nake rubuta maki text ɗin nan, Ina akan hanyar zuwa airport wlh idan nabar ƙasar nan bazan sake dawowa Cikinta ba, tun da yace baison gani na, aneelerh agaban kowa Yaci mutunci na, agaban maids ɗin gidanmu, yayi mun korar kare hada tsine mun yayi kamar wani jahili shi baisan ƙaddara ba ne? Idan har na biyewa zuciya zansha poison ne in mutu........" Sosai aneelerh ta fashe da kuka, lokacin da ta kammala tariyo abunda ya faru, A fili tace"Allah sarki Aisha! Bansan A ina zan ƙara ganinta ba, Allah ya kare ki aduk inda kike, ni shaida ce akanki, Ke mutuniyar kirkice, bana fata, ƙaddarar rayuwa tayi silar canzaki daga yadda nasanki, ' Cikin shessheƙar kuka aneelerh tace"Narasa Aisha saboda korar karan da mahaifinta yayi mata, na kuma zo narasa Benazir, duk da ita don san ranta ta gudu, daga baya kuma Narasa Mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata, " jefar da wayarta tayi saman mattress, Ta kifa kanta Jikin pillow, junaid tuni ya jima da komawa bacci, Tasha kuka kafin bacci yayi awon gaba da ita, Wuraren ƙarfe 9 na safe, Mami ta shigo ɗakin Jikinta sanye da atampa , murmushi ta saki ganin yadda uwa da ɗanta suke ta sharar bacci, Girgiza kai ta ɗanyi "Jikana mai abun ban mamaki, dama nasan bai wuci nan ka gudo ba, wurin mommyn taka, bayan ka sace mun rigar mijina, Allah dai ya shirya mun kai,' Takai ƙarshen maganar, tare da ƙarasawa Cikin ɗakin agaban gadon aneeleerh ta tsaya tare dakai hannu tana ɗan bubbuga kafarta" Daughter baccin ya isa haka, Ki tashi muje muyi breakfast," Buɗe ido aneelerh tayi sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, koda ganin busassun hawaye akan fuskarta, sai mami ta ɗaure fuska"aneelerh when zaki daina kuka? Sai kace wata ƙaramar yarinya? Abu kaɗan sai kuka duk kin maida kanki wata sauna," rai aɗan 6ace tayi maganar, yayin da take zama gefen gadon idonta akan fuskar aneelerh, Miƙewa zaune aneelerh ta yi, batare da tace komai ba, "Fada mun me kuma ya saki kuka"? Muryarta a disashe tace"Mami kiyi hakuri idan kukana ya 6ata maki rai, nasan bakya son ganin zubar hawaye na, nima ba so nake yi ba, sai dai wani abunne ko nayi kokarin na danne saina kasa, idan ba hawayen na zubar ba, bana jin daɗi," yanayin yadda tayi maganar ba ƙaramin kashe ma mami jiki tayi ba , Ruƙo hannayen aneelerh tayi acikin nata"Aneelerh, kodai zaki ɗauki shawarar mahaifinki ne, ki koma abuja gidan Uncle ɗinki da zama? ina ganin kamar in kina acan zaki fi samun sauƙi acikin zuciyarki, amma zamanki anan sam babu cigaba," girgiza kai aneelerh tayi yi"Mami dan Allah kudaina yi mun maganar komawa gidan uncle da zama, ya kuke so nayi da rai na? A halin da nake Ciki, ku kaɗai nake gani inji sanyi acikin raina, indai nayi nesa da ku, bazan ta6a samun natsuwa ba" takai karshen maganar fuskarta a yamutse, Mami ta fahimci halin da aneelerh take Ciki, dama tasan zaiyi wuya ta amince tayi nesa da su, "Shikenan, bazan ƙara yi maki zancen komawa can ɗin ba, ina fata hakan yayi maki" jinjina kai aneelerh tayi alamar eh, "Yanzu ki tashi ki shiga toilet ki wanke fuskarki sarkin kuka, Allah idan baki daina ba sai yaronki ya raina ki, ga shi nan yanzu shima ya fara zama irin ki, ko kallon banza mutun yayi mashi sai ya fara ta6e baki zaiyi ma mutane kuka," murmushi gefen fuska aneelerh ta saki, tare da juyawa tana kallon junaid dake kwance, har lokacin wuyanshi na sanye da cazbaharta daya sanya, Dariya mami tayi don ita sai lokacin ta lura da cazbahar da ke sanye a wuyan junaid, "Wayaga ɗan Sarkin malamai," dariya sukayi atare, gwanin ban sha'awa, Miƙewa mommy tayi"xan koma dining ki same ni acan ina jiranku," Amsa mata tayi da toh mami, kafin ta sauko daga saman gadon ta shige toilet, after some minutes ta fito tana gyara doguwar rigar material ɗin dake ajikinta,' Har lokacin Junaid Bai farka ba, tasan dole yana jin yunwa, hannu takai tare da ɗauko shi, aikuwa kamar ta tsunkule shi, Yaita kuka yana fadin shi bai gaji da baccin ba, tana dariya tace"Am sorry My baby Boy, breakfast zamuyi da zarar mun kammala, Sai ka koma baccin ka, daƙyar ta samu ta shawo kanshi Ya daina kuka, Toilet ta shiga da shi, ta yi mashi wanka, ta fito dashi sa6e saman kafaɗarta, ta nado shi Cikin towel, Gyara mashi Jikin shi tayi kafin ta sanya mashi riga da wando, rungume dashi ta fito ta nufi dining table, Mami ta hango a zaune tana Shan tea, Kujera taja ta zauna suna fuskantar juna da mami tace"ɗazu ban gaishe ki ba, My first love, Ina kwana mamina, ina fata kin tashi cikin koshin lpy," fuskar mami dauke da murmushi ta amsa mata da cewa"Alhamdulillah, my lovely daughter, Ya grand son ɗin nawa naga yana ta tur6une fuska uwa alkubus, halan tashinsa ki kayi daga bacci"? Takai ƙarshen maganar idonta akan junaid, dake zaune saman cinyar mommynsa, sai shan mur yake yi, yana hura hanci, Shi an takura mashi, "Mami saboda fa ya ci abinci na tada shi, amma da yake shi baisan abun arziki ba, shine yake ta hura mun hanci," Mami tace"kwantar da hankalin ki, ae da zarar yayi arba da noodles zai wartsake" hannu mami takai tare da ruƙo plate ɗin dake shaƙe da noodles ta tura ma aneelerh agabanta, Hannunshi har kerma yake yi wurin kokarin tsoma shi Cikin taliyar, da sauri aneeleerh ta damƙi hannun nashi tare da cewa"Baka ga akwai zafi ba? So kake bakin ka ya ƙone"? ta6e baki ya soma yi alamar zaiyi kuka, lallashin shi ta shiga yi"haba my baby boy, Fushi ba naka bane bari na baka da hannu na" hannu ta sanya ta soma ɗibowa tana bashi abaki yana Ci, "Mami Ina abie? Ko har sun tafi"? Jinjina kai mamie tayi"tun yaushe kuma, tun bayan sallar asuba yace mun bazai dawo gida ba, daga can zasu wuce, " "Shi ne ko ya jira muyi sallama dashi" rai adan 6ace tayi maganar, mami tace"sauri yake yi ne, idan mun kammala cin abinci sai ki kira shi awaya ki yi mashi Allah ya kiyaye hanya," amsa mata tayi da toh, daga haka suka Cigaba da cin abincin su, *south korea🌹* Seoul City, Hajiya adama ce zaune saman Sofa mai mazaunin mutun uku, A cikin katafaren Palourn gidansu, jikinta na sanye da doguwar cord lace milk colour, idanuwanta na a manne da farin glass medicated, Ta natsuwa tana daddana laptop ɗinta dake asaman Table ɗin gabanta, da alama Komai ya daidaita don yanayinta bai nuna tana acikin damuwa ba, Gaba ɗaya ta tattara kwandon hankalinta akan aikin da take yi acikin laptop ɗinta, Sautin Dirar motoci ta juyo acikin Apartment din nasu, dakatawa ta ɗanyi da daddana laptop din ta ɗago tana kallon bakin kofar shigowa falon, duk da tasan ba lallai In baƙin su bane tun da basu kaɗai bane akwai sauran mutanan dake Haya Acikin Ginin, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Uncel abdallah ne Ya shigo Falon, Hannun shi ruƙe da key ɗin motarshi, Suit ne ajikin shi, Miƙe wa Hajiya adama tayi fuskarta asake tace "Welcome back dear, I heard the sound of cars Coming in ko munyi baƙi ne"? sai da ya samu wuri ya zauna tukunna ya kalle ta fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Ni ne baƙon ae, fatan na same ki lafiya, Yau naga walwala atattare dake, Ga shi kin ɗau wanka kinyi kyau abunki," Ta6e baki ta yi "Ae tun da kayi mun albishir game da komawarmu gida, Nake ta sakin fara'a ni kaɗai abuna, Yanzu haka ma da kaganni a zaune, Ina duba kayayyakin da zan siyane na tsaraba da zanyiwa mutanan gida," takai ƙarshen maganar tare da kama hanyar zuwa kitchen tace"Bari na kawo maka Ruwa mai sanyi kasha" "Da kanki Hajiyata? Ina mai aikin gidan take ne"? A sukwane ta Juyo tana bin shi da kallon bansan rainin wayau, "Oh kamanta irin Korar da kayi ma Ajumma daga gidan nan, Saboda laifin da ba nata ba, ƴar baiwar Allah, dama burinka kaga ina shiga kitchen da girmana, ae yanzu hankalin ka ya kwanta, Hajiya adama ta zama kukun mijinta" Dariya Uncle abdalla Yayi"Matar nan kina sani nishaɗi, Abun alfahari ne mace ta girka ma mijinta abinci da hannunta yaci ya sanya mata albarka, Ta samu lada, Ni ae naga Cigaba sosai, da na kori wannan tsohuwar matar, Tun barinta gidan, kika daina shan Soju, gashi yanzu kin samu natsuwa kin dawo Hajiya adamar dana sani," Hararar wasa ta jefa mashi daga inda take a tsaye" korar ajumma da kayi ba shi ne yasa na daina shaye shaye ba, Da naso zan fita inje in siyo da kaina ne, Allah ne yayi silar shiryuwata, dama ba halina bane, tsautsayine da ƙaddara, da kuma damuwar da na shiga na rashin mutun uku masu mahimmanci acikin rayuwata.........." muryarta a karye takai ƙarshen maganar, da sauri tajuya ta shige Cikin kitchen, Jingina bayan shi Yayi a jikin Sofa ɗin da yake zaune, Har ga Allah Shi kanshi yana acikin matsanaciyar damuwa na rashin ya'yan shi da ya yi, Yaji raɗaɗi sosai, sai dai ba yadda zai yi, daure wa kawai ya ke yi, A duk lokacin daya tuna rashin Da yayi, Na ɗan uwansa, Kuma yayansa Malam zahiru, da mahafiyarsu deeja, Sai ya dinga Jin kanshi tamkar marayan da baida mafaɗi aduniya, Dama wake gaya mashi gaskiya idan yay badai dai ba? malam zahiru ne, tun yana yaro shi yake zaunar dashi yayi mashi nasiha game da rayuwar duniyar nan, kalmar da yafi faɗa mashi itace "ABDALLAH KAJI TSORON ALLAH, ' tuna wannan yasa shi kai hannu ya dafe goshinsa, Idanuwanshi suka Cicciko tab da kwalla, haƙika yaji mutuwarsu, Hatta yahana su Mahaifiyar Tajuddeen, Yaji mutuwarta sosai, Mutanan kirkiki, Mutane masu ƙima da daraja, Ajiyar zuciya ya sauke, tare da lumshe idanuwanshi, Bakomai yake tunawa ba face Tajudeen lokacin da zai raba shi da iyayenshi, Suna kuka yana kuka saboda basu son rabuwa da juna, Suna matuƙar ƙaunar ɗansu, Amma saboda son zuciya yabi ta ƙarfi da yaji don yana da arziƙi, ya ba mahaifiyarsu Cin hanci, aka damƙa mashi yaro, tun da yake bai ta6a danasanin raba tajudeen da iyayenshi ba, Sai bayan rasuwarsu, tsawon shekaru basu yi tozali da dansu ba, har sun koma ga mahaliccin su, Shi ma kuma ɗan nasu An neme shi ƙasa ko sama babu shi, Wannan wata irin ƙaddarar rayuwace? Yanzu idan Allah yasa aka ga su tajudden Taya zai Iya Sanar dashi game da mutuwar Iyayenshi!!? innallahi wa'inna ilaihirraji'un............ Tun ɗazu Hajiya adama ta fito daga cikin kitchen, hannunta ruƙe da plate mai ɗauke da glass cup na ruwa mai sanyi tare da snacks, ta jima a tsaye tana kallon Mijinta nata da ya yi zurfin Cikin tunani, Hawaye ta gani kwance a cikin idanuwanshi, Da alamun damuwa attare da shi ba kamar yadda ya shigo mata ba, A saman C table ta ɗaura plate ɗin dake hannunta, Kwala mashi kira Tayi A firgice yakai idanuwanshi akanta yana kallonta "wai lafiya dear, Ina ta kiran sunanka Amma hankalinka sam baya atare dakai, Meya faru ne? Yanzu fa nabarka fuskarka asake, amma kuma na dawo na taras dakai cikin damuwa" tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki Cup ɗin ruwan ta miƙa mashi, Hannu yasa ya kar6a, tare da kaishi saitin bakinshi yana sha, Zama hajiya adama tayi tana fuskantar shi, Jira take yi ya gama sha yayi mata bayanin dalilin shiga damuwarshi, A hankali ya sauke Cup ɗin saman table, ya zura hannu Cikin trouser pocket ɗinshi ya zaro hanky ya goge fuskarshi, sai da ya daidaita natsuwar shi tukunna ya kalle ta, gaba ɗaya hankalinta na akanshi, sam baison ya faɗa mata dalilin shiga damuwar tashi, don yasan halitta, Yanzu ta kama yi mashi kuka, shiyasa ko zancen su Taj bai cika son yi mata ba, Rauni ne da ita, Gudun kada ta ƙara tambayar shi meke damunshi, yasa shi yin saurin canza zancen ta hanyar cewa"Yawwa, Yanzu wani shirye shirye yakamata muyi na komawa Ƙasar mu? Naji kince zaki yi siyayyar kayan tsaraba da zaki yi ma mutanan gida," Jinjina kai Hajiya adama tayi tare da cewa"eh, idan ya rage kamar saura 4 weeks Mu tafi, Inaso zamuje Shopping mall atare, Akwai kayayyakin da nake so Na Siyawa ƙanne na, kasan su mayun kallon korean drama ne, suna san suturarsu ba ƙaramin burgesu yake yi ba, inaso na siya masu, hada Jikana zan siyawa kayan wasan yara, da kayansu na al'ada suna burgeni, ita Fatima ma hada cewa in yi masu tsarabar abincinsu, In banda shiririyata, zan dai siya masu chocolates ɗinsu kalar wanda bamu dasu a gida, " magana take yi mashi amma hankalin shi gaba ɗaya baya akanta, har saida Tace"Kai fa? Me zaka yi tsaraba da shi Murmushin yaƙe ya yi mata, muryarshi a karye yace"Wa nake da shi da zanyi ma tsaraba? Dama ƴa'ƴana ne, yanzu kuma babu su, amma duk da haka zan siyawa Angel kalar suturarsu, a ƙiyashin da nayi yanzu takai 15years a duniya, Zan yi mata siyayya sosai in ajiye mata, hada bags and shoes da teddys, komai ma zan siya mata, duk ranar da Allah ya bayyanar dasu, sai in damƙa mata abunta,' yakai ƙarshen maganar, tare da duƙar da kanshi ƙasa, Shi kanshi baisan yayi waɗannan Zantuttukan ba, Saboda su ne aranshi shiyasa yayi maganar, Shessheƙar Kukan Hajiya adama yajiyo acikin kunnanshi, Kafin ya ɗago da kanshi tuni ta miƙe da sauri ta wuce zuwa bedroom ɗinsu, Binta yayi da kallo har saida ta 6ace ma ganinshi, Girgiza kai kawai yayi, kafin ya miƙe ya nufi ɗakin, Don ya samu yayi wanka Ya canza kayan jikinshi, *Back To Prison🥺* Mutsu mutsun farkawa daga bacci ta ke yi, eye lashes ɗinta sun manne ma juna, daƙyar ta samu ta ware idanuwanta basu sauka akan kowa ba, sai akan fine face ɗin Danish dake ta sharar bacci, kasalalliyar ajiyar zuciya ta sauke a yayin da take kallon shi cikin natsuwa, kamar wani baby ya naɗe Jikinshi cikin bargo, fuskarshi kaɗai ce awaje, tun daga kan yadda yake fitar da numfashin shi, zaka shaida yana acikin kwanciyar hankali, baƙaramin daɗi taji ba, tana fatan Allah ya yaye mashi lalurar dake damunshi, Almost 15 mins tana kallon shimfiɗarshi, kafin ta yunƙura ta miƙe zaune ta jingina bayanta a jikin bango, gadajensu batool tabi da kallo, Tayi mamakin ganin basu farka ba, Kamar wasu matattu sai sharar bacci suke yi, kowa ya kudundune jikinshi cikin bargo, sunyi matuƙar burgeta sai ta dinga jin inama ace Acikin Gidan Mahaifinta suke ba'a Cikin Gidan Kurkukun ba, da sun more rayuwarsu, tasan cewa Danginta zasu kar6esu hannu bibbiyu, musamman aunty aneelerh, da hajiya adama suna son yara sosai, taci alwashin idan Allah ya bata Ikon musuluntar dasu, Zata nema masu hanyar da zasu gudu daga Cikin Gidan kurkukun ƙaddara, Sai dai babban abunda take yi ma fargaba shine, Taya za'ae Su fita daga Cikin kurkukun da ransu da lafiyarsu? Idan Allah yasa sun samu ƙopar fita kenan, Bayan wannan abunda take matuƙar jimawa Anya kuwa GIDAN KURKUKUN ƘADDARA A cikin ƙasar Nigeria yake!? idan har ba'a Nigeria yake to kuwa dai suna acikin tsaka mai wuya! Fatanta Allah yasa ba awani ƙurmin dajin ginin yake ba, Don kuwa akan hanyar guduwa ma wata dabbatar na iya kai masu hari ta Cinye Naman Jikinsu......." Tana Cikin yin wannan Zancen Zucin nata, Karaf idanuwanta suka sauka akan danish dake ƙoƙarin faɗowa daga saman gadonshi, Cikin magagin bacci, A hanzarce ta duro daga saman gadonta tayi gaggawar tarbe shi, ƙiris Ya rage ya tiƙo ƙasa, ba don Allah yasa tayi saurin zuwa ba, da kanshi yayi mugun buguwa, Nannaɗeshi tayi tare da turashi saman gadon, Ya koma yadda yake, Ajiyar zuciya ta sauke yayin da take kallonshi, Soft red lips ɗinsa ta gani suna motsi, alamar yana sambatu, miƙewa tayi ta hau saman gadon, ta duƙar da kanta saitin la66ansa, ta natsu tana sauraron me yake cewa, _the sounds is soothing me, I can't stop listening to ur voice, pls keep reading it in my ears, am really enjoying it_ Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, jin sambatun da danish yake yi, duk akan Karatun kur'anin da tayi mashi jiya ne, ta fahimci cewa ba ƙaramin daɗi yaji ba, shiyasa ma har yake sambatu acikin Baccinsa, Whispering tayi mashi acikin ear ɗin nashi tace"Kana so In koya maka"? sam batayi tunanin zai amsa bata, sai ji tayi yace"yeah," da sauri ta kalle fuskarshi, Abun mamaki Bacci yake yi bai farka ba, amma yana magana, ƙumshe dariya tayi kafin ta ƙara cewa"Dame zaka biya ni idan na koya maka"? Tayi tambayar Tana sauraron amsar da zai bata, Cikin muryar bacci yace"I ave nothing to pay you, but I can promise you myself if you want" Cikin nishaɗi angel take dariya, A maganar da yayi mata idan har zata fassarata a matsayinta na wadda tayi rayuwa awajen kurkuku, Tamkar kalaman soyayya ne, Amma shi awurin shi bakomai bane, ya faɗi mata hakan ne saboda baida abunda zai iya biyanta da shi, idan ba kan nashi ba, "does that mean you will be my slave? If I give you an order, will you follow?" Amsa mata yayi"yeah" koda wankin Uniform ɗina ne? Tayi tambayar tana kallon fuskarshi, idanuwanshi na arufe gam, wannan karan bai bata amsar tambayarta ba, da alama ya kuma yin nisa Cikin baccin sa, Ruƙo bargon shi ta yi tare da ƙara janshi ta rufe mashi har zuwa saman fuskarshi, Tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon danish, Ta ji yo motsin buɗe ƙopa, da alama giants ne suka ƙaraso, Yau Abinci ya riga masu Cin shi, ƙarasowa, Ƙarasa saukowa tayi daga kan gadon nashi, ta tsaya a tsaye tana Jiran su ƙarasa shigowa Ciki, Takun tafiyarsu ta soma jiyowa, kafin su bayyana su ukun nan hannayensu a ruƙe da wooden trays, mai ɗauke da kayan Kalacinsu, Akan idonta suka wuce zuwa saman dining carpet ɗinsu, Kowa ya sauke Farantin dake a hannunshi, Ja da baya su kayi atare suka ƙame kamar yadda suka saba, tunani ta shiga yi Kowanene acikinsu Ya damƙeta aranar nan har yayi wurgi da ita, bazata ta6a manta azabar da tasha ba, Ta tsani giants a rayuwarta, ko son ganinsu bata yi, Saboda basu da Imani, Ga ƙarfi kamar na dawakai, ta jima tana kokwanto akansu Anya kuwa Cikakkun mutanene? Kodai half jins ne? Ta yi zurfi Acikin tunaninta, taji motsinsu, Ras taji gabanta ya faɗi ganin suna tattara kayan abincin da suka ajiye masu, aruɗe tace" ina zaku tafi da abincin mu? Bayan bamu Ci ba" babu alamun suna sauraronta, "Magana fa nake Yi maku, idan saboda suna yin bacci ne yanzu zan tashe su, pls kada ku tafi" ko waiwaye wannan basuyi mata ba, Tana ji tana gani suka haura saman bene da abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Tana Jiyo sautin garkame ƙopa da su kayi, "Ya salam" ta ambaci hakan tare da dafe kanta, muryar batool ce ta katse ta da cewa"Angel lafiya naji kina sambatu ke kaɗai"? Da sauri angel ta juya baya tana kallon batool dake kwance saman gadonta, farkawarta kenan daga bacci, "Giants ne, Sun kawo abinci kuma sun tafi dashi bansan meyasa ba"? Waro ido waje batool tayi fuskarta da alamun tashin hankali tace"mun shiga uku! Shikenan yau mun rasa abincin da zamu ci, angel meyasa baki tada mu daga bacci ba lokacin da suka zo"? Fuskarta a hargitse tayi maganar, "Ina fa kokarin in tada ku daga bacci, sai naga suna tattara kayan abincin, kuma har roƙonsu nayi su tsaya amma basu saurare ni ba....." tunkan takai ƙarshen maganarta, suka soma Jin shessheƙar kukan Parveen, gaba ɗaya suka kai idanuwansu akanta, zaune take saman gadonta, ta wage baki tana ta kuka, Jin cewa Giants sun zo sun tafi da abincinsu, Sautin Kukan Parveen ne ya farkar da sauran Ƴan uwan nasu, Hanna tana hamma tace"wai meke faruwa ne? Me akayi ma Parveen take kuka" Javed yace"Yanzu haka rigimartace kawai, duk tabi ta tashi mutane daga bacci, saboda tsabar jarabarta, Hannu danish ya sanya tare da zame bargon da ke lullu6e a jikin shi, idanuwanshi sun ƙanƙance daƙyar yake iya ware su, saboda baccin bai ishe shi ba, Haris dake faman yin miƙa yace"kun yi shiru baku bamu amsa ba, Meyasa take kuka"? Batool ce ta bashi amsa da cewa"Saboda giants sun kawo abinci, Angel bata samu damar tada mu daga bacci ba, har suka tafi da kayan abincin shine take ma kuka" saboda tsabar tashin hankali Har suna haɗa baki wurin cewa"What? giants sunxo sun tafi da abincin mu"? Amatuƙar ruɗe kowannasu yake faman baza ido, Dafe kai javed yayi"ae shikenan mun rasa abinci yau, Mu da ganinsu kuma sai gobe, kafin lokacin mun gama jigata," Yana rufe baki Rubina tace"Wlh bazan iya jurewa ba, da matsiyaciyar yunwa na farka yau...." mubeen yace"ae ba ke kaɗai ba, Cikina har wani kukan yunwa yake yi" yayi maganar yana shafa stomach ɗinshi, "Yanzu ya zamu yi kenan"? Naufal ne yayi tambayar yana kallonsu, Azeeza tace"Mu ci hakuri kawai, Idan munji ƙishi musha ruwa sai mu kwanta muyita bacci har gobe tayi, Harara Hibba ta jefa mata daga inda take zaune saman gadonta"Wannan fa ba abun wasa bane azeeza, magana ake ta babu abincin da zamuci yau, " azeeza tace"idan bamuyi haƙuri ba, to ya zamuyi" tayi maganar tana watsa hannayenta, Da buɗar bakin deeja sai cewa tayi"bakowa bane ya jamana xama da yunwa ba face angel, meyasa da suka zo baki tashe mu daga bacci ba? Saboda tsabar mugunta,' Shiru angel tayi don bazata biye mata su yi cece kuce ba, tun da ita halinta ne bata gajiya da shiga sabgar mutane, "Kodai naje na faɗa ma tsohuwa, ta taimaka tayi magana, su giants su dawo mana da abincin mu," fuska amarairaice parveen tayi maganar, tagama shan kukan nata, taga babu mai lallashinta ta haƙura don kanta, "Koda kinje babu abunda tsohuwa zata iya yi mana, kema kinsani" yasmin ce tayi maganar, fuskarta a hade, shi dai danish yayi lamo saman gadonshi yana bin bakunansu da kallo, sam baison hayaniyar da suke yi, don ba yadda ya iya ne daya dakatarsu, Bakowa Angel tafi jima tausayi ba, Sai danish sanin cewa Jiya baici abincin shi ba, ya basu suka cinye, yanzu ga shi sun rasa abincin yau, dole yafi kowa jin yunwa bawan Allah, Yau fa ba kanta, Duk jikinsu yayi laushi, Ko toilet babu wanda ya shiga don yin wanka ko wanke fuska, damuwarsu Yunwar da zasu kwasa yau, an sanyasu yin azumin dole batare da sunyi niya ba, Saukowa haris yayi daga saman gadonshi, Ya wuce gadon danish, daga ƙasa ya zuƙunna tare da ruƙo hannun danish acikin nashi, idonsu cikin na juna, yace"ɗan uwana, ya jikin naka"? Cikin sanyin murya ya amsa mashi da cewa"da sauƙi sosai," murmushin haris yayi"Am glad to hear that, Nayi kewarka sosai na tsawon kwana biyar din nan, saina ji kamar na rasa wani sashe na jikina ne" wannan maganar ta haris ba ƙaramin faranta mashi rai tayi ba, shi kanshi ya shaida irin ƙaunar da haris ke yi mashi aduk duniya bai da tamkar shi, "Haris, nima nayi missing ɗinku sosai, har bazan iya misaltawa ba........." dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, ya juya bayan shi yana kallonsu batool, "Can i talk to u"? Danish ne yayi tambayar yana kallon kowannnsu, Jin haka yasa suka sauko daga saman beds ɗinsu, suka Nufi gadon danish, a kewaye da gadon suka tsaya curko cirko suna yi mashi Yaji ki, ƙasa ƙasa da murya yake amsa masu, yayin da idanuwanshi ke akan fuskar angel dake a tsaye can nesa da su, Batool ce ta lura da kallon angel da yake yi, ta fahimci yana son itama tazo ne, amma tasan bazai iya kiranta ba, hakan yasa ita ta kira ta da kanta tace"Ki zo mana, danish yana son yin magana damu" tafiya ta soma yi xuwa bakin gadonshi ta tsaya a gefensu tare da goya hannayenta saman kirjinta, Calmly yaci gaba da cewa"dama inaso nayi maku godiya ne, bisa irin nuna kulawarku agare ni, kun damu dani sosai, nasan kunyi missing ɗina na tsawon 5 days da bana acikin ku, nima kuma duk da bana atare daku kuna araina, i luv u so much guys......" tun da ya soma magana suka natsu suna sauraronshi, Yaushe rabon da suji danish yayi magana mai tsayi irin wannan har sun manta, lallai jiki yayi sauƙi suka ayyana hakan acikin ransu, still bai janye idanuwanshi daga kan fuskar angel ba, itama shi ɗin take kallo, So yake yayi mata godiya amma ya kasa, ita kanta angel ɗin ta lura da hakan amma saita basar, Jira take taga idan zaiyi mata magana, Muryar javed ce ta janyo hankalinta wurin kallonshi" Angel Amadadin danish, muna matuƙar yi maki godiya, bamu ta6a tsammanin zaki iya taimakon shi ba, a lokacin da kika nemi alfarmar mu baki dama, Sai gashi kin bamu mamaki, Ta silarki danish ya fara wartsakewa, tabbas ke ɗin alkhairi ce agare mu, Kuma yakamata Gaba ɗayanmu mu fahimci cewa angel masoyiyarmu ce ba maƙiyiyar mu ba" ya ɗan dakata da yin maganar yana kallon fuskokin sauran ƴan uwan nashi, kafin yaci gaba da cewa"Idan har muka yi ma angel biyayya zamu koyi abubuwa da dama awurinta wanda bamu Iya ba, zata wayar mana da kanmu, kuma zata ɗaura mu akan hanyar dai dai, Amma fa shawara ce nake bamu muyi tunani," yakai ƙarshen maganar yana jira yaji amsar da zasu ba shi, Deeja ce tace"Amma ae tsohuwa tace mana kada mu yarda da ita, mu daina sakewa da ita, zata gur6ata mana tarbiyarmu ne, kuma tana yi mana ƙarya nidai gaskiya bazan yarda da angel ba, " tayi maganar tana maƙe kafaɗarta, maimakon angel taji haushin maganar deeja, Saima ta saki murmushi saboda ta lura hada quruciya ke ɗawainiya da ita, "maganar da Javed ya faɗa gaskiya ne, Angel masoyiyarmu ce, kuma komai take yi mana tana ƙoƙarine don taga mun dawo akan hanyar dai dai, Ina roƙon duk wani dake ƙyararta acikinmu ya ajiye makaman yaƙin shi, yazo mu rungumi juna, faɗa ba namu bane," a tsanake batool takai karshen maganarta, "Silar angel, danish ya samu sauƙi, bashi kaɗai ba, Tun jiya da angel ta raira mana waƙar nan mai daɗi da sanyaya zuciya, gaba ɗaya jikin kowannanmu yayi sanyi,......" dariya angel tayi jin abunda azeeza tace, "Ba waƙa bace, Karatun al'qur'ni ne mai girma, " cike da mamaki suka maimaita kalmar"Karatun al'qur'ani mai girma" Hanna tace"menene ma'anar hakan? Ko zaki iya fahimtar damu"? Tayi maganar a ƙagare da son Jin amsar da angel zata basu, Ƙoƙarin buɗe baki tayi da niyar ta ba Hanna amsar tambayarta, Sai dai kafin tayi yunƙurin yin hakan, Suka Jiyo Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Nan fa hankalinsu gaba ɗaya ya koma akan ƙopar ɗakin, Fitowa tayi daga Cikin ɗakin tana dogara sanda, Fuskarnan a tur6une babu walwala acikinta, da sauri Su hanna suka Nufe ta, Cikin girmamawa suka gaishe da ita, babu yabo babu fallasa ta amsa masu, Parveen tace"tsohuwa Yunwa muke ji, Giants sun kawo mana abinci, A lokacin bamu farka daga bacci ba, har suka tafi da shi" Jinjina kai tsohuwa ta ɗanyi tana bin fuskokinsu da kallo, Su kansu sun lura da canjin dake atattare da ita, kamar wani abu na damunta, Hanna tace"tsohuwa Baki da lafiya ne? Naga kamar bakya Acikin walwala," sai lokacin tsohuwa ta buɗe baki tace" kunyi kuskure da ku ka bari giants suka juya da abincin nan, ai kunsan basa wasa da lokaci, meyasa baku farka daga bacci ba har suka tafi? Bayan kunsan cewa Ba dawowa zasuyi ba, idan har suka tafi dashi"! Muryar Parveen tamkar zata fashe da kuka tace"yanzu shikenan bazamu samu abinci ba yau"? Idanuwanta suka cicciko da ƙwalla, angel dake acan tsaye ruƙe da qugu, ta tunkari inda suke, agaban tsohuwa ta tsaya tare dacewa"Irin ƙaunar da kike masu kenan? ashe uwa zata Iya barin ƴa'ƴanta da yunwa? Alhalin ita tacika cikinta ta ƙoshi! Waye bai kuskure rayuwa? Yin bacci ya zama laifi kenan? Inbanda rashin lissafi taya mutumin dake bacci zai zama mai laifi? Meyasa su giants ɗin da suka zo basu ajiye mana farantan abincin ba, su sai su tafi idan yaso aduk lokacin da muka farka sai mu ci, Amma saboda tsabar zalunci shine suka tattara kayan abincin suka tafi dashi, Anya kuwa tsohuwa? Cike da tuhuma takai ƙarshen maganar tana kallon fuskar tsohuwa, ta tsareta da waɗannan Jagwalallun idanuwan nata, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Haka dokar Aikin Giants suke! Lokaci gare su, basa wasa da aikinsu, idan suka kawo abinci suka ga babu wanda yazo yaci zasu kwashe ne su tafi dashi," wannan itace amsar da tsohuwa taba angel, Mamaki akan fuskar angel tace"Wannan wata irin dokace mara kan gado mara tsari? Wannan ae horo da yunwa ne! Abincin ma da sau ɗaya ake bamu shi a rana, mun ƙoshi bamu koshi ba wannan ba damuwarku bace, Shine kuma harda wata dokar in an kawo abinci bamu hallara ba, za'a juya dashi? Me hakan ke nufi? Wai mu me kuka ɗauke mu dabbobi ko me? A harzuƙe angel tayi maganar, Wata irin gigitacciyar tsawa Batool ta daka ma angel, gaba ɗaya saida kowa ya razana hatta danish dake a kishingiɗe saman gadonshi saida ya firgita ya nemi zaucewa, A matuƙar ruɗe Angel ke kallon batool, ta ɗaure fuska tamkar ba ita ba, Cikin fushi ta soma magana "Yakamata ki kiyaye harshenki aduk lokacin da zakiyi magana da tsohuwa, don me zaki dinga yi mata magana a gadarance? Babu tausasa harshe? Idan ma kina son shiga tsakaninmu da ita ne, Inaso ki sani bazaki ta6a yin nasara ba, ita ɗin uwace agare mu kuma bazata ta6a iya cutar damu ba......" ba angel ba, hatta su haris sai da suka sha Jinin jikinsu, Jin yadda Batool ke magana a faɗace abunda bata ta6a yi ba, Muryar angel adisashe tace"Batool! Yau keda kanki kike Yi mini tsawa! Saboda kawai ina son ƙwato maku haƙƙinku da aka tauye....." kafin takai ƙarshen maganarta, Javed ya dakatar da angel ta hanyar ɗaga mata hannunshi"Is enough! Kawai kiyi mana shiru, Kina so ne, Ki shiga tsakaninmu da ita, babu ruwanki da rayuwarmu, Ki barmu a yadda kika ganmu, haka muka saba rayuwa, bin dokar kurkuku wajibi ne agare mu prisoners" wani irin shu'umin murmushi tsohuwa ta shiga saki Nan da nan walwalar fuskarta ta dawo Jin yadda Suke Goyan bayanta, ashe har yanzu Hayaƙin sihirinta na aiki yadda ya dace, ta ambaci hakan acikin zuciyarta, Tuni idanuwan angel sun Ciko tab da kwalla, tsabar baƙin Ciki Ya hana ta ƙara cewa komai, Juyawa tayi a fusace ta koma saman gadonta, Ta zauna tare da ruƙo pillow ta rungume a kirjinta, Kallonsu tsohuwa tayi da alamun farin Ciki akan fuskarta tace"Ku cigaba da yi mun biyayya ƴa'ƴana, albarka zata tabbata akanku, " muryar parveen a ƙule tace"Abincin fa"? Tsohuwa ta bata amsa da cewa"Ku jira ni, Ina zuwa" ta ambaci hakan tare da juyawa ta shige Cikin ɗakinta, baka iya hangen komai ko ka leƙa sai duhu, Badajimawa, Sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya a ruƙe da Kwandon kayan marmari, Miƙa ma Su tayi" Ku je kusha, Kafin zuwa gobe zaku samu abinci" Hannunsu har kerma yake yi wurin kar6ar Kwandon daga hannunta,' Juyawa tayi tana dogara sanda ta koma Cikin ɗakinta, tare da jan kopa ta datse, Ita dai angel sam bata yarda da kayan marmarin da tsohuwa ta basu ba, Cike fa da kwando, manyan apples ne tare da damin ayaba," a kalla kowa zai samu apples uku, da Ayaba Uku, Batool ce ta rarraba masu kayan marmarin kowa ya kar6a yana sha, koda ta miƙa ma angel hannu tasa takar6a amma bata sha ba, A ƙarƙashin pillow ɗinta ta 6oye su, tana jira taga idan sun kammala sha batare da wani abu ya faru dasu ba, itama sai tasha, Har batool sai da tayi mata magana akan bazata sha ba, tace mata ba yanzu zata sha ba, Sai zuwa anjima, Tun da suka kammala Cin apples ɗinnan da ayaba, wani irin matsiyacin bacci ne yazo masu, lamarin ya ɗaurewa angel kai, Ganin su kwakkwance A ƙasa suna bacci, kamar waɗanda suka Sha kayan maye, Juyawa tayi da sauri tana kallon gadon danish, cike da fargabar kada ace shima baccin ya ɗauke shi, idonshi biyu ta same shi, ya kwantar da kanshi saman pillow, babu alamun bacci attare dashi, Su biyu suka rage idonsu biyu, Tabbas tafara zargin Kayan marmarin da tsohuwa ta basu ne ya sanya su yin bacci, da yake ita da danish basu sha ba, shiyasa bacci bai ɗauke su ba, ko meyasa tayi masu haka? Kodan kada su ji yunwa ne"? "Meyasa ba zaka sha ba"? Tayi tambayar tana kallon danish, ganin ya ajiye nashi apples ɗin a gefenshi, Cikin sanyin murya ya amsa mata da cewa"bana ra'ayi, zuwa anjima xansha" ya ƙarasa maganar, tare da miƙewa zaune, ya zuro da dogayen ƙafafuwanshi ƙasan gadon kafin ya yunƙura ya miƙe tsaye, Har yanzu jikin nashi babu ƙwari, shiyasa tun ɗazu ya gaza saukowa daga saman gadon, Daƙyar yake ɗaga ƙafar yana tafiya, Ji take kamar taje ta taimaka mashi sai dai batasan tana kusanta kanta dashi, Tafiya yake yi yana waiwayon su Haris dake baje a ƙasa suna sharar bacci, sam bai kawo komai aranshi ba, Shigewa Ƙopar toilet ɗinsu yayi, Sai da ya 6ace ma ganinta tukunna ta ɗauke idonta daga kanshi, Cike da fargabar kada ya raunata kanshi, tun da ba ƙoshin lafiya gare shi ba, Tsawon lokaci da shigarshi cikin toilet ɗin, ta Lumshe idanuwanta tare da kishingiɗawa, da niyar ta ɗan runtsa itama, Takun tafiyar mutun tajiyo acikin kunnata, tana buɗe ido ta fasa wata irin gigitaciyar ƙara tare da sanya hannu ta rufe idanuwanta, Jikinta na kerma, A matuƙar ruɗe Ya koma Cikin 6angaren toilet ɗin nasu, Ya la6e abakin ƙopa yana leƙen ta, Abunda ya faru Lokacin data buɗe ido, Karaf idanuwanta suka sauka akan Surar danish, Ya fito naked babu sutura ajikinshi, Wannan ne yasa tayi matuƙar firgita, Jikinta ya hau kerma, dole ta ruɗe saboda halittar dake gare shi, Dogone sosai komai Na jikinshi ba ƙarami bane, shi kuma tsawar da tayi ne yasa shi gigicewa ya juya aruɗe ya koma sashen toilet ɗin, Yana leƙenta, Ƙanƙame jikinta tayi ta gaza motsawa, tayi matuƙar tsorata, ranta ya 6aci sosai batare data buɗe idanuwanta ba, taci gaba da surfa mashi masifa ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai da ta gaji da zazzaga mashi masifa tukunna ta yi shiru tana faman huci har lokacin bata buɗe idanuwanta ba, Jin yayi shiru bai ce mata komai ba, yasa ta sassauta muryarta tare da cewa"Go back, I don't wanna see you naked, if you need something, you should ask me to give it to you" a ƙule tayi maganar, don ba ƙaramin haushin sa taji ba, ƙato da shi zai fito babu kaya ajikinshi, yanzu da ace idonsu Batool biyu ba bacci suke yi ba, duk haka zasu ganshi, tarasa gane wani irin mutunne shi, duk da tana yi mashi uziri na halin da yake Ciki na rashin lafiyar da take tunanin ɗaura mashi ita akayi, shiyasa ya zama wani sauna dashi, Kasa kunne tayi sosai don ta samu damar jin me yake ce mata, magana yake yi mata akan ta miƙo mashi bargonshi, yana so zai lullu6e jikinshi, Sai lokacin ta fahimci cewa, Ya wanke kayanshi, dama haka suke Yi idan suka wanke kayansu, sai su sanya bargo su lullu6e jikinsu, maimakon tunkafin ya shiga cikin toilet ɗin ya tafi da bargon shine bai tsaya ya ɗauka ba, yanzu gashi yasata kallon haramun, ta ambaci hakan acikin zuciyarta, "wait, I will hand it to you ka koma toilet" amsa mata yayi da toh, bayan wasu daƙiƙai, ta ɗan zame tafin hannunta daga kan fuskarta, ta saci kallon Hanyar toilet ɗin, Ganin babu shi yasa ta yi saurin saukowa daga saman gadonta, takai hannu saman nashi gadon ta ɗauko bargonshi, Ta nufi bakin door ɗin farko ta tsaya tare da ɗaga murya tace"Ga bargon" zuro mata da hannun shi yayi, maimakon ta miƙa mashi bargon saita tsaya tana kallon kyawawan yatsun hannunshi, sai kace bana ɗan bil'adama ba, saboda tsabar kyau, matsalarsu ɗaya basu yanke akaifa, yadda kasan hannun shaiɗanu, Ƙumba zaƙo zaƙo, "Bring me am waiting" figigit tayi jin muryarshi, harya gaji da miƙa hannu, da sauri ta damƙa mashi bargon, ya kar6a, Abakin ƙofar ta tsaya tana jiran ya kammala sanya bargon ya fito itama ta samu ta shiga wankan, Tana Cikin tsawuwar nan, Taji takun tafiyarshi, bin ƙopar tayi da kallo, Fitowa yayi, Jikinshi ɗaure da bargon daya sanya, har zuwa chest ɗinshi, Bata bari sun haɗa ido ba, Ya wuce ya nufi gefen gadonshi Ya zauna, tare da jingina bayanshi a jikin bango, Tunani tayi kodai itama ta wanke kayanta ne ? Domin kuwa tajima bata wanke su ba, har tsami suke Yi mata, Komawa tayi ta dauko bargonta dake yashe saman gadonta, da sauri ta nufi toilet ta shige, tsawon lokaci tana aciki, sai da ta kammala wanke kayan ta ta shanyasu, bayan tayi wanka ta ɗaura bargon a ƙirjinta, A bakin ƙofar fitowa daga sashen makewayin nasu ta la6e tana satar kallon danish, Sam bata so ya ganta in zata wuce, Ganin ya lumshe idanuwanshi ne, yasa ta yi tunanin yin sauri ta wuce, Cikin sanɗa take tafiya, har ta samu takai bakin gadonta ta haye ta kwanta, yinin ranar su biyu suka yi shi, ita da danish, lokacin da kayansu suka bushe ita taje ta dauko masu uniform ɗinsu, ganin ya fara bacci yasa tayi saurin warware bargon dake ajikinta, ta xura uniform ɗinta, sai daga bisani taje bakin gadon danish ta tada shi daga bacci, ta miƙa mashi nashi unifom ɗin yasa hannu ya kar6a, Ta juya ta koma gadonta, ta zauna daga gefe, idonta akansu batool dake ta sharar bacci, koda taga yana kokarin zame bargonsa don ya zura kayanshi da sauri ta kifa kanta saman pillow, ba ita ta ɗago ba har saida ya kammala sanya kayan ajikin shi, tukunna ta ɗago da kanta, Abu kamar wasa har dare yayi su batool basu farka daga bacci ba, Hankalin angel yaƙi kwanciya shi kanshi danish jikin shi duk yayi sanyi, har sauko yayi daga saman gadonshi yaje ya duƙa agabansu yana tatta6a su, wannan wani irin dogon bacci ne da mutun zai kwashe yini guda tun safe har dare? Anya kuwa tsohuwa abunda tayi ta kyauta masu? Sai kace wasu matattu, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* "Danish Ko dai inzo in kama maka, Mu mayar dasu saman beds ɗinsu? Ta yi tambayar tana kallon danish dake zuƙunne agaban Haris dake ta bacci, batare daya juyo ya kalle ta ba, yace mata eh, saukowa tayi daga saman gadon ta ƙarasa inda danish yake, yasa hannu ya ruƙe ƙafafuwan Haris ita kuma ta ruƙe hannayenshi Suka ɗaga shi zuwa saman gadonshi suka kwantar da shi, Haka suka bi kowannansu ɗaya bayan ɗaya suka ɗauko shi daga ƙasa suka mayar dashi saman gadonshi, suna ajiye batool saman gadonta, gaba ɗaya hasken ɗakin ya ɗauke duhu ya mamaye idanuwansu, basa iya ganin juna, "Bari naje na kunna fitilun ɗakin, kada ka motsa" ta faɗa mashi hakanne don tasa halin shi da ruɗu, yanzu ya rikice mata, tafiya take yi cikin ɗakin tana laluban hanya har Allah yasa taci karo da table ɗin da fitilun suke, takai hannu ta kukkuna su, ɗakin yayi haske sosai, ta ɗauko ɗaya daga Cikin fitilun ta juyo tana hasko inda danish yake a tsaye, Ya goya hannayenshi saman chest ɗinshi ya ɗan jingina bayanshi jikin bango, tunkararshi tayi adai dai inda yake ta tsaya, Da sauri ya rufe idanuwanshi saboda hasken fitilar dake a hannunta, ba ƙaramin cika mashi ido yayi ba, ganin haka yasa ta kawar da fitilar gefe, "Muje mu kwanta ko"? tayi tambayar tana kallonshi, babu musu ya amsa mata da toh, juyawa tayi gaba ta wuce nata gadon shima Ya wuce gadonshi, a tsakankanin beds ɗinsu ta ajiye fitilar, kusan atare suka haura saman gadonsu suka kwanta suna fuskantar juna, ya tsareta da sexy eyes ɗinshi yana kallonta without blinking, ganin kallon yayi yawane yasa tace"ba zaka yi bacci ba"? Wit low voice ya amsa mata da cewa"bana jin bacci," yatsina fuska tayi sam ba haka taso ba, saboda ta shirya yin amfani da wannan damar da take da ita, "Danish Baka jin yunwa? Naga jiya baka ci komai ba, yau ma kuma babu abinci, why bazaka Ci apples ɗinka ba? Sai in haɗa maka da nawa ka ci"? Angel sarkin wayau, so take yaci don shima yayi bacci mai nauyi irin nasu batool, ko ta samu ta shige toilet ɗin can ta fara gudanar da aikinta na fasa Glass window ɗin nan domin Shiga Cikin gidan Kurkukun ƙaddara, "Bana jin yunwa" shine amsar da yabata, tunani ta shiga yi ta wace hanya zata yi mashi wayau don ya yi bacci, "Tunda ba zaka yi bacci ba, to ka daina kallona mana, Ni inaso nayi bacci bana iya bacci idan ana kallona" jin abunda tace ne yasa shi yin saurin rufe idanuwanshi, Tsawon mintuna angel tana kallon shi, tunanin kiranshi tayi don taji idan yayi bacci" Danish" amsa mata yayi"yeah" wai bazaka runtsa ba, da buɗar bakin sa sai cewa yayi"If you don't sleep, nima bazanyi ba." serious yae maganar, rufe idanuwanta tayi"its okey, ga shi nan zanyi baccin kaima kayi" Ya amsa mata da toh, daga haka kowa yayi tsit acikinsu, A lokacin da tayi tunanin ya nutsa cikin Baccin shi, ta sauko daga saman gadonta, takai hannu ta ɗauki fitilar da ta ajiye a tsakankanin beds ɗinsu, cikin sanɗa take tafiya tana tunkarar sashen toilet ɗinsu, duk taku ɗaya saita waiwo ta saci kallon Shimfiɗar danish, Tana kawowa bakin ƙopar shiga sashen ta afka ciki, ta buɗe toilet ɗin ta shige taja ƙopa ta garƙame ta, A ƙasa ta sauke fitilar, ta taka zuwa gaban bokitin ƙarfen nan ta ɗauke shi, tsayinta bazai kai ga tagar ba, dole sai ta ƙara da tsalle, cike da ƙwarin gwiwa ta daddage ta daka uban tsalle ta ɗaga Bukitin ta bugashi jikin glass ɗin da iya ƙarfinta na ƙarshe, sai dai wani abun mamaki glass ɗin Ko zagewa baiyi ba, Kamar ta daki ƙarfe ashe abun bana wasan yara bane, Tsalle taci gaba dayi tana kwaɗa bokitin jikin glass ɗin a ƙalla tayi kusan sau Talatin amma glass ɗin Ko yaƙi tsagewa, jikinta duk ya saki ga uwar zufa dake tsastsafo mata, sai faman haki take yi kamar wadda tasha uban gudu, ta galabaita sosai, sauke bokitin tayi ƙasa, ta zukunna tana mayar da numfashi, hatta idanuwanta sai da suka Canza launi, Idan tahuta ta dawo normal saita kuma mikewa ta ɗauki bokitin Ta cigaba da buga shi jikin Windon, Har saita galabaita tukunna saita koma ta zukunna tana haki, A wannan Karan Da azama ta miƙe ta ɗauki Bokitin ta daddage ta ɗaga shi da niyar ta kwaɗa shi jikin glass ɗin, kwatsam Taji motsin mutun acikin Makewayin, Ras gabanta yayi wani irin mugun bugu, tsananin tsoro ya bayyana akan fuskarta, batasan Lokacin data jefar da bokitin hannunta ba, Sam ta kasa juyawa taga wanene Ya shigo Cikin toilet ɗin, Bayan kafin ta shiga sai da ta garƙame ƙopar ta ciki ta sanya jam lock, ta yadda ba wanda zai iya shigowa, tabbas kuwa wannan ko wanene to ba mutun bane sai dai aljani, tuni tasha Jinin jikinta, Zufa ta ko'ina ta shiga wanko mata, Takun tafiya taci gaba da ji ana tunkaro inda take, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, kafin tayi tunanin juyawa baya taga wanene taji an rungumeta, sai da ya zagayo da hannayenshi saitin shafaffan cikinta tukunna ta gane wanene, tsabar ruɗi takasa furta komai, muryarshi ta juyo ƙasa ƙasa yana faɗin"mu koma ɗaki, i was scared of being alone, kin tafi kin barni ni kaɗai," tashin hankalin da ba'a dama shi date! Kwanto da kanshi yayi ta gefen wuyanta, tsigar jikinta duk ta tashi, domin kuwa wannan daƙyar ya kasance danish ne! Taya akai ya shigo toilet ɗin bayan tayi locking ƙopar, saukar numshinsa taji asaman skin ɗinta, sai ƙara ƙanƙameta yake yi yana faɗin su koma ɗaki," acikin zuciyarta ta shiga ambaton"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin," Daƙyar ta samu ta daure ta cije Takai hannu ta raba hannayenshi daya tamke cikinta dasu, a ruɗe ta juya tana kallon fuskarshi, dagaske dai shi din dai ne, danish da ta bari akwance yana bacci, da sauri takai idonta kan ƙopar toilet ɗin don taga idan ta nan ya biyo, wani abun al'ajabi, ƙopar a datse take da jam lock ɗin kamar yadda ta barta, kallonshi tayi sai faman lumshe idanuwanshi yake yi, "Ki wuce mu tafi, bacci nake ji" yadda yayi mgnr voice dinshi a raunace, Babu musu ta yi gaba yabi bayanta, abakin ƙopar ta tsaya ta cire jam lock ɗin, tasa kai ta fuce yana abiye da ita, ta yi tsammanin Idan aljani ne zai 6ace na aihin kuma ta ganshi kwance saman shimfiɗarshi sai da ba haka ta gani ba, Shi ɗin daine da kanshi ya taso, Tabɗi akwai gwarama domin kuwa dole ɗaya ya kasance gaskiya, Danish Ana sarrafa shi? Ko kuwa yana da sihiri ne ajikinshi ne? Ita damuwarta ba faɗo mata da yayi cikin toilet ba, a'a Taya akai ya shiga bayan ta sanya jam lock ta Ciki? Ta ina ya shigo? Takai ƙarshen zancen zucin nata tare da haye wa saman gadonta, shima ya hau nashi gadon ya kwanta, yana fuskantar inda take kallo, Zuba mashi ido tayi cike da tuhuma, shi kuwa ya lumshe ido alamar bacci zaiyi, ta jima tana kallonshi kanta ya gama ɗaure wa, daga bisani ne bacci yae awon gaba da ita, tsakar dare ta farka ta miƙe tabi kowani gado ta tofe su da addu'a, Bayan ta kammala ta koma ta kwanta wani sabon baccin ya kuma ɗaukarta, *in the morning🌹✍️* A washe garin ranar, tun kafin ta farka ta soma Jin hayaniyar su Batool, tsabar farin ciki yasa tayi saurin kai hannu ta zame bargon jikinta, ta ware round eyes ɗinta tare da kallon gadajensu, a zazzaune ta same su sai surutu suke yi kamar ba waɗan da suka sha uban baccin nan ba, na yini guda, Miƙewa tayi zaune ta sauko daga saman gadonta, a hankali take tafiya tana binsu da kallo, a lokacin danish bai farka ba, yana naɗe Cikin bargonshi, Abakin gadon Batool ta tsaya tare da kasa kunne tana sauraron firar da suke Yi "ko wanka bansamu nayi ba, Jikina duk tsami yake yi mini, tun ɗazu da muka ci apples ɗin nan bacci ya ɗauke mu bansamu nayi ba" azeeza ce tayi maganar, Batool tace"Nifa nayi mamaki, ya akai mu kayi bacci daga Cin tufa da ayaba, kuma ba'a floor muka kwanta ba, to waye ya dawo damu saman gado"? Fuskarta da alamun ruɗi tayi maganar, "i was confused, na kasa gane tsawon wani lokaci muka ɗauka muna yin bacci, amma gani nake kamar bamu daɗe ba, tun da har yanzu safiya ce" Ƙumshe dariya angel tayi jin abunda suke tattaunawa, wai su duk a tunaninsu suna a jiya ne, basu san cewa sun ɗauki tsawon rana ɗaya suna bacci ba, har wata ranar ta shigo, kamar waɗan da a kayiwa wahayin surutu, Sumar kawunansu duk ta cukurkurɗe, Bakunansu hada yawun bacci, "Yanzu haka zamu yini kenan muna jin yunwa babu abinci'? Nifa apples ɗin da tsohuwa ta bani ba abunda ya tsinana mini saboda wata irin matsiyaciyar yunwa nake ji" acewar parveen, duk fa wannan surutun da suke yi basu san cewa angel tana atsaye ta ruƙe ha6a tana kallonsu, "Yanzu ya zamuyi kenan? Sam lokacin baya tafiya yadda ya dace, Nayi expecting ɗin ma idan muka farka daga bacci zamu ga marece yayi amma sai naga wai har yanzu muna a safiya" baki a kumbure Hanna tayi magana, Ita dai deeja sai buga tsoki take yi, abun ya motsa, haris na kwance saman gadonshi idonshi na fuskantar ceilling, Juyawa angel tayi tare da kallon shimfiɗar Danish, samun shi tayi a kishingiɗe, For the first time da ta ta6a yin tozali da Kyakkyawan murmushin akan fuskarshi, masha Allah, Waya ga zumar kyau, Dimples ɗin shi biyu sun lotsa sosai, yadda kasan kanshi farau kyau, ɗan zaro ido tayi tana kallon fuskarshi, farkawarshi kenan daga bacci, gaba ɗaya hankalinshi na akan su batool dake ta faman yin sambatu, Su yake yi ma murmushi jin wata shiririta, Su ɗauki tsawon Yini ɗaya suna bacci, Su kwana suna bacci amma suna faɗin cewa Basu son komai ba, Rashin ma bugi ne ke damunsu Ɗauke idonshi yayi daga kansu batool, ta wutsiyar ido ya hangi angel tsaye tana kallonshi, da sauri ya kalleta suna haɗa ido, ya ɗauke murmushin dake akan fuskarshi, Can kuma ya kifa kanshi saman pillow, girgixa kai tayi fuskarta dauke da murmushi aranta tace"Ka gama rowar murmushin naka, wata rana abanza xaka dinga yi mini shi batare dana roka ba," Gyaran murya tayi masu Batool, kamar masu jira kusan atare suka ɗago suna kallonta, har suna haɗa baki wurin ambaton sunanta"ANGEL"! saukowa Batool da azeeza su ka yi daga saman gadonsu suka nufi inda take a tsaye, rungumeta azeeza tayi tana faɗin"Angel kema kinyi bacci da kika ci apples," Bata bata amsa ba, sai da tafara zagayo da hannayenta saman bayan azeeza tukunna tace"Ae ni banci appales ɗina ba, Ni da danish, Ku da kuka Ci ku kayi bacci, gaya nan yanzu kun wartsake," ɗagowa azeeza tayi daga kan Jikin angel tace"Amma ae lokaci bai motsa ba, har yanzu fa safiya ne, yau zamu yini muna jin yunwa" aɗan shagwa6e tayi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba angel ba, "Sister"! Batool ce ta ambaci sunanta, tana atsaye kusa dasu, ruƙo hannunta Angel tayi acikin nata tace"My other half, nayi missing dinki, ina fata kin tashi lafiya, an sha bacci" lumshe ido batool tayi fuskarta a yamutse tace"am not feeling well, sai nake ji kamar wani abu ya faru da muna bacci, na shiga ruɗu," janyota angel tayi zuwa jikinta, ta rungume ta, batool ta kwantar da kanta saman kafaɗar angel, hannu tasa tana shafa bayanta tace"Ki kwantar da hankalin ki, ba abunda ya faru, bacci kawai kuka sha," ajiyar zuciya batool ta sauke tare da raba jikinta daga na angel, still idonsu acikin na juna "Yakamata Ku je ku yi wanka, bazan 6oye maku ba, tsami ku ke yi, daurewa kawai nake Yi ina yin magana daku" cikin zolaya tayi maganar, gani tayi suna shinshina Jikinsu, harara batool ta jefa mata"Sister kinyi wanka shine baki tada mu daga bacci ba, Munyi wanka mu ma,"? Fuskarta akwa6e tayi maganar, "Ae ni bana tada mutun idan yana bacci, yanzu tun da kun farka, sai kuje ku yi," Juyawa batool tayi tare da kallonsu Hibba dake zaune saman gadajensu, Ko motsawa basuyi ba, "Ku tashi muje mu yi wanka," saukowa Kowannan su yayi daga saman gadon shi, "Jiya nida danish mun wanke hada uniform ɗinmu," su6uce mata maganar tayi Cike da mamaki batool tace"Jiya kuma"? Da sauri angel tace"Ina nufin ɗazu da safe, lokacin da kuna bacci, ae na fada maki ni da shi bamu Ci namu apples dinba," takai ƙarshen maganar tana ƴan kame kame, Batool kamar bata yarda da maganarta ba, gyaɗa kai kawai ta yi tare da wuce ta nufi toilet, Batool ce tabasu shawarar suma su wanke nasu Uniform ɗin, Sai da kowa ya cire uniform ɗinshi, Suka yi ɗaurin gaba da Bargunansu, Hada maxan su, tattara Uniform ɗin Batool tayi ita da Angel da Hanna, Suka shiga toilet sec ɗinsu, Anan Suka tara kayan wankin, Azeeza da javed ne suka ɗebo ruwa a buckets, rubina ta ɗauko masu detergent, Su Uku Suke wankin kayan suna yi suna fira, Sauran ƴan uwan nasu ba wanda ya taya su dama su suka sanya kansu zasu wanke masu kayan, don sunce su baza su yi wanki ba kada ƙarfinsu ya qare, Gashi yau babu abinci, angel dai jinsu kawai take yi, ta ƙosa taga reactions ɗinsu idan su giants suka zo kawo masu abinci, zasu sha ruwan mamakin sanin cewa Sunyi baccin kwana ɗaya, Angel ta dage sai Cuɗa kayan take yi, Koda tazo kan Uniform ɗin haris saita yatsina fuska, Ta ɗago su tana shinshina su, A karshe ta wurga ma batool saman fuskarta tace"ki wanke su, Ni bazan wanke ma ƙato kaya ba" Dariya su kayi gaba ɗayansu, azeeza tace"Amma kuma kike wanke ma Mubeen dasu javed? Su ba ƙattan bane"? Girgiza kai angel tayi a yayin da take matse rigar data kammala Cuɗawa, tace"Idan kika lura Haris duk yafi su girman Jiki, shifa tuttu6e6ene ga Tumbi, Kuma mummuna......" bata ƙarasa maganar ba, karaf idanuwanta suka sauka akan haris dake atsaye bakin ƙofar toilet ɗinsu, Fitowarshi kenan daga wanka, ya ruƙe qugu jikinshi na sanye da bargon daya lullu6a, fuskarnan babu walwala attare da ita, harara angel ta watsa mashi, ita fa idan ta ɗauko magana ba wanda ya isa ya hana ta ƙarasawa, don haka taci gaba da cewa"sam baida kyau, Hancinshi gajere ne, gashi baƙi, idanuwanshi mitsi mitsi," tayi maganar tana murguɗa mashi baki, Tayi tunanin haris zai tanka mata, amma sai taga ya girgiza kai kawai, Ya wuce cikin ɗakinsu, Batool tace"Na lura angel baki son haris, bansan meyasa ba," takai karshen maganar tana kallonta, "batool, he hates me for no reason, that's why I don't like him" takai ƙarshen maganar, a yayin da take kai hannu ta ɗauki Bucket ɗinta, da niyar taje cikin toilet ta zumar da ruwan kumfar ta ɗebo wani ruwan da zasuyi ɗauraya da shi, A bakin fanfo, ta tsaya ta tura bokitin ta kunna tap din ruwa ya shiga kwararowa, zuƙunnawa tayi tana jiran bokitin ya cika, Bakomai ya faɗo mata arai ba, face Lokacin da Tana agida Tare da daddynta, Ita ko hanyar laundry bata sani ba, daddynta da kanshi yake zuwa ya wanke mata uniform ɗinta na makaranta, Yayi goge mata su, duk wannan wahalar bata san da ita ba, shi ne yi mata wanka ya zura mata kayan ajikinta, Allah sarki rayuwa kenan, Ganin ruwan ya Cika bokitin, yasa takai hannu ta kashe fanfon, ta miƙe ta ruƙo handle ɗin bokitin ta fuce dashi, a lokacin har su Batool sun kammala Yin nasu sa6in, saura ɗauraya, atare suka dinga ɗauraye kayan, Azeeza ce take zuwa ta shanya su asaman igiyar dake a cikin toilet ɗinsu, Suna dab da zasu kammala, Sai ga Yasmin ta faɗo Cikin toilet sec din Fuskarta aɗauke da murmushi sai faman washe baki take yi "Lafiyarki kuwa kike ta faman zabga murmushi"? Batool ce tayi mata tambayar, Daƙyar ta samu natsuwar cewa"Giants ne suka zo kawo mana abinci, " Da mamaki akan fuskar batool tace"are u serious? Jinjina kai Yasmin tayi"Ku dai kuzo muje mu ci abinci," azeeza tace"amma nayi mamaki, yau ba rabon mu kwana da yunwa," angel dai sai murmushi take saki tana kallonsu, ganin har yanzu basu gane cewa wata ranar bace ta zagayo, "Bari mu mayar da buckets din Gamu nan zuwa, Allah yasa dai ba wasa kike yi mana ba," acewar azeeza, Yasmin tace"Am serious ku dai kuyi sauri kuzo, " ta juya cike da zumuɗi ta fuce," Da sauri suka ƙarasa shanyar kayan nasu, hannayensu a ruƙe dana Juna suka Faɗo Cikin ɗakin, A tsaye suka samu Giants Sun ƙame, Ga kayan abinci nan saman dining carpet ɗinsu, A shaƙe, Su Mubeen duk suna a zazaune Kowa Ya natsu Jikinsu sai kerma yake Yi saboda tsabar yunwar da suke Ji, Ƙarasa shiga Cikin Ɗakin su ka yi, a gefen ƴan uwansu suka zauna a jere, Batool, azeeza da angel, Parveen ce ta yaye masu jan ƙyallen tray na farko, waro ido tayi tare da wage baki ganin Tsiren nama A shaƙe Da tray din, saboda yawanshi har suci su rage da anjima su ci, Wani irin maiƙo tsiren ke yi, yaji kayan ƙamshi hada su albasa da tumatur, batare da 6ata Lokaci ba, kowa ya zura hannu yana ɗaukar tsiren naman yana Ci, yadda kasa akuyoyi haka suke taunarshi, mutun ɗaya ne yake Ci atsanake tamkar baison ci, sam baison Cin abinci, karasa uban me yake ci ya ƙoshi, ranshi ne ya bashi cewar ana kallonshi, slowly ya ɗago da idonshi, da sauri angel ta duƙar da nata idon don kada ya gane shi take kallo, "Kinsa min ido sosai," ya ambaci hakan acikin zuciyarshi, "Saboda ban yarda dakai ba, kai ɗin abin tuhuma ne, dole na sanya maka ido, duk wani motsinka akan idona," acikin zuciyarta tayi maganar, tamkar ta bashi amsar maganarshi alhalin kuwa batasan me yake saƙawa aranshi ba, "Bansan meyasa kike tuhumata ba, laifin me nayi maki ne? Yayi tambayar acikin zuciyarshi, Itama tabashi amsa acikin zuciyarta"baka yi mun laifin komai ba, sai dai Ina zarginka, taya akai jiya ka faɗo mini cikin toilet? Bayan na datse ƙopa ta ciki? Taya akai ka shigo? .........." bata kai ƙarshen zancen zucin nata ba, muryar rubina ta katse mata hanzarinta, "Kuna ta Cin nama kun manta da shan ruwa" Tayi maganar tana kallon kowannan su, dakatawa su kayi da Cin naman, Hibba tace bari ta zuba masu ruwan, Bottle water ta ɗauka me sanyi, Ta tsirara masu ruwan acikin Wooden cups ɗin dake a jere, Kowa Ya mika hannu ya ɗauka yana sha, Saboda tsabar kallon angel da yake yi har sai da ya shaƙe ya hau yin tari, da sauri haris ya ɗaura hannunshi akan bayan danish yana ɗan bubbugawa, sai da ya daina yin tarin tukunna ya zame hannunshi, Dariyar gefen fuska angel tayi saboda ta gane itace silar daya shaƙe, Ta san ya tsargune da irin kallom da tayi mashi ɗazu, abunda ke faruwa su duka biyun basu yarda da Junansu ba, Shi yana kokwanton canzawarta, ita kuma tana zarginshi da ba cikakken mutun bane, tun Daren jiya daya faɗo mata toilet batare da ya kwankwasa ta cire jam lock ya shigo ciki ba, ta ina ya shigo? Shine abunda ya sanya mata ruɗi agame da shi, Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran da suka rage, Hada kayan marmarin da aka kawo masu da kuma snacks, Batool ta tattarasu ta kwashe acikin kwandonta, takai karkashin gadonta ta 6oye masu, Tattara Kayan abincin giants su kayi, Javed Ya ɗauko masu Na shekaran Jiya da suka kawo ma danish Ya miƙa masu suka kar6a, kafin suka fuce daga Cikin ɗakin, Lokacin da Uniform ɗinsu suka bushe Kowa Ya ɗauko Ya sanya kayanshi ajikin shi, Saboda tsabar Jin daɗin da su ka yi, Hanna ta basu shawarar suyi wasa, Gaba ɗayansu suka taru, a tsakiyar ɗakin nasu, raba kansu su kayi gida Biyu, mutun bakwai bakwai, sai mutun ɗaya ya rage, itace me gabatar da wasan, wato hanna, bayani ta soma Yi masu akan yadda zasu gudanar da wasan, "Duk wanda na canko acikin ku, zan rufe ma shi ido da tafin hannaye na, in matse su, zan ba shi sunan wanda zai gano mana, idan har ya kuskura bai canka dai da ba, da shi da wanda ya canko, kowa zaiyi masu dundu ɗaya abayansu, kun amince" Haɗa baki su kayi wurin cewa Eh mun amince," Duk wannan abun da suke Yi tsohuwa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta tana kallonsu, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta ɗauke da wadataccen murmushi, "Haris come out dakai zan fara, zaka gano mini deeja," fitowa haris yayi daga Jerin layin da yake yaje gabanta ya tsaya yana fuskantar sauran ƴan wasan, Hanna ta tsaya daga bayan shi ta zagayo da hannayenta saitin fuskarshi ta rufe mashi idanuwanshi da tafin hannayen ta, Tafiya su ka yi agaban layin na farko, Kowa yasha Jinin jikinshi, daga haris yakai hannu zai canko mutun, sai kaga suna girgiza kai, gudun kada yaja masu dundu, Cikin rashin sa'a haris Ya ruƙo hannun mubeen yace Itace, aikuwa gaba ɗaya suka fashe da dariya, mubeen kuwa rai a6ace yace"amma dai haris anyi hamago, kai baka gane hannun mace da namiji ne? Deeja ce fa akace ka kamo ba ni ba," Maganarshi tayi matuƙar basu dariya, hatta tsohuwa saida ta murmusa, "Kamar yarda nace a dokar wasa, Idan mutun ya canko ba dai dai ba, Da shi da wanda ya canka kowa xaiyi masu dundune, don haka Mubeen da haris ku zuƙunna ku bamu bayanku,, Mubeen yana Cika yana batsewa ya fito daga cikin layi, ya Duka shima Haris Ya duƙa, kowa ya naɗe hannun rigarshi, babu tausayi babu imani, haka suka jera layi, suka dinga kai masu dunduna abayansu, koda akazo kan angel dama haushin haris take ji, Muguwar da gwiwar hannunta ta daddage ta buga mashi ƙulli a baya, har wani sauti ya bata durum! nan take ya kife ƙasa, dama shi mubeen tuni ya zube yana mayar da numfashi ido sun ciko tab da kwalla, koba a faɗa mashi ba yasan wacece tayi mashi wannan dundun, idanuwanshi akan fuskar angel yaci alwashin sai ya rama idan idan aka zo kanta, Hanna tace"the next person is, " kowa ya kasa kunne yana jira yaji su wanene, Murmushin mugunta ta saki kafin tace"Batool! Ki gano mana Javed," Jiki ba ƙwari Batool ta fito daga Ciki layinta, Hanna ta rufe mata ido da tafin hannunta, suka soma tafiya suna Bin layin na farko, Duk wanda ta ruƙo hannunshi saita saki, harfa ta ruƙe hannun javed ta murza shi kamar tace shine sai kuma ranta ya bata cewar bashi bane, ƙasa ƙasa da murya yake ce mata ke ni ne, ki ce ni ne,' amma ina batool sai ta tsalleke shi ta ruƙo hannun Parveen, wadda tuni fitsari ya kamata, motsa lips ɗinta tayi tare da cewa"He is the one" Hanna tace"you're wrong" tayi maganar tare da zame hannunta daga kan fuskar batool, Waro ido tayi ganin parveen, gaba ɗaya suka fashe da dariya, Cikin shessheƙar kuka parveen tace"Ban yafe ba, Kinja min bala'e, " Janyo kwalar rigarta batool tayi'hakuri zakiyi, dama kinfi kowa Cin abinci yau, Kizo kawai mu basu baya suyi mana dunduna, ba yadda ta iya haka suka duƙa, kowa yayi masu dundu abaya, parveen tasha kuka, ita kanta batool saida ta matse ƴar kwalla, don da mugunta suke yin dundun, Komawa su kayi Cikin layi, next person da aka kirawo, Azeeza ce aka ce ta Canko masu Naufal, hanna ta rufe mata idanuwanta, Da yake Allah yayi mata baiwa, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita shinshina kamar mayya, wai da ƙamshin jikinsu take amfani, tana zuwa kan hannun naufal ta shinshina, sai ce wa tayi"Shi ne" gaba ɗaya suka sanya sowa, " tsohuwa fa yau ta samu abun nishaɗi, sai faman murmushi take yi, har lokacin basu son cewa tana atsaye bakin ƙopar ɗakinta ba, tana kallonsu, Babu rabon azeeza tasha dundu, angel dai sai fargaba take yi, ta ƙosa layi yazo kanta taji wa za'ace ta canko, Har Allah Allah take Yi acikin zuciyarta, Mutane na gaba da aka kira, Deeja ce akace ta gano Danish!!, hanna ta rufe mata idanuwanta suka tafi suna bin layi, duk wanda ta ruƙe hannunshi saita saki tace bashi bane, hankalin angel yayi matuƙar tashi, fargabarta kada Deeja ta cankota, taja mata bugu, aikuwa dai deeja tana zuwa gaban angel ta damƙi hannunta, har kusan fitsari saida angel tayi, aruɗe take girgiza mata kai kamar tana ganinta, har ta buɗe baki zatace shi ne, sai kuma ta saki hannun angel ta ƙara gaba, nauyayiyar ajiyar zuciya angel ta sauke hada sanya hannu ta shafa ƙirjinta, taji daɗi, Cikin rashin sa'a deeja ta canko Rubina tace shi ne" rubina taji haushi, shaƙo wuyan Deeja tayi tana jijjigata tace"saboda ke shashasha ce, ta ina hannuna yakai na danish tsayi? Ba ki ga yatsun hannayena guntaye bane? Ke baki banbancewa ne? Gaba ɗaya suka fashe da dariya, hatta danish dake a tsaye saida ya ɗan saki murmushin gefen fuska, Hanna tana dariya tace"Ba faɗa bane wasa ne, Kuyi haƙuri kuzo ku xuƙunna, Ku kar6i la'adarku" rai a6ace Rubina ta fito daga Cikin layi, takai hannu ta jan yo wuyan rigar Deeja, suka shiga tsakiya, Suka duƙa, ɗaya bayan ɗaya kowa yazo yana yi masu dundu abaya, koda aka zo kan angel, saida ta naɗe hannun rigarta, dama haushin deeja take ji, ta daddage da iya ƙarfinta na ƙarshe ta Buga mata dundu abaya, har saida deeja ta kife ƙasa tana kuka, Girgiza kai tsohuwa tayi ganin irin muguntar da angel ke yi masu wurin Yin dundu, ta kosa layi yazo kanta taga idan ita zata Iya tsira🤣 "Tun da naga mutane sun ragu, saura mutun huɗu suka rage, bazai yiyu abaku za6i ku canka ba, Sabo da za ku yi nasara Cikin sauki, don haka gaba ɗaya ƴan wasa su dawo Kan layi," hanna ce tayi maganar idonta akan su Haris dake zuƙunne suna jinyar bayansu, Miƙewa su kayi kowa yana hura hanci, Suka Koma Kan Layi, Tofa su angel murna ta koma Ciki, ganin sun koma su goma sha huɗu, "Adai dai ta natsuwa, Last 4 person da suka rage, zan fadi sunayensu, akwai Eve, Angel, danish and hibba, sai kuma Ni hanna cikon ta Biyar, Yanzu Zan koma Cikin ƴan wasa, Batool ke ce zaki wakilce ni, A matsayin alƙalin wasa, a dokar wasan Sabon alƙali zai Iya faɗin nashi sabbin dokokin," murmushin mugunta batool tasaki, harta hango haɗin da za ta yi, Fitowa ta yi daga kan layi, Ta koma ta tsaya a inda hanna take, Ita kuma hanna ta koma Kan layi ta jera da sauran ƴan wasa Idon kowa ya koma kan alƙalin wasa Wato batool, a tsanake ta soma magana" A matsayina na sabon alƙalin wasa, Ina da tawa sabuwar dokar, Mutane biyar da suka rage idan har na canko ɗaya daga Cikinsu, na bashi sunan wanda zai za6o mini, idan ya kuskura ya canko ba dai dai ba, dashi da wanda aka bashi sunan shi ya gano kowa Zai yi masu dundu A bayansu, Sa'an nan babu su babu Cin sauran abincin da muka rage, kason su za'a raba ma sauran Ƴan wasa ne su Cinye" tun da batool ta soma kora jawabi, hankalin angel ya ɗunguzuma, ba ita kadai ba hatta hibba da eve da hanna sai da hankalinsu ya tashi, Jin wannan Dokar ta batool, taya za'a raba ma sauran ƴan wasa abincinsu idan suka yi failing, akwai matsala babba, Idon batool akan Na Angel data cika ta batse, murmushi ɗauke akan fuskar batoo tace"Next person Is......." Gaba ɗaya sun baza ido suna sauraronta, hatta tsohuwa a ƙagare take da taji wa batool zata Canko, "Danish! " a hankali ya ɗago da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu kan batool, Yana jiran Jin wa zata ce ya canko, Tunkafin batool ta ƙarasa maganarta, angel ta shiga girgiza mata kai daga inda take a tsaye Cikin layi, Alamar kada tace ya gano ta, don tasan halin danish zaiyi wuya ya iya canko ta, ita da take da tarin maƙiya acikin wasan kowa so yake tayi failing don tasha dundun, expecially haris da Deeja, a ƙule suke da ita, don har yanzu basu daina jin raɗadin dundun da tayi masu ba, "Danish zaka Canko mana ANGEL, kafin mu fara zan ƙara tunasar dakai dokar wasa, idan har kayi kuskuran canko wadda ba ita ba, Kowa zaiyi maku dundu, sa'annan babu ku babu Cin abinci an jima, za'a raba ma sauran ƴan wasa naku" wani irin murmushin mugunta haris da deeja suke saki, daɗi kamar ya kashe su, don sunsan cewa Danish bazai iya canko daidai ba, saboda halinshi da suka sani, Cike da shaƙiyanci deeja tace"Ina fata Danish Ya gaza canko ki, Na rantse hatta spinal cord ɗinki sai ya amsa idan nayi maki wani mugun ƙulli" tayi maganar tana kwatanta yadda zata bugu bayan angel da hannunta, gaba ɗaya suka sanya dariya, angel kuwa ta ɗaure fuska babu walwala kwata kwata, duk tasha jinin jikinta, Haris yace"ni kuwa Da gwiwar hannuna zan daki bayanta har sai ya 6urma, In yaso su Giants sunyi jinyarta a treatment room," gaba ɗaya suka sanya dariya cikin nishaɗi, idanuwan angel tuni sun cicciko tab da kwalla, tabbas ta gama karaya domin kuwa tasan danish bazai ta6a iya gano ta ba acikinsu, "Danish come forward" Batool ce ta yi maganar tana nuna shi, fitowa yayi daga Cikin layi, ya ƙarasa gaban Batool ya tsaya, saboda tsabar mugunta haris hada cewa ajira ya cire rigarshi, a ɗaure ma danish fuska da ita, don yasan tsayin Batool bazai kai na danish ba, hakan na nufin bazata Iya datse mashi ido da tafin hannayenta ba, batare daya samu ƙofar da zai iya kallonsu ba, jama'a kowa fa yaci burin bugun angela, Hannu haris ya sanya tare da tu6e rigarshi, Ya wurga ma batool ta sanya hannu biyu ta ca6eta, idon danish akan na angel da tabi ta kame kanta, kamar ta fashe da kuka, Ɗaure mashi fuska batool tayi da rigar haris, ta matse mashi ido sosai har saida yaji zafi, "U can Start" ta ambaci hakan tana kallon shi, tafiya ya soma Yi yana lalubansu, ya ruƙo hannun rubina ya saki, ya ruko na azeeza ya saki, ya ruƙo na eve ya saki, ya kuma ruƙo na parveen ya saki, Kowa ya zuba ido yana kallon shi, ya cafko hannun javed ya murza shi, Kowa yayi tunanin shi zai canka amma sai suka ga ya saki hannun, "A ƙa'idar wasan, Ba'a magana, idan na kama mutun yayi magana, kowa zaiyi mashi dunduna Biyu, sannan ya rasa abincin shi, Bayan wannan kuma Zai wanke mana uniform ɗinmu idan su ka yi ɗauɗa, zai kuma wanke toilets ɗinmu, Bayan wannan kuma ɗan wasa yana da damar da zai iya ta6a ko'ina ajikin sauran ƴan wasa domin ya samu damar canko wanda akace ya za6a, wannan ba laifi bane" alƙaliyar wasa ce ta kora masu wannan jawabin, tayi hakanne don tasan halin angel da shegen wayau, tana iya cewa zata yi ma danish raɗa don ya gano ta, Cigaba da tafiya Danish Yayi yana ruƙo hannayensu, yana zuwa kan saitin angel ƴan hanjin cikinta suka kaɗa, kowa ya tsaresu da ido, jira kawai suke su ga idan danish zai iya gano ta, Ruƙo hannunta na dama yayi da hannayenshi biyu, ya shafa su ya matsasu sosai, runtse idanuwanta ta yi jikinta na kerma, ba halin tace mashi itace, saboda idon kowa dake akansu, Sakin hannunta ya yi, nan take su deeja suka soma Sakin murmushin mugunta, wani irin wahalallan yawu ta haɗiya, A wani slow danish Ya ɗaga ƙafarshi har zai wuce sai kuma ya ɗan dakata, kowa ya baza ido yana kallon ikon Allah, Komawa ya yi gabanta ya tsaya tare da miƙa hannu tamkar zai kamo hannunta, sai kuma ya kauce hannunshi ya cafko sumar kanta, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, cikin sanyin murya yace"she's the one, am i right? Gaba ɗaya su Azeeza suka Daka sowa suna Tafa mashi hannu, hatta tsohuwa saida Ta ɗanyi murmushi duk da ba haka taso ba, amma Abunda ya burgeta kaifin basira irin na danish, yayi wayau, saboda yayi amfani da yanayin kakarwar da jikinta keyi, da ya ruƙo hannunta da farko ya fuskanci hakan, shiyasa ya sake dawowa ya kai hannu kamar zai damƙi hannunta, sai yayi wayan kaucewa ya damƙi gashin kanta, saboda yasan idan itace, zai samu gashin kanta har wurin qugunta, wato danish yayi amfani da kwakwalwarshi, Wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya angel ta sauke, lokaci ɗaya kuma ta fashe da wata irin mahaukaciyar dariya hada dafe ciki, Taji daɗi data tsalleke tarkonsu Haris da deeja, kamar su fashe da kuka saboda tsabar 6acin rai da takaici, plan ɗinsu ya rushe, Sai da ta kammala shan dariyar, tukunna ta sanya hannayenta biyu ta warware ma danish ɗaurin da akayi mashi akan fuska, bayan ta kammala ta xame rigar tare da wurga ma haris ita saman fuskarshi, rai a6ace haris ya ca6e rigarshi yana faman kumbura baki Natsuwa tayi tana kallon danish dake ta faman ƙoƙarin bude idanuwanshi, eyes lashes ɗinshi sun cukurkuɗe sun hana shi buɗe ido, matsawa tayi kusa dashi sosai, ta sanya yatsun hannunta wurin buɗe mashi idanuwan, yadda zai gani da kawai, Fuskarta ɗauke da murmushi tace mashi"thank u so much danish, ka taimake ni, da yau an karya mini spinal cord ɗi na, gaba ɗaya suka saki dariya, banda haris da deeja, Ruƙo hannunta danish yayi acikin na shi, ya jata suka koma gefe ɗaya, aka cigaba da buga wasa, juyawa tsohuwa tayi batare da kowa ya ganta ba, ta koma Cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe, Lokacin da suka kammala wasan, Saman gadajensu suka koma, waɗanda suka sha bugu sai faman jinyar kansu suke yi, rabi da kwatarsu ba'a ɗauko tsawon lokaci ba suka kama baccin wahala, In the night 🌌 Lokacin da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke, suka ɗauko fitilun ɗakin suka kunna su Saman Dining carpet ɗin su, Dakin yayi haske sosai, Kowa ya samu wuri saman Carpet ɗin ya zauna, Batool taje ƙarƙashin gadonta ta ɗauko masu Kingin Tsiren namansu, Ta rarraba masu Kowa Ya kar6a Yana ci, da suka kammala Suka ci snacks ɗinsu da Sauran kayan marmarinsu, Suna Ci suna fira gwanin ban sha'awa, Bayan sun kammala Ci, Kowa ya kasa runtsawa, dama angel tayi tunanin daƙyar su iya yin bacci saboda baccin da suka sha A jiya, idanuwansu sunyi wuƙi wuƙi, babu alamun bacci, Duk suna a zaune saman gadajensu, Tunani ta soma yi kodai taje toilet ta ƙara jaraba fasa glass window ɗin nan? Wata'ƙil idan ta dage kullum tana zuwa tana Bugun jikinshi, Allah ya taimaketa ya fara tsagewa, juyawa ta ɗanyi tare da kallonsu, kowa ya kishingiɗa saman gadon shi, kallon shimfiɗar danish tayi ya kifa kanshi saman Pillow, Aranta tace Allah yasa yayi bacci, kada yayi mini irin na jiya, don na lura akwai almatsutsai akanshi, ba shi kaɗai bane, Zuro ƙafarta ƙasa tayi daga saman gadon, ganin sun rufe idanuwansu yasa ta lalla6a cikin sanɗa taje gaban Carpet ta ɗauki fitila, da sauri ta wuce ta shiga sashen toilet ɗinsu, Taja ƙopa ta garƙame ta, ajiyar zuciya ta sauke yayin da bayanta ke ajingine da ƙopar, Glass window ɗin ta ƙurawa ido daga inda take a tsaye, tana ƙoƙarin motsawa da nufin taje ta fara aiwatar da aikin fasa shi, kwatsam Tajiyo shessheƙar kuka tare da Iface iface daga Can Cikin ɗakinsu, A matuƙar kiɗime ta juya takai hannu ɗaya ta Zare jam lock ɗin kopar, da gudun gaske ta faɗo Cikin Ɗakin, Tunkafin ta ƙarasa Ciki, Ta hango su batool da hanna, agaban gadon Deeja, su javed kuma suna a tsaitsaye gaban gadon parveen, ga kuma haris da danish agaban gadon Rubina, Hankalinta yayi matuƙar tashi, Iskokai ne suka tashi Ko kuwa menene? Karasawa ciki ta yi da sauri taci burki agaban Gadon Parveen, Idonta akanta, Ta daddafe Cikinta sai juyi take yi tana kuka tana fadin Cikinta Ciwo zata mutu su taimaka mata, Arude ta kalli fuskokinsu Batool, Bakomai ta gani ba face tsantsar tashin hankali, sun rasa ya zasu yi mata, da sauri angel ta matsa gadon Deeja dake ta ihu tana fadin Cikinta ciwo yake yi mata, wuce wa tayi zuwa gadon rubina ta tsaya tana kallonta itama ta daddafe Ciki sai kuka take yi tana matse idanuwanta, fuskarta tayi jaga jaga da kwalla, Kallon Su haris Tayi muryarta na kerma tace"MEKE FARU WA NE'?_ Fuskar Haris a hargitse ya bata amsa da cewa"mu ma bamu sani ba, muna a kwance muka Ji sautin kukansu, mun rasa ya zamuyi da su" Shiru angel ta ɗanyi ta ruɗe ta rasa madafa, Komawa Tayi bakin gadon Parveen, su batool duk suna a tsaitsaye cirko cirko, a ƙasa ta sauke fitilar hannunta, kafin ta ɗago takai hannu ta janyo Parveen zuwa Jikinta, ƙanƙameta praveen ta yi sosai tana kuka tana faɗin" angel ki taimaka mun ciki na, bana jin daɗi, xafi yake yi mini raɗaɗi nake ji, Ƙura ido angel tayi tana kallon ɗigon Jinin dake ajikin wandon Parveen Nan take ta gane cewa Jinin al'ada ne, a karo na farko kenan da ta ta6a ganin sunyi jini, ta jima tana mamakin ya akai basu fara ba, saboda a shekarunsu ya isa ace sun fara Shi tuntuni saboda sun girmeta, abun ya ɗaure mata kai,' shessheƙar kukan Parveen ne Ya dawo da ita Cikin hayyacin ta, Ɗago da kanta tayi daga Jikinta, ta dafa kafaɗunta"Kiyi haƙuri kiyi shiru parveen zanje in faɗa ma tsohuwa," takai ƙarshen maganar tare da saukowa daga saman gadon, ta kalli su batool dake atsaye Cikin yanayi na damuwa, "Ku kula da su, Bari nayi mata magana tazo ta duba su, in yaso sai tayi maku bayanin Abunda ke damun su," amsa mata su kayi da toh, da sauri ta nufi ƙopar ɗakin tsohuwa takai hannu ta bubbuga ƙopar, almost 3 times tana knocking ƙopar, Kafin tajiyo motsinta, Buɗe ƙopar tayi tare da fitowa Hannunta ruƙe da sanda, "Meke faruwa ne nake Jin koke koke" tayi tambayar tana kallon Wurin gadajensu, Muryar angel na rawa ta bata amsa da cewa"ciwon Ciki suke yi Ina tunanin menstruation ne, suna buƙatar magani da kuma pads ɗin da zasu sanya" Maimakon taga damuwa akan fuskar tsohuwa sai taga ta duƙar dakai ƙasa tana sakin wani irin shu'umin murmushi, ran angel ya 6aci sosai, "Magana fa nake yi maki akan lalurar dake damunsu, don me xaki 6uge da yi mun murmushi? Maimakon Inga damuwa akan fuskarki? Kina ji suna kuka suna ihu amma ke ko ajikin ki? Ba zaki je ki duba lafiyar Jikin su ba"? Ɗagowa tsohuwa tayi tare da kallonta, da wannan Shaƙaƙƙiyar muryartata ta tsoffi ta soma magana "I ave no responsibility to check their health, the giants will come and take them to the treatment room" har saida angel ta zabura jin abunda tace, Can kuma ta wurga mata harara, "Amma dai baki da Tausayi kuma baki da Imani, taya zaki ce za'a zo a ɗauke su? bayan kina da halin da zaki iya duba su da kanki? Kenan Giants su zasu duba Lafiyar su, Ke fa yakamata ace Kin duba su, Ba wani ƙato ba," zuciyarta a harzuƙe takai ƙarshen maganar, Kafin tsohuwa ta mayar mata da martani, Suka Soma Jin motsi buɗe ƙopa daga can saman benan......................... *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* A matuƙar kiɗime angel ta juya tana kallon stairs ɗin, hatta su Batool a ruɗe suka kai idanuwansu kan benan, tunkafin ma su ƙarasa saukowa sautin takalmansu ya karaɗe kunnuwansu, Cikin takun nan nasu na majiya ƙarfi suke tafiya bakowa bane face GIANTS, a jere suka sauko daga saman Stair cases ɗin, haƙiƙa hankalin angel yayi matuƙar ta shi, Jikinta har tsuma yake yi, juyawa tayi tare da kallon tsohuwa, Cikin karyayyiyar murya tace" na roƙe ki dan Allah Ki taimaka, kada ki bari a tafi dasu parveen, abar mana su acikin mu, Ni nayi alƙawarin zan kula dasu," idanuwanta cike tab da ƙwalla takai ƙarshen maganar, Girgiza kai tsohuwa ta yi babu alamun sassauci akan fuskarta tace"Ba hurumina bane shiga abunda ba ruwana, Dokar Prison ce, Wadda bani na tsarata ba, duk wani mara lafiya za'a zo a ɗauke shi akai shi inda za'a duba lafiyar shi, idan kinga na duba mutun to ciwon bai yi tsauri bane, Giants da ki ke gani basa sauraron kowa, Koda kuwa nice, saboda ba a ƙarƙashina suke ba, dukan mu Ma'akaita ne dake aiki gidan kurkukun ƙaddara, Kuma a ƙa'ida wani baya shiga hurumin wani........." kalaman tsohuwa sunyi matuƙar girgiza angel, kafin ta yi yunƙurin buɗe baki ta furta wata kalma, tajiyo muryar parveen tana kuka tana faɗin Kada su bari a tafi da ita, mutuwa zata yi, ita bazata bi su ba ' a hargitse angel ta juya tana kallonsu, Kusan atare giants suka kai hannuwansu saman gadajensu Deeja da rubina da parveen, Wata irin ɗauka su kayi masu ta hanyar ruƙe waist ɗinsu suka yarfa su saman faffaɗan kafaɗunsu, bayin Allah Sai kuka suke Yi suna Bugun bayan giants da hannayen su, Nan take zuciyoyinsu Batool suka karaya Jikin kowan nan su yayi sanyi, har ma basu san lokacin da suka fashe da matsanancin kuka ba, Juyawa giants su kayi atare suka soma tafiya dasu ɗauke saman kafaɗunsu suka nufi stairs ɗin, Da gudun gasken Angel ta tunkaresu Tana ƙarasawa bayansu Ta cafko hannayen parveen dake abayan giant ɗin dake ɗauke da ita, da iya ƙarfinta na ƙarshen ta janyota gaba ɗaya ta faɗo ta baya, baiwar Allah jikinta sai 6ari yake yi, ɗagowa tayi tare da rungume angel ta ƙanƙameta tana kuka tana faɗin"dan Allah angel kada ki bari su tafi dani, saboda basu dawowa da mu, bana so nabar Cikin ƴan uwana bansan inda zasu kai mu ba, Ina ji araina kamar na tafi kenan......." Giant ɗin dake a ɗauke da Parveen Ya tsaya Tsak wanda ko ba'a faɗa maka ba, zaka shaida cewar A fusace yake, domin su ba'a katse masu aiki, Da gudun gaske su Hanna da su Javed suka ƙaraso Inda su angel ke a zaune ƙasa suna kuka, Kallonsu kawai take yi idanuwanta sun rune ita kaɗai tasan irin tashin hankalin da take ci, Na raba ta da ƴan uwanta da ake ƙoƙarin yi, Cikin shessheƙar kuka Batool tace" Dan Allah ki daina kuka Parveen, tsohuwa ta faɗa mana cewa Cuta ba mutuwa bace, Sai in kwanan mutun ya qare, Zasu yi maki magani ne zuwa gobe idan ku ka ji sauƙi zasu dawo mana da ku," Ita kanta batool ta karaya sosai ta yi maganar ne kawai donta ƙarfafa mata gwiwa, Zufa ta ko'ina Ajikin Parveen Muryarta na kerma tace"Koda ace ban dawo ba, Idan an kawo abinci, ku dinga ajiye mini nawa" Hawaye sharkaf akan fuskarta tayi maganar, angel dai takasa cewa komai, Zuciyarta ta gama karaya, Kafin wani ya kuma cewa wani abu, Giant ɗin yakai Hannu da niyar ya ɗauki parveen, a tsorace ta ƙankame jikin angel tana faɗin" kada ki bari su tafi dani, bazasu dawo dani ba, idan har kuna sona dagaske ku taimake ni, kada ku bari araba ni daku......" ƙanƙameta angel tayi ajikinta, Giant ɗin ya damƙi qugun Parveen, ta ƙarfi ya fisgeta daga Jikin angel ya ɗaura ta saman kafadarshi Ya juya Cikin zafin nama Ya haura saman benan, Sauran Giants ɗin guda Biyu dake a ɗauke da rubina da Deeja suna abakin ƙofar fita suna jiran ƙarasowar shi, yana daga cikin dokar aikinsu Basa tafiya dole sai suna atare da juna, wani irin jiri ne Ya rufe idanuwan angel, anan ƙasa ta kwanta idanuwanta na zubar da hawaye, Suna Jiyo sautin muryar parveen cikin shessheƙar kuka take faɗin cewa"Angel dan Allah kiyi mini addu'a, Kuma idan gobe ba'a dawo dani ba, ku ajiye mini abinci na" Wannan maganar ta parveen ta yi matuƙar kashe masu sassan Jikinsu, A nan suka wuni zuƙunne suna kuka, Mutun biyu ne acikinsu basu zubar da kwalla ba, Danish da Haris Saboda sun sa ma ransu cewa Za'a dawo masu da ƴan uwansu ne, duk da haka sun yi matuƙar damuwa da halin da su Parveen suka shiga, Na raɗaɗin ciwo ga kuma maraicin da zasu Yi na raba su da ƴan uwansu, Tsohuwa dake a tsaye Bakin ƙopar ɗakinta, Ko a ha6ar xaninta bata sanya damuwar Halin da yaran suka shiga ba, Sai da taga Sun sassauta da yin kukan tukunna Ta dogara sanda ta nufi inda suke a zuƙunne ta tsaya tana kallon fuskokinsu da suka jiƙe sharkaf da hawaye "Idan ku ka yi haƙuri, Za'a dawo maku da ƴan uwanku ne da zarar sun samu warakar Lalurar dake damun su, Kuka bazai ta6a yi maku maganin komai ba, Illa iyaka ya ƙara haddasa maku wata damuwar, Shawarar da zan baku shi ne, Ku sanyawa zuciyar ku haƙuri da juriyar rashin ƴan uwanku, kada ku cusawa kanku damu......." bata ƙarasa maganar ba angel ta yunƙura ta miƙe zaune idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, muryarta a zafafe ta soma magana "Har kina da bakin zuwa ki bamu haƙuri akan mu yi shiru mu daina kuka? Wlh tun da nake 6anta6a ganin Muguwar mace azzaluma irinki ba! Ɗan zaro ido tsohuwa tayi da kwala kwalan idanuwanta tamkar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, "Kince ke uwa ce agare su, meyasa da naje na faɗa maki cewa Cikinsu na ciwo, baki zo kin duba jikin su ba? Koda sannu ne kiyi masu Amatsayinki na mahaifiyarsu, Amma bakiyi hakan ba, sai dai wasu ƙattai suka zo suka ɗauke su da sunan zasu duba lafiyarsu, bayan ke ya dace kiyi hakan a matsayinki na Ƴa mace, duk da bani da ilmi akan abun amma auntyna ta ta6a faɗa mini cewa Menstruation lalura ce ta mata da suke yi a kowani wata, zaki iya taimaka masu idan kinso basai an kaisu wani wuri ba......" cikin shessheƙar kuka takai ƙarshen maganar, Su batul duk sunyi zugudum suna sauraronsu, "Banta6a jin tausayin wani ɗan adam ba aduniyar nan ba, kamar wadannan bayin Allah, wai su haka rayuwarsu zata ƙare? A tagayyare basu da me share masu hawayensu, basu da kafaɗar da zasu ɗaura kansu akai suyi kuka a lallashe su, Wannan wata irin Makauniyar ƙaddara ce? Tayi tambayar idonta akan tsohuwa dake a tsaye ruƙe da sanda, baka Iya gane awani hali take Ciki, domin kuwa fuskarta a haushine take, tsufanta da muninta sun ƙara bayyana Juyawa tayi da sauri tana dogara sanda ta nufi ƙopar ɗakinta, tana ƙoƙarin kai hannu ta buɗe ƙopar muryar angel ta katse mata hanzarinta "Ba zaki ce komai ba? Saboda rashin gaskiya? Zuciyarki ta bushe baki ji baki gani zalunci kaɗai kika sa agaba, wlh rantsuwar ɗan musulmi idan har ba'a dawo mana da ƴan uwanmu ba, SAI NA KASSARA RAYUWAKI, koda kuwa zan rasa raina ne' Girgiza kai tsohuwa tayi batare data waiwayo ta kalleta ba ta soma magana "Zaki Iya zagina ki ci mutuncina son ranki, saboda a yanzu ni kike ganin laifina, Unaisah ga shawara...." a ruɗe angel ke kallon bayan tsohuwa, Jin yau ta ambaci asalin sunanta, Cigaba da magana tsohuwa tayi"ME ZAI HANA KIYI TUNANI AKAN WAƊANƊA SUKA SADAUKAR DAKU A GIDAN KURKUKIN ƘADDARA? mutun baya ta6a kasancewa acikin gidan kurkukun ƙaddara dole sai in Na JININSA NE YA SADAUKAR DASHI!!, nifa ba kowa bace agidan kurkukun nan face Ƴar Aiki me rainon Yara," tsohuwa nakai karshen maganarta, ta yi saurin tura ƙofar ɗakinta ta shige taja ƙopa ta garƙame, ta tafi tabar angel da tunani, Zuciyarta ta shiga ruɗani, Kenan dama Tsohuwa bakowa bace Agidan kurkukun ƙaddara? Su kuma prisoners dake rayuwa acikinshi na Jininsu ne suka sadaukar dasu?tayaya kenan? Wata irin sadaukarwace wannan? Meyasa aka sadaukar dasu? Me za'ayi dasu? danginsu basa ƙaunarsu ne shiyasa suka sadaukar dasu ko kuwa? Wani irin matsanancin ciwon kai ne Ya taso mata, me raɗaɗin gaske, da sauri ta sanya hannu ta dafe kanta, Ɗaƙyar ta iya ɗaga kafarta ta juya tana kallonsu Batul, waɗanda ke zazzaune Cikin jimamin rashin ƴan uwansu, da alama Basu ji komai ba game da abunda tsohuwa ta tattauna da angel, "Wa suke dashi A duniyar nan? Zuciyarta ce ta bata amsa da cewa "ALLAH" biji biji take gani acikin idanuwanta, daƙyar ta samu ta iya zuƙunna agabansu, Muryarta a disashe tace"kuyi haƙuri dare yayi sosai, Ku zo muje mu kwanta, " miƙewa kowannansu Yayi, Suna jan ƙafa suka Nufi gadajensu Kowa Ya haye ya kwanta, sai da tabi su ɗaya bayan ɗaya tayi masu addu'a, taja masu bargunansu ta lullu6e masu Jikinsu, koda tazo saitin gadon Parveen sai da ta matse kwalla, bakomai take tunawa ba face kukan parveen da kuma kalamanta na karshe da take cewa Tayi mata addu'a kuma idan an kawo abinci su ajiye mata, angel tasha kuka kamar ba gobe, lokacin data zo kan gadon Deeja, tuni jikinta yayi sanyi tunawa da irin muguntar da tayi mata ɗazu da suna wasa, ta sanya gwiwar hannu ta daki bayanta harta kife ƙasa, cikin shessheƙar kuka angel ta furta "NAYI DANA SANI" Wuce wa tayi zuwa bakin gadon Rubina, Ta jima tana kallon shimfiɗarta, Kafin ta nufi gadonta ta hau sama ta zauna daga tsakiya, Hannayenta ta ɗaga sama Ta soma yi masu addu'o'i, Yayin da hawaye ke fita acikin idanuwanta, wasu na bin wasu, A daren Ranar Kowa Ya runtsa banda Angel, Ta dage sai addu'a take yi masu ta hana idonta bacci duk don saboda su Parveen, A washe garin ranar, dayawansu basu farka daga bacci ba, har lokacin tana a zaune tsakiyar gadonta, ta jingina bayanta jikin bango, fuskarta ta kumbura sumtun, tayi ja sosai, ga jirwayen hawaye, Mutsu mutsun da taji ne yasa ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta Sun kumbura ga raɗadi da suke yi mata, daƙyar ta samu ta ware idanuwan sosai, gefenta ta ɗan kalla don ganin wanene ya motsa, Danish ne ta gani zaune saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi fuskarshi babu alamun damuwa atattare da ita, Zuro da ƙafafuwanta ƙasan gadon ta yi tare da gyara zama daga gefen gadon tana fuskantar danish, Cikin sanyin murya ta ambaci sunan shi"Danish" a hankali ya buɗe idanuwanshi ya juyo yana fuskantarta, "Ka tashi lafiya"? Jinjina mata kai yayi alamar eh, ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin tace" Inaso na tambaye ka wani abu idan ba damuwa" ya amsa mata da toh, Saukowa tayi daga saman gadon, taje bakin gadonshi ta ɗan zuƙunna daga ƙasa, ta ɗago tana kallonshi idonsu acikin na juna tace "Shekaran jiya da daddare, lokacin da na shiga cikin toilet ka biyo ni, Taya akai ka shigo bayan na datse ƙopa ta ciki na sanya jam lock"? ta tsare shi da ido tana jiran jin amsar da zai bata, ɗan tahalikin nan yayi shiru yana binta da ido batare daya motsa lips ɗinsa ba balle ma tayi tunanin zai bata amsa, "Ba ka yi mini kama da maƙaryaci ba, duk da bana yarda da mutun ta yanayinsa, pls tell me the truth kawai inaso na sani ne, saboda kafin na shiga toilet ɗin sai da na tabbatar na barka a kwance kana bacci kafin na shiga ciki, Kuma ko bayan dana shiga saida na Haska ko'ina babu mutun, amma wani abun mamaki sai gaka acikin toilet ɗin, wanda nayi Imanin bata ainihin ƙopar ka shigo ba, Kuma baka Biyoni abaya ba" Cikin tuhuma take yi mashi maganar, muryar shi a sanyaye yace" Bazan iya baki amsa ba, saboda ni kaina bansan ta ina na shiga ba, abunda na sani shine Na sanyawa raina inason nabi bayanki ne, kuma na samu kaina Acikin toilet ɗin shine kaɗai abunda zan Iya tunawa amma bayan wannan bansan komai ba" Zuba mashi ido tayi tana kallonshi, har cikin ranta ta yarda da maganarshi, domin kuwa babu alamun wasa a fuskarshi ya bata amsar, kwara tabi komai asannu wurin yin bincike, Idan ba haka ba, zata iya tarwatsa lissafin kwakwalwarta ne, Ƙaƙaro murmushi ta yi akan fuskarta, yayin da take kallon shi, Mayar mata da martanin murmushin yayi Calmly yace" kin sanya damuwa aranki, Jiya kinyi kuka kuma baki yi bacci ba Why? Akan su Parveen ne"? Jinjina mashi kai tayi alamar eh, ta ƙara da cewa"na damu dasu sosai, Ina ji araina kamar baza a dawo mana dasu ba, shiyasa zuciyata ta karaya har nagaza runtsawa" Duƙowa taga ya yi saitin fuskarta, har saida ta ɗan tsorata, Zuciya da saƙe saƙe sai tayi tunanin ko kiss zaiyi mata, ƙiris ya rage tsinin hancinshi ya gogi nata, runtse ido tayi tana jin me zai mata "Ki kwantar da hankalin ki, Zasu dawo na yi maki alƙwarin hakan," ɗagowa tayi tare da kallon shi, "Taya akai kasan cewa zasu dawo"? Tayi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi, Murmushin gefen fuska ya ɗanyi, Can kuma yace"Kin manta anzo an ɗauke ni, Kuma an dawo dani, Suma zasu dawo ne" Girgiza kai angel tayi"amma koda aka dawo dakai, baka Acikin hayyacin ka, kamar an ƙara maka Ciwon Ajikin ka, danish zaka Iya tuna ina aka kai ka bayan an ɗauke ka daga Cikin mu"? ta jefa mashi tambayar, "Angel, ba zan iya tuna komai ba, tun bayan da giants suka ɗauke ni bansan meya faru ba, har sai ranar da suka dawo dani cikinku tukunna na iya tuna wanene," Shiru angel ta yi bata kuma cewa komai ba, Lamarin ne yafi ƙarfin tunaninta, Wata irin Murɗaɗɗiyar sarƙaƙiyace Acikin Kurkukun mai wuyar fassaruwa, Miƙa hannu danish yayi tare da ruƙo nata hannun acikin na shi, Magana ya soma yi idonshi acikin nata"angel, ina neman yafiyarki, for everything that happened because of our misunderstanding, I hate you for no reason, but now I can say that I love you more than anyone........" kalaman shi ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, sai taji tamkar an yaye mata damuwarta na ɗan wani lokaci, ƙayataccen murmushi ta saki tana motsa lips ɗinta, alamar tana so tace wani abu amma ta kasa furtawa, sam batayi tsammanin jin hakan daga gare shi ba, ta yi farin Ciki saboda yana ɗaya daga Cikin nasarar da take so ta samu na Jituwa atsakaninta da kowannan su, tana so ta shiga cikin zuciyoyinsu sosai ta yarda zata samu damar janyo ra'ayinsu, yanzu saura mutun biyu ya rage mata haris da deeja, taci alwashin Idan aka dawo da deeja bazata ƙara bari faɗa ya haɗa su ba, Shi ma haris ɗin bazata biye mashi ba, xata jasu ajikinta, "What are u thinking about"? Jin voice ɗin danish yasa ta ɗanyi firgit ta kalle shi, still idanuwanshi na akan fuskarta, " baki bani amsa ba," ya tambaya yana sauraranta, "Dama ni ban ruƙe ka azuciyata ba, Ni baka yi mini laifin komai ba, dani dakai tamkar ƴan uwana ne jini," ba ƙaramin daɗin kalamanta yaji ba, har cikin zuciyarshi yaji sanyi, zame hannunshi yayi daga Cikin nata, ganin ya lumshe eyes ɗinshi yasa tayi tunanin ko bacci zai koma ne, Yunƙurawa tayi tare da miƙewa daga gaban gadon shi, A dai dai Lokacin Batool ta fito daga sashen makewayinsu, itama fuskarta a kumbure, suna haɗa ido da angel ta nufeta, rungume juna su kayi kowa yayi shiru, batare da sunyi magana ba, Azeeza dake zaune saman gadonta, farkawarta kenan idanuwanta na akansu, Sun ɗauki lokaci kafin suka raba Jikinsu daga na Juna," "Idanuwanki sun nuna alamun baki yi bacci ba jiya, meyasa"? Batool ce tayi mata tambayar, "Taya xan iya runtsawa, alhalin ƴan uwana suna Acikin mawuyacin hali, anzo an raba ni dasu, an kaisu wani wurin, dole na damu, Nayi kewarsu sosai, Na gaza jurewa ne....." kukane ya ciyota, da sauri ta duƙar da kanta ƙasa, sam bataso ta nuna rauninta agabansu, saboda zata ƙara karya masu zuciya ne, sai dai duk ƙoƙarinta na hana kanta yin kukan hakann ya faskara, ita dai sam hankalinta bai kwanta da ɗaukar su parveen da akayi ba, Dafa kafaɗunta Batool ta yi da hannayenta biyu, Cikin sigar lallashi tace"pls angel, u should stop shedding your tears, kina ƙara sanya mana damuwa ne, ke da kike ƙarfafa mana gwiwa yau ke ce da kanki ki ke zubar da hawaye to mu me zamu yi kenan"? Idon batul cike tab da kwalla tayi maganar, Ta wutsiyar idonta ta hangi azeeza dake a zaune ta kasa kunne tana sauraronsu, da alama baccin bai sake ta ba, bata fahimtar me suke tattaunawa, Sanin raunin azeeza yasa tayi saurin sanya tafukan hannayenta, ta share hawayen da suka wanke fuskarta, murmushi tayi wanda kai zuci ba takalli batool dake kallonta tace "Nadaina batool, bazan ƙara ba, kema kada kiyi kuka" jinjina kai batool tayi"Nima bazan bari hawaye na su zuba ba, Angel inaso mu haɗa hannu wurin taimaka ma sauran ƴan uwanmu, mu dinga lallashinsu muna basu baki har Allah yasa adawo dasu Parveen, Inaso mu sama ma junan mu farin ciki koda kuwa babu wani acikin mu, kamar ke da kika jure rayuwa batare da Mahaifinki ba, haka nakeso muma mu ƙarfafa zuciyoyin mu, mu yi rayuwa da sanin cewa wata rana samu iya rasa wani, Tun da batool ta soma magana angel ta natsu tana kallonta, acikin zuciyarta tana Jinjina Ma batool, Yarinyar akwai tawakalli, Tana da hankali da tunani, Allah yayi mata baiwar iya sarrafa harshe wurin tsara kalamai masu kwantar da hankali, Haƙiƙa Iyayensu sunyi babbar asara Na rashin ya'ya kamar su, "Angel kinyi shiru baki ce Komai ba, Ina ta surutu Ni kaɗai," ajiyar zuciya angel ta sauke tare da kallon Batool tace"Am sorry Sister, naji maganganunki, sunyi mini daɗi sosai kuma in sha Allahu, zamu yi hakan, Zamu haɗa hannu wurin sama ma kanmu farin ciki," Muryar azeeza ce ta katse su da cewa"Wai har yanzu ba'a dawo mana dasu parveen ba? Jiya har mafarkinsu nayi," saukowa tayi daga saman gadon ta nufi su angel dake a tsaye ta ruƙe qugu tana kallonsu, "Ba'a dawo dasu ba Azeeza, Mu ƙara haƙuri zuwa anjima may be Giants su kawo mana su" Batool ce ta bata amsar tambayarta, Ta6e baki azeeza tayi tare da cewa"Ni dai indai ba'a dawo mana dasu ba, Bazan ƙara Cin abinci ba" maganartace ta basu dariya, Sauran ƴan uwansu dake bacci ɗaya bayan ɗaya suka dinga farkawa, duk wanda ya buɗe ido saiya tambayi su deeja, Angel da batool ne ke kwantar masu Da hankalinsu akan su ƙara haƙuri zuwa anjima, lokacin da kowa Yayi wanka, Suna a zazzaune saman gadajensu, Sai ga giants sun shigo kawo masu abinci, Bayin Allah duk sunyi tsammani za'a zo masu da ƴan uwansu amma sai suka ga akasin, Koda suka koma saman dining carpet domin Cin abinci, saboda damuwa, kaɗan suke tsakura suna ci ba don suna jin daɗin abincin ba, Angel hada ƙoƙarin mikewa taje karkashin gadon batool ta ɗauko kwando, tazo tana kwashe kingin abincinta, Yasmin tace"meyasa ba zaki ci ba? Bafa Ki ci dayawa ba'? Angel tace"su parveen zan ajiye mawa, kada su dawo da yunwa anjima, Jin abunda tace ne yasa suma suka rage sauran nasu abincin don a ajiye ma su parveen, angel ta kwashe duka cikin kwandon, Taje ta 6oye a karkashin gadon batool, Bayan tafiyarsu Giants, Hanna ta basu shawarar su motsa Jiki Ko sun samu Lokaci yayi saurin wuce wa duk don saboda tsammanin za'a dawo masu da ƴan uwansu yau, bayan sun kammala motsa Jikin nasu Kowa Ya gaji sai uwar xufa ke tsastsafo masu, A dole suka je toilet kowa ya watsa ruwa a jikin shi, ba ƙaramin ɗaɗi suka Ji ba, saman gadajensu suka koma kowa Ya hau ya zauna fira suka soma yi atsakanin su, wani irin bacci ne yazo ma angel batare data shirya mashi ba, dama jiya ana binta bashin baccin da batayi ba, gyara kwanciyarta tayi asaman gadonta, tare da jan bargo ta lullu6e kanta, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yayi awon gaba da ita, *ANEELERH* Almajirai ne daddabe a gaban motarta, sunyi dandazo suna jiran Ta basu sadakar kuɗi kamar yadda ta saba basu a duk lokacin da tazo zata wuce ta wurin makarantar allonsu, Sai faman zumuɗu almajiran suke Yi, Kayan Jikinsu duk sun yayyage, kowannan su na aruƙe da kokwan bararsa, Zuge glass ɗin motar ta yi, almajiran sai kallonta suke yi, tana a zaune saman driver seat, Jikinta na asanye da atampa, riga da skirt sunbi shape ɗin jikinta, Ta yafa mayafi akanta, ba ƙaramin kyau ta yi ba, Yayin da baby junaid ke akwance saman passenger front seat, Kayan sanyi ne ajikinshi sunyi matuƙar yi mashi kyau, baccin shi yake yi hankali kwance, ga wani irin ƙamshi dake fita ajikin shi, Ƙoƙarin Zaro kuɗi take Yi acikin ƴar purse ɗinta Bendir guda ta ciro na ƴan ɗari biyar biyar, zarowa ta dinga yi tana miƙa ma almajiran, Sai murna suke yi, suna kai hannu suna karba tare da yi mata addu'o'e Sai da ta kammala raba masu, tana yunƙurin Zuge glass ɗin motar, taga an zuro mata hannu, ras taji gabanta ya faɗi ganin hannun babban mutun sanye cikin baƙar safa, Da sauri ta kalli fuskar mutumin, ya sanya Mask a fuskarshi, Baƙaƙen kaya ne ajikinshi, bakomai ya faɗo mata araiba face mutumin da ya Ɗauke mata baby junaid ɗinta lokacin da taje gidanta, nan take gabanta yyi mugun bugu, A tsananin tsorace ta shiga kiciniyar zuge glass ɗin motar, ganin zata datse mashi hannu yasashi yin saurin zame hannunshi Key tayi ma motan hannunta na kerma ta ruƙe steering da wani irin speed ta fusgi motar da gudu ta haura saman titi tana ambaton"La'ila ha illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" tarasa ina zata dosa, saboda tsabar ruɗi, Gani take kamar mutumin yana abiye da ita, ashe dama bibiyar rayuwarta yake yi? Tayi tambayar acikin zuciyarta, Marece ne sosai Tana kokarin shan kwana, muryarshi ta ratsa kunnata"Baki bani sadakar ba" a gigice taja burki ta tsayar da motar, idanuwanta azazzare ta ɗago tana kallon shi ta cikin Rear view mirror ɗin motar, Mutumin Yana a zaune Cikin back seat na motar, a hakimce, Tayi matuƙar razana ganin shi acikin motarta, taya akai ya shigo bayan ta rufe motar, Anya kuwa mutunne ba aljani ba? muryarta na rawa tace"dan..dan Allah na roƙe ka, kada ka cutar damu, bansan wanene kai ba, ban kuma san laifin da nayi maka ba, ka faɗi kome kake so zanyi maka shi" idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar, "Kome nake so zaki yi mini"? Ya yi tambayar yana kallonta, a tsorace tace"Eh, wlh zanyi" Ya amsa da "Okey, " hannu taga ya zura cikin aljihun wandon Jikin shi ya lalubo wayarshi, Ya ɗan daddana ta kafin ya miƙa mata wayar"Location ɗin nan zaki bi, " batare da musu ba ta kar6i wayar tashi, idonta akan google map ɗin daya buɗo mata, daga gefenta ta ɗaura wayar, Ta ci gaba da driving tana bin location ɗin, yayin da zufa ke tsastsafo mata, zuciyarta a firgice take da tsoron inda zai kai su, Wayar shi kanta abun tsoro ce saboda ta banbanta da sauran wayoyin da ta saba gani, Babu sunan Company ajikin wayar, Dogon titi suka Miƙa sham6al har zuwa cikin wata area, Ta jigunannun masu kuɗi, Manya manyan gine gine, Unguwar shiru babu yawaitar mutane acikinta, a bakin wani katafaren Gida ta ƙaraso da motar, yace tayi horn ta danna horn nan take Wagegen gate ɗin gidan Ya zuge awani slow, kutsa motar tayi acikin gidan, har saida ya bata umarnin ta tsayar da motar tukunna ta tsaidata, Buɗe murfin motar yayi tare da fitowa ya zagaya other side ɗin da junaid yake a kwance, Ya buɗe motar ya zura hannu ya ɗauke shi, Aruɗe aneelerh take kallon shi, ganin ya ɗaukar mata yaro, "Let's go in" yayi maganar yana nuna mata hanyar zuwa cikin gidan, Jiki asanyaye ta buɗe motar ta fito tabi bayanshi, Wa'iya zubilla Ta yi matuƙar girgiza da ganin kyawun gidan ya tsaru iya tsaruwa kai kace ba'a 9ja yake ba, Duk da a tsorace take hakan bai hanata bin ko'ina da kallo ba, suna ƙarasowa bakin glass door ta falon gidan, Muryar na'ura ta karaɗe kunnuwansu, wani abun mamaki daya ɗaure mata kai, na'urar da ta soma magana tana sanar da zuwan su, sai da ta faɗi Cikakken sunan aneelerh, wato Aneelerh muhammad falgore, Ras taji gabanta ya faɗi, a karshe na'urar tace"you're permitted to come in" nan take ƙopar glass ɗin ta zuge, Mutumin yace mata su shiga Ciki, ta zura kafarta acikin katafaren falon, Tsayawa faɗar irin kyawunshi 6ata baki ne sai wanda ya gani, wani irin sanyin a.c ne ta ko'ina, Komai na Cikin falon White Colour ne atsaftace yadda kasan ba'a ta6a amfani dashi ba, saboda kyawunshi da sabuntakar furniture ɗin dake acikin shi, Miƙa mata Junaid Ya yi, da sauri ta sanya hannu ta kar6eshi, ta rungume shi ajikinta, A saman Sofa 3 seater Ya bata Umarnin ta zauna, xama tayi tana faman baza ido, Jira take taga me za ayi mata, Acikin zuciyarta sai addu'o'in neman tsari take karantowa, Takun takalma ta soma ji daga can saman twin stairs ɗin dake a falon, a hanzarce takai idanuwanta wurin tana kallonsu, waro ido waje tayi Jikinta ya shiga 6ari ganin Gabza gabzan Mazan dake saukowa saman benan, kowannansu na asanye Cikin shiga ta baƙaƙen kaya, A ƙalla sunkai su takwas, bakwai Suna a left hand na benan, Yayin da mutun ɗaya ke tafiya atsanake ta right hand ɗin stairs ɗin Kusan atare suka sauko daga saman benan, Aneelerh bata Iya ganin komai na Jikinsu ba, Gaba ɗaya sun rufe kansu daga ƙasa har sama Cikin black dress, Dogayen riguna na maza masu haɗe da huluna kamar alkebba, Guda bakwai ɗin suka Ƙame a tsaye tare da goya hannayensu saman ƙirjinsu, shima wanda ya kawota gidan Yana a tsaye gefen hand sofa ɗin da take a zaune Ya ƙame kamar yadda sauran su ka yi Mutum ɗayan nan daya rage, shine Ya zauna saman sofa 2 seater, Ya ɗaura ƙafarshi ɗaya bisa ɗaya, aneelerh fa tasha jinin jikinta, sai faman ƙanƙame junaid ta ke yi ajikinta, Yaro sai bacci yake yi baisan halin da Mommynsa ke ciki ba, "Ki natsu Ki saurari maganganun da zamu tattauna dake, mintina ƙalilan zamu salleme ki ki tafi" Na gefenta ne yayi maganar, wanda suka zo tare da shi, Jin haka yasa ta daidaita natsuwarta, ta kasa kunne tana jiran Jin me zasu Ce, wanda take tunanin shine team leader ɗinsu, wanda ke zaune saman Sofa 2 seater akanshi ta tsayar da idanuwanta, wata irin ƙirar ƙarfi ce gare shi, taban al'ajabi, mai matuƙar jan hankali da tsoratarwa, kai daga ganin wannan babu wasa acikin lamuranshi, baƙaƙen kayan sun zauna mashi sosai, sun bayyanar da zazzafar surarshi, tayi tunanin shi zai yi mata magana amma sai taji yayi shiru, Takun tafiya ta kuma jiyowa ta can 6angaren, Wani ƙaton ne Ya fito sanye da bakaken Kaya, Hannunshi a ruƙe da plate me ɗauke da Glass Cup, ruwan sanyi ne aciki, a saman table ɗin dake a kusa da sofa ɗin da aneelerh ke a zaune ya ɗaura plate ɗin, Cikin girmamawa yace mata"Zata iya sha" ya ambaci hakan tare da juyawa Ya bar falon, duk fa waɗannan Garadan mazan na a kewaye da ita, Da farko taji tsoron tasha kada ace An sanya mata wani abu, amma daga baya saita kai hannu ta ɗauka ta ɗan kur6i ruwan, sanyi gare shi ga daɗi, bayan ta ajiye Glass ɗin, Sai ga wannan katon daya kawo mata ruwa, Ya dawo Cikin falon hannunshi ruƙe da Laptop Tsadaddan gaske, Adai dai gaban aneelerh Ya ajiye laptop ɗin saman table gefen plate ɗin da ya kawo mata ruwa, Daddana laptop ɗin Ya shiga yi Cikin ƙwarewa, Aneeelrh dai ta zuba ido tana jiran ganin me za'a nuna mata, Bakomai bane Ya bayyana akan screen ɗin Laptop ɗin nasu, Face Hotonsu da su kayi ranar birthday ɗin Angel, Su Huɗu, Angel ce a tsakiyarsu, Taj yana agefenta ya zuƙunna, Aneelerh da Uzair Suna atsaye fuskokinsu ɗauke da murmushi, Tsananin mamaki ne ya kama Aneelerh ganin wannan hoton, duk da tasan Zasu Iya samun shi a social media, saboda sunyi share ɗinshi a insta da Facebook, twitter da tiktok, hada videos na birthday ɗin angel, "Kin gane su"? Muryar mutumin ce ta katse mata tunaninta, da sauri tace"Eh, ƴan uwana ne," ya nemi ta yi masu bayanin menene alaƙarta da su" da hannu ta nuna mashi hotonta dana uzair tace mijina ne, wannan kuma ɗan uncle ɗin shi ne, Sunan shi Tajuddeen, Ita kuma yarinyar Ɗiyarshi ce, sunanta Unaisa amma muna kiranta da Angel,' Jinjina kai ya yi tare da cewa"Mu jami'ae ne masu zaman kansu, muna da interest akan case ɗin 6acewarsu, that's the reason why muke Bibiyarki, saboda sanin cewa ke kaɗaice zaki Iya bamu bayanan da muke so, Zamuyi maki tambayoyi, da zarar kin amsa mana zamu sallame ki ki tafi, kuma bazaki sake ganin mu ba," ta amsa ma shi da toh, Tambayoyi suka shiga yi mata, tun daga kan alaƙar dake tsakanin su tajuddeen da Uncle abdallah har izuwa kan Alhaji ubaid, da ita kanta hada iyayenta duka saida su ka yi mata tambayoyi a dangane dasu, hatta Benazir sai da suka yi mata tambayoyi akanta, duk ta amsa masu wanda ta sani, abunda ya ɗaure mata kai hada ƙawarta Aisha suka Yi mata tambayoyi akanta, game da yarda akai mahaifinta yayi mata korar kare daga gidan shi, Lamarin ya ɗaure ma aneelerh kai, taya akai suka san kowa da take atare da shi? Su wanene waɗannan jami'an masu Uniform baƙaƙen Kaya, Taso ta tambayesu daga ina suke, amma sai suka ce mata, basu bata iznin tambayar komai agame dasu ba, Sannan suka ce ta sawa ranta cewa a mafarkine Ta haɗu dasu, kada tayi tunaninsu kuma kada ta kuskura ta yi gigin faɗa ma wani agame da su, bayan sun kammala Yi mata tambayoyin har bakin motarta suka rakota, ta buɗe ta shiga, suka yi mata godiya taja motar ta fuce daga Cikin gidan, Tana cikin yin driving saman titi Junaid Ya farka yana ta tsala kuka, a dole ta kashe motar daga gefe ɗaya ta rumgumo shi ajikinta tana lallashinshi, yace mata Yunwa yake Ji, ta bashi abinci yaci," tunawa da madararsa da ta ajiye mashi a backseat na motar yasa ta juya ta kai hannu ta ɗauko mashi ita, acikin bottle take, ta cire murfin ta kafa mashi abaki yana sha, yayin da ta shiga zurfin tunani, abun ya tsaya mata aranta, ita gaba ɗaya rayuwar duniyar tsoronta take ji, meya faru dasu uzair? Shiru ba labarinsu kusan shekara huɗu? Sannan ga wasu mutane suna Bibiyar rayuwarta da sunan jami'ae ne, Anya kuwa bazata gudu tabar ƙasar nan ba, na wani lokaci? Gani take kamar zata rasa ɗanta ne, kamar yadda ta rasa mutun ukun nan masu mahimmanci, tana cikin yin wannan xancen zucin junaid ya fashe da kuka yana faɗin"tasa mashi madara a hanci," da sauri takai idonta kanshi, fuskarshi ta 6aci da madarar, batasan ya akai ta janye robar daga bakinshi ba ta kwafa mashi a hancin shi, rufe bottle ɗin tayi tare da ajiyeta gefe ɗaya, ta zaro hanky cikin ƴar purse ɗinta ta shiga goge mashi madarar, bayan ta kammala ta maida hanky a cikin purse ɗin, Ta rungumeshi ajikinta tana lallashinshi, har saida yayi shiru lamo ajikinta tukunna ta tashi motar ta miƙi hanya ta nufi gida, Lokacin da ta koma Gida, a palour ta taras da Mami da wasu ƙawayenta suna fira, sai da ta fara gaishe su, suka amsa mata, tare da miƙa mata hannu ta basu junaid, Ita kuma ta wuce cikin ɗakinta, tana shiga ta rage kayan jikinta ta faɗa toilet tayi wanka, ta fito waist ɗinta a ɗaure da towel tana kokarin zama saman mirror chair, alert ya shigo Cikin wayarta dake ajiye saman mattress, da sauri takai hannu ta ɗauki wayar, kamar a mafarki take ganin credit alert ɗin da aka turo mata via dollar account ɗinta, wanda a kuɗinmu na nigeria kuɗi ne bana wasa ba, har saida ta dafe ƙirjinta da hannu ɗaya, ta shiga ruɗu akan wannan kuɗin da aka turo mata, bayan ita ba wanda ta ba acct number ɗinta, Shi kanshi dollar account ɗin ta jima bata yi amfani dashi ba, Komawa ta yi gefen gadonta ta zauna hannunta ruƙe da wayar tana kallonta, wani saƙonne ya kuma shigowa cikin wayarta, cikin harshen turanci aka rubuto shi, karantawa tayi kamar haka _mun gode da haɗin kan da kika bamu_ Nan take ta gane cewa Jami'an nan ne suka Turo mata da kuɗin, ajiyar zuciya ta sauke tare da jefar da wayar saman pillow, Ta gyara kwanciyarta saman mattress ɗin, Yayin da idanuwanta ke fuskantar ceilling, zuciyarta a cunkushe take da tunani kala kala duk akan Jami'an nan, Su kuma ko daga ina suke? Waye ya sanya su bibiyar case ɗin su tajuddeen? amma tasha ruwan mamakin Irin Ƙirar jikinsu, especially wannan ɗayan daya zauna saman sofa wanda take tunanin shi ne team leader ɗinsu, Kamar shi ya ƙera kanshi, daga gani dai jami'ae ne su bana wasa ba, ita dai fatanta Allah ya tabbatar da alkhairi akan bincikensu dana su Uncle bash, Ta yi zurfi acikin tunaninta, tajiyo muryar baby junaid yana faɗin"Mommy kizo inji mami, " daga kwancen da take ta juya tana kallonshi, ya ruƙe qugu abakin ƙopar ɗakin, yana ta faman zumbura baki yace"Bake kika sanya mun madara a hanci ba, ae na faɗa mata, tace zata rama mini" Yadda yayi maganar ne ya bata dariya, har fararen haƙoranta suka bayyana, Miƙa mashi hannu tayi"zo nan My baby boy" maƙe kafa ɗa yayi"Ae baki sona, Tunda kika sanya mun madara a hanci," saukowa tayi daga saman gadon ta wuce wurin closet ɗinta, Jallabiya ta ɗauko ta zura ta ajikinta, kafin ta dawo ta nufi inda yake a tsaye, ta zuqunna agabanshi tare da kai hannu tana shafa sumar kanshi tace"My baby boy, nifa mommynka ce, ni na haife ka, bani da tamkarka aduniyar nan inasonka fiye da kaina, jinka nake kamar bugun zuciyata,' takarasa maganar tare da sanya hannu ta ɗauke shi, kafin ta mike ta wuce cikin falon, A lokacin ƙawayen Mami sun tafi, A zaune ta same ta saman Sofa, Riga bubu ce a jikinta, idonta na akan plasma tv, tashar arewa 24 take kallo Takun tafiyar aneelerh ne ya janyo hankalinta, ta juyo tare da kallonta, fuskarta asake tace"My daughter Kinyi mana laifi, Junaid ya faɗa mini abunda kika yi mashi acikin mota, ashe dama shirin kashe shi ki kayi"? cikin zolaya tayi maganar, Fuskar aneelerh ɗauke da murmushi tace"Kuskure ne mami bansan nayi mashi haka ba, kuma fa har hakuri na bashi amma shine bai kar6i uzirina ba," takai karshen maganar a yayin da take zama saman Sofa tare da junaid, Ya manne ma jikinta, Kallon shi mami tayi"ka yafe mata ko in rama maka"? Ashagwa6e yace"nayi mata amma idan ta ƙara, afaɗa ma uncle bash ya sanya gun ya harbe mata kai," gaba ɗaya suka kwashe da dariya aneelerh tace"amma baka da mutunci junaid, uwar taka zaka sa a harba da bindinga? Idan na mutu ya zaka yi"? Watsa hannu yayi tare da cewa"Shikenan, sai aje kasuwa asiyo wata uwar" tuntsirewa su kayi da dariya, mami tace"Aku sarkin ɗumi, Kwanan nan xan sanyaka makaranta, tun da bakinka ya buɗe, ga surutu" Aneelerh tace"nima tunanin da nake yi kenan, ko islamiyace a fara sanya shi yana zuwa kafin asanya shi ta bokan," fira suka cigaba da yi har baby junaid yayi bacci a jikinta, aneelerh bata fada ma mami game da abunda ya faru da ita ba, kamar yadda jami'an suka gargaɗeta akan ta manta da komai nasu ta ɗauka tamkar mafarki tayi shiyasa taja bakinta tayi shiru gudun kada taja ma kanta, *Back to Prison* After One Day👌 Wani irin narkakken Jini ne mai kauri da ƙarni yake gangarowa ta cikin ƙoramar ruwan dake Gudana, Sassan Jikin mutun ta gani gunduwa gunduwa tsulundum acikin Jinin, Hannu tasa ta dafe kanta tare da fashewa da matsancin kuka na fitar hayyaci, A firgice ta farka daga baccin da take yi sakamakon bugun ƙafarta da aka yi, wata irin Zabura Ta yi tare da miƙe wa zaune, Tana binsu Da Kallo, ɗaya Bayan ɗaya, Suna a kewaye da gadonta, Batool Hanna hibba, Azeeza, yasmin, eve, javed Sai kiran sunanta suke Yi suna tambayarta lafiya? Me take ma kuka? Abunda ya faru suna a kwance saman gadajensu suka soma Jin shessheƙar kukan angel, Hakan yasa suka yi gaggawar zuwa gaban gadonta don suji dalilin yin kukan nata, "Angel meya faru ne? Duk kin bi kin ruɗe? ko kinyi mummunan mafarki ne"? batool ce ta jefa mata tambayoyin, Ƙanƙame Jikinta Ta yi da hannayenta, wata irin zufa Ce ke tsastsafo mata ajikin fatarta, Sai faman zazzare Manyan idanuwanta take Yi, gaba ɗaya bata Acikin hayyacinta, tayi matuƙar tsorata da mafarkin da tayi, muryarta na kerma ta soma Magana"Ina parveen? ina rubina da Deeja an dawo dasu? Ko kuwa har yanzu? Takai ƙarshen maganar tana kallonsu Batool, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* "Angel Still ba'a dawo dasu ba, Abincin da muka rage musu tun jiya ya riga da ya lalace, da mun sani mun cinye shi," Hanna ce ta bata amsa, Azeeza tace"Yanzu shikenan baza adawo mana da su Parveenar mu ba? sun tafi kenan"? Muryarta a sanyaye tayi maganar, Hibba tace"Pls Azeeza stop sayin that bana jin daɗi, kuna karya mana zuciya, Tsohuwa fa tace za'a dawo dasu da zarar Sun samu lafiya," Eve ce ta kalli Hibba da tayi maganar tace"Hib kin manta lokacin baya? Ƴan uwanmu da muke atare dasu? Wasu in an ɗauke su ba'a dawowa dasu sun tafi kenan"? Idon angel akansu tana sauraronsu, kwata kwata bata acikin natsuwarta, tana matuƙar jin tsoron ta yi mummunan mafarki, saboda Xaiyi wuya mafarkinta yaƙi xama gaskiya, kafin zuwanta gidan kurkukun ƙaddara saida tafara mafarkin kasancewa acikin shi kuma sai ga shi ta tabbata, ta tsinci kanta acikin shi, "Yakamata mu daina wannan maganar, Muna ƙara tayar wa junan mu hankali, Idan muka kwantar da hankalin mu, za'a dawo dasu ne," acewar Javed, yasmin tace"Yanzu me zamuyi toh? Ni nagaji da zama zugudum, " fuskarta a yamutse Tayi maganar, Azeeza tace"Muna da abunyi mana, Angel zata Wanke mana gashin kanmu, ta kuma gyara mana shi, " tunkan takai karshen maganar, yasmin ta harare ta"Kefa matsalarki kenan, Sai ana magana ta hankali ki wani soko wa mutane Shiririta aciki," zum6ura baki Azeeza Ta yi tare da murguɗawa mata shi tace"To me kike so Muyi? Wanka ko motsa Jiki? Ko kuma bacci? Ko giants xamu Jira su kawo mana abinci"? Banza yasmin tayi da ita, Zama batool tayi a gefen gadon angel, ta ruƙo hannun angel acikin nata tace"Sister, na lura sam bakya acikin hayyacin ki, Ki faɗa mini, me kika gani acikin baccin ki wanda ya tsoratar dake"? Idanuwan angel cike tab da ƙwalla ta ɗago ta kalli fuskar batool, bazata Iya faɗa mata ainihin abunda ta gani acikin mafarkin ta ba, Saboda Bata son ta tayar mata da hankali, Kuma faɗin baida amfani, sannan ma babu kyau mutun yayi mummunan mafarki ya faɗi ma wasu, Don haka tace mata"bakomai batool Just bana Jin daɗin Jikina ne," "Ko zakiyi wanka ne? May be kiji daɗin Jikin ki," cikin sanyin murya tace"eh, xanyi, " tana rufe baki Azeeza tace"Angel me zamuyi yau"? Murmushi angel ta ƙaƙalo, yayin da take kallonta tace"Little Kome kike so Shi za'ayi, " ashagwa6e Azeeza ta bubbuga ƙafar tare da cewa"Ni kidaina ce mun little bana so," gaba ɗaya su kayi dariya, Hanna tace"Ae gaskiya ta faɗi, kallarki fa? Wata ƴar ƙarama dake, Ko kafaɗarmu baki kai ba, banta6a ganin wadda bata cigaba ba acikinmu irin ki, Duk yawan abincin da kike Ci sam baki ƙara auki, ba ƙiba ba tsawo," dariya suka saki gaba ɗayansu, Rai a6ace Azeeza Ta zuƙunna kasa tana yin kukan ƙarya, Angel tace"pls kudaina janta, Nima na faɗi ne kawai don ayi nishaɗi, amma azeeza ae itace babbarmu," ta yi maganar tana ƙyaftawa musu ido, atare suka haɗa baki wurin cewa"hakane Azeeza itace babbarmu, muma wasa muke Yi mata, don kawai ayi raha ne" Sunsan azeeza da son girma, jin wannan maganar tasu yasa ta miƙe tana gumtse dariya abaki, Angel tace mata"Me kike so Muyi yanzu? "Ki wanke mana gashin kanmu, Kuma ki gyara mana, keda batool kamar yadda ku kayi mana ran nan kin tuna'? Zaro ido angel tayi"Azeeza Baki ga yadda na farka ba yau, sam babu natsuwa atare dani, Taya zamu Iya wanke maku wannan uban gashin kan naku, Kuma mu gyara shi,? Ta6e baki azeeza ta yi, Itafa in taso abu to ayi mata kawai, idan ba haka ba yini zatayi tana faman tur6une musu fuska duk da tana da yawan fara'a kamar Gonar auduga, "Kada Ki damu sister azeeza, Koda angel bata samu damar tayani ba, Ni xan gyara maku gashin kanku, Mu barta ta huta, tun da bata Jin daɗi, Kuxo muje toilet," Batool ce ta yi maganar, Ta juya ta nufi toilet suka bi bayanta, Bayan tafiyarsu Cikin toilet, Angel ta sauke ajiyar zuciya, tare da jingina bayanta Jikin bango, Gefe ta juyar da kanta tana kallon Gadon danish, kamar dai kullum yana a kudundune Cikin bargo, Haris da mubeen da Javed hada naufal duk basu farka daga Bacci ba, sakamon daren da su kayi jiya batare da sun runtsa ba, Suna Xaman Jiran adawo musu ƴan uwansu, Saƙe saƙe ta shiga Yi acikin zuciyarta, game da wasu tambayoyi da suka cunkushe mata kwakwalwarta, sun hanata sakat, idan ta takura kanta akan tunaninsu Har wani matsanancin ciwon kai take ji, tabbas tana son Yin magana da tsohuwa duk da tasan zaiyi wuya tsohuwa ta amsa mata tambayoyinta, amma zata jaraba tunkararta, Yau ɗin nan, A6angaren su Batool, sai da tabi kowannan su ɗaya bayan ɗaya ta wanke musu sumar kawunansu, Baƙaramar wahala tasha ba, domin kuwa Dukansu tsayin gashinsu Ya zarce midback ɗinsu, Ga uban yawa dake gare shi, bayan ta kammala wanke musu gashin, Sai da kowannan su Yayi wanka, Kafin suka dawo Cikin ɗakin, Kamar yarda suka bar angel zaune saman gadonta haka suka sameta, ganin sun fito daga wankan Yasa itama ta miƙe domin zuwa yin wankan, Shigarta da ƴan mintuna ta fito, A lokacin Danish dasu Mubeen duk sun farka daga bacci, saukowa su ka yi daga saman gadajen su, Atare suka Nufi Toilet domin suma suyi wankan ko sunji daɗin Jikin su. A zaune ta samu batool gefen gado ta ruƙe Comb, Zata Gyara musu gashin kansu, hakanan taji tana sha'awar Tayi musu Kitson kalaba Guda Biyu akansu don ta Iyata, Kallon batool tayi tare da cewa"Ki bari In yi musu kitson Kalaba, Nasan ba'ata6a Yi maku ba, Yau zan jaraba mu gani idan zan iya" Cike da Jin daɗi Batool ta mika mata Comb ɗin, Tasa hannu ta kar6a, tare da samun wuri gefen gadon batul ta xauna, Ta ɗago ta kalli su Azeeza dake ta murna za'a gyara musu gashi tace Su zazzauna a ƙasa, zata fara gyarawa azeeza nata idan ta kammala mata zata Kira ta gaba da zata yi mawa, A ƙasan gadon azeeza ta zauna tsakankanin ƙafafuwan angel, Hannu angel ta sanya tare da Ruƙo sumar kan Azeeza, Launin gashin kanta Dark blonde, mostly Turawa ne suke da irin wannan gashin kan, sharce sumar kan angel tayi, Kafin Ta raba gashin zuwa gida Biyu, a tsanake Ta soma yi mata kalaba, Tunkafin ta kammala su Hanna sai santin kalabar suke yi, duk sun ƙagara a kammala Yima azeeza suma ayi musu, Guda Biyu tayi mata shima daƙyar ta samu Tayi su saboda santsin gashin Ga tsayi da yawa, Tun da aka kammala Yima azeeza kitson, ta miƙe ta koma gefe tana ruƙe wutsiyoyin kalabar da hannayenta, Sai tsalle Take yi Wutsiyoyin kalabar suna yin sama da ƙasa, ita fa yau ta samu abun wasa, Ɗaya Bayan ɗaya saida angel tayi musu kitson kalaba guda Biyu, Koda akazo kan Batool sai cewa tayi ta gaji bazata Iya ba, bakomai yasa tace haka ba face Fargabar Ta yadda zata Iya kama Gashin batool, Baƙar wahala zata Ci saboda yawan dake gare shi gashi kamar roba kuma Curly irin nata, a dole batool ta haƙura badan taso ba, Danish Basu Jima da fitowa daga wanka ba, Giants suka zo Kawo musu abinci, Kamar Jiya haka Yau ma suka ɗibarwa Su Parveen Abincin acikin kwandonsu, Da niyar idan Allah yasa Aka dawo dasu Yau sai su basu su ci, gudun kada adawo dasu Da yunwa, Bayan sun Kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka Fuce daga Cikin ɗakin, Duk sun damu da rashin ƴan uwansu, hakan yasa suka kasa samun natsuwa especially angel, Zarya ta soma Yi acikin aɗakin, idan takai ƙarshen bango saita dawo ta sake zagayowa, Har saida ƙafafuwanta suka soma Yi mata raɗadi tukunna ta dakata da yin zirga zirgar, Ta nufi gadonta da niyar ta huta, gefen gadon ta zauna Zugudum, Zuciyarta acike fal da tunanin duniya, wuraren marece su ka Jiyo alamun motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, Bayin Allah da gudu suka duro daga saman gadajensu, Jikinsu na 6ari suka ƙarasa ƙopar ɗakin nata suna jira ta fito, Sandar hannunta ce ta fara leƙowa, Kafin ta zuro kai ta fito waje, Jikinta sanye da jan doguwar rigar nan ta gado, Kusan atare suka haɗa baki Wurin gaishe da ita, Ta amsa masu fuskarta asake, Sai faman mamular baki take Yi kamar me cin goro, fuskarnan a jagwale saboda tsabar tsufa ta koma kamar aljana, hurhura ta ko'ina, "Tsohuwa Ya jikinsu Deeja? Tun jiya muke ta tsammanin jiran dawowarsu amma shiru ba'a dawo mana dasu ba, Munyi kewarsu sosai, Bacci ma daƙyar muka Yi shi, Ko abinci bama Jin daɗin Cin shi saboda rashin ƴan uwanmu" yasmin ce tayi maganar cikin nuna damuwarta, Mubeen Yace"tun daga Lokacin da aka ɗaukesu har zuwa Yau, kullum Cikin zullumi muke," Angel dai ta tsareta da ido kamar yarda itama tsohuwar idonta ke akan angel, Kowa da abunda yake saƙawa aranshi, "Kinyi shiru baki bamu amsa ba? Yaushe za'a dawo mana da ƴan uwanmu? Idan mensturation ne Yanzu ya isa ace jikinsu Yayi sauƙi," Fuska aɗaure angel ta yi mata maganar, Jinjina kai tsohuwa Tayi, Sai da ta mula tasha Iska Tukunna tace"Ƴan uwanku suna acikin koshin Lafiya, Bazan Iya sanar daku lokacin da za'a dawo dasu ba, Saboda bani da masaniya, amma nasan bazasu wuce Cikin week ɗin nan ba," A ƙagare Azeeza tace"Dagaske Su parveen Sun Ji sauƙi? Kuma Suna tambayar mu? Suma sunyi kewarmu"? Murmushi tsohuwa ta sakar mata tare da cewa"Eh mana, sun damu daku sosai, Kuma suna tambayarku, da zarar Sun ƙarasa Jin sauƙi za'a dawo maku da su" wani irin murmushin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, In ka cire mutun Huɗu Batool Angel da javed sam babu walwala akan fuskokinsu, Baka iya tantance awani yanayi suke ciki, da alama suna kokwanton kalaman Tsohuwa, sun dai yi shiru ne kawai, "Just for today, Ki kaimu inda suke domin muyi musu Ya jiki, Tunda Kince Suma sun Yi kewar mu, hakan zai rage musu damuwa" angel ce tayi maganar Girgiza kai tsohuwa Tayi tare da cewa"Ba'a bada iznin ɗaya daga Cikin ku, Yaje inda suke ba, Idan Ku ka yi hakuri zasu dawo ne" batare da angel ta yi mata musu ba tace"Shikenan zamu zuba ido mu gani idan za'a dawo mana dasu" Kallon su Batool angel tayi tare da cewa"Ku koma kuje ku zauna, inaso zanyi magana da tsohuwa" Jin wannan maganar yasa tsohuwa tayi saurin kallon angel fuskarta da alamun mamaki, Juyawa su batool suka Yi atare suka tafi izuwa saman gadajensu, duk wannan abun dake faruwa danish Yana a kwance saman shimfiɗarshi, ko sarki bazai nuna mashi Jin daɗin gado ba, Ya cancanci da akirashi da MAJI DAƊIN GADO, "Ƴar nan ina sauraron ki, wata Irin magana ce ki ke son Yi dani kuma? Yau ke da kanki"? tsohuwace tayi maganar, fuskarta akwa6e, cikin sanyin murya angel tace"Inaso mu shiga daga Cikin ɗakin ki, Muyi magana" zaro ido waje tsohuwa tayi jin abunda angel tace, Can kuma saita yamutsa fuska tace"Ba dole sai mun shiga daga Ciki ba, Kome Ki ke son tattaunawa dani, Kiyi mini magana anan ya wadatar" "Meyasa baki son in shiga ɗakin ki"? Ko akwai wani abu da bakya son in gani ne? Da tuhuma angel tayi mata maganar, girgiza kai tsohuwa ta yi tare da cewa"Babu abunda nake 6oyewa kawai dai bana bada iznin A shiga ɗakina, idan magana zakiyi dani to mu yi ta anan, babu wanda zai ji mu," Ta6e baki angel ta ɗanyi still idanuwanta akan tsohuwa tace"yau tsawon shekarata Biyu agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a ganin wani ya shiga Cikin ɗakin ki ba, Bansan me kike 6oye mana ba, Amatsayinki na uwa agare su, meyasa baki bari muna leƙawa cikin ɗakin ki? Kuma bakya zama acikin mu domin Yin fira, Ko hakan ya sa6awa dokar prison ne"? Bazawarin murmushi tsohuwa tasaki kafin ta Juya Tana dogara sanda tace da angel"Ki shigo daga Ciki," tsananin mamaki ne Ya kama angel, Jin ta amince mata akan ta shiga Cikin ɗakin nata, Sai da angel ta fara juyawa ta kalli su batool, ganin hankalinsu gaba ɗaya baya akansu Yasa ta bi bayan tsohuwa, Kafin ta shiga ɗakin tsohuwa Sai da takaranta addu'o'in neman tsari, sannan ta zura ƙafarta Cikin ɗakin, bakinta ɗauke da sallama, A tsakiyar ɗakin Angel Ta tsaya tana bin Ɗakin tsohuwa da kallo, Abun mamaki abun al'ajabi, Bakomai bane aciki face Shufke sufken fulawowi,Ta ko'ina tamkar ɗan garde, Sai wasu tsoffin Kujeru guda Biyu suna fuskantar Juna, tsakiyarsu table ne mai ɗauke da Tea pot, da ƙananun Kofina guda Biyu, bayansu babu wani abu na furniture, Gado ko katifa, Bayan ta kammala Kallon Cikin ɗakin na tsohuwa, Ta wurga idanuwanta kan tsohuwa dake yunƙurin zama saman ɗaya daga Cikin kujerun guda biyu dake fuskantar juna, Muryarta angel ce ta katse mata hanzarinta da cewa"ina kayan ɗakin suke? Naga babu gado ko katifa? A ina kike kwana"? Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa tasaki, Mai matuƙar sautin gaske, Angel tuni tasha jinin jikinta, Muryar tsohuwa ashaƙe tace"Ƴar nan Badai Iya tambaya ba, Dama ganin kwakwaf kika zo Yi mini acikin ɗakin nawa? Keda kika ce Magana zamuyi ae kamata Yayi ki zo ki zauna ga kujera har ma da shayinmu na tsoffi in zuba maki musha don muji daɗin tattaunawa" Takai ƙarshen maganar tana nunawa angel kujerar da hannunta, Jikinta tamkar na wadda aka zarewa Laka haka Taci gaba da tafiya Ta nufi kujerun Ta shiga Ciki ta zauna, tana Bin tsohuwa da kallon Ban yarda dake ba, Ƙarasa xama saman kujerar tsohuwa Tayi, a yayin da suke fuskantar Juna ita da angel, Ido cikin ido suke Kallon juna, "Ina sauraronki wata magana ce kikeson tattaunawa dani"? Ta yi tambayar a ƙagare da son ji, Angel da ƙarfin hali tace"Tambayoyi ne nake son Yi maki, Ina fata zaki amsa mani" Wani irin kallo tsohuwa ta jefa mata, da mitsi mitsin idanuwanta, Cigaba da magana angel tayi"Badan Hali na ba, Alfarmace nake nema awurinki, duk da nasan zaiyi wuya ki amsa mini tambayoyina, bansani ba ko yin hakan ya sa6awa dokar Prison" Gajeren murmushi tsohuwa ta saki, kafin tace"A dokar gidan kurkukun ƙaddara, Ba'a ba mu damar Yin magana da prisoner ba dangane da abunda ya shafi Kurkukun, Yin hakan babban laifina wanda hukuncinsa mutuwa ne.........." aruɗe angel ta ɗan zaro ido tana kallonta, Tsohuwa tace"Kinga kuwa babu ta yadda za'ai In iya amsa maki tambayoyinki kodan saboda in tsira da raina" Angel tace"Amma ae babu mai ganin mu, Daga Ni sai ke ne acikin ɗakin nan, Babu wanda zai san anyi" Cikin sigar wayau angel ta yi maganar, hakan ba ƙaramin dariya yaba tsohuwa ba, ganin ƙaramar yarinya na neman raina mata hankali, su da suka ga jiya suka yau "Mu sha Tea mana, " tayi maganar tare da kai hannu ta ɗauki tea pot, tana tsirara musu ruwan tea Acikin Cups, "Ko kin zuba bazan Sha ba," acewar angel, kallonta tsohuwa tayi"saboda me"? "Ban yarda da duk wani abu da zai fito daga gare ki ba," "Amma meyasa ƴar nan"? "Saboda Ina kokwanto Akan shayin da da zaki bani, Shekaran Jiya da kika ba su batool apples Sunyi bacci Na tsawon yini guda batare da sun farka ba, Har safiya tayi, ina da tabbacin cewa silar apples ɗin da kika basu ne, Shiyasa nake tsoron in sha tea ɗin nan, wata'ƙil kinsa Poison aciki," Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Da ace naso kashe ki da tuni na aiwatar da hakan, kada ki manta kina acikin ɗakina ke kaɗai, Koda sandar hannu zan Iya cutar dake, ƴan uwanki kuma dana bawa Apples Taimakonsu Nayi saboda bani da ikon da zansa Giants su dawo masu da abinci, Shiyasa na baku Apples ɗinmu na gidan kurkukun ƙaddara, Domin kuyi bacci Har gobe Ta yi saurin zagayowa ko kun samu Ku ci abinci" dariya angel ta ɗanyi Tare da cewa"Hakan Yayi kyau, yanzu dai tun da bakyaso In tambayeki agame da kurkukun ƙaddara, Inaso Nayi maki tambaya biyu bata Cikin kurkukun bace...."tsohuwa tace "ina sauraronki" "Gidan Kurkukun ƙaddara A Cikin Nigeria Yake? Sa'an nan kince Mutum baya ta6a kasance Acikin kurkukun nan dole sai in na Jininsa ne Ya sadaukar da shi, Abunda da nake so In sani, Na jinin naka daya sadaukar dakai Kamar wa kenan"? "Kin manta abunda na faɗa maki kenan? kiyi mini ko wace irin tambaya amma kada Ki tambayeni game da gidan kurkukun nan....." tunkan takai karshen maganar angel ta katse ta da cewa"Amma ae ba'a Cikin kurkukun Nayi maki tambayar ba, Kawai ni inaso insan a wace nahiya Yake, Sannan Na jininka da zai Iya sadaukar dakai Kamar wa kenan"? Tsohuwa bata amsa mata tambayarta ba, sai da ta fara miƙa hannu ta ɗauki kofin da ta zuba shayi acikin shi, takai bakinta tana kur6arshi kusan sau uku, Angel dai ta zuba mata ido, bayan ta Ajiye kofin saman table ɗin, Tana faman mulmula baki tace"Shayin da daɗi, Ki jaraba sha mana" girgiza kai angel tayi"Na ƙoshi, ni dai kawai ki amsa mini tambayata" dariya tsohuwa tayi"Ban ta6a ganin yarinya mai wayau da kaifin basira ba irin naki, Gaskiya Iyayenki Sun Iya haihuwa gaki Kyakkyawa Kamar ke kika ƙera Kyanki,.." ɗaure fuska angel tayi ganin tsohuwa Na ƙoƙarin Kaucewa Tambayarta, ta hanyar canza wani zancen, Rai a6ace tace"ba wannan na tambayeki ba, Ki bani amsar tambayarta," Jinjina kai tsohuwa Ta yi idonta acikin na angel tace"idan na baki amsar tambayarki, Ni kuma me xaki bani? Kinsan ance gwammanti bata aikin banza" kallon rainin wayau angel tayi mata"Amma ae kinsan bani da abunda zan Iya biyanki da shi ko?, Ni dai kawai ki amsa mini tambayata" Tea pot tsohuwa Ta ɗauka ta ƙara tsirara ruwan tea ɗin acikin cup ɗin gabanta, kafin ta ajiye pot ɗin ta ɗauki kofin takai baki tana sha" Sai da ta kur6e shi duka ta sauke kofin saman table, Tukunna tace"Tambaya ta farko, Gidan kurkukun ƙaddara Ni kaina bansan awace Nahiya yake ba, Abunda na sani shi ne ba'a Cikin kowace ƙasa Yake ba, mashin ko mota bazasu Iya kawo ki cikin kurkukun nan ba" aruɗe angel ke kallonta, sai da takai karshen maganarta angel tace"Amma Ni lokacin da za'a kawo ni acikin mota aka ɗauko Ni, idan har zan Iya tunawa" dariya tsohuwa Ta saki, "iya saninki kenan, A mota aka Cafko ki, Amma Bayan nan bazaki Iya tuna Ta Cikin ina aka ƙaraso dake nan ba," shiru angel ta yi Zuciyarta cike da was wasin maganar tsohuwa, Gani take kamar ƙarya take Yi mata, Muryar tsohuwa ce ta katse mata Zancen nata da cewa"Tambaya ta biyu, Na jinin ka da zai Iya sadaukar dakai, Mafi rinjayen sadaukarwa Iyayene waɗanda suka Yi silar zuwan ka duniya sune suke sacrificing ɗin ɗansu, Uwa Ko Uba, Bayansu Kuma sai Cikin Blood relatives ɗinka, Domin kuwa Bare bazai ta6a Iya sadaukar dakai ba" A matuƙar kiɗime angel ke kallon tsohuwa, Muryarta har rawa take yi wurin furta"Iyayen mutun? uwa ko Uba? Anya kuwa zan Iya yarda da maganarki? Duk irin ƙaunar dake a tsakanin Iyaye da ɗansu Zasu Iya sadaukar dashi zuwa ga wannan ƙuntatacciyar rayuwar? To Meyasa zasu Yi hakan? Fuskar tsohuwa ɗauke da murmushi tace"Kina mamaki ne?, dama nasan zaiyi wuya ki yarda da magana ta, Yanzu dai Ina sauraronki, Idan akwai tambayar da kike da ita, Ki faɗa mini kafin in tafi" Angel dai ta jinjina maganar tsohuwa abun Ya tsaya mata arai, ya cunkushe kwakwalwarta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"Tambaya Ta ƙarshe da nake so Inyi maki, Mu prisoners dake rayuwa a gidan Kurkukun ƙaddara, Jinsi ɗaya ne? Dukanmu ƴan nigeria ne? Naga da yawan mu kamar fararen fata ne, Tsohuwa tace"meyasa Ki kece haka"? Angel tace"saboda Sam babu kamanceceniyar Jinsin baƙar fata atare da mafi rinjayenmu, Misali Kamar danish da Parveen da Javed Sun fi kama da ƴan ƴankin Asia, Azeeza Kuma kamanninta sak da European, Ita kuma batool tafi kama da Jinsin Larabawa, idan muka koma 6angaren Hanna da Hibba, sun fi kama da buzaye Ƴan ƙasar niger....." ɗaya bayan ɗaya saida angel ta korawa tsohuwa Bayani adangane da Jinsin da kowannan su take hasashen yana kama da shi, takai ƙarshen maganar, a ƙagare da son jin amsar da tsohuwa zata bata, "Lokacin da kina atare da Iyayenki, Mutane da wani jinsi suke kwatantaki"? Tsohuwace ta jefa mata tambayar yayin da take sakin murmushi, Yatsina fuska angel ta yi tare da cewa"Sun fi tsammanin Ni balarabiyace wasu kuma baturiya, amma asalin mahaifiyata half cast ce, auntyna ce ta faɗa mini cewa kakata mace balarabiyar ƙasar egypt ce" Tsohuwa tace"Kinyi kyan kai, Wannan tambayar da kikayi mini, Kina da amsarta ahannunki, ina fata zaki tashi ki tafi Cikin ƴan uwanki tunda na amsa miki tambayoyinki," maƙe kafaɗa Angel tayi alamar bazata tafi ba "Korata kike Yi daga ɗakin ki? Tsohuwa tace"a'a kawai dai Akwai inda nake son xuwa ne" Mamaki akan fuskar angel tace"ta ina xaki bi ki fita daga Cikin ɗakin nan naki bayan naga babu ƙopa, Koda yake ba abun mamaki bane, ae naga kafin ma in shigo Ciki, Kincanzawa ɗakin suffarshi duk don kada In yi maki leƙen asiri" tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya, Itama angel ɗin dariyar tayi, sai da suka kammala shan dariyarsu kamar wasu ta6a66u, bayan sun tsagaita da yin dariyar angel tace "Na jima inaso in tambayeki, Ya akai kika san Tarihin rayuwata? Kinsan komai dangane dani, Bayan haka kuma inaso insan asalin sunanki, Daga kin amsa mini waɗan nan tambayoyin xan Tashi intafi Cikin ƴan uwana" Tsohuwa bata amsa tambayar ba, har sai da ta ɗauki tea pot ta ƙara zuba ruwan shayi a kofi ta kur6a sau biyu, Sannan ta ajiye kofin ta soma magana atsanake, "Amsar tambaya ta farko, Duk yaron da aka sadaukar agidan kurkukun ƙaddara, Muna bibiyar rayuwarshi ne tun Yana acikin Cikin mahaifiyarshi, Har zuwa lokacin da zata haife shi, zamuyita bibiyar rayuwarshi da zarar yakai shekarun da muƙe buƙatarsa To babu makawa xamu ɗauke shi ne...." "hakan na nufin tun ina jaririya kuna atare dani? Kenan kune kuke sanyani duk wani mugunta da nake Yiwa daddyna"? Da ruɗu akan fuskarta tayi tambayar, tsohuwa tace"A'a, bamu bane, baƙin aljanine dake atare da mahaifiyarki, Yana matuƙar sonta, Kuma yana da zafin kishi, shine maƙasudin rashin jituwar Iyayenki, Ya tsani Mahaifinki tajudden yaso ya tarwatsa shi, Amma hakan ya faskara saboda Daddnyki mutunne maison yin ibada, bai wasa da azkhar, kuma yana yawan yin sadaka, sannan babbar kariyar dake atare dashi, Yana Yin nafilfilin tsakar dare, A lokacin da benazir ta haifeki, Baƙin Aljani Ya fita daga jikinta ya koma a jikin ki, domin ɗaukar fansa akan mahaifinki, yayi amfani dake wurin ƙuntata mishi, Amma A yanzu Baƙin Aljanin baya atare dake, Angel fa ta shiga ruɗu, duk da tana kokwanton maganar tsohuwa, Bakasafai Take yarda da zantuttukan ta ba saboda sanin Cewa Ita ɗin Babbar maƙaryaciya ce, "Kin tambayi sunana, Zaki iya kirana Da TAMIRA Shine Asalin sunana," Tsohuwa Na kai ƙarshen maganarta, Ta yunƙura ta miƙe daga saman Kujerarar, Da sandar hannunta ta nuna ma angel hanyar fita daga ɗakin, batare da musu ba, Angel ta miƙe ta nufi hanyar fita daga Cikin ɗakin Har takai bakin ƙopat fita, Muryar tsohuwa ta dakatar da ita, "Shawarar Da nake so Na baki, Kada ki kuskura kice zaki Sanya naci akan sai kin gano ainihin ma'anar Kurkukun ƙaddara, domin kuwa daga ranar da kikasan ma'anarshi, Bazaki sake runtsawa ba, Kuma ba zaki sake Jin daɗin abinci ba, duk wani kingin jin daɗi da ya yi saura acikin rayuwarki, Zaki rasa shi ne! Wani irin mummunan faɗuwar gaba angel taji, Har saida ta dafe kinjinta saboda bugun da zuciyarta tayi mai sautin gaske, Tsohuwa taci gaba da cewa"Ƴan uwanki suna farin Cikin kasancewarki acikinsu, Saboda Kin kawo musu canji acikin rayuwarsu, Ina fata zaki mayar da hankali wurin faranta musu rai, Amma fa kinsan da sanin duk ranar da kika Binciko ma'anar The destined prison, daga ranar daga ke har su, Zaku fuskanci matsanancin tashin hankali, Kuma daga wannan Lokacin bazaku ƙara Yin tozali da TSOHUWA TAMIRA ba, Zaku yi ta yin gwagwarmayar rayuwa ne atsakaninku, na gargaɗe ki ne saboda Ina sane da duk wani ƙudurinki nasan bin kwakkwafin Gidan kurkukun ƙaddara, Shiyasa na sanar dake irin matsalar da zaki jefa kanki da kuma ƴan uwanki" angel na ƙoƙarin Waiwayowa baya ta kalli tsohuwa taji an ingizata waje, Ƙopar ɗakin ta rufe, Kamar an jehota ta faɗo ƙasa, Cikin ɗakinsu, har kanta saida Ya bugu, Tun daga wannan Ranar Angel tashiga ruɗani, Kalaman tsohuwa sunyi matuƙar ɗaure mata kai, Tarasa Ina zata tsoma ranta taji daɗi, Kowa Saida Ya lura da canzawar da tayi, Sam tadaina shiga cikinsu, Gani take kamar Dukansu mutuwa zasuyi shiyasa take janye jikinta gudun kada sabon Yayi yawa ta yadda zata rasa kanta idan ta rasa wani acikinsu, Su batool duk sunyi tsammanin rashinsu Parveen Ne yasa ta canza ta shiga damuwa, Kullum cikin Lallashinta suke yi, Akan tayi haƙuri su koma kamar yadda suka ada, Daƙyar suka samu angel ta koma Yi musu wasa da dariya, Harma tana koya musu wasu wasanni donsu farantawa junansu, Akwana a tashi Yau tsawon Sati Biyu kenan, Ba'a dawo musu da ƴan uwansu ba Har sun fidda rai da sake ganinsu, tun suna tambayar tsohuwa har sun gaji sun daina, kowa ya zubawa sarautar Allah Ido👀 Yau Tun da Suka tashi daga bacci suke ta jiran a kawo musu abincinsu suci amma shiru giants basu zo ba, Tun safe Har marece, Jikinsu duk Ya yi laushi, azeeza tuni ta fara Yi musu kukan yunwa, Lokacin da dare Ya ratsa hasken ɗakin Yayi duhu, Nan fa suka ƙara shiga tashin hankali ganin zasu kwana basu Ci abinci ba, la66ansu duk sun bushe, Ruwa kaɗai suke tasha tun safe, Cikinsu harya ɗaure, wasu daga Cikinsu hada amanshi su ka yi, a ƙarshe suka haƙura Da abincin, Kowa Ya hau saman gadonshi ya kwanta, Cikin sa'a bacci ya ɗauke su, Ganin sun nutsa acikin baccin su yasa angel ta sanya hannu ta yaye bargon data lullu6e fuskarta da shi, Saukowa ta yi daga saman gadonta, Sumar kanta duk ta cukurkuɗe kamar ƴar mahaukaciya saboda rashin gyara, Cikin duhu take tafiya tana laluban hanya, Fitila taje ta ɗauko ta kunnata, Tana haske Saitin gadajensu Hannah, ganin babu mai motsi acikinsu Yasa tayi sauri Cikin sanɗa ta nufi sashen toilet ɗinsu, har yanzu bata haƙura da Ƙudirinta ba, Nason fasa gilashin nan, Alwashi ne ta ɗaukarwa kanta Koda zata rasa ranta saita Ga uban me ake aikatawa acikin gidan kurkukun, Duk da tana Jin fargaba akan irin gargaɗin da tsohuwa tayi mata, don a lokacin harta fara tunanin ajiye makaman yaƙinta, amma daga baya sai ta dinga jin tamkar ana tunzurata akan taje taci gaba da jaraba fasa gilashin zata Ci nasara, Zuciya da saƙe saƙe, gani take kamar idan ta fasa gilashin ta dira ta cikin tagar, zata samu damar zuwa wurinsu deeja ne, Harma ta dawo dasu Cikin ɗakin, Da yake sune damuwarta, Tana shiga Cikin toilet ɗin, Taja ƙopa ta garƙameta da jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, ta ɗaga hannayenta Sama tana roƙon Allah Ya bata Ikon Fasa Glass ɗin a karo na karshe don daga yau ta sanyawa ranta cewa idan har bata fasa shi ba, ta gama zuwa tana shan wahala, zata haƙura ne, Bayan ta kammala yin addu'ar, Da ƙwarin gwiwarta ta kai hannu ta rarumi bokitin ƙarfen, Sai da taja da baya ta watsa dagudu ta buga tsalle ta daki glass ɗin Da iya ƙarfinta na karshe, Amma wani abun takaici ko tsagewa Baiyi ba, kamar dai kullum haka taci gaba da bugun glass ɗin da bokitin amma Yaƙi nuna alamar ana bugunsa, saboda tsabar zufar dake tsastsafo mata ajikinta Tamkar wadda aka tsamo daga Cikin teku, Idanuwanta sun rune saboda wahala, Hannunta sai zogi yake yi mata, ga wani irin fitsari daya Matseta, da sauri ta jefar da bokitin gefe ɗaya ya gangara ƙasa, Tasanya hannu ta kwale wandon jikinta, Zuƙunnawa tayi a bakin magudaji tana fitsari, sai da ta kammala taje gaban fanfo tayi tsaki, tana kokarin miƙewa kwatam ta hango mutumin jingine da bango, Ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, Tun kafin ma ta ƙarasa juyawa ta gane kowanene, Sakamakon doguwar sumar kanshi data hango, Muryarshi ce ta ratsa kunnuwanta, "Can I give u a hand"? ras taji gabanta ya faɗi, azuciyarta tace"Danishi! Nashiga uku, kada ace ya ga abunda nake ƙoƙarin Yi, wayyo Allah na" rai a6ace ta ƙarasa juyowa tana fuskantar 6angaren da yake atsaye ya jingina bayan shi jikin bango, Rai a6ace ta nuna shi da yatsa"Wannan wani irin shashanci ne danish? Why zaka dinga faɗo mini Cikin toilet? yanzu da ace na tu6e kaya ina wanka ko ina wani uzirin Shikenan ka gane mini tsiraci na, Wlh bazan ƙyale ka ba" A fusace ta nufi bokitin data jefar ƙasa tasa hannu ta ɗaukeshi Ta daddage ta wurga mashi bokitin, Da sauri danish ya sanya hannayen shi biyu ya cafke bokitin a hannunshi, ɗagowa yayi da lumsassun idanuwanshi ya ɗaurasu akan fuskantar, "Raunata ni kike so Ki yi? A ƙule tace"kashe ka zanyi " Cikin sanyin murya yace"Am really sorry, na kar6i laifina, kada ranki ya 6aci, daga yau bazan sake ba faɗo maki cikin toilet ba," yakai ƙarshen maganar a yayin da ya ajiye bokitin ƙasa, ya ɗago idonshi Yana kallon Tagar da angel ke ƙoƙarin fasawa, Zaro idanuwanta ta yi ganin yana kallon glass window ɗin da alama yaga abunda take Yi, muryarta na kerma tace"Nasan kaga abunda nake kokarin yi, So nake in fasa gilashin tagar nan, Saboda Ina da matsalar kwakwalwa, Tun lokacin da ina agidan daddyna kafin zuwana kurkukun nan, Na fasa gilassai bila adadin saboda Ni idan nayi tozali da gilas tsoro Yake bani, kuma hakan yana jaza mini matsala, Likita ma yace Idan ina yawan zama inda ke akwai glass zan Iya mutuwa" angel sarkin wayau, idanuwanta cike tab da kwalla takai karshen maganar, hada marairaice mishi fuska don Yaji tausayinta, ya kuma yarda da maganarta, Danish bai kawo komai aranshi ba, har cikin zuciyarshi ya yarda da kalamanta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya tallabo fuskarta, Idanuwan su acikin na juna, Cikin sigar lallashi yace"Am sorry angel, don't cry pls, da kin faɗa mini tuntuni da na jima da sauke miki gilashin," ta6e baki tayi tare da cewa"Ae bazaka Iya ba, ko Ni nasha gwada cirewa amma na kasa, kullum saina sha wahalar," ta fadi hakanne don tasan Cewa danish bazai Iya ba, ita kanta da take da ƙarfi ta jaraba ta kasa balle shi da yake sai a hankali ba ƙoshin lafiya ba, "xan jaraba in gani idan zan iya," yakai karshen maganar yana tattara hannun rigarshi, da sauri angel ta ɗauko mashi bokitin ta miƙa mashi, bakinta ƙumshe da dariya So take yasha wahala kamar yarda ta sha, Shima Yaji ajikinshi, Girgiza mata kai yayi"bana buƙatar yin amfani da bucket, I will use my hands" dariyar rainin wayau angel tayi mashi"wlh bazaka Iya ba, Da hannu fa ka ce, haba dai, kai dai ka kar6i Bokitin inga iya ƙarfin ka," Bai saurareta ba, Ya tunkari Glass window din, Da yake Allah yayi shi da tsawo, Yafi angel tsayi ba sai yasha Wahalar yin tsalle ba kamar yarda take yi, Agaban tagar ya tsaya yana kallonta, Angel ta ruƙe qugu, Tana jiran ganin Ikon Allah, Fuskarta ɗauke da dariyar mugunta, hannayen shi biyu ya sanya yana shafa Jikin glass ɗin da ya yi uwar ƙura, ƙasan glass ɗin Ya ruƙo da yatsunshi, Ƙura ido angel tayi ganin glass ɗin kamar ya fara motsi, Gabanta ne ya faɗi ganin Danish ya daddage Ya 6a66ako glass ɗin tun daga tushen shi can cikin ginin dutsen da aka zura shi, Haka ya zaƙulo shi gaba ɗaya ya curo faskeken glass ɗin, Tashin hankalin da ba'a sama shi date, Kanta Ya gama ɗaurewa, Ta zazzaro idanuwanta waje, kwayar idon kamar zata faɗo ƙasa saboda tsabar mamaki, Gaba daya tabi ta ruɗe ta rikice, Tarasa bakin magana sai bin shi da ido take yi kamar wadda aka dasa ma Aya, A ƙasa Ya jingine glass ɗin Jikin bango, Ya ɗago yana kakka6e tafin Hannayenshi da ƙura ta buɗe su, A wani slow Ya juya bayan shi Yana kallon angel dake atsaye Ko motsi bata Yi, Ta ƙame kamar abun bautar ƙasar india wato kirishna, Cikin sanyin mirya ya ambaci sunanta"Angel"? Shiru bata amsa mashi ba, domin kuwa sam bata acikin hayyacinta, matsawa yayi kusa da ita, Ya sanya hannayenshi biyu ya dafa kafaɗunta, "Meke faru ne? Maimakon inga farin Ciki akan fuskarki, Ko baki ji daɗi bane? Na sauke maki glass ɗin, daga yanzu kin daina shan wahalar bugun shi da bokiti" shi kaɗai yake ta maganarshi, kwata kwata bata a hayyacinta, hura mata iska Yayi asaman fuskarta da bakinshi, Amma ƴar tahalikar nan ko ƙyata idonta bata yi ba, Janyota yayi zuwa jikinshi Ya kwantar da kanta saman chest ɗinshi, Ya sanya hannunshi abayanta yana shafa sumar kanta, kafin ya matso da lips ɗinshi saitin kunnanta yayi mata raɗa"angel, faɗa mini meya faru? Ko kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet ɗin gaba ɗaya, yadda bazaki sake ganin shi ba? Jin taƙi yi mishi magana, ya raba jikin shi daga nata, Ya nufi gaban fanfo Ya kunna ruwa ya ɗebo a tafin hannunshi, Ya dawo inda take atsaye kamar gunki, Ya watsa mata ruwan saman fuskarta, Nan take Taja dogon numfashi, har wani zabura tayi ganin shi agabanta, a ruɗe ta wurga idanuwanta kan tagar, Tayi tsammanin ko mafarki take Yi, amma sai taga akasin Hakan dagaske dai Danish Ya cire Glass ɗin tagar da take ta shan wahalar son fasa shi, Tsawon kwanaki, Lamarin Yayi matuƙar ɗaure mata kai, yadda har ya iya 6a66ako shi tun daga tushen shi ya zaro shi, Wanda Tayi imanin Babu wani mahaluƙin da zai Iyayin wannan aikin hakanan siddan ragadan batare da Akwai wani shiri atare da shi ba, Tsohon ginine fa kuma na dutse, A yanayin fuskarta baka iya gane halin da take Ciki, Ta yi farin Ciki da cire glass din da Danish Yayi ko kuwa batayi ba? Tabbas tayi fari ciki mara misaltuwa sai dai mamaki Ya hana ta nuna wannan farin Ciki, Ayanzu ta ƙara zargin cewa danish Ba shi kaɗai bane, Kuma ba wani ke sarrafa shi ba, tunda da ace wani ke sarrafa shi da baza a bari Ya cire glass ɗin nan ba, ganin irin kallon da take Yi mashi ne yasa shi ruƙo hannunta acikin nashi yace"Angel baki bani amsa ba, kina so in kawar da glass ɗin daga Cikin toilet din"? kamar wata sakarya haka take binshi da ido, sai da ya sake maimaita maganar tukunna ta iya bashi amsa da cewa"Inaso ka maida shi yadda ka ciro shi, Kaga duk lokacin dana shigo cikin toilet ɗin sai in zaro shi in kawar dashi wani wurin yadda bazai iya yin affecting ɗina ba" amsa mata yayi da toh, Ya juyawa ya nufi inda ya ajiye glass ɗin Ya ruƙo shi ya shiga kiciniyar mayar dashi, Bayan Ya kammala Ya juyo yana kallonta a lokacin Ta juya baya tare da ranƙwafawa Ta ruƙo hannun fitilar da tazo da ita, ɗagowa tayi suka haɗa ido da shi, Daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tasakar mishi, muryarta na rawa tace "Nagode sosai danish, you're so kind, ka damu dani kuma kana bani kulawa, miƙa mashi hannunta tayi"Zo mu koma ɗaki mu kwanta, Dare yayi sosai," ƙarasawa danish yayi inda take atsaye ya zura hannunshi acikin nata, ta ruƙe sosai tana faɗin"pls keep it under wraps, saboda bana so kowa Yasan cewa Mun cire glass ɗin nan kaga tsohuwa za ta yi mana faɗa idan taji awurin wani, koba haka ba" ɗaga mata kai yayi alamar eh, tare da cewa"I will zip my lips, daga ni sai ke," Cike da jin daɗi tace"Mu biyu kaɗai muka sani, Idan naji maganar awurin wani To kaine, duk da nasan bazaka faɗa ma kowa ba," Ba ƙaramin daɗi danish yaji ba ganin yadda take ta fara'a saboda Ya cire mata gilashin dake Sanya mata jin tsoro, yayin da ita kuma angel ɗin Shine abun tsoro awurinta, don kuwa ga dukkan alamu Akwai wani abun al'ajabi attare dashi, Kusan atare suka duro da ƙafafuwansu Cikin ɗakin nasu, Adai dai Lokacin kunnuwansu suka soma Jiyo musu motsin buɗe ƙopar ɗakinsu, Mamaki ƙarara akan fuskarsu suka kai idanuwansu saitin benan dake a ɗakin, daga saman matattakalar benan suka Fara kallon ƙafafuwan Mutun Uku dake saukowa, masu sanye da jajayen Uniform, daga bayansu Kuma Giants ne Hannayensu a ruƙe Da Kayan abinci......shin su wanene? *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Tun daga ƙasa har sama su Angel ke binsu da kallo, Yayin da giants suka Wuce Cikin ɗakin zuwa Inda Dining carpet ɗinsu Yake, Bayan sun ajiye masu dinner ɗinsu, Batare da 6ata lokaci ba, Suka fuce daga Cikin ɗakin, Atare Suka kalli juna ita da danish fuskokin su da alamaun mamaki, ga dukkan alamu basu gane su wanene ba, duk sunyi tsammanin Ko sabbin ɗauka ne aka kawo musu acikin kurkukun, "Danish su wanene ko ka gane su"? Girgixa mata kai Yayi alamar a'a, Jan hannunshi Tayi"muje mu gani," Tayi gaba Yabi Bayanta, Suna ƙarasowa bakin benan Inda suke atsaye, Ta haska fuskokinsu da fitilar Hannunta, Ras taji gabanta ya faɗi, da ƙarfi ta ambaci sunayensu"PARVEEN! RUBINA! DEEJA" sai da ta kira sunayen su Tukunna danish Ya gane cewa sune, Sunyi matuƙar girgiza da yanayin da suka Yi tozali da ƴan uwan nasu, Sam sun kasa Yi masu magana, Fatar Jikinsu Tayi haske sosai, Fuskarsu tayi jawur abunka ga farar fata, Idanuwansu duk sun kumbra suntum ga dukkan alamu ba ƙaramin kuka su kayi ba, Kayan jikinsu sun yi uban squeezing Kamar waɗanda aka kwato daga Bakin kura, Sumar Kansu Kuwa Ta hargitse ta fita hayyacinta, kai kace sabbin mahaukata ne, Kwata kwata babu natsuwa atare dasu, Yatsun hannayensu dana ƙafafuwansu sae kerma suke Yi, kamar waɗanda sanyi yayi ma mugun kamu, Tsabar ruɗu Ya hana Angel da danish su furta wani abu, Duk irin Zumuɗin da suke Yi nasan adawo musu Da ƴan uwansu Jikinsu Yayi laƙwas, domin kuwa ba haka suka tsammaci ganinsu ba, wani tashin hankalin ma La66ansu dake a bushe sun faffashe, hada busasshen jini ajikinsu, Muryar angel cikin damuwa ta ambaci "Innalallahi wa'inna ilaihirraji"un! Parveen! Deeja! Rubina! Meya faru daku? Meyasa kuka canza har haka? Dan Allah kuyi mini magana, Me akayi maku? Duk kun canza kun rame kun fita hayyacin ku," Idanuwanta acike tab da kwalla ta yi maganar, hawaye ne masu ɗumi suka soma gangarowa akan fuskokinsu, Lokaci ɗaya suka fashe da matsanancin kuka mai tsuma Zuciya, hankalinsu danish Yayi matuƙar tashi, Koke koken Da suke Yi ne Ya yi silar farkawar su Batool, har cikin kunnuwansu sautin kukansu parveen ke kai musu, Aikuwa Jiki na rawa suka Yaye bargunan da suka lullu6a dashi, Da gudun gaske Suka nufi wurin su ɗaya bayan ɗaya suka ƙaraso bakin stairs ɗin banda mutun ɗaya, Azeeza dake fama da lalurar makarantar dare, Ta farka daga bacci amma bazata Iya kawo kanta inda suke ba, Koda su Batool Suka ɗaura idanuwansu akan fuskokinsu Parveen, wani irin farin Ciki ne Ya bayyana akan fuskokinsu, Sam basu Lura da yanayin da suke Ciki ba, Saboda tsabar murna Batool ta cakumo deeja da niyar ta rungumeta aikuwa Ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara, wadda tayi matuƙar girgizasu, da sauri Danish ya sanya hannayenshi Saman Ears ɗinshi Ya toshe su gudun kada lalurar shi ta motsa, aruɗe suka haɗa baki suna tambayar lafiya meya faru dasu? Meyasa su ke Kuka? maimakon suga farin Ciki akan fuskokinsu, Muryar batool a sanyaye tace"deeja meyasa kika saki ƙara saboda ina ƙoƙarin Rungumarki ajikina? Ba ku yi farin Ciki da dawowa Cikin Mu bane"? shiru babu wanda ya amsa mata acikinsu sai kuka suke Yi, Yasmin tace"Na lura gaba ɗaya ma basa acikin hayyacinsu zaiyi wuya ace sun gane mu" javed yace"pls Stop shedding ur tears kuna ƙara tayar mana da hankali, meyasa duk kuka canza? Tsohuwa ta faɗa mana cewa kuna acikin ƙoshin lafiya, Har ma tace mana kuna kewarmu, amma sai gashi Yadda muka ganku a yanzu ba haka mukayi tsammani ba, why pls"? Zuciyarshi a hautsine ya ƙarasa maganar, "Angel Ki yi mana bayani? Yaushe aka dawo dasu? Meyasa kuma basa Iya magana" Cikin shessheƙar kuka Batool Ta jefa mata tambayar, Itama angel ɗin kukan take Yi, daƙyar ta iya tsagaitawa ta bata amsa da cewa"Kamar yarda kuka gansu haka muma muka gansu, Giants ne suka shigo tare dasu, Hada abincin ma suka kawo mana gashi can sun ajiye farantan saman dining carpet, Dukkan mu mun shiga ruɗanin halin da muka riskesu, Ko magana ma sunƙi yi mana" Matsawa haris yayi tare da kai hannu Ya ruƙo yatsun hannun Rubina, afirgice ta zame hannunta daga nashi, ta runtse idanuwanta tana faɗin"Zafi nake ji ku daina ta6ani bana so, Ku ƙyale ni ku rabu dani, bana son ganinku" lallashinta hannah tayi"Shikenan tunda bakya so ba zamu ƙara ta6aki ba, Kiyi shiru kinji" Tayi maganar tana leƙen fuskarta, Angel tace"Ni dama nasan za'a rina, Mutanan nan raina mana wayau suke yi, Tsohuwa tayi mana ƙaryar cewa An kaisu treatment room inda za'a duba lafiyarsu, tsawon 2 weeks kenan, Ga shi yau an dawo dasu babu alamun sauƙi ajikin su, ga dukkan alamu ma wani sabon Ciwon aka jaza musu " rai amatuƙar 6ace angel tayi maganar tana huci, Mubeen yace"pls Mubi komai a hankali, ko dan saboda su Deeja, Ni inaga yakamata aje a sanarma tsohuwa tazo ta duba halin da suke aciki...."tun kafin mubeen yakai karshen maganar shi angel ta wurga mashi uwar harara, kamar zata rufe shi da bugu tace"Amma baka da hankali wlh, wai har yaushe ne zaku fahimci cewa matar nan Muguwace ba sonki take Yi ba, Kuma babbar maƙaryaciya ce! Tayi mana ƙaryar cewa A cikin satin da aka ɗauki su parveen za'a dawo dasu, Sai gashi yau tsawon 2 weeks kenan, Sannan bayan haka ta sanar damu cewa Su parveen sun samu lafiya harma suna tambayarmu, To yau gashi dai an dawo dasu Ba kamar yarda aka ɗauke su ba, kwata kwata babu cikakkiyar lafiya atare da su, ku baku lura da canzawar da su kayi bane? Muryarta a harzuƙe tayi maganar, Jijiyoyin wuyanta duk sun bayyana jikin fatarta saboda tsabar masifa, Kowa yayi shiru yana sauraronta, Cigaba da magana tayi"Kun maida kanku kamar gumaka, Ana cutarku baku ganewa, Yanzu ku kalli fuskokinsu deeja da la66ansu, wlh ko makaho ya shafa jikinsu sai yaji ajikinshi cewa basu da ƙoshin lafiya, Balle ku da kuke Mutane, Su parveen ba Maganin ciwonsu akayi musu ba, Ƙara musu wani ciwon akayi bisa wanda suke dashi" Wannan bayanin Da angel ta kora musu Yasa sun fara Kokwanton Kalaman tsohuwa, Sun kuma fara yarda da ita, Muryar hibba asanyaye tace"angel ae mu bamu san komai ba, Rayuwa kawai muke Yi acikin duhu, ba lallai mu iya fahimtarki ba," Haris Yace"Tun da kike atare damu ban ta6a Yarda dake ba, Saboda ina zargin ke ɗin Kamar babu gaskiya acikin lamurranki, Yau ce rana ta farko Da kika fara sanya mini kokwanton wani abu acikin raina, Sai dai bazan ta6a Yarda dake ba har sai kin bani kwakkwaran Hujja da zata tabbatar mani cewa Cutar da rayuwarmu ake Yi,' haris na kai karshen maganar shi, Batool tace"Muna goyan bayan haris, Idan har dagaske Ana Cutarmu a gidan kurkukun nan, To kiyi ƙoƙari ki bayyanar mana da kwakkwarar hujjar da zamu aminta dake, Ɗaya bayan ɗaya Angel ke binsu da kallo, wai wace irin hujja ce suke so Ta kawo musu? Bayan ga abu nan zahiri sun gani, acikin zuciyarta tayi tambayar, Tunawa da irin rayuwar da suka taso suna yi yasa ta Yi musu uziri, dole suna da ƙarancin fahimta, kansu Yana acikin duhun Jahilci, idan har bata lalubo hujjar da zasu Gasgata maganarta ba, to kuwa bazasu ta6a yarda da kalamanta ba, taya za'ae ta samo hujja bayan tsohuwa ta gargaɗe ta akan kada ta kuskura Tace zata Zurfafa bincike akan Gidan kurkukun, har ga Allah tana matuƙar fargabar Abunda zai biyo baya idan har tace zata Kawo musu hujja, Sautin kukan Azeeza ne Ya jawo hankulansu, kusan atare suka Waiwaya baya suna kallonta, Har ta sauko daga saman gadonta, Sai faman laluban hanya take Yi tana faɗin" Wai bakowa ne akusa, Ni baza'a nuna mini su parveenar mu ba, dagaske an dawo mana dasu? Ina ta magana tun ɗazu babu mai ji na," Kallon Naufal Haris yayi tare da cewa"Kaje ka ruƙo ta kada ta faɗi" Naufal ya amsa mashi da toh, Da hanzari Ya tunkari parveen, Yana ƙarasawa gabanta, Ya ruƙo hannunta acikin nashi, Ya janyota zuwa inda suke abakin benan, "to ina su parveenar suke Ae ban ganinsu" Tsoki Haris Ya ɗan ja"kefa matsalarki kenan abu kaɗan sai kuka, Kamar kinfi kowa baki, Ki barmu muji da abunda Ya ishe mu," a ƙule yayi maganar, cikin sanyin murya danish yace"haris ka bi ta a hankali, banaso kana yi mata magana irin haka" jinjina kai haris yayi tare da cewa na daina, kawai bana son yawan kukanta ne," "Ni dai ku nuna mini Su, kuma kuka bazan daina ba, Yanzu na fara sai dai ka buge ni" rai a6ace azeeza tayi maganar, mutumin dake fama da kanshi, kwata kwata bata iya ganin fuskokinsu, Biji biji take gani, Matsar da ita naufal Yayi zuwa gabansu deeja da suka ƙame Sai shessheƙar kuka suke yi, ko gajiya basa yi, "Gasu nan Agabanki Kiyi musu magana" naufal ne yae maganar, Hannayenta ta ɗaura asaman kirjin deeja tana shafata, Harta samu ta ruƙo hannunta ta ɗago shi zuwa saitin hancinta ta shinshina shi, duk suna kallonta, farin Ciki ne ya bayyana akan fuskarta, rungumeta tayi tana faɗin"Deeja Ashe kune dagaske, Nayi farin Ciki da aka dawo mana da ku, yanzu shikenan kunji sauƙi baza'a ƙara raba mu daku ba, Ni dai na roƙe ku kada ku ƙara Yin rashin lafiya, Kodan saboda kada araba mu daku, Saboda bamu jin daɗin rashin ganinku acikinmu" ita kaɗai take ta sambatunta, Javed ya kira sunanta"Azeeza Kiyi hakuri ki ƙyaleta, Basu son ana ta6a su, Har yanzu da sauran Jikin nasu" Cikin shessheƙar kuka tace"meyasa toh basu son ana ta6a su? Basuyi farin Ciki da dawowa Cikin mu bane? Duk irin kewarsu da muka Yi," babu alamun zata fahimce su, angel ce tace"Javed ka barta, tun da naga yanzu Deeja bata Yi ƙara ba kamar yarda tayi ɗazu da batool ta ruƙota," Eve tace"Nima na lura da hakan" "Nidai kuyi mini magana, Wai sai kace baku Ji na, ko fushi kuke Yi damu ne"? matsawa tayi gaban Rubina Ta ruƙo hannayenta takaisu saitin hancinta ta shinshinasu, kafin ta faɗa jikinta ta rungumeta tana faɗin rubina, Kema bazaki Yi mini magana ba? Duk kun shareni," jin shiru bata amsa mata ba, yasa ta janye jikinta daga na rubuna, da alama Jikinta yayi sanyi, Ruƙo hannun Parveen Tayi, batare data shinshina shi ba tace"parveen, Ke ma ba za kiyi mini magana ba? Meyasa bakwa farin ciki da dawowarku Cikinmu ne? Duk irin kewarku damu kayi, Munji raɗaɗin rashinku acikinmu, Tun ranar da Giants suka zo suka tafi daku, Kusan kullum ne sai Mun ajiye maku abinci, amma abanza yake lalacewa, mun yi maraicinku sosai" takai kai karshen maganar tare da ɗaura kanta saman kirjin parveen, hada ƙoƙarin zagayo da hannayenta zuwa bayan parveen ta ƙanƙameta, "Yanzu ya zamuyi da su? nifa nagaji da tsayuwa ƙafafuwana har sun fara Yi mini zogi, Yakamata Mu koma Cikin ɗaki Mu xauna, yasmin ce tayi maganar, Kallonsu Deeja Angel ta yi tare da cewa"Ku zo mu shiga Cikin ɗaki, Nasan Kuma kun gaji da tsayuwa" pls ku wuce mu tafi dare yayi sosai" ta karasa maganar tare da nuna musu Hanya, sai lokacin deeja ta iya buɗe baki tace dasu"Ni bazan Iya tafiya ba, ƙafafuwana zafi suke Yi mini," Kallon Juna su ka yi, Hatta muryarta ta canza, kamar ba deeja da suka sani ba, Muryar parveen na rawa tace"Nima Bazan Iya tafiya ba, raɗaɗi nake Ji," daƙyar tayi maganar saboda raɗaɗin da bakinta ke Yi mata, wanda shi ya hana su yin magana tun ɗazu amma duk suna jin me suke cewa kuma suna fahimta, Rubina tace"nima bazan Iya ba," lamarin yayi matuƙar ɗaure musu kai, Haris yace abunda za'ae yanzu, Zan Goya deeja abayana, danish ka goya rubina ita kuma angel ta goya parveen kai kuma naufal Ka taimaka Ma Azeeza ku shigo ciki, Zuƙunnawa su ka yi agabansu Deeja, Suka haye saman bayansu, Atare suka miƙe suka nufi Cikin ɗakin dasu, Sauran ƴan uwan nasu duk suna abiye dasu, A saman gadajensu suka sauke su, angel ta tambayesu ko suna jin yunwa, suka ce mata a'a, bacci suke so suyi sun gaji," acikin zuciyarta ta kudiri aniyar idan Suka farka gobe zata Tambaye su game da abunda ya faru dasu, duk da tasan zaiyi wuya su iya tunawa, Basu kwanta bacci ba har sai da suka Ci abincin da giants suka kawo musu, bayan sun kammala ci suka koma saman gadajensu suka kwanta zuciyar kowannan su acukunshe take Da tunanin halin da suka riski ƴan uwansu, A daren ranar bayan kowa Ya koma saman gadonshi Ya kwanta, Angel tabi su ɗaya bayan ɗaya Ta tottofe su da addu'a, Ta lullu6e musu jikinsu da bargunansu, Wani abu daya ƙara ɗaure mata kai, A lokacin harta koma saman gadonta ta zauna ta ɗaga hannayenta sama tana Yin addu'o'i kamar yadda ta saba, Kwatsam Taji shessheƙar kukan Deeja, ga dukkan alamu mafarki take Yi, da hanzari angel ta sauko daga saman gadonta taje bakin gadon deeja ta ɗan ranƙwafa tare da kasa kunne tana sauraron me take cewa, Kuka take Yi tana faɗin bana so ku daina kuna cutar dani, zafi nake ji, kashe ni kuke Yi, Ni ku ƙyaleni ku rabu dani" Ciccije la66ata tayi tare da kai hannayenta saman mattress ɗinta tana damkar jikin katifar, Idanuwanta na fitar da ruwan hawaye, Can kuma sai taga deeja ta kai hannu tana sosa gaban wandonta, tana faɗin ƙaiƙayi take ji, zafi yake yi mata, mutuwa zatayi," Daga bisani ne Deeja tadaina sambatun da take Yi, taci gaba da yin baccinta Haƙika angel tayi matuƙar girgiza duk da bata Iya gano komai game da sambatun deeja ba, amma Jikinta yayi mugun yin sanyi, tabbas tana hasashen An yi masu wani mugun abunne kuma agabansu a Kayi musu, tun da gashi nan ta gani da idonta deeja na sosa wurin tana faɗin cewa ƙaiƙayi yake Yi mata, Ikon Allah kenan, An juya musu tunaninsu don kada su Iya tuna komai Da akayi musu, Amma sai gashi Allah Ya haska mata wani abu ta cikin mafarkin da deeja ta yi, yanzu ya rage nata tayi ƙoƙari ta gano me akayi musu, Kasa kwanciya tayi Domin kuwa baccin ya qauracewa idanuwanta, damuwa ce cunkushe acikin zuciyarta, safa da marwa ta shiga Yi acikin ɗakin yayin da zuciyarta ke tariyo mata abubuwan da suka faru ɗazu, na farko tana so Ta yi bincike akan danish, Taya akai yake Iya shiga cikin wurin dake a kulle, 6acewa yake Yi ne ko kuwa bango yake ratsawa ya shigo? Dole ne ɗaya ya kasance Cikin Biyun nan, Bayan wannan Kuma Ta yi matuƙar girgiza lokacin daya shafa glass Ya ruƙo ƙasan shi Ya 6a66ako shi tun daga tushen shi, to wai shi ɗin Aljani ne Ko mutun? Ko kuwa shigarshi A kayi? Ta rasa gane dawa zata Yarda, Lokaci ɗaya kuma Ta fara tunanin meyasa Uniform ɗinsu Ya banbanta dana sauran ƴan uwansu? Su Uku ita da danish da batool su kaɗai suke da baƙaƙen Kaya, Yayin da Su Azeeza nasu Uniform ɗin Jajaye ne dukansu, Tabbas akwai dalilin dayasa aka Banbanta masu launin uniform ɗinsu, don me nasu zai kasance launi ɗaya dana GIANTS? Ta sanya alamar tambaya, ranta ne ya bata cewar bazata ta6a Iya gano menene atattare da danish ba, Har sai ta fara gano Dalilin banbance Uniform ɗinsu dana sauran Ƴan uwansu prisoners!!! Nauyayiyar Azuciyar zuciya ta sauke, saboda yawan tunanin da take Yi da sanya damuwa aranta, Zuciyarta har wani nauyi take Yi mata a ƙirjinta, ita kanta tarasa Ya zatayi wurin rage ɗaura ma kanta damuwa akan hakan Ya faska, Canza akalar tunanin nata Ta yi zuwa gasu Parveen, a yayin da take Cigaba da yin zirga zirga acikin ɗakin nasu, Tana zargin ana cutar dasu ne sai dai takasa gane wata irin cutarwa ce a ke yi musu, Ɗaukarsu da ake da sunan za'a je a duba lafiyarsu, Ga dukkan alamu Ba Lafiyarsu ake dubawa ba, Wani ciwon ake ƙara Danƙara musu ajikinsu, Shiyasa idan aka ɗaukesu daga Cikinsu Ba'a barinsu Cikin hayyacin su, har sai time da aka dawo da su, Tun akan danish ta lura da hakan, sannan kuma Lokacin da giants suka Shigo cikin ɗakin nasu atare da su parveen, da ƙafafuwansu suka tako, Amma daga baya suka ce baza su Iya tafiya ba, Hakan na nufin adai dai lokacin da suka sauke ƙafafuwansu acikin ɗakin daga nan sihirin da akayi musu ajikinsu Ya warware, Suka dawo hayyacinsu har suka gaza taƙa ƙafafuwansu,' Jinjina kai angel ta yi a fili tace"Sannu ahankali zan binciko koma menene, babu fashi domin kuwa Alwashi ne na ɗaukarwa kaina Koda Kuwa zan rasa raina saina gano uban me ake aikatawa A Gidan kurkukun ƙaddara,! Komawa tayi saman gadonta ta kwanta, tare da jan bargo ta lullu6e jikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci Bacci yayi awon gaba da ita, A washe garin ranar, babu wanda Ya farka daga bacci acikinsu, Saboda daren jiya basu kwanta da wuri ba, A firgice ta farka sakamakon sautin shessheƙar kukan parveen daya karaɗe kunnuwanta, ware manyan idanuwanta tayi tare da kai hannu ta zame bargon jikinta, Saukowa tayi daga saman gadon ta nufi gadon parveen a zaune ta same ta tsakiyar gadon, fuskarta ta ƙara kumbura sumar kanta duk ta hargitse, Jikinta hada zufa, Da sauri ta ƙarasa daga gefen gadon ta zaune, tare da kallon fuskar parveen tace"Sister are u ok? Why are u crying? Ko jikin ne"? Daƙyar parveen ta ɗago ta kalli Cikin idanuwan angel, batare da tace komai ba, angel ta kuma cewa"Dan Allah ki faɗa mini meyasa ki kuka? May be Ina da abunda zan iya taimaka maki" cikin nuna damuwa tayi maganar, muryar parveen a disashe tace"bana Jin daɗin Jikina, ƙaiƙayi nake ji, kuma ina so Inyi wanka amma na kasa miƙewa saboda bazan Iya tafiya ba, wahala nake sha" tsananin tausayinta ne ya kama angel, Cikin muryar lallashi tace"shikenan ki daina kuka, kada wannan ya dame ki, Ni zan Iya yi maki komai, Yanzu zan Goya ki in kaiki toilet, idan ma kina so har wankan sai inyi maki" "Nagode sosai Angel," saukowa Angel tayi daga saman gadon nata, ta juya tare da zuƙunnawa tace da parveen ta hau bayanta, Matsawo Parveen Tayi ta lalla6a ta haye bayan Angel, hannayenta ta sanya ta ruƙe parveen, Ta daddage ta miƙe ta wuce toilet ɗauke da ita abayanta, Shigarsu toilet keda Wuya acan Cikin ɗakin Deeja da Rubina suka farka da wani irin sautin kuka mai razanarwa, Duk wani mai bacci saida Ya farka sakamakon Kukan nasu daya karaɗe Cikin ɗakin, Jiki na 6ari suka sassauko daga saman gadajensu, Banda Danish Yana kishingiɗe saman gadonshi, Ya farka amma bai buɗe idanuwanshi ba, da alama baccin bai ishe shi ba, ko kuma tsiwar tasu ce ta addabe shi, Agaban Gadon deeja Haris da Batool, da hibba hada hanna Suka tsaitsaya suna kallonta Fuskokinsu ɗauke da damuwa, Su javed da sauran ƴan uwan nasu suna a zuƙunne gaban gadon Rubina, Duk sun ƙanƙame Jikinsu Dake ta kerma, Sun rasa gane masu, gaba ɗaya sun canza, xama batool tayi daga gefen gadon Deeja, muryarta a sanyaye tace"Deeja, Meya ke faru dake ne? Jikin ki Yana yi maki ciwo ne? Ɗaga mata kai ta yi alamar eh, Haris yace"Ni narasa gane wannan ciwon naku, ance Ana baku treatment amma ya akaiba wani sauƙi atattare daku? Kun wani fige kun fita hayyacin ku," aruɗe yakai karshen maganar, Hanna tace"Deeja zaki Iya faɗa mana inda aka kai ku? Da kuma abunda aka Yi maku? Girgiza kai deeja tayi har lokacin hawaye basu daina zuba kan fuskarta ba, "Bazan Iya tuna komai ba, tun lokacin da aka ɗauke Ni daga Cikin ku, sai Jiya da aka dawo dani Tukunna Na Iya tuna wacece Ni!" Kaitsaye maganar deeja taje kunnan Angel dake Kokarin Fitowa daga sashen toilet ɗinsu, Bayanta ɗauke da parveen data goyo, ta taimaka mata tayi wanka hada sumar kanta ta wanke mata, Kasa Cigaba da tafiya tayi, ta kasa kunne tana sauraronsu Hibba tace"Abun da ɗaure kai, Ni fa gani nake kamar an ƙara musu Ciwon ma, To inba haka ba Kallarsu fa ku gani, sati biyu da suka wuce kafin azo a ɗauke su daga Cikin mu, Da ƙibarsu jikinsu da auki amma Yanzu Kamar an ɗibi naman jikinsu," Kowa fa ya fara Kokwanton wani abu aranshi, Hakan ba ƙaramin daɗi Yayi ma angel ba, saboda sun fara tunani na hankali, Jin muryoyinsu javed dake a zuƙunne gaban Gadon Rubina. yasa takai idonta kansu, Ta kasa kunne don taji su me suke tattaunawa "Rubina Acan inda aka kai ku suna baku abinci? Naga duk kun rame kamar akwai Yunwa attatare daku, Sa'an nan Ya akai la66anku suka faffashe wani Ya cije ku ne? Eve ce tayi mata tambayar. idanuwan rubina cike tab da kwalla tace"A'a ni bazan Iya tuna komai ba, ku daina Yi mini tambayoyi dangane da inda aka kaini saboda bansani ba ni kaina" Mamaki ne ya kamasu, Jin tace batasan komai ba, yasmin tace"Nayi matuƙar damuwa da hankalin da kuke Ciki, bamu yi tsammanin Zamu ganku haka ba a wulaƙance, kwata kwata Jikinku babu alamun sauƙi, saima abunda yayi gaba, Gaskiya nidai ban yarda da wannan treatment room ɗin ba, Yakamata mu yi ma tsohuwa magana, idan wani bai da lafiya acikinmu kada a ɗaukar mana shi, abar mana shi acikinmu muyi jinyarshi" Naufal yace"Wai Ina parveen ne? Naga babu ita asaman gadonta"? A hanzarce suka juya suna kallon Gadon Parveen, Muryar angel ce ta janyo hankalinsu zura gareta, "Gata nan abayana, Ta farka tana buƙatar Yin wanka shine na taimaka mata Tayi, Yakamata suma su deejan su yi wanka, Ko sunji daɗin Jikinsu" Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, Wuce wa angel tayi zuwa cikin ɗakin Abakin Gadon parveen Ta ɗan rankwafa tare da kwantar da ita saman mattress ɗin, Da gudu Azeeza ta nufo gadon parveen ta haye gefenta, fuskarta ɗauke da murmushi tace"Ƴar uwa ya Jikin naki? Daƙyar parveen ta ƙaƙalo murmushi tare da cewa"Da sauƙi sister, Nayi missing dinku sosai Ƴan uwana, Ina abincin da nace ku ajiye mini"? Fuskarta aɗaure tayi maganar tana kallonsu, Azeeza tace"Ki tambayi angel kiji, tun ranar da aka ɗauke Ku daga Cikin mu, Kullum sai mun ajiye maku abinci yana lalacewa, Har mun fidda rai da za'a dawo mana da ku ashe da rabon Mu sake sanya ku acikin idanuwanmu," tana kai karshen maganar ta kifa kanta saman mattress tana kukan karya, murmushi parveen tasaki, tare da miƙa hannunta saman kan azeeza ta ruƙo kalabar da akayi mata, "Azeeza wa yayi maki wannan"? ɗagowa azeeza tayi tare da kallon kalabarta da parveen ta ruƙe a hannunta tace"Angel ce tayi mini, kema in kina so sai tayi maki idan kika ji sauƙi" "Batool da Hannah, Ku taimaka masu deeja suyi wanka, " Angel ce tayi musu magana, Batare da 6ata Lokaci ba, Batool Da Hanna suka Goya su deeja da rubina asaman bayansu, suka nufi toilet da su, Ataƙaice Yau dai kusan Sati ɗaya da aka dawo dasu parveen, Jikinsu Yaƙi sauƙi Lafiya ta yi ƙaranci A jikinsu, basu Iya tafiya sai an taimaka musu, ko sunyi yunƙurin miƙewa da niyar su taka ƙafafuwansu Sai kaga ƙafar ta gurɗe, ko daga baya da suka fara Jin sauƙin jikinsu, sai tafiyarsu ta koma irin ta gwami, basu Iyayin tafiya lafiya lou batare da ƙafarsu ta gwame ba, Hankalinsu Batool Yaki kwanciya, Har zuwa bakin kopar ɗakin tsohuwa su kayi domin Su sanar da ita halin da ƴan uwansu suke aciki, Koda suka kwankwasa ƙopar ɗakin tsohuwa ta fito, Suka sanar da ita abunda ke faruwa dasu Parveen Na rashin Iya tafiyarsu, Sai cewa tayi su cigaba da basu kulawa, Zasu dawo dai dai, tana faɗi musu haka Ta juya ta koma ɗakinta tare da jan ƙopa ta rufe, Babu yadda suka Iya haka suka Cigaba da kulawa dasu, Idan zasu Yi wanka Dole sai An taimaka musu, Batool da angel sune ke ɗawainiya dasu, Hatta wankin Uniform ɗinsu sune suke Yi musu, Hakan ba ƙaramin daɗi yake yi musu ba, Hankalinsu Ya kwanta ganin irin soyayyar da ƴan uwansu ke nuna masu, Da taimakon Allah, jikinsu Yayi sauƙi sosai suka koma yadda suke ada, Tafiyarsu ta dawo dai, Ranar Har wasa su batool suka yi saboda murnar samun sauƙin su deeja, Yanzu babu faɗa a tsakanin Deeja da angel sun daina ƙin junansu, Tun lokacin da aka dawo dasu, angel ta lura da irin canzawar da deeja ta yi, Bata jan kowa faɗa, babu ruwanta da kowa, Sai In ana wasa ne zaka ga ta sanya baki itama ayi da ita, hatta haris Yanzu sun samu jituwa atsakaninshi Da angel, Suna yin rayuwarsu Cikin so da ƙaunar juna, Tsawon kwanaki, Sun samu kwanciyar hankali, A daren Wata rane ne, Angel Ta kawo masu shawarar su yi wasan Ƴar 6urun 6urun, ta gabatar musu da yarda zasuyi wasan, Gaba ɗayansu suka hallara atsakiyar ɗakinsu, mubeen Ne ya cire rigarshi Ya miƙa ma angel, ta kar6a ta ɗaurewa batool idanuwanta da rigar, Da gudu kowanansu Ya ruga zuwa ma6oyarsa, Wasu suka shige ƙarƙashin gado, wasu suka Nufi Cikin toilet suka 6oye, Hada wanda ya 6oye Ƙarkashin table ɗin da suke ɗaura fitilinsu, Batool taci gaba da bin hanya tana lalubensu tana fadin"6urun 6urun ku 6oye ku 6oye da nisa, Garin gudu ku faɗi ku gurje abanza, Kun 6oye" suka ce a'a, Kusan sau uku Tana tambayarsu sun 6oye sai suce a'a, Ana huɗun ne suka ce mata Eh sun 6oye, nemansu ta dinga Yi acikin dakin, Tarasa ina suka 6oye, ga shi sun ɗaure mata idanuwanta sosai bata Iya gani, Angel da azeeza Suna a rungume da juna ƙarƙashin Gadon Batool ɗin, Sai tiƙar dariya suke Yi, Danish kuma Yana a karkashin gadonshi tare da parveen, Haris da deeja suna a Karkashin gadon angel, Naufal da Mubeen Sun 6oye kasan table, hanna da hibba hada javed suna a la6e Cikin toilet, kamar aljanu ko tsoro basa Ji, Su rubina da yasmin hada Eve, A jikin bango suka la6e, Don sunsan bazata iya gano su ba, tunda an kulle mata idanuwanta, Sai wahala take sha sunƙi bari ta kamasu, na cikin toilet ne Suka Ji motsi aikuwa gaba ɗaya suka watso da gudu waje cikin sa'a ta cafki wuyan rigar Javed, Ta dinga tsalle tana faɗin ta kama ta kama, Jin haka yasa sauran ƴan uwan nasu suka firfito daga ma6oyarsu, angel ta warware mata ɗaurin dake akan fuskarta, ta ɗaure ma Javed idanuwanshi, Da gudu kowa Ya rugo Zuwa wurin 6oyenshi, wannan karan Azeeza ta tona musu asiri, fitsari ya matse ta, tace ma angel ta rakata suje toilet tayi, angel tace mata ta jira akama wani acikinsu sai su fita, Aikuwa ta fashe mata da kuka tana faɗin ta taso su tafi ya matseta kada tayi shi awando , Maganar azeeza tayi matuƙar basu dariya, Javed najin muryoyinsu ya dinga laluban hanya Cikin sa'a Ya kamo rigar azeeza a lokacin ta fito daga karkashin gadon, ta buge mashi hannu tana fadin Ita fitsari take Ji, fitowa daga karkashin gadon angel tayi Tace da danish"Ya jira ta rakata tayo fitsarin, Idan suka dawo ita zata Yi wasan amadadin Azeeza" Yace mata toh , Bayan sunje toilet ɗin sun dawo, Sauran ƴan wasan duk suka fito daga wurin 6oyansu, Batool ta kar6i rigar hannun javed ta ɗaure ma angel idanuwanta sosai, wannan karan basu 6oye ba, Raina mata wayau suka dinga Yi suna zagayeta, daga ta miƙa hannu za ta cafkosu sai suyi sauri suja da baya, baƙaramar wahala tasha ba, Daƙyar ta samu ta ruƙo wandon Hibba, Ta dinga murna tana faɗin ta kama, Daren Ranar Ba ƙaramin nishaɗi suka yi ba, Sai da dare ya ratsa tukunna suka kwanta domin Yin bacci, A washe garin da su ka yi wasan ne ta farka fuskarta dauke da murmushi, ta miƙe zaune saman gadonta, Babu wanda ya tashi daga bacci sai ita, Saukowa tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi toilet, da niyar yin wanka, Tana shiga Ciki, taja kopa ta datse, Tsayawa tayi atsaye tana kallon glass din jikin tagar, abunda yasa har yau bata dura ta cikin windown ba, Saboda fargabar maganar da tsohuwa ta faɗa mata na cewa Zata ja musu bala'e, A yanzu bata son duk wani abu da zai tashi hankalinsu, tafi son su kasance Cikin farin Ciki, har zuwa lokacin da Allah Zai Taƙaita zamansu agidan kurkukun idan suna da rabon fita, idan kuma Anan ƙaddarar rayuwasa ta tsaya tana yi musu fatan da cewa, Hannayenta ta sanya tare da kamo ƙasan rigarta, tana yunƙurin tu6e rigar, Hancinta ya shaƙo mata ƙarnin Jini, Nan take gabanta Yayi wani irin mugun bugu, A matuƙar ruɗe ta saki rigar ta fasa cireta, ta soma bin ko'ina na jikinta tana shinshinawa a ƙoƙarinta nata gano Inda ƙarnin jikin ke fitowa, Hatta wandonta saida ta ɗaga ta leƙe ciki don taga idan itama tafara Period ɗin, amma koda ta bincika bata ga Jinin ba, Sai da ta gama shan wahalar duba Jikinta a karshe idanuwanta suka sauka akan busasshen jinin dake a saman tafin hannunta, waro ido waje tayi tana kallon Jinin, tarasa a ina ta same shi, tun da ta duba ko'ina na jikinta bata ga ciwo ba, a kalla ta kwashe fiye da awa acikin toilet din Cikin yanayi na jin fargaba, Ta shiga ruɗani sosai, Da gudun gaske ta fito daga Cikin toilet ɗin, bata nufi ko'ina ba sai bakin gadon azeeza, Saboda itace Jiya suka 6oye a karkashin gadon batool atare, Tabbas kuwa tana hasashen Jinin daga Jikinta yake, bubbuga ƙafar azeeza tayi da hannunta tare da ambaton sunanta"Azeeza"! Har cikin kunnan ta tajiyo kiran da angel ke yi mata, rai a6ace ta farka tana faman mutsustuke idanuwanta, muryarta adisashe tace"Wai lafiya? Wanene ke kirana, Hakanan mutun na yin baccin shi an wani katse mishi" angel na yunƙurin buɗe baki tayi mata magana tajiyo muryar hanna tana fadin"Nashiga Uku, Jini A jikina! Wanene Ya goga mini jini" afirgice angel ta juya tana kallon hannah dake zaune saman gadonta, Bata gama ruɗewa ba, Suka juyo muryar Eve tana fadin itama Jini ajikinta, hankalin fa angel yayi mugun tashi ganin kusan mutun huɗu acikinsu sun fara Jinin al'ada, da ace tana da halin da zata dakatar da jinin da tayi hakan saboda ta fuskanci ba ƙaramin barazana bane Yin Jinin Agidan kurkukun ƙaddara Sai kuka suke ta Yi sunga Jini Ajikinsu, Da yake basu da ilmi akan Jinin, Ita kuma angel ɗin Tagaza buɗe baki tayi musu bayani saboda ruɗun da kwakwalwarta ta shiga, koke koken da suke Yi ne ya farkar da Batool daga bacci, aruɗe ta sauko daga saman gadonta tana tambayarsu lafiya koda itama tayi tozali da jinin daya 6ata wandonsu a firgice ta ɗaura hannayenta asaman kanta tana faɗin mun shiga uku, hibba Hanna yasmin Jinin menene ajikin ku? kodai Ciwo kukaji wurin Wasan Ƴar 6oyen da mukayi Jiya"? har suna haɗa baki wurin bata amsa da cewa"Suma basu sani ba, kawai sun farka sun ganshi ajikinsu ne," Lamarin ya ɗaga musu hankali ba matan kaɗai ba, hatta mazan da suka farka daga bacci suka ga abunda ke faruwa da ƴan uwansu jikinsu duk Yayi sanyi, don sun san cewa huɗun ɗin nan duka xa'a zo akwashe su da sunan za'a bincika lafiyar jikinsu daga nan kuma su da ganinsu sai In Allah Ya nufa za'a dawo dasu Cikinsu, kafin su yanke shawarar zuwa su faɗa ma tsohuwa, sai ga giants sun shigo Cikin ɗakin wannan karan ba Su uku suka zo ba, wani iko na Allah Su huɗu suka shigo giants ɗin, Iya adadin marasa Lafiyan dake akwai, Abun ya basu mamaki matuƙa, ka rasa wake sanar dasu game da duk wani abu dake faru atsakaninsu, Babu irin haukan da angel batayi musu ba akan bazasu Ɗaukar musu ƴan uwansu ba, Amma duk abanza, Ba ita kadai ba wannan karan hada su deeja suna kuka suna faɗin Kada su bari a ɗauki ƴan uwansu, Ba duba lafiyarsu xa'ayi ba ƙara musu Ciwon za'ayi, Wani abun ban tausayin ma. lokacin da giants suka ɗauki su Hanna, Suka nufi kopa zasu fita dasu, Da gudu Azeexa da batool da su deeja suka bi bayan giants abunda basu ta6a yunƙurin Yi ba, Aikuwa sunyi danasanin Binsu da sukayi da niyar su ƙwaci ƴan uwansu domin kuwa, Wurgi giants su kayi dasu, gaba ɗaya suka kife saman benan kansu Ya bugu sosai, Kuka hada majina, danish bai ta6a sanya kokwanto akan Giants ba, Sai yau da suka jefar da su Angel yaga rashin Imani tsantsa atattare dasu, kuma ranshi yayi mugun 6aci, zuciyarshi ta hasala, bashi kaɗai ba Hatta haris da naufal da mubeen Sun fusata sosai, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Saboda tsabar buguwar da su ka yi, ga6o6in jikinsu sun jigata sosai, Angel tana yashe saman last step na benan, Azeeza da batool sun yi gefen dama atare aka wurgar dasu kamar kayan wanki, Deeja da Parveen da rubina suna ata 6angaren hagu, kowa Ya tarwatse, Sun yi kuka har sun gaji ga takaicin ƴan uwansu da aka tafi dasu ta ƙarfi da yaji, ga kuma takaicin wurgin da akayi dasu kamar wasu dabbobi marasa Ƴanci, ita angel ma hancinta har ya fara bleeding sakamakon bugun ƙasan da yayi, hakan ba ƙaramin tayar masu danish da hankali Ya yi ba, haris Yana zuƙunne gabansu azeeza dake a kwance ƙasa sunata kuka Yana lallashin su, Mubeen da naufal suna a 6angaren da aka wurgar dasu deeja, suna ta aikin lallashi, Danish ke a zuƙunne Inda angel take kwance ƙasa, ya rasa ya zaiyi da ita saboda sautin kukanta dake neman hargitsa mishi lissafi, yana so ya lallashe Amma ya kasa, Yanke shawarar ɗaukarta yayi zuwa toilet don ya samu ya wanke mata fuskarta ko jinin ya daina zuba, Hannayenshi Ya sanya duka biyun Ya ruƙo waist ɗinta Ya ɗago da ita zuwa saman kafaɗarshi, Ya yunƙura ya miƙe ɗauke da ita Ya nufi sashen toilet ɗinsu, A bakin fanfo Ya sauketa, Ta zuƙunna saman ƙafafuwanta, idanuwanta sunyi jawur launinsu Ya ciza sun koma kamar na zombie, hawaye duk sun wanke fuskarta sharkaf, Jikinta har kerma Yake yi, Giants bala'e ne, duk yadda suka ta6a mutun sai yaji jiki, "Am sorry angel" ya furta hakan Yayin da idanuwanshi ke akan fuskarta, a raunace ta ɗago tana kallon shi without saying anything, ita kaɗai tasan Azabar da take ji ajikinta, Zuciyarta ta hasala, har wani tafarfasa take yi, Janye idanuwanshi yayi daga kan fuskarta, Yakai hannu saman tap ɗin ya kunna shi, Ruwa ya soma kwararowa, Da tafin hannayenshi Ya dinga tarbo ruwan yana wanke mata fuskarta, Ba ƙaramin sanyi taji ba lokacin daya watsa mata ruwan a fuskarta, har saida ta lumshe idanuwanta, Bayan ya kammala Ya kashe tap ɗin, Ya ɗan juyo yana kallonta, Cikin sanyin murya yace"zaki sha ruwa? Girgiza mashi kai tayi dakyar ta iya buɗe baki tace"bana jin ƙishi, wanka nake so In yi, U can wait for me out side," amsa mata Yae da okey, kafin ya miƙe Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya tsaya Abakin ƙopar Yana jira ta kammala, lalla6awa tayi ta miƙe taje bakin ƙopar toilet ɗin ta datse ƙopar ta koma ciki, tsawon mintuna bata fara wankan ba, takaicin duniya ya isheta, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, yanzu shikenan an ɗauke su hanna? Suma za'aje a cutar da rayuwarsu kamar yarda aka cutar da su parveen, Ya salam, fashewa tayi da wani sabon kukan mai cin rai, Tana jiyo cool voice ɗin danish daga bakin door ɗin yana yi mata magana, "Angel stop crying, its hurting me, idan ba haka zan shigo daga ciki," tana Jin yace haka da sauri ta taja baki tayi shiru don tasa halin shi, Yanzu ya faɗo mata Cikin toilet, Miƙewa Tayi jiki duk ba ƙwari ta zame kayan jikinta ta ɗaura su saman igiya, Ta cika ruwa abokiti Ta soma Yin wankan, Yana a tsaye Bakin door ɗin ya jingina bayanshi, fararen idanuwanshi na fuskantar ceilling, Yayin da zuciyar shi ta yi nisan kiwo Cikin tunanin Abunda Ya faru ɗazu Zuwansu Giants, tambayoyi ya shiga jefa ma kan shi wata irin lalura ce ke damunsu Hannah? Jinin menene Yake fita ajikinsu? And why tsohuwa bata nuna damuwa a kansu ba? Bakomai yafi ɗaure mashi kai ba, face yarda giants suka nuna rashin tausayi wurin yin wurgi dasu azeeza, don kawai suna ƙoƙarin hana atafi da ƴan uwansu, Yayi zurfi acikin tunaninshi, kunnuwanshi suka soma Jiyo mashi muryar haris a kausashe yana magana daga Can Cikin ɗakinsu, Da sauri Ya bar ƙopar toilet ɗin Ya shigo ɗakin nasu, kaitsaye Eyes ɗinshi suka sauka akan tsohuwa dake A tsakiyar ɗakinsu Hannunta ruƙe da sanda haris ne agabanta Ya ruƙe qugu, Yana mata maganaTamkar zai rufe ta bugu, "Saboda me zasu yi wurgi da su? Saboda rashin tausayi da mugunta suka jefar dasu, kamar wasu barguna, gasu nan kina gani da idanuwanki ko tashi sun gaza yi saboda raɗaɗin da jikinsu yake Yi musu, wai mu me aka maida mu ne eye? nifa nafara kokwanto akan kowa ma dake atare damu, " Yana magana yana watsa hannayenshi kamar zai buge tsohuwa dama fa shi haris akwai zuciya, Idan ya fusata Ya isa masifa, Tun da haris Ya soma magana, Tsohuwa ta zazzaro kwarkwararrun idanuwanta waje, Kwayar idon kamar zasu rubzo ƙasa saboda tsabar zaro su da ta yi, Bakomai bane yasa tayin hakan face Mamaki da al'ajabin daya kamata, karo nafarko kenan da aka fara samun wani acikin su Ya ɗaga mata murya, haƙika tayi matuƙar girgixa, sai da yakai karshen maganarshi Ya juya mata ƙeya yana ƙunƙuni, Ruƙe ha6arta tayi idonta akan keyarshi, Muryarta Na rawa tace"HARISU!! yau ni kake gaya ma magana babu tausasa harshe? A ina ka samu wannan ƙwarin gwiwar? Kamanta matsayina ne awurinku? Wato ina can ina tufka ana nan anayi mini warwara," a wani sukwane Haris Ya juyo Yabi ta da wani irin kallo Yace"Indai akan ƴan uwana ne fiye da haka ma zan Iya fada maki, Wannan matsayin da kike dashi awurin mu kina dab da rasa shi, Saboda Na fara zargin ba ƙaunar mu kike Yi ba," kasa karasa maganar haris yayi idanuwanshi cike tab da kwalla, tsohuwa sai faman gyaɗa kai take Yi kamar wata ƙadangaruwa, Ganin tana ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin dakinta Ne yasa Danish Yin saurin dakatar da ita, ta hanyar yi mata magana" meyasa a koda yaushe muka sanar dake agame da rashin lafiyar ɗaya daga Cikin mu baki nuna damuwarki? jin muryar danish Yasa tayi saurin Juyowa tare da kallonshi, A tsanake Yake tafiya yana tunkarar inda take atsaye, Duk wannan abun dake faru Su azeeza sun natsu suna sauraronsu, a lokacin sun dakata da yin kukan sai dai har yanzu basu iya miƙewa daga kwacen da suke a kasa ba, A gefen haris Danish Ya tsaya tare da ɗaura hannunshi na hagu saman kafadar haris, still idanuwanshi akan tsohuwa Yana jiran Jin amsar da zata basu, Sai faman zare ƙwalaƙwalan idanuwanta take yi, Da alama zuciyarta ta shiga ruɗani, Bata gama kiɗima ba, zazzaƙar muryar angel ta ratsa kunnuwanta da cewa"Ki basu amsar tambayarsu mana? Daga anyi magana kaɗan sai ki dogara sanda Ki koma ɗaki, saboda rashin gaskiya, Meyasa kike 6oye mana gaskiya ne? Tun rana ta farko dana tsinci kaina acikin kurkukun nan raina ya bani cewa ba abun arziƙi ake aikatawa acikin shi ba, saboda bai kwanta mini araina ba, Kina yawan yi mana ƙarya, wanda bani kaɗai ba hatta su kansu yanzu sun fara kokwanto akanki, kince mana ana kaisu treatment room domin duba lafiyarsu, to meyasa ake dawo mana dasu a haukace? Maimakon Muga sauƙi ajikinsu saima dai muka ga tashin hankalin akan fuskokinsu, Da jikinsu, mutumin dake yin jinin al'ada meya haɗa shi da ƙaiƙayin gaba? Da kuma gwamewar ƙafafuwa? Uwa uba da fashewar le6e, ga rama, Wannan wani irin treatment ne tsohuwa"! Tayi tambayar tana kallonta, Tsohuwa dai tarasa bakin magana, sai faman gyaɗa kanta take yi, Angel taci gaba da cewa"Allah dai ba Azzalumin bawansa bane, idan ma cutar mu ku keyi, To ku sani Allah Yana kallonku, Kuma akwai ranar hisabi, ranar da duk wani abu da kuke taƙama dashi aduniyar nan bazai ta6a taimakonku ba......." Angel bata kai ƙarshen maganarta ba, Tsohuwa ta buga sandar hannunta, Cikin nuna 6acin ranta, Da sauri danish ya dafe kanshi da hanneyenshi, Ranta amatuƙar 6ace tace"Kin manta abunda na faɗa maki? Nifa bakowa bace agidan kurkukun ƙaddarar nan? Don me zaki titsaye ni kina gaya mini magana yadda kika dama? Meyasa bazaki tuhumi Iyayenku da suka sadaukar daku ba sai ni? Da bani da wata alaƙa ta jini da ku? Ga dukkan alamu baki Ji gargaɗin da nayi maki ba, Ina matuƙar Tausayawa rayuwarku! Domin kuwa duk ranar da kika kuskura Kika bari Ƴan uwanki prisoners suka gasgata maganarki akan tawa, to daga wannan ranar ba zaku ƙara Yin tozali da ni ba, Zan barki dasu ne, Kiga idan zaki iya taimakon rayuwarsu," Tsohuwa Nakai karshen maganarta, Ta Juya fuu kamar zata tashi sama Ta nufi dakinta, Ta shige taja kopa ta rufe, Sai lokacin danish Ya zame hannayenshi daga saman kanshi, Wato a lokacin da tsohuwa ta buga sandar hannunta, basu ƙara fahimtar me take cewa ba, tamkar ta wanke masu tunaninsu na tuhumar da su ke yi mata, ita kanta angel ta lura da hakan, Sai dai ko kaɗan hankalinta bai tashi ba, Domin kuwa tasan dole su cigaba da tuhumarta, da zarar an dawo musu da ƴan uwansu da aka ɗauka, Kallon juna su kayi ita da danish, Kafin ta ɗauke idonta daga kanshi ta mayar dasu kansu Batool, tafiya tayi zuwa inda take a kwance, Ta zuƙunna tare da kai hannayenta saman kafaɗun batool ta ɗago da ita tare da kwantar da kanta saman kafaɗunta, "Sister, yanzu Haka zamu zuba ido muna ji muna gani, Ana raba mu da ƴan uwanmu"? Cikin shessheƙar kuka batool ta yi maganar, kafin angel ta bata amsar tambayarta, Naufal ya rigata cewa"Haƙuri zamuyi, Giants sunfi ƙarfin mu, Ni dai na roƙe ku nan gaba kada ku ƙara gigin shiga huruminsu, Ina gargaɗinku, Idan ku ka yi haƙuri za'a dawo mana da su ne, kamar yarda aka dawo mana dasu Parveena, Mubeen yace"Nima abunda nake so naja musu kunne akai kenan, Mutanan nan ƙarfi ne da su, They are extremely dangerous! Da ace tun farko baku Yi yunƙurin tunkararsu ba da duk hakan bata faru ba, kun riga da kunsan halinsu, Basa ji basa gani, duk wani koke koken da za ku yi musu abanza, ba saurarar ku zasu Yi ba" Danish yace"pls let it be past, tunda sun riga sun tafi dasu, Koke koken Ya tsaya iya haka, " Jinjina kai Angel ta yi tare da binsu Azeeza da kallo tace"Ku daure ku tashi, ku je toilet ku wanke fuskokin ku," amsa mata Su ka yi da toh, daƙyar suka iya miƙewa tsaye a daddafe suka Nufi toilet, "Batool kema kije Ki wanke fuskarki, koma Kiyi wanka" amsa mata tayi da toh, Ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar angel, Hannunta adafe da sumar kanta, ta miƙe ta wuce cikin toilet, Ba Iya wanke fuska Su kayi ba, Hada wanka su Kayi, Time da suka fito, mazan gaba ɗaya sun koma saman gadajensu, Angel ma tana zaune daga gefen gadonta, Kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi, Lokacin da giants suka zo kawo musu abinci, Fushi suka Yi, suka ƙi zuwa su Ci, naufal yace"da rabon muyi ma kanmu asara, domin kuwa su basu san bihim ba, ko ajikinsu, Mu zamu Ji jiki," wannan maganar da naufal yayi ce tasa parveen ta sauko daga saman gadonta, Ta nufi saman dining carpet ta samu wuri ta zauna, Ɗaya bayan ɗaya suma sauran suka sauko daga saman beds ɗinsu, Suka Nufi Carpet ɗin suka zazzauna, Lafiyayyan abinci aka kawo musu, ba don suna jin daɗinshi ba suke Cin shi, Kamar waɗanda aka Yi ma dole, In ka cire parveen dake ta zuba loma, dama ita bata wasa da abinci, Abinci take Ci amma hankalinta na akan giants dake a tsaye sun ƙame, Harara ta dinga jefa musu tamkar ƙwayar idonta zata faɗo kasa, ita kaɗai take haukanta domin kuwa babu tabbacin ko suna kallonta, Bayan sun kammala Cin abincin, Sauran daya rage Batool ta 6oye musu shi acikin kwandonsu, saboda su samu wanda zasu Ci da anjima, Bayan tafiyar giants, Safa da marwa suka shiga Yi acikin ɗakin duk babu daɗi saboda rashin ƴan uwansu, an rairaye su yanzu sun koma su goma sha ɗaya, Babu mutun Huɗu acikinsu, dole suyi maraicin rashinsu atare dasu, ga zullumin da suke Yi da fargabar ko awani hali suke Ciki? Idan suka gaji da zagaye ɗakin sai su koma saman gadajensu su zauna, a haka har dare ya rutsa dasu, Ɗakin Ya yi duhu, Rubina ce ta kunna musu fitilun Ɗakinsu Haske Ya gauraye ko'ina, Kowa Ya kishingiɗa saman gadonshi, Ta yi tsammanin sunyi bacci Jin ɗakin Yayi tsit, Juyawa tayi tare da fuskantar gadon danish, idonshi biyu Ya kwantar da kanshi saman pillow, "Meya hana ka bacci"? Amsa ya bata da cewa"ke zan tambaya, me kike Yi har yanzu baki runtsa ba"? Ta6e baki ta ɗanyi"Damuwace ta hana ni bacci, ina jin duk babu daɗi zuciyata" Shiru baice mata komai ba, sai dai kallonta da yake yi, kamar yadda itama take kallonshi, Gani yayi ta miƙe ta sauko daga saman gadonta, a bakin gadonshi ta zuƙunna tare da ɗaura hannayenta saman mattress ɗinshi Da ɗan mamaki yace"lafiya"? Murmushi ta ɗansaki kafin tace"Bakomai kawai ina so Muyi fira ne," mayar mata da martanin murmushin yayi, har dimples ɗin shi ya lotsa, "Ai ni ban Iya fira ba, in fact ko surutu ban iya ba, sai in ta kama dole," tace" toh ka ƙaddara ta kama dolen ne, tambaya ce nake so In yi maka hope zaka amsa mini" ɗaga mata gira yayi tare da cewa" Am all ears" Kame kame ta shiga Yi, abun ma sai yaso ya ba shi dariya, hannun shi yakai saman sumar kanta ya ruƙo gashinta tare da cewa"Faɗa mini mana, indai nasan amsa zan baki," tace"Dama nayi mafarki ne, kana da wuƙa, shin dagaske ne"? Da budar bakinshi sai ce mata yayi"you're trying to be smart, tell me the truth waya faɗa maki cewa ina da wuƙa? Nasan ba mafarki ki kayi ba," Hararar shi Tayi jin ya ganota, taso tayi mishi wayau, "Na ta6a tambayar batool, cewa Inaso zanyi amfani da wuƙa, shine take faɗa mini cewa Akwai wadda tsohuwa ta baka lokacin da kace mata kana so ka rage yawan sumar kanka," Wani kallo taga yana binta dashi, Can kuma yace"me zakiyi da ita"? Dariya tayi tare da cewa"bafa kai zan kashe ba, Nasan abunda kake tunani kenan, ni kawai inaso In rage sumar kaina ne, bama ni kadai ba hada batool itama Gashin kanta yayi yawa yana takura mana" tayi maganar tana yamutsa fuska, Ta6e mata baki yayi"Nima namanta inda na ajiye ta, ko na mayar mata da ita ko ban mayar mata ba, namanta, " A ƙagare tace"pls ka daure ka tuna, Zata yi mana amfani," "Angel idan Kina son In rage maki gashin kanki ne, Ba buƙatar Yin amfani da knife, i can use my nails to cut it for u" zaro ido ta ɗanyi da mamaki tace"taya zaka Iya amfani da akaifa wurin rage yawan gashin kaina, baka ga yawanshi ba ne" "Idan kin bani dama zan Jaraba" girgiza mashi kai tayi"a'a, Ni dai nafi so Inyi amfani da wuƙar, Idan Allah yasa ka tuna inda ka ajiyeta sai ka ɗauko mini" ta faɗi hakanne saboda ba gashin take so ta rage ba, Wuƙar take buƙata saboda tsaro, "Its Okey, Kije ki kwanta, duk time dana tuna i will let u know" ya karasa maganar tashi tare da jan bargo ya lullu6e jikinshi har zuwa kanshi, Miƙewa Ta yi tare da juya ta koma saman gadonta ta kwanta, A daren ranar saida ta roƙi Allah Akan Yasa itama ta fara Menstruation kodan saboda giants su ɗauketa sukaita ɗakin nan taga uban me suke aikatawa, Idan Allah yasa Hankalinta bai gushe ba kenan, Wasa wasa Yau har tsawon One week kenan ba'a dawo dasu Hannah ba, Tun suna sanya damuwa aransu har suka haƙura suna zaman jiran tammani, Tun daga ranar da aka ɗaukesu Kullum sai ta roƙi Allah tsakar dare Akan Ya karesu aduk inda suke, Bayan haka kuma Tana yawan yin addu'ar akan Allah yasa ta fara jinin itama, duk don saboda da taga me ake yi musu, Yanzu ta kaiga ko tsohuwa basu tambaya dangane da ƴan uwansu, saboda sun fahimci cewa ita ɗin bata da banbanci da totan masara awurinsu, bi ma'ana bata da amfani duk wani magiyar da zasu Yi mata bazata iya Sanyawa adawo masu da ƴan uwansu ba, sai da ta gaya musu ƙarairakinta, Yau tsawon 3 weeks kenan Suna ta baza ido suga an dawo musu Da ƴan uwansu, Sai acikin satin karshe na watan da suka shiga, Aranar da daddare suna zaune saman carpet Suna fira sun kunna fitilun ɗakinsu, Ba zato ba tsammani sai ga giants Huɗu sun shigo cikin ɗakin nasu Kafaɗunsu Ɗauke dasu Hannah, A wani irin zabure suka miƙe suna kallonsu, wuce wa cikin ɗakin giants su ka yi adai dai bakin gadajensu hannah masu ɗauke da numbobinsu suka kwantar da kowannansu, Atare suka juya suka fuce daga cikin ɗakin, Azeeza sai tsalleta take Yi tana murna an dawo musu da ƴan uwansu, Su batool kuwa Kallon Kallon suka shiga Yi atsakaninsu, sun rasa gane farin Ciki zasu Yi ko baƙin Ciki? Ga shi dai an dawo musu da ƴan uwansu da suka daɗe suna jimamin rashinsu, Sai dai ga dukkan alamu Basu acikin hayyacinshi, Har ƙwarama lokacin da aka dawo dasu parveen sunyi magana, Amma waɗannan bayin Allahn, Idanuwansu ne kaɗai suke motsi, Numfashin su da hucin zafi yake fita, ƙafafuwansu duk sun tale, Wani abun tashin hankalin ma, Hada Yakushin akaifa asaman wuyansu, fatar wurin tayi jawur, jini ya kwanta, La66ansu sun faffashe, Hankalinsu danish ba ƙaramin tashi yayi ba, Matan kuwa Sun sha kuka kamar ransu zai fita, Angel tace Yanzu babu buƙatar saita yi musu bayani game da cewar cutar dasu ake yi yau dai gashi nan zahiri idanuwansu sun gane masu, Sahun yakushin akaifar dake asaman wuyansu, Haƙiƙa sun yi matuƙar girgiza, hatta mazan saida suka zubar musu da hawaye saboda tsabar tausayinsu daya kama su, daren ranar basu Iya runtsawa ba, A gefen gadajensu Hanna suka zaune suna Jimami, har garin Allah Ya waye, Koda suka je bakin ƙopar ɗakin tsohuwa suka kwankwasa mata, Munafukar bata fito ba, Hakan ya ƙara tabbatar musu da cewa Bata da gaskiya, Haƙiƙa sunsha wahala wurin Yin jinyarsu Hannah, kamar bazasu Rayu ba, jikinsu yayi tsauri sosai, babu sauƙi saima abunda ya qara gaba, sai da takai ga Komai daga kwance suke yin shi, fitsari kashi, duka dai, a ƙalla sun ɗauki tsawon one month suna yin jinyarsu kafin Allah yasa suka samu sauƙi Jikinsu ya warware, Suka koma kamar yarda suke da, Sai dai babu wani walwala atattare dasu, Suna yawan firgita, Ko kiran sunansu Kayi sai kaga sun ɗan zabura, Idan suna bacci kuma Sun dinga sambatu suna koke koke, Ahaka ahaka dai da taimakon Allah angel Tana yi musu addu'a duk rana ta Allah, Sai gashi sun wartsake, Sun dawo normal, Bayan sunji sauƙi, Sai ga tsohuwa ta shigo ɗakinsu, Wani irin mugun kallo da suka dinga jefa mata, ba arziƙi taja sandarta ta koma Cikin ɗakinta, Angel taso ace su hanna sun Iya tuna abunda ya faru dasu amma sun kasa, kwata kwata basu Iya tuna komai, Da ace sun tuna koda kaɗan ne to kuwa tabbas sauran ƴan uwan nasu zasu Ƙara gasgata maganarta, duk da ayanzun ma ta fara cin nasara saboda kokwanton su Ya ninku akan gidan kurkukun, Sun sha jinin jikinsu, Sun fara tsorata da lamarin, Haris har alƙawari ya ɗauka akan bazai ƙara bari giants su ta6a wani acikin su ba, Sai dai in bayan babu ranshi, danish dai bamu san matsayarshi ba, Shi dai baice komai ba, Iya nuna 6acin ranshi akan fuskarshi ne, Amma su naufal mubeen da javed duk sun ɗauki wannan alƙawarin na hana atafi da ƴan uwansu idan basu da lafiya! Kallonsu kawai angel take Yi domin kuwa tasan babu abunda zasu Iya yi, ba wani ƙarfi gare su ba, balle suce zasu Iya ja da giants, Mutanan da take tunanin Ba cikakkun mutane bane, Ƙarfinsu bana jinsin bil'adama bane, Bayan komai Ya lafa tsawon Watanni uku wani iko na Allah, cikin matan ba wanda ya ƙara Yin Menstruation, kamar an ɗauke musu da jinin, Hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma angel ba, Yanzu hakalinsu ya ɗan kwanta, Ganin sun samu natsuwa yasa Ta fara jan hankalinsu zuwa ga addinin musulunci, Idan dare Yayi bata barinsu Yin bacci, Tarihin annabawa take basu tun daga kan tarihin Annabi Muhammad (SAW) Cikin hikma take Basu tarihin, Kuma ga dukkan alamu ba ƙaramin daɗin shi suke Ji ba, domin kuwa idan ta fara basu tarihin, Ko fitsari mutun ke ji sai kaji yace a jira ya dawo sai acigaba, idan kuwa tace ta gaji abari gobe zata ƙarasa musu kamar su yi mata hauka, Taci wahala sosai Wurin janyo hankalinsu duk da bata ci nasara ba saboda duhun jahilcin dake akansu, Suna Yi mata tambayoyin ƙural da suka fi ƙarfinta musamman haris, Da yace idan har akwai Allah wanda ya halicce su to meyasa bai ta6a zuwa ya kawo musu ziyara ba? Ire iren irin waɗannan tambayoyin sune kesa tana karaya wani lokacin, Ita dai tayi iyakar bakin ƙoƙarinta wurin sanar dasu gaskiya, Sauran kuma tabar ma Allah domin kuwa shi kaɗai ne zai basu ikon musulunta idan yaso, mutun huɗu ne acikinsu ta lura da suna matuƙar son Addinin, Batool, Azeeza da Javed, sai kuma parveen, sauran kuwa kokwanto ne Ya hana su yarda da ita saboda wasu tambayoyin su da ta gaza amsa musu, shi danish bama tasan a wata matsaya yake ba, Yana dai son tarihin annabawan da take basu, Sai dai Babu alamar yana da niyar kar6ar addinin nata, mutun huɗun nan da suka nuna suna da interest sune suka fara kar6ar addinin musulunci acikinsu, Ta biya musu kalmar shahada, Kusan Yini guda suka ɗauka tana ta fama dasu akan su maimaita sun kasa furta ta, Sai cikin dare Wani iko na Allah tana sake biya musu sai gashi sun maimaita lafiya lou batare da inda inda ba, Tayi farin Ciki sosai kamar ta zuba ruwa a ƙasa tasha, Duk da farin Cikin nata ragagge ne tun da sauran basu kar6a ba, Tafi damuwa akan danish saboda tana ji aranta idan har ya kar6i addinin zai taimaka ma sauran ƴan uwan nashi saboda suna jin maganarshi sosai, duk da haka bata ƙyale shi ba, ta addabi rayuwarshi ta hana shi sakat, Sai yana tsaka da yin bacci ya dinga jin muryarta acikin kunnanshi tana karanta mashi kalmatusshahada, wato da tsiya sai ya kar6i addinin, babu yarda batayi dashi ba, Amma Yaƙi bata haɗin kai a ƙarshe da ta gaji ta ƙyale shi badan ta haƙura ba, Ta dai bashi lokaci ne ya ɗan sarara, duk da haka bata yi fushi dashi ba, Sai ma ƙara janshi da take yi ajikinta, saboda sanin mahimmanci da yake da shi, dole saida shi wasu abubuwan zasu tafi dai dai, a 6angaren su batool da suka musulunta, tafara ƙoƙarin Koya musu addu'o'i da karatun kur'ani, sai dai wani abu dake ɗaure mata kai, Wahalar da suke sha wurin furtawa, Ita parveen ma hada amai take Yi idan angel ta matsa mata akan ta furta karatun kur'ani, ita kuma azeeza daga anfara sai ta kama bacci, ba ƙaramin takaici angel ke ji ba, daga bisani tayi wani zazzafan nazari, Acikin kwanakin kowani sati akwai wace rana da idan dare yayi tayi musu karatu suke amsawa lafiya lou batare da sun kakare ba, a irin ranar ne ta ta6a yi ma danish karatun kur'ani da daddare lokacin da giants suka dawo dashi kuma dai dai lokacin ne take basu tarihin annabawa batare da ta samu targaɗe ba, Kuma a irin lokacin ne su batool suka furta kalmatusshahada batare da sun yi inda inda ba, duk irin lissafin kwanakin da take yi Tun lokacin da daddynta Ya gudu da ita bata ta6a bari lissafin kwanakin wata sun ku6uce mata ba, Sai dai wannan karan ta kasa gane wace rana ce wannan mai tarin albarka? Meyasa take samun dama A ranar? Bata iya hasashen wace rana bace sai dai tana ganeta ne da alamominta, duk irin ranar ta zagayo bata bari ta tafi abanza, kusan kwana suke Yi da daddare tana Koya musu karatu tare da yi ma sauran ƴan uwan nasu da'awa kota samu suma Su kar6i addinin, Allah mai yarda yaso, Sai gashi ɗaya bayan ɗaya suna zuwa wurinta suna cewa suma zasu musulunta, cikin waɗan da suka kar6i addinin musulunci akwai, batool, azeeza, Hannah, Hibba, deeja, parveen, Eve, yasmin, Angel, Batool, rubina, Cikin maza mutun uku, Javed, Naufal da Mubeen, yanxu mutun biyu ya rage mata acikinsu, Haris da danish, Su kaɗai suka yi mata cikas, Duk da Tayi matuƙar yin farin Ciki, Da Allah ya bata ikon musuluntar dasu Hanna, Ranar da suka kar6i shahadar ko bacci bata yi ba, A tsakiyar gadonta ta zauna tana kukan farin ciki tare da Yi ma Allah godiya, daya bata wannan damar, Nima dai Na matse kwallata kuma na tayasu murna koba komai sun tsira da imanin da su ka yi, Allah zaiji ƙansu, A wani dare Ne, dukkansu Sun kwanta bacci, Angel tana a kudundune cikin bargonta, kwatsam ta soma Jin shessheƙar kukan mutun acikin kunnuwanta, tun bata ɗauki abun serious ba har sautin kukan ya fara disturbing ɗinta, Sai kuma ta dinga jin hannun mutun asaman jikinta kamar ana bubbuga ƙafarta ƙasa ƙasa ta jiyo miryar mutun yana yi mata magana, A hanzarce ta yaye bargon jikinta ta ɗago da idanuwanta masu ɗauke da bacci biji biji take Iya ganin fuskarta, tana a zuƙunne gaban gadonta, fuskarta sharkaf da hawaye, Mutsustsuke idanuwanta ta yi da yatsun hannunta don ta samu damar ganin kowacece, koda tayi arba da deeja sai taji gabanta ya faɗi rass! Tun kafin ma takai ga faɗa mata abunda ya kawo ta, "Angel Jinin nan ne ya dawo mini, Na shiga toilet in yi fitsari shine naganshi, hankalina Ya tashi sosai bansan Ya zanyi ba," fuskarta a yamutse tayi maganar, dafe kai angel tayi tare da ambaton"INALALLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN! wannan wata irin masifa ce, mun shiga uku! Ni nayi tunanin Kun daina gaba ɗaya, ashe da sauranshi," idanuwanta cike tab da kwalla tayi maganar, Ruƙo hannunta deeja tayi acikin nata"Dan Allah angel, Ki san yadda za'ae ki hana atafi dani, wlh gani nake kamar idan aka ɗauke ni wannan karan baza'a dawo dani ba," tana kuka ta yi maganar, Hankalin angel ya tashi matuƙa, Saukowa Tayi daga saman gadon ta nufi gadon Danish, Hannu takai ta ruƙo bargon daya lullu6a dashi ta yaye shi, Bubbuga ƙafadarshi tayi tare da ambaton sunashi"Danishi!danish!" daƙyar ta samu ya farka, Yana faman yamutsa fuska Yace"menene"? "Pls ka tashi deeja bata da lafiya, Menstruation ne Yazo mata" ware idanuwanshi ya yi jin abunda tace, Saboda ya gane me take nufi, tun da tayi musu bayanin komai dangane da jinin, "Dan Allah Danish kada ku bari Giants su ɗauke ta, mu taimaka mata," yunƙurawa yayi tare miƙewa ya zauna saman mattress ya jingina bayanshi jikin bango, batare daya ce komai ba, idanuwanshi na akan deeja dake a zauƙunne sai kuka take Yi, Ganin baida niyar tanka mata yasa ta wuce gadon haris, ta tada shi, daya farka ta sanar dashi abunda ke faru wa, Jikinshi har 6ari yake Yi, duk yabi ya ruɗe ya sauko daga saman gadonshi, Yana tambayarta Ina deejan take, Tun kafin ma ta bashi amsa sai ga deeja ta nufo su, Tana karasawa gabanshi ta fashe da kuka, Ruƙo hannunta yayi acikin nashi Ya janyota jikinshi Yana lallashin ta yana faɗin"ta kwantar da hankalinta, Ba wanda ya isa ya tafi da ita sai dai ahaɗa dashi atafi amma bazai ta6a bari giants su ɗauke ta ba, muddin Yana numfashi" Angel taji daɗin kalaman da haris yayi duk da tasan zaiyi wuya ya iya hana su tafiya da ita, Ga wanda taso Ya harzuƙa can saman gado Amma Yaƙi cewa komai, Haushin shi duk ya cikata, ta tsani halayyarshi ta lalaci da rashin son ta6uka komai, "Haris Bari in tada su Naufal, In yaso sai mu haɗu mu duka mu hana su tafi da ita" Yace mata"toh" ɗaya bayan ɗaya tabi kowannan su saman gadanshi ta tada shi, duk wanda ya farka, Yaji abunda ke faruwa sai gaka ya zare ido saboda fargaba da tashin hankali, A tsakiyar ɗakin suka hallara su goma sha huɗu, sun sanya deeja a tsakankanin su suna jiran giants su ƙaraso, da alama yau sun shirya yin faɗa da Giants, Motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa suka Jiyo, Da sauri suka kai idanuwansu kanta, a lokacin ta ƙarasa fitowa daga Cikin ɗakin Hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a yamutse babu annuri babu walwala, Ɗagowa tayi tare da kallonsu Babu wanda yayi yunƙurin yi mata magana, Sun ɗaure fuskokinsu, Saboda mugun haushinta da suke Ji, Azeeza ce tace"ni dai bari in je in roƙeta kada ta bari atafi da deejan mu" har ta ɗaga ƙafa zata je wurin ta, Haris Ya damƙi hannunta tare da cewa"Ashe baki da hankali? Idan kinje kin roƙe ta me zata Iyayi mana? In banda ƙarya"? Wannan maganar ta haris tayi matuƙar girgiza tsohuwa, Angel tace"Allah ya kamata ki roƙa ba ita ba, saboda shi kaɗai ne zai Iya taimakon mu amma waccan matar, Ba abunda zata yi mana," takai karshen maganar idonta akan tsohuwa, Jinjina kai tsohuwa ta yi jin abunda haris yace, daga bisani ta Dogara sandarta zuwa inda suke atsaye taci burki ta tsaya, ɗaya bayan ɗaya ta shiga binsu da wani irin kallo, sun rasa gane kallon menene take Yi musu, Juyawa tayi tare da kallon danish dake zaune saman gadonshi, Dama shi kaɗaine baiyi yunƙurin miƙewa ba, da alama baya goyon bayan abunda suke shirin aikatawa, "Saboda shi yafi ku wayau da hankali shiyasa bai biye maku ba," tsohuwa ce tayi maganar a lokacin da ta janye idanuwanta daga kan danish ta mayar dasu kan angel, Ido cikin ido suke kallon juna, Murmushin takaici ne ya bayyana akan fuskar tsohuwa, "Koda gigin wasa kada ku kuskura kuce zaku Hana giants tafiya da deeja!! ina gargaɗinku idan har kuna son zaman lafiya to ku daina yunƙurin shiga huruminsu....." Haris ne ya dakatar da ita ta hanyar daka mata tsawa yace"Wai ina ruwanki da rayuwarmu ne? Bakin nuna baki damu da mu ba? To ki fita sabgarmu mana? Idan ke bazaki Iya hana su tafi da ita ba, to mu ki barmu muyi da kanmu" rai a6ace yai maganar, Muryar danish ce ta ratsa kunnuwansu, a yayin da yake saukowa daga saman gadonshi yace"Haris ka sassauta kalamanka, Abunda tsohuwa ta faɗi gaskiya ne, Baza ku Iya ja da giants ba, Kuna Yunƙurin jefa rayuwarku cikin hatsari ne, Na rasa ya zanyi in fahimtar daku," wani irin mugun kallo haris ya jefa mashi, "Danish kana goyan bayanta ne? Bayan duk irin ƙarairakin da take yi mana, da kuma Nuna rashin damuwarta akanmu , Sannan da ita fa ake haɗa baki ana cutar da rayuwar ƴan uwanmu amma duk ahaka kake binta"? Zuciyarshi a hasale yayi maganar, sam baiyi tsammanin danish zai mara mata baya ba, "Haris u ave to understand me, Bazamu iya yin komai ba, saboda mu ba komai bane, Ni bana so na rasa wani acikin ku......." Kasa karasa maganar yayi ganin irin kallon hararar da angel ke jefa mashi, shiru yayi tare da duƙar da kanshi ƙasa, Tsohuwa ta dasa da cewa"Bawai bana son taimakon ku bane, kawai ba yadda zanyi ne, Ni kaina giants sunfi ƙarfi na, matsayinsu da nawa ba ɗaya bane, sunfi ni ƙarfin iko, Idan nace zan hanasu tafiya da wani daga Cikin ku zan rasa raina ne......" Angel tace"Oh ashe ta ranki kike Yi? Su baki damu da rayuwarsu ba, Ae ni nayi tsammanin har rayuwarki zaki iya sadaukarwa akansu ashe ba haka bane, ƙaunar da kike yi musu ta bogi ce, Ni na tabbata da ace ƴa'ƴan da kika zuƙunna kika haifa ne da baki faɗa musu wannan maganar ba" Girgiza kai tsohuwa tayi wannan karan idanuwanta hada farin ruwa kwance acikinsu tace"Bazaki ta6a fahimtata ba, Koda ace na sadaukar da rayuwata akansu nayi abanza, saboda yin hakan bazai canza komai ba, Ae ƙwarama Ni dana 6ata tsawon shekaru ina rainansu, Iyayensu fa da suka sadaukar dasu? Suna can suna sharholiyarsu sun ma manta da suna da wasu ƴa'ƴa da suka sadaukar, Nifa kaɗaice na damu daku, Ni da ban haɗa alaƙar komai daku ba, ae na cancanci a jinjina mini" Maganar tsohuwa ta yi matuƙar girgizasu, Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu, batare da wani ya kuma Yin magana ba, "zan Koma ɗakina, Amma kafin nan zan ƙara ja maku kunne, Kada Ku kuskura ku shiga hurumin giants, Idan Kunne Yaji Jiki ya tsira" tsohuwa na kammala maganarta, Ta juya tana dogara sanda ta shige Cikin ɗakinta, Idanuwansu akan abayanta har saida ta 6ace ma ganinsu.... *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Haƙiƙa maganar tsohuwa ta yi matuƙar ta6a zuciyoyinsu, Jin cewa Iyayen su suna can suna sharholiyarsu sun manta da suna da wasu ƴa'ƴa da su ka sadaukar, Wai ashe dama su ba Marayu bane marasa Iyaye! ? Jikin su ya yi mugun sanyi, kamar waɗanda aka zarewa laka, ita dama angel ta san da wannan shiyasa ta ƙudiri aniyar idan har Allah yasa tayi nasarar fita daga Cikin kurkukun, Kaitsaye zata fara neman Azzalumin da ya yi sacrificing ɗinta acikin danginta, don a halin yanzu kowa suspect ne awurinta, Mahaifinta da aunty aneelerh kaɗai ta cire aciki, Amma sauran dangin nata da wanda ta sani dama wanda bata sani ba, Kaf ɗinsu she's suspecting them, ɗakin nasu ya yi shiru babu mai magana saboda ruɗanin da tsohuwa ta jefa su aciki, Kowa da abunda yake saƙawa aran shi, kuma har lokacin suna atsaitsaye kewaye da deeja, babu wanda Ya motsa, danish Yana a gefe ɗaya ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi, Lokaci ɗaya kamar an zungure su gaba ɗaya suka ɗago da idanuwansu suna kallon saman benan Jin motsin buɗe ƙopa, Hankalin deeja yabi ya tashi haiƙam Jikinta ya soma kerma ta ƙanƙame Jikin haris tana kuka tana faɗin kada su bari atafi da ita, duk ta cukuikuye mashi rigarshi, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba, "Pls kada wanda yayi yunƙurin dakatar dasu, am warning u," danish ne ya gargaɗe su, Babu wanda Ya kalli inda yake sai dai duk sun sare zuciyoyin su sun karaya, Takun tafiyar giant ne Ya ja hankalinsu zuwa ga kallon staircase ɗin dayake saukowa, Shi ɗaya yazo musu wani gabjejen ƙato dashi a bubbuɗe yake tafiya, Ganin Yana tunkarosu gadan gadan Yasa duk suka watse saboda tsoratar da suka Yi, batool taja hannun azeeza duk suka ja gefe, Ya rage daga angel sai haris daya fusata Yana jiran shi ya ƙaraso, da sauri danish ya sanya hannyenshi biyu ya ruƙo wuyan rigar haris dana angel da ƙarfi Ya janyesu gefe ɗaya batare daya saki wuyan rigarsu ba, duk yadda suka so su kwace daga ruƙon da yayi musu sun kasa, Angel hada yakushin shi tadinga yi da hannayenta amma ko ajikinshi, Giant ɗin na ƙarasowa Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗauki deeja saman kafaɗarshi tana ta kuka baiwar Allah, a haka Ya juya da ita ya fuce daga Cikin ɗakin, suna ganin an tafi da ita, su ka fashe da kuka kamar ransu zai fita, Kamar Jira take Giant ɗin Ya fita, Danish na sakin wuyar rigarta, Awani fusace Ta juya ta fuskance shi ta ware yatsun hannayenta biyar cuf, ta wanke shi da zazzafan mari ji kake tasss, Har saida kanshi yayi gefe ɗaya, Ranta amatuƙar 6ace tace"Banza daƙiƙa, ban ta6a sanin kai wawa bane dolo sai yau, Kana ji kana gani za'a tafi da ita baka iya ta6uka komai ba, don me zaka hana mu taimakonta? Ta yi maganar tana ciccije le6enta, ɗagowa yayi da fuskarshi, tafin hannunshi dafe da inda ta mara, wurin yayi ja saboda hasken fatarshi ga sahun dogayen yatsun hannunta nan ruɗu ruɗu asaman fatar, wani irin raunataccen kallo yake binta dashi batare daya furta komai ba, Sauran ƴan uwan nasu duk suna a tsaye cirko cirko suna kallonsu, Haris dai baice komai ba, duk da baiji daɗin marin da angel ta yi ma danish ba, Sai dai shi kanshi yaji haushin yadda danish yaƙi nuna fusatarshi akan tafiyar da aka yi da deeja, "Angel meyasa kika mare shi? Kalli yadda kika raunata mashi fuska! shi fa bashi da laifi, yana ƙoƙarine Ya dakatar da ku gudun kada ku jefa rayuwarku cikin hatsari, saboda Lafiyarku yayi hakan, taya zamu Iya ja da giants? Kin manta irin wurgin da su ka yi damu lokacin da muka yi yunƙurin hana atafi dasu Hannah"? Juyawa angel tayi tare da kallon batool da ke magana, nuna danish tayi ta yatsan hannunta tace"batool kina supporting ɗinshi? duk irin halin ko in kulan da ya nuna akan deeja? Kowa ya nuna tausaya agareta ganin irin halin da take ciki tana kuka tana roƙonmu akan kada mu bari atafi da ita, Amma wannan Kwankon ashanan Koda naje na faɗa mishi Ba abunda yace saima ya share ni kamar wata ƴar iska, ni shi ne abunda yafi ƙona mini rai" azafafe ta ƙarasa maganar tana jifarshi da harara, duk ya sha jinin jikin shi, Muryar azeeza kamar zata fashe da kuka tace"Ni dai dan Allah kowa yayi haƙuri, tun da an riga an tafi da deejan mu, Muje mu kwanta dare yayi sosai," harara haris ya wurga ma azeeza duk da bata iya ganinshi yace"Baki da ƙafa ne? Ki wuce kije ki kwanta ko wani ya ruƙe ki ne"? Da alama dai duk sun fusata, Jikin danish a sanyaye Ya juya ya nufi azeeza ya ruƙo hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta ta hau ta kwanta ya sanya mata bargo ya lullu6e mata Jikinta, kafin Ya koma Saman gadonshi Ya kwanta idanuwanshi na fuskarta ceilling, Angel itace mutun ta farko da ta ta6a bugunshi, karo na biyu kenan tana ta6a lafiyar jikin shi, abun ya tsaya mashi arai, Ɗaya bayan ɗaya suka nufi gadajensu kowa Ya haye ya kwanta, Ya rage saura angel ita kaɗai a tsaye, tsabar baƙin Ciki Ya hana taje ta kwanta, saboda mugun haushin danish da take ji, ga zarginshi da take Yi, gani take kamar shi ɗin secret Giant ne acikinsu, Sai da ta bari Kowa Yayi bacci, Ta haura saman gadonta ta janyo pillow ta ɗaura kanta akai, Yau ta juya ma danish baya, ada kullum Juna suke fuskanta idan zasu yi bacci, Sam ta kasa runtsawa tunanin deeja ya hanata sakat, tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, Muryar danish ce ta ratsa kunnata, "Angel" Ya kira sunanta, Yana daga kwance saman gadonshi, tana ji tayi banza ta ƙyale shi, ya kasa bacci saboda fushin da take yi da shi, Sake kiran sunanta ya yi"Angel" kusan sau Biyar amma bata amsa ma shi ba, miƙewa yayi tare da saukowa daga saman bed ɗinshi, Ya matsa daga gefen gadonta ya zauna, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba, duk da bata waigo ta kalle shi ba amma taji alamar yana akusa da ita, Cool voice dinshi ce ta kara ratsa kunnanta, "Am really sorry, I don't mean to hurt u, just bana son Su cutar da ku ne that's the reason why na hana ku abunda ku ke ƙoƙarin yi, Giants sunfi ƙarfin ku, ba zaku iya ja dasu ba....."kamar an katse shi ya dakata da yin maganar yana kallon gefen fuskarta, pillow yaga ta sanya saman kanta ta toshe kunnanta, don ma yasan ba sauraronshi take yi ba, duk sai yaji ba daɗi, Gaba ɗaya ya rasa sukuni, shi dai bai ƙaunar yaga wani na fushi da shi, ko zafin marin da ta yi mashi ɗazu baiji ba, da ace wani ne tayi ma marin nan ko bai rama ba sai ya fusa ta, "Angel pls talk to me. i realized my mistake, and I regret it, ba zan sake ba" shiru bata tanka mashi ba, " wannan karan muryarshi tayi zaƙi da sanyi kamar zaiyi kuka, Miƙa hannunshi yayi tare da ruƙo doguwar sumar kanta, aikuwa a fusace ta sanya hannunta da ƙarfi ta ka6e mashi hannunshi,' batare da ta yi magana ba, Still baiyi fushi ba ya kuma cewa"Angel if you don't talk to me, I won't sleep, I will spend the whole night here" babu wasa a fuskarshi yayi maganar, Ji take gaba ɗaya ya takura mata, zaman shi agefen gadonta kamar saman kanta take jin shi, Tasan halin shi Ba cikakken hankali ne dashi ba, Yana iya aiwatar da abunda ya fada, Tuna wannan yasa ta miƙe xaune har ya fara sauke ajiyar zuciya atunaninshi ta yafe mashi ne, ashe masifa ta tashi ta zazzage mashi, Cakumar wuyan rigarshi tayi da hannayenta biyu, ta zazzare mashi manyan gray eyes ɗinta Ta jijjiga wuyan rigar tashi, Saboda masu bayyaci yasa ta sassauta muryarta, "Wai menene alaƙata dakai ne? Ka addabi rayuwata ka hanani sakat, kai nifa bansan ganin wannan mummunar fuskar taka, na tsani ragon namiji irin ka, pls na roƙe ka ka tashi kabar gefen gadona ko na samu inyi bacci" Takai karshen maganar tare da ture shi gefe, ko motsi baiyi ba, kallonta kawai yake yi da lumsassun idanuwanshi, A hasale tace"idan har bazaka sauko daga saman gadon ba, Ni zan tashi in baka wuri," ganin tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon yasa shi yin saurin damƙar hannunta, wani irin mugun kallo ta jefa mashi"sakar mini hannu na," ba musu ya saki hannun. ta sauko daga saman gadon, Ta dauƙi bargonta da pillow, Ta juya ta nufi tsakiyar ɗakinsu Ta shimfiɗa bargon ta jefa pillown saman shi, Ta haye ta kwanta, duk yana a zaune gefen gadonta yana kallonta, Lumshe idanuwanta ta yi da niyar bacci ya ɗauketa, kamar daga sama taji an sanya hannu an ɗauketa da ita da bargon da pillown duka ya tattare su ya ɗaga sama Ya nufi gadonta, Yana zuwa ya jefe ta saman gadonta, aɗan tsorace ta ware idanuwanta tare da wurgasu kan fuskarshi Yana atsaye ya kafe ta da ido, Tsabar mamaki ya hana ta furta komai, kamar walƙiya haka Yaje ya daukota, Cikin nuna jin takaici tace"Nashiga uku! Wai ina ruwanka dani ne? idan na kwana a ƙasa matsalarka ce ko tawa"? Ya bata amsa da cewa"tamu" guntun tsoki taja, bata ƙara furta mashi komai ba, tana jin motsin shi abayanta, haukanshi na matuƙar ɗaure mata kai, Lokacin da bacci yayi awon gaba da ita, A zaune ya fara gyangyaɗi, A ƙarshe da baccin yafi ƙarfinshi a bayanta ya kwanta saman gadonta, lallai ya taro march, *ANEELAH* Wuraren ƙarfe 12 na safe, Tana a ƙudundune Cikin bargonta, Tun bayan sallar asuba data kwanta bacci bata farka ba, wani irin nauyin bacci ne ya ɗauketa, Hada ƙarin maganin muran da tasha a daren Jiya, Baby junaid ne ya shigo cikin ɗakin yana azaune Cikin motar shi ta wasan yara, Da hannu Yake juya streering wheel ɗin motar, Ba ƙaramin kyau yayi ba, jump suit ne a jikinshi launinsu ɗaya da ƴar motar wasan shi, Army green, da alama ba ƙaramin daɗin motar yake ji ba, daga ya juya steering saita tafi da gudu, agaban gadon Mommynshi Ya tsaya, tare da kai hannu ya danna wani maddani A jikin motar, nan take motar ta soma yin Jiniya, Afirgice aneelerh Ta farka tare da yaye bargon data lullu6a dashi hannunta dafe da ƙirjinta, jallabiya ce a jikinta, Muryarta na kerma take ambaton" Innallahi wa'inna ilaihirraji'un" tayi matuƙar tsorata, Duk a tunanin ta ƴan sanda ne suka zo gidan ashe motar wasan junaid ce, Fuskarta a yamutse take kallon shi, ya wage baki yana dariya fararen hakoranshi tar dasu, Dimples ɗinshi biyu sun lotsa sosai, a fusace ta miƙa hannu ta ɗauki pillow ta wurga mashi saman fuskarshi, nan take ya kwa6e fuska zai yi kuka, Cikin nuna 6acin ranta ta soma Yi mashi magana"Karka kuskura kace zaka yi mini kuka stupid, Wlh nayi regretting dana fidda kuɗina na siya maka motar nan ashe kaina abun zai ƙare!, bazaiyiyu ba ka hanani kwanciyar hankali, zan 6a66alla motar In jefata cikin bola kowa ya huta" Jin wannan maganar yasa shi ƙara sautin kukan nashi, Ganin tana yunƙurin saukowa daga saman gadon yasa jin tsoro, gudun kada ta 6alla mashi motarshi kamar yadda tace, aikuwa da sauri yaja streering Ya juya motar da gudu yajata ya nufu ƙopa, Murmushi ta saki tana bin bayanshi da kallo, aranta tace"Allah kaɗai yasan irin ƙalin sharrin da zaije yayi mini a wurin mami, yau nifa na shiga uku, Wata'ƙil ma yaja a hanani Yin breakfast, " takai karshen maganar tare da saukowa daga saman gadon takai hannu ta ɗauko filon data jefa mashi a ƙasa ta wurgo shi saman gadon, miƙa tayi tare da yin hamma ta wuce toilet, after some minutes ta fito tana tafiya a slow ta nufi gaban mirror ta zauna, wata irin yunwa take ji kamar taci ƴan hanjin cikinta, wayarta ta ɗauka dake ajiye gaban mirror, ta danna power hasken screen ɗin ya kawo, hoton angel ne a matsayin wallpaper ɗinta, ta yi mata hoton ne saman gado tana bacci ta saki baki, Tana matuƙar son angel, Tayi missing ɗinta sosai, duk rana ta Allah idan tafarka daga bacci ta ɗauki wayarta saita sumbaci hoton, Yanzu ma kiss ta manna mashi, aranta tace"I really missed u angel, kamar in yi hauka, Allah ya kare mini ke aduk inda kike, Inaji araina cewa Kina araye kuma kina tunani na, I luv u so much" tuni hawaye sun Cika idonta, Tana yunƙurin miƙewa daga saman mirror chair ɗin, Sai ga Ana Mai aikin gidansu ta faɗo Cikin ɗakin tana Haki hannunta ruƙe da wayarta, Jikinta sanye da Riga da skirt, Sun matseta, Hankalin aneelerh ba ƙaramin tashi yae ba, Ta cikin mirror ta hangota, da sauri ta ƙarasa Juyawa Baya tana kallonta tace"Ana lafiyarki kuwa? Babu neman excuse kin faɗo mini ɗaki? Kamar wadda tasha ƙwaya"? Tayi maganar tana tunkararta, Duƙar dakai ƙasa ana tayi Muryarta na ɗan rawa tace"Am sorry madam, Wani abune na gani daya bani mamaki, shi ne nazo in nuna maki," Matsawa aneelerh tayi kusa da ita, Tare da miƙa hannu ta kar6i wayar Ana, tana ɗaura idanuwanta kan screen ɗin, Ras taji gabanta ya faɗi waro ido waje tayi tana kallonta, mamaki ƙarara akan fuskarta tace"Abun mamaki! ana a ina kika samu hoton nan? Kuma daga gani sabuwar ɗauka ce!" murmushi ana ta ɗan saki kafin tace"Yanzun nan Na ganshi A instagram, shafin twins Na Family ɗin Obinna, Zayn da zaid pravin Obinna, Su ne su ka yi posting ɗin a page ɗinsu na insta, madam i was shocked da naga pic ɗin nan nace ashe matar nan tana araye da ranta da lafiyarta! " jinjina kai aneelerh tayi da alama tayi matuƙar girgiza tace"Wonders shall neva end" kallon Ana tayi tare da cewa"Ki jira ni ina zuwa, dole mami taga hoton nan, amma dai matar nan ta bani mamaki matuƙa" Jiki na rawa aneeleh ta fuce daga Cikin ɗakin, gudu gudu sauri sauri ta nufi bedroom ɗin mami, bayan tafiyarta ana ta fito ta tsaya a falo tana jiran dawowarta, Aneelerh Na yunƙurin yin sallama a ƙopar ɗakin Mami, sai ga mamin ta fito Jikinta sanye da riga da zani na atampa, Ƙiris Ya rage su bangaji juna ita da aneelerh, Sakin baki mami tayi tana kallonta, Da sauri aneelerh tace"Am sorry mami, a ruɗe nake ne, wani abun mamaki ne Ana ta gwada mini acikin wayarta, Shi ne na kawo maki kema ki gani" tana inda inda tayi maganar, tare da miƙa ma mami wayar hannunta, tasa hannu ta kar6a, koda mami ta kalli hoton saita ruƙe ha6arta da hannu ɗaya, ta ɗan zaro ido da mamaki akan fuskarta tace"Kai! Wa nake gani kamar BENAZIR"! aneelerh tace"Mami itace, Kalli dakyau ki gani, ba'a jima da yin posting ɗin ba, " Mami tasha ruwan mamaki, Sai ƙarewa hoton kallo take yi, dagaske ɗin dai benazir ce, Daga gani hoton batasan an yi mata shi ba, tana a tsaye, hannunta ɗaya ta dafa murfin danƙareriyar motarta, tsadaddiyar gaske, jikinta na sanye da business suit black colour sunbi shape ɗinta sun zauna mata cuf cuf, kamar don ita aka ƙera kayan, hips ɗinta sun fito sosai, hannunta ruƙe da wayarta ƙirar i phone 15 pro, kanta babu hula ko ɗan kwali, Zallar gashin kanta ne daya sha gyara Har midback dinta, idanuwanta na manne da glass, idan ka ganta a hoton ba zaka ta6a yarda cewa ta ta6a aure ba, Ko tana da ƴa, saboda tsabar haɗuwarta, Jikinta Badai kyau ba, agogon diamond ɗin dake sanye a hannunta, a ƙalla Price ɗinta yakai 100m, Kallon Juna mami da aneelerh su ka yi kowa Fuskarshi ɗauke da al'ajabi, mami tace"Abun mamaki baya ta6a ƙarewa, Wai dama ƴar nan tana nan da ranta da lafiyarta? Hankalinta kwance tsawon shekara da shekaru bata ta6a waiwayar ƴarta da mijinta ba, Anya kuwa benazir ce aneelerh? Kodai watace me kama da ita? to ae abunne da ɗaure kai wlh, ' Murmushin takaici aneelerh ta saki tare da cewa"wlh mami itace! Babu shakka benazir ce, ae ina ganin hoton ko doubting ban yi ba, na shaida itace, Kinsan dama ita tun fil'azal wayayyiyar macace akwai son gayu, Kuma tafi sha'awar rayuwar ƴanci, " mami tace"Haka fa take, Oh Ni ƴarsu, duniya da abun tsoro take, Anya kuwa Benazir tasan ciwon kanta"? aneelerh tace"Ina fa, ae babu alama, Yanzu haka ko Iyayenta basu da masaniya akan inda take rayuwa, Duk da Naga kamar Ƙasar waje ne, idan kika ƙura ido a jikin Ginin dake a bayan hoton an rubuta Rbc (Royal bank of canada) dake acikin toronto, Kuma ga dukkan alamu mami hoton bada saninta aka ɗauke shi ba, don da ace ta sani da bata bari an ɗauke shi ba, kodan kada asirinta ya tonu agane inda take, tun da ko Iyayenta basu son awace nahiya take zaune ba suma nemanta suke Yi ruwa ajallo," Mami tace"Nama rasa me xance, kawai dai Allah ya shiryeta in me shiryuwace, amma dai wannan rayuwar da ta ɗaukarwa kanta bamai 6ullewa bace, Wlh zata yi danasanin mara amfani, kwata kwata benazir bata yi wayau ba, Allah kanta tayi mawa, Ace da ranka da lafiyarka, Ka gudu kabar Jinjira acikin kwamin wanka, da mijinka batare da ka waiwaye su ba almost 4 years, Saboda shafewar basira da rashin hankali, tana can tana yawon biɗiɗi," takarasa maganar tare da jan dogon tsoki Ranta ya 6aci ta miƙe ma aneelerh wayar"kar6i nan nagaji da ganin kayan takaici," kar6ar wayar aneelerh Tayi, Har ta juya zata Bar ƙopar ɗakin mami sai kuma ta ɗan dawo baya tace"mami Baby junaid fa"? "Yana aciki kwance saman gado yana bacci, Yazo yana kuka ya faɗa min wai kin ce zaki 6alla mashi mota, Daƙyar na samu na lallashe ya daina kuka ya kwanta," dariya aneelerh tasaki tare da cewa"Ya takura mun ne mami, ina tsaka da yin bacci na ya daddage ya danna jiniyar motar, baki ga yarda na zabura ba, Ni nayi tunanin ƴan sanda ne suka zo ashe shine" Dariya mami tayi tana girgiza kai tace"Allah ya shirya min jikana, " aneelerh ta amsa da amin, kafin Ta juya ta nufi falo, Agaban dining ta hango ana tana jera kayan breakfast ɗinsu, Ƙarasawa tayi inda take atsaye ta miƙa mata wayar tare da yi mata godiya, don ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease tasan benazir tana araye, Idan Allah yasa suna da tsawaicin kwana wata rana Allah zai haɗa su ne, ta wani 6angaren kuma Abun ya tsaya mata acikin zuciyarta, Irin yadda taga benazir a hoton hankalinta kwance babu wata damuwa akan fuskarta, Yinin ranar da tunanin benazir tayi shi, Da rana ne Abie Ya dawo daga wurin aikinshi, Yazo musu da babban albishir Na ƙara mashi matsayi da akayi zasu koma Abuja da zama, mami tayi farin ciki, aneelerh kuwa sam bataso haka ba, Ita fa duk wani abu da zai rabata da jos ba son shi take Yi ba, gani take kamar idan ta ɗaga ƙafa tabar garin shikenan ba zata ƙara ganin mutanan nan ukun da ta rasa ba, waɗanda a koda yaushe take Addu'ar Allah ya Bayyanar mata dasu, babu yarda ta iya yanzu dole tabi iyayenta don bata son rabuwa dasu, tafi so duk Inda zasu je ƙafarta ƙafarsu, *Back To prison* Ƙwaƙƙwaran Juyi angel tayi da niyar ta gyara kwanciyarta, sai ji tayi an tokare bayanta, A matuƙar ruɗe ta juyo tana kallonshi, waro ido waje tayi ganin danish saman gadonta, Aikuwa rai a6ace ta sanya ƙafarta da ƙarfi ta ture shi gaba ɗaya ya gangara ƙasa Kanshi Ya bugu sosai har saida yafirta"ash!!" saboda zafin da ya ji, Zazzaga mashi masifa ta soma Yi ta inda ta shiga bata nan take fita ba, sautin muryarta ya karaɗe Kunnuwan masu bacci ɗaya bayan ɗaya su batool suka dinga farkawa Suna tambayar lafiya me ya faru? Nuna danish ta yi da yatsan Hannunta tace"wlh kaɗan ka gani, Idan har baka fita sabgata ba, Ina mace kana namiji Ka kwana a gadona, Salon kawai kaja mini zunibi," Tun da ta fara Yi mashi faɗa, bai motsa daga kwancen da yake a ƙasa ba, ya dafe gefen goshin shi da hannu, Yaji zafin buguwar da kanshi yayi, Saukowa su batool su Ka yi daga saman beds ɗinsu, fuskokinsu duk A yamutse idanuwansu sun kumbura sakamakon kukan da suka sha Jiya da za'a tafi da deeja, Abakin gadon angel suka tsaya suna kallonsu ita da danish, Ta rufe ido sai faɗa take mashi hada pillow ta jefe mashi saman fuska, Ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji daɗi, shouting ɗin da take yi mashi ba ƙaramin gigita shi yake yi, daurewa kawai yake yi, "Pls angel, Ki yi haƙuri Ki ƙyale shi hakanan, kodan saboda lallurarshi ta rashin son hayaniya zai iya rikicewa, Hanna ce tayi maganar, angel ta watsa hannu tare da cewa"Idan ya tashi ya haukace ƙarewa ma, wlh ko ajikina, tun farko saida naja mashi kunne akan ya ni santa kanshi dani amma yaƙiya, saboda head fish ne dashi" Girgiza kai batool ta ɗanyi idonta akan angel tace"Sister badan halina ba, Pls Ki bar maganar nan, Ki barshi yaji da kanshi, Nasan kina fushi dashi ne saboda abunda ya faru jiya, Ki yi haƙuri ki manta komai, kuma ki daina fushi dashi saboda Baya ƙaunar yaga ana share shi, Yana shiga damuwa" daƙyar batool takarasa maganar ganin irin kallon da angel ke jefa mata, Gyaɗa kai tayi tare da jinjina kai tace"Shikenan zan ƙyale shi amma babu ruwanshi dani! Ni kawai bana son Yana kallona ko Yana yi mini magana, " Tana kammala maganar ta sauko daga saman gadonta ta bi ta gefensu Ta shige toilet, Zuƙunnawa batool tayi agaban Danish Ta ruƙo hannunshi acikin nata, Ba ƙaramin tausayin shi taji ba, ganin sahun marin da angel tayi mashi asaman fuskarshi har yau bai disashe ba, Cikin sanyin murya tace"Am sorry danish, Kamar yarda tace ka ƙyale ta, to ka rabu da ita har zuwa time da zata huce, if not zata cigaba da Ƙyararka ne, Nasan zata dawo da kanta ne ta nemi yi maka magana," sai lokacin ya samu ya miƙe zaune, ya jingina bayanshi jikin bango, ɗaya bayan ɗaya ya shiga binsu azeeza dake atsaye da kallo, matan ne gaba ɗayansu, Sai daga bisani Haris da su naufal Suka Sauko daga saman gadajensu, A inda yake zaune suka tsaya cirko cirko suna kallon shi, "Kuma fushi ku ke yi da ni? Kamar yadda take fushi dani"? Yayi masu tambayar idonshi akansu, atare suka haɗa baki wurin cewa a'a, Kallon haris yayi tunkafin yayi mashi magana haris yai saurin cewa"am not angry with u, kaima ka sani bazan iya fushi dakai ba, just banji daɗin abunda ya faru ba jiya, amma komai ya riga daya wuce" jinjina kai danish yayi kafin ya kuma cewa"komi nake yi ina yi ne saboda ku, amma nasan zaiyi wuya ku fahimci hakan, sai nan gaba" Naufal yace"Pls danish, mu komai ya wuce awurinmu, abunda ya faru ya riga daya faru ba wanda ya isa ya dawo dashi baya, so pls mu manta kawai, baida amfani tuna baya," Danish yace"idan ku kun fahimce ni, ita taƙi ta fahimce ni, tun daren jiya nake bata hakuri amma taƙi ta saurare ni," sai lokacin suka gane inda damuwarshi ta dosa, dama shi haka yake sam baya son wani yana fushi dashi tun fil azal, gaba ɗaya yake rasa sukuni, "Danish kada ka damu kanka, In dai angel ce Zata kula ka, Ae bata iya fushi ba, tana da saurin hawa da kuma saurin sauka," acewar javed, Ta6e baki yai tare da cewa"Its okey, ngde da kulawarku agare ni, " daga haka Ya miƙe jiki ba ƙwari Ya Nufi toilet, domin yin wanka, Kafin Giants su kawo musu Breakfast ɗinsu, Sai da kowannan su Ya yi wanka, Basu jima da hallara A cikin ɗakin nasu ba, Sai ga Giants ɗin sun shigo ɗauke da kayan abincinsu, bayan sun ajiye musu saman dining carpet, duk suka zazzauna kewaye da farantan, Yau farfesun naman kaza aka kawo musu da zafinshi hada tiriri Yaji kayan ƙamshi, ga kuma dambun nama da aka haɗo musu dashi, sai Kayan marmari kamar kullum da kuma soft drinks, Abun na ɗaurewa angel kai, ganin irin badagon da ake yi da nama agidan kurkukun, sam bata yarda da irin wannan Lafiyayyar cimar da ake kawo musu ba, kullum basu da abinci sai nama kala kala! Na kaza na shanu na rago, wani naman ma batasan na wace dabbar bane, tana yawan tambayar kanta ko su wanene ke girka abincin kurkukun daga gani ƙwararru ne a 6angaren catering, sun iya sarrafa abinci, wani naman saboda tsabar dahuwar shi kana jefa shi abaki tunkafin ka taune da haƙori zai dagargaje da kanshi, ita dai fargabarta kada ace abincin da ake basu su naci, da ransu za'a fanshe, duk in zuciyarta ta saƙa mata hakan sai taji gabanta ya faɗi rasss! Don kuwa ko gwamnati bata aikin banza, balle kuma mutanan da Ba Allah ne aransu ba, Sunsan dalilin dayasa suke basu lafiyayyan abinci wata'ƙil kodan suna amfani dasu ne, Allah wa'alamu kafin su fara Shan farfesun saida ta tunasar dasu akan su yi bismilla, Kullum ne sai ta tuna musu, hatta haris yau da tace su yi bismillah sai da yayi duk da bai musulunta ba, danish ne kawai baiyi ba, Ta lura dashi duk wani abu daya ƙunshi sunan Allah aciki bai furta shi, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, Har suka kammala cin abinci, da zarar sun haɗa ido dashi sai ta dinga jefa mashi harara, duk yabi ya tsargu ya hana zuciyarshi sakat, farfesun ma ba'a cikin kwanciyar hankali yasha shi ba, Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan Suka fuce daga Cikin ɗakin, Ganin suna yunkurin zuwa saman gado su kwanta ne, yasa angel ta dakatar dasu, tace su motsa jikinsu, Idan sun kammala su watsa ruwa ajikinsu, Sannan Sun kwanta su huta, babu musu suka amsa mata da toh, banda danish da haris, tuni sun haye saman gadajensu, Shi haris damuwar rashin deeja ne yasa shi ƙin ta6uka komai, tunanin abunda ya faru daren jiya kafin atafi da ita ya tsaya mashi arai, Yaji tausayinta sosai, su kansu sauran ƴan uwan nasu sun damu da deeja, Ba yadda zasu yi ne shiyasa suka barma Allah komai, A tsakiyar ɗakin suka Jera layi suna yin exercise, kamar wasan ƴar tseral haka suka dinga zubawa da gudu idan suka kai ƙarshen bango sai su dawo su sake komawa, Sai da suka tara uwar zufa ajikinsu tukunna kowa Ya nufi toilet domin watsa ruwa, Bayan sun fito ne, parveen ta matsa ma angel akan tayi mata irin kalabar da tayi ma su azeeza, Dama tun ranar da ta ganta ta kwallafa rai akan tana so itama, kafin marece yayi angel tayi ma parveen kalaba biyu akanta, ba ita kaɗai ba hada rubina tayi mawa, Bayan ta kammala musu kitson, Kowa Ya koma saman gadonshi ya zauna, Fira suka soma yi atsakaninsu acikin firar ne, suka tambaye ta, wai da tace musu wata rana zasu fita idan suka fita ina zasu je? Su da basu san komai na wajen kurkuku ba, murmushi tayi tare da cewa su kwantar da hankalinsu, Gaba ɗayansu zasu yi rayuwa agidan daddynta, Tace daddyna yana da gida, kuma gidanmu ɗaki Shida ne, Akwai palour ɗaya, dani da azeeza da batool zamu ware ɗaki ɗaya, Parveen da deeja da hanna zasu ware nasu ɗakin ɗaya, sai Eve da hibba da rubina suma zasu ɗauki ɗaya, nawa kenan? Suka ce mata Uku, tace toh, sauran ɗakunan guda uku, Javed da Naufal tare da Mubeen zasu ɗauki ɗaya, sai Haris shi da wancan Maji daɗin gadon suma zasu ɗauki ɗaki ɗaya," da ta ambaci maji daɗin gado hada harara ta wurga ma danish, ya lumshe idanuwanshi tamkar baiji me tace ba, Azeeza tace"Saura ɗaki ɗaya ya rage, wa za'a bamawa" angel tace"Na daddyna ne idan Allah yasa yana araye, ko ince daddynmu" gaba ɗaya suka saki murmushin farin ciki, parveen tace"amma kina ganin daddynki zai so mu," angel tace sosai ma, In ma daddyn nawa baya araye, zamu zauna wurin auntyna adama ne, Ko gidansu aunty aneelerh na, zasu ɗauki nauyin duk wani abu da zamu buƙata, Cin mu shan mu da suturarmu, kuma zamu yi rayuwar ƴanci, Zamu je inda muke so, Muje shan ice cream, muje cinema kallo, hada shopping mall zamu dinga zuwa kowa ya za6i abunda yake so, " parveen na murmushi tace"Zamu dinga samun abinci akai akai"? Dariya angel tayi tare da cewa"Sau uku arana, za'a bamu breakfast, lunch and dinner, Idan ma kinga dama tsakar dare kika farga da yunwa zaki Iya zuwa kitchen ki girka abunda ranki yayi maki, " Gaba ɗaya suka sanya ihu suna murna jin tace zasu Iya girki da kansu, Ga kuma abinci available, A lokacin jikin angel yayi mugun sanyi, ganin yadda suke ta farin Ciki, gani take kamar bazasu rayu ba, balle aje ga maganar fita daga Cikin wannan Kurman kurkukun ƙaddarar, Batool tace"wlh angel baki ji irin daɗin da naji ba, sai naji dama ace yau mu fita daga kurkukun nan, muje gidanku, kinga shikenan mun rabu da giants, bazasu ƙara zuwa su ɗauki wani acikin mu ba, balle har su cutar dashi," Azeeza tace"Nima na ƙosa inga ranar da zamu fita daga prison ɗin nan, wlh Ina so inyi rayuwa irin wadda ki kayi tare da daddynki, ae kince mana zai so mu, muma zai maida mu kamar ya'yanshi, zai dinga zuwa damu yawo yakaimu wuraren da kika bamu labari ko"? Angel tace"Eh, kuma koda ace babu daddyna, akwai sauran dangina duk zasu so ku, kuma zasu gatanta ku kamar ya'yansu ku," acikin zuciyarta tace"sai dai fitar ce keda wuya, bansan ya zamuyi ba, gidan kurkukun nan yafi ƙarfi na, sai dai bai fi ƙarfin mahaliccin mu ba, Har dare Yayi suna fira Gwanin ban sha'awa, ta faranta musu sosai, Bayin Allah sun ƙwallafa rai da son yin irin rayuwar da tayi, wato rayuwar ƴan ci, yanzu a shirye suke da zarar sun samu hanyar fita zasu bita ne, hmmmmmm *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Saboda daɗin fira yasa suka dawo bakin gadon angel kowa ya samu wuri a gefe da gefen gadon suka zauna waɗanda basu samu wuri ba daga ƙasa suka zauna, Javed hada ƙoƙarin ɗauko fitilun ɗakin guda uku Ya kunna a ƙasa ya ajiye su, ɗakin ya yi haske, sun ɗauki tsawon lokaci, sai da angel taga sun fara gyangyaɗin bacci, ta Katse masu firar tare da cewa"its time to sleep, Kowa Yaje ya kwanta, gobe in Allah ya kai mu da rai da lafiya zan ƙarasa baku labarin" suka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya kowa Ya miƙe suna tafiya suna bangaje juna a haka suka nufi gadajen su, har sun kwakkwanta Muryar angel suka ji yo tana cewa"Su yi addu'a kafin su kwanta" suka amsa mata da toh, Danish yana lafe saman gadonshi, ya lumshe idanuwanshi, amma babu alamun bacci yake yi, Gyara kwanciyarta ta yi, yau bata ju ya ma shi baya ba, suna fuskantar Juna, Ganin yana mutsu mutsun buɗe idanuwanshi yasa tayi saurin Fuskantar ceilling, tare da rufe idanuwanta, Sam bata ji lokacin daya sauko daga saman gadonshi ba, sai dai taji hucin numfashin mutun yana kokawa da Nata numfashin, da sauri ta buɗe idanuwanta, Tsabar firgitar da ta yi ne yasa ta zare ido, Ganin fuskarshi a kusa da ta ta, Saman gadonta Ya hau Ya yi mata rumfa da ƙirjinshi, ƙiris Ya rage tsinin hancin shi ya gogi nata, Tsananin mamaki ne Ya kamata, Tuni ta shiga ruɗanin kome zai yi mata, Gashi ya tsareta da idanuwanshi ko ƙyaftawa babu, muryarta na inda inda tace"La..fi..ya"!? Yace"haƙuri nazo na baki, ki daina fushi dani, tun jiya baki yi mini magana ba, Idan muka haɗa ido sai ki ta harare na," daƙyar yakai ƙarshen maganar throat dinsa na moving kamar yana swallowing ɗin wani abu, yana ganin ta fara yunƙurin motsa la66anta alamar zata yi magana da sauri ya ɗaura dogon yatsan shi saman ƙaramin bakinta, Cikin sanyin murya yace"Pls don't shout at me, Idan kinsan ba me daɗi zaki faɗa mini ba, Kiyi shiru kawai, nafa baki haƙuri, Kuma na gane kuskure na," Hawayen da ta gani kwance a cikin fararen idanuwanshi ne yasa taji zuciyarta ta karaya, sai ma taji tausayin shi yakamata, Shi dai haka rayuwarshi take, Yana da matuƙar saukin kai, ga haƙuri matsalar shi ɗaya ragwanci, hannu tasa ta kawar da yatsanshi daga saman bakinta, Sai da ta fara jefa mashi harara, kafin tace"Zan yafe maka amma sai ka yi mini alƙawarin wani abu" yace"komene ne zanyi" ɗan ta6a baki tayi tare da cewa"kada ka ƙara bari a ɗauki wani daga Cikin mu, Saboda nasan kana da ƙarfin da zaka Iya hana wa" tunkafin ta karasa maganar, Yae saurin girgiza kai yana faɗin"That's impossible, ki fahimce ni, Ni ba kowa bane face prisoner, bani da ƙarfin da zan Iya yin fighting da giants, sunfi ƙarfina, idan ba so kike in rasa raina ba" tsoki taja"hmmm dama nasan haka zaka ce, Idan har dagaske baka da ƙarfi, to ta ya akai ka ke Iya shiga toilet bayan na datse ƙopa ta Ciki? Kuma ya akai ka iya 6a66ako glass door ɗin dake acikin toilet, tun daga tushen shi, taya zan yarda da maganganunka? Ta yi tambayar tana kallon cikin idanuwanshi, Har lokacin yana a yadda yake bai ɗago ba, Runtse idanuwanshi ya yi, tare da biting lower lip ɗinshi, A hankali ya ɗan ware su akan fuskarta, Muryar shi arauna ce ya soma magana"Bansan ya zanyi in fahimtar dake ba Angel, Ni kaina bansan Ya akai nake iya shiga wurin dake a rufe ba, Also ƙarfin da yazo mini time dana cire glashin nan yanzu babu shi ajikinta...." kawar da kanta gefe tayi tare da cewa"Ban yarda dakai ba, danish Ina zargin kai ma Giant ne, kamai da mu shashasha kana 6oye mana ainihin wanene kai, Sannan kuma kasan Komai game da kurkukun nan, Amma kaƙi ka sanar damu, kafi so mu yi ta shan wahala har mu rasa rayukan mu, Kana ji kana gani ana cutar da rayuwar ƴan uwan mu amma kai hankalin ka kwance, Ko ajikinka.....' Kafin ta rufe bakinta, Taji saukar ɗigon ruwan acikinsu, da sauri ta kalle shi, Hawayen shi ne suka sauka cikin bakin ta, Yana girgiza kai yace"angel stop accusing me, am not a giant, Bana jin daɗin maganganun da kike gaya mini, its hurting my heart," Daƙyar Ya kai karshen maganar, wani irin raɗadi zuciyarshi ke Yi mishi, idan akwai abunda ya tsana Ya biyo bayan Giant, Yaji zafin Kalaman angel fiye da zafin marin da ta yi mi shi, ita kanta angel da ta yi maganar sai daga baya ta yi danasanin furta mashi zargin da take yi akanshi, bata ta6a ganin fushi akan fuskar danish ba, sai yau, Jikin shi har kerma yake Yi, wurin saukowa daga saman gadonta, da sauri ta mike xaune tana kallon shi, Ji take kamar ta kira shi ta lallashe shi, girman kai ya hana tayi hakan, Ta yi tsammanin zai kwanta asaman gadon shi ne, amma sai taga ya ɗauki pillown shi tare da bargonshi, bai nufi ko'ina ba sai cikin toilet area ɗinsu, duk sai taji ba daɗi, Ya rasa ina zai kwanta sai cikin toilet, In da madaddalar shaiɗanu suke? Dama Ya lafiyar giwa, har ta koma ta kwanta da niyar tayi bacci amma sai ta gaza runtsawa, Damuwa duk ta cika ta, a ƙarshe dai ta ji bazata Iya jurewa ba, ta miƙe Ta sauko daga saman gadonta, sai da ta fara zuwa gaban table ta ɗauko fitila ta nufi cikin sashen toilet ɗin, Tana zura ƙafarta Ciki, ta same shi a kwance saman shimfidar da yayi, hawaye ta ko'ina asaman face ɗinshi, ya lumshe idanuwan shi jin motsin mutun yasa shi ɗan buɗe idanuwan da suka canza launi, koda ya yi arba da ita sai ya ju ya mata baya, A ƙasa ta ajiye fitilar ta zauna gefen shimfiɗar tashi, Kusan mintuna tana kallon gefen fuskarshi, Daƙyar ta iya buɗe baki ta soma magana, "Danish fushi ka ke yi dani? nayi nadama, da nasan kalamaina zasu 6ata maka ranka, da ban furta maka su ba, nima na faɗi ne kawai badan ina nufin hakan ba, " Babu irin lallashin da bata yi mishi ba, amma ɗan tahalikin nan yaƙi tanka mata, Muryarta a karye tace"Nagaji da lallashinka, Kaga Idan ma bazaka haƙura ba, to ka tashi mu koma ɗaki ka kwanta, Amma kwana a wurin toilet ɗin nan sam bai dace ba, Akwai shaiɗanun aljanu zasu iya cutar dakai,' sai lokacin yace"Meye damuwarki idan sun cutar dani? Jikin ki ko nawa"? Ta bashi amsa da cewa"Namu, saboda na damu dakai, dani dakai abu ɗaya ne, jinin dake yawo ajikin ka shi yake yawo ajikina, taya ɗan uwa zai share ɗan uwansa? Duk da nasan laifina ne amma na gane kuskure na na yin fushi dakai bazan ƙara ba," Bai ƙara tanka mata ba, "Pls danish, mu koma ɗaki, " magiya ta dinga yi mashi amma yaƙi tanka mata, har ta fara tunanin ko ya yi bacci ne jin shiru, matsawa ta yi sosai kusa dashi, ta ɗan kwanto saman jikin shi tana leƙen fuskarshi, ya rufe eyes ɗinshi, kamar ya fara bacci, yanke shawarar ɗaukar shi ta yi kamar yarda ya ɗauketa jiya da ta yi fushi ta kwanta a ƙasa tsakiyar ɗakin su, Murmushi ta saki yayin da take nannaɗe hannun rigarta, tana kammalawa, ta soma kiciniyar ɗaukar shi, duk yana jin motsin hannayenta a bayanshi, wani irin nauyi ne dashi yadda kasan dutse, Ta tattara Iya ƙarfinta na ƙarshe ta ɗaɗɗago dashi, ta samu ta raba shi da saman bargon, tana ƙoƙarin Juyawa don ta nufi ɗaki dashi, wani irin nauyi Ya fisgeta, ba arziƙi ta sake shi ta rubza saman jikinshi, tana faman haki hana nishi kamar wadda tayi uban gudu, bawan Allah, kanshi ya bugu sosai, ba yadda ya iya, Jarabar angel tafi ƙarfin shi, har time ɗin bai buɗe idanuwanshi ba, bai kuma motsa ba, saboda nauyin jikinta dake asaman nashi, Babu alamun zata ɗaga shi, ta kifa kanta saman kirjinshi, sumar kanta duk ta tarwatse, slowly ya ɗan ware idanuwan shi, ya ɗaurasu akan sumar kanta, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta""An..gel" Ƙasa ƙasa ya furta sunan, bata amsa mashi ba. Kuma bata ɗago ba, ranshi ne ya bashi cewar kodai tayi bacci ne Zagayo da hannayen shi yae saman bayanta, a wannan yanayin bacci ya yi awon gaba su, manne da juna, A washe gari Haris ne ya fara farkawa daga Bacci, Cikin buƙatar zuwa toilet, Saukowa Ya yi daga saman gadonshi ya nufi toilet yana hamma tare da yin miƙa duk a lokaci ɗaya, Zura ƙafar shi keda wuya ya yi arba da su angel dake a kwance saman bargon danish, sun ƙanƙame juna suna bacci, Yadda kasan tip da tyre, Tsabar mamaki ne ya kama dashi, har wani leƙen su yake yi don ya gane ma idonshi da kyau, hada sanya hannu ya ruƙe ha6arshi, can kuma sai ya saki murmushi, Mutumin da ke jin fitsari maimakon ya shiga toilet, Sai ya juya saboda gulmar data ciyo shi, Jikin shi har rawa yake Yi, wurin komawa cikin ɗakin, agaban gadajensu Javed, Yaje yana tashin su daga bacci, ɗaya baya ɗaya ya dinga tada su, Kowa Ya mike yana miƙa da hamma tare da tambayar shi lafiya? Yace musu Su zo suga wani abun ban mamaki, Koda jin haka jiki na rawa, Kusan atare suka sauko daga saman beds ɗinsu, lokacin da su batool suka shiga, Suna Yin arba dasu Danish manne da juna, Kowa Ya buɗe baki haɗi da zare ido, Kamar sun samu tv, A kewaye da shimfidar Suka zuƙunna suna kallonsu, Yayin da su masu baccin basu san wainar da ake toya ba, Angel ce ta fara farkawa, A hankali ta ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, ras taji gaban ta ya faɗi ganinta ajikin danish, sam ta manta meya faru jiya, waro ido ta ɗanyi tare da sanya tafin hannunta ta rufe bakinta, Gyaran miryar Da haris yai mata ne yasa tayi wuff ta sauka daga saman jikin danish ta koma gefe ɗaya, Ta yi tunanin zata ga haris shi kaɗai amma sai ta gansu kaf ɗinsu kewaye dasu, Tawaga guda, sun baza na mazurinsu suna kallon Ikon Allah, Muryarta na in ina tace"Am..kun..gane..jiya..um" bata ƙarasa maganar ba, Batool tace"Ai mun riga mun gane komai ba sai kin yi mana bayani ba," azeeza tace"ƙwarai kuwa, Aljanu ne suka kawo ku nan, koba haka ba"? Ta yi tambayar tana kallon faces ɗinsu Hannah, har suna haɗa baki wurin cewa eh, wani kallon rainin wayau taga suna Yi mata, Kafin ta ƙara furta wani abu, danish ya farka yana kokarin buɗe idanuwanshi, Biji biji yake iya ganinsu, Haris yakai hannu ya bugi ƙafarshi"tashi ka yi mana bayani, meya faru a daren jiya," gaba ɗaya jikin shi kasala yake Ji, Yunƙurawa Yayi tare da miƙe wa zaune, a lokacin idanuwan nashi sun washe yana ganinsu, One by one ya dinga binsu da kallo, sai wani sakin murmushi suke Yi kamar sabbin mahaukata, ɗauke eyes ɗinshi yae daga kan fuskokinsu, Ya mayar dasu kan angel da tayi wuƙi wuƙi da ido, Suna haɗa ido dashi, ta fara zazzaga mashi masifa"Duk kai kaja mini ina zaman zaman lafiyata, Tun farko basai da nace Ka koma ɗaki ka kwanta ba amma saboda kafiya irin naka kaƙi jin maganata, Ka nace saika kwana anan, Ni banma yarda dakai ba, kaine ka janyo ni jikinka, har bacci ya ɗauke ni, saboda rashin tsoron Allah, gashi kaja min zunubi," tun da tafara faɗa suka zuba mata ido suna kallonta, Ita fa gani take kamar suna zargin wani abu, yayin da su kuma basu kawo komai aransu ba, saboda ilminsu bai kai nan ba, Abun ma burgesu Yayi, don su a wurinsu ba wani bane don mace ta haɗa jikinta dana namiji, sun saba ba tun yanzu ba, saboda haka suka taso suna rungumar junansu, abu ɗaya ne basu yi neman junansu, shima saboda basu da shauƙin sha'awa kwata kwata, an cire masu shi, amma fa suna ƙaunar junansu sosai, sai ma mutun ya yi tsammanin akwai soyayya asakaninsu, Alhalin nan kowa babu wannan aransu, Kawai ƙaunar juna ce, "Angel ki daina ƴan kame kame, Mun riga mun san komai," harara ta jefa ma hanna da ta yi maganar tace"Me kuka sani? Idan ma wani abu ku ke zargi to shine ke da laifi ku tambaye shi ku ji,"a ƙule tayi maganar, shi dai baice komai ba, idonshi na akan fuskarta, Parveen tace"danish ka faɗa mana gaskiyar abunda ya faru? Dagaske ne Kaine silar komai? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, saboda gudun jarabar angel, Javed yace"Ni ban yarda ba, Nafi zargin Angel, Cos danish bazai ta6a kawo ki nan ba, sai dai ko kece kika biyo shi, wama ya sani ko faɗa ne ya haɗa ku, " miƙewa tsaye angel tayi"Ni kun ga tafiya, Ina da abun yi" Takai karshen maganar tare da Juyawa ta Nufi toilet ta buɗe ta shige, Jamlock ta sanya ta datse ƙopar, kafin ta le6e tana sauraron me suke cewa, "Danish faɗa mana gaskiya, Meya faru daren Jiya a tsakaninku? Ya akai kuka baro ɗaki kuka dawo nan"? Batool ce ta jera mashi tambayoyin, angel dake la6e ta yatsina fuska aranta tace"Wannan batool ɗin sai kace ƴar jarida, ko ina ruwansu da abunda ya faru adaren jiya in ban da gulma da son jin kwakwaf mtsww"taja tsaki daga ƙarshe, Tana Jinsu suna ta tambayarshi ya faɗa musu, Amma yaƙi basu amsa sai dai ce musu ya yi, ya manta komai, bazai iya tunawa ba, dole suka haƙura da tambayarshi, Ajiyar zuciya angel ta sauke, a fili tace yayi ma kanshi ƙiyamul laili, dama Bata son ya faɗi ne don kada ajinta ya zube, su ji cewa itace ta biyo shi don ta ba shi haƙuri, Bata fito daga Cikin toilet ɗin ba, sai da ta yi wanka, A waje ta samu Su haris suna Jiran Na cikin toilets ɗin su fito su ma su shiga ko sun samu su yi wanka, Wuce su ta yi zuwa Cikin ɗakin, Babu kowa duk suna a can sai ita kaɗai, daga gefen gadonta ta zauna, bakomai ya faɗo mata acikin ranta ba face Deeja, Ko awani hali take ciki yanzu Allah wa'alamu, ɗaga hannayenta sama tayi cikin harshen labarabci ta soma jero addu'o'i tana karanto da niyar Allah ya tsare musu ƴar uwarsu, tana Cikin Yin addu'ar taji yo motsin buɗe ƙopar ɗakin tsohuwa, da sauri takarasa shafa addu'ar, Ta juya tana kallon ƙopar, tsohuwa ta fito daga cikin ɗakin, hannunta ruƙe da sanda, fuskarta a harmutse baka Iya gane awani yanayi take, haɗa ido su ka yi da angel, da buɗar bakinta sai cewa ta yi"Ba zaki zo ki gaishe ni ba"? Murguɗa mata baki angel ta yi tare da cewa"Mutanan kirki nake gaisarwa, ba masu matattar zuciya ba" bazawarin murmushi tsohuwa tasaki, haɗi da girgixa kai tace"kin tsane ni kamar mutuwarki" angel tace"fiye da haka" dariya tsohuwa tayi, "Idan ba ki son ganina to ki kwantar da hankalinki, nan badajimwa ba, Zaku daina gani na," babu yabo ba fallasa angel tace"Da munji daɗi wlh, kwara mu daina ganinki, tun da dama babu amfanin da kike yi mana, sai sai kawai kullum ki leƙo da ƴar sanda a hannu," wannan maganar ta angel ba ƙaramar dariya ta bata ba, Musamman data kwatanta yadda tsohuwa ke leƙo wa da kanta, "Ba zaki yi kewata ba"? Ta jefa mata tambaya, angel tace"Kin ta6a ganin anyi kewar maƙiyi? To idan ma ana yi ni bansani ba, Ni dai burina shine ki fita arayuwar mu, saboda baki da amfani, " hannu takai ta ɗauki pillow Ta ɗago dashi tana nuna ma tsohuwa tace"Kinga wannan matashin kan na hannu na? wlh yafi ki amfani yafi ki daraja da ƙima a wurin mu, ai ke dake da waccan tukunyar fulawar ta Cikin toilet ɗin mu baku da banbanci," Tuntsirewa tsohuwa ta yi da wata irin mahaukaciyar dariya hhhhhhhh, da gudu su Hannah suka shigo cikin ɗakin sakamon Jin sautin dariyar tsohuwa wanda yajawo hankalinsu, A tsakiyar ɗakin suka tsaitsaya suna Kallonta, Ɗauke ido tsohuwa tayi daga kan angel ta mayar dasu kansu Batool tace"Kuma bazaku gaishe ni ba"? Maimakon su gaishe ta, Sai suka juya suna kallon angel, Tsohuwa tace"ba shakka, Uwarku kuke Jira ta baku Umarni kenan"? Shiru suka Yi basu ce mata komai ba, Still idonsu na akan angel data maƙe musu kafaɗa alamar kada su gaishe da ta ita, Shigowa cikin ɗakin mazan su ka yi gaba ɗayansu duk sun yi wanka, Suna ƙarasowa inda tsohuwa take, cikin girmamawa Danish Ya ɗan russuna tare da gaishe da ita, hakan ba ƙaramin fusata Angel yayi ba, har saida taja dogon tsoki, Dogara sanda tsohuwa ta yi zuwa inda danish yake a tsaye, Ta miƙa hannunta ɗaya ta shafa sumar kanshi tace"Albarka zata tabbata akanka, Yarona, ina matuƙar alfahari dakai, Saboda kai na musamman ne, Zan yi kewarka sosai" Cikin sanyin murya danish yace"meyasa kika ce haka"? gajeran murmushi tsohuwa tasaki kafin tace"Bakomai," ta ambaci hakan tare da kallon su Batool dake a tsaitsaye cirko cirko tace"Ko kaɗan banji haushi ba da kuka ƙi gaishe ni, Saboda bancancanci hakan ba, Naji daɗi da ku ka nuna min cewa Kun girma kun mallaki hankalin ku, zaku iya tafiyar da rayuwarki even without me," tana kai karshen maganarta, A sukwane ta juya tana dogara sanda ta nufi ɗakinta, Har ta kusa shiga sai kuma taci burki, kamar an dakatar da ita, a hankali ta waiwayo baya ta kalli angel dake zaune tana hura hanci, tace"me ma ki kace? Dani da tukunyar fulawar dake acikin makewayin ku bamu da banbanci"? Ɗaga mata gira angel tayi alamar eh, dariya tasaki tana girgiza kai tace"Tukunya fulawar dake a makewayinku tafi ni mahimmanci Angel, Ku dage da bata ruwa akai akai, Furannin dake Acikinta zasu Yi tsuro su girma, gwanin ban sha'awa," tana faɗin hakan ta juya ta karasa shigewa cikin ɗakinta, taja ƙopa ta rufe, Ta6e baki angel ta yi tare da watsa hannayenta tace"Abanza" batool tace"bansan meyasa naji jiki na yayi sanyi ba, sai naga kamar bamu kyauta ba da muka ƙi gaishe da tsohuwa" Harara angel ta watsa mata"Ae sai ki bita cikin ɗakin ki gaishe da ita, Ni ko me matar can zata yi wlh bazan ta6a girmamata ba, muguwa azzaluma macuciya kawai da ita," Cikin sanyin murya danish yace"Ki daina angel badai dai bane, ita tamkar mahaifiya ce agare mu, koda ace kuwa muguwace ita, saboda tafi iyayen mu, idan har dagaske suna araye kuma su ne suka yi silar zuwan mu nan" daƙyar ya kai ƙarshen maganar, ganin tana nuna shi da yatsan hannunta"Kai ka kiyaye ni! Wato raini ya fara shiga tsakanina dakai saboda jiya mun kwana a shimfiɗa ɗaya ko"? yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya taba su batool ba, Haris yace"Da alama Jiya kunji daɗin baccin nan, shiyasa muka taras daku a manne da juna, Yadda kasan ANTA da JINI,' dariya su hanna suka saki, Angel kuwa tasha mur, tana jifar danish da harara, murmushi ne ya bayyana akan fuskar danish, tana ƙunƙuni tace"zamu haɗu" juya mata ƙeya ya yi, batare da ya tanka mata ba, Azeeza tace"Ni dai bari naje toilet, In zuba ma fulawar nan ruwa, Saboda tsohuwa tace mana tana da amfani" ruƙo wuyan rigar azeeza haris Yayi"Zo nan Sullu6iyo, Ke har kin yarda da maganar ta? Bayan irin ƙarairakin da take gaya mana? Shin idan kin bama fulawar ruwa ta girma, wani amfani zata yi mana? Ko ɗibarta zamu dinga yi muna ci ne"? Yayi tambayar yana Leƙen fuskarta, Gatsina mashi hanci ta yi, tare da cewa"Oho, Nima bansani ba," ta faɗi hakan tare da buge hannunshi, Ya zame daga ruƙon da yayi mata, Hanna tace"Dama ita mashiririciya ce narasa me ke damun azeeza, Kwakwalwarta gaba ɗaya shirme ne acikinta, saboda rashin aikin yi flower zaki je ki zuba ma ruwa? bubbuga ƙafa azeeza tayi rai a6ace tace"To wai ina ruwanku dani ne? Bani naji zan iya ba, Sai ku ƙyale ni," Da ɗan tsoki ta ƙarasa maganar, Parveen dake ta faman Yin hammar yunwa tace"Dan Allah ku yi shiru, Surutunku Yana ƙara Harzuƙa Yunwar Ciki na," Rubina tace"damuwarki kenan, abinci abinci, Kowa dai da abunda ya ishe shi," Haris yace"Ni kuma damuwata deeja, " Yana faɗin hakan gaba ɗaya walwalar dake akan fuskar kowannan su ta canza zuwa damuwa, "Ba kai kaɗai ba haris, Gaba ɗayan mu mun damu da deeja, tana acikin ran mu, Mun yi shiru ne saboda bamu da yarda zamu yi, damuwa ko yin kuka bazasu ta6a dawo mana da ita ba, Haƙuri Shi ne yakamata mu yi, Sai kuma mu bi ta da addu'a, Allah Ya tsare mana ita aduk in da take" Angel ce tayi maganar a yayin da ta miƙe daga saman gadonta, walking Slowly Ta nufi inda suke a tsaitsaye itama ta tsaya, Jikin kowannan su Ya yi sanyi, shessheƙar kuka azeeza ta fara, aikuwa haris ya daka mata tsawa tare da cewa"Zaki yi shiru ko saina buge maki baki? Ƴar rainin wayau, yanzu kika gama zancen bama flower ruwa amma daga jin anyi maganar Deeja kin wani 6are baki zaki ma mutane kuka ke da kika fi kowa ƙaton baki acikin mu" idamuwanta cike tab da kwalla take kallon haris, sai kuma ta duƙa ƙasa ta ɗaura kanta saman guiwowinta ta fashe da kuka, girgiza kai danish yai idonshi akan na haris, Shi ma haris din kallon nashi yake yi, don yasan dole ya tanka mashi, Saboda sanin halin shi na rashin son ana 6ata musu rai, musamman azeeza kodan yana ganinta ƴar ƙarama ne acikinsu, Tunkafin danish yace wani abu haris ya riga shi cewa"Its ok Bazan ƙara ba, amma itama ta daina Yi mana kuka" Azeeza dake a tsugunne tana kuka ta ɗago da kai Cikin shessheƙa tace"Bazan daina ba, In ka tashi ka kashe ni, Kuka yanzu na fara" yanayin yadda ta yi maganar taso basu dariya, Matsawa angel tayi kusa da azeeza, Ta sanya hannayenta biyu ta ɗago da ita, tare da rungumeta ajikinta, tana lallashinta, Cikin ƙanƙanin lokaci azeeza ta yi shiru, kamar wadda ta samu jikin mahaifiyarta, ta lafe ma angel, hada zagayo da hannayenta biyu abayan angel ta ƙanƙame, Batool dake kallonsu ta saki murmushi, tare da cewa"gwanin ban sha'awa," angel tace"kema idan kinaso kizo in rungumeki" kafin batool ta bata amsa, Hanna tace"Ni baki ta6a rungume ni ba ajikin ki" Tun da hanna tace haka gaba ɗaya sauran Ƴan matan suka ce suma bata ta6a yin hugging ɗinsu ba, Lokaci ɗaya ta ji gabanta ya faɗi rass! Da sauri ta sanya hannayenta Biyu ta janye azeeza daga Jikinta, Hannunta na dama ta ɗaura saman ƙirjinta a saitin zuciyarta, Yayin da la66anta suke kerma, Hankalin su Hanna ba ƙaramin tashi ya yi ba ganin irin canzawar da angel ta yi, Ji su ka yi ta fara ambaton"Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un"! har suna haɗa baki wurin tambayarta lafiya, Girgiza kai ta ɗanyi tare da cewa"Bakomai kawai bana Jin daɗi," Tana kai karshen maganarta, Jiki na kerma ta koma gefen gadonta, duk sunata kallonta, Haris yace"Yakamata Mu je mu zauna, kafin giants su kawo mana abinci," hibba tace"Yau bazamu motsa jiki ba"? Parveen tace"Sai mun ci abinci tukunna," Basu kai ga zuwa sun zauna ba, Sai ga Giants sun shigo kawo musu abinci, Bayan sun sauke abincin Jiki na rawa kowannansu Ya samu wuri ya zauna saman dining carpet, Suna tsaka da cin abincin Angel ta miƙe suka tambayeta Harta ƙoshi sun ga bata Ci dayawa ba, tace masu ta ƙoshi, gaba ɗaya sun lura da yanayinta, kamar bata Jin daɗi, ko bayan da suka kammala Cin abincin giants suka tafi, Agaban Gadon angel suka je suka tsaitsaya Suna kallonta, Ta kwanta idanuwanta na fuskantar ceilling, cikin nuna damuwa suka tambayeta ko lafiya tace musu babu komai su kwantar da hankalinsu, Badan sun yarda da maganarta ba suka ƙyaleta kowa ya koma saman gadon shi ya zauna, Yau ko motsa jikin basu samu sun yi ba, saboda canzawar da angel ta yi musu, tana daga kwance ta kasa kunne tana jin muryoyinsu suna fira, parveen tace"idan angel ta gudu damu, zuwa gidansu, Shikenan mun huta da ganin giants, Zamu sakata mu wahala, Kuma zamu dinga fita yawo, Wlh ni duk na ƙosa inga ya wajen kurkukun nan yake, Nasan zaiyi kyau sosai, kuma zaifi daɗi," Azeeza tace"kuma ta faɗa mana cewa daddynta zaiso mu kamar ya'yanshi, hada sauran ƴan uwanta ma, mu ma zamuyi rayuwa kamar kowa, " can kuma tajiyo muryar javed yana cewa"dama kun daina wannan mafarkin da bazai ta6a zama gaskiya ba, In banda abunku taya za'ai ku fita daga Cikin kurkukun nan? kuna tunanin Giants zasu Barku? haris yace"faɗa musu dai, Nima jinsu nake kawai, Ni bana so ma suna ƙwallafa rai akan son Yin rayuwa awaje, saboda suna wahalar da zuciyoyinsu ne, ita kanta angel ɗin da take Sanya musu rai, bata da hanyar da zata Iya ku6utar dasu" Hanna tace"Amma ae ta faɗa mana cewa, Idan muka dage da addu'a, muna kai kukan mu wurin Allah, Zai ji ƙanmu ya taimake mu, Mu fita cikin kurkukun" koda tayi wannan maganar sai haris Ya tuntsire da dariya tare da cewa"Taya kenan hakan zata Iya faruwa? Wannan fa ba gaskiya bane....." Bai ƙarasa maganar ba, sakamakon Tsawar da angel ta daka mashi, a yayin da take ƙoƙarin miƙewa daga saman gadonta, Hankalinsu duk ya dawo kanta, Harara ta wurga mashi tamkar ƙwayar idanuwanta zasu faɗo ƙasa, Muryarta da rauni tace"Ya isa haka haris! Bana so kana shiga hurumina, kuma Ka daina ƙaryata magana ta! Idan kai baka Yi imani da Allah ba, Su sunyi, Kuma in sha Allahu zamu samu mafita ne bi'iznillahi, ka zuba ido ka gani" Jinjina kai haris yae fuskarshi ɗauke da murmushin rainin wayau, yaso ya mayar mata da martani, Amma danish ya dakatar dashi ta hanyar yi mashi magana, gyaɗa kai ya yi tare da jan baki Ya yi shiru, Ɗakin Ya yi tsit babu mai magana, wuraren marece, Duk sun kwanta saman gadajensu, wasu sun fara bacci, yayin da wasu kuma sun lumshe idanuwansu ne badan suna jin bacci ba, Damuwar duniya ta ishi angel, Ga wani irin faɗuwar gaba da take ji, tarasa gane dalilin hakan, addu'o'i kawai take janyowa Acikin zuciyarta, Tana ji aranta kamar wani abune zai faru, wasa wasa suna kwancen nan har dare Ya ratsa hasken ɗakin Ya yi duhu, tun tana iya jiyo hirarsu suna faɗin har yanzu ba'a dawo da deeja ba, har tadaina Jin surutunsu alamun sunyi bacci, Aranta tace"ita kuma wannan Makauniyar rayuwar haka zata ƙare? Kullum muna ƙunshe a ɗaki Ɗaya tsawon shekara da shekaru, Gaskiya bazai yiyu ba, Nifa ina da burikan da nake son Cimmawa don haka bazan zauna in zuba ido ba, dole in nema ma kaina mafita, tana karasa zancen zucin nata, ta yunƙura ta sauko daga saman gadonta, Cikin duhu ta shiga laluban Fitilun ɗakin su, ko da ta ɗauko fitilar bata kunnata ba, saboda gudun kada Danish ya farka daga bacci Ya bi bayanta, Cikin sanɗa taci gaba da tafiya ko sautin tafiyarta baka Iya ji, tana shiga sashen toilet ɗin Abakin door ta kunna fitilar, Ta buɗe toilet ta shiga ta zura jamlock, A ƙasa ta sauke fitilar, Ta ɗauko bokitin ƙarfen nan, ta Ajiye shi jikin bangon da tagar Nan take, saboda ta sa mu tsawonta yakai, Daddagewa ta yi tare da haye saman bokitin, tana yunƙurin kai hannu ta zame glass ɗin muryar danish Ta ratsa kunnata "Angel!" ras taji gabanta Ya faɗi, gaba ɗaya jikinta ya hau kerma, tsantsar 6acin rai ne ya bayyana akan fuskarta, a tsiyace ta juya saitin Da yake tana kallonshi, A tsakiyar toilet ɗin taganshi A tsaye, tun kafin yai magana ta riga shi cewa"kai nifa nagaji, Don me zaka dinga faɗo mini cikin toilet? Bayan ka yi mini alƙawarin cewa bazaka ƙara shigowa ba? Cikin sanyin murya yace"Ina Bibiyarki ne saboda sanin ƙudirin da kike dashi na son shiga Cikin prison, wanda yin hakan zai iya haddasa mana shiga mummunan haɗari, " Har saida taji gabanta Ya faɗi, jin abunda yace, Da mamaki tace"Oh dama kasan abunda nake son yi kenan? Taya akai ka sani? "kawai naji araina ne, kina son ki dura ta tagar, ko last time dana Sauke maki glass, Ban yarda da abunda kika faɗa mini ba, na cewa bakya son kallon glass yana affecting ɗinki, da ace dagaske ki ke, to da tun lokacin kin kawar da shi daga Cikin toilet ɗin amma sai baki yi hakan ba, " Ya ƙarasa maganar a yayin da yake tunkararta, Runtse ido ta ɗanyi tare da cizon lips ɗinta, Rai a6ace tace"wlh duk bala'in ka baka isa ka hana Ni yin abunda nayi niya ba, kada ka kuskura kace zaka ma dakatar dani, idan har ba so kake In yi maka Illa ba" "Angel Na roƙe ki kada ki je, Zaki jefa rayuwarki da tamu Cikin hatsari, Ba'ayi musu leƙen asiri, Ki fahimce, yafi muyi rayuwarmu Cikin duhu akan musan ainihin abunda ke faruwa acikin prison, amma daga ranar da kika haura tagar nan, xaki ja mana ne gaba ɗayan mu ne"... Tamkar zai fashe da kuka Yake yi mata magiya akan karta dura, A ƙarshe daya ga ta kafe tasa naci akan saita dura, ai kuwa da ƙarfi Ya sanya hannu ya janye bokitin da tahau sama, Gaba ɗaya ta tafi zata kife ƙasa da sauri ya sanya hannayenshi biyu Ya tarbo ta, ta faɗo saman jikin shi, Suka rubza ƙasa atare, kanshi ba ƙaramar buguwa yai ba, ita kuwa kamar jira take yi su faɗo aikuwa ta daddage ta dunƙule hannayenta, Ta shiga kai mashi bugu a ƙirjinshi, Ya yi shiru batare daya dakatar da ita ba, zuciya ce ta fusgeta, a karshe ta kifa kanta saman ƙirjinshi tana kuka tana faɗin"Ya rabu da ita taje, Ita ta gaji da rayuwar kulle, Bazata Iya jure azabtar da ƴan uwansu da ake Yi ba, " Haƙiƙa Danish yaji tausayinta, Sai dai bazai Iya barinta taje yin leƙen asirin ba, saboda shi ya fita wayau da hankali, Ya kuma san Abunda sai biyo baya, Idan har ta dura ta tagar nan, Tuntana yin kukan har tagaji tadaina muryarta ta disashe, Sai lokacin ya samu damar yunƙurawa Ya ɗago da ita a jikinshi, A saman kafaɗarshi ya kwanto da ita, ranƙwafa yayi tare dakai hannu ya ɗauki fitilar da tazo da ita, Ya juya ya fuce daga cikin toilet ɗin, Yana shiga ɗakinsu Ya kwantar da ita saman gadonta, Daga ƙasa ya ajiye fitilar hannun shi, Ya zauna daga gefenta yana kallon fuskarta, Wadda ta yi jaga jaga da hawaye, hannayenta ya ruƙo acikin nashi, ya soma lallashinta, ya ɗauki tsawon lokaci Amma ko kallo bai isheta ba, Sai da ya gaji don kanshi tukunna Ya ƙyaleta, Ya koma nashi gadon Ya kwanta, A daren ranar daƙyar bacci ya ɗauki angel, Ranar da Deeja ta Cika 4 days da aka ɗauketa, A daren Ranar Giant Ya dawo da ita, Babu wanda ya sani duk sunyi nisa a cikin baccin su, A tsakiyar ɗakinsu Giant Ya sauke ta, Baiwar Allah duk ta fita hayyacinta ta rame ta fige, kamar wadda aka ɗibi naman jikinta, kasancewar sun kunna fitilun ɗakin su, Hakan ya bata damar bin Cikin ɗakin, Bata nufi ko'ina ba sai bakin gadon angel, a gefe gadon ta zauna, fuskarta sharkaf da hawaye, hannu takai saman shimfiɗar angel ta ɗan bubbuga kafadarta, Ƙasa kasa da murya take ambaton sunanta don kada ta takura ma masu yin bacci, koda angel taji muryar deeja acikin baccinta, a matuƙar ruɗe ta yaye bargonta, muryarta na kerma tace"deeja! Dagaske kece? Ko dai mafarki nake yi," jinjina kai deeja tayi cikin shessheƙar kuka tace"its me angle, am back, Giant ne ya dawo dani, na same ku kuna bacci, bana so na tashi kowa shiyasa nazo wurinki, saboda akwai abunda nake son faɗa miki," Tun da angel taji haka, Sai ta yaye bargon dake a jikinta, Ta kalli fuskar deeja da kyau, Gaba ɗaya ta zabge Duk ta bushe, janyota tayi zuwa jikinta ta rungumeta sosai, kamar zata maida ta cikin cikinta, Tayi matuƙar yin kewarta, Sun ɗauki tsawon lokaci, Kafin angel ta raba jikinta daga na deeja tace"Ki faɗa mini menene? Deeja tace"za'a iya jin mu idan muka Yi magana anan, amma zan shiga toitet, sai ki biyo ni" angel ta amsa mata da toh, Miƙewa deeja ta yi jiki duk ba ƙwari ta shige toilet, angel ta miƙe ta bi bayanta, bayan sun shiga, deeja ta sanya jamlock ta datse ƙopar, ta juyo suka fuskanci juna ita da angel, "Faɗa mini menene kikeson Gaya mini? Duk na ƙagara inji" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"Angel yanzu na ƙara yarda da maganarki na cewa ana cutar da rayuwar mu, wani iko na angel, Duk da bakomai zan iya tunawa ba, Amma lokacin da giant ya tafi dani, ina Cikin hayyacina, Inata karanta addu'ar nan da kika koya mana acikin zuciyata, Har yakai ni wani part inda wasu jerin daƙuna suke, Bayan ya shiga dani ɗaya daga cikin su, duhu ya mamaye idanuwana, ban iya ganin komai sai dai biji biji nake gani, Har lokacin ban fita hayyaci na ba, Sai dai bana iya gani da kyau, Naga mutun shida wanda ba baƙaƙen kaya bane ajikinsu kalar na giants, naga launin Ja a ƙugunsu, angel daga nan ne na fita hayyacina, bansan me akayi mani ba, Sai dai naji ajikina an cutar da rayuwata, nayi kukan mutuwa, Na azabtu iya azabtuwa, " Deeja nakai karshen maganarta, Ta zube saman gwiwowinta, tare da fashewa da matsanancin kuka, kamar ranta zai fita, Hankalin angel yayi matuƙar tashi, duk da bata ji me mutun shiddan nan suka Yi mata ba, amma tana ji aranta cewa Lalata suke yi dasu, idan har zata iya tunawa, can lokacin baya,Ta ta6a yunƙurin guduwa daga islamiya zata je gida, Tazo giftawa ta ofishin head master ɗinsu, Tajiyo shessheƙar kuka, da kuma maganganun mutane, duk da ƙarancin shekarunta a time ɗin tana dab da shiga 11 years, Har zata wuce ta la6e ta kasa kunne tana sauraronsu, ɗaya daga Cikin ɗaliban makarantar ne aka samu wani malami yayi ma fyaɗe ya kuma cigaba da lalata da yarinyar da bazata wuci shekara sha bakwai ba batare da sanin kowa ba, idan tazo islamiya aka tashi sai ya ɗauketa saman mashine ɗinshi zuwa gidanshi da ya gina da niyar yin aure, amma sai ya 6uge dakai yara yana 6ata musu rayuwa tare da yi musu barazana, Mahafiyar yarinyar ce ta fara lura da canzawarta, Bata iya tafiya ƙafafuwanta sun gwame, ga yawan yin amai, da su ka kaita asibiti likita ya tabbatar musu cewa ƴarsu Cikine da ita, iyayen yarinyar sun shiga damuwa, bayan sun baro asibiti sun dawo gida, mahaifiyar yarinyar ta ɗauko wuƙa ta ɗaura akan wuyan yarinyar tayi mata barazana akan ta faɗa musu wa yake yin lalata da ita har ta samu ciki, in ba haka ba zata kashe ta, atsananin tsorace yarinyar ta faɗa musu cewa malaninsu ne na islamiya, Koda jin haka sai suka tasa ƙeyarta gaba suka zo makarantar don su tabbatar da abunda ta faɗa musu, A lokacin angel bata fahimci komai ba, amma ta naɗi komai a acikin kanta, sai yanzu da Deeja ke faɗa mata wannan maganar ta soma tariyo abunda ya faru da ɗalibar nan ta makarantar islamiyarsu, duk da bata da tabbaci akan hakan amma tana zargin Suma lalatar ake yi dasu, ' Zuƙunnawa ta yi agaban deeja, Ta sanya hannayenta biyu ta rungumota ajikinta, Lokaci ɗaya ta fashe da matsanancin kuka tamkar ranta zai fita, itama deejan kuka take yi sosai, ta ƙanƙame angel da hannayenta, Abun da ciwo idan har ya tabbata cewa lalata ake yi dasu saboda rashin imani kuma a lokacin da suke Yi jinin al'ada, 😭😭😭 *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna suna ta kuka, Sai da suka yi mai isar su tukunna kowa Ya yi shiru, ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba, Muryar deeja a disashe tace"Na gaji da irin wannan rayuwar angel, bazan iya jure ganin ƴan uwana suna shan wahala ba, tun da ba yanzu suka fara ba, zasu ci gaba da zuwa suna ɗaukar mu ne ɗaya bayan ɗaya har sai sun ƙarar damu, nayi tunanin cewa gata ne ake nuna mana acikin kurkukun nan ashe ba haka bane, tsohuwa ta yi mana ƙarya da tace mana gidan marayu ne, za'a gatanta rayuwarmu, ta yaudare mu ta cuce mu, ba zamu ta6a yafe ma duk wanda yayi silar sadaukar damu zuwa cikin kurkukun nan ba......." katse maganar ta yi, batare da ta kaiga ƙarasa ta ba, saboda wani irin ƙululun baƙin ciki da ya tokare mata maƙoshinta, Sai lokacin angel ta iya buɗe baki tace"Dama ni nasani tun farkon zuwana kurkukun nan na gane cewa Ba orphanage home bane, Tun daga kan sunanshi, shiyasa nayi ta ƙoƙarin in fahimtar daku, saboda ni nayi rayuwar ƴanci da hankalina da wayau na, sihirin tsohuwa tamira bai yi tasiri a Jikina ba, shiyasa Tunina bai gushe ba, dama taya za'ae Gidan marayu ya kasance Kurkuku? Kuma ba shige ba fuce, Abinci sau ɗaya arana! Uniform kala ɗaya, sai dai idan munyi wanka mu cire mu wanke mu maida a jikin mu? Ga shi babu wani mai kula damu, Rayuwa muke yi kara zube, wlh ko dabbobin dake garari acikin daji sun fi mu ƴan ci, koba komai zasu yawata inda suke so, Kai ni da irin rayuwar nan ma ƙwara mutuwa, saboda ɗaci ne da ita, rayuwar kulle, babu wanda zaiso ya kasance cikin irin wannan makauniyar rayuwar, Ai ko maƙiyi na bazan yi ma fatan shigarta ba....." Sai lokacin angel ta raba jikinta daga na deeja, Idanuwan kowannan su ya yi jawur saboda tsabar kukan da suka sha, Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ni bana Jin ma zanyi tsawaicin kwana, Gani nake kamar nice gawar fari acikin mu...." kafin ta karasa maganar angel ta yi saurin sanya tafin hannunta ta toshe mata baki, tana girgira kai, Hawaye na bin fuskarta tace"in sha Allah ba ke bace gawar fari, wlh bana Yi mana fatan mu rasa rayuwar mu acikin kurkukun nan, ina matuƙar so inga kuma kunyi rayuwa kamar kowa, Idan ma mutuwar ce na ƙwammace ni in fara yinta, saboda bazan Juri rashin wani acikin ku ba, bakisan yarda nake jinku ba, akan ku bana jin tausayin kaina, saboda ku ne abun tausayi" Daƙyar takai ƙarshen maganarta, hawayen deeja duk sun wanke hannunta data rufe mata baki dashi, "Kowani ɗan adam da irin tashi ƙaddarar rayuwar, kowani bawa da irin ƙalubalan da yake fuskanta acikin rayuwarshi, Allah yana jarabtar bayin shi ba dan baya sonsu ba, face don ya jaraba imaninsu, babu wanda zaice maka 100% yana rayuwa Cikin jin daɗi, dole akwai ranakun farin ciki da kuma na baƙin Ciki, wani farkon rayuwarshi Jin daɗi ne, tsakiyar rayuwarshi wahala ce har zuwa ƙarshenta, wani kuma da farko zai ci baƙar wahala amma daga ƙarshe sai kaga Ya samu farin Ciki, Akwai wanda kuma Kaf rayuwar shi tun daga zuwanshi duniya Allah zai fara jarabtar shi, har zuwa ƙarshen rayuwar shi bazai ta6a jin daɗin duniya ba, zai fuskanci ƙalubale iri iri wanda idan Baida ƙarfin imani da tawakkali zai fidda rai da rahamar ubangiji ne, Zaiyi tunanin cewa ko Allah baiso na ne? At end har yakai ga tunanin salwantar da rayuwarshi don ya huta, wanda yin hakan kuma zai ƙara Jefa kanshi Cikin matsala ne, Kazo duniya a wahalce kuma ka koma a matsayin zero duka kayi asara, Amma idan kayi haƙuri ka miƙa lamurranka ga Allah subhana'hu wata'ala Koda baka ji daɗi anan ba, acan ana kyautata zaton zaka dace, akwai wanda kuma bai ta6a shan wahalar duniya ba, gatanci ta ko'ina, wahalarta kaɗan ya sani, in kaga 6acin ranshi to wani Ya rasa na kusa dashi, aduk halin da bawa ya tsinci kanshi Ya kasance mai godiyar Allah, Kafi wani, wani yafi ka, yanzu kamar rayuwar waɗannan bayin Allah, tunda suka zo duniya A garƙame suke kamar dabbobi, An tauye musu duk wani haƙƙinsu na rayuwa, basu son komai game da jin daɗin duniya ba, sun yi rayuwa acikin duhun jahilci, Basu son iyayensu ba, Basu son danginsu ba, su kansu basu Su wanene su ba, Haba jama'a, wannan rashin imanin har ina? A haka ake so su mutu su fuskanci mahaliccinsu, ai ƙwara wanda ke rayuwa acikin mutane yana fuskantar jarabawar rayuwa, Amma akwai imani azuciyarshi, Atlease Ya tsira da wannan idan yayi tawakkali, amma waɗannan bayin Allahn fa? Ba don zuwan angel acikin rayuwarsu ba da shikenan An kashe su da ransu an gama dasu, yakamata mu ƙara jin tsoron Allah acikin zukatanmu, mu kasance masu tawakkali, kuma mu kasance masu godiya ga Allah aduk halin da muka tsinci kanmu, tun da bamu rasa komai na rayuwa ba, ka kwana ka tashi da ranka da lafiyarka, ka je inda kake so, Ka ci mai kyau kasha mai kyau, ka sanya sutura mai kyau, kana a tare da iyayen ka ko babu su akwai danginka, kai idan ma babu dangin naka Allah Yana atare dakai, Zaka Iya rayuwa ko babu su, da daɗi da ba daɗi, Allah ya baka rai da lafiya, Amma sai kaga bawa yana Ƙorafi don ya rasa wani abu ƙalilan, ko angaza biya mashi buƙatarshi, dayawa gajan haƙuri kesa wasu harsu fara neman duniya ido rufe, Allah dai yasa mu dace, Shiyasa ake so mutun ya dinga ziyarta asibitoci da wuraren da faƙiran talakawa suke yin rayuwa, Kodan ya ƙara imani, Allah dai ya tsare mu ya kare mu daga faɗawa tarkon halaka, kada amanta adunga taya ƴan uwan mu addu'a waɗanda ke a hannun kidnappers da kuma ƴan boko haram, da matsafa, muna roƙon Allah ya kawo mana ƙarshen wannan masifar da muke fama da ita a ƙasarmu badan halin mu ba, Alfarmar Annabi muhammad (SAW) addu'a takobin mumini ce da ita ne kaɗai zamu Iya yaƙar su, tun da mu bamu da yadda zamuyi, waɗanda keda ikon Yin sun gaza, saboda rayuwar mu bata da mahimmanci awurinsu, takansu suke yi, wanda nayi imanin da ace yau hada ƴa'ƴansu aka ɗauka da anga tashin hankali, cikin ƴan awanni sai sun san yadda zasuyi an dawo musu dasu, Akwai dai ranar ƙin dillaci, ranar da dukiya ko ya'ya ko wani muƙami na duniya bazai amfane su da komai ba, A ranar zasu shaida cewa ALLAH ƊAYA NE. A hankali angel ta zame hannunta daga saman bakin deeja, "Deeja kodai in taimaka maki ki yi wanka? Naji jikin ki wani iri, daga gani baki jin daɗin shi" girgiza kai deeja tayi"a'a, bazan Iya yin wanka da ruwan sanyi ba, Jikina zai ƙara tsauri, ki barni kawai ahaka, " tsananin tausayinta ne ya ƙara kama angel. "To Mu je mu kwanta, ko kin samu ki yi bacci ki huta" shiru deeja ta ɗan yi batare data amsa mata ba, har sai da angel ta ƙara maimaita mata, tukunna ta buɗe baki tace"bazan iya tashi ba, ki kije ki tada su daga bacci, ki faɗa musu cewa an dawo dani, su zo mu gaisa," maganar deeja ta yi matuƙar girgiza angel sai taga kamar bankwana ne take so ta yi dasu, muryarta na kerma tace"amma meyasa? Idan baki iya tafiya ne, ni sai in ɗauke ki abayana in kai ki cikin ɗakin ki kwanta, In yaso gobe da safe sai ku gaisa da su" idanuwan deeja a marairaice take kallon fuskar angel, da wata irin raunatacciyar murya tace"dan Allah ki kira mini su in gansu, kada na mutu batare da nayi tozali da ƴan uwana ba," girgiza kai angel tayi cikin shessheƙar kuka tace"In..sha.. Allah ba zaki mutu ba, har sai mun fita daga cikin kurkukun nan, Na roƙe ki ki daina Yi mini maganar mutuwa, kina karya mini zuciyata, Kinsa Jikina duk ya yi sanyi" hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar deeja, idanuwanta sunyi jawur sosai, la66anta na kerma tace"dan Allah ki kira mini su mu gaisa, inaso inga ƴan uwana." Juya mata baya angel ta yi tare da cewa"Ki hau in kai ki cikin ɗakin, Sai in tada maki su ku yi magana" fashewa deeja tayi da kuka tana faɗin"bana ce maki bazan Iya miƙewa ba, Kije ki kira mini su ko so kike saina mutu ne batare da nayi bankwana dasu ba"? Yanayin da tayi maganar yayi matuƙar girgiza angel, Hatta muryar deeja ta canza sosai, a ƙarshe ta sassauta muryarta tana yi mata magiya akan ta kira mata su, Muryar angel na rawa tace"shikenan ki jira dan Allah, yanzu zanje in tada su daga bacci kinji," Aruɗe ta yi maganar, ta miƙe da sauri tana tafiya tana waiwayon deeja, fargabarta kada ta mutu kafin ta dawo daga kiran nasu, bayan ta cire jamlock ɗin ƙopar da gudun gaske ta faɗo Cikin ɗakin har kusan tuntu6e ta yi, tun kafin ta ƙarasa cikin ɗakin ta dinga kwala musu kira, Haris danish, naufal hanna hibba batool yasmin ku tashi an dawo da deeja, da alama sunyi nauyin bacci babu wanda ya motsa, gaban gadajensu taje tana bubbuga ƙafafuwansu tare da cire musu bargunan da suka lullu6a dasu, Wannan karan muryarta da sauti mai ƙarfi take kwala musu kira, a matuƙar firgice kowannansu ya farka Yana faman Yin hama, Ba ta bari sun wartsake ba, tace musu"ku tashi muje toilet, deeja tana aciki, An dawo da ita, amma bata da ƙoshin lafiya, ita ce tace in kira mata ku, tana son ganinku" Jiki na rawa suka sauko daga saman gadajensu, Haris yafi kowa zumuɗi, shine agaba sai naufal da mubeen da danish, tare da javed, Matan kuma batool ce agaba sai su hanna hibba eve da su Parveen, Mutun ɗaya ce bata sauko daga saman gadonta ba, Azeeza amma ta farka tana ta kuka tana faɗin ita ba wanda zai kai ta wurin deeja, saboda anga bata da ido, har angel ta juya zata bi bayansu Batool sai kuma ta fasa jin muryar azeeza da sauri taje bakin gadonta ta ruƙo hannunta, tare da taimaka mata ta sauko daga saman gadonta, suka nufi toilet section ɗinsu, lokacin da kowannansu ya hallara acikin toilet ɗin da deeja take, hankalinsu Yayi matuƙar tashi, Ganin yadda jikinta ke ta kerma, wata irin zufa ce ke tsastsafo mata a jikinta, gaba ɗaya ta jiƙe sharkaf, a sukwane suka zuƙunna gabanta suka kewayeta, suna ambaton sunanta, hannu biyu haris ya sanya tare da tallabo fuskarta, daƙyar take iya buɗe idanuwanta da suka rune tana kallonsu, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin azabar da take ji ajikinta, muryar haris a ruɗe ya ambaci sunanta"deeja! ke ce kika koma haka? me ke damunki? kina iya ganinmu"? jinjina ma shi kai ta yi alamar eh, Azeeza dake ta kuka tana faɗin su nuna mata deeja, angel ta zuƙunnar da ita agaban deeja, Ta haɗa hannun azeeza dana deeja, Sosai deeja ta ƙanƙame hannun azeeza dake acikin nata, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanta"Azeeza"! Amsa mata tayi"na'am, deeja ashe an dawo mana dake muna ta bacci bamu sani ba, Mun yi missing ɗinki sosai, " shafa fuskar azeeza ta yi da hannunta, nan take azeeza ta ɗan zabura tana faɗin"Zafi hannunki deeja, baki da lafiya ko"? Bata amsa mata ba, sai dai binsu da take yi da kallo, matsawa batool ta yi daga gefenta ta ɗaura hannunta saman wuyan deeja, da sauri ta zame shi, jin wani irin zafi na fitar hayyaci, hankalin ta ya yi matukar tashi tace"Yakamata mu kira tsohuwa ta duba jikinta, kwata kwata babu alamun lafiya atattare da ita" haris yace"me tsohuwa zata Iya yi mata? Ai kawai ku taimaka mata ta watsa ruwa ajikinta, zata ji sauƙi," girgiza kai batool ta yi tare da cewa"bazaka gane ba, kwara a kira ta, tun da ita tafi mu sanin meke damunta" Angel ta lura dasu kowa yana tofa albarkacin bakin shi, amma banda Danish tunda suka shigo ya zuƙunna na ɗan wani lokaci sai kuma taga ya miƙe ya jingina bayanshi jikin bangon da deeja take a zukunne, ya goya hannayen shi saman ƙirjinshi, ya ɗaga kanshi sama idanuwanshi na fuskantar ceilling, tsabar haushin shi ne ya kamata, shi da yake amatsayin babba acikinsu yaƙi buɗe baki ya yi magana, Koda lallashin deeja ne yayi duba da irin halin da take aciki,' "Ko da ace kun kira tsohuwa, ba abunda zata Iya yi mini, nidai tunda na gan ku Alhamdulillah hakan ma ya wadatar" Deeja ce ta yi maganar, Hanna tace"pls ki tashi mu koma ɗaki ki kwanta," kallon hanna deeja ta yi, ƙarfin hali kawai take yi wurin yi musu magana"Ae bazan iya miƙewa ba, ƙafafuwana sun ruƙe," Juya mata baya haris yai tare da cewa"ki hau in goya ki, mu shiga" nan ma tace mishi bazata Iya motsawa ba,' lamarin yayi matuƙar girgiza su, jikinsu yayi mugun yin sanyi, Rubina tace"nidai zanje na kira tsohuwa ne" tana kai karshen maganarta, da sauri ta juya ta buɗe kopar toilet ɗin ta fuce, gudu gudu sauri sauri ta ƙarasa bakin ƙopar ɗakin tsohuwa, Tasa hannu ta kwankwasa ƙopar, kusan sau uku tana yin knocking, kafin ta samu tsohuwa ta buɗe mata ƙopar ɗakin, fitowa daga Ciki tayi hannunta ruƙe da sanda, ta ɗago da ido tana kallon rubina, Muryarta na rawa tace"dan Allah kizo ki taimaka mana an dawo da deeja amma jikinta babu sauƙi, ko iya miƙewa bata Yi," duƙar dakai ƙasa tsohuwa ta ɗanyi batare da tace komai ba, "dan Allah ki taimaka badan halinmu ba, kada mu rasa ƴar uwarmu," kafin tsohuwa ta ɗago da kanta sai ga su Javed da hibba hada yasmin sun fito daga Cikin sashen toilet dinsu, Hankalinsu duk atashe, ɗaya bayan ɗaya tsohuwa take binsu da kallo, Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin yi mata magiya akan tazo ta duba jikin deeja bata da lafiya, duk sun ruɗe bayin Allah, Girgiza kai tsohuwa ta ɗanyi fuskarta babu yabo ba fallasa tace"Ni da bani da amfani awurin ku?me kuma zan Iya yi maku? Ita uwar ta ku bata iya duba mata jikin nata ne"? Duk sun gane akan wa take magana wato angel, hibba tace"pls ki taimaka mana mu dai, ki manta da komai kizo ki duba Jikinta, mun gane kuskuren mu, bazamu ƙara ba" suna kai karshen maganarsu gaba ɗaya suka zube saman gwiwowinsu, suna roƙonta, Da buɗar bakinta sai cewa ta yi"zan iya taimakon ku, bisa sharaɗi ɗaya"! A ƙagare suka tambayeta menene tace"Su je su kira babarsu angel, tazo ta durƙusa agabanta ta roƙe ta, idan har ta yi hakan ita kuma zata duba lafiyar deejan su," da sauri suka miƙe da gudu suka nufi cikin toilet ɗin, a lokacin Deeja tana kwance saman ƙirjin haris, ya ƙanƙameta da hannayenshi, su angel duk suna a kewaye da ita, banda Maji daɗin gado daya ke atsaye kamar gunki, Yadda suka banko ƙopar toilet ɗinne yaja hankalinsu angel zuwa ga kallonsu, a fujajen suka faɗo, kusan atare suka haɗa murya wurin cewa"Ki zo angel, tsohuwa tace zata duba jikin deejan mu, amma dole sai kin durƙusa agabanta kin roƙe ta," Waro ido waje angel ta yi bakinta asake galala take kallonsu, lallai wannan tsohuwar ta ɗauko ta da zafi, taya zata ce saita durƙusa mata sannan zata duba lafiyar deeja? Mamaki ya hana ta motsa, magiya su javed suka dinga yi mata akan tazo suje ta duƙama tsohuwa, ko sun samu ta duba Jikin deeja" kasa tanka musu ta yi, Har saida batool tace"Angel ki taimaka ma rayuwar deeja, dan Allah badan halin mu ba, Kije ki roƙeta, wannan ce kaɗai damar da muke da ita, idan ba haka ba, deeja zata Iya mutuwa ki kalli yadda jikinta keta kerma yana zufa, duk ta fita hayyacinta" Batool na rufe baki azeeza ta fashe da kuka tana faɗin"Dan Allah angel kije kada mu rasa deejan mu, muna son ƴar uwar mu," ɗaya bayan ɗaya angel take kallonsu, a karshen ta tsayar da idanuwanta kan fuskar deeja dake kwance saman kirjin haris, la66anta sai kerma suke Yi, " ganin zata 6ata musu lokaci yasa suka nannaɗe hannuwan rigunansu, batayi wani aune ba, taji sun sunkuceta gaba ɗaya suka cuccu6ota suka juya da ita zuwa cikin ɗakin, tana ta kiciniyar ƙwace kanta amma sunƙi bari ta kubce musu, a haka suka shigo da ita cikin ɗakin, Tsohuwa na ganinsu ta saki wani irin bazawarin murmushi, dama tasan taurin kan angel da kafiyarta baza su ta6a bari ta tako da ƙafafunta zuwa gabanta ba, su javed na ƙarasowa inda tsohuwa take a tsaye suka saki angel ta faɗi ƙasa, Idon tsohuwa na akanta, ɗagowa ta yi fuskarta a hargitse, saboda tsabar masifa ta rufe idanuwanta tana zazzaga masu masifa tana faɗin don me zasu je su ɗauko ta? Ita fa bazata ta6a duƙama wannan tsohuwar najadun ba, mai kafirar zuciya wadda batasan Allah ba, 'ta inda take shiga bata nan take fita ba, Hankalinsu Rubina ya ƙara tashi ganin tana ƙoƙarin 6ata musu lokaci, ga deeja can tana jin jiki ita kuma da suka ɗauko donta taimaka masu gashi tazo tana ƙara Kwafsa musu, Zuƙunnawa su ka yi gaba ɗayansu saman gwiwowinsu suna roƙon angel akan ta taimake su badan su zata yi ba, ta dubi girman Allah ta roƙi tsohuwa taje ta duba lafiyar deejansu, " tsananin tausayinsu ne ya kama angel ganin hada hawaye akan fuskokinsu, saboda tsabar jaraba da jin takaici ta fashe da kuka tana faɗin"wayyo Allah na na shiga uku, yau zan aikata babban zunubi arayuwata, wlh na tsane ki kamar mutuwa ta, bansan ganinki, muguwa azzaluma, mai zuciya irinta kafiran farko, ke daga ganinki kin hada iri da jinsin fir'auna, saboda rashin imani taimakon ne bazaki iya yi mana ba, dole saina roƙe ki....." Bata ƙarasa maganar ba, yasmin ta sanya hannu biyu ta toshe mata baki, Cikin shessheƙar kuka tace"dan Allah angel kidaina, idan baxaki Iya ceton ran ƴar uwarmu ba, bai kamata kina ƙara fusata tsohuwa ba, so kike ta fasa taimakon mu" A tsiyace angel ta buge hannun yasmin data toshe mata baki dashi, idanuwanta sun yi jawur tamkar garwashin wuta, kallon kallon suka shiga yi ita da tsohuwa, "Lokaci Yana ƙure maki, idan har kika bari na juya na dogara sandata na koma Cikin ɗakina, To ku fidda rai da zan sake fitowa, wannan ce kaɗai damar da kuke da ita" tsohuwace tayi maganar, fuskarta ɗauke da shu'umin murmushi, mai nuna tsantsar farin Ciki, bata ta6a jin nishaɗi ba irin na yau, a hankali angel ta kawar da idonta daga kan fuskar tsohuwa ta mayar dasu kan fuskokinsu Javed da yasmin da hibba dake a zuƙunne saman gwiwowinsu, fuskarsu sharkaf da hawaye, gyaɗa kai kawai tayi Jiki ba kwari ta maida idonta ga tsohuwa, murya na kerma tace"zan roƙe ki ne bada son raina ba, dan haka kada ki yi tunanin kin ƙasƙantar dani ne, zanyi ne saboda waɗannan bayin Allahn, da kuma ƴar uwata dake acikin mawuyacin hali, Sannan kada ki yi tunanin kece zaki bata lafiya, Allah subhanahu wata'ala shine ya baki ikon yin hakan, domin kuwa saida yardar shi ne komai yake wakana" daƙyar takai karshen maganar ganin tsohuwa na ƙoƙarin juyawa ta koma Cikin ɗakinta, aikuwa da sauri angel ta ɗago ta zuƙunna saman gwiwowinta, Muryarta a disashe tace"Na roƙe ki dan Allah badan Ni ba, kije ki duba lafiyar Deeja" Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta fashe da ita, tamoji tamojin fuskarta har rawa suke yi, saboda tsabar yarda jikinta ke jijjiga, Angel kuwa wani irin ƙululun baƙin Cikine ya Turniƙe zuciyarta, har wani zazza6i taji ajikinta, Kusan atare su javed suka sauke ajiyar zuciya, saboda tsabar mugunta saida tsohuwa tasa angel ta maimaita maganar da tayi kusan sau uku tukunna tace"hakan ya yi mini, haƙiƙa yau na shaida irin ƙaunar da kike yi musu, ke ɗin uwace ta gari agare su, Ina ji araina cewa nan gaba har rayuwarki zaki Iya sadaukarwa akansu, don ba ƙaramin mamaki nayi ba ganin irin yadda kika sauke duk wani girman kai naki da kafiyarki wurin roƙo na akan lafiyar ƴarki deeja, Naji daɗi sosai Albarka zata tabbata akanki, ni kuma yau ta kasance ranar tarihi arayuwata, wato ranar da the most arrogant young lady in the world ta zuƙunna saman gwiwowinta domin ta roƙe ni......"Tsohuwa bata karasa maganarta ba, muryar angel Cikin fushi tace"Kinga surutun ya isa haka, tunda nayi maki abunda kike so, kema saiki biya ni" cike da shaƙiyanci tsohuwa tace"To gimbiya sarautar mata, Ai ko me kike so yau zanyi maki shi" Harara angel ta watsa mata kamar kwayar idanuwanta zasu faɗo kasa, Juyawa tsohuwa tayi zata koma cikin ɗakinta, muryar javed ta katse ta"deeja fa? Naga zaki koma Cikin ɗaki" batare da ta juyo ta kalle shi ba tace"Ku jira ni yanzu zan fito," Tsayawa su kayi suna jiran ta, Badajimawa ba sai ga tsohuwa ta fito hannunta ɗaya ruƙe da gorar ruwa ta gargajiya, miƙa ma javed tayi"Ruƙe mun nan, Mu je ciki ka nuna mini ita" da sauri javed ya sanya hannu biyu ya kar6i gorar ruwan, Suka shiga gaba tabi bayansu, angel dai bata bi su ba, A nan ƙasa ta kwanta zuciyarta na tafarfasa, Ji take yau ta bata kanta, tun da harta durƙusawa tsohuwa, Lokacin da suka shiga Cikin toilet ɗin, Tsohuwa ta basu umarnin su fita waje su jirata, haris dai bai yarda da ita ba, ya ƙyaleta ne kawai yaga iya gudun ruwanta, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga Cikin toilet ɗin, kafin javed ya fita sai da ya fara ajiye mata gorar ruwan a kasa, Tukunna yasa kai ya fuce, Cikin ɗakinsu suka koma Kowa zuciyarshi cike da zullumi, daga Cikin toilet ɗin suka soma Jin kukan deeja yadda kasan ana zare ranta, hankalinsu yai matuƙar tashi, gaba ɗaya suka gaza jurewa, Komawa su kayi Cikin sashen toilet, Koda suka je bakin ƙopar toilet ɗin a datse suka same shi, A dole suka zauna ƙasa zaman jiran fitowar tsohuwa, danish dai yana acikin ɗakinsu, bai bi bayansu ba, Saman gadonshi ya koma ya zauna, yana satar kallon angel dake kwance a ƙasa, Yana so yaje ya lallashe ta amma yana tsoron masifarta, don kuwa yau sai Allah, Taci ka ta batse, jira take kawai ta samu wanda zata huce haushinta akanshi,' wannan dalilin ne ya hana shi tunkararta, gudun kada yasha mari, Yau fa babu bacci, Dare ya koma musu tamkar rana, azeeza ce kaɗai take gyangyaɗin bacci, tana atsakankanin Batool da naufal, ta ɗan ɗaura kanta saman kafadar batool, ga dukkan alamu bacci take so ta yi, Naufal ne ya lura da ita, ruƙo hannunta yayi acikin nashi yace"azeeza tashi muje in raka ki cikin ɗaki ki kwanta, kada ki yi bacci anan" maƙe mashi kafaɗa tayi muryarta adisashe tace"ba yanzu zan kwanta ba, sai na jira an fito da deeja" Haris dake sauraronsu yace"naufal, Kada ka biye mata, pls ka ɗauke ta, ka kaita cikin ɗaki," rigima ta sanya musu, akan ita bazata je ta kwanta ba, sai ta ga deeja" Naufal bai tsaya sauraronta ba, ya sanya hannayenshi biyu ya sa6e ta, kamar wata ƴar baby haka ya ruƙota ya nufi Cikin ɗakin da ita, A saman gadonta ya kwantar da ita, tare da janyo bargonta dake a nannaɗe ya lullu6e mata jikinta, sai gashi ta yi shiru alamar bacci yai awon gaba da ita, ajiyar zuciya naufal ya sauke sai da ya fara ɗagowa ya kalli danish dake kishingiɗe saman gadonshi, Ya kuma kallon angel dake kwance a ƙasa, Ya ɗan girgiza kai, kafin Ya juya ya nufi Cikin sashen toilet ɗin, Lokacin da naufal ya shiga Ciki, Ya yi dai dai da buɗe ƙopar toilet da tsohuwa ta yi, aikuwa Jikinsu har 6ari yake yi wurin miƙewa tsaye idon kowa akan Ta, fitowa tayi hannunta ruƙe da sanda, Ta ɗago ta kallesu tace"Ina babar taku take Ne"? Suka haɗa baki wurin cewa"Tana acikin ɗaki" tsohuwa tace"Ku je kuce mata ta ɗauko bargo tazo, ta ɗauki diyarta, " amsa mata suka Yi da toh, Batool ce taje cikin ɗakin ta isar da saƙon zuwa ga angel, atare suka dawo hannun angel ruƙe da bargo, fuskarta a kumbure take hararar tsohuwa, Matsa mata Hanya tsohuwa tayi"Ki shiga Ki lullu6a mata shi ajikinta, ki fito da ita, " batare da ta amsa mata ba ta nufi ƙopar toilet ɗin ta shige Ciki, tsohuwa ta kalli javed tare da cewa"idan sun fito ka ɗauko mini gorar ruwan nan, ka biyo ni da ita" ya amsa mata da toh,'. Har ta fara tafiya ta dan juyo tana kallon fuskokinsu tace"Yakamata kuje ku kwanta, duk da ma naga kamar Lokacin ya ƙure garin ya waye" bata rufe baki ba, sai ga hasken ɗakin su Ya gauraye ko'ina, sun yi matuƙar yin mamaki, maganar tsohuwa ta tabbata, har gari ya waye basu sani ba, Atare suka haɗa baki wurin yi mata godiya, bata amsa musu ba sai cewa tayi"bani yakamata ku yi ma godiya ba, Babarku ce ta cancanci hakan," Fuskarta ɗauke da murmushi tayi maganar, tare da juyawa ta fuce daga cikin sashen toilet ɗin ta nufi dakinta, Fitar tsohuwa keda wuya, Sai ga angel ta fito hannunta ɗaya talla6e da deeja, da alama hada wanka tsohuwa tayi mata, uniform dinta na sanye a jikinta, Daga sama kuma bargon da angel ta lullu6a mata ne," wani irin farin Ciki ne Ya lullu6esu, Ganin ƴar uwarsu ta wartsake har tana iya taka kafarta, Sai faman sauke ajiyar zuciya suke Yi, wuce wa gaba angel ta yi suka bi bayansu, a bakin gadon deeja suka tsaitsaya, angel ta taimaka mata ta kwantar da ita saman gadonta, muryar deeja na ɗan kerma tace"Sanyi nake ji, ku ƙara mun wasu bargunan akaina, Ko jikina ya yi ɗumi," Da sauri kowannan su ya nufi gadon shi suka ɗauko bargunansu suka lullu6a mata ajikinta, Cikin ƙanƙanin Lokaci bacci ya yi awon gaba da ita, duƙawa angel tayi agaban gadon deeja daga gefe, ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata, bayan ta kammala ta ɗago da idanuwanta ta kalli su Batool dake a kewaye da ita, tace dasu suyi mata addu'a suma, kowa ya ɗan zuƙunno da kanshi saitin gadon, suka karanta abun da taɗan koya musu suka tofa mata, daga bisani haris yace dasu, Su koma su kwanta, ganin jiya basu samu isasshen bacci ba, ba musu suka amsa mashi da toh, kowannan su Ya wuce saman gadon shi, suka kwakkwanta, Ya rage saura haris dake a tsaye sai angel dake zuƙunne agaban gadon deeja, wuri ya samu gefen gadon deeja ya zauna, ba laifi yanzu hankalin shi ya ɗan kwanta, kallon angel yae tare da cewa"Ke fa? Baki jin bacci"? daƙyar ta iya ɗago da ido ta kalle shi, baiwar Allah damuwar duniya ta isheta, maganganun da deeja ta faɗa mata sune suke ta yi mata yawo a cikin kanta, "Dake nake magana" muryar haris ce ta kuma katse ta, batare data amsa mashi ba, ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadonta, tana isa ta haye sama ta kwanta, koda suka haɗa ido da danish dake kishingiɗe saman gadon shi, harara ta watsa mashi, kafin ta juya mashi baya, lumshe idanuwanshi yayi, zuciyarshi duk ba daɗi, saboda ya gane dalilin dayasa ta harare shi, dole taji haushin shi, saboda rashin ta6uka komai, shi kuma aganinshi indai baida maganin abu to baida amfani ya tsoma baki, shiyasa yake yin shiru, Amma har ga Allah yana matuƙar damuwa dasu, Yana jin tausayin ƴan uwanshi, Yana matuƙar ƙaunarsu fiye da kan shi, Rabi da kwatarsu tuni bacci Ya yi awon gaba dasu, mutun uku ne suka rage, Haris da tuni ya jima da komawa saman gadonshi, damuwar halin da deeja ke aciki ce ta hana shi runtsawa, Sai kuma Parveen da Yunwa ta addabe ta, ta lafe kwance saman gadonta sai juyi take yi, bayan ita kuma sai Angel wadda babu alamun zata runtsa, ita fa babban abunda ke damunta, irin takurawa rayuwarsu da ake yi, da kuma cutar dasu da ake yi, tana matuƙar jin tsoran tarasa wani acikinsu, tabbas zata ji raɗaɗin da yafi wanda taji a lokacin da ƙaddara ta rabata da daddynta, a yanzu tafi jinsu acikin zuciyarta fiye da kowa ma nata, yanzu bakomai yafi tsaya mata arai ba, face mutun shiddan nan da Deeja ta faɗa mata cewa ta gansu akanta, Shin su wanene su? Uban me suka aikata mata? Kodai su duka suka afka mata a lokaci ɗaya suka lalata rayuwarta? Innallahi wa'inna ilaihirraji'un, Allahumma Ajirni fil musibati...... wani irin ɗaci take ji acikin zuciyarta, idanuwanta suka cuccuko tab da ƙwalla, ta tausaya ma rayuwarsu, Idan har suka cigaba da kasancewa acikin kurkukun nan tabbas kuwa wata rana za'a nemi koda gawawwakinsu ne arasa, Ita dai bata fatan tarasa ranta acikinsa, kodan saboda ta gano su wanene suka assasa ƙungiyar da kuma waɗanda suka sadaukar dasu, Wannan alƙawarine ta ɗaukarwa kanta, sai sun ɗanɗani kuɗarsu, sai sunyi danasanin haihuwarsu da uwarsu ta yi acikin duniyar nan!!! Acikin zancen zucin da take yi, kwata kwata bata sanya tsohuwa aciki ba, duk da itama taji haushin abunda tayi mata ayau, amma ta ajiyeta gefe ɗaya, saboda ba ita bace agabanta, masu ƙungiyar kurkukun ƙaddara sune agabanta, da kuma waɗanda suka yi sacrificing ɗinsu. Lokacin da giants suka shigo kawo musu abinci, Mutun ɗaya ce ta Iya miƙewa, har zata tada su daga bacci, Haris yace ta ƙyalesu, taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko kwandon da suke ajiye abinci, ta kwaso musu aciki, idan suka farka zasu Ci, ta amsa mashi da toh, Bayan ta ɗauko food basket ɗin taje gaban jerin farantan da giants suka sauke musu, Ta zuƙunna ta ajiye kwandon gefe, ta sanya hannu ta yaye jan ƙyallen dake akan farantin farko, Steak and onions ne, Yankan nama manya manya sunji albasa da kayan ƙamshi, Hannu tasa ta dinga ɗebowa tana zubawa cikin kwandon, duka ta kwashe, Ta kuma buɗe faranti na biyu dake ɗauke da Snacks tare da madaidaicin bowl Na kayan marmari ta kwashe komai ta ɗaura akan naman, Faranti na ƙarshe Bottles waters ne, Miƙewa tayi tare da sanya hannu biyu ta ɗauke kwandon, Yayi nauyi, A agaban gadonta ta ajiye shi, ta koma domin kwaso robobin ruwa, dake a jere saman faranti na ƙarshe, Ta ruƙo su a hannayenta, Bayan ta kammala giants dake a tsaye suka raƙwafa atare suka ɗauke farantan, Tare da kama hanya suka fuce daga Cikin ɗakin, Zama parveen tayi agaban gadonta, ta ɗago ta kalli haris dake kallonta tace"Ba yanzu zaka Ci ba? Yana daga kwance saman gadonshi, Yace mata"sai sun farka zai ci" tace"Nima in jira sai sun farka"? Ba don taso ba ta faɗi hakan, Girgiza mata kai yai alamar a'a kafin yace"zaki iya ci mana, kici iya cinki, sauran da kika rage sai muci, ae nasan duk haɗamarki ba zaki iya lamushe abincin duka ba, ko rabi ma ba zaki iya tadawa ba" murmushine ya bayyana akan fuskar Parveen, jin abunda yace, bata ƙara tanka mashi ba, takai hannu tana zakulo naman tana turawa abaki, Sai da taci iya cinta, ta haɗa da snacks ɗin duka, har saida cikinta yayi ƙato, tukunna ta dakata da ci tana faman shafa ciki, bottle water ta ɗauka ta buɗe tasha ruwan, Data kammala ta tura kwandon ƙarƙashin gadonta, Haris yace"Salon da anjima idan kinga muna cin namu, kice kema zaki ci," dariya ta ɗanyi har dimple ɗinta na saman chin ɗinta ya lotsa, komawa saman gadonta ta yi tare da hayewa, da niyar itama ta samu baccin ya ɗauke ta, Basu suka tashi farkawa ba, sai da suka kwashe tsawon awanni suna bacci, daga bisani yunwa ta fara farkar dasu, ɗaya bayan ɗaya, kowa ya miƙe yana hamma, Haris yace suje su wanko bakinsu suzo suci abinci, Suka amsa mashi da toh, Kowa ya nufi toilet, bayan sun kammala wanke fuskokin suka zo suka zazzauna ya dauko musu kwandon abincin dake a karkashin gadon parveen, Ya ajiye musu atsakiyarsu, ba yadda baiyi da angel ba akan tazo taci abinci amma taƙiya saima ce mashi tayi ita bata jin yunwa su dai su ci, Komawa yayi bakin gadon danish a lokacin ya ɗan fara bacci, ya tada shi tare da cewa" ka taso mu ci abinci," danish yace"suje su ci baijin yunwa" lamarin yai mutuƙar ɗaurewa haris kai, su biyu sunce basu jin yunwa, Anya kuwa lafiya? Ko dai duk don saboda rashin lafiyar deeja ne yasa suka ƙi Cin abinci? A ƙarshe daya gaji dayi musu magana akan su taso sai ya ƙyale su, ya koma wurin dasu batool suke a zazzaune shima ya zauna, Suka tsoma hannayansu suna Cin abincin, Ba duka suka cinye ba, Sai da yace su rage ma Deeja idan ta farka, Sai kuma Angel da danish, Yankan nama shida shida suka ajiye ma kowannan su, Sai fruits, banda snacks duka suka cinye shi, Sun dai ajiye musu bottle water Biyu, bayan sun kammala suka ajiye musu nasu a karkashin gadon batool, Wuraren marece, Deeja ta farka muryar ta a disashe take faɗin, Ruwa zata sha, ƙishi take ji, da sauri haris Yaje ya ɗauko robar ruwa cikin wanda suka ajiye musu, Ya koma gefen gadonta ya zauna yana kallonta a lokacin ta yaye bargunan da suka lullu6a mata, daƙyar ta yunƙura ta miƙe zaune ta ɗan jingina bayanta jikin bango, Yadda kasan fatalwa, tayi haske ga rama, ƙashin wuyanta duk ya fito 6aro 6aro jikin fatarta, Gashin kanta kuwa duk ya hargitse, Baiwar Allah daga gani ba ƙaramin Jiki taji ba. *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ ************************** "Sannu deeja ya jikin naki" ya yi maganar tare da buɗe murfin robar ruwan ya kwafa mata baki, Hannu bibbiyu tasa ta tallabe hannanyenshi dake a ruƙe da robar, saboda tsabar yadda take shan ruwa kana Iya jin sautin throat ɗinta kwat kwat! Har sai da yace mata tasha a hankali kada ta shaƙe, janye robar ta yi da hannunta alamar ta ƙoshi, Sai lokacin ta samu damar ƙare mashi kallo, su batool dake a zazzaune saman gadajensu suna yin fira, Ganin deeja ta farka yasa suka dawo bakin gadonta, wasu suka zauna wasu kuma suka tsaya atsaye, A hankali take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Ba ƙaramin daɗi taji ba, irin yadda suka nuna mata kulawa, sai dai a yayin da take kallonsu, wani irin tausayin kansu ne ya kamata, domin kuwa tasan ƙarshen su yana dab da zuwa, a yanzu bakowa tafi jimawa ba face waɗanda ba'a ta6a ɗauka acikinsu ba, musamman azeeza da tafi kowa rauni acikinsu, gata ƴar ƙarama duk da ba shekaru suka fita ba, amma babu alamun girma atattare da ita, saboda rashin tsawonta, idan suka miƙe tsaye ko kafaɗarsu bata kai ba, farat ɗaya ka kalleta sai ka yi hasashen shekararta Goma, saboda ƙarantar jikinta, tana Cikin yin zancen zucin nan muryar batool ta katse ta da cewa"deeja me kike tunani muna ta yi maki magana tun ɗazu amma kin yi shiru baki ce komai ba, ina fata kina lapiya," ajiyar zuciya ta ɗan sauke, still idonta na akan azeeza data zauna gefen gadonta ita dasu Yasmin, haɗa baki suka yi wurin yi mata ya jiki ta amsa musu da cewa"Alhamdulillah Jiki da sauƙi, Naji daɗi sosai da irin kulawar da kuka bani, Ina matuƙar alfahari da ku ƴan uwana nakaina" Murmushi suka saki gaba ɗayansu, ta mayar da idonta kan haris dake kallonta, ta lura da irin damuwar da ya yi akanta, "Lokacin da aka tafi dani, haris ya iya Cin abinci kuwa"? da zolaya tayi maganar, gaba ɗaya suka yi dariya, yasmin tace"ae tunda aka ɗauke ki, ya gaza samun natsuwa, idan ya kwanta saman gadonshi idanuwanshi na fuskantar ceilling sai ya ɗauki tsawon lokaci bai tashi ba, wata'ƙil hoton fuskarki yake gani" Harara haris ya watsa ma yasmin da tayi maganar, Kafin yace "Abunda ta faɗa ba ƙarya bane, Na damu dake sosai, Ko bacci nake yi sai nayi mafarkin ki, Bani kaɗai ba Kowa ya damu dake" duƙar dakai deeja ta yi hawaye suka cicciko idanuwanta, muryar azeeza ce ta ratsa kunnan ta"Sister deeja pls don't cry, muna cikin farin cikin samun sauƙin ki, kada ki karya mana zuciyoyin mu," azeeza na rufe baki, deeja ta karasa kifa kanta saman gwiwowin ƙafarta, sosai ta fashe da kuka, Sai faman lallashinta suke yi, ita bakomai ne yafi damunta ba, face tuna cewa wata rana fa dole wani ya mutu a cikin su, gashi sun shaƙu da juna, Allah kaɗai yasan raɗaɗin da zasu ji aranar da suka rasa wani acikin su, Haris ne yace dasu"kubarta ta huta, kowa yaje yayi wanka, zan kula da ita" kasa tafiya suka yi har saida ya maimaita musu maganar tukunna suka miƙe, azeeza hada bubbuga ƙafarta tana faɗin"wai shi yacika takura, yana ganin kamar yafi kowa girma, shine zai wani kore su" murmushi haris ya saki batare da ya mayar mata da martanin ba, bayan sun bar bakin gadon deeja, suka nufi toilets domin yin wanka, hannunshi ɗaya ya ɗaura asaman bayan deeja yana ɗan bubbuga shi cikin sigar lallashi yake yi mata magana"its ok my lovely sis, kukan ya isa haka, ki daina pls kina ƙara ma kanki ciwo, kuma kina sanya mu cikin damuwa" Sai lokacin deeja ta ɗago da idanuwanta sunyi jawur da su, yadda kasan na mashayin giya, kallon shi kawai take yi kamar yarda shima yake kallonta, matsawa yaɗan yi dab da ita, ya sanya hannunshi ya ruƙo arm ɗinta tare da janyo da ita, ta kwanto saman kafaɗarshi, lallashinta yaci gaba da yi har saida ta daina yin kukan, Cikin sanyin murya tace"Danish baizo ya duba jiki na ba, naga fuskar kowa amma banda tashi, meyasa"? Girgiza kai haris ya ɗanyi dama saida ranshi ya bashi cewar saita yi magana akan danish, Yaji haushi da takaicin irin halin ko'in kulan da danish yake nuna musu, duk da yasan yana yi badan baya ƙaunarsu ba ne, Amma aduk lokacin da basu jin daɗi zaiyi wuya yaja su ajiki, har ƙwara Azeeza, itama ɗin ya lura don yana mata kallon ƙaramar halitta ne shiyasa yake damuwa da ita sosai, muryar deeja ce ta kuma katse shi"haris naji ka yi shiru? Ko dai danish bai yi farin ciki da dawowata ba ne?"da sauri yace"A'a, Ke ce baki ganshi ba, danish ya damu dake, ko adaren jiya da angel tazo tada mu daga bacci, hada shi muka shigo cikin toilet ɗin," Deeja tace"Amma shi bai jani ajiki ba, kamar yadda kayi" runtse ido haris ya ɗanyi kafin ya buɗesu a hankali yace"ki yi haƙuri yanzu bacci yake yi, amma ina da tabbacin zuwa anjima idan ya farka zaizo da kanshi ya duba jikin ƴar uwarshi" ta6e baki ta ɗanyi tare da cewa"da kamar wuya" ruƙe hannunta haris yai acikin nashi yace"Akwai steak da muka ajiye maku tare da fruits in ɗauko maki ki ci" yayi mata maganar ne don ya kawar mata da zancen danish, ɗago da kanta ta ɗanyi daga saman kafaɗarshi tace"Anya zan iya ci, baki na babu daɗi, amma ina jin yunwa aciki na" "Don't worry ur self xan taimaka maki ki ci shi" yakai karshen maganar, tare da miƙewa daga saman gadonta, Ya juya ya nufi gadon batool dake gefen na Danish, yana kwance sai baccin shi yake sha hankali kwance, guntun tsoki haris yaja ji yake kamar yaje saman gadonshi ya shaƙon wuyanshi, Bayan ya ɗauko kwandon ƙarƙarshen gadon batool, Ya juya ya koma gefen gadon deeja, a tsakankaninsu ya ɗaura basket ɗin, Deeja sai kallon shi take yi don ba ƙaramin burgeta yake yi ba, saboda irin yarda yake nuna damuwarshi akanta, "Angel ta yi bacci ne"? Yace"I don't think so, Kinsan jiya ranta ya 6aci sosai, saboda tsohuwa tace bazata duba lafiyar jikin ki ba, har sai ta durƙusa agabanta ta roƙe ta, Inaga shiyasa ta lafe saman gado ta rufe ido, amma ba bacci take yi ba" juyawa deeja tayi tare da kallon gadon danish dana angel, duk suna kwance abunsu, kafin ta juyo da kanta tana fuskantar haris dake miƙo mata yankan Nama, buɗe baki tayi ya tura mata aciki, tasa hannu ta dafe tana Ci, sai da ta kammala taunewa tace"Haris, naji daɗin abunda angel tayi saboda Ni, farkon zuwanta prison din nan, Nayi tsammanin bata ƙaunata, duk da a lokacin Mune muka fara nuna mata ƙiyayya, Amma yanzu na gane kuskure na, domin kuwa angel tana matuƙar son mu sosai, kuma ita ɗin Alkhairi ce agare mu," jinjina kai haris ya ɗanyi, tare da cewa"Nima na fahimci hakan, yanzu dai ki maida hankali ki ƙarasa cinye naman kisha fruit ɗin sai ki kwanta, ki ƙara hutawa" murmushi tasakar mashi, shima ya mayar mata da martani, A tsanake yaci gaba da bata Naman tana ci, bayan ta kammala tasha fruit ɗin ta kwanta saman mattress ɗin, Ya lullu6a mata bargo ajikinta, baisan ya zai ƙare dasu angel ba idan suka farka suna Jin yunwa, ganin deeja tana Ci yasa ya ƙara yankan nama Shida Cikin nasu Ya haɗa mata, kuma duka ta cinye shi, wanda ya rage acikin kwandon yanka shida ne na mutun ɗaya sai dai su raba uku uku ita da danish, Sai apple guda ɗaya, ayaba biyu, ɗauke basket ɗin yae daga saman gadon deeja, Yaje ya tura shi ƙarƙashin gadon batool, A lokacin duk sun fito daga wanka, ba ƙaramin daɗin jikinsu suka Ji ba, a tsakiyar ɗakin nasu suka hallara, Hannah ce ta shirya musu wasan da zasu Yi, Angel dake kwance sautin hayaniyarsu duk ya cika mata kunnuwanta, pillow ta sanya saman kanta ta toshe kunnuwanta, Ƙasa ƙasa take jin hayaniyar ta ɗan ragu, wani irin baccine yayi awon gaba da ita batare da ta shirya yin shi ba, su batool sunsha wasansu, har sai da dare yayi hasken ɗakin ya ɗauke sannan kowa ya koma saman gadonshi ya kwanta, Batare da sun kunna fitilun ɗakinsu ba, yayi duhu sosai, Har time ɗin bacci bai ɗauke su ba, fira suka soma yi a tsakaninsu kowa yana daga kwance saman gadon shi, Batool ce ta fara cewa"kun lura da angel duk yinin yau bata sauko daga saman gadonta ba" Haris yace"Kije ki tada ta mana" muryarta ƙasa ƙasa tace"So kake in jama kaina, ae tun ɗazu naso inje in lallashe ta, amma fargaba ta hana ni, kasan halinta, zata iya sauke fushinta akaina"Hanna tace"nima abunda ya hanani tunkararta kenan, kada in sha mari" Gaba ɗaya suka tuntsire da dariya, Javed yace"gaskiya banji daɗin abunda tsohuwa ta sanyata tayi ba, kawai don ba yadda zamuyi ne shiyasa muka tursasa mata akan ta durƙusa mata" Haris yace"nifa Haushin tsohuwa nake ji, don me zata ce dole sai angel ta durƙusa mata tukunna zata duba lafiyar deejan mu? Kenan koda ace mutuwa za ta yi bata iya duba ta ba, in har angel bata bi umarnin taba, sai dai tarasa ranta?Anya kuwa tsohuwa tana son mu? Eve tace"nima nafara kokwanto akanta, ae bata ƙaunar mu, shiyasa ran nan naƙi gaishe da ita," eve na rufe baki hibba tace"kuma hada cewa wai angel ce babar mu, baku ji me tace ba ɗazu ba da muna a wurin toilets, " waɗanda basu sani ba, suka tambayeta me tsohuwa tace, Nan hibba ta kwashe maganganun da su ka yi da ita, ta sanar musu, aikuwa sunsha dariya, batool tace"oh shiyasa naji tace aje akira babar mu tazo ta ɗauki ƴar ta, tsohuwa ta iya zolaya, gashi yau ta fusata mana Mamanmu,' rubina tace"Abunda ta faɗa gaskiya ne, angel itace babar mu, saboda tafi kowa damuwa da mu, bazan ta6a manta irin wahalar da ku kasha ba, ita dake batool wurin yin jinyarmu lokacin da giants suka dawo damu, kun nuna mana ƙauna, muna matuƙar alfahari daku,' azeeza tace"Da Batool da angel sune zasu zama iyayen mu idan muka fita daga Cikin prison ɗin nan, zasu bamu kyakkyawar kulawa" eve tace"Nifa ina tsoran ranar da zamu fita, mutanan dake awajen kurkukun nan zasu Iya su cutar damu, ko su kashe mu ma," parveen tace"waya faɗa maki? Ba angel tace mana gidan daddynta zamu zauna ba, ina ruwan mu da wasu mutane, ae ba akansu zamu zauna ba, dangin angel ne zasu taimake mu"da ƙwarin gwiwa parveen tayi maganar, Haris dai sai dariya yake yi musu, jin irin wasiƙar jakin da suke saƙawa, wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, azeeza tace"Na ƙosa Allah, zamu ji daɗin rayuwar mu, kowa zai sakata ya wala, muje inda muke so, ni dai kawai burina inga ga gidansu angel da kuma daddynta," "Amma fa ita kanta angel ɗin bata da tabbacin cewa daddyn nata yana araye koya mutu," acewar Batool, azeeza tace"Ae ko baya araye akwai auntynta aneelerh, da mommynta adama tace duk danginta ne kuma zasu ɗaukin nauyin ɗawainiya damu" sai lokacin javed ya tsoma baki, muryarshi da alamun bacci yace"pls, surutun ya isa haka, kun takura mana, dare fa yayi sosai, yakamata kowa yaja baki yayi shiru ku kwanta ku yi bacci, kun zauna kuna ta tsara shirme da shiririta, kuda fita daga Cikin kurkukun nan sai dai ata mafarki, amma badai zahiri ba" a ƙule ya ƙarasa maganar, shi kanshi javed ɗin da yayi maganar ba ƙaramin buri yake dashi ba akan su fita, kawai dai baison suna ƙwallafa rai ne, tun da babu ƙopar da zasu Iya guduwa acikin kurkukun, tun da javed yai musu magana babu wanda ya kuma cewa wani abu, tuni bacci ya fara ɗaukarsu, mutun ɗaya ce bata runtsa ba, Jira take suyi nisa dayin bacci ko ta samu ta lalla6a taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko Yankan naman da aka ajiye masu danish ta cinye, dama ta ƙware wurin iya satar ragowar abinci, lokacin da parveen ta tabbatar da cewar sun nutsa Cikin baccin su, Cikin sanɗa ta sauko daga saman gadonta, duk da duhun dake akwai hakan bai hanata gano inda gadon batool ya ke ba, daga gefen gadon ta zaƙunna tare da zura hannu cikin ƙarƙashin gadon ta janyo kwandon, har wani lumshe idanuwanta take yi tana shaƙar ƙamshin naman, tana yunƙurin tsoma hannu da niyar ta ɗauki tsoka ɗaya, kwatsam taji an damƙi wuyan rigarta ta baya, A matuƙar tsorace ta wage baki zata fasa ƙara, yayi saurin sanya tafin hannunshi ya toshe mata baki, ta yadda bazata iya yin ihun ba, Saboda tsabar tsoratar da tayi har saida ƴan hanjin Cikinta suka kaɗa, Jikinta sai kerma yake yi, shegen tsoro ne da ita, duk a tunaninta ɗaya daga Cikin aljanun da tsohuwa ta basu labarin akwaisu agidan kurkukun ne yazo ya damƙeta, zazzaro idanuwanta tayi waje, jikinta ya ɗau zafi, Cool voice ɗinshi ce ta ratsa kunnanta"its me, me kike yi agaban gadon batool? Ko kinzo ne ki sace mana steak ɗin mu da aka ajiye mana ne? wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya ta sauke jin muryar danish, Ta harzuƙa sosai ashe shine ya firgitar da ita, tayi matuƙar yin mamakin taya akai ya iya ganinta Cikin duhu? Kuma har yasan cewa tazo satar naman da aka ajiye musu ne, bayan basu da masaniyar sun ajiye musu, "Am talking to u, ki amsa mini, dama har yanzu baki daina bin abincin mutane kina satar musu ba"? Yawu ta haɗiya, tare da sanya hannayenta ta zame mashi hannunshi daya toshe mata baki dashi" ta juyo tana fuskantar inda yake atsaye, duhu ya hana ta ganshi dakyau, Muryarta kamar zata fashe da kuka tace"Ae zuwa nayi inga idan ya lalace, in zubda, tunda naga tun ɗazu da safe aka ajiye maku amma baku ci ba" muryarshi asake yace"A cikin Cikin ki zaki zubda shi ko?" shiru tayi bata bashi amsa mishi ba, "Maza ki wuce kije ki kwanta, tunkafin in yi wurgi dake" tana ƙunƙuni ta juya tana laluban hanya harta gano gadonta ta haye ta kwanta, zuciyarta duk ajagule, taso ace tacinye naman duka, ita uwar haɗama, kuma ba yunwa take ji ba, Bayan tafiyar parveen, danish ya duƙa inda ta ajiye kwandon, yana ƙoƙarin ruƙe handle ɗin yaji an damƙi hannunshi, har sai da ya ɗan ji bugun zuciya, duk da bai iya gane wacece ba, amma yaji aikin shi cewa ANGEL ce, itama parveen ɗazu daya Canko sunanta, saboda yasan halinta ne, Ya farka yana Jin yunwa, ɗazu yaji haris yana cewa arage musu nasu naman shiyasa ya yi tunanin akwai saura, wannan dalilin ne yasa shi saukowa daga saman gadon shi, ya nufi gadon batool donya duba yaga idan an rage musu nasu, Yana tunkaro bakin gadon yaji motsin mutun, nan take ranshi ya bashi cewar itace, dama halinta ne, Kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, gashi dai basu ganin juna dakyau, saboda duhun da ya mamaye idanuwansu, muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunanta"Angel" Muryarta a kausashe tace"Ni ce, sai me? Idan ma yankan naman nan kazo ka ɗauka sai dai ka haƙura kabar mini saboda nafi ka jin yunwa " yadda tai maganar babu sassauci, dagaske yunwa take ji sosai, kamar ta cinye ƴan hanjin Cikinta, shima kuma yunwar yake ji, cikin sanyin murya yace"me zai hana mu ci atare, sai mu raba" kamar tana ganin shi tace"A'a, kawai dai ka haƙura kabar mini, saboda ba isata zaiyi ba" "but why ɗazu baki ci ba? Da haris ya yi maki magana"? A harzuƙe tace"Saboda bana jin yunwa a lokacin yanzu kuma ina jinta, meyasa ma ka tambayeni? bata jira yabata amsa ba, ta kuma cewa"To kai meya hana ka cin naman ɗazu"? Tayi tambayar tana jiran jin amsarshi, sai da ya ɗanyi jim before yace"saboda ke, na damu da halin da kika shiga, naji kince ba zaki ci abinci ba, shiyasa nima naƙi ci, saboda bana so ki ji yunwar ke kaɗai," sam bata ji ɗaɗin maganarshi ba, saima haushin shi data ƙara ji, muryarta ƙasa ƙasa tace"Nifa baka burgeni komai zaka Yi, ko son ganinka ma bana yi, wlh haushinka nake ji kamar in nannaushi fuskarka, ka 6ata mini rai sosai, Kana nuna ka damu dani wannan duk abanza ne, tun da baka iya nuna damuwarka akan deeja, da aka dawo da ita daren jiya, kowa yana tofa albarkacin bakinsa amma kai kaja baki kayi shiru amatsayinka na babba acikin mu, har haris ma yafi ka sanin yakamata," Tana kai ƙarshen maganar, ta fusge kwandon daga hannunshi ta miƙe, cikin duhu ta nufi table dinsu ta ɗauko fitila ɗaya ta kunnata, A saman dining Carpet ta zauna, Ta ajiye kwandon agabanta, ita kuma fitilar ta ajiyeta a gefe, Zuciyarta duk ba daɗi, ita kanta bada son ranta take gaya mashi magana ba, daurewa kawai take yi, Daga inda yake a zuƙunne bakin gadon batool yana hangenta, jikin shi yayi mugun yin sanyi, duk sai yaji ya rasa kuzarinshi, tamkar ya fashe da kuka haka yake ji, baya son angel tana yin fushi da shi, hatta faɗan da take yi mashi baya so, dan ba yadda zai da ita ne, kasa jurewa yai ya yunƙura ya miƙe ya nufi saman dining carpet ɗin, Yana ƙarasawa ya zauna tare da lanƙwashe ƙafafuwanshi Yayi zaman cin tuwo kamar yadda tayi, Ya kasance suna fuskantar juna ita dashi, Ko kallo bai ishe ta ba, bakinta acunkushe da yankar naman data tura sai tauna take yi, duk in suka haɗa ido saita jefa mashi harara, bawan Allah miyan sai tsinkewa yake yi, yana so ya ɗauki naman yaci, sai dai ya kasa saboda gudun faɗan ta, Muryarshi arauna ce yace"pls angel, ki bari na ɗauka naci nima, koda fruit ɗinne, am serious yunwa nake ji" sai da ta kammala taunar naman dake abakinta tukunna tace"baka da ƙarfin da zaka ƙwata ne? Wai kai wani irin namiji ne? Mace kake marairaice ma fuska? duƙar da idanuwanshi ƙasa ya yi batare daya tanka mata ba, dogon tsoki taja, takai hannu ta ƙara ɗaukar yankan naman ta tura abaki tana ci, Sai da ya rage saura biyu, tace mashi"in kaga dama ka ɗauka kaci," tayi maganar tana daukar fruits din ciki tana sha" muryarshi na rawa yace"bazan ci ba, saboda me zaki dinga yi mini faɗa? Nifa haka rayuwata take, ki ƙyale ni mana, bana jin daɗin yadda kike kushe ni," Ranshi amatuƙar 6ace ya miƙe, Ya juya ya nufi gadonshi ya haye ya kwanta, Sai bayan daya tafi, Jikinta yayi sanyi, daƙyar ta iya shan fruits ɗin, idanuwanta suka Cicciko tab kwalla, yunƙura ta yi tare da miƙewa ta ɗan ranƙwafa ta ɗauki fitilar ahannu ɗaya, yayin da ɗayan hannun kuma ta ruƙe handle na kwandon, wurin gadon shi ta nufa, daga gefe ta ajiye fitilar tare da kwandon, idanuwanta na akan gefen fuskarshi, ya ƙanƙame pillow aƙirjinshi, jikin shi har wani kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki, Zuciyarta ce ta dinga tunzurata akan kada ta kuskura tace zata lallashe shi ta ƙyale shi wata'kil yayi hankali, gani take ma idan taci gaba da lallashin shi zai ƙara lalacewa ne, ƙwara ta koya mishi hankali, jinjina kai ta ɗanyi alamar gamsuwa da shawarar da zuciyarta ta bata, "Idan kaga dama ka tashi ka ɗauki naman kaci, idan kuma baka ci ba, matsalarka ce" Takarasa maganar tare da watsa hannayenta, Irin bata damu din nan ba, wuce wa tayi zawa gaban table ta ƙara ɗauko wata fitilar ta kunna ta, kaitsaye ta nufi gadon deeja, domin ta yi mata yaji ƙi, tun ɗazu da safe take ta son taje wurinta amma damuwa ta hanata, zuciyarta tayi mata nauyi a ƙirjinta, shiyasa ta tagaza tashi daga saman gadon ta yi kwanciyarta, Daga gefen gadon deeja ta zauna, tana haska fuskarta da fitilar hannunta, da alama tayi nisa acikin baccinta, har cikin zuciyarta taji daɗin yadda deeja ta samu sauƙi, don jiyan nan zuciyarta ba ƙaramar karaya tayi ba, harta fara fidda ran da zata rayu, sai gashi Allah ya taimake su, deeja ta wartsake, a hankali ta ɗaura yatsun hannunta saman fuskar deeja ta ɗan shafata, kafin ta soma karanto addu'o'i tana tottofa mata, "Bazan tashe ki daga bacci ba My lovely sis, gobe in sha Allah, idan kika farka daga bacci zanzo in yi maki ya jiki, Allah ya ƙara maki Lafiya, " janye hannunta tayi daga kan fuskar deeja ta mayar dashi saman sumar kanta, dake a hargitse duk ta yamutse babu gyara, aranta ta ayyana cewa, idan deeja ta samu lafiya sosai jikinta yae kyau zata gyara mata gashin kanta, ta kuma yi mata kalaba, kalar tasu azeeza, sauƙin ma ita gashin nata bai kai nasu tsayi da yawa ba, ya dai sauko har saman kafaɗarta, baƙi wulik, kamar na ɗiyar roba, Ta jima zaune tana kallon deeja, daga bisani ta miƙe hannunta ruƙe da fitilar tabi gadon kowannan su ta tottofesu da addu'o'i, lokacin da ta dawo zata wuce gadonta, Sai da ta saci kallon shimfiɗar danish, Still bai ɗauki naman shi yaci ba, duk sai taji ba daɗi, Duk yinin yau baici komai ba, ko ruwa bata tunanin yasha mutun sai kace aljani, anya kuwa zata biye mashi, kodai taje ta lallashe shi ya tashi yaci? A ƙasan gadonta ta ajiye fitilar hannunta, wurin ya ɗanyi haske hada ƙarin ɗayar fitilar dake a kusa da gadon danish, daga Gefen gadonta ta zauna tana kallon bayanshi, still babu alamun yayi bacci, yatsun ƙafarshi basu daina yin kerma ba, Zuciyar imani ce ta zo mata, ta miƙe taku ɗaya biyu, ta zuƙunna abankin gadon shi, Cikin sanyin murya ta ambaci sunanshi"Danish" shiru bai amsa mata ba, "Fushi kake yi da ni, saboda kawai na faɗi gaskiya," ta ɗanyi maganar tana hararar bayanshi, "Its ok komai ya wuce, bazan ƙara ba, pls ka tashi ka ci naman nan kasha fruit din idan ma baka Iya Ci da hannunka sai in baka abaki, ba wani abu bane, ni kawai bana so ne ka kwana da yunwa, dama ka faɗa mini cewa saboda ni ne baka Ci abinci ba, To yanzu ni naci kaima saika tashi kaci, ko ba haka ba My man"? Bakinta ƙumshe da dariya tayi maganar, babu alamun zai tanka mata, Cikin zolaya tace"dama ance mutun mai haƙuri bai iya zuciya ba, yau na tabbatar da hakan, danish yayi fushi da angelar shi," babu irin lallashin da bata yi mashi ba, amma yaƙi tanka mata a ƙarshe ranta ya 6aci a fusace tace"Kai ni fa ko daddyna bana zama in lallashe shi kamar yadda nake yi maka, don ma ka samu ina kula ka shine kake wani shamin ƙamshi, to shikenan, Nasan me zanyi, Zanje ne kawai in dura tagar nan ta cikin toilet, kome zai faru ya faru, " tana kai ƙarshen maganar, ta miƙe da sauri ta ɗauki fitilar dage ƙasa gefen gadonshi, Ta nufi sashen makewayinsu har ta kusa kaiwa bakin ƙopar shiga, Kamar walƙiya taganshi agabanta tsaye yana faman lumshe idanuwanshi, doguwar sumar kanshi duk ta yamutse, Tsananin mamaki ne ya kamata, da sauri ta ɗan juya ta kalli gadon shi donta tabbatar idan shine dagaske, bata ga kowa ba, sai taga kamar 6acewa ya yi daga saman gadonshi ya faɗo gabanta, Kafin ta yi mashi magana ya riga ta cewa"zan ci shi kenan ko"? Ɗaga kai tayi alamar eh, ya ruko hannunta acikin nashi yaja ta suka koma Cikin ɗakin, a gefen gadonshi ya zauna, Suna fuskantar juna shi da angel, tana azaune saman nata gadon, ta tsareshi da ido tana jiranshi ya kammala Ci, kwandon Ya dauka ya ɗaura shi saman laps dinshi, A tsanake ya kai hannu ciki ya ɗauki yankan nama yana ci, Bayan ya gama taune shi duka, Ya ɗauki sauran 6allin apple data rage mashi yakai baki yana gatsa, jefi jefi yakan ɗan ɗago ya saci kallonta, Ko uwarsa Albarka yadda ta tsare shi da ido, "Zaka sha ruwa"? Ɗaga mata kai yayi alamar eh, ta miƙe tsaye sai da tafara ɗaukar kwandon, Kafin ta nufi gadon batool, A ƙarƙashi ta tura kwandon ta ɗauko mishi robar ruwa guda ɗaya, Ta dawo ta miƙa mashi, yasa hannu ya kar6a ta koma saman gadonta ta kwanta tana facing ɗinshi, Buɗe murfin bottle ɗin yayi tare da kwafata abakin sa, kusan rabi ya sha, bayan ya gama shan ruwan, ya maida murfin bottle ɗin ya ajiye ta daga ƙasa, Sannan ya gyara kwanciyarshi, suna fuskantar juna, kallan ƙurulla suka shiga yi ma junansu, bakomai take tunawa ba, face yadda ya sha gabanta ɗazu saboda tace zata dura tagar nan, tarasa gane dalilin dayasa baison tasan komai dangane da kurkukun, Ta fahimci cewa danish yasan komai, shiyasa yake lalla6ata don kada ta gani taja musu wata matsalar, Abunda kuma bazai ta6a yiyiyuwa bane, Da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba da ita, shima danish ɗin tuni bacci ya ɗauke shi, A washe garin ranar, kafin kowa ya farka daga bacci, batool ce tafara tashi tana miƙa tare da Yin hamma, ta sauko daga saman gadonta, cikin sauri ta nufi toilet saboda wani irin fitsari daya matseta, Ya ɗaure mata mararta, hada ɗan gudunta wurin shiga toilet, batare data yi locking door din ba, hannayenta ta sanya wurin zame wandon jikinta ta zuƙunna tana Yin shi, bayan ta kammala ta kunna fanfo ta yi tsarki, Ajiyar zuciya ta sauke tare da miƙewa tsaye tana gyara wandon Jikinta, kafin ta nufi ƙopar fita, harta miƙa hannu zata buɗe sai ga azeeza ta faɗo cikin toilet ɗin. jikinta sai kerma yake yi, batool tace"lafiyarki kuwa kika faɗo mini Cikin toilet ba neman excuse? Batare da azeeza ta kalli batool ba tace"ke dallah fitsari ne ya matse ni, ni ina nasan da mutun a ciki, " tana faɗin hakan ta wuce cikin toilet ɗin, girgiza kai batool tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta fito daga waje, taja mata ƙopar ta rufe, tana ƙoƙarin shiga cikin ɗakinsu, Tajiyo muryar azeeza daga Cikin toilet tana kwala mata kira na fitar hayyaci, da sauri ta koma ta nufi ƙopar toilet ɗin, Fitowa daga Ciki azeeza tayi idanuwanta azazzare hannunta dafe da saitin ƙirjinta tace"Batool, naga ɗigon jini a cikin toilet wurin magudaji ke ce kika zubda shi"? Wata irin mummunar faɗuwar gaba ce tazo ma batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke, amatuƙar ruɗe tace"Bani bace, sai dai ko kece da kika shiga ciki yanzu, saboda ni har na fito banga wani ɗigon jini ba"aruɗe azeeza tace"Wlh bani bace, Ae ni yanzu na shiga, Ko tsugunnawa ban kaiga yi ba, naga jinin, hakan na nufin daga Jikin ki yake, " a tsiwace batool tace"Nifa bani bace na zubda shi ba, wlh bani bace" tuni hawaye sun wanke fuskarta, Azeeza ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh kece, Ae ni ban kaiga yin fitsarin ba, Ki yadda ko karki yadda naki ne daga Jikin ki ya fito," shaƙo wuyan rigar azeeza batool tayi da hannunta biyu ta jijiigata, cikin shessheƙar kuka tace"You're lying to me azeeza, Kina so ki ƙala min sharri ne, Kiji tsoron Allah, ki faɗi gaskiya," Hankalinsu yayi matuƙar tashi, Kowa Ya haƙiƙance Yana ƙoƙarin kare kanshi, *Jinin wanene AZEEZA OR BATOOL ❓❓❓* *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Saboda tsabar firgicin da azeeza ta shiga nan take ta saki fitsarin da take ji ya soma gangarowa ta cikin wandonta, an rasa me lallashin wani acikin su, kowa sai kuka yake yi, Kuma har lokacin Batool bata saki wuyan rigar azeeza da ta shaƙe ba, bayin Allah su kaɗai suka san Fargabar da suke aciki, babban abunda suke jima tsoro shi ne azo araba su da ƴan uwansu, Basu da tabbacin za'a dawo dasu ko baza a dawo dasu ba, Cikin shessheƙar kuka ta wanda ya galabaita azeeza ta kware maki tana faɗin"Wayyo Allah na, Na shiga uku, batool kin shaƙe min wuyan rigata, Ki sake Ni, inji da abunda ke damu na....."daƙyar ta kai ƙarshen maganar, tana kiciniyar ƙwace wuyan rigarta da ga ruƙon da batool tayi mata, wata irin zufa ce ta wanke fuskokin su, Sun yi jawur, idanuwansu sun kumbura luhu luhu saboda tsabar tashin hankalin da suke aciki. Waɗan da ke acikin ɗaki basu san meke faruwa ba, babu alamun zasu farka daga bacci, Wata irin gigitacciyar ƙara batool ta saki sakamakon Cizon da Azeeza ta gartsa mata a hannunta, kaitsaye sautin ƙarar ya daki dodon kunnuwan su, Aikuwa a firgice kowannan su Ya farka, at same time suka ya ye bargunansu tare da yin wurgi dasu, Kowa yana faman zazzare ido, fuskokin su da alamun ruɗani, lokacin da suka ankara daga inda sautin ke fitowa, Jiki Na rawa kowannan su Ya sauko daga saman gadonshi, da gudun gaske suka nufi sashen toilet ɗinsu, kamar an jeho su suka faɗo Ciki, Kowa yana faman baza na muzurinsa, Angel ce farko sai Hanna da hibba, kaf matan da mazansu hada danish da haris, Hankalin su yai matuƙar tashi, ganin Jinin dake ɗigowa daga hannun batool sai yarfa shi take Yi, ta runtse idanuwanta sai kuka take yi kamar ranta zai fita, Tun da suke a rayuwar su basu ta6a ganin batool tana kuka mai sauti ba irin na yau, saboda tsabar hakurinta da juriyarta, Ita kanta azeeza data gartsa mata Cizon, duk tabi ta ruɗe jikinta sai kerma yake yi, ta manne jikin bango, Sai zazzare idanuwanta take yi fuskarta sharkaf da hawaye, "Innallallahi wa'inna ilaihirraji'un! Batool meya faru dake? Me kuke yi anan keda azeeza? Badai faɗa kuke yi ba"? Angel ce ta jefa musu tambayar, a yayin da take matsawa kusa da batool, takai hannunta tare da ruƙo hannun batool dake bleeding, Hanna tace"ashe dama kune kuke faɗa? Tun ina bacci nake ta jin hayaniya cikin kunne na, amma kun bani mamaki, yanzu batool ki rasa da wa za ki yi faɗa sai azeeza"? Hannah na rufe baki haris yace"Ku faɗa mana meya haɗa ku da har kuke ƙokarin illata junan ku, wannan wani irin abun kunya ne, " Lamarin duk bai yi musu daɗi ba, sai tambayar su suke yi akan su faɗa musu dalilin yin faɗan na su amma sun kasa tanka musu, saboda kukan da suke yi. "Hannunta yana zubar da jini, Ya zamu yi? Ko dai muje mu faɗa ma tsohuwa"? Mubeen ne yai maganar, muryar danish da alamun bacci bai ishe shi ba yace"Basai an faɗa mata ba," ya ƙarasa maganar tare da matsawa ya tsaya gefen angel dake a tsaye gaban batool, ya miƙa hannu ɗaya ya damƙo hannun batool dake zubar da jini, tare da kaishi saitin bakinshi tamkar zai gartsa mata cizo, ya kama wurin, kamar yana tsotsar jinin, duk suna kallon shi, Musamman angel da mamaki ya kamata ganin wani sabon salon treatment da bata ta6a gani ba, Sosai batool ta runtse idanuwanta, tana faman cizon brownish lips ɗinta, a hankali danish ya zame bakinsa daga saman hannun batool, wani iko na Allah jinin ya tsaya da zuba, sai dai a bunda ya ɗaure ma angel kai, ganin bai zubar da jinin daya sha ƙasa ba, A ruɗe take bin fuskarshi da kallo batare daya lura da ita ba, Sauran ƴan uwan babu wanda Ya kawo komai aranshi sai ita data ankara da abunda ya yi, zuciyarta ta shiga ruɗanin, taya akai ya ke iya swallowing ɗin jini!? Muryar azeeza cikin shessheƙar kuka tace"Dan Allah batool ki yafe ni wlh bada son raina na gartsa maki cizo ba, ke ce kika shaƙe mini wuyan rigata har naji zafi na cije ki," wani irin jiri batool take gani acikin idanuwanta, biji biji take bin kowannan su da kallo, Angel tace"Batool meke damunki? Wai baza ku faɗa mana me ya haɗa ku ba? Meyasa ku ke yin kuka? Ga zufa duk ta wanke jikin ku," matsawa batool ta yi kusa da angel ta kwantar da kanta saman kafaɗarta, da sauri angel ta sanya hannayenta biyu ta rungumeta sosai ajikinta, cikin muryar kuka batool ta zayyane musu abunda ke faruwa, Hankalinsu yayi matuƙar tashi, deeja dake a gefen haris ta fashe da kuka tana faɗin"mun shiga uku, abunda nake gudu sai da ya faru, wannan wace irin masiface? Fuskarta a yamutse takai kai ƙarshen maganar, haris yace"gaskiya bazaiyiyuwa ba, nidai bazan bari atafi da wani daga Cikin ku ba, sai dai a haɗa dani," cigaba da magana deeja tayi yayin da hawaye ke bin fuskarta tace"Dan Allah mu hada kanmu, wannan karan kada mu bari atafi da ƴan uwan mu, ina matuƙar tausayin azeeza da batool, bazan so su ɗanɗani irin raɗaɗin azabar da muka sha ba, musamman azeeza zamu iya rasata," maganar deeja ba ƙaramin tsorata azeeza ta yi ba, jikinta ya hau 6ari, haƙoranta har kakarwa suke yi kamar wadda sanyi ya kamata, da sauri javed ya janyota jikinshi, kamar jira take yi dama ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka, lallashinta ya shiga yi, yana ɗan bubbuga bayanta da hannun shi, Zuciyoyinsu duk sun karaya, Fuskar Rubina ɗauke da matsananciyar damuwa tace"Wai shin Jinin wanene acikin su? Ta ya zamu iya ganewa? ɗagowa azeeza ta yi daga jikin javed tana faɗin"I just know it's not my blood, wlh ba jini na ba ne, sai da na faɗa ma batool cewa banawa bane, Saboda ni ko da na shiga toilet ɗin ban kai ga cire wandona ba, na yi tozali da shi" cikin shessheƙar kuka batool tace"Nima banawa bane, ba daga jikina yake ba, har na shiga na fito daga Cikin toilet ɗin ban ganshi ba" koda batool tae maganar bata raba jikinta daga na angel ba, ta ƙanƙameta, ji take kamar in ta raba jikinta daga nata za'a zo arabasu ne, Hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskar angel. Har cikin zuciyarta tana jin wani irin mummunan faɗuwar gaba, muryar na ɗan rawa ta ambaci sunayensu Batool azeeza, "duk suka natsu, suna jiran jin me zata ce musu, "Since we were all confused, we couldn't figure out whose blood was in the toilet, abunda yakamata muyi zamu shiga toilet ɗin mu duba jinin da kyau, idan muka tabbatar jini ne, Azeeza da batool kowannan ku zai shiga cikin toilet ya bincika jikin shi, ta hakanne kaɗai zamu Iya gane daga jikin wa jinin ya ɗigo" gaba ɗaya kowa yayi amanna da maganar angel, koda suka shiga toilet ɗin suka duba dakyau, jini suka gani har ya ɗan bushe a ƙasa, Hankalinsu ya ƙara tashi, angel tace abunda ya rage yanzu, su shiga su duba jikinsu, Batare da 6ata lokaci ba, azeeza da batool suka shiga cikin toilet, kusan atare suka fito daga Ciki, Har suna haɗa baki wurin faɗi "Ba daga jiki na yake ba" Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, To wai jinin wanene toh? dole dai acikinsu ne wani ya zubar dashi, kuma azeeza ta tabbatar musu da cewa sabon Jini ne, domin kuwa lokacin da ta shiga cikin toilet ɗin, da ruwa ruwa jikinshi, kafin yakai ga bushewa, Kowannan su ya shiga ruɗani, in a low voice danish yace"ku daina wahalar da kanku, Idan ma dagaske jinin ne, Giants ne zasu banbance wanene acikin su," harara angel ta watsa mashi tare da cewa"danish har fata kake yi azo a ɗauke su"? duƙar da kanshi ƙasa yai batare daya bata amsa ba, haris yace"yanzu duk ba wannan ba, ku zo mu koma ɗaki mu jira mu gani me zai biyo baya" muryar azeeza a rauna ce take fadin"Ni wlh bazan fita daga nan ba, ku rufa mana asiri mu yi zaman mu acikin toilet mu datse ƙopar, ta yadda ba zasu Iya shigo wa su ɗauke mu ba" la66anta har shaking suke yi saboda tsabar firgici. Tsananin tausayin su ne ya kama ƴan uwansu, haris yace"Azeeza ta kawo shawara mai kyau, mu rufe su kawai acikin toilet, kun ga shikenan munyi maganin Giants ba zasu Iya shiga su ɗauke su ba" Jinjina kai angel ta ɗanyi alamar gamsuwa da bayanin Haris, ta ƙara da cewa"Ni zan zauna a atare dasu cikin toilet ɗin" Girgiza kai danish yayi yana binsu da wani irin kallo mai wuyar fassaruwa yace"that cannot be possible, if you say you will stop the giant from taking her you'll bite off more than u can chew........." daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da suke watsa mashi asaman fuskarshi, Tsabar takaici ya hana Haris furta komai, Sai angel ce tai ƙoƙarin cewa"Kome zamu yi be shafe ka ba danish, u should stay away from us, tun da ba ka supporting ɗin mu that's mean baka da amfani awurin mu, ka koma saman gado ka kwanta zai fi maka kwanciyar hankali. If not wlh zan yi maka abunda baka tsammani," angel na rufe baki deeja tace"Danish baya atare damu, na fara zargin cewa Yana atare dasu, shiyasa ko jiya da aka dawo dani duk irin baƙar wahala dana sha, Kowa Yana yi mini sannu duk da bata maganin ciwo amma ina ji daɗi, atlease ƴan uwana sun nuna sun damu dani sun yi kewata, amma danish ko kusa dani baizo ba, sai kace wata maƙiyiyar shi. hawaye na bin fuskar deeja takarasa maganar, Ran haris ya 6aci sosai, a fusace ya kai hannun shi ya damƙi damtsen hannun danish ya fusgo shi ya ja shi da ƙarfi ya fitar dashi daga cikin sashen toilet din. har cikin ɗakin su bakin gadon shi ya kawo shi, anan ya dakata Ya ɗago suna kallon juna ido cikin ido shi da danish, "Ba ka da amfani a wurin mu, duk da haka bawai ina gudun ka bane, ko Ina fushi dakai a'a ko ɗaya, har yanzu kana nan a yadda kake cikin zuciyata, sai dai bama buƙatar ka a halin da muke ciki yanzu, Gado shi ne ya dace dakai ka hau ka kwanta" ya ƙarasa maganar tare da jan dogon tsoki, kafin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin. Jikin danish ya yi sanyi, slowly ya ɗan juya baya yana kallon haris dake ta sauri har sai da ya shiga ƙopar tukunna danish ya ɗauke idonshi daga kallon bayan nashi da yake yi, Kamar yadda suka ce ya hau saman gado, aikuwa gadon ya haye ya kwantar da kanshi saman pillow, shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, ganin yadda ƴan uwanshi suke nuna rashin amfanin shi acikin su, abun yana mishi ciwo acikin zuciyarshi. Daurewa kawai yake yi dan ba yadda zaiyi, Bayan haris Ya koma cikin toilet ɗin, atare da angel suka tsara yadda zasu shirya ma Giants don su hana atafi da ƴan uwansu, Bayin Allah sun damu da ƴan uwansu sosai, babu mai tunanin abinci acikinsu ba don basu jin yunwa ba, sai dan damuwar da suka shiga, na fargabar kada azo a ɗaukar musu ƴan uwansu, Haris ne yace da angel ta shiga Cikin toilet ita da batool su datse ƙopar ta yadda giant ba zasu Iya shiga Ciki ba. ita kuma azeeza a ƙarƙashin gado zasu 6oye ta, hanna tace ae zasu Iya gano azeeza tunda suna kallon komai suke Yi, amma ita a ganinta, abar azeeza ta shiga cikin toilet ɗin tare dasu angel, Haris yace su yi hakan kawai, toilet ɗin ƙarshe suka buɗe angel da su azeeza suka shiga Ciki, kafin su rufe ƙofa haris yace"su kwantar da hankalin su, idan an kawo abinci zasu kawo musu nasu su ci," suka amsa mashi da toh, daga bisani angel ta datse ƙopar da Jam lock, Kallon juna suka shiga yi atsakaninta dasu azeeza dake a tsaitsaye, fuskokinsu sharkaf da hawaye, sam babu kwanciyar hankali atare dasu, Tsananin tausayinsu ne ya kamata, gaba ɗaya ta sanya hannayenta biyu ta rungumesu ajikinta, Cikin sigar lallashi take Yi musu magana, "In sha Allah giants bazasu raba mu da ku ba, bazan bari a cutar mini da ku ba, ina ji ina gani, wlh sai inda ƙarfi na ya ƙare, koda kuwa zan rasa raina ne, amma wannan karan ashirye nake dana fuskanci kowani irin tashin hankali ne" with Confidence angel tayi maganar, babu wasa akan fuskarta. Hankalin su batool ya ɗan kwanta, saboda jin abunda tace, ɗagowa batool tayi daga jikin angel, idanuwanta sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, cikin sanyin murya tace"Angel, bana so wani ya cutu acikin ku ta dalilin mu, idan har giants sun zo zasu tafi damu, kada kuce zaku shiga huruminsu, " girgiza kai angel ta ɗanyi tare da cewa"ki daina faɗin hakan, batool da ace kinsan me suke Yi maku idan suka ɗauke ku, da baki ce haka ba, ke kanki bazaki so atafi dake ba, mutanan nan basu da imani basu da tausayi, kashe mana rayuwa suke son yi ta yadda ba zamu ta6a amfanuwa ba, burinsu shine su ƙarar damu," tamkar zata fashe da kuka ta kai ƙarshen maganar, azeeza dake kwance jikin angel, taƙi ɗagowa baiwar Allah, Jikinta sai kerma yake yi, ta ƙanƙameta tamkar zata koma cikin cikinta, wani irin faɗuwar gaba take ji, ita kanta angel tana iya jiyo sautin bugun zuciyar azeeza, fargabatar kada tsoro yasa zuciyar azeeza ta buga harta mace kafin ma su ƙaraso, "Mu samu wuri mu zauna, nasan kun gaji da tsayuwa" daga jikin bango suka zauna, still azeeza bata saki jikin angel ba, hannu bibbiyu ta ƙanƙameta koda suka zauna, itama batool ta ɗan kwantar da kanta saman kafaɗar angel, toilet ɗin yai tsit ba ka jin hayaniyar komai, tsawon lokaci kafin angel ta fara faɗa musu addu'o'in da zasu karanta na neman tsari, saboda tsaro, Lokacin da angel ta datse ƙopar toilet ɗin, Ajiyar zuciya kowannan su Ya sauke, Haris yace dasu su koma ɗaki su zauna su jira su ga waye zaizo ɗaukarsu azeeza, Hada ja musu kunne akan karsu kuskura su bari tsoro yasa su faɗa ma giants inda suka 6oye su azeeza, duk runtsi duk wuya suja bakinsu su yi shiru, Suga iya gudun ruwansu, suka amsa mashi da toh, atare suka nufi cikin ɗakin, Idanuwansu akan danish dake kwance saman gadonshi, haushin shi duk ya kama su, wani sullu6iyo dashi, Suna yunƙurin haurawa su zauna saman gadajenshi, kwatsam suka soma Jin motsin buɗe kofa tacen saman bene, wa'Iya zubillahi zoka ga tsantsar tashin hankali akan fuskokinsu, A matuƙar ruɗe suke kallon matattalar benan , Takun tafiyar giants suka soma Jiyo wa acikin kunnuwansu, kafin su bayyana su uku masu kawo musu abinci hannayen su ruƙe da farantai, wata irin nauyayyiyar ajiyar zuciya suka sauke ganin basu zo da shirin tafiya da wani ba, Bayin Allah hada murmushin su, saboda sun sa ma ransu cewa baza a ɗaukar musu ƴan uwansu ba, Da ido suka bi giants da kallo har suka sauke musu farantan abincin, da sauri suka nufi saman dining carpet ɗin suka zazzauna, babu wanda yae tunanin yayi ma danish magana akan yazo yaci abinci, sai ma ta ƴan uwansu suke yi dake acikin toilet, ƙasa ƙasa da murya suke yin magana don kada giants su ji su, "A ina zamu ɗibar musu abincin mu kai musu"? hibba ce tai maganar, hannah tace"ku daina magana kada Giants su ji mu, abunda za'ae mu ɗauko kwandon batool mu ɗibi abinci, sai mu ajiye, bayan sun tafi sai muje mu kai musu acikin toilet ɗin," haris yace"kin kawo shawara mai kyau," batare da 6ata lokaci ba, hanna ta miƙe taje ta ɗauko kwandon daga ƙarƙashin gadon batool ta dawo ta zuƙunna gaban farantan, ta yaye jan ƙyallan da aka rufe faranti na farko dashi, fried fishes ne aka kawo musu, manya manya sun soyu sai maiƙo suke Yi, a ƙalla kowa zai samu ɗaya, Kifin akwai tsoka jikinshi sosai, A hankali take kai hannu tana ɗaukar kifin tana ajiyewa acikin kwandon, ganin ta ɗauki uku, yasa haris yace"Ki ƙara ɗaya kodan saboda danish" duk da fushi da yake yi dashi hakan bai hana shi jin damuwa dashi ba, Hanna tace toh, tasa hannu ta ƙara ɗaukar ɗaya ta ajiye, Ta ɗibar musu fruits tare da robar ruwa guda uku ta ɗauka, miƙewa tayi hannunta ruƙe da kwandon taje bakin gadon batool ta ajiye shi ta dawo ta zauna, a tsanake suke Cin nasu fried fish ɗin, Suna ci suna satar kallon giants dake atsaye sun goya hannayen su saman ƙirjinsu yadda kasan Gumaka, ko gajiya da tsayuwa basa yi, A 6angaren su angel dake acikin toilet, Tuni bacci yai awon gaba da azeeza da batool, duk suna akwance saman jikinta, itama angel ɗin wani irin bacci take ji ga yunwa dake addabarta, sai faman lumshe idanuwanta take yi, Daga wajen ƙopar toilet ɗin ta soma Jin ana yi musu knocking ras taji gabanta ya faɗi, hatta su azeeza dake baccin jin bugun ƙopar yasa suka farka a firgice suna faman zazzare idanuwan su, Muryar hanna suka jiyo tana faɗin"Ni ce angel, ku buɗe mini kopa, breakfast ne na kawo maku" Kusan atare suka sauke ajiyar zuciya, duk sunyi tsammanin ko Giants ɗin ne suka zo tafiya dasu, "Ku jira na amso mana abincin" tai maganar tare da zame jikinta daga nasu ta miƙe ta nufi ƙopar, ta cire jam lock ɗin, ta janyo ƙopar tare da leƙo da kanta waje, Hanna ta gani atsaye ita da haris, kwandon Yana a hannun hanna ta ruƙo shi, "Angel Giants sun zo kuma sun tafi, Ni ina ganin kamar ɗigon jinin nan ba jini bane. Tunda da ace shine, Giants zasu tafi da su azeeza ne, Amma kinga har sun kawo mana abinci sun tafi" shiru angel ta ɗanyi tana nazarin maganar Hanna. Ita gani take kamar jini fa ne, kawai dai bai kai ga zuwa bane gaba daya shiyasa basu zo sun ɗauke su ba Muryar haris ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take yi, "Nima ina tunanin ba jini bane gaskiya, tun da ga shi har zunzo sun tafi batare da sun buƙaci tafiya dasu ba" abunda za'ae yanzu ku fito mu koma cikin ɗakin ku zauna ku yi breakfast ɗinku" Gyaɗa kai angel tayi badan taso ba tace"Allah yasa abunda muke hasashe ya zama gaskiya, bari nayi musu magana su fito mu koma daki amma kafin nan, zan taimaka musu su wanke fuskokinsu," haris ya amsa mata da toh .kafin ya kalli hanna yace"Mu jira su acikin ɗaki" juyawa suka yi atare suka koma ɗaki, Badajimawa ba, Sai ga angel ta fito hannayenta ruƙe da nasu azeeza, Bayin Allah har faɗa wa sun ɗan yi saboda damuwa, Ƴan uwansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, da su kayi tozali dasu, A saman dining carpet suka zauna su uku, Hanna ta ajiye musu kwandon. Angel da azeeza suka ɗauki fried fish ɗinsu A hankali suke Ci, Sauran ƴan uwansu duk suna a kewaye dasu suna kallonsu, ganin batool ta kasa ci ne yasa haris yi mata magana yace"batool meyasa baki ci? Muryarta na ɗan kerma tace"Hannuna Zafi yake yi mini" sai lokacin suka tuna da cizon da azeeza ta gartsa mata, Zuƙunnawa haris yai agabansu, ya kai hannu cikin kwandon ya gutsiri tsokar kifin ya mika mata abaki, ta ɗan buɗe shi tana Ci, sai ƙara kwantar musu da hankali ƴan uwan nasu suke Yi, bayan sun kammala Ci, suka sha fruit ɗinsu, tare da ruwa, Angel tace yakamata suje suyi wanka, jikinsu duk zufa, suka amsa mata da toh, har tana cewa idan bazasu iya yin wankan ba zata taimaka musu suyi, batool tace ita zata Iya, azeeza kuma tace tafi son angel tayi mata wankan, hannun su aruke dana juna suka nufi toilet, bayan tafiyarsu, Haris ya ɗauki kwandon yana kallon sauran Fried fish din daya rage na danish tare da Rabin gwanda, Ta6e baki ya ɗanyi kafin ya nufi gadon danish, Ya ajiye mishi kwandon daga gefen shi yace"Idan kaga dama ka ɗauka ka ci, breakfast ɗin ka ne" ko motsi danish bai yi ba, ya runtse idanuwanshi, kuma ga dukkan alamu idonshi biyu ba bacci yake yi ba, Watsa hannu haris yai alamar bai damu ba, Ya wuce abunshi, bayan wani lokaci, angel tafito daga Cikin toilet tare dasu azeeza, Wani irin sanyi suke Ji, asaman gadajensu suka kwanta, angel ta lullu6esu da bargunansu, Cikin ƙanƙanin lokaci bacci yai awon gaba dasu, Ajiyar zuciya kowannan su ya sauke, yanzu sun ƙara tabbatar da cewa ba jinin gaske bane suka gani acikin toilet tunda har marece ya doso amma ba'a zo an ɗauki wani daga Cikin su ba, Ita dai angel ta kasa samun natsuwa acikin zuciyarta, abu biyu ne ya dameta, na farko Jinin batool da danish yasha da niyar ya taimaka mata wurin dakatar da bleeding ɗin da yake yi, amma wani abun mamaki bai zubda jinin ba sai ya shanye shi, hankalinta bai kwanta da hakan ba, abu na biyu daya tsaya mata arai shi ne wannan ɗigon jinin dake acikin toilet na wanene? Dole akwai wanda ya zubar dashi, Zuciyarta cike fal da tunani ta ɗan kishingiɗa saman gadonta, da niyar ta samu ta runtsa, juyawa ta ɗanyi tana satar kallon danish dake kwance saman gadonshi, yatsun hannunshi dana ƙafarshi sai kerma suke Yi, hakan ya tabbatar mata da cewa idonshi biyu, ta6a baki ta ɗanyi aranta tace"Haka zaka ƙare, mutun sam baya gajiya da hawan gado, mai matacciyar zuciya kawai" takarasa xancen zucin tana mai jan tsoki, ta ɗauke idanuwanta daga kan jikin shi, ta mayar dasu kan kwandon da haris ya ajiye mashi daga gefen gadonshi, yau kuma kowa zai lallashe shi yaci abincin shi? murmushin takaici ta dan saki, wani lokacin in yana abu kamar ƙaramin yaro, har mamaki yake Ba ta *after some hours💔* Kafin marece ya yi sai da kowan nan su ya yi wanka, Suka koma saman gadajensu suka kwanta, har lokacin danish bai motsa ba, Yana ayadda yake lafe saman gado, Angel tana ƙoƙarin nutsawa cikin baccinta, ta soma jin motsin mutun a jikinta, aɗan firgice ta ware manyan idanuwanta akan fuskar wanda ke zaune saman gadonta, Tayi mamakin ganin batool, fuskarta duk a yamutse. Idanuwanta sun ƙanƙance, tunkafin ma batool tayi mata magana taji wani irin faɗuwar gaba, Muryarta na ɗan rawa tace"Lafiya? Batool meke damunki"? Cikin sanyin murya ta soma magana"Bana jin ɗaɗin jikina angel, gaba na sai faɗuwa yake yi, na gaza jurewa, shiyasa nazo wurinki, don kiyi mini addu'a, ko na samu naji sanyi araina" ajiyar zuciya angel ta sauke a yayin da take yunƙurin mikewa xaune tace"Wlh har gabana ya faɗi dana ganki nayi tunanin ko jinin ne kika gani yazo miki ashe bashi bane" jinjina kai batool ta ɗanyi alamar eh, tace"Bashi bane, bana jin daɗi ne kawai" "Tun da nake dake batool ban ta6a ganin ki cikin damuwa ba, irin na yau, kin canza sosai, duk sai naji ba daɗi jikina," daƙyar batool ta ɗan ƙaƙalo murmushin dole akan fuskarta tace"kada ki damu sister, zan dawo dai dai ne, just fargabar abunda ya faru ɗazu ce tasa duk na canza, Amma yanzu da ɗan sauki" Ido cikin ido suke kallon juna. angel ta ruƙo hannayenta acikin nata tare da cewa "Zanyi maki addu'a, amma nafi so naji ki ajiki na, don naji daɗin kwantar miki da hankali kamar yadda kika saba yi mini" murmushi suka sakar ma juna atare, A saman chest din angel batool ta kwantar da kanta, tare da sanya hannayenta, ta zagayo dasu ta bayanta, sosai tayi tighting ɗinta, wani irin tsananin ƙaunarta take ji, suna matuƙar son junansu fiye da tunanin mai tunani, addu'o'i angel ta soma karantowa tana tottofa mata asaman kanta, har cikin zuciyarta take jin wani irin daɗi yana ratsata, har tana fadin"sister kada ki daina yi mini addu'ar nan, ki cigaba, ina jin wani irin sanyi acikin raina," murmushi angel tasaki, tare da ɗaura hannayenta saman sumar kan batool dake a dumbuje babu gyara, ta shiga shafata tana faɗin"indai akanki ne, zan iya kwana batare dana runtsa ba, wurin yi miki addu'a, ina matuƙar ƙaunarki my batool, " muryarta asanyaye ta karasa maganar, "Mu kwanta mu yi bacci, mu ma, " acewar batool, a manne da juna suka kwanta saman mattress ɗin, angel taci gaba da yi mata addu'a har sai da bacci ya ɗauke su gaba ɗayansu," To jama'a, ɗaki fa ya yi shiru baka jin hayaniyar komai, hankalinsu kwance sai sharar baccinsu suke yi, kamar waɗanda aka yanka mutuwa agabansu, Lokacin da marece Ya nutsa, deeja tafarka daga bacci ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta rungume da pillow, ɗaya bayan ɗaya take bin gadajensu da kallo, kafin ta tsayar da idonta akan shimfidar haris, ta jima tana kallon shi, kafin ta ɗauke idanuwanta, hakanan taji tana ra'ayin tabi kowani gado ta kalli fuskokin ƴan uwanta, Don haka ta sauko daga saman gadonta, Still jikinta ba ƙwari sosai, kamar ɗiyar roba hake take yin tafiya, tun daga kan gadon su hanna taso ma bi tana kallonsu har zuwa gadon azeeza, Ta ɗan dakata da tafiya tana kallonta, wani abu daya ɗaure mata kai bacci take yi amma sai firgita take Yi, numfashinta kuma a hargitse take fitarshi, matsawa ta ɗanyi tare da samun wuri gefen gadon azeeza ta zauna, hannunta ta ɗan ɗaura bayanta ta ɗan bubbugata, aikuwa a firgice azeeza ta farka tana faman zazzare idanuwanta, lokaci ɗaya kuma ta dafe kanta da hannu ɗaya tana faman sauke ajiyar zuciya ganin deeja ce, "Azeeza lafiya kike ta firgita kina bacci? Ko dai baki da lafiya ne"? Tayi mata tambayar cikin nuna damuwarta, Muryar azeeza adisashe tace"Hankalina ba a kwance yake ba, deeja bana jin daɗi, baccin nan da kika ga ya ɗauke ni har mafarkin Giants sai da nayi" idanuwanta acike tab da kwalla takai ƙarshen maganar, Janyota deeja tayi zuwa jikinta ta dan rungumeta da hannu ɗaya, tana lallashinta, "Ki kwantar da hankalin ki My little sis, muna atare dake, babu abunda zai faru daku," Azeeza tace ina jin ƙishin ruwa," da sauri deeja ta raba azeeza daga jikinta, ta sauko daga saman gadon ta nufi gadon batool ta zuƙunna ta tura hannu ƙarƙashi ta ɗauko robar ruwa, Ta miƙe ta koma gadon azeeza, ta zauna tare da cire murfin ta kwafa mata ita abaki, sosai ta shiga shan ruwan, A wani irin firgice Azeeza Ta jefar da robar ruwan dake ahannun deeja. Ta zabura ta yunƙura ta duro daga saman gadonta ta faɗo ƙasa, Ta shige ƙarƙashin gadonta, Jikinta sai kerma yake yi, Lamarin yae matuƙar ɗagawa deeja hankali, muryarta da alamun ruɗu take kwala ma azeeza kira tana tambayarta lafiya? Meyasa ta jefar da ruwan! Kafin deeja tayi yunƙurin saukowa daga saman gadon azeeza da niyar ta duƙa ƙarƙashin gadon ta janyota, kwatsam ba zato ba tsammani taji motsin buɗe ƙopar ɗakin su hankalinta a matukar tashe ta ɗago tana kallon Benan, Ba ita ba hatta masu bacci sai da suka farka jin sautin buɗe ƙopar, wani gabjejen Giant na ya faɗo Cikin ɗakin, mai faffaɗan ƙirji bayyanar shi tamkar baiyanar mutuwa ne agaresu, Wani abun ɗaure kai ma Giant ɗin daya shigo yasha banban da waɗanda suka saba zuwa kawo musu abinci, domin kuwa shi hada Star ɗaya a jikin baƙar rigar jikinshi daga gefen hannun hagu, sai lokacin deeja ta gane dalilin dayasa azeeza ta gudu ta 6oye ƙarƙashin gado, Wata irin faɗuwa gaba ce tazo ma deeja, lokaci ɗaya ta fasa ƙara mai matuƙar firgitarwa muryarta na rawa take ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! wayyo Allahna mun shiga uku! Mun bani!' wannan maganar da deeja tayi ce tasa duk wani mai bacci ya ƙarasa wartsakewa, Hankalin angel da batool yai matuƙar tashi, a matuƙar ruɗe angel ta ruƙo hannun batool suka sauko daga saman gadonta, da gudun gaske taja ta suka faɗa cikin sashen toilet ɗinsu, Suna shiga ɗaya daga cikin makewayin, Angel ta zura jam lock ta datse ƙopar, tana juyowa batool ta faɗa jikinta tana kuka take faɗin"Angel tafiya za'ayi dani, naji ajikina nice aka zo ɗauka, shikenan za'a raba ni da farin Ciki na ina ji ina gani, za'a ɗauke ni a tafi dani inda za'a cutar da rayuwata, Ba lallaima ne a dawo dani Cikin ku ba" Fashewa da kuka angel tayi Cikin shessheƙa tace" wlh bazaiyiyu ba, haƙurina ya ƙare, komai xai faru sai dai ya faru amma wlh bazan bari atafi dake ba, duk runtsi duk wuya ina atare dake, Sai dai su kashe ni" gaba ɗaya sun shiga matsanancin tashin hankali, su biyu acikin toilet sun ƙanƙame juna A hankali giant ɗin yake saukowa daga saman staircases ɗin, haris yai matuƙar harzuƙa, Su rubina duk sun zazzare idanuwansu, damuwace ƙarara kwance akan fuskokinsu. Wasu har sun fara kuka, tun kafin ma a ɗauki ƴan uwan nasu, Duk wannan budurin da akeyi danish bai motsa ba, haka zalika Azeeza bata fito daga inda ta 6oye ba, domin kuwa tuni ta jima da sumewa, Yadda kasan zaki Haka giant ɗin nan Ya tunkaro wurin gadajensu, Yana zuwa tsakiyar ɗakin Yaja burki ya tsaya ga dukkan alamu kamar kallonsu yake yi duk da basu Iya gane hakan. Tunda jikinsu gaba ɗaya a lullu6e yake da baƙaƙen kaya, hatta idanuwansu Ƙasa ƙasa da murya haris yace"ku ƙyale shege kada ku faɗa mishi inda suke muga ya zaiyi, Na rantse yau sai dai ayi duk wacce za'ae amma bazan Bari wannan ƙaton Ya ɗauki ɗaya daga Cikin mu ba" Muryar Hanna Cikin shessheƙar kuka take take roƙon giant ɗin tana faɗin"Dan Allah kada ku raba mu da ƴan uwanmu, Idan ma ɗaukar ta zama dole to ni ku ɗauke ni ku tafi dani amma na roƙe ka ka ƙyalesu, sun tsorata sosai zasu Iya rasa ransu, " hannah na rufe baki, sauran matan suka fashe da kuka suna roƙonshi, bayin Allah hada ƙoƙarin saukowa daga saman gadajensu suna yi mashi magiya akan ya ƙyale musu ƴan uwansu, su sun amince ya ɗauke su amma kada ya ta6a musu Azeeza da batool, tabɗijancan Iska na wahalar da me kayan kara, sufa duk atunaninsu zai ji tausayinsu Ya ƙyalesu, Sai dai abunda basu sani ba, Zuciyar giant tamkar dutse take. basu da tausayi ko misƙala zarratin, babu ɗigon Imani akansu, Su fa kawai Umarni suke bi daga sama, haris da ranshi ke a6ace yace"Ku daina wahalar da kanku, babu alamun zai saurareku, tun da ba tausayi ne dasu ba, Ae mun riga da mun 6oye su, kuma babu wanda zai nuna mishi inda suke idan yaga dama yai ta tsayuwa daga yau har jibi, idan ya gaji ya kama hanya ya koma," haris fa ya ɗauko ta da zafi, Tunda suka fara magana, gabjejen giant ɗin nan baiko motsa ba, Kamar yana sauraron me suke tattaunawa, Da mamaki su ke kallon Giant ɗin, ganin ya ɗaga hannayen shi biyu yai clapping ɗinsu, Cikin rashin fahimtar me yake nufi yasa suka zazzare ido suna kallon Juna, Danish ne ya fara motsawa daga saman gadonshi, Ya miƙe ya sauko da ƙafafuwanshi ƙasa, ya ɗan ɗago ya kalli giant ɗin dake a tsaye na wani lokaci kafin ya ƙarasa saukowa daga saman gadon, Yaje gaban giant ɗin ya sara mashi, a matuƙar ruɗe suke kallon danish, abun mamaki abun al'ajabi Daga bisa ni, su ka ga danish ya juya Ya nufi sashen toilet ɗinsu, gaba ɗaya suka bi shi da ido, Batare da wani ya motsa ba, Zuciyoyinsu cike da fargabar me danish zaije yi acikin sashen toilet ɗinsu, A lokacin batool da angel suna a zuƙunne jikin bangon toilet, sun ƙanƙame juna, Unexpected Angel tajiyo motsin buɗe kopa, tashin hankalin da ba'a sama shi date, Ƙopar dake a rufe kafin su shigo ta ciki ta sanya jamlock ta garkame ta, A matuƙar ruɗe take kallon Jikin ƙopar ganin jam lock ɗin yana motsi da kanshi ya zame kanshi, ƙopar ta buɗe, saboda tsabar tsoron da taji tuni zufa ta wanke fuskarta, batool kuwa tuni jikinta ya ɗauki wani irin zafi na fitar hayyaci, Duk a tunaninsu giant ne zai shigo wani abun al'ajabi sai ganin danish su ka yi ya faɗo Cikin toilet din, yana ƙarasa shigowa, Ya miƙa ma Batool hannu yace ta taso su tafi, wani irin kallon tashin hankali angel da batool suke binshi dashi, Ganin taƙi miƙa mashi hannunta yasa shi yin saurin damƙo damtsen hannunta ya janyota ta ƙarfi ya fiddo da ita daga Cikin toilet ɗin, da gudu angel tabiyo bayanshi, ta cafko hannun batool tana ƙoƙarin ƙwato ta, amma abun ya faskara domin kuwa ba ruƙon wasa yai mata ba, Adai dai lokacin da danish ya fado Cikin ɗakin, su haris suka ga ya ruƙo batool, zuciyarsu tai matuƙar karaya, lamarin yai matuƙar girgixasu, tsabar ruɗanin da suka shiga yasa suka gaza ta6uka komai, Kafin su yi wani yunƙuri, Danish Ya ƙarasa gaban Giant ɗin tare da batool Ya damƙa mashi ita, Giant ɗin ya sanya hannu biyu ya ɗauki batool saman kafaɗar shi batare da 6ata lokaci ba. ya juya ya nufi hanyar fita daga ɗakin, Al'ajabi ya hana su motsa, Suna ji suna gani giant ya tafi da batool tana ta kuka tamkar ranta zai fita, Nan take angel ta yanke jiki ta faɗi ƙasa asume, kamar jira suke Yi giant ɗin Ya fita, Haris yai wani irin kukan kura ya duro daga saman gadonshi, Ya kai ma Danish farmaki, kwalar rigarshi ya damƙa ya jijjiga shi, Hawaye na fita Cikin idanuwanshi yace"Ka kashe mu danish! Ashe dama baka da hankali? Kai wani irin wawan mutun ne sakarai soko maloho, wanda baisan Ciwon kanshi ba, wlh ka karya mini zuciyata ko a mafarki ban ta6a tunanin zaka Iya ruƙo hannun batool ka damƙa ma giant ita, don aje acutar da rayuwarta, ashe na yaudari kaina bansani ba, mugu azzalumi, wawa daƙiƙi...." Kafin haris ya ƙarasa maganar shi, Gaba ɗaya sauran ƴan uwan nasu suka tarar ma danish, bugu ta ko'ina suka shiga kai mashi, Kamar sun samu jaki, Hada matan duka suka nannaɗe hannayen rigunansu suka dunga bugunshi, amma ko gizau baiyi ba. Har saida suka fasa mishi hancin shi da bakin shi jini ya soma zuba, tukunna suka sake shi, anan ƙasa ya kife idanuwanshi sunyi jawur tamkar garwashin wuta, wani irin jiri yake gani, ya rasa meke yi mishi daɗi, ta ko'ina ga6o6in jikinshi raɗaɗi suke yi mishi domin kuwa ba ƙaramin bugu suka yi mashi ba, sun haɗa mishi Jini da majina sun xautar dashi, Kowa sai faman haki yake yi, Kuma babu wanda yaji tausayin shi, suna a tsaitsaye cirko cirko suna kallonshi, sai faman juyi yake yi, tun da suke dashi basu ta6a jin tsanar danish ba sai yau daya nuna musu true colour dinshi, mugun zargin shi suke yi, tabbas shima yana atare da giant shiyasa yake goya musu bayan duk abunda suke yi. Ɗan jakar uba, Haƙiƙa Danish ya yi breaking heart dinsu, hawaye ta ko'ina akan fuskokinsu, Ji suke kamar su tattake shi ya mutu su huta, tun da baida amfani acikinsu, tare da shi ake haɗa baki a cutar da ƴan uwansu, "Daga rana irin ta yau kada ka ƙara kiran mu da sunan ƴan uwanka, mugu azzalumi" Javed ne yai maganar, deeja tace"dama tun jiya da aka dawo dani, naga sauyi atare dashi, ko sannu baiyi mini ba, ashe hada shi ake haɗa baki a cutar damu," Mubeen yace"ae ni banso muka barshi da rai ba, wlh da mun sani mun karkarya ƙasusuwan Jikin shi, " yana magana yana cije le6e, "Danish baida tausayi baida imani, yau ya tabbatar mana da hakan, shi ɗin ba jinin mu bane, don haka ya tattara ya san inda dare yai mishi tun kafin muyi silar mutuwarshi," Duk wannan suratan da suke Yi, danish yana kwance, numfashinsa na fita sama sama, daga gani yana acikin mawuyacin halin da shi kanshi baisan Ina zai tsoma ranshi ba, Hancin shi dake bleeding jini duk ya wanke farar fatar fuskarshi, muryarshi adisashe yake faɗin "ku taimaka mun da ruwa in sha" wani irin kallo mai kama da harara suka shiga jefa mishi, haris yace koba ruwa ba? Ka jira ka gani, don ubanka, " rai a6ace yaje ya ɗauko robar ruwan dake a ƙarƙashin gadon Batool ya dawo ya tsaya agaban danish, Ya buɗe murfin robar ya watsa mashi ruwan duka akan fuskarshi, yana gamawa ya jefar da robar ruwa aƙasa yace"Iya taimakon da zamu Iya yi maka kenan, ni banga ma amfanin kallonka da muke Yi ba, ku wuce muje mu xauna. Mubar shege ya ji ajikin shi". Yana ji yana gani ƴan uwanshi suka juya mishi baya, Suka nufi gadajensu su ka zazzauna, zuciyoyin su acike da alhinin rashin Batool da suka Yi, Hanna ce ta lura babu angel acikinsu, babu wanda ya lura da cewar ta sume a bakin ƙopar shiga sashen toilet dinsu.da sauri ta miƙe daga zaunan da take a gefen gadonta, sai da ta fara zuwa karkashin gadon batool ta ɗauko wata robar ruwan, Ta nufi inda angel take kwance ƙasa, Ta buɗe murfin robar ta ɗan ɗebo ruwan a tafin hannunta ta watsa mata saman fuskarta, nan take angel taja dogon numfashi ta fatser dashi, muryar ta cikin shessheƙar kuka take ambaton sunan batool tana faɗin An raba ni da ƴar uwata, innallahi'wa' inna ilaihirraji'un! Wannan wata irin rayuwace "Angel ki tashi xaune," muryar hanna ce ta katse ta, jikinta duk ba daɗi, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe xaune tana faman huci sumar kanta duk ta tarwatse har tana kokarin rufe mata idanuwanta, bakowa ta ke kallo ba face danish dake kwance a ƙasa yana juyi, hannayenshi dafe da forehead ɗinshi, Da buɗar bakinta sai cewa tayi"me danish yake yi araye batare da kun kashe shi ba"? Fuskarta babu wasa tai maganar, haris yace"munso muyi hakan amma sai muka ƙyale shi, bawai don mun haƙura ba ne, Xamu jira ne har time da za'a dawo mana da batool muga awani yanayi take ciki, idan ta tsira shima xai tsira da ranshi, muddin kuwa batool tarasa ranta a silar shi, wlh shima sai yabi bayanta, duk irin ƙaunar da nake yi mishi, xan rufe ido ne da hannu na zan kashe shi. Inya so nima daga bisani in haɗiyi zuciya in mutu" Zuciyar angel har wani tafarfasa take Yi, sam ba haka taso ba, ta yi niyar tayi mishi bugun mutuwa har saiya haukace, Amma sai ta haƙura ta ƙyale shi ganin irin yadda jini ya wanke fuskarshi, koba komai Ya ɗanɗani irin zafin da suka ji acikin zuciyoyinsu, "Angel, ki tashi muje saman gado ki kwanta" girgixa kai angel tayi tare da cewa"Kibarni anan kawai, ba inda zanje yau sai naga abunda ya ture ma buzu naɗi," gyaɗa kai hanna tayi tare da miƙewa ta juya ta koma saman gadonta ta zauna,.. Duk sunyi zugudum cike da zullumin awani hali batool take aciki, a lokacin da ba su yi tsammani ba, suka ga hasken ɗakinsu ya ɗauke, duhu ya mamaye idanuwansu, Da sauri javed Ya miƙe ya lalubo fitilunsu Ya kunna su, ɗakin yayi haske, yau fa ba bacci dare ya koma tamkar da rana, Jimamin rashin ƴar uwarsu suke ta yi, ba wanda ya damu da danish, gaba ɗaya sun manta da azeeza dake a sume Cikin ƙarƙashin gado, Har dare ya tsala, babu wanda ya runtsa acikinsu, sai daga bisani ne, Haris ya lallashe su, har ya samu suka kwanta, shima ya kwanta zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin tausayin danish, amma haushin shi ya hana ya taimake shi, bashi kaɗai ba. Hatta sauran ƴan uwan nashi, duk sun damu. Da danish, tsoransu kada ya rasa ranshi, Ganin sunyi tsit Yasa ta fara tunanin ko sunyi bacci ne, duk da tasan zaiyi wuya yau su iya runtsawa, sai dai su yi likimo, amma wannan duk bai dame ta ba, Don yau taci alwashin saita dura tagar nan kodan taje ta taimaki rayuwar ƴar uwarta, kamar yadda tayi alƙawari, bazata bari a lalata mata rayuwar ƴar uwarta ba, yunƙurawa tayi tare da miƙewa, taje saman table ɗinsu ta ɗauko fitila, Ta juya ta nufi cikin toilet ta buɗe ta shiga ciki, wannan karan ko jam lock bata sanya ba, a buɗe tabar ƙofar, domin kuwa jininta akan akaifa yake, Komai zai faru sai dai ya faru ko a mutu ko arayu,, tsakanin ita da danish, yau saita dura tagar nan, Ita kaɗai tasan irin ƙuncin da take ji acikin zuciyarta, bayan ta ajiye fitilar a ƙasa, da ƙarfi ta janyo bokitin ƙarfen ta jingina shi jikin bangon tagar, tana ƙoƙarin hawa taji motsin mutun ya shigo Cikin toilet ɗin, a waske ta juyo baya don taga wanene, Bata yi mamaki ganin shi ba, ai yanzu ta daina ganin shi a matsayin mutun, ita da taga zahiran ɗazu da jam lock ya cire kanshi, A tsaye yake jikin shi duk ba ƙwari, wani abu daya ɗan ɗaure mata kai, Jini daya 6ata fuskarshi yanzu babu shi, aranta tace"nasan bai wuci shi ne ya lashe shi ba, tun da ɗazu ma naga yasha na batool, Maye kawai, " Yadda suke fuskantar juna, kamar abokan gaba ne suka haɗu a filin daga, banbancin kawai babu makami ahannun su, Cikin muryar fushi tace"kada ka kuskura ka matso ku sa dani, because I can harm you, I hate you Danish, I don't wanna see you, you are a bad person without faith and compassion," Muryarshi tamkar zai fashe da kuka yace"You should understand me, I am innocent, I am doing what is right........" wata irin tsawa ta daka mashi yayin da take nuna shi da index finger ɗinta tace"ban damu da duk wani abu da zaka ce ba, wawa daƙiƙi, wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har ka kuskura kace zaka hana In dura tagar nan sai na yi maka mummunar illar da zata sa ka gaza takawa da ƙafafuwanka," A matuƙar ruɗe danish yake kallonta, baisan ya zai yi ya fahimtar da ita ba, Ganin yana yunƙurin taka ƙafarshi xai tunkarota yasa ta takai hannu ta fusgi bokitin data ajiye ta ɗaga shi sama tana faɗin"Idan ka kuskura ka ƙara taku ɗaya, I will drop this bucket on your head idiot," a wani irin raunace yake binta da kallo, duk da irin gargaɗin da take yi mishi hakan baisa ya dakata da yin tafiyar ba, yana tunkararta, ganin dai dagaske so yake ya hanata, aikuwa da sauri ta ajiye bokitin ta haye tare dakai hannu ta ɗaɗɗago da glass ɗin, Ta dure shi ƙasa, Tana yunƙurin hawa bisa tagar, Taji ya damƙi ƙafafuwanta daƙarfi, a ƙoƙarin ya janyota ta faɗo Cikin rashin sa'a ya zame wandon Jikinta gaba ɗaya ya sabule ƴan fararen cinyoyinta santala santala suka bayyana a suffarsu, saboda tsabar jaraba ko waiwayon wandonta bata yi ba, A haka ta dire tagar ta faɗa ta baya.................." Ta tafi tabar danish a tsaye hannun shi ruƙe da wandonta, don ma Allah yasa rigar uniform ɗinsu tana da ɗan tsayi ta rufe ass ɗinta duka, *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Tun da ta dure tagar nan , danish ya kasa motsawa tamkar an ruƙe ƙafafuwan shi, Jikin shi yai mugun sanyi tamkar wanda aka zarewa laka, idanuwan shi na akan wandonta data bar mishi ruƙe a hannun shi, Kallon shi yake yi batare da ƙyaftawar ido ba, tsabar tashin hankali ne ƙarara akan fuskarshi , babban abunda yake jima tsoro Hannun da Angel zata faɗa, ba lallai ta Iya ganewa Ginin kurkukun ba. Domin kuwa a birkice yake. Idan har ba ka da ilmi akan shi, har ta6in hankali zaka iya samu saboda ruɗanin da zaka shiga, Muryar shi na rawa ya furta"bazan ƙyale ta ba, why angel? Dole na bi bayanki, " Yana yunƙurin haura tagar, kunnuwan shi suka jiyo mishi sautin muryar haris dake ta ƙwala ma shi kira daga can cikin ɗakin su, Aikuwa a matuƙar ruɗe Ya fasa Yunƙurin dura tagar, da sauri Ya nannaɗe wandon angel. Ya wurga shi saman tukunyar fulawar nan ta Cikin toilet ɗin, kafin ya miƙa hannu ya ɗauki fitilar da angel ta ajiye acikin toilet ɗin, Ya juya ya nufi hanyar fita, buɗe ƙopar shi keda wuya, Sai ga haris ya faɗo sashen toilet ɗin hannun shi ruƙe da fitila, Haska fuskar danish yai, ganin shi ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, sam ya gaza runtsawa saboda tunanin mutun biyun nan batool da kuma danish, fargabar Halin da suke aciki Ya hana shi sakat. danish ya yi mamaki zuwan haris nemanshi , bai ta6a tsammanin wani daga Cikin su zai waiwaye shi ba. Duba da irin aika aikar da ya yi musu. Sun ɗauki tsawon mintuna suna kallon Juna, sai daga bisani haris ya jefa mashi harara tare da cewa"Ya jikin naka"? daƙyar danish ya samu ya dai daita natsuwarshi, Cikin sanyin murya yace"Da sauƙi" ta6e baki haris yae kafin ya kuma cewa"ka zo mu koma ɗaki, naga baka ci breakfast ɗinka dana ajiye maka ba, kuma nasan kana jin yunwa, tun safe har dare ko ruwa baka sha ba," yana magana yana wurga mashi harara dake nuni da cewa ba don yaso yake yi mishi maganar ba, har yanzu akwai sauran haushin shi da yake ji acikin zuciyar shi, Danish bai motsa ba, kallon haris kawai yake yi, shi damuwarshi akan angel ne, Baya jin zai Iya bin haris su koma ɗaki, Jin yayi shiru yasa haris sake cewa"magana fa nake yi maka"? Fuskarshi a yamutse ya soma magana, "Meyasa ka damu da ni? Duk irin abunda na aikata mu ku? Rai a6ace haris yace"ba wannan na tambaye ka ba, abinci nake magana, kazo muje ka ci" girgixa kai danish yai alamar a'a yace"Na ƙoshi, ka ƙyale ni koda yunwa zata kashe ni, bai shafe ka ba, lokacin dana buƙaci taimako awurinku, akan ku bani ruwa in sha, ka tuna abunda ka yi mani? A fusace haris yaja dogon tsoki tare da matsawa ciki ya ruƙo hannun danish da niyar ya fusgoshi su tafi, da sauri danish ya ƙwace hannun shi, cikin kakkausar murya yace"Nace maka bazanci ba! Ka rabu dani! Babu ruwan kowa da rayuwata, tun da kun nuna cewa bani da amfani acikin ku," wani irin kallo haris yake bin shi da shi, kowannan su sai faman huci yake yi, Shi burin shi haris ya tafi ya bashi wuri ko ya samu yaje ya taimaki angel, don yasan yanzu haka tana can tana neman ɗauki ta gama furgicewa, Haris Na ƙoƙarin buɗe baki don Ya mayar mishi da martani, Muryar Deeja Ta katse mishi Hanzarin shi, daga can cikin ɗaki Ya jiyota tana ƙwala mishi Kira, don dole ya saki hannun Danish Ya juya da gudu ya koma Cikin ɗakin, Shigar shi ke da wuya, Ya yi arba dasu deeja gaba ɗayansu agaban gadon Azeeza, tunkafin ma ya ƙarasa shiga hankalin shi yai matuƙar tashi, Ganin azeeza rungume jikin deeja, babu numfashi, kamar matatta, Su parveen sun tasa ta gaba sai kuka suke Yi, A bunda ya faru, Tun lokacin da azeeza ta 6oye ƙarƙashin gado ta 6oye don kada giant ya ɗauke ta, gaba ɗaya sun manta da azeeza, da ta 6oye a ƙarƙashin gadon ta, Har suka kwanta basu tuna da ita ba, sai daga baya ne deeja tana kwance saman gadonta, ta yi zurfi acikin tunaninta, kwakwalwata ta soma tariyo mata abunda ya faru kafin atafi da Batool, Nan take ta dafe ƙirji, ta miƙe zaune tana Ambaton sunan azeeza, Koda sauran ƴan uwan nasu suka ji tana kiran sunan azeeza, suma sai suka wartsake kowa Ya sauko daga saman gadon shi, A gaggauce Deeja ta ɗauko dayar fitilar data rage a ɗakin, Ta ajiye ta daga ƙasa gefen gadon Azeeza, Ta zuƙunna tana leƙa kanta ciki, Anan ne taganta xaune Kamar gunki babu abunda ke motsi ajikinta, Ta fashe da kuka Tare da kai hannu ta 6an6arota daga Jikin bangon data jingina, ta janyota wajen gadon, ta kwantar da ita saman jikinta, Su Hanna duk suka kewayesu, kowa ya zuƙunna suna ta kuka suna ambaton Sunan Azeeza, Zuciyoyinsu duk sun karaya, ganin yadda jikinta ya sandare, Cikin shessheƙar kuka hibba tace su jira ta dauko ruwa a yayyafa mata wata'ƙil su samu ta farka, tana karasa yin maganar ta miƙe ta ɗauki fitilar ta nufi gadon batool, tana laluban robobin ruwan da suka ajiye, sai dai bata samu ko ɗaya ba, duk sun ƙare, Jiki amace hibba ta dawo tana haska su da fitilar hannunta tace babu ruwa, bari naje toilet na ɗebo, har ta juya zata nufi toilet ɗin, Muryar deeja ta katse ta da cewa"Ina haris yake? Naji motsin shi ɗazu, Ya sauko daga saman gadon shi, ina tunanin toilet ya shiga, Bari na kwala mishi kira yazo," Batare da6ata lokaci ba, deeja ta shiga kwala mishi kira, Sai gashi ya faɗo Cikin ɗaki, Haris na ƙarasawa kusa dasu, Muryarshi na ɗan rawa ya ambaci sunan azeeza tare da cewa Meya faru da ita? Nan suka sanar dashi komai, tun daga zuwan Giant, dafe kanshi yai da hannu ɗaya, idanuwanshi sunyi jajur, zuciyarshi duk ba daɗi, Yau dai gaba ɗaya basu ji daɗin ranar ba, sun yini da baƙin Ciki acikin ransu, Kallonsu parveen yae ganin yadda suke ta yin kuka babu ƙaƙƙautawa, Cikin sigar lallashi yace"Ku kwantar da hankalin ku, azeeza zata farka suma ne tayi, bari naje na ɗebo ruwa a yayyafa mata" yakai karshen maganar tare da juyawa Ya nufi cikin ɗakin, Yana laluban Inda ya jefar da robar ruwan daya watsa ma danish ɗazu, Cikin sa'a yaci karo da ita can gefen dining carpet ɗinsu, Da azama ya je ya ɗauko bottle water ɗin Ya juya ya nufi sashen toilet ɗin su. Lokacin daya shiga, baiga danish ba, babu shi babu alamarshi, Sai dai bai kawo komai aranshi ba, ganin ɗaya daga Cikin ƙopar toilets ɗin nasu a garƙame, sai yayi tsammanin ko yana aciki ne, ɗayan toilet ɗin ya shiga ya kunna fanfo ya tarba robar ruwan, sai da ta Cika tab, kafin Ya kashe fanfon Ya fito daga Cikin toilet ɗin Ya koma inda su deeja suke a zazzaune, Zuƙunnawa yai, bayan ya ajiye fitilar hannunshi, Ya tarba ruwan a tafin hannun shi ɗaya, Ya watsa ma azeeza saman fuskarta, Kowa ya baza ido yana jiran ganin ta farka, amma shiru ko motsi bata Yi ba, Nan fa hankulan su suka ƙara tashi matuƙa, Cikin shessheƙar kuka suka haɗa baki suna roƙon azeeza akan ta taimaka musu ta farka, Haris dasu Javed sai lallashinsu suke Yi, ganin yadda duk suka shiga damuwa, parveen na kuka tace"tun da muke arayuwar mu ba mu ta6a fuskantar tashin hankali, irin na yau ba, An ɗauke mana batool, ga azeeza kuma taƙi farkawa, Ni tsorona ma kada ace ta mutu....." kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, ta kifa kanta saman gwiwarta, muryar deeja adisashe tace"dan Allah ku daina maganar mutuwa, wlh bana sonji, in sha Allah azeezan mu zata farka, babu abunda zai same ta, addu'a ya kamata muyi mata," Haris yace"wace irin addu'a? Babu abunda zata yi mana, kawai dai mu jira zuwa lokacin da zata farka," idanuwanta cike tab take ƙwalla take kallon shi, Tsananin tausayinsu ne ya kamata haris, bayin Allah, tun safe hankalin su ba'a kwance yake ba, ga shi har dare ya ratsa basu runtsa ba, Kusan sau uku haris yana yayyafa ma azeeza ruwa akan fuskarta amma taƙi farkawa, Jikinsu duk yai sanyi, haka suka zauna a kewaye da ita, suna kallonta yayin da hawaye ke cigaba da sauka a kan fuskar kowannan su. "To ko dai mu yi ma tsohuwa magana tazo ta duba ta kada ta mutu" acewar yasmin, har suna haɗa baki wurin cewa"Taje ta kirawo ta," Da sauri yasmin ta miƙe ta dauki fitila ta wuce ɗakin tsohuwa, lokacin da yasmin ta bubbuga ƙopar ɗakin tsohuwa bata buɗe mata ba, kusan sau takwas tana yin knocking kamar zata 6alle ƙopar har saida haris yace mata ta dawo zai iyayiyuwa bata nan,Tukunna ta ƙyale ƙopar ta dawo wurinsu ta zuƙunna, Magiya suka soma Yi mata akan tafarka "Azeezan mu ki tashi dan Allah, Badan halin mu ba, wlh ba mu gaji dake ba Muna matuƙar ƙaunarki ƙaramar mu kuma babbar mu, pls wake up, kome kike so zamuyi maki, bazamu ƙara 6ata maki rai ba, kuma ba zamu bari giants su ɗaukar mana ke ba" kamar wasu sabbin mahaukata haka suka dinga yi mata sambatu akan tafarka, tun sunayin maganar da ƙwarinsu har ta kai ga muryoyinsu sun disashe, kowa yaja gefe suna matsar ƙwalla, idanuwansu duk sun kumbura saboda tsabar kukan da suka sha, "Wai ina angel take ne!? Nifa banganta acikin mu ba? Yakamata wani yayi mata magana tazo taga halin da azeezan mu take aciki, tayi mata addu'a ko mun samu tafarka" Kallo kallo suka shiga yi a tsakaninsu, Jin abunda deeja tace, gaba ɗaya sun manta da babu angel acikinsu sai da tayi wannan maganar su ka tuna da ita, Hanna tace"ɗazu acan nabarta zaune bakin ƙopar shiga sashen toilets dinmu," tayi maganar tare da juyawa tana nuna musu wurin, Basu ga komai ba, naufal yace"kodai tayi bacci ne"? Haris ya bashi amsa da cewa"ae bata a saman gadonta, ɗazu da zan shiga toilet na duba naga babu ita" a matuƙar ruɗe suke kallon juna, Eve tace"kodai ta shiga toilet ne? Bari inje in dubo ta" da sauri haris ya dakatar da ita tare da cewa"Ni zan dubo ta" Ya miƙe tare da kai hannu ya ɗauki fitila Ya juya ya nufi sashen toilet ɗinsu, yana gab da zai shiga, ba zato ba tsammani sai ga danish Ya faɗo hannayenshi biyu suna rungume da angel, ya tallabota a jikinshi, babu alamun tana motsi, A wani irin yanayi Su Hanna suka mimmiƙe tsaye suna kallon shi, mamaki ƙarara akan fuskokinsu, Yayin da zuciyoyinsu ke acunkushe da tambayoyi dangane da abunda ya faru da ita da har ta sume bata motsi, An rasa me buɗe baki yayi mishi magana A cikinsu, ko kallo basu ishe shi ba, kaitsaye Ya wuce da ita saman gadonta Ya kwantar da ita, sumar kanta duk ta hargitse, Fuskarta tayi jawur, musamman tsinin hancinta, hada ɗigon Jini, daga gani ba ƙaramar wahala tasha ba, hawayene ta ko'ina akan fuskarta, kayan Jikinta sunyi uban squeezing, Hada wandonta Daya maida mata ajikinta, Da gudu Su Hanna suka Tunkaro gadon suna tambayarshi Meya faru da angel a ina ya ɗaukota? bai tanka musu ba, Domin kuwa A yanzu baya atare dasu, itace A gabanshi, zuciyarshi sai harbawa take yi da sauri sauri, numfashin sa da hucin zafi yake fita, a wani irin yanayi yake bin fuskarta da kallo...................." "Shin meya faru da angel Bayan ta dura tagar nan"? Lokacin da Angel ta haura tagar nan, ta faɗo ta baya wani irin duhu ne ya mamaye idanuwanta, kanta ya soma juyawa, Ta sanya hannayenta bibbiyu ta dafe kanta, Jikinta ya soma kerma a hanzarce ta fara ƙoƙarin kamo sunan Allah acikin bakinta, sai dai abun ya faskara, sautin shessheƙar kuka ta dinga Ji acikin kunnuwanta, ranta ya dinga bata cewar batool ce take kuka, Cikin duhunnan, ta miƙi hanya gudu gudu sauri sauri hada tuntu6e, ita kanta batasan ina zata dosa ba, domin kuwa notikan kwanta sun kwance, bata ji bata gani, a makance take tafiya burinta takai ga inda take jiyo sautin shessheƙar kukan nan, Haske ta fara hangowa a ƙarshen hanyar data biyo, da gudu ta nufi inda take hango hasken nan, tana faɗowa cikin wurin, Idanuwanta suka sauka akan katafaren filin dake da manya manyan benaye, a ƙalla sun kai Shida benayen kuma kowane matakalarshi ta haura goma sha, don akwai wanda matattakalarshi takai talatin shine wanda idan ka hau zai kai ka har third floor na ginin, Ginin yana da tsayi da faɗi, Daga sama wasu irin manya manyan fitilune da suke haskaka wurin, idan ka kalli kowani hawa na benan zakaga Wasu Tagogi wadanda glass din Jikinsu launin Ja ne, Masu girma, Babu ƙofofin ɗakuna Sai dai da alama za'a Iya samun ƙofofinsu ta can cikin hanyoyin dake akwai, wani irin kurman Ginine, Mai matuƙar ruɗarwa, wani irin fargaba ne ya ɗarsu acikin zuciyarta lokacin da tafara Jin wani irin gurnani, Ginin Ya dinga juya mata, benayen suka dinga motsi Suna Yin ƙasa da sama, Waro ido waje angel tayi Jikinta na 6ari, Ta zabura zata Juya ta koma Inda ta fito, sai dai ina babu hanya, tama rasa gane ta inda ta faɗo Cikin wurin, Tsabar ruɗi yasa ta baza da gudu ta faɗa tsakiyar wurin, hannayenta dafe da kanta saboda wani irin firgici da take aciki, tuni zufa ta wanke Jikinta sharkaf, Bata gama rikicewa ba, Daga can saman hawa na uku ta soma Jin muryar mahaifinta tajudden Yana kuka yana kwala mata gira, A matuƙar ruɗe ta juya ta baya tare da ɗaga kanta saman benan, A tsaye ta hango shi, tare da Wasu irin haluttu masu gashi gashi ajikinsu, Jibga jigba, Sun kewaye shi, Sai Cuzgar naman Jikin shi suke yi, Wata irin gigitacciyar ƙara angel tasaki, mai kuwar gaske, Ta fashe da matsanancin Kuka tana fadin"Daddy! wayyo Allah na daddyna! Shikenan sun kashe mini daddyna!! nashiga uku, Dan Allah ku ƙyale mini daddyna" Tana kuka ta watsa da gudu ta nufi ɗaya daga Cikin benayen da nufin taje ta taimaki daddynta, tana gudu ana maida ta baya, Da zarar takusa kaiwa saman benan sai taga Sun juya mata, Benan yaja da baya, Ya koma can Ciki, Haka ta dinga bin benayen tana ƙoƙarin hawa samansu, Amma wani abun ruɗarwa benayen tamkar masu Rai, sosai suke motsawa wurin yin ƙasa da sama, Jikinta duk zufa ta galabaita sosai, idanuwanta sunyi jawur, Jijiyoyin wuyanta duk sun fito ruɗu ruɗu Jikin fatarta, Muryarta har ta disashe, Duk da mawuyacin halin da tashiga na tsoro da firgici hakan baisa ta fasa yunƙurin hawa benan ba, Bakomai take ji ba face mahaifinta da take hangowa can saman waɗannan halittun suna Cin naman jikinshi, sai kuka yake Yi yana miƙa mata hannu akan tazo ta taimake shi, Akan idonta halittun suka gutsire ƙafafuwanshi, Jini ya dinga tartsatsi yana gangarowa ta saman benan, Angel tashiga ruɗani, addu'a ta kubce mata, gaba ɗaya tunanin ta ya gushe, Tun tana yin kuka har ta koma tana yin na zuci, Ƙafafuwanta sai zogin azaba suke yi mata, saboda zarya da tadinga Yi, Lokacin da benayen suka gama yi mata wasa da hankali, Suka koma yadda suke, waɗannan halittun suka 6ace ma ganinta, sai dai gangar jikin mahaifin ta dake a yashe saman hawa na uku, Da gudu ta haura saman dogon benan nan wanda ya ke da matattakala Talatin, Tana tafiya tana zamewa, a haka harta samu ta haura saman shi, Tana ƙarasawa inda gangar jikin tajudden take, ta zuƙunna saman gwiwowinta, ta dinga kuka hada majina tana ambaton sunan shi tana faɗin sun kashe mini daddyna, sun rabani da farin Cikina, Wayyo Allah na, Ya Allah ka ɗauki raina nima in huta, yatsun hannunta na kerma ta ɗaga su da nufin ta shafa gangar jikinshi, nan take gangar jikin ta 6ace 6aat, a matuƙar gigice ta zazzare idanuwanta eye lashes ɗinta suka bubbuɗe, tsigar jikinta ta dinga tashi, zufa ta ko'ina, kwakwalwarta ta burkice, kafin ta yi wani yunƙurin motsawa ta soma Jin motsin tafiyar wasu abubuwa ta ko'ina, a firgice ta ɗan juya baya tana kallon Jikin wata taga dake a datse, Ras taji gabanta yai wani irin mugin bugu, Bakomai bane angel ta gani face wasu irin manyan kunamu sun ɗaga ƙarin su, Yayin da suke gangarowa daga Jikin bangon suna tunkaro inda take zuƙunne, wa'iyazubillah, ƙiris ya rage zuciyarta ta buga, saboda tsabar razanar da ta yi, ga shi jikinta babu ƙwarin da zata Iya saukowa daga saman benan, Jikinta na 6ari ta soma rarrafawa tana tunkarar banen dan ta sauko ƙasa, tana kuka tana waiwayon kunamun dake tunkarota, a wannan lokaci ta dinga kwala ma danish kira na fitar hayyaci tana faɗin yazo ya taimake ta, zasu kashe ta, ta mutu ta bani ta lalace ƙarshenta yazo, Adai dai wannan Lokacin Danish Ya faɗo Cikin wurin, Hannun shi ruƙe da wandonta, sai faman waige waige yake yi, karaf idanuwanshi suka sauko akan angel da ke yin rarrafe tana saukowa daga saman benan, Hankalinshi yai matuƙar tashi, da ƙarfi ya ambaci sunanta yana faɗin ta tsaya kada ta motsa ba abunda zasuyi mata, sai dai kash angel bata Iya fahimtar maganar shi, saboda bata acikin hayyacinta, Da gudu ya nufi benan da niyar yaje ya taimaka mata, kafin ya ƙarasa gwiwowin ƙafarta suka sage, Tun daga kan matattakalan farko Angel ta burki ce ta dinga mirginowa tana gangarowa ƙarshen stair ɗin, kanta da hancinta duk suka fashe suna bleeding, kafin ta faɗo ƙasa, sai da ta fita hayyacinta, Jini ya wanke fuskarta, har saman wuyanta, hatta knuckles ɗinta saida suka gurguje, A ƙarshe ta ƙundumo kan ground floor ɗin, kanta ya dake shi, goshin ya fashe, ƴar rigar uniform ɗin dake ajikinta, tuni ta yaye ta nannaɗe ta dawo saman Cikinta, tsiraicin ya bayyana sosai, gashi ko pant babu ajikinta, Wasu irin zafafan hawaye ne suke wanke fuskar danish time ɗin daya ƙarasa ya zube agabanta saman gwiwowinshi, yayin da numfashin shi ke fita a wahalce, A wani irin yanayi mara misaltuwa yake kallonta, dama abunda yake guje mata kenan, Amma ta ƙi jin maganarshi, hannunshi na kerma ya ruƙo rigarta data nannaɗe, ya janyota ya rufe mazaunanta, a saman laps ɗinshi ya ɗaura wadonta, kafin ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da ita, zuciyarshi ta ƙara karaya ganin irin mummunan raunin da taji akan fuskarta, idanuwanshi ba zasu juri ganin angel cikin mawuyacin hali ba, da sauri ya kwantar da ita saman ƙirjinshi, ya matseta da hannayenshi biyu, ya kwanto da kanshi saman sumar kanta dake a yamutse, ya ɗan lumshe idanuwanshi, saboda tsabar zafin jikinta har a jikinshi yana ji, cikin wata irin raunatacciyar murya ta wanda ya galabaita ya jigata ya fita hayyacinsa ta dinga kira mishi sunan daddynta, ta zagayo da hannayenta zuwa bayanshi, ta cakumi rigarshi tana yamutsa ta, babu alamun hankali atattare da ita, santala santalan cinyoyinta sun fito farare sol dasu, sai faman motsa su take yi, tana harɗesu jikin juna, ganin rigarta na ƙoƙarin kwarewa ta ƙara nannaɗewa yasa shi yin saurin kai hannu ya damƙi ƙasan rigar ya gyara mata ita, A hankali Ya sanya hannayenshi biyu ya ɗago da kanta daga saman ƙirjinshi, Jininta duk ya 6ata mishi gaba rigarshi, ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, Idanuwanta sun ƙanƙance, tausasan la66anta sun kumbura sun ciza launinsu, tsinin hancinta yai ja sosai, jinin ne ke gangarowa ta cikin ƙofofin hancinta, Cikin karyayyiyar murya ya ambaci sunanta Angel, bata amsa mashi ba, don a halin da take aciki batasan wanene akanta ba, sunan daddynta kawai take iya ambato, Cikin harshen turanci yaci gaba da cewa "Angel, kinga abunda kika ja ma kanki ko? Yanzu da ace banzo ba ya zaki yi? Kalli yadda kika raunata kanki, ta ko'ina babu lafiya a jikinki, saboda kafiya irin taki na gargaɗe ki amma kika ƙi jin magana ta, saboda baki ɗauke ni abakin komai ba, kin ɗauka cewa shiga cikin prison abune mai sauƙi, yanzu gashi nan kin ja ma kanki yin jinya, nasan ko gobe aka nuna maki hanya fita ba zaki ƙara gigin binta ba" shi kaɗai yake ta sambatun shi, baiwar Allah, sai nishi take yi, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji ajikinta, Haɗe fuskokinsu yai wuri ɗaya, ya mayar da hands ɗinshi Tsakanin sumar kanta da wuyanta, harshen shi ya ɗaura saman fuskarta, a hankali ya soma lashe jinin dake zuba, har sai da yaga babu sauran jinin dake ɗiga tukunna ya zame tongue ɗinshi, idanuwanta sai rurrufewa suke Yi, biji biji take ganin shi, tun tana yin numfashi daƙyar daƙyar har ta kai ga sumewa saman jikinshi, da dabara ya samu ya zame wandon unform ɗinta daga saman laps ɗin shi, Ya damƙo dogayen ƙafafuwanta, Ya shiga kiciniyar sanya mata shi, daƙyar ya zura mata wandon yaja shi har saman waist ɗinta, bayan ya kammala, Ya ɗaɗɗago da ita, ya yarfata saman kafaɗarshi Ya miƙe Ya juya Ya nufi hanyar komawa ɗakin su, sai dai da alama danish bata taga ya koma Cikin ɗakinsu ba, 6acewa yai ya faɗo Cikin toilet ɗinsu ɗauke da ita a hannunshi, a lokacin Har ya gyara ɗaukar da ya yi mata, ya sauko ta daga saman kafaɗar shi, Ya yi mata irin ɗaukar da ake yi ma jariri, Yana kan hanyar fitowa daga Cikin toilet ɗin, Yaji motsin mutun Yana tunkaro ɗakin Da wani irin sauri Ya faɗo bakin ƙopar sashensu, Kunji yadda akai danish Ya ɗauko angel, *PRISONERS💔* hankalinsu yaƙi kwanciya, Ganin irin raunatar da angel tayi, masu karyayyiyar zuciya acikinsu tuni sun fashe da kuka, Hibba tace"wannan wata irin rayuwace, daga wannan sai wannan, yau dai bata yi mana daɗi ba, muna fama da azeeza data sume ga kuma Angel itama asume jikinta duk ciwuka, wai dan Allah meya faru da ita ne? Tana rufe baki hanna tace"pls danish ka faɗa mana a ina kaga angel, can fa nabarta a zaune, Yanzu kuma sai gashi ka shigo da ita daga Cikin toilet, yaushe ta shiga ciki? A matuƙar ruɗe tayi mashi tambayar, haris yace"Allah yasa ba wani mugun abun ka yi mata ba, Wama ya sani ko bugunta ka yi don ka huce haushin abunda muka yi maka," da sauri danish ya ɗago da idanuwanshi ya ɗaurasu kan fuskar haris da ya yi maganar, wani irin raɗaɗi yake ji acikin zuciyar shi, ƴan uwanshi suna yi mishi kallon mugu mara tausayi mara imani, duk sai yaji ya tsani kanshi, sam ya kasa furta komai, duk da ya ɗago ne da niyar ya mayar mishi da martanin maganar shi amma sai ya kasa, "Yakamata muyi ƙoƙarin wurin ceto rayuwan ƴan uwanmu bawai mu tsaya muna surutu mara amfani ba" Acewar Mubeen, Cikin fushi haris yace"Ka faɗa mana me ka yi ma angel da har ta suma? Hawaye ne suka cika idanuwanshi, Cikin sanyin murya yace"ka bari tafarka sai ka tambaye ta me nayi mata, idan har ni na zalunce ta, kuna da right da xaku iya rama mata, amma bai kamata ace kuna tuhumata ba" Naufal yace"zamu zuba ido mu gani har zuwa lokacin da zata farka wlh idan har ta fada mana cewa kaine silar halin da tashi ga, to ka kwana da sanin cewa ba zamu ƙyale ka ba," Yana magana yana galla mishi harara, Girgiza kai danish ya ɗanyi batare daya tanka ma naufal ba, ya lura gaba ɗaya shi suke zargi akan halin da angel ta shiga, basu son cewa itace ta ja ma kanta ba, "Ina azeeza take"? Yayi tambayar yana bin fuskokinsu da kallo, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa"Ina ruwanka da ita? Ka damu dasu ne"? Girgixa kai ya ɗanyi tare da cewa'taya bazan damu dasu ba, ƴan uwanane su, baku isa ku hanani tambayarsu ba" Javed yace"Har kana da bakin cewa su ɗin ƴan uwanka ne? Mugu dakai saboda rashin imani ka damƙi hannun batool ka miƙa ma wani ƙato ya ɗauke ta don aje acutar da ita, a haka har kake kiransu da ƴan uwan ka"? Tuni idanuwanshi sun cicciko tab da kwalla, tunawa da rashin imanin da ɗan uwansu danish yayi musu, jikin shi duk yayi sanyi, har lokacin yana zaune gefen gadon angel, daƙyar yake kallonsu saboda nauyin haɗa ido da su ya ke ji. "Ka faɗa mana wanene kai!" har saida gabanshi ya faɗi jin tambayar da haris ya jefa mishi, muryarshi na kerma yace"wha..what u mean? Haris ni kake tambaya wanene Ni"? jinjina kai haris yai tare da cewa"Eh, so nake insan wanene kai! Danish bani kaɗai ba gaba ɗayan mu nan zargin ka muke Yi, Kawai ka faɗa mana gaskiyar wanene kai, meyasa kake atare damu" a ruɗe danish yake kallonsu, Naufal yace"bana tunanin danish cikakken mutun ne, Saboda babu zuciya a ƙarjinshi, Haba rashin imanin yayi yawa, ka duba kaga yau tsawon shekara nawa, danish yana atare da batool, tun kafin mu mallaki hankalin mu yake atare da ita, baida wani makusancin daya wuce ita, in ka cire haris, amma yau rana ɗaya ka gaza ceton rayuwarta, sai ma ka taimaka wurin miƙa ta ga azzaluman da zasu azabtar da rayuwarta......" wani irin kukane yazo ma naufal ba arxiƙi ya katse maganar, hawaye suka soma bin fuskarshi, Haris ya ɗaura da cewa"ba zamu ta6a mantawa da wannan ranar ba, danish ka cika butulu, mara imani da tausayi, Yarinyar nan babu irin ciwon kan da batayi ba akanmu, tana matuƙar son ƴan uwanta, idan wani baya lafiya acikinmu, batool ko bacci bata iya yi har sai yaji sauƙi, ka cuce mu danish, kuma ka karya mata zuciya, nasan batul bazata ƙara yarda dakai ba, saboda kaine silar duk wani hali da zata tsinci kanta," Tun da suka soma yi mishi magana, yayi shiru yana binsu da kallo bai ko tanka musu ba, duk yadda zaiyi musu bayani yasan ba lallaine su fahimce shi ba, amma yafi su jin raɗaɗin rabuwa da batool, shi kaɗai yasan irin ƙuncin daya shiga lokacin daya janyota ya miƙa ma giant, Sun tasa shi gaba suna jiran jin amsar dai basu, bai bi ta kansu na, ya miƙa ya tunkari inda su deeja suke zuƙunne, yana yunƙurin zuƙunnawa don ya duba lafiyar azeeza, naufal ya damƙi hannun shi tare da cewa"kada ka kuskura ka ta6a ta, babu ruwanka da rayuwarmu" murmushin takaici danish ya sakar mashi, batare daya mayar da martanin maganar shi ba, ya fusge hannun shi daga ruƙon da yae mishi, Ya zuƙunna agabansu deeja, wani irin haushin shi take ji kamar ta shaƙe wuyan shi, Tun da ya zuƙunna take ta aika mishi da harara kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wanda ake yin hararar domin shi baima san tana Yi ba, hankalin shi gaba ɗaya yana akan azeeza, dake rungume jikin deeja, Robar ruwan da haris ya ajiye a ƙasa, Danish Ya miƙa hannu ya ɗauko ta, A baki ya kur6i ruwan, duk suna a tsaye suna kallonshi, A saman fuskar azeeza ya watsa ruwan, Wani iko na Allah nan ta ke azeeza taja dogon numfashi, Jikinta ya soma kakarwa, Cike da mamaki suka dinga kallon danish da kuma azeeza, ganin yadda yai nasarar watsa mata ruwa ta farfaɗo, Hannayenshi biyu ya sanya ya tallabo fuskar azeeza yana kallonta, muryarta adisashe take faɗin dan Alah kada ku bari su ɗauke ni, wlh mutuwa zanyi, ni bazan bi su ba, " "Azeeza"! Muryar danish ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, ta ɗan buɗe idanuwanta tana kallon shi biji biji saboda matsalar idanuwanta, da sauri su haris dasu hanna duk suka zuƙunno agabanta, suna ambaton sunanta, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, badan tana gane su ba, yayin da idanuwanta ke lumshewa, muryarta na ɗan rawa tace"Dagaske ba'a tafi dani ba, ina atare da ƴan uwana"? Atare suka haɗa baki wurin bata amsa da cewa"Eh, muna atare dake" har xatayi murmushi sai kuma ta fasa, tunawa da batool, nan da nan walwalar fuskarta ta ɗauke. A tsorace tace dasu"Ina Batool take" nan fa kowa yai shiru, hakan yasa ta fahimci cewa An ɗauke batool, shessheƙar kuka ta fara yi musu, Danish yace"its okey azeeza, ba lafiya gare ki ba, kina buƙatar ki huta" girgixa mashi kai tayi hawaye ta ko'ina akan fuskarta tace"Yanzu shikenan an ɗauke mana batool dinmu, an tafi da ita, baiwar Allah, nayi danasanin cizon ta da nayi, dame xata ji"? Fashewa tayi da kuka, Cikin sanyin murya haris yace"Pls azeeza stop shedding ur tears, Ya riga daya faru babu wanda ya isa ya dawo dashi baya, abunda nake so daku shine muyi haƙuri mu rungumi ƙaddararmu, idan da rabon za'a dawo mana da batool, Ko min daran daɗewa, ƴar uwarmu zata dawo cikinmu ne" Sosai haris ya shiga kwantar musu da hankalinsu, sai gashi kowa daga Cikinsu yaja baki yae shiru, danish yace"Yakamata kuje ku kwanta....." daƙyar ya ƙarasa maganar, ganin irin kallon da suke watsa mishi, Haris yace"Itafa angel? Kaƙi faɗa mana meya faru da ita, a ina ka ɗauko ta? Me kuma ya haɗa ka da ita da har kayi mata wancan jahilin bugun," "Haris, bani da amsar da zan baka, amma idan tafarka, zaka Iya tambayarta, " yana kai karshen maganar, Ya miƙe tare da ɗaukar robar ruwan Ya nufi gadon angel, Bai kai ga ƙarasawa ba, Ya ɗan dakata da yin tafiyar, Batare daya juyo ya kalle su ba, da wata irin kakkausar murya yace"ku wuce ku je ku kwanta," Tun da ya ambaci hakan suka fara Jin wani irin matsiyacin bacci yana niyar dauƙarsu, A daddafe kowannansu Ya miƙe Deeja ta ruko hannun azeeza a saman gadonta suka kwanta su biyu ta rungumeta ajikinta, Cikin ƙanƙanin lokaci ɗakin yai tsit Baka jin hayaniyar komai bacci duk yae awon gaba dasu, Ajiyar zuciya yaɗan sauke, Aranshi yace"nasan da hakanan nace su kwanta bazasu bi umarni na ba" Daga gefen gadon angel ya zauna, Yana binta da kallo, sai yaji sam baya son ya tada ta daga bacci, saboda sanin tsiwarta, Its better ya ƙyale ta zuwa wani lokaci, A hankali Ya ajiye robar ruwan daga ƙasa, ya haura saman gadon, ya sanya hannayen shi biyu ya damƙi ƙafafuwanta, A tsanake Yake daddana mata su, Yana yi mata tausarsu, duk inda ya ta6a sai kaji ya bata sauti ƙass, daga bisa ni ya ruƙo yatsun hannayenta, Ya dinga jansu, bayan ya kammala, Ya kwanta daga gefenta, idanuwanshi akan fuskarta, "Idan tana bacci tafi kyau, da sanya zuciya natsuwa, amma idan tafarka, tsiwarta tafi komai ɗaga hankali," da wannan zancen zucin bacci yayi awon gaba dashi, Daƙin yai tsit, Ba ka Jin sautin komai saina minsharinsu, Bayan wani lokaci, Hasken fitilun saman ɗakinsu Ya gaure ko'ina, wanda ke nuni da cewa gari ya waye, babu alamun masu bacci zasu farka, Motsin buɗe ƙopa ne Ya karaɗe kunnuwan danish, A hankali Ya ɗan ware sexy eyes ɗinshi, ya yunƙura ya miƙe daga zaune ya jingina bayan shi da bango, Angel na a kwance gefenshi, idanuwanshi sai faman lumshewa suke Yi, da alama baccin bai ishe shi ba, jikinshi duk ba daɗi, A buƙace yake da son Yin wanka, gaba ɗaya hankalin shi ya koma kan staircases jin Sautin tafiyar mutane. Giants ne suke shigowa hannayensu ɗauke da sabbin gadaje kalar nasu, duk mutun ɗaya yana ruƙe da gado ɗaya, A jere suke saukowa daga saman benan, kusan su Goma sha biyar, Kaitsaye suka wuce can Cikin ɗakin, 6angaren da gadajensu danish suke fuskanta, A nan suka jera sabbin metal beds ɗin da suka shigo dasu, Duk akan idonshi, Bayan sun kammala jera gadajen, Sai ga Wani giant ɗin Ya shigo Hannun shi ruƙe da doguwar ledar kaya, mai ɗauke da sunan Prison, Bargunane acikinta tare da bedsheets da kuma pillow, Yana ƙarasowa Ciki, Batare da 6ata Lokaci ba, suka curo da zannuwan gadon suka shimfiɗa ma kowani gado, daga bisani suka ɗaura bargunan, tare da pillow, Bayan sun Kammala A jere suka Juya suka fuce daga Cikin ɗakin, Mamaki ne ya kama danish, yayin da yake saukowa daga saman gadonshi, Ya nufi inda gadajen suke a jere, Yana ƙare musu kallo, aranshi yace sabbin prisoners za'a kawo mana, Har mutun goma sha biyar? Mun cika talatin kenan," ta6e baki ya ɗanyi, Shi dai fatan shi Allah yasa kar akawo musu masu ɗan banzan surutu da tsiwa, Sai da yabi kowani gado ya ƙare ma numbobin jikinsu kallo, sun fara daga no16 har izuwa No30, Jinji na kai yai kafin Ya juya ya nufi gadon angel, daga gefe ya zauna, tare da kai hannu daga ƙasa gefen gadon, Ya ruƙo bottle water ɗin daya ajiye, har ya tarba hannu zai ɗibi ruwa ya watsa mata, Yaji motsin buɗe ƙopa, dakatawa ya ɗanyi yana jiran ganin wanene zai shigo, Yayi tsammanin xaiga new prisoners ɗin da za'a kawo musu, amma sai yaga Giants suna shigowa, Ukun farkon masu kawo musu abinci ne, Hannayensu ruƙe da wooden trays, Na bayansu kuma su biyu ne hannayensu ruƙe da wasu jibga jibgan akwatuna kusan guda biyu masu girma, Suna da tayoyi daga ƙasan su, daga bayan masu ruƙe da akwaitin, akwai wani Giant ɗin kuma hannun shi ruƙe da Floor laps Masu girma, daga gani zasu yi haske sosai idan aka kunnasu, Danish dai ya zubawa sarautar Allah ido, sai kallonsu yake yi, A saman dining Carpet ɗinsu, Giants ɗin suka sauke kayan breakfast ɗin nasu, waɗanda ke a ruƙe da akwatin nan, a tsakiyar ɗakin suka ajiyesu, Saura Giant ɗin dake ɗauke da floor lamps a hannun shi, Daga ƙasa Ya ɗaura su, Atare suka juya hada masu kawo musu abincin suka fuce daga Cikin ɗakin, Fitarsu keda wuya, Danish ya soma Jin takun tafiyar wani kuma again yana saukowa daga saman benan, da sauri yakai idonshi kan me shigowa, Gaba ɗaya Jajayen kayane ajikin mutumin, doguwar riga ce bazai Iya tantance macace ko Namiji ba, gaban rigarsa taurari ne guda uku, hannunshi na dama yana a ruƙe da sanda Golden colour, daga gani tsohone, hatta takalmin shi jajaye ne, a bayanshi wasu Giants ne su Huɗu, kowanne hannayenshi na a ruƙe da kayan amfani na toilet, A tsakiyar ɗakin Mai sanye da jajayen kayan ya tsaya, Ganin haka yasa danish ya miƙe ya ɗan sara mashi, Da hannu yai mishi alamar Jinjina, kafin Ya juya ya kalli giants da suka zo atare, Da hannu yayi musu nuni da sashen shiga toilet ɗinsu, suka nufi Ciki suka shige, kusan Minti talatin Suna aciki, Kafin daga bisani suka shigo cikin ɗakin, Babu kayan da suka zo dasu a hannunsu, sun barsu acikin makewayin nasu, Tamkar sojoji haka suke ƙame abayan Wannan ɗan tahalikin mai sanye da jajayen kaya, Danish Yana a tsaye yana binsu da kallon mamaki, Ware ido yayi ganin mutumin ya ɗaga hannun shi ɗaya ya ɗaura shi saman fuskarshi, nan take ya zame mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, dattijuwace fara tass, launin idanuwanta blue ne, daga gani baturiyace, tana da dogon hanci, gaban kanta hurhurace, Ƙayataccen murmushi tasakar ma danish tare da cewa"Ƴan uwan naka bacci suke Yi? Muryarshi na ɗan rawa yace"eh" lumshe idanuwanta tayi yayin da take kallonsu tace"gwanin ban sha'awa, tunkafin in fara zama acikin ku har naji kun kwanta mini araina, aɗan ruɗe danish yake kallonta, kai daga ganinta kasan babu wasa atare da ita, Sam batayi kama da masu Imani ba. "Zan tafi but I will come back. When they wake up, tell them that their new guardian has come to visit them," fuskarta asake tayi maganar, Ya amsa mata da toh, Har ta ɗaga ƙafa zata juya sai kuma ta dan dakata, yayin da idanuwanta suka sauka akan Angel dake kwance saman gadonta, Shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta tsohuwar, A hankali ta furta sunan ta *Unaisa zaheer tajudeen Our destiny* Ta ambaci hakan tare da juyawa ta nufi hanyar fita daga Cikin dakin,da sauri Giants ɗin suka Bi bayanta, bayan tafiyarsu danish ya maimaita kalmar ƙarshe da tsohuwar ta furta *Our destiny* kalmar ta tsaya mashi arai, yayi mamakin jinta, shin meyasa ta kalli angel ta ambaci sunanta a amtsayin ƙaddararsu? ta6e lips ɗinshi ya ɗanyi tare da komawa saman gadon angel ya zauna, A tsanake yake kallon fine face ɗinta, soft lips ɗinta sun bushe sosai, robar ruwan dake a hannun shi ya kai saitin bakinsa ya kur6i ruwan tare da watsa mata shi saman fuskarta.................. *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Ruwan na sauka saman fuskarta, awani irin firgice ta farfaɗo ta zabura zata miƙe, ga6o6in jikinta suka ƙi bata haɗin kai, wani irin raɗaɗin azaba taji a jikin ta, ba arziƙi Ta koma ta kwanta, Cikin shessheƙar ku ka take ambaton sunan daddynta bakomai idanuwanta su ke hango mata ba face waɗannan halittun da ta gani suna cuzgar naman Jikin daddayn, abun ya tsaya mata aranta, daƙyar ma sautin muryar ke fita saboda raunatar da la66anta suka yi, ga maƙoshinta dake abushe ƙamas tana cikin buƙatar ruwan sha, jikinta sai kerma yakeyi, a hankali danish ya ajiye bottle water ɗin daga ƙasa gadon, rumfa ya yi mata da ƙirjinshi yana jiran ta ƙarasa dawowa cikin hayyacinta, yana ganin ta fara ƙoƙarin buɗe idanuwanta, ya yi saurin sanya tafin hannun shi ya toshe mata ƙaramin bakinta, saboda gudun tsiwarta, yasan muddin ta haɗa ido dashi sai ta zazzaga mishi masifa, jin hannun mutun saman fuskarta yasa ta ƙara firgita, da ƙarfi ta buɗe idanuwanta tana faman zazzare su, launin gray ɗinsu ya ciza, eye lashes ɗin sun cukurkuɗe Cikin juna, kaitsaye eye balls ɗinta suka sauka akan fuskar danish, biji biji take iya ganin shi, Muryarshi na ɗan rawa ya fara yi mata magana "Angel.....ki natsu ba ki da ƙoshin lafiya" a dabarbarce yayi maganar ganin irin kallon da take watsa mishi, wanda ke nuni da tsantsar ƙiyayyarshi da take ji, Sassauta muryar shi yai batare da ya zame tafin hannun shi daga saman fuskarta ba, yaci gaba da cewa"Nasan yanzu bani da sauran mutunci a wurin ki, kin gaya mini cewa kin tsane ni, baki son gani na, Angel Ni mai laifi ne a wurinki, duk yadda xanyi maki bayani ba lallai ne ki fahimce ni ba, Amma bazan takura maki ba, idan har da akwai abunda za ki yi mini wanda zaisa ki huce haushinki a kaina, Ni na amince ki yi mini shi, amma kada kice xaki ƙaurace mini, zuciyata zata iya bugawa........" bai kai ga ƙarasa yin maganar ba, Sakamakon damƙar hannun shi da angel tayi, Cikin fushi ta janye shi daga saman bakinta, batare da ta tanka mishi ba, da yasan yadda take jin tsanar shi a halin yanzu da bai wahalar da kanshi ba wurin neman yafiya agare ta, ji take kamar ta shaƙe wuyanshi ta jijjiga shi ta buga kanshi jikin bango har sai ya sheƙe tukunna ta ƙyale shi, Ba don Allah yasa jikin nata ba isasshen lafiyace dashi ba, da ba abunda zai hana yau ta Illata shi, Tuni yasha jinin jikinshi, domin kuwa yana ji a jikin shi irin tsanar shi da take Ji, wasu irin zafafan hawaye ne suka cika idanuwan shi, muryar shi tamkar zai fashe da kuka yace"Ki bani dama ta ƙarshe xan gyara kuskure na," lumshe idanuwanta ta yi, Yayin da maƙoshinta ke motsi tamkar tana haɗiyar wani abu, sam bata jin zata Iya tanka mishi gani take kamar in yaji muryarta zai ji sanyi acikin zuciyarshi, that's the reason why taƙi yi mishi magana, tafi son Yaji a jikin shi irin halin da ya jefasu, har abada baxata ta6a mantawa da abunda ya faru Jiya ba, duk irin alƙawarin da ta ɗaukar wa batul akan zata taimaki rayuwarta, bazata ta6a bari a cutar da ita ba. Yanzu ya tashi abanza kenan? taya hankalin ta zai kwanta? Bayan batasan awani hali batool take aciki ba, tana can hannun waɗannan azzaluman mutanan da deeja ta bata labarin ta gansu akanta, suna Cutar da rayuwarta, Sai ta dinga imagining ga batul can itama sun danneta tana ta kuka tana buge buge. Lokaci ɗaya angel ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hankalin danish ya tashi matuƙa, duk yabi ya ruɗe, yana so ya lallashe ta, Sai dai yana jin shakkar ta6ata, "Am sorry angel....ni ne silar komai, pls stop crying it's hurting my heart, bazan juri ganin ki, cikin wannan Yanayin ba......" Wani irin matsiyacin kallo ta jefa mishi, idanuwanta sunyi jawur gwanin ban tsoro, dama tunda ta farfaɗo daga suman da ta yi fuskarta take a kumbure, cheeks ɗinta sunyi ja, La66anta sunyi luhu luhu , Duk da irin kallon da take wurga mishi hakan baisa shi ya dakata da yin maganar shi ba, "Angel, nima bada son raina ba, Na miƙa batul ba, bana tunanin akwai wanda yakai ni ƙaunarta acikin ku, Batul tamkar jinin dake yawo ajikina take, Na rayu da ita tun ban mallaki hankali ba, mun shaƙu da juna, kusan komai atare da ita muke yi, a duk lokacin da lalurata ta tashi ta rashin son hayaniya, ita ce take jana ajikinta, ta rungume ni har sai taji na samu natsuwa tukunna take saki na, Meyasa ba zaku fahimce ni ba? Ku yi tunani mana, Ni har raina zan iya sadaukarwa akanta...." daƙyar ya ƙarasa magnar tare da kifa kanshi saman katifar gadonta, da alama kuka yake yi, Gaba ɗayan su kuka suke yi babu mai lallashin wani acikin su, duk wannan budurin da ake yi ƴan uwansu dake ta sharar bacci babu wanda Ya motsa acikinsu, kamar matattu, idan har ba danish Yaje ya tashe su ba, zaiyi wuya su farka da kansu, In ba wani iko na Allah ba, saboda baccin nasu bana Allah da annabi bane, shi kaɗai yasan mai ya yi musu da har suka kama yin shi, duk da yai hakan ne don ya kawar musu da damuwar dake acikin zuciyarsu, a hankali ya ɗago da kanshi daga saman mattress ɗin, idanuwanshi sunyi jawur dasu, launinsu ya ciza sosai, fuskarshi tayi jawur da ita, Cikin sanyin murya yace"dame xanji? Idan har kuka juya mini baya zan shiga damuwa, Ni bazan hana Ku tsane ni ba, idan ma takama ku buge ni son ranku, but please don't say that you'll cutt me off from u, abun zaiyi mini yawa, ga rashin batool ga kuma rashin ƴan uwana," Tun da ya soma yin maganar, ta tsagaita da yin kukan idanuwanta na fuskantar ceilling, Haƙiƙa kalaman danish sun kashe mata jiki, sun so suyi tasiri akanta, Sai dai a duk lokacin da ta tuna da irin yadda ya damƙo hannun batul Ya rabata da ita, Yaje ya miƙa ma Giant, Sai ta ji tsanarshi Ta ƙara ninkuwa acikin zuciyarta, Ɗauke eyes ɗinta tayi daga kallon ceilling da take Yi, ta tsayar dasu akan fuskarshi, bakomai take gani ba acikin idanuwanshi face tsantsar nadama. Sun ɗauki tsawon lokaci suna kallon juna batare da wani daga Cikin su Ya ƙyafta idanuwan shi ba, Kowa Da abunda zuciyarshi take raya mishi, ganin ta fara motsa la66anta alamar za ta yi magana, sai yaji sanyi acikin ranshi, yayi tsammanin zata yafe mishi ne, amma sai yaji tace"inaso ka yi mini alƙawari..." a ƙagare yake kallonta cike da son jin wani alƙawari ne takeso Ya ɗaukar mata, Don a shirye yake daya bi umarninta. Muryarta adisashe taci gaba da cewa"idan ka yi mini wannan alƙawarin zanyi farin Ciki, kuma zan tabbatar da cewa Kai ɗin mai ƙaunata ne," aɗan ruɗe yake kallonta, shi dai fatan shi Kada tasa yayi mata alƙawarin da ba zai Iya cika mata shi ba. Calmly ya furta"Ki faɗa mini menene kike son in ɗaukar miki alƙawari akanshi? Girgixa kai ta ɗanyi, Still hawaye na bin kuncin tace"Ka fara ɗaukar alƙawarin kafin na faɗa maka akan menene" Hawaye wasu nabin wasu akan fuskarshi Yace"I can't, saboda nasan ba alkhairi xaki faɗa mini ba," Saukowa yai daga saman gadonta, Ya zuƙunna saman gwiwowinsa, a ƙoƙarinsa naya nemi yafiyarta, don shi har ga Allah baison tayi fushi dashi, Yana matuƙar Jin ƙaunar angel acikin zuciyarshi, "Nasan idan nace ka dawo mini da batool bazaka Iya ba, Haka zalika idan nace Ka faɗa mini wanene kai? Still amsa ɗaya zaka bani shi ne baka sani ba, kaga kuwa baka da amfanin da zaka Iya mini...." bai bari ta karasa maganar ba, yai saurin katse mata hanzarinta da cewa"I know bani da amfani awurinki, amma ki tuna abunda ya faru jiya, may be kin manta, ni ne naje na ceci rayuwarki, na faɗa miki ne badan Ina tunƙaho da hakan ba, sai dan kisan cewa ni ɗin mai ƙaunarki ne kuma ina da amfani awurinki," awahalce yai maganar, daga shi har ita babu mai ƙoshin lafiya acikinsu, Daƙyar suke magana kamar anyi musu dole, kayan jikinsu ba ƙaramin tsami suke yi ba, hada ƙarnin jininta da yai bleeding jiya, Fuskarta a yamutse tace"danish, ban damu da duk wani abu da zaka faɗa mini ba, alƙawarin da nake so ka ɗaukar mini shi ne, Ka nesanta kan ka dani! Ras! Yaji gabanshi ya faɗi, tun kafin ma yaji ƙarshen xancen nata, Ya soma girgiza kai alamar bazai Iya ba, "Bana son ka ƙara kusanto ni, balle ma har kayi tunanin zuwa wurina, koda gigin wasa kada ka kuskura ka bari mu haɗa ido da juna, ya zamar maka dole ka janye jikinka daga nawa, idan har kana son zaman lafiya acikin kurkukun nan......." Bawan Allah ya rasa ina zai tsoma ranshi yaji dadi, ya riga dayasan Halinta, tana da wuyar sha'ani, ga kafiya idan ta furta magana zai yi wuya ta canza ta, duk da wani lokacin tana da saurin sauka idan tayi fushi sai dai wannan karan babu sassauci akan fuskarta, "Har tsawon wani lokaci kike so in janye jikina daga naki"? Idanuwanshi cike tab da kwalla yayi mata maganar," "Har zuwa lokacin da za'a dawo da batool, Idan tace ta yafe maka shikenan nima zan yafe maka mu cigaba da yin rayuwar mu kamar yarda muka saba, idan kuma har ba'a dawo da ita ba, hmmmmm....." ta ambaci hakan saboda tagaza idasa maganar, sai faman taunar la66anta take yi, har sun ɗan ƙara fashewa dama abushe suke. Ba ta yi tsammanin zai ɗaukar mata alƙawarin ba, sai ji tayi yace"I promised u angel, bazan sake koda kallon ki ba, ballantana har inyi miki magana, Inaso in tabbatar maki da cewa ni mai ƙaunarki ne, Kuma inason farin Cikin ki,......." dakatawa ya ɗanyi da yin maganar, yana bin fuskarta da kallo, tun yanzu ya fara jin kewarta a tare da shi, wahalallan murmushi ya sakar mata har dimples ɗinshi suka lotsa sosai, da sauri ta kawar da fuskarta gefe ɗaya, saboda wani irin shock da taji, Kyanshi na ƙoƙarin jan hankalinta, idan har taci gaba da kallonshi zata fara danasanin janye jiki dashi, "Angel zan tafi, Amma kafin nan, ina neman alfarma a wurinki, ina fata zaki yi mini abunda nakeso a ƙaro na karshe, Muryarta ƙasa ƙasa tace"menene"? "Ki kula mini da kanki, sannan an kawo mana breakfast ɗin mu, kada damuwa ta sanya ki gaza cin abinci nasan kina jin yunwa, ki samu wanda zai taimaka miki acikinsu wurin yin tafiya saboda ƙafafuwanki sun raunata sosai, ba zaki Iya taka su ba, bayan haka Jiya na same ki acikin mawuyacin hali kina ambaton sunan daddynki, zai iya yiyuwa kinyi ƴan gane gane da suka shafi mahaifinki, wanda ba gaskiya bane, inaso ki kwantar da hankalin ki, akan wannan, after that, akwai taimakon da zan Iya yi maki, ta yadda zaki gane cewa, mahaifinki da batool awani hali suke ciki, idan har kin amince mini zan nuna maki," wani irin kallo angel take binshi dashi na rainin wayau, sai kace wani malamin duba, da alama yana ƙoƙarin yi mata wasa da hankaline, "Nasan zaiyi wuya ki yarda dani, but pls Ki bani dama"muryarshi ce ta katse mata zancen zucinta da take Yi, shiru ta ɗanyi tana was wasin kalaman shi acikin zuciyarta, kafin ta ɗan yamutsa fuska tace"its ok, ka nuna mini ta wace hanya zan iya gane a wani hali suke Ciki," Ba ƙaramin daɗi yaji ba, da sauri ya Juya mata bayan shi tare da cewa"Ki hau in goya ki," fuskarta a ɗaure tace"Ina zaka kaini"? Ya bata amsa da cewa"Cikin toilet ɗin mu," ba don taso ba, ta yunƙura daƙyar ta miƙe xaune tana faman cizon la66anta, ta sanya hannayenta biyu ta ruƙoshi, Ta hau saman bayan shi, ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu ɗauke da ita a bayan shi, Sam bata lura da sabbin gadajen da aka kawo musu acikin ɗakinsu ba, Saboda ta lumshe idanuwanta, yayin da yake wucewa da ita cikin toilet ɗin, Bayan ya shiga cikin makewayin nasu, wanda keda glass window ɗin nan, Yayi mamakin ganin Kayan amfanin da aka zuba musu sababbi acikin toilet ɗin su, An gyara shi tsaf komai a tsaftace, An ajiye musu trash can mai girma, Daga can sama Jikin bango inda cabinet dinsu Yake, Care product ne a jere tun daga kan hair gel, shower gel, conditioner, komai ma aka tarkata musu hada Toothbrushes da aka ajiye musu acikin holder dinsu, tare da toothpaste, Kuma kowani product yana ɗauke da sunan kurkukun ƙaddara, hakan na nufin ma'aikatan Prison ɗinne suka haɗa su, Ya yi farin Cikin ganin sabbin kayan amfanin da aka sanya musu acikin toilet, ta wani 6angaren kuma sam Bai ji sun kwanta mishi a ranshi ba, tun da ba dawwama zasu yi cikin farin ba, Jin yaƙi cigaba da tafiya yasa ta ɗan ɗago da kanta daga saman kafaɗar shi, Ta cunkuli fatar cikinshi da hannunta, Har saida ya ɗan ciji la66ansa saboda zafin daya ji, Muryarta a kausasace tace"Idan ba zaka nuna mini ba, ka sauke ni in koma ɗaki," Muryarshi a sanyaye ya furta mata am sorry, Taja tsoki, tafiya yaci gaba da yi cikin toilet ɗin ya nufi ƙatuwar tukunyar fulawar nan dake a killace Jikin bango, Anan ya ɗan zuƙunna ya sauke Angel, ta xauna a ƙasa tana faman lumshe idanuwanta, ta ko'ina raɗaɗi take ji ajikinta, sai lokacin ta lura da sabbin kayan dake a cikin toilet dinsu, da mamaki akan fuskarta take binsu da kallon ƙurulla, Sai ta dinga gani kamar ba gaskiya idanuwanta suke nuna mata ba, "Lokacin da kuna bacci, Giants suka shigo da su, hada new metal beds da boxes guda biyu, ina expecting din sabbin prisoners xa'a kawo mana" Danish ne ya kora mata bayani, Ganin yadda take bin ko'ina na toilet din da kallo yasan dole ta buƙaci jin daga ina aka same su, Ko kaɗan bata yi farin Ciki da ganinsu ba, Ita fa a halin yanzu komai na kurkukun ta tsane shi, abu ɗaya ne idan aka daina Yi musu xata so shi harma ta haƙura ta rungumi ƙaddararta, su cigaba da yin rayuwarsu Har Illah masha Allahu, shine a daina ɗaukar ƴan uwansu ana lalata rayuwarsu, sai dai tasan abune mai wuya, wannan dalilin ne ma yasa zata cigaba da neman hanyar da zata ku6utar dasu, domin kuwa babu fashi, Shiga Cikin kurkuku yanzu ta fara, Babu gudu babu ja da baya! ba'a halicce ta don ta zama raguwa ba, ita ɗin Jinin jarumai ce, masu dakakkiyar zuciya, waɗanda suka Yi imani da Allah batare da was wasi ba! duk da abunda ya faru da ita jiya, hakan baisa zuciyarta ta karaya ba, Sai ma taji kamar ana ƙara encouraging ɗinta akan taci gaba da bibiyarsu, a mutu ko ae rai, Kuma taci alwashin daga rana irin ta yau bazata ƙara sakin baki tayi bacci ba, Zata dinga raba dare biyu, kodan ta dinga kai kukanta wurin Allah, akan halin da suke aciki da kuma ƴar uwarsu batool!........" Ya jima yana kallonta ganin yadda numfashinta ke fita, ta ciccije la66anta, bakomai yajawo hakan ba face zancen zucin da take Yi, daga cikin zuciyarta, "Angel!!" Firgigit tayi Jin muryarshi acikin kunnuwanta, wani irin kallo ta jefa mishi, da sauri yace"Ki ɗan jira ni, Yanzu xan dawo" Bata amsa mishi ba, dama bai sanya ran zata tanka mishi ba, don ya lura yau mulki take ji. Miƙewa Yayi da sauri Ya juya ya fuce daga Cikin toilet ɗin, badajimawa ba sai gashi Ya shigo ciki hannun shi ruƙe da robar ruwan daya yayyafa mata afuskarta ɗazu Cikin ɗaki, Bin shi da kallo tayi har ya ƙarasa gaban fanfo. ya zuƙunna Ya kunna shi, ruwa ya shiga kwararowa ya tarba robar, saida taci ka tukunna ya miƙe da azama ya dawo inda take zaune jikin bango, Ya zuƙunna agaban tukunyar fulawar, ya ɗan saci kallonta ta wutsiyar idanuwanshi, harara yaga tana jefa mishi, ƙayataccen murmushi ya saki tare da cewa"Idanuwanki basu gajiya da yin harara"? Murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi, tana faman hura hanci tace "Bai shafe ka ba" Yace "its ok am sorry, abunda zan nuna maki ayanzu, sharaɗin shine, Koda ace zuciyarki ta ƙaryata hakan to kada ki amince just ki yarda kawai da duk wani abu da zan faɗi batare da kokwanto ba," bata amsa mishi ba, sai ma ta juya mishi ƙeya, Bai damu ba, yaci gaba da cewa"yanzu inaso ki rufe idanuwanki", rai a6ace tace"saboda me xan rufe idanuwana"? Yatsina fuska yayi don tafara hayaƙa shi da tsiwarta, "Kiyi kawai abunda nace miki, asannu zaki fahimce ni" Sai da taja guntun tsoki mai sauti, kafin ta runtse idanuwa nta, tana faman murga baki, Bai san ya akai ya tsinci kanshi da kallon kyakkyawar fuskarta ba, sai yaga tafi yi mishi kyau a haka, duk da raunin dake akan fuskarta, sai ma suka ƙara mata kyau especially heart shaped lips ɗinta da suke abushe sun faffashe, kamar ta shafa musu jan baki pink, bakomai ya ƙara ƙawata fuskarta ba face gashin jagirarta masu tsayi dark brown dasu. Jin shiru Danish baice ta buɗe idanuwanta ba, yasa ta harzuƙa ta yunƙuro zata wage baki ta zazzaga mishi masifa, Yai saurin cewa"Saura kaɗan" ajiyar zuciya ta ɗan sauke Cikin ƙagara da son jin me zai ce next, "Ki buɗe idanuwanki a hankali," mutsu mutsu ta soma yi cikin wani irin yanayi ta ɗan waresu ta ƙara buɗesu kafin ta zarosu tana ƙarewa tukunyar fulawar kallo, abun mamaki abun al'ajabi, yauƙanannun fulawowin dake acikinta waɗanda sun jima da bushewa duk sun yagalgale sun lafe cikin ƙasar dake acikinta, ɗaya daga Cikinsu tagani ta miƙe ta bubbuɗe ganyayyakin jikinta sun wawware tayi matuƙar ɗaukar hankalinta, musamman launin Jikinta Ja da ya ciza, tsabar mamaki ya hana ta rufe bakinta, Idan ta kalli furan sai kuma ta kalli fuskar Danish, Har dai tagaza jurewa tace"taya akai kayi hakan? Kamar a mafarki," "Ba shi yakamata ki tambayeni ba, wannan furen da kika gani ki ɗauka cewa ran mutun ne mai numfashi a jikin shi " Ya ƙarasa maganar tare dakai hannu ya shafa ganyen shi tare da cewa"Batool ɗinki ce, Our lovely sister, idan kika kalli furan da kyau, zaki ga yana da cikakkiyar lafiya ajikinshi, Launin shi ya ciza, hakan na nufin batul aduk inda take a yanzu tana acikin ƙoshin lafiya, Idan kuma ki gaka ganyen jikin furan Yana fitar da ruwa kamar zufa batare da an yayyafa mashi ruwa ba, that mean batool kuka take yi tana kewan ƴan uwanta, idan kuma ganyen ya kwanta jikin ƙasar dake acikin fulawar, to batool bacci take yi........" tunda ya soma kora bata jawabi, take kallonshi babu wasa a fuskarshi, Yadda kasan irin malamin duban nan, sai da yakai ƙarshen maganarshi tukunna tace"to idan furan ya mutu fa me hakan yake nufi? Maimakon ya bata amsa sai ya sadda kanshi ƙasa, tuni ta gane me hakan ke nufi wato mamallakin furan ya mutu kenan, "Baka amsa mini tambayata ba," ɗagowa yai da kanshi ya ɗaura idanuwanshi akan fuskarta yace"idan ganyen dake ajikin furan Ya bushe ƙamas Ya tsotse ko ya fiffige, Hakan yana nufin mamallakinsa yana acikin mawuyacin hali, Idan kuma ganyen furan ya mutu, ko ansa mishi ruwa bazai tashi ba, ma'anar hakan mamallakinsa ya mutu baya araye" duk da bata gasgata maganarshi ba, amma sai da taji gabanta ya faɗi ras, muryarta na ɗan rawa tace"Shi...shi fa daddyna? Ina nashi furan yake? Taya za'ae in iya gane cewa yana a raye ko ya mutu?" aruɗe take jera mashi tambayoyin, Kwantar mata da hankali yayi, "Ki natsu yanzu xan duba maki na daddyn ki amma kafin nan Kiyi mini alƙawarin cewa komai ki ka gani ba zaki yi kuka ba, idan kuma muka yi nasarar ganin furan daddynki Cikin ƙoshin lafiya, zaki bani abinci abaki. Nima in baki, a karo na ƙarshe kafin mu ƙauracewa juna," da yake a ƙagare take da son gani, da sauri tace mashi eh ta amince, yace to ta rufe idanuwanta, Bayan ta rufe su, Na ɗan wani lokaci, Yace ta buɗesu a hankali, Kamar wata sakarya haka take bin umarninshi, tunkafin ta ƙarasa buɗe idanuwanta ta soma hango fure Launin Kore, a gaggauce ta zare eyes ɗinta akan furan har zata fara Farin ciki sai kuma ta lura da naƙasar dake a ƙasan furen ya ɗan lanƙwashe alamar ba lafiya atattare da shi. Wasu irin zafafan hawayene suka wanke fuskarta, Har wani zazza6i taji ajikinta, muryarta adabarbarce take faɗin" Danish Ya mutu ko? Naga ganyen kamar ya karye, Dan Allah ka faɗa mini, zuciyata zata Iya bugawa...." tsananin tausayinta ne ya kama shi ganin yadda tabi ta ruɗe, bakomai yake tunani ba face Iyayen shi, Shi da bai rayu dasu ba, kuma ba shi da tabbacin Suna araye ko sun mutu, shin dagaske sune suka sadaukar dashi? Anya kuwa shima yana da iyaye kamar kowa? A lokacin baya kafin zuwan angel bai ta6a tunanin wasu iyaye ba, gani suke Yi kamar tsohuwa itace komai na rayuwarsu, zuwan angel ne yasa suka fara tunanin suma ina iyayen su suke? Idan tana basu labarin irin ƙaunar da daddynta yake yi mata sai suji inama ace suma sunyi rayuwa da nasu Iyayen........." Sautin kukan angel daya ƙaru ne yasa shi Barin yin zancen zucin nashi ya ɗago ya kalleta, ta wage baki sai kuka take Yi, baisan time daya saki murmushi ba, bai ta6a ganin ƙuruciyarta ba sai yau, da ta gasgata abunda shi kanshi baida tabbaci akanshi, kawai yana nuna mata ne don ya samu ya kwantar mata da hankalinta, Ahankali ya sanya hannayenshi biyu Ya tallabo fuskarta, Yana ƙare mata kallo, hawaye ta ko'ina, Cikin sanyin murya yace"kin manta bayanin da nayi maki? Idan har furan bai bushe ba ko ya fiffige ya mutu, to mamallakinsa yana araye," Cikin shessheƙar kuka tace"Am...amma ae ya naƙasa, kai ba ka ga Ciwo a jikin iccen shi ba" Da lumsassun idanuwanshi ya ɗan kalli furan kafin yace"na gani, sai dai ba hakan yana nufin mamallakinsa ya mutu ba, sai dai ko karyewa ƙafarshi tayi sakamakon wani rauni daya ji, ko kuma wani ciwonne na daban ya same shi a ƙafar shi, kinji ma'anar raunin dake ajikin furen" hannu tasa tana share hawayenta hankalinta har ya ɗan kwanta, "Kuma Allah idan har na gane cewa ƙarya kake Yi mini, to ka sani har bada babu ni babu kai, kuma kullum xan dinga zuwa ina duba furennin ina basu ruwa akai akai. Kodan kada su mutu, hakan kuma ba yana nufin na yarda da maganganun ka bane kawai dai zanyi amfani dasu ne" ƙiris ya rage ya saki dariya, jin wautarta, Ta wani 6angaren kuma yaji daɗi sosai, koba komai yasanyata farin Ciki, ya kuma bata aikin yi, duk da shima yana jin fargabar ranar da zata gane cewa ƙarya yake yi mata, Taso ta tambaye shi furan aunty aneelerh kodan tasan awani hali take aciki, amma sai ta fasa don ta gaji da zama Acikin toilet ɗin, Gashi tana buƙatar Yin wanka sai dai tasan bazata Iya ba saboda ga6o6in jikinta dake yi mata ciwo, "Muje mu ci abinci, Ko xaki yi wanka in taimaka maki"? Sakin baki tayi tana kallon shi jin abunda yace, "Yanzu idan nace ka taimaka min inyi wanka? Kuma saika amince"? Fuskarta a ɗaure tayi mishi maganar, baisan sadda ya furta"ae naga komai jiya so ba wani abu bane, nima ae kin ta6a gani na naked, bai kamata ki damu ba, har wankan ma sai mu yi atare," ras taji gabanta Ya faɗi, Ta zazzare gray eyes dinta tana kallonshi, Da sauri ya sanya tafin hannayenshi biyu ya toshe kunnuwanshi, saboda gudun tsiwar da zatayi mashi, shi kanshi baisan Ya furta maganar ba, su6ul da baka yai, sosai ta runtse idanuwanta, tana ƙoƙarin tariyo abunda ya faru jiya, saboda lokacin data dura tagar nan, batasan cewa Ya zame wandon jikinta ba, Ita dai kawai tasan ta dura ta miƙi hanya, sai yanzu da ya yi wannan maganar ya tuna mata da komai, aikuwa ta daddage ta fasa wata irin gigitacciyar ƙara, Jikinshi ya kama rawa, saboda sautin daya fita hatta masu bacci na Cikin ɗaki saida suka farka, Kusan atare suka yaye bargunansu, agaggauce suka dudduro daga saman gadajensu, da gudun gaske suka nufi sashen toilets dinsu hada masu Yin tuntu6e garin sauri, Haris ne agaba su Hanna na abiye dashi, kamar wasu sabbin mahaukata haka suka faɗo Cikin toilet ɗin, Gaba ɗayansu ne suka shugo ciki, Sai faman haki suke yi, a matuƙar ruɗe suke kallon angel da danish, ta runtse idanuwanta jikinta har wani jijjiga yake yi kamar mai iskokai, muryarsu da alamun baccin bai ishe su ba, suka shiga tambayarsu lafiya, azeeza tuni ta nufi angel ita da parveen suka zukunna suna shafa fuskarta tare da tambayarta lafiya meya faru da ita? Meyasa take kuka, Hanna dasu rubina suka karasa suma suka zuƙunna agabanta, Mazan da suka rage a tsaye sai aika mishi da harara suke Yi, gani suke kamar wani mugun abun yayi mata, dama tun Juya suke zargin shine yayi mata bugun tsiya da har ta raunata, Haris yana huci yace"wato saboda kaga muna bacci shine ka ɗaukota daga saman gadonta ka kawo ta cikin toilet ka naɗe hannun rigarka ka nannausheta saboda bugun da ka yi mata jiya bai ishe ka ba, Wai danish me kake so ka zama ne? Slowly Ya xame hands dinshi daga saman ears ɗin shi daya toshe, hawaye ne kwance acikin fararen idanuwanshi, Tsawar angel tayi matuƙar ta6a kanshi ta tsokano mishi da lalurarshi, shiyasa jikinshi ya kama kakarwa, Javed yace"Ae bazai ta6a buɗe baki ya bamu amsa ba, mugu kawai, yanzu xamu ji komai abakinta tunda ta farfaɗo, serious idan har tace kaine ka dake ta, zaka ji a jikinka ne," Mubeen dai bai ce komai ba, Ya jingina bayanshi Jikin bango yana kallonsu, Gaba ɗayansu babu wanda Ya lura da sabbin kayan da aka sanya musu acikin toilet ɗinsu, saboda hankalin su ba a kwance yake ba, Su Deeja sai faman lallashinta suke Yi, Ganin yadda take ta kuka, Tana faɗin Wlh ka cuce ni, Na tsane ka Danish, ashe kai ɗan iska ne ban sani ba, Allah ya isa bazan ta6a yafe maka ba, tun da ka gane min budurci na....." muryarta ashaƙe ta ƙarasa maganar, ita kanta batasan menene ma'anar budurci ba, tadai san kalmar acikin kanta, azeeza ta janyota ajikinta ta rungumeta tare da zagayo da hannayenta saman bayanta, tana ɗan bubbugashi, Hankalinsu Haris yai matukar tashi jin abunda tace har suna haɗa baki wurin maimaita kalmar budurci, basu ta6a ji ba sai abakinta, Amma sai suka ɗauka cewa wurin bugunta ne Ya ta6a wani organ na jikinta, Shi take kira da budurci, nan fa suka harzuƙu, Naufal Ya shaƙo wuyan rigar Danish Ya ɗago dashi Yana huci yace"ka faɗa mana uban me kayi mata? Taya akai ka gane mata budurcinta? Saboda baƙin hali irin naka"! bawan Allah ya rasa ya zaiyi, hayaniyar su ba ƙaramin tafasa zuciyarshi take yi ba, Ga wani irin zafi da jikinshi ya ɗauka, haris ne ya lura da yadda yake lumshe idanuwanshi, Da sauri ya ƙarasa gabansu Ya ruƙo hannun naufal ya janye shi daga jikinshi, wani irin jiri ne ya kwashi danish Ya tafi xai faɗi ƙasa sai dai bai kaiga ƙarasawa ba, haris Ya tallaboshi da hannu biyu, ya ruƙo shi zuwa saman jikinshi, Ya rungume shi sosai, yana ambaton sunanshi, duk da ƙarnin Jinin da ke a jikinshi hakan baisa haris Ya guji ta6a shi ba, kallonsu mubben yai tare da cewa"Pls ku taimaka mini, mu kai shi daki" Turo baki Javed, Naufal kuma ya juya mishi ƙeya, mubeen Ya ɗaga kai ya kalli ceilling ɗin toilet, alamar bazasu ta6a shi ba, "Ka bani mamaki haris, Kafi kowa nuna 6acin rai akan abunda Danish yayi mana, amma sai gashi yanzu nema ka ke yi ka taimake shi" Rai a6ace naufal yai maganar, Fuskar haris ɗauke da matsananciyar damuwa yace"bazan iya jure ganin shi acikin mawuyacin hali ba, Shi ɗan uwanmu ne, tabbas yayi mana kuskure amma abunda nake so ku fahimta, koda ace danish Bai miƙa ma giant batool ba, to xasu ɗaukota ne da kansu, don su tafi da ita, baida za6ine," Sunyi mamakin canzawar da haris yai lokaci ɗaya, duk dan sunsan irin ƙaunar dake a tsakanin shi da Danish, dole yaji tausayin shi a halin dayake ciki, Ganin sunƙi taimaka shi yasa shi yin fushi, Yaja danish shi kaɗai ya shiga dashi cikin ɗaki ya kwantar dashi saman gadon shi, idonshi biyu sai dai jikin nashi ne ba ƙwari, Shigowa cikin ɗakin Hanna da deeja su kayi angel tana a goye bayan hannah, Ta rurruƙeta da hannu biyu. A saman gadonta hanna ta kwantar da ita, sai faman sauke ajiyar zuciya take yi, a can ƙasan zuciyarta wani irin ƙunci ne ya cunkushe mata, danish yaga tsiraicinta, Babu sauran kwanciyar hankali, yanzu shikenan zai dinga ganinta tsirara koda ace da kaya ajikinta, tuna wannan yasa ta ƙara fashewa da wani sabon kukan, gaba ɗaya hankalinsu Ya dawo kanta, baiwar Allah bakinta duk ciwo amma ahaka take riskar kuka, "Dan Allah angel ki daina kuka, Kiyi haƙuri, Ki faɗa mana me danish yayi maki? Hibbe ce tai mata magana, duk sun shiga damuwa, Azeeza tace"ina matuƙar jin tausayin angel, taji jiki ba kaɗan ba, danish bai kyauta mana ba Allah," Kowa yana tofa albarkacin bakinsa, danish dai duk yana sauraronsu ya lumshe idanuwanshi yayin da hannayen shi biyu ya rungume pillow dasu, sai da Angel ta gama shan kukanta mai isarta, tukunna tace musu ita fa bashi bane Yayi silar halin da tashiga ba, hasalima taimakon ta yayi a jiyan nan, a dole ta ƙirƙiro ƙarya ta fada musu cewa, Ta fita hayyacinta ne Saboda ɗauke batool da akayi shine ta fada toilet ta ɗauki bokitin nan na ƙarfe ta bubbuge jikinta dashi, da ta galabaita shine ta faɗi ta sume cikin toilet ɗin, ta faɗa musu hakan ne badan tana so ta kare shi ba, face don ta kwantar musu da hankalinsu, Gaba ɗaya sunyi amanna da abunda ta fada musu, har suka ɗanyi danasanin maganganun da suka gaya mishi duk da haushin sa da suke ji, Duk wannan abunda dake faruwa babu wanda ya ankara da sabbin gadajen da aka sanya musu acikin dakinsu, Har sai da suka fara Jin yunwa, Parveen tana hamma tare da kai hannu ta shafa cikinta ta soma ambaton Yunwa take ji, Tana rufe baki Danish yace "An kawo mana breakfast tun ɗazu da safe, time da kuna bacci," batare daya buɗe idanuwanshi ba, yayi maganar, Atare suka Juya baya don suka ga In dagaske ne an kawo musu abinci, duk da sun cewa danish baya ƙarya..... *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Kaitsaye idanuwansu suka sauka akan sabbin gadajen da aka jera a cikin ɗakin nasu, gaba ɗaya suka zazzare idanuwansu saboda tsabar mamaki duk suka bi suka ruɗe, Sun saki baki suna kallon Ikon Allah saboda ba su yi tsammanin zasu yi arba da wani baƙon abu a cikin ɗakin su ba, da mamaki akan fuskar parveen Tace"Kuna ganin abunda nake gani kuwa? ko dai idanuwana ne suke nuna min ba dai dai ba"? Azeeza tace"Ae duk mun gani sabbin gadaje ne har kusan goma sha biyar tare da Akwatuna Biyu, ko a ina aka same su"? Danish ne ya basu amsa da cewa Ɗazu da safe kuna bacci giants suka kawo su, akwai ma kayan amfani da aka sanya mana a toilets" deeja tace"hakan na nufin zamu kar6i baƙuncin wasu prisoners ɗin"? Tai tambayar fuskarta babu walwala, domin kuwa ba abun farin ciki bane agare su, da duk wani mai hankali ba zai so wani bawa ya ɗanɗani irin rayuwar ƙuncin da suke yi ba. "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Ni dai har ga Allah bana farin ciki da zuwan waɗannan Sabbin prisoners ɗin, Saboda bana so suma su ɗanɗani irin rayuwar da muke Yi acikin kurkukun nan" Deeja ce tai maganar, Haris yace"ni kaina bana son mu ƙara yawa, muna fama da kanmu xa'a ƙaro mana wani ciwon kan" hibba tace" ni babban baƙin ciki na, Mu da muke fatan wata rana mubar kurkukun nan, sai gashi ana ƙoƙarin kawo mana wasu har mutum goma sha biyar zamu ƙara cunkushewa, tashin hankali kuma zai ƙaru" hannah tace mu je mu duba gadajen ni sunyi mini kyau, Dama mu ma a canza mana sababbin," wani kallon harara deeja tai mata "Wato ke ta gado kike yi, to Allah yasa acanza miki gadon kiyi ta zama cikin prison ɗin, mu kuma Allah ya bamu sa'ar fita daga cikinsa" hanna tana ƴar dariya tace ba amin ba, Aniyarki tabi ki," Agaban gadajen suka tsaitsaya cirko cirko suna ƙare musu kallo, Sabbi gal dasu sunyi matuƙar yin kyau, Azeeza da parveen hada ƙoƙarin hawa saman wasu daga Cikinsu suna faɗin Bari su ɗana kafin baƙi su ƙaraso, azeeza tace ita yau ma asaman sabon gado xata kwana, suma sauran su ka ce duk anan zasu kwana su sha lagwada, sai da suka gama kallon gadajen kafin suka koma kan akwatunan suna kallonsu tare da Floor laps ɗin da aka ajiye musu, ba ƙaramin daɗi suka ji ba, dama fitilun dake gare su sunyi kaɗan, Idan dare yayi sai dai mutun yai ta yawo da fitila zuwa toilet, amma yanzu sun yanke shawarar zasu ɗauki ƙananun fitilun guda uku, su ajiye su a kowani toilet, don su sawwaƙawa kansu. a cikinsu an rasa wanda zai buɗe boxes ɗin nan, duk sunyi tsammanin Ba mallakin su bane, na sabbin prisoners ne da za'a kawo shiyasa basu ta6a su ba, saima suka kawar dasu zuwa bakin gadajen, bayan sun gama da ɗaki, eve tace"su je su duba toilets suga sabbin kayan da aka sanya musu, Parveen ta bubbuga ƙafa tare da cewa"Mu fara Cin abinci tukunna idan ku ba ku jin yunwa ni ina ji" sai da ta yi maganar suka tuna da cikinsu, hankalinsu gaba ɗaya yana akan Kayan da aka kawo musu, Atare suka nufi dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Kowa ya natsu zasu fara Cin abinci, Duk wannan abun dake faruwa angel da danish suna kishingiɗe saman gadajensu, sun Juyawa juna baya babu mai fuskantar wani, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarshi, ita dai damuwarta batool ɗinta, ko awani hali take ciki? Fatanta Allah yasa maganar da danish ya faɗa mata akan furen nan ta zama gaskiya, Bayan su parveeen sun kammala Cin abinci. Sauran da suka rage ma angel da danish, Haris yace su je su ɗauko kwandon batool a kwashe musu nasu aciki, Nan fa duk jikinsu yae sanyi tunawa da batool ɗinsu, duk da dama tana acikin ransu ba yadda za su yi ne, tsakaninsu da ita addu'a ce kawai. Hanna ce taje ta ɗauko kwandon batool dake a kusa da gadon danish Kifin da suka ajiye mishi tun jiya duk ya bushe jikinshi, hada ƴar rabin gwandar da baici ba, nuna musu kwandon tai tare da cewa"Fried fish din ma ya lalace bari naje na zubar dashi, in wanko basket din sai asanya musu abincin aciki....." tunkan ta ƙarasa maganar parveen tai wuf ta sanya hannu ta kar6e kwandon tana faɗin"Inji wa yace maki ya lalace, bani nan ki gani, yanzu nan zan sanya shi a hanya..." Murmushi suka saki gaba ɗayan su yayin da suke kallonta, A ƙasa ta zuƙunna ta ajiye kwandon tare da kai hannu Ciki tana tatta6a Jikin kifin, azeeza tace"amma parveen baki da hankali, tun jiya fa yake a buɗe cututtuka duk sun hau jikin shi a haka zaki ce? Salon Cikin ki ya 6aci," Harara parveen ta watsa mata tare da cewa"Bai shafe ki ba ae cikina ne ba na ki ba" duk yadda suka so su hanata Cin fried fish din nan taƙi ji, tai kunnan uwar shegu dasu, Zama tayi na musamman tacinye shi tass bayan ta gama da kanta taje toilet ta wanko kwandon tass ta shigo dashi Cikin ɗakin ta miƙa ma Hanna kwandon, tasa hannu ta kar6a ta zuƙunna gaban farantin da niyar ta ɗibar musu wanda suka rage musu, Muryar Angel ta dakatar da ita, "Kada ki haɗa mini abinci dashi, Ki ware mini nawa daban" idanuwanta arufe tai maganar, batare data motsa daga kwancen da take asaman gadonta ba, Haris yace ki ɗibar mata nata ki je ki taimaka mata taci, Ni kuma zan kaima Danish nashi, ta amsa mashi da toh, Kafin marece yayi saida suka shiga cikin kowani toilet suka dudduba sabbin kayan da aka sanya musu, bakomai yafi burgesu ba face Hair gel kodan sabo da gashin kansu, sun samu na gyara shi, basu fara amfani dasu aranar ba, saboda sunfi so sai angel ta samu sauƙi ta taimaka masu wurin gyarawa. A daren ranar Saman Sababbin gadajen nan kowannansu ya kwanta, in ka cire mutun biyun nan, Angel da kuma danish suna asaman gadajen su, jiki duk ba daɗi da ga ita har shi, ko wanka sun kasa tashi su yi, room ɗinsu yayi wani irin haske tamkar da rana saboda sabbin fitilun nan da suka kunna hasken su ya gauraye ko'ina gwanin ban sha'awa, Cikin nishaɗi suke ta wasa da pillows, Idan wannan ya jefa ma wannan sai shima yaɗauko pillow Ya jefa ma na kusa dashi, yadda kasan basu da wata damuwa bayin Allah, Angel tana jiyo hayaniyar su suna yin fira bayan sun gama wasa da pillown deeja tace"Nifa gani nake kamar zamu dawwama acikin kurkukun nan, tunda ga wasu ma za'a ƙaro mana" Parveen tace"ai kwara su zo suma su ɗanɗani irin zaman da muke yi, su ji in akwai daɗi," Azeeza tace muguwa parveen yanzu har wasu kike yi ma fatan suyi irin rayuwar da muke yi"? Parveen tana dariya tace"Nifa na faɗi hakanne kodan mu samu a ƙyale mu adaina ɗaukarmu mu tsaffin prisoners, su kuma sabbin sai acigaba da ɗaukarsu, Kunga mun hutu ko ba haka ba,' Murmushi angel ta ɗan saki, yayin da idanuwanta suke fuskantar ceilling, ta ɗan ɗaga murya tana faɗin"parveen maganar da ki kayi sam ba ta yi mini daɗi ba bai kamata kina yi musu mummunan fata ba, tun kafin zuwansu ma, Ni tausayinsu ma nake ji, su da basu san komai ba, wlh ko maƙiyina bana yi mishi fatan shiga wannan kurkukun ƙaddarar, ballanta su da za'a kawo mana, musamman in ya kasance daga waje za'a kawo su, Ba ƴan asalin cikin kurkukun bane" jin wannan magnar ta angel yasa parveen tace"patient Ashe baki yi bacci ba, da ace nasan idonki biyu da ban furtata ba," dariya su kayi gaba ɗayansu, Angel tace"Oh, wato ni sarkin yin wa'azi ko? Kiji tsoron Allah parveen, Nidai komai na faɗi inayi ne don in taimaka muku wurin gyara rayuwarku," hanna tace"ai kina ƙoƙari kuma muna jin dadi sosai, muna fatan Allah yabarmu tare dake har bada, har mu shiga aljanna," murmushi angel ta ɗan saki, tare da yunƙurawa ta miƙe zaune saman gadonta ta jingina bayanta jikin bango, ta wutsiyar idonta take satar kallon danish, Ya rungume pillow sai bacci yake yi, aranta tace shi ko tsamin jikinshi baiji, " can kuma ta ta6e baki tana faɗin to ni meye ruwana dashi, " ta ambaci hakan tare da jan tsoki, Muryar Javed ta jiyo daga inda take fuskantarsu Yana ta yi musu faɗa akan su yi musu shiru sun hanasu runtsawa, su kuma sun dage sai zuba suke yi kamar kanyar da bata da daɗi, kasa kunne ta yi tana sauraron firar da suke Yi, sai taji akan gidan daddynta su ke magana, lamarin ya ɗan bata mamaki, jin parveen tana faɗin ai wlh idan suka gudu daga Cikin kurkukun suka koma gidansu angel ita acikin kitchen zata dinga kwana, ko dan ta dinga dafa abunda take so" Sakin baki angel tai tana sauraron ikon Allah, aranta tace wato ita parveen burinta na duniya shine abinci, taci abinci bata gajiya, mai iya rainonta sai manomi, amma wannan in baka da ƙarfin jari saita naƙasa ka," bata kammala zancen zucin nata ba, ta jiyo muryar azeeza tana faɗin"Ni dai ba ruwana da wani abinci, Idan Allah yasa muka bar kurkukun nan muka koma gidansu angel, A ɗakin daddynta zan dinga kwanta, nima ya rungumeni kamar yadda yake yi ma angel suna kwana tare," Haris yace"Sannu uwar son banza, menene alaƙarki dashi da har xaki kwana a ɗakinshi Ya rungume ki," zum6ura baki tae ashagwa6e ta bashi amsa da cewa"Ae ta faɗa mana cewa, Daddynta yana son ƴa'ƴa, Kaga kenan muma zamu zama kamar angel awurinshi" naufal yace"Kuna yaudarar kan ku dayawa, ku ɗan sarara mana, kada wata rana zuciyarku ta karaya, a garin sanyawa rai abunda bazai ta6a yiyuwa ba," Kafin wani ya kuma cewa wani abu angel tace"Inji wa ya faɗa maka cewa bazai ta6a yiwuwa ba? Ƙarancin imanin ku shine zaisa mu dawwama acikin kurkukun nan, bai kamata kuna sage musu gwiwa ba, Idan Allah yaso a yau ɗin nan zamu iya barin kurkukun nan wannan ba abun mamaki bane, amma nasan zaiyi wuya ku yarda da maganata har sai ranar da Allah yasa muka ku6uta inda rai da lafiya, tukunna zaku tuna da wannan maganar dana faɗa maku!!!" Haris yace"kada ki damu, Ni zan tuna maki, wannan ba wani abu bane" yana magana yana dariya kamar wani zautacce, Ya raina maganarta, ba ƙaramin haushi taji ba, tadai yi shiru ne ta ƙyale shi saboda sanin irin jahilcin dake ɗawainiya dashi. Lokacin da bacci yai awon gaba dasu ita kaɗai ta rage bata kwanta ba, kamar yadda tai alƙawarin xata dinga raba dare biyu domin ta samu damar yin addu'o'inta, tana Cikin yin addu'oin hawaye ta ko'ina akan fuskarta, danish ya farka ya ɗan miƙe xaune saman gadonshi yana kallonta, ganin tana ƙoƙarin juyowa ta kalli inda yake yasa shi yin saurin kawar da kanshi gefe, gudun kada ya sa6a alƙawarin daya ɗaukar mata, saukowa yai daga saman bed din shi Ya janyo bargonshi Ya nufi Cikin toilet dashi, Tana ta bin bayan shi da kallo Cike da mamakin me zai yi a irin wannan lokacin, tsawon mintuna sai gashi ya shigo ɗakin chest ɗin shi ɗaure da bargon, Alamar ya wanke uniform ɗin, Sun ishe shi da tsami, Sai lokacin ta tuna da yadda jikinta yake, ta dage tana ta yin addu'o'i batare data tsarkake shi ba, Yanke shawarar zuwa toilet din tayi don ta wanke kayanta ta samu tayi wanka, tana ƙoƙarin saukowa daga saman gadon ƙasusuwan jikinta suka rurruƙe har wani sauti suke badawa ƙas! ƙaƙas!! wani irin raɗaɗi taji ajikinta, ta ɗan cije la66anta tana faman ambaton wash Allah na, duk akan kunnan danish dake zaune saman gadonshi, Ya lumshe idanuwanshi, Tun da yai wanka sai yaji daɗin jikinshi, wata irin ni'ima ta saukar mishi, yaso ace suna shiri da juna daya taimaka mata wurin yin tafiya don ya fahimci cewa so take itama ta yi wankan, Ba yadda ta iya dole ta haƙura da yin wankan tayi zamanta tsakiyar gadon, a haka baccin yai awon gaba dasu, A kwana atashi ba wuya wurin Allah, Yau tsawon Sati biyu kenan ba'a dawo musu da batool ba, babu ita babu alamarta, Kullum sai sun sanya ran zasu ga an shigo da ita amma sai suji shiru, hatta sababbin prisoners da suke tsammanin za'a kawo musu har yau ba azo dasu ba, rashin dawo musu da batool yafi komai ɗaga musu da hankali, ganin sun sanya damuwa sosai yasa angel ta faɗa musu maganar da suka ta6a yi ita da batool, a inda take ce mata, tana so su haɗa hannu wurin sama ma junan su farin Ciki koda kuwa babu wani acikinsu, wannan maganar tayi matuƙar karya musu zuciya, domin kuwa ranar da angel ta faɗa musu ita, kusan kwana su ka yi a zaune suna jimamin rashin ta, sunyi matuƙar yin kewar ƴan uwarsu fiye da tunanin mai tunani, a ƙarshe da suka rasa abunyi sai suka koma suna biye ma angel, atare da ita suka zuwa toilet wurin tukunyar fulawar nan don suga awani hali batool take aciki, tun da ta basu labarin Abunda danish ya faɗa mata na cewa batool ɗinsu ce a jikin Jan furen nan shi kuma koren Na daddynta ne, abun ka ga masu ƙarancin hankali ga kuma ƙuruciyar dake ɗawainiya dasu duk sai suka yarda da zancen danish, a rana sau uku suke zuwa wurin furannin nan domin su basu ruwa, da safe da rana da daddare, wani lokacin har tsakar dare suna zuwa duba furen suga a wani yanayi yake, idan suka samu furen batool yana tsastsafo da ruwa ajikinshi, haka zasu zauna sunata kuka suna lallashin furen amatsayin batool suna yi mashi magiya akan yayi haƙuri ya daina kuka, Suna atare dashi, Idan kuma suka samu furen ya kwanta cikin ƙasar dake a ruƙe dashi, sai su yi ta jin daɗi suna faɗin batool bacci take yi, kada su takura mata su tafi su barta ta huta, duk wannan haukan da suke yi danish yana kallonsu, Ya rasa gane wani irin kaine dasu, shi yayi abu don ya faranta ma angel rai, su kuma sun ɗauka dagaske ne, gashi har suna ƙoƙarin zautar da kansu akan furennin bogi. A kowace rana idan dare yai kafin su kwanta bacci sai sunyi ma batool addu'a Akan Allah ya kare musu ita aduk inda take, tsawon kwanakin nan sunƙi sakewa da Danish suna atare dashi ne, badan sun yarda dashi ba, musamman angel ko kallo bai haɗa ta da shi, bawan Allah duk ya shiga damuwa daurewa kawai yake yi, amma rashin tanka mashi da take yi ba ƙaramin illata zuciyarshi take yi ba, yanzu takai ga ko wasa suke yi da zarar ya tsoma baki, to zata zame hannunta ne tace ta fasa, ƙiri ƙiri ta guje shi ta maida shi abokin gabanta, a ƙarshe daya gaji da irin wulaƙancin da take yi mishi, aikuwa ya janye jikin shi daga gare ta, Ya nisanta kanshi da duk wani abu da zai haɗa shi da ita, hakan ba ƙaramin takurata yai ba, itafa tafi son yai ta binta tana yakice shi, sai gashi reshe na neman ya juye da mujiya. *PRISONERS❤* A wata rana suna kwakkwance saman sabbin gadajen da suka gaje na baƙin prisoners sai sharar baccinsu suke yi, babu wanda ya farka acikin su, Gari tuni Ya jima da wayewa, A wannan lokacin ne motsun buɗe dakin tsohuwa Ya karaɗe Cikin ɗakin, A hankali ta buɗe ƙopar Hannunta ruƙe da sanda kamar kullum, fuskarta babu walwala, tsufanta ya fito sosai, jikinta na sanye Cikin rigar ta, Ta gado Launin Ja, Cigaba da dogara sandar tayi yayin da take tun karar Cikin dakin, Tayi mamakin ganinsu kwance saman sabbin gadajen da aka kawo maimakon ta gansu A saman nasu beds ɗin, Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, a fili tace"Zaman Prison yayi maku daɗi Jikokina, Kuna hutawarku Cikin walwala, Sai dai kun manta da Tsohuwa Tamira," Sai da tabi kowani gado ɗaya bayan ɗaya tana binsu da kallo, tun daga kan gadon haris da deeja, zuwa nasu Javed da rubina, a bakin gadon da angel take kwance ta ɗan dakata tana kallonta, ganin wani irin sabon salon kwanciya, ta wawware ƙafafuwanta, har sun sauko daga ƙasan gadon, gashin kanta duk ya tarwatse ya barbazo saman mattress ɗinta, fuskar tsohuwa asake tace"Unaisah mutuniyata sarkin tsiwa Ina matuƙar yinki," tana ambaton hakan taɗan ja da baya kaɗan, ta daddage ta buga sandar hannunta a ƙasa, Nan take ta bada wani irin sauti kamar fashewar bomb, agigice suka farka suna faman zazzare idanuwansu, saboda tsabar ruɗu parveen da rubina suka sauko daga saman gadajensu, Da gudun gaske suka nufi toilet zasu shige su 6oye, azeeza da tafi kowa jin tsoro tuni ta jima da shigewa ƙarƙashin gadonta, tsohuwa ta rikitar dasu, babu wanda ya lura da ita, sai da suka gama tsorata, Tukunna Ta soma Yi musu gyaran murya, Nan fa Hankalin kowa Ya dawo kanta, sai faman mutsustsuka idanuwansu suke yi, Na cikin toilet da suka 6oye sai gasu sun fito hannunsu ruƙe cikin na juna, azeeza ta leƙo daga ƙarƙashin gado don ta ga wanene yai musu gyaran murya tana yin tozali da fuskar tsohuwa sai gata ta fito tana faman sauke ajiyar zuciya, Da alama ta nishaɗantu da abunda ta yi musu, Sai tiƙar dariya take Yi, su kuwa sai faman sauke ajiyar zuciya suke yi hada masu dafe ƙirjinsu, hanna tace"Tsohuwa kin bamu tsoro, ƙiris ya rage in saki fitsari a wando," Dakatawa ta ɗanyi da yin dariyar da take yi, Ta dago tana kallonsu tace" Naji daɗin ganin ku cikin ƙoshin lafiya, Ina fata baku da wata damuwa"? Tai tambayar tana jiran amsarsu, atare suka haɗa baki wurin cewa"Ƴar uwarmu batool ba a dawo mana da ita ba, almost 2 weeks kenan, bamu san awani hali take ciki ba," shiru tsohuwa ta ɗanyi na wani lokaci kafin tace"ku ƙara haƙuri idan da rabon za'a dawo da ita, to za ku ganta ne, amma abunda nake so daku, ku daina sanya damuwa aranku" tsohuwa na rufe baki muryar Danish ta ratsa kunnanta, "Long time, ba mu ganki ba, kin daina zuwa wurin mu" Murmushi tayi tare da nuna shi da sandar hannunta tace"Shikaɗai ya damu dani, dama nasan babu wanda zaiyi kewata acikin ku idan bashi ɗin ba, maimakon da kuka ganni ku tambayeni lafiya na ɗauki tsawon lokaci banzo wurinku ba, amma babu wanda yae tunanin hakan," ta karasa maganar tana kwa6e fuskarta, hada jefa musu harara tana murguɗa musu baki, gaba ɗaya suka kama tiƙar dariya ganin yadda take murmura idanuwanta yadda kasan na gwaggwon buri, da alama yau wasa tazo tayi musu, "Kodan bani da amfani awurinku ne shiyasa kuka ƙi damuwa da rashina" shiru suka ɗanyi, angel dai tana zaune ta jingina bayanta jikin bango, Haris ne yai ƙoƙarin cewa"taya za'ae mu ƙi yin kewarki tsohuwa? ae munji daɗin irin taimakon da kika yi ma deeja, gashi ta samu sauƙi sosai ta wartsake," yakai karshen maganar tare da ɗan juyawa yana kallon deeja dake zaune gefen gadonta dake kusa da nashi, muryarta aɗan disashe tace"Nima inata so inyi maki godiya amma ban samu damar ganin ki ba, ranar da aka ɗauki batool, azeeza ta sume muka rasa ya zamuyi da ita, mun yayyafa mata ruwa ajikinta amma bata farka ba, Har ƙopar ɗakinki muka ƙwanƙwasa don kizo ki duba jikinta baki buɗe ba, shiyasa muka yi tsammanin ko baki nan ne," Jinjina kai ta ɗanyi tare da cewa"Hakane na ɗanyi nisan kiwo, Yanzu ma zuwa nayi don In duba ku ko akwai wani abu da kuke buƙata kafin in tafi" Basu fahimci me take nufi ba "Mu ba abunda muke buƙata, Batool kawai muke so a dawo mana da ita" acewarsu parveen, Tsohuwa tace"zata dawo ne, yanzu dai ku faɗa mini me ku ke so kafin in tafi, inji idan zan Iya yi maku shi" Ta6e baki angel tai tare da cewa"kamar dagaske, nasan ko mun nemi taimako awurinki bazaki Iya yi mana shi ba" Kallonta tsohuwa tay, kafin tace"Me ki ke so Unaisah"? Yadda tayi maganar ba bu wasa akan fuskarta, "Ki nuna mana hanyar da zamu fita daga Cikin kurkukun nan" shi ne abunda muke so" maimakon tsohuwa ta bata amsa saita fashe da dariya tana ɗan girgiza kai, daga bisani da ta tsagaita da yin dariyar tace"Kin buƙaci abunda bazan Iya yi maku shi ba, saboda yafi ƙarfina, Abunda nake so ki fahimta shine, Ni bakowa bace a gidan kurkukun nan, tun ban mallaki hankalina ba nake acikinsa, tsawon shekara da shekaru na rayu acikin kurkukun nan a matsayin prisoner kamar dai ku din nan, Nima tun ina ƙarama na taso acikinsa, Na jure duk wata gwagwarmayar dake acikinsa kafin na kawo wannan matsayin da nake dashi acikin kurkukun, ba lallai bane ku yarda dani ba, amma zan fada muku gaskiyata, Ni ban ta6a fita daga Cikinsa ba, Anan aka haifeni anan na rayu acikinsa nayi aure har na hayayyafa, akwai ya'yana da jikokina acikin kurkukun nan suna rayuwa". Tunda ta soma kora musu jawabi, angel take binta da wani irin kallon rainin wayau har sai da takai ƙarshen maganarta, sannan angel ta soma magana "Idan har dagaske bakisan Hanyar fita daga Cikin kurkukun nan ba, to taya akai kikasan tarihin rayuwata? Kinsan komai agame dani, bayan haka ke da kanki kika faɗa mini cewa Mashine ko mota bazasu ta6a Iya kawo mutun Cikin kurkukun nan ba, kenan ƙarya kike yi mini"? Dogon numfashi tsohuwa taja kafin tace"banyi maki ƙarya ba, tabbas hakane, Duk da bana fita daga cikinsa amma ina iya sanin meke wakana awajen kurkukun nan," lamarin yayi matuƙar ɗaurema angel kai, Wannan wata irin baƙar ƙaddarace? Kenan itama tsohuwa tun tana kamarsu ta ke rayuwa agidan kurkuku matsayin prisoner? Itama batasan kowa nata ba? anya kuwa zata Yadda da maganarta? Kafin angel tayi yunƙurin ƙara tambayarta wani abu, muryar naufal ta katse mata hanzarinta, "Tsohuwa mun ga canji sosai, ga sabbin gadaje an kawo ga kuma akwatuna guda biyu, bayan haka kuma acikin toilets ɗinmu an zuba kayan amfani acikinsu, mun yi mamakin ganin sauye sauyen nan, kamar zamu dawwama acikin farin ciki ne " Tuntsirewa tsohuwa tayi da dariya tana faɗin"Ae ba'a dawwama cikin farin Ciki a gidan kurkukun ƙaddara, Waɗannan sabbin gadajen da ku ka gani, Ƴan uwanku ne za'a kawo, Nan badajimawa ba, daga yau zuwa gobe zaku Iya ganinsu, Sa'annan kayan amfanin da aka zuba muku acikin makewayinku, Nice nayi fafutuka wurin ganin an sanya muku su....." dakatawa ta ɗanyi da yin maganar, haƙiƙa sun ji dadin jin cewa itace ta sanya aka kawo musu kayan amfanin, a karo na farko kenan da tayi musu abun kirki, gani suke kamar akwai wani abu da take so ta fada musu, wanda ba lallai bane yayi musu daɗi ba, Duƙar da kai ƙasa tsohuwa tayi na wani lokaci, suna ta kallonta, kafin ta ɗago idanuwanta akan fuskokinsu, sai suka ga kamar ruwan hawayene kwance acikinsu. Kafin su yi yunkurin yi mata magana ta riga su cewa"Ku ɗauko mini akwatin nan da aka kawo muku" da sauri naufal da haris suka je suka janyosu agabanta suka kwantar da akwatin nan, "Kunsan menene aciki"? Suka haɗa baki wurin cewa a'a, murmushi ta saki tare da cewa"Sabbin Uniform ɗinku ne masu kyan gaske, tare da takalma, da sauran abubuwan da nasan zaku buƙata, Zaku Iya buɗewa ku gani" Wani irin farin Ciki ne ya bayyana akan fuskokinsu, Jiki na rawa suka zuƙunna agaban akwatunan haris ne jagaba wurin buɗe akwatin farko, Kaya ne danƙare acikinshi, A ninke suke an jera su, uniform ɗin farko Launin baƙaƙe ne sun sha banban da kalar style din na jikinsu, "Mutun Uku, Su fiddo da kayan a hankali sai ku dudduba a tsanake" acewar tsohuwa, Suka amsa mata da toh, haris da deeja ne sai angel suka sanya hannayensu cikin akwatin suna zaro kayan tare da ɗago dasu suna warware ninkin da aka yi musu, haɗaɗɗun riguna ne masu kyan gaske, basu da banbanci da Wrap coat, suna da igiyoyi guda biyu a jikinsu, tsayin su zai kai har gwiwowinsu, sannan suna da dogon hannu, gefe da gefe akwai aljihu ajikin rigunan, yadin jikinsu mai matuƙar kyau da ɗaukar ido, kowace shirt tana da ƴar vest launin red acikinta, Uniform ɗin farko masu launin Black, Mallakin angel da batool ne tare da Danish, Numbobinsu ne akai no 1 no 2 zuwa 3, A bayan rigunan, wani abun mamaki daga ƙasan numbers na jikin uniform ɗinsu, Kowa da sunan da aka sanya mishi su ukun nan, da turanci aka rubuta sunayen anyi amfani da launin Ja, A bayan rigar Batool an rubuta *HEART BEAT*(Bugun Zuciya) rigar danish an rubuta *PRISON SHIELD* (Garkuwar kurkuku) yayin da ita kuma Angel abayan rigarta aka rubuta *DESTINY* Wannan suna dai ya ɗaure musu kai, Har tsohuwa su ka tambaya menene ma'anar sunayen tace masu kada su damu, suna ne kawai, Angel bata yadda da sunayen ba, basu kwanta mata aranta ba, tabbas akwai dalilin dayasa aka rubuta musu sunayen abayan rigunansu, su ukun nan, Ita dai fatanta Allah yasa ba wani mugun abun bane. kowace riga tana da dogon wadonta masu kyan gaske, Uniform dinsu azeeza sunyi kyau sosai launin Ja, iri ɗaya ne dana su Danish banbancin kala ne kawai, Sai kuma rubutun dake abayan rigunansu Angel, babu anasu rigunan sai dai numbobinsu, abun burgewa kowace riga tana da cotton scarves, Irin ɗan mayafin nan da mazan indiya suke ɗaurawa asaman wuyan su. *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Launin ja, tun daga kan fuskokinsu zaka shaida irin tsantsar farin cikin da suke aciki, tun kafin ma su sanya kayan ajikinsu har sun fara Imagining irin kyan da zasu yi musu, tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, daga ƙasan Uniform ɗin nasu, wasu haɗaɗɗun rigunan sanyi ne masu dan banzan kyau, launin bright rust red da kuma dark brown, sai faman ɗaɗɗaga rigunan suke yi suna kallonsu, sun rasa bakin magana saboda tsabar murna, ga wasu hats haɗaɗɗun hulunan gayu na mata dana maza masu kyan gaske, Ƙasan akwatin gaba ɗaya sabbin takalmansu ne kala bibbiyu, zubin anckle boots da kuma slippers, Yara fa sun zama ƴan gayu, kaf saida suka zazzage kayan akwatin suna ta kallonsu suna yaba kyawunsu haɗi da nuna irin farin cikin da su ka yi. Tsohuwa tace su buɗe ɗayan kwatin su duba kayan dake acikin shi, tasan zasu Yi farin ciki, akwai wata ƴar kyauta data sanya musu aciki, taban mamaki, Jin wannan maganar yasa suka tattara uniforms din da komai na akwatin farko suka maidasu ciki suka datse shi, cike da zumuɗi Angel ta buɗe musu akwati na biyu, a danƙare yake da kaya, abu na farko da suka fara Cin karo dashi, hankys ne launin ja da baƙi, mai ɗauke da sunayen kowannan su, sun yi matuƙar Yi musu kyau, Hada mayukan gyaran Jiki dana gyaran gashi, da Set na kayan gyaran akaifa, ga wasu ribboms na ɗaure gashi, Yawanci duk basu san yadda zasu yi amfani dasu ba, amma tunda ga angel sunsan zata Yi musu bayanin komai. "Tsohuwa, kince akwai gift da kika sanya mana, Ta na ina? Ko su ne waɗannan kayan"? Angel ce tai mata tambayar tana kallonta, Tsohuwa tace"Ku duba daga can ƙasan akwatin zaku same ta" Jiki na rawa suka ɗaɗɗaga kayan har suka taddo wrapping sheet ɗin dake nannade da wani abu, wanda shape ɗinshi daga sama round ne mai faɗi, ƙasa kuma ya ɗan tsuke, kallon juna suka yi cikin ƙagara da son ganin menene aka nannaɗe haka, kowa ya baza ido suna jiran ganin menene, A tsanake angel ta soma warware wrapping sheet ɗin awani slow, Sai da ta taddo ƙarshen shi ta yakice paper ɗin da aka nannaɗe shi, A hankali take bin shi da kallo, Su azeeza duk suka zazzaro idanuwansu ganin wani abun ban mamaki da basu ta6a gani ba, shin kunsan menene? Nasan Kun ƙosa kuji, To ba komai bane face*MADUBI,* wani irin farin Cikine ya bayyana akan fuskar angel da ƙarfi ta ambaci sunanshi MIRROR, yayin da take kallon kyakkyawar fuskarta wadda yaushe rabon da taga suffar face dinta tun tana atare da daddynta tsawon shekara huɗu da watanni yama kusa ci ka 5yrs, Ya burge ta sosai, madubin Round shaped ne mai matuƙar ɗaukar ido, Yadda kasan ƴan ƙauyen ido sama, Haka suka kewaye madubin Suna Kallon fuskokinsu, sun saki baki kamar lehen sakarai, In ka cire mutun ɗaya wanda Yaja gefe ɗaya kamar baya maraba da ganin sabon abunda basu ta6a gani ba, su kuwa sai ihu suke Yi suna Murnar ganin fuskokinsu kamar suyi hauka, Ɗakin nasu ya cika da Hayaniyar su, abun nema ya samu, Tsohuwa dai sai murmushi take yi tana kallonsu, Sun tasa madubin gaba Na tsawon lokaci, sai faɗi suke wai dama haka fuskokinmu suke? azeeza tace Wai Allah na, dama haka nake da kyau? Komai na fuskata ɗan ƙarami mai kyau, Hanna tace"Nima fa kyakkyawace, Idanuwana farare ƙyal, ga dogon hanci, " deeja tace"duk da ban kai ku kyau ba, amma Nima ba daga baya ba, Manyan kyau ne dani," tana rufe baki yasmin tace"ni matsalata idanuwana ƴan mitsi mitsi kamar zasu shige ciki, hancina luluyayye, har ƙwara bakina ma, " gaba ɗaya suka kwashe da dariya hada tsohuwa, parveen dai ta ƙura wa madubin ido ita da Rubina sai kallon fuskokinsu suke yi kamar zasu lashe su, har sai da haris Yakai hannu ya danƙwashi kawunansu tukunna suka zabura, suna faman wurga mashi harara, "Idan kun gama kallon ƙurallan ku bamu abun muma mu duba kyawun fuskokinmu" Wani irin kallo parveen tai mishi tare da cewa"shawara kyauta haris, Ka haƙura da duba abun nan, saboda Ina jiye maka tsoron munin fuskarka da zaka gani, zai iya sawa zuciyarka ta buga" kafin haris ya bata amsa deeja ta riga shi cewa"Ki Iya bakin ki Parveen, Ƙarya kike kice wai haris bai da kyau, don kawai yana da duhun fata ne, kuma ahakan Ba ƙaramin kyakkyawa bane, kawai kina yi mishi baƙin Ciki ne," takai ƙarshen maganar tana jifarta da harara, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma haris ba, koba komai deeja ta yabe shi, abunda ma ya ƙara burgeshi, da kanta ta ruƙo madubin daga hannun angel ta kanga mashi saitin fuskarshi, Atare suka haɗa faces ɗinsu suna kallon juna ta cikin madubin sai dariya suke saki, Satar kallon danish angel tai don taga a wani yanayi yake ciki, Yana zuƙunne a tsakaninsu javed da mubeen, yaɗan duƙar da kanshi ƙas, Yayin da idanuwanshi suke akan yatsun hannun shi, Aranta tace Shi kuma haka zai ƙare! Kowa Yana kallon fuskarshi acikin mirror, banda shi, wama ya sani ko aljani ne, shiyasa yake tsoron Ya haska fuskar shi Cikin madubi, Amma dai zanso Ya kar6i mirror ɗin nan kodan yaga irin baiwar kyan da Allah yae mishi......." kasa ƙarasa maganar tai ganin yana ƙoƙarin ɗago da kanshi da alama yaji ajikinshi ana kallonshi, da sauri ta duƙar da nata kan ƙasa tana faman tsuke baki, koda ya ɗago Bai ci sa'ar haɗa ido da ita ba, Sai suka haɗa ido da Haris Ya sakar mishi murmushi yana faɗin" Deeja bani abun nan in haska ma Sarkin kyau fuskarshi, Nasan yau danish ko bacci bazai iya yi ba idan har yayi tozali da kyakkyawar fuskarshi," Ya ƙarasa maganar tare da sanya hannu Ya ruƙo madubin, Ya ɗan yunƙura ya miƙe ya nufi danish, sai dai kafin ya ƙarasa danish yae saurin kifa kanshi saman gwiwarshi, bubbuga bayanshi haris yae tare da cewa "Kar ka bani kunya mana, Kowa ya share ka sai ni na damu dakai, pls bro Ka ɗago ka kalli fuskarka," batare daya ɗago da kanshi ba yace"Haris i can't bana son ganin shi, pls ka janye shi daga saiti na, zai iya affecting lafiyata," jin wannan maganar ta Danish yasa duk suka ɗago da idanuwansu suna kallon shi, Lamarin ya ɗaure musu kai, Deeja tace"But why danish? Kowa fa ya duba fuskarshi Kuma lafiya lou ba wani abu daya cutar damu, sai kai zaka ƙi kallon fuskarka? Javed yace "Haba danish idan ma saboda abunda ya faru a tsakanin mu dakai ne yasa kace ba za ka duba abun nan ba, Ina mai baka haƙuri just for today a matsayin mu na ƴan uwa mu kalli fuskokinmu acikin baƙon abun nan," Lamarin yae matuƙar ɗaure musu kai, sai roƙonshi suke yi suna yi mishi magiya akan ya kalli madubi amma ɗan tahalikin nan yaƙi ɗagowa, rai aɗan 6ace Haris Ya damƙi sumar kanshi da niyar ya ɗago da kanshi Ya tursasa mishi akan ya kalli madubin, aikuwa rai a6ace danish ya bangaje haris Madubin dake hannun shi ya kubce zai kife ƙasa, Jiki Na kerma Ƴan matan su kayi sauri ruƙo shi, Ran haris ya ƙara 6aci ya shiga zazzaga mishi masifa, deeja tace"Su rabu da shi, dama baya atare dasu, Shi kaɗai yasan dalilin shi na ƙin kallon madubin, danish ba abun yarda bane, Tsohuwa dai tana atsaye tana binsu da kallo bata tanka musu ba, duk wanda yai magana idonta na akan la66ansa. Naufal yace" Ku ku ka damu da shi, ae gaya nan ya baku kunya, Kar Allah yasa ya kalli madubin, don ma ya samu ana lalla6a shi ne, Kuma wlh da ace Madubin nan ya fashe silar hankaɗe haris da kayi, Da ka ji ajikinka, shashasha" yana huci yai maganar, "Ni dai A iya sani na, Aljanu ne basu son kallon madubi ko su gifta Ta wurin da aka ajiye shi, idan su ka yi suffar mutane saboda baya 6oye ainihin suffarsu ta jinni, na ta6a kallon wani film da irin hakan ta faru, ina da tabbacin cewa danish Ba cikakken mutun bane, Yana da alaƙa da aljanu," Angel ce tai wannan tunanin acikin ranta, Gyaran muryar da tsohuwa tayi musu ne yasa suka ɗago suna kallonta, Banda Danish daya kifa kanshi saman gwiwowinsa. "Ku ƙyale shi, Idan ya nu na baya son abu to ku daina ƙoƙarin tursasa shi, kuma kada hakan yasa ku zarge shi, Danish ɗan uwan ku ne, tamkar uba yake agare ku shi da Haris, Tun ɗazu Na lura da irin wariyar da ku ke ɗan nuna mishi, shin meya faru atsakaninku ne? Ko wani zai iya faɗa mini"? Tai tambayar tana bin faces ɗinsu da kallo, Deeja ce ta kwashe duk abunda ya faru tsakaninsu tun daga kan batool daya bi cikin toilet ya ruƙo hannunta ya damƙa ma giant ita, har izuwa irin bugun da suka yi mishi, da kuma yanke alaƙar da suka yi da shi" tun kafin deeja takai ƙarshen maganarta, tsohuwa ta soma girgiza kanta, Yayin da idanuwanta ke akan Danish daya kifa kanshi, duk sun lura da irin damuwar dake akan fuskar tsohuwa, magana ta soma yi cikin nuna 6acin ranta ga abunda suka yi mishi "Kada ku kuskura ku ƙara ɗaga hannu kuce zaku ta6a lafiyar jikin shi, bama shi kaɗai ba, Kowa ma, Nayi mamakin jin cewa kun haɗa kai kun bugeshi sai kace wani jaki, ko a shekaru Danish Ya ɗare maku amma ahaka kuka rufe ido kuka jibge shi kamar bawan ku, ina hankalin ku ya tafi ne? Musamman ke angel," tai maganar tana nuna angel da sandar hannunta, Yatsina fuska angel tae tare da cewa"Ae ni ban ta6a shi ba, lokacin da suka jibge shi, Na suma bana ahayyacina kuma da ace idona biyu saina 6alla hannun shi daya ruƙe batool, saboda baida tausayi mugu ne shi, inaji ina gani Ya raba ni da batool ɗita, tana kuka ina kuka" daƙyar angel ta karasa maganar tare da ɗaura kanta saman laps ɗinta tana shessheƙar kuka tunawa da irin abunda ya faru aranar, gashi har yau babu alamun za'a dawo musu da ƴar uwarsu, Deeja tace"Har ga Allah danish ya ƙona mana rai, yayi mana abunda bazamu ta6a mantawa ba, tabbas shi dan uwanmu ne amma baya atare damu, akwai wata mummunar manufa atare dashi, In ba haka ba meyasa duk irin shaƙuwar dake a tsakanin shi da batool bai duba wannan ba, ya rasa dame zai saka mata saida sharri, ae wlh duk abunda ya faru da batool alhakinta na akan wuyanshi, Kuma jira muke ta dawo muga awani hali take aciki, kafin mu ƙarasa yanke mishi hukunci" Daga cikin zuciyarta take magana, fuskarta babu alamun wasa, tsohuwa sai jinjina kai take yi, Tana kallonta, sai da takai ƙarshen maganarta tukunna tace"Aikuwa indai kuka ce zaku Cigaba da ta6a lafiyar jikin shi da rabon wata rana ku rasa madafarku, nayi mamaki da Danish ya ƙyale ku har kuka jibgeshi, bayan yana da ƙarfin da zai Iya rama abunda ku ka yi mishi, amma saboda ƙaunar da yake yi maku sai baiyi hakan ba, Saboda baya son wani acikin ku ya cutu, baku da masoyi a duniyar nan daya wuce Danish, shi tamkar jagora ne acikin rayuwarku, ku daina raina shi, akwai ranar da zaiyi maku amfani, amma muddin kuka ce zaku cigaba da nuna mashi wariya acikunku, to tabbas kuwa xakuyi danasani mara amfani......." Tunda tsohuwa ta soma kora musu jawabi, suka kasa kunne suna sauraronta, batare da suna fahimtar taƙameman abunda take son ganar dasu ba, donsu ana su tunanin basu ga amfanin da zai iya yi musu ba, in banda ya hau gado ya naɗe kamar wani basarake, "Ba lallai ne ku fahimce ni ba, saboda na karanci hakan akan fuskokinku, Shawarace nake baku kyauta, Bana so ku yi danasani Anan gaba, " har suna haɗa baki wurin furta Kalmar danasani, deeja tace akan me zamu yi danasani? Bata bata amsa ba, tace"Ku tattara kayayyakin nan ku maidasu cikin akwatin, Ku rufe shi, sannan Ku kawar dasu gefe inaso muyi magana daku kafin in tafi" da sauri Su haris suka mayar da kayan da suka curo cikin akwatin suka datse shi, tare da jansu gefe ɗaya suka jingine su jikin table ɗin dakinsu, bayan sun dawo Tsohuwa ta basu umarnin su miƙe tsaye, Gaba ɗayansu suka yunƙura tare da miƙewa suna kallonta, duk sun ƙagara da suji me take son faɗa musu, Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo na ɗan wani lokaci kafin ta soma magana cikin muryarta ta tsoffi, "Tsawon shekara da shekaru Ina Rainon Yara agidan kurkukun ƙaddara, Ban ta6a samun Yaran da suka kwanta min araina ba naji ina ƙaunarsu har cikin zuciyata irin ku ɗin nan ba, Kun ciri tuta, domin kuwa kun kafa tarihi acikin rayuwar tsohuwa tamira......." murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Inka cire mutun huɗu, Angel, deeja, Haris da Danish, Babu walwala attare dasu, "Naso ace ina da hanyar da zan Iya taimaka maku, saboda ƙaunarku da nake yi sai dai kash bani da damar yin hakan, Amma ina fatan nan gaba idan muna da tsawaicin kwana mu sake haɗuwa daku, duk da nasan zaiyi wuya ........." Kallon kallo suka shiga yiwa junansu, Kamar sun fara fahimtar inda zancenta ya dosa, "Tsawon lokaci Ina atare daku, Duk da ban amfane ku da komai ba, Amma nafi waɗanda su ka yi silar zuwan ku kurkukun nan, Na raini wasunku tun suna ƙanana tun basusan kansu ba, har suka fara tasawa suna rarrafawa yanzu gasunan sun girma gwanin ban sha'awa, wannan abun farin Ciki ne kuma abun ayaba mini ne, ga wanda yasan ya dace" tai maganar fuskarta ɗauke da murmushi, bayin Allah duk jikinsu yai sanyi, Sai kallon suke yi, "Acikin ku akwai waɗanda suke Yi mini kallon muguwa maƙaryaciya, Mara amfani, Akwai ma wadda tace dani da tukunyar fulawar dake acikin toilet dinku bamu da banbanci, " duƙar da kai ƙasa angel tai, Cikin jin Nauyin maganar da tsohuwa tayi, "Ba za ku ta6a sanin amfani na ba, sai ranar da bana atare daku, A ranar zaku tuna da irin mahimmancin da nake dashi acikin rayuwarku, kuma a wannan lokacin zaku yi danasanin rashina atare daku, Amma bana son hakan ya karya zuciyoyinku, Inaso ku ƙarfafa ma juna gwiwa kusanwa ranku cewa, ko babu ni, ko babu wani acikin ƴan uwanku xaku Iya rayuwa! Domin kuwa ba'a halicci duniya don mu dawwama acikinta ba, dole ne akwai ranar da kowa zai barta, ko muna so ko bama so......." dakatawa ta ɗanyi da yin maganar idanuwanta sunyi jawur a yayin da take kallonsu. "Abunda yasa na buƙaci abaku waɗannan sabbin kayan saboda Inaso nima wata rana ku tuna dani acikin rayuwarku, A ƙalla dai nayi muku abun kirki........" bata ƙarasa maganar ba, sakamakon shessheƙar kukan da suka fara, Batasan ya akai suka ɗagota ba tunkafin ma takarasa zance, girgiza kai ta ɗanyi tana murmushi tace"Jikokina kenan, meyasa zaku karaya tun yanzu? Haba Kar muyi haka daku, kada ku bari hawayen ku su xuba, akwai ranar da zasu yi maku amfani," "Dan Allah ki fahimtar damu me kike son faɗa mana? Gaba ɗaya kin jefa mu acikin ruɗani" azeeza ce tayi magana, "Bankwana nake Yi muku! " wani irin bugu zuciyarsu tayi, Tsabar tashin hankali ne ya bayyana akan fuskokinsu, Sam sun kasa furta komai, "Dama na faɗa maku cewa, Ni mai raino ce, a ƙa'idar aikin masu raino na gidan kurkukun ƙaddara, da zarar yaran da yake raino sun mallakin hankalinsu, to za'a canza wanda zai dinga kula da su ne," A matuƙar ruɗe suke kallonta, Wasu har sun fara matse ƙwaalla, ashe basu ji komai ba, "Zanje naci gaba da rainon ƙannanku masu taso wa, Ku kuma Za'a canza muku sabuwar da zata cigaba da jagorantar rayuwarku, sai dai fa zaku ga banbancin domin kuwa, Ni ba komai bace akanta, bansani ba kota kawo muku ziyara....." Cikin sanyin murya danish ya bata amsa da cewa"tazo, namanta ban fada musu bane" Tsohuwa tace"Bakowa bace face TSOHUWA ZAFREEN! Ita ɗin takasance ɗaya daga Cikin shuwagabannin dake ruƙe da gidan kurkukun ƙaddara! Kaifi ɗaya ce, zuciyarta bata da banbanci da dutse, a rashin tausayi Cikin kaso ɗari tana da casa'in da tara....." tashin hankalin da ba'a sama shi date!! Tuni gwiwowinsu sun jima da sagewa, Zuciyarsu ta tsorata sosai, tunkafin ma suyi toxali da tsohuwa zafreen, Kusan atare ƴan matan suka zube saman gwiwowinsu, banda angel da mazan, Sai kuka suke yi suna rokonta akan karta bari akawo musu tsohuwa zafreen, Idan ma yazama dole ta rabu dasu to ta taimaka ta hana akawo musu ita, abarsu suyi rayuwarsu batare da kowa ba, zasu Iya kula da kansu," Cikin raunin murya tsohuwa tace"Ae ni bani da ikon da zan hana tsohuwa zafreen zuwa wurinku, Saboda A matsayi ko ƙafarta ban kama ba, wani abun ɗaure kai ma, Ita da kanta ta nemi da abata sashen ku don taci gaba da kula daku, saboda ita ba cikin ma'aikata take ba, Shugaba ce Ra'ayin kanta ne zuwa wurinku, kai Danish ae ka ganta, Tana da babban muƙami, agaban rigarta taurari uku ne, idan baku san ma'anarsu ba, bari in sanar maku, duk wanda kuka gani da Star uku agaban rigarshi To shugabane na gidan kurkuku, A mataki na ma'aikatan prison daga star ɗaya yake farawa zuwa star biyu kafin ka samu taurari ukun nan, Idan kuka duba Jikin rigata babu star ko ɗaya saboda bani da wani matsayi agidan kurkukun ƙaddara, Raino kawai nake yi" Cikin shesshekar kuka su parveen suke faɗin wayyo Allah mun shiga uku mun bani mun lalace, tsohuwa dan Allah kada ki rabu damu wlh zamuyi biyayya, zamu biki sau da ƙafa, Tun yanzu mun gane kuskuranmu....." haƙiƙa sunyi matuƙar bata tausayi sai dai ba yadda zatayi, haka Allah ya riga daya ƙaddara musu rayuwarsu, amma fa zasu ci baƙar wahalar da ba lallai bane su Iya rayuwa, Angel duk tafi su shiga damuwa, ita gani take hada ƙarin donta ƙetare Iyakar data faɗa mata na cewa duk ranar da ta kuskura ta yi leƙan asiri to bazasu sake ganinta ba, amma kuma ae koda ta dura tagar bata ga komai ba, sai ma wahalar da tasha, sai dai idan ko dama ƙarya tayi mata data faɗi hakan tun da ta saba canza magana," numfasawa tayi tare da kallon tsohuwa tace. "Idan ma saboda sa'in sar da muke Yi atsakanina dake ne yasa zaki tafi ki barmu, ina mai baki haƙuri, zan ma iya zuƙunnawa saman gwiwowina akan in roke ki, dan Allah badan halin mu ba, kiyi haƙuri ki cigaba da zama damu....." da sauri tsohuwa ta ɗaura idanuwanta kan wadda tayi maganar, tayi mamaki ganin angel ce, idanuwanta sun Cicciko tab da kwalla duk da basu zuba ba, Wata irin mahaukaciyar dariya tsohuwa ta tuntsire da ita, Jikinta har jijjiga yake yi saboda tsabar yadda take yin dariya kamar zata kife ƙasa, Duk suka ƙura mata luhu luhun idanuwansu da suka canza launi saboda kukan da suka sha, Daga bisani tsohuwa ta dakata da yin dariyar tana kallon angel tace"Unaisa kenan, Ban ta6a tunanin zaki Iya furta hakan da kanki ba, lallai kun tsorata da tsohuwa zafreen tunkafin zuwanta, to agaskiya dai ba taimakon da zan Iya yi maku, shawarar da zan baku shine, koda gigin wasa kada ku kuskura tana magana kuna kallon cikin idanuwanta, na farko kenan, sa'an nan, ba'a sa'insa da ita, musamman ke unaisa, Kina da gangancin ya6awa mutun magana, ina mai gargaɗin ki da ki kiyayi harshenki, wurin Yi mata magana, abu na ƙarshe da zan fada maku, idan tana awuri ba'a tsegumi, ko ƙyafcen ido, da yafu ce, Har kisa tana iya yi, idan har akai hakan agabanta, idan har kuna son ku ci ribar zaba da zafreen, to kuyi mata biyayya tamkar zaku bauta mata, idan ta bada Umarni, Jiki na rawa kuyi gaggawar yi mata shi, babu musu, idan har baku kiyayi abunda na fada muku ba, tabbas zaku yiwa mutuwar ku kutse tunkafin lokacinku yayi, " wani irin wahalallan yawu kowannan su Ya haɗiya, wasu har sun fara jin zazza6i ajikinsu, sun tsorata da tsohuwar nan da za'a kawo musu, "Ba lallai bane, kullum ku dinga ganinta, kamar yadda kuka saba ganina jefi jefi, saboda ita ɗaya ce daga Cikin shuwagabannin kurkukun, zaima yi wuya a sati ku ganta, Zata iya ɗaukar tsawon kwanaki bata leƙo ku ba, Ta inda zaku samu sauki kenan, domin kuwa baiyanarta ba alkhairi bane......" Muryar su azeeza ce ta katse mata hanzarinta, "Tsohuwa yanzu shikenan tafiya zakiyi kibarmu? Fuskokinsu sharkaf da hawaye hada majina, Daƙyar ta ƙaƙalo murmushi akan fuskarta tace"ƙwarai kuwa tafiya zan yi in barku, babu tabbacin zamu ƙara haɗuwa, ni dai shawarata agare ku shine, Ku daina gaba da junanku, ku hada kanku, kuma ku kawar da idon ku ga duk wani abu da ɗan uwanku Danish zaiyi, ku daina fushi dashi, hakan zai iya haddasa mashi matsala acikin zuciyarshi," ajiyar zuciya ta ɗan sauke kafin ta ɗago suka haɗa ido da angel, "Jikata unaisa, Baki ya mutu, tsohuwa zata tafi ki huta da ganin mummunar fuskarta, meyasa banga kina farin Ciki ba"? Tai tambayar tana sakin ƴar dariya, angel kuwa fuskarta aɗaure take, ta tsuke baki, baiwar Allah damuwa ce danƙare akan fuskarta, " a hankali tsohuwa take buga sandar hannunta, wanda ke nuni da cewa akwai wani abu da hakan ke nufi, sai dai basu fahimci dalilin dayasa take bubbuga sandar ba, dakatawa ta ɗanyi still idonta na akan angel taci gaba da cewa "Ƙaramarsu babbarsu, ki cigaba da taimakon su kamar yadda kika saba, Inajin daɗin hakan sosai, haƙika zuwanki cikin rayuwarsu tamkar bayyanar haske ne acikin duhu, ki haɗa ka ƴan uwanki, kada ki bari wani abu ƙalilan ya shiga tsakaninki da waninsu, kuso junanku, ku sama ma kanku farin ciki, duk runtsi duk wuya kada kuyi kuskuren da zaisa ku raba kawunanku, idan har kuna son cimma burinku, Inaso ku ɗauka cewa ku kamar *MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MAKU FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARKU, TABBAS KUNA DA DAMA* Amma fa dole sai kun yarda da kanku, kun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare daku, Sa'annan *KU NE MAKULLAN DA ZAKU BUƊE TA* Nasan a yanzu bazaku ta6a fahimtar kalamaina ba, sai nan da wani lokaci, Aranar da kuka fita hayyacinku, wasu ma basa araye, To awannan lokacin ne zaku gane me nake nufi............" Tunkafin ta ƙarasa maganarta, Da ƙarfi Ta buga sandar hannunta, wata irin ƙura ta mamaye idanuwansu, Kafin wani lokaci hayaƙin ya washe, Sai dai koda suka buɗe idanuwansu, ba su yi nasarar samun TSOHUWA TAMIRA ba, Ta riga da ta tafi, ta barsu da kewarta, sun shiga ruɗanin maganganun data faɗa musu, ga fargabar da suke aciki na baƙuncin TSOHUWA ZAFREEN, Lamarin yayi matuƙar gigitasu, yinin ranar da jimamin rashinta suka Yi shi, babu wanda bai matse kwalla ba acikinsu, Sunyi kuka tamkar ransu zai fita, sunyi danasanin duk wani abu da ya shiga atsakaninsu da ita, dama ance sabo turken wawa, hatta angel da tafi kowa tsanar tsohuwa a yau Saman gado ta haye ta rungume pillow tana matsar kwalla, fuskokinsu sunyi jawur gwanin ban tausayi, babu wanda yai kwakkwaran motsi acikinsu, kowa yana tuna irin rayuwar da suka yi da tsohuwa Tamira, Har giants suka kawo musu abinci basu motsa ba, badan Allah yasa parveen tayi tunanin kwashe musu abincin Cikin kwando ta ajiye musu shi ba, da sun yi asarar shi, duk irin zumuɗin da suke yi na sabbin kayan da aka kawo musu babu wanda Ya ta6a su, Kai hatta akwati nan basu ishe su kallo ba. Sai da yunwa ta fara kai musu karo tukunna suka fara neman abinci, A lokacin dare ya nutsa Haka suka zazzauna saman dining carpet dinsu, parveen ta ɗauko musu abincinsu, Yadda kasan waɗanda akayiwa dole, Suna cin abincin suna matsar kwalla, Musamman parveen idan ta cunkusa Naman abaki, tana tauna Tana ambaton sunan tsohuwa, shikenan ta tafi tabarsu, Yanzu ya zasuyi, Bayan sun kammala cin abincin, babu wanda yai tunanin yin wanka, ga jikinsu sai tsami yake yi, ahaka suka haura saman sabbin gadajen nan kowa ya kwanta, zuciyoyinsu cike fal da jimamin rashin tsohuwa Tamira, da kuma fargabar irin rayuwar da za su yi da tsohuwa Zafreen, ɗaya daga Cikin shuwagabannin kurkukun ƙaddara, suna daga kwance suke Yin fira, Haris yace daga Jin sunanta babu imani atattare da ita, Ni inaga toilet zan koma da kwana, zaifi mini kwanciyar Hankali, ashagwa6e azeeza tace Ni dai Allah ƙarƙashin gado zan dinga 6oyewa duk idan naji takun tafiyarta" parveen tace nidai in har bazata hanani cin abinci ba, babu ruwana da shiga huruminta, zanyi mata biyayya kodan in tsira da Ciki na," deeja kuma tace"Allah ya jiƙanmu badan mun mutu ba," rubina tace"Ai kawai mu ɗauki shawarar tsohuwa mu bita sau da ƙafa, Har Allah ya kawo lokacin da zamu Rabu da ita," dogon tsoki javed yaja mai sautin gaske kafin yace"Kunga surutun ya isa haka, pls kowa ya lallashi zuciyarshi, Ku rungumi pillows dinku, aja bargo a lullu6e jiki, kowa Yae bacci, zuwan tsohuwa Zafreen ba fashi," Sai da duk suka gama surutansu, tukunna Angel ta soma magana muryarta adisashe tace"In sha Allah, babu abunda zai faru, koda tazo bazata Iya cutar damu ba, Ni babu bawan da nake jin tsoronshi aduniyar nan, In ba mahalicci na ba, saboda nasan babu wanda ya isa ya cutar dani face da izninsa, Allah shine maganin duk wani mugu mai kafirar zuciya, kafin ayi azzaluman kurkukun kaddara Anyi waɗanda suka fisu, irinsu fir'auna yanzu duk babu su a doron duniyar nan sai dai kajisu a tarihi,' Tunda angel ta ambaci sunan fir'auna, nan fa suka addabeta akan ta basu tarihinshi suna son Sanin wanene shi, tace musu su yi haƙuri yanzu kanta ke yi mata ciwo, amma ta yi musu alƙawarin idan taji sauƙi zata basu tarihin Annabi musa (AS), bayan haka saida ta kwantar musu da hankulan su, kafin ta samu bacci ya ɗauke su, Lokacin da dare Ya ratsa, Angel ta sauko daga saman gadonta, zuciyarta duk ba daɗi, ahaka ta lalla6a ta nufi toilet ɗinsu, ba don komai ba, sai don ta duba awani hali furen batool yake aciki, Tana sanya ƙafarta Cikin toilet din ta hango furen batool da alamun lemar ruwa ajikinshi, kamar zufa haka ya tsastsafo ajikin ganyen shi, nan fa hankalinta ya ɗan tashi, da sauri ta ƙarasa inda tukunyar fulawar take, Ta zuƙunna tare dakai hannu tana shafa Jikin ganyen shi, sosai ruwan ke tsastsafowa, Duk saita rasa sukuni, ta shiga damuwa, muryarta na ɗan rawa ta soma faɗin"dan Allah batool ki daina kuka, Ina atare dake, ban manta dake ba, kina araina, kullum ina yi maki addu'a, Duk da nagaza zuwa in taimake ki amma nasan cewa Allah yana atare dake kuma zai kare ki ne," cikin shessheƙar kuka angel take lallashin Furen, Batasan cewa Danish Yana tsaye bakin ƙopar toilet ɗin ya la6e yana kallonta, tsananin tausayinta ne ya kama shi, sai dai baijin zai iya zuwa ya lallashe ta, saboda alƙawarin daya ɗaukar mata, abunda baisani ba ita kanta, A halin yanzu a matuƙar ƙagare take da son su shirya da juna don ba ƙaramin azabtuwa take yi ba, Shiru ta ɗanyi tana ƙarewa furen kallon, ganin Ya daina tsastsafo da ruwa ajikinshi, wani iko na Allah sai taga furen ya kwanta cikin ƙasar tukunyar, alamar mamallakin shi bacci yake yi, murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, aranta ta raya cewa Batool taji lallashin da take yi mata shiyasa tayi shiru ta kwanta tana bacci, A hankali ta mayar da idanuwanta kan furen daddynta, tafi yarda dana batool akan nashi, saboda shi bata da tabbacin yana raye koya mutu, Jikin furen yayi kore shar dashi, kuma iccen yaɗan miƙe ba kamar lokacin farko da ya fito a lanƙwashe ba, Ziraran yatsun hannunta ta ɗaura asaman furen daddynta tare da shafa ganyen shi, a fili ta furta I wish kana araye daddyna, har yanzun kana nan acikin zuciyata, ba abinda ya sauya daga ƙaunar da nake yi maka, I luv u so much, zan cigaba dayi maka addu'a kaida batool ɗina da kuma ƴan uwana prisoners, Alƙawarine na ɗaukarwa kaina," murmushi tasaki tana faɗin"Har na tuna lokacin da na ƙala maka sharrin cewa kai ba mahaifina bane, ɗan yankar kaine, aranar kasha bugu wurin ƴan ƙato da gora, kuma duk da abunda nayi maka hakan baisa ka guje ni ba, saima ka ƙara ƙaunata, ashe babu rabon xamu ƙare rayuwarmu atare.....haka na dinga burin in zama house wife, ashe da rabon in zama prison wife, Gidan hutun da nake burin inyi aure, har ina faɗa ma aunty aneelerh zan auri hamshaƙin mai kuɗi saboda masu aiki su dinga yi mini hidima ina daga kwance, sai gashi na ƙare agidan kurkukun ƙaddara, wayyo Allah na, babu daddyna babu aunty aneelerh da uncle uzair, babu mommy adamana da uncle abdallah, babu makaranta, babu house wife, duk waɗannan burinkan sun tashi a tutar babu....." daƙyar ta ƙarasa yin maganar saboda kukan da yafi karfinta, ta kifa kanta saman gwiwowinta taci gaba da kuka, tana fadin nayi danasani daddyna ka yafe mini, wlh ina matuƙar ƙaunarka, dama saida ka fada mini cewa bani da tamkarka a duniyar nan yanzu na shida hakan.....' Duk wannan suratan da take yi akan kunnan Danish, Ya ɗan jingina kanshi jikin ƙopar toilet ɗin, Ya natsu yana sauraronta, Hakanan taji aranta kamar akwai mutun abayan ta, a hankali ta ɗan dago da kanta, tana ƙoƙarin juyawa ta kalli bayanta danish yai saurin fita daga Cikin toilet din ya tsaya daga waje, Yana faman sauke ajiyar zuciya, Baiyi tsammanin ta biyo shi ba, Sai dai yaji ta ambaci sunan shi, "Danish"! Kasa juyawa baya yae don ya kalleta, duk yabi ya kama kanshi, "Shine kana ji inata kuka ko kazo ka lallashe ni" Yayi mamakin jin abunda ta ce, cije lips ɗinsa yae kafin yace"Saboda me zanzo in lallashe ki? Ko kin manta alƙawarin dana ɗaukar miki? Batare daya juyo ya kalleta ba, yayi maganar, "Meyasa kake bibiyata? Nasan saboda ni kazo bakin ƙopar toilet din nan ka tsaya, Allah kaɗai yasan tun lokacin da kake kallona, kaga kuwa Alƙawarin Ya jima da karyewa," girgiza kanshi ya ɗan yi tare da cewa"bana sa6a alƙawari, idan kin manta bari in tuna maki, kin ce kada na kurkura na ƙara hada ido dake kinaso in nisanta kaina agare ki, Tabbas nazo bakin ƙopar toilet din kuma na kalle ki amma ban bari mun hada ido ba. Hope kin fahimta yanzu ban karya miki alƙawarinki ba, Tun da bamu haɗa ido da juna ba kuma banzo kusa dake ba," Harara ta shiga jefa ma bayan shi, kamar ƙwayar idanuwan zasu faɗo ƙasa, wani irin kewarshi take ji kamar tae hauka, tayi danasanin sanya shi ya ɗaukar mata alƙawarin nan, ta manta cewa Prisoners basu Iya karya alƙawari ba, ta inda suka banbanta da mutanan dake rayuwa awaje kenan, majority dinsu basa ƙarya kuma basu Iya gulma ba, musamman DANISH! Takaici ne ya isheta, Can dai tace"Idan nace na fasa alƙawarin fa"? Danish ya bata amsa da cewa"Idan kin fasa Ni bansa fa, bazai ta6a yiyuwa ba" yana faɗin hakan Ya wuce cikin dakinsu yabarta a tsaye tana faman cizon le6enta, Daga bisani ta gyaɗa kai tare da wuce wa ta nufi cikin dakin, a kwance ta same shi saman gadon shi ya rungume pillow, ta6e baki tayi kafi ta nufi nata gadon ta haye ta zauna daga tsakiyarshi ta ɗaga hannayenta sama tana jera addu'o'i, Cikin harshen larabci, ta ɗauki tsawon lokaci daga bisani ta shafa hannayenta saman fuskarta, kafin ta gyara kwanciyarta, Sai da ta lumshe idanuwanta, Zuciyarta ta soma tariyo mata maganganun da tsohuwa ta faɗa musu kafin tafiyarta, tabbas akwai wasu kalamai da tayi aciki waɗanda suka ɗaure mata kanta, ta kasa fahimtar inda suka dosa, Duk irin kaifin basirarta, ta gaza gano menene tsohuwa take nufi, da tace musu su dauka cewa su makullaine da zasu Iya buɗewa kansu ƙopar farin ciki, tayaya kenan? daƙyar ta samu bacci ya ɗauketa a daren ranar,! Ko a washe garin ranar babu wanda ya sanya sabon uniform ɗinshi acikinsu, damuwar rashin tsohuwa ta hanasu sukuni, ga fargabar zuwan tsohuwa Zafreen, da kuma new prisoners, daga Sunji motsin ƙopa a firgice suke kallon ƙopar, don suga wanane, a ƙarshe sai su ga bakowa, Kunnuwansu ne kawai suke Jiyo musu hakan, sakamakon sanya rai da suka yi, wasa wasa yau har tsawon 2 weeks da tafiyar tsohuwa babu wani sabon Labari, ta ko'ina shiru kake ji, su kaɗai suke rayuwarsu, hankalinsu har ya ɗan kwanta don a tunaninsu, An ƙyalesu ne su yi rayuwarsu su kaɗai, Bakomai yafi ɗaga musu hankali ba, face rashin batool don a lissafinsu yau Wata ɗaya kenan babu Ƴar uwarsu acikinsu, Ba'a dawo musu da ita, har sun fara fidda rai da sake ganinta 🥺 *PRISONERS💔* Yau tun da sassafe Angel da hanna suka taimaka ma ƴan uwansu mata wurin gyara sumar kansu, gwanin ban sha'awa kowa saida suka wanke mashi sumar kanshi, suka gyara musu ita, su kansu ba ƙaramin daɗi suka ji ba, ganin yadda sumar kansu tayi kyau ga laushi da kyan gani a ido, ga wani irin ƙamshi da gashin nasu yake fitarwa mai daɗin shaƙa, Bayan Sun kammala gyara ma su azeeza, Hanna da angel suke koma toilet, saboda su wanke nasu gashin kan, sai da angel ta kammala wanke ma hanna, ya rage saura ita, duk yadda hanna taso ta wanke mata gashin kanta, hakan ya faskara, saboda uban yawan dake gare shi, Gashi ya nannaɗe yadda kasan taliyar indomi, Tun tana nish tana ƙoƙarin tattaro gashin kan Angel, kamar hannunta zasu 6alle, a ƙarshe data ga abun yafi ƙarfinta, sai ta fita tabar angel acikin toilet ɗin, sai gasu sun shigo kusan su Shida hada su javed da naufal, wai sun zo wanke mata kai, ashe bayan da hannah ta fita daga cikin toilet ɗin, ɗakinsu ta shiga taje ta kira su, donsu taimaka mata, mamaki Ya kama angel, ganin sun shigo suna nannaɗe hannuwan rigunansu, Kusan dambe akayi acikin toilet din, tana faɗin ita bata so su barshi ta haƙura da wanke gashin, Su kuma suka ce bata isa ba, Yadda aka wanke ma kowa gashi, Itama sai sun wanke mata nata, ko tana ko bata so, A lokacin Danish Yana la6e bakin ƙopar toilet din yana kallonsu, don ba ƙaramin nishaɗi ya samu ba, ganin yadda suke ta yawo acikin toilet din sai zagaye shi suke yi, Ita tana gudu su kuma suna bin bayanta hannayensu ruƙe da shower gel da comb, da sauran abubuwan da zasu yi amfani dasu wurin wanke mata gashin su gyara mata shi, Sai da kowannansu Ya gama galabaita, tukunna suka samu ta basu haɗin kai, Su shida suka wanke mata gashin kanta, tadaici azaba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, saboda yadda suke ja mata gashin, Bayan sun kammala wanke mata shi, waɗanda ke ruƙe da combs, suka soma sharce mata shi, daga bisani suka bi da mayukan gyaran gashi suka shasshafa mata, ' Lokacin da suka kammala, Sunyi mamaki Ganin irin yadda gashin kanta ke ta ɗaukar ido, yayi dark brown dashi ya warware tamkar hijabi yayi mata abayanta, ta yi farin Ciki sosai da suka taimaka mata wurin gyara mata gashin kanta, ta ƙara jin ƙaunarsu acikin zuciyarta, Kafin marece ya doso, ɗaya bayan ɗaya suka soma shiga toilet suna Yin wanka, saboda yau sun shirya canza Uniform dinsu, sai ɗauki suke Yi zasu sanya sabbin kaya, Bayan sun kammala Yin wankan, Ya rage saura Danish Yaƙi zuwa yai wanka, Hatta mazan sun wanke sumar kansu, amma shi duk ya takure kanshi, Ya hana kanshi sukuni acikinsu, duk da ayanzu babu wanda yake nuna mishi wariya, tun ranar da tsohuwa tayi musu faɗa akan su daina ware shi acikinsu, tun daga ranar suka daina gaba da shi, Shi ɗin ne dai kamar baison suna kusanto shi, Kuma bakowa yaja hakan ba face Angel, ita ɗin dai ce da baya son ya karya mata alƙawari. Ganin baida niyar tsohuwa ya wanke sumar kanshi Yasa haris zuwa har saman gadonshi, Ya damƙo hannun shi ya janyoshi, Har saida ya sauko daga saman gadonshi suka nufi toilet, Yana fadin Allah idan bakai wanka ba, Ni zanyi maka da kaina, kowa yana nishaɗi sai kai kaɗai duk kabi ka takura rayuwarka sai kace wani bare, Idanma don abunda ya faru ne ae mun yafe maka komai ya wuce mana, tun da ya riga daya faru," Kamar wani ubanshi haka haris ya dage yana tayi mishi faɗa, har suka shiga cikin toilet din, bawan Allah yai shiru bai tanka mishi ba, haris bai fito daga cikin toilet din ba sai da ya taimaka mashi ya wanke sumar kanshi, Kafin Ya fito yabarshi aciki, don yayi wankan, Kafin wani lokaci, duk suka hallara acikin ɗakinsu, Angel ta janyo musu akwatin kayansu Ta bude shi, a hankali take zaro uniforms ɗin tana miƙa musu, da yake tasan numbers ɗinsu, shiyasa ba ta sha wahala wurin banbanta na kowa ba, Bayan kowa ya kar6i nashi, nan fa suka soma sanya su ajikinsu, Cikin dabara, Idan suka cire tsohon wandon, sai su zura sabon a jikinsu ta yadda tsiraicinsu bazai fita ba, kafin ma su sanya kayan ajikinsu saida angel ta biya musu addu'ar sanya sabbin tufafi, duk suka yi banda Danish, Ya ruƙe kayan a hannunshi yana zaune gefen gadonshi, babu alamun zai zurasu ajikinshi, Uniform din sunyi bala'in yi musu kyau, yadda kasan ɗaliban high school na ƙasar Korea, Tabarakallahu ahsanul khalikin, Kyau ne ya haɗu da kyau, abunka ga farare kayan sun fiddo da hasken fatarsu, Sun bi shape din jikinsu sun zauna musu cuf cuf, Especially angel, Wow abun ba'a magana, Yarinyar dama can kalar kyau ce, Ƙarshe ce afagen kyau, Hatta ƴan uwanta su azeeza sai santin kyanta suke Yi, duk da irin kyan da su kayi don itama azeeza ba daga baya ba, jajayen kayanta sun mayar da ita tamkar fure awurin kyau, musamman in tayi dariya fararen hakoran nan suka bayyana ajere kamar gonar auduga, tubarkalla, Danish fa sai satar kallon angel yake yi da zarar Ta juyo zata fuskanci inda yake sai yae saurin kawar da kanshi gefe, baisan cewa ta lura da irin satar kallon da yake yi mata ba, hakan ba ƙaramin dadi ya yi mata ba, bakomai Yafi ƙawata kyan uniform ɗinsu ba face Cotton scarves din da suka daura awuyansu, da kuma igiyar wrap coat dinsu da suka daure, Sai takalmansu, da kuma ribbom da matan suka ɗaure Sumar kansu dashi, Banda angel saboda sanin yawan gashinta shiyasa bata yi gigin sanya ribbon ta daure shi ba, don zai iya tsinkewa, hatta giants da suka zo kawo musu abinci, sai da suka yi musu wani abu daya basu mamaki, da hannu suka yi musu thumbs up, wato alamar jinjina, wannan abun dai ya gigitasu, basu ta6a yi musu hakan ba sai yau da suka ga sun ɗauki wanka, angel dai bataji dadi ba, saboda tasan ƙarshe duk wannan gayun da suke Yi, abanza zai tashi, tun da ba fasa daukarsu za'ayi ba, sai daga baya tadinga danasanin Gyaran gashin da su kayi da sabbin uniform ɗin da suka sanya ajikinsu, don ba ƙaramin fiddo da kyawun surar jikinsu kayan su kayi ba, hakan zai ƙara ma ƴan iskan ƙaimi wurin biyan buƙatarsu da su, zasu ji daɗin gur6ata musu rayuwa, in ba haka ba taya akai giants da basu magana Yau kawai don sunga sunyi kyau shine suka yi musu alamar jinjina wato sun burgesu da suka yi gayu, aiko dai akwai matsala babba!! *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Lokacin da marece ya nutsa, duk sun gaji an gama shan gayu, Anci an ƙoshi, wata irin gajiya ce ta rufar musu, ba arziƙi suka lalla6a kowa Ya nufi Sabon gadon daya mallaka suka kwanta, tun suna yin fira ƙasa ƙasa har bacci yai awon gaba dasu, Ya rage saura Danish Kaɗai zaune gefen gadonshi, don shi bai canza gado ba, har time ɗin hannayen shi na aruƙe da uniform ɗinsa Ya ƙanƙame su, Daga bisani ne Ya ɗaura su saman mattress ɗin shi. A hankali ya sauko daga saman bed din nashi, Cikin sanɗa yake tafiya yana tunkarar gadon da angel take a kwance, Yana ƙarasawa bakin gadon ya zagayo ta left side Ya ɗan zuƙunna, yayin da kyawawan idanuwanshi ke akan fuskarta, ta natsu sai sharar bacci take yi, numfashinta yana fita cikin kwanciyar hankali da natsuwa, lumshe idanuwan shi yai tare da buɗe su kan fuskarta, wata irin natsuwa yaji acikin zuciyar shi, Angel ta yi mishi kyau, fiye da ko yaushe, zuciyarshi ce ta dinga tunzura shi akan ya ta6a sumar kanta, dama itace ta tsole mishi ido, Yatsun hannun shi na kerma ya ɗan ɗago dasu Ya ɗaura su samar doguwar yalwatacciyar sumar kanta, tun da ya soma shafa gashin, ya gaza janye hannayenshi, da zarar yaga tafara mutsu mutsu kamar zata farka, sai kaga yai wuf Ya zuƙunne gefen gadon yana faman sauke ajiyar zuciya, a hankali Yake sake ɗagowa Yana kallonta, Wannan karan Hada Tausasan la66anta Ya shafa da yatsan hannun shi, ya shagala Yana kallonta, Kamar daga sama Yaji an damƙi wuyan rigarshi ta baya, a matuƙar firgice Ya ɗago don ya ga wanene, Ajiyar zuciya ya sauke ganin haris Ne, har wani numfashi yake fitarwa kamar wanda yasha gudu. "Bro, Me kake Yi anan? And why are u looking at her"? Yai tambayar yana kallon fuskar Danish da alamun tuhuma, a yayin da yake ƙoƙarin zame hannunsa daga ruƙon da ya yi ma wuyan rigar shi. Cikin sanyin murya yace"Bakomai" Iya abunda ya furta kenan, Ya miƙe daga bakin bed ɗin nata, Ya nufi gadonshi Ya zauna daga gefe, Girgiza kai haris Ya yi, tare da bin bayan shi ya zauna a kusa dashi. "Ka faɗa mini menene damuwar? May be ina da hanyar da zan Iya taimaka maka, Ka canza sosai Danish, Mun rasa gane kan ka, Kowa yana walwala amma banda kai, hatta sabbin uniform ɗinka dana baka, baka sanya ba, why Danish? Idan ma saboda abunda ya faru ne, ae mun yafe maka ko? Komai ya wuce" Cikin Kulawa Yake yi mishi maganar, daƙyar ya samu Danish Ya buɗe baki ya furta "Ita ce" Aɗan ruɗe haris ya furta"Wa kenan"? "Angel mana, tasa na ɗaukar mata alƙawari akan cewa zan nisanta kaina da ita, ko kallo kar in bari ya haɗa ni da ita, haris na shiga damuwa sosai, " Shiru haris ya ɗanyi Na wani lokaci, Yana kallonshi, shi kanshi Ya lura da irin damuwar dake atattare dashi, Duk ya rasa sukuni, ashe duk akan angel ne, Murmushi haris ya saki tare da cewa"ka kwantar da hankalin ka, Mutumina, indai angel ce zata nemi hanyar da zaku shirya, ae itama ta damu dakai, So bana so kana tada hankalin ka, gashi ko abincin ka baka ci ba, "Ae bana jin yunwa...." tunkan ya rufe baki Haris Ya katse shi da cewa"ƙarya kake yi, look at ur stomach, A shafe kamar Bangon ɗakin mu, " yatsina fuska Ya ɗanyi ba tare da ya kuma cewa komai ba. "Yanzu dai, bari na ɗauko maka chicken leg ɗinka da fruit kasha, after ka gama Sai in taimaka maka ka canza uniform ɗinka" kafin haris yai yunƙurin miƙewa tsaye Danish Ya ruƙo hannun shi, Yana faɗin"Bana Jin yunwa, zan ci da anjima, Yanzu so nake in kwanta" ɗaure fuska haris yai"meyasa kake yi min haka? Ko dan saboda na damu dakai ne"? Girgixa kai yai 'Ba haka bane, just bana jin yunwa, Nayi maka alƙawarin da anjima zanci" gyaɗa kai haris yai, tare da cewa"Uniform ɗin Fa? Yakamata Ka canza na jikin ka," Yatsina fuska yai don ba ƙaramin takura shi haris yake yi ba. rai a6ace haris yace"Na lura ba ka damu da kan ka ba, Kamar yadda na damu dakai, shiyasa ka ke ta yi min wulaƙanci, Shikenan, Zan tafi nabarka, wlh idan har baka canza kayan nan ba, ka ci abinci, kada ka ƙara tunanin zan tanka maka" yana kai ƙarshen maganar, Yaja tsoki tare da miƙewa Ya juya ya nufi gadon shi, Ya haye ya kwanta, zuciyarshi duk ba daɗi, yana matuƙar jin haushin abunda Danish ke yi mishi, Gashi Allah ya jarabce shi da ƙaunar ɗan uwansa, Shi dai yana son Danish, baya son 6acin ran shi, tun suna yara, haka yake fama da shi, Baison Cin abincin baisan hayaniya, baisan yin magana, ga nuna halin ko in kula, da yake yi musu, wani lokacin ka rasa gane kan shi kamar ba cikakken mutun ba, shi dai yafi gane ma hawa saman gadon Ya rungume pillow a ƙirjin shi. "Haris meya faru ne naga fuskarka ta canza"? Muryar deeja ce ta katse mishi zancen zucin da yake yi, kasancewar suna fuskantar juna, Gadon da yake kwance Yana facing ɗin nata, Farkawarta kenan daga bacci, Ta yi arba dashi kwance saman gadon shi ya ƙurawa ceilling ido, sai tsoki yake bugawa, "Haris ka yi shiru baka bani amsa ba" ta6e baki ya ɗan yi kafin yace mata"Nida mutumin ne, ina ta fama dashi ya tashi yaci abinci, ya canza uniform ɗinshi, amma yaƙiya, narasa meke damun Danish, Yafiye taurin kai da kafiya" Mirmushin takaici deeja ta saki,"Kaine ka damu dashi ae, shiyasa yake yi maka abunda yaga dama, Tunda baya cin abincin ka ƙyale shi mana, ba cikin shi bane, idan yunwar ta addabe shi zai nema ne" girgiza kai haris yayi "Bazaki fahimta bane, ni bazan Iya ƙyale shi ba, saboda ina zargin wani abu atattare dashi, gani nake wani abun kamar ba yin kanshi ba, Danish fa ya canza sosai, Sa6anin lokacin baya da muka sanshi, shiyasa nake yi mishi uziri, kuma gaskiya ni, Ina matuƙar son ɗan uwana, bana jin zan iya share shi, idan shi bai son ciwon kanshi ba, Ni nasani," Murmushin dake akan fuskarta bai washe ba tace"Haris you're so special, fiye da tunaninka, ni shaida ce akan irin ƙaunar da kake yi mishi, bama shi kaɗai ba, kowama acikin mu, kana son mu, kana bamu kulawa, kai tamkar jagora ne acikin rayuwarmu....." Tun da Deeja ta soma magana cikin sanyin murya mai daɗi, haris Ya tsare ta da idanuwanshi batare da ƙiftawa ba, saboda wani irin daɗin da yake ji, sai da takai karshen maganarta, sannan yace"Haka nake fata wata rana Danish Ya ɗauki ragamar kula da ku kamar yadda nake yi, shiyasa kika ga ina ƙoƙari don ganin na gyara mashi tunaninsa," "Ka yi tunani mai kyau, nima ina fata Wata rana Danish Ya canza ya zama kamar kai, tabbas zamu Ji daɗi," shiru suka yi na wani lokaci suna kallon juna. Kafin Haris yace"bakomai yafi damuna ba, face rashin batool, Deeja ya zamu yi? Sun ɗauke ta almost one month babu alamar zasu dawo mana da ita, na damu sosai, duk in na tuna da batool baki ji yadda nake ji ba, gaskiya bai kamata ace mun yi shiru ba, mutanan nan fa mugayene azzulamai, zasu iya cutar da ita, kamar yadda suka yi maku," hawaye ne kwance acikin idanuwanshi, yayin da yake yin maganar. Cikin karyayyiyar murya deeja tace"Ae batool sai addu'a, Har ƙwara mu da aka ɗauke mu an dawo damu within weeks, amma ita fa har One month! Wlh ji nake kamar sun kashe mana ita....." bata ƙarasa maganar ba, saboda kukan da ya tari numfashinta, da sauri ta kifa Kanta saman pillow taci gaba kuka. Hankalin haris duk yabi ya tashi, muryar shi araunace yake lallashinta, yana bata haƙuri, akan tayi shiru tadaina kuka kodan saboda ƴan uwan su dake bacci kada su farka, suji suma su shiga damuwa. Abunda basu sani ba, tunda suka fara magana angel ta farka, ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, duk da akwai tazara atsakanin gadajensu amma tana iya jiyo maganganun da suke tattaunawa, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, zuciyarta sai tafarfasa take yi, Tamkar zata 6allo ƙirjinta, aduk lokacin da ta tuna da batool, saita dinga jin kamar ana tunzurata akan ta ƙara dura tagar nan akaro na biyo taje ta nemo ta, ko Allah yasa ta dace, Dama fa ba haƙura ta yi ba, akwai dalilin dayasa ta dakata da kudurin nata, saboda ta lura shiga cikin prison ba abune mai sauƙi ba, dole saita yi mishi kyakkyawan shiri na musamman, kafin ta aiwatar da aikinta, can ƙasan zuciyarta kalaman tsohuwa tamira ne suka shiga yi mata yawo acikinta kanta, tarasa gane dalilin dayasa Suka tsaya mata aranta, tabbas akwai abunda take nufi game da makullan farin cikin nan, kuma tace Idan suka Cigaba da nuna ma danish wariya to wata rana zasu rasa madafar su, ko dan saboda haka dole ta nemi hanyar da zata karya alƙawarin dake a tsakaninta dashi, numfasawa ta yi tare da ƙoƙarin miƙewa zaune hannunta ruƙe da pillow, ta ɗan juya 6angaren hagu ta kalli su Deeja, har lokacin bata daina kukan ba, haris sai aikin lallashinta yake yi, tun yana akan gadon shi har ya kai ga dawowa gefen gadonta ya zauna, tare da kai hannu yana shafa sumar kanta, daƙyar ya samu Deeja ta yi shiru, ya kwantar da kanshi gefen ta, yana leƙen fuskarta da ta yi sharkaf da hawaye, Angel tana jiyo shi yana faɗi"Hakan ma bazata ta6a faruwa ba, ki daina zancen mutuwa, inaji araina ƴar uwarmu tana araye, zasu dawo mana da ita ne" Cikin shessheƙar kuka deeja tace"bayan sun gama amfani da ita ko? Sai sunyi mata kamar yadda su ka yi mana, ko ka manta yadda aka dawo dani ne? Tae tambayar tana kallonshi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa Jawur dasu, Zuciyarshi ta karaya sam ya kasa magana Ta ci gaba da cewa"A wulaƙance, aka dawo dani, ji lokacin da aka dawo dasu Hanna, Hada yakushin akaifa akan wuyansu, le6e duk ya bushe ya faffashe jini yana tsastsafowa, idanuwa sun jagwale da ruwan hawaye.....haris duk da bamusan me akeyi mana ba, amma munji raɗaɗin azaba ajikin mu, mun yi jinya, mun yi kuka tamkar rayukanmu zasu fita daga gangar jikin mu, Iya cuta dai ancuci rayuwarmu," tana faman jan majina ta ɗaura da cewa"Ina tsoron Awani hali za'a dawo mana da BATOOL! ita da ta ɗauki tsawon lokaci ahannun su, mugaye azzalumai Allah kaɗai yasan me su ke ƙunsa mata a yanzu haka......" Deeja bata kai ƙarshen maganar ta ba. Sakamakon jin sautin kukan angel, A matuƙar ruɗe su ka ɗago daga saman mattress ɗin suna kallon shimfidarta, A lokacin harta duro daga saman gadonta, da gudun gaske ta nufi sashen toilet ɗinsu ta shige, damuwa ce ta bayyana akan fuskokinsu. "Tun yaushe ta farka? da ace na sani da ban yi maganar ba, bari naje in lallashe ta, nasan dole taji raɗadi acikin zuciyarta," Deeja na yunƙurin miƙewa haris yae saurin katse ta, ta hanyar yi mata magana, "kada kije, Ayanzu bata buƙatar kowa a kusa da ita, ganinki zai ƙara karya zuciyarta saboda kece kika yi maganar..." "Amma tana buƙatar wanda xai lallashe ta, kana ji fa tana kuka" "Nasani, kema yanzu kika gama kukan inata aikin lallashi, Ki koma ki kwanta, Zanji da ita" sai da ya samu ya kwantar ma deeja da hankali, kafin ya miƙe ya nufi sashen toilet ɗinsu, Har satar kallon shimfiɗar danish yai ta wutsiyar idanuwanshi ya hange shi kwance saman gadonshi, aranshi yace"Kaji haushin rayuwarka, wato baka ci abincin ba, sabbin uniform ɗin ma ba za ka sanya ba, saboda Taurin kai irin naka," Guntun tsoki yaja yayin da yake shigewa cikin toilet, tunkafin ya ƙarasa ciki ya same ta zuƙunne agaban tukunyar fulawar nan, Ta tasa ta gaba sai kuka take yi kamar ranta zai fita, "Why angel? Wannan kukan fa da ku ke yi bazai kare ku da komai ba, Ina fama da deeja, kema kuma kin kama kuka, nasan saboda kinji maganganun da muke tattaunawa ne," a bayanta ya tsaya hannayenshi rungume saman ƙirjinshi, Cikin shessheƙar kuka tace"Bazan Iya jurewa bane, Batool tana can Hannun fasiƙan mutanan can, Cikin mawuyacin hali, Nagaza zuwa in taimake ta, nasan Ta jira zuwana taji ni shiru, dole taji ba daɗi duk irin ƙaunar dake a tsakanina da ita," A gefenta haris Ya zuƙunna Ya soma lallashinta kamar yadda yayi ma deeja, A ƙarshe Ya ruƙo hannunta yace"Ki taso mu koma ɗaki" Maƙe mashi kafaɗa tayi"a'a Kabarni anan, Inaso zanyi ma furennin addu'a" gyaɗa kai yai tare da miƙe wa, da niyar yabar toilet ɗin, har ya juya zai fita sai kuma ya ɗan dakata tare da kallonta yace"Angel, badan halina ba, badan na isa dake ba, pls Ki karya alƙawarin dake a tsakaninki da Danish! Idanuwanta jawur ta juyo tana kallon haris, yaci gaba da cewa"Ki tausaya mashi, dama ba cikakkar lafiya ce dashi ba, yanzu kuma kin ƙara jefa shi cikin wani hali, duk fa saboda ke ya gaza sakewa acikin mu, yaƙi cin abinci yaƙi canza uniform ɗin jikin shi, ni bansan ya akai kika sa ya ɗaukar maki alƙawari fa" fuskarshi a yamutse yayi maganar, Hannu tasa ta matse tsinin hancin ta, yayin da take kallon shi, muryar ta ƙasa ƙasa tace"haris, Nasan ban kyauta ba, nima nayi regretting da na sanya shi ya ɗaukar min alƙawari, raina ne yake a6ace, Amma har ga Allah ni bana fushi dashi ayanzu, sai da nace mashi nafasa promise ɗin, Mu shirya amma yace min shi bai fasa ba......" kaf angel ta kwashe duk yadda su ka yi atsakaninta da Danish ta sanar mashi, Dafe goshi haris yae da hannun shi na dama kafin ya zame shi ya ruƙe qugu yana faɗin"Oh my God, Danish matsala, kin san shi da ruƙe alƙawari, idan har mu ka ce zamu biye mashi bamu san har tsawon wasu kwanaki za'a ɗauka ba, Yana Cutar da kanshi, Tun da ba mu san ranar da za'a dawo da Batool ba, kuma bamu da tabbacin cewa idan an dawo da ita zata yafe mishi," Dakatawa yae da yin maganar yana kallonta, itama shi take kallo, "Yanzu ya zamu yi kenan? Alƙawarin Ya karye" Haris ne yai tambayar, shiru angel tayi na wani lokaci tana yanke shawara daga cikin zuciyarta, "Kin yi shiru" a ƙagare yae mata maganar, har ya fara gajiya da tsayuwa, "Kada ka damu haris, Ni nasan yadda zanyi dashi, In sha Allah a daren yau ɗin nan zan karya alƙawarin, " ajiyar zuciya haris ya sauke fuskarshi asake yace"Dama nasani zaki Iya!" ya ambaci hakan tare da juyawa da sauri ya fuce daga Cikin toilet ɗin, Lokacin daya shiga Room ɗinsu, Su parveen duk sun farka daga bacci, sai surutu suke yi. Kamar ba waɗanda suka sha bacci ba, Kowacce Tana daga zaune saman gadonta, Hannah tana hamma tace"Wai ina angel ɗinmu take ne? Naga banganta ba" hibba tace"yanzu haka tana acikin toilet, wani uzirin ne ya kamata," saukowa daga saman gado azeeza tayi tare da cewa"Nima toilet ɗin xan shiga" takarasa maganar tare da wuce wa ta nufi sashen toilet, tuni haris ya jima da komawa saman gadon shi, ya zauna yana yi musu sannu da farkawa bacci, sarakan ɗumi yanzu xa'afara, gaba ɗaya suka kama dariya, Parveen na miƙa tace"Motsa Jiki zamuyi, Jiki na duk ya ruƙe, " Haris yace'ae dole, An cika ciki yayi haiƙam ta ko'ina babu space ai dole ki nemi motsa Jiki, ko kin samu Cikin ya kwance Aje toilet kamar yadda aka saba," Wani irin kallon harara take jefa mashi, Eve tace"Haris ka sanya ma sis parveen ido Allah, bansan me tayi maka ba" Ta6e baki yai"ae tunda tace ban da kyau saita gane kuren ta," Deeja dake kwance tana jin muryoyinsu Acikin kunnanta, taƙi motsawa ne don kada suga halin da take ciki na damuwa, "Yakamata Baƙin prisoners ɗin nan su ƙaraso tunkafin Ku 6alla musu gadajensu" javed ne yai maganar idanuwanshi rufe, yana kwance saman nashi gadon, "Idan ma akwai wanda zai 6alla musu gado to bai wuci ku ɗin nan ba, saboda kune ƙattai da kai da haris da mubeen da naufal, gadon ma yayi maku ƙanƙanta" parveen ce tai maganar tana gatsina mashi hanci, Wani irin kallo haris da javed suke jefa mata jin abunda tace, Naufal dai bai tanka musu ba, tun da ya farka bai mike zaune ba, mubeen dai ne ya tada kanshi saman pillow, "Kina wuce gona da iri parveen, da alama yau kinci kin ƙoshi, shiyasa kike gaya mana magana" kafin parveen ta mayar mashi da martanin maganar da yayi, muryar naufal ta katse su da cew "wai ba dai har yanzu, maji daɗin gadon can Bai sanya uniform ɗinshi ba? Nagan su ajiye gefen shi," yai maganar yana kallon gadon Danish Bawan Allah ya baje sai sharar baccin shi yake yi, haris yace"ae kasan halin shi, ba yadda banyi dashi ba, akan ya sanya kayan amma yaƙiya, abincin shi ma yaƙi ci, narasa ya zanyi da Danish yafi ƙarfina...." Haris na ƙarasa maganar, parveen tace"ae wlh indai cinyar kazar shi takai anjima tsakar dare bai ci ba, Sai na cinye ta, in haɗa da fruit ɗin, Ni natsani inga ana wulaƙanta abinci, " Tana magana tana hura hanci, Harara Naufal Ya jefa mata Daga kan gadon shi, Yace"Sannu MAJI DAƊIN ABINCI, uwar haɗamammu, ke da ba ki gajiya da abinci, Ga shi ni ko ajiki banga kina ƙiba ba, " murguɗa mashi ƙaramin bakinta ta yi, batare da ta bashi amsa ba," A6angaren Angel dake a tsugunne gaban tukunyar fulawa, ta ƙurawa furennin idanuwanta, Hankalinta ya ɗan kwanta ganin furen batool Lafiyar shi ƙalau, jikin shi yai kyau launin shi ya ciza, haka zalika furen daddynta Yayi kore shar dashi, Addu'o'i ta shiga jerowa tana tottafa ma furennin, bayan ta kammala bata miƙe ba, Zurfin tunani ta shiga akan yarda za'ae ta karya alƙawarin da ke tsakaninta da Danish, Dole ta yi mishi dabara. "Angel!" firgigit tayi Jin an ambaci sunanta, da sauri ta sanya tafin hannayenta ta share hawayen dake akan fuskarta kafin ta juya ta kalli ƙopar shigowa cikin toilet ɗin, bakowa bace face Azeeza, fitowarta kenan daga cikin ɗaya daga Cikin makewayin nasu, sai faman sakin murmushi take yi, "Azeeza, haka na koya maki yadda ake shiga toilet? Batare da neman izni ba"? Fuskarta aɗan ɗaure tayi mata magana, ɗaure fuska azeeza tayi tana tur6una fuska, kamar zatayi mata kuka tace"Ae Naji muryoyinku keda haris kuna magana, duk da bana jin ku sosai, naga ya shigo, shiyasa nima na shigo" zuba mata ido angel tayi ganin yadda take magana tana wani farfari da idanuwanta, miƙewa tsaye angel tayi tare da juyowa ta nufi bakin door ɗin inda azeeza take a tsaye, Ruƙo hannunta ta yi acikin nata, taja ta suka dawo Cikin ɗakin, a tsakiyar ɗakin suka samu su Hannah, Sun ɗauko madubin nan suna kallon fuskokinsu, Yadda kasan sun ruƙe Waya a hannunsu Suna ɗaukar Selfy, gayun ne bai ƙare ba, dama ɗazu gajiya suka yi shiyasa suka ɗan kwanta, Yanxu sun wartsake, mutun Uku ne basu sauko daga kan gadon su ba, Danish da Haris sai deeja, amma su mubeen duk sun sauko, suma suna kallon madubin, ba ƙaramin burgeta su ka yi ba, tana fata wata rana Idan Allah yasa suna da rabon tsira su ɗauki pics tare da ƴan uwanta. kafin su ƙarasa inda su hanna suke, Tana jiyo muryar Rubina tana faɗin"Allah yasa baƙin da za'a kawo musu basu kaisu kyau ba" Yasmin tace"ke damuwarki kenan, Ni fatana Allah yasa akawo mana masu hankali da natsuwa," parveen tace'Ni kuma bana son masu shegen cin abinci, Allah yasa akawo mana Irin Danish, marasa son cin abinci, sai mu dinga yi musu wayau idan sun rage abinci mu kwashe mu cinye" tana magana tana kwatanta yadda zasu dinga kwashe abincin da hannunta, gaba ɗaya suka saki dariya, "Allah ya shirye ki parveen, baki da burin daya wuce abinci abinci, " mubeen ne yai maganar, Naufal yace"ae shiyasa na sanya mata maji daɗin abinci, sabon sunan parveen kenan, ita kuma azeeza maji daɗin shagwa6a" Yana rufe baki, Hanna tace"ita fa angel"? hannu yasa ya toshe bakin sa tare da cewa"Rufa min asiri, kunfi kusa da ita, ku bata sunan daya dace da ita," murmushi angel tasaki yayin da take kallonsu tace"Ae basai wani ya faɗi ba, Ni da kaina zan bama kaina sunan daya dace ni," Hayaniyarsu ce ta farkar da Danish, gaba ɗaya sun cika mashi kunnan shi sun hana shi sakat, bakomai ya faɗo mashi aranshi ba, face maganar da haris ya faɗa mashi akan sabbin uniform da kuma cin abinci, baya so haris ya daina Kula shi, ko dan saboda haka zaisa kayan, a hankali Ya miƙe zaune yakai hannu ya ɗauki uniform din ba wanda ya lura dashi acikinsu, saukowa yae daga saman gadon cikin kasala Ya nufi sashen toilet dinsu Ya shige, Bayan wasu ƴan mintuna, Suna Cikin yin firarsu da raha, Kwatsam Suka ji parveen ta fasa ihu, Mai matuƙar razanarwa a gigice suka kalle ta, Ta zazzare idanuwanta, Yayin da take kallon bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗinsu, Da sauri Suka kai idanuwansu kan ƙopar, Wa'iya zubillah, Tabarakallahu ahsanun kaliqin, Kusan atare suka waro idanuwansu waje tamkar eye balls ɗinsu zasu faɗo ƙasa saboda tsabar yadda suka zazzare idanuwan, Sun saki baki Galala suna kallon shi yayin da yake shigowa cikin ɗakin, Tsarki ya tabbata ga wanda Ya halicci wannan bawa, Maƙerin wannan kyakkyawar Halittar, mai matuƙar jan hankali da ɗaukar ido, Hatta haris da deeja dake kwance saman shimfiɗarsu, sai da su ka miƙe zaune sakamon Ƙarar da parveen ta saki, A wani irin yanayi suke bin shi da kallo from head to toe, black trouser ɗin Ya xauna mashi sosai, A bunka ga dogon namiji, daga sama Ya sanya red vest ɗin shi, tayi tighting ɗinsa, tayi mashi kyau ta fito da ainihin Farar fatarshi, Daga saman Jar vest ɗin ya ɗaura wrap Coat ɗinsa black colour, Abunda ya ƙara ƙawata kyanta, bai ɗaure igiyoyinta ba, hakan zai baka damar ganin ƴar ta cikin, saman dogon wuyanshi ya rataya Cotton scarves ɗinshi red colour, Ya ɗaure yalwatacciyar sumar kanshi ta baya Ta zubo mashi, Wohoho, A fagen kyau Danish Yana a mataki na farko, don da ace zai shiga gasar kyau to kuwa yana ɗaya daga Cikin waɗanda zasu lashe gasar babu tantama, Kayan sun dace dashi, yadda kasan don shi akayi su, tausasan red lips ɗinsa launin su yayi Ja sosai sunyi matching da Cotton scarves dinsa da kuma Red vest ɗinsa, Launin ƙwayar idanuwanshi, russet brown sai ɗaukar ido suke yi, ga eye lashes ɗin nan nashi masu tsayi da cukowa sun ƙawata zagayen idanuwanshi, Wallah An rasa me magana acikinsu gaba ɗaya Danish Ya shammace su, Mamaki ne da al'ajabin kyawunsa sunyi matuƙar gigitasu, sun rasa gane a tsakanin shi da Angel waya fi wani kyau, ita irin zazzafan kyau ne da ita, wanda farat ɗaya ka kalle ta sai gabanka ya faɗi, shi kuma nashi wani irin sanyi ne dashi, mai narkar da zuciya, Ganin yadda suka zuba mashi na mazurinsu suna kallon shi nan take yabi ya rikice, a ruɗe ya juya ya koma sashen toilet ɗinsu, Ya jingina bayan shi jikin bango yana faman sauke ajiyar zuciya, "Allah yasa bani kaɗai nake gani ba" parveen ce tai maganar, azeeza tace"Ae duk mun gani, wlh Danish Yayi min kyau, kamar in sace shi, muryar parveen kamar zatai kuka tace"Yafi abinci kyau da kyan gani," gaba ɗaya suka saki dariya, Hanna tace"Speechless bansan da wasu words zanyi amfani wurin Bayyana irin kyan da danish yayi mini ba" naufal dai sai jinjina kai yake yi, da alama shima ya rasa tace wa, Inaga uwar gayya wato Angel, babu wanda ya lura da ita, tuni ta zuƙunna ƙasa, zuciyarta kamar zata buga, Bakomai take tunani ba face Hamshaƙin Kyan Fuskar Danish, Mamaki take wai a ina ya gado wannan kyan nashi? Su wanene Iyayen shi? Tama rasa da wani jinsi zata kwatanta shi, Larawa ba ne indiyawa ne, turawa ne, South korean ne, Ko kuma Nigerian ne!! A ƙarshe dai Zuciyarta ta bata amsa da cewa"Yafi kama da jinsin aljanu, kiyi tunani xaiyi wuya ya kasance mutun ne" murmushi taɗan saki, ƙuruciya ta motsa, nan take ta yadda da abunda zuciyarta ke raya mata, Muryar haris ce ta dawo da ita daga zurfin tunanin da ta shiga "Ina takalmanshi suke, " yai tambayar Yayin da yake saukowa daga saman gadon shi, Jiki na rawa parveen ta nufi akwatinsu, Ta buɗe ta curo takalman Danish Ta miƙa ma haris Ya sanya hannu biyu ya kar6a, ya juya ya nufi sashen toilet ɗin nasu, yana fadin"kada wanda ya kuskura ya biyoni, Duk kunbi kun ruɗamin ɗan uwa," da zolaya yai musu maganar, Yana shiga ya samu Danish Ya lumshe idanuwanshi, A gaban ƙafafuwan shi, haris Ya zuƙunna, Ya ajiye takalman tare da kai hannu Ya damƙo ƙafar shi, a firgice Danish Ya ware fararen idanuwanshi akan fuskar Haris, ya ɗan tsorata saboda bai yi tsammanin zaiga mutun ba, Fuskar haris dauke da murmushi yace"Allah ya taimake ka, da ace yau ba ka sanya kayan nan ba, da babu ni babu kai, amma tun da ka sanya to muna atare," murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish, A tsanake Ya sanya mashi takalman, Bayan ya kammala ya ɗago, suna fuskantar juna, Ya ruƙo igiyar Coat ɗin, Ya ɗaure mashi ita, Kafin ya sanya hannayenshi biyu Ya tallabo fuskarshi wani irin murmushi suke sakar ma juna, "Dole na ƙaunace ka ɗan uwana, kai ɗin na daban ne," haris ne yai maganar, tare da janyo shi jikin shi, yae hugging dinshi, zagayo da hannayenshi yayi abayan haris yaɗan ƙanƙame shi, Muryarshi asanyaye yace"Nima ina ƙaunarka haris, ina jinka kamar yadda kake ji na acikin zuciyarka, am so proud of u, kai tamkar kyauta ne agare ni, bana tunanin zan samu madadin ka a duniyar nan......." tsabar farin Ciki yasa haris sakin dariya yana bubbuga bayanshi da hannun shi, haƙika yaji daɗin kalaman danish agare shi, cos this is the first time daya ta6a furta mashi hakan, "Mu kuma fa"? kamar daga saman suka jiyo muryoyinsu Naufal, da sauri suka raba jikinsu daga Na juna, Su ukun nan ne, Mubeen da Javed, sai kallon su suke yi, ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish Ware masu hannuwanshi yae alamar suzo suma ya rungumesu, aiko da sauri suka ƙarasa Ya haɗasu duka ajikinshi, Lamarin yayi matuƙar burgesu, Gwanin ban sha'awa, musamman yadda Danish Ya sake dasu Yana faɗa masu da ɗaɗan kalamai akan irin ƙaunar da yake yi masu abunda bai ta6a yi ba," Suna Cikin hakan suka Jiyo muryar azeeza da shagwa6a tana fadin"To mu fa? Baza a rungume mu ba," atare suka ɗago suna kallonta, ta ruƙe qugu abakin ƙopa, Haris yace"sarkin rigima, ki koma ciki, gamu nan zuwa, ɗaya bayan ɗaya sai Danish yabi ku ya rungume ku," Fuskarta ɗauke da murmushi ta watsa da gudu ta koma cikin ɗakin, tana faɗa masu parveen cewa Ga Danish nan xai zo ya rungumesu ajikin shi, Parvee tace har na ƙosa in shaƙi ƙamshin Jikin shi," kamar wata mayya, Kusan atare suka shigo Cikin ɗakin, Haris yana a ruƙe da hannun Danish, ya zama tauraro Acikin taurari, A tsakiyar ɗakin suka tsaya, A lokacin angel ta koma gefen gadonta, har ta cire wrap coat dinta, ta ɗaurata saman mattress, ta ɗaure fuska babu walwala, "Ka faɗa musu irin mahimmancin da suke dashi awurinka kamar yadda ka faɗa mana" acewar haris, Natsuwa Danish yayi, A yayin da yake bin su da kallo sun jera layi kamar mabuƙatan dake jiran abasu sadaka, duk sun ƙagara su ji mai zaice, Bakowa yake son gani ba face ANGEL, ta wutsiyar idon shi ya hangota, saman gado sai hura hanci take yi, kamar Zakaran daya sha sigari, "A yau inaso na faɗa maku, irin mahimmancin da kuke dashi awurina, You are more than just a friends saboda kun xarce hakan, Na ɗauke ku tamkar iskar da nake shaƙa, wurin yin numfashi domin in tsira, baku da banbanci da bugun zuciyata, Ina matuƙar ƙaunar ku, I luv you more than words can say bani da tamkarku a duniyar nan, i can even sacrifice my life for u guys" tunda ya soma jawabin nan, angel take ta satar kallon la66ansa, wani irin yanayi take ji mara misaltuwa, duk ta rasa sukuni, "We're not only prisoners, we're life partners, bonded together by fate. We were meant to be under the same roof, sharing a common destiny. My hope is that one day we can be proud of each other, and Proud of the journey we've taken and the challenges we've overcome, we are more than just cellmates, we are family." saboda tsabar daɗin kalaman shi da suke ji, har wani lumshe ido sukeyi, muryar tashi ce kamar ana busa sarewa gashi ya iya jawabi kamar jinin sarakai, "Abubuwa da dama sun faru atsakaninmu, masu daɗi da marasa daɗi, dama shi haka zaman tare yake, sai ana haƙuri da juna, ni mai laifine amma still ina da damar da zan gyara kuskure na, duk da nasan akwai waɗanda suke yi min kallon mara amfani, inaso suyi mini uziri, nima bana so na dawwama ahaka, kodan saboda farin cikin ku, Zanyi ƙoƙari na gyara alaƙar dake atsakanina da kowannanku......." wannan magnar da Danish yayi tayi matuƙar karya musu zuciyoyinsu, musamman deeja da Angel, sunji wani irin acikin zuciyoyinsu, "Aduk lokacin dana aikata ba dai dai ba, ku yi min uziri kada kuce zaku ƙaurace min, cos that's not the solution, kamata yae ku ja ni, ajikinku kamar yadda haris yake yi min shi kaɗai ne acikin ku yake faɗa min cewa nayi kuskure in gyara, kuma ina jin dadin hakan, Bayan shi mutun ɗaya ce nasan zata Sanya ni ahanyar dai dai, ko ban fada ba kunsan kowacece......." daƙyar ya ƙarasa maganar, saboda raunin da zuciyarshi tayi mashi, tunawa da ƴar uwarsu Batool, mai kyakkyawar zuciya, "Duk da abunda nayi ma batool, Ni shaida ne akanta, idan yau ta dawo Cikin mu, bazata ta6a gudu na ba, zata fahimce ni, but why wasu suke ganin laifi na"? da sauri angel ta kifa kansa saman pillow, wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke mata fuskarta, sosai ta ƙanƙame pillow ɗin, kalaman shi sun kashe mata jiki, yanayin yadda yake furta su, da alama abun yana hurting ɗinsa. "Ƙaurace min bashi bane mafita, saboda muna son junanmu, zamu cutar da kanmu ne, gaba bata da amfani, amma in mu ka yi haƙuri da juna, wata rana xamu cimma nasara," tana ji aranta cewa waɗannan kalaman saboda ita yake furta su, Bai ƙara cewa komai ba, tun da yakai ƙarshen maganarshi, Jiki na rawa azeeza da parveen suka nufe shi, atare suka faɗa jikinshi, suna kuka, Hannayenshi biyu ya sanya wurin rungumesu, Jiki asanyaye Deeja da su hanna suka matsa kusa dashi, Suma suka kwanta bayan Su parveen dake rungume ajikinshi, Tsabar farin Ciki ne yasa su haris suka ɗaga hannayensu suna tafa mashi, Hada su naufal da javed and mubeen, atare ƴan matan suka haɗa baki suna faɗin"We luv u so much our elder bro Danish, muna matuƙar ƙaunarka, munsan cewa ba za ka ta6a bari a cutar damu ba, da son ranka, sai don ba yadda xaka yi ne, mu ma mun gane kuskuren mu naƙin fahimtarka......" Sosai Danishi yaji daɗin kalamansu, hada yafiyarshi suka nema akan bugun da su kayi mashi lokacin da aka ɗauki Batool, Yace masu bakomai ya cancanci hakan ne, Ɗaya bayan ɗaya saida yabi kowaccensu, Ya rungumeta ajikin shi, Su parveen an samu abunda ake so, Har wani ƙanƙame shi take yi, kamar zata 6alla wuyanshi da hannayenta, har sai da haris yaja wuyan rigarta, ya janyeta daga jikin Danish Cikin zolaya yake faɗin"Halan Yayi maki kama da Tsokar nama ne? Shiyasa kike ƙoƙarin lashe jikin shi," Gaba ɗaya suka saki dariya, shima Danish ɗin murmushi ne akan fuskarshi, Mubeen ne ya lura da angel data kifa kanta saman pillow, ya ɗaga murya tare da cewa"Jama'a mun manta da Mai girma Angel" yayi maganar yana nunata da hannun shi, haris yace"yawwa ƙwara daka tuna min, Angel ki taso kema ki rungumi ɗan uwanki, kamar yadda kowa yayi, yau muna Cikin nishaɗi," da biyu haris yai maganar yasan basu shiri, banza ta yi dasu bata ce komai ba, Azeeza ta ruƙo hannun danish tana faɗin"Pls Muje wurinta ka rungume ta itama," janye hannun shi yai daga ruƙon da azeeza tayi mashi, Saboda ba zuwa zaiyi ba, A sharuɗɗan alƙawarin da suka ɗaukar ma juna, Zai nisance ta, da kuma gujewa haɗa ido, idan har yaje kusa da ita Alƙawarin xai karye, Atare suka hada baki suna fadin Pls Danish Muje dan Allah, itama mu sanyata farin Ciki, " ganin yaƙi basu haɗin kai yasa suka koma wurin angel suna lallashinta akan ta taso suje itama ta rungumi ɗan uwanta, duk tana jin sautin muryoyinsu acikin kunnuwanta, sai magiya suke yi mata amma taƙi ɗagowa daga kan pillow, ransu ya 6aci, haris yace Tunda mun bisu ta arziƙi sun ƙiya, muyi amfani da ƙarfin mu" Ya kai ƙarshen maganar yana nannaɗe hannun rigarshi, suma sauran suka nannaɗe nasu hannuwan rigunan, alamar xasu yi dambe, dama ɗabi'arsu ce, naɗe hannun riga, Atare suka tarar ma danish, suka dinga janshi, kamar dutsi sai nishi suke yi, saboda ya toge yaƙi basu haɗin kai, duk yadda yaso su ƙyale shi amma hakan ya faskara, ba zato ba tsammani suka wurga shi saman gadon angel gaba ɗaya ya faɗa saman jikinta, Har wani firgita ta ɗanyi, sai kuma ta lafa, Su azeeza sai ihu suke Yi suna dariya, Hada tafa musu hannu, Bawan Allah Fargaba duk ta cika shi, so yake ya ɗaga ta amma yana shakkar su haɗa ido da ita, kusan atare zuciyoyinsu ke bugawa, Tana iya jiyo sautin numfashinsa dake sauka saman fatar kafaɗarta, "Alƙawari Ya karye tunda Kun hada jiki, Ko ba haka ba guys? Haris ne yae musu tambayar suka haɗa baki wurin cewa"Yeah" sai tiƙar dariya suke yi hankalinsu kwance, kamar waɗanda A ka yi wa Albishir da mukullin fita daga cikin kurkukun ƙaddara, Ita kanta angel mutuwar kwance ta yi, tun da ya faɗo saman jikinta, ta gaza motsa koda yatsun hannunta ne, sai faman sauke ajiya zuciya take yi, yafi a ƙirga, maimakon taji haushin kwanta mata jiki da yayi saima taji wani irin sanyi mai daɗi yana ratsa zuciyarta, ta yi matuƙar yin kewar shi, almost 1 month Basu shiri da juna, till today da Allah yasa Su haris suka taimaka wurin hankaɗo shi, yanzu aiki ya rage nata wurin ƙoƙarin ganin sun haɗa ido, hakan zai tabbatar da cewa Alƙawarin su ya karye...............💋 *❤❤❤PRISONERS❤❤❤* Ƴar ƙara ta saki kamar wadda aka Cixa, a matuƙar ruɗe Danish ya ɗago da kanshi daga saman shoulder ɗinta, sam bai yi tsammanin idanuwanta a buɗe suke ba, saboda ta ɗan lumshe su, tana ganin ya ɗago ta zaro su acikin nashi, har saida yaji gaban shi ya faɗi, Su haris dake kewaye da gadon sai ihu suke yi suna faɗin"Alƙawarin Ya karye, Ya 6alle, Ya ruguje Ya rushe," gwanin ban dariya Sai nishaɗi suke yi abun su, A wani irin yanayi suke kallon juna, ɗaga mashi gira tayi tare da kashe mishi ido ɗaya yadda kasan ƴar duniya tace"Alƙawari Ya karye, Irin wannan kallo haka kamar xaka Lashe ni," lumshe idanuwan shi yae still ya sake opening dinsu slowly on her face, ya rasa dalilin kallon ƙurullan da yake yi mata, ko na second ɗaya baya son ya kawar da eyes ɗinshi daga kallon kyakkyawar fuskantarta. yana jin wata irin natsuwa mai kwantar da tarzoma acikin zuciya, Dariya haris yae tare da cewa"Danish fa suman kwance yae, Da alama Mun kashe mashi baki, Parveen ɗauko musu Madubi Su kalli fuskarsu atare, Ki haɗo mishi Da Naman kazar shi da bai ci ba, xamu tasa shi gaba sai angel ta bashi abaki Yaci, Ko yana so ko baya ehe" gaba ɗaya suka haɗa baki wurin cewa"Dolen shi ne ma, Idan yasa taurin kai Mu tarar masa, kamar yadda mu ka yi a yanzu," jiki na rawa parveen ta nufi akwatin da madubin yake, A jiye ƙarƙashin table ɗinsu, Nan suka kwantar dasu, ɗaya saman ɗaya, ta janyo akwatin Ta buɗe shi, daga sama Mirror ɗin yake, Ta sanya hannu ta ruƙo handle ɗin shi, da gudu taje ta miƙa ma Haris Ya sanya hannu ya kar6a, kafin Ta juya ta nufi gadon Batool, Allah sarki, Har yanzu a ƙarƙashin gadonta suke Ajiye kingin abincin da suka rage, Zuƙunnawa tae tare da tura hannu ta janyo basket ɗin, maimakon taje ta kai musu, sai da ta fara Kai naman baki ta ɗan 6alla, tukunna ta miƙe da sauri taje ta miƙa ma Haris kwandon, yace da azeeza ta kar6a ta ruƙe, tun da shi madubi ne a hannun shi, Bayan azeeza ta kar6a suka ɗan dakata suna jiran Danish Ya miƙe daga Jikin Angel, sai dai basu ga alamun xai ɗago ba, don ya tsare ta da waɗannan fararen eyes ɗin nashi, sun ƙurawa juna ido, kamar ranar suka fara ganin juna, muryarta ƙasa ƙasa tace"Ka ɗaga ni, na fara jin nauyi," da alama bai ji me tace ba, Xaro mashi gray eyes ɗinta tae gwanin ban tsoro ta kuma cewa"Am talking to u my man, Alƙawari ne dai ya karye, ko kana so ko baka so," Bata yi tsammanin zai tanka mata ba, in a smoky voice ya furta"kin shammace ni," murmushi ne ya bayyana akan face ɗinta, "Bani na shammace ka ba, sune suka shammace ka, Kuma taimakon ka su ka yi, ko ba haka ba"? Tae maganar tana ɗan jifar shi da harara, martanin mirmishin ya mayar mata, kafin ya daure ya yunƙura ya ɗaga jikinta, ya koma daga gefe ya gyara zaman shi sama mattress din, ya jingina bayan shi jikin bango, Itama ta miƙe ta jera kafaɗa dashi suka xauna, Yayin da suke fuskantar ƴan uwansu, dake a kewaye dasu, Sai murmushi suke sakar musu, musamman azeeza hada wani kashe musu ido. Matsawa haris yai daga gefen gadon Ya miƙa ma Angel madubin, Tasa hannu ta kar6a, tun kafin ta saita shi saitin fuskar Danish yae saurin shutting eyes ɗinshi, muryar shi tae low wurin furta"Pls angel, ki janye shi bana son ganin shi," sosai ya datse idanuwanshi, naufal yace"Why? Its just a mirror, face ɗin ka zaka gani ba wani abu ba, muna so ne kawai kaga irin kyan da ka yi acikin Sabon Uniform ɗinka, ko ba haka ba guys"? Atare su haɗa baki wurin cewa"Yeah"! Kallon shi Angel tae ganin har jikin shi ya fara kakarwa, Mamaki ya kama su, ko meyasa baisan Kallon madubi, wannan itace tambayar da suke yi ma kansu. "Idan ma tsoron kallon shi ka ke ji, remember that am with u by ur side, u can hold me," jin wannan maganar ta Angel, yasa shi yin saurin xagayo da hannun shi ta bayanta zuwa saman kafaɗarta ta hagu, Ya ɗan kwantar da kanshi saman right shoulder ɗinta, Har ga Allah bai son kallon Mirror, Ba yadda zai yi ne don sun matsa mi shi, kuma a yanzu yana son farin cikin su shiyasa ya amince musu, Kanga madubin ta yi saitin Fuskarshi tare da cewa"Ka buɗe idanuwanka a hankali," bin umarnin ta yae wurin buɗe eyes ɗinshi slowly ya ware su akan Round mirror ɗin, har wani lumshe su yake yi, Murmushi angel ta saki ganin yana kallonta ta cikin madubin tace"Bani xaka kalla ba, Fuskarka zaka kalla" ta6e mata lips dinshi yae irin an takura shi ɗin nan, Su haris sai dariya suke tiƙa, sun samu Abun kallo, hada ƙoƙarin zuƙunnawa bakin gadonsu, saboda sun gaji da tsayuwa, duk yadda ta so Danish Ya kalli fuskarshi acikin mirror yaƙiya sai dai ya kalli fuskarta, Javed yace"its okey, Hakan ma ya wadatas, Yanzu A ajiye madubin gefe, Ga chicken leg ɗinsa nan ki bashi ya ci, idan ya kammala da kazar sai ki ba shi fruit ɗin shi" Amsa mashi tae da toh tana murmushi ta miƙa ma parveen madubin ta sanya hannu biyu ta kar6e shi, ta juya ta nufi box ta ajiye shi, ta dawo ta zuƙunna gefen su hanna, Duk fa wannan budurin da suke Yi basu san cewa Dare Yayi ba, don tuni Hasken Fitilun ceilling ɗinsu Ya ɗauke, Na floor lamps ne Ya Haskaka Room ɗin nasu, ba tare da sun ankara ba, Wasu irin fitilune Da zarar duhu yayi da kansu suke kunna kansu, Kamar dai na saman ceiling ɗinsu, banbancin shi ne, da zarar dare yae suke ɗauke wa su kuma na ƙasan sai in duhu yayi suke kunna kansu, Kuma haskensu baida banbanci, da alama babu mai jin bacci acikinsu, sakamakon baccin da suka sha ɗazu da marece, hada ƙarin hakan yasa suka gaza gane cewa Dare ya yi. Azeeza ce ta miƙa ma Angel Kwandon Tasa hannu biyu ta kar6a ta ɗaura shi saman Laps ɗinta, kafin ta zura hannun ta na dama ta ruƙo cinyar kazar ta ɗago da ita, saitin bakin shi ta kanga mashi ita, Sai gashi Ya xaƙe dai ci ya ke yi su mubeen suna ta yi mishi clapping, sai da ya Cinye rabi Ya janye bakin shi, ta tambaye shi ko ya ƙoshi ne? yace mata eh, zata iya cin sauran, parveen kamar zatai kuka tace mufa,' Dariya angel tae tare da miƙa ma azeeza Naman kazar maimakon parveen tace"Saboda rashin tsoron Allah Parveen Nafa ga wurin da kika yaga, hada sahun haƙoran ki, a jikin cinyar kazar, ko an gaya maki ban lura ba ne," Yatsina fuska parveen tayi, Hada murguɗa baki, Azeexa kuwa ta kar6a cinyar kazar daga hannun Angel, ta ɗan gutsira ta miƙa ma hanna itama ta yaga, ɗaya bayan ɗaya saida kowa Ya Ci naman, A ƙarshe suka miƙa ma parveen Ƙashi, su ka ce Ta gwaigwaye shi, Hada ƴar ƙwallarta saboda tsabar baƙin ciki, kuma hakan baisa taƙi kar6ar ƙashin ba,. Apples ta curo kusan Uku da suka rage mashi, Yace mata shi ɗaya ya ishe shi, sauran ta basu su ci, tace mashi hada sauran fruit din? Don akwai ayaba guda uku, Yace mata Ta ajiye mashi ayaba ɗaya ta basu sauran su ci, Sai daɗi suke Ji, Ta miƙa ma haris Apples biyu da ayaba Biyu Yasa hannu ya kar6a, Shi ya rarraba musu, tare da miƙa ma kowannan su, suka kar6a suna ci. Abaki angel taci gaba da bashi apple ɗin yana Ci, sai da ya ci rabi, yasa hannu ya kar6a, Ya koma yana bata abaki tana ci, Ayabar ma shi ya 6are 6awon Ya zura mata a baki, taci kusan rabi kafin ya ƙarasa cinye sauran, bayan sun kammala suka sha ruwan su dake acikin bottle, Haris ne ya kawar da kwandon Ya maida shi a ma ajiyarsa, Parveen kuma ta kwashe 6awon Ayabar da su ka 6are ta nufi toilet ta zubda su cikin trash can, Daga bisani ne suka gane cewa dare ya nutsa, Angel tace su jira tayi musu addu'a kafin su kwanta, Suka amsa mata da toh, Saukowa tae daga saman gadonta, tabar Danish zaune yana kallonsu, Cikin harshen larabci ta shiga karanto musu addu'o'in tana tottofa masu, suna amsa mata da ameen, bayan ta kammala, Hannah ce ta basu shawarar su Cire sabbin Uniform ɗinsu, Su sanya tsoffin gudun kada su yi squeezing, In yaso gobe da safe sai su maida sabbin, Angel tace kin kawo shawara mai kyau, daga yanzu old uniforms ɗinmu sun zama sleeping dress ɗinmu, Kowa Ya ji daɗin wannan shawarar, without wasting time suka sauya Kayan jikinsu, Kowa Ya ninke nashi ya tura a cikin akwati, Suka ɗauko Tsaffin suka sanya ajikinsu, daga bisani Kowannan su Ya nufi gadon shi ya kwanta Suka ja bargunansu, in a short time bacci yae awon gaba dasu, ɗakin yae tsit ba ka jin hayaniyar komai, Mutun biyu ya rage angel da Danish, babu alamun zasu runtsa, Ae yau suna cikin farin Ciki, Ya yi tsammanin zata dawo ta kwanta saman gadonta, sai kuma yaga ta nufi ƙopar shiga sashen toilet dinsu, har sai da ta shige, kafin ya sauko daga saman gadon yabi bayan ta, A bakin ƙopar toilet din ya la6e yana kallonta, A yayin da take zuƙunne gaban tukunyar flowers din nan, kamar mai ta6in hankali, haka ta zauna tana ba furen Batul labarin abunda Ya faru Yau, hada ƴar ƙwallarta tace"Naso ace kina atare damu, a ka yi wannan shagalin, nasan zaki yi farin ciki sosai, saboda burin ki ne, kiga mun haɗa kan mu, Ina matuƙar ƙaunarki ƴar uwata rabin raina..." kasa ƙarasa maganar ta yi sakamakon hawayen da suka wanke mata fuskarta. Sam ba ta ji takun tafiyar shi ba, sai dai ta ji shi, a gefenta Ya zuƙunna, ɗagowa ta yi da rinannun idanuwanta suka haɗa ido da juna, a hankali ya cire hannun shi ya ɗaura shi saman sumar kanta, Ya ɗan kwanto da kanta saman shoulder dinshi, cikin sanyin murya ya soma lallashinta, Har ya samu ta ɗan lafa, Da kanshi ya share mata hawayen dake akan fuskarta, a tsanake suke kallon furen batool Ya miƙe tsaye babu lanƙwasa, Red leaves ɗin shi sun bubbuɗe sun cixa launinsu, Haka furen daddynta Yana a tsaye launin shi kore Ya cixa, sai dai wani abun mamaki furen Ya xuƙunna, kamar mutun " aɗan ruɗe tace mashi"me hakan ke nufi? Furen dad ɗina Ya zuƙunna," hannu Danish ya kai tare da shafa ganyen furen yace"Bani da amsar tambayarki, amma A ilmin da nake dashi kan furenni, Daddyn ki, Yana yin wani abu adai dai irin wannan lokacin" bakomai ya faɗo mata arai ba, face Sallah, saboda sanin cewa a lokacin baya daddynta yana yawan Yin nafilfilin dare, duk da bata da tabbacin cewa idan Yana araye, ko kuma Lokacin ƙasar Nigeria da kuma Na kurkukun ƙaddara Ɗaya ne, zai Iyayiyuwa asamu banbanci tunda kurkukun tana hasashen ba acikin ƙasar Nigeria Ya ke ba," jin ta yi shiru yasa shi kallonta in a cool voice yace"what are u thinking"? Da sauri tace mashi ba komai, yace mata"muje mu kwanta, idan ma kina so zan goya ki abaya na" murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, har time ɗin ba ta ɗago da kanta daga saman kafaɗar shi ba. wani irin daɗi take ji, ita fa jin Danish take yi kamar wani sashe na sassan Jikinta, da ke taimaka mata wurin yin numfashi, idan ta haɗa jiki da shi, ba komai take tunawa ba, face Daddynta, Yadda take tumurmusarshi, idan suka kwanta a gado ɗaya, wani lokacin da gangan take ɗaura mashi ƙafafuwanta saman ƙirjin shi, duk don saboda ta takura mishi, a lokacin data addabi rayuwarshi, Allah sarki tajuddeen Namijin Duniya! Numfasawa ta yi kafin ta Canza akalar tunanin nata zuwa ga Aunty Aneelerh, Bakomai ya fado mata arai ba, face ranar da ta faɗo musu ɗaki babu sallama, Sun fito daga Cikin toilet Kowannan su ɗaure da white towel a ƙugun shi, hankalinsu ya tashi ganin Angel, Uwar gulma da son tsegumi ga tambaya kamar ƴar jarida, A lokacin ita da uzair duk suka sha Jinin jikinsu aka rasa me magana acikinsu, Ita ko ta ruƙe qugu tana binsu da kallon tuhuma. ta ce su fada mata me suke yi acikin toilet su biyu, har suna haɗa baki wurin ce mata, babu abunda suke yi, dama sunga yayi datti ne shine suka shiga suna mopping ɗinshi, wani irin kallo ta jefa musu tace"To meyasa suka fito da ɗan towels a ƙugunsu? Ina kayan su suke"? Saboda tsabar ruɗi uzair yace"ita ce take wanka, ta kira ni don in cuɗa mata bayanta, saboda hannun ta bai kaiwa" Dariya angel tasaki tana fadin"wai ita zasuyi ma wayau, sun ganta ƴar ƙarama, hmm basu san tasan komai ba, tun da sunƙi faɗa mata, zata je ta faɗa ma daddyn ta ne abunda suke aikatawa acikin toilet, tana kai ƙarshen maganar, ta watsa da gudu zata fuce, aikuwa aguje suka bi bayanta, har suna bangaje juna Abakin ƙopar fita bedroom dinsu, ta dinga yi musu yawo da hankali, tana zagaye falon suna bin bayanta, daƙyar suka samu Allah ya taimake su, suka damƙota, Suna faman sauke ajiyar zuciya, a saman sofa suka zaunar da ita, sai tiƙar dariya take yi tana kallonsu, su fa duk a tunaninsu tasan komai game da ma'aurata, tunda sun san halinta, kamar aljana haka take ga shegen wayau, sai da suka tambayeta me zata faɗa ma daddynta, tace musu abunda suka faɗa mata suna yi acikin toilet, ba ƙaramin kwanciya hankalinsu yae ba, ganin bata fahimci komai ba, yasa aneeerh ta miƙe taje ta buɗe frigde ta dauko mata fura acikin roba, ta miƙa mata, Duk don saboda su mantar da ita komai, Aiko tun da tasha furar nan taji daɗi yakai mata karo, tace musu, ae ta fasa faɗa ma daddynta su kwantar da hankalinsu, Ita yanzu ma gida zata tafi ta kunna kallo" sai bayan da tabar gidan suka dinga yima juna dariya, murmushi ne ya bayyana akan fuskar angel hada ƴar dariyarta, sam ta manta cewa Danish Yana a tare da ita, "Why are u laughing? Ko kin tuna wani abu ne"? Muryar Danish ce ta ratsa kunnuwanta, a shagale ta kalle shi tare da cewa"Aunty aneelerh, matar daddy uzair, su na tuna, ina matuƙar ƙaunarta, saboda tana so na, kamar ita ta haife ni, ba kamar mahaifiyata ba, da ta gudu tabar ni, na tsane ta fiye da mutuwa ta," Fuskarta a ɗaure ta ambaci hakan, Saboda ya faran ta mata rai yace"Idan kina so, zamu Iya duba furen auntynki Aneelerh," da sauri ta ɗago da kanta daga saman kafaɗarshi tace"Are u serious"? Jinjina mata kai yae alamar Eh, Cike da zumuɗi tace mishi Toh, ya duba mata" ta ambaci hakan tare da runtse idanuwanta, tun kafin ma yace ta rufe su, Sai da ya gama kalle kyakkyawar fuskarta, kafin ya miƙe Ya nufi fanfo, Ya kunna shi ruwa ya soma kararowa, Ya tarba tafin hannuwanshi biyu ya ɗebo ruwa ya gumtse shi abakin shi, Da sauri Ya juya ya Koma bakin Tukunyar fulawar, Har lokacin Angel bata buɗe idanuwanta ba, shi kawai take jira Ya bata umarnin ta buɗe su. "Za ki iya buɗe wa yanzu," A hankali take mutsu mutsun buɗe eyes ɗinta, biji biji ta fara Hango tsiron wani kyakkyawan Fure dogo, Launin Ɗorawa, Yellow kenan a turance, mamaki ne ya kamata Ganin wani ɗan ƙaramin fure A jere da dogon furen Shi kuma Launin shi fari fat, Ganyansa masu kyan gaske, ' waro ido waje ta yi yayin da take kallonsu, Tsabar ruɗu ya hana tace komai, Idan ta kalli furen da saita kalli fuskar Danish, Ya tsareta da idonshi ba tare da ƙyaftawa ba, muryarta na rawa tace"Am..ma.ya akai naga furenni Guda biyu? Ɗaya dogo ɗaya kuma ƙarami? What does that mean? Tae tambayar Cikin ƙagara da son jin amsar shi, "I don't know what that means, nima ban yi expecting ɗin furennin zasu futo su biyu ba, bansan ma'anar hakan ba" Tamkar zata fashe mashi da kuka tace"pls Danish, Think about it, am so eager naji ma'anar wannan ƙaramin furen mai kyan gaske," ashagwa6e ta ƙarasa maganar, sai kallonta yake don ba ƙaramin kyau take yi mishi ba, ɗauke idanuwanshi yai daga kan fuskarta, Ya kalli ceilling na tsawon mintuna, Da alama nazari yake yi, can dai ya dawo da dubanshi gare ta, yace"faɗa min ko kina da ƙaramin ƙani ne"? Tur6une fuska tae"A'a, Bani da ƙani, auntyna ma bata ta6a haihuwa ba," murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, kafin yace"duk da bani da tabbaci, but apparently the little flower means a little boy, so there might be a little boy in your aunty's house, a hasashe na kenan, Cos duk wani fure da kika na fitar to mutunne mai rai" Yadda kasan malamin duba haka ya zaƙe yana kora mata bayani, babu alamun wasa akan fuskarshi, tun kafin ya kai ƙarshen maganar, ya lura da irin kallon hararar da ta ke jefa mashi, bata ta6a yarda cewa ƙarya yake yi mata ba, sai yau, ta ya zai ce ƙaramin mutunne furen can, Bayan Ita a iya saninta, Har ta bar Gida babu wata ƙaramar halitta, dama i tace Yarinyar, kuma yanzu ta girma" taso ta ƙaryata shi amma sai takasa, saboda ta fara jin bacci a idonta. "Muje mu kwanta" tayi maganar tare da ruƙo hannun shi, Yace mata ta hau bayan shi Ya goya ta, ba tare da tayi mishi gaddama ba, Ya juya mata back din, Ta daddage Ta haye, ya yunƙura ya miƙe ɗauke da ita suka nufi cikin ɗakin su, ba ka jin hayaniyar komai saita sautin minsharin su parveen, A saman gadonta Ya kwantar Da ita, Yaja mata bargo ya lullu6eta, kamar wata ƴar baby, har ya juya zai nufi gadon shi, Ta ruƙo hannun shi, tare da cewa"Why ba zaka kwana asaman sabon gado ba? Akwai ɗaya daya rage ka kwanta mana" girgiza mata kai yae alamar a'a yace"Nafi son, tsohon gadona, saboda wannan ba mallaki na bane, duk ranar da masu shi suka zo, bazan Ji daɗi ba, saboda na saba dashi" kalaman Danish sunyi matuƙar burgeta, Tana murmushi tace"Ka faɗi gaskiya, don haka nima bazan kwana asabon ba, Muje mu kwana a saman tsaffin gadajen mu" ba ƙaramin daɗi yaji ba, dama yana ta tunanin tafiya ya kwanta shi ka ɗai, tun da sun shirya da ita, yafi son su kwanta suna fuskantar juna,' saukowa tayi daga saman gadon, hannunsu ruƙe Cikin na juna, suka nufi gadajensu, Sai da ta fara bari ya hau saman bed din shi ya kwanta, Ta yi mashi addu'a ta tottofa mishi saman jikinshi, har yana cewa"wai duk tabi ta tofa mishi yawu ajiki," ta bashi amsa da cewa addu'a ce tae mishi, bai dai ce mata komai ba," bayan ta gama Ta koma saman nata gadon ta kwanta suna fuskantar juna, wani irin kallo suke jefa ma juna, tsawon lokaci kafin Bacci 6arawo yai awon gaba dasu............ Good Morning🌅 A washe garin ranar babu wanda ya farka acikinsu, bacci ya yi daɗi, sun saki baki da hanci anata minshari, a hankali motsin buɗe ƙopa Ya soma karaɗe Cikin ɗakin nasu, kafin wani lokaci, Sai Ga Giant Su Uku Masu Kawo musu abinci, Hannayensu ruƙe da wooden trays, Daga bayansu Wani Giant din ne Guda ɗaya Hannun shi biyu ruƙe da table mai ɗauke da tanƙameman Cake, Haɗaɗden gaske, daga gani zai yi daɗi a baki, launin uniform ɗinsu red and black, saman try din da aka ɗaura Cake ɗin Akwai Ƙaramar wuƙa ta yanka cake, tare da spoon, abun dai sai wanda ya gani, a Jikin Cake ɗin an yi mishi rubutu da ya bayyana sunan kurkukun ƙaddara Cikin harshen turanci aka yi shi kamar haka _Welcome to the Destined Prison and happy prisoner's day_ Ya yi matuƙar yin kyau, kusan hawa bakwai ne ajikin cake ɗin, A tsakiyar ɗakin Giant mai ɗauke da table ɗin Ya sauke shi, Sauran dake ruƙe da wooden trays suka sauke farantan saman dining Carpet ɗinsu, basu tsaya jiran su farka ba, a tare suka juya tare da fuce wa daga cikin ɗakin, " ƙarar rufe ƙopar ne Ya farkar da Azeeza daga bacci, abun ka ga ruɗaɗɗa. A firgice ta ware Idanuwanta, Hannunta dafe da saitin zuciyarta, dake ta faman harbawa, Tayi tsammanin ko zuwa za'ae a ɗauki wani daga Cikin su, jikinta na kerma ta ɗan yunƙura ta miƙe zaune don taga su wanene, A tsorace take kallon Cikin ɗakin, Karaf idanuwanta suka sauka akan Ƙaton cake ɗin, mai matuƙar ɗaukar ido, Mamaki ne Ya kamata, Ta zaro ido tamkar ƙwayar zasu ƙundumo ƙasa, Jiki na 6ari ta sauko daga saman gadon ta nufi Cake din, Saboda tsabar girman shi, da kuma tsayin table din dake dauke shi, sun kere mata, bata iya ganin ƙarshen cake ɗin idan tana a kusa dashi, Kamar wata baƙauyar Daji haka ta dinga zagaye Cake din har saida kanta Ya fara juyawa tukunna ta ɗan dakata, Hannunta ruƙe da qugunta, Sai faman Jinjina kai take yi, alamar mamaki, ta wutsiyar idonta, ta hango kamar kayan abincinsu, Da sauri Ta juya ta 6angare da Daning Carpet ɗinsu yake, waro ido tayi, badan tana mamakin Abincin da aka kawo musu ba, face Sabbin farantan da aka canza musu masu tsayi. Wani irin ihun farin Ciki ta saki, kai tsaye sautin ihun ya daki dodon kunnan masu bacci, Saboda tsabar firgitar da su ka Yi, kusan atare suka Yaye bargunan da suka lullu6a dasu, Kowannan su Ya miƙe xaune, wasu suna hamma wasu suna Yin miƙa, hada masu miyan bacci abaki irin su parveen da mubeen, At same time suka kai idanuwansu kan Azeeza Kafin suyi yunƙurin Yi mata magana tai saurin Nuna masu ƙaton Cake ɗin da hannunta," Zallar mamaki da al'ajabi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Nan take baccin da bai ƙarasa sakin su ba, ya washe, ɗaya bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajensu suna tunkarar ƙaton Cake ɗin, a wani irin kasalance, Danish ne kaɗai bai sauko daga saman bed dinshi ba, Yana zaune daga bakin gadon idonshi akan cake ɗin, Ga dukkan alamu baccin bai ishe shi ba, katse mashi shi akayi, sai faman lumshe eyes ɗinshi yake yi, A jere Suka kewaye Cake ɗin, Kowa Ya baza na mazurinsa, Ko ƙyaftawa ba su yi, parveen ce tai ƙoƙarin kai hannu don ta ta6a shi da sauri Javed Ya ka6e mata hannu tare da cewa"Uwar Hankali, Daga ganin cake kinsan Wanda Ya ajiye shi ne? Azeeza ce ta bashi amsa da cewa"Ina tunanin Giants Ne suka kawo shi, tare da breakfast ɗinmu," ta ƙarasa maganar tare da Juyawa tana nuna mashi Dining Carpet ɗinsu, atare Su naufal suka kai idanuwansu kan abunda take ƙoƙarin nuna musu, mamakine Ya ƙara kama su ganin an canza musu farantan abincin su, don suna sane da Irin trays din da ake kawo musu abinci cikinsu, To yau an canza musu wasu sabbin farantai, masu tsayi, Angel dai ta rasa bakin magana, tarasa gane wannan sabon salon na Kurkukun ƙaddara, abubuwa suna ta canzawa, Anya wannan farin Cikin bana ƙarshe bane acikin xamansu Prison? Na farko an canza musu kayan amfani na toilets da sabbin uniforms duk da tsohuwa tace musu itace ta buƙaci abasu akayan don ta faranta mu su, Tsawon kwanaki tunda aka tafi da batool ba'a ƙara ɗaukar wani acikinsu ba, duk da bata ga wani ya ƙara yin menstruation ba, wata'ƙil shiyasa ba'a zo an ƙara ɗaukar wani ba, ta yi zurfi Acikin tunaninta, muryar Naufal ce ta dawo da ita Cikin hayyacinta "Nifa ina tunanin Sabbin prisoners za'a kawo mana Yau, yakamata muyi wani abu akai, Mu gyara musu gadajensu, sannan muje muyi wanka mu sanya sabbin uniform ɗin mu kada suxo su ganmu kaca kaca suce xasu raina mana wayau," Naufal na kai ƙarshen maganar tashi, Yasmin tace"Nima nayi tunanin hakan, idan ku ka lura da rubutun dake akan cake ɗin, Kamar Ana yi ma wasu barka da zuwa ne," eve tace"in dai haka ne kuwa nayi mamaki, daga gani waɗanda za'a kawo mana ƴan gata ne, don ko time da aka kawo Angel ba'a shirya mata cake ba" Mubeen ne ya bata amsa da cewa"ae ita angel ita kaɗai aka kawo daga waje, su kuma waɗannan ina hasashen dukansu ba acikin prison suke ba, Sannan kuma ki duba da kyau Ajikin Cake ɗin an rubuta Prisoner's Day, that mean an shirya shi ne domin mu kan mu muyi enjoying ɗin ranar mu ta prisoners," Da mamaki akan fuskar Hanna tace"Abun da ɗaure kai, Har wani prisoner's day gare Mu," ta6e baki Haris yae, yama rasa ta cewa, kwata kwata baiyi farin ciki da ganin cake ɗin ba, acewarshi maimakon adawo musu da ƴar uwarsu batool, An dage sai faranta musu akeyi, gani yake kamar ana ƙoƙarin ɗauke musu hankali ne daga tunaninta,' a fili Yaja guntun tsoki, fuskarshi amurtuke babu walwala, Deeja ta lura da yanayin fuskarshi, tunaninsu yazo ɗaya, itama abunda take hasashe kenan acikin zuciyarta, sai dai basu fito sun faɗa ma sauran ƴan uwan nasu ba, kodan gudun kada su tarwatsa musu farin Cikin da suke ci. Ganin yadda suke ta zagaye cake ɗin, Cikin Jin daɗi, "Muje mu yi wanka, mu canza kaya, kafin Mu zo mu yanka Cake" Rubina ce tai maganar, da gudu suka nufi sashen toilets, suna ƴar rige rigen shiga, Mutun uku ne suka fara shiga, sauran suka tsaya suna jiran su fito suma su shiga, Waɗanda suka rage Acikin ɗakin Danish dake zaune gefen gadonshi, Sai angel da haris and deeja da kuma naufal dake tsaye gaban ƙaton Cake ɗin, daga bisani ne Angel ta koma gefen Danish ta zauna, tare da kallon fuskarshi tace"Ka tashi lafiya"? Ya mutsa fuska yae muryarshi adisashe yace"A'a, baccin bai ishe ni ba, azeeza ne ta farkar dani," "Ka kwanta mana, ka yi bacci, amma idan kana jin yunwa ka bari mu fara cin abinci, in yaso daga bisani sai ka koma baccin" girgixa mata kai yae tare da cewa"na haƙura da komawa baccin, tun da kin farka ƙwara nima na kasance a farke" Yaƙarasa magnar yana faman lumshe idanuwashi akan fuskarta, "Ko zamuje muyi wanka ne"? amsa mashi tae da toh," Ya ruƙo hannunta acikin nashi, suka nufi toilet, a lokacin su Parveen sun kammala nasu wankan sun fito daga sashen toilet ɗin, Sai da suka je bakin ƙopar toilet ɗin Taga yaki sakin hannunta, tace"Ka shiga mana" ni sai na shiga ɗayan toilet ɗin" da buɗar bakinshi sai cewa"why bazamu shiga atare ba? Ni inaso na taimaka maki ne wurin yin wankan" fuskarshi a yamutse yai maganar, ita ko ta saki baki tana kallon shi, Mamaki Ya hanata magana,' har saida yaja hannunta da niyar su shiga ciki, da sauri ta fusge tana faɗin"Kai fa ba cikakken hankali ne da kai ba, na faɗa maka babu kyau ka daina cewa mu shiga toilet ɗaya, hakan bazai ta6a yiwuwa ba, Kana namiji ina mace kuma ka ce zaka yi mini wanka" ta ƙarasa maganar tana jifar shi da harara, ta lura haryan zu Danish baida linzami, shi dai burin shi yayi mata wanka, sai kace wata ƴar tsana, "Angel ba wani abu bane fa, kafin zuwanki prison ɗin nan, munayin wanka dasu Batool, so wannan ba wani matsala bane....."daƙyar ya ƙarasa maganar saboda kallon da take watsa mishi, "Ba ka ji me ka ce ba? Kafin zuwana kurkuku, That's mean lokacin kuna a jahiliya period! bayan nazo Kuma saina zo maku da tsarkakakken addini, da ya hana mace da namiji su ke6e awuri ɗaya, sannan babu kyau kallon tsiraici, baida amfani ma mutun ya dinga kallon tsirai cin shi balle ya kalli na wani kuma, fatan Ka fahimce ni" ta yi maganar tare da yi mashi gwalo, tana dariya ta fada toilet taja ƙopa ta datse, bayan ta shiga ciki, ta sanya hannu ta dafe ƙirjinta, tana faman sauke ajiyar zuciya, lamarin Danish yafi ƙarfinta, Dole sai tana taka mishi burki, idan ba haka ba, wata rana zaifi ƙarfinta ne ya ɗauketa yakai ta toilet da sunan zai mata wanka, Saboda ta ɗauke su tamkar Ciki ɗaya suka fito, shiyasa ma take bari suna ruƙe juna, don Lokacin da take tare da daddynta, babu namijin daya isa Ya ruƙe mata hannu tun tana ƴar ƙaramarta, bayan shi sai Uncle abdallah sai kuma Uzair, saboda ta tsani Namiji ya ta6a jikin ta, akwai ranar da wani malaminsu na makarantar boko yayi gigin Shafa la66anta, ya gansu pink sun burgeshi, aikuwa ta daddage ta gartsa mashi cizo, ɗan tahalikin nan jinya har gadon asibiti, saboda cizonta tamkar dafi gare shi, zai yi wuya ta ciji mutun batare da zazza6i ya rufar mashi ba, kamar dai yadda ta yi ma danish a kwanakin baya kafin su fara shiri daya tona mata asirin ta ɗauki wuƙa, ta yakushe shi tare da gartsa mashi cizo, zazza6i ya rufe shi har giant suka tafi dashi," tana Jiyo alamun buɗe ƙopor ɗayan toilet ɗin dake a jikin wanda take Ciki, murmushi tasaki saboda ta gane shine Ya shiga, aranta tace"ɗan rainin wayau, saboda kawai ka ganmin budurcina shine zaka sa naci akan sai ka yi mini wanka," ta ƙarasa maganar tana faman Cizon la66a, Kafin wani lokaci gaba ɗayansu su kayi wanka, Kowa Ya cire tsaffin uniform ɗinshi suka maida sababbin ajikinsu, Wani irin kyaune ya bayyana akan fuskokin kowannan su, Farin Ciki ta ko'ina, Sun kewaye Cake ɗin suna ƙare mashi kallon kafin suyi tunanin Yanka shi, Angel tace su jira ta fara yi musu addu'a, Suka amsa mata da to, Kowa Ya natsu A yayin da take karanto musu addu'o'in ta tofa ma Cake ɗin, Haris yace"kin fake da addu'a kina watsa mana yawu akan cake ɗin mu" Da zolaya yayi maganar yana hararanta, gaba ɗaya suka sanya dariya, fararen haƙoransu kamar gonar auduga, "Waye xai yanka mana cake ɗin? maji daɗin gado ko kuwa Maji daɗin abinci"? naufal ne yai maganar, parveen uwar zumuɗi tace"Ni xan yanka" Azeeza tace wlh baza abaki ba, indai aka baki sai an bani nima na yanka" harara parveen ta watsa mata tana faɗi"Dallah jibarki can ƙasa, In banda rigima taya za'ae ki iya yanka cake ɗin nan"? Saboda tsabar baƙin cikin kalaman Parveen yasa azeeza ta zuƙunne kasa tana raira musu kuka," rai a6ace angel ta kalli parveen"bansan meyasa kike son kushe halittar mutun ba, Bakisan babu kyau ba, yanzu ita da kike ma gorin halitta, shin ita ta halicci kanta? Ke kanki fa Girma kikayi kika ganki ahaka, Ko ke kika tsara ma kanki halitta ne" ɗaure fuska parveen tayi tuni idanuwanta sun ciko da kwalla, angel tace"ni ban faɗi hakan don na 6ata maki rai ba, kawai inaso kisan cewa ba abu bane mai kyau kushe halittar mutun, cos bashi yai kanshi ba, haka Allah ke son ganin shi, ke kanki, nafi ki tsayi, Ni kuma Danish Yafi ni, so kinga ni kowa Da irin nashi halittar" ganin zasu 6ata masu farin Cikin su yasa haris, Yin saurin dakatar da Angel ta hanyar yi musu magana"its okey, pls maganar ta wuce, indai akan yankar cake ne na yanke shawarar Danish Shine xai fara Yankawa, saboda shiyafi dace wa Daya yanka shi, Idan ma kuka kwantar da hankalin ku kowa ma xai yanka, ba kuga girman Cake ɗin ba? Ai mutun ɗaya bazai iya yanka shi ba, dole sai an haɗa hannu," Duƙawa Danish yai tare dakai hannu ya ruƙo Azeexa ya ɗago da ita, gaba ɗaya hankalinsu ya dawo kanshi ganin ya ɗaurata Saman wuyanshi kamar wata ƙaramar yarinya, nan fa ta fara washe baki ta koma tana yi ma parveen gwalo saboda anyi mata makawuya tsayinta ya zarce na kowa, "Ku bata knife ɗin, Ita nake so tafara Yankawa" Acewar Danish, da sauri Haris ya ɗauki wuƙar Ya miƙa ma Azeeza dake asaman wuyan Danish, Tasa hannu ta kar6a tana dariya, Ita kanta parveen batasan lokacin data kwashe da dariya ba, ganin yadda Azeeza take alfahari da tsawon da ba nata ba, sai da suka fara ƙirga one two three Kafin Azeeza ta ɗaura wuƙar zata yanka Cake ɗin, sai dai bata kai ga yankawa ba, Suka Ji motsin buɗe ƙopa, a firgice suka kai idanuwansu kan benan, A matuƙar ruɗe suke kallon ƙafar matashiyar budurwar data fara leƙo wa, wasu matsiyatan Highheels ne a ƙafar masu shegen tsini, Kai daga ganin fatar ƙafar ta rainon madara ce fara tas, saboda tsabar ruɗi azeeza batasan time da ta saki wuƙar yanka cake ɗin dake a hannunta ba, Tabarakallahu ahsanul khalikin, wata irin tafiya yadda kasan bata son taka ƙasa, Daƙyar take taka staircases ɗin, takalmanta har wani sauti suke badawa ƙwas ƙwas! Daga gani ba ita kaɗai bace, akwai sauran dake abayanta, kowannan su sanye Cikin Uniform ɗinshi...........❤ Haƙiƙa Ta yi matuƙar tafiya da hankalinsu, Kyakkyawar matashiyar budurwa, jawur da ita, Uniform ɗin Jikinta Style ɗin yasha banban da nasu, Ita nata gajeran skirt Launin Ja Ko laps ɗinta bai rufe ba, fararen tsala tsalan cinyoyinta sun bayyana a suffarsu kamar ba'indiya, daga sama Coat ce launin Ja, daga Ciki ƴar vest ce, Hannunta na Hagu na ruƙe da igiyar ƙatuwar backpack ɗin data rataya saman shoulder ɗinta. yarinyar bata da ƙiba ko misƙala zarratin, sai dai wani abu dake da matuƙar jan hankali ajikinta, shi ne ƙirjinta, duk rashin ƙibarta ƙirjinta a cike suke fam, Boobs ɗinta tamkar zasu fasa rigar jikinta, tana da doguwar fuska, dara daran idanuwanta farare ƙal launin ocean blue, Jar sumar kanta anyi mata kitso guda biyu, bata da yawan gashi sai dai akwai tsayi, wutsiyoyin kitson sun sauko ta side by side na shoulders ɗinta, hancinta hada nose ring golden colour, earrings ɗinta na zallar gold ne, gefen wuyanta zanan tattoo ne na bindin ɗawisu, Launika daban daban, A bunka ga farar fata zanan yayi bala'en yi mata kyau, daga gani yarinyar ƴar gidan wani shege ce, mai ji da Naira, sai dai daga ganin fuskarta, ba ƙaramar wayayya bace, zai yi wuya tayi kunya a ido. Hankulansu Haris gaba ɗaya yana akanta, Har sai da taƙarasa saukowa daga saman benan, ta ɗan dakata da yin tafiyar tana faman wurwuga manyan idanuwanta akan fuskokinsu, Sauran Sabbin Prisoners ɗin dake a bayanta, Daga Cikinsu akwai wani matashin saurayi dogo twins ne shida ƴar uwarshi, wuyansu na sanye da sarƙar cross wanda ke nuni da addininsu, kyawawan gaske, Launin fatarsu kala ce mai tsada wadda ake kira da Chocolote, yadda kasan ɗan wrestling haka ƙirar Jikinshi take, ga wata irin haɗaɗɗiyar sumar kai, Curly har ta gaban goshin kanshi, Uniform dinsu jajayene, Bayansu Akwai wani Ƙaramin yawo da bazai wuci shekara sha biyu ba, Albino ne (Zabiya) Hatta sumar kanshi Fara ce fat kamar hurhura, daga gani baida cikakken hankali don tunda suka faɗo ɗakin ya ke ta tsalle Yana dariya, Bayan su akwai wata Doguwar budurwa yadda kasan fatalwa, Bata da ƙiba ko kaɗan, sai tsawo tubarkalla kamar qugunta zai karye, duk tsayin Danish To ga wadda ta taka shi, gwanin ban tsoro tana tafiya kamar macijiya, launin wankan tarwaɗa ce ta ɗaure guntuwar sumar kanta da ribbom, Tashin sense, tsabar ruɗu Ya hana su angel cewa komai sai kallon kallo suke yi a tsakaninsu da sabbin prisoners da aka kawo musu, Aranta tace wannan karan Hada Jinsin Aljanu aka bankaɗo mana, Mun shiga ukun mu, Ashe Zaune bata ƙare ba, Daga Cikin sabbin prisoners ɗin akwai wata ƴar ƙaramar yarinya da bazata wuci 10 years ba, Komai na jikinta sak irin na azeeza, banbancin shine ita azeeza tana da shekaru, girman jiki ke babu, Ita kuma wannan yarinya ce da gaske, Gata kyakkyawa itama, ga wani ƙato mai manyan kumatu, da mazannai, Namiji ne baƙi wulik, yana tafiya tsokokin Jikin shi na motsawa, hatta ƙirjinshi acike yake kamar na mace, tashin hankali akwai gwarama fa, a hankali Danish Ya sanya hannayen shi biyu ya sauke azeeza daga saman wuyan shi, Ya ajiye ta ƙasa, Yanayin fuskar kowannan su Ya canza, Lokacin da Sabbin prisoners ɗin suka kammala shigowa ciki Su Goma sha takwas ne, Sanye Cikin Uniform jajaye kalar nasu Parveen, A jere suka tsaya cikin ɗakin kamar masu jiran abasu Umarni, Kallon kallo su ke ta yi a tsakanin su dasu Deeja, Kowa Yasha Jinin Jikin shi, A hankali suka soma Jin takun tafiyar mutun daga can saman stair ɗin, Da sauri Su angel suka kai idanuwansu kan Mai shigowa bakowa bace face*TSOHUWA ZAFREEN*cikin shigarta ta jajayen Kaya Ta rufe ko'ina na Jikinta, Idanuwanta kaɗai ne awaje, Yayin da hannayenta ke a ruke da sandar ta, daga bayanta Giants ne kusan su Uku, Gabza gabza, Masu ƙirar Samudawa, suna ƙarasa saukowa Cikin ɗakin, Da sauri Danish Yace masu Parveen su gaishe ta, Atare suka ɗan russina Cikin girmamawa suke gaishe ta, Wani abun mamaki Mutun ɗaya ce bata russina mata ba, Saboda ƙarfin hali irin na angel hada goya hannayenta saman ƙirjinta, Fuskarta babu annuri, don ta gane cewa itace tsohuwa zafreen, Ba ta yi tsammanin zata ankara da ita ba, Sai ji tayi tace"Ke baki Iya gaisuwa bane"? Cikin ƙarfin hali angel tace"Na iya, Ina kwana," Al'ajabi ne ya kama Zafreen, Hankalin Danish kuwa idan yai dubu toh ya tashi, da ido yake yi ma angel magana akan ta duƙa ta gaishe da ita, amma ƴar tahalikar nan sai tayi kamar bata gan shi ba, hada ƙoƙarin ɗaure fuska idonta na kallon ƙasa, Da kakkausar Murya Tsohuwa zafreen tace"Ki gaishe ni kamar yarda sauran ƴan uwanki suka yi mini" Cikin jin fargaba da ƙarfin hali angel tace"wuya na ke ciwo, bazan Iya russina kai na ba, amma ki gafarce ni" Tsabar mamaki yasa Idon kowa ya koma kan Angel, Hatta Giants dake a bayan Zafreen Acike suke da al'ajabin maganar Angel, Idan ka kalli fuskarta zaka ga ta ɗaure ta tamau, kuma babu alamun wuyan nata na ciwo, ita kanta amma a firgice take, saboda wani irin mugun tsora da take ji, kuma da gangan taƙi russina mata, Saboda ba ta yi Niyya ba ne, don bata ga dalilin da zaisa ta ƙasƙantar da kanta wurin gaishe da tsohuwa Zafreen ba. Jinjina kai tsohuwa zafreen tayi babu alamun ta fusata, Sai ma ta miƙa mata hannu don su gaisa, a ruɗe angel ta kalli tafin hannun zafreen dake a sanye cikin jar safa, Wani irin fagaba taji "am happy to see your face, my granddaughter, Ƙwarin gwiwarki ya burge ni, tun da nake a duniyar nan ban ta6a ganin mahalukin da baya jin shakkar Yi min magana irin ki ba, ga ki ƙarama Kamar insa ƙafa in take" Jin wannan magana yasa angel taji hankalinta ya ɗan kwanta, har ta samun damar ɗaura hannunta acikin na tsohuwa tsaffin, Sosai ta ruƙe hannun angel acikin nata, Kafin daga bisani ta sakar mata hannunta, Cikin ƙasaita Ta Juya baya ta kalli Giants da ta zo dasu, Da hannu ta yi masu magana ba tare da ta furta musu a baki ba, Yatsu Biyar ta watsa musu sau biyu, Gaba ɗaya su angel suka shiga ruɗani sunyi tsammanin wani mugun abun zata yi musu sakamakon Abunda Angel tayi mata, Amma sai suka Giant Sun Kalli Sabbin prisoners da suka zo dasu, Da hannu Suka nuna mutun biyar na farko da suka fara shigowa, su ka yi musu alamar su tsaya a ɗakin, Sauran Goman Cikin su Da hannu su kayi musu alamar su wuce su tafi, A matuƙar ruɗe Su angel suke kallon su Cike da mamakin Ina za'a kai Mutun Goma da Giants suka ware? kenan an fasa ajiye su a ɗakin su? can kuma ta tuna da maganar da Batool ta ta6a faɗa mata na cewa Akwai wasu 6angarorin da prisoners suke rayuwa a gidan kurkukun basu ka ɗai bane, wata'ƙil can za'a kai su. A jere mutun Goman nan suka nufi saman Benan zasu koma, Christian ɗin nan Namiji Ya fasa wata irin ƙara da taja hankalinsu, da gudu yabi bayan waɗanda aka tafi dasu, Sai dai bai kai ga ƙarasawa ba, Giants suka Damƙo hannun shi, sosai idanuwanshi suke fitar da hawaye Yayin da yake miƙa hannu yana nuna ƴar uwarshi mace, Yana faɗin"My twin sister pls kada ku raba ni da ita, bazan iya rayuwa babu ita ba, " Fashewa da kuka ƴar uwar tashi ta yi kamar ranta zai fita, da gudu ta dawo ta faɗa jikinshi ta ƙanƙameta, Kamar zai maida ta Cikinsa, wani irin tausayin su ne ya kama su angel, azeeza tuni ta fara yi musu kuka saboda sun yi matuƙar ta6a mata zuciyarta, bayin Allah Kamanninsu sak iri ɗaya, Daga gani suna matuƙar ƙaunar junan su, saboda rashin Imani na Giants suka sa ƙarfi wurin raba su da juna, Su ka tasa ƙeyar macen gaba suka haura saman benan, Sai kuka take tana faɗin"My twin bro, Ka kula min da kan ka, Duk inda za'a kai ni zan dawo wurin ka," shima yana kuka yana kiran sunanta, Ahaka har aka fuce da ita" Bayan fitar su ɗakin yai tsit Ya rage Saura Su Angel da tsohuwa Zafreen sai mutun biyar da aka Bar musu cikin sabbin prisoners, Haƙika Tagwayen sunyi matuƙar ta6a Zuciyoyin su, Namijin sai share kwalla yake yi, idanuwanshi sun yi jawur dasu, ga wata irin zufa dake tsastsafo mishi, Allah kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji acikin zuciyarshi, An raba shi da twin sister ɗinshi, Giant sun yi yankan ƙauna. Gyaran murya tsohuwa zafreen ta yi musu kowa Ya shiga natsuwarshi, Cikin harshen turanci ta soma Yi musu magana "Ina fata tsohuwa Tamira ta yi maku bayanin komai a dangane dani, ba sai na maimaita ba," Har suna haɗa baki wurin ce mata eh, Jinjina kai tayi Yayin da take kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kafin ta tsaida Tsoffin idanuwanta kan fuskar angel, "Sai dai ga dukkan alamu akwai waɗanda basu san wacece ni ba, Amma asannu zasu fahimta" Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta kalli Sabbin prisoners da aka Bar musu tace"Ya rage naku, Ku zauna lafiya ko akasin hakan, Bata shafe ni ba, zan dinga zuwa akai akai ina duba ku, A koda yaushe ku kasance Cikin shiri" A hankali ta soma ja da baya Still idonta akan Angel, Kafin ta ɗauke su tare da juyawa ta nufi stairs ta haye, Giants su ka take musu baya, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin, Nan fa kowannan su Ya shiga sauke ajiyar zuciya, don ba ƙaramin shakkarta suke ji ba, Sai lokacin su Haris suka samu damar yin magana "Wannan wani irin rashin imani ne? Don me za'a raba shi da ƴar uwarshi? Bayan akwai sauran gadajen da kowannan su zai samu wurin kwana, Ni bansan me ke damun waɗannan mutanan ba, tsabar zalunci ne kawai" Haris ne yae magana yana mai jan tsoki, Azeeza tace ni wlh tausayi suka bani bayin Allah, hakanan an raba su" Angel ta shiga ruɗani, Ita damuwarta ina za'a kai sauran toh? Ga kuma gadajen su A ajiye, Allah dai yasa ba wani mugun abun za'ayi musu ba, bakowa tafi jima tausayi ba face christian ɗin nan, Ya yi tsaye hawaye ta ko'ina akan fuskarsa. Danish ne yai ƙoƙarin zuwa wurin shi Ya janyo shi tare da rungume shi yana lallashinsa, Cikin shessheƙar kuka yake faɗa mishi cewa ƴar uwarshi, tun da suka taso atare suke rayuwa komai atare suke yi, basu ta6a rabuwa ba, Amma yau An raba shi da ita," daƙyar Danish ya samu Ya lallashe shi, Har ya daina kukan, Tukunna Ya raba jikin su, Tun da suka shigo ɗakin Yaron nan da aka bar musu zabiya, Sai tsalle Yake Yi yana dariya, babu wanda ya lura dashi saboda Halin da suka shiga, Ya haye saman gadajensu Yana ta ɗaukar fululluka yana watsar dasu ƙasa Hada bargunansu. "Hey, y'all! my name is Unaiza, and i'm excited to get to know u all." Da sauri suka kalli bakin mai magana, wata irin zazzaƙar murya mai cike da kwarkwasa da duniyanci, Bakowa bace face Ƴar madarar nan, da alama taji sunyi tsit basu tarbesu ba, Shiyasa tayi fara yi musu magana, ae daga ganinta wayayyiya ce, Murmushin yaƙe kowannansu ya sakar mata, Batare da sunce komai ba, ta kuma cewa "It seems like we're not welcome at all" Jin wannan maganar yasa Danish Yin ƙoƙarin yi mata magana "it's not like that, We welcome you with open arms. We are excited to have you here and look forward to getting to know you. You are highly welcome here" Fuskar shi ɗauke da murmushi ya ƙarasa maganar, Yana yi musu nuni da gadajen su, don su shugo ciki su zauna. shu'umin murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, irin na tatattun ƴan iska, Ba zato ba tsammani, su angel suka ga ta nufi Danish Tana ƙarasawa gabanshi Ta sanya hannu biyu Tayi hugging ɗinshi ajikinta, Cikin harshen turancin dake nuni da ƙwarewar ta ta furta"Tayi matuƙar jin daɗin haɗuwa da shi, tana fata za'a kar6e su hannu bibbiyu," Ran angel ya 6aci da sauri ta nufi inda suke atsaye, Suma sauran suka bi bayanta, Tana ƙarasawa gabansu ta sanya hannu Ta ruƙo damtsen hannun Danish Ta janye shi daga Jikin yarinyar, ta dinga jefa mata harara, Amma ko ajikinta sai ma ta sakar mata ƙayataccen murmushi tare da miƙa mata hannu don su gaisa "Hi, Am unaizah ƴar gidan daddy, can i know u"? Ta jefa ma angel tambayar, Yatsina fuska angel ta yi, Kamar bazata tanka mata ba, Sai kuma tace"My name is Unaisah, Amma daddyna Yana kira na Angel, shine sunan da kowa Yake kira na" Dariya su ka ga ta saki tare da cewa"Wow, sunan mu yae shige dana juna, banbancin kawai harafin ƙarshe ne, ina fata zamu zama abokai" Da hausa tayi maganar amma sai ka rantse da Allah da turanci tayi ta, Saboda Yadda take furta ta, daga gani baturiyace amma ta iya hausa ba laifi,' Murmushin yaƙe angel ta sakar mata tare da cewa"why not, tun da zama ya haɗu mu wuri ɗaya" murmushi ta kuma saki tana kallon fuskokin su Tace Idan ba damu tana son su gabatar mata da kansu, batare da sun Yi mata musu ba, ɗaya bayan ɗaya Kowannan su Ya gabatar mata da kanshi, koda a kazo kan Danish Yana yi mata bayani dangane dashi har wani lumshe ido take yi tana kallonshi, ran angel ya gama 6aci gani take kamar an kawo musu annoba ne, saboda babu natsuwa atare da yarinyar, bayan sun gama da kansu, Haris ya kalli sauran sabbin prisoners ɗin yace"saura ku ya rage ku faɗa mana sunayen ku, sannan muna son musan daga ina ku ke"_ Ƙaramar yarinyar nan ce ta fara Yi musu magana tace sunanta *JAMIMAH* Itama Prisoner ce a gidan kurkukun ta taso shekararta Goma cuf aduniya," Bayan Jamima Ta kammala gabatar musu da kanta, Wannan Doguwar mai zubin Taliyar indomi Ta faɗa musu cewa"ita Sunanta *SARAH* shekararta, Sha bakwai, Itama rainon kurkukun ƙaddara ce" Jinjina kai su kayi yayin da suka maida dubansu ga kirista ɗin nan suka ce mashi Ya faɗa musu wanene shi, Cikin sanyin murya yace musu Sunan shi*GABRIEL* twin sister ɗin shi kuma sunanta *GABRIELA* shekararsu goma sha bakwai," su angel sun yi mamakin jin shekarun su ashe duk Yara ne, Girman Jikine kawai, Naufal yace"rainon kurkukune ku ma Ko kuwa daga waje aka kawo ku"? Gabriel yace mishi bazai iya tuna komai dangane da rayuwarsu ta baya ba, shi dai kawai a bunda zai iya tunawa twins ne su, yana matuƙar ƙaunar ƴar uwarshi itama tana son shi, tare suka taso basu ta6a rabuwa ba" Maganar shi ta ɗaurewa Angel kai, ga dukkan alamu suma tagwayen ba rainon kurkuku bane, daga waje aka zo su, Saboda babu addini agidan kurkukun ƙaddara, Su kuma Akwai sarƙar cross a wuyansu, hakan na nufin An canza musu tunaninsu ne, Gaba ɗaya sun manta da mutun ɗaya daya rage basu su tambayi wanene shi ba, Kowa ya shafa'a da ɗan ta halikin nan, Sai da Parveen ta tuna da Abincinsu, Da sauri ta waiwaya baya don ta kalli Kayan abinci, Ras taji gaban ta ya faɗi ganin Mahaukacin yaron nan zuƙunne gaban faranti Ya ɗauki Chicken shawarma Yana turawa abaki, rabi na shiga rabi na zubewa ƙasa duk ya cakalkala ta, ga kuma Bargunansu daya wurgo ƙasa da fululluka, Da ƙarfi Ta ambaci"Innalallahi! " gaba ɗaya suka kalle ta, Ganin Tana kallon saitin dining carpet ɗinsu Yasa suma suka kalli wurin, Da gudun gaske parveen ta nufi yaron ta shaƙo wuyan rigarshi Ta wurgar dashi gefe ɗaya, Ya faɗi ƙasa kanshi ya bugu, Maimakon yayi kuka sai ya kama Dariya Yana Wuntsila ƙafafuwanshi, Rai a6ace Parveen ta shaƙo wuyanshi tana faɗin"Wanene kai?daga zuwa yau zaka fara Yi mana hauka? kana da hankali Kuwa....." bata kai ƙarshen maganar ba, sakamakon jin saukar Yawun daya watsa mata akan fuskarta, tsabar fusata yasa ta kikkifa mishi maru ka, ya dinga dariya ba ƙaƙƙautawa, daga gani jaki ne bai jin bugu. Hankalinsu yae matuƙar tashi, saboda sun fahimci cewa Yaron yana da ta6in hankali, Mahaukaci ne aka kawo musu, "Parveen ki daina bugun shi, Baki ga yaro bane"? Azeeza ce tai mata magana, Rai a6ace tace"Babu ruwana da yaro ne, Ubanshi zanci, har ni zai watsa wa miyau a fuska"? Da alama ta fusata, Rigarshi ta damƙo ta goge miyan daya watsa mata a face ɗinta, duk da haka bata ƙyale shi ba, sai da ta sanya hannu ta dunguri kanshi, Kafin ta miƙe ta nufi toilet don ta wanke fuskarta, badajimawa ba Sai ga parveen ta dawo Cikin ɗakin fuskarta ɗauke da lemar ruwa, Sai Jifar yaron take yi da harara kamar ƙwayar idon zasu faɗo ƙasa. Deeja tace"Mun shiga uku, tamu ta same mu, Yanzu haka zamu rayu da wannan Ta6a66an? Naufal yace"Bazamu zuba mishi ido ba, Dole mu koya mishi hankali," tsoki haris yaja batare daya ce komai ba, Danish ne yace da sauran"Idan kuna jin yunwa ga abinci nan, Idan zaku huta ga beds ɗinku nan, sannan......." bai ƙarasa ba yaɗan kalli ƙopar shiga sashen toilet ɗinsu yace"Game buƙatar watsa ruwa ko yin wani uziri wannan ƙopar zaku bi, Anan toilets ɗin mu su ke" Yana magana hankalin shi na akan Matashiyar yarinyar nan, dake ta kallon shi tana faman cizon pink lips ɗinta, ran angel idan yai dubu ya 6aci, bakomai yafi ƙona mata rai ba face ganin yadda take kallon Danish tana cizon le6e, tarasa gane me hakan ke nufi, to ko dai halittarta ce ahaka? Ko kuwa wani sabon salon iskancin ne"? "Bana jin yunwa, I need to take bath, before in kwanta In huta" Ƴar gidan daddy ce tayi maganar tana ƙoƙarin sauke School bag ɗinta, Idon kowa na akanta, Miƙa ma Danish Backpack ɗin tai tare da cewa"Ka ajiye min ita, sannan ka raka ki toilet ɗin, bazan iya ganewa ba" Wani irin kallon harara angel take jefa ma Danish, duk yasha jinin jikin shi, Sam ya kasa kar6ar jakar Unaiza, Sai angel ce ta kar6e jakar tace"Zan ajiye maki ita, sannan zan raka ki toilet ɗin, idan ma kinaso har cuɗa maki baya zan Iya yi" Girgiza kai Unaiza tae tana fadin"No, bana so, ki dai ajiye min back pack ɗin, Shi sai ya raka ni toilet ɗin" mamaki ne ya kama angel, aranta tace"that's impossible, kinzo da bidi'a," Kar6ar jakar tayi daga hannun unaiza taje ta ajiye mata ita gefen donta mai ɗauke da no 16, juyowar da za ta yi, karaf idanuwanta suka sauka akan Unaiza da ke ƙoƙarin cire Coat ɗinta, Bakomai ne ya faɗar mata da gaba ba, face Ƙirjin Unaiza, Musamman da ta ƙarasa Cire rigar Hankalin Kowa Ya koma kansu, Kamar babu riga ajikinta saboda Yadda surar su ta bayyana ajikin vest din, Manya manya dasu kamar balan balan, shatun nipples ɗin sun fito sosai, kamar zasu huda ta, gata yarinya amma tubarkalla, Allah yayita da boobs, " Kwanciyar hankali ya ƙarewa angel, Kishi ne ya addabi zuciyarta, kodan hada ƙarin ita bata da su ne, Oho dai, Bayan Unaiza ta ɗebe Coat ɗin Ta miƙa ma Danish tace Ya ruƙe mata, Hannun shi na kerma ya ruƙeta, wani irin ƙamshi ne ke fita jikin coat ɗinta," hannayenta ta ɗaura saman gajeran skirt ɗinta, Waro ido angel tae baki a sake take kallon ikon Allah, Cire shi tae ya rage daga ita sai Short na mata, " duk su naufal suna a tsaye suna kallon ikon Allah, Miƙe ma Danish Skirt ɗin ta yi"Ka ajiye min su" Kafin yai yunƙurin kar6ar skirt ɗin angel tai saurin komawa wurinsu ta sanya hannu ta kar6i skirt din ta kuma ƙwaci coat ɗin dake a hannun Danish, Fuskarta a ɗaure ta nufi akwatinsu ta sanya mata su a ciki, Kafin ta dawo ta tsaya agefen Danish, "Muje ka raka ni toile ɗin" ta yi maganar tana ƙoƙarin ruƙo hannunshi, Angel tae saurin ka6e mata hannun"Ni zan raka ki," Bata jira amsar da unaiza zata bata ba, Taja hannunta, ta wuce da ita zuwa sashen toilet ɗinsu, sai bayan da suka shige, azeeza da parveen suka kalli juna, Alamar mamaki, sufa sunga abunda basu ta6a ganin irin shi ba, tun da ko tsohuwa nata azube suke kamar silifas, Cikinsu kuwa ba wadda ta ke da su irin na ƴar gidan daddy, har ƙwara waɗan da suka fara manyanta, Sune ya fara fito mawa, amma ita ko wannan ƴar shilan ƙirjinta sunfi ƙarfin jikinta da shekarunta. "Gabriel, banji kace komai ba"? Danish ne yae mishi magana ganin yayi tsaye bai motsa ba shi da sauran ƴan uwan nashi, Cikin sanyin murya yace"Inaso na kwanta, saboda kaina ciwo yake yi min" Nuna mashi gadonshi danish yae da hannu, Yace mashi thanks kafin Ya nufi gadon, Sai da ya fara cire coat ɗinsa, Ya ɗaura ta gefe, Sannan ya haye gadon ya kwanta, Kallon Jamima su kayi ƴar ƙaramar yarinyar nan, parveen ta raya aranta cewa"Wannan dai rainonta zamuyi da alama" Haris ne yace da ita"Kefa? Zaki kwanta ko xaki ci abinci" Ta6e baki ta ɗanyi kafin tace"Yunwa nake ji," Deeja tace"amma ke kike yin wanka da kanki"? Ɗaga mata kai tayi"Eh, inayi yanzu, amma sai ana cuta min bayana saboda hannu na bai kai wa" Murmushine ya bayyana akan fuskokinsu, don ba ƙaramin burgesu tayi ba, gata ƴar kyakkyawa da ita, Hibba tace"idan ma kinaso har wankan sai muyi maki," dariya tasaki tare da sanya tafin hannayenta ta rufe fuskarta, alamar taji kunya. Ruƙo hannunta Haris yae acikin nashi yace"muje muci abinci ko"? Tace mishi eh, " mubeen yace"to itafa Wannan bamu ji ra'ayinta ba, " yae maganar yana nuna Sarah dake atsaye Ta ruƙe qugu, Yatsina fuska Ta ɗanyi can kuma saita ƙaƙaro murmushi tace"Nima bana Jin yunwa, zan kwanta na huta ne" tae maganar tare da juya ta nufi gadajensu, Ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, a sukwane Ta juyo ta kalle su Deeja tace"wai a ina zata kwanta ne"? Nan take su ka fahimci cewa Ta raino gadon ne, Wato yayi mata ƙanƙanta, Hannah tace"Acan inda kuka Baro, a saman Ina ki ke kwana ne"? ta6e baki Sarah ta yi Ba tare da ta bata amsa ba, Ta maida idonta kan gadon, Ta curo bargon saman shi, Ta shimfiɗashi a ƙasa, ta ɗauko pillow ta jefa, Kafin ta cire coat ɗin Jikinta ta ɗaura a ƙasa, Ta faɗa sama gadon ta kwanta. A bunda ya faru bayan Angel ta raka ƴar gidan daddy toilet, suna shiga ciki taja burki ta tsaya Tana faman zazzare blue eyes ɗinta haɗi da yatsina fuska, Angel tace"Ni xan Koma, ayi wanka lafiya" har zata juya muryar Unaiza ta dakatar da ita "Nifa ban fahimta ba, Ina bathtub yake ne? tana nufin (kwamin wanka) Wannan wani irin toilet ne kamar na Marasa galihu" Tsabar mamaki yasa angel sakin baki kamar sakarya tana kallonta, Daƙyar ta iya buɗe baki tace"ba mu da bathtub, Iya a bunda idonki suka gane maki acikin toilet din su muke dasu, Ga Shower nan, Sai kuma bokiti, can kuma Soso ne da sabulu," aruɗe unaiza tace"that's Impossible, ae ni bana sharing soson wanka, Kuma bana wanka in ba a cikin bathtub ba, I can't stay here i wanna go home, cos daddy ba haka Ya kwatanta min school ɗin ba, Yace min fa komai irin na Gidan mu ne, but why naga banbanci"? tamkar zata fashe da kuka tayi maganar, har saida gaban angel ya faɗi jin abunda tace, Wato ita duk a tunaninta School ce aka kawota batasan cewa Prison bane, To me hakan ke nufi? Kodai mahaifinta ne ya yi mata ƙarya kan cewa za'a kawo ta makaranta! Tashin hankali Sai lokacin angel ta tuna da irin uniform ɗinta na gayu, dama ta yi mamakin ganinta da haɗaɗɗun takalma ƴan ƙwaras ƙwaras, Ga gajeran skirt na gayu, Ga kuma ƙatuwar School bag Ta goyo, Tabɗijancan, In dai a bunda take hasashe ya tabbata to kuwa Iyayenta sun Cuce ta, Mamaki Ya hana angel cewa komai, taya akai basu gusar mata da hankalinta ba? Kamar yarda aka yi ma Gabriel? Ko kuwa sihirin ne bai kama Jikinta ba? ta yi zurfi acikin tunaninta muryar unaiza ta katse ta"Pls talk to me! Ni ban fahimci komai ba, game da school din nan," tashin hankali ne Ya bayyana ƙarara akan fuskar angel, miryarta na ɗan rawa tace da unaiza"wacece ke? Dama ke ba rainon Kurkuku bace"? Waro ido tae tare da maimaita sunan prison da angel ta faɗi, Ba don ta fahimci me hakan ke nufi ba, "Ban fahimce ki ba, Naji kince prison, Nifa daddyna yace dani xai sanya ni a high school Na south korea, saboda inason kallon drama ɗin su komai nasu yana ƙayatar dani, Daddyna yana yi min komai nake so, shi ne Da kanshi, Ya sama min admission a school ɗin nan, a gida aka kawo min uniform na sanya ajiki na......" unaiza bata ƙarasa maganarta ba, Angel ta ɗaura hannunta akai,! Irin ta shiga ukun nan, fito wa ta yi daga Cikin toilet ɗin Ta tsaya daga waje tana ambaton"Innallahi wa'inna ilaihirraji'un"! da sauri ƴar gidan daddy ta biyo bayan angel, baiwar Allah duk ta ruɗe ta rasa gane me angel ke nufi, "Pls tell me the truth Ko ba school bane nan ɗin? I ave to know" wani irin kallon tausayi angel ke binta dashi, muryarta kamar ta mashayin giya tace"Zaki iya tuna Ta ina aka kawo ki Nan" girgiza kai tayi"I can't remember, Ni dai nasan time da masu aikin gidan mu, suka taimaka min nayi wanka na sanya uniform da daddyna ya bani, so bayan nan sun rakoni zuwa wurin da motocin bodyguards ɗina su ke, sun buɗe min mota, Na shiga Ciki na zauna, ina ta farin ciki, duk na qagara mu ƙarasa Airport sai bacci ya ɗauke ni, daga nan ban ƙara tuna komai ba, sai dai na ganni Acikin School ɗin nan tare da sauran students din da muka zo da su" Tana magana tana yatsina fuska daga gani ɗabi'arta ce yin hakan, Jinjina kai angel tae yayin da take kallonta, haƙika ta yi mamakin da basu canza mata tunaninta ba, tun da har ta iya faɗin yadda aka kawota Cikinsu, tabbas kowanene Ubanta ba ƙaramin Mugu bane, Azzalumi, Wato shi wayau yayi mata ya fake da cewa za'a kaita Sk don ta yi karatu batasan cewa Sadaukar da ita ya yi ba zuwa Gidan Kurkukun ƙaddara, don biyan wata buƙata tashi, Rayuwarta abun tausayi baiwar Allah, Sai da aka gama sangartata, Daga gani an gama jiyar da ita duk wani daɗi na duniyar nan kafin aka tsamota daga aljannar duniya aka kawota gidan kurkukun ƙaddara, Ganin irin kallon da angel take binta dashi ne yasa tace"Pls Ke nake jira ki bani amsa," A ƙagare tayi maganar, "Ya sunan mahaifinki? Kuma wanene shi"? Muryarta A disashe tace"Ae ni bansan real name nashi ba, na dai san ana kiran shi Jan wuya..." bata ƙarasa maganar ba angel ta katse ta da cewa"Ba ki ta6a zuwa school bane? Da wani suna kike amfani"? Ta bata amsa da cewa"ni tunda na taso ban ta6a zuwa school ba, daddyna bayaso ina shan wahala, A gida ake koya min karatu, yanzu ma don na kwallafa raine akan inason zuwa south korea karatu shine yace zai sani...." Jinjina kai angel tae kafin tace"Amma awace ƙasa ku ke zaune duk da naji kina magana da yare biyu, hausa da turanci so na kasa gane wani jinsi kike" Wannan karan tamkar zata fashe mata da kuka ta yi maganar don ta gaji da tsayuwa, "My dad is from Nigeria and my mom is from England. I've never been to Nigeria, and I don't know my dad's hometown or his job, Ni da Mommyna ne kawai muke rayuwa a england sai ƴan Aikin gidan mu, amma yana yawan zuwa kawo min ziyara daga Nigeria" Hankalin angel ya ƙara tashi, daƙyar tace mata yanzu kiyi haƙuri kiyi wankan idan kin kammala zanyi maki bayanin komai" Girgiza kai tayi"ae bazan iya wanka awannan toilet din ba, saboda ba irin na gidanmu bane, ni nasaba acikin bathtub nake yi, kuma masu aikin gidan mu ne suke taimaka min wurin yin wankan" Kallon ta kawai angel ke yi, Iya cutuwa dai an Cuci yarinyar nan, tama rasa taya zata fahimtar da ita cewa Nan kurkuku ne, ba high school ta ƙasar korea ba? Zaiyi wuya ta fahimce ta, babbar matsalar irinsu Suna da ƙarancin imani, sannan basu da tawakkali, Tana iya ta faɗa mata azo asamu matsala, Ya za tayi da ita? Yayin da su Angel suke a sashen toilet dinsu ita da ƴar gidan daddy, Su kuma can ɗaki suna fama da wannan mahaukacin Yaron, abunda ya faru Suna ƙoƙarin zuwa suci abinci, Eve tace dasu, "Wai nikam Ina Yaron nan yake ne"? Kafin wani ya buɗe baki ya bata amsa suka Ji ƙarar karyewar wani abu acikin kunnuwansu, Agigice suka kai idanuwansu wurin da suka Jiyo sautin ƙarar, ransu yae mutuƙar 6aci ganin Irin uwar 6arnar da Yaron yayi musu, Gaba ɗaya Ya kado da cake ɗinsu ƙasa, Table ɗin Ya 6alle, Cake ɗin ya ƙundumo kasa Ya tarwatse, hakan bai ishe shi ba, sai da ya hau saman Cake ɗin Ya dinga duma hannuwanshi aciki Yana Kwaso shi Yana turawa abakinsa, duk ya 6ata uniform ɗin jikin shi da cake ɗin, A ƙarshe ma sai ya hau saman Cake ɗin ya dinga burgima yana dariya, a fusace parveen ta nufi inda yake, Haris da Danish suna ta ƙoƙarin dakatar da ita akan kada ta buge shi, amma ina ko waiwayon su bata yi ba, wata irin damƙa takai ma wuyan rigar shi, ta ɗago dashi ta daddage ta buga kanshi a ƙasa, azabar zafi yasa shi fashewa da kuka mai tsiwar gaske, tana huci tace"Shege ashe kana jin bugu, ae nayi tunanin kurma ne kai" Sautin kukan yaron ne ya karaɗe kunnuwansu angel dake a sashen toilet ɗinsu, da gudu suka nufi ɗakin suna shugowa suka ci burki suna kallon Yaron dake ta kuka, Hatta gabriel dake kwance yana bacci shi da Sarah sai da suka farka saboda sautin kukan fitinannan Yaron, An rasa me lallashin shi acikin su, haushin shi suke Ji, Ya baƙanta musu rai, duk irin yadda suka ƙwalla fa ransu ga son cin cake ɗin nan ya tarwatsa komai, Farin Cikinsu Ya gushe, Har ga Allah basu Ji daɗin zuwan prisoners ɗin nan ba, Saboda mutun biyun nan dake acikinsu, Mahaukacin yaron nan da Angel ta sanyawa suna Majnun saboda Yaƙi faɗa musu sunanshi, Sai kuma Unaiza ƴar gidan daddy, A ranar Bayan Danish ya lallashi Yaron Yaje dashi toilet ya wanke mishi Jikin shi Da uniform ɗinshi da ya 6ata da cake, Ya shanya su saman igiyar toilet ɗinsu, ya ɗauko bargo Ya ƙudundune shi ajiki yakai shi Daki ya kwantar dashi saman gadon shi, Cikin ƙanƙani lokaci bacci yayi awon gaba dashi, Hankalinsu har ya kwanta, ashe ƙura bata lafa ba, Sun gama shan wahalar gyara ɗakin nasu da ya 6ata musu ya hargitsa komai, Suna ƙoƙarin zama su huta, Unaiza tace musu Yunwa take ji, Suka ce mata Ga abinci can saman dining carpet ɗinsu taje taci, Saboda damuwa ma yasa babu wanda ya waiwayi abinci acikin su, Sai wannan ƙaramar yarinyar jamimah ita kaɗai ta zauna tana ci. Ita ko Unaiza ƴar gidan daddy ta ce musu ba zata ci ba saboda a gidansu saman dining table ake jera mata abinci kala goma sha biyar, sai ta za6a ta darje, hatta abincin ma abaki masu aikin gidansu suke bata tana ci" gaba ɗaya ta rikita su da maganganunta, sun gaza gane inda ta dosa, Duk yadda suka so su lallasheta akan taci abinci taƙi ci, tace musu dole a kira kukun da suke girƙa abinci a makarantar ta, don ta faɗa musu kalar wanda ake girka mata agidan daddynta, idan har suna son zaman lafiya, idan ba haka ba zata yi magana da shugaban makarantar yayi musu magana, " Su angel sun sha dariya kamar zautattu jin wani sokiburutsi na Unaiza, Sun maida ta mahaukaciya, ta zamar musu tamkar Comedy, kuma ita har ga Allah dagaske take basu Umarni, Rashin sani yafi dare duhu. Lokacin da dare Ya tsala, Babu wanda Ya runtsa acikinsu daga su har sabbin prisoners ɗin saboda rigimar Mahaukacin yaron nan MAJNUN! ya addabi rayuwarsu tun da ya farka daga bacci, Ya dinga Tsalle tsalle har saman gadajen su, Ya hanasu sakat, Su azeeza sun sha kuka saboda ƙululun baƙin cikin daya dasa musu, Har bugunshi suka so suyi amma Danish ya hana su, ya basu haƙuri akan kada su ta6a shi yaro ne, ba dan sun so ba suka Haƙura suka ƙyale shi, Taimakon da Allah yayi musu yaron baison duhu, Sun gane hakan ne lokacin da Danish Ya sauko daga saman gadonshi yaje ya kashe floor lamps ɗin ɗakin, Duhu ya gauraye ko'ina, ai kuwa ya birkice musu ya dinga kuka yana fadin su taimaka mashi, dodo zai cinye shi, angel tace munafuki ai kaine dodon daka addabi rayuwarmu ashe kana magana, nayi tunanin kurma ne kai. Daƙyar Danish Ya ruƙo hannun shi Cikin duhu Ya kai shi saman gadonshi ya haye Yana faman sauke ajiyar zuciya, ganin ya samu natsuwa ne, ya tambaye shi ya sunanshi, Muryarshi adisashe ya ce"CHINONSO" jinjina kai Danish yai kafin ya miƙe ya rufa mishi bargo saman Jikin shi. A washe garin ranar da aka kawo musu sabbin prisoners, lokacin Da Giants suka zo kawo musu Abinci, Sun ga haukan da basu ta6a gani ba, wato unaiza ce ta tsare giants tana zazzaga musu masifa akan su bi tsarinta, na gidan daddynta, hada ƙoƙarin ɗauko jotter acikin school bag ɗinta tare da biro ta rubuta musu list na abunda take so adinga girka mata tana ci, bayan ta gama ta je gaban su ta miƙa musu paper ɗin data yago cikin jotter din, tace dasu su kar6a, Kamar gumaka babu wanda ya motsa a cikin su, Su haris suna ta ƙoƙarin fahimtar da ita akan ta matsa daga gabansu basa magana, amma taƙi sauraransu, ba don Allah yasa Naufal Yaje ya janyeta ba, da ranar ta yabawa aya zaƙinta, don wlh mazga zata sha awurin su, don basa ɗaukar raini. A taƙaice Cikin kwana uku sai da suka fita hayyacinsu, Akan mutun biyun nan Unaiza ƴar gidan daddy da kuma Majnun Chinonso, Wata sabuwar rigima ta unaiza, ta faɗa musu cewa ita fa Ta saba agidansu masu aiki suna yi mata tausa, don haka suma dole suyi mata, Kuma idan zata kwanta bacci, Da pillow uku take kwana saman gadonta, ta saba duk in zata kwanta, tana ɗaura kanta saman pillow, ɗaya kuma A tsakankanin ƙafafuwanta, Cikon na Ukun A ƙirji take rungume shi, Ba tare da sun yi mata musu ba, Su Parveen su ka yi mata tausa, Lokacin da dare ya yi Danish da Mubeen suka bata pillows ɗin su don ta kwanta kamar yadda ta saba yi agidansu, Idan fa tace su yi mata abu su ka ƙi yi mata, Kamar ƙaramar yarinya haka zata zauna tana raira musu kuka, waya ga shagwa6a66a Haris yace"Su ƙyaleta Ai wadda tafita iya masifa tazo kuma ta miƙa wuya sun yi rayuwa da daɗi da ba daɗi balle kuma ita, " Wato yana magana akan angel, sai dai fa akwai banbanci sosai tsakanin Angel da Unaizah. Ranar da haƙurinta ya ƙare, ganin anƙi yi mata abunda take so, Tace musu zata kashe kanta, a lokacin sun ɗauka wasa take Yi ashe dagaske take, dama irinsu basu Cika imani ba, basu da tawakkalli, gata dai da sunan musulmai amma babu musuluncin acikin zuciyarta, Suna zazzaune acikin ɗakinsu kamar masu zaman makoki, ba zato ba tsammani suka soma Jin Ihunta Acikin Toilet, Da gudun gaske suka faɗa Sashen makewayin nasu, sai dai koda suka isa ta datse ƙopa, Suka dinga bugu taƙi buɗe musu, Danish ne ya bugi ƙopar da hannayenshi nan take ta buɗe, Suna Shiga Ciki suka same ta kwance Ƙasa Tana burgima, gefenta ledar detergent ce da tasha duk don ta kashe kanta, Rai a6ace Danish yasa hannu ya damƙo damtse hannunta, ya ɗago da ita, tana ta faman shessheƙar kuka, Da gwiwar hannun shi ya daki bayanta, gaba ɗaya saida ta amayar da abunda tasha kaf ɗinsa, cikinta kamar zai 6alle saboda ɗamewar da yayi, Idanuwanta su kayi luhu luhu, Saboda tsabar kuka hada majina ta hanci ta baki, Angel ce ta taimaka mata wurin wanke mata fuskarta, ta kuskure bakinta, kafin ta ruƙota ita da hanna suka shigo da ita Cikin ɗakin a saman gadonta suka kwantar da ita, sai nishi take yi, launin idanuwanta sun ciza, daga gani tana acikin mawuyacin hali, zazza6i ya rufe jikinta ta ko'ina, A kewaye da gadon Su angel suka zazzauna tare da Danish, Sauran Ƴan uwan nasu suna atsaye suna kallonta, "Yanzu idan kika kashe kanki wa kika yi ma asara"? Haris ne yai mata maganar, saboda ƙarfin hali tace mashi"bansani ba, Ni ba ruwana da kowa, Ku ƙyale ni ku bar ni inyi rayuwata, Na tsani ganin ku, bana son Zama acikin ku, i just wanna Go home" Jinjina kai su ka yi, Haris ya kuma cewa"kin ɗauko ta da zafi, Ae duk wanda ya shigo kurkukun ƙaddara, To ya shiga kenan ba hanyar fita, Zaifi ki kwantar da hankalin ki, Ƴar gidan daddy ki yi rayuwarki Cikin salama, kamar yadda kika ga muna yi," Wani irin kallon harara ta dinga jefa ma haris da yae maganar, Cikin harshen turanci ta zazzage shi tas hada yi mishi sharrin halittarshi wai baƙi mummuna kamar buri, A fusace Deeja ta ɗaga hannu zata kwashe ta da mari Danish yai saurin ruƙo hannunta, Suka haɗa ido ya girgixa mata kai alamar karta mare ta, zame hannu deeja ta yi yayin da take kallon Ƴar gidan daddy dake kwance saman gadonta, Wani irin kallon tsana take binsu dashi, angel tace"duk wani abu da kike taƙama dashi muma muna dashi, Idan hasken fata ki ke taƙama dashi Muma duk farare ne balle kice xaki nuna mana wariyar launin fata ehe, Sannan kuma idan gashi ne ki kalli kaina da kyau, Nesa ba kusa ba, Nafi ki tsayin gashi da yawa, haka zalika idan launin ƙwayar ido ne, Na ki blue nawa Gray, Idan wayewa ce, yadda kike taƙama da daddynki, Nima haka na taso Gidan daddyna, Yana gatanta ni duk da bamu da ƴan aiki kamar yadda kike faɗin akwai su a gidan ku, Shawarar da zan baki shine idan har kina son xaman lafiya to kija baki kiyi shiru ki rungumi ƙaddararki, Bawai kice xaki ƙi cin abinci ba, ko ki ce zaki kashe kanki, Domin kuwa babu wanda ki kayi ma asara face kanki. hatta shi daddyn naki da kike taƙama dashi Yana can hankalin shi kwance ya sadaukar dake zuwa ga rayuwar ƙunci da takaici, saboda ya samu abunda yake so........." tun da angel ta doma magana, Ƴar daddy ta zazzaro idanuwanta akan fuskar angel, duk da bata fahimci abunda take nufi ba amma ta shiga ruɗani sosai, Muryarta na rawa tace"Naji kince daddy na ya sadaukar dani what does that mean"? Angel na ƙoƙarin yi mata bayani, Danish yae mata gyaran murya nan take ta fahimci me yake nufi, Wato kada ta faɗa mata. A tsanake Danish Ya soma yi mata magana "Yanzu baki da ƙoshin lafiya, ga shi ko abinci kin ƙi ci, why? Ki faɗa mana me kike so muyi maki wanda zaisa ki saki jiki damu" yanayin yadda yake yi mata magana cikin sigar lallashi ba ƙaramin fusata angel yae ba ganin yadda Unaiza ta tsare shi da idanuwanta har wani lumshe su take yi akan fuskarshi, cikin shagwa6a tace mashi"indai zai bata abaki, zata haƙura taci abincin ko ba daɗi" sakin baki angel tai tana kallonta, Shi ko hada ruƙo hannayenta acikin nashi, saboda jin ta amince indai zai bata abaki, yace mata"ae ba wani abu bane, fiye da haka ma zai iya yi mata, indai zata saki jiki dasu ta xauna batare data ƙara yunkurin kashe kanta ba" Tun kafin ya rufe baki, Ta miƙe zaune tana faman cizon la66anta, Su haris su ka baza ido suna kallon ikon Allah, duk wannan budurin da suke yi, Majnun yana kwance daman gadonshi yana bacci, Shiyasa suka samu salama. Hankalin Angel fa ya tashi ganin Unaisa ta kwantar da kanta saman ƙirjin danish, Hada sanya hannu biyu ta ƙankame shi, tana faɗin"In dai ya ɗaukar mata alƙawarin zai yi mata komai take so, to zata daina tunanin kashe kanta, kuma zata xauna dasu lafiya" tana magana tana tura mashi ƙirjinta ana shi, tsabar takaici Ya hana angel buɗe baki tae mgana, Ba ita ba hatta su Hibba sun lura da irin yadda take matse jikinta dana Danish, Lamarin ya ɗaure musu kai matuƙa, sai kace ba ita bace take ƙoƙarin kashe kanta ba, ta zaƙe sai zuba ma Danish shagwa6a take yi, ba lallai su fahimci me take so ba, saboda su awurinsu bawani abu bane don mace ta haɗa jikinta da na Namiji shiyasa basu kawo komai aransu ba, shi kanshi Danish ɗin Bai janye ta daga Jikin shi ba, Duk da atsorace yake da irin mugun kallon da angel take jefa mashi, Ta riga ta gane ainihin wacece yarinyar, tantiriyar ƴar iskace tazo musu da bidi'a...... (Yakamata angel ta koya mata Sunnah🤣) *❤❤❤PRISONERS❤ Har wani ƙara narke mashi take ji ajikin shi, duk hakan bai ishe ta ba, sai da ta zagayo da hannunta ta bayan shi ta ɗaura yatsun saman gaban trouser dinshi, runtse ido angel ta yi don bazata juri kallonsu ba, Su mubeen hada cewa"tun da ta amince zai bata abincin a baki, Aje a ɗauko food basket ɗin," da sauri parveen tabar bakin gadon unaiza taje ƙarƙashin gadon batool ta ɗauko kwandon abincin da suka rage mata, sai da ci rabon ta kamar yadda ta saba kafin ta miƙe ta koma wurin su ta miƙa ma Danish kwandon Yasa hannu ɗaya ya kar6a Ya ɗaura shi daga gefe saman mattress ɗin. shi kan shi a takure yake da irin yadda take matse shi da hannunta, hada nishi take saki tana cizon le6enta na ƙasa da teeth ɗinta, zuciyar angel sai tafarfasa take yi sam bata so su haris su fahimci cewa Tana Kishin Danish ne, ko shi Danish ɗin ya gane cewa ta damu dashi, duk da ita har ga Allah babban abunda take gudu shine yarinyar ta gur6ata musu tunaninsu, cos daga gani yarinyar ba ƙaramar tantiriya bace, ga dukkan alamu ta saba bin maza, shiyasa ta gaza jurewa take manne mishi duk don ta samu a bunda take so, hakan kuma ba zai ta6a yiwuwa ba, muddin tana numfashi, yanzu ma tayi shiru ne don taga iya gudun ruwanta................" muryar unaiza ce ta sa angel buɗe idanuwanta da suka kaɗa suka canza launi, ashagwa6e take yi mishi magana tana faɗin"ni bana so kana sanya min dayawa, a hankali za ka dinga tura min a baki, ko so kake baki na ya ƙara girma" tana magana tana kallon idanuwanshi cikin shauƙi, babban takaicin angel taƙi cire hannunta daga gaban trouser ɗinshi, har wani murza wurin take yi da hannunta, bawan Allah duk ya rikice ya kasa ɗagowa ya kalli fuskar angel, Su haris kuwa ganin ta fara cin abincin yasa suka bar bakin gadon, Ya rage saura su uku, Unaiza da Danish dake bata abinci abaki sai kuma angel da ta Zabga uban tagumi tana kallon su, abun duniya ya ishe ta. Kamar jira take Danish Ya kammala ba Unaiza abinci, Ta ruƙo Hannun shi acikin nata, Ya ɗago suka haɗa ido, babu wasa akan fuskarta tace"Tashi muje" kallon harara ƴar gidan daddy tayi mata tare da cewa"Wai ke ina ruwanki dashi ne? Na lura Kin sanya mashi ido, kowa yabar ni dashi sai ke"? Jinjina kai angel ta yi batare da ta tanka mata ba, Saboda gani take ma 6ata baki ne yin magana da ita, muryarta da tsiwa tace da Dashi ba zaka tashi ba"? jiki na rawa ya sauko daga saman gadon, sai da ta fara ɗaukar kwandon abincin, kafin taja hannun shi suka nufi nasu gadajen, A ƙasa ta sauke kwandon kafin ta kalle shi duk ya wani sha jinin jikin shi kamar mara gaskiya "Ka kwanta ka yi bacci" shaking head ɗinsa yae tare da cewa"bana jin bacci" harara ta jefa mashi"ƙarya ka ke yi, ni naga bacci a cikin idanuwanka, don haka dole ne ka kwanta ka yi bacci," Lamarin ya ɗaure mishi kai, Jin yadda ta dage akan sai yayi bacci bayan yace shi bai jin bacci, hannayenta biyu ta ɗaura saman fuskarshi, yayin da suke kallon juna, muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"Danish ka kwanta kayi bacci nace, bana so na sake maimaita ba" ganin yadda yanayin ta ya canzane yasa shi ce mata toh, zai kwanta amma indai ta amince zata kwanta suyi baccin atare, tace mishi ta amince, ba tare da 6ata lokaci ba, ta hau saman gadonta ta kwanta tana fuskantar shi, yayin da shima ya kwanta saman nashi gadon, suka cigaba da kallon juna, da zarar taga zai gyara kwanciya muryarta har shaƙewa ta ke yi wurin furta mashi kada ka motsa, duk don saboda kada ya ɗaga kan shi su yi tozali da Ƴar gidan daddy. Kamar tasan kuwa Idonta na akansu, sai faman cizon le6e take yi don ba haka taso ba, taci buri akan Danish, guntun tsoki taja tare da cewa"Ba dai muna a ɗaki ɗaya dashi ba? Zan nuna maki shaiɗanci, zakisan koni wacece, Saina lalata shi ta yadda bazai Iya samun sukuni ba in har baiji ni ajikin shi ba" ta kai ƙarshen zancen zucin nata tare da sakin murmushin shaƙiyanci, ta ɗaura kanta saman pillow, tana shafa tudun ƙirjinta da yatsun hannunta. "Haris banji daɗin abunda yarinyar can ta furta akan ka ba, Allah naso ace Danish ya ƙyale ni na wanka mata mari data gane bata da wayau, wawiya kawai, Ni bata birgeni ba, ƙyamarta ma nake ji" deeja ce tai maganar yayin da suke zaune saman beds ɗinsu, ta6e baki haris ya ɗanyi tare da cewa"Ni banji komai ba Deeja, Na yi mata uziri ne saboda bata da hankali, kuma ban ji haushin kalaman da ta faɗamin ba saboda kina ƙaunata, kuma baki ta6a kushe ni ba" wani irin ƙayataccen murmushi deeja ta saki jin abunda haris yace mata. "Nifa awurina, hatta Danish kafi shi kyau Allah," dariya haris yasaki yana faɗin"Anya kuwa Deeja, Danish fa kika ce? Ɗage mashi gira tae tare da cewa"wallahi dagaske nake, tabbas Danish kyakkyawane sosai, Yafi ka nesa ba kusa ba a idon kowa amma banda nawa, Ni kai kawai nake ganin kyanka, Yadda kasan fure" Saboda tsabar jin daɗin kalamanta, Haris hada ɗaukar pillow ya rungume a ƙirji yana dariya. Yayin da su deeja suke Nan suna shan fira ita haris, Su parveen suna acikin toilet su shida kewaye da tukunyar fulawar nan, Duk sun zuƙunna suna kallon furennin, da alama Gulmace ta ciyo su abunda basu ta6a yi ba, abun ne Ya tsaya musu aransu, Ya hana zuciyoyin su sakat, Lamarin ƴar gidan daddy da Majnun Yasha musu kai, "Wlh an cuce mu, Sai daga baya na dinga regretting kawo mana waɗannan Ciwon kan da zazza6in, mahaukacin yaron nan duk yadda na ƙwallafa rai akan son Cin cake ɗin nan saida ya lalata shi, Har Yau na gaza manta suffar ƙaton cake ɗin acikin idona" Parveen ce tai maganar rai a6ace, Azeeza tace"Allah ni sai naji dama ba'a tafi da ƴar uwar Namijin nan ba, menene ma sunanta? Ta kasa faɗan sunan saboda yae mata wahalar furtawa, Hannace ta taimaka mata wurin cewa "Ni kamar Gabriella naji yace, shi kuma Gabriel, Allah yafi sauran hankali da natsuwa, babu ruwanshi da kowa ko surutu baiyi, yanzu haka yana can kwance saman gadon shi, tausayi ma yake bani, hakanan an raba shi da ƴar uwarshi" Hibba tace"Ae itama Sarah babu ruwanta, matsalarta ɗaya, ƙorafi kullum sai ta ma mutane ƙorafi akan gado yae mata ƙanƙanta ita ala dole ga me tsawo, Ni fa duk wannan Ƙaramar yarinyar tafi burgeni, Menene ma sunanta"? Tae tambayar tana kallon sauran, Rubina tace"Jar miya take da suna ko jimina namanta, nima tana burgeni, babu ruwanta, ita indai zata samu abinci, taci ta ƙoshi gado take hayewa ta naɗe abunta, sai in zatayi wanka, acuɗa mata baya shine kawai damuwarta," Ta6e baki yasmin ta yi, tsegumi ya samu wurin zama a prison, ƴar daddy tazo da bidi'a. "Ni haushina wannan Figaggar yarinyar, wuyanta kamar na cokali mai yatsu, Tun da tazo take ta Turo mana abubuwanta, Allah ji nake kamar insa hannu in matse su, su fashe kowa Ya huta" dariya suka saki gaba ɗayan su jin abunda yasmin tace, Cikin zolaya eve tace"Na lura baƙin Ciki kuke mata don kun gansu tubarkalla ba kamar naku ba, " harara suka watsa ma Parveen da ta yi maganar, Hanna tace"Allah ya kiyaye me za muyi wa baƙin ciki? da alama kin manta a ina muke ne! Ae ba a tunƙaho da kyawun sura a gidan kurkukun ƙaddara, wlh ba fata nake mata ba, amma duk ranar da ta kuskura giants suka ɗauke ta, bana tunanin zata dawo da ƙirjinta yadda su ke" Gaba ɗaya Sun shagala suna ta zuba ɗumi, babu wanda ya ji takun tafiyarta, ashe ta shigo Cikin toilet din da alama taji suna gulmarta ne, shiyasa ta faɗo musu, Kamar daga sama suka ji zazzaƙar muryarta ta karaɗe kunnuwansu "You gossip about me because you're jealous, wow," Wuff suka mimmiƙe kusan atare suka Juya suna kallonta, Daga ita sai jar vest da short, Ƙirjin nan gasu nan tulu tulu, kana ganin fatarsu daga sama ga zanan tatoo ɗinta na bindin ɗawisu, Da yake basu iya gulmar ba, da wasu ne cewa za su yi a'a amma sai suka haɗa baki wurin cewa"Eh, muna faɗin ra'ayin mu ne akan ki, An kawo mana masifa ke da Majnun," ruƙe ha6a tayi can kuma saita saki dariya tana nuna su da zira ziran yatsun hannunta, cike da shaƙiyanci cikin harshen turanci tace"Idan na fahimce ku, kamar kuna kishi ne akaina, saboda kunga abu tubarkalla ba kamar naku ba, ashafe kamar allon bango, Ni fa kokwanto nake yi akan ku anya mata ne kamar ni? Cos ba ku da banbanci da ƙattan dake acikin ku, Komai naku irin na maza ne babu ƙirar mace a jikin ku" tsabar mamaki yasa suka saki baki kamar wawaye suna kallonta, Hibbe ce tai ƙoƙarin mayar mata da martani wurin cewa"To angaya miki muna son nonon ne, ƴar rainin wayau, sai kace ba ɗazu kika gama yunƙurin kashe kanki ba, ae da mun san haka ki ke wlh da mun ƙyale ki....." hibba bata ƙarasa maganar ba, sakamakon tsawar da ƴar gidan daddy ta kwatsa mata, har saida suka ɗan girgiza saboda sautin ta da tsiwa yake fita. "Da alama ku ɗin dabbobi ne, Nasan ba ku san me ake nufi da dabba ba, saboda na lura Jahilai ne ku baku san komai ba, shiyasa aka killace ku kamar yadda ake yi ma dabbobin, A katafaren gidan daddyna akwai irin ku da ake killace wa, muna da zoo don dai banzo da wayata ba dana nuna maku yadda nake watsawa ƴan uwanku dabbobi hatsi Suna Ci" Duk da basu fahimci me take nufi ba, amma sun yi matuƙar har zuƙa, Sai tsuma suke yi. ita ko sai tiƙar dariya take yi fararen haƙoranta kamar bata ta6a cin abinci ya gifta ta cikinsu ba, hannu takai tana shafa boobs dinta hada matsasu Yayin da take kallon su tace"Gaskiya najiye maku baƙin ciki, Waɗannan da kuke gani, majiyar daɗi ne su, sai da su ake ado, dasu ake jan hankalin Namiji, ae duk macen da bata da wannan to bata da banbanci da dutse a idon namiji, babu wani wuri da za'a ata6a ajikin ku aji shauƙi, A bushe ku ke. A matuƙar ruɗe suka kallonta, sun gaza gane inda zancen ta ya dosa, da ya ke ta mai da su shashashu hada cewa idan suna son ganin nata zata nuna musu, don su tabbatar cewa ita ɗin macace ba kamar su ba da suke abushe," shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata. Dariyar shaƙiyanci ta kuma saki tana wasa da harshe tace dasu"wai sun ma san yadda ake yin mu'amala da mace da Namiji? Ko mace da mace? Idan suna so zata koya musu har ma da yadda ake samun baby" Kallon kallo su ka shiga yi atsakaninsu, kamar suce mata eh saboda suna san sanin me take nufi amma sun kasa. "Alamu sun nuna cewa kuna so, to zan fara koya maku yadda ake yi, ni kawai i naso in wayar maku da kan ku ne, ta yadda zamu dinga jiyar da junanmu daɗi," babu wanda ya lura cewa azeeza ta gudu zuwa cikin ɗakin su, tana shiga taje gaban gadon angel ta fashe da kuka tana kiran sunanta, a lokacin angel har ta fara bacci can cikin kunnanta ta dinga jin shessheƙar kuka Azeeza, a firgice tafarka tana faman yamutsa fuska, azeeza bata jira ta gama buɗe idonta nata ba, taci gaba da magana tana fadin "Angel kizo ki gani, ƴar gidan daddy zata 6ata mana tarbiya, wai zata koya mana yadda ake samun baby," tashin hankalin da ba'a sama shi date, saboda tsabar ruɗu, A fujajen angel ta ƙarasa waro manyan idanuwanta akan fuskar azeexa hannunta dafe da ƙirjinta take kallon azeeza sai ku ke ta ke yi baiwar Allah. "Wai hada cewa mu ba mata bane, ƙattai ne, saboda bamu da irin ƙirjinta, kuma ma wai jahilai ne mu ana kullemu kamar dabbobin gidansu....' daƙyar angel ta samu tatattaro maganganun azeeza da suka tarwatsa kwakwalwarta, ta haɗesu wuri ɗaya ta karance su tsaf, tunaninta ya dawo kan saiti lokaci ɗaya ta fahimce su sosai, Muryarta afusace tace"yaushe akai hakan? Ki faɗa min tana ina" Ta yi maganar tare da wurga eye balls ɗinta kan gadon unaiza bata ga kowa ba, Ruƙo hannunta azeeza tayi ta sauko daga saman gadon taja ta har zuwa sashen toilet ɗin su, tun kafin su shiga ta soma jiyo sautin muryar Ƴar gidan daddy tana koya musu yadda zasu Kusanci junansu, Wata irin kururuwa angel tasaki Yadda kasan Badakare ya durfafi filin yaƙi haka ta faɗa Cikin toilet ɗn, Hankalinsu gaba ɗaya ya dawo kanta, Sai huci take yi idanuwan nan sun kaɗa sunyi jawur, Unaiza kuwa koda angel ta faɗo toilet din bata daina magana ba, saboda tsabar futsara hada cewa"halan itama tazo ɗaukar lecture ne" Wani irin kukan kura angel tayi bata dira akan kowa ba sai asaman jikinta, gaba ɗaya suka kife ƙasa, wani irin jahilin bugu tadinga kai mata kamar xata kashe ta, tana kuka tana fadin"wlh baki isa ba, ashe baki da hankali wawayi kawai Jakkar banza, Ae babu babban jahili sai ke daƙiƙiya, Kuma ke ce dabbar badai su ba, Dama ni nasan zuwanki Cikin rayuwarmu ba alkhairi bane, saboda babu kunya atattare dake ƴar iska kawai....." kuka sosai Angel da unaiza suke yi, Duk ta gurjar mata baki hada jini, Su hannah sai kuka suke yi suma suna roƙon Angel akan ta ƙyaleta kada ta kashe ta, tace musu ae ƙwara ta mutu saboda shaiɗaniyace ba mutun ba, Sautin Kukan Unaiza ne Ya isar ma kunnuwan masu bacci na cikin ɗakin, ba arziƙi suka farka danish da Gabriel hada Sarah da jamima, hatta majnun sai da ya farka, Bomb ya tashi sauƙi sai wurin Allah, Da gudun gaske Su Gabriel suka nufo Ciki toilet ɗin, a lokacin har Unaizah ta sume, Amma ita angel bata sani na, bugunta kawai take yi ta haukace bata ji bata gani, Da ƙarfi Danish ya sanya hannu ya damƙi damtsen hannun angel ya janyeta daga saman Unaiza ya jefar da ita gefe ɗaya, Sai faman haki take yi hawaye ta ko'ina kan fuskarta, Sai kace ita aka buga bayan itace tayi mata jahilin bugu, abunda bata ta6a tsammani ba, Danish Ya rufe ta da faɗa ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, Kowa laifin Angel yake gani saboda basu ga hujjar da zaisa ta tayi mata irin wannan mugun mutuwarba, hatta haris sai da yayi mata faɗa, Deeja dai bata ce komai ba, saboda ita ta yarda da angel sosai tasan cewa tabbas wani mummunan abunne Ƴar gidan daddy ke ƙoƙarin bijiro musu dashi shiyasa tayi mata wannan kafurin bugun, Su hanna ma suna abayan angel, gaba da baya, kawai basu ji daɗin bugun da ta yi mata ba ne, Javed ma yana goyan bayanta, shi ko gabriel babu wanda ya ke supporting acikin su, shi da sarah, Waɗanda ke goyan bayan Unaiza danish da haris, ba yadda ba su yi da ita ba akan ta faɗa musu me unaiza tayi mata da har ta sumar da ita amma taƙi gaya musu, gudun kada ta rudar da tunaninsu, abune da basusan da shi ba, yanzu idan suka ji tofa za'a samu matsala wani daga Cikinsu zai ƙwallafa rai akan son sanin ya akeyin abun, daga nan kuma za'a iya samun matsala, su kuma da suka ga taƙi faɗa musu sai suka yi tsammanin ta tsani Unaiza ne shiyasa ta bugeta ba gaira babu dalili. Zuciyarta ta ƙuntata sosai Musamman lokacin da Danish ya nuna ta da indext finger ɗinshi ya gargaɗe ta akan karta kuskura ta ƙara ta6a lafiyar jikin ƴar gidan daddy," Ta zazzaro idanuwanta waje tana kallonshi, muryarta cikin kuka tace"Bazan daina ba, bugunta yanzu na fara wlh, kai ɗin banza har ni zaka nuna da yatsa akan na bugu wannan jakar yarinyar" Sosai angel ta zazzaga musu masifa, daga cikin sashen toilet ɗinsu har zuwa cikin ɗakinsu kana Iya jiyo muryarta, saboda tsiwarta, bayan ta gama masifar, ta kalli su hanna tace su biyo bayanta, su koma ɗaki, Su kuma su haris ga ƙanwar babarsu nan suyi jinyarta, kuma idan ta farka su gargaɗe ta akan karta kuskura koda gigin wasa tace zata ƙara shiga gonarta, babu ruwanta da ƴan uwanta, " Bayan fitarsu angel daga Cikin toilet ɗin, suna shiga Cikin ɗakin su suka samu Majnun, Ya hargitsa duk wata shimfiɗa, Ya watso da bargunansu da fululluka, wannan karan hada akwatin kayansu ya zazzage komai na Ciki Ya watso su waje, Ya kinkimo madubin nan nasu Yana ƙoƙarin kwaɗa shi da ƙasa, Suka haɗa baki suna faɗin Karya kuskura Ya fasa musu madubi," Dariya ya kama yi yana yi musu gwalo, hada ɗaga musu gira yana murmura musu idanuwanshi Sai ma ya maida abun wasa idan ya ɗaga sama sai yace musu"In fasa? Zan fasa" Daga ya yi yunƙurin ƙunduma shi da ƙasa da gudu suke tunkarar shi, Ya dinga yi mu su yawo da hankali, har suna tuntu6e wurin binshi, Saboda bargunansu dake yashe ƙasa, duk in suka ɗaura ƙafarsu, laushin jikinsu ke fusgarsu kamar zasu kife ƙasa, Sun ci baƙar wahala gashi suna matuƙar son madubin, Sun rasa ya zasuyi da majnoon akan Ya ƙyale musu madubinsu. Angel tuni ta nufi gadonta ta kwanta tana ci gaba da yin shessheƙar kuka, zuciyarta duk ba daɗi, zuwan unaiza ya tarwatsa farin cikinsu, Ta zamar musu tamkar annoba, bakomai yafi tsaya mata arai ba face yadda Danish Ya nuna ta da yatsa, duk don saboda ta bugi ƴar gidan daddy, dama ta lura ba ƙaramin jan hankali shi take yi ba da ƙirjinta, nan take zuciyarta ta dinga raya mata cewa sonta yake yi, shiyasa yake goyan bayanta, kamar jinjira haka tadinga kuka bame lallashinta,. Acan Cikin toilet kuwa, Bayan fitarsu angel, Ya rage saura Danish da Haris sai Sarah da Deeja, don tuni gabriel Ya koma cikin ɗakin su, Da taimakon shi su parveen suka kar6e madubin nan daga hannun Majnun, shi ya damƙe musu shi da dabara, ya cafko shi ta baya, aiko yasha bugu a wurin parveen har zaune shi tai, yai ta ihu yana faɗin zata kashe shi, daƙyar su Hibba suka raba ta dashi, tana huci tana jifar shi da harara, tafi kowa tsanar yaron kamar ta kashe shi. *Toilet* Sarah ce ta ɗebo musu ruwa a tafin hannunta suka watsa saman fuskar Unaizah nan take tafarka tana kuka tana ambaton Sunan mommy da daddy tana faɗin where are they? Suna gani mahaukaciya zata kashe ta, zata rabata da rayuwanta amma basu iya zuwa sun cece ta ba, ita ba za ta Iya zama School ɗin nan ba, ko dai su cire ta ko kuma ta kashe kanta, ta gaji da rayuwa cikin dabbobi, " duk wannan Sambatun da ta ke yi akan kunnan su haris, kuma ko kaɗan basu ji haushin kalamanta ba, saboda kallon yarinya suke yi mata, "Jikinta zafi, ba ƙoshin lafiyane da ita ba, amma taƙi natsuwa ta kwantar da hankalin ta," sarah ce tai maganar, Haris yace"Batasan ciwon kanta bane shiyasa, Ni zan koma ɗaki, Danish gata nan kusan yarda zaku yi da ita, lamarinta ya fara gundurata," da biyu yae maganar ganin irin kallon tsanar da Unaiza ta ke jefa mashi, jini duk a hancinta amma masifa ta hana ta shiga taitayin ta. Fuce wa yae daga cikin toilet ɗin, kamar jira ta ke haris ya fita, ta ɗaura idonta akan Danish dake zuƙunne gabanta, duk da tana acikin mawuyacin hali, hakan bai hana ta nuna halin nata ba, hannayenta ta ɗaura saman shoulders ɗinshi, ta rurruƙeshi tana zuba mashi ruwan shagwa6e, A ƙarshe ma sai ta kalli sarah da ta rage acikin toilet ɗin tace da ita"Ki tafi kawai, nagode da taimako, Danish zai ɗauke ni mu dawo ciki," Sarah na fita daga cikin toilet ɗin Ya rage saura su biyu, Cikon na ukun su shaiɗan sai kuma ni da nake rubuta littafin. janyen hands ɗinta tai daga saman kafaɗunsa ta tallabo fuskarshi da su, ta marairaice mashi fuska tana faɗin"Kana ganin irin bugun da ƴar uwarka tayi mini duk ta fasa mini jiki, ni bansan me na mata ba, she hates me for no reason, i don't know why bata son gani na" magana take yi amma hankalin shi gaba ɗaya yana kan ƙirjinta da take ta turo mishi su, sun cika mishi idanuwan shi, ta ko'ina ya rasa sukuni ya rasa madafarshi, linzamin shi na niyar kubce mishi, Shu'umin murmushi ta saki ganin yadda maƙogaran shi ke ta yin sama da ƙasa kamar yana haɗiyar yawu, Ƙara kashe mishi mirya tayi tana fadin"kalli fa gani duk ta raunata min jikina" tae maganar tare da sakin face ɗin nashi da ta tallabe da hannunta biyu, ta zaune dirshan tana ƙoƙarin zame ziririn hannun vest dinta, Gabanshi yae mugun faɗuwa, da sauri ya damƙi hannunta yana girgixa mata kai, muryar shi ƙasa ƙasa ya furta"Ba sai na gani ba its ok, ki yi haƙuri bata kyauta miki ba, amma kema ki daina yin abunda zai 6ata mata rai, angel tana da mutunci bata tsani kowa ba, sai dai rashin fahimta ne dake atsakaninku," Yatsina fuska tayi, tana faman cizon le6enta, ta kuma cakumo gaban rigarshi tana yamutsa tace"ni ba wannan bane damuwana ba, ka tuna alƙawarin da ka yi mini na cewa komai nake so zaka yi min" lumshe mata ido yae alamar ya tuna, hakan ba ƙaramin daɗi yae mata ba, ɗaga mashi gira tai tare da cewa zan fada maka, amma a kunnanka, bana son wani yaji," kafin yace wani abu ta rungumo shi jikinta, tare da kai bakinta saitin kunnan shi tayi mishi raɗa, Ni kaina bansan me ta faɗa mishi ba, raba jikinta ta yi daga nashi, yayin da idanuwansu ke kallon Cikin na juna, batare da ƙyaftawa ba, Allah kaɗai yasan me ta faɗawa babyn angel, Babu wanda yasan wainar da ake toyawa Acikin toilet, tsawon awanni Na cikin ɗaki Suna zazzaune, gefen gadajensu, Majnun ne kaɗai yaketa rawa shi kaɗai yana tsalle tsalle, Marece ya nutsa sosai, Dare Ya doso kai, tuni hasken saman ɗakinsu Ya ɗauke na Floor lamps ya kama, a hankali kowa ya gyara kwanciyarshi ya kwanta, Majnun kuwa anan ƙasa bacci yae awon gaba da shi. Tana kwance tadinga Jin zuciyarta ba daɗi, lokaci ɗaya ta soma tunanin Ina Danish yake? Ta lura har yanzu bai shigo ɗakin ba, gashi har su haris sun jima da shigowa ciki, Zumbur ta miƙe tana kallon gadajensu, wasu har sun kwanta, domin shirya ma bacci, saukowa tayi da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu, shigarta Yayi daidai da fitowar Danish, Ras taji gabanta ya faɗi, kallon kallo suka shiga yi atsakaninta da shi, duk ya kame kanshi, jikinshi har ya soma kakarwa, eyes ɗinshi sai lumshewa su ke yi. Hankalinta atashe take ƙare mishi kallo, sai ta dinga ganin kamar sumar kanshi ta hartse ta nannaɗe, la66anshi sun ɗan kunbura sun ciza launinsu, a ƙarshe ta tsayar da idonta gaban trouser ɗinshi, lokaci ɗaya zufa ta dinga karto mata ta ko'ina, Idanuwanta suka makance, gani take kamar wani abu ya faru, wanda ta gaza gane menene shi, jikinta yae zafi, la66anta na kerma har ta yunƙuro za ta yi mishi magana, kwatsam sai ga Unaiza ta buɗe ƙopar toilet din ta fito, Sai wani miƙa take yi, Hankalinta kwance, Babu wani damuwa atattare da ita, sai kace ba ita bace tasha bugun tsiya a hannun angel ba, Tun da take arayuwarta bata ta6a ganin jaka irinta ba, Hawayene suka cicciko idanuwanta, ta soma girgiza kai tana ja da baya, kafin ta juya da gudu ta koma ɗaki ta haye saman gado, hannayenta toshe da bakinta, gudun kada masu bacci su farka sakamakon jin sautin kukanta, gani take kamar amafarki komai ke faruwa, zuciyarta har wani tafarfasa take yi, wai haka ma don batasan me, su ka yi ba acikin toilet ɗin, kawai ranta ne ya bata cewar wani abu ya shiga tsakaninsu, Zuciya ta gama tunzurata, Atare suka shigo cikin dakin, Unaiza ta wuce saman gadonta, ta haye ta kwanta tana faman sakin murmushi, Danish kuwa Yana tsaye bakin ƙopar sashen toilet dinsu, Wani irin tsorone ya ziyarci zuciyarshi, Sam baison angel tace za ta yi fushi dashi, baisan dalilin dayasa take yi mishi wani irin kallo ba, Daƙyar ya motsa ya nufi gadonta, A hankali ya zauna daga gefen gadonta, muryarshi na rawa ya ambaci sunanta"Angel" kamar jira take yi, ta ɗago idanuwanta jawur ta shaƙi wuyan rigarshi, ta runtse idanuwanta, taci burin ta zazzaga mashi masifa harma ta mare shi amma sai ta kasa, Numfashinta na fita da hucin zafi ta ware gray eyes ɗinta akan fuskarshi, muryarta adisashe ta furta"me namaka Danish? dana cancanci irin wannan ƙuntatawar, ka faɗa min me ku ke yi acikin toilet tsawon lokacin nan kai da ita"? Muryarshi na kerma ya furta"koda bazaki yarda dani ba, zan faɗa maki gaskiya, ta nemi alfarmar tana so ta kwanta ajikina tayi bacci saboda tana tunanin zata samu relief na zazza6in da take ji, shine nace mata bakomai, tsawon time da muna a toilet tana kwance ajikina, tana bacci, sai yanzu tafarka.......' daƙyar ya ƙarasa maganar ganin irin kallon da take yi mishi, acan cikin zuciyarta 100% ta yarda da maganarshi, saboda tasan halinshi sarai, bazai ta6a yi mata ƙarya ba, ku ma koda ace sun aikata wani abu to kuwa tabbas idan ta tambaye shi zai faɗa mata gaskiya ne koda zata kashe shi, Ajiyar zuciya ta shiga saukewa a jere, batare da tayi tsammani ba, taji saukar hannayenshi saman fuskarta, Yana share mata hawayenta, harara ta ɗan jefa mishi tare da cewa"kada ka yi tsammanin saboda kai nake zubar da hawaye na," ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, yace"nasani, amma faɗa min meyasa ki zubar da hawayen ki" yatsina fuska tayi still bata daina hararar shi ba tace"haushinka nake ji, ɗazu kamar in shaƙe ka, saboda me zaka nuna ni da yatsa kana min faɗa akanta? Bayan itace bata da gaskiya bani ba" cikin sanyin murya ya furta mata"Am sorry bazan ƙara ba" gyaɗa kai tayi kafin ta kuma cewa"daga yau idan har kana son zaman lafiya, kada ka ƙara yarda ta ta6a jikin ka, ko kallonta bana son yi," mamaki akan fuskarshi yace"why"? Harara ta wurga mashi"saboda bana so Danish, bana son ganinka da ita, inaso kayi min alƙawarin hakan" shiru yae bai bata amsa ba, nan take taji gabanta ya ɗan faɗi, "Ba zaka Iya ɗaukar min alƙawarin hakan ba ko"? Ƙura mata kyawawan idanuwan shi yae, ba tare daya furta komai ba, ta6e baki tae idanuwanta suka cicciko da ƙwalla tace"nasani dama ae, kana sonta ne shiyasa kake liƙe mata," girgiza kai yai muryarshi a tausashe yace"Ki daina tunanin hakan, dalilin dayasa bazan ɗaukar miki alƙawari ba, saboda ina son kowannan ku, mu tamkar ƴan uwa ne, bazan iya raba alaƙa da waninku ba, sai dai inyi ƙoƙari wurin ganin na haɗa kanku, ke da ita," fuskarta a daure tace banso, ka tashi ka bani wuri idan har bazaka min alƙawari ba," Ƙin miƙewa yae sai ma ya ruƙo hannayenta acikin nashi yadan matsasu, Yayin da idanuwansu ke kallon na juna, ya rasa gane dalilin dayasa take so ya yanke alaƙa da Ƴar gidan daddy, magana ya soma yi atsakane"Its okey, zan yanke alaƙa da ita, amma bazan iya daina kallonta ba, saboda ni tana burgeni, tana da abunda baki dashi, wanda yake jan hankali na, " Ras! taji gabanta ya faɗi, shi kanshi baisan ya akai maganar ta su6uce mishi ba, a matuƙar ruɗe take bin shi da kallon mamaki da Al'ajabi, Yau dai ta tabbar da cewar Danish mutun ne, ba kamar su haris fa, yasan me yake yi, kalamanshi sun tabbatar mata da hakan, "Am sorry angel, am sorry bana nufin na fusata ki, na faɗa maki ne saboda kema kiyi irin nata, saboda in dai na kallonta" Kamar sakarya hake take binshi da kallo, Tsabar mamaki Ya hanata tayi motsi, ta koma kamar gunki, idanuwanta ko ƙyaftwa basa yi, su kaɗai suka rage acikin ɗakin basu runtsa ba, Hatta ƴar gidan daddy ta jima da yin bacci abunta, ta baje saman gado tana sharar murshari, kamar jaki, "Angel, kinyi shiru baki ce komai ba," muryarshi a araunace yayi mata maganar, wani irin wahalallan miyau ta haɗiya, zufa ta ko'ina ajikinta duk irin sanyin da ke akwai, da ƙyar ta daidata natsuwarta, ta kalle shi da kyau, damuwace ƙarara akan fuskarshi, jinjina kai ta ɗanyi muryarta ƙasa ƙasa tace"Shikenan, Amma ni bani da hanyar da zansa su fito a ƙirjina, zan dai yi addu'ar Allah ya bani su, yanzun ma da kaga bani dasu saboda ban kai lokacin yin sun bane, tun da nima macace kamar ita, zasu fito minne," ajiyar zuciya ya sauke jin abunda tace, hankalin shi har ya kwanta, don shi har ga Allah burge shi suke yi sosai, Murmushi ya ɗan saki, Yana kallonta yace"Yanzu zamu fara ƙirga time da zasu fito miki kenan"? Girgiza mashi kai tayi"a'a, basai mun ƙirga ba, Allah ya riga dayasan lokacin daya dace dani," jinjina kan shi yae"i will wait for the time......" bai ƙarasa maganar ba jin yadda ta kwashe da dariya, Har fararen hakoranta suka bayyana, mamakine ya kama shi, Ko me ya bata dariya? Tsagaitawa tayi da yin dariyar tace mishi"kaje ka kwanta, ka huta," ya amsa mata da toh, ya miƙe ya wuce gadonshi ya kwanta suna fuskantar juna, kowa da abunda yake saƙawa acikin zuciyarta, bakomai ne yasa ta yin dariya ba face imagining da tayi wai gata nan da abubuwa manya manya fiye dana unaiza a ƙirjinta ne, Shine ya bata dariya, Can kuma ta koma tana tunanin wai me yasa suke burge shi? Sannan kuma idan suka fito mata ƙirjinta to mexai yi dasu? Ita dai a iya saninta Na baby ne da ake shayarwa, " Da wannan tunanin bacci yae awon gaba dasu, ɗakin yae tsit baka jin hayaniyar komai saina sautin minsharin su parveen maji dadin bacci, tsakar dare Angel tafarka, ta dinga addu'a tana roƙon Allah akan yabata abun arzikin nan wanda yafi na Unaiza, hada ƴar ƙwallarta, itafa bilhaƙƙi so take itama su fito mata, ko dan saboda Danish ya daina kallon na ƴar gidan daddy, ya koma kallon nata, ƙuruci dangin hauka🤣 tun lokacin da Danish ya ɗaukar mata alƙawari bai ƙara kula Unaiza ba, gashi ta nace mashi, ko toilet ya shiga sai ta bishi, idan yana bacci sai dai yajita a jikinshi tana lalubarshi, ta zamar mashi masifa, Da angel ta lura da hakan saita koma tana bashi kulawa ta musamman, Ta sanya mishi ido sosai, Idan suna cin abinci unaiza tana kashe mashi ido, sai angel tace mishi ya tashi ya koma saman gado zata kawo mishi abincin shi yaci acan, da yake yana son farin cikin ta, ga kuma alƙawari da aka yi mishi na abubuwa idan sunfito, shiyasa yake bin umarninta sau da ƙafa, idan dare ya yi zasu kwanta bacci, Angel bata runtsawa gefen gadonshi take zama tana bashi labarai masu daɗi har sai bacci ya ɗauke shi, kafin ta koma tana Yin addu'o'inta na dare da saba yi, Idan ya tashi zuwa toilet da kanta take raka shi ta tsaya abakin ƙopar har sai ya kammala ya fito tukunna su ke komawa ɗaki atare, hakan ba ƙaramin ƙona ma Unaiza rai yake yi ba, angel ta toshe duk wata ƙopa da zata haɗa ta da Danish, taƙi samun yarda take so kamar tayi hauka, yarinyar ba ƙaramar jarababbiya bace, Idan abun ya motsa da kanta take Amfani, Saboda tsabar shaiɗanci, hatta su Haris saida taso su bata haɗin kai, a ƙarshe taci ubanta hannun Naufal, saboda bai ɗaukar raini, Ta addabi rayuwarsu, Wani sabon shaiɗancin saita koma tana binsu Azeeza tsakar dare saman gadajesu, tun arana tafarko data fara yi musu hakan suka tarar mata, dama angel ta faɗi musu cewa mayyace kuma idan suka bari ta ta6a jikinsu to zata shanye musu Jinine har sai sun mutu, tsoro ya kamasu, shiyasa aranar su kayi mata bugun mutuwa, a ƙarshe suka kulleta Cikin toilet, Ta dinga kuka tana faɗin su buɗe mata ƙopa bazata ƙara ba, amma suka ƙi buɗe ta, babu ci babu sha Yinin ranar, sai tsakar dare ne suka je suka buɗe mata ƙopa, a ƙasa suka sameta kwance tana fitar da numfashi sama sama, Angel ta ciko bokiti da ruwa suka sheƙa mata shi a jikinta, sharkaf su ka jiƙa ta, ta dai ci baƙar wahala awurinsu, dama masu lallashinta haris da Danish ne to duk sun fita sabgarta, shiyasa su angel suka samu damar koya mata hankali, Sai gashi tafara yin hankali ta koma tana jin shakkarsu, bata ƙara gigin ta6a wani acikinsu ba, Sai dai har yanzu bata daina yi musu gorin ƙirji ba, idan rashin kunyar ta motsa haka zata dinga yada musu habaici acikin ɗaki babu mai tanka mata, kuma duk da haka bata hakura da Danish ba, dama kawai take jira da zata ke6e dashi. idan muka koma 6angaren Majnun, Babu abunda ya sauya, Mahaukaci ne na gaske, 6arnar daya ƙara yi musu wadda ta gigitasu, Aranar sun taru aɗaki Gabriel Yana koya musu rawa, da yake ya iya sosai, Ba ƙaramin daɗi suke Ji ba, sun dage suna ta tiƙar rawa iri iri, Ashe Yaron nan Ya gudu Zuwa toilet ɗinsu bai nufi ko'ina ba, Sai Wurin tukunyar fulawar nan, Yasa Hannu Ya tsige furen Batool dana daddynta, Hada Na aneelerh, ba zato ba tsammani sai gashi ya faɗo ɗakin hannun shi ruƙe da su Yana Faɗin Wai su kalli Ya curo musu shukokinsu, hankalin su yae matuƙar tashi, musamman angel, gani suke kamar ya kashe rayukan masu Furennin ne, ransu ya 6aci sosai, da gudu suka nufe shi da niyar su buge shi, da sauri ya juya shima ya watsa a guje Ya shige Cikin toilet ɗin, da yake mahaukaci ne, Ya buɗe murfin trash can ɗinsu, Ya faɗa ciki ya 6oye yana haki, gudun kada su buge shi, koda su ka shigo basu same shi ba, kuma ba su yi tsammanin ya 6uya acikin abun zuba sharar ba, Kaf suka bincika kowani sashe na toilet basu gan shi ba, Danish ya basu haƙuri akan su ƙyale shi, yace musu ae ba wani abu bane don ya cire furen zai iya fitar da wani tsiran, jin hakan yasa hankalinsu ya kwanta aranar saida ya sake tsuro wasu flowers ɗin masu kyau, sak irin wanda Majnun ya cire musu, sukai ta murna sam sun manta da yaron nan, Ashe bayan ya shige cikin trash can ɗin Bacci ya ɗauke shi, ga bola duk da babu wani abun datti sosai 6awon kayan marmarin da suke sha ne wani harya fara ru6ewa, Har dare yayi babu chinonso, Hankalinsu yaƙi kwanciya, Suka soma nemanshi saƙo da lungu har ƙarƙashin gado, har toilet suka koma neman shi tsakar dare amma basu ganshi ba, saboda su ba son cewa ana Iya cire murfin abun zubda sharar ba, shiyasa ba su yi tunanin yana aciki ba, Arufe saman shi yake sai dai ƴar ƙopar da za'a zubar da shara ciki, da suka gaji da neman shi ɗaki suka koma kowa ya kwanta, tsakar dare Chinonso Ya farka daga bacci, ya ganshi acikin trash can, Yasa hannu zai ɗage murfin yaƙi curuwa, Ya dinga kurma ihu yana faɗin su zo su taimake shi, dodonni zasu cinye shi, babu wanda ya iya jinshi saboda sun nutsa cikin baccinsu, Tun yana kuka da ƙarfi har muryarshi ta disashe, Hada fitsari ya saki aciki, Jikin shi duk zufa, sai kerma yake yi, wani irin tsoro ne ya mamaye shi, saboda bai ƙaunar duhu, saboda sun manta basu kunna ƙaramar fitilar dake acikin toilet ɗin ba. bari dai in taƙaice mu ku zance sai da Chinonso yae kwana biyu acikin Abun zuba sharar nan, basu san dashi ba, ba komai yajawo hakan ba face rashin kawo musu fruit, dama shine ke kaisu zubda shara acikin trash can ɗin, Aranar da zai Cika kwana Uku cuf aka kawo musu fruit, Bayan sun gama Cin abinci Parveen ta tattara 6awon taje zata zubda, sai da ta tsaya ta lashe na lashewa, Don har 6awon wani lokaci tana Ci, Bayan ta gama ɗan kingin da ta rage irinsu 6awon lemu da bata sha, ta buɗe murfin zata zubda nan take idonta suka sauka akan hurhurar gashin kan Majnun, Ya sandare aciki Ya ƙame, babu alamun yana motsi, wata irin gigitacciyar ƙara tasaki saboda ta tsorata sosai, Da gudun gaske su Angel suka faɗo ɗakin suna tambayarta lafiya hannunta na kerma tadinga nuna musu abun zuba sharar tsoro yasa kowa yaƙi zuwa ya duba, Sai da Azeeza taje ta kira Danish Ya taso daga saman gadon shi, ya shigo toilet ɗin Ya buɗe murfin trash can ɗin, yayin mamakin ganin yaron nan, Hannu biyu yasanya ya tsamo shi daga Ciki ya sauke shi ƙasa, yaji jiki kuma idonshi biyu amma baya motsi, ko magana ya kasa, Jikin shi sai wari yake yi, gefen bakin shi hada 6allin ganyen furennin daya cinye lokacin da yunwa ta addabe shi, ' Su parveen sun sha mamaki, Wai harya iya buɗe murfin gaba ɗaya ya shige, kuma ya maida murfin Ya datse amma Ya kasa fitowa daga Ciki. Ba tare da 6ata Lokaci ba, Hanna da hibba suka taimaka wurin cire mashi kaya, Yasmin ta kar6a tasa abokiti ta wanke mishi su, Wankan tsarki su kayi ma jikinshi, da sosa da sabulu suka wake shi, Bayan sun gama Aka ɗauko bargo ɗaki suka ƙudundune shi aciki, suka kaishi ɗaki saman gadon shi, Allah yaso sun rage sauran abincinsu da aka kawo musu, Yana daga kwance suka dunga cusa mashi abaki daƙyar yake wuce wa, Sai da yaci ya ƙoshi cikin shi yae ƙato, tukunna ya dawo hayyacin shi, ya fashe musu da kuka yana faɗin wai basu ƙaunarshi yana ta kiran sunansu akan suzo su taimake shi amma suka ƙi zuwa,' dariya kamar zata kashe su, parveen tace ashe kasan sunayen mu? Nayi tunanin baka sani ba, Cikin shessheƙar kuka yace"nasani mana, ba wanda bankira ba, hada Angel da danish da hanna, amma kuka ƙi zuwa, dodo yae ta tsorata ni" saboda tsabar dariya hada dafe ciki, Tun da suke dashi bai ta6a nuna yasan fuskokinsu ba balle sunayensu, Amma yau ya zaƙe yana zazzaga musu masifa, tass saida ya lissafa musu sunayensu, Sun sha mamaki, Angel hada yi mishi nasiha akan ya daina rashin ji da 6arna, ya dinga kwanciya saman gadon shi yana bacci, kamar mutumin kirki ya amsa mata da toh, suka ce to ya kwanta, yanzu, Batare da yayi musa ba, Ya gyara kwanciyarshi, sai gashi bacci ya ɗauke shi, hakan ba ƙaramin daɗi yayi musu ba, duk da sunsan zaiyi wuya ya daina 6arna tunda abun daga kwakwalwarsa ne. 💋PRISONERS💋 Kwakkwance suke saman gadajensu, Sarah kaɗai ce kwance a ƙasa ta shimfiɗa bargonta kamar yarda ta saba. Mutun ɗaya ce ta rage acikin ɗakin idonta biyu, sam ta kasa runtsawa sai juyi take yi saman gadonta, tarasa meke mata daɗi acikin duniyar nan, komai ya tsaya mata cak, babu alamun zata runtsa a daren yau, Yayin da take fuskantar ceilling, Jikin ta na asanye da tsoffin uniform ɗinta da suka maida kayan baccin su, ɗakin nasu yayi tsit sai sautin minsharin masu bacci, basu kashe hasken floor lamps ɗinsu ba, Saboda yau majnun bai yi musu haukan dare ba, tun da suka tsamo shi daga cikin trash can suka lalla6a shi ya kwanta bacci ya ɗauke shi, Har dare bai sauko daga saman gadon shi ba, Ya ji jiki da alama. Kamar an tsunkule ta, ta zabura ta miƙe ta zauna saman gadonta, hannunta dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa da sauri sauri, sakamakon tunawa da ƴar uwarsu batool da ta yi, zuciyarta sam ba daɗi, sai yanzu ma take jin haushin damuwa da tayi akan ƴar gidan daddy, Sun saki jiki suna ta rayuwarsu batare da sun ta6uka komai ba, akan ƴar uwarsu. Saukowa ta yi daga saman gadonta, ta ɗaura eyes ɗinta akan shimfiɗar Danish, Ya rungume pillow abun shi sai sharar baccin sa yake yi, Cikin sanɗa ta nufi tsakiyar ɗakin tana tunkarar sabbin gadajen da su parveen suka gaje, don har yanzu basu daina kwana saman su ba, tun ranar da aka kawo su Jamima, aka koma da mutun goma, su ka ci gaba da kwana saman su, Mutun biyar ne ba su kwana saman tsaffin gadajensu, Ita da Danish sai haris da Deeja, da kuma naufal, Amma sauran kowa ya samu sabon gado. Agaban gadon Unaiza ta tsaya tana kallon wani sabon salon kwanciya, ta tura hannayenta cikin short ɗin jikinta, saboda jaraba Cikin bacci tayi wurga da bargonta ƙasa, Tana numfashi boobs ɗin ta na yin sama da ƙasa, Ta6e baki angel ta yi, Ji take kamar ta sanya hannu ta maida su cikin ƙirjinta su shafe, A nemesu arasa, ko sun huta da guyabarta, " Guntun tsoki taja tunawa da abunda ya taso da ita daga saman gadonta, da sauri ta nufi ƙopar shiga sashen toilet ɗin su, bakomai take son gani ba face furen batool tana so taga awani hali yake ciki, Tana ƙoƙarin shiga toilet ɗin taji motsin shigowar mutun ta bayanta, a firgice ta juya don taga wanene, lokaci ɗaya ta sauke ajiyar zuciya ganin Danish ko me ya tada shi daga bacci, rayawa tayi aranta may be yayi tsamanin zata ƙara dura tagar ne shiyasa yabiyo bayanta. Harara ta shiga jefa mashi, Yana daga tsaye ya goya hannayenshi saman ƙirjinshi, red vest ɗin Jikin shi ta fiddo mashi da hasken fatarshi sosai, Idanuwanshi da alamun bacci acikinsu, "Halan Ka biyo ni ne don kaga me zan yi acikin toilet? in banda sa ido, mutun na jin bacci amma ya kafe sai ya takura rayuwar wani, ni nasan saboda ni kazo nan" ta yi maganar tana murgaɗa mishi ƙaramin bakinta. Bai tanka mata ba har sai da ya tako zuwa gabanta ya tsaya ya ɗan duƙo da kanshi saitin fuskarta, Cikin Cool voice ya furta mata"abunda kika faɗa gaskiya ne, Saboda ke nazo nan" ta6e mashi tausasa la66anta tayi tare da cewa"Kasan dai baka isa ka hana ni yin abunda na yi niya ba, zaifi ka daina wahalar da kanka akaina" ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarshi, ganin yadda take mishi magana tana jifar shi da harara hadi da murguɗa mishi baki, a ƙarshe ma taja mishi tsoki ta juya zata shige toilet, da sauri ya damƙo damtsen hannunta ya dawo da ita jikin bango yayi mata rumfa, mamaki ne ya kama ta, Ta zuba mishi ido tana jiran ganin me zai yi mata. "Saboda na damu dake ne shiyasa na biyo bayan ki ba don wani abu ba" yatsina fuska tayi tare da cewa"Ni ban damu da kai ba don haka kaima ka daina damuwa dani, pls ka koma ka kwanta ni ka bani hanya in wuce ka na 6aramin lokaci" Hada bubbuga ƙafa irin ya takura ta ɗin nan, Hakan ba ƙaramin dariya yaso ya bashi ba, "Kince ba ki damu dani ba, but why kike hana idonki bacci don ki roƙi Allah akan ya baki abunda zai faranta min raina"! Har saida gabanta ya faɗi jin abunda yace, wani irin kallo ta soma binshi dashi, gaba ɗaya ya kashe mata ba." Daƙyar ta iya buɗe baki tace "Danish kana nufin duk time da nake farkawa tsakar dare ina addu'a idon ka biyu? why ka sanya min ido, ko time dana ɗaukar maka alƙawarin na faɗi ne kawai don in kawar maka da tunaninka akan wancen yarinyar, kuma ni nayi hakanne gudun kada ta 6ata maka tarbiyar ka, saboda Nifa basa burgeni, bata su nake ba" tana magana tana hura hanci, Hannu yasa yaja tsinin hancinta tare da cewa"Nafa san me nake yi angel, ki daina ƙoƙarin nuna kamar ba donni kike yi ba, kina 6oye min irin ƙaunar da ki ke yi min," ranta a6ace tace"waya ce maka ina ƙaunarka ni? To wai ni akan me ma xan yi addu'ar Allah ya bani su...." ya bata amsa da cewa"Saboda inaso" fuskarshi a ɗaure ya bata amsa, kamar tasa hannu ta shaƙe wuyanshi haka take ji, muryarta a fusace tace"Dallah ni bani wuri na wuce, kunnuwana ba zasu juri sauraran waɗannan kalaman naka ba," tana ƙoƙarin janye shi don ta wuce yae saurin cewa"Its okey, kin bani damar in cigaba da kallon nata kenan"? Girgiza mishi kai ta yi alamar a'a, "nifa bance bazanyi bane, maganarce ke bana so," ta faɗi hakan tare da sanya hannayenta ta ture shi gefe, Ta nufi ƙopar shiga toilet, har ta kusa shiga sai kuma ta ɗan dakata da alama wani abu take tunani ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace"Ni abunda ban fahimta ba, me zakai dasu da kake son su fito min? Ka san dai bana manya bane, Na jarirai ne, don haka ka daina murna, iya kallo ne shima ba koda yaushe zan bari kana kallan min abuna ba, da zarar Mun rabu da unaiza, zan haramta maka ganinsu," ta ƙarasa maganar tare da faɗawa cikin toilet din hada sanya jamlock ta datse ƙopa, ta kifa kanta jikin ƙopar tana Kanga kunnuwanta ta yi ajikin ƙopar don taji idan yana nan ko ya tafi, ba zato ba tsammani taji saukar hannun shi saman bayanta, a firgice ta juyo tana kallon shi, Yayin da shima yake kallonta, Ba ta yi mamakin ganin shi acikin toilet din ba tun da ba yau bane rana tafarko da ya fara Yi mata irin hakan ba, runtse idanuwanta tayi tare da bubbuga ƙafa tace"Nashiga uku! Wai meye ruwanka dani ne eye? Ba mun shirya ba, kuma nace maka nima zanyi irin nata to me kuma kake so"? Fuskarta a hautsine tayi mishi maganar, wani irin kallo yake binta dashi idanuwanshi kamar zasu lumshe saboda baccin da yaje ji, "Angel, kin ɗaga min hankalina why zaki ce wai na jarirai ne, menene haka ba daɗin ji, kuma kince da zarar mun rabu da unaiza shikenan ko kallon su ma bazan ƙara yi ba, Ni na yi tsammanin duka zaki mallaka min su, tun da donni zakiyi su, idan kika min hakan baki min adalci ba," muryarshi asanyaye sautinta ke fita, Lamarin yayi matuƙar ɗaure mata kai, har wani zazzare mashi ido take yi don ma yasan cewa ba wasa take yi ba, a cikin zuciyarta kuwa tunani take yi Anya Danish bai da ta6in hankali? Taya zai tsareta akan abunda ma basu da tabbacin zasu fito ko ba zasu fito ba. "Kin yi shiru baki ce komai ba"? Muryarshi ce ta dawo da ita cikin hayyacinta, Ganin yana ƙoƙarin dagula mata lissafi yasa ta ruƙo hannun shi acikin nata, Tace mishi"muje mu kwanta," bata jira amsar shi ba, ta buɗe ƙopar toilet ɗin, taja shi suka fuce har zuwa cikin dakinsu, Abakin gadon shi ta tsaya tare da kallon shi tace"nasan damuwarka, yanzu mu kwanta mu yi bacci, zamuyi magana zuwa gobe" ba don yaso ba ya ƙyale ta ya hau saman gadon shi ya kwanta itama ta wuce nata gadon ta haye, tana faman sauke ajiyar zuciya, ganin yana kallonta yasa ta janyo bargo ta rufe har kanta, lumshe idanuwanshi yae tare dajan nashi bargon ya lullube jikinshi, kowannansu da abunda yake saƙawa acikin ranshi, gani take kamar akwai shaiɗanu ajikin danish, waɗanda ke sanya shi yana yin abubuwa, Da farko yace yana son yi mata wanka yasa naci taƙi amincewa yanzu kuma so yake ƙirjinta sun fito ko uban me zaiyi dasu, Anya kuwa Danish bada biyu yake yi mata wasu abubuwan ba? Ta fara kokwanto akanshi, da wannan tunanin bacci yae awon gaba da su. A washe garin ranar, majnun ne ya farkar dasu daga bacci, Tun da ya farka daga bacci ya sauko daga saman gadonshi yana miƙa da hamma, ya nufi gadajensu ɗaya bayan ɗaya ya dinga bubbuga ƙafafuwansu, yana faɗin su tashi ayi wasa, One by one su ka soma farkawa idanuwansu a kumbure fuskokin su duk a yamutse an sha bacci, su parveen hada miyan bacci a gefen baki, sun ji haushin tada su da ya yi, sai faɗa su ke yi mishi amma ko ajikin shi. tsotai ne yakai Majnun gadon Unaiza ƴar gidan daddy, Ya sanya hannu yana bubbuga ƙafafuwanta don ta farka yaga ita kaɗai ce bata tashi ba, can cikin bacci ta dinga jin bugun da akeyi mata, a hautsine ta farka tare da miƙewa fuskar nan tayi jawur da ita babu annuri, suna haɗa ido da majnun Ya washe mata baki, ranta ya 6aci sosai dama ta tsani yaron, zabura tayi ta damƙo wuyan rigarshi, Haris da Danish har suna haɗa Baki wurin ƙoƙarin dakatar da ita akan karta ta6a lafiyar jikin shi, ko kallo basu isheta ba, ta daddaga ta kwakkwasa mashi zafafan maruka saman fuskarshi, azabar zafi yasa yaron ya dafe kuncinsa ya fashe da kuka, parveen hada cewa"Allah shi ƙara maka, Ae kaine da shegen jan faɗan tsiya," duk sun yi tunanin za ta sake shi ne tun da ta mare shi, amma sai suka ga ta sanya hannu ta shaƙe wuyanshi da ƙarfi kamar zata kashe shi, idanuwanshi suka firfiro waje, A gigice Danish ya yunƙura tare da angel hada deeja suka nufi gadonta, Suna ƙoƙarin ƙwace shi daga hannunta amma taƙi sakin shi, rai a6ace Danish ya daddage ya watsa yatsun hannayenshi biyar saman kuncinta, ji kake tass! Abun da bata ta6a tsammani ba, Da sauri ta saki Wuyan majnun idanuwanta akan fuskar Danish, tun da take arayuwarta bata ta6a jin azabar mari irin wanda Danish yayi mata ba, har wani jiri take gani acikin idanuwanta da suka cicciko tab da ƙwalla, hannayenta bibbiyu dafe kuncinta. Su azeeza dake kallonta, dariya ce ƙumshe acikin bakunansu, Musamman da ta dinga binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, kamar tana tunzurasu ne akan su yi dariya, Angel ce ta rungume majnun ajikinta, tana lallashinshi, Sai kuka yake yi, Wuyan shi hada sahun akaifar Unaiza wurin yayi ja sosai jini ya kwanta abunka ga zabayyana dama ya lafiyar giwa. "Wani ya samo min ruwa in bashi" angel ce tae musu maganar, da sauri parven ta sauko daga saman gadonta, ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko bottle water cikin wanda suka ajiye taje ta miƙa ma Angel tasa hannu ta kar6a tare da cire murfin ta kwafa mishi abaki, sosai yasha ruwan har yana shaƙewa, kusan rabin robar ya shanye, kafin ya janye bakin shi, Yana faman tatta6e fuska ya kalli unaiza a lokacin ta dawo da kallonta kan Danish, da alama bakinta ya gama mutuwa saboda marin da yayi mata ba. Cikin shessheƙar kuka Chinonso Ya nuna ta da yatsa yana faɗin"I hate u, mai idon dodo, bana son ki," Dama ranta a6ace yake, azabure ta yunƙura ta sauko daga saman gadon da niyar ta sake bugun chinonso, a tsorace yaron Ya yi saurin faɗawa jikin angel ya ƙanƙameta, Wata irin gigitacciyar tsawa Danish Ya daka mata, wadda tayi silar dakatar da ita, Da kakkausar murya yace mata"kada ki kuskura kice zaki ƙara ta6a shi, ke baki da hankali ne baki ga yaro bane? Ko so kike ki kashe shi ne shiyasa kika shaƙe mishi wuya" yae maganar idonshi akan fuskarta, wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, la66anta har kerme suke yi wurin faɗin"Ni ka mara? Sannan ka rufe ni da faɗa sai kace wata ƴar cikin ka, To ni ko ubana bai ta6a ɗaga min murya ba, balle har yayi gigin ta6a lafiyar jikina, rana ta farko da mahaifiyata ta fara yi min tsawa akan idona daddyna ya kwashe ta da mari, Amma zuwana Cikin ku, kun maidani kamar wata jaka, Wai me kuke nufi dani ne? Na kasa ganewa........" daƙyar ta ƙarasa maganar, hawaye ta ko'ina saman fuskarta, Still idonta akan fuskar Danish, su Deeja sun kasa kunne suna sauraronta babu wanda ya tanka mata, hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yai ba. tana magana jijiyoyin wuyanta duk sun firfito ruɗu ruɗu saman fatarta, Sautin muryar ma daƙyar yake fita "Ni bazan cigaba da zama acikin wannan Munafukin Ginin ba, nafara kokwanto akan ku, Kun ƙi ku sanar dani ina ne nan, wai me ake nufi dani ne? So ake dole sai nayi rayuwa kamar dabba! to nagaji! nagaji!! bazan Iya cigaba da zama acikin Ƙuntataccen dakin nan ba, wlh ban yarda da kowa ba, so ake akashe ni, Ni ku faɗa min me ake aikatawa acikin ginin nan? Kowa ya maidani jaka, Ni da nazo ɗaukar karatu? Ance min school ce but why har yau ba'a kai mu class room ba? Na yi shiru ne don inga ko akwai wani shiri da ake yi mana amma naji shiru har yau, babu zancen zuwa aji mu ɗauki karatu, nayi expecting ɗin zan samu abunda nake so shima kun hanani saima neman kassara rayuwata da ku ke yi, ta ko'ina kun ƙuntata min, Nifa ban saba da irin wannan rayuwar kullen ba, Ni school din ma na fasa amaidani gidan daddy na, wlh bazan zauna ba!!! " tana magana tana matsar hancinta, fuskar tayi jaga jaga da hawaye,. Da alama marin Danish ba ƙaramin zaburar da ita yayi ba, sai sambatu take yi tana zazzaga masu masifa ta inda ta shiga bata nan take fita ba. "magana fa nake yi maku, duk kunyi min shiru sai kace kurame, Ku faɗa min ina ne nan? Kuna ƙara jefa ni cikin ruɗani! Abubuwa dayawa suna neman rikita min lissafin ƙwaƙwalwata! meyasa tun da nazo babu wani sauyi, ni fa ba haka daddyna ya faɗamin ba, yace min school ɗin akwai wuraren shaƙatawa acikinta, amma ni bangani ba, shi fa ya faɗamin hada lunch room da garden da swimming pools ga zoo irin na gidan mu, hada cinema but why are we always locked in the same room like an animal? Nifa na saba agidan mu, Ina yin duk abunda nakeso, ban saba da wahala ba, duk rana saina fita yawon buɗe ido, Har night club ina zuwa sometimes a hotel nake kwana tare da friends ɗina, Taya rana ɗaya za'a kawo ni wannan gurin me kama da Gidan Yari!" a hargitse ta ƙarasa maganar, Cikin raunin murya da sagewar gwiwa ta zube saman ƙasa tana ci gaba da yin kuka tamkar ranta zai fita, basu ta6a jin tausayinta ba irin na yau, ganin yadda duk tabi ta burkice, tsawon lokaci babu wanda Ya tanka mata, da zarar angel ta yi yuƙurin buɗe baki ta yi mata magana, da sauri Danish ke dakatar da ita, ta hanyar girgiza mata kan shi alamar karta fada mata, tuntuni take son faɗa mata gaskiyar zance akan daddynta mugune sadaukar da ita yayi kuma nan ɗin kurkukun ƙaddara ne, da komai da suka sani dangane dashi wata'ƙil ta dawo hayyacinta, ta gane cewa Allah ɗaya ne! Sai dai Danish yaƙi bari a sanar da ita. Sosai take yin kuka babu mai lallashinta, Gefen fuskarta inda Danish ya mara hada sahun yatsun hannun shi ruɗu ruɗu, Tamkar da bulala aka shafi wurin, shi kanshi sai daga baya ya yi danasanin marinta da yayi duk da laifinta ne itace taja ma kanta,. Saukowa gabriel yae daga saman gadon shi, gaba ɗaya hankalinsu ya koma kan shi, Bai nufi ko'ina ba sai wurin da Unaiza take zuƙunne tana kuka, Zuƙunnawa yayi tare da sanya hayyanshi biyu ya rungumota jikin shi yana lallashinta, sai ya dinga ganin kamar twin sister ɗin shi ce take kuka, muryar shi ƙasa ƙasa yake faɗin"its okey unaiza, Stop shedding ur tears, ina atare da ke" kallon kallon sauran ƴan uwan nasu suka somayi atsakaninsu, sun yi mamaki ganin yana lallashinta, bayan shima yasan halinta na dabbanci da rashin kamun kai, dakatawa tayi da yin kukan tayi lamo ajikin shi, dama Gabriel akwai ƙira, Ta samu wurin zama, kamar zata shige cikin shi, jin tayi shiru yasa shi ɗagowa ya kalli su Danish dake atsaye suna kallon su, Magana ya soma yi musu "Nima na jima ina so in tambaye ku game da kurkukun nan amma nakasa, Mu tamkar baƙi ne acikinsa, ina so insan komai agame da shi, Tsawon kwanaki, Banga an dawo min da ƴar uwata ba, kuma ni banga ana fidda mu waje ba, kullum muna kulle a room ɗaya, sannan waɗannan mutanan dake zuwa wanda ku ke kira da giants sam basu kwanta min araina ba, meyasa koda yaushe suke zuwa cikin shiga ta baƙaƙen kaya? Suna 6oye kan su don kada mu gansu, na fara zargin wani abu, it seems like something strange is going on in this prison. I wonder what they're hiding from us." Shiru suka yi babu wanda ya tanka mashi, A ƙagare yace "Na yi magana anyi shiru ba'a tanka mini ba, hakan na nufin hasashe na ya zama gaskiya kenan? Akwai wani abu dake faruwa wanda ba'a so mu sani, pls ku faɗa mana abunda ku ka sani tattare da gidan kurkukun ƙaddara, ku wayar mana da kanmu Ni da Unaiza! ni ƴar uwata ma itace damuwata, bansan Ina aka kaimin ita ba, awani hali take! Idan naci gaba da 6ata lokaci za'a iya cutar min da ita batare da sanina ba," Wani irin mugun bugu zuciyoyinsu su ka yi bakomai ne ya faɗo musu aransu ba, fa ce Ƴar uwarsu batool, haƙiƙa Gabriel Yayi wata magana da su ba suyi tinaninta ba, lokacin da suke 6atawa na rashin ta6uka komai akan adawo musu da ƴar uwa, kamar suna ƙara jefa ta cikin matsala ne, idan ma mutuwa ce ae yanzu ya isa ace batul ta mutu saboda azabtarwar da su ke yi musu idan su ka ɗauke su. Shessheƙar kukan su Azeeza ne ya karaɗe cikin ɗakin, Jikin su yae mugun sanyi, ita kanta angel hawaye ne suka cicciko mata acikin idanuwanta, a marairaice take kallon Danish. kukan su parveen ya ƙara dasa tsoro da firgici acikin zuciyar Gabriel, Yana ƙoƙarin Tambayarsu meyasa su ke ku ka, Danish yae saurin dakatar dashi ta hanyar yi mishi magana "Gabriel, is enough! Maganarka bata da amsa, kamar yarda ka tsinci kanka acikin kurkukun nan ba tare da kasan komai dangane dashi ba, mu ma haka muka tsainci kan mu, Ƴar uwarka da aka ɗauka ba'a ita kaɗai ba ce, ka tuna su goma ne aka juya dasu, so ka kwantar da hankalin ka, Su ma suna acikin kurkukun nan kuma suna rayuwa kamar yarda muke yi". Cikin karyayyiyar murya gabriel yace"Bana tunanin haka, Saboda ina ji acikin zuciyata wani abu yana faruwa da ita, ya za'ae na tabbatar da cewa tana Lafi......." bai ƙarasa maganar ba, sakamakon ganin angel da ya yi ta miƙe da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu tana kuka, Da sauri gabriel Ya janye unaiza daga jikin shi ya miƙe Ya nufi hanyar shiga sashen toilet ɗin da niyar yabi bayan angel, sai dai kafin yakai ga ƙarasawa Danish yasha gabanshi, damƙar damtsen hannun shi yae tare da cewa"Kada ka yi gigin cewa zaka bi bayanta, Ka koma ka lallashi waɗanda ka fama ma ciwon dake acikin zuciyarsu, har sai sun yi shiru," Kamar wani ubanshi haka ya bashi umarni, ku ma abin mamaki gabriel bai musa mishi ba, Ya amsa mishi da toh, kafin ya juya ya nufi su azeeza, ɗaya bayan ɗaya ya dinga zuwa bakin gadonsu yana lallashin su, Har sai da ya samu su ka yi tsit Sannan Ya koma bakin nashi gadon ya zauna, Jikin shi duk ba daɗi kewar ƴar uwarshi ta addabe shi, tuni unaiza ta koma saman gadonta, chinonsa ma ya hau nashi gadon. Sam bata ji alamar shigowar shi cikin toilet ɗin ba, tana zuƙunne gaban tukunyar furennin nan, Sai kuka take yi kamar marainiyar da ta rasa gata a duniya, Furen batool ya ƙara tayar mata da hankalin ta, ganin yadda Jikin shi ya bushe Ƙamas, Ganyayyakin jikinsa duk sun tsamure, Alamar babu lafiya atattare da mamallakin furen, A gefen ta Danish ya zuƙunna Tare da ambaton sunanta, Angel kusan sau uku Yana kiranta bata ɗago ba, sai da ya ɗaura hannun shi ɗaya asaman kafaɗarta tukunna ta ɗago ta kalle shi da rinannun idanuwanta waɗanda suka kaɗa jawur dasu, fuskar tai jaga jaga da hawaye wasu nabin wasu Cikin shessheƙar kuka tace"Me zaka faɗa mini? Kai idan ma lallashina zaka yi to banso! Ko ka yi abanza tun da ba iya dawo min da batool za ka yi ba, Ku ma wlh rantsuwar ɗan musulmi, zanje na dawo da ƴar uwata ne, ko da zan rasa raina ne akan hanyar zuwa wurin ta...." bata ƙarasa maganar ba, Ta daura kanta saman gwiwowinta, gaba ɗaya ta kashe mishi baki, Ya rasa me zaice mata, don ya lura babu sassauci akan fuskarta, shiyasa tun farko bai so Gabriel Ya fara maganar ƴar uwarshi ba. Ga shi yanzu yaja mishi masifa, Jim ya ɗan yi kafin cikin cool voice ya furta"Angel, nasan bazan iya dawo maki da ita ba, kamar yarda kika faɗa, ku ma kema haka koda ace kin ƙara dura tagar nan da niyar kije neman ta, ba lallai bane Ki iya tsira, ko kin manta abunda Ya faru dake ne a rana ta farko da kika haura....."? Daƙyar ya ƙarasa maganar saboda yadda ta ɗago tana wurga mishi harara gwanin ban tsoro launin idanuwanta kamar na zombie, masifa ta soma zazzaga mishi "Bana son ganinka, sai iya daɗin baki, Danish idan har ni bazan iya shiga prison ba, kai zaka Iya, tun da har ka iya zuwa ka ɗauko ni, dan haka inaso kaje ka dawo mana da batul ɗin mu, Danish ka taimaki rayuwar batul, tsawon wata ɗaya da weeks babu ita, ka duba ka gani fa, ko su deeja 2 weeks ne aka dawo mana su, amma Jibi kaga yarda aka canza musu halittarsu to inaga ita da ta jima a hannunsu" Baisan ya zaiyi ya fahimtar da angel ba, ya san koya lallashe ta abanza don ba jin shi zatayi ba, hakan ya sa shi miƙewa Ya fuce daga Cikin toilet din tabi bayan shi da kallo, Zuciyarta akarye ta miƙe, Tana sharar kwalla, Bata fito daga Cikin toilet din ba, Sai da ta goge bankinta, Tayi wanka, Lokacin da ta fito, su hanna ta taras A cikin sashen toilet ɗin nasu, suna jiran wanda ke aciki su fito suma su shiga, kallon su kawai tai batare da tayi musu magana ba tasa kai ta fuce daga wurin, shigarta ɗaki keda Wuya, Sai ga Giants sunzo kawo musu abinci, nan take ta ɗaure fuskarta, su uku hannayensu ɗauke ta farantan kayan abincin su, ciki suka shiga tare da sauke trays ɗin saman dining carpet ɗin su, Atare suka ja baya kamar yadda suka sa6a ƙame wa, Kaitsaye angel ta nufi inda suke, Danish na jin takun tafiyarta ya ɗan ɗago daga kishingiɗan da yake saman gadon shi, Hatta haris da Gabriel da suke acikin ɗakin hankalinsu na akanta "Har yaushe ne zaku kammala amfani da ita ku dawo mata da ita? Nasan kun gane akan wa nake magana, Ƴar uwar mu batul tana ina"? Ranta a6ace take yi musu magana, babu wanda ya motsa, tsawa ta daka musu tare da cewa"Da ku fa nake magana? Nasan kuna ji na, mugaye kawai......" jiki na 6ari danish Ya sauko daga saman gadon shi ya nufi angel ya ruƙo hannunta yana ƙoƙarin janyeta baya, gudun kada su cutar da ita, fashewa tayi da matsancin kuka, Tana bugun Danish akan ya saketa, wlh sai sun fito musu da ƴar uwarsu, Wannan maganar tayi matuƙar ɗaure ma Gabriel, da Unaiza kai, don tuni ta miƙe zaune saman gadonta, idanuwanta luhu luhu take kallonsu, Saboda sautin kukan Angel har na cikin sashen toilet dinsu saida suka fito, hankalinsu yayi matuƙar tashi ganin yadda take kuka tana ƙoƙarin kwace kanta daga hannun danish donta kaima Giants hari, A ƙarshe da ta ga dagaske Danish bazai Ƙyale ba, ta daddage ta gartsa mishi ciwo a damtsen hannun shi tare da sanya hannayenta biyu ta ingije shi gefe ɗaya, taku ɗaya zuwa biyu takai ga farantan kayan abincin da aka kawo musu, Robar ruwa ta ɗauko ta buɗe murfin, Cikin zafin nama ta watsa ma giants ruwan ajikinsu kaf ta zazzage musu shi. waro ido waje su Parveen su ka yi ganin irin bala'en da take so taja musu, kowa yasha jinin jikin shi, Tana haki tace"Dama nasan bazaku motsa ba, saboda ku ɗin dabbo bi ne, Marasa imani, Allah dai yana ganin ku mugaye, Wlh rantsuwar ɗan musulmi, idan har wani abu ya sami batul sai kun gane ba ku da wayau, domin kuwa saina addabi rayuwarku, inyaso ku kashe ni, kai bazan ma mutu ba bi'iznillahi har sai na ga bayan ku..." Bata kai ƙarshen maganar ba, Danish Ya sake damƙota, kamar ƴar dambe sai harba ƙafarta take yi, ahaka yaja ta har zuwa saman gadonta, Ya jefar da ita, Kafin ya juya ya kalli Sauran yace dasu su je su ci abinci," da sauri suka nufi kayan abincin nasu kowa ya zauna banda Gabriel da Unaiza, kalaman angel sun yi matuƙar ɗaga musu hankali, tunani suke yi wacece batul? Meyasa aka ɗauke ta? A gefen gadon Angel Danish ya zauna yana gadinta, gudun kada ta ƙara zuwa ta 6allo musu aiki, Shi kaɗai yasan me yae mata, da har tagaza ɗagowa, hawaye sai bin fuskarta suke yi, ta ɗaura kanta saman pillow, Bayan sun kammala cin abinci sauran da suka rage ma waɗanda basu samun damar xuwa suci ba, acikin kwando suka adana mu su nasu, Giants na fita daga Cikin dakin, Gabriel ya soma tambayarsu wacece batul? su azeeza suka bashi amsa da cewa ƴar uwarsu da aka ɗauka, yaso ya ƙara tambayarsu dalilin dayasa aka ɗauke ta amma Danish Ya hana shi, ta hanyar Ƙura mishi ido yana kallon shi, nan take yaji maganar ta fita aranshi, bai ƙara tada ta ba. Yinin ranar babu daɗi suka yi shi, Saboda halin da suka shiga na tunawa da ƴar uwarsu, Kowa jikin shi yae sanyi, Har marece ya yi babu wanda ya motsa acikin su, majnun ne kaɗai yake ta tsalle tsalle shi kaɗai atsakiyar ɗakin su. Lokacin da marece ya nutsa, Gabriel ya bukaci yin wanka, Saukowa Yae daga saman gadon shi, Ya nufi toilet ɗinsu Ya shiga, bayan yasanya jamlock ya datse ƙopar Ya dan jingina bayanshi Jikin ƙopar, yayin da zuciyarshi ke acunkushe da tunanin abubuwan da suka faru ayau, Tabbas ya razana sosai da gidan kurkukun nan, duk da baisan komai adangane dashi ba amma yana ji aranshi cewa wani abu yana faruwa badai badai ba, Shi bakomai yafi jimawa ba face ƴar uwar shi Gabriella, maganganun da angel tayi ɗazu akan tasu ƴar uwar sun tsara mishi aranshi. A ƙalla ya ɗauki kusan minti talatin Yana tunani acikin toilet ɗin ba tare daya ta 6uka komai ba, Sai daga bisani ne ya soma ƙoƙarin cire rigarshi, Kwatsam idanuwanshi suka sauka akan Glass window ɗin nan, A wani slow yake kallonta sai yake ganin kamar glass ɗin jikinta bai zauna dakyau ba, nan take ranshi ya bashi cewar Yaje ya duba ya gani, wata'kil ma ya samu hanyar shiga Cikin kurkukun ko dan yaje ya ɗauko ƴar uwarshi, ba tare da yayi shawara da zuciyarshi ba, Ya fasa cire rigar ya nufi tagar, Yakai hannu ya tatta6a jikin glass ɗin Yaji yana girgiɗi, ya daddage ya zame shi daga jikin tagar ya sauke shi ƙasa, wani irin farin ciki ne ya mamaye zuciyarci, bakomai yake hange ba face fuskar sister ɗinshi. Rashin sani yafi dare duhu, cike da ƙwarin gwiwa Gabriel ya dura tagar ya faɗo ta cikin wannan hanyar da angel ta tsinci kanta lokacin da ta ta6a durawa, hada saurin shi wurin miƙar hanyar, babu wadataccen haske, amma yana iya gani dakyau, yana kaiwa ƙarshenta, Ya faɗo cikin wannan babban filin mai ɗauke da dogayen benayen nan, A hankali yake ƙarewa ginin kallo, bai ta6a ganin wuri mai matuƙar ruɗarwa ba irin wannan wurin, hakanan ya dinga jin faɗuwar gaba, tun daga kan hauwa na farko har zuwa na biyu, a ƙarshe ya tsayar da idanuwanshi kan hawa na uku, ba zato ba tsammani idanuwanshi suka hango mashi kyakkyawar matashiyar budurwa tana gudun ceton rai saman hawa na uku, fara fat kamar fatalwa, Jikinta sanye da riga ja, wadda bata kai gwiwarta ba, fararen cinyoyinta santala santala, daga gani babu hankali atattare da ita, tana gudu tana waiwayon bayanta, ga uban gashin kanta dake yarfowa harta saman idanuwanta, hakan yasa ta dinga faɗuwa ƙasa tana miƙewa saboda bata ganin gabanta dakyau, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyar Gabriel, Ganin tana saukowa daga saman benan mai hawa talatin, Girgiza kanshi ya dinga yi, zufa tako ina saman fuskarshi, Ya rasa gane shin mutunce ita ko aljan, ko kuma fatalwa ce, Idanuwanshi ne suka dinga nuna mashi kamar sister ɗinshi ce, sai dai akwai banbanci sosai, Ƴar uwarshi ba fara bace, kuma bata da tsayin sumar kai da yawa irin na wannan yarinyar, ' A tsorace ya juya zai koma hanyar daya fito, A lokacin harta ƙarasa saukowa saman benan, sai miƙa mishi hannu ta ke Yi, tana magana sautin muryarta sam baya fita, ranshi ne ya bashi cewar Ya juya ya kalle ta, ya ɗan dakata ya waiwayo baya yana kallonta, sai jan ƙafarta take yi, saboda nauyin da tayi mata, Taya zai iya yarda cewa mutunce ita? Bai gama yanke shawara da zuciyarshi ba, yaga ta faɗi ƙasa kanta ya bugu, ' Gaba ɗaya sumar kanta ta rufe mata fuskarta, Tsananin tausayinta ne ya kama gabriel, koma dai aljana ce wannan ba ƙaramin jiki taji ba, sai motsi take yi alamar tana son ɗagowa da kanta amma ta kasa, kuma duk da tana kwance ƙasa hakan baisa ta fasa miƙa mishi hannunta ba, yayi niyar yaje wurinta amma sai yaga Benayen dake awurin sun soma motsi suna yin sama da ƙasa, Ya zazaro ido ganin suna tunkaro shi, aiko da gudu ya juya ya bi ta hanyar daya fito Ko waiwaye babu ya koma bakin tagar nan, Allah ne ya taimake shi bai 6ace hanyar ba, Jiki na kerma ya haura tagar Ya dura Cikin toilet ɗinsu Yana ta haki, Sai da ya samu natsuwa tukunna yakai hannu ya ɗauki glass ɗin daya jingine jikin bango ya maida shi jikin tagar kamar yadda ya ganshi, Kamar amafarki yake tariyo abubuwan da suka faru Cikin ƙanƙanin lokaci, zuciyarshi cike fal da tunanin matashiyar yarinyar nan daya gani .............."! 💋PRISONERS💋 Ya jima tsaye jikin tagar ba tare daya motsa ba, zuciyarshi na raya mashi akan ya koma ya taimake ta, sai dai tsoro ya hana shi yin hakan, Ajiyar zuciya ya sauke tare nufar cikin toilet ɗin, wankan ma da ya shigo da niyar yi ya fasa, ƙopa kawai ya buɗe ya fito ya shiga ɗakin su. A zazzaune ya same su saman gadajen su, angel ce kaɗai kwance saman nata gadon da alama bacci ya ɗauke ta, tunda Gabriel ya shigo idanuwanshi na akan kowannan su, damuwace danƙare akan fuskokinsu, In ka cire mutun uku, Majnun da jamima da ke ta yin rawa tsakiyar ɗakin su, yau ta biye mishi suna wasa a tare, duk da a shekaru Majnun ya girmi Jamimah. bayan su sai Sarah dake yanke akaifar hannunta da nail cutter ɗinsu, tana zaune saman shimfidarta dake a ƙasan gado, don ita tuni ta yafe hawa gado, komai nata a ƙasa take zama ta yi shi, Hankalin ta kwance babu damuwa akan fuskarta, Danish yana daga kishingiɗe saman bed ɗinsa, ya ɗan lumshe eyes ɗinta, sam babu walwala akan fuskar shi, Azeeza tana zaune saman gadon parveen, ta ɗaura kanta saman shoulder dinta, magana su ke yi ƙasa ƙasa a takaninsu, haris da deeja suna fuskantar juna, sun nutsa cikin tattaunarsu duk dai akan Batul ne, idan muka koma 6angaren su Hanna ita da hibba da Yasmin da eve da rubina kowaccensu na kwance saman gadonta, sun yi likimo kamar masu yin bacci, Zuciya ce ba daɗi, dole jiki yai sanyi, yar gida daddy kuwa bacci ta ke yi sai dai ga dukkan alamu babu lafiya ajikinta, kamar zata faɗo daga saman gadonta, a cikin bacci take murza cikinta da hannunta na dama, idanuwanta sun kumbura, ga sahun marin da Danish yai mata gefen fuskarta kamar jini ya kwanta. Zuciyarshi a hautsine Ya ƙarasa gefen gadon shi ya zauna, Ya rasa wa zai tunkara game da zancen haura war shi taga, so yake ya sami wanda zai faɗa mawa, ko don su je su ɗauko yarinyar nan da ya gani, tabbas yana ji aranshi cewa mutun ce ita ba Aljana ba, shiyasa abun ya tsaya masa aranshi, gani yake kamar bai kyauta mata ba, yanzu da ace sister ɗin shi ce, acikin wannan mawuyacin halin bazai ta6a ƙyale ta ba, duk runtsi duk wuya sai ya taimake ta, but why ya gaza taimakon ita wannan yarinyar, girgiza kai ya ɗanyi kamar wanda aka zunguri bayanshi ya miƙe Ya cigaba da yin zarya cikin ɗakin nasu, Ji ya ke kamar ya je ya faɗa ma Danish sai dai yana matuƙar kokwanto a kan shi, Kuma yana ji aranshi zaiyi wuya ya bashi haɗin kai don su shiga cikin kurkukun. To waye zai iya faɗa ma zancen nan? Nutsawa yae cikin tunaninshi, nan take zuciyarshi ta Amabaci sunan ANGEL, tunawa yai da lokacin data watsa ma Giants ruwa a jikin su tana zazzaga musu masifa, hakan yasa shi yarda cewa Yarinyar ba ƙaramar jaruma ba ce, bata da tsoro kuma tana da ƙwarin gwiwa, dama tun ranar da aka kawo su ya lura da yadda take tafiyar da rayuwarta da kuma ta ƴan uwanta tamkar itace ta haife su, ta zama jagora acikin su, kuma ya fahimci cewa yarinya ce ita bata kai shekarunsu Hanna ba, amma tafi su wayau da hankali. Tun da ya fara zarya acikin ɗakin, su parveen su ke ta kallon shi, hatta Danish ya ankara dashi, kamar akwai wani abu dake damun shi, sam bai lura da kallon na shi da suke yi ba, A ƙarshe zuciyarshi ta saƙa mishi cewa _Ita kaɗai ce zata Iya taimaka maka wurin nemo ƴar uwarka, tun da itama tana neman tasu ƴar uwar da aka ɗauke, Idan ku ka haɗa hannu da ita, za ku iya cimma nasara, don haka karka kuskura ka faɗama kowa, Ita kaɗai zaka sanar mawa_ Muryar Azeeza ce ta katse mishi zancen zucin mashi ta hanyar yi mishi magana "Ɗan uwa, me ka ke tunani ne? Tun ɗazu na lura da kai sai zarya ka ke yi mana acikin ɗaki, nace anya lafiya kuwa" Murmushin yaƙe ya ƙaƙalo akan fuskarshi tare da juyar da kanshi Ya fuskanci inda azeeza take zaune ita da parveen. Kamar wasu tagwaye "Ina tunanin rawar da zan koya ma ku ne ko ba ku so"? Ya faɗi hakan ne don kar su yi tunanin wani abun ne na daban ke damunsa. Har suna haɗa baki wurin cewa"Muna so mana, dama zuciyar mu duk ba daɗi wlh, kwanakin nan mun rasa farin cikin mu" "Kada ku ta6a bari damuwa ta hana ku jin daɗin rayuwar ku, saboda kowa yana da damar da zai sanya kan shi farin ciki, yawan zama kuna tunanin zai iya haddasa muku matsala, just ku yi abunda ranku ke so, zaku samu farin ciki" acewar Gabriel Parveen tace"Angel tana koya mana yadda zamu motsa jiki, da karatu sannan tana bamu tarihi da labarin gidan daddynta, har ma ce mata tayi wata rana zata yi ƙoƙari don mu fita daga cikin kurkukun nan........." natsuwa gabriel yai a yayin da yake sauraran maganar parveen, da alama ya ƙara samun wani abu da yake son ji agame da angel, da sauri ya nufi gefen gadon dasu azeeza suke zaune, shima ya zauna. "Inaso ku bani duk wani labari da angel ta baku agame da rayuwar ta, da kuma abubuwan da ta koya maku" Buɗe ido sosai Danish yai daga can saman gadon shi yake kallon bayan Gabriel dake zaune gefen su parveen, Mamaki ne ya kama shi for what reason Gabriel zai dinga yi musu tambayoyi kan angel! Menene alaƙar shi da ita? Why yake son ji"? Miƙewa zaune Danish yai saman mattress ɗin, ya jingina bayanshi jikin bango, ya tsare su da ido, Tabbas da ace yasan dalilin da yasa gabriel ya tambayi su azeeza su bashi labarin angel da ya dakatar shi. Parveen ce ta labarta mishi komai game da angel, tun zuwanta kurkukun da irin ɗawainiyar da ta yi masu, har zuwa ranar da aka kawo su Gabriel cikin kurkukun. Jinjina kai gabriel yai alamar ya gamsu da labarin da parveen ta bashi na angel, Azeeza tace"mu taso ka koya mana rawar? Idon shi akan fuskarta yace"nafi so mu yi tare da angel, mu bari ta farka," su ka ce mi shi toh, zasu jira ta farka, Miƙewa Gabriel yae daga gefen gadon parveen, yana juyawa suka haɗa ido da Danish, ya ɗaure fuska, ta6e baki Gabriel yae tare da wuce wa Ya nufi nashi gadon ya zauna yana jiran farkawar Angel. Lokacin da marece ya nutsa, suna zaune, Unaiza tafarka jikinta nata kerma hannayenta dafe da Cikinta, saukowa tai daga saman gadonta, da gudu ta nufi sashen toilet ɗinsu, har wani jiri take gani acikin idanuwanta, bayan ta shiga toilet ɗin agaban magudaji ta zuƙunna tana ƙwara amai, tamkar ƴan hanjin cikin ta zasu zazzago, temperature ɗin jikinta ya yi zafi sosai, tana acikin mawuyacin hali, an rasa me zuwa wurinta ya taimake ta. Tun daga cikin sashen toilet ɗinsu har izuwa cikin ɗakin su, Sautin kakarin amanta ne Ya karaɗe ko'ina, Ya addabi kunnuwansu, ganin sunƙi motsawa suje su taimake ta, yasa azeeza ta sauko daga saman gadonta, parveen hada cewa"Zuwa za ki yi? Baki ji abunda angel tace mana akanta ba? Salon saita shanye maki jinin ki ko"? abunda suke jima tsoro kenan shiyasa suka ƙi zuwa su taimake ta, shi kuma Danish abunda ya hana shi zuwa wurinta gudun kada yabar ɗakin Gabriel ya samu damar zuwa wurin angel, saboda ya fahimci cewa so yake yayi magana da angel. "Ai bata da lafiya, ba zata iya shan jini ba, ni dai zanje na taimake ta ne, kada ta mutu" azeeza ce tai maganar tare da kama hanya ta nufi sashen toilet dinsu, Cikin toilet ɗin da take jin sautin shesheƙar kukan Unaiza, ta buɗe ƙoparshi tasa kai ta shiga, A zuƙunne ta same ta, Baiwar Allah taji jiki, Cikinta ya ɗame dama bata ci abincinta ba, jikinta sai kerma yake yi. Ƙarasawa gabanta Azeeza tayi fuskarta da alamun tausayinta ta zuƙunna suna fuskantar juna, bata ta6a tunanin wani daga cikinsu zaiji tausayinta ba har yazo wurinta sai ga azeeza tazo, daƙyar take kallonta saboda nauyin da idanuwanta su ka yi mata, sunyi luhu luhu da su kamar ƙwayar cikinsu zasu faɗo ƙasa launin idon nata ya ciza, la66anta sun yi suntum, sai nishi take yi tana matse cikinta. "Sannu sister, baki da lafiya ne"? Bata samu damar amsa mata ba, azeeza ta kuma cewa"Pls talk to me, I wanna help you." Ganin taƙi tanka mata yasa azeeza ta Miƙewa tare da nufar inda bucket ɗinsu yake, ta tarba shi bakin fanfo ta kunna ruwa ya soma sauka acikinsa, Sai da yai rabi ta ja bokitin tana nishi don ba ƙaramin nauyi yayi mata ba, gefen unaiza ta ajiye bokitin, kafin ta karkatar dashi ruwan cikin ya kora aman da tayi dukan shi, Sauran da ya rage, ta taimaka mata wurin wanke fuskarta, ita kanta azeeza sai da gabanta ya faɗi jin irin zafin da jikin unaiza yae, lokacin da ta ke wanke mata fuskar da hannunta, kwata kwata babu ƙoshin lafiya atattare da ita, hada baki ta kuskure mata. "Mu koma ɗaki, kinji" a wahalce ta ɗago da ido tana kallon azeeza ta ɗan girgiza mata kai, yayin da take cizon lower lip ɗinta, wani irin raɗaɗin azaba take ji. "Pls ki yi min magana mana, ni inaso na taimake ki ne" runtse ido unaiza tayi na ɗan wani lokaci, azeeza har ta gaji da tsayuwa, ba dan tana jin tausayinta ba da tuni ta jima da komawa dakin su, Tana so ta yi ma azeeza magana sai dai ta kasa motsa la66anta, jini har ya fara bleeding ta hancinta, ganin hakan yasa hankalin azeeza ya tashi, da gudu ta nufi cikin ɗakin su, a sukwane ta faɗo Ciki, Hankalinsu Naufal ya dawo kanta, muryarta har tana shaƙewa wurin faɗin"Ƴar gidan daddy bata da lafiya, Hancin ta yana bleeding, dan Allah ku zo ku taimake ta" Shiru su ka yi babu wanda ya tanka mata, duk da sun tsorata da jin abunda ta faɗi, Ran azeeza ba ƙaramin 6aci yae ba, hawaye har sun fara wanke fuskarta, cikin ƙunar rai tace"wai ba zaku zo ku taimake ta ba"? Kamar kurame sai dai suka bi ta da ido, fuskarta a hautsine ta nufi gadon angel, tana bubbuga ƙafarta tana ambaton sunanta "Angel wake up, ga ƴar gidan daddy can bata da lafiya, ina ta roƙon su akan su zo mu taimake ta amma sun ƙi saurarana" tana kuka tana magana, Daƙyar ta samu Angel ta farka, tana faman yamutsa fuskarta da tayi jawur, saboda kukan da tasha, A hankali ta tsayar da idanuwanta kan fuskar azeeza dake ta kuka, Muryarta adisashe ta furta"meya faru ne"? Cikin shessheƙar kuka azeeza tace"Ƴar gidan daddy ce, tana acikin toilet bata da lafiya hada jini a hancinta, ina ta roƙonsu akan su zu su taimaketa amma sunƙi su saurare ni" Ɗaya bayan ɗaya angel tabi kowannansu da kallo, ita Sarah bacci ne ya ɗauketa bayan ta gama yankar akaifar, amma sauran idonsu biyu, lokaci ɗaya ta fahimci dalilin dayasa suka ƙi zuwa su taimake ta, saboda tace musu ita mayyace, zata iya shanye musu jini, duk da ita ta yi hakan ne don ta sanya musu tsoronta acikin zuciyar su, gudun kada ta lalata musu rayuwa. Saukowa Angel tayi daga saman gadonta, da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu azeeza tabi bayanta, Suna shiga Cikin toilet ɗin da Unaiza take suka same ta kwance ƙasa, idanuwanta sun juye, Hankalin angel ba ƙaramin tashi yai ba, zuƙunnawa tayi agabanta tare da sanya hannayenta biyu ta ruƙo kafaɗunta, ta ɗago da ita zuwa ƙirjinta, ta faɗa, nan take angel taji zafin da ke ajikin unaiza na fitar hayyaci, hatta nunfashinta da hucin zafi yake fita, ta rasa gane wani irin ciwo ne ke damunta, kamar hada zazza6i, raba jikin su tai daga na juna, ta sanya hannu ta tallabo fuskarta, muryarta na kerma tace"Unaiza meke damun ki? Wani irin ciwo ne wannan"? Biji biji ta ke kallon angel, duk da tana acikin mawuyacin hali, sai da tayi mamakin ganinta, don bata ta6a tsammanin wani daga cikinsu zai iya taimaka mata ba, motsi ta soma yi da la66anta, sunan allura ne take faɗa musu wadda ake yi mata agida, idan ciwon ya tashi, sai dai sun gaza fahimtar me take cewa, koda ace ma sun gane, basu da hanyar da zasu iya samo mata allurar, "Azeeza ɗauko min mayafin nan na kayan mu," ta amsa mata da toh, ɗaki azeeza ta shiga ta ɗauko Cotton scarve ɗinta, ta dawo ta miƙa ma angel bayan ta kar6a, tace ma azeeza ta zauƙunna ta ruƙe unaiza ajikinta, a cikin bokiti Angel ta tsoma mayafin cikin sauran ruwan da azeeza ta kora aman unaiza, sai da ya jiƙa ta matse shi, ta ɗaura shi saman jikin unaiza, ta dinga goga mata shi, ta ko'ina, ta yi mata hakan ne don ta samu relief ɗin zafin jikin ta. sai nishi take yi tana fitar da numfashi awahalce, duk in ta ɗaura mayafin ajikinta sai ta zabura, alamar bata son ruwan jikin mayafin na ta6a jikin ta, bayan ta kammala, ta miƙe taje bakin igiyar toilet ɗinsu ta shanya Mayafin, Kafin ta dawo ta sanya hannu biyu ta ruƙo unaiza ta miƙar da ita, jikin ta babu ƙwari, dama ba wata ƙibar kirki ke gareta ba, a haka taja ta zuwa cikin ɗakinsu, Suna shiga ciki, idanuwansu Hanna suka dawo kansu, gadon unaiza angel ta wuce da ita, tare da kwantar da ita sama, ta juya ta nufi akwati nansu, ta buɗe ta ɗauko tissue ta koma saman gadon unaiza. Dashi tai amfani wurin goge mata sauran jinin dake a hancinta, bayan ta kammala ta nannaɗe wanda ta goge jini da shi ta cusa su acikin wanda ta kuma yagowa, ta miƙa ma azeeza tace taje ta zuba a acikin trash can, ta amsa mata da toh, bayan ta kar6a ta juya ta nufi toilet dinsu, bada jimawa ba, Azeeza ta dawo ɗakin, gefen gadon unaiza ta koma ta zauna, ya kasance su biyu ne akusa da ita, jikinta ya ɗanyi sauƙi, ta ɗaura kanta saman pillow, still bata daina nishi ba, hannayenta na asaman mararta, addu'o'e angel ta karanto mata ta tottofa mata saman fuskarta da jikinta. Hankalin Gabriel gaba ɗaya yana akan angel, yayin da shi kuma Danish nashi hankalin ke akan Gabriel, Ya kafe shi da ido ba tare da ƙyaftawa ba, sarai gabriel ya lura da kallon tuhumar da Danish ke yi mishi, amma sai ya basar. Saukowa yai daga saman gadon shi ya nufi angel, da sauri Danish Ya miƙa shima Ya nufi gadon Unaiza, atare suka tsaya bakin gadon, har suna haɗa kafaɗa, Kallon mamaki Gabriel yai ma Danish, fuskar angel a yamutse ta kalle su, harara ta watsa ma Danish, muryarta ƙasa ƙasa tace"Shi ne ku na ganin bata da lafiya amma an rasa wanda zai taimaka mata acikin ku sai Azeeza"? Gabriel ne yace"Bansan time da ta farka daga bacci ba, hankalina baya akanta,"Danish yace"saboda ke yasa ban je wurin ta ba" ta6e baki ta ɗanyi, tare da juyar da kanta, Ta kalli su Hanna tunkafin ta yi magana parveen tace"ae kin hana mu zuwa wurinta saboda mayyace zata shanye mana jini, shiyasa mu ka ƙi taimakon ta" Numfasawa tayi yayin da take kallonsu, Acan cikin zuciyarta tana tunanin taya zata fahimtar dasu cewa ba mayya ba ce? Kada su ɗauke ta maƙaryaciya, tun da ita ta faɗa mu su hakan da bakinta. "Ae bance kada ku taimaka mata ba, idan bata da lafiya, a bun dana hana ku shi ne ku daina bari tana ta6a jikin ku, saboda babu kyau, wani ya kalli tsiraicin ka koya ta6a shi, Itama don batasan babu kyau ba ne shiyasa take yi, amma in muka ja ta ajikin mu mu ka fahimtar da ita zata daina ne....." tun kan ta rufe baki, Rubina tace"Hada jinin zata daina sha"? Ɗaga mata kai angel tai alamar eh, su ka ce toh zamu dinga taimakonta daga yanzu, amma itama kija mata kunne ta daina rashin jin magana, kuma ta daina yi mana gorin ƙirji," angel tace musu toh, zata ja mata kunne. Mayar da idanuwanta ta yi akan su Danish dake atsaye, kowannan su ita ya ke kallo, ta rasa gane dililin yin tsayuwar na su akanta. "Lafiya"? Tai tambayar tana jiran jin amsar su, kusan atare suka haɗa baki wurin cewa ba komai," juyawa gabriel yai tare da komawa gefen gadon shi ya zauna, shi ma danish ya koma nashi gadon ya zauna. Duk wani motsin Gabriel Akan idon Danish, Ya hana shi sakat, Abu kamar wasa, Ko toilet Angel zata shiga sai Danish yabi bayanta, lamarin ya ɗaure mata kai, a bakin ƙopar toilet ɗin zai tsaya har saita fito sannan yaja hannunta su koma ɗaki, hakan ba ƙaramin 6ata ma Gabriel rai yai ba, shi burin shi su zauna da ita su tsara yarda zasu ɗauko ƴan uwansu, da kuma yarda zasu gudu daga Cikin kurkukun tun da yaji cewa itama tana da wannan ƙudirin aranta, Sai dai ga dukkan alamu, akwai mutun ɗaya da baison hakan ta faruwa, shiyasa ya hana shi sukuni, dama can bai yarda da Danish ba, tun zuwanshi, daga gani yana da wayau, akwai abunda yake 6oye musu, kuma yasan komai akan gidan kurkukun kallon su kawai ya ke yi. Lokacin da dare ya yi kowannansu yai shirin kwanciya, mutun biyu ne babu alamun zasu runtsa. Jikin Unaiza ya ɗan lafa, da taimakon su azeeza taci abinci kaɗan, tun ɗazu bacci yayi awon gaba da ita. A tsakiyar ɗakin Gabriel ya dinga sintiri yana jiran bacci ya ɗauki Danish, Ko ya samu yaje su yi magana da Angel, amma ɗan tahalikin nan Yaƙi kwanciya, ƙarshe ma daya ga dagaske Gabriel ba bacci zaiyi ba, sai ya ɗauki pillow ɗinshi, Ya koma saman gadon Angel da ke kwance tana yin bacci, Ya ɗaura pillow ɗinsa saman mattress ɗinta, ya hau ya zauna tare da jingina bayan shi jikin pillow ɗin,' mamaki ƙarara akan fuskar gabriel, Ganin wani iko na Allah, a dole ya haƙura ya koma kan nashi gadon ya kwanta zuciyarshi acunkushe da tunani kala kala,. Dare Ya nutsa sosai, Sunyi nisan kiwo acikin baccin su, har time ɗin Danish na zaune saman gadon angel, ahaka bacci yai awon gaba dashi, Ba zato ba tsammani, Unaiza tafarka tana ihu tana daddafe cikinta, wata irin kururuwa kamar ana zare ranta, a matuƙar firgice masu bacci suka soma farkawa Kowa Yana faman zazzare idanuwanshi, Haƙiƙa sunyi matuƙar firgita, ɗaya bayan ɗaya suka soma saukowa daga saman gadonsu suna tunkarar gadonta, mutun biyu ne basu farka ba, Jamima da majnun, kamar matattu sai sharar baccin su su ke yi, A kewaye da gadon unaiza suka tsaitsaya curko curko suna kallonta hankalin su yai matuƙar tashi, suka dinga tambayarta lafiya meke damunta, amma ta kasa buɗe baki ta basu amsa, Sai cizon la6en ta take yi, yayi suntum dashi, Angel tafi kowa shiga damuwa tsoranta, har ga Allah bata son wani abu ya samu unaiza duk da baƙin halinta tana ƙaunarta. "Yanzu ya zamuyi da ita? Danish ba wani taimako da zaka iya yi mata? Angel ce tai maganar tana kallon shi, yae shiru bai ce mata komai ba, Haris yace"ni fa inaga kamar kalar ciwon da su Hanna suka ta6a yi ne" gabansu ne yai wani irin mugun bugu jin abunda Haris yace, muryar deeja na arude tace"In sha Allah ba shi bane," Azeeza tuni ta fashe musu da kuka, tana zaune saman gadonta, ta kasa saukowa gudun kada ta faɗi ƙasa saboda lalurarta, tana jiyo muryoyinsu acikin kunnuwanta Suna Cikin yin maganar nan, sautin motsin buɗe ƙopa ya karaɗe kunnuwasu, hankalin su ya ƙara tashi, nan take ransu ya basu cewa Anzo atafi da ita ne' jikin su duk yai sanyi, lokacin da su ka yi arba da Giant ɗin dake saukowa saman benan, basamudan ƙato, Mai ɗauke da star 1 agaban rigarshi, tunkan ya ƙaraso ciki, suka bashi hanya, Ya sanya hannu biyu ya ɗauki unaiza saman kafaɗarshi ya juya ya fuce da ita daga Cikin ɗakin, kamar wasu sakarkaru haka suka bi bayan shi da kallo har ya 6ace ma ganin su, Suna jiyo datse ƙopar ɗakin nasu da akayi, shi kenan an tafi da Ƴar gidan daddy, Gabriel yaso ya tambaye su ina za'a kai ta? Sai kuma ranshi ya bashi cewar wata'ƙil zasu kaita inda zasu duba lafiyarta ne, hakan yasa shi dakatawa da yin tambayar tashi, dama bai shirya yinta ba agaban Danish, don zai ƙara sa mashi ido ne. Ba su ta6a tunanin zasu zubar mata da ƙwalla ba, saboda babu shaƙuwa atsakanin su da ita, Amma sai gashi yau saboda ita sun gaza runtsawa, a gefe da gefen gadonta matan su ka zauna shiru babu mai magana, Babu yadda haris baiyi dasu ba akan su koma su kwanta saman gadajen su, amma suka ƙiya, A ƙarshe nan suka kwana. A washe garin ranar da safe, suna ta sharar bacci, wasu sun jingina bayansu jikin bango wasu kuma sun ɗaura kawunansu saman cinyoyin ƴan uwansu, Waɗan da suka kwana asaman gadonsu, mazan ne duka sai Jamima da azeeza, Cikin sa'a Gabriel ya riga Danish farkawa daga bacci, Ae yana buɗe ido ya hango Danish baje saman gadon shi, yai wuff ya duro daga nashi gadon Cikin sanɗa ya nufi bakin gadon unaiza inda suke zazzaune suna bacci, A hankali ya zuƙunna inda angel ta jingina bayanta jikin bango, hanna ta ɗaura kanta saman laps ɗinta, haka su kai bacci jiya, saitin kunnanta yakai bakin shi cikin raɗa ya shiga kwala mata kira "Angel! Angel" har cikin dodon kunnanta, ganin tana ƙoƙarin buɗe idanuwanta yasa shi yin sauyin ɗaura tafin hannun shi saman bakin ta, gudun kada ta razana ta saki ƙara Danish ya farka, tsantsar mamaki ne ya kamata ganin Gabriel, Zuƙunne agabanta, hada ƙoƙarin toshe mata baki, zazzare mishi idanuwanta ta soma yi, tare da kai hannu zata ka6e mishi nashi hannun daya toshe mata baki. Da sauri yace"ina son magana dake, tun jiya, bana so kowa ya sani, pls ki bani haɗin kai, ki taso mu shiga sashen toilet ɗin mu" yana ƙare maganar ya zame hannun shi daga saman bakinta, Ya miƙe cikin sanɗa ya nufi 6angaren toilet ɗinsu, yana tafiya yana waiwayon shimfiɗar Danish, wata irin kasalace ta baibaye Jikinta, A hankali takai hannu ta ɗauke kan Hanna daga saman laps ɗinta ta kwantar da ita ƙasa, kafin ta miƙe ta bi bayan Gabriel, tana shiga sashen toilet ɗin ta same shi atsaye ya jingina bayan shi jikin bango. Yana ganinta yai saurin ruƙo hannayenta biyu acikin nashi, kamar wani mara gaskiya, yana magana yana kallon bakin ƙopar shigowa sashen toilet ɗin, Nan take ta fahimci cewa akwai wanda baya son yaji abunda zai faɗa mata. "Tun jiya nake son na yi magana dake amma ɗan uwanki ya hanani sakat, na rasa gane dalilin dayasa baya son na tunkare ki" "You mean Danish"? Ɗaga mata kai yai alamar eh" Tace mai ka ke son faɗa min ne"? Har ya buɗe ba ki zai yi magana ya ji ta yi saurin katse shi da cewa"Oh wai kana magana akan Unaiza da aka tafi da ita jiya? Nasan ka tsorata da ganin an ɗauke ta, bawani abu zasu yi mata ba, za'a kai ta treatment room ne aduba lafiyar jikinta" tun da angel tai wannan maganar nan take Gabriel ya fahimci cewa DANISH yazo wurin, shiyasa tai saurin tarar numfashi shi, Saboda ita ta hango shi, kamar walkiya, ko yaushe ya tashi daga bacci. ta wutsiyar ido Ya hango shi tsaye bakin ƙopar shigowa wurin ya goya hannayen shi saman ƙirjin shi, ya kafe su da ido. Yatsina fuska Gabriel ye ba tare daya kalli fuskar Danish ɗin ba, yaji takaicin bayyanar shi, ɗan hana ruwa gudu, sauƙin ma Angel ta gan shi da baisan me zai biyo baya ba, idan ya faɗa mata ya shiga cikin kurkukun. "Zan shiga toilet in yi wanka, yakamata kaima ka shiga ka yi" tana magana kamar batasan da zaman Danish a wurin ba, Ta juya ta nufi toilet ta buɗe ta shiga, duk akan idon Danish, Shima Gabriel ya nufi ɗayan toilet ɗin ya shiga Ciki, Ya datse ƙopa. Sun so ace ya koma cikin ɗaki amma yaƙi tafiya, kowannan su sai da yae wanka time da suka fito daga cikin toilet ɗin, Yadda suka barshi haka suka same shi, Gabriel bai tanka mishi ba ya wuce ɗaki, Angel ce ta tsaya tana kallon shi fuskarta ɗauke da murmushi tace"ya ka ke? Fatan ka tashi lafiya"? Wani irin kallo taga yanayi mata, kamar ba zai amsa mata ba, muryarshi da alamun kasala ya amabaci sunanta "Angel, na tashi lafiya, ina fata kema haka" matsawa tai kusa dashi, jikinta da lemar ruwan wankan da tayi, Tace"jiya nashiga damuwa da aka tafi da unaiza, banma san time da bacci ya ɗauke ni ba, zuciyata ba daɗi" ta ƙarasa maganar kamar zata fashe da kuka, Ruƙo hannunta yae acikin nashi, ya ɗan janyota kusa dashi, "Fuskarki harta kumbura, yakamata ki koma kiyi bacci, ko kin samu relief," girgiza mishi kai ta yi "a'a, baccin ya ishe ni, zan jira abinci ne, ka shiga toilet ka yi wanka zan jira ka anan" (Angel sarkin wayau, tana so ne ya shiga don ta samu damar yin magana da Gabriel, ta ƙagara amatse take da taji me zai faɗa mata) Maƙe mata kafaɗa Danish yai tare da cewa"Bana buƙatar yin wankan, mu koma ɗaki mu zauna, mu jira abinci nima yunwa nake ji," kallon shi kawai ta ke yi, wato ta fahimci wani abu agame da Danish, shegen wayau ne dashi, mutun sai yana da kaifin basira zai iya gane hakan. "Dan Allah ka shiga ka yi wanka, inaso ne kaima ka ji irin daɗin da naji ajikina, idan ka kammala sai mu koma ɗaki," kamar maroƙiya haka tadinga yi mishi magiya akan yaje yae wanka, hada bubbuga mishi ƙafa da shagwa6a, sai taga ya saki ƙayataccen murmushi akan fuskar shi, ta yi tsammanin zai amince ne hakan yasata sakin murmushi tace"Ka amince zaka shiga ka yi wankan"? Ɗaga mata gira yai tare da cewa"Eh amma atare zamu shiga, sai kiyi min, idan har baki amince mun shiga atare ba, to ki daina roƙona akan yin wanka don ba inda zanje INA ATARE DA KE!" takaici ne ya isheta A ƙule tace "ai ni nayi wanka akan me zan bi ka mu koma toilet"? Tai maganar tana gatsina mishi hanci, yace"nasan kinyi ae, ni zaki yi mawa yanzu" tsoki taja tare da bi ta gefen shi ta wuce cikin dakin, Ya juya yabi bayanta, Suna shiga Ciki suka sami Gabriel zaune gefen gadonshi ya zabga uban tagumi, Takaicin Danish ne ya ishe shi, sam baya son aja tsawon lokaci ba tare da yayi gaggawar sanar da angel game da yarinyar nan ba, zata iya rasa ranta. Saman gado Danish ya zauna, angel kuma ta nufi akwatin kayansu, ta ɗauko red vest ɗinta, tare da dogon wandonta baki, Ta nufi sashen toilet dinsu ta shiga, acan ta canza kayan jikinta, ta cire tsaffin ta maida sabon, Vest ɗin tabi jikinta ba ƙaramin kyau ta yi mata ba, duƙunƙune tsohon uniform din ta yi a hannunta. Bata fito ba, sai ta tsaya tana leƙen Cikin ɗakin su daga cikin sashen toilet ɗin, bakowa take kallo ba face Gabriel, ranshi ne ya bashi cewar ana kallon shi, hakan yasa shi juyowa don ya tabbatar, Cikin sa'a su ka haɗa ido da ita, Da hannu ta dinga yi mishi alamar ya iya rubutu? Ta kwatanta mishi biro ta hanyar yin amfani da hannunta na dama kamar tana rubutu, nan take ya gane me take nufi, bai amsa mata ba saboda Danish daya tsare shi da ido, shiyasa ya kawar da kanshi gefe ɗaya, Fitowa angel ta yi daga cikin toilet din ta shiga ɗakin ta zauna gefen gadonta, ta daura idonta akan Gabriel, so take ya bata amsar tambayarta idan ya iya rubutu, tana so ta sanar dashi akan ya buɗe backpack ɗin Unaiza ya ɗauko jotter dinta da biro yae mata rubutu, Ya jiye mata, ta hakanne kaɗai zasu iya magana da juna, if not Danish bazai ta6a bari su ke6e ba, sai dai batasan koya iya rubutun ba, zaiyi wuya ma ace bai iya ba, tun da a hasashenta ba rainon kurkukun ƙaddara ba, Akwai wayewa atattare da shi. Yaso ya bata amsa amma Danish Ya kafe su da lumsassun idanuwanshi, Su uku ne idonsu biyu acikin ɗakin, Sauran har yanzu basu farka ba, Sai daga bisani ne Ɗaya bayan ɗaya su azeeza suka soma tashi daga bacci, da tunanin unaiza suka farka, suna ta jimamin halin da aka tafi da ita jiya, abun ya ta6a zuciyoyinsu, Angel tace dasu suje suyi brush suyi wanka, idan suka fito zasu motsa jiki yau, hakan yasa suka miƙe atare suka nufi sashen toilet ɗinsu, kafin wani lokaci duk su kayi wanka, kowa ya sanya red vest din shi da dogon wandon shi na sabon kaya ba ƙaramin kyau, su ka yi musu ba. Ba su kai ga fara motsa jikin nasu ba, Giants suka kawo musu abinci, Dama da yunwa suka farka, Kowa ya samu wuri ya zauna, tsiren nama ne aka kawo musu da kayan marmari, hada robobin lemu dana ruwa, suna cin abinci idon Gabriel akan fuskar angel, yana so ya bata amsar tambayar da ta yi mishi ɗazu shiyasa ma ya zauna yadda zasu fuskanci juna, ko da ta ɗago suka haɗa ido dashi, saboda rashin gaskiya atare suka saci kallon Danish, shi da yafi su iyawa, ashe tun ɗazu ya ajiye cin tsiren naman don kada ya janye mishi hankali daga kansu har su samu damar yin wani abu ba tare daya gani ba, kyawawan idanuwanshi na akan faces ɗin su. Danish bai ta6a bata mamaki ba irin na yau, ashe dama yana da wayau? Yake nuna kamar sakarai ne shi? yau dai ta shaida hakan, har tambayarshi ta yi meyasa bazai ci Abincin shi ba? ya ce mata kada ta damu, zai ci ne zuwa anjima. tasa naci akan saiyaci, yace idan har tana so yaci, to ta dawo saitin inda yake zaune, don yaji daɗin ganinta da kyau, ba tare da ta yi mishi musu ba, ta miƙe tabar saitin Gabriel ta koma saitin inda ya ke ta zauna, Sai gashi ya sanya hannu yana ci yana kallonta, a haka har suka kammala Cin abincin, Giants suka tattara farantan kayan abincin suka bar ɗakin, fitarsu ke da wuya, Angel ta nufi toilet, Da sauri Danish yabi bayanta, tana shiga ya fado ciki, murmushi ta sakar mashi tare da cewa"My bodyguard, wankan zaka yi ne"? yace mata a'a, ita ya biyo tace mashi toh, su shiga dama tazo duba furenni ne taga awani hali suke ciki, ta kuma basu ruwa, Atare su ka shiga, da kanshi ya ɗabo mata ruwa a bucket yazo da shi gaban tukunyar fulawar, har yanzu dai furen batul Yana nan yadda yake, ya bushe Ganyan sun tsamure, suna a tsaye ta kalle shi tare da cewa"furen batul ya nuna alamun bata da ƙoshin lafiya, amma banji ka ce komai ba"? Ba tare da ya ɗago ya kalle ta ba, ya bata amsa da cewa"bani da masaniya akan yanayin ganyan jikin shi, zai iya yiwuwa ruwa furen ke buƙata" ya ƙarasa maganar tare da kwarara ruwan da ya ɗabo saman furennin, bayan ya kammala ya sauke bucket ɗin, Kallon juna su ka yi ita da shi, ba tare da ƙyaftawar ido ba, "Irin wannan kallo haka, me kake gani akan fuskata"? Tae tambayar tana dan harararshi, Bai bata amsar maganarta ba, sai ce mata yai "Pls angel, bana so in gan ki tare da yaron can, ni ban yarda da shi ba, kuma na lura kamar yana son shisshige miki ne......" dariyar da tayi ne ya sa shi dakatawa da yin maganar, sai da tayi mai isarta tukunna ta dai dai ta natsuwarta. "Ka faɗi min dalili ɗaya da zaisa in janye jiki da shi, in banda abun ka ni menene alaƙa ta dashi? Ko ka ga wani abu ne"? Shaking head ɗinsa yai "just ni bai kwanta min araina ba" fuskarshi ayamutse ya bata amsa, ta6e baki ta ɗan yi, tana ƙoƙarin motsa lips ɗinta da niyar ta yi magana, ɗan juyi da zatayi keda wuya ta hango wani sabon tsiron fure kyakkyawan gaske a gefen na daddynta, waro ido waje tayi cike da mamaki, Ta zuƙunna gaban tunkunyar fulawar, a gefen ta Danish ya zuƙunna, launin ganyen furen pink colour, tsabar kyau kamar ka cinye, A ruɗe ta kalli Danish Alamar tana son ƙarin bayani game da sabon furen daya fito, girgiza makai yai alamar shima baisan ya akai ya futo ba, wani irin kallon rainin wayau tayi mashi tare da cewa"Ni dai ka faɗa min ran wanene akan sabon furen nan" shiru yai still idonshi akan fuskarta, sam baiso ta canza musu firar da su ke yi ba, Yaji haushin fitowar sabon furen da bai san Ran wa ke akanshi ba, saboda ya katse musu maganar da su ke yi. "Magana fa nake maka, inaso nasan furen wanene wannan mai kyan gaske," motsa lips ɗinsa ya soma yi "Angel, bansan na wanene ba, Amma tabbas mallakinsa, zai iya kasancewa wani ne daya maye gurbinki a wurin daddynki, ina nufin wanda daddynki yake matuƙar ƙauna kuma yake atare dashi" kallon harara angel ta jefa mashi, "Lier, Ae daddyna baida madadina a duniyar nan, Ni ɗaya ce tak, babu wanda zai iya replacing ɗina acikin zuciyarshi, balle ma baya araye da har za'a samu wani ɗan shisshigi ya amshi matsayin da nake dashi awurinsa" murmushi ne ya bayyana akan fuskar Danish maganar da ta yi ba ƙaramin nishaɗi ta sanya shi ba, Cigaba da magana tayi"daddyna da kanshi yace min ko aure zanyi bazan iya rabuwa dani ba, sai dai mijin ya dawo gidanmu ya zauna, ko kuma shi daddyna ya koma gidan shi da zama idan har yace bazai zauna a gidan mu," gaba ɗaya ta manta atare da wa take magana, surutu take ta zubawa kamar radio mai jini. "shi kanshi daddyna yasan irin burin da nake dashi, Ni nan da kake gani Hamshaƙin mai kuɗi zan aura, wanda ya shahara a duniya, ko Jinin sarauta, Hatta aunty aneelerh tasan da wannan maganar, wai hada ce min banson talaka nace mata Annabi ma yace mu nemi tsari da talauci, atoh, wa zai kai kanshi inda zai sha wahala, ae wlh ƙwara inda zanyi rayuwar hutu, adinga take min baya......." shiru ta ɗanyi kamar mai tunanin wani abu, shi ko mutumin ya tsareta da ido yana jiran ta ƙarasa sambatun nata, don ya lura kamar bata acikin hayyacinta ne. "Kurkukun ƙaddara Ya canza min rayuwata, na ɗauki darussa sosai na zaman duniya, a yanzu bani da wannan burin da nake dashi a lokacin da nake agidan daddyna, na faɗi maka ne kawai, ni da ma bani da tabbacin zanyi tsawaicin kwana" yanayin fuskar Danish ne ya sauya ganin ƙwalla sun tarar mata acikin idanuwanta, "Burin da nake dashi A yanzu shi ne, In taimaki ƴan uwana mu fita daga cikin wannan Kurkukun ƙaddarar, Su yi rayuwar ƴanci kamar kowa, wlh Ni ban damu da in tsira ba, su kawai nake so su ku6uta, bayin Allah ina amfanin ma iyayen da zasu sadaukar da ya'yansu don neman wata biyan buƙata ta duniya, yanzu jibi Unaiza, mugun ubanta da ya ke yasan bayar da ita zaiyi shiyasa bai bata tarbiya ba" sosai ta fashe da kuka, har cikin zuciyarshi ya ke jin kukan nata, hannu biyu ya sanya wurin janyota jikin shi ya ɗan kwanto da ita saman ƙirjin shi, yana lallashin ta. *PRISONERS✍️* Tun lokacin da Angel ta shiga toilet Danish yabi bayanta, Gabriel yae saurin miƙewa ya nufi saman table din dakinsu inda unaiza take ajiye backpack ɗinta, Sai da ya tabbatar babu mai kallon shi, dama already ya ɗauke musu hankalinsu, ta hanyar basu training ɗin rawar da za su yi, Sun dage sai tiƙar rawa suke yi atsakiyar ɗakin, Zuge zip ɗin jakar yai, Jerin text books ne da jotter hada diary ɗinta, wanda ke ƙunshe da tarihin rayuwarta, biro ya ɗauko tare da jotter ɗin ya ɗaura saman table, bayan ya buɗeta a tsanake Ya soma rubutu cikin harshen turanci, kusan shafi ɗaya ya cika, ya yagi paper ɗin da yayi rubutu akanta, Ya maida jotter ɗin da biron cikin jakar, Ya zuge mata zip ɗinta. Sai da ya ninke takardar, tukunna ya doshi gadon angel, Haris da deeja idonsu na akan Su parveen dake rawa, Haka zalika su naufal da mubeen duk hankalinsu akansu yake, Tsabar iyayi hada Majnun da Jamima cikin masu yin rawar uwa uba, Sarah, kamar macijiya sai karkarɗa ƙugu take yi, ita ala dole rawa take yi, Ya rasa a ina zai ajiye mata takardar inda zata gani, fargabarshi kada ya ajiye inda Danish zai iya ganinta, don zai iya yage ta ne. A ƙarshe ya yanke shawarar tura mata ita Cikin rigar pillow, ɗaukar pillow ɗin yai ya zuge zip ɗin jikin shi, ya saƙa takardar aciki, " kafin ya ajiye mata shi, a hankali yake ja da baya, cike da saran Allah yasa Angel ta karanta saƙon nashi. 💌 💋PRISONERS💋 Koma wa Gabriel yae saman bed dinsa ya zauna yana kallon masu yin rawa, yayin da acan cikin zuciyarshi tunanin yadda za'ae angel taga wasiƙar daya ajiye mata ya ke yi. Jin ta yi tsit ta manne masa a saman chest ɗinsa, yasa shi ɗan leƙa fuskarta, ta lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci, cikin sanyin murya ya ambaci sunanta"Angel"! ba tare da ta buɗe eyes ɗin ta ba, ta amsa mashi "na'am" a hankali ya ɗago da hannun shi zuwa saman sumar kanta, buɗe idanuwanta ta yi jin saukar hannun shi asaman gashin kanta, tana kallon cikin idanuwanshi, hakanan taji gabanta ya ɗan faɗi, launin idon shi ba ƙaramin kyau ne da shi ba. "Mu koma ɗaki, kada dare yai mana anan" yawu ta haɗiya kafin tace mashi"wankan fa? Haka zaka kwana ba tare da ka yi wanka ba, bazan ji daɗi ba gaskiya" tai maganar tare da ɗaure fuskarta. "Zanyi, amma sai dai in kulle ki a cikin toilet ɗin nan, in shiga ɗayan idan na kammala zan buɗe ki, mu koma ɗaki a tare" da mamaki akan fuskarta ta ke kallon shi, jin wani ƙarfin hali, shi ala dole baya son ta nisanta da shi, kuma tasan duk akan Gabriel ya ke wannan kishin. "Okay, I'll wait for you here. je ka yi wankan, idan ka kammala don't forget to come and open the door for me." ya amsa mata da toh, kamar kar ya raba jikin shi daga nata, haka yake ji, yana matuƙar ƙaunar kasancewa tare da Angel ɗinsa, ɗagowa da kanta ta yi daga saman ƙirjinsa, ya yunƙura ya miƙe ya fuce daga cikin toilet ɗin, tare da ja mata ƙopa ya rufe, ganin ya fita yasa ta miƙe ta nufi ƙopar don taji idan dagaske locking ɗinta yai, hannu tasa taja ƙopar taji ta adatse, Girgiza kai ta ɗan yi lamarin Danish ya fara tsoratar da ita, Ga shi yabar ta garƙame cikin toilet. A bakin ƙopar ta tsaya na tsawon 30 mins, tana tunanin ko awani hali Unaiza da Batool su ke a ciki, ta yi matuƙar damuwa da waɗannan bayin Allah. Motsin buɗe ƙopa taji da sauri ta ɗan ja da baya, ya turo ƙopar, tun daga ƙasa ta soma kallon shi, dogon wandon shi ne baƙi na old uniform ɗin sa, bai sanya rigar shi ba, fatarshi har wani salƙi take yi saboda tsabar haske da kyau, cikin shi a ɗame ya ke, kamar ba a zuba abinci a cikin sa, jikin shi hada lemar ruwan wankan da ya yi. Kallon kallon suka tsaya suna yi ma juna, ƙarasa shiga ciki yai tare da miƙa mata rigar hannun shi, aɗan rude ta kalli rigar, harara ta wurga mashi "Me zan yi da ita"? Fuskarshi babu wasa yace"jikina zaki tsane min" ta6e baki ta ɗan yi, can kuma sai ta saki murmushi tunawa da Aunty aneelerh, da ta ta6a leƙen su a ɗaki, tana goge ma uncle uzair jikin shi da towel, lokacin ya fito daga wanka. "Meyasa ki ke mirmishi"? Muryar shi ce ta katse mata tunanin nata, har lokacin bai janye rigar tashi da ya ke miƙo mata ba. Maƙe mashi kafaɗa tai tare da cewa"ae babu kyau, bazan goge maka ba, sai mun yi aure" maimaita kalmar aure yai"what does that mean"? Jujjuya eye balls ɗinta ta yi, tare da sauke su kan fuskar shi tace"Zan faɗa maka amma ba yanzu ba, sai mun fita daga cikin kurkukun nan," ta ƙarasa maganar tare da fashewa da dariya, tabi ta gefen shi, ta fuce daga cikin toilet ɗin, bin bayanta da kallo yai har ta 6ace ma ganin shi, ta tafi tabar shi da aikin maimaita kalmar Aure, tunawa da Gabriel dake acikin ɗakin, yasa shi yin saurin bin bayanta. Tana shiga ɗakin ta samu su azeeza zazzaune saman dining carpet ɗinsu kamar masu cin abinci, Alhalin nan kuwa fira suke yi a tsakanin su, gwanin ban sha'awa, Gabriel Na ganin ta yae saurin yunƙurawa zai miƙe daga zaunan da yake a gefen gadon shi, suna haɗa ido da ita, Sai ga Danish Ya faɗo ɗakin, da sauri Gabriel Ya koma ya zauna fuskarshi babu walwala, bai ta6a ganin ɗan takura irin Danish ba. A bayan angel ya tsaya tare da yi mata magana"muje ki kwanta" ba tare da ta kalle shi ba tace"bacci a yanzu? A'a gaskiya, Ni sai dare yayi zan kwanta, Zanje wurin su hanna mu yi fira ne, " yace mata"Okey, my eyes on u," yana faɗin hakan ya nufi akwatin kayan su, ya buɗe ya ajiye rigarshi, ya ɗauko red vest ɗinsa ya zura ta a jikin shi. Su hanna na ganin Angel, suka soma sakar mata murmushi suna faɗin Ga Masoyiya angel nan, Ku bata wuri ta zauna, mayar musu da martanin murmushin ta yi, taji daɗin sunan da suka kira ta dashi Masoyiya Angel. A tsakankanin Jamima da azeeza ta zauna, tana fuskantar Hanna da parveen, kowannansu yai zaman cin tuwo kamar ɗaliban makaranta allo. "Ku fada min akan me ku ke tattaunawa ne"? Tai tambayar tana kallon fuskar kowannan su, Sarah ce ta fara magana"Labari su ke bamu akan abubuwan da ki ke koya musu, Lokacin da bamu nan" Parveen tace"Namanta ban faɗa maki ba, lokacin da ki na yin bacci kamar jiya ne, Gabriel ya tambaye mu, wai mu bashi labarin ki sannan mu faɗa mashi abubuwan da kika koya mana, kuma duk mun faɗa mashi" a tsanake ta ke sauraron su, yayin da idanuwanta ke a kan la66an masu yin maganar. "Yau har training ɗin rawa ya bamu, duk mun gaji, shiyasa muka zauna muna ɗan zantawa" acewar Hannah. "Pls Angel, ki koya mana abunda ki ka koya musu muna so" Jamimah ce tai maganar, Hibba tace"damuwa tasa kin daina koya mana karatu," numfasawa tayi kafin ta soma magana "In sha Allah zamu cigaba da yin karatu, nima ban ji dadi ba, dana daina koya ma ku, yanzu dai kowa ya faɗi abunda yake so mu dinga yi, don mu sanya junan mu farin ciki" Duk wani a bu da suke tattaunawa akan kunnan Danish, da ke a zaune saman gadon shi, nan ya zauna bayan ya sanya vest dinsa, idon shi akan la66an Angel da ke cikin yin magana tana kora masu parveen jawabi akan abubuwan da zasu dinga kullum. Ko ƙyaftawa baiyi, Gabriel kam Idon shi na akan Danish, lamarin ya ɗaure mashi kai, ganin irin kallon ƙurullan da ya ke yi ma Angel, kamar zai lashe ta, Firgit! ya yi jin saukar hannun mutun saman kafaɗar shi, da sauri yakai idonshi kan wanda ya ta6a shi, Haris ne ya zauna gefen shi. "Da alama ka manta da ɗan uwan ka, na lura kwanakin nan hankalin ka gaba ɗaya yana akan Angel tun da ku ka shirya da ita, wai menene a tsakanin ku ne? Tell me ɗazu ma mu na kallon ku ni da Deeja, Angel ta shiga toilet ka bi bayanta, tsawon lokaci ba ku fito ba, sai daga bisani mu ka ga ta fito, kai ma ka biyo bayanta kamar ma wanka ka yi" tun da haris ya soma magana Danish Ya baza kunnuwanshi yana sauraron shi, sai dai har yanzu bai janye idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba saboda tsabar jaraba. Da mamaki akan fuskar Haris yace"kai magana fa nake maka? Ko kallo ban ishe ka ba kenan," motsi yae da la66ansa wurin furta mashi"Am all ears," haris yace"ae nasan kana ji, saboda ka maidani shashasha ina magana idon ka na akan Angel, wai me ka ke kallon akan fuskarta ne"? Yai tambayar yana leƙen fuskarshi, da buɗar bakin Danish sai cewa yai"kyau nake kallo, ko ba ka gani ba" sakin baki haris yai,"Dama kyau yana kallon kyau"? ɗaga mashi kai ya yi alamar Eh. "Bari na tashi na baka wuri, ka gama kallon kyan, don na lura gaba ɗaya bata ni ka ke ba," kafin haris ya miƙe Danish yai saurin ruƙe hannun shi yace"Hankalina akan yake, idanuwana ne kawai basu atare da kai, amma ina sauraronka" Guntun toki haris yaja"dalla ni sakar min hannu na, ɗan rainin wayau," Ƙin sakin hannun nashi yai, ya damƙe shi acikin nashi, su naufal dake zaune saman beds ɗinsu, gaba ɗaya hankalinsu na akan Danish da haris, Mubeen yace"ku tashi muje wurin su mu ma muyi fira, tun da suma matan sun haɗa kansu" Kamar dama jira su ke yi yai maganar, kowannan su ya sauko daga saman nashi gadon su ka nufi Danish, gefe da gefen mattress ɗin suka zazzauna. Javed yace"me kuke tattaunawa ne? Shi ne baza a kira mu ayi zantawar damu ba," Haris yace"kun ga alamun muna tattaunawa ne? tun da nazo na zauna gefen shi, bai juyo ya kalle ni ba, idanuwanshi na akan Angel, na rasa gane me yake kallo akan face ɗinta, ya dai ce min kyau yake kallo" dariya su ka saki gaba ɗayan su, naufal yace"abun mamaki, kyau na kallon kyau," Ba tare da Danish ya kawar da idanuwanshi daga kan fuskar Angel ba ya bashi amsa da cewa"ba abun mamaki ba ne, ni nasan me nake kallo" mubeen yace"ban yarda ba, sai dai wani abun na daban, idan kyau ka ke son kallo, ka ɗauki mirror ka kalli fuskarka mana," shiru bai tanka mashi ba, don ba ƙaramin takura shi su ka yi ba, Gabriel da ke zaune gefen gadon shi, a takure, yaso ace angel tana fuskantar inda yake ne don ya ji daɗin faɗa mata inda ya ajiye mata wasiƙar, sai dai ta juya mashi baya. "Tun da baka son mu zauna a kusa da kai, ku tashi mu je wurin ƴan uwan mu mata, su yi firar tare da mu," haris na faɗin hakan kowannan su ya miƙe su ka nufi Dining carpet ɗin su, inda su Angel su ke zazzaune kowannan su Ya samu wuri ya zauna, cikin sa'a Naufal ya zuƙunna bayan Hannah da ke fuskantar Angel, da ya ke dogo ne shima tubar kalla, gaba ɗaya ya kare ma Danish Fuskar Angel, baya iya ganinta da kyau, takaicin duniya ya ishe shi, sai ya mayar da kallon shi ga Gabriel, su ka haɗa ido da juna, Jira ya ke yaga in gabriel zai miƙe da niyar yaje wurin su, kamar Gabriel yasan me ya ke ayyanawa acikin zuciyar shi, da gangan ya miƙe zai nufi wurinsu, a hanzarce Danish ya miƙe, komawa Gabriel yai ya zauna gefen gadon shi, sai gashi shima Danish ɗin ya koma nashi gadon ya zauna, Ikon Allah. Su biyu ne basu je wurin ƴan uwan nasu da ke yin fira ba, hatta Majnun yana a tsakankanin Deeja da Rubina, Ya natsu kamar mutumin arziƙi, duk wanda yai magana acikinsu haka zai ƙurawa la66ansa ido har sai ya gama magana, wani lokacin sai ya tintsire da dariya, ko ba abun dariya aka faɗi ba. "Tun da yanzu mun ƙara yawa, A faɗa mana waya fi kyau a cikin mu"? Acewar Yasmin, hibbe tace"wa zai faɗi? Sai dai ko Angel,' girgiza kai angel tai " a'a, a samu wanda yafi kowa hankali a cikin mu ya faɗa mana wanda yafi kyau,' ta yi maganar tana nuna musu majnun da idonta, dariya su ka saki gaba ɗayan su, Deeja tace da shi"Chinonso faɗa mana waya fi kowa kyau a cikin mu, yau zamu tabbatar da idan kana da cikakken hankali" murmushi suka ga ya saki yana murmura idanuwanshi, hada ƙoƙarin miƙewa tsaye yana kallon fuskokin su, tsawon lokaci sun kasa kunne suna sauraron shi, yadda kasan me nazarin wani abu, har wani leƙa fuskarsu yake yi, a ƙarshe yace"Haris" shiru su ka yi, haris ko sai tiƙar dariya yake yi, itama Deeja murmushi ta saki, Jamima tace"Ƙarya kake yi, ba haris bane yafi kyau, ba ka ga shi baƙi bane," Harara chinonso ya watsa mata, tare da ruƙe qugunshi, ya turo ciki gaba yana faɗin"ke ne kike ƙarya, harisu ba baƙi bane, Fari ne fat," waro ido su kai gaba ɗayan su suna kallon shi, Angel tace"Anya kuwa Majnun Ƙwaƙwalwarka tana aiki dai dai? Haris ɗin ne yafi kowa kyau kuma fari ne" jinjina mata kai yai fuskarshi a ɗaure yace"Eh mana, yafi kowa haske aciki ku, shi ne yafi kowa kyau" Mubeen na murmishi yace"anya haris ba wani abu ka yi mishi ba? Ko dai ka yi mishi ƙyafcen ido ne"? Haris na dariya ya ce"Ka tambaye shi mana sai ka ji idan ni ne nasa shi ya faɗi hakan" Miƙewa mubeen yai tare da komawa gefen chinonso da ke a tsaye, ya duƙo yadda tsawon su zai dai dai ta"faɗa min wata irin barazana haris yai maka"? Ta6e baki majnun yai, ni bai min komai ba, gaskiya na faɗi yafi kowa kyau acikin ku, shine fari" fuskarshi a ɗaure yai maganar babu alamun wasa don shi har ga Allah gaskiyar shi ya ke gaya musu. "Yau naga ikon Allah, wai dole sai ya ƙaryata abunda ya faɗi? Nifa na sani dama, haris yafi kowa kyau a cikin ku"! acewar Deeja, haris ya kar6e da cewa faɗa mu su dai, Ni ɗin kyakkyawa ne, da alama kishi su ke yi dani, ' ruƙo hannun Majnun mubeen yai tare da jan shi zuwa gaban Danish da ke zaune gefen gadonsa, Yace"yanzu faɗa min tsakanin haris da Danish wanene fari"? Jin muryarsu yasa Danish kawar da idon shi daga kan fuskar Angel, ya dawo da dubanshi akan fuskar chinonso daya ƙura mishi ido, har wani kashe ido ɗaya yake yi. "Idan har ya kasa banbance waye fari acikin su, to kuwa dole mu zubda chinonsu Cikin Kwandon shara, don banga amfanin shi acikin mu ba, abincin da yake ci ma ya tashi abanza," parveen ce tai maganar, kowannan su ya saki murmushi, Angel tace"da alama ƙarya ta ƙare, Ya tasa Danish gaba sai kallon shi ya ke yi, yaƙi magana" "Kai muke jira" acewar mubeen, girgiza kai chinonsu yai fuskarshi a hargitsa ya kalli mubeen'"to..ae na kasa ganewa, shima haris ɗin ya dawo gefen shi ya zauna, sai in banbance" Miƙewa haris yai tare da komawa gefen Danish ya zauna, Suka tasa chinonso gaba Akan saiya gano musu wanene fari acikin su, shifa bilhaƙƙi Haris fari ne, Ya dai ce musu Danish yafi kyau, matsalar shi ɗaya Baƙi ne wulik, Shiyasa Haris yafi shi kyau, wannan maganar ba ƙaramar dariya ta basu ba, Ga dukkan alamu bayan ta6in hankali da yake dashi Chinonso yana fama da matsalar Gani, yau sun tabbatar da hakan, tun da gashi ya tabbatar musu da cewa Danish yafi kyau, sai dai baƙi ne, har tambayarshi su ka yi shi fa wani kala ne, yace musu shima baƙi ne Mutumin da ya ke albino, hasken ma ya wuce na lafiya, Amma yana kiran kan shi da baƙi, kusan mutun uku fararen Cikin su, su ka tambaye shi ya faɗa musu wani kala ne su, yace musu duk baƙaƙe ne. Ba ƙaramin nishaɗi su ka yi ba a ranar, Lokacin da dare yai, Kowannansu Ya canza kayan shi zuwa tsoffinsu, Wanda suka maida na bacci, Kafin suka haura saman gadajensu suka kakkwanta. Gabriel ya kasa runtsawa Yana zaune tsakiyar gadon shi, Sarai Angel ta lura dashi, hakan yasa itama taƙi kwantawa tayi baccin, Haka zalika, Danishi yaƙi runtse idanuwanshi, Ga bacci yana ji amma yaƙi bari ya ɗauke shi, Saukowa tai daga saman gadonta, zumbur Danish Ya mike zauna, tare da kallon ta yace "Angel where're u going, ba zaki bacci ba" yatsina fuska ta ɗanyi tare da kallon shi" Addu'a nake so inyi maku kafin in kwanta...." tunkan ta ƙarasa maganar taga ya sauko daga saman gadon shi, Ya ruƙo hannunta acikin nashi tare da cewa"Nima zan ta ya ki, mu yi musu addu'ar a tare" dariyar yaƙe ta sakar mashi"kai da baka iya ba, taya zaka iya taya ni mu yi musu addu'ar? "Ni dai muje," duk yadda taso ta yi mashi wayau don ya koma ya kwanta ita kuma ta samu damar zantawa da Gabriel Ya hana hakan faruwa, Atare su ka bi gadajen su Hannu tana karanta musu addu'o'i tana tottofa musu saman bargunan su, hatta sarah da ke a kwance ƙasa sai da ta zuƙunna ta yi mata addu'a, kafin ta miƙe bayan ta kammala, ta tsaya a Tsaye tana satar kallon Gabriel da ya hana idon shi bacci tasan duk don saboda ita ne, Ganin tana kallon shi yasa Danish damƙar hannunta yaja ta har zuwa saman gadonta, fuskarshi a ɗaure yace"ki kwanta ki yi bacci," ba tare da ta yi mishi musu ba, ta hau saman mattress ɗin ta kwanta, tare da ɗaura kanta saman pillow, ' ta yi tsammanin zai haura nashi gadon ya kwanta amma sai taga ya zauna gefen gadonta, Ya tsareta da waɗannan kyawawan idanuwanshi nashi "Why danish? What's going on? Why don't you go to bed? You're bothering me." A hasale tai maganar tana jifar shi da harara, cikin sanyin murya yace"idan kina so in yi bacci to ki fara yi, if not sai dai mu kwana idon mu biyu," muryarta a takure tace"hakan ma bazata faru ba," runtse idanuwanta ta yi, zuciyarta nata saƙa mata yarda zata yi mashi wayau, yayin da shi kuma Man ɗin Ya jingina bayanshi da bango idonshi akan Gabriel, Dake zaune tsakiyar bed nasa. A hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, ta saci kallon fuskar Danish, miƙewa tayi zaune, Jin motsinta yasa shi kallon ta Yamutsa fuska ta ɗanyi tare da cewa"Zan shiga toilet ne," ruƙo hannunta yai acikin nashi"muje in raka ki" fusge hannunta tai fuskarta a ɗaure tace"Banaso, Ka zauna anan inje in dawo," bai damu ba, tun da yasan ita kaɗai zata shiga, zai zauna ne ya tsare Gabriel kada ya motsa, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi sashen toilet ɗinsu, tana jiyo muryar Shi yana bata umarnin kada ta daɗe acikin toilet ɗin, idan ba haka ba zai biyo bayanta. ta amsa mashi da toh, tana shiga ƙopar sashen toilet ɗin, ta juyo tana leƙen Gabriel, Dama abunda ya kai ta kenan, tun kafin ta shiga ran shi ya bashi cewar ba wani abu zatai acikin toilet ɗin ba, za ta je ne don ta samu damar yin magana dashi, Satar kallon Danish yai, ganin ya ɗan lumshe idanuwanshi yasa shi yin saurin kallon ƙopar shiga sashen toilet ɗin, cikin sa'a ya hango angel tana ɗaga mashi hannu, A hankali ya janyo pillow ɗinsa da ya jingina bayanshi da shi, Ya rungume shi a ƙirjinshi, Ya sanya hannu yana ta6a zip ɗin jikin shi, ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta fahimci abinda ya ke son nuna mata, buɗe ido Danish yai tare da saukowa daga saman gadon shi, Ya nufi sashen toilet ɗin, da sauri Gabriel yai mata alamar gashi nan zuwa, kamar walkiya ta buɗe toilet ta shige, Yana shigowa wurin, ya soma kiran sunanta"Angel! Angel!" buɗe ƙopar tai tare da fitowa tana yarfa hannunta data wanko shi da ruwa, Kallon shi tai aranta tace"Jarababbe kawai" a fili kuma tace"lafiya"? "Na jira ne baki fito ba, shine nazo in duba ki" harara ta wurga mashi, kafin taja hannun shi, suka koma ɗakin, tace mashi"ka hau gadon ka, ka kwanta nima in kwanta a nawa, in yaso sai mu fuskanci juna" Ya amsa mata da toh, bayan kowannan su ya haura saman gadonshi, suka ci gaba da kallon juna, tun yana ganinta biji biji, har ya kai ga rufe eyes ɗinshi, tsawon mintuna ta fahimci cewa bacci ne yai awon gaba dashi. Ajiyar zuciya ta sauke, a hankali ta miƙe ta ɗauki pillow ɗinta, ta zuge zip ɗin ta curo ƴar takardar da Gabriel ya ajiye mata, ta buɗe ta cike da fargabar kada Ya farka, Saukowa tai daga saman gadonta ta nufi tsakiyar ɗakin nasu tana karanta wasiƙar, yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi, wani irin ruɗani ne ya bayyana akan fuskarta, Takasa yarda da abunda Gabriel ya rubuta mata, Shin dagaske ne ya haura tagar nan ya shiga cikin prison ba tare da wani abu ya same shi ba? To ya akai ita ta kasa shiga? Can kuma ta koma tunanin yarinyar da ya ce mata ya gani tana neman taimakon shi, Anya kuwa Gabriel ba ƙarya ya ke faɗa mata ba? Sai dai kuma abunda zai sa ta iya yarda da maganar da ya rubuta mata, na farko bai yi kama da maƙaryaci ba, sa'annan idan har dagaske ƙarya yake yi mata to taya akai yasan da Tagar da aka cire glass ɗinta, nannaɗe takardar tayi tare da ɗagowa ta kalli shimfiɗar Gabriel, Har yanzu bai kwanta ba idanuwanshi na akanta, sai da ta fara juyawa ta kalli Danish da ke bacci, taga bai motsa ba, kafin ta maida dubanta ga Gabriel, Saukowa yai daga saman gadon shi ya tunkareta, hannunta ya ruƙo acikin nashi, Yaja ta suka shiga sashen toilet ɗin su, saboda su samu damar tattaunawa da juna ba tare da Danish Ya farka ba. Ba acikin toilet su ka shiga ba, acikin sashen suka tsaya, muryarta da alamun mamaki tace"Abun da na karanta acikin wasiƙar nan taka dagaske ne? Jinjina mata kai yai"tabbas dagaske ne angel, naso tun time dana haura tagar na dawo ciki in sanar da ke amma Danish ya hanani yin hakan, Nasan ke kaɗai ce zaki iya taimaka min wurin nemo ƴar uwata tun da kema kina nema taki ƴar uwar, kuma naji awurin ƴan uwanki cewa, kina da burin fita daga Cikin kurkukun nan, shiyasa na ƙara samin ƙwarin gwiwar tunkarar ki in faɗa maki,' Tun da ya soma magana Angel ta ke binshi da kallo mai tattare da tsantsar mamaki da al'ajabi, Shi dai gashi ba musulmi ba, amma wani iko na Allah, ya samu damar shiga prison ba tare daya fuskanci irin matsalar daga fuskanta ba, a lokacin da ta dira tagar, ta wani 6angaren kuma ba ƙaramin daɗi taji ba, atlease ta samu wani mai ra'ayin son guduwa daga prison, idan su ka haɗa hannu dashi zasu iya sama ma kansu mafita. "Angel kin yi shiru bai kamata muna 6ata lokaci ba, wannan ce damar da mu ke da ita, ta taimakon yarinyar nan, ita ka ɗai sai garari take yi acikin prison" fuskarshi da alamun damuwa yai mata maganar. "Gabriel, ina kokwanto fa, zai yi wuya ace mutunce ita, may be barazana aka yi maka da ita don a tsorata ka, Nima time dana fita an tsoratar dani ta hanyar nuna min daddyna wasu haluttu munana suna cin naman jikin shi, aranar nasha wahala, ba don Allah yasa Danish yaje ya ɗauko ni ba, da shikenan tawa ta ƙare" girgiza mata kai Gabriel yai"Bana tunanin cewa anyi min barazana da itane, mutunce ita Angel I saw her from the top of the third floor. She was running, looking for help. fara ce kamar ke, tana da yawan sumar kai kalar naki, itama nata, Nannaɗaɗɗe ne harma yaso yafi naki yawa da nannaɗewa.......' Tun da ya suffanta mata matashiyar yarinyar, Hankalinta yai matuƙar tashi, Ta zazzaro idanuwanta waje, La66anta na kerma ta furta sunan"BATOOL" domin kuwa a bayanin da ya yi mata kaf irin suffar batul ne, "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Wlh inaji araina ƴar uwatace batul," tuni hawaye sun wanke mata fuskarta, jikinta ya kama kerma. "Gabriel why, ba ka taimake ta ba! Ae da ka sani ka taho da ita, Batul ce fa ƴar uwar mu" Shima aruɗe yace mata"Angel ni bansan cewa ƴar uwar ku bace, tun da bansan ta ba, naso na taimake ta, sai dai tsoro ya hana in ƙarasa wurinta, cos stairs ɗin dake kewaye da ground floor ɗin naga suna motsi kamar masu rai, that's the reason why na rikice, cos abunda ban saba gani ba ne....." shessheƙar kukanta ne ya katse mashi maganar tashi, ya zuba mata ido yana kallonta, sassauta muryarsa ya ɗanyi"Ki daina kuka, Danish zai iya jin sautin kukan ki ya farka, Yakamata mu tattauna akan abunda ya dace mu yi," cikin matsananciyar damuwa tace"ae wlh Saina je na ɗauko ta, koda zan rasa raina ne, komai zai faru sai dai ya faru, amma bazan runtsa acikin daren nan ba, dole naje!!!' tana ƙarasa maganar ta nufi toilet ɗin da tagar take da sauri Gabriel yabi bayanta yana fadin"ki tsaya Angel, kada mu yi gaggawa, yanzu dare ne, why ba zamu bari sai gobe ba"? Ba tare da ta juyo ta kalle shi ba tace"In bari sai gobe, salon sai wani abu ya cutar da ita, Ina ji araina Allah ne ya taimaki batul ta gudu daga wurin su, shiyasa ta ke neman hanyar da zata dawo cikin mu, wannan munafukin ginin bazai bari ta iya gane komai ba, wahala zata sha ƙarshe ma ta rasa ranta,' Ba ƙaramin daɗi Gabriel yaji aranshi ba, dama abunda yake so kenan, Su je atare da ita su nemo ƴan uwansu, dama koda yace mata kada su yi gaggawar yin hakan ya faɗi ne kawai ba don yana nufin hakan ba. "Amma angel kina ganin zamu iya shiga lafiya lou? Na fahimci cewa ginin yana da rikitarwa, ga ban tsoro. "zan roƙi Allah ya kare ni daga sharrinsu, in sha Allah zamu je mu dawo lafiya ba tare da wani abu ya same mu ba" da ƙwarin gwiwa ta bashi amsa da alama ta manta abunda ya faru da ita, saboda amakance take burinta kawai taje ta nemo batul,. "Amma Baki tunanin Danish zai iya hana mu? Suna tafiya suna magana har ta isa bakin tagar, ta bashi amsa da cewa"Shi da yake bacci, koda ace ya farka, bai isa ya hanamu ba, Akan batul ba abunda bazan Iya yi ba" tana magana tana jan majina. Ganin tsayinta bai kai wa yasa Gabriel matsawa bakin tagar, tun da yana da tsayi, Ya soma ƙoƙarin cire glass ɗin. "Idan muka ga sister ɗinki, Nima zaki taimaka min in gano ƴar uwarta Gabriella, " ta amsa mashi da eh," ajiyar zuciya ya sauke, yayin da yake cigaba da ƙoƙarin cire glass ɗin, Lokaci ɗaya taji gabanta ya yi wani irin mugun bugu, nan take ranta ya bata cewar, Danish Ya iso inda suke, Kafin tayi yunƙuri Juyawa, Muryarshi ta ratsa kunnuwansu "Bazan ta6a bari ku haura tagar nan ba! " da sauri Gabriel ya zame hannun shi daga saman glass ɗin, kusan atare suka juya baya suna kallon shi, Ya ɗaure fuskarshi sosai, tare da goya hannayen shi saman ƙirjin shi, mamaki ne akan fuskar Gabriel, Taya akai ya farka har yazo inda suke yaji abunda suke Shirin yi? Anya kuwa wannan cikakken mutun ne? Muryar angel tamkar zata fashe da kuka tace"wlh Danish bazan saurare ka ba, dole nabi shi mu haura tagar nan, da kanshi ya faɗamin cewa ya bi ta cikinta jiya, har ya ga wata yarinya tana gudu a hawa na uku, tana neman taimakon shi, kuma a yadda ya suffanta min ita, sak batul ce" matsawa tai kusa dashi, ta sassauta muryarta"pls Danish, ka bamu haɗin kai, muje mu ɗauko batool, kana da damar da zaka iya taimaka mana dan Allah, Ni idan ma kayi min alƙawarin zaka je ka dauko min ita, sai in koma ɗaki in jira ka....." cikin shessheƙar kuka ta ƙasa maganar, hawaye ta ko'ina saman fuskarta. Idon Danish akan fuskar Gabriel, wani irin haushinsa yake ji, saboda shine silar komai, cikin kakkausar murya yace"Ba gaskiya ya fada maki ba, yarinyar daya gani ba batul bace, cos babu yarda za'ae batul ta iya fitowa daga inda aka killace ta, shin ko kin manta ranar da kika dira window din abunda ya faru dake? Let me remind u, Kin ga daddynki, alhalin bashi bane, idanuwanki ne suke nuna maki hakan, that mean shima Gabriel abunda idon shi su ka gane mashi ba gaskiya bane........" tunkan Danish ya rufe bakinsa gabriel yace"Dama na lura da kai tuntuni kaƙi bani dama in yi magana da Angel, saboda kai ɗin munafuki ne, baka son gaskiya, shiyasa zaka ƙaryata abunda idanuwana suka nuna min, Angel karki ce zaki yarda da kalamansa, kada hakan yasa kice kin fasa bina mu shiga cikin kurkukun, Ki tuna halin da ƴar uwarki take aciki, zata iya rasa ranta..... Gaba daya sun rikita mata tunaninta, kowa yana ƙoƙarin jan ra'ayinta, ta rasa wa zata bi acikin su, domin kuwa sun raba hankalinta gida biyu, zuciyarta na raya mata cewar tabi Danish su koma ɗaki, saboda akwai ƙamshin gaskiya a maganarshi, zai iya yiwuwa ba batul bace Gabriel ya gani, anyi amfani da matashiyar ne don a tsoratar da shi, kamar yarda itama a ka yi mata amfani da daddynta, yayin da awani sashen na zuciyarta yana raya mata cewar, tabbas Gabriel baiyi mata ƙarya ma, Ƴar uwarsu ce ya gani, kada Tabi Danish azo asamu matsala idan ya kasance dagaske Ita dince, tana fargabar halin da zata shiga, ita kaɗai acikin prison, zaifa iya yiwuwa Danish Yasan gaskiya Gabriel yake faɗi, Tun da baison dama tana dira tagar shiyasa zai kafe akan cewa ƙarya ya ke yi mata. Ta yi zurfi acikin tunaninta, taji an damƙi hannunta, da sauri ta kalli hannun wanda ya ruƙeta, Danish ne ke ƙoƙarin fusgarta don su koma ɗaki, rai a matuƙar 6ace, Gabriel Ya damƙi ɗayan hannun nata yana huci, Zuciyar kowannansu takai wuya, A shirye suke da su farmaki junansu. "Ka sakar mata hannu tunkafin ranka ya 6aci!" Danish ne yai maganar fuskarshi a murtuke, tsoki Gabriel yaja "bazan saki ba, saboda ba hannunka na ruƙe ba," "Bana so ka yi danasani, tun wuri ka ajiye makaman yaƙin ka, kazo mu koma ɗaki, mu sasanta kanmu, amma idan ka nace akan sai ka ƙwaci hannun Angel ta ƙarfi don kuje ku dirar tagar can, Zanyi maka abun da ba ka ta6a tunani ba" Gabriel na huci yace"kai duk abunda kaga dama, bazan ta6a sakin hannunta ba, saboda ba mallakin ka bane, ni ban ta6a ganin mutun mai ƙarfin hali irin naka ba, Yarinyar nan fa ba dangin ka ba ce, Zaman Prison ne ya haɗa ka da ita, we're all prisoners babu wata alaƙa ta jini, don haka yadda ka ke taƙama da ita, nima haka nake taƙama da ita........" zaro eye balls ɗinsa yai jin abunda Gabriel ke faɗa masa, maganar ta ƙona masa rai, wato har yana da bakin da zai ce Hannun Angel ba mallakinsa bane? To na wanene idan ba nashi ba? sannan yace bai da alaƙar komai da ita, me hakan ke nufi,? Shima yana da iko akanta kamar yadda yake dashi? Ta ya hakan zai yiwu! Girgiza kai ya somayi yana huci ya furta"Kada ka kuskura ka maimaita kalaman da ka yi min Ayanzu, Domin kuwa Angel tawace ni kaɗai, ba wani mahaluƙin da ya isa ya shiga tsakanina da ita...." yana ƙarasa maganar Ya fusgi hannun Angel, ta fashe musu da kuka saboda raɗadin da taji, An rasa wanda zai haƙura yabarma wani, shima Gabriel yaƙi sakin hannunta, suka dinga janta kamar wata ɗiyar roba, Har cikin zuciyarshi yake jin kukan nata sai dai ba yadda zaiyi ya lallasheta, don bai jin zai iya haƙura yabar wa Gabriel ita donsu haura taga, duk a bunda ya ke yi yana yi don ita ne baison abunda zai cutar da ita, A ƙarshe da ta gaji ta fasa ƙara mai tsiwar gaske, Ta zame hannayenta daga cikin na kowannansu, tana kuka tace"ya isa haka! Ya isa, Ni ku ƙyale ni inji da abunda ke damuna, so ku ke ku kashe ni ne! " cikin sanyin murya Danish yace"Am sorry angel, laifinsa ne, kizo mu koma ɗaki," harara ta wurga mashi da idanuwanta wadanda suka rune zuwa ja, "Ni banzan bika ba danish, dole inje in ɗauko batul ɗinmu, idan har kai bazaka iya zuwa ka ɗauko min ita ba, to ka ƙyale ni inbi Gabriel mu je" Muryarshi araunace yace"Angel ki fahince ni, ba gaskiya bane abunda ya gaya maki, bana so ne ku yi danasani," Harara Gabriel ya watsa mashi tare da cewa"idan har dagaske ƙarya na ke yi akan abunda na faɗa mata, to ka bari muje tare da ita mu duba, idan har bamu ganta ba, shi ne ka ke da damar da za ka iya ƙaryata ni," rai a6ace Danish ya nuna shi da yatsa "Ka yi min shiru! Bana so na ƙara jin maganarka, wawa kawai, kaine silar komai, kuma bazan ƙyale ka ba," Gabriel ya daki ƙirjinshi da hannu tare da cewa nima bana so ka ƙyale ni, Ɗan rainin wayau, dama daga ganin fuskarka ba mutumin kirki bane, wama yasani ko ɗan leƙen asiri ne kai acikin mu......." Ɗaya daga Cikin abunda Danish ya tsani Ya ji an faɗa mashi kenan, aiko ranshi yayi mugun 6aci har baisan time daya damƙi wuyan Gabriel da hannu biyu ba, ya tura shi zuwa jikin bango ya matse shi, Da gudu Angel ta nufe su da niyar ta dakatar dashi, sai dai kafin ta isa, tai tuntu6e ta kife ƙasa, Kafin ta yi wani yunƙurin ɗagowa faɗa ya kaure a tsakanin Danish da Gabriel, Yadda kasan dawakai suna kokawa, dunƙule hannu Gabriel yai ya dinga naushin cikin Danish, Don ya sakar mashi wuyanshi daya shaƙe mashi amma yaƙi saki, duk da irin jahilin naushin da yake kaima Cikin shi, ko girgiza baiyi ba tamkar baisan ma ya na yi mata, ganin dagaske so yake ya kashe shi yasa Gabriel daddagewa Ya sauke mashi naushi saman idon shi na hagu, nan take Danish ya saki wuyan Gabriel Gaba ɗaya ya faɗi ƙasa hannun shi dafe da idonshi, kamar zaiyi hauka, shi kanshi Gabriel da ya yi silar jefa shi cikin halin da yake ciki sai da gabanshi ya faɗi, ganin Jini yana gangarowa ta cikin idon nashi daya nausa, wata irin gigitacciyar ƙara Angel ta saki, A matuƙar razane ta miƙe daga kwancen da take akasa ta watsa da gudu ta zube sama gwiwowinta agaban Danish, Hannu biyi ta sanya wurin ɗago dashi ta ƙanƙame shi ajikinta, Sai kuka take yi tamkar ranta zai fita, Gaba ɗaya tabi ta gigice, ta ruɗe ganin yadda idon shi ke fitar da jini jawur dashi, "INNALALLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN! Gabriel ka kashe mishi idonshi, Ka kashe min Danish ɗina! wayyo Allah na! nashiga uku na bani na lalace!!" Hankalin Gabriel idan yai dubu to ya tashi, Kamar ya ɗaura hannu akai ya fasa ihu haka yake ji, la66ansa sai kerma suke yi, ya haɗa uban gumi, Muryarshi aruɗe yake faɗin"Angel bada son raina na aikata mishi hakan ba, shine ya shaƙe min wuyana! sosai ta ƙanƙame Danish ajikinta, Jikinshi yai wani irin mahaukacin zafi na fitar hayyacin, ko ina kerma yake yi, ga wani irin nishi da ya ke fitarwa. hannunta data ɗaura saman nashi hannun daya rufe idon da ke bleeding dashi, tuni ya jima da jiƙewa sharkaf da jininsa, wa'iya zubillahi, Lamarin tamkar a mafarki yake faruwa, sun yi fatan ace mafarki ne su ke yi ba agaske ya faru ba, ta yi Danasanin Biye ma Gabriel da tai da duk hakan bata faru ba, da tasan Danish zai rasa idonshi silar yunƙurinsu na haura taga da bata yi gigin yin hakan ba, Yanzu gashi dare ɗaya sun ja mashi bala'e, Gabriel ya naƙasa shi, akan abunda bai taka kara ya karya shi ba, duk wannan koke koken da suke yi na cikin ɗaki basu farka daga baccin da suke yi ba, kamar waɗanda suka sha sleeping pills, tana kuka tana faɗin Gabriel ya zamuyi Dashi kada ya mutu, jinin shi sai zuba ya ke yi, Ya Allah kasa mafarki ne nake yi, bazan iya jure ganin danish cikin mawuyacin halin nan ba! Bazan ta6a yafe ma kaina ba, da kai kanka Gabriel kaine silar komai, Ga shi zan rasa ɗan uwana.... Da gudu Gabriel Ya nufi igiyar shanyarsu ganin mayafin azeeza da ta manta Tun ranar da akazo aka tafi ƴar gidan daddy, Angel ta shanya shi don ya bushe bayan ta kammala sanyaya mata jikin ta dashi, aranar suka barshi saman igiyar, ɗaukowa Gabriel yai jiki na 6ari garin sauri hada tuntu6e ya ƙarasa inda Angel take a zuƙunne ta ƙanƙame shi ajikinta, daƙyar Gabriel ya iya 6an6aro kanshi daga saman ƙirjin Angel, ya dawo dashi saman jikin shi, ya sanya mashi mayafin ya tamke mashi idanuwanshi dashi, sai nishi ya ke yi yana yarfa dogayen yatsun hannayenshi, Bawan Allah shi kaɗai yasan irin raɗaɗin azabar da yake ji acikin idonshi, jijiyoyin hannanyenshi dana wuyanshi shatunsu yafito ruɗu ruɗu saman fatarshi, hatta saman goshinsa jijiyoyinne, gwanin ban tsoro, sosai Gabriel ya ɗaure mashi mayafin duk don jinin ya dakata da zuba, haƙiƙa na yi baƙin Cikin ganin kakkyawar fuskar Danish da jini ya wanke ta, har saman wuyan shi, Gabriel na gama daure mashi idon nashi, angel ta sanya hannu biyu ta dawo dashi jikinta, ta ƙanƙame shi tana cigaba da yin kuka mai cin rai, tana faɗin"ɗan uwana rabin raina dan Allah kada ka mutu kabarni Danish ɗina, na gane kuskure na, ban da wayau, ga shi naja maka ka rasa idanuwanka, duk laifina ne, namanta cewa duk abunda ka ke yi kana yi ne don ka kare ni daga faɗawa halaka amma saboda taurin kai irin nawa nagaza fahimtar hakan, mun cuce ka Danish mune silar komai!!........ Sosai ta fashe da kuka, Shima Gabriel ɗin kukan yake yi tamkar ranshi zai fita, tashin hankalin da ba'a sama shi date!! Mexai faru da danish? Ga ido yana ta bleeding zai mutune ko zai rayu a matsayin makaho mara ido ɗaya? Wani irin hukunci su haris zasu ɗauka idan suka gane cewa Gabriel ne silar da Danish ɗinsu Ya makance? Wani hali zasu tsinci kansu? Alƙamina Ya tsaya Cak! sai mun haɗu next page in Allah yakaimu da rai da lafiya, amma fa ga dukkan alamu Danish ɗinku saiya leƙa treatment room! Daga nan kuma.6arna zata auku, Don angel bazata juri zama babu shi ba, dama shine mai tsawatar mata akan karta haura taga, inaga idan babu shi........😳 hasashe na ne kawai🥱 💋PRISONERS💋 Saboda tsabar yadda jinin ke fita hatta Mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi idon nashi ya jiƙe sharkaf da jininsa, Lamarin ya yi matuƙar gigitasu, Sautin muryarta har ya fara disashe wa saboda tsabar kukan da tasha, Gabriel da ke a zuƙunne ƙasa gabanshi sai yarfa hannayen shi ya ke yi, Yarasa uwar ubanshi zuciyarshi sai bugawa ta ke da ƙarfi da ƙarfi duk ya firgice tsoranshi kada Danish ya rasa ranshi silar naushin da yai mashi. Jikinta ba ƙaramin zafi yai ba, har time ɗin hannayenta biyu na ƙanƙame da kanshi a ƙirjinta, Jikin shi ya saki sosai shi kaɗai yasan zogin azabar da ya ke ji a cikin idon shi. Sama sama numfashin sa ke fita, maƙoshin shi ya bushe, ta ko'ina babu sauƙi a jikin shi, addu'oi ta dinga karantowa tana tottofa mashi samar sumar kanshi, Cikin fitar hayyaci ya ke yamutsa vest ɗin jikinta da hannayenshi masu dogayen akaifu, duk ya faffasa mata fatar bayanta, amma ko kaɗan bata ji zafi ba, batasan ma yana yi ba, damuwarta gaba ɗaya akanshi ne, Da ace tana da halin da zata iya ɗauke mashi ciwon ta maida shi akanta da tuni ta yi hakan, Zaifi mata sauƙi akan taga Danish acikin mawuyacin hali. la66anta na rawa ta soma ambaton sunan shi tana faɗin dan Allah Danish kada ka mutu kabarni, kada ka daina motsi, ni ko idona ne ma zan iya badawa asanya ma ka, Ya Allah ka kawo mishi ɗauki, Wannan wata irin baƙar rana ce, Sosai take kuka, idanuwanta sun yi jaga jaga da hawaye ta rasa ya zata yi dashi ga jinin yaƙi daina bleeding, Gabriel da ya gama rikicewa Sai magiya ya ke yi ma Angel akan ta cire idon shi ɗaya ta sanya ma Danish tun da shi ne silar rasa idon nashi. Duk da halin da ya ke ciki hakan bai hana shi ƙoƙarin motsa red lips ɗinsa da su ka jiƙe sharkaf da jinin da ke ta gangarowa ta cikin ƙarƙashin mayafin da Gabriel ya ɗaure mashi ido da shi, magana ya ke so yai mata amma ya kasa, la66ansa sun ƙi bashi haɗin kai, Jikin shi gaba ɗaya ba sauƙi, Yanke shawarar fita tai don ta sanar ma sauran ƴan uwansu ƙwara kowa ya sani, don su nemi mafita atare, Tana kuka tana ƙoƙarin 6an6are shi daga jikinta sai dai yaƙi bari ta raba jikinta da nashi, idanuwanta cike tab da ƙwalla ta kalli Gabriel muryarta na kerma tace "Ka... ruƙe shi, Zan je na faɗa ma su haris," duk yadda gabriel yaso ya raba Angel da Danish abun ya faskara, mugun ruƙo yai mata bana wasa ba, Kallon Gabriel din tai"kaje ka yi musu magana kowa ya tashi su zo, " hawaye ta ko'ina a fuskarshi yace"Angel Pls kada ki faɗa musu cewa ni ne silar rasa idon shi......" tun kan ya ƙarasa maganar ta rufe ido tana zazzaga mashi masifa "Har kana da bakin da za ka ce kada na faɗa mu su? Dole su san cewa kaine silar komai, mugu kawai ai bansan haka ka ke ba da tun farko ban biye maka ba.....hada zagi ta haɗa mashi, Jiki duk ba ƙwari Gabriel ya miƙe har wani jiri yake gani acikin idanuwanshi ga ciwon mai raɗaɗi da ya addabe shi, a haka ya fuce daga Cikin toilet din, bai shiga ɗakin ba a bakin ƙopar ya tsaya yana matse kwalla. Fitar Gabriel ke da wuya, ta soma jin muryarshi ƙasa ƙasa yana yi mata magana, da sauri ta ɗaura kunnanta saman la66ansa don ta samu damar jin me ya ke son faɗa mata. Angel ki daina zubar da hawayen ki saboda ni, lafiyata qalou, ba abunda ya sami idona....." Cikin muryar ku ka tace "ƙarya ka ke yi min Danish nasan ka faɗamin hakan ne don ka kwantar min da hankali na...." ku ka yaƙi bari ta ƙarasa maganar, Sassauta ruƙon da yai mata ya yi tare da ɗagowa da kanshi fuskar ta 6aci sosai da jiki, kasa tsayar da kan nashi yai, Sai dai ya kwantar da shi saman wuyanta, jikinta yai mugun sanyi, saboda ƙarfin hali irin nashi a haka ya cigaba da yi mata magana cikin raunin murya ta wanda ya gama galabaita. _Angel, za'azo atafi dani, babu tabbacin zan dawo cikin ku, that doesn't mean that I'll die. Even if I'm not around, ki yi min alƙawarin ba za ki haura tagar nan ba_ cikin shessheƙar kuka tace"damuwar ka kenan Danish Ni yanzu bata wannan nake ba, lafiyarka nake so, kuma ni bazan juri rashin ka atare dani ba, wlh bazan iya zama babu batul sannan babu kai a tare dani ba....." kwantar da kanta tai gefen wuyanshi. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka sai shesseƙar ku ke ta ke yi, muryarshi ce ta ƙara katse mata kukan nata daƙyar yake iya furta maganar "Angel, ki tashi mu shiga ɗaki, ki ruƙe ni mu tafi, inaso inga ƴan uwana kafin atafi dani, nasan yanzu haka suna akan hanyar zuwa ɗauka na" Jin wannan maganar tashi yasa ta ɗaga murya ta ƙwala ma Gabriel kira, Jin sautin muryarta yasa shi yin saurin buɗe ƙopa ya faɗo toilet ɗin Muryarta asanyaye tace mashi "Ka taimaka mini mu shiga da shi ɗaki" jiki na 6ari ya ƙarasa ciki, atare da Angel su ka ruƙo Danish, daƙyar daƙyar suke jan shi saboda jikin nashi ba ƙwari, kamar lagwanin fitila, A haka suka janyo shi har zuwa bakin ƙopar fita daga cikin sashen toilet din nasu, duk inda suka taka sai jinin shi ya ɗiɗdiga Kamar jira ake su dira ƙafafuwansu saman floor ɗin ɗakinsu, Ba zato ba tsammani, Su ka soma Jiyo motsin buɗe ƙopa, A matuƙar gigice Gabriel da Angel suka kalli ƙofar, Wata irin zufa ce ta shiga wanke fuskokinsu, damuwa ce ƙarara akan fuskar Angel. Wani gabjejen Giant Ne ya shigo ɗakin Yana tafiya Tsokokin Jikin shi na motsawa, zazzafan gaske Star biyu ce a gaban rigar shi, a gaggauce yake taka staircases ɗin benan tsabar sauri kamar zai tashi sama, Da zafin shi Yake taka ƙafafuwan shi. batasan lokacin da ta fashe da wani sabon kukan ba, don tasan zuwa akai araba ta da Danish dinta, Sautin kukan Angel ne ya farkar dasu Haris, Hakalinsu a matuƙar tashe suka soma buɗe idanuwansu kusan atare Kowannansu ya yaye bargon da ya lullu6a da shi, sai dai kafin su yi yunƙurin saukowa daga saman gadonsu, Tuni wannan giant ɗin Ya jima da ƙarasowa ciki, tsabar tsoratar da Gabriel yai ne yasa shin Yin saurin sakin Danish yabar Angel da ruƙon shi, kamar amafarki su haris suke kallon Danish da Jini ya wanke ma fuska, ruɗu ya hana su gane wanene. Yayin da wasu daga cikin su ke kallon Giant ɗin da ke tafiya yana tunkarar su Angel, Lamarin yai matuƙar ɗaure musu kai, Sun gaza yarda da abunda idanuwansu ke nuna masu, Tana ji tana gani, Giant ɗin nan ya sanya hannu biyu Duk irin tsayin Danish Kamar jinjiri Haka giant ɗin ya ɗauke shi tare da ɗaura shi saman kafadar shi, Cikin Zafin nama Ya juya dashi, Ya nufi Benan, Da gudun gaske Angel tabi bayan shi, tana kuka tamkar ranta zai fita tana ambaton sunan Danish, Adai dai bakin stair ɗin tai tuntu6e wurin taka staircases ɗin Gaba ɗaya ta kife kanta Ya daki ƙasa, ko motsi bata yi ba. Ga dukkan alamu ta sume ne, sai bayan da Giant ɗin Ya fuce daga Cikin ɗakin, Ƙopar na rufewa ta bada wanj irin sauti Garam!! Shi ne silar dawowar su Cikin hayyacin su, Azeeza ta fashe da wani irin matsanancin kuka tun kafin ma taji meya faru, sautin rufe ƙopar ɗakin su ne yasa ta fahimci cewa Giants ne suka tafi da wani, shiyasa ta fashe da kuka, Jikin Haris har 6ari yake yi wurin saukowa daga saman gadon shi yana bin Fuskar Gabriel da kallo wanda Ya ƙame jikin bango tsabar tashin hankali ne akan fuskar shi, ɗaya bayan ɗaya kowannansu Ya sauko daga saman gadon shi, Tun kafin ma su soma tambayar Gabriel a ruɗe yake girgiza musu kai hawaye nabin fuskarsa, Muryar haris aruɗe ya furta"wanene aka fita dashi? Meya faru ne naga jini a jikin ka? Meyasa Angel ta ke kuka tana ambaton sunan Danish? Allah yasa mafarki nake yi ba gaske ba, zaifi min kwanciyar hankali na, akan ace wani abu ne ya faru da shi"! tsabar ruɗanin da Gabriel ya shiga ne yasa shi Yin su6ul da baka wurin furta"Bada son raina na aikata mishi hakan ba, bansani ba, Ku ƙyale ni ku rabu dani inji da abunda ke damuna! ' zuƙunnawa yai saman gwiwowinsa kamar ƙaramin yaro haka ya fashe da wani sabon kukan. "Hakan na nufin wani abu ya samu Danish! Kada ka ce min Jinin shi ne wannan a jikin ka," haris ne yai maganar tare da sanya hannu biyu ya damƙi gaban rigar Gabriel ya ɗaɗɗago dashi Ya buga shi jikin bango, Idanuwanshi tuni sun rikiɗa sunyi jawur dasu "ka faɗa min Me ka aikatawa Danish? Jinin wanene a jikin rigarka! Yana magana tsokokin fuskarsa na motsawa, Kasa buɗe baki Gabriel yai duk yabi ya firgice, Hankalin su Deeja ya tashi sosai, Har sun fara sharar ƙwalla Saboda sunji a jikin su wani abu ne ya faru da Danish ɗinsu, Da gudu Su hanna su ka nufi Angel da ke baje saman matakalar bene A saman laps ɗinsu suka kwanto da ita, Sai ku ka su ke yi suna ambaton sunanta haɗi da bubbuga jikinta akan ta tashi ta faɗa musu meya faru da su. Kukan azeeza yafi na kowa sauti, Ta cika ɗakin nasu, Takaici biyu ga rashin ido, Ga takaicin halin da take tunanin waninsu ya shiga, Na tashin hankali, Abun ba ƙaramin ƙona mata rai yake yi ba, tana matuƙar jin zafin makantar daren da take fama da ita. Takaicin duniya ya ishe su, kamar su yi hauka, Gabriel ya ƙi buɗe ba ki ya basu amsar tambayoyinsu, kuma shi kaɗai ne zai iya faɗa musu abunda ya faru. Ga Angel taƙi farkawa, Har ruwa suka yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Babu wanda ya iya runtsawa acikin su, Zuciyoyinsu sun karaya sosai musamman Haris da ya gane cewa An tafi da Danish din shi Cikin mawuyacin hali, tuni zazza6i ya kama shi mai zafin gaske, Ciwon kai mai raɗaɗi ya kama Azeeza da ke ta ku ka, Babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, Bacci ya ƙaura ce wa idanuwansu, An rasa wanda zai lallashi wani acikin su, matan gaba ɗayan su asaman benan Suka kwana kewaye da Angel har ruwa suka ƙara yayyafa mata amma bata farfaɗo ba, Sun yi kuka har sun gaji sun gode ma Allah, Mazan cikin su A zuƙunne suka kwana, Yadda su ka rana haka su ka dare. Kafin safiya ta yi kowannan su ya fita hayyacin sa, babu mai iya motsa la66ansa yai magana acikinsu, zazza6i duk ya lullu6e su, Don shi Gabriel ma suman zaune yai, bawan Allah duk ya damu kan shi, ga matsanancin ciwon kai da ya ke fama dashi. A cikin su mutun ɗayane hankalin shi ya ke akwance, majnun dake ta sharar baccinsa, ko daren jiya da Angel ta ke ta kuka za'a tafi da Danish bai farka ba, hatta jamima da ta kasance autar cikin su saida ta tashi daga bacci hada ita cikin waɗanda suka kwana zaune saman benan ɗakin su. Tsawon lokacin babu wanda ya iya buɗe baki ya furta wata kalma, Jamima ce tai ƙoƙarin cewa"Bari naje na ɗebo ruwa a ƙara yayyafa mata asaman fuskarta" ba wanda ya kalle ta, miƙewa tai da sauri ta nufi sashen toilet ɗinsu, tun da ta shiga hankalinta yai matuƙar tashi ganin jinin Danish daya ɗiɗɗiga a saman floor ɗin ya bushe ƙamas, ɗago wa tai da sauri tana kallon Jikin ƙopar toilets ɗin da suke a jere guda uku, kafin ta tsayar da idonta akan ƙopar toilet ɗin da A kayi badaƙalar nan jiya, Jikin ta na kerma ta ƙarasa tare da turo ƙopar shi ta faɗa ciki, gabanta yai wani irin mugun bugu ganin uban jinin da Danish ya zubar a inda ya faɗi jiya yana birgima, a gigice Jamimah ta fasa ƙara wadda ta yi silar janyo hankalin su haris, da gudu suka shigo cikin toilet ɗin kaitsaye idanuwansu su ka sauka akan uban jinin, Lamarin yai matuƙar girgiza su, jinin duk ya daskare acikin toilet ɗin, Zuciyarsu ta dinga azalzalarsu tana tunzura su akan cewa Gabriel ne yai mishi wani abu, shiyasa yaƙi faɗa musu, Ransu yai matuƙar 6aci don gani suke kamar ma kashe musu ɗan uwa yai, Hakan yasa suka koma ɗakin mazan dukansu, Suka tarar ma Gabriel sai da suka fara Farfaɗo dashi ya dawo cikin hayyacin shi, Su ka tasa shi gaba akan ya faɗa musu gaskiyar abunda ya faru idan har yana son zaman lafiya, a lokacin yaso ya sanar dasu sai dai yakasa motsa bakinsa, saboda halin da ya ke aciki, zuciyace ta fusge su, Su ka yi mashi jahilin bugu har sai da su ka ga ya suma, Tukunna suka ƙyale shi, Babu wanda yabi ta kanshi, Kwance suka barshi ƙasa, la66ansa duk sun fashe, ƴan matan sai kuka su ke yi ba ƙaƙƙautawa, An rasa me lallashin wani acikin su, Haris ne ya je wurin da su ke zazzaune bakin benan, ya sanya hannayenshi biyu ya ɗauki Angel ya nufi tsakiyar ɗakin su da ita, Miƙewa su kai gaba ɗayan su suka bi haris, wanda ke ƙoƙarin kwantar da Angel saman floor, Yace da azeeza ta ƙara ɗebo mishi ruwa ya watsa mata, ta amsa mashi da toh, Da gudu azeeza ta nufi sashen shiga toilet ɗinsu, shigarta ke da wuya, su ka soma jin motsin buɗe ƙopa, Saboda halin da su ke aciki babu wanda Ya kai idonshi ga ƙopar, Giants ne da ke kawo musu abinci, A jere su ka shigo hannayen su ruƙe da kayan abincin su, Ko ajikin su jin kukan da su Hanna ke ta yi, wuce wa su ka yi zuwa saman dining carpet dinsu, bayan sun ajiye kayan abincin basu tsaya jiran su taso su ci ba, a tare suka fice daga cikin ɗakin, Babu wanda ya kalli kayan abincin, hatta parveen damuwa ta hana taje taci abinci. Badajimawa ba Azeeza ta shigo hannunta ruƙe da bokiti, Kusan rabi ta ciko, don a watsa ma Angel ko sun samu tafarka, Hanya suka matsa mata ta sauke bucket din gefen haris. duk da hankalin su ba a kwance ya ke ba sai da su ka dubi fuskar azeeza ganin ta kawo musu ruwa a bokiti Sai nishi ta ke yi tana haki, Hannu biyu haris ya tsoma acikin bokitin Ya ɗebo ruwan da ƙarfin gaske ya watsa Ma Angel saman fuskarta, Nan take taja dogon numfashi ta fara mutsu mutsun buɗe idanuwanta. Ajiyar zuciya kowannansu ya sauke, tunkan ta buɗe idanuwanta ta soma ƴan buge buge tana ambaton sunan Danish tana kuka tana faɗin Wlh ba za ku rabani dashi ba, Duk inda zaku kai shi saina bi ku, Wayyo Allah na Danish shikenan sun rabani da farin ciki na, Gabriel kaine silar da ya rasa idon shi ɗaya...." Kalaman Angel sun girgiza su Har suna haɗa baki wurin furta Danish ya rasa idon shi ɗaya!? Cikin rashin fahimtar zancenta su ke kallonta, A lokacin tafara dawowa cikin hayyacinta jin sautin muryoyinsu akanta, Wani irin matsanancin ciwon kai ta ke ji, Hannunta ɗaya dafe da goshin ta, da taimakonsu Hanna Ta miƙe zaune tana faman yin shessheƙar kuka, Idanuwanta har sun ɗan kumbura saboda kukan da tasha, daƙyar ta buɗe su, sunyi jawur dasu, awani irin galabaice take binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya............' "Angel ki yi mana bayani meya faru daku ne? Meyasa aka tafi da Danish! Jinin menene Agaban rigarki? Da wuyanki'? Kamar ƴan jarida haka suka tsareta da tambayoyi. "Dan Allah ki fidda mu daga cikin ruɗanin da mu ke, mun ga ɗazu kun fito toilet Jini duk ya wanke fuskar Danish, ba mu gasgata abunda idanuwanmu suka nuna mana ba, Kafin mu yi wani yunƙurin Giant Yazo ya tafi Dashi" Naufal ne yai magana maganar, Cikin muryar kuka parveen ta soma magana"wlh muna acikin matsanancin tashin hankali Angel, Mun rasa gane meya faru ne! Pls ki yi mana bayani, " Sai da ta gama sauraransu ɗaya bayan ɗaya, Muryarta a raunace ta furta sunan gabriel ba tare da ta ƙarasa maganar ba, Sai nishi take yi, Harsuna haɗa baki wurin cewa"Me Gabriel yai masa? Shi ne Ya kashe mishi idon"? Haris yace"idan ma shine Ya ta6a shi, gashi can kwance ƙasa a sume mun yi mashi bugun tsiya" Zafafan hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskarta, Ko ƙarnin jinin jikinta basa ji, don bashi bane agabansu, Magiya suka dinga yi mata akan ta faɗa musu abunda ya faru, Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana faman lumshe idanuwanta kafin daƙyar ta motsa la66anta. "Bazan iya tuna komai ba, dan Allah Na roƙe ku, Ku ƙyale ni, kaina ciwo ya ke min," Ba don sunso ba, suka rabu da ida, babu wanda ya ƙara tambayarta, duk da sun fahimci kaɗan daga cikin abunda ya faru tsakanin Gabriel da Danish, sai dai basu san menene ya jawo da har faɗa ya kaure a tsakaninsu, kwantawa ƙasa angel tayi idanuwanta na fuskantar ceilling, Jikin ta duk ba dadi, bakomai take tariyowa ba face abubuwan da faru kafin zuwa lokacin daya rasa idonshi, Bawan Allah ya dinga bibiyarta duk don kada Gabriel ya samu damar Yin magana da ita, ashe tsautsayine ke bin shi. Sosai ta fashe da ku ka. "Angel kina ƙara jefa mu cikin damuwa, tun da ba za ki faɗa mana abunda ya faru ba, Zamu jira har zuwa lokacin da za'a dawo mana da ɗan uwan mu wlh idan har ya tabbatar mana da abunda muke hasashe to kuwa tabbas Ba zamu ƙyale Gabriel ba, dole ya fuskanci hukunci dai dai da abunda ya akaita ma Danish ɗin mu! sai ya yi danasanin zuwan shi cikin kurkukun nan!" Naufal ne yai maganar yana fitar da huci, Haris yace"Ae basai mun tsaya jiran Danish Ya dawo cikin mu ba, Idan har Angel taƙi faɗa mana gaskiyar abunda ya faru dashi, Zamu tsare Gabriel ne ta ƙarfi sai ya faɗa mana abunda ya aikata mashi, " "Wannan wata irin rayuwace! Muna cikin jimamin rashin ƴar uwarmu batul, ga wata masifa ta kunno kai, Ni bansan meya haɗa Gabriel da Danish ba, Shi da babu ruwanshi da shiga sabgar da bata shi ba, bana tunanin Danish ne ya fara tsokanar shi, Gabriel shine mai laifin'!! Deeja ce tai maganar fuskarta a yamutse, "Bawan Allah Hakanan An naƙasa mishi rayuwarshi, wlh ba zamu ƙyale Gabriel ba, dama can ni bai kwanta min araina ba, don kawai yaga yana da ƙirar ƙarfi saboda tsabar mugunta yake neman lahanta mana ɗan uwanmu" Acewar Javed, kowa sai tofa Albarkacin bakinsa yake yi, Sai faman tada jijiyoyin wuyansu suke yi, dole ne su damu bayin Allah, Suna matuƙar ƙaunar shi, duk da irin halin ko'in kulan da ya ke nuna musu wani lokacin, hakan bai canza ƙaunar da suke yi mashi ba, ga yunwa suna ji amma damuwa tahana su fahimci hakan, don bata cikin su suke yi ba. Babu wanda ya lura da chinonsu da ya farka daga bacci, Idon shi bai sauka akan komai ba, Sai kan kayan abincin da aka kawo mu su, Saukowa yai daga saman gadon shi, Yaje ya samu wuri saman dining carpet ɗin su ya zauna, Ya dunga kwasar abinci yana cusawa abaki Yana ci yana satar kallon su, kamar munafuki, Parveen ce ta lura da abunda ya ke yi, aikuwa rai amatuƙar 6ace ta nufi inda ya ke, tana ƙarasawa ta ɗauki Burger ta kifa mashi ita saman fuskarshi, ta dagargaje ta tare da cunkusa mashi har cikin hancinshi tana faɗin"munafuki Kanaganin muna kukan rashin ɗan uwanmu amma kai ta abinci ka ke yi," Tsabar mugunta sai da ta 6ata mashi fuskarshi yai ta kuka yana buge hannunta, kamar zata kashe shi, daƙyar ya samu ta ƙyale shi ta koma wurinsu Haris ta tsaya tana hangen Majnun da ke ta yin birgima a kasa. "Azeeza ɗauki ruwan nan ki watsa ma wancan ƙaton a saman fuskarshi," Haris ne yai maganar, Dama kamar jira take yi don ba ƙaramin damuwa tayi da Gabriel ba, Allah yayita da tausayi, Hannu biyu tasa ta kimkimi bokitin zuwa gaban gabriel, A saman fuskarshi ta yayyafe mashi ruwan, nan take yaja dogon numfashi tare da saukr ajiyar zuciya, "Sannu Gabriel," muryar azeeza ce tasa shi yunƙurin buɗe idanuwanshi, zuƙunnawa ta yi saman gwiwowinta agaban shi, tare da kai hannayenta saman kanshi ta ɗago da shi ta kwantar saman cinyoyinta, Ganin ya farka yasa su haris Tunkarar shi Da niyar su takurasa akan ya faɗi masu me ya yi ma Danish, Idan yaƙi faɗa musu zasu ninka mashi bugun da su ka yi mashi ne, sai dai kafin su kaiga ƙarasawa inda ya ke muryar Angel ta katse masu hanzarin su. "Haris kada ku ce zaku buge shi, saboda ba laifin shi bane abunda ya faru, shima bada son ranshi ya akaita mashi hakan ba........" daƙyar take magana duk don kada su bugi gabriel yasa take Ƙoƙarin faɗa masu abunda ya faru, duk da ta 6oye musu Ainihin dalilin faruwar hakan, ta dai ce musu tsautsayi ne da ƙaddara suka ja har Gabriel ya naushi idon shi, ba tare daya sani ba, sun ɗan samu sa6ani ne akanta, haris yace taya zasu yarda da maganarta? Wani irin tsautsayine wannan da har danish zai rasa idonshi ɗaya? Kawai saboda da ita zasu kama yin faɗa? Shifa bai fahinci zancen ba! Anya kuwa taga uban jinin da ya wanke toilet ɗinsu, Ga shi nan har a jikinta, Ya ƙara da cewa bazasu yarda ba, dole shima Gabriel su cire mashi idon shi ɗaya, in yaso Giant sunzo su ɗauke shi shima akaishi treatment room ɗin don ayi jinyarsu atare!! ganin dagaske haris ya ke yi Ne yasa tai saurin cewa"Danish bai rasa idonshi ba, da kanshi ya faɗa min cewa lafiyar shi ƙalau, babu abunda ya sami idon shi, kada ku yi gaggawar yanke hukunci, ku jira har zuwa time da za'a dawo da shi. Angel taci wahala kafin ta samu ta shawo kansu, ba don sun haƙura ba, sun dai jira ne zuwa lokacin da za'a dawo musu dashi don suga idan idon nashi yana nan ko ya naƙasa. Yinin ranar babu daɗi su ka yi shi, sai wuraren marece Ne suka ɗan motsa, Da taimakon mazan suka gyara toilet ɗin daya 6aci da jini tass suka wanke shi, kamar wani abu bai ta6a faruwa ba acikinsa, Har wajen shi zuwa bakin ƙopar shiga sashen duk suka wanke, Bayan sun gama suka gyara cikin ɗakin nasu, Ko'ina ya dawo fes sai dai zuciyoyinsu a ƙuntace su ke, ƙarfin hali kawai suke yi babu wani mai lafiya a Cikinsu, sai da marece ya nutsa tukunna su ka ci abincin su, banda Angel da mazan cikin su, ko kallo abincin bai ishe su ba. Hannah ta yi fama da Angel akan taje ta yi wanka ta wanke uniform ɗinta idan ma bazata iya ba, ita zata wanke mata uniform ɗin da kanta, Amma ta maƙe kafaɗa, gani take kamar inta wanke jinin Danish dake ajikin Uniform ɗinta shikenan bazata ƙara ganin shi, shiyasa taƙi zuwa tai wanka. idan mu ka koma 6angaren Gabriel, Bawan Allah azeeza ce kaɗai ta damu dashi, ganinta ya ke kamar ƴar uwarsa daya rasa, saboda mutuncin da ta yi mashi, Ita ta wanke mashi tsoffin uniform ɗinshi da suka 6aci da jinin Danish, tun bayan da yayi wanka, Ya cire su ya bata, Ya maida tsoffin a jikinsa. Saman Gado ya koma ya kwanta yanata juyi kanshi na sara mashi, Har sai da ya samu bacci ya ɗauke shi tukunna ya ji sauƙin ciwon nashi, A taƙaice Cikin kwanakin Nan Jin daɗin su Ya zama ragagge, me faranta musu rai Angel babu lafiya, Gashi taƙi zuwa ta yi wanka ta cire kayan Jikinta, Ta zama ƙazamar ƙarfi da yaji, duk akan Danish, kwana ɗaya da faruwar abun ko ruwa bai gifta ta maƙoshinta ba, ta haranta ma kanta duk wani jin daɗi ta ƙuntata sosai, A daren ranar da aka tafi dashi, gefen gadon shi ta kwana a zaune kamar gunki, A cikin kwana na biyu ne su Deeja suka tasa ƙeyarta gaba akan taje tayi wanka idan ba haka zasu yi mata, Su kan su tsananin tausayinta su ke ji, Ba irin lallashin da basu yi mata ba, amma taki sakewa, hatta Haris daya fi kowa Kusanci da Danish Ya haƙura yabarwa Allah tun da ba yadda za su yi, babban abunda yafi damunsu shine awani hali ya ke aciki? Ya idon shi ya ke? jikin shi da sauƙi ko akasin hakan? Daƙyar suka samu Angel ta je ta yi wanka, A cikon kwana na uku da aka tafi dashi, Hanna ce ta wanke mata uniform ɗinta, Dogon wandonta sabo da vest ɗinta, dama su ne ajikinta aranar da abun ya afku, Tsaffin kayanta ta maida ajikinta, yanzu ta daina kwana gefen gadonshi, Asaman gadon take kwanciya tasha kukanta, duk Idan dare ya nutsa tashi take ta zauna, tana yi masu addu'a shida batul, Da daddynta, Kwana ta ke yi a zaune tana kai kukanta wurin Allah, Da ga ita har Gabriel babu wanda ya ƙara tada zancen haura tagar nan saboda babu lafiya atattare dasu, baiwar Allah azeeza ita keta yin jinyar Gabriel, Yaji jiki sosai, Gashi ƴan uwa nasu haushinsa suke ji, gani suke kamar baya ƙaunar Danish ne shiyasa ya ke neman naƙasa musu ɗan uwansu, A kwana atashi ba wuya wurin Allah yau tsawon 2 weeks kenan Ba'a dawo da Danish ba, A lissafi na Batul ta shiga Cikin wata na biyu kenan ba'a dawo musu da ita ba, Haka zalika Unaiza ƴar gidan daddy, Yau ta cika sati Sati biyu da kwanaki ba'a dawo da ita ba.......... (Iya abunda ku ka samu yau kenan, Da babu ƙwara ba daɗi, Mu haɗu next page In Allah yakaimu da rai da lafiya) 💔PRISONERS💔 Kwance ta ke asaman gadonshi, hannunta rungume da pillow ɗin sa ta ƙanƙame shi a ƙirjinta, bacci take yi amma sam babu kwanciyar hankali atattare da ita, sai jan numfashi ta ke yi ga cikinta da ke ta yin kukan yunwa, hatta ƙirjinta wani irin nauyi yai mata, zuciyarta na harbawa da ƙarfi da ƙarfi, duk irin sanyin da yanayin ke da shi hakan bai hana zufa tsastsafo mata ba, saboda damuwa da kuma rashin cin abinci har rama ta yi fuskarta ta faɗa, sai uban hasken da ta yi, gashin kanta kuwa kamar na mahaukaciya, rabon da ta sharce shi tun lokacin da aka tafi da Danish, wankan ma sai in sun matsa mata ta ke yin shi akai akai, haka abinci sai sun mata dole sun tasa ta gaba tukunna take ɗan tsakurar kayan marmari tasha idan ta gama ta kora da ruwa, fruit kaɗai ta ke iya sha, duk ta takura kanta,Ta hana kanta sakat kamar wadda ta aikata zunubi, ga shi rayuwarta gaba ɗaya ta koma saman gadon Danish, idan kaga ta sauko to toilet zata shiga domin yin wani uziri amma bayan haka babu ruwanta da kowa, Saman gado take naɗewa ta addabi zuciyarta da tunane tunane na damuwa, depression tuni ya fara samun gur6i acikin zuciyarta, idan damuwa ta yi mata yawa kanta har sara mata ya ke yi da matsanancin ciwon kai, zuciyarta tai mata nauyi kamar an ɗaura mata dutse saman ƙirjinta haka ta ke ji, wani lokacin idan abun yai mata yawa har amai take yi, Rayuwar Angel ta zama abun tausayi, kowa tausayinta ya ke yi acikin su, sun damu da damuwarta, suna matuƙar jin takaicin halin da ta shiga kamar ba Angel ɗin su ba.................💔 Ƙasa ƙasa ta ke jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, sai surutu su ke yi duk sun cika ɗakin, tana ta faman ƙoƙarin buɗe idanuwanta amma sunƙi bata haɗin kai baccin ne bai ishe ta ba, ga kuma matsiyaciyar yunwar da ta ke ji, A hankali take motsa la66anta tana karanto addu'ar tashi daga bacci, kafin daƙyar ta iya buɗe manyan idanuwan nata waɗanda suka raunata sosai saboda kukan da take yawan yi akowani dare na Allah, bismilla ta furta yayin da ta ke yunƙurin miƙewa zaune ta jingina bayanta jikin bango, old uniform trouser ɗinta ne a jikinta baƙi, Sai jar vest ɗinta data sanya, don tafi sha'awar kwanciya bacci da ita, buɗe baki tai sakamakon hammar da tazo mata ba shiri ta ɗaura hannunta saman bakin nata Tana ambaton Alhamdulillah. bayan ta sauke hannun ta ɗaura su saman pillow, kafin ta tsayar da idanuwanta kan ma su yin Surutun, kusan su Biyar, Zazzaune a ƙasa saman shimfiɗar Sarah, Hannah da Yasmin tare da Hibba da kuma rubina, sai Eve hada mai shimfidar Sarah, Hannunta ruƙe da nail cutter, Ita kuma Hanna tana ruƙe da nail filer, suna fira Sarah na yanke musu akaifa, idan tagama yi ma mutun ɗaya sai Hanna ta kankare mashi akaifar ta gyara mashi ita, idan ka gan su ahaka sai ka yi tsammanin basu da wata damuwa alhalin nan kuwa zuciyarsu a cunkushe take da matsananciyar damuwa. tun da ta ɗaura idanuwanta akansu bata ɗauke ba, bakomai yake burgeta dasu ba, face yarda suke matuƙar ƙaunar junan su, Suna da kyakkyawar mu'amala a tsakanin su, Sau dayawa basu jin komai don su yi ma ɗan uwansu hidima, sa6anin wasu mutanan da zaka ga ƙashi ya hana su taimaki junan su, amma su waɗannan bayin Allahn suna da haɗin kai, tun da ta fara rashin lafiya basu ta6a bari ta wanke koda uniform ɗinta ba, hatta kayan marmarin da ta ke sha su ne suke kawo mata su har saman gadonta don ta sha, shiyasa take matuƙar ƙaunarsu. Ɗauke idanuwanta tai daga kansu sarah, ta shiga bin kowani gado da Kallo, Parveen tana ƙudundune saman gadonta, bata farka daga bacci ba, sai juyi take yi saman mattress ɗinta kamar zata faɗo ƙasa, Sauran gadajensu Deeja tabi da kallo, Da alama idonta biyu, ta ƙurawa ceilling ido fuskarta ɗauke da damuwa, Haris ma Yana a zaune gefen gadon shi Ya zabga uban tagumi, gwiwowin hannayenshi asaman na ƙafafun shi, tasan bai wuci damuwar rashin ɗan uwansa bane, bawan Allah duk da irin juriyar shi hakan bai hana shi yin rama ba, sauran mazan duk suna a kwance saman gadon su basu farka daga bacci ba. Tana cikin bin gadajen su da kallo, ta soma jiyo sautin dariyar Azeeza ta cikin sashen toilet ɗin su, Da sauri takai idonta kan ƙopar, Majnun ne ya fito babu kaya ajikin shi sai gudu ya ke yi jikinsa duk lemar ruwan wankan da ta yi mashi, Gaba ɗaya su Hanna suka ɗago Suna kallon su, Lamarin ya ɗaure musu kai ganin yadda yadda ya fito babu kaya yana ta gudu acikin ɗakin su, hauka tuburan yana ta tiƙar dariya ko kunya bai ji ko da ya ke ina yasanta. Azeeza ce Ta biyo bayanshi hannunta ruƙe da uniform ɗin shi, Sai zagaye cikin ɗakin nasu su ke yi tana ta Ƙwala mashi kiran tana faɗin"Wai ba zaka tsaya in sanya maka kayan ka ba? Salon sai ka faɗi ko, don ma ka samu na yi maka wanka shine ka ke min wulaƙanci, ba don zuciyar imani ba Allah da bazan yi maka wankan ba ƙazami kawai, mutun jiki duk ciwo, har tsoron ta6a fatar shi nake yi kamar zata fashe saboda haske........" Su hanna sai dariya su ke yi musu, ita kanta Angel sai da ta ɗan murmusa ganin yadda take ta faman bin shi yana yi mata yawo da hankali, da ga ita har shi Sai ka rasa gane wanene babba acikin su, shiyasa duk suka rainata, kamar sun samu tv haka suka dinga binsu da kallo, babu wanda ya lura da Angel ta farka da tuni sunzo wurinta. Fitowa daga Cikin ƙopar sashen toilet ɗin su Jamima ta yi, hannunta ruƙe da rigar uniform ɗinta, daga ita sai ɗan wandonta ja, fuskarnan a murtuƙe ta sha mur, ƴan kumatuntu sun yi suntum dasu saboda tsabar fusata, Gashin kanta da aka ɗaure mata da ribbom Ya cika bayanta, kamar na ɗiyar roba, sai baƙin rai ta ke yi, Hayaniyarsu Ce ta farkar da sauran da suke rage suna bacci, hatta haris daya zabga uban ta gumi da deeja dake kallon ceilling saida suka dawo da dubansu akan Majnun da Azeeza. "Azeeza!" haris ne ya kira sunanta, hakan yasa ta tsaya tana haki, Ta waigo tana kallon shi. Tun kafin ya soma yi mata magana, ta ɗan ɗaure fuskarta, muryarta tamkar za fashe da kuka ta soma magana "Na gaji da raina min wayau da su ke yi, don sun ga na damu dasu, shiyasa suke yi min wulaƙanci dashi da waccan mai fuskar tumaturin, tsawon one week ba wanda yai tunanin yayi musu wanka, da yake ba hankali ne dasu ba, ko tsamin jikin su basa ji, a tunani na yi musu gwaninta, yau da safe na tada dasu daga bacci naja su muka shiga toilet na datse ƙopa don inyi musu wanka, nasa su ka fara yin brush, bayan sun gama nace toh su tu6e kaya in yi musu wanka, ba ku ga irin wulaƙancin da su ka yi min ba, Jamima hada ce min wai ita bazata tu6e kaya inyi mata wanka ba, saboda tsarata ce ita, ban fita da komai ba, daƙyar na samu shi majnun nayi mashi wanka ahaka ma saida ya dinga watsa min kumfa a ido ina wanke wa, ita kuma jamima kusan dambe mu ka yi da ita, taƙi yarda inyi mata wankan, hada cewa sai dai inyi mata da wando a jikinta don kada in gan mata jiki............kasa ƙarasa maganar ta yi idanuwanta cike tab da ƙwalla, sai kace ba ita bace ta gama shan dariya tana bin majnun da gudu ba, ita babban baƙin cikinta, Jamima da take yi mata kallon tsararta, ta raina mata wayau, da ga ita har majunun sun raina azeeza saboda ƙarantarta, duk a tunaninsu tsararsu ce basu san cewa ta girmesu nesa ba kusa ba. Dariya suka dinga yi mata, musamman parveen da bata jima da farkawa ba, Hada gabriel dake kishingiɗe saman gadonshi, farkawarshi kenan yaji azeeza tana kora jawabi. Ganin yadda su ke ta yi mata dariya yasa ta bubbuga ƙafafuwanta ƙasa, ta zuƙunna tana kuka, Muryar Angel ce ta katse musu dariyar tasu da wani irin kasala take magana da busassun la66anta "Ku daina mata dariya kuna ƙara 6ata mata rai, Azeeza ki daina kuka, yanzu fa ki ka gama shan dariya, ke kanki sun baki nishaɗi, sai kina yi musu uziri, kinga ke yayarsu ce, su kuma ƙannanki, dole sai ana haƙuri da juna.....' ta kai ƙarshen maganar tare da ɗan juyawa ta kalli jamimah dake ta faman ɗaure fuska tana tsino ƙaramin bakinta. "Zo nan" jin kiran Angel yasa ta ɗan saki fuskarta, ta soma tafiya tana tunkarar gadon ta, a bakin gadon ta tsaya tana kallonta"ba nan nace ki tsaya ba, dawo nan gefe na" tai maganar tana nuna mata gefen gadon, dawowa tai daga gefen gadon ta tsaya tana faman mutsustsuka rigar hannunta, numfasawa tai tare da juyawa ta kalli majnun dake tsaye yana ta faman raba ido, hannayen shi biyu rufe da gabanshi, Parveen tace"Abanza, bayan ka gama nuna mana abun na ka shine yanzu zaka wani sa hannu ka rufe, kai ɗin nan ba ƙaramun shaƙiyi bane, ae wlh da ace nice zan maka wanka, da duk saina gurje farar fatarnan ta ka, aljani kawai" Tana magana tana jifarshi da harara idonshi akanta sai murguɗa mata baki ya ke yi. "Zonan Majnun uban masu hankali" Angel ce ta kira shi, A hankali ya ke nufar inda take ba tare daya zame hannun shi daga gabanshi ba, a gefen gadon Ya tsaya dab da ita, Jamima tana a 6angaren dama shi yana a 6angaren hagu, kowa ya natsu yana jiran jin sasancin da Angel zata yi musu. "Ku faɗamin meyasa kuka raina azeeza ne? Tsarar wasan ku ce ita? Daga taimako? Yau one week ba wanda ya kula da ba ku yi wanka ba, don ita ta taimaka zata yi muku shine kuke yi mata iya shege ko"! Tai maganar tana duban kowannansu, Jamima ce tafara magana tana tsino baki "Ae ni sai da nace mata, tabarnin inyi wankan ta ƙi bari inyi, bana son tayi min wanka, nafison su hanna su cuɗa min bayana ko ke...." tun kan ta ƙarasa maganar Angel tace"Oh saboda sune manya wanda suka isa dake, banda ita ko? Ɗaga mata kai tai alamar eh ta ƙara da cewa"azeeza fa ƴar ƙarama ce the same height as me, ta ya za'ai tayi min wanka." Mamaki ne ya kama su Hannah, Kowa ya ɗan zaro ido suna kallonta, Angel tace"Okey," kafin ta maida duban ta ga majnoon"what about u? Meyasa ka rainata"? da buɗar bakinsa sai cewa yae"I don't want her to bathe me because she's so little, nafa girme ta, da ma ba ita ta ke yi min ba, Danish ne yanzu baya nan, Haris yana min da naufal" Har cikin zuciyarta taji gabanta yaɗan faɗi saboda sunan Danish da majnon ya ambata, nan take taji wata irin kewarshi ta baibaye sassan jikinta, kasa magana tai, idanuwanta bakomai suke nuno mata ba face kyakkyawar fuskarshi, da sauri ta kwantar da kanta ta kifa fuskarta saman pillow, ganin hakan yasa suka fahimci dalilin shiga damuwarta, su kansu da Majnun Ya ambaci sunan Danish sai da zuciyoyinsu suka amsa. Haris ne yaci gaba da yin magana yana duban su Jamima dake a tsaitsaye gefe da gefen na gadonta "daga yanzu kada na kuskura na ƙara ganin wani a cikin ku ya raina azeeza, Ƴan ranin wayau, just because u saw her a little girl like u that's why ku ka raina ta, Let me tell you that even Angel, whom you respect, is younger than azeeza." A matuƙar ruɗe Jamimah da majnoon suka kalli haris suna faman zare ido, Mamaki ƙarara akan fuskarsu, Hatta Gabriel da Sarah sai da suka jinjina maganarshi don basu ta6a sanin hakan ba, sai da ya faɗi yanzu, Cigaba da magana haris yai,"Angel itace ƙaramar cikin mu kafin zuwan ku, tafi kowa ƙananun shekaru, ƴar azeezar nan da kuke rainawa yayarku ce,......." muryar Jamima da kokwanto ta furta"amma ae ƴar ƙaramace ko, meyasa ita bata yi tsawon Angel ɗin mu ba"? Hada ruƙe qugu tana magana. Kafin haris yabata amsa deeja ta kar6e da cewa"Saboda haka Allah ya halicce ta, baki ga banbancin da ke a tsakanin kowannan mu bane? Wani yana da tsawo wani Jiki wani mara ƙiba, ahaka kowa da shekarunsa" da alama jamima bata fahimci me take nufi ba, Majnun sarkin mahaukata yace"to itama taje Allah ya ƙara mata tsawon mana sai ta koma kamar Angel" bismilla parveen tai tare da yunƙurawa ta sauko daga saman gadonta, ta rarumi pilow, majnun na ganin ta yi hakan ranshi ya bashi cewar shi zata buga, aiko da gudu ya nufi sashen toilet ɗinsu yana dariya, Sai da tafara zuwa ta kar6i kayanshi da azeeza ta jefar ƙasa ta ruƙo su da hannu ɗaya, yayin ɗayan hannun ke ruƙe da pillown data ɗauko Tabi bayan shi Cikin sashen toilet ɗin, Bata jima da shiga ba suka jiyo sautin kukan shi yana zazzaga mata masifa. Murmushi kowannan su ya saki, har lokacin Azeeza na zuƙunne ƙasa kanta saman gwiwarta, Saukowa daga saman gado Gabriel yai tare da nufar inda take, har ya kusa ya isa muryar haris ta katse shi"me zaka mata" Kallon shi Gabriel yai ba tare daya bashi amsa ba, Ya cigana da tafiya "Kada ka kuskure kace zaka yi mata magana, shisshigin yayi yawa, wannan fa ba ƴar uwarka ba ce, yakamata kadaina manne mata" rai 6ace haris ke yi mashi magana, ko ta kanshi Gabriel baibi ba, damuwarshi akan Azeeza ne, baya son yaga tana kuka, saboda ƙaunar da ta ke yi mishi, zuƙunna yai agabanta tare da kai hannu ya ɗago da kanta fuskar nan sharkaf da hawaye ta ɗaura idonta akan nashi "Its okey azeeza, stop shedding ur tears, i don't know why ki ke son zubar da hawayen ki, akan abunda bai kai ya kawo ba," hannayen shi ya ɗaura saman fuskarta yana goge mata hawayen, duk sun zuba ido suna kallon su banda Angel da ke ta shan kukanta ba tare da sauti na fita ba, An fama mata ciwon dake damun zuciyarta. Ganin yaƙi jin maganar shi hada share mata hawaye hakan yasa haris yunƙura ya miƙe zai nufe su, Muryar azeeza na kerma tace"dan Allah haris ka ƙyale shi, ni bansan meyasa ku ka ɗaura mashi karan tsana ba, koda ace Gabriel shine silar abunda ya faru da Danish, bai kamata kuna mishi haka ba, tunda ya nemi yafiyarmu ya gane kuskurenshi, shi kanshi fa bada son ranshi hakan ya faru ba, Angel ta riga ta yi mana bayanin komai......" Tunkan ta ƙarasa maganarta, deeja ta katse ta da cewa"Azeeza kina da matsala! Tausayin ki bazai ta6a bari ki ga laifin shi ba, ke kowa naki ne, dame gaskiya da mara gaskiya, yanzu dik irin abunda Gabriel yai ma ɗan uwan mu Danish ke baki gani ba? Cikin mu ba wanda bai yi zazzza6in rashin Danish ba, wannan ƙaton Ya haddasa mana baƙin Ciki acikin zuciyar mu, ya naƙasa mana ɗan uwan mu, amma ahaka kike biye mashi, har wankin kayan shi ke kike yi kamar baiwarsa, kamar fa kina ƙara bashi damar da zai cigaba da cutar da mu ne" cikin nuna 6acin rai Deeja ta yi maganar, Dama sun fi kowa tsanar Gabriel ita da Haris, Su biyun nan sun zame mashi ciwon kai da masassara, Deeja da haris tamkar abu ɗayane, Kusan halinsu ɗaya, Idan suka tsani mutun sai ya ji kamar ya haɗiyi zuciya, kamar dai lokacin da Aka kawo Angel da suka addabe ta kafin asasanta, Zafin zuciya ne dasu, suna da wuyar sha'ani sai dai duk da hakan suna da kyakkyawar zuciya. Ranshi bai ta6a 6aci ba irin na yau, Zame hannayenshi yai daga saman fuskar azeeza da yake share ma hawaye, Ya miƙe tare da juyawa yana kallon haris dake a tsaye yana jifar shi da kallon tsana. "Bafa tsoron ku nake ji ba, sannan ba ƙarfi kuka fi ni ba, duk abunda ku ke yi min na ƙyale ku ne saboda nasan laifina ne, na rasa gane ku wasu irin mutane ne, sai kace ba kusan tsautsayi ba, nifa bada son raina na aikata mashi hakan ba! yadda ku ka ji zafi acikin zuciyarku bai kai kwatankwacin wanda naji ba, a lokacin dana naushi idonshi, ga Angel nan ku tambayeta irin tashin hankalin dana shiga ae ita tasa komai, har cewa nayi ta cire idona ta sanya mashi duk don saboda tausayin shi da naji........." kasa ƙarasa maganar yai, idanuwanshi cike tab da kwalla, jikinsu Hanna ba ƙaramin sanyi yayi ba, saboda akwai ƙamshin gaskiya a kalaman shi, shigowa cikin ɗakin parveen tayi hannunta ruƙe dana majnun da ta sanyawa kaya, har sun shirya, Ganin Gabriel dake tsaye ido ya canza launi ga kuma haris agabanshi, hakan yasa ta dan dakata da yin tafiyar tana kallonsu, "kuna ɗaukata tamkar wani maƙiyin ku, nifa ba bare bane acikin ku, kawai don bamu arayu atare bane sai daga baya na tsinci kaina acikin, da ku da ni duka prisoners ne da ƙaddara ta haɗa mu rayu a wuri ɗaya, akan me zan cuci wani acikin ku? Babu wanda yafi wani fa acikin mu! Bana jin daɗin juyamin baya da ku ke yi, nifa mutunne ba dutse ba, ina da zuciya a ƙirjina, dole in ji zafin ƙiyayyar da ku ke nuna min, meyasa nima baza ku soni ba ku ƙaunace kamar yadda kukeson junan ku? Yai tambayar cikin ƙunar rai yayin da ya ke bin kowannansu da kallo. "Hatta azeeza da take ƙarama acikin ku tafi hankali, ita da Angel, sune waɗanda nasan ba za su ta6a juyamin baya ba, kuma ɗin rashin fahimta ne, a bun da baku sani ba, Danish shine silar da hakan ta faru, mun samu sa6ani dashi, ya sanya hannu ya shaƙe min wuyana, nayi nayi ya saki yaƙi saki kamar zan mutun a lokacin koda ace wani daga cikin ku ne yaji an shaƙe mashi wuya za'a kashe shi cikin fitar hayyaci zai iya yin komai donya ƙwaci kanshi, to nima shine abunda nayi at end nazo ina danasani, da ace da son raina na aikata mashi hakan ai baza ku ganni ina jinya ba," Haƙiƙa kalaman Gabriel sun yi matuƙar yin tasiri acikin zukatansu, duk sai su ka ji ba daɗi irin wariyar da suka nuna mashi. Hannu yasa ya share hawayen dake akan fuskarshi, Idonshi akan na haris yace"ina ƙara baku haƙuri, idan ma hakan bai yi maku ba, zan duƙa saman gwiwowina in roƙe ku akan ku yafe min, kai idon ma kuna so ku cire min idona ne don ku huce takaicin abunda nayi maku to gasunan, ku yi abinda ku ka ga dama, amma karkuce zaku raba ni da azeeza, saboda tana bani kulawa, ina jinta tamkar ƴar uwata Gabriella," Yana kawo nan a maganarshi, Ya zube saman gwiwowinsa, Da sauri azeeza ta miƙe tana roƙonshi akan ya tashi tsaye ya daina zubar da hawayen shi. "Kada ka damu, komai ya wuce awurina, koda ace su basu yafe maka ba ni na yafe maka" acewar Hannah. Tana rufe baki parveen ce"tunda dai ya riga ya faru, bamu isa mu canza komai ba, don haka nima na yafe maka" Ɗaya bayan ɗaya suka dinga cewa sun yafe mashi, Mutun ukune basu tanka mashi ba, Haris da deeja da kuma Naufal, Su sunce sai an dawo musu da ɗan uwansu sun ga awani hali yake ciki tukunna zasu Yafe mashi, a ƙalla ya ji sanyi aranshi ganin dayawan su sun yafe mishi sunce zasu cigaba dayi mashi magana bazasu ƙara nuna mashi wariya ba, Yaji dadin hakan ga kuma Azeezar shi mai sanya shi farin ciki, itama tana Atare da shi, bayan komai Ya lafa, Gabriel Ya miƙe ya nufi sashen toitet ɗinsu, don yayi wanka, ƙarasa shigowa cikin ɗakin parveen ta yi hannunta ruƙe da na majnun don tun ɗazu tana a tsaye tana sauraronsu Gabriel ganin sun samu maslaha atsakanin su yasa ta motsa, sai da ta fara wurga pillown hannunta saman gado tukunna ta nufi jamima da ke a tsaye gefen gadon Angel ta damƙo hannunta, ta haɗa su duka biyun takaisu gaban Gadon azeeza a lokacin harta koma ta zauna. "Ku bata hakuri idan ba so kuke ranku ya 6aci ba," acewar parveen, Ɗagowa su kai suna kallon fuskar azeeza da tayi jawur. "Idan har baku bata haƙuri ba, Yau babu wanda zan bari yaci abinci acikin ku, kunsan dai halina tau," jin haka yasa suka haɗa baki wurin furta"We're really sorry sister azeeza ba zamu ƙara ba" hada kama kunnansu kamar zomaye, hakan da su ka yi ba ƙaramin dariya yabata ba, Miƙa ma Jamima hannu tayi"muje inyi maki wankan tun da mun shirya" Ba musu ta amsa mata da toh, Saukowa azeeza tayi daga smaan gadon ta ruƙe hannun Jamima acikin nata, suka nufi toilet, Bayan shigarsu, Parveen ta koma saman gadonta tana yi musu sambatun yunwa take ji, majnun kuma ya nufi tsakar ɗakin su Yanata Yin ƴan tsalle tsallen shi. Ɗakin yai tsit na ɗan wani lokaci, Fitowa daga cikin sashen toilet dinsu Gabriel yai su azeeza na a biye da bayanshi ita da jamima da ta yi ma wanka, Sai murmushi suke saki Shigowasu yayi dai dai da turo ƙopar ɗakin su da aka yi, Gaba ɗaya hankulan su suka koma akan benan, Banda Angel data mannewa pillow, ta kammala shan kukan nata, ta lallashinta kanta ta yi shiru, Ajiyar zuciya suka sauke ganin Giants ne masu kawo musu abinci, Hannayensu ruƙe da Wooden trays kamar yadda aka saba, A jere suka nufi ɗakin bayan sun ajiye su saman carpet, suka ja da baya tare da ƙamewa, "Abinci ya iso, wanda bai wanko bakinshi ba, yai sauri yaje toilet muna jiran ku" Hannah ce tai musu magana, su ka amsa mata da toh, ɗaya bayan ɗaya su ka dinga miƙewa suna shiga sashen toilet ɗinsu, within minutes kowannansu ya dawo suka zauna saman carpet domin cin abinci, ganin taƙi tasowa tazo suci yasa Deeja ɗaga murya ta ƙwala mata kira"Angel Ki taso muci abinci" shiru bata tanka mata ba, haris ma yai magana amma shiru taƙi tasowa, naufal yace su ƙyale ta, inyaso sun ajiye mata nata acikin kwando, Har sun yi nisa da fara cin abincin, kowa ya natsu yana ci, Majnun sai cusawa ya ke yi abankinshi Parveen nata jifar shi da harara ganin yadda yake yin cin mugunta. Babu wanda ya lura da ita, Saukowa tai daga saman gadonta fuskarnan sharkaf da hawaye ta yi jawur da ita, tafiya take yi kamar zata kife ƙasa saboda rashin kuzarinta, bata nufi ko'ina ba sai wurin Giants dake a tsaye kamar dakarun Yaƙi. Dab dasu ta tsaya kamar zata faɗa musu, fuskarta babu annuri ko misƙala zarratin, zuciyarta a bushe take, muryarta a sanyaye ta soma yi musu magana "Bawani abu ya kawo ni wurinku ba, so nake ku faɗamin, yaushe zaku dawo mana da ƴan uwanmu? Batool shiru har yau, Danish kuma bansan awani hali yake ciki ba, ni dai don Allah na roƙe ku, ku taimaka ku faɗamin awani hali suke ciki, shin suna raye ko sun mutu ne, idan naji sai in haƙuri in fidda rai......" tun da Angel ta soma yi musu magana Hawaye nabin fuskarta, gaba ɗaya muryarta ta janyo hankalin su Mubeen akanta, tuni sun dakata da cin abincin suna kallonta, an rasa me buɗe baki ya dakatar da ita. Girgiza kai ta yi tare da lashe hawayen daya gangaro saman la66anta da harshenta, kafin taci gaba da cewa"wai ku ba zaku ta6a aikata abun kirkiki ba arayuwarku? Haka zaku ƙare wurin aikata zalunci......." muryar Haris ce ta katse mata maganarta "Angel, pls ki matsa daga wurinsu! Kodan saboda mu, idan wani abu ya same ki mu zata shafa, mun rasa mutun uku acikin mu yanzu idan kema wani abu ya faru da ke ya kike tunanin rayuwarmu zata kasance'? Fashewa tayi da matsanancin kuka, azeeza tuni ta kama yin kukan itama. Cikin shessheƙar kuka Angel tace mashi"don bakasan yadda nake ji acikin zuciyata bane, ni ƙwara ma su kashe shi in huta, da irin wannan rayuwar mara amfani....." daƙyar ta ƙarasa maganar saboda wani irin jiri da ta soma gani acikin idanuwanta, ƙirjinta yai mata nauyi tamkar zai dare biyu, hannu ɗaya tasa ta dafe kanta, ganin yadda jikinta ke rawa yasa Gabriel saurin miƙewa shi da yake a zaune ƙarshen carpet din dab da inda suke hannu biyu yasa wurin tarbeta, Ya ɗauke ta Ya nufi Gadonta, a sama ya kwantar da ita, hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, abincin ma ya fita aransu, duk suka miƙe da sauri suka nufi Gadonta don ganin meke faruwa da ita, Mutun biyu suka rage kan abincin, majnun da Jamima, kallon juna su ka yi kowannansu ya cunkusa abinci abakinshi, Suna tauna suna magana "Ki ɗauko kwandon batul mu ɗibar masu abincin kada waɗannan dodonnin su tafi dashi," Majnun ne yai mata magana, harara ta wurga mashi"Kai bazaka je ka ɗauko ba, saini," ƙarasa cinye abincin bakinsa yai tare da yunƙurawa ya miƙe ya nufi gadon batul hada ɗan gudunsa, Ya zuƙunna a gaban ƙarƙashin gadon ya zaro kwandon da sauri ya dawo ya zuƙunna kamar mutumin kirki, Ya dinga kwasar abincin Yana zubawa ciki komai Ya haɗe musu kusan Duka ya kwasar musu har saida kwandon yai soro, ya ɗago ya kalli Jamima dake ta tura plaintain chips abakinta. "Tun da ni na ɗauko kwandon, Ke zaki maida yanzu" ta6e baki tayi"ae bani da ƙarfin iya ɗaukarshi, faɗuwa zanyi ƙasa, kai ka ɗauka mana" Girgiza kai majnun yai kamar babban mutun Yasa hannu ya ɗauki kwandon, Ya nufi ƙarƙashin gadon Ya tura shi ciki, yana ƙoƙarin miƙewa Yaji muryarta abayanshi"Gashi na ɗauko" kallonta yai, Robobin ruwa ne ta rungumo guda uku a ƙirjinta, sai yatsina fuska take yi, Hannu yasa ya kar6a Ya tura a ƙarƙashin gadon, yace mata ta kwaso sauran, Ta koma ta daukosu, Ta miƙa mashi ya kar6a ya ajiye musu, babu wanda Ya tuna da abinci ba su san ma sun ajiye musu ba, Hankalinsu gaba ɗaya yana akan Angel sun kewaye gadonta damuwa ce danƙare akan fuskokinsu, sai kiran sunanta suke yi tare da jijjiga jikinta don ta farka amma taƙi motsawa, hakan ba ƙaramin ɗaga musu hankalin yai ba, "Angel! Pls ki tashi! Dan Allah ki farka!' azeeza ce keta magana tana matsar kwalla, Deeja tace"Allah yasa ba waɗancan mugayen bane su ka yi mata wani abu ba," haris yace"nima abunda na ke hasashe kenan" muryar Gabriel ce ta janyo hankalinsu akan shi" Ba abunda ya same ta, Yunwa ce take ji, ku miƙo min ruwa" yatsina fuska Naufal yai"kawai saboda tana jin yunwa saita yanke jiki ta faɗi? A ina ka sami wannan ilmin" Banza Gabriel yae dashi bai tanka mashi ba, Haris yace"Shisshigi ne kawai," Dogon tsoki Gabriel yaja tare da kallon Azeeza da ke ta yin kuka yace ta ɗabo mashi ruwa, Kafin tayi yunƙurin zuwa ɗebowa Sai ga majnun bakin gadon hannun shi ruƙe da bottle water yaji suna nema shine ya kawo musu, karo nafarko kenan da majnun ya ta6a yi musu abun kirki. Ba tare da 6ata lokaci ba, Gabriel ya kar6i robar ruwan, ya samu wuri daga gefen gadonta ya zauna tare da sanya hannun shi ɗaya ya ɗago da kanta ya ɗaura shi gefen chest dinshi, azeeza ce ta buɗe mashi murfin robar hannun shi ta ruƙe a hannunta, Ya kanga ma Angel robar abakin ta, Duk suka baza ido suna jiran ganin in zata motsawa, aiko kamar jira take taji an daura mata robar ruwan abakinta, ta dinga kur6arshi kamar zata shaƙe maƙoshinta har wani sauti yake badawa kwat kwat! Saboda tsabar kunyar da ta kama su haris da Naufal Sai gashi sun sadda kansu Ƙasa, Kusan rabin ruwan ta shanye, wani irin yunƙurin amai ne yazo mata, saboda rashin ƙwarin jikinta bazata iya miƙewa taje toilet ba, asaman rigar Gabriel ta shiga kwara aman, tsananin tausayinta duk ya kamasu sai sannu suke yi mata, kamar zasu ɗauke mata ciwon haka su ke ji, duk da irin aman da ta ke yi ajikinshi bai ji komai ba, ko irin ƙyanƙyamin nan, saima ƙara ruƙe ta da ya ke yi da hannayenbshi don tuni ya miƙa ma Azeeza robar ruwan, bakomai ke fita acikin bakin nata ba face kayan marmarin data sha tun jiya da zallar ruwa, Sai nishi take yi tana faman lumshe idanuwanta. "Sannu sister, Allah ya baki lafiya" acewar javed, Suma saura suka ƙara yi mata ya jiki, sam ta kasa motsa la66anta donta amsa musu, daƙyar tafara magana kamar ma sambatu ta ke yi musu tana ambaton sunan Danish da batul, miryar deeja ce tasa ta ƙoƙarin buɗe idanuwanta "Angel ki daure kidaina sanya damuwa aranki, Idan kina yin hakan ba ƙaramin raunata mata zuciyoyin mu kike yi ba, ke da kika saba ƙarfafa mana gwiwa, amma yau kece kike neman zaucewa saboda rashin su, kowa ya jure amma kin gaza, Ya ki ke so muyi"? Idanuwanta acike tab da ƙwalla tayi mata maganar. Cizon la66a ta ta yi ba tare data iya furta mata komai ba, ruwan hannun Azeeza ya kuma kar6a Ya kuskure mata bakinta dashi, tare da wanke mata fuskarta, Kafin ya miƙa ma Azeeza robar tasa hannu ta kar6a, "Akwai sauran abinci"? Yai tambayar yana kallon su, har suna hada baki wurin rabka salati suna faɗin"Mun manta Bamu ɗebi abincin ba, gashi giants sun tafi dashi" Kamar zasu fashe da kuka. Chinonsu dake sauraronsu shida jamima, jin suna neman abinci yasa Suka nufi ƙarƙashin gadon Batul atare suka ruƙo hannun kwandon, suka nufo wurinsu, tunkan su ƙaraso Ƴan uwan nasu suka ga uban tulun abincin da suka ajiye musu, Wani irin farin Cikine ya lullu6e su, Ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, Bakin parveen washe da annuri tace"Kai ba dai kune ku ka ɗebi abincin nan ba"? Har suna haɗa baki wurin furta"Mune nan muka ajiye shi" with proud su kai maganar, suna ƙarasowa parveen ta kar6i kwandon daga hannunsu ta ruƙe shi, tace da Azeeza ta ɗauko Mayafi da zasu goge aman da Angel tay, ta masa mata da toh, ta juya ta nufi akwatin kayansu kafin ta dawo Gabriel yace ta miƙo ma shi abunda zai fara bata ta ci. Zura hannu tayi cikin kwandon ta ɗauko meat balls ta miƙa mashi, ya kar6a ya soma bata abaki tana ci, ba ƙaramin daɗin shi su ka ji ba ganin yadda ta zaƙe tana ci. Dawowa Azeeza tai hannunta ruƙe da ɗan mayafi ta shiga goge mashi aman da Angel ta yi a jikin vest dinsa, da saman laps ɗinsa, bayan ta kammala tace mashi ya curo mata taje ta wanke mashi, murmushi yaɗan saki tare da kallon ta yace"bakya gajiya da yi min wanki Azeeza, kibar shi zan wanke da da kaina" maƙe mashi kafaɗa tai alamar bazata bari ba, yace toh bari na ƙarasa bata abincin, sai na baki rigar, sai da ya kammala bata ya kwantar da Angel kamar me bacci ta lumshe idanuwanta, hankalinsu ba ƙaramin kwanciya yai ba, Kowa ya nufi gadon shi ya zauna, parveen ta ɗauki kwandon taje ta ajiye musu a ƙarƙashin gado, miƙewa Gabriel yai daga gefen gadonta, Ya tu6e rigar jikin shi ya miƙa ma azeeza tasa hannu ta kar6a, ta nufi toilet shima yabi bayanta don ya watsa ruwa ma jikinsa. Bacci mai daɗi ya ɗauki Angel, Su majnun dake shirin yin wasa atsakar ɗakinsu, parveen ta lalla6asu akan su yi shiru kada su tada Angel tunda sun ga bata da lafiya, suka amsa mata da toh, Kafin marece yai kowannansu na zaune, wasu sun ɗan kishingiɗa da niyar bacci ya ɗauke su, rabi da kwatansu idanuwansu arufe yake, duk don saboda Angel sunyi tsif babu mai magana, gudun kada su katse mata baccin ta. 💔PRISONERS💔 Kunnuwansu ne suka soma jiyo musu motsin buɗe ɗakin su, Ras gabansu Ya faɗi ba tare da sanin dalilin hakan ba, kusan atare kowannansu Ya buɗe idanuwanshi Hankalinsu gaba ɗaya ya koma Kan staircases ɗin, Jira suke suga waye zai shigo ko wani ne za'a dawo musu dashi tunda an riga an kawo musu abinci, Yadda suke zazzare idanuwansu akan ƙafafuwan masu shigowa tamkar ƙwayar idanuwansu zasu faɗo ƙasa, Bakowa bace face tsohuwa Zafreen Hannunta ruƙe da sanda cikin shigarta ta jajayen kaya, Rabin fuskarta rufe yake, Iya idanuwanta ne awaje, Hankalin su ba ƙaramin tashi yai ba, Abayanta Wasu Gabza gabzan Giants ne Su biyu garada masu ɗauke da Star 2 agaban baƙar rigar jikinsu, Takun tafiyarsu yadda kasan na wani namun dawa. Wahalallan yawu kowannansu Ya haɗiya, hakanan suka dinga jin bugun zuciyarsu na hauhawa, Chinonso dake ta tsalle tsalle ganinsu yasa shi yin saurin nufar gadon parveen ya haye ya zauna gefenta hada ɗaura kanshi saman kafaɗar ta, Azeeza kuwa cikin sanɗa ta duro daga saman gadon ta faɗa ƙarƙashinsa ta la6e jikinta nata kerma, ganin ta 6oye yasa jamima lalla6awa itama ta sauko daga saman gadonta, ta shige ƙarƙashi. sauran kuwa ba wanda ya motsa kowa yasha jinin jikinsa. Lokacin da mai girma tsohuwa Zafreen ta ƙaraso Tsakiyar ɗakin nasu, Sai kowannansu ya sadda kanshi ƙasa ba tare da sun furta komai ba, ɗaya bayan ɗaya take binsu da kallo, duk sun kame kansu. "Fatan na same ku lafiya" tai tambayar tana kallon fuskokinsu, wasu daga cikinsu ne suka samu damar amsa mata da cewa"Muna lafiya" tace"tsawon lokaci banzo na duba jikokina ba, saboda uzurirrika da suka yi min yawa, sai yau na samu damar leƙo wa, hope you're happy to see me" kamar waɗanda aka ma dole haka suka furta mata"eh" Jinjina kai ta ɗanyi yayin da take cigaba da binsu da kallo kafin ta tsayar da idanuwanta akan fuskar haris Ya ɗaure fuskarshi sosai, Idonshi na kallon ƙas "Zuwan nawa ba lallai bane yayi maku daɗi ba, domin kuwa nazo ne na raba ku da zaratan samarin dake a cikin ku" a firgice suka ɗago suna kallonta la66ansu na kerma ba tare da wani ya iya furta wani abu. "Haris, Mubeen, Naufal, Javed, and Gabriel, A kan ku nake magana, Ba'a ta6a zuwa an ɗauke ku ba, wannan karan kurkukun ƙaddara ya buƙace ku, Don haka ba tare da 6ata lokaci ba, kowannan ku ya sauko daga saman gadon shi, A jere zaku tafi," A matuƙar ruɗe su parveen ke kallonsu, wani iko na Allah babu wanda ya musa acikinsu, Kamar yadda ta basu umarni haka suka sauko a jere suka nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, Sai waiwayon ƴan uwansu suke yi, idanuwan kowannansu cike tab da kwalla kai daga gani bada son ransu suke yin tafiyar ba, Sarrafa su aka yi, Hankalin Deeja idan ya yi duba toh ya tashi, Ba ita kaɗai ba hatta sauran matan da ke acikin su, Gashi sun gaza ɗaga koda yatsan su, Sai hawayen da ke gangarowa ta cikin idanuwansu. "Albino, Follow their back" tai maganar ba tare da ta juya ta kalli inda chinonso yake zaune gefen parveen, Jikinshi nata kerma ya sauko daga saman gadon idon parveen akanshi, Yana tafiya yana waiwayonta kamar zaiyi tuntu6e, ahaka harya haura saman starcases ɗin Yabi bayansu Haris, Tashin hankalin da ba'a sama shi date! Kaf an kwashe mazansu, Cikin su 20 yanzu saura mutun goma sha ɗaya, Shin Ina za'a kai su haris? Tsayar da idanuwanta ta yi akan gadon Angel dake ta sharar bacci, babu alamun zata farka, "Ba'a san ƙaddarar kurkuku da rauni ba, tana bacci gwanin ban sha'awa, nan badajimawa ba, zamu buƙace ki" Tayi maganar tare da matsawa dab da gadon Angel Ta ɗaura sandarta asaman ƙafarta, Nan take angel tayi wani irin juyi ta fuskanci ceilling ba tare data farka daga baccin ba, A saman ƙirjinta zafreen ta ɗaura sandar hannunta Saitin zuciyarta, Wani irin numfashi Angel ta shiga fitarwa ahargitse, Su Deeja dake kallon abunda ke faruwa kamar su ɗaura hannu aka su fasa ihu, Sai dai kash babu mai iya motsawa a cikinsu, Sai da Angel tagama banƙarewa kamar zata koma zombie, tukunna tsohuwa zafreen ta sauke sandar daga saman ƙirjinta. 💋PRISONERS💋 A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kan fuskarta Angel, ta mayar dasu kan fuskokinsu Parveen da suka jiƙe sharkaf da hawaye, La66ansu sai kerma suke yi kamar waɗanda sanyi ya kama. "Tun da ku ka taso a gidan kurkukun nan ba ku ta6a gabza faɗa a tsakanin ku ba, kullum kuna a cikin farin ciki, ba'a ta6a samun prisoners masu ƴanci irin ku ba, Prison ta gatanta ku, Sai dai kash a dokar gidan kurkukun ƙaddara prisoners basu da ƴan cin kansu, bamu amince ma wani daga cikin ku ya ji daɗin rayuwar shi ba, yakamata ace a yanzu kun yi bankwana da farin ciki, fatan an fahimce ni" tai maganar tana binsu da shu'umin kallo. kamar ta yi magana da duwatsu, babu wanda ya tanka mata, Wata ƴar iskar dariya zafreen ta saki tare da cewa"Dama na sani ba za ku Iya magana ba, saboda ban baku iznin yin ta ba," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa Giants ɗin da ke abayanta suka take mata baya, Tana tafiya Cikin ƙasaita, sai da ta kai bakin matakalar benan ta ɗan dakata da yin tafiyar suma Giants ɗin suka tsaya da yin tafiyar, magana ta soma yi masu ba tare da ta juyo ta kalle su ba. "Idan ƴar uwar ku ta farka, ku isar min da saƙon gaisuwata agare ta, nabarku lafiya" tana ƙarasa yin maganar tasa kai ta fuce daga cikin ɗakin tare da masu take mata baya. Fitar su keda Wuya! Sautin rufe ƙopar ya fargar dasu, a firgice su ke kallon kallo a tsakanin su, fuskokin su ɗauke da matsananciyar damuwa, kukan ma yaƙi zuwa masu sai hawayen da ke ta wanke fuskokin su, tsananin tausayin kansu ne ya kama su, wannan wata irin rayuwace suna ji suna gani anyi masu yankar ƙauna An rabasu da ƴan uwansu, babu mai iya magana acikinsu, saboda tsabar takaici da baƙin cikin da su ke ji, Azeeza da ke la6e ƙarƙashin gado, tasha kuka kamar ranta zai fita, ta ƙanƙame jikinta da ke ta kerma tarasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, itama jamima tana nan ƙarƙashin gadonta bata motsa ba, ta dai ji duk maganganun da tsohuwa zafreen tayi acikin ɗakin su, sai faman zare idanuwanta ta ke yi. Yunƙurin buɗe baki deeja ta yi, sai dai bata kai ga furta abunda take son faɗi ba, idanuwan su, su ka sauka akan Angel da ta soma motsi tana banƙarewa, yatsun hannayenta nata kerma, wani irin gurnani take fitarwa da huci, Nan take maganar tsohuwa zafreen ta faɗo musu aransu, wani irin mugun tsoro ne Ya kamasu, la66an Deeja na kerma tace dasu"ku tashi mu 6oye in ba haka ba, Angel zata iya cutar damu......" kafin wani daga cikin su ya kuma furta wata kalma, Angel ta duro daga saman gadonta Yadda kasan gardin ƙato, facial muscles ɗinta har kerma su ke yi, launin ƙwayar idanuwanta sun 6ace 6at sai farin, Har wani gyara wuyanta ta ke yi, tana banƙare ƙirjinta da bayanta, gadan gadan ta nufo gadajen su, aiko jiki na 6ari Suka soma ƙoƙarin saukowa don su nemi wurin 6uya, Kamar walƙiya deeja taga Angel agabanta, Damƙar wuyanta tai tare da wujijjiga ta, kafin ta ɗaga ta da hannu ɗaya ta buga ta ga ƙasa, nan take deeja ta suma, ganin hakan yasa hankalin sauran yai matuƙar tashi, da gudu Parveen ta nufi sashen toilet ita da Hibba da Rubina da niyar su 6oye, kafin su kai ga ƙarasawa jikin ƙopar ta riga su isa, sai dai suka ganta agabansu, Hannu biyu tasa ta shaƙi wuyan Parveen dana hibba, Ta ɗaga su sama, suna ta kuka kamar ransu zai fita, Rubina na ƙoƙarin bi ta gefe ta shige, aiko ta sanya ƙafarta ɗaya ta taɗiyeta, kanta ya bugu da ƙasa jini harta hanci, Innallahi wa'inna ilaihirraji'un. Basu ta6a ganin tashin hankali makamancin na yau ba, Angel bata ji bata gani, bugun mutuwa take nakaɗa musu, ko da ta ɗaga su pareen da hannayenta, A saman floor ta maka su, babu wanda hancinsa baiyi bleeding ba a cikinsu, saboda wani irin ƙarfine irin na dawakai, idan ta daki mutun dukkan sassan jikin shi ke amsawa. Waro ido waje Hanna da sauran su ka yi, kowannan su Ya shiga ja da baya suna a jere tsakiyar ɗakin Jikin su nata kerma muryar su a tsananin tsorace suke roƙonta suna faɗin Dan Allah Angel kada ki kashe mu, ki tausaya mana halin da mu ke a ciki, laifin me muka yi maki? Yau ke da kanki kike neman halaka mu! Magana suke yi amma sam babu alamun tana jinsu, abunda basu sani na, A halin yanzu Angel ba ita ɗaya bace. Ganin maƙiya ta ke yi musu, Burinta kawai ta kashe su har Lahira, shin ina labarin azeeza da jamima dake a la6e ƙarƙashin gado, kowannan su yasha jinin jikinshi, tsabar tsoro yahana su motsa, Sai da suka ji kukan su Hannah ya cika ɗakin, tukunna suka soma ƙoƙarin fitowa, cikin tashin Hankali yasmin da ta hango kan azeeza dana jamima dake shirin fitowa ta ƙarƙashin gado, ta dinga girgiza musu kai alamar karsu fito su koma, da hannu ta dinga yi masu alamar su koma ƙarƙashin gadon. Ƙwaƙƙwarar damƙa Angel ta kai ma wuyan Eve da Yasmin, ta juyar dasu su ka fuskanci bango, ta daddage ta buga kansu jikin sa, tuni jininsu ya wanke jikin bangon a ƙasa suka sulale kowannan su ba numfashi, Mayar da idanuwanta ta yi akan Sarah da Hanna da suka rage, Sai faman zazzare idanuwansu suke yi, Zufa ta ko'ina ta shiga tsastsafo musu, sai kuka su ke yi haɗi da yi mata magiya, Sai kewaye cikin ɗakin su ke yi, Ganin da gaske fa ba ƙyale su zata yi ba, hakan yasa Sarah ta watsa da gudu zata shige sashen toilet ɗinsu, sai dai kafin ta ƙarasa, Taji an damƙi ƙafafuwanta ruƙo bana wasa ba, Gaba ɗaya ta kife saman floor Kanta ya daku, ƙugun ta ya bada wani irin sauti ruƙuƙus. Hanna ce ta yi saura a tsakiyar ɗakin, tsautsayi ya fiddo da jamimah, Karaf akan idon Hanna tana ƙoƙarin buɗe baki tace mata ta koma ƙarƙashin gadon, kwatsam Angel ta nufo wurin Jamima, tana tafiya tamkar damusa har wani gyara wuyanta take yi, tana lashe baki, da gudun gaske Hanna ta ɗauke jamima ajikinta ta ƙanƙame ta tana faɗin "Dan Allah kada ki yi mata komai, Kin ga ita ƙarama ce na roƙe ki, idan ma bugun ne ki haɗa da nata ki yi mini, amma ki ƙyale jamima, zata iya rasa ranta....." kafin ta ƙarasa maganar, Angel ta ware hannayenta biyu ta yi masu ƙwaƙƙwaran ruƙo, da hannar da jamimar da ta rungume a jikinta, Dukkan su ta haɗa, ta cuccu6esu ta daddage ta maka su ga saman floor, nan hake haƙorin jamima ɗaya ya 6allo daga bakinta jaga jaga da jini, har saman kumatunta, kuka tamkar ranta zai fita, tuni ta saki fitsari ta cikin wandonta saboda tsabar raɗaɗin da ta ji. Hannah da ke ruƙe da ita tuni ta sume, kunnuwanta ne suka dinga motsi suna jiyo mata shessheƙar kukan mutun, nan fa ta shiga neman wanene, Gadajen ta dinga bi tana ɗaɗɗaga su har Allah Ya kawo ta kan gadon da azeeza ta 6oye, Tana ɗaga gadon idanuwanta suka sauka akan azeeza da ke ta yin kerma ta ƙanƙame jikinta, sam ta kasa ɗagowa ta yi tozali da fuskar Angel. Gyara wuyan ta ta yi kamar yana yi mata ƙaiƙayi har wani sauti ya bada muƙus, A tsananin tsorace Azeeza ta soma yin rarrafe don ta gudu daga wurin, aiko ta daddage ta ɗaura ƙafarta ɗaya saman yatsun hannun azeeza ta ta ke su ta murje duk suka faffashe, jini ya soma tsastsafowa, a nan ƙasa ta baje a sume, wata irin mahaukaciyar dariya Angel ta fashe da ita. Sautin kukan jamimah daya karaɗe cikin ɗakin nasu ne ya janyo hankalin Angel kanta, ita kaɗai ce bata kai ga suma ba, Lashe baki ta yi tare da Nufar inda jamima take a kwance ƙasa cikin mawuyacin hali, Kafin ta ƙarasa gare ta ta ji an damƙi ƙafafuwanta, Sai dai wanda ya ruƙe ƙafafuwan nata, ya gaza Kifar da ita ƙasa saboda tsabar ƙarfinta. A sukwane ta jiyo da kanta don taga wani isasshen ne Wannan mai ƙarfin halin, Karaf idanuwanta suka sauka akan fuskar Deeja wadda hawaye suka wanke ta, muryarta cikin shessheƙar kuka ta ke faɗin Angel kin bamu mamaki yau ke da kan ki ki ke neman kashe mu, ashe dama ba ƙaunar mu ki ke yi ba, ban ta6a tunanin zaki iya raunata wani a cikin mu ba....." Ɗaga ƙafarta ɗaya ta yi da niyar ta murje kan deeja da ƙarfi deeja ta ambaci"La'ila ha'illah anta subhanaka inni kuntu minazzalimin! " shi kaɗai ne abunda ta iya furtawa la66anta na kerma. tamkar an daki kanta da guduma, haka ta sanya hannayenta biyu ta daddafe kanta, wani irin jiri ta soma gani acikin idanuwanta, muryarta na rawa ta shiga ambaton "La Hawla Wala Quwwata Illa Billah" Jikinta ne ya soma jijjiga, ta runtse idanuwanta saboda wata irin sarawa da kanta ke yi mata, Deeja nata kallonta, tangal tangal ta soma yi zata faɗi ƙasa. Allah sarki duk da irin abunda ta yi musu hakan bai hana Deeja yunƙurawa ta miƙe tare da yin saurin tallabo Angel don kada ta faɗi ƙasa ta bugu, A hankali ta zaunar da ita, tare da zuƙunnawa gefenta, tana ambaton sunanta cikin sanyin murya ta wanda ya karaya"Angel, Allah yasa kin dawo hayyacin ki, Ni nasan ba yin kan ki bane" Tana magana hawaye nabin fuskarta, hannayenta tallabe da Angel, tsawon lokacin tun sautin kukan jamima na fita da ƙarfin shi har yakai ga disashewa, a ƙarshe ma ta sume, yanzu su biyu ne su ka rage a cikin ɗakin masu numfashi. Muryarta ƙasa ƙasa ta soma magana"idan har dagaske ne abunda ya faru ba mafarki ba, Deeja ki kashe ni, kawai in mutu, meyasa na aikata ma ku hakan? Da hannayena nabi kowannanku da jahilin bugu, duk da irin haƙurin da ku ke bani amma naƙi sauraron ku, saboda rashin imani........' girgiza kai deeja ta shiga yi tana faɗin "ba laifin ki bane Angel, Ba yin kan ki bane, ko a mafarki bana tunanin zaki iya yi mana hakan balle kuma a zahiri......" raba jikin ta ta yi daga na Deeja ta yunƙura ta miƙe jiki ba ƙwari take bin kowani 6angare na ɗakin su da kallo, bakomai ta ke gani acikin idanuwanta ba face jinin su, gasu nan a kwankwance kamar gawawwaki, Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Lamarin ya yi matuƙar girgizata, kamar mahaukaciya haka ta shiga bin hannayenta da kallo, Acikin zuciyarta kuwa tsantsar tashin hankali ne da fargaba, lokaci ɗaya ta fashe da kuka tamkar ranta zai fita, da gudun gaske ta nufi bangon ɗakin su, Deeja ta miƙe da hanzari tabi bayanta, Daddagewa ta yi ta dinga buga kanta jikin bango da niyar ta kashe kanta, bugu bana wasa ba, Goshinta da hancinta dukansu sai da suka faffashe, Zallar jininta jawur dashi ya dinga gangarowa ta saman goshinta yana wanke fuskarta, hatta la66anta bata bari ba, cizonsu ta dinga yi da haƙoranta duk ta gurgujesu, jini ya dinga tsargowa, duk yadda Deeja taso ta janye Angel daga jikin bangon abun ya faskara, Saboda bata acikin hayyacinta, takai maƙura, idanuwanta sun makance kunnuwanta basu ji, mutuwa kawai take son ta yi awannan lokacin, ta tsani kanta, tsana mara misaltuwa, zuciyarta tagama hasala. Cikin muryar kuka Deeja ke roƙonta tana faɗin ta yi hakuri tadaina cutar da kanta, saboda ba yin kanta bane abunda ya faru, tace Angel ki tsaya in yi maki bayanin abunda ya faru, kada ki kashe kan ki don Allah, idan ki ka mutu kika barni ya ki ke so inyi da raina, mu kaɗai fa muka rage da zamu iya taimakon ƴan uwan mu da su ke acikin mawuyacin hali, Ki tausayamin Angel, wayyo Allahna, Ya Allah ka kawo mana ɗauki, wannan wata irin masiface! Zubewa ta yi a saman gwiwowinta, ta ci gaba da kuka hannunta dafe da goshinta. Angel kuwa bayan tagama Wanke fuskarta da jikin jikinta, Jiri ne ya ɗebe ta, ta sulale ƙasa babu numfashi, kafin wani lokaci ɗakin nasu yai tsit, baka jin sautin hayaniyar komai, Ko'ina ka kalla a cikin ɗakin, Jinin su ne, ita kanta Deeja da ta rage idonta biyu, A gefen Angel ta kwanta idonta arufe, busassun hawaye ta ko'ina akan fuskarta, kukan zuciya take yi mai raɗaɗin haske, batasan ya za ta yi ba, ita kaɗai ta rage taya zata iya ceton rayuwar ƴan uwansu? Ita kanta ba ƙoshin lafiya gare ta ba, don ba ƙaramin dakuwa kanta yai ba, lokacin da Angel ta bugata ga ƙasa har ta sume, Allah ne ya farfaɗo da ita harta tashi. Cikin zuciyarta ta soma magana _Ya Allah bamu da kowa face kai da ka halicce mu, Angel itace silar da muka san komai agame da mahaliccin mu, ta faɗa mana cewa kana ƙaunarmu kamar yadda ka ke son sauran bayin ka, kana ganin mu kuma kafi kowa sanin halin da muke aciki, mun yi imani da kai, duk da bamu da wadataccen ilmi akan ka, Ya Allah ta tausaya mana kaji ƙan mu, ka kawo mana ƙarshen wahalar nan, rayuwar mu a ƙuntace ta ke, bamu ta6a cutar da wani ba amma mu ana azabtar da rayuwar mu, babu mai taimakon mu, babu wanda yasan da zaman mu balle a kawo mana ɗauki, muna ji muna gani ana neman halaka mu saboda rayuwar mu bata da amfani awurin su, Bafa sune silar zuwan mu duniya ba! Mu ba bayin su bane, bayin ka ne Ya Allah! Baka halicce mu don a azabtar da rayuwarmu ba face don mu bauta maka, amma meyasa waɗannan mutanan suke ƙoƙarin mayar damu dabbobin su, Ya Allah idan har dagaske kai maji roƙon bayin ka ne, Ya Allah kajiƙanmu kaji koken mu, ka kawo mana ɗauki, koda ranmu ne ka ɗauka mu koma gare ka, zaifi mana sauƙi akan wannan wulaƙantacciyar rayuwar da muke yi mara ƴan ci, Ya Allah badan halinmu, mu ci albarkacin Annabin mu Annabi muhammand (SAW) mafi soyuwa agare ka_.........." sosai ta runtse idanuwanta, ta yi zurfi acikin zancen zucin nata, ta soma jin motsin buɗe ƙopar ɗakin su acikin kunnuwanta, wani irin tsoro da firgici ne ya lullu6e ta, hakan yasa taƙi buɗe idanuwanta don taga wanene Takun tafiyar mutun ta soma ji a cikin ɗakin nasu, kamar ana kewaye ɗakin, ji take kamar ta buɗe idanuwan nata sai dai tsoro ya hana tayi hakan, tana cikin wannan Halin taji wani irin matsiyacin bacci yana fisgarta, na ban mamaki, duk yadda taso ta tsayar da kanta don kada ta runtsa hakan ya faskara don tuni yai awon gaba da ita anan inda ta ke a kwance, Tsawon lokaci Deeja tana sharar baccinta, Har dare ya nutsa, hasken saman ɗakinsu ya ɗauke Na floor lamps ɗinsu Ya kunna kanshi, Haskensu ya gauraye ko'ina tamkar da rana. A matuƙar firgice ta farka tare da ware manyan idanuwanta kan ceilling ɗin ɗakin, Zuciyarta na harbawa sama sama cike da fargaba, tunawa da ƴan uwanta ne yasa tai wuf ta miƙe a zaune, wani iko na Allah Kaf ɗinsu babu wanda ke kwance a ƙasa sai ita, duk suna asaman gadajen su, tamkar wani abu bai ta6a faruwa ba, babu ɗigon jinin mutun ɗaya daya kasance a cikin ɗakin, an goge komai babu shi, ɗakin ya koma fes ɗin shi, tsabar mamaki ne Yasa ta miƙe Jiki na kerma ta ke bin kowani gado da kallo, bacci su ke yi Hankali kwance, Jikinsu lullu6e da bargunan su, da sauri ta kalli gadon jamimah, tana a kwance Ga azeeza itama kwance saman nata gadon, Haka zalika parveen da rubina, eve and yasmin, suna kwance saman nasu gadajen Hada Sarah da hibba, uwa uba, Angel itama tana naɗe cikin bargonta tana bacci, kaɗan daga cikin ikon Allah kenan, wannan bakomai bane, Jikinta na kerma ta nufi gadon Angel ta sanya hannu tare da yaye bargon jikinta, don taga idon raunin goshinta na nan, babu jini akan fatar fuskarta, sai dai akwai alamun fashewar goshinta dana tsinin hancinta, sai la66anta, yanayinta ya nuna alamar cewa babu raɗaɗin ciwo atattare da ita, kamar an kwashe mata shi,' sakin bargon Angel ta yi tare da juyawa da sauri ta nufi gadon jamima, hannu tasa tana duba fuskarta itama babu jini, tunawa ta yi da haƙorinta data gani ɗazu a ƙasan ɗakin su, koda ta buɗe bakin ta, tabbas haƙorin ta ɗaya ya cire, sai dai babu kumburi abakinta, lamarin ya ɗaure mata kai, mamaki ne ƙarara akan fuskarta. matsawa ta yi zuwa gadon Azeeza ta yaye bargonta tare da leƙa fuskarta, ko hawaye babu, yatsun hannayenta dai ne da suka faffashe, amma babu jinin daya tsastsafo akansu, idan ka kalli ciwon kamar ya kwan biyu. Ɗaya bayan ɗaya saida Deeja tabi kowannan su ta duba shi, lafiyar su ƙalau, Babu ko zazza6i a jikin su. Deeja ta ruɗe sosai ta rasa tunanin me za ta yi game da wannan iko na Allah, har aranta ta aminta da cewa Allah ne ya ji ƙansu ya kawo musu ɗauki, sai dai ba ta san takun tafiyar wanene taji ɗazu ba, a cikin ɗakinsu, tabbas akwai wanda ya shigo. "Ruwa zan sha, maƙoshi na zafi"! Muryar Angel ce ta fargar da ta, a hanzarce ta mayar da dubanta gare ta, farkawarta Kenan daga bacci, Ko idonta bata buɗe ba, a gaggauce Deeja ta nufi ƙarƙashin gadon Batul ta ɗauko ɗaya daga ciwon bottle waters ɗin da Su Jamima suka 6oye musu ɗazu, ta nufi gadon Angel ta haye sama tare da taimaka mata ta miƙe zaune, bayan ta buɗe murfin ta kafa mata abaki, ta dinga kur6ar ruwan,' Hankalin Deeja ba ƙaramin kwanciya yai ba, bayan ta kammala ta maida murfin robar ruwan ta ajiyeta daga ƙasan gadon, kafin ta ɗago idonta akan fuskar Angel dake ƙoƙarin buɗe nata idanuwan. Ido cikin Ido suke kallon Juna ita da Deeja, muryarta na ɗan rawa ta furta"Ina Danish ya ke"! Abunda ya fito daga bakinta kenan, fuskarta ɗauke da matsananciyar damuwa ta amsa mata da cewa"Har yanzu ba a dawo dashi ba" girgiza kai Angel ta yi"ba'a dawo dashi ba, meyasa naji a jikina cewa danish ya ta6a ni!" A ruɗe Deeje ke kallonta, Jin abunda tace, tunani ta shiga yi anya Angel bata samu ta6in hankali ba? Da alama ta manta abubuwan da su ka faru, ta manta jahilin bugun da tayi musu, kamar wadda tayi loosing memory ɗinta. Ganin yadda Deeja ta tsareta da ido yasa tace"meyasa kike kallo na? Wani abu ya faru ne? Nayi ma ki tambaya baki bani amsar da zata gamsar dani ba, nifa naji Danish Ya ta6a jikina, taya zaki ce min ba a dawo dashi ba'? A ruɗe ta yi mata maganar. Deeja bata amsa mata tambayarta ba, saima ta sanya tafin hannayenta biyu ta tallabo fuskar Angel, murmushin yaƙe ne ya bayyana akan fuskarta wanda bai kai zuci ba, a hankali ta furta Alhamdulillah, Allah na gode maka, daka kawo min mafita, da yanzu bansan ya zan yi ba, Naji daɗi dana ga ƴan uwana suna bacci cikin kwanciyar hankali, na ƙara yarda cewa addinin musulunci gaskiya ne, Kuma ubangijin mu Allah maji roƙon bayinsa ne, idan su ka yi imani dashi, babu tantanma zai agaza musu a lokacin da suke cikin buƙatar taimakon shi. da alama taji daɗi sosai, da irin taimakon da Allah ya yi musu, daba don haka ba, da yanzu batasan awani awani hali zasu tsinci kan su ba, domin kuwa ba ƙaramin jiki zasu ji ba, Jinya ce zasu yi bata wasa ba, sai kowa yaji a jikin shi, musamman Jamima da haƙorinta ya 6alle, da kuma Sarah wadda aka buga ta da ƙasa qugunta ya daku, da sauran waɗanda aka buga kansu jikin bango. "Deeeja na kasa fahimtar komai, dan Allah ki yi min bayani, inaso inji meya faru ne, naji araina kamar wani abu ya faru, sai dai na kasa tunawa......" da sauri Deeja tace"in sha Allah ba za ki tuna ba" Maganar Deeja ta ɗaure mata kai, yunƙurin saukowa tai daga saman gadonta, da sauri Deeja ta ruƙo hannunta"Ina zaki je? Dare ne fa! Ki koma ki kwanta" ba tare data juyo ta kalle ta ba, tace"Toilet zan shiga" Jin haka yasa Deeja sakin hannunta, Hankalinta bai kwanta da kalaman deeja ba, shiyasa tace mata za ta shiga toilet ne don ta samu damar ƙarewa ɗakin nasu kallo, duk don ta samu ta tuna abunda ya faru, don ta fahimci cewa akwai wani abu da take 6oye mata. Tana ƙarasa saukowa daga saman gadon, kaitsaye idanuwanta suka sauka akan shimfiɗar su Haris, nan take taji gabanta yai wani irin bugu na tashin hankali, ganin babu kowa asaman gadajen su, sai bargunansu da matashin kansu, babu haris babu naufal babu javed da mubeen. A fujajen ta waiwayo tana fuskantar gadajensu Sarah, Tsayar da idanuwanta ta yi akan shimfiɗar Gabriel wayam babu kowa saman gadon shi, zuciyarta a hautsine ta wurga eye balls ɗinta kan gadon Majnoon, babu kowa, tsabar ruɗanin da ta shiga ya hana ta furta komai, Tuni deeja ta lura da yanayin da ta shiga. saukowa ta yi daga saman gadon, ta nufi Inda Angel ta ke atsaye ta ɗaura hannunta ɗaya saman kafaɗarta, idanuwan ta acike tab da ƙwalla ta soma magana "Ko ban faɗa maki ba, nasan kin riga da kin fahimci komai, abunda zuciyarki take faɗa maki gaskiya ne ba ƙarya ba, sai dai inaso mu rungumi ƙaddarar mu, mu yi haƙuri mu daure, tun da ko munyi kukan ba abunda zai haddasa mana face ciwon kai, damuwa bazata ta6a sanyawa adawo mana da ƴan uwan mu ba, haƙurin nan dai shine magani, Gaba ɗaya maganganun dana faɗa maki ayanzu, a wurinki na saba jinsu, don haka ina roƙonki, kada kice zaki sanya damuwa aranki, dama ba ƙoshin lafiya gare ki ba, kuma kinga ƴan uwan mu suma suna acikin mawuyacin hali, mune kaɗai muka rage waɗanda za su iya kwantar musu da hankali, idan ba haka ba, dukkan mu zamu fuskanci matsala ne........." tun kan ta ƙarasa maganar, Angel ta daddafe kanta saboda wani irin jiri da ta ke gani, ba arziƙi ta zunna ƙasa ta yi zaman cin tuwo, yayin da hawaye masu ɗumi ke bin fuskarta. "Deeja ki faɗamin! Meya faru dasu Haris? Tafiya aka yi dasu ne? Inaso na sani"! Daƙyar take magana cikin raunin na murya. Ita kanta Deeja daurewa kawai take yi, "Zan faɗa maki Angel, amma kiyi min alƙawarin, ba zaki sanya damuwa aranki ba....." jinjina kai Angel ta yi tare da cewa "Nayi maki alƙawari" numfasawa deeja tayi Cikin ƙanƙanin lokaci ta labarta mata dukkan abunda ya faru, tun daga kan zuwan tsohuwa Zafreen, har izuwa sandar data ɗaura mata asaman ƙirjinta da kuma abunda ya faru bayan tafiyar zafreen!" Lamarin yayi matuƙar girgizata, Hankalinta yai mugun tashi, zuciyarta har wani tafarfasa take yi tamkar zata 6allo daga ƙirjinta saboda tsabar bugun da take yi, Idanuwanta sun kaɗa launinsu ya ciza sosai. Hannu biyu tasa ta dafe kanta, muryarta na kerma ta shiga ambaton "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un! Duk addu'ar da tazo bakinta karanto ta ta ke yi cikin fitar hayyacin duk don ta samu ta tsayar da zuciyarta daga tafarfasar da take yi mata, ta kuma samu sassaucin raɗaɗin da take ji, idan ba haka ba, ita kanta bazata Iya sarrafa ta ba, zata ƙara yunƙurin kashe kanta ne, kamar yarda ta yi ɗazu. Deeja sai tausarta ta ke yi tana bata baki akan su yi haƙuri, su lallashi junansu, tun da basu da yadda zasuyi, a ƙalla sun ɗauki kusan minatuna talatin, zuƙunne a ƙasa suna jimami, a ƙarshe ma sai suka rungume junansu, hakan da su ka yi ba ƙaramin sanyaya musu zuciyarsu ya yi ba. Raba jikin su su kayi daga na juna, idanuwansu sunyi luhu luhu da su, "Angel yakamata muje mu kwanta, mu yi bacci muma, inyaso gobe da safe idan su azeeza suka farko, sai mu ƙara duba jikin su, wlh na tausaya musu sosai, Musamman Jamima da ta rasa haƙorinta ɗaya......" Muryar Angel ce ta katse ta"babu komai akwai Allah, akwai kuma mutuwa da hisabi, ae Allah ba azzalumin bawansa bane, Yana ji yana gani, a sannu zai bi mana haƙƙin mu, naji zafin tafiya da aka yi dasu haris, saboda rashin imani da tausayi hada majnoon suka tafi ƙaramin yaron da ba cikakken hankali ne dashi ba, Allah kaɗai yasan ina zasu kai su, me zasu yi masu, Hmmmmm, in sha Allah bazan gaji dayi musu addu'a ba, Allah ya kare su aduk inda zasu kasance, duk runtsi duk wuya idan suna da rabon ƙara shan ruwa aduniya, duk irin azabtarwar da zasu yi masu, zasu rayu ne! Bansani ba zamu ƙara haɗuwa da su ko kuwa shikenan silar rabuwar mu kenan........" ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta, hakan yasa ta kasa ƙarasa maganar, ta ɗan dakata tana mayar da nunfashi, kafin ta samu ta dai dai ta maganarta, "Zan yi mana addu'a dukkan mu idan mutuwa sauƙi ce agare mu, Allah ya ɗauki ran mu mu huta, don banga amfanin irin wannan rayuwar da mu ke yi ba, Da farko na yi mana kwaɗayin mu samu ƙopar da zamu gudu daga cikin kurkukun nan ko dan ku ɗanɗani rayuwar ƴanci, amma yanzu na zauna nayi wani tunani, Rayuwar tamu gaba ɗaya atare da kurkukun ƙaddara take, saboda ko mun samu hanyar tsira zasu cigaba da bibiyar mu ne, saboda waɗanda suka sadaukar damu na jinin mu ne! Suna atare da mu, ba zama arasa samun wasu daga Cikin su ba acikin kurkukun ƙaddarar nan! Duniyar nan acike take da ruɗani, wai har na jinin ka ne zai sadaukar da kai? mahaifi ko mahaifiya! Ko wani danginka! Idan har hakane kuwa banga abunso ga rayuwar duniyar nan ba! Saboda babu gaskiya acikinta, halaka ce tsantsa, son zuciya da kwaɗayin abun duniya yasa mutane sun rufe idonsu suna aikata abunda suka ga dama, sun manta cewa dukkan mai rai mamaci ne, zamu yi kwanciyar ƙabari, sannan za'a tada mu domin yin hisabi, Ga duk mai hankali yasan cewa rayuwar duniyar nan bakomai bace, Duk wani abu daka mallaka da zarar ka mutu zaka rasa shi! dukansu kaf ba wanda za'a rufe ka da su acikin ƙabarinka, Iya halinka ne kawai zai cece ka, to wai su irin waɗannan mutanan makafi ne? Ko kuwa kurame ne? Abun da zai ba ka mamaki mafi rinjayen su, Sun sani su ke ta ke sanin, ko dabba tafisu tunani mai kyau, zuciya ta bushe, sun mayar da zalunci hanyar cin abincin su, duniya kawai suka sa gaba, Anata sharholiya an manta da mutuwa.......wa'iya zubillah! Ya Allah ka karemu daga fadawa hannun irin waɗannan azzaluman mutanan, Ya Allah ka shiga tsakanin mugu dana gari......" Ruƙo hannunta Deeja tayi acikin nata"Angel, Bana so kiyi mana fatan mutuwa, saboda inaso mu samu hanyar tsira kodan mu tona asirin azzaluman mutanan da su ka cutar da rayuwar mu, ke da kan ki kika faɗa mana cewa kada mu fidda rai da rahamar ubangiji duk runtsi duk wuya, Angel idan muka mutu ki tuna bamu kaɗai bane akwai sauran ƴan uwan mu dayawa acikin kurkukun nan, bayan su akwai waɗanda ake shirin kawowa cikin sa, Idan har aka cigaba da aikata zaluncin nan har yaushe ne zai tsaya? Daga ni har ke babu wanda yasan tun lokacin da aka gina kurkukun ƙaddara, Dukan mu mun tsinci kan mu ne acikin sa ne......." hawaye ta ko'ina kan fuskarta taci gaba da cewa"Inaso mu kafa tarihi, agidan kurkukun ƙaddara, duk da nasan ba lallai bane mu rayu gaba ɗayan mu ba, amma raina yana bani cewar wasu zasu iya ku6uta, daga ciki har dake Angel nake sanyawa ran fita" dakatawa ta yi da yin maganar idonta akan fuskar Angel da ke kallonta, ajiyar zuciya ta sauke tare da cigaba da yin maganar "Tarihin da nake so mu kafa shine mu kawo ƙarshen Mugayen shuwagabannin Gidan kurkukun ƙaddara, Mu tabbatar asirinsu ya tonu, inaso inga ranar da za'a rugurguza ginin nan ya dagargaje ya zamana babu shi adoron duniyar nan, zan roƙi Allah yabamu ikon aiwatar da hakan! Domin kuwa saida iznin shi ne komai zai wakana......." tun da Deeja ta soma magana Angel ta tsareta da ido, tsantsar mamaki ne ya kamata, yanayin yadda Deeja take yin maganar da ƙwarin gwiwarta, ya yi matuƙar ɗaure mata kai, zuciyar imani ta shige ta, yayin da ita take ƙoƙarin sarewa ta fidda rai da fita sai gashi Deeja tana ƙarfafa musu gwiwa, ko a mafarki bata ta6a tunanin Deeja zata iya tsara kalami irin haka ba, Tabbas ta samu wani ƙwarin gwiwar awurinta, nan take taji cewa zata Cigaba da nema masu hanyar fita, kodan su cimma burinsu na kawo ƙarshen kurkukun ƙaddara!! "Zamu iya Angel in sha Allah"! Fuskar Angel ɗauke da murmushi ta ɗan jinjina kanta tare da cewa"Kin faɗi gaskiya, zamu Iya bi'iznillahi, mune zamu kawo ƙarshen KURKUKUN ƘADDARA"! Da alama su Deeja sun manta cewa duk abunda su ke tattaunawa a tsakanin su, Jami'an Gidan kurkukun ƙaddara suna kallon su Sun ɗauki tsawon lokaci zaune a ƙasa suna ɗaukarwa junansu alƙawari, har saida dare ya tsala tukunna, Suka miƙe atare jiki duk ba ƙwari, hannunsu ruƙe dana juna suka nufi gadajen su parveen. ɗaya bayan ɗaya Angel take binsu da kallo, tsananin tausayin su ne ya kamata ganin irin illar da ta yi masu, babban abunda ta ke ji ma fargaba kada su farka da safe su tuhume ta akan abunda ba laifinta bane, tuna wannan yasa hawaye suka wanke mata fuskarta, Deeja sai tausarta take yi daƙyar ta samu ta shawo kanta, Bayan ta gama kallon su tabi su da addu'a, tana tottofa musu saman bargunansu. Sallama su ka yiwa juna ita da Deeja, akan idonta deeja ta nufi gadonta ta kwanta. wuce wa tayi zuwa gadon Jamimah, A hankali ta haye tare da kwantawa gefenta, tasa hannu ta janyota jikinta, ta rungumeta sosai, saboda tsananin tsauyinta da take ji, baiwar Allah bata ji ba, bata gani ba, ta cire mata haƙori ɗaya, dole taji ba daɗi, ga azeeza da ta gurjewa yatsun hannayenta, kowa dai da irin tabon da tabar mashi, taji tsanar tsohuwa zafreeen fiye da tunanin me tunani saboda itace silar komai! ta kwana da tunanin abubuwan da su ka faru awannan ranar, Bakomai yafi tsaya mata arai ba, face yarda aka goge kowani jini na jikinsu da wanda ya zuba a ɗakin su, aka kuma maida su saman gadajen su, wannan abun ya yi matuƙar ɗaure mata kai tun lokacin da Deeja ta sanar da ita, Shin wanene yayi musu hakan❗❓ Deeja ta sanar da ita cewa Tajiyo takun takalmin mutun acikin ɗakinsu tsoro da firgici ne su ka hana ta buɗe ido taga wanene har saida baccin ya yi awon gaba da ita........ (Nima kuma nayi awon gaba da alƙalamina) 💋PRISONERS💋 A washe garin ranar babu wanda ya farka daga cikin su, tun jiya su ke ta sharar baccin su, jamimah ce ta fara mutsu mutsun buɗe idanuwanta gaba ɗaya atakure ta ke A jikin Angel ta matse ta kamar zata mayar ita cikin cikinta, hada zufa a jikinta, shessheƙar ku ka ta soma yi tana ta faman ƙoƙarin janye jikin ta daga na wanda ya rungumeta ko ta samu ta miƙe. sautin kukanta ne ya farkar da Angel a hankali ta buɗe idanuwanta waɗanda su ka kumbura, muryar jamimah ce ta janyo hankalin ta "ni asake ni, wai wanene ya matse ni," Da sauri Angel ta zame hannayenta da ga jikin Jamima, ta yi zumbur ta miƙe zaune, ɗagowa jamimah ta yi fuskarta jawur da ita ƴan kumatun sun yi suntum da su, Suna haɗa ido da Angel, ta zazzaro idanuwanta waje jikinta ya hau kerma a gigice ta duro daga saman gadon tare da ɗaura hannayenta sama ta fashe da wani irin matsanancin kuka na tashin hankali. Lamarin yayi matuƙar girgiza Angel tasan bai wuci a bun da ya faru jiya bane yasa ta tsorata da ita, Jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba, Saukowa tai daga saman gadonta tana tunkarar jamima tare da miƙa mata hannu muryarta na ɗan rawa tace"Jamima nice fa Angel ɗin ki, meyasa kike gudu na"? Girgiza kai ta dinga ki bakinta ƙumshe da kuka ta shiga faɗin"Ni ba Angel ɗita bace, Saboda baki son mu, Jiya kamar zaki kashe ni, kika cire min haƙorina,' ta yi maganar tare da zura yatsanta ɗaya cikin bakinta don taji idan dagaske ba haƙorin, rushewa ta kuma yi na wani sabon kukan jin gi6in da ke a bakinta, Tuni hawaye sun wanke fuskar Angel, tsananin tausayinta ne ya kamata. "Bana son ki Angel! i hate you! I don't want to see you, because you're not human, you're a genie!" Cikin shessheƙar ku ka Jamimah ta furta maganar, yayin da ta ke ƙoƙarin ja da baya ganin Angel na tunkaro ta, A jikin bango Jamima ta manne tana girgiza mata kai, alamar karta kuskura tazo wurin ta, zuciyar Angel ba ƙaramar karaya ta yi ba, ta rasa ina zata tsoma ranta ne taji daɗi, a gaban jamimah ta zuƙunna saman gwiwowinta, ba tare da ta iya furta komai ba. Duk wannan abun da ke faruwa akan kunnuwan masu bacci waɗanda tuni sun jima da farkawa tun lokacin da Jamima ta rushe da kuka, Sautin ya daki dodon kunnuwan su, Tashin su kenan, hankalinsu gaba ɗaya akan Jamima da Angel, Azeeza ce ta soma shessheƙar kuka tana zaune saman gadonta, idanuwanta akan yatsun hannayenta da su ka jigata, duk sun faffashe sai sai babu ɗigon jini ko raɗaɗi, muryar ta adisashe ta ke yin magana. "Na gaza yarda da abunda idanuwana su ka nuna min, bazan zargi Angel ba, amma meyasa ta take min yatsun hannuna? Meyasa ta buge mu? Laifin me mu ka mata"? Sosai ta fashe da matsanancin ku ka, Hakan ba ƙaramin rikita Angel yai ba, tana fama da jamimah ga su Azeeza sun ɗauka su ma. Idanuwan kowannan su acike yake tab da ƙwalla, zuciyoyin su ba ƙaramin karaya su ka yi ba, Muryar Hanna tamkar zata fashe da kuka tace"Duk irin haƙurin da nake baki Angel baki saurareni ba, har cewa nayi ki haɗa da bugun da za ki yi ma jamimah ki yi min amma shine kika ƙi saurarena, ki ka haɗamu duka ni da ita, kika buga mu ƙasa har saida haƙorinta ya cire, ko ita baki tausaya mawa ba, ita da ta ke ƙarama" Gaba ɗaya suna neman zautar da ita, sam ta kasa juyawa ta kallesu saboda nauyin haɗa ido da su ta ke ji, still bata motsa ba, tana a zuƙunne gaban Jamima dake ta shessheƙar kuka, Abun ya ta6a zuciyoyin su, sun kasa fahimtar cewa ba yin kanta bane, dama zai yi wuya su fahimci hakan, kawai sun yi imani da abunda idanuwansu suka nuna musu ne. "Da yanzu na mutu babu ni babu ƙara cin abinci, mu fa biyu Angel ta haɗa dani da hibba ta buga mu ga ƙasa, hakan bai isheta ba, sai da ta taɗiye ƙafar rubina ta kife ƙasa tukunna hankalinta ya kwanta.........." parveen bata ƙarasa maganar ba saboda kukan daya ciyota, Angel taga haza, Zuciyarta sai tafarfasa ta ke yi, ta runtse idanuwanta sosai, tana sauraron kowannan su "Har yanzu ƙuguna ba dai dai ya ke ba, ni banma san ya akai na dawo saman gado ba, Angel taso naƙasa min rayuwa" Acewar Sarah, tana magana tana dafe qugunta da hannu ɗaya........ Eve da ke ta matse ƙwalla ido jawur tace"Haka muma ta haɗa kawunan mu nida Yasmin Ta buga mu jikin bango, daga nan ma ni ban ƙara sanin meya faru ba" Sai da ta kammala sauraron kowan nan su, gwiwowinta duk sun sage, har wani jiri ta ke gani acikin idanuwanta, sunan Allah take ta ambato acikin bakinta, a daddafe ta samu ta miƙe tsaye tare da juyawa tana fuskantar su. A Yayin da hawaye ke cigaba da yin sintiri saman fuskarta, sai faman jinjina kanta ta ke yi tana kallonsu da rinannun idanuwanta, babu wanda ya motsa daga saman gadon shi, duk suna a zaune suna kallonta, Kamar yarda idanuwan ta ke fitar da hawaye haka suma nasu ke tsiyaya, magana ta ke so ta yi amma ta kasa, wani irin raɗaɗi ta ke ji acan cikin zuciyarta, ga maƙoshinta da ke a bushe sai ƙaiƙayi ya ke mata. "Kun yarda cewa ANGEL zata iya cutar da ku!"? Muryar Deeja ce ta janyo hankalin su zuwa ga dubanta, ta yi masu tambayar ne a yayin da ta ke saukowa daga saman gadonta, Tafiya take yi kamar babu wadataccen jini a jikinta, a tsakiyar ɗakin nasu ta tsaya tana bin faces ɗinsu da kallo, ta ɗaura da cewa"Tambayar ku na ke yi, ba ku bani amsa ba, jiya da abun ya faru me ya zo maku acikin ran ku"? Azeeza ce ta fara yin magana acikin su"ni dai nasan Angel baza ta ta6a iya cutar da wani acikin mu ba, amma narasa gane meyasa ta yi mana hakan"? tai tambayar tana kallon Deeja, Kamar yarda azeeza ta ce, suma sauran duk haka su ka ce, sun san bazata Iya cutar dasu ba, Angel koda wani ta gani zai cutar dasu bazata ƙyale shi ba, balle kuma ace ita da kanta ne ta yi musu hakan, abunda ya sanya musu kokwanto ya ruɗar dasu shine taya akai ta yi musu Jahilin bugun nan da kanta kuma da hannayenta! Juyawa Deeja ta yi ta fuskanci Angel da ke atsaye kamar an dasa mata aya, Jikinta sai kerma yake yi. "Ba laifin ta ba ne, kuma ba yin kanta bane, bakowa bane Ya jawo hakan fa ce muguwar matar nan, tsohuwa Zafreen! Itace silar komai, Idan har ba za ku manta ba, akan idon ku ta ɗaura mata sanda saman ƙirjinta, ni dama tun a lokacin raina ya bani cewar wani mugun abun ne za ta yi mata, dama tace bamu ta6a gabza faɗa a tsakanin mu ba, kuma wai a dokar prison ba'a amince ma kowani prisoner yaji daɗin rayuwar shi ba, Allah ya isa tsakanin mu da tsohuwa Zafreen, wlh ban ta6a danasanin tafiyar Tsohuwa Tamira ba irin na jiya, Mun yi babban rashi, ƙwara ita da daɗi da ba daɗi wani lokacin tana yi mana mutunci in taso" Babu wanda jikin shi bai yi sanyi ba, yanzu sun fahimci cewa Ba yin kanta bane, dama basu yarda cewa zata iya yi musu hakan ba, Angel ɗin da take matuƙar ƙaunar su, in dai a kansu ne har ranta zata iya badawa don ta fanshe su, Ni shaida ce akan hakan! Atare suka hada baki wurin bata haƙuri, tace masu basu ne ya kamata su bata haƙuri ba, duk da ba yin kanta bane, Ita ya dace ace ta basu haƙuri tun da da ita a ka yi amfani wurin cutar da su, don haka tana me neman yafiya agare su, su yi hakuri su yafe mata, kuma in sha Allah hakan ba zata ƙara faruwa ba, ita kanta ta yi mamakin yarda akai Sihirin tsohuwa Zafreen Ya kama jikinta, duk da shi sirihi gaskiya ne, kuma babu wanda yafi ƙarfin ya shiga jikin shi sai wanda Allah ya tsare! Shiyasa ake so bawa ya kasance mai neman tsari awurin ubangiji, ba dole sai abu ya risƙe ka ba, kace zaka fara roƙon Allah, a'a a koda yaushe ka kasance cikin neman tsari daga gare shi, addu'ar nan itace takobin mumini, after that azhkar na safe dana marece, mutun ya dage da yin shi ba fashi, da wuya kaga wanda ke yin azhkar mummunan abu ya faru dashi ba tare da Allah ya tsare shi ba!, Allah dai yasa mu dace. Bayan Angel ta nemi yafiyar su Hankalin kowannan su ya kwanta banda mutun ɗaya, Jamima itafa har ga Allah tsoron Angel ta ke ji, Abun ka ga yaro Ta ƙame jikin bango sai kuka take yi musu tana faɗin itafa bata son ganin Angel, cos she's a genie ba mutun bace, ba zata zauna a ɗaki ɗaya da ita ba, sai dai su rufe ta a cikin toilet, idan an kawo abinci su dinga kai mata acan tana ci, idan har ba su yi hakan ba, ita zata koma da yin rayuwa acikin toilet ɗinne, Abu kamar wasa ta sanya musu rigima, babu wanda bai lallashe ta ba acikin su akan ta yi haƙuri amma taƙiya, ƴar tahalikar nan har bayani su ka yi mata yadda zata fahinci cewa ba laifin Angel bane amma tace musu tasan me ta ke yi, su daina ganinta ƴar ƙarama kar take kallon su, Har ita za su yi ma wayau, so su ke ta zauna tare da Angel ɗaki ɗaya don ta samu damar ƙarasa 6alle mata sauran haƙoranta da suka rage abakinta. Maganganun Jamimah sun yi matuƙar basu dariya, ita abunda yafi 6ata mata rai, Haƙorinta ɗaya da Angel ta cire mata, Angel har ce mata ta yi ta kwantar da hankalinta, ita yarinya ce ba ta gama fanfara ba, wani haƙorin zai fito mata, amma taƙi yarda da zancenta, Ko kusa da ita taƙi bari Angel ta je, Tsabar yarda take zabgawa Angel harara kamar idonta zai faɗo ƙasa. Har tambayar Angel su ka yi ya akai Jiya suka dawo saman gadajen su? Sannan ya a kai basu ga jinin su da ya yi bleeding ba, a jikin bango da ƙasan ɗakin, sannan kuma ya akai Basu tashi da raɗaɗin ciwon su ba, Deeja ce ta basu amsa da cewa"Allah ne ya kawo mana ɗauki, narasa ya zanyi a lokacin saina roƙe shi, akan ya bani mafita, kuma cikin ikon Allah Sai gashi kowannan mu ya tashi babu ciwo a jikin mu," Mamaki ne ya kama su jin abunda tace, jamimah uwar masu hankali hada cewa Meyasa ita ba a dawo mata da haƙorinta ɗaya ba? Angel tace idan kika kwantar da hankalin ki, kema zanyi maki addu'a akan Allah yasa haƙorin ki daya fita ya dawo, Wani kallon rainin wayau ta yi ma Angel hada gatsina mata hanci, ƙiri ƙiri itafa ta tsangwami Angel, ganin aljana ta ke yi mata. Yunwa ce ta fara addabar su, dama dole suji yunwa wannan jijjigar da Angel ta yi masu a jiya, Kamar an kwashe abincin da suka ci, dama jiyan basu ƙarasa cinye abincin su ba, Sakamakon sumewar da Angel ta yi, hakan yasa suka ƙi ƙarasa cin abincin. Tunawa da abincin da su Majnoon suka ajiye musu a jiya ne yasa Parveen ta sauko daga saman gadonta, ta nufi ƙarƙashin gadon Batul, Ta janyo kwandon, Hibba tace"Anya bai lalace ba? Kada fa mu ci abunda cikin mu zai 6aci" Parveen ta bata amsa da cewa"Ai wlh ko ya lalace sai na ci shi, idan ma cikin ya 6aci iya kaci in ta yin zaryar shiga toilet ne, dama na saba" A saman Dining carpet ɗinsu ta ajiye musu kwandon tace musu Mai jin yunwa ya sauko suci, Jiki duk ba ƙwari kowan nan su ya sauko daga saman gadon shi duk da babu raɗaɗin ciwo a jikin su, sun rasa kuzarin jikin su, idan ka kalli fuskokinsu gaba ɗaya babu wanda bai faɗa ba. Sai da suka fara zuwa toilet su ka wanko bakunan su da fuskokin su tukunna su ka dawo ɗakin, kowa ya samu wuri saman dining carpet dinsu, su ka zazzauna, Jamima sarkin rigima, ba yadda ba su yi da ita ba akan tazo ta zauna su ci abinci tace musu taya zata iya cin abinci, bayan babu haƙori ɗaya a bakin ta. Ganin zata 6ata masu lokaci yasa Deeja ɗaukarta, ta nufi toilet da ita, ta wanke mata bakinta da fuskarta, ta fito da ita rungume a jikinta. Sai da Angel ta fara dudduba abincin don taga idan akwai wanda ya lalace, lafiyar shi qalau, ya dai yi sanyi, kayan marmari ne sai flat bread wraps, da snack Hada ragowar meat balls, " Bismilla su ka yi, suna cin abincin hawaye na bin fuskokin su, tunawa da ƴan uwan su, carpet ɗin yayi musu faɗi saboda waɗanda babu acikin su, rayuwa kenan, da ta ko'ina gefe da gefen carpet ɗin zaka gan su zazzaune sun kewaye shi. basu ta6a tunanin za'a kwashe su haris ba, sun yi matuƙar yin kewarsu, Sun damu dasu sosai, Parveen ba kowa take tunawa ba face MAJNOON, duk in ta tuna yadda ya zo saman gadonta ya haye tare da ɗaura kanshi saman kafaɗarta, Sai taji hawaye sun cika idonta, haka da zai tafi ya dinga waiwayonta, duk da irin bugun da take yi mashi kamar ta samu jaki, yaron ba ƙaramin ƙaunarta ya ke yi ba, ta yi danasanin muguntar da ta ke yi mashi, da tasan haka zata faru da ko dungurin shi ba zata yi ba, Allah sarki majnoon. Idan muka koma 6angaren Deeja tunaninta akan HARIS ne, zuciyarta kamar zata fashe saboda kewar shi da ta ke yi, Allah sarki haris masoyi, a duk lokacin da ta shiga wani hali yafi kowa damuwa da ita, bashi da magana saita Deeja, Yana matuƙar kyautata mata tare da sauran ƴan uwan shi, haƙiƙa sun yi babban rashi na ɗaya daga cikin jagoransu, wanda suka fi damuwa dasu, wato Haris, a zuciyar Angel waɗanda suka fi tsaya mata arai duba da irin halin da aka tafi dasu, mutun na farko BATUL ce! ba zata ta6a mantawa da irin yanayin da aka tafi da ita ba, Allah sarki batul, itama tana ɗaya daga cikin jagoran su, masu ƙarfafa musu gwiwa masu nuna damuwa akan ƴan uwan su, Bayan ita sai mutun na gaba Maji daɗin gado wato DANISH, dole ne kowa yaji jiki na rashin shi, saboda shi a raunace aka tafi dashi, babu ido ɗaya fuskarshi a wanke da jinin shi, Allah kaɗai yasan awani hali ya ke ciki a yanzu. Anyi masu babban gi6i, ɗaya bayan ɗaya haka suka zauna suna tariyo irin muhimmancin da suke da shi awurin su, bayan Danish mutun na gaba JAVED ne! yana ɗaya daga cikin waɗanda suka ƙaunaci Angel farkon kasancewarta a gidan kurkukun ƙaddara, kyawawan halayansa abunso ne, kowa nashi ne, yana matuƙar ƙaunar ƴan uwan shi, bayan javed mutun na gaba bakowa bane face NAUFAL, Tazarar halayan shi dana haris kaɗan ne, Yana da zafin zuciya idan aka ta6a ƴan uwan shi yana ɗaya daga cikin masu tada jijiyoyin wuya, shima ba daga baya ba, in dai akan ƴan uwan shine a shirye ya ke daya zare takobi don ayi yaƙi. Bayan Naufal Sai MUBEEN yana ɗaya daga cikin masu faranta musu rai, ya iya jan ƴan uwan shi a jiki, mutun na ƙarshe a cikin jerin waɗannan bakowa bane face GABRIEL! duk da shi daga baya ya tsinci kanshi agidan kurkukun, Amma tabbas da ace yai rayuwa dasu ba ƙaramar gudummuwa zai bada ba! Saboda yana da zuciya, ga tausayi kowace mace yana ganinta kamar ƴar uwarshi ne, sannan yana da burin su ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddara! Tabbas sun yi babban rashi na zaratan samarin dake acikin su, hatta ɗakin su ya yi musu girma saboda rashin su. duk yadda suka so su hana kansu damuwa saida abun yaci tura, Sun sha kuka tamkar ba gobe, Deeja da Angel sai aikin lallashin su su ke yi, a ƙarshe suma suka koma suna taya su kukan, sautin kukansu ya karaɗe cikin ɗakin, Dama ba ƙoshin lafiyace da su ba, Sai da su ka yi mai isarsu tukunna suka haƙura kowa ya lallashi zuciyarshi, A saman floor ɗin ɗakin kowan nan su ya kwanta kamar matattu tsabar baƙin ci ne kawai da raɗaɗin da su ke ji a cikin zuciyarsu. Yinin ranar babu wanda ya yi wanka a cikin su, Jikinsu sai tsami yake yi, koda giants su ka zo kawo musu abinci babu wanda ya motsa a cikin su, dama ba yunwa su ke ji ba sun ɗan samu sun ci ragowar na jiya, babu yunwa atare dasu, Jamimah ce tai ƙoƙarin ɗauko kwandonsu tunawa da yadda su ka yi jiya ita da majnoon, itama fa hada ƴar ƙwallarta, saboda an tafin mata da abokin wasan ta, duka abincin ta dinga kwasa da hannu biyu tana turawa cikin kwandon, sai da ta kammala ta kasa ɗaukar kwandon saboda yai mata nauyi, hakan yasa ta barshi asaman dining carpet ɗin, Giants na ganin ta kammala tattara abincin, su ka kwashe trays din tare da barin ɗakin, Zama jamima ta yi ta dinga ɗaukar abincin tana ci tana kallon su Hanna dake kwance ƙasa hawaye na bin fuskokin su, Sai da ta cika cikinta ta yi kulu wash rabu hani'an tukunna ta miƙe tare da komawa cikin su itama ta kwanta kamar yadda su ka yi, ta ci gaba da matsar ƙwalla tana ambaton sunan Majnoon. A cikin waɗannan kwanakin babu wanda bai ji jiki ba a cikin su, kamar za su yi hauka, idan Giants suka zo kawo masu abinci haka zasu dinga zazzaga musu masifa akan su dawo musu da ƴan uwan su, sun gaji da jira, a ƙarshe da su ka fahimci cewa Giants ba sauraron su su ke yi ba, don dole su ka haƙura. yanzu ta kai ga da zarar sun ji motsin buɗe ƙopa da gudu suke zuwa bakin benan don suga idan ƴan uwan su ne aka adawo musu da su, ashe kunnuwan su ne, su ke jiyo musu hakan saboda tsabar yarda suka sanya damuwa aran su. Bayin Allah duk sun rame sun fige sun fita hayyacin su, kamar ana ɗibar naman jikin su, ƙasusuwan wuyan su duk shatunsu ya fito saman fatarsu, idanuwansu sun faɗa, ganin zasu zauce saboda rashin ƴan uwansu ne yasa Angel ta tattarasu tana yi musu nasiha akan su yi haƙuri subarma Allah komai, shi zai kawo musu mafita, ta dage sosai wurin cigaba da koya musu addu'o'in da zasu dinga yi don su samu maslaha acikin zukatan su, har tsakar dare ta ke tada su daga bacci, su zauna su na addu'a suna kai kukan su wurin Allah, kullum suna zama cikin jimami, kafin Allah ya kawo musu sauƙin damuwar da ke damun su, Sun haƙura suna zama harma su ɗan ta6a fira a tsakanin su, su yi murmushi su yi dariya. *💔PRISONERS💔* *After one week (bayan sati ɗaya)* Tun bayan da aka tafi dasu Haris, babu wanda yai wanka a cikin su, sun zama ƙazaman ƙarfi da yaji, Saboda rashin sukuni da walwahala, hatta gashin kansu Ya fita hayyacin shi saboda rashin gyaran da bai samu akai akai, sai yau da Angel ta lalla6a su tace su je su yi wanka zata gyara musu kansu, tukunna suka amince za su yi, Ita kanta Angel ɗin ba wankan ta ke yi ba, yau dai ne ta ke son su ɗan gyara jikin nasu. Gaba ɗayan su suna a sashen toilet ɗin su, banda Jamimah ita kaɗai ta rage a ɗakin zaune saman gadonta, Hannunta ruƙe da madubi, ta wage baki tana kallon gi6inta, kullum ne saita ɗauki madubi ta duba bakinta don taga idon wani haƙorin ya fito, har yanzu babu jituwa a tsakaninta da Angel. Su hanna da ke a sashen toilet ɗinsu, kowanansu Ya zuƙunna suna fuskantar juna, kusan su bakwai ne suna jira na cikin toilets ɗin su fito don suma su samu shiga su yi wankan, Waɗanda ke acikin Makewayin Angel ce da Sarah sai Azeeza. Angel da ke acikin toilet, tun da ta shiga, ba wanka ta ke yi ba, tana a zuƙunne gaban tukunyar fulawan nan tsawon lokaci basu ba furennin ciki ruwa ba, saboda rashin kwanciyar hankali. Furennin duk sun bushe sun fita hayyacin su, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta miƙe taje bakin fanfo ta cuko bokiti da ruwa ta dawo ta kwarara shi acikin tukunyar, bayan ta kammala ta juya ta kai bucket ɗin gefen fanfon ta ajiye shi, kamar ance ta waiwayo ta kalli furennin, unexpected idanuwanta suka sauka akan Sabbin tsiron furennin da suka cika tukunyar fulawar, A matuƙar ruɗe ta ke kallonsu, launuka daban daban daga cikin su akwai wani dogon fure wanda tsayin shi ya kere sauran, Lafiyayyan gaske, Ganyayyakinsa sun bubbuɗe launin punch pink ya ciza sosai. Zazzare idanuwanta waje ta yi, Hannunta dafe da saitin ƙirjinta, don ba ƙaramin faɗuwa gabanta yai ba, walking slowly ta nufi tukunyar fulawar kamar wadda taga wani abun tsoro, duƙawa ta ɗanyi tana ƙare musu kallo, kusan guda takwas ne sabbin furennin, bakwai daga cikin su, ganyayyakin jikinsu sun ɗan bubbushe, akwai wani ɗan ƙarami fari fat irin na jikin aunty Aneelerh, sai dai wannan ganyayyakinsa kamar sun mutu, duk sun tsomare. Tarasa tunanin me zata yi agame da waɗanann sabbin furennin da su ka yi tsiro, ta gaza fahimtar na wanene su? tunawa tai da maganar Danish, a inda yake faɗa mata cewa kowani fure yana ɗauke da ran mutun, idan har dagaske ne, taya za'ae tasan ran wanene akansu? Ga biyu ma daga cikin furennin sunfi jigata. Wani irin faɗuwar gaba taji, ba tare da sanin dalilin hakan ba, sai ta dinga ji aranta kamar Danish yana atare da ita cikin toilet ɗin, da sauri ta juya tana ƙarewa makewayin kallo, babu kowa a wuri. Muryarta na ɗan rawa ta furta sunanshi "DANISH"! cike da sa ran zai amsa mata, shiru ba'a amsa mata kiran nata ba, kusan sau uku tana ambaton sunanshi, "Danish, are you here with me? Please answer my call. I really miss you my Man," she said, her voice on the verge of tears. Sai faman wurwuga idanuwanta take yi acikin toilet ɗin, duk da taga babu kowa amma ita ranta ya bata cewar Yana atare da ita. "Danish Even if you can't speak, please make some kind of sound to let me know that you're here. I need to know if my suspicions are true, saboda a duk lokacin sa ka zo kusa dani, Inaji a jikina kuma na yarda da hakan," kamar mahaukaciya sai sambatu ta ke yi a cikin toilet. Da ƙarfi ta ƙara furta sunan shi"Danish ka amsa min" karaf akan kunnuwansu Deeja dake zuƙunne cikin sashen, su azeeza har sun fito daga wankan, hibba da parveen sun shiga, ita kaɗaice bata fito ba, "Kamar muryar Angel nake ji acikin toilet!" yasmin ce tai maganar, Deeja tace"kin riga ni faɗi, nima naji maganarta tana ambaton sunan Danish" hanna tace"Anya lafiyarta kuwa? Yakamata muje mu duba," Kusan atare suka miƙe, zuwa bakin ƙopar toilet ɗin, knocking deeja tayi mata tare da ɗaga murya tace"Angel! Lafiya mu ka ji kina kiran sunan Danish"? Jin muryoyin su Yasa ta dakata da yin sambatun, idanuwanta acike tab da ƙwalla, ta nufi ƙopar, bata buɗe ba, magana tayi masu cikin sanyin murya "Babu komai, banma san na ambaci sunanshi ba, nayi missing din shi ne" "Shiyasa kike ta ƙwala mashi kira a cikin toilet, gaskiya Angel ba ƙaramin ƙaunar ɗan uwan nan namu ki ke yi ba, muna nan munata jiran ki ki fito, ashe kina nan kina ta sambatu halan ko wankan ba ki yi ba"? Fuskarta a yamutse ta basu amsa da cewa"ban kai ga yi ba, na tsaya bama furenni ruwa ne, idan na fito zan nuna maku wani abun mamaki, amma yanzu ku koma ku zauna kunsa inata magana acikin toilet bayan babu kyau,' a ƙagare take da su tafi, jin shiru yasa ta fahimci cewa sun tafi, ajiyar zuciya ta ɗan sauke, ba tare da 6ata lokaci ba, ta yi wankan, suna a zaune sai gata ta fito, adai dai time ɗin da su parveen da hibba suma su ka fito daga wankan. Kallon su ta yi gaba ɗaya idanuwansu akanta, jira suke suji me zata faɗa musu "Kunsan me ya faru"? Girgiza mata kai su ka yi alamar a'a tace"dana shiga toilet na ɗebo ruwa na zuba ma tukunyar fulawar nan, naje in ajiye bucket ɗin, Juyowar da zan yi idanuwana su ka yi tozali da sabbin furenni masu kyan gaske, dayawa fa nayi mamakin fitowar......." bata kai ga ƙarasa maganar ba, da gudu su deeja suka shige cikin toilet ɗin, a bakin tukunyar flower ɗin suka tsaitsaya cirko cirko suna kallon furennin, gwanin ban sha'awa, sunyi matuƙar burgesu, sai dai abun da ya ruɗarsu sun kasa gane furennin wanene, sun 6ata lokaci wurin kallonsu, kamar su cinye su, daga bisani ne suka bar wurin, sauran da basu yi wanka ba a cikinsu suka shige toilets. Lokacin da Angel ta shiga ɗakinsu, Jamima na nan yadda suka barta, zaune tana duba madubi, azeeza tana azaune saman shimfiɗar sarah, tana sharce mata gashi, sai santin shi ta ke yi, saboda ita tsayin gashinta bai kai nasu ba, "Sumar kan ki sak irin na Unaiza ne ƴar gidan daddy, banbancin kaɗan ne ita nata tsawo ne da shi ba yawa ke kuma naki yana da yawa kamar roba jikin shi" "Allah sarki har kin tuna min da ita, ko yanzu tana awani hali, oho, " acewar parveen, ta yi maganar ne a yayin da ta ke ƙarasa shiga cikin ɗakin. Angel tuni ta wuce gefen gadonta, parveen ce ta ɗauko mata comb donta gyara masu gashin kan su, atare da Sarah suka zauna zaman gyara masu sumar kan nasu, ɗaya bayan ɗaya suka yi ma kowan nan su bayan sun fito daga wankan, mutun ɗaya ta rage bata yi wanka ba, har magana azeeza ta yi mata akan tazo ta yi mata wanka tace ita bataso, Su ƙyale ta, haƙorinta ke ciwo, alhalin ƙarya ta ke yi babu wani ciwon haƙori da ta ke yi, wankan ne bata so, Dama angel neman hanyar da zasu shirya da ita take yi, aiko tana zaune saman gadonta, ba zato ba tsammani taji an ɗauketa, ta dinga kuka tana wuntsila ƴan ƙafafuwanta tana faɗin bata so ta sauke ta, hada ƙwala masu deeja kira tana faɗin bazasu zo su cece ta ba, suna ganin genie zata cutar da ita, dariya suka dinga yi mata babu wanda ya motsa. A cikin toilet ta sauketa, da gudu ta nufi ƙopa zata fuce Angel tai saurin rigata isa ta datse ƙopar da jamlock, kallon kallo su ka shiga yi a tsakaninsu, Nuna jamimah tai da yatsan hannunta tare da cewa"dama daga ganin ki ba ƙaramar fitinanniya bace, amma duk masifarki baki kai ni ba lokacin da ina ƙarama, kawai daga tsautsayi yasa na 6alle maki haƙori, shine zaki ɗaura min karan tsana, nifa ce Angel ɗin ki,' ta yi maganar tana marairaice mata fuska. Murguɗa mata baki jamima tayi tare da juya mata ƙeya, Dariya angel ta saki tana kallon bayanta, Kamar kasanya ƙafa ka take ta saboda ƙarantarta, komai nata gwanin burgewa irin na azeeza, tana matuƙar jin tausayin su. Jin shiru Angel din bata motsa ba yasa ta ɗan waigo ta saci kallonta, suna haɗa ido ta wurga mata harara. Dafe ƙirji Angel ta yi da hannu ɗaya "Genie ɗin kika harara, aiko yanzun nan zan ƙarasa 6a66ake sauran haƙoran na bakin ki ki koma wawulo, " jin wannan maganar yasa Jamimah fashewa da wani sabon kukan. matsawa Angel ta yi dab da ita, ta ɗan zuƙunna saman ƙafafuwanta, tare da ɗaura hannayenta biyu saman kafaɗar jamima ta juyo da ita, suna facing ɗin juna Sassauta muryarta tayi Cikin sigar lallashi tace"its okey my little sis, stop crying, bakisan cewa hawayenki, tsada ne dasu ba, " zumbura mata ƙaramin bakinta ta yi, fuskarnan a tur6une, har wani hura hanci ta ke yi, shafa gefen fuskarta Angel ta yi da hannunta, "Ƴar kyakkyawa da ke kamar Azeeza ta, idan muka fita daga cikin kurkukun nan, zamuje gidan daddyna, akwai suturar sanyawata da daddyna ya siya min tun ina ƴar ƙarama, nasan zasu yi maki, bayan haka ina da kayan wasa, irinsu teddy nasan baki san su ba, hada piano ɗina, duk zan baki su, sannan in sanya ki makaranta, kema ki yi karatu, kamar yarda sauran yara su ke yi, ko baki so" ta6e baki tayi don ita bata fahimci zancenta ba, amma taji an ambaci kayan wasa, Ɗaga mata gira tai"ina so," mirmushi Angel ta saki"amma fa sai mun shirya," hura hanci ta yi, tare da cewa "Ae mun shirya" dariya Angel ta saki, Tare da janyota jikinta, ta rungumeta sosai, kafin ta raba jikin su. Wanka ta yi mata a cikin toilet ɗin, ta kuma wanke mata gashin kanta, bayan ta gama ta goyota saman bayanta, Suna shiga cikin ɗakin, su parveen suka dinga sowa suna tafa musu hannu, Ganin sun shirya da juna, ba ƙaramin daɗi su ka ji ba, A saman gadonta ta zaunar da ita, ta ɗauko comb ta sharce mata sumar kanta, bayan ta gama, Kalaba ta yi mata guda biyu, sun sauko gefe da gefen kafaɗarta, ta zura mata ribbon ɗinta jikin wutsiyar kalaba ɗaya, ba ƙaramin kyau ta yi ba. Lokacin da marece ya nutsa kingin abincin su na safe da su ka ajiye, Hannah ta ɗauko musu, asaman dining carpet ɗinsu suka zazzauna, Suna ci saboda gatanci abaki Angel ta dinga ba jamimah, ran azeeza ya 6aci musamman da ta dinga yi mata gwalo, yarinyar ta rainata, kishi ya rufeta, ganin yadda azeeza ke ɗaure fuskarta, yasa Angel ta koma tana basu abincin su biyu ita da Jamima, idan ta basu abaki su ka ci, itama sai taci, a haka har suka kammala. Saman gadajensu suka haye tare da kwantawa, a ƙasa Angel ta shimfiɗa bargonta, su uku suka kwanta asaman shimfiɗar, ita da Jamima da Azeeza, sarakan kishi, duk abunda jamimah tayi sai azeeza tayi, suna a kwance saman shimfiɗar, jamima ta rungume Angel, itama azeeza ta baya ta rungumeta, sai dariya take yi, abin ba ƙaramin nishaɗi yake sanyata ba. Ba su kwanta da niyar yin bacci ba, saboda Angel ta hanasu yin baccin marece, saboda su samu damar tashi tsakar dare su dinga yin addu'o'insu, wani irin bacci ne mai daɗi ya ɗauke su, hada masu yin min shari irinsu parveen aci ci mala ikun tauna. Dare yana gab da yi, aka buɗe ƙopar ɗakin su, sautin bai farkar dasu daga bacci ba, A hankali Giant ɗin ke saukowa saman staircases, kafaɗarshi ɗauke da mutun, daga gani macace duba da irin shape ɗin ƙafafuwanta, uban gashin kanta ya sauko ta bayanshi inda kanta yake, ya lullu6e fuskarta, Ƴar rigar dake a jikinta guntuwa ce launin ja, daƙyar ta rufe mazannanta, hakan ya bayyana suffar fararen cinyoyinta, kamar ka ta6a jini ya ɗigo, Yanayin tafiyar Giant ɗin da ya ɗauko ta, ta banbanta da ta sauran Giants da suka saba zuwa kawo musu abinci, akwai natsuwa da kamala atattare da shi, jikinshi gaba ɗaya a rufe yake da baƙaƙen kaya, baka ganin koda yatsan hannun shi ne, bai nufi ko ina ba, sai saman gadon da ke ɗauke da no 3 a saman shi ya kwantar da ita a hankali, tare da janyo duvet ɗin dake a saman mattress ɗin Ya lullu6e mata jikinta dashi, a hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai daya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin ɗakin.......nima kuma na ajiye alƙalamina🤟 💋PRISONERS💋 A hankali yake ja da baya batare da ya juya ba, kamar yana kallon su, Har sai da ya kai bakin benan tukunna ya juya da sauri ya haura benan ya fuce daga cikin ɗakin. Ko sautin rufe ƙopar bai farkar da su ba, kamar matattu, yaushe rabon da su yi irin wannan baccin su kansu sun manta, tsawon lokaci babu wanda ya farka, har dare ya yi, Hasken ceilling ya ɗauke, Na floor lamps ya kunna kan shi. Azeeza ce ta fara yin motsi zata farka, hannunta dafe da mararta, wani irin azababben fitsari ne ya matse ta, da kasala a jikinta ta yunƙura ta miƙe zaune saman shimfiɗarsu, idanuwanta biji biji bata iya ganin komai. muryarta cikin shessheƙar kuka ta soma magana tana laluban Jikin Angel. "Angel ki tashi ki raka ni toilet, fitsari ni ke ji ya matse ni sosai....pls Angel ki tashi kada in yi shi a wando," Ko motsi Angel ba ta yi ba, balle har ta sa ran za ta farka. Jamimah ce ta jiyo muryar Azeeza da ke ta yin kuka, farkawarta kenan, ta zame jikinta daga na Angel, ta miƙe zaune tana mutsustsuka idanuwanta da yatsun hannayenta, fuskarta a ɗaure babu annuri. Ƙura ido ta yi a kan fuskar azeeza Dake ta kerma tana kuka, Muryarta da alamun bacci bai isheta ta ambaci sunanta"Azeeza...' tana jin muryar jamimah tai saurin katse kukan nata tare da cewa"Jamimah fitsari nake ji, dan Allah ki taimaka ki raka ni toilet, ya matse ni" baki asake Jamimah ke kallonta, "Toilet dinne saina raka ki? Ke baki iya zuwa? Ko tsoro kike ji ne"? ta yi tambayar tana binta da kallon rainin wayau. Jamimah ba ta san cewa azeeza na fama da lalurar rashin gani ba, Muryarta na rawa tace"Jamimah bana gani, idan dare yayi, makauniyace ni...." Ta6e baki jamima tayi mata tare da cewa"ƙarya ne, Ni zaki raina ma wayau? Idan da gaske baki gani to ya akai da rana kike gani? Nafa san me nake yi," Takaici ne ya ishi azeeza duk yadda taso ta fahimtar da jamima taƙi yarda cewa bata gani, hakan yasa ta miƙe a makance ta soma tafiya tana laluban hanya, jamimah sai kallon bayanta ta ke yi, abun ya ɗaure mata kai ganin yadda ta ke ta sanya hannu tana laluban hanya, cikin rashin sa'a Azeeza ta nufi bango gadan gadan duk a tunaninta ta ƙaraso bakin ƙopar shiga sashen toilet ɗin ne, ta daddage zata buga kanta, Jamimah ta kware murya tare da cewa"Bango ne fa ba ƙopa fa", Ta yi maganar tare da miƙewa da gudu ta nufi in da Azeeza ta ke a tsaye jiki na kerma don ba ƙaramin firgita ta yi ba, da taji muryar jamimah tana faɗa mata cewa bango ne ba ƙopa ba. ba ta yi tsammanin zata taimaka mata ba, sai jin hannunta ta yi a cikin nata, ta ruƙo ta tare da jan ta zuwa cikin sashen, kafin su ƙarasa toilet ɗin tuni ta fara sakin fitsarin a wando, Suna shiga ciki ta zame wandon jikinta, da sauri jamimah ta kawar da kanta gefe don kada taga tsiraicinta, bayan ta gama yin fitsarin, ta yi tsarki kafin ta maida wandon jikinta, ta kira sunan jamimah, ta taimaka mata a daddafe su ka nufi ƙopar fita. "Amma dai idon ki a rufe ya ke lokacin da nake cikin yin fitsarin ko? Azeeza ce tai maganar, murmushi jamimah ta saki tare da cewa"naga komai, daga yanzu sai ki daina raina min wayau kina kira na ƴar yarinya, nima ae kina min wanka, kuma kina ganin nawa" Shiru Azeeza ta yi ba tare da ta tanka mata ba. A lokacin sun fito daga sashen toilet din "Amma wai dagaske baki gani da daddare? To ya akai kike gani da rana? yamutsa fuska azeeza tai"ko nace maki eh, ba yarda za ki yi dani ba, ki bari idan Angel ta farka daga bacci ki tambaye ki ji, " ta amsa mata da toh. A lokacin sun shiga cikin ɗakin nasu, har zasu nufi shimfiɗar da Angel ta yi musu, ba zato ba tsammani idanuwan Jamimah suka sauka akan Gado mai ɗauke da no 3, dakatawa ta yi da yin tafiyar, ta ƙurawa gadon ido ta hango mutun naɗe cikin bargo, tunani ta shiga yi wanene saman gadon? Saboda a iya saninta tunda aka kwashe mazan cikin su, babu mai kwana saman tsaffin gadajen su sai Angel! Ita kaɗaice ta ke kwana saman gadon Danish, da sauri jamimah ta juya ta kalli ɗayan 6angaren don taga ko wani daga cikin su Hibba ne Ya dawo saman gadon ya kwanta, sai dai ko da tabi gadajen su da kallo kowannan su yana nan,' A firgice ta wurga eye balls ɗin ta kan shimfidar Angel don ta tabbatar idan Angel ɗin tana nan, lamarin ya yi matuƙar razana ta ganin Angel baje saman bargo sai sharar baccin ta ke yi. Azeeza da ta gaji da tsayuwa jin taƙi motsawa su tafi, muryarta a kasalance tace"Jamimah! Ke fa nake jira naji kin dakata da tafiya, Me kike yi ne, dan Allah ki kaina saman shimfiɗarmu in kwanta," Hankalin Jamimah ba ƙaramin tashi yai ba, muryarta atsorace ta furta"Azeeza Genie a ɗakin mu, saman gado no 3" ta yi maganar tana zazzare idanuwanta. duk da Azeeza bata iya gani hakan bai hanata zare idanuwanta ba, zuciyarta ta yi wani irin bugu tamkar zata faso kirjinta, Azeeza sarkin tsoro, "Innallahi wa'inna ilaihirraji'un! Jamimah ki faɗa min gaskiya, ko dai ƙarya kike yi min, wani irin genie kuma a cikin ɗakin mu, ki dai duba da kyau," jamimah tace" kin san Allah dagaske na ke maki, kamar mutun ne saman gadon, kuma na dudduba su hibba mun cika mu goma sha ɗaya, na saman gadon shine cikon na sha biyu." Girgiza kai azeeza tai jiki nata 6ari tace"jamimah bargo ne da pillow ba mutun ba, ni dai mu je mu kwanta, " ta yi maganar tana ƙoƙarin jan hannunta, duk tabi ta tsorata kanta. "Ni dai sai naje na duba gadon inga wanene, ke ki ke je ki kwanta" Ran Azeeza ba ƙaramin 6aci yai ba, zuƙunnawa ta yi ƙasa tana rarrafawa don ta gano inda shimfiɗar Angel ta ke. A hankali jamimah ke tafiya tana tunkarar gadon, ga tsoro tana ji amma ta nace sai taga wanene, tana ƙarasawa bakin gadon, ta ɗan dakata, tare da miƙa hannunta yatsunta nata yin kerma ta ruƙo bargon, wani irin tsorone ya ziyarci zuciyarta, a hankali ta yaye bargo, a gigice ta runtse idanuwanta ta daddage ta fasa wata irin firgitacciyar ƙara wadda ta yi silar farkawar masu yin bacci. A matuƙar ruɗe Azeeza ta faɗa saman jikin Angel da ke kwance, Allah yaso ta isa ga shimfiɗar da kuwa zuciyarta ta buga silar ƙarar da jamimah ta fasa. Bakomai ne ya tsoratar da ita ba face Sumar kan matashiyar dake akwance saman gadon, dama can a tsoroce take shiyasa bata iya tantance gashine ko ba gashi ba, ita dai taga abu kamar hauka, Mai uban yawan gaske ya nanannaɗe, idanuwanta ne suka dinga nuna nata kamar gashin yana motsi, aiko ta rushe da kuka da gudun gaske tabar bakin gadon har tana tuntu6e garin gudu, hankalin su Deeja ba ƙaramin tashi yai ba, ganin yadda jamimah ta furgice tana kuka, bata nufi ko'ina ba, sai saman jikin Angel ta faɗa mata, suka ƙanƙameta ita da azeeza, sun tada mata hankali, ko motsi sun hana tayi tun da tafarka, duk sunbi sun furgice. Babu wanda ya lura da abunda ya tsoratar dasu. "Me ke faruwa ne? Wanene ke yi mana kwaratsi a cikin ɗaki"? Parveen ce ta yi maganar fuskarta a yamutse, deeja tace"Jamimah ce, bansan me suke ma ihu ba" ta yi maganar tare da saukowa daga saman gadonta, tare da nufar shimfiɗar Angel. Su yasmin duk suna zazzaune saman gadonsu basu motsa ba, idanuwansu akansu Jamimah. Zuƙunnawa Deeja ta yi agabansu tare da ambaton sunayensu "Jamimah! Azeeza! Lafiya ku ke yin ku ka? Wani abu ya faru ne"? Bakin Angel ya mutun, takasa magana, saboda faɗuwar da gabanta ke yi. Cikin shessheƙar kuka Jamima tace"Ge..nie a ɗakin mu, ga ta can kwance saman gado number 3" Jin ta ambaci bed no 3 yasa kowan nan su yin saurin kai idanuwan shi kan gadon, ganin kamar mutun ne yasa su ka soma kallon junan su, a ƙoƙarin su na su gano wanene acikin su yaje ya kwanta gadon, Ɗaya bayan ɗaya suka dinga saukowa daga saman gadajen su, tun daga kan Eve yasmin hibba hannah rubina, Sarah, kaf ɗinsu, A tsananin tsoroce su ke ƙarewa gadon kallo sai faman zazzare idanuwansu su ke yi. "dagaske mutunce kwance saman gadon batul ɗin mu"! Jin wannan maganar da Parveen ta yi ne yasa Angel ware idanuwanta, ta sanya hannu tare da janye su Azeeza daga Jikinta. Ta yunƙura ta miƙe jikinta na rawa ta nufi gadon Itama Deeja tabi bayanta, Ya rage saura azeeza da jamimah, sun fi kowa tsorata, rungume juna su ka yi kamar zasu haɗe jikinsu ya zama ɗaya. A kewaye da gadon suka tsaitsaya curko curko, suna ƙare mata kallo, farat ɗaya Angel ta gane wacece muryarta na rawa ta ambaci sunanta da ƙarfi * "BATOOL!" * Ras! Gaban kowan nan su Ya faɗi, a ruɗe su ke kallonta, Basu tabbatar cewa ita bace, har sai da Angel ta hau saman gadon, Jiki na rawa ta sanya hannayenta biyu ta yaye sumar kanta gefe ɗaya, kyakkyawar fuskar batul ta bayyana, zazzare idanuwansu waje su ka yi, abun ne da basu tsammace shi ba, ba zaka iya tantance yanayin da su ke a ciki ba, suna so su yi farin ciki sai dai suna fargabar ace batul ɗinsu wani abu ya same ta, tun daga kan fuskarta su ka shaida hakan, kamar an ninka hasken fatarta, dama fara ce sol kamar Angel ko tabo babu a jikinta, hatta gwiwar ƙafarta jawur ta ke, ta canza masu sosai ta rame kamar an ɗibi naman jikinta, brownish lips ɗinta sun ciza sun bushe ƙamas, hankalinta a kwance ta ke fitar da numfashi sai dai kamar a firgice ta ke. Halin da suka shiga furta shi 6ata baki ne, Zuciyoyin su sun karaya, Jiki yayi la'asar, Idanuwan kowannansu hawaye ne kwance a cikin su. Muryar Angel cikin shessheƙar kuka ta furta"Ya Allah kasa ba mafarki na ke yi ba, Batul ɗina ce ta koma haka? Waye ya dawo mana da ita? Ta ina ta shigo? Dama dagaske ne abunda Gabriel ya faɗa min na cewa yaga matashiyar yarinya tana gudu asaman third floor! Batul ɗina ce kenan! ' Zuciyarta a hautsine ta yi maganar, ita kanta batasan ta furta hakan ba. yayin da idanuwanta ke akan jikin batul. Hawaye ne masu ɗumi suka wanke fuskarta, ta ɗaura hannayenta biyu saman kafaɗunta, ta ɗago da ita, tare da kwantar da ita saman ƙirjinta, nan take taji wani irin yanayi mara misaltuwa ya ratsa jikinta, hakan ya ƙara tabbatar mata da cewa Batul ɗinta ce babu tantama, cikin rauni na murya ta shiga faɗin"wlh itace! Batul ɗin mu ce aka dawo mana da ita, tsawon wata uku, till today ashe da rabon zamu sake yin tozali da ƴar uwar mu! Alhamdulillah ya Allah bazan iya misalta farin cikin da nake a ciki ba........" Sosai ta fashe da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, suma sauran ƴan uwan nasu suka kama yin kukan farin ciki. A gefe da gefen gadonta kowannan su Ya zauna, wasu ma saman gadon suka haye, kamar sun samu tv suna kuka suna kallon ƴar uwarsu dake a kwance jikin Angel, don tunda ta ƙanƙameta bata saketa ba, sosai ta yi tighting ɗinta a jikinta kamar zata mayar da ita cikin cikinta, Allah sarki tsohuwar zuma, Gaba ɗaya sautin shesshekar kukansu Ya karaɗe cikin ɗakin, bakomai yasa su yin kukan nan ba face tsabar farin cikin da su ke aciki, sai dai duk da hakan akwai fargaba acan ƙasan zuciyoyin su, saboda ba su san me aka yi mata ba, na tsawon lokacin da ta ɗauka a hannun su. suna matuƙar jin fargabar abunda zasu ji daga gare ta, wani abu da ya ƙara tada masu hankali, Taƙi farkawa, duk wannan koke koken da su ke yi baisa ta buɗe idanuwanta ba, Azeeza dake rungume da jamimah tun da taji muryar Angel tana ambaton sunan Batul, tabi ta ruɗe ta shiga laluban hanyar da zata kai ta gare su, sai dai takasa, sai rarrafe ta ke yi a tsakiyar ɗakin tana ambaton sunan batul. Jamimah ce ta taso itama tuni ta daina yin kukan jin cewa ƴar uwar su ce ba Aljanna, sai taji hankalin ta ya kwanta, tafiya tayi zuwa inda azeeza ta ke a zuƙunne ta ruƙo hannunta ta miƙar da ita, tare da yi mata jagora zuwa gaban gadon batul inda su Angel su ke a zazzaune, da taimakon Hannah ta samu ta haye gadon bayan sun matsa mata hanya, muryarta da zumuɗin ta ke faɗin ina batul ɗin ta ke ne? Dagaske itace aka dawo musu da ita? fuskarta sharkaf da hawaye ta ke yi masu tambayar. Makanta ba ta yi ba, idanuwanta akansu Angel saidai bata iya ganin su, ganin yadda take ta sharar ƙwalla tana ambaton sunan batul, Yasa deeja ta ruƙo hannunta ta ɗaura shi saman sumar kan batul data cika bayanta. shafa gashin ta dinga yi da hannunta, muryar hanna a sanyaye tace mata"azeeza bacci ta ke yi, bata farka ba, tana rungume ne a jikin Angel ne" koda hanna ta yi mata magana, bata haƙura da laluban jikinta ba, har saida ta ɗaura hancinta a saman bayan batul, ta tabbatar da cewa ita ɗinta ce, tukunna hankalinta ya kwanta, farin ciki ya cika zuciyarta, sai zabga murmushi ta ke yi, Angel fa taƙi basu damar su rungumi ƴar uwarsu, tunda ta ƙanƙameta a jikinta taƙi sakinta, yadda kasan uwa da ƴarta, hannayenta biyu daddafe da bayanta, ko lokacin da azeeza take shasshafa sumar kan batul duk tana ji, sai dai bata motsa ba, gani take kamar in ta saketa za'a ƙara rabata da ita ne, Angel na matuƙar ƙaunar batul, fiye da tunanin mai tunani, irin ƙaunar da ta ke yi mata bata da banbanci data uwa da ɗanta, ji take kamar ciki ɗaya suka fito da batul. Sarah da ke a tsaye tun ɗazu tana kallonsu, bata furta komai ba, sai dai da alama itama ta tayasu kukan don hada hawaye kan fuskarta, bakomai ne ya ta6a zuciyarta ba, face yarda taga sunata kuka, da kuma yarda Angel ta ƙanƙame ƴar uwar ta su a jikinta, hakan ya tabbatar mata da irin son da su ke yi mata, duk da batasan wacece batul ba, amma tana yawan jin suna ambaton sunanta, ta shaida irin ƙaunar da suke yi mata, ba ƙaramin burgeta su ka yi ba. "Angel har yanzu bata farka ba? Ya za'ae muna so musan awani hali take ciki, A ƙagare muke da mu rungumi ƴar uwar mu, muji ɗuminta a jikin mu, tsawon lokaci bama a tare" Deeja ce tai magnar, fuskarta a yamutse don hankalinta ba'a kwance yake ba. Dare ya koma masu tamkar da rana, babu mai jin bacci a cikin su, dama sun sha bacci yau. "Bari na ɗebo ruwa a yayyafa mata ko mun samu ta farka" acewar rubina, kafin tayi yunƙurin mikewa Yasmin ta dakatar da ita ta hanyar yi mata magana"ai ba suma tayi ba, bacci ta ke yi, bana so mu takura mata, tunda tana nunfashi mu jira har zuwa time da zata farka"! Fasa zuwa ɗebo ruwan rubina tayi, Cikin sanyin murya parveen tace"Allah yasa kada ta farka tana jin yunwa, wlh da ace mun san yau za'a dawo mana da ita, ai da mun ajiye mata abinci dayawa," ta yi maganar tana matse ƙwallar idonta, ɗakin yai tsit masu yin shessheƙar kukan duk sun dakata. Sun yi zugudum kamar masu zaman makoki, kowa da abunda yake saƙawa a cikin ranshi dangane da tsintar batul da su ka yi a cikin su, Damuwace ƙarara akan fuskokinsu, fatansu Allah yasa ba acutar masu da ita ba, duba da irin baccin da take yi mai nauyin gaske, deeja ce tai tunanin yi magana akan suje su kwanta. "Yakamata kuje ku kwanta ku yi bacci, dare ne sosai, nasan kafin gobe da safe in sha Allah zata farka......" tun kan ta kai ƙarshen maganar, su ka haɗa baki wurin cewa"ai bazamu iya runtsawa ba, idan har ƴar uwar mu bata farka ba, kusan wata uku bamu atare da ita, till today aka dawo mana da ita, Ta yaya kike tunanin zamu iya yin bacci? Ba tare da mun gana da juna ba" Ita kanta Deeja ta yi masu maganar ne kawai, don tasan ba kwanciyar za su yi ba, duk wannan maganganun da suke yi Angel bata fahimtar su, domin kuwa hankalinta na akan batul ɗinta, dake kwance saman ƙirjinta, ta natsu tana sauraron bugun zuciyarta, sai faman lumshe idanuwanta ta ke yi, waɗanda suka canza launi saboda kukan da tasha, har yanzu hawayen basu daina gangarowa ta cikin idanuwanta ba. "pls Angel ki kwantar mana da ita, yadda zamu samu damar ganin fuskarta da kyau, munyi kewarta sosai" Acewar eve, shiru Angel bata motsa ba, babu alamun zata kwantar da ita, hannu Deeja ta kai saman bayan Angel ta ɗan bubbugata don ta dawo hayyacinta. "Angel muna son ganin fuskarta, ki kwantar mana da ita" deeja ce tai maganar, still bata tanka masu ba. "Ko dai ta yi bacci ne"? Hibba ce tai tambayar, Sarah dake a tsaye ta matso kusa da gadon, ta sanya hannayenta biyu da niyar ta raba jikin batul daga na Angel, amma ta kasa, Lamarin ya ɗaure masu kai, suka dinga kiran sunanta taƙi amsa masu, kuma ba bacci ta ke yi ba. Parveen da Deeja ne suka haɗa hannu wurin ƙoƙarin 6an6are batul daga jikinta, abun ya ɗaure masu kai, yadda taƙi sakinta, kamar su fashe da kuka saboda yadda suka ƙagara da son ganin fuskarta. "Bani na ruƙe ta ba, itace ta ruƙe ni" Muryar Angel ce ta yi masu magana, abunda basu sani ba, tun lokacin da Angel ta rungumo batul a jikinta ta farka daga baccin, koda taji jikin ƴar uwarta ne, ta ƙanƙameta sosai, hannayen batul na abayan Angel ta zagayo da su, sumar kan Angel ce ta rufe su shiyasa basu lura da cewar itace ta matse ta a jikinta ba, tun da farko da su ka buƙaci ganin fuskarta, Angel tai ƙoƙarin sakinta, sai dai ita batul ɗin taƙi bari ta raba jikinta daga nata, that mean batul ta farka daga bacci tuntuni. Sun yi mamakin jin abunda Angel tace masu, na cewa itace ta ruƙeta, muryar Deeja a sanyaye tace"Batul, idan kina jin mu ki juyo ki fuskance mu, mu ma minyi missing ɗin ki sosai, muna buƙatar mu yi hugging ɗin ki a jikin mu......." Kafin Deeja ta rufe bakinta, batul ta zame hannayenta daga ruƙon da ta yi ma Angel, kamar bata son raba jikinta daga nata, slowly ta zame kanta daga saman kafaɗar Angel, ta ɗago da kanta, yayin da ta ke ƙoƙarin buɗe idanuwanta kamar sunyi mata nauyi. Angel sai kallonta ta ke yi, hatta su parveen sun zagayo ta inda zasu dinga ganinta da kyau, a wani irin yanayi ta buɗe kyawawan idanuwanta akan fuskar Angel da ke kallonta kamar zasu haɗiye juna, tun daga kan kallon da ta ke yi mata zai tabbatar maka da cewa ta yi matuƙar yin kewarta, ta yi kukan rashinta atare da ita, A hankali ta ɗauke idanuwanta daga kan fuskar Angel ta mayar dasu kan fuskokin su Deeja, Ɗaya bayan ɗaya take ƙare masu kallo kamar yau ta fara ganin su, haka suma su ke ta kallonta kamar sun samu tv, tambayoyi suka shiga jera mata kamar ƴan jarida "Batul kina lafiya? Babu abunda ke damunki? Kin gane mu kuwa? Meyasa kike ta kallon mu! Ba zaki iya magana ba? Ko akwai inda ke yi maki ciwo? Dan Allah ki yi mana magana, mun damu dake sosai, munyi kewarki, munyi kuka rashinki kamar mu zauce........" suna magana hawaye na bin fuskokin su, basu yi tsammanin zata tanka masu ba. Tausasan la66anta ta soma motsawa muryarta a sanyaye ta soma ambaton sunayensu ɗaya bayan ɗaya Angel, Hannah, Hibba, Deeja, Parveen, Eve, Yasmin, Rubina," tsabar farin ciki yasa suka fasa ihu Jin ta kira sunayen su hakan na nufin Tana acikin hayyacinta, wani irin farin ciki ne ya lullu6e Su, kamar waɗanda akayiwa albishir da mukullin fita daga cikin kurkukun ƙaddara. Tana so ta bayyana masu irin kewarsu da tayi sai dai takasa magana, saboda hawayen da suka ciko idanuwanta, daƙyar ta iya buɗe masu hannayen ta tare da yi masu alamar su matso kusa da ita, da sauri suka matsa ta haɗa azeeza da parveen da deeja ta rungumesu, sai lokacin ta samu damar fitar da kukan da take 6oyewa, sosai ta fashe masu sa ku ka, suma kukan suke yi an rasa me lallashin wani acikin su, ta ɗauki tsawon lokacin kafin ta saki su deeja, ta miƙa masu Hibba hannu suka matso suma ta rungume su a ƙirjinta, dukkan su saida suka ji ɗumin jikinta, da hannayensu suka dinga share mata hawayen dake akan fuskarta, itama ta sanya hannunta tana share ma kowannansu na kan fuskarshi. Cikin sanyin murya ta furta"ashe da rabon mu sake ganin juna nida ƴan uwana! ashe mafarkina zai zama gaskiya na sake yin rayuwa a cikin ku? Jan numfashi tai kafin taci gaba da cewa"duk yadda zan faɗa maku irin kewarku da nayi ba zaku fahimta ba, haukane kawai banyi ba, amma naji jiki na rashin ku atare dani, na zubar da hawayena kamar bazan rayu ba, Allah ne kaɗai yasan irin raɗaɗi da ƙuncin da na shiga........" kasa ƙarasa maganar ta yi saboda kukan daya ciyota, da sauri Angel ta sanya hannayenta biyu ta dafa shoulders ɗinta tana lallashinta. "Batul ki daina kuka dan Allah, kuma ku daina zubar da hawayen ku, godiya yakamata mu yi ma Allah daya dawo mana dake lafiya, duk da naga sauyi atattare dake, bamu san ina aka kaiki ba! Me a ka yi maki na tsawon watannin nan! Na yi maki tambayoyin nan ne saboda su ne damuwar mu, amma bamu buƙatar amsar su ayanzu, saboda kwanciyar hankalin ki mu ke so, ashirye mu ke da mu sanyaki farin ciki, wanda zaisa ki manta da duk wata damu da kika shiga na rashin mu atare dake," Kalaman Angel ba ƙaramin sanyaya mata zuciya su ka yi ba, atare suka ɗaga hannayensu sama suna yiwa Allah godiya haɗi da yi ma ƴar uwarsu batul addu'a, duk tana sauraronsu, wani irin sanyine ya ratsa zuciyarta, bayan sun kammala yi mata addu'ar ne, ta ɗago da kanta daga jikin Angel, Ganin tana kallon gadajensu Danish yasa duk suka sha jinin jikin su, aruɗe take ƙare masu kallo, abun da basu ta6a tsammanin zata tambayesu ba, sai ji su ka yi tace"Ina Danish!" shine mutun na farko da ta fara tambayarsu, sun yi mamakin hakan duk irin abunda yayi mata, cigaba da tambayarsu ta yi cikin ruɗu. "Meyasa bangan su asaman gadajen su ba? Ina Haris ina Javed da Mubeen da Naufal? Ina su ka je ne? Ko sun shiga toilet ne"? Angel ce ta yi mata magana"ki yi haƙuri batul, zuwa gobe da safe zamu faɗa maki komai, yanzu dare yayi sosai, ki kwanta ki huta ," ta yi maganar tare da ruƙota, ta kwantar da ita tare da janyo bargo ta lullu6a mata shi saman jikinta zuwa ƙirjin ta. Ta yi mata hakan ne duk don ta kawar mata da tunaninta, na tambayarsu agame da su Haris. Mayar da dubanta ta yi gasu Deeja"Ku je ku kwanta, Zuwa gobe za mu yi magana da ita" Ba don sunso ba suka miƙe kowa ya nufi tsohon gadon shi, duk don saboda ita suka kwanta saman su yau, itama sarah ta nufi shimfiɗarta ta kwanta, zuciyarta cike da saƙe saƙe dangane da ƴar uwarsu batul da ta gani yau, da alama akwai wani abu daya ɗan sha mata kai. Mutun biyu ne ya rage Azeeza dake zaune saman gadon batul, sai jamimah dake zaune gefen gadon sai gyangyaɗi ta ke yi kamar zata faɗo ƙasa. "Azeeza taso muje in raka ki ki kwanta," maƙe kafaɗa Azeeza tayi tare da cewa"Inaso na kwana a gefen batul" shiru Angel ta ɗanyi tana kallon fuskarta, taci burin ta kwana tare da batul dinta, ga Azeeza ta nuna tanaso. Ita kanta batul ɗin, bata son Angel tabar gadon nata, sai satar kallon juna su ke yi, da alama akwai wani abu daya ɗaure masu kai agame da canjin da kowan nan su ya yi, Sai da Angel ta ruƙo azeeza ta kwantar da ita gefen batul, tukunna ta sauko daga saman gadon, still idon batul akan fuskarta. "Zanje na kwanta, ki kulamin da kanki, gobe zamu yi magana" ta ƙarasa maganar tana sakar mata murmushi. lumshe ido batul ta yi tare da ɗan jinjina mata kai, hawaye ne masu ɗumi suka soma gangarowa ta cikin idanuwan nata, nan take Angel taji gabanta ya faɗi, sai dai bata tambayeta hawayen menene ba, ta bari sai zuwa gobe su yi magana. kasa tafiya tayi, komawa tayi daga gefen gadon ta ɗan zauna tare da duƙar da kanta saitin fuskar batul, ta manna mata kiss saman forehead ɗinta da cheek nata, a hankali batul ta ɗan ware idanuwanta tana duban Angel wadda tuni ta miƙe daga gefen gadon, sai da ta fara ɗaukar jamimah, kafin ta juya ta kwantar da ita saman gadon Danish itama ta kwanta daga gefenta tare da rungume jamimah a jikinta, sai kallon juna suke yi ita da batul da ke akwance saman gadonta, Da yake suna fuskantar juna. Tsawon lokaci sunata ta kallon juna, ɗakin yai tsit baka jin sautin komai, sun ƙi bari bacci ya ɗauke su, gani su ke yi kamar in suka runtsa za'a ƙara zuwa a ɗauke masu ita, zuciyoyinsu a cike suke da tambayoyi iri iri da suke son su yi mata, idan gari ya ware, sun kwana da wadataccen farin ciki acikin zukatansu saboda dawowar ƴar uwarsu batul, kaɗan daga cikinsu ne suka samu damar tuntsawa. ❤PRISONERS💖 A washe garin ranar tun da sassafe, ta soma jin hayaniyarsu a cikin kunnanta, muryoyinsu da alamun farin ciki atattare da su, a hankali ta ɗan buɗe idanuwanta, biji biji ta fara ganinsu a kewaye da gadonta, har saida ta ɗan firgita, daga bisani ne idanuwanta suka dawo normal taga fuskokinsu a washe sai murmushi suke sakar mata, azeeza da ke a gefenta kwance, ta ɗan tada kanta saman gwiwar hannunta, ta ƙura mata ido sai kallonta ta ke kamar zata lashe ta. "Alhamdulillah, Alhamdulillah, Alhamdulillah! Allah mun gode maka daka dawo mana da ƴar uwar mu batul, Nifa jiya da daddare dana kwanta, gabana ya dinga faɗuwa gani nake kamar in na runtse idanuwana zan farka inga babu batul ɗin mu" Deeja ce ta yi maganar fuskarta ɗauke da murmushin farin ciki. Parveen tace"wlh nima haka naji araina, shiyasa yau da safe ina farkawa nai wuff nazo gaban gadonki don in duba in ga ko kina nan" ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskar batul, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, sai faman jujjuya eye balls ɗinta ta ke yi akan faces ɗin su. "Ni kaina da mafarkin ki na kwana, ƴar uwata rabin raina" da sauri ta wurga eye balls ɗinta kan fuskar Angel wadda zuwanta kenan, Tana agefen Hibba, wani murmushin ne ya ƙara bayyana akan fuskarta, wanda ke nuni da irin farin cikin da take a ciki. "Fatan ba mu takura maki ba, mun tada ki daga bacci, wlh mun yi kewarki ne kamar mu zauce" acewar hibba, calmy ta soma magana"Nafi so ku takura min hibba, aini abunso ne a wurina, in gan ku atare dani, ko na minti ɗaya bana son wani a cikin ku ya nisanta dani, ba dan ƙaddara ta rabani da ku ba, ku kan ku kun sani, da ƙafafuwana bazan ta6a yin nesa da ku ba" muryarta na ɗan rawa ta ƙarasa maganar, tuni idanuwanta suka cicciko da ƙwalla, ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta. "Batul pls don't cry, idan har ba so kike zuciyoyin mu su raunata ba, mun fi buƙatar farin cikin ki ayanzu, ki daure pls," Deeja ce tai maganar, lumshe idanuwanta ta ɗanyi yayin da take binsu da kallo, su kansu sun fahimci akwai wani abu dake damunta. "Azeeza irin wannan kallo haka, " daƙyar ta furta maganar, tana kallon azeeza, murmushi ta sakar mata tare da cewa"Ƙaunarki nake yi batul, dole in kalle ki don baki san irin kewarki da nayi ba. Kamar in haɗiye ki" tayi maganar tana wage bakinta, Hakan da ta yi ba ƙaramin dariya ta basu ba. Ita kanta batul ɗin saida ta ɗan murmusa, a hankali ta yunƙura ta miƙe, itama azeeza ta miƙe zaune saman mattress ɗin, Saukowa ta yi daga saman gadon taci gaba da tafiya tana bin ɗakin nasu da kallo, ganin irin sauye sauyen da a ka yi mashi, gaba ɗaya suka bi bayanta suna tafiya atare da ita, dakatawa tayi da yin tafiyar tare da juyowa ta kallesu tace"Jiya na tambaye ku amma ba ku bani amsa ba, ina Danish dasu haris su ke ne"? Deeja ce tai ƙarfin halin faɗa mata cewa anzo an tafi dasu almost one week, An riga tafiya da Danish," iya abunda ta sanar da ita kenan, bata faɗa mata awani hali aka tafi da shi ba, jinjina kanta ta yi ba tare da tace komai ba, sai dai fuskarta ta nuna alamun damuwa, kuma idanuwanta hawaye ne acike dasu. "An kawo mana sabbin prisoners ne? Jiya kamar naso inga wata ƙaramar yarinya," tai tambayar tana kallonsu "naga kuma sabbin gadaje, kusan goma sha biyar" yasmin ce ta bata amsa dacewa"Eh, bayan tafiyarki aka kawo su, Amma mutun biyar ne prisoners ɗin, sai dai daga cikinsu Giants sun tafi da mutun uku, yanzu biyune atare damu. jamimah itace ƙaramar sai Sarah," ajiyar zuciya ta sauke tare da cewa"ku bani labari mana, dame dame ya faru bayan bana nan"? A taƙaice Angel ta sanar da ita duk wani abu da ya faru bayan bata nan sai dai bata faɗa mata wanda zai sanyata damuwa ba. "Mu koma mu zauna batul," yasmin ce tai mata maganar, ganin sai yawo su ke yi cikin ɗakin, ga shi daga gani jikin nata babu ƙwari, ga ƴar guntuwar rigar dake a jikinta sai ɗagewa ta ke yi. "Kina jin yunwa" parveen ce tai mata tambayar, ɗaga mata kai ta yi alamar eh, langwa6e kai parveen"wayyo Allah, ga shi babu abinci sai giants sun kawo mana" ƴar dariya Batul ta saki kafin tace"Ki kwantar da hankalin ki, kallon ku da na ke yasa naji na ƙoshi, babu wani yunwa atare dani," "Batul baki bamu labarin ina aka kai ki ba tsawon wata uku? Sannan waye ya dawo mana dake ko giant ne, mun ga kin canza mana sosai, kin rame kamar babu ƙoshin lafiya atare da ke" rubina ce tayi maganar, Shiru ta ɗanyi kamar bazata amsa mata tambayoyin ta ba, duk su ka tsareta da ido suna kallonta, tun kafin ta fara magana Angel ta raya aranta cewa batul baza ta faɗa masu gaskiyar abunda ya faru da ita ba, ko dan kada ta sanya su damuwa. A tsanake ta soma magana"bakomai ne zan iya tunawa ba, tun time da aka tafi dani, na dai san ba a cutar dani ba, ramar da ku ka gani a jikina bata komai bace face rashin ku atare dani, na tsinci kaina acikin wani ɗaki ina rayuwa ni kaɗai, ban rasa ci da sha ba, ana kawo min lafiyayyen abinci, ina yin wanka har ma in kwanta in yi bacci, mafi yawancin lokutta, ina yawan yin kukan rashin ku, in dinga ihu ina ambaton sunayen ku don kuzo ku ɗauke ni sai dai shiru babu mai jina........." iya abinda ta faɗa masu kenan, kuma sun yarda da maganarta, banda Angel, don koda tana basu labarin idonta akan Angel don tasan bazata yarda da ita ba, abunda yasa su deeja suka yarda da labarin da ta basu, saboda an dawo masu da ita ba kamar yarda aka saba dawowa dasu ba, Cikin mawuyacin hali, wasu ma basa a cikin hayyacin su. "Batul yakamata kije ki yi wanka, akwai sabbin kaya da muka fada maki tsohuwa tamira ta bamu zamu ɗauko maki naki ki sanya, sannan muna so zamu gyara maki gashin kan ki" fuskarta ɗauke da murmushi tace masu toh, Eve tace"wai ina Uniform ɗin ki su ke ne? Ya akai aka sanya maki wannan guntuwar rigar launin Ja"? Muryarta da en ina tace"am..in..nima bansani ba, bansan waye ya canza min ita ba, kawai rana ɗaya na farka na ganni da ita a jikina" wani irin kallo Angel take binta dashi, kallon ban yarda da maganar ki ba, sai faman wurwurga ƙwayar idanuwanta ta ke yi, da zarar sun haɗa ido da Angel saita kawar da kanta gefe. Ganin hakan yasa Angel ta ruƙo hannunta a cikin nata sosai ta damƙe shi tare da cewa"Muje na taimaka maki kiyi wankan" da sauri ta girgiza kai tare da cewa"Zan iya Angel, ki bari zanje nayi da kaina" a ruɗe tayi maganar, hakan ya ƙara tabbatar ma Angel abunda ta ke hasashe akanta, ta 6oye masu abunda ya faru da ita. Gyaɗa kai Angel tayi"Its ok, amma mu fara shiga toilet ɗin, mu wanke maki kanki, In yaso daga bisani saimu fito mu barki ki yi wankan" muryarta adarare ta amsa mata da toh. Mutun uku ne suka haɗu wurin wanke mata gashin kanta saboda yawanshi, Angel da Hanna sai Seeja, Sosai suka murje gashin kan nata, Bayan sun kammala wanke mata kan, suka barta cikin toilet din don tayi wanka, Angel fa jikinta duk ya yi sanyi, a ƙagare take da su samu damar da zasu ke6e da ita don suyi magana, sai dai ga dukkan alamu ita batul ɗin bata son su yi magana, shiyasa take kakkauce mata, Bayan wasu ƴan mintuna, Batul ta fito daga wakan, dama tun kafin fitowarta Angel ta ɗauko mata sabbin kayanta, ba tare da 6ata lokaci ba, ta zura uniform din a jikinta, Masha Allah, zayyana irin kyan da batul tayi a cikin kayan nata 6ata baki ne, abunka ga fara sol, Sun ƙara fiddo mata da kyanta, don ma ta ɗanyi rama. daga ciki ta sanya red vest dinta, sama ta ɗaura wrap coat dinta, kafin ta sanya black trouser din, Angel ce ta taimaka mata wurin ɗaure igiyar coat ɗin, ta ɗaura mata Cotton scarves ɗinta saman wuyanta, Bayan ta kammala gyara mata su tsaf a jikinta. Su Parveen sai santin kyanta su ke yi, Hannu biyu angel ta sanya wurin janyota a jikinta, sosai ta rungumeta, tana ɗan bubbuga bayanta, in a low voice ta furta mata"Ina son magana da ke, amma na lura kamar baki so why"? Muryarta na ɗan rawa tace"Angel, banason tuna abunda ya faru dani, pls kada ki matsa min kada ki tambaye ni komai, na roƙe ki, kuma bana so hakan ya 6ata maki rai" suna yin maganar ne ba tare da sun raba jikinsu daga na juna ba. "Shikenan batul, bazan tambaye ki ba, ni kaina bana son na takura maki, zan jira ki har zuwa time da kika ji zaki iya sanar dani sai ki faɗa min" ta amsa mata da toh," Deeja dake ta kallonsu manne da juna ta fahimci cewa magana su ke yi, bayan sun raba jikinsu, ta dinga bin su azeeza tana rungume su a jikinta tana faɗa masu irin kewarsu da ta yi, Deeja kuma taja hannun Angel su ka koma gefe ɗaya, Tambayarta ta yi me suka tattauna da batul, ta sanar da ita cewa ta tambaye ta ne game da abunda ya faru da ita amma bata faɗa mata komai ba, Deeja tace"kada mu takura mata, tunda ta nuna bata son mu sani, mu ƙyale ta kawai, wata kil hakan zaifi mana kwanciyar hankali," Angel ta gamsu da maganar deeja. Badajimawa ba, Giants suka kawo masu lafiyayyan abinci, Saboda tsabar ƙauna, a baki suka dinga ba batul tana ci, sunƙi bari ta sanya hannunta taci, hakan ba ƙaramin karya mata zuciya yayi ba, tabbas an zalunce ta da aka raba ta da ƴan uwanta, amma yanzu Alhamdulillah tunda gata a cikinsu, da ranta da lafiyarta. Bayan sun kammala Cin abincin, Giants suka tattara Farantan suka tafi dasu, A saman shimfidar sarah, suka zazzauna suna fira tare da batul, Angel tana zuƙunne gaban akwatinansu, Ta buɗe ta ɗauko Nail cutter da nail filler tare da madubi, ta dawo ta miƙe ma Sarah tace gashi ta gyara ma ƴar uwarsu akaifa, Murmushi sarah tasaki, tare da sanya hannu ta kar6a, Kafin su fara gyaran akaifar, Angel tace ta ɗan dakata, tana so su kalli faces ɗinsu a cikin madubi, ita da ƴar uwarta batul, Gefen batul ta zauna tare da ɗaga madubin, Ta haɗa fuskokinsu wuri ɗaya, Suka natsu suna kallon juna, hakanan Angel ta dinga jin faɗuwar gaba a yayin da take kallon fuskar batul ta cikin mirror, su azeeza sai faman leƙo da fuskokinsu suke yi suna kallon su. "An ta6a faɗa maku cewa, Kuna bala'en kama da juna" Sarah ce tai maganar, parveen tace"wlh kuwa nima saida ki ka yi maganar nan tukunna na lura da hakan, Angel da batul suna kama sosai, musamman ta wurin shape ɗin bakinsu, duk da ba launi ɗaya bane, da kuma hasken fatarsu, gashin kansu ma Ya yi shige, hatta tsawonsu iri ɗaya," Deeja tace"ae hatta Yatsun hannuwansu dana ƙafafuwansu iri ɗaya ne sak babu bambanci, najima da sanin wannan ban ta6a faɗi bane" sarah tace"to kodai ƴan gida ɗaya ne"? Girgiza kai Yasmin tai tare da cewa"A labarin da Angel ta bamu, ita kaɗaice Awurin daddynta, mommynta ma, tun tana yarinya ta gudu tabarta, bata da ƴar uwa mace tun da ta taso a rayuwarta," Sarah tace"hmmm adai yi shiru kawai amma fa ni akwai abunda nake zargi, ina da wata baiwa da ku ba ku sani ba, tun kasancewa ta a prison, nake wannan hasashen, nasha ganin masu kama da juna wanda su basu lura da hakan ba, sai dai ina tunanin zaman tare ne yasa muke kamanceceniya da juna, yanzu a cikin ku nan, kaf ɗinku Naga kamanceceniya atsakaninku da junan ku, Hatta wannan yarinyar da aka kawo mu tare da ita, Me take da suna....." Eve ce ta ƙarasa mata maganar da cewa"Kina nufin Ƴar gidan daddy" jinjina kai tayi "eh ita nake nufi, akwai kamanceceniyarta da wani acikin ku, amma bazan faɗi ba" tana ƴar dariya ta yi maganar, "Ko kina nufin azeeza? Don kinga kalar gashinsu yayi shige da launin fatarsu," girgiza kai tayi"a'a, ba azeeza ba, bana so na faɗi maku ne" Roƙon ta su ka dinga yi haɗi da yi mata magiya akan ta faɗa masu da wa take kama, da kuma sauran waɗanda ta ke hasashen suna da kamanceceniya a tsakaninsu, tace masu itafa su daina yarda da maganarta, Ƙarya ta ke yi masu" Haushin da suka ji ne yasa suka dunƙule hannu suna yi mata dundu abayanta, Abun saiya koma wasa, duk wannan abun da suke yi Angel da batul suna sauraronsu, sai dai hankalinsu ba akansu Ya ke ba, Yana akan junansu, Sai kallon fuskokinsu suke yi ta cikin madubi kamar zasu lashe juna, Sai da suka gama ƴar buge bugen da sarah, kafin daga bisani, kowannansu Ya natsu, suna ta nishi kamar waɗanda suka sha gudu. Bayan sun samu natsuwa, Sarah ta soma gyarama batul akaifarta, Allah yayi mata baiwar Iya gyara akaifa, Batul taji daɗin ganin yadda ta gyara mata akaifarta, ta dinga yi mata godiya, Sarah tace tadaina yi mata godiya, domin kuwa babu godiya a tsakanin prisoners," Ataƙaice, Cikin ƴan kwanakin nan da aka dawo masu da batul, Sun samu farin ciki mara misaltuwa, Tamkar an ya ye masu damuwar dake damun so, koda yaushe suna atare da ita, dama batul akwai iya kalami mai ratsa zukata, haka zata zauna tana kwantar masu da hankalinsu, da deeja tare da Angel, waɗannan mutun ukun sun zama tamkar iyaye agare su, yanzu batul ta fara murmurewa, tsawon sati biyu da aka dawo da ita Jikinta yafara dawowa normal, babu ramar nan, hakan ba ƙaramin daɗi yayi masu ba, har tambayar Angel tayi bayan bata nan an ƙara ɗaukar wani cikin su Hibba, ta sanar da ita cewa ba a ƙara zuwa ɗaukarsu ba, saboda babu wanda ya ƙara yin jinin a cikinsu, Allah ya yaye masu, sun samu salama, har cikin ranta taji daɗin jin hakan, Angel taso ta tambayi batul game da labarin da Gabriel ya bata na yarinyar daya gani tana gudu saman hawa na uku, saboda a suffar da aka dawo da batul yayi dai dai da yarda ya zayyana mata ita, hada guntuwar rigar daya gani a jikinta, Tabar abun a cikin zuciyarta ne, tun da ta nuna bata son maganar. Har ila yau shiru ba'a dawo dasu Haris ba, Sun zuba ma sarautar Allah ido, addu'a kawai suke binsu da ita, A 6angaren Angel bata ƙara tada zancen dura tagar nan ba, saboda alƙawarin da Danish yace ta ɗaukar mashi akan bazata haurata ba, duk da a lokacin bata amsa mashi ba, sai dai taji ba za ta iya karya mashi alƙawarin ba.......... 💔PRISONERS💔 Kwakkwance suke saman gadajensu, suna ta sharar bacci, har safiya ta yi amma basu farka ba, Jiya sun aikatu sosai, sai da suka wanke uniform ɗinsu duka da tsafaffin da sababbin kamar yarda suke yi in zasu wanke su sai su ɗaura bargunansu a jikin su, Bayan sun kammala wankin su ka shanyasu zuwa lokacin da suka bushe suka mayar da tsoffin a jikinsu, sababbin suka ninninke su acikin akwatinansu, basu huta ba saida suka wanke bargunansu, suka shanyasu saman igiya, bayan sun kammala suka wanke toilets dinsu duka uku, suka bama furennin nan ruwa, Daga bisani, suka dawo cikin ɗakinsu, shima suka gyara shi tsaf tsaf komai Ya koma normal, a lokacin dare yayi suka kwanta don su huta, in the midnight Angel ta tada kowannansu don su yi addu'a kamar yarda suka saba, ga bacci a idonsu da gajiya amma ahaka suka zaune tare da ɗaga hannayensu sama suna kai kukansu wurin Allah, bayan sun kammala ne wani baccin ya ƙara yin awon gaba dasu, Shiyasa har gari ya waye basu tashi ba, saboda basu samu isasshen bacci ba jiya. Azeeza da Jamimah suna a kwance saman gaɗo ɗaya, sarah tana a kwance ƙasa saman shimfiɗarta, yayin da batul ta ke a kwance saman gadon Danish ita da Angel, ƙudundune cikin bargo, atakure su ke gadon ya yi masu kaɗan ahaka suka kwana, su parveen duk suna asaman nasu gadajensu. Wata irin zufa ce ta soma wanke fuskarta, ta dinga tsastsafo mata daga jikinta, Yatsun hannayenta da ƙafafuwanta suka soma kakarwa, Mafi yawancin lokaci idan hakan ya faru to mafarki ne ta ke yi acikin baccin ta, _Ta tsinci kanta acikin wani gini mai girman gaske, mai ɗauke da tagogi babu ƙopa ko ɗaya a jikin shi, tsananin tsoro da firgici ya kamata, ta dinga kuka tana ambaton sunan Allah akan ya kawo mata ɗauki, wasu halittu ne ke fitowa ta jikin bango ɗauke da suffar namun daji, munanan gaske, gaba ɗaya ita suke tunkarowa, gashi babu hanyar da zata gudu daga cikin ginin, fashewa tayi da matsanancin kuka mai cin rai tana girgiza kanta tamkar zai 6alle, Halittun na dab da ƙarasowa gabanta, Sai ga wata halitta ta faɗo ta saman ginin ɗauke da manyan fuka fuki sai shawagi take yi tana kewaye tsakiyar Ginin, kafin ta karyo kwana ta sanya hannayenta biyu ta ɗauke Angel tayi sama da ita ta fuce daga Cikin Ginin_ A dai dai nan mafarkin nata ya katse, A firgice ta farka daga baccin tana faman zare idanuwanta, hannunta ɗaya dafe da saitin zuciyarta da ke ta harbawa, zufa duk ta wanke fuskarta, muryarta na rawa ta soma ambaton "A'oothu billaahi minash-Shaytaanir-rajeem" sau uku tana ambatonta. Bayan ta kammala taji sauki acikin ranta, ta juya ta kalli batul dake ta sharar baccinta, ajiyar zuciya ta sauke tare da zuro ƙafafuwanta ƙasa ta sauko daga saman gadon, zuciyarta acunkushe da tunanin mafarkin da ta yi yau, ta rasa gane me ma'anar mafarkin ke nufi kodai shaidan ne ya haddasa mata yin shi, sai dai tana ji acikin ranta kamar akwai wani abu da ake son nuna mata acikin mafarkin, Taya zata iya fahimtar hakan? Wani ginine ta gani acikin mafarkinta? Babu ƙofa a jikin shi sai dai tagogi, ga wasu halittu na ƙoƙarin kawo mata hari, abun da ya ɗaure mata kai, wannan halittar data 6ullo ta saman ginin dake a datse babu ƙopa, taya akai ta shigo ita? Harta taimake ta kuma ta fitar da ita daga cikin ginin da babu ƙopa a jikin shi? Ganin tana ƙoƙarin burkita lissafin ƙwaƙwalwarta ne yasa ta dakata da yin tunanin, da sauri ta juya ta nufi toilet don ta yi fitsari, shiga ciki tai tare da jan jam lock ta datse ƙopar, Juyawar da zatayi keda wuya taji gabanta ya faɗi ras! Ba tare da sanin dililin hakan ba, Acikin zuciyarta ta soma ambaton Innalallahi wa'inna ilaihirraji"un" kusan sau shida har saida taji zuciyarta ta ɗan lafa tukunna ta ƙarasa shiga ciki, Tayi abunda ya kawota, bayan ta kammala kafin ta fita ta ɗan juya ta kalli furennin dake acikin tukunyar, wannan dogon furen daya kere tsayin sauran launin punch pink, ganyayyakin Jikin shi sunyi baƙiƙƙirin dasu, hankalinta ba ƙaramin tashi yai ba, da sauri ta koma ta ɗebo ruwa a bucket takai shi bakin tukunyar ta zuƙunna tana goge bakin jikin shi da hannayenta gani take kamar goga mashi baƙin akayi, sai dai koda ta goge babu abunda ya canza har ruwa ta zuba mashi ta wanke shi yaƙi canza launi, miƙewa tayi taje ta ɗauko detergent tsabar hauka hada Soso ta zuƙunna gaban tukunyar ta dinga goge ganyayyakin jikin furen don su koma launinsu na asali, sai dai kash sunƙi komawa, kamar tana ƙara masu baƙi, a ƙarshe data gaji ta maida soson da omon, ta fito daga Cikin toilet ɗin Jikin ta ba ƙwari, hakanan ta dinga jin kamar faɗuwar gabanta yana da nasaba da canzawar launin ganyan furen nan, duk da batasan ran wanene akan shi ba. A bakin ƙopar toilet ɗin ta jingina bayanta, Idanuwanta acike tab da ƙwalla, daga Cikin ɗakinsu ta soma jin motsin buɗe ƙopa, da farko ta yi tunanin giants ne masu kawo masu abinci, shiyasa taƙi motsawa kwatsam! Ta soma jin shessheƙar kukan mutun acan cikin ɗakinsu, Da gudun gaske ta faɗo ɗakin a sukwane ta kai idanuwanta kan benan inda take jiyo sautin, Bakowa idanuwanta ke nuna mata ba face Majnoon fuskarshi ta yi jawur da ita, jan tabo ta ko'ina a jikin shi, jini ya kwanta sosai, daga shi sai jan wandonshi a jikin shi babu riga, ya rame sosai, kamar ba mutun ba, hankalin ta ba ƙaramin tashi yai ba, tana ƙoƙarin motsa la66anta donta kira sunanshi karaf idanuwanta suka sauka akan fararen ƙafafuwan mutumin dake a gefen shi, a matuƙar ruɗe Angel ta shiga bin ƙafafuwan da kallo daga gani macace, koma wacece taji jiki na fitar hayyaci ta jigata sosai, duba da irin yarda jikinta keta kerma babu alamun lafiya atattare da ita, Hannunta ɗaya ruƙe da pant na mata launin Pink colour..........." 💋PRISONERS💋 Muryarta a ruɗe ta ambaci sunan ta, "UNAIZA"! a yayin da ta ke ƙare mata kallo na ban al'ajabi, kamar fatalwa ta rame ta bushe ta ƙanjame, Irin rigar da aka dawo da batool itace a jikinta launin ja guntuwa wadda da kadan ta zarce mazaunanta ta yi wani irin haske, babban abunda ya tayar ma Angel hankali yakushin akaifar da ta gani akan fuskarta, wuyanta da fuskarta duk sun faffashe ta ko'ina red marks ne, hatta la66anta a fashe su ke sun kumbura, idanuwanta sun ƙanƙance daga gani ba ƙaramin kuka tasha ba, kamar ma bata a cikin hayyacinta, tsananin tashin hankali ne akan fuskar Angel, zuciyarta ba ƙaramin tashi tai ba, ta rasa akan wa zata tsayar da idanuwanta, tsakanin majnun da ya ke yin shessheƙar kuka da kuma Unaiza da ke A tsaye jikinta na kerma, gabanta na faɗuwa ta soma tafiya tana tunkarar su, koda majnoon yai arba da fuskar Angel nan ta ke ya kware baki yana kuka yana ambaton sunanta, da gudun gaske Angel ta nufe shi tunkan ta ƙarasa gaban shi a wani slow ta zube saman gwiwowinta dab da shi ta sanya hannayenta biyu da ke yin kerma ta rungumo shi zuwa jikinta, tsabar tausayin shi da ta ji ne yasa ta fashe da matsanancin kuka mai sautin gaske tamkar ranta zai fita, sautin kukanta ne ya karaɗe cikin ɗakin nasu, Wanda silar hakan ya farkar da masu Bacci, A firgice kowan nan su yai wurgi da bargon shi a lokaci ɗaya su ka mimmiƙe zaune saman gadajen su suna faman mutsustsuke idanuwan su da hannayen su, ba zato ba tsammani idanuwan suka sauka akan Angel da ta rungume majnoon a ƙirjin ta, babu wanda Ya lura da Unaizah a cikin su, Da ƙarfi Deeja ta furta sunan shi"CHINONSO!" ai ko da gudu Suka diddiro daga saman gadajen su Jamimah hada tuntu6e garin yin sauri jin an ambaci sunan abokin wasan ta, Azeeza ta watso da gudu, Gaba ɗayan su ne suka hallara a bakin benen Suna kallon shi, Hankalin su yai mugun tashi Zuciyoyinsu sun karaya, ganin irin tabbunan da ke a saman fatar shi, masu saurin kuka tuni sun fara irin su azeeza, tuni ta zube saman gwiwowinta tana yin kuka. Hawaye ne kwance a cikin idanuwan su, Batool dake a tsakiyar su tana bin bayan majnoon da ido, tuni ta gane cewa su ne sabbin prisoners ɗin da Angel ta bata labari akan su, waɗanda giants su ka tafi da su. Muryar deeja a rauna ce ta furta "Inna lillahi wa inna ilayhir raji'un! Mutanan nan basu da Imani, mugaye ne azzalumai, Ku jibi yadda suka canza mishi halittar shi! Bawan Allah dame zai ji! Da ta6in hankalin dake damun shi ko kuwa da lalurar da yake fama da ita? Ga shi ƙarami dashi baisan komai ba, amma a haka su ka yi amfani dashi, Allah kaɗai yasan irin cutarwar da su ka yi mashi, nashiga uku ni yau! Mu kuma haka rayuwar mu zata ƙare a wulaƙance......." wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya tokare mata maƙoshinta wanda ya hanata ƙarasa maganar, Jamimah sai kuka take yi tana faɗin "Wayyo Allah Majnoon ɗina, Waya yayi maka haka? Jikin ka duk jini! Waye ya cutar min da kai"! Tsananin tausayin shi duk ya kamasu, Jikin batool ba ƙaramin sanyi yayi ba, ta duƙar da idanuwanta ƙasa hawaye ne kwance a cikin su, har yanzu babu wanda ya lura da Unaiza acikin su, Angel kaɗaice tasan da zamanta a wurin. "Wacece wannan?" Ras gaban su Ya faɗi jin muryar batul tana tambaya, kusan atare suka ɗago da idanuwan su suka sauka kan fuskar Unaiza, Muryar su da alamun mamaki suka ambaci sunanta "yar Gidan daddy!" A tsorace suke kallonta, tun daga ƙasa har zuwa sama, girgiza kai Deeja tai muryar ta aruɗe ta furta "I can't believe it! Unaizah ke ce kika koma haka? Ko dai idanuwana ne su ke nuna min ba dai dai ba? Meya same ki har haka? Ina abubuwan ki su ke"? Maganar da Deeja ta yi ce ta jawo hankalin su zuwa ga kallon ƙirjin Unaiza, Tsabar firgici ne yasa wasu daga cikinsu suka daddafe saitin zuciyoyinsu da tafin hannayen su, hatta Angel da ke a zuƙunne rungume da majnoon sai da ta zabura ta miƙe tana kallon ƙirjin Unaiza dake a shafe kamar Allon bango, babu nono babu alamar shi a wurin, yanayin kallon da su ke bin ta dashi ya nuna tsantsar mamaki da al'ajabi, ruɗani da firgici. Batul ce ta yi ƙarfin halin cewa bai kamata mu tsaya muna kallonta ba, tana a cikin mawuyacin hali, mu taimaka mata ta shiga ciki" miƙa hannu batul ta yi da niyar ta ruƙo hannun Unaiza, a firgice ta shiga girgiza mata kai, babu wanda yai tsammanin zata iya yin magana duba da irin raunatar da jikinta ya yi. "Don't let anyone touch me, just leave me alone, I don't want to see any of you, I hate you, saboda kun 6oye min gaskiya, a lokacin dana tambaye ku ina ne nan ba ku faɗa min ba......" A wahalce ta ke yin maganar cikin karyayyar murya, "Tuntuni naso na faɗa maki gaskiya amma Danish shine ya hanani saboda gudun halin da zaki shiga idan kika ji, Unaiza kada ki ga laifin mu, because we're not the reason you came to this prison! Your father is an evil tyrant who sacrificed you to meet his needs, Unaiza mahaifin ki ya cuce ki baya son ki fiye da yadda baki tunani......" zafafan hawaye ne suka wanke fuskar Angel, Yawu ta haɗiya mai ɗacin gaske, ga dukkan alamu zuciyarta ta gama karaya. "I can't believe what my heart is telling me, that my father lied to me and brought me here to humiliate my life, ko a mafarki ban ta6a tsammanin hakan ba, saboda yana sona fiye da yadda ya ke son kan shi....." cikin shessheƙar kuka ta yi maganar tana nuna ƙirjin ta da index finger ɗinta, girgiza kanta ta yi hawaye na cigaba da bin fuskarta, ta ɗaura da cewa "Duk da ba a ƙasa ɗaya muke rayuwa dashi ba, yana bani kulawa, kowace rana sai ya kira ni video call don yaji lafiyata, yasha faɗa min cewa bashi da tamkata a duniyar nan, nifa har ce min yai akaina zai iya 6atawa da kowa har mahaifiyar shi saboda ƙaunar da ya ke yi min, tun da na taso rayuwata ba a ta6a yi min tsawa ba, balle har ta kai ga ata6a lafiyar jikina, nayi rayuwar gatanci, Masu aikin dake kula da ci na da sha na sun fi mutun shidda, abunda nake so shi ake girka min, sannan a baki suke bani abinci, ina da likitocin da ke duba lafiyar jikina wanda mahaifina ne ya ɗauki nauyin yin hakan, Angel ko tari nayi sai an kira Dr ya duba ni, komai na ke so sai daddyna ya yi min shi, I don't ave any financial problems, before nabar gida ina da dala miliyan 2 a cikin account ɗina, wanda shine ya zuba min su don in yi sharholiyata, idan zanyi birthday sai na za6i ƙasar da nake so inje a shirya min party, suturar sanyawata duka babu na ƙasa da dubu ɗari, duk wani abu da kika sani mai tsada na mallake shi, a rayuwata bansan babu ba, bansan menene rashi ba............" dakatawa ta ɗan yi da yin maganar tana jan majina, tun da ta soma magana hawaye basu daina gangarowa saman fuskar Angel ba, idanuwanta sun canza launi sosai, tausayin unaiza ya ta6a zuciyarta, da zuciyoyin su Deeja da ke sauraronta, Azeeza tuni ta ɗauki majnoon ta ɗaura shi saman laps ɗinta ta ƙanƙameshi tana ta lallashin shi ita da jamimah kamar zasu ɗauke mashi ciwon da ke a jikin shi. "Dan Allah ki daina magana, kina ƙara ma kan ki ciwo, ni tausayi kike bani," idanuwan batul cike tab da ƙwalla ta yi maganar, murmushin takaici Unaiza ta saki tana kallonta, "Idan banyi magana ba zuciyata zata fashe ne, bakisan irin raɗaɗin da nake ji acikin zuciyata bane, nagaza yarda da abunda zuciyata ke raya min na cewa mahaifi na ne ya yaudare ni, Shine ya kawo ni nan don a Wulaƙanta rayuwata, Mahaifina fa! Wanda yayi silar zuwana duniya!......." girgiza kai ta ɗan yi fuskarta jawur, tasa harshe ta lashe ƙwallar da ta gangaro ta saman la66anta, duk suna kallonta gwanin ban tausayi. "Nasan bana jin magana, sannan bani haƙuri indai akan biyan buƙatar kaina ce, amma ban ta6a ganin masifa da bala'i ido da ido ba sai dana tsinci kaina a hannun waɗanda suka fi ni iya shaiɗanci, sun ƙarar min da komai, sun kashe min rayuwata, babu abunda yai saura a jikina, yadda su ka yi treating ɗina ko dabba sai haka, An ci zarafi na an wulaƙanta ni an ƙasƙantar dani kamar karya........." A gigice Angel ta daka mata tsawa wadda ita kanta bata san ta furta ta ba, Ta yi hakan ne saboda gudun kada Unaiza ta furta abunda aka yi mata agaban su Hannah, saboda ta fahimci cewa tana acikin hayyacinta tasan komai da aka yi mata, tunanin ta bai gushe ba, idan kuwa harta buɗe baki ta faɗi ainihin me aka yi mata, zasu fuskanci tashin hankali. Sosai Ta fashe da kuka Saboda tsawar da Angel ta yi mata, jikin su duk yai sanyi, ta sagar masu da gwiwa, Angel ta yi danasanin tsawar da ta daka mata, ganin yadda take ta yin kuka, ga jikinta da ke ta yin kerma yasa Angel ta miƙa mata hannu, cikin sanyin murya tace "Am sorry bada son raina na yi maki tsawa ba, ki yi haƙuri ki daina kuka, ki zo mu shiga ciki, na yi maki alƙawarin zan taimaka maki akan duk wani abu da ya dace," hawaye jaga jaga akan fuskar Unaiza da ke kallon Angel, cikin sanyin murya tace "idan kin yi min alƙawarin zaki taimake ni inaso dani da ke mu ke6e, akwai maganar da nake son yi da ke," Jinjina kai Angel tayi alamar gamsuwa da maganar ta, sai da ta fara kallon su Deeja waɗanda ke a tsaye cirko cirko, hawaye sharkaf akan fuskokin su, "Zan shiga da ita sashen toilet, dan Allah ku kula da majnoon, yana buƙatar ku atare dashi" amsa mata su ka yi da toh, zuciyoyin su duk ba daɗi, ran su yana basu cewar kamar wani mummunan abu zai faru" Deeja ce ta ɗauki majnoon ta nufi cikin ɗakin su, suma sauran suka bi bayanta, ya rage saura Angel da Unaiza. "Bazan iya tafiya ba, idan zaki iya ki goya ni a bayanki muje" juya wa Angel tayi tare da zuƙunnawa tace mata ta hau, baiwar Allah da ƙyar ta iya hayewa saman bayanta ta ƙanƙameta, Su hanna sai satar kallon su suke yi, Miƙewa Angel tayi ɗauke da ita a bayanta ta nufi sashen toilet da ita, koda suka shiga ciki tace mata ta buɗe toilet tafi so suyi nisa da kowa, bayan Angel ta buɗe toilet ɗin ta shiga ciki da ita, A jikin bango ta sauke unaiza da ke ta faman yin nishi, ta sanya jamlock ta rufe ƙopar kafin ta dawo ta zauna suna fuskantar Juna, "Pls ki daina zubar da hawayen ki unaiza, kina ƙara karya min zuciyata," runtse idanuwanta tayi sosai, hawaye ne masu ɗumi su ke tsattsafowa daga cikin su, ba tare da ta buɗe idanuwanta ba tace "Angel inaso ki fahimtar dani komai agame da gidan nan, saboda inaso insan dalilin daya sa kika ce mahaifina ne mugu wanda yai silar sadaukar dani, ki bani hujjojin da zasu sa in gamsu da maganarki........." hannu Angel ta ɗaura saman fuskarta tana share mata hawayenta ayayin da ta soma magana cikin tausasa harshe "Farkon zuwana gidan kurkukun ƙaddarar nan, Sato ni aka yi cikin Mota, a lokacin na gudo daga hannun fulanin daji......" Labari Angel ta fara bata dangane da rayuwarta, tun daga kan haihuwarta da mahaifiyarta tayi ta barta acikin kwamin wanka har zuwa rayuwarta a hannun fulanin Daji, da gudowarta daga wurinsu, da sace ta da aka yi, har izuwa ga rayuwarta cikin gidan kurkukun ƙaddara, tunkan ta ƙarasa bata labarin taga unaiza ta fashe da wani irin kuka na fitar hayyaci, Da sauri Angel ta daddafe kafaɗunta da hannayenta biyu tana lallashinta haɗi da tambayarta me yasa ta kuka? Daƙyar Unaiza ta sassauta da yin kukun nata, muryarta a raunane take faɗin"Daddyna ya cuce ni! Ya karya min zuciyata! Ya gama da rayuwata......" Mamakine ya kama Angel jin abunda tace tun kafin ta bata hujjojin da zasu sa ta yarda da cewa shine ya yaudareta sai gashi tana ambaton ya cuce ta ya gama da rayuwarta..., "Unaiza meyasa kika ce haka?" Angel ce ta jefa mata tambayar, Cikin ƙunar rai tace "Angel ni ba musulma bace! Bani da addini, daddyna da kanshi yace min karna kuskura ince zanyi addini ko wani kala ne saboda ba gaskiya bane, babu wani wanda ake bautamawa, nasha tambayar shi ince ya ake safkar da ruwan sama? da sauran abubuwan ban al'ajabi sai yace min they are natural babu wani wanda ya ke yin su, Angel na ta6a kama shi yana yin ibada irin wadda musulmai suke yi, idan bazan manta ba, da safe ne na shiga bedroom ɗinsa na same shi saman carpet, mamaki ya kama ni ganin yana zuƙunnawa ya duƙa ya ɗaura goshi saman carpet, sai mamaki ya kama ni sosae, har zuwa nayi gaban shi na tsaya ina yi mashi magana bai tanka min ba, na zauna agaban shi saman carpet ɗin wanda hakan yasa shi katse abinda ya ke yi, tunkan yayi min magana nace daddy what are u doing? meyasa kake duƙawa ka kai goshin ka ƙasa? A time din bansan menene ba, fuskar shi ɗauke da murmushi yace min motsa jiki ya ke yi, fuskata ɗauke da murmushi nace mashi daddy amma wani kalar motsa jiki ne wannan da ban sani ba? yace min ba buƙatar in sani, saboda yana da wahala manya su ke yin shi, koda nayi yunƙurin ƙara tambayar shi sai yayi saurin janyo ni jikin shi yana shafa min bayana da hannayen shi, dama haka ya ke yi min da zarar na fara jera mashi tambayoyin da su ka shafi rayuwar shi wanda baiso na sani, Sai ya haɗa jikina da nashi yana shafa ni, ko ya haɗa bakina da nashi, da zarar yayi min hakan nake rasa natsuwata saboda bani da linzami, ina da ƙarfin sha'awa da idan ta motsa kamar in zauce, shiyasa idan na rasa wani a kusa dani nake biya ma kaina buƙata da kaina..........." Dafe kai Angel ta yi sakamakon sara mata da ya ke yi, zuciyarta har tashi ta ke yi, Jikin ta ya hau tsuma, tayi mamakin yadda mahaifin unaiza ya zalunce ta, ya hana ta sanin komai game da addinin shi da ahalin shi, ya barta a cikin duhun jahilci, Daƙyar ta iya buɗe baki tace "Kinsan cewa abubuwan da kike yi basu da kyau? Allah ya haramta su? Zunubi ne mai girma," girgiza kai tayi"Ni bansani ba, saboda ba'a ta6a fadamin cewa babu kyau ba, tun kafin na mallaki hankalina nasha kama daddyna da mommyna suna saduwa da junan su a cikin ɗakin su, baya gajiya duk in yazo ƙasar mu, kullum ne sai sunyi safe rana da dare, idan nasan za su yi ko bacci bana yi idan ya kasance dare ne, wani time ɗin a ƙarƙashin gadon su nake 6oyewa da zarar naji zasu fara nake fitowa in zauna ina kallon su kamar na samu tv ba tare da sanin su ba, tun daga nan ne abun ya fara burgeni, da na fara mallakar hankalina, nan fa na fara neman wanda zan fara yi dashi, irin abunda naga iyayena su na yi,........" Numfasawa ta yi kafin ta ɗaura da cewa"mutun na farko da ya fara kar6ar budurcina idan bazan manta ba, daddyna ne yazo dashi gidan mu, matashin saurayi jinsin baƙar fata ne, ya gabatar min dashi a matsayin ɗan uwana ranar nayi murna saboda shine mutun na farko dana fara gani cikin dangin shi, saboda ƙaunar da na ke yi mashi yasa na liƙe mashi na hana shi sakat ko toilet zai shiga saina bi shi, daƙyar yake koro ni waje ya rufe toilet din, Idan dare yai kafin ya kwanta nake riga shi hawa gadon shi a ɗakin da ya sauka cikin gidanmu, haka zai ruƙo hannuna ya fitar dani waje yana nuna min cewa babu kyau mace da namiji su ke6e amma na gaza fahimtar shi, ranar da abun ya faru, sai da na bari dare ya ratsa na samu damar shiga ɗakin shi ya manta bai rufe ƙopa ba na hau saman gadon shi, na same shi kwance daga shi sai short a jikin shi nan take naji sha'awar shi ta kamani, sai na dinga tunanin yadda naga mommyna tana yima daddyna idan suna having sex, anan nima na soma gwadawa dashi Cikin bacci ya ji ina laluban jikin shi, a lokacin na shammace shi nayi mashi abunda ni kaina nasa bazai iya janye ni daga jikin shi ba, na riga dana sanya mashi ƙwaɗayin son kasancewa dani, a lokacin ina da shekara 14 aduniya Angel, nasan za ki yi mamaki, silar abunda ya faru tsakanina dashi a daren ranar har jinya nayi gadon asibiti, kamar bazan rayu ba, naci baƙar wahala har bansan inda kaina yake ba, har ɗinki aka yi min saboda yadda ya shige ni, nayi tunanin daddyna zai dauki mataki akan bunda yayi min duk da laifina ne amma bani da hankali ae bansan zan cutu ba nidai kawai nayi abunda raina ke so ne bansan haka abun yake ba, Angel daddyna ko zagin shi baiyi ba, dana ji sauƙi bayan jinyar da nasha ta wata biyu, na nuna inaso abi min hakkina sai ce min yai inyi haƙuri ai ya nemi yafiyar shi, tafiya ma zaiyi ya bar ƙasar, in kwantar da hankalina bazan sake ganin shi ba idan ya tafi, jin hakan yasa na haƙura, da jikina ya warware sosai na dawo dai dai naci gaba da yin rayuwata kamar yarda na saba har lokacin bai tafi ba, ɗan uwan nawa yana nan yana rayuwa a gidan mu duk da bamu magana da juna, amma muna zama wuri ɗaya, sai gashi mun koma muna cigaba da neman juna ni da shi, har ta kai ga bana jin daɗin jikina idan bamuyi ba, duk rana muna yi sau uku, abun da zai baki mamaki momnyna tasan komai ranar data kama mu naked atsakiyar gado mun yi tunanin zata yi mana faɗa, amma sai tace mu kwantar da hankalin mu abune mai kyau mu cigaba da faranta ma juna, wannan maganar da tayi ne ya ƙara bamu ƙwarin gwiwar cigaba da neman juna, ina matuƙar ƙaunar shi ya saba min da komai nashi, ya 6ata ni fiye da tunanin ki, duk da nice sila, lokacin daya tashi tafiya nigeria kamar inyi hauka naso daddyna ya barni in bishi amma ya hanani, a ƙarshe sai da aka rufe ni cikin ɗaki tukunna aka samu damar fitar dashi daga cikin gidan mu, Angel bayan tafiyar shi na kasa samun natsuwa, na soma bibiyar masu aikin gidan mu suka din ga bani haɗin kai, a ƙarshe ta kai ga hatta daddyna yana biyan buƙatar shi dani, da ita kanta momnyna babu wanda bai ta6a jikina acikin su, musamman ƙirjina da suka fi jan hankalin su...,...............' Bata ƙarasa maganar ba Angel ta fashe da kuka tana ambaton “Inna lillahi wa inna ilayhir raji'un!!! Unaiza iyayenki sun cuce ki, wlh sun zalunce ki, basu baki tarbiya ba, sai dai suka ba ki gudunmuwa wurin lalata rayuwarki, Unaiza ba ki yi dacen iyaye ba, a labarin da kika bani na fahinci cewa basu ƙaunar ki dama can sun haife ki ne don su sadaukar dake zuwa ga kurkukun ƙaddara, Mahaifinki Ya hana ki yin addinin shi ne saboda ana shi wayon don kada Allah ya kama shi da laifin zaluntar ki da ya yi aranar gobe ƙiyama, yayi tunanin cewa babu hisabi tsakanin ki dashi tunda ke ba musulma bace, tun da baki da addini baza a Tuhume shi akan ki ba da yake shi wawane, daƙiƙi, jahili shiyasa ya hana kiyi addinin musulunci, ya barki acikin duhun jahilci, ban ta6a ganin Jaki irin daddynki ba!........." cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar, "Angel na kwaɗaitu da son yin irin rayuwarki, labarin ki da kika bani ya fahimtar dani game da cin zalun da iyaye na su ka yi min, ashe duk Soyayyar da su ke nuna min ƙiyayya ce ba ƙauna ta su ke yi ba, nayi asarar rayuwata, gashi yanzu komai ya qare min, lokaci ya qure min da zan iya......" bata kai ga ƙarasa maganar ba, Angel ta yi saurin sanya tafin hannunta wurin toshe mata baki, Jikinta wani irin zafi na fitar hayyaci, idanuwan su cikin na juna, hawaye na bin fuskokin su, "Lokaci bai ƙure maki ba Unaiza! Tunda har kina numfashi to kina da sauran damar da zaki iya gyara rayuwar ki, inaso ki bamu dama ni da ƴan uwana mu nuna maki tsantsar soyayya, mu baki kulawa ta musamman har kiji sauƙi, nayi maki alƙawarin zan taimaka maki wurin gyara rayuwarki in sha Allah, saboda inaso ki rayu kodan saboda ki yi tozali da idon mugun mahaifinki, ki maida mashi martani sannan ki fille mashi kai da adda," Cikin ƙunar rai Unaiza ta furta "Bazaki fahimce ni bane, komai ya qare min, bazan iya rayuwa ba, Nifa matatta ce, maganar da nake yi maki a yanzu ji nake kamar an bani umarni ne in sanar dake kafin rai na ya fita daga jikina,......." numfashi taja, idanuwanta sun ciza launinsu, Baiwar Allah ita kaɗai tasan raɗaɗin azabar da take ji, Ga ciwon jiki ga ciwon zuciyar da mahaifinta ya dasa manta, hakika ya karya mata zuciya. "Bayan an ɗauke ni daga cikin ku, bana acikin hayyacina, amma zan iya tuna abubuwan da suka faru, Angel naga tashin hankalin da ban ta6a gani ba a rayuwata, na shiga firgici da tsoro kamar zan haɗiyi zuciya in mutu, mutun shidda akaina ba ƙananun mutane ba, kuma ba su kasance a suffar mutane ba, sai da su ka rikiɗa suka koma wata irin mummunar halitta tukunna suka soma yin sex dani, nayi kukan nayi ihun babu mai jina, har a bakina saida suka zuba min sperm ɗinsu mai ƙarni da zafi......" a gigice Angel ta ke kallonta Zuciyarta ta soma tashi...unaiza bata dakata ba taci gaba da cewa tun ina haɗiyewa ta ƙarfi har ya cika min bakina na fita hayyacina, Angel tsawon kwanaki shidda da nake cikin yin menstruation amfani aka dinga yi dani, sun rabani da abun da nake alfahari dashi, Ta yi maganar tare da sanya hannayenta biyu da niyar ta ɗaga mata rigar ta gani, da sauri Angel ta damƙi hannayenta, tana kuka tace"ba sai kin nuna min ba unaiza wlh na yarda da maganar ki, ashe dama abun da suke yi mana kenan, na jima da zargin hakan ban tabbatar ba sai yanzu da kika faɗamin........" "Angel bani da isasshen lokaci, inaso nabar maki wasiya ki kaima daddyna idan har Allah ya ba ku damar fita daga cikin kurkuku........" Girgiza kai Angel ta yi a yayin da zuciyarta ke tafarfasa tace "a'a unaiza dan Allah ki daina faɗin zaki rubuta min wasiyya, gani nake kamar mutuwa za ki yi, Wlh bana so ki mutu ba tare da kin ɗauki fansar abinda mahaifinki yayi maki ba," murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, muryarta asanyaye tace "Ɗaukar fansa ba dole saini zanyi ta ba, tun da ina dake bani da damuwa, Unaisa da Unaiza kusan abu ɗaya ne banbancin kaɗan ne na rayuwar mu, kinyi dacen uba wanda ya tsaya maki tsakani da Allah, don ki nemi duniyarki da lahirarki, Yayin da ni kuma nayi rashin dacen uba, ko ince iyaye, sun tauye min haƙƙina, Angel inaso ki yi min alƙawarin cewa Zaki ɗaukar min fansa! Inaso kiyi amfani da hannayen ki wurin sare kan mahaifina da gatari bayan ya kammala karanta wasiƙar da zan rubuta maki......." rurruƙe hannayenta Angel tayi acikin nata "ni bani zan ɗaukar maki fansa ba, ke zaki ɗauki fansa da hannayen ki, inaso ya ganki a matsayin musulma da ranki da lafiyarki, Ki fayyace mashi duk irin zaluncin da yayi maki, ki tofa mashi yawu akan fuskar shi kafin ki sare kanshi da gatari" sosai Unaiza ta fashe da kuka tana faɗin "ba zaki fahimce ni ba, Nifa matattace a yanzu haka, nayi fatan ace zan iya yin yadda kika fadamin sai dai ba zan iya ba Angel, shiyasa na rataya nauyin yin hakan akan wuyanki, ke nakeso ki kashe min shi da hannayenki tare da mahaifiyata, Angel koda ace sun ganni ba zasu damu ba saboda dabbobine su, babu zuciya a ƙirjinsu, sufa ne suka haifeni suka raine ni cikin so da ƙauna, amma hakan baisa sun ƙaunace ni ba, tayaya kike tunanin zasu ji zafi idan su ka yi tozali dani...'? ta jefa mata tambayar, Kafin ta cigaba da yi mata magiya akan ta ɗauko mata Jotter da biro don ta rubuta mata wasiyya. Jiki ba ƙwari Angel ta miƙe, tana tafiya ta nufi ƙopa ta buɗe ta fita tana jiyo shessheƙar kukan Unaiza ta cikin toilet, ji ta ke kamar in tayi nesa da ita zata dawo ne ta taras da gawarta, Lokacin da ta shiga Cikin ɗakin su, A kewaye da gadon Majnoon ta taras dasu Hanna, Yana kwance sun lullu6e shi tare da jamimah, da alama bacci ya ɗauke shi, Jin motsin tafiyar ta ne yasa duk suka ɗago da idanuwan su zuwa ga dubanta damuwace ƙarara akan fuskokin su, tasan dole su jiyo shessheƙar kukan unaiza, da sauri su Deeja suka tunkareta tare da batul da sauran ƴan uwan nasu, suna tambayar ta lafiya mai ya faru da unaiza......." Muryarta a disashe ta ce masu "Ku je ku duba jikinta, ku lallashe ta yanzu zan dawo" Da gudu suka nufi sashen toilet ɗin, mutun biyu ya rage Azeeza sai jamimah dake rungume da majnoon, kallonsu Angel tayi na ɗan wani lokaci kafin ta nufi table ɗin ɗakin su, inda unaiza ta ɗaura backpack ɗinta tun da jimawa, ta sanya hannu ta zuge zip ɗin jakar tare da ciro jotter da biro da sauri ta juyo ta nufi toilet ɗin, tunkan ta ƙarasa ta soma juyo sautin muryoyin su Deeja suna ta lallashinta, tana ƙarasa shiga ciki ta same su Zuƙunne agaban Unaiza da ke a rungume saman ƙirjin batul, ta ɗaura hannayenta saman sumar kanta tana shafata cikin sigar lallashi, "Angel bata da lafiya, Jikinta zafi sosai yakamata musan abun yi tun kan ciwon yaci ƙarfinta" deeja ce tai maganar, jin ta ambaci sunan Angel yasa Unaiza ɗagowa da kanta, tana kallonta, Miƙa mata jotter ɗin tayi da biro, bayan ta kar6a ta ɗaurata saman laps ɗinta yatsun hannunta na kerma ta soma rubutu cikin harshen turanci, "Idan ba zaki iya rubutun ba, ki fada min ni saina rubuta" Angel ce tayi maganar, unaiza ta girgiza mata kai tare da cewa "Nafi so yaga handwritting ɗina, zaifi gane cewa ni ce da kaina na rubuta mashi" kusan shafi uku ta cika da rubutun, biyu na daddynta ɗaya na mommynta, bayan ta kammala ta rufe jotter ɗin, fuskarta ɗauke da murmushi ta ke kallon fuskokin su ɗaya bayan ɗaya, damuwace ƙarara akan nasu fuskokin, duk sun sha jinin jikin su ganin irin kallon da take bin su dashi, mai wuyar fassaruwa, "Zan mutu ina farin ciki, saboda samun ku da nayi acikin rayuwata, ku ne mutane na farko da suka fara nuna min soyayya ta gaskiya kuma na tabbatar da hakan, naga damuwa akan fuskokin ku duk don saboda ni, dole inyi farin ciki na samun ƴan uwa masu ƙaunata, zanyi kewarku sosai, bansan dame zan saka maku ba, saboda bani da komai a yanzu, Amma ina da backpack, tare da earrings ɗina na gold tun a washe garin ranar da aka kawo ni prison na cire su daga kunne na, na ajiye su a cikin backpack ɗita, Na mallaka maku su, wata rana za su yi maku amfani idan Allah ya baku damar fita daga cikin kurkukun nan..." tun sautin kukansu na fita har takai ga muryoyin su sun disashe sai kallon ta su ke yi, ɗagowa ta yi da Rinannun idanuwanta akan fuskar Angel da ke kallonta, Miƙa mata pant ɗin dake a dunƙule cikin tafin hannunta ta yi tare da cewa "na baki shi kyauta Angel, dan Allah kada ki ce min baki so, inaso ku dinga tunawa dani acikin rayuwar ku, kodan saboda in samu masu yi min addu'a idan na mutu. fashewa su kayi da matsanancin kuka, Hannu biyu angel ta sanya wurin kar6ar pant ɗin da unaiza ke miƙo mata, sosai ta matse shi acikin tafin hannunta muryarta na rawa tace"nah..na kar6a Unaiza, kuma zanyi amfani dashi, nagode sosai," Murmushi ne ya bayyana akan fuskar unaiza, "Inaso ku bayyana min irin ƙaunar da kuke yi min," Atare suka haɗa baki wurin furta"wlh bazamu iya misalta maki irin ƙaunar da mu ke yi maki ba, muna son ki ƴar uwarmu, bamu ta6a ƙin ki ba, muna fatan mu kasance atare da ke har ƙarshen rayuwar mu," Dariyar farin ciki Unaiza ta saki, fararen haƙoranta kamar gonar auduga, Nan ta ke gaban su ya faɗi ganin Jinin dake gangarowa ta cikin ƙofofin hancinta, wata irin zufa ta fitar hayyaci ta soma tsastsafo mata, agigice suke kallonta sun kasa motsawa, ta tsakanin cinyoyinta jini ya shiga kurɗaɗowa, idanuwanta suka kaɗa jawur dasu, ta soma cizon la66anta, Da sauri Batul ta sanya hannu ta ruƙo ƙasan rigarta ta janye ta, Hankalinsu yai mugun tashi ganin yadda gabanta ya 6urma wurin ya jagwale sai uban rami, basu ta6a ganin tashin hankali irin na yau ba, gaban unaiza ya lalace, Da ƙarfi suka shiga ambaton “Inna lillahi wa inna ilayhir raji'un” tsabar fargabar abun da su ka gani yasa mutun huɗu daga cikin su suka sume nan take, Angel ce ta yi ƙoƙarin biya mata, Kalmatusshahada ita da Deeja suka dinga maimaita mata, itama batul ta ɗauka atare suke karanto mata ita, A lokacin Allah ne ya nufi Unaiza zata furta kalmar nan saboda takai matakin ƙarshe, Harshenta yana dab da karyewa muryarta da wani irin sauti ta furta kalmar shahada, tana ƙarasawa murmushi ya bayyana akan kyakkyawar fuskarta idanuwanta a buɗe kanta ya faɗa saman kafadar batul dake a kusa da ita, rai yayi halinsa. Kullu nafsin za'ikatul maut, Rest in jannatul firddaus Unaiza rai yayi halin shi, munayi mata fatan dacewa.........." Alƙalamina ya girgiza, Bazan iya fayyace irin tashin hankalin da bayin Allahn nan su ka fuskanta ba, a wannan lokacin, Tun da su ke arayuwar su basu ta6a ganin gawar ɗan uwansu agabansu ba Sai yau da su ka ga gawar Unaiza, suman zaune su ka yi, hawayen ma sun daina shararowa kan fuskar su, Komai ya tsaya masu cak! zuciyarsu da tsananin fargaba take bugawa, Idanuwan su sun kaɗa jawur da su, mutuwar Unaiza ta girgiza su fiye da tunanin mai tunani, tsawon awanni babu wanda ya motsa a cikinsu, Muryar Angel babu sauti take karanto addu'ar da ake yiwa mamaci duk wasu addu'o'i da aka koya mata a islamiyyar su wanda su ka shafi mamaci sai da ta karanto su duk da bata acikin hayyacinta, ta dinga tottafa mata saman jikinta, haƙiƙa sun ji ɗacin da yafi na maɗaciya a cikin zuciyoyinsu, sunji raɗaɗi mara misaltuwa, Sunga tashin hankalin da basu ta6a ganin makamancin shi ba........" Yayin da suke acikin toilet, Suna jimamin mutuwar Unaiza, basu san meke faruwa ba acikin ɗakin su, Tun bayan da suka ɗunguma zuwa toilet, Ya rage saura Azeeza da jamima dake rungume da majnoon cikin bargo, Azeeza ta zabga uban tagumi tana kallon bargon da suka lullu6e shi, Ashe Jikin shi ya fara bleeding, ta hanci da baki da ƙasan shi babu wanda Ya ankara a cikin su, tuni ya farka daga bacci, yana ta ƙoƙarin ƙwace kan shi daga ruƙon da jamimah tayi mashi amma ya kasa saboda rashin ƙwarin Jikin shi, gashi ita jamimar bacci ya ɗauke ta, Fashewa yai da matsanancin kuka yana faɗin "dodo zai cinye ni, Ku sake ni ku ƙyale ni, kaina ciwo ya ke yi min, jiki na zafi" a firgice azeeza ta farga da sautin kukan shi, tai saurin sanya hannu ta yaye bargon, karaf idanuwanta suka sauka akan Fatar jikin shi dake neman ɗaɗewa ta fashe, jikin shi ya kumbura, Ga jinin dake bin Cinyoyin shi, A gigice ta fasa wata irin razananniyar ƙara wadda tayi silar farfaɗowar Su batul suka dawo hayyacin su, A matuƙar ruɗe suke zazzare idanuwan su, kusan atare Deeja da Angel suka yunƙura cikin zafin nama suka watsa a guje zuwa cikin ɗakin su, shigar su keda wuya suka tarar da tashin hankalin daya kara gigitar dasu, Gaba ɗaya suka ci burki suna kallon shi, a lokacin Jamimah ta farka Jin ƙarar da azeeza ta fasa, tana buɗe idanuwanta taci karo da jinin majnoon da ya wanke fuskar shi, Nan take ta fashe da kuka tare da sakin shi ta miƙe zaune hannayen ta biyu asaman kanta, zuciyoyin su sun gama karaya sun riga sun fidda rai da rayuwar Majnoon, duba da yadda Jikin shi ya kumbura gwanin ban tsoro, ahaka ya dinga ambaton sunayen su yana neman taimako daga gare su don suzo su agaza mashi ko ya rage raɗaɗin da yake ji, A sukwane Angel ta faɗa saman gadon tsananin tsoro da firgici sun hana ta ta6a jikin shi, gudun kada fatar ta fashe, sunan Allah ta dinga ambato a cikin bakinta, Jamimah tana kuka tace "Majnoon kada ka tafi ka barni, dan Allah ka daina zubar da jini, ka daina kumbura jikin ka, bana son ganin ka haka, Muryar shi na rawa ya soma faɗin "Zafi jikina babu daɗi, dodo sun kashe ni, sun rabani da rayuwata, sun rabani da ƴan uwana......" wannan maganar da yayi ta yi matuƙar ta6a zuciyoyin su, Muryar Angel cikin shessheƙar kuka ta soma magana "Majnoon ka yi haƙuri, Allah yana atare da kai, shi zai kawo maka sauƙin abunda ke damunka, waɗanda suka cutar da kai kuma Zasu ɗanɗani kuɗar su ne Ranar gobe ƙiyama, domin kuwa duk wanda ya cuci wani Allah zai bi mashi haƙƙin shi, kai yaro ne ba ka mallaki hankalin ka ba, ga ta6in hankali dake damun ka, majnoon ba ka da zunubin kowa akan ka, Nayi maka farin ciki idan ka mutu, saboda itace hutu agare ka, Allah zaiji ƙanka ya tausaya maka, ya baka farin cikin da baka samu ba a gidan duniya........" kuka ne yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar, juriyace da ƙarfin hali yasa harta samu damar furta waɗannan kalaman, Idanuwanta akan fuskar shi data kumbura, Tayi jawur idanuwan shi duk sun gwale fatar su tayi jawur da ita, "Majnoon don't die, ban gaji da ganin ka ba, ina matuƙar ƙaunarka, inaso mu cigaba da yin wasa atare muci abinci atare, Angel tace zata kai mu gidan su su bamu kayan wasan yara, dan Allah kada ka mutu kaji majnoon ɗina......" Jamimace take yi mashi magiya fuskarta jaga jaga da hawaye hada majina, Magana ta ƙarshe da majnoon ya furta masu itace"Zan tafi kira na akeyi, naga wani mutun sanye da fararen kaya yana miƙo min hannun shi, yace min inzo gare shi zai sama min farin ciki, zan bi shi mu tafi, Angel jamimah azeeza......." bai kaiga ƙarasa maganar shi ba, Numfashinsa ya ɗauke, jikin shi ya saki, nan take rai yayi halin shi............" Ya Allah kajiƙan waɗanan bayin naka! Da dukkan waɗanda suka rigamu gidan gaskiya, waɗanda su ke acikin irin wannan ukubar ta rayuwa, Ya Allah ka kawo musu ɗauki, Waɗanda su ka yi silar shigar su cikin wannan Masifar ya Allah ka tona asirin su, Ka kawo mana ƙarshen su, Kai kaɗaine zaka Iya dasu!. Zuciyar Angel kusan bugawa tayi, a gefen majnoon ta sume, ba itaba hatta Azeeza da deeja A nan ƙasa suka kwakkwanta, Kansu Na bala'en sara masu, Basu ta6a ganin baƙar rana irin ta yau ba. Jamimah sai kuka take yi tana ambaton sunan shi, ita kaɗai ta rage mai motsi a cikin ɗakin nasu, batasan cewa ya mutu ba, muryarta har shaƙewa ta ke yi wurin ambaton sunan shi. 💔PRISONERS💔 Kafin wani Lokaci Giants su ka turo ƙopar ɗakin su, Uku daga cikin su masu kawo masu Abinci ne hannayensu ruƙe da trays, daga bayan su wasu Giant ɗinne Su huɗu hannuwan su ruƙe da gadaje guda biyu kalar wanda ake ɗaukar marasa lafiya, masu ɗauke da sunan Kurkukun ƙaddara, A tsakiyar ɗakin suka ajiye gadajen, Giant ɗaya ya nufi sashen toilet ɗinsu, Jim kaɗan ya fito hannun shi ɗauke da gawar Unaiza, a saman ɗaya daga cikin gadajen ya kwantar da ita, kafin ya nufi gadon majnoon Ya ɗauko gawar shi Ya ɗaurata a ɗayan gadon da ya rage, biyu suka ruke ɗaya, yayin da biyun suka ruƙe ɗayan gadon, A haka suka Ɗaga su tare da haurawa saman benen su ka fuce dasu........" *RIJF MAJNOON AND UNAIZA ƳAR GIDAN DADDY😭😭😭* *Ni ina rubuta littafine kan abunda ke faruwa a rayuwarmu ta zahiri, duk abunda ya faru a labarin yana faruwa dagaske, harma fiye da haka, don haka kada aji ba daɗi, idan mutun zaiyi faɗakarwa dagaske dole ya ta6a zuciyar mutane cos ba tatsuniyar gizo yake rubutawa ba, fatan za'a fahimce ni, ni kaina dana rubuta page din nan nasha kuka kamar wani na rasarasa, saboda ina jin abun tamkar dagaske ne😭* Prisoners sun ga rayuwa, Sun ɗanɗani raɗaɗi mai ɗaci a cikin zukatan su, babu wanda ke a cikin hayyacin shi, bayin Allah sun ji jiki fiye da a misalta, sun ga tashin hankali tsirarar shi, Yinin ranar babu wanda Ya motsa tun bayan da aka kawar da gawawwakin su Majnoon, kamar matattu haka su ka koma, su batul da ke a cikin toilet kamar gumaka, sun ƙame babu mai magana, hawayen dake zuba akan fuskokinsu tuni sun jima da ƙamewa, sun bushe ƙamas a saman faces ɗinsu, kukun zuciya su ke yi wanda yafi ciwo, mutun huɗu da suka suma a cikin toilet ɗin daga ciki akwai parveen, hibba, Yasmin da Rubina, waɗanda suka rage basa motsi, batul da ta lagwa6a kanta jikin bango, eve ta ɗaura kanta saman Laps ɗin batul, Sarah dake kwance ƙasa, Hanna ta ɗaura kanta saman waist ɗin Sarah, kamar hotuna babu mai moving. A cikin bedroom ɗin su, har ila yanzu su Angel basu motsa ba, tana anan inda ta suma saman gadon majnoon, yayin da su Deeja su ke a sume saman floor, Hatta Jamima da ta rage tana kuka tuni kanta ya fara sara mata da matsanancin ciwo, zazza6i ya yi mata mugun kamu, ta rasa ina zata tsoma ranta taji daɗi, ga shi babu mai motsi a cikin su balle ta samu wanda zai jata a jikin shi ya rungumeta ya lallasheta gwanin ban tausayi. A ƙarshe da ciwon yaci ƙarfin ta a saman bayan Angel ta kwantar da kanta tare da sanya hannayenta biyu ta ƙanƙameta, Allah ne ya sawwake mata ciwon nata ta hanyar bacci da ya ɗauke ta, mutuwar Majnoon da Unaiza sun ta6a zuciyata ni kaina da nake rubuta littafin, na zubar masu da hawaye tamkar rayuka ne masu numfashi, duk da ina ɗaukar labarin tamkar true life story ne saboda akwai waɗanda suke fuskantar irin wannan uƙubar, tabbas akwai su babu tantama, laifin me unaiza ta aikata data cancani wannan sakamakon daga mahaifinta? Laifin me majnoon ya akaita da ya cancanci irin wannan rayuwar, unaiza just 16 years mahaifinta ya wulaƙanta rayuwarta, ya barta acikin duhun jahilci, saboda mugunta da son zuciya na wasu mutanan masu hali irin na dabbobi, masu neman duniya ido arufe wai ace yau ɗanka na cikin ka zaka sadaukar don ka biya buƙatar kanka wadda a gidan duniya zaka bar koma me ka mallaka. Ya hana ta mori duniya sannan lahirar ma ya hana ta nemeta, da ya ke Allah ba azzalumin bawan shi bane sai ya haɗa ta da Angel agidan kurkukun ƙaddara, Abunda yake baƙin cikin ta sani game da addinin Shi, Angel ta fahimtar da ita, finally Unaiza ta koma ga mahaliccin ta amatsayin musulma, ta tafi atsarkaken ta, tamkar a ranar aka haife ta, don haka unaiza ba ita bace abun tausayi, mugun ubanta shi ne zai ji tausayin kan shi, domin kuwa ire iren su tun a gidan duniya zasu fara gir6ar abun da su ka shuka, ya yi asarar rayuwar shi, saura ya jira haɗuwar shi da mahaliccin shi, Ya Allah duk masu Hali irin na Uban unaiza Jan wuya, ka hanasu jin daɗin rayuwarsu Allah ka toni asirinsu ka kawo mana ƙarshensu, saboda basu da amfani acikin rayuwar mu, Idan muka koma 6angaren majnoon, Yaron baisan komai ba, just 12 years ahaka aka sadaukar dashi! Shin su wanene iyayenshi? Dabbobine ko makafi ne ko kurame ne? yaron da bashi da ƙoshin lafiya, ga ta6in hankali ga ƙuruciya, a haka aka samu wani mara imanin mai zuciya irinta kafuran farko ya sadaukar dashi, Tsakanin iyayen shi ko danginshi, tabbas zasu ɗanɗani kuɗarsu, wannan alwashine alƙalamina ya ɗauka, kowa sai yaji a jikin shi! Ɗaya daga cikin su bazai sha ba! Muddin ina numfashi! In sha Allahu. Kusan kwana uku da rasuwar Majnoon da Unaiza, Ko ruwa bai gifta maƙoshin su ba, waɗanda suka suma har yau basu farfaɗo ba, tamkar ba zasu rayu ba, Jamimah kaɗai ce ta ke rayuwa acikin ɗakin nasu, ta yi kukan har ta gaji ta gode ma Allah, babu mai jinta balle a samu wanda zai lallashe ta, Yadda suka ga rana haka su ke ganin dare, yadda ake kawo masu abinci haka ake ɗaukar shi ba tare da sunci shi ba, Jamimah kaɗaice wani lokacin ta ke kwasar shi a kwando ta 6oye, ko ta yi niyar cin abincin bata jin daɗin shi, kayan marmari kaɗai take iya sha, sai ruwa, Haka zata dinga bin su tana ambaton sunayen su haɗi da yayyafa masu ruwa don su farfarɗo su dawo cikin hayyacin su amma babu mai motsi, hatta su batul ga dukkan alamu suman su ka yi su ma. A cikon kwana na huɗu ne, Batul ta motsa, da matsanancin ciwon kai da zazza6i, idanuwanta biji biji take kallonsu kamar matattu, daƙyar ta iya buɗe baki ta soma ambaton sunayen su ɗaya bayan ɗaya. "Sarah! Hibba! Hannah! Parveen! Pls ku tashi, ku tashi mu rungumi junan mu, bana so na ƙara rasa wani a cikin ku.........." numfashi taja tare da ɗaura hannunta saman sumar kan eve tana ɗan bubbuga shi"Eve ki tashi, wai ba ku ji ina kiran sunayen ku," ta yi maganar a wahalce sautin ke fita, A hankali ta janye kan eve daga saman laps ɗinta ta kwantar da shi bisa floor, ta yunƙura ta matsa kusa dasu Parveen ta sanya hannu tana bubbuga jikinsu, Haka ta dinga binsu tana tatta6a su tare da ambaton sunayen su, Jin muryar Batul yasa Jamimah ɗago da kanta daga jikin Angel, don anan take wuni, rungume da ita, duk da bata motsi, jikinta na rawa ta sauko daga saman gadon da gudu ta nufi sashen toilet ɗin, tana shiga ta tura ƙopar makewayin da su ke a ciki ta shiga, a zuƙunne ta samu batul tana yin shessheƙar kuka, sanyi ne ya ratsa zuciyar Jamimah. Ta ji daɗi sosai ganin sun fara farkawa, idanuwanta a cike tab da ƙwalla ta ambaci sunanta"Sister BATOOL" jin muryar Jamimah Yasa ta yi saurin juyar da kanta don ganin me magana, suna haɗa ido da Jamimah, a hanzarce ta miƙe jiki ba ƙwari ta nufi bakin ƙopar, ta zuƙunna tare da janyota a jikinta ta rungumeta sosai tana cigaba da matse ƙwallar dake acikin idanuwanta. Cikin muryar kuka jamimah take faɗin"Sun tafin min da majnoon ɗina, bazan sake ganin shi ba, ko zai dawo ne? Ta yi tambayar tare da ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul, sam takasa amsa mata tambayarta, saboda bata fahimci me take nufi ba, tun da su basu san cewa hada Majnoon ya mutu ba, su na acikin toilet, ko lokacin da giant ya shigo ya ɗauki corpse ɗin Unaiza basu fargaba. "Majnoon ɗina jikin shi duk jini, inata kuka ina kiran sunan shi, babu mai jina, pls sister batul ki faɗi min gaskiya, mai ya faru da majnoon ɗina zasu dawo min dashi, ko in fidda rai," Tana magana hawaye na bin cheek ɗinta, fuskarta ta yi jawur da ita, har rama ta yi, tsananin tausayinta ne Ya kama batul, ta sanya tafin hannayenta biyu tana share mata mata su. "Sister batul, baki bani amsa ba, yau 3 days kenan, Ni kaɗai nake motsi a cikin ɗakin mu...." bata ƙarasa maganar ba, ganin yadda batul ta zazzare idanuwanta tsananin mamaki ne akan fuskarta, jin abunda tace A ruɗe ta maimaita 3 days! Ras gabanta ya faɗi don bata fahimci cewa sun ɗauki tsawon kwana uku basa a cikin hayyacin su ba, sai da Jamimah ta furta mata. "Ina ta kiran sunayen ku babu mai amsa min, gashi bani da lafiya zazza6i da ciwon kai, Har ruwa nake watsa maku a jikin ku don ku farka amma babu wanda ya motsa, itama Genie ɗita taƙi farkawa inata kiran sunanta......." Tun kan jamimah ta ƙarasa maganar batul ta zabura ta miƙe Jiki ba ƙwari ta soma ƙwala masu kira na fitar hayyaci, tamkar maƙoshin ta zai 6allo, babban abunda take ji ma tsoro kada ace zuciyoyin su ne suka buga, da sauri ta tsallake su ta nufi bucket ta ɗebo ruwa a fanfo, kusan rabi ta cika, daga inda ta ke a tsaye ta ɗaga bokitin ta daddage ta watsa masu Sarah saman jikin su, Cikin sa'a suka soma jan numfashi, da sauri ta juyar da bokitin saitin jikin su Parveen ta watsa masu ruwan a jikinsu, nan take suka soma Jan numfashi da ƙarfi, Ganin ruwan ya qare ne yasa ta sake ɗebo wani abakin fanfo, ta sungumi bokitin zuwa cikin room ɗin su, tana shiga tsakiyar ɗakin inda su Deeja su ke a kwance, ta ɗaga bokitin ta daddage ta watsa masu ruwan a jikinsu A figice Azeeza da Deeja su ka farka suna faman sauke ajiyar zuciya, ragowar ruwan daya rage a bokitin ta watsa ma Angel da ke kwance saman gadon Majnoon, koda ruwan ya sauka a jikinta, bata buɗe idanuwanta ba, sakamakon nauyin da su ka yi mata, sai dai ga dukkan alamu ta farfaɗo, duba da yadda take motsa la66anta kamar tana ambaton sunan Allah. Sanyayyiyar Ajiyar zuciya batul ta sauke, a yayin da ta ke bin su da kallon, A galabaice su ka miƙe zaune saman floor suna ambaton ruwa zasu sha, maƙoshin su zafi, ƙishi su ke ji, ' ajiye bokitin hannunta ta yi a ƙasa da sauri ta nufi ƙarƙashin gadonta tana laluban robobin ruwan da Jamimah tace mata ta ajiye masu, kusan guda shida ne, ta rungumo huɗu A ƙirjinta, taje ta miƙa ma Deeja da azeeza yatsun hannayen su na kerma suka kar6a tare da cire murfin, Yanayin yadda su ke shan ruwan ne ya bata tausayi, Kamar ta fashe masu da ku ka. Motsin da Angel za ta yi ke da wuya ta ƙundumo daga saman gadon ta faɗo saman floor, kanta ba ƙaramin buguwa yayi ba, Da sauri Batul ta nufe ta tare da zuƙunna agabanta, sai da ta fara A jiye bottle waters dake a hannunta a ƙasa kafin ta sanya hannayenta biyu wurin tallabo da kanta ta ɗaura shi saman laps ɗinta, muryarta a sanyaye ta soma yi mata magana. "ƴar uwarta rabin raina, Pls ki tashi, nasan kina jina, ki yi haƙuri ki jure, komai ya wuce, bana son abunda ya faru ya yi silar tarwatsewar farin cikin mu" a hankali Angel ta buɗe idanuwanta waɗanda suka canza launi sun ƙanƙance, biji biji ta ke ganin fuskar batul. Hannu batul ta miƙa ta ɗauko ɗaya daga cikin robobin ruwan da ta ajiye gefenta, bayan ta cire murfin, ta ɗago da kan Angel zuwa saman ƙirjinta, "Nasan kina jin ƙishin ruwa, Ki buɗe baki kisha" ganin taƙi motsa lips ɗinta ne yasa ta cusa mata bakin robar abakinta, don dole tasha ruwan, sosai ta kur6e shi, kusan rabin robar ruwan ta shanye, yunƙurin amai ne yazo mata gaba ɗaya ta sheƙar da ruwan data sha saman jikin batul, a ruɗe batul ta ajiye robar ruwan da ke a hannunta, ta rungume Angel ajikinta, tamkar zata mayar da ita cikin cikinta, ita kanta ba lafiyar ce da ita ba, a haka ta dinga lallashinta, Azeeza da Deeja sun yi zugudum babu mai iya magana a cikin su, Bayin Allah sunyi fatan ace mafarkine abunda ya faru ba gaske ba, Sai da kash ƙaddara ta riga fata, idanuwansu akan gadon majnoon, jinin shi ne daskare akan zanin gadon, Allah sarki rayuwa kenan babu wanda yafi ƙarfin mutuwa, idan ajali yazo dole ka miƙa wuya. "Deeja Yakamata Mu daina zubar da hawayen mu, mu lallashi ƴan uwan mu tunda mune masu juriya a cikin mu, idan har bamu fi ƙarfin zuciyoyin mu ba, zamu rasa ƙwarin gwiwar da mu ke dashi, dama su abunda su ke so kenan, saboda basu san ciwon kan mu ba, da biyu suka dawo mana da Ƴan uwan mu bayan sun san cewa mutuwa za su yi, meyasa basu ruƙe su a wurin su ba? Suna so ne kawai su kashe mu da ran mu shiyasa su ka dawo mana da su a wulaƙance don muga irin mutuwar da za su yi, Allah ya isa tsakanin mu da su!" daƙyar ta ƙarasa maganar cikin ƙunar rai. Shigowa Cikin ɗakin su parveen su ka yi, Hannun su ɗaya dafe da goshin su, Tafiya su ke yi tamkar zasu kife ƙasa, saboda jirin da suke gani acikin idanuwansu, ga ciwon kai da yunwa da ke addabarsu, ga damuwar da ke ƙunshe cikin zuciyoyin su. Gaba ɗayan su ne na cikin toilet ɗin suka fito a jere, a saman floor su ka zazzauna, Parveen na ƙoƙarin zama idanuwanta su ka hango mata gadon majnoon. A gigice ta furta "Innalillahi...." ba tare da ta ƙarasa maganar ba, tsananin tsoro ne da firgice su ka bayyana a cikin akan fuskokin su, Hankalinsu ba ƙaramin tashi yai ba, musamman parveen a ruɗe ta nufi gadon majnoon ganin daskararren jini asaman shimfiɗarsh, hannayenta biyu ta ɗaura saman bargon shi, yayin da zuciyarta ke tafarfasa. Muryar Hannah na rawa ta furta"INA MAJNOON YA KE? JININ MENENE MU KE GANI A SAMAN SHIMFIƊAR SHI, DAN ALLAH KADA KU CE MANA YA MUTU SHI MA"! Babu wanda ya iya buɗe baki ya basu amsa, hakan yasa su ka fahimci cewa Majnoon ya mutu babu shi, hawaye ne masu ɗumi su ka wanke fuskokinsu, A saman shimfiɗarshi Parveen ta kifa kanta da ke sara mata da ciwo, ta dinga kuka tamkar ranta zai fita, bakomai take tunawa ba face Irin rayuwar da su ka yi dashi, ta yi matuƙar tsaya mata arai, ta yi danasanin duk wani bugu da ta yi mashi, tun ranar farko daya fara kasancewa a cikinsu, Ya 6arar masu da Cake, Tana matuƙar son yaron tsanar da ta yi mashi a lokacin saboda 6arnar da ya ke yi masu ce, ɗago da hannayenta tayi tare da ɗaga su sama tana kallon fingers ɗin ta da ke kerma, Hawaye jaga jaga akan fuskarta, sautin kukanta ya cika ɗakin nasu, Muryarta da wani irin sauti ta ke faɗin"YA ALLAH KA ƊAUKI RAINA IN HUTA! BAZAN IYA JURAR TASHIN HANKALIN NAN BA! Bana fatan na sake yin tozali da gawar wani a cikin ƴan uwana, So nake na mutu in huta, Narasa Majnoon abokin Faɗa na ga Unaiza ma ta tafi tabar mu da kewarta, wayyo Allah nah! ' sosai ta rushe masu da kuka, kamar mahaukaciya haka ta cusa hannayenta cikin sumar kanta, ta dinga hargitsa gashin cikin ƙunar rai, kafin ta mayar da kanta saman mattress ɗin Majnoon. Duk suna jin sautin kukanta, Jikin su duk ya yi sanyi, mutuwar mutun biyun nan ta raunata zukatan su, ta sagar masu da gwiwarsu, komai ya fita aran su, babu mai sauran walwala acikinsu, ba don zuciyar Imani ba da tuni wasu daga cikin su sun zauce, musamman Azeeza ta shiga halin ha'ula'u, tsoro da firgici sun hana ta sak, har zufa ke tsastsafo Mata saman goshinta, tun da ta farfaɗo daga suma ta zauna ko motsi ta gaza yi sai dai tabi su da ido. Miƙewa tsaye Sarah Ta yi jikinta kamar zai 6alle, saboda rashin kuzari, fuskarta a bushe muryarta asanyaye ta soma magana"Idan har mu ka cigaba da zama ba tare da mun ɗauki mataki ba, za'a cigaba da yi mana ɗauki ɗai ɗai ne ana kashe mana rayuwa, Yakamata musan abun yi, wlh na tsorota Na firgita da ganin irin mutuwar da Unaiza ta yi, Tare da ita fa aka kawo mu cikin ku, bazan ta6a manta farkon gani na da ita ba, ban ta6a tunanin cewa zan shaida mutuwar ta ba, na girgiza sosai, please na roƙe ku, idan zaku iya ku kashe ni zaifi min kwanciyar hankali akan aƙara zuwa a ɗauki wani acikin mu, saboda na fahimci cewa rayuwar mu bata da amfani awurin su, mutuwa ta zamar mana dole yanzu ma aka fara yinta, bansan wanene next zai mutu ba, bana so na gani shiyasa nake so in mutu................" daƙyar ta ƙarasa maganar, saboda raɗaɗin da ta ke ji a cikin zuciyarta, miƙewa tsaye Hannah ta yi, idanuwanta jawur dasu ta soma magana tana fuskantar sauran ƴan uwan nasu da ke a zazzaune ƙasa "Meyasa har yau Allah bai dube mu ba? Mu ma fa bayinsa ne kamar kowa, Angel ke da kan ki kika faɗa mana cewa wanda ya halicce mu yana sane damu, but why mu ke fuskantar irin wannan tashin hankalin? bawani mai taimakon mu, sau nawa muna hana idon mu bacci don mu kai kukan mu agare shi, amma shiru...! Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yai ba, jin maganganun da Hanna ke yi, duk da matsanancin halin da ta ke a ciki sai da ta girgiza, ganin sun soma ƙoƙarin kauce hanya, dama ba wadataccen ilmin addini gare su ba, ba lallai bane a yanzu da suka fara fuskantar tashin hankalin nan su iya jurewa ba, saboda suna da raunin imani da tawakkali, a haka ma sunyi ƙoƙari saboda basu ta6a ƙaryata maganar ba, sai dai awannan karan tana tsoron Su juye mata su canza ra'ayinsu. Runtse idanuwanta ta yi sosai tare da cusa kanta a ƙirjin batul, ba ta yi tsammanin zata samu sauran hawaye a cikin idanuwanta ba, sai gasu sun soma tsastsafowa saman kuncin ta masu ɗumi. zuciyar batul ba ƙaramin karaya tayi ba, Jin yadda Jikin Angel ya yi zafi sosai, tasan dole taji raɗaɗin a cikin zuciyarta,' ƙara ƙanƙameta ta yi a jikinta, hannayenta asaman sumar kanta, A hankali take shafa sumar Angel tana lallashinta, zuciyarta tamkar ta fashe saboda ƙunar da ta ke yi mata, gudun kada ta zauce ta rasa madafa, yasa ta soma furta duk wasu addu'o'i da tasan zasu kwantar mata da hankalinta. A yayin da ta ke yin addu'o'in idanuwanta suna arufe, sosai ta matse su, tana jiyo muryar Yasmin tana faɗin "Angel Kin yi shiru baki bamu amsa ba, har yaushe ne zamu tsara Jiran taimako daga wurin Allah! Kina ganin mun fara mutuwa, tsoro da firgici kaɗai kaɗai sun isa su sa mu zauce, Mun yi tunanin cewa idan muka kar6i addinin ki, Mu ka yi Imani da Allah, komai zaizo mana da sauƙi, Amma shiru sai ma ƙara shiga tashin hankali da mu ke yi, lokacin da kika zo cikin rayuwar mu Ba ki ji daɗin da mu ka ji ba, saboda alƙawarurrukan da kika ɗaukar mana na cewa Zaki taimaka mana wurin ganin mun ku6uta daga cikin kurkukun ƙaddarar nan, Ki ka sanya mana kwaɗayin son yin rayuwar ƴan ci kalar wadda ki ka yi awaje, Meyasa angel muke ganin ba dai dai ba? Idan da ace kinsan ba zaki iya taimakon mu ba, meyasa kika sanar damu hakan? Kuma kika bamu labarin rayuwarki har muka sanya rai da yin irinta........" Yasmin bata ƙarasa maganar ba, ta rushe da kuka, Hankalin Angel idan yai dubu to ya tashi, Dama fa dole ta fuskanci wannan matsalar, cos itace mutun ta farko data fara sanar dasu komai agame da mahaliccin su, Nauyin komai ya rataya akan wuyanta! Duk idan su ka ji ba daɗi dole ita zasu tunkara, to ayanzu dai mutuwar Unaiza da Majnoon ta kwance notikan kawunansu, sun fara tsorota shiyasa su ke waɗannan maganganun. "Angel idan har akwai abunda ya rage mana wanda ba mu yi ba dangane da addinin ki, to ki faɗa mana shi don muyi wata'ƙil Allah zai ji ƙanmu ya tausaya mana, ya dube mu da idon rahama ko mun samu mu tsira da ranmu!" Eve ce ta yi maganar, Duk sun mimmiƙe tsaitsaye Agaban Batul da ke a rungume da ita, sai ƙara tighting ɗinta ta ke yi a jikinta, ita kanta batul ɗin hawaye ne sharkaf akan fuskarta, cigaba da ambaton sunan Allah ta yi acikin zuciyarta, tana roƙonshi akan ya basu bafita kada yasa su ga gazawarta. "Angel Mun san kina sauraron mu, kin yi shiru ba ki ce komai ba, kada ki sanya mana kokwanto A cikin zukatan mu, Mun yarda dake, Munsan kina ƙaunarmu, kuma kina son Farin Cikin mu, don haka Muna jiran amsar ki me ya rage mana wanda ba muyi ba a cikin addininmu wanda zaisa Allah ya jiƙan mu......" Cikin rauni na murya Hibba ta yi maganar, daga ganin fuskokin su a matuƙar tsorace suke. Angel tana a cikin tsaka mai wuya, ta kasa ɗago da idonta ta dube su, saboda bata da ƙwarin gwiwar yi masu magana, to me zata ce masu? Itama fa A tsoroce take da abunda ya faru na mutuwarsu Unaiza. Muryar Rubina a hargitse tace"Babban abunda nake jimawa, Ƴan uwan mu da aka kwashe Shin suna araye ko sun mutu, bamusan a wani hali su ke aciki ba, Tun da yanzu mun fahimci cewa kashe mu ake yi, Lalata rayuwarmu ake yi a kwashe wani sashe na jikin mu! Kamar yarda aka yi ma Unaiza, Da Majnoon......." Bugun zuciyar Angel ne ya ƙaru tunawa da Mazan su da aka kwashe, ba ita ba Hatta su Deeja damuwace ƙarara akan fuskokinsu, Tabbas Suna fuskantar barazana a cikin rayuwarsu. "baƙin Cikin da mu ke ƙunsa da barazanar da muke fuskanta sun isa su sa zuciyoyin mu su buga mu mutu" Eve ce tayi maganar tana faman huci, idanuwanta a zazzare, ruwan hawaye ne kwance a cikinsu. Kowa Yana tofa albarkacin bakinsa, mutun biyar ne basu tanka ba, sai da su ka yi mai isar su tukunna Deeja ta miƙe cikin kakkausar murya ta soma magana tana duban kowan nan su. "Na yi mamakin jin maganganun da harsunan ku su ke furtawa, saboda abun da ya faru ne yasa ku ke kokwanto Akan Addinin da Angel tazo mana dashi, Kun bani kunya duk da na fahimci cewa ba'a cikin hayyacin ku kuke ba, banaso mu yi abunda zamuyi danasani acikin rayuwar mu, Angel ba ita bace silar halin da muka shiga ba, Akan me za ku dinga ɗaura mata nauyin komai akanta! Yarinyar nan fa ƙanwar mu ce, babu wanda bai girmeta ba a cikin mu...." Numfasawa Deeja ta yi a yayin da take bin fuskokin su da kallo. "Ya ku ke so tayi da ranta ne? Kalaman ku zasu iya sanyawa ta zauce, itama fa tana jin raɗaɗin da mu ke ji, saboda ta ɗaurawa kanta nauyin kula da rayuwar mu, so ku ke ku ƙara sanya mata damuwa har zuciyarta ta buga mu rasa ta? Meyasa za ku yi kokwanto akan addinin da tazo mana dashi? Saboda kun ji shiru har yau Allah bai kawo mana ɗauki ba? Ƙaddarar mu ce tazo a haka, ba lallai bane mu moriya rayuwar duniyar nan ba, amma ku tuna abunda Angel ta faɗa mana, ko kun manta ne, zai iya yiwuwa namu jin daɗin ba anan yake ba, sai ranar da muka koma ga mahaliccin mu! Itafa wannan rayuwar duniyar ƙanƙanuwa ce jin daɗinta na wucin gadi ne, kowa zai mutu ne, damu da wanda ke rayuwa awajen kurkukun nan da waɗanda suka azabtar da rayuwar mu, kaf zamu koma agare shi ne, mutuwa dole ce, zamu mutu zamu koma ga Allah, za'ayi mana hisabi tsakanin mu dasu! Allah zai bi mana haƙƙin mu, zasu ɗanɗani kuɗarsu, Ai mu abun farin ciki ne agare mu, Haƙƙinmu ya rataya akan wuyan waɗanda suke sarrafa rayuwar mu, don haka daga yau bana son wani ya ƙara yin kukan mutuwa acikin mu, Mu sanya wa ranmu cewa dole mu rasa wani acikin mu, ko muna so ko ba mu so, dole mu mutu, Mu zama masu tawakkali kada mu butulce wa Ubangijinmu, Abun da na fahimta wanda ba lallai bane ku fahince shiba, Allah shine ya ƙaddara zuwan Angel a gidan kurkukun nan donta sanar damu komai agame dashi, yanzu mu musulmai ne, kuma munyi imani da Allah, don haka babu gudu babu ja da baya, Duk runtsi duk wuya kada mu kuskura Mu rasa ƙwarin giwar da mu ke da shi, tsakanin mu da Angel sai godiya, Allah ya saka mata alkhairi, Allah ya bata ikon cigaba da taimakon mu...." Kalaman Deeja sun sanyaya zuciyar Angel, Jikin kowan nan su Ya yi sanyi, sun yi danasanin maganganun da suka soma gaya mata, kusan atare suka haɗa baki suna bata haƙuri haɗi da lallashinta, hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalinta yayi ba, har lokacin bata ɗago da kanta daga saman ƙirjin batul ba' Deeja tace masu su share hawayensu, Su yi rayuwar su tamkar babu abunda ya faru dasu, suka masa mata da toh, Duk da sun san abune mai wuya su dawo kamar yarda suke ada, A ranar sun ɗan samu sunci abincin Da Jamimah ta ajiye masu a cikin kwando, Bayan sun kammala ci, Kowan nan su ya yi wanka, A saman gadajen su suka kwakkwanta, zuciyoyin su a ƙuntace. Rayuwar prisoners ta zama abun tausayi Cikin kwanakin nan, jimamin rashin ƴan uwansu ya hanasu sakat, Babu wasa babu dariya, kullum fuskokin su a bushe su ke, abu ɗaya ne su ke yi su ji daɗin shi, su kuma samu natsuwa da kwanciyar Hankali, Karatun qur'ani da Angel ta ke yi masu tsakar dare, a lokacin da take samun damar yin shi murya abuɗe ba tare da ta samu targarɗa ba, tasha ware kanta ita kaɗai, Ta ke6e a sashen toilet ɗinsu, ta ɗaga hannayenta sama hawaye nabin fuskarta, ta dinga roƙon Allah akan ya taimaka mata, kada yasa taji kunya a idanuwansu, ya agaza masu yajiƙan su, Ya kawo masu mafita ko dan taci ka masu alƙawarin data ɗaukar masu na ku6utar dasu daga Cikin kurkukun ƙaddara! Ta zama abun tausayi, ga duk mai imani idan yaga yadda ta ke roƙon Allah sai ya matse mata ƙwalla. dukkan wasu ladubban yin addu'a ta iyasu, Saboda an koyar da ita, mutun biyun nan sun bata gudummuwa a cikin rayuwarta, shiyasa bazata ta6a mantawa dasu ba, mutun na farko Mahaifinta Tajuddeen, nagartaccen uba wanda ya tsaya mata tsayin daka don ta nemi duniyarta da lahirarta, lokacin da Unaiza ta bata labarin nata uban daya tarwatsa rayuwarta, sai taji ta ƙara ƙaunar daddynta, kuma har aranta taji cewa Mahaifinta bazai ta6a iya sadaukar da ita ba, ɗan adam ba abun yarda bane, amma ita ta yarda dashi har cikin ranta, saboda tasan halin daddynta ita shaida ce akan shi, ko dabba bazai Iya sadaukar ba balle ita da ya ɗauke ta tamkar ranshi! Mutum na biyu da bazata ta6a mantawa ba, ANEELERH CE, matsayin da ta bata a cikin zuciyarta na mahaifiyarta ne data gudu tabarta, Aneelerh uwace ta gari agare ta, dayawa wasu abubuwan da Angel ta iya da suka shafi addini da rayuwar duniya, Aneelerh ce ta koyar da ita su, hatta karatun makaranta idan aka yi mata, Aneelerh ce ke ƙara koya mata shi idan daddynta bai nan, Tana matuƙar son aunty aneelerh, kuma bata zarginta cikin waɗanda su ka sadaukar da ita! bayan aunty aneelerh da daddynta babu wani shege da take tunanin zata ɗaga ma ƙafa, muddin ta fita daga cikin kurkukun nan sun shiga uku, Hatta hajiya Adama da uncle Abdallah, da Alhaji ubaid kakanta, da maigadin gidansu, da abokan dadynta na wurin aiki, da makwabtan dake a kusa da gidansu kaf ɗinsu abun zargine awurinta, Ba wanda ta cire a cikinsu, dama kawai take jira ta samu, duk wani mai hannu acikin sadaukar da su, sai ta binciko su, alwashine ta ɗaukarwa kanta, shiyasa bata son ta dawwama agidan kurkukun saboda idan har tana aciki bazata ta6a Iya gano su wanene shuwagabannin kurkukun ba, Dole sai tana awaje zata samu damar gano munafukan, ta ci buri akan su, musamman mahaifin Unaiza JAN WUYA, wannan ɗan tahalikin duk ranar daya bari Angel ta dira ƙafarta daga cikin kurkuku, sunanshi matacce, muddin ta gano shi. Tuntuni Angel ta ɗauko Jotter ɗin unaiza da ta ajiye mata a cikin toilet ɗinsu, tare da pant ɗin data bata kyauta, tana matuƙar son pant ɗin musamman da ya fito daga hannun Unaiza, yanzu haka pant ɗin yana sanye a jikinta ko wanke shi ba ta yi ba, saboda ta shaida tsaftar da ke a jikin shi, daga gani ranar da za'a kawota kurkukun ta sanya shi a jikinta, saboda sabuntakar shi. a cikin backpact ɗin Unaiza ta sanya jotter ɗin tare da biro din duka ta tura su ciki ta zage zip ɗinta, tana fatan Allah ya bata damar isar da wasiyyarta. Bayin Allah sun zubama sarautar Allah ido, almost two month Yau, babu labarin su Haris, Danish kuwa yafi kowa daɗewa don Yana acikin wata na uku da aka tafi dashi, tsakaninsu dasu addu'ace wadda ba fashi, kullum ne sai sunyi masu ita tare da waɗan da su ka rasu. 💔PRISONERS💔 Wuraren marece, Angel tana kwance saman gadonta, ta rungume pillow a ƙirjinta, ba zaka ta6a gane awani hali ta ke a ciki ba, ta lumshe idanuwanta tamkar mai yin bacci, Azeeza ce kwance a gefenta saman gadonta, Jamimah tana asaman bayanta ta haye ta ɗaura kanta, sun zamar mata alaƙaƙai, Kullum suna atare da ita, tana matuƙar son jinsu a tare da ita, babu mai yin magana a cikinsu, Parveen tana a kuɗundune cikin bargo saman gadon majnoon, kullum nan take kwana, da hannunta ta wanke jinin da ke abargon shi, ta gyara gadon taci gaba da kwana saman shi, saboda ƙaunar da ta ke yiwa majnoon ɗinta, wani lokacin har pillown shi ta ke yi ma wasa a matsayin majnoon kamar mai ta6in hankali. Sarah na a zaune saman shimfiɗarta tare da Hibba da eve sai yasmin da rubina, babu mai magana acikin su duk sun yi zugudum, Deeja tana a kwance saman gadon Haris idonta na fuskantar ceilling, kowa dai da abunda ke damun shi, itama Hanna tana a naɗe saman gadonta. Saukowa batul ta yi daga saman gadonta, Ta nufi sashen toilet ɗinsu, ba tare da kowa Ya ankara da ita ba, shigarta ke da wuya Angel ta buɗe idanuwanta muryarta asanyaye tace da jimamah ta sauka zata miƙe, zame jikinta ta yi daga na jamimah ta sauko daga saman gadon, Jikin ta duk ba ƙwari ga ramar da ta yi. Sashen toilet ɗinsu ta nufa, tana shiga ta soma jin shessheƙar kukan batul, Hankalinta yai mugun tashi, bata zo da niyar tabi bayanta ba, tunawa da furennin dake a cikin tukunyar fulawar nan ne yasa ta zo sashen makewayin nasu, tun bayan rasuwar Unaiza babu wanda ke ba furennin ruwa saboda halin da su ka shiga, Cikin sanɗa ta nufi ƙopar toilet ɗin da batul ta shiga, A hankali ta tura ƙopar tare da Leƙa kanta ciki, karaf idanuwanta su ka sauka akan Batul da ke ta faman leƙa cikin wandonta da ta zame kamar wani abu ta ke dubawa, Jin motsin shigowar mutun yasa ta firgice ta ɗago da idanuwanta fuskarta sharkaf da hawaye suna haɗa ido da Angel tasha jinin jikinta, da sauri ta gyara zaman wandon jikin ta. "Batul me ya ke damun ki? Na jiyo shessheƙar kukan ki ne," wahalallan yawu ta haɗi, ba tare data furta mata komai ba. Hakan ba ƙaramin ɗaga ma Angel hankali yai ba, fargabarta kar ace wani abu ne ya sami gabanta shiyasa ta ke kuka "Ƴar uwata rabin raina, dan Allah ki faɗamin meke damun ki, Na yi maki alƙawarin bazan faɗama kowa ba, Hankalina ya tashi dana ga kina duba wandon Jikin ki, ina tsoron ace wani abu ne ke damun ki" Ta ƙarasa maganar yayin da take nufar batul, girgiza mata kai ta dinga yi muryarta Ƙasa ƙasa take faɗin"Kada ki matso kusa dani Angel, babu abunda ke damuna, lafiyata qalau....." adabarbarce ta yi maganar. "ƙarya ki ke yi min batul! Wai har ni zaki 6oye ma abunda ke damun ki? Me ki ka ɗauke ni ne? Nifa ƴar uwarkice, idan baki faɗamin ba wa zaki faɗa mawa, ni dama tun da aka dawo mana dake ban yarda dake ba, meyasa zaki 6oye min abunda su ka yi maki"? Fuskarta a ɗaure ta yi maganar, kafin taci gaba da cewa"Allah yajiƙan unaiza ba ta mutu ba sai da ta sanar dani komai daya faru da ita, don haka ki daina 6oye min, idan har kina son zaman lafiya to ki faɗamin me aka yi maki!! Cikin shessheƙar kuka batul tace"nifa ba abunda ya faru dani, ki daina tambayata bana so ki tafi kawai," Jinjina kai Angel tayi tare da sassauta muryarta"Its ok xan tafi batul tun da baki so in sani," Ta ƙarasa maganar tare da juyawa ta nufi ƙopar fita, ajiyar zuciya batul ta sauke duk a tunaninta Angel tafiya zata yi tabar toilet ɗin ashe ƙopa ta je ta rufe don kada sauti Ya fita, jamlock Ta sanya ta datse ƙopar da kyau, fuskarta a ɗauke ta juyo ta kalli batul dake manne jikin bango, jikinta sai kerma yake yi "Zaki Faɗamin meke damun ki ko kuwa kin fi so in bi ta ƙarfi"! Shiru batul bata tanka mata ba, sai faman zazzare mata idanuwanta take Yi, Cizon le6e Angel tayi tare da naɗe hannun rigarta, gadan gadan ta nufi batul, ganin tana tunkarota yasa batul ta bar jikin bangon ta watsa da gudu da niyar ta fuce, Cikin rashin sa'a Angel ta cafko Sumar kanta, ta janyota da ƙarfi ta maka ta jikin bango ta yadda bazata ji zafi ba, Faɗane ya kaure a tsakanin su, Sai nishi su ke yi sun cakumi juna, ga jikin nasu duk ba ƙwari, tuni sun haɗa uban gumi, ƙarfi Angel ta sanya wurin kada batul ƙasa, tare da sanya hannu ta damƙi wandon jikinta ta soma kiciniyar zame mata shi daga jikinta, duk don ta gane ma idonta abunda batul ke 6oye mata........." 💋PRISONERS💋 Ba ta kai ga ƙarasa cire wandon ba, sautin dariyar Batul ta janyo hankalin ta ga kallon fuskarta, tsabar mamaki ne yasa Angel ta sakar mata trouser ɗinta, ta tsaya tana kallon ikon Allah sai tiƙar dariya ta ke yi kamar ba ita bace ta ke ku ka. "Batul bana son iya shege, menene haka? Dariyar me ki ke yi mini? Kin fara sanya mi kokwanto akan ki" ta yi maganar tana binta da kallon tuhuma yunƙurawa batul ta yi tare da miƙe wa ta zaune, Sumar kanta duk ta tarwaste har ta saman fuskarta, tana dariya ta sanya hannu tare da yaye sumar ta mayar da ita bayanta, A hankali ta ke bin fuskar Angel da kallo, ta haɗe rai har wani huci ta ke yi. "Meyasa ki ke yi mini haka? Ko dan saboda kin ga na damu da ke ne? rai a6ace ta yi maganar, shiru batul taƙi magana sai kallonta ta ke yi, Gyaɗa kai Angel ta yi"shikenan tunda na zama abun tsokana a wurin ki zan tashi in koma ɗaki, don't ever expect me to worry about you anymore." Ƙoƙarin miƙewa ta yi da niyar ta fuce daga cikin toilet ɗin, muryar batul ce ta dakatar da ita. "Ba za ki iya daina damuwa dani ba, that's why ki ka sanya mini ido, ko bacci nake yi idon ki a kaina, duk wani motsi idan na yi sai kin ji ba'asin shi, irin wannan ƙauna haka........" ta yi maganar da zolaya, hakan ba ƙaramin 6ata ran Angel yai ba. "Nifa ba abunda ke damuna, lafiyata qalau, don kin ga ina bincikar trouser ɗina shiyasa ki ka ɗaga hankalin ki nasan me ki ke tunani nima abunda na ke tunani kenan, sai dai abun da mu ke hasashe bashi ba ne, It's just a rash ya fito min a wurin, ya addabe ni da ƙaiƙayi, ɗazu dana kwanta bacci, nayi mafarkin Unaizah, hankalina na ya tashi, a lokacin bansan ƙurji bane nadai ji zafi a wurin, gani nake kamar zai yi irin na unaiza, kin ji dalilin dayasa na shigo toilet ina shessheƙar ku ka tare da bincika wandona don inga menene awurin daya haddasa min jin ƙaiƙayi, ban yi tsammanin za ki biyo ni ba, amma tunkafin ki shigo naji motsin mutun nan take raina ya bani cewar Ke ce, shiyasa na ƙara sautin kukan nawa don in firgitar da ke......." bata ƙarasa maganar ba, ta tuntsire da dariya ganin irin kallon rainin wayon da Angel ta ke Yi mata, tana a tsaye ta ruƙe qugu. "Idan ba ki yarda da magana ta ba, zan nuna ma ki" ta yi maganar tare da sanya hannu tana ƙoƙarin zame wandon jikinta. "Bana so ba sai na gani ba" ta faɗa tana harararta "Idan ban nuna maki ba hankalin ki bazai kwanta dani ba, " bata jira jin me zata ƙara ce mata ba, ta yi saurin zame wandon kaɗan ta yadda tsiraicinta bazai baiyana ba, ƙaramin ƙurjine yayi jawur dashi daga gani ba ƙaramin zafi ya ke yi mata ba, Ajiyar zuciya Angel ta sauke hankalinta har ya kwanta, gyara wandon batul ta yi ba tare da ta ɗauke idon ta daga kan fuskar Angel. Zuƙunnawa Angel ta yi agabanta"Idan har ba ki so raina ya 6aci to ki faɗamin me aka yi maki tsawon time da Giants su ka ɗauke ki," ganin irin kallon da batul ke yi mata ne yasa ta kuma cewa"Kada ki ce zaki 6oye mini komai batul, idan har baki so nima wata rana in 6oye maki wani abu dangane dani, " A tsanake ta soma magana tana kallon cikin idonta "Angel bayan an ɗauke ni daga cikin ku, kamar yarda na faɗa maku, ɗaki ne su ka kaini ni kaɗai, a saman gadon su ka kwantar dani, bakomai zan iya tunawa ba, na dai san sun cire min kayan jiki na, sannan Naji ana shafa jikina ta ko'ina, ba tare dana iya motsawa ba, kafin daga bisani naji ana tsotse......." bata ƙarasa ba ganin yadda Angel ta runtse idanuwanta, muryarta ƙasa ƙasa tace mata ina sauraronki ki ci gaba da magana "Jinin da ke fitowa ta gabana shi naji ana tsotse shi" Zuciyar Angel tuni ta soma tashi. "Naji zafi sosai kamar zan zauce, tsawon lokaci Ana tsotse shi har zuwa time da naji bacci ya ɗauke ni, daga nan bansan me ya faru ba, lokacin da na farka banga komai ba, sai kayan abincin da aka ajiye mini Saman table, a bunda ban yarda dashi ba a cikin kayan abincin akwai wani luluyayyan abu fari fat guda ɗaya aka ajiye shi a tsakiyar tsokokin Nama......." Ba ta kai ƙarshen zancen nata ba, Angel ta yi saurin katse ta da cewa" Allah yasa ba ki ci ba" jin haka yasa ta haɗiyi yawu fuskarta da alamun damuwa tace"Naci Angel, yunwa nake ji sosai a lokacin, komai sai da na ci" Angel tace"amma bayan kinci sai me ya biyo baya"? Numfasawa Batul ta yi kafin taci gaba da cewa"bugun zuciyata ne ya ƙaru, na dinga jin faɗuwar gaba, yanzu haka da na ke yi maki magana, akwai Jan tabo saitin zuciyata, zan nuna ma ki shi idan na gama baki labarin abunda ya faru, tsawon 4 days da inayin menstruation abunda ake yi min kenan kamar na ranar farko, Bayan jinin ya ɗauke, saina samu sassauci, sai dai kewarku da ta addabe ni, damuwa ta hana ni yin walwala, haka zan zauna ni kaɗai a ɗakin ina ƙwala maku kira babu mai jina, kamar zan yi hauka Angel, tun ina kuka har na gaji na daina, Sai na koma ina yin addu'o'in da ki ka koya mana, idan na karanta su sai inji sanyi a cikin raina, har ma in shiga toilet in yi wanka, idan na fito sai in kwanta saman gadon da ke a cikin ɗakin, kullum sai an kawo min abinci amma ban ta6a ganin waɗanda su ke kawo min shi ba, sai dai in gan shi A jiye saman table, sannan duk in a ka kawo min abinci sai naga wannan Abun dana faɗa maki luluyayye, Ina jin daɗin cin shi, cikin wata uku da bana atare da ku sau Uku ina yin jinin nan akowani ƙarshen month, kuma duk in nayi abunda su ke yi mini kenan, tsotse jinin da ke fitowa......." hawaye ne kwance a cikin idanuwan ta, ita kanta Angel ɗin idanuwanta A cike suke fal da hawaye gani take kamar Akwai wani abu da su ka yi mata ta hanyar abincin da su ke bata tana ci, musamman da ta ji ta ambaci luluyayyen abun nan fari da a ke sako mata cikin abinci, hankalin ta bai kwanta da shi ba. "Batul inaso ki faɗamin ko kin ta6a gudowa daga Cikin ɗakin da aka kai ki?" ɗaga mata kai Batul ta yi alamar eh kafin ta ɗaura da cewa"Na ta6a samun damar durawa ta window ɗin da ke a cikin toilet ɗin ɗakin, na watso da gudu Ina neman hanyar da zata dawo dani cikin ku, A tsorace na ke a lokacin bani acikin hayyacina bansan meya faru ba, na dai ji kamar na faɗi ƙasa, kaina ya bugu, Bansan wanene ya mayar dani ɗakin da aka kai ni ba, lokacin dana dawo cikin hayyacina acan na ganni kwance saman gado, tsabar takaici yasa Na fashe da kuka har na kai ga zazzaga masifa ni kaɗai kamar mahaukaciya, a ƙarshe na haƙura na koma na kwanta, ina kukan zuci......." dakatawa ta yi da yin maganar tare da sanya yatsun hannunta ta share ƙwallar da ke gangarowa ta cikin idanuwanta. "Ina so insan a hawa na nawa ne aka kai ki, Na ta6a yin mafarki da ginin kuma ni idan nayi mafarki yana zama gaskiya, a yadda aka tsara mini ginin hawa Uku ne, a cikin su wannene aka kai ki'? Girgiza kai Batul ta yi tare da cewa"Ae bazan Iya tunawa ba, amma inaji kamar ginin dana na biyo time dana gudo Acan sama Ya ke," jinjina kai Angel ta yi"shikenan Iya abunda ya faru da ke? Wanene ya dawo da ke? Ko giants ne? Kamar ƴar jarida haka Angel ta tsare ta da tambayoyi. "A ranar ina zaune tsakiyar gado, ina ta kuka ina ambaton sunyen ku, ina faɗin ni na gaji amaidani wurin ƴan uwana, idan ba haka ba zan haɗiyi zuciya in mutu, saboda na gaji da maraicin ku gani na ke kamar mutuwa zanyi, Angel shiru babu wanda yazo gare ni, hakan ya ƙara hasala zuciyata, Dama akwai wata ƙaramar wuƙa ta fruit da aka sako min cikin kayan abinci, sai nayi tunanin in ɗauke ta in yi kamar zan kashe kaina wata'ƙil asamu wani yazo gare ni tunda suna ganin komai da na ke yi, na sauko daga saman gadon na ɗauki wuƙar tare da buɗe murya ina faɗin"ko dai su zo su maidani wurin ƴan uwana ko in kashe kaina, kowa ya huta," ina kammala yin maganar Na watsa da gudu na shige toilet ɗin ɗakin naja ƙopa na rufe, ina jiran ganin ko zasu zo gare ni, jin shiru yasa nayi tunanin in ɗan yanka hannuna Jini Ya fito ko sun gani su zo, Ina ƙoƙari ɗaura wuƙar saman hannuna da niyar in yanka, ba zato ba tsammani kunnuwana su ka soma jiyo min takun tafiyar mutun a cikin toilet ɗin, a tsananin tsorace na ɗago don inga wanene ya shigo bayan na rufe ƙopa, Tsabar tsoro Yasa na jefar da wuƙar dake a hannuna Yayin da nake kallon Shi, Giant ne sanye Cikin baƙaƙen Kaya, dogo ne yana da faffaɗan ƙirji sai dai tafiyar shi ta banbanta dana sauran Gaints da su ke kawo mana abinci, kuma shi wannan Yana magana Don har ce min yai yazo ne ya taimake ni ya maidani cikin ƴan uwana idan inaso" cikin shessheƙar kuka nace mashi kada ka cutar dani, idan har dagaske za ka iya taimaka mini, ka nuna min hanyar da zan bi in koma wurin su, ko ka ɗauke ni ka kaini." Tun da na ambaci hakan sai naji wani irin bacci acikin idanuwana, daga nan ban ƙara sanin me ya faru dani ba, sai dai na farka na ji kin rungume ni. Ajiyar zuciya Angel ta dinga saukewa, Hankalinta ya kwanta sosai, jin cewa ba su yi mata irin na Unaiza ba, sai dai akwai wani abu da ya ɗaure mata kai dangane da labarin da batul ta bata, shin meyasa ita basu yi sex da ita ba kamar yadda su ka yi da Unaiza? Kuma har abinci su ke bata lafiyayye, basu cutar da ita ba ko kaɗan, Iya jinin al'adarta ne su ka tsotse, after that Angel ta yi mamakin Giant ɗin daya taimaki batul ya dawo da ita cikin su, a iya saninta Giant basa magana, sai dai ko tsakaninsu da manyan su zai iya yiwuwa suna magana, Amma ita Batul Giant ɗin ya yi mata magana har ya nemi taimakonta!! lamarin ya ɗaure mata kai. Ta yi zurfi acikin tunaninta, muryar Batul ta katseta da cewa"Rabin raina, Me ki ke tunani ne? Allah yasa labarin dana baki bai ɗaga maki hankalin ki ba, dama saida nayi fagabar hakan" Girgiza kai Angel Ta yi"a'a hankalina bai tashi ba, just na ɗanyi mamakin wasu abubuwa ne, Yanzu dai nuna min Jan tabon da ke a saman ƙirjin ki inaso na gani" da sauri batul ta sanya hannu ta soma nannaɗe ƙasan rigar da ke a jikinta har zuwa saman ƙirjinta, daga ƙasan boobs ɗinta da suka fara tasawa, Angel ta yi tozali da Jan tabon da ke a wurin, kasancewarta fara sosai, fatar wurin ta yi jawur. "Yana yi maki zafi"? Angel ce ta yi maga tambayar, batul tace"A'a, bana jin zafi," jinjina kai Angel ta yi"zan yi maki addu'a, in tofa maki saman fatar wurin a yanzu, sannan da Anjima kafin mu kwanta zan ƙara yi ma ki, don inaji araina cewa Jan tabon nan ba alkhairi bane, dole akwai wani abu da ya ke nufi" ba tare da 6ata lokaci ba Angel ta karanto addu'o'i tare da tottafa mata saman fatar wurin, bayan ta kammala yin addu'ar ta ɗago su ka kalli juna. "Allah ya tsare min ke ya kare min ke tare da sauran ƴan uwana daga sharrin waɗannan azzaluman mutanan" fuskar Batul ɗauke da murmushi ta amsa mata da ameen, ruƙo hannunta Angel ta yi acikin nata"taso mu koma Ɗaki, kada ajimu shiru, " A tare su ka miƙa tare da nufar ƙopar fita daga cikin toilet ɗin, sam ta manta da zancen ainihin abunda ya kawota Cikin toilet ɗin. Shigar su ɗakin keda wuya, kunnuwan su su ka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙopa, ras! gaban su ya faɗi, Azeeza da jamimah jiki na kerma su ka sauko daga saman gadagen su, atare su ka shige ƙarƙashin gado, Hankalin su sarah ba ƙaramin tashi yai ba, Kowan nan su Zuciyar shi ta hau harbawa da ƙarfi da ƙarfi, Deeja da ke kwance saman gadon Haris tuni ta zabura ra miƙe zaune, Gaba ɗaya idanuwansu na akan Matakalar benan, A bakin ƙopar fitowa daga sashen toilet ɗinsu Batul da Angel su ka dakata da yin tafiya Hannunsu ruƙe Cikin Na juna, Kowa Jira ya ke yaga wanene zaya shigo. Jin takun tafiyar ta yasa hankalin su ya ƙara tashi, A hankali ta ke saukowa daga saman matakalar benan hannunta a ruƙe da sandarta, Kamar kullum Cikin jar shiga ta doguwar riga, Takunkumin da ke akan fuskarta Iya saman tsinin hancinta Ya tsaya, blue eyes ɗin ta, sai ɗaukar ido su ke Yi, Daga bayanta Giants ne masu take mata baya, Majiya ƙarfi dogaye masu ƙirar dakarun Yaƙi, Tuni kowan nan su yasha Jinin jikin shi. A tsakiyar Ɗakin nasu tsohuwa zafreen Taci burki, tana binsu da kallo ɗaya bayan ɗaya, Babu wanda yai tunanin ya gaishe ta a cikin su saboda tsoratar da su ka yi, a ƙalla ta ɗauki mintuna tana ƙare masu kallo, kafin ta soma magana da kakkausar murya "Ba ku Iya gaisuwa bane? Ko jira ku ke yi ni in fara gaishe da ku"? Muryoyin su na rawa su ka soma gaishe da ita, banda mutun ɗaya Angel da su azeeza waɗanda su ka 6oye a ƙarƙashin gado ita da jamamah, sun rungume juna jiki na kerma saboda tsoron da ke gare su. "Ba haka nake so ku gaisar dani ba, saukowa za ku yi daga saman gadajen ku, Ku russina min," da sauri Sarah dasu hibba da ke zaune saman shimfiɗa su ka miƙe tsaye su Deeja su ka sauko saman gadajensu ita da parveen, a tsananin tsoroce su ka ƙarasa gabanta, Da niyar su zuƙunna mata kamar yarda ta buƙata, muryar Angel ce ta katse su "Karku kuskura ku russina mata! Ae ita ba Allah bace, banga dalilin da zaisa mu girmama ki ba, because you don't deserve it!" A firgice su Deeja ke kallon Angel da ta yi maganar cikin ƙwarin gwiwa, tsabar mamaki ne yasa tsohuwa zafreen Saurin wurga ƙwayar idanuwanta kan fuskar Angel tamkar zasu faɗo ƙasa, Tun da take arayuwarta wani mahaluƙi bai ta6a yi mata katsalandan ba kamar yarda Angel ta yi mata ayanzu ɗin nan, Sam ta kasa magana sai kallonta ta ke yi haɗi da jinjina kanta. Hankalin su Deeja idan yai dubu to ya tashi, muryoyin su na rawa su ka soma ambaton sunan Angel suna bata haƙuri akan ta daina magana karta ja masu bala'e. Dogon tsoki Angel taja mai sautin gaske, Tare da cewa"Ku ku ke jin tsoronta, Ni bana tsoron kowa sai Allahn da ya halicce ni shi nake tsoro, amma ba wani bawa ba, mai hannu biyu irin nawa mai ƙafafuwa biyu, wanda in mutuwa tazo ɗaukar shi bai isa ya kubce mata ba"! Idanuwan zafreen azazzare ta ke ƙarewa Angel kallo tun daga ƙasa har sama, Giants ɗin da ke a bayanta Har sun yunƙura zasu motsa tsohuwa zafreen ta dakatar da su ta hanyar ɗaga masu hannu. "Angel dan Allah ki rufa mana asiri, Mu za ki jamawa ki yi shiru ki daina magana, Na roƙe ki badan halin mu ba," Batul ce ta yi mata maganar Atare su Hibba su ka haɗa baki suna yi mata magiya akan ta yi shiru, ita kanta Angel ɗin ƙarfin haline kawai amma can cikin zuciyarta a tsorace take, sai dai bakinta yaƙi mutuwa, tana ƙoƙarin cigaba da yin magana Batul ta sanya hannu ta toshe mata bakinta, hannu ta sanya tana kiciniyar 6an6are hannayen Batul. Ido cikin Ido Su ke kallon Juna ita da tsohuwa Zafreen, Abunda wani bai ta6a gigin yi mata ba, ba'ayi mata magana ana kallon Cikin idanuwanta, Yau sai ga wata ƴar ƙaramar cikin prisoners tana yi mata fitsara da rashin kunya akan idonta. A hankali tsohuwa Zafreen ta ɗaura hannunta ɗa ya saman fuskarta, tare da zame takunkumin da ya rufe fuskarta, Kowa yasha jinin jikin shi, muryarsu na kerma suka zuƙunna saman gwiwowinsu agabanta suna roƙonta akan ta yi haƙuri kada ta cutar masu da Angel ɗin su. Tuntsirewa tsohuwa zafreen ta yi da dariya tamkar bakinta zai 6are, duk su ka bi su ka ruɗe, a lokacin Angel Ta samu damar 6an6are hannun Batul data toshe mata baki da shi, Sai faman haki ta ke yi tana zare ido. "Well done Unaiserh!" ta ambaci hakan tare da yi mata alamar jinjina da hannunta ɗaya. "Dole in yaba ma ki, saboda Ke ce prisoner ta farko da kika fara gaya mini magana ido cikin ido, ba tare da jin shakkata ba, sannan ke ce mutun na farko da kika fara furta min kalmar cewa ni baiwa ce kamar kowa, sa'an nan baki jin tsoro na" Bazawarin murmushi tsohuwa zafreen tasakar mata, kafin ta ɗaura da cewa"Wuyan ki Ya isa yanka, tun da har kika iya gaya mini magana, Ina jinjina maki, kin kafa tarihi a zuciyar tsohuwa Zafreen" ta ƙarasa maganar fuskarta ɗauke da shu'umin murmushin nan nata mai wuyar fassaruwa. "Ni bana hukunta mutumin da ya nuna baya jin tsorona, sai dai in ta6a zuciyarshi, ta hanyar cutar da wanda ya mutu akan ƙaunarsa"! ras gaban Angel ya faɗi, Hankalinta Ya tashi, ta zazzaro idanuwanta akan fuskar zafreen, saboda ta fahimci me ta ke nufi, hatta su Deeja sun gane me ta ke nufi, gwiwowin su a sage, su ka mimmiƙe tsaye suna ja da baya, yayin da hawaye ke bin fuskokin su. "Dan Allah kada ku cutar mu, Ku ƙyale mu mu yi rayuwarmu, Lafin me mu ka aikata ma ku ne, da ku ke son ƙarar da mu....." Kafin Deeja ta ƙarasa maganar tsohuwa zafreen ta buga sanar hannunta, muryarta a kausashe tace"Ban baku iznin Yin magana ba, " tun da ta ambaci hakan babu wanda ya ƙara magana, A hankali ta ɗaura idanuwanta kan fuskar Angel ta soma magana yayin da take tunkararta "ZA6I UKU ZAN BAKI! A CIKI DOLE KI ƊAUKI ƊAYA, SAKAMAKON RASHIN KUNYAR DA KIKA YI MINI"! runtse ido Angel ta yi Jikinta na kerma zuciyarta a tsorace ta ke da fargabar jin Za6in da Tsohuwa zafreen za ta furta mata. A tsanake tsohuwa Zafreen Ta ci gaba da cewa" za6i na farko shi ne I will order the giants to do terrible things to your sisters while you watch, or I will kill two of your sisters. The last option is that you will no longer get healthy food. From now on, you will only have to eat leaves like animals, Sannan ruwan shan ku zai koma na zafi," Tsabar tashin da hankalin ta yai batasan sa'adda ta furta Innalillah wa'inna ilaihirraji'un! Muryarta adisashe . Haƙiƙa ta yi danasanin maganar data gaya wa tsohuwa zafreen, Wasu irin zafafan hawaye ne suka wanke fuskarta, Muryarta A raunace ta soma magana "Idan har maganar dana faɗa maki ce tasa kika bani wannan za6in, ina neman alfarma a wurin ki, Ba dan hali na ba, zan zuƙunna akan gwiwowina dan in nemi yafiyarki, saboda ni na yi maki laifi bai kamata hukuncin da za ki yi mini ya shafi ƴan uwana ba. Girgiza kai tsohuwa zafreen tayi tare da cewa"kin ƙara tabkar wani kuskuren, Ni Ba'ayi min jayayya, sannan idan na zartar da hukun ci, babu wanda ya isa yasa in canza, Bayan haka kina yi min magana idanuwanki a cikin nawa, Anya kuwa kinsan wacece tsohuwa zafreen? Ta yi tambayar da izza, Angel dai bata ce komai ba, Jikinta duk yai sanyi. "Idan ba ki za6i ɗaya daga cikin za6in dana lissafa ma ki ba, zan aiwatar da duka uku" fuskokin su Deeja tabi da kallo bayin Allah, Jikin su sai kerma ya ke yi, da yatsun hannayen su su ke yi mata nuna da ta ɗauki za6i na uku, duk da basu san menene ganyan ba hankalin su yafi kwanciya da shi tunda abin ci ne. Zuciyar Tsohuwa zafreen ta hasala sosai Jin yadda ta yi shiru bata amsa mata ba, har ta buɗe baki zata zartar da hukunci muryar Angel ta katse ta da cewa"Za6i na uku amma duk da haka ina baki haƙuri, akan ki cire ƴan uwana daga horon da zaki bani" Girgiza kai tsohuwa zafeen ta yi fuskarta babu sassauci rashin imani ne tsantsa, Juyawa tayi tare da nufar Benan ɗakin da sauri gaints ɗin dake take mata baya su ka bi bayanta, atare su ka fuce daga cikin ɗakin. Zubewa Angel ta yi saman gwiwowinta, sosai ta fashe da matsanancin ku ka tamkar ranta zai fita, takaici duk ya ishe ta, ji ta ke kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu saboda baƙin cikin halin da ta jefa ƴan uwanta. Tsananin tausayinta ne ya kama su Deeja, Jiki asanyaye su ka nufo wurinta hada su azeeza da ke a 6oye ƙarƙashin gado, A kewaye da Angel suka zuzzuƙunna suna lallashinta, Cikin shessheƙar kuka tace"Na tsani kaina, nayi danasani, zuciya ta ja mini na gaya mata magana, ga shi yanzu naja ma ku Cin ganye, Duk laifina ne, ni da ya kamata ace ina taimakon ku sai gashi ni nake ƙara jefa maku cikin matsala, " daƙyar ta ƙarasa maganar. "Angel Ki yi haƙuri ki daina zubar da hawayen ki, ki daina ɗaurawa kan ki laifi, Allah ya riga da ya ƙaddara faruwar hakan, pls kidana kuka bamu san ganin hawayen ki na zuba" Deeja ce ta yi maganar, Sarah tace"tun farko banso kika tanka mata ba, da duk hakan bata faru ba" idanuwanta jawur ta kalli fuskar Sarah da ta yi maganar ta mayar mata da martani"wlh zuciyace ta ɗebe ni, bansan ma na furta mata maganar ba, amma meyasa zata hukunta mu, mu duka bayan nice mai laifi"? Cikin ƙunar rai ta yi maganar, Batul tace"Saboda zalunci! Dama ai ba zata ɗauki mataki akan ki ke kaɗai ba , saboda kin nuna baki tsoronta, shiyasa ta haɗa damu don ta ƙuntata ki, kuma in sha Allah ba abunda zai faru damu, Ki kwantar da hankalin ki Angel, su ci gaba da kawo mana ganyen zamu ci, ruwa kuma ai muna da shi a cikin toilet sai mu koma muna shan na fanfo, ba dole sai wanda su ke kawo mana ba, ' Idanuwanta arauna ce ta ke bin su da kallo mai nuni da tsantsar tausayin su da ta ke ji, ta lura basu san me ganyen ya ke nufi ba shiyasa su ka aminci za su ci, duk da acikin za6in da tsohuwa zafreen ta bata shi ne mafi sauƙi agare su. Muryarta asanyaye tace"Amma ae ba ku saba cin ganyen ba, ba mu san wani irin ganye zasu kawo mana ba, ina jin fargabar su kawo mana wanda zai cutar damu" Cikin kwantar da murya Hanna ta soma magana" kada ki damu kan ki, Da daɗi da ba daɗi zamu ci" Ta yi mamakin kalaman su agare ta, maimakon su ji haushin Abunda taja masu amma sai ga shi suna lallashinta. A hankali ta ɗaura idanuwanta akan fuskokin su Azeeza da Jamimah da Parveen tun kafin ta yi masu magana parveen ta riga ta cewa "ba sai kin ce komai ba Angel, kwanciyar hankalin ki yafi mana komai, tabbas naji ba daɗi saboda ƙaunar da ke a tsakanina da abinci amma na haƙura tunda bamu da za6i, ƙaddarar mu ce tazo mana a haka, zamu jure muci ganye....." runtse ido Angel tayi yayin da hawaye ke cigaba da tsastsafo mata saman kuncin ta. Cikin sanyin murya Azeeza tace"Nima bani da matsala Angel, zanci ganye da babu ƙwara ba daɗi, sannan duk runtsi duk wuya idan Allah yaso mu rayu ba wanda ya isa ya hana, nidai fata na shine Allah ya ba ki ikon ku6utar damu daga Cikin kurkukun ƙaddarar nan, wlh banaso in mutu acikin shi, " maganar Azeeza ta yi matuƙar ta6a zuciyoyin su, su kansu basu fatan suyi wulaƙantacciyar mutuwa a gidan kurkukun kamar yarda ƴar uwarsu Unaizah ta yi, idanuwan Angel jaga jaga da hawaye ta ke kallonsu ɗaya bayan ɗaya. Muryar jamimah tamkar zata fashe da kuka tace"Nidai banason ganye, na saba da cin nama, amma in dai Genie ɗita zata daina kuka to nima zan haƙura inci ganyen" Murmushi ne ya bayyana akan fuskokinsu, Da sauri Angel ta miƙa hannu ta ruƙo Jamimah zuwa jikinta ta rungumeta sosai tamkar zata mayar da ita cikin cikinta. "Nima bani da damuwa Angel, duk idan na tuna abunda kika faɗa mana dangane da irin tanadin da Allah yayiwa bayinsa salihai, waɗanda suka yi imani dashi sannan su kayi tawakkali, basu sa6a mashi ba, Sai inji daɗi araina, wahalar mu a gidan duniya ne, idan muka mutu zamu ji daɗi," sosai Angel ta kuma fashewa da wani kukan jin abunda Yasmin tace. "Yana daga cikin rukunan Imani mutun yayi imani da ƙaddara mai kyau da mara kyau, kamar yarda kika koyar damu, don haka munyi imani da ƙaddararmu, zamu rungume ta hannu bibbiyu, har zuwa lokacin da Allah zai ɗauki ranmu mu huta, amma duk da haka bamu sare ba, sannan bamu fidda rai da rahamar ubangiji ba, wata rana zamuji daɗi sai dai bamu sani ba, jin daɗin namu daga gidan duniya zai fara ko kuwa sai mun koma gare shi Allah wa'alamu," eve ce ta yi maganar, hibba tace"ai ni tunda Angel ta faɗa mana cewa kowa zai mutu harda waɗanda suka cutar damu da waɗanda suka sadaukar da mu, wlh sai naji daɗi araina, tunda ba dawwama za mu yi acikin duniyar nan ba, dukkan mu zamu koma ga mahaliccinmu ne, Allah zai yi mana hisabi tsakanin mu dasu zaibi mana haƙƙin mu, aranar da basu isa su ƙwaci kansu ba, " Maganganun dasu ke yi sun yi matuƙar faranta ma junansu, Musamman Angel taji daɗi da su ka yi imani da ƙaddarar rayuwarsu, a shirye su ke da su fuskanci kowani irin ƙalubale da zai zo masu acikin arayuwarsu a mutu ko ayi arai. Tun daga wannan ranar ba'a ƙara kawo masu abinci mai rai da lafiya ba, Faranti Biyu ake cuko masu Da ganye ganyen ma mai ɗaci, ga ruwan zafi har tiriri ya ke yi, saboda tsabar mugunta haka ake kawo masu shi don su sha, Rana ta farko da aka fara kawo masu ganyen babu wanda ya iya ci, ga yunwa suna ji kamar suci ƴan hancin cikinsu, suka rasa ya zasuyi, saboda bai ciyuwa agare su, basu saba cin ganye ba, Yadda aka kawo shi haka giants suka koma dashi, a cikon kwana na biyu ne da yunwar ta kusa yi masu Illah Kamar dabbobi suka zauna suna cin ganye, saboda mugun kamun da yunwa ta yi masu kamar zasu zauce, suna ci suna kuka maƙoshinsu na ƙaiƙayi ahaka suka cinye shi tass, Basu sha ruwan zafin da a ka kawo masu ba, sai dai su ka koma suna amfani dana fanfon da ke a cikin toilet ɗinsu, Ganyen da su ke ci ba ƙaramar illa ya ke yi masu ba, saboda basu saba ba, hakan yasa cikinsu ya dinga 6aci, babu wanda bai yi gudawa ba a cikin su, duk sun rame sun fita hayyacin su, sun zama mahaukatan ƙarfi da yaji, addu'ar da suke samu suyi yanzu sun daina saboda Rashin lafiyar da suke fama da ita, Kullum ne sai an samu wanda zai kwanta jinya acikin su, sun jigata sosai, kamar ba za su rayu ba, tun suna ci yana 6ata masu ciki har ta kai ga yanzu sun daina yin gudawa idan su ka ci ganyen, sun fara sabawa da cin shi, cikin nasu ya daina 6acewa, Idan aka kawo masu shi zama suke yi suci shi kamar dabbobi, ruwan kuma Basu iya shanshan shi da tsafi don zai iya yi masu illah, sai sun hura shi da bakunansu kafin su samu su kora shi ta cikin maƙoshin su, yaushe rabon da su wanke uniform ɗin jikin su yau tsawon wata ɗaya kenan, babu mai yin wanka a cikin su, damuwa da baƙin cikin halin da su ke aciki sakamakon canza masu abinci da akayi da kuma rashin dawo masu da ƴan uwansu yasa duk sun rasa kwanciyar hankali. Sai da Angel ta yi dagaske wurin ƙoƙarin danne zuciyarta dake shirin bugawa ta hanyar dagewa dayi masu addu'a tukunna suka ɗan samu salama, natsuwa ta shiga jikinsu, yanzu suna samun damar runtsawa su yi bacci sosai, amma fa dukkan su bana tunanin za'a iya samun ɗaya wanda bai fama da depression, wani lokacin idan ƙirjinsu yayi masu zafi zuciyoyinsu suka yi masu nauyi, haka zasu zauna su dinga karanta duk wasu addu'o'i da su ka san zasu Sanyaya masu zukatansu, kuma cikin ikon Allah da zarar sun yi komai su ke samun sauƙi, harma su samu damar yin bacci, yanzu sun fidda rai da za'a dawo masu da ƴan uwan su duba da irin tsawon lokacin da aka ɗauka babu su, Danish Yana acikin wata na biyar a hannunsu, Su haris suna acikin wata na huɗu, basu san awani hali su ke aciki ba, Allah kaɗai yasan irin azabtarwar da ake yi masu, suna raye ko sun mutu basu da tabbacin hakan....................." 💔PRISONERS💔 Dare ya nutsa sosai, babu mai motsi acikinsu, Bacci su ke yi kamar matattu, numfashin Angel ne ya soma canzawa, zufa ta soma wanke fuskarta, bugun zuciyarta ya ƙarfafa, yatsun hannayenta dana ƙafarta suka soma Yin kerma, Ga dukkan alamu mafarki ta ke Yi, wanda yasa ta shiga wannan yanayin da take a ciki, su uku ne a kwance saman shimfiɗar da ta yi masu a ƙasa, Ita da Jamimah sai Azeeza. Sai faman yin sambatu ta ke yi tana ambaton Sunan tsohuwa Tamira! Wata irin firgita ta yi Sakamakon Ta6a jikinta da akayi, a hanzarce ta yi wuff ta miƙe zaune tana faman zazzare idanuwanta, gashin kanta duk ya tarwatse saman bayanta. "Angel ni ce! Meyasa kike sambatu kina ambaton sunan tsohuwa Tamira? A tsananin tsorace ta ɗaura idanuwanta kan fuskar batul da ke yi mata magana, Farkawarta kenan daga bacci, fitsarine ya matse ta bayan taje toilet ta yi shi ne ta dawo ɗakin har zata kwanta sai taji muryar Angel tana sambatu acikin baccinta, wannan dalilin ne yasa ta nufi shinfiɗar su don taga meke faruwa da ita. Bata amsa mata tambayarta ba, saboda bata a cikin natsuwarta, ganin ta miƙe tsaye ne yasa itama batul ɗin ta miƙe tana tambayarta lafiya meya faru? Babu alamun zata tanka mata, sai faman bin ɗakin su ta ke yi da kallo kamar ranar ta fara ganin shi. "Angel dare ne fa, Me ki ke kallo? Magana fa na ke yi ma ki amma kin share ni....." tunkan batul ta ƙarasa maganar, Angel ta damƙi hannun batul tare da Janta da sauri ta nufi sashen toilet ɗin hannunsu aruƙe dana juna, bayan sun shiga sashen ne Angel ta saki hannunta, aruɗe batul ke kallon fuskarta gani take kamar angel tafara haukacewa ne shiyasa ta janyota a tsakar daren nan zuwa sashen toilet ɗinsu. Fuskarta da alamun ruɗi tace"kiyi min magana mana, meyasa kika kawo ni nan"? Sai da ta fara tattara natsuwarta guri guda kafin ta soma magana "Batool na yi wani mafarki da ban ta6a yin irin shi ba, dangane da wani kalami da tsohuwa Tamira ta ta6a furta mana......" daƙyar tayi maganar tana faman haɗiyar yawu, batul duk ta gama ruɗewa "Wani kalami kenan"!? Ta jefa mata tambayar. "Zan faɗa maki amma kafin nan inaso ki sanar dani, Kafin zuwana gidan kurkukun nan, a ina ku ke yin rayuwa? Meyasa aka canza maku ɗaki daga asalin wanda ku ka baro"? "Angel meyasa kika tambaye ni"? A tsiwace tace"nidai ki bani amsar tambayata"! Yawu batul ta haɗiya kafin tace"Ni kaina bansan dalilin dayasa aka dawo damu nan ba, kawai dai nasan tsohuwa Tamira tace zata sanya a canza mana ɗaki saboda asalin wanda muke aciki yayi mana ƙanƙanta, babu wadataccen filin da zamu sakata mu wala........" A dabarbarce take yin maganar saboda yadda Angel tayi mata rumfa kamar zata rufeta da bugu. "Amma ranar da aka kawo ni kurkukun nan, Na tsinci kaina nikaɗai acikin ɗakin nan, sai daga bisani aka buɗe ƙopa sai gaku kun shigo Ciki, daga ina ku ke"!? girgiza mata kai Batul tayi"bazan iya tunawa ba Angel, bansan inda aka kaimu ba, " numfasawa Angel tayi tare da sanya hannunta biyu cikin sumar kanta, kamar akwai wani abu da take son ganowa, ganin yadda duk tabi ta ruɗe ne yasa Batul tambayarta"meke damun ki ne? meyasa ki ka tambayeni"? "Saboda ina hasashen Akwai ƙopar da zamu Iya guduwa ta cikin ɗakin nan da muke rayuwa........." batul bata fahimci inda zancen nata ya dosa ba. "Angel ƙopa fa kika ce a cikin ɗakin nan ta ina kenan? Anya kuwa kinsan me kike faɗa kuwa"? Jinjina kai ta ɗanyi kafin ta soma magana" akwai wata magana da tsohuwa tamira ta ta6a furta mana, ban tashi tunawa ba sai Acikin mafarkin da na yi yau, abun tace mana shi ne tana so mu ɗauka cewa mu kamar *MUKULLAI NE NA MABUƊIN WATA ƘOFA GUDA ƊAYA WADDA ZATA SAMA MANA FARIN CIKI ACIKIN RAYUWARMU, TABBAS MUNA DA DAMA* Amma fa dole sai Mun yarda da kan mu, mun haɗa hannu, domin kuwa Ƙofar farin cikin nan tana atare mu Sa'annan *MU NE MAKULLAN DA ZAMU BUƊE TA* Numfashi Angel taja tare da cigaba da yin magana "Kalamaine tayi mana cikin hikma, a hasashe na, dama tun fil azal tsohuwa tamira tana son taimakon ku, shiyasa tayi silar da aka canza maku ɗaki aka kawo ku nan, bayan haka tasan da zuwana gidan kurkukun nan........" Ba ta kai ga ƙarasa maganar ba, Batul ta tari numfashin ta da cewa" kin manta wacece tsohuwa tamira, itama fa muguwace kamar sauran, banbancin kaɗan ne sannan ma'aikaciya ce ita agidan kurkukun nan, taya kike tunanin zata iya taimakon mu? ta yi mata tambayar tana bin da kallo. "Mutun koda dutse ne a ƙirjin shi ba zuciyaba, idan Allah ya so ka da rahama sai kaga Ya rikiɗa daga mara tausayi zuwa mai tausayi, Zai iya yiwuwa tsohuwa tamira taji tausayin halin da ku ke acikine shiyasa ta nemi hanyar da zata ku6utar daku, Ita da kanta ta faɗa mana cewa tun da ta ke rainon prisoners bata ta6a samun waɗanda su ka kwanta mata aranta ba irin mu, da alama tun kafin zuwana kurkukun nan take so ta taimake ku sai dai tagaza gudun kada taja ma kanta, Shiyasa ta dakata har zuwa lokacin da aka kawo ni sai tayi amfani da kaifin basirar da nake dashi wurin sanar dani cikin hikma akan hanyar da zamu bi don mu gudu daga prison!" Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikma donta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai ........................❓❗ Dai dai nan Na ajiye alƙalamina, Shin kuna ganin dagaske ne hasashen Angel akan kalaman tsohuwa tamira? 💋PRISONERS💋 Cike da ƙwarin gwiwa ta yi maganar, Nazari sosai batul tayi dangane da kalaman da Angel ta furta mata, Na ɗan wani lokaci babu wanda ya furta wani abu a cikinsu, can batul tace"Kamar fa akwai ƙamshin gaskiya a maganarki, Amma idan har ta tabbata dagaske ne tsohuwa tamira ta yi kalaman hikima don ta fahimtar damu hanyar da zamu ku6uta, Tayaya zamu iya ganin ƙopar da zamu gudu? Sannan taya akai muka zama makullai Zama Angel ta yi dirshan a saman floor, ta jingina bayanta jikin bango, Hannayenta Biyu Dafe da kanta, Ganin ta zauna yasa itama batul ɗin ta zauna, Ya kasance suna fuskantar Juna ita da Angel, Kowa Da abunda Ya ke nazari a cikim kanshi duk a ƙoƙarinsu na su gano fassarar kalaman tsohuwa Tamira, Sun ƙurawa Juna ido Kamar Malaman Duba, tsawon mintuna kafin Angel ta soma ƙoƙarin motsa bakinta wurin furta"idan ya kasance ƙopa ce, to kuwa mun rasa Makullin da zasu Iya buɗe ta ko da ace mun gano ta, saboda adadin makullin da zasu iya buɗe ta basu Cika ba, Babban makullin ma baya a cikin mu, idan mu ka gano ƙopar tayaya zamu iya tattara makullan da basa atare damu"? ta jefa ma batul tambayar, numfasawa batul ta yi kafin tace"Shi ne Abunda nima nake tunani amma anya kina ganin kalaman tsohuwa tamira suna nufin ƙofa ce ke akwai? Kodai kawai tana nufin mu zamu haɗa hannu don mu ku6utar da kan mu"? Fuskarta da alamun ruɗu ta yi maganar, Angel tace"Abin da zaki lura anan shine, Cewa ta yi mu ne makullan buɗe ƙofar, that mean ƙofar daban ta ke bamu bane ƙofar, sai dai mu zama makullan buɗe ta, ni dai a hasashe na kenan" kowa kanshi ya ɗauki zafi, Girgiza kai batul ta yi"A'a ni nafi hasashen Mu ne zamu sama ma kanmu ƙopar fita idan muka haɗa hannu, Ba wai tana nufin Akwai ƙopa a cikin ɗakin mu ba, kaina ya fara rikicewa, Ko dai inje in yi ma su Hannah magana Su zo mu haɗu Kowa ya faɗi nashi ra'ayin? Kinsan abokin shawara nada daɗi, wata'ƙil acikin su asamu wanda zai faɗi ainihin me ma'anar ta ke nufi tunda mu kan mu ya kulle, Amma idan aka kira su wanda su ka fi raja'a akan cewa ƙopa ce kin ga sai mu fara binciken inda zamu ganta, Idan Allah yasa muka gano ta sai mu yi ƙoƙarin tattara makullan da muka rasa!" Angel ta gamsu da bayanin da batul ta yi mata. "Kina ganin mu tayar da su daga bacci yanzu ko mu bari sai gobe da safe"? Batul ce ta jefa mata tambayar. "Wani irin gobe? ai yanzun nan zamu farkar da su, Babu zancen 6ata lokaci, zuciyoyin mu da fargaba su ke buga wa, duk daƙiƙa ɗaya na rayuwar mu a tsorace mu ke yin shi don haka bamu da lokacin 6ata lokaci, wannan dama ce agare mu, ba zamu yi wasa da ita ba, dama tsohuwa tamira ta faɗa mana cewa Ba zamu fahimci me ta ke nufi ba sai nan da wani lokaci da muka fita hayyacin mu, wasu ma su ka rasa ransu, A yanzu mun rasa mutun biyu, bamu da tabbacin ma Ƴan uwan mu maza da aka ɗauka zasu dawo mana da su dukkan su ba tare da an samu wanda ya rasa ran shi ba acikin su, fita hayyaci kuma mun yi sau ba adadi, Yanzu ne yakamata mu nema wa kan mu mafita tun kafin su ƙarar da mu don inaji araina Bamu ga komai ba, domin kuwa har yanzu muna a TAKUN FARKO na kurkukun ƙaddara, Idan har muka kai TAKUN TSAKIYA a cikin Kurkukun nan ba tare da mun ku6uta ba, bana tunanin za'a samu rai ɗaya da zai rayu acikin mu In ba wani iko na Allah,' muryarta asanyaye ta ƙarasa maganar, Batul da ke sauraronta ganin ta ƙare maganarta yasa ta yunƙura ta miƙe tare da cewa"Ki taso muje mu tashe su daga baccin"! Miƙewa Angel tayi tare da kallonta. "Batul duk wani motsi namu akan idon su! Dole sai mun yi takatsantsan idan ba haka ba Garin neman gira zamu rasa ido. "Ya zamu Yi kenan"? Acewar batul Angel tace"Ni aganina, mu kashe hasken ɗakin mu wata'ƙil idan mu ka yi hakan ba zasu Iya ganin mu ba, Sannan Ba kowa zamu tayar daga bacci ba, Mu za6i kamar mutun uku sun isa, Kinga mun cika mu biyar kenan, Sai mu ji ra'ayoyinsu." "Ni nafi tunanin atada su duka saboda kowa da irin baiwar da Allah ya yi mashi, musamman Azeeza da Deeja ga kuma Parveen sannan Hannah bayan ita sai sarah zata taimaka mana Tunda tana da tsawo sosai wani abun da ba zamu Iya hangowa ba zata iya hango shi. Girgiza kai Angel ta ɗanyi"Gaskiya baza a tada azeeza ba, kinmanta bata gani idan dare yayi? Ita kuma Jamimah tayi ƙaranta ba abunda ta sani" "Shikenan, Zan je na kashe hasken ɗakin, Kafin mu dawo tare dasu Ki Buɗe ƙofofin kowani toilets saboda mu samu hasken Fitilun da ke a cikin su Ya haskaka sashen,' Angel ta amsa mata da toh, Juyawa batul ta yi tare da fuce wa daga Cikin sashen. Ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da kifa kanta Jigin bango tana jiran dawowarsu, Ɗuff Taji hasken ɗakin su Ya ɗauke duhu ya gauraye ko'ina, A hanzarce ta lalubi ƙofofin Toilets ɗin ta buɗe su duka, Hasken Fitilun cikinsu Ya haskaka Sashen Duk da bai wadata sosai ba" Jin motsin shigowar su Yasa ta yi saurin fuskantar su, sai faman murza idanuwansu su ke da yatsun hannayensu, Parveen sai hamma ta ke Yi bakinta hada miyan bacci. "Sai da nace maki ban da Azeeza meyasa kika tado ta"? rai a6ace ta yi maganar idonta akan Azeeza, da Batul ta ruƙo hannunta "Bani na tada ta ba, Ina cikin tada su Deeja ta farka tana Jin fitsari shi ne na ruƙo hannunta muka shigo atare" mayar da idanuwanta tayi akansu, Kusan su dukane banda Jamimah ita kaɗaice basu Tada ta ba, tana can ƙudundune Cikin bargo saman shimfiɗar su. "Wai lafiya aka tayar da mu daga bacci? Ko an kawo abinci ne"? Parveen ce ta yi tambayar fuskarta a yamutse, Harara Angel ta watsa mata"Halan mafarkin shi ki ke cikin Yi aka tada ki, shiyasa kike tambayar ko an kawo abinci" Kwa6e fuska ta yi ba tare da tace komai ba, Sai faman murza ido su ke yi, fuskokin su a tur6une. "Hakanan muna yin baccin mu mai daɗi an tada mu," hannah ce ta yi maganar tana murgaɗa ƙaramin bakinta. Jan hannun Azeeza Batul ta yi zuwa cikin toilet su ka shige. "Ganin Yadda su ke ta kwa6a magana ransu a6ace saboda an katse masu bacci, har suna cewa ta tsare su da ido, idan ba abunda zata gaya masu zasu koma ɗaki su kwanta ne" Har sun yunƙura zasu Juya muryar batul ta katse masu hanzarinsu da cewa"AN SAMU ƘOPAR DA ZAMU GUDU" A ruɗe Suka dakata da yin tafiyar suna kallonta, tamkar saukar aradu Haka maganar ta dirar masu acikin kunnuwan su, wani irin kallon rainin wayau su ke binta da shi, ƙarasa fitowa ta yi daga Cikin toilet ɗin hannunta ruƙe dana Azeeza. "Idan ku ka natsu zamu Yi maku bayanin komai" ga dukkan alamu sun shiga ruɗani duba da irin kallon da su ke yi mata. "Wannan maganar daga jinta a cikin mafarki ake yinta ba'a gaske ba" Hibba ce ta yi maganar, idanuwanta kamar na mashayin giya. Sarah tace"Nima nafi tunanin mafarki ne mu ke yi, idan har ta tabbata dagaske mu ke ganin batul da ta yi maganar to kuwa tabbas Ganyen da muke ci ya fara zautar da ita, shiyasa ta fara mana sambatu" Sarah na rufe baki Hannah tace"ni bazan tsaya sauraron wannan shirmen ba, Kun ga tafiyata" ta yi magnar tare da nufar ƙopa zata fuce da sauri batul ta saki hannun azeeza tai wuff ta ruƙo wuyan rigar Hannah ta janyo ta tare da dawo da ita ta jinginar jikin bango. Angel ta kasa kunne tana sauraron su, gani ta ke kamar ba za su iya fahimtar su ba koda ace sun faɗa masu, saboda basu ɗauki abun serious ba. "Kun tasa mu agaba kuna kallo kamar kun samu madubi, idan ba za ku buɗe baki ku yi magana ba, Ni zan koma ɗaki" acewar Rubina. "Ki yi masu bayani mana ko ni zan yi masu"? Batul ce ta yi ma Angel magana. Gyaran murya tayi Kafin ta sassauta muryarta ta yadda sautin ba zai fita sosai ba, kamar maiyin gulma, ta soma fayyace masu komai dangane da hasashen da su ke yi akan Kalaman tsohuwa tamira. Sun natsu suna sauraronta, Yadda suka tattara hankulan su akanta sai ta yi tsammanin ko sun Fahimci inda zancen nata ya dosa ne, sai da ta kai ƙarshen Maganar, kusan atare suka haɗa baki wurin jan tsoki. "Kawai don ta yi kalami sai asamu ƙofa, sai ka ce ba ku san wacece tsohuwa tamira ba, In banda ma rainin wayau taya za'ace mune makullan buɗe ƙopa? Ƙanzon kure ge ne wannan" Parveen ce ta yi maganar tana hura hanci ita ala dole an 6ata mata rai. "Da nasan abunda zaku gaya mana kenan Allah da ban farka ba lokacin da batul taje tada ni daga bacci" acewar Eve "Ni dama kwanakin nan ban yarda da ku ba, Ku biyun nan Batul da Angel, damuwa tasa kun fara zaucewa," Yasmince ta yi maganar , kamar zasu rufe su da duka Kowa Da abunda ya ke furtawa, Mutun Biyu ne a cikin su basu yi magana ba, Deeja da ta jingina kanta Jikin bango ta lumshe idanuwanta sai Azeeza da ke a tsaye bakin ƙofar toilet, Ta kasa kunne tana sauraronsu duk bata ganin su. "Koda ace baku yarda da maganar mu ba, Inaso ku bamu dama, Mu fara neman ƙofar da ke a cikin ɗakin mu. Idan ba'a ganta ba ni na yarda Ku yi min duk abunda ya dace dani," cikin sanyin murya Angel tayi masu maganar. "Deeja! Banji kince komai ba? Ke baki faɗi naki ra'ayin ba, dangane da kalaman tsohuwa Tamira," Daƙyar deeja ta iya buɗe idanuwanta masu ɗauke da bacci ta ɗaura su kan fuskar Batul da ke Yi mata magana, da buɗar bakin ta sai cewa ta yi"Oh wai da ba mafarki bane? Baki asake Take kallon su, Dafe kai batul tayi da hannu ɗaya"Wai meye haka? Idan har ba ku ɗauki maganar nan serious ba kun bamu haɗin kai tayaya zamu Iya ganin ƙofar...." Tun kan ta ƙarasa maganar Rubina tace"Ae ba za ku ta6a ganin ƙofa ba, hasashen ku akan kalaman tsohuwa tamira Wasiƙar jaki ce wadda bazata ta6a zama gaskiya ba, in banda wahalar da kai ta ya tsohuwa Tamira zata Taimake mu? Ku yi amfani da kwakwalwarku mana, koda yake dama ba cikakken hankaline damu ba, " Murmushin takaici Angel tasaki Jin abunda Rubina tace, wato dama basu da cikakken hankali. Muryar azeeza ce ta janyo hankalin su ga kallonta. "Ni ina goyan bayan maganarsu Angel, tsohuwa tamira tana son taimakon mu, kafin tabar cikin mu, Ta yi mana abubuwan da zata faranta mana rai wanda ke nuni da za ta yi kewar mu sanna ta faɗa mana cewa tana so wata rana mu tuna da ita acikin rayuwar mu, duk mutumin da ya furta maka wannan kalami dole asamu ƙaunarka da tausayinka acikin zuciyarshi, yakamata muyi nazari sosai, Koda ace bazamu yarda da maganar su Angel ba dangane da hasashen su akan kalaman tsohuwa, Kada muƙi bin maganarsu Mu jaraba duba ko'ina na cikin ɗakin, kafin mu yanke hukunci, Sannan inaso na tuna mana wani abu, kamar yadda Angel ta faɗa mana ba'a ganin wanda ya halicce mu, That mean idan zamu samu taimako daga wurin shi ba kai tsaye zai bayyana ba don ya taimake mu, sai dai Ya haɗa mu da wanda zai taimaka mana, ko ya fahimtar damu ta wata hanyar Kamar dai yadda Angel tayi mafarki da kalaman tsohuwa tamira.........." tun da Azeeza ta soma Yin magana Hankalinsu ya dawo kanta, Ko ƙyafta idanuwan su basa yi, Sun natsu suna sauraronta, Musamman Angel tsabar mamaki yasa ta saki baki tana kallonta, Yarinyar Allah ya yi mata baiwa, Ita takasa fahimtar dasu yadda zasu gane sai gashi kalaman Azeeza sun yi ta'asiri acikin zukatan su. Nauyayyiyar ajiyar Zuciya kowan nan su ya sauke, sarah tace"yanzu abunda za'ae mu fara neman ƙofar! idan Allah yasa aka same ta sai mu fara tunanin ta yadda zamu tattara makullan buɗeta," Atare suka haɗa baki wurin cewa"Haka Ya dace, " "ita fa azeeza da bata gani? Ko dai in kai ta ɗaki ta kwanta"? Deeja ce ta yi maganar. Tun kafin Wani ya bata amsa Azeeza ta bubbuga ƙafafuwanta Muryarta tamkar zata fashe da kuka tace"wlh ba in da zan je, dani za'ayi komai kawai don anga bana Iya gani shine za'a ware ni" ganin zata ja masu hayaniya yasa Angel yin saurin kai hannu ta janyota zuwa jikinta, ta rungumeta tana faɗin"Its okey azeezata, Ai dole ma ayi tafiyar nan da ke, kwantar da hankalin ki" ajiyar zuciya azeeza ta sauke tare da sanya hannayenta Biyu ta ƙanƙame Angel. "Kafin Mu fara bincike, Yakamata Mu fara Yin addu'a akan Allah ya bamu Ikon ganota Cikin sauƙi," Angel ce ta basu shawarar Yin hakan, atare suka ɗaga hannayen su Sama ta dinga jera masu addu'o'i suna amsa mata da ameen, bayan sun kammala Hibba tace"Bafa lallai yakasance ƙofa ta ke nufi ba, A kalamanta, " Batul tace"ae shiyasa zamu fara dubawa, Kunga idan ba'a samu ƙofar ba, sai muyi wani tunanin na daban" Gyaran Murya Angel ta yi Hankali ya dawo kanta. "Zamu Raba kan mu wasu zasu shiga toilets, wasu ɗaki, Amma na ɗaki dole su ɗaga gadajen mu, don ina hasashen ƙofar ta sirri ce, ta in da bamu tsammani zamu Iya ganinta, don haka mu sanyawa ran mu cewa har cikin Tukunyar fulawa zamu Iya samunta, kota jikin bango, kota ƙarƙashin gado, kai harma ta inda ruwa ke bi ya wuce, amma fa Wanda zasu duba Ƙarƙashin gadajen mu dole su yi taka tsantsan saboda ana ganin duk wani motsin mu, don haka Na ɗaki mu bari sai gobe zan shirya mana wasan Ƴar 6uya, zamu dinga shigewa da sunan mun 6oye kunga zasu yi tsammanin wasa muke Yi, ba wani abu muke nema ba" Murmushi su ka saki gaba ɗayan su, kafin daga bisani Batul ta rarrabasu zuwa gida uku, Nan fa suka baza cikin toilets ɗinsu suna neman ƙofar nan, Angel tana ruƙe da hannun Azeeza saboda makantarta, Uban gumi suka haɗa akan fuskokin su, Sun bada himma sosai, wurin neman ƙopar ba inda basu ɗaga ba, hatta tukunyar fulawar da ke a toilet ɗinsu saida batul da Deeja suka haɗa ƙarfi wurin ɗaɗɗagota amma basu ga komai ba, Bangon da aka jingine ta dashi ashafe Ya ke haka ƙasantama Ashafe Yake babu wata ƙofa, Kamar zasu fashe da kuka su ka sauke tunkunyar, furennin cikin ta ma duk sun bushe babu mai lafiya, Ko'ina Ciki da bai na sashen toilet ɗinsu saida suka bincika amma babu ƙopa, A ƙarshe sarah Ta hango masu Tagogin nan da ke a saman ceilling waɗanda tun farkon zuwan Angel ta yi tozali dasu a garƙame da kwaɗo, Kowani toilet akwai tagogin saman ceilling guda biyu, hankalin su gaba ɗaya ya karkata akan tagogin ransu ya gama basu cewar Za'a samu hanyar da zata 6ullar da su wajen kurkukun, Sai dai basu san ta yadda zasu Iya kaiwa gare su ba saboda basu da tsauni tsayin su kuma ba zai kai su ba, hatta Sarah Da tafi su tsawo bazata Iya koda ɗaga hannu ta ta6a jikin su ba, Bayan haka kuma basu da Makullin da zasu Iya buɗe tagogin, daga bisani tunani su ya canza akan Su nemo makullan buɗe tagar, A daren ranar basu koma bacci ba, Saboda Aikin neman makulli, Sunci baƙara wahala ga bacci a idonsu amma Sun nace akan neman makullai, wasa wasa har Gari Ya waye suna aikin neman makulli, A ƙarshe da su ka galabaita, don dole suka haƙura, Ga yunwa suna Ji ga bacci a idanuwansu. A saman floor na sashen toilets ɗinsu, Kowan nan su Ya samu wuri ya zauna suka fuskanci juna, Sai haki suke Yi kamar waɗanda suka Sha Gudu, Baccin wahala ne Ya ɗauke su mai nauyi, duk sun ɗaɗɗaura kawu nan su saman kafaɗun Junansu, Baka Jin sautin komai saina minsharin su. Daga cikin ɗakin su muryar Jamimah ce ke ta ƙwala masu kira, babu mai jinta, farkawarta kenan daga bacci, Hankalinta atashe ya ke ganin babu su asaman gadajen su, saukowa ta yi daga saman gadonta, tare da nufar Sashen toilet ɗin su, shigar ta keda wuya ta yi arba dasu zazzaune suna bacci, Mamaki ne ya kama Jamimah, ganin su anan maimakon saman gadajen su, ƙarasa shiga ciki ta yi a yayin da ta ke leƙa fuskokin su don taga Idan baccin gaske su ke yi ko kuwa tsokanar ta su ke Yi, Kallon ƙurulla jamimah take binsu dashi, adai dai saitin fuskar Angel ta tsayar da eye balls dinta, muryar ta ƙasa ƙasa ta furta"My Genie" shiru bata amsa mata ba, da ta fahimce cewa dagaske baccin su ke yi, Sai ta zauna tare da kwantar da kanta saman laps ɗin Angel ta lumshe idanuwanta kamar maiyin bacci, Tsawon Lokaci babu wanda ya farka, Sun saki baki suna bacci. A firgice Parveen Ta farka tana ambaton"Nagansu wlh nagansu" Sautin muryarta ne Ya farkar dasu Angel a fujajen su ka wawware Idanuwansu masu ɗauke da bacci suna kallon Parveen, Har suna haɗa baki wurin tambayar Ta"Makullan kika gani? a ina su ke"? Yawu ta haɗiya tana faman Zare ido, tare da ƙare masu kallo, Sam babu natsuwa atattare da Ita, Muryarta Ashaƙe tace"Kamar mafarki na yi nagan su a cikin ƙasar tukunyar fulawar nan, Makullan........" Tun kan ta ƙarasa maganar Zumbur suka mimmiƙe har suna bangaje juna wurin shiga toilet ɗin Saboda tsabar sauri, Jamimah batasan Kan me suke magana ba, binsu kawai ta ke Yi kamar bindi. A Gaban tukunyar fulawar Su ka zuzzuƙunna, Deeja da batul na ƙoƙarin tsoma hannu cikin ƙasar Angel ta dakatar dasu ta hanyar yi masu magana"Bana so acire furennin nan saboda raine dasu, Ina gudun kada silar cire su su mutu......" Bata kai ƙarshen maganar ba, Deeja ta tari numfashinta"A halin da muke cikin yanzu bamu buƙatar furanni, ganinsu ma ƙara tayar mana da hankali ya ke yi, don haka cire su zamuyi" ba tare da 6ata lokaci ba, Mutun Biyar ne su ka tsoma hannayensu Ciki, duk suka tsige furennin tare da jefar dasu ƙasa. Hankalin Angel sam ba akwance ya ke ba, Saboda ta yi believing da furannin rai Ne dasu, Ko da su Deeja su ka jefar dasu Ƙasa da sauri ta zuƙunna ta sanya hannu ta ɗauki furen daddynta dana Aunty aneelerh hada ƙaramin furennin nan, Har zata miƙe idonta Ya sauka Akan Dogon furen nan da ganyen shi ya koma baƙi, yanzu ya koma asalin colour din shi, Punch pink Ya ciza sosai, hakanan ta dinga jin gabanta Na faɗuwa, Ayayin da ta ke kallon shi, Kasa miƙewa ta yi har saida ta ɗauke shi ta hada da sauran furennin da ke a hannunta, tukunna taji Hankalinta Ya kwanta. Fasa ƙara Azeeza Tayi tare da faɗin "Mun samo shi! Gashi nan Makulli ne" jin muryarta Yasa Angel matsowa kusa dasu, Hankalin kowa Akan hannun Azeeza Ta damƙe wani abu dake a nannaɗe Cikin ƙasa, Wani irin farin Cikine Ya bayyana akan fuskokin su, Tun kafin Ta buɗe masu tafin hannun nata su ga menene. A hankali Azeeza Ta ware tafin hannunta, Ta soma kakka6e ƙasar da ke nannaɗe da abunda ta damƙo, ko da ta kammala Kakka6e ƙasar jikin shi, Murnar da su ke yi ta koma Ciki, Ashe jijiyar fure ce, tsabar takaici Yasa kowaccen su ta dafe goshin ta da hannu, Ƙululun bakin Ciki Ya tokare masu maƙoshin su, Ji su ke kamar su rufe Azeeza da bugu, don ba ƙaramin sanya rai su ka yi ba, Kamar masu zaman makoki Haka suka zazzauna Cikin toilet ɗin Abun duniya ya ishe su, Jamimah ce kaɗai a tsaye ta ruƙe qugu Tana bin su da kallo. "Wai ni kun barni aduhu me ake nema ne? Duk kun cire mana furennin mu, Genie Ki fada mini," hada ƴar shagwa6arta Ɗago da ido Angel ta yi tare da kallonta kafin ta miƙa mata hannu"Zo nan" matsawa ta yi kusa da ita, Ta sanya hannu biyu ta janyota zuwa jikinta "Yaushe kika farka daga bacci bamu sani ba"? Yatsina fuska ta yi"tun ɗazu na farka ina ta kiran sunayen ku babu wanda ya amsa mini, Sai da nazo sashen toilet tukunna nagan ku kuna bacci, ni kun barni a ɗaki" Harara Azeeza ta watsa ma Jamimah kafin ta soma kwaikwayon maganarta, salon jan faɗa, Hakan ba ƙaramin dariya ya basu ba. "Yanzu fa ba lokacin Yin nishaɗi bane, Yakamata Mu nemi mafita, Ni dama tun farko raina bai bani cewar Akwai wasu makullai ba, Mu ɗin dai mune makullan, Ƙofa ce kaɗai zamu gano, Saboda a jawabin da tsohuwa Tamira ta yi mata cewa ta yi Mu ɗauka cewa mu ɗin makullan Wata ƙopa ce guda ɗaya wadda zata sama mana farin ciki, To kunga anan tana nufin we're the keys da zamu buɗe ƙofar" Angel ce ta yi jawabin "Ni kuma aganina akwai makullan, Ma'anar abunda ta ke nufi, Mu zamu haɗa hannu don mu gano su, Sa'annan waɗannan munafukan tagogin da suka zuba mana ido suna kallon mu, Ina zargin ƙofar tana A cikin su," Deeja ce ta yi maganar, Kowa sai tofa albarkacin bakinsa ya ke yi kamar masu gabatar da shirin wasa ƙwaƙwalwa. "Ni ma nafi hasashen acikin su ne za'a samu ƙofa, saboda su kaɗai ne hanyoyin da zasu Iya 6ullewa wajen ɗakin nan" Acewar Hibba. "Ku dakata, Kada Mu ɗaura buri akan waɗannan Tagogin, Har yanzu fa akwai wuraren da bamu Bincika ba, Na farko akwai ƙarƙashin gadajen mu, Da kuma ɗakin tsohuwa Tamira" Yasmin ce ta yi maganar, Rubina tace"Ai babu ta yadda za'ai mu iya buɗe ɗakin Tsohuwa Tamira, tun da mu ke bamu ta6a shiga ɗakin ba, saboda kullum agarƙame ya ke kuma babu makulli ta waje balle muyi tunanin balle shi mu shiga" Gaddama ce ta 6alle atsakanin su kamar za su yi faɗa kowa Ya kafe akan tashi shawarar, Sai tada jijiyoyin wuya suke Yi, Ko yunwar cikin su basa Ji ga Jikinsu da ke ta tsami saboda rashin wanka, Hayaniyarsu ta cika ko'ina, ganin zasu hargitsa mata lissafine yasa ta dakatar dasu ta hanyar daka masu tsawa, Nan fa kowa yaja bakin shi yai shiru, Hankalinsu ya koma kanta, Miƙewa tayi tsaye kamar malami agaban ɗaliban sa, A tsanake ta soma magana. "Idan har mu ka rasa natsuwar mu to kuwa ba zamu ta6a Iya gano ƙofar nan ba! Mu kan mu hankalin mu ba a kwance ya ke ba, ta ya ya ku ke tunanin zamu Iya gano ƙofar bayan mun ƙi haɗa kan mu, mu sanya natsuwa wurin bincikota"? Ta jefa masu tambayar tana ƙare masu kallo, duk sunyi ƙuri da idanuwansu, "Maganarki gaskiya ce Angel, komai yana buƙatar kwanciyar hankali da natsuwa, Yanzu ki faɗa mana me ya kamata mu yi? Tun da kinfi mu kaifin basira" Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, Jin an wasa ta, Miƙa ma Jamimah furennin dake a hannunta tayi tare da cewa"Ruƙe mini su My little sis" Kar6ar furannin Jamimah ta yi a hannunta. "Abu na farko da yakamata Mu fara yi shine mu tsaftace jikin mu, ta hakanne zamu Ji daɗin Jikin mu brain ɗinmu ta yi fresh, mu samu natsuwar fara yin bincike na hankali, nasan kafin mu kammala Yin wanka Giants sun kawo mana Ganye, Idan mu ka Ci mu ka ƙoshi Sai mu fara wasan Ƴar 6urun 6urun kamar yarda na tsara mana, don kada ayi zargin wani abu tunda suna kallon duk wani moving ɗin mu" Tun kan ta ƙarasa yin maganar, murmushi ya bayyana akan fuskokin su, gaba ɗaya sun yi amanna da maganarta, without wasting time kowan nan su ya miƙe tsaye, ɗaya bayan ɗaya suka fuce daga cikin toilet ɗin, Ya rage saura Angel da Jamimah, Kallon Juna su ka yi atare suka sakar ma Juna murmushi"My Genie, Ƙofar da zamu gudu ku ke nema mana? Ɗaga mata kai Angel ta yi alamar eh, Dariyar Farin Ciki Jamimah ta saki har fararen haƙoranta sai da su ka bayyana, Bin ta da kallo Angel tayi dariyarta ba ƙaramin burgeta ta yi ba, sai da ta tsagaita da yin dariyar ta kuma cewa"Genie Zamu Koma Gidan ku da zama ko? Kuma can babu giants sannan ba zamu ƙara cin ganye ba ko"? Maganar da jamimah ta yi ba ƙaramin ta6a mata zuciya tayi ba, yadda suka ƙwallafa rai akan son zuwa gidan daddynta ba ƙaramin karya mata zuciya ya ke yi ba, duk idan ta tuna cewa ba lallai bane su samu damar tsira dukkan su ba koda ace sun samu ƙopar, wata'ƙil ma babu wata ƙofa tunda hasashene kawai suke yi basu da tabbaci akanta. "My genie kin yi shiru, pls ki amsa mini, inaso inji a ƙagare na ke," yadda ta ke yin maganar farin cikine tsantsa akan fuskarta, tuni idanuwan Angel sun cicciko tab da ƙwalla, sam ta kasa buɗe baki ta amsa mata. "Genie Am talking to u pls ki amsa mini, idan ba haka ba zan cinye furannin da ke a hannuna" Ta yi maganar tare da yin kamar zata cinye su, Nauyayyiyar ajiyar zuciya Angel ta sauke tare da cewa"Kada mu 6ata lokaci My little sis, Zan yi maki wanka amma kafin nan ki taya ni mu mayar da ƙasar tukunyar nan sai mu mayar da furennin" Amsa mata tayi da toh. Ba tare da ta ƙara tambayar Angel ba, Atare su ka zuƙunna jamimah ta kwantar da furennin a ƙasa, kafin su ka sanya hannu Suna ɗibar ƙasar da ke a ƙasa suna zubawa cikin tukunyar fulawar bayan sun kammala Angel ta ɗauki furennin ta tsirasu Cikin ƙasar, har ta yunƙura zata miƙa Karaf idanuwanta su ka sauka akan wasu furenni guda biyu da ke yashe ƙasa, ƙura masu ido ta yi tana kallonsu Jamimah sai magana take yi mata amma sam bata Jinta, Wani irin faɗuwar gaba taji tamkar zuciyarta zata faso ƙirjinta, a matuƙar ruɗe ta ke kallon Furennin, Ganyen jikinshi ya bushe ƙasa ya mutu, bakomai ya faɗo mata araiba face Majnoon da Unaiza da suka rasu, Zazzare idanuwanta tayi Hannunta ɗaya dafe da ƙirjinta, Nan take ta fahimci cewa furennin su ne suka mutu, Tun da basa araye that mean sauran furennin dukkan su rayukan ƴan uwansu ne akai, A hanzarce ta ɗaura eye balls ɗinta kan Dogon furen nan Muryarta Na rawa ta furta"DA...NISH!" Zungurar hannunta jamimah tayi hakan yasa tayi firgit ta dube ta Fuskarta a ɗaure tace"Kin shanyani Genie, ko ba za ki mini wankan bane? Inje inyi da kaina" Yawu ta haɗiya zuciyarta duk ba dadi, Furen Danish ya tsaya mata aranta, musamman da ta tuna da Lokacin nan da ta tarass Ganyayyakin jikinshi Sunyi baƙi sosai, tana ji aranta cewa wani mummunan abune ya faru dashi wanda silar hakan yasa furen shi canza launi, "Genie!!" jamimah ce ta ambaci sunanta da karfi ganin ta ƙara shiga zurfin tunani, Numfasawa tayi tare da ruƙo hannun Jamimah, Cikin sanyin murya tace"Am sorry Muje inyi maki wankan" Tayi maganar tare da janta zuwa gaban fanfo, Ta cika bokiti da ruwa ta ɗauko kwandon soso da sabulu, Bayan ta cire mata kayan Jikinta ta ɗaura su saman igiya, wanka ta ke yi mata amma hankalinta gaba ɗaya yana akan dogon Furen nan, A shiririce ta gama Yi mata wankan hada sumar kanta ta wanke mata, bayan ta kammala bata mayar mata da uniform ɗin jikinta ba, saboda sun yi datti, sai tace mata ta koma ɗaki ta Ta lullu6e da bargo kafin kayan da zata wanke mata su bushe saita maida su a jikinta, bayan fitar Jamimah daga Cikin toilet ɗin, komawa Angel tayi gaban tukunyar fulawar ta zuƙunna tana ƙarewa Dogon furen kallo, Yayin da zuciyarta ke harbawa da sauri da sauri, Yatsun hannayenta na kerma ta ɗaurasu kan furen tana shafa leaves ɗinsa, Har cikin zuciyarta ta ke jin kamar sumar kan Danish ta ke shafawa, A hankali ta rufe idanuwanta a yayin da ƙwaƘwalwarta ke tariyo mata Rayuwar su ta baya dashi, baza ta ta6a manta Rana ta farko da ta fara Yin tozali da kyakkyawar fuskar shi duk da bata a cikin kwanciyar hankalinta sai da gabanta ya faɗi ganin irin baiwar kyan da Allah ya yi mashi, Tana matuƙar ƙaunar danish, Jin shi ta ke yi tamkar oxygen ɗin da ta ke shaƙa don ta rayu, taya hankalinta zai kwanta? Bayan ta riga da ta gane furen Masoyinta ne, idanuwanta sun yi maraicin shi, zuciyarta sai azalzalarta ta ke akan ta nemo shi aduk inda ya ke, don taga awani hali ya ke ciki, ya idon shi ya ke? Meya faru dashi da har furen shi Ya canza Launi............" 💔PRISONERS💔 Hankalin su Yaƙi kwanciya Jin shiru Angel bata fito daga Cikin toilet ɗin da ta shiga ba, Tun suna saran fitowarta har sun fara tunanin Anya kuwa lafiya? Ita kaɗai ya rage ta fito su fara wasan Ƴar 6urun 6urun, don su gano inda ƙofar nan ta ke, tun ɗazu Giats sun kawo masu Ganye kamar kullum tare da ruwan zafi, babu wanda yasan da cewa An kawo masu abinci. Jamimah kaɗai ta rage a cikin ɗakin nasu, kwance saman gado ta lullu6e jikinta da bargonta, Jin motsin shigowar Giants, ta yi hanzarin yaye bargon data lullu6a dashi ta yi ɗaurin gaba har yana jan ƙasa saboda rashin tsawonta, Ahaka ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta ɗauko kwandon abincinsu taje ta zuƙunna agaban dining Carpet ɗinsu, ta kwashe ganyan Ta zuba masu Acikin kwandon, bayan ta kammala kwashewa, Giants suka Ɗauki farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, Zama Jamimah tayi saman carpet ɗin, ta soma ɗibar ganyen tana Ci yadda kasan ƴar akuya, Kunnuwanta har motsawa su ke yi saboda daɗin da ya yi mata. "Angel ke fa mu ke jira! Tun ɗazu kowa ya fito daga wanka, Saura ke kaɗai kin shige toilet kin garƙame ƙofa kin barmu a tsaye" Deeja ce ta yi magnar Batul tace"Ko dai ta fito daga wankan ne bamu sani ba? ta yi tambayar tare da yin saurin juyawa ta shiga ɗakinsu, Jamimah ta hango zauna tana cusa ganye abakinta, babu alamun Angel acikin ɗakin, dawowa ta yi sashen toilet ɗin tun kafin su tambayeta ko ta ganta, ta riga su cewa Na duba bata a ciki, Nan fa hankalinsu Ya ɗungunzuma Sunanta suka dinga kira shiru bata amsa masu ba, Atare suka haɗa ƙarfi wurin bugun ƙofar sai dai ga dukkan alamu An garƙame ta da Jamlock, Tamkar zasu fashe da kuka suka dingayi mata magiya akan tayi masu koda tari ne don su san cewa tana acikin toilet ɗin, saboda su samu hankalinsu ya kwanta amma shiru Angel bata tanka masu ba, kamar zasu 6alle ƙofar saboda Yadda su ke kai mata zazzafan naushi da hannayensu, a ƙarshe da suka Gaji agalabaice suka zuzzuƙunna Haɗi da jingina bayansu Jikin bango, jin motsin shigowar mutun cikin sashen Yasa suka kai idonsu ga mai shigowa, Jamimah ce ta shigo hannunta ruƙe da kwando ta ajiye masu shi a tsakiyarsu, Bakinta a cunkushe ya ke da kingin ganyen da bata ƙarasa taunewa ba ahaka ta ke yi masu magana, "Ku ci naku ne na kawo maku" kallonta kawai su ke yi, Ta zumbula bargo ajikinta sai ja da ƙasa Yake yi, jin sunyi shiru basu tanka mata ba, yasa ta haɗe girar ta"Ni ba ruwana Idan ba ku ci ba, Ku yunwa zata kama, Sannan Ina GENIE ɗina ta ke? Ko haryanzu bata fito daga wankan bane? .................... WHERE'S ANGEL❗❓ 💋PRISONERS💋 "Ita mu ke jira ta fito daga wanka, Ki koma ɗaki ki kwanta, Yanzu zamu shigo Ciki" Hibba ce ta bata amsar tambayar ta, juyawa jamimah ta yi zuwa cikin ɗakin su ta koma saman gado ta haye tare da kwantawa. "yanzu haka zamu zauna muna ta jiranta? Shiru duk irin bugun ƙofar da mu ka yi babu alamun zata buɗe mana, Anya kuwa lafiya? Ni tsoro na kada ace wani abun ne ya same ta," a cewar Deeja, hankalin su duk ba a kwance ya ke ba. "In sha Allah ma ba abun da ya same ta, Zai iya yiwuwa bacci ne ya ɗauke ta a cikin toilet ɗin ko kuma zurfin tunani ta shiga....." tunkan Batul ta rufe baki Sarah tace "wani irin bacci ne wannan mai nauyin gaske da har za'a dinga bugun ƙofa mutun bai farka ba? In kuma zurfin tunani ta shiga ai yaci ace bugun da muke ya dawo da ita hayyacin ta, Gaskiya bana tunanin haka sai dai wani abun ne na daban," kowa na tofa albarkacin bakinsa, "Yunwa nake ji, ƙwara ku zo mu haɗu Mu ci ganyen nan idan mu ka kammala sai mu ƙara jaraba Bugun ƙofar" A cewar Parveen, Atare su ka matso kusa da kwandon, Kamar akuyoyi haka suka dinga kwaso Ganyen Suna Cunkusa shi Cikin bakunan su, a tsiyace su ke taunar shi, Zuciyoyin su duk ba daɗi, damuwar rashin Angel ta hana su sakat. Suna tsaka da Cin Ganyen kunnuwan su suka soma Jiyo masu motsin buɗe ƙofar ɗakin su, A firgice su ka ɗago Suna kallon Junan su! Zuciyar su cike da fargabar Motsin buɗe ƙofan da su ke Ji, Tun da sun riga sun san An kawo masu Abinci, shiru su ka yi an rasa mai ƙwaƙƙwaran motsi A cikin su, hatta ganyen da suka cusa a Cikin bakunan su sun dakata da taunar su, babban abunda suke jima fargaba kada ace Tsohuwa Zafreen ce ta kawo masu ziyara, Tuni kowannan su Yasha Jinin Jikin shi. Garam! Su ka ji an datse ƙofar alamar wanda Ya shigo Ya fita, nauyayyiyar Ajiyar zuciya kowaccen su ta sauke, Kafin wani yai yunƙurin motsa La66ansa Muryar Jamimah ta karaɗe kunnuwan su. Wata irin razananniyar ƙara ta fasa Mai kuwar gaske, Hankulan su A tashe su ka mimmiƙe da gudun gaske suka faɗo Cikin ɗakin a sukwane Suka ci uban burki Suna faman Haki, A tsakiyar ɗakin su ka ganta Ɗaure da bargo a jikinta Sai tsalle ta ke yi, babu wanda Ya lura da me ta ke Yima Murna, Rai a6ace Parveen tace"Wannan wani irin rashin Hankali ne jamimah? Salon kawai ki kara tada mana hankulan mu shine kika fasa Ihu kamar mai ta6in Hankali"? Jin muryar Parveen Yasa ta juyo tana kallon su fuskarta ɗauke da murmushin Farin Ciki,. "An dawo mana dasu Ƴan uwan mu dole in yi farin Ciki....." Tun kan ta ƙarasa maganar Kusan atare Suka kai idanuwan su akan benan Ɗakin su! Wani irin bugu zuciyoyin su suka yi atare, Abu ne da basu Yi tsammanin shi ba, Tamkar A mafarki Haka suke ganin su, sun kasa Yarda da abunda idanuwan su suke nuna masu! A tsaye su ke cirko cirko saman Matakalar benan, su biyar babu Danish Daga ganin su babu ƙoshin Lafiya atattare dasu, Fatar Jikin su Ta yi haske Hatta Haris da ya ke da duhu fatar shi ta canza, Sun rame sun bushe kamar babu Jini a jikin su, ƙafafuwan su kansu ba adai dai su ke ba, musamman ƙafar Mubeen da ta javed rawa su ke Yi kamar zasu kasa, Sumar kansu Kuwa Duk a hargitse Dama Allah yayi su da tarin sumar kai, Ba kamar Javed Da Gabriel sai Naufal, yanayin yadda suka yi tsayuwar Ya nuna sam babu kuzari a jikin su Kamar waɗanda Aka ɗebi Naman Jikin su, Sun faɗa sun zabge........" Muryar Deeja Na rawa ta furta sunan HARIS! Mamaki ne ƙarara akan Fuskokin su, Lamarin Ya yi matuƙar ɗaure Masu Kai, Cikin karyayyiyar Murya Parveen Ta furta Sunan NAUFAL! Hannun Batul dafe da saitin Zuciyar ta ta furta Sunan JAVED!! Muryar Hannah A disashe ta ambaci Sunan MUBEEN! Cikin shessheƙar Kuka Azeeza Ta ambaci Sunan GABRIEL! kamar a mafarki haka suke ganin su, Jikin su ba ƙaramin sanyi yayi ba, zuciyoyin su sun karaya sosai, Ganin yadda ƴan uwan nasu Suka Ƙi motsawa, Bakomai ya ɗaga masu hankali ba face Ganin Yadda Haris daya fi su ƙiba Ya koma Ramamme uwa su Javed, Sun fita hayyacinsu, Daga ganin idanuwan su ba ƙaramar izaya suka sha ba, Allah kaɗai yasan Azabtarwar da su ka yi masu na tsawon watannin da su ka yi a hannun su. Tuni idanuwansu Deeja sun Cicciko tab da ƙwalla, Parveen tana kuka tace"Wlh kamar basu ba! Kamar an canza mana ƴan uwanmu! Ku kalli yadda suka rame ko magana ma basu Iya yi, Ni ina tsoron kada ace irin na unaiza su ka yi masu........" daƙyar ta ƙarasa maganar saboda kukan daya ciyota, Cikin rauni na murya Deeja Tace"Haris kaine ka koma haka? Ina Jikin ka ya ke? Javed Mubeen Naufal baku Iya magana? Meyasa ku ke kallon mu kamar Ba ku gane mu ba"? "Ba kallon su Ya kamata mu tsaya muna yi ba, Yakamata muje gare su, wata'ƙil Sun kasa yin tafiyar ne" A hankali su ke tafiya suna tunkarar su kamar sunga abun tsoro, Koda su ka ƙaraso gaban benen Atare suka dakata da yin tafiyar suna kallon su, Gwanin ban tausayi farar fatar wuyan su harda jajayen ta66una na yakushi, Wurin yayi jawur La66an su duk sun faffashe sun bushe, Gabriel hada busasshen jini saman Ƙaramin lower lip ɗinsa daya ciza launin shi pink, Fatar idanuwan su sun yi ja alamar sun yi kukan mutuwa Sakamakon wata azabtarwar da aka yi masu. Fashewa su ka yi da kuka tamkar ransu zai fita Yayin da su ke cigaba da bin ƴan uwan nasu da kallo mai nuni da tsantsar Tausayin su da su ke ji. Azeeza Ce tai Ƙoƙarin matsawa ta haura saman matakalar farko har takai ga inda Gabriel Ya ke atsaye, Faɗawa ta yi saman jikin shi tana cigaba da yin kuka, Ganin ta ta6a shi bai nuna yaji zafi ba yasa Deeja matsawa Ta rungume Haris a jikinta, Da sauri batul ta hau benan ta Ruƙo Javed ta kwantar da kanshi saman kafaɗarta, Parveen ta nufi Naufal ta janyoshi ta rungume shi sosai tana cigaba da yin kuka, Hanna ce ta ruƙo Mubeen ta haɗa shi da jikin ta, Yadda suka ƙanƙame su A jikin su suna yin kuka tamkar ran su zai fita, Sun yi kewar ƴan uwan su sosai. Matsawa saman benen Yasmin da su rubina su ka yi, A bayan su Batul dake rungume da ƴan uwansu maza suka ɗaura kawunan su, Gaba ɗaya sautin shessheƙar kukan su ce ta karaɗe Ɗakin nasu, Jamimah da sarah ne kaɗai su ka rage a tsaye bakin benan suna kallon su Idanuwan su cike tab da ƙwalla. Batul da ke ruƙe da javed taji Jikin shi ya saki gaba ɗaya ya tafi zai sulale ƙasa da sauri ta daddafe shi a haka suka Zauna saman Matakalar benen, ta tallabo fuskar shi da Hannayenta biyu "Javed! Pls ka yi mini magana Inaso insan a wani hali ku ke ciki" Daƙyar ya ke iya kallon fuskar ta, saboda raunin da idanuwan shi su ka yi mashi kamar zasu lumshe, hatta numfashin su da hucin zafi Ya ke fita. "Haris Ɗina ne ya koma haka? Inna lillahi Wa'inna ilaihirraji'un! Wlh ba zamu ta6a yafe masu ba, Allah ya isa tsakanin mu dasu Mugaye Azzalumai, Duk sun canza masu Halittarsu, ko magana ma ba su iya yi" cikin jin Ƙunar rai Deeja ta yi maganar, har lokacin bata janye haris daga jikinta ba, Kamar zata maida shi Cikinta, "Dan Allah Naufal ka buɗe baki Ka yi magana, Hankalin mu ba a kwance ya ke ba, Muna so Muji koda muryoyin ku don mu tabbatar da cewa kuna da Lafiya" parveen ce ta yi maganar, fuskar ta sharkaf da hawaye yayin da ta ɗago da kan Naufal daga saman kafaɗar ta, Bawan Allah sai bin su da ido Ya ke yi, fuskar shi Ta yi jawur saboda hasken da ke gare shi, Dama duk Cikin mazan In ka cire Danish a wurin haske sai Naufal mutun na gaba Javed ne Duk da shi ba fari bane sosai amma Baya a cikin jerin baƙaƙe Launin fatar shi Chocolate ce, Yana da tarin sumar kai, iya kafaɗar shi ta tsaya, Bayan shi sai Gabriel Kalar fatar su Kusan ɗaya Da Javed babu bambanci, Kamar za suyi hauka wurin yi masu magiya akan su yi masu magana ko sun ji sanyi acikin ran su, Gaba ɗaya sun manta da zancen Angel tun da su ka yi tozali da Ƴan uwan nasu. "Jikin su ba ƙwari, Muna ƙara masu ciwon nasu, Mun ishe su da surutu, Mu taimaka masu Su shiga cikin ɗaki su kwanta," Hibba ce ta yi maganar, Ruƙo hannun haris Deeja tayi a cikin nata, Ba ta yi tsammanin zai motsa ba sai ji ta yi ya sanya hannu ya dafa kafaɗarta, Hakan ba ƙaramin kwantar mata da hankalin ta Yayi ba, A hankali su ke yin tafiya suna tunkarar cikin ɗakin, Ruƙo hannun Naufal Parveen tayi da taimakon ta ya dinga ɗyangyasa ƙafar shi suka nufi gadon shi, Yayin da Batul ta ruƙo javed ya kwantar da kanshi saman kafaɗarta a haka suka nufi cikin daki, Ita kuma Hannah ta taimaka ma Mubeen, Ya rage saura Gabriel da Azeeza ke a rungume dashi, ta rasa ya za ta yi ta taimaka mashi su shiga ɗakin, Gaba ɗaya su Hibba sun bar bakin benen babu wanda Ya lura da Gabriel da su ka bari saboda babu shaƙuwa mai ƙarfi a tsakaninsu dashi, Sunfi Jinsu Javed shiyasa Hankalin su yafi karkata akansu. Tana so ta taimaka mashi sai dai bazata Iya ba, Saboda tsayin dake gare shi Ga ƙirar Jiki, tsawonta daƙyar Ya kai waist ɗin shi, ruƙo hannun shi ta yi a cikin nata tare da jan shi don su shiga ciki ko motsi wannan baiyi ba, hakan yasa ta fashe da kuka tare da ɗaga murya tana yi ma su batul magana "Wai bazaku zo ku taimaka mashi ba? Kun barshi shi kaɗai a tsaye" babu wanda Ya juyo ya kalle ta Hankalin su ba akanta ya ke ba, Tsagaitawa tayi da yin kukan tare da kallon fuskar shi wata irin zufa ce ke tsastsafo mashi, Ya galabaita sosai, Cikin shessheƙar kuka ta ambaci sunan shi, bai amsa mata kiran da ta yi mashi ba, Sai dai taga Ya zuƙunna saman matakalar benan Yana faman Fitar da numfashi mai ɗumi. "Ka tashi mu shiga ciki, Inaso na taimaka maka" A hankali yake bin ta da kallo fararen idanuwan shi sun canza launi zuwa ja, daga gani ba ƙaramin jin jiki ya ke yi ba, azeeza sarkin tausayi hada sanya Ƙasar rigarta saman fuskar shi tana share mashi gumin da ke tsastsafowa, acikin zuciyarta ba ta ji dadin yarda su Batul suka manta da zancen shi ba, Shi kaɗai suka ware, marairaice mashi fuska tayi "Pls ka tashi mu je ka kwanta, baka da lafiya fa, Nasan baka jin dadin Jikin ka,......" tunkan ta ƙarasa maganar Gabriel ya yunƙura ya miƙe, Daurewa kawai ya ke yi don ba ƙaramin jiri yake gani acikin idanuwan shi, ƙoƙarin Yin tafiya yayi Ƙafarshi ta Hagu taƙi bashi haɗin kai, Gaba ɗaya Ya tafi zai kife ƙasa, Azeeza ta fasa uwar ƙara haɗi da ambaton sunan shi, hakan ne ya jawo hankalin su Parveen ga kallonta A lokacin har sun taimakama su Haris sun kwanta saman gadan su, Da gudun gaske suka nufi Gabriel dake ƙoƙarin faɗuwa, Da ya ke Namiji ne Allah yayi shi da ƙarfi bai bari Ya faɗi ƙasa ba, Handrail ɗin benan Ya dafe da hannun shi, Sai faman Huci ya ke fitarwa, Nannaɗaɗar sumar gaban goshin sa duk ta rufe idon shi, Koda su parveen suka ƙaraso ganin ya dafe Hannun benan yasa suka sauke ajiyar zuciya, Azeeza kamar jira ta ke yi su ƙaraso ta dinga surfa masu bala'e akan sun tafi sun bar ta da shi, bayan sun san ita ƙarama ce, da ace ya faɗi kasa kanshi ya bugu me suke tunanin zai biyo baya, Faɗa sosai ta rufe su dashi, ta inda take shiga bata nan take fita ba, sai faman tada jijiyoyin wuyanta take yi duk akan Gabriel. "Allah ya huci zuciyarki Azeeza bada son ranmu muka ƙyale shi ba, Hankalin mu ba a kwance Ya ke ba, Amma yanzu kiyi haƙuri, zamu shiga dashi Ciki" Fuskar Yasmin a hautsine tayi mata maganar, ɗaure fuska azeeza tayi hada ruƙe qugu tana binsu da kallo. Parveen da Yasmin ne suka taimaka wurin ruƙo Gabriel Suka nufi Cikin ɗakin dashi, agaban gadon shi suka sake shi ya hau ya kwanta, Daga gefen shi Azeeza ta hau ta kwanta tana ƙare mashi kallo mai nuni da tsantsar ƙaunar shi kewar shi da Tausayin shi. a 6angaren Haris Deeja ce zaune saman gadon shi, Eve da yasmin suna zazzaune gefen gadon shi, Sai sannu su ke yi mashi, Sam ya kasa amsa masu, Sai dai yabi su da ido, Javed Yana a kwance saman gadon shi, Batul da Sarah ne Zaune gefe da gefen mattress ɗinshi, Ji su ke kamar su ɗauke masu ciwon Jikin su saboda tsabar tausayinsu da su ke Ji, Idan muka koma 6angaren Naufal Shima Yana kwance Ya lumshe idanuwan shi, Parveen da Hibba suna a zaune saman gadon nashi, suna yi mashi sannu. A yayin da Hannah da Rubina suke akan gadon Mubeen, hakan ba ƙaramin sanyaya zuciyoyin ƴan uwan nasu yayi ba, Ganin yadda suka nuna damuwa akan su, "Yanzu ya zamuyi? Ko abinci babu da zamu Iya basu nasan dole suna jin yunwa," parveen ce ta yi maganar, "Ko ruwa ne mu fara basu Mu ga idan zasu sha" a cewar Batul, Jin suna maganar ruwa yasa Jamimah ta nufi ƙarƙashin gadon batul ta lalubo robobin ruwa taje ta miƙa ma Deeja, Bayan ta kar6a taje ta miƙa ma parveen kafin ta nufi Batul ta bata ɗaya" da sauri ta koma ta ɗauko sauran robobin ruwan guda biyu Ta kaima Hanna ɗaya, sannan ta nufi gadon Gabriel Ta miƙa ma Azeeza, Hannu tasa ta kar6i robar ruwan tare da miƙewa zaune ta cire murfin kallon shi tayi, Still idanuwan shi Na akan fuskarta, "Ruwa ne ka tashi ka sha" tayi maganar tana nuna mashi robar ruwan, Da ƙyar ya yunƙura Ya tada kanshi saman pillow, Yatsun hannun shi sai kerma suke Yi ya gaza iya ruƙe robar, hakan yasa ta kafa mashi ita saitin bakin shi ya soma kur6ar ruwan Yana bi ta makoshinsa, A tsanake Azeeza ta ke kallon fuskarshi Ya canza sosai, kamar ba Gabriel ɗin da ta sani ba. Bayan kowannan su Yasha ruwan, Jamimah ta tattara robobin ta maida su ƙarƙashin gado ta killace su, Har yanzu babu wanda Ya tuna da Angel a cikin su, bacci ne ya fara ɗaukar su Javed, cikin ƙanƙanin lokaci baccin yai awon gaba dasu, ganin sun samu bacci yasa hankalin su Batul ya ƙara kwanciya. Kamar sun samu tv haka suka tasa su agaba suna kallon su yayin da su ke yin bacci, Farin Cikin su ragagge ne, Abu Biyu ya tsaya masu aransu, Na farko Meyasa ba a dawo da Danish ba, Bayan An riga tafiya dashi? Na biyu me aka yi masu na tsawon watannin nan? basu da amsar tambayoyinsu. "Allah sarki Danish ɗinmu shi ba'a dawo mana dashi ba, Na yi tsammanin dukan su zamu gansu" Batul ce tayi maganar, Deeja tace"saboda mugun nufin su akan shi sunƙi dawo mana da ɗan uwanmu, Nafi damuwa dashi saboda halin da aka tafi dashi, " Da alama ransu ya 6aci sosai na rashin dawo masu da Danish, tsawon Awanni Sunyi zugudum babu mai Magana a cikinsu, Wuraren marece Mubeen Ya farka daga bacci, A matuƙar firgice ya zabura ya miƙe zaune Yana haki Gaba ɗaya idanuwan su akan fuskar shi, Kafin su yi yunƙurin tunkarar shi Ya duro daga saman gadon shi kafar shi kamar zata 6alle A haka ya dinga janta ya nufi Sashen toilet ɗinsu, Da gudu Hannah dasu Yasmin suka bi bayan shi, A cikin toilet suka tarar dashi Ya zuƙunna gaban fanfo Yana kwara amai, Wani irin Farin abu mai yauƙi yauƙi ya ke fitowa daga bakin shi har ta hancin shi ya dinga gangarowa, Wa'iya zubillahi! Zuciyoyin su sun karaya da ganin yadda Mubeen ke kwara aman fargabar su kada ya mutu kamar yadda unaiza ta tafi tabarsu, Tuna wannan yasa hawaye wanke fuskokinsu, A gaban shi suka zuƙunna suna kallon fuskar shi, Sai nishi yake yi Yana jan numfashi a wahalce, "Mubeen dan Allah ka jure, bamu so wani abu ya same ka, Kaga Muna ƙaunar ka sosai" a hankali ya ɗago da idon shi kan fuskar Parveen da tayi maganar, Girgiza kanshi ya yi yana faman cizon la66an shi ya soma magana "Kada ku tada hankalin ku akaina, lafiyata qalou," tun daga kan yarda yai maganar zai ƙara tabbatar maka da Babu lafiya a jikin shi, ya faɗi hakan ne kawai don ya kwantar masu hankalin su, "Wlh baka da lafiya Mubeen, Kalli yadda idanuwan ka suka canza launi, kamar ba mubeen ɗin mu ba", murmushi ya ƙakalo akan fuskar shi Yayin da ya ke kallon Hanna da ta yi maganar, "Nifa lafiyata qalou, Nagode da kulawar ku agare ni, nayi missing ɗinku sosai," Cikin sanyin murya ya furta hakan, A hanzarce Batul ta miƙa hannu ta kunna fanfo ruwa ya soma zubowa, tarba tafin hannayen ta tayi Ruwa ya taru a cikinsu ta wanke mashi fuskar shi tare da zuba mashi ruwan a bakin shi Ya kuskure shi, Bayan ta kammala ta ruƙo hannun shi "Mu koma ɗaki Mubeen" Sai da suka taimaka mashi tukunna Ya iya miƙewa, fitowa su ka yi daga Cikin toilet zuwa ɗaki, A saman gadon Shi Ya kwanta Yana faman sauke ajiyar zuciya, kewaye da gadon shi suka tsaya suna tottafa mashi addu'o'i, hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mashi ba, bayan sun samu komai ya lafa suna shirin komawa su zauna Kwatsam Gabriel Ya farka Hananyen shi biyu daddafe da kanshi Ya fasa wata irin gigitacciyar ƙara da ta janyo hankulan su Gare shi, Jikin shi sai kerma yake yi musamman la66ansa, Sambatu ya ke yi na fitar hayyaci, A hankali Su ka soma tafiya suna tunkarar gadon shi, A kewaye da gadon shi suka ja burki suna ambaton sunan shi Muryoyin su a tsorace "Gabriel! Meke damun ka? Faɗa mana ina ke yi maka ciwo," Shiru bai tanka masu ba, Hankalin Azeeza duk yafi tashi don tuni tafara sharar ƙwalla, tsananin tausayin shi ne ya kama su, musamman da ya daddafe kanshi sai ya tuna masu da Danish, duk idan ciwon shi ya tashi haka ya ke yi masu ya dinga fasa ƙara, "Gabriel are u okey? Kan ka yana maka ciwo ne"? Azeeza ce ta ke tambayar shi, Deeja tace "Ku ɗan jira in jaraba yi mashi Karatu kamar yarda Angel ta ta6a Yima Danish wata'ƙil shima yaji sauƙi, ta ƙarasa maganar tare da hawa saman gadon ta matsa kusa dashi ta tallabo kanshi da yatsun hannayenta tare da ɗago dashi, Saitin kunnan shi na dama ta kai bakinta, Kafin a tsanake ta soma Yi mashi karatun qur'ani, surorin da ta haddace akanta, fatiha, iklas, Falak da nasi, da wasu ayoyi irinsu Ayatul kursiyyu, Amanar rasulu da sauransu, A nutse Deeja take karanta mashi su cikin kunnan shi, su Parveen duk suna a tsaye bakin gadon suna kallon shi azeeza tana zaune daga gefen shi, ga dukkan alamu natsuwa ta fara shigar shi, don tun da ta fara Jikin shi ya daina kakarwa, natsuwa ta fara shigar shi, A hankali ta zame Hannayenta daga saman kanshi, "Da sauƙi jikin naka"? Tayi maganar tana kallon fuskar shi, sai faman lumshe idanuwan shi ya ke yi, daƙyar ya iya buɗe baki Ya amsa mata da cewa "Am ok, Ina fata mun same ku lafiya," har suna haɗa baki wurin furta mashi "Muna Lafiya" parveen tace "faɗa mana su wanene mu, don ni ban yarda ka dawo dai dai ba," A hankali ya ke kallon fuskokin su ɗaya bayan ɗaya Ya soma faɗa masu sunayen su Hannah Hibba Deeja, Parveen, Eve, Yasmin, Batool, Rubina, Aziza, Sarah, Jamima......." tunkan ya rufe baki yaga suna ta murna ganin ya dawo dai dai, haƙiƙa Yaji daɗin kulawar su gare shi, Sai dai abu ɗaya daya faɗar mashi da gaba rashin mutun ɗaya acikin su, Yarinyar da ya ƙwallafa rai akan son ganinta, don su dasa daga inda su ka tsaya "Where's ANGEL"? Ras gabansu Ya faɗi Jin tambayar da ya yi masu, Nan fa suka fara kallon kallon a tsakanin su fuskokinsu ɗauke da matsananciyar damuwa "Inna lillahi..! Mun manta da Angel! Tun ɗazu da safe ta shiga toilet ta datse, Ba irin bugun da bamuyi ma ƙofar ba amma ta ƙi buɗewa, bamusan me ta ke yi a ciki ba" Muryar Haris ce ya janyo hankalin su ga kallon shi, Farkawar shi kenan daga bacci Yana ji suna zancen Babu Angel, Jikin shi A raunane Ya yunƙura Ya miƙe zaune, Da sauri Deeja ta nufi gadon shi ta haye sama ta zauna tana kallon shi, "Haris Sannu Ya jikin Naka? Ina fata ba inda ke yi maka ciwo" murmushi ya sakar mata yayin da ya ke bin ta da kallo, daga gani ba ƙaramar kewar ta yayi ba, "Deeja lafiyata qalou, Jiki na da sauƙi, Naji ana zancen babu Angel me ya faru da ita? Ko sun zo sun ɗauke ta ne"? Girgiza mashi kai tayi alamar a'a "Ɗazu da safe ta shiga toilet yin wanka, bamusan meya faru da ita ba, mun jira ta buɗe mana ƙofa amma shiru, mun yi iyakar bakin ƙoƙarin mu wurin ganin mun 6alle ƙofar amma taƙi buɗuwa,' deeja na kai ƙarshen maganar ta, Batul ta jefa masu tambaya "Haris Ina Danish ɗinmu"! Ɗago wa yai da idon shi tare da kallonta, Mamaki ne ya bayyana akan fuskar shi "Kamar batul nake gani! Yaushe aka dawo da ke?" Murmushi ta sakar mashi tare da cewa "Tuntuni na dawo, Na yi kewar ku sosai," Jinjina kan shi ya yi kafin yaci gaba da magana "Bansan inda Danish ya ke ba, saboda ba'a tare mu ke dashi ba, tsawon lokacin nan bamu ta6a Yin tozali da shi ba," Idon Gabriel akan Batul Sai yanzu da ya dawo hayyacin shi ya gane ta, Yasan cewa ƴar uwar su ce da suke ta nema, kuma itace Yarinyar da ya gani a kwanakin baya saman Third floor Tana gudun ceton Rai! Baisan ya akai ta dawo ba, Sai dai yaji daɗin ganin ta da ranta da lafiyarta. "Ƴar uwar mu ce Batul, nasan baka santa ba" Azeeza ce tayi mashi magana ganin yana kallonta, Numfasawa ya yi tare da saukowa daga saman gadon kamar zai kife kasa saboda rashin ƙwarin Jikin shi "Ina zaka je"? Atare su Hibba su ka haɗa baki wurin yi mashi magana "Inason ganin Angel, ku nuna mini ƙopar toilet ɗin da ta shiga, zan yi ƙoƙari in 6alle ta" "Kana fama da kanka Gabriel taya zaka iya 6alle ƙofa, tafiyar ma daƙyar ka ke yinta, Pls Ka koma ka zauna bazamu bari ka Ƙara raunata kan ka ba, " Hannah ce tayi maganar tare da ruƙo hannun shi, ba don ya so ba ya koma ya zauna daga gefen gadon shi. Hankalinsu Ba ƙaramin tashi yai ba, sun gama murnar dawowar su Haris damuwar rashin Angel ta hana su sakat ga dare har ya gabato amma babu ita, Jamimah sai kuka take yi masu akan Su Je su buɗe ƙofa su ɗauko Mata Genie ɗinta Idan suna son zaman Lafiya, Sun saba atare su ke kwaciya bacci, kwanakin nan ita ke yi masu shimfiɗa a saman floor. Komawa Cikin sashen toilet ɗin su ka yi, Don su ƙara jaraba ƙarfi ko sun samu ƙofar ta buɗe masu, Gabriel da haris sun so su taimaka masu Wurin buɗe ƙofar sai dai sun hanasu yin hakan saboda babu ƙoshin lafiya a jikin su. Kukan Jamimah Ya karaɗe Cikin ɗakin su, Hatta Javed da Naufal sai da su ka farka daga bacci saboda sautin kukanta daya cika kunnuwan su, Taƙi samun wuri ta zauna, Ga uban bargon data zumbula a jikinta, Angel ta rufe mata uniform a cikin toilet shiyasa take ta yin zarya da bargo, Kanta har ya fara sara mata, Gabriel ne ya miƙa mata hannu tare da ambaton sunanta, Kamar jira ta ke yi da gudu ta nufi gadon shi ya ɗauketa saman jikin shi yana lallashinta, cikin shesshesƙar kuka take ce mashi "Dan Allah kaje ka ɗauko mini Genie ɗita, tun ɗazu tana a cikin toilet, ƙofa ta rufe da ita sunƙi su taimaka mata, Uniform ɗina ma suna a ciki itace ta yi mini wanka tace zata Wanke mani su, in sun bushe sai in saka su a jiki na...." duk ta cika shi da surutun ta, shi kanshi hankalin shi ba a kwance ya ke ba, Kowa da abunda yake saƙawa a ranshi dangane da rashin Angel gani su ke kamar fa an ɗauke ta shiyasa taƙi buɗe ƙofar, saboda babu alamun mutun acikin toilet ɗin, Ko motsi wannan baka Ji. Ina Angel ta shiga meya faru da ita? abunda ya faru Lokacin da Angel ta zuƙunna a gaban tukunyar fulawar nan, Hankalinta ba'a kwance ya ke ba, tun da ta fahimci Furen Danish, Azalzalar da zuciyarta ke yi mata akan taje ta nemo shi taga a wani hali ya ke ciki shi yaja hankalinta, miƙewa tayi a fujajen ta nufi glass window ɗin nan ta sanya Hannu ta sauke glass ɗin ta dire shi ƙasa Jikin bango, duk da irin tsoron da take ji hakan baisa ta fasa ƙudirinta ba, Bayan ta janyo bokiti ta haye sama sai da ta fara Ambaton Bismillahi da kyakkyawar niyya tare da wasu addu'o'in neman tsari masu ƙarfi Kafin ta daddage ta haura tagar ta duro ta bayanta, tsananin tsoro ne ya kamata da firgici Amma a haka ta daure ta cije saboda idanuwan ta a makance suke bata ji bata gani burinta Kawai ta gano inda Danish ɗinta Ya ke, Cike da ƙwarin gwiwa ta miƙi doguwar hanyar nan wadda zata sada ta da ground floor ɗin Gidan kurkukun, Tana tafiya tana ambaton sunan Allah, Duk addu'ar da tazo mata a cikin bakin ta karanta ta take yi, hada ɗan gudu gudun ta wurin yin tafiyar, lokacin da ta kawo ƙarshen hanyar ta faɗo ta cikin babban Filin dake a kewaye da waɗannan Dogayen benayen, Ras taji gabanta ya faɗi tunawa da abunda ya faru da ita a rana ta farko da ta fara zuwa wurin, ba zata ta6a manta irin baƙar wahalar da tasha ba, A tsananin tsoroce take ƙare ma benayen kallo don ta ga ko zasu motsa kamar yarda su ka yi mata aranar farko, ganin sunƙi Motsawa yasa ta soma tafiya Cikin sanɗa tana tunkarar su, shiru baka jin hayaniyar komai, ita kaɗai kwallin ƙwal kamar ba mutane A gidan Kurkukun. Har ta kai bakin benan ta soma Jin sautin Wata shaƙaƙƙiyar murya tana ambaton sunanta, A gigice ta juya tana kallon bayanta don taga wanene Sai dai bata ga komai ba, Sautin dariya mai kama da haniniyar Doki ta dinga Ji a cikin kunnuwan ta, Tuni zufa ta wanke fuskarta sharkaf, Can kuma ta dinga jin kukan jarirai Enyaaa enyeeh, Da sauri ta toshe kunnuwan ta da tafin hannuwan ta, bugun zuciyar ta na ci gaba da hauhawa, Jikin ta ya hau rawa, Saboda taurin kai irin nata a haka ta soma hawa benen la66anta na kerma wurin ambaton sunan Allah, ba zato ba tsammani taji Matattakalar Benan ta soma Motsawa, hakan ya sa ta daddage ta watsa da gudu tana haura matattakalar Yayin da benan ke mayar da ita baya har tuntu6e take yi ta kife Ƙasa, Staircases ɗin suka dinga janyeta suna mayar da ita baya kamar zasu saukar da ita daga saman gadon, Cikin zafin nama ta ɗago da kanta tare da miƙewa ta dinga gudu zufa na bin jikinta har sai da Allah ya bata nasarar kaiwa ga Second Floor, Ta ƙarfi ta buga tsalle ta haye sama tana faman Haki, sumar kanta duk ta rufe fuskarta, Ƴan hanjin Cikinta sai kaɗawa su ke Yi, A hankali ta yunƙura ta miƙe tsaye tare da juyawa tana kallon benan, Wani abun mamaki Gaba ɗaya ya daina motsawa sauke ajiyar zuciya ta yi, Angel da kasada taci gaba da tafiya Saman hawa na biyu, Sai faman baza ido ta ke yi tana ƙarewa ginin kallo, tsarin shi yadda kasan Ƴan hanjin Cikin mutun saboda kwana kwanar da ke gare shi, A dai dai Bakin wani corridor taci burki tana leƙa Ciki, Ɗakuna ta hango A jere Kusan guda Huɗu biyu suna fuskantar biyu, Ƙofofin su a rufe su ke sai dai bata da tabbacin Ko an sanya masu Kuba. "Ya Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abun cutarwa, Ya Allah ka haɗa ni da abunda nazo nemo Cikin sauƙi ba tare da nasha wahala ba," acikin zuciyar ta take ambaton hakan, ɗaga kafarta tayi tare da nufar Ƙofofin, Hannu ta kai ta ɗan ta6a Jikin ƙofar farko ba zato ba tsammani taji ƙofar tana lilo alamar a buɗe ta ke, Sai da ta fara karanta addu'ar neman tsari ba tare da Jin tsoro ba, ta faɗa Ɗaya daga Cikin ƙofofin, wurga ƙafar ta ke da wuya wani uban wari ya daki hancin ta, Idanuwan ta a zazzare ta ke ƙare ma Ɗakin Kallo, tamkar Igiyar Shanya ce kewaye A cikin shi ta kowane 6angare, babban abunda yayi mugun ɗaga mata hankali Gangar Jikin Matasan Ƴan mata ta gani da maza Wanda basu haura shekarun su Batul ba, zindir babu kaya a jikin su, An ɗaure wuyan su sagale Jikin Igiyoyin nan kamar kayan wanki da alama Sun gama amfani dasu, wasu An cire nonuwan su,wasu kuma an cire gaban su,Wasu Idanuwan su aka kwalkwale Yayin da wasu kayan Cikin su aka wawake, Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un!! Wata irin narkakkiyar zufa ce ta wanke ko'ina na jikinta da ke ta yin kerma kamar wadda ake kada ma mazari, duk ta bi ta furgice ganin komai ta ke yi tamkar a mafarki, Hannayen ta daddafe da kanta cikin fitar hayyaci ta fito daga Cikin ɗakin, Maimakon tayi reverse ta koma Inda ta fito sai ta ƙara gaba saboda gushewar da hankalin ta yayi, A gigice Ta fito daga ɗakin Wani irin jiri take gani a cikin idanuwan ta, Hannunta dafe da ƙirjinta Zuciyar ta sai tashi take yi ga wani irin zazza6i da ya lullu6eta. A bakin Ƙofar ɗaki na biyu ta faɗa tana faman haki, Karaf idanuwan ta suka sauka Akan Giants da ke gudanar da aikin su na Theatre, gadaje ne sunfi talatin Cikin Ɗakin mai faɗin gaske, kowani gado Yana ɗauke da mutun kwance saman shi, Sun fafe cikin su suna ɗibar kayan cikin nasu tare da ɗaura su saman table ɗin da ke a gefen su, A matuƙar razane ta juya tana neman hanyar da zata bi ta Fitar da ita daga Cikin Corridor ɗin, Allah Yaso basu lura da ita ba babu wanda Ya ganta don gaba daya hankulan su na akan aikin da suke kuma basu zaton wata matsala , Watsawa ta yi da gudu Ita kanta batasan inda take tunkara ba Sunan Allah kaɗai ta ke iya ambato a cikin bakinta, adaidai saitin wata ƙopa ta soma jin Wata kakkausar murya tana magana da wani irin gur6ataccen yare mara daɗin ji, A hautsine takai idonta Ƙofar Dogon labule ne launin Ja ya rufe ta, Yatsun hannunta na kerma ta ɗan yaye labulan. Babban ɗaki ne mai girman gaske kamar palour, komai Na cikin shi Red & black Colour ne, bangon ɗakin Zanunnukan kan ƙwarangwal ne dana kunama, da na wasu halittu masu dogon harshe Da zaƙo zaƙon akaifu irin na shaiɗanu, Zanen su ne ta ko'ina gwanin ban tsoro, Mutane ta gani a jere sunkai su Talatin Kowannan su na sanye Cikin Jajayen dogayen riguna masu huluna, hannuwan su ruƙe da ƙoƙuna masu ɗauke da jini, daga tsakiyar su wasu tiƙa tiƙan mutane ne kusan su Shidda, Yadda kasan Irin malaman Majami'u na ƙasar India, Tumbur babu Kaya ajikin su, Sae dai wani ƙaramin Jan ƙyalle da su ka ɗaure ƙugunan su dashi, ga wani uban tumbi da suka tara, Jikin su bulbul ansha Jini An ƙoshi, Jan fentin da ke saman fuskokin su Ya rufe ainihin Suffar su sun koma kamar dodonni, Sun kewaye wani Dodon tsafi dake a zaune saman armchair, Wata irin halitta mai matuk'ar muni miyau sai zalalowa yake yi daga bakin shi, Zir Jikin shi babu kaya sai uwar yanar da ta nannaɗe gangar Jikin shi tayi mashi tamkar sutura. A kowace kusurwa ta cikin ɗakin jajayen ƙwaryoyi ne a jere an rufe su da faifai, Ga wasu ƙananun Yara da basu haura 7 years ba mata zuƙunne saman gwiwowin su babu kaya a jikin su, gabansu ca6a ca6a da jini, daga gani amfani aka yi dasu. Wani ikon Allah duk tashin hankalin da idanuwanta su ka yi tozali dashi baisa ta kurma ihu ba saida taga waɗannan yaran ƙananu tukunna sautin muryar ta ya dawo har ta ƙware Baki zata Kurma Ihu ba zato ba tsammani taji saukar hannun mutun saman bakinta, sosai Ya toshe mata baki! Batasan wanene ba hakan yasa ta zazzare idanuwan ta waɗanda su ka kaɗa su ka yi jawur dasu, tsoro da firgici ne acikin ƙwayar idonta 💋PRISONERS💋 Gaba ɗaya taji an ɗauke ta, Batasan Ina aka dosa da ita ba saboda suman da tayi. Tsawon mintuna, Kafin taji saukar ruwa saman fuskarta wanda ya yi silar farfaɗowar ta, Sambatu ta soma yi tana ambaton Danish nifa danish ɗina nazo nema, wlh bada niyar leƙen asiri na fito ba, ni banga komai ba, dan Allah a maidani Cikin ƴan uwana, Kada acutar dani, tsautsayi da ƙaddara ne suka fito dani, kuma bazan Ƙara ba......." kamar daga sama taji an ambaci sunanta da wata irin murya mai sanyin gaske daga ji mamallakinta ba ƙaramin mutun ba ne. "UNAISERH ZAHEER TAJUDDEN"! kai tsaye kiran Ya daki dodon kunnanta, idanuwan ta dake a cike tab da ƙwalla sun mata nauyi ta buɗe tana Kallon saman ceiling ɗin da ta ke fuskanta, Fitilu ta gani guda Ukku suna Lilo, Sune suka haskaka cikin ɗakin da take a kwance saman fata mai gashi gashi a jikinta, gaban ta na faɗuwa ta zabura ta miƙe zaune tana faman bin ko'ina na ɗakin da kallo A ƙoƙarinta nata ga wanene ke yi mata magana. "Ina a bayanki!" Jin hakan yasa ta yunƙura ta miƙe tare da juyawa tana kallon shi, Giant ne Sanye cikin shigar su ta baƙaƙen Kaya ya goya hannayen shi saman faffaɗan ƙirjin shi, Waro ido waje ta yi Kafin ta zabura ta watsa da gudu da niyyar ta nemi ƙofar da zata gudu, Sai dai har ta gama kewaye ɗakin babu ƙopa, A jikin bango ta manne kamar zata shige mashi idonta akan shi yayin da yake tunkarota, ta dinga girgiza mashi kai muryarta A dabarbarce ta ke yi mashi magana "Wlh kada ka kuskura ka ta6a ni, idan ba haka ba zan ƙona ka da ayar Allah, Mugaye kawai ai ni bansan na fito daga inda aka killace mu ba, kuma ni Danish Na fito nema ba wani abu ba....." a gigice ta ke yi mashi magana, Gani ta ke kamar zai rikiɗa ya koma wannan halittar da Unaizah ta bata labari, tuni hawaye sun wanke fuskar ta, Har ta fara tunanin yadda zata koma Idan Ya kusance ta kamar dai yadda aka yiwa unaizah ta mutu. Duk haukan nan da ta ke yi bai tanka mata ba, Yayi tsaye a gabanta Kamar yana ƙare mata kallo ne. "La'ila ha'illa anta subhanaka inni kuntu minazzalimin" A saman jikin shi ta dinga tottofa mashi addu'ar da ta ke karantowa. Hakan yasa shi Sakin dariya sautin ya karaɗe Cikin ɗakin da su ke a ciki, A matuƙar ruɗe take kallon Giant ɗin Jin yana dariya, ita dai a iya saninta Giant basa magana balle har suyi dariya, bakomai Ya faɗo mata a cikin ranta ba fa ce Giant ɗin da ya taimaki Batul ya dawo da ita cikin su, nan take ranta ya fara raya mata cewa ko dai shine!? Tun daga ƙasa har sama take kallon shi, Muryarta na rawa tace "wah...nene kai"? A tsanake ya soma magana "ɗan adam ne ni, sai dai mun banbanta da juna saboda ni Giant ne ba cikakken mutun ba" Mamaki ne ƙarara akan fuskar Angel. "Ki kwantar da hankalin ki, ni bamai cutarwa bane, Mai taimako ne, kada ki yi tsammanin nima mugu ne kamar sauran," wannan maganar da yayi ce tasa hankalin ta ya ɗan kwanta, har cikin ranta taji ta yarda dashi sai dai ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba, taya akai Ya kawota nan, Sannan Yake yi mata magana? Anya kuwa Giant ne? Ko dai ɗan leƙen asiri ne Ya shigo masu kurkukun......." "Ba ɗan leƙen asiri bane, nima Ma'aikaci ne na gidan kurkukun ƙaddara kamar yarda na faɗa maki Am A Giant! " ya ƙara jaddada mata maganar shi, Aruɗe ta kalle shi jin ya bata amsar tambayar da ta ke acikin zancen zucinta. "Wanene kai? Meyasa ka kawo ni nan? Kuma meyasa kake magana bayan ni a iya sanina Giant basa magana" Juya mata Baya yayi taku ɗaya zuwa uku Kafin Ya dawo gare ta, rumfa yayi mata Da faffaɗan ƙirjin shi Duk tabi tasha Jinin Jikinta "Tambaya ta farko, sunana SALSABEEL! Tambaya ta biyu na kawo ki ɗakin nan ne saboda in isar da saƙona! Tambaya ta ƙarshe Giant Suna magana ba kurame bane, A tsakanin su da prisoners ne ke basa magana, Idan kika natsu zan fayyace maki komai, ki bani haɗin kai saboda bani da isasshen lokacin da zan 6ata, Mintuna talatin suka rage man kafin garkuwar sautin dana sanya ta karye," Jinjina kai Angel tayi alamar gamsuwa da bayanin shi. "Da ace tuntuni mun haɗu da juna, da baku kai tsawon lokacin nan a gidan kurkukun nan ba, " Sakin Jiki ta yi jin abunda yace, har ta buɗe baki zatayi magana Ya dakatar da ita "Kada ki katse ni, Idan na kammala magana daga bisani za ki Iya jera min tambayoyin ki idan lokaci bai ƙure mana ba" jinjina mashi kai tayi alamar taji maganar shi. "Ni da mahaifiyata bamu da burin daya wuce mu kawo ƙarshen Zuluncin da ake aikatawa agidan kurkukun nan, Dukkan mu bada son ran mu muka kasance ma'aikata A cikin shi ba, mun miƙa wuya ne saboda fansar da mu ke so mu ɗauka da kuma kawo ƙarshen Matsafan dake a cikinsa, Mun jima da wannan ƙudurin acikin zuciyoyin mu sai dai ƙarfin mu bai kai mu iya ja da Shuwagabannin dake mulkar kurkukun ƙaddara ba, Saboda shaiɗanun mutane ne masu haɗarin gaske Mai iya ja dasu Sai Allah ba dai mutun ba" Angel ta natsu tana sauraron shi, ko motsi bata yi, Har yanzu bata fahimci kan zancen shi ba, gashi ya hana ta tambaye shi. Cigaba da magana yayi "Nasan har yanzu baki fahimci inda zancena ya dosa ba, " dafe bangon da ta jingina dashi yayi da tafin hannun shi, "Tun kafin zuwan ki kurkukun nan munsan komai dangane da rayuwar ki! kaifin basirar ki da hankalin ki shiyasa muka kwaɗaitu da son zuwan ki tun da labari yazo gare mu na cewa kece ƙaddarar Prison! ," gaba ɗaya Ya gama ruɗar da ita, Duk tabi ta kakkame Jikinta. "Ma'anar hakan shine ke kaɗaice zaki iya tarwatsa tarihin kurkukun ƙaddara! Kamar yadda yazo mana a allon tsafin mu, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba nida mahaifiyata TSOHUWA TAMIRA!!!!" ƙara zare idanuwan ta tayi akan mask ɗin da ya 6oye ainihin fuskarshi, Al'ajabi ne ya kamata Jin ya ambaci sunan tsohuwa tamira a matsayin mahafiyar shi! "Ƙaddara kala Biyu ce, Mai kyau da mara kyau, A hasashen matsafa Idan suka killace ki a hannun su zaki zamar masu kyakkyawar ƙaddara, Amma idan suka bar ki a cikin Jama'a kina yawo shine zaki zamar masu ƙaddara mara kyau......." Kasa haƙura ta yi hakan yasa ta katse mashi maganar shi da cewa "Taya akai na zama ƙaddarar su"? Ta jefa mashi tambayar tana kallon shi da zararrun idanu. "Kin manta me na faɗa maki?" Ko da ya ke halin ki ne Iya tambaya kamar ƴar jarida shiyasa kika gaza haƙura har saida kika katse mini magana ta" muryarta a dabarbarce tace "Bazan ƙara ba" Gyaɗa kai Ya yi kafin ya ɗaura da cewa "rayuwarku tana a cikin haɗari mai munin gaske, musamman ɗan uwanki Danish"! Gabanta ne ya faɗi jin ya ambaci sunan Abun ƙaunar ta. "Kasancewar shi garkuwar kurkukun ƙaddara, Matsafa sun ƙwallafa rai akan shi, Saboda shi ɗin tamkar wata nasara ce agare su, idan dashi baza a ta6a Iya rushe Ginin kurkukun ƙaddara ba, su kansu matsafan baza a iya cin nasara akan su ba, shiyasa suka bashi babban matsayi Na Prison Shield! A halin yanzu da na ke yi maki Magana, Ɗan uwanki Danish Ba cikakken Mutun bane, He's a dangerous Giant! Sun riga da sun bashi horon zama Giant duk wani zunubi da kika sani mai girma a duniyar nan na rashin imani da tausayi sun koya mashi, sun riga sun yi Transforming ɗin shi into a Giant, Horo Ne wanda ba mutane zalla suke basu shi ba harda baƙaƙen shaiɗanun aljanu, Harshe na bazai Iya furta maki abubuwan da su ka yi mashi ba da kuma wanda su ka sashi ya aikata kafin su tabbatar da komawar shi Giant........" Bai ƙarasa maganar ba ganin ta sulale daga jikin bangon zuwa ƙasa, zuciyarta ba ƙaramin karaya tayi ba, idanuwanta suka cicciko tab da ƙwalla, bakomai take hangowa ba face fuskar Danish ɗinta! Yanzu shikenan Sun canza shi zuwa Giant, Sun 6ata mashi rayuwar shi sun gur6ata mashi tunanin shi. Zuƙunnawa Salsabeel Yayi agabanta Saman ƙafafuwan shi, "Lokaci Yana tafiya, agurguje Zan faɗa maki yadda za ku Yi don ku gano ƙofar nan da zata fitar daku daga Cikin kurkukun nan, shine abu mafi muhimmanci agare ku! Cikin shessheƙar kuka tace mashi "Idan dagaske ne Zaku iya taimaka mana mu fita zanji dadi sosai, sai dai Ni bazan Iya barin kurkukun nan ba tare da Danish ba, Dole in tafi dashi, in ba haka ba, Ni zan tsaya in yaso sauran ƴan uwan mu su ku6uta," sosai ta fashe mashi da kuka. "Ni kaina bazan bari ku tafi ba tare da Danish ba! Domin kuwa shi ba iya garkuwar kurkuku bane, Ku kanku garkuwa ne agare ku! Fita prison ba abu bane mai sauƙi, Shi kaɗai ne zai Iya taimaka maku don ku gudu cikin sauƙi, dalilin da yasa nace haka saboda ginin kurkukun nan a cikin ƙurmin Daji ya ke, Idan har Allah yasa kuka samu damar fita zaku faɗa cikin Daji ne mai hatsarin gaske mai ɗauke da mugayen namun dawa, Sannan tafiya ce wadda ƙafa bazata ta6a iya yin ta ba, amma in dai Garkuwa Yana a tare daku bazai bari wata dabba ta cutar daku ba, Koda kuwa Zaki ne ko Kura zai Iya rikiɗa ya koma irin suffar su don yayi faɗa dasu harma yayi nasara akan su......." dakatawa ya ɗanyi da yin jawabin, Itama Angel tuni ta dakata da yin kukan tana kallon shi, Zuciyarta cike da mamaki haɗi da rudanin maganganun shi, Kuma daga gani ba ƙaramin mutun bane. "Bana so ku ƙara Wata ɗaya a gidan kurkukun nan saboda muna gab da shiga watan da za'a gabatar da Black Night, taro ne na matsafan duniya da zasu halarta a gidan kurkukun nan daga ƙasashe daban daban zasu zo, ranar gwada rashin Imani, ranar zubda jinin prisoners, Idan muka bari ranar ta riske ku a cikin kurkukun nan, bana tunanin ɗaya daga Cikin ku zai Rayu! Dalilin da yasa suka daina zuwa ɗaukar ku saboda sun dakatar maku da Jinin al'adar ku na mata saboda tanadin da su ke yima wannan ranar, tsawon watannin da kuka ɗauka ba ku yi Jini ba, a ranar zasu yi maku sihirin da zaisa ya dawo maku gadan gadan don su gwada rashin imani akan ku......" Hankalin Angel ba ƙaramin tashi yayi ba, Idanuwanta azazzare ta ke kallon mask ɗin fuskar shi, tsigar jikin ta duk ta tashi haiƙam jin abunda yace, "Lokaci Yana ƙure mini, Yanzu Zaki Iya yi mini duk wata tambaya dake a cikin zuciyar ki" Numfasawa tayi kafin ta soma jera mashi tambayoyi akan abubuwan da suka cunkushe mata kwakwalwar ta. "Ka ce mini kai ɗan tsohuwa Tamira ne! Dama tana da ɗa? Da farko ta ta6a faɗin cewa da ace ta ta6a yin aure da tuni ta yi jika dani, daga bisani kuma ta gaya min cewa Itama prisoner ce kamar mu tun tana ƙarama aka kawota gidan kurkukun ƙaddarar harta girma ta yi aure harta haifi ya'ya da jikoki, kaina ya ɗaure, Kuma meyasa ku ke son ɗaukar Fansa? Sannan taya za'ai mu iya ganin ƙofar da zata fitar damu daga Cikin kurkukun, Bayan haka inaso insan ta yadda zamu taimaki ɗan uwanmu Danish Ya dawo Cikin hayyacin shi, menene dililin dayasa ake kira na da Ƙaddarar Kurkuku? Itama ƴar uwata Batul Akwai sunan da aka sanya mata a bayan rigarta Heart beat of prison, na jima inason sanin meyasa aka banbanta mana uniform ɗinmu dana sauran Ƴan uwanmu? Suwane ne keda gidan kurkukun nan? Waye ya sadaukar dani?" tun da ta fara jera mashi tambayoyi bai katse ta ba, har sai da takai ƙarshe tukunna ya soma magana a tsanake. "Kamar yarda na faɗa maki da farko haka zan maimaita maki a yanzu, Ni ɗa ne ga tsohuwa Tamira! Ni kaɗai ne ɗa da ta haifa, wata'ƙil ta gaya maku hakan ne gudun kada asirinta ya toni a fahimci cewa Kamar tana son kusan wani abu dangane da rayuwar ta ne, wanda Yin hakan Babban matsala ce agare ta, Shiyasa ta ke yi maku ƙarya a kalamanta, Dalilin daya sa muke son ɗaukar fansa Saboda mahaifi na da su ka yi silar mutuwar shi, Babban malami ne wanda duniya tasan da zaman shi ana kiran shi da Habibullah, Yana ɗaya daga cikin manyan Malamai na duniya masu zagaye ƙasashe domin yin da'awa, Allah yayi mashi baiwar ilimi, ɗan ƙasar Nigeria ne, Tun da ya ke bai ta6a yin aure ba, a zamanin shi baida burin daya wuce Yayi koyi da manzo SAW wurin karkato da hankulan waɗanda basuyi imani da Allah ba don Ya Musuluntar dasu, Ita kuma mahaifiyata tsohuwa Tamira Ƴar Ƙasar America ce ba musulma bace bata da addini, Farkon haɗuwar su da mahaifiya ta yaje ƙasar Dubai domin gudanar da gasar Musabaƙa ta karatun alƙur'ani ta duniya da aka gayyace su tare da manyan malamai na sauran ƙasashen duniya A babban birnin Dubai wato Abu dhabi, A can Allah ya haɗasu itama lokacin taje ƙasar Gudanar da harkokin kasuwancin ta, kamar yarda ya bani labari tun da yake bai taba sanyawa ran shi zai so wata ƴa' mace har takai su ga yin aure ba, sai gashi ƙaddara ta haɗa shi da auran Baturiya ƴar ƙasar america, bakomai ne yasa shi amincewa da tayin soyayyar da tayi mashi ba, face don ta nuna tana so ta musulunta in har ya amince zai aureta, kinji dalilin daya sa har ya aureta ba tare da sun samu matsala ba, kinsan su turawa da zarar yaro ya haura 18 years Yana da ƴancin da zai yi komi yake so, Iyayenta basu son auran sai dai ba yadda zasu yi dole suka haƙura tabi za6in ranta, Bayan sun dawo ƙasar Nigeria ne ta musulunta, hakan ba ƙaramin daɗi yayi ma dangin shi ba, tun da iyaye na suka yi aure basu ta6a haihuwa ba, Har saida auran su yakai shekara goma tukunna Allah ya ƙaddara samuwata, A lokacin sun manyan ta mahaifina Ya tsufa, Ita kuma Mahaifiya ta tana da shekara arba'in a duniya.." dakatawa ya ɗanyi da yin Maganar, Angel ta zuba mashi ido tana jiran yaci gaba da bata labari. "Akwai wata baiwa da Allah yayiwa mahaifina, duk idan ya haɗu da mutun mai sihiri a jikin shi sai ya gane, To haka ce ta faru a tsakanin shi da ɗaya daga cikin shuwagabannin dake ruƙe da kurkukun ƙaddara, a lokacin an gayyace shi wani taro jihar Kano state za'a yaye ɗalibai da suka Haddace alƙur'ani mai girma, A filin taron Allah ya haɗa su dashi, tun da sukayi tozali da idon junansu hankalin shi yaƙi kwanciya, Saboda matsafa suna jin shakkar habibullah, tun bayan da aka kammala taron Mahaifina ya dawo gida yana ta tunanin wannan mutumin da su ka haɗu a wurin taro, Abun da ya ɗaure mashi kai Duk wurin shine babban Mutun da aka gayyata, basu ta6a haɗuwa dashi ba sai ranar, shigar mutuncin da ke a jikin shi ta bashi mamaki matuƙa, kuma sananne ne a idon jama'a, Bibiyar rayuwar shi mahafina yaci gaba da yi don ya gano me suke aikatawa saboda ya gane bakin sihiri yake da shi, duk inda yasan za'ayi taro na manyan mutane sai yaje don ya haɗu da wannan mutumin kuma cikin sa'a suke haɗuwa dashi harma su gaisa, A wata rana ne Bayan an yi wani taro na manyan mutane, mahaifina yabi bayan su a 6oye basu sani ba har yaga kaɗan daga cikin abunda suke aikatawa, Hankalin shi ya tashi matuƙa a daren ranar bai kwana a garin da akayi taron ba, Tsakar dare ya dawo Kaduna, babu wanda yasan da dawowar shi a wannan ranar sai dai muka gan shi ya shigo gida, ashe tun lokacin da yake yi masu leƙen asiri sun gan shi suka ƙyale shi don suga iya gudun ruwan shi, a lokacin da ba muyi tsammani ba Matsafan nan suka kawo mana hari, tsakar dare su ka yi mana zuwan bazata a cikin gidan mu, Gaba ɗaya suka tattara mu da mahaifiyata dani kaina da mahaifina, kinji silar kasancewar mu agidan kurkukun ƙaddara! Ɗakin da kuke rayuwa acikin shi anan suka kulle mu, mu duka ukun, tun kafin a sabunta ginin tun yana tsoho, Mahaifina yayi ƙoƙari wurin ganin ya nema mana hanyar da zamu ku6uta amma abun ya faskara saboda babu ƙopa a cikin ɗakin a datse yake tako Ina, Akan idon shi mugayen matsafan nan suka yi amfani da mahaifiyata da kuma ni kaina duk don su ƙuntata mashi, tsabar baƙin Cikin wannan abun yasa shi kamuwa da ciwon zuciya, mun fuskanci tashin hankali a hannun Giants dake tsaron kurkukun nan, Kamar yadda ake baku abinci sau ɗaya a rana haka suke bamu, Mahaifina bai cin Abincin shi ni yake ajiye mawa don kada inji yunwa, yana matuƙar sona, Nima ina ƙaunar shi, har roƙon mu yayi akan mu yafe mashi saboda shine silar jefa mu cikin halin da muka tsinci kan mu, da ace baiyi masu leƙen asiri ba da duk hakan bata faru ba, Ire iren waɗannan maganganun da yake yi mana ba ƙaramin karya mana zuciya yake yi ba, da kanshi ya faɗa mana cewa zaiyi mana hanyar da zamu gudu daga Cikin kurkukun Amma baya jin zai rayu, Yayi ƙoƙarin sama mana hanya koda ta bango ne mu bi mu wuce Sai dai hakan ya faskara, gashi komai muke yi idon su akan mu suna kallon mu, da zarar sunga ya fara ƙoƙarin yin ibada sai su shigo su kamamu suna azabtar damu nida mahaifiyata duk don ya dakata, Da zarar sun fara yake dainawa saboda baison su halakar damu, Bayan mun ɗan samu sassauci daga wurinsu ne yaci gaba da neman hanya a cikin ɗakin, Har Allah yasa ya gano wata tsohuwar Hanya da ruwa ke bi ya wuce ta cikin ta, Girman ƙofar mutun zai Iya bi da rarrafe ya wuce ta cikinta, koda ya gano hanyar bai bari sun fahimci hakan ba, Ya dinga bi a sannu wurin ganin ya tono ta saboda A garƙame take sun rufe ta da dakakken ƙarfe wanda Idan har ba Sihiri Mutun ke gare shi a jikin shi ba bazai Iya buɗe ta ba, Taya zai Iya buɗe murfin ƙarfen dake a jikinta bayan komai muke yi suna kallon mu? Zasu gane ne Asirin shi ya tonu, Silar hakan kuma zamu iya rasa rayukan mu, Abunda mahafina yayi a wurin da ya zauna yayi amfani da Baiwar ilimin addini da Allah ya bashi, addu'o'i ya dinga yi yana tottofe cikin ɗakin, Tsawon kwana biyu ya ɗauka bai motsa daga wurin ba, babu ci babu sha haka ya zauna yana kai kukan shi ga Ubangijin mu Allah subhanahu wata'ala, Silar wannan addu'o'in da mahaifina yayima wannan wurin yasa garkuwar sihirin da ke a zagaye da sashen ta karye, har yau har gobe matsafan basu Iya sanin meke wakana a ciki ba, Muddin Mutun ya shiga wurin baza su iya ganin shi a allon tsafin su ba, Mu kan mu sai daga baya muka fahimci cewa garkuwar sihirin da ke a wurin ta karye, hakan ba ƙaramin daɗi yayi mana ba, sai dai kash muna shirin 6alle ƙofar don mu gudu ciwo ya turniƙe mahaifina ya faɗi ƙasa Yana ambaton kalmatusshahada, Dama yace mana da wuya ya rayu saboda cuwon zuciyar da matsafan suka dasa mashi ga ba magani, Munyi kuka tamkar ran mu zai fita, Yana a cikin mawuyacin hali yake roƙon mu akan mu tafi kada mu tsaya jiran shi, kada suzo su kamamu. Bamu ji maganar shi ba, Muka ƙi tafiya saboda mun sanyawa ranmu cewa dole sai dashi zamu gudu, Muna tsaka da ƙoƙarin dawo dashi hayyacin shi don ya tashi mu tafi, Giants ɗin dake kawo mana abinci suka ritsa damu, Nan take kuma mahaifinmu Ya cika, Mu kuma suka tasa ƙeyar mu zuwa can cikin kurkukun, nasan dole an neme mu an kuma yi Addu'oi sosae saidae bawa baya wuce ƙadddarar sa, tun daga wannan lokacin Suka maida Mahaifiyata ma'aikaciyar su ni kuma suka bani horon zama Giant, horo mafi wuya a duniyar nan, Miƙa wuyan da mu ka yi gare su muka zama masu biyayya shiyasa suka yarda damu sosai musamman mahaifiyata tsohuwa tamira, Tabbas mun aikata babban kuskure na bin umarnin matsafa saboda son ɗaukar fansa duk da da farko da suka yi mana tayin aikin ko su kashe mu kin yarda mukai sai daga baya ita Mahaifiyar tawa ta amince saboda a tsarin su ba su yi ma mutun sihiri don ya amince zai yi masu aiki sun fi so da kan ka Amince kana a hayyacin ka, sai daga baya ne ake baka sihirin a koya ma abubuwa, lokacin ba irin ƙoƙarin da ban yi ba wurin nusar da ita kan illar hakan don kuwa sai mun yi ridda amman ta kafe dama kuma tubabba ce, ina ji ina gani mahaifiyata tabar addinin musulunci ta shiga Cikin matsafa sosai saboda taci galaba akan su, a lokacin ta roƙe su kan kar su wulaƙanta gawar Mahaifina su maida ta gida a samu ai masa sutura suka amince don dama ba zatai masu Amfani ba sai ma taja masu matsala, Amma ni an sha daga dani kan in amince naki, k'arshe dai soyayyar uwa ta kwashe ni da kuma nuna man da tayi in muka kawo k'arshen su hakan kaman jahadi ne mukai daga baya sai mu tuba mu rok'i Allah ya yafe mana, da haka na amince saidae ni har yanzu musulmi ne don zuciyata tak'i yarda in bar musulunci sai dai kuma bana sallah gaskiya, Saboda a gidan kurkukun ƙaddara ba'ayin sallah shine abu mafi muni da suka tsana shiyasa a duk lokacin da mutun yai niyyar yin sallah suke burkita mashi lissafin ƙwaƙwalwar shi, Ba don mun so muka kasance Ma'aikatan gidan kurkukun nan ba, kafin mutuwar mahaifina yayi mana addu'a mai ƙarfi akan Allah Kada ya basu nasara akan mu, Ya roƙi Allah da ya bamu ikon Tarwatsa matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddarar nan, Inaji araina cewa Addu'ar mahafina ce take bibiyar Rayuwata shiyasa har yau har gobe hankalina bai ta6a gushewa ba, ina sane da komai, duk wani zalunci da ake aikatawa bana ɗaya daga Cikin masu yi, ban ta6a kisa ba tun bayan da aka horar dani nazama Giant, silar hakan yasa har yau basu bani matsayi mai girma ba amman suna d'aga man sosae sakamakon mahaifiyata da tay mubaya'a gaba daya, Ina matuƙar tausayin rayuwar Danish! ni na fara rayuwa a gidan kurkukun nan na mallaki hankali na, shi kuma tun yana jinjirin shi bana tunanin ko cibi an yanke mashi a haka aka kawo shi nannaɗe cikin Towel, Matsafa sun girgiza da ganin irin kyan da Allah yayi mashi, wlh banji daɗin yadda suke sarrafa rayuwar shi ba, Yaron yana da kaifin basira fiye da tunanin ki, Allah yayi mashi baiwar da zaiyi wuya asamu mai irinta, Yana da saurin haddace abu, he's a gifted sannan Yana da ƙarfi tunkafin su sanya mashi sihiri ajikin shi Danish Yaro ne mai ƙarfin gaske, ko ni nasha jaraba yin dambe dashi a gidan kurkukun nan tun yana da shekara sha biyar yake bamu wahala, Da biyu suke haɗa mu Faɗa dashi, don su jaraba ƙarfin shi, Abun da zai baki mamaki mu tsafi ne ajikin mu, shi kuma babu sihiri a haka yake cin uban mu......" Sosai Angel ta fashe da matsanancin kuka tausayin danish ya kamata, ashe tun yana jariri aka sadaukar dashi agidan kurkukun ƙaddara, maganar da Salsabeel ya gaya mata ta ƙara Sanya mata ƙaunar Danish acikin zuciyar ta, son shi ya ƙara ninkuwa, Ji take kamar tayi fiffike taje inda zata ganshi don ta rungume shi a jikin ta. "Sauran tambayoyin da kikayi mini bazan iya amsa maki ba saboda babu isasshen lokaci, zasu iya riskar mu, Abu ɗaya da nake so kiyi mini alƙawari shine kiyi ƙoƙarin ganin kinbi duk wasu sharuɗɗa da zan faɗa maki don ku tsira daga Cikin kurkukun nan, Mun ɗaura buri akan ki Unaiserh, saboda ta hanyarki ne kaɗai zaki iya tona asirin matsafan da ke ruƙe da kurkukun ƙaddara! Muna so duniya tasan da zaman su, A san me ake aikatawa a gidan kurkukun, yin hakan da zakiyi shi zai janyo hankalin mutanan duniya daga nan za'a samu waɗanda zasu Iya kawo masu farmaki, Inaso ki ɗaurawa kan ki nauyin yin hakan ko dan saboda rayukan dake rayuwa acikin kurkukun nan cikin mawuyacin hali! Akwai ire iren ku da yawa wadanda basu ji ba basu gani ba, An kulle su an hanasu sakat, Kullum ne sai an rasa rayuka agidan kurkukun nan, kashe mutane suke yi tamkar kyankyasai, Idan har bamu kawo ƙarshen kurkukun nan ba to kuwa zasu cigaba da aikata 6arnar da babu ranar dainawa, Muna matuƙar jin tausayin yaran da ke rayuwa a kurkukun nan, Dan Allah Unaiserh ki taimaki rayuwar su! Ki daure ki jure wurin ganin kun tona asirin abun da ake aikata......" hannayenta Ya ruƙo a cikin nashi ya dinga yi mata magiya sautin muryar shi kamar zai fashe da kuka, Ga dukkan alamu sun gaji da ganin Zaluncin da ake aikatawa agidan kurkukun ƙaddara Tun tana yin kuka har muryarta ta disashe da ƙyar ta samu ta tsagaita tana kallon shi tace "NAYI MAKA ALƘAWARI Idan Allah ya bani damar fita daga kurkukun nan zan tona asirin su harma mu bada gudunmawa wurin ganin an kawo ƙarshen su, Bi'iznillahi, Ajiyar zuciya ya shiga saukewa kafin ya daidaita natsuwar shi yaci gaba da cewa "Silar sabunta ginin da aka yi ƙofar ta 6ace mana, amma muna hasashen tana a cikin ɗaya daga cikin waɗannan makewayin naku guda uku, akwai wata tukunyar fulawa da ke ajiye Cikin toilet ɗinku Mahafiyata ce ta ajiyeta saboda bayan an sabunta ginin shafen dake a ƙasan wurin bai zauna da kyau ba, kuma bakomai ya jawo hakan ba face silar zaman da mahaifina yayi awurin na tsawon kwana biyu yana ibada, to duk wani abu da ke da sihiri idan ya ta6a wurin bazai zauna ba sai ya nuna alama, gudun kada ta manta da ƙofar yasa ta ajiye wannan tukunyar fulawar, Idan kuna so shafen dake akan ƙopar Ya 6a66ako batare da kun sha wahala ba, Ku yi amfani da ruwan zafin da ake kawo maku a matsayin ruwan shan ku, da zarar kun yayyafa shi asaman wurin zai tsastsage daga nan ƙofar zata bayyana, amma fa sai kun yi takatsantsan, kada farin cikin ganin ƙopar yasa ku fasa ihu wanda zai janyo hankalin su........." Wani irin Farin ciki ne ya lullu6e Angel, Bakinta yaƙi rufuwa "Kada ku sanyawa ranku cewa dukkan ku zaku tsira, ba abune mai sauƙi ba, dole ku fuskanci tarin ƙalubale wurin ku6uta, musamman Makullin nan ɗaya da baya a cikin ku wato Danish dole ku dawo da shi saboda shi kaɗai ne zai Iya Cire murfin ƙarfen da ke a jikin ƙofar cikin sauƙi ba tare da kun sha wahala ba. Cikin shessheƙar kuka tace"Taya zamu iya gano Danish har mu iya dawo dashi Cikin hayyacin shi"? bai amsa mata tambayar ta ba, ganin ya miƙe tsaye yasa itama ta miƙe tana kallon shi, "Akwai ruwan zam zam da mahaifina yake yawo dashi cikin aljihun rigar shi, ya mallake shine a wurin wani hamshaƙin malamin addini wanda ake kira da Shaykh al-ikhlass ɗan ƙasar Madina, shi ya yi mashi kyautar jarkar ruwan zam zam ɗin duk mutumin da ya kur6i ruwan abakin shi ya haɗiya to zaiyi wuya Sihiri yayi tasiri a jikin shi, sannan waraka ne ga kowace irin lalura da izinin ubangiji, Dubarar da mahaifina yayi sai ya dinga ɗibar ruwan xam xam din yana ɗura shi cikin ƙananun robobi, duk in zai fita a cikin aljihun shi yake ɗauka ya tura, saboda tsaro baisan ko Allah zai haɗa shi da mai buƙatar taimakon wata lalura dake damun shi, shiyasa Yake yawo da robobin ruwan cikin aljihun shi, to aranar da matsafa suka farmake mu tsakar dare suka kawo mu kurkukun nan akwai kingin roba ɗaya da ta rage a cikin aljihun jallabiyar shi, Kafin ya rasu ya damƙa ma mahaifiyata ita mun 6oyeta wurin da babu wanda ya sani daga ita sai ni, Robar ruwan zam zam ɗin tana a cikin ɗakinta inda ku ke rayuwa, da zarar kun dafa jikin bangon ƙofar zata buɗe da kanta, Sai ku shiga ku ɗauko ta. Ke za ki nemo Danish a gidan kurkukun nan saboda ke kaɗaice zaki iya sarrafa tunanin shi amma fa sai kinci baƙar wahala domin kuwa baisan wacece ke ba a yanzu, Har kashe ki zai Iya yi, komai zai iya aikata maki, duk runtsi duk wuya karki bari tsoron shi yasa ki kasa watsa mashi ruwan a cikin bakin shi, ki tabbatar ya haɗiye shi. Sannan Giant basa jin Bugu, Wuƙa bata iya tsaga jikinsu, haka zalika harsashin bindiga bai iya tsaga fatar su, Mutane ne masu hatsarin gaske, ƙarfin shaiɗanun aljanun da ke a jikin su ya rinjayi halittar su ta ɗan adam, Giant's heart ba irin zuciyar mutun bace, ta shaiɗanin aljani ce, Ko da ace kinyi nasarar sanya mashi ruwan abakin shi zai dawo hayyacin shi na ɗan lokaci ƙanƙani amma duk lokacin da Giant's heart ɗin shi ta motsa zaku ci baƙar wahala, Shiyasa ni ke so ki dage dayi mashi addu'a saboda ku samu ya fitar daku daga Cikin kurkukun nan, In yaso daga baya idan kuka faɗa cikin mutane zan baki Address ɗin gidan mu da mahaifiyata ta rubutamin don in baki, idan ku ka duba zaku iya samun sauran robobin ruwan zamzam na mahaifina daya ajiye a ƙarƙashin gadon shi, da shi zaku dinga yin amfani wurin shawo kan Danish a duk lokacin da Giant's heart ɗinshi ta motsa. Ki kula da rayuwar shi Angel Ki ɗauka cewa amanar Danish na baki, ki ruƙe mini shi hannu bibbiyu, kada ki kuskura ki bari yayi nesa dake, ku kasance atare domin mu samu muyi nasara agidan kurkukun nan, Danish yasan komai fiye da tunanin ki, mun riga shi zuwa kurkukun nan amma yafi mu sanin komai, shi kaɗai yasan hanyar da za'a iya ruguza su, Matsalar shi ɗaya mugun miskili ne kuma yana da taurin kai, zaku ci wahala kafin ku samu Ya baku haɗin kai.........." Yana kai ƙarshen maganar shi da sauri ya zura hannu cikin ajihun baƙin wandon dake ajikin shi ya zaro takardar dake a ninke ya miƙa mata, Address din gidanmu ne dake a Kaduna state, Daga yau ba zaki sake gani na ba, duk wani taimako daya dace inyi maku na riga nayi, yanzu saura ku ya rage ku fara naku, Zamu jira har zuwa lokacin da zaku dawo mana da kyakkyawan sakamako, Sai dai bamu da tabbacin zamu kai lokacin a raye nida mahaifiyata ko kuwa....." bai ƙarasa Maganar ba Angel ta faɗa jikin shi ta rungume shi sosai ta fashe da kuka mai sautin gaske, Hannayen shi biyu ya ɗaura a saman bayanta ya ƙanƙame ta sosai tamkar ƴar cikin shi, Sun ɗauki tsawon lokaci rungume da juna, kafin daga bisani taji kanta ya fara sara mata, nan ta ke idanuwan ta suka lumshe bacci mai nauyi yai awon gaba da ita......... ❤PRISONERS❤ Tsawon lokaci da su Batul su ke ta faman bubbuga ƙofar toilet, Angel tana aciki tana bacci kanta jingine da bango, Salsabeel ne Ya dawo da ita tun da jimawa, tasha uban baccin ta hankalinta akwance yayin da ƴan uwanta su ka shiga matsananciyar damuwa na rashinta. Ba ta tashi farkawa ba, Sai da dare Ya tsala Lokacin Sun yi nisa acikin baccin su, A hankali ta soma ƙoƙarin buɗe idanuwanta, Yayin da la66anta ke ambaton Sunan Allah, Wata irin kasala ta ke ji a jikinta sam babu kuzari, duk yinin yau bata ci abinci ba, Ko ruwa bai gifta maƙoshinta, azababbiyar yunwa ce ta addabe ta, daƙyar ta samu ta yunƙura ta miƙe tsaye Tana ƙarewa toilet ɗin nasu kallo, kamar ranar ta fara ganin shi, Hasken filitar da su ka ajiye acikin shi ce ta gaure ko'ina, Bakomai ne ya faɗo mata acikin ranta ba, Fa ce maganganun da Salsabeel Ya faɗa mata, tamkar a mafarki ta ke tariyo komai da ya faru a tsakanin su, kwokwanto ta soma yi a cikin zuciyarta Anya da gaske ne Haɗuwar su da shi? Gani ta ke yi kamar haduwarta mafarki ce, da sauri ta juya tare da ɗaura kyawawan idanuwanta kan tukunyar fulawar nan da ke ajiye saman floor, Walking slowly ta nufi tukunyar, zuƙunnawa ta yi agabanta idanuwanta akan furen Danish, A tsanake ta ke tariyo duk wani abu da Salsabeel Ya faɗa mata dangane da shi, ba za ta Iya misalta irin ƙaunarshi da ta ke ji ba, Taji takaicin mayar dashi Giant da su ka Yi, zuciyarta ba ƙaramin tafarfasa ta ke yi ba duk in ta tuna cewa yanzu Danish ɗinta Giant ne mai haɗarin gaske, Tayaya zata Iya tunkarar shi? Ba tare da ta samu matsala ba, ' runtse idanuwanta tayi sosai hawaye na cigaba da wanke fuskarta, idanuwanta sun canza launin, ciwon kanta ya tsananta sosai. "GENIE!" Ras ta ji gabanta Ya faɗi jin muryar Jamimah, A hanzarce ta miƙe tare da sanya tafin hannunta ta share hawayen da ke tsastsafo mata saman kuncin ta, sai da ta fara zuwa gaban Fanfo ta wanke fuskarta sosai, har ta nufi ƙofa zata buɗe sai kuma ta fasa tunawa da Uniform ɗin Jamimah da bata wanke mata ba, kamar yarda tabar su saman Igiyar shanya haka tayi tozali da su, Matsawa tayi gaban Igiyar ta janyo uniform ɗin, kafin ta zame jam lock ɗin da ke a jikin ƙofar, zuciyarta acike fal da tunanin amsar da zata basu idan suka tambayeta Ina taje? Slowly ta buɗe ƙofar, ba zato ba tsammani ta yi arba da mutun zaune ya jingina bayanshi jigin bangon sashen toilet ɗinsu, gabanta ba ƙaramin faɗuwa ya yi ba, ta ɗan tsorota kafin ta gane wacece, Ashe batul ce bacci ya ɗauke ta a wurin ita da Jamimah sunƙanƙame juna, yadda kasan ƴan gudun hijran da suka rasa wurin kwana, jamimah sai sambatu take yi tana ambaton sunan Genie, da alama bacci ne ya ɗauke su zaune awurin su kaɗai, ta kwanta da tunanin Angel shiyasa ta ke yin sambatun kiran sunanta, murmushi ta saki yayin da take ƙare masu kallo, Har zuwa ta yi gabansu ta zuƙunna tana ƙare masu kallo kamar zata lashe su saboda tsabar ƙaunar da ta ke yi masu, tunawa da Maganar Salsabeel Yasa tayi saurin miƙewa ba tare da ta tayar dasu daga baccin ba, ta nufi cikin ɗakin su, shigarta keda wuya Tayi arba da Su Deeja kwakkwance saman gadajen su, tsit ɗakin sautin minsharinsu Parveen ya cika ko'ina, mamaki ne ƙarara akan fuskarta, wai ashe dare ya yi bata sani ba? a iya sanin ta tsawon mintuna talatin su ka ɗauka suna yin magana da salsabeel, Kenan Baccin ne mai nauyi ya ɗauke ta A jikin shi? Kuma shine ya dawa da ita? Lamarin ya ɗaure mata kai sosai. Allah ka ɗai yasan irin farin Cikin da ta ke aciki, Sai ta dinga ganin kamar suna a kwance ne saman Gadan daddynta dake a gidansu, Wani irin annuri ne ya bayyana akan fuskarta, kamar wadda aka yiwa albishir Da gidan Aljanna, Ji ta ke yi kamar ta Zuba ruwa ƙasa ta sha, A ƙalla ta ambaci Alhamdulillah ala Kulli Haal Yafi sau aƙirga, Ta gode ma Allah da wannan ranar domin tasan cewa shine silar komai, Allah maji roƙon bayinsa ne ya kar6i koken su Zai kawo masu ƙarshen Zaman Su A GIDAN KURKUKUN ƘADDARA, Fatan ta Allah yasa Kada su ƙara rasa wani acikin su, tafi so dukansu su tsira atare kamar yarda su ka sha wahala atare, Zuƙunnawa tayi saman gwiwowinta tare da fuskantar gabas ta yi sujud shukr domin nuna godiyarta ga Allah, kafin ta ɗago kanta tuni hawaye sun wanke fuskarta, yau tasha kuka idanuwanta har kumbura sun ɗan yi, bayan ta kammala ta miƙe tsaye Har zata nufi ɗakin tsohuwa tamira, ta wutsiyar idonta ta hango Haris kwance saman gadonshi, Da sauri ta Kai idonta gare shi, Abun mamaki sai taga Hada Naufal da javed Ga mubeen kwance saman gadonshi, Ga kuma Gabriel kwance ana shi gadon, Azeeza tana agefenshi, Nan bacci ya ɗauke ta, Waro Ido waje tayi bakinta a sake ta ke kallon su, farin Cikinta ya ƙara ninkuwa ɗaya bayan ɗaya ta ke binsu da kallo Agaban gadon haris ta tsaya tana kallon shi, Gwanin ban tausayi, Ya canza mata sosai, Zuƙunnawa tayi gaban gadon shi tsawon mintuna biyar tana bin shi da kallo kafin ta yunƙura ta miƙe ta nufi gadon Javed, bayan ta gama bin su da kallo ta tabbatar da jikinsu da sauƙi, sai taji sanyi aranta. Ataƙaice daren ranar Angel Ta kashe hasken ɗakin su, Ta koma sashen makewayin su, ta ɗauko Fitila ɗaya, ta kashe haskenta, Cikin duhu ta dinga tafiya tana laluban Hanyar da zata kai ta ɗakin tsohuwa Tamira, cikin sa'a ta samu nasarar shafa jikin bangon da ƙopar ta ke a manne, nan ta ke ta buɗe. Ajiyar zuciya ta sauke, ba tare da jin shakkar komai ba ta faɗa ciki, bakin ta ɗauke da bismillah, bayan ta shige taja ƙopar ta rufeta, kafin ta kunna Fitilar hannunta haskenta ya gauraye ɗakin sosai tamkar da rana, Mamaki ne ƙarara akan fuskarta, Ganin Gadon ƙarfe da wooden Book shelves Jikin bango, Jerin littattafaine tsoffi da suka daɗe a ajiye cikin shelves ɗin, daga can tsakiyar ɗakin kujeru ne guda biyu, A tsakankanin su madaidaicin teburi ne mai ɗauke da Tea pot da ƴan kofina. A bun da ya ɗaure mata kai, Kwanakin baya da ta ta6a zuwa ɗakin Ba ta ga gadon ƙarfe da book shelves ɗin ba, sai dai Shufke shufken fulawowi da teburin nan mai ɗauke da teapot, Lallai tsohuwa Tamira ta ƙware wurin Iya Canza ma ɗaki suffar shi Ta hanyar yin amfani da sihirin ta. Shiga ciki ta yi adai dai gaban teburin ta ɗaura fitilar hannunta, Ba tare da 6ata lokaci ba, ta bazama neman ruwan zam zam, Ko'ina ta shiga dubawa Har ƙarƙashin gado, ba ƙaramar wahala ta sha ba wurin neman shi, ta haɗa uban gumi a kan fuskarta, A ƙarshe ta gano ta a saƙon littattafan da ke a cikin shelf ɗin, (plastic vial) Ƴar Karamar roba kalar wadda ake zuba ruwan allura, wasu kuma suna amfani da ita wurin zuba ruwan turare, farace ƙal duk tsawon shekarun da ta ɗauke ajiye bata canza ba, kana iya hangen ruwan dake acikinta, bai wuci ka yi ma shi kur6a ɗaya ba Ya ƙare, A cikin aljihun wandonta ta zura robar, dama anan ta 6oye takardar adireshin da ya bata na gidan su. Kafin ta baro Cikin ɗakin sai da ta kashe filitar, Tukunna ta ruƙo handle ɗinta, Cikin duhu ta fito ta nufi toilet dinsu Ta shiga ta ajiye fitilar, bayan ta fito ne, ta samu wuri daga gefen batul ta zauna tare da kai hannu ta janyo jamimah zuwa saman laps ɗinta sosai ta rungumeta a ƙirjinta, A saman kafaɗar batul ta ɗaura kanta, tamkar an wanke mata zuciyarta da ruwan farin ciki, Ba ta runtsa adaren ranar ba, saboda a ƙagare ta ke da gari yawaye, duk don ta samu damar cigaba da gudanar da aikin ta, gaba ɗaya daren idonta biyu ta yi shi, tunanin Danish da ƙofar nan sun tsaya mata aranta, sune abun harinta. A washe garin ranar da su ka farka daga bacci, ba ƙaramin farin ciki su ka yi ba ganin Angel ɗinsu ta dawo acikinsu, ɗaya bayan ɗaya suka dinga rungumarta a ƙirjin su, haɗi da tambayarta meyasa taƙi buɗe masu ƙopar toilet? Meya faru da ita? Tsawon lokacin da ta shige cikin toilet. Angel ta ce masu Bacci ne mai nauyi ya ɗauketa, gaba ɗaya sun yarda da maganarta, basu kawo komai aran su ba, Su Haris ba ƙaramin farin ciki su ka yi ba, ganin Angel musamman Gabriel don ba ƙaramin kewarta ya yi ba, jikin nasu babu wadatacciyar lafiya amma da ya ke mazane suna da ƙarfin hali da juriyar 6oye damuwar su, duk don kada su tayarwa ƴan uwansu da hankali, Ita kanta Angel ta lura da yanayin da suke aciki tabbas anyi masu wani mummunan abun da basu son sanar dasu, abunda yasa Angel bata matsa ma su akan su faɗa mata ba, saboda hankalinta ba a kwance ya ke ba, ta ƙwallafa rai akan son aiwatar da alƙawarin da ta ɗaukar wa Salsabeel, in har bata ci nasarar dawo da Danish a cikin su ba, ta kuma gano ƙofar nan to bazata ta6a samun natsuwa ba, ko su Deeja bata sanar dasu ainihin abunda ya faru da ita ba, ta yi hakanne saboda gudun kada murnar da za su yi ta yi silar janyo hankalin giants zuwa gare su, shiyasa ta ɗan jinkirta tana jiran su zo kawo masu abinci, saboda ta ɗauki ruwan zafin da za'a kawo masu, bayan giant ɗin sun tafi, zata ja su zuwa cikin sashen toilet ɗin saita sanar dasu komai, haka ta tsara acikin zuciyarta. Kamar Giants sun san da shirinta ranar suka ƙi kawo masu Ganye da wuri, Ranta yai mugun 6aci, har sai da ta fara hasashen ko asirin su ya tonu ne shiyasa suka ƙi zuwa kawo masu ganyen, Wuraren marece sai gasu sun shigo ɗauke da farantan ganye da robobin ruwa mai zafin haske, Lamarin ya ɗaure wa su Haris kai ganin An kawo masu ganye amatsayin abincin su, Har tambayarsu Hanna su ka yi meyasa aka canza masu abinci? Nan suka kwashe duk abunda ya faru tsakanin Angel da tsohuwa zafreen suka sanar dasu, Ransu ya 6aci sosai, tsabar tausayin su da su ka ji har ƙwalla sai da su ka zubda masu. Ko da Giant suka kawo masu ganyen bata bari su hanna sunci ba, duk don saboda Giant su yi saurin tafiya yasa ta kwashe masu ganyen da ke acikin wooden trays ɗin ta zuba su cikin kwandon batul, gaba ɗaya robobin ruwan zafin Angel ta tattarasu duka ta ajiyesu, Ganin sun gama kwashe Ganyen yasa Giants ɗaukar Farantan tare da fucewa daga Cikin ɗakin, kunnuwanta na jiyo mata ƙarar rufe ƙofa ta yi zumbur ta miƙe tare da ɗaukar robobin ruwan guda uku ta nufi sashen toilet ɗinsu Mamaki ya kama su batul ganin ta shiga da robobin ruwa cikin toilet, Hakan yasa suka bi bayanta da sauri don ganin me za ta yi da su. Bayan sun shisshiga Ciki, tace da Azeeza ta kira su Haris su shigo gaba ɗayan su, da gudu Azeeza taje ta kirasu, bayan sun shigo daga Ciki, taja ƙopa ta datse ta da jamlock. Atare suka haɗa baki wurin tambayarta"ANGEL WHY KIKA SHIGO TOILET DA BOTTLE WATERS A HANNUNKI? MEYASA KIKA SA AKA KIRA MU GABA ƊAYAN MU". "BANA SO KUNA YIN MAGANA! KU YI SHIRU KU ZUBA IDO KU GA ABUNDA NAKE SON NUNA MAKU, AMMA KAFIN NAN INASO IN GARGAƊE KU, KOME IDANUWAN KU ZASU GANE MA KU KADA KU KUSKURA KU CE ZAKU YI MAGANA, " Amsa mata su ka yi da toh, zuƙunnawa tayi agaban tukunyar fulawan tare da ajiye robibin ruwan dake a hannunta ƙasa. "Batul ke da Deeja ku kawar min da tukunyar nan" Da sauri suka sanya hannayensu tare da ɗaga tukunyar suka sauke ta gefe ɗaya. Buɗe murfin robobin ruwan tayi har tiriri ya ke yi saboda zafin shi, ɗaya bayan ɗaya ta soma ɗaukarsu tana kwarara ruwan jikin bangon da tukunyar ta ke a jingine dashi, wurin yayi shaida saboda da daɗewar tukunyar. Kowanan su Ya ƙura ido yana kallon ikon Allah, Shin me Angel ta ke son nuna masu ne? Ras gabansu ya faɗi, A matuƙar ruɗe su ka zazzare eyes ɗinsu akan bangon dake tsastsagewa Nan ta ke ginin dutsen da aka yi shafe dashi ya soma 6a66akowa, tamakar an sanya wuƙa an tsargashi haka ya dinga zazzagewa, gaba ɗaya ya rubzo ƙasa, Kallon kallo suka shiga yi atsakaninsu Tsantsar al'ajabi ne ya kamasu, lokacin da tsohon murfin ƙofar ya bayyana a suffar shi, Jikin ƙarfen duk yayi tsatsa. "Angel menene wannan"? A matuƙar ruɗe suke tambayarta, Ɗagowa tayi tare da kallonsu wani ƙayataccen murmushi ne ya bayyana akan fuskarta mai nuni da tsantsar farin Cikin da ta ke a ciki, dimples ɗinta duka biyu sun lotsa sosai, Tunkafin ta motsa la66anta da niyar amsa masu tambayarsu, muryar batul ta katse mata hanzarin ta "Kamar Ƙofar da mu ke nema"? jinjina masu kai tayi alamar eh ta ƙara da cewa"FINALLY MUN YI NASARAR GANO ƘOFAR DA ZA MU BI MU GUDU DAGA CIKIN KURKUKUN ƘADDARA SAI DAI KASH! BOSS TA ƊAUKE ALƘALAMINTA DOLE MU JIRA TAKUN TSAKIYA DOMIN JIN YADDA ZA TA YI DA RAYUWARMU IN ALLAH YA KAIMU DA RAI DA LAFIYA!" ALHAMDULILLAH END OF TAKUN FARKO🥳🥳🥳🥳🥳 *Ga masu son cigaba da Karanta Littafin kurkukun ƙaddara 500 ne kacal, Labarin yanzu nake Cikin rubuta shi babu Complete sai dai ka biya asanyaka agroup inda zaka dinga samun update akai akai, Inka biya za'ayi adding naka a paid group kuma za'a sanyaka a comment section, Sa'annan Ba'a share Ko yin forwarding duk wanda yayi gigin fitar da littafin, akwai ta inda zamu ga sunan shi da alamar yayi forwarding to zamu cire shi a group ne👌 Kuma yaja ma kanshi zamu ɗauki mataki👌* *Littafin Kurkukun ƙaddara 3 part ne, Yanzu muna gab da ending na Takun farko free kenan, Sai kuma Takun tsakiya wanda ya kasance na kuɗi ne, da takun karshe duk akan 500 zaku karanta shi* *Ga wanda ya shirya Yin payment, ga details nan, Idan ka tura kuɗin zaka bamu shaida, Bamu kar6ar kati, Ta bank ake turawa ko ta pos, In yaso saika ɗauko hoton reciept ka tura mana* *3196407426* Bature Hafsat Muhammad First bank *Zaka tura da shaidar Biyanka ta wannan Numbers ɗin (0816985 6268) ko kuma ta (08103884440)* ********************** ⬇ ************************** ********** Ai Hausa Novels **************** *************************⬆ ********************** DOWNLOAD More complete Hausa Novels, Education Books, Adventure, Drama, Mystery, Religion, Fiction, Non-Fiction, Romance, Meimor, True Life Stories & Others from our blog. Visit > https://www.aihausanovels.com.ng Ka tura mana sako ta adireshinmu na email, domin tuntubarmu ko turo mana hausa novel ko kuma post. Email > aihausabooks@gmail.com ******* FOLLOW US ****** Facebook: Ai Hausa Novels Twitter: Ai Hausa Novels Telegram Channel: https://t.me/Aihausanovels WhatsApp Number: 08138873799 Haka kuma domin shiga kowanne daga cikinsu za ku iya ziyartar shafinmu ku yi search na AI HAUSA NOVELS, hatta facebook group dinmu ma za ku samu. ********************** ⬇ ************************** *************** Ai Hausa Novels **************** ********************** ⬆ **************************