[13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *watpadd:safiyya huguma* © *haske writers asso*💡 (Home of expert and perfect writers) ____________________________ *_BISMILLAHIR RAHMANIRRAHIM_* *_dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala,tsira da aminci su sake tabbata ga shugaban halitta annabi Muhammad S A W_* *_ina mai farincikin sake haduwa da masoyan rubutu na,sannan ina roqon Allah s w a ya sanya dukkan abinda zan rubuta ya zamo mai amfani mai amfanarwa cikin wannan sabon rubutu nawa_* *_saidai wannan karon masu karatu sai kunyi min afuwa ba kullum ne ranakun da zan rinqa post ba,ranakun posting sune kamar haka in sha Allahu_* *lahadi* *talata* *alhamis da juma'a* *Babi na daya* Tun daga cikin kitchen take iya jiyo muryarta cikin ihun kuka tana dosowa tsakar gidan,da sauri ta ajjiye wuqar hannunta ta fito daga kitchen din da nufin taryarsu tun kafin su su iso mata. Rayyan ne akan gaba bayansa sabe da school bag dinsa,hannunshi daya riqe da tata school bag din,yayin da daya hannun nashi kuma yake riqe da hannun rumana dake digar jini,Raihana ce ke biye da su a baya itama goye da tata jakar idanunta jage jage da hawaye wanda har ya jiqa medicated glass din dake kan fuskarta. Da sauri ummu ta qarasa ta karbi hannun rumana dake cikin na rayyan cike da fargaba take tambayar rayyan din wanda idanunshi suka kada sukayi jawur tamkar wanda aka zazzabgawa mari"garin yaya haka?,dame ta yanke?"ummu ta tambayeshi tana qoqarin tsaida jinin. Daga kanshi yayi ya zabgawa raihana harara wanda jikinta yayi laqwas ta lafe a bayan ummu"raihana mana ummu,wai qawarta ce ta bata ajiyar reza ita kuma rumana ta gani ta karba a gunta zata fiqe pencil,garin fiqewar ta yanke hannu" "Ashsha,ai na hanaku amfani da reza ko?,tunda dukanku kuna da sharpner" "Ai tana sane wawiyar yarinya data karbi ajiyar kuma har ta bada wai aro" ya fada yana sake hararta duk da ta buya,ji yake kamar ya janyo raihana ya sake mammarinta kamar yadda yayi dazun. "To ya isa,rumana kukan ya isa haka mana,dadina dake raaki,kai rayyan maza shiga bedroom dina ka dauko first aid boxs dinku"da sauri ya sabule jakar makarantar tasa ya shige parlour inda daga nan zai sadashi da dakin gadon. Cikin 'yan daqiqu ya dawo hannunshi dauke da akwatin ya miqawa ummu,ta sanya ruwa ta fara wanke jinin kafin ta saka spirit ta soma wanke mata,aifa rumana an samu abunyi,bare baki tayi sosai ta dinga sharbar kukanta yayin da rayyan da raihana baki daya suka rasa sukuni suka dinga zuba mata sannu tamkar su maido ciwon jikinsu. Raihana ce ta gaza daurewa tace cikin qwalla" ummu da zafi don Allah ki mata a hankali",da sauri rayyan da ya harde hannayensa a qirji yana kallonsu idanunsa sun kada ya sake zuba mata harara"yi mana shiru,duk bake kika jawo mata ba","rayyan ya isheni haka nan"ummun ta tsawata masa,suna tsayen ta kammala gyara matan rayyan ya janye hannunta zuwa falo raihana ta kwashi jakankunansu tabi bayansu,ummun ta bisu da kallo,idan da sabo tuni ta saba,irin wannan damuwa da sukayi da junansu,cikinsu babu wanda keson wani abu ya samu dan uwanshi kada ma rayyan da rumana suji labari,hakan ya sanya cikin makaranta ko unguwa wasu ke musu laqabi da AMINAN JUNA. Ciken tray daya ta shirya musu abincin,don ta sani lokuta irin wadan nan tare suke cin abinci,musamman yau da aka jangwale rumanan sarkin raki. kan kujera kuwa ta tadda rumana a lafe kamar wadda ke ciwon jiki,yayin da rayyan ke gefanta hannayensa dauke da papers wanda da alama na neco da suke zanawa ne yake sake dubawa,ajjiye tray din tayi wanda ke dauke da shinkafa da miya,gefe kuwa hadin salad ne "A sauko aci abinci maza kada lokacin islamiya yayi"cewar ummu,ai kuwa sai rumanan ta sake lafewa tana ahirin zubda wasu sabbin qwallan,sarai ummu ta fahimci me take nufi tunda tai hakan,ko dama can kullum da daru rumanan ke tafiya makarantar walau islamiyya ko boko,sauqinta daya rayyan da take shakka,duk da sabon dake tsakaninsu hakan baisa ta rainashi ba. Tana shirin neman raihana sai gata ta fito sanye da unifoarm din islamiyar tasu baqar doguwar riga da farin hijabi,yarinyar na da nutsuwa da son makaranta,sau tari takan fahimci abinda ya kamata tun kafin a furta duk da qarancin shekarun nata da basu shige tara da 'yan watanni ba "Oya,sauko muci abinci"rayyan ya fada yana duban rumana,ta kyebe baki don babu damar yin musu haka ta janyo jiki ta sauko qasa inda ta tanqwashe qafarta kamar yadda duk sukayi,hannunta ta kalli kana ta kalli rayyan,shima dubanta yayi ba tare da yace komai ba ya soma diba yana bata a baki,ya juya zai dauki ruwa ya lura raihanan ma ba wani cin kirki tajewa abincin nata ba,sai yaji tausayinta ya kamashi da ya tuna marin da ya mata dazu,hannu yasa ya karbe cokalin hannunta ya hadasu duk su biyun ya dinga basu,ummu dake gefe wadda ta idar da sallar azahar tana kallonsu fuskarta qunshe da murmushi,zuciyarta cike fal da farincikin yadda rayyan din ke kulawa da qannen nasa. Sai da suka qoshi su duka kana ya tasa rumana a gaba ta shirya fuskarnan babu digon annuri don kada ta kawo wargin cewa ba zata je ba. Hakan bai sanyata tayi shiru ba lokacin da taga ya sanyasu a gaba suna qoqarin ficewa a gidan ba tare da shi ya sanya nashi unifoarm din ba,fuska a narke tace"ya rayyan....yauma mu kadai zamu je kai ba zaka je ba?"dariya ce taso kubce masa ya dan dake"amma da karatu ne wannan rumana yaci kin dade da haddaceshi,wata na nawa da yin sauka aka sallamemu?,ranar saukan ba ke na bawa ajiyar zayyanata ba?"shiru tayi ba tare da tace komai ba tana mai ci gaba da son zubda qwalla,"kinayin kuka ni da raihana ba ruwanmu da ke,ke bakyason kema wataran ace kinyi saukar kamar ni?","inaso mana ya rayyan" xto dole ki dage da zuwa makaranta kinji ko?" "To amma ya rayyan idamukayi sauka shikenan mun daina zuwa ko?" "Qwarai ma kuwa my angel"da yake wani lokaci haka yake kiranta,murna ta soma yi jin ance sun daina zuwa da sunyi sauka harda rawa da yake ba baya ba wajen son rawa,shi da raihana na gefe na kallonta raihana nata dariya,da haka ya kada kansu suka fice yana jansu da labarai masu dadi dasa dariya don su kuma sakewa har ya kaisu qofar makarantar dake bayan layinsu ya juya ya komo gidan don yayi wanka *mrs Muhammad ce* 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *watpadd:huguma* © *haske writers asso*💡 (Home of expert and perfect writers) *_An karbo daga uwar mumunai ummu abdullahi wato nana Aisha R.A tana cewa:Manzan Allah S a w yace "haqiqa dukkan ayyuka basa yiwuwa sai da niyya,kuma kowane mutum akwai abinda ya niyyata"(ma'ana ladan aikinka da sakamakon da zaka samu ya ta'allaqa da irin niyyar dake zuciyarka akan aikinka,irin niyyarka irin sakamakonka agun ubangiji)* _ruwayar bukhari_ ______________________ *babi na biyu* Hikimar ubangiji ce haduwar jini qauna da shaquwa tsakanin wane da wane,yakan sanya irin wannan jituwar da qaunar juna tsakanin bayinsa,hakan itace ta kasance tsakanin wadan nan bayi nasa guda uku wadanda suka fito daga mabanbantan yare har ma da qabila,wanda daya daga cikinsu ma suka samu banbancin qasar haihuwa a tsakaninsu *Alhj yusufa adamu* Haifaffen jamhuriyar nijer,cikin garin DIFFA,garine dake da qarancin jama'a cikin duka qasar ta nijer,tattalin arziqin yankin ya ta'allaqa ne kan noma da kiwo,mazauna garin sun hada da hausawa,fulani da larabawa. alhj yusufa na daga cikin jinsin fulani wadanda a nan mukafi kira da sadakar yalla,duk da yake ruwa biyu ne shi,saboda asali mahaifiyarsa na daya daga cikin larabawan dake zaune cikin yankin wanda auratayya ta hadata da adamu mahaifin alhj yusuf. Bai fuskanci wani qalubale wajen samun auren rahinatu ba saboda suna da wani yanki na sarautar garin diffa,mahaifin adamu a lokacin shine wazirin sarkin garin na diffa wanda ko bayan rasuwarshi sarautar bata bar gidansu ba adamu dinne yaci gaba da jan ragamar,kasancewarsa d'a na fari kuma babba a gurin mahaifinsu. Yusuf tun yana qaraminsa zuciyarsa da tunaninsa sunfi ta'allaqa ga harkar siye da siyarwa wato kasuwanci,wanda hakan shi ya zama sanadiyyar haduwar jininsu da qanin mahaifinsa muhammadou wanda ke kasuwancin dabino da cukui tsakanin nijeria da niger. Yadda ya lura da hazaqar yusuf da qulafucinsa na son kasuwanci yasa ya fara daukarsa rakiya zuwa nijeria tun shekarun yusuf din basu taka kara sun karya ba,cikin qanqanin lokaci sai ga yusuf din ya zama cikakke kuma gogaggen dan kasuwa tsakanin nijeria da nijer. Tun zuwan yusuf na farko qasar nijeria ta burgeshi,yanayin garin al'ummarsa wayewarsu da kuma mu'amalarsu da jama'a,musamman da ya soma shiga garin kano ta dabo ci gari jalla babbar hausa,wanda da iyakacinsu sokoto katsina,harkarsa a kano sai tafi garawa ta kuma fi bada armashi kasancewarta cibiyar hada hadar kasuwanci,hakan ya sanya bayan cukui da dabino sai yake hadawa da mazarqwaila da sauran abubuwa da mu bamu da su. A lokacin cikin kasuwar kwari suke sauka inda anan ya hadu da alhj *dalhatu attahir* wanda yake da makekiyar rumfa,nan cikin rumfar tasa yake ajjiye kayansa idan yazo kafin ya rarrabawa 'yan kasuwa da masu sara. Kunsan hali sai yazo daya ake abota,yadda alhj yusuf yake mutum mai matuqar kirki,gaskiya riqon amana taimako da son jama'a haka alhj dalhatu take,nan da nan abota da shaquwa mai qarfi ta shiga tsakaninsu duk da bambancin nau'in kasuwanci dake tsakaninsu,saboda shi alhj dalhatu yana saida atamfofi ne kala daban daban kaama daga qarama mai sauqin kudi zuwa mai tsada,sau tari alhj yusuf kan karbi atamfofin daga hannun alhj dalhatu idan zai koma qasarsa nijer ya tafi da su ya saida,ko kadan alhj attahiru bai karbar kudin atamfofin daga hannunshi har sai ya siyar ya sake dawowa nijeria duk da cewa bawai baida kudin bane babu ma zancan matsalar kudi tattare da shi da kudinsa a hannunsa,tafi tafi sai Allah ya sanuyawa harkar atamfar tasa albarka wanda babu dadewa ya bude babban shago na atamfofi zalla,ba'a dauki wani dogon lokaci ba shagon ya karbu cikin garin diffa da sauran maqwaftan garin,don wani lokaci wasu tun daga dosso tillaberi niamy ko zinder zaga ga sun shigo sari,hakan ya sanya ya sake bude wasu shagunan cikin wadan nan garuruwan,wadansu nashi shi kadai wadansu kuma shi da alhj dalhatu ne. *Alhj dalhatu* Haifaffen qasar nijeria ne cikin garin kano qaramar hukumar kano municipal,kowa ya sani cewa 'yan cikin gari a kano irin unguwannin da suka hada zage,daneji,marmara aisami,qoqi makwarari da sauransu mafi yawancinsu kasuwanci shine babbar sana'arsu,to haka yake ga alhaji dalhatu shima kasuwancin ya gada daga wajen mahaifinsa alhj attahiru,alhj dalhatu shine da na hudu a gidansu a cikinsu su goma da Allah ya bawa mahaifinsu wanda yake da matan aure guda biyu,maza su shida mata hudu,wannan kenan. *alh bukar ibrahim* Shima haifaffen nijeria ne cikin garin maiduguri qaramar hukumar kwaya kusar,familynsa asalinsu iyali ne ga malam muhammad al'amin elkanemi wanda ake kira da shaihu laminu wanda asalinsu daga yankin larabawa ya fito ya zama kuma ya zauna a kukawa,babban malami ne da ya taimakawa barno tun zamanin da fulani suka zo yaqar bare bari,mutum ne da ya bada gudun mawa mai yawa cikin qasar borno baki daya,daga baya ne da zuri'ar tayi yawa aka samu sauyawar muhalli gun wasu daga cikin zuriyyar tasa. Shi din ma kasuwanci ne yake kawoshi kano,yana kusuwancin huluna ne cikin kasuwar kwarin,wanda ya zama tamkar shi dila ne na huluna,yana rabasu ga manya da qananun 'yan kasuwa,to shi din ma dai karamci da mutuncin alhj dalhatu yasa yake sauke kayansa a rumfar tasa kafin ya gama rabawa wanda zai bawa din,anan tasu tazo daya su ukun baki daya,alhj dalhatu alhj yusuf da kuma alhj bukar. Duk alaqar da aka ginata domin Allah to da ikon Allahn kuwa shike riqe da ita,babu wani abu da zai bata ta,hakanne kuwa ya kasance tsakaninsu,aminci mai sunan aminci,shaquwa mai sunan shaquwa da yarda da juna ita ta wanzu tsakaninsu,mutanen da suka sansu daga baya da yawansu sun dauka 'yan uwane na qut da qut,tunda ba zaka kallesu kace mahaifiyarsu daya ba saboda bambancin harshe da siffa. Shi alhj yusuf fari ne tas har yellow yake,sumarsa a kwance take kamar ta larabawa,hakanan harshensa ya dan karye wanda dole idan yana hausa ka fuskanci ba tsantsar bahaushe bane,yayin da alhj bukar ya kasance wankan tarwada,fuskarsa na dauke da tsagu qwaya daya daga hancinsa zuwa goshinsa irin na bare bari,shima alhj dalhatu baqine kamar yadda akasan ainihin kalar fatar bahaushe na usuli. A lokacin daga bukar har dalhatu babu wanda yayi aure a tsakaninsu sabanin yusuf da yake da aure a lokacin har matarsa ma na dauke da juna biyu wanda take 'yar garinsu ce yarensu kuma daya. Yau da gobe sai kasuwancinsu dukka yayi qarfi cikin kano,hakanne ya sanya tilas alhj yusuf ya dauko matarsa fatimatou suka dawo nijeria kuma cikin garin kanon tunda shi yafi alhj bukar nisa,alhj dalhatu yaso ya samu gida nan kusa da shi saidai hakan bata samu ba kasancewar yawancin cikin gari a cike yake,babu wani fili da zaka iya siya,saidai kasai gida ka rushe idan kana so kayi irin ginin da kake so,to ko samun gidan ma aiki ne don yawanci basa yarda su siyar din,ba don sansu ba ya samu gida cikin unguwar sharda mai kyau da girma ya ajjiye fatima a ciki. Basu cika shekara a nijeria ba fatima ta haihu ta samu yaro namiji,santalelen yaro kuwa wanda ya kwashe kamannin fulanin buzaye da kuma kakarsa rahinatu wadda ta fito cikin jinsin larabawa,jajir da shi suma har goshi,fafin irin murnar da alhj dalhatu da bukar suka nuna bata baki ne,kusan sunfi ma uban dan doki da murna. Sosai yusuf ya rufe idonsa shi da mai dakinsa fatima suka dinga yi musu gori don suji haushi suyi aure suma,don tace ta gaji itama tana da buqatar qawaye(wato matan da zasu aura din kenan)dariya suka dinga yi suna fadin su sha kuruminsu sun kusa ai. Allah bai nufi auren nasu ba sai bayan shekara biyar da haihuwar RAYYAN wanda yaci sunan mahaifin kakansa,kusan tsiran wata guda ne tsakanin auren dalhatu da bukar,dalhatu ya auri rabi'atu bukar ya auri fanna,duk da a maiduguri akayi bikin hakan bai hanasu zuwa ba dukkansu. Sai da suka shekara bibbiyu sannan sukayi haihuwar fari,rabi'atu ta samu UMMA RUMANA fanna ta samu RAIHANA,shekarar rumana hudu rabi'ah ta kuma haifa ,yusuf suna kiransa khalifa da abubukar(bukar) suna ce masa amir,fanna ma ta sake haihuwa ta haifi diya mace wadda zainaba,fatima ce tun daga kan rayyan haihuwar bata kuma tsaya mata ba,ta haihu sau hudu maza biyu mata biyu amma dukkansu mutuwa suke,tun tana damuwa har ta miqa lamarinta ga Allah,hakanne ya sanya ta janye umma rumana wanda ya kasance duka weekend din duniyaa gidan takeyi,bata komawa gida sai ran monday,idan aka daukota daga makaranta sai a wuce gida da ita sai kuma wani qarshen makon. Zumunci ne sosai tsakaninsu har ma da matansu da 'ya'yan nasu,musamman gidan alhj dalhatu da gidan alhj yusuf,kasancewar alhj bukhar sunyi nisa saidai saqon gaisuwa da waya a tsakaninsu. Sannu a hankali arziqinsu ke dada yalwata wanda hakan ya sanya tilas alhj bukar ya dawo kano shima kusa da 'yan uwansa a lokacin raihana da umma rumana na da shekara takwas a duniya rayyan na da sha biyar,unguwarsu daya da alhj yusuf saidai akwai 'yar tazara tsakaninsu. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *watpadd:huguma* © *haske writers asso*💡 (Home of expert and perfect writers) *Manzan Allah S a w yace:duk wanda yayi salati a gareni sau goma da safe sau goma da yamma cetona zai riskeshi ranar qiyama* _duba sahihut targib wat tarhib mujalladi na daya shafi na 372_ ____________________________ *Babi na uku* Mai glass shine sunan da rumana ta fara kiran raihana da shi da fari farkon tarewarsu,kasancewar da glass din raihana take zuwa makaranta saboda lalurar rashin ganin abun da ke can nesa da kyau da take fama da shi. Lokaci lokaci raihanan na zuwa gidansu rumanan,musamman idan abbansu ya kaisu ko kuma mamansu zata je,hakanne yasa suka dan saba da rumanan duk da rashin son magana irin na raihana,yarinyace da bata qiriniya ko rashin ji ko kadan,hakanan surutu bai dameta ba,iyakacinta da abu kallo sai ko murmushi,sabanin rumana dake da surutu rawar kai tsokana da rashin ji,hakan ya sanya tun a lokacin hajiya yaaya kakarsu rumanan wadda ta haifi alhj dalhatu tasu tafi zuwa daya da raihana,don lokaci lokaci itama suna zuwa mata Sam bata damu da zuwa gidan alhj yusuf ba duk da cewa suna kusa,hakanan ko rumana taje weekend bata damu da zuwa gidan ba,haj fatimatou takan alaqanta hakan da ko don bata da 'yar budurwa ne sai rayyan kadai dake gabanta. Yawan zuwan rumana gidan hakan na yiwa rayyan dadi da debe masa kewa,don lokacin ne yake samun abokin hira da wasa kasancewarsa ba mai son yawace yawace ba ya sanya bai da wani aboki,hakanan yanayin unguwar tasu ma bai wani jama'a ta cika ba,jama'ar da take da ita kuwa kowa na qule cikin gidansa ahi da nasa iyalin. Wannan shine musabbabin shaquwa mai qarfi da ta shiga tsakanin rayyan da rumanan,wanda har takai ta kawo odan bata zoba shi yana zuwa gidansu yayi weekend dinsa hankalinsa kwance kasancewar gidansu rumanan akwai yara ba kamar nasu gidan ba da yake shi daya qwal *dukkan mai rai mamaci ne* Wannan haka yake kuwa,domin alhj bukar bai wuce shekara daya da zuwa dawowa garin kano ba Allah ua yi masa rasuwa,a lokacin duka duka shekarun raihana tara a duniya. Hakan ya faru ne sakamakon hadarin mota da ya samu daga hanyar mai duguri zuwa kano,wanda dama yakan je garin nasu lokaci lokaci yaga dangi kuma ya karbo huluna gurin mutunen da yake siya a gurinsu,basu kai ga qarasowa ma cikin garin kanon ba lamarin ya afku,wanda sai gawarsu aka qarasa da ita asibitin koyarwa na malam aminu kano. Mutuwar ba qaramin girgiza zuriyar uku tayi ba baki daya,kada ma mai dakinsa alhj dalhatu da alhj yusuf suji labari,kai kace mahaifansu ne suka rasu,sunyi matuqar gigita,to amma ya aka iya da lamarin ubangiji tilas suka haqura suka rungumi qaddarar ubangiji. Bayan share makoki ne 'yan uwan fanna sukayi niyyar tafiya da ita amma alhj yusuf da alhj dalhatu suka kafe kai da fata kan cewa a barta a dakinta tayi takaba kamar yadda addinin musulunci yafiso,tunda dai gida na bukar ne mallakinsa ne,sanin irin alaqar da take tsakani suka janye qudurinsu ba haufi suka barta a gidanta tayi takaba,sun barta da 'yan uwa mutum biyu masu tayata zama. Cikin zaman takabar ta ta qara yadda da jadda da girman abota dake tsakanin wadannan mutane guda uku,don babu wani abu da wani cikinsu zai siya bai hada da gidan bukar ba,ficika basu bari an taba cikin dukiyar bukar din ba da nufin a ciyar da iyalinsa,babu abinda suka rasa bangaren ci sha sutura da buqatun rayuwa na yau da kullum,haka matansu ma kullum suna tafe,banda rashin mai gidan da sukayi babu wani rashi da suka dandana. Tana kammala idda kuwa suka dawo don tafiya da ita din,a nan ne su alhj dalhatu suka gabatar musu da buqatarsu na a bar musu raihana da zainaba zasu kula da su,mutanen nada qima da daraja a idonsu babu abinda zasu tambaya su kasa basu kamar yadda suka san ko bukar na raye bazai iya hanasu komai ba,sun amince zasu bada daya amma dayar saidai suyi haquri don dangin mahaifin bukar ma sun matsa suna son riqon. Ba yadda suka iya haka suka amshi raihanan don a son ransu a basu duka kowa ya dauki dai dai,alhj dalhatu shi yaso karbeta alhj yusuf yace haba ba za'ayi haka ba,kai da gidanka ke cike da yara,ni kuwa da muke mu uku daga ni sai fatima sai rayyan,ai a tausaya mana ko?,bai ja ba alhj dalhatun yace ba komai ya riqe din don da gaskiyarsa,amma fa shima ba za'a samu ladan babu shi ba,shi zai dauki nauyin karatun raihanan kamar yadda ya dauke na yaransa da rayyan ma baki daya,baice komai ba bayan godiya don yasan abotarsu tafi gaban haka don daga Allah take. Komawar raihana gidan alhj yusuf ita ta kawo komawar rumana ma baki daya ta bar yin weekends kawai ta koma ta din din din,hakan ba qaramin dadi ya yiwa raihana na don jininsu ya hadu sosai da rumana,tanason surutunta iyayinta da rawar kanta,sai ta sata gaba ta yita kallo tana bata dariya,haka ma hajiya fatima ba qaramin dadi taji ba,ganin an share mata hawayen yara da bata samu ba,ta kamasu qam ta riqesu,duk qwaqwqwafinka baka isa kace ba ita ta haifesu ba,tana matuqar ji da su. Hakanan rayyan sai yake jin shima yanzu gidansu akwai mutane ba kamar da ba da yake shi daya qwal,suka zama abokansa musamman rumana da shaquwarsu dama tafi qarfi kasancewar sun dade tare. Wannan shine tarihin wadan nan iyalai guda uku,gidansu RUMANA RAIHANA da kuma RAYYAN *mrs muhammad ce* 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *watpadd:huguma* © *haske writers asso*💡 (Home of expert and perfect writers) *An karbo daga usman dan affan R.A yace:manzan Allah S A W yace"duk wanda ya sallaci isha'i acikin jam'i tamkar yayi tsaiwar dare ne ta rabin dare,wanda kima ya sallaci sallar asuba cikin jam'i tamkar ya raya daren ne baki dayansa"* _muslim ne ya rawaito_ ________________________ *babi na hudu* Tafe yake da 'yar sassarfa har ya qaraso bakin get din gidan nasu,bai wani saurari a bude masa qofa ba ya tura 'yar qaramar qofar dake maqale da madaidaicin get din nasu,ba bata lokaci ya bayyana cikin 'yar madaidaiciyar harabar gidan nasu dake shimfide da interlock,wadda motoci uku kawai take iya dauka,duk da ba girma ne da ita mai yawan gaske ba amma sai ta baka sha'awa,don qawace take da shuke shuke da kuma wadatar tsafta. Tsaye suke cirko cirko bakin motar,daga raihana har rumana uniform ne a jikinsu,raihana na goye da jakar makarantarta daya hannun nata kuma riqe da lunch boxs dinta,yayin da daya hannun nata take riqe da lunch boxs din rumanan. Ita kuma rigimammiyar na sabe da tata jakar makarantar,kai maqale kan kafadarta tana sharbe qwalla. A hankali dariya ta subucewa rayyan,tabbas mai hali baya fasa halinshi,babu ko shakka yau ma darun tafiya makarantar akeyi da rumana. Ya qarasa inda suke tsaitsaye su da auwal wanda abba yusif ya daukeshi don kaisu makaranta duk sanda baya gari ko ya fita kasuwa da wuri,don yace rayyan yayi qanqata da driving tunda duka duka shekarunsa basu wuce goma sha shida ba. Tun kan ya qarasa ta hangoshi da gudu ta ratsa ta gefan motar ta nufeshi,ba bata lokaci ta maqalqaleshi tare da sakin kukanta baki daya "To ya isa?,me kuma aka yi miki rigimammiya?" "To yaya ba kaine ba,kayi tafiyarka bayan kasan da makaranta,kuma gashi ummu tace mu biyu yau zamu","amma dai rumana kinsan exams ke kaini makaranta kuma na gama nayi candy?,me kuma zanje nayi?"ta sake barkewa da kuka tana fadin" "Nima yaya na daina zuwa tunda ka gama,muyi zamanmu a gida"fuska ya dan hade don uasan darun mutuniyar tasa sarai,indai ba haka yayi mata ba ba za'a daidaita ba"a'ah,kina so muyi fada kenan?"kai ta girgiza tana kebe baki"good,me yasa kullum ke ke qin makaranta?,kin taba ganin rumana na kukan zuwa makaranta?"nan ma ta girgiza kai"kina son mu bata na daina yi miki magana?"da sauri ta sake sakin kuka tana bubbuga qafa tare da fadin"a'ah...a'ah"murmushi yayi a boye don yasan abinda tafi tsana ya fada kenan zai daina kulata. "Ok to daga yau kada ki sake cewa ba zaki je makaranta kina jina ko?"tace "to" "Promise?" Kai ta gyada kana yace "da kyau"ya miqe yana amsar lunch boxs dinta daga hannun raihana ya damqa mata,ya yiwa auwal magana ya bude motar ya kaisu,sai ta ja ta sake cogewa tana narai narai da ido. "Rumanaaaa...ya kuma akayi?" "Nidai yaya ka rakamu..makarantar babu dadi yaya" "Rumana baki ganin...." DA sauri ta katseshi ta hanyar bubbuga qafa da shirin wani sabon kukan"don Allah yaya". Baya son kukan da take tayi,kuma yasan halin rumanan da kafiya,hakanan kayan motsa jiki ne a jikinsa riga armless da boxer,idan yace zaya koma ciki kuma canzo kaya zasu makara ne kawai,don haka baice komai ba ya bude qofar motar yace raihana ta shiga,ta fara shiga rumanan ta shiga,yana shirin rufe murfin motar ta qiya dole shima bayan ya shiga,kafin sukai makaranta sai gashi baki ya bude tana ta zuba masa hira shi kuma yana biye mata tamkar ba ita ke faman sharar hawaye ba dazun. Bata yarda ta barsu sun koma ba sai da ya dauki alqawarin tare da shi za'a zo daukarsu,cikin motar ya dinga murmushi shi kadai yana tuna rigima irin ta rumana,shi kansa yana jinjina shaquwa irin tasu,shi yasa ko gidansu baya yadda ta tafi da zummar kwana saidai su tafi tare ko su yini su dawo ************* shigowarsa ta uku kenan yana tambayar ummu su rumanan basu dawo ba?,dubarsa tayi tana saka jug na lemon zobo da ta hadawa abba cikin freezer "Basu dawo ba,ina zaton kwana fa zasuyi,ka dauki abincinka kawai kaci,don ko sun dawo dare ya riga yayi,qila ma sunyi bacci" "Kwana ummu?" "Eh,da matsala ne?",ba mai yawan son jan zance bane sai kawai ya girgiza kai yace ba komai ya juya ya sake ficewa Tana zaune ita daya a falon, itama gidan ya mata shiru da yawa saijin sallamarsu tayi,rayyan ne a gaba riqe da hannun rumana wadda dankwalin after dress dinta ke hannu,kitson da suka tafi a yi musu acan gidansu gashinan rangadau a kanta,saidai idon nan yayi jazur da alamu kuka ta sha,raihana na binsu a baya saidai jikinta ba qwari ko bacci ta fara ya tattagosu?. Riqe baki ummu tayi tana duban rayyan tare da fadin "daga ina?" "Daukosu mukaje mukayi,lawan ya rakani"ido ta zare kana ta rufeshi da fada akan saboda me zaiyi haka?,tana cewa can ma gida ne kamar nan,kuma yau juma'a gone da jibi duka ba makaranta? "Kiyi haquri ummu,gobe da jibin ne kawai naga muke zama tare,ragiwan kwanakin duka suna makaranta"abinda ya iya fadi kenan ya zube saman kujera "Sai kace ba gid daya kuke kwana ba?ko weekend din cewa akayi ta qare ne,to naga yadda zakayi idan lokacin tafiyarka yayi"ta fada tana janyo wayarta ta nemo lambar hajiya rabi'ah maman rumanan ta kirata lumshe ido yayi, yayi shiru don ko maganar tafiyar baiso,idan banda baba muhammadou da ya matsa a gida zai qarasa karatunsa shikam. Gaisawa suka fara yi da haj rabi'ah kana tayi mata qorafin barin rayyan ya taho da su raihana "Daina bata bakinki hajiya,ko rayyan baizo ba dama komai dare nayi niyyar dawo miki da yaranki,nikam bazan iya da su ba,kuka ta zauna dirshan tanayi tana kiran sunansa qatuwa da ita kamar wata yayayya,taqi cin abinci ganin haka yasa raihanan ma ta kasa ci,a haka yazo ya taddasu nace su tafi Allah ya raka taki gona" Murmushi haijya fatima tayi"to ai shikenan,a gaida sauran yaran da abbansu" "Zasuji in sha Allahu,Allah ya bamu alkhairi" "Ameen sai da safe" Ta ajjiye wayar tana dubansu,wuni daya tak duk sunyi wani fiqi fiqi dasu su ukun baki daya,damuwar ayyan da rumana ta hada har raihanan duka,duk sai suka bata tausayi don tasan nan da dan qanqanin lokaci zasuyi mai dalili. Ba abinda ta kuma cewa da su illa kitchen da ta shiga kai tsaye raihana ta bita a baya ta tayata daukar plate ta hado musu abincin ta ajjiye musu,tana gefe tana kallonsu har suka kammala *mrs muhammad ce* 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga Abu Hurairah R.A yace:Manzan Allah S A W yace"dukkan al'ummata zasu shiga aljanna,saidai wanda yaqi"sai sahabbai sukace:ya manzan Allah,waye zaiqi?,sai annabi yace"wanda ya bini zai shiga aljanna,wanda ya saba min kuwa wannan shi yaqi"* _imam bukhari ne ya rawaito_ _________________________ *babi na shida* "Hala fushi ake da yaya rayyan kenan,shine aka hade masa kai"shiru dukka sukayi,murmushi ya sake yi ya kama hannayensu guda dai dai ya riqe yace"kun sani bana son ku dinga wasa da karatunku,ilimi abune mai muhimmanci,shine yake banbanta tsakanin mutum da dabba,amma ayimin afuwa ko?,kada yaya rayyan ya tafi ana fushi da shi,an yimin afuwan?" Ya fadi yana dubansu,raihana ta fara murmushi ta gyada kai sannan rumanan itama tayi"good"yace kana ya dora"inason inga kun dage sosai kun maida hankali ga karatunku,kun fahimceni"suka gyada kai a tare"ok,yanzu ku yimin alqawarin zakuyi karatu sosai babu wasa koda yaya rayyan baya nan" "Munyi alqawari ya rayyan" inji raihana "Eh yaya zamuyi" inji rumana "Yauwa 'yan qanne na,ni kuma idan na tashi dawowa kowacce zan siya mata tsaraba mai yawa indai naga kun dage din". Zo kaga murna gurin rumana har da tsalle,hira ya dinga jansu da ita suna tayashi qananun ayyukan da zasu iya,a haka suka ware _washegari_ cikin motar abba sienna suka shirya yin tafiyar tare da auwal,idan abba ya gaji da tuqi auwal din ya karbeshi,anyi haka ne saboda raihana da rumana wadanda basu da passport,duk da cewa abba yayi alqawarin yi musu saboda gaba. Raihana rumana da rayyan na can seat din bayan,rayyan ya biyewa surutu da rawar kan rumanan sosai,saboda yana jin kamar suna sallama ne,cikin jikinsa kewarta kawai da wani yanayi maras dadi ke ratsashi,yasan ba zaya samu tamkar qannen nasa ba Tafiya ce miqaqqiya,tun suna hira su ukun har raihana tayi bacci ta barsu,a hankali itama rumanan baccin ya dauketa suka bar rayyan din shi kadai *_jamhuriyya nijer_* Ba qaramin murna da zuwan iyalan yusoufu cikin masarautar akayi ba,don sun dan jima rabon da suzo dukkansu ,kasancewarsa mutum mai taimakon da son jama'ar masarautar tasu hakan ke qara qaunarsa cikin zuciyar iyaye da 'yan uwansa Sati guda sukayi suna yawo cikin garin diffa da qauyukanta,gidajen 'yan uwa da kakanni,sosai suka sake suka manta ma da tafiyar yayan nasu. Kwanansu goma kawu muhammadou ya iso,saboda haka yace nan da kwana uku zasu wuce *********** Qarfe goma sha daya da kwata na safiyar ranar a airphort din tayi musu,motoci biyu sukayi don rakiyar rayyan din,baya ga motar dogarai daya da ta barorin hajiya rahinatu itama guda daya Jiki a sanyaye suke tafiya yana riqe da hannun rumana da raihana,abbanshi da ummu na biye da su,sai kakarshi rahina da kawunsa alhassan da d'an kawun nasa hamza wanda kusan sa'anni suke,hakanan alhj dalhatu ma ba'a barshi a baya ba,har nijer din yayo tattaki a daren jiya ya biyo jirgi don ganin tafiyar rayyan din,sai da suka qaraso inda babu dama su shiga sannan ya saki hannayensu. Juyowa yayi yana dubansu,badon dakiya da yayi ba babu abinda zai hanashi fitar da qwalla,gaban ummun ya fara zuwa ta masa addu'a sosai sannan ya wuce gun alhj dalhatu kana ya wuce gun abbansa ya dire gaban kakarsa,duka addu'a ce da nasihohi da suka masa tare da fatan alkhairi. Ya tako a hankali ya qaraso gaban qannen nasa,kuka sosai rumana take yayin da raihana ke sharar qwalla,tabbas sabo turken wawa ne,hannayensu ya kama sannan yace "Ba kuka zaku yimin ba addu'a zaku yiwa yayanku,ya kammala karatunsa da sauri cikin nasara ya dawo gurinku kunji ko?" Sautin kukan rumana ya kasa boyuwa sai da ya fito fili,kama hannayenta yayi yana fadin "Rumana......"katseshi tayi ya hanyar cewa " yaya,mu kadai kenan zaka bari,mun koma daga ni sai raihana a gida?" "Yaya rayyan,shikenan yanzu ba wanda zai dinga yi mana karatu ko labari?" Inji raihana. Duk yadda yaso ya daure sai da yayi qasa da kansa yana jin idanunsa na tara qwalla amma yayi qoqarin maidasu "Ku yiwa ya rayyan addu'a kamar yadda nace kunji bana so......" Kafadarsa yaji an dafa daidai lokacin da sanarwar neman masu tafiyar ta karade ilahirin filin jirgin,alhj dalhatu ne da suke kira daddy,gefansa kuma kawu muhammadou ne "Rayyan,wuce ka tafi kada su bata maka lokaci,Allah ya bada sa'a yasa anje a sa'a" tilas ya miqe din kana ya saki hannayensu ya juya. Gefan rigarsa yaji an riqe,ya waiwayo a hankali yana dubanta,rumana ce fuskarta jiqe da hawaye"yaya rayyan" "Na'am" ya amsa mata da sauri "Naji ance idan mutum sukayi aure nasa rabuwa da matarsa?" kusan sai da ta bawa kowa dariya a gun da mamaki,da sauri rayyan din yana murmushi ya gyada mata kai"eh haka ne" "To me yasa ba zaka auremu ba ka tafi da mu kawai" dariya ta sake basu baki daya ciki kuwa har da raihana,tabbas akwai quruciya mai yawa tattare da rumanan,rashin sanin ma meye auren da muhimmancinsa baki daya ya bayyana tattare da ita. Saidai lokaci guda baki dayansu hankalinsu ya koma kansi rayyan din lokacin da sukaji yana bata amsa"saidai na aureki ke kadai?,kina so?"murmushi ta saki cike da quruciya tana gyada kai"eh ya rayyan ina sonka" "Kina sona?" "Eh" "Nima ina sonki,zan aureki amma kinsan yaushe?"da sauri ta shiga girgiza kai tana kallonsa"na farko sai kin daina kuka yanzu kita yimin addu'a har na dawo,idan na gama karatu na dawo,na tadda rumana bata wasa da karatu,ta dagewa karatu,ta daina wasa kinga shikenan",hakanan yaji maganar na fita daga can cikin zuciyarsa tamkar a ire iren litattafan da yake karantawa,ya samu kansa da tsare rumanan da ido don yaji me zata ce,dan jim tayi don ta fuskanci baza'a iya auren a yanzu kuma a tafi tare ba,kamar tace a'a sai kuma ta fasa,cikin murmushi tace" na yarda ya rayyan" "Ok,na faara gani tun yanzu" da sauri ta fara goge hawayen fuskarta tana fadin"a dawo lafiya ya rayyan"kai ya girgiza sannan ya miqe,bai iya juyowa ya sake dubansu ba gudun kada zuciyarsa ta karaya,kawu muhammadou ya kama hannunsa sukayi gaba. Tun suna hangosu har suka bace musu,yayin da rumana tayi saurin cusa kanta a kafadar raihana tanason boye kukanta wai don kada ta karyawa yaya rayyan din alqawari,da qyar ummu ta lallashesu kana ta kamasu suka nufi gun motocinsu don komawa gida Cike da mamaki suke tattauna maganar tsakanin alhj dalhatu da alhj yusuf"ina zaton akwai wani al'amari mai girma tsakanin yaran nan alhaji" "Ko ba rayyan da rumana ba?" Cewar hajiya rahinatu kakar rayyan din "Eh sufa hajiya" inji abba yusuf"murmushi alhj dalhatu yayi kana yace"ni kam dama na dade ina suranta wannan tunani cikin raina,ashe bani daya nake ganin hakan ba"murmushi itama hajiya rahinatu ta saki sannan tace"mu din ma gashi da muke nesa da ku yau mun gani,ja'irai harda alqawarin soyayya da aure kamar wasu manyan matasa"dariya hajiyan ta bawa alhj dalhatu da alhj yusuf din baki daya "Ai hajiya ina zaton wannan alqawari kuwa sai mun tabbatar da shi da izinin Allah,tunda juma'ar da zatayi kyau ai tun daga laraba ake ganeta,da alamu akwai abinda Allah ya dasa cikin zukatansu,qanqantar shekaru yasa basu ganewa mu din ma haka,sai Allah ya bar abun ta fuskar shaquwa,ko ya kake gani dalhatu?" "Alhamdulillah,ai bani da ta cewa yusuf,da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne,ni kaina kana da iko da ni balle rayyan ko rumana,Allah ubangiji ya tabbatar mana da alherinsa,ko ba haka ba hajiya" ita din ma cikin burgewar abota irin tasu take gyada kai cike da gamsuwa"qwarai kuwa,fatanmu idan da alkhairi a al'amarin Allah ya sake hade kansu sosai" "Ameen hajiya,ina zaton kafin rayyan ya dawo hankali ya gama gamesu,don a yadda kawu ya nunan koda rayyan ya kammala karatun yana da ra'ayin riqeshi zuwa lokacin da zai mallaki abun hannunsa" "Eh nima haka mukayi maganar da shi,Allah ya zuba masa qaunar rayyan duka cikin jikokin gidan nan,ko da yake dai bashi kadai ba,kusan duka cikin masarautar babu yaron da yayi irin farin jininsa"cewar hajiya rahinatu " ai hajiya rayyan yarone na gari,dole ka soshi idan ka zauna da shi ko dan qanqanin lokaci ne"cewar alhj dalhatu,daganan suka zarce da zancan rayyan din har zuwa wani lokaci suka kawo gida *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* *watpadd:huguma* _______________________ *An karbo daga abu hurairah R.A yace:Manzan Allah S.A.W yace"mala'iku sunayin salati akan dayanku,matuqar yana zaune a inda yayi sallah bai tashi ba kuma baiyi magana ba,suna cewa:ya Allah ka gafarta masa,ya Allah kaji qansa kayi masa rahama"* _imam bukhari ne ya rawaito_ ________________________ *babi na bakwai* Kwana uku suka qara a nijer din don qarasa ziyarce ziyarcensu da basu kammala ba suka dawo qasata nijeria gida kanon dabon. To duk yadda suka tsammaci kewar rayyan abun ya wuce haka,ba rumana ba ba raihana ba,hatta ummu da abba sun shiga sawun kewar rayyan din,sai a lokacin suka qara banbance shaquwar dake tsakanin ahalin gidan. Wasa wasa sai da rumana tayi sati kwance tana taba zazzabin rashin rayyan din,yayin da raihana ke mara mata baya wajen tayata kwanciya da rashin walwala,a haka ummu ta dinga qoqarin daidaita lamuran gidan ta yadda zasu dawo suci gaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba a baya. Ba'a samu sauqin lamarin ba sai da rayyan din yayo waya,rumanan taji muryarsa ya kuma sake jadda da mata cewa lallai ta daina damuwa sannan lamuran suka fara daidaita. Kusan kullum rayyan din yakan kira sau biyu sau uku a rana,safe rana dare,suna gaisawa da kowa,saidai yakan bata lokaci mai yawa tare da rumanan fiye da kowa cikin gidan,sannu a hankali itama sai ta fara koyon waya,abinda da bai dameta ba,dabi'a ce ta raihana,zakayi mamakin yadda ta iya sarrafa waya,ko bai kira ba zata faki idon ummu ta dauki wayar ta kirashi su sha hira yana biyewa shirmenta,saidai ummu ta laluba account din wayarta ta taradda 0.00,indai taga haka to tasan ranar mutanen england sun sha hira kenan. *********** Sannu a hankali kwanaki suka dinga jujjuyawa suna haifar da nisan al'amura da kuma maida abu ya zama tarihi. Hakance take kasancewa ga kowanne bawa,tamkar dai iyalan gidan abba yusuf,wanda zuwa yanzu su rumana sun fara sabawa da rashin ganin ya rayyan din nasu,duk da koda yaushe suna tare a waya,indai kaji shiru to babu shakka karatu ne ya sha masa kai. ************ _*Bayan shekara takwas*_ Bakayi kuskure ba ta wani fannin idan ka kirasu da *'yan biyu* ko *tagwaye*,saidai ta sun sha banban ta wasu fuskoki da dama,zaifi kyau a sauqaqe ka kirasu da *AMINAN JUNA* RAIHANA yarinya matashiya mai kimananin shekara goma sha tara babu watanni,yarinya ce mai sanyi tun daga kan maganganunta halayenta da life style dinta. Launin fatarta zaka iya kiransa da ruwan qasa wato kalarnan da ake kira da chaculet colour mai kyau da bin jiki,irin launin fatar garinta na haihuwa wato maiduguri,tana da baiwar suma wadda hakan ya bayyana hatta a girarta wadda take a cike kamar yadda gashin idonta yake wanda koda ta saka *MEDICATED GLASS* baya boyuwa,cikar girarta ya sanya suka hade,har wani lokacin rumana kan matsanta mata tace ta bari ta gyara mata,bata da qiba kuma ba ramammiya bace,kamar yadda ba zaka ce da ita doguwa ko gajera ba,medium ce,a murje jikinta yake tana da diri wanda baya iya boyuwa,hancinta mai tsaho ke da tudu ba irin siririn nan ba. Shigarta a koda yaushe ta doguwar riga ce,walau atamfa ko leshi,shadda ko material,mawuya cine ka sameta da riga da skert,duk da tana da su daidaiku wadanda rumana ke tilastawa a dinka mata,riga da wando kuwa saidai na pakistan. Komai nata natural ne,bata fiya damuwa da qyale qyale ba,tafi maida hankalinta kan abu mai quality da nagarta,ma'abociyar karance karance da binciken sabbbin abubuwa,wadanda wasunsu sun shafi qasarta da al'ummarta,yayin da waasnsu sukan shafi rayuwar al'umma walau daidaiku ko a jimlace. Murmushi kusan shine amsarta cikin magana,bata fiya surutu ko doguwar magana ba matuqar ba cikin gida bane cikin wadanda ta saba da su ko familynta ba,a yanzu haka tana shekarar ta ta farko a jami'ar bayero dake kano,inda take karantar law islamic law, RUMANA matashiyar budurwa wadda shekarunta yake daya da na raihana,tazarar dake tsakaninsu bata wuce satittika ba,yarinya ce mai fara'a,faran faran da saurin sabo da jama'a,yawan surutu da rawar kai da son hira,ma'abociyar son yin sababbin qawaye da abokai,matashiya mai son yin rayuwa mai kyau da burgewa. Rumana na da hasken fata,duk da cewa ba fara bace qal,amma kai tsaye zaka iya kiranta da farar mace,don ta dan debo launin fatarau ta fulani,tana da zagayayyar fuska mai dauke da dogon hanci,cikakken gashin gira da na ido har ma da sumar kai,idanunta ne basu cika girma kamar na raihana ba dake da manyan idanu,ta zarta raihana tsaho da kadan amma ba lallai la gane hakan ba,bata da qiba kamar yadda take na siririya ba,saidai duk da haka raihana ta fita cikowa. Dinkunanta basa wuce riga da skert don ko kusa bata son daura zani,don har raihana ta fita daura zannuwa,saita riqe ne zata yiwa raihana kara a yimata doguwar riga ita din ma fitted gown,to anan zakaji kansu,don ita raihana ta tsani fitted gown a rayuwarta,tana son english wears don haka lokaci lokaci tana sanyasu,saidai ba masu fidda tsiraici bane. Rumana akwai son kwalliya da qale qale,duk wani abun yayi na zamani mai aji ba gama gari ba zaka rasashi a gun rumana ba,haka duk arahar abu indai qyale qyalensa yayi mata to zata siya tayi amfani da shi. Ma'abociyar ta'ammali da kafafen sadarwa na zamani ce,don zaka sami charting kala kala rumana nayi,kamar facebook,watsapp,snapchart,instagram,palmchart da dai sauransu,hakanan ta bangaren kallan fina finai ba baya bace,kama daga na gida nijeria kudu da arewa dama na qasashen qetare Indai ka zauna tare da rumana dole ta sanyaka surutu ko bakayi niyya ba,dramer su kenan kullum da raihana,don sam bata yadda ta zama kurmar qarfi da yaji ba,hakan ne ya sanya take da tarin abokai da qawaye ciki da wajen makarantarsu. Ita din ma b.u.k take zuwa saidai sun banbanta a coarse,ita rumana na karantar mass communication ne. Sun hadu ta bangaren tarbiyya,tausayi jin qai da qaunar junansu kamar ciki daya suka fito,sai turaruruka da da wasu daga takalma gyalalluka da mayafai iri daya da suke amfani da su,walau a kamfani daya ko kuma masu kaloli iri guda,hakanan wani lokaci ra'ayoyinsu kanzo daya kan wani batu yayin da wani lokaci yakan saba. ************ Ta kusa a qalla mintina goma zaune gefan gadon tana zaman jiranta,yayin da ita kuma take ci gaba da makeup dinta kamar ma babu wanda ke zaman jiranta. Zaro wayarta tayi ta shiga danne danne cikin zuciyarta tana ayyana ta qara mata minti biyar taga gudun ruwanta,tana shafa jambaki ta mudubin rumana ke kallon raihanan wadda kanta ke duqe bisa screen din wayarta,dariya ta kusa kufce mata,tasan sarai ta gaji da zaman jiran amma ba zata iya bude baki ta mata masifa ba,sau tari hakan suke sai ranar data qureta. Har ta cinye mintinan rumanan bata kammala ba,sai kawai ta ciro glass dinta tasa tissue ta qara gogeshi ta maidashi kan fuskarta,ta miqe tsaye bayan ta jefa wayarta cikin hand bag ta kulle,mayafinta ta dauka wanda ya dace da kayan jikinta tana yafawa ta dubi rumanan,kamar zata ce wani abu sai kuma ta nufi qofar ficewa a dakin. Da sauri rumana tabi bayanta ta kamota,dariyar da take boyewa ta kufce mata "Sorry my blood sis,ai kece wlh kinsan banason wannan kurmantakar taki,ki bude baki kice rumana kiyi sauri amma ba zaki iya ba,kin zauna kin tasani gaba" "So kike na rufeki da duka?" Ta tambayeta hannayenta goye a qirjinta "Nop" rumanan ta bata amsa tana komawa ciki don ciro kayan da zata sanya din "Saif ne ya tsaidani wallahi,shi yasa bana son ya kirani idan ina da abunyi" ta fada tana zaro kayan,daga kai raihana tayi ta dubeta ta cikin glass dinta,sai ta dan bita da kallo,kamar ta tanka sai kuma ta fasa taja bakinta ta tsuke,tana tsaye rumanan ta gama shiryawa a gaggauce,don ko dankwalinta bata samu ta daura ba a hannu ta riqeshi suka fito daga dakin. A zaune a falo suka tadda ummu suka yi mata sallama,ta basu kayan da zasu kaiwa hajiya babba surukarta,wanda kilishi ne da zuma sai dambun naman kaza,don unguwar qoqi gidan kakannin rumanan suka nufa. Tuni auwal direbansu tun na quruciya ya gama gyara parking su kawai yake jira,rumana ta fara shigewa sannan raihana ta mara mata baya "Kayi haquri don Allah yaya auwalu,mun barka kana ta jira" cewar raihana lokacin da take rufe motar,dariya yayi yana tada motar"ba komai anty raihana,nasan daga inda matsalar take ai"ya fada cikin son tsokanar rumana,ta dagoshi kuwa,kuma bata iya yin shiru ba "Eh nikam saidai haquri,tunda nace banayi ba shikenan ba,uwar garkenka dai ta isheka" ta fada itama cikin salon wasa da yake mutum ne mai barkwanci sai biyu ta hadu,nan kuwa suka fara sana'ar tasu raihana na jinsu bata tanka ba har zuwa wani lokaci kafin suyi shiru sanadiyyar kiran wayar rumana da akayi. Juyawa tayi tana sake kallon rumanan lokacin da take rufe murfin wayar suka hada idanu,har rumanan ta dauke kanta sai ta kuma juyowa ta dubi raihanan"madam wannan kallon nasan da magana a bakinki,fadi kar ta kasheki"kamar ba zata tanka din ba sai kuma ta fuskanci rumanan sosai cikin sanyin muryarta "Dazu saif ya kiraki,yanzu kuma ibrahim,anjima kuma ina da yaqinin salis ko wani daban zai sake kiranki"dariya rumana ta fashe da ita" abun naki kuma ya koma sharri mss raihana?",kai raihanan ta girgiza"ba batun sharri ko kadan,gaskiya ce...rumana,duka wadan nan,gefw guda ga yaya rayyan....shin ina shi zaki kaishi?". Lumshe ido rumanan tayi gami da runguma hannayenta aqirji,ta saki ajiyar zuciya fuskarta qunshe da murmushi"haba,har kin sani a wata duniya daga ambatar sunan rayuwata,me kike tsoro?,rayyan jini da tsoka da kuma jijiya ne,kuma mijin aure na da yardar Allah,duka wadan nan dama wasu da kike lissafawa mutunci ne kawai tsakaninmu,friendship ne ba wani abu ba,temporary ne su"lumshe ido raihana tayi ta kuma bude duka lokaci guda "Rumana....ki fahimceni....babu wata alaqa tsakanin mace da namiji mai sunan abokantaka data wuce soyayya,ko ke ba haka bane cikin zuciyarki su na tabbata haka ne a zuciyarsu"dariya ta danyi "Babe wannan ba fagenki bane bafa,ko na miki bayani ba fahimta zakiyi ba,tunda ke dubeki,budurwa mai kyau da aji amma ba wanda kika taba budewa zuciyarki ya shiga,a rufe take ruf,kinga kuwa kona gaya miki...ba zaki fahimceni ba". Ci gaba tayi da kallonta ba tare da tace mata komai ba,daga bisani ta dauke idon daga kanta tana jijjiga kai,can qasa tace" Allah ya kyauta miki rumana"dariya ta saki tana kama hannunta"ni da ke my sister,na gaji so nake naga wane mai sa'ar ne zai samu nasarar daukar wannan 'yar uwar tawa"murmushi raihanan ta saki ba tare da ta shiryawa hakan ba,tasan da biyu rumanan ta fadi hakan don taji amsar da ta saba bata ko da yaushe,saidai taqi bata irin amsar a yau face shiru da ta bita da shi,itama rumanan taso tace wani abu don ta samu space din shigar mata da maganar al'ameen daketa kama qafa da ita. Da wannan suka iso unguwar qoqin *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* __________________________ *An karbo daga nana Aisha 'yar abubakar saddiq R.A tace:Manzan Allah S A W yace"duk wanda yakeson haduwa da Allah to Allah zai so haduwa da shi,duk kuma wanda yake qin haduwa da Allah to Allah zai qi haduwa da shi,sai nana Aisha tace:amma dukkaninmu muna qin mutuwa,sai annabi yace"abun ba haka yake ba,saidai shi mumini idan akayi masa bushara da irin ni'imar ubangiji(da ya tanadar masa)sai yaso(yayi begen) haduwa da Allah,amma kafiri idan aka masa bushara da azabar ubangiji(da ya tanadar masa)sai ya guji haduwa da Allah,to shima sai Allah ya qi(guji/qyamaci)haduwa da shi* _bukhari da muslim ne suka rawaito_ ___________________________ *babi na takwas* A bakin qofar gidan auwalu ya tsaida motar"qarfe nawa zaku koma sai na dawo na daukeku?"ya tambayi su raihana dake shirin fita a motar,agogon dake daure a tsintsiyar hannunta ta duba kana ta dago ta dubeshi"kada ka damu yaya auwal,idan muka bar nan ba gida muka nufa ba,zamuje wankin kai,amma ka tadda mu can inda muka saba zuwa,kamar qarfe biyar na yamma,ina tsammani kafin lokacin mun kammala"kai ya gyada yana tada motar "To shikenan,kuce ina gaida hajiya babba din" "Ba wanda zai gaya mata tunda baka shigo da kanka ba" inji rumana tana masa harar wasa "Ko baki fada ba qanwata raihana nasan zata fada" murmushi raihana ta saki kawai ta shige gaba rumana nabin bayanta tana mata hira. Tsarin ginin irin tsarin asalin ginin gidan bahaushe ne da muka sani,wato gida mai dauke da dakali hauni da dama daga qofar gidan sai zauruka guda uku da zaka wuce kafin ka isa ga ainihin tsakar gidan,fes ginin yake mulmul shafe da fenti ruwan madara,tamkar sabon gini,tsakar gidan ma mulmule yake da sumunti da ya shafu yayi kyau,hakanan fes yake gidan a share ko tsinke babu,duk da ranar da take a take,saboda sha biyun rana tayi a lokacin Dakuna ne ke kalloka guda biyu da ka shigo gidan,dukansu masu dauke da qofofi irin na zamani masu fadi masu qofa biyu,ciki da falo ne manya da bandakuna a cikinsu,wadanda suka wadatu da kayan more rayuwa daidai da tsofin masu gidan,daga hannun dama kuwa wasu dakunan ne falle daidai guda hudu,uku spare ne daya kuma jikokin gidan da ake riqo ne su hudu,duk da baka raba gidan da jikoki masu kwana biyu kwana uku da masu zuwa hutun makaranta,biyu samari ne wadanda dakunan sa na zauren na biyu na gidan,biyun 'yammatan kuwa daya dakin suke amfani da shi,hannun dama kuwa kitchen din gidan ne qato da shi,kitchen ne irin na zamani,sai bandakuna biyu na wanka da na toilet sai store din gidan daga can gefe guda,wannan shine tsarin gidansu alhj dalhatu wanda Allah ya yiwa mai gidan rasuwa shekara goma baya,amma iyalan na zaune cikin hadin kai da zaman lafiya. Sallama sukayi kana suka nufi dakunan kai tsaye,daga kitchen aka leqo aka amsa musu,baba ramma ce,itace mai musu girkin rana da na dare,sai kuma wanke wanke,ba wata tshohuwa bace,don ba zata haura shekara arba'in da biyar ba,ta jima agidan tun kafin rasuwar alhj attahiru mahaifin alhj dalhatu. Dakin hajiya qarama abokiyar zaman haj babbar kakar rumana suka soma leqawa,tana kashingide tana qailula don haka basu tasheta ba tunda ba tafiya zasuyi da wuri ba,suka juya suka shige dakin hajiya babba. Tana zaune qasan tiles,ta miqe qafafunta tana gurza gori fari sol jikin magogin qarfe,daga kai tayi tana amsa musu sallamar,da gudu rumana 'yar tsalle kamar yadda hajiya babba ke kiranta tayi halin nata,wato rugawa da gudu ta fada jikinta tana juye juye tare da fadin"yar tsohuwa mai ran qarfe,Allahk kasheki musha gumba"dogon salati hajiyan taja,bayan ta dire tace"dagani don qaniyarki,gyatumarki ce zata mutu bani ba,yanzu ace har yau 'yar tsalle baki bar tsalle tsallenki ba...to dagani tun kafin nasa tsohon qashina na maujeki"janye jikinta rumana ta fara yi tana muzurai"kajifa,ke sai ki damu kan kin dade bakiga mutum ba,amma da zarar yazo kuma saiki gallabeshi,gobe ma rana ce" "Ta jibi ma ta fita don gidanku" ta bata amsa tana watsa mata daquwa,"ni dama bake na nema ba,kinga wadda na nema nan"ta fada tana nuna raihana da baki wadda ke kallonsu tana murmushi kadan kadan tare da tuno nata kakannin da sai tayi wata da watanni bata gansu ba,kai wani lokacin ma har shekarewa take yi. Qwafa rumana taja"kinji ko raihanah,daga yau kada ki qara cewa nazo na rakaki tunda abun haka ne"ta fada tana janye jikinta ta koma saman kujera tana latsa wayarta da alama an fara sana'ar kenan "Ke kika jiwo sautin kidan mahaukaciya.....raiihana" hajiya babba ta fada tana dubanta,fuskarta qunshe da murmushi ta sauko daidai qafar hajiyan cikin girmamawa ta rusuna tana gaidata,cike da kulawa ta amsa tare da tambayarta mutanen gidan,hajiya babba nason raihana,tun tana qarama tun kafin rasuwar mahaifinta alhj bukar takeson yarinyar. Ta miqawa hajiyan saqon ummu tana karbar goron da magogin tana ci gaba da gogawa hajiyan,sosai tayi farinciki da saqon tana cewa"oh,fatima basa gajiya,to Allah ya bar zumunci,Allah yayi albarka"kadan kadan suke hirarsu da hajiyan,yayin da rumana ma sam batajin me suke fada,ta nitsa cikin chart da qawaye da abokai,hajiya ta dauka fushi tayi,yayin da raihana tasan ta cikin da bai sarai tasan me ya sanyata shiru da nutsuwa haka. Baba ramma ce ta katse hirar tasu ta hanyar yin sallama tare da shigowa da kulolin abincin rana,hajiya tayi mata sannu kana ta tambayeta taji shiru hajiya qarama ko lafiya?,ta sanar mata bacci tayi amma yanzu ta farka sallar azahar,jin haka yasa rumana ta miqe ta nufi dakinta,don a can ne take samun damar cin karenta babu babbaka,don haj qarama kam ba ruwanta. Tana fita qofar dakin haj babba ta saki ihu gami da yin kan kausar jikar gidan da ake riqo,mutuniyar rumana ce sosai sakamakon hali da yazo daya. Da sauri hajiya babba ta fito tana zaton ko wani abu ne ya samu rumanan tana ambatar subhanalla,hajiya qarama ma dake salla ta shiga gaggawar sallamewa. itama gun shukran gun rumanan tayo suka rungume juna tana tambayar yaushe suka zo suka bar hajiya babba da kama baki tana tafa hannu hadi da salallami kana ta juyo cikin dakin baki bude tana fadin"anya raihana 'yar uwar nan taki babu motsi bisa kanta kuwa?,bari dai dalhatu yazo naji"wannan karon sai da hajiyan ta bawa raihana dariya,ta dara kadan har sai da fararen haqoranta suka bayyana "Lafiya qalau fa take hajiya,me zaya sameta" "Um_um raihanatu ina tantama". Koda hajiya qarama ta leqo taga meke faruwa ita din ma komawa dakinta tayi tana fadin" Allah ya sawwaqe muku,ko yaushe zaku girma oho"kasancewar duka tasan halinsu,da rumanan jikar hajiya babba,da tata jikar wato shukra,basu bi ta kanta ba sai rabe ta da sukayi suka wuce uwar dakanta suka baje hirar da suka saba koda yaushe. Tun suna jiran rumana don suci abinci har hajiya babba tace raihana ta barta ta zuba musu suci,qila suna can sunci ita da abokiyar sakarcin nata,itadai raihana murmushi kawai tayi,don ita babu baqo cikin halayen rumanan da ta gani. Sai da taga hudu saura babu motsin rumanan, hakan ya sanya ta miqe tace zata leqa dakin hajiya qarama ta tuna mata qarfe hudu zasu tafi saboda wankin kan da zasu biya,ko da ta shiga hajiya qaraman kawai ta tarar zaune,ta sanar mata ai tun qarfe uku suka fice ita da shukran don haka ta juya ta koma daki,har hudu basu dawo ba don haka tayi kiranta "Ina kuka shiga ne lokaci na tafiya zamu saloon" "Bari kawai sis,muna cikin nasarawa,shukra na raka wlh" "Kika rakata ina?" "Kedai share kawai,new catch tayi sis sai nazo zaki sha labari" tsaki taja a ranta tana fadin"Allah ya sawwaqe muku" "Kiyi sauri dai kawai" "Kada ki damu muna hanya" Ganin har biyar na neman yi babu rumanan ba dalilinta yasa ta tura mata texs na ta tafi su hadu kawai a can,ranta ba dadi sukayi sallama da hajiya babban don ta tsani tafiya ita kadai inda ta gaya mata zasu hadu da su a can,fada sosai hajiyan ta dinga kan don me zasu zo tare ta fita shegen yawo ta barta ita daya,murmushi kawai tayi "ai ba komai hajiya,tare zamu koma gida", kayan amfani irinsu kuka kubewa karkashi da man shanu hajiyan ta baiwa raihanan tace ta kaiwa fatiman,tace tana gaidata,ita kuma ta dauko atamfa novou ta bata,godiya tayi mata kana ta leqa ta yiwa hajiya qarama sallama,itama fadan ta dinga amma ta gaya mata abinda ta gayawa hajiya babban,ita dinma kyautar humra ta bata 'yar matsakaiciyar kwalba,hannu biyu ta karba ta mata godiya. A hankali ta dinga takowa cikn nutsuwa kanta a qasa har ta iso bakin titin unguwar ta fara tsimayen adaidaita sahu,bata yi minti biyar da tsaiwar ba farar motar ta giftata,a hankali ta dinga rage gudu har ta gangara gefan titi ta tsaya kana ta fara ribas ta dawo da baya,sam bata ma lura ba don idonta na daya gefan tana duban motocin hayar dake wucewa. A hankali aka sauke glass din motar mamallakinta ya bayyana,matashin saurayi ne wanda yayi amanna da zamani yake kuma amfana da shi,sanye yake da qananun kaya da hular feecap " ranki ya dade"taji an ambata,a hankali ta maido kanta gun,ta dubeshi ga zatonta ba da ita ake ba,amma ganin irin kallon da ya tsareta da shi yasa itama ta dubeshi na 'yan sakanni "Ko zaki iya min alfarmar shigowa na rage miki hanya?" Ya fada yana dubanta fuskarsa dauke da murmushi,gabanta ke dukan uku uku,haka take tun fil'azal,duk lokacin da wani namiji ya tsaidata ko ya furta kalmomin so ko qauna a gareta,ita kanta tasan 'yar qauyece futuk ta wannan janibin,bata iya zance ba balle akai ga soyayya,hasalima bata taba tsayawa da wani d'a namiji ba da sunan so,tsabar rashin sabo da lamarin ke dawainiya da ita,shi yasa rumana ke mata dariya son ranta,kana tace baki da maraba da mutanen daji sis,kamar ba cikin gari aka haifeki kika taso ba "Ranki ya dade inata magana anqi amsa min" saurayin ya sake fada ganin yayi magana takai sau uku babu guda wadda ta amsa masa,ji take kamar ta tura motar tasa yayi gaba. Kanta ta sake daukewa zuwa daya bangaren tana addu'ar Allah ya kawo mata mota,duk rumana ce ta janyo mata,cikin sa'a taga tsaiwar adaidaita sahu,shukra ce ta sauko daga ciki kana ta nufo gurin rumanan "Afuwa sisinmu,munyi laifi afuwa,rumana tace na miki magana ki qarasa ciki ku tafi ta gaya masa inda zai kaiku" bata ko amsa ko daya cikin maganarta ba ta nufi gun adaidaitan tana jin dadin yankewar tsaiwarta da mutumin Sai da ta shiga adaidaitan sannan ta fuskanci ya fito, yana tsaye shida shukra,wanda da alama tambaya yake mata kan rumanan saboda nuno adaidaitan nasu da yake da yatsa Ajiyar zuciya ta saki tana jin yadda zuciyarta ke ci gaba da bugawa,idanunta a lumshe kana ta jingina da makaarin kujerar "Hmmm,sisi na kenan,bisa dukkan alamu dake mutumin can ke son yin magana kika gwada masa halin,wai sai yaushe ni raihana zata bude zuciyarta ga tarin masoyanta?yaushe zaki yarda kisan yadda soyayya take da dadi,koda friendship ne raihana?" Tayi maganar cikin sigar tambaya,bude idanunta tayi kawai tabi rumanan da kallo kana ta dauke kai ta maida kanta titi,kamar bazata tanka ba sai kuma tace"lokacin da hakan ya dace" "Amma fa kada ki manta ke ba yarinya bace,a qalla dab kike da cika shekara sha tara cif ko?,shine har yanzu lokaci baiyi ba" shiru ne ya ratsa tsakani,a maimakon ta amsa mata ma saita jefo mata tambaya "Rumana ina kuka je?" "Gidansu qawata jawahir,naje ganin wasu sabbin samples na lace da mamanta ke kawowa daga dubai,su za'ayi yayi wannan sallar su nakeso mu saka ni dake" ta fada cikin sigar tsokana,don tasan halin raihanan sarai,bata fiya son kayan yayi ko wadanda aka san tsadarsu ba, "daga nan zuwa gidansu sabon saurayin shukhra kuma ba nisa,sai ya leqo suka gaisa shi yasa kika ga mun dade". Tasan hakanne don ba dabi'ar ruma ce yin qarya ba,hakanan bata iya boye mata komai,amma mamaki suke bata,qawaye da samarinsu bazata iya cewa ga yawansu ba,duka duka yaushe shukran ta hadu da tsohon saurayin ta da har ta sake wani,sai ta zabi tayi shiru don duka babu muhallin magana agurinta ciki batun,wayarta ta ciro wadda take iri daya ce da ta raihanan ta shiga nuna mata hotunan laces din " sunyi kyau,Allah ya hore ya kuma kaimu lokacin da rai da lafiya"tace mata don kada taga kamar ta gwaleta. Cikin wani plaza dake titin gyadi gyadi saloon din yake,don haka abakin wakekiyar qofar shigan ya saukesu,suna shigowa rumanan ta sake kacibus da wata qawarta suka tsaya surutu yayin da raihanan taja baya tana jiransu su gama,idan da sabo ta riga ta saba,da wuya su fita su dawo rumanan bata ga wanda ta sani ba,tsaki taja tana neman motar da zata jingina ganin tsaiwarsu tayi yawa,daga kanta tayi tana kallon saloon din da zasu shiga din. Daafe yake da qarfen daya kare barandar qofar shagon da suke saida botique na maza wanda ke daura da shagon saloon din,ya kafe ta ido tamkar wani wanda yaga wata sabuwar halitta,sosai ta tafi da imaninshi tun tsaiwarta agun,karaf suka hada idanu,tayi gaggawar dauke idonta,don batason kallo ko kadan,daidai da isowar rumana suka jera sukayi soma haurawa saman. Gyaran qafa aka yi musu da faratansu bayan wankin kai,wannan dabi'arsu ce da suka koya gun ummu,kusan duk qarshen wata tare suke zuwa,wannan karon ne tace ita sai gobe din jibi abba zai dawo daga tafiyar da yayi england ya duba su rayyan da kawu muhammadou,sai raihana da aka yiwa jan lalle iya yatsu,ita kuma rumana ka mata baqi a hannu aka mata gyaran fuska,basu fito daga gurin ba sai da aka kammala sallar magariba gari ya dan fara duhu. Suna dab da qarasowa inda auwal yayi parking motarsu sukayi kacibus da shi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga abdullahi dan umar R.A yace:((naga manzan Allah S A W yana irga tasbihi da yatsun hannunshi na dama))* ________________________ *Babi na tara* Kicin kicin tayi da fuska kana ta janye hannun rumana suka isa bakin motar ba tare da ta barshi ya furta kalma ko guda ba,don ta gama fuskantar abinda yake shirin yi ************** Tafi mintin talatin zaune gefan gadonta tana duban rumanan wadda ke kwance ruf da ciki tsakiyar gadonta,jinta take tamkar cikin gajimare take yawo tsabar soyayya,ba sai ta tambaya ba tasani cewa da ya rayyan suke waya,indai kaga ta nutsa cikin duniyar masoya irin hakan to babu tambaya tasan ya rayyan ne ya murda kambunsa. Sosai yadda suke gudanar da soyayyarsu take burgeta,har wani lokacin hakan yakan sata taji itama tana sha'awar yin soyayya,tana sha'awar dandanata taji yaya take,saidai tsoronta takeji,don a karance karancanta tasha cin karo da mutanr daban daban da soyayyar ta yamutsa duniyarsu,duk da tasan wataran dole tayi tunda zatayi aure,saidai hasalima har yau bata ga mutumin da ya cancan ci ta bude masa zuciyarta ba,wadda take jigo ce ga rayuwarta. Ganin basu da niyyar gama wayar ya sanya ta daukar tata wayar ta kira layin mamanta fanna wadda take kira da ammi,zainabu ce qanwarta ta fara dagawa,sai da suka gaisa sannan ta miqawa maman,hira suka dinga yi da maman nata tana bata labarin abubuwan da suka faru a dangi da wadanda ma ke faruwa,tana jin farinciki sosai tare da kewarsu kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a can,sai da ta qone katin wayar baki daya sannan ta haqura,daidai lokacin da rumana suka kammala wayar da rayyan din. Ta dan zubawa rumanan ido ganin yadda ta kafe wayar da ido tana kallonta,gyaran murya tayi mata a maimakon magana,a hankali rumanan ta dago tana duban raihana fuskarta qunshe da murmushi wanda yayi sanadiyyar bayyanar dimple dinta "Mtswee,kin ganni ko sisi,duk sanda mukayi waya da ya rayyan sake dulmiya nake cikin tafkin qaunarshi,baya ga iyaye na a duniya banga abinda nakeso sama da ya rayyan ba" "Har da ni kenan?" Raihana ta fada bayan ta miqe tana gyara shimfidar gadonta,dariya rumana ta qyalqyale da ita tana fadin"ai kalar qaunar da na miki dabab da wadda nakewa ya rayyan,kema wani sashe ce ta rayuwata raihana,babu abinda bazan iya miki ba" "Nasan da haka,nima kuma haka kike a gareni,hasalima kin wuce hakan" "Allah ya bar min ke sisi na" murmushi ta saki tace "ameen" tana komawa saman gadon taci gaba da karanta tarihin garin daura da take ************ Kusan tun safiyar ranar raihana ta hana kanta sakat da girke girken taryan abba,rumana na tayata idan ta gaji ta gudo falo ta sha wayarta ko ta hau charting kana ta koma. Ba yadda ummu bata yi da ita ta zauna ta huta ba amma taqi sai data kammala,tana qaunar abba tana masa kallo ne na mahaifinta,bata manta alkhairinsa a gareta dama mahaifiyarta,ya daukesu tamkar 'ya'yansa na cikinsa,idan yana hidimta masu sam baya sakawa a tunaninsa bashi ya tsuguna ya haifesu ba,baya gajiya da hidimarsu,babu abinda suka nema suka rasa,don haka itama take qoqari taga tayi duk wani abu da ta lura abban yana so,tana jin hakan shine kadai hanyar da zata iya nuna masa jin dadinta da godiyarta. Zuwa la'asar ta kammala komai,kasancewar biyar zuwa da rabi suke saka ran shigowarsa cikin gidan,tuwon alkama tayi masa miyar kubewa danya wadda ta wadata da zallar tsokar nama da kuma tantak'washi wato k'ashi mai taunuwa ga me buqata,sai lafiyayyen alkubus da tayi miyar taushe,daga bisani da taha zobo wanda ta tafasashi da citta da kanunfari,ya wadatu da lemon tsami,sam bata zuba flavours din nan irin nasu tiyara ba haka ta barshi da original din kayan hadi,sai suger syrup da ta zuba daidai misali yadda bazai cutar ba. Tun kafin abban yaci su ummu suka fara nasu santin ita da rumana,murmushi kawai ta dinga musu ganin yadda suketa zabga santin ta shige dakinsu don ta watsa ruwa ko zata ji sanyi a jikinta ********** Qarfe takwas da kusan rabi ne na dare cikin falon abban suke bayan sun kammala cim abincin dare wanda girkin da raihanan tayi ne,suna zaune ita da rumana sanye da kaya iri daya wato material dinkin doguwar riga wadda raihanan ce ta zaba musu style din,daga gefe guda kuwa abba ne da ummu,hira suke abba na bude jakar da ya dawo da ita yana fidda tsaraba "Abba ka bari sai gobe mana idan ka huta sai ka raba" inji rumana "Um um rumana,tsaya dai na sallami kowa,don akwai saqonninku da rayyan ya bani,shi din ma bana tunanin zasu wuce wata biyu zasu dawo baki daya har kawu muahhadun,don shima yace ya gaji da zama a can din ga girma na zuwa masa,gwara ya dawo cikin dangi" kamar ta taka rawa don murna amma ta kanne ta dake ganin idanun abba da ummu a gun,duk da haka sai da ta kasa haquri ta qanqame hannayen raihana dake kusa da ita,idanu suka hada kowacce fuskarta dauke da murmushi,ita kanta raihanan ta taya rumanan murna,addu'a take Allah yasa ya hado mata da hotunansa,don rabon da ya turo din an din kwana biyu,kota watsapp ma,gashi tunda ya bar qasar bai sake waiwayota ba. Jakankuna ne madaidaita guda biyu iri daya ya miqawa raihana daya ya miqawa rumana daya,hannu biyu suka sanya suka amsa suna godiya,ya fidda wata jakar wadda ta dan fi tasu girma ya miqawa ummu yana fadin "Ga saqon yaronki" cikin alkunya tace"Allah ya amfana"abban ya ajjiye mata a gabanta,ya sake fidda wasu jakankunan ledar wadda daya tafi daya girma,ya miqawa rumana daya,raihana daya yace"saqon yayanku"hannu biyu suka amsa suna sake godiya kana suka miqe suka yiwa su ummun sai da safe,don rumana ta qagu taje ta bude tana meye a ciki. Har sun kusa ficewa daga falon abban ya sake kiransu suka dawo,wasu litattafai abban ya ciro ya miqawa raihana,daya tarihin masarautar kano ne,dayan kuma tarihin sahabbai ne maza da mata guda dari dari na hausa guda biyu,kana ya fidda doguwar baqar riga ya miqa mata "Wannan litattafan abbanki dalhatu ne yace na kawo miki yasan ke gwanar karatu ce,rigar kuma tukuicin garar girkin da na diba yau ne" kanta a qasa tasa hannu ta amsa a kunyace tana fadin"na gode abba,Allah ya saka da alkhairi,ya qara girma" "Ameen ameen,Allah yayi muku albarka" "Ameen suka amsa" sai ya fidda wani qaramin turare ya miqawa rumana yace gashi itama ladan ganin ido,tana dariya ta karba tana godiya,don ita saqon data samu daga rayyan ma kadai ya isheta,burinta kawai ta isa daki ta bude. Suna isa ta daka wani wawan tsalle ta dira kan gadonta tana dan ihun murna,tsayawa kawai raihana tayi tana kallonta fuskarta dauke sa murmushi,tabbas ba qanqanin so rumananta kewa ya rayyan ba,tun tafiyarsa daidai da second daya bata taba mancewa da ambatonsa ba,duk da tarin abokanta kuwa amma basuyi isar da suka samu damar shafe koda d'ani daya na soyayyarsa dake cikin zuciyarta ba. Tsagaitawa tayi tana fidda idanu tana duban raihana "Sisi,bayan shekaru ya muradina zai dawo,raihana ya rayyan dinmu zai dawo gida,gidanmu zai dawo kamar yadda yake da,sis bazan buda kayan nan yanzu ba,sai na gama shirin yi bacci,so nake su zama abu na qarshe da zan kalla kafin zuwan bacci idanuna" "Ya kamata..." Cewar raiha tana ci gaba da murmushi Miqewa tayi har yanzu murmushi yaqi barin fuskarta ta rage kayan jikinta ta daura towel ta shige bandakinsu dake cikin dakin. Gefan gadonsu rumana ta zauna tana girgiza kai cikin zuciyarta tana fadin "Rumana....ruma kenan,rumana tawa,rumanan ya rayyan,Allah ya barki da shi" ta qarashe zancan zucin tana janyo jakar da abban ya musu tsaraba ta soma budeta. Dogayen riguna ne kamar yadda ya riga ya sani kayan da tafi so kenan,ba qaramin burgeta kayan sukayi ba har ta dinga sakin murmushi ita daya,sai mayafai suma masu kyau da takalma,sai turare guda uku irin wanda take amfani da su,maidasu tayi cikin jakar kana ta janyo ledar da ya rayyan ya basu ta zazzage kayan ciki *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Manzan Allah S A W yace"mutane)masu jinqai da tausayi,ubangiji mai rahama girma da daukaka suma yana jin qansu* _________________________ *Babi na goma* Duk kayan dake cikin ledar suka zubo kan katifar,littafin love story ta soma cin karo da shi sabo qar,a bangon littafin wata gajeriyar takarda ce da aka linke ta gida biyu aka maqale ta a jiki. Murmushi ta saki saboda tuna mata baya da littafin yayi,sanya hannunta tayi ta ciro takardar ta budeta. Rubutune qanana masu kyau a jiki wanda basu wuce layi bakwai ba _assalamu alaikum,nasan zuwa yanzu qanwata tayi girman da zata iya karanta wannan littafi,to ga tsarabata nan,asha karatu lafiya_ Ita kadai amma sai taji kunya ta kamata tamkar yana kallonta"ya rayyan,baka da mantuwa"ta fada cikin zuciyarta,ragowar kayan note book me masu kyau farare tas masu zanen furanni da tsuntsaye har cikin shafukan cikin littafin haka suke,kana gani kasan masu tsada ne,guda shida ne da biruka masu kyau da burgewa suma guda shida,murmushi ta sakeyi tana fadi a zuciyarta"baka mance quruciyarmu ba". Turaren oud guda uku masu qamshi,sai set na sarqa da dan kunne na english gold sirara masu kyau da tsari. Sosai kayan suka burgeta,tana tsaka da maidasu cikin ledar rumana ta fito "Ke har kin bude naki tsarabar kenan" ta fada tana qarasowa gefan raihanan "Eh kam,duba ki gani" ta fada tana tura mata ledar kana ta miqe don shiga itama tayi wankan. Dariya rumanan ta dinga yi tana tsokanar raihana "Wato my rayyan bai manta satar novel da kike masa ba ko,da maitar karance karance,hala nima bai mance halaye na na quruciya ba kenan" murmushi kawai raihana keyi tana sauya kayan bacci "Bai mantawa da nawa attitude din ba ballantana naki,kedai jeki bude musha kallo,hala harda 'yar tsana mai koyar da rawa ya aiko miki" tayi maganar yayin da tayi rub da ciki kan gadon nata tana fuskantar rumana dake gefan nata gadon itama tana saka kayan baccin. Sai da ta gama komai sannan tayi dare dare tsakiyar gadon,jakar da rayyan ya aiko mata da ita ta fara budewa,wasu plates din cd ne guda biyu suka fara fadowa,ra daga tana dubasu,'yar qaramar dariya ta saka cikin nishadi,dayan album din waqoqi ne wanda ke qunshe da waqa goma dukka masu dauke da kalaman soyayya da tsuma zukata,daya kuma waqoqine kala kala suma duk na soyayyar ne,tana iya tuna wasu daga cikinsu rayyan din kanyi lokaci lokaci kafin barinsa gida,ta sake duba kayan english gold ne irin na raihana sak,banbancinsu kawai nata akwai zobe a ciki wanda akayi zanen RR guda biyu sarqafe da juna,sai turaruka guda biyar,packet uku uku na irin biscuite da chacukets din da yake bata da can lokacin quruciya,tana daga kayan tana nunawa raihana tana tayata dariya"wato tsokana kawai tasa ya rayyan yin aikenan nan da alama"ta fada tana cin dariya. wata envalope mai fadi ta hago a qasan dan akwatin agogon hannu mai siffar heart,ta miqa hannu da sauri ta bude,takarda ta fara cirowa ta warwareta ta soma karantawa,murmushi kawai ke fita daga fuskarta,da sauri tayi cilli da takardar ta wawuri envalope din ta kuma budeta. Wasu zuqa zuqan hotuna ne guda biyu ta samu nasarar fiddosu,idanu ta zaro gami da fidda idanu waje kana ta saki wani qaramin ihu da ya sanya raihana miqewa zaune tana tambayarta lafiya,kasa bata amsa tayi sai cewa da take "Zo ki gani.....zo ki gani sisi,wayyo Allah na" tana fada tana zillo kan gadon ta kasa tsaiwa guri guda. Da sauri ta sauko daga nata gadon ta qaraso gadon rumanan a dan kidime,a hankali takai idanunta kan abinda rumanan ke nuna mata,hotunan rayyan ne duka guda biyun,yayi masifar kyau cikin hotunan,daya yana sanye da courte baqa da ja,sumar kansa ta kwanta luf,ya sake girma da cikar zati sosai ya zama cikakken saurayi,dayan kuma yadi ne a jikinsa tissue na maza fari qal,an masa dinkin boda,tun daga sama har qafafunsa aka dauki hoton,ya dan karkace kadan yana murmushi,hannayensa saye cikin aljihunsa, "Sisi na kalli ya rayyan dina don Allah,kalli yadda ya rayyan ya zama.....", ido itama ta dan fiddo tana fadin"masha Allah,fatabarakallhu ahsanul khaliqin,kinyi dace da ya cancanci a taya ki murna kam sister,congrats"ta fada tana kama hannun rumana "Alhamdulillah,na gode sis". Bakin gadonta ta koma ta zauna tana kallon yadda rumana ke ta maimaita kallon hotunan,dariya ta dinga yiwa rumanan har ta dan tsokaneta " da alamu yau dakin nan babu bacci kenan"dariya rumanan ta saka"haka nake ji a jikina,don yau hira ni da pics din ya rayyan har asuba" "Allah ya bamu alkhairi to" inji raihana tana dariya kana ta shige cikin bargo Tun daga ranar hotunan suka zama abubuwan kallo da kuma debe mata kewa,ko waya zasuyi da rayyan din sai ta daukosu ta saka su a gabanta. Raihana ce tayi suprising dinta ta kwashi hotunan takai aka buda su aka sanya su cikin frame masu kyau,ta kafa mata daya saitin gadonta,ta dora mata daya kuma kusa da bedside lamp dinta,tana ganinsu kuwa ta daka tsalle ta dale raihana tana fadin, "Wayyo sisi na bani da kamarki" "Nima ban da kamarkin ai,gudun mawata kenan kan irin son da naga kinawa hoton" "Kin biyani wallahi,Allah ya biyaki kema"ta fada tana daukar daya hoton dake kan bedside din tana juyashi a hannunta,frame din kawai ma abin kallo ne ballantana yadda hoton ua qawatu a cikinsa Ta lumshe idonta kana tace "ameen 'yar uwa,fatan kawai Allah ya nuna mana aurenku"tayi maganar tana dariya qasa qasa don tasan ta gama soso mata inda yake mata qaiqayi,tayi kuwa far da ido sannan ta amsa"kai....ameen ya Allah" harda daga hannayenta sama ************* Duk lokacin da rana ta fito ta fadi sai rumana ta rage ranakun da suka rage rayyan din ya dawo,haka shi din ma daga bangarensa,ya qagu yaga ya dawo qasarsa ta haihuwa,gaba daya zaman england ya gama fice masa aka,ya k'agu ya ganshi cikin familynshi tamkar ce masa akayi ranar ba zata zo ba. Sosai take shiryawa zuwan nashi,don gaba daya hirarta ta koma ta dawowar yaya rayyyan,duk son hira irin na rumanan daga kun zauna hira mawuyacine ku cinye minti biyar bata sauya akalar hirar taku zuwa ta yaya rayyan ba,dariya sosai raihana ke mata don har canza mata suna tayi, wani zubin takan tsokaneta da lailah majnun,hatta da laces din da taso su sanya wannan sallar ta amso musu takai an dinka musu ita da raihana,don tace shi zasu saka ranar da ya rayyan din zai iso,ragowar kuma idan zasu masa rakiyar gaida family,na raihana dai baya wuce to,babu shakka ita kanta shaida ce na ba qaramar soyayya bace ke gudana cikin jininsu ba. Hakanan watarab rumana kan zauna tana bayyanawa raihanan kwatankwacin yadda takejin rayyan cikin zuciyarta,don ba zata iya kamantawa ba,wani lokacin raihana ta tayata,wani lokacin tayi dariya,wani lokaci ma tausayi hakan ke bata,tana ganin itakam bata fatan koda zata fara soyayya tayi mata irin wannan kamun,don tana ganin wahala ce zallah cikin irin hakan,zuciya da gangar jiki sam basu da hutu,dariya sau tari rumana keyi "Raihana kenan,irinku ba shiru shiru din nan,wallahi kunfi kowa rungumar soyayya gadan gadan,gwara mu da bakinmu zamuyi ta fada" murmushi kawai take ta kada kai "Rumana tawa" "Raihana tawa" sai su sanya dariya baki daya,don kowa yana ganin cewa yana kan ra'ayinsa,kuma bazai yiwu hakan ya sauya ba ************* Tsaye suke bakin titi ita da rumana,yammaci ne na ranar jum'a wanda ke dauke da gajimare mai yawa da ya fara canza yanayi zuwa na hadari irin na farkon damina,kasancewar daga kowanne lokaci zuwa yanzu za'a iya samun saukar ruwan sama. Saloon suka je kamar yadda suka saba,saidai na yau ya banbamta da na ko yaushe,ya zama na musamman din kuwa sanadiyyar kwanaki biyu da suka rage rayyan ya dawo. Tsaki rumana ta dan ja tana sake kallon titin"mtswee,motar nan ta mana tsiya wlh,da tuni mun jima da mantawa muna gida,for now ya kamata mu yiwa abba complain a kanta ta fara gajiya da mu"dariya maganar rumana ta baiwa raihana,don ta sani sarai wata kalar motar ta hango musu shi yasa ta fara sharhi kan waccar,duk da ita din ma ba wai ta tsufa bane "To ya za'ayi,qarfen nasara ne da bashi da tabbas" inji rumana. Tana rufe bakinta motar ta gilmasu qirar sienna light brown, a hankali ta dawo da baya tayi parking gabansu,gilasan motar suka sauka qasa mamallakin motar ya bayyana "Ranki ya dade hajiya rumana" a hankali ta maida kanta inda akayi maganar,sai ta dan saki fuskarta maimakon dazu da take a daure "A'ah,farouq dama ana ganinku" "Gamu kuwa,kune ai ke wuyar gani.....daga ina haka da yammacin nan" "Wallahi daga wankin kai" Ya saki murmushi idanunsa na kafe kan fuskar raihana wadda sai ka rantse bata san Allah yayi ruwanshi a gun ba,da ido yayiwa rumana nuni da raihana,dariya taso kubce mata amma ta kanne gami da dafe baki "To bismillah mana,ku shigo na saukeku a gida" yayi maganar yana bude musu qofofin motar. Da saurin raihana ta damqe hannun rumana tare da tsaidata,ta san hakan me yake nufi wato ita ba zata shiga ba,qasa qasa tace "Pls sisi,mota taqi samuwa kuma kinsan akwai abubuwan da zamuyi a gida da yawa da bamu gama ba,gashi hadari ya fara tasowa,kiyi haquri ya rage mana hanya mana" shiru tayi kamar ba zata amsa ba ita kuma tana ta matsa hannunta,ganin yadda mutumin ya zuba mata ido yana son yaji me zai faru tsakaninsu ya sanya kawai ta share ta bita din. Hira suka dinga yi jefi jefi yana jinsu bata tanka ba,duk da kuwa yadda yaso sanyata cikin hirar sai ta kauce,sosai ua shiga damuwa, don ya dade qaunar ta na wajigashi,koda numberta ya kasa samu don rumana tace ba zata bashi ba sai da yardar 'yar uwar tata. Cikin mintina qalilan sai gasu a unguwar tasu,ita tafara balle murfin motar ta fice ta shige ciki don a gajiye take sosai,bayan wasu mintina rumana ta biyo bayanta. Sai bayan sallar magariba suna zaune ta dubeta "Raihana" ta kira sunanta,dagowa kawai tayi ta dubeta hakan ya nuna tana jinta "Farouq na neman alfarma na bashi lambar wayarki" "Dalili da me?" Ta tambayeta kai tsaye "Saboda yana sonki,so kuma na aure" Raihana,lokaci yayi da ya kamata ace kin maida hankalinki guri guda kin zabi wanda zaki rayu da shi rayuwa ta har abada wato rayuwar aure,sanin kanki ne cewa a son ran abba a cikin dakunanmu zamu qarasa karatunmu,ke kika gayan yace ya rayyan na dawowa za'a tsaida lokacin bikinmu,to ta yaya kike so nayi aure na barki ke daya?,ke kanki ba zakiji dadi ba,don Allah sis na roqeki ki bude zuciyarki ki saurari masu begenki ko Allah zaisa kiyi katarin dacewa da wanda ya dace da ita,don Allah"ta qarashe cikin sassauta murya. Murmushi ya subuce mata ganin yadda rumana keta faman lallashinta,ita kanta ta sani cewa ba laifinta bane,hakanan zuciyarta taqi buduwa balle ta karbi kowanne baqo dake karakainan neman shiga cikinta,ba shakka tasan cewa yadda suke qaunar juna ita da rumanan ko 'yan uwansu da suka fito ciki guda basu qaunarsu haka,to ta yaya kuwa zataji dadin zama ita daya idan rumanan ta tafi ta barta "Yanzu madam me kike so ayi kenan" murmushi ta saki tana sake matsowa kusa da raihana "Yauwa sisi na,don Allah ki daure ki karbi farouq,koda bai miki ba akwai al'amin tukur ahmad nasan zaki iya tunashi?,yanzu haka mun gama magana da shi na farouq na riga da na bashi number wayarki zaya kiraki....pls and pls sisi kada ki masa miskilancin nan naki" sai ta hade rai,saidai can qasan ranta na wasa ne "Ok,har ma kin bashi num dina kenan ba tare da izini na ba ko.....kice min rabon num dina kike kawai ga duk mai so" dariya sosai ta baiwa rumana har ta soka qyaqyatawa,kafin tace wani abu ummu ta shigo falon hannunta dauke da leda "A'ah,tagwayen ummu,da alama ta samu kenan?,ko duk murnar dawowar ya rayyan din ce?" Ta fada tana zama gefan kujera,murmushi rumana tayi yayin da raihana ta dubi ummun fuska a hade"yauwa ummu.....gwara kizo ki rabani da yarinyar nan,ki gaya mata ta daina rabawa mutane numberta" "Kamar yaya?" Ummu ta tambaya "Wai kawai bata san mutane ba sai ta dinga basu number dina". Tuni ummun ta gano inda maganar ta dosa " banda abun raihana number dai ba wani abu ba,ai lokacinki ne wataran babu mai bada number taki ko kuwa?,nidai fatana kawai ki a kawo min suruki na gari na hadaku nasha bikinku rana daya,ko ba haka ba"su rumana har da sunne kai wai anji kunya,raihana kuwa murmushi kawai tayi. Ledar hannun nata ta tura musu tana fadin "Wannan dinkunanku ne na laces da kuka kai a ciki dazu tailor din ya kawo muku,wannan kuma tawa gudun mawar dinkunan dawowar ya rayyan. Allah sarki ummu,uwa daya da daya,sam basu san ma yaushe ta bada ayi musu dinkin ba,hada baki sukayi wajen yi mata godiya,ta tashi ta basu guri. Rumana ce ta fara fidda kayan cikin santin yadda dinkunan suka tsaru,atamfofi ne vlisco 'yan ubansu kala uku uku ummun tayi musu,daya dogayen ringuna masu shape din pieces daya aka musu riga da skert,daya kuma riga da zani,duk sai da rumana ta gwada,sun yi mata cif kuwa a jiki tamkar a jikinta aka dinkasu,hakanan sun haskata tare da fidda shape dinta "Allah ka barmin surukata kuma uwa ta gari" Dariya ta bawa raihana "Ameen ni kuma Allah ya barmin uwata ta kaina" ta fada cikin dariyar tana tayata ninke kayan tare da jerasu cikin wardrobe dinsu,don da guda suke amfani,kowa na iya amfani da kayan kowa,ba wani banbanci tsakaninsu ************** *_monday_* A qalla ba akasara ba ta shafe sama da awa daya da rabi gaban mudubin tana shafe shafe,goga wancan zana wancan goge wancan,a yau jinta take babu wata halitta da ta kaita farinciki a doron qasa,yau ranar da zatayi tozali da farincikinta rayyan,wanda suka shafe a qalla shekaru kusan tara ba tare da sunga juna ba. Tun rumana na zaman kallonta har ta gaji ta koma tayi kwanciyarta kan gadonsu,tuni dama ta gama ita nata shirin,kamar yadda halinta yake bata cika sin qyale qyale ba,concealer kawai ta shafa tabi bayanta da hoda wadda ta dace da kalar fatarta,sai mascara data sake tada gazar gazar din gashin idonta,girarta kawai ta gyara don bata amfani da eye brow,kwalli ta zizara da ya sake fidda shape da kyawun idonta,sai dan pink din jambaki data shafawa labunanta,tana sanye ne cikin daya daga cikin laces din da suka tsara sakawa. Lace ne dan ubansu wanda ko ba'a gaya maka ba kasan ba na qananun kudade bane,orange na aka masa adon baqi da torches na lemin green,abu daya yasa raihana taji ya fita akanta dinkin riga da skert da rumana tasa aka yi mata a maimakon doguwar riga kamar yadda ta zaba. "Tabdi,yau kam bansan kalar haukar da zaki sanya ya rayyan ba a airphort,irin wannan ado haka sister" Dariya ta saka taba miqewa daga gaban mirrow din"kada dai ki fasan kai da yawa,kuma naje na kasa burge ya rayyan din"miqewa raihanan tayi daga kwanciyar da tayi dazun"haba.....haba don Allah wuce nan wallahi.......ba irin sister na ba dai,ta wuce wannan class din wallahi" Dago labulen dakin da ummu tayi shi ya katse musu hirar,a shirye take cikin atamfa holland mai asalin kyau da tsadar,itama tayi kyau sosai,cas da ita ba alamun girma ko tsufa tattare da ita,wanda mutane da yawa kan alaqanta hakan da rashin haihuwa da batayi mai yawa ba "Mun fito fa mu" "Ummu muma mun gama" inji raihana tana saukowa daga kan gadon tare da daukar gyalenta ta yafa bisa kanta ba tare da ta daura kallabi ba,qasa qasa rumana ke wa raihanan magiya ta tsaya su fita tare don Allah kunya takeji,sai da ta gama zolayarta kan cewa taqi din,batasan da su ummun ba ta zuba ado haka sannan ta jirayeta ta gama daurinta suka fito *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo hadisin daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace((haqiqa farkon abinda za'a fara yiwa bawa hisabi a kansa ranar qiyama shine SALLARSA,idan ta gyaru tayi kyau haqiqa ya rabauta yayi nasara(ya haye kenan),idan kuma ta baci haqiqa ya tozarta yayi asara,idan aka samu naqasu ko rashin cika daga cikin ayyukansa na ibada na farilla,sai ubangiji mai girma da daukaka yace:ku duba,shin bawa na yana da wasu ayyuka da yayi na neman lada(wadanda ba farilla bane)sai a cika masa abinda (da ayyukan da yayi na neman ladan)inda aka samu naqasu cikin ayyukan farillarsa"* _________________________ Abba da kansa yau yake tuqin don zuwa tarbo yaron nasa,shi da ummu na gaba,yayin da rumana da raihana ke zaune gidan baya,kallo daya zaka yiwa fuskokinsu su baka amsa cewar iyalin cikin farinciki da nishadi suke Basu wuce mintina arba'in ba suka sauka cikin filin jirgin sauka da tashin jirage na mal aminu kano,a hankali suka qarasa har zuwa gurin da aka tanada domin zaman jama'ar dake jiran isowar 'yan uwansu. Raihana ce ta miqe rumana ta kalleta bayan ta dubi agogon hannunta tana tambayarta ina zata "Qishirwa nakeji,zan siyo ruwa yanzu na dawo" "Saikin dawo,don ni daga nan babu inda zan dara sai naga isowar ya rayyan" murmushi ta saka ta soma tafiya tana cewa "Dama nima bance ki rakani ba madam". Fitowarta daga kantin hannunta dauke da gorar ruwan swan guda biyu mai sanyi suka kusa cin karo,ta dan ja baya da sauri yayin da shi kuma ya sakar mata murmushi,dauke kai tayi tana neman rabeshi ta wuce tamkar ma bata taba ganinsa ba,da azama ya sha gabanta har yau da murmushin dauke a fuskarsa yana fadin " ranki ya dade ayimin afuwa idan nayi laifi"ya fadi yana hade tafukan hannayensa "Na tuba nabi Allah na biki"inji al'amin. Shiru tayi kamar mai nazari,kana ta dan saki fuska ganin yadda damuwa ta bayyana akan fuskarsa qarara " ba wani laifi fa"ta fada a gajarce,ajiyar zuciya ya saki yana fadin"har naji dadin wallahi,ga zatona laifi nayi,kawo na rage miki nauyin"yayi maganar yana qoqarin karbar robobin ruwan daga hannunta,ganin yadda mutanen dake shige da fice a shagon suka zuba musu na mujiya yasa ta sakar masa kana ta fara tattaki don yin gaba,da hanzarinsa ya biyota din samun damar jerantawa da ita kada ta wuceshi,yana son qara mata da drink yana tsoron kada garin neman gira ya rasa ido. Yana mata wani mugun so,saidai ya rasa ta yadfa zaiyi ya shawo kanta,ya samu number dinta saidai ta kusan zame masa hoto,don ko ya kira ba amsawa takeyi ba,hakanan ko yayi saqo ba reply. Ya danyi gyaran murya kadan ganin sunata tafiya kamar kurame"sai kuma na ganki anan,hala wani guri zaku?"kai ta kada sannan ta numfasa tace"munzo taryar yayanmu ne"cikin zumudin da baisan yayi ba yace"kice yau zamu gaisa da 'yan gida ko?"sai taci burki ta tsaya inda take tana dubanshi hannayenta harde a qirjinta Tun rumana na duban hanyan dawowar raihana har ta shagala saboda jin isowar jirgin dake dauke da su rayyan,gaba daya ta maida idanunta sashen da take saka ran fitowarsa "Af,kin ganshi can ma" inji abba "Kai,kai,kai,kai,masha Allah,masha Allah,Alhamdulillah" inji ummu da bakinta ya kasa rufuwa bayan hango yaron ta kuma gudan jininta da tayi,wani farin ciki ta dinga ji soaai,shekara tara ba wasa bace,yayin da rumana ta sandare gu daya,ashe babu abinda ta gani cikin hoto,indai haka ne ma to ba shakka hoton rage masa kyau yayi ya boye. Sanye yake da suite ash colour masu bala'in kyau da daukar ido,gashin kansa a kwance luf baqiqqirin sai sheqi yakeyi,fuskarsa saye take cikin sun glases,yayin da qafarsa ke saye cikin sau ciki na maza mai matuqar kyau da tsada,idan ka hangoshi sai ka rantse da Allah daya daga cikin jaruman bollywood ne,ya sake fari,tsaho kuwa ba'a magana,saidai ya masa kyau don yana tafe ne da 'yar qibar da tsawon ya boyeta Hangosun da yayi yasa fuskarsa ta fadada da murmushi,sannu a hankali ya tako zuwa inda suke,rungume juna sukayi shida abba yana masa sannu da zuwa bayan ya saki abban ya dan rungume kafadar ummun yana dariya qasa qasa,sannun itama take masa. A hankali ya saketa ya juya,suka hada ido da rumana wata iriyar kunya ta sauko ta lullubeta saboda kallon da yayi mata na ido cikin ido,sosai yayi mata kwarjini gami da cire mata baki daya lakar jikinta,sai ta sanye gefan mayafinta ta rufe idonta,taku uku ya qaraso gabanta "Yar qauye,ya rayyan din naki kike jin kunya?" Sai ya waiwaya ya dubi ummu "Ummu haka yarinyar nan ta zama?me kuke bata ne?" "Abincin 'yan nijeria" inji ummu tana murmushi,ya sake maida kanshi gunta tare da kashe mata ido daya "Well,haka naso fa dama" kunya ya sake bata ta sake sunne kanta tana satar kallonsa ta cikin mayafin,don ba kadan ba ya tafi da imaninta,wani sabon sonshi wanda ada bata jishi ba yazu ya ke kafa kansa a sansanin zuciyarta da gangar jikinta,sosai take yabawa kanta zabin da tayi. "Alhj ina za'a ajjiye maka kayan" cewar daya daga cikin leburorin da suka tayashi da jakansa "Mu qarasa mota sai a zuba a both ko?" Inji abba,sukayi gaba shi da ummu rayyan da rumana na binsu a baya. "Yammatan naijeria,ina twin sister din taki?"ya fadi yana zuba kata ido fuskarsa dauke da murmushi,shaf ya mantar da ita raihananta sai a lokacin ta tuna da ita,ta balle jakar hannunta ta fidda wayarta tana laluben layinta " daga zuwa siyo ruwa kaga har yanzun shiru". Da sauri ta duba wayar hannunta taga kiran rumana ke shigowa,tun dazun take qoqarin yakiceshi su rabu a gun din batasan ya qarasa gunsu ummu,don har yau bata da wani feelings ko ra'ayi a kansa,ko daya al'amin bashi da wata makusa wajen halaye halitta nasaba ko dukiya,saidai shi so sam babu ruwansa da ko daya daga cikinsu,cikakken saurayi me mai ji da kyau da nasaba,mahaifinsa sannanne ne wanda yayi fice gun sana'ar fidda fata qasashen qetare wato alhj mansur mai fata,yana da sanyin hali shima da iya mu'amala da jama'a,sam dukiyarsu bata sanyashi dagawa ko jin kai ba. "Ni zan wuce rumana na jirana" tayi maganar tana miqa hannu don karbar ruwanta,ya saki murmushi "na gode da wannan lokacin ma da kika bani,amma kada ki manta kyan alqawari cikawa,bari ja sake maimaita miki,zaki dinga daga kirana ko gaisawa mu dinga yi" Kai ta gyada cikin qagauta tace"in sha Allah". Daidai lokacin da ta miqa hannu ta amshi ruwan su abba suka iso wajen,kunya kamar tayi me,cike da girmamawa al'ameen ya gaida su abban,sannan ya qarasa sukayi hannu da rayyan,sannan suka gaisa da rumana,farin ciki ya lullubeshi yayin da gefe daya haushi ya cika raihana hakanan,kai tsaye ya bisu har gun motarsu,bai barsu ba sai da yaga sun shiga sukayi sallama. Wannan karon rumana da raihana da ummu ne a baya,abba da rayyan a gaba,tamkar wata mara gaskiya haka tayi tsuru tsuru cikin motar ta kasa sakewa,duk da hirar da ake tabawa cikin raha da barkwanci,ko magana ta kasa yi da kowa "Wai har yau qauyancin yarinyar nan bai barta bane ummu?" Rayyan yayi maganar yana duban gefan titinanmu "Wakenan fa?" "Raihana mana,dubeta sai kace wata kurma,ta kasa koda cewa ya hanya,bayan yanzu ta gama hira da saurayinta" dariya gaba daya sukayi har itama raihanan ta murmusa,batasan me ya riqe bakinta ta kasa gayas da shi ba,a sanyaye tace "Kayi haquri ya rayyan,ina yini an dawo lpy" shiru yayi tamkar baiji ta ba,sai da ummu tace "To ai ka haqura dai tunda an baka haquri"sannan ya amsa "Lafiya lau,ya karatu?" "Alhamdulillah" Bayan sun isa qananun jakunkunansa da zasu iya dauka ita da rumanan suka dauka masa suka rakashi daki,gyaran da aka yiwa dakin ya burgeshi sosai,yayi dan tsalle ya fada saman kujera yana fadin "Wash Allah na"suka hada ido da rumanan ta sakar masa murmushi tare da kada ido " ka shiga kayi wanka ka huta,zuwa azahar idan ka tashi sai muyi lunch.....uhn?" "Is ok,amma hira naso muyi"murmushi tayi " me kake ci na baka na zuba ya rayyan,muna tare fa,ni din ma ban gaji da ganinka din ba"dage girarsa yayi,kyakkyawar fuskarsa ta wadatu da murmushi "Yes my angel...." Tasa tafin hannunta ta rufe fuskarta saboda tuna mata da sunan da yake kiranta tun zamanin quruciya. Itakam raihana kunya ce duk tabi ta kamata,kanta na duqe tana murmushi kadan kadan,rumana ta kama hannunta tace"muje sisi". Sun kusa da qofa rayyan din ya sake kiranta cikin muryansa mai sanyi "Ina so anjima na sake ganin wata kwalliyar irin wannan" farin ciki ya kamata,murmushi ya wadatu a fuskarta har kamatunta suka loba "Wadda tafi wannan ma zaka samu" "Thanks" ya fada yana dage giransa yana kallonta,girgiza kai tayi har yau murmushin bai bar fuskarta ba ta janye hannun raihana suka wuce tana ji kamar sonsa zai faso qirjinta,binsu ya danyi da kallo har suka fice,suna nan dai tamkar twince,saidai shuru shurunta da yake jin haushi lokacin quruciyarsu har yau yana nan,wato hali zanen dutse ne kenan kamar yadda hausawa suka ce,sai ya tabe baki tare da dage kafadunsa ya shige bedroom din sa. Tsayawa yayi yana kallon yadda ta qawata dakin,a hankali ya dinga bin komai da kallo yana sakin murmushi gefe guda tana sake burgeshi,kan gadonsa cike yake da balloons da aka hurasu masu siffar heart,yayin da ta kewaye fuskar gadon da wasu,sai hotunanta da aka bude medium size a kowacce kusurwan daki,wani qamshi mai mai taushi ke tashi,sai wani abu mai kama da frame wanda ke bada kaloli masu kyau tare da rubuta welcome back sai ya dauke ya rubuta na larabci marhaban. Sai da ya gama kallo son ransa kana ya saki dariya ya fada toilet. Suna kitchen din suna aikin abincin rana,bakin rumana yaqi rufuwa sam,hira take yiwa raihana kala kala,sam bata lura da shirunta ba don ta san dama can halayyarta ce,har sai da aka kirata a waya tukun taga ta duba kuma taqi dagawa gami da jan tsaki "Bake ake kira ba sisi?" "Share kawai,al'amin ne" "A'ah,me kuma yayi da baza'a daga wayar sa ba" Dagowa tayi daga goga kubewar da takeyi"ni na bashi izinin gaisawa da su abba ne?,ni na sashi?,koni na aikeshi?" Tsayawa rumana tayi ta zuba mata ido ganin masifa fal idanun raihanan "Wannan ne laifi raihana,sai kace wanda ya aikatawa wani mummunan abu?" "Ok,ke a gunki ba laifi bane kenan.....ok,dama bakinku daya,ke kika sashi kenan....good,dadin abun ai ba'a so dole ko?,to bana yi ki gaya masa ya qara gaba" ta qarashe maganar cikin masifa kana ta maida kanta tana ci gaba da goga kubewarta. Shiru ne ya biyo baya na mintina,sukato rumanan tayi tana duban fuskarta ganin yadda ta dauki lamarin da zafi har irin haka,sai da ta bata rata ta kusan minti biyar sannan ta tako inda take,hannunta tasa kan kafadarta tana fadin "Kiyi haquri sister,tunda hakan laifi ne agurinki nima na yarda ya miki laifi,amma sis meye laifin wanda ke sonka?,meye laifin wanda ya damu da kai,na tabbatar har yau bakisan ciwon so bane shi yasa kike zargin al'amin kan abinda ya aikata,amma zan roqeki alfarma daya indai na isa ayimin ita..... Kada ki kori al'amin kada kuma ki nuna masa komai,kinsan cewa gaida su abba baya nufin komai,hakanan bazai canza komai ba,abba bazaice shi zaki aura ba ba tare da yaji ta bakinki na,aure dai ke kanki shaida ce abba baya yarda ayiwa wasu auren dole bare mu 'ya'yansa,just ki bashi chance idan kikaji ya kasa kwanta miki kina da right din da zaki sauya shi da wani,pls sisi na naroqeki". Babu shakka rumana tafi qarfin komai a gurinta,ita kanta batasan me yasa ta dauki zafi har irin haka ba,sai ta saki murmushi tana juyo tana dubanta " yadda kika ce haka za'ayi,kinfi qarfin haka a gurina"tsalle ta saka ta rungume raihana tana fadin"thank you my sisi,in sha Allahu al'amin ya kusa canza wannan zuciyar wadda taqi buduwa,ya kusa sa miki soyayya cikin rayuwarki"dan tureta tayi daga jikinta tana fadin "Abun yazo wato tsallen ya dawo,jeki duba girkinki kada ya qone hajiya" suka sa dariya baki daya Qarfe daya da kusan rabi suka kammala,ummu bata nan bangaren tana wajen abban,don haka daki suka wuce,suna zuwa raihana ta zube kan gado yayin da rumana ta wuce kai tsaye cikin wardrobe dinsu ta fitar musu da kayan da zasu saka. Daya daga cikin atamfofin da ummu ta dinka musu ne wadda akayi wa dinkin riga da zani,sea green ce sai pinch da dison baqi su kenan kalolin jiki,ta gwada ta cillawa rumana tata "Ga naki sisi" ta cafe kayan tana cewa"wai nufinki wata kwalliyar zamuyi bayan wadda mukayi dazu,tab....barni kawai idan na watsa ruwa ba wata kwalliya da zanyi"sai rumanan ta langabe wuya tana fadin "Haba mana don Allah sisi,kunya nakeji nayi kwalliyar nan ni daya,kuma kinga ya rayyan naso nayi mishi,don Allah sai ki kasa yimin kara muyi mu duka?" "Rumana....rumana problem,shikenan naji" "Yauwa ko kefa" ta fadi tana shigewa bayan gida. Har ta fito ta soma kwalliyarta raihana na kwance,banda vibration din wayarta ba abunda ke hargitsa mata kwanya,ta tsani nacin kira a waya,ta fuskanci idan ba dagawa tayi ba al'amin ba qyaleta zayayi ta huta ba,tilas daga qarshe ta daga wayar ta kara a kunnenta "Ranki ya dade sarauniyar duka kyawawan duniya,har kullum ni mai neman afuwa ne a gareki,cewa nayi bari naji ko kunje gida lafiya?" "Lafiya qalau"ya saki ajiyar zuciya " to alhamdulillah,haka daka nake son ji" "Ok,in ba damuwa zan danyi wani abune yanzu" "A gama lafiya princess,godiya nake" katse wayar tayi ta cillar ba tare da tace komai ba baya ga tsaki da taja,rumana na kwalliya amma hankalinta duka na kan raihana,dariya ke cinta na yau ga raihana na hira da wani karo ka farko a tarihin rayuwarta,bakinta nata motsi tana son ta tsokaneta amma tana tsoron kada ta tsokano musu ita da al'amin din,dan daga wayar tashi data soma ma ta daina ya shiga uku. Sai da taga biyu saura sannan ta miqe ta fada bandakin,sanda ta fito rumana ta kammala kwalliyar,ba qarya kam tayi mata kyau kamar dazun,abunka da farar mace,ana zaune ana dauri "Kai masha Allah sister,gaskiya ya rayyan ya tsinci dami a kala" tayi harr da ido ta juya ta dubi raihana "Kamar yadda nima na tsinci dami a kala ba,Allah ban taba zaton na iya zabi ba irin yau,samun ya rayyan a rayuwata ba qaramin nasara bace,sai yanzu na sake tabbatarwa zuciyata da irin qaunar da nake masa" kallonta raihana take tana karantar yadda maganar ke fita bilhaqqi daga cikin zuciyarta,murmushi tayi ta soma shafa mai "Allah ya barku tare" "Ameen ya Allah" ta amsa da gaske tana jin wani rauni da soyayya ta gaskiya na mamayarta Rumana ce a gaba suna fitowa daga daki sukayi kacibus da ummu na shigowa falon "Inyeee,masha Allah,gaskiya bari abba yazo,irin aurensu raihana zan miki,rayyan sisin gwal zai biya sadakinki,don gaskiya diyata mai tsada ce" kunya irin wadda bata taba shiga tsakaninsu da ummu ba ta kamata,sai ta sunkuyar da kai tana murmushi tare da rabewa gefe,hakan ya bawa ummun nasarar gano raihana dake a bayan rumana rana dariya "Kai masha Allah,gaskiya na iya haihuwa" ta fadi tana duban raihana "Allah yayi muku albarka,ya nunan ranar aurenku" "Ameen ya Allah" sukaji an amsa. Abba ne ke shigowa sanye da jallabiya hannunsa riqe da casbaha,rayyan biye da shi shima sanye da jallabiya baqa mai gajeran hannuda alama daga sallar azahar suka dawo,idanunsa kan rumanan suka fara sauka,dukkaninsu sai suka shagala da kallon juna,kwalliyarta ta bugar da shi yayin da ita kuma jallabiyar da ya saka ta sake haska mata shi,sai taga ya koma mata kamar balarabe,hankalin abba da ummu bai kansu shi yasa basu lura ba,raihana ce dake bayan rumana ta sanya hannu ta zunguri rumanan bayan ta sake matsowa dab da ita,wanda hakan shi ya katse kallon da sukewa junansu "Zaku tafka abun kunya idan bakuyi wasa ba"ta radawa rumana tana mata magana qasa qasa daidai kunnenta dariya nason subuce mata. Da sauri rayyan ya maida hankalinsa gun ummu bayan abba ya fita a falonyana jin kunya ko ya gansu?,kada su yaran su rainashi fa,don ya gane mai raihana ke cewa da rumana " nifa yunwa nakeji,alkunyata ta gama qarewa" "Ku debi kayan abincin kuje can kuci nima da nawa mai gidan zanci" inji ummu. Raihana ce ta fidda musu kayan abinci rumana ta tayata dauka sukabi rayyan din bangarensa a baya. Cikin plate guda ya zuba musu abincin yace tuna baya,duk su saka hannunsu suci tare,hakan ya yiwa rumanan dadi,yayin da raihana taji wani banbarakwai,ta mance tuni da wannan tsarin nasu,ganin ta soma noqewa yasa rayyan din wani shan kunu kamar yana magana ne da raihanan shekara tara da suka wuce "Maza sanya hannu kici,kijimin yarinya,kina gani yanzun kin zama qatuwa ko?,to har yau zan iya zaneki,ya rayyan ne dai ba wani ba" dariya ya basu duka saidai shi a dakensa yake,sai da suka soma ci sannan ya sassauta fuskarsa ya soma basu labari sama sama kan abinda ya karanta wato cumputer science cikin muryarsa mai dadi da hikimar salon iya tsara magana daki daki,sai kuma yanayin garin england,raihana mai son jin sabbin abubuwan da bata da masaniya akansu,sosai labarin ke nishadantar da ita. Shagwabarta ta dinga masa sosai kamar yadda suka saba abaya idan suna cin abinci musamman mai zafi kamar tuwo,saidai ya gutsuro ya ajjiye mata a gabanta ta dauka,to yauma tarihin da suka maimaita kenan,tun abun na bawa raihana kunya har ta saki jiki,a hankali taji yanayin salon soyayyar na burgeta tamkar cikin karance karancenta da takeyi. Ita ta harhada kayan abincin da suka gama cin ta zuba cikin kwando ta miqe da niyyar basu sarari,kamar yasan nufinta kuwa yace "Ke raiha bebiya.....dawo"dariya sosai rumana ta sanya,irin sunan da yake kiranta kenan da shi farkon zuwanta gidan,wanda daga baya ummu ta sokeshi ta hanashi gaya mata tunda tace ita ba bebiya bace,ita kanta raihanan sai data murmusa,jerarrun fararen haqoranta da babu ko wushirya suka fito,ba musu ta ajjiye kwandon ta dawo ta zauna gami da cewa"gani" Sai da ya shanye lemon hannunsa yana dubansu duka su biyun ya dire kofin sannan yace "Hira zamuyi shekara tara me ya faru bayan bani nan,saboda anjima lokacinmu ne ni da angel......maza labarin karatu da samarukanku zaku bani" Dariya rumana ta saka yayin da raihana ta yi murmushi tare da kau da kai don batasan me zata ce ba,bata da wannan tarihin cikin kundin rayuwarta,indai ba labarin al'amin da suka hadu last week zata bashi ba,wanda ko full name dinsa bata gama riqewa ba,gwara ma dai karatun,don anan tafi kauri. "Uhmmm,ina saurare fa"saidai kafin sukai ga cewa komai wayar rumana dake gabanta ta shiga ringing,gabanta ya buga ganin sunan sadiq na yawo kan screen din,suka hada ido da raihana. Sai raihanan ta dake tare da dauke kanta,da sauri ta dubi wayarta dake hannunta kana cikin muryarta mai sanyi tace " af,afuwa ashe exchanging phone mukayi"ta fada tana dauke ta kan cinyar rumanan ta maye mata gurbinta da tata wayar wadda tama kasheta don kada al'amin ya sake damunta da kira. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga nana Aisha R.A tace:manzan Allah S A W ya kasance yana son damantawa(wato fara komai da dama),cikin tsarkinsa ne,ko cikin sanya takalminsa,ko cikin taje kansa,da cikin al'amuransa ma baki daya))* _______________________ *Babi na sha biyu* _note_ _Shekaran jiya babi na goma sha daya mukayi na manta ban rubuta ba_ Sanya wayar tayi a silent tana ci gaba da kallonta har kiran ya katse ba tare data daga ba,yana katsewar kuwa tayi gaggawar kashe wayar baki dayanta,yayin fa gefe daya rumana da rayyan ke kallonta,rumana na kallonta ne cike da fargaba da faduwar gaba,ganin ta kashe wayar ne ya sanyata sakin boyayyar ajiyar zuciya tana hamdala cikin ranta tare da godewa raihana. "Nifa na yiwa abokina kamu?" Duka suka waiwaya suka dubeshi,rumana dariya na cinta tace"kamun wa?" "Kamun raiha mana" kasa boye dariyar tayi sai ta fashe da ita tace "Tab,lallai ya rayyan ashe kana gab da shan kunya" girarsa ya dage yaba dubanta "Kamar yaya?" "To ai raihana da kake gani ba abokiyar hada kai bace ta wannan bangaren,wallahi kunya kawai zata baka,nan da kake ganinta ko zance bata taba tsayawa ba". Cikin mamaki ya dubeta kana ya dubi rumana " dalili dame?"baki ta tabe gami da dage kafadarta "Nima bana ce ba,amma ta taban gayan har yau bata samu wanda ya dace da ra'ayinta ba" Komawa yayi rayyan dinshi sak yana dubanta "Am seriouse raiha,na miki sha'awar amir,abokin karatu na ne,tare muka kammala da shi,dan jigawa ne kazaure,amma asalinsu 'yan kano ne,yana da hankali da nutsuwa,kuma nayi imanin taku zato zo daya da shi,na sanshi kema na sanki" kanta na sunkuye ba tare data ce komai ba,yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta. Tana jin bata data cewa,abinda ya rage mata kawai ta baiwa amir din dama tunda har rayyan din ya yaba da shi don haka "to" kawai tace da shi,cikin dabara ta sullubewa hirar tasu ta shige cikin gida ta barsu anan suna tsinkar fure ************* To yadda suka tsara yin ziyarce ziyarcensu a dangi cikin satin da rayyan din ya dawo hakan bata samu ba,sai da yayi hutun kwana uku ba inda yake zuwa yana gida,cikon kwana na hudu ne motocin da yayi odarsu suka iso,guda uku ne sababbi fil masu azabar kyau da daukar ido,daya tashi,daya ta ummu daya abba ya sayawa,shekara shida yayi ya kammala masters degree dinsa a fannin computer science,wani kamfani ne mai zaman kansa suja riqe shi har shekara uku yana musu kyau,suna matuqar ji da rayyan din sakamakon basira da qwaqwalwa da Allah ya bashi,mutum ne shi dan gaske tsayayye,jajirtacce kuma mai riqo da gaskiya da amana,to kasan halin malam bature,irin mutanen da yake son hulda da su kenan,shi kansa yasan ba qananun kudade ya samu da su ba,don suna ninka masa albashinsa ne duk don ya yarda yaci gaba da aiki da su,ko da ya tashi tahowa ya ajjiye musu takardar barin aikin ba haka suka so ba,hakanan suka qyaleshi don babu yadda zasuyi,amma sun sanar da shi duk lokacin da ya sauya ra'ayi suna maraba da shi. Ba qaramin murna sukayi da wannan kyauta ba,sosai suka dinga sa masa albarka,sannan ya sanar da abba filayen da ya siya guda biyu,daya anan jikin gidan su da suke ciki yanzu,daya kuma cikin unguwar rijiyar zaki ne,yace na rijiyar zakin nashi ne yana so ua fara ginawa,wannan na kusa da su kuma nasu ne "Masha Allah,da kyau hakan yayi rayyan,Allah ya albarkaci rayuwarka,ya baka zuriya ta gari,ina ganin zuwa ko zuwa sati na sama lokacin abbanku dalhatu ya dawo daga tafiya sai ayi maganar sa auranku kai da rumanan,koda ginin bai kammalu ba indai an samu iya inda zaka iya ajjiyeta falil lahil hamdu" ya dan sadda kai kawai yana sakin murmushi cikin jin kunya Sun zaga dangi kuwa sosai yadda ya kamata,wanda kusan mafi yawa dangin alhaji dalhatu ne,tunda sune mazauna kano,nasu ahlin kadan jigon suna nijer,amma duka daya ne haka suke daukar junansu. Kusan ziyarar kamar qara wata 'yar manuniya ta zama kan soyayyar dake tsakaninsa da rumana,wanda baisan da maganar ba a yanzu yasan da ita,kowa murna yake da sam barka tare da addu'ar ganin lokacin aurensun. Hutun da suka samu na makaranta saboda gama exams dashi sukayi amfani suka mori lokacinsu,hakanan rumana ta samu damar bargaje soyayyarta da rayyan yadda ya kamata. Abu guda tak dake mata barazana,yawan kira daga abokanta na makaranta maza da take samu,wanda hakan sau tari yana dagula mata lissafi,duk da qoqarin kaucewa idon rayyan da take amma fargabar na nan tare da ita ************* Kimanin awarsa biyu kenan da shigowarsa cikin gidan,banda wanka da ya sake da abinci da yaci babu abinda ya iya tsinanawa,damuwar da take danqare qasan zuciyarsa ita tayi tasiri har gangar jikinsa ta haifar masa da kasala,bai son damuwa sam a rayuwarsa saboda bai tashi cikinta. Daya daga cikin littattafansa da yakan duba lokuta irin wannan da yakeson kautarwa kansa da tunani ya dauka ya soma duba shafi bayan shafi,wanda hakan ya daukeshi mintina kusan arba'in da biyar. A hankali ya sauke littafin,halayyar tauraruwar ciki sai ta burgeshi,ya dinga bitar dabi'un cikin kwanyarsa daya bayan daya,damuwar dake ciki ta kwaso a guje ta tsinke zaran tunanin nasa,tsaki ya ja bayan daya gama tuna abinda ya farun dazu gami da ajjiye littafin a gefansa,wayarsa ya dauka ya lalubo lambarta ya kira. Tana tsakiyar dakin nasu wanda ta baje littattafanta na makaranta tana daidaita kansu saboda cikin satin zasu koma,sanye take da mutuniyar tata wato duguwar riga amma ta atamfa ce mai shan umbrella,kanta babu dankwali ta cireshi gefe saboda zafin da takeji,sakamakon tsefe kan da tayi gashi da cika,don haka bata fiya tsifa ba indai tasan ba wankin kai ko kitso zata ba saboda damunta da yakeyi. Lokaci lokaci takan daga kai ta dubi rumana dake kwance rigingine kan gadonta,tun dazun ta lura akwai damuwa sosai kan fuskarta,amma ganin bata ce da ita komai ba ya sanya itama tayi shiru,bata da aqidar shishshigi da son sanin halin da mutum yake ciki,mawuyacine tabi qwaqwqwafin abinda bakai ka gaya mata ko ka nemi ta sani ba. Ringing din wayar tata ne ya dan ja hankalinta,da fari qin dubawa tayi ga zatonta farouq ne ko al'amin,sai da ajjiye littafan hannaun nata sannan ta duba,ganin me kiran ya sanyata daga wayar ta kara a kunnenta,magana yayi da bata wuce sakan biyar ba duka suka ajjiye wayar,ta juya tana duban rumana dake kwance tana charting amma damuwa kwance kan fuskarta "Ya rayyan ke kirana rumana" ajjiye wayar tayi da sauri ta miqe daga kwanciyar tana dubanta "Ya shigo gidan kenan?" "Eh tunda gashi yace yana daki.....ko zaki tashi muje tare,tsoron fitar nake ni kadai" Kai ta girgiza tana tabe baki "Jeki kawai,ba inda zani.....bakisan fada mukayi dazun ba?" Cikin zare ido raihana data soma nada mayafinta aka ta dubeta tace "Fada kuma?,me ya hadaku?" Ajiyar zuciya ta saki sannan tace "Sadiq yaga ya kirani,kuma fa bawai wani hira bace,kawai gaisawa mukayi,ya gayan ya dawo daga tafiyar da yayi japan,shikenan fa" kai raihana ta shihga girgizawa "Bakiyi daidai ba rumana,banga inda kika kyauta ba anan gaskiya.....hana rumana,wai maza nawa zaki aura ne?" "Ce miki akayi soyayya nake da su?....duk wanda kika ganni da shi mutunci ya hadamu kuma bazan iya wulaqanta su ba.....me yasa kuka kasa fahimta ne?,kunsan matsayin ya rayyan kuwa a zuciyata,ke kinfi kowa sanin matsayinsa raihana,a yau idan na rasa ya rayyan inajin har na koma ga mahaliccina bazanyi aure ba". Shiru ne ya ratsa dakin,tausayin rumanan ya fara ratsata ganin yadda idanunta suka soma hada qwalla,da alamu maganar ta taba zuciyarta ne,ita kanta shaidace lamba daya kan son rayyan dake zuciyar rumana shekaru bila adadin da batasan yawansu ba,tunda ko ita din ma tare tazo ta taras da su,matsalar rumana sakin fuska ga kowa da saurin sabo,hakan sau tari sai tace ka kori wanda yake yinka tamkar ka wulaqantashi ne,itakam ta rasa yadda zata fassara abun " bari naje na dawo,kada ki damu zanzo mu tattauna kinji sisi na 'yar tsalle"ta qarashe maganar cikin sigar zolaya,ta kuwa samu yadda takeso,don murmushi rumanan ta saki tana share hawayen fuskarta,cikin zuciyarta tana godewa Allah da ya bata 'yar uwa irin raihanan "Saikin dawo ina jira" "Ince to kina gaida shi?" Kai ta kada sauri "Nidai ban aikeki ba" "Zaki aikenin ne ma,kowa fa ya sani fadan masoya hutu ne" tayi maganar tana ficewa a dakin tana murmushi A hankali ta tura qofar dakin ta shiga da sallama,yana zaune kan kujera ya jingina bayansa a makarin kujerar,yayin da ya miqe qafafunsa bayan ya hardesu saman center table,idanunsa a lumshe suke,tsaf dakin yake cike da qamshi da sanyin na'urar sanyaya daki,rayyan badai tsafta,akwaishi da qyanqyami hakan ya sanya yake gwani wajen tsafta. Ya bude ido ya kalleta na 'yan sakanni kanna ya masa mata ta maida qofar ta qaraso,da hannu ya mata nuni da kujerar dake fuskantarsa "Gani ya rayyan" ta fada cikin muryarta mai sanyi Sauke qafafun nasa tayi qasa sannan ya gyara zamanshi "Raihanah" yanayin yadda ya kirata dinne ya sanya ta sake shiga nutsuwarta "Na'am" ta amsa masa tana duban gefensa bashi din ba "Ina so ki gayan wace rumana,ma'ana wace rumana bayan barina gida,ya rumana ta kasance bayan ta girma?". Cikin rashin fahimta ta dago tana dubansa "Yaya ban gane me kake nufi ba" "Kin gane tunda gwari gwari nayi miki,saidai kice kina buqatar qarin bayani ko?...."ya fada yana sake daidaita zamansa "Ina nufin ki gayan meye halayen rumana,na tambayeki ne saboda wasu abubuwa da na lura tattare da ita wadanda zasu iya haifar mana da matsala". Shiru tayi tana jin ya dora mata nauyi mai girma,tabbas rumana ta jama'a ce maza da mata yara da manya,ta yaya zata gayawa rayyan haka ta sigar da zai fuskanceta?,ta sani kuwa sarai idan ta bude baki da niyyar cewa komai to zatayi qarya ne. Ci gaba yayi da zuba mata ido har tsawon kimanin minti goma,tuni ya gama karantar ma'anar shirunta,gyaran murya yayi kadan sannan yace "Ni bari na gaya miki tunda ke bazaki gaya min ba,rumana nada tarin jama'a da take mu'amala da su,bawai ina nufin mummunan mu'amala ba,irin abinda kuke kira da friendship ko?" Batasan sa'ar da ta dubeshi,da sauri ta fara girgiza kanta "A'ah,ka fahimceta ya rayyan,kowacce budurwa idan ta taso dole ta masu masu son qulla mu'amala da ita,haka yake ga kowacce mace indai tana kan lokacinta......" "Ke haka kike?" Ya tambayeta kansa tsaye,dif tayi masa kama daga bisani ta daga masa kai a sanyaye alamar eh. Wani murmushi ya saki ya maida bayansa jikin kujerar ya sake jingina ganin ta raina masa hankali,a hankali ya dinga kada kansa sannan yace "Kin manta tun kuna da majina ahanci na sanku?,ba sanin jiya ko yau bane ko gobe.....dubeni nan raihana,ki dago kanki ki gayan ni raihana nima haka nake" Tanajin rumana ta cancanci ta bata kowacce iriyar kariya daga gareta,da qarfin gwiwarta ta dago ta dubeshi,tashin farko wani irin kwarjininsa ya cika mata ido,ta gaza ci gaba da kallonsa yayin da shi kuma ya kafeta da ido,kunyar yi masa qarya ta mamayeta,a hankali ta janye idanunta ta maida kan yatsun hannunta da suka sha ja lalle tana qare musu kallo,shi din ma maida idonsa yayi kan inda take kallo din kana daga bisani ya janye idanunsa "Kayi haquri ya rayyan zamu gyara in sha Allahu,rumana na matuqar sonka" "Ni din ma ina sonta,amma kuma ina da matuqar kishi" "In sha Allahu zamu gyara ya rayyan,yanzu haka tana daki cikin damuwa don Allah kayi haquri"shiru yayi yana dubanta kamar bazai tanka ba,har sai data dago taga yana gurin,sai ta sake sadda kanta " please ya rayyan" "Is ok.....ki turomin ita" Murmushi tayi ta dubeshi "Yauwa yayanmu,mun gode" shima martanin murmushin ya maida mata ta juya ta fice a dakin ************* Da dan sassarfa ta qaraso motar kana ta bude gidan gaba ta fada ciki,ta dubi rayyan dake zaune cikin motar cikin shagwaba tace da shi"afuwa mai gidana,kaga ko kwalliyar ma baban kammala ba na fito"ya dan saki fuskarsa yana qoqarin tada motar "Kin wuce haka gimbiya,ya wuce",sai ta waiwaya ta dubi raihana dake gidan baya a zaune " afuwa sisi na" kada kai tayi tana murmushi"ya zamemin jiki"sukayi dariya ita da rumanan. dukkansu sanye suke da material pinch sai abun daurinsa maroon,ba qaramin kyau sukayi ba kasancewarsu cikin sahun wadanda Allah ya wadata da kyau,biki akeyi na 'yar qanwar alhj dalhatu sumayya wadda take jika ce agun hajiya babba kamar yadda rumana take,yau ne dinner din,ummu tace rayyan din ya kaisu,dama yayi niyyar yin haka don baison suje su shiga motar wasu. Daya hannun nasa yasa ya zari cd plate ya tura ciki ya danna play sannan ya rage sautinta qasa qasa,waqar shehu kan giwa ta soma tashi cikin motar,duk da tsohuwar waqace amma kidanta ya fito rangadadau,hakan baitukan cikin waqar a bayyane suke,sosai raihana keson waqar ita da waqar ahmad a ruwa suna burgeta,rumana ta tsaya da daurin da take sannan ta bushe da dariya "Haba ya rayyan,ni na dauka wata hadaddiyar waqa zaka saka mana" "Wannan din ma nada ma'ana ki saurara kiji" "Na dade da saninta a gun sisi,ta dade tana gayan hakan nikam har yau bani da ra'ayinta,ita din ma mayyarta ce,wani lokaci ra'ayinku da halayyarku daya,yanzu ya rayyan waye zaice ka rayu cikin england don Allah" ta fada tana masa dariyar tsokana,ci gaba tayi da daurin dankwalinta tana cewa "Wannan waqar ai sai su abba da daddy" "Bakya ganewa rumana,bakisan karatun dake cikin irin wadan nan tsaffin waqoqin bane" inji raihana "Rabu da ita,batasan waqoqi masu ma'ana bane" nan qaramar muhawara ta hadu wadda ita ta tayasu hira har suka kai wajen. A bakin wajen hall din ya ajjiyesu,raihana ta fidda glass dinta ta saka sai ya qarawa kwalliyar tata kyau,rumana ta waiwayo ta dubeshi a shagwabe "haba yaya rayyan,yanzu ba zaka shiga ba" kai ya kada "Akwai gurin da zani,idan an tashi ki kirani nazo na daukeku" Kicin kicin tayi da ranta sannan ta dubi agogonta cikin kishi tace "Ina zakaje a irin wannan lokacin" "Zance zani" ba rumana ba,hatta raihana dake qoqarin ficewa daga motar sai data dakata,tuni rumana ta fara hada qwalla "Wanne irin zance kuma yaya rayyan?" Raihana ta tambaya a sanyaye "Eh sabo nayi?" Ya fada fuskarsa a daure,qasa tayi da kanta tana kadashi "a'ah ba sabo kayi ba" inji raihana,basu ankara ba saiga k'walla kan fuskar rumana "Subhanallah...rumana daga wasa?" Ai kuwa saita qarasa fashewa da kukan "Haba ke kuwa wasa fa nake miki....ungo share hawayen" ya fada yana ciro tissue daga gaban motar ya miqa mata,ta amsa ta soma gyara fuskarta yayin da shi kuma ya zuba mata ido yana sakin murmushi qasa qasa,girarsa ya dage yana fadin "Kinga nayi nasara,wannan kwalliyar da kikayi dama tayi yawa ni kadai ya kamata na gani,yanzu kuwa kinga da na saki kuka na rage farashinta" sai ta soma dan bubbuga qafarta cike da shagwaba,raihana ta rufe bakinta tana yiwa rumanan dariya ta fice daga motar ta tsaya a waje tana jiransu don ta fuskanci abun nasu na masoya ne,ita kadai ta dinga sakin murmushi. Minti kusan uku saiga rumanan ta fito,shima ya fito daga nashi gun ya dubeta yana cewa "Idan an tashi ban kammala abinda nakeyi dinba ku wuce qoqi kawai ban yadda ku hau motar kowa ba,zan bi ta can na daukeku" "An gama ranka ya dade"inji rumana,suka juya suka fara tafiya ya bisu da kallo. Kiranta taji yayi ta dubi raihana "sisi minti daya,ko yayi mantuwa ne"kai ta gyada mata ta juya da dan sauri zuwa inda yake tsaye,murmushi ta kuma saki dai,bata taba jin soyayya ta burgeta ba sai yau. " me yasa aka banbanta muku dinki?"abinda ya fara tambayarta kenan,sai ta dubi rigar jikinta ta dubi ta raihana dake can dan nesa kadan da su,doguwar riga ce a jikin raihanan ita kuma fitted gown "Kowa choice dinsa ake masa damakuma ma duk daya ne yaya rayyan" kai ya gigiza "Ba daya bane rumana,kalli shigarki kalli tata" ya fada yana tsareta da ido,sai lokacin ta kula,ko mayafansu duk da iri daya ne amma na raihana ya danfi nata girma,duk a ganinta wannan ba komai bane tunda bata fitar da tsiraici ba,ta mayar da kallonta gurinsa "Kayi haquri yaya" Baice komai ba ya juya ya shige motar sannan ya sauke glass din ya dubeta "Kina iya tafiya,ki kula da kanki..." "Insha Allah" ta fada ranta ya mata sanyi da bai mata fada ba,tana tsaye tana kallonshi har ya bar gurin sannan ta nufi gun raihana,ra'ayi ne nasu yasha banban,amma tana qoqari sosai wajen canza abubuwan data fuskanci bai dace da ra'ayinsa ba,amma yata iya dabi'arta ce tun asali a sannu take san ran komai zai sauya yadda ya kamata ta yi boyayyar dariya tana jin yadda son rayyan din ke sake ratsata,duk wani tsaruka nashi burgeta yake,bata jin za'a kuma halittar namiji kamarsa a zamaninta. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Manzan Allah S A W yace "ku guji addu'ar wanda kuka zalunta,domin babu hijabi tsakaninta da Allah(ma'ana kai tsaye take wucewa,take kuma Allah yake amsata)* ______________________ *Babi na goma sha uku* Suna shirin shiga hall din sukaji ana kiran rumana, "Rumana dalhatu attahir" suka juya duka ita da raihanan,'yammata ne guda biyu suke nufosu fuskarsu dauke da murmushi,itama murmushin tayi ta nufi inda suke tana kiran sunayensu,kai raihana ta kada cikin zuciyarta tana fadin "Rumana.....rumana mai jama'a". Tare suka qaraso gun suka gaisa da raihana suka shige inda ake gabatar da bikin. Qarfe goma aka tashi na dare,sumayya amaryar ta tsaidasu don haka kusan lokaci guda suka bar gun,motar wani abokin angon usman ce su uku kawai ya debo,rumana raihanan da kuma wata Aisha qawar sumayyan. Rumanan ce a gaba,gaba daya da na sanin shigarta motar take saboda yadda usman ke janta da hira,tuni jikinta ya gama gaya mata inda ya dosa a matsayinta na wayayya gogaggiyar mace,wadda ta saba hulda da mutane kala kala,duk yadda ta kai ga hade ranta hakan bai damu usman ba qoqarin kafa kanshi kawai yake. Tafiyar minti talatin suka iso qoqi,dukkansu suka bude murfin motar suka fito har da rumanan,ganin hakan ya sanya usman hanzarin fitowa tare da shan gabanta,gefe raihana ta janye ta samu daya daga cikin dakalin qofar gidan ta zauna tana kallon yadda ake ta dawowa tare da shige da fice cikin gidan,sun gama tsara ba zasu shiga cikin gidan ba zasu tsaya nan waje su jira rayyan saboda gobe suke so su taho gidan kuma ba zasu koma ba sai ranar litinin ko talata an gama biki kenan. Tana tsaye ne kawai ba tare da tana fuskantar me usman ke fadi ba,Allah Allah take ya bata guri ta wuce,saidai kash abinda take tsoro tuni ya faru. Motar rayyan ne ce ta shigo layin a hankali bayan ya kunna fitulun motar full light,motoci biyu ne kadai suka rage a gun daga ta usman sai ta anwar wani jikan gidan. Tsayuwar motar rayyan din daga can baya ya bata cewa mawuyacine idan ba ganinsu yayi da usman din ba,raihana dake latae latsen wayarta batasan meke faruwa ba sai da taga haske ya cika inda suke,kallon sakanni biyar ta yiwa motar ta ahaida motar rayyan ce,da hanzari ta rufe wayar ta nufi inda rumana ke tsaye zuciyarta na tsinkewa tare da addu'ar Allah yasa bai gansu ba,ta matsa gefan rumanan cikin dabara ta rada mata ta tafi gun ya rayyan ita zata ci gaba da tsaiwa da usman zata sallameshi,gyada kai rumanan tayi cikin sarewa tare da addu'ar Allah ya sanya plan din nasu yaci,ko ta kan usman din bata kuma bi ba ta nufi motar rayyan din. Sai da raihana taga shigarta motar sannan ta maida kanta gun usma "Kayi haquri don Allah,rumana an yi mata miji,dan uwanta zata aura,yanzu haka shine a can yake jiranmu"sai ya saki murmushi yana dubanta " tunda an yiwa rumana miji idan banyi kuskure ba naji tana kiranta twin sisternta,me zai hana ki canjeta"wani kallo ta bishi da shi sannan tace "Nidin ma da nawa mijin,sai anjima" ta juya ta nufi inda motarau ke fake. Da sallama ta shiga gidan bayan saidai tun kafin ta daidaita zamanta cikin motar gabanta ya buga sakamakon sheshsheqar kukan rumana ta ta cika motar "Kayi haquri ya rayyan,nima ban san shi ba fa kuma ma bani....." Tuni ta fahimci kan zancan saboda haka da sauri ta katse rumana "Ya rayyan,guri na fa yazo,ba gunta yazo ba,tsayawa tayi kawai suka gaisa sabo......" "Ya isa da Allah!" Ya daka mata tsawar data kada hantar cikinta,runtse idonta tayi zuciyarta na harbawa da sauri da sauri,rabon da taji irin wannan tsawar tun kan tafiyarsa england "Dukkaninku a qalla na baku shekara dai dai kusan bakwai,so ni ba yaro bane,na girmemaku bare kuce zaku dinga wasa da tunani na" ya juyo yana duban raihana,tsoro ya sake kamata,saita hade guri guda ga zatonta mangari zai kawo kata saboda ganin yadda tashi guda fuskarsa ta sauya "Daga yau ina mai gargadinki kada ki sake bawa rumana kariya kamar yadda kika dinga mata a baya,gargadi ne ba shawara ba,idan kuma kika sake kika karyamin doka,ranki sai yafi na kowa baci" daga haka ya kunna motar yayi ribas ya jata a guje suka fice daga layin suka harba titi. Shiru ne ya ratsa motar,sai sautin sheshsheqar rumana kawai ke tashi,wanda hakan ya daga hankalin raihana saidai tsoro ya haba qwaqwqwaran motsi,gudun da yake tsalawa da su kawai ya isa ya gaya maka tafasar da zuciyarsa keyi,cikin mintina qalilan suka iso gida,ya sauka ya tura get din gidan kana ya dawo ya shigar da motar. Rumanan ce ta fara ficewa tana ci gaba da kukanta,ta zura qafarta a waje jiki a sabule tana shirin ficewa ya dakatar da ita "Amir ya shigo kano dazu mukayi waya da shi,gobe in sha Allah zai qaraso gidan nan don ku gana ke da shi" ya fadi maganar cikin dacin rai "Allah ya kaimu" kawai tace ta fice daga motar tana son cimma rumana don ta rarrasheta. Kusan raba dare sukayi zaune raihana na aikin lallashi rumana na aikin kuka da qunan zuciya,hakan ne ya jawo tilas washegari suka haqura da tafiya gidan hajiya babba su kwana suka barwa washegari,sannan kuma ga maganar zuwan amir wanda har ummu ta sani. Washegari Allah yasa rumana tatashi cikin kuzari da qwarin jiki saboda jin labarin zuwan amir din gurin raihananta,sai kuma kasalar ta koma kan raihana,hakanan takejinta wani banbarakwai wai ita zata tsaya zance da wani,wanin ma da ake fatan ya aureta,kusan duk wani shiri da ya kamata raihanan tayi na zuwan amir din rumana ce ta gabatar da shi,har ummu na tsokanarta "Irin wannan canzawa haka raihata(da yake haka take kiranta wasu lokutan idan zata jata da wasa)sai kace wadda akace an bada ita amir din ya kawo sadaki?" Murmushi tayi cikin jin kunya tana sunne kai Rumana ce ta sanyata a gaba kan wallahi yau ko zata mutu ta dawo sai tayi kwalliya,akan me,raihananta mai kyau da aji amma ta dinga boye baiwar da Allah yayi mata,badon taso ba don kada ta bata ran rumanan ta haqura ta zauna ya fara gyara mata fuskar. Kyan da raihana tayi kuwa ba qarami bane,saboda rumanan tayi amfani da kayan kwalliyar da suka dace da kalar fatar raihanan "Gaskiya yau na qaryata da ake cewa wanda bai saba kwalliya ba ranar da yayi baya kyau,kin ganki kuwa my sisi?" Kallon kanta tayi cikin madubin,ita kanta ta yaba sosai da irin kyan da tayi,saidai a son ranta tafiso ta jewa amir din a yadda take,idan zaya sota ya sota da ainihin kyanta bana qyale qyale ba,kamar yadda take ta kuma saba rayuwarta ta ainihin gaskiya da gaskiya ba rayuwar qyale qyale ba,saidai bata furtawa rumanan ba don batason taga kamar ta kushewa qoqarinta da fadi tashin data wuni yau tanayi duk don jin dadinta. Atamfarta ta dauko sabuwa wadda tare suka kai dinkin ita da raihanan,saidai ita raihanan ba'a gama nata ba ta bata tace ita zata sanya saboda kalar zata dace da fatarta,ba mutuminta bane dinkin riga da skert,kamar ta tunasar da rumanan sai kuma tayi shiru,hijabi ta dauko mai kyau wanda ummu tasa aka dinko musu daga zariya wanda ya dace da atamfar ta zata sanya ba tare data daura dankwalin kayan ba,riqe hijabin rumana tayi "Haba sisi,duk wannan kwalliyar?" Wannan karon kam dole ta shigar da qorafinta "Ki barni in sashi don Allah,kinsan dai bana son sanya riga da skert fa,bare wannan duba fa ki gani yadda ya fidda shape dina,pls my sisi kada ki hanani" sai ta sakar mata hijabin kawai. Qarfe hudu da mintina Amir ya qaraso,bai tadda rayyan ba don baya gida,tun safe suka fice shi da abba,don haka rumana da kanta tayi masa iso suka gaisa,ta shigo da shi cikin zaure na biyu na gidan,ta shimfida masa carfet tare da gabatar masa da kayan motsa bakin da aka tanada saboda shi kafin raihanan ta fito. Tun daga shigowarta zauren yaji tayi masifar yi masa,saboda kallo daya zaka yi kamata ka karanci yanayin natsuwarta sanyin hali da kamun kanta,ita din ma ba laifi a hakan yayi mata,duk da ba wani sonsa taji cikin zuciyarta ba,amma yanayinsa da dabi'unsa sun mata,amir nada kyau ajin farko,don idan basuyi kunnen doki da yaya rayyan dinsu ba to bazai fishi ba,dogo ne shima fari,yana da kamala a fuska da nutsuwa,sun shafe a qalla a wanni biyu suna tattaunawa,ya mata tambayoyi soaai ta amsa mishi,haka itama ya bata dama ta masa duk tambayar da taga dama,saidai sam bata jinta a sake, kunya da rashin sabo suka hanata tambayarsa komai,sannan daga bisani ne ya soma shirin tafiya. Leda ce 'yar madaidaiciya ya miqa mata yana fadin"ga wannan babu yawa sai ayi haquri da shi,babban fatana shine Allah yasa na samu muhalli,duk da an gayan baki sauraren kowa,ina fata nine mutum na farko da zaya samu wannan damar"qin amsa tayi hakan yasa yayi rantsuwar bazai koma da kyautar da yayi niyya ba,hannu biyu tasa ta karba kanta a qas tana dada yi masa godiya,ya bita da kallo yana ji tana dade burgeshi tare da shiga zuciyarsa. Har qofar gida inda ya faka motarsa tayi masa rakiya,saidai kafin ya kai ga shiga ciki motar rayyan ta shigo layin,hakan ya sanyashi fasa tafiya ya fito ya tarbi rayyan din fuskarsa fal annuri,ita kuma raihanan sai ta barsu nan ta koma cikin zauren ta kwashe kayayyakin da sukayi amfani tayi cikin gida A kitchen ta tadda ummu da rumana na hada abincin dare,rumanan na murmushi ta dubi raihana da alama tana son taji kanun labaran ne,tilas amma tayi shiru ta haqura saboda idon ummu da 'yar kunyar dake tsakaninsu da ita,ummu ce ta tambayeta"har ya tafi ne?" "A'ah suna tare da yaya rayyan" "To Allah ya daidaita lamarin"rumana ce ta amsa da "amin". Basu bar kitchen din ba sai da aka fara kiran sallar magariba zuwa lokacin sun kammala don haka suka fita baki daya donyin sallah. A hankali ya tura qofar dakin nasu hade da yin sallama,sanye yake da t.shirt maroon da baqin trouser wanda suka haskashi,farinshi da kyansa ya qara fitowa,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa kamar yadda kusan dabi'arsa ce hakan,rumana dake zaune gefan gadon dauke da dan littafi ta dago ta amsa masa,gabanta ya dan fadi,wani kyau taga ya sake mata,sonshi ya sake fisgarta,da sauri ta maida kanta ta sadda tana ci gaba da kallon littafin,shima ya dan bita da kallo,sai ya dauke idonsa ya maida kan raihana dake saman darduma tana zaman tahiya,shiru ne ya ratsa dakin,kowa najin qyashin cewa dan uwansa wani abu,yayin da rumana zuciyarta ke bugawa da sauri sauri sabanin yadda ta saba,ya dan jingina jikin qofar yana harde hannayensa a qirjinsa ganin zaman tahiyar nata ya ja lokaci,idonsa ya sauka kan hotonshi dake saman gadon rumana,sai ya dan saci kallonta,har yanzu idonta na kan littafin,duk da itama satar kallon nasa take,ya sake maida idonsa bangon dakin,hoton raihana da ruma na dinne su biyu,rumana na bayan raihana ta dora fuskarta kan kafadar raihanan suna qyalqyalta dariya,dukkansu suna sanye ne da skert dogo har qasa sai ruga 'yar ciki kai gajeran hannu,sai suka dora wata mai sogon hannu wadda tazo musu har saman gwiwarsu,kansu yasha gyara ba dankwali sai siraran mayafansu dake rataye a kafada,boyayyen murmushi ya saki da ya tuna can wani lokaci baya,sanda aka yi masu gyaran kai ake ajandaf na wane yafi kyau?,sai yaji tambayar ta dawo masa kamar a alokacin rumana ke masa ita,samun kansa yayi da tsurawa gyaran gashin dake hoton ido yana son tantance wanda yafi kyau din,sallamar sallar raihanan ce ta tsinke masa zaran tunaninsa,ya dubeta yana tsaiwa kan qafafunsa sabanin dazu da yake jingine da qofa "Me ya samu wayarki ne bata shiga?,ki hado mana abinci ki kawo mana dakina ni da amir" ya gaya mata saqon yana mai juyawa yabar dakin ba tare da ya jira ta bashi amsar tambayar da yayi mata ba. Ta miqe tana ninke abun sallar sai suka hada ido da raihana,qwalla ta gani taf idon rumanan,a sanyaye ta ajjiye abun sallar don tasan inda matsalar take,ta qaraso kusa da rumanan "Rumana kiyi haquri" kai ta girgiza tana murmushi "Ko kadan bana ganin laifin ya rayyan yanzu raihana,ni ja jawowa kaina,ya riga yamin shaidar tarin abokai,kinga kuwa ko dawa ya ganni a tsaye koba kulashi nayi ba zan dauka magana muke,zan gyara matsalar da kaina insha Allahu.....ki kai musu abincin nasan yunwa yakeji,ki kuma dawo ki bani labarin amir,nasan ya rayyan ya miki zabi ingantacce" murmushi ta sakar mata kamar yadda itama murmushin ne bisa fuskarta,ta miqe ta maida glasa dinta tafice daga dakin tana jin qaunar 'yar uwarta. Tana sallama da shi suka fara hada ido,yana zaune kan daya daga cikin kujerun falon rayyan din,ya kafe ta da ido kuwa har taji kunya kamar zata kayar da ita,daidai lokacin rayyan ke fitowa daga cikin dakin sanye da jallabiya da alama wanka yayi amir ya miqe ya karbi tiren hannunta yana fadin "Sannu gimbiya,Allah ya saka da alheri" murmushi tayi ta juya ta fice ya bita da kallo tamkar ya tsaidata yayita kallonta. Rayyan ya taboshi yana fadin'"to ai ta fice,sai abar kallon qofar kuma haka ko?"kai ya kada yana dariya "Allah yarinyar ta tafi da ni rayyan,bansan kana da qanwa kamar haka ba da tuni na dade da yiwa kaina kamu" "To ai yanzun gashi da lokaci yayi an hadun ko?" Rayyan ya fada yana sauke musu tiren a qasa ya zuba musu abincin cikin plate ya sanya musu cokula,amir ya dauki cokalin amma sai ya kasa cin abincin ya hau sumbatu kan raihanan "Allah babban yaya don yanzu sunanka ya koma haka ka gama min komai duniya da lahira,kasan raihana irin matan dake masifar tsada ne a wannan zamanin?,irin matan dake wuyar samuwa ga mazaje?" Murmushi rayyan ya saki "Daga haduwa yau ta yaya akayi kasan haka?" Dariya amir shima ya saki,"haba rayyan,ya kake magana kamar ka manta waye amir isma'il uba?,'yammata nawa na yi maka hasashen halayensu haduwar farko kuma daga qarshe hakanne,ka manta baiwar da Allah yayimin ta wannan fannin,tunaninka kamanninka fa,haka daga maganarka kawai nake gano inda ka dosa,ko ka mance naji wasu daga halayenta tun kafin na iso gareta,wasu kuma na gansu da idona?"shiru rayyan yayi saboda tuna amir din,wanda a da kafin su ganeshi shi da wasu abokansa kallonsa suke kamar mai aljanin gano halayya. "Yanayin raihanan kawai da kalamanta sun isa su gaya maka wacece ita?,ban taba zaton zanyi katarin samun matar aure irinta ba,sai gashi dare daya Allah yayi min kyauta mafi tsada wato raihana,irin matan da suke zamewa kwanciyar hankali wa mazajensu,gaskiya na gode da wannan kadara mai tsada daka hadani da ita,koda raihana batasona zanyi qoqarin koya mata sona,tunda alhamdulillah ni dinne na farko data fara saurara,kenan kafa kaina agunta bazaya zamemin abu mai wahala ba,don bazanyi saken da zata subucemin ba,ina tunanin da wuya in samu kamarta idan na rasata". Shidai rayyan cin abincinsa kawai yake yana duban amir din,yana kallon yadda ya susuce kan raihanan cikin qanqanin lokaci " kaga babab soyayya,ka fara cikamin kunne,kaci abinnci idan zakaci ko kuma na hanaka raihanan baki daya naga ta tsiya"ido ya zaro yana fadin "Gwara kayimin ai kowanne irin hukunci da kayimin wannan kasassabar" ya saka cokalin da tun dazu yake riqe a hannunsa ya soma cin abincin duk da haka bakinsa ya gaza yin shiru Daga gunsu rayyan din sai ta samu kanta da nufar dakin ummu,magana takeson tayi da ita wadda zata kawo qarshen komai kowa ya huta. A gaban mirrow ta sameta ta fiti daga wanka ta sanya kaya tana shafa mai "Sannu raihana,ya akayi ne?,naga bakin kin nan kamar a kwai magana" Murmushi tayi sannan ya yi qasa da kant"uhmmm,inajinki raihana" "Ummu dama akan yaya rayyan ne da rumana" sai ta dakata da abinda takeyi din tana duban raihana "Uhmmm,wani abun ya faru ne?"zuciyarta taji ta dada sauri kan bugunta nada,tana jin wani iri amma zuciyartata ke qarfafarta kan zatayi abunda ya dace ne,zatayi abinda zai zama kwanciyar hankali ga kowa,don haka cikin qarfin hali ta bude baki " ummu,rumana da ya rayyan ne,sabanin da suke yawan samu ummu yana damuna,shine nake ganin me zai hana a matso da batun aurensu kusa ko hakan zaisa su maida kai su kawar da duk wani sabani dake tsakaninsu....."sai kuma tayi shiru,kai ummu ke jinjinawa,tabbas ita din ma ta lura,kawai batason matsa masu da tambaya ne ko shiga lamarinsu,tunda ko da can dama su suka hada kansu,tabbacin suna son juna kenan,amma yanzu raihanan tazo da wani hanzarin wanda taji dadinsa matuqa,tayi mata hangen da ita batayi ba,shi yasa take sake qaunarta kullum saboda kaifin basirarta da tunaninta "Tabbas don kada shaidan ya shiga ya wargaza lamarin ba,tunda dama shi babu abinda yaqi jini irin sunnar ma'aiki,gaskiya ne,bari abbanku ya dawo insha Allahu yau zan sake tuntubarsa da batun,Allah yayi miki albarka raihana kinyi tunani qwarai da gaske" Dakinsu ta nufa saidai tanajin gwiwarta sam ba qwari,bangaren zuciyarta na sake qarfafarta daidai tayi,don haka ta qara saurinta don ta isa dakin ta yiwa rumanan albishir kan maganar da sukayi da ummun,don tasan tabbas maganar zata wanke duk wani bacin rai take ciki. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga nana Aisha r.a tace"manzan Allah yana kasancewa cikin hidimar iyalansa ta cikin gida(yana taya matansa ayyukan gida),yana dinke tufafinsa ko takalminsa da kansa,har sai an kira sallah sannan ya fita zuwa masallaci"* ________________________ *babi na sha hudu* A inda ta barta anan ta taras da ita zaune,qarasawa tayi gefan rumanan ta zauna fuskarta qunshe da murmushi,ajjiye litattafin itama tayi tana dubanta,raihana ta kama hannayenta tace "Albishirinki sisi" "Goro fari qal" ta fada tana murmushin itama tare da yatsina fuskarta cikin qaguwa da son jin me zata ce "Yanzu daga dakin ummu nake,kan maganarki da ya rayyan,tace in sha Allahu yau idan abba ya dawo zata sake tunasar da shi maganar". Ido ta dan zaro" da gaske kike?" Kai ta jinjina mata "Zan miki qarya sisi?" Batasan sanda ta Rungume raihanan ba hawaye ya cika idonta"na gode sisi na,bani da kamarki,Allah ya saka miki da alkhairi" "Yiwa kaine ai" inji raihanan. Sai data nutsu kana tace"bani labarin amir"murmushi raihana ta mata sannan ta lanqwashe qafafunta tana duban rumana "Ai kin ganshi ko?" "Eh amma ina fatan yayi miki?" Fuska ta dan yamutsa"eh,ba laifi kam" Kai rumana ke jinjinawa tana cewa"ki bashi dama kawai sisi,tunda har ya samu makin ba laifi na tabbata wataran zaici nasara"dariya sukayi baki daya sannan suka fara hada kayansu na tafiya gidan biki ************ Ranar lahadi aka kammala biki aka kai kai amarya,don haka gidan aka samu sauqin jama'ar dake cikinsa. Ran monday raihana duka ta rigasu tashi,yawancin jama'ar gidan da sukayi saura nata baccin gajiya,saboda tana da lacture qarfe tara na safe,saboda haka tun takwas da rabi ta kammala shirinta ta wuce makarantar ko rumana bata tasa ba. Biyu na rana ta fito,sai ta samu qasan bishiya ta zauna tana duban yadda garin ya qwalle da rana mai zafi,don har yau ba'a samu saukan ruwan sama ba,tunaninta kawai yadda zata shiga ranar ta wuce qoqi,gashi bata sanar da auwal yazo ya dauketa ba,kuma bata sani ba ko yana da wanu uziri kada ta katse masa. Wayarta ce ta soma ruri,ta janyo jakarta da bata rufu ba saboda handout da ta zuba a ciki,ta zura hannu ta lalubo wayar,sunan ya rayyan ta gani,ta daga ta kara a kunnenta "Kuna cikin makaranta ne?" Ya fara da tambayarta "Eh"ta bashi amsa ga tunaninta yana sane ne " ok,ina capteria" Ya katse wayar,ta fuskanci me yake nufi don haka ta maida wayar jaka ta miqe. Yana gaban kanta hannunshi riqe da bottle na cook mai sanyi yana kurba kadan kadan,ya amshi canjinsa ya zuba a aljihu "Ga yarinyar nan fa man" "Me ya kawota capteria ita da ba zuwa take ba" "Oh my god,yarinyarnan tana firgitani,tana yimin kwarjini,har yau na kasa tararta na gaya mata meke zuciyata" "Kwarjininta da natsuwarta ne yayi yawa wlh,ba kaiba ma,mutane da yawa basa iya tararta saidai su kama qafa da 'yar uwarta,ita ba ruwanta,tana da sakin fuska da son mutane,bata da girman kai irin nata". Maganganun wasu samari dake gefansa kenan su hudu,a hankali ya waiwaya ya dubesu,kana shima ya maida idonsa inda yaga suna kalla,a hankali ya taka ya koma bakin qofar shigowa gun cin abincin,ya hade hannayensa a qirji yana naxarinta. Sanye take da atamfa dinkin riga da zani,sai laffaya da ta nade jikinta da ita mai kyau ta asalin bare bari wadda tayi marching da atamfar jikinta,jakarta na maqale a singalalin hannunrmta,wanda baka iya gani saboda dinkin mai dogon hannu ne,takalminta plate ne mahadin jakarta,kanta na duqe a qasa bata kallon ko ina sai inda zata sanya qafarta " budurwar jami'a?"ya yiwa kansa tambayar cikin zuciyarsa yana ci gaba da kallonta,sam ba zaka taba cewa budurwar jami'ar bace,babu wannan qyale qyale da rawar kan nasu _"yanayin raihana kawai da kalamanta ya isa ya gaya maka wacece ita,kasan raihana irin matan dake masifar tsada ne a wannan zamanin?"_ Wasu daga cikin kalaman amir suka dawo masa fes akai. "Daga kan mana haka ki kalli gabanki kada ki fadi" rayyan ya fada lokacin da take dab da shigowa gurin,don ya lura sam bata ma kula da shi ba agurin,kan nata kuwa ta daga ta saki murmushi "Allah ya rayyam dan dai kaine,ko rumana ban rakowa nan,bana son zuwa gurin nan kwata kwata" ta fada tana jingina da bakin qofar gun,kallo ya sake binta da shi _"yanayin kalamanta kawai sun isa su gaya maka wacece ita"_ zancan ya sake fado masa,jin yayi shiru ta dago suka hada ido,sai tayi saurin janye idonta ganin yadda yake kallonta,gabanta ya fara dukan uku uku "Ina rumanan,ko ita bata kammala ba?" "A'ah,yau duka bata da lacture,na barota gidan hajiya" kafadarsa ya dage tare da ware hannayensa ya fara tattaki "Ok,dama zuwa nayi na maidaku gida,kwanan ya isa haka,gidan babu kowa shiru babu dadi"ya fada yana yin gaba,a baya ta soma binsa tana fadin " muma yau muke shirin mu koma,saboda ummu kewa zata yi mata yawa" Shiru ne ya biyo tsakani har suka qaraso bakin motar,suka shige dukkansu ya tada motar sukabar makarantar. "Abba sun sa ranar mu da rumana?" Rayyan ya fada tamkar ba da ita yake maganar ba idonshi bisa titi,da sauri idonta awaje ta dubeshi fuskartar dauke da murmushi "Wayyo Allah!,da gaske yaya?" "Zan miki wasa ne?" Ya fada ba tare da ya dubeta,irin murnar da yaga tana nunawa shi ya sashi sawa juyowa ya dubeta,fuskarta tamkar wadda aka yiwa albishir da aljanna,fadi take suyi sauri taje ta yiwa sisinta albishir. A hankali tari ya soma sarqeta wanda tun yana mata sannu ssi da takai ga ya faka motar gefan titi ya rirriqeta,minti kusan biyar tana yi babu qaqqautawa kafin ya fara sauqi "Ko mu wuce kiga likita?" Ya tambayeta yana dubanta,kai ta girgiza tare da qirqiro murmushi "A'ah,ba komai,ai ban taba irin hakan ba,yau ne kawai", ya tada motar yana cewa " ok shikenan,amma idan kika sake ji kiyi magana kada kice zakiyi shiru" "To" tace tana jinginar da jikinta a makarin kujerar,tayi luf jikinta ya dan saki,shiru ya ratsa motar lokaci lokaci yana juyowa ya dubeta tare da yi mata sannu,da haka har suka qarasa qoqi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ *Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S.A.W yace"idan mace ta sallaci sallolinta guda biyar(na farilla)ta azumci watan ramadan,ta kiyaye farjinta,ta yiwa mijinta biyayya,ranar qiyama za'ace da ita ta shiga aljanna ta duk qofar da takeso(cikin qofofin da aljanna take da su)* _________________________ *Babi na sha biyar* Ita yace ta soma shiga ta gayawa hajiya babban zai shigo su gaisa,ta gyada kai ta dauki jakarta ta rataya sannan ta fice,binta yayi da kallo yana duban yanayin salon takunta,komai a nutse kamar wadda ke qirga adadin takun har ta shige gidan sannan ya dauke idonsa gami da lumshesu yana sauraren zuciyarsa kana a hankali ua budesu 'Yammata ne ke shigowa layin su uku,kallo daya zaka yi musu ka fassara su waye su,don duka cikinsu babu wadda babu tabon bleeching bisa fuskarta,biyu daga ciki sanye suke da atamfa,yayin da dayar ke sanye da material,dinki ne aka yi musu na badala wanda bashi da maraba da babu,musu suke ko me suke oho Allah masani,amma kana iya jiyo hayaniyarau tun kafin su qaraso inda kake,suna tafiya jikinsu ta kadawa,duk da hirar da suke kwararawa hakan bai hanasu tafiya suna taunar chewing gum dinsu ba,da haka har suka qaraso inda motar rayyan ke fake,daya daga cikinsu taja birki tana cewa,"bari ja sake gyara fuskata a nan"saboda baqin glass ne basa gano na ciki,biyun ma dawowa sukayi suka dan dubi layin sukaga ba jama'a,ba bata lokaci suka hau gyara makeup dinsu jikin glass din motar,rayyan na zaune yana kallon ikon Allah har suka kammala suka qara gaba,idon nashi ya sake lumshewa abun na bashi dariya dariya _ban taba zaton zanyi katarin samun matar aure irinta ba a wannan zamanin,sai gashi dare daya Allah ya yimin kyauta mafi tsada_ zancan amir ya dawo masa fes cikin kwanyar kansa,sai ya bude ido a hankali yana dubi seat din da ta zauna,wayarta na gefe da alama mantata tayi,yasa hannu a hankali ya dauka,ko daya babu irin qyale qyalen nen da ake cikawa jikin waya,ta haka yake gane wayarta data rumana tunda iri daya ce sai banbancin cover da suke sawa lokaci lokaci,hoton heart ne kawai pink guda biyu mai qyalli a jiki a fuskar wayar daga gefe da kuma bayanta wajen murfi,babu password cikin wayar don haka kai tsaye ya bude,contact nata ya duba duka numbers din da suke kai basu wuce talatin ba,suma din duk na 'yan uwanta ne mai duguru da wasu daga take hulda dasu a nan,number din amir kawai ya gani da sunan namiji,ya sauka ya shiga gallery dinta,nan din ma hotunan ummu abba da mamanta ne fanna,sai na zainab qanwarta,sai nata sai na babbar 'yar uwa rumana,wanda majority hotunan rumanan ma sunfi naya yawa. Murmushi yake yana duba hotunan,idan yazo kan wanda sukayi tare yakan tsaya ya kalla sosai kana ya wuce,tsaki yaja lokacin da ya tuna binciken waya kenan ya mata ya maida wayar da sauri ya ajjiyeta yana istigfari saboda binciken da ya mata bada izininta ba. Rumana kawai ta taras a falon tana cin abinci,murmushi suka yiwa junansu sannan rumanan ta amsa mata sallamarta,zaro ido raihana tayi"sisi kada dai kice min sai yanzu kika tashi?"ta fada ganin kayan data kwanta barci sune a jikinta" "Ke dai bari,gajiya ce ta dannemu in gaya miki" ta bata amsa tana bula ruwa pure water mai sanyi ta soma sha,darita raihana ta qyalqyale da ita "Tab,kice yau ya rayyan zaiga matarsa qazama,to tare muke yana qofar gida yana jira a masa izini ya shigo" qwarewa ramanan tayi,ta saki ruwan tana zaro ido "Bama haka da ke sisi,da gaske kike?" Hararar wasa tayi mata "Zaki gasgatani idan kika ganshi cikin falon nan". Dire kwanan abincin nata tayi tana qoqarin shigewa toilet din dake falon,da sauri raihana ta tambayeta" ina hajiyan take?" "Tana bandakin tsakar gida" ta qarasa shigewa tare da rufe qofar,girgiza kai raihana tayi,rumana kenan,tana shirin fita sukayi kacibus da hajiyan na shigowa sai ta gaya mata zuwan rayyan din "Kice mai gidana ne da kansa,ke cene da shi ya shigo mana" inji hajiyan tana murmushi,raihana ta amsa da to sannan ta kuma ficewa. Yana zaune dai cikin motar shiru,sai sanyin a.c da ya karade motar ta qwanqwasa glass din,ya danna madanni yayi qasa da shi yana duban qwayar idonta,bata iya wannan kallon ba don haka ta maida qwayar idon nata kan sitiyarin motar bayan ta zira hannu ta dauki wayarta tana cewa"hajiya tace ka shigo" "Tsayani mana mu shiga tare,ko so kike na bata?" Ya fada yana fitowa daga cikin motar ganin tana niyyar shigewa ciki ta barshi,tsayawa tayi har ya qaraso daidai kafadarta sannan yace"muje to". A hankali suke takawa cikin gidan,tafiya suke kamar wadanda basu son shiga cikin gidan haka nan,suna cikin zauren gidan wayarta ta fara tsuwwa,ta duba mai kiran,amir ne,sai ta rasa ta yadda zata amsa kiran,saboda bata iya amsa waya indai ta wani bane gaban mutane,saidai ko rumana,kuma batason ta qi daga wayar sabida tun dazun amir din ke kiranta lokacin tana lacture,tana ganin qima da girman amir din,batason tayi masa wani abu ba daidai ba har yaji babu dadi ya gayawa rayyan,a sanyaye ta daga ta kara wayar a kunnenta,ajiyar zuciya ya fara saki sannan yace "Alhndlh,ina nan cikin zulumi na jiki shuru tun dazun inata kira ba amsa" "Afwan,ina cikin uziri ne" "To Allah yasa kin gama don muryarkin nan mai sanyi nakeson ji" "Eh to,da saura kam" "Omg,shikenan amma pls idan kin kammala ki kirani" "Ba damuwa" "Na gode,ki kular min da kanki da kyau" "K" ta amsa masa tana qoqarin katse kiran. A hankali ya dauke idonshi daga kanta tare da yin sallama cikin tsakar gidan. Har hajiya babba ta shimfida masa carfet duk da kujerun dake falon "Maraba da ango na,hala dai ni ka biyo ba waccar 'yar tsallen ba" cewar hajiya babba,murmushi ya saki kansa a qasa ya qarasa saman carfet din "Qwarai kuwa,ni ke na biyo,saboda kece ta qarfen,idan bake ba sai rijiya" qaramin murmushi raihana tayi ta wuce cikin daki kai tsaye don tasan yanzu haka rumana na ciki. Ai kuwa tana cikin tana tsala ado,ta baya raihana ta rufewa rumana ido tana fadin "Sisi,ina mai farinciki da alamun kasancewata mutum ta farko wadda zata miki wannan albishir din" itama murmushin take "Qwarai kuwa,ko da yaushe albishir dinki ke dadi ne gareni sis,bakya taba bari naji wani abu mara dadi daga bakinki,ina da yaqinin yau din ma haka take,saboda haka ina saurarenki" Sai da ta danyi shiru na wasu daqiqu kana tace "Sisi,an sa ranar aurenku ke da ya rayyan" suman zaune tayi na dan wucin gadi kana ta fasa wata qara,hadi da daka tsalle ta dale raihana,qarar da ta ja hankalin hajiya babba a gigice itada da rayyan ta soma tambayar lafiya?,me ya samu rumanan,qoqarin saisaita kanta sabida tunawa da tayi rayyan na falon tace "Babu komai,ke kin fiya tsoro 'yar tsohuwa" Shi kansa rayyan da ya san halin rumanan kai kawai ya kada don yasan wataqila wani abune da bai kai ya kawo ba ya sanyata hakan. Hawaye ne suka biyo baya kuma,rumana ta rasa inda zata sa kanta saboda farincikin da ya cikata yaso ya mata yawa,itadai raihana binta take kawai da kallo fuskarta qunshe da murmushi,yayin da gefe dayan can qasar zuciyarta takejin wani feelings na maraici,sai take jinta tamkar ita daya jal,tayi qas da kanta ta shiga ninke musu kayansu cikin jakarsu. Dariya taso kamata ganin yadda dukkansu rumana da rayyan din kowa yayi kicin kicin da dan uwansa,hasalima gidan baya rumanan ta shige abunta tabarwa raihana gaba. Ta kalli rayyan ta sake juyawa ta dubi rumanan karo na kusan biyar "Rumana rigima, ya rayyan dakiya da shariya wasu lokutan da guntun miakilancinsaHaka za'ayi zaman auren?" Raihana ta fada cikin zuciyarta, Sai taji sam bata ji dadi ba yanayin zaman shirun "Don Allah ya rayyan kayi haquri" ta fada tana marairaicewa har hakan yasa ya juyo ya dubeta sai ya dauke kai kamar bazaya tanka ba kuma sai yace "Me kika yimin?"ta gane sarai me yake nufi,sai ta juya ta makawa rumana harara ganin taqi cewa komai,sai ta dauke kai can qasa tace da rayyan din" kayi haquri ya rayyan"itama shirun yayi har sai da ya gama shan iska kafin yace "Baki dauki turba ba,sam bana daga cikin jerin maza marasa kishi,wanda annabi s a w yace ba zasu koda qamshin aljanna ba,ina da kishi rumana.....ina da kishi kuma kinsan da hakan" sai yayi shiru yana maida numfashi,raihana ta saci kallonsa,duk da gefan fuskarsa take iya gani hakan bai hanata gane bacin ran dake kwance bisa fuskarsa ba,a shagwabe rumanan ta shiga neman afuwa,tunda ta riga data sani laifi kam ta yishi,suna gab da shiga layinsun ya kada kai a taqaice yace "Ta wuce,ki kiyaye gaba" "Thank you,na gode dan uwana yaya na kuma mijina" tayi maganar cikin salon jan hankali tare da sakar masa fari ta mirrow,murmushi ya dan saki yana faka motar. ************ Qarfe takwas na dare ne da minti goma sha biyu,shiru kakejin dakin nasu sakamakon littafinta da kowacce ta saka a gaba,karatun jarabawa suke saboda daf suke da farawa. Raihana ce sarkin son laushi saman gadon ta,yayin da rumana ke zaune qasan carfet,qarar wayar rumana ce ta katsesu,raihanan ta dago tana duban rumana,kiran ta duba sannan ta kalli raihana tana murmushi,don tunda suka fara karatun exam ya rayyan din ya qaranta zaman zance da sukeyi don ta samu cikakken lokacin yin karatun "To ba mutanen naki bane,yaya rayyan ne" jin ta fadi haka yasa ta maida kanta kan littafinta,magana sukayi da bata wuce sakan goma ba ta katse wayar tana duban raihana "Ya rayyan ke kiranmu" "Tow,Allah yasa alkhairi" raihana ta fada tana dagowa daga durqushen da tayi "Eh da alamun haka dinne" rumanan ta bata amsa tana ture tarin litattatafanta gefe gami da miqewa,itama raihanan miqewa tayi ta janyo lafayarta data cire dazun ta mayar jikinta ta nada,ta zira silifas dinta tana jiran rumana dake shirin canza dressing,tana tsaye ta sauya kaya sannan ta dan shafa powder suka fito,sai da suka leqa dakin ummu suka gaya mata sannan suka wuce Raihana ce a gaba don haka ita ta tura qofar falon,sanyin ac gauraye da qamshin turarensa da air freshner ta gauraye falon,kida ne ke tashi a hankali can qasa,waqar hamisu breaker ce mai taken a duniya ke kikazam farincikina,yana zaune qasan carfet bayanshi jingine da kujerar falon,sanye yake da wani irin yadi mai kyau na maza ruwan toka,wanda aka yiwa dinkin riga three quater mai dogon hannu da dogon wando,qafafunsa a miqe suke harde da juna,yayin da ya tallafe qeyarsa da duka hannayensa biyu da ya sarqesu cikin juna,qarar bude qofar ta sanyashi bude lumsassun idanunsa ya saukesu fes a kansu su duk biyun,raihana ta janye idonta a hakali tana jin wani nauyi,rumana dake kallonsa tana ganin ya sake sauya mata ya sake wani kyau tare da yin fresh ta matso bayan raihana ta rada mata "Don Allah kallemin ya rayyan,ya saki zama wani handsome ko sisi" murmushi tayi har fararen haqoranta suka bayyana,idanunta suka sake sauka kan rayyan wanda har yanzu su yake duba,sai ta sake dauke idon nata tana gyadawa rumanan kai "Idan kun kammala gulmar ku shigo kada ku gayyatomin sauro ya cikan daki" ya fada a hankali sannan ya maida idonshi ya sake rufewa tamkar bashi yayi maganar ba. Mintina biyu kafin waqar ta qare ya bude idon nasa,yasa hannunshi ya dauki wayarsa ya kashe,rumana da waqar ta tsumata,ji take tamkar rayyan din ke mata ta dubeshi tana dariya "Yaya,a ina ka samo wannan waqar?,kai da bansanka da jinsu ba" "Nima ji nayi ana ji nace a turan ko nayi laifi?" Kai ta kada"a'ah,dama don dai basu dameka bane,amma akwai kalamai masu tayar da tsumin qauna cikin waqoqin" "Na yadda da wannan" ya fadi yana duban idanunta wanda hakan ya sake haifar mata da wata iriyar qauna tasa. "Gashi ku dubamin wannan" ya fada yana tura musu wasu takardu tare da duban raihana wadda tunda suka shigo bayan ta samu gu ta zauna ta dauki daya daga cikin litattafanshi da suke zuwa daukar karatu da daddare gun wani malamin addini ta soma dubawa,ajjiye littafin tayi sannan ta dauki takarda daya,yayin da rumana ma ta dauki daya tana dubawa,raihana ce ta soma dago kai,sai suka hada ido,wani nauyi taji ya saukar mata,ta yaada kanta gefe tana cewa cikin sassanyar muryarta "Kamar takardar kamfani ko ta neman kazo kayi aiki tare da su?" "Eh nima ta hannuna haka ne" inji rumana tana sake jujjuya takardar dake hannunta. Qafafunsa ya janye ya tanqwashesu sannan ya zauna sosai "Bayan dawowata na samu aike daga kamfanini daban daban da suke so nayi aiki da su,to duka a ture tasu,cikin guda biyun nan nakeso na zabi daya don sunfi kwanta min" shiru sukayi na dan sakwanni kowacce da kalar nata tunanin,rumana ce ta fara magana bayan ta duba takardar dake hannun raihana ta duba itama ta karbi tata ta duba "Nikam yaya inaga ka dauki wannan kafanin na alj suraj dauda,naga albashin da suka ce zasu baka yafi na wannan kamfanin yawa ko?" Ta qarashe maganar tana dubanshi "Yayi my angel,to kefa raiha?,bakice komai ba" murmushi tayi don shi kadai ke kiranta da sunan,tilas sai ya maida ta 'yar qauye dai "Nidai inaga yaya da farko ka fara yin istihara kamar yadda annabi ya fada mana yayin da duk ka tunkari wami lamari da kake neman zabin daya daga ciki ya faru gareka,idan yaso ko zuwa kwanaki uku ko hudu idan Allah ya kimsa maka saika zabi daya daga ciki din,ko kuwa sisi?" Ta fadi tana duban rumana,dariya rumanan keyi "Yes my sisi,kinga fa kinyi hange mai kyau,hakan yayi yaya rayyan,shine daidai" inji rumana,sosai shawarar tata ta burgeshi,ya dinga kada kai yana lumshe ido,wani abu ya dinga masa tasiri da yawo tsakiyar kanshi,hakan ya sanya ya basu damar tafiya. Kan gado yayi watsi da takardun kamar wasu marasa amfani kana ya fada saman gadon da ruf da ciki sai kuma ya juya ya koma rigingine yana kallon p.o.p din saman dakin _irin matan da suke zamewa kwanciyar hankali wa mazajensu_ Daya daga cikin maganganun suka fado masa,sai ya mirgina ya koma barin hannun damanshi tare da yin ta'awizi wai ko shedan ke son ribatarsa _don bazanyi saken da zata subucemin ba,ina tunanin da wuya in samu kamarta idan na rasata_ Ya sake jin maganar cikin kunnensa kamar a lokacim amir din ke fada "Don me zaka bari wani ya dauke kadara mai tsada din daga gabanka kana kallo?,don me zaka bari wani ya dauke ta bayan irinsu ne ke zamewa kwanciyar hankali wa mazajensu?,idonka ne a rufe rayyan?" Yaji zuciyarsa na karanta masa,rintse idonsa yayi yana son hanawa zancan samun gurbi a zuciyarsa balle yaci gaba da yi masa tasiri,tura kansa tayi qasan filo yana girgiza kansa,amma zuciyarsa bata ci gaba da yi masa kuwwa da magiya ba. Cikin qanqanin lokaci ya wani firgice,tamkar ba sadaukin namijin nan ba rayyan,wani irin rudani ya shiga lokaci guda,bai taba jin abun ya ta'azzarar masa ba irin yau,bai taba daukar haka zuciyarsa ta dauki lamarin ba sai yau da zuciyarsa ke neman jigatashi,wanda a qarshe saman carfet yayi barci a maimakon kan gadonsa,ko sallar nafilar daya sabayi kafin ya kwanta bai samu damar yi ba balle a kai ga sanya kayan bacci ************ Wani iri ya tashi washegari,abinka da wanda bai saba saka abu cikin ranshi ba balle ya sashi damuwa,tunda yake bai taba shiga wata damuwa ba,ko yaushe rayuwa na tafiyar masa daidai ba tare da cin karo da wata matsala ba. Qarfe tara yunwa ta addabeshi don jiya bai samu yaci wani abincin kirki ba,jallabiya ya zura ya saka silifas dinsa ya biyo ta zauren gidan ya wuce tsakar gidan kai tsaye inda kitchen dinsu yake. Daidai lokacin tana tsaye cikin kitchen din tana soya qosai bayan ta gama dama kunun tsamiya ta juye a flask wanda tun qarfe takwas almajirinsu yazo ya kai mata markaden qosan saboda rana daidai ne bata yiwa abba,kasancewarsa mutum mai son kunu da qosai,da wuya ka ganshi yasha tea,tea sai su,don ko rayyan sai dare idan zai kwanta yakesha black tea,wanda ya zame masa qa'ida tunda yaje england ya dawo,daga gefan gas din littafinta ne ajjiye tana suyar tana bitar karatun nata saboda qarfe goma takeson fita don sha daya suna da test,hakan ne yasa kan ta fara aikin ma ta gama shirinta cikin riga da skert ta dora afron akai,wanda indai ta sanyasu to sai ta dora musu after dress. Tun kafin ya qaraso ya gane ita ce,sai ya tsaya daga nesa ya goye hannayensa a qirji yana monitoring duk wani movements dinta,tana gama saka qosai sai ta dawo kan littafin,wani lokaci idan wani abun ya kakare mata takan dan tsaya ta bubbuga qafafu tare da yarfe hannu kota dafe goshinta,murmushi ya saki ganin tana abu kamar yadda rumana keyi sometimes,ashe itama shagwababbiyar ce,lallai dabi'a naso take. A hankali ya qaraso bakin qofar kitchen din yayi tsaye yana qare mata kallo,komai nata natural ba artificial ba,tun daga yanayin fatarta kawai ya isa ka gane hakan,wanda sau da yawa wasu Allah na musu baiwar fata irin nata wato chaculet colour black beauty sai su bata ta,su butulcewa Allah su dauki kururuwar iblis su dinga bleeching suna dashewa,wanda duk mai wannan dabi'ar Allah yayi fushi da ita,kuma burin shaidan da yaci a kanta ya cika kenan,don dama alqawari yayi sai ya samu munyi hakan. "Alhamdulillah" ta fada a hankali tana rufe littafin bayan da ta tabbatar karatun ya zauna yadda takeso,har ta kammala suyar yana tsaye ba tare data sani ba,don ta juyawa qofa baya ne,sai da ta kashe gas din ta juyo da niyyar daukar flask da zata zubawa abba nasa taga mutum wanda bata tantance ko wane ba ta saki ihu tare da ja baya da sauri jikinta na rawa,ga zatonta ma rumana ce da salon taikanarta sai taga rayyan ne,kunya da tsoro suka rufar mata "Matsoraciya kawai,idan abun tsoron ne ma wannan ihun naki ai ya isa yasa ya cinyeki baki daya" "Ina kwana ya rayyan" ta gayas da shi duk da har yanzu qirjinta bai daina bugawa ba kanta a qasa "Lafiya raihana naji ihunki?" Cewar ummu data nufo kitchen din,ya dan kauce ya bata hanya "Waifa daga gani na ta saki wannan ihun" "A'ah.....hala dai bakayi mata sallama ba" sai ya dan sosa kanshi sannan yace "Eh" "Atoh,kaga laifinka ne kenan,kada ka sake haka kaji ko?" "To ummu" itadai bata ce komai ba tana ta hidimar zubawa abba qosanshi ta kammala ta miqawa ummun,tasa hannu ta amsa tana sanya mata albarka sannan ta juya ta fice daga kitchen din ta barsu nan. *mrs muhammad*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"kalma mai dadi sadaqa ce* ______________________ *Babi na sha shida* Bayan fitar ummun shiru ne ya ratsa kitchen din,duk sai ta duburbuce duk da batasan kallonta yake ba,hakanan takejin wani iri,ya mata kwarjini fiye da kullum,ta dago ta saci kallonsa tayi gyaran murya kadan ga zatonta wani abu daban yake tunani "Wani abu kake buqata ne ya rayyan?" Ta fadi maganar tana sa duster tana goge gefe da gefen gas din daya baci da mai. Baici komai ba sai taku da yayi,ya qaraso kusa da ita,hannu yasa gefanta ya janyo flask din da ta zuba qosan,ya budeshi ya dauki qosai daya yakai bakinsa ya gutsura,dadinsa ya kewaye kunnensa,'yammatan ba baya bane wajen iya girki rainon ummu ne,ba ganda ba qiwa ba qazanta,hakanan yasan dandanon girkin kowacce cikinsu,walau rumana raihana ko ummu duk yana iya banbancewa "Ki kawo min qosan daki tare da kunun?"ya fada yana juyawa zaya bar kitchen din " shikenan abinda kake da buqata?"sai ya waiwayo yana gab da ficewa daga kitchen din,gira ya daga mata tare da sakin murmushi wanda ya sake fidda ainihin sigar kyawunsa "Ko zaki iya bani wani abu ne da yafi wannan muhimmanci?", duk da bata fahimci tambayar tasa ba amma sai taci zuciyarta tayi wami irin bugawa,tayi hanzarin dauke idonta daga gareshi tana girgiza kai " a'ah,iya abinda muka dafa kenan yau da safen,saidai ko ifan kanason wani abun sai ka fada na hada maka kafin na wuce school" "Ko na fadi babu lallai na iya samunsa lokaci daya kuma kai tsaye" yayi maganar yana ficewa,binsa ta sakeyi da kallo tana son gane me yake nufi,yau duka maganarsa kamar bada ita yakeyi ba,kodai zancan zuci yake yi ne,ta sake dauke kanta tana jefa zancan kwandon shara ta shiga hada masa abinda ya buqata din Ta taras ya shiga toilet wanka saboda haka ta jera masa ta fice gudun kada ta tsaya jira tayi latti. Powder kawai ta sake shafawa,ta fidda turarenta na dindin din da take amfani da shi ta sake fesawa,bata ajjiye kwalbar ba wayarta ta dauki ruri,ta kai hannu ta dauka,rayyan ne,ba jinkira ta amsa kiran tare da kara wayar a kunnenta "Kin kawon abinci sannan kinyi ficewarki,ni zanyi sarving da kaina?" Sai taji tambayar wani iri,saboda ta saba koda ta kai abincin tahowa take,rumana yake tsaidawa tayi sarving nasa "Kayi haquri yaya,ina da test ne qarfe sha daya,gashi goma har da ashirin,ina tsoron makara" shiru yayi yana jin yadda sautin muryarta ke fita,ko dama can raihanan tun quruciya haka muryarta take mai sanyi "Its ok,turomin rumana" "To yaya" ta fada tana ajjiye wayar,shi din ma ajiyar zuciya ya saki,yayi shiru yana jin wani abu na yawo cikin jininsa da qwaqwalwarsa har ma da zuciyarsa Ta waiwaya tana duban rumanan dake bacci abinta,qarasawa tayi gaban gadon ta sanya hannu tana bubbuga pillow din da take kai,a hankali ta bude idonta,bata barta tace komai ba tace da ita "Kije ya rayyan na kira" tamkar ba a bacci ta tashi ba ta miqe zumbur ta dira daga saman gadon,kai tsaye ta fada bandaki,kallo raihanan ta bita da shi baki a bude kana ta saki murmushi tana kada kai "Inda cewa nayi ki tashi muyi wani abun saikin batan lokaci,amma da yake ya rayyan ne har baccin ya sakeki ko?" Tana daga cikin bandakin take bata amsa "Haba sisi,ya rayyan fa kika ce,kema ai kinsan yasha gaban komai"baki ta tab" to lailah majnun,nidai na wuce makaranta" "A dawo lafiya sisi" Falon abba ta nufa don tasan ummu ma na can,sai da ta tsaya bakin qofa tayi sallama abba yace "Shigo mana raihana,kullum ke kamar baquwa kike" da murmushi kan fuskarta ta shiga ta sameshi yana karyawan,gefe ta tsugunna ta gaidashi ya amsa yana murmushi "Qosai da kunu duka sunyi dadi diyata,Allah yayi albarka" "Amin abba" ta amsa Rayyan ne yayi sallama ya shigo falon hannunsa dauke da key din mota,sanye yake da shadda light blue dinkin tazarce wadda ta masa kyau sosai,gashin nan irin na buzaye yasha gyara sai qyalli yake tamkar ba shi dazun suka hadu a kitchen ba,ta miqe ta soma yiwa su abbab sallama ya tsaidata "Ba motarku na gun gyara ba" Kai ta gayada "Shikenan rayyan ya ajjiyeki zaice gun abbanku dalhatu yakai masa saqo" "To abba" ta fada,tana tsaye abba ya kammala bashi saqon itama ya sallameta har da tukuicin girkinta na yau,tana dariya ta amsa tayi godiya,don haka dabi'ar abban take,ga duk wadda tayi girki yayi masa kyau yadda yakeso,tun kafin sukai wadannan shekarun ma,hakan shi ya qara musu qwarim guiwar zage damtse wajen iya girki,rayyan yayi gaba ta biyo shi a baya. A tsakar gida sukayi kacibus da rumana wadda itama tuni ta kammala kwalliyarta cikin atamfa riga da skert,murmushi suka sakarwa junansu ita da rayyan din,ta dan langwabe kai tana dubansa "Hala yaya fita kuma zakayi bayan ka tasheni a bacci kace nazo" "Nima bansan da fitar ba,ina gama bada saqon kiran naki abba ya kirani yace nazo zaya aikeni gun daddy" dan daga kafada tayi tana cewa "Shikenan kace ina gaida su mama,amma Allah yasa ba jimawa zakayi ba don ban gaji da kallin fuskarka ba" murmushi ya saki sannan yace "Dana bada saqon zan juyo,sai sisinki da zan ajjiye makaranta" "Shikenan sai kun dawo" ta juya ta shige falon tana musu murmushi tare da dagawa raihana hannu. Ya maida kallonsa ga raihanan wanda ta janye gefe don ta basu guri "Anya rayyan anya?" Wani sashi na zuciyarsa yace da shi,cikin sakanni sai yaji bugun zuciyar tasa ya dadu,shi kadai ya shiga jijjiga kai cikin zuciyarsa yana fadin "Bazan iya ba,bazan iya ba". Maimakon ya fara ajjiyeta a makaranta sai taga ya zarce da ita hanyar gidansu rumanan,a marairaice ta juyo tana kallonsa " yaya na zaci zaka fara saukeni ne?"shareta yayi sai daga bisani yace "Inaso muyi magana ne idan mun dawo kafin na ajjiyeki" ta sake duban agogo tana jin babu dadi don sam batason makara,saidai dole tayi shiru ganin yanayin yadda fuskarsa ta juye lokaci guda. Sam ita ba maison tashin hankali ko bacin rai bace,don haka sai ta ciro glass dinta daga cikin gidansa ta gogeshi ta sanya,ta zaro littafinta daga cikin jaka ta shiga dubawa don ta sake zaunar da karatun. Baice mata ta fito ba,a ganinta ya dace ta shiga su gaisa,don tana kallon ahalin gidan a matsayin nata ahalin,don haka ta dire littafin ta biyoshi a baya. Maimuna(qanwar rumana)suka taras a falon tsaye cikin unifoarm tana kurbar tea,ta ajjiye kofin tana musu barka da zuwa sannan ta rusuna ta gaidasu kafin ta haye ta yiwa mommy magana "A'ah,manyan baqi mukayi kenan" cewar mummy tana murmushi,a ladabce rayyan ya gaidata sannan raihana ta gaidata itama,bata tambayi diyarta ba rumana saboda alkunya,ita raihanan ce tace tana gaidasu,bangaren daddyn mummy ta wuce ta gaya masa zuwan rayyan yace ya shigo,nan ma sai maimuna ta raka raihanan ta shiga ta gaidashi sannan suka fito don ta basu gu,suna tafe ta tambayi maimuna ya bata wuce makaranta ba goma ta gota?,ta sanar mata suna zana wa'ec ne ta mata fatan alheri suka dawo falon,mummy ta mata tayin breakfast tace a qoshe take,sai data karya sannan suka fito,suna taba hira maimunan ta musu sallama ta wuce makaranta falon ya zama daga ita sai mummy dake sako mata hira jifa jifa wadda kusan rabi ta karatunsu ce. Minti goma kacal rayyan ya fito suka yiwa su mummy sallama suka wuce. Maimakon taga ya kama hanyar makaranta sai taga ya sake daukan wata hanyan ta daban,ta sake juyowa ta dubeshi kamar zatayi magana sai kuma ta hadiye maganar ganin sun hada ido,ido daya ya kashe mata tare da fadin "Sorry sisinmu,wani guri xan kaiki ki gani,ba zamu wuce minti goma ba zan kaiki,kada ki damu,bazan bari ki makara ba" kai ta dauke tamkar wadda aka zarewa laka saboda wani lugude da taji zuciyarta na mata,sai ta kasa ci gaba da karatun ta rufe littafin ta lumshe idonta bayan ta zare glass din,ta rasa wanne tunani zatayi,wasu irin dabi'u take gani yau sababbi tattare da rayyan din. Satar kallonta ya dinga yi yana tuna abubuwa da dama a kanta,bazai manta ba baya ga amir mutum uku ne cikin abokansa suka yi masa magana kan raihanan,akan me zai yiwa kansa ta'asa?,saboda me zai cuci kansa?,gida bata qoshi ba kenan?,kyautar shiga daka kayi kuka?,haka suka ci gaba da tafiya kowa da abinda yake saqawa cikin zuciyarsa. Minti goma suka isa bakin wani babban gini wanda kallo daya zaka yi masa ka bawa kanka amsar kamfani ne,saidai da alama sabo ne ba'a kai ga fara aiki a cikinsa ba,tun daga bakin get security suka fara kai gaisuwa yana amsawa a mutunce,a haka har suka kai makeken gurin ajiyar motocin dake gefe guda,ya tsaida motar ya kasheta sannan yayi mata umarnin ta fito. Binsa take a baya kamar raqumi da akala,jifa jifa suna cin karo da mutane daidaiku wanda da alama kowannansu cikin aiki yake su gaisa su wuce da haka har suka isa bakin elevetor suka shige,a third floor suka tsaya sannan suka fito,corridor ne mai kyau wanda aka qyatashi sosai,duk da tsawon guri office din dake wajen bai wuce guda shida ba,uku a dama uku a hagu,office na ukun qarshe taga ya sanya key ya bude,ya tura qofar ta bude sannan ya dubeta,da hannu ya mata alamar ta shige,bata ce komai ba ta shige din tana mamakin yadda zuciyarta ke tsananta mata bugu duk yayin da wata sa'a ta shude. Maida qofar yayi ya rufe kana ya qaraso tsakiyar office din yana dubanta,wani irin kallo ta gani a idanunsa wanda ya sanya gwiwarta yin sanyi,sai tayi baya ta zauna kan kujerar cushion dake zagayd da qayataccen falon,basarwa yayi ya dauke idonshi daga kanta yana fadin "Wannan shine gurin da Allah ya zaba min nayi aiki bayan na kammala istihara ta"yayi maganar yana janyo daya daga cikin kujeru biyun dake gaban teburinsa ya zauna a kai yana fuskantar ta tare da zubawa fuskarta ido. A hankali ta daga kyawawan idanunta masu cike da gashin ido zara zara ta fara qarewa office din kallo,sabo ne shima fil kamar yadda ginin kamfanin duka yake,yana dauke da wani kyakkyawan dunqulallen table da kujerar ma'aikaci baya ga wasu guda biyu a gaban table din suna fuskantar juna da alama na baqon da yazo gunka ne yakeson ku tattauna,sai kujeru zagayayyau na cushion masu masifar kyau a kusa da shi,daga daya bangaren kuma na'urar sanyaya abubuwan sha ce fridge daga gaba da ita kuma carfet ne mai laushi da dadduma akai da alama gun ibada ne,daga can sama kuma na'urar sanyaya guri ce a.c,dukkan bango office din dauke suje da frame mai rubuce da falaqi nasi da qulhuwallahu hadi da ayatul kursiyyu,labulayen dake kewaye da office din sai kayi zaton ba na ma'aikata bane saboda kyansu,kusan komai na cikin office din milk ne mai haske wanda hakan ya sake haskaka office din da taimakon fararen qwayayen da suka kewaye shi. Murmushi ta saki don ba qaramin kyau office din yayi mata ba "Masha Allah,masha Allah yaya,amma ka shammace mu,kyanta wannan suprise din sisi na na nan" "Ke da ita ai duk daya ne" kai ta kada ba tare data gane me yake nufi ba "Haka ne,ai kam ina zuwa ni zan fara yi mata albishir,Allah ya albarkaci gurin,ya barkaci aikin ya taimaka yayi maka jagora yasa afi haka,yanzu kawai lokacin bikinka da sisi na nake jira yaya" ta fada murmushi dauke a fuskarta tana dubansa,sai ya maida bayansa ya jinginar jikin kujera ya daga girarsa yace "Da sisinki da kuma ke" sai ta dan qanqance ido tana dariya "Sai kun rigani aure yaya,ni ba yanzu bs,bana so ma duka mu tafi lokaci daya mubar ummu" "Ba wannan ne dalilin ba,ki sake lalubar wani" sai ta sake dubansa,seriouse Alamun muhimmancin maganar ta gani sosai kan fuskarsa,bugu da qari ya kafeta da idanunsa da ta washi taga ya zuba mata su,sai ta basar tana cewa "Nikam bani da dalilin da ya wuce wannan" "Maqaryaciya kawai.....idan ban manta ba sisinki ta dade tana min qorafin har yau kinqi bawa kowa qofa cikin rayuwarki.....uhmmmn haka ne?" Murmushi ta saki tana son ragewa maganar muhimmanci "Sharrin ruma ne,amma ko a baya ban bada ba,a yanxu ai na bayar" "A zahiri ko a badini?" Sai tayi shiru tana naxari wanda qarar wayarta ne ya katse nazarin,shi da ita duka sukabi wayar da kallo,takai hannu tana daukan wayar ganin kiran abokiyar karatunta ne Rashida ahmad,sha daya saura ta gani tuni ta saddaqar ta rasa test dinta "Raihana kina ina ne?" "Ina hanya rashida lacturer din ya shigo ko?" "Ina fa,gwara da Allah yasa baki qaraso ba ma,muna nan muna jira ashe wai ya gayawa monitor baxai samu shigowa yau ba,ya dage test din sai gaata,nan da kwana uku" batasan ta saki ajiyar zuciya ba,sosai taji dadi don gaba daya hankalinta ya tashi,batason ta barwa karatunta wani gibi,godiya ta yiwa rashidan sukayi sallama. Wayar ta maida jaka sannan ta miqe tsaye"mu tafi ya rayyan"ta fada ba tare data dubeshi ba,don bata buqatar hakan,yanzu haka kanta tuni ya soma sara mata "Ina cewa test ce kuma an fasa ko?,kinga sai mu zauna muyi hira,ki tayani in qarasa arranging office din ko?"ta dan dubi gefanta,hirar tasu ce bata da buqatar ci gaba da yinta,don kuwa bata ga amfaninta ba in banda matsala da zata iya sanya mata wanda ita daya tasan da wannan " amma naga komai neat yake ko?"ya dage kafadunshi sannan yace "Eh to.....inason duba setting na computers din nan,batason musu tilas ta dire jakar ta koma ta zauna zuciyarta naci gaba da bugawa. Tana kallo ya bare computer din ya jona jikin socket ya haye kujerarsa ya soma latse latse,duk dagowar da zatayi sai sun hada idanu,kamar zata zauce haka ta dinga ji,ta rasa me zatayi?. Cikin freezer yasa ta ciro masa lemo ta zuba masa,yana sha yana aikinsa,saidai duk yadda yaso yayi aiki mai yawa ya kasa,shi kansa baisan yana kallonta haka ba,sai da suka shafe awa biyu a haka sannan kira ya shigo wayarsa,ya kara wayar a kunnensa sannan ya jingina bayansa da kujerarsa " my angel,am so sorry wani uzuri ya tsaidani,amma i promise da wuri zan dawi gida yau,harda sisinki ma duka"ko bata tambaya ba tasan rumana ce,batasan me tace masa ba taga dai ya saki murmushi ya katse kiran,ya dubeta,saita marairaice wai ko zai tashi su tafi,din kadan ya rage ta saki kuka,ta gaji da jin abinda takeji a jikinta. Ya gane sarai me take nufi sai ya kashe computer din ya dago yana dubanta "Its ok,yanzu zamu tafi amma ina son in miki wata tambaya,ki amsa min su perfectly"kai ta gyada yayin da yayi shiru na wasu 'yan lokuta sannan ya sauke ajiyar zuciya " raihana kina son amir?"tambayar a bazata tazo mata,ta cira kai a hankali ta dubeshi "Kamar yaya ya rayyan?" "Kamar yadda ya dace mace taso namiji saurayi,kada ki fadan qarya,don zan iya ganoki". Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi,meye muhallin wannan maganar ne?,take tambayr kanta,a lokacin shi kuma yake dada qare ma raihanan kallo,komai nata cikin nazari take yinsa,nutsuwarta tayi yawa,cike da karsashi tace " ba lallai lokaci daya so yake iya shiga zuciyar mutum ba,koda banso amir yanzu ba ina sa ran zan soshi nan gaba saboda yayimun"kansa ya shiga kadawa "Son baikai bane raihana,duk son da yakai ya kuma tumbatsa so to yana iya shiga zuciyar duk wanda yaga dama lokaci guda" yayi shiru yana maida numfashi,wani sashe na zuciyarsa na tunzurashi tare da bashi karsashi "Raihanah" ya kirata da wani salon kira da ya sanya tsigar jikinta tashi,bugun zuciyarta ya dadu fargabarta da fatanta suka dada qaruwa ninkin ba ninkin "Raihana.......Rayyan yana sonki!,yana son ya aureki!ni rayyan"yayi maganar kamar maiyi mata rada cikin kunne baya ga idanunsa da suka sauya launi da ya kafeta da su,tsintar kalaman tayi cikin kunnenta na amsa kuwwa,ji tayi kamar qure volume na muryarsa yayi lokacin ambatar kalmar saboda yadda taji office din ya cika da sautin muryarsa lokaci guda taji jikinta ya dauki dumi,tanaso ta dubeshi ko idanunta zasuyi masa kaifi ya dawo hayyacinsa ya daina fadar maganar amma ta kasa,ji tayi kamar an daureta,lokaci daya taji kamar an kafta mata sara a kanta,ba shiri ta kife kanta kan teburin dake gabanta,shikenan ta faru ta qare ta dinga maimaitawa cikin zuciyarta. Bai kula ba don haka yaci gaba da cewa.......... "Raihana....zuciyata ta kamu da soyayyarki,irin soyayyar dake wahalar da zukata,irin soyayyar da bansan irinta ba ban kuma saba da ita ba,ina fatan zaki fahimceni raihana,ba son zuciya bane ya kaini,halayenki kadai sun isa su saya miki so daga gun duk wani namiji da yasan me yakeyi,ina fatan zakiyi wa rayyan adalci......" "Dakata....." Ta fada a zabure bayan ta samu nasarar dago kanta "Haba yaya rayyan,haba....don Allah na roqeka idan wasa kakewa raihana kada ka sake yi mata makamancinsa har abada,idan da gaske kuma kake don Allah kayi gaggawar tuna me harshenka ke fada,kayi gaggawar tuna wace raihana,raihana fa qanwarka,'yar uwa kuma aminiya qanwa kuma yayar rumana,rumananka fa wadda aka sa muku rana da ita....rumana fa mai sonka.....yaya rayyan raihanan rumana ce fa kake magana da ita b rumana bace....." "Ya isa" shima ya daga mata hannu a birkice "Kin manta so babu ruwansa da komai?,kin manta so baya ji baya gani baya kuma fahimtar kowane yare?,idan da so yana fahimtar wani yaren da ya dade da barin zuciyata indai a kanki ne,ki daina lissafomin wacece ke,na fiki sanin hakan,kada ki manta ni mijin mace hudu ne......" Ya fada yana nuna qirjinsa "Mijin mace hudu?mijin mace hudu?" Ta maimaita tana dubansa "Mace hudu amma ciki babu raihana" sai ta saki murmushi tana miqewa ta sake gyara glass din idonta saboda gani dusu dusun da take tana zaton glass dinta ne ya goce daga ainihin qwayar idonta "Mubar wannan wasan ya rayyan don Allah,kaga wasan ma baima yi maka kyau ba saboda bai dace ba,mu tafi gida don Allah,kaga rumana nacan tana jira" ta qarashe maganar tana juyawa ta nufi qofa,batayi auneba sai ta tsinceshi a gabanta ya tare hanyarta,duk da rudanin da take ciki hakan bai hanata hango birkicewarsa ba,fuskarsa ya hade tsam yana dubanta "Niba yaro bane dubeni da kyau idan kin manta duk da kin fi kowa sani,abinda na fada shi nake nufi,ni rayyan ina son raihana,shine me?,sabo nayi?" Tuni hawaye ya fara wanke mata fuska,kai ta shiga kadawa "Wallahi yaya rayyan wani abu ya sameka ne hala yau,na shiga uku ni raihana" ta fadi jakar hannunta na sulalewa daga hannunta ta fadi qasa,shima kai ya fara gyadawa "Eh yes,wani abu ya sameni raihana,wanda ni kadai nasan yaya yake,ni kadai nasan me nakeji" kujerar data tashi ya nuna mata da yatsa yana cewa "Koma mu qarasa maganarmu,don ba wasa nake ba"ya fada fuskarsa tamkar hadari,ta gama haqiqancewa da gaske yake sai ta kasa tafiya don bata iya ganin komai,wasa gaske sai gata ta harde wanda tsananin ciwon kai da jiri ya taimakawa hakan,sai ji tayi ta sulale tana shirin zubewa a qasa *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Manzan Allah S A W yace"kada ku hana bayin Allah (mata)zuwa masallacin Allah* ____________________ *Babi na sha bakwai* Kafin ya kai ga tallafa mata tuni ta tallafi kanta ta hanyar riqe handle din qofar ta tsaya qam,sai ya qaraso gabanta ya ja birki yana dubanta,kasa tsaiwar tayi kawai tabi jikin bango ta sulale ta zauna dirshan,kai ta hada da gwiwa sannan ta saki wani kuka mai dauke da siririn sauti "Ya ilahal alamina,shin ko dai laifinta ne?,ko tayi wani abu ne daya fallasata,wanda ya janyo rayyan ke mata wannan maganar mai barazanar tarwatsa mata qwaqwalwa,wannan wace iriyar magana ce mara makama?" Take zancan cikin zuciyarta,tsayawa kawai yayi harde da hannayensa yana kallonta,duk da cikin zuciyarsa yana jin babu dadi amma baya jin zai iya haqura ta subuce masa,saboda muddin hakan ta faru ya tafka asarar da har abada zai dade yana jinta cikin zuciya da gangar jikinsa,asarar da baya fatan ace ta sameshi,duk wannan kukan tashin hankalin da bore na dan lokaci ne kuma mai wucewa ne,amma kuma rashinta fa?. Baice da ita komai ba sai da yaga kukan yaqi sararawa "Ya kamata ki tsagaita da kukan haka nan don bazai zamar miki mafita ba" ya fada yana nufar table dinsa,ya rufe computer ya tattare duka kayan aikinsa guri daya ya kwashe wayoyinsa ya zuba a aljihunsa sannan ya kuma dubanta "Ki shiga toilet ki gyara fuskarki mu wuce gida" ya fada still yana tsaye rungume da hannunsa,kamar an tsikareta haka ta miqe duk da jirin da take ji,domin babu abinda takeso yanzu da ya wuce ta ganta a gida kwance kan gadonta ko zata samu sassaucin abinda takeji. Tafiya kawai take amma ji take iska ce tafiyar da ita,haka take jinta babu nauyi ko kadan. A 'yar harabar ajiye motocinsu yayi parking,ya dubeta lokacin da take kici kicin bude qofar motar "Duk tunanin da zakiyi kiyi shi,amma kada ki taba zaton ko da wasa rayyan zai barki" sabbin hawaye masu dumi suka biyo kuncinta,bata iya furta komai ba face ficewa daga motar. A hankali take kutsawa cikin gidan tamkar ba zata shiga ba,addu'a take cikin ranta kada Allah yasa tayi karo da wani cikin rumana ko ummu,don bata da amsar da zasu bata idan sukaga yadda fuskarta ta sauya,wanda kukan da tayine ummul aba'isin komawarta haka. Cikin kitchen ta hangi rumana da alamu girkin rana take shirin dorawa,hakanan taji wata mummunar faduwar gaba,cikin sanda tamkar barauniya ta shigeta ta kutsa falonsu,nan ma babu kowa hakan ne ya bata damar shigewa cikin dakinsu,a qasa ta watsar da duk wani abunda ke hannunta ta fadi bisa gadon bayan ta dora kanta saman filo,wani sabon kuka ne mara sauti ya qwace mata,kadaici da kewa irin wanda bata taba ji ba ya mamayeta,me yasa?,me yasa rayyan zaiyi mata haka?,me yasa yakeson tuno mata wani abu da ta jima da yin jana'izarsa cikin babin rayuwarta? Cikin qanqanin lokaci zazzabi mai zafi ya garzayo ya rufeta kirif,ta dinga rawar sanyi ita kadai,hakan ya sanyata jan bargo babu shiri ta lulluba,tafi minti ashirin cikin wannan matsanancin halin kafin wani wahalallen barci ya saceta wanda ko daya babu jin dadi cikinsa. Sai data daura alwala ta shigo cikin dakin nasu bayan ta kammala girkin rana,qarfe biyu ne harda minti goma,mamaki take na rashin ganin raihana ko rayyan kamar yadda yayi mata alqawarin zasu dawo da wuri,ta shigo da niyyar idan ta idar da sallar azahar tayi kiransu taji ko lafiya sai kuma idanunta ya hango mata mutum lullube cikin bargo,ta qarasa bakin gadon a hankali ta janye bargon tana duban ta,kallo daya tayi mata ta tabbatar ba lafiya take ba,tafin hannunta ta dora saman goshinta da niyyar tashinta. Sanyin da taji saman goshinta yasa ta bude idanunta a hankali sukayi tozali da rumana wadda dumin da taji jikin raihanan ya jefata cikin damuwa,take abinda ya farun dazu ya dawo mata fes cikin kwanyarta,addu'a ta shiga yi Allah ya sanya cikin mafarki ne "Sisi,me ya sameki haka?" Maganar rumana cikin damuwa ta dawo da ita hayyacinta,sai ta maida idanunta ta lumshe,zuciyarta ta karye wasu hawaye masu dumi suka shiga fita daga idanunta,ji takeyi ta tsani kanta gaba daya "Subhanallah,sisi na me ya sameki don Allah kiyi magana mana,ga zafi a jikinki ko baki da lafiya" daure zuciyarta tayi cikin dan qwarin gwiwar da ta bawa kanta tace "Ciwon kai da zazzabi ne ke damuna" "Ayyah,sannu kinji sisi,ki tashi ki watsa ruwan famfo ki daura alwala ko zazzabin zai ragu,sai na kawo miki abinci da magani kisha ki kwanta,ko kuma na gayawa ummu muje asibiti kada anjima yafi haka" da sauri ta riqe hannun rumanan zuciyarta na sake karyewa,kuka nason qwace mata amma tana danneshi "Kada ki gayawa ummu kinsan yanzu zata daga hankalinta,bari naje na watsa ruwan in sha Allah zai sauka" ta fada tana qaarara jikinta tare da miqewa,jiri taji na sake dibarta gudun zuciyarta na kuma daduwa amma sai ta lallaba ta shige bayin. Kafin ta fito har ta kawo musu abinci wadda mostly tare suke ci dama matuqar suna tare,doguwar rigar wani material mara nauyi ta saka,ta goga roll on ta tufke kanta dake tsefe ba tare da ta damu da ta sake tajewa ba,sallah tayi sannan ta zauna suka fara cin abinci duk cikin dakiyar ta,don babu wani dandano na abincin ko kadan da ke tasiri kan harshenta,turashi kawai take rumanan nayi mata sannu jifa jifa,ga tsammaninta duk ciwon ne,a daddafe suka gama ta balli maganin ta sha ta koma gado,rumana ta gyara gun ta dawo ta nade saman nata gadon ta hau charting lokaci lokaci kuma tana gadin raihanan. A boye take sake wani kukan,nauyin rumana takeji sosai,ji take tamkar sun sabawa mahaliccinsu ne ita da rayyan,har gab da la'asar tana abu daya,daidai lokacin da rumana ta fita dora sanwar dare kira ya shigo wayarta,mama fanna ce ke kiran,tsayawa tayi tana kallon sunan data sanyawa maman nata,wani rauni ya ziyarceta,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gabanta ko zataji sanyi cikin zuciyarta,ita kadai tasan masifa da fitinar da rayyan yau ya haddasa mata cikin zuciyarta,gashi har gangar jikinta ta amshi nata kason ta hanyar zazzabi da ciwon kai. Katse kiran tayi sannan tabi maman nata,tayi mata sallama da dasashshiyar muryarta da kuka ya dausasheta ya kusa sawa hancinta mura "Lafiya kike raihana?" Maman ta tambayeta,kai ta kada tamkar tana ganinta "Lafiya lau mama mura ce ta kamani,ya gida yasu ya gana da su zainabu" "Lafiyansu qalau" maman ta bata amsa ba tare data bi takan tambayarta ta farko ba,tunda ta riga data sani lafiya lau raihanan take,don ko ita data haifeta da ubanta marigayi alhj bukar riqon da zasuyi mata kenan. "Dama cewa nayi bari na gaya miki bikin falmata ya taso('yar qanwar mama ce),jiya aka kawo lefenta an saka sati shida,wata daya da sati biyu kenan" "To mama Allah ya sanya alkhairi,zan kirata nima in sha Allahu,idan kuma mun gama exams lokacin in sha zan halarta" "To Allah ya yarda,ina diyata rumana?,na kirata wayarta a kashe" "Ta saka a chargy ne tun dazun" ta fada a gajarce saboda kanta da taji yana ci gaba da sarawa"to masha Allah,ki gaishesu har fatiman duk da dazu ma munyi waya" "Zasuji mama" "To Allah ya qara sauqi" "Ameen mama na gode" ta fada sannan ta katse wayar a sanyaye. Bata kai ga tuna komai ba taji sallamar ummu hadi da turo qofar tasu,ta daga labulen ta shigo,a hankali tayi qoqarin miqewa ta zauna tare da jan dankwalinta da ya zame tana qoqarin daurawa "Da kinyi kwanciyarki ma,sannu raihana,ashe babu lafiya?" Kanta a qasa tana tsoron su hada ido da ummun kada ta jefo mata tambayar da bata da amsarta tace "Eh wallahi" "Ashsha,Allah ya sawwaqe sannu,baya bata da kadan,kamar ba dazu kika tafi makaranta ba lafiyar Allah" tayi dan murmushin yaqe "Yanzu to ya kikayi da gwajin?" "Lacturer din ma baizo ba" "To alhamdulillah,Allah ya qara afuwa,zuwa anjima idan kinji baki ware ba sarai kiyi magana sai yayanku ya kaiki ko clinic din nan na gaba da mu ne" fadarsa kawai da ummu tayi sai da ya haddasa mata faduwar gaba,kai ta daga kawai ummun ta sake yi mata sannu kana ta fita. Wunin ranar sur a kwance tayi shi,ko daya ciwon kan bai saketa ba saboda azabar tunani fargaba da tsoro,har bayan sallar magariba sannan taji zazzabin ya sauka ciwon kanne jiya i yau. Qarfe takwas da minti goma na dare ya shigo gidan,wata iriyar gajiya ke dukansa,bawai don yayi aikin da ya cancanci ace ya gajin bane,zuciyar tasa ce kawai a jigace hakan shi yayi tasiri har zuwa gangar jikinsa,rufe motar yayi sannan kansa tsaye ya wuce cikin gidan. Parlour din babu kowa hatta da kayan kallon dake cikinsa a kashe suke,da alamu yau babu wanda ya zauna ciki,sai ya sakejin gajiya da kasala ta sake saukar masa,kan kujerar falon ya yiwa kansa masauki yana qarewa falon kallo,gun ummu zashi ko gun raihana da rumana?,yake wa kansa tambayar,bai kai ga amsawa ba rumana ta fito daga dakinsu hannunta riqe da cup da tea flask,bata ganshi ba sai data qaraso daf da inda yake zaunen suka hada idanu,murmushi ya sakar mata ita kuma ta daure fuska tana jifansa da hararan wasa "Kada ka gayan komai,don nasanka gwanin iya dadin baki ne kai din" "Kaina bisa wuya na,na dauki duk laifin da kike tuhumata da shi,amma yanzu dai a yimin afuwa da sassauci,kinga shigowata kenan ina buqatar tallafi" ta gyara tsaiwarta har yau bata bar hararsa ba "Tallafi wanne iri?" "Yunwa,gajiya,kasala,damuwa duk ni daya rumana,kunga ai ya cancanci a tausaya min ko?" Fari tayi da idanunta sannan tace "Eh,zan iya tausaya maka ta hanyar kai maka abinci,abinda zan iya kenan?" Kai ya langabe sannan yace "To kuma hirar fa,da yau fa cikin dakinku zamuyita a gaban sisinki" hannu ta daga masa ta hade fuska "A'ah,ba dai yau ba,don tun rana sisi bata da lafiya,banason abinda zai takurata". Miqewa yayi daga kashingidar da yayi wanda baisan sanda yayi hakan ba " subhanallah,me ya sameta?"ya fada yana zare ido,itama sai ta narke masa damuwar rashin lafiyar raihanan ta sake tabata,hakan suke dukkansu idan waninsu baida lafiya sun damu da juna, "Zazzabi yaya,ga ciwon kai,amma zuwa yanzu zazzabin ya sauka sai ciwon kan",sai ya maida idonsa ya lumshe yana jijjiga kai ba tare daya bude ba yace" je kikai kayan hannunkin in shiga in dubata" "To" tace sannan ta fice daga falon,sai lokacin ya bude idonsa yana binta da kallo,babu wani abu da ya sauya dangane da rumanan a cikin zuciyarsa,yana jinta yadda take dai,tabbas babu ko tantama maganarsa ce ta haifar mata da lalurar,amma baya jin akwai wani abu da zaya sanyashi sauya ra'ayinsa,babu gudu babu ja da baya,da rumanan da raihanan duka halalinshi ne,addini ya bashi damar aurensu baki daya. Miqewarta kenan daga kan gadon zata shiga toilet tayi fitsari suka shigo,rayyan dinne a gaba rumana na binsa a baya,suna hada ido taji kamar an maidata an zaunar,jikinta gaba daya ya dauki rawa tayi qas da kanta,gaban dresaing mirrow dinsu ya je ya zauna wanda shike facing raihanan,idanunshi fes a kanta yana dubanta,kanta babu dankwali hakan shi ya bawa hargitsatstsen gashinta damar bayyana,sai yaga har rama ma tayi "Sannu ya jikin?" Murya can qasa tace"da sauqi" "To Allah ya qara afuwa" "Ameen" rumana ta karbe zancan "Don Allah ya rayyan kayi mata magana,yau daya don tana ciwon kai sai kuka take kamar yau ta fara cuta?"sake tsareta yayi da ido cikin nutsuwa yace " wai haka?...."shiru tayi babu amsa hakan ya bashi damar dorawa "Take it easy raihana,kada ki qarawa kanki stress kinji,duk abinda Allah ya rubuta bazai taba kankaruwa ba,kuma ba kai kake dorawa kanka abu daga Allah ne,ballanta na abu irin wannan,so kada ki damu ki tsaida kukanki hakan shi zaisa ki warke da wuri,kuma ita rashin lafiya duk qanqantarta kaffara ce ta zunubi,kuka babu abinda zai yaye miki face qaruwar ciwon" "Atoh,nima haka na gaya mata" inji rumana,tuni raihana ta fahimci inda zancan nasa ya dosa,don haka ta bude baki a hankali tace "Haka ne,na gode da shawarwarinka,amma wani abun ganganci ke jawo aikatashi,kamar yadda nayi gangancin tsawaita kuka har ya hana ciwon kaina sauka" rumana baki ta bude "Kada kiyi sabo raihana" dubanta tayi tana jin tausayin kansu baki daya,murmushin yaqe ta sakar mata "Kada ki damu sisi,nasan me nake fada fa" Miqewa yayi yana yana daga kafada tare da duban rumana "Babu gudu babu ja da baya,ba zamu kasa gayawa sisi gaskiya ba ko?" Ya fada yana dageqa rumana gira "Qwarai kuwa" inji rumanan tana dariya,tuni raihana ta fada toilet abinta bayan tace"na gode"don kada rumana ta fahimci wani abu "Ki kawo min abincin pls,na ji na yafe hirar yau din" "Yes sir" ta fada tana sakar masa murmushi shima ya maida mata raddi sannan ya fice,ko babu komai a yau yana jin wani nauyi dada yake jinsa saman zuciyarsa ya ragu daka kaso dari zuwa kaso hamsin,bayajin duk wani abu da zaya biyo baya mai sauqi ne,abu na gaba da zai faru shine yarda,neman yardar raihana,wanda yasan kafin ya samu hakan zai fafata da ita bisa dukkan alamu,shi kuwa sam bazai yadda al'ada ta haramta masa halal da addini ya halasta masa ba. Sai da ya leqa dakin ummu ya sanar mata ya dawo sannan ya wuce,bai tambayi abba ban don yasan irin wannan lokacin yana makarantar magariba ta manya,shi dinma rashin dawowarsa ne daga gurin aiki akan lokaci ya hana masa zuwan. Kwana biyu tayi tana jinyar zuciyarta a badini wadda rayyan ya fame mata ciwon dake ciki wanda ada tabo ne yanzun ya koma danye sharkaf,sa'an nan ya cikata da tsoro da firgici,wanda kuma a zahiri jinyar gangar jikinta take na zazzabi da ciwon kai. Cikon kwana na biyun da daddare bayan sallar isha'i bayan ta kammala bitar test din da take saka ran gobe zata je ta zana,ta zauna tana gyara musu kayan sawarsu ita da rumana,yayin da rumanan ke zaune gefe tana tayata hira,duk da tayi tayi ta hanata amma tace ta barta,tanason gobe ta tashi da qarfinta sosai don ko girkin dare ita tayi makarbiya ta karba tayi musu tunda abincin nasu dama ba wani yawa gareshi ba. Tun da yayi sallama bakin qofar dakin nasu kafin ya kai ga shigowa gabanta ya buga,rabon data ganshi tun randa ya shigo dubata,aikin bai samun zama kwana biyun sosai,sakamakon shirye shiryen fara aiki da kamfanin da suka daukeshi zaiyi,duk da hakan a rana idan ta samu kadan daga saqonninshi to ta samu guda biyar,wadanda da sun shigo take gogesu cike da fargaba,don kowanne lokaci wayarta na iya zuwa hannun rumana,bugu da qari kuma bata buqatar abinda zai qara ruruta marurun da take jinyarsa take kuma fata da burin ya koma kamar yadda yake da. Dif tayi har ya shigo dakin hannunshi dauke da littafin sunanu abi dawuud da alama daga makaranta suka dawo,sannu da zuwa rumana tayi masa cike da kulawa ya mayar mata da raddi shima,tilas ta danne zuciyarta itama tayi masa ba tare data dubeshi ba gudun kada rumanan ta darsa wani abun,duk yadda yaso ya kalli qwayar idonta kamar ta sani taqi bashi dama,don babu shakka yayi missing dinta fiye da yadda ya zata,bai kuma fahimci hakan ha sai da ya ganta a yanzu,tana sanye da doguwar riga amma buba wadda aka dinkata daidai jikinta,kanta babu dankwali sai kitsonta qwaya biyu daya bayyana wanda ya zuba kafadar ta ta hagu da dama "Angel a kawomin abinci" "Yaya yau bani nayi girki ba,sisi ce,kaga ita ya kamata ka tambaya nima yau na huta" can qasan ransa yaji dadi amma bai nuna hakan ba,saima ya juya ya fita yana cewa"nidai a kawomin abinci yunwa nakeji,banason bata lokaci" Fuskarta dauke da murmushi tace"don Allah sisi ki amsheni yau mana tunda ke kin gama naki karatun,karatun test nima nakeso nayi,nasan kuma ya rayyan yana iya riqeni"kai ta kada ba tare data dubeta ba "A'ah,bazan iya ba ban gama warkewa ba nima" rai ta bata sannan tace "Haba sisi,alfarmar da zakiyimin kawai,ok na gode" ta fada cikin nuna jin haushi,rumana tafi qarfin duk wata alfarma daga gareta don haka tayi maza ta riqe hannunta "Kaina bisa wuyana,wasa nake miki,yanzu zan cika umarninki 'yar uwa" dariya suka saka baki daya,raihana ta ciri hijabinta mai hannu ta zura ta fice,ta tsaya a tsakar gida ta hada masa abincin cikin basket na kaba da ake hada masa abincinsa ta wuce gefansa zuciyarta na bugun uku uku,a yanzu kam jin rayyan take tamkar wani dodo da bata qaunar haduwar inuwarsu guri guda,don ta tabbatar hakan bazai taba haifar musu da da mai ido ba. Waya ta sameshi yanayi bisa alamu da mai company din suke magana,ta juya da niyyar ficewa ya dauke wayar daga kunnensa kana ya mata umarnin ta tsaya,kamar ta fice abunta amma sai taga ya zama tilas ta tsaya tunda ko banza rayyan ba sa'anta bane. Ya kammala wayarshi tsaf ya kasheta ya ajjiye,kafeta yayi da ido yana morewa kallonta kafin daga bisani yace"me kuka dafa?"batace komai ba sai bude masa flask din da tayi,couse couse ne da miyar kayan lambu daya hada da cabbage,carrot,green beans,piece sai hanta a ciki,girkin ya masa kasancewarsa mutum mai son ganyayyaki,hakan yasa baya yarda yaci abinci tsurarsa haka babu ganye a ciki "Zuba min" ya sake bata umarni,tana zuba abincin yana karantarta,komai a nutse sannan a tsaftace,sake qarfafawa kansa gwiwa yake yaci gaba da yaqin da ya fara tabbas shi ya cancanci ya mallaki raihana ba wani can daga waje ba. Ta gama zubawa ta miqa masa,ba tare da yace ba taje ta ciro masa lemo da ruwa don duk ta gama da wuri ta fice ta bashi guri,ko bata sani ba tasan kallo yake qare mata,tana shirin miqewa yace "ina zuwa?" "Daki" ta bashi amsa "Zauna inaso muyi magana" qam ta tsaya kamar ba zata zauna ba din har sai da ya kuma maimaitawa,tamkar ta fashe da kuka haka ta dinga cikin zuciyarta,shi kuwa hakan dadi yayi masa musamman lokacin da ya fara cin abincin test din ya fara ratsashi "Yadda kike ta daban haka komai naki yake daban raiha ta" ya fada yana kallonta tare da lullumshe ido kamar mai jin barci,da sauri ta dauke kai saboda wani yanayi da salon maganar tasa da kallon suka haifar mata lokaci guda "Ya salam!" Ta fada cikin zuciyarta tare da maida kanta gefe guda,wasu hawaye masu dumi suka gangaro mata,abinda take qoqarin dannewa ya taso har yafi qarfinta,ta soma jin tasirinsa kadan kadan wanda hakan ya sanya take jin bazai yiwu taci gaba da zaman ba,miqewa tayi tsaye har yau da ragowar hawayen kan fuskarta "Zan iya tafiya?" "Ban baki izini ba" sai da ya cinye abincinsa tas sannan ya dubeta "Kina da test gobe qarfe tara.....idan kin fito ki jirani ni zan ajjiyeki...." "Amma tare zamu fita da rumana,duja test din namu lokaci daya ne" ta tari numfashinsa da sauri "And so what" ya fada hankalinsa a kwance "Ke da ita din duka matsayinku guda" kai ta shiga girgizawa ranta a bace"ba matsayinmu daya ba,ka daina fada,kuma ni din bazan jira ka ba,zan tafi auwal zai kaini kamar yadda na saba" Zamansa ya gyara sosai sannan dubeta cikin ido "Well,hakan zaiyi kyau,kinga kenan zai dace da lokacin da zan sanarwa kowa muradina a kanki,idan kin shirya hakan tun kafin ki gama natsuwa da tayin da nayi miki.....fine kina iya hakan,kinga komai yazo min kenan a sauqi" saura kadan numfashinta ya dauke,ji tayi kamar ma ya fada din ne kowa yaji,sababbin hawaye suka sake silalo mata,wai rayyan wanne irin mutum ne? "Namiji ne jarumi da baya iya boye abinda ke ransa,mai jumuri da juriyar nema da samun duka abinda ya sanya a gabansa" bata san a fili tayi maganar ba sai da taji wannan amsar,kasa ci gaba da zama tayi ta tabbatar idan taci gaba da zaman zai iya fasa mata wani sashe na zuciyarta,cikin sassarfa ta miqe don ficewa a dakin. Tunanin da ya ziyarceta cikin gajeran lokaci tun kafim takai ga barin falon shi ya sanyata cin birki tare da tsaywa cak,wani murmushi ya qwace mata,a nutse tamkar ba ita ba ta juyo tana duban rayyan wanda itama shi take kallo,ta samu hanyar yakice rayyan cikin ruwan sanyi koda hakan shi zai dawwamar da tata zuciyar cikin kewa da damuwa,bai dauke ido daga kallonta ba kamar yadda itama bata dauke ba,wanda cikin qanqanin lokacin kallon ya sake zama guba a garesu baki daya "Yaya rayyan" "Yes" ya amsa yana jin dadin yadda ta ambaci sunan nasa" "Kace min kana sona,na tabbata ka fada ne ba tare da dogon nazari kan me zaya biyo baya ba" "Idan haka kike tunani muje a hakan ne,go straight to the point"ta kada idonta cike da farincikin samun mafita gareta mafi sauqi,wadda tasan rayyan baida mafitar daya daga cikin abinda zata gaya masa,tilas kenan ya haqura ya janye qudurinsa.... _shin haqarta zata cimma ruwa kuwa?,muje zuwa.........._ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga anas dan malik R.A yace:manzan Allah S A W yace"haqiqa ubangiji yana yarda da bawan da zaici wata loma(yaci abinci)ya godewa Allah a akanta(wannan abincin da Allah ya ciyar da shi),sannan ya sha abun sha ya godewa Allah akan sa(abinda Allah ya shayar da shi din)"* _ruwayar imamu muslim ce_ _______________________ *Babi na sha takwas* "Yaya rayyan,duk duniya kafi kowa sanin alaqarmu da rumana,ina son sanin yaya zakayi da rumana idan har zaka aureni?,me zaka ce da ummu da abba?,yaya zakayi da amir?,idan kuma mi din bana sonka fa?,me kuma kake son na gayawa duniya?". Murmushi sosai rayyan din ya dinga yi har ta saki baki tana kallonsa sannan daga bisani ya tsaida idonshi a kanta " raihana,ke 'yace ta ummu da abba kamar yadda ni da rumana muke 'ya'ya a gunsu,ina mai tabbatarwa yadda suke farin ciki da tarayyata da rumana haka zasuyi yayin tarayyata da ke,kema 'yarsu ce,rainonsu ce,amir kuwa ina tunanin kin manta cewa ni na kawo shi,ni na hadashi da ke,ni na bashi ke,to a yanzun kuma nace na fasa,sabida ni nafi cancanta da ke,hakanan ke kika fi cancanta da ni,baxan cuci kaina ba ina kallo a dauke ko a qwace abu mai qima da daraja daga hannu na ba,hannun karba hannun maidawa,mutanen duniya kuwa magana aikinsu ce,walau kayi mai kyau ko mummuna,babu wanda ke iya musu koda Allah mahaliccinmu yayi abu sai sunyi magana a kai,so ya rage gq kai dan adam kaui kawai abinda ya dace a lokacin da ya dace,ka toshe kunnuwanka daga dukkan wasu qananun maganganu ko gutsiri tsoma ta mutane"yayi shiru yana sake kallonta tate da maida numfashi. Wannan karon cikin sanyi da nutsuwa yace da ita"Raihana!,nace miki bana son rumana?,ko na gaya miki na fasa auren rumana?,kin mance na gaya miki cewa ni rayyan mijin mace hudu ne,bayan ke da rumana ina da ikon sake auren wasu matan har guda biyu?"ya qarashe maganar cikin sigar tambaya,itama nata idanun na kanshi,wani abu mai kama da kishi taji ya tokare mata wuya,sai taji hawaye nason balle mata,inda tayi namijin qoqarin maida shi,kai ta shiga kadawa,babu shakka rayyan ya wuce duk tunaninta,yayi nisa wanda ya sanya baya ko waiwaye bare yaji kira. Matsowa ya sakr yi sosai gabanta har tana jiyo hucin qamshin turarensa,ya narkar da idonsa cikin nata tare da yin qasa da zazzaqar muryarsa ya sake kiran sunanta,kiran da ya haddasa tashin duk wata tsiga ta jikinta "Ina sonki raihata,inajin wani irin so na daban kuma na musamman tattare da ke irin wanda ban taba jin irin nau'insa ba,raihah......ki bani dama don Allah,ki ban damar da zan mallakeku ke da rumana baki daya,in zaunar daku qarqashin inuwata in baku kulawa bisa adalci da amana,ki bani dama in sanar da rumana da kaina.......na tabbatar da cewa yawan qaunar da take miki ba zata bata damar da zata bijirewa zamanku tare ba....raihanah,na tabbatar da cewa shakku kike cikin son da nake miki,saboda kina ganin rumana na fara so?,da rumana nake soyayya?,da ita aka sanya mana rana?,raihanahh,ban yaba zato zan tsinci zuciyata cikin irin soyayyar da take miki a yanzu ba,komai namu raihana iri daya ne,ra'ayinmu,halayenmu da zabinmu duka sunzo daya....me zaihana ki bawa zukatanmu damar da zasu rayu tare?,su morewa dacen da sukayi da juna?". A hankali ta ware idanunta a kansa wadanda sukayi jazur,wanda ada suke a lumshe,tana dab da gazawa kan yadda yake dafata da kalamansa,ta kusa gaza jurewa ne,tana jin idan ta bashi dama ta hanyar ci gaba da saurarensa zuciyarta ba zata iya daukar nauyin kalamansa ba,zai maidata ne euwa tsundum cikim dan k'ank'anin lokaci,ruwan da bata fatan ya tabata ko kadan,don ta riga ta sani babu ta yadda za'ayi tana cikin hankakinta ta iya hada inuwar aure guda k'ark'ashin jagorancin namiji guda ita da sisinta muddin ranta kuwa. Kai ta sake kadawa a sanyaye,dab take da sake sakin wani kukan "Kayi mana adalci yaya rayyan,ka yiwa kanka a dalci" "Kema ki yiwa kanki adalci raihana,kanki ya kamata ki fara yiwa adalci kafin kowa......" ya fada cikin alamu da suke nuna cewa ya fita daga hanyar lallashi ya fara hasala "ko kinsan tunda muka fara wannan maganar har yau baki taba bude baki kince BANA SONKA ba rayyan!,zuciya ta BATA SONKA!,don haka bazan iya aurenka ba,magana daya kike RUMANA RUMANA RUMANA dai,ke ba mutum bace ruma ce kawai mutum,ke baki da zuciya a gangar jikinki!,rumana daya ke da zuciya?!" Idanunta da suja qara girma ta sake warewa a kansa,zuciyarta na wani urin bugu tamkar mai shirin yin tsalle tayo waje,cikin wata iriyar sarqaqaqqiyar murya tace"don me bazan kira rumana ba?,don me bazan kira 'yar uwata ba,'yar uwata mai son farinciki na" Idonshi cikin nata yace"ok,kin amincewa kanki kina son rayyan?,rumana ce shamakin tsakanin soyayyata da taki?" So take ta gaya mishi maganar kai tsaye ba tare da shayi ba,ta yadda zata shige shi,amma tasan bata isa ta furta masa ba muddin idanunshi na cikin nata,saboda haka ta janye qwayar idonta sannan tace "Bana son rayyan so na soyayya,bana sonka yaya rayyan,so nake maka na 'yan uwantaka ba na soyayya ba" sai kuma ta dawo da idon nata kansa "kai,koda ina sonka rayyan NA SADAUKARWA DA RUMANA SOYAYYYAR......saboda har abada bazan iya shiga tsakanin rumana da farincikinta ba,QAUNAR dake tsakani na da ita ta siya mata komai,babu abinda bazan iya SADAUKAR MATA BA CIKI KUWA HARDA KAI YAYA RAYYAN" ta qarashe maganar hawaye na layi a kan kuncinta,saboda wani irin daci dake tasowa daga qasan zuciyarta har ya zuwa saman harshenta na sadaukar da abinda bata taba son wani abu daban cikin rayuwarta kamarshi ba,abinda ta soshi tun tana mitsitsiyarta,abinda ta soshi tyn batasan darajarsa ba,abinda ta soshi tun batasan wace ita ba,ta soshi a lojacin da take tunanin tsoronsa take,ta soshi kuma a lokacin da take zaton shirme take,ta kuma soshi a lokacin da take zaton 'yar uwarta take tayawa sonshi. Idanunsa da suka koma launin ja kadai zaka kalla su gaya maka me yake wakana cikin zuciyarsa,da yake namijin duniya ne maimakon taga tsananin bacin ransa sai taga ya jingina da makarin kujerar da yake kai sannan ya lumshe idonsa,siririn murmushi ke fita bisa fuskarsa,shi kadai yasan azabar da yake fuskanta cikin zuciyarsa,so yake yayi cooling kansa da kansa,baison yayi magana cikin halin da yake ciki. Kimanin mintina biyar sannan ya daga hannunshi murya can qasa yace"tashi ki tafi raihanah,tashi ki tafi"izinin tafiyar takeso ya batan amma batasan me ya hanata tashin ba,maimakon hakan sai ta cure guri guda ta saki wani kuka mai ratsa zuciya,ji take kamar ta fidda zuciyarta tayi wurgi da ita kota huta da jin abinda take ji din,tana ji tamkar zuciyarta bata yi mata adalci ba da ta ci gaba da nacin rayyan din tsawon shekaru,ta kasa mancewa da rayyan"sallamar rumana cikin falon shi ya tsinke wa raihana duk wata jijiya ta jikinta,ganin babu wanda ya amsa mata a cikinsu ya sanyata yin mamaki,rayyan dai na jingine jikin kujera idanunsa a rufe kamar mai bacci,raihana kuma na gefe guda kanta hade da gwiwa,sai ta rasa gurin wa zata nufa,wa kuma zata tambayi meke faruwa a tsakaninsu?,cikin sa'a rayyan din ya bude idonshi,saidai duba daya yayi mata ya maida idanunsa ya rufe,duka bayason ganinsu a gabansa a halin da yake ciki yanzu,yayi tur da soyayya,ashe da gaske babu abibda ke cikinta face takura qunci da raunana zukata?,da gaske dama babu farinciki cikinta?,abinda ya hanashi kula ko son kowacce mace kenan saboda a gaban idanunshi soyayya ta dinga diban karan mahaukaciya da abokan karatunsa,har dariya yake musu yace su suka cusa kansu,ya karkatar da hankalinsa kan idan ya dawo gida yana da matar dake sonsa zai aura wato rumana,ashe dan adam bai gujewa jarrabarsa,baya kuma taba gujewa qaddararsa?. Ganin haka yasanyata qarasawa gaban raihana tana dafa kanta"me ya sameku sisi"cikun muryar kuka tace "Kaina rumana...kaina...." "Dauketa kubar dakin nan,don nima ta goga min ciwon" ya fada still idanunsa suna rufe "Dama ai kai ka gayyatomu" inji rumana tana taimakawa raihana suka fice daga dakin tana mata sannu da jimamin dawowar ciwon kan tare da gaya mata tabar kukan mana,ta rasa wani raki raihanan ta koyo da take ta yiwa ciwon kai kuka haka. Tausayinsu ne duka su ukun ya kamata,tabbas dukkansu suna cikin jarrabawa so,shi kam duk yadda kaso guje masa saidai idan bai kama ka ko ya kamaka din ba,idanunta ta rufe bayan ta sha panadol guda biyu da rumana ta bata tana mai bawa kanta qwarin gwiwa,tana ji a ranta cewa ya kamata ta zama jaruma,bai kamata ba taci gaba da kukan da babu mafita ba,bai kamata ta bari damuwa ta ruguza rayuwarta,abu mafi muhimmanci gab suke da fara jarabawa wadda daga ita zasu tafi aji na gaba,idan har taci gaba da dawwamarwa ranta damuwa to babu shakka zata samu faduwa ne,zatayi biyu babu,babu wan babu qanin. Ganin ta rufe ido ya sanya rumana tafiya gadonta ta kintsa itama ta kwanta ga zatonta bacci ne ya dauke raihanan,abinda bata sani ba shine ko kadan babu alamun bacci tattare da ita,ko marmarin yinsa ma bata yi. Ganin yadda dare ya nausa ba bacci babu alamunsa ya sanyata miqewa,tunawa da tayi da ayar nan da Allah yake cewa ((Ku saurara,da ambaton Allah kawai zukata ke samun nutsuwa)),toliet ta shiga a daddafe ta daura alwala,sannan ta fito ta shimfida abun sallah,ba zata iya tsaiwar sallar ba saboda jiri jiri da take ji,sabida haka ta fidda qur'ani cikin ma'ajiyar litattafansu ta soma karatun can qasa yadda ba zata tashi rumana ba,tana yi tana sharar hawaye har sai data ji ta gaji,zuciyarta tayi sanyi sosai sannan ta rufe,ta dade sosai tana addu'a har sai da bacci ya rinjayi idanuwanta sannan ta kwanta ************ Cikin kwanakin duka tayi duk wani qoqari na kawar wa da kanta damuwar da take ciki,ta samu nasara bakin gwargwado,kasancewar shi kansa rayyan din ba ganinshi take ba,tayi qoqarin toshe duk wata kafa da zata hadata da shi,hatta da wayarta kusan ko yaushe a kashe take don kada saqo ko kiransa ya shigo,saidai ko da ta bude din bata samun daya cikin biyun abinda take tunanin,sosai walwalarta ta ragu haka kuma ta dan fada kadan,saidai duka babu wanda ya kawo komai kasancewar cikin jarabawa suke,kuma sun riga sun santa da naci da qwaqwar karatu,bata da wani sukuni idan suka fara jarabawa har sai sun kammala ta fita da kyakkyawan sakamako. Cikin nasara da taimakon addu'a ta kammala jarabawarta rumana kuma guda daya ta rage musu,har zuwa lokacin bata kuma sanya rayyan cikin idonta ba,ganin zaman hutu kawai zasu fara ya sanyata fara shirin tafiya mai duguri,tunda sati guda ya rage a fara bikin falmata,sannan a gefe guda tana ganin wannan dama ce da zata sake nisanta kanta da rudanin da take ciki,ta sanar da abba tuni ya fara yi mata shirin tafiyar,wanda ya riga daya saba daga shi har daddy dalhatu,har yau ji suje kamar bukhar na raye ne,basu bar yiwa ahalinsa komai ba,duk lokacin da zasu maidugurin basa gajiya da tafiya da hidima mai yawa. Qauracewar da yayi wa cikin gidan baki daya yayi ta ne don ya samu sassauci itama ya bata damar samun sassauci cikin zuciyarta,bai karaya ba koda na sakan daya,yana jin nasara na biye da shi koba dade ko ba jima,duk da yanakanji zafin kalmar qi data ambata masa,amma ya dauki hakan a matsayin wata barazana ce kawai wadda bata dada shi da qasa ba. Bazai yiwu su tafi tare da rumana ba saboda jarabawarta guda daya da bata rubuta ba,wadda zata rubuta ta ne ana ya gobe za'a fara bikin,sun yanke cewa ranar data gama zata taho tunda qarfe tara ce zuwa sha daya sun fito,ana ya gobe raihanan zata tafi rumana tayi mata rakiya gidansu gun daddy dalhatu tayi masa sallama,auwalu ne ya kaisu haka suka dawo both din motar dauke da saqonnin da za'a kaiwa umminta fanna,yana qoqarin shigewa cikin gidan raihana ta hangoshi,bayansa kawai ta gano yana sanye da qananun kaya da takalmi rufaffe irin na maza saye a qafarsa,gashin kansa irin na fulanin buzaye ya kwanta har qeyarsa,hannunshi dauke da jakar office da alamu dawowarsa kenan daga office din don taji hucin zafi na fita daga motarsa,ko bata kalle fuskarsa ba tasan yayi kyau don babu suturar da zai sanya bata karbeshi ba,shiru tayi bata nuna ta ganshi ba kamar yadda ta fuskanci rumana bata ganshi ba don batason ta janyo masu shi. Tana daki tana hada kayan nata jifa jifa tunaninsa na fado mata tana irga yawan kwanakin data dauka rabon data ganshi,wani lokaci ta kwabi kanta wani lokaci taja tsaki har sai da rumana ta dubeta "Lafiya kike sisi?" Sai ta saki murmushi tana jefar da rigar hannunta "Lafiya qalau" "Meke going to?" "Bana son in tafi ne ni kadai na barki,tafiyar ba zata mun dadi ba" da gaske haka maganar take har cikin zuciyarta,sai rumanan tayi murmushi ta rausayar da kanta "To ya za'ayi,duk dr buba ne ya janyo mana,da tuni tare zamu tafin,amma kada ki damu,nan da kwana shida kacal zan biyo bayanki" suka saki murmushi tare ************** Sammakon fita yayi saboda wasu baqi da company din nasu zaiyi,ita din ma qarfe takwas ta gama shirinta tana parlour din abba suna sallama,kudi masu yawa ya miqa mata "Ga wannan ki kaiwa su fannanan,ki gaishesu da kyau....wannan kuma" ya sake miqa mata wasu "Ki riqe a hannunki saboda sha'anin biki,duk wani abu da kanuri keyi kada ki yarda a barki a baya kema kiyi ki saje da su kinji?" Ya qarashe maganar cikin barkwanci,abban ba baya bane gun barkwanci da jan iyali a jiki,babu muhallin cewa ba zata karba domin kuwa bataso yaji ta maisheshi baare,ma'ana bata daukeshi matsayin mahaifinta ba,godiya tayi masa mai tarin yawa tana sake jin qaunarsu da ganin girma qima da mutuncinsu cikin idanunta. haqiqa babu abinda yakai abota da mutanen qwarai dadi,gashi dai abbansu baya doran qasa amma har yau suna cin ribar alaqar da aka ginata domin Allah,har yau suna kula da daukar nauyin iyalansa tamkar yana raye,aboki na gari babu shakka riba ce duniya da lahira,Allah kaci gaba da hadamu da masu sonmu domin Allah,taci gaba da fada cikin ranta ganin irin yadda ciki da booth din motar ke cike da kaya kala kala duka tsarabar daddy dalhatu da abba ne,baya ga kudi masu yawa da suka damqa mata. Lokacin da auwal ke qoqarin tada motar takai idanunta sashen da yake ajjiye motarsa,wayam bata nan,hakan ke alamta mata mamallakinta ne baya nan,ta rufe idanunta a hankali wani abu mai ciki da rauni na kewaya zuciyar tata,baya kadan ta tuno,wato duk lokacin da zata maiduguri ita kadai ko da rumana ko da ummu ne,shike daukarsu ya kaisu har tasha idan ta kama ta tashar zasu tafi,baya tafiya sai yayita tsokanarsu da zaiyi missing dinsu,har sai motarsu ta daga zaya dawo gida cike da kewa,haka shike komawa daukarsu. Bayan doguwar tafiya da suka sha cikin ikon Allah suka shigo garin na maiduguri lafiya qalau,kamar ko yaushe gidan kakanninta take sauka,ummin nata ma na can gidan saboda tazo kenan ba zata koma gidan da take aure ba sai bayan an kammala bikin,wannan karon gidan akwai jama'a 'yan uwa ba laifi kasancewar gida ne mai girma da yalwa anan aka yanke za'a gabatar da taron bikin,gida ne part part wani part din ma babu kowa ciki. Tana parlourn tsohuwa hajja yakura kakarsu wanda yake makeke ne mai dauke da dakuna har biyar,'yan uwa duka na ciki anata murna da ganin juna. Family ne mai cike da hadin kai da qaunar juna,don haka kusan yawanci 'yammatan familyn wadanda duka kusan age mate din raihana ne shekaru da kuma matakin karatu ma baki daya suna gidan sunata shirye shiryen bikin,suna da wayewa daidai gwargwado don dukansu suna makarantun gaba da secondry baya ga ilimin addinin islama da suke da shi,lallai kowa ya bar gida gida ya barshi,bata bar cikin 'yan uwan nata ba sunata hira anata tsokanarta sabida yadda yaren nasu yaso barin harshenta,don ba komai take iya ganewa ko mayarwa ba,baba gana shi yafi takura mata,abokin wasanta ne abbanshi dan gidan ne. Dare suka raba bayan sun kebe ita da umminta, sosai takejin wani farinciki na ratsata,duk wani bacin rai da qunci da yayi saura cikin zuciyarta ya dinga qaura daga ranta,lallai uwa ba wasa bace,uwa maba da mama,Allah ka jiqan iyayen wadanda suka rasu namu kuma ka dade su da lafiya da nisan kwana mai amfani,kasa suyi kyakkyawan qarshe,ummin ta dubeta tace "Wato su abbanki basu gajiya da hidima dai koda yaushe,shekaru kusan goma amma har yau basu mance da Abubakar ba,Allah ya saka musu da alkhairi ya basu ladan abinda suke aikatawa duniya da lahira" murmushi raihana kawai takeyi ta amsa mata da amin. Kiran rumana ne ya shigo wayarta,sosai suka sha hira take gaya mata ashe bata gayawa ya rayyan zata tafi ba "Awww,na manta ne sisi" "Aikam nidai na ruwana,don ya nuna bacin ransa sosai" Wani zancan daban ta soko mata don kawar da wancan,bata dade da ajjiye wayar rumana ba kiran amir ya shigo,katsewa tayi ta yiwa mamanta sallama ta tafi dakin 'yammatan don sai tafi sakewa a can,sosai amir ke jin dadin yadda yakr ganin sauyi tattare da raihanan,takan sake da shi yanzu ta amsa wayarshi duk da har yanzu bai samu yadda yake burin samu daga gareta din ba. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"shin wanda yake daga kansa(daga ruku'u ko sujjada)kafin liman ya d'aga nashi,baya jin tsoron Allah ya maida kansa kan jaki(ranar qiyama)"* ___________________ *Babi na sha tara* Ta sake sosai cikin danginta,ta mance da duk wata qura da ta baro a baya,da ita aka ci gaba da shirye shiryen bikin,inda ta fidda kudi cikin kudin da abba ya bata tayi duk wata siyayya irin ta bikinsu wadda zata sata ta saje da 'yan uwanta itama ta fito a babarbariyar asali. Kitso aka yi mata mai kyau irin wanda akewa 'yammatan kanuri a al'adance kamar yadda aka yiwa sauran 'yammatan,hakanan aka yi mata jan lallensu mai kyau wanda ya sake qawata fatarta,sai take jinta a kanurinta sosai,musamman idan ta waiga ko ina ta ganta cikin 'yan uwan nata,tabbas gida da dadi yake. Ranar da rumanan ta taso ta kirata a waya ta sanar mata,da kanta ta shirya zuwa daukarta ita da siyama da najwa wasu cousing dinta da tasu tafi zuwa daya,tun daga tasha suka daukota cikin motar baba gana,gwanin hira sai ya samu abokiyar yi,cike da raha suka iso gidan. Suna zaune a dakin su biyu rumana na cin abinci tare da huce gajiyar tafiya ta dubi raihana "Dubeki sisi,wallahi kin koma kanurinki sak" dariya raihana tayi "Kema jira nake ki huta nan da anjima zan sa a maida ke,don har irin kitso na sai an miki" dariyar itama tayi,tana shirin yin magana wayarta ta fara ringing,murmushi ya wadaci fuskarta kana ta tsame hannunta daga abincin ta jingina da kujera ta daga kiran "Ranka ya dade,kamar kasan cewa kana raina" inji rumana,ba ko tambaya raihana tasan cewa rayyan ne ta kuma san hirarsu da tsawo,sabida haka ta miqe ta kwashe sauran tarkacen kayan da rumana ta gama amfani da su ta fice a dakin. Washegari ya kama ranar daurin aure ne,qarfe biyu na rana za'a daura saboda dangin angon daga damaturu zasu zo,ankon shadda kafatanin 'yammatan sukayi sea green,ba qaramin kyau 'yammatan kanurin sukayi ba wanda rumana da raihana tuni suka saje cikinsu,babu abinda ke tashi sai yaran kanuri. Part guda suka ware 'yammatan amarya,suna ciki suna harkokinsu. Muhsin jikan gidan wanda bazaya wuce shekara goma ba ya shigo yace raihana da rumana suzo inji hajja yakura,rumana kam basa nan an samu qafa,tabi Aishatu wata cousing din raihana gidansu zata debo kayanta na dinner din anjima,don rumanan tace bazata zauna ba gwara taga gari,tafiya mabudin ilimi ce. Ankon shaddar ne itama a jikinta saidai dinkin buba ne iya gwiwa da zaninta,rigar ta fita ajikinta sosai,ta soke daurin dankwalinta kitson da aka yi mata ya fito,ba wata tazara bace tsakanin part din hajja yakura da nasu ba,sa'an nan sashen babu yawaitar zirga zirga sabida can bayan gidan suke,don haka haka ta fice abinta kai tsaye. A dan tsakar gidan hajja yakura ma ba mutane sosai,gwaggwanninta ne tayi musu sannu ta wuce. Sallama tayi sannan ta daga labulen qofar dakin,hajja yakura ce kadai zaune a falon nata,itama sanye take da shadda ruwan lemo wato orange wadda tasha aiki tayi mata kyau sosai,hakanan tsufanta ya buya,tsokanar hajja yakura da tayi niyyar yi ce ta koma ciki sakamakon turaren daya sheqa,babu bata lokaci kuma idanunya suka sauka a kansa,tuni dama nashi idanun na kanta tun sanda ta nufo bangaren jikinsa ya bashi. Rayyan ne,zaune yake gaban hajja yakuran abinsa tamkar shima daya ne daga cikin jikokinsa duk da kusan haka suka daukeshin,sanye yake da farar shadda qal mai azabar kyau da daukar ido,riga 'yar ciki da wando hadda babbar riga,dukkansu sun sha aiki ash colour,hular kansa safa da agogo kuma duka ash har da sau ciki data gani a bakin qofa ga zatonta wani baqon hajja yakuran tayi na daban,ya zuba kyau wanda fadarsa ma bata baki ne,tamkar wani kyakkyawan balarabe da ya ari kayan hausawa ya sanya,idanunta ta janye tana jin wata fargaba da zullumi na maye gurbin nutsuwa da kwnciyar hankalin da ta dan samu,wani zullo zuciyarta ta fa yi mata,qafafunta sukayi sanyi tamkar an dokesu. Cike da dakiya ta saki labulen ta qaraso cikin dakin,har yau bai dana kallonta ba,ji yake bazai iya janye idanunsa daga kanta ba,wani irin kyau yaga tayi masa,tsohon tsumin sonta da yake zaton raguwarsa ya fara dawo masa sabo fil ya soma taso masa,komai nata mai sanyi ne kamar yadda halayyarta take,tabbas haka yake "Gani hajja" "Gaki kuma......baki ga yayanku bane?" Murmushin yaqe ta saki tare da zama kusa da ita "Ki bari na zauna mana tsohuwa.....sannu da zuwa yaya rayyan,ya hanya?,an iso lafiya?ya mutanen gidan?" Ranqwashi hajja yakura ta sakar mata aka tana fadin "Jimin saunar yarinya?,sai kace 'yar jarida,haka kanawan ke saukar baqi da tambayoyi?" Murmushi ya saki yana duban dan qaramin bakin raihanan da ta sake tsukeshi tare da yamutse fuska alamun taji zafin ranqwashin "Barta hajja,wata gajiyar takeson taramin da wadannan tarin tambayoyin bayan wadda ke jikina ko?" "Eh tsabar iya shashanci ne ai" cewar hajja yakura,idanunsa ya lumshe ya budesu,har yau idanunshi na akanta,ita kuma taqi dubansa don so take su raba lafiya ba tare da ya haddasa ma zuciyarta komai ba"komai lafiya lau raihata....."yanayin yadda ya fidda sautin sunan ya sanyata daga kai ta dubeshi,ya kashe mata idonshi daya,tofa abinda take gudu sai da ya faru,tuni ya aikewa zuciya da gangar jikinta wani irin dafi da ya zare mata dukka wata laka ta jikinta tashin farko,qasa tayi da kanta tana jinjina shu'umancin rayyan din,tana jin tamkar da biyu yayi mata irin wannan kallon Hajja yakura ta mata umarnin ta bashi masauki sannan tazo ta karbar masa abinci,tamkar ta zura da gudu su nemeta su rasa haka taji,tabbas idan batayi wasa ba sai rayyan ya fama mata ciwonta,amma yata iya,bashi yiwuwa ta bijirewa umarnin hajjan tunda bata da wata hujja da zata bata,sai lokacin take data sanin barin rumana tabi aishatu,da tuni ta janyr jikinta ta barta da shi su qarata. Ta bayan gidan suka kutsa yankin da tasan ba mutane,tana gaba yana binta a baya,hakan ne ya bashi damar qare mata kallo,cikin jikinta ita kanta a tsarge take,tafiya kawai take tana hardewa,jinta take tamkar tare take da dodo "Kinyi kyau raihata,kinyi kyau sosai,tilas na biyo bayanki saboda 'yan fashi da makami" "Idan akwai babban dan fashi ai kaine na farko,baka da na biyunsa" ta fada cikin dakiya,da kuma manufar katse duk wata hira da zata hadata da shi,dafin da yake zuba mata da idanunsa kawai sun isheta basai ya qara da kalamansa ba,wata sassanyar dariya ya saki,bata ankara ba yasha gabanta lokaci guda suna daf da bakin falon da zai sauka din,yayi daf da ita,da sauri ta ja baya tana dubansa,idanunshi tsakiyar nata yace "Idan d'an yankan kai za'a kirani akan sonki raihata a shirye nake da hakan,saboda matsayinki cikin nan....." ya nuna qirjinsa ".....ya wuce duk yadda kike fasaltawa" cikin tata salon dakiyar ta harde hannayensa a qirji tana dubansa,wanda hakan baa qaramin sake tafiya da rayyan din yayi ba,kunne ya zuba don yasanta sarai,magana zata yanko masa cikin sanyi amma mai nauyi "Yaya rayyan,ba'a so dole fa,ni bani da ra'ayin aurenka.....ina ganin qimarka da mutuncinka a matsayinka na yaya na,don Allah kaci gaba da kare martabarka,kada ka yarda qanwarka ta rainaka" murmushi ya sake kasheta da shi har sai data ambaci sunan Allah "Son da nake miki da wanda rumana ke miki na tabbatar ya isa ya riqe mana gidan aurenmu,so kada ki damu zamu rayu cikin farinciki da aminci fiye da yadda baki zato kinji?" "Bana sonka kuma ina nufin abinda na fada din" ta fada a zahirance a hasale,yayin da can qasan zuciyarta take jin rauni da tausayin kanta,shiru yayi yana qare mata kallo,tsahon minti biyu ta kewayeshi ta bude falon ta shiga,bayanta yabi amma sai yaja tunga a bakin qofar falon "Ga masauki nan" ta fada tana duban wani sashen tare da neman hanyar ficewa daga falon,ta gefansa ta rakuba ta fice din. Jikinta har rawa yake haka ta dinga neman number din rumanan,don bata jin zata iya sake komawa gun rayyan din,hawaye ne ke layi bisa kuncinta tana sharewa,ita kadai tasan azabar da take ji a qirjinta,kusan sau biyar tana kiran rumana wayar a kashe,saita sauya akalar kiran nata zuwa wayar aisha,najwa ce ta daga a gida kenan ta barta,ta kashe wayar tata ta jingina da bango,kuka tayi nadan lokaci wai ko zataji sauqin abinda takeji cikin zuciyarta,sannan ta ja qafafunta bakin fanfon dake tsakanin shuke shuken bayan gidan wanda shike basu ruwa ta wanke fuskarta,take duk wata 'yar kwalliya dake kan fuskarta tayi nata guri,sai data ratsa dakinsu ta shafa powder sannan ta koma gun hajja yakura ta dauki abincin rayyan din. Yana zaune saman cushion din falon,ya cire babbar rigar da 'yar ciki da hukar,daga wandon shaddar sai singlet a jikinsa sai kace wanda ke a gidanshi,inji raihana data masa kallo daya ta dauke kai sabida wani nauyin ganinsa haka da taji, Kafin ta ajjiye tray din dake hannun nata har ya taso ta tallafi qasansa inda hannunta yake,take hannayensu suka hadu,wani shock dukkaninsu suka ji wanda basu taba jin hakan ba tattare da su,karo na farko a rayuwarsu,nata kam ya boyu saidai nashi bai boyuwa ba,kamar ta sakin farantin haka takeji gashi yaqi ya riqeshi sosai tana sakin ba shakka kwanukan zasu tarwatse ne a qafafunsu. Muryarsa can qasa tamkar mai maye ta yadda yasan ba shakka zai iya illata ta,don yaci burin sai ya tarwatsa duk wani qarfi da take ji ko qin da take iqirari cikin zuciyarta a yau din nan "Shine kika wanke kwalliyar duk sdon saboda rayyan ya yaba?,saboda nãce kinyi kyau?...." Ya tambayeta yana mata kallon qasan ido "Dama ba don kai nayi ba...saboda haka baka cancanci ka gani ba" ta fada muryarta na rawa bayan sanyin da tayi,wanda ita kanta batasan da hakan ba,murmushin gefan kumatu yayi yana sake matsowa kusa da ita,badan farantin dake tsakaninsu ba tabbas da hadesu zaiyi guri guda,sassanyan qamshinsa ya dinga bugun hancinta "Ni rayyan ni kuwa na cancanci ganinta tunda gashi ni din nazo,dayan da kike qaryar shi kika yiwa ina yazo?,shaidar bai damu da ke ba kenan?". Zuciya a kusa sai wasu sabbin hawayen suka balle mata,bakinta na rawa ta fara fadin "amir shi ya damu da ni kuwa tunda yana son farinciki na sabanin kai.....ko daama bai damu da ni ba to ni na damu da shi,kuma ni shi nakeso,kai din da kake qwaqwar bana sonka bana sonka na fad......."kasa ci gaba da maganar tayi sakamakon yatsansa manuni da ya sanya yana zagaye tausasan lebunanta da su,wani abu taji yana zagaya jinin jikinta,bugun zuciyarta ya qara gudu. Cikin rawar jiki ta janye hannayenta da jikinta daga jikin farantin da niyyar barin gun,ba don yayi zafin naman tallafe kwanukan ba tuni duka abincin ciki sun kife a qasa,da sauri sauri ta nufi qofar ficewa daga falon,tuni ya ajjiye kwanukan abinci sannan ya isa bakin qofar falon ya rufeta da faffadan qirjinsa sannan ya zuba ma raihanan idanunshi wadanda ke mata kaifi,don duk wasu alamu da yakeson gani ya samesu tattare da ita,koda bakinta bai furta ba yasan yayi nasara a kanta,duk da haka bai qyaleta ba sai da ya faki idonta ya cafko hannunta,ya sanya tafin hannunshi cikin nata ya rumtse yana kallon qwayar idonta dake digar da hawaye,bacin ransa ya fara tasiri kadan kadan cikin ido da kuma saman fuskarsa,bai iya shiga damuwa ba sam shi yasa baya yadda wani abu ya dameshin,face soyayyar raihanan da tafi qarfin ikonsa "Kekam bakijin kunyar yin qarya?.....baki jin nauyin budar baki ki cewa dan adam bana sonka?" Ta lura so yake ya fasa mata zuciya,a hasale ta daga kai "Eh ai gaskiya na fada." Kai ya shiga kadawa tana qoqarin qwace hannun nata sai yayi mata riqon tsauri "Da kyau,kici gaba da fada din,shi kuma rayyan xai baki mamaki,kafin kibar maiduguri idan bakiyi wasa ba zaki koma kano da aurensa a kanki" ya fada yana sakin hannun nata,sannan ya juya ya koma kan kujerar abinsa yaja kwanukan yana budesu. Ji tayi zuciyarta kamar zata fado,a iya saninta da rayyan baya qarya,hasalima tunda suke ba zata iya tuna wani abu guda da ya taba fada ba na qarya,wato da gaske kenan idan batayi wasa ba rayyan zai jaza mata tashin hankali?,zai janyo mata abinda zai sanya farinciki yin qaura daga rayuwarta?,aurensa fa na nufin faruwar komai game da ita,ta raba rumananta da shi,sannan ta zama butulu mayaudariya maci amana a idon duniya,ba zata iya ba,ta gwammace ta dawwama cikin qunci,ta gwammaci ta rasa nata farincikin. Ba shakka ta lura nuna qiyayya barazana da nuna duk wani qarfin zuciya da qwanji bazaya tafiyar da rayyan daga kan ra'ayinsa,abu guda take ganin yanzu zai iya mata aiki,lallashi wayo da dabara har ta samu su rabu lafiya din. Ta sake dubansa tana goge hawayen fuskarta tare da qoqarin daidaita yanayinta,ya zuba abincinsa yana ci a nutse tamkar baya da wata damuwa,a hankali ta taka inda yake ta samu gefansa ta zauna *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 Shiru tayi yayin da shima yaqi tanka mata har ya kammala cin abincin yayi gefe da kwanukan "Yaya rayyan" ta fada cikin murya mai cike da rauni,idanunsa ya daga kawai ya kalleta,sai ta zame qasa kan gwiwoyinta,wasu sabbbin hawayen na neman zubo mata "Na roqeka yaya rayyan ka janye dukkan qudurinka,kana sakani cikin tsaka mai wuya duk lokacin da ka bijiromin da wannan maganar,na roqeka don Allah yaya rayyan ka barmu mu koma kamar yadda muke a baya,mu koma 'yan uwa masu qaunar juna da fahimtar juna" ci gaba yayi da kallonta har ta kammala,a hankali ya bude bude baki ya fara magana,yanajin wani abu ja zagaya jikinsa "Zanso hakan,nina zanso hakan idan da zuciyata zata iya haqura da ke raihana,raihana.....na tabbata babu qiyayyata cikin zuciyarki,kina pretending nr kawai saboda rumana,me yasa kikeson haramta halas?,me yasa kike son dora son zuciyarki gaba da abinda Allah ya halatta,kada ki yarda raihana ki shiga hurumin ubangiji,dukkaninmu bamu muka dorawa kanmu a binda muke ji cikin zukatanmu,ban damu ba raihana kuma bazan damu ba da dukkan ma abinda zai faru,abinda na sani kawai shine ina son RAIHA". Ji tayi tamkar yana sosa mata zuciyarta ne,zuciyarta ta sake yin rauni,sai kawai ta sanya tafukam hannayenta kan fuskarta tana jin yadda hawaye masu dumi ke fitar mata,tabbas da tana da iko da babu abinda zai hanata tsaga zuciyarta ta jefar ko kuma ta tsaga ta uban tafiyar rayyan ta sauya masa da wata wadda rumana kawai zata so ba tare da ta hadata da raihana,sai yanzu take gasgata kalaman wasu kalamai da wani yayi wanda ta taba cin karo da su garin bincike bincikenta,inda yake cewa _babu shakka so dafi ne,so masifa ne kuma bala'i ne ga wanda Allah ya jarabceshi,so yakan iya zama linzami ga duk wanda ya tsinci kansa a tarkonsa,so wani maruru ne da kan azabtar da zukatan masoya,wani tsiro ne da yakan tsiro a zuciyar duk wanda yaga dama,so na gaskiya baya buya a zuci ko a baki,ba zaka taba sanin mene ne farinciki ko baqinciki ba sai lokacin da kake soyayya,soyayya tafi komai dadi amma tafi komai azabtar da zukata_ Lokacin da taci karo da kalaman murmushi kawai tayi tare da kada kai,ashe tabbas haka suke,ta tserewa fadawa irin wanna yanayin kamar yadfa mutum ke qoqarin tserewa mutuwarsa ashe gudun da babu tsira tayi tayi tsawon shekaru,sai kawai ta miqe tana niyyar ficewa daga parlour tana jin jiri na dibanta,numfashinta na daukewa,wani abu ya tokare mata qirji *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *manzan Allah S A W yace "ku yawaita tuna mai yanke jin dadi(wato mutuwa kenan)* _______________________ *Babi na ashirin* Karon da suka ci da rumana ya sanya jarumatarta dawowa cikin 'yan daqiqu,murnar ganin rayyan din ya sanya bata tantance halin da raihanan ke ciki ba,sai tayi ciki fuskarta dauke da murmushi tana fadin "Suprise ya rayyan?" Murmushin ya maidata mata gimi da dage girarsa yana fadin "Yes,ko ba'a yi murna da zuwana ba?" "Haba ya rayyan,ko yaushe ai mu masu maraba da kaine ko sisi?" Ta fada tana duban raihana dake coge bakin qofar falon,murmushin yaqe ta qaqalo tana fadin "Haka ne,bari na baku guri ku zanta sosai,zan shiga ciki" "Amma dai kinsan tafiyar tamu ce mu duka biyu ko?,ba a gida muke ba balle kice" wani yaqen ta sake yi "Na sani,na sadaukar muku da lokacin ne don kufi sakewa sosai" fari rumana tayi sannan tace "Shi yasa nake alfahari dake sisi na,godiya nake" kai ya jinjina kawai tayi hanzarin ficewa. Ita kadai tana tafiya kamar iska zata kayar da ita,hakanan sai ta dinga ji me yasa ta fito ta baro su,idanunta naci gaba da hangosu su biyun,saurin kwabar kanta tayi,a haka ta isa sashen hajja yakura,kai tsaye dakin gadonta ta shige,can quryar gadon tsohuwar ta samu ta lafe ta saki wani marayan kuka,a ranar tayi kukan data jima batayi irinsa ba,tayi kukan tausayin kanta da kanta ita kadai,sai data gaji don kanta ta lallashi kanta da kanta gudun samun matsala saboda yadda taji zuciyarta na mata zugi,sunayen Allah ta dinga ambata dari ba daya,idan ta gama ta dawo daga farko,tun tana iya jiyo surutan mutane jifa jifa har wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita. Har aka kammala daura auren bata farka ba,tun rumana na cigiyarta harta haqura ta koma gun baqonsu saboda babu wanda yaga shigarta dakin hajja ya kura,hakanan ta kikkira wayarta a kashe. Qarfe biyar na yamma ya dauki rumanan tare da aisha ta rakasu ya samu masauku cikin wani hotel dake gabansu,tafiyar da yake da shirin yin ya fasata yace sai washegari. Qarfe biyar da kwata ta farka,salati ta saka lokacin da ta duba agogo,Allah ya taimaketa tayi sallar azahar la'a sar ce kawai a kanta. Parlour din ta fito,hajja yakura ce zaune gefanta hajja salma yayar ummin raihanan,sai hajja bilkisu da hajja batula qannen ummin raihana,sai wasu mata dake shigiwa da kayayyaki suna ajjiyewa,sannan basma da alawiyya da shigowarsu falon kenan sanye da ankon dinner din da za'ayi bayan sallar magariba,da alama sun fara shiryawa,hajja yakura ta dubeta riqe da baki "O ni 'yasu,duk neman da yarinyar nan take miki ashe kina qunshe a daka?". Murmushi tayi tace"bacci ne ya daukeni hajja,yanzun tana ina?" "Sun fita ita da aysha da yayanku" inji basma "Ok"cewar raihana kana ta wuce bandaki,wanka tayi ta hado da alwala ta bada faralin salla sannan ta shirya cikin nata ankon,lokaci lokaci tana yi tana duba wayarta ko zata ga kiran rumana amma shiru kake ji,zuwa lokacin 'yammatan sun fara cika gidan wasu daga cikinsu ma sunyi gaba can hall din da aka kama don gabatar da bikin. Parlour ta dawo ta kwanta hannunta riqe da wayarta tana game,a hankali har aka yoye sai amarya da daidaikun qawayenta makusantan ta,sai ta dinga ji ta damu da rashin dawowar nasu,ba rumana ba rayyan din. A hankali ta daga wayar tata ta sake dubawa a karo na barkatai,sai ta dan ja tsaki ta maida wayar ruwan cikinta,ta rasa dalilin da ya sanya ta damu da yawa haka,gashi ta gaza kiran rumanan taji basu dawo din ba,batason taga kamar ta matsa musu ko tayi musu katsalandan,rayyan kuwa dama bata da ra'ayin kiransa ko kadan. Baba gana ne yayi sallama hadi daga labulen falon ya shigo yana kiran hajja yakura,sanye yake cikin shadda light blue sai qyalli take wadda aka yiwa dinkin tazarce,turus yayi yana duban raihana " a'ah,ke bahaushiya ya naganki nan zaune bayan kusan duka an tafi?"murmushin yaqe tayi tana gyara kwanciyarta "Banajin zanje ne ma baba gana" "A'ah,me yasa kuma?"ya fada yana qarasowa cikin falon tare da samun kujerar dake gefanta ya zauna,tashi tayi itama ya zauna sannan tace " rumana har yanzu basu dawo ba,kaga bazan tafi babu ita ba ko?",murmushi yayi "To banda abinki ba naga tare suka fita da yayanku rayyan ba?"kai ta gyada masa " kizo kawai mu wuce nima can zani,nasan idan ya dawo zasu wuce can tunda da mota hannunsu,amma ya zaki zauna ke daya bayan gidan babu kowa sai tsofaffi?"kamar ta qiya sai kuma taga zaman bai da amfani,bata son taci gaba da zama har tunane tunanen dake bijiro mata suci gaba da uzura mata. Uwar dakin hajja yakura ta shiga ta sake gyara fuskarta ta sanya glass dinta sannan ta yafa mayafinta mai kyau wanda ya dace da ankon jikinta da aka yiwa dinkin doguwar riga,ta saqala 'yar madaidaiciyar jakarta mai hannun sarqa (chain). Miqewa baba gana yayi yana dubanta tare da murmushi,jakar kafadarta din ya amsa yana cewa "Bani na tayaki ta riqon wannan" murmushi ta saki tace"dama ka barshi ai babu nauyi" "Ke dai ladan kike kin baqinciki" ya fada yana karbe jakar. A hankali suka jero yana janta da hira har suka fito harabar gidan inda motarshi ke fake gefe daya,mamanta ce tsaye ita da qannanta zainab da ammi sanye suke suma da nasu ankon duk da basu wuce shekara sha biyu ba da goma ba amma sunyi kyau sosai,black beauty ne suma kyawawa kamar yanayin yayar tasu raihana "Sannu ummi" raihana ta fada tana dan ranqwafawa cikin girmamawa,waiwayowa tayi fuskarta qunshe da fara'a "A'ah,baba gana baku tafi ba dama?" "Eh ummi,na shiga amsar saqo hannun hajja naga wannan bakanuwar zaune shine na sanyata ta fito wai da bazata je ba" "A'ah,dalili da me?" "Eh mama,rumana ce bata dawo ba,ni kuma banson tafiya ni kadai" "A'ah,da rayyan suka fita inajin ai ko?,kuma har da aysha,babu mamaki ma sun wuce can din tunda zasuyi tunanin zaki taho" "Haka nace mata ummi" inji baba gana yana fiddo maqullin motarsa daga aljihunsa. "Yaya,bamu samu mota ba muzo mu tafi tare don Allah?" Cewar zainabu "Me zai hana qanwata ku taho mana" cikin murna suka bi bayansa yayin da raihana ta yiwa ummin sallama ta bi bayansu. Remote ya danna su zainab suka bude gidan baya suka shiga,motarsu rayyan ne ta kunno cikin gidan,ta kalli sashen da motar ke shigowa sai kuma ta dauke kai,baba gana ya miqa mata jakarta tayi hanzarin bude gidan gaba ta shige,shima ya zagaya ya tada motar tasu suka fara ficewa daga gidan lokacin da motar su rayyan din ke tsayawa. Shiru tayi cikin motar tana jin hira da hayaniyar su zainab din da baaba gana,kanta jingine da makarin kujera tana jin wani bacin rai kadan kadan,tsuwwa wayarta tayi alamun kira ne ya shigo cikin wayar tata,ta daga ta duba sannan daga bisani ta amsa "Sisi,shine kikayi tafiyarki ki barni ko?" "Ya zanyi to,inata jiranku shiru baku dawo ba ga lokaci na tafiya" daj shiru rumanan tayi sannan tace "Sisi ko na bata miki rai ne?,nayi nemanki kan na fita har na gaji ban ganki dole na haqura muka wuce" Idanunta ta lumshe tana qoqarin tuna me ta gayawa sisinta ne?,a hankali ta saki murmushi wanda har rumanan sai da ta jiyoshi "Ba wani abu bane ba fa sisi,kada ki samu damuwa 'yar uwa,naga kuna tare da ya rayyan babu damuwa ai ko?" "Ki dawo yanzu ina son ganinki" taji muryar rayyan maimakon rumana "Kamar yaya?" Taji tambayar ta subuce a bakinta "Kamar yadda kika ji" sai kawai ta cire wayar daga kunnenta ta kasheta baki daya don ta fuskanci rayyan so yake ya raina mata hankali "Ya dai?" Taji baba gana na mata tambayar "Lafiya lau" ta fada tana yaqe,duk da sanyota da yake cikin hayaniyar sun ta kasa ce musu komai har suka qarasa gurin. Duk da tarin 'yammatan dake kara kaina a gun da ya qayatu matuqa amma sai ta samu table dake can qurya da dakin taron ta kebe kanta,hakanan take ji rashin sukuni cikin zuciyarta,duk yadda takai ga son sanya walwala cikin fuskarta da zuciyarta abun ya faskara,dole ta dan saki kadan tana maidawa baba gana hirar da yake mata don kada ya tsammaci wani abu ne hakan da takeyi. Tsawon mintina talatin ana gabatar da abinda ya tarasu a gun,yayin da taci gaba da zama a inda take din ita da baba ganan,daga nan suke hango duka abinda ke faruwa,daga can ta hango rumana na ratsa mutane da teburan dake cike da harabar gun,ido ta zuba mata har ta qaraso inda take zaune,cikin murmushi raihana tace "Hala yaya rayyan ne ya kawoki ko,irin wannan sauri haka sharp sharp?" Harde hannunta tayi cikin fushin wasa tana daure fuska "Mu da muka damu dake ai mun biyoki,kije yaya rayyan na kira",kai ta girgiza "Allah yasa lafiya" hannu ta ware "Oho,wannan karan kam bazan tare miki ba koda laifi kikayi na gaya miki tunda kika taho kika barni" qaramar dariya raihana ta saki "To ai ni nasan ban muku laifin komai ba sisi,kije gani nan zuwa yanzun in sha Allah"sai da rumanan ta harereta sannan tayi gaba,dariya raihanan ta bita da ita tana cewa "afuwa sisi mana,ba haka tsakaninmu". Hirarsu suka ci gaba da yi da baba gana tamkar ma ta mance da kiran rayyan din,minti kusan goma tsakani ba zato ta tsinci rayyan tsaye gaban table dinsu,sanye yake da qananun kaya t.shirt mai dogon hannu ruwan bula wato dark blue da wandonta,ba qaramin kyau yayi ba,sosai kayan suka haska fatarsa,idanunsa saye da sun glasses mai fadi,yayin da kwantacciyar sumar kansa ta sake yin luf sai sheqi take,ba qaramin daukan idanun 'yammatan dake gurin yayi ba,rayyan din na musamman ne, duk hassadarka dole ka fadi hakan,yanayin qirar da halittar da Allah yayi masa ya sanya yawancin wadanda basu sanshi ba sukanyi tsammani sam baisan wani yare waishi hausa ba,shirun ya faru ne saboda lokacin da ya shigo din gurin ya nutsu ana sauraran jawabi daga bakin abokin ango,domin da dama basu sanshi ba,idanun raihana sun gane mata hakan,sai taji wani abu na taso mata,wanda bata raba dayan biyun kishi ne,saidai kanta takewa kishin ko 'yar uwarta?,wannan ne kuma bata sani ba. Taku yake irin na cikakkun matasa har ya iso inda suke zaune din,tun dazun ta ganshi amma sai ta dauke kai kamar bata ganshi ba,kallo daya tayi masa taji yayi mata kwarjini,jikinta sai ya mutu laqwas tayi,duk wani kuzari da karsashinta ya fice lokaci guda tamkar wadanda sukaji tsoron ganin rayyan din,fuskarsa a hade ba tare da ya dubi baba gana ba yace da ita "Wuce muje"ya sanya hannu yana daukar jakarta daje ajjiye saman kujerar shuru tayi ta dan dubi baba gana,ita yake kallo ba tare da yace komai ba,ta sake maida idonta ga rayyan yana tsaye qyam cike da wata iriyar izza da isa,sai ta kasa cewa komai face miqewar ta dubi baba gana "ina zuwa" "Ba damuwa" shima ya amsa mata a taqaice. "Wannan saunan shi ya hanaki zuwa ko kuwa da zan kiraki sama da minti talatin ina jirankin?" A dan rude ta waiwaya tana fata Allah yasa baba gana baiji sunan da rayyan din yayi kiransa da shi ba,tana gaba yana binta a baya,ya wani hade rai yayi kicin kicin,yayin da idanuwa sukayi yawa a kansu,kowannensu dacin rai ya kama shi,shi yana kishin mazan dake gun yayin da ita ke kishin matan. Ajiyan zuciya ta saki a hankali data fuskanci kamar baba ganan baiji ba "Ai ya isa ne,ko ka manta dan uwa na ne" "Ni kuwa nasan hakan,amma kuma baiyi isar da zan kiraki ya tareki ba,kada ki yarda ki sake maimaita irin wannan kuskuren" baki ta murguda kana ta turo shi gaba lokacin da suke ficewa daga hall din "Ni kike murgudawa baki,kinsan kadan daga aiki na cinyeshi yanzun naga na rashin kunya nan gaba?" Ya fada cikin dinkakkiyar fuska tare da jan tunga ya tsaya yana dubanta bayan ya zare gilashin fuskarsa yana duban nata qwayar idon dake cikin medicated glass dinta,rasa abinda zata ce tayi,ga mari ga tsinka jaka?,kawai ji tayi hawaye na shirin zubo mata "Ka daina min abinda kake min ya rayyan" "Sonki ne,kuma bazan daina ba yanzu na fara" ya fada tare da jan gefan mayafinta,tasa hannu ta janye mayafin sannan taci gaba da binsa "Bakajin kunya ne yaya rayyan?,gani ga rumana,kana son 'yar uwarta ba tare da saninta ba,shin da wanne irin ido kake iya kallonta ko kum......" Shiru tayi saboda ganin sun iso bakin motar,hannu ya sanya ya bude mata gidan baya tare da maida mata da amsa "Ku mata ku kukasan wannan,mu muna duba abinda yake daidai ne ba abinda ya dace ba" ya fada yana watsa mata wani irin kallo,dole tayi shiru saboda idanun rumana wadda ke zaune gaban motar,a hankali ta sanya jikinta cikin motar sannan ta kwashe qafafunta da sukayi sanyi ta shigar da su suma har lokacin idanunta mai cike da qwalla na kansa wai ko zai duba rauninta ya janyr qudurinsa,saidai ki kadan batasan wano saqo take aikama ruhi da gangar jikinsa ba,wasu abubuwa yake sake gani tattare da ita dake sake tafiyar da shi sosai,yana jin wani irin so mai qarfi na fisgarsa. *mrs muhammad ce* 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga abdullahi dan abbas R.A.M yace:manzan Allah S A W ya la'anci namiji mai kamantuwa da mata (dan daudu),da mace mai kamantuwa da maza,kuma yace"ku fitar da su daga gidajenku"* _bukhari ne ya rawaito_ _______________________ *Babi na ashirin da daya* Cikin wata iriyar kasala ya maida murfin motar ya rufe kana ya zagaya mazauninshi ya zauna "Ina ga sisi dai kora da hali kawai kike mana mubar muku garinku ko?" Rumana ta fada tana danna wayarta,wani abu ya tsirgawa raihana,sai taji wani iri,irin abunda bai taba shiga tsakaninta da rumana ba wato sabanin fahimta,Allah sarki,wannan shi ake kira da rashin sani wanda yafi dare duhu,duka abinda take yi tana yinsa don rumanan ba tare da ita rumanan ta sani ba,bata san cewa qoshi ta samu kuma take kwanan yunwa ba duk don saboda farincikin ta,tana gujewa tarayyarsu su uku ne lokaci guda kuma a tare don gudun faruwar wani al'amari,rayyan nason haifar musu da jirkicewar kyakkyawar DANGANTAKAR dake tsakaninsu kenan?,murya a sanyaye raihana tace "Haba sisi,bai kamata ki fadi haka ba,kinfi kowa sanin wace raihana ko?" "Afuwa sisi na,nima ba wani abu nake nufi ba tsokana ce dai kawai irin ta sisinki 'yar tsalle" inji rumana ta fada tana dariya,itama dariyar tayi duk da batakai har cikin zuciyarta ba. Kiran amir da ya shigo wayarta shi ya katse sauran maganar tasu,tana sane yau ta sauya wani salo na daban saboda rayyan din,ta wani saki jiki tare da narkewa ta dinga zuba masa hira mai dadi,ta kuwa qona rayyan din sosai,zuciyar 'yan maza ta motsa,ya dinga fidda numfashi mai zafi shi kadai,wani kishi mai zafi ya dinga diga tsakiyar zuciyarsa,yana jin cewa ya kamata ya kawo qarshen alaqar dake tsakaninsu don ya samu damar cimma burinsa,yayin da ta sake dilmiyar da amir cikin tafkin qaunarta,ya sake susucewa don bai taba samun haka daga gareta ba,a nan yake gaya mata antynsa(matar babansa da yake a hannunta yake)tana son ya kawota ta ganta su gaisa,babu musu ta sanar masa cewa tana dawowa daga maiduguri zata sanar masa ya sanya musu rana,sai da taga rayyan din na parking qofar wani babban super market alamar nan suka zo sannan tayi sallama da shi,ta kashe wayar ta maida cikin jaka. Shi da rumana na gaba yayin da tabi bayansu har suka shiga ciki,bangaren kayan maza yayi yace su zabi duk abinda suke so kafin ya kammala,rumana ta narke tace sai ta bishi ta tayashi zabi,bai ce mata komai ba sabida zafi da ranshi keyi yayi gaba ta bishi bayan ta juyo tace da raihana ta zaba musu abinda taga ya dace da su ta bita da to,kujera ta samu tayi zamanta tana kalle kallenta,bata da niyyar daukar kada tsinke ne. Kusan minti talatin suka kwashe sannan taga bullowarsu,turus rumana tayi "A'ah,ya na ganki a zaune sisi?,banga alamun kin dauka mana komai ba fa?" Rayyan dauke kansa yayi tare da yin gaba abinsa kamar bai gane meke faruwa ba,kama hannunta rumana tayi suka fara kewaye gurin. Laffaya ta daukar musu masu bala'in kyau mai tsada ta barebarin asali kala bibbiyu sai jaka da plate mahadin lafayar din takalmi duk iri daya,ita kanta raihana kayan sun burgeta don ta sani sisinta dama ba daga baya ba wajen iya zaban abu mai kyau dan yayi,a gun biyan kudi suka taddashi aka hada da nasu aka lissafa ya biya,a kan hanya ya tsaya wani restaurant mai kyau ya siyi take away sannan suka isa gida. Kusan qofae gidan a cike take saboda 'yan dinner dake ta dawowa,qaryar fitsari takeji tayi musu tayi shigewarta gidan ta barsu da siyayyarsu,rumanan bata shigo ba har sai da raihana ta gama shirin kwanciya. **************** Tun daga ranar bata kuma bari sun sake hada hanya da shi ba,ranar lahadi da daddare bayan sun dawo daga kai amarya rumana ke gaya mata gobe zata bi ya rayyan su wuce kano,yace gidan babu kowa ba dadi,wani abu taji ya taba zuciyarta saboda tayi zaton tare zasu koma da rumanan,tunda gobe take son zuwa wa dangin abbanta "Yayi kyau kam,nikam da sauran ziyara gabana" abinda tace kenan. Qarfe takwas suka gama shirinsu,har bakin motar rayyan din ta raka rumanan,tun ranar sai yau ta ganshi,tamkar ma wani abu bai faru ba haka ta dake ta gaidashi tare da yi musu godiyan zuwa da addu'an sauka lafiya,tace su gaida ummu bayan uwar tsarabar da umminta ta bada a kaiwa gidajen iyalan guda biyu. ************** Duk da tayi kewar sisinta haka ta ture gefe ta shiga kuma dangin abbanta,ina suka sa ina suka ajiye haka suka dinga yi da ita,kaf dinsu babu wanda bata je ta kwanan masa ba wanda hakan ba qaramin dadi yayi musu,sannan kuma shi ya sake ja mata lokacin komawarta kano,don sai da tayi wata guda cur sannan ta dawo cikin dangin umminta,tun rumana na qorafi har ta koma mita,da qyar ta lallabata kan cewa tana hanya kada ta damu. Duk lokacin data tuna koda ta koma din abinda ke gaba yana jiranta duk sai taji komawar ta fita fit a ranta,wani lokaci zuciyarta kan bata qwarin gwiwa na babu abinda wani abu da zaici gaba da faruwa,tunda har yau tun ranar da suka bar maiduguri bata qara ganun kira ko saqon rayyan ba,koda yaushe addu'a take Allah ya sanya ya haqura ne,sau tari sai ta kammala addu'ar kuma sai ta dinga jin wani iri tare da ganin baiken kanta da take roqar Allah ya nisanta tsakaninta da rayyan din duk da yadda take ji a zuciyarta,duk sanda ta tuna hakan sai kuma wani sashe na zuciyar tata ya tuna mata wane rayyan?,hawaye kan zuba sosai cikin idanunta,takan kada kai tare da sake tabbatarwa da kanta cewa koda rayyan ne kadai namijin da ya rage a duniya ta haramtawa kanta aurensa saboda RUMANA,ta yarda ta kuma amince zatayi SADAUKARWA koda hakan na nufin qarewar jin dadin rayuwarta,albarkacin QAUNA SOYAYYA DA ABOTA dake tsakaninta da 'yar uwarta. Wani lokaci idan tayi zurfi cikin irin wannan tunanin sai taji zuciyarta na zafi har ta kasa control din temper din da takeji,babu ko tantama tanason rayyan so irin wanda zaiyi wuya ka iya fassara yadda kakeji,duk wani qoqari na dakiya shariya da fada masa magana mara dadi idan tayi tanajin tamkar kanta take hukuntawa ne,don zafin da takeji a lokacin ita kadai tasan irinsa. Rayyan ne irin namijin da ta dinga yiwa kanta fata da sha'awa tun kafin tasan darajar kanta,tun kafin tasan irinshi dinne zuciyarta ke da muradi,wata iriyar halittar zuciya Allah ya bata mai nutsuwa da gane daidai tun tana qanqanuwarta,hakan ya sanya take iya gane dabi'u kyawawa abun koyi tunda wuri,hatta da ummunta tun a lokacin tasha mamakin nutsuwa da kaifin fahimta da Allah ya bawa raihanan a qananan shekarunta. Sai da ta cinye wata biyu a maiduguri hutunsu ya kusa qarewa sannan ta fara shirin komawa gida,tana jin tamkar tayita zamanta ne cikin danginta,kusa da mamanta tacu gaba da jin dumin mahaifiyarta,a yanzu ji take tamkar bata da kowa,rumanan da take gayawa damuwarta su samu mafita tare a yanzu wani qaton abu ya gitta tsakaninsu,a yanzun bata da wani abokin shawarw,bata da wani majibancin lamari,bata da wani wanda zasu iya raba damuwarsu tare,wanda hakan ya sake taka muhimmiyar rawa wajen qara dorawa zuciyarta nauyi mai yawa. Ranar lahadi ta bar garin maidugurin wanda bata isa kano ba sai bayan sallar magariba. ************** Yara ne suka fara shigar mata da kaya sannan tabi bayansu. Da su idanunta suka fara cin karo,saidau fuskarsa ta fara gani saboda shike fuskantar get din gidan yayin da rumana ke zaune gabansa tana fuskantarsa. Har zata wuce sai suka hada ido da shi,ta daura damarar nuna masa har yau yaya yake gareta ba wani abu ba daban,hakan ya sanya ta nufi inda suke,zuciyarta tayi wani irin bugawa har tsakiyar kanta,sai ta lumshe ido tare da qoqarin saisaita kanta sannan ta sake bude idon nata,har yau hannayensu na sarqafe da juna rumana na hawaye,sai ta taka a hankali ta dafa kafadar rumanan,juyowa tayi suka hada ido,tsalle ta daka ta rungume raihanan tana mata barka da dawowa,sai kuma ta sake barkewa da wani kukan,dagata tayi adaga cikinta qirninta na bugawa,addu'a take ya Allah kada kasa wani abu rayyan ya gayawa rumana dangane da DANGANTAKAR ZUKATANMU da har ya sanyata cikin wannan halin. Jikinta na rawa haka ma bakinta tace"lafiya rumana?,me ya sameki?" "Yanzu don Allah yaya rayyan ya kyauta min kenan?,ya yiwa zuciyata adalci?" Ta fada cikin muryar kuka,ji tayi qafafunta na barazanar kayar da ita,don haka ta sake dafa rumanan da dukka hannayenta biyu "Me yace miki rumana?,me yayi miki?" "Sisi wai course zai koma uk yayi har na wata shida,kusan gab da lokacin bikinmu kenan fa" wani abu taji ya tsirga mata har ta kasa ci gaba da tsaiwar ta nemi daya kujerar ta zauna,wadda sam saboda tsabar rudewa bata fuskanci ma gaf take da rayyan ba. Nannauyar ajiyar zuciya ta saki sannan tace "Kinsan Allah ba qaramin razanani kikayi ba?" Idanun rumanan a gwale tace "Sabida me?" Da sauri tayi qoqarin canza akalar zancan "Nayi zaton wani mummunan abu yayi miki ne sisi na,kinsan ban da kamarki" "Haba sisi?,amma dai ai kinsan ba'a yiwa zuciyata adalci ba,har yau fa bai wuce shekara guda da baro uk din ba,sai da ya dawo muka sake sabawa sannan yace zai sake komawa?,gaskiya yaya rayyan nidai ban yarda ba" ta fada tana dubansa,dukkan alamu sun nuna da gaske take "Already ba mun gama zancan dake ba rumana,ci gaba ne ya sameni fa,idan na kammala course din na gaya miki tamkar wata dama ce da na samu da zan gina nawa company din na kaina ko?". Bubbuga qafa ta yi har sau kusan shida kana ta wuce cikin gida hawaye na bin kuncinta,wani abu take ji mara dadi sosai tattare da ita,ji take idan rayyan ya tafi tamkar ta rasashi kenan har abada haka zuciyarta ke gaya mata,ta rasa dalili ta kasa jurewa halin da take ciki. Binta dukkansu sukayi da kallo har ta shige din sannan suka dauke kansu lokaci guda suka hada ido,kallo daya tak amma kowa sai da yaji cikin jikinsa,shi ya fara janye idanunsa ya tashi yabi rumanan,itama bayansu tabi amma suna zuwa falo suka raba jaha,shi ya shige dakinsu gun rumanan yayin da ita kuma tayi dakin ummu. Ummun na ninke hijabin sallarta tayi sallama,fuskarta fal fara'a har cikin zuciyarta tace "Oyoyo raihanata,oyoyo mutan birnin shehu" tana dariya ta qarasa inda ummun take ta rusuna tana gaidata,ta amsa tana mata barka da hanya,zamanta tayi a dakin ummun suka dinga hirarsu,kasancewar abba ya fita yayi baqir bai dawo haka suka kashe a qalla awa kusan daya da rabi tana bata labarin maiduguri da yadda bikin ya kasance,basu rabu ba har sai da ummun tace taje ta huta hakanan,dakin nasu ne bata son shiga din tana zaton ko rayyan na ciki har yanzu. *************** Cikin kwanakin daru sosai rumanan keyi masa,ya rasa yadda zayayi da ita,ranar juma'a da yamma raihana na zaune na cin abinci bayan ta dawo daga makaranta ta duba time table nasu,lokaci lokaci tana kallin rumana dake kwance ruf da ciki tana danne dannan waya da alamu sana'ar tata take charting,saidai sam fuskarta babu wannan walwalar,haka ta koma kwana biyun har ummu ta lura da hakan. Juyi tayi ta dawo da fuskarta bangaren da raihanan ke zaune saman carfet dinsu "Yaya rayyan yace mu shirya,zamu rakashi wani guri" shuru ta danyi tamkar tace ba zata je ba,sai kuma taga idan tayi hakan zai iya haifar musu da matsala ita da rumanan,bai kamata ta dinga nuna abubuwa da zasu sanya kokwanto ko ganin rashin kyautatawarta kan rayyan a idanuwan rumana ba,tunda ko babu komai abinda zuciyarta keso ne "Ok qarfe nawa kenan" "Qarfe biyar na yamma yace" kanta ta daga ta dubi a gogo qarfe uku da ashirin lokacin,akwai awa kusan daya da rabi a gabansu. "Ruma" raihana tayi kiranta,sai ta daga kanta ta dubeta tace na'am "Me ya sanya ba zakiyi haquri ki sawa zuciyarki nutsuwa ba,kin saka damuwa mai yawa a kanki kan tafiyar yaya rayyan,naga a baya shekara tara yaje yayi balle yanzu da bazaya wuce wata shida ko bakwai ba" tashi tayi ta zauna sosai sannan ta girgiza kanta "Raihana,akwai banbanci tsakanin shekarun baya da na yanzu,kin riga kin sani zuwa yanzu ya rayyan ya gama zama cikakken cikakken namiji da duk wata mace zata yiwa kanta sha'awar mallakarsa" "To me yayi zafi haka rumana shi ba wuta ba,meye abun tashin hankali?" "Bana son in rasa yaya rayyan ne,zuciyata na raya min kamar hakan na iya faruwa,kinsan yawan 'yammatan dake son rayyan acan garin?,ni nasan da zaman kowaccensu,bazan iya jurewa ba idan na rasashi ne" murmushi raihana tayi tana jin tausayin kanta na taso mata,babu shakka rumana kukan dadi take,ina ma ina ma,cikin salo na lallashi tace da ita "Bai kamata a ganina ki tada hankalinki ba,rumana rayyan naki ne,ke kin riga da kin sani tun baya ma ballantana a ayanzun,babu wani abu da ya isa ya shiga tsakanin alaqarku su abba kin sani sarai ba zasu bari ba,ballanta na ni da sai inda qarfina ya qare" murmushi rumana ta saka,har kullum tana jin dadin yadda raihana ke nuna qauna gareta "Ina fatan haka in sha Allah" "Allah zai amsa da yardarsa" Rage gudun da yakeyi yayi sannan ya gangara a hankali ya shiga daya daga cikin layukan anguwar,qofar wani gida da ake kan gininshi yaja ya tsaya sannan ya kashe motar. Kallo daya zaka yiwa gidan kasan ba qaramin tsarashi aka yi ba duk ba a kammala gininsa ba "Bismillah ku zagaya ku gani" yace da su yana tsaye hannyensa soke cikin aljihun trouser dinsa yana duban rumana,gidan nada girma shi ya sanya qarshe kowa ya rasa dan uwansa ya shiga wani saqon daban. Kallon ginin take tana murmushi babu shakka ya tsaru kam,ko ba'a gaya mata ba tasan tsarin rayyan dinne,mutum ne mai tsari doka da qa'ida,a hankali tabi wani dogon guri sai gata ta bulle baya,tsugunne suke duka su biyun yana riqe da singalalin hannunta "Na kawo ki ne nan don ki sake tabbatarwa kanki rayyan bazai yaudareki ba,don ki sake tabbatarwa rayyan baya magana biyu,ki kuma sake nutsuwa da cewa ni din bazan guje miki ba,riqe alqawari sai dan halak rayyan kuwa dan halak ne,wannan shine ginin da nakeyi akwai part dinki a ciki inda zaki zauna,wanda nake saka ran kafin dawowata akammala ginashi"ya qarasa maganar murmushi mai sanyi da kyau kwance bisa kyakkyawar fuskarshi,ita din ma martanin murmushin ta maida masa,a hankali ta samu ta janye jikinta,sannu sannu ta jingina da ginin da take tsaye kusa da shi,wasu hawaye da batasan na meye ba suka bi kuncinta,iyakar saninta burinta shine rayyan ya janye mata,ya janye matan ya kuma ja baya da ita,maimakon ta samu farinciki da nutsuwa kamar yadda take hasashe sai kuma taga akasin hakan,koda yaushe kewarsa take,koda yaushe sake jin wani bala'i take cikin zuciyarta,wani rashin sukuni ne ke sunno kai cikin rayuwarta,tana tsoron kada dai a ce zuciyarta ce ta soma qoqarim bijire mata,zuciyarta ce ta gaza da ci gaba da boye dubun nan abubuwan dake bunne cikinta. Cikin saurin ta tsaya sosai da qafafunta tare da goge hawayen idanunta bayan ta cire glasa dinta ta gogeshi shima,da sauri ta dora hannunta saitin zuciyarta tamkar mai magana da wani tace "Baki da ikon bujire min alhalin ina da iko a kanki,na dade da haramta miki abinda kake hanqoron a kansa,na kuma yiwa kaina alqawari" Ta sauke hannun nata a sanyaye ta maida glass dinta. Tana shirin juyawa ta fice a gun,idanu suka hada da shi yana tsaye ya jingina kafadarsa jikin bango hannunsa da qafafunsa harde cikin 'yan uwansu,duk sai taji wani iri,babu ko shakka yaji me take fadi "Muna iya tafiya?" Yace da ita,bata amsa masaba face gaba da tayi. *************** Shigowarsu kenan daga makaranta shi da abban,rayyan din na qoqarin wucewa sashensa abban ya dakatar da shi "A,rayyan idan ka gama abinda kake ka sameni cikin gida,akwai maganar da nakeso mu tattauna" "To abba" ya fada ya wuce ciki. Hadisan hannunsa ya ajjiye sannan ya shiga toilet ya watsa ruwa,bayan ya fito ya sauya kaya yayi shafa'i da wutiri,har ya daga waya zai kira rumana ta kawo masa abinci sai kuma ya fasa,wunin yau duka hakanan yaji baya jin yunwa. Su uku ne cikin falon abban,shi abba sai kuma ummu,yana zaune ne daga gefansa yana jira abban ya kammala wayar da yake yi,minti biyar ya dada sannan sukayi sallama da wanda yake wayar ya ajjiye "Rayyan" abban nashi ya kirashi "Na'am abba" alhj yusuf ya gyara zamansa yana dubanshi "Kwanaki nawa ya rage maka ka tafi uk" "Eh abba,saura sati biyu" "To masha Allah,mun gama magana da alhj dalhatu duk da ahi yace aji ta bakinka tukun,amma mun gama magana da mahaifiyarka gata nan,tsawon watannin da zaka diba a can din ya haura kwanakin aurenka,hakan ya sanya ruma ta shiga damuwa ko ba haka bane?" Kai ya gyada "Haka ne abba" "To abinda muka ga yafi dacewa kawai shine a daura aurenku hankalin kowa ya kwanta,idan yaso duk wata bidi'a da zata biyo baya kuma idan Allah ya kaimu ka dawo daga tafiyar koma mene ne ya rage naku sai kuyi,zuwa lokacin gininka ya kammala,sannan raihana ma in sha Allah kafin lokacin muna saka ran ta samu miji,sai a hada duka ayi a gama,don bai kamata mu takura ta ta fidda miji ba,tausayin maraicinta nake" Maganganun biyu masu nauyi duka suka yi masa dirar mikiya lokaci guda "Abba.....na gode Allah ya saka da alkhairi,duk abinda kuka yanke yayi daidai abba,a tayamu da addu'a....amma abba...." Sai kuma yayi dan shiru "Amma me?" "Raihana ai ta samu miji abba" *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 [13/04, 18:52] Hassan Atk: 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"kada mace ta aurar da mace,kuma kada mace ta aurar da kanta* _______________________ *Babi na ashirin da biyu* Murmushi abba yayi sannan yace"eh na sani ai rayyan,ko ba amir ba?,yazo ya sameni har mun gaisa ma,abinda yasa bakaji nayi saurin zartarwa ba na basu lokaci ne su fahimci juna sosai,yadda raihanan da kanta zata zo ta gabatar min da maganar,bana son tursasata,nafiso tayi zabi a hankali don ta dace da na gari,tunda naga duka duka watansu nawa da haduwa baici sun gama sabawa da juna ba,musamman ita raihanan da bata saba hulda da kowa ba". Qasa yayi da kansa yana jin wani abu mara dadi,baiso abba yayi masa yankan hanzari ba,bazai iya maida maganar abban baya ba da yace masa "abba nine mijin da raihana tayi" "Gaskiya ne alhaji,yaron kuma na fuskanci yana da hankali,don har ni yake kira wani lokaci muna gaisawa" cewar ummu,wani kishi ya kamashi jin suna yabon amir,hakan ya sanyashi miqewa yana fadin "Abba zan wuce" "To rayyan,Allah yayi muku albarka,Allah ya albarkaci aurenku ya sanya nutsuwa da kwanciyar hankali a cikinsa,inaga sai ka fara shirin daurin auren ko,don nan da sati biyu za'a dara,satin gaba kuma sai ka wuce course dinka" "To abba,na barku lafiya" ya fada yana juyawa ummu ta bishi itama da addu'a farinciki fal zuciyar su na ganin aurem dansu da 'yarsu rumana. Zazzafan huci ya fesar sannan ya fada saman kujerar,hannayensa biyu ya sanya yana yamutsa gashin kansa,gaba daya kansa ya dauki caji,babu tantama yayi farinciki da aurensa da rumana,saidai abinda ya kassara rabim farincikin nasa rashin samun cikakkiyar matsaya dangane da mallakar raihana,babban abinda ya masa burki kan sanar da DANGANTAKAR ZUCIN da sukeyi shida raihana rashin samun hadin kanta,ya bata dama ne ta gamsu da kanta ta amince zata aureshi,ya tabbatar da ya samu hakan daga gareta da tuni an dade da wuce gun,yanzun haka zaya zuba ido ya rasata kenan?,kansa ya shiga girgizawa shi kadai yana fadin"bazai yiwu ba"bayajin zai iya barwa raihana wani,ba zai taba yarda al'ada ta cuceshi ba,bazai yarda al'ada ta haramta masa abinda addininsa ya halatta masa ba wanda ko a gun Allah baiyi laifi ba idan ya auri raihana,irin macen da annabi ya kwadaitar da mu mu aureta,kan me zai yarda wata banzar al'ada ta haramta masa halas,abu guda ne zai yarda ya haramta masa raihana yasa hannu bibbiyu ya karba ba tare da haufi ba shine ADDINI. Baisan tsawon lokacin da ya kwashe haka ba sai daga ido yayi yaga qarfe sha biyu saura na dare,ko abincin bai samu yaci ba,duk tunaninsa ya tafi kan yadda zaya bullowa lamarin,daga qarshe bedroom dinsa ya shige ya sakarwa kansa ruwa a shower kusan mintina ashirin sannan ya samu sauqin abinda yake ji,sallah raka'a biyu yayi ya rufe da wutiri,addu'a yayi sosai kan neman zabin Allah ya hada da istihara,kafin ya bar saman abun sallar sai yaji duk wani fargaba da damuwa tasa ta yaye,nutsuwa da kwanciyar hankali na ratsashi tamkar ya samu rumana da raihana baki daya. Sai da ya nutsu saman gadonsa bayan ya rage hasken dakin sannan ya fidda wayarsa ya shiga gun rubuta saqo ya lalubi lambar rumana ya fara rubuta mata gajeran saqo kamar haka _haqiqa babu wani bawa da ya isa ya hana abinda Allah ya qaddara afkuwarsa faruwa,ina farincikin sanar miki da yardar Allah ni rayyan yusuf zan zama miji gareki rumana sati biyu masu zuwa,goodnight and sweet dreams my angel_ Daidai lokacin wayar na hannun raihana tana duba wasu litattafai cikin dacument din rumanan,ko kadan ji tayi bata jin bacci hakan ya sanyata bayan ta gama abinda zatayi ta karbi wayar,da shigowar saqon tayi zaton kamfanin waya ne,murmushi tayi tana cewa mutanen sisi na"don tasan halin rumanan ta tsani saqon da kamfanin waya ke nacin aikowa,musamman idan ta ciro wayar da karsashinta tana zaton ko rayyan ne ya turo saqon taga sune,yanzun nan zakaji qorafinta. Idanunta ta lumshe bayan ta gama karanta saqon,wani sashe na zuciyarta na taya rumana samun cikar burinta,tana tayata murnar mallakar rayyam,yayin da wani bangaren na zuciyarta ya samu rauni,hawayen da batasan manufar zubarsu ba suka fara kwaranya mata,sai ta ajjiye wayar a gafanta ta kwanta gefan damanta,kuka ya subuce mata har sautinsa na shirin fitowa,hakan ne ya sanya ta toshe bakinta da blanket dinta,kuka ta dinga yi sosai irin kukan dake sosa zukata,irin kukan dake bayyana rashi da kewa,kukan bankwana da farinciki,kuka ne dake karya zuciyar duk wanda yasan halin da zukata suka tsinci kansu,tun tana yin kukan da dan sauti har ya zaman sautin bai fita,a hankali idanunta suka kumbura lebunanta da fuskarta,fuskar ta dinga mata wani radadi da fitar huci,kanta ya dinga sarawa tana daga kwancan amma jiri ke dibarta. Qarfe biyu harda rabi amma idanunta tangaran tamkar an yaye mata wami hijabi,biyu da arba'in ta miqe daga kan gadon nasu ta shige toilet ta daura alwala ta dawo kan gadonta wani sanyi ka ratsata,guri guda ta cure,da hannunta ta dinga tasbihi ga ubangiji,don ita kanta ta gaji da radadin da zuciyarta ke mata sauqi kuma take nema,sai kusan uku da arba'in bacci ya saceta. Bata farka ba sai da taji rumana na bubbuga filonta tana fadin "Sisi yau kece da makara kuma,ki tashi kiyi salla har wasu masallatan sun fara idarwa" bata yarda ta tashin ba saboda idanunta sai data tabbatar rumana ta tayar da sallah sannan ta miqe,jikinta a mace murus tamkar wadda aka lakadawa duka,hakanan zuciyata wani iri takejinta kamar wadda ake shirin jefawa kurkuku. Ko kafin ta idar da tata sallar rumana ta koma bacci,don haka tayi hanzarin shigewa toilet tayi wanka. Qarfe bakwai da rabi ta gama shirinta tsaf cikin doguwar riga ta lace wadda tayi mata kyau,saidai yadda fuskarta ta jirkita ya rage fitar kyawun nata baki daya,ta sake kallin fuskarta a madubi har yanzu a tashe take,shi yasa ta shirya ficewa daga gidan da wurwuri,don batason wani yaga fuskarta har ya nemi ba'asin abinda ya haddasa mata faruwar hakan,duk da bata da lacture sai qarfe goma zuwa sha biyu na rana. Paper ta fidda 'yar qarama tayi gajeran rubutu akanta _da kin tashi wayarki nakeso ki fara dauka ki duba inbox dinki,ni na wuce schl sisi_ Ta dauki wayar rumanan da takardar ta sanya mata gefan kanta ta yadda tana tashi su zata fara gani sannan ta rataya jakarta ta fito. Babu motsin kowa kamar yadda ta zata,don haka hankali kwance ta fito daga gidan,layin nasu tsit yake kasancewar bai da yawan mutane koda da rana ne ma balle da sassafe irin haka. Ta bayan layin nasu tabi,tana tafe a hankali iskar safiya na kadata kamar yadda tunaninta ke ci gaba da kaduwa,zuciyarta nason ta fara zafi kamar yadda take mata amma ta daddage ta hanata,daga nesa kadan da ita ta hango shi yana tafe yana sassarfa sanye da kayan motsa jiki green and white,bata tabbatar da shi bane har sai da yazo gaf da ita,dauke idonta tayi a hankali tayi gaba,shi din ma baice komai ba yayi gaban,saidai kuzarin jikinsa da ya sake raguwa,ya hangi abubuwa masu tarin yawa cikin idonta da ma fuskarta baki daya,saidai yaya zaya yi?,duk yadda yaso ta bashi daka ta qiya,a yanzun da ya ganta ya tabbatar akwai damuwa mai yawa cikin zuciyarta kamar yadda take cikin zuciyarsa,duka su biyun ta gwammaci su zauna cikin damuwa da takurar zuciyoyinsu,ta gwammace ran mutum daya ya faranta na mutum biyu kuma ya shiga qunci akan wani dalili mara tushe bare makama,sam baya jin hakan adalci ne take shirin yi musu. Ba wasu mutane cikin makarantar sai jefi jefi wanda basufi ka qirgesu da yatsun hannunka ba,kai tsaye ta wuce hall din da zasu dauki lacture din yau,kusan itace mutum ta farko data shiga gurin,babu kowa sai jerun kujeru reras da suke cike da hall din,can baya ta tafi ta zabi daya daga cikin kujerun ta zauna akai sannan ta dora kanta a gurbin da ake dora littafi,kamar ta fiddo zuciyarta waje ta huta da abinda takeji,kukan ma yaqi zuwa ballantana ta samu salama kan abinda takeji. Qarfe tara da rabi wayarta ta shiga ruri,share kiran tayi saboda tana zaton ko amir ne,kiran da akaci gaba da yi ya sanyata sanya hannu ta ciro wayar ba tare da ta duba mai kiran ba ta kara wayar a kunnenta "Wayyo sisi,kin tafi kin barni da kayan murnata ni kadai dawa zanyi sharing farincikin da nakeji cikin zuciyata"muryar rumana ta doki dodon kunnenta,lumshe idonta tayi tana ci gaba da jiyo karadin rumanan " sisi bansan da me zan saka miki ba a rayuwa,duk wani abu na farinciki ke kike fara sanar da ni a rayuwa" "Farincikinki shine nawa sisi" qwalla suka tararwa rumanan "Allah ya bani abinda zan saka miki da shi sisi na" "Kada ki damu,duk abinda raiha tayiwa rumana tamkar ta yiwa ita kanta raiha dinne"cikin karyayyar murya rumana tace " duk da haka sisi farinciki na bai cika ba,Allah ya sani nayi farinci qwarai da gaske da Allah ya bani damar mallakar miji daya da daya irin yaya rayyan,amma sisi banason ace anyi bikina ba tare da ke ba,bana so na tafi na barki ke kadai"dariyar qarfin hali raihana tayi "Kada ki damu rumana,komai lokaci gareshi,hakanan kowa da irin tasa QADDARAR,idan Allah ya kawo nawa lokacin babu tsumi babu dabara ai" "Hakane sisi na,amma zan tanada miki wani abun mamaki kafin ki dawo tukuicin albishir din da na gani" Murmushi ta danyi "Ina maraba da hakan" "Ok saikin dawo" Tunda ta ajjiye wayar ta sake maida kanta yadda yake a dazun,tun tanajin shigowar mutane da dai dai da dai dai har hall din ya soma cika daga bisani malamin ya iso. Zata iya cewa bata fuskanci komai ba cikin darasin yau,ta dai tsinci kawai abinda ta tsinta shima din tana daga kwance,yadda ta zama farkon zuwa haka ta zama qarshen tashi wajen qarfe biyu saura na rana,ta miqe da qyar tana jin yadda qirjinta yayi nauyi,da qyar takai kanta bakin titi ta samu a daidaita sahu ta hau,bata sha'awar zuwa gida don tasan rumana na can na jiranta,kuma tasan bazataji dadi ba idan ta ganta cikin yanayin da take ciki,kewar danginta ya kamata,duk yadda takai ga 'yan uwa a garin kano bata da ko daya,bata tabajin hakan cikin jikinta ba sai yau,saboda haka tace kawai mai motar ya kaita qoqi gidan hajiya babba kakar rumana. Cikin 'yan mintuna suka iso,gidan shiru babu kowa kasancewar babu yara a gidan kamar yadda muka sani,saidai fes yake kamar ko da yaushe,hajiya qarama na bakin fanfo tana daura alwala suka gaisa,ta fara zolyarta ina amare?,kuma yau naga zahra banga wata ba ina kika baro 'yan biyun naki?"murmushi tayi tace "Daga makaranta na biyo ai hajiya ba daka gida nake ba" "Ayyah,koda naji",jakarta ta cire itama ta daura alwalar kawai sannan ta wuce dakin hajiya babba. Kan abun salla ta sameta saidai ta idar lazumi take,fuskarta fal fara'a tace " a'ah,raihanatu kece kike tafe?"murmushi tayi "Wallahi hajiya daga makaranta nake ina yini" "A'ah,fara yin sallarki naga kamar alwala kika daura" ta fada tana tura mata wata daddumar dake kusa da ita ta shimfida. Kafin ta idar din har baaba ramma ta kawo mata abinci cikin kula guda biyu,bayan ta idar suka gaisa "Ina kika baro ruma.....oh wai ruma da aure akwai kallo" inji hajiya babban tana dariya tare da tabe baki,dariya hajiyan ta bawa raihana har ta dan dara "Tana gida hajiya" "To Allah ya sanya alkhairi,jiya baban nata yake sanarmin ai da ya shigo gaidamu da daddare,Allah ya nuna mana naku,Allah ya kawo muku na gari kuma" inji hajiya babban,har zuciyarta tan son raihana,jininsu ya hadu sosai,murmushin jin kunya kawai tayi ba tare da ta amsa ba "Nikam so nayi ma wallahi ace rayyanun ya hadaku baki daya keda 'yar uwarki,kinga shikenan an huta,tuwona maina,kowa yasan kowa babu wani sauran fargaba" wani mummunan faduwa gabanta yayi,ta qwalalo ido kamar wadda aka hurawa yaji ba tare data san tayi hakan ba,sai qwalla ta cika mata ido saboda sosa mata ciwonta da hajiyan tayi ba tare da ta sani ba "Haba hajiya,Allah ya sawwaqe na auri mijin 'yar uwata" maganar ta fito ba tare data shirya ba. sakin baki hajiyan tayi tana dubanta,abinka da gwanar salati sai kuwa ta debo shi"la'ilaha illallahu muhammadarrasulullahi,oh ni 'yar nan,yo meye?,haramun ne ko kuwa",sai kuwa hawayen ya gangaro kan kuncinta "Don Allah hajiya kiyi shiru maganar ma babu dadin ji,indai zan auri mijin rumana zan iya auren mijin zainab kenan" kama haba hajiyan tayi,ganin lamarin ya girmeta "Tabdijan,ashe kema wawiya ce ban sani ba?nace haramun ne?" Kai ta girgiza cikin zaquwa a bar maganar "A'ah hajiya,amma ai ana barin halas don kunya ko?" Haushi ya kama hajiyan,a hasala tace "A wanne hadisin ko kuma a wanne qur'anin?" Shiru tayi ta rasa wacce amsa zata bata ma,sai yau ta taba yarda da zancan rumana da tace mata hajiyan muguwar rigimammiya ce "Mu to ba haka muke ba,ke da rumana ganinku muke kamar mahaifa daya kuka kwanta,kuma wallahi kinji na rantse miki da rayyan yace yana so da sai an hada masa ku duka,akwai abinda yafi haka kwanciyar hankali ne,yaranmu munsan hannun wanda suke,wanda koda mun mutu munsan ba zasu wulaqanta ba". Da sauri ta kuma kallin hajiyan zuciyarta na kadawa,godiya ta dinga yiwa Allah da bai matsi bakin rayyan ya gayawa kowa ba,da sauri ta saki murmushin yaqe don son kawar da maganar tace " hajiya kwantar da hankalinki,ina ma da miji ni,lokaci kawai nake jira don mu sake fuskantar juna,bari na kira miki shi ma ku gaisa"hannunta na rawa ta fito da wayarya ta fara neman lambar amir "Oho dai,bazamu shaideshi ba kamar namun ba ko?" Daidai lokacin da kiran ya shiga,cikin zumudin ganin rana ta farko raihana ta kirashi da kanta ya daga "Kashe na kiraki" amir din ya fada,ba'a wuce sakan biyar ba ya kira din kuwa,bayan sun gaisa ta miqawa hajiya wayar suka fara gaisawa. Wasa wasa saiga hajiya hira ta miqa ita da amir harda kwasar dariyarta,raihana na kallon ikon Allah,sai kawai ta janyo kular abincin ta bude ta zuba ta soma ci kadan kadan tana kallon yadda suke hira kamar sun dade da sanin juna,sai da taci rabin abincin sannan sukayi sallama hajiyan ta miqa mata wayarta. "A haka dai yaron akwai hankali da shiga rai" hajiyan ta fada,murmushi raihana tayi ko banza ta toshe wata kafar da take qoqarin balle mata ta zame mata babbar barazana,don ta riga ta san matuqar hajiya babba ta fara tada wannan maganar to babu wanda zai musa mata tsakanin abba da daddy dalhatu,hannu hajiyan tasa suka ci gaba da cin abincin tare,tuwon dawa ne miyar kuka da yasha man shanu "Da Allah zai kawo rayyanu nasan ba qaramin jin dadim tuwon nan zaiyi ba" inji hajiya babba,itama raihana abinda take qissimawa cikin ranta kenan,saboda ta sanshi gwanin son abincin gargajiya ne kamar ita,a nan suke fada da rumana. Ba qaramin jin dadin zuwanta gidan tayi na,sunyi hira sosai da hajiyan,ta dinga bata labarukan yadda rayuwa take a ashekarun baya da yanayin yadda ake aure a lokacin,har ta dinga jin sha'awar irin auren gargajiya babu dorawa kai nauyi ko a'ala masu yawa,sannan ta dinga jin cewa zata iya auren amir koda bata sonshi,saboda yadda hajiyam ke bata labari ita kanta batasan waye mijinta ba wato marigayi tahir babansu daddy dalhatu sai da aka kaita dakinta,kuma gashi mutuwa ce ta rabasu wato auren mutu ka raba kenan,sai wajen qarfe uku ta haye kujerar hajiyan,ba dadeqa bacci ya dauketa anan saboda bashin baccin da ta dauka daren jiya. Cikin baccinta ta dinga ji kamar muryarsa,a hankali ta dinga bude idonta,shi dinne yana zaune gaban hajiya babba suna ta hira abinsu,yana sanye da shadda baqa dinkin tazarce da wando kansa babu hula,fadin kyawun da tayi masa ma bata bakine,ta haska fatarsa sosai,ta dauke idonta tana qoqarin tashi zaune,shima yana ankare da ita tunda ya shigo falon yayi arba da ita,rigar jikinta ta fidda shape dinta sosai,hakan dankwalin kanta yayi nashi gu sabida bacci,wani kyau yaga ta qara yi masa har ya tsaya ya morewa kallonta na sa'o'i kafin fitowar hajiyan "Yauwa dama yanzu nake shirin tashinki kiyi salla hudu garda rabi" inji hajiya babban "Eh na tashi" ta fada tana neman dankwalinta jikin hanzari ganin yadda yake qare mata kallo da ya qarasa kashe mata jiki da daure jijiyoyin jikinta. Sai data nemo shi ta daura sannan ta gaidashi,ya wani amsa ba tare da ya maida hankalinsa gun amsawar ba,ficewa tayi ta daura alwala ta dawo ta dauki jakarta ta koma dakin hajiya babba,a can ta tadda kausar mutuniyar rumana,suka gaisa cikin sabo da juna sannan tace "Dazun mutuniyar ke mini albishir daurin aurenta next week da ya rayyan"murmushi raihana tayi kamar yadda al'adarta " eh wlh" "Wuuu,Allah ya kaimu ya dawo lafiya,dole mu bargaje biki na kece raini wlh" ta fada tana jijjiga hannu irin na wanda zance ya yiwa dadi "Hmmm,ai aikinku kenan,dama idan bakuyi ba ai ba rumana da kausar bane wasu ne" murmushin raihana ta kuma kawai ta tada salla. Powder ta sake shafawa bayan ta idar suna hira da kausar lokaci lokaci har biyar tayi,ta yafa mayafinta ta dauki jakarta bayan ta maida glass dinta ta yiwa hajiya qarama sallama. Daga bakin qofa ta toge tana yiwa hajiya babba sallama zata tafi "A'ah,shigo mana ina zuwa" inji hajiya babban ta fada tana miqewa,bakin hannun kujerar qofar dakin ta zauna kanta na kallon qasa,ya daga idonsa a hankali yana kallonta tare da kallon yanayin shigarta,komai tayi kyau yake mata,hakanan komai tayi yana qara nuna sanyin ta da sanyin halinta,babu shakka bai ganin aibunsa ko daya kan soyayyarta da ya shiga,bama shiba duk wani namiji mai lafiya da hankali tabbas dole raihana ta dauki hankalinsa,bawai don kyau wayewa ko wani qyale qyale ba,a'a sam,nagartarta kadai ta isheka. "Ungo wannan raihanatu" inji hajiya tana miqa mata leda,tasan halin hajiyan ba'a maida mata kyauta don haka ta karba hannu biyu tana mata godiya sannan ta miqe a hankali ta fice. Har ta fara gajiya da tsaiwar saboda qarancin wucewar motoci a titin,daidai lokacin da wata farar matrix tayi parking a gabanta motar rayyan ta fito daga layin,baya ta danja kadan ganin ana sauke glass din motar,magidanci ne wanda a qalla zaya yi shekaru hamsin,sanye da shadda 'yar ciki da babbar riga "Sannu 'yammata" ya fada yana washe baki,ta kalleshi sannan ta dauke kanta gefe guda a hankali ba tare da ta furta kamai ba,wani takaici ya kamata. Har ya wuce yanajin zai iya daurewa zuciyarsa sai kuma ya gaza hakan,wani zugi ta dinga yi masa,yayi ribas ya dawo da baya da gudu wanda saura qiris ya bugawa daya motar,a gaggauce ya fito hannunsa riqe da muqullin motar yana karkadashi cike da jin masifa,ya zagaya inda raihana ke tsaye,sai da ya tsaya ya qarewa mutumin kallo sannan ya dubeta "Wuce muje" ya fada yana duban qwayar idonta,ba tare da ya tsaya saurerenta ba qarasa cikin qasaita ya isa bakin window din motar mutumin,hannayensa duka biyun ya sanya ya dafe window sannan ya duqa saitin fuskarsa din yana dubansa "Ya kamara kabar gurin nan haka,matar aure kake magana da ita", cikin kidimewa da ganin yadda rayyan din ya dinke girar sama da qasa kamar wani mayunwacin zaki mutumin yace " af,ai ban sani ba,yi haquri don Allah"ya fada yana tada motar yana tsaye rayyan na kallonsa har ya bace a titin sannan ya juyo inda raihana ke tsaye. Hannunsa kawai taji cikin nata ya riqe gam yayi gaba tilas ta biyo bayansa tamkar wata doluwa,ya bude gaban motar ya sanyata sannan ya koma mazauninsa ya shiga ya tada motar,tuqi yake a hankali kamar motar bata da lafiya ko shi matuqin,a hankali ya samu gefan titi bayan ya hau titin da bai da cikowar mutane ya faka motar,sai ta daga kai ta kalleshi ga zatonta ko motar ce ta samu matsala,idanunta ta dauke ganin yadda ya juyo baki daya inda take zaune bayan ya cire belt din da ya daura. Kallonta kawai yake ba tare da ya furta komai ba,kusan minti biyar yana a haka,a hankali ta tsinci kyakkyawan hannunsa mai dauke da zara zaran yatsu saman nata hannun,sai ta dubeshi sannan ta janye hannun nata tana boyeshi cikin mayafinta sakamakon wani shock data ji "Raihana...." Ya kirata tamkar mai yin rada,wani yarrrr taji cikin jikinta mai hade da wani sanyi da taji ya tsirga tsakiyar zuciyarta "Kinga asarar da kike son janyo mana ko?,raihana kinqi bani hadin kai da tuni na tabbatar cewa ke da rumana ne ke shirin zama iyali na,me yasa raihana bayan nasan kina sona?,me yasa?" "SADAUKARWA yaya rayyan,na gaya maka wannan batun yanzu ba,ka taba ganin inda wuta da ruwa suka hadu guri daya?,bazai yiwu ba don haka don Allah don Allah ka barni yaya rayyan ka barni,rumana ta isheka" Tayi masa maganar tana dubansa. Kansa ya dinga kadawa yana murmushi,bai taba ganin inda mutum ke qin kansa ba sai a gun raihana,hakan na sake dilmiyashi cikin tafkin qaunarta ne kawai,ya tabbatar da cewa ba kowacce mace ce zata samu irin damar data samu ba ta wofantar kadai saboda farincikin watanta,hakan na sake tabbatar masa da nagartarta tare da kwadayin ta zama mallakinsa. Zare daya daga cikin zoben dake hannunshi yayi wanda ke dauke da tambarin double RR sarqafe da juna,bata ankara ba ya kama hannunta yana kallan dogayen yatsuntsa sannan ya zabi daya daga ciki ya zura mata zoben,bai saki hannun nata ba yace "Rayyan zai qyaleki kamar yadda kika buqata,amma kada ki zargeshi da rashin neman yardarki duk lokacin da kika tsinci kanki a dakinsa,na riga da na nema,nabar takura raihana amma maganar ban barta ba,bazan kuma barta ba har muddin raina har sai ranar da numfashina ya bar jikin,ko kuma burina ya cika" yana gama fadin hakan ya sakar mata hannu ya gyara zamansa sannan ya tada motar. A hankali ta maida idonta kan zoban,irin zoben rumana ne sak,banbancin kawai wannan na azurfa ne sabanin wancan da yake na qarfe,zuciyarta tayi rawa,ta yaya zata zauna da zoben a hannunta a gaban idanun rumanan?,ta cire tayi jifa da shi shine muradinta amma sai taji ta kasa hakan,sai taji kamar ana sake manna mata son zama da shi cikin jikinta,a hankali ta sauke hannun nata saman cinyarta tana kallonshi maimakon dazun data daga shi da niyyar fidda zoben. Ko daya rumana bata bawa kanta wani sukuni ba,shirye shiryen tarbar ranar daurin aurenta kawai take tare da taimakon sisinta raihana,wadda tayi dukkan qoqarinta na danne komai dake cikin ranta tare da hana masa tasiri don farincikin 'yar uwarta qawarta aminiyarta kuma abokiyarta,duk da irin azabar da zuciyarta ke fuskanta,ta kan raya a ranta na wani dan lokaci ne,da zarar anyi komai an gama tanajin zuciyarta dole ta dauki haquri. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *manzan Allah S.A.W yace"sadaka tana kankare zunubbai,kamar yadda ruwa yake kashe wuta,sallah kuma haske ce"* ______________________ *Babi na ashirin da uku* _fans gani na dawo,ina godiya ga dukkan jama'ar da suka kirani ko suka turon saqon cigiya ko sukayi cigiyata,na gode qwarai👏🏼_ _ga jama'ar kuma dakemin saqo ta account na watsapp dina suna qorafin naqi kulasu ko nayi blocking nasu, afwan,na sauya number ne saboda wadansu dalilai,ina kuma godiya,jazakumullah_ Duk da daurin aure kawai za'ayi hakan bai hana suyi shiryen shiryen da ba'a rasa ba,kamar sabbin dinkuna da gyaran jiki,komai tare sukeyi kuma iri daya,ko wani abun raihanan ta noqe rumanan bata yarda sai an mata hatta da dan gyaran jikin da akayi mata. Saura kwana uku biyu daurin auren mutanen nijer suka iso,sun kusa mutum sha biyar maza da mata ciki harda kakar rayyan wato rahinatu wanda shine zuwanta na farko gidan dan nata,nan take yanayin gidan ya fara sauyawa aka shiga hidima da baqi,duk da raihana da rumanan ba kasafai suke samun zama a gidan ba,wani lokaci suna makaranta wani lokaci suna can wajen sabgoginsu. ************** Ana ya gobe daurin auren suna dawowa daga qoqi ita da rumanan da kausar,sunje an yi musu lalle da kitso,yamma ne liqis don bazai wuce awa daya ayi kiran sallar magari ba ba,a bakin get din gidan dan adaidaita sahu ya ajjiyesu suka biyashi ya wuce. Motar rayyan ce fake a qofar gidan daga gefe,daga bayanta kuma motar amir ce sai wata motar daban ta wani abokin rayyan din mujahid. Angon na jingine jikin tashi motar yana amsa waya,sanye yake da qananun kaya,jeans brown da t.shirt fara qal mai gajeran hannu wadda ta fidda murdadden damtsensa da gargasar dake kwance kan qaurin hannunsa,a idonshi suka sauka,idanunsa fes kansu musamman raihanan da ta tafi dashi,saboda yadda gyaran jikin ya amshi chaculet colour din fatarta fiye ma da farar fatar rumana,sun hada ido amma sai ta dauke kai,wani abu ya dinga ji yana tsirga masa,sai yaga ta fita daban cikin su ukun,duk da kallo guda zaka yi mata matuqar kana fa zurfin fahinta da saurin ganiya ka gane jikinta a sanyaye yake,duk da ita din mai sanyi ce amma sanyin nata ya sake qaruwa fiye da yadda take ainihi. Kai tsaye rumana ta kama hannun kausar wadda tafi kusa da ita tana mata radar ga angonta can,kausar ta qyalqyale da dariya "Gwara dai ayi a gama kowa ya huta" dariyar itama rumanan tayi ta waiwaya ta dubi raihana dake tsaye a bayansu "Sisi,gafa mutimin naki can har ya iso" murmushi tayi tare da yin far da fararen qwayar idonta wanda akan idon rayyan tayi,wani siririn murmushi ya saki irin na gefan baki ganin yadda farin yayi mata kyau matuqa,cewa tayi da rumanan "Eh,tun muna qoqi jikina ya bani,kinsan abinka da zuciya guda"kama baki rumana tayi tana dariya " oh sisi,dama na fadi,irinku ne idan kuka fara soyayya baku daukarta da sauqi"duka suka sanya dariya. "Yammata ya kuka tsaya daga nan,ku qaraso mana" sukaji muryar amir yana fadi,idanunsa kan raihanan,murmushi rumana tayi sannan suka fara takowa a hankali zuwa inda suke "Kaidai kawai kace mu sake matsowa ko ka samu damar ganin sahibarka sosai" tamkar ta soki rayyan da mashi a qirjinsa haka yaji,take 'yqr fara'a da farincikin da ya samu sukayi qaura,wani kishi ya kamashi,ji yake tamkar yace da su su wuce cikin gida babu halin haka saboda haka sai ya daure fuska kawai "To laifi nayi,na tabbata kema angonki na da muradin ganinki ko ba haka ba?" Ya qarashe zancan da sigar tambaya sannan ya waiwaya yana duban rayyan,sam tunda yazo ya fuskanci rayyan din ya sauya,amma bai kawo komai ba cikin ransa ganin kusan haka yanayinsa dama yake,sai ya ta'allaqa hakan da cewa qila akwai wani abu daban dake dumunsa. Kafada rayyan din ya daga hadi da yarfar da hannu "a'ah,wannan ai zancanku ne bana shiga ba" ya fada yana sake duban wayarsa dake tsuwwa da alamu wani kiran ne ya sake shigowa wayar tasa,ya daga wayar ya kara a kunnensa kana ya matsa dan nesa da su,saidai duk da haka yana hango duk abinda ke faruwa. Mintina tsakani ya sake dawowa yana dubansu amir da mujahid "Ko na wuce ne ni kadai,su mansur sun qaraso don na fuskanci ku kun samu wani aikin ko?" "A haba,ai ana tare muje kawai mu sama musu masaukin kada su qosa da jira" inji amir da yake miqawa raihana wayarta dake hannunshi tare da fadin "Princess zamu je mu dawo,a tanada min abu mai dadi" so take ta maida masa amsa ta irin salon da yayi mata maganar ko don rayyan da yasa musu ido amma sai bakinta yayi nauyi ta kasa illa cewa "to" da tayi tana qoqarin bin bayansu rumana. Har sun kusa shigewa get din gidan rayyan din yayi kiran rumanan ta koma da baya,kusan minti goma basusan me yake gaya mata ba,hakanan raihanan taji ranta ya dan sosu musamman data jiyo rumanan na qyalqyaltar dariya,sai tayi hanzarin kwabar kanta da zuciyarta,mujahid ne ya dan daga murya yace da rayyan "Kai man,kaifa muke jira ka ishemu da qorafi kuma kai ka tsaya tsinkar fure" "Ku tafi mana,ai ba makaho bane mi bare na nemi dan jagora" rayyan din ya fada yana sallamar rumana ya juya gunsu mujahid din yayin da ita kuma ta koma wajensu raihanan. Ajiyar zuciya ta saki lokacin da suke takawa zuwa cikin gidan,ta lumshe ido kana tace "Na godewa Allah da ya mallakamin burin raina yaya rayyan,askiya babu abinda yafi soyayya dadi" "Idan kayi dace da masoyi ba" inji kausar,idanu rumana ta bude tana duban kausar "Ai duk duniya banajin akwai wanda yayi sa'ar masoyi kamata ko ba haka ba sisi?"ta waiwaya daya barin nata tana jefa tambayar ga raihana,wadda tayi shiru tanajin yadda bugun zuciyarta ke tafiya a hagunce,kokawa take da zuciyarta na kada ta yarda tace zata ji kishin 'yar uwarta,murmushi tayi cike da nuna jarumta da dakiya " qwarai kuwa sisi na,qyale kausar kawai" "Ni din ma tsokanarta nake,kowa ya riga da ya sani ai sa'a kam kin yita,saidai Allah ya sanyamu a danshinku" "Amin wallahi kausar ina muku sha'awar haka" inji rumana. Jefi jefi suka dinga wuce baqi suna gaisaqa da wadanda sukazo ranar,a kitchen suka tadda ummu tana hada kan kwanukan abincin dare da tuni aka kammala jiran lokacin cinsa kawai ake,sai raihana taji tausayinta,tunda satin ya shigo ita kanta bata samu hutu ba,gashi su ba zama suke sosai ba ballantana su kama mata aikin "Sannu ummu,sannu da aiki" raihana ta fada cikin qauna tana shigewa cikin kitchen din tare da karbar babban ludayin hannunta da take kwashe shinkafa cikim cooler taci gaba da zubawa "A'ah raihana,aisai ki bata jikinki,ku da aka yiwa gyaran jiki?'dariya ta danyi "Lah,sai kace nice rumanan,ai ita kadaice ba'aso ta bata jikinta" murmushi ummun tayi tana kallonta cike da qauna "Kema Allah ya bada na gari ya nuna mana lokaci dai" kasa amsawa tayi illa murmushi kawai da tayi,daidai lokacin da rumana da kausar suka qaraso don ta barsu bakin fanfo suna magana da wata maqociyar su wadda zata musu friedrice din walimar da zasuyi gobe bayan gama daurin aure saboda gwanace tayi bala'in iyawa. Sannun suma suka yi mata,raihana ta kammala zubawar ta sauke tukunyar ta tarata bakin fanfo,ummu ta sake matsowa "Kinga barshi hakanan,ai an kammala komai,kuje ciki umminki fanna ta iso dazun da azahar" wani tsalle rumana tayi tayi waje cike da murnar jin ummin tazo,shiru raihana tayi,take taji jikinta yayi sanyi,farincikin zuwan mahaifiyar tata ya lullubeta har ta rasa me zata yi?sai kawau tace "to" ta wanke hannayenta ta fice a kitchen din A bedroom dinta ummu ta sauketa kasancewar babu kowa ciki,hajiyan nijer dakinta daban ita da 'yan tafiyarta tace ba zata zauna dakin surukarta ba,rumana an baje anata kwasar hira da labarin maiduguri,tana ta tambayar mutanen da ta saba da su da wadanda ta sani ummin kuwa ta biye mata sunata hirarsu kausar na tayasu. Gefen ummin nata ta samu ta zauna,fuskarta qunshe da murmushi tace"sannu da zuwa ummi" "Yauwa raiha" ta fada tare sa sake maida kanta gasu rumana,sai ta waiwaya gun qannenta zainab da amira dake ta faman murnar ganin yayar tasu,ta yafitosu suka dawo kusa da ita nan suka fara hira tana tambayarsu wasu al'amura,musamman kan karatunsu,alhmdlh komai yana tafiya fiye da yadda take zato,don mutumin da ummin nata ke aure yanzun mutum ne mai wadata ga matuqar sauqin kai,ya rasa matarsa ne ta fari wadda ta rasu data haifa masa samari har uku. Basu qara minti goma ba rumanan ta miqe tace bari suje su fara shirin yin sallah magariba ta gabato suka fice,zamewa tayi daga tsakiyar su zainab din ta dawo gefan ummin sosai,a hankali ta dora kafadarta saman ta ummin nata Haqiqa uwa daban take,wani karyewa taji zuciyarta tayi sai kawai ta saka kuka,zainan da amira sai suka saki baki suna kallonta "Me haka kuma raihana?,meye akayi miki na kuka da girmanki?" Inji ummin ta tambayeta,kasa amsa mata tayi don kota bude bakin bata da abinda zata gaya mata,ganin bata amsa mata din ba ya sanya ta qyaleta ba tare data sake ce mata komai hakanan bata hanata yin kukan ba,don tana jiyo qamshin damuwa mai yawa cikin kukan nata,amma ko damuwarce bata son tambayarta bare ta bata hanyar kawo mata qarar wani idan ya bata mata,tayi tsit tana sauraren sautin kukanta har sai data more da kanta,a hankali taji zuciyarta na yin sanyi,quncin daya tare mata a qirji ya sassauta,ta bude bakinta muryarta can qasa tace "Kukan murna nake ummi,murnar ganinki,yaushe rabonki ummi da kano?" Murmushi kawai tayi sannan tace "Raihana,har yau akwai wautar 'ya'yan fari tattare da ke,ke da zakiyi farinciki sai kuma ki buge da kuka?,Allah ya shirya". Dole ta dauki dangana ta dorama zuciyarta don ta bawa ummin da sauran qannen nata jin dadin ziyartarsu da sukayi,tare sukaci abincin dare rumana nata mata tsiya yau ta gujeta ko?,murmushi kawai tayi mata ************* Qarfe tara ne na safe amma gidan cike yake da 'yammata qawaye da 'yan uwan rumana,abinka da mai yawan qawaye da mutane kala daban daban. Tana daga kan gadonta tana kallo da saurarar duka abinda ke faruwa cikin dakin dake cike da 'yammata,har yanzu kayan bacci ne jikinta ta kasa tashi balle ta tabuka komai,tsananin faduwar gaba take ji da wata iriyar kasala. Rumana wadda ta kusa shafe awa daya gaban madubi ana mata makeup ta juyo ta dubeta "Sisi wai ba zaki tashi hakanan ki shirya ba?,baki gani gidan sai sake cika yake,kuma akwai abubuwa fa da ke zakiyi su" murmushi ta danyi sannan tace "Afuwa sisi,yanzun zan tashi in sha all Cikin minti goma sha biyar ta fito daga wanka,shadda ce iri daya suka dinka ita da rumanan maroon colour da aka yiwa aikin stone work daga sama har qasa da milk da maroon din stones,banbancin kawai raihana doguwar riga ce rumana riga da skert ne,miqewa tayi daga kan kujerar bayan an kammala yi mata kwalliyar tana duban raihana "Bismillah ni an gama min" langwabar da kai raiha tayi tana shirin yin qorafi,sarai rumanan ta gane me take son fadi saboda haka tayi saurin rigata ta hanyar dora yatsanta kan lips dinta tace "Shshshsh just obey before complain,yau rana ce ta musamman,saboda haka dole ki zauna amiki makeup malamarsu,oya bismillah" hakanan ta zauna saman kujeran yayin da sauran 'yammatan suka sa dariya suna tsokanar raihana kan rashin son makeup,itakam murmushi kawai ta bisu da shi da batason cewa komai,kafin mai kwalliyar ta fara saidata roqeta lite make up zata mata don Allah. Cikin minti arba'in saiga raihanan fes,tayi wani kyau na daban,kai kace itama amaryar ce musamman lokacin da aka yi mata daurin dankwalinta yabi kanta ya zauna gwanin sha'awa "Wow,wow sisi na,gaskiya ke ta dabance shi yasa bakison amiki make up wallahi,sai duka na raina kyan mu" cewar rumana tana qarewa raihanan kallo "Nima haka zance kika riga ni" inji umaima cousing din rumana,masha Allah haka kowa ke fadi,camera umaiman ta fidda ta fara musu hotuna su biyun,sai suka tashi tamkar wasu tagwaye masu mabanbantan kamanni. Shigowar ummi dakinne ya katse musu hotunan da sukeyi,ita kanta sai data tanka kyan da sukayi,sosai yaran nata suka burgeta,sai ta tsinci kanta cikin zuciyarta tana mai addu'ar Allah ya fiddawa raihanan itama miji na gari nan kusa "Kizo ki karba muku abincinku kafin anjima ki kasa fita don tsakar gidan namu ya fara cika" inji ummu tana duban raihana "To ummi" inji raihanan tana yafa milk din mayafinta daya dace da kayan tabi bayan ummun. Aikam dai tsakar gidan nasu masha Allah,don har duburcewa taso tayi ganin yadda ido yayo kanta,hakan kuwa baya rasa nasaba da saninta da sukayi ba gwanar qyale qyale bace sai yau gashi bisa fuskarta,da kuma yadda shigar tayi musu kyau,kusa da hajiya babba ta tsaya kanta qasa tana murmushi jin yadda hajiyan keta tsokanarta wai yau 'yar tsalle ta koya mata rawar kan kwalliya. "Ayyyiriririririri ango kasha qamshi" maganar data daki dodon kunnenta kenan,ko ba'a fadi mata ba tasan ko waye,saboda yadda qamshinsa ya game ilahirin tsakar gidan,duk yadda taso ta dake ta hana kanta kallon sashen da yake zuciyarta taqi aminta da hakan,a hankali ta daga kanta tare da fara juya idonta zuwa sashen da jikinta ke bata yana tsaye,karaf idanunsu suka hade guri daya,wani irin maganadisu ya fisgi kowannensu,hakanan kwalliyar kowannensu ta burge dan uwanshi,wani lumshe mata ido yayi tare da kashe mata ido daya wanda ya sanya tsigar jikinta tashi,dauke kanta tayi gefe daya zuciyarta na bugawa,wani abu da batasan ko mene ne ba ya taso ya tokare mata wuya,kwalliyar da yayi ta shiga yawo cikin idanunta,sanye yake da shadda fara qar tamkar takarda wadda keta faman maiqo da daukar ido,riga da wando ne da babbar riga wadda tasha surfani irin na maza,wanda ko ba'a gaya maka ba kasan ba qananun kudi ya lasa ba,komai da yayi amfani da shi fari ne,kama daga hula agogo da takalmi,yayi gyaran fuska tare da rage kwantacciyar sumarsa sai hakan ya sake fidda masa wani sigar kyawun na daban. Laushin da jikinta ya sakeyi shi ya haddasa mata jin kamar ba zata iya ci gaba da tsaiwar ba don haka ta juya don shigewa kitchen ta karbi abinda ya fiddo da ita,qarar shigowar tex taji cikin wayarta,ta bude wayar a hankali,numbobin wayar rayyan suka bayyana,sai ta samu kanta da saurin budewa _ina fatan kwalliyar da nayi ta burgeki kamar yadda taki tayi masifar tafiya da imanina,much love my dear raiha_ Sai ta tsinci kanta da waiwayawa a hankali sashen da yake din,har yanzu idanunsa na kanta din,murmushi ya sakar mata wanda saura kadan yayi gaba da numfashinta,hakan ne ya haddasa mata saurin shigewa kitchen din ta fada kan kujerar plastic dake ajjiye cikin kitchen din don kada ta zube a qasa "Ke,meye haka?" Taji muryar umminta na tambayarta,gaggawar daidaita natsuwarta tayi sannan ta saki murmushi "Babu komai ummi,abincinmu nazo dauka" "Gasunan,zo ki dauka" inji ummu tana nuna mata matsakaitan coolers din,hannu tasa ta dauki ta abincin daya hannun kuma ta dauki ta miyar kana ta juya zata fice,kacibus sukayi a bakin qofar yana niyyar shigowa ita kuma tana niyyar fita,sai ta ratse don ta wuce ta gefansa hannu taji ya sanya yana niyyar amsar kular abincin hannunta,dagowa tayi a rude tana dubansa,shima nashi idon na kanta,ta tabbatar daga kitchen din har tsakar gidan ko ina jama'a ne kuma wani kallonsa na iya kaiwa kansu yayi musu fassara,ta lura rayyan din ta bare yake nema,neman magana da rigima ta hanga fal qwayar idanunshi,hakan ya sanya ya ta sakar masa kular tayi gaba cikin azama,ba bata lokaci ya biyo bayanta,qasa qasa yake mata magana "Tafi a hankali mana 'yammata na,duka saurin na meye?" Bata tanka masa ba illa kadawar da zuciyarta keyi kamar ta faso qirjinta ta fito. A bakin qofar dakin taja tunga ta tsaya tana dubanshi a marairaice idanunta fal qwalla,roqonta daya ya barta a nan kada Yace zai shiga dakin,don ta riga da ta san kadan ne daga aikinsa Miqa mata cooler din yayi ta sanya hannu ta amsa,sai yabi lallen hannunta da kallo "Ina fatan yadda lallen nan ya miki kyau haka ya yiwa amaryata?" Bin lallen tayi da kallo kamar yanzu ta fara ganinshi sannan ta sake dubanshi,har yanzu ita yake kallo fuskarsa qunshe da murmushi,sai tayi shiru tare da juyawa don shigewa dakin ba tare da tace da shi komai ba "Ki gaida min amaryata,i love you" taji daddadan muryanshi saitin kunnenta wanda ya sanyata zabura ta shige dakin _11:30 pm_ Qarfe sha daya da rabi na ranar juma'ar alqawarin Allah ya cika,wato daruruwan jama'a suka shaida daurin auren RAYYAN YUSUF ADAM da kuma UMMA RUMANA DALHATU ATTAHIR,ba qaramin farinciki iyayen ango da amaryar ke ciki ba,ganin sun sake qulla wani zumunci mai qarfi tsakaninsu. Daga gefe guda kuwa farinciki ne fal zuciyar rumana musamman lokacin da hayaniya ta sake cika tsakar gidan alamun an gama daurin aure 'yan uwa na shigowa ana gaisawa,yayin da wata iriyar fargaba da tsoro wadanda batasan daga inda suke ba suka mamaye raihana,a hankali ta dinga jin wani sanyi na ratsata,da fari tayi zaton a.c din suka qurewa dakin ne,don haka ta ja mayafinta ta lullube jikinta tana zaune daga gefan gado,sai daga bisani ta fahimci sanyin ya wuce na a.c don haka taja jikinta saman gadonta ta cure guri guda,sannu a hankali kidan da kausar ta sanya cikin dakin suna cashewa ya soma hawa mata ka,cikin 'yan mintina qalilan wani zazzafan zazzabi ya rufeta kirif. Sam ki kadan rumanan bata lura ba,har sai da suka fita tsakar gida ana hotuna rayyan din ya gaza haqurin rashin ganinta ya tambayeta,sai a sannan hankalinta ta dawo jikinta,lokacin da ta isa dakin babu abinda jikinta keyi sai fidda hucin zafi,a rude ta dinga mata sannu sannan ta fita ta gayawa ummu,ce mata tayi ta daure suje taga likita,sam ita ta riga data sani ba wani magani na zamani ko na gargajiya da zai iya mata aiki yanzu,sauqin dai na gurin Allah,don tun daga cikin zuciyarta take iya jin ciwon,hakan ya sanya ta kafe kan a bata paracitamol tasha kawai ya isheta,idan bai sauka ba taje asibitin,babu musu rumana ta lalubo ta bata,ummu ce ta dubi rumana "Hayaniyan nan ma na daya daga cikin abinda ke qara mata ciwon kan,nasan halin raihana sarai batason kwarafniya,maza kamata ki kaita bangaren yayanku ta kwanta a can ta huta,tunda duka gidan a cike yake da mutane saahensa ne kawai ba kowa don sun wuce reception sai kuma yamma ina zaton zai shigo" rumanan ta amsa mata da to,sam batason zuwa sashen nasa,bata son gani ko mu'amala da duk wani da ya jibanceshi,amma babu yadda ta iya haka rumanan ta kamata suka bi ta qofar baya har sashen nasa,taso ta barta a falo amma tace sam sai data danganata da gadonsa sannan taja tattausan bargonshi ta rufeta ta fice bayan ta ja mata qofofin baki daya. Wata masifaffiyar qaunarshi ce ta dinga taso mata tamkar ta halakata lokacin data tsinci kanta kwance saman gadonshi cikin tattausan bargonshi,qamshinn turaren baccinshi ya buwayi hancinta,ji takeyi tamkar shine kusa da ita din,da gaske kam ta rasa rayyan,ta rasashi kenan,ya mata nisa na har abada,ya kuma haramta ya zama miji a gareta,wasu hawaye masu zafi da radadi suka biyo kuncinta,tabbas babu shakka so shine mafi girman abinda yafi hukunta zukata da sanyasu cikin qunci radadi har ma da bacin rai,kanta ta dinga mirginawa hagu da dama saboda wani qunci da taji qirjinta yayi,ta rasa inda zata dora kanta taji sanyi,a hankali ta dinga karanto addu'ar yaye qunci da damuwa babu qaqqautawa,wata tayita afili wata tayita a zuci,batasan yaya akayi ba bacci ya saceta wanda ta tabbatar albarkacin addu'ar data yi ne,idan banda haka bata jin duk iya satar tasa ya isa ya saceta din. A gaggauce ya shiga dakin don ya sake watsa ruwa ya kuma sauya kaya don su wuce wajen reception din wanda aka sauya shawara kan a bari a sauko sallar juma'a sannan a gabatar ganin yadda lokacin sallar juma'ar ya qarato sosai,ganin mutum ba zata kwance kan gadonsa ya sanyashi tsayawa turus,a hankali ya taka bakin gadon ya sanya hannu ya yaye bargon,idonshi fes kan fuskarta da tayi fayau tare da wata rama ta lokaci guda,jin yadda bargon yayi dumi ya sanyashi taba goshinta,take yaji zafin dake jikinta ya ratsa fatarsa "Subhanallah" ya fada a gajiye yana zama gefan gadon,wani irin tausayi mai cakude da so ya rufeshi "Har yaushe raihana har yaushe zaki ci gaba da cutar da zukatan bayin Allah?" Yayi tambayar a fili duk da ya sani babu mai amsa masa tunda bacci take,shiru yayi yana mai ci gaba da kallonta tare da qulla hanyoyin tsira garesu baki daya kala daban daban wanda saida kira ya shigo wayarsa yasa ya ankara da jama'ar dake jiransa,jikinsa babu qwari ya debi kayan da zaiti amfani da su ya koma toilet din falon ya shirya. Dakin ya sake komawa bayan ya gama shiryawa,yana tsayae yana balle botiran rigarsa yana ci gaba da duban raihanan rumana ta turo qofa ta shigo "Yauwa yayanmu,dama inata tunanin kota farka?" Ta fadi tana qarasowa kusa da shi tasa hannu tana ci gaba da rufe masa maballayan da bai qarasa ba,murmushi ya saka sannan ya dan sake janyota jikinsa ta hanyar sanya hannayensa ya zagaye qugunta da su yana dubanta "Bata farka ba,har yanzun bacci take" ya bata amsa yana dubanta lokacin da suke musayar numfashi,mutuwar da jikinta yayi ya sanya ta kasa ce masa komai har ta kammla rufe masa rigar,sai ya janyota ta fada qirjinsa ya matseta sosai cikin jikinsa yana fatan samun sauqin zugin da zuciyarsa ke masa. A hankali raihana ta maida idanunta ta sake runtsesu,yadda basu ganta ba bata fata su ganta din,dago kai tayi tana duban qwayar idanunsa "Yaya rayyan,meke faruwa ne?" Tayi masa tambayar tana sake dubansa,shima kallonta yayi sannan ya sake maidata cikin jikinsa tare da dora habarsa saman kafadarta kana yace "Me kika gani?" "Jikinka yana nuna weakness dinka,sannan a yanzun ma zuciyarka bugawa takeyi sosai" ajiyar zuciya ya saki sannan ya maida mata amsa "Gajiya ce my angel,na gaji na gaji sosai" ya fada cikin wani irin yanayi,sai ta tashi daga jikin nashi tana fadin "Ayyah sorry yaya na,daga yau dai ai shikenan ko?" Sake riqe qugunta yayi yana duban qwayar idonta wanda hakan ya sake sanya mata kasala "Bashi kenan ba angel,tunda na tabbata ba za'a bani ke ba sai na dawo daga tafiyar wata shida" kunya ta dan kamata sai tace "Ai kamar yau ne" kiran wayarsa da aka sakeyi ya katse hirar tasu dake sukar zuciya da duka sassan jikin raihana,ya ansa wayar a gaggauce sannan ya dubi rumana "Ki kula da ita angel,idan ta farka kika ji zazzabin bai sauka ba is better taga likita,kimin waya zanzo na kaiku" "Ok sai ka dawo" ya manna mata kiss a goshi sannan ya fice. Wani tsalle ta daka ta sauka gefan gadon dakin,wani farinciki takeji kamar an mata kyautar duniya da abinda ke cikinta,zamanta tayi tana ci gaba da gadin raihana,duk zaman da take tana jinta amma taci gaba da yin likimo,har akayi sallar azahar ganin bata motsa ba tayi zaton barcin take har yanzu sai ta sake ficewa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Manzan Allah S A W yace"idan kaga wani bawa da Allah ya jarabceshi da wata cuta ko lalura ko nakasa,ka godewa Allah ka karanta(alhamdulillahil lazai Aafaani mimmabtalaka bihi,wa faddalani ala kasirin mimman khalaqa tafdilaa)"* _______________________ *Babi na ashirin da hudu* Cikin kwana biyu rak gidan ya zama sai masu shi,dukkansu kowa ya samu kansa,idan ka cire raihana dake jinyar zuciyarta wadda kullum take cikin ciwo da radadi,sau tari takan tsinci kanta cikin wani yanayi maras dadi duk lokacin da idanunta suja gane mata rumana da rayyan jone da juna,ta sake abinta sosai da mijinta,duk shagwabar nan ta dawo,takan bata lokaci tana yuwa zuciyarta gargadi kan kada ta shiga hurumin da ba nata ba,tana shafe tsawon awanni tana tunasar da kanta wace rumana a gurinta?,meye matsayin rumana da rayyan a yanzu,sosai take takawa kanta da burki don batq fatan bawa zuciyarta dama balle har ta samu taci galaba a kanta. Ta jima da sanin cewa zuciya bata da qashi,hakanan babu abinda shaidan keso irin ya samu kafar da zai ruguza duk wata alaqa ko DANGANTAKA da aka ginata saboda Allah kuma cikin tsarki da tsafta kwatankwacin DANGANTAKAR dake tsakaninsu da rumananta. Takanyi qoqarin kauce masu duk lokacin da suka kadaita su ukun ta basu guri shi da rumanan,musamman cikin da yaketa shirye shiryen tafiyarsa cikin wannan satin,kusan kullum suna tare tana zuba shagwaba ko tayashi wasu shirye shiryen,abu guda ke damunta idan ummu ta hadasu tare kan suje dakin rayyan din da ita,batasan manufar ummun ba,amma ita tana hakan ne duk don qoqarin hana wani abu faruwa ga rumanan har sai rayyan din yaje ya dawo anyi biki an kai masa ita,takanji kamar ta zura da gudu ta bar gidan idan ummu ta hanata barosu su kadai sai tace tare zasu je tare zasu dawo,wani lokaci takan fito falon rayyan din ta kunna t.v ta barosu cikin dakin,don tanajin bai cancanci a addinance a hanasu kadaicewa ba tunda halalin juna suke ga junansu,bugu da qari kuma hakan yana zamar mata wani makami fa take yaqar zuciyarta da shi,don matuqar suna zaune da rayyan din bai bari zuciyarta ta huta,da gayya yake yin duk wani abu da zai sanya dole ya tsaya mata a rai. ************* Kwance take saman doguwar kujerar dake cikin dakin baccinsu,fuskarta na kallon saman dakin wayarta kife kan qirjinta,yayin da hannunta ke riqe da wani littafin tarihin masarautu tana karantawa,batafi awa guda da raka rumana part din rayyan ba ta samu ta gudo ta barsu. Qarar wayar tata ya sanya kife littafin kan ruwan cikinta ta daga wayar,amir ke kiranta,a sanyaye ta daga don cikin kwanakin nan ta sakar masa jiki sosai tana bashi dama,don ta riga data sani cewa babu wata mafita gareta da ta wuce wannan,hakanan kulawar da bawan Allahn ke nuna mata ya cancanci ta bashi lokacinta,ta kara wayar a kunnenta tayi masa sallama,cike da farinciki da zumudi ya amsa mata bayan sun gaisavya soma janta da hira ita kuma ta biye masa,kusan minti ashirin sannan yace mata "Ina sa ran gobe in sha Allahu zan shigo kano" tadan ware ido kamar yana gabanta "Ka shigo kayi me?" "Naga gimbiyata mana" sai ta saki ajiyar zuciya,tausayinsa ya kamata,babu shakka son maso wani bala'i ne,ba zata hanashi zuwa ba amma tana tausayin yadda amir ke dawainiya da sonta "Amma duka duka yaufa kwananka biyar da barin kanon,kana ganin baiyi wuri ba ace ka sake dawowa ba amir" dariya yayi wadda ta jiyo sautinta sannna yace "Ke kike ganin hakan raihana,amma kin manta salon zancan hausawa garin masoyi baya nisa?,duka bama wannan ba,kin zarta duk yadda kika dauki matsayinki a gurina raihana,koda ace kullum zanzo kano ganinki bazan taba gajiya ba,saboda ke din ta daban ce cikin mata kamar yadda kike ta daban cikin zuciyata" murmushi ta saki tana jin dadin yadda yake yabonta "To shikenan,Allah ya kaimu da rai da lafiya,Allah ya kawoka lafiya" "Amin ya Allah,amin sarauniyata" daga haka sukayi sallama ta ajjiye wayar tana tunanin amir din kamar ba yanzu suka rabu ba,tana ganin qimarsa hakanan tana respecting dinsa ko don wanda ya kawoshi,bama haka ba yana da managartan halaye wadanda su kadai abun yabawa ne. Zaren tunaninta ya katse lokacin da gogon dakin ya kada alarm ya nuna mata qarfe goma na dareda azama ta miqe don komawa gunsu rumana gudun kada ummu tazo ta taddata anan ta barsu a can,don tasan bata bari su wuce goma da 'yan mintina basu dawo dakinsu ba,ta rasa hikimar yin hakan iya tunaninta,murmushi kawai tayi kamar kullum cikin ranta tace "Koma dai menene abinda babba ya hango yaro bazai hangoshi ba koda ya hau dala da gauron dutse" ta janyo hijabinta dake hannun kujera ta sanya ta fice . Ta tura qofar falon ba tare da tayi tunanin suna ciki ba,don a abedroom ta barsu dazun suna shirya kaya cikin trolly,suna zaune ne kamar zasu shiga jikin juna rumana nata 'yan koke kokenta saboda jibi iwar haka rayyan din ya huce gajiya a england din,kamar ta juya sai kuma ta dake ta qarasa "Ke ganta ko ya rayyan,yanzu sai tace zuwa tayi tafiya da ni fa" inji rumanan ta fada tana dubansa,murmushi raihanan tayi sannan ta ware hannayenta "Kwantar da hankalinki ni mai iya tafiya ce ta barku,amma ki tabbatar idan ummu ta biyo sahunki ki cire suna na a ciki" sai ta miqe tana lalubar mayafinta "Ai duk kece,me yasa ba zakiyi zamanki ba kema idan tazo taga mu biyun ne ai ba zata matsanta ba,ni gaskiya ban gaji da ganin yaya na ba" "Au ehhh,zaman gadinku zan tqyi kenan sai kun gama abinda kuke,gaskiya ne,to ai nima akwai mai buqatar jina malama" raihanan ta fada tana yima rumana harar wasa,rayyan dake zaune yana kallonsu suna sake burgeshi,yana jin inama ace duka mallakinsa ne,yana jin ua zama dole daya dawo koda yardar raihana ko babu ayi duk wacce za'ayi,don yaci alwashin da duka su biyun zai tare cikin gidansa a matsayin matansa da yardar Allah. Maganar da raihanan tayi ita ta tabashi,sai ya sanya idonsa cikin nata,yana kallo ta wani cije da dauke kai,wanda hakan ke tabbatar masa cewa tana sane ta furta abinda ta furta din,sai ma tayi gaba ta coge bakin qofar falon qeyarta na kallon cikin falon fuskarta na kallon waje ta tsaya a nan tana jiran rumanan ta fito. Tare suka jero da rumanan suna hirarsu kadan kadan,suna gab da shiga dakin nasu gajeran saqo ya fado wayarta _ki kiyaye ni raihana ki fita ido na,bawai kasawa ko gazawa nayi ba da na zuba miki ido ba,dama na baki,amma ina gab da baki mamaki_ Gogr saqon tayi don bata barin dukka saqonshi cikin wayarta,cikin zuciyarta ta saki murmushi,tana sane tayi masa haka,tanajin qila da shine ita da tuni ya dade da barin kishi ya yagalgala zuciyarsa kenan,babu kulawa ta miji da mata da baya bawa rumana gabanta,saidai tana yiwa kanta waigi tunda tasan halas ne duk wani abu da zasuyi "Ina roqon Allah ya bani damar baka mamaki kafin kai ka bani rayyan" tayi furucin cikin zuciyarta ************* Kasancewar tana da lacture washegari ranar da amir din zaizo,hakan ya sanya tilas ta shirya zuwa makaranta tunda duka duka qarfe sha biyu ta fito,tasan kuma zai iya kaiwa azahar bai qaraso ba,tunda bauchi da kano akwai tazara,bata barwa rumana saqon tayi mata komai ba tunda tasan bata da time,duk da idan ta fada din zata yin,amma bata son takura don tasan suna tare da rayyan. Tana dawowar ko zama bata yi ba ta shiga kitchen ta fara shirya masa abinda zata taryeshi da shi,qarfe biyu ta kammala komai ta killace guri guda,tana shirin fita rayyan ya shigo,yau kam sun dan sake don ummun bata nan ta fita bikin 'yar qawarta,sanye yake da farin t.shirt mai gajeran hannu da farin wandonta Gashinsa ya kwanta luf sai qyalli yake,hakan ya qarawa fuskarsa kyau "Hmmm,hala an fara qyallin angwanci ne" raihana ta raya cikin zuciyarta tana tabe baki,bake bake yayi ta rasa hanyar da zata wuce,gashi ya rutsata da idanu,ya numfasa a hanakali sannan yace "Me aka dafa mana?" "Me na dafawa baqo na dai,saidai ko na kira maka rumana ka tambayeta" ta fada tana ware dankwalinta ta yafa saboda yanayin rigar dake jikinta,wani dan qaramin murmushi ya saki bayan ya harde hannayensa a qirji "Da alama kishi kike kenan ko?" A razane ta waigo ta dubeshi,take idanunta suka tara qwalla "Allah ya sawwaqe ya kiyaye,cewa akayi kowa ma irinka ne?" "Da zaki zama kamar ni din ai da naji dadi,any way,a bani abinci yunwa nake ji" "Ban dafa da kai ba" ta fada tana hade rai "Wannan kuma baki isa ba yarinya wallahi" ya fada kai tsaye yana durfafar flask din abinciccikan data shirya yana cewa "An haramta min soyayyar na daga qafa kuma abincin ma sai ace min na wani ne" ya dauki plate yana diban abincin aciki,baki ta saka galala tana dubansa cike da takaici,don duk adon da ta yiwa abincin ya kwashe ko ajikinsa ma tuni ya soma kaiwa cikinsa. Rumana ce tayi sallama ta shigo kitchen din,kai tsaye idanunta kan rayyan "Kai kai,yaya kace min kai dinner ka samu ina can ina nemanka" kasa magana yayi sabida dadin abincin har sai daya hadiye na bakinsa "Abincin ma da ake mana rowa har ma da gori" ya fada yana sake diban wani zaikai baki,tasan sarai da wa yake don haka ta dubi raihana tana qunshe dariya "Garin yaya sisi?" Raihana da wani irin baqinciki ya tokarewa wuya ta buda baki da qyar "Haba sisi,abincin da na shiryawa amir ne fa,duba yadda ya bata min tsarin baki daya" cikin boye dariyar tace "Ah....gaskiya miji baifi miji ba,ci kayanka yaya na,amma fa....gsky baka kyautawa sisi na ba" sai kawai kuka ya qwace ma raihana ta juya da sauri ta fice,binta sukayi da kallo baki daya,rumana na mamakin daga dan wannan abu?,ta yunqura zata bita rayyan ya hanata ya tsaidata suka cinye abincin tare don yasan meke mintsinin zuciyarta. Maimakon taji zuciyarta tayi sanyi kamar yadda ta saba yawancin lokuta idan tayi kuka sai taji akasin haka,tsoro fargaba da wani irin faduwar gaba ne suka mamayeta,ga wata iriyar kasala da mutuwar duka gabban jikinta,tana zaune har uku saura sannan ta yunqura ta shiga toilet cike da mamakin rashin isowar amir har zuwa wannan lokacin,don tayi tunanin kafin ta kammala shiryawa ya iso me yiwuwa har yama zauna jiranta. Har ta fito ta kammala shirinta babu labarin amir,ta daga waya ta soma lalubar number dinsa don jin lafiya ganin hudu saura ta kawo kai. Bugu uku aka daga saidai maimakon muryar amir din muryar mace taji,a hankali cikin shaqaqqiyar murya tace "Ba amir bane,husna ce" "Ayyah husna an yini lpy ya mutan gidan" "Lafiya" husnan wadda take qanwa ce ga amir din ta amsa a agajarce "Hala amir din bai kusa ko?,ko a gida ya bar wayar?" Ta sake tambayarta,maimakon ta amsa mata sai ta saki kuka kawai wanda ya gigita raihanan ta shiga tambayarta,da qyar ta iya bude baki tace da ita "Allah ya yiwa amir rasuwa anty raihana a hanyarsa ta zuwa kano,yanzu haka ga gawarsa nan ana shiryata"abinda kunnenta ya iya ji kenan wayar ta sulale daga hannunta. Wani irin tashin hankali taji an rufto mata wanda bata taba jin irinsa ba,hannu ta dora akai ta fasa qara wadda ta jawo hankalin rumana da rayyan dake zaune a falo take kuma zuciyarta ta tunasar da ita haramcin hakan da kuma azabar da hakan yake jawowa mamaci,jiri na shirin kayar da ita ta zame daga gefan gado zuwa dandagaryar carfer tana furta innalillahi wa inna ilaihi raji'un a jejjere kuma a fili tana mai fatan abinda taji ya zama mafarki ne ba gaskiya ba. Rayyan ne a gaba rumana na biye da shi,zuwa lokacin da suka iso tuni raihanan ta qarasa birkicewa,da sauri rumana ta zube gabanta tana jijjiga kafadarta tare da tambayarta lafiya,sai a sannan ta saki innalillahin da take ambata,saidai ta kasa yi musu bayanin komai baya ga sunan amir da take ta kira. A hankali rayyan din ya samu gefan katifarsu ya zauna,sannan ya fidda wayarsa ya kira layin amir,ba jimawa aka daga,bayanin da ta yiwa raihana shi ta yiwa rayyan,a hankali shima ya dinga ambatan hasbunallahu wa ni'imal wakil kana ya kashe wayar ya yiwa rumana bayani,itama kukan ta sanya,sai suka sakashi a tsakiya ya rasa da wacce zaiji,gashi ummu bata nan,da qyar ya shawo kan rumana ya nuna mata ita ce mai lallashin raihana suka hadu suka dinga bata baki,saidai duk a banza,abinda take ji na zafi da radadi cikin zuciyarta babu abinda ya canza,hakanan ta kasa tsaida hawayenta a haka ummu ta tarad dasu. Haqiqa ba qaramin jin mutuwar sukayi ba baki dayansu,kada ma raihana taji labari,hatta da rayyan ua girgiza matuqa,mutuwa ba wasa bace,washegari tun bakwai na safe suka shirya baki dayansu sai garin bauchi . Zuwan na raihana sai ya sake ruruta wutar rashin da sukayi,batasan amir ya bata matsayi mai yawa a rayuwarsa ba sai wannan karon da take cikin danginsa,kusan kowa yasan raihana a baki,sanin ido da ido ne kawai basuyi mata ba,dakinsa kuwa hotunanta ne birjik wadanda batasan lokacin da ya samesu ba,tayi kuka tayi kuka sosai,ta tausayawa kanta na rashin masoyi da tayi,ta tabbatar ba qaramin so amir yayi mata ba,babu yadda ta iya haka Allah ya rubuta tun usul ba zasu zama ma'aurata ba. Wannan mutuwar ya sanya rayyan ya daga tafiyarsa ya maidata wani satin,domin suna can bauchim shi da rumanansa da raihanan ana karbar gaisuwa da su,raihana taga karamci da qauna gun 'yan uwan amir din,lokaci guda ta dinga ji kamar an dauke wani sashe na gangar jikinta,ki babu komai akwai SHAQUWA da SABO hausawa kuwa sunce SABO TURKEN WAWA NE. Ranar da akayi sadakar uku suka dawo kano,sun baro bauchi cike da jimami alhini da kuma jajantawa juna rashin da sukayi. Sosai mutuwar ta dinga tabata har ta dinga rama,bata iya hana kanta kuka duk lokacin data tuna da amir din,duk lokacin data tuna cewa a hanyar zuwa wajenta ya rasa rayuwarsa,itakam mai zata je da wannan masoyin gaskiyar,tabbas babu abinda yayi shaura a tsakaninsu yanzun face addu'a. Sosai rumana ta dage gun kula da sisinta haka ummu da abba wanda suke zaton tsantsar soyayya ce tsakaninta da amir din,hatta da rayyan ba'a barshi a baya ba,tausayinta yake ji sosai,ya ja baya sosai da ita duk don su samu ta dawo nutsuwarta . A hankali ta dorawa zuciyarta tawakkali,ta dauki duk wani rudu da take ciki tayi wurgi dashi bayanta,ta azama ranta zata yi karbi rayuwa duk yadda tazo mata,qaddarartace haka haka Allah ya tsara mata. ************* Kusan awa biyu suka dauka suna kwabe kwaben meatpie,doughnout da chin chin,sai kuma dambun naman kaza da raihan ta sarrafashi da kanta,duka wannan idea dinta ce data cewa rumana ta yiwa rayyan din,saboda tana iya tuma labarin da yake basu wancan tafiyar na dadewa da yayi kafin test na spices da girkin garin yabi harshensa,sai da suka gama tsaf rumanan tace ta mata mai wuyar,taje ta kwanta ta huta ta barta ta soya,murmushi tayi tana yaba irin qaunar dake tsakaninsu,har yau wani rarrashinta suke suna duba damuwar dake cikin zuciyarta. Dawowarta dakin ya kasance ita daya,sai tunani kala daban daban ya dinga bijiro mata,sanye take da wani material sil dinkin doguwar riga umbrella mai dogon hannu ruwan sky blue mai zanen hadari,kanta babu dankwali amma yana matse da ribbom kalar kayan jikinta mai laushi,a hankali ta miqe ta isa ga locker dinta ta janyo wadda ke shirye da littattafai kala daban daban,kama daga na karatu da kuma na rubutu,dagawa ta dinga yi tana dubawa idonta ya fada kan wani littafi mai kyau ruwan hoda turarre da mai haske wanda rayyan ya taba aiko musu da shi,a qalla ya qunshi shafi sittin tasan kuwa ya isheta rubuta duk abinda takeso,sai ta ciro shi hade da wani biro ta dawo baki gadonta ta dora qafafunta duka saman gadon,shiru tayi tana tunanin me zata rubuta,murmushi ta saki daga bisani sannan ta fara rubuta duk abinda yazo ranta. Sannu sannu sai gashi tana shirin tasan littafi dangane da rayuwarta,tun daga randa tasan me takeyi a duniya,quruciyarta da 'yar uwarta rumana da rayyan,wani abun idan ta rubuta tayi murmushi wani ya girgiza kai,wani kuma ta share qwalla,musamman mutuwar abbanta da ta tuna da zamowarta ita kadai a inda bata saba rayuwa ba wato garin kamo gidan abbanta yusuf,sai take jin wani dadi,yanayin yana mata dadi,ji take tamkar tana hira da wani ne rubutun da take,tamkar tana gayawa wani damuwarta ne da ita din wacece,tsaye yake kanta hannayensa harde a qirji yana biye da duk wani harafi da ta rubuta ba tare da ta sani din ba,shi kansa saita rubuta wani abun sai ta tuna masa da moment din ya kanyi murmushi lokavi bayan lokaci. tayi rubutu mai tsawo kafin ta fado fagen da batasan ta fado din ba _na gujeshi irin gudun da dan adam kan iya yiwa ajalinsa,na gujeshi gudun da ban taba yiwa wani abu ba a rayuwata ba,na rufe zuciyata saboda shi,na hana kaina dukkan wani 'yanci dalilinsa,ashe yana biye da ni?,ashe yana zai riskeni sannna zai kuma wahalar da ruhi gangar jiki zuciya da ma rayuwata baki daya,na fara son rayyan tun bansan sone ke yawo a zuciyata,na fara sonsa tun lokacin da bana zaton 'yar uwata ta fara sonshi,na fara sonshi lokacin da nake tsammani tsoronsa nake,infact ina zaton da sonshi aka haifeni,nakanji bugun zuciya duk lokacin da aka ambaci sunanshi tun ina gaban iyayena kafin zama ya hadamu da shi,ashe duka sone wanda yarinya da tsoro duka suka hadu suka boyeshi,ban farga da mugun tarkon da na fada ba sai bayan wani lokaci da hankali ya game jikina,wanda zuwa lokacin yayimin nisa baya qasar,zuwa kuma lokaci na makara saboda tuni soyayya tayi nisa tsakaninsa da 'yar uwata,a lokacin da ya bijiromin da buqatarsa bakin alqalami ya riga ya bushe,bazan iya maida masa raddin kan abinda ya nema ba,bazan iya sallama masa kaina ba,ba wai don bana sonshi ba,hasalima nafi duk wata halitta dake doron duniya qaunarsa,saidai da ya riga ya mallaki zuciyar rumana 'yar uwata,wadda nake jinta tamkar cikin mahaifa guda muka kwanta,nake jinta har cikin jina na,na riga da na SADAUKARWA 'yar uwata RAYYAN,SADAUKARWA ta har ABADA,domin ta cancanci fiye da haka ma a gurina,na sallamawa rumana farincikina soyayyata da kwanciyar hankalina,na bar mata shi har ABADA._ A hankali jikinta ya raunana kamar yadda zuciyarta ta raunana,sai ta gaza ci gaba da yin rubutun sakamakin dishi dishin data fara gani saboda rashin glass kan fuskarta,ga wani irin zafi da zuciyarta ke mata,sai ta kifa kanta kawai saman littafin ta soma sheshaheqa don ta gaza boye sautin. Zare biron da akayi daga tsakanin yatsunta ya sanya ta dago kai zuciyarta na wani matsanancin bugu ga zatonta rumana ce,saidai sabanin rumanan sai taga rayyan ne,da sauri ta janye littafin tana qoqarin rufewa,bai hanata ba don ya na biye da ita,ya riga da ya gama karanta komai,zagayowa yayi gabanta ya zauna a gefan gadon har gwiwarsu na gogar ta juna,tayi yunqurin janyewa daga gurin sabida tsoron kada wani ya shigo ya gansu saidai ya hana mata hakan. Qasa tayi da kanta don ba zata iya jurewa kallon qwayar idonta da yake ba "Qarya kike raihana......qarya ne da kike iqirarin kinfi kowacce halitta dake doron qasa qaunata,dalili kuwa banga hakan ba,banga alama ba raihana,banga alama ba" ya fada cikin zafi,kallo daya zaka yi masa ya gaya maka zuciyarsa tafasa take,sai ta sake sadda kanta kawai ganin yadda lokaci guda idanunsa suka kada suka koma launin ja,tabbas da zai yiwu da kuma akwai dama data ciro masa zuciyarsa ya ganewa idanunsa,saidai bata da buqatar hakan,tafiso ya tafi a yadda yace yazun,su tafi a bata qaunar tasa "Raihana" ya kirata cike da zafi,bata dubeshi ba shima bai damu ba yaci gaba "Na baki dukkan wata dama data dace,shiru da nayi da maganarmu nayi ne don na baki dama da 'yanvin da kike da su,na baki damar gamsuwa da kanki cewa zaki aureni ni rayyan,na baki dama wadda koda munje gaba da maganar bamu da banbamcin ra'ayi,amma na fuskanci baki da adalci,hakan yasa kika kasa yi mana adalci ni da ke,to ina so na sanar dake...... wannan ce damarki ta qarshe,wallahi,wallahi,wallahi,kinji na rantse miki....,ni rayyan matuqar na dawo daga england baki tsaida shawarar da zata zama adalci tsakaninmu baki daya ba....ko da yardarki ko babu zan sanar da magabata,kuma sai na aureki ko ta halin qaqa,qarshen qiyayya ki kashe rayyan a daren da kika zama matarshi,fine,wannan ya rage naki" ya fadi yana miqewa ya gyara t.shirt din jikinsa sannan ya sanya kai zai fice,cike da qarfin hali tace "Hmmm,sai mu gani ai,yadda ba'a yi muku auren dole ba wallahi nima babu mai yimin" har ya daga labulen zai fice sai ya sakeshi kana ya waiwayo,murmushi ya saki sannan yace "Zaki gani kuwa,ki jira lokaci shike da amsa" ya fada kana ya fice abinsa. *mra muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga abu hurairah R.A yace manzan Allah S A W yace"idan aka kirayi dayanku zuwa walima to ya amsa,idan ya kasance mai azumi to yayi addu'a,idan kuma baya azumi to yaci(daga abincin walimar)"* _______________________ *Babi na ashirin da biyar* Za'a iya cewa tarihi ne ya maimaita kansa,kamar wancan karon tafiyarsa england na farko cikin filin jirgin saman malam aminu kano,saidai wannan karon akwai banbance babance masu tarin yawa. Tsaye take gefe gudu harde da hannayenta,kanta na kallon wani sashen daban,sai ka rantse da Allah batasan me rayyan da rumana keyi ba,duk da tayi qoqarin janye zuciyarta daga lamarinsu amma kunnuwanta na iya jin komai. Kwance take saman qirjinsa tana zubar hawaye,yayin da shi kuma hannunshi daya ke gadon bayanta yana shafawa alamun rarrashi,idanunshi kafe kan raihana da taqi yarda ko sau daya su hada idanu,yana jin duk cikinsu babu wadda ke jin abinda yakeji cikin zuciyarsa,dauriya da dakiya kawai yake gwadawa irin ta maza. Da qyar ya samu ta tsagaita kukan sannan ya rabata da jikinsa,ya dubeta "Sai ku kira sisinki muyi sallama ko?" murmushi ta sakat mishi sannan ta qarasa inda raihana take,hannunta ta riqe wanda ya sanya raihanan juyowa ta dubeta,fuskarta cike da damuwa yanayin idanunta a birkice "Lafiya sisi?" Rumana ta tambayeta,murmushin yaqe ta saka a hankali sannan ta girgiza kai "Babu komai sisi na,me kika gani,kawai banjin dadin jikina ne" "Cuta kike a tsaitsaye raihana,kuma kinqi yarda da maganata,har yanzun kin kasa yarda da qaddarar rashin amir,tabbas babu abinda yafi rabuwa da masoyi zafi,koni yanzu ni kadai nasan me nakeji tafiyar da ya rayyan zaiyi na wata shida,bare ke da kukayi rabuwa rabuwa ta har abada,kiyi haquri Allah zai maida miki mafiyinsa insha Allah" kai kawai ta iya jinjinawa,babu shakka baka taba sanin muhimmancin abu sai lokacin da ka rasashi,a yanzun take sake jin rashin amir din sosai,take kuma sake jin maraici cikin jikinta gaba da baya. Ta rasa abbanta,ta rasa amir sannan gashi finally ta rasa rayyan,tabbas jarrabawa ce sosai cikin rayuwarta da Allah ke rabata da wadanda take da buqatar zama da su,tana fata kuma zata cinyeta. Mintina biyar ya rage a fara nemansu don haka ya dube raihana a gaggauce sannan yace "Haka ake sallama da mutum,kin koma gefe guda kin tsaya" cike da dakewa da basarwa gefe guda kuma saika tsammaci wasa ne tace masa "Ina laifina ma da na rakoku?" "Madalla,zan miki tuni dai,kada ki mance da maganarmu,ki jirayi dawowata" "Wacce magana ce ni aka wareni ba'a gayan ba,wariyar launin fata za'a nunan?" Rumana ta fada a shagwabe,gaban raihana ya buga,ta saki ajiyar zuciya sanda ta jiyo rayyan na fadin "Me kike ci na baka na zuba,ki bari na dawo mana,ni da kaina zan gaya miki" murmushi ta saki kana tace "Allah ya dawo min da kai lafiya to" "Amin my angel" ya fada yana kissing dinta a goshi. Share qwalla tayi tana daga mishi hannu ya juyo ya dubesu baki daya kafin ya qarasa bacewa ganinsu *************** To xamu iya cewa ya tafi yabar kowaccensu da zazzafar soyayyarsa cikin zuciyarsa,yayin da shima yake can yana dakon nasa,sau tari takan ga kewar rayyan da rumana keyi nafila ce akan tata,dalili kuwa shine ita tana iya fada,tana iya bayyanawa hakanan tana da 'yancin nunawa,itakam bata da wannan da 'yancin sam. Ta sha ganin kiransa amma sai ta share taqi dagawa,wanda idan yaga hakan sai ya cillo mata saqon karta kwana ma sms tunda ita ba charting take ba, .. Kalaman soyayya ne danqare a cikinsa da kuma sake jadda da mata qudirinsa na babu gudu babu ja da baya ta jirayi zuwansa,duk sanda ta karanta hakan qirjinta kan tsananta bugawa,duk da cewa bata taba mancewa da maganar tasa ba,kullum wayewar gari da ita take kwana da ita take tashi,addu'a sosai kawai ta tsananta tare da neman mafita wajen ubangiji,don ta lura rayyan ya shallake tunaninta. ************* Kwanci tashi babu wuya wajen Allah,hakanan yau da gobe bata bar komai ba,sai gashi rayyan ka dosar wata na hudu da tafiyarsa,watanni buyi kacal suka rage masa ya dawo. Cikin satin da ake ciki jikin hajiya babba ya motsa,har takai ta ga kwanciya a sibiti,randa aka kwantar da itan suna makaranta,ummi tayi musu waya ta gaya musu idan sun tashi daga lactures da wuri suyi abinci su kawo asibitin tana can su taddata. Qarfe biyar saura suka isa asibitin suka fara bin kwatancan dakin da suke,suna shiga barandar da zata sadaka da kebantattun dakunan rumana tayi kacibus da qawarta,suka gaisa da raihana,ba zata juri tsaiwa ba don haka tayi gaba taba duba lambobin dakunan. Daki na uku ta murda qofar ta tura tare da yin sallama,mutum uku ne cikin dakin banda marar lafiyar dake kwance ta hudu,biyun mace da namiji saman carfet dake shimfide a dakin suna hira kadan kadan,yayin da dayan wanda ya da alamu ya girme musu yake zaune kan kujera hannunshu dauke da waya yana danne danne wanda shigowarta ya sanyashi daga idonsa. Ganin ba dakinsu bane ya sanyata cewa"sannunku ya musu jiki"wadanda ke saman carfet din ne suka amsa mata da cewa da sauqi "To Allah ya qara afuwa" "Ameen ya Allah" suka sake amsa mata har na kan kujerar "Hala dakin gaban nan ne daki na uku ko?" Wannan karon macen ce ta amsa mata da eh shine "To na gode" ta fada da hanzarinta ta fice kana ta rufe masu qofar saboda zuba mata ido da na kan kujera yayi kamar wani sabon maye. Sun samu jikin hajiyan da sauqi ba laifi alhmdlh,raihana na gefanta hajiyan na mata hira kadan kadan tana amsa mata. Basu tashi tafiya ba sai wajen takwas na dare,sun tsaya jiran halima qanwar daddy dalhatu da zata kwana da hajiya gashi bata zo ba,uncle salis ne ya kirata ta shaida masa cikin nuwaira yarinyarta ke ciwo wlh shi ya sanya tayi jinkiri amma gata nan zuwa,daddy dalhatu yace tayi zamanta ta kula da ita Allah ya bata lafiya. Ganin ana shirin zuwa dauko hauwa'u dayan qanwar tasa ya sanya raihana tace a barta ita zata kwana,daddyn ya dubeta yace "Kiyi yaya kuma raihanatu da makarantar idan banda abinki?" "Ai daddy gobe da jibi duk bani da lacture bazan ma shiga makarantar ba" "To shikenan yayi kyau,Allah yayi miki albarka" "Ameen daddy", ya juya ya dubi rumana " to kefa?"sai ta dan ya mutsa fuska "Zuwa zan dinga ina komawa..." Ko kafin ta qarashe ma hajiyan ta tareta cikin muryar marasa lafiya "Banso ma ki zauna,raihan ta isheni" "Dama nima ba zaman zanyi ba,a hana mutum wayar dare" ta fada ciki ciki tana ficewa a dakin "Za kici qaniyarki" inji maman rumanan ta fada din ita taji me tace. Bayan tafiyarsu hirarsu suka ci gaba da yi da hajiyan,sai data gaji ta kwantar da ita ta gyara mata rufar sannan ta fita don siyo musu ruwa da basu da shi ta sanya cikin fridge din dakin. Saura kadan suyi gware,ya danja da baya tare da cire eye piece din kunnensa yana qare mata kallo ya furta "Am sorry,ban kula ba" kai kawai ta kada ta kewayeshi ta wuce ya bita da ido Da safe ummu ce ta fara aiko da breakfast,auwalu ta aiko gashi yayi wuri basu fara bari ana shiga bangaren nasu dakunan ba,don haka yayi kiranta ta fito don ta karba,kamar jiya da shekaran jiya,yauma yana tsaye bakin qofar nasu dakin,ya bita da kallo kamar yadda ta fuskanci kusan ko al'adarshi ce haka oho masa,dauke kai itama tayi kamar kullum din tayi gaba abinta. Ta fara dauko kwandan farko don ba zata iya dauka duka ba,data dawo ba taddashi bakin qofar ba ta shige dakinsu ta ajjiye sannan ta sake fitowa,yana tsaye bakin qofar dakin hannunshi riqe da daya kwandon,murmushi ya sakar mata sannan yace "Ina kwana,don naga bakison kula kowa,ko dakinmu baki sake shiga kin gaida mamarmu ba"yayi maganar yana miqa mata kwandan,amsa tayi kawai tare da ce masa "na gode" ta juya ta koma ciki. Ta gama bawa hajiyan tea kenan aka turo qofar,idan bata manta fuskarba budurwar da ta gani ce shekaran jiya a maqotan dakinsu. Gaisawa sukayi ta yiwa hajiyan sannu da jiki sannan tace "Don Allah ko zaki taimaka min na daga hajjaju zan bata ruwan zafi zata sha magani lokacin shan maganinta ya kusa,gashi yaya ammar ya fita bai shigo har yanzun" "Ba komai yarinya,Allah ya sawwaqe,raihana jeki ku dagata" "To" ta amsawa hajiyan sannan ta ajjiye kayan hannunta tabi bayanta zuwa dakin. Tare suka daga hajjajun da budurwar mai suna fatima,taso tafiya amma fatiman ta daj tsareta da surutu,ta lura mai yawan magana ce "Taku zata zo daya da sisi na" raihana ta raya cikin ranta. Da kaya a hannunshi ya shigo dakin fatiman ta karba tana masa sannu da dawowa,raihana ta miqe tana musu sallama zata fice lokacin da yake tambayarta waya daga hajjajun ta gaya masa ita da raihana ne,tana bakin qofar ficewa ya biyo bayanta,ya cimmata lokacin da take gab da shiga nasu dakin "Amma ai ko godiya kya tsaya 'yammata nayi miki ko?" "Wa ya gaya maka ni budurwa ce?,matar aure ce ni" ta fada don ta soma lura da take takensa,dariya ya saki kana yace "Ni kuwa bakiyi min kama da matar aure ba sam,amma tunda kince haka muje a hakan,nima mijin aure ne" "Mun gode Allah ya saka da alheri,kuma don Allah idan ba zaki damu ba zan iya samun lambar wayarki?"kai ta kada ta tura qofar dakin nasu tana shirin shigewa tace " bani da waya"sannan ta maida qofar ta rufe. Idanun hajiya na kanta "ke da waye kike cewa baki da waya" kamar ba zata amsa ba sai kuma tace "Wani ne hajiya" "Har yau baki bar kora samari ba kenan raihana,kada ki manta kefa ba yarinya bace,hakanan wanda ya mutu baya dawowa,ya kamata ki haqura hakanan ki barwa Allah lamarinsa ki fidda wani mijin kuma,amir ki masa addu'a Allah ya jiqansa ya gafarta masa ko?" Shiru tayi tana hadiyar zuciya,itakam ta gaji da wannan walagigi haka,tana buqatar bigire guda da zata tsauda zuciyarta kota hutashshe da kanta da zuciyar tata ma. Sosai fatima ta dinga shige musu,da yake mai surutu ce itama sai nan da nan aka saba da ita,musamman rumana data samu abokiyar yi,su hajiya babban aka fara sallama don haka suka tattara komatsansu suja barsu a asibitin. Ranar farko da ya soma kiranta tayi mamaki sosai kan inda ya samu lambar wayarta,daga baya kuma tayi zaton fatima ce ta samar masa gun rumana,don data tambayeta dariya ta dinga yi tace kawai ki bashi dama. Saurarensa kawai takeyi shima don ta huta da surutun taqi kula kowa,amma ji take sam bai mata ba,yadda taji amir ko rabin haka bata ji ammar ba,amma ko banza yana debe mata kewa,saboda mutum ne mai iya labari tsara zancan da ban dariya,wannan dalili yasanya lokaci lokaci idaj taso ta kan daga kiran nasa,duk da shima din ba mai damun mutum bane a waya,don ko gidansu bai matsantawa sai yazo,idan ya tambayeta yaushe zaizo tace ba yanzu ba,yace sai yauahe tace sai nan gaba yakance to Allah ya nuna mana lokacin,hakan kuwa yana mata dadi sosai. Sosai fatima suka saba da rumana,don tana ziyartarsu lokaci lokaci,duk sanda kuwa zata zo din baka rasata da wani saqo daga hajjajunsu,ta lura matar na sonta sosai,hakan 'yan gidansu ammar din suke sonta,abun har mamaki yake bata yadda suke nuna mata qauna,amma fatima tace yayan nasu ne yakai shekara kusan talatin da takwas babu aure,kuma shine babba a maza,hakanan bai taba kawo wata yace yana so ba,kullum zancansa aure lokaci ne,da kawunsusu ya matsa masa ma zancan aure sai ya fara wasan buya da shi,bai yarda su hadu,da yake shekara goma baya Allah ya yiwa babansu rasuwa,hakan da fatima ta gaya mata yasa ta rage mamaki kan yadda suke nuna mata qauna,don ba wanda fatima bata zo da shi ba yaga anty raihana . Rana ta farko data yarje masa ya ziyarceta tare suka zo da abokinsa ko ace amininsa wato maisara,komai nasu iri daya hatta da takalmin qafarsu,hakan shi ya shaida mata qarfin amintar dake tsakaninsu,ya iso mata hannunshi fal da tsaraba daga hajjajunshi,tana mamakin yadda hajiyan ke sonta da ji da ita,amma ba abun mamaki bane yadda ta lura cewa hajiyan naji da ammar din bisa ga dukkan alamu "Abokina,nifa inaga ayi abun nan da wuri fa kafin kwado ya maka qafa" cewar maisara kenan wanda ke duban ammar,ajiyar zuciya ammar din ya saki yana duban raihanan "Nima abinda nakeso kenan abokina,saidai gimbiyar ce har yau nake ga kamar ban karbu ba,baka ga da yadda ta amince nazo mu gaisa ba?",maisara ya dubi raihana "gimbiya raihana,abokina yafa kamu da yawa,ya kamata arage masa wahalar hakanan a bashi dama ya fito ko kuwa?" Murmushi kawai raihanan tayi sannan tace "Me kuke ci na baka na zuba,gaggawa ai aikim shaidan ne,mubi komai a sannu har lokaci yayi" ajiyar zuciya ammar din ya saki sannan yace "Shikenan,Allah dai ya nuna mana lokacin" "Amin"maisara ya amsa musu. Turmin atamfar da umminta ta siya mata ta hada da turare ta baiwa ammar din tace ya kaiwa hajiyan,don ta rasa me zata baiwa dattijuwar,sukayi sallama bayan ya ajjiye mata kudi shi da maisaran amma sam taqi amsa,don bata taba yarda ta amshi kyautarsa ba tace ta hajiyan ma ta isa ************** A qalla sun shafe awanni kusan biyu suna waya,raihana na kwance saman gadonta tana duba wata jarida da abba ya gaka dubawa da safe ya bata,don idan ya gama din dama ita yake baiwa,don ya santa da maitar karance karance. Tayi nisa cikin tunani har rumanan ta iso gareta bata sani ba,sai da ta sanya hannu ta bubbuga bayanta sannan ta dago " haba sisi?,karatu ko tunani?" "Amma jarida kika gani a hannu na ko 'yar rainin hankali" dariya rumanan ta saka tana cewa "Allah ya baki haquri,idan ma tunanin ammar kike wa ya isa ya hanaki,ungo nan yaya rayyan ne yace na baki wayar,yanata kiran naki layin is switched off" kamar tace ba zata karba amma don kada rumanan ta nemi ba'asin abinda yasa wanda bata da amsarsa yasa ta karba din,tana sane ta kashe wayar don taga saqonshi na zai kirata anjiman,juyawa rumanan tayi ta fice tana cewa "Bari ka dauko mana abincinmu". Ringing wayar ta dinga yi tana hannunta amma ta kasa dagawa,yadda bata daga ba haka bai fasa kira ba har kusan minti biyar gajeran saqo ya shigo "Mafi kyau shine ki daga kira na,idan kika qi kuwa duk abinda zai biyo baya kada kiyi kuka da ni" da hanzari ta goge saqon wanda garin hakan har wani kiran ya shigo ta daga bata sani ba,ganin kiran ya dagu din ya sanyata karawa a kunnenta. Shiru tayi ba tare data ce komai ba "Ba maqaryaciyar soyayya nake miki ba wadda zata sanyani barinki da wuri haka duk da qoqarinki na nesanta kanki da ni" karo na farko muryarsa ta daki dodon kunnenta tun bayan watanni biyar da sati biyu daidai da tayi rabon da taji ta,murya ce ta musamman cikin kunnuwa da zucuyarta,bawai don tana sonshi ba,a'ah,tunda can dama yadda Allah ya masa baiwar kyau kwarjini haka yayi masa baiwar dadin murya "Koda ba zaki amsa ba zan isar da saqona gareki,ina sonki har yau raihana,son da nake miki bai taba canzawa cikin zuciyata ba daidai da second guda,ina mai miki albishir din ki saurari isowata nan da sati biyu in sha Allah,bance ki sanarwa kowa ba,kema din don na sake tunatar dake alqawarinmu,ko ince alqawarin da na daukawa kaina wanda nake tabbatar miki wannan karon babu abinda ya isa ya sauyashi banda qaddarar Allah,kiyi bacci mai kyau sahibata" ya qarashe zancansa yana mai kissing din wayar wanda ya ratsa kunnenta zuwa gangar jikinta,ya kuma haifar mata da tashin tsigar jiki wadda ke cakude da tsoro da fargaba,rayyan na nufin nan da sati biyu ya dawo?,hakan na nufin bayyanuwar wani babban asiri dake rufe?,wannan na nufin bayyanar soyayyar da rayyan ke mata ga rumana,abba,ummu da duka sauran iyalin guda uku?,wannan na nufin zata iya zama matarsa kishiyar rumana?,kai ta dinga girgizawa ita kadai tana ji har cikin zuciyarta ba zata iya lamuncewa hakan ba,ba zata iya lamuncewa kallon da duniya zata mata ba,ta tabbatar cewa mutane ba zasu taba bin ba'asi ba,mutane ba zasu taba yi musu uziri ko adalci ba,zasu kallesu ne a butulu maciya amana,a ma ture ta mutanen,shin da wanne ido ita rumana zata dubesu su duka biyun?,ta gwammace da hakan ya faru gwara ita ta rasa farincikinta,kai bama farincikinta ba har zuciyar tata a shirye take ta SADAUKARWA rumanan da su baki daya. Batasan yadda ta iya sauke wayar daga kunnenta ba,ta dai samu kanta da rarumo wayarta ta kunnata,cikin 'yan daqiqu kadan komai ya hau satinsa,ta lalubo lambar ammar hannunta na rawa ba tare da wani dogon tunani nazari hasashe ko hangen nesa ba ************** Kusan dakin cike yake da mutane kowa na nashi harkan,wanda hakan ya kawo cikar dakin da hayaniya da surutai,wanda raihana dake kwance quryar gadon rumana cikin dakin nasu take jin tamkar hayaniyar kasuwannin duniya aka hada cikin dakin,hayaniyar tasu babu abinda take bisa kanta sai sukar qwaqwalwarta,wani irin yanayi taji ta shiga tamkar zata bar duniya,sosai jikinta ke wani irin rawa wanda ta tabbatar da a tsaye take babu abinda zaya hanata zubewa qasa warwas. A hankali zuciyarta ta dinga wani irin bugu da bata taba jin makamancinsa ba,jikinta ya saki baki daya,sannan idanunta suka dinga lumshewa a hankali lokacin da kunnuwanta suka jiyo mata sanarwa a tsakar gidansu,kunnuwanta basu daina jin amsa kuwwar maganar da mutumin ke fada ba har sai da idanunta suka kammala rufeqa ruf ta daina ji ta daina gani. Zaune yake cikin daya daga cikin mitocin airphort da ya dauko don ta kawoshi gida,wani irin zumudi yake ji na ya isa gida tamkar zaiyi tsuntsuwa,sai ya danganta hakan da son ganin irin farincikin da ummunsa har ma da abbansa zasuyi idan suka ganshi,mamaki yakeso ya basu,hakan ne ya sanya bai sanar da kowa ranar dawowarsa ba idan ka dauke raihana,gefe guda kuma na zuciyarsa lokaci lokaci na qara gudunta kan wanda take da shi,lumshe idonsa yake ya dafe zuciyar yana tunanin maganar da yake shirin bayyanata a yau ne take zullumi. Ya bude idonsa daidai lokacin da yaji mai motar ya tsaya "Yallabai saidai fa muyi parking dole a nan,idan yaso sai na taimaka maka da kayan zuwa qofar gidan naku,don naga layin a cike yake da alama taro ake" a hankali ya dinga bin layin nasu da kallo ba tare da ya furta komai ba,tabbas taro ake,kuma taron yafi kama da na daurin aure,saboda maroqa da yake hangowa,hakanan tufafin mafiya yawan mahalarta taron fari ne,saidai amma bai gane a ainihin wanne gida cikin layin nasu ake taron ba,murya a sarqe yace da driver din "Ok,ba damuwa" ya fada yana bude qofar tare da fitowa a kasalance. . A hankali ya dinga ratsa mutanen yana wucesu,sai ya dinga ganin daidaiku wadanda ya sansu amma babu wanda yacewa qala haka har ya kutsa cikin gidan,a bakin get sukayi kacibus da abbansa na fitowa cikin manyan fararen kanya,tsayawa yayi yana dubansa "Ikon Allah,kace kai kana tafe,yanzu yanzu muke maganarka nace qila cikin satin nan ko satin gaba zaka dawo ashe ma kana hanya,shi yasa nayita neman wayarka jiya da shekaran jiya kenan bata shiga,saika qarasa ciki yau gidan a cike yake" abban ya fada yana yin gaba,shima din bai iya cewa komai ba baida karsashin yin magana ma ya cusa kansa ciki. Kai tsaye dakinsa kawai ya lalubi maqullansa cikin aljihun trolly dinsa ya bude ya shiga,takalmansa ya watsar sannan ya jingine jakar tasa tare da fadawa saman daya daga cikin jujerun falon dafe da kansa da haka kurum yaji ya fara sarawa. Mamaki ne sosai ya kama rumana data wucewa ta qofar tasa ta ganta a bude,cikin wasi wasi ta nufi gun ta tura qofar,mamakinta ya sake daduwa ganin rayyan din zaune,murza idanunta tayi ta juwa tabbatar shine,sai ta saki wani dan ihun murna tare da tsalle tayi gurinsa,a hanzarce ya dago kansa,miqewa yayi ya bude hannayansa ta fada ciki tana cewa "Da gaske yaya rayyan kaine don Allah?" "Nine mana rumana" ya fada muryarsa can qasan maqoshi "me yasa baka fadi kana dawowa ba,ban tanadar maka komai ba,gashi kazo ka tadda mu cikin hidima kaima bakasan da ita ba,munata neman layinka mu gaya maka baya shiga hankalina ya tashi sosai" sai a lokacin ya samu kuzarin yin magana,a gaggauce yace "Me akeyi?,naga gidan duk mutane" "Nima sai na baka mamaki yadda ka bamu,daurin auren sisi na ake" "Sisinki wa kenan?" Ya tambaya cikin jirkicewar tunani,baki ta dan zumburo ba tare data kula da shi ba don kanta na qirjinsa "Kaji yaya rayyan,wace sisin nake da ita bayan RAIHANANMU" *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and _________________ _____ *Daga abdullahi dan umar R.A yace:manzan Allah s a w yace"ku biya dan qwadago(ko wanda ya muku wani aiki)tun guminsa bai bushe ba"* _ibnu majah ne ya rawaito_ _______________________ *Babi na ashirin da shida* Wani abu yaji ya soki zuciyarsa "Ya salam" ya bata can qasan maqoshi da murya kamar ta dan maye yana dafe da qirjinsa,take jikinsa ya dauki rawa yaji tsaiwar ma na neman gagararsa,rumana dake jikinsa ta dago tana dubansa jin yadda jikinsa ke rawa ta fara tambayarsa a rude "Yaya rayyan lafiya?" "Zaunar da ni ruma,kaina da qirjina" cikin sauri ta kamashi ta zaunar da shi saman kujera tana jero masa sannu "Yaya dama baka da lafiya?" Kai kawai iya daga mata,ji yayi duniyar na juya masa hakan ya sanya ya maida bayansa saman kujerar ya kwanta rigingine,rawar da jikinsa yake bai fasa ba,lokaci guda wani azababben zazzabi yayi masa kirif,hatta da numfashinsa huci yake fiddawa,idanunsa tamkar wanda aka gambadawa yaji haka suka koma jazur da su. Ba qaramin tashi hankalin rumana yayi ba cikin rudewa tace masa "Yaya,ko nayi kiran abba muje asibiti?" "Kada kimin kiran kowa,bana buqatar kowa" ya fadi idanunsa a rufe,shi kadai yasan kalar azabar da qirjinsa yake masa,wani suya yake masa tamkar an zuba masa garwashi,wani kumburi yaji zuciyarsa na masa kamar zata fashe ta fito. A hankali yanayin da yake ciki ya soma ta'azzara,rumana ta tsorata sosai,abun tamkar jinnu, ganin yadda rawar sanyin da yake ta fara jijjiga kujerar da yake kai tamkar wanda ke shirin yin jijjiga,babu shiri ta miqe a gigice ta fito don neman dauki. Harabar gidan babu jama'a da alama 'yan daurin auren sun gama watsewa,karo sukaci da abba wanda ke tsaye yana sallamar likitan daya gama duba raihana yanzun wanda ta suma,babu wanda ya kula cikin jama'ar dake dakin har sai da ummu ta shigo neman rumana ta tabata taji shiru,sai data kai hannunta fuskarta ta lura numfashi baya fita "Abba,yaya rayyan,yaya rayyan" rumana ta fadi tana nuna bangaren rayyan din da yatsunta idanunta na fidda hawaye cike da tsananin rudewa "Me ya samu rayyan din umma rumana gayamin" "Abba baida lafiya,don Allah kazo ka gani kada ya mutu" jin hakan ya sanya abban sanya kai bangaren nashi tare da yiwa likitan umarnin ya biyoshi. Yanayin yadda yaga rayyan din ya sanya yace da abba "Shikam bai yiwuwa na dubashi a nan,abinda zaifi kyau mu daukeshi mu wuce da shi asibiti" ba tare da bata lokaci ba abban da likitan suka kama rayyan din suka fice da shi. Gaba daya gidan sai ya koma na jajjabi,wadansu ma basusan da dawowar rayyan din ba sai lalurar tashi wanda suka fi danganawa da cewa dama can baida lafiya ne ya taho gida a hakan "Oh Allah mai yadda yaso mai juya lamura,dazu dai muna cikin farincikin daura auren raihana tashi daya kuma ya juye ya koma mana tashun hankali,ya Allah ka kawo mana da sauqi"cewar maman rumana " babu yadda Allah bai iya ba ai,da mutuwa ce ma haka duka zata zo mana ba zata"inji ummu. **************** Zaune take gaban raihanan wadda keta bacci yayin da qarin ruwan ke shiga jikinta a hankali,jin duniyar take gaba daya ta quntace mata guri daya,rayyan ba lafiya raihana ma haka?,har gwara jikin raihana ma da kyau akan na rayyan din,don shi tun jiyan bai farfado ba,tana zaton hakan ne ma ya sanya su abba suka hajata zuwa ta ganshi. A hankali ta sanya hannunta ta share hawayen fuskarta kana ta miqe don shigewa bandaki ta daura alwalar sallar azahar sai taga raihanan ta bude idanunta,ta dawo da sauri ta koma ta zquna a inda ta tashin,fuskarta dauke da dan murmushi tace "Yauwa sisi,don Allah ki tashi ki warke hakanan,na rasa da wanne zanji,da cutarki ko data yaya rayyan" shiru tayi tana duban rumanan din bata san ya dawo din na,hakanan batasan me ya sameshi ba,wai rayyan baida lafiya shima?,take ta dinga jin ya kamata ta warke din don kauda zargi,ya kamata ta warke don hankalin rumana ya kwanta,ya kamata ta warke don kowa yasan matsayinsa,kowa ya kama rayuwar da Allah ya riga ya tsara masa "Me ya samu yaya rayyan din?" Ta girgiza kai cikin sarewa "Nima ban sami ba har yau,don abba ya hanani zuwa,idan da lafiyarki qalau nema nasan zaya barmu muje mu biyun". Sai ta saki murmushin qarfin hali,ta tattaro duka ragowar qarfin da ya rage mata ta yunqura ta tashi rumana na cewa tayi a hankali "Na riga da na warke fa sisi kada ki damu,taimaka ki zaren ruwan nan na shiga bayi" a hankali ta kama hannun nata ta cire mata ruwan kamar yadda likitan ya nuna mata,ta kamata don taimaka ta miqe sai ta yi dariya kana ta tsaidata "Nifa da qwarina,bari kiga" tayi maganar tana yunqurawa tare da miqewa cikin dakiya,ji take iska na yawo da ita amma haka ta daure ta shige bandakin,wani dadi ya kama rumana ganin raihanan ta miqe har ta taka da kanta,fatanta Allah ya sanya rayyan ma haka. Ta fito daga bandakin a hankali rumana ta dubeta "Yan gidansu ammar nata zuwa sisi,hankalinsu ya gaza kwanciya,gaskiya ki godewa Allah,sun kasa sukuni gaba daya amaryarsu ba lafiya" murmushu tayi tana zura hijabin da rumanan ta miqo mata,ita kanta ta dade tana yaba irin qaunar da suke mata,ko donsu zata zauna da dan uwansu zama na gaskiya da amana *********** Ajjiye file din likitan yayi bayan ya gama 'yan rubuce rubucensa a jiki,a hankali ya tako ya iso bakin gadon da rayyan din ke zaune bayansa jingine da filo ya zauna gefansa. Dubansa yayi na 'yan wasu daqiqu sannan yace "Rayyan" kai tsaye saboda abokinsa,abokin da zai iya kira kai tsaye aboki na kusa da shi sosai wanda sukan iya musanyan ra'ayi shawarwari da kuma sirrika,abotarsu ta samo ne tun tafiyarsa england na farko,inda suka hadu da shi mukhtar da amir. Bai amsa ba face daga shanyayyun idanunsa da yayi ya dubeshi,yasan babu lallai ya amsa din saboda haka ya dora "Wacce iriyar damuwa ka shiga haka lokaci guda mai zafi wadda take barazana da lafiyar zuciyarka?me yasa kake son cutar da zuciyarka?" Mai makon ya amsa masa sai ya hau girgiza kai na tsawon lokaci ba tare da ya furta ko kalma daya ba "Rayyan,ni abokinka ke ta wani bangare amininka,ka gayamin me ya sameka ko meke faruwa da kai?,barin kashi a ciki baya maganin yunwa" tabbas haka maganar take,saidai duk sanda ya rasa ta yadda zai iya furta maganar,saboda duk lokacin da yayi yunqurin hakan sai yaji wani abu yazo ya tokare masa qirji,numfashinsa ya hau kai komo ya fara jansa da qyar. Ya dade idanunsa a rufe hannayensa cikin na mukhtar,a hankali kuma karon farko yace "Laifi nayi don ka sota kuma naso 'yar uwarta wadda ba ciki daya suke ba?,laifin me na mata ta yanke mana irin wannan mummunan hukuncin?,wanne irin tsana ta yiwa tarayyarmu da ta yi mana wannan kisan mummuqen?" "Wacece?" Mukhtar ya tambayeshi kai tsaye "Mukhtar raihance.....raihana ta qini saboda rumana......" Sai maganar ta maqale masa,wani abu ya tokare masa qirji,nauyi yaji an azawa qirjinsa wanda ya sanya shi jan numfashi da qyar,abun yayi matuqar bawa mukhtar tsoro,a tsorace ya dinga cewa "Kabar idanunka suyi kuka mana rayyan ko zaka ki sanyi,kada ka bari ciwo ya kamaka rayyan pls mana". A hankali wasu siraran hawaye suka fara zirya bisa fuskarsa,jikin mukhtar din yayi tsananin sanyi,ya riga da ya dade da sanin waye rayyan,jarumin gaske da bako wanne abu ke saurin karyashi haka ba,saidai baiyi mamaki ba,so yana da qarfin da zai iya karya dukkan wani mutum komai girma da qarfinsa kuwa,kusan zai iya cewa bai taba ganin karaya ko hawaye tattare da rayyan ba,sai yau karon farko a tarayyarsu. Hawayen na sauka ne tare da radadi da zugi mafi tsoka da zuciyarsa ke masa,sai ya dinga jin sanyi na sauka cikin zuciyarsa,fiye da rabin nauyin da qirjinsa yayi ya zabge,mintina kusan talatin kafin ya sanya mukhtar ya taimaka masa ya miqe tsaye,da kansa ya shiga toilet ya daura alwala sannan ya dawo inda ya zauna ya tashi yana duban mukhtar " ya riga ya wuce mukhtar,qaddara ta riga fata,raihana ta zama matar wani,bai da muhalli ci gaba da tattauna maganarta,Allah ya riga ya qaddara hakan ce zata kasance,abinda kawai nakeso daga gareka kada ka gayawa kowa cewa damuwa ta kwantar da ni,ko wanene,maganar ta tsaya iya mu biyu" Kai mukhtar ya jinjina "Ko baka fadi haka ba akwai sirri tsakanin likita da mara lafiyansa,Allah ya sanya haka shi yafi alheri gareku baki daya" "Inaso ka rubutan sallama,inaso na koma gida hakanan,yau kwanan biyar a asibitinku,inata sa mutane zirga zirga,kuma nima na gaji hakanan" murmushi mukhtar din ya danyi "Ba damuwa ai sai amarya ta qarasa jinyarka ko?" Shima mayar masa da martanin murmushin yayi ba tare da yace komai ba **************** Gaba daya ta tattara qarfin qwanjinta dana zuciyarta ta hana kanta yin wani motsi da zai bayyana halin da zuciyarta ke ciki,ta gayyato walwala farinciki da sakewa ta azawa kanta,ta dauki duk wani abu da ya faru a baya a matsayin mafarki ko almara,wani lokacin tsantsar qarfin hali takan nuna a fili tamkar tafi rumana kuzari da walwala,saboda har yau rashin komawar rayyan daidai ke mintsinar zuciyarta. Kusan tunda ya dawo gidan shima yayi namijin qoqarin maida komai ba kamai ba,musamman duk lokacin da tunaninta ko wani abu yaso tasiri a kansa,yakan tunawa kansa da jaddadawa kansa matar wani ce a yanzu,dukkansu gudun juna suke,don kowa baya bari ya hadu da dan uwansa,shi iyakarsa da cikin gidan ya shiga ya gaida ummunsa,gadan gadan ya tayar da aikin gyaran gidan da na nashi gidan baki daya,cikin sati biyu komai ya kammala,gidan ummun ya koma sabo,sati na gaba kuma suka sanya za'ayi sauran shagulgula irin na mata. Ba qaramin rawar gani daddy dalhatu yayi ba,don kowa ya gwagwaje kowaccensu da kayan jere na gani na fada,kowacce set bibbiyu ta samu,yayin da umminta daga maiduguri ta musu komai na kayan kitchen da kayan humara da turaren wuta,maman rumana kuma duka sauran tarkacen qyale qyale da sauran abinda ba'a rasaba ita ta hadasu. Cikin gidansu ammar aka yi mata jeranta,da yake gidan akwai girma,part ne guda yalwatacce wanda ya cinye duka kayanta,ita din ma hakan ya mata dadi,tunda ko babu komai zata zauna cikin mutane,mutanen kuma dake sonta suke kuma ji da ita. Sosai rumana taso a hada dinner ta gani ta fada,saidai daga raihanan har rayyan din zuqewa sukayi,ita raihana ta bada hanzarin cewa ammar bazaya samu damar zuwa ba,yayin da rayyan yaqi cewa komai yace dai kawai baida ra'ayi,tunda ya sani dole su hade da raihana da ammar,bugu da qari har yau qarfin hali kawai yakeyi amma bai soma jinsa daidai ba. Wunin biki kadai akayi sai walimarsu ta iya su,kausar ta shaqi takaici don ba haka suka so ba,sunso su gwangwaje matuqa da gaske. Ranar lahadin qarfe takwas kowacce tana gidan mijinta,rabuwar rumana da raihana abune da babu wanda bai koka musu ba,kasancewar babu wanda baisan irin shaquwar da take tsakaninsu ba,sun rabu suna masu qauna da kewar junansu,kowanne zuciyarsa cike fal da alhinin rabuwa da dan uwansa. _kashin farko kenan ku biyoni din jin gaba ta biyu ta labarin_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Manzan Allah S A W yace"imanin dayanku baya cika,har sai ya sowa dan uwansa abinda yake sowa kansa(na duk wani abu na alkhairi)"* _______________________ *_saqon gaisuwa da fatan alkhairi ga duk fans na dangantakar zuci_* *_sadaukarwar shafi dungurun gum ga 'yan_* *Z B I* *Babi na ashirin da bakwai* Inda suka tafi suka barta a nan taci gaba da zama,kukan kam babu kalar wanda bata yi ba,fargaba take na wacce kalar rayuwa zata shiga,tabvas tasha ji daga bakunan ma'aurata cewa rayuww ce mai wuya,hakanan rayuwa ce mai cike da qalubale iri daban daban,koma meye dai itakam ta shigo cikinta da niyyar yin bauta wadda take fatar ta samar mata aljanna madaukakiya. Su biyu rak suka shigo shi da maisara,hannayensu dauke da ledoji,barkwanci na 'yan mintina maisaran ya jata da shi wanda ta gaza amsawa,kana daga bisani ya dubi ammar yace "To ni zan fa wuce,amma zo na ganka mana" "Ok muje,raihana ina zuwa" inji ammar wanda yabi bayan maisara. Tun tana kasa kunnen dawowarsa har ta janye,sai bayan shudewar awa guda sannan ya shigo,har ya sauya kayan jikinsa,ya dubeta "Au,baki tashi hakanan ba,ya kamata ki tashi ki rage gajiya ko?" Ya fada yana zama kan kujerar dake daura da ita,cike da kasala gajiya damuwa da baqunta ta miqe ta shige bedroom dinta,tayi wanka ta daura alwala,babu sallar da ake binta bashi saboda haka ta maida kayan jikinta ta dawo falon. Yana inda ta barshi,saidai wannan karon gabansa akwai plate wanda ya juye kazar da suka shigo da ita,daya hannun nashi kuma riqe yake da wayarsa yana danne danne,dubanta yayi sannan ya sauko qasa yana tura mata plate din kazar da lemo mai sanyi. Kasa sakewa tayi taci,ya lura da hakan sai yace da ita "Ki sakit jikinki,kada ki wani damu ko takura,ni babu wani abu da zan miki kinji" yayi maganar yana dubanta,tilas ta sake ta danci don kada ya sanya tunanin hakan a ransa. Ta rigashi kammalawa daya gama shi ya hada kwanukan ya maida kitchen din sannan ya umarceta taje ta kwanta. Tana tsakiyar lallausan gadon nata amma tsoro ya hana barci yayi nasarar saceta,sai data kashe kusa awa guda sannan ammar ya shigo "Baki bacci ba raihana,kiyi bacci nasan kin gaji,nima a gajiye nake" ya fada yana rabewa gefanta yaja filo ya dora kansa,tun tana dari dari har ta saki jiki jin shiru babu wani motsi da ya biyo baya,da haka nannauyan bacci mai cike da gajiya yayi awon gaba da ita **************** Tare sukayi komai da ammar din wanda kiran maisara ne ya tashesu,shi ya tayata ta sake gyara gidan tayi goge goge ta hada musu break fast,suna shirin karyawa saiga aiken break din daga hajjaju,fatima ce dauke da kwando niqi niqi "Ayyah anty dama bakiyi ba,tun dazu dama naje cewa hajiya ta kawo na kai muku tace a'ah bari rana ta dan sake dagawa,mai yiwuwa baku tashi ba kada na tasheku" murmushi raihana tayi tace "Babu komai,nikam na hajiyan ma zanci,don dama ruwan tea da qwai kawai na hada mana,kice ina gaisheta kafin na shigo" "Zata ji anty,su anty sabira ma suna gaisheki,sai anjima idan zasu koma gida zasu shigo" "Ina amsawa" ta bata amsa fuskarta qunshe da murmushi. Suna gama karyawa ammar yace zai fita maisara na nemansa,tayi masa a dawo lafiya sannan ta dawo cikin falo ta jona kayan kallo ta fara rage lokaci ganin batayi baqo ba,sisinta na ranta saidai batason musu katsalandan ta hanyar fara kiranta,'yar halak sai kuwa ga kiran nata,cikin murna ta daga,sunsha hira sosai kamar ba zasu rabu ba,sai da rumanan tace bari ta koma gun ya rayyan ta baroshi daga shi sai kayan kallo,sukayi sallama kowa ya ajjiye wayar. Da azahar ma hajiyan ce ta aiko musu da abincin rana ita da ammar din,ganin ammar bai dawo ba sai ta dibi nata taci ta ajjuye ragowar. Qarfe shida ta shiga toilet ta gyara kanta tare da sake tsala kwalliya cikin atamfa,bata jima da zama ba aka fara knocking ta bada izini aka shigo,yayar ammar ce sauda da qanwaraa sabira da yaransu guda takwas wanda manyan ciki ke riqe da kula,da fara'arta ta tarbesu suma suka amsa mata da fara'a sannan suka bata kular abincin daransu inji hajjaju,godiya tayi sosai tare da yabawa qoqarin matar,iyalan mutane ne masu mutunci da karamci,haka suka ta hira har aka kirayi sallar magariba suka ce zasu koma cikin gida don anjima duka zasu koma gidajensu,cikin kayan gararta danginsu alkaki dublan,nakiya,meatpie ta zuba musu mai yawa bayan botiki guda babba da ba zuba tace a a kaiwa hajjaju. Sai kusan qarfe tara da wani abu ammar ya shigo,ya mata sannu da gida sannan ya wuce dakinsa dake can gefe guda cikin wani corridor yayi wanka ya sauya kaya ya fito sannan ta gabatar masa da abinci,ya dinga janta da hira har ya kammala cin abincin,sukayi yi kallo na dan wani lokaci sannan suka tafi bedroom,kamar jiya yau ya rigata ma yin bacci,don haka hankalinta kwance tayi baccinta. Sai washegari mutan maiduguri sukazo saidai babu mamanta ciki,bata kuma so hakan ba,don taso ganinta kafin ta koma sukayi mata sallama kan gobe zasu wuce,tare suka wuni,sun sake sosai don yauma ammar kamar jiya bai dawo da wuri ba,da zasu tafi kamar ta bisu don har kuka tayi **************** Cikin sati biyu ta fara sabawa da sabuwar rayuwar da take ciki,tanajin dadin zamanta cikin gidan,duk da kasancewar ammar ba mazauni ba yakan fita tun safe sai dare hakan bai fiya damunta sosai ba sabida tana da 'yan tayin hira,ko tayi tafiyarta bangaren hajjajun bata dawowa sai magariba tayi 'yan abinda zatayi kafin ammar ya shigo. Sam bata damu da rashin neman ta da ammar baiyi ba,tana ganin hakan bai komai bane,mai yiwuwa yana mata uzurin rashin sabo ne ko tausayinta yake ji ************** Zaune yake cikin falon nashi wanda yake kusan daidai da aljannar duniya,gama cin abincinsu kenan ta kwashe kwanukan ta kai kitchen,kusan minti goma bata dawo ba,hakan ne ya bashi damar janyo computer dinsa ya fara wasu aiki a ciki,don har yau bayajin kuzarin da zai iya fita office. Baisan ta qaraso ba sai daya ji sallamarta,sanye take da kayan bacci baqaqe wadanda suka haska farar fatarta,abinda ya tsaidata kenan wanka tayi tayi shirin kwanciya,murmushi ua sakar mata yana jin tausayinta har cikin ransa,tana ta dawainiya da shi tana bashi kulawa,yana ji a ransa zuwa yanzu yaci ace shima yayi wani abu,ya kamat ace ya kawar da duk wani rauni dake cikin zuciyaraa wanda shike janyo masa jin raunin a gangar jikinsa. Miqa mata hannu yayi fuskarsa qunshe da murmushi Ba tare da bata lokaci ba ta sanya nata hannun cikin nashi itama,ya janyota ta fada jikinsa,luf tayi tana jin wani dadi na shigarta,don yau kusan shine karo na farko data samu irin wannan tarbar "Amaryata,naga alama rashin lafiyata ta takuraki ko,ya kamat mudan matsa daga inda muke nasan sai kinfi sakewa" murmushi tayi sannan ta dage masa gira "Ok,good,inaga zamu koma england" zaro ido tayi tana cewa "Da gaske yaya" "Na taba miki qaryane" ruqunqumeshi tayi tana dariya tare da girgiza kai cike da farinciki "Wayyo yaya na gode na gode" "Amma fa zamu dan jima" ta dubeshi tace "Kamar kwanaki nawa?" Shiru ya danyi sannan ya saki ajiyar zuciya "Eh to.....idan so samu ne idan mukaje gaskiya ba nan kusa zamu dawo ba,inaso na hada masters dina ne a can,kinga kuwa atleast zamu yi shekara biyu ko uku" ashagwabe ta dubeshi "Kuma nawa karatun fa yaya,shekara daya fa ta rage mana mu kammala"cikin tsokana ya daga mata girarsa daya " ni da karatun wanne yafi muhimmanci"dariya ta saki sannan tace "Fada ma ai bata baki ne,amma dai nima yaya da zaka sama min wata makarantar a can basai na dinga zuwa ba?" Shiru ya danyi sannan yace "Bari mu gani" sosai ya cukuikuyeshi tana ta murna. ************** Cikin sati biyu rak ya kammala musu komai na tafiya,yanajin cewa shine mafita qwalli daya da ta ragewa sauran rayuwarsa na samun sabuwar rayuwa da farinciki mai dorewa,hakanan hanya guda daya da zata sashi mantawa da duk wata qura data taso taso birne rayuwarsa. Da kansa ya dauketa ya kaita gidan raihana don suyi sallama,saidai shi bai shiga ba yace zai dawo ya dauketa. Wayyo Allah,kada kaso kaga irin farincikin da sukeyi ma ganin juna,mutanen da bacci ma baya rabasu sai gashi aure yasa sun kwashi kusan watanni biyu rabon da suga juna,wuni sukayi hira ko abinci basu bi ta kaiba,sai fatima ce ta agaza ta dafa musu,yadda raihanan ta canza haka rumanana,saidai rumanan ta fita canzawa sosai,don har wani qiba ta fara yi. Sosai raihana tayi murna da jin tafiyar tasu,tana fata wannan shine ragowar murfin rufewar case dinsu rufewa ta har abada,addu'a ta musu sosai tare da fatan samun kykkyawar rayuwa mai dadi. Yamma lis rayyan ya dawo daukarta don zai kaita gidansu can na suyi sallama,sai data shiga ta gaida hajjaju sannan raihanan ta rakota,sun gaisa tamkar kowanne dan uwa da dan uwansa,don ko kallo cikakke babu wanda ya yiwa dan uwansa,tana daga musu hannu har suka fice. Sashen hajjaju ta koma don kota koma sashen nata bata da wani abunyi,har ya zame mata jiki rashin dawowar ammar din akan kari,ta taddasu fatima a kitchen nata kici kicin kwaba alkubus ta rasa yadda zata sarrafa,hajiya na gefe tana sille mata,raihana tayi murmushi ta karbi bowl din ta fara kwabawar "Hajiya Allah dai ya ceceni baquwar anty ta tafi gashi ta fansheni,don Allah kada ki cewa su nasir bani na kwaba ba yau na shiga tara a gidan nan,zan tsaya dai naga yau yadda take kwabawar yake tashi yayi kyau" "Dadai ya fiye miki" inji hajiyan ta fice ta bar musu kitchen din. Basu bar kitchen din ba sai da suka gama kwabin suka dora sannan suka dawo falo,raihana ta bawa fatiman kanta tace ta kitse mata ki guda shida ne don ya dameta,bayan sun kammala girkin fatiman tace basai tayi nata ba,ta dauko flask din ammar ta diba musu ta kai mata har sashen nasu. Haka suke zamansu mai dadi ita da surukan nata babu sawa babu fitarwa,wani lokaci ka tana iya cewa tafi jin dadin zama da su fiye da ammar din,wanda tsakaninta da shi umarni ne da hani,ba mugunta ko cutarwa dai tsakaninsu,ci sha sutura da tufafi kudin kashewa saidai ta baiwa wani,hakanan ya siya mata mota ya ajjiye mata driver kasancewarta ba maison tuqi ba,hakanan duk abinda takeso ko takeson zuwa waya kawai zata masa ya barta,saidai baisan damuwarta ko matsalarta ba,sau tari da hajjaju data dauka kamar uwa ko fatima data sanwa matsayin rumana take shawara,da safe yake fitarsa bai shigowa sai tara ko goma,da yayi wanka ya ci abinci sai bacci sai kuma wata safiyar. Kullum ta Allah sai tayi waya da sisinta,amma ko sau daya bata taba cewa da ita wani abu ba,ganin yadda ta samu kwanciyaf hankali kada ta daga mata hankali ko ta sata wani tunani ja daban,duk da itama bata ajema ranta wani abu can ba,kawai ta barshi ne kan cewa harkar kasuwancinsa ne suka sha masa kai suka fi qarfinsa *************** Sannu a hankali rayuwa ke miqewa tana tafiya tare da juyawa da bawa yadda Allah yaso. Shekara guda kenan da aurensu inda take lissafin zama cikakkiyar lauya nan da 'yan watanni masu zuwa,zuwa lokacin ta fara dora ayar tambaya a kan zamanta da ammar,koda wasa bai taba marmarin rabarta da niyyar sauke haqqin aure ba,bawai damuwarta ce hakan ba,amma ta riga data sani babu wani aure da aka taba ginashi ya tafi a haka,nauyi da kunya irin ta 'ya mace ta hanata tunkararsa ko sau daya da maganar,ta maida hankalinta kan al'amuranta wanda duk ciki kowanne yake tafiya mata daidai cikin taimakon Allah. Bata fara damuwa ba sai da ta lura da yadda su fatiman ke maitar ganin 'ya'yan yayan nasu,haka yake ga hajjaju ma don ita bata taba nunawa ba ma,amma ga mai hankali ya isa ya gane,duk da ba wani canji suka nuna mata ba amma tana jin damuwa cikin ranta,damuwarta bata dadu ba sai da ciki ya bayyana jikin rumana,tayi farinciki tayi murna tayi dariya duka ita kadai,ji take tamkar itace zata haihun,don dan sisinta nata ne,a lokacin ne taci damarar tunkarar ammar da maganar ************** Sanye take da kayan bacci ruwan madara,riga ce doguwa wadda ta zarta gwiwarta mai hannun best sai 'yar samanta mai digon hannu mai wuyan v shape,tsawonsu daya da ta ciki da ta wajen,kayan sun mata kyau sosai,jikinta nata qamshin turaren maidoguri,kusan duk dare shigarta kenan,amma bata taba ganin ammar ya kalla sau uku ba,duk da hakan bata fasa ba don tana ganin tana yin abinda ya dace ne. Kamar ko yaushe ta taras da da shi a falo ya kammala cin abincinsa suna waya da maisara wanda duk dare bayan ya dawo sai ya kirashi,tana gefansa har ya kammala,ya dubeta yana gyara zamansa "Ya akayi ne gimbiya" murmushi tayi kawai ta kauda kai"kamar gaske ta fada cikin zuciyarta" "Naga alama bakin nan naki akwai magana" ya sake yin maganar yana danne danne a wayarsa,gyara zama ta sakeyi sannan ta dubeshi "Haka ne,amma dai labari nazo in baka" "Uhmmm,gaya min Allah ya sa alkhairi ne" "Shine ma" ta fada ataqaice sannan ta dora "Kasan sisi na ciki gareta wajen watanni biyar baya?" Ido ya zaro yana dubanta "Haba don Allah" cikin qarfin gwiwa ta kada kai "Wallahi Allah" sai ya sake maida kansa ga wayarsa "Kai amma fa na musu murna" "Bama ita kadai ba,yawanci sa'annin bikinmu wasu sun haihu,wasu sun kusa...." Sai ta dan tsagaita tana jan numfashi ko zata ga wani canji tattare da shi,babu abinda yace illa "Amma sunyi qoqari" maganar taji wani bawai,amma sai ta dora din da abinda takeson cewa "Nace ammar baka sha'awansu don Allah,baka sha'awan kaima ace ga yau ga danka na cikinka" dubanta yayi kana ya sake dauke kansa still dai bisa wayarsa "Hmmmm,ina so man" "Amma banga ka dauki hanya ba ai,tunda dai ammar 'ya'yan nan ba a kasuwa ake zuwa a siyosu ba,ba kuma a ruwa ake sha ba,baka taba kama hannun matarka da wani manufa ba,to ta ina kake so mu samu zuri'a?" Shiru yayi ba tare da yace komai ba yana danne danne a wayarsa,har tayi zaton bazaice komai ba sannan ya ajjiye wayar gefansa ya kalleta "Amma dai raihana babu abinda kika nema kika rasa cikin gidan nan ko?,me zai hana mubar wannan maganar" kai ta shiga kadawa "Wannan kadai ba shine aure ba,idan shine aure da sai nayi zamana a gidanmu ba tare da na dora maka nauyin ciyar da ni ba" sai ya harde hannayansa guri guda yana kallonta "Yanzu kenan sha'awa ke damunki" sai tambayar ma taso bata dariya "Ko kusa,amma ammar babu wanda zaiyi aure baiso ganin jininsa ba,burin duk wanda yayi aure shine ya samu zuriya,ko bayan haka laifi nayi don naji wani feelings a matsayina na wadda ke da miji kuma shekarunta suka kai?" Tayi masa tambayar kanta tsaye tana zuba masa idanuwa,sai ya kasa ci gaba da kallonta saboda kwarjinin da idanunta suka mata,yayi shiru yana nazari sannan daga bisani yace "Nasan kinyi haquri kuma kinyi kawaici,amma ki dada,ban da lafiya ne kuma ina kan neman magani" sai duka jikinta yayi sanyi,tausayinsa ya kamata,idanunta suka cika da hawaye,cikin rauni tace "Ayyah kayi haquri ammar,ban sani ba,me yasa baka gayan ba tuntuni,da ka gayan da bazan ma tambayeka ba,Allah ya baka lafiya yasa kaffara ne a gareka" "Ameen,na gode" ya fada yana miqewa tare da cewa zaije ya kwanta ya wuce ciki. Ta dade zaune a gun jikinta a sanyaye,tausayinsa ta dinga ji sosai,ta dinga nadamar ma yi masa maganar data yi,sai daga bisani itama ta miqe ta bishi. . Cikin lokutan kanta ya dauki zafi sosai semester tazo qarshe,karatu take tuquru saboda ta samu ta fidda sakamako mai kyau,sau tari a gajiye take dawowa gida,gurin hajjaju ma wani lokaci suke karbar abinci da su fatima keyi. Cikin nasara ta kammala jarrabawar sai kuma sauran tsarabe tsarabe da kan biyo baya. **************** Cikinta na shiga wata na tara rayyan ya dawo da ita gida don ta haihu a nan bisa umarnin ummu,saidai shi bai samu zuwa ba sai zata koma zaizo su tafi tare. Randa ta iso washegari raihana ta yiwa gida tsinke cikin motarta,a falo ta samu rumanan na zaune,gaba daya ta zama wata 'yar lukuta,dariya raihana ta dinga mata tana tsokanarta "Yar tsalle haka kika koma?" Itama rumanan tayata dariyan ta dinga yi har sukayi suka gama sannan suka hau hiran yaushe gamo. Sunci abinci sun ture kwanukan gefe lantana mai aikin da rayyan yasa aka samawa ummu zata zo ta kwashe,kallon raihana sosai rumanan keyi har sai data gaza shiru "Amma sisi kina lafiya?" cikin yanayi na rashin fahimta tace "Kamar yaya kenan?" " Kin sauya ne sisi,duk da fatarki ta nuna kina cikin hutu da jin dadi amma yanayinki ya qaryata hakan"sai ta saki murmushi harda 'yar dariya cikin basarwa "Da a watannin baya kika zo ba zaki fadi haka ba,ko kin manta ban fi sati uku da gama jarabawa ba,kin kuma san yanayin karatun namu ba sauqi,bani da kwanciyar hankali fa har sai dana kammala ta" jinjina kai rumanan tayi tana murmushi "Au kuma fa hakane,amma naji dadi da nayi zaton ko da matsala ne" "A'ah,babu wata damuwa kamar yadda nake miki fata kema babu" murmushi ta kuma yi sannan ta dafa hannun raihanan "Duk inda ake neman miji na qwarai sisi na yaya rayyan ya kai,namiji ne wanda ya amsa sunansa ta kowanne fanni" ta kanne mata ido"idan nace miki ta kowanne fanni hakan nake nufi"sai suka saka dariya don ta fuskanci inda zancan nata ya dosa,ta katse dariyar ta dora "Matsalata daya ce idan ma akwaita,wani lokaci sai naga yaya rayyan din cikin damuwa,idan zanyi tambayar duniya yakan ce min babu komai,wani lokaci yace ba damuwa bace mai amfani da zai sanar dani,sai ya wuni ya kwana haka,sai daga baya kuma don kansa ya koma normal" shiru raihanan tayi zuciyarta na son fara wuce qa'idar gudunta. A hankali ta sauke numfashi sannan tace "Bai kamata ya barki cikin damuwa haka ba,amma ina ganin tunda damuwar tasa ya riga ya sanar dake ba wata muhimmiya ko mai amfani bace ki haqura da saninta,tunda bai tauye wani abu daya na rayuwarku ba ko?" "Haka ne,kawai bana son ganinsa cikin damuwar ne" ta danyi murmushi "To ya za'ayi,babu dan adam da zai rayu baida damuwa totally,bare ma maza wani lokaci wani abun nasu basa bari ka sani wani haka attitude dinsa yake,kici gaba da addu'a da godiya ma Allah" "Haka ne sisi,to Allah ya bamu dacewa" "Amin ya Allah" daga haka suka dora wata hirar Bata bar gidan na sai wajen takwas na dare,tamkar kada ta tafi,tamkar su zauna da sisinta kamar yadda suke a da,saidai babu dama haka ta baro gidan cikin kewa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga ibn abi aufa R.A yace:"munyi yaqi tare da manzan Allah S A W yaqunquna guda bakwai muna cin faara"* _bukhari da muslim ne suka rawaito_ _____________________ *Babi na sha takwas* Ranar lahadi da safe rumana ta sauka,a lokacin raihanan na bangaren hajjaju taga kiran wayar ummu,wani tsalle ta saka har da juyinta,fatima ce ta shiga tambayarta me ya faru? "Munyi 'ya fatima,na zama mama" tunda ta fadi haka ta fahimci wadda ta haihun,murna suka taya ta har da hajjaju,ba tare da bata lokaci ba ta daga waya ta kira ammar,missed call uku bai daga ba,har ta qagu ta samu gu daya ta zauna tana addu'ar Allah yasa yaga kiran. Shudewar minti kusan goma ya biyo kiran,ta gaya masa haihuwar tare da neman izinin zuwa,yace ba komai saita dawo ta gaishesu,toilet ta fada kai tsaye cike da zumudi ta sake wanka sannan ta sauya kayan jikinta,cikin mintina qalilan ta kammala komai ta rufe sashen,kai tsaye bangaren hajjaju ta wuce don ta miqa musu muqullin,da yake idan zata fita can take bar musu key din. A parlourn ta tadda sauda da yaranta,bata ji shigowarsu ba,da alamu tana barin sashen suka zo,da fara'arta ta qaraso cikin falon ta samu hannun kujera daya ta zauna,gaida anty sauda ta fara yi saidai sama sama take amsa mata abinda bata saba gani ba,bata sanyo komai cikin ranta ba tunda ba haka suka saba yi ba,tabi yaran daya bayan daya tana musu wasa suna gaisawa,ta miqawa fatima maqullin tana cewa "Gashi faty sai ja dawo?" "Ina zuwa haka ne?" Anty sauda tayi tambayar a dage,murmushi raihana tayi "Sisi na ce ta haihu dazun" "Wace kuma haka?" Ta kuma tambaya,sai taji tambayar wani banbarakwai,don kowa ya santa yasan wace sisinta,sai ta basar ta bata cikakkiyar amsa "Rumana ta" "Ayyah,da kyau,su kam Allah ya sosu,haihuwa mai dadi,kukam naga ma kamar baku damu ba ko hajiya" dan murmushin yaqe hajiyan tayi,don ita din macace ba maison tashin tashi na ba "Banda abin sauda ai haihuwa lokaci ce,idan yazo tofa babu tsumi babu dabara,jeki raihana sai kin dawo ki gaishesu" a ladabce ta rusuna "To hajiya" ta fadi kama ta miqe ta fice. A zahiri bata nuna komai kan fuskarta ba,don dama tana da wannan baiwar ta kawaici da yakana,amma sosai maganar ta sosa mata qirji,ya ilahi da zarar anyi aure ba'a samu qaruwa ba shikenan sai a tattara dukkan laifi a azawa mace?,ko cewa akayi shi mijin qalau yake?,ko kuwa ance ne su mazan Allah bazai iya jarrabtarsu da rashin haihuwa ba tilas sai diya mace?,Allah ka iya mana wannan muguwar dabi'ar tamu abinda ta fada kenan tana rufe murfin motar tare da bawa driver umarnin su wuce. Lokacin da ta isa gidan har sun dawo a asibiti sunyi wanka abinsu suna hutawa ita da babyn,jikinta har rawa yake taga ta dauki babyn,wai yau babyn sisinta ce a hannunta,lallai babu shakka yau da gobe wataran jariri zai zama ango. Baby girl ce kyakkyawa fara tas tamkar iyayenta wadda ta kwashe kamannin rumanan tsaf ba inda ta barota,nannade cikin kayan sanyi da shawul,wani qaunar ta shiga zuciyar raihana lokaci guda,qauna mai qarfi,rungume yarinyar tayi a qirjinta cike da qauna . "Allah ya nuna min nima ranar da zan dau baby sisi na" inji rumana tana kallonsu cike da sha'awa,murmushi raihanan tayi ta dubeta "Kin riga da kin haifa mana ai sisi,nikam wannan babyn ta isheni" ido daya ta kashe sannan tace "Naqi wayon,nima inaso naga jinin jikinki,inaso naga mun tara yara,inaso naga yaranmu sunyi aure don mu sake qarfafa DANGANTAKARMU" murmushi tayi cike da qaunar 'yar uwar tata "Allah ya nuna mana sisi na" _RAYYAN_ Tunda labarin haihuwar suka sameshi fuskarsa ta kasa hutawa da fidda murmushi,wani irin farinciki da ya dade rabon da yaji irinsa shike ratsashi,ya dade rabon da ya samu kansa cikin irin wannan farinciki. Ya daga wayarsa ya sake qoqarin kira saboda dazun da ya kira bai sameta ba,bugu biyu ta daga,sassanyar muryarsa ta daki kunnenta,ta lumshe ido cike da qauna da kewar mijin nata "Sannu my angel" ya fada cikin sanyi,cikin shagwaba tace "Ba wani nan,sai yanzun zaka kirani,baby nata kewar daddynta" "Kaina bisa wuyana my angel,na kira na kira har sau babu adadi amma ban sameki ba" sai sannan ta tuna a gida suka bar wayar kuma ma babu chargy duka duka mintina kadan kenan da samun cajin "Qorafi ya karbu,ya england" ya dan shafa kansa "Alhmdlh,gani nan inata kewarku,musamman baby na ma,sannu kinji maman baby,Allah ya raya mana little RAIHANA" ido ta zaro cike da zumudi "Da gaske kake daddy?,sunan raihan zata amsa?" Raihana dake ruqunqume da baby sai ta dago kai tana duban rumanan jinta ambaci sunanta,idanu ya lumshe kana ya bude tamkar yana gabanta "Da gaske my angel" "Kai daddy thank u,thank u,thank u,na gode daka samin sunan sisi na,Allah ya biyaka da aljanna" "Ameen,ameen ya Allah" ya amsa tare da fata a cikin zuciyarsa yarinyar ta biyo mai sunan da ta ci. Tuni ta fahimci inda maganar ta dosa,wani abu mai qarfi ya taso mata hade qwalla,sai tayi hanzarin miqewa dauke sa babyn ta fice tana qoqarin danneshi,dakin ummu ta shiga,tayi daidai da dakin da alamu gyara take,ga kayan baby da sabbin atamfofi cikin akwati gefe guda,da alama kayan jikalle ne da na mamanta,goye babyn raihana tayi ta shiga tayata suka kammale dakin tsaf. Sosai su ummu sukaji dadin sunan da rayyan din ya saka,kowa cewa yake Allah yasa ki gaaji mai halin,wuni tayi a gidan sur suna amsar baqi 'yan barka,kamar kada ta tafi amma tilas ta koma gida. Bata tadda ammar ba idan da sabo yaci ace ta saba,don haka wanka tayi ta nade a gado. Haka ta dinga jelen zuwa gidan masu jegon,wani lokaci ta tafi da su fatima wani lokaci ita kadai,tun suna saura kwana biyu ta tafi gida,kusan duk wani shiri na sunan ita tayi uwa tayi makarbiya,jiki nayi aljihu nayi. Suna akayi na gani na fada,little raihana tayi goshi,itakam raihana tace bata so a boye mata suna a dinga kiranta da raihananta duk da haka sai da kausar suka mata laqabi da ISLAHA,kwana biyu da suna ta koka gida cike da kewar takwararta,ji take kamar su bata ita ta taho da ita. Sai da sukayi arba'in suka zo mata yawon arba'in,kwana sukayi a gidan,a nan ne rumana ta fahimci abubuwa dangane da tarayyar raihana da ammar din,amma bata ce komai ba ganin raihanan na qoqarin boye komai,tasan tsakanin miji da mata sai Allah. Watan baby islaha uku rayyan ya matsanta su koma,yarinyar akwai wayo da saurin girma,gwanin sha'awa idan ka ganta kamar ka sace,itakam rumana kamar ba zata koma din ba,saboda ba qaramin dadin zaman nata take ji ba,duk da tayi kewar mijin nata,babu yadda ta iya haka suka tattara suka koma tunda duka duka baifi shekara daya da watanni ba su dawo gida baki daya, ************* Cikin taimako na ubangiji raihanan ta fita da first class,wanda hakan ya sanya jami'ar suka riqeta suka dauketa aiki a matsayin lacturer wadda zata rinqa koyarwa sau biyu cikin sati,taji dadi sosai haka abba,ba qaramin alfahari yayi da diyar tasa ba,fadi yake "Dama bukar na raye a yau yaga yadda diyarshi ta zama zaqaqura",duk da taso ace ta wuce direct ta dora masters dinta,abban ne ya tambaya mata suka shaida mata tana da damar da zata hada dukan ai,wannan ma wara dama ce da zata sa ta sake samun matsayi,ba bata lokaci abban ya nemi izinin ammar,shikam baida damuwa ko matsala yace duk yadda abban yayi dai dai ne,cikin qanqanin lokaci komai ya zama daidai,tana karatunta kuma tana karantarwar. Hakan sai ya sake sawa sauda ta sa mata qahon zuqa,gani take kamar ma raihanan na sane ne taqi haihuwar,kamar da wata a qasa,itakam bata duba duk wani kallo da zata mata,tunda hasalima ba gidansu daya ba sai randa tazo zata ganta,kuma ita kadai ke kidanta tayi rawarta 🎈 _Bayan shekaru biyu_🎈 Rayuwa bata fasa garawa ba yadda Allah ya nufa,hakanan sauye sauye ci gaba da koma baya babu wanda bai haifu ba. Zuwa lokacin raihana ta kammala masters dinta tare da samun qarin girma ta hanyar daukarta a matsayin malama ta din din din,ummu tayi mata sha'awar yin aiki a court saidai tana ganin a matsayinta na matar aure koyarwar din shi yafi dacewa da ita,saboda tana samun cikakken lokaci na gidanta. Gefan mu'amalarta da mai gida ammar babu wani canji da aka samu,duk da ko yaushe cikin masa addu'ar samun lafiya take,sau tari idan suna zaune ta daga maganar sai ya basar da ita ya kawo mata wata,itama sai ta biye masan don tana ganin bai kamata ta dameshi da batun lalurar tasa ba babu dadi kamar cin fuska ne. Watanni uku baya kenan da dawowar su rumana gida nijeria,daga ita har ogan sun wani canza,sunyi fresh sun zama bula bula idan ka dauke rayyan da banda fresh din da yayi baiyi wata qiba ba,saidai kallo daya zaka masa kasan hutu da jin dadi sun ratsashi,sai wata kamala kwarjini da cika da ya sake yi,zuwa lokacin tuni sun hada hannu shi da mukhtar sun soma gina kamfanin dake sarrafa auduga ya maidata zuwa suturar mu ta sawa,wannan company din ba qaramin ji da shi ake ba,don hatta da gwamnatin tarayya na ji da ginin don tasan ba qaramin kudin shiga da daukaka zai janyowa qasar nan ba,ga ma'aikata da zasu dauka masu yawa wanda hakan zai rage zaman banza da matasanmu ke fama da shi. Wani sabo sukayi sosai tsakanin raihana da takwararta,don kamar quruciyar uwarta ne,gidan raihanan wadda take kira da mamma take weekend duk satin duniya,tun rayyan na qorafin ana dauke masa babynsa bai da ikon ganinta weekend har ya haqura,wayo da basira mai yawa yarinyar ke da shi har sun dara shekarunta,saidai kuma ikon Allah suna linzami,ta debo wasu daga halayen takwarar tata kuwa,har rumana kan zauna wani lokaci tayi ta dariyar abin,ko da yake lamari ne na ubangiji,shi yasa manzon rahama ya mana umarni da sanyawa yaranmu kyawawan sunaye don suna na tasiri kan mutum,halayensa da dabi'unsa. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ ______________________ *Babi na sha tara* Qarfe biyu ta fita daga makarantar bayan ta gama da dalibanta wadanda dama sune na qarshe da zata bawa darasi a ranar,sallah kawai tayi ta rufe office din nata don wucewa gida,sauri take ta koma ta shirya ta riski su hajjaju gidan sunan 'yar da anty saudah ta haifa,surutu kam tasan zata shashi gurinta,dama ya lafiyar giwa bare tayi hauka,a wuyanta take qiris take jira,shi yasa ta shaidawa ammar daga makaranta kawai zata wuce,zafi da yunwa suka ssnyata jin buqatar komawa gidan ta sake kintsawa. Cikin mintina ta isa gida,horn tayi sau uku ba'a bude mata ba,sai kawai ta koma gefan gidan ta faka motar cikin rashin damuwa saboda dama dole ta sake fitowa da itan,ta kulle motar tana fitowa dai dai lokacin da maqociyarsu ke fitowa daga gidanta,ta tsaya suka gaisa ta dauki yaronta noor ta masa wasa sannan sukayi sallama ta wuce itama ta doshi gidan "Afuwa hajiya" taji an ambata daga bayanta,sai ta saurara ta juyo tana dubansa,mai gadin gidan ne "Dan nan layin bayan mu na zagaya ganin ba kowa a gidan,kuma alhajin ma yace zan iya zuwa" "Au,gida ya dawo?" Ta tambaya cikin mamaki don bata taba ganin ammar din ya dawo gida ba a irin wannan lokacin "Eh ya dawo,amma ban sani ba ko baya jin dadi ne,naga tare suke da abokinsa" ya fada yana kada kai,itama kan ta kada tana jin cewa lallai qila baida lafiyan. Kafin ta kammala tunanin har ya bude qofan don haka ta sanya kai ta shige gidan,kai tsaye sashen sa ta nufa ganin hakan ne yafi dacewa ta fara dubawa ko lafiya din kuwa,tana gab da shiga wayarta ta dauki qara,ta cirota tana duba mai kiran rumana ce,saita dakata ta amsa kiran,muryar little raihana ce ta fara dukan kunnenta,murmushi ta saki kana ta biye ma shirmen islahan,lokaci suka bata sosai sannan ta fara mata rigimar tazo ta dauketa "Kada ki damu my little kinji,jibi saturday da kaina zanxo na daukeki" da qyar ta lallabata sannan ta baiwa rumanan wayar suka gaisa kana itama rumanan ta shigar da nata qorafin "Na fuskanci fa islaha ta qwace mun fada" dariya raihana ta saki "Haba sisi,mutu ka raba fa muke,amma dai gaskiya na raba faadar nan na baiwa islaha ta rabi" dariya suka saki baki daya suka dan taba hira kana sukayi sallama ta maida wayar jaka sannan taci gaba da tattaki zuwa cikin falon Bai cikin falo don haka ta nufi dakin gadin kai tsaye tana fargabar ko ciwon yayi zafi ne haka . Dora hannunta tayi kan handle din dakin,sautin da ta ringa juyowa shi ya sanyata saurin tura qofar cike da fargaba. Cikin 'yan sakanni idanunta suka dauko mata hoton abinda ke faruwa suka aika ma qwaqwalwarta saqon,lokaci daya taji ana neman birkita qwaqwalwar tata up side down,wani irin rudewa da gigicewa tayi,abinda ta gani yafi qarfin idanunta,bata taba baqin gani ba tunda uwarta ta haifeta ba a rayuwarta irin na wannan lokaci,abinda bata taba gani ba da wasa sai dai jin labari yau shi take gani quru quru,cikin gidansu a dakin mijinta kan gadonsa kuma shi da amininsa maisara haihuwar uwarsu,wa'iya zubillah. Kasa barin gurin tayi,sai kawai taji ta sulale ragwaf ta zube a gun,tamkar wata zautacciya ta soma rarrafe don barin dakin,sam bata da buqatar ci gaba da kallon wannan qazantar,haka ta dinga rarrafawa da gwiwoyinta tamkar zautacciya har ta samu ta fice daga bangaren yayin data bar ammar da maisaran cikin rudani da tashin hankali kowannensu na neman suturar sawarsa. A daddafe ta isa bangarenta,da qyar ta iya bude bangaren nata,tamkar yau ta soma gwada bude qofa a duniya,gashi dai muqullin qofar ne amma sai da ta gwada sashi kusan sau goma kafin ta cimma nasarar budeshi,bata iya qarasawa dakin gadon ba anan ta zube qasan carfet daga bakin qofa tana dafe da kanta,ta fidda glasa dinta tayi wurgi da shi haka dankwalinta,ji take kamar ciwin hauka ne yau zai kamata,kuka take da buqatar yi amma zuciyarta ta qeqashe ta soye,wani matsanancin tsoro ne ya lullubeta lokaci guda,tsoron ubangijinta,ji take tamkar a yanzu wani gagarumin bala'i zai saukarwa gidan saboda sanin muni girma da illar abinda idanunta suka ruska ana aikatawa cikin gidan,gidan da ake karatun qur'ani,gidan da ake salloli biyar a rana,gidan da ko yaushe suke neman rahamar Allah,tsoro na biyu kuma na ammar ne,ganinsa take yanzun ya koma mata wani baqin maciji mai dauke da muguwar guba,wacce iriyar masifa ce wannan?,wanne irin bala'i ne mai girma haka?. Sai a lokacin zuciyarta ta tsinke,ta saki kuka mai cike da sauti iya qarfinta,wanda ta tabbatar da da wami cikin gidan tsaf zai iya jiyota "Astagfirullah ya Allah wa'atubu ilaik" abinda bakinta ya dinga furtawa kenan ba qaqqautawa,takurewa tayi guri guda tana jin wani bala'i na ratsa sassan jikinta tako ina . Me yasa ammar ya zabi irin wannan mummunar rayuwar?,me ta yiwa ammar da ya mata irin wannan sakayyar?,me yasa ammar zaiyi haka,ammar ya cuci kansa ya cuci mace mai mutunci irin hajjaju mahaifiyarsa,yaci amanar mahaifinsa dake kwance cikin kabarinsa. Ta dade a gun tana rusa kuka ta kasa motsi,kanta kawai take mirginawa ta rasa awacce duniya ayau take,wayarta tayi ruri har ta gaji,da qyar ta iya miqewa lokacin da kiraye kirayen sallar la'asar ya cika unguwar ta shige cikin dakinta ta daura alwala ta tada sallah,kafin ta idar kuwa ciwon kai da zazzabi sun mata dirar mikiya,da qyar ta samu ta idar ta ja jikinta kan gado,har yanzu hawaye basu bar fita daga idanunta ba,hoton ammar da maisara sun kasa barin idanunta,hotunan da take fata su goge daga idaniyarta amma ina,hotuna ne marasa kyau da basu taba gogewa cikin qwaqwalwarta ba,a haka ta kasance har sallar isha'i wadda ta gagareta yi a tsaye sai a zaune ta bada ita ta sake kwanciya. Wajen takwas na dare taji dirin mota,tasan su hajiya ne amma ba zata iya tabuka komai ba,hajjaju ce ta dubu fatima "Maza fatima shiga wajen antynku ki duba kiga lafiya,bata zoba kuma wayarta anata kira babu amsa hankalina ya gaza kwanciya je ki duba ta" fatima ta amsa da to tana yin gaba. Du dum falon babu haske ko qanqani,duk da kuwa wadatar na'urar dake bada wuta a gidan,wayarta ta haska ta kunna qawayayen falon tana kiran sunan anty raihana,tana daga cikin dakin tana jiyota saidai bata da qarfin da zata bude baki ta amsa mata har sai da Allah yasa ta qaraso dakin "Anty lafiya kuwa kike?" Kai ta kada a hankali "Banajin dadi ne fatima" "Ayyah anty sannu,shi yasa mukaji shiru,me ya sameki?" "Zazzabi da ciwon kai" ta bata amsa murya qasa qasa "Sannu anty bari na sanarwa hajiya,dama tacw hankalinta bai kwanta da shirun nan ba" fatima tayi maganar cike da damuwa tana ficewa. Ko zama hajjajun batayi ba ta biyo fatiman don duba raihanan,sanda hajiyan ta shigo tana mata sannu cikin damuwa sai tausayin hajiyan ya kamata,duk duniya babu wanda zai kaita cutuwa ko shiga halin ni 'yasu idan tasan halin da danta yake ciki,har ta kasa daurewa ta dinga fakar idanuwansu tana sharar qwalla,wayarta hajiyan ta fidda ta soma kiran layin ammar din,sai data kusa katsewa ya daga "Kana ina ne?ko baka dawo ba?" "Ina cikin gida hajiya" "Au kana cikin gidan amma shiru kamar baka ciki" sai ya hau in ina,bata bi ta hakan ba tace da shi "Maza kazo matarka na buqatar ka a kusa bata da lafiya gata a kwance" sai ya qarasa daburcewa baki daya "To....to ai.....to gani nan....eh ganinan hajiya" ya fada yana katse kiran,idanunta na runtse,roqon Allah take kada Allah yasa ammar din yazo don bata buqatar ya rabi inda take,hajiyan ta dubi fatima "Muje ki kawo mata abinci ta daure taci don tace tun rana bata da lafiya,maiyiwuwa babu abinda ta sawa cikinta,idan yazo din ko asibiti sai kuje" ta fada tana duban raihana cikin tausayawa "To hajiya" ta amsa muryarta a sanyaye. Da qyar ta samu tayi cokali uku abincin ya cunkushe mata a qirji taji numfashinta na neman tafiya,dole ta ture abincin fatima ta kwashe kwanukan don ta maida bangarensu. Yafi minti talatin qofar dakin ya rasa yadda za'ayi ya shiga dakin,daga baya tilas yayi shahadar quda ya cusa kai tare da cewa "Salamu alaikum" shiru tayi idanunta na a rufe zuciyarta na suya,bata ko motsa ba ballantana ayi maganar ta amsa masa,ci gaba yayi da sallamar kasancewar baida abinda zaice,a fusace ta bude baki don ta gaji da jin muryarsa "Qarya kake ammar,wannan kalma bata cancanci fita daga bakin mutum wanda ya kafircewa rahama da ni'imar Allah irinka ba,ina mai umartarka daka gaggauta ficewa daga inda nake" "Raihana......" Idanunta ta bude ta watsa a kansa kana ta kafeshi da su,wani kwarjini tayi masa wanda hakan shi ya kawo katsewar abinda yake shirin fadan "Kada ka sake gangancin ambatar sunana na,abinda nake buqata kawai ka fita.....ka fita ammar bana son ganinka" ta qarasa maganar a tsawace,jikinsa na rawa ya juya ya fice,kuka ta saka tana kiran sunan Allah tare da buqatar taimakonsa. Baifi mintina ashirin ba fatima ta shigo,tace ya ammar ne yace tazo ta tayata kwana. Cikin daren sam batayi bacci ba,sallah ta dinga yi tare da neman gafarar ubangiji da neman mafita,tabbas tasan tayi kuskuren saurin zabar ammar da tayi,wannan zai iya zama hukuncinta kenan,ta zabi ammar ba tare da neman zabin Allah ba,ta zabi ammar cikin gaggawa,yauga abinda gaggawa ta janyo mata,dama ma'aiki ya fada gaggawa daga shaidan take,jinkiri kuma daga ubangiji ne. Darajar sallahr data kwana yi sai ta tashi washegari babu kaso sittin cikin dari ka quncin data shiga,duk da bata da walwala bare kuzari,abinda yafi damunta a yanzu shine tausayin ammar,ba don komai ba sai don sanin halakar da yake ciki,sai don sanin bala'in da zai afka duk sanda Allah ya dauki ransa a halin da yake ciki,hankalinta kan tashi idan ta tuna azabar da har yau mutane da garin annabi ludu suke ciki sanadiyyar wannan halayyar,gefe guda kuma tausayin hajjaju da qanne da ma yayyen ammar din take ji,tanbas babu shakka tasan cewa babu wani da yasan halin da yake ciki illa ita. Ta sani cewa babban jihadi zatayi idan ta zama silar shiryuwarsa,Allah ne kadai yasan sakamakonta idan ta zama sanadin dawowarsa hanya madaidaiciya,idan har ta kasa cimma nasara ne sai kuma ta nemawa kanta mafita,sai duka akalar tunaninta ta sauya kan yadda zata fidda shi daga wannan babbar halakar. Bai sake shigowa ba sai dare,lokacin tana falo a zaune,t.v na kashe hakanan babu abinda takeyi banda zallar tunani,tun wankan safe bata sake wani ba,haka kaya da hijabin jikinta duka na safiyar ne,yana rabe rabe ya shigo a darare yayi mata sannu kansa a qasa,ya juya zai fita ta kira sunansa cikin kakkausar murya,gabansa yayi wani mummunar faduwa,wani kwarjini take masa,da qyar ya samu ya dawo ya zauna,shiru tayi tana maida numfashi ba tare data dubeshi ba kana tace "Ammar,haqiqa naga abinda ban taba zaton gani daga gareka ba,naga mummunar dabi'a tattare da kai irin dabi'ar da ko cikin dabbobi babu mai irinta,ko dabba wadda Allah bai bata baiwar hankali ba bata bin jinsinta . "Irin sakayyar da zaka yiwa ubangijinka kenan?,wanda ya samar da kai daga babu?,ya raineka daga ni'imominsa,ya baka hankali,bai yika dabba ba bare kayi yawo tsairara ko kaci daga bola ba,ya baka lafiya cikakkiya,da yaso sai yayi ka gurgu kuturu ko makaho,ya baka lafiyar kanta,bai jarabceka da mutuwar barin jiki ko ciwon zuciya ko ciwon hanta qoda ko wata cutar mai wuyar magancewa ba,ya baka wadata,kana da dukiyar da zakaci mai kyau kasha mai kyau ka sanya mai kyau ka hau mota mai kyau,ka shiga gida mai kyau,ka biyawa kanka buqatu 'yan uwanka da iyayenka,ya sanyaka ka fito daga tsatso mai kyau ta hanya mai kyau,da yaso sai ya sanya a haifeka ta hanyar zina,ka tashi dan shege,ko ka tashi gidan marayu,bakasan danginka ba,bakasan uwa uba 'yan uwa da danginka ba,baka tsoron wanda ya halicceka ya zare numfashinka lokacin da kake tsaka da saba masa?,kasan hukuncin wanda aka kama da irin wannan aikin a addinance?,kisa!,kisa ne hukuncinka kai da maisara baki daya,kasan cewa mutanen da suka fari irin wannan aikin har yau garinsu na kife sama ta koma qasa,qasa ta koma qasa suna nan suna cin wuta tazarce garesu har qiyama?,kasan cewa saboda munin aikin da bala'insa duk sanda za'a aikata shi duk mala'iku guduwa suke su koma sama?ta yaya ba zamu dinga ganin masifu na arayuwarmu,ta yaya rayuwa zata mana kyau yadda muke so?yaushe zamu daina ganin bala'i kala kala cikin rayuwarmu irin wannan abu na faruwa cikin al'ummarmu,tsakanin mutanenmu ba mazan babu matar," "Baya ga haka sakayyar da zaka yiwa uwa ta gari kenan hajjaju?,wannan shine sakamakon da zaka miqa mata na tarbiyyar da ta baka?,da wanne ido zaka kallesu ranar qiyama ranar da aka tasheku don muku hisabi gaban mutanen farko da na qarshe?yauma tublassara'ir wato ranar tona asirai,me kake tanadarwa qiyarmarka,shimfidar daka zabi ka yiwa qabarinka kenan duk ranar daka koma zuwa gareshi?" Kai kawai take kadawa hawaye na fita daga idanunta,ita kanta ji take tamkar a yanzu azabar zata samesu "Ka gaggauta tuba zuwa ga ubangijinka tun kafin ranka yazo ficewa daga gangar jikinka,ka gaggauta tuba ammar tun kafin Allah ya toshe maka qofofin tuba" ta miqe da hanzarinta ta shige daki tana rusgar kuka,da qyar ya iya tashi ya fice. Ji tayi an fado kanta da sautin kuka,da sauri ta tashi tana dubanta,fatima ce tayi wujiga wujiga,da sauri bakinta na rawa ta soma tambayarta "Lafiyarki fatima?" "Wayyo any raihana,dama halin ya ammar kenan anty?,dama dalilin shigarki wannan halin kenan?" Sosai ta kadu da jin fatima taji maganarsu,tsawa ta daka mata data baiwa fatimam tsoro "Labe dama kike mana fatima?" Kai ta fara girgizawa tana kuka "Wallahi anty ba labe nayi muku ba,fura hajjaju tace na kawo miki ko kina sha'awa nazo shigowa naga yaya nanan shine kunnena ya ji abinda kike magana akai". Jikin raihana yayi sanyi,la shakka ba zata so zancan ya isa kunnen hajjaju ba,ba lallai ne ta iya jurewa jin batun ba,girma ya fara kamata ga hawan jini dama yana damunta,saita daidaita nutsuwarta,ta kama hannun fatima ta zaunar da ita " fatima,kinsan me nakeso da ke"kai ta girgiza "Banason naji zancan nan gun kowa,daga ni sai ke sai yayanki sai Allah" "Amma anty don me ba zaki gayawa hajiya ba?" Da sauri ta katseta "Baida amfani fatima baya ga bala'i da qunci da zamu shigar da baiwar Allah tana fama da ciwo dama,abu daya yayanku yanzu yake buqata addu'a da nasiha gami da jan hankali,ita nakeso kimin alqawari zaki tayani,amma ko mun sanarwa hajiya shiriya ai ba a hannunta take ba a hannun Allah take,zai iya tuban muzuru kuma ya koma a boyr yana ci gaba da aikatawa,so muke yayi tuba tuba na haqiqa,kin gane ko?" Kai ta dinga jinjinawa cike da yabawa da gamsuwa da kyawawan halaye irin na raihanan,tabbas samun mace ta gari irinta zaiyi wuya a wannan zamanin,mace mai hankali tunanin da hange nesa hadi da saya asirin miji,sai taji tana yiwa kanta sha'awar zama kamar raihanan,qaunarta ta sake kamata,tabbas raihanan ta cika mace "Insha Allahu anty zanyi duk abinda kika umarceni" "Yauwa fatima,Allah ubangiji ya shirya mana shi yasa al'amarin yaa zo qarshe" "Ameen anty,ameen ya Allah" **************** Kwanaki hudu kenan da faruwar al'amarin,tun daga ranar bata sake takawa koda qofar gidan ba,ta koma duka wata iri tamkar mai takaba,tayi qozai qozai,ko sau daya bata fasa addu'ar Allah ya shirya ammar kan hanya madaidaiciya ba,tun ranar data masa wannan maganar bata sake sanyashi a idanunta ba,hakan bai dameta ba,don nisan da yayi da ita ya rage mata nauyi sosai,don har yau ta kasa cire wata muguwar tsanarsa data mata dirar mikiya ta kafa sansani cikin zuciyarta tun randa ta kamasu suna aikata masha'arsu. Sunyi waya da rumana tace ta rarrashi islaha sai nextweek zata zo ta dauketa,hakan ya yiwa rumanan dadi don dama ta rasa ta inda zata fuskanci raihanan ta gaya mata rayyan ya hana yace wannan satin tare zasuyi weekend dinsu. ************** Ta idar da sallar magariba tana kan abun sallah tana addu'o'i tare da dakon kiran sallar isha'i taji sallamarsa kamar wanda aka jeho,amsa masa tayi ta duqar da kanta don batason taci gaba da dubansa shaidan na raya mata muna nan abubuwa masu dama game da shi,gefe ya samu ya zauna kafin ya bude baki "Ya jikin naki?" "Alhmdlh" ta iya amsawa da qyar "Ko zamu iya magana dake?" Ya tambayeta,a gajarce tace masa "Bismillah" tana ci gaba da jan carbinta "Da farko dai kafin nace komai ina mai baki haquri bisa cutar dake da nayi,babu shakka ko baki fada ba,ko ba'a gayan ba,ko duniya bata sani ba raihana na cuceki na zalunceki,na auroki shekara kusan uku ba tare da na taba koda gwada sauke haqqinki dake wuya na ba,kiyi haquri,haqiqa sanda nayi aure nayi shine don kawai na farantawa hajjaju da 'yan uwa na,hakanan nayi shine don na kawar da zargi daga zuciyar jama'a da suketa raya abubuwa a kaina,a zahiri ko sau daya mace bata taba bani sha'awa ba ko sau daya sakamakon qazamar harkar da nake ciki,kece mace ta farko data taba burgeni har nayi niyyar nayi auren kare zargi dake,maisara shine mutumin da ya jefani cikin wannan harkar kuma da shi kadai na tabayi,mun fara harkar da shi tun lokacin......" "Dakata,banason jin wannan tarihin ko kadan" raihana ta katseshi ta hanyar daga masa hannu ba tare data dubeshi ba wanda hakan ya sanyashi hadiye maganarsa. ajjiye numfashi yayi sannan ya dora"haqiqa ke din mace ce kamila mai tsoron Allah mai bin dokokin Allah,na gane hakan ta hanyar kame kanki,baki fada harkar banza ba ko neman wasu mazan saboda rashin samun biyan buqata daga gareni ba,sai kika ma duqufa da yimin addu'ar samun waraka,ke maca ce ta gari,kin kama ni da laifi mafi muni amma sai kika shiga nema min shiriya gurin Allah,kika SADAUKAR da lokacinki wajen nema min komawa tafarki na gari wajen ubangiji,kin SADAUKAR min da yawa raihan kin SADAUKAR,kin SADAUKARA da shekaru uku cikin rayuwar aurenki ba tare da samun wani kulawa ta zamantakewar auren ba,kin SADAUKAR da lokacinki kina nema min lafiya ta hanyar addu'a da hana idanuwanki bacci,har yashe ne raihana zaki ci gaba da SADAUKARWA ina ha'intarki,ina cutarki ima cin amanar Allah?,maca ce ke wadda samun kamarta sai am tona,maca ce wadda tafi dacewa da miji na gari mai tsoron Allah irinta,miji mai biyayya wa Allah irinta,ko kadan raihana baki cancanci miji irin ammar ba,hakanan ammar bai cancanci ya samu mata irinki ba,bamu dace da juna ba" ya fada a hankali yana sauke numfashi "Kiyi haquri da abinda zai fito daga bakina raihana koda zai bata miki rai,ina ganin shi kadai ne adalcin da zan miki,na barki kije ki gina sabuwar rayuwa ingantacciya,na barki kije ki auri nagartaccen miji da zaku haifi kyakkyawa kuma tsaftatacciyar zuri'a" sai ya sake yin shiru wanda wannan karon ya sanya raihanan dago kai tana kallonsa qirjinta na dukan uku uku "Kiyi haquri raihana ki yafemin,ni ammar mu'azzam na sakeki saki biyu" yayi furucin yana miqa mata wata takarda ninkakkiya a miqe. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"wanda ya riqi kare wanda ba karen kiwo ba(wanda zai dinga raka dabbobi kiwo),ko karen faruta ba kona gadin yabanya,za'a dinga cirar lada daya kullum cikin aikinsa"* _bukhari da muslim ne suka rawaito_ *_(qalubale gareku masu kiwon karnuka cikin gidajensu haka kawai saboda ado ko qawa ko burgewa,bugu da qari mala'ikun rahama basa shiga gidan da yake da shi,yaya kake zato idan kazo mutuwa mala'ikun rahama suzo daukar ranka?)_* ________________________ *Babi na talatin* _na samu mantuwa wajen sanya number din page a baya,ashirin da takwas ne da ashirin da tara,ga babi na talatin nan in sha Allah_ Kamar yadda kowa ya sani duk duniya babu macen da za'a ce an saka taji farinciki koda ita ta buqata balle ita da bata shiryawa hakan ba haka kuma bata tsammaci haka ba,kasa miqa hannu tayi ta karbi takardar illa baki da ta bude ta bishi da kallo,babu abinda ke dada masa nauyi irin qwayar idonta,ji yake ta dora masa wani nauyi mai yawa,wani kwarjini yake jin ta masa fiye da yadda yake kallonta a baya. A hankali ya qarasa gabanta ya sanya hannu cikin aljihunsa ya zaro bandir din kudi 'yan dubu dubu guda uku ya hada da takardar ya ajjiye a gefanta ba tare da ya iya kallonta ba sannan yace "Kiyi haquri raihana,ki yafe min,idan kinso tafiya yanzu na kira driver dinki yana waje zai kaiki har gida,Allah ubangiji ya saka miki da mafificin alkhairi,ya haska rayuwarki,ya miki sauyi mafi alkhairi" yana gama maganar yayi gaba da hanzari yana ficewa daga falon. Tafi sama da minti ashirin zaune tamkar mutum mutumi,ta rasa me zata tuna?,wanne abu ya kamata ta aiwatar?,miqewa kawai tayi tsam ta shiga dakin gado ta dauki wayarta,ko hijabin jikinta bata damu da sauyawa ba ta zura silifas dinta tayo waje. Driver din kuwa na tsaye jikin motar tata,yana hangota ya bude mata qofa,dama yasan da fitowar tata amma saidai baisan dalili ba,ta shiga ya rufe sannan ya tada motar suka fice. Sai da motar ta saitu kan kwalta sannan taji wasu hawaye masu dumi sun fara bin kuncinta,mutuwar aure ba abu bane mai dadi sam ga diya mace,kanta ta kifa saman cinyoyinta ta dinga risgar kuka ba tare da sanin driver ba. Ta daga kai tana duban gidan nasu lokacin da suka iso,fargaba da tsoro suka cikata,me zata ce da ummu da abba?,wanne irin daci zasu ji idan suka ganta agidan da sunan wadda aurenta ya mutu,babu yadda zata yi haka ta sanyo qafafunta waje ta fito kamar mai ciwon qafa,drivern ya miqa mata muqullin motar yana fadin "Hajiya ga muqullin" kai ta kada "Ka koma da ita gida kawai" "Hajiya mai gida ai yace idan na kawoki lallai lallai na damqa miki muqullin" bata da buqatar doguwar magana saboda haka ta miqa hannu kawai ta karbi muqullin tare da yin gaba. Ummu na zaune cikin falon ita da mai aikinta,suna hada ido da ummun wasu sabbin qwalla suka zubo mata "Subhanallahi,lafiya raihana,daga ina haka ke da wa?" ummun ta fadi tana miqewa tare da taro raihanan,tuni ta fada jikin ummu ta ida sakin kukan da take ta riqewa,kama kafadunta ummun tayi sannan ta shige da ita bedroom dinta wanda a yanzu ya koma saman benan da rayyan ya dora musu. Kusan minti ashirin suna zaune gefan gadon suna fuskantar junansu,kallonta kawai ummu keyi tun dazu take risgar kuka,ta qyaleta ne tayi iya son ranta ko wataqila hakan zaisa ta samu sauqin radadin da takeji a zuciyarta har ta samu damar yi mata bayani,da qyar tayi controlling kanta ta miqawa ummu takardar hannunta "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un" shine abinda ummun ke maimaitawa,sai ta daga takardar tana sake karantawa amma wannan karon a bayyan "Ni ammar ammar mu'azzam na saki matata raihana abubakar saki biyu ba tare da ta yimin laifin komai ba,hasalima nine mai laifin kuma nina zalunceta,ina mata fatar samun miji na gari tamkar ita". Numfasawa ummun tayi bayan ta kai zuciyarta neaa da qyar "Baki cancanci kiyi kuka ba raihana,tunda Allah ya sanya bake kika zalunceshi ba,shi din da ya zaluncekin ya jira sakamako,Allah ai baua barci yana madakata yana jiranmu,bari abban naku ya shigo" haka ummu ta dinga kwantar mata da hankali,ganin har goma ta kusa abban bai shigo ba yasa ummu ta sanyata tayi wanka nan cikin dakinta,ta kuma bata kayan barci ta saka sannan ta tusa ta a gaba da abinci tace sai taci. Kallonta take cike da rausayi,sai a sannan ta lura da ramar da raihanan tayi,tun asali zurfin ciki ne da raihana na masifa tun suna yara,kusan tun kafin ta dawo hannunta tasha jin yadda umminta kan rufeta da fada kam shegen zurfin cikinta,don a haka a yanzu ta rage kaso tamanin cikin dari,sanadiyyar ma da ya sanya cutar idonta tayi tsananin da ya kaita da sanya glasa kenan har yanzu qin faden abinda ke damunta da wuri "Duk wanda ya kalleki raihana ko ammar bai fada ba yasan yana zaluntarki" cewar ummun cikin zuciyarta,bayan ta gama ta sanyata ta kwanta,tace kuma kada ta soma sanya wani abu cikin ranta,bacci takeso tayi sosai. Rashin dawowar abban da wuri ya sanya bata tada masa maganar ba ta barwa washegari,cikin daren kasa bacci tayi,amma batayi kwanan zaunem banza ba,sallah tayi mai yawa har sai data dinga jin gajiya sosai cikin jikinta ***************** "Haqiqa naji dadi qwarai da ya zamanto bake kika zalunci ammar ba,saboda girma da nauyin haqqi irin na aure,wanda duk wanda ya kuskura ya zalunci dan uwansa tofa yawanci tun a duniya Allah yake sakayya,haqqin aure na da saurin bibiyar mutum tun a duniya kafin aje ga lahira,na bincika kuma na tabbatar da cewa baki da laifi ko guda daga bakinsa,to alhamdulillah,inaso ki saka a ranki cewa haka Allah ya tsara miki,mutum bai isa ya gujewa qaddararsa ba,bana so ki sawa ranki damuwa,ki nufi ubangiji da dukka buqatunki,na tabbatar da cewa in sha Allahu ba zaki taba wofinta ba,Allah ya miki albarka" cewar abba yusuf kenan yana duban raihana dake durqushe gabansa kanta na duban qasa cikin hawaye "Ameen abba,in sha Allah zanyi amfani da nasiharka,na gode Abba Allah ya qara girma" "Ameen" ya amsa mata "Tashi kije abinki kinji" ya sake mata magana,ta miqe a sanyaye ummu ta kalleta cike da tausayi "Idan kinyi wanka break fast dinki na kitchen" "To" ta amsa tana ficewa daga bangaren abban. A bakin qofa sukayi kacibus da shi wanda sauran kadan suci karo lokacin da take share qwallar idonta "A'uzu billahi minash shaidanir rajim" ya furta,da sauri ta daga kai ta kalleshi,wannan ne karon farko da ta sanyashi a idanunta tun bayan da suka dawo nijeria gaba daya,sanye yake da yadin maza tissue fari qal,wanda aka yiwa dinkin dogon wando da riga iya gwiwa mai gajeran hannu,yayi kyau ya sake haske,jikinsa babu abinda ke fiddawa sai daddadan qamshinsa sumarsa ta sake kyau da yawa sai walqiya take alamar hutu da jin dadi,yana dauke da islaha a kafadarsa wadda take kallon bayansa tana ta zuba masa surutu,daga nesa sai kayi tsammanin bacci take bisa kafadar tasa. Wani haushi ya quleta,ita yakewa ta'awizi kome?,sai kawai ta kewayesu ta shige ciki. Yana direta tayi gun abba da gudu ta daleshi,ya qarasa gaban iyayen nasa fuskaraa qunshe da murmushi,suma murmushin suke cike da qaunar dan nasu da jikanyarsu suna sauraran shirmen surutunta,cikin girmamawa ya gaidasu suka amsa tare da tambayar rumana "Tana tafe ma,na barta gida tana qarasa wani ayyuka ne,data kammala din nan zata zo" "Masha Allah,hala sunyi waya da 'yar uwarta raihana ne" sai ya kada kai "A'a,gaskiya abba ban sani ba ko sunyi" "Ok,na dauka ta sanar da ita mutuwar auren nata ne" abban ya fada yana barewa islaha ayaba wadda yaci ya rage yana miqa mata. Cikin rashin fahimta ya dago ya dubi abban,jin yayi shiru baice komai ba ya sanya ummu tayi zaton baiji abinda abban yace ba don haka ta dora bayani "Jiya bayan isha'i sai gata da mummunan labari,kuma da kansa yake fadin babu abinda tayi masa sai shima da ya zalunceta" shiru ya sakeyi kana daga bisani yace "Allah ya kyauta ya rufa asiri ban sani ba kam banda yanzu"sai yayi saurin sako zancan kamfaninsa da ake ta aikinsa a yanzu,ganin hirar tasu ta kasuwanci ce yasa ummu miqewa,islaha sarkin son yawo tayi saurin tashi daga gun abban tayo gunta,dungure mata kai ummu tayi " kaji ni da ja'irar yarinya,tun dazu ai qina kikayi sai yanzu da kika ga na tashi,to nikam bazan dauki kishiya ba,muje ki taka fa qafafunki"qememe taqi kuwa dole ummun ta dagata,dariya su abban suka yi musu don sun saba da ganin dramer dinsu. Toilet ta shiga tayi wanka sannan ta fito ta saka wata doguwar Riga da ummun ta bata,kitchen ta shiga ta dauki abincin nata sannan ta koma dakin ummun,ba laifi ta samu kam taci albarkacin maganganun da abba yayi mata,ba qaramin kwantar mata da hankali suka yi ba,tabbas babu shakka ba qaramin dace tayi da uba ba nagari,nagartaccen uba irin abba yusuf din. Ummu na gama wankewa islaha jikinta data bata da yoghourt a bakin fanfo rumana tayi sallama ta shigo,kallo daya zaka mata ka gane tana cikin kwanciyar hankali da dacen gidan aure "Sannu,sai yanzu?" "Wallahi ummu,sauri nake tayi nazo na gaidaku don gidan sisi na ma zan wuce?" "Au to daina saurin itama tana ciki,tama dakina" ummu ta fada tana daukar islaha tare da rigarta data dauraye mata "Wayyo,ai bata gayan yau zata zo ba itama,kinga da tuni munyi sabani kenan" ta fada tana shigewa ciki da gudu gudu sauri sauri. Kallo daya tayi mata jikinta ya bata ba lafiya sisin nata take mata ba,ita din ma hada idon da sukayi sai ya haifar mata da rauni,duk yadda taso danne damuwarta ta gaza hakan har suka kai ga zubowa,jakarta ta saki wadda take mahadi da lace din jikinta ta qaraso inda raihanan take,hannuwanta ta kama itama muryarta na rawa tana tambayarta meke faruwa,kuka tayi sosai bisa kafadar sisin nata,a hankali ta dinga ware mata zare da abawa don ranar wanka ba'a boyon cibi. Tashin hankali rumanan ta shiga ba kadan ba,idanunta sun rufe bala'i take zabgawa kamar yanzu abun yake faruwa,ta zagi ammar ta zagi maisara ta zago anty saudat,tama rasa da wanda zatayi,miqewa tayi tace gidan hajjajun zata,qarshe raihanan ce ta koma ban baki,da qyar ta zauna sai ta saki kuka tana jin ciwon rayuwar da raihananta tayi,sai ya zama babu mai rarrashin wani tsakaninsu har sai da ummu ta shigo ta musu fada ta dora da "Ke kuma da zakiyi lallashi sai kika zauna kuka hada kai baki daya kuka zama daya,banso kada na qara ganin hawayen daya daga cikinku,abinda ya faru ya riga ya faru,Allah ya sanya haka ne yafi alkhairi" ta fice,kira ya shigo wayar rumanan,ta janyo wayarta a kasalance ta daga "Hello yaya" ta fada tana jan majina,shiru yayi daga can bangaren yana saurarenta "Kuka kikayi ko?'rayyan din ya tambayeta,sai zuciyarta ta sake karyewa,muryarta ta soma rawa " is ok,ya isa,shi yasa dama na kiraki na ja miki kunne,ashe ma nayi latti ko?,to bana son koke koke kin gane?"kai ta daga tamkar tana gabansa "Insha Allah yaya" "Ok,take care" "To yaya" daga haka suka ajjiye wayar baki dayansu Cikin dakunan dake falon dakin rumanan ta zage suka gyarashi tsaf yadda raihanan zata ji dadin zamanta,babu abinda babu cikin dakin komai ya zama neat. Har dare rumanan na gidan bata tafi ba,sosai wunin da sukayi ya debe mata kewa ya sake sakata sakewa tare da hana mata damuwa,musamman islaha daketa shirmenta da wasanni raihanan na biye mata,farincikin yarinyar ya ninku,wuni tayi ajikin raihanan taqi kowa. bayan sallar magariba rayyan ya iso gidan don tafiya da su,kicin cikin rumanan tayi tana fadi qasa qasa don ummu taji "Sisi kadai zamu bari a gida,kawai mu tafi da ita don Allah" sarai yaji abinda take fadi din amma sai yayi banza ya share,ummun ma bata ji ba sai da ta tako musu zuwa qofar waje,a lokacin rayyan tuni har yayi gaba da islaha,daman ita raihana ma bata ma fito daga daki ba "Ummu,don Allah mu tafi da raihana,kinga nan gida babu kowa,inaga sai tafi sakewa a can gurinmu" kai ummun ta kada "Haba dai rumana,daga mutuwar auren jiya kawai sai yau ta fice,abbanku bazaya bari ba,kuma nima ina da buqatar diyata kusa da ni,baya ga haka ma idda zata fara ai kin sani" a shagwabe tace "Ummu sisi na fa ba zaman iddan da zatayi,bai dora mata idda ba" wani iri ummu taji zancan,sai tasa ido tana duban rumanan jin zancan banbarakwai,sai kuma lokacin rumanan taji nauyin zancan da ta fada,a kunyace tayi gaba ta shige motar da rayyan ke ciki yana ta faman doko mata horn. A sanyaye ummun ta juya ta koma cikin gidan,kai tsaye dakin raihana ta nufa,akan abun sallah ta taddata tana lazumi saboda tana fashin sallah ne babu damar yin sallah,shigowar ummun ya sanyata yunqurin tashi sai tayi saurin dakatar da ita "Yi zamanki,magana dama nazo muyi" "Tom" ta fada tana komawa ta xauna "Da gaske ne ammar bai dora miki idda ba?" Sunkuyar da kanta tayi qasa saboda yadda maganar tayi mata ba zata,kunya ce ke dawainiya da ita,ummun ta fuskanci hakan don haka tace da ita "Daga kanki muyi magana raihana kada ki cuci kanki kiyi zaman iddar da bai wajaba a kanki ba,ni mamarki ce da bai cancanci ki boyen komai ba" da qyar ta iya bude bakinta bayan wasu daqiqu tace "Eh,bai dora min ba"shiru kawai ummu tayi tana tunanin wanne irin zama ne haka raihanan tayi?,wacce iriyar cutarwa akayi mata tsawon zamansu?,wanne irin haquri da zurfin ciki take da shi " ikon Allah"shine kawai abinda ummun ke iya fada tana jijjiga kai kana daga bisani ta miqe ta fice,ajiyar zuciya raihan ta saki,tasan babu wanda yayi wannan katobarar sai rumana. Da fari zancan da ya je kunnen amminta na mutuwar auren fada ta dinga har da shirinta na zuwa ta tarad da raihanan har kano,sai da abba ya zauna ya fayyace mata abinda suka sani sannan jikinta kuma yayi laqwas bata sake cewa komai ba face Allah ya zaba abinda yafi alkhairi. ***************** Cikin sati guda ta samu kwanciyar hankali,wanda bata taba tsammamin zai yiwu ta sameta haka da sauri ba,ranar da ta cika kwana bakwai ranar ta koma baki aikinta,yadda ta zaci abubuwa sai suka dinga zuwa mata da sauqi wanda hakan ya sake kwantar mata da hankali,babu abinda ta nema ta rasa. Dawowarta kenan daga makaranta,wanka kawai tayi taci abinci tana falo tana hutawa ita da mai aikin ummu lantana suna taba hira taji sallama,babu ko shakka muryar fatima take ji,tsaye ta miqe tana amsa sallamar tare da cewa a qaraso ciki,fatiman ce a gaba sai anty saudat da anty sabira,ta qarasa a hankali tana musu sannu da zuwa tare da amshe babyn anty sauda dake hannun fatima wanda bata samu ganinsa ba sai yau,ta musu masauki cikin falon,ta saka lantana ta kawo musu lemo da ruwa,sai meatpie data yi musu jiya da dambun naman kaza. Dukkansu babu wadda ta iya cin komai,daga gaisuwa ma shiru ne ya ratsa falon,kallo daya zaka yiwa fuskarsu ka karanci alhini qarara saidai babu abinda tace,da taga shirun yaqi katsewa ne ta sake cewa karo na biyu "Yaya hajjaju take fatim?" "Uhmmm,tunda abin nan ya faru hajjaju jikinta yaqi dadi raihana,kwana shidan nan da kikaji shiru duka hankalinmu a tashe yake hajjaju na kwance a asibiti sai jiya aka sallamomu,don Allah raihana kiyi haquri ki yafe mana,sanda ammar ya sanar da hajiya washegari ya sakeki ina gida na zarto daga asibiti da nakai musaddiq allura,ni na fara zaginki ina cewa gwara da ya rabu da juya,hajiya namin magana amma idona ya rufe haka,fatima na gefe tana kuka bata ce komai ba sai da ammar din ya fita bayan hajiya ta masa umarnin ya dawo dake ya bata haquri kan bazai iya dawo dake ba ni kuma ina sake zugashi cewa dai dai ya yimin,sai da ya fita ne fatima take gayawa mana komai,a nan ciwon hajiya ya tashi,ammar ya cucemu ya bata mana zuri'a,yanzu haka bamusan ma ina yake ba....." Ta qarashe maganar tana sakin kuka fatima da sabira na sharar qwalla,sabira ce ta bude baki tana fadin "Don Allah kiyi haquri raihana,haqiqa babu shakka an cutar da ke,kuma ke din 'yar halak ce da kika gaza fallasawa dan uwan mu asiri,tabbas bashi kadai kika rufawa asiri ba har da mu kanmu kin rufa mana kuma kin mana gata,Allah ubangiji ya miki sakayya da alkhairi,ya hadaki da dukkan wani alkhairin rayuwa". Qwallar itama take sharewa saboda tsabar tausayinsu,haqiqa babu wani wanda zaiso yaga wani dan musulmi cikin irin wannan harkar ransa ya masa dadi,bare ace dan uwanka na jini ne yakeyi " babu abunda aka yimin dama,ni tsakanina da ku sai fatan alkhairi,kun nunan so da qauna,abinda ya shiga tsakanina da anty sauda kuwa nasan ajizanci ne irin na dan adam,ammar kuwa iya zaman mu da shi banda wannan abun bai taba takuran ko muzan tani ba,addu'a zamu tayi ubangiji Allah yasa qarshen abun ne yazo,Allah ya tsare musulmi baki daya" "Ameen ya Allah,mun gode raihana,Allah yayi miki sauyi mafi alkhairi" da zasu tafi ta basu saqon gaisuwa gun hajjajun,ta kuma ce zata kira layin fatima sai su gaisa,sai kuma ta hararu fatiman "Koda yake babu ruwana ma da ke,tunda kika karya alqawarin da kika yimin" Murmushi tayi"anty bazan iya zuba kunnuwa na bane naji ana zaginki bayan kece ke da gaskiya,ke kikayi SADAUKARWA tare da RUFIN ASIRI ga dan uwanmu" "Gara data fadi din,ai kinga ko addu' ma zage damtse da yi masa" cewar sabira,har qofar gida ta rakosu sukace ta gaida ummu tunda basu sameta ba,taje gadon qaya gidansu rumana duba jikin umman rumaman da bata jin dadi. ***************** Cikin watanni uku komai ya wuce tamkar ma ba'a yi ba,suna waya da fatima akai akai suna gaisawa har ma da hajjaju,hakanan anty sauda da sabira ma na kiranta lokaci lokaci,saidai babu wanda ya taba yi mata zancan ammar kamar yadda itama bata taba tambayarsu. Sosai take rayuwarta a sake,taje makarantarta ta dawo,idan ta dawo kuwa bata sake fita sai da wani babban dalili,rumana kam tayi ciwon baki har ta gaji,dom babu yadda batayi tazo ta ko kwana biyu bane amma sam ta qiya,ko islaha saidai ta turata a daukota idan babanta yaga dama ya yarda,rayyan kuwa sau biyu ta ganshi cikin watanni ukun,saboda ba zama take gidan ba,lokacin da zai zo gaidasu ummu wani lokaci ta fice makaranta,idan da daddare ne tana daki tana karance karancanta na al'ada. Zuwa lokacin tamkara jarrabi sai ga maneman aure sun fara mata caa,idan tana ganin qimarka ta rangada maka qarya tace ita din matar aure ce,idan ka fiya naci kuma tayi maka fata fata,sam bata yarda su biyota koda hanyar unguwarsu ne balle akai gidansu,ko kadan bata jin sha'awar yin aure dai dai da misqalazarratin,jarrabawa kawai take jira zuwa yanzu dalibansu su kammala ta dage zuwa maiduguri ta bawa kano iska. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga sa'ad dan abi waqqas R.A yace:naji manzan Allah S A W yana cewa"haqiqa Allah yana son mutum mai taqawa mai wadatar zuci,mai shagala da ibada da neman na kansa"* _Allahumma salli wasallim ala khatimunnabiyyina wa imamul mursalina_👏🏼 _____________________ *Babi na talatin da daya* _abinda nake son jan hankalin makaranta da shi shine,ku kula,raihana da rumana kowacce nada managartan halaye kyawawa,kowacce nason 'yar uwata tsakani da Allah,kowacce nason farincikin 'yar uwarta,koda kuna ganin kuskure ko ba daidan daya daga cikinsu,to ku daukesu a 'yan adam ajizai kamar kowa,har yau babu wadda tayi wani abu da niyya ko nufin cutar da 'yar uwarta da gangan,muje zuwa_ Fushin da rumana ta hau yi da ita gadan gadan na yadda ta nisanci zuwa inda take ya sanyata yau asabar ta tashi da niyyar zuwa mata ta yini,daga nan ta dauko takwara su taho ta musu weekend. Qarfe sha biyu ta gama shirinta cikin wani lace mai azabar kyau blue light and dark wanda aka qawata shi da tsadadden dinki na doguwar riga,da takalmi mai tsinin dunduniya tayi amfani mai igiyoyi,wanda ya mata kyau,haka 'yar madaidaiciyar hand bag dinta wadda ta shiga da kayanta da mayafinta dukka irin na wayayyun mata masu aji da tsara ado mai sanyi. Tana kammala sanya sarqa da dan kunnenta ta dauki turarenta mai taushi da sanyin qamshi ta fesa,kana ta yafa mayafinta ta zari jakarta a gaggauce ta fito saboda tex din rumana da tace mata indai ta wuce sha biyun bata zo ba to wallahi saidai ta kwana. A kitchen ta tadda ummu ita da lantana tana gwada mata abincin da zata dafa musu da rana tunda su biyu ne kawai a gidan,cike da sha'awa da qauna ummu ta dubi raihanan "Kinyi kyau diyata,saikim dawo ki gaidasu" murmushi tayi wanda ya fidda fararen haqoranta sannan tace "To ummu zasuji" sannan ta fice,a harabar gidan ta tsaya ta dauki motarta sannan ta fice daga gidan. "Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ta fara ambata jin motar na shirin tsaya mata,gefe ta samu ta faka ta sannan ta bude murfin ta fito,kusan minti arba'in ta shafe tana tabe tabenta amma ko motsawa motar taqi yi,rufe gaban motar tayi sannan ta koma jikinta ta jingina tana duban titin,hanyar sam bata wucewar jama'a bace,bugu da qari gashi rana a take take,babu yawaitar zirga zirgar motoci. Motar ta koma ta fiddo jakarta sannan ta kulle ta baki daya ta sake matsowa gaban titin ko zata samu abun hawar da zai qarasa da ita hannunta riqe da wayarta tana neman number din bakaninken dake musu gyara,lokaci bayan lokaci tana daga idonta ta sauke kan titin cike da fatan samun adaidaita ko taxi. Da qyar ta samu lambar john ya shiga,ta kara a kunnenta suka fara magana,dai dai lokacin da wata doguwar baqar motar mai baqaqen glass data gifta yanzun take ribas tana dawowa da baya,tsayuwar mintina kusan hudu tayi sannan taga murfin baya na budewa lokacin da ta gama wayar ya shaida mata zaizo ya karbi key din gidan rumanan ya duba mata motar. Tana kici kicin sanyata a jaka hancinta ya soma jiyo mata wani qamshi,ta daga dara daran fararan idanunta suka sauka kan farin matashin wanda ke sanye da baqar kufta ya kafa baqar hular damanga akansa,murmushi ya sakar mata sannan ya tako zuwa inda take . Sallama ya mata amma tayi burus kamar bata jishi ba har sai daya maimaita sannan ta amsa a ciki,motar tata ya duba sannan ya kalleta "Kash,amma wannan mota bata yi adalci na data macewa sarauniyar mata,tayi silar tsaiwarta cikin rana" sai ta daga idonta ta dubeshi kawai,ko waye ya gaya mata mutuwa tayi? "Ko za'a yimin izinin in duba miki motar ko zan iya tashinta?" Wannan karon ma kallonshi tayi,sam ko guda bai mata kama da wanda zai iya wani aiki ma daya danganci haka ba gyaran mota ba balle tayi zaton ko bakanike ne,zallar hutu ne muraran bayyane a jikinsa "Waye ya gaya maka mutuwa tayi?"murmushi ya saka sannan yace " jikina ne ya bani" "Da kyau,ba mutuwa tayi ba to,kuma koda mutuwar tayi ban tsammanin zaka iya tayar da ita" "Kika sani ko da bakanike kike magana?" Sai maganar tasa ta bata dariya har ta dan murmusa bata sani ba "Good,tunda nayi nasarar saka wannan daurarriyar fuskar murmushi nasan ina da sa'a" sai ya dunqule hannunshi guru guda yace "Don Allah ranki ya dade kada kimin musu,nasan mutuwa motarki tayi,kuma haka qarfen nasara ya gada,kizo muje na saukeki zuwa inda zaki" shiru ta masa don bata da sha'awar hakan,shirunta bai sanya shi fasa roqonta ba,cikin haka aka bude seat din driver,wani kakkauran mutum ne baqi ya fito sanye da kaya wadanda suka mata kama da na dogarawa . Sa sassarfa ya qaraso gabansa ya rusuna yace "Ranka ya dade ya yallabai ya sanya anata kira,yana ta fadan rashin isowarmu kan lokaci" wani kallo ya masa sai kawai ya jinjina kai ya juya ya koma cikin motar. Ganin bazai daina roqonta ba,kuma ita dinma idan tace zata ci gaba da jiran abun hawa tabbas zata iya kaiwa azahar a gun ya sanya ta amince,da kansa ya bude mata ta shiga sannan shima ya zagaya ya shiga,sanyi da qamshin motar ya ratsata. Shiru ne ya biyo baya sannan daga bisani taji yace "Na gode da kika yimin alfarama na rage miki hanya,duk da baki tambayeni ba suna na sultan abdul_ra'uf ahmad,ni haufaffen garin azare ne,anan aka haifeni nayi karatu na primary da schdry nayi jami'a ta a south africa,mahaifina shine wazirin sarkin azare,wannan ne tarihina a taqaice,bazan boye miki ba,ganin farko da nayi miki naji kin kwanta min a raina,zuciyata kuma ta gayan ma samu macen aure,Allah yasa bazakice nayi miki tsufa ba" ya fada da yana shafa sajensa da salon tsokanarshi data fuskanci halayyarsa ce,dariya ya bata sosai har sai data murmusa,jin tayi shiru bata ce komai ba yace "Uhmmm,baki gayan wace ke ba,hakanan baki fadan matsayin da kika dauki maganata ba" "Nikam an riga an badani" abinda tace dashi kenan. A hankali ya qaraso cikin kitchen din,yana sanye da long sleeve t.shirt ja da farin wando wanda tsahonsa iya qaurinsa yake,bata kula sam da saukowarshi ba hankalinta yayi gaba wajen ganin ta kammala girkin,yaci gaba da takawa a hankali har ya isa bayanta,yasanya hannunsa ya janyota jikinsa ya rungumeta tsam,da fari ta dan tsorata,amma qamshi da taushin fatar data ji su suka sanar mata ko wanene,ba tare data juyo ba ta sake narkewa ajikinsa tana sauke ajiyar zuciya tare da lumshe idanu "Ka bani tsoro abban islaha" "Ayimin afuwa,mun gaji ne da jira ni da islaha,kin shanyamu a sama kinzo kin tashi dukka hankalinki cikin kitchen" "Ayyah kuyi kin haquri ai na kusa kammalawa yaya na" "Mukam indai don mune mun yafe,kizo kawai muje mu huta,yaufa weekend ne" "Ku qara min minti ashirin na kusa gamawa,bana son sisi na tazo ban gama abincin tarbarta ba" sai ya sanya hannayenshi kan kafadarta ya juyo da ita yana fuskantarta "Wai kina nufin kice min baqi zamuyi yau din ma,bayan wancan weekend din ma babu islaha mu biyu ne kawai,wannan karon kuma da muke ku ukun kice zamuyi baqi?" Sai ta narke fuska"sisi na ce fa,ai ita ba baquwa bace" " a gurinki" "Har da kai din ma" sai yayi shiru ganin yadda take dubansa,kai ya dan jinjina sannan ya sakar mata kafadar yana fadin "Ok,bari naje na samo credit zanyi waya da mukhtar,kafin na dawo ki tabbatar kina sama" "In sha Allah" ta fada tana juyawa da sauri sauri tana qarasa hada abinda bata hada din ba. Hannayensa soke cikin aljihun short neeker dinsa,kansa a duqe zuciyarsa na harbawa,baisan meye matsayin zuciyarsa a yanzu ba,yawan harbawar da takeyi ne ke damunsa,dalilin da ya sanya yake son kiran mukhtar kenan ya duba shi. Da sauri mai tsaron qofar ya taso yana tambayarsa "Yallabai duka su yakubun basa nan,wani abu za'a siyo maka?'hannu ya daga masa " a'ah barshi sama'ila,katin waya ne zan gangara ma siyo"yana son fita ne da qafafunsa ya dan taka,sama'ilan ya qaraso ya bude masa qofa ya fito. Daidai qofar gidan motar tayi parking,shi ya sake bude mata qofan wanda fes a idon rayyan,ta gefansu ya wuce yana sakeyin qasa da kansa tamkar bai gansu ba duk da yadda yaji zuciyarsa ta masa nauyi,gabanta ya tsaya yana dubanta "Tunda bazan samu adress ba, Ataimaka a bani koda phone number ne,pls ranki ya dade,kinga ni ba mazaunin kano bane,zuwa nake na fita duk qarshen sati" tabbas a yanzi ba zata iya hanashin ba,sabida babu wani abu da ya sani a gunta baya ga sunanshi wanda sai da yayi ta magiya,kuma ta lura mahaifinsa ne ke jiransa,a hankali ta karanto masa lambobin yayi serving,ya saki ajiyar zuciya yana mata godiya,yana tsaye har ta shiga gidan sannan ya koma cikin motar yaja suka wuce. Rayyan na tsaye gun mai credit din motar ta wuce ya bita da wani irin kallo,ya karbi katin tare da yin gaba ba tare da ya tsaya amsar canjinsa ba "Yallabai canjinka" "Ka riqe kawai" ya fada yana tafiya ba tare da ya waiwayo ba "Yallabai suna da yawa fa" wannan karon bai amsa mashi ba ya wuce kawai,murna ta cika mai katin,duk da daman yasan halin rayyan din,don duk ranar daya tashi fidda zaka dukka sai kowa ya daara. Tsalle rumana tayi ta dale raihanan duka suka zuba saman carfet,hararata tayi tana mata qorafin lattin da tayi na zuwa a makare,ta kare kanta ta hanyar gaya mata abinda ya samu motarta,saiga islaaha wadda dan ihun mamanta ya fiddota,ganin momman nata ya sanyata saukowa da gudu itama daga saman tana kiran sunan momma din,da sauri raihana ta tallafi islahan ta dagata sama ta wurga ta tacafeta suna dariya. A tsakiya suka sanyata,rumana tace "Oh,wai nima sai na nemi alfarma ake zuwa min,kamar ni,sisinki rabin jikinki?,ai shikenan" "Wallahi idan kina fadin haka sai kisa ayi mana dariya,haba sisi ai kinsan dai yadda sisin naki ta zama,babu zama makaranta ma kawai ta isheka" kafin rumanan ta sake cewa komai ya shigo falon,kamar yadda ya fita yanzun ma haka ya shigo,hannayensa soke a aljihunsa yana kallon gabansa,banbancin kawai wannan karon fuskarsa a dinke take tsaf,rumana ta miqe tana cewa "Na kammala dai yaya kafin ma ka dawo din" "Da kyau,kinyi qoqari" ya fada yana hayewa saman,saita bishi da kallo ganin sauyawar yanayinsa lokaci guda,sai da ya qulewa ganinta sannan ta maida dubanta ga raihana tana daidaita yanayinta "Baku gaisa bafa da ya rayyan" murmushi tayi cike da basarwa "Kai haba,mun hadu fa a qofar gida" "Ok,bari naje ina zuwa sisi pls minti biyar"murmushi ta kuma yi " na qara miki goma ma ya zama sha biyar"tana dariya rumanan ta haye saman. Islaha ta janyo ta dora saman cinyarta ta bude jakarta ta fito mata da chaculets din da ta siya mata ta fara bare mata tana bata tana shanyewa tare da zabga mata surutu tana ta biye mata. Tana shiga da minti uku yayi sallama fa mukhtar kana ya shiga wanka,yana shiryawa ta dubeshi cikin damuwa "Yaya amma cewa fa kayi yau muna tare fa" "Ai mun dadu bamu kadai din bane" "Amma yaya ai raihana" kiss ya mata saman labbanta wanda ya sanyata yin shiru,ya janye bakinsa yana ci gaba da sanya links din hannun rigarsa "Kada ki damu,zanje naga dr mukhtar ne" kamar ba zata fada ba sai kuma tace "Amma yaya na dade ina son gayama qorafina,kwanaki naga magungunanka na tambayeka na meye kaqi gayan,yanzu kuma kana zuwa ganin mukhtar kona tambayeka dalili ba gayan zaka yi ba,me yasa?,me yake damun mijina har haka?" Kai ya girgiza yana sakin murmushi,ya fesa turarensa sannan ya isa inda take ya dagata ya rungumeta sannan ya sanya bakinsa cikin kunnenta "Bana so ki sanyawa ranki damuwa ko kadan kan cewa wani abu yana damuna,lafiya qalau mijinki yake my angel,pls bana so ki sake tambayata kan wannan batun tunda nasan am fine,mai lafiya ma na shan magani,da wata cuta ce kece ta farko da zata fara sani,but kawai ina ganin mukhtar lokaci zuwa lokaci ne yana min checkup,kuma kinsan hakan yana da kyau"daga haka ya zarme da gaya mata wasu sanyayan kalamai da suka ida kashe mata jiki duk da bata gama gamsuwa ba amma ranta yayi fari qal,ita ta riqe masa wayoyinsa da key din motarsa suka sauko qasa. Da gudu islaha ta zame daga cinyar raihana ta iso gunsa,ya durqusa gabanta ya mata kiss a goshi,ta daga masa hannu tana masa byebye shima yana mayar mata " a dawo lafiya"suka fadi kusan a tare,ya juyo yana duban ruman"iya nan rakiyar take yau?"kai ta daga tana murmushi tare da yi masa nuni da raihana. Kallonta yayi karo na farko saidai baiga fuskarta sosai ba saboda islaha dake tsaye gabanta "Kya gaida gidan ko?" Ya fada yana ficewa "Zaiji" itama ta bashi amsa a hagunce kamar yadda ya mata maganar. Hakanan yake jin wani zafi cikin zuciyarsa,bai sani ba so ne ko kishin ne?,haushin qinsa ne ko kokuwa?,ya kasa banbancewa,kawai dai yasan yana jin wani abu guda biyu cakude a zuciyarsa,saidai daya yafi daya qarfi da nauyi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga ma'aqil dan yasar R.A yace:naji manzan Allah S A W yave"babu wani mutum da Allah zai bashi kula da lamarin talakawa,kuma ya mutu ranar da ya mutu alhali yana mai zaluntar talakawansa face Allah ya haramta aljanna a gareshi"* _bukhari da muslim suka rawaito_ _______________________ *Babi na talatin da biyu* Sai misalin qarfe tara da wasu mintina na dare ya dawo gidan. Saman dining suka isa ta ja masa kujera ya zauna sannan ta fara sarving dinsa,ya cira kansa daga danna wayar da yake ya dubeta "Ina islaha ta shiga ne?,tunda na shigo banji motsinta ba,hala ta gaji da jira na tayi bacci?"sai data tura masa plate din abincin tana shirin zama sannan tace " daddy ka manta yau weekend ne,kuma wancaj satin bata je gun mammanta ba,dazu ta dauketa suka tafi" Hade fuska yayi yana dubanta "Da izinin wa suka tafin?" Sai tayi sakato tana dubanshi "Amma ina cewa daddy kasan tana zuwa ko?,baya ga haka sati biyu kenan kana hana zuwan nata,me laifi a ciki don taje?,da nan da can duka ba gida bane?,me yasa nake gani ka sauyawa ne daddy?,anya lafiya qalau kake?" Sai ya basar ya ja plate din abincin ya soma ci "Lau nake,ko dazun ba naje cheakup ba?an gaya miki ni irinki ne lanjare?"sai tayi murmushi kawai tana dubansa,komi yayi burgeta yake. Shiru ya ratsa tsakani kafin daga bisani ya ajjiye spoon din hannunsa " bake kikayi girkin dare ba yau"sai ta dage masa gira "Eh sisi na ce,zazzabi ne ya dawomin dazu sai ta karba tayi kafin su wuce,nasan kuma ba wai rashin dadi yayi ba,don sisi ma ta fini qwarewa" "Ke kikasan wannan,ni girkin matata kawai na sani" yayi maganar yana ci gaba da cin abincin,dariya ta saki sannan tace "Wallahi yau yaya na lura rigima kake ji" "Kuma ke zaki sauketa ba,ya zazzabin,na lura har yau yaqi tafiya baki daya,ko zaki ga likita ne?" Sai ta narke tana dubansa "Ni kaina ya dameni wlh yaya,da ya tafi sai ya dawo Idan bai tafi duka ba nan da next week sai naje din" "Allah ya qara afuwa" "Ameen" ta amsa masa *LAHADI* Kasancewar weekend ne tana gida,hakanan tayi niyyar zuwa duba jikin hajjaju da har yanzu yaqi dadi,gashi batason tarar rana,don haka tun qarfe ta gama hada abun karin kumallo ta dawo daki,tayi wanka ta yiwa islaha,ta musu makeup daidai,bayan ta gayar gashin yari yar ta rabashi gida biyu ta daure kowanne da ribbom,baka rasa dakinta da kayan kwalliyar yara duk saboda yarinyar,wani material ne mai tsada ta fiddo musu wanda ta bata aka yi musu dinki ita da islahan dogayen riguna,iri daya komai da komai,sai suka tashi tamkar uwa da 'ya,ta sanya mata safa da takalmanta ta kamata suka fito don su karya su wuce gidan hajjajun. Bai wuce mintina da shigowa ba,yana falon suna gaisawa da ummu suka fito,da gudu islahan ta saki hannun raihanan tayi gunsa tana fadin "Daddy oyoyo"shima cafe 'yar tashi yayi ya azata kan cinya suka soma gaisawa da salon shirmen islahar,sosai kwalliyar yarinyar ta masa kyau ya fidda wayarsa ya mata hoto yace zai nunawa mommy. " ina kwana"ta fada tana giftashi ba tare data tsaya ba,kamar wanda aka toshe masa baki da tsumma ya amsa a gajarce ganin ummu na gurin "Ummu me kika dafa yau,ban karya ba na fito" "Garin yaya?" Ummu ta tambayeshi tana miqewa zata wuce sashen abba don taga ya gama sallar walhar da yake zasuyi magana da rayyan din "Bata jin dadi ne matar gidan,a kwance na barota" "Ashshsha,me ya sameta haka?" Ta tambaya tana dakatawa da tafiyar da takeyi "Zazzabi ne kawai" "Ai ya wuce kawai rayyan,kuyi qoqarin zuwa asibiti,Allah ya qara lafiya" "Insha Allah" "Ka qarasa kan teburin bani na shiga kitchen ba,nasan ba zaka rasa abinda zaka ci ba" tayi maganar tana ci gaba da wucewa. Sai da ya bata kusan minti goma zaune kana ya miqe ya saba islaha a kafadarsa yana takawa zuwa kan dining din inda raihana ke zaune tana hadawa islaha tea tare da fifitashi yadda zata iya sha,kujera daya yaja ya zauna daga can wani sashen ya janyowa islaha daya ya dorata kai,sai ta zame ta sauko ta nufi gun raihanan,hannu tasa ta dauketa tare da dorata kan cinyarta ta soma bata tea din tare da chips da waina ba tare data daga kai ta dubeshi ba,islaha na mata gwalantonta tana amsa mata. Ido ya kafeta da shi,zahiri ta masa kyau amma wani abu mai kama da fushi na son danne zuciyarsa ga barin ganin haka,har yau halayyarta na nan,miskilancin tsiya zurfin ciki da sanyi,natural choculet colour skin nata,murmushi a maimakon dariya ko bada amsa,ta ammali da abu natural da sauqaqawa kai kan abubuwa. Tsaki ya ja a bayyane wanda hakanan yaji wani haushin ya sake turniqe shi,sarai ta jishi saidai ko a fuska bata nuna alamun taji din ba,tunda bata ga wani abu data masa wanda zai mata tsakin ba,dacin ran da yake bata san masa dalili ba,shi sani ne baiyi ba amma tafi kowa qyamatar tarayyarsu waje guda "Ke.....rayya" Sai ta daga dara daran fararen idanunta ta watsa masa,sannan ta tsaidasu qyar a kanta tana jiran abinda zaya fada,wani yarrrrr yaji cikin jikinsa har ya haifar masa da raunin da sai daya lumshe idanunaa sannan shima ya sake watsa mata su tamkar suna son nunawa juna baiwar idanu da Allah ya bawa kowannensu. Tamkar ramuwa yayi gareta,itama sai ta janye nata idon ta maida kan fuskar islaha data yagi tissue ta fara goge mata fuskarta da bakinta daya baci da maiqon chips "Ke wacce iriyar baqauyiya ce?" Sai ta sake dagowa ta dubeshi ba tare data ce komai ba,ya lura halin nata ne ya motsa kuma ya tabbatar ba zata ce komai din ba sai ya dora "Tunda kika ganni a nan kinsan cewa abinci nazo ci ko?" "Ba gidan saida abinci bane wadanda suke neman custumer koda yaushe da idan sunga mutum zaune zasu zo su tambayeshi me yakeso...."kai ya kada " kinyi na farko kinyi ka qarshe da zan miki magana kice zakiyi qoqarin maida min,ki hada min breakfast yanzun nan"yayi maganar yana dora qafarsa daya kan daya tare da yin relaxing kan kujerar yana dubanta. Sauke islaha tayi daga kan cinyarta tace taje ta gaida abba gata nan zuwa su tafi unguwar,miqewa tayi tana duba girmansa na yayanta,girmansa na wanda ya girmeta,girmansa na mijin sisinta abban takwararta,ba don haka ba tana jin da yau saidai ya rube a gun,don dacin ran da yake fama da shi bai shafeta ba. Tea ta hada masa ta ajjiye gabansa sai ya dubeta "U know bana shan tea da madara ko?" Ta manta da hakan sabida haka ta janyeshi daga gabansa ba tare da tace komai ba,haushin shurun da take masa yake ji a badini,so yake tace wani abu amma ta qiya,tana cikin zuba masa black tea a cup wayarta ta dauki tsuwwa,cube uku ta zuba masa maimakon daya garin sarin daukar wayar,yana kallo kuma baice da ita komai ba,sultan ke kiranta,sai ta saki murmushi a hankali tace "sultan"har ga Allah bata ma san ya fito ba,sai kawai ta tura masa kwanukan duka abinda ta dafa din gabansa ta sauko daga dining area din a gaggauce tana amsa wayar ta shige daki. Binta yayi da kallo yana jin kamar an shaqeshi,lallai babu shakka yarinyar nan ta rainashi,zai ko yi maganinta,yaja qwafa ya zubda tea din ya hada wani. Kusan shi kadai ya iya sha,daya gama maimakon ya bar gurin sai ya zauna yana tsimayen fitowarta,yana jin yau sai ya sauke duk wani bacin ran da yake ji,yana zaune a hakan hannayensa harde a qirji yana duban qofar dakin ummu ta fito riqe da islaha,dubansa tayi " af,ashe ka gama,kaje to abban naku ma ya gama" "Ok kawai yace ya miqe ya wuce sashen abban,ummu kuma ta qwalawa raihana kira tace ta fito su tafi kada suyi rana sosai Duk ta taras dasu kuwa a gidan,anty sauda sabira da fatima sai salim qaninsa da halima,murna suka dinga yi da ganinta,suka rasa inda zasu sanyata,haka ma hajjaju wanda jikin nata yayi dama dama,farinciki duk ya cikasu,abinci da abin sha har ta rasa da wanne zata fara,islaha na gunsu babyn ta burgesu,fatima tace " anty ki bar mana ita don Allah"murmushi ta saki "Nima arota nayi fatima" hajjau ta danyi murmushi "Da tuni taki ce raihana,ammar bai kyautatawa rayuwarmu ba baki daya" sai qwalla ta soma qoqarin fita,da sauri raihanan ta dubeta "A'ah hajiya,don Allah kada ki sake sanyashi a wani bala'in,kada ki zubar masa da qwalla wallahi abun sai yayi masa yawa,addu'a zaki ci gaba da yi masa" "Hmmm,raihanatu kenan,bakisan duk cikinmu babu wanda yasan inda ammar yake ba ma,ko a waya bamu samunsa?" Batun ya girgizata amma duk da haka ta kwantar musu da hankali tare sa qarfafa musu gwiwar yi masa addu'a. Basu baro gidan ba sai la'asar,shima da qyar suka barta ta taho cewa sukayi sai dare zata koma. Tun azahar ya rufr affice dinsa,hakanan ya kasa yin kowanne aiki,duk motsin da yayi sai ya hangeta sanda take ambatar sunan tare da qoqarin amsa wayar da gaggawa. Yana bakin gun da ma'aikatan ke ajjiye motocinsu driver dinsa ya qaraso da sauri cikin girmamawa ya rusuna "Alhaji,ina zamu je" hannu ya daga masa "Yi tafiyarka gida zan wuce,sai Allah ya kaimu gobe" ya fada yana miqa masa hannu,da sauri ya saka masa a tafin hannun nasa yana fadin "Allah ya kaimu yallabai" ya bude motar ya shige. Maimakon ya koma gida sai ya tsinci kansa da karya akalar motar tasa zuwa gidansu,ummu na bakin kintchen zaune tana zuge zogalen da za'a yiwa abba tuwo da shi lantana na daga ciki tana hade haden abincin dare ya shigo,daga kai ummu tayi ta dubeshi "Lafiya rayyan ka dawo gida a irin wannan lokaci?ko jikin ruman ne?" Kai ya girgiza yana dafe kujerun falon "A'ah ummu,kawai na gaji hutawa nake son nayi" "To,dama jiki da jini ai yana buqatar hutu,banda lafiya ma da Allah ya baku ga aikin wani companyn ga aikin ginin naka,Allah dai ya qara lafiya kawai" "Ameen" ya amsa yana sosa tsakiyar kansa da maqulli "Ummu akwai kuwa irin lemon mangwaron nan?" "Eh ai kuwa kaci sa'a,jiya da daddare raihana ta hadashi saboda abbanku ma na sonshi" turus ya danyi,yanzu komai yace a bashi raihana ce tayi,baisan sanda yace "Gidan nan babu wani meyin abu ne sai raihana?" "To waye a gidan?,daga ni sai ita sai lantana,tafi lantana kuzari da himmar aiki,ni kuwa indai tana nan bazata taba yarda nayi wani abu ba...." "Shikenan,kisa lantanan ta kawomin ina gun lilon can" ya fada da sauri yana juyawa sai kuma ya waiwayo "Halan islaha tayi bacci?" "Ai tun safe suka fita ita da mamanta,suna gidan su yaron can data taba aure,taje duba mamarsa ba lafiya,wallahi tunda akayi abun nan har yau jikin yaqi dadi" wani abu ya shaqa,har ya bude baki zaiyi magana sai kuma ya fasa yasa kai ya fice . Guri ne mai kyau daga gefan gidan wanda yayi kama da garden,saidai kana iya hango harabar gidan duka,wata da'ira aka yi masa mai kyau da shuke shuke tsakiya kuma qananun fareren dutsuna na wuta,sai teburi na qarfe mai kyau da kujerunsa guda hudu,gafe daya kuma lilo ke qwaya daya amma irin dogon nan,duk aikin raihana ne lilon kuma saboda islaha ya siya aka saka shi,kofin glass guda ya cika da lemon sannan ya jingina bayansa da lilon dake lilashi kadan kadan yana kurba,sanyinsa da dinsa suka ratsa qwaqwalqarsa . Kan idonsa motar raihanan ta shigo gidan,a hankali ta samu gefe guda ta ajjiyeta sannan ta kashe,mintina qalilan qofar motar ta bude ta fito sabe da islaha da tayi bacci ta kulle motar sannan ta nufi cikin gidan. Ganinsa kawai tayi a gabanta,hannayensa harde da qirjinsa ya dubeta yana fidda huci kadan kadan,hannu ya miqa mata don ta bashi islaha,ganin bata fahimta ba ya sanyashi sake matsowa daf da ita har tana sheqar qamshinsa,ya sanya hannayensa don dauketa daga kafadarta wanda garin hakan hannun sa mai dauke da kwantacciyar gargasa ya shafi wuyanta,wani shock taji wanda ya sanya ta sakar masa yarinyar ba shiri ta ja baya tana dubansa. Sai da ya dorata saman kafadarsa sannan ya dubeta "Daga yau kada ki sake fitarmin da yarinya yawo,idan kin tashi bibiyar gidajen ki tafi abunki ke daya ba damuwata bace,amma bada yarinyata ba" ya kewayeta ya wuce ta bishi da kallo ba tare data iya cewa komi ba,sai wani abu yake sai kace wadda ta kashe masa wani nasa?. ,muqullin motarsa ya saka ya bude ya kwantar da islahan a baya sannan ya dawo ya shige mazauninsa ya tashi motar suka fice a gidan yana faman hadiyar numfashi shi daya. Jin falon shiru babu kowa ya sanyashi hayewa sama don yasan tana can,a dakinta ya sameta kwance tana waya da wata qawarta jamila meela da suka hadu a saloon,ta gayyaceta birthday dinta amma saboda batajin dadin jikinta ba zata iya zuwa mata ba,shigowarsu ne ya sanyata katse kiran,ta miqe daga kwanciyar da take bayan ta ajjiye wayar tana duban rayyan din dauke da mamaki,ya samu gefan gadon ya kwantar da ita sannan ya qaraso gefanta ya zauna "Daddy ya na ganka da islaha,yaufa sunday?"idanunsa ya watsa mata sannan yace "Wai yarinyar nan me ta tsare miki da kika wajabta mata dole tayi weekend a waje?,ko ni nace miki na gaji da ganinta ne ko ke kin gaji da ita?,bama wannan ba daga dawowata baki tambayi komai ba sai na dawowar raihana?" Ta karyar da kai "Ayyah,afuwa yaya ba haka nake nufi ba" bai bi ta kan maganar tata ba ya sanya hannunshi ya shafi wuyanta da goshintan sannan yace "Ya jikin naki?,ina fata da sauqi" murmushi tayi tace "Alhamdulillah" "Masha Allah" ya fada yana miqewa,drower din da yake ajjiye magungunansa ya qarasa ya jawota ya balli uku kala daban daban,sannan ya qarasa gaban 'yar qaramar freezer dake dakin ya ciro ruwa mara sanyi ya balle murfin ya kora maganin "Yaya ina fata kaima ba jikin naka bane,naga ma yau ka dawo ba lokacin dawowarka ba" dan qaramin murmushin da ya sake qawata fuskarsa yayi "Babu wani jiki,kawai hutawa nake so nayi,ina buqatar hutu" ya fada yana balle botiran rigarsa ya cire ya janyo towel ya rataya "Na hada maka ruwan wanka to"dakatar da ita yayi " a'ah my angel,kema kina buqatar hutun,ki barshi zan hada"kai ta gyada tana murmushi tana kallonsa har ya shige toilet din **************** Da sauri sauri ta fito daga dakin saboda kiran da taji ummu na qwala mata sanye da kayan bacci masu sulbi ruwan hoda mai haske mai dogon hannu iya cinya da dogon wando,kanta matse da qaramin ribbom. Su biyu ta taras cikin falon wanda bata tsammaci ganinsa ba,rabonta da ganin nasa tun ranar da ya karbi diyarsa,zaune yake ya kwantar da bayansa jikin kujera yana duban falon da qasan idonshi,sai ta rage saurin nata tare da duban agogo,qarfe tara ne na safiyar ranar jum'ar,rabawa tayi gefan ummun tana yin tamkar bata ganshi ba tace "Gani ummu" "Kinji 'yar uwarki jiya a asibiti suka kwana tayi bari amma babu wanda suka kira,yanzu haka daga asibitin suke an sallamota ya maidata gida" sai ta narke fuska cikin tausayin sisin nata tace "Subhanallah,wayyo sisi,Allah ya bata lafiya" "Ameen,abbanku yace ki shirya kije gidan ko kwana uku ki mata kafin jikin nata yayi qarfi" "To ummu" ta amsa da sauri tana miqewa zata shige daki ummu ta sake kiranta,tana waiwayowa idanunta suka fada kansa,ta qasan ido yake kallonta idan baka lura ba sai ka zaci a lumshe idanun nasa suke,ta janye idonta tana jinta duk a takure "Idan da tea din nan hadawa yayanku ya sha kafin ku wuce,ki hado masa da panadol shima kanshi wai ke ciwo,inaga kwanan rashin baccin da sukayi ne,ga rigimar islaha" "To ummu" ta fada tana juyawa akalarta da sauri zuwa kitchen saboda irin kallon da yake mata. Ta fito hannunta dauke da qaramin cup na tangaran dauke da tea,a hankali ta qarasa inda yake har yanzu bai sauya zaman shi ba,saidai ummu bata falon "Gashi" ta fadi tana miqa masa,shiru yayi tamkar bai ji ta ba har ta fara qaguwa,bata jin zata sake masa magana ko zasu shekara hakan tunda ta tabbatar yaji din "Ajjiye kije ki cire kayan jikinki,kada na kuma ganinki kina yawo da night gown" ya fada cikin wata ginshira,baki ta tabe tana ajjiye cup din a gefansa "Dama bada su nake yawo ba" ta fada tana juyawa zata bar gurin,hannun rigarta taji an damqo ya janyota har sai da botiran rigar biyu sauka bude kana ta fadi a gefansa,da sauri ta sanya hannunta tana maida maballan,idanunsa duka ya ware a kanta wadanda suka sauya launi yana dubanta "Wato ke mara kunya ko?,idan aka fada miki sai kin rama,kin girma kenan kema kin taba aure ko?,kin manta sanda kike majina a gaba na?,me kike taqama da shi?" Ita tsoro ma ya bata ganin yadda ya wani juye baki daya,mai ta masa don kawai ta bashi amsa,eh lallai ta yadda da wata a qasa shi yasa rayyan din ke nuna mata wasu halaye,da alama ci mata mutunci yake sonyi ita kuma wallahi ba zata lamunta ba,a yanzu kam ai ita ba yarinya bace aqalla ta mallaki hankalin kanta,tana gama rufe maballan ta zame hannunta a zafafe ta miqe ta wuce ya bita da kallo,sai data shige dakin ya saki ajiyar zuciya ya maida bayansa jikin kujerar kamar yadda yake dazun yana fidda numfashi tare da tsurawa cup din shayin data kawo ido,ji yake kamar a film kamar bashi yayi ba,bai san meke tunzura zuciyarsa haka ba,a hankali ya miqa hannunsa ya dauki tea din ya kai bakinsa ya kurba. Bakin gadon dakin ta zauna,sai taji qwalla kawai ra subuce mata,me rayyan ke nema daga gareta ne ya soma takura walwalarta haka?,miqewa tayi da zummar zuwa ta samu ummu sai kuma ta koma ta zauna a sanyaye,bata jin zata iya cewa ummu ba zata je ba,ko don darajarta darajar abba da kuma darajar sisinta wanda tasan zataji dadin zuwanta qwarai,hakanan sunfi qarfin komai a gunta,saidai dole ta takawa rayyan birki hakanan tunda ita bata matsa masa ba bata ga dalilin da zai sanya ya tsangwameta ba,a hankali ta miqe ta shirya kayanta da duka a binda tasan zata buqata cikin qaramar jaka sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito ta shirya cikin baqar doguwar riga tayi rolling da mayafinta. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *An karbo daga iyad dan himar R.A yace:manzan Allah S A W yace"wanda ya kare mutuncin dan uwansa (musulmi)alhali baya nan,to,Allah zai kare wuta daga fuskarsa a ranar qiyama(bazai shigeta ko ya ganta ba)"* ______________________ *Babi na talatin da uku* A falo sukayi sallama da ummu ta bata key din motarta saboda a tashi zasu tafi sannan ta fito. Cikin motar ta tarad da shi,yayi kicin kicin,bata dubeshi ba ta bude gidan baya tayi zamanta,ga zatonta zaice wani abu,sai kuma taji baice komai din ba. Basu wuce minti goma da fara tafiya ba wayarta tayi tsuwwa,sunan sultan ke yawo kan screen din wayar tata,sai ta saki dan qaramin murmushi tana jinjina yadda sultan din ya faye damuwa da ita,ta daga wayar ta kara a kunnenta tare da sake jingina jikinta da kujerar. Batasan ya akayi ba sai ji tayi anja wani wawan birki da ya sanyata yowa gaba,wayar dake kennenta ta subuce ta fadi goshinta ya daku seat din dake gabanta,gabanta ke dukan uku uku ta daga kai da sauri ga zatonta hadari sukayi,saidai babu wani abu data gani dake nuna hadari ne,asalima yana zaune daidai kan seat dinsa,hannunsa yasa ya saita mirrow din motar daidai fuskarta,ta nan suka hada ido,kawar da kanta tayi ganin yadda gaba daya fuskarsa ta sauya,wani irin mahaukacin kishi wanda bai san daga ina ya faro ba ke cin zuciyarsa,wayar da take kamar ruwan zafi yake jin ana watsa masa,idanu ya zuba mata ta glass din yana qarewa fuskarta kallo,masifar da ya qudiri aniyar yi sai ya nemeta ya rasa jikinsa yayi sanyi har ta kaishi ga lumshe idanunsa sanda ya tuna wani abu,ya tuna wasu maganganu data taba gaya masa _Bana son raytan so na soyayya,bana sonka yaya rayyan,kai koda ina sonka rayyan na SADAUKARWA da rumana soyayyar,saboda har abada bazan iya shiga tsakanin rumana da farincikinta ba,qaunar dake tsakanina da ita ta siya mata komai,babu abinda bazan iya SADAUKAR MATA BA CIKI KUWA HAR DA KAI YAYA RAYYAN"_ hanzarin bude idanunsa yayi maganar na masa amsa kuwwa tamkar a lokacin take furta masa su,ko da gasken raihana take bata sonshin?wa take so to?,wa take qauna baya ga shi,baya da hurumin tilasta mata tabbas,amma yana jin wani qarfi da jin cewa yana da hurumin tilastawa zucuyarsa ta qi raihana,ta gujeta kamar yadda ta gujeshi,abinda bai sani ba shine,ita zuciya ba'a mata tilas tayi so ko qi,tana yin su ne a duk sanda taga dama,yana jin wani bala'i a zuciyarsa duk sanda ya tuna ta taba auren waninsa,ta kuma zauna da shi wanda hakan sau da dama yake sanyashi yi mata misbihaving ba tare da ya sani ba,hannunsa ya sanya kawai ya tashi motar sannan yaci gaba da tuqinsa,saidai a wannan karon a kasalance yake, itama maida kanta tayi gefe guda ta saku ajiyar zuciya bayan ta gama hada wayarta data tarwatse qasan motar,tunane tunane fal cikin ranta . Ba laifi jikin nata da sauqi,don data isa ma har ta hada tea tana sha saboda yunwar data fara ji,raihanan bata zauna ba sai data gama kimtsa gidan tsaf wanda yayi dadai da gama breakfast dinta,tare suka sauko da rumana dukkansu sunyi wanka,wanda da alama ma shi shirin fita yayi,daki ta koma itama tayi wankan ta barsu nan. Zamanta a gidan wani irin zama ne data riga ta tsara takunta,matuqar yana gidan zata yi zamanta a daki,tayi waya ko tayi wasu 'yan karance karancenta,rumana nata qorafin me yasa ba zata dinga fitowa ana hira da ita ba,takance kinsan malamar makaranta ce ni dole sai da bita da binciken karatuttuka kada ajefo tambayar da dalibai zasu qureni,tun tana mitar har ta gaji,a kwana uku da tayi cikin gidan tun randa ya kawota bata kuma bari sun hadu ba,ita take komai a gidan bata bari sisin nata tayi komai,har kuwa da hidimar islaha,cikin lokaci qanqani rumanan ta warke sumul wanda hakan ya sanya raihana cewa zata koma,tsalle tayi ta dire tace babu inda zata je wallahi sai ta cika kwana goma cif. A lokacin rayyan din na kan carfet shi da islaha suna cin abincin dare,bai ko dubesu ba duk da yana jinsu sarai,rumana ta juya ta dubeshi "Yaya kana jin mu fa,ko baki ba zaka saba don Allah,tunda take ta taba kwana a gidan nan,ni gani nake kamar fa sisi kin rage sona,yanzu yaya ta qarasa kwanakin sai taqi tace tafiya zata yi?" "Sai me?" Ya fada kansa tsaye bayan ya dubeta "Da can tare bake kadai ke zama a gidan ba?" Sai suka zuba masa ido gaba dayansu kowa da abinda yake saqawa,bai damu ba yace "Ki barta,tunda bata son zama da mu muma mun yafe"dira qafa rumana tayi ganin raihana ta juya ta shige dakin da take,bata jin zata sake qara ko minti daya cikin gida " kai yaya,kai yaya,kai da zaka mana sulhu kuma don Allah sai ka fadi haka"shiru yayi yana ci gaba da cin abincinsa,ta san halin miskilancinsa sarai bazaya amsa ba tunda yaci gaba da abinda yake,saboda haka ta juya da sauri ta bi raihana. Tuni har ta kammala hada kayanta cikin jakarta,rumana ta kama hannunta tana dubanta "Haba sisi,kinsan fa halin ya rayyan sarai tun ba yau ba,kada ki bari a ganmu a rana ayi mana dariya haba sisi na" murmushin qarfin hali tayi "Wallahi ko a jikina,dama ai na gaya miki tun safe yau zan tafi bayan magariba,ina da abubuwan yi da yawa a gida,ya rayyan kuma kada ki damu ko saka wani abu,tunda na fito daga gida na yakejin haushina,qila ya aza laifi na ne" ta fadi haka ne don ta kawar da hankalin rumanan daga zargin wani abu,babu yadda bata kada ba tace sam itama hankalinta yayi gida tana so taje taga ummu,hakanan ta daukar mata jakar "A'ah sisi ajjiye,har yanzu fa patiente ce ke" harara ta watsa matq "Kada ki sake cewa komai idan baso kike na sake tunzura ba" dariya tayi "Allah ya baki haquri tawan", babu kowa cikin falon,da alama ya gama cin abincinsa ya dauke diyarsa sun haura sama,haurawa saman itama rumanan tayi bayan ta ajjiye kayan tana fadin" ina zuwa"mintina kusan biyar sai gata ta dawo dauke da key din motar rayyan din "Muje parking space na bude miki ku zauna kan ya sauko,shike bata islaha wallahi,yanzun sai ya lallabata tayi bqcci sannan zai fito" "Idan bai shagwabata ba ke kuwa wa kike so ya shagwaba,nikam ina goyon baya wallahi" "Eh dama ai jirginku daya ke da shi,kun samu aiki kam,indai islaha ce dama Haka take so ai" da wannan hirar suka qarasa wajen motar ta bude matq,tare suka shige sannan rumana ta kunna musu a.c,sanyinta ya fara ratsa mitar tare da qamshin daddadan turaren take manne da motar gauraye da qamshin turaren mamallakin motar,hira suka ci gaba da tabawa rumanan najin kamar ta daure qafafun raihanan ta hanata tafiyar. Sai da ya bata kusan minti talatin sannan ya fito,jallabiya ce a jikinsa ruwan toka mai turuwa,da alama har wanka ya sauya ya barsu zaune cikin mota,fita tayi daga motar tana duban raihanan "Sisi ki gaida gida Allah ya qara zumunci,amma fa ki sani,Allah sai na rama duk randa kikayi aure" murmushi tayi "Dadin abun islaha na nan ai" hararta tayi "Au,ai dama na sani tuni faadaata ta koma hannun ta ai,ni bansan ya zamu qarke da ita ba idan ta tashi taga baki nan,ki gaida min ummuna da abba" "Zasuji" ta fada itama tana jin kewarsu,ta dubi rayyan dake gyara zamansa yana qoqarin kunna motar "Dear,sai ka dawo,a tuqamin sisi na a hankali" wani dan qaramin murmushi ya sakar mata sannan yayi kissing hannunta dake kan window din qofar,sannan tayi baya ya tada motar suka fice. Tsit cikin motar tayi har suka isa gidan,ya samu gefe ya ajjiye motar,ita ta fara ficewa wanda shima cikin zafin nama ta bude murfin ya fito ya sha gabanta,wanda ba don Allah yasa tayi baya da hanzari ba da gware zasuyi,cike da qasaita ya fara cewa "Mun gode da zuwan da kika mana,amma ina son shawartarki,don Allah ki sake nesanta kanki da iyali na hakanan,saboda ci gaba da shaquwarku ba alkhairi bane,ba zaki iya musu maganin komai ba,a bala'i kike jefa mu,bamu buqatar ki cikin mu kinji?" Wani irin duba take masa,rainin wayonsa ya fara isarta haka,tanajin ya zama dole yau suyi wadda zasuyi "Wai me kake nufi da ni ne?,mutuwar aure hauka ne?,a kaina aka fara?,tunda na fito daga gida na na fuskanci wani duba kake min,ya isheni haka,naji....naji zan nisanci iyalinka kamar yadda ka buqata,idan na sake taka gidanka ko na mu'amalanci diyarka ni raihana ba 'yar halak bace" ta fada hawaye na qoqarin kufce mata tare da qoqarin kewayeshi ta fice,baisan sanda ya sanya hannunshi ya damqi hannunta ba tare da jawota ta dawo gabansa,ba haka yake nufi ba,ba haka yakeson ce mata ba,yana son gaya mata yadda kullum kwanan duniya yake tashi cike da masifar qaunarta,yana son gaya mata ne yadda yake shiga bala'i a duk sanda ta qara taqi na kusanci a tsakaninsu,yana son ya gaya mata me yake ji,wacce azaba yake fuskanta aduk sanda ya tuna ta taba auren wani,wanin kuma ya kasa riqeta da daraja har ya sakota ba tare da ta aikata masa laifin komai ba,bawai yana son mata gori wulaqanci ko cin fuska ba ne "Ka sakeni yaya rayyan,sakar min hannu" ta fada idonta cikin nashi hawaye na sintiri "Naqi na sakekin raihana,dole ne na gaya miki yadda kike azabtar da zuciyata,tunda na fara sonki har yau zuciyata bata taba hutawa ba,kin janyo min abubuwa masu dama,na rasa dukkan wata nutsuwa da kwanciyar hankali na,sai kice kuma bazan gaya miki ba?,a dakeni a hanani kuma kuka?,sam bazai yiwu ba" sai da zuciyarta ta buga jin abinda ya fadi,duk da dama tana zargin hakan ke yawo a zuciyarsa,duk da ta qaryata ganin abubuwan da yake mata "Nasha gaya maka bana sonka ko?,nasha gaya maka cewa babu wannan maganar tsakanina da kai,har yau rumana 'yar uwata kake aure,so pls na roqeka kabar wannan maganar ni bana sonka baki daya bare akai ga wani batu ma na daban" ta fada tana daga masa hannu fuskarta na kallon qasa zuciyarta na daka. Tuni idanunsa suka kada sukayi ja,idan da abunda yafi tsana shine yaji tace bata sonshi,bayan yasan ita din tantiriyar maqaryaciya ce ta wannan fanninin,baisan sanda ya matse mata hannu sosai ba yana son rage zafin da yake ji cikin zuciyarsa,kai da zaya iya ma mari zai dauke ta da shi don ya nuna mata yadda ya tsani tace bata sonsa,wata iriyar zuciya ce ta dinga ciyoshi ransa ya dinga tafasa,sai ya sake fincikota ta sake matsowa dab da shi "Me kika dauki kanki ne raiha?,me kike zaton kanki?,saboda rayyan na sonki kike masa haka?,kina zaton rayyan wani abun banza ne?,to bari na gaya miki" yayi maganar yana daidaita tsahonshi da nata tare da sake matsowa dab da ita har suna musayar numfashin juna "Daga yau ki saka aranki rayyan bai taba sonki ba,ki saka aranki babu wani abu makamancin haka da ya taba shiga tsakaninku,sai meye ne raihana idan hakan ya faru,zaki gani zan fasa yin rai?" Ya fada yana sakinta tare da yin baya,da idanuwa ta dinga binsa har ya juya ya koma cikin motarsa,wani daci da bala'in qunci da zugi ta dinga ji na zagayata,ashe haka kalmar qiyayya take da daci?,ashe haka take dafa masa zuciya duk sanda tace bata qaunarsa,babu shakka yau ya dandana mata irin abinda yake ji,babu dadi sam babi dadi,sai taji wasu hawaye na bin kuncinta,kai ta shiga girgizawa tana goge hawayen "Bai kamata kiyi kuka ba raihana,bai kamata ba,abinda ya dace kenan,abinda ya kamata kenan,rayyan ya rabu dake kema ki rabu da shi"haka ta dinga gayawa kanta da kanta,sai ta kasa barin gurin har aka dage masa get ya fice. Kasa kaiwa qarshen layin yayi ya kashe motar tsakiyar hanya ya jingina kansa da makarin kujerar,wani irin motsi yaji zuciyarsa nayi tana gaua masa bai kyautu ya furta kalaman da yayi ba,bai kamata su fita abakinsa ba,sai ya dinga girgiza kai,a hankali yaji danshi kan fuskaraa yasa hannunshi ya shafo su,hawaye ne,da gaske hawaye kake rayyan?,ta shiga tambayar kansa,sai ya kasa hana kansa,ya basu mintina biyu suka zuba son ransu sannaj ya ja handkherchief yana gogesu,saidai babu wani radadi da yaji ya ragu,da sauri ya ja motar yana fatan isa gida yasha maganinsa ko zasu taimakeshi ya kashe 'yar qaramar gobarar da ta taso masa a qirji. Kusan dukkaninsu kwana sukayi cikin wani irin mawuyacin hali,damuwoyinsu suka tsananta,hatta da rumana adaren taha wani muhimmin sauyi da bata taba gani ba agun rayyan din,damuwar data gani ta sanyata itama dakuwa,tilas yayi cooling kansa ya sanyata ajikinsa ya takurata yace suyi bacci,ba don taso ba ta rufe idanun ta cikin qanqanin lokaci baccin ya saceta . Washegari ya qarfafa kansa da zuciyarsa,ya tashi cike da qwarin gwiwa da jarumta duk don ya kwantar mata da hankali,ta biye mishi ne kawai don ta nuna masa ta gamsu,saidai ko daya tunanin meye damuwarsa bai bar qwaqwalwarta ba ***************** Ranar da suka kammala jarrabawa washegari ta debi takardun dukka dalibai da zatayi marking sai maiduguri,garine da yakan mantar da ita dukka wata damuwa tata,musamman idan ta ganta gefan ammanta,ta samu nutsuwa sosai duk da cewa ba yadda taso ba,sabida abu biyu da suma suka taso suka so hade mata,na farko sultan da ya fara matsantawa kan zai turo magabatansa,ya bata dukkan wani information a kansa yace suje suyi bincike a kansa,ta sani abun zaizo musu da sauqi tunda ba boyayyun mutane bane,na biyu kuma baaba gana wanda shima ya taso wwnnan karon haiqan da qarfinsa,kwatsam kuma saiga sultan din ya biyo jirgi takanas yazo maidugurin,baima nemeta ba sai da ta gama kusan gaisawa da duk wani na sama da ita,ya samu tarba ta mutunci saidai dukkansu babu mai ikon aurar da ita idan ba abba ba,sunce shine ubanta,randa ya nemetan suna gidan amma suna hira saiga baba gana a birkice,labari ya iskeshi na zuwan sultan sai kuma ya sake zuwa ya iskesu tare da raihanan . Kowannensu hankalinsa a tashe yake kada ya rasa raihanan,sai ta rasa inda zata sanya kanta,wa ya kamata ta tausayawa?,kanta?,sultan?,ko baba gana?,wannan rikici ya sanyata kwana biyu ta sake qarawa kan kwanakin da tayi ta hada ya nata ya nata ta fara shirin dawowa,tana ganin gwara kano din tunda atleast ko sultan yazo bazaya hadu da baba gana ba,haka nan ko da baba ganan yazo bazai hadu da sultan ba. Sauyin fuska ta gani sosai gun amminta sanda zata taho wanda ya saka jefata adamuwa,abu na qarshe data gaya mata shine "Ki tsaida hankalinki guri guda raihanah ki fidda miji,ba mutuncin diya mace bane tara manema,mutuncinta dakin mijinta" haka ammi tace da ita,ko a cikin mota ma babu abinda ta tsinana illa zallar tunani har suka sauka a kano,sai yanzu tsoro ke shigarta,tsoron kada ta sake komawa 'yar gidan jiya,sultan ko baba gana wanne ya kamata ta dauka,a zahiri kowanne da irin nashi qualityn,amma a badini fa?,babu wanda tasan badininsa. *************** Qarfe tara na saafiyar ranar yana zaune a falon abban nashi,sakamakon kiransa da yayi jiya yace yana son ganinsa da safe,tunda sukayi wayar hakanan yaji hankalinsa ya gaza kwanciya,sanye yake da voile na maza light green wanda yayi luf ajikinsa ya masa kyau,sumarsa tayi kyau gwanin sha'awa tana ta zuba sheqi kasancewar bai sanya hula ba,jaridar abban ce riqe a hannunsa yake dubawa lokaci lokaci tare da jiran fitowar abban,har ummu ta shigo suka gama gaisawa ta fara jera ma abban kayan kari bai fito ba. Sanye da dogon hijabi mai hanni ruwan sararin samaniya,fuskarta tayi fayau da 'yar rama kadan da tayi,fitowarta kenan daga wanka tazo daukar kayan karin zata karya don zata shiga makaranta ta qarasa wasu ayyuka na dalibai da bata kammala ba ummu tace ta sake daukar wani flask din ta zuba kunu a kai falon abban,batasan wanda za'a kaiwa ba ta shigo ne kawai hannunta dauke da flask din,cikin jikinsa yaji alamun shigowarta,ya daga kansa ahankali idanunsu suka hadu,ba zai iya tuna kwanaki nawa rabon da ya ganta ba,zai dai iya tuna haduwarsu ta qarshe ita ce ranar da ya maidota gida daga gidanshi,yaso dauke idonsa daga kanta amma sai ya kasa kamar yadda itama taso daukewar ta gaza,can qasan zuciyoyin kowannansu kewar dan uwansa ke taso masa ba tare da sun ankara ko sun yarda da hakan ba,shi ya fara jarumtar dauke kansa wanda hakan ya taimaka mata ta qaraso inda zata ajjiye flask din ta ajjiyr,can qasan maqoshi ta gaidashi ta amsa mata cikin basarwa ta juya ta fice a hankali. A shirye abban ya fito da alama shirin fita ya gama yi,ya zauna yana janyo tray din da aka shirya kayan karina akansa gabansa yana cewa "Irin wannan sammako haka rayyan,daka bari ma sai ka taso daga aikinka ai duk daya ne ina gida" murmushi yayi yana shafa sumarsa "Ai abba gwara dai na fara zuwa din" "To yayi kyau" inji abban yana qoqarin bude flask din kunun,rayyan yayi hanzarin karba ya bude ya zuba musu a kofi guda biyu yana fadin "Abba barka da asuba,an tashi lafiya?" "Yauwa rayyan barka kadai,lafiya qalau ya gidan ya iyalin" "suna nan lafiya abba,suna gaidaka" "Masha Allah muna amsawa da kyau" ummu ce ta shigo dakin ya abban ua dubeta, "Jeki abinki fadimatu,yau tare zamu karya da rayyan kada ki damu" murmushi tayi sannan ta amsa ta juya ta fice. Suna karyawar abban na tambayarsa game da aikin ginin kamfaninsa "Abba ai baka samu har yau ka shiga ka duba ba" "Kaidai bari rayyan,sabgogi ne sukayi yawa,amma zan shiga na gani,gida ma can nijer nakeso mu je gabaki daya,an kwana biyu ba'a sada zumunci ba,amma hidima tayi yawa ta hana" "Gaskiya kam abba,nima ina maganar ya kamata muje din,an kammala ginin kamfani abban,yanzu haka abinda ya rage kawai injinan da za'a zuba,sai ma'aikatan da za'a dauka tunda tuni gwamnati tayi masa rijista dama,suma injinan shekaran jiya nayi cinikinsu ta internet a wani kamfani ,lokaci kawai nake so na samu muje ni da mukhtar mu dubasu mu aunosu a kawosu a kafa" "Yayi kyau,yayi kyau,Allah ya taimaka yayi muku albarka,sannan yayi muku jagora" "Ameeen ameen abba" ya amsa yana maijin dadin addu'ar da yayi masa,zancan da suka dinga tattaunawa kenan har suka kammala karin rayyan ya adana kayan a gefe sannan abban ya dubeshi. "Abinda yasa na kiraka rayya,kan maganar qanwarka ne raihana" sai ya daga kai da sauri ya dubi abban sabida rawa da yaji zuciyarsa tayi "Ka dade da sanin wace raihana agurinmu,marainiya ce wadda take amana ce a gurinmu,koda baka da wayo sosai amma ma tabbata kasan mahaifin raihana gaba da baya,to duka ba wannan ba,burin kowanne uba shine diyarsa ta samu gidan aure mai nagarta,miji mai nagarta,rayuwa mai nagarta,Allah ya sani fiye da haka na yiwa raihana sha'awa,saidai kuma ba haka Allah ya hukunta ba,kuma abinda duk ya hukunta din shine daidai" "Gaskiya ne abba" ya fada kansa a qasa cikin zaquwa da jin abunda abba zai furta "To,a yanzu haka akwai mutum biyu da suka fito suna neman aurenta,akwai wani yaro sultan dan gidan wazirin azare,sai kuma dan uwanta wanda ke can maiduguri wato baba ghana,dan baffanta ne" wata tsawa yaji cikin kunnensa wadda ta toshe jinsa na wasu 'yan mintina,zuciyarsa ta hau tsere,yaji jini na neman haurawa har qwaqwalwarsa,meke shirin sake faruwa?,qaddara ko sakaci?,asara yake shirin sake tafkawa karo na biyu ko kuma me?,abubuwan da ya ringa nanatawa kansa kenan,kusan duk wani bayani na abban baijishi ba sai da ya ambaci sunansa daga qarshe "Rayyan" "Na'am abba" ya amsa bakinsa na bari,lebansa na rawa "Nayi nawa binciken a kansu baki daya babu mai wata matsala,amma gudun sake tafka kuskure karo na biyu ya sanya na baka dama kaima kaje kayimin naka binciken a kansu duka su biyun,tunda ku yaran zamanine kusan kun fimu ido da sanin dabaru,babu wani abu da za'a iya muku alaye a cikinsa,kada ka manta.......RAIHANA MARAINIYA CE KUMA AMANA CE" "to abba....to abba....in sha Allah" abinda yaji yana nanatawa kenan tare da miqewa kamar wanda aka tsikara,dubansa abban yayi "A'ah,har tafiya kuma?" "Eh abba,a huta lafiya"ya fada da hanzari yana ficewa don yanajin zai iya faduwa a duk sanda yaci gaba da tsaiwa gabansa "To" abban kawai ya fada tare da binsa da kallo ganin sauyawar da yayi lokaci guda,janye idonsa yayi ya miqe yana hada takardunsa da zai fita da su. Kusan da qyar ya kai kansa a sibitin mukhtar din,wanda cikin sa'a ya sameshi yana nan,kusan tunda mukhatr din ya tallafoshi ya fito da shi daga motar ya fara daina gane abubuwa sosai,duk tambayar da mukhtar din yayi masa babu wadda ya iya amsa masa,ganin tambayoyin basu da amfani ya sanyashi fara bashi taimakon gaggawa,sai daya tabbatar bugun zuciyarsa ya daidaita sannan ya kaishi wani daki na musamman ya jona masa qarin ruwa,ido kawai ya zubawa rayyan din,ashe da gaske akwai irin wannan soyayyar a duniya?,eh gata kuwa yana gani akwai din,amma daidaikun mutane Allah ke jarabta da ita,wani irin so ne da baya badin zuciya ta huta,baya taba baiwa zuciya 'yanci,sone da kakejin idan ka sameshi ka samu komai idan ka rasashi ka rasa komai(kada kuyi tunanin matsanancin so irin wannan cikin littafi ke kawai,a'a a zahirance akwai wadanda Allah ke jarabtarsu da irinsa,saidai a kaso dari kaso uku ne suka gamuwa da irinsa,naga mutane hudu irin hakan). Tausayin rayyan ne sosai cikin zuciyarsa,tsoronsa daya kada zuciyarsa ta gaza daukar damuwar dake cikinta,tabbas so ba qarya bane,duk yadda kakai ga son fiddashi cikin zuciyarka hakan bai yiwuwa komai dadewar zamani kuwa,har zuwa azahar rayyan na barcin,so yake ya fita ya duba wasu allurai na zai masa idan ya farka a wani pharmacy can hanyar zaria road kuma baya son barinsa shi kadai,dole ya dauki wayar rayyan din ya duba lambar rumana don tazo ta kula da shi kafin anjima ya sallamesu,don sau tari da yayi irin wannan baccin dare yayi ya farka yana iya komawa gida. Tana zaune islaha na kan cinyarta tana raba mata kanta gida biyu tana matse mata shi da ribbom kiran ya shigo . Murmushi tayi tana daga wayar ganin sunan wanda ke kiran ta kara a kunnenta. Kasaqe tayi jin ba muryarsa bace,hankalinta atashe ta shiga tambayar mukhtar din,ya kwantar mata da hankali kan cewa ba wani abu bane,tazo tadan zauna da shi basai ta sanarwa kowa ba,da hanzarinta ta haura sama ta sauya kayan jikinta ta rufa hijab ta sunkuci islaha suka fito,driver dinsu baya nan a lokacin tilas tayi shahadar quda don na qwarewa tayi can ba wajen tuqi ta tuqa su. Cikin ikon Allah kuma suka kai lafiya,hawaye ne ya subuce mata tana kallon rayyan tare da girgiza kai,a yau kuma zuciyarta ta qure haqurinta,kawaicinta ya gaza,tana son sanin damuwar mijinta,tana son tasan meke taba ransa,bata kuma shakka mukhtar ya sani,ta waiwaya ta dubeshi idonta na fitar da hawaye "Mukhtar,na gaji hakanan,na gaji da wannan qumbiya qumbiyar,inason sanin wane hali mijina ke ciki?,inason nasan mene damuwarsa me yake damunsa" "Calm down rumana,kawai lalura ce......" Dakatar da shi tayi ta hanyar daga masa hannu "Kada ka gayan haka,kada kacemin babu komai,mukhtar wallahi zan iya hadaka da ubangiji idan baka sanar da ni ba" sai tayi sanyi da muryarta "Yanzu a matsayina na matar rayyan idan bansan damuwarsa na wa kake so ya sani?,idan ban damu da shi ba wa kake so ya damu da shi?,kafa fa ka manta shine uban 'yata,haba mukhtar,ka taimaka ka gayamin na fita daga kokwanto da rashin kwanciyar hankali,a qalla ko bazan iya bashi lafiya ba ai zan masa addu'a,zan kwantar masa da hankali duk sanda damuwar ta motsa masa" shiru mukhtar din yayi yana auna kalamanta,tabbas gaskiya ta fada,saidai ya ruga da ya yiwa rayyan din alqawari tun ba yanzu ba sirri ne tsakaninsu "Rumana,ba wai wani abu yasa na qi gaya miki ba,na riga na yiwa rayyan alqawarin rufe maganar can wasu shekarun baya...." "Indai don wannan ne wallahi Allah na yi maka alqawarin rayyan bazai taba sanin cewa kai ne ka gayamin ba,na maka alqawari kuma tsakani na da Allah" shuru ya sakeyi sannan ya gyada kai ya duqa ya dauki islaha dake ta carkwada masa surutu sannan yace ta biyoshi,yana gaba yana taya islahan surutunta har suka isa office dinsa. Kujera ya nuna mata yace ta zauna sannan shima ya samu wata ya zauna yana dubanta "Rumana,ina da yaqinin kina da ko kuma zaki iya bawa rayyan magani idan har da gaske kina sonshi ya kuma warke sumul tamkar babu wani abu da ya taba damunshi" *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _______________________ *Manzan Allah S A W yace "haqiqa Allah madaukakin sarki tsarkakakkene,kuma baya karba sai mai tsarki"* _______________________ *Babi na talatin da hudu* Idanunta qyar kan mukhtar,ta zaqu taji me zaice?,meke da akwai "Bana zaton duk duniya akwai wanda ya kaini qaunar ya rayyan,hakanan babu wanda zai kai ni son ya samu lafiya,maganar ma idan ina sonshi bai taso ba mukhtar,ka gayan kai tsaye meke damun ya rayyan dina". Kai yake girgizawa,a nutse ya fara bayyana mata duk wani abu da ya sani dake tsakanin rayyan da raihanan,tun idanunta na bude tana saurarenshi har ta lumshe ido tana ci gaba da sauraren nasa,kafin ya kammala tuni hawaye ya jiqe idanunta. Shirun da taji yayi shike bayyana mata cewa ya kammala,a hankali ta bude idanun nata,ta sanya gefan mayafinta ta goge fuskarta " na gode qwarai doctor,na tabbata cewa badon kai ba babu yadda za'ayi nasan da zaman wannan BOYAYYEN SIRRIN,na gode"ta qarashe maganar tana miqewa tare da saba islaha a kafadarta. A hankali take takawa zuciyarta na wani irin harbawa cakude da al'amura daban daban,a hankali ta tura dakin da rayyan din ke kwance har yanzu bacci yake,har ta zura qafarta sai ta cireta ta dawo da baya,sam sai taji ba zata iya zama ba,kai tsaye ta juya ta fice daga asibitin,motar data zo da ita ta bude ta shige sannan ta tayar da ita a hankali suka fice daga asibitin. Cikin daqiqu suka isa gida,ta kulle ta riqe hannun islaha suka shige ciki,shiru gidan yake kasancewar babu yara,sai lantana kawai a kitchen tana girki,sannu da zuwa ta yiwa rumanan ta tambayeta ina raihana ta gaya mata tana makaranta,ummu fa?,ta sake bata amsa "Bata dade da shiga daki ba,bacci take" "Ok,qyale kawai kada ki tasheta" ta fada tana wucewa kai tsaye cikin falon,dakin raihana ta tura don a bude yake,bakin gadon dakin ta qarasa tana zaunar da islaha kai,sai kuwa ta bingire tayi kwanciyarta jinta akan gado,itama gefan gadon tabi ta zauna tana maida numfashi. A hankali take bin dakin da kallo tana tuna zamanin 'yammatancinsu,abubuwa da yawa suka dinga fado mata,duk da cewa yanayin dakin ya sauya amma har yanzu gadajensu na nan da yanayin tsarin dakin,sai ta miqe a hankali ta isa ma'ajiyar hotunansu,yau tana son gani,tana son tuna wani abu,ta jawo album daya ta koma gefan gadon ta zauna. Daya bayan daya ta dinga bin hotunan tana dubawa wadanda ba qaramin sake yi mata tasiri sukayi ba,tamkar wani tishi suka yi mata game da wacece raihana a wajenta,tazo tsakiya taci karo da littafin,zata iya tuna sanda taga raihanan na boyon littafin tare da hanata tabawa shekaru kusan uku baya,sai ta zari littafin ta ajjiyr album din ta bude littafin. Murmushi ta dunga yi a hankali ganin yaffa raihanan ta zauna tana zana quruciyarsu,a hankali ta gangaro kan kalaman,kalaman da suka sanyata ta sake imani ta kuma miqe tsaye hawaye na fita daga idonta,a hankali ta koma ta zauna tare da kifa littafin kan fuskarta "Dama da gaske doctor mukhtar yake?,ashe da gaske ne?,don me sisi me yasa?,wannan wace iriyar SADAUKARWA ce wannan?wace iriyar ZUCIYA ce haka?,wacce iriyar 'YAR UWA CE wannan?,me yasa kika zalunci kanki raihana,me yasa kika haramtawa kanki farinciki saboda ni?,me yasa kika sa na zama silar azabtuwar zuciyarku da rayuwarku tsawon wadan nan shekarun,tabbas na zama wawiya da na kasa fahimtar abinda sisi na ke so,na zama azzaluma da na zama silar azabtuwar sisi na,wadda burinta ako da yaushe taga taga nawa farincikin,taga cikar burina . Da sauri ta jiye littafin ta dauki photo album din ta maida littafin ciki ta miqe ta mayar da album din inda yake ajjiye,garin juyowa taji wani abu ya fado,a hankali ta duqa,zobe ta gani mai dauke da double R,irin nata ne sak,abinda ya rabasu da nata wannan na azurfa ne,ba shakka daga rayyan ta sameshi don da tasanshi a hannunsa daga bisani ta bar ganisa,hakanan bata taba ganinsa a hannun raihanan ba,kai ta girgiza ta maida zoben gurinsa,a fili tace "Ya isa haka,ya isa,wannan karon fagen na rumana ne" ta fadi tana juyawa wajen da islaha take ta dauketa sannan ta fice daga gidan ba tare da ummu tasan tazo din ba. ***************** Duk cikinsu babu wanda tace da shi komai. Kujera ta sanya gaban gadon da yake zaune bayan ta gama bashi tea,idanunta cikin nashi take kallonsa "Nifa kije ki gayawa mukhtar yazo ya sallameni,babu kwanan asibitin da zanyi maman islaha" murmushi tayi sannan tace "Dama ai ko bai sallameka ba ka warke yaya rayyan,qila ko bai sallamemu ba mu gudu gida kawai,wannan ciwon daga yau ya qare yazo qarshe" cikin alamar tambaya yake dubanta,sai ta daga masa gira "Eh,duk cutar da ta samu magani ai kaga waraka ta samu ko?,zaka samu RAIHANA kaga ya zama dole sauqi yazo" ci gaba yayi da dubanta ba tare da yace komai ba,itama kallon nasa take tana so taga reaction dinsa,saidai duk yadda yaji mamakin furucin daga bakinta hakan bai bayyana ga fuskarsa ba,abinda ya sake saka mata yaqinin lallai rayyan din jarumi ne,bata tsammaci dakiyar har haka daga gareshi ba,koda yake ba abun mamaki bane tunda ta fuskanci irin wannan dakiyar har ta tsahon shekara uku ko hudu. Ganin cewa baida niyyar furta komai baya ga kallonta da yake yasanya cewa "Eh yaya rayyan,wannan karon zaka samu raihana,zaka mallaketa......" "Mtswee,wane irin zance kike irin haka ne rumana,bana son shirme da Allah?" Gira ta daga cikin alamun tambaya "Shirme kamar yaya?,raihana ce silar ciwonka,raihana ce silar rashin sukuninka tsahon shekaru,raihana kake burin mallaka,eh.......hakan ma ba laifi bane,sisi na ta cancanta,ta cancanci hakan,tana da hakaye dabi'u da kyaun da zata samu haka,meye laifi a ciki?" Wani kallo yake mata jin maganar da take furtawa "Wa ya gaya miki wannan maganar?" Kai tsaye tace da shi "Bai zama lallai kaji ba,wannan ba itace damuwarka ba,damuwarka ka samu raihana kuma zaka sameta" shigowar doctor mukhtar shi ya katse musu maida maganar da suke. Idanun rayyan din qyar kan mukhtar,wani numfashi yaje fiddawa cike da bacin ran da baisan dalilinsa ba,kallon da yaga rayyan din na masa kadai ya sanyashi shan jinin jikinsa "Da kyau!,baka cika alqawari ba,hakanan kaci amanar da na baka!"tsaf ya gane kan meye yake magana,don haka ya tako a hankali inda suke yana duban rayyan din " babu wata mafita rayyan sai wannan,zuciyarka ba zata taba daina son raihana ba,hakan na nufin dawwamarka cikin cuta mai barazana ga yankewar rayuwar dan adam,don me zamu zauna mu zuba ido ka halaka bayan akwai mafita?"hannu ya daga masa ba tare da ya dubeshi ba "Tashi ka fita,kaje ka rubutomin takardar sallamata" ya fada kansa tsaye,yasan rayyan din sarai,miqewa kawai yayi yana murmushi ya kama hanyar ficewa. Idanunsa ya maida kan rumanan "Ki bar maganar nan inda take" "Zan barta matuqar ka tabbatar min bakwa son juna kaida raihana" ido ya dan zubata mata sannan yace "Naso raihana kuma har yau ina son raihana,saidai na zamuyi aure ba kamar yadda tasha alwashi a baya . Da sauri ta tari numfashinsa "Alwashin da ta sha nice sila,kuma a yanzu nice salar zamowarta matarka in sha Allah" "Idan kuma nace ni bana so fa?" "Ko baka so indai ita tana so to dole ka aureta,dole na bata farinciki kamar yadda ta bani" Murmushi yayi yana kada kai "To sai mu gani ai,zanga ta yadda zaki ma mijinki auren da ya riga yace baiso ya haqura" "Zaka gani kuwa"rai ya hade tsaf sannan yace " kina son bacin ranki kenan ko?"kafada ta daga "Indai akan wannan ne na shiryawa hakan,na shiryawa duk wani abu daka shirya" ta fadi kanta tsaye,ido ya zuba mata na wasu 'yan sakanni sannan ya jinjina kai. A hankali ya sauka daga kan gadon,ya nufi kujerar dake ajjiye gefe,ya dauki rigarsa 'yan saman ya zura,ya sanya takalmansa yana duban rumanan,itama sai ta miqe tana gyara rufin mayafinta,baice mata komai ba ya isa inda islaha ke kwance tana bacci ya dauketa ya saba ta akafadarsa,daidai lokacin doctor mukhtar ya shigo riqe da takarda,ya dubi rayyan yana murmushi "Au da gaske guduwar zaka yi kenan?" "Eh,banga dalilin ci gaba da zamana bane a nan"dariya mukhtar din yayi cike da tsokana " eh kam,lallai, a yanzu baka da dalilin zama nima na yarda da hakan,tunda magani na dab da samuwa ko?"harara ya maka masa sannan ya murda qofar yayi ficewarsa,rumana ya miqawa takardar "Ni da rayyan duk daya ne,basai kunje kun biya komai ba,wannan maganin kawai zaisha na sati biyu,kiyi qoqari madam kiga komai ya tabbata,na tabbatar kema hakan zai qara kwantar miki da hankali,uwa uba ladarki na ga Allah" kai ta gyada tare da fadin "Insha Allah mukhtar,na gode" sannan tabi bayan rayyan. _sai kun yimin uziri,muna hidimar biki ne_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _______________________ *An karbo daga abu huraira R A yace,manzan Allah S A W yace"wani mutum yana cikin tafiya a hanya,sai yaci karo da reshen bishiya mai qaya,sai ya kawar da shi,sai Allah ya gode masa kuma ya gafarta masa(sakamakon kawar da wannan abun da zai iya cutar da wani da yayi daga kan hanya)"* _______________________ *Babi na talatin da biyar* Yadda ya shareta itama haka ta shareshi har tsawon kwana biyar tana ta hidimarta ba tare data sake tada maganar ko ce masa wani abu ba tana so taga gudun ruwansa. Da dare tana shiri cikin kayan bacci yayin da shi kuma ya kammala nashi shirin yana tsakiyar gado zaune harde da hannayensa yana dubanta,gefansa take shirin kwanciya ya janyota ta fada jikinsa ya matseta,luf tayi a jikinsa don bata iya bijirewa duk sanda ya sata atarkonsa,cikin dakiya da shan mur yace "Wai me kike nufi ne?,kina nufin don kin min tayi naqi amsa ahine kika tsiri gaba da ni?" "Laifi nayi don na aikata hakan?" "Ok a gurinki ba laifi bane kenan?" "Eh tace da shi" sai ya shareta ya shiga sha'aninsa don ya fuskanci maganar take so ayita ja. Da safe yana shirin fita ta dubeshi "Daddy ina so naje qoqi"ya daga kanshi yana kallonta " da daddare kuma?" "Eh" shiru yayi sai da ya kammala abinda yake sannan yace mata "Ki shirya da yamma kije,bayan sallar isha'i zani gidan sai na daukoki mu taho tare" "To" tace masa Qarfe biyar da mintina ta isa gidan,lokacin hajiya babba na zaune suna ta dambe da gyangyadi,bata so bacci ya dauketa ganin la'asar ce "Oh ke kuma daga ina?" Ta fadi tana gyara dankwalinta da ya karkace yana shirin faduwa,sai data zauna sannan tace "Kai hajiya,ke dai ko yaushe kamar tsohuwar 'yar jarida,ai ko sannu da zuwa kya fara yimin ko kafin tambayar ta biyo baya" "Ah ah,to,ai dole na tambayeki,na ganki haka la'asar sakaliya" sai da suka gama 'yan barkwancin nasu sannan suka gaisa,ta miqe ta shiga dakin hajiya qarama don su gaisa,can ta tadda kausar sun baje ita da meela,baki rumanan ta kama tana fadin "Da kyau,wallahi kuna sha'aninku,wato meel abun ma dan waken zagaye ce?" Tana dariya tace "Kinsan Allah yanzu nake maganarki,nace mu saka rana zanje na miki wunu,dama nasan dole kimin mita" nan ta zauna cikinsu ta gamu da abokan surutu irinta,sai shida ta fito ta koma gun hajiyan. "Nifa magana nazo muyi hajiya" ta fada tana zama gabanta" "Yar nema,dama nasan taki ce ta kawoki" inji hajiyan wadda ke gyarawa islaha da tayi bacci kwanciyarta,lokaci daya fuskarta ta sauya kafin ta fara maganar,wanda ke nuna cewa magana ce muhimmiya,hakan ya sanya hajiyan tattara hankalinta kan rumanan "Hajiya,kinsa cewa akwai alaqar soyayya ta shekaru tsakanin rayyan da raihana?" Sqi hajiyan ta dan ya mutse fuska "Kamar yaya?" "Hajiya,rayyan da raihana suna son junansu tun kafin raihana tayi auren fari,dalilin hakan ne ma ya sanyata yin auren saboda ni". A hankali ta warwarewa hajiyan dukkan abinda ta sani,da kanta hajiyar ta sanya rumanan tayi mata kiran doctor mukhtar ta waya don ta sake samun tabbaci,shi din ma bai boye komai ba ya yiwa hajiyan bayani. Miqawa rumanan wayar tayi fuskarta qunshe da murmushi " alhamdulillahi rabbil Aalamin,Allah ya amsa addu'ata"inji hajiyan,sai ta sake gyara fuskarta tana duban rumana "Ina fatan kunnuwa na bazasuji wani abu mara dadi ba dangane da ke ba,don na tabbatar ba tarbiyyar mu bace koda kin bayyana hakan" kai ta kada tana duban hajiyan "Haba hajiya haba,kafin wani ya gayan hakan ni ya kamata na gayawa kaina,kafin na yiwa raihana halacci ita ta fara yimin,rama halacci sai dan halak,ta SADAUKARMIN da farincikinta taje ta auri wani alhalin bata da yaqinin zasu rabu,ta auri wani ta barmin rayyan din na rayu da shi har abada itama ta rayu da wancan har abada,ta SADAUKARMIN da rayyan alhalin tana tsananin sonshi don me ni zan kasa raba rayyan tsakanina da ita duk da son da nake masa?,duk yadda na kai ga kishinsa?,wannan ne kawai halaccin da zan mata,wamnan ne abu na farko da zan fara SADAUKARWA sisi na a rayuwarmu,ta dade tana SADAUKARMIN da abubuwa tun quruciyarmu,duk abinda na nuna inaso tana iya barmin shi ita ta haqura,itace wadda ta zama silar daidaituwar alaqata da rayyan a sanda yazo ya taddani mai tarin abokai da qawaye,sau nawa tana rufan asiri,tana maida laifukan dan aikata zuwa kanta?,hajiya shekara nawa raihana tayi tana jure radadin rashin wani abu kuhimmi da tafi sonsa a rayuwarta wanda na tabbatar ni a karan kaina bazaj iya jureshi ba" kai tavi gaba da kadawa hawaye na fita daga idonta "Bani da juriya da jarumtar gami da zurfin ciki irin ja raiha amma wannan karon ina fatan na fita dukkan wadan nan abubuwa,ina fata na mata sadaukarwa wadda zata tattara dukkan wata SADAUKARWAR data taba yimin,ina fatan na bata farinciki kamar yadda ta bani,na bata faata nayin ingantacciyar rayuwa" jikin hajiyan a sanyaye take duban jikar tata,tabbas ta riga data sani kishi ba qaramin abu bane,halas ne a gun rayyan ya auresu duka,hakananbsuma suna da haqqin bawa zukatansu abunda suke so,bai kamata ba ba kuma adalci bane su rintse ido suqi kowa sai diyarsu,su take gaskiya da duk wani abu da ya kamata saboda jin dadin tasu 'yar,amma raihana mutum ce,suna jinta cikin jininsu kamar yadda diyarsu take,tana da dukkan wasu halaye managarta wanda sau tari a gunta diyar su take koyo "Allah yayi miki albarka umma rumana,na godewa Allah da baki zama mai son zuciya ba,duka ita duniyar dama nawa take?,yaran yanzun ne suka dauketa wajen zama,ko yanzu ko anjima ko yau ko gobe dole ka barta,bayan ka barta din kuma babu abinda zai tsaya za'a fasa shi saboda kai,saboda baka nan,Allah ya sani na dade ina yiwa raihana sha'aqr auren rayyan,saboda nasan zaki samu managarciyar abokiyar zama,'ya'yanki zasu sami abokiyar zaman uwa ta gari,hakan mijinku zai samu walwala da kwanciyar hankali" kai rumanan take gyadawa tana share qwallarta sannan ta dubi hajiya. "Amma hajiya akwai matsala,dalilin da ya sanyani tukararki da maganar kenan" "Matsala kuma wacce iri ruma,nayi zaton daga gareki ne idan ma za'a samu matsalar" "Rayyan ne hajiya" bata boye mata dukan yadda sukayi da rayyan din ba ta bayyana mata,kai hajiyan ta girgiza "Barni da shi,dauki wayarki ki kiramin yusufu da dalhatun dukkansu kice inason ganinsu bayan sallar magariba,yau nake so a gamata" wayarta ta zaro ta kirasu dukkansu suka amsa cewa suna tafe daga kasuwa zasu zarto da yardar Allah,ajjiye wayar tayi tana kallon hajiya "Amma hajiya ina neman alfarma guda daya" ba tare data jira hajiyan ta amsa ba ta dora "Idan zai yiwu bana son raihana ta san da maganar nan,a barta arufe har zuwa wani lokaci,wallahi hajiya nasan halinta sarai,tana iya bijirewa zancan,ni na gani na ji kuma ajikina,ta sha alwashi hajiya ta kuma kage kan ra'ayinta tsawon shekaru,to na tabbata a 'yan watannin nan babu abinda zai iya sauyata,hajiya,indai raihana ce tana iya sake auren wani akan ta auri yaya rayyan" kai hajiyan ke gyadawa tana sake nazarin maganar. Shiru dukkansu sukayi suna jin jina lamarin,zuciyar daddy dalhatu fes hakan ya nuna har kan fuskarsa,yayin da alhj yusuf shima haka tashi zuciyar take amma ya nuna kara bai bayyana ba,yana tausayin yarinyar yana tausayin maraicinta,yana ganin qimar ta yana qaunarta kamar daga cikinsa ta fito saboda nagartar da take gareta "Alhamdulillah,wallahi hajiya na dade banji wami al'amari da ya faranta min rai kamar wannan ba,kullum da batun yarinyar nake kwana nake tashi,sai na dinga gamin kamar gazawarmu ce ta fito da ita daga dakin mijnta alhalin ruma har yau tana nata dakin,kuma a yanzu babu wanda zamu bawa aurenta mu koma ku kwanta muyi bacci hankalinmu kwance kamar rayyan din,wannan zance ya yimin dafi hajiya qwarai" ya qaraage maganar fuskarsa qunshe da murmushi,hajiyan ta sake maida dubanta ga alhj yusuf "Yusufu banji kace komai ba" gyaran murya ya danyi "To hajiya ai ni gani nayi ita rumana kamar bamu kyauta mata ba idan mika ce zamuyi haka" dakatar da shi tayi da sauri "Au abinda yara suke so zamuyi ko abinda ya dace?,wa yasan da zancan ma acikinmu idan banda tazo da maganar?,muji tsoron Allah mu duba maraicin raihana muyi mata gatan da koda bayan ranmu ba zata taba tizarta ba,za kuma taci gajiyar abinda mukayi din daga kan 'ya'aya har jikokin jikoki" kai yake jinjinawa cike da gamsuwa,kusan shine mutum na farko da zaya so hakan,ba ya fadi bane saboda yana adawa da abun,kawai kara ya nuna da kawaici "Hakane hajiya,ubangiji Allah yayi musu albarka,ya tabbatar da alkhairi,yasa albarka" "Ameen ya Allah" sai ta kuma gaya musu alfarmar da ruman ta roqa sannan ta dora "Ni kaina na amince da abinda ta fada din,din ta rayyan nasan yadda zan biyar da shi,amma ita yarunyar tabbas zata yita jin nauyinku,balle tana tsakaminmu zata dinga gani kamar wami abu ne,barin ma mu mata da ba'a raba mu da gutsiri tsoma,din haka bana son ta sani,koda tasan cewa za'ayi auren nata amma kada ta san cewa rayyan ne wanda zata aura din,kosu maidugurin ku barsu kawai a zuwan wani ne,idan lokaci yayi ko ta kama ko zancan ya fito ta sani" basu da damar musawa,duk abinda hajiyan ta fada ya tabbata,nasu kawai ameen ne. Alhj dalhatu ne ta fara sanya hannunshi cikin aljihun rigarsa yana fafin "Barima ki gani kawai hajiya" ya fiddo da 'yan dubu dubu ,duk da cewa ba sababbi bane amma ashirye suke,da alama daga banki ya karbosu zaiyi wata hidimar,a tsakaninsu ya ajjiye "Ga sadakin dana nan rayyan,naira dubu hamsin ce" murmushin farinciki ya kufcewa hajiyan,tabbas babu shakka wata DANGANTAKAR daga Allah take,musamman idan aka gina ta saboda Allahn "Ubangiji ya yi muku albarka,kai yusufu dauki sadakin diyarka ka qirga da kanka" shi din ma fuskarsa qunshe da murmushi ya dauki kudin,qasan zuciyarsa cike fal da qaunar bayin Allahn masu tarin karamci da sanin ya kamata,A aljihu ya sanya yana fadin "Banu haka tsakaninmu hajiya ai babu lissafi tsakani na da dalhatu,Allah ka duba niyyarmu da nufinku ka sanya albarka ka cikin wannan hadi" basu bar gaban hajiyan ba sai da ya kira tasa mahaifiyar rahina ya fede mata komai sannan ya hadata da hajiya babban suka sake magana,itama addu'a tayi sosai tare da sanya albarka mai tarin yawa. . A bakin qofa sukayi kacibus da rayyan din wanda ke qoqarin shigowa gidan,cike da girmamawa da ladabi ya tsugunna ya gaidasu sannan ya shige ciki. Sai da ya leqa ya fara gayar da hajiya qarama,rumana na dakin zaune ita da kausar suna hira,duk da rabin hankalinta ba a nan yake ba,yana dakin hajiya babba,bin bayansa tayi bayan sun gama gaisawa da hajiya qarama ya fice. Tana zaune inda take zuciyarta cike da farinciki,fuskarta kadai zaka kalla ta gaya maka hakan,ta daga kai tana amsa sallamar rayyan din tare da yi masa maraba da kuma dan tsokanarsa irin na jika da kaka kamar yadda suka saba,ya dauketa ne tamkar kakarsa wadda ta tsugunna ta haifi abbansa,rashin kakar a kusa yasa ita yake dan jan wasan jika da kakar lokaci lokaci. Gefansu rumanan ta zauna,ya waiwaya ya dubeta bayan sun gama gaisawa da hajiyan "Yaya dai madam,naga kamar a gajiye kike" kai kawai ta kada masa alamun ba komai,nazarinta yayi kadan sannan ya maida kansa gun hajiya "Ga furarka,yadda yau kake na musamman haka na maka daamu na musamman" cewar hajiyar data tashi da kanta ta dauko masa furar daga freezer dinta ta ajjiye masa hade da ludayi,kusan duk sanda yazo gidan sai yasha furar,yana jin dadin damun na hajiyan nononsu kai kyau ne har maiqo yake,bude kwanon yayi yana sanya ludayi ya fara motsawa yana murmushi yace "Yau nine na musamman din,hala yau auren akeyi sosai da ni hajiya" "Qwarai kuwa,qiris ya rage ka zama angon mutum hudu,kaga mun rufe qofa" dariya yayi cikin rashin bawa batun muhimmanci ya dauki duka wasa ne irin na hajiyan "Wa da wa kenan,nidai nace banyi da ku kun mana tsufa,umma rumana ta kawai na sani" "Ai kuwa aure da mu dolen doliya,ni uwar gida,sai hajiya qarama ta biyu,rumanan taka dole ta biyo mu a ta uku,ga kuma RAIHANA tafe" wani saukar lugude yaji cikin qirjinsa,har ya kasa hadiye furar da ya kurba din,zuciyarsa ta shiga da wurwurar maganar da hajiyan keyi,raihanan gaske ko ta wasa,ko kunnensa ne baiji daidai ba,ko wasa hajiyan ke masa,kamar tasan meke yawo a qirjinsa sai tayi murmushi "Ina cewa ma kaga fitar iyayen naka,sadakin raihana na aljihun abbanku yusufu daddynku dalhatu har ya bayar" wannan karo dukansu shi da rumanan maganar ta daka,shikam muqut ya hadiye furar bakin nasa baki daya lokaci guda har yaso qwarewa,sabanin rumana data lumshe ido,tana jin yadda zuciyarta ke daka,dakan data rasa dalilinsa,gefe daya kuma zuciyarta na mata sanyi ganin cewa ta kusa cika burin sisinta. "Wai wacce raihanan hajiya kike magana?" Ya tambayi hajiyan bayan ya dauke kansa daga kallon rumana wadda ya zubawa ido cike da tuhuma "A'ah,raihana nawa ke garemu?,ina cewa daya ce ko,qanwarka 'ya ga bukar Allah ya masa rahama" sai jikinsa ya mutu baki daya,ya ajjiye kwanon silbar hannunsa ya jingina jikinsa da kujera yana kallon rumana,sai kuma ya maida dubansa ga hajiya "Hajiya,raihana bata sona,nima na haqura da ita tun tuni,na fadawa rumana amma taqi jin maganata,ya za'ayi ku tilasta bazawara auren wanda bata so,ko a musulunci ba daidai bane,nidai hajiya bana so kamar yadda bata so" daquwa ta watsa masa bayan ta hade rai kamar bata taba dariya ba,abinda bai taba shiga tsakaninsu ba kenan "Indai baka son auren raihana to qarya kake na rumana ba ka so,abinda yayi rumana shi yayi raiha,matuqar kuma kana son ganin bacin rai daga gareni ni maimunatu ka ja da auren nan,idan kuma kana son nunawa duniya maimuna yusuf da dalhatu basu isa da kai ba bismillah" maganar ta ratsa shi matuqa,musamman da yake ko yaushe shida hajiyan babu maijin kansu,sai ya rasa me zaice,duk wata gabarsa tayi sanyi,miqewa yayi kawai ya dauki islaha a kafadarshi yace "Hajiya sai da safe" "Allah ya bamu alkhairi", miqewa itama tayi ta lalubi mayafinta ta sanya,hajiyan na sanya mata albarka tare da bata qwarin gwiwa,sannan ta sake jaddada mata kada ta bari shaidan yayi galaba akanta ta yawaita addu'a. Cikin motar ta sameshi ya cika yayi fam,banza tayi da shi ta shiga seat din kusa da shi ta zauna,kusan minti goma bai tayar da motar ba " daddy muje ko dare na dada yi"tamkar jira dama yake ya bude mata wuta "Wato kin maida ni shashasha ko?,wai ana dole ne?,ya mukayi dake kan maganar last week ashe baki barta ba saboda taurin kai,dama munafurci zakiyi shi ya sanyaki cemin zaki zo" sai taji zuciyarta ta mata zafi,a hasale itama ta yunquro "Ya isheni hakan abban islaha ya isa,ka daina pretending haka kaji,har yanzun kana son raihana kamar yadda ka fada,kuma na zaka taba iya daina sonta ba,hakan na nufin kaci gaba da zama da lalura ko?,to akanme zan zuba ido zuciyarka ta samu matsala nayi asararka?,akan me zan yarda na rasaka bayan ina da hanyar kubutar da kai,indai nayi haka har abada banyiwa kaina adalci ba,bana son na sake jin wata magana daga bakinka rayyan ka barni haka,idan ma saboda ni kuke yin haka ko kakeyi hakan baku burgeni ba....." Sai kuka ya qwace mata,take jikinsa yayi sanyi,ya dinga sakin ajiyar zuciya,baisan me yasa zuciyarsa ke yawan daukar zafi ba kan batun raihana,abunda ya sani kawai yana jin wani kishi da bacin rai mai zafi duk sanda ya tuna cewa ta taba zaben wani ta barshi,ta taba zaman aure da wani,ta taba bawa wani kanta,wanda idan ya tuna haka shi kadai sai yaji kamar ya dawo da baya ya goge wannan,mutum ne shi mai kishi musamman kan abinda yake so. Janyota jikinsa yayi yana bubbuga bayanta yana fadin "Am sorry my angel,bana nufin bata ranki,amma don me kike son na auri wata bayan mata da yawa basu son kishiya" a qufule ta dubeshi yana qara son hasala zuciyarta "Raihana ba wata bace,idan da wata ce din da bazan bata damar shigowa rayuwarmu ba,ban dauketa a matsayin wai kishiya ba,tana nan a matsayin sisinta,so babu ruwanka" "Shikenan,amma dai wannan ba alamu ne na kina sona ba" "Son da nake maka ne ya janyo hakan,idan banda ina sonka din babu ruwana da damuwarka ko matsalarka" sai ta janye kanta daga jikinsa "Mu tafi gida don Allah na gaji" sai da ya yagi tissue ya gyara mata fuskarta tas,ita din ma bata hana shi ba da idanu take binsa cike da quna sannan ya kunna motar suka bar unguwar ********** Sai daya yayi wanka yaci abinci ya gama kallon labaran qasa a NTA sannan ya sata ta dauko masa rigar da ya cire,kudin ciki ya fidda ya miqa mata ta karba tana juya kudin a hannunta sannan ta tambayeshi na meye?,a nutse ya zayyane mata komai,mamaki da tausayi suka kamata lokaci guda "Dama raihana na son rayyan amma ko a fuska ban taba ankara ba har tayi wani auren?,yanzu rumana da kanta ta fasa wannan qwan?" Abinda ta dinga nanatawa kenan,jinjina qaunar da kowanne ke ma dan uwansa bilhaqqi take,ta dade cikin zurfin tunani har sai da abba yayi magana sannan ta maido hankalinta kansa "Ni kaina sai da maganar ta fito sannan na dinga hasaso wasu al'amura da na dan dinga fuskanta a gurin rayyan din,kamar lalurarsa ranar daurin auren yarinyar,da kuma yadda naga sauyin yanayi na farat daya daga gunsa sanda na masa maganar maneman yarinyar,wanda har yau binciken ma da na sakashi bai maida hankali yayi ko na mutum daya ba" "Allah mai iko" ummu ta fada tana sake jinjina lamarin,abban ya gaya mata abinda hajiya babba tace su bar raihanan kada su sanar mata ummun tace in sha Allahu,ta dade tana mamakin lamarin,juriyar yarinyar da irin SADAUKARWARTA da kyakkyawar zuciya ke tsumata,babu shakka akwai qauna ta fusabilillahi tsakaninsu,sun cika AMINAN JUNA fili da badini,ba wai iya zahiri ba ta ganin ido. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _______________________ _______________________ *Babi na talatin da shida* Tsaye take bakin titin wanda a qalla ta kusan shafe minti talatin,tun a gida yau motar ta ta mata tsiya hakan ya sanya bata ma fito da ita ba,ganin daliban da zata yiwa karatu biyu zuwa biyar na yamma ne tana ganin rana tayi sanyi,saidai ga sabanin zatonta har a lokacin akwai sauram zafin ranar. Duka bama wannan ne yafi damunta ba,kusan tun shekaran jiya da abba ya kirata ya mata maganar sun fidda mata miji har sadakinta sun amsa jikinta yake a sanyaye,duk da bai gaya mata waye ba ta yankema ranta sultan ne,tunda wancan satin magabantansa suka zo shima kuma asatin tafiya ta sameshi baya qasar. Tsaki ta yiwa kanta da kanta na ganin baiken damuwar da fargabar da take ji cikin ranta,ta sake maida kanta ga titin ko zata dace,a hankali farar kyakkyawar motar ta wuce ta gabanta wanda hakan ya bata damar ganin wanda ke ciki,ba wani bane rayyan ne,kanta ta dauke tare da jan siririn tsaki haka kawai. Karo na biyu motar tashi ta sake wucewa ta bangaren da take,wannan karon ya ganta don sun hada idanu,dauke kansa yayi kamar yadda itama tayi masa,wucewarsa babu jimawa ta samu abun hawa. A qofar gida mai adaidaitan na shirin sauketa taga motar rayyan din fake a qofar gidan,hakan ne ya sanyata cewa mai motar ya juya da ita. Suna falon qasa bakin dayansu yayinda ta cika musu gabansu da kayan maqulashe,don tasan halin kausar da meela dukkansu babu baya wajen kwadayi,meela ce ta ajjiye meatpie din da ta gutsira tana dubansu "Wai kunsan meke faruwa kuwa?" Kusan hada baki sukayi wajen fadar a'a "Wai kishiya fa za'a yiwa sanaya" wata qawarsu ce duk da cewa gaisuwan mutunci suke kawai da rumanan,kausar ce ta fidda idanu dafe da qirji tana duban meela "Bari don Allah,sanayan?,me sanaya ta rasa da mustafa zai kwaso mata alaqaqai don Allah,innalillahi" tace baki meela tayi tace "Hmmm,kema dai kya fada,amma haushin da ta bani wai matar nan yadda kika san ba wadda za'a kawowa abokiyar gaba ba,tana zaune hankalinta kwance,wai har kiranta yarinyar take su gaisa" cikin wani zare idon kausar tace "Sanayar?,anya lafiyarta qalau,ita kuwa me ya sameta haka?" Sai ta waiwaya ga rumana wadda ke zaune tana kallonsu "Ruma kiji min wannan zance don Allah,kinji sanaya" murmushi ta saki na gefan baki sannan ta gyara zamanta "Meye to a ciki" cikin mamaki suke dubanta,kusan tare suka furta "Meye kuma?" Gira ta daga sannan tace "Eh qwarai,meye,ni kaina ni na hada auren mijina,kwanan nan zaku ji biki ya taso" dariya suka saki su biyun tare da tafawa suka dubeta "Ki daina yiwa kanki wannan fatar kada mala'ikun rahama su amsa" ta fuskanci wasa suka dauki zancan,hakan ya sanyata hade fuska "Wallahil azim da gaske nake,kuma raihana ce sisi na in sha Allah". Wani irin zabura kausar tayi ta gyara zamanta tana duban rumana,yayin da meela ta wamgame baki itama ta zuba mata ido,meela ce ta samu qarfin halin yin magana " wai wacce raihanan kike nufi?,nidai nasan sisinki guda daya ce,raihana bukar ko?"kai ta gyada "Qwarai kuwa ita" "Kut......kina me rumana?,hankalinki daya kuwa?,kinsan ke kike fada?wacce iriyar cakwakiya ce wannan?" "Tambayar min ita meela" inji kausar wadda keta jujjuya kai cike da ta'ajjubi,murmushi ta kuma yi "Ras nake,don qila ma na fiku shiga nutsuwa ta" "Wallahi ba lafiya kike ba ina tantama" cewar meela tana girgiza kai,qaramar dariya ta saki "Meela,bakisan wace raihana ba a gurina,bakisan me raihana ta yimin ba,bakisan me ta dade tana yimin ba a rayuwa,idan na gaya miki wace ita saiki yanke hukuncin daga baya". A nutse ta fayyace musu iyakar abinda ya kamata su sami,ajiyar zuciya kausar ta saki " don ta sadaukar miki da saurayi shine zaki sadaukar mata da miji?maimakon ki sadaukar mata ke da wani abun daban tunda ramawa kike so kiyi"kai ya kada "Babu wani abu da zan sadaukar mata wanda zaiyi daidai da irin abinda ta yimin,kunsan ciwo da radadin rabuwa sa masoyi kuwa?,course ya rayyan zai tafi na watanni shida na kasa daurewa a lokacin sai da aka daura aurenmu,ina ga ita data shafe wasu shekaru tana dakon son da batasan ina ne makomarsa ba,kada ki manta kausar,raihana na da damar da zata iya bata tsakamina da ya rayyan saboda son da take masa...bata aikata ba,tana da damar da itama zata iya mallakarsa....ta haqura ta barmin ni kadai duk da tsananin son da take masa,ta kare darajata a gunsa da martabata fili da boye,ta qaunaceni daidai da qwayar zarra bata taba sauya matsayina cikin zuciyarta ba,tabbas kishi ba qarya bane abune kuma mai ciwo da wahala,halittar muce haka baki daya walau mutum ko dabba,amma bazan bari son zuciya ya rinjayeni ba,bazan bari son zuciya ya kaini ya baro ba,to idan ma ban amince irin wannan ta zama abokiyar zamana ba wa kuke so na yarda ta zama?,wa kuke so a kwaso min?". Kai meela kawai ta kada" wallahi duk da haka bakiyi dabara ba wallahi sam,tabdijan,raihanan me,akan me zan bawa wata dama ta shigo min gida haka siddan?" "Kema kya fada meela,ban taba zaton baki da wayau ba rumana sai yau wallahi" fuskarta ta hade tsaf ta dubesu "Idan meela ta fadi haka zan iya mata uziri da cewa ita din bare ce bata dadin da saninmu ba,amma kekam kausar bazan iya miki wannan uzurin ba,son kai da sin zuciya shike mana jagira agaba zuwa ga kogin nadama" sai ta dubi meela "Meela,inaso ki tsaya iya matsayinki kada ki taka shingen da ba naki ba,kinsa me zaki dinga furtawa kanmu ni da raihana,matuqar babu wadda zata bani shawara ta gari kota agaji zamanmu da addu'a to bana maraba da ita" ta fada tana maida numfashi,sai suka kalli junansu sannan suka fara lalubar mayafansu suka miqe,meela kam ta kasa magana kausar ce tace "Eh da alama bare bari sunyi aikinsu,bayin kanki bane rumana,ban taba ganin saunar matar da tayi aiki irin naki ba,mudai gaskiya ce ba zamu daina gaya miki ba ko zaki tsiremu" ta kama hannun meela wadda har waiwayen rumana take cike da al'ajani suka fice Kai tsaye gidan rumana tayi bayan dogon fushi da dauke mata wuta da tayi na daina zuwan gidanta,wanda rabonta da gidan tun ranar da sukayi fada da rayyan din randa ya kawota. Jin tashin maganganu kamar fada fada shi ya tsaifata tana fatan ba rigima sisinta keyi da wasu ba,cikin qanqanin lokaci jikinta ya dauki bari 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ *Manzan Allah S A W yace"babu sallah ga wanda bai karanta fatiha ba* ____________________ *Babi na talatin da bakwai* Gaba daya ta sauya,walwalarta da kuzarinta gaba daya sun ja baya. Ranar juma'a bayan sallar juma'a tana zaune ita daya cikin falon,sanye take da material mai santsi yellow da ratsin green,dinkinta na ko da yaushe ne jikinta daguwar riga,babi kwalliyar komai fuskarta saidai duk da haka bai hana kyanta fitowa ba,tsadaddar fatarta chaculet colour ta kwanta sosai ta sake fidda ainihin kalarta,fuskarra tayi wani fayau da alamun rama tattare da ita,hakan sai ya sake fidda sigar zubin halittarta,sai dan siririn dankwalin data daure kanta da shi,wanda hakan bai hana gashinta dake tsefe a matse cikin ribbom fitowa ba,littafin tarihin garinsu ne a hannunta kanem borno empire take dubawa,tana jin dadin littafin sosai,babu kowa gidan ummu da lantana sun fita,wanda kusan kullum ummun yanzu sai ta fita,kuma bata shigowa sai da ledoji manya manya niqi niqi,itakam nata a yanzu ido ne,ta kawo ido ta zubawa kowa,tun da qoqarin data dinga yi baiyi mata aiki ba,sai ma qara jaddada mata matsayarta da rumanan tayi,kullum takan tura mata saqon neman alfaramar ta janye abinda ta shirya amma ko amsa bata samu,daga qarshe ne ta sake gaya mata zata janye din,amma ta fara gyara mata wajen zama gida don itama ba zaman zata yi ba,bata so ko kadan rumanan ta furta hakan,takanji kamar ta soketa ne duk sa'ilin data furta haka. Sallamarsa ce ta daki dodon kunnenta,ya tako a hankali ya yaye labulan falon,har ta daga kai da niyyar amsawa ga zatonta wani baqon ne sai kuma ta maida kanta kan littafinta sabida hanzarin tantance mata muryar waye da qwaqwalwarta tayi kana ta amsa ciki ciki ba tare data dubeshi ba,yaso dauke kansa daga dubanta amma sai ya gaza haka,idanu ya zuba mata,ya manta rabon da ya sanyata cikin idanunsa,tayi kasa kyau sosai,a yanzu duk wani zafi da yake ji cikin zuciyarsa ya kau,sai dan kadab wanda lokaci lokaci idan ya tuna yake motsa masa yake kuma yi masa radadi,ci gaba yayi da kallon nata ganin da gaske bata da niyyar dubansa bare ta kulashi,cikin jikinta ta dinga jin ana kallonta,duk sai ta dinga jin ta takura,idanunta qur kan littafin saidai ba karatun takeyi ba,daga qarshe sai kawai ta miqe tana gyara dogon hannun rigarta da da tadan nadeshi tare da rufe littafinta tayi hanyar dakinta. Ruf da ciki tayi kan gadon,tunaninta ya tsaya ca"rayyan,rayyan,jarrabi ne kawai a rayuwarta"haka take nanatawa kanta ba tare data iya furta komai ba,ta dade a haka har sai da agogo ya nuna mata qarfe uku da rabi na rana,ta miqe da sauri saboda tunawa da tayi zata yiwa abba tuwon alkama,falon ta fito kai tsaye,ga mamakinta sai ta sameshi zaune cikin kujeru ya miqar da bayansa,idanunsa lumshe kamar mai yin barci,wuceshi tayi na tare data sake kallon saahen da yake ba. Tukunya ta dauka ta kunna fanfo ta debi ruqa ta dora saman gas,sannan ta dafe kantar tana tunanin meye abu na gaba da zatayi bawai don batasan me zata aiwatar din ba,da sauri ta juyo don isa drowee da suke ajjiye kayan kadin miya taga mece da su kuka ko kubewa,karo sukayi har jikinsu ya hade da juna,da sauri taja baya tana fadin "A'uzu billahi....." "Shshshsh....kada ki sake ki qarasa tunda ni ba shaidan bane" yayi saurin katseta,sai ta dubeshi cike da takaici,wato ita ba mutum bace,har yau bata mance ranar da yayi mata ta'awizi,sai ta watsar da shi ta taho da jarumtar ta da niyyar wuceshi ta dauki abinda take da buqata,binta yayi tsaya a bayanta har tana iya jin hucin numfashinsa,ko yaya kuma ya motsa jikinsa na gugar nata,take gabanta ya fadi,jikinta ya fara dan rawa,har taso tayi barin robobin kayan kafin miyar dake jere cikin cupboard din data daura hannunta akai,hannunsa ya miqe da yake ya fita tsaho ya kwaso dukka robobin ya ajjiye mata a gafe cikin sauri ta zame jikinta ta koma gefe guda tana sauke numfashi,cikin dakiya da rashin walwala yace "Wai ke nan har gaba kike da mijinki,don bazance qiyayya ba saboda wallahi qarya kike kice baki sona" kamar zata tanka masa sai 'yan halin nata suka motsa,bata dubeshi ba ta fara tsintar waken da zata daka cikin miyar kanta duqe,sake matsowa yayi kusa da ita yana shirin dora hannayensa kan kafadarta,da sauru ta janye jikinta kamar wanda ke shirin dana mata wuta "Kaga malam kada ka soma tabani wallahi" kamar wanda ta zuga sai yayi caraf ya cafki hannunta yana dubanta "Idan na taba din kuma sai yaya,ko za kici sadakina ne a bulus?"harar ta watsa mas" dadin abun dai ai ba da kudinka ka biya ba ko?"girarsa ya daga "Au haka kika ce?,taqamarki kenan?" "Eh haka nace" ta fada cikin tsiwar da bai taba gani ta yima wani ba "Ok,zaki gani,zaki san cewa ba kasawa rayyan yayi ba,haka naj idan naso ko ban bada sadaki ba ina da qarfin da zan iya tabaki ko?" "Wannan kuma kayi kadan,tunda ba'yar iska ka samu ba bal....." Bata qarasa ba ya birkitota baki daya cikin zafin nama ya hadeta aqirjinsa,cikin azama ya fara lalubar bakinta lokacin da take yunqurin qwace kanta tana kai masa bugu,sai da ya tabbatar ya hade bakinsu guri daya sannan ya fara aika mata da wasu makamai wadanda tun tana iya kare kanta da qoqarin yin tawaye har abinda yake mata ya fara galaba a kanta,ji tayi ta tureta idanunsa cikin nata wadanda suka sauya launi tare da qanqancewa " Tunanin da ya fado masa wanda ya sanya motsuwar kishinsa shi ya sanyashi tureta,ya dubeta idanu a qanqance sun dan canza launi kadan "Uhmmm,wato na sosa miki inda yake miki qaiqayi ko shine har da yin wani likimo ko?" Ta fuskanci me yake nufi sarai,takaici ya kamata sai kawai ta saki kuka "Allah sai ya saka min wallahi,kaji haushi dai,ko kunya baka ji ka hada hada 'yan biyu zaka aura" wani mayaudarin murmushi ya saki kana yace "Ba zaki gane hakan na sai ranar da na hada ku a labour room duka ku biyun" sake qufula tayi "Allah ya sawwaqe wallahi,aniyarka ta bika"murmushin ya sakeyi " kema zata biki ne yarinya"ya juya yana shirin fita ya barta da sharar qwalla,har ya kai bakin qofa ya dawo "Ki dafa duk abinda zaki dafa da ni,don yau madam ba zata yi girki ba na bata hutu tayi kwanciyarta" "Can ta matse maka,amma wallahi kabar cin girki na" sai ya zuba mata ido yana murmushin qeta "Tabbas kuwa zakiyi kaffara,girkinki kuma ai yanzu na fara ci,kinga.....kima fa daina wannan fiffiqar,ba don my angel bafa da wannan auran baza'a yishi ba,kiyi a hankali"baqinciki ya mamayeta ta rasa me zata gaya masa ta rama,da hanzari ta bude bakinta "na tsaneka wallahi rayyan"ya jita sarai amma sai ya kada kai yayi ficewarsa bai waiwayeta ba. Tana girkin tana hawayen zuci da zahiri,gab da magariba ummu ta dawo,tana jiyosu a falo tayi zamanta kitchen har bayan ta kammala,sai da aka kira sallah taji shiru alamun kowa ya nufi gun yin sallah sannan ta fito tayi dakinta bayan ta shiryawa abba abincin. Qarfe takwas ta isa falon abban suna tare da rayyan din suna hira,ta soma zuba masa abincin sai yace ta hada musu da rayyan din,suka hada ido ya mata dariyar mugunta " kinyi rantsuwar banza,koda yake dama kin saba yin rantsuwar banza ai"ya fada qasa qasa yadda abban bazaiji ba sanda ta duqa da niyyar ajjiye kwanukan tuwon,bata tanka masa ba tayi ficewarta,ko falon bata zauna ba ta qule daki ranta na mata daci,da baqinciki ya ciyota kawai saita janyo waya ra kira rumana,babu dadewa ta daga sai kawai ta sanya mata kuka,shiru tayi tana saurarenta,sai da tayi mai isarta sannan tace "Wallahi sisi baki sona Allah" ko bata tambaya ha tasan kwanan zancan,bai wuce maganar aure ba "Eh,indai kan wannan ne bana sonki,farin cikinki shine nawa,amma bakison nafison farincikin mijina akan nawa ba?" Wani qarin takaici kenan, aqufule tace "To shikenan,wallahi Allah ki jawa mijinki kunne idan ba haka ba zan muku rashin mutunci ke da shi" dariya ta kwashe mata da ita sannan tace "A shirye muke,ai amarya bata laifi" ganin tuburata kawai rumanan ke sonyi ya sanyata kashe wayar ta saki kuka,babu jimawa taji shigowar saqi cikin wayarta _"kiyita dai damun kanki saboda ni,ki shigo gidan a rame uwar gida ma ta fiki kyan gani"_ wani haushin ya sake turniqeta sai kawai ta kashe wayar ta maida kanta ta kwantar tana ci gaba da tsiyayar da hawaye **************** Tun bakwai na safe ta tsinkayi rumana cikin gidan wanda batasan dalilin zuwanta ba,tadai ganta taci kwalliya sosai cikin wata shegiyar shadda maroon da tayi mata bala'in kyau,kallo daya zaka mata kasan lallai tana hutawa gidan rayyan. Tana daki tana jiyo hidimarsu tsakanin falo tsakar gidan da harabar gidan,tuni lantana ta gama break fast har tayi mamakin yadda yau tayishi da wuri,sai kawai ta shiga wanka ta fito ta shafa mai tare da turare ta goga hoda ta zura doguwar rigar atamfa,daki ta cewa lantanan ta kawo mata kayan karin donta fuskanci wani abu suke da ya shafi bikinta,ita juwa ranta soyuwa yake idan taga rumana ta saki jiki ana hidimar da ita,wani lokaci har gorin ta koyi kishi take mata,qyalqyala dariya take tace "Akan me,bayan na samu saunar kishiya wadda bata iya kula da mijinta ba" da biyu itama take gaya mata haka wai ko hankalinta zaya dawo ga rayyan din,Allahu akhabar(wa yu'usiruna ala anfusihim walau kana bihim kasaasah). Tana gab da kammala break din rumanan ta shigo hannunta dauke da wata leda ta dubi raihana "Dama tashi kikayi kika yi kwalliya,don yau zamu karbi lefanki" sai ruwan tea din ya tsaya mata,wata faduwar gaba ta ziyarceta idanunta qir kan rumana dake ajjiye ledar tana bude jakarta tana zarar kudi,sai ta janye idanunta ba tare data ce komai ba,ta tattare duka kayan karin guri guda. Hijabinta kawai ta dauka da key dinta,babu wanda yaga fitarta tayi ficewarta,sai ta rasa inda zata je,qarshe ta zabi zaman office dinta,nan taje ta bude ta shiga ta qulle tayi kwanciyarta,lokaci lokaci hawaye na zuba a idonta. Kafin azahar 'yan maiduguri suka zo,ciki harda amma,tunda suka zo take baza idanun ganin raihanan don dama da biyu tazo ba karbar lefe ne ya kawota ba saidai bata ganta ba,ganin haka ya sanya tayi tafiyarta qoqi gun hajiya babba,sanin matsayar hajiya babba kan batun ya sanya har suka gama hirarsu bata ce komai ba,bata koma gida ba sai data tabbatar masu kawo lefen sun watse. Lefe ne akwati dai dai na alfarma wanda rumana ta zaba ta darje har guda shida rayyan din yayi,yana qorafi yana komai haka yayi su,komai na ciki mai tsada ne babu mai qaramin kudi,sai ganin shi tayi da wasu akwatunan irinsu guda uku maqare da kaya yace nata ne itama,daddy dalhatu ashe tuni ya gaka nashi,akwati shida ragowar shi ya hada suka zama sha biyu,yayin da ya yiwa rumanan itama guda uku ta tashi da shida itama,ba'a rasa tsaigumi tsakaninmu mata,musamman akan batu na kishiya,kishiyar ma irin rumana da raihana,babu abinda ba'a gayawa rumana ba amma ta sanya auduga ta toshe kunnuwanta,tayi namijin qoqari gun ladabtar da zuciyarta,a duk sanda taso yunquro mata da wani abu takan tunasar da kanta wace raihana ne a gunta,hakan shi yayi mata jagora matuqa wajen samun salama cikin birnin zuciyarta. La'asar amma ta dawo gidan,ko kallon inda kayan suke bata yi ba,raihanan kawai take jira,ba ita ta shigo gidan ba sai da aka soma idar da sallahr magariba a wadansu masallatan,mamaki ya cikata ganin 'yan uwanta na maiduguri,matan qanne da yayyen mamanta harda maman nata ma,saidai rashin sakin fuska da harara da amma ke mata ya sanya jikinta mutuwa. Tara na dare ne tana dakin raihanan wanda ita daya ce ciki baqi har yanzu suna falo anata kallon lefe da yaqi qarewa,dubanta amma tayi "Kin bani mamamki raihan,kin bani kunya,yanzu ashe zaki iya auran mijin 'yar uwarki" sai ta daga kai fuskarta cike taf da qwalla tana duban mahaifiyar tata,tabbas tasan babu mai wanketa wajen wasu sai Allah,abinda ta guda kenan tunda fari gashi yazo ya risketa,kai ta kada "Ba laifina bane wallahi amma,ba laifina bane" "Najibkuma na sani,amma babu wanda nake gani da laifi sai ke,me kike so duniya ta daukeki?" Ta fada cikin fushi,kasa daurewa raihanan tayi duk yadda taso da hakan,sau ta saki kuka ta sauko qasa kan gwiwarta tare da dora fuskarta kan cinyarta ammin tata,tsakanin da da mahaifi sai Allah,tausayin diyartata sai ya kamata,batason duniya ta zageta ne,tunda tasan mutum kome zakayi baka iya masa,tabbas iyayen yarinyar da kakanminta basu da matsala ko kisqala zarratin,amma cikin danginta fa?,me zasu ce? "Amma na ki gafarceni,ina roqonki da sunan Allah ki yiwa abba magana su warware maganar nan,irin abinda kike gudarmin amma nima shina gudarwa kaina shekarun baya,sau gashi a yanzu yazo ya riskeni,wallahi amma bani da sha'awar zaman aure da yaya rayyan". . Qarar wayar amman ya katse maganar tasu,ta ciro wayar sannan ta kara a kunne "Gata" kawai tace tana kara mata wayar,hajja yakolo ce,ta soma gaidata,bata amsa mata ba ta hauta "Na kira ki ne na jiki naso idanunki ma na gani,hajiya babba ta gaya min komai,ai bansan ke butulu bace raihana sai yau,ashe har kina da bakin da zakiqi jinin yusufu?,har yauahe kika zama mutum da zaki nunawa jinin yusufu qiyayya,nayi zaton ko wani kika ga yaqi jininsa sai inda qarfinki ya qare ki" "Ya ialahi ina zan sanya kaina ne?,ba qinsu nake ba hajja ina duba 'yar uwata ne,ina duba alaqarmu fa......" "Kinga yimin shiru ya isheni,yarinyar ba ita ta bankada abinda kuke ciki ba?,to ki shiga hankalinki,wallahi kika sake kika musguna mata ko kika bata ranta kan wannan batu sai munyi tur da ke don na fahimci take takenki....yauwa,sannan uwarki ma na fuskanci inda tasa gaba ta biyosu sun taho,to wallahi kada naji kada na gani,kada naga sabanin alkhairi idan ba haka ba ku duka biyun sai kun gamu da bacin raina" duban amman tata tayi,handsfree ne saboda haka tana ji "Kina jina ko?" Inji hajja yakolo ta dora "Ki biyo su meram ku taho tare,su furma da kaajima zasu zo jibi su daukesu,ki biyosu nan ina son ganinki" "To hajja" ta fadi a sanyaye daga haka ta katse kiran,miqawa amma wayar tayi ta karba ba tare data ce komai ba ta miqe ta fice,don ba al'darsu bace babba ya fada kaima ka fada . Kwanansu biyu a kano suka dauki hanya sai maiduguri,bata iya tafiya ba sai data turawa rumana tex na tafiyar tata,ta yi mata fatan alkhairi,sai kuma ta kirata ta fara mata qorafin ta nemi izinin tafita gun rayyan ne,tsaki taja sannan tace "Kinga ke da mininki ku fita sabgata wallahi" ta kashe wayar baki daya ta cillata cikin jakarta don tasan halin rumana da neman abun fada tsaf zata sake kiranta ta kuma tubure mata,gidan hajjan ta sauka wanda a baya na gaya muku gida ne mai girman gaske mai dauke da part part wani part din ma babu kowa ciki,tare take surukanta saidai babu takurawa kowa cikin gidansa yake yana rayuwarsa yadda yake so,tunda taje hajja yakolo ke mata mita har sau da tayi kuka ta sarara mata,wani gyara da shiri da sukewa amaren barebari aka fara yi mata,kusan zamanta a can yasa ta dan samu nutsuwa har ta fara manta wasu damuwoyin nata,ga matan baffanninta akwai kirki meram,fatime,ayysa da kuma nafissa,kowacce nan nan take da raihana,yau tana parta din waccan gobe tana na waccan,sukan sata a gaba kowacce da irin darasin da zata dora mata wandabkowacce macen kanuri ke taqama da shi,ganin cewa bata girma cikinsu ba batasan da yawa daga al'adunsu da surrukansu ba,baki kawai take sakewa tana kallonsu,basu san babu wani tanadi da take buqata ba?,gidan 'yar uwarta fa zata shiga,binsu kawai take da kunne da baki,nan ta soma ganin al'adar garinta tsantsa,al'ada ta uwa da uba,cikakken isa girma da iyawa irinta kanuri,ta lura kowanne bangare wannan karon a shirye yake da aurenta ba kamar wancan karon da akayi cikin gaggawa ba ba tare da shiri ba,yadda taga suna mata kyautar sai ta tsaya dubansu,gold wani 'yar sarqar hannu,wani ya bata zobe wani ya bata barima ta kunne kota hanci,dariya falmata cousing dinta take mata sosai tana fada mata haka al'adarsu take lokacin bikin aure,kwalliyar gold sukewa amarya musamman idan dangin irin nasu ne masu wadata. _A nan zamu tsaya in sha Allah saboda gabatowar watan azumi wata mai albarka sai zuwa bayan sallah da yardar Allah,muna fatan Allah ya yafe mana kurakuranmu,ya bamu dacewa,yasa muna daga cikin 'yantattun bayinsa ameen summa ameen_ *subhanakallahumma wa bi hamdika,ashhadu an ilaha illa anta,astagfiruka wa'atubu ilaika*🤲🏼🤲🏼🤲🏼 *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* *dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki da ya bamu aron rai da lafiya,tsira da aminci su sake tababbata ga wanda ba'ayi ba kuma baza a yi kama tasa ba dan gatan Allah annabi muhammad s.a.w,Allah ya karbi ibadunmu ya yafe mana kura kuranmu,yasa muna cikin bayinsa da ya 'yanta amin* *Babi na talatin da takwas* Cikin sati biyu ita kanta a jikinta tasan ta sauya,gyara suke mata irin na wadda ta taba yin aure duk a tunaninsu hakan take. Bata sake gasgata qaunar da 'yan uwanta ke mata ba sai ranar da aka fara biki,dangi ne masu zumunci gami da kara wadanda basu manta alkhairin da abbanta ya mata ba lokacin da yake raya,kamu sukayi mata irin na al'ada,washegari aka hada dinner na dukka family,wata washegarin akayi yini,a ranar aka yi mata hadadden qunshi irin na bare bari ja wanda ya sake fidda kyawun ainihin kalar fatarta chaculet wadda gyaran da ta sha ya sake fidda mata kyawunta na musamman. ************* Qarfe goma na safe ta farka saboda gajiya,anata hada kaya da shirin tafiya kano da zasuyi washegari don a miqawa su ummu ita su gabatar da nasu bikin,masu zuwan nada dan yawa don haka gidan kusan kowa cikin shiri yake,toilet ta shiga tayi wanka ta shirya cikin mutuniyar tata doguwar riga ta wani lace dinkin buba wadda tana cikin kayan da hajja yakolo ta mata,tayi matuqar karbarta,bata wani yi kwalliya ba sai dan kwalin data daura kawai ta fito falon hajja yokolon don ta samu abinda zata karya. Tana gefan hajjan tana shan farfesun kaza mai hade hade,tana yi tana mita hajjan na doka mata harara. Baba gana ne ya shigo hade da yin sallama idanunsa kan raihana,ya samu gefen hajja yakolo ya zauna yana janta da wasa,ta biye masa suka dan taba barkwanci,raihana ta gaidashi ya juyo yana amsawa gami da yi mata Allah ya sanya alkhairi,ta amsa kanta a qasa tana dan jin nauyinsa sabida yana ganin kamar ta gujeshi ne,tana jinsu suka gama hirarsu da hajja yakolo ya miqe ya fidda kudi daga aljihunsa,rafar dari biyar biyar ya ajjiye gefanta "Amarya ga tawa gudun mawar" kai ta kada gami da cewa "Ba haka tsakaninmu fa" hannayensa ya zuba cikin aljihun wandonsa yana fadin "A'a,saidai idan kin raina ne" da sauri ta kada kanta tana fadin "Ni na isa,na gode qwarai,Allah ya saka da alkhairi" ya amsa yana musu sallama ya fice. Kamar a mafarki ta fara jiyo muryar rumana daga harabar gidan,da sauri ta miqe tana nufar qofa ta yaye labulen falon,ita dince kuwa sanye cikin swiss orange dan ubansu,gefanta zainab ce dauke da Islaha,juwairiyya qanwar rumana na gefanta,sai wasu mata su uku dangin abba yusuf daya kuma qanwar ummu ce dukansu daga nijer. Bakinta har kunne ta qarasa ta rungume sisinta,duk ta manta wani fushi da take da ita,sunyi kewar juna sosai,ta yi musu jagora zuwa babban falon hajja yakolo,karba ta girma da mutunci aka yi musu sannan daga bisani suka kebe dakin da raihanan ke zaune ita da sisinta. Tsaf suka kammala shirin kwanciya bacci,rumana na saman gado tana ta faman amsa waya,ko ba'a gaya mata ba tasan da wanda suke wayar,hakan ya sanya ta janyo akwatinta tana ci gaba da shirya kayayyakinta. A hankali ta sauke wayar daga kunnenta bayan sun kammala tayi murmushi tana duban raihana "Amaryarmu kinga kuwa yadda kika qara kyau,gaskiya kanuri sun iya gyara,kice gwara da nazo da kaina Ba aike ba kada agudar mana da ke,da alama ma ke baki kewar angon naki"harara ta jefa mata tana sake kin zafin yadda rumanan bata kishinta "Wa ya damu da shi,ke dai daya dama kuje can ku qarata" gira ta hade tana duban raihana sannan ta tashi ta zauna "Gaskiya na fara gajiya da rashin karar da ake nuna mana,ko kunyata baki ji kike gasawa mijina baqaqan maganganu a gaba na?" "Ko me aka yi muku ma ku kuka jiyo,kuyi zuciya ku huta mana,muma mu huta da shigegen da ake son mana ta dole"tabe baki tayi tana dubanta " dadin abun dai kin san waye mijina wallahi yafi qarfin talla balle ma kice"itama bakin ta tabe tana sanya atamfar hannunta cikin jaka "Ke kikasan wannan,ni kam bai dameni ba,ku yarda qwallon mangwaro kawai ku huta da quda shine zaku birgeni" "Baki isa ba kuma wannan,duk dabararki" rumanan ta fada tana matsowa tana tayata hada kayan "Gwara ma na tayaki don ki sake tabbatarwa tafiya wajib,aure daram" bata sake cewa da ita komai ba don ta fuskanci abun nata har da neman magana,kusan raba dare sukayi suna hira saboda rumanan bata sake jangwalo mata zancan rayyan ba. Goma na safe kowa ya kammala shirinsa don tafiya kano wanda acan za'a qarasa bikin da daurin aure baki daya. Fitowarta kenan daga dakin hajja yakolo cikin dinkin lace riga da skert wanda aka rufe da laffaya mai asalin kyau da tsada ta bare bari wanda ke fidda wani sihirtacce qamshi bayan dogon fada da jan hankali da tasha,idanunta ya hada ja saboda kukan da tasha,kowanne sake jaddada mata yake taci gaba da riqe rumana 'yar uwa,ammanta har da qarawa da cewar matuqar ta musguna mata ko ta cutar da ita bata yafe mata ba,ta yaya ma zata iya cutar da 'yar uwarta?,ta wacce hanya ma zata iya cutar da sisinta?,ba shakka rayyan ya gama da ita ya shiga rayuwarta,ranta cunkushe suka dauki hanyar kano ita da sauran jama'arta dangi 'yan uwa da abokan arziqi. Ko cikin motar duqunqunewa tayi tana ci gaba da zabga kukanta,haushin rayyan take ji da zafinsa sosai cikin ranta,bata yadda sun shiga mota daya da rumana ba don batasan kukanta ya daga mata hankali. Sai la'asar sakaliya suka isa kano,sama ta gama hada hadari iska kawai take bayarwa mai dauke sa qamshin qasa kasancewar damina ta shigo wadda da ita ake azumin ramadan,tun kan su kammala parking idanunta suka sauka kan motarsa dake ajjiye a gurin ajjiye ababan hawa na gidan,tsintar kanta tayi cikin faduwar gaba,ko kadan bata da muradin su hadu da shi,ta lumshe idanunta tana jin kowa na ficewa daga motar amma ita ta kasa motsi har sai da taji an kama hannunta,ta bude idanunta a ahankali don taga waye _kuyi haquri da wannan saboda cika alqawari ku bini bashi gobe da yardar Allah_ *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _______________________ *Daga abu hurairah R.A yace,manzan Allah S A W yace "yana daga cikin abinda yasa aka halakar da wadanda suka gabacemu,yawan tambayoyinsu(tambayar qure da tambaya kan abinda baida ma'ana ko fa'ida),da kuma sabawa annabawansu"* ______________________ *Babi na talatin da tara* A hankali ta bude zara zaran idanunta,rumana ce tsaye dafe da hannun nata tana kallonta,kai ta girgiza sannan tace " kullum ranar Allah sake nunan kike DANGANTAKAR dake tsakaninmu bata kai haka ba,kina sawa ranki cewa akwai wani abu da ya isa ya kutsa cikin alaqarmu,alaqar da babu wanda ya ginata face Allah subhanahu wata'ala,alaqar da dangantakar da Allah kadai yasan yawan qaunar dake cikinta,me yasa raihana?"kai take girgizawa hawaye na son qwace mata,cikin raunin murya tace "Ba haka bane rumana ki fahimceni,kishi mugun abu ne,mugun ciwo ne da baka da qarfin da zaka iya dakatar da shi,ina tsoro kada ya zama silar rusa kyakkyawar alaqar dake tsakaninmu,me yasa ba zamu ci gaba da zama kamar yadda muke ba?,me yaaa za kiyiwa rayuwarki gibi ki gayyato qata cikin duniyarki?" Kai ta kada itama tana murmushi mai taba zuciya gami da janyo hannun raihanan daga cikin motar tana cewa "Tabbas kishi halitta ce,kuma kisan kowanne jinsi na halitta walau mutum ko dabba yana da ita,saidai ya rage naka ka sarrafashi ta hanyar data kamata ko akasin haka,qarshe dai sakamakon kai zai dawowa,bana dana sanin sadaukar da farinciki ga wanda ya sadaukar min da nashi farincikin ba tare da na san da hakan ba ma,tabbas ina son rayyan ina kishinsa amma ki sani cewa ke ta dabance raihana,bazan kuma taba zama butulu ba,kome duniya zata kirani da shi wannan ya rage nasu" "Amma rumana......" "Shshshsh" rumanan ta fada tana dubabta bayan ta dora yatsanta kan lebanta idanunta sa suka dan sauya suna duban raihana "Bana buqatar sisi ki sake cewa komai kan wannan magana,aski ya riga yazo gaban goshi,nan da jibi magana ta qare" tilas ya sawa bakinta kwado rumana na jaye da hannunta taci gaba da binta har cikin gidan tana hadiyar zuciya. A cike ta tarad da gidan har abun yaso bata mamaki,tamkar bikin fari za'ayi,ta daure zuciyarta ta gaggaisa da jama'a saidai bata ga ummu ba aka ce mata tana dakinta,bazata iya wucewa sabgarta ba bata ga uwar tata ba sabida haka kai tsaye ta wuce dakin nata. Da sallama ta tura qofar dakin ta shiga,idanunta fes kansa yana zaune gefan gado sanye da shadda ruwan qasa wadda tayi matuqar amsarsa,ya daga kai a hankali daga danna wayar da yake yana amsa sallama,idanunsu suka jone guri guda,wata faduwar gaba taji wadda ta sanyata sakin mariqin qofar ta koma da baya da niyyar ficewa yayin da shi kuma yaci gaba da kallonta da narkakkun idanunsa,kewa ke damunsa sosai,ya jima bai sata a idanunsa ba ga kuma rumanan itama bata kusa,ji yake kamar ya janyota ya sanyata cikin qirjinsa,sosai tayi masa kyau don haka yaci gaba da kallonta yana sauke numfashi shi kadai. "Muryar wa nake ji kamar ta raihana?" Cewar ummu wadda ke fitowa daga bandaki da alu alwala tayi,maganar ummun ita ta katse mata aikata abinda tayi niyyar yin,sai ta qarasa shigowa dakin tana jaddada sallamarta kanta sunkuye a qasa saboda ta gaji da mayen kallon da rayyan din ke jifanta da shi babu gaira babu dalili . Aladabce kamar yadda ta saba ta gaida ummun,ta amsa mata cikin kulawa tare da tambayarta yadda ta barosu,miqewa ummun tayi tace bari nayi sallah lokacinta har ya qwacen,ki jirayeni na idar akwai saqon da zan baki inji mai martaba(kakan rayyan na nijer)"kai ta gyada mata sannan tace "To ummu" ta waiwaya ta dubi rayyan "Kai mun gama da kai ko da saura" ido ya dan lumshe sannan ya budesu "Akwai saura amma ba damuwa zan qarasa rubutasu anan saboda idan na fita ba lokaci,ina da baqi zai iya yiwuwa na mance" "To yayi kyau" ummun ta fada sannan ta juya ta tada sallarta. Tsit ne ya biyo baya,tana takure saman carfet gata a saitinsa,yayin da shi kuma ya tsareta da ido yana son ta daga kai su hada ido saboda saqon da yakeson aika mata,kamar tasan da hakan tayi qasa da kanta tana wasa da yatsunta da suka sha lalle,gaba daya jinta take duniya ta takureta gu daya,ji take kamar ko ina yi ake da ita,ji take kamar kowa zargi da zaginta yake,hakan shike qara quntata mata zuciya. Saidai duk da haka zuciyarta na mata zillo tare da gaya mata kallonta fa ake daga gefw guda,saita daga kai a hankali don ta tabbatar,bai kuwa yi qasa a gwiwa ba ya aika mata da saqon take kuwa ya isa gareta har kwanyarta wanda ya haifar mata da wani kasala ta daban,ta janye idonta tare da lumshesu taja numfashi can qasa ta sauke,sai ta maida kanta ta kwantar kan qafafunta bata sake muradin kallonsa ba,don ta fahimci abun nashi mugunta ne,duk lokacin da tayi niyyar wancakali da shi sai ya ruguza mata shiri,duj sanda zuciyarta ta soma jin zafinsa sai ya sauyawa zuciyar tata akala,ta dade da sanin rayyan dan garari ne,bai iya riqe soyayya da sauqi ba,bai iya sanya wajen cimma muradinsa ba. Cikin wannan yanayin ummu tayi sallama,sif dinta ta bude ta fiddo wani dan akwati mai azabar kyau ta ajjiyewa raihana "Ke da 'yar uwarki ne ita na bata nata" tun kafin ta bude ta soma godiya "Saiki duba" inji ummu ta fada tana ficewa a dakin,kamar wadda aka tsikara ta miqe itama ta dauki akwatinta tana shirin bin bayanta,cikin azama ya sha gabanta tamkar zasu hade jiki har sai da tayi baya "Haba yarinya baki isa ba,ai sai kin biya farashin abinda kika yimin" cikin rashin fahinta take dubansa,girarsa ya dage sannan yace "Kina nufin duka abinda kikayi baki sani ba?,ok zan lissafa miki,na farko kinyi tafiya babu izinina,na biyu kin dauke min mata ta biki can,na uku kuma daga dawowarki kinzo kin ishi mutane sa kallo har sai da kika......." "Don Allah ya rayyan ya isheni matsa na wuce" "Ta qarfi ce hanyar" ya bata amsa kai tsaye,sai ta raba gefansa zata wuce ya tare hanyar ta sake komawa dayan side din nan ma ya bita ya tare,haka suka dinga yi har ta gaji sai kawai ta saka masa kuka,abinda yake nema dama kenan,baiyi qasa a gwiwa ba ya tarairayota jikinsa . Zamewa taso yi saidai ina tuni ya soma kashe mata jiki,sai ta samu kanta da yin luf kan qirjinsa tana sauke ajiya zuciya kafin daga bisani ta sanya dukka hannayanta ta tureshi,sai yayi baya luuuu kamar zai fadi sai kuma ya turje tare da fadin "Wash" waiwayo tayi ta dubeshi ga zatonta ko wani abune ya sameshi,sabanin haka ta gani,ya zuba mata ido yana dubanta,suna hada idon ya kashe mata idonsa daya hadi da sakin murmushi qasa qasa yace da ita "Raiha ta!",takaici taji ya kamata,da hanzari ta dauki akwatinta ta fice hawaye na layi kan fuskarta,shi din ma bai hanata ba don yasan meke damunta,zuwa wani lokaci yasan dole kukanta ya tsaya. Haka ta dinga wuce jama'a kanta sunkuye don kada suga fuskarta,Allah yasota ma duhun magariba ya soma kawo jiki don haka ba wanda ya kula har ta isa can bayan gidan,wajen babu kowa hakan yasa tayi zamanta a nan,Allah ya sani tana qaunarsa har cikin jininta,to amma tana jin hakan sam bai da wata fa'ida tunda sukayi tarayya da 'yar uwarta,baida amfani bai kuma kamata su raba abu guda da kowacce keso ba,tana ganin mafi kyau ta sallama mata,saidai sam rayyan ya ruguza tsarin ya hana damar,itama kuma rumanan ta biye mishi saboda farincikinsa. *************** Washegari aka gabatar mata da kamu mai matuqar qayatarwa,yare uku ne suka hadu agun saboda haka dole abun ya burgeka,kowa na qoqarin nuna tashi bajintar da kuma al'adar,ga hausawa,ga buzaye ga uwa uba iyayen gida bare bari wato KANURI. Kusan komai da raihanan ta saka ko tayi amfani da shi iri daya ne da na rumana,wannan kuwa tsarin raihanan ne,rumanan taso ta turje amma ta kafeta da manyan idanunta tana kallonta " ni da kika tursasawa,kika lanqwasani dole,kika wajabtamin aikata abinda na dade da haramtawa kaina shi banda baki ko ikon bijerimiki sai ke?" "Ba haka bane sisi,amarya daban take kuma komai nata ya kamata ya fita daban" kai ta shiga girgizawa qwalla ta tarar mata tana shirin zubowa "Banda wannan amaryar,amaryar dake shirin auren mijin 'yar uwarta?" Da sauri itama ta shiga kada mata kai "A'ah,kada muyi haka dake raihana,aure zakiyi tamkar kowacce mace,namiji zaki aura kamar kowanne namiji....kada ki kuma daga wannan maganar na gaya miki,kaya na amsa zan kuma yi amfani da su don faranta ran sisi na" ta fada tana kama hannuwanta,kai raihanan ta kada tana fidda murmushin yaqe yayin da rumanan ta mayar mata da martani. Qememe taqi kowanne dinner party ko walima don ta bangaren qawaye babu daya data gayyata,tilas rumanan ta zuba mata idanu,daga kamu babu abinda suka dada sai yini da daurin aure. Ranar juma'a aka daura auren kamar yadda aka daura na rumana,qarfe sha daya na rana alqawarin ubangiji ya tabbata, RAYYAN ya zama miji ga RAIHANA. Tana zaune gefan gado wanda tunda ta shirya take zaune kai kamar mutum mutumi ta kasa motsawa,sanye take cikin wani swiss voile dan gasken peach colour wanda yasha aikin sea grean,tayi kyau qwarai kwalliyar da aka mata ta karbeta,saidai sam hankalinta baya wajen,saboda tunda rumana ta fita bata sake ganin ta ba har aka kammala daura auren,idanu taketa rarrabawa ko zata hangota amma ba ita. Islaha ce ta shigo dakin cikin wata gown ta yara baqa,adon baqi akayi mata wanda ya sake qawata yarinyar kamar ka saceta,hannu raihana ta dago mata tana sakar mata murmushi direct yarinyar tayo gunta da tsallenta tana fadin ke nake nema mamma ki bani chaculet,saman cinyarta ta dorata tana fadin "Zan baki kuwa amma sai kin gayan inda mommynki take" ta dan bata fuska "Ni bazan rakaki ba bayan koroni tayi wai zatayi wanka" zaro ido raihana tayi "Wa ya gaya miki ana fushi da momy,babu kyau kice kin daina ko?" Akwai ta da jin magana haka suka horata take ta gyada kai tare da fadin na daina "Da kyau ahsanti ya ibnati,yanzu zaki rakani inda take?" Kai ta sake daga mata,ta sauketa daga saman cinyar tata ta dauki mayafinta sea grean ta lulluba,umaima coursing dinta dake gefe tana kwalliya ta dubeta cikin tsokana "Ina kuma zuwa amarya"bata waiwayo ba tace " ina zuwa"ta kama hannun islaha suka fice. Sashen rayyan na da wanda ke cikin gidan har yanzu akwai komai a ciki na furniture taga sun durfafa,sai islahan taja tunga ta tsaya tana fadin "Tana nan,ni mamma ki ban chaculets din zanu gunsu nasrin" murmushi tayi ta saki hannun nata sannan tace "Kije daki gun anty umaima,wannan me yin kwalliyar,kice ta bude jakata ta baku chaculets" da sauri ta juya na tsalle ta wuce,raihanan ta bita da kallo tana murmushi,tana son yarinyar komai nata irin na sisinta,ta girgiza kai ta nufi sashen. A hankali ta tura qofar falon wanda ga zatonta babu kowa shi ya sanya bata yi sallama ba,suna tsaye su biyun tana kwance a jikinsa kansa bisa fuskarta,sanye yake da shadda fara qal 'yar ubansu riga 'yar ciki da wando da babbar riga saidai kansa ba hula wanda hakan ya bayyaba hadaddiyar kwantacciyar sumarsa irinta buzaye da tasha gyara,tissue ne riqe a hannunsa yana goge mata fuska da alama hawaye take "Meye ban gaya miki ba tun ba yanzu ba?"taji yana fadi,gabanta ya fadi har sai data runtse idanu,kuka sisinta take?,da sauri ta qarasa inda suke tsayen ba tare data yi sallama ba don ta mance "Kinga irinta ko rumana?kinga irinta ko?" Ta fada tana dafa kafadarta muryarta na rawa,da sauri ta daga kanta tana duban raihanan "Don me yasa zaku cutar da kanki?me yasa rumana kika dage bayan na dade da sadaukar miki,na dade da cireshi daga rayuwata?,bana muradin zama inuwa guda da shi,yanzu me kika yiwa rayuwarki adalci?" Sai ta saki rayyan din ta kama hannuwanta "Ban fahimci me kike cewa ba me ya faru?" "Kuka fa sisi na kike,kukan da kowacce mace ke kasa daurewa sai ta yishi kan mijin ta da takeso a irin wannan ranar" kai ta kada tana shirin yin magana rayyan din ya rigata,wanda tun sanda ta furta bata muradin zama da shi ya hasala "Hey malama ya ishemu soki burutsunki,get out" sai ta daga idanunta tana dubansa "Baka da bakin magana rayyan,kome ya faru da mu kaine sila,kaine tushe mafari" sai ya zuba mata idonsa da ya dan sauya launi saboda bacin rai,abubuwa da yawa ke sukar zuciyarsa,ya soke hannayansa cikin aljuhunsa yana ci gaba da dubanta kana ya sake taku ya kuma matsowa inda suke "Kina maida kanki wata tsiya fiye da kima raihana,me zai faru idan rayyan ya rabu da ke?,me kike tsammani ehen?" Kafada ta daga itama cikin bacin rai "Muradin raihana dama kenan" "Ok....to...." Kiran sunansa da rumana tayi da qarfi ya maida hankalinsa kanta,qwalla take fitarwa,sai kawai ta finciki hannun raihana suka shige bedroom din falon ta maida muqulli ta rufe ta samy gefan gadon ta zauna ta kallonta,itama gefanta ta samu kwai ta zauna din. Aqalla mintina kusan goma kafin rumana ta bude baki ta fara magana cikin masifa "Mijinki raihana kikewa haka?,kinsan zunubin da kike diba,waye ya gaya miki ma kuka nake?kaina ke ciwo zazzabi ya saukarmin nasha magani na kwanta,ki iya bakinki kisan me zaki gayawa mijinki,haka zaku sani a tsakiya cikin gidan kyna masifa?,to bazai yiwu ba,kuma matuqar kina so na huce kije ki bawa ya rayyan haquri" daga haka ta miqe ta hau shiryawa ba tare data sake tanka mata ba. Ji take ko haushin me rumanan zata ji ba zata iya bashi haquri ba,saboda haka tayi hayewarta gadon baki daya tayi kwanciyarta tana sauke ajiyar zuciya cikin bacin rai,ya rabata da kowa kowa shi yake bawa gaskiya?sisin tata ma 'yar bayanshi ce,ita mai miji komai tace ba za'a bata masa rai ba,bacin rai kuwa su suka siyeshi,ta fadi ita kadai a zuciyarta tana masifarta. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ ______________________ *manzan Allah S A W yace"idan dayanku ya shiga bandaki(zai biya buqatarsa)kada ya fuskanci alqibla kuma kada ya juya mata baya,saidai ya kalli kudu ko arewa* ______________________ *Babi na arba'in* Tana kwancen babu wanda ya sake tankawa har rumanan ta gama shirinta tsaf sannan ta waiwayo ta dubeta "Tashi muje" inji rumanan,fuska ta yatsina tare da gyara kwanciyarta,tasan sarai so take su fita ta bawa rayyan din haquri "Jeki kawai zan fito"ta fahimci me take nufi kai ta gyada kawai ta dauki mayafinta ta rufe mata qofar. Har yamma tana cikin dakin,sallah kawai take tashi tayi ta koma ta kwanta,ba neman da ba'a yi mata ba amma an rasata,rumanan ma bata gaya musu inda take ba saboda so take ta samu iska sosai,saida lokacin kai amarya yayi sannan ta fadi musu inda take din. Ta dade cikin bandakin tana kuka har sai da binto yayar mamanta ta fara buga qofar bandakin tana fada cikin barbarci,umaima ke mata dariya tana tuna mata ta mance cewar raihan ba ji take can ba sannan ta sauya harshe. Cikin awa daya suka gama shiryata cikin shiga ta alfarma,leshi ne dandatsestse mai ainihin tsada riga da zani sannan aka rufe saman da lafiyayyar lafaya,duka hannayanta banguls ne na gold zuwa wuyanta da kunnenta,tsumammen qamshi ke tashi jikinta na musamman,saidai duka wannan kwalliyar hawaye ya nemi bata ta wanda ta kasa tsaidashi,wai yau ita ta auri mijin sisinta,yau ita zata shiga gidan sisinta a matsayin kishiya. Fada da nasihar data karba mai tsaho ita taja lokaci wajen kaita,sai zuwa bays An sallar magariba aka fito da ita,kuka take haiqan na zuci da badini,babu batun tayi gardamar fita saboda ta lura bata da wani magoyin baya,ta fuskanci babu mai bin bayanta duka 'yan jam'iyyar rumana da rayyan ne,haka ta dinga binsu tamkar raqumi da akala har zuwa motar da aka tanada don kaita. Tun la'asar din ta koma gida don shirin tarbar 'yan kawo amarya,kusan komai a sanyaye take yinsa amma hakan ban hanata aiwatar da duk abinda ya kamata ba,bangaren nata akwai wasu daga cikin 'yan uwanta na bangaren mamanta,kausar da meela ma ba'a barsu a baya ba,suna gefe guda suna cika suna batsewa tamkar ma sune rumanan,da biyu suka zauna nan,sunyi ne don son ganin gudun ruwan rumanan a yau,fes ta shirya cikin hadadden code net tayi kyau kamar budurwa saboda kwalliyar yadda ta amsheta . Meela da kausar suka dubi juna gami da tabe baki,kausar ta maida kallonta ga rumana wadda ta maida kai wajen danna wayarta "Allah ya kyauta,kiyashi dai garin jaye jaye yake janyo abinda yafi qarfinsa wallahi" "Hmmmm,ni wallahi ko qanwata uwa daya uba daya bazan iya yiwa haka ba" cewar meela,a nutse ta dago ta dubesu "Zuciya ce ai kowa da irin tasa,amma abinda nakeso da ku shine,ke kausar jini na ce bazan iya yanke alaqa da ke ba,abinda zance kawai da ke shine abinda nayi dai kaina na yima wa bake ba,so don Allah ki barni haka kinji,amma ke meela babu wani hadi tsakanina dake,matuqar ba zaki iya saka ido kiyi kallo ba kawai kina iya fita daga rayuwata,zaki iya yanke alaqar dake tsakaninmu" tana gama fadin haka ta miqe ta shige dakin gadonta. ruf da ciki tayi tana maida numfashi,babu shakka cikin mutane ma akwai shaidanu,so suke qarfi da yaji su dasa mata baqon lamari cikin zuciyarta. Zaren tunaninta ya yanke lokacin da taji budewar get tare da dannowar motoci cikin kantamemiyar harabar gidan,gabanta ya fadi sai tayi hanzarin kiran sunan Allah sannan ya lalubi mayafinta ta yane kanta ta fito,ita ta kama hannun raihanan har cikin part dinta,part ne da aka masa qawa ta ban mamaki,bedroom uku ya mallaka da falo biyu,daddy dalhatu ya mata kayan gado daya ita da rumana,dangin abbanta suka sake yi musu tare da rumanan dai,sai kuma wanda dangin mamarta suka yi mata,falo daya kuwa abba yusuf ne ya shirya musu ita da rumanan,yayin da rayyan ya shiryawa rumanan daya itana ita kadai. Hayaniya ta 'yan kawo amarya ta lafa,ya rage saura manya kawai wadanda dangin raihana ne rumanan da kuma dangin ummu,su suka hadasu su biyun suka musu nasiha sosai mai ratsa jiki,baya ga dogon yabo da fatan alkhairi da rumanan ta sha na namijin qoqarin da tayi wajen baiwa 'yar uwarta farinciki "In sha Allah yadda aka sanmu tun usuli haka za'a ci gaba da ganinmu,da ikon Allah babu shaidan da zaiyi tasiri tsakaninmu" cewar rumana,raihana kam kasa magana tayi sabida wani abu dake tokare da wuyanta,tana jin ta gama quntata rayuwat sisinta,ba zata iya furta komai ba baya ga kuka data ci gaba da yi sosai,irin kukan dake tsuma zuciya wanda ya haddasa tausayinta cikin zuciyar duk wanda ke gun,saboda kowa yasan me take kokawar,amma suna ganin hakan shine gata kuma babban rufib asiri gareta,din babu wanda zaya so ta sake aure makamancin wanda tayi a baya,auren da babu abinda aka tsinta cikinsa face tarin da na sani. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ *Daga abu hurairah r.a yace:abul qasim S A W yace"da ace wani mitum zai leqoka(ya leqa maka gida)ba tare da izininka ba,sai ka jefe shi da tsakuwa,sai ka tsiyayar da idonsa,to baka da wani laifi"* bukhari da muslim ne suka rawaito *a wani lafazin kuma na imam ahmad da nisa'i sukace babu biyan diyya kuma babu qisasi* _______________________ *Babi na arba'in da daya* Bayan ta yiwa 'yan rakiyar raihanan rakiya bangarenta ta wuce don ta sallami baqinta,sai data tabbatar ta sallami kowa sannan ta shiga kintsa bangaren nata kasancewar ba wani baci yayi mai yawa ba don taron kusan duk gidan abba yusuf aka yishi,wanka ta yiwa islaha dake faman gyangyadi ta sauya mata kayan bacci ta kwantar da ita sannan itama ta shiga ta sake nata wankan. A kasalance take shiryawa gaban madubi wanda hakan ya dauketa mintina masu tsaho bata kammala ba,tana gaban drower rana fidda kayan da zata sanya taji dirin mota,ta ajjiye kayan ta yaye labulenta ta leqa,motar rayyan ce ke shigowa ita kadai,sai ta saki labulen ta koma ta hau shiryawa a gaggauce. Inda suka fita suka barta bata ko sake motsawa daga gurin ba,bata motsa ba sai da taji shigowar mota gidan,ta miqe sannu a hankali har ta isa ainihin qofar falon ta turata sannan ta murza maqullin data gani jiki ta kulle,bata cire key din na ta barshi a jiki kai tsaye ta wuce daya daga cikin bedroom din da aka fara shigar da ita ta fada saman gadon ta tana ci gaba da matsar hawaye. Kafin ya kai ga shigowa har ta kammala shiryawa,a falo sukayi kacibus da shi yana shigowa hannayensa dauke da ledoji,yayi kyau abunsa cikin yadin kufta ruwan bula wanda yasha aikin sarauta a jikisa,yadda yake mai kyau haka komai nashi yaje,daddadan qamshi ke tashi a jikinsa,ta dan zuba masa ido sai taga kamar yau din an qara masa kyau,wani abu ya taso mata tayi hanzarin danneshi,murmushi ya sakar mata lokacin da take qoqarin amaar ledojin hannunsa ta zubesu saman table,ya sanya hannunsa ya janyota jikinsa ya rungumeta yana sakin ajiyar zuciya,a hankali yace "I missed you my angel,yauahe rabon da naji duminki,haka kawai kin hana mana zama"boyayyar ajiyar zuciya ta saki sannan tace "Cikon farinciki nake nema mana ai babu komai din na sarayar mana da wani dan qanqanin lokaci namu" yatsansa ya dora saman lips dinta kana daga bisani ya sauke "Ina islaha?" "Tayi bacci,muje kaima kayi wanka don nasan a gajiye kake" ta fada tana miqewa daga jikinsa,babu musu yabi bayanta har cikin dakinta,a nan ta hada masa ruwan wanka,sai wani narke mata yake yaqi yin komai shi daya,ita kuma ta biye masa har ya shirya ta zabi wasu kaya cikin drower dinta ta miqa masa,lallausan yadine mai azabar kyau da ka tsarawa dinki mai kyau,sai ya bita da kallo yana neman qarin bayani "Su zaka sanya kaje gun amaryarka da su" tsaki ya saki sannan ya wurga mata harara,ya miqe ya zari jallabiya daya cikin irin kayansa da yake bari cikin dakinta ya zura "Ni bansan ma baki sona ba sai yau rumana" Murmushin yaqe kawai ta saki,wato baisan wayeshi cikin zuciyarta ba shi ya kaishi gangancin furta haka,yayi maganar ne yana zura slippers a qafarsa zai fice daga dakin,da sauri ta sha gabansa,idanunta cikin nasa "Kana so ka nuna min cewa ni ba kowa bace kawai gurinka ya rayyan" ta fada ashagwabe idanunta na tara qwalla,hannunta ya riqe don baison kukanta don bata cancanceshi ba "Shikenan dauko min in saka indai kayane" ita ta dinga ware maaa tana miqa masa yana sakawa har ya kammala,wani kyau taga ya sake mata har ta tsaya kallonsa,yatsansa ya saka saitin idanunta kamar zai tsole mata ido,haka ne ya sanyata sakin murmushi tana fadin "U r d best husband in d world" sai ta fada jikinsa ya rungumeta tsam,hawayen da taso boyewa suka gaza boyuwa,da sauri ta hau sharewa don kada ya gani jin yana niyyar dagota daga jikinsa. Idanu ya zuba mata yana kallonta,ta qaqalo murmushi tana cewa "Muje ya rayyan na raka ka kada sisi ta gaji da jira" tsam ya hade ranshi tare da girgiza kai "Babu inda zanje kuma kada kice zaki tursasani wallahi" ya saketa ya wuce falon,ya fadi hakan ne don ita din,ya gama karantarta tunda dazun da yashigo. Kanta ta sake qarfafawa gwiwa ta iskeshi zaune a falo hannunshi dauke da remote yana jujjuya tashoshin tvn,gefansa ta zauna ta fara zuba masa qorafi da mita har sai da ya gaji "Tunda kin matsa jeki ki kirawota kuzo nan tare" "Amma ai ba haka akeyi ba kai ya kamata kaje ban......" "Shshshshs" ya fada yana dora yatsansa saman lebansa "Idan hakan bai muku ba to ku qyaleni naji da gajiyar dake damu na" ganin yadda ya dinke fuska tsaf ya sanyata miqewa ta nufi sashen raihanan. Ta dade tana buga qofar saidai ko kotsin mutum bata ji ba balle ta saka ran za'a bude,har ta gaji ta soma da kiran sunanta amma shiru kake ji,tsori yadan shigeta ko wani abu ne ya samu raihanan,da sauri ta juya ta koma bangaren nata ta gaya masa,baki taga ya tabe ya janyota jikinsa ya hau bude ledojin da ya shigo da su masu dauke da gasassun kaji a ciki da fresh milk ya ciro tsokar ya tura mata a baki,sai ta saki baki tana dubansa bayan ta hadiye wadda ta tura matan tace "Amma ya rayyan bakaji me nace ba,naje inata bugu ba alamar da mutum aciki" "To me kike son nayi,so kike naje in balle qofar?" "A'ah,amma a qalla ai tunda kana da muqallanmu kaje ka dauko mu bude muga lafiya" Shiru yayi mata ba tare daya tanka mata ba yaci gaba da zare tsokar yana bata shima yana ci. Sai da suka kammala taga yana shirin shigewa bedroom dinta yasa ta dubeshi "Ina kuma zaka haka?" "A irin wannan lokacin me ya kamata nayi,bacci ko?" "Eh zakayi amma ba'a nan dakin ba,ko ka manta daren yau waye kai?" "Ke kika sani tunda ke kika qulla abunki" ta fuskanci da gaske yake,yau dramer sukeso lallai a tada cikin gidan daga shi har raihanan sabida haka tayi wuf ta shige dakin ta saka maqulli ta zare shi ta jefa saman madubinta kana tadan daga murya tace "Allah ya bamu alkhairi" "Dadin abun dai nima ina da nawa dakin ai" taji ya fada,ta maqullin take leqensa yana zaune abinsa saman kujera ya sanya t.v a gaba,tun tana leqensa har bacci ya fara rinjiyarta ta kasa taahi saboda tsabar gajiya. **************** Gab da asuba rumana ta farka firgigit gabanta na bugawa,sai kuma ta jita kamar a jikin mutum,rayyan ne ke rungume da ita yana baccinsa hankalinsa kwance,babu shakka maqullinsa spare yaje ya dauko ya bude dakin ya shigo bayan tayi bacci,sai ta hau tureshi wanda hakan ya sanyashi farkawa,sai ya sake janyota jikinsa idanunsa lumshe da alama baccin bai isheshi ba cikin muryar bacci yaje rada mata wata magana,laqwas tayi bata sake motsi ba cikin qanqanin lokaci baccin ya sake awan gaba da su saboda gajiyar dake jikinsu. Ita ta sake rigashi tashi,lokacin shida saura,salati ta saka tana qoqarin sauka daga gadon,idanunta suka sake fadawa kansa,fuskarnan tayi wani kyau,tadan zuba masa ido tana jin qaunarsa na sake ratsata,sai kuma ta tuna abinda sukayi,ya kwaso kwanan raihana ne fa ya kawo mata. . Har suka idar da jam'in sallar da sukayi fuskarta na a hade tsaf,taqi koda kallansa,shima yasan ko yayi magana qorafin da zata masa hakan ya sanya bai ce mata komai ba,haka nan itama bata ce mishi uffan ba tunda ya riga da yasan abinda ya aikata din. Daga nan miqewa tayi ta sake gyara bangaren nata sannan ta zarce kitchen ta shirya breakfast,cikin wasu sabbin warmers ta zuba su sannan ta ware wani daban ta zubawa raihana sannan ta wuce toilet don yin wanka. Can ta tarad da shi ya hada ruwa cikin bathtub yana kwance ciki,ya daga kai ya kalleta sai ta juya zata fita,ya sanya hannu ya fincikota ta fado cikin ruwan,zatayi magana ya hade bakinsu guri guda ya hanata cewa komai,tare sukayi wankan suka fito,duk wani daure fuskarta sai da ya sanyata dariya har da qyaqyatawa,ya riga da yasan kan kayansa,rayyan ba baya bane wajen sanin kan soyayya,tare suka gama shiryawa har lokacin islaha nata barcinta,ya sake komawa gadon yana dubanta idanunsa a lumshe "Ba zaka karya bane,sha daya fa ta kusa" "Bacci bai isheni ba madam, a barni na qara" "Is ok" ta ce masa ba tare data matsa ba ta fita,don tasan yau me ta qulla musu duka shi da raihanan sai tayi maganinsu. Kitchen ta shiga ta hada kayan break fast din cikin kwando ta nufi sashen raihanan,bugu biyu kawai tayi aka bude,raihanan ce cikin shigar shadda orange doguwar riga wadda aka yiwa adon stone work da lemon green,kanta yane da siririn mayafi lemon green,duk da ba wata makeup tayi ba kamar rumana ba qaramin kyau tayi ba,murmushi ta sakarwa rumanan duk da itama tana son maida mata martani amma ta dake ta hade rai saboda son nuna mata laifin da tayi,ta rabeta ta wuce,kan daining taje ta ajjiye kayan sannan ta dawo falon "Yanzun nake shirin zuwa gaida sisi na" harara ta balla mata "Gaskiya ne,don kinzo gaidani ma ba burgeni zakiyi ba" ta sake hade rai sosai tana dubanta "Raihana.....ban yi zaton haka daga gareki ba,me kike tunanin kin aikata jiya?,sai kace wata yarinyar qauye ko wadda batayi karatu ba,to idan ma saboda ni kikayi baki burgeni ba wallahi ko kadan" da sauri ta qaraso gaban rumanan tana kama hannunta "Haba sisi,sisin ki ce fa...." Katseta tayi ta hanyar cewa "Ba ruwana da wata sisi,farincikin mijina kadai na sani" qwalla ta taru idanun raihanan "Tun yanzun ya rayyan ya shiga tsakanin qaunarmu kenan?"wani tausayin raihanan ya kama rumanan,ta sani da cew dukkanau suna qaunar juna,kawai dukansu suna hakan ne don qoqarin faranta mata,ita kuma tana jin zatayi duk mai yiwuwa don bawa kowa haqqi da farinciki gwargwadon iyawarta. Sake dakewa tayi sannan tace " babu ruwan mijina,bai shiga tsakaninmu ba ke kikeson raba tsakanin daya da biyu,inaso naga sisi na tana rayuwa irinta cikakkiyar matar aure cikin gidan mijinta,ina so naga rayyan ya rasa gane wadda tafi iya kula da sonshi tsakaninmu,inason naga sisi na ta zama cikakkiyar matar aure kamar kowacce mace" "Cikin gidan rumana 'yar uwata tare da mijinta?" Raihanan ta tambayeta tana bude idanuwanta kan rumanan,kai ta gyada cike da tabbatarwa "Eh,idan kuma kika qi,ban taba kai qararki ba tunda muke....amma wannan karon,zan kai qararki gaban hajja yakolo,gaban hajiya babba,kai har gaban abba da daddy ma,na rantse kuma tsaf zan aikata hakan karki dauka da wasa nake,saboda haka ki shirya daga yau zaki amsa sunanki na amarya kuma matar gida" bata kai ga furta komai ba muryar islaha ta cika dodon kunnensu tana kiran rumanan,ta shigo falon sanye da kayan bacci tana haki na gudun da tayi,tayi turus tana duban raihana sai kuma ta kwasa da gudu tayi gurinta,duk da yanayin da take ciki hakan bai hanata cafe yarinyar ba fuskarta qunshe da murmushi,tana bala'in son yarinyar,tana jinta kamar rumana "Momma,a gidanmu yau kika kwana?" Kai ta gyada mata tana murmushi tare da shafa gashin kanta "Itama ta dawo gidanku,ta zama 'yar gidanku" inji rumana, "Yeyyyyy" islahan ta fada cikin murna "Da gaske momma anan zaki dinga kwana kema?,nan ne dakinki?" Kai ta sake kada mata,rumana ta sake matsowa inda suke "Amma kice mata ta ta so daddynki kinji?" Sai ta dubi raihanan ta kwabe fuska "Momma bakya son daddyna?,daddy na nada kirki fa momma,zai dinga siya mana chaculets da ice cream,yana kaimu yawo,don Allah kice kina son daddy na" hararar rumana raihana tayi irin harar zaki hadani da diyata kenan? "Ina son daddyn islaha"dariya yarinyar ta saki tare da yiwa raihana kiss a kumata tana cewa " zan gayawa daddy nasan zai sai miki chaculet". Tare sukayi break fast dukansu sannan rumanan ta fice ta barsu nan din dubawa ko rayyan din ya tashi,sosai raihana ta dinga biyewa islahan,sai taji damuwarta cikin kaso dari babu hamsin,sai far gaba da take ahiga duk sandabta tuna maganarau da rumana,tasan tsaf zata iya gayawa mutanen da ta lissafo din,tasan kuwa indai hakan ta faru kashinta ya bushe,don babu mai ganin laifin rayyan cikinsu sai nata,me ya kamata tayi?. Ita ta yiwa islahan wanka ta shiryata tsaf tare da yi mata kwalliya,yarinyar tayi kyau,kamarta da mamanta ta sake fitowa,ta samu baqi ba laifi wadanda suka kaita har wajen la'asar sannan suka tsagaita. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ *Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace "lallai da sannu zaku dinga nuna kwadayi akan shugabanci,kuma da sannu zai kasance NADAMA a ranar qiyama"* _ruwayar imam bukhari_ _________________________ *Babi na arba'in da biyu* Gidan ta sake gyarawa inda ya dan baci sannan ta sake turareshi da turaren wuta kana ta zauna kallo ita da islaha. Qarfe shida rumana ta turo qofar falon hadi da sallama,tayi kyau cikin dinkin atamfa riga da skert wadda tayi mata cas a jikinta,make up ne sosai a fuskarta. Ta zauna kan daya daga cikin kujerun tana duban raihana "A zaune kike kenan?" Ta mata tambayar tana dubanta ganin ba wani shiri da take "Eh wallahi" raihanan ta bata amsa ba tare da nuna ta gane me take nufi ba "Islaha nazo dauka to,oya muje a sake wanka,daddy ya kusa dawowa"ta fada tana miqawa islahan hannu " oh,tafiya zakuyi ku barni?" Ta waiwayo ta dubeta "Amma dai baki manta maganar da mukayi ba dazun?"tabe baki raihanan tayi sannan tace " oho to sai me?"murmushi tayi tace "zaki gani ne" ta fita tana sake cewa "Sai kinzo cin dinner,bance kiyi girki ba" . Ci gaba tayi da kallonta saidai hankalinta na kan rumana,bata so ko daya tayi wani abu da zai sosa ran 'yar uwar tata,amma tana ganin dole ta sabawa tsarin rumanan saboda tana jin nauyin bin tsarin nata yadda take so. Bata tashi daga kallon ba sai da taga an kusa kiran sallar magariba,toilet ta shiga ta hada ruwan wanka tayi wanka sannan ta fito ta shirya cikin wani material lemon grean me sulbi dinkinta na yau da kullum doguwar riga,mai kawai ta shafa da powder sai man lebe,ta daure jelar qananun kitsonta da aka mata daga maiduguri da wani dan madaidaicin ribbom orange,ta sake shafe jikinta da humra sannan ta wuce kan abun sallarta ta tada sallah. Kai tsaye bangaren rumanan ya wuce wanda sai da yayi knocking wajen sau biyar abinda bai taba ba sannan ta bude qofar falon nata,tana dauke da islaha a kafadarta wadda tayi mata kwalliya itama kamar yadda suka saba cikin riga da wando farare duka,idanunshi cikin nata ya miqa hannu ya amshi islaha dake qoqarin sauka daga jikin mamanta zuwa babanta tana cewa "Oyoyo daddy" yana fadin "Daddy's girl,kinyi kyau"yayi kissing kumatunta sannan ya maida dubansa ga rumana wadda ta tsare qofar shiga falon " yau kuma sai na roqi a bani hanya ne madam"gira ta daga mashi tana murmushi hannayenta harde a qirjinta "Muje sashenka,yau can zaka sauka" yayu dan jim sannan shima ya daga girarsa duka biyun yace "Toh,yau kuma?" Itama sake daga masa girar tayi tace "Yes" tana qoqarin amsar islaha daga hannunshi tare da cewa "Taho ki bar daddy ya huta kinga ya gaji" qememe taqi yarda tazo gurin ta hakan ya sanya yace ta rabu da ita suka jera zuwa sashen nasa. A falo ya ajjiye islaha bayan rumanan ta kunna mata cartoon a tashar m.b.c 3 sannan suka wuce bedroom ta hada masa ruwan wanka ya kintsa sannan ya fita sallar magariba. Bai dawo ba sai da aka idar da isha'i,ya tadda su a falon tana taya islahan kallon cartoon din,zama yayi kusa da islahan ta dawo jikinsa ta kwanta,ya kalli sashen da rumana take yana shafa cikinsa da hannu daya "Madam yunwa nakeji,naga alamar yau komai ma roqa nake" miqewa tayi tana dubansa "Ok,bani minti biyu" ya bita da kallo sanda take ficewa ba tare da yace komai ba. Kan kujera ta sameta a kwance tana amsa waya,shigowarta ya sanyata katse wayar ta miqe daga kwanciyar fuskarta qunshe da murmushi "Amarya ki taso muje muci abinci"tsaki raihana tayi tana hararta "Amaryar wa?,kada ki sake wani cemin amarya wallahi matuqar baso kike muyi fada ba" "Fada kuma na nawa?" Rumanan ta fada tana mele baki,sam bata kawo rayyan na gurinka ba don bata ji ma shigowarsa ba hakan ya sanya ba musu ta miqe ba tare data damu da yafa koda mayafi ba tabi bayan rumanan. Bangaren da taga suna shiga ne ya sanyata tsayawa turus ta dubi rumanan "Ina kuma zamu haka?" Ta tambayeta,shiru tayi mata tare da ci gaba da tafiyar,juyawa tayi da niyyar kowama taji an riqo hannunta,waiwayowa tayi sai suka hada ido da rumanan,wani irin fushi da bacin rai da bata taba gani ba ta hango idanunta,sai jikinta yayi sanyi ta kauda kai daga kallonta "Zan iya jure komai aa banda cin fuska ko wulaqanci wa mijina,zan kuma iya miki uziri kan komai banda taka doka ko iyakokin Allah" ta saki hannunta tayi gaba,binta tayi da kallo sannan daga bisani tabi bayanta jikinta a sanyaye. A hankali ta daga idonta bayan shigarsu falon,yana zaune gefan islaha ya bude mata cheesy yana miqa mata tana karba tana ci,ganin suna qoqarin hada ido ya sanyata kau da kai,baiyi tsammanin ganinta ba sam hakan ya sanya masa wani yanayi lokaci guda ya mamayeshi saboda ganin da yayi mata na rashin zato,sai ya maida kallonsa kan rumana yana jifanta da wani kallo,qin dubansa tayi face dauke kai da tayi cikin basarwa sannan tace "Sai ku tashi muci abincin tunda kowa ya hallara" ta fadi tana miqewar,ta saitin raihana tabi tana sane ta take mata qafa tare da cewa can qasa cikin rada "Allah ya sawwaqe miki tunda ko gaisuwa baki iya ba" da sauri ta daga kai ta cilla mata harara "Eh din ban iya ba" ta gaya mata tare da murguda baki,caraf kan idon rayyan,yabi dan qaramin bakin nata da kallo,ya manta kwana nawa rabon da ya ganta din,sai yaga kamar an sake sauyata,sanyinta ya sake daduwa,yanayinta da komai nata ya sauya,kanta na kallon can wani sashen tana tafiya zuwa dining din tace dashi cikin hade rai "Barka da yamma"banza yayi da ita tamkar baiji ta ba,sai da yazo saitin bayanta sannan ya furta shima can qasa "nafi qarfin irin wannan gaisuwar,ki riqe kayanki"sai ta tabe baki cikin ranta tace "ka hutar da ni" ta bar maganar tasa tabi ruwa ba tare da rumanan ta ankara da abinda ya farun ba. Tamkar kurame haka suka zama kan table din,rumana da islaha kawai ke karadinsu,kallonsu kawai takeyi don ta gama shirya tsiyar da zata musu,haka suka kammala cin abincin,ita ta soma miqewa jin garin ya fara qugin hadari wanda dama kwanansa biyu yana haduwa a sama ba'a samu ruwan ba ta dauki islaha tana fadin "Oya,muje na sauya miki kaya duk kin bata kayanki,shi yasa banson saka miki fararen kaya wlh" "Ni momy ban gama kallon cartoon din ba,kuma momma ma tace zata tayani kallo" "Muje in canza miki sai mu dawo,nima hira nakeso muyi da daddy" dukkansu babu wanda ya fahimci manufarta sai data fice gurin ya zama sai su biyu,sai itama ta ture kujerarta baya ta miqe ta sauka daga wajen cin abincin tayi qofar ficewa daga falon. Wasa gaske sau uku tana murda handle din qofar taqi buduwa. Iya qarfinta ta sake murzawa amma ina sai data kalla sosai ta lura da key aka rufe qofar,tuni jikinta ya bata abinda rumana ta aikata,sai ta saki qofar ta koma kan kujerar dake daura da bakin qofar ta zauna jikinta a mace,bata san meye mafita ba mai zata aikata?,me yasa rumana ta mata haka,tasan girman abinda ta aikata mata kuwa?,sam ba zata iya daukan abin kunya ba dole ta samu hanyar ficewa,babban tashin hankalinta ma wayarta a bangarenta ta barta balle ta kira rumana,yana daga gun dining din ya fuskanci meke faruwa,bai tanka mata ba har ya kammala ya miqe ya shige bedroom a nutse,idanunta suka sauka kan wayarshi,ta miqa hannu ta dauka cikin sauri ta duba number din rumanan da sunan da yayi mata seving my angel ta danna kira,jiki babu qwari ta sauke wayar a kunnenta saboda amsar da kamfanin waya suka bata na cewa wayar a kashe take,sai ta maida wayar muhallinta daidai lokacin da ya sake fitowa daga bedroom din sanye da kayan bacci na maza launin ruwan madara mai haske da digo digon orange a jiki,hannunsa dauke da kwalin fresh milk da kofin glass,kallonta yayi sannan ya maida idonsa kan wayar tasa,baice mata komai ba ya sanya hannu ya dauki wayar tasa sannan ya wuce can gefe kan wani dan qaramin table da aka tanada mai kyau da tsari wanda aka shirya masa litattafai da takardu sai system guda biyu dake jone jikin socket da alama gun ya tanadeshi ne don yin wasu aikace aikacensa na office,ta gefan ido take satar kallonsa hankalinta a jagule,ya haye kan kujerar da take mahadin table din ya kunna system din tare da zuba mata ido yana jira ta gama daidaituwa,madararsa ya tsiyaya cikin cup ya fara kurba hankalinsa kwance,wani haushi ya turnuqeta,wato shi ko a jikinsa ma,baya tunanin kallon da sisinta zata musu gobe sa safe?,bazayayi wani yunquri ba ma na bude mata qofar bare ta fita,hasalima ya nuna kamar baisan meke faruwa ba. Ta runtse idonta zuciyarta na bugawa kadan kadan,qamshin turarensa ya dinga hijira daga inda yake zaune zuwa inda take zaunen ya buwayi hancinta,sannu a hankali yayyafi mai dan qarfi ya soma sauka hade da iska mai sanyi,wanda sanyin ya cakudu da sanyin ac din dake falon ya dinga ratsata,tilas ta kwashe qafafunta daga saman tiles din ta maida kan kujerar saboda yadda sanyin ke ratsa mata qasusuwa tare da curewa guri guda bayan ta cire dankwalin kantaa ta lullube jikinta tana ci gaba da satar kallonshi ta gefan ido tana addu'ar Allah yasa ya tashi ya gwada bude qofar. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _______________________ *Daga anas R.A yace:manzan Allah S A W yace"addu'a tsakanin kiran sallah da iqama ba'a maidata(Allah yana amsata a take)* ________________________ *Babi na arba'in da uku* Ci gaba tayi da satar kallon nashi,saidai ko kusa bata ga alamun zai tashin ba,aikinsa ma ya shiga yi cikin computer din,sai zuciyarta ta karye hawaye ya balle mata ganin da gaske kwanan dakin zata yi,ta dinga share hawayenta da gefan dankwali tana tunanin da wanne ido zata kalli rumanan gobe duk da ita ga janyo komai itace sila. Kusan hankalinsa gida biyu ya kasu,sau kusan biyar shima yana satar kallonta ba tare da ta lura ba,wani sashi can na gefan zuciyaraa yake jin wani nauyi na sauka,wani nishadi na ratsashi,yau gashi shida raihana a matsayin miji da mata,abu daya zuwa biyu ke masa burki yaji mizanin farincikin ya ragu a ransa,na farko yadda raihanan ta juya ma soyayyarsa baya,na biyu kuma yakanji kamar ya dawo da hannun agogo baya ya shafe qaddarar auren raihana da ammar. Hannunsa ya harde kan qirjinsa ya zuba mata ido daga inda yake din yana kallonta bayan awanni kusan uku da ya shafe kan computer din yana aikin tsara bikin bude katafaren kamfaninsa irinsa na farko a arewa,ta daina mutsu mutsun da take ta gaji ne ko kuma bacci ne ya kwasheta bai sani ba,zuwa lokacin ruwan saman dake sauka ya qara qarfi,sanyin garin da ni'imarsa sun dadu,ya maida idonsa kan computer din ya kasheta bayan ya adana komai ya miqe. A hankali ya dinga takawa har inda take kwancen yana ci gaba da kallon doguwar fuskarta wadda baccin da take ya qara mata kyau,baya ga dankwalinta da ya zame yiri yirin kitsonta ya fito tar,sai ya tsugunna a gabanta daf da ita har yana sheqar numfashinta dake fita a hankali,wani sonta ke qara fusgarsa,zuciyarsa na sakw narkewa,baisan yayi kewarta fiye da qima ba sai yanzun da yake zaune daf da ita,ya sanya hannunsa a hankali yana shafi gefan fuskarta,motsin da ta danyi ne ya sanyashi saurin janye hannunsa,ta dan gyara kanta kadan sannan taci gaba da barcinta ba tare sa tasan meke faruwa ba. A hankali ya miqe ganin taci gaba da baccin,sai ya zuba hannunsa cikin aljihun wandon kayan barcinsa yana dubanta tare da tunanin ya zaiyi mata?,bazaya iya barinta ta kwana a nan ba ko don sanyin da garin yayi,sai ya wuce gun makunnin a.cn ya kashe duka har zuwa ta can cikin dakin,cikin toilet ya shiga yayi brush ya daura alwala kamar yadda ya saba yayi shafa'i da wutirinsa wadda dama mafi yawancin lokuta sai zaya kwanta yake yinta,sannan ya dawo ya kashe duka wasu qwayaye dake falon ya sake dawowa inda take,hannunsa ya sanya ya dauketa cak bayan ya tsaya yana dubanta,juyi kawai ta danyi taci gaba da barcinta,ganin bata sake motsi ba. Saman gadon ya shimfideta yana qoqarin tashi dan zif din gaban rigarta ya maqale jikin madaurin rigarsa,ya sake sunkuyawa sosai don cirewa cikin rashin tsammani ta farka a firgice wanda hakan ya sanya ya fadi kanta baki daya,kiciniyar tureshi ta fara yi qirjinta na bugawa cikin muryar fushi ba tare data daina yunqurin tureshi din ba ta soma fadin "Malam meye haka,daga ni" idanu ya zuba mata ganin yadda takeyi sai kace wani kwartonta,ranshi ya dan baci,sai yaci gaba da kallon nata ba tare da ya tashi din ba yayin data ci gaba da qoqarin tureshi amma ta kasa ya aza mata nauyinsa baki daya "Haka kika yima mijinki na baya ma ko ni kadai kika raina?" Ya tambayeta idanunsa cikin nata cike fal da kishi,sai ta dubeshin itama,burinta kawai ta masa abinda zaya ji haushi "Ina ruwanka da wannan,ko ba haka nayi masa ba ai shi ana sonsa ne ba cushe bane" wani dan banzan kishi ya sake kamashi,zuciyar 'yan maza ta motsa,take idanunsa suka sauya launi,a lokacin ji yake da ya halatta ya kauda wani ammar zai fara nemowa ya kawar,yanajin ya masa illa soaai har cikin zucuyarsa,mutum ne shi mai azabar kishi qwarai da gaske. Suka hada ido da sauri ta janye nata idon gabanta na faduwa,nadamar furucinta nason kamata saidai bata so tayi a lokacin har ya fahimta,a zafafe ya sake dora mata nauyinsa baki daya ya kama fuskarta da tafun hannayensa biyu saitin tashi har suna musayar numfashi "Muma da ba'aso zamu karba da qarfi,idan yaso saiki zauna kiyi lissafi ki banbance tsakanin aya da tsakuwa" ya qarashe maganar yana sanya hannunsa gaban rigarta ya kama zif dinta,kafin tayi wani yunquri ya jashi ya zugeshi har qasa wanda har sai da qarfen zif din ya fice baki daya,kici kicin qwatar kanta ta shiga yi yayin da shi kuma ya nuna mata da bambanci,duk da haka baya karaya ba bakinta bai mutu ba har sai da ya kame bakin nata baki daya ya hanata damar furta komai. Bata tashi nadama ba sai lokacin,dana sanin furucinta bata kamata ba sai a lokacin,tabbas rayyana qule yake kuma daidai yake da ya nuna mata kurenta,hawaye ne suka soma zirya a fuskarta,zuwa lokacin bata da wani sauran qarfin komai,sai da ya gama gajiyar mata da duk wata gaba dake jikinta sannan ya sake mata baki,cike da tsoro da dana sani ta fara roqarsa kafin ya mata mai gaba daya,wani irin tsorinsa da bata taba ji ba ya dinga shigarta ganin yadda ya sauya mata baki daya kamar ba rayyan din data sani ba,yaya rayyan dinsu cikin qananun mintina ya sauya mata,saidai ina ta makaro,cikin zafi da son ladabtarwa ya soma daga baya ya juye ya zame masa wani irin tsumammen shauqi,shauqi ne da d'ad'd'e daya jima danqare cikin zuciyarsa wanda yau ta takalo shi,sam baima fahimtar yaren da take magana da shi burin da yasa a gaba kawai yakeso ya cimma. Ko daya bai taba kawota cikin wani sahu ba baya ga na wadda ta taba yin aure,hakan ya sanya kai tsaye ya fara aiwatar da nufinsa a matsayinta na wadda yake zaton tasan komai,kuka take masa irin wanda bata taba yinsa ba,rana ta farko data fara raina kanta da wayonta ma baki daya,babu kalar sunan da bata kirashi da shi ba ko zata samu sassauci amma babu alamun hakan,gaba daya baisan me yake yi ba,a hankali ya dinga rage kaifin duk abinda ya tanadar mata yana maida nutsuwa jikinsa bayan daya fahimci wanne matsayi raihanan take kai,duk da haka taji jiki iyaka,kuka take harda majina,mamaki ne fal zuciyarsa,ta yaya hakan ta faru?,ya akayi haka ta kasance?,da gaske ne?,da gaske ne shine mutum na farko daya karbi mutuncin raihanan?,da gaske shine mutum na farko cikin rayuwarta?,to me hakan me nufi?,kawai sai yayi zaman dirshan saman gadon bayan ya jingina bayansa a fuskar gadon ya janyota jikinsa ya matae tsam,bata da wani sauran qwari a jikinta hakan ya sanyata bata yi wani yunquri ba,kanshi ya daga sama yana kiran sunayen Allah tare da yi masa kirari "Tabbas Allah kana sona,ubangiji na gode maka da kyautar da ka yikin,na gode maka da tsaremin mata ta da kayi" haka ya dinga fada kamar wani zautacce,baisan qwalla yake fitarwa ba sai da hawayen ya gangara zuwa kunnensa,ya tabbata Allah ne ya dubi irin kushin da yake da shi ya bashi waraka. Gaba daya ya rasa ta inda zai fara lallashinta,da baki zai lallasheta ko da me?,kallonta yake yana shafa kanta duk da ta kifa fuskarta taqi dubansa,azabar da takeji ne kawai ya isheta,ga wani haushin rayyan din da tsoronsa daya rufeta,ji take kamar ta tashi ta fella da gudu,gani take kamar zai sake mata wani abun ne,da zata iya gaya masa daya barta kada ya sake rabar jikinta, . Ajiyar zuciya ta dinga saukewa,ya sake dubanta wata qaunarta na sake ratsashi,tausayinta na irin shigar zafin da yaso yi mata ya kamashi,babu shakka Allah ya masa baiwa da managartan mata har biyu,wanda babu abinda zaya ce masa sai godiya,babbar baiwa ce da ba kowa ke samun irin hakan ba,ya kasa jurewa har sai daya ranqwafa cikin sanyi ya sumbaci goshinta,duk da barci ya soma fusgarta amma ta jiyoshi,taci gaba da sakin ajiyar zuciya har baccin yayi awon gaba da ita. Tunda ta koma bangarenta ta sake gyarawa islaha jikinta ta kaita bedroom dinta ta kwantar sai ta miqe ta zauna "Mommy mu koma gun momma" sun riga da sunyi barci kema ki kwanta kiyi"sai ya maqe kafada cikin shagwaba "Mommy" yatsanta ta dora kan lebanta tare da zaro mata idanu "Banason shirme,c'mn ki kwanta nace miki" tilas ta koma ta kwanta tana sonyin kuka. Dauke idonta tayi daga kan yarinyar bayan taga ta kwanta,wayarta ta dauka ta kamo suratul baqara ta dan rage volume ta ajjiye kan bedside drower ta kana ta miqe ta shige toilet ta daura alwala,ta jima saman abun sallar tana bin sautin karatun wata nutsuwa na saukar mata,ta tabbatar tayi abinda ya dace kuma tana da yaqinin Allah bazai barta taji wani radadi ko dana sani ba,kayi abinda ya dace da sai Allah ya tsaya maka,ko sanda ta kwanta kan gadon bata fasa bin karatun ba,sautin na ratsata nutsuwa na saukar mata,sannu a hankali bacci ya sureta ba tare data sani ba cike da nutsuwa. Har ya gama shirin fita masallaci bata sani ba,sai lokacin ya tuna aqulle suke,laluba ma'ajiyar maqullan gidan yayi yayi sa'a ya samu guda daya da shi yayi amfani ya fice. A hankali ta bude idanunta da suka daddaure,ta juya idanunta ta qarewa dakin kallo,bata ga alamun yana ciki ba,miqewa tayi ta lallaba ta sauka daga gadon ta fice daga bangaren baki daya. . Sau uku yana gwada spare key don bude bangaren nata amma yaqi buduwa,alama ce ta cewa ta bar wani key din kenan jikin qofar,tausayinta ke ratsashi,yaso ace ta bashi damar lallashi,ko ba'a gaya masa ba jikinsa ya bashi tana can tana kuka ne. Qarfe goma ya shiga sashen ta,a gaban dining ya sameta tana shirya abinci,tayi kwalliya kuma kyau cikin dinkin material riga da zani,ta daga kai suka hada ido,sai tayi saurin kau da kai jin gabanta na faduwa,ya isa inda take din ya janyota ta fada jikinsa ya matseta gam,ta saukar da ajiyar zuciya tana gaidashi tare da sake shigewa jikinsa,ya amsa sannan yayi kissing lips dinta yana qorafi "Ko ki leqo ki dubani bayan ke din mai laifi ce ko?" Ya fada yana dan mintsilarta a kafada,ta saki dariya cikin son basar da maganar,don tasan qorafin kullesun da tayi jiya zaiyi "Yanzun nake shirin kiranka dama,na gama shiryawa zan wuce" "Zuwa ina" ya fada bayan ya dagota yana duban fuskarta "Qoqi mana,ka manta yau za'a karbi lefan alawiyya(qanwarta)" kai ya gyada yana shafa sumarsa "Ok...ok,haka ne fa,amma da dai kin haqura angel ina da....." Da sauri ya katseshi ta hanyar bubbuga qafanta a qasa "Haba dear,da kanta fa ina cewa ta gaya maka tun ran daurin aurenku,kuma kaga nice babbar yaya ya kamata ace ina gurin" "To Allah ya kiyaye hanya,qarfe nawa zaki dawo" tadan yi far da ido alamun tunani sannan tace "Ko bayan magariba ne pls dear.....ko kazo ma kawai mu dawo tare?" Ta fada cikin sigar tsokana tana kanne masa ido daya,murmushi kawai yayi tare da jan kumatunta,qimarta da yake qara gani a yanzun tafi gaban haka,ba kowacce mace bace zata iya yin abinda tayin,wani girma tare da qauna ta musamman ta sake samu daga gareshi,ita ta zama silar dawowar farinciki cikin rayuwarsa,ta zama silar mallakar abu mai daraja da tsada a duniyarsa "Duk yadda my angel tace" juyi tayi jikinsa tace "Thnaks abban islaha" sannan ta miqe tana daukar mayafi da jakarta dake saman kujera tana cewa "Ga breakfast dinku nan na sallameku,ka gaida sisi kace na dauke mata basai taje ba" shiru yayi ba tare da yace komai ba,sai hannu da yasa ya amshi jakar hannunta da zummar yi mata rakiya "Ina kuma islahan?" "Wai,ai tun safe safina(daya qanwar tata)tazo ta dauketa zata rakata karbo kayan snacks na baqi,daga nan kuma naji shiru nasan qoqin suka wuce", driver ne ya jata suka fice daga gidan sannan ya juya ciki. Sake komawa yayi karo na hudu don sake gwadawa,cikin sa'a ya samu ta bude,ya tura ya saka kansa ciki,shiru bangaran haka nan bata falon,ya sake shiga yana kallon dakunan baccin dake jere har zuciyarsa tafi karkata ga guda daya wanda ke saitinsa kai tsaye ya nufi ciki. Tana zaune takure kan abun sallah,tunda tayi wanka tayi sallah take zaune a gun,tsabar kukan da take ya sanya mata wani shegen ciwon kai,duk yadda taso taji haushin rayyan kuma zuciyarta taqi aminta,ta kasa jin haushin nasa yadda duk taso cusawa zuciyarta,tsayawa yayi yana kallonta hannayensa harde a qirjinsa kafin ya taka sannu a hankali zuwa gabanta,zaman dirshan yayi har gwiwarsa na taba tata wanda hakan ya sanyata dago kai tana duban wanda ke gabanta . Yatsunsa ya sanya ya soma share mata hawayen dake malala kan fuskarta,sai ta sanya hannunta ta riqe hannun nasa gami da kau da fuskarta,cikin rawar murya tace "Tunda Allah yasa ka samu cikar burinka ka sallameni rayyan,ka fidda ni daga inuwarka" zame hannun nasa yayi ya kama dukka hannayenta ya sanya cikin nashi "Bana son wannan zancan raiha bana sonshi,kina qona zuciyarta kina cutar da ita,kinfi kowa sanin ba don haka nake sonki ba,ba wannan soyayyar nake miki ba,me yasa kike neman sauyawa daga raihanan da na sani,so silent,innocent girl,mai good characters?,kina sanya zuciyata tana aikata abinda bai kamata ba,kinga jiya kin jawo na kusa cutar da ke,inda wani mummunan abu ya faru da ke kina zaton zan iya yafewa kaina?,ina sonki ina kishinki,so please nd pls na roqeki ki tsaida duk wani abu da kike tunani,wadda kike son farantawa ba ta haka takeso ki faranta mata ba,nine mai faranta mata ke kuma ki faranta min" "Amma dai kasan cewa bai kamata......" "Na gaji na gaji da jin kalmar bai kamata ba,bamu kyauta ba,bai dace ba and so on" ya fada a dan tsawace,sai ta saki sabon kuka,janyota yayi jikinsa yana dan bubbuga bayanta cike da tausasawa tare da sauke ajiyar zuciya,saita tsinci kanta da ci gaba da kwanciya cikin jikin nasa tana fidda hawaye. Tsawon mintina ta diba tana yi ba tare da ya hanata ba kana daga bisani da yaga bata niyyar tsagaitawa ya dagota yana dubanta "Is ok bana son sake jin sautin kuka,kinyi sallah?" Kai ta gyada masa "Wanka fa?" Kamar tayi banza da shi sai kuma ta sake daga masa kai,miqewa yayi ba tare da yace komai ba ya shiga toilet dinta ya hada ruwa mai zafi sannan ya dawo ya sameta inda take zaune "Oya muje ki sake wanka ki gasa jikinki" dagowa tayi tana dubansa baki sake duk da bata iya ganinsa tar saboda hawaye da ya cika idanunta babu glass kuma a fuskarta,yana nufin shi zaya yi mata wanka ma?,ganin tayi shiru ya sanya ya sake maimaita maganarsa,sai ta sauke idonta qasa tana tura baki hawaye na sake sintiri kan fuskarta "Kai baka jin kunyar sisi na?" "Kada ki sake min maganar wani idan muna tare idan ba haka ba ranki zaya baci,get up!" Ya fada cikin daga murya,tsoro ya kamata ganin yadda ya tsare gabas da yamma ya kafeta da wani kallo da ya yiwa nata idanun kaifi wanda ya sanyata ba shiri ta miqe tsaye,wani sashe na zuciyarsa cike fal da tausayinta,amma ya fuskanci idan ba hakan ya biyo mata ba bazai yiwu ta saitu yadda yakeso ba,Allah ne ya soshi ya tuna cewa raihanan gwanar tsoro ce,bata son tsawa ko fada ko kadan. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _______________________ *Daga abdullahi dan mas'ud R.A yace:manzan Allah S A W yace"haqiqa mafi cancantar mutane da ni ranar qiyama shine mafi yawaitarsu salati a gareni"* *_Allahumma salli ala sayyadina muhammadin wa 'ala ahlihi sahbihi wasallim tasliman kasira_* _______________________ *Babi na arba'in da hudu* Sum sum ta shige bandakin yayin da ya rufa mata baya,tsayawa tayi cak tana dubansa ganin ya biyota,ya fidda towel babba guda daya ya ajjiye gefan kwamin wankan,ta dubeshi ido taf da qwalla ta kauda kai gefe daya "Zan iya da kaina,ka fita don Allah" dubanta yayi na tsawon wasu daqiqu sannan ya dauke idonsa ya fice ba tare da yace mata komai ba. Kusan awa ta shafe kamar ba zata fito ba saboda wani nauyi da takeji Fitowarta kenan shi kuma ya fita daga dakin,hakan ya sanyata saurin shiryawa a gurguje cikin dinkin atamfa riga da skert,turare kawai ta fesa ta koma bakin gadon ta zauna jikinta duk a mace,baya ga wani dan banzan zazzabi da taji yana hura qashinta. Dawowa yayi dauke da kayan karin bisa wani faranti,ya dire a asa saitin qafafunta sannan shima ya samawa kansa gurbi gaban farantin,tea ya hada cup biyu ya daidaita zafinsa yadda baki zai iya sha,sannan ya zuba farfesun kai cikin wani dan qaramin plate ya dubeta "Sauko ki yi break" kai ta girgiza idanunta a lumshe "Na qoshi" sai ya hade fuska cikin son tilasta mata cin abincin "Da kika ci me?" Ya maida mata tambayar lokacin da ya tsurawa fuskarta ido,shiru tayi ba tare da ta amsa ba don tasan bata da amsar tambayar,ganin bata da niyyar cewa komai sai ya dauki cup da plate din ya haura gadon kusa da ita ya zauna wanda hakan ya sanyashi jin hucin zazzabin da jikinta ke fitarwa,ya fidda hannusa ya sanyashi saman goshinta take dumin jikin nata ya ratsashi "Ya salam" ya ambata yayin da ya lumshe idonsa sannan ya budesu a kanta,tuni idanunta har sun tara qwalla,hannunsa ya dora kan lebensa yana alamta mata kada ta soma yi mishi kuka,sai tayi qas da kanta tana jin nauyin yanayin kusancin zamansu na dab da juna. Cokali ya sanya ya dinga diban ruwan tea din yana bata,zuciyarsa shaqe da tausayi gami da tarin tambayoyi,shin soyayyarsa ce ta hanawa raihana bawa waninsa kanta ko kuwa,bai da amsar tambayar kuma bai cancanci ya tare ta da tambayar ba a irin wannan lokacin. Sai da ya tabbatar ruwan zafin ya ratsa hanjinta sannan ya dinga diban farfesun da kadan kadan yana bata,ta qoshi amma baida niyyar tsayawa,ta lura kuma idan ba tsaidashin tayi ba ba zaya daina batan ba,hakan ya sanya ta daga hannunta a hankali ta riqe tsintsiyar hannunshi lokacin da yake niyyar sake bata,ya daga narkakkun idanunsa ya zuba cikin nata,take idanunsu suka hadu waje daya,wani nauyinsa da kunyarsa wadda bata taba jiba ta sarqafeta,sai ta janye idanun nata da sauri ta maida kan kwanan dake gabansu,cikin sanyin murya tace "Na qoshi" "Kin tabbatar" ya fadi yana laluben qwayar idonta cike da burin su sake hada ido saboda shauqin da hakan ya haifar masa,bata yarda ta sake dubansa ba face kai da ta gyada masa,sai ya sauka ya tattare duka kwanukan ya fita da su. . Bai barta cikin dakin ba don kada zazzabin yaci gaba da yin tasiri,bayan magani da ya sanyata ta sha suka dawo falo,kanta ya dora bisa cinyarsa bayan ya kunna t.v don rage zaman shirun,kunya ta dabaibayeta har ta hanata motsi,wani abu taji yana ci gaba da motsa zuciyarta game da rayyan din wanda keson dawo mata da rayyan din cikin rayuwarta,wata iska ke kadawa cikin zuciyarta tana sin lallai ta dawo da duk wata so qima da martaba tashi,tanason tambayar rumananta tana jin nauyi,hakanan tana so ta sashi ya bar sashenta don ga zatonta rumanan na gida amma sai ta gaza,nauyinsa take ji,sai tayi shiru kawai,a haka bacci yayi awon gaba da ita,sai da yaji shirun yayi yawa sannan ya juyata yaga tayi barci,murmushi ya saki yana duban kyakkyawar fuskarta,yana sake tuna raihana a baya quruciyarsu zuwa tasowarsu,har yau dai ita dince sai wasu abubuwa qalilan da suka sauya tattare da ita,a hankali ya duqa ya bata kiss kan tattausan lebenta kana ya gyara mata kwanciya. Ko da ta farka sai taji qwarin jikinta sosai,sukayi sallah a tare sannan aka kawo musu lunch wanda kallo daya ta masa tasan takeaway ya bada akayi musu,tamkar kurame haka suke zaune sai satar kallonshi da take,yayin da shi kuma kai tsaye yake kallonta hakan ya sanya sukayita hada ido. Bayan sallar la'asar ta yanke shawarar shiga kitchen ta musu abincin dare tunda ta fuskanci rumana bata nan,ko banza kuma ta yanke zaman kurumtakar da suke,don a matuqar takure take,yau daya rayyan din ya koma mata kamar wani surukinta. A hankali taji an sanya hannu an karbe wuqar dake hannunta wadda take qoqarin fere dankali,bata ji shigowarsa hakan ya sanya tadan tsorata,sai ya sake matsawa jikinta ya rungumeta ta baya baki daya tare da dora habarsa kan kafadarsa,cikin wata murya mai sanyi data ratsa dodon har kwanyarta yace "Wa ya saki girki?"idanunta a lumshe qirjinta na bugawa tace cikin daburcewa " abincin darenmu,sisi na bata nan...." "Ok,bari in taimaka miki,da fatan kina maraaba" bata ce komai ba sai zare jikinta da tayi gefe tare da sakar masa wuqar tana maida numfashi qasa qasa. Kusan tare sukayi girkin,saidai shiru kitchen din yake kamar kurame ne a ciki sai 'yar satar kallo,qarfe shida da ashirin suka kammala couse da miyar alayyahu wadda taji busasshen kifi da dankalin turawa,cikin bangaren nata ya barta ya tafi nashi don yin wanka,ita dinma wankan ta shiga bayan komai ya kammala. Ana idar da sallar magariba ya shigo,sanye yake cikin wani farin yadi mai taushi mai adon light blue,yayi mata kyau sosai har sai da zuciyarta ta gaza sharewa ta qyasa can qasan ranta,ya dubeta tana zaune kan abun sallah "Zanje na dauko rumana daga gida kada kiji bakiji motsina ba" take tsoron zama ita kadai a gidan ya kamata,sai ta gyada kai kawai ta sauke idonta qasa,ya fuskanceta sbd haka ya dubeta "In kuma zaki tashi ki shirya muje" sai ta girgiza kai,don a ganinta bai kamata su wuni tare kuma ta sake binsa ba "Sai ka dawo,Allah ya kiyaye hanya" amsa mata yayi sannan ya juya ya fice bayan ya kulleta ta waje. Sai da suka gaisa da mama mahaifiyar rumanan ya musu Allah ya sanya alkhairi sannan suka fito,basu taho da iftihal ba a can suka barta kasancewar ta riga da tayi bacci. Gaban motar ta zauna gami da cewa "Wash Allah na" tana dubansa,gira ya dage mata tare da cewa "Gajiya ko" "Kaidai bari,ango kasha qamshi" ta fada cikin sigar zolaya tana murmushi wani abu na dan tsinkulinta,hannu yasa ya dalle mata baki sai tasa tafin hannunta ta damqe bakin cikin kukan qarya "Shine zaka fasan baki ko"ta fada tana matse ido,'yar qaramar dariya ya saki tare da janyota jikinsa yana qoqarin cire hannun daga kan leban nata yana cewa "ayyah,bari mu gani"ta saki hannun tare da turo leban sai ya qyalqyale da dariya tare da sanya bakinsa kan leban ya tsotse tas sannan ya kalleta "ya warke?"kai ta gyada masa tana murmushi " alright to sannu my angel,amma as from today angon mutum biyu ne ni,r&r kin fahimta?"dariya ta saki tana dage gira "See you don Allah"shima girar ya daga yana fadin "to qarya ne" "Mu tafi don Allah ka barmin 'yar uwa ita daya a gida bayan baqunta har yau take" ta fada tana miqa masa key din motar,murmushi yayi yana kallonta,adalcinta na burgeshi,ya tada motar suka fice. Bakin wani katafaren super market ya fara tsayawa ya dubeta yace su shiga ciki,itama kallonsa tayi "Me kuma zamu siya saboda asaran kudi,duk wani abun buqata muna da shi" qasa qasa yayi da murya yana mata wani irin kallo "Yes na sani,but i hv suprise for my beautiful wives" sai ta saki murmushi sannan tace "Ko?,well,muje na rakaka" "Ko kin rakanin ma ba zaki ga ko meye ba duk abinki sai munje gida" ya fada yana fita a motar,cikin dariya tabi bayansa tana fadin."dadin abun ma koma meye mu za'a bawa ko". . Bai barta cikin dakin ba don kada zazzabin yaci gaba da yin tasiri,bayan magani da ya sanyata ta sha suka dawo falo,kanta ya dora bisa cinyarsa bayan ya kunna t.v don rage zaman shirun,kunya ta dabaibayeta har ta hanata motsi,wani abu taji yana ci gaba da motsa zuciyarta game da rayyan din wanda keson dawo mata da rayyan din cikin rayuwarta,wata iska ke kadawa cikin zuciyarta tana sin lallai ta dawo da duk wata so qima da martaba tashi,tanason tambayar rumananta tana jin nauyi,hakanan tana so ta sashi ya bar sashenta don ga zatonta rumanan na gida amma sai ta gaza,nauyinsa take ji,sai tayi shiru kawai,a haka bacci yayi awon gaba da ita,sai da yaji shirun yayi yawa sannan ya juyata yaga tayi barci,murmushi ya saki yana duban kyakkyawar fuskarta,yana sake tuna raihana a baya quruciyarsu zuwa tasowarsu,har yau dai ita dince sai wasu abubuwa qalilan da suka sauya tattare da ita,a hankali ya duqa ya bata kiss kan tattausan lebenta kana ya gyara mata kwanciya. Ko da ta farka sai taji qwarin jikinta sosai,sukayi sallah a tare sannan aka kawo musu lunch wanda kallo daya ta masa tasan takeaway ya bada akayi musu,tamkar kurame haka suke zaune sai satar kallonshi da take,yayin da shi kuma kai tsaye yake kallonta hakan ya sanya sukayita hada ido. Bayan sallar la'asar ta yanke shawarar shiga kitchen ta musu abincin dare tunda ta fuskanci rumana bata nan,ko banza kuma ta yanke zaman kurumtakar da suke,don a matuqar takure take,yau daya rayyan din ya koma mata kamar wani surukinta. A hankali taji an sanya hannu an karbe wuqar dake hannunta wadda take qoqarin fere dankali,bata ji shigowarsa hakan ya sanya tadan tsorata,sai ya sake matsawa jikinta ya rungumeta ta baya baki daya tare da dora habarsa kan kafadarsa,cikin wata murya mai sanyi data ratsa dodon har kwanyarta yace "Wa ya saki girki?"idanunta a lumshe qirjinta na bugawa tace cikin daburcewa " abincin darenmu,sisi na bata nan...." "Ok,bari in taimaka miki,da fatan kina maraaba" bata ce komai ba sai zare jikinta da tayi gefe tare da sakar masa wuqar tana maida numfashi qasa qasa. Kusan tare sukayi girkin,saidai shiru kitchen din yake kamar kurame ne a ciki sai 'yar satar kallo,qarfe shida da ashirin suka kammala couse da miyar alayyahu wadda taji busasshen kifi da dankalin turawa,cikin bangaren nata ya barta ya tafi nashi don yin wanka,ita dinma wankan ta shiga bayan komai ya kammala. Ana idar da sallar magariba ya shigo,sanye yake cikin wani farin yadi mai taushi mai adon light blue,yayi mata kyau sosai har sai da zuciyarta ta gaza sharewa ta qyasa can qasan ranta,ya dubeta tana zaune kan abun sallah "Zanje na dauko rumana daga gida kada kiji bakiji motsina ba" take tsoron zama ita kadai a gidan ya kamata,sai ta gyada kai kawai ta sauke idonta qasa,ya fuskanceta sbd haka ya dubeta "In kuma zaki tashi ki shirya muje" sai ta girgiza kai,don a ganinta bai kamata su wuni tare kuma ta sake binsa ba "Sai ka dawo,Allah ya kiyaye hanya" amsa mata yayi sannan ya juya ya fice bayan ya kulleta ta waje. Sai da suka gaisa da mama mahaifiyar rumanan ya musu Allah ya sanya alkhairi sannan suka fito,basu taho da iftihal ba a can suka barta kasancewar ta riga da tayi bacci. Gaban motar ta zauna gami da cewa "Wash Allah na" tana dubansa,gira ya dage mata tare da cewa "Gajiya ko" "Kaidai bari,ango kasha qamshi" ta fada cikin sigar zolaya tana murmushi wani abu na dan tsinkulinta,hannu yasa ya dalle mata baki sai tasa tafin hannunta ta damqe bakin cikin kukan qarya "Shine zaka fasan baki ko"ta fada tana matse ido,'yar qaramar dariya ya saki tare da janyota jikinsa yana qoqarin cire hannun daga kan leban nata yana cewa "ayyah,bari mu gani"ta saki hannun tare da turo leban sai ya qyalqyale da dariya tare da sanya bakinsa kan leban ya tsotse tas sannan ya kalleta "ya warke?"kai ta gyada masa tana murmushi " alright to sannu my angel,amma as from today angon mutum biyu ne ni,r&r kin fahimta?"dariya ta saki tana dage gira "See you don Allah"shima girar ya daga yana fadin "to qarya ne" "Mu tafi don Allah ka barmin 'yar uwa ita daya a gida bayan baqunta har yau take" ta fada tana miqa masa key din motar,murmushi yayi yana kallonta,adalcinta na burgeshi,ya tada motar suka fice. Bakin wani katafaren super market ya fara tsayawa ya dubeta yace su shiga ciki,itama kallonsa tayi "Me kuma zamu siya saboda asaran kudi,duk wani abun buqata muna da shi" qasa qasa yayi da murya yana mata wani irin kallo "Yes na sani,but i hv suprise for my beautiful wives" sai ta saki murmushi sannan tace "Ko?,well,muje na rakaka" "Ko kin rakanin ma ba zaki ga ko meye ba duk abinki sai munje gida" ya fada yana fita a motar,cikin dariya tabi bayansa tana fadin."dadin abun ma koma meye mu za'a bawa ko". Suna shiga ya ja mata kujera yana dubanta "Oya,jirani a nan,idan kuma kinga wani abu da kike so ki dauka" murmushi kawai tayi ta zauna tana gyada kai shima ya maida mata sannan yayi gaba. Bai wuce minti goma ya dawo hannunshi dauke da leda mai kauri,leqan ledar take tana dariya da son ganin meye a ciki shi kuma ya hanata,ya miqa mata hannunshi yana fadin "Mu tafi". Bude warmers din tayi tana dariya gami da zaro ido " wow sisi,kamar kuwa kinsan abinda nake ta sha'awa kenan tun dazun"murmushi tayi kawai don nauyin yin magana take ji,rayyan da tuni ya fara kaiwa cikinsa dadin abincin na ratsashi yace "To ai ba ita tayi ba" ya nuna kansa "Nine nan" sai data saka loma daya bakinta sannan ta kada kai tace "Wannan test din ba na girkin ka bane daddyn iftihal maganar gaskiya" ta fada cikin dariya sa sigar tsokana,janye abincin gaban nata yayi yana fadin "Tunda kika ce haka sai kici mu gani" narke fuska tayi ta koma kalar tausayi "Haba mana abban iftihal afuwa,wlh yawuna tsinkewa kawai yake,sisi ki masa magana" ta fada tana duban raihana,murmushi tayi ba tare data ce komai ba ta janyo warmer din da wani plate din ta cika mata sannan ta tura mata "Barshi,dauki wannan kici kinji" da sauri ta dauka ta soma ci tana fadin "Thanks" hannu ya sake sanyawa zai dauke farantin raihanan tayi hanzarin riqe hannun nasa har sai da ya dago kai suka hada ido,tayi kicin kicin tare da buga masa harara,sai ya janye hannun yana jujjuya kai tare da kama kunnensa tare da fadin "Kabi a sannu,a shirye raiha take sa tama duka akan sisinta" yanayin yadda yayi maganar ya bada dariya,musamman rumana dake qyaqyatawa har da masa gwalo,ita din ma duk yadda taso cinye dariyar tata sai data fito,har ta samu kanta da maida masa amsa "Ato,gwara da rayyanu ya gano haka" sai kuma tayi gum ganin yadda ya tsareta da kallo yana murmushin dariyar da tayi. Rumana na shirin tashi ya dakatar da ita,ya janyo ledar sa yayi siyayya daya ajjiye gefansa ya zazzage kayan ciki,iphone 7 ce guda biyu,sai wasu dogayen riguna masu bala'in kyau guda biyu wanda rumanan ta taba bashi labarin tanason siya,su ake yayi wannan shekarar(baku manta halin rumana da son kayan burgewa),kowacce daya dubu talatin ne kudinta,ido da zaro cikin farinciki tun kafin yace komai,ya dauki kwalin waya daya ya miqawa rumana dayar kuma ya miqawa rihana yana fadin "Ga dai waya kyauta,amma riga nawa za'a bani kafin na bayar?" Cikin zumudi tare da kiciniyar bude wayar tace "A dai bamu tukunna ni zan biya kudin" kai ya gyada yana murmushi sannan ya miqawa kowacce rigar,sai data tabbatar sun amsa suka masa godiya sosai kana ta miqe "Kayi sadaqatul jariya daddyn iftihal,ko sisi ba zamu bayar ba" ta fada cikin dariya tare da yin gaba,ya bita da kallo yana fadin "Don tuwon gobe dai......" "Ake wanke....." Sai kuma ta katse maganar sannan ta dawo da baya,tayi kalar tausayi tana dan in ina "Don Allah abban iftihal,furarka zaka sanmin,wlh tawa ta qare" "Kinyi kadan yarinya,yazu kika gama min butulci fa,sannan gaba daya kin zama wata kwadayayya duk kin bi kin lamushe kayan sanyin gidan nan kamar wata sha zumamu" raihana ta miqe tsam bata ce komai ba,ta bude fridge din ta ciro robar furar damammiya mai kwakwa har guda uku sannan ta dubi rumana "Muje sisi na rakaki da ita" "Sata kuma kuka koma?" Ya fada yana dage girarsa da qwalalo ido, "Eh din" inji rumana ta kama hannun raihana suka fice. A bakin part dinta ta dakata tana amsar furar "Bani nan ki koma,Allah ya bamu alkhairi" harara ta watsa mata sannan tace "Basai kinmin kora da hali ba,amma duk abinki wallahi baki isa ba sai na qarasa" ta fada tana wuceta ta cusa kai. Kusan wata hirar suka dasa har sai da rumanan tayi kicin kicin tace itakam ta yafe gobe sa hadu. Qin komawa bangarensa tayi saboda tsaron daren jiya kai tsaye tayi wucewarta bangarenta,hankali kwance ta tura qofar dakin gadon nata,batayi zato na ta ganshi zaune kan sofar dake dakin ,sanye yake cikin kayan bacci light blue da sukayi matuqar amsarsa,ko dama can shi da wuya yasa kaya suqi yi masa kyau ko wadanne iri ne kuwa,hannunsa riqe da littafinsa na LOVESTORY yana maimai dinsa,ya daga idanunsa da suka sake lumshewa ya zubesu a kanta,hada ido sukayi gabanta ya yanke ya fadi,ya dan zuba mata idon yana kallonta sai tayi qas da kanta har tana hardewa wajen qarasowa ciki. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ *Daga sa'id dan zaid R.A yace:manzan Allah S A W yace"duk wanda ya yanke taqi guda na qasa(fili ko gida ko gona)da zalunci,to,Allah zai rataya masa shi ranar alqiyama tun daga qasan bakwai"* _bukhari da muslim ne suka rawaito shi_ ______________________ *Babi na arba'in da shida* Tana idar da sallahr magariba ta isa gaban madubi bayan tayi wanka tun shigowarta,saita kuma tsintar kanta da yin kwalliya mai qayatarwa,tana daura dankwalinta cikin sauri don komawa gun sisinta suci gaba da hira don ba qaramin dadin hirar da suka wuni yau sunayi ba taji. Sallamarsa gami da turo qofarsa ce ta katse mata hanzarin,ya shigo dauke da jakar office dinsa,kwalliyarta ta ta tsone masa ido har ya tsaya kallonta,hakan sai ya bata kunya bayan lokaci mai tsawo rabon da taji hakan,ya qaraso a hankali ya rungomota ta baya ya dora habarsa kan kafadarta sannan ya saki ajiyar zuciya yana ci gaba da kallon kwalliyar tata ta madubin dake gabansu qamshin jikinta na ratsashi,a hankali ta bude bakinta kanta na duban qasa ta masa sannu da zuwa ya amsa mata cikin wani irin salo "Raihata kinyi kyau,dama kin iya kwalliya har irin haka amma bakiyi?" "Wa zanwa a wancan lokacin,bayan na fidda rai da samun wani wanda zaya zamemin SANYIN IDANIYATA,wani wanda zaya zamewa rayuwata GARKUWA,meyw amfani ko ma'anarta idan nayi" ta fada cikin zuciyarta. Anan ya narke mata,sai data masa duk wani abu da rumana ta sabar masa,kama daga wanka tayashi shiryawa har ma da qarin zaba masa kayan da zaya saka din,ganin an kusa kiran isha'i ya dubeta fuskarsa fes da walwala "Ki jirani naje sallah na dawo sai mu wuce gun sisinki muci dinner ko?" Ya rada mata a kunnenta,ta dan janye jikinta saboda yadda salin maganar tasa ta sanya tsigar jikinta tashi tana dubansa "To" kawai tace masa,ya dauki carbinsa mai dannawa ya maqalawa yatsansa ya fice. Tana idar da tata sallar ta wuce wajen rumanan,don bata son ya iskota bare ya matsanta mata kan dole sai sun jera sun tafi tare don tana kunyar hakan. Hira ya tarad da suna yi,ya jefa mata harara ya gayada kai tare sa daga hannusa ya mata alamar zan kamaki ne,sai ta kawar da kai gami da basarwa cikin zuciyarta tana sake tuna tsiyar da zata qulla,don ko bai fada ba idanushi da kallon da yake mata ya gama gaya mata fitinar da ya tanada. Kamar yadda suka aaba cike sa raha da barkwanci suka ci abincinsu,ita tafara zamewa da zummar tana zuwa ta barau falon suna kallon wani film a tashar mama africa,tana shiga falonta ta mayar da key ta rufe ta bar key din a jiki ta yadda ba wani key da za'a saka a sake bude qofan,ta fada saman kujerarta bayan ta kunna kayan kallonta taci gaba da kallin film din da ta barsu suna kallo saboda ya mata kyau,a nan barci ya kwasheta ba tare data sani ba. Cikin barcinta ta soma jinta cikin wata duniya,a fari taso ta tsorata amma qamahin mayen turaren baccinsa ya gaya mata waye,cikin fargaba da tsoron rayyan din ta sakar masa kuka sosai wanda shi ya taka masa birki,murmushi ya saki mai hade da 'yar dariya sannan ya lakace mata hanci "Raiha raguwar kawai" ya fada yana janta cikin jikinsa ya matseta gam yana sauke numfashi,luf tayi a jikinsa tana jin dadin yanayin tare da rage farashun kukan nata ahankali kadan kadan har wani dddadan bacci wanda ya sakata sake qudundunewa jikin rayyan din yazo ya saceta bata sani ba,shi kuwa sake rungumeta yayi yana sakin murmushi din ya tabbata da idanuwanta biyu ba zata riqeshi hakan ba. *************** Randa ta cika kwana hudu ta gama lissafinta na cewa ta fita girki tunda kwanan zawarawa zatayi kwana uku kenan,ta kammala sallar magariba kenan ta fito falo tana jiran isha'i,sanye take da dogin wando pink colour sai rigar itama pink 'yar cikin mai gajeran hannu iyakarta saman cikinta wadda daga gabanta aka yiwa don furanni ash mai qyalli,ta saman kuma ash ce mai tsawo har gwiwarta,gabanta gaba daya abude yake hakanan tana da dogayen hannuwa pink colour,ba qaramin kyau kayan suka mata ba,hade rai tayi data ganshi yana fitowa daga kitchen dauke sa kofin qarau wanda ya cikashi da fresh milk da zuma,itakam tsoronsa yanzu take ji,tsoro ma take kada gaba yafi qarfinta,cikin sauri tace da shi "Ka manta yau girkin sisi na ce" sai ya qaraso kusa da ita tamkar zai fada jikinta ya kashe mata ido daya hadi da daga mata girarsa yace "Raihata ba bazawara bace ko kin manta?,hakanan siain tata ma ta san da hakan,ta kuma san kwanaki bakwai sisinta zatayi,amma....." Ya dan dakata kadan yana lalubar qwayar idanunta sannan ya dora "Bansan ya akayi haka ta kasance ba duk da rayyan dan gatan Allah ne,sisinki tasan ke wace ya akayi sweet rayyan bai sani ba?,ummmm" ya qaraahe maganar yana kama qugunta tare da mannata ajikinsa ya kuma hade fuskarsu guri guda har hancinsu na gogar na juna,gama daya ya gama kashe mata jiki,ba zata iya wata magana ba,rawa jikinta ya soma har ya fuskanci haka,sai ya saki dariya ya dago fuskarta yana kallonta idanunta ta runtsesu gam "Shikenan,adana amsar tambayarki,zuwa anjima kya gaya min,ungo qarasa shanye wannan,saboda anjima ko......" Ya qarashe gaya mata maganar cikin kunnenta wanda hakan ya sanyata saurin bude idanunta da sukayi narai narai kamar zata faahe da kuka tana kallonsa,murmushi ya saki ya kai mata cup din bakinta tare da fara zuba mata madarar yana cewa "Ba wannan raihar nake son gani ba,jarumar raiha nakeso,wadda zata karbi mijinta duk yadda yake,banason ganin karaya gunki tun yanzu ubmm,saboda rayyan mayen raihana ne kin manta tun a baya,so kiyi haquri da shi hakanan" bata ce komai ba ta bude baki ta kurbe sauran madarar,tasa harshenta tana lashe lebanta,ya sa mata ido yana kallonta sai shima ya sanya harahen nasa yana tayata lashewar wanda sauran kadan hakan ya zubar da su a qasa rayyan din yaui jarumtar tararsu,suka hada ido sai duka dariya ta kubce musu lokaci guda,ta cusa kanta a qirjinsa tana boye fuskarta sabida wata iriyar muguwar kunya da ta kamata. ************* Kwanaki bakwai rayyan din yayi mata kamar yadda addini ya tanada,cikin kwanakin rayyan din ya sake mata wani mugun tasiri cikin rayuwarta,ya sake yiwa zuciyarta wata babbar illa a sonshi,yayi nasarar tone duk wami sirri da tayi niyyar boyewa dangane da irin tsntsar so da qauna da take masa,a kullum kwanan duniya bata gajiya da yiwa rumana addu'a data tsamo rayuwarta daga halaka,sai yanzu take sake gasgatawa rayuwarta ba zata taba zama dai dai ba ba tare da rayyan ba,wani sone ashe boye can qasan birnin zuciyarta mai tarin yawa wanda tsantsar QAUNA ABOTA SON SADAUKARWA DA DANGANTAKA suka taka muhimmiyar rawa wajen boyeshi,tabbas babu shakka alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,idan da tabi son ranta abaya qila da zuwa yanzu dukkansu basu samu wannan farincikin ba,duk wanda yayi alkhairi zaiga alkhairi a can gaba,walau a nesa cikin rayuwarsa ko a kusa. Randa ya koma dakin sisin nata ita da kanta ta musu sai da safe,data dawo bangarenta taji kewarsa nason kamata sai tayi shirin kwanciya kawai,ta kunna karatun qur'ani abinta,haqiqa maganar Allah gaskiya ce da yace DA AMBATON LLAH KADAI ZUKATA KE SAMUN NUTSUWA,mafi akasarin mutane dakan tsinci zuciyarau cikin wani hali na qunci ko quntata sun saki Allah ne ko hanyar Allahn,tilawa tayi mai yawa kafin bacci ya sureta,cikin aminci farinciki da nutsuwa tayi cikakken bacci mai cike da kwanciyar hankali. Qarfe tara ta kammala yi musu break fast wanda tun jiya ta cewa rumanan ba ita ba shiga kitchen da safe gobe itama amarya take,wanda ta musu ma na kwana bakwai Allah ya bada lada,zuwa goma na safe ta kammala komai ciki harda wanka da kwalliyar data cakare cikin wata shadda ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,abinka da chaculet colour sai tayi masifar haskata,bata je ganin ko sun taahi ba don kada ta takurasu,sai ta kunna kallo ta kama tashar arewa arewa 24 tana kallon maimaicin shirin haske matan arewa . Tare suka shigo hannyensu sarqafe da juna "Sannu da hutawa amaryarmu raiha" rumana ta fada da yanayin salon da rayyan kan kirata da shi,dariya ta saki tana juya ido sannan tace "A ga wace amaryar dai tsakanin ni da ke" dariya sukayi baki daya,raihanan ta dora da cewa "An tashi lpy sisi" "Lafiya qalau,ya kwanan kadaici" "Ban yishi ba" ta fada tana miqewa tare da gyara daurin dankwalinta sannan tace "Muje mu karya har lokaci na shirin qwacewa,ko yau mijin naki ba fita zaya yi ba?" Ta qarashe cikin salon tsokana,rayyan dake harde da hannayensa yana faman kallon adonta tun dazun yace "Me ruwanki da ni?,tunda ko arziqin gaisuwa ban samu ba" itakam wani kunya da nauyi ne ya hanata ce masa komai,rumana tayi gaba taba cewa "Me zaya hana,bari na fara hada masa tea ya dan sha iska"sai ta danyi murmushi sannan ta qaraso gabansa ta rage tsawo tace " barka da warhaka yallabai,Allah ya taimakeka"lumshe ido yayi,kirarin ya masa dadi,sai ya dan janyo ta jikinsa yana cewa "Wannan irin gaisuwa haka raihata,kada fa ki rudani" ta janye jikinta da sauri tana duban sashen da rumana ke tsaye can wajen dining area tana hada masa tea tare da amsa kiran da ya shigo wayarta,sai tayi fari da idanunta tare da harde hannayenta itama tana dubansa,murmushi yayi sannan yace "Na rasa gane wanda yafi wani iya ado tsakanin ke sa sisinki,any way ina son aci gaba da wannan kwalliyar,tana burgeni" "An gama yallabai" ta fada tana dariya ganin yadda ya wani langabe yana sake bin kwalliyar tata da kallo har sai da ta tunkuda qeyarsa cikin salon wasa ta dan daga murya tace da rumana "Zo ki dauki mijinki don Allah hakanan" "Ko baki fada ba" inji rumana tana dariya itama. Da yammaci tana qoqarin shiga kitchen raihanan ta fado cikin kitchen din,ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani simple,kanta lullube da mayafi hannunta saqale da jaka,dubanta rumana tayi bayan ta dora tukunya saman gas "Hala fita zakiyi" "Eh,amma zuwa magariba zan dawo in sha Allah" Tayi mata Allah ya tsare sannan ta fita. Batasan ma islaha taje daukowa ba sai da suka zo cin abincin dare,ta shigo riqe da hannunta,yarinyar tayi kyau cikin shigar riga da wando "Eh lallai,abun ma 'yar wariyar launin fata ce ko?,hala daddy da hadin bakinka ma" gira ya daga mata yace "Yes......haka kawai ki bar mana gida shiru bayan muma muna da buqatarta" murmushi kawai tayi daga bisani suka soma cim abincin wanda islaha duk ta buwayi kowa da karadi raihana na biyewa takwarartata. . **************** Ranar daya ga watan daya itace ranar da ta kama rayyan zaya bude katafaren kamfaninsa wanda a qalla ya kwashe kusan shekaru shida yana gina shi. Tamkar 'yan biyu haka suka fito a ranar,komai nasu iri daya ne,hatta da jaka takalmi zuwa sarqa da dan kunne,ranar ba qaramin burge mutane sukayi ba,sai wajen la'asar suka dawo gida,wanda nan ma sun dan taho da mutane saboda washegari rayyan ya shirya musu gagarumar walima da za'a gabatar a cikin gidan,qannan rumana ne sai kausar da meela,wannan karon kam raihana ma ta samu baqi qannanta su zainab tun daga maiduguri kasancewar lokacin yayi daidai da hutun makaranta da aka nawa dalibai,amma ta barsu da qyar zasuyi kwanaki uku. Tun dazun meelan ke bin rumana da kallo ganin yadda mu'amala ke gudana tsakaninta da da raihana tamkar wasu 'yan biyu,kishi takeji sosai cikin ranta tare da ganin baike da rashin wayo na rumanan,tana jin idan itace kam qila da ta dade da mutuwa bayan faruwar auren rayyan da raihana. Bata samu sararin tarar rumana da maganar ba sai data dauki warmers daga kitchen ta bawa zainab qanwar raihana data aiko a bata warmers ta sake musu girki saboda baqi,a balcony ta cimma rumanan tana shirin shiga falon,sai ta dubi meelan ganinta a gaggauce "Ah,ba dai har tafiya ba?" Kai ta girgiza gami da tabe baki "Ba tafiya zanyi ba,wani abu na gani da zuciyata ta gaza jureshi" sai rumanan ta dan sauya fuska tare da cewa "Kamar me fa?" Dan shiru tayi tana kallon rumana kafin daga bisani tace "Wallahi har yau mamaki kike bani rumana,wai kishiya kikewa hakan?,kin manta kishiya ko ta'yar tsana ce sunanta kishiya?,wallahi Allah kinji ja rantse miki,tsaf na lura da take taken raihanan nan,shi yasa sam bata kwanta min ba naji na tsaneta,idan bakiyi da gaske ba kin maida hankalinki ba sai ta zamemiki qarfen qafa,wake wani son kishiya ko amince mata banda ke?,to wallahi ki sauya taku,qauna ce tasa nake gaya miki gaskiya,don bazan ga abinda zai cutar da ke ba na kasa gaya......." "Dakata don Allah jamila" rumana ta fada cikin fushi "Wannan itace qaunar da kike min din?,qaunar da zata saki bani gurguwar shawara wadda banu komai cikinta sai wahala?,shin kin manta tun kafin ki sanni raihana ta sanni?,kin manta tun kafin ki fara qaunata raihana ta fara qaunata?,bari kiji,ko bansan raihana ba ayadda halayyarta take bazan iya cutar da ita ba,sau nawa ma jamila ina gaya miki ki fidda idonki kan zamantakewata da 'yar uwata?,kinsan me raihana ta yimin a rayuwa?,kinsan cewa da raihana muguwa ce da tuntuni ta jima da tarwatsa rayuwata cikin ruwan sanyi ba tare da na san cewa ita ta aikata hakan ba?,bakisan cewa da raihana taso kanta ba da tuni bani a kan bigiren da nake kai yanzu?,kin qureni jamila.....kin qureni,abu daya nakesom sanar miki,daga yau babu ke babu rumana,sai hali yazo daya ake abota ko,to ta wannan fannin halayyarmu tasha banban sabida haka qarshen qawancenmu yazo". Cikin jin haushi meela ta dubi rumana " au,don ina gaya miki gaskiya?,to shikenan,basai kin koreni ba,daga yau ba zaki qara ganin fuskata ba,kuma duk abinda ya sameki nan gaba kiyi kuka da kanki tunda baki daukar shawara...." "Babu abinda zaya samesu sai alkhairi,kuma ko baki fadi haka ba bazan sake barin wata cikin mata na taga wannan fuskar taki ba,ballantana ta saurari mugunyar shawara daga wannan masharrancin bakin naki ba,wannan ta zama rana ta qarshe da zaki sake biyowa koda ta layin gidan nan ne,idan kuma kinqi ji bakya qi gani ba" suka ji muryar rayyan cikin kaushi zafi da bacin rai yana fada,gaban meela ya fadi jikinta ya dauki qarma,ba shiri ta rabasu ta wuce qafa na rawa da gaggawa ta fice daga gidan. Sai da yaga ficewarta sannan ya qara taku ya iso inda rumana ke tsaye,ya dubeta qimarta na dada qaruwa cikin ransa,dattakonta na sake ninkuwq haka nan qimar iyayenta na sake hauhawa a idanunshi,sai kawai ua janyota jikinsa ya rungumeta,cikin taushin murya yace da ita "Allah yayi miki albarka,ya baki aljanna,ba shakka da za'a samu uwayen gidan irinki da gidan aure ya zauna lafiya,don Allah ruma ta kada ki yarda da zugar qawaye ko misqala zarratin,yawancinsu basu da burin da ya wuce suga sun haifar da tashin hankali a gidajen auren qawayensu,pls rumana kimin alqawari....." Sai ta dago tare da dora yatsanta saman lebansa "Kada ka roqeni daddy,nasan kaina,nasan wace raihana hakanan nasan waye kai,ka manta cewa dukanmu mu ukun AMINAN JUNA NE?,DANGANTAKAR ZUCINMU kuma Allah ne ya ginata ba mutum ba?DANGANTAKA CE tun quruciya,duk katangar da ubangiji ne ya ginata kuwa ba wanda ya isa ya rusata,na godewa Allah da ya sa ka zamanto adalin miji a tsakaninmu,soyayya bata rufe maka ido ka wancakalar da haqqin wata daya a kan 'yar uwarta ba,na kuma sake godewa Allah da ya sanya na samu sisi na fiye ma da yadda nayi zato,wannan kawai ya isheni" "Allah ya albarkaceku,ya muku sakayya da aljannatul firdaus" ya fada yana sake matseta cikin jikinsa tare da bata kiss a goshi. Yadan rabata da jikinsa yana dubanta "Baqi sun hanani sakat my angel,yunwa nakeji a bani abinci naci na koma cikinsu" Hannunshi ta kama tana cewa "Muje na rakaka gun sisi na kaci acan,dutynta ne,kuma na tabbata ta tanada maka kalar abincin da kake so" yana biye da ita yace "Iyeee,wato ke ba zaki iya da ni ba,matan nan fa na fahimci ma ball kawai kuke da ni,kowacce so take ta nunan 'yar uwarta ta fita,haka jiya raiha ta yimin saura kadan na zaneta da tsintsiyar kwakwa" ya qarashe maganar nayan wani cin magani kamar gaske,harara ta watsa masa sanda suka isa bakin qofar falon raihan "Kai kama fara dukanmin sis?,wlh da mun maka yaji dukanmu ka zauna kai daya" wata dariya ce ta kamashi har sai da ya qyaqyata har da 'yar qwallarsa,saiga raihanan ta fito tayi kuwa biji biji da alama tasha girki "Yauwa gashinan sisi ki bashi abinci yaci" kai itama ta langwabe "Haba sisi babu 'yar kara ma,maimakon ki karbeni ni da na fito daga kitchen yanzu dubi jikina fa?" Sai rayyan ya dubesu yana bata rai "You see,yanzu na gama fadi qwallo kawai kuke da ni,idan abincin ma baza'a bani ba basai na haqura ba"da sauri suka kama kunnuwansu raihana tace " tuba muke yallabai mun mun isa"ya wani dake shi bai yarda ba fushi ya rabe raihanan yana wucewa ciki tare da fadin "Dadin abun ai zan iya sake kawo wata,idan kuna abinku na tafi wajenta nasan ita ai tana maraba da ni" "Kambu,wallahi ya rayyan mafarki kake,mu kadai aka haifa maka na gaya ma gaskiya" "Barshi sisi" inji raihana tana hararan bayansa kana ta juya ta bishi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* ______________________ *Daga sa'id dan zaid R.A yace:manzan Allah S A W yace"duk wanda ya yanke taqi guda na qasa(fili ko gida ko gona)da zalunci,to,Allah zai rataya masa shi ranar alqiyama tun daga qasan bakwai"* _bukhari da muslim ne suka rawaito shi_ ______________________ *Babi na arba'in da shida* Tana idar da sallahr magariba ta isa gaban madubi bayan tayi wanka tun shigowarta,saita kuma tsintar kanta da yin kwalliya mai qayatarwa,tana daura dankwalinta cikin sauri don komawa gun sisinta suci gaba da hira don ba qaramin dadin hirar da suka wuni yau sunayi ba taji. Sallamarsa gami da turo qofarsa ce ta katse mata hanzarin,ya shigo dauke da jakar office dinsa,kwalliyarta ta ta tsone masa ido har ya tsaya kallonta,hakan sai ya bata kunya bayan lokaci mai tsawo rabon da taji hakan,ya qaraso a hankali ya rungomota ta baya ya dora habarsa kan kafadarta sannan ya saki ajiyar zuciya yana ci gaba da kallon kwalliyar tata ta madubin dake gabansu qamshin jikinta na ratsashi,a hankali ta bude bakinta kanta na duban qasa ta masa sannu da zuwa ya amsa mata cikin wani irin salo "Raihata kinyi kyau,dama kin iya kwalliya har irin haka amma bakiyi?" "Wa zanwa a wancan lokacin,bayan na fidda rai da samun wani wanda zaya zamemin SANYIN IDANIYATA,wani wanda zaya zamewa rayuwata GARKUWA,meyw amfani ko ma'anarta idan nayi" ta fada cikin zuciyarta. Anan ya narke mata,sai data masa duk wani abu da rumana ta sabar masa,kama daga wanka tayashi shiryawa har ma da qarin zaba masa kayan da zaya saka din,ganin an kusa kiran isha'i ya dubeta fuskarsa fes da walwala "Ki jirani naje sallah na dawo sai mu wuce gun sisinki muci dinner ko?" Ya rada mata a kunnenta,ta dan janye jikinta saboda yadda salin maganar tasa ta sanya tsigar jikinta tashi tana dubansa "To" kawai tace masa,ya dauki carbinsa mai dannawa ya maqalawa yatsansa ya fice. Tana idar da tata sallar ta wuce wajen rumanan,don bata son ya iskota bare ya matsanta mata kan dole sai sun jera sun tafi tare don tana kunyar hakan. Hira ya tarad da suna yi,ya jefa mata harara ya gayada kai tare sa daga hannusa ya mata alamar zan kamaki ne,sai ta kawar da kai gami da basarwa cikin zuciyarta tana sake tuna tsiyar da zata qulla,don ko bai fada ba idanushi da kallon da yake mata ya gama gaya mata fitinar da ya tanada. Kamar yadda suka aaba cike sa raha da barkwanci suka ci abincinsu,ita tafara zamewa da zummar tana zuwa ta barau falon suna kallon wani film a tashar mama africa,tana shiga falonta ta mayar da key ta rufe ta bar key din a jiki ta yadda ba wani key da za'a saka a sake bude qofan,ta fada saman kujerarta bayan ta kunna kayan kallonta taci gaba da kallin film din da ta barsu suna kallo saboda ya mata kyau,a nan barci ya kwasheta ba tare data sani ba. Cikin barcinta ta soma jinta cikin wata duniya,a fari taso ta tsorata amma qamahin mayen turaren baccinsa ya gaya mata waye,cikin fargaba da tsoron rayyan din ta sakar masa kuka sosai wanda shi ya taka masa birki,murmushi ya saki mai hade da 'yar dariya sannan ya lakace mata hanci "Raiha raguwar kawai" ya fada yana janta cikin jikinsa ya matseta gam yana sauke numfashi,luf tayi a jikinsa tana jin dadin yanayin tare da rage farashun kukan nata ahankali kadan kadan har wani dddadan bacci wanda ya sakata sake qudundunewa jikin rayyan din yazo ya saceta bata sani ba,shi kuwa sake rungumeta yayi yana sakin murmushi din ya tabbata da idanuwanta biyu ba zata riqeshi hakan ba. *************** Randa ta cika kwana hudu ta gama lissafinta na cewa ta fita girki tunda kwanan zawarawa zatayi kwana uku kenan,ta kammala sallar magariba kenan ta fito falo tana jiran isha'i,sanye take da dogin wando pink colour sai rigar itama pink 'yar cikin mai gajeran hannu iyakarta saman cikinta wadda daga gabanta aka yiwa don furanni ash mai qyalli,ta saman kuma ash ce mai tsawo har gwiwarta,gabanta gaba daya abude yake hakanan tana da dogayen hannuwa pink colour,ba qaramin kyau kayan suka mata ba,hade rai tayi data ganshi yana fitowa daga kitchen dauke sa kofin qarau wanda ya cikashi da fresh milk da zuma,itakam tsoronsa yanzu take ji,tsoro ma take kada gaba yafi qarfinta,cikin sauri tace da shi "Ka manta yau girkin sisi na ce" sai ya qaraso kusa da ita tamkar zai fada jikinta ya kashe mata ido daya hadi da daga mata girarsa yace "Raihata ba bazawara bace ko kin manta?,hakanan siain tata ma ta san da hakan,ta kuma san kwanaki bakwai sisinta zatayi,amma....." Ya dan dakata kadan yana lalubar qwayar idanunta sannan ya dora "Bansan ya akayi haka ta kasance ba duk da rayyan dan gatan Allah ne,sisinki tasan ke wace ya akayi sweet rayyan bai sani ba?,ummmm" ya qaraahe maganar yana kama qugunta tare da mannata ajikinsa ya kuma hade fuskarsu guri guda har hancinsu na gogar na juna,gama daya ya gama kashe mata jiki,ba zata iya wata magana ba,rawa jikinta ya soma har ya fuskanci haka,sai ya saki dariya ya dago fuskarta yana kallonta idanunta ta runtsesu gam "Shikenan,adana amsar tambayarki,zuwa anjima kya gaya min,ungo qarasa shanye wannan,saboda anjima ko......" Ya qarashe gaya mata maganar cikin kunnenta wanda hakan ya sanyata saurin bude idanunta da sukayi narai narai kamar zata faahe da kuka tana kallonsa,murmushi ya saki ya kai mata cup din bakinta tare da fara zuba mata madarar yana cewa "Ba wannan raihar nake son gani ba,jarumar raiha nakeso,wadda zata karbi mijinta duk yadda yake,banason ganin karaya gunki tun yanzu ubmm,saboda rayyan mayen raihana ne kin manta tun a baya,so kiyi haquri da shi hakanan" bata ce komai ba ta bude baki ta kurbe sauran madarar,tasa harshenta tana lashe lebanta,ya sa mata ido yana kallonta sai shima ya sanya harahen nasa yana tayata lashewar wanda sauran kadan hakan ya zubar da su a qasa rayyan din yaui jarumtar tararsu,suka hada ido sai duka dariya ta kubce musu lokaci guda,ta cusa kanta a qirjinsa tana boye fuskarta sabida wata iriyar muguwar kunya da ta kamata. ************* Kwanaki bakwai rayyan din yayi mata kamar yadda addini ya tanada,cikin kwanakin rayyan din ya sake mata wani mugun tasiri cikin rayuwarta,ya sake yiwa zuciyarta wata babbar illa a sonshi,yayi nasarar tone duk wami sirri da tayi niyyar boyewa dangane da irin tsntsar so da qauna da take masa,a kullum kwanan duniya bata gajiya da yiwa rumana addu'a data tsamo rayuwarta daga halaka,sai yanzu take sake gasgatawa rayuwarta ba zata taba zama dai dai ba ba tare da rayyan ba,wani sone ashe boye can qasan birnin zuciyarta mai tarin yawa wanda tsantsar QAUNA ABOTA SON SADAUKARWA DA DANGANTAKA suka taka muhimmiyar rawa wajen boyeshi,tabbas babu shakka alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,idan da tabi son ranta abaya qila da zuwa yanzu dukkansu basu samu wannan farincikin ba,duk wanda yayi alkhairi zaiga alkhairi a can gaba,walau a nesa cikin rayuwarsa ko a kusa. Randa ya koma dakin sisin nata ita da kanta ta musu sai da safe,data dawo bangarenta taji kewarsa nason kamata sai tayi shirin kwanciya kawai,ta kunna karatun qur'ani abinta,haqiqa maganar Allah gaskiya ce da yace DA AMBATON LLAH KADAI ZUKATA KE SAMUN NUTSUWA,mafi akasarin mutane dakan tsinci zuciyarau cikin wani hali na qunci ko quntata sun saki Allah ne ko hanyar Allahn,tilawa tayi mai yawa kafin bacci ya sureta,cikin aminci farinciki da nutsuwa tayi cikakken bacci mai cike da kwanciyar hankali. Qarfe tara ta kammala yi musu break fast wanda tun jiya ta cewa rumanan ba ita ba shiga kitchen da safe gobe itama amarya take,wanda ta musu ma na kwana bakwai Allah ya bada lada,zuwa goma na safe ta kammala komai ciki harda wanka da kwalliyar data cakare cikin wata shadda ja wadda aka yiwa adon stone work baqi,abinka da chaculet colour sai tayi masifar haskata,bata je ganin ko sun taahi ba don kada ta takurasu,sai ta kunna kallo ta kama tashar arewa arewa 24 tana kallon maimaicin shirin haske matan arewa . Tare suka shigo hannyensu sarqafe da juna "Sannu da hutawa amaryarmu raiha" rumana ta fada da yanayin salon da rayyan kan kirata da shi,dariya ta saki tana juya ido sannan tace "A ga wace amaryar dai tsakanin ni da ke" dariya sukayi baki daya,raihanan ta dora da cewa "An tashi lpy sisi" "Lafiya qalau,ya kwanan kadaici" "Ban yishi ba" ta fada tana miqewa tare da gyara daurin dankwalinta sannan tace "Muje mu karya har lokaci na shirin qwacewa,ko yau mijin naki ba fita zaya yi ba?" Ta qarashe cikin salon tsokana,rayyan dake harde da hannayensa yana faman kallon adonta tun dazun yace "Me ruwanki da ni?,tunda ko arziqin gaisuwa ban samu ba" itakam wani kunya da nauyi ne ya hanata ce masa komai,rumana tayi gaba taba cewa "Me zaya hana,bari na fara hada masa tea ya dan sha iska"sai ta danyi murmushi sannan ta qaraso gabansa ta rage tsawo tace " barka da warhaka yallabai,Allah ya taimakeka"lumshe ido yayi,kirarin ya masa dadi,sai ya dan janyo ta jikinsa yana cewa "Wannan irin gaisuwa haka raihata,kada fa ki rudani" ta janye jikinta da sauri tana duban sashen da rumana ke tsaye can wajen dining area tana hada masa tea tare da amsa kiran da ya shigo wayarta,sai tayi fari da idanunta tare da harde hannayenta itama tana dubansa,murmushi yayi sannan yace "Na rasa gane wanda yafi wani iya ado tsakanin ke sa sisinki,any way ina son aci gaba da wannan kwalliyar,tana burgeni" "An gama yallabai" ta fada tana dariya ganin yadda ya wani langabe yana sake bin kwalliyar tata da kallo har sai da ta tunkuda qeyarsa cikin salon wasa ta dan daga murya tace da rumana "Zo ki dauki mijinki don Allah hakanan" "Ko baki fada ba" inji rumana tana dariya itama. Da yammaci tana qoqarin shiga kitchen raihanan ta fado cikin kitchen din,ta shirya tsaf cikin atamfa riga da zani simple,kanta lullube da mayafi hannunta saqale da jaka,dubanta rumana tayi bayan ta dora tukunya saman gas "Hala fita zakiyi" "Eh,amma zuwa magariba zan dawo in sha Allah" Tayi mata Allah ya tsare sannan ta fita. Batasan ma islaha taje daukowa ba sai da suka zo cin abincin dare,ta shigo riqe da hannunta,yarinyar tayi kyau cikin shigar riga da wando "Eh lallai,abun ma 'yar wariyar launin fata ce ko?,hala daddy da hadin bakinka ma" gira ya daga mata yace "Yes......haka kawai ki bar mana gida shiru bayan muma muna da buqatarta" murmushi kawai tayi daga bisani suka soma cim abincin wanda islaha duk ta buwayi kowa da karadi raihana na biyewa takwarartata. . **************** Ranar daya ga watan daya itace ranar da ta kama rayyan zaya bude katafaren kamfaninsa wanda a qalla ya kwashe kusan shekaru shida yana gina shi. Tamkar 'yan biyu haka suka fito a ranar,komai nasu iri daya ne,hatta da jaka takalmi zuwa sarqa da dan kunne,ranar ba qaramin burge mutane sukayi ba,sai wajen la'asar suka dawo gida,wanda nan ma sun dan taho da mutane saboda washegari rayyan ya shirya musu gagarumar walima da za'a gabatar a cikin gidan,qannan rumana ne sai kausar da meela,wannan karon kam raihana ma ta samu baqi qannanta su zainab tun daga maiduguri kasancewar lokacin yayi daidai da hutun makaranta da aka nawa dalibai,amma ta barsu da qyar zasuyi kwanaki uku. Tun dazun meelan ke bin rumana da kallo ganin yadda mu'amala ke gudana tsakaninta da da raihana tamkar wasu 'yan biyu,kishi takeji sosai cikin ranta tare da ganin baike da rashin wayo na rumanan,tana jin idan itace kam qila da ta dade da mutuwa bayan faruwar auren rayyan da raihana. Bata samu sararin tarar rumana da maganar ba sai data dauki warmers daga kitchen ta bawa zainab qanwar raihana data aiko a bata warmers ta sake musu girki saboda baqi,a balcony ta cimma rumanan tana shirin shiga falon,sai ta dubi meelan ganinta a gaggauce "Ah,ba dai har tafiya ba?" Kai ta girgiza gami da tabe baki "Ba tafiya zanyi ba,wani abu na gani da zuciyata ta gaza jureshi" sai rumanan ta dan sauya fuska tare da cewa "Kamar me fa?" Dan shiru tayi tana kallon rumana kafin daga bisani tace "Wallahi har yau mamaki kike bani rumana,wai kishiya kikewa hakan?,kin manta kishiya ko ta'yar tsana ce sunanta kishiya?,wallahi Allah kinji ja rantse miki,tsaf na lura da take taken raihanan nan,shi yasa sam bata kwanta min ba naji na tsaneta,idan bakiyi da gaske ba kin maida hankalinki ba sai ta zamemiki qarfen qafa,wake wani son kishiya ko amince mata banda ke?,to wallahi ki sauya taku,qauna ce tasa nake gaya miki gaskiya,don bazan ga abinda zai cutar da ke ba na kasa gaya......." "Dakata don Allah jamila" rumana ta fada cikin fushi "Wannan itace qaunar da kike min din?,qaunar da zata saki bani gurguwar shawara wadda banu komai cikinta sai wahala?,shin kin manta tun kafin ki sanni raihana ta sanni?,kin manta tun kafin ki fara qaunata raihana ta fara qaunata?,bari kiji,ko bansan raihana ba ayadda halayyarta take bazan iya cutar da ita ba,sau nawa ma jamila ina gaya miki ki fidda idonki kan zamantakewata da 'yar uwata?,kinsan me raihana ta yimin a rayuwa?,kinsan cewa da raihana muguwa ce da tuntuni ta jima da tarwatsa rayuwata cikin ruwan sanyi ba tare da na san cewa ita ta aikata hakan ba?,bakisan cewa da raihana taso kanta ba da tuni bani a kan bigiren da nake kai yanzu?,kin qureni jamila.....kin qureni,abu daya nakesom sanar miki,daga yau babu ke babu rumana,sai hali yazo daya ake abota ko,to ta wannan fannin halayyarmu tasha banban sabida haka qarshen qawancenmu yazo". Cikin jin haushi meela ta dubi rumana " au,don ina gaya miki gaskiya?,to shikenan,basai kin koreni ba,daga yau ba zaki qara ganin fuskata ba,kuma duk abinda ya sameki nan gaba kiyi kuka da kanki tunda baki daukar shawara...." "Babu abinda zaya samesu sai alkhairi,kuma ko baki fadi haka ba bazan sake barin wata cikin mata na taga wannan fuskar taki ba,ballantana ta saurari mugunyar shawara daga wannan masharrancin bakin naki ba,wannan ta zama rana ta qarshe da zaki sake biyowa koda ta layin gidan nan ne,idan kuma kinqi ji bakya qi gani ba" suka ji muryar rayyan cikin kaushi zafi da bacin rai yana fada,gaban meela ya fadi jikinta ya dauki qarma,ba shiri ta rabasu ta wuce qafa na rawa da gaggawa ta fice daga gidan. Sai da yaga ficewarta sannan ya qara taku ya iso inda rumana ke tsaye,ya dubeta qimarta na dada qaruwa cikin ransa,dattakonta na sake ninkuwq haka nan qimar iyayenta na sake hauhawa a idanunshi,sai kawai ua janyota jikinsa ya rungumeta,cikin taushin murya yace da ita "Allah yayi miki albarka,ya baki aljanna,ba shakka da za'a samu uwayen gidan irinki da gidan aure ya zauna lafiya,don Allah ruma ta kada ki yarda da zugar qawaye ko misqala zarratin,yawancinsu basu da burin da ya wuce suga sun haifar da tashin hankali a gidajen auren qawayensu,pls rumana kimin alqawari....." Sai ta dago tare da dora yatsanta saman lebansa "Kada ka roqeni daddy,nasan kaina,nasan wace raihana hakanan nasan waye kai,ka manta cewa dukanmu mu ukun AMINAN JUNA NE?,DANGANTAKAR ZUCINMU kuma Allah ne ya ginata ba mutum ba?DANGANTAKA CE tun quruciya,duk katangar da ubangiji ne ya ginata kuwa ba wanda ya isa ya rusata,na godewa Allah da ya sa ka zamanto adalin miji a tsakaninmu,soyayya bata rufe maka ido ka wancakalar da haqqin wata daya a kan 'yar uwarta ba,na kuma sake godewa Allah da ya sanya na samu sisi na fiye ma da yadda nayi zato,wannan kawai ya isheni" "Allah ya albarkaceku,ya muku sakayya da aljannatul firdaus" ya fada yana sake matseta cikin jikinsa tare da bata kiss a goshi. Yadan rabata da jikinsa yana dubanta "Baqi sun hanani sakat my angel,yunwa nakeji a bani abinci naci na koma cikinsu" Hannunshi ta kama tana cewa "Muje na rakaka gun sisi na kaci acan,dutynta ne,kuma na tabbata ta tanada maka kalar abincin da kake so" yana biye da ita yace "Iyeee,wato ke ba zaki iya da ni ba,matan nan fa na fahimci ma ball kawai kuke da ni,kowacce so take ta nunan 'yar uwarta ta fita,haka jiya raiha ta yimin saura kadan na zaneta da tsintsiyar kwakwa" ya qarashe maganar nayan wani cin magani kamar gaske,harara ta watsa masa sanda suka isa bakin qofar falon raihan "Kai kama fara dukanmin sis?,wlh da mun maka yaji dukanmu ka zauna kai daya" wata dariya ce ta kamashi har sai da ya qyaqyata har da 'yar qwallarsa,saiga raihanan ta fito tayi kuwa biji biji da alama tasha girki "Yauwa gashinan sisi ki bashi abinci yaci" kai itama ta langwabe "Haba sisi babu 'yar kara ma,maimakon ki karbeni ni da na fito daga kitchen yanzu dubi jikina fa?" Sai rayyan ya dubesu yana bata rai "You see,yanzu na gama fadi qwallo kawai kuke da ni,idan abincin ma baza'a bani ba basai na haqura ba"da sauri suka kama kunnuwansu raihana tace " tuba muke yallabai mun mun isa"ya wani dake shi bai yarda ba fushi ya rabe raihanan yana wucewa ciki tare da fadin "Dadin abun ai zan iya sake kawo wata,idan kuna abinku na tafi wajenta nasan ita ai tana maraba da ni" "Kambu,wallahi ya rayyan mafarki kake,mu kadai aka haifa maka na gaya ma gaskiya" "Barshi sisi" inji raihana tana hararan bayansa kana ta juya ta bishi. *mrs muhammad ce*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽 🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊🕊 💔 *DANGANTAKAR ZUCI*💔 ( _soyayya qauna abota da sadaukarwa_) *NA* *SAFIYYA ABDULLAHI MUSA HUGUMA* * *wattpad:huguma* *©haske writers asso💡* *(home of expert and perfect writers)* _____________________ *Daga abu hurairah R.A yace:manzan Allah S A W yace"Allah madaukakin sarki yana cewa,ni ina tare da bawa na matuqar ya ambaceni,kuma labbansa suka motsa saboda ambatona"* _imam bukhari ne ya rawaito_ _______________________ *Babi na arba'in da bakwai* Zama ne suke mai cike da aminci ban sha'awa gami da qayatarwa,kowacce na iya nata bakin qoqarin wajen ganin ta kyautatawa 'yar uwarta,ta boye damuwarta,ta kaucewa abinda zai taba ran 'yar uwarta,hakanan kowaccensu na qoqari matuqa wajen ganin ta kyautatawa yayan nasu kuma mijinsu rayyan,wanda ko da yaushe cikin yabawa matan nashi yake,ko da yaushe cikin godiya ga Allah da kuma godiya ga iyayensa yake,wani lokaci idan suka shagwabashi da yawa yakanji tamkar babu yashi duk cikin fadin duniya. Sau tari wadanda basu sansu sukan qaryatasu idan aka gaya musu cewa abokan zaman juna ne,kamar wani lokaci da rumana ta sake bari,taji jiki sosai raihana ke jinyarta,wata mata dake kusa da dakinsu take nuna sha'awar yadda raihanan ta damu da lalurar rumanan,tana yaba yadda take kula da ita,tace da alama 'yar uwar nan taki ita kafai ke gareki ko,qirji ta dafe gami da qwalalo idanu sanda raihana ke gaya mata yadda suke "Amma gaskiya da alama yarinya quruciya ke dibanki,waye ya gaya miki ana yiwa kishiya hakan?,kinsan ma me kishiya ke nufi kuwa,tun wuri ki rufawa kanki asiri ki janye rawar qafar da kike akan wata aba wai kishiya,ba amana tsakaninku har abada" wani banzan kallo raihanan ta yi mata,baqincikin da ya tokareta ya hanata cewa matar komai,bugu da qari kuma dama can ba mai surutu bace sabida haka sai ta tashi kawai ta barwa matar gurin,bata sake yarda sun hada inuwa ba har suka baro asibitin. **************** Yau da gobe ta Allah ce,a hankali rayuwa ta dinga tafiya musu yadda ya kamata,dama hakan take,ita rayuwa duk yadda ka dauketa haka take zuwa maka,idan ka debota da zafi bakinka ne,idan a sanyaye ka daukota ka hutama ranka,sannu a hankali rayyan ya rabata cire mata sha'awar zuwa aiki,ga 'yar kanzaginsa a gefe rumana,babu haufi ta tattara aikin ta ajjiye shi gefe,ta tattara hankalinta kacokam kan kula da mijinta gami da tattalinsa,wanda zuwa lokacin ta tabbatarwa kanta cewa rayyan din saboda shi aka halicci zuciyarta,shine rayuwarta,taso ta zalunci kanta da zuciyarta ma baki daya da taso fifita DANGANTAKAR ZUCI akan ta FILI DA GANGAR JIKI. _*8:30 pm ado bayero mall zoo road*_ A hankali kowane daya cikin iyalin mai cike da ban sha'awa ke zagayawa cikin makeken kantin yana zabar abinda yake so,wadanda sukayi qanqanta cikinsu suna tare da yayyensu da suka fisu hankali,duk da suna yin hakan lokaci lokaci amma na yau din na musamman ne,saboda maamaa(raihana)zata kwashesu ne da zarar sun samu hutun qarshen zangon karatunsu sai maiduguri wanda dama lokaci bayan lokaci tana tafiya da su suyi hutu na mako daya ko biyu haka suke,wannan kuma yazo daidai da bikin zainab qanwarta. Ihun kukan little rumana da raihana taji shi ya sanyata dafe goshinta,suka hada ido da rayyan ya saki dariya tare da kashe mata ido daya,yana riqe da hannun ummu salma daya hannun nasa kuma dauje da qatuwar tedde da ta zaba tace ya riqe mata "Kaga abinda ka jawo mana ko daddy,sai da sisi ta gaya maka tunda last week ta kawo su ka bari yau muje iya mu da kai,kace sai mun sake kwasosu mun taho baki daya" "Bakusan albarkacinsu kuka ci ma nace kuzo muje ba?" Harara ta watsa masa mai dauke da soyayya,rayyan akwai son 'ya'ya,bata sani ba ko hakan baya rasa nasaba da kasancewarsa shi daya tilo wajen ummu,inda Allah ya taqaita duk son yaranshi hakan bai sanya ya shagwabasu ko yayi wasa da tarbiyyarsu ba,raihana tace "Au to ko mu koma gida ne mu barka da su?",kafin yace wani abu sai ha rumana ta zagayo inda suke dauke da takwarar tata,raihana ta dubesu " uhmmm,Allah ku kuke sake tabara ummu,yanzu don Allah sisi ki ajjiye abdul_majid ki dauki wannan qatuwar?" "Ba ruwanki,i tamu" cikin salon tsokana rayyan yana kashe mata ido yace "Like mother like daughter,haka kike sanda kina qarama fa rumana,nasha fama da ke wajen qiriniya,ga wata qaramar 'yar tsallen mun samu nan" sai ji sukayi an tuntsure da dariya,islaha ce ita da Aabida wadda ke bima islaha diyar da raihana ta haifa,sai sagir wanda shine na uku shima yaron raihana ne "Mommy dama 'yar tsalle ake ce......" Aabida ta fara fadi raihana ta katseta ta hanyar wurga mata harara "To 'yar jarida zaki fara aikin naki ne?" "Idan kun kammala ya kamata mu wuce hakanan zamu biya mu duba jikin abba" rayyan ya tunasar da su,hakan ya sanya raihana hada kansu rumana ta sanyasu a gaba suka nufi gurin biyan kudi. Tana kan layi kafin a zo kanta hankalinta na kan takwararta litle rumana tana bare mata waper taji muryar matar dake gabanta kamar ta santa,biscuite din hannun yaron ne ya fadi bayan sun gama biyan kudi zasu fice ta durqusa ta dauko masa ta miqa masa,tana dagowa suka hada ido,meela ce,baki meelan ta riqe tana duban rumana "Ashe rai kanga rai hajiya rumana?" "Kinji maras kirki aini zan fadi haka meela,ko labarin bikinki sai bakin kausar na ji"murmushi tayi rumanan na ankare da ita,akwai alamun sauyi da nutsuwa sosai tattare da meelan,ba meelan data sani ba can shekarun baya " kin manta an haramtamin zuwa gidanku?"murmushi ta kumayi data tuna abin "Ai ya riga da ya wuce meela" "Nima sai daga baya naga gaskiyar mai gidan naki" Rumana ta kawar da zancan da cewa "Wannan baby boy din fa?,kar dai naki ne" ta dubi yaron dake hannunta tayi murmushi sannan ta maida dubanta ga rumana "Ba nawa bane,dan kishiyata ne" idanu rumana ta zaro tana duban meela "Kishiya kuma meela?,yi miki kishiya akayi?" Dariya meela ta saki sannan tace "Da labari rumana" "Bari na biya kudi inzo inji how comes meela da kishiya har da daukar yaronta" tayi maganar suna sakin dariya baki dayansu,qarasawa rumana tayi ta biya duk bill din da yake atm din rayyan din na gurinta sannan ta damqi hannun meela suka fice. Gefe daya suka samu daura da inda ake ajjiye motoci,meela ta kalli rumana "Tabbas na yarda idan kana son mutum babu abinda wannan son bazai jagoranceka ka aikata ba,sanda muka hadu da adeel har muka fada cikin soyayya yana da matarsa daya da yaransa biyu,lokacin da yake gaya min hakan tuburewa nayi kan cewa bazani zauna da kowa ba saidai ya saketa,ga zatona son da adeel yake min zai yarda ya saki matarsa,saidai adeel irin mazan nan ne da suka san darajar matarsu ta gida,ya gayan ba zaya iya sakin matarsa ba,saboda babu abinda ta rageshi da shi,hakanan yana sonta kamar yadda yake sona,ganin haka ya sanya nace saidai mu rabu,yace tunda haka na zaba Allah ya hada kowa da rabonsa,na zaci zan iya rabuwa sa deel sai gashi cikin qanqanin lokaci zuciyata ta gaza daukar hakan,tilas na lalubo adeel,ya bayyanan har yanzu yana kan bakansa idan zan iya zama da matarsa da yaransa to,na amince da hakan saboda shawarar da qawata ta bani kan idan na shiga zan iya amfani da son da adeel kemin na gallaza mata yadda naga dama har ta gaji ta fita ta barmin gidan" "Haka kuwa akayi,bayan shigata na dinga gasata,ita da gidanta amma bata da sukuni,wahala babu irin wadda ban gasa mata ba ita da yaranta a bayan idanun adeel,amma a gaban idonsa sai ka rantse da Allah duk duniya babu wadda ta kaini sonsu,hakan yasa adeel ya saki jiki da ni ya bani amanna,ke in taqaice miki daga qarshe sai da nayi sanadiyyar kamuwar daya daga cikin yaranta da cutar limoniya wanda sai a lokacin adeel ya gane me nake aikatawa cikin gidan,babu bata lokaci ya sallameni,bayan komawata gida na kasa haqura da adeel,nayita bibiya kan ya dawo da ni,yace sam baisan wannan zance ba,qarshe rahama matar tasa abun mamaki ita ta saka baki,abun ya dauren kai matuqa ya sanyayan jiki,don ban taba tsammanin cewa zata ma shiga maganar ba,ke a qarshe da ita na dinga kamun qafa,yace zai dawo da ni amma sai da amincewar rahaman,wallahi rumana na fidda tsammani amma ga mamakina sai tace ta yarda na dawo din,saboda ta yarda har ga Allah nayi nadama bisa ga yadda taga sauyawata,wallahi a lokacin babu wadda ta fado min a rai sai ke da raihana,bayan komawata rumana baki ga yadda zamanmu yake dadi ba,har mancewa nake rahama kishiya ta ce,wannann yaron dake hannu na yanzu yaronta ne wanda ya samu limoniya ta sanadiyyata,na yanke hukuncin karbarsa na kula da shi,rahama kuma ta barminshi halak malak,Allah ya jarabceni da jinkirin rashin samun haihuwa,sai cikin watan da ya wuce Allah ya dubi zuciyata ya bani nawa rabon". Ajiyar zuciya rumana ta saka kausar ta fado mata a rai wadda itama yanzu ke aure gidan mai mata biyu ita ce cikon ta uku, sannan ta dubi meela "Kin gani kuma kinji duk abinda nake gaya miki,baka isa ka hana Allah ikonsa ba meela,duk sanda kace sai kasa qarfin qwanjin hana Allah aiwatar da abindabyayi nufi tabbas sai ka fada wahala mai girma,ki godewa Allah da ya soki ya nuna miki hanya ya daidaita rayuwarki tun da wuri,matuqar kace zaka dinga sanya soyuwar zuciyarka gaba da tsarin ubangiji kana cikin wani hali,na tayaki murna meela ina fatan zaki dore" "Haba rumana,aiko wani naji zai yi irin tawa kasassabar na farkar da shi...." Maganarta ta yanke sakamakon isowar raihana gurin tana dube dube da alama rumanan take nema,bata gane meela ba don haka tana murmushi tace "Hali zanan dutse,sisi na mai qawaye,yau ke da daddy ne,duk kin wahalar masa da yara sun zagaye shoprite kaf basu ga mommy ba,affan ne yace ya ganki anan" dariya ta saka saboda tuna mata can zamanin 'yammatancinsu da raihana tayi "To sai ku maida wuqarku,yau meela Allah ya hadani da ita" sai a sannan raihana ta dubi sashen da take,fara'ar fuskarta tadan ragu,don har ga Allah bata aon duk wani mutum da zai zama sikar ruahewar kyakkyawar alaqa fahimta da DANGANTAKAR dake zagayawa tsakanin ahalin nasu ya rabesu,tana tsoro kada meela ta sake dawowa rayuwarsu karo na biyu ta samu nasarar rarraba kawunansu,ga iyali a yanzun sun tara,yaran da suka samu kyakkyawan horo da basa rabewa tsakanin rumana ko raihana,kowacce uwarsu ce. Ita kanta meela ta karanci raihana,sai ta saki murmushi ta miqawa raihanan hannu,jiki a sanyaye ta bata nata itana sukayi musabaha,meelan ta dora da cewa "Ki saki jiki raihana,yanzu ni din ba meelan da kika sani bace a baya wadda batasan rayuwa ba,batasan ya rayuwa take ba,zallar quruciya kecin gangar jikinta" sai ta dubi rumana tana neman qarin bayani,kada kai rumana tayi alamar baya tabbacin haka ne,ta yadda da sisinta dari bisa dari hakan ya sanya ta sakarwa meelan murmushi sannan suka gaisa kafin daga bisani sukayi sallama bayan sunyi musayar lambar wayar juna. Kafin su qarasa inda motarsu ke fake tana jiransu rumana ke bawa raihana labarin meela,kai kawai take kadawa tana sake godema Allah da ya kubutar dasu daga soye soyen zuciyoyinsu *************** Kamar yadda suka tsara gidansu,wadda bata da girki ita zata kula da yaran baki daya da safe har su wuce makaranta,mai girki kuma kiji da mai gida breakfast dinshi da sauransu,ba ruwanki da hayaniyar yara ki dawainiyarsu naki kawai kula da mai gidan. Girkin rumana ne zuwa dare ita zata amshi girkin don haka raihana ke dawainiya da yaran da taimakon babbar yayarsu islaha,yara takwas ke garesu,rumana nada uku saboda yawan barin da take samu,islaha sai abdul_majid da suke cewa majid sai ummu salma,raihana nada biyar,abida ce babba,sai sagir,sai mai sunan daddy dalhatu suna ce masa affan,sai abubakar mai sunan babanta suna kiransa musaddiq sai takwara kuma qaramar cikinsu ummu rumana,suna ce mata mimi. Dukkansu kowa yayi neat cikin unifoarm dinsa,yara ne da ki yaushe baka isa kaga datti jikin unifoarm dinsu ko ka ganshi babu guga ba,hakan ne ya sanya kowannansu shike daukar kyautar wanda yafi kowa tsafta cikin ajinsu,yaran rayyan sunyi fice cikin makarantar saboda baya ga tsafta akwai baiwar qwaqwalwa da Allah ya bawa kowannensu. Kowa breakfast dinshi yake ci,suna kan dining kowa yasan gun zamansa dama,raihana na tsaye kansu tana kula da kowannensu,haka take musu shi yasa sau tari tare suke cin abinci,saboda ta haka ne take iya gane wanda ke da matsala taci gyaransa,kamar rashin yin bismillah farkon fara cin abinci,ci da hannun hagu,qatuwar loma ko zubar da abinci,rumana(mimi) ce kawai ke rakube kan tata kujerar sabida yanzun raihana ta gama maketa,haka Allah ya yita da tsokanar tsiya,ita bata fara zuwa makaranta ba amma da 'yan makaranta sun tashi itama ta gama nata barcin,tsokani wancan tsokani wannan har sai sun fice sun bar mata gidan. Sallamar daddynsu rayyan ce tasa suka cika da murna,indai suka ga ya sake fitowa a irin wannan lokacin to ranar shi zaya kaisu makaranta da kanshi kenan,duk da yake akwai driver amma wani lokaci shike kaisu don ua binciki yadda karatun kowannensu ke tafiya cikin ajinsa,yaji idan akwai mai wata matsala yayi gaggawar kawo gyara,da daya da ya suka gaidashi mazan na bashi hannu suna musabaha duk da cewa duk asubar duniya shi zai tada su su wuce masallaci tare da mazan,matan kuma suyi tasu cikin gidan,idan ya dawo su gaisa sannan ya sake komawa ya kwanta agun wadda keda girki idan ba fitar wuri zaya yi ba. Har suka gama gaisuwansu da karadinsu mimi rumana na gefe tana kallonsu,murmushi ya saka ya isa gareta don yasan da alama yau ma an tafka tsiyar da ita "My little angel waye ya tabamun ke" kafin tace wani abu affan yayi karab yace "Maamaa ce(haka suke kiran raihana),an zuba mata nata abincin taqi ci ta dinga sawa anty islaha hannu a cikin nata tana jagwalgwala mata,maamaa ta mata magana taqi ji sai ta duketa" "Ayyah my lil angel,yau kam ni da maamaa ne,amma me yasa idan aka ce ki bari bakiji?,ban hana irin hakan ba?" Ya fada yana zama seriouse "Ai nikam daga wannan term din idan yara suka gama exam aka shiga sabon aji mimi ta gama zaman gida,makaranta zata fara zuwa,qiriniyarta ya isheni haka nan,sai shegen baki da surutun tsiya"ta fada tana fitowa daga kitchen dauke da lunch boxs din affan da ya manta. A hankali ya daga kai ya dubeta,duk da cewa cikin kayan barci take maroon colour don sai ta sallamesu take iya wanka sai yaga ba qaramin kyau tayi masa ba har baisan sanda ya kashe mata ido daya ba yana jifanta da wani kallo,da ido ta masa alamun akwai yara fa agun,tuni islaha taga 'yar maganar da ake da ido,dariya ta dan saki saboda yadda zamantakewar gidan nasu ke birgeta,hakan yasa ta miqe ta fara tattara kan qannan nata zuwa wajen mota bayan ta dawo ta gyara inda sukayi breakfast din sannan ya sunkuci mimi tana fadin " muje lil sis dinmu ki rakamu kinji,daina kuka haka"tuni ta ware dama akwai son yawo. Yarinyar na qarasa ficewa yayi hanzarin jawota jikinsa,ya rungumeta tsam yana sinsinar wuyanta da jikinta baki daya wanda ke fidda qamshin turaren barcinta "Wannan kyau haka maamaan yara,meyw sirrin ne?" Murmushi ta saka "Wani kyau a kayan bacci,ki wanka banyi ba fa hidimar yaranka ta hanani sakat" hannunshi ya dora saman cikinta yana shafawa sannan yace "Um_um,kodai na sake ajiya ne anan" dariya ta saki tana qwacewa daga jikinsa "Rufamin asiri don Allah" murmushin ya saki shima ya harde hannunsa yana kafeta da ido "Meye abun rufin asiri a ciki,i need more,ina so naga gidan nan ya cika da yara fa kinsan ni daya ne gun ummu ko kin manta" "Yara takwas sun isheka my man don Allah" kai ya kada "Allah ya sani ina son qari da gaske kuma nake,ki shirya yau da wuya idan ban baki ajiyata ba kamar yadda nake zaton na bawa sisinki,tana can tana zazzabi" Idanu ta zaro tana dubansa "Ayyah my man kuma ka barta kwance ita kadai?" "Bacci takeyi" sai ta saki ajiyar zuciya tana mata addu'ar Allah ya tsaida mata wannan,hannunta ya sake kamowa ya kashe mata ido daya "Na gaya miki yau ki shirya sosai,ki shirya karbar ajiyata kema,dama naci alwashin kaiku labour room tare keda sisin taki"ya qarasa maganar yana dariya qasa qasa tare da kama siririn hancinta ya dan jashi kadan,qasa tayi da kanta tana murmushi bayan ta dunqule hannunta ta dan daki qirjinsa cikin wasa,hannunsa ya sa ya dafe gun a shagwabe yace "wayyo" da sauri ta dago tana dubansa bayan ta ware idonta a kansa alamun lafiya? "So kike ki fasa min zuciyar,bayan ta cika taf da qaunar raiha ita da sisinta,riritata kawai nake don kada ta fashe" sosai maganar tasa ta bata dariya,jin taku ya sanyata janye jikinta da sauri,majid ne ya shigo ya nuna agogon hannunshi yana cewa"daddy zamuyi latti fa yau" "Ok muje abdul majid" yaron ya juya ya fice rayyan din yabi bayansa yana cewa ta tanada masa abun kari kafin ya dawo,bata iya zama ba sai da taje duba sisinta,saidai ta taras da ita tana bacci,don haka ta dawo tayi aikace aikacenta don basu yarda sun dauki mai aiki ba,ta hadawa rumana source din hanta zalla saboda taji dadin bakinta,sannan tayi wanka ta tsara kwalliya kamar yadda suka saba . Ta kowanne bangare ci gaba da qaruwar arziqi ne ke riskarsa,sirrin hakan baya ga addu'ar iyaye ga dimbin jama'a da yake taimakawa iyalinsa sune na biyu,kyakkyawar DANGANTAKAR ZUCI da ta fili,fahimtar juna,goyon baya kwanciyar hankali da nutsuwa da yake samu daga garesu ko da yaushe suma wani sirri ne na qaruwar arziqinsa. Weekend ne yau,rayyan kan wuni a gida ya sake shida matan nasa,kasancewar yaran kan je weekend lokaci bayan lokaci mabanbantan gurare,misali ga islaha tafi ganewa ta tafi wajen hajiya babba tsohuwa mai ran qarfe can qoqi ita da sagir sune mutanenta,rumana mimi kuwa sarkin rigima mama ce (maman rumana)ke iya mata,don ummu tarkato musu abarsu take ba'a qulla abun arziqi da ita,ummu salma dama ita kyanwar lami ce ba cizo ba yakushi tana gun ummu ita da affan,abdul majid kuwa shi bai da zabi duk inda ta raya masa tafiyarshi yake,gidan sai ya zama isu isu suma su samu su wataya yadda suke so,amma mafi yawanci sunfi yin hakan a weekend din qarshen ko wanne wata,wanda daga nan ran lahadi da yamma zai dibi matan nasa subi kowanne gida su dauko yaran nasu,daga nan kuma su wuce asibiti ko gidan marayu ko gidan nakasassu suyi ziyara,manufar hakan don dasa tausayi da jin qai a zuciyar yaran nasu tun suna qanana,su dinga ganin irin baiwar da su da suke garau Allah ya basu don su kasance ko da yaushe masu godiya a gareshi. Yauma hakan ce ta kasance,hudu da minti goma suka fito tsaf,rumana da raihana na sanye sa baqar doguwar riga mai azabar kyau da tsada,sau tari shigarsu takan zama iri daya ne musamman idan zasu fita,kowaccensu tayi kyau ta sake cika da kwarjini da kamala ta cikakkiyar mace wadda hankali da nutsuwa ya lullube,tare suka jero har cikin motar raihana na tsokanar rumana wadda ta fara nauyi yanzun,rayyan na zaune cikin motar yana kallosu ta madubi,ranshi fes yana godiya ga madaukakin sarki da kullum yake sake hade masa kan matan nasa. Kai tsaye gadon qaya suka fara sauka gidansu rumana suka dauki mimi,sannan suka sauka a qoqi suka dauki sagir da ummusalma wadanda hajiya babba ta cika da su goruba,taura,kurna,magarya da sauran kayan da yaran basu samu,daga can kuma suka tafi gidan ummu wanda ke cikin nasarawa wanda rayyan din bai jima da gina musu shi ba,a can ne suka dan jima kadan saboda sun tarar da abba yana gida,sun sha hira abinsu kam farinciki na cika zuciyar abban na ganin yadda rayuwar yaran nasa gaba daya tayi kyau take tafiya yadda ya kamata,sun sha albarka da addu'o'i,anan ya sanar masa tafiyarau nijer daya tsara dukansu a qarshen sabon wata don zuwa duba dangi,hakan ya yiwa abba dadi sosai yace"kaga ma yayi daidai da nadin da za'a yiwa babanka nasiru shima qarshen sabon watan ne,sannan ya sake dibansu,mota ta cika kenan gida ya dawo full,tuni suka cika motar da karadi da hayaniyarsu kowa na tashi sabgar,rumana ce kusan uwar gayyar ita ke iya ji da kowa,yayin da raihana ke saka musu ido saboda ta fuskanci yaran irin uwarsu rumanan ne 'yan hayaniya ne kada ma takwararta ita da abida suji labari,har gwara islaha da majid. Ganin cewa sunfi kusa da asibitin nasarawa yasa rayyan din ya yanke shawarar su nufi can kawai suyi ziyara wa marasa lafiya. Sau uku tana sake kallon gadon zuciyarta na gaya mata bashi bane,ganin isowar fatima gun dauke da baby a kafadarta wadda da alama diyarta ce ita ta sanya zuciyarta wasi wasi,jin an dafa kadarta ya sanyata waiwayowa,fuskarta fadade da fara'a fatiman ke gaida raihana,sai tarasa inda zata sanyata sabida dadi,don har yau suna qaunar raihanan "Waye baida lafiya?" Raihana ta tambayi fatiman tana amsar babyn dake hannunta,sai ta juya ta kalli mutumin dake yashe saman gado kamar ba halittar bil'adama ba,hawaye ya silmiyo mata tasa hannu ta share "Kema baki gane ya ammar ba ko anty raihana" duk da ta zaci hakan amma ba qaramin girgizata maganar tayi ba,jikinta yayi matuqar yin sanyi,kafin ta tambaya fatiman tace "Dabi'ar nan tasa da bai bari ba anty,bayan rabuwarku bai sake dawo mana ba sai da ya fara cuta,kin ganshi har yanzu an rasa gane wace iriyar cuta ke damunsa,iyakacin gwaje gwaje anyi amma a banza kullum abun qara gaba yake,kashi da fitsari duk fita yake tako ina babu banbancin guri,ga wasu tsutsotsi da suke fita masa babu kyan gani jazur da su,duk sanda suka soma fita haka zaita qaraji saboda azabar cizon da suke masa,wani lokaci cikinsa idan ya kumbura kamar an saka masa wani abu,kin ganshi anty raihana sai ido babu um babu um um" ta qarasa maganar hawaye naci gaba da fita,tausayi sosai ya kama zuciyarta,babu shakka ta tausaya masa,suka hada ido idanunsa qur ita yake kallo hawaye na fita daga idanunsa,da alama magana yake son yi mata amma babu baki,zuciyarta ta karye hawaye ya fara fita a idanunta,duk da bata tsinci komai a zamanta da ammar ba amma bai taba cuaguna mata ko cutar da ita ba "Inna hajjaju" kai fatima ta girgiza "Hajjaju na nan har yau taqi koda zuwa ta ganshi,ko maganarsa bata so ayi mata,kamar yadda taqi yarda a gayawa kowa bai da lafiya,daga ni sai sa'ida sai anty sa'adah muke dawainiya da ciwonsa" cikin zuciyarta take jin tabbas yana buqatar taimako,taimakon kuwa shine na yadda za'a ja hankalin hajja tazo gareshi,ta yafe masa ta kuma yi masa addu'a ko zai samu sassaucin halin da yake ciki,a haka rumana ta iskesu,suka gaisa da fatiman ta tambayeta mai jiki suka wuce ba tare data fuskanci waye kwance saman gadon ba. Cikin mota ta kasa tsaida hawayenta,mutum ce mai tausayi tun asali,tana tsoratarwa ammar haduwarsa da Allah da irin wannan tarin manya manyan zunuban,sam sai hankalin rayyan yaqi kwanciya saboda mutum ne shi da baison damuwar iyalinsa,hakanne yasa ya ajjiyesu cikin wani dan lambun shaqatawa dake nasarawar sannan suka kebe don yaji meye damuwarta,bata boye masa komai ba aranar ta fayyace masa zaman aurenta da ammar da dukkan wasu abubuwa da suka biyo baya,ta kuma dora da roqarsa alfarmar tana so a yau don Allah basai gobe ba taje ta samu hajjaju saboda ragewa ammar nauyin dake kansa,koba komai dan uwansu ne musulmi wani babban taimako me zasuyi,ya lumshe idonsa,tausayinta na ratsashi na irin zaman da tayi shekara wajen hudu,ashe ba'a banza ba rumana ta jajirce kan ganin sunyi aure?,tabbas ba qaramar qauna ce a tsakaninsu ba,baice komai ba face "Allah ya kiyaye hanya,ki rage wannan kukan kuma bani son ganin zubar hawayenki"ya fidda maqullan motar ya miqa mata ya kira rumana wadda ta iso cike da damuwa ga zatonta wani abu ya samu sisin nata ya gaya mata inda zasuje,suka wuce shi kuma ya zauna da yaran suna dakon dawowarsu. Sosai hajjaju ta dinga murna da ganin raihanan,aun aha wuya kafin au sauketa daga dokin naqin data hau,amma cikin qwalla da takaicin rayuwar da yaron nata ya fada tace ta yafe masa kuma zata ci gaba da addu'ar Allah ya bashi lafiya,tamkar kada raihana ta tafi haka suka rabu. Koda suka koma ya sake dibansu bai zarce ko ina da su ba sai PIZZA AND GURASA,ya juyo yana dubansu bayan yayi parking fuskarsa qunshe da murmushi " nasan dai an gaji ga yunwa,so babu batun dora girki idan an koma gida,muje kowa ya zabi abincin da yake so yaci"tuni yaran suka cika motar da hayaniyan murna kafin su balle qofar motar su firfito,tuni ma su riga iyayen nasu yin gaba. Tsakiyan matan nashi ya shiga ya kama hannun kowaccensu suka dinga takawa a hankali,har yau ya fuskanci damuwar dayansu itace ta dayan,tunda raihana tayi kuka dazu jikinta yayi sanyi haka ma jikin rumana yake,to shi dinma sai yaji duka yanayin bai masa saboda rashin cikakkiyar walwalarsu,a hankali cikin sassanyar sautinsa yace da su "Gaskiya a sauya yanayi,wannan yanayin naku sam baimin ba" rumana ta daga kai ta dubeshi "Kamar yaya daddy" tamkar wani qaramin yaro ya narke murya "To don kawai mai glass tayi kuka ke kuma 'yar tsalle sai ki tayata ku zama duka baku da kuzari?(ya kirasu da sunayensu tun na quruciya),yaya kukeson ya rayyan dinku yayi?,bayan komai tare kukeyi,AMINAN JUNA MUKE FA" dariya suka qyalqyale da ita sosai har taja hankalin wadanda ke zaune gun suna cin abinci saboda yanayin da yayi maganar tasa tilas ta baka dariya "Ayi mana afuwa yaya rayyan mun tuba" inji raihana,yadan karasu a kafadarsa yayi qasa da murya cikin rada yace "Ina sonku,ina alfahari da ku" kowaccensu maganar tayi mata dadi,yaci gaba da riqe hannayensu har zuwa gun zama. Ganin ana dab da kiran sallar magariba gashi ba hanyar gida ya sake nufa da su ba ya sanya raihana kallonsa "Nikam yau ya rayyan sai mu zagaye garin kano ne?,ko ka manta sisi na ba ita daya bace?" "Barshi,ai yau idan na sashi tausa bazan tausaya masa ba har sai gari ya waye" rumanan ta rada musu,dariya raihana ta saka "Kinmin daidai" baice musu komai ba baya ga murmushi da yayi. Ana qwala kiran sallah suka qarasa qofar gidan,gidane mai azabar kyau da tsari wanda ke dauke da sassa biyu,duk sashe daya ya isa gida na alfarma ga mutum mai iyali kuma a wadace,bangare daya ya bude suka shige baki daya yaran nata surutun kyawun gidan,suna shiga bai barsu sun zauna ba ya nuna musu toilet yace duk suje suyi alwala,qatuwaf dardumar dake motar tasu wadda da ita dama suke yawo saboda fita irin wannan ya dauko ya shimfida musu cikin qawataccen falon ya jasi jam'in salla,addu'a sukayi sosai bayan sun idar ya dubi islaha "Anty babba maza kuje ke da qannenki kuga cikin gidan sosai,sagir ka tayata kula da su banda barna banda fitina" cikin zumudi suka miqe kana suka fice gaba dayansu. Sai da yaga fitarsu sannan ya dawo da dubansa wajensu raihana,ya sakar musu murmushi kana ya miqa hannayensa duka biyun yana cewa "Ku matso kusa dani 'yan aljanna" kowacce cike da qauna da alfahari da mijin nata ta matso kusa da shi sosai,ya zira hannunshi cikin aljihu ya fiddo maqulli ya miqawa kowacce,ido suka sa masa suna buqatar qarin bayani "Maqullin wannan gidan da muke ciki ne,naku ne halak malak" rasa bakin magana sukayi,sai kuma suka rude da godiya cike da farinciki da yabawa mai tarin yawa,ya ya dora kan lebansa alamar suyi shiru,ya miqa hannunsa ya riqe hannun kowaccensu,cikin shauqi yace da su "Wallahi kunfi qarfin hakan,kungi qarfin komai a gurina,haqiqa ku aljannar duniyata ne,kun yimin komai a rayuwata,kun aureni kun zauna da ni,kun haifa min yara wadanda mallakina ne ni rayyan jina ne,uwa uba kun hada kanku kun bani kwanciyar hankali da nutsuwar da nakejin labari maza masu tarin yawa wadanda ke da mata biyu sun rasata,kun hana wani ko wata ya sauya DANGANTAKAR ZUCIYARKU,me zance muku umm?,meye bazan iya yi muku ko baku shi ba,matsayinku a azuciyata ya zarta duka inda kuke tunani,a taqaice kune rayuwata" sai jikinsu duka yayi sanyi,kowacce qaunar mijin nata na zagaya jikinta,raihana ta dora kanta saman kafadarsa yayin da rumana taci gaba da murza hannunsa dake cikin tafin hannunta ta kasa furta komai itama tamkar 'yar uwarta. Rumana ce ta fara sakin ajiyar zuciya sannan tace "Insha Allahu banu abinda ya isa ya sauya DANGANTAKAR ZUCIYARMU har ABADAN" raihana ta dago a hankali fuskantar qunshe da murmushi "Zamu ci gaba da SADAUKAR maka da farincikinmu,SOYAYYAR MU QAUNARMU DA ABOTARMU har lahira bi'iznillah" farinciki ya sake mamayeshi,sai ya hadasu baki daya ya rungumesu cikin ingarman qirjinsa cikin wani salo da siga ta jan hankali ya furta "Ta tabbata mu AMINAN JUNA NE na har ABADA,rayyan raiha mai glass da rumana 'yar tsalle" dariya suka saka baki dayansu zuciyarsu cike fal da farinciki da qarin godiya ga Allah bisa ga adalin miji da Allah ya basu. *ALHAMDULILLAHI RABBIL AALAMIN* _INA MIQA SAQON GAISUWA DA FATAN ALKHAIRI GA MASU BIBIYAR RUBUTU NA_ _INA MAI NEMAN ALFARMA GA DUK WANDA YA TABA KARANTA RUBUTUNA KODA LAYI GUDA NE DA YAMIN ADDU'A,KODA IYA YANZU NE DA KAKE KARANTA WANNAN SAQO ZANJI DADI KUMA ZANYI ALFAHARI DA HAKAN_ _SANNAN INA YABAWA DUKKAN JAMA'AR DAKE QAUNATA,WADANDA NA SANI DAMA WADANDA BAN SANI BA,KUNYI YAWA HANNUN HUGUMA BAZAI IYA LISSAFO DUKKA SUNAYENKU BA,AMMA KU SANI INA JI DA KU INA SONKU KAMAR YADDA KUKE SONA,INA ROQAR MANA UBANGIJI YASA SOYAYYAR DA MUKEWA JUNA TA AMFANEMU_ _FATAN ALKHAIRI GA DUK WATA MACE DA AKE SHIRIN KAWOWA ABOKIYAR ZAMA,INA MATA KYAKKYAWAN FATAN SAMUN KYAKKYAWAR ZAMANTAKEWA FIYE DA YADDA YAKE FARUWA GA WANNAN IYALI NA RAYYAN,DUK DA CEWA LABARINA QIRQIRARREN LABARI NE AMMA INA MAI FATAN ZAI RAGE KASO MAFI YAWA DAGA ZAZZAFAN KISHIN DAKE DAMUN DA YAWA DAGA CIKIN 'YAN UWA NA MATA,SU DAUKI AURE IBADA,DUNIYA KUMA GIDAN JARRABAWA CE,LAHIRA ITA CE GIDAN SAKAMAKO_ _BAZAN WUCE BA SAI NA MIQA GODIYA TA DA JINJINATA GA DUKKAN MARUBUTAN DAKE CIKIN GIDAN HUGUMA,ALLAH YA QARA DAUKAKA_ _FATAN ALKHAIRI GA HASKE WRITERS,UBANGIJI YA QARA HADA KANMU YA QARA MANA QAUNAR JUNA_ *ANAN NE NAKE SALLAMA DA KU MAKARANTA NAKE CEWA ALLAH YA QADDARA SADUWARMU,WANDA NA BATAWA INA NEMAN YAFIYA DA AFUWA DAGA GARESHI*🤝🏽 *MRS MUHAMMAD CE*👑 📚📚📚📚✍🏽✍🏽✍🏽✍🏽