YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA BY HARUNA USMAN Jun 28, 2022 0 19 Add to Reading List YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 1 BY HARUNA USMAN SABON LITTAFI DAGA WWW.GISTROG.COM.NG HAJI Hamidu dan Usman mutum ne da Allah Ya yi wa baiwar ilmi da aiki da shi, ga hankali da hakuri da riKon amana da kuma rashin girman kai. Daidai gwargwado kuma yana cikin rufin asiri. Babbar dacewa ita ce irin yadda Allah Ya albarkace shi da mace ta Kwarai, wadda samun irin ta sai an tona ta bangaren sanin ya kamata da hakuri da kyau da cikar halitta. Sunanta Ramlah. Www.bankinhausanovels.com.ng Ma’‘auratan suna da ‘ya’ya maza da mata, amma manyan da suka isa misali su uku ne. Babban sunansa Idrisu, mai bi masa kuma Abubakar wanda suke kira Habu, sannan sai Yahaya. Dukkan su sun sami ilmi daidai gwargwado. | Wani abin sha’awa shi ne irin yadda wadannan samari ba su bar komai na kyawawan halaye da siffofin iyayensu ba, hakan ya sa halayyarsu ta zama abar misali kuma kyan halittarsu ya zama abin tsegumi a gari. } Fara jin dadi da kuma taka wani mataki na ilmi ne suka sa wadannan matasa a rayuwa ba abin da suka fi bukata da kauna fiye da tsunduma cikin duniya don Karo sani. A karshe dai suka yanke shawarar tafiya din. Kuma saboda sanin muhimmancin ilmi da kuma daidai gwargwado aminta ko yarda da tarbiyyar ‘ya’yansu suka sa ko kadan iyayensu ba su ki yarda da wannan buKata ta tafiya ba, har maa karshe mahaifinsu ya kara da yi musu gargadin cewa, “Ya ku ‘ya’yana, babban abin da nake so in tunatar da ku kuma in gargade ku a kai shi ne, duk inda kuka tsinci kanku, to ku rike amana, kuma ku rika tuna sanadin fitarku daga gida, wato ~ilmi; jagoran _ rayuwa.” Www.bankinhausanovels.com.ng Yara suka ce in Allah Ya yarda ba za su taba mantawa ba. A daya bangaren kuma akwai Bashari, shi ma wani yaro ne mai hankali, makwabci kuma abokin wadannan yara. Duk shirye-shiryen da ake yi na tafiya da shi ake yi, don irin shakuwar da ke tsakanin su. Shi ma ya nemi yardar nasa iyayen kuma sun amince. ” Su hudu ke nan. Bayan addu’o’in fatan alheri da sa albarka irin wadanda iyaye kan yi wa ‘ya’yansu, wadannan matasa suka yi sallama da jama‘arsu suka bi hanya. Kwana arba’in ba biyu suna tafiya, sai suka isa wata mararraba wadda hanyoyin da ke jikinta suka rabu hudu, Gabas da Yamma, Kudu da Arewa. A nan suka tsaya don shawartawa. Habu ya ce, “Ina ganin ya kamata daga nan sai mu rabu, kowa ya bi tasa hanyar, don in mun tuna daga cikin maganar mahaifinmu ta kwanakin baya, ya ce za mu fi kwazo in har ba ma ganin juna.” Ba tare da gardama ba suka yi sallama, suka rabu kowanne zuciyarsa cikin halin raurawa. Babbansu Idrisu ya fuskanci Gabas, shi kuma Habu ya doshi Arewa, Bashari ya tsinkayi Kudu, Yahaya kuwa Yamma ya nufa, kowa ya mika. IDRISU ya ci gaba da tafiya kwana da kwanaki ba tare da sanin inda ya ke nufa ba, ba dare ba rana, shi dai nutsawa ya ke yi. Bugun ruwan sama kuwa har ya zame masa jiki. Amma maimakon ya fara ganin alamar gari ko Kauye, kullum sai kungurmin daji ya ke sake kutsawa. Ya wuce wannan Korama, ya ratsa ta wancan tafki, ya sakala ta tsakanin wadancan duwatsu, namun daji iriirl ya yi ta haduwa da su, wadanda ya sani ko kuma ya taba jin labari da wadanda ko tunanin irinsu ma bai taba yi ba, manya da Kanana. Ba ya jin kukan komai sai zakoki da damisoshi da giwaye da sauransu, Allah dai Ya yi ta kiyaye shi. Wasu koke-koken ma sam bai san ko dabbobi ko mene ne ke yin su ba, shi dai ya ci gaba da tafiya bai san inda ya ke nufa ba. Bayan guzurin da ya riko ya Kare sai ‘ya’yan itatuwa suka koma su kadai ne abincinsa, har dai ya zo cikin wani kungurmin daji da babu alamar ko dan Adam ya taba wucewa ta wurin ma. Kwatsam a cikin dokar daji sai ya rika jiyo haniniya, ya nufi inda sautin ke fitowa yana lellekawa har dai abin da ya ke zato ya tabbata daidai, wato doki ne. Shi dai Idrisu bai taba ganin doki mai kyau irinsa ba. Yanzu kam a cikin zuciyarsa ya tabbata cewa zai sami taimako ko kuma labari, kasancewar akwai alamar ya iso inda mutane suke. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya duba ko ina ko zai ga mai dokin amma abin mamaki babu alama ko daya. Ya Kara matsawa kusa, sai ya tarar ashe saiwar wata irin itaciya mai yado da sarkakiya a kasa ce ta rike wa dokin Rafa, amma ya kasa cirewa da kansa. Ganin Idrisu kusa da shi sai ya yi ta harbe-harbe, shi kuma yana ta lallabar sa yana matsawa kusa a hankali. Ya je ya samo masa ciyawa mai kyau ya mika masa don nuna cewa ba shi da mugun nufi gare shi. A haka dai har ya kai ga shafa shi. Idrisu ya zaro wuka daga kuibinsa ya yayyanke saiwar, ya janyo Kafar a hankali, wadda ya tarar ta dan yi rauni, kuma ba tare da bata lokaci ba ya yagi rigar jikinsa ya daure masa. Doki dai ya fahimci taimakon ,,. sa ake yi, saboda haka sai ya saki jiki. Idrisu ya hada wata ‘yar bukka a wannan wuri ya yi kwanaki yana jinyar doki har Allah Ya sa ya warke garau. Shi ke nan ya sami abin hawa. Kuma yanzu ba ya samun wata wahala wajen hawa da sarrafa shi, kuma duk abin da ya umurce shi, to babu gardama ya ke aikatawa. Shi wannan doki da wahala duk yadda mutum ya taba ganin doki a ce ya ga mai kyansa, Kosasshe ne, fari, mai kwarjini. Dole ne idan ka yi sa’ar ganin sa ka dimauta da son sa. Ba da dadewa ba Idrisu ya fara tunanin irin sunan da ya kamata ya rada wa wannan ingarman doki nasa. Can yana cikin tunani sai kwatsam ya tuna da wata kalma da mahaifinsu ya yi amfani da ita a lokacin da za su bar gida, wato nunin da ya yi musu cewa ilmi shi ne jagoran rayuwa, saboda haka sai ya shafa jikin doki ya ce masa, “Sunanka Jagora.” Nan take dokin ya yi wata irin haniniya ta jin dadi kamar ya fahimci abin da ake nufi. | Bayan dukkan su sun sami isasshen hutu sai Idrisu ya cewa Jagora, “Ya kamata mu bar wannan wuri mu nufi inda Allah Ya kai mu.” Yau da kullum ta sa ya dauki wata dabi’a ta yin magana da wannan doki nasa kamar yana yi da mutum dan’uwansa. Haka nan babu sirdi ya hau Jagora ya sake tsunduma cikin daji, ya sa masa idanu sai inda ya kai shi, kuma duk inda ya nufa ba ya kwabon sa. Bai ankara ba sai ga su a bakin wani lambu cikin dokar daji, wanda tun da ya ke a duniya, bai taba mafarki ko jin labarin mai ban sha’awar sa ba, ga furanni masu Kanshi da launuka iri-iri, Korama tana kaiwa tana kawowa gwanin ban sha’awa, ga ‘ya’yan itatuwa nan iri-iri sai tsuntsaye suke ta wakoki da mabambantan sautuka masu natsar da zuciya. Kai a takaice dai irin wannan lambu da zarar ka gan shi, to tunanin da zai fara biyo baya shi ne, “Allah ba mu Aljanna.” Www.bankinhausanovels.com.ng Sai dai kuma lambun yana da wani abin mamaki. Shi kansa kungurmin dajin dai ba shi da alamar rairayi ko kadan a cikin sa, duk itatuwa ne da sarkakiya da sunkuru da duwatsu da Koramu, amma sai ga shi lambun ya fita daban. Ga yashi nan fari fat har da wasu ‘yan dunkulallun duwatsu na Karau masu ba da haske kamar fitilu a cikin sa. Daga gani ka san ba aikin mutum ba ne sai dai aljan. A can daga gefen lambun kuma wasu dakuna ne ake iya hangowa, guda biyu masu kyau; babba da karami, su ma suna da launuka iri-iri gwanin ban sha’awa. A tsakanin su da lambun akwai wata Korama wadda ruwa ke gudana gwanin ban sha’awa. A cikin ruwan ga kifaye nan masu kyau iri-iri da mabambantan launuka Karara ana kallon su. Da Idrisu ya tsallake Koramar sai ya saki Jagora karKashin inuwar itace, shi kuma ya nufi inda katon dakin nan yake. Ya yi sallama, “Assalamu alaikum.” Abin mamaki sai ya ji an amsa, “Wa’alaikumus salamu, shigo.” Shigarsa sai ya ga ashe wannan daki Kato ne kamar wani dan karamin gida. Wani dattijo ne a ciki mai yawan shekaru, ga dogon gemu da saje da gashi fari fat mai kyau. Da ganin sa ka san yana da wata daraja da Allah Ya yi masa saboda tsananin kwarjinin fuskarsa. Yana zaune a kan wani farin buzun rago zagaye da litattafan karatu iri-iri, masu tarin yawa. Idrisu ya Karasa kusa da shi ya gai da shi cikin girmamawa da tausasa murya. Dattijo ya kalle shi wanda kuma a cikin kallon ya nazarci cewa yaro ne saurayi kyakkyawa mai alamar natsuwa. Ya ba shi damar zama, sannan ya ce, “Ya kai wannan saurayi mene ne sunanka? Daga ina ka fito? Me kake nema? Kuma inazaka?” Cikin natsuwa ya mayar da amsa, “Sunana Idrisu dan Hamidu, na fito daga garinmu Dutsen-ruga ne don neman ilmi, tafiya kawai nake ba tare da sanin inda nake fuskanta ba har Allah Ya kawo ni nan.” Bayan ya gama shaida wa dattijo labarinsa sai shi ma ya tambaya cewa, “Ya kai wannan dattijo mai daraja, kai kuma mene ne naka labarin? Mene ne labarin kasancewarka a wannan kungurmin daji kai kadai? Kuma mene ne labarin wancan lambu mai ban mamaki?>” Dattijo ya ce, “Ya kai Idrisu ina so ka sani, ni sunana Ibrahim dan Yahaya, kuma labarin kasancewa ta a nan da kuma labarin lambu kada ka sake tambaya ta. Ina so in shaida maka wata magana, in ka yarda, to zan koyar da kai abin da ka fito nema, wato ilmi, in kuma ba ka amince ba, to sai ka ci gaba da tafiyarka.” Www.bankinhausanovels.com.ng Sai Idrisu ya ce masa, “Allah gafarta malam ai sai ka shaida mini, in abin da zan iya yarda da shi ne in yarda, in kuma ba wanda zan iyaba ne in tafi.” . Dattijo [brahim ya ce, “Ya kai Idrisu, mutane suna lissafta ni daga cikin mashahuran malaman wannan zamani don irin dumbin ilmin da Allah Ya yi mini baiwa da shi.” Ya ci gaba da bayani, “Ya kai dan Hamidu, na dade a cikin wannan Kungurmin daji, sai dai kuma labarina a cikin sa da kuma labarin shi kansa wurin yana da tsawo, kuma ba zai yiwu ka ji shia yanzu ba, sai dai ko’ watakila nan gaba. Sharadi na farko da zan ba ka shi ne, daga yanzu komai ka gani kada ka tambaya. Abu na biyu kuma shi ne, lokacin da za ka shigo ka wuce ta wurin wata rijiya ko? To abin da nake so shi ne a kullum ka je ka debo ruwa daga cikin dan rafin can kana zubawa a cikinta har na tsawon yawan kwanakin shekara daya babu fashi, kuma kada ka manta na ce maka babu tambaya, kai dai aikata abin da na ce kawai. Ga daki A can ka rika kwana a ciki, kuma kada ka kuskura a tsawon kwanakin shekarar nan ka makara har in riga ka fitowa. Sauran abubuwan da za ka rika gani in dare ya yi kuma, sai ka san yadda za ka fitar da kanka. In har ka yarda da wadannan sharudda, to zan karantar da kai har na tsawon shekara daya. Kar ka damu da maganar abinci, wannan akwai shi. Na hango tahowarka daga nesa a kan zakakurin dokin nan wanda daga ganin yadda ya ke takawa ma kawai duk mai lura zai iya gane cewa yana da wata baiwa ta musamman, wato ba gama-garin doki ba ne, Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai ga shi kai kana sarrafa shi yadda ka ga dama, ya zama KarKashin ikonka. Shi yasa nake zaton akwai nasara a cikin lamarinka. Ina jaddada maka cewa lallai ka riKe shi da mutunci don zai taimake ka taimako mai yawa.” Dattijo ya ci gaba da yi wa Idrisu bayani, “Ya kai dana babu shakka za ka yi gwagwarmaya da yawa a cikin tafiyarka.” To, da Idrisu dan Hamidu ya ji wannan zance na dattijo sai ya ce, “Ya kai wannan dattijo mai daraja, na ji abubuwan da ka ce, kuma na yarda na amince, sai dai kuma na ba ka amana, ina fata kada ka yaudare ni. Kuma ga shi ka ce kada in yi tambaya, ba don haka ba, ina da tambayoyi masu yawa da nake matuKar bukatar amsoshinsu daga gare ka.” ‘ Dattijo ya ce, “A’a kada ka yi, da sannu za ka zo ka san komai.” Idrisu ya nemi Karin bayani, “Idan muna karatu har abin da ya shige mini duhu ban gane ba kada in tambaya?” Sai dattijo ya ba shi amsa cewa, “A‘a banda in an zo fagen karatu, ai karatu babu tambaya ya zama labari ke nan.” Dattijo kuma Shaihin malami Ibrahim ya Kara da cewa Idrisu, “Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, in dai karatu ka zo nema, to kuwa ka samu in dai har za ka tsare Ka’idoji. Bayan ka kammala karatu a wurina na shekara daya, za ka je ka ci gaba da karatu a wurin wasu. Amma kafin ka sadu da su jan aiki ne.” Yana matukar bukatar sanin abin da dattijon ke nufi, amma kuma ya tuna cewa babu tambaya, sai ya yi shiru. | | Sai ya cewa dattijo, “Babu shakka zan yi iyakacin Kokarina in kiyaye dokokin da ka sa mini, in Allah Ya yarda.” Cikin annashuwa dattijo ya ce, “To sai ka je ga dakin can ka shiga ka gani, a ciki za ka rika kwana, kuma ga wata ‘yar Karamar rumfa can a jikin dakin ka rika daure dokinka. Kuma shi wannan daki akwai komai da dan Adam zai buKata. In Allah Ya kai mu gobe, sai ka fara debo ruwa daga rafin kana zubawa a cikin rijiyar. Kada ka manta a kullum za ka zuba tulu goma ne, kuma kana kammalawa sai ka zo mu fara karatu.” Ya yi wa dattijo godiya, ya nufi inda daki ya ke, ya shiga ya tarar akwai gado da kujera da komai na more ” rayuwa fiye ma da yadda ya ke zato. Ya zauna bakin Www.bankinhausanovels.com.ng gado yana ta tunanin maganganun da suka yi, musamman ruwa da zai rika zubawa a cikin rijiya maimakon ita rijiya a debi ruwa daga cikin ta, amma an ce kada ya tambaya. Kuma ga irin wannan lambu mai ban mamaki. Sannan kuma babu wani mutum ko daya a wannan wuri sai dai wannan dattijo, duk dai an ce kada ya tambaya. | Tun da Asubahin fari ya dauki tulu ya fara debo ruwa yana zubawa a cikin rijiya kamar yadda aka umurce shi, har sai da ya zuba tulu goma daidai. | Bayan ya kammala sai ya je wurin dokinsa Jagora ya shafa shi, shi kuma dokin ya yi haniniya mai kamar gaisuwa kafin ya juya ya shige cikin daji kiwo abin sa. Shi kuma Idrisu sai ya nufi dakin malam ya yi sallama aka amsa tare da umurnin cewa ya shiga. Ya gai da malam cikin girmamawa shi kuma ya amsa cikin murmushi irin na Kauna. Idrisu ya ce, “Na zuba ruwan.” Dattijo ya amsa, “Ai na sani.” Idrisu ya yi mamakin yadda aka yi ya sani alhali kuwa ba ya fito ba ne, sai dai kuma babu dama ya yi tambaya. Suna gama karya kumallo sai Shehi Ibrahim ya ce, “Ya kai Idrisu, kafin mu fara, ina so ka ba ni dalilin da ya sa kake so ka sami ilmi ko ta halin Kaka, ko kuma a takaice ince ba ni labarin muhimmancin ilmi.” Sai Idrisu ya ce, “Ya kai wannan malami mai daraja, ni dai yaro ne, saboda haka na san cewa lallai kadan ne kawai abin da na sani game da muhimmanci da amfanin ilmi. Www.bankinhausanovels.com.ng Ilmi yana fitar da mutum daga duhu, ya yi masa jagora zuwa ga haske, kuma in kana da ilmi, to kana da mutunci, kuma komai ikonka, dukiyarka da kwarjininka in ba ka da shi, to da kai da jaki bambancinku halitta, kawai kai mutum ne shi kuma sunansa jaki. | Ilmi bargo ne da duk wanda ya lulluba da shi ba ya tozarta. Sai ka ga mutum dan talakawa amma matukar ya sami ilmi sai ya zama babban mutum mutane suna ba shi girma har ma ya iya rike mukaman da mai unguwarsu bai taba mafarki ba. ilmi shi ne babban makamin da ko lahira za ka tafi, to tare za ku, kana tafiya yana yi wa rayuwarka jagora, kuma duk inda za ka shiga, to kana gani radau don ko idanunka ba sa budewa, to kai ba makaho ba ne, wato ko idanunka a rufe suke matukar dai kana da ilmi, to kafi jahili wanda idanunsa ke bude sau dari. Wannan wani abu ke nan daga cikin abin da na sani na daga muhimmancin ilmi.” | To, da Shaihi Ibrahim ya ji zancen saurayi Idrisu sai ya ce, “Lallai ka ambaci dan kadan daga cikin _ muhimmancin ilmi. Amma duk da haka ka yi Kokari, = kuma a hankali za ka yi ta Kara gani da fahimtar muhimmancin na ilmi. » Yanzu sai ka Kara da sanin cewa shi ilmi takobin ~~ yanke jahilci ne. In kana son ganin bakin cikin duniya, ne to ka zauna da jahilci, kuma yadda ilmi ya ke jagora, to shi ma jahilci babban jagora ne, amma fa ta Bangaren halaka. Jahilci ne rawanin girman kai. Jahili ne kan soki . kansa da kansa amma ko kadan bai sani ba. A takaice dai innaci gaba da baka maganar jahilci sai mu yi kwana da . kwanaki muna yi. Yanzu sai mu ci gaba da karatu.” ‘ Lokacin Sallah ya yi suka tashi suka gabatar, suka ci > abinci sannan suka sake komawa fagen karatu. In banda Sallar La‘asar ba su tsaya ba sai gab da Magriba Ne lokacin da malamin ya ba dalibinsa damar yin tambayoyi a game da karatun da suka yi a ranar, daga nan suka yi Sallah suka ci abinci, kafin su kammala | Www.bankinhausanovels.com.ng lokacin Sallar Isha’i ya shiga. Suka gabatar da ita daga nan sai dattijo ya ce, “Mun kammala na yau, yanzu sai ka hanzarta ka koma dakinka, kuma kada ka kuskura “ ka sake zuwa wannan daki nawa sai gobe da safe. Kuma kamar yadda nake jaddada maka komai ka gani kada ka kuskura ka yi mini tambaya.” _ Idrisu ya yi sallama ya tashi. Yana shiga dakinsa sai ya tsunduma cikin tunani tare da mamakin irin abubuwan da ya ke gani daga wannan dattijo, musamman irin yadda abinci ke zuwa masa. Ga shi babu wani mutum a kusa da shi, ballantana a ce shi ke kawowa, sai dai kuma an ce banda tambaya. Ya dai Kare tunane-tunanensa ya shiga bitar karatun da ya dauko. Yana cikin nazarinsa sai ya ji dattijo a bakin dakinsa yana kira, nan da nan ya fita cikin gaggawa. Dattijo ya ce, “Na manta in shaida maka cewa lallai ka lura da dokinka, muddin ka ji yayi haniniya, to babu shakka yana yi maka nuni da wani abu ne, saboda haka sai ka kula.” Idrisu ya ce, “Na gode malam, kuma in Allah Ya so zankula” Www.bankinhausanovels.com.ng Dattijo ya koma dakinsa, ya bar Idrisu cikin tunani, “To ni ko ina cikin garin aljanu ne? An ce kada in yi tambaya, kuma ga abinci mai dumi muna ci ban ga mai dafawa ba, shi ma an ce kada in tambaya, dokina kuma in ya yi haniniya wai yana yi mini ishara ne, shi ma babu halin tambaya, kuma komai na gani a cikin dare kada in yi tambaya. A gaskiya ba don tsohon nan Musulmi ba ne, to lallai da na gudu daga wannan wuri, amma na tabbata dai ba zai yaudare ni ba daga dukkan alamu dai… to, zan zauna in ci gaba da bin umurninsa.” Ya shige ya haye gado ya yi kwanciyarsa. Can cikin dare bayan barci mai nauyi ya dauke shi, kamar a cikin mafarki sai ya ji ana rera waka, kuma lallai muryar ta mace ce mai dadin gaske kuwa, kuma tun da ya ke a rayuwarsa, bai taba jin waka da kidan molo mai dadi irin wannan ba. Ya farka a firgice, ya bude idanunsa amma sai ya ci gaba da jin wannan kida da waka wanda hakan ya tabbatar masa da cewa lallai da gaske ne ba mafarki ba. Hasali ma ba molo kadai ba ne, akwai wasu sauran kayan kade-kaden dake tashi a hankali. Ya tashi ya leKa waje daga cikin dakinsa, ai kawai sai ya ga lambun nan na kusa da su ya dauki-wani irin haske Kau da wasu irin fitilu masu launi iri-iri gwanin ban sha’awa, kuma ga wasu ‘yan mata nan su goma sha hudu, sun yi ado iri daya, ta cikon sha biyar din ce kayanta daban a cikin su, kuma ita ce ke ba da waka suna amsawa. Ita wannan yarinya duk ta fi sauran kyau, kamar dai yadda ake iya hango wata a cikin taurari, duk inda Sarauniyar kyau ta kai, to ba ta kai ta ba, kuma duk inda wani mai gani ya ke ganin kyau bai taba ganin mai kyanta ba, komai rashin begenka, idan ka gan ta, to dole sai ta dama maka tunani. Sa’arka dai kawai ba ka gan tadin ba. Kasance da www.bankinhausanovels.com.ng Idan ta sako waka sauran suka amsa, sai ya ji kamar zai narke saboda tsananin dadi. | Idrisu ya tabbatar da cewa ko mafarkinsa bai taba nuna masa wata yarinya da ta yi kusa da ita a fagen kyau da cikar halittar jiki ba. Abin da ya fito daga cikin bakinsa shi ne, “Tsarki ya tabbatar wa Ubangijin talikai. Ni na tabbata wannan yarinyg Sarauniyar kyau ce ta aljanu.” In yarinyar ta sake ba da wata waka sai Idrisu ya jj kamar ya tashi ya tsallake ‘yar Koramar da ke tsakanin, su ya isa wurinta, amma sai wata zuciya ta tsawatar masa ya fasa. Can dai da ta rero wata waka wadda dadinta ke ratsa sasannin Kwakwalwaar Idrisu bai san lokacin da ya tashi ya yi waje ya nufi wurinsu ba, yana KoKarin duba ta gefen da zai tsallaka Koramar ke nan sai kawai ya ji Jagora ya yi haniniya, ai nan take sai hankalinsa ya dawo jikinsa ya tuna cewa haniniyar dokinsa ishara ce a gare shi. Ya fahimci lallai zuwa wurin wadannan ‘yan mata ba alheri ba ne a gare shi, sai ya dawo ya shige daki yana mai ci gaba da sauraren wakoKinsu. , Lokacin da Asubahi ta kusa sai ya ji shiru, ya tashi ya leka amma sai ya ga babu kowa, duk ‘yan matan sun bace tare da dukkan fitilun, sai dai lambun kawai. Mamaki ya sake rufe shi, “Da ma na san wadannan ‘yan matan aljanu ne.” Kwanciyarsa ke da wuya sai barci mai Karfin gaske ya dauke shi har sai da dokinsa ya zo ya yi haniniya sau biyu. Nan da nan ya farka. Ya tashi ya yi sallah ya roki Allah nasara da kariya, kuma cikin gaggawa ya dauki tulu ya tafi yana debo ruwa Hmm ko mai zai faru kudai kuci gaba da kasancewa da wannan website www.bankinhausanovels.com.ng namu don samun ci gaban wannan kayataccen littafin YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 3 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng JIYA MUN TSAYA Yanzu ma abin da ya sa ya kawo ku wannan tsibiri shi ne don babu aljanin da zai iya zuwa nan sai wanda ke da jinin sarautar gidanmu a jikinsa. Kuma ya kawo ku nan din ne don kada wani abu ya taba ku. Niyyata ita ce in kashe ku in ya so duk abin da zai faru ya faru, amma da ya ke kuna da sauran shan ruwa, sai kika yi mini magana, kuma a cikin maganarki na ji kin ce mini kyakkyawa, to mu kuma matan aljanu babu girmamawar da ta fi ki cewa aljana tana da kyau. Duk wadda kika ce wa haka, to kin gama da ita.” Www.bankinhausanovels.com.ng Shaihi Ibrahim dai ya ci gaba da ba Idrisu labari cewa, da ‘yarsa ta ji jawabin aljanar nan sai ta sami makama, don irin dabi’ar dan Adam na dogon tunani. Sai ta ce ZAMU TASHI wa aljanar, “Ko kadan babu wasa ko yaudara cewa ke kyakkyawa ce, duk hassadar mai hassada sai dai ya yi a game da wani abin amma ba game da tantamar kyanki ba, don ni na tabbata irin ki a wannan duniyar sai an tona. Abin da nake so ki gane shi ne, ganin mu da kika yi a nan ba a son ranmu ba ne, a’a, dole aka yi mana don fin Karfi da kuma kasancewar babu yadda za mu yi. Ke kanki idan kin yi tunani za ki fahimci cewa babu abin da ya hada aljani da mutum. Shi wannan dan’uwa naki ba shi da imani, ki duba zuwa yau din nan mu hamsin da daya ne a nan, kuma har gobe in ta kama kawowa ya ke yi, garuruwa da Kasashenmu kowacce daban ne, wasu ‘ya’yan sarakuna ne, wasu na malamai, wasu kuma ‘ya’yan talakawa ne da masu dukiya, duk an kamo mu ba,a son ranmu ba, aka raba mu da iyayenmu da ‘yan’uwanmu da samarinmu, kin ga an raba mu da jin dadi ke nan. To ke inda kika yi kuskure ke nan, ki ka riKa kashe ‘ya’yan mutane ba tare da hakkinsu ba. Kin ga wannan ba laifinsu ba ne don babu yadda za su iya da shi, laifin dan‘uwanki ne, in ma halakawa ne shi ya kamata ki kashe. Saboda haka ya ke kyakkyawar yarinyar aljanu, muna fata ki yi tunani mu zama Kawayenki ba abokan gaba ba.” Www.bankinhausanovels.com.ng Da aljana ta ji jawabin ‘yata, sai ta fara Kwalla sharshar. Bayan ta nisa sai ta ce, “Lallai kuna da gaskiya, babu shakka na cuci ‘ya’yan mutane, na halaka su baa kan hakKinsu ba, duk a dalilin wannan mugun aljanin, amma babu komai, kwanansa sun kusa karewa.” Suna jin haka sai suka ce mata, “Ai yakan yi barci a nan, muna iya taruwa mu yi ta soka masa wuka har sai ya mutu.” Aljanar nan ta KyalKyace da dariya sannan ta ce, “Ku dai ‘yan Adam ba ku rabuwa da almara, ai shi wannan aljani in duk aljanun duniya da mutane sun taru ba za su iya masa ba. Ni ce zan taimake ku, kuma daga yau kun zama Kawayena, ke kuma ke ce babbar Kawata. Ni dai na yi muku alkawari duk ranar Asabar da ya ke ba ya zuwa nan zan rika zuwa. Kuma na dauki alkawarin ba zan sake kashe wata mace ba saboda wannan mugun aljani.” Bayan ta gama zayyana musu duk wadannan bayanai, sai kuma ta ce musu, “Zan yi iyakacin KoKarina in sato wani littafi da asirin rayuwarsa ke ciki, Shi ma kansa wannan aljani dan‘uwana bai taba ganin wannan littafi ba, don kuwa yana nan wurin wata kakarmu mai shekaru sama da dubu hudu. Kada ku yi mamaki na ce dubu hudu na shekaru, to ko kadan babu mamaki don mu aljanu ba mu mutuwa da sauri kamar ku mutane.” , Daga nan fa sai ta shiga cikin ‘yan matan nan suka sha kade-kade da’ raye-rayensu. In ka ga aljanar nan a cikinsu lallai za ka ga yadda Allah Ya yi ikonsa. Daidai goshin Magriba ta ce musu za ta koma, suka rabu suna kuka kamar sun yi shekaru tare, amma kafin ta tafi sai da ta gargade su da cewa kada ko da da wasa su kuskura su fada wa Sarkin aljanu cewa ta zo. Www.bankinhausanovels.com.ng Kafin ta tafi sai ta daga hannunta sama, sai ga wata Katuwar kwalbar turare, ta bude ta fesa duk a cikin gidan, sannan ta ce musu, “Abin da ya sa ni fesa wannan turare shi ne, don in ban fesa ba, yana zuwa zai ji Kanshin jikina. In kuma ya gane na zo, to ni na shiga uku ke nan.” Tana kammalawa sai ta yi dariya, kafin ta rufe baki sai hayaki ya turnuke ya tashi sama ya fita ta taga, ta tafi ke nan sai ranar Asabar. Wannan shi ne lamarin aljana. Amma lamarin ‘yata da sauran ‘yan mata bayan tafiyar aljana sai suka ci gaba da hirarsu, dare ya yi suka kwanta. Bayan wayewar gari da kuma daidaitar lokacin zuwan aljani, sai suka fara wake-wake da raye-raye. Can kuwa sai ga shi ya iso. Yana ganin su cikin wannan hali na farin ciki da ” walwala, sai murna ta kama shi, su kuma ‘yan matan sai suka zagaye shi suna yi masa marhaban-lale, sannan Www.bankinhausanovels.com.ng suka ci gaba da wakoKinsu. Bayan sun gaji sai suka dakata, aka yi ciye-ciye da tande-tande, aka sha ‘ya’yan itatuwa masu dadi. Babu shakka Sarkin aljanun nan yana cike da farin ciki, kuma ga ‘yata kusa da shi, komai ya ce nan da nan sai su tashi su yi masa. Wasu ‘yan matan kuma na tausa masa jikinsa. Duk suna yi masa haka ne don hila irin tasu ta mata, ba wai don suna son sa ba, don ka san su mata su ma kansu aljanun kansu ne. To bayan aljanin ya natsu, can sai ya cewa ‘yata, “Ni fa ina jin wani Kanshi ne kamar na aljani.” Sai ta ce masa, “Wace irin magana kake yi haka? Ka tara mu har hamsin da dori, sannan ka ce ba za ka ji Kanshi daban-daban ba? Kuma ka san mu mutane kowa Kanshin jikinsadabanne.” Sarkin aljanu ya amsa mata cewa, “E lallai kam kin yi gaskiya. Ni ma kuskure na yi.” A wannan rana ma kamar kullum, Sarkin aljanu ya yi murna da farin ciki mai tarin yawa. Da yamma lokacin tafiyarsa sai suka rera masa wata waka mai dan karen dadi har ya rude ya tafi yana begen su a cikin ransa. Bayan tafiyarsa sai suka taru wuri daya suna cewa, “Babu shakka za mu kama wannan mugun aljani a hannu, in ya san wata ai bai san wata ba, in shi aljani ne, to mu mutane ne, za mu ga wanda ya fi wani.” A haka har Juma’a ta kewayo, za su yi sallama da shi Www.bankinhausanovels.com.ng sai ranar Lahadi ke nan don ba zai zo ranar Asabar ba. Kafin su rabu duk sai ‘yan matan nan suka fara ‘yan koke-koke wai ba zai zo gobe ba, shi kuma da ya ga haka sai ya rude yana rarrashin su, can sai ‘yata ta tashi ta ce masa, “Ya kai rabin raina, wanda na fi so a cikin rayuwata, wai ku aljanu haka soyayyarku take ne? Ana ta buga soyayya babu sanin suna? Ko ni ban isa in san sunanka ba don ni ba aljana ba ce ‘yar’uwarku?” To su aljanu a irin tasu al’adar, in mace ta tambayi namiji sunansa, to wannan mata babu wanda take so a rayuwarta kamarsa. Da Sarkin aljanu ya ji yarinya ta tambaye shi sunansa sai ya sake dimaucewa, hankalinsa ya tashi, ya rude ya rasa halin da ya ke ciki don dadi, sai ya nisa ya ce mata, “Ya ke hasken rayuwata, ya ke abar Kaunata, sunana Sarki Sham’una dan Sarkin aljanu Damsalu.” Yarinyar nan tana jin haka sai nan take ta rera waka da sunansa, tana hadawa da sunanta sauran ‘yan matan suna amsawa. Sunan wannan ‘ya tawa Nur. Da Sarkin aljanu ya ji sunansa a cikin waka sai Kwalla shar-shar saboda murna. Ya daga hannunsa sama sai ga lu’ulu’u yana zuba kamar ruwan sama. Ya ce, “Ga kyauta nan irin tamu ta aljanu.” Nur ta ce, “Godiya muke ya Sarkin duniya. Amma ya kai wannan Sarki mene ne dalilin yin hawayenka>” Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin aljanu ya ce, “Ya ke rabin raina Nur, kin san mu aljanu ba ruwanmu da lissafin shekaru irin yadda ku mutane ku ke yi, amma da yake ni masani ne na irin wannan lissafin saboda irin gagarata sai in ce yau kimanin shekara dari hudu da hamsin da bakwai da wata biyar ke nan ban yi hawaye ba sai yau, ga shi kuwa na yi karo da mazaje da yawa a filayen yake-yake mabambanta, na kashe mazaje shahararru, na ga farin ciki da bakin ciki amma ba su taba sa ni Kwalla ba sai yau, dalili kuwa don tsananin son da nake yi miki.” Sai Nur ta ce, “Ya kai wannan kyakkyawan Sarki, babu shakka ina da abin da ke damu na.” Sarkin aljanu ya tambayeta, “Ke kuwa mene ke damun ki a wannan duniya alhali ina kusa da ke? Kan mutum nawa kike so? Ko kuwa kan aljan nawa kike so yanzu-yanzu a kawo su nan?” Nur ta ce, “A’a, ba kawunan aljanu ko mutane ke damu na ba, ni abin da ke damu na shi ne rayuwarka, don ka ce mini kana yake-yake da yawa. Ni kuwa kaicona ranar da za a kashe ka, ni ma ranar ba zan kwana da rai ba.” Sarkin aljanu Sham’‘una yana jin zancen yarinya Nur sai ya kece da dariya har yana Kyakyatawa. Bayan ya gama dariyarsa sai ya ce mata, “Kai, ku dai mutane kuna da ban dariya, shi ya sa kullum na zo nan sai na www.bankinhausanovels.com.ng koma cikin farin ciki, shi ya sa yanzu talakawana ke matukar jin dadina. Tun daga lokacin da kika zo nan har yanzu ban sa an yi wa wani aljani ukuba ba, don ina komawa fadata ne cike da farin ciki daga nan wurinki.” Ya ci gaba da cewa, “Ya ke kyakkyawa Nur, a yau lokaci ya Kure, yanzu ana can an fara zama a fadata.” Yarinya Nur ta tambaye shi, “Ya kai masoyina yaushe ne ake maka fadancin? Ga shi kullum a nan kake yini sai yammaci kake komawa?” Sai ya ce, “To ai mu aljanu baa mana fadanci da rana sai dai da dare, da rana kuma shiru. Ai kamar ku mutane ne da daddare shiru amma da rana ku yi ta hidima.” Sai ta ce, “E lallai gaskiyarka, ya kai Sarkin aljanu, lallai ya kamata ka tafi yanzu kada in rike wa talakawa Sarkinsu, don dole wani lokaci in riKa adalci in rika tuna cewa ba ni kadai ce da kai ba.” Yayi murmushi, ya ce, “E wannan kuma daidai ne.” Nan da nan ya yi sallama da su ya bace yana mai cike da annashuwa. Wannan shi ne lamarin ‘yan mata da Sarkin aljanu Sham’‘una. Yana tafiya sai suka shiga hira suna yaba wa yarinya Nur, saboda hikima da dabara da iya hilarta. Ranar Asabar ‘yan matan nan suka shirya suna ta nishadi suna sa ran zuwan Kawarsu wato aljanar nan. Can kuwa sai suka ji wani Kanshin turare da ba su Www.bankinhausanovels.com.ng taba jin irin sa ba a wurin tare da waka mai sanyaya rai daga cikin irin wakoKin da sukan yi, can sai suka ga lokaci ya Bace, sai ga aljanar ta zo cike da farin ciki don wannan zuwan ta yi shi ne don Kawance ba mugunta ba. Kai irin kayan adon ma sai wanda ya gani. Tana bayyana sai suka tarbe ta da murna da farin ciki da nuna Kauna, bayan sun gaisa ta kawo ‘yan ciye-ciye masu dadi ta ba su. Da suka natsa sai suka shaida mata yadda ta kasance tsakanin su da Sarkin aljanu da kuma irin yadda ya saki jikinsa da su, har ma da yadda ya tambaye su labarin yana jin wani Kanshi na daban, da yadda suka shashantar da tambayarsa, har da yadda ya yi Kwalla. Bayan sun gama shaida mata sai ta ce musu, “Ai dama na gaya muku cewa shi wannan aljani fa duk cikin aljanu da wahala a sami wanda ya fi shi jarunta da saurin fahimtar abubuwa. Sai dai kuma namiji komai jaruntarsa mace ce maganin sa.” Suka ci gaba da gudanar da nishadinsu kamar yadda suka saba. Can zuwa La’asariyya sai suka shiga wani lambu da ke cikin gidan suna zagayawa suna tsinkar ‘ya’yan itatuwa. Nur ce ta yi wa aljana magana, “Ya ke wannan kyakkyawar Kawa tamu, ga shi mun zama Kawaye kuma mun yarda da junanmu, mun bai wajuna Www.bankinhausanovels.com.ng amana da aminci, amma abin mamaki har yanzu ba mu san sunanki ba, saboda haka yanzu muna son sanin sunanki, amma fa in kin yarda.” Da aljana ta ji zancen yarinya Nur, sai ta yi dariya mai daukar hankalin wanda ya ga hakoranta, sai ta ce, “Ya ke Nur, ke da Kawayenki babu shakka kun san yanzu ina son ‘yan Adam. Na rantse da rana, a da mu aljanu ba mu da abokan gaba kamar ku mutane, don muna zaton ku miyagu ne, shi ma ya karfafa mini guiwa wurin kashe-kashen da na yi ta yi, ashe ba haka ba ne. _Yanzu na fi son ku fiye da ‘yan’uwana aljanu, kuma yanzu zan iya sadaukar da kaina domin ku. Sunana Dailanu ‘yar Kailanu. Shi mahaifin Sham’una wato Damsalu shi ne yayan mahaifina.” Sai wata daga cikin ‘yan matan nan ta tambaya, “Ashe Sarkin aljanu dan’uwanki ne na kusa?” Dailanu ta ce, “Kwarai kuwa.” Dayamma tayi sai Dailanu ta ce musu za ta koma sai ranar Asabar. Tace, “Kuma nayi muku alkawari zan zo muku da littafin da asirin kurwar Sarki Sham’una ke ciki, Littafin yana nan a wurin kakarmu Bakayalu kuma babu wanda ya isa ya shiga ma’ajiyarta sai ni. In tana nan babu wanda zai tunkari wannan littafi. Ni ma abin da ya sa zan sami damar dauko shi don za ta yi wata ‘yar tafiya ne, kuma ni ce kawai a dakinta, saboda Www.bankinhausanovels.com.ng haka in akwai wadda ta iya karatu da rubutu daga cikin ku sai ta juyi bayanin ciki don in koma da shi. Ko kadan babu dama wannaan littafi ya kwana a waje. Kul! Wannan littafi ya kwana a nan, to kuwa kwananku ya Kare, ni kuma na shiga ukuba har abada.” Sai yarinya ‘yata Nur ta ce, “Babu shakka, akwai wadanda suka iya karatu da rubutu. Na tabbata za mu iya juye shi cikin lokaci komai yawan shafukansa kuwa.” A haka suka tsayar da shawara. Lokacin da Dailanu za ta tafi sai Nur ta ciro wani warwaro na zinare daga hannunta ta sa mata. Aljana ta yi murna mai tarin yawa, a Karshe dai ta koma tana begen wadannan Kawaye nata. Bayan tafiyarta sai suka zauna suna kewar ta, suna ambaton kyan halinta tare da labarin irin kyau da cikar halitta da Allah Ya yi mata, tare kuma da tausayawa game da wulakancin da Sarkin aljanu Sham’una ya yi mata. Washegari Sarki Sham’una ya zo, su kuma ‘yan mata suka ci gaba da abubuwan da suka saba. Da suka natsa sai ya kalli yarinya Nur ya ce mata, “Ya ke kyakkyawa, ranar Juma’‘a na ji kin ce wani abu game da tsoron da kike yi game da rayuwata.” Sai ya yi murmushi sannan ya kalli sauran ‘yan matan yana mai ci gaba da bayani, Www.bankinhausanovels.com.ng “Ya ku wadannan ‘yan mata, ina so in sanar da ku cewa, tun can shekaru masu yawa da suka shude na gagari mazajen jarumai na aljanu. An dade aljanu suna shiri suna kawo mini hari ina wargaza rundunoninsu. A haka sai da na zo na gagari dukkan tarayyar aljanu. A cikin shahararrun aljanun da muka fafata sai wani Sarkin aljanu daga Yamma ne kawai ya dan wahalar da ni cikin shekarun da kasashenmu suka rika bugawa. Yanzu haka yana nan a cikin battar Karfe a kulle, ita kuma battar tana can karkashin tekun nan da babu wandakezuwa. | Www.bankinhausanovels.com.ng To ai ni Bata lokaci ne tunanin mutuwa a gare ni, don kuwa babu wanda ya san sirrin rayuwata sai wata tsohuwar kakata wadda ta san duk salon mugunta sannan kuma tana da tsananin mugun fushi, ko da mafarki babu wanda ke son ya kusanceta, kai in takaice muku labari ba wanda ya isa ya je wurinta daga ni sai wata yarinya ‘yar’uwata sunanta Dailanu. Ita wannan tsohuwa ita ce shugaba a wurin bautarmu, kuma a wurinta ne asirin rayuwata ya ke, kun san kuwa raina yana cikin garkuwa mai wuyar karyawa. Wannan shi ne kadan daga cikin labarina,dondazan _ tsaya ba ku labarin yake-yaKen da na buga ne, to da sai “mu yi shekara ba mu gama ba.” . Bayan Sarkin aljanu ya kammala wannan labari nasa Www.bankinhausanovels.com.ng sai Nur ta ce, “Ya kai wannan Sarki mai tsananin Karfi, lallai babu shakka ranka yana cikin katanga, katangar kuwa mai tsabagen Karfi, saboda haka yanzu hankalina ya kwanta kuma na yi murna mai yawan gaske.” Tana gama fada masa haka cikin murna sai ta barke da waka, tana yi tana hadawa da sunansa sauran suna amsawa. Yamma ta yi, wato lokacin tafiyarsa, sai ya yi sallama da su ya koma kamar kullum cike da farin ciki. Bayan bacewarsa sai suka zauna suna ta labari gami da tunani. Ran nan dai ‘yan matan nan cikin bakin ciki suka kwana, saboda jin irin kariyar da ran wannan mugun aljani ke ciki, amma kuma daga baya suka tattara lamarinsu zuwa ga Allah, suka ci gaba da roKon Sa da Ya Kwace su. Sarkin aljanu Sham’una ya ci gaba da zuwa har ranar Juma’a. A ranar Asabar wasu daga cikin Musulmin ‘yan matan nan suna zaune suna karanta wata sura daga cikin Alkur’ani mai girma, sai ga aljana Dailanu. Tana isowa ta ji karatun nan sai hankalinta ya tashi, ta rude jikinta ya yi sanyi, taji ba abin da take so kamar karatun, saboda haka sai ta sami wuri ta koma gefe ta zauna har sai da suka gama. Kafin su kammala sai ga aljana tana hawaye saboda irin firgicin da karatun ya jefa mata. Suna gamawa sai suka ga Dailanu ba kamar kullum ba Www.bankinhausanovels.com.ng Hmm labari fa nata tafiya kudai kuci gaba da kasancewa damu Www.bankinhausanovels.com.ng YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 2 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng Jiya mun tsaya inda Mamaki ya sake rufe shi, “Da ma na san wadannan ‘yan matan aljanu ne.” Kwanciyarsa ke da wuya sai barci mai Karfin gaske ya dauke shi har sai da dokinsa ya zo ya yi haniniya sau biyu. Nan da nan ya farka. Ya tashi ya yi sallah ya roki Allah nasara da kariya, kuma cikin gaggawa ya dauki tulu ya tafi yana debo ruwa ZAMU TASHI zubawa a rijiya har sai da ya zuba tulu goma. Bayan ya kammala, sai ya je wurin dokinsa yana shafa shi, kuma ya fahimci ba don dokin ba, to lallai da ya makara, alhali kuwa Shehi ya gargade shi a kan haka. Gari na wayewa tangaran sai ya zauna a Karkashin wata bishiya yana tunanin abin da ya gani daren jiya, irin wakoKin ‘yan matan nan, ya kuma tsunduma cikin begen kyan yarinyar nan da dadin muryarta da kuma irin kwarjininta, ya dai tabbatar wa kansa cewa lallai wadannan ‘yan matan aljanu ne. Babban abin bakin cikin ma a wurinsa shi ne irin yadda bai sami damar yin magana da ita ba ballantana ya sami labarinta, shi kuma wannan dattijo babu damar a ji daga gare shi, don ya ce babu tambaya. Wannan tunani shi ne a tsakanin wannan lokaci ya dabaibaye zuciyar saurayi Idrisu dan Hamidu, wani lokaci kuma sai ya rika tunanin iyaye da ‘yan’uwansa, ko wane irin hali suke ciki? Ya tuna shi dai ga shi ya rabu da su ya shigo tsakiyar daji, ko a cikin mutane ya ke ko kuwa aljanu? Shi dai ba ya iya tantancewa. Da gari ya waye sosai sai ya yanke tunaninsa, ya nufi dakin malam ya tarar da shi zaune rife da littafi a hannu. Idrisu ya gai da shi cikin girmamawa, malam ya amsa da murmushi, sannan ya gabatar masa da abinci mai alfarma da duminsa yana Kanshi, suka ci suka Koshi, suka dukufa cikin karatu tare da sauran Www.bankinhausanovels.com.ng al’amuransu kamar dai jiya. Dattijo bai tambayi Idrisu abin da ya faru daren jiya ba, shi kuma Idrisu bai ce masa komai ba. Ya Kare karatu da tambayoyinsa a kan darussan wannan ranar sannan ya yi sallama ya nufi dakinsa, bayan ya kewaya ta wurin dokinsa don duba halin da ya ke ciki. Kammala nazari da kwanciya da barcinsa ke da wuya, sai ya sake jin kida da wakoki kamar daren jiya, ai sai kawai ya yi waje, kuma ya tarar da lambun nan an kawata shi fiye da jiya, yarinyar nan kuwa babu wanda zai iya bayyana hakikanin kyanta, don babu shakka Allah Ya yi ikonSa a wurin. Tsunduma cikin kallonta ya sa Idrisu neman fita daga hayyacinsa, yana jin dadin wakoKinta, musamman yau da ya ke da shantu aka zo ana kadawa. Bege ya yi ta Karuwa cikin zuciyarsa a kan ta alhalin bai san mutum ce ko aljana ba. Shi dai ya tabbatar da cewa ya kamu da son ta sai dai kuma bai san yadda zai bullo wa lamarin ba, kowace waka yarinyar nan ta rero, sai ya ji kamar a wata duniyar ya ke. Bai san lokacin da ya nufi lambun ba, ya daga kafarsa ke nan zai sa cikin ‘yar koramar da ke tsakaninsu sai kamar a cikin mafarki ya ji haniniyar dokinsa, ai nan take kamar wanda ya farka daga barci firgigi ya tsaya, ya dawo da baya ya koma cikin dakinsa, a lokacin Asubahi ta kusa. Yana shiga sai ya ji shiru, ya yi sauri ya leKo amma sai ya tarar babu Www.bankinhausanovels.com.ng yarinyar, babu fitilun duk sun bace sai dai lambun nan a yadda ya ke a da. Saurayi Idrisu ya shiga magana da kansa a kan abin da ya dauka tunani ya ke yi a cikin zuci, “To ni dai wannan yarinya ko mutum ce ko aljana in Allah Ya yarda sai na aure ta, komai wahala komai dadi, ko rai ko mutuwa ni duk daya ne a wurina, sai dai in ita yarinyar da kanta ta ce ba ta so na… amma kuwa idan ta ce ba ta so na… hmm, to ai gara in mutu kawai in huta da rayuwa cikin tunanin ta tsawon rai. Af, to ta yaya zan gan ta har ma in ji ko tana so na din? Shi ke nan in dai har zan zauna a wannan daji har Karshen raina kuma wannan aljana tana fitowa duk dare ina gani tare da jin wakarta, to ni na yi alKawaria nan rayuwata za ta Kare.” Tun daga wannan lokaci bai sake barci ba, yana ta tunani daban-daban har zuwa lokacin da gari ya yi sha zai waye, nan da nan ya tashi ya yi Sallah waddaa ciki ya roki Allah bukatunsa. Bukatar farko da ya gabatar a kan ilmin da ya fito nema ne, sai kuma bukata ta biyu wadda yanayi ya sa shi, wato samun wannan kyakkyawar yarinya da ya ke gani cikin dare, wadda kuma bai san labarinta ba. Ya dauki tulu ya rika debo ruwa yana zubawa a cikin rijiya har sai da ya yi sawu goma. Ya je wurin dokinsa yana goggoge masa jikinsa yana tunani a cikin ransa yana cewa, Lallai komai yana da dalili, kuma duk Www.bankinhausanovels.com.ng wanda ya yi biyayya ga malaminsa, to babu shakka ba zai yi a banza ba.” Yana mai Kara mamakin abin da ke wannan wuri. Gari ya waye sosai, rana ta bayyana, ya nufi dakin malam, suka gaisa tare da cin abinci kamar yadda suka sabaa kullum. Malam ne ya fara magana, “Ya kai Idrisu, yau ranar hutu ce ba ranar karatu ba, saboda haka idan hantsi ya yi sosai, sai ka zo da dokinka mu tafi ga fili can zan fara koya maka dabarun yaki iri-iri.” Idrisu ya ce, “To.” : Idrisu ya shiga tunani a cikin zuciyarsa, “Kai wannan dattijo yana da ban mamaki, ina wannan tsoho mai yawan shekaru zai iya yin wani abu game da yaki bayan duk ya kwararrabe?” Dagawar hantsi ke da wuya sai ya je ya janyo dokinsa, sannan ya shiga cikin dakin malam ya sanar da shi cewa shi ya riga ya shirya. Nan da nan dattijo ya yi damara kamar wani shahararren mayaki ya fito, sai Idrisu ya cewa kansa, “Lallai wannan mutum da gaske ya ke.” Idrisu ya bi shi har suka isa Katon filin nan, dattijo ya sa takobi ya saro wani dogon itace, ya sassake shi ya yi tsini kamar mashi. Daga nan fa ya fara koya wa Idrisu yadda ake dabaru da hilolin yaki. Suka yi ta yi har rana ta take, jikin saurayi ya yi liKis sannan suka koma dakunansu suka yi wanka. Shi Idrisu yana cikin wanka yana tunanin irin Karfin wannan dattijo, yana kuma tunanin, “Ni da na fito makaranta neman ilmi ga shi na buge da koyon yaki? … amma dai baa Kin ta manya.” , Ya gama, ya sa suturarsa ya je wurin malam, suka ci abinci tare da yin Sallar Azahar. Bayan sun idar ne sai malamin ya shiga karantar da shi hilar yaki a karance cikin darasi har sai da Idrisu din ya fara yin hamma saboda gajiya da kuma tsamin da jikinsa ya yi. Www.bankinhausanovels.com.ng Dattijo ya ce, “Kamata ya yi ka je ka dan huta.” Idrisu ya yi matukar jin dadin wannan kalami. Cikin dan Kankanin lokaci sai ga shi a kan gadonsa, kuma kafin ka ce haka, barci ya kwashe shi. Malam ya ga Magriba ta Karato babu ko motsinsa, sai ya tabbatar da cewa lallai gajiyar dazu ce ke tambayar sa, saboda haka sai ya je Kofar dakinsa. Ya kira shi karo na daya, ana biyu ya ji ya tashi. Dattijo ya ce, “Ya kamata ka tashi don Magriba ta kusa. Na Kyale ka ka dan kara ko da sa’a daya ne don ka dan warware.” Idrisu ya tashi ya gabatar da Sallar La’asar sannan suka yi Magriba tare. Isha’i ta yi suka yi tare da cin abinci kamar dai yadda suka saba. Www.bankinhausanovels.com.ng IDRISU dai yana tare da malaminsa Shaihi Ibrahim dan Yahaya yana ta daukar darussa tare da bin umurninsa, kumaa kullum dare yana ganin yarinyar nan mai tsananin kyau amma bai san labarinta ba kuma babu dama ya yi tambaya. Ya kamu da tsananin son ta amma ba su taba magana ba, kumaa duk ranar da ya yi nufin tsallakawa zuwa wurinta, sai dokinsa Jagora ya hana shi. Yana nan a cikin wannan kungurmin daji daga shi sai malaminsa da dokinsa da kuma abubuwan mamakin da ya ke ta gani har na tsawon shekara amma bai taba tambaya ba kamar yadda aka umurce shi. Cikin shekara daya Idrisu ya sami karatu mai dumbin yawa a wurin dattijo, kuma bugu da Rari ya koyi dabarun yaki iri daban-daban da tsananin juriya. Daga cikin mafi muhimmancin dabarun da ya koya akwai kariyar kai da zamiya a wurin yaKi ba tare da amfani da garkuwa ba, alhali kuwa hakan babbar baiwa ce wadda samun irin ta sai an tonaa duk fadin duniya da wajenta. A kwana a tashi ba wuya, wata rana sai dattijo Ibrahim dan Yahaya ya ce masa, “Gobe ne kake cika shekara daya cur a nan muna tare ba ka taba saba mini ba, na tabbata ka yi mini biyayya kamar yadda na umurce ka. Na tabbata kai yaro ne mai cikakken ladabi, kuma wannan ya nuna irin ingantacciyar tarbiyyar da ka samu daga wurin iyayenka, babu shakka kana da iyaye nagari, kuma ga shi za ka shiga duniya. Ni dai na tabbata za ka yi nasara in ka ci gaba da kyawawan halaye irin wadanda ka nuna minia nan.” Www.bankinhausanovels.com.ng Dattijo ya sa hannu ya dauki akushin dabgen naman jiminar da ke gabansa ya ajiye gefe yana mai ci gaba da yi wa Idrisu bayani. “Ya kai dana Idrisu, a yau zan ba ka labarina da sauran abubuwan da kake gani a wannan wuri na mamaki. Na farko dai shi ne, wannan doki naka da ka sa wa suna Jagora, to babu shakka ka rada masa sunan da ya dace da shi don zai yi maka jagoranci har sai ka sami nasara. Babu irin rukukin da ba za ka iya shiga da shi ba, kuma sauran abubuwan mamaki na wannan doki sai nan gaba za ka rika gani. Sannan kuma dai, matuKar ka kasa gane hanya, to duk inda ya nufa da kai ka yale shi, in Allah Ya yarda zai kai ka inda alheri ya ke.” Www.bankinhausanovels.com.ng Dattijo ya ci gaba da cewa Idrisu, “Kamar dai yadda na taba shaida maka ne cewa al’umma tana sakani daya daga cikin shahararrun malaman zamani, wanda kuma shi ne dalilin da ya sa mutanen Kasarmu suke kira na da suna Shaihu kuma suke ganin a wurinsu babu masanin fannoni kamar ni. Da ace ana gadon karatu, to da sai in ce ni na yi gadonsa ne daga wurin mahaifina shi kuma daga wurin nasa mahaifin. In dai girmamawa ce daga Sarkin Kasarmu sai ni. Abin da ya faru da ni shi ne Allah da ikonSa Ya ba ni ‘ya guda daya tak, ita kuma wannan ‘ya tawa Allah Ya jarrabe ta da wani abu wai shi kyau, tsananin kyan nata har mamaki ya ke ba ni, ko da yake babu abin da ya fi Karfin Allah. Saboda tsoron yawan surutai na mutane, ya sa gaba daya ma na hana ta fita waje. Na karantar da ita karatu mai dumbin yawa, kuma fanni-fanni. Ta fuskar manyan harsuna na duniya kuwa, Allah Ya yassare mata iya yin magana da masu yawa daga cikin su. Da wuya a sami malamin da zai Kure ta ta fannin ilmi sai dai in an yi da gaske. Saboda wannan ne da kuma hankalinta Allah Ya sa nake matuKar Kaunar ta. Kaunar kuma mai tsananin Mutane sun yo ca kowa yana kawo caffa amma Allah da ikonSa ba ta fitar da miji ba. Ya kai dana Idrisu bayan almajirci kuma Allah Ya sa Www.bankinhausanovels.com.ng ina da wadata irin ta dukiya daidai gwargwado, don har ina da kuyangi mata guda bakwai tsarorin ‘yata. Sannan kuma ita wannan ‘ya tawa, Allah Ya yi mata baiwa da wani abu da ake kira fasaha, sannan ga dadin murya. Ta gauraya wadannan abubuwa biyu a cikin daya daga cikin abubuwan da ta fi sha’awa wato waka, babu shakka wannan yarinya ta shahara a fannin waka, in suka hadu ita da wadancan kuyangi nawa tana bayarwa suna amsawa, to ko kai wane ne sai bege ya kama ka. Kullum dare abin ka da yara, sai su shige lambun cikin gidana suna wasanni tare da rera wakoKinsu. Wani dare kamar yadda suka saba, sai hanya ta biyo da wani Sarkin aljanu ta wurin, yana kuma ganin ta sai ya rude, hankalinsa ya tashi kuma son ta ya kama shi yana mamakin wai dan Adam ne da irin wannan kyau. Tun daga ranar sai ya kasance shi wannan Sarki na aljanu babu daren da ba zai zo wurin ba don sauraren wakokinsu, kuma abin ka da aljani, ka san shi yana kallon su amma su ba sa iya ganin sa. Ya shiga tunanin yadda zai hudo wa lamarin. A karshe dai ya yanke shawarar dauke ‘yar tawa kawai ya kai can inda babu mutane ta zama mallakinsa, Ya yi tunanin wani tsibiria daya daga cikin manyan tsibirai uku da ke bayan duniya. Babu dan Adam din da ya taba sa Kafarsa a wurin. Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan yanke wannan shawara sai aljanin ya nufi wancan tsibiri ya gina wani Kasaitaccen gida, ya rika zabo ‘yan mata ‘ya’yan mutane daga sassa daban-daban na duniya yana fyauce su yana kaiwa yana ajiyewa. Babu wadda ya Kyale, ‘ya’yan sarakuna, malamai, masu dukiya da talakawa, kuma kowacce ko kadan ba za ka yi kuskure ba in ka ce ita ce Sarauniyar kyau a gari ko Kasarsu. Kamar kullum, wani dare yarinyar nan tawa da wasu daga cikin kuyangina suna cikin lambu suna wasanni da wake-wakensu sai wannan Sarki na aljanu ya sammace su da barci mai nauyi, ya dauke ‘yata ya nufi wancan gida na bayan duniya da ita, yana zuwa sai ya tashe ta. Farkawa da kuma tsintar kanta a wannan wuri suka sa hankalinta ya tashi, tsoro ya kama ta, tayi nan a guje, ta ruga can. Ta gama guje-guje da koke-kokenta kaf ta koma ta zauna tare da zuba wa sarautar Allah ido, tana mai mamakin irin halin da ta sami kanta. Ganin ta natsu sai aljanin ya rikida ya zama mutum, ya fito, tana ganin sa sai ta sake rudewa, amma darasin da ta samu a baya ya tabbatar mata da cewa babu wurin gudu a wannan wuri, saboda haka ko tunanin hakan ba ta sake yi ba, amma dai a firgice ta ke. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya ce mata, “Ki kwantar da hankalinki, babu abin da zai same ki. Ni ne na gina wannan wuri kuma ni na kawo ki. Nan kina bayan duniya ne, babu wani dan Adam da ya taba zuwa nan cikin mutane sai wanda na kawo, kuma babu wanda zai taba zuwa. Kai ko aljani ma zuwa wannan wuri ya gagare shi sai dai irin gidanmu kawai. Don yankinmu ne, kuma kowa ya sani.” Ya shaida mata cewa shi ne babban Sarkin aljanu na babbar daular aljanu ta Jarirul Waki-waki, sannan kuma ya nuna mata hadarin wannan gida da take ciki, cewa a kan wani dogon tsibiri ya ke cikin tsakiyar ruwa, saboda haka KoKarin gudu yana nufin mutuwa ke nan. Ya ce a cikin wannan gida akwai duk abin da za ta iya tunanin nema. Ya fuskance ta ya ce, “Duk wannan abu na yi saboda ke ne, saboda irin Kaunar da nake yi miki, shi ya sa ma na shiga cikin duniya da kaina na zabo miki mutane ‘yan’uwanki don su rika debe miki kewa.” Yana gama fadin haka sai ya bude wani sashe daga cikin gidan, sai ga ‘yan mata zuRa-zuka su hamsin, ya cewa ‘yata, “Wadannan duk bayinki ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng Su kansu sun yi mamakin kyan ‘yar tawa. Bayan ya gama labarinsa sai ya Bace, ya tafi ke nan. BaKin ciki ya rufe ‘yata har ta rera waKar bakin ciki mai ban tausayi. Ta yi ta koke-kokenta sauran ‘yan matan nan suka zagaye ta, wasu suka rungume ta, suna ba ta hakuri don su har sun saduda sun fara sabawa. Bayan hankalinta ya dawo jikinta sosai, sai ta yi musu jawabin cewa, “Ya zama dole mu kwantar da hankalinmu don tabbas babu yadda za mu kubuta daga wannan aljani, dole sai mun yi hakuri watakila Allah Www.bankinhausanovels.com.ng Ya kawo mana hanyar kubuta. Tilas ne mu sami _ natsuwa ta yadda za mu iya hilatar wannan mugun shaidani yadda za mu yi masa irin tamu ta mata mu kai shi mu baro, amma in muka ce za mu tayar masa da Kayar-baya, to babu shakka halaka mu kawai zai yi. Shawara dai guda daya ce, ita ce kada mu kuskura ya – gane cewa muna cikin bakin ciki. In mun ji alamar zuwansa sai mu saki jikinmu mu shiga ‘yan wake-wake har shi ma ya saki jiki da mu, wanda daga nan ne a hankali zan sami damar binciken sirrinsa.” Bayan yarinya’ ta kammala bayaninta sai dukkan su suka Kara sakankancewa da ita, suka sakar mata komai a hannunta, suka kuma saki jikinsu kamar suna gidajensu. Sai dai su yi wanka, su yi kwalliya don ga kayan kwalliyar nan birjik, kuma iri-iri sai wanda suka zaba. In sun ji aljanin yana zuwa sai su shiga kida da waka, suna rawa da rausaya da rangwada. In ya iso ya ga irin halin da suke ciki sai dadi ya lullube shi. “Yata ita ce ke ba da waka sauran suna amsawa. Ba alfahari ba, idan Www.bankinhausanovels.com.ng ka gan ta a tsakaninsu, sai ka ce wata ne dan daren goma-sha-hudu a tsakiyar taurari. Yadda suke gane zuwan aljanin kuwa shi ne, wani irin Rugi sukan ji yana cida kamar ana hadari. Bayan wani lokaci mai tsawo aljanin nan ya saba da su sosai, ya saki jikinsa kamar da ma sun yi shekara da shekaru tare. A duniyar nan kuma ya kasance babu abin da ya ke so kamar wannan yarinya ‘yata. In suna waKoKinsu sai ka ga kafin lokaci Kankani barci ya kwashe shi saboda tsananin natsuwar da yakan samu a dalilin haka. A kullum yana tare da su, kumaba ya barin wannan tsauni sai yamma ta yi likis sannan zai koma cikin ‘yan’uwansa aljanu. Ranar Asabar ce kawai ba ya zuwa saboda ranar bauta ce a wurinsu. Wata Asabar ‘yan matan nan suna cikin wani Katon daki mai shimfidun alfarma suna kewar gidaje da garuruwansu don sun san cewa aljanin ba zai zo ba, sai kwatsam suka ji wani irin ruri mai Karfin gaske kamar gidan zai tsage. Dole suka firgita don ba su taba jin rugi mai tsoratarwa kamar haka ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Nan da nan suka shiga addu’a suna neman tsari wurin Allah. Bayan lokaci kadan da jin waccan mummunar Kara, sai suka ji shiru. Daga nan sai wani irin Kanshi wanda ba su taba jin mai dadin sa ba ya budade wurin gaba daya. Bayan sa sai suka ga wani irin hayaki ya turnuke, siffarsa kamar bakan gizo, yana da launin shudi, ruwan goro, kore, ja da algashi. Can bayan wannan hayaki ya baje, sai suka ji muryar wata mace tana cewa, “Yau kwananku sun kare. Sai dai wasu ba ku ba.” Suna jin haka sai hankalinsu ya tashi suka dimauce suka sakankance da mutuwa, amma duk da haka sai suka ci gaba da yin addu‘o’in neman tsari, kowacce tana yi da irin abin da ya zo bakinta ko kuma ta yi imani da shi. : Www.bankinhausanovels.com.ng Allah cikin ikonSa Ya amshi addu’arsu, Ya ba ‘yata Karfin hali ta ce, “Ko wane ne ke son halaka mu ya kamata ya fito fili mu gan shi tukuna, kuma ya fada mana dalilin halakawar, in muna da ta cewa sai mu ce. Amma in wanda ke son halaka mu din ya aikata haka ba tare da mun gan shi ba, to kuwa lallai yana daga cikin azzalumai.” -Suka sake ganin hayakin ya murtuke jajawur, sai ya Bace, sai ga wata mace wadda ta dan dara su shekaru ta bayyana. Babu shakka wannan mace Allah Ya yi mata kyau, kai da ganin ta ka san ba mutum ba ce. Irin adon jikinta kurum ba su taba mafarkin ganin irin sa ba. Suka ga fuskarta a daure babu annashuwa ko kadan. Lallai da gani ta shiryo sharri a ranta. Aljana ta ce, “Yau kwananku sun kare, mugaye, Www.bankinhausanovels.com.ng mazinata! Babu mai ceton ku, babu mai kare ku don kuwa lallai yau za ku bakunci barzahu.” Furta haka ke da wuya sai wadannan ‘yan mata suka firgita, firgici mai tsanani tare da kara sakankancewa da mutuwa. ‘Yata ce ta yi Karfin hali ta yi saurin amsa mata. “Abin kuwa da mamaki, irin yadda kyakkyawar mace wadda ga dukkan alamu kyan ba na jiki ba ne kawai har zuci… a gaskiya Bacewar basira ce kawai za ta sa kyakkyawa kamar ki ki aikata mugun hali. Me muka yi miki da kike son hallaka mu?” Sai suka ga fuskarta ta yi haske har ta dan murmusa sannan ta cewa ‘yata, “Ashe ina da kyan da har ke kike yabawa? To gaskiya a da na zo da sharri ne amma yanzu na ji zuciyata ta yi sanyi. Yanzu kuma zan ba ku dalilin da ya sa nake son halaka ku. Www.bankinhausanovels.com.ng Na dade ina kashe mata da yawa ba don komai ba sai kishi. Ina daya daga cikin kyawawan matan aljanu, kuma . shi wannan Sarkin aljanu da ya kawo ku nan dan‘uwana ne. Tun yana saurayi soyayya ta shiga tsakanin mu. _ Muna cikin kogin soyayya, haka kurum wata rana sai ya shiga soyayya da wata mace ‘yar. Adam ya yi mini wulakanci mai yawa, ya karya alkawari, kuma -a Www.bankinhausanovels.com.ng al’adarmu in Sarki ya taba neman mace, to ita wannan aljana babu wanda zai sake neman ta har abada. Wannan yana daga cikin dalilan da kan sa ku ga wasu matan aljanu suna auren wasu mazajen na mutane.” Aljanar ta Kara da cewa, “Bayan wannan aljani ya yi mini wulakanci, sai na yi yunkurin tayar masa da kayar~ baya amma sai ya sa aka kulle ni a cikin wani daki har na tsawon shekara ashirin. Daga baya kakarmu ta roke shi ya sa aka sake ni. Ni kuma na yi alkawarin in dai zan gan shi da mace ‘yar Adam, to babu shakka zan halaka ta. Na kashe ‘yan matan mutane sun fi a kirga a dalilin wannan mugu. . Yanzu ma abin da ya sa ya kawo ku wannan tsibiri shi ne don babu aljanin da zai iya zuwa nan sai wanda ke da jinin sarautar gidanmu a jikinsa. Kuma ya kawo ku nan din ne don kada wani abu ya taba ku. Niyyata ita ce in kashe ku in ya so duk abin da zai faru ya faru, amma da ya ke kuna da sauran shan ruwa, sai kika yi mini magana, kuma a cikin maganarki na ji kin ce mini kyakkyawa, to mu kuma matan aljanu babu girmamawar da ta fi ki cewa aljana tana da kyau. Duk wadda kika ce wa haka, to kin gama da ita.” Www.bankinhausanovels.com.ng Shaihi Ibrahim dai ya ci gaba da ba Idrisu labari cewa, da ‘yarsa ta ji jawabin aljanar nan sai ta sami makama, don irin dabi’ar dan Adam na dogon tunani. Sai ta ce Hmmm kuci gaba da bibiyarmu donjin cigaba Www.bankinhausanovels.com.ng YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 9 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Yahaya ya ce mata, “A nawa zan nome miki ciyawar?” Gimbiya ta ce, “A matsayin Gimbiya ‘yar Sarki.” Yahaya ya ce, “Albarka.” Gimbiya Lubna ta ce masa, “To don soyayya.” Sai Yahaya ya kalle ta don tabbatar da cewa ita ce da kanta ta fadi abin da kunnuwansa suka ji, kuma tabbatar da hakan ya sa kawai ya ji zuciyarsa da bakinsa a lokaci daya suna amsa mata cewa, “An sayar. Saina Zo.” Ya juya zai tafi sai ta ce, “Mu je in raka ka.” Sai yace mata, “Haba yaya ‘yar Sarki za ta raka bawa mai lambu?” Gimbiya ta amsa masa, “Ba ‘yar Sarki ce ke yi maka rakiya ba, masoyiya ce take yi wa masoyinta rakiya. Kuma ba na fata mai magana ya sake irin maganganun da suka wuce a baya, don da ace a yau mahaifina ba ya wannan duniya, kuma a ba ni damar zabo mai maye gurbinsa, to babu shakka zan ce mai lambu, don irin tsananin dimauta da na yi a kan rashin tsoronsa game da gaskiya.” Sai Yahaya ya ce, “Da ace mai magana ta san yadda ZAMU TASHI mai lambu ke ji a zuciyarsa game da kyakkyawa abin son kowa, to lallai da kin tausaya mini, ni ma duk maganganun da na yi dole tasa ni, don ba na son raini, sannan kuma da irin zancen nan da masu iya magana ke cewa, “Abin da ba ka samu, to hada shi da bana so.” Lallai ni ina tsoron kada mu zurfafa cikin kogin soyayya, a karya mini zuciya daga baya kuma masu mulki su ki amincewa da talaka mai lambu.” Gimbiya ta yi murmushi sannan ta ce, “Kada mai magana ya karaya, ba a san namiji da tsoro ba. Kuma ina son mai lambu ya tuna cewa ita fa duk wanda zuciyarta ta amintu da son sa, to shi ne sarkinta. Amma in ka ga mace dukiya ko mulki su ne dalilan da take gina soyayya a kansu, to babu shakka mayaudariyar kanta ce.” Jin haka ya sa Yahaya yin murna da kuma tabbatarwa kansa cewa lallai wannan yarinya ta san abin da take yi. Sai ya ce, “Ya ke kyakkyawa, yanzu lokaci ya yi da zan koma lambu, don na tabbata Sarkin lambu zai damu in ya ga ban dawo da wuri ba. Kin san mutumin nan yana ji da ni kamar dan autansa.” Washegari bayan kammala aikin lambu, ma’aikata duk suna ta haramar komawa gidajensu, sai Sarkin lambu ya kira Yahaya yana jan sa da labari a hankali Www.bankinhausanovels.com.ng suna tafiya har sai da suka yi nisa da sauran jama‘a, suka sami Karkashin wata itaciya mai yawan inuwa suka zauna. Sarkin lambu ya ce, “Ya kai Yahaya. Kai dai saurayi ne wanda babu shakka Allah Ya yi maka hankali da natsuwa. To abin da nake son shaida maka shi ne, ni — na aminta da kai wanda kuma har hakan ne ya sa nake shaida maka wannan sirri. Tun da Sarki ya amince da kai har ya yarda ka rika kai wa Sarauniya kaya marmari, to ina yi maka gargadin cewa ka yi hankali da ita wannan mata ta Sarki, don kuwa ba ta da mutunci ko kadan, sannan kuma ba ta da kamun kai. Ko kadan ba ta jin tsoron Allah. Sannan kuma wani babban abin takaici shi ne ko kara ta gifta a gaban Sarki, to ba zai Ketara ba saboda tsananin tsoron kada ya bata mata rai da ya ke yi. A yau da a ce Sarauniya za ta ce tana son kan Waziri, to babu shakka kuwa Sarki zai sa a saro mata.” Sarkin lambu ya Kara da cewa, “Ai ka gaa da nine Sarkin yaki na wannan kasa, kowa so ya ke yi ya ganni don tsananin jaruntar da Allah Ya ba ni, na shahara matuka da farin jini fiye da yadda kake zato. To wata rana an yi shiri tsaf za a tafi fagen fama, sai Sarauniyar nan ta ce da ita za aje, haka kuwa aka yi. Www.bankinhausanovels.com.ng Aka dauki mako biyu ana gwabzawa. Na yi budawar tawa irin ta jarumai, na zubar da kawunan mazaje, kowa ya ganni a wannan fili zai ce ni zaki ne. Kai kada in yi ta zuga kaina, amma dai ko babu komai, ka san cewa duk wanda aka kira da sunan Sarkin yaki na wannan makekiyar kasa, ka san lallai ba karamin jarumi ba ne. To ashe duk kaiwa da komowan can da nake yi a fagen fama Sarauniya hankalinta yana kaina ban sani ba. Bayan dawowarmu sai ta shiga farauta ta. Kai in takaice maka labari, wannan muguwar Sarauniya sau biyar tana KoKarin neman aikata alfasha da ni amma Allah da ikonSa Yana kiyaye ni. Lokacin da ta tabbatar da cewa ba za ta sami nasara game da bukatarta a kaina ba, sai ta kai mugun suka na a wurin Sarki wanda hakan ya yi sanadin raba ni da rawanina na Sarkin yaki. Ba don Sarki na shakkar askarawa da jarumai ba, to babu shakka da tsire ni zai sa ayi. Wannan shi ne dalilin mayar da ni Sarkin lambu don wulakanci. Shi ya sa ya kai Yahaya nake gargadin ka a kan cewa ka yi hankali don kada ta halaka ka kamar yadda ita ta halaka.” Ranar kai kayan lambu Yahaya ya cika Www.bankinhausanovels.com.ng kwandunansa guda biyu da kayan marmari, daya na Sarauniya, dayan kuma na Gimbiya. Sai ya fara zuwa gidan Sarki. Da zuwansa sai Sarauniya ta fara yi masa wasu ‘yan take-take irin na mace mara kamun kai, nan da nan cikin ladabi Yahaya ya juye kayan marmarin ya kama hanya zai fita sai ta kira shi. Ta kawo riga da wando da hula ta ba shi hade da takalma irin na alfarma, sannan kuma ta dauko kudi masu tsoka ta mika masa tana murmushi tana kallon sa. . Yahaya ya amshi kyauta ya yi godiya, ya dauki kwandonsa ya fice. Yana fita sai ta yi wata irin ajiyar zuciya saboda zakuwa da ta yi da shi. Ya tsaya wurin masu tsaron fada ya dauki daya kwandon kayan lambun da ya ajiye, bai zame ko ina ba sai Kofar gidan Gimbiya. Daya daga cikin masu tsaron Kofa ya shiga ya ce da Gimbiya, “Ranki ya dade ga mai kayan lambu ya zo.” Ai kamar wata zautacciya, zumbur sai ta mike ta nufi hanyar Kofar gida ta yadda har sai da kuyanginta suka tsorata suka tashi suka bi ta a guje. Ta yi sauri ta sauke kwandon da ke kan Yahaya ta dora a kanta cikin murna da farin ciki, ta dubi masu tsaron Kofa ta ce, “Daga yau duk ranar da mai lambu ya zo, to a rika barin sa yana shigowa babu iso.” Www.bankinhausanovels.com.ng suka amsa, “An gama ranki ya dade!” Ta juya ta nufi cikin gida, sai ‘yan mata masu yi mata hidima suka yi KoKarin karbar kwandon kayan ~ marmarin da ke kanta amma sai ta ce su yi hakuri wannan kaya nata ne. Da suka shiga ciki sai ta ce, “Yahaya da a ce zan iya yin fushi da kai, to lallai kuwa da na yi, sai dai kuma ba ni da karfin zuciyar da zan iya yin fushi da kai din ne, saboda son ka ya riga ya cika cunkus a cikin zuciyata.” Sai Yahaya ya ce, “Ko da ya ai wanda zaa yi fushin da shi bai riga ya san laifinsa ba, amma yana tuba. Tuban masoyi kuwa, tamkar taki née na soyayya.” Gimbiya ta ce, “Amma dai ai kyan masoyi in ya yi alkawari, to ya riKa cikawa. A kan alKawari tun da safe ya kamata ka zo amma ka bar ni cikin kogin tunani, ba na jin dadin ruwa ballantana abinci a dalilin rashin zuwan ka.” Shi kuma Yahaya sai ya ce, “Lubna lallai na yi kuskure, kuma ki yi mini hakuri a kan haka, kuma ina son in shaida miki kada ko kadan ki dauka cewa ni ma cikin jin dadi hakan ta faru gare ni, a’a, mai gidana ne ya shagaltar da ni da wani aiki. Amma lallai ne ki sani cewa tun daga ranar da na zo nan muka ga juna, to rabin dare kawai nake iya runtsawa, Www.bankinhausanovels.com.ng rabi kuwa na tafiya ne wurin tunanin ki.” Gimbiya ta sa aka kawo wa Yahaya abincin alfarma nau’i daban-daban, ya zauna ya ci ya sha, sannan ta zo ta same shi suka yi ta hirarsu ta masoya. Can sai idanunta suka kai kan daya kwandon wanda kayan kwalliya da Sarauniya ta bai wa Yahaya suke ciki. Gimbiya ta dube shi ta ce, “Yaya na gan ka da wani kwandon daban, kuma har da wasu suturar sawa a ciki?” Sai Yahaya ya ce, “Aina kai wa babarki kayan lambu ne can gidan Mai martaba, shi ne ta yi mini kyautar wadannan kaya, har da ‘yan kudi.” Tana jin wannan magana game da Sarauniya, sai ta sauya fuska, ta ce, “Ya kai masoyina, ka yi hankali da macijiya don kada ta sareka. Lallai na cuci kaina kuma na cuce ka in har ban sanar da kai cewa Sarauniya tana da mugun dafi ba, kuma in ba ka yi hankali ba, lallai za ka rufta don ta saba saran manyan mutane da Kanana. Saranta bai kyale na kusa ba ballantana na nesa, don ta sari manyan sarakunan duniya da ‘ya’yansu kuma duk saran ya kai musu. Ni dai ina rokon ka ya kai masoyina, ka yi taka-tsantsan, in kuma ka Ki, to tabbas sunanka halakakke. Wata rana zan ba ka labarinta. Kuma ina roKon ka, matufar dai akwai soyayya tsakani na da kai, to don Www.bankinhausanovels.com.ng albarkacin soyayyar kada ka kuskura ko a mafarki ka taba sanar da Sarauniya cewa kana kawo mini kayan lambu.” Sai Yahaya ya yi murmushi ya ce, “Babu shakka kin yi gaskiya ya ke tauraruwa, labarin wannan macijiya da dafinta tuni ya riga ya sami masauki a kunnuwana, kuma in Allah Ya yarda zan rika kaffa-kaffa da ita.” Bayan wani lokaci Gimbiya ta raka Yahaya har Kofar gida kuma ta tsaya tana kallon sa har ya bace sannan ta koma ciki. Da ya koma lambu sai ya nunawa Sarkin lambu kyautar Sarauniya, shi kuma sai ya Kara ja masa kunne cewa, Kai dai na gaya maka cewa ka kiyaye.” Aka dauki lokaci mai tsawo Yahaya na aikin lambu, yana ci gaba da zuwa gidan Sarki yana kai kayan marmari, kuma soyayya ta yi karfi tsakaninsa da Gimbiya har yadda abin ke nema ya zame musu kamar ciwo. Sarauniya Zizaratu a duniyarta kuwa, babu abin da tasa a gaba kuma take kwadayi kamar aikata masha‘a da saurayi Yahaya. Ta gwada shi kamar sau shida amma ko alamar gane abin da take nufi ba ta gani a wurinsa ba. Ran nan dai sai ta kasa hakuri ta ce masa, “Yahaya kana son rayuwarka kuwa? To wannan ita ce rana ta Karshe, in ka sake dawowa ba ka aikata abin Www.bankinhausanovels.com.ng da nake nufi ba, to babu shakka ka gama rayuwa.” Shi dai sai ya fita yana mai tunani tare da cewa, “Allah Ka yi mini tsari daga sharrin wannan halakakkiyar mace.” Ya koma ya sanar da Sarkin lambu abin da ya wakana tare da sanar da shi cewa, “Ni daga yau ba zan sake kai mata kayan lambu ba.” Sarkin lambu ya amince yana cewa, “Gaskiyarka, kuma na goyi bayan ka, in ranar ta zo sai mu aiki wani yakaimata. RANAR kai kayan lambu ta kewayo, aka tura wani ma’aikaci da na gidan Sarki, shi uma Yahaya ya dauki na gidan Gimbiya. Mai kai na gidan Sarki na zuwa sai Sarauniya ta -tambaye shi, “Yau ina Yahaya?” Shi kuwa sai ya ce, “Ranki ya dade ai an sauya shi yanzu ni zan rika kawowa.” Sarauniya Zizaratu tace, “Af, to… shi ke nan.” Sai ta shiga tunani, “Wato yanzu matsiyacin yaron nan sun hada kai da Sarkin lambu suna son su tona mini asiri ko? To ai ba su isa ba, don kuwa wutsiyar rakumi ta yi nesa da Kasa. In sun san wata ai ba su san wata ba.” Ta ce a sanar da Sarki cewa lallai tana bukatar ganin sa a cikin gida, nan da nan Jakadiya ta cika aikinta. Ana tsakiyar fadanci Sarki ya yanke shari’ar da ke gabansa ya shigo cikin gida ya sami Sarauniya kace-kace cikin kuka da hawaye mai dumbin yawa, hankalinsa ya tashi har da durkusawa a gare ta yana Www.bankinhausanovels.com.ng tambayar abin da ya faru. Sarauniya ta dube shi ta ce, “Allah Ya taimake ka, ina tausaya maka ne, na ga irin yadda kake son mutane da tausaya musu, amma kuma kullum abin mamaki ba a kaunar ka. Ni ce kadai mai son ka tsakani da Allah wanda hakan ya sa ba na son in rika ganin ka cikin bacin rai, shi ya sa ba na fada maka wasu abubuwan.” Sarki ya ce, “E, lallai na san haka ya ke abar Kaunata. Amma don Allah mene ne dalilin kukan ki a halin yanzu>” Ya sa gefen alkyabbarsa yana goge mata hawaye. Sarauniya ta ce, “Allah Ya karya makiyanka, in banda raini da wulaKanci da kuma rashin ganin girman sarauta, ina mai aikin lambu ina Sarauniyar Sarki mai dumbin mulki da iko irin naka?” Ta Kara barkewa da kuka tana cewa, “A gaskiya in ba ka gama da Sarkin lambu ba, to watakila shi ne ajalin ka, don gabar da ke tsakanin ku tun daga lokacin da ka sauke shi daga Sarkin yaki Allah ne kadai Ya sani, Wai don ya ga saurayin nan Yahaya kyakkyawa ne, shi ne ya sa shi ya zo ya neme ni… kamar ni? Ko me ya mayar da ni oho? Kai wannan wulakanci da yawa ya ke. Sai ka ce kai ba Sarkin yanka ba ne?” Www.bankinhausanovels.com.ng To fa da Sarki ya ji wannan zance sai hankalinsa ya tashi, ya yi fushi; fushi mai tsanani, idanunsa suka kada suka yi jajawur, ya tashi ya dunkule hannu yana ta bugun bango don bacin rai. Ita kuma Sarauniya sai ta mike tana rarrashin sa tare da sanar da shi cewa shawara kawai ita ce ba tare da shawartar kowa ba, ya zartar da hukunci. Ya tashi ya koma fada, ya tarar da shari’ar da ya fara tana jiran sa. Nan take ya ba da umurnin cewa a kai wanda ake Kara da shi kansa mai Karar gidan yari a kulle. Sun hadu da fushin Sarki. Sannan sai ya cewa ‘yan majalisarsa ba ya son ganin kowa, yana buKatar zama shi kadai. Can sai ya nisa ya kira Sarkin dogarai ya ce masa, “Ka je ka zo mini da Sarkin lambu da mataimakinsa Yahaya.” Sarkin dogarai ya ce, “An gama Allah huci zuciyarka.” Sarkin dogarai da tawagarsa suka nufi lambu — amma Yahaya kadai suka samu, domin shi Sarkin lambu ba ya nan, ya yi dan tattaki zuwa Kauye kuma zai yi ‘yan kwanaki. Ya sa aka yi wa Yahaya daurin goro, aka auna shi zuwa wurin Sarki. Ana isa wurin tun kafin a yi wani bayani, sai Sarki ya daka wa Sarkin dogarai tsawa, “Sarkin lambu fa?” Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin dogarai ya amsa, “Allah Ya ba ka nasara an ce ya je Kauye amma ‘yan kwanaki kawai zai yi ya dawo. Saboda haka na aike da dogarai gidansa, yana zuwa a taho da shi.” Sarki ya ba da umurnin cewa a kai Yahaya gidan kurkuku a rufe tare da horo mai tsanani, bayan kwana bakwai kuma a dandake shi ya zama baba, wato ya zama ba namiji ba. Kwanaki biyar da yin haka sai Sarkin lambu ya dawo gari, amma maimakon ya fara zuwa gidansa sai ya ratse ta wurin aiki tukuna, su kuma suka ba shi labarin cewa an zo an tafi da Yahaya, shi kuma ana can ana dakon zuwansa. Ya nufi gidansa a fusace, yana zuwa zai shige sai dogarai suka firfito suka nufo kan sa. Ya roKe su don Allah su bar shi ya shiga iyalinsa su gan shi tukuna, sannan ya fito su tafi. Wani dogari ya ce, “Mu Kyale ka ka shiga? Ai kai ma ka san ba zai yiwu ba, kamar ba Sarki ne ya aiko mu ba?” Nan suka nufo shi za su cafke, amma sai ya watsaf da su, dama su goma ne. Ya bi su ya fara daka musu kashi, suka watse. Ya shiga gida ya ga iyalinsa. Ya wuce dakinsa ya yi shiga irin ta yaki. Ya rataya takobinsa gaya wa-jini Www.bankinhausanovels.com.ng na-wuce, ya dauki garkuwarsa, ya sungumi mashi, sannan ya sauyawa dokinsa sirdi. Ya nufi gidan Sarki, mutane na kallonsa suna ta mamakin yau lafiya kuwa? Tsohon Sarkin yaki a cikin kayan yakir Sarkin lambu ya isa fada, ya shiga har gaban Sarki da dokinsa, babu wanda ya tare shi, don kowa ya san jaruntarsa. Ya dubi mutane ya ce, “Duk wanda ke son ransa ya fita, ina bukatar ganawa da Sarki, wanda kuma ya gaji da zaman duniya, sai ya zauna ko kuma ya yi wani mugun motsin da ban yarda da shi ba.” Cika-aiki suka zaburo za su nufo shi shi kuma sai ya zare takobi, Sarki ya yi musu tsawa ya ce su fita. Kowa ya tashi yana fita, har da malamin nan da ke koyar da Yahaya, amma sai Sarkin lambu ya ce, “Allah Ya gafarta malam banda kai, ka zauna.” Bayan duk sauran jama’a sun fice, wato sun rage su uku kadai, sai Sarkin lambu a kan dokinsa ya ce, “Na ji ka sa an kamo Yahaya babu gaira babu dalili, alhali yaro ya kiyaye mutuncinka, kasancewar shi ba mutumin banza ba ne. Yau zan sanar da kai gaskiya, matarka Zizaratu ita ce bakar makira don sau shida tana neman sa don aikata masha’‘a da ita, amma yana Ki, a kullum al’amarin ya faru, sai ya sanar da ni. Www.bankinhausanovels.com.ng Kuma ganin abin yayi yawa ne ya sa yaron ya ce shi ba zai sake zuwa gidanka ba, kuma na goyi bayansa, don kiyaye mutuncinka. Hasali ma tun farko ni na gargade shi a lokacin da na fara ganin alamu na tabbatar sai hakan ta faru. Ni kaina ba don tsoron Allah ba da kuma gudun kada in ci amanarka ni ma wani ya ci tawa, to da tuni na gama da ita. A Kalla sau biyar tana kai mini farmaki, kuma don na ki amincewa ta kai sukana wurinka, kuma ka amince har ka cire ni daga Bangaren yaki ka mayar da ni na kayan lambu don wulakanci, a dalilin makircin da Sarauniya ta Kulla. Ka riga ka yi nisa, babu wanda ya isa ya fada maka gaskiya don kana Sarki, sai dai daga baya a je ana ta zunden ka. Ranka ya dade, idan kana so a zauna lafiya a wannan gari, to kada a kuskura a taba Yahaya, in kuwa aka taba shi, to jini kuwa zai kwarara. Kar ka ga rannan ka sa an yi mini bulala a lambu ban ce komai ba, ka dauka ko jaruntata ta Kare ne, a‘a biyayya ce kawai. Ni da Yahaya in ba ka bukatar mu ne a Kasarka, sai mu tattara mu Kara gaba.” Da Sarki ya ji abin da Sarkin lambu ya ce, sai ya yi shiru, ya sunkuyar da kai cike da mamakin irin maganganun da Sarkin lambu ya farfada masa. Can bayan wasu ‘yan dakikoki, sai Sarki ya nisa ya daga kai, ya juya gefen malamin nan ya ce masa, “Ko mene malam ya gani game da jawabin Sarkin lambu?” Sai malam ya ce, “Allah Ya ba ka nasara ai abin da ka sani ne lallai kafin a yanke wa mai laifi hukunci, to ya kamata a bincika sosai, kasancewar in aka yanke hukunci ba tare da bincike ba, to lallai akwai zalunci ko kuma son kai. Saboda haka Allah Ya ba ka yawan rai, lallai a bincika al’amarin wannan yaro cikin natsuwa. Ni kaina na yi matukar mamakin a ce wannan yaro ya farar da wannan al’amari da ake magana don kuwa na dade ina lura da shi a matsayinsa na dalibina, duk da cewa ba a shaidar mutum gaba daya amma ni dai a iyakar fahimtata ban ga alamar yiwuwar samuwar irin wannan babban laifi daga gare shi ba. Ranka ya dade ya kamata a yi nazarin irin halayar wasu matan don kuwa su da shaidan duk tafiyarsu daya ce.” Sarki ya ce, “Lallai gaskiya ce Allah gafarta malam, to amma ni nasan abin dazan yi.” Ya dubi Sarkin lambu ya ce, “Na ji duk abin da ka ce amma ni zan bincika, sai dai akwai sharadi, in har na fahimci cewa akwai sharri a cikin zancenka Www.bankinhausanovels.com.ng tsakaninka da Sarauniya, to babu ko shakka zan saa tsire ka gaba daya kai da Yahaya. Amma in zancenka ya tabbata gaskiya, to lallai zan mayar da kai mukaminka na Sarkin yaKi. Sai dai kuma ko kadan ba na son kowa ya ji wannan magana har sai na gama bincikena, wato kowa ya koma ya ci gaba da harkokinsa yadda aka saba, ko da yake akwai dan bambanci kadan da za a samu, wato yanzu Yahaya zan dauke shi daga lambu zuwa inda zan iya samun saukin nazartar maganar da kyau.” Haladu Sarkin lambu ya ce, “naji davi, Allah Ya taimake ka!” Aka ba Sarkin dogarai umurnin fitowa da Yahaya daga kurkukun zuwa fada. Sarki ya ce masa, “Ya kai Yahaya an yi min bayani, kuma fushi ya sa na yi saurin yanke hukunci a game da kai ba tare da bincike ba. To yanzu wannan ya wuce, kuma daga yau na nada ka a matsayin mai kula da gidana na hutawa. Akwai dakuna biyu kusa da gidan, nan ne masaukinka.” Yahaya ya yi godiya ya tashi ya fita. Sarki ya sallami Sarkin lambu, shi maya yi gaisuwa ya fice. Bayan ficewar Yahaya da Sarkin lambu, sai Sarki ya fuskanci malam ya ce, “Malam Ahmadu ka ga wannan lamari mai bakanta rai dai? Ni kuwa in har Www.bankinhausanovels.com.ng wannan magana ta tabbata gaskiya, to zan zamo wanda ya fi kowa mamakin mata, don irin yadda na amincewa wannan mata, na sakar mata komai, na kori sauran matana saboda son da nake yi mata. Kuma Allah gafarta malam, saboda amincewar da na yi mata, ta sa na wulakanta ‘yata har na sauya mata gida. Don ma a wancan lokacin na yi dacen daukar shawarar wasu mutanen kirki cewa kada in sa a sare wa ‘yar tawa kai. Malam in har wannan magana ta tabbata, to daga yanzu matan Kasata kaf za su riKa wahala kamar yadda mazaje suke yi, har yaki za su rika zuwa, kuma za mu sa su a gaba sai an fara kashe su tukuna kafin maza su shiga, kai har da ‘yata duk za a hada, don ba zan kara saurarawa wata ‘ya mace ba.” Sai malamin ya ce, “Allah Ya huci zuciyarka, ai laifin wani ba ya shafar wani, don duk ‘yan Adam ba su taru sun zama daya ba. Allah cikin hikimarSa Ya yi kowa daban-daban, kowa da irin halinsa da kuma irin fahimtarsa, don kuwa akwai matan da in ka gansu har zuciyarsu sai ka rantse cewa waliyai ne, kuma hakan suke. Saboda haka ina rokon Sarki ya huce kuma ya bi komai cikin natsuwa.” Sarki ya ce, “Haka ne malam.” Shigar Sarki cikin gida ke da wuya, sai ya sanar da HMMMM LABARI FA NATACI GABA DA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 10 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Sarki ya fuskanci malam ya ce, “Malam Ahmadu ka ga wannan lamari mai bakanta rai dai? Ni kuwa in har Www.bankinhausanovels.com.ng wannan magana ta tabbata gaskiya, to zan zamo wanda ya fi kowa mamakin mata, don irin yadda na amincewa wannan mata, na sakar mata komai, na kori sauran matana saboda son da nake yi mata. Kuma Allah gafarta malam, saboda amincewar da na yi mata, ta sa na wulakanta ‘yata har na sauya mata gida. Don ma a wancan lokacin na yi dacen daukar shawarar wasu mutanen kirki cewa kada in sa a sare wa ‘yar tawa kai. Malam in har wannan magana ta tabbata, to daga yanzu matan Kasata kaf za su riKa wahala kamar yadda mazaje suke yi, har yaki za su rika zuwa, kuma za mu sa su a gaba sai an fara kashe su tukuna kafin maza su shiga, kai har da ‘yata duk za a hada, don ba zan kara saurarawa wata ‘ya mace ba.” Sai malamin ya ce, “Allah Ya huci zuciyarka, ai laifin wani ba ya shafar wani, don duk ‘yan Adam ba su taru sun zama daya ba. Allah cikin hikimarSa Ya yi kowa daban-daban, kowa da irin halinsa da kuma irin fahimtarsa, don kuwa akwai matan da in ka gansu har zuciyarsu sai ka rantse cewa waliyai ne, kuma hakan suke. Saboda haka ina rokon Sarki ya huce kuma ya bi komai cikin natsuwa.” Sarki ya ce, “Haka ne malam.” Shigar Sarki cikin gida ke da wuya, sai ya sanar da ZAMU TASHI Sarauniya cewa ya sa an kama Yahaya har ya daure shi na tsawon kwanaki biyar yana jiran a yanke masa hukunci, amma da ya ke jama’a ba su san laifin da ya yi ba, sai suka yi ta ba da hakuri, ni kuma don kada a ga kamar kan zalunci ne na daure shi, sai na nuna musu cewa ke ce ya yi wa rashin biyayya. Amma da roKo ya yi yawa a gaban mutane da aka zo da shi, sai na yi masa gargadi mai Karfi cewa ke uwargijiyarsa ce kuma daga yanzu duk abin da ki ka umurce shi, to lallai ya aikata. Kuma kada ya sake yin kuskure irin wanda ya yi da. Kuma don in nuna wa jama’a cewa na huce da kuma irin adalcina, sai na nada shi matsayin mai kula da gidan hutawana, kin san tun da yaron nan Sallau mai kula da wurin ya koma Kauyensu don lura da tsohuwarsa ban sake daukar wani a wurin na dindindin ba. Sai dai dogarai su je su share su rufe kawai. Sannan kuma sai na ga gaskiyar masu ba ni shawara ne, bai kamata a kashe yaro saurayi kuma kyakkyawa kamar Yahaya ba. Gara dai a tsawatar masa.” Murna ta lullube Sarauniya a Boye don jin cewa Sarki ya umurci Yahaya da yi mata biyayya a game da duk abin data umurce shi. Nan take kuma ta ji wani ‘shaufi mai tsananin gaske na kadaituwa da Yahaya in din ya zo mata. Www.bankinhausanovels.com.ng Shi kuwa Yahaya sai ya mayar da hankalinsa wurin ci gaba da kulawa da gidan hutawar Sarki. A kullum in ba aiki ya ke yi ba, to yana tare da Sarkin lambu ko kuma yana makaranta wurin malaminsa don kuwa akwai mai tsaro a gidan hutawar kuma a dabi’a Sarki ba ya zuwa sai ya aiko cewa yana nan tafe. Wadancan abubuwa da suka yi ta faruwa wadanda kuma suka sa tsoro a cikin zuciyar Yahaya da kuma tunanin cewa yanzu ba shi ne ke kai kayan lambu gidan ‘yar Sarki ba, sai suka sa aka dauki kwanaki Yahaya bai je wurinta ba. Ran nan dai ya kasa hakuri yace a cikin ransa, “Bari dai in je in gai da Gimbiya.” Ya je ya same ta cike da bakin ciki kuma har ta fara fita hayyacinta. Yahaya ya yi maganar duniyar nan amma Gimbiya ta ki amsawa, can sai ga hawaye shar-shar suna gangarowa daga cikin idanunta. Ta bude bakinta tana magana, “Babu shakka ku maza kuna da wuyar rike al’amarin soyayya, bayan mace ta amince tare da sallamawa ta ba ku amana, amma ga shi ko ina ba a kai ba har ka soma biri-biri. To ina kuma ga ka aure ni na koma Karkashin ikonka? Saboda haka ina roKon ka ya kai masoyina, don Allah kada ka ci amanata.” Yahaya ya duKar da kai, ya ce, “Ni dai hakuri kawai zan ba ki saboda rashin zuwana tsawon kwanaki masu yawa haka.” Gimbiya ta ce, “Yo mene ne dalilin rashin zuwan naka har kwana goma sha daya?” Yahaya ya amsa mata da cewa, “Masoyinki yana can kwana biyar a gidan yari cikin tsutsotsi da sauro da Kwari da sauran wahalhalu, amma fa ki sani cewa wadannan ba su suka fi damuna ba fiye da Kaunar ki da kuma tunanin ki. Babbar sa’ar da na yi kasancewar zobenki yana hannuna, da na kalle shi sai in sami natsuwa har in sami damar yin barci. Kuma lokacin da na fito, sai tsoro ya lulluBe ni da kuma kasancewar duk hankalina ba ya jikina, kuma in na zo a wancan lokaci kika gan ni, to hankalinki na iya tashi. Shi ne na je na sarara tare da fuskantar sabon aikina, a haka har hankalina ya dawo jikina. Wannan shi ne dalilin rashin gani na tsawon wadancan kwanaki. Amma kuma yanzu ina fatan komai ya wuce don ga ni a wurinki ya ke Sarauniyar raina.” Tausayin sa ya kama Gimbiya, ta ce, “Ya kai inuwar raina, kai kuwa mene ne dalilin da ya sa aka kai ka wancan mugun gida>?” Yahaya ya ce, “In kin tuna kwanaki kin yi mini gargadi a kan cewa in kula da macijiya kada ta sare ni ko? To zancenki ya tabbata gaskiya don kuwa ta kawo mini sarar, amma cikin ikon Allah ba ta yi nasara ba.” Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakaninsa da Sarauniya ya labarta mata, sannan ya ce, “Sarki ya yarda da zancen matarsa, ya sa aka kama ni aka kai ni gidan yari tare da umurnin cewa a dandake ni bayan kwana bakwai. Allah Ya taimake ni Sarkin lambu ya je ya fanshe ni, amma ba don haka ba, ai da tuni na gama yawo.” Wani gaurayen tausayi da kuma murna ya kama Gimbiya, sai ta ce, “Ai dama na gaya maka. Ita wannan mata gara saran gamsheka da saranta. Ni dai babu abin da zan ce sai dai in sake ba ka hakuri, kuma in yaba maka don ka isa da, don da a ce kai mutumin banza ne irin ta, to lallai da ka biya mata buKatarta kun halaka tare.” Suka dai ci gaba da hirarsu irin ta masoya har zuwa lokacin komawar Yahaya gida ta raka shi. Aka dauki lokaci kamar baa taba yin wata magana irin wadda ta shafi Yahaya da Sarauniya ba. Ran nan sai Sarki ya shirya tafiya zagaye na kwana bakwai, amma ya ce ba ya son tafiya da mutane da Www.bankinhausanovels.com.ng yawa don yana son wannan ta kasance ziyarar bazata ce a wurin hakiman da zai ziyarta din. Saboda haka sai ya debi mutane goma kacal, ya bar Waziri tsaron gari. Aka yi masa rakiya kamar yadda aka saba, shi kuma ya ci gaba. Ya iso yankin wani Hakimi, sai ya sanar da shi cewa yana son zai yi ‘yan kwanaki a nan don hutawa, amma ba ya son kowa ya sani. Aka kai jama’arsa masaukai, ya ce su je su huta har sai lokacin da ya neme su. Ba tare da sanin kowa ba, ya debi amintattu guda biyu daga cikin su, tare da Sarki suka sauya kamanni kamar masu fatauci suka juya suka koma cikin gari. Akwai wani gida wanda ba shi da nisa da gidan hutawar Sarki wanda kuma mallakinsa ne, a nan ya sauka. Ya umurci wadannan amintattu nasa cewa su je kusa da fada su yi ta karakainarsu cikin sirri, su lura da kyau, matuKar Sarauniya ta fito, komai: dare komai rana, duk inda ta sa Kafa ko kuma ta je, to su rugo su sanar da shi. Suka ce, “An gama.” Washegari tun safe har dare babu abin da ya faru. A rana ta uku da tafiyar Sarki, can bayan dagawar hantsi, sai ga Sarauniya ta fito tare da wasu yardaddun bayinta su biyar, uku maza biyu mata. Ta nufi gidan hutawar Sarki, ta shige tare da kuyangi, ta bar mazan a Kofar gida KarKashin wata itaciya suna hutawa. Duk a idanun wadancan amintattun bayi na Sarki haka ta faru. Suka shiga wurin Sarki suka ce yanzu dai ba ta da nisa da shi don kuwa tana cikin gidan hutawarsa. Ya fito cikin sauyin kamanni da umurnin cewa kada kowa ya bi shi. Akwai wata ‘yar hanya da ta bi ta bayan gidan, ta nan Sarki ya kewaya ya kama katanga ya haye. Ya sadada ta baya har sai da ya gane dakin da Yahaya ya ke, kuma ga alama yana aiki ne a daya daga cikin dakunan Sarki, kuma ga alama ya riga ya gaida da Sarauniya kafin ya koma bakin aikinsa. Sarki ya hango Sarauniya can tsakar gida tare da kuyanginta tana ta shawagi cikin iko da isa. Sarki ya yi Kokari ya ja jikinsa zuwa Karkashin wasu furanni da ke bayan tagar dakin hutawarsa. Ya labe a daidai lokacin da ya ke jiyo maganar Sarauniya tana cewa kuyangin, “Sai ku koma can babban gida, ni ina tahowa can an jima, don ba na son yawan damun mutane ne nake tunanin in Zo nan kawai in dan huta kadan.” Ba su dade da tafiya ba, sai ta yi wuf ta shiga ainihin dakin da Sarki ke hutawa, ta kama tagar dakin ta bude, Sarki da ke labe bai ankara ba kawai sai ga shi yana kallon Sarauniya Karara, ya dukar da kansa, ita kuma ta kalli inda ya ke labe. Www.bankinhausanovels.com.ng Amma ikon Allah hankalinta ashe ba a wurin ya ke ba. ‘Ta rafkawa Yahaya kira, shi kuma ya shigo yana zaton ko za ta ce an yi wani abin ne ba daidai ba. Ta dube shi ta ce, “Ya kai kyakkyawan saurayi Yahaya, na lura dai kai yaro ne, ba ka san mai son ka ba, kuma ba don ina matukKar son ka ba, da tuni ka zama dan gida a lahira. To dai ka ga yanzu daga ni sai kai, kuma lallai ne yau ka biya mini buKatata, ko na samu Kwalamata ta koma, kuma kai ma in Kyale ka ka huta, ba zan sake damun ka ba. In kuma har ka amince cewa bayan wannan karon za ka ci gaba da biya mini buKatata a duk lokacin da na buKace ka, to lallai ka sani cewa babu wanda zai fi ka jin dadi a garin nan, don duk tsananin mulkin wannan tsohon idan na gifta masa kara, ba ya tsallakewa don tsananin so na da ya ke yi. Bai taba yi mini musu ba. In kuma har kana tsoronsa ne, to ka sani cewa yana can ya tafi gewaya.” Sarki da ke labe da yaji irin butulcin matarsa, ransa ya yi matukar baci, hankalinsa ya tashi duniya ta yi masa baki Kirin. Ya tuna irin yadda ya sakar mata komai, iko da mulki duk a hannunta. Ya tuna yadda ta yi sanadi da makirci ya kori sauran matansa uku, ya Www.bankinhausanovels.com.ng tuna yadda ta sa ya wulakanta Sarkin yakinsa wanda ya ke matukar ji da shi ba tare da hakKinsa ba, da kuma yadda wannan makirar mata ta sa ya wulakanta ‘yarsa da sauran wasu abubuwa marasa kyau ga jama‘arsa. Ya ciji dan yatsarsa da Karfi har jini ya rika diga amma Zafin bai dame shi ba, don yana so sai ya ga kwal-uwar-daka. Sai Yahaya ya ce, “To amma ya kamata ki ji tsoron Allah, ki sani cewa abin da kike nema na da shi haramun ne, sannan kuma akwai wani hakki na aure a kanki, kin zama maci amana. Kuma in shi mai martaba ba ya kallon mu, to ai Allah ba Ya gyangyadi, Yana kallon abin da muke ciki. Don Allah ina rokon ki ki Kyale ni kuma ni a wurina zan dauka cewa wannan bai taba faruwa ba kuma ba zan fadawa kowa ba cewa kin zo nan.” Sarauniya Zizaratu tace, “To shin ko ka manta cewa Allah din da kake magana Mai gafara ne, kuma kullum neman gafararSa muke yi? Sannan kuma da kake maganar cin amanar mijina shin ka san ko kuyangi nawa shi Sarkin ya ke kebewa da su wadanda na sani da wadanda ban sani ba, ko kuwa ni kadai ya tsayawa?” Yahaya ya ce, “Watakila in ba ki manta ba kin ce Www.bankinhausanovels.com.ng kuyanginsa, kuma kin sani cewa halas ne su a wurinsa ya keBe da su ko?” Sarauniya ta sake cewa, “Yaro yaro ne, shin ka manta da ni da shi ai duk abu daya ne, duk ba sha’awa ake yi wa ba? Kai dakata, kada ka tsaya ka nemi kawo mini wani Kabli da ba’‘adi, idan kana son ranka, to ka biya mini bukatata kawai ka huta. In ba haka ba kuwa, to lallai zan yi maka sharri fiye da wanda na yi wa Sarkin yaKi, na san wataKila ko ya taba ba ka labari ko Tana yin wannan magana sai ta yi wuf ta rufe dakin ‘ da suke ciki, ta riKe mabudin a hannunta. Kafin Kiftawa da bismillah sai ga ta tinbirbir huntu. Yahaya na ganin haka sai ya sa tafukan hannayensa biyu ya rufe idanunsa ya ce a zuciyarsa “Allah ka tsare ni daga sharrin wannan shaidaniya.” Sai ya ce mata, “Babu shakka ke mayaudariya ce. Kin cuci kanki kin cuci mijinki, kuma kin ci amana, kuma ga shi kin yi rashin sa’a bukatarki ba za ta taba biya ba a kaina, ba iri na ake tunkara da wannan sharri ba. Na yi rantsuwa da wanda raina ke hannunSa, da in biya miki bukatarki ta irin wannan hanya, gara in fada wuta ta cinye ni da raina. Allah dai wadaranki!” Duk maganar nan da ya ke yi idanunsa na rufe, ita kuwa tana tsaye tinbirbir, zuciyarta ta hasala saboda Www.bankinhausanovels.com.ng bakaken maganganun da yaro karami ke dankara mata, tana tunanin wai har zagin ta ya ke yi, abin da ko Sarkin garin bai isa ba. Sai ta fara zagin Yahaya zagi mai tsanani, ta matsa jikin ragaya ta dauko wata wuka da ke wurin ta nufo shi. Ganin haka Sarki da ke labe bai san lokacin da ya yi kundumbala ya kama taga ya duro cikin dakin a daidai lokacin da ta daga wukar za ta dabawa Yahaya wanda har yanzu idanunsa ke rufe bai san abin da ake ciki ba. Da gaggawa kafin ta san abin da ya duro cikin dakin Sarki ya ture ta ta fadi Kasa wuKar ta fadi gefe daya. Jin irin wannan motsi sai Yahaya ya bude idanunsa, suka yi ido hudu da Sarki, ai nan da nan sai jikinsa ya fara rawa yana cewa, “Na rantse da Allah yallabai ita ce ta ke so ta yaudare ni, wallahi tallahi ba ruwana ranka ya dade.” Sai Sarki ya ce, “Aminci a gare ka ya kai dan Hamidu, lallai kana daga cikin samari masu mutunci, gaisuwata ta girmamawaa gare ka ya kai dan halas.” Da Sarauniya ta ji abin da Sarki ya ce da Yahaya sai ta fashe da kuka ta ce, “Wato ka yarda da maci amanarka? Lallai na san ba ka so na, saboda haka yau ba zan kwana a wannan gari ba.” Sarki ya juya gare ta cikin fushi ya ce, “Yi mini shiru, Www.bankinhausanovels.com.ng yau dai asirinki ya tonu algunguma, maci amana! Yau makircinki ya Kare, yaudararki ta fallasu. Na godewa Allah da ba ki kawo mini mugun da gidana ba. Muguwa, bakar shaidaniya. Allah dai wadaran irin ki.” Yana gama magana sai ya sa takobi ya dauke mata kai, nan ta yi ‘yan shure-shurenta ta mace babu mutunci babu lada. Ta yi shahadar bunsuru. Sarki ya juya ga Yahaya wanda a yanzu ya ke ta kaduwa da kyarma, ya matsa kusa da shi, ya dafa kafadarsa ya ce, “Ya kai dana Yahaya, babu shakka kana daga cikin mutane amintattu, duk yadda aka yi daga babban gida ka fito wato gidan tarbiyya. Daga yanzu ni na dauke ka dana. Mahaifinka ya haife ka ne kawai amma ni ina ji a raina yadda ya ke Kaunar ka ni ma haka nake Kaunar ka. Na gode yadda ka kare mutuncina, ba ka yarda ka biya wa wannan shaidaniya buKatarta ba, don duk mutumin da ya san matarka, to babu shakka ya gama da kai. Da a ce ta hadu da irin ‘yan banzan samarin nan ne, da tuni ya gama da ita, ya riga ganina sororo wai ina mulki, alhali ga wanda ya fi ni mulki can gefe guda. Yanzu ma Allah ne kadai Ya san wadanda ke ganina ahaka.” Ya ci gaba da yi wa Yahaya jawabi, “Tun lokacin Www.bankinhausanovels.com.ng haduwar mu ta farko da kai a lambu na amincewa raina cewa kana da natsuwa da hankali. Ni dai ina yi maka addu’a da fatan gamawa da rayuwarka ta duniya lafiya.” Yahaya ya yi godiya saboda girmama shi da Sarki yayi. Sarki ya ce masa, “Akwai sauran magana ya kai dana, ina son ka yi mini alKawarin amincewa da abin da nake so in fada maka.” Yahaya ya ce, “Allah Ya ba ka nasara, in abin da zan iya ne, to zan amince tare da alKawari. Amma in wanda ba zan iya ba ne, to yallabai don Allah sai ka yafe mini.” Sarki ya ce, “To ya kai Yahaya da ma ina da wata ‘ya guda daya wadda ta yi ilmi mai yawa kuma fannifanni, tana da hankali da natsuwa, kuma ga kamun kai. Allah kuma da ikonSa Ya yi mata kyau kamar ‘yar aljanu. Ko da yake ‘yata ce amma na tabbata cikin abin da na fada maka babu Kari. Ya kai Yahaya ita ce nake so in hadaku aure, don ina son in hada zuriya da kai.” Wani irin gauraye na tsananin murna da mamaki suka kama Yahaya, sai ya riKa jin kamar ya mutu ne an yi masa albishir da Aljanna don tsananin dadi da farin ciki. Ya rasa yadda zai yi wa Sarki godiya, sai dai Www.bankinhausanovels.com.ng wani natsatstsen murmushi kawai da ya like a fuskarsa. Sarki ya ce masa, “Biyo ni.” Yahaya ya bi shi a baya, ba su zame ko ina ba sai gidan Gimbiya. Sarki ya cewa Yahaya, “Dakata mini a wannan zauren.” Ya shiga wurin ‘yarsa ya tarar suna ta hirarsu da dariya ita da masu mata hidima, sai ya yi gyaran murya. Suna ganin sa duk sai suka tashi suka yi gaisuwa. Ita kuwa Gimbiya mamaki ne ya lullube ta, kasancewar tun dawowarta wannan gida, Sarki bai taba zuwa ba, kuma ya hana ta je ta gaishe shi don matarsa ta rigaya ta shiga tsakanin su. Ta Kura masa ido Kurui kamar wanda ba ta sani ba, Kwalla na ta kwararowa daga idanunta tana gudana a kumatunta. Ganin ta a cikin wannan hali shi ma Sarki sai da Kwallar ta riKa gangarowa daya bayan daya, abin dai gwanin ban tausayi. Ya matsa kusa ya rungume ta yana ta tausarta da cewa ta yi hakuri da wasu abubuwa da ya yi mata a kan kuskure. Ya yi mata alKawarin hakan ba za ta sake faruwa ba, tare kuma da albishir cewa zai mayar da mahaifiyarta gidansa. Suka dan yi hirarsu irin ta mahaifi da’ya. Sarki ya dube ta ya ce, “Ya ke gudan jinin zuciyata, Www.bankinhausanovels.com.ng na zo ne don in sanar da ke cewa na yi miki miji kuma ranar Juma’a zan daura miki aure da shi.” Yarinya tana jin abin da mahaifinta ya ce sai gabanta ya, fadi, hankalinta ya tashi. Ta tuna soyayyarsu da Yahaya da kuma irin alkawarin da ta yi masa. Sai kawai ta sunkuyar da kai Kasa tana zubar da wata wala, Ganin haka sai Sarki ya ce mata, “Ya ke’ yata, kin san dai cewa ba. zan zabar miki abin da bai cancanta ba, ko ba: komai a kan da abubuwan da suka gabata, ina ganin bai kamata in sake Kokarin sa ki ko kuma yi miki sanadin abin da zai cutar da ke ba. Ina so ki share mini hawayena ki, auri wannan saurayi da nake SO, hadaki dashi Yarinya ta sunkuyar da kai Kasa tana mai cewa, “Ya kai babana mai girma, ai ba sai ka roKe ni ba, don kuwa ni kayanka ce, kuma dole ne in bi abin da kake so. Amma a gaskiya abin ne ya yi mini nauyi, na ji kamar an dora wani gungumen dutse a zuciyata. Don a duniya in ba ka zauna da wanda kake so ba, to babu shakka akwai damuwa. Akwai wani alKawari ne da na dauka wanda ya sa nake jin dama a ce mutuwa na yi maimakon saba shi. Amma Baba na amince, don duk dan kirki dole ya share wa mahaifansa hawaye in yana neman Www.bankinhausanovels.com.ng albarka.” Da Sarki ya ga hankalin ‘yarsa ya yi matukar tashi ‘Sai ya ce mata, © Ya ke ‘yata, na ga hankalinki ya tashi, kuma daga yau na kudiri aniyar cewa ba zan sake yin wani abu wanda zai tayar miki da hankali ko kuma jefa ki cikin damuwa ba, matukar dai ba kya so.” Sai ya mike ya fuskanci hanyar zaure ya yi kiran Yahaya yana mai nufin cewa ya shigo cikin gida, shi kuma Yahaya ya amsa ya shiga. Ita dai Gimbiya kanta na sunkuye kasa ko bukatar ganin kowane ne sai ya ce, “Ya kai dana Yahaya, ka yi hakuri kan alkawarin da na yi maka, don kuwa ‘yata ta ce ba ta son ka, amma kada ka damu, ni zan auro maka wata.” Jin mahaifinta ya ambaci sunan Yahaya, ai sai yarinya taji kamar wata aradu ce ta sauka, firgigi ta dago kanta suka yi ido hudu sai ta ga ashe Yahayanta ne. Sai ta bude baki cike da mamaki ta rika muttsuke idanunta, tana tunanin ko dukkan abubuwan da ke faruwa mafarki take yi ne ko kuwa ta tsunduma ne cikin kogin tunani? Da Sarki ya lura da abin da ke faruwa, sai wata irin murna ta sirri ta lullube zuciyarsa. Ya shuri takalmansa ya kama hanyar fita yana mai cewa, “To nina koma fada, bari in bar ku ku dan zanta ko?” Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan fitarsa sai suka yi ta mamakin irin wannan al’amari mai ban mamaki. Yahaya kuwa cewaya ke yi, “Tsarki ya tabbata ga wanda ke hada abin da Ya ke sO. Ta tambayi Yahaya labarin yadda abin ya wakana haka, shi kuma ya kwashe kaf ya fada mata har da yadda Sarki ya sare kan Sarauniya da takobi. Komawar Sarki fada sai ya sa Sarkin dogarai a je – gidan hutawarsa a dauki gawar Sarauniya a tsaftace wurin. Ya ce, “Ina so a kai gangar jikin can Jakara a jefa cikin ramin da ake kai wadanda aka kashe, ungulai su ci. Kuma ina so a feke itace a soke kantaa kafa a Kofar fada don kowa ya gani.” Aka kafe kan Sarauniya a kofar fada, mutane suka yi ta zuwa birni da Kauye suna ta kallo da maganganu barkatai. Wasu na cewa Sarki ya yi zalunci, wasu kuma na ganin lallai akwai dalili. Bayan kwana biyu Sarki ya sa aka yi yekuwa birni da Kauye. Ya aike wa abokanansa manyan Sarakuna cewa su yi hakuri saboda irin wannan gayyata ta gaggawa da ya aike musu, wato gayyatar daurin auren ‘yarsa ranar Jumaia. Aka Kawata gari da kayan kwalliya, manyan baki kuwa sai barkowa suke ta yi daga ko ina. Gari dai ya cika maKkil, babu masaka-tsinke. Ranar Juma’‘a kowa HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA BY HARUNA USMAN Jun 28, 2022 0 6 Add to Reading List YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 11 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Komawar Sarki fada sai ya sa Sarkin dogarai a je – gidan hutawarsa a dauki gawar Sarauniya a tsaftace wurin. Ya ce, “Ina so a kai gangar jikin can Jakara a jefa cikin ramin da ake kai wadanda aka kashe, ungulai su ci. Kuma ina so a feke itace a soke kantaa kafa a Kofar fada don kowa ya gani.” Aka kafe kan Sarauniya a kofar fada, mutane suka yi ta zuwa birni da Kauye suna ta kallo da maganganu barkatai. Wasu na cewa Sarki ya yi zalunci, wasu kuma na ganin lallai akwai dalili. Bayan kwana biyu Sarki ya sa aka yi yekuwa birni da Kauye. Ya aike wa abokanansa manyan Sarakuna cewa su yi hakuri saboda irin wannan gayyata ta gaggawa da ya aike musu, wato gayyatar daurin auren ‘yarsa ranar Jumaia. Aka Kawata gari da kayan kwalliya, manyan baki kuwa sai barkowa suke ta yi daga ko ina. Gari dai ya cika maKkil, babu masaka-tsinke. Ranar Juma’‘a kowa ZAMU TASHI ya hallara aka daura auren Yahaya dan Hamidu da Lubna ‘yar Sarki Salahuddin. Bayan addu’o’i, sai Sarki ya mike ya yi godiya tare da bayanin kashe matarsa da kuma dalilin yin haka din, wato tsananin makirci da rashin amanarta. Ya ba da doka cewa duk wanda matarsa ta yi masa irin haka a fadin kasarsa gaba daya, to Sarki zai aike da ita lahira matuKar dai akwai hujja tabbatacciya ko kuma ingantattunshaidu. Daga nan kuma ya ba da sanarwar mayar da Sarkin yakinsa kan mukaminsa. Ya mayar da matansa uku da ya kora sannan kuma ya nada ango Yahaya a matsayin sabon Magajin gari, tare da mallaka masa gidan hutawa na Sarki wanda yanzu aka yi matukar Kawata shi fiye ma da gidan Sarki, don tarewar amarya. Sarki ya kammala jawabinsa da cewa, “Daga yau kuma na bude biki na kwana bakwai.” Shagali ya kankama babu kama hannun yaro, mawaka da maroka kowa sai washi ya ke yi. Abinci da abin sha kuwa kamar ba sarrafa su ake yi ba. In aka ce za a ba da labarin duk abubuwan da suka faru a wurin sai kifin rijiya ya Karyata mutum a banza. A kwana a tashi ba wuya, kwanakin biki bakwai suka cika, wato za a kai amarya gidan mijinta don a sallami kowa ya kama gabansa. Aka dora ta a kan wani irin doki na alfarma, in ka ga irin yadda dokin nan ke sassarfa cikin takama, dole ne ko kai waye abin ya burge ka. Masu kadekade da raye-raye suna yi. Mata masu rakiyar amarya kuwa.a Kalla ba akasara ba a sami dari biyar. Abin bakin ciki, ana gab da isa gidan ango, wato Magajin gari Yahaya, sai kawai Sarkin aljanu Sham’una ya sure ta ya yi sama da ita. Mutane babu yadda za su yi su cece ta, sai dai daga kai sama kawai. Ita kuwa amarya sai ihu take ta kwallawa, tana kiran sunan mijinta Yahaya, har ta bace aka daina ganin ta. Bakin ciki ba ya misaltuwa a wurin mahaifinta da mijinta a lokacin da kowannen su ya sami labarin abin da ya faru. Sarki fadowa ya yi daga karagar mulki, shi kuwa Yahaya nan take ya fadi sumamme. Aka yayyafawa ango ruwa ya farfado, ya nufi fada yana kuka, Sarki na ganin sa sai shi ma ya fashe da kuka, Sauran mutanen gari kuwa duk kowa sai ya yi zugun-zugun cikin Bacinraida jimami. Bayan ‘yan kwanaki da faruwar wannan lamari, sai Sarki ya tara ‘yan majalisarsa ya ce musu, “Ina mafita?” Malam Ahmadu, wato malamin Magajin gari Yahaya ya ce, “Allah Ya ba Sarki nasara, a kwanakin baya na yi wani baKon malami daga can Kasar Arewa, muna hira da shi ya ba ni labarin Sarkinsu, cewa wani aljani ya dauke masa tasa ‘yar. Sun sami labarin cewa akwai wani gida ne a kan daya daga cikin tsibiran nan na cikin tekun da ke bayan duniya, to a nan ya ke ajiye ‘yan matan. An yi bayanin cewa ko a mafarki ba a taba samun dan Adam din da ya taba zuwa wurin ba. Na kuma ji labarin cewa wancan Sarki ya koma gida ya dakatar da fita neman ‘yar tasa. Sauran labarin ne ban sani ba.” Da Yahaya ya ji wannan bayani sai ya mike a gaban Sarki ya ce, “Yau rana ce ta farin ciki a wurina, tun da ya ke har za a iya samun wanda ya san inda matata ta ke. Ni dai ban ga ta zama ba, ina roKon Sarki ya yarda, gobe zan nufi Arewa don neman labarin wannan aljani. Kuma ba aljani daya ba, ni ina jin ko sun kai dubbai daruruwa ne, to zan tunkare su, kuma da Karfin Allah sai na gano matata ko kuma in mutu a kan haka.” Sarki ya ce, “Ina yi maka addu’a da fatan samun nasara. Amma lallai in za ka tafi sai ka sami jarumai, ina ganin kamar guda dari su yi maka rakiya.” Sarki ya juya ya dubi Ma’aji ya ce masa, “Sai a shirya musu dinare dubu ashirin don yin guzuri.” Gari na wayewa Yahaya ya shiga gidan Sarki ya yi www.bankinhausanovels.com.ng sallama da shi da kuma mahaifiyar matarsa. Suka yi masa addu’o’in samun nasara da fatan alheri, suka rabu kowa na kuka. Shi da askarawansa suka hau suka rankaya. Wannan shi ne labarin Yahaya dan Hamidu. Bashari dan salihu kuwa wato saurayinnan makwabci kuma abokin da ya fito neman ilmi tare da yayan dan hamidu baiyi tafiyar data wuce ta kwanaki goma sha uku ba saiya tsinci kansa yana kutsawa cikin wani daji mai yawan duhu da itatuwa Wahala da gajiya suka sashi fara tunanin juyawa da komawa gida amman kuma sai ya tuna da cewa aikata hakan zai iyq zame masa babban abin kunya nan gaba haka nan dai yayi haquri yayi ta kunna kai ciki har saida jikinsa yakai yanayin da bazai iya kara motsawa koda taku daya daga inda yake ba lallai yana buqatar hutu Sbd haka saiya sami tsakanin wasu duwatsu biyu da sukayi makaifa da juna ya shige yayi rigingine Bai dade da fara hutawa ba saiya hango wasu mutane suna tahowa wadanda kuma da ganinsu kasan cewa kowannensu akwai alamar kwarjini irinta sarauta tattare dashi sunsa shugabansu a tsakiya www.bankinhausanovels.com.ng gaba suna biye. Kasancewar Bashari bai san abin da ke tafe da su ba, sai ya sake boyewa a tsakanin duwatsun yadda ba za su iya ganin sa ba, amma kuma shi yana hangen su. Suna wuce daidai inda ya ke kadan, sai ya ga daya daga cikin mahayan ya lababa ya sa kokara ya buge kan shugaban nasu da ke gaba, ya fado daga kan doki. Suka taru suka yi ta bugun sa har sai da ya daina motsi, ga alama dai ya mutu. Abin da ma ya sake dakatar da su shi ne, suna cikin wannan aiki sai kawai ga wani katon zaki ya fito daga cikin daji yana gunji, ya nufo su. Suka taru suka fafata har sai da suka kashe shi, kuma ga dukkan alamu sun yi matukar jin dadin fitowar zakin a daidai wannan lokaci. Dalili kuwa shi ne irin yadda suka tube wancan shugaba na su da suka kashe daga cikin tufafinsa, suka yayyaga sannan suka sa su face-face cikin jini. Suka ciccibi mataccen zakin suka daura a kan dokin marigayin. } Suka dawo kan gawar mamacin suka dauke ta suka sa a cikin wani buhu na algarara suka daure bakin, suka yi kama-kama, suka jefa cikin wani rami mai . zurfi, sannan suka juya suka koma cikin daji. Duk fa abin da suke yi a kan idanun Bashari ne. Bayan tafiyar su sai ya fito daga inda ya ke boye a tsorace jikinsa na rawa, yana ta mamakin yadda hakan ta kasance. Ya fara tunanin ko zai bi mutanen nan ne don ganin yadda za su yi da rigar dan’uwansu, kuma ina za su je? Sai kuma ya tuna ai su akan dawaki suke, shi kuma yana kasa kuma in har suka gane yana bin su, to babu ko shakka halaka shi za su yi. Sai ya sauya shawara. Ya Kudiri aniyar cewa duk yadda za a yi, ya kamata ya shiga cikin ramin ya gwada ceto mutumin nan, mai yiwuwa yana da rai. In kuma ba shi da rai, to shi dai Bashari dan Salihu ya yi iyakacin abin da zai iya. Ya tube rigar jikinsa ya nufi rami da niyyar shiga, amma da ya leka ya hango zurmukeken zurfi mai duhu da ke wurin ai sai tsigar jikinsa ta tashi. Ya tabbatar da cewa ba zai iya ba. Ya zauna yana ta tunanin abubuwan da suka faru a cikin abin da bai kai sa’a daya ba da ta wuce, zuciyarsa ta rika fada masa cewa, “Babu yadda za a yi a jefa mutum cikin wannan rami sannan a ce zai rayu.” Sai ya yanke shawarar rabuwa da al’amarin wannan mutum wadda tasa ta Kare. Bai bar wurin ba sai ya ji nishi kamar na dan Adam, ya dudduba amma bai ga kowa ba. Can sai sautin nishin ya rika Karuwa, shi kuma sai ya saurara da kyau, ya kuma fahimci cewa lallai mutumin nan na cikin rami na da sauran numfashi, wato bai mutu ba. A zuciyarsa sai ya ji cewa ko zai halaka ne wurin Kokarin ceto wannan bawan Allah, to shi kuwa zai gwada. Ya tashi ya dan kewaya cikin dajin, ya sami itacen kargo ya sara ya yi ta bare bayan yana tarawa har sai da ya sami wanda ya tukka igiya mai tsawo da kaurin gaske. Akwai wata itaciyar kirga kusa da ramin, a jikinta ya daure igiyar kamar dabaibayi. Ya zura cikin rami ya kama ya yi ta shiga har lokacin da ya ji cewa igiyar tana gab da Karewa, kuma ya sakankance cewa lallai akwai sauran tafiya. Wato dole ya koma ke nan. Ya laluba Kafarsa ta dama Kasa, sai ya ji ya tokari wani abu. Ashe an yi sa’a a lokacin da aka jefa buhun ya sarke a jikin irin itacen nan da kan fito a gefen rami ta ciki. Ai sai murna ta kama Bashari, ya lallaba da sauran igiyar da ta rage ya daure buhun tamau sannan ya saba a wuyansa ya rika kamo igiyar don kokarin fita. Hannayensa duk sun gaji, babu abin da suke fitarwa sai jini saboda sabulewar da suke yi, a dalilin nauyin shi kansa da kuma na mutumin da ke cikin buhu. Ashe matsala na nan waje tana jiran sa. Ya rage kadan ya fito, sai kawai ya ji wata murya daga bakin ramin tana cewa, “Yau kwananku sun Kare kai da shi. Ashe gara da aka ce in dawo, to yau a lahira za ku kwana.” Wannan mutumi daya ne daga cikin wadanda suka aikata aika-aikar nan ta dazu, kuma an umurce shi ne da dawowa don tabbatar da cewa ba su bar baya da Kura ba, amma da ya iso bakin ramin sai ya ga igiya a daure. Kuma ba tare da bata lokaci ba ya fahimci abin da ke faruwa, wato wanda suka halaka wani ke son ya ceta. Hasali ma babu mamaki ya gan su lokacin da suke aikatawar ke nan. Gaban Bashari ya rika duka uku-uku. Nan da nan bakinsa na rawa ya ce, “Ka yi wa Allah ka yi hakuri ka Kyale mu.” * Mutumin ya ce, “In Kyale ku ka ce? Wato in rufa muku asiri mu kuma namu ya tonu ko? To ko da wasa haka ba za ta yiwu ba.” Da Bashari ya ji haka sai ya ce, “To yi yadda ka so, amma kada ka manta cewa rayuwarmu tana hannun Allah ne baa hannunka ba.” Mutumin a fusace ya ce, “E lallai, wato kana bakin kabari amma kana fadar bakar magana ko?” Ya daidaici igiyar, ya daga takobi don sare ta a daidai lokacin da ya ke cewa Bashari, “Yi addu’arka ta Kar…”Www.bankinhausanovels.com.ng wata macijiya mesa da ke saman itacen ta duro masa a wuya. Da ma tuntuni take ganin kamar tsayuwar shi mahayin barazana ce a gare ta. Sai kuwa ga shi zatonta ya tabbata; don ta ga ya dago makami ya nuna inda take, alhali kuwa ba ta san cewa shi bai ma san tana wurin ba. Haka wannan Katuwar mesa ta murde mutumin suka fadi Kasa suna ta murkususu yana ihu. Shi kuma Bashari da ma hannayensa tuni sun gama yin tsami, yana gab da sakin igiyar ke nan ko kuma jin an sake ingiza su cikin ramin amma sai ya ji wancan mutumi na ihu. Haba ai sai ya ji wani sabon Karfi ya zo masa da kuma kwadayin ya fita ya ga abin da ke wakana. Saboda haka sai ya Kara yunkurawa yana fitowa har ya samu ya ingizo buhun da ke wuyansa bakin rami shi kuma ya sa hannayensa ya yiwo waje. Yana fitowa ya dan taka daya biyu sai ya zube saboda matsananciyar gajiya, amma duk da haka yana iya kallon abin da ke faruwa. Wancan mutumin da ke Kokarin kwatar kansa da kuma macijiyar da ke Kokarin halaka shi suka shiga wani irin artabu, kowa na ta kansa ba su san halin da suke ciki ba, har suka mirgina suka afka cikin mugun ramin nan. Bashari ya shiga tunani a zuciyarsa, “Da ma ana cewa in za ka gina ramin mugunta, to ka gina shi gajere don watakila kai za ka fada. To wannan ya gina wanda ya fi shi zurfi. Allah mun gode maKa da Ka kubutar da mu.” Bayan kuzarinsa ya dan dawo jikinsa, sai ya yunkura ya kwance bakin buhun. Ya ga ashe wani dattijo ne fari mai farin gemu da saje, duk ya daddauje ko ina jikinsa raunuka ne, ga su nan ba sa kirguwa, sai nunfarfashi ya ke ta yi sama-sama. Bashari ya debo ruwa ya yi addu’a ciki, ya sa wa mutumin a baki. Aka yi sa‘a kuwa ya dan tsotsa, ya sa ruwan ya wanke masa jikinsa. Ya duba jikin dokin mutumin can da ya fada rami sai ya sami madara a cikin wata gora, ga kuma nama soyayye. Aka yi sa’a mara lafiyar ya dan kurbi madarar. Ya ciccibe shi ya dora kan doki. Ya sami igiya ya daure shi sakwa-sakwa yadda ba zai takura ba. Ya duba wurin don tabbatar da cewa bai bar wata alama da za ta nuna cewa wani abu ya faru ba, ko da mutanen nan sun yi tunanin sake biyo sawu. Ya shiga gaba ya kama linzamin doki yana ta tafiya don neman wani Kauye nan kusa wanda zai samu ya Yi jinyar sa yadda ya kamata. Wannan dattijo da aka lakadawa duka tare da neman halakawa ashe wani Kasaitaccen Sarki ne mai girman mulki, mai farin jini a wurin talakawansa. GaShi yana da dumbin sani ta yadda bayan kasancewar ‘sa limamin Juma’a na garinsa kuma shi ne malamin malamai. Da yammaci sai ka ga an cika makila kofar gidansa kamar ana fadanci, amma ba fadancin ake yi ba,a’a, manyan malamai ne ke Kara ilmi. Sarki Shahzad kuma,dai mutum ne wanda bai yarda da zalunci ba a,Kasarsa, Babu yadda za ka ga wata ;’yar–banza . karuwa: ko: ,kuma ;.dan, daudu ballanta wani shege barawo,; www.bankinhausanovels.com.ng Kasan mutane babu miai iya musu sai Allah. Ashe duk kyan halin wannan Sarki akwai wasu ‘yan tsiraru daga. cikin, mutanen; fada:wadanda ba sa jin dadin yadda mulki ke-gudana. Babba daga,cikinsu shi, ne kanin Sarkin, wanda maganar.da ake ciki a lokacin ita ce Sarki ya fara shawara a.cikin zuciyarsa cewa ya kamata ya sauka daga.karagar mulki ya nada Kanin don shi ya fuskanci harkar karantarwarsa kadai, Shi,wannan kani na Sarki mai suna Rufaidu babu inda suka daidaita da Sarki ta bangaren hali, don, shi mutum ne,wanda yayi amanna da a Kyale kowa ya Sakata ya wala, kowa ya yi nishadinsa da walwalarsa yadda ya ga dama matukar dai bai taba mulki ba, Mai bukatar karatu ya yi mara bukata ya bari. Karuwai da yan daudu in suna bubatar zama www.bankinhausanovels.com.ng a Kasar a Kyale su, in ba su bukata shi ke nan, amma fa a raayinsa. Ko da yake koyaushe yakan yi KoKarin Boye wa Sarki wannan ra’‘ayi tare da nuna masa cewa yana goyon bayansa dari bisa dari. Ya ci da zuci game da sarautar garin, musamman kasancewar Sarki bai taba haihuwa ba a rayuwarsa. Ya sha Kullawa Sarki tuggu da makirci iri dabandaban amma yana tsallakewa. Dole wani lokaci ya kan hakura da Kulla makircin in ya lura da irin yadda jama ar Kasar ke matuKar son Sarkinsu. To shi wannan adalin Sarki mutum ne da ya jarabtu da son fita farauta, kuma can cikin Kungurmin daji. In aka je sai a kafa tantuna a yi sansani, tantinsa a tsakiya, na sauran askarawa kewaye. al’adarsa kuma in za a shiga cikin daji, to yakan ce kowa ya kama gabansa ne ya je tasa farautar, duk abin da mutum ya kamo, to kansa ya kamawa. Sarkin kuma in zai shiga tasa farautar, to ba ya son kowa ya bi shi, sai dai wani lokaci wannan Kani nasa, don ya dauke shi ne kamar dan cikin sa. Karewa ma shi ya raine shi, ya ba shi ilmi da duk wani abu da da kan bukata daga majibintansa. A ranar da lamarin ya faru an fito wata gagarumar farauta ce ta kusa da gida, don Sarki ya ce ya tuna wani wuri da zakoki suke a cikin dajin, shi ne ya ke son ya gwada ko zai yi sa’a ya samo ‘ya yansu don kiwatawa. Ya cewa wannan Kani nasa ya samo jarumai shida duk da shi na bakwai su tafi, su kuma samo buhu wanda in an sami ‘ya’yan zakin za a zubo a ciki. Jin haka sai murna ta kama Kanin Sarki, ya lissafta tare da kintata cewa yanzu dama ta zo wadda bukatarsa za ta biya cikin ruwan sanyi. Saboda haka sai ya je ya zabo irin mutanensa ya sanar da su abin da Sarki ya ce, sannan ya sanar da su shi kuma irin shirin dayayi. Yace, “Kun dai riga kun san cewa irin wannan rana muke jira, to yau ga ta ta zo da kanta. Kun ga sarauta ta zama tawa ke nan, mu sheke ayarmu mu ci karenmu babu babbaka.” Ya shiga nuna su daya bayan daya yana cewa, “In mun yi nasara, kai zan nada ka Waziri babba, kai kuma Waziri karami. Kai Magajin gari zan yi maka, kai kuma Madaki, kai kuma kujerar Maji dadi na tanadar maka, kai kuma ta Sarkin fada.” Jarumai cikin murna suka ce, “Mun ji mun dauka.” Shi ne Bashari ya gan su suna zartar da wancan mugun nufi nasu. Bayan sun ga sun sami nasarar jefa shi cikin wannan mugun ramin ne, sai suka nufi sansani cike da murna, amma da suka kusa sosai sai suka Bbarke da kuka, suna ihu. Da sauran askarawa suka gan su cikin irin wannan hali, sai suka zo suna tambayar su abin da ya faru da kuma yadda aka yi ba su ga Sarki ba. Shi kuwa gogan naka Rufaidu Kanin Sarki, sai kukan kawai ya ke ta zabgawa, ya kasa yin magana ma saboda nuna irin baKin cikin da ya ke ciki, yana ihu yana yayyaga rigar jikinsa tare da marin kansa. Sai daya daga cikin su ne ya iya ba da labarin cewa wai Sarki ya ce su Kyale shi zai kutsa cikin daji, shi ne aka sami wani Zaki ya fi Karfinsa ya halaka shi ya cinye shi bai bar komai ba sai kai da Kafafuwa kawai. Saboda haka suka haka rami suka bizne shi. Amma Allah Ya ba su ikon kashe zakin. Da mutane suka ji wannan mugun labari sai kowa ya barke da kuka, wani ba ya jin na wani. Kanin Sarki kuwa sai birgima ya ke ta yi a Kasa, ana rirriKe shi ana ba shi magana. Wasu kuma suna tausaya masa saboda rashin yayansa mai kama da mahaifi da ya yi. Nan take masu busa Kaho suka yi ta busawa, wadanda suke cikin daji suka yi ta fitowa suna dawowa sansani don sun san babu lafiya. Bayan an kammala taruwa, sai aka dunguma zuwa gari kowa na hawaye. Kanin Sarki kuwa duk ya Kuje fuskarsa da faratansa wai shi bakin ciki. Lokacin da labari ya kai gari ai abin babu kyau, kuka yaro da babba, kuma ba mace ba namiji. Da ganin mutanen wannan gari lallai ka san suna cikin wani lamari mara dadi. Shi kuwa Kanin Sarki sai aka sa mutane kusa da shi don su lura da shi, wai kada a Kyale shi shi kada ya kashe kansa. To yadda al’adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al’amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne ‘yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda, HMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA BY HARUNA USMAN Jun 28, 2022 0 3 Add to Reading List YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 12 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA To yadda al’adar mutanen garin ta ke, in Sarki ya rasu, sai an yi watanni uku sannan za a nada wani. Haka al’amarin ya kasance, wato sai aka shiga jira tare da ‘yan shiryeshiryen da suka dace kafin zuwan lokaci. . Amma shi Bashari sai ya ci gaba da tafiya yana jiyyar Sarki gwargwadon iyawarsa da dan abubuwan da ya sani har Allah Ya kawo shi wata riga ta Fulani. Aka kai shi wurin Sarkin Fulani wanda ake kira Ardo Jumare, wani dattijo mai farin gemu da yawan shekaru. Bashari ya yi gaisuwa cikin ladabi da girmamawa, sai Ardon ya tambaye shi labarinsu, amma tsoron rashin sanin wadanne irin mutane ne zai sake haduwa da su, da kuma tunanin in ya fadi gaskiya labari na iya komawa kunnen wadancan mutane su sake zagayowa su halaka su, sai Bashari ya ce, “Mu fatake ne ‘yan kasuwa ni da mahaifina, sai na nemi izininsa don zuwa in wanke rigata wadda ta yi dauda, ZAMU TASHI ‘yan fashi suka far masa suka Kwace mana dukiyarmu. Shi kuma suka yi masa dukan tsiya, na dawo na same shi cikin wannan hali.” Nan da nan Ardo Jumare ya sa aka ba su bukka, ya ce aje wurin ‘yarsa can cikin daji a ce ta kawo madara mai zafi za a ba baki. Wannan Ardo yana da shanun da sun fi dubu biyu. A dalilin haka ne ya dauko jingar wani saurayi yana taya ‘yarsa da suke yi wa lakabi da Bingyel da Kaninta mai suna Harande kiwo. Yarinya ‘yar Fulani ta tatso madara ta cika gora – makil ta kawo. Mahaifinta ya umurce ta cewa ta mika wa bakin da ke cikin bukka, sannan ta gaggauta ta koma daji ta hado wa mara lafiyar maganin jini. Lokacin da ta shiga cikin bukkar don mika madarar, sai suka yi ido hudu da Bashari. Nan fa suka Kurawa juna ido kamar sun san juna, shi bai karbi gorar ba yana kallonta, ita kuma ba ta ajiye ba. Can sai kunya ta kama ta, abin ka da mace kuma bafillatana, sai ta ajiye gorar madarar ta ruga cikin daji don kawo maganin. Fitarta ke da wuya sai Bashari ya fara sambatun cewa, “Allah da iko Ya ke, tun da na zo duniya ban taba ganin yarinya mai kyau da cikar halitta irin wannan ba, kuma ikon Allah a cikin rigar Fulani. Ni Www.bankinhausanovels.com.ng na tabbata ko birnin Misra ko Sin da ake cewa manyan birane ne a duniyar nan ba za a sami mai kyan ta ba.” Ya tsiyayi madara ya tallafo kan Sarki ya dura masa. Can bayan wani lokaci sai Ardo ya fito da wani garin bakin mahadi ya cewa Bashari, “Gobe tun kafin mara lafiyar ya ci abinci, a duntsi maganin dan daidai Kima a gauraya shi da wanda yarinya za ta kawo. Maganin ya zama shi ne zai fara sha, kuma a cika masa cikin sa da shi.” Da yamma yarinya ta dawo daga daji rike da wasu saiwoyin magani, tana zuwa ta gyara su ta hau su da daka har sai da suka daku likis, sannan ta kwashe a cikin wani akushi ta rufe ta miKawa Bashari kanta a sunkuye. Watakila saboda kunyar kada a maimaita abin da ya faru dazu. Bayan an kammala cin abincin dare, sai ta dauko wata sarewa ta fito waje ta yi kwanciyarta rigingine a kan buzun ragon da ta shimfida cikin hasken farin wata. Busarta na tattare da wani irin sanyi wanda a cikin zuciya kawai ake iya jin sa. A daidai wannan lokaci kuwa, shi Bashari abin ya gauraye masa ne da cewa yana can gefe daya kwance a kan tasa tabarmar. Zuciyarsa ta yi sanyi, idanunsa kuma na ta kallon yadda wata ke ta kaiwa da komowa cikin giragizai, -_ Www.bankinhausanovels.com.ng ko kuma giragizan ne ke kai wa da komowa? Oho! Shi dai ba ya iya tantancewa. Lokacin da dare ya dan daga, sai yarinya ta shige cikin bukkarta. Shi ma kamar ita ya ke jira, tana shigewa sai ya yi zumbur ya mike ya shige wurin mara lafiya. Har gari ya waye dukkan su shi da ‘yar Fulani babu wanda ya samu ya yi wata cikakkiyar runtsawa. Tabbacin cewa sun fara kamuwa da son juna. Wayewar gari ke da wuya, sai Bingyel ‘yar Fulani ta tatsi madara ta dafa ta zuba zuma ‘yar kadan ta nufi bukkar su Bashari. Tana zuwa sai ta yi sallama, ta shiga ta gaishe shi cikin ladabi, ta ba shi ta ce masa – nasa ne shi kadai tare da tunatar da shi cewa mara – lafiyar ba zai ci komai ba wannan safiyar sai dai magani kadai. Ta yi murmushi shi ma ya yi, ta dukar da kai ta juya cikin . hanzari Bashari ya tallafo Sarki ya ba shi hadadden maganin nan. Abin mamaki aka yi sa’a ya yi ta sha har sai da ya rage kadan, shi kuma Bashari ya dauki madararsa ya shanye sai kwaryar. Yana ajiyewa sai gyatsa. Bayan dagawar hantsi sai ga Sarkin Fulani ya shigo don duba mara lafiya. Ya tarar barci ya dauke shi, sai ya cewa Bashari “Da ma na san barci zai dauke shi saboda haka al’adar maganin ta ke, kuma ba zai tashi ba sai misalin yammaci. Saboda haka kada ka kuskura ka tashe shi sai ya tashi da kansa.” Bashari ya ce, “To Baba, Allah Ubangiji dai Ya saka muku da alheri.” Ardo ya amsa da cewa, “Amin yaro, ai irin wannan yi wa kai ne, yau gare ka ne gobe ga waninka.” Ardo Jumare ya fice ya nufi gindin wata itaciyar cediya ya zauna yana tufkar igiya. Bingyel ta fito ta nufi garkensu ta kora shanu zuwa cikin daji, tana tafiya tana busa sarewar nan ta jiya. Shi kuwa Bashari gaba daya sai hankalinsa ya rika bin inda sautin sarewar ke nufa. Can bayan wani lokaci, kasancewar ya san cewa mara lafiya ba zai neme shi ba, sai ya sulale ya nufi inda sautin sarewar nan ya nufa dazu. Ya yi tafiya mai tsawo amma bai gan ta ba, ya sami gindin wata bishiya ya zauna tare da tsunduma cikin kogin tunanin abubuwa mabambanta. Can sai ya sake jiyo sarewar na tashi, ai kamar wata kibiya ya mike ya nufi wurin. Yana zuwa sai ya gan ta a kan reshen wata bishiya tana wasa da Kafafuwanta. Bashari ya yi zamansa KarKashin bishiyar alhalin ita ba ta ma saniba. Can sai hankalinta ya yi wo Kasa, sai ta ga mutum Www.bankinhausanovels.com.ng zaune, kuma ba tare da bata lokaci ba ta gane ko wane ne. Mamaki ya rufe ta, sai ta diro. “Yar Fulani ta ce, “Kai kado yaya aka yi ka zo amma ba ka yi mini magana ba Bashari ya ce, “Don Allah ki yi hakuri, busarki mai sanyaya zuciya nake matukar jin dadi, sai na yi tunanin in kin san na Zo, to kina iya dainawa, shi ya sa ko sallama ban yi ba. Sai na yi burin da ace ni ma na iya busa irin wannan sarewar mai daukar rai fa?” Sai ta yi murmushi ta duKar da kai ta ce, “Ai babu wuya, duk abin da mutum ya saa ransa cewa zai koya, ai zaiiya matufKar dai akwai mai koya masa a kusa.” Jin haka sai Bashari ya ce mata, “Ai kuwa da wannan mai koyo ya yi sa‘a.” ‘Ta mika masa sarewar ta ce ya rike, ita kuma sai ta ruga cikin daji. Can bayan kamar rabin sa‘a, sai ga ta ta dawo rife da gwandar daji masu kyau sun nuna lugub-lugub, ga kuma Kokiya da tsada duk ta hada ta mikawa Bashari. Ya yi godiya a daidai lokacin da ya dauki wata tsada ya jefa a bakinsa. “Yar Fulani ta ce, “Ya kai wannan saurayi, ni ko wani abu ne ya ke ta ba ni mamaki.” Bashari ya ce, “Ya ke ‘yar Fillo ke kuwa mene ne ke ta ba ki mamaki?” Ta ce, “Tun ranar da ka zo sai na ji kamar wata Www.bankinhausanovels.com.ng sabuwar rayuwa ta zo mini, don ko tunaka na yi sai in ji wani farin ciki na shiga cikin zuciyata, in kuma kana kusa da ni, duk sai in rude. Ka ga daren jiya ma na kasa yin barci saboda tunanin ka, wai mene ya sa haka ne?” Bashari ya Kyalkyace da dariya. “Yar Fulani ta yi wani sansaraKwai tana mamakin mene ne abin dariya a cikin maganarta, don ita tana ganin iyakar gaskiyarta ta fada. Can sai Bashari ya sake kallon ta da kyau sannan ya gyara murya ya ce, “Yarinya ‘yar Fillo, wannan abu da kike ji ya nuna miki saurayi kado ya yi kasuwa ke nan. A taKaice dai wannan abu shi ake kira soyayya.” Ta dukar da kai da fahimtar cewa lallai abin da ya fada fa haka ne, sai ta ce, “Ai ko kadan haka ba za ta yiwu ba.” Bashari da ke kashingide jikin bishiya, sai ya gyara zama ya ce, “Ko mene ne dalilinki na cewa hakan ba za ta yiwu ba?” Ta amsa da cewa, “Ya kai saurayi, shi so nauyi gare shi, ya fi dutse nauyi kuma ya fi teku zurfi. Yana da dadi da Kanshi da kuma haske. In kuma baayi sa’a ba, to shi so babban hadari ne, kuma ga yawan mahassada a cikin sa. Ya kai saurayi, idan muka shiga cikin kogin so ni da Www.bankinhausanovels.com.ng kai, to ina ganin ma abin zai yi wuya. Ka ga da farko dai kai ba dan Fulani ba ne, halayenmu da naku sun sha bamban. Mutanen gari za su rika zunden ka cewa ka auro ‘yar Kauye, sannan kuma daga ganin ka kai da mahaifinka masu wadata ne, mu kuwa talakawa ne.” Sai ya katse ta ya ce, “T’saya kada ki yi nisa. Ke Bingyel, ba ki da hujja ko daya, zan iya ci gaba da rayuwata gaba daya a riga ko daji saboda ke, in hakan kika fiso. Zancen ni ba Bafillatani ba ne ki kau da shi, in kuma zai fi miki dadi, to ni ma daga yau ina iya zama dan Fulani. Ya ke hasken wanda ya yi sa’a ya gan ki, maganar arziki da ki ka yi, to shi so babu ruwansa da arziki ko sarauta ko talauci, kuma ni ina ganin duk son da ya ke duba wadannan abubuwa, to ba hakikanin son gaskiya ba ne. ‘To wai ma in kina maganar arziki ne, shin kin san cewa mahaifinki da a cikin gari ya ke dole a kira shi Sarkin kudi? Ya ke farin cikina, ina so daga yau ki sani cewa babban abin da soyayya ke bukata shi ne alkawari. Ke in takaice miki ni na sadaukar da kaina zuwa gare ki, sai dai ko in ke kika ki ko kuma mahaifinki. Ni dai sai yadda kika yi da ni.” Murna ta lullube ‘yar Fulani, ta ce, “Ya kai masoyina, ni kuma na dauki alkawari in dai muna da Www.bankinhausanovels.com.ng rai, to babu mai raba mu. Sai dai matsala daya ce kawai nake ganin za ta iya kawo mana dan cikas.” Ya tambaye ta, “Wace irin matsala ce?” ‘Yar Fulani ta ce, “Ina kyautata zaton, ko kuma in ce maka mun riga mun yanke shawara nan ba da dadewa ba za mu bar wannan Kasar zuwa wata, don kwanciyar hankalinmu gaba daya. Akwai kanin Sarkin kasar nan wanda ya nuna cewa wai dole in so shi ni kuma na ki, kuma ga shi yanzu shi za a yi wa sarauta. Wannan ya sa za mu tashi mu bar masa Kasarsa da zarar an nada shi, kada ya zo ya ci mana mutunci.” Hakan ya tsunduma Bashari cikin tunanin irin rudanin da soyayyarsu za ta shiga. Ko kuma wane irin hali shi kansa zai shiga in har wani can daban ya aure ta? Ya shiga sake-sake a zuciyarsa yana cewa “In kuwa haka ne, to wannan dattijo da nake jiyya yana samun sauki za mu yi sallama in tsallake in bi Fulanin nan duk inda za su.” “Yar Fulani ta yanke masa tunaninsa ta ce, “Ya kai saurayina kana tunanin mene ne?” Sai ya ce mata, “Ke nake tunawa.” Ta ce, “To ai ga ni kusa da kai. Kuma ai mun riga mun yi wa juna alkawari.” Suka dubi juna suka yi wani murmushi a daidai Www.bankinhausanovels.com.ng lokacin da wancan dan Fulani da aka dauka don taya ta kiwo ya iso wurin. Samun su a cikin irin wannan hali wanda ke nuna cewa akwai soyayya ya sa zuciyarsa Kuntata, ransa ya baci, ya rasa abin da ke yi masa dadi a duniya. Ya wuce dai bai ce komai ba. Suka zauna nan gindin bishiya, ta fara koya masa yadda ake busa sarewa. La’asar sakaliya suka tashi suka koma riga cike da farin ciki da annashuwa. Wancan dan Fulani makiyayi kuwa sai da ya san yadda ya yi ya kewaya ya je ya sami Ardo ya tsegunta masa cewa ya ga ‘yarsa tana zance da wani bako kado. Nan da nan Sarkin Fulani ya kwabe shi tare da umurnin cewa kada ya sake jin irin wannan magana daga bakinsa. Tun daga wannan rana kuwa dan Fulani ya shiga Rulle-Kulle a cikin zuciyarsa, amma fa ba Kullin alheri ba. Dawowar wadannan yara sai suka tarar da Sarkin Fulani a wurin mara lafiya, wanda a karon farko ya fara samun sauki har an fito da shi yana jingine a jikin dannin gidan. Murna ta kama Bashari duk da cewa har yanzu mara lafiyar bai fara iya magana ba, sai dai daga hannu kawai. Da Magriba ‘yar Fulani ta kawo wa Bashari dambu ya ci, bayan Isha’i kuma, sai ta dauko tabarmarta ta je can kusa da bukkarsa suka zauna suna ta zantawa har Www.bankinhausanovels.com.ng dare ya fara shiga sosai kafin ta tashi ta shige tata bukkar. Haka makamancin wannan al’amari ya yi ta faruwa, in Bashari ba ya wurin majinyacinsa, to yana cikin daji wurin ‘yar Fulani suna hira. A haka sai da suka sami kusan watanni uku. Yanzu Bashari ya kware sosai a fagen busa sarewa ta yadda in yana busawa, sai ka ga shanu sun kewaye shi a cikin daji suna saurara. Soyayya kuwa tsakaninsa da ‘yar Fulani sai abin da ya kara gaba. Mara lafiya kuma ya gama murmurewa, sannan duk abin nan da ake yi bai taba gayawa Bashari ko kuma sabon abokinsa Sarkin Fulani cewa shi ne Sarkin wannan kasa ba. Wata rana suna cikin hirarsu irin ta dattijai, sai ya cewa Sarkin Fulani, “Babu shakka akwai soyayya a tsakanin dana da ‘yarka, ko mene ka gani?” Sai Sarkin Fulani ya ce, “Ai niba ni da ta cewa, abin da ‘yata take so shi nake so, don na fi son farin cikinta fiye da komai. Ita da dan’uwanta fa kadai suka rage gare ni. Akwai dai wani abu ne da muke hange. Wato Kanin Sarkin wannan kasa tamu yana son wannan ‘ya tawa amma ita ko kadan ba ta Kaunarsa, to kuma ga shi goben nan shi za a nada Sarki, kuma na tabbata Www.bankinhausanovels.com.ng zai kyale mu ba. Saboda haka muke ta shiryeshiryen washegarin nada shi mu kora shanunmu mu bar masa Kasarsa don kada ya tozarta mu. Ba don rashin lafiyarka ba ma da tuni mun yi nisa. Dama ka san shi kanin Sarki yana shakkar tsohon Sarki ne saboda ba zai yardar masa da zalunci ba. To yanzu abu ya lalace, don ko shiga gari da na yi ranar kasuwa, duk mutane suna ta dari-dari kan wannan sarauta tasa. In ka ga irin mutanen da aka gayyato don bikin nadin ma kawai abin zai ba ka takaici, ko ina gari ya cika da shaidanun mutane suna ta sheKe ayarsu, kai abin babu kyau. Babu shakka mun yi rashin adalin Sarki.” Jin haka sai Sarki ya ce masa, “Ai komai na Allah ne. In niyyarsa ba ta alheri ba ce sai ka ga wani abu ya faru, sai dai kuma akwai wani abu da nake roKo ka yi, wato Kokarin halartar bikin nadin sabon Sarki, don akwai hikimar da ta sa na ce maka haka. Ni da dana ma duk za mu halarta,in Allah Ya so.” Sarkin Fulani zai yi jayayya, sai kuma ya lura da yanayin da abokin nasa ya yi masa magana. Sai ya yanke shawarar yin shiru tare da amincewa. Sarki Shahzad ya fara tunani cewa, “Ikon Allah, yanzu har watanni uku sun cika, ashe ni lissafina ba daidai ba ne.” Www.bankinhausanovels.com.ng Bayan kiwo su Bashari suka koma gida. Yana kammala dauraye jikinsa sai ya shige cikin bukkarsu ya tarar da Sarki zaune yana lazimi. Bayan ya kammala, sai ya gaishe shi cikin girmamawa, shi kuma ya amsa cike da murmushi. Sarki ya ce, “Ya kai dana Bashari zauna ina son mu yi magana ni da kai.” Bashari ya nemi wuri ya zauna yana saurare a tsorace abin da Sarki zai ce, don shia zatonsa ko ya yi wani laifin ne. Ya ci gaba da cewa, “A wancan lokaci da wannan masifa ta faru da ni na san wadanda nake tare da su, har suka yi Kokarin salwantar da ni, wato ba barayi ne suka nemi halaka ni ba kamar yadda mutanen gidan nan suke zato. Saboda haka ina son ka ba ni labarin hakikanin abin da ya faru tun daga farko har karshe. A takaice kuma ina son in san labarinka kai kanka.” Bashari ya kwashe labari bai rage komai ba ya ba Sarki, tun daga fitowarsa gida har zuwa zamansu gidan Sarkin Fulani da kuma dalilin da ya sa ya yi Karyar cewa barayi ne suka nemi halaka shi har ma don su yarda ya ce musu mahaifinsa ne. Sarki ya ce, “Ya kai dana, na gode maka, Allah Ya saka maka da alheri, Yasaka gama lafiya.” Daga nan sai Sarki ya ba Bashari labarinsa tare da Www.bankinhausanovels.com.ng sanar da shi cewa gobe tun Asubahin fari za su nufi gari, kasancewar bayan Sallar Azahar ne a kan yi nadin sarautar. Ya kammala da cewa Bashari, “Sai dai kuma ina fata wannan labari namu ya ci gaba da kasancewa sirri har zuwa lokacin da za a bayyana shi.” Suka sami Ardo suka yi masa godiya mai tarin yawa tare da sanar da shi cewa tun Asubahin fari za su tafi. Sarki kuma ya Kara jaddada roKonsa ga Sarkin Fulani a kan cewa lallai yana buKatar ya halarci wurin nadin sabon Sarki gobe. Bashari da ‘yar Fulani kuwa har kuka suka yi saboda za su rabu. Ya yi mata alKawarin cewa za ta rika ganin sa, zai rika zuwa duk inda take. Asuba na yi suka kama hanya. Bayan sun dan fara tafiya kadan, sai Sarki ya sauya shigarsa ya yi irin ta makiyayan daji, sannan ya kawo wani rawani ya nade kansa ruf, ba ka ganin komai sai idanu. In ka gan shi sai ka rantse cewa wani Ridahumin bakauye ne. Suka isa cikin gari, sai suka ga an Rayata shi da tutoci da sauran kayan Kawa, ko ina ka duba sai gungun baki, masu goge na yi, masu molo da dara na yi, ‘yan caca da masu bori kuwa kowa ya baje hajarsa. “Yan daudu da karuwai sai rangwada suke suna ta kurkurdawa tsakanin jama’a suna sheKe ayarsu wai Www.bankinhausanovels.com.ng nasu ya kama, gari ya zama nasu. Sarki na gaba Bashari na biye da shi, ba su zame ko ina ba sai gidan Waziri, suka tarar da zaurensa a bude kuma ga dukkan alama yana ciki, saboda haka sai suka shiga. Suka tarar da shi zaune a kan buzu ya yi tagumi, cike da bacin rai. Sarki ya ce, “Salamun alaikum ya kai Waziri.” Waziri ya yi wuf ya dubo zuwa gare su da mamaki don ya ji muryar ta yi kama da ta Sarki. Ya mayar da sallama sannan ya ce, “Ku su wane ne, kuma mene ne labarinku?” Sarki ya warware nadinsa. Waziri ya yi tsalle ya tsallake kujeru ya yi cikin gida a guje yana cewa, “Ni mene ne nawa a ciki za ka yi mini fatalwa? Je ka can wurin Kaninka shi ne zai haye maka karaga.” Da Sarki ya ga cewa lallai Wazirinsa ya firgita, sai ya zauna kan kujera tare da umurtar Bashari cewa shi ma ya zauna. Zamansu ba dadewa sai ga dan Waziri ya shigo da cikakken tabbacin cewa mahaifinsa ne a cikin zauren, amma sai ya yi arba da Sarki a zaune, mamaki ya kama shi. Ya yi tirya-tirya zai gudu, sai Sarki ya kira sunansa, “Abdallah.” Sai ya tsaya ya sakankance cewa lallai wannan Sarki ne, saboda haka sai ya yi gaisuwa. Sarki ya ce masa, “Ka je ka cewa Waziri ina son ganin sane.” Yaro ya shiga cikin gida ya tarar da mahaifinsa wato Waziri cikin halin tsoro, yana ta kyarma. Waziri ya tambaye shi, “Ia ina ka biyo da za ka shigo? Ba ka ga fatalwar nan ba a zaure?” Yaro ya ce, “Baba ka kwantar da hankalinka, ba fatalwa ba ce, Sarki ne da kansa ya ce yana son ganin ka. Ina ganin gara ka je, wataKila akwai wani al’amari ne wanda muka kasa ganewa.” Da kyar Waziri ya fita. Sarki ya ce masa, “Haba Waziri, ko dai da ace ni fatalwa ce ka san ba zan cuce ka da komai ba.” Ya dafa kafadarsa ya ce, “Kwantar da hankalinka.” Waziri ya dan sami natsuwa, ya yi gaisuwa cike da mamaki. Sarki ya dan gutsura masa labarin a taKaice Kwarai sannan ya ce masa ya tashi yanzu babu lokaci. Ya ce, “Abin da nake so da kai yanzu Waziri, ka je ka kawo mini kayan yaKi, amma fa kada wani ya sani. Kuma ka gargadi yaron nan Abdallah ya kame bakinsa.” Aka kawo wa Sarki sulke ya shige, haka nan shi ma Waziri, don ko data Baci. Jama’‘ar gari da baki, babba da yaro, mace da namiji, duk kowa ya hallara a filin nadin Sarki. Sarkin Fulani Www.bankinhausanovels.com.ng da’yarsa su ma suna cikin ‘yan kallo. Yanzu Waziri da sabon Sarki kawai ake jira don aci gaba da gudanar da harkokin nadi. Jimawa kadan sai aka ji tambura na tashi, sabon Sarki ya tunkaro ke nan. Ya zo ya zauna, yanzu sai dai masu nadi kawai su fara aikinsu. Kuma a daidai wannan lokaci zuciyar Sarkin mai jiran gado tuni ta harzuka irin yadda wai har Waziri ne ya yi sakaci har ya riga shi fitowa. Ya Kulla a cikin ransa cewa ana nada shi cikin jawabinsa na farko zai fara ne da sauke Waziri ya nada nasa. Wato an sami dalilin da za aba jama’‘a na sauke Waziri; komai ya zo da sauki ke nan. Can sai aka hango wani mutum ya keto fili a kan doki ga Waziri biye da shi tare da wani kyakkyawan saurayi. Kuma shi wannan mahayi ya rufe fuskarsa, sai idanunsa kawai ake iya hangowa. Mutane sai suka rika zaton cewa wannan lallai wani babban amini ne na masarautar ya halarci wurin nadin Sarki, shi ma sabon Sarki haka ya ke zato. Saboda haka nan da nan aka ba shi kujera ya zauna a cikin tantin da Sarki ya ke. Albarkacinsa shi ma Bashari ya sami zama cikin wannan babbar inuwa. Ita ko Bingyel ‘yar Fulani da ke can cikin taro da ta hango saurayinta sai ta fara tsalle tana daga hannu wai ko zai hangota, amma ina, saboda yawan jama’a. HMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 13 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA BY HARUNA USMAN Jun 28, 2022 0 0 Add to Reading List YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 13 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng A JIYA MUN TSAYA Can sai aka hango wani mutum ya keto fili a kan doki ga Waziri biye da shi tare da wani kyakkyawan saurayi. Kuma shi wannan mahayi ya rufe fuskarsa, sai idanunsa kawai ake iya hangowa. Mutane sai suka rika zaton cewa wannan lallai wani babban amini ne na masarautar ya halarci wurin nadin Sarki, shi ma sabon Sarki haka ya ke zato. Saboda haka nan da nan aka ba shi kujera ya zauna a cikin tantin da Sarki ya ke. Albarkacinsa shi ma Bashari ya sami zama cikin wannan babbar inuwa. Ita ko Bingyel ‘yar Fulani da ke can cikin taro da ta hango saurayinta sai ta fara tsalle tana daga hannu wai ko zai hangota, amma ina, saboda yawan jama’a. ZAMU TASHI Sarkin Fulani ya tambaye ta dalilin daga hannunta, sai ta ce, “Dubi babban bakon can da ya zo yanzu, kusa da shi wane ne zaune?” Dattijo ya kyalla ido sosai, ya ce, “Ai kuwa Bashari ne, yaya aka yi ya sami zama cikin sarakuna?” Bayan an kintsa, sai aka fara al’adun da aka saba na nadin Sarki, aka kammala aka yi addu’o’i sannan aka dauki rawani wanda nada shi a kan zababben Sarki shi ne tabbatuwar sarauta. Sai suka ji wata irin tsawa tace, “Kul! Kada a nada rawanin nan.” Duk sai hankalin jama’a ya komo ta inda tsawar ta fito, sai aka ga ashe mahayin nan ne da ya zo dazu. Nan take sai ya bude fuskarsa. To fa, da mutane suka ga Sarkinsu ne da suke matukar Kauna, sai shewa mai cike da mamaki ta cika wurin. Wadanda ke kusa kuwa sai suka fara zubewa kasa don gaisuwa. Wasu kuma cewa suke yi fatalwa ce. Kanin Sarki saboda rudewa sai ya jawo wata gorar ruwa da ke kusa da shi yana wanke fuska don tunanin ko idanunsa ne ke zagi. Wuri ya rude haya-haya sai Sarki ya ce, “Jama’a don Allah a saurara, akwai labari.” Wuri ya yi tsit, Sarki ya cewa Bashari ya tashi ya labarta wa mutane abin da ya faru. Ya mike ya labarta Www.bankinhausanovels.com.ng ba tare da rage komai ba, yana ma gab da kammalawa ne sai kawai ya hango ‘yar Fulani a cikin taro ita da mahaifinta, sai ya kira su ya nuna wa jama’a ya ce, “Wadannan bayin Allah a gidansu muka yi jinyar Sarki har na misalin wata uku.” Da mutane suka ji wannan labari sai takaici ya kama su, wasu ma har kuka suka yi ta ribzawa. Nan fa mutane suka nemi yin hargowa suna cewa, “A ba mu su mu kashe! A tsire su! A dafa su da ransu!” Sarki ya sa aka kama su don gudun abin da jama’a za su iya yi musu a wurin, amma da ya ke mutane sun san halinsa na tsananin tausayi da yafiya, sai nan take suka birkice a kan cewa lallai a wurin suke bukata a mika su zuwa ga Alqalin Kasar ya yanke musu hukunci kafin a ci gaba da komai don kuwa maciya amanar kasa ne. Sarki ya rasa yadda zai yi, kuma ya tabbatar yadda hankalin jama’a ya tashi, matukar ya hana wannan bukata tasu, to komai na iya faruwa. Akan dole ya amince aka mika wa Alkali shari’ar. Shi kuma ba tare da bata lokaci ba, ya ba da umurnin a tafi da su jakara a tsire su gaba daya. Jama’’a dai ba su sakankance ba sai da dubban mutane suka bi su a baya suna tsine musu albarka. A takaice ba a kyale su ba sai da aka tabbatar sun sami masauki na dundundun a lahira Www.bankinhausanovels.com.ng tukuna, sannan aka dawo filin nadin sarauta. Sarki Shahzad ya yi godiya saboda irin kaunar da aka nuna masa, sannan ya kammala jawabinsa da cewa, “Jama’‘a kun dai san ba ni da da, to daga yau ku shaida wannan yaro Bashari ya zama dana, shi ne magajina.” Fili sai sowa, mutane suna cewa, “Mun amince! mun amince!” Aka fa shiga shagalin dawowar Sarki abin kamar Sallah. Bata gari kuwa nan da nan kowannen su sai Kokarin barin gari, murna ta koma ciki. Bayan an gama natsawa sai Sarki ya kira Bashari ya ce masa, “Ya kai dana, ina rokon ka da ka kare mutuncinka a cikin wannan al’umma, wato ka kiyaye mana mutuncin da jama’a ke ganin mu da shi, kar ka yi abin da za mu ji kunya. Daga yau zan fara karantar da kai ilmi na addini da sauran harkokin yau da kullum, in Allah Ya yarda. In kuma na ga ka kware tare da gogewa game da sha’anonin mulki, to akwai abin da nake shawartawa a cikin zuciyata.” Bashari ya yi godiya. Sarki ya ci gaba da cewa, “Abin da nake bukata da kai yanzu shi ne, ka je rigar Sarkin Fulani ku zo tare da shi.” Nan da nan Bashari ya zaburi doki sai rigar Fulani. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya ko yi saa ya tarar Ardo Jumare zai fitake nan, ya – gaishe shi cikin girmamawa. Ardo ya ce, “Bashari amma ku mutanen birnin kuna da wayo, ashe Sarki ne muka zauna da shi na tsawon wata uku amma bamu sani ba?” Shi dai Bashari bai iya cewa komai ba sai dai murmushi kawai. Bashari ya ce, “Allah Ya taimaki Ardo, mai martaba Sarki ne ya ce don Allah yana da bukatar ganin ka.” Sarkin Fulani ya ce, “Yaro, waye zai Ki kiran Sarki?” Bashari ya fara shafa keya yana cewa, “Kafin ka kintsa bari in dan shiga daji in duba kanwata a wurin kiwo, mun kwana biyu ba mu gaisa ba.” Sarkin Fulani ya ce, “E ita ma ko dazun nan take ta maganar ka, ashe dan halas kana tafe.” Shigar Bashari daji fa ya ga ‘yar Fulani sai hira ta sarke, bai farga ba sai da rana ta fara shigowa cikin inuwar da suke, sannan firgigi ya ce, “Ke! Na bar yana can yana ta jira na za mu tafi wurin Sarki da shi. Kin ga kin sa na zama mara kirki ko? Na bar tsofaffi suna ta jira.” Suna cikin haka sai ga dan Fulanin can mai taya ta kiwo ya zo, ya yi niyyar daga sanda ya sheme Bashari sai dai wata zuciya ta hana shi. Ya wuce dai bai ce Www.bankinhausanovels.com.ng komai ba. Ardo da Bashari suka rankaya zuwa gidan Sarki a birni. Suka yi gaisuwa ya amsa musu da irin murmushin nan nasa mai ban sha’awa kuma mai cike da Kauna. Ya taso daga kujera ya rungume Sarkin Fulani, ya ja shi don su zauna kamar yadda suka saba yi a riga lokacin da ya ke jinya. Idan ka gan su sai ka dauka wa ne da Kani. Ga su farare, masu fararen gemmiai da saje. . Bashari ya nemi izini ya fita daga waje. Bai yi nisa ba don ya san zaa iya neman sa. Sarki ya dubi Sarkin Fulani ya ce, “Ardo.” Ardo ya amsa, “Ran Sarki ya dade.” Sarki ya ce, “Ardo daga yau ina son in sanar da kai cewa ka zama dan’uwana, tsakanin ni da kai babu iso. ‘Tun lokacin da na zauna da kai na fahimci cewa kana da ilmin addini da mutunci da karimci. Saboda haka na ba ka amanar kaina, matukKar ka ga na yi wani abu wanda ya kamata a ce an kwaba mini amma ka kyale ni, to ban yafe maka ba. Ni da ‘yan majalisata mun zauna mun yanke shawarar nada ka Sarkin Fulanin wannan Kasa baki daya, maimakon Sarkin rigarku kawai. Sannan kuma yanzu kana daya daga cikin ‘yan majalisar Sarki. Za a yi nadin ne ba da dadewa ba, kamar Www.bankinhausanovels.com.ng Juma‘a mai zuwa. Kana da ikon dawowa gari da zama duk lokacin da ka ji hakan ya yi maka dadi. Na riga na sa an shirya maka gidanka yadda ya kamata. Kuma akwai wasu kayayyaki da na tabbatar cewa za su dace da kai na sa an shirya su yanzu, in za ka koma zaa bikadasu.” Sarkin Fulani tun yana godiya har ya koma ya yi shiru, ya zura wa Sarki ido kawai kuru. Can sai suka koma suka ci gaba da hirarsu kamar yadda suka saba. Sarki ya ce, “Don Allah in Ardo ba zai damu ba, ina da wata bukata guda daya ko kuma alfarma da nake nema ayi mini.” Jin haka sai Sarkin Fulani ya ce, “Ran Sarki ya dade ai ka wuce nan. Fadi abin da kake bukata kawai in har lallai kana da bukatar fada din, amma ko ma mene ne nina amince.” Sarki ya ce, “Ina so ne ka aurar da ‘yarka Bingyel ga dana Bashari.” Sarkin Fulani ya ce, “Na ba shi. To ai ni wannan kamar Karin girma ne a gare ni. ‘Yata ta auri dan mutunci kuma dan Sarki mai adalci.” Abin ka da dattijai, nan suka yanke shawarar za a yi bikin cikin wata biyu masu zuwa. Shi ma abin da ya sa za a dan dauki lokaci haka shi ne dalilin da Sarki ya Www.bankinhausanovels.com.ng bayar cewa wasu daga cikin manyan bakin da za a gayyata daga nesa suke, kuma bai kamata a ba su dan gajeren ‘okaci ba, don baa san irin hidimomin da ke gabansu ba, musamman kasancewar mafi yawancinsu ba su dade da barin garin ba a dalilin nadin sarauta da suka zo. Sarki ya yi kiran Bashari ya ce masa, “Ai sai ka ba da tukuici, babanka Sarkin Fulani ya mallaka maka Kanwarka kake ce mata ko? To za a yi bikinku cikin wata biyu.” Bashari bai san lokacin da ya buga tsalle ba saboda tsananin murna, ya manta cewa a gaban Sarki ya ke, watakila kuma kasancewar don ya riga ya saba da su ne? Nan take ya fara zabgawa Sarki kirari da addu’a, “Hadari sa gabanka inda kake so. Allah dai Ya sa ka gama lafiya.” Ya juya wurin Sarkin Fulani ya yi godiya cike da kunya. Sarki ya yi magana, “Yauwa Bashari sai ka je da babanka ka nuna masa gidansa?” Sarkin Fulani da Sarki suka yi sallama, Bashari kuma na gefe ya kasa zaune ya kasa tsaye, har sai da suka fita suka nufi sabon gidan Sarkin Fulani. Bayan ganin gida sai ya rasa abin da zai ce, da Kyar Bashari ya ciyo kansa ya hau ingarman dokin da aka ba shi ya nufi riga, don da ya ce ne sai ya sake komawa ya yi wa Sarki godiya. Kafin Ardo ya isa gida, tuni Bashari ya kewaye a sukwane zuwa can cikin daji inda budurwarsa ke kiwo, don ya rigaya ya san cewa ba ta riga ta taso zuwa gida ba. Yana zuwa ransa a bace ya ce mata, “Kin ji wai za a yi mini aure nan da wata biyu.” Ta ce, “To mene ne amfanin ka zo ka fada mini? Da mana gaya maka ina ‘yar Fulani mai kiwo ina dan Sarki>” Bashari ya katse ta, “Af na manta ban yi miki albishir ba, Sarki ya yi wa babanki sarautar Sarkin Fulanin wannan kasar gaba daya, sannan kuma yanzu shi ne babban mai ba Sarki shawara na musamman.” “Yar Fulani tana jin haka sai cikin bacin rai ta ce, “Da ma mahaifina ai Sarkin Fulani ne, kuma wannan abokantaka da Sarki babu wani amfani ko kuma tabbas ciki, don da a ce yana son sa ai ba zai hana dansa ya auri ‘yarsa ba. To ni zan fada wa babana kada ya amshi ko daya daga cikin abin da Sarki ya ba shi, kuma jibi-jibin nan za mu tattara mu bar muku Kasarku, kai kuma ka je ka auri Sarauniyar kyau ta duniya. Da ma an ce mini ku kado ba ku da alkawari amma Www.bankinhausanovels.com.ng ji ba, na ga kamar kai daban ne. Amma babu komai.” Ya jawo sarewarsa ya fara yin wata irin busa da sukan yi tare, sai ta sa hannu ta fisge, ta ce, “Kaicona da na koya maka yadda ake busa wannan abu, ga shi yanzu za ka je kana busa wa wata.” Bashari ya Kyalkyace da dariya sannan ya ce, “Ke, ba na son shirme. Ga sanarwa ta musamman, Bashari dan Salihu kuma dan Sarki Shahzad, kado, zai auri Bingyel ‘yar Fillo a cikin watanni biyu masu zuwa. Kuma ga ta nan a gabansa tana kallon sa har an gama shirya komai tsakanin Sarki da mahaifinta.” Murna kuma ba sai an labarta ba. Sai ya kasance a duk ranar da babu karatu ko kuma wata hidima da zai yi wa Sarki, to Bashari yana wurin ‘yar Fulani a cikin riga suna tsimayin bikinsu. Ji suke yi kamar su jawo ranar. Sarkin Fulani kuwa tuni ya yanke shawarar cewa sai an yi bikin ‘yarsa sannan zai koma cikin birni ya tare. Ana nan dai har ya kasance yanzu saura kwana uku kacal a daura auren. Bashari ya nufi riga don ganin budurwarsa, amma abin da ya tarar ya yi matukar ba shi mamaki, wato bukkokin gidan Sarkin Fulani ne gaba daya a Kone. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya yi tunanin samun wani Bafillatani ya tambaya amma sai ya sauya shawara don babu kowa a wurin, kuma kasancewar tsakanin gidan Sarkin Fulani kafin a sake samun wani gidan akwai tafiya mai ‘yar tazara. Ya ji kamar zai zautu don tsananin rudewa. Ya nufi inda suke kiwo, ba kowa, ya dauko sarewarsa yana busawa ko ta ji ta amsa, amma shiru. Sai ya yankewa kansa shawarar cewa lallai duk yadda aka yi ‘yar Fulani yaudarar sa ta yi ba auren sa za ta yi ba, tun da dai ga shi sun kora dabbobinsu sun gudu. Kuma abin mamaki ita da dattijo babanta. Ya rasa inda zai sa kansa. Ya sake komawa can riga din amma dai abin da ya bari shi ya tarar. Daga Karshe dai ya dauki dangana. Ya hau dokinsa don komawa cikin gari. Ya fara tafiya ke nan sai ya hango tarin wani abu a cikin ganyayyaki. Da ya matsa sai ya ga ashe Sarkin Fulani ne kwance male-male cikin jini, ya Kusa da shi kuma Harande ne dansa, Kanin ‘yar Fulani, shi wannan ma ba sai an tambaya ba, daga gani ka san ya mutu. Ya gaggauta ya dora su a kan doki ya daure ya wuce gaba yana ja har cikin gari. Ya je ya ba Sarki labarin irin wannan abin bakin ciki da ya afku. Aka dauki Sarkin Fulani aka shiga da Www.bankinhausanovels.com.ng shi. shi don fara yi masa magani, shi kuma marigayin aka yi masa janaza. Zaton sarki yafi karfi a kan cewa ko makiyansa ne suka yi wa Sarkin Fulani wannan aika-aika don irin taimakon da ya bayar wurin jinyarsa. Suka yi zaton shi ma Sarkin Fulanin sun halaka shi ne, suka kwashe masa dabbobi, suka kashe masa da, watakila ma ita kanta yarinyar ba a nan suka kashe ta ba. Daga Karshe dai aka yanke shawarar saurarawa har sai Sarkin Fulani ya farfado don gane hakikanin wannan danyen aiki. Kafin nan sai aka baza jarumai, Kudu da Arewa, Gabas da Yamma ko za a dace a samo dabbobin tare da kamo wadanda ke kora su kafin su Ketare kasa. Kana ganin Bashari ka san yana cikin tashin hankali, don duk ya fita hayyacinsa. A kullum yana cikin dajin nan inda suke kiwo da ‘yar Fulani, wani lokaci ya dauki sarewa yana wata irin busa wanda duk rashin tausayinka za ta iya sa ka hawaye, in ma ba ka barke da kuka ba. Bayan misalin kwana uku da faruwar lamarin, sai aka samu Sarkin Fulani ya farfado yadda zai dan iya magana. Aka tambaye shi abin da ya faru, sai ya rika nuna wa Bashari alama, hadi da ‘yan kalmomin da ke iya fitowa daga bakinsa cewa ita ‘yarsa ba a kashe ta Www.bankinhausanovels.com.ng ba An tafi da ita ne, kuma ba kowa ne ya aikata wannan ba ta hanyar dauko jingar miyagu, sai Jae, wato dan Fulanin nan da ke taya su kiwo. Jin wannan fa sai hankalin Bashari ya tashi. Nan take ya nemi izinin Sarki cewa yana son a ba shi dama ya je ya nemo ta duk inda take, Sarki kuwa ya amince. Aka hada shi tare da jarumai dari da isasshen guzuri. Ya yi sallama bayan an yi masa addu’ar samun dacewa. Abin da ya fara yi sai ya koma rigar su Sarkin Fulani, daga nan sai ya wuce inda suke kiwo ya daga hannunsa ya nuna wa jarumansa Kudu ya ce, “Ina zaton ‘yar Fulani wannan hanyar aka bi da ita, saboda haka nan za mu bi.” Ya wuce gaba suna biye. Kwana tara suna tafiya ba dare ba rana, sai dai in gajiya ta yi yawa a tsaya a huta. Kusa da kan iyakar Kasa sai suka hango shanu fululu farare fat, Bashari ya cewa jama’arsa su dakata. Ya lababa har sai da ya kai kusa da dabbobin sosai ta yadda zai iya tantancewa, kuma cikin gaggawa ya tabbatar wa kansa cewa babu shakka wadannan shanun su ‘yar Fulani ne. Sai dai kuma abin mamaki ga shanun nan su kadai suna tsaye babu kowa tare da su. Saboda haka sai Bashari ya yi zaton ko sun ya da zango ne don hutawa. Www.bankinhausanovels.com.ng ya koma zuwa ga jama’arsa ya ba su izinin yi wa yankin wurin gaba daya zobe amma cikin dabara. Shi kuma Bashari sai ya nufi cikin dabbobin shi kadai. Dan Fulani da sauran abokansa ashe duk suna kan bishiyoyin da ke wurin, kuma ganin Bashari ya nufi cikin shanu sai suka dudduro. Murna ta rufe Ja’e dan Fulani kasancewar yau ga shi ga Bashari su kadai, zai aika da shi lahira. Da ma tun asali shi dan Fulani ya rabi Sarkin Fulani ne kan nufinsa na samun damar lallaBar ‘yar Fulani ta aure shi har ya sami kusantar dukiyar, to ga shi wannan kadon ya shigo duk ya lalata masa shiri, yana neman tashi a huhun-ma’aho. Wai har kado zai aure yarinya shi kuma Ardo zai koma cikin birni. Saboda haka sai ya yanke shawarar gayyato abokansa suka zartar da wancan danyen hukunci, suka sace yarinyar suka tattara dukiyar gaba daya suka gudu. Daga dirowar dan Fulani sai ya fara surfa wa Bashari ashariya tare da cewa, “Yau kwananka sun Kare.” Amma kafin shi da mutanensa su isa wurin Bashari, tuni askarawa sun kawo kan su. Sun yi Kokarin kariyar kai wanda a sanadin haka, biyu daga cikin Bata-garin suka rasa rayukansu, aka kama sauran har da jagoransu dan Fulani. Bashari ya tambaye shi inda’yar Fulani take, amma takaici da taurin kai suka hana shi magana. Aka yi aka yi amma ina. Daga karshe dai Bashari ya tunzura ya ce su yi ta bugunsa ko zai mutu shi ake so ya mayar da jawabi ba sauran abokansa ba. ‘Yan cika aiki suka fara aikinsu, har sai da dan Fulani ya tabbatar da cewa yana gab da tafiya kiyama matukar bai yi magana ba, sai ya ce zai yi magana. Ya ce shi dama a cikin zuciyarsa ya san cewa ba shi da wata cikakkiyar bmkata ta auren ‘yar Fulani. Kuma abin da kawai ya sa bai kashe ta ba tun farko saboda ya tabbatar da cewa in ya sayar da ita, to zai sami isasshen guzuri da Karin dukiya don tana da kyau. Ya ce kwana biyar ke nan da ya sayar da ita dinare dubu uku ga wasu fatake, kuma sun riga sun tsallake Kasa da ita. Ya nuna hanyar da suka bi. Bashari ya ware mutum talatin daga cikin askarawansa, ya ce su kora shanun da masu laifin su kai su wurin Sarki, kuma su sanar da shi cewa shi ya shiga cikin wata kasa neman ‘yar Fulani don kuwa an sayar da ita. Aka yi wa dan Fulani daurin goro shi da abokansa hudu da suka rage, aka kama hanyar babban birni da su. Bashari kuwa da sauran jama’arsa sai suka bi hanyar da aka nuna musu, suka fara tafiya kwana da kwanaki. Kwatsam ba zato ba tsammani sai suka shiga wani yanki cikin wata kasa wanda babu komai cikin sa sai rairayin hamada. Amma tunanin cewa zai Kare da wuri sai suka yi ta kutsawa ba dare ba rana har dai guzurin ruwansu ya Kare, suka fara mutuwa da daidai da daidai. Babu damar komawa baya, gaba kuma ba a san yawan nisa ba. Kafin kwanaki kadan duk sun fadi sun mutu in banda Basharida mutane shida kawai. Baa . ma maganar dawakansu don yanzu babu ko daya. Allah cikin ikonSa sai aka yi sa’a wani dan Sarki ya Zo zai wuce ta hamadar. Ya ci karo da mutane duk sun marmace, ya ce a bincika ko akwai masu sauran shan ruwa, shi ne fa aka samu aka ceci Bashari da sauran wadanda ke tare da shi. Aka ci gaba da tafiya ana jinyar su don duk ba su san inda suke ba. Bayan sun wuce wannan hamada sai suka iso bakin wata Korama wadda ke kewaye da korayen ciyayi laya-laya. A nan suka yada zango har aka kammala jiyyar marasa lafiya, suka murmure tare da dawowa cikin hayyacinsu. Ya yi wa dan Sarkin matukar godiya tare da labarta masa dalilin fitowarsa daga gida. Dan sarki ya ce, “Ashe duk kanwar ja ce, mu ma abin da ya fito da mu ke nan, soyayya Ce. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya fara ba Bashari labari cewa, “Sunana Amir. Ni dan Sarki me, wanda ya fada cikin wata irin matsananciyar soyayya. Mun yi alKawari ni da wannan yarinya cewa za mu yi aure bayan watanni uku, kawai sai yarinya ta Bace. Mun yi nema ni da rundunata da ‘yan leKen asirina cikin duniyar nan lungu-lungu ko za mu dace, amma ina? Mun fara yanke tsammani ke nan sai muka sami labarin cewa akwai wani shahararren Sarki a can Kasar Arewa wanda za a iya samun cikakken labari a wurinsa, don shi ma irin wannan ta faru ga ‘yarsa, ta Bata Bat. An ce wani Sarkin aljanu ne ke sace ‘ya’yan mutane kyawawa yana tafiya da su. Weannan shi ne dalilin da ya sa na karkato na fuskanto gida don in sake shiri mu tafi Kasar wancan Sarki don samo labari, daga can kuma mu wuce neman wannan barawo na ‘ya’yan mutane. Ba aljani ba ko Shaidan ne sai mun ga abin da ya ture wa buzu nadi.” A haka ayarin Amir dan Sarki ya mika, a kwanaa tashi har suka isa garinsu. Labarin dawowarsu ya bazu ko ina a gari, mata sai rafka guda suke ta yi, babu abin da ake ji ko ina sai kade-kade da wakewake; kowa yana ta murnar cewa wani nasa ya dawo. Dan Sarki da Bashari suka wuce unguwar dan Www.bankinhausanovels.com.ng Sarki don kintsawa kafin su je gai da Sarki. Cikin lokaci suka fito suka nufi fada, in ka ga samarin nan biyu sai ka dauka wasu taurari ne saboda irin kyan da Allah Ya yi musu. Sarki ya rungume dansa yana mai cike da murnar dawowar sa. Ya ba mahaifinsa labarin Bashari, shi kuma ya karbe shi cike da girmamawa. Sarki ya ce, “Ku dai samarin wannan zamani al’amarinku sai ku, yanzu kowannenku ya bar yankinsu, ya shiga cikin hadarin neman yarinya? Kun san halin mata kuwa? Ko da yake yanzu dai duk a Kyale wannan zance. Shin ka yi nasara game da abin da ka fita nema?” Yarima Amir ya ce, “A’a, Allah Ya taimaki Sarki, amma na sami labarin inda za mu iya samun labarinta. Shi ne na dawo in shirya in sake fita, an ce can kasar Arewa akwai wani Sarki wanda shi ma hakan ta faru ga ‘yarsa kuma an tabbatar cewa yana da cikakken labari. Daga wurinsa kuma sai in tsunduma duniya neman ta.” Da Sarki ya ji zancen dansa sai ya ce, “Ya kai dana, ina ji maka tsoron yawo cikin duniya, ka dai ga dan Karamin misalin abin da ya faru ga abokinka, mafi yawancin jama’‘arsa sun rasa rayukansu, kuma ga shi kai ne mutane suka sa wa ido a matsayin magajina. HMMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 14 BY HARUNA USMAN YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM'UNA BY HARUNA USMAN Jun 28, 2022 0 1 Add to Reading List YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 14 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sarki ya ce, “Ku dai samarin wannan zamani al’amarinku sai ku, yanzu kowannenku ya bar yankinsu, ya shiga cikin hadarin neman yarinya? Kun san halin mata kuwa? Ko da yake yanzu dai duk a Kyale wannan zance. Shin ka yi nasara game da abin da ka fita nema?” Yarima Amir ya ce, “A’a, Allah Ya taimaki Sarki, amma na sami labarin inda za mu iya samun labarinta. Shi ne na dawo in shirya in sake fita, an ce can kasar Arewa akwai wani Sarki wanda shi ma hakan ta faru ga ‘yarsa kuma an tabbatar cewa yana da cikakken labari. Daga wurinsa kuma sai in tsunduma duniya neman ta.” Da Sarki ya ji zancen dansa sai ya ce, “Ya kai dana, ina ji maka tsoron yawo cikin duniya, ka dai ga dan Karamin misalin abin da ya faru ga abokinka, mafi yawancin jama’‘arsa sun rasa rayukansu, kuma ga shi kai ne mutane suka sa wa ido a matsayin magajina. ZAMU TASHI Sai dai kuma soyayya ta rufe maka idanu ko mulkin ma naga kamar ba ka damu da shi ba. Kuma shi mulkin nan in ka bari ya Kwace maka, to ba za ka sami wani ba, amma ita mace kana zaune sai a kawo maka ko guda nawa kake buKata. Yanzu ma maganar da ake yi akwai wata yarinya da da na ajiye musamman don kai. Kuma na tabbata kyan ta da cikar halittarta in bai wuce na yarinyar da kake wahala a kanta ba, to ba ko zai gaza ba. Ka je yanzu bayan mun gama cin abinci ka gan ta.” Da dan Sarki ya ji zancen mahaifinsa, sai ya yi godiya sannan ya ce, “Ya kai babana mai girma, ina fata ka yi mini gafara a game da abin da zan fada.” Sai Sarki ya ce, “Aminci gare ka ya dana. Fadi jawabinka.” Dan Sarki ya ci gaba, “Godiya nake. To a cikin jawabin mai martaba ya ce akwai mata da yawa, sai dai kuma abin da Sarki ya sani ne cewa ko a cikin rigunan Sarki akwai guda daya wadda ya fiso. Haka ma dawakin Sarki da ‘ya’yansa. Haka nan ma a duk cikin abin da Sarki ya mallaka ballantana kuma cikin matansa. Saboda haka ya babana, ni yanzu hankalina yana wurin wata kuma ina ji a cikin raina cewa ban yanke tsammani ba. Ni yanzu in ba ita na aura ba, to gaskiya ina jin hankalina ma ba zai dawo kan sarauta ba. Ranka ya dade ita kuma waccan yarinya da ka tanadar mini, to na gode Allah Ya Kara girma, amma Baba ka yafe ni. Ni ko ganin ta ma bazan yi ba don na san ba zan so ta ba alhali masoyiyata na raye…” Bashari ya yi sauri ya dubi abokinsa ya kifta masa ido, yana mai masa nunin cewa ya bi a hankali, har ma a daidai nan Basharin ya katse masa magana ya ce, “A‘a, kai dai kada ka yi saurin yanke hukunci, ka bari ka gan ta mana.” Sarki ya ce, “Yauwa, ka ji magana ke nan.” Sarki na zaton lallai in ya ga yarinyar, to dole ya ji yana son ta ko da ba kamar waccan ba, ta yadda zaa iya lallaba shi ya aure ta. Daga nan ko ba komai zuciyarsa za ta fara rage tunanin waccan da baa san inda take ba. Aka gabato da abinci da kayan marmari iri-iri, a kan cewa in sun kammala Bashari zai raka abokinsa su shiga su ga yarinya. AMMa al’amarin yarinya ‘yar Fulani kuwa, lokacin da Ja’e mai yi wa mahaifinta kiwo shi da abokansa suka sassari mahaifinta a gabanta suna tunanin sun kashe shi kamar yadda suka kashe kaninta, to ita sai suka daure ta suka kada tare da shanu. A kan hanyarsu suka sayar da ita ga wasu fatake a kan dinare dubu uku. Da fataken da suka saye ta suka lura da kyanta, sai suka yi ta tattalin ta suna kulawa da ita yadda ya kamata har suka isa birnin Jagirgiri inda Sarki Mus’ab yake sarauta. Suka Ki kai ta kasuwa don wayo da kuma lura irin ta kasuwanci. Maimakon haka sai suka tsayar da shawarar tallatawa Sarki. Suka sa Bingyel ta yi wanka sannan suka kawo sutura da kayan kwalliya irin na alfarma suka ba ta ta fece ado. Babu shakka in ka gan ta za ka ce ko watakila tana cikin kyawawan aljanun nan ne da akan yi labari. Wadannan fatake ba su zame ko ina ba sai fada, aka yi musu iso suka shiga har wurin Sarki. Ita kuma yarinya ta rufe jikinta kaf har da fuska. Aka yi sa’a kuwa a ranar Sarki Mus’ab na matukar jin nishadi. Ya tambaye su dalilin zuwansu. Fataken nan suka rusuna, sannan sai babbansu ya ce, “Ran Sarki ya dade, haja ce irin taku ta manyan sarakunan duniya muka kawo maka, yarinya ce balagaggiya wadda har yanzu yarinya ce ba ta zama mace ba tukuna. Kyakkyawa ce wadda za ta iya bugawa da kowace mace a bangaren kyau.” Sarki ya umurci yarinya ta bude fuskarta, ai yana ganin ta sai ya zuba mata idanu kurui yana mamakin irin wannan kyau nata. Zuciyarsa ta fara sarke Www.bankinhausanovels.com.ng sarken cewa, “ tsarki ya tabbatar wa wanda Ya halicci wannan kyau.” Yace, “Nawa kuka sayi wannan yarinya?” Suka ce, “Dinare dubu uku ne Allah Ya ba ka yawan rai.” Sarki ya ba Ma’aji umurni cewa a ba su dinare dubu goma, sannan a ba kowannensu manyan riguna goma-goma, suka fadi suka yi godiya don tsananin murna da irin wannan sallama. Ita kuma yarinya Sarki ya sa aka shiga da ita cikin gida tare da umurnin cewa kada a kuskura a sa ta aikin komai, kuma a rika ba ta abinci na alfarma da isasshen kayan marmari don jikinta ya Kara kyau da ni’ima, tare kuma da sutura irin wadda ta dace da kyakkyawa irinta. Jakadiya ta ce, “An gama, ran Sarki ya dade.” Tun daga wannan rana da aka shiga da ‘yar Fulani cikin gidan Sarki, babu abin da ya sauya na irin halin Bacin ran da take ciki tun daga lokacin da dan Fulani ya yi musu wancan mugun alkaba’i. In ta tuna dan’uwanta da mahaifinta da a iyakar saninta ta tabbatar da cewa an kashe su a gabanta, da kuma saurayinta Bashari, duk sai abubuwa su dugunzuma su cakude mata a zuciya, sai ta fashe da kuka. A mafi yawan lokuta kuma da zarar hakan ta faru, to sai ta dauko sarewarta tana busawa, wata irin busa mai sa tausayi a wurin mai sauraren da ke da masaniyar yadda busa ke tafiya. Amma a wurin sauran gamagarin mutane, sai mutum ya ji busar kamar don sa nishadi ake yi, wanda hakan ya sa in ta fara sai mutanen cikin gidan Sarki duk su natsu suna ta saurare. Duk abin nan da ake yi da duk lokacin nan da aka dauka, Sarki bai taba shiga inda take ba. Sai dai duk lokacin da ya ji busa, to ya tabbatar da cewa ita ce. Kuma shi kansa yana matuKar jin dadin busar. Wannan shine al’amarin ‘yar Fulani. Amma shi Bashari mun bar shi a fadar Sarki yana cin abinci da abokinsa dan Sarki tare da Sarkin suna ta hira irin tasu ta saraki. Sarki na ta nuna musu irin kyan wannan yarinya da kuma KoKarin tausa dansa a kan cewa ya bar wa Allah, in waccan yarinya da ya ke nema an gan ta, sai ya yi ta biyu ko ta uku da ita. Shi kuma yaro yana ta kewaye-kewaye cikin kunya. Can sai suka ji busar sarewa na fitowa daga cikin gida, sai Sarki ya ce musu, “To, yarinyar da na tanadar maka ce ke wannan busa.” Suka yi tsit suna sauraro, shi kuwa Bashari sai tsigar jikinsa ta shiga tashi, ya tabbatar da yanayin busar kuma ya fahimci wadda ke yin ta. Ai nan take ya sa hannu cikin aljihunsa ya zaro tasa sarewar ya fara Www.bankinhausanovels.com.ng mayar da busa. Mamaki ya rufe Sarki da dansa, amma tun kafin su sami damar yin tambaya sai ga yarinya ta fito daga cikin dakinta a guje ta nufe inda su Sarki ke cin abinci, don ita ma ta riga ta tabbatar da wanda ke busar. Matan gida suka biyo ta a guje suna zaton ko ta zautu ne. Tana shigowa Bashari ya gan ta, ai bai san lokacin da ya tsallake Sarki da gudu ba ya nufi inda take ya tsura mata idanu. Kafin ka ce mene ne wannan, dukkan su sun yanke jiki sun fadi a sume saboda tsananin mamaki da kuma rashin zaton yadda hakan ta kasance a gare su. Aka zuba musu ruwan randa mai sanyi suka farfado, shi kuma dan Sarki sai ya fara labarta wa mahaifinsa cewa wannan yarinya da aka tanadar masa ita ce abokinsa ya fito nema, kuma Allah Ya sa abokin nasa ya dace. A nan Sarki ya sake hakikance cewa lallai soyayya ba Karamar aba ba ce. Bashari ya gabatar da abokinsa Amir dan Sarki ga ‘yar Fulani da irin taimakon da ya yi masa lokacin da suka fito neman ta. Ya kuma shaida mata cewa mahaifinta bai rasu ba yana nan yana samun sauki. Amir dan Sarki ya ce, “To ai faduwa ta zo daidai da zama ke nan, yanzu sai in kammala shirina na tafiya Kasar Arewa kawai. In na je na kai Bashari da ‘yar Www.bankinhausanovels.com.ng Fulaninsa gida, sai in wuce.” Bashari ya ce, “Haka daidai ne, amma maganar ka wuce ba ta taso ba, don kuwa in mun mika ta gida hankalin iyayenmu ya kwanta, to Kafata-Kafarka za mu je neman taka budurwar. A cikin hankalina ba zan taba samun natsuwa ba irin alherin da ka yi mini da kuma yanayin yadda Allah Ya Kaddara yanke wahalata sanadinka sannan kuma a ce in kyale ka ka tafi kai kadai alhali kuwa na san matsayin soyayya.” A haka rundunar dan Sarki ta mutum dubu ta motsa zuwa garin su Bashari. Aka fito taryar su har da Sarki da Sarkin Fulani don yanzu ya sami sauKi. Bingyel ta ga mahaifinta, ta ruga ta rungume shi suna kukan barka da arziki. Bayan sun sauka sai aka kawo Ja’e dan Fulani da sauran abokansa aka yi musu shari’ar fashi da makami da kuma kisan kai. Laifi ya tabbata a kansu, aka sa hauni ya dauke musu kawuna. Bashari ya ba Sarki labarin abokinsa yarima Amir da irin taimakon da ya yi masa tare kuma da labarin cewa shi ma yarinyar da zai aura ce ta Bata. Kuma yanzu zai wuce Kasar Arewa neman labari, yana son zai bi shi in ya so in sun gano yarinyar, sai su dawo gaba dayaa fara hidimar biki. Sarki ya ce, “Ni ban Ki ka raka abokinka ba, amma Www.bankinhausanovels.com.ng da sharadi, muna iya gaggauta daurin aurenku da Bingyel tukuna, bayan biki da kamar mako daya sai ku yi tafiyar ku.” Dole suka amince. Aka daura auren Bashari da ‘yar Sarkin Fulani, aka yi gagarumin bikin da a iyaka tarihin Kasar wanda aka sani, ba a taba irinsa ba. Sai dai kuma wani babban abin bakin ciki, ana gobe amarya za ta tare sai kawai aka ga wani abu ya zo ya sungume ta ya yi sama da ita, masu ihu na yi, masu jifa na yi, amma kafin ka ce haka, yarinya ta bace a cikin sararin samaniya aka daina ganin ta. Labarin bakin ciki da Bacin rai kuma dai ba sai an tona ba. Surutai suka cika gari iri-iri, wasu na cewa ai yarinyar Kashin tsiya gare ta ba ta da sa’a ne, wasu kuma cewa suke yi ai kyanta ya yi yawa ne, shi ya sa aljanu za su aure ta. Maganganu dai ba kai ba gindi. A karshe dai Sarki ne ya yi ta rarrashin Bashari da Sarkin Fulani a kan cewan Allah Ya so yadda aka ga yarinyar da farko haka ma za a sake ganin ta. Aka yi ta addu’ar Allah Ya bayyana ta tare da tona asirin wancan aljani mai sace ya ‘yan mutane. Yanzu kam tafiya zuwa Kasar Arewa ta tashi daga matsayin rakiya a wurin Bashari ta zama ta dole. Aka Kara musu runduna ta mutum dubu suka nausa, A kwanaa tashi cikin wata uku da kwana goma sha bakwai suka isa kusa da gari, suka aike wa Sarkin Kasar cewa su bakinsa ne, kuma ga su nan Karasowa. Kasancewar Wazirinsa ba ya nan ya tafi rangadi, sai aka turo wasu manyan hakimai suka tarbe su aka sauke su a gidan saukar manyan baki na Sarki. Su kuma tawagarsu suka yi tantuna a wajen gari, aka aike musu da shanu da awaki da sauran kayan abinci da na sha don su huta sosai. Bayan dan Sarki Bashari da abokinsa sun kintsa, sai suka tafi fada don yin gaisuwa, Sarki ya tarbe su cikin mutunci da girmamawa. Kowannen su ya labarta wa Sarki labarinsa tare da cewa abin da ke tafe da su shi ne don su sami labarin wancan aljani wanda aka ce a wurinsa ne kawai za su samu don shi ma hakan ta faru ga tasa ‘yar. Hawaye suka shiga gangarowa daga idanun Sarki shar-shar har sai da suka rude suna mamakin abin da zai sa dattijo kamar wannan kuka. Sai ya ce musu, ) “Ya ku ‘ya’yana, kun fama mini ciwon da ke cikin zuciyata ne, amma fa ba na ce kun yi laifi ba ne, don kuwa matambayi ba ya bata. Kuma gaskiya ne kamar yadda kuka sami labari cewa ni ma ‘yata tana can wurin wannan aljani ya sace ta. Allah dai Ya karya Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin aljanu Sham’una!” Nan Sarki ya kasa mallakar kansa, ya sake barkewa da kuka su kuma suka rika ba shi hakuri har sai da hankalinsa ya dawo tukuna. Daga nan sai yace musu, “Ku koma masaukinku, in Allah Ya so yau Wazirina zai dawo, shi ne zai ba ku cikakken labarin wannan maridi.” Suka yi sallama suka fita suna tausaya masa. Suka je bayan gari wurin jama’arsu, kowanne ya warware ‘yan matsalolin da suka taso, sannan da yammaci suka koma masaukinsu. Shigowar su gari sai suka ji gari ya rude da sowa da murna, da suka tambaya sai aka shaida musu cewa Wazirin gari ne ya dawo lafiya daga rangadi. Waziri ya shiga wurin Sarki ya yi gaisuwa. Bayan sun gama ganawa sai Sarki ya ce, “Waziri muna fa da bakin wasu ‘yan Sarki su biyu, sun zo ne don neman bayanin mugun aljanin nan da ya sace mana ‘ya. Su ma hakan ce ta faru gare su, saboda haka gobe in Allah Ya kai mu sai a shirya liyafa, ka yi hira da su don na ga samari ne tsarorin ka.” Waziri ya ce, , Allah Ya taimaki Sarki.” Da gari ya waye, dan Sarki Bashari da abokinsa yarima Amir suka nufi fada suka yi gaisuwa, suka koma gefe suna ta ‘yar tattaunawa. Can sai ga Waziri Www.bankinhausanovels.com.ng ya zo don yin gaisuwa. Sarki ya gabatar da Wazirinsa ga ‘yan Sarki, ai Waziri na waigawa don gaisawa da su sai kawai suka yi ido hudu da Bashari sai ya ce, “Bashari.” Bashari ya ce, “Na’am, Habu.” Sai suka rungume juna cike da farin ciki. Waziri ya labarta wa Sarki cewa wannan dan’uwansa ne wanda suka fito neman ilmi tare da shi. Ana cikin haka sai ga wani sakon ya shigo fada cewa ga wasu bakin nan sun zo, Waziri ya sa Madaki ya je ya tarbo su, suka shigo suka yi gaisuwa, kuma ga alama su ma neman labarin ne ke tafe da su. Sai jagoran bakin ya ce, “Don Allah Bashari ne da Habu ko kuwa idanuna ne ke yi mini gizo?” Waziri Habu ya ce, “Ba gizo ba ne, gaskiya ne idonka ya nuna maka Yahaya.” Bayan duk an kammala gabatar da juna, sai Sarkiya ce, “Lallai yau babbar rana ce a gare mu, saboda haka a buga tambari akwai Kasaitacciyar walima.” Sarki ya gode musu sannan ya alKawarta musu cewa matukar dai Allah Ya fitar da wadancan ‘yan mata daga hannun Sham’una, to zai halarci garin kowannensu don a yi biki da shi.” Ran nan ba su yi barci ba, haka suka zauna suna ta hira. Waziri Habu yana labarta musu abin da ya sani Www.bankinhausanovels.com.ng game da aljani Sham’‘una da irin Karfinsa da kuma cewa tunkarar wannan aljani ba nasu ba ne, sai dai su yi ta addu’ar Allah Ya bai wa dan’uwansu Idrisu nasara a kan haka. Kowannen su ya gamsu. Sarki ya umurci Waziri Habu da ya yi musu rakiya don komawa garuruwansu. Yanzu kam kallo ya koma sama, kowa nasarar jarumi Idrisu ya ke saurare. Don dole sai dai a ce saurare din, ko kuma zato, don qalubalen ba gama garibane… LOKACIN da Sarki Zulkiflu da Wazirinsa Habu suka sauke jarumi Idrisu dan Hamidu a gabar teku sai ya shige cikin dajin da ke gabansa ya ci gaba da ketawa, kuma kasancewar irin wannan tafiya ba bakuwarsa ba ce, sai abin ya zo masa da dan sauki. In ya gaji sai ya saki Jagora shi kuma ya nemi wuri ya huta, bai tsayawa ko ina sai dai in akwai matukar bukatuwa zuwa ga hakan. Yi ya ke ta yi ba dare ba rana har ya iso bakin wani Katon kogi. Babu hanyar hayewa, kuma ba wasu manyan itatuwa ballantana ya dan sassaka jirgin da zai iya daukarsa shi da dokinsa, saboda haka sai ya karkata dama ya yi ta tafiya ta gefen rafin har na misalin yini sannan ya yi sa’a ya iso wata gaba wadda a kusa da ita akwai wani dan Kauye, kuma abin kamar an shirya aka dace jirgin ruwan da kan zo sau daya a kowane mako don ketarewa da jama’‘a zuwa daya gabar ya iso. A cikin wannan dare masu jirgi suka ce za su juya, Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu ya yi cinikin Ketarewa da shi da dokinsa, aka daidaita suka shiga aka mika, a haka suka yi ta yi har sai da suka yi tafiyar kwana uku sannan suka iso wani tsibirl mai matukar ban sha’awa. Ko ina a tsibirin ciyawa ce kake gani koriya shar ko kuma ka ga wani irin yashi fari sal, ga itatuwan dabino da inabi ko ina barjak, kan hanya ko ina ka duba sai inuwa linkim, don itatuwa ne ta kowane gefe suke sa kowace hanya a tsakiya. Tsuntsaye launi daban-daban kowanne da irin kukan gidansu. Wata irin iska mai sanyin dadi da ke kewayawa a tsibirin dole ne a ambace ta musamman irin yadda kowane lokaci take hadewa da Kanshin da kan fito daga furannin da ke kofar kowane gida suna ba da gudummawar wani irin tabbaci na natsuwa da cikakkiyar lafiya ga duk wanda ya tsinci kansa a yankin. Yawancin abincin mutanen wurin ‘ya’yan itatuwa ne wadanda suke da su, sai kuma zuma, nono da cukui da ake kawo musu. Allah Ya yi musu arzikin ma‘adinaina KarKashin Kasa da kuma na gefen ruwa. Wani babban abin ban sha’awa game da tsibirin shi ne mutanensa, masu kyawawan halaye, girmama juna, kula da addini da kuma son baki, kowanne ka gani babba da yaro, mace da namiji ta bangaren ilmin Www.bankinhausanovels.com.ng addini sai abin ya ba ka mamaki. Sai dai kash, akwai wani abu da ke matukar damun su a tsibirin. Wato wani irin dodo ne, shi ba mutum ba shi kuma ba dabba ba. Kansa kawai ya kai girman akawalin doki, kuma yana da idanu hudu, daya a goshi, daya a keya, daya a kasan kunnensa na dama dayan kuma a saman kunnensa na hagu. Kowane kunne ya fi matsakaiciyar tabarma fadi kuma yana da bakuna guda biyu, daya a baya dayan kuma a gaba, kuma kowane baki zai iya hadiye Kato komai girmansa. Wannan dodo dai yana da hannaye guda hudu wanda kowanne yana iya daukar babban dutse da shi, kafafuwansa kuwa kamar wasu manyan itatuwan rimi, cikin sa Kato wanda ko da wasa ba za a iya misaltawa da na toron giwa ba. Jikinsa kuma rabi da gashi daya rabin kuma babu, sannan yana wani irin doyi mai tsananin tayar da hankali. Ba kananan dabbobi irinsu kaji, talo-talo da awaki ba, kai hatta dawaki da rakuma in suka ji doyinsa ba duka ne suke rayuwa ba. A dabi’a, a duk shekara wannan dodo kan fito daga cikin ruwan rataye da wani irin akurki mai girman katon gida, ya yi ta farautar mutane yana jefawa a ciki sai ya cika shi taf da mutane sannan zai juya ya nufi HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 15 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sai dai kash, akwai wani abu da ke matukar damun su a tsibirin. Wato wani irin dodo ne, shi ba mutum ba shi kuma ba dabba ba. Kansa kawai ya kai girman akawalin doki, kuma yana da idanu hudu, daya a goshi, daya a keya, daya a kasan kunnensa na dama dayan kuma a saman kunnensa na hagu. Kowane kunne ya fi matsakaiciyar tabarma fadi kuma yana da bakuna guda biyu, daya a baya dayan kuma a gaba, kuma kowane baki zai iya hadiye Kato komai girmansa. Wannan dodo dai yana da hannaye guda hudu wanda kowanne yana iya daukar babban dutse da shi, kafafuwansa kuwa kamar wasu manyan itatuwan rimi, cikin sa Kato wanda ko da wasa ba za a iya misaltawa da na toron giwa ba. Jikinsa kuma rabi da gashi daya rabin kuma babu, sannan yana wani irin doyi mai tsananin tayar da hankali. Ba kananan dabbobi irinsu kaji, talo-talo da awaki ba, kai hatta dawaki da rakuma in suka ji doyinsa ba duka ne suke rayuwa ba. A dabi’a, a duk shekara wannan dodo kan fito daga cikin ruwan rataye da wani irin akurki mai girman katon gida, ya yi ta farautar mutane yana jefawa a ciki sai ya cika shi taf da mutane sannan zai juya ya nufi ZAMU TASHI wani dutse da ke cikin tekun, kuma wani abin takaici ma shi ne tun daga wurin farautar ya ke fara cinye wasu, ka ji yana taunar mutum garas-garas kamar yana cin risga. Ta yin la’akari da irin girmansa da aka bayyana ya sa kowa ya ke tsoron tunkarar sa ballantana a buga. An taba gayyatar jarumai misalin dubu daga garuruwa mabambanta don su halaka shi, amma Karshe dodon bai taba samun ganima irin ta wannan shekarar ba, don kuwa su ya kame kawai ya juya ya koma cikin ruwa abinsa. Wata shekarar kuma an taba hada wata wuta ganga-ganga da nufin in ya zo ya fada amma a banza, don kuwa komawa cikin ruwa ya yi ya guntso ruwa ya zo ya fesa mata ta bice. A Karshe dai mutanen yankin suka dukufa zuwa ga rokon Allah a kan Ya raba su da wannan fitina. Yanzu shekarar dodon ta takwas ke nan da ya gane wannan tsibiri. Amma in ba don wannan masifa ba, to ko kai wane ne ba za ka so tafiya daga wurin ba. Kuma da ma in kai bako ne da zarar mutanen tsibirin suka ga lokacin zuwan dodon ya karato, to za su yi KoKarin sallamar ka ko kuma gargadin ka gaggauta tafiya don kada dodo ya hada da kai. Lura da irin tasirin da ilmi ya yi a tsibirin da kuma Www.bankinhausanovels.com.ng irin ni‘imar da ta linkime wurin ta sa Idrisu dan Hamidu yanke shawarar cewa zai yi wata uku don Karin neman ilmi da kuma hutawa kafin ya wuce. Nan da nan aka isar da shi wurin wani dattijon malami wato Shehi Salim, wanda kuma shi ne Sarkin tsibirin. Ya karbe shi da mutuntawa kamar ya taba sanin sa. Idrisu ya roKe shi ko zai taimaka ya sanar da shi wani abu daga cikin ilmi na tsawon wata uku? Don shi matafiyi ne. Sarki ya ce, “Kwarai da gaske kuwa, mu ai da ma abin da muke so ke nan. Ina amfanin kana da ilmi ka bar wa cikinka kai daya? In ba ka koyawa wani ba to kai yaya aka yi aka koya maka?” Ba wata-wata Idrisu ya dukufa zuwa ga neman ilmi a wurin Shehin malami kuma Sarki Salim har sai da watanni ukun nan suka cika, kuma a cikin irin hirar da Idrisu kan yi da Sarki ya sami labarin wannan dodo da kuma irin sharrinsa tare da cewa yanzu sauran misalin watanni biyu ya zo ya debi na diba, mai rabon ganin badi kuma sai ya gani. Sai Idrisu ya ce wa Sarki, “Ranka ya dade ina son zan zauna sai dodon ya zo in ga irin yadda ya ke.” Sarki ya ce, “Kai dana rufa wa kanka asiri kada ka yi ganganci. Ka ga mu madon ba mu iya rayuwa a wata Www.bankinhausanovels.com.ng Kasar ne in banda nan, ba don haka ba da ko kare ba za kasamu ba.” Da Idrisu ya ji zancen Sarki sai ya ce, “Ranka ya dade ina rokon ka yafe mini in ga wannan maridi, kuma na yarda in Allah Ya Kaddara cewa a nan zan mutu babu yadda zan yi, kamar dai karatun da muka yi dazu da kai, Akaramakallahu.” Sarki ya ce, “Tun da yadda kake so ke nan, to Allah Ya kiyaye mu baki daya.” Idrisu ya ce, “Amin Allah gafarta malam.” A kwanaa tashi lokacin zuwan dodo ya yi, Sarki ya sa aka yi yekuwa cewa duk wanda ba dan gari ba, to ya gaggauta tafiya, duk kuma wanda ke rike da hakkin wani bako, to ya gaggauta sallamar sa tun kafin dodo ya iso. Baki suka yi ta shiga cikin jiragen ruwa, kuma kafin ka ce mene ne babu kowa sai mutanen tsibirin nan kadai sai kuma Idrisu da ke zaune gidan Sarki wanda mutane suka yi ta mamakin rashin gudunsa. Bayan kowa ya shirya, masu neman wurin buya sun tanada sai can aka fara jin doyin dodon, wanda hakan ke tabbatar da cewa cikin kwanaki biyu zai iso. Mutane suka fara shigewa maboyarsu ta Karkashin kasa, dawaki da sauran dabbobi kuma tuni sun fara mutuwa, amma shi Jagora dokin jarumi Idrisu sai Www.bankinhausanovels.com.ng ‘harbin iska ya ke yi yana wata irin haniniya ta nishadi. Can sai aka fara jin wani irin Rugi da Karaji mai Karfin gaske da ban tsoro. Ruwan ya dauki zafi kamar ana dafa shi, wanda hakan ya sa Kanana da matsakaitan halittun ruwa fara mutuwa. Lura da haka sai Idrisu ya shiga kayansa na yaki, ya dora sirdi, ya rataya takobinsa, ya rike mashi. Ya yi tsalle ya haye Jagora, wanda shi kuma kamar jira ya ke yi. Idrisu ya nufi bakin ruwan ta bangaren da ya sami labarin cewa ta nan dodon ke fitowa ya tsaya abinsa. Can sai ya ga wani abu yana dagowa daga cikin ruwan nan kamar tsauni, yana buga ruwa da hannayensa, yana furzar da wani abu mai kama da wuta daga bakunansa, yana matsowa yana wani irin Karaji. Idrisu ya tabbatar wa kansa cewa lallai wannan mugun maridi ne. Ga akurkinsa nan rataye a kafadarsa, na jefa mutane in ya kama. Lokacin da dodo ya kusa abin mamaki sai Jagora dokin Idrisu ya Kara tsawo da fadi. Idrisu ya zaro takobinsa, shi ma abin mamaki wurin fitowar takobin daga kubensa sai ka dauka Karar aradu ce, kuma kammala fitowar takobin ke da wuya sai ya kara tsawo yana wani irin hayaki kamar an fito da shi Www.bankinhausanovels.com.ng daga cikin wuta. Da dodo ya hango su sai ya yi wani irin Kumayji ya nufo su da cikakken tabbacin cewa ga wadanda zai fara somin tabi da su nan cikin sauki, amma Idrisu da dokinsa Jagora ko gezau, hasali ma lokacin da dodon ya zo gab-da-gab sai Idrisu ya riKka kewaya shi kasancewar shi dodon ba ya iya juyawa da sauri, sai dai kuma da ya ke yana da ido ta kowane Bangare yana ganin Idrisu din, ya rikKa daga manyan hannayensa yana kai bugu shi kuma dokin yana zamewa ba ya samun su, can ya dago hannaye biyu ya yarfo, shi kuma Idrisu sai ya sa takobi ya datse su, habawa! Jini kamar wasu manyan idanun ruwa ne suka Balle, ga hannayen dodo kuma kamar wasu manyan itatuwa a Kasa. Dodo fa sai Karaji ya ke yana tsalle-tsalle don tsananin Zafi, itatuwa sai faduwa suke ta yi, ya fusata gaba daya ya nufo Idrisu, shi kuwa sai ya zame ya sa takobi ya sare masa cinya guda daya. Ya girgiza mashinsa ya auna tare da sakar masa a cikin idonsa na gaban goshi, nan take sai wuta ta kama baki daya, Idrisu kuma ya janye mashinsa ya koma gefe yana kallo. Dodo ya yi ta Karaji yana motsawa ita kuma wuta tana ta cin sa har sai da ya kasa motsi ya Kone Kurmus. Www.bankinhausanovels.com.ng ‘Tokarsa ma kawai kamar wani tsauni. To in ba ka sani ba bari ka ji yadda nauyin mashin nan na jarumi Idrisu dan Hamidu ya ke, wato matukar dai in ba shi Idrisu din ne da kansa ya girgiza shi ba, to nauyinsa kan koma kamar na wani babban tsauni ne, kuma babu mai iya daga shi sai jarumi Idrisu kadai, ko da yake shi a wurinsa yana jin nauyin ne kamar na kowane irin mashi. Bayan yi wa dodo irin wannan kisa na wulaKanci sai ya koma cikin gari yana kiran mutane don su fito daga wuraren da suka boBboye, amma ‘yan kadan ne kawai suka fito, su ma,a tsorace. Da mutuwar dodo ta tabbata sai gari ya rude da sowa da murna, Sarki ya sa aka shirya biki irin na tseren kwale-kwale da sauran wasanni iri-iri cike da murna irin wadda ba su taba yi ba. Aka zabi wasu Katti daga cikin matasa aka ba su alhakin daukar kwanduna da kwashe tokar dodo sannan kuma su kona hannayensa da Kafarsa wadanda Idrisu ya sare. Cikin sa’a uku suka kammala suka share wurin kamar babu abin da ya taba faruwa. Da aka natsa Sarki ya sa aka tattara mutane ya gabatar da Idrisu ga wadanda ba su rigaya sun san shi ba, gaba daya aka yi masa godiya kuma suka roKe shi akan ya amince ya zauna tare da su. Www.bankinhausanovels.com.ng A wurin ma Sarki ya ce ya ba shi ‘yarsa don ya aura. Jarumi Idrisu ya mike ya yi musu godiya saboda karamcinsu, ya kuma sake yi wa Sarki da mutanensa godiya saboda yarinya da aka ce za a ba shi aure, ya ce shi yanzu ba shi da lokacin yin aure don irin babban aikin da ke gabansa wanda kuma bai san hakikanin ranar da zai kammala ba ma, in ma har ya yi tsawon rai zuwa ga kai wa ga nasara ke nan. Ya ce musu daga nan yana nufin danganawa da bayan duniya ne don saduwa da Sarkin aljanu Sham’una, barawon ‘ya’yan mutane. Suka ya gamsu da bayaninsa, suka kuma yi masa addu’a da fatan samun nasara. Wani dattijo a cikinsu ya yi wa Idrisu gargadi cewa a kan hanyarsa ya yi hankali don kuwa zai ratsa ta garin wata Sarauniya mayaudariya, sannan kuma ga ta jaruma, komai Karfin jarumi, to kuwa za ta iya kashe shi don ta kashe sun fi a Kirga. Ya kuma sanar da shi cewa dukkan fadawanta mata ne, jarumai na Kin Karawa. Sannan kuma tana da wasu macizai guda biyu da suke bauta wa, abincinsu shi ne mutane, kuma mazaje. Dattijo dai ya ci gaba da bayanin cewa, “Su wadannan macizai tsawon kowannensu ya fi kamu hamsin, kaurin jikinsu kuwa kamar kaurin babban Www.bankinhausanovels.com.ng jaki.ne Dafinsu kuma idan suka tsartawa mutum, to lallai ba zai kai rabin sa‘a daya ba zai zagwanye. Ita wannan Sarauniya kuma dai tana da wani sihirtaccen ruwa mai dafi wanda in har ka sha shi, to za ka koma ba ka da sauran laka a jikinka sai yadda aka yi da kai. Ba a taba samun mahalukin da ya taba nasara a kanta ba, hasali ma an ce har aljanu shakkar ta suke don ana hasashen Shaidan ne ya daure mata gindi. ‘Tana da abubuwa uku wadanda take saurin samun rinjaye da su, na farko tana da wani irin doki da babu mai irinsa, na biyu akwai tsafaffen takobi, na uku kuma shi ne ba ta da na biyu a fannin kyau da cikar halitta. Kana ganin fuskarta sai jikinka ya mutu a kama ka kamar kaza. Kai sai kaza ma ta fi ka wahalar kamawa.” Dattijo ya Kara da cewa, “Ya kai Idrisu tun da ka taimake mu har Allah Ya raba mu da wannan babbar masifa ta dodo, to mu ma za mu dan taimaka maka da irin abin da Allah Ya huwace mana. A duk fadin duniyar nan babu inda maganin dafi ya ke kamar wannan tsibiri namu, ni kuma wannan ilmi shi ne babban abin da nake tinkaho da shi na gadon gidanmu.” Dattijo ya sa hannu a cikin wata ‘yar jaka da ke Www.bankinhausanovels.com.ng rataye a kafadarsa ya dauko wani Kullin magani ya ce wa Idrisu, “Ga wannan magani ka sha kai da dokinka, ba dai dafi ba, sauran kuma sai ka Boye saboda yiwuwar taimaka wa wani.” Nan da nan aka miko masa Kwarya ya jika magani ya cika cikin sa ya kuma zuba ya mika wa Jagora ya sha sosai sannan sai ya sa sauran Kullin a cikin jaka. Ba a tashi daga wannan gagarumin taro ba sai da aka sauya wa wannan tsibiri suna zuwa Tsibirin Idrisu. Daga nan kuma sai jarumin ya sanar da su cewa da ma shi a shirye ya ke, abin da ya dakatar da shi ke nan, wato yakar wannan mugun dodo. Ya yi musu godiya sannan ya ce zai wuce. Sarki da kansa tare da mafi yawancin jama’ar – tsibirin aka shiga cikin jiragen ruwa aka nutsa cikin teku don yin rakiya ga wannan babban bako na su, bayan kamar tafiyar kwanaki biyar suka kawo bakin gaba, Idrisu ya sauka shi da dokinsa aka rabu ana kewar juna. IDRISU ya kama hanya ya ci gaba da tafiya har ya cim ma wata itaciya mai yalwatacciyar inuwa da kuma wani irin falali a Karkashinta, ya sauka daga dokinsa ya sauke masa kaya tare da kwance masa Www.bankinhausanovels.com.ng sirdi ya sake shi zuwa cikin daji don kiwo, shi kuma sai ya je Karkashin bishiyar nan ya yi kwanciyarsa rigingine, kafin ka ce me har barci ya sace shi, can ya fara nisa cikin barcin sai ya ji wani abu ya fado masaa fuska, ya bude ido da gaggawa har da wata irin zamilya irin tasu ta manyan jarumai, amma sai ya ga ashe takarda ce, kuma har da rubutu a cikinta. Mamaki ya kama shi. Yana budewa sai idanunsa suka tabbatar masa da ~ cewa lallai ya taba ganin irin wannan rubutun, hasali ma nan take ya gane daga inda takardar ta fito. “ Daga masoyiyarka mai begenka wadda tunaninka ya zama abincin ruhinta safe da maraice, ina fata kana cike da koshin lafiya kuma cike da taimakon Ubangiji. Yaya ka ji da karo da mazaje da dodanni? Watakila ka yi mamakin yadda na san halin da kake ciki ko? To tun daga ranar da ka bar wurin malaminka wato mahaifina, ni kuma na dawo nan bayan duniya sai ya kasance halin da kake ciki shi ne babban abin tattaunawa da bibiyarmu a kowane lokaci. Hasali ma duk mako kawata aljana Dailanu kan kewayo ka, kuma wannan takarda ma ita ce ta kawo maka. Www.bankinhausanovels.com.ng Ina samun labarin mahaifina kuma yana can lafiya lau a kullum yana yi maka addu’a da tambayar labarinka, don har yanzu Dailanu kan je wurinsa daukar karatu, kuma duk Asabar takan zo nan wurinmu. Sauran ‘yan matan da aljanin nan ya tsare mu tare kowacce tana nan lafiya sai dai tunanin iyaye da masoyansu kawai dake damun su. Ina kuma sake sanar da kai cewa ka yi takatsantsan da Sarauniyar da za ka tarar a gabanka, don mayaudariya ce kuma tana da tsananin jarunta, sai dai kuma muna yi maka addu’ar Allah Ya ba kanasara,a kanta. in har kana bukatar rubuta mini jawabi game da wannan wasika da aka ba ka yanzu, to Dailanu tana nan kusa da kai, in ka rubuta jefa takardar sama kawai, za ta kawo min. Ka huta lafiya. Ni ce masoyiyarka, Nur ‘yar Ibrahim.” Murna ba sai an bayyana ba a wurin jarumi Idrisu, tun farkon karanta wasikar har zuwa kammalawa murmushi kawai ya ke yi wanda ke gab da kecewa da dariya. Yana kammala karantawa sai ya daga hannayensa sama yana mai roKon Allah a kan Ya Www.bankinhausanovels.com.ng cika masa nufinsa. Ya dauko takarda da alkalami daga cikin burgaminsa ya fara rubutawa kamar haka, “Daga Idrisu dan Hamidu zuwa ga rabin rayuwata baki daya. Da farko dai zan fara ne da ba ki labarin wani abu wanda ya faru a tsibirin dana kashe dodon nan, inda suka yi mini gargadi game da Sarauniyar da kike magana, wai a kan cewa in yi hankali da kyanta don wai yakan dimauta mazaje har kama su yafi sauki fiye da kama kaza. A gaskiya wannan almara ta sa ni koyaushe na tuna sai in ta BabBaka dariya, lokacin da suke magana nake cewa a zuciyata da a ce gwanayen sanin kyau za su yi dacen ganin ki ko da sau daya ne, to da kuwa har abada sun daina zancen kyan wata mace adoron duniyar nan. Ko da yake aka ce rashin sani ya fi dare duhu, don kuwa ba su san cewa a dalilinki ne Sarkin aljanu Sham‘una ya mayar da matan da suka tuke a fagen kyau suka zama masu debe miki kewa ba dalilin cewa ko kadan ba zaa misalta ki da su ba. Ni dai ganau ne ba jiyau ba, don kuwa na gan ki a cikinsu, yadda kike haskakawa kamar wata cikin taurari. Ya ke wadda zakin muryarta babu zumar da ta kai Www.bankinhausanovels.com.ng ta, wadda babu wani abu mai haske da na taba gani da ya kai farin idanunta, ina tabbatar miki da cewa soyayyarmu ta fi teku zurfi da fadi. Saukin da kawai nake samu shi ne kullum da adikonki nake rufe fuskata sannan in sami lafiyayyen barci, kuma duk lokacin da kasala ta rufe ni shi nake ratayawa a wuyana sai in ji wani sabon Karfi ya lullube ni. Ya ke Nur, ina ganin ya kamata in dakatar da rubutuna haka sai kin gan ni, in Allah Ya so. Sai dai kuma kafin nan, akwai taimako da nake so ki rokar mini Kawarki Dailanu ta yi min: ga wasikar gaisuwa nan zuwa ga dan‘ uwana Waziri Habu, Wazirin kasar Arewa. Shi ma akwai budurwarsa tana nan tare da ku. Ki huta lafiya. Daga masoyinki har abada, Idrisu dan Hamidu.” Idrisu na kammala rubuta wannan takarda sai ya dauko wata takardar ya rubuta sakon gaisuwa zuwa ga dan’uwansa Waziri Habu, wanda a ciki ya ke sanar da shi cewa yana lafiya kuma ‘yan matansu duk suna lafiya sai dai begen masoyansu kawai da suke yi. Ya tambaye shi ko yana samun labarin iyayensu da sauran ‘yan’uwansu da suka fito karatu wato Yahaya Www.bankinhausanovels.com.ng da Bashari, da sauran bayanai dai irin na ‘yan’uwa. Da ya kammala sai ya daure wasikun biyu ya jefa sama, kamar wasa sai ya ga sun bace, wato aljana Dailanu ta cafe ta tafi da su. Kasancewar faruwar haka a ranar Asabar ya sa yarinya Nur ta sami wasikarta da jarumi Idrisu ya rubuta mata ba tare ba wani Bata lokaci ba, ‘yan mata suna kewaye da ita amma ta kasa Karanta takardar a gabansu saboda kada zuciyoyinsu su sosu irin yadda saurayinta ya fifita ta, tana karantawa tana murmushi, da suka tambaye ta sai ta ce musu, “Abin sirri ne, kuma sirrin irin na masoya biyu masu matukar begen juna.” . Sai abin ya zame musu abin wasa da dariya, har maganar ta shiririce. Can sai Nur ta ce wa aljana Dailanu, “Don Allah ko za ki taimaka, sako za mu ba ki zuwa Kasar Arewa.” Ai kafin ta kammala sai Dailanu ta yi farat ta ce, “Haba Nur, ai ni yanzu tsakaninmu ya wuce ki roKe ni wani abu don ni ‘yar’uwarku ce, sai dai ko bambancin cewa ni ba’yar Adam ba ce kurum.” Aljana ta Kara da cewa, “Wannan dan Karamin aiki, kin san kuwa in na ga dama yau cikin sa‘’a uku zan iya zagaye duniya sau biyarP” Www.bankinhausanovels.com.ng Nur ta ce, “to ranki ya dade, ai ban ce ina jayayya ba.” Suka yi dariya gaba daya. Sai Nur ta ce, “Wannan takarda ta Wazirin Kasar Arewa ce, Waziri Habu, dan’uwan_ saurayina. Jarumin jarumai Idrisu dan Hamidu ne ke so a kai masa.” Budurwar Waziri Habu tana jin an ambaci sunansa sai ta tambaya, “Wane Habun ne wai kuke ta magana ne? Ko wanda dai na sani ne Habu dan Hamidu?” Nur ta amsa, “EF, shi fa. Af, Fa’izah ke ce budurwar tasa da aka ce muna tare?” Ai fa sai yarinya ta mike tsaye tana ta Kwalla ihu, “Habuna ne, Habuna ne, ni zan tafitare da Dailanu.” Ko kadan ba su yi fushi da ita ba, hasali ma sai suka shiga lallabar ta don sun san yadda so ya ke, suka nuna mata cewa ai su ma duk suna da masoya amma suke hakuri. Wata daga cikin ‘yan matan ta tambayi budurwar Waziri Habu, “Kina son tona wa Dailanu asiri ne, a halaka ta?” A haka suka samu suka fara ciwo kanta kafin Bingyel ‘yar Fulani matar Bashari ta yi wa Nur wata tambayar, “Ko kina nufin Habu dan Hamidu yana da yaya Idrisu da abokinsu Bashari>?” a Www.bankinhausanovels.com.ng Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?” Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.” Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan’uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.” Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk ‘yan’uwa muke ba mu sani ba?” “Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su. Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.” A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sama ta fado jikinsa. Firgigit ya dan tsorata kadan kafin dai ya yanke HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 16 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Nur ta ce, “Kwarai kuwa, yaya aka yi ki ka san wannan labari?” Sai Bingyel ta ce, “Ai mijina Bashari duk ya ba ni labari. ‘Tun daga ranar da suka fito neman ilmi har zuwa rabuwarsu.” Yarinya Nur ta ce, “Lallai haka ne, Idrisu yana da ‘yan’uwa, su hudu ne suka fito zuwa cikin duniya don neman ilmi.” Can sai wata murya ta fito tana cewa, “Duk na ji ku sarai, ban yi magana ba ne, sai da na fahimci kuna magana har da mijina Yahaya dan hamidu, Kanin Idrisu yayan Habu, abokin Bashari dan Salihu, duk ni ma mijina ya ba ni labarinsu. Ashe duk ‘yan’uwa muke ba mu sani ba?” “Yan mata suka yi ta mamakin irin wannan saduwa ta su. Aljana Dailanu ta katse su, “Kai ni lokaci na neman Kurewa, zan tafi abina sai wani makon. Kun dame mu da labari. To mu ma dai Allah Ya ba mu namu masoyan.” A. can Kasar Arewa, Waziri Habu ya fito yana shiryeshiryen zuwa Sallar Magriba sai ya ji takarda daga sama ta fado jikinsa. Firgigit ya dan tsorata kadan kafin dai ya yanke ZAMU TASHI shawarar daukar takardar yana mai cike da tararrabi. Ya bude a hankali bayan zuciyarsa ta natsu kuma ya tabbatar cewa shi ake nufi ya duba takardar, duk da cewa bai ga mai kawowa ba. Yana budewa sai fuskarsa ta cika da murmushi tun da ya fahimci rubutun dan’uwansa. JARUMI Idrisu ya mika kamar yadda ya saba ba dare ba rana har sai da ya sami kwana sittin da hudu yana kutsawa cikin daji, kuma duk cikin anakin nan bai hadu da dan Adam ba ko daya. In dai ya ji motsi, to babu shakka manya ko kuma miyagun namun daji ne. Ya iso wata mararraba wadda ta rabu gida uku, tsakiya, dama da hagu. Bai yi wata-wata ba sai ya mike sanbal. Wannan hanya ita ce ta zuwa birnin Salsala, wato garin Sarauniya Zinkadaziyya, kuma matukar mutum zai nufi bayan duniya, to dole sai ya bi ta nan. Sai da ya yi kwana biyar yana tafiya cikin wani irin mugun sanyi da ke zubowa fari sal daga sama kamar KanKara sannan ya hango garin. Ganuwar garin kamar an gina ta da azurfa ne saboda wani irin sheki da take yi. Shi kansa Idrisu sai da mamakin irin wannan katanga ya rufe shi. Fitilu WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG kuwa a kowace kusurwa ta wannan gari ko allurarka ce ta fadi da dare, to za ka dauka ba tare da wahalarwa . ba, ko kadan ba abin mamaki ba ne in aka ce wannan gari aljanu ne suka gina shi. Sai dai kuma mutane ne ke zaune a cikin sa ba aljanun ba. Ga wasu itatuwa da furanni iri-iri masu matukar ban sha’awa da Kanshi. Abubuwan bukata na yau da kullum dai babu abin da mutum zai buKata ya rasa, komai suna da shi. Sai dai kuma wani abin mamaki shi ne duk garin babu namiji ko daya sai dai mata. In kuwa har ka ga namiji, to an kamo shi ne kawai don ya zama abincin macizan da mutanen garin ke bauta wa. Musamman sukan fita farauta don kamo mazaje, ballantana kuma wanda ya kawo kansa. Ba su ba macizan nasu ramammen namiji, a’a sai sun kiwata mutum ya yi Bulbul tukuna. Wadannan mata sun Kware matuka wurin jarunta, suna da wata irin tarbiyya wadda mace daya ko kadan ba ta tsoron tunkarar jarumai arba’in, ita kuwa Sarauniyarsu saboda irin siddabarunta da _ sanin lagon yaki sai an tara jarumai dari sannan ta kan fafata dasu. ‘Ta Bangaren kyau kuma mutanen wannan gari baa magana, ballantana Sarauniya Zinkadaziyya wadda WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG duk Karfin halinka in har kuka yi ido hudu da ita kuma ka ga zahirin fuskarta, to sai jikinka ya yi sanyi saboda irin cikar halittar da Aah Ya yi wa fuskar tata da jikinta. Yadda suke jin dadinsu kuma shi ne su sha giya, su yi kida da raye-raye sannan su bauta wa macizai. ‘Tsakanin su da maza kuma sai kisa. Da Idrisu ya kusa da garin sai masu tsaro da ke kan husumiya suka hango shi, nan take suka sanar, kafin ka ce mene ne wannan mata goma sun yiwo masa dauki a kan dawakansu dauke da makamai. Da suka Karaso sai suka daka masa tsawa, suka ce, “Kai tsaya, dakata a nan, wane ne kai? Daga ina kake? Me ya biyo da kai nan? Ba ka san ka biyo hanyar mutuwarka ba ne sannan kuma ba damar juyawa baya? To, yi maza ka sauka daga dokinka ka kawo takobi da mashinka. Ko kana so ko ba ka so ka zama abincin macizan da muke bauta wa.” Da ya ji jawabin jaruman ‘yan matan nan sai ya ce, “Haba, ku ba ku kyautata wa bako ne? Shin ba ku san cewa mutumin da ba ya kyautata wa bako ya yi hasara ba? Shin ku ba ku zuwa wani gari ne ku ga yadda ake karramawa tare da mutunta baki? Kuma idan kun ga cewa ba za ku iya sauke ni ba ne, to ku Kyale ni mana in yi wucewata zuwa inda na yi niyya. Don Allah ku Www.bankinhausanovels.com.ng yi hakuri ni ba rikici nake nema ba.” “Yan matan suka ce, “Kai ba doguwar magana muke so ba. Yaya mu da musamman mukan fita farautar mazaje, kuma ga shi ka zo har gida sannan ka ce mu Kyale ka? Ai sai dai wani ba kai ba. Shi kuma wannan kyakkyawan doki naka Sarauniyarmu ce ta fi cancanta da hawan sa… ko da yake kai ma ba baya ba ne a fagen kyau din.” Suka fara zagaye shi da dawakansu, shi kuma yana tsakiya, suka zazzare takubba, ai sai Idrisu ya yi wa dokinsa Kaimi. Jagora ya buga wani irin tsalle na Kwararren doki ya tsallake ‘yan matan nan ya koma gefe a daidai lokacin da Idrisu ke jawo takobinsa ya saro wani babban reshe na bishiyar da ke kusa dainda dokin ya dira. Jarumin ya rike reshen ya mayar da takobinsa cikin kube. “Yan matan nan suka yiwo kansa. Idan sun kawo sara sai ya goce, har sai da ya fahimci cewa da gaske suke yi sannan ya fusata ya sa wannan reshe na itace ya yi ta bugun su yana kauce wa saran takubbansu har sai da ya yi musu tilis. Da Kyar suka koma cikin gari. Kai, ‘yan matan nan sun sha wuya. Jina-jina suka je suka sami Sarauniya, abin ya yi matukar ba ta mamaki, amma duk da haka saida tasa aka kama su aka daure don sun kasa kamo mutum Www.bankinhausanovels.com.ng daya tak, ta riKa fada cewa sun cika da mayen giya ne har aka yi musu haka, amma za ta koya musu darasi. Ta sa wasu jarumai wadanda an tabbatar da jaruntarsu a kan cewa abin da take so shi ne azo mata da wannan mutumi da ransa don a azabtar da shi kafin a ciyar da macizai namansa. “Yan mata suka je suka yi shirin yaki, daga ganin su ba sai an fada ba cewa jarumai ne, suka nufi bayan gari inda Idrisu ya ke. Suka hango shi zaune Karkashin wata itaciya kashingide, ga alama ba abin da ke damun sa. Shugabarsu ta ba da umurnin cewa ashirin su je su kamo shi, amma fa kada a kashe shi. Idrisu dai ya fahimci sun nufo shi gadan-gadan, sai ya yi wuf ya suri itacensa na dazu ya haye doki. Bai Bata lokaci ba wurin fara jibgar su alhali shi ko rigarsa ba su iya tabawa ba. Duk ta hanyar da suka Bullo sai su tarar ashe ya fi su sanin ta. Tun da suke ba su taba ganin jarumi kamarsa ba wanda hakan ya ba su mamaki. Fada ya yi fada, ‘yan matan Sarauniya suka ga dai in aka ci gaba a haka, to babu shakka wannan mutumi zai halaka su, don a halin da ake ciki ma akwai guda goma kwance, saboda haka sai sauran suka juya linzami suka rufa a guje sai cikin birni. Idrisu ya koma ya daure wadannan jikkatattu guda Www.bankinhausanovels.com.ng goman tamau kamar ya daure goro. Sauran talatin da suka sha da kyar suka sami Sarauniya suka tabbatar mata da cewa babu shakka lamarin ba na wasa ba ne, don su dai wannan mutum ba su taba samun jarumi kamarsa ba. Sarauniya ta fusata ta yi musu bulala sannan ta ba da umurnin cewa su maaje a kulle. Sai suka ce, “Ranki ya dade, mun yarda ma a kashe mu ba daurewa ba kawai, matukar dai aka samu wanda ya je ya kamo shi.” Jin hakan sai hankalin Sarauniya ya dawo jikinta tace a Kyale su, sannan ta ce, “Lallai babban al’amari ya zo mana.” ‘Tunanin Sarauniya na gaba shi ne a sako wa wannan jarumi zakoki. Su wadannan zakoki Kwararru ne wadanda aka yi wa kyakkyawan horo na komai jaruntarka sai sun gama da kai. Guda daya kawai daga cikinsu kan karya jarumai fiye da dari biyu. Babban abin da sukan yi kuwa shi ne da sun iso wurin jarumai sai su yi wani irin ruri mai tsananin Karfin gaske, wanda kuma suna yi sai dawaki su rude su yi ta karo suna kayar da mahayansu suna gudu, shi ke nan sai zakokin su bi su karkashe jaruman. Dasun kammala wannan aiki sai su koma cikin gari a guje su shige inda ake killace su. Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya ta ba da umurnin a sako wa jarumi Idrisu su. Cikin kanKanin lokaci suka nufo bayan gari suna ruri da gunji Da ya hango su sai ya yi tunani a ransa ko dokinsa zai firgita, shin zai iya fuskantar wadannan girdagirdan zakoki kuwa? Sai ya shafa wuyan Jagora ya dan bubbuga, wato alamar yana Karfafa masa guiwa tare da tausar sa a game da irin Kalubalen da ke tunkarar su. Jagora ya fahimci abin da ake nufi sai ya yi haniniya wadda ta tabbatar wa Idrisu cewa babu fargaba. Nan da nan sai tunanin Jarumin ya hararo masa dodon da ya taba artabu da shi, irin girmansa, ban tsoronsa da mummunar kamarsa amma ba su sa Jagora ya tsorata ba, ballantana zakoki, saboda haka sai ya sami cikakkiyar natsuwa. Da suka kusa karasowa sai Jagora ya yi ta harbin iska abinsa yana wani irin rimi yana kewayawa. Cikin murna Idrisu ya sake gode wa Allah da Ya ba shi irin wannan jarumin doki. Zakokin nan goma da suka Karaso kusa da Idrisu sai suka fara, mai Karaji yana yi, mai ruri yana nasa amma Idrisu ko gezau, su kuwa wadancan ‘yan mata da ke daure sun zuba ido ne suna jiran ganin abin mamaki yadda zakokin nan za su yi watandar naman Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu da dokinsa a tsakanin su. Bai yi wata-wata ba ya zare takobinsa, Kara kamar aradu. Wasu irin shimfidaddu kuma dogayen sararraki guda biyu kawai ya kai ta gefen dama da hagu amma ya raba zakoki hudu kowanne da gangan jikinsa. Ko shurawa ba su yi ba. Sauran shida suka ja baya suna jiran su yi masa dirar mikiya, amma kuma sun makara don kuwa ya rigaya ya gane nufinsu. Kafin su iso ya daga takobinsa sama, sai kuwa baki dayansu suka diro masa, amma kafin su gama sauka har yasara sau uku kamar walkiya. Sai dai wasu ba su ba. Duk Idrisu ya halakar da su. Daurarrun ‘yan mata dai sun rigaya sun yanke tsammani da duk wata tantama ko shakka game da jaruntar Idrisu. Tunaninsu ma yanzu ya karkata zuwa ga cewa lallai shi ba mutum ba ne, a’a sai dai wani jarumi ne daga cikin manyan jaruman aljanu, dalilinsu kuwa shi ne, su dai ba su taba ganin mutumin da ya yi nasara a kansu ba ballantana a ce kuma ya yi nasara a kan zakokinsu. Ga shi kuma kyansa ya kai ace dan aljanu. Idrisu ya karasa wurin wani tafki da ke nan kusa ya wanke jinin zakokin da ya fantsamar musu a jiki shi da dokinsa, sannan suka sha ruwa ya kuma debo ya zo ya bai wa ‘yan matan nan wadanda tuni da ma Www.bankinhausanovels.com.ng kishirwa ta rigaya ta dame su. Yanzu kam sun tabbatar cewa tun farko ya Ki kashe su ne saboda tausayi. Suka ce, “Mun gode saboda ruwa da ka ba mu.” Ya amsa musu cewa, “Af, ashe kuna da saukin kan da za ku iya yin godiya? Don ni ina fahimtar ku ne a matsayin masu girman kai da jin mugunta a rai. Ga alama kuma a fuskarku duk wanda ya gan ku ya ga kyawawa amma a zuciyoyinku za ku iya cinye mutum danye saboda tsabagen rashin imani da kumia rashin tausayi.” Suka ce masa, “E, lallai ba ka yi Karya ba ya kai wannan jarumi, amma kafin mu ce maka komai, me yasa baka kashe mu ba bayan ka yi nasaraa kanmu?” Ya ce, “Babu shakka kun yi tambaya, idan za ku iya tunawa dazun nan nace ba ku da tausayi, kuma duk mutumin kirki dole ne ya zamo mai tausayi. Kamar yadda kuke jin zafin jikinku haka ma wani ya ke jin zafin nasa jikin.” Da ‘yan mata suka ji jawabin Idrisu sai suka ji a zuciyarsu sun natsu da shi, sai suka ce masa, “Lallai mun yarda da abin da ka fada mana, kuma yanzu za mu gutsura maka labarinmu. Mu dai yadda ka gan mu din nan ba mu jin tausayin kowa. Babu soyayya tsakaninmu da sauran mutane Www.bankinhausanovels.com.ng don muna ji a jikinmu cewa mun fi kowa, kuma daga cikin mutane wadanda muka fi ki da tsana su ne mazaje. Mu din nan da ka gan mu da yawanmu tun da suke ba su taba sha’awar wani da namiji ba, ballantana har su san shi. Wasu kuma bacin ran da da namiji ya Cusa musu a rayuwa ne da kuma tunanin daukar fansa a kan dukkan jininsa ya sa suka gudo suka zo nan suka zauna. Duk wadda ta kuskura aka ‘ gan ta tana magana ma kawai da wani namiji, to kuwa ranar ba da ranta za ta kwana ba. ; A yanzu haka akwai mazaje sun fi dubu goma suna ‘ nan a kulle a gidaje daban-daban ana kiwon su, don mu tsakaninmu da maza sai dai kawai mu kama, mu ; kiwata mu bai wa macizan da muke bauta wa su ci.” Sai Idrisu ya tambaye su, “Macizai kuke bauta wa?” Suka ce, “K:warai kuwa, abin mamaki ne? Ai bayan bauta musu ma akwai irin macizan da har dafinsu mukan rika sha don mun yi imanin cewa zai riqa sa mana tsattsaura kuma mugun hali irin na rashin tausayi.” Da jarumi Idrisu ya ji zancen wadannan ‘yan mata sai ya tambaye su, “To yanzu mene ne abin yi?” Suka ce, “Abin yi shi ne kawai mu gudu, don mu daga yau mun yarda da kai.” Idrisu ya ce, “A’a ba za mu gudu ba, don kuwa tun Www.bankinhausanovels.com.ng da har hanya ta biyo da ni ta nan, to ya zama dole a kaina in hana zalunci in ceci duk wanda ke cikin garin nin da kuma duk wanda hanya za ta biyo da shi nan gaba. Saboda haka ina zaton abin yi kawai shi ne yanzu bari in sake ku ku koma cikin gari, ni ma ba da dadewa ba ina nan shigowa.” “Yan mata suka ce, “Wai! Ai babu yiwuwar haka. Dalili kuwa shi ne yanzu in ka sake mu muka koma, to Sarauniya tana da matsanancin wayon da za ta iya gane cewa mun yi wani shiri ko kuma wata magana da kai, kuma ko shakka babu da ranmu za a dafa mu. Kasancewar ita a irin nata tunanin babu yadda zaa yi ka yi nasara a kan mutumin da ke son kashe ka amma kai kaqi kashe shi.” Sai suka ce, “Abin da zai fi dai shi ne ka sa mu a gaba a daure, mu nufi cikin gari, in ta ga haka, to ba za ta yi wani zato ba. Kuma da ya ke mun ga akwai amana tattare da kai, to za mu fada maka wani sirri don kada ka cutu. In kuma ka kuskure, to kuwa ba shakka za ta halaka ka. Lallai ka yi matukar taka-tsantsan da kyau, kasancewar mun san a irin abubuwan da ka aikata babu shakka yanzu za ta bukaci halaka ka da kanta ne. Na farko dai tana da wani tsafaffen takobi, ko da yake mun ga naka takobin ya fi nata ban mamaki. Www.bankinhausanovels.com.ng Tana da wani irin doki, wanda ya yi matukar horuwa, kai hasali ma wani lokaci ya fi dan Adam dabara. Ita wannan Sarauniya tamu tana da wani irin kyau wanda in har ka kalli fuskarta kuma kuka hada ido, to dole ka ji ka yi sororo ka kasa tabuka komai har kama ka ya fi sauki fiye da kama kaza, har in ta ga dama tana iya sa takobi ta buge wuyanka ba tare da ka ankara ba. In kuma har ta ba ka ruwa ko kuwa waniabin sha, to shi ke nan ka gama yawo, don akwai wani irin dafi da kan lalata kuzarin jiki a ciki. Tana kuma dai da wata kujera ta zinare wadda za ka dauka ta alfarma ce, amma matukar ka zauna a kai, to Sarauniya tana iya sa kujerar ta zame da kai kuma bazakazameko ina ba sai ramin macizanta. Ko kuma duk in ba ta Bullo maka ta nan ba, to tana iya neman aikata masha’a da kai, wanda kuma matukar ka amince, to sai wani ba kai ba.” Da Idrisu ya ji zancensu sai ya tabbatar da cewa lallai gaskiya suke fada masa, saboda haka sai ya yi musu alkawarin lallai zai yi iyaka Kokarinsa wurin kare su daga sharrinta. Bayan wannan tattaunawa sai ya sa su a gaba, shia saman doki su kuma a Kasa daure tamau da juna, suna tafiya Kafafuwansu na sarsarkewa ya nufi cikin Www.bankinhausanovels.com.ng gari yana yi musu hargowar da ke nuna kamar ba ya tausayin su. Da aka hango su nan da nan ‘yan kar-takwana dake kusa da kofar gari suka sanar da Sarauniya ita kuma ta ba da umurnin cewa a bude Kofar gari. Idrisu bai zame ko ina da su ba sai Kofar fada. Ta kasa zaune ta kasa tsaye a zaurenta na shiga, tana cikin kaiwa da komowa aka sanar da ita isowar jarumi da ‘yan matan da ya daure. Ta ce a sanar da shi tun da ya shigo cikin garinta, to ya sako mata mutanenta. Shi kuma sai ya amince don kokarin tabbatar mata da cewa ba tashin hankali ya kawo shi ba. Wadannan daurarrun mata suka sami Sarauniya suka zube suka yi gaisuwa. Ta tambaye su dalilin da suka kasa samun nasaraa kan wannan mutum. ; Suka ce mata, “Ran shugabar duniya ya dade, mun yi iyakacin kokarinmu amma ya fi karfinmu. Kumaa gaskiya mu mun tabbata cewa in ba ke da kanki ba wannan mutum samun wanda zai iya masa sai an tona. Zakokin nan ma fa kashe su ya rika yi kamar , yana kashe ‘ya’yan kyanwa.” Da Sarauniya ta ji an yabe ta a kan cewa ita ce za ta iya maganin abin da ya gagara sai ta ji dadi a cikin ranta, ta umurce su da su je su yi wanka su ci abinci su Www.bankinhausanovels.com.ng huta su kuma kasa kunne tare da zura idanu su ga yadda za ta yi da wannan dan tahaliki. Idrisu kuwa yana can tsaye a inda aka umurce shi a Kofar fada yana ta mamakin irin kyan garin yana kuma sauraren abin da zai je ya zo a daidai lokacin da Sarauniya ta zagaye ta je gidan sarkar da ake ajiye manyan gagararrun jaruman da aka kama ana kiwonsu don bai wa macizai, ta same su ta fitar da wadanda suka fi gogewa guda dari ta kawo kayan yaki ta basu. Ta fara yi musu jawabi, “Ya ku wadannan jarumai, ga rana ta zo wadda kowannenku zai nuna tare da tabbatar da jaruntarsa har in yi farin ciki da shi. A da na jarraba ku ne na sakaya ku anan don in ga wanda a zahiri zai zauna a garin nan saboda ni, kuma yanzu duk na tabbatar ku masu Kaunata ne, sai dai kun san kuma dole daga cikin gwanaye a fitar da gwani guda daya. Akwai wani jarumi yana can a Kofar fada, kashe shi ko kuma kamo mana shi a hannu shi ne sadakina, saboda haka daga cikinku duk wanda ya sami nasara zai zama mijina, kuma in har hakan ta kasance, to kun ga dole ke nan in sauka daga karagar mulki mijin da na aura ya hau.” Nan fa suka shiga Karaji wai su manyan jarumai, Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai dai kash, akwai wani babban abin da ke damun su, wato rashin Karfin jiki a dalilin dafin da Sarauniya ta taba shayar da su. Ita ta san cewa a irin wannan halin da suke ciki sai dai kururuwar kawai, don ko bera ba za su iya kamawa ba, saboda haka sai ta dauko wata katuwar gora ta fuskanci jaruman nan, kuma tana sane ta yi kamar ba ta sani ba ta kyale lullubin fuskarta ya yaye, ta yadda dumbin kyan da ke dankare a fuskarta ya bayyana har jaruman suka gani sau daya sannan ta yi sauri ta rufe. Ai fa wannan sai ya Kara tunzura tare da haukata su wurin hankoron fita don cinye wancan jarumi. Babu ko tantama sun isa jarumai, ballantana kuma ga shi sun huta, an kiwata su sun yi bulbul. Kafin wani lokaci ta sa duk an dora wa dawaki sirada, kuma kafin kowane jarumi ya hau sai ya amshi moda daya ta magani ya sha tukuna. Wannan maganin shi ne makarin dafin da ke jikinsu wanda ke hana su katabus. Yanzu sai suka ji kamar an cire musu kaya, kuma Karfinsu ya dawo jikinsu. Duk abin nan da Sarauniya ke yi akwai wani saurayi daga cikin jaruman nan da ke ji kamar ya kashe ta don irin wulaKancin da ta yi musu a baya, HMMM LABARU FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 17 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Nan fa suka shiga Karaji wai su manyan jarumai, Www.bankinhausanovels.com.ng amma sai dai kash, akwai wani babban abin da ke damun su, wato rashin Karfin jiki a dalilin dafin da Sarauniya ta taba shayar da su. Ita ta san cewa a irin wannan halin da suke ciki sai dai kururuwar kawai, don ko bera ba za su iya kamawa ba, saboda haka sai ta dauko wata katuwar gora ta fuskanci jaruman nan, kuma tana sane ta yi kamar ba ta sani ba ta kyale lullubin fuskarta ya yaye, ta yadda dumbin kyan da ke dankare a fuskarta ya bayyana har jaruman suka gani sau daya sannan ta yi sauri ta rufe. Ai fa wannan sai ya Kara tunzura tare da haukata su wurin hankoron fita don cinye wancan jarumi. Babu ko tantama sun isa jarumai, ballantana kuma ga shi sun huta, an kiwata su sun yi bulbul. Kafin wani lokaci ta sa duk an dora wa dawaki sirada, kuma kafin kowane jarumi ya hau sai ya amshi moda daya ta magani ya sha tukuna. Wannan maganin shi ne makarin dafin da ke jikinsu wanda ke hana su katabus. Yanzu sai suka ji kamar an cire musu kaya, kuma Karfinsu ya dawo jikinsu. Duk abin nan da Sarauniya ke yi akwai wani saurayi daga cikin jaruman nan da ke ji kamar ya kashe ta don irin wulaKancin da ta yi musu a baya, ZAMU TASHI kuma ya tabbata cewa duk wadannan alkawura da take yi musu na Karya ne da yaudara, amma babu yadda zai yi, musamman da ya lura da yadda sauran abokansa suka dimauta. Saboda haka sai ya zura idanu don ganin abin da ya gagare ta da har za ta yi Kokarin jefa su cikin hadari, watakila ma, kai ba ma wataKila, ya tabbata abin nan duk yadda aka yi ya fi ta gaskiya. Wannan saurayi mai suna Abdurrahman dan wani babban Sarki ne. Dalilin fadawarsa hannun Sarauniya kuwa shi ne ya fito neman budurwarsa ne wadda Sarkin aljanu Sham’una ya sace. Sarauniya ta ba da umurnin cewa a je a cika wa Idrisu aiki. Nan da nan jarumai suka sukwani dawakansu, suka nufi inda jarumi Idrisu ya ke, kowanne yana gudu yana jefa mashi sama yana cafewa, yana sarar iska da takobi. Sai dai kuma da suka kusa da inda ya ke sai gardama ta sarke tsakanin su a kan cewa kowannesu yana son shi ne zai je ya cafko jarumin. Suna tafiya suna jayayya, har suka zo gab da gab. Jarumi Idrisu ya daka musu tsawa, “Kai! Ku dakata, ina so ku dawo cikin hankalinku, ku tuna cewa wannan mata mayaudariya ce, ku tuna abin da ta yi muku da farko, babu shakka in kuka yi nasara a kaina Www.bankinhausanovels.com.ng za ta sake yaudarar ku. Saboda haka ina kira a gare ku cewa ku zo mu hada kai mu yake ta.” Sai jaruman nan suka fara maganganu, “Kai ba mu son rashin kunya, yaya ga Sarauniya Zankadaziyya da sarautarta gaba daya muna kallo an kasa a faifai sannan ka ce za ka yi mana wani dadin baki? In ba ka son wulakanta ka zo mu je kawai ba tare da wani bata lokaci ba.” Idrisu ya tambayi dalilin sa sarautar Sarauniya a faifai sai suka ce, “Ranka. Duk wanda ya kashe ka shi zai auri Sarauniya kuma ya zama Sarki a wannan gari.” Idrisu ya yi murmushi ya ce, “Na tabbatar tare da rantse muku cewa yaudarar ku take yi. Ku yi tunani da kyau, ba na son yin fada da ku, saboda haka ya ku wadannan jarumai masu daraja ku yi hakuri ku kauce kawai ku Kyale ni da ita.” Sai suka ce, “Zancen banza, ai yau ko digon jininka ne ya rage sai mun lashe shi.” Can sai saurayin nan dan Sarki, wato Abdurrahman ya ce wa Idrisu, “Lallai malam kana da gaskiya, ni kam ina tare da kai, kuma na ba ka aminci. Ko mutuwa ce, to ni na amince mu mutu tare.” Yana gama wannan magana sai ya zaburi dokinsa Www.bankinhausanovels.com.ng ya Karasa wurin Idrisu ya mika masa hannu suka gaisa. Ya ce wa Idrisu, “Kyale ni da wawayen nan marasa tunani, kyan fuska ta sa sun mance masifar da tasa mu ciki.” Sauran jarumai da suka ga daya daga cikinsu ya Balle, wanda a da suna zaton wata hila ce ya yi don kama Idrisu, amma sai suka ga da gaske ya ke yi cewa ya koma wurinsa, sai uku daga cikinsu suka zaburo, shi kuwa wannan saurayin jarumi ya fuskance su, kuma ba tare da wata matsananciyar wahala ba ya aike da biyu barzahu, dayan da ya ji wuya sai ya juya a guje. Ganin haka sauran jaruman suka yanke shawarar kai dauki baki daya. Idrisu ya juya gindin mashi, shi da saurayin nan suka zaburi dawakansu, fada ya barke. A gaskiya jaruman nan ba don irin Idrisu din suka samu ba, to lallai kuwa da sun gama da su cikin ‘yan dakikoki kadan, don kuwa jaruman ne sosai. Duk Kokarin da Idrisu ya ke ta yi har ya ja artabun ya yi tsawo shi ne ko za su ji sun sha wahala su mika wuya don a fahimcijuna amma ina. Bayan kamar sa’a daya da rabi ana gwabzawa sai su Idrisu suka sami nasara a kan jaruman Sarauniya. Sun kashe hamsin da uku, suka ji wa tara rauni, suka kuma kama bakwai suka daure, sauran kuma suka Www.bankinhausanovels.com.ng gudu suka koma wurin Sarauniya a guje suka ba ta labarin yadda lamari ya wakana. Ta ce musu, “Af, kun yiwo gudun mutuwa ne? To ai ita za ku tarar. Kuma in banda wautarku, ai ko da kun yi nasara a kan wannan jarumi kashe ku zan yi, ballantana kuma ku ne aka yi nasara a kanku.” Ta sa takobi ta yi ta dauke musu kai, kasancewar da za su karasa wurinta sai da kowanne ya zubar da makamansa, wanda hakan ya sa babu wani motsi mai tasiri da za su iya yl. Daya daga cikinsu ne ya yi sa’ar zullewa a guje ya sami nasarar hayewa doki ya zabure shi, kuma umurnin da Sarauniya ta bayar na cewa kadaa bar shi ya kai bai yi amfani ba, don kuwa ya samu ya fice har ya isa gaban Idrisu. Yana zuwa sai ya zube yana cewa, “Ka cece ni kada ta kashe ni, ashe zancenka gaskiya ne.” Su kuwa ‘yan matan da suka biyo shi da suka ga ya isa wurin Idrisu sai suka toge, suka koma suka sanar. Hankalin Sarauniya fa ya yi matukar tashi, duniya ta yi mata baki-Kirin, Kirjinta ya yi Kunci, ta shiga tunani da magana ita kadai, ta sa aka kawo mata tulun giya ta fara kwankwada babu KakKautawa tana tunanin yadda za ta Bullo wa lamarin. Can dai ta yanke shawarar fuskantar wannan Www.bankinhausanovels.com.ng jarumi ita da kan ta, kuma ta amince a cikin zuciyarta cewa duk ta yadda za ta yi sai ta ga bayansa. Saboda haka sai ta fito da kanta, ba cikin shirin fada ba, ‘yan mata biye da ita. Ta sa wata daga cikin ‘yan matan ta yi masa shela cewa Sarauniya Zankadaziyya mai girma tana son yin magana da shi, ba fada ba, saboda haka ya mayar da takobinsa cikin kube. ‘Ta matso shi ma Idrisu ya matso, amma duk da haka dai bai saki jikinsa ba. Ta ce, “Me ya kawo ka Kasarmu?” Idrisu ya amsa mata cewa, “Hanya ce ta biyo da ni, asali na zo wucewa ne kawai.” Sarauniya ta katse shi, “To dakata. Ka sani cewa ka yi mana Barna mai dumbin yawa a Kokarin da muka yi na kare garinmu daga bakin da ba mu sani ba. Kuma ko kadan kada ka dauka zan yafe maka ne kai tsaye haka kawai, kuma ko kadan kada ka dauka cewa ka gagara ne, A dalilin dan Kokarin jaruntar da ka nuna ne nake ganin ya kamata ka sami arzikin yin magana da ni. Akwai jarrabawa da na shirya zan ba ka, in har ka yi nasara, to sai ka ambaci buKatarka a biya, in kuma ba ka yi nasara ba, to dole ka amince in yi yadda na ga dama da kai. Sakamakon barnar da ka yi mana. Shin ka amince?” Www.bankinhausanovels.com.ng Jarumi Idrisu ya ce ya amince. Ya Kara da cewa, “Ai jarumi ba ya qin takala.” Sai Sarauniya ta ce, “tsere ne kawai a kan doki za mu yi, in dokin ka ya tsere nawa, to shi ke nan ka ci jarrabawa, in kuma dokina ya tsere wa naka, to ka fadi jarrabawa, sai ka mika wuya sai yadda na yi da kai.” Abin da dan Hamidu bai sani ba shi ne babu komai a cikin wannan tsere na dawaki da Sarauniya ta bukaci a yi face yaudara, musamman in an lura da irin gagarumin sharrin da ke wurin da akan yi tseren. Ramuka ne aka harhaka masu zurfi sannan aka sa wasu irin masu wadanda ke da tsananin tsini da dafia jikinsu. Mutum yana fadawa, to sai dai wani ba shi ba. Wanda bai sani ba babu yadda za a yi ya taba ganewa domin an bi duk ramukan an lullube da wata irin shimfida da kuma turbaya yadda sai ka rantse babu komaia wurin. Shi wannan doki na Sarauniya a gabansa duk aka harhaka wadannan ramuka, kuma ya sami kwarewa matuka yadda duk ya san wuraren da suke. Babu yadda zaayi ya auka. ‘Ta wannan hanya Sarauniya ta halaka mutane masu dumbin yawa. Nan da nan aka nufi fili, Sarauniya tana kan Www.bankinhausanovels.com.ng ingarman dokinta, yana tafe yana harbin iska. “Yan matan Sarauniya kam sai murna, don sun tabbatar da cewa ta faru ta Kare a kan wannan jarumi wanda ya wahalar tare da kashe musu mutane. Wadanda ba sa murna daga cikinsu kawai sai dai daurarrun ‘yan matan nan da ya shigo tare da su cikin gari, su babu abin da suke yi sai jimami tare da tausaya wa rayuwar Idrisu don sun tabbatar da cewa tasa ta zo Karshe, kuma sun yi mantuwar sanar da shi wannan tsere, don an daden gaske ba a yi irinsa ba. Babu damar su tsegunta masa, kuma babu damar su nuna bakin cikinsu, don sun san sakamakon haka, saboda haka sai suka yanke tsammani da shi. Jagora dokin Idrisu kuwa sai haniniya ya ke yi yana wata irin rawa da tafiya yana dandangala Kafafu cikin Kasaita. Dole in ka gani abin ya burge ka. Aka saki dawaki, suka ruga a guje, shi Idrisu bai san abin da ke Kasa ba, amma abin mamaki in ana cikin gudu sai ya ga Jagora ya daka tsalle, ashe ramukan nan ne ya ke tsallakewa. Maimakon fadawa cikin rami sai ya kasance yanzu akwai tazarar gaske tsakaninsa da dokin Sarauniya. Kai rannan har ‘yan matan Sarauniya sai da suka tafa wa Idrisu. Bayan jarumin ya dawo har ya dan huta sai ga Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya Zinkadaziyya ta Karaso. Tana zuwa sai ta yi masa jinjina, amma fa na ciki na ciki ne kawai, ta dube shi ta sake duban Jagora ta ce, “Lallai na yarda kai jarumi ne kuma dokinka jarumi ne, to sai mu koma fada ka fadi bukatarka.” A fadar Sarauniya duk sai aka zaunaa kan kujeru na alfarma. Cikin dabara jarumi Idrisu ya ki zama a kujerar da aka fara nuna masa, maimakon haka_ sai ya je ta nesa da ita ya zauna. Sarauniya ta ba da umurnin a kawo abinci da kayan shaye-shaye, to a cikin wannan abin sha akwai wani mugun dafi, wato dafin nan wanda kan sa mutum ya kasa tabuka komai sai kawai a kama shi yana kallo. To da ma Idrisu yana sane da wannan, sai dai kuma ko kadan hakan bai ba shi tsoro ba, hasali ma sai ya bude cikin sa ya nadi abincin nan ya debi abin sha ya sha har ma da Karawa. A lokacin ne ma ya tuna cewaa cikin kayansa akwai sauran maganin dafi wanda aka ba shi ko da zai taimaka wa wasu, wato wanda ya samo a tsibirin da ya kashe dodo. Shi da dokinsa tuni da ma wancan maganin dafin ya rigaya ya huda su. Amma fa duk abin da ake yi shi wancan jarumin dan Sarki da ke Bangaren Idrisu, wato Abdurrahman, da kuma jarumin nan da ya gudu dazu zuwa wurin Idrisu din don samun mafaka ko kadan ba su yarda Www.bankinhausanovels.com.ng sun ci ba, don sun tuna cewa daga wurin cin abinci ne suka manta inda suke a wancan karon lokacin da suka shigo garin. Dan Sarki ma har sai da ya tsawatar wa Idrisu cikin dabara a kan kada yaci ko shan komai wurin amma sai ya ga ko sauraron sa jarumin bai yi ba. Bayan an kammala cin abinci tsaf, sai Sarauniya ta yi wata irin dariya har da kyakyatawa, sannan saitace, “Dan kyakkyawan jarumi, yanzu fa da kai da kazar da ke cikin akurki tafiyarku daya.” Sai Idrisu ya tambaye ta abin da take nufi, sai ta ce, “Ai da ace ba ka yarda ka sha wani abu daga gare ni ba da sai in ce har yanzu kana tare da jarunta da Kwarewarka, amma yanzu ai labari ya sha bamban. Yanzu jijiyoyin jikinka ma sun fi ka Karfi. Da ma an ce ta yaro kyau take yi bata Karko.” Idrisu ya yi murmushi sannan ya ce, “Allah Sarki. Sarauniya ke nan, to wai kina ce duk mutane daya ne? – ‘To, wannan yaudarar ma ba ta yi nasara ba, sai ki sake wata.” : Yana gama magana sai ya yi zumbur ya mike tsaye ya daga hannayensa sama da Karfi ya girgiza jikinsa. Wato guba bata yi masa komai ba ke nan. Mamaki ya rufe Sarauniya, don ita wannan guba ko giwa ce ko zaki suka lashe ta za su lalace su rasa katabus ballantana dan Adam. Nan da nan Www.bankinhausanovels.com.ng Sarauniya Zinkadaziyya ta mike ta nufi wurin masu kawo abinci ta sami ‘yan matan ta ce, “Wato ni za ku munafunta ko? Na ce ku sa dafi a cikin abin shan jarumin nan amma…” Suka yi sauri suka ce, “Ranki ya dade mun rantse da macizai mun zuba masa.” Ba ta ce komai ba, ta umurci wata daban akan cewa ta je ta kwaso kayan abin shan da ke gaban jarumi Idrisu, wanda ya sha ya rage. Da kanta ta tsiyaya ta bai wa ‘yan matan kuma ta umurce su a kan cewa su sha matukar dai da gaske suke yi cewa sun zuba. In kuma sun Ki sha, to a kai su a jefa a ramin macizai. Dole suka saddakar suka sha, nan da nan jikinsu ya langabe kamar ba mutane ba, Sarauniya ta tabbatar da cewa lallai kam sun zuba kuma shi ne dai Idrisu dan Hamidu ya sha. Mamaki ya sake kama ta. ‘Ta debo makarin gubar ta ba ‘yan matan suka sha, bayan wani dan KanKanin lokaci sai ga shi sun wartsake tangaram. Sarauniya ta dawo wurin su Idrisu, ta yi umurnin cewa tana bukatar kowa ya fita ya ba ta wuri za ta yi tattaunawar sirri da wannan jarumi. Bayan kowa ya fita sai ta tashi tana wata irin tafiya ta takama tana magana, “Babu shakka ka isa jarumi, domin kuwa na yi karo da jarumai masu yawan gaske, Www.bankinhausanovels.com.ng na kashe dakarun da ban san adadi ba, amma babu wanda ya taba nasara a game da dukkan tuggun dana shirya masa sai kai kadai. Abin mamaki sai na ji na sallama maka, kuma watakila ka yi mamaki in kajina ce a yanzu gaskiya son ka ya shiga cikin zuciyata yana neman mamaye ta. Ko kadan a da ban yarda da wani abu da ake kira soyayya ba, shi ya sa ba na yin ta. Amma yanzu na fahimci kuskurena, ashe dai soyayya gaskiya ce. Wannan ya sa ba zan bar ka ka tafi ba, a taKaice dai bukata nake yi ka zama mijina, kuma gobe a tabbatar maka da sarautar gari, kuma na yi maka alKawarin zan zama mace mai biyayya a gareka. Ka yi hakuri abubuwan da suka wakana abaya.” Idrisu dai bai ce komai ba, ya yi kasake yana sauraren ta. Ta ci gaba da bayani, “Yanzu halin da ake ciki gaskiya babu abin da nake buKata, saboda irin shauKinka da nake yi, face, ko kuma a taKaice ina sanar da kai cewa na sallama maka kaina, ka aikata masha’‘a da ni, yanzu ba sai an jima ba.” Da Idrisu ya ji abin da Sarauniya take buKata sai ya ce, “Ina neman tsari daga Allah Mai girma da daukaka, Allah Ya kiyaye ni daga wannan mummunar bukata taki. Ki sani cewa ni ba irin mutanen nan ne da kika sani ba masu dulmuya kansu Www.bankinhausanovels.com.ng a cikin halaka. Ni addinina ya hana ni rabar matar da ba tawa ba.” Jin wannan magana sai Sarauniya ta ji kamar an sake zuga ta ne a kan cewa lallai sai bukatarta ta biya, ta tuna yadda sarakuna da jarumai kan niko gari su bar garuruwansu don su zo su ga fuskarta da kyanta da ake labari, amma a karshe duk ta mayar da su bayi, sun yi mata kuka, ta sa su rarrafe da sauran abubuwan da a cikin hankalinsu ba za su yarda su aikata ba. Ta ce masa, “Dan saurayi ina ji maka tsoron kada ka zo daga baya kana rokona a kan kana son in sake nuna maka fuskata kawai. Ka ga dai tun da ka zo in banda Kwayar idanuna ba ka ga komai na daga jikina ba, amma na ce zan sallama maka kaina, saboda haka kada ka yi saurin ki ko kuma kore alherin da ya tunkaro ka. Ya kai jarumi ka sani cewa ba wai yabon kaina nake yi ba, amma ina da kyau da halittar da ba maza kadai ya ke girgizawa ba har mata.” Jarumi Idrisu ya ce, “Watakila su wadancan masu begen naki ba su taba ganin kyakkyawa ba ne sai ke. Kuma ina tabbatar miki da cewa duk namijin da har ya sake kyanki ya debe shi, musamman ma jarumi, to bai cika da ba, kuma ni zan fada miki abin da yasa nace kyanki bai kai ba…” Sai ta katse masa magana ta harare shi tace, “Irinku Www.bankinhausanovels.com.ng ne kuke ce wa mace dokin lado… amma zuwa an jima za mu gani idan kai daban kake da sauran mazaje.” Ta bar Idrisu a nan ta shige cikin wani daki, fitowar da za ta yi sai ga ta daga ita sai ita, ta warware gashin kanta ta rufe rabin jikinta da shi. Lallai ne duk namijin da ya gan ta, in dai ba wata kariya daga Allah ba, to zai zamanto kamar wadancan mazaje na baya da aka ba da labari. Don irin cikar halittar Sarauniya kada ma wani ya fara Kokarin ba da labari, don kuwa dole sai ya rage ta. Ta matso kusa da Idrisu, kansa na duke yana kallon Kasa. Sarauniya ta ce, “Kai Duba nan.” Idris ya ce, “Ai na gan ki.” Sarauniya ta sake tausasa murya ta ce, “To sake dubawa mana.” A hankali bai san lokacin da kansa ke kokarin sake dagowa don sake gani ba, amma sai tsoron Allah ya shige shi kuma ya tuna da yarinya Nur, kawai sai ya sa hannunsa a wuyansa ya shafa adikonta, ya daga kansa ya zare idanunsa ya kalli Sarauniya da ke tsaye Kerere a gabansa ya ce, “Kin ga adikon nan da ke daure a wuyana, to a wurina ya fi ki daraja, ke da mulkinki da duk abin da kike takama da shi wadanda duk na banza ne tun da dai ke fasika ce. Sannan kuma Www.bankinhausanovels.com.ng ga shi kina da mugun halina kashe ‘ya’yan jama’a. Kin hana wa ‘‘ya’yan mutane ‘yanci, kuma ga shi kina bauta wa abubuwan banza; macizai, kina ba su ‘ya’yan jama’‘a suna cinyewa. To ina yi miki albishir da cewa wata rana ke za su cinye, kowa ya huta. ‘To yanzu dai duk wani kawaici da kawar da kai da nake yi miki ya kare. Abin da nake bukata dake shi ne, ki saki duk jama’ar da kike tsare da su kina ba macizanki. Ki Kyale kowa ya koma garinsu. Ke kuma ina ba ki shawara ki daina bautar macizai, ki bauta wa Allah Mahaliccin macizan, ki yi aure, kuma ki Kyale ‘yan matanki su ma su zaBi mazaje su yi aure. Wadanda ba su da buKatar zama tare da ke kowacce ki bar ta ta koma garinsu wurin iyayenta.” Da Sarauniya ta ji irin wannan zance da Idrisu ya ke yi mata gatse-gatse haka sai ranta ya Baci, ta yi fushi mai tsanani har sai da ya bayyana a fuskarta, ta ji kamar ta sha jininsa. Ta ce, “Lallai kai kana da mummunan jawabi, maganarka ta fi dafin bakin kumurci daci, zancenka yana iya kashe mutum kafin Karewar kwanakinsa. A gaskiya da a ce na san zan same ka yadda kake, to kuwa da ban bari ka shigo garina ba, har ka guma mini bakin cikin da tun tsawon rayuwata ban taba samun rabinsa ba ma.” Sarauniya ta Kara da cewa Idrisu dan Hamidu, Www.bankinhausanovels.com.ng Wai ga shi ma har kana ce mini in bar bautar macizai, to in bauta wa me? Kuma don tsabar wulakanci in nuna maka jikina amma ka ce adikon da ke daure a wuyanka ya fi ni daraja a wurinka. Lallai ka zalunce ni, kuma ina roKon macizanmu masu girma su tsine maka albarka! Yanzu dai abin da nake so da kai shi ne na sallame ka, yanzun nan ka bar mini garina, in kuwa ka Ki, to zan karya Karfinka in yanka ka da kaina, in raba jikinka biyu sannan in bai wa macizaina masu girma, su cinye namanka.” Idrisu ya ce, “A’a, saurara, ya ke wannan Sarauniya mai taurin kai da rashin fahimta, ki sani cewa zancen banza kike yi. Ai in kin ga na bar garin nan, to babu shakka na ‘yanto ‘ya’yan jama’a ne maza da mata da ke cikin tarkon makircinki. Ina kuma sanar da ke cewa a game da wannan ba ki da wani sauran zabi, ko dai ki yarda ne ki tsira da mutuncinki, ko kuma ki Ki yarda ki rasa sarautarki.” Yanzu kam zuciyar Sarauniya ta gama kumbura don tsananin fusata da maganar Idrisu. Mamaki da Kunci da bakin ciki suka lulluBe ta, kamar walKiya sai ga shi ta zaro tsafaffen takobinta, kuma kafin Kifta ido ta buga wani irin tsalle kamar wadda ta fado daga sama ta diro wa Idrisu da wani irin suka, amma Www.bankinhausanovels.com.ng saboda tsananin kwarewa sai ya goce ya fado daga kujerar da ya ke zaune. Takobinta ya soki kujerar, kuma duk da kasancewar kujerar ta dunkulallen bakin karfe amma sai da takobin ya huda ta, kuma saboda tsananin dafin takobin da sihirin da ke jikinsa sai ga kujerar tana zagwanyewa, Karfe na narkewa kamar kankara. Nan da nan fada ya kaure aka yi kaca-kaca da kayan da ke cikin fadar don tsananin gumurzu, babu shakka Idrisu ya san cewa Sarauniya jaruma ce. FADA ya yi fada tsakanin jarumi Idrisu da Sarauniya Zinkadaziyya, ita tana Kokarin samun sa a makasa ta aike da shi lahira shi kuma yana KoKarin takura ta, don ya kama ta ya daure, kasancewar shi ko kadan ba ya bukatar kashe ta, shi ya sa ma ko takobinsa bai fitar ba. Tun daga cikin fada har sai da suka yiwo waje suna ta gwabzawa. Babu shakka wannan Sarauniya ta fi Karfin a kama da hannu, ko da a wurin irinsu Idrisu din, don kuwa ba Karamar jaruma ba ce. Suna dai ta bugawa. Kwatsam sai ga su a wata ‘yar unguwa da ke jikin fada, a can gefe sai ya hango wasu ‘yan matan Sarauniya sun bude wani tafkeken rami, HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 18 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA saboda tsananin kwarewa sai ya goce ya fado daga kujerar da ya ke zaune. Takobinta ya soki kujerar, kuma duk da kasancewar kujerar ta dunkulallen bakin karfe amma sai da takobin ya huda ta, kuma saboda tsananin dafin takobin da sihirin da ke jikinsa sai ga kujerar tana zagwanyewa, Karfe na narkewa kamar kankara. Nan da nan fada ya kaure aka yi kaca-kaca da kayan da ke cikin fadar don tsananin gumurzu, babu shakka Idrisu ya san cewa Sarauniya jaruma ce. FADA ya yi fada tsakanin jarumi Idrisu da Sarauniya Zinkadaziyya, ita tana Kokarin samun sa a makasa ta aike da shi lahira shi kuma yana KoKarin takura ta, don ya kama ta ya daure, kasancewar shi ko kadan ba ya bukatar kashe ta, shi ya sa ma ko takobinsa bai fitar ba. Tun daga cikin fada har sai da suka yiwo waje suna ta gwabzawa. Babu shakka wannan Sarauniya ta fi Karfin a kama da hannu, ko da a wurin irinsu Idrisu din, don kuwa ba Karamar jaruma ba ce. Suna dai ta bugawa. Kwatsam sai ga su a wata ‘yar unguwa da ke jikin fada, a can gefe sai ya hango wasu ‘yan matan Sarauniya sun bude wani tafkeken rami, ZAMU TASHI sai kawai ya ga kamar Riftawar ido an zo da wani jibgegen Kato an angiza shi cikin ramin, babu yadda Idrisu zai itya hana wannan don irin yadda Sarauniya ta ba da Kaimi wurin Kokarin halaka shi ko ta halin Kaka. Aka zo da wani Katon shi ma aka cilla cikin ramin abin kamar a mafarki. Ba sai an yi wani dogon bayani ba Idrisu ya fahimci cewa wannan ramin shi ne wanda macizan da Sarauniya da mutanenta ke bauta wa suke ciki, kuma ramin da ake tura ‘ya’yan mutane, musamman mazaje da sauran wadanda suka yi wani babban laifi, don macizan su yi kalaci da su. “Yan matan da ke kula da ramin macizai ba su ankara ba sai suka ga Sarauniyarsu a cikin yanayin da ba su taba ganin ta ba tana ta fada da jarumin da labarinsa ya karade gari, ai sai suka bar wurin suka koma gefe suna kallon abin da zai ture wa buzu nadi. Yanzu dai Sarauniya ta matsa kamar wadda ta haukace, da Idrisu ya ga haka kuma ya tabbatar da cewa ba za ta kamu masa da hannu ba sai ya zare takobinsa, karar zarewar kawai kamar faduwar aradu. Ita kanta Sarauniya sai da ta tsorata, amma saboda taurin kai da jarunta sai ta ci gaba da fada. Ta daga takobinta da Karfi ta kawo wa Idrisu wata Www.bankinhausanovels.com.ng irin sara, shi kuma sai ya sa takobinsa ya kare, haduwar takubban nan fa sai kawai takobin Sarauniya ya lankwashe ta yadda ba shi da sauran mamora. Da Idrisu ya ga haka, kuma ya ga alamar cewa jikinta ya yi sanyi sai ya ce mata, “Haba, ya ke wannan Sarauniya, ki ba da kai mana, ki mika wuya, ni da ma ba ni da niyyar kashe ki, ina so ne ki yarda ki zama Sarauniyar kirki, ki kyautata wa talakawanki, kuma ki saki mutanen da kika tsare kowa ya kama gabansa. Ki je ki ci gaba da sarautarki don ni ba sarauta nake so ba, ina ji miki tsoro kada ki zama kamar Sarkin aljanu Sham’una…” Ai kafin ya rufe baki sai ta zaro wuka a kuibinta ta auno Kahon zuciyarsa ta sako, Idrisu ya sa takobi ya buge wukar ta fadi can Kasa. Da Sarauniya ta ga cewa ta kowace fuska an yi galaba a kanta, sai ta ce a cikin ranta, “Ai kuwa dajin kunya ga Sarauniya gwamma rasa rai.” ai kuwa sai ta ruga ta nufi ramin macizan can da ba a rigaya an sakaya ba saboda kallon fadan da masu aikata hakan suka tsaya yi, ta yi kundumbala ta afka ciki, ai cikin ‘yan dakikoki sai ya kasance babu sauran ko digon jininta, allolinta sun shanye. Bayan mutuwar Sarauniya sai Idrisu ya juya wurin Www.bankinhausanovels.com.ng jama’arta ya ce musu, “To ku mene ne abin yi?” Sai suka ba shi amsa, “Meene ne abin yi kuwa ranka ya dade, ai yanzu kai ne Sarki, umurninka kawai muke jira.” Sai ya ce, “To da farkon farawa dai abin da nake so shi ne a je a kwanto mini dukkan mutanen da ake daure da su a gidajen sarka da ma duk wani wuri da ake azabtarwa. Ban ce a rago ko daya ba.” Mutane suka shiga fitowa salalaf babu laka a jikinsu amma kuma fuskokinsu cike da murna bayan sun fahimci abin da ya faru. Suka Karaso wurin jarumi Idrisu suna yi masa addu’o’in alheri da kyakkyawan fatan samun biyan buKata a game da duk abin da ya sa,a gaba. Nan da nan Idrisu ya sa aka tara ruwa a wasu manya daro-daro guda biyar, daga _ nan sai ya dauko maganin dafin nan nasa da ya samo a tsibirin dodo ya zuzzuba a cikin kowane daro, aka gaggauraya sannan jama’‘a suka yi ta kurbar ruwan. Sihirin guban da ke jikinsu ya karye ke nan. Mutane kowa ya ji jikinsa ya warware garau kamar yadda a da ya shigo cikin garin. A nan fa suka Kara sakankancewa da lamarin dan Hamidu. Umurni na gaba da Idrisu ya bayar ga zaratan ‘yan matan nan masu tsaron ramin maciji shi ne a tattaro manya-manyan guma-gumai don cika ramin, da Www.bankinhausanovels.com.ng kuma Kone abin da ke cikin sa kowa ya huta. Sun kammala cikawar ke nan suna zuba mai sai suka ga itatuwan suna yunkurowa sama, ai nan da nan sai suka ruga suka sanar da Idrisu abin da ke faruwa, ya Karaso ya ce kowa ya ja baya, shi kuma ya yi tsaye rike da zararren takobia bakin rami. Can kuwa cike da fushi sai macizan suka ingizo mafi yawancin guma-guman da aka zuba, suka dago kawunansu kamar kawunan manyan jakuna, idanunsu jajawur, harshensu kamar cinyar Kato, jikinsu kuma sai wani irin bawo-bawo ya ke yi kamar bayan itaciya. Kowa ya san cewa sun yi niyyar sharri, amma Idrisu bai bari sun kammala fitowa ba ya sa takobinsa mai ban mamaki ya dauke musu kawuna, dole sai da ya sake sara na biyu sannan kan dayan ya kammala rabuwa da gangar jikinsa. Gawarwakin suka koma cikin rami. Yasa aka mayar da guma-guman nan sannan ya sa aka hura wuta. Sai da aka sami misalin sa’o’i tara wuta na ci don irin kitsen da ke jikinsu. Bayan nan Idrisu ya sa aka cike wurin aka shafe shi kamar ba a taba yin sa ba. Babu shakka mutane sun yi mamakin irin yadda Idrisu ya kashe wadannan shaidanu, shi ma kansa ya Www.bankinhausanovels.com.ng tabbatar da cewa ba don taimakon Allah ba, to babu yadda zai yi. Ana kintata cewa tun kafin kafa garin da misalin shekaru dari takwas macizan suka zo wurin, kuma mutanen garin sun yi imani cewa fushin macizan na iya kama wanda ke nisan duniya ma, ya lalace, amma kuma abin mamaki yau ga wani mutum, dan Adam ya zo ya halaka su, har maya Kone su. Jarumi Idrisu ya tara dukkan jama’a ya yi musu jawabi mai dadi, kuma ya jawo hankalinsu a game da cewa su rabu da bautar wani abu in ba Allah ba. Bayan ya kammala sai’yan matan nan suka ce, “Mun amince da duk abin da ka zo mana da shi, saboda haka mun amince da addinin Islama din da ka ke bayani.” Idrisu ya yi wa Allah godiya mai tarin yawa tare da farin cikin cewa a dalilinsa ne mutane dubbai kan dubbai suka musulunta. Ya nuna musu cewa addinin Musulunci addini ne da ba ya son zalunci, kuma addini ne da ba ya yiwuwa sai da ilmi. Ya ci gaba da bayani cewa, “Ya ku wadannan kyawawan ‘yan mata, akwai babban abin lura ko kuma shawara da nake so in ba ku. Lallai ne ya zama dole ku yi aure, don ita ‘ya mace darajarta ba ta cika sai da miji. Saboda haka in kun Www.bankinhausanovels.com.ng amince ga mazaje nan ku zaBi junanku mu kuma mu yi ta daura muku aure bisa sharuddan da addininmu ya tanada. Wata babbar sa’a da aka yi ita ce mafi yawancin mazajen nan naku da ma tun _ tuni Musulmi ne masu ilmi wadanda za su taimaka wurin sa ku a kan hanya.” Aka fa shiga hidimar zaben juna da daure-dauren aure. Ana haka sai ga gungun wasu kyawawan mata sun zo suka ce duniyar nan babu wanda suke so ya aure su Sai jarumi Idrisu. Ya yi murmushi sannan ya ce, “Na gode saboda Kauna. A duniyar nan duk wanda ya ce kai ya ke so ya gama maka komai, sai dai kuma ina mai ba ku hakuri, don akwai wani babban aiki kwatankwacin wanda na yi a garin nan na gabana, kuma wancan aikin ya ninninka wannan hadari, alhali kuwa ba na son ya kasance akwai hakKin wata mace a kaina in tafi in barta a cikin halin jiran tsammani wanda babu tabbas a ciki. Saboda haka ina mai Kara godiya tare da ba ku hakuri a kan cewa ku yi hakuri ku zabi wasu mazajen.” Babu ta inda ‘yan matan nan ba su Bullo masa baa kan cewa sun amince da komai, amma yatirje ya Ki. Cikin lokaci aka samar da babban masallaci da Www.bankinhausanovels.com.ng makaranta a wannan gari, kuma matan garin suka fara fahimtar addini fiye da duk yadda ake zato. Jarumi Idrisu dan Hamidu ya ba su shawarar zaben Sarkin da zai gabatar musu da jagoranci, sannan kuma a nada Waziri, alKalai da sauran masu mulki don tabbatar da ingantacciyar tafiyar harkokinsu na yau da kullum. Jama’ar gari da suka ji haka sai suka ce wa Idrisu, “Yallabai ai kai ne Sarki.” Jarumi Idrisu ya ce, “Ku kuwa kuna da saurin mantuwa, ina ta maimaita muku cewa ni ba zama na zo yi ba, akwai babban aiki a gabana, saboda haka ina ba ku hakuri.” Sai suka dage a kan ce masa, “To mun amince maka, ka zabar mana wanda kake ganin ya dace.” Idrisu ya ce, “A’a, ba zaa yi haka ba. Ko ba komai dai kun dade tare da junanku, kuma zuwa yanzu ya kamata a ce kuna iya fahimtar wadanda kuke kyautata zaton za su yi muku adalci, don kun fi ni sanin kanku. Sannan kuma za ku fi samun natsuwa da ‘yanci in kuka ji cewa da kanku ne kuka zaba, ba wai dora muku aka yi ba.” A nan fa mutane suka shiga shawarwari tsakanin su, kuma ba tare da wata doguwar takaddama ba suka zabi Abdurrahman a matsayin sabon Sarki. Wato Www.bankinhausanovels.com.ng jarumin dan Sarkin nan da ya fara goya wa Idrisu baya a zamanin Sarauniya Zinkadaziyya. Abdurrahman ya tashi ya yi wa jama’a godiya kan irin yadda suka amince da shi har suka zaBe shi a matsayin shugaba, ya ci gaba da jawabi cewa, “Sai dai kuma ina ba ku hakurin cewa ku zabi wani, don kuwa tun da farko na Kudurta wa zuciyata cewa zan bi wannan jarumin bawan Allah zuwa inda duk ya nufa don in tallafa masa tare da Karfafa masa a wurin da bukatar hakan ta taso.” Jin haka sai Idrisu ya mike ya mayar da martani, ya kalli Abdurrahman ya ce, “Kada ka yi wannan magana. Tafiyata tana da hadarin gaske, wannan tafiya sai ni kadai, kuma ma da a ce ina buKatar abokan tafiya ne, to babu shakka da ka gan ni tare da dubban mutane. Saboda haka ya kai Abdurrahman, na roKe ka da ka yi hakuri, ka daure tun da dai mutanen nan ne suka zabe ka don zama shugaba, to sai ka yi Kokari ka yi, sannan wani abin sha’awa kuma da ma ga shi kai dan Sarki ne wanda daidai gwargwado na ga alamar ka san harkar mulki.” A dalilin irin girmama Idrisu da jin nauyinsa da ya ke yi ya sa Abdurrahman ya amince da amsar Sarautar garin, amma kuma duk da haka sai da ya Www.bankinhausanovels.com.ng tunatar da Idrisu wani abu, cewa, “Amma fa ka san cewa asalin fitowata daga gida a kan neman budurwata ce wadda ta bata, kuma kai can inda take ka nufa.” Sai Idrisu ya ce masa, “Na yi maka alKawari, idan na je na yaki Sarkin aljanu Sham’una kuma Allah Ya ba ni nasara a kansa, to in akwai budurwarka daga cikin ‘yan matan da ke hannunsa, to babu ko shakka in Allah Ya yarda zan dawo maka da ita. Sai dai kuma kafin nan, ba ya yiwuwa a ce kana Sarkin wannan Kasaitacciyar kasa a ce ba ka da mata, saboda haka lallai sai ka zabi guda biyu mu daura muku aure.” Ba tare da wani bata lokaci ba aka daura auren Sarki da ‘yan mata biyu, aka nada Waziri da dagatai da hakimai da wadanda za su rike sauran madafan iko, sannan kuma aka zabi matasa majiya Karfi aka kafa rundunar dakaru. Komai dai irin na mulki ya tsayu tsaf akan kafafuwansa. Sarki Abdurrahman ya sanar da jama’a cewa an sauya wa wannan birni suna daga birnin Salsala zuwa birnin Idrisu, kuma mutane sun yi matukar murna game da haka. Sarki ya rubuta wasiku yana sanar da manyan sarakuna makwabtansa na kusa da na nesa cewa yanzu fa salama da aminci sun kafu a wannan Www.bankinhausanovels.com.ng daula tasu, saboda haka yana gayyatar kowa da kowa da kuma’yan kasuwa don huldar kasuwanci. Lallai kuwa an amsa gayyata. Komai ya zauna daram, masu mulki sun kama shugabanci, ‘yan kasuwa sun tsunduma cikin harkar nema, malamai da dalibai kowa ya dage, to daga nan fa sai Idrisu dan Hamidu ya fara tunanin ci gaba da tafiyarsa. Washegarin ranar da Idrisu zai tafi shi da Sarki Abdurrahman suka zauna cikin dare suna tattaunawa. Ya ke ce wa Sarki, “In Allah Ya so dai ka san gobe ne zan kama hanya, saboda haka nake so in sake jaddada maka wata tunatarwa. Ya kai Sarki Abdurrahman, ina so ka yi tunani ka Kara yi wa Allah Mai girma godiya, ka riKe amanar da Ya ba ka, ka tuna cewa kana cikin kurkuku Ya fito da kai, Ya shugabantar da kai, wanda kuma ba don : taimakonSa ba watakila da tuni ka zama abincin macizai, saboda haka ka yi Kokarin yin mulkinka da adalci. Ka riKa Kokarin bincika hakimai, dagatai da alkalanka, da duk masu rike da kowane irin bangare na mulki don tabbatar da cewa suna aikata gaskiya. Kada ka kuskura ka bari Kasarka ta zama dandalin sabon Allah da kuma aikata Barna.” Sarki Abdurrahman ya yi shiru cike da natsuwa Www.bankinhausanovels.com.ng yana sauraron Idrisu har sai da ya kammala bayaninsa sannan ya ce, “Na gode wa Allah da Ya Kaddara haduwata da kai. Ko da yake tuntuni na san wani abu a rayuwa, wato in mutum yana aikata wani abu mara kyau, to wata rana dole sai zuciyarsa ta hararo tare da tabbatar masa da cewa abinda fa yake aikatawa babu kyau, wanda kuma daga nan ya rage nasa, wato in ya so ya ci gaba da aikatawa ko kuma ya tuba ya daina. Saboda haka ya kai shugabana ina son yin wani alwashi a gabanka, ko kuma in ce in yi maka alKawari, cewa a cikin wannan mulki da nake yi, duk ranar da na gane cewa ba na daukar shawarar kirki, ko kuma na fahimci cewa ana jin tsoron a fada mini gaskiya, ko kuma na ji cewa ba zan iya yin adalci ba, to na rantse maka da Allah zan tara al’umma in sanar da su cewa ni da kai mun yi alkawari a kan cewa inna kai tsawon lokaci kaza a kan mulki zan sauka in koma garinmu, su kuma mutane su zabi sabon Sarki, kuma wallahi zan sauka din don su zabi wani.” Da Idrisu ya ji jawabin Abdurrahman sai murna ta lullube shi don ya tabbatar da cewa zai yi adalci. Wayewar gari tun da Asuba mutane suka fara taruwa, kafin ka ce wani lokaci an cika Kofar fada makil ana jiran fitowar Sarki da jarumi don a yi rakiya. Kafin dagawar hantsi an kammala shiryawa Www.bankinhausanovels.com.ng tsaf, Idrisu ya fito ya hau Jagora, shi kuma Sarki ya hau nasa dokin aka bi su a baya aka dunguma. Bayan tafiyar kwana uku sai Idrisu ya ga alamar ba su da niyyar juyawa, kuma ya fahimci nufinsu na yi masa rakiyar kwana bakwai ne sai ya ce musu ya kamata a tsaya haka nan don yin bankwana. Aka dauki lokaci mai tsawon gaske ana addu’o’i kafin daga baya aka rabu, kowa yana hawaye saboda irin kauna da kuma shakuwar da suka rigaya suka shiga tsakani. KWANA goma kawai tsakanin rabuwar jarumi Idrisu da ‘yan rakiyarsa sai ga shi yana fuskantar wani Kungurmin dajin. A cikin sa kuma sai da ya yi wata biyu da kwana goma sha tara yana tafiya ba dare ba rana, ba ya tsayawa saidai in don hutawa ko kuma wata lalura ta rayuwa kadai. Duk tafiyar nan da ya ke yi bai taba haduwa da dan Adam ba ko daya ba sai namun daji; su ma miyagu. Ba Kankanin bugun ruwan sama suka sha ba, shi da Jagora, don irin ruwan da ke sauka a dajin tun da Idrisu ya ke ko a mafarki bai taba zaton cewa a kan yi irinsa ba. A haka suka iso wani wuri wanda babu komai a cikin sa sai kankara tana zuba daga sama kamar ana yayyafi. Tsananin sanyi ya yi kamar ya halaka shi saboda bai taba shiga cikin irin wannan yanayi ba. Dole a tausaya masa, don ba shakka ya sha wuya. Yana cikin irin wannan mawuyacin hali sai ya ga Www.bankinhausanovels.com.ng Jagora ya karkata ya nufi wani babban kogon dutse wanda a da saboda gigicewa bai lura da shi ba, ai sai wata murna ta rufe shi don tunanin cewa yanzu zai dan sami dumi har Karfin jikinsa ya dawo. Abin mamaki sai Idrisu ya ga ana ta tafiya kwana da kwanaki cikin kogo amma ba a Kure shi ba, kuma in ya waiwaya don ganin inda ya biyo sai ya ga hanyar ta Bace sai dai dutse kawai. Wani lokaci cikin dutsen ya yi sanyi, wani lokaci kuma dumi ko tsananin zafi. Wani lokaci sai jarumin ya ga haske gwanin ban sha’awa, wani lokacin kuma duhu. Wani lokaci ma sai cikin dutsen ya gauraye da Kanshi ko kuma ya dume da wari. Shi dai yana ta tafiya bai damu . A haka sai da ya yi kwana ashirin kafin ya kawo Karshe. A irin wannan wuri, kuma a irin wannan tafiya da Jagora ya yi cikin kwana ashirin, to lallai da a ce wani irin gama-garin doki ne wanda ba shi ba, to tafiyar watanni ce kafin ya Bulle, duk saurinsa kuwa. Bayan Idrisu ya kawo bakin Kofa kuma ya fito sai ya ga fili ya tafi kore shar, babu komai sai ciyawa kanta daya babu wadda ta fi wata tsawo, abin dai gwanin ban sha’awa, ga lumshi da yayyafi yana ta dan sauka. Gaba dayan wurin ba dutse ko itaciya, ko kuma wani wuri busasshe, a’a; babu. Www.bankinhausanovels.com.ng Idrisu bai yi wata-wata ba wurin hawa kan hanya guda daya tilo da ke wurin. Yanzu kam dan Hamidu ya tabbatar da cewa lallai ya fara shiga sashen aljanu. Yana nan yana tafiya kwana da kwanaki a cikin wannan ciyawa wata ranar Asabar sai ya iso wurin wata katuwar bukka mai dan karen kyau, ga ta nan kamar a wurin aka halitta ta don daidaituwa. Ya yi kamar ya wuce, amma sai wata zuciya ta ce masa ya tsaya ya leka mana. Ya sauka daga kan dokinsa ya je bakin Kofar ya yi sallama, sai ya ji shiru. Jin haka sai ya yi sauri ya zare takobinsa yana wani irin walKiya wal-wal bisa zaton ko wata kila bukkar bakaken aljanu ce saboda kada su kawo masa ba zata. Ya sake yin sallama sai ya ji muryar mace ta amsa, “Wa’alaikumus salam. Shigo, ya kai masoyina Idrisu.” . To, da Idrisu ya ji an amsa masa, kuma har da kiran sunansa a matsayin masoyin mai amsawar sai yace a cikin zuciyarsa, “Allah Ka tsare ni in akwai yaudaraa cikin wannan kyakkyawar bukka.” Ya kutsa kai ciki amma bai ga komai ba sai kayan marmari da kayan ciye-ciye iri-iri, da kuma abubuwan sha na alfarma, kuma ga wasu kujeru guda uku na zinariya a ajiye an shirya su a kan wata Www.bankinhausanovels.com.ng darduma mai launukan baki da fari. Kai daga gani ka san cewa akwai magana. Amma kuma dai babu kowa a ciki. Ya je ya yi zamansa a kan daya daga cikin kujerun har na misalin rabin sa’a. Ya dai fahimci abin akwai wasa da hankali a ciki, saboda haka sai ya mike don yin tafiyarsa. Sai muryar da ya ji da farko ta sake yi masa magana, “Kada ka tafi ya kai Idrisu.” Ya koma ya sake zama yana jiran ganin Kwal-uwardaka. Bayan wani lokaci kuma sai ya ji wani irin Kanshin turare da ya taba jin irinsa a dajin nan da ya fara karatu na tsawon shekara daya. Sai ya ji wata murya wadda a tunaninsa za ta iya narkar da dutse ta ce masa, “Gaisuwa gareka ya kai Idrisu dan Hamidu, Sarkin yakin mayaka, kyakkyawan kyawawa, jarumin jarumai, kwantar da hankalinka, ni ce hasken zuciyarka wadda ta fi son ka fiye da rayuwarta.” Shi dai bai ga mai magana ba, alhali kuwa ga dadin maganar ya daki dodon kunnensa, sannan kuma ga Kanshin turare yana ta zagaye hancinsa yana kaiwa zuwa ga zuciya da kwakwalwarsa, sai ya ce, “Ya mai wannan magana mai dadi, na dai san cewa mace ce, Www.bankinhausanovels.com.ng kuma na san na taba jin muryar, saboda haka in dai babu yaudara, to ya kamata a fito fili. In kuma an Ki, to babu ko shakka ni zan ci gaba da tafiyata don na zaku da ganin abin da ya fito da ni.” Shiru kake ji. Idrisu ya mike zai tafi, sai ya ga an dan daga labule, sai ga wata yarinya wadda duk wanda ya ce zai siffanta hakikanin kyanta, to babu ko shakka zai zalunce ta ta hanyar rage ambaton wani abin. Suna hada ido sai gaban Idrisu ya fadi, kuma babu abin da ya fado masa a cikin zuciya sai kamannin yarinya Nur da ya taba hangowa daga nesa. Yana Kokarin tantancewa shin ashe a duniyar nan akwai kyakkyawar da za a iya hadawa da Nur su yi daidai? Ko kuwa yarinya Nur tagwaye ne? A’‘a ai malaminsa bai taba fada masa haka ba. ‘To idan ko wannan yarinya da ke tsaye a gabansa Nur ce, to ya aka yi ta zo nan? Kuma me ya faru da Sarkin aljanu Sham’una? Ko kuwa wani tarkon ne aka dana masa? Idrisu ya ce, ke kuwa yarinya don Allah ke aljana ce ko kuwa mutum? Mene ne labarinki? Yaya aka yi kamarki ta yi daidai da Nur? Kuma yaya turarenki ya yi daidai da nata? Yaya aka yi kika san sunana? Abin da ya sa nake yin wadannan tambayoyi HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 19 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Shi dai bai ga mai magana ba, alhali kuwa ga dadin maganar ya daki dodon kunnensa, sannan kuma ga Kanshin turare yana ta zagaye hancinsa yana kaiwa zuwa ga zuciya da kwakwalwarsa, sai ya ce, “Ya mai wannan magana mai dadi, na dai san cewa mace ce, Www.bankinhausanovels.com.ng kuma na san na taba jin muryar, saboda haka in dai babu yaudara, to ya kamata a fito fili. In kuma an Ki, to babu ko shakka ni zan ci gaba da tafiyata don na zaku da ganin abin da ya fito da ni.” Shiru kake ji. Idrisu ya mike zai tafi, sai ya ga an dan daga labule, sai ga wata yarinya wadda duk wanda ya ce zai siffanta hakikanin kyanta, to babu ko shakka zai zalunce ta ta hanyar rage ambaton wani abin. Suna hada ido sai gaban Idrisu ya fadi, kuma babu abin da ya fado masa a cikin zuciya sai kamannin yarinya Nur da ya taba hangowa daga nesa. Yana Kokarin tantancewa shin ashe a duniyar nan akwai kyakkyawar da za a iya hadawa da Nur su yi daidai? Ko kuwa yarinya Nur tagwaye ne? A’‘a ai malaminsa bai taba fada masa haka ba. ‘To idan ko wannan yarinya da ke tsaye a gabansa Nur ce, to ya aka yi ta zo nan? Kuma me ya faru da Sarkin aljanu Sham’una? Ko kuwa wani tarkon ne aka dana masa? Idrisu ya ce, ke kuwa yarinya don Allah ke aljana ce ko kuwa mutum? Mene ne labarinki? Yaya aka yi kamarki ta yi daidai da Nur? Kuma yaya turarenki ya yi daidai da nata? Yaya aka yi kika san sunana? Abin da ya sa nake yin wadannan tambayoyi ZAMU TASHI shi ne don yanzu yaudara ta yi yawa.” Bayan kyakkyawar yarinya ta ji zancen Idrisu sai ta yi murmushi, kyanta ya Kara bayyana, hasken hakoranta ya fizgi wani sashe na hankalinsa, sannan ta ce, “Haba, ya kai masoyina Idrisu dan Hamidu, babu shakka na yi matukar murna da jin dadin cewa har yanzu kana nan kan bakanka na soyayyar Nur. Ya kai Idrisu babu yaudara, Nur ‘yar Ibrahim ce a gabanka. Na san za ka yi mamakin yadda ka gan ni yanzu a wannan daji, sai dai kuma in ba ka manta labarin da mahaifina malaminka ya ba ka ba cewa yau Asabar ranar bauta ce a wurin su Sarkin aljanu Sham’una, wanda kuma ba ya zuwa ko ina a ranar. Kuma ai ka san labarin aljana Dailanu wadda ke ta koKarin kaiwa da komowa tsakaninmu ko? To wai ma in tambaye ka, ina adikona da na taba jefo maka? Ko kuwa in rera maka wakar da na taba shirya maka ne lokacin kana wancan Kungurmin dajin kana daukar karatu?” Ai nan da nan sai ta rero wasu baituka guda biyu, za ta fara na uku ke nan sai Idrisu ya daka wani irin tsalle cike da murna, don yanzu ya sakankance babu yaudara cewa wannan yarinya da ke gabansa masoyiyarsa ce; yarinya Nur ‘yar babban Shehi Www.bankinhausanovels.com.ng Ibrahim. A rayuwar Idrisu wannan ne karo na farko da ya taba magana da ita fuska da fuska, baki da baki, kunne da kunne. Duk sadarwar da ke tsakanin su gabani a takarda ce kawai, sai dai kuma kallon ta da ya taba yi daga nesa. Idrisu ya ce, “Har yanzu dai ina da bukatar sanin labarin zuwanki nan.” Nur ta amsa masa cewa, “Ya kai rabin rayuwata, kamar yadda na fada maka ne cewa yau Asabar, wato ranar bautar su Sham’una, a duk irin wannan rana ba ya zuwa wurinmu, shi ya sa na saci fage kawata Dailanu ta dauko ni. Mun kintata isowarka nan cikin wannan dan tsakanin, shi ya sa muka tareka. Kuma ka san wani abu? Tun ranar da Sarkin aljanu ya sace ni ban taba irin wannan fitowa ba sai yau. Kuma a yau ya kamata ka san Kawata aljana Dailanu. Ka dai san irin kokarin da take ta yi, kuma duk inda kake, to takan kewayo ka har muke samun labarinka. Na manta ma ban tambaye ka labarin gwagwarmayarka da Sarauniya ba.” Idrisu ya ce, “Ke! Ai wannan Sarauniya shaidaniya ce; babba kuwa, amma mun gode wa Allah tun da har aka sami nasara a kanta da abubuwan bautarta.” Www.bankinhausanovels.com.ng Sai yarinya Nur ta yi kira, “Dailanu… Dailanu, yau dai ya kamata ki zo ku gaisa da mutumin don shi ma ya san fuskarki a zahiri.” Dailanu ashe tun bayan rabuwarsu da Nur a wannan tanti sai ta nufi waje tana ta sunsunar wata irin ciyawa. Jin kiran Kawarta sai ta fahimci abin da ake nufi, wato ta zo a gaisa, saboda haka nan da nan sai ta koma cikin siffar mutane ta nufi tantin, ta yi sallama, jarumi Idrisu ya amsa, ta shiga. Yana ganin ta ya gane cewa aljana ce, don irin hasken jikinta da kyanta sai dai wanda ya gani. Ba don yarinya Nur kyanta ya kai a ce lahaula wala Kuwwata ba, to da saiace Dailanu ta fi ta, amma ina? Wane ita da kyan Nur. Ta gai da Idrisu cikin girmamawa, fara’a da walwala. Bayan ya amsa sai ya ce, “Ya ke Dailanu, na san labarinki daidai gwargwado, da kuma irin taimakon da kike ta yi wa wannan baiwar Allah.” Ya nuna yarinya Nur da hannunsa. Dailanu ta ce, “Ai ranka ya dade ni ce da godiya, don dalilinta ne Allah Ya qaddara na fita daga cikin bakin duhun bautar abin da ba Allah ba. Yanzu kullum cikin farin ciki nake.” Cikin dabara Dailanu ta fice abinta don ba su wuri su zanta, ta koma can cikin ciyayin da take sunsuna. Www.bankinhausanovels.com.ng Hira fa ta barke tsakanin Nur da Idrisu, ta ba shi labarin mahaifinta, wato malaminsa dattijo Shaihi Ibrahim, da irin zaman da suke yi ita da sauran ‘yan mata a can bayan duniya. Cikin hirarsu ne take shaida masa cewa, “tun ranar da muka rabu da mahaifina a lambun nan ba mu sake haduwa ba, sai dai kowane lokaci ina jin labarinsa in Dailanu ta je daukar karatu. Kuma ka san wani taimakon Allah? Har yanzu wadannan shaidanun ‘yan’uwan nata ba su san ta musulunta ba, ballantana har su gane cewa tana zuwa wurinmu, ai da tuni sun halaka ta.” Labari fa ya yi dadi, har lokacin tafiya ya Karato. In sun tuna cewa za su rabu sai su yi ta fata da addu’ar Allah Ya hada su haduwar da babu rabuwa sai dai ko mutuwa. Ita ma mutuwar ba su Ki ta dauke su tare ba; a irin yadda suke ji dai, saboda tsananin son juna. Yarinya Nur ta ce, “Labari ya yi dadi, na manta ban fada maka ba cewa, cikin ‘yan matan da muke tare da su akwai guda uku. Akwai ta dan’uwanka Waziri Habu, da ta Yahaya, da kuma ta Bashari dan Salihu, suna nan lafiya in dai banda matsalar begen masoyansu da ke ci musu tuwo a Kwarya.” Ta ci gaba da yi wa Idrisu bayani, “Miu dai kullum babbar addu’armu ba ta wuce Allah Ya ba ka nasaraa Www.bankinhausanovels.com.ng kan halaka wannan bakin maridi Sham’una. Babu shakka wannan mugu ya zalunce mu, ko da yake zaluncin nasa ne sanadin haduwata da kai amma dai irin su Sham’una ne ke haifar da dacin soyayya…” Idrisu ya katse ta, “To, kafin ki yi nisa, shi kuma mene ne dacin soyayya?” Sai yarinya Nur ta yi wani irin murmushi mai dauke hankalin wanda ya ga wushiryar daidaitattun hakoranta, ta ce, “Ya kai namijin mazaje, idan ba ka san dacin soyayya ba, to saurara, dacin soyayya shi ne masoya biyu suna matuKar son juna amma ba su tare da juna, kuma da zarar sun tuna juna sai bakin ciki ya lullube zukatansu don babu yadda za su yi su hadu. Abu daya ne kuma kawai kan kawo irin wannan daci. Shi ne takobin soyayya. In ba ka san takobin soyayya ba ya kai hasken masu haske, to shi ne hassadar mahassada, suna bakin cikin su ga masoya biyu cikin jirgin ruwan so, duk yadda za su yi don huda jirgin ya nutse sai sun yi, don bakin ciki. Kamar dai yadda la’anannen aljanin nan ya hana ‘ya’yan mutane shan inuwar zuciya.” Ai kafin ta kai jawabinta duk Idrisu ya tsuma da irin yadda ya ji bayani na fita filla-filla daga bakinta, sai ya ce, “Babu shakka kina da gaskiya, iya magana, Www.bankinhausanovels.com.ng kuma babu shakka duk ranar da Allah Ya ba mu nasara a kan wannan azzalumi na mayar da ke wurin malam aka daura mana aure, to na yi alwashin yin raka’a ashirin don godiya ga Allah da Ya ba ni wayayya irinki.” Da yarinya Nur ta ji abin da masoyinta ya ce sai ta dukar da kanta Kasa, irin ‘yar kunyar nan sannan tace, “Ni kuma na yi alwashin in Allah Ya so ba kai kadai za ka yi ba. Tare za mu yi raka’o’in godiya ashirin din.” Lokaci ya yi nisa, Magriba ta yi gab matuka, sai yarinya Nur ta ce wa saurayinta Idrisu, “Yanzu lokacin komawa ya yi, ka yi hakuri ka kwantar da hankalinka, sai mun sake saduwa ranar da ka tumurmusa hancin tsinanne.” Masoyan nan biyu suka dubi junansu sai dukkan su hawaye ya yi ta kwaranyaa kan kumatunsu. Nur ta sa hannu a cikin wata jaka wadda aka yi wa bakinta ; kwalliya da danyen zinare ta zaro wani kyalle fari sal wanda a jiki akwai taswirar da aka yi Kokarin debo kamanninta, ga ta nan ta sa wasu tufafi masu ruwan dorawa, da mayafinsu wanda ya rufe rabin gefen kanta. A cikin taswirar ta yi wani irin dan sunkuyar da kai kamar tana kallon kasa. An daje kyallen da taswirar ke jiki da dusar zinare. Ta mika masa. Www.bankinhausanovels.com.ng Ya karba ya bude, ai sai murna ta lullube shi, ya ji kamar ba rabuwa za su yi yanzu ba. Can kuma sai ya daure tare da murtuke fuska, ya mayar mata da kyallen yana mai cewa, “Na rantse in dai har Sham’una ne ya sa aka zana wannan taswira taki, to ba na bukata.” Nur ta yi dariya tana mai cewa, “To sarkin kishi, kai in banda abinka ai Sham’una ma bai san da wannan ba. Matar dan’uwanka Yahaya, gwana ce wurin zane da dinka taswira, ita ce ta dinka mini shi, saboda haka ka kwantar da hankalinka, babu wani a fadin duniyar nan sai kai.” Tana kammala fadin haka cike da murmushin da ke tabbatar da abin da bakinta ke furtawa. Wannan jawabi kuma shi ne abin da ya warware sakar kishin da ta dabaibaye zuciyar Idrisu. Yarinya Nur ta yi kiran Kawarta don su tafi, Dailanu ta zo don yin sallama da Idrisu, ta ce masa, “Akwai wani abu da nake so wanda kuma naka ne, amma kuma ba zan fada maka ko mene ne ba yanzu, sai ranar da Allah Ya ba mu nasara tukuna. Sirri ne wanda in na fada maka yanzu za ka yi matukar mamaki, saboda haka don Allah kada ka tambaye ni.” Jin haka sai Idrisu bai matsa don jin labarin ba, sai ya ce, “Ya ke shugabar matan aljanu, kwantar da Www.bankinhausanovels.com.ng hankalinki, raina ne kawai ba zan iya ba ki ba, wadda kawai zan iya ba raina sai dai Kawarki Nur.” * Sai Nur ta yi mata irin wasan nan na Kawa da kawa ta ce, “Kada dai ki Kwace mini miji, kin gan shi dan kyakkyawan saurayi.” Dailanu ta ce, “Kamar kuwa kin san shi nake so in kwace.” Nur ta amsa mata tare da murguda baki, “Mhm, wai ma.” Sai dukkan su suka yi ‘yar shewa irin tasu ta mata in suna nishadi. Nur ta dafa kafadar kawarta Dailanu sai kawai ya ga sun tashi sama suna dago masa hannu, shi ma bai Bata lokaci ba wurin daga musu. Tun yana iya hango su har dai suka bace a cikin sararin samaniya. Sauke idanunsa sai ya ga babu komai a wurin da tantin nan ya ke sai ciyawa koriya shar. Bai yi mamaki ba, don ya san aikin aljanu ya fi da haka. IDRISU ya ci gaba da tafiya har ya iso Karshen filin nan mai koriyar ciyawa. Dole ya ja linzami ya tsaya. Yanzu abin da ke fuskantarsa fuska da fuska wani irin hayaki ne jajawur kamar wuta, wanda kuma ya Www.bankinhausanovels.com.ng zama kamar wata katanga mai shiga tsakanin wannan kyakkyawar ciyawa da ya fito daga ciki da kuma inda yanzu ya ke nufin shiga. Sai ya fara addu’a yana cewa, “Allah ina rokon kiyayewarKa daga sharrin wannan hayaki da ban taba ganin irinsa ba.” Bai yi wata-wata ba ya kutsa kai cikin hayakin, ba ya ganin komai sai dai inda Jagora ya bi da shi kawai, wani lokaci ya ji Jagora ya karkata da shi, wani lokaci ya ji kamar ya tsallake wani abu, a haka sai da suka yi misalin kwana uku suna tafiya. Bayan Karewar mugun hayaki sai kawai Idrisu ya tsinci kansa gab da wani babban birni. Kofar garin kuma a bude, saboda haka sai suka shiga. Babu shakka birnin na da matukar kyan gine-gine, dogaye wadanda suka wuce tunanin dan Adam. Sai dai kuma wani abin mamaki, babu kowa a garin. Ya shiga tunani cikin zuciyarsa, “Aljanu ke nan, kun gina gari amma kun Ki ku zauna a ciki.” Bai zame ko ina ba sai gindin wata Katuwar bishiya mai kauri da wasu ganyaye masu fadi lif-lif gwanin ban sha’awa, ya kwance sirdi KarKashinta. Da ma kuma gajiya da rashin barci tun tuni sun rigaya sun yi wuji-wuji da shi. Ya dora kansa a kan sirdin da ya kwanto ya bar Jagora nan tsaye ya san nayi. Www.bankinhausanovels.com.ng Barci da minshari ya ke ta yi har sai da dare ya fara tsalawa. Can sai ya rika jin motsi ana ta kaiwa da komowa, kamar dai ana cin kasuwa. Ya bude ido sai ya ga wasu irin halittu, su ba mutane ba, su ba dabbobi ba, su kuma ba tsuntsaye ba. Idanunsu jajawur kuma jikinsu da wani irin gashi kamar na rago. Wannan birni cike yake makil da irin – wadannan halittu kowa yana ta harkar gabansa amma babu mai magana da wani. Ga kuma wani gungu nan sun taru suna kallon sa. Idrisu ya daga hannu ya yi musu sallama, “Assalamu alaikum.” Babu wanda yaamsa. Sai ya tambaye su, “Don Allah in ku mutane ne, to wadanne iri ne? In kuma ba mutane ba ne shin ku aljanu ne ko kuwa tsuntsaye?” . Babu dai wanda yace masa uffan-kanzil. Ya ce, “To ni dai na fita hakKinku. Kuma in ku masu sharri ne, to ina neman tsarin Allah daga gareku.” Ya juya ya sake dora kansa a kan sirdi ya rungumi takobinsa da mashi ya ci gaba da barci, Jagora kuma yana tsaye kusa da shi. A takaice dai jarumin bai farka basai Asubahi. Farkawarsa abin mamaki sai ga wannan birni ya Www.bankinhausanovels.com.ng Bace babu ko alamarsa, filin babu komai sai wannan itaciya da ya ke Karkashinta kawai, ganin haka sai Idrisu ya ce, “Na san a rina, wai an saci zanin mahaukaciya. Wane mutum da aikin aljanu.” Ya tashi ya gabatar da ibada da addu’o’insa na neman samun nasara sannan ya dora wa Jagora sirdi suka ci gaba da tafiya. Bayan kamar kwana goma sai ya iso wani fili fari fat wanda babu ko digon baki a cikin sa, abin da kawai ya hanawa jarumin sukuni a wurin babu kamar tsananin zafin rana. Can a gefe sai ya hango wasu mazaje su goma, Karfafa, ba tare da wani bata lokaci ba sai ya nufe su ya yi sallama, “Assalamu alaikum.” Suka ce, “Wannan kuma kai ka san abin da kake nufi, mu ba shi ya dame mu ba, ba ruwanmu da shi, mu yau ranka kawai muke bukata.” Idrisu ya ce, “Ban ki ba, amma shin ko kuna da wani dalili na bukatar raina?” Abin mamaki gaba dayansu suke magana, a lokaci daya kuma da kalamai iri daya kamar sun haddace, sai dai kuma shi Idrisu wannan bai rudar da shi ba don ya san ba karamin aikinsu ba ne. Wadannan halittu suka ci gaba da mayar masa da martanin cewa, “Mu kuwa ke da kwakkwaran dalilin kashe ka. Ka ga birnin da ka wuto wanda babu wanda ya yi maka Www.bankinhausanovels.com.ng magana a cikin sa? To birninmu ne, ka gan shi can.” Suka yi nuni da hannayensu, yana dubawa sai kuwa a gefe shirim ya hango birnin da ya wuto misalin kwana gona da suka gabata. Jarumi Idrisu ya tambaye su, “Amma ku kuwa mene ne labarinku, kuma mene ne labarin wannan birni da ya bace ya dawo nan?” Suka amsa masa cewa, “E lallai za mu sanar da kai, akalla kafin mu kashe ka mu shanye jininka, mu cinye namanka, kuma mun yi maka alkawari cewa ko digo na jini ko tsoka ko kuma wani bangare na kashi ko sashe daga jikinka ba za mu rage ba. Ka ga wannan gari garinmu ne wanda yau ya kai kimanin shekaru dubu tara da dari tara da kafuwa. Duk kuma da ka gan mu cikin wannan siffa ba mutane ne ba ne; aljanu ne. Tun farko abin da ya sa ba mu zartar maka ba shi ne dalilin kwanciyar da ka yi a karkashin waccan itaciya da ka wuto kwanakin baya. Ko kiyashi ba mu iya kashewa Karkashin waccan itaciya saboda girmama ta da muke yi, don duk aljanin da ka gani a yau yana rayuwa, to ya tarar da wannan bishiya ne, kuma duk wani aljani da ya shahara, to in ka bi diddigi da tarihi za ka tarar yana da wata dangantaka da bishiyar. Kai ko Sarkin aljanu Www.bankinhausanovels.com.ng Sham’una ma lokacin da ya ke Karami sai da ya taba kwana a kanta. Daga cikin darajar wannan itaciya da kuma irin yadda muke girmama ta shi ne babu wani aljani da ya isa ya yi magana a lokacin da ya ke kusa da ita, shi ya sa ka ga ko amsa maganarka ba mu yi ba.” Wadannan aljanu dai suka ci gaba da yi wa Idrisu bayani, “Mu aljanun wannan birni muna iya daukarsa mu kai shi inda muka ga dama. Kuma mun kawo shi nan ne don mu tare ka.” Idrisu ya ce, “Duk na ji wannan, to amma mene ne dalilin bukatar kashe ni? Ko kuwa za ku kama mutum ne da laifin da bai sani ba? Ina kyautata zaton cewa yanzu laifina shi ne hutawa da kuma yin barci a Karkashin itaciya ko? To a gaskiya da ace na san haka kuka dauki itaciyar to babu abin da zai hana ni sare ta kowa ya huta.” Suka ce masa, “To ai mu in mun kashe ka ma bakin cikinmu raguwa kawai zai yi, amma ba zai kare duka ba, sai dai kuma akwai dan sauki in mun tuna cewa ba ka numfashi, don ka zalunce mu, ka cuce mu, ka halaka mana kakanninmu ta hanyar kashe su kisan gilla ba tare da wani laifi ba.” Idrisu ya tambaya, “Su wane ne kakannin naku da na kashe? Yanzu dai dole sai kun Kakaba mini laifi da Www.bankinhausanovels.com.ng karfin tsiya don ku zalunce ni?” Suka ce, “Af, har ka manta, macizai biyu da ka kashe a birnin Sarauniya mai macizai, to ai wadannan macizan ne kakannin namu. Su ne ke da wannan birni namu da ka gani, duk wanda ka gania cikinmu daga ‘ya’ya ne sai jikoki da tattaba-kunne nasu, kuma dukkanmu mun yi alkawarin cewa sai mun shayar da kai modar mutuwa a duk inda kake a duniyar nan ko wajenta.” Da Idrisu dan Hamidu ya ji jawabin wadannan aljanu sai ya ce musu, “E, lallai kam babu shakka ni ne na kashe wadancan tsinannun kakanni naku, kuma muna rokon Allah Ya gaggauta rayukansu zuwa cikin wuta, Ya kuma dandana musu azaba. To ku ai wadannan kakanni naku ai ko Sarkin aljanu Sham‘una ba na zaton ya kai su zalunci. A kullum fa sai sun kashe mutane, sun shanye jininsu sun cinye namansu, ana kuma bauta musu alhali su ba Ubangiji ba, saboda haka Allah Ya tsine musu, da ku ma baki daya don kuwa kun ki gaskiya. Saboda haka tun wuri ku bace mini da gani, ku ba ni wuri in wuce, don ni ba don ku na fito ba.” Sai wadannan aljanu suka ce, “Lallai ka isa azzalumi, ka kashe mana kakanni, sannan ka bi su da mugun zagi da mummunar addu’a, ko kunyarmu ba Www.bankinhausanovels.com.ng ka ji ba. Kuma maimakon ka roke mu arziki mu Kyale ka amma mu kanmu sai da ka zage mu tare da raini.” Idrisu ya tambaya, “In roke ku? Ai wannan zancen banza ne irin naku na ‘ya’yan azzalumai. Bayan zagin ma ingiza ku lahira zan yi don ku je ku tarar da su can.” Saboda irin tunzura da suka yi sai wani daga cikinsu ya yi wata irin magana wadda Idrisu bai san abin da take nufi ba, sai ga aljanu kamar su dubu biyar sun kewaye shi sun yi masa zobe, dukkan su kumaa cikin siffarsu ta aljanu don su tsorata shi kafin su yi watanda da namansa wadanda suka samu sun samu wadanda kuma ba su samu ba su yi hakuri. Amma kuma shi Idrisu ko gezau. Da suka ga haka, sai suka fara rikidewa suna komawa wasu irin macizai, iri-iri, launi dabandaban, jajaye da farare, algashi da masu dabbaredabbare, kai wasu ma har da dan kunne. Wasu manya kamar girman giwaye, wasu kuma Kanana. Wasu na kukan jaki wasu suna haniniyar doki, kai wasu har tashi sama suke yi suna sauka. Lura da haka sai Idrisu ya zaro takobinsa daga kubensa, kuma wani abin mamaki shi ne takobin na fitowa sai kawai bakunansa suka koma goma sha biyu, kuma dogaye masu tsawon gaske. Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka fara kai masa hari, amma da zarar ya kai sara sai ka ga aljanun macizan nan suna ta fadowa kasa kamar fari, kafin wani dan lokaci ya kashe duk macizan da ke shawagi a kansa da kuma wani kaso mai yawa daga cikin wadanda ke Kasa. Sauran sai suka raba junansu kashi-kashi, koraye daban, jajaye daban, tika-tiKka daban, haka nan sirara, ga su nan dai kowanne sun ware gefe. A haka kungiya-kungiya suka shiga kai wa Idrisu da dokinsa farmaki. Tsartuwar dafi kake ji babu KakkKautawa har sai da suka jike su shi da dokinsa sharkaf, amma wannan babu tasirin da ya yi musu don tun a tsibirin dodo jikin Idrisu da dokinsa sun zama babu dafin da zai iya tasiri a kansu. Cikin wani dan KanKanin lokaci sai ga Idrisu ya gama da wani kashi da ya fado masa. Ganin haka sai wadannan aljanu suka tunzura suka koma cikin mummunar siffa irin tasu ta aljanu suka nufo shi gaba daya, shi ma sai ya yi fushi ya kara kaimi wurin sara da suka. Babu ko tsoro ko razana haka ya ke ta yi, sai dai ka ga ya matsa gaba, ya ja baya ya buda Kafafuwa ya yi wani irin juyi ya tunkari wadanda suka nufo bayansa kafin sauran su gyagije ya sake juyowa kansu, kai fada da dan Hamidu ba dai gaba da gaba ba, kai ko ta bayan ma sai an shirya. HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 20 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Da suka ga haka, sai suka fara rikidewa suna komawa wasu irin macizai, iri-iri, launi dabandaban, jajaye da farare, algashi da masu dabbaredabbare, kai wasu ma har da dan kunne. Wasu manya kamar girman giwaye, wasu kuma Kanana. Wasu na kukan jaki wasu suna haniniyar doki, kai wasu har tashi sama suke yi suna sauka. Lura da haka sai Idrisu ya zaro takobinsa daga kubensa, kuma wani abin mamaki shi ne takobin na fitowa sai kawai bakunansa suka koma goma sha biyu, kuma dogaye masu tsawon gaske. Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka fara kai masa hari, amma da zarar ya kai sara sai ka ga aljanun macizan nan suna ta fadowa kasa kamar fari, kafin wani dan lokaci ya kashe duk macizan da ke shawagi a kansa da kuma wani kaso mai yawa daga cikin wadanda ke Kasa. Sauran sai suka raba junansu kashi-kashi, koraye daban, jajaye daban, tika-tiKka daban, haka nan sirara, ga su nan dai kowanne sun ware gefe. A haka kungiya-kungiya suka shiga kai wa Idrisu da dokinsa farmaki. Tsartuwar dafi kake ji babu KakkKautawa har sai da suka jike su shi da dokinsa sharkaf, amma wannan babu tasirin da ya yi musu don tun a tsibirin dodo jikin Idrisu da dokinsa sun zama babu dafin da zai iya tasiri a kansu. Cikin wani dan KanKanin lokaci sai ga Idrisu ya gama da wani kashi da ya fado masa. Ganin haka sai wadannan aljanu suka tunzura suka koma cikin mummunar siffa irin tasu ta aljanu suka nufo shi gaba daya, shi ma sai ya yi fushi ya kara kaimi wurin sara da suka. Babu ko tsoro ko razana haka ya ke ta yi, sai dai ka ga ya matsa gaba, ya ja baya ya buda Kafafuwa ya yi wani irin juyi ya tunkari wadanda suka nufo bayansa kafin sauran su gyagije ya sake juyowa kansu, kai fada da dan Hamidu ba dai gaba da gaba ba, kai ko ta bayan ma sai an shirya. ZAMU TASHI Yaki ya yi yaki, ba ka jin komai sai Karajin aljanu, wuta kuwa sai faman tashi take ta yi kamar walkiya, aljanun nan idan suka buga suka buga sai su kara tsawo don su bai wa Idrisu tsoro, amma ina? Ba ruwan jarumi da tsoro, duk lokacin da suka Kara tsawo suka kere shi sai shi ma dokinsa Jagora ya Kara wani irin tsayi da fadi don daidaita da sabon matsayinsu yadda za a ji dadin bugawa. Kwana biyu ana gwabzawa kafin jarumi Idrisu ya sami nasara a kan wannan jama’a ta aljanu, ya karkashe su ya yi musu fata-fata da runduna. ‘Yan sauran wadanda suka rage; ba su wuce ashirin ba, da suka ga ba za su iya ba, sai suka tashi fir kamar tsuntsaye suka fantsama cikin duniya. Idrisu ya yi wa Allah godiya sannan ya karasa zuwa wurin wani karamin kogi ya wanke dokinsa Jagora, shi ma ya wanke jikinsa, ya yi alwala ya gabatar da ibada sannan ya zauna yana cin abinci tare da hutawa yana mai kara yi wa Allah godiya. – Cikin wannan hutun da ya ke yi ne sai kuma tunanin soyayya ya shige shi. Ya rika tuna yarinya mai dumbin kyau da hankali, wato Nur ‘yar Ibrahim, yana tuna irin cikar halittarta, muryarta da irin kalamanta masu cike da hikima. Nan da nan ya sa hannu a cikin burgamensa ya janyo taswirar da ta ba Www.bankinhausanovels.com.ng shi ya shiga kallo yana Kara tsunduma cikin kogin so. Idrisu ya shiga tunani a cikin zuciyarsa cewa, “Lallai hutu bai gan ni ba, akwai aiki a gaban maza.” Zumbur ya tashi ya dora wa Jagora sirdi yana mai yi masa magana cewa, “Jagora ba mu ga ta zama ba.” yA ci gaba da tafiyarsa, har dai ya iso Kofar wani babban gari, shi ma na aljanu. Bai tsaya wani Bata lokaci ba ya kutsa kai. Abin da ya ba shi mamaki shi ne shigarsa ke da wuya sai ya fahimci cewa mafi yawan aljanun da ke garin suna da wata irin kyakkyawar siffa, kuma mafi yawancinsu suna sanye da fararen tufafi ne, wasu har da rawuna a kawunansu, sun kuma yi gungu a gefe daya suna ta gabatar da Sallar jam’i. Wannan, babu shakka ya yi matukar burge jarumi Idrisu tare kuma da cika shi da farin ciki. Bayan sun idar sai ya yi musu sallama, suka amsa masa. Ya ce, “Don Allah jama’a ni bako ne, matafiyi, ina so ne in kun amince in dan huta a wannan gari naku kafin in wuce.” Suka ce, “A’a ko kadan babu matsala, ai kamar ka zo gida ne, amma don Allah mu tambaye ka kai mutum ne ko kuwa aljani>” Idrisu ya amsa, “Babu shakka ni mutum ne dan Adam.” Sai mamaki ya rufe su, yadda za a ce wai mutum ne ya biyo ta wannan hanya ya shigo garinsu lafiya. Hanyar da ko aljani ya biyo ta, to lallai ya isa a nuna shi a matsayin mai tsananin tsawon kwana. Abu na biyu shi ne irin yadda da kuma wanda ya wanke idanunsa ta yadda rangadadau yake iya ganin aljanu, ba su iya Boye masa. Aljanun nan suka ce, “Ya kai bawan Allah, abin da zaa yi shi ne yanzu za mu je mu gabatar da kai zuwa ga shugabanmu, kuma abin da ya ce da shi za a yi aiki.” Idrisu ya amsa musu cewa, “Wannan kuma daidai ne.” Suka wuce gaba yana biye har tsakiyar gari, suka umurce shi da ya jira. Suka shiga wurin shugabansu, suka sanar da shi cewa ga wani matafiyi nan dan Adam, Musulmi, kuma ya shigo cikin aminci ne ba sharri ba, yana bukatar masauki kafin ya wuce. Aka ba da umurnin shiga da shi. Shigar Idrisu sai mamaki ya kama shi, don tun daga Kofa har zuwa inda kujerar Sarki take askarawa ne aka jera dama da hagu sun tafi reras gwanin ban Www.bankinhausanovels.com.ng a. Sai da ya yi tafiya mai dan tsayi kafin ya iso wurin shugaban. Akwai manyan kujerun alfarma, daya babba daya kuma Karama. Shi wannan shugaba da Idrisu ya tarar yana zaune ne a kan Karamar kujerar. Idrisu ya yi sallama aka amsa, aka ba shi umurnin zama a kan wata kujera ta azurfa da ke nan gefe. Ya gai da wannan shugaba na aljanu da gaisuwa irin wadda ake yi wa manyan sarakunan duniya, shi kuma ya amsa cike da murmushi, farin ciki da jin dadi, kuma ya fahimci cewa lallai Idrisu saurayi ne mai mutunci wanda ya san darajar na gaba. Dattijon aljani ya ce, “Ya kai wannan saurayi dan Adam mene ne labarinka? Mene ne labarin tafiyarka? ‘Wane aljani ya zo da kai nan? Don kuwa in ba dauko ka aka yi aka tashi da kai sama ba, to babu yadda zaa yi ka biyo wannan hanya guda daya tilo da muke da ita ta wannan fuskar. Dalili kuwa shi ne akwai wasu bakaken aljanu masu zama macizai, miyagu ne wadanda duk Kasashen aljanu an san irin muguntarsu da yadda ba su barin ko kuda ya ratsa ta inda suke face sai sun halaka shi, ballantana dan Adam. Kai ko Sarkin aljanu Sham’una yana sane da irin sharrinsu. Ya kai saurayi, da a ce ta wannan hanya ka biyo, to Www.bankinhausanovels.com.ng babu shakka zan ce ka shigo ta cikin wani kogo wanda shi ne kamar katanga da ke tsakanin Kasashenku na mutane da namu na aljanu. Ko kuma tsakanin cikin duniya da wajenta. Kuma dai ya kai wannan saurayi, da a ce ta wannan hanya da nake magana ka biyo, to babu makawa ka ga wata babbar gona wadda ciyawa ta tafi Gabas da Yamma, Kudu da Arewa, to asali gonarmu ce, kuma duk yankin wurin garinmu ne wanda muka gada shekaru dubbai da suka wuce amma wadancan bakaken aljanu suka yi mana fin Karfi suka kwace. Kuma saboda yawan zalunci da kisan da suke yi mana ne muka lallaba muka matso nan muka kafa wannan gari. Yanzu ma da ka gan mu nan albarkacin addu’o’i ne muke ci, Allah Ya shafa mana lafiya Ya kiyaye mu, ba don haka ba da tuni wadancan miyagu kuma bakaken aljanu ko kuma wannan la’anannen Sarkin aljanu Sham’una sun gama da mu.” Da Idrisu ya ji jawabin wannan dattijo sai murna ta fara kama shi don ya fara shiga wurin da ya ji ana ambaton sunan Sarkin aljanu Sham’una sosai, wato ya fara kusantar Kasarsa ke nan. Sai ya ce, “Ya kai wannan dattijo mai daraja, ni sunana Idrisu dan Hamidu. Wannan hanya kuma da kake magana ta Www.bankinhausanovels.com.ng cikinta na biyo, hasali ma ita wannan gona taku sai da na share kusan sa‘o’i bakwai cikinta kafin na ci gaba da tafiyata. Babu shakka wadancan miyagun aljanu da kake magana na ci karo dasu, kuma daga yau din nan kada ku sake tayar wa da kanku hankali don kuwa Allah cikin ikonSa Ya ba ni nasara a kansu, duk na halaka su, in banda in ban manta ba… na kirga su lokacin da suke guduwa, su goma sha takwas kawai. Suka rage wadanda suka gudu Kuma kamar yadda aka sanar da kai ne cewa ni matafiyi ne. Babban burina ko kuma ince abin da ya biyo da ni nan shi ne don in je in yaki wannan azzalumin Sarkin aljanun da ka ambaci sunansa yanzu, wato Sham’‘una, in Allah Ya yarda, kuma ina fata Allah Zai ba ni nasaraa kan haka.” . Da dattijon aljanu ya ji bayanin Idrisu ko kadan bai Karyata ba, sai ya ce masa, “Yo .fa Sai dai kuma tsugune ba ta Kare ba tsakaninka da wadancan bakaken aljanu da ka kashe, don kuwa jikoki ne da tattaba-kunne na wasu bakaken kafiran aljanu marasa imani wadanda ba su da wani abinci sai jini da naman dan Adam, kai hasali ma wannan dalili ne ya sa suka Ki zama cikin aljanu ‘yan’’uwansu suka koma garin wata Sarauniya ‘yar Adam suka hada guiwa da ita don cin ma burinsu. Ina tabbatar maka Www.bankinhausanovels.com.ng ko kadan ba za su Kyale wannan ya tafi a banza ba, wato sai ka daura damarar karawa da su, kuma duk aljanin da ka san ya kwana duniya ya san cewa su ba kanwar-lasa ba ne wurin jarunta. Ka ga yanzu zuwan ka nan ka shafa mana kashin kaji ke nan, don na tabbata yanzu suna nan suna shirin neman ka, in ma ba su fito din ba ke nan. Sai dai kuma Allah Ya kiyaye mu da kariyarSa! Da Idrisu ya ji zancen dattijo sai ya ce, “Ya shugabana, ina so ka kwantar da hankalinka, kuma ka saki jikinka. Dalilina kuwa shi ne, su wadancan miyagun aljanu, wato kakannin bakaken da aka kashe, to ta kansu na fara, yanzu maganar da ake yi ko tokar su babu. Su ma Allah Ya sa mun yi nasara a kansu har ita Sarauniyar. Su ne suka cinye ta, ni kuma takobina ya cinye su.” Dattijon aljani ya bude baki yana mamaki, “Yanzu takobinka ya kama jikinsu?” Idrisu ya ce, “Kwarai kuwa Allah Ya taimake ka.” Sai aljani ya ce, “Lallai akwai mamaki cikin lamarinka, ina kyautata zaton addu’o’in da ake ta yi ne Allah Ya amsa a kanka. Saboda haka muna fata Allah Ya taimake ka, Ya kuma ci gaba da kiyaye ka. Allah Ya dora kaa kan Sham’una.” Idrisu ya amsa, “Amin.” Www.bankinhausanovels.com.ng Dattijo shugaban aljanu ya ci gaba da bayanin cewa, “Ya kai Idrisu, na tabbata tun da ka biyo ta cikin kogon dutsen nan ka fito lafiya, kuma har ka kashe aljanun nan biyu su da jikokinsu kuma ko kwarzane ba ka yi ba, to babu shakka za ka iya karawa da Sham’una. Ina son sanar da-kai labarinmu ya kai jarumi. Ka ga wannan babbar kujera wadda ta fi wadda nake kai girma? To ita ce ta Sarkinmu. Shi wannan Sarki namu na ifritai yana da mulki, kuma ga shi jarumi mai yawan dabarun yaki, sau da yawa aljanu kan kawo masa hari amma sai ya tarwatsa su. Mu aljanun wannan gari muna da wata al’ada, ba mu da sarautar da ake kira Waziri, a’a Limamin gari shi ne Waziri kuma Alkalin gari. In Sarki ba ya nan kuma shi ne a matsayin Sarki kamar yadda ka gan ni yanzu haka nan. Sunana Abdallah, kuma sunan wannan daula ta mu Yaminul-Ausad. Sai Idrisu ya tambaya, “To shi Sarkin naku ina ya ke?” Sai Limamin aljanu Abdallah ya amsa da cewa, “Abin da ya faru ya kai Idrisu shi ne, mu dai aljanun wannan gari muna matukar son zaman lafiya, babu abin da muka fi so fiye da shiga cikin duniya neman Www.bankinhausanovels.com.ng abinci, sai kuma neman ilmi da bautar Allah da yabon shugabanmu Annabi Muhammadu tsira da amincisu tabbata a gare shi. Sauran aljanu makwabtanmu babu abin da ya fi bakanta musu rai game da mu sai don tafarkin da muke bi na addinin Islama, su bukatarsu ita ce mu zama kafirai kamar su mu rika bauta wa tarkace kamar yadda suke yi, amma kuma a kowane lokaci sai mu riKa nuna musu cewa haka ba zai taba yiwuwa bain Allah Ya so. Bangarori biyu ne suka fi tsananta mana, Bangaren farko shi ne na wadancan macizan aljanu, har ma suka kore mu daga garinmu na ainihi, sai kuma daya sashen wanda Sarki Sham’una ke yi wa mulki, wato daular Jarirul Waki-waki wadda take da manyan birane har guda goma sha biyu. Bayan wadancan aljanu sun kore mu daga birninmu mun dawo nan, sai jama’ar Sham’‘una suka shiga tsananta mana, kullum sai kashe mana jama’‘a suke yi suna yi wa’ya’yanmu mata fyade. Da tura ta kai bango sai shugabanmu Sarki Ifritu ya tara jama’a aka tsayar da shawara a kan cewa dole ne mu yaki Sarki Sham’‘una don mu kare kanmu, in kuwa ba haka ba, to da dai-dai da dai-dai za su yi ta halaka mu. Www.bankinhausanovels.com.ng Muka yi shirin yaki tsaf muna jiran zuwan dalili. Can kuwa bayan wasu ‘yan kwanaki sai ga wasu katti daga bangaren Sham’una su ashirin sun shigo har cikin gari suka kama mana ‘yan mata goma suka lalata. To da labari ya zo, ai ba mu bari sun bar garin ba, aka tare su aka yi musu lugude, aka yi kaca-kaca da su, da Kyar biyu suka kai labari. Ashe shi maSham’una Kiris ya ke jira, saboda haka sai ya turo runduna, amma ko labari ba su kai ba, mun aika da su inda ba a dawowa, ya sake turo wasu mayakan su ma ba su kai ba. A haka sai da ya turo rundunoni biyar muna halaka su. Dalilin haka shi da kansa Sarki Sham’unan ya shiryo gagarumin yaki ya tunkaro mu, muka fita aka fara gwabzawa. An dauki tsawon kwanaki ana karawa, kuma a kullum sai Sham’una da shugabanmu sun buga. Babu shakka a tarihin yakukuwan aljanu, Sham’una bai taba samun jarumin Sarki kamar Sarki Ifritu ba; Sarkinmu. Kuma yawan jarumai da dakarun Sarkin aljanu Sham‘’una dubban daruruwa ne kan dubban daruruwa in ka misalta da yawan jama’armu, saboda haka nan da nan suka ci Karfinmu, suka kashe mana jama‘a da yawa kuma suka kama da yawa. Mu sauran Www.bankinhausanovels.com.ng da muka rage sai Sarkinmu ya umurce mu da janyewa zuwa cikin gari. A Ka’ida ba ma jayayya da Sarki, saboda haka sai muka fara Kokarin janyewa din, a gajiye. Sarki Sham‘una ya ba da umurnin cewa a bi mua kashe na kashewa a kama na kamawa, amma sai Sarki Ifritu ya yi wata irin tsawa mai tsananin firgitarwa, wuri ya yi tsit. Ya ce shi ya ba da kansa don a Kyale jama’arsa kada a bi su, ya zubar da makamansa, aka kuwa zuba masa ankwa shi da jama’ar da ke tare da shi a lokacin, su dubu saba’in da uku. Shi Sarkinmu sai aka saka shi a cikin wata Katuwar batta ta bakin karfe. Akwai wani dutse a can cikin tekun Tsagirgi, shi ne Sham’una ya tsaga shi biyu ya sa wannan batta ya mayar da dutsen ya hade. Wannan bayani mun same shi ne daga majiya mai tushe, hasali ma har izgili mutanen Sham’una ke yi mana in suna fada mana inda Sarkinmu ya ke. Su kuma sauran jama’armu da aka kama sai aka kai su saman wani babban dutse da ke gefen tekun aka kulle aka ba Sham’‘una makullan yana rike da su a hannunsa. Da wancan dutse da aka saka Sarkinmu da kuma sarkokin da aka daure ‘’yan’uwanmu ba wanda zai iya Www.bankinhausanovels.com.ng bude su sai Sarki Sham’una. Kuma ya kai Idrisu, shi wannan dutse da ‘yan‘uwanmu ke daure a kai ta nan ne ma hanyarka, za ka gan su da idanunka.” Liman ya ci gaba da labarta cewa, “Shi wannan dutse ya kai Idrisu ya tafi a kwance ne, in ka fara hawa a hankali za ka ga kamar kana hawa sama ne. Kafin ka kai Karshen samansa za ka dauki misalin watanni masu yawa a tafiya irin taku ta mutane, amma in aljani ne, kakkarfan saurayi zai kai cikin kwana bakwai. Babban abin da nake son jawo hankalinka a nan shi ne ita tafiya a cikin Kasashenmu na aljanu, to ko a wurin aljanin ma ba ta da sauri sabanin yadda muke da tsananin sauri a cikin Kasashenku na mutane, sai dai ko in aljani na da waniirin shiri ne na musamman, shi ne za ka ga ko a cikin Kasashen namu yana sauri kamar walkiya, wanda kuma samun irin wannan sai an tona.” Limamin aljanu Abdallah ya ci gaba da yi wa jarumi Idrisu bayani cewa, “In ka Kure saman dutsen, to za ka ga fadinsa ya tafi ta kowane bangare, har ma ka dauka cewa ba a kan dutse kake ba. In kana son Ketare shi da sauri, to ka bi ta fuskar Gabas, wanda akan yi tafiyar kwana bakwai kawai. Www.bankinhausanovels.com.ng Karshen wannan dutse ne za ka ga wani ruwa baki Kirin ya tafi iyaka ganinka, to a ciki ne Sham’una ya tsaga dutsen da ke cikin sa ya sa Sarkinmu. Wannan shi ne labarinmu ya kai Idrisu.” Bayan Idrisu ya kammala jin wannan labari daga bakin Limamin aljanu har ma da taimako a game da siffanta masa irin hanyar da zai bi sai murna da farin ciki suka kama shi, musamman ma da ya ji cewa yana wurin da labarin Sham’una sananne ne, wato yanzu ya Kara tabbatar da cewa lallai ya kama hanyar haduwa da shi. Sai Idrisu ya ce wa Liman, “Ya kai wannan dattijo mai dumbin daraja, ina so ka kwantar da hankalinka, kuma ka sani cewa in Allah Ya yarda shekarar jin kunyar Sham’una ta tsaya, tura ta kusa kaiwa bango, kuma da yardar Allah Sarkinku ya kusa fitowa daga Kangi.” Dattijo ya ce, “Ya kai Idrisu abin da nake yi maka tunani shi ne hawa dutsen nan, kuma bayan hawa dutse sai maganar shiga cikin kasar Sham’una, wanda ba abu ne mai sauki ba ko da ga aljanun da ke tashi, balle dan Adam. Da ma ace Sarki Ifritu na nan ne, to babu shakka da ya taimaka maka.” Idrisu ya amsa masa da cewa, “Baba wannan kada ka damu kanka, don in Allah Ya so matuKar dokina Www.bankinhausanovels.com.ng Jagora yana tare da ni, to ba na tsoron nisan tafiya ko kuma wahalarta, kuma ma ina tabbatar maka da cewa in Allah Ya so tare da Sarkinku za mu yaki azzalumi Sham’una.” Aka shirya gagarumar walima, aka ci aka sha, suka yi ta murna da raye-raye irin nasu na aljanu. Babu shakka Idrisu ya ji dadin wannan karramawa da aka yi masa. Aka nuna masa dakin da zai sauka, saboda girman dakin gaba daya shi da Jagora suka shige, ko da yake zuwa yanzu ya fara daina mamaki game da irin aikin aljanu. A haka, kuma cikin matukar jin dadi da farin ciki sai da ya kwana bakwai yana hutawa, jikinsa ya warware. Daga nan sai ya sanar da Shehi Abdallah Limamin aljanu cewa shi fa yanzu ya yi harama yana bukatar wucewa, kuma ya gode game da dukkan irin tarba da kyautatawa da aka yi masa. Liman ya yi gayyar dumbin jama‘ar aljanu don yin rakiya ga wannan babban bako nasu. Kwana uku suna tafiya tare da Idrisu, daga nan aka tsaya aka yi addu’o’in dacewa da nasara gare shi sannan suka yi sallama suka juya don komawa gida. Yanzu aikin da ke gabansa shi ne hawa dutsen da HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 21 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Idrisu ya amsa masa da cewa, “Baba wannan kada ka damu kanka, don in Allah Ya so matuKar dokina Www.bankinhausanovels.com.ng Jagora yana tare da ni, to ba na tsoron nisan tafiya ko kuma wahalarta, kuma ma ina tabbatar maka da cewa in Allah Ya so tare da Sarkinku za mu yaki azzalumi Sham’una.” Aka shirya gagarumar walima, aka ci aka sha, suka yi ta murna da raye-raye irin nasu na aljanu. Babu shakka Idrisu ya ji dadin wannan karramawa da aka yi masa. Aka nuna masa dakin da zai sauka, saboda girman dakin gaba daya shi da Jagora suka shige, ko da yake zuwa yanzu ya fara daina mamaki game da irin aikin aljanu. A haka, kuma cikin matukar jin dadi da farin ciki sai da ya kwana bakwai yana hutawa, jikinsa ya warware. Daga nan sai ya sanar da Shehi Abdallah Limamin aljanu cewa shi fa yanzu ya yi harama yana bukatar wucewa, kuma ya gode game da dukkan irin tarba da kyautatawa da aka yi masa. Liman ya yi gayyar dumbin jama‘ar aljanu don yin rakiya ga wannan babban bako nasu. Kwana uku suna tafiya tare da Idrisu, daga nan aka tsaya aka yi addu’o’in dacewa da nasara gare shi sannan suka yi sallama suka juya don komawa gida. Yanzu aikin da ke gabansa shi ne hawa dutsen da ZAMU TASHI aljanu suka rako shi karkashinsa, dutsen da ‘yan’uwansu ke daure a kai, wanda kuma aka ba shi labarin cewa ita ce kadai hanyar bi. KWANA uku, ba dare ba rana, tafiya suke suna hawa kan wannan dutse har suka Kure hawansa. Babu shakka wannan doki Jagora ba irin sauran dawaki ba ne, kuma wannan ya Kara tabbatar da cewa yana tare da wasu martabobi na daban, don kuwa ya yi tafiyar da kakkarfan saurayin aljani zai yi a kwana bakwai cikin kwanaki uku kacal. Tabbas abin a yaba masa ne. A kololuwar saman dutsen nan kuwa sai Idrisu ya ga abin da aka ba shi labari, ga aljanu nan fululu daddaure cikin wata irin muguwar sarka mai hakora wadda ba don aljanu ba ne, to dai ko babbar giwa ce aka yi mata dabaibayi da ita to sai dai wata ba ita ba. Idrisu ya yi matukar tausaya musu irin ganiyar azabar da suke ciki, ga su nan daddaure tamau, ba su samun sararawa, sannan kuma suna cikin irin wannan hali tsawon shekaru masu yawa kamar yadda ya sami labari, kai lallai Sham’una ya isa babban mugu, kuma irin wannan ukuba ba don aljanu suna da tsawon rai ba ai da tuni sun dade da zama ‘yan gida a lahira. Www.bankinhausanovels.com.ng Fushi nan take ya kama Idrisu, ya zare takobinsa, ya dubi wata mahada a jikin wannan Katuwar sarka ya yi mata wata irin sara wadda ta sa ta warwarewa tun daga farkonta har Karshe. Aljanun nan suka kubuta, cike da mamakin irin wannan baiwa ta Idrisu dan Hamidu. Jarumi Idrisu ya ce musu, “Assalamu alaikum. Sannunku da juriya.” Murna ta lulluBbe wadannan aljanu jin tabbacin cewa wannan dan Adam da ya zama sanadiyyar kuButarsu Musulmi ne. Nan da nan suka amsa. Suka ce, “Da a ce dai mu ba Musulmi ba ne, to a irin abin da ka yi mana sai dai kawai mu fadi mu yi maka sujada, don hakan ne nuna makurar godiya, to amma Allah Ya san mun gode, kuma sai dai kawai mu yi maka addu’ar Allah Ya saka maka da alheri.” Idrisu ya amsa cike da farin ciki, “Amin.” Suka tambaye shi, “Kai kuwa a matsayinka na dan Adam, mene ne labarin zuwanka har wannan wuri?” Idrisu ya amsa musu cewa, “Labarina akwai dan tsawo wanda ba zan iya faro muku daga farko ba, sai dai kawai abin sani ta garinku na biyo, kuma na sami labarinku ne a wurin shugabanku; Liman Abdallah.” Dole Idrisu ya ya da zango a saman wannan dutse don wadannan aljanu su samu su dan warware. Www.bankinhausanovels.com.ng cikin wadannan ‘yan kwanaki uku da suka yi suna hutawa ne ya ba su labarin dalilin fitowarsa da kuma inda ya nufa. Idrisu ya tambaye su, “Shin za a iya samun wasu daga cikinku kuwa da za su iya kai ni karkashin teku, inda Sham’una ya tsare Sarki Ifritu?” Ai nan fa wuri ya rude, kowa yana cewa shi ne zai kai shi. Jarumi Idrisu ya ce, “To ku saurara, ina ganin abin da ya fi kamata yanzu shi ne sai a sami manyan jarumanku guda ashirin da biyar kawai, da su za mu yi wannan aiki, saura kuma duk sai a yi harama a lallaba a sauka Kasan dutse don ya fi rashin zafi, a jira mu can, a ci gaba da warwarewa tare da yi mana addu’ar nasara.” A haka shawara ta daidaitu. Sauran jama’ar aljanu suka fara haramar gangarawa, shi kuma Idrisu da wadannan jarumai ashirin da biyar sai suka nufi gabashin dutsen suka fara tafiya, a haka sai da suka kwana takwas kafin su kawo Karshe, a dalilin rashin cikakken kuzarin da ke tattare da aljanun. Idrisu ya leKa ya ga ruwan nan ya tafi, ya kere sasannin samaniya ta kowace fuska. Abin dai gwanin ban al’ajabi. Www.bankinhausanovels.com.ng Aljanun nan suka ce wa Idrisu, “Ya _ kai shugabanmu, a nahiyar nan kaf babu ruwan da ya kai wannan girma da zurfi, babu wanda ya san hakikanin iyakansa sai wanda Ya halitta shi wato Allah. A karkashinsa ne wancan katafaren dutse mai tsananin girma ya ke, wanda Sham‘’‘una ya tsaga tsakaninsa da wani tsafi irin na zamanin farko ya sa shugabanmu a ciki. Ko aljanu sun kai dubu nawa ba za su iya tsaga shi ba.” Da Idrisu ya ji wannan bayani nasu sai ya ce, “In Allah Ya yarda mu ne za mu bude shi.” Jin wannan sai wani masanin ilmin kimiyya daga cikin aljanun ya shiga dudduba saman dutsen da suke har sai da ya dace da wani wuri, ya kuwa je ya kama wurin ya hau shi da latsaww da Karfin tsiya har sai da wani irin abu mai kumfa da launin niwa ya rika fitowa, to wannan abu ne ya tattara ya gaggauraya da hannunsa ya fitar da wasu abubuwa ai sai ga abin ya koma kamar wani mayafi. Da ya kammala sai aljanun suka ce wa jarumi Idrisu ya rufe fuskarsa da kansa da shi. Shi wannan abu amfaninsa shi ne ko kwana nawa zai yi a cikin teku to ba zai rasa iskar shaka ba, ruwa ba zai shiga cikin kunne ko hancinsa ba, kuma tangararan zai riKa ganin komai. Suka ce, “In ka shirya yanzun nan za mu yi Www.bankinhausanovels.com.ng Kundumbala da kai cikin ruwa.” Kafin nan sai da jarumin ya bukaci aljanu biyu su tsaya a waje tare da dokinsa, aka sami wani KakKarfa daga cikinsu ya goya Idrisu a bayansa ya afka cikin tekun nan, sauran ashirin da biyu suna biye. Tun hantsi suke buga nutso, amma ba su isa tsororuwar dutsen ba sai misalin La‘asar sakaliya, sa’ar da suka ci ba Karkashinsa za su tafi ba, don duk saurinsu da sai sun yi kwana biyar ba dare ba rana kafin su kai. Ganin irin wannan dutse ya sa Idrisu Kara ganin girman Ubangiji Mabuwayi Mai halitta tare da aikata yadda Ya so. Idrisu ya yi duba da kyau zuwa ga Kololuwar dutsen sai ko ya ga alamar kamar an taba tsaga shi biyu an mayar an hade. Ya tabbatar cewa lallai abin da suka fito nema ke nan. Ya ce wa aljanun da ke biye da shi su dan ja baya. Shi kuma sai ya janyo mashinsa ya auna mahadar dutsen, sai ga mashin ya Kara tsawo da kauri, abin mamaki da ya tura ya danna kadan sai ga dutsen yana budawa. Sai ya umurci aljanun cewa su matso kusa don tallafar battar Karfen da Sarkinsu ke ciki, su kinkimo ta. Hakan kuwa aka yi. Bayan kamar sa’a bakwai sai ga su a saman ruwa, daga nan sai suka tashi sama kamar tsuntsaye, suka Www.bankinhausanovels.com.ng dire battar a saman dutsen da jarumi Idrisu ya bar dokinsa Jagora da aljanu biyu suna jira. A jikin battar sai suka tarar da kwaduna guda goma sha biyu wadanda Sarki Sham’‘una ya kulle ta da su ya rike makullan a hannunsa. Idrisu ya sa takobinsa ya sassare kwadunan daya bayan daya, sannan ya kama bakin battar ya bude murfin. Budewarsa ke da wuya sai ga wani irin hayaki launi biyu, ja da baki yana fita, ya yi sama can da nisa, har sai da ya kammnala fita gaba daya, daga nan kuma sai ya shiga saukowa Kasa, yana gama sauka sai ya Bace, can sai ga wani irin zabgegen Ifritu, gangarangan da shi cikin siffar aljanu a Kasa. Kai sai ka dauka wani tsauni ne. Yana fitowa sai ya ce, “Alhamdulillahi.” Aljanun nan ashirin da biyar gaba dayansu suka yi masa wata irin gaisuwa wanda sai su suka san abin da take nufi, shi kuma Idrisu sai ya daga masa hannu da nufin gaisuwa. Sarki Ifritu ya tambayi mutanensa abin da ke faruwa har ya sami kubuta, su kuma cikin wani irin harshe nasu suka dan labarta masa labarin jarumi Idrisu. Nan take sai Sarki Ifritu ya yi wata irin girgiza sai ga shi ya koma cikin siffar mutane, babu shakka daga ganin sa da irin kyakkyawan farin gemunsa ka ga alamar aljanin kirki, kuma duk da cewa ya yi sama da Www.bankinhausanovels.com.ng shekara dari biyu a daure amma kuma fuskarsa cike take da annuri. Ya kebe Idrisu suka yi wata irin ‘yar ganawa tare da tambayar sa labarinsa bayan ya yi masa godiya mai dumbin yawa irin yadda har ya yi tunanin taimaka masa haka, shi da jama’arsa. Sarki Ifritu ya ce, “Ya kai Idrisu, yanzu ba zai yiwu ka wuce ba. Komawa za mu yi zuwa garina mu dan huta sannan mu yi shiri mu tunkari azzalumi Sham’una, kuma in Allah Ya so wannan karon sai buzun makiyin Allah.” Da jarumi Idrisu ya ji abin da Sarki Ifritu ya ce sai bai yi musu ba, ya amince a kan su tafi din. Suka kama hanya suka sauka daga kan dutse, haba aljanun da ke jira a karkashin dutse sai murna da shewa ganin cewa Sarkinsu ya sami kubuta. Aka zabi aljanu guda dari suka zabura suka nufi gari don sanar da cewa ga su nan su dubu saba’in da dorin nan har da Sarki duk sun sami kubuta. Lokacin da jarumi Idrisu da Sarki Ifritu da sauran jama’a suka isa kusa da gari sai suka tarar da jama’a babba da yaro, mace da namiji kai har da marasa lafiya duk an fito tarba. Aka dunguma cike da murna ana farin ciki da annashuwa har aka isa cikin gari. “Yan’uwa suka ga ‘yan’uwansu, ‘ya’ya suka sadu da Www.bankinhausanovels.com.ng iyayensu, haka nan mata suka ga mazajensu. In an ce za a misalta irin farin cikin da wadannan aljanu ke ciki, to wanda bai gani ba sai ya nemi karyata mutum kawai a banza. Zangonsu na farko shi ne babban masallacin garin inda aka yi sallolin nafila don godiya ga Ubangiji, sannan Sarki ya wuce fada ya shiga wurin iyalinsa, shi kuma Idrisu da ma ya san masaukinsa. Sai da aka yi mako uku ana zuwa gai da Sarki Ifritu. Bayan an dan shakata, duk daurarrun da aka kwanto har ma da shi kansa Sarki kowa ya mayar da jikinsa ya murmure sai Sarki Ifritu ya sa aka yi yekuwa cewa yana son ganin mayaKansa gaba daya, suka taru a fada yana da jawabi. Aka yi cincirindo, Sarki ya fara jawabi kamar haka, “Ya ku jama’‘ata, kun san cewa mun dade muna shan bakar wahalar azzalumin nan Sarki Sham’‘una, kuma mun dade muna bugawa da shi, har ma wasu lokuta kamar za mu sami alamar nasara a kansa, amma kuma alhamdulillahi, duk abin nan bai taba samun nasarar Karar da mu Karkaf ba, to wannan karon za mu fita, ko a mutu ne gaba daya ko kumaayi rai. Ya ku jama’‘a, wannan shaidanin aljani, wato Sham’una ya cika babban azzalumi. Zaluncin nasa ma har ya wuce kan mu aljanu ya kai kan bil-Adama, Www.bankinhausanovels.com.ng duk ya kame musu ‘ya’ya mata ya kai can bayan duniya ya kulle. Don Allah ina zaluncin da ya fi wannan? Ko kuwa don ya ga ba su da Karfi ne kamar nasa? Ko da yake mu ma aljanun in kun tuna shin wane Sham’una ya Kyale ne? Kuma ina Kara tambayarku, shin wane jinsi ko Kasa ta aljanu ne Sham’una bai yi wa barnaba? To da ma kamar yadda kuka sani mu kadai ne da kuma macizan aljanu muke tsone masa ido, muka zame masa alakakai, su kuma yanzu macizan aljanu ta su ta Kare, Allah Ya kawo halakarsu ta hannun wannan saurayin jarumi, dan Adam, Idrisu dan Hamidu. Wannan babu shakka ya yi musu daidai, don da ma su ma mugayen ne da suka dade suna zaluntar mutane da aljanu.” Sarki Ifritu ya ci gaba da bayani cewa, “In har wani dan Adam daga can cikin duniya zai taso, ya fuskanci tare da shan wahalhalu iri-iri ba don komai ba sai don yakar azzalumin aljani, to mu kuwa me zai hana wannan ya zama Karin Karfafa guiwa a garemu na fuskanta tare da ragargaza wannan azzalumi?” Jama’ar aljanu suka yi wata irin kabbara gaba daya wadda ke nuna sun yi matukar tsuma da jawabin da Sarki ke yi, har ma wasunsu cewa suke, “A fita yanzu kawai.” Www.bankinhausanovels.com.ng Sarki Ifritu ya ce, “Saboda haka ya ku jama’‘ata, daga yau na ba ku wata shida a je a shirya sosai, a sake horo a game da batun dabarun yaki, saboda za mu je mu yi ta ta kare tsakanin mu da Sarki Sham’una. Ko mu, ko shi. Ina kuma fata, kamar yadda muka saba rike sirri da amana, kada wani wanda ba cikinmu ya ke ba ya san cewa na kubuta ni da sauran jama’‘a daga Kangin da Sham’una ya saka mu, don kun san cewa hakan zai iya wargaza mana tsari.” Bayan jawabin Sarki sai kowa ya koma nasa wuri, jarumai suka shiga tayar da Kwanji ana ta motsa jiki da sake sanin dabarun yaki, ko da yake da ma can ba ragwaye ba ne. Sarki Ifritu kuma sai ya shiga tausar Idrisu a kan cewa lallai ya hakura har zuwa watanni shida tukuna ta yadda za a hadu gaba daya a tunkari Sarki Sham’una. Bayan doguwar tattaunawa da kuma girma da Idrisu ya ke gani na Sarki Ifritu dole ya amince cewa zai zauna din, ammaa kan sharadi daya, wato maganar Kara ilmi. Sarki Ifritu ya ce, “Wannan ai mai sauki ne. Ga Limaminmu nan Shehi Abdallah, shahararren malami ne daga masana addinin Islama, saboda haka sai ka ci gaba da daukar karatu kawai. Ni ma da ma Www.bankinhausanovels.com.ng wurinsa nake dauka.” Haka Idrisu ya ci gaba da daukar darasi, kuma lallai ya yi mamakin irin dumbin sani da kuma bayanin da ake ganewa da sauri na wannan Shehi na aljanu. Duk yammaci Idrisu da Sarki Ifritu sukan fita wajen gari don ci gaba da gwajin yaki. In ka gan su suna gwabzawa sai ka rantse da Allah cewa fadan gaske ne. Idrisu ya Karu da wasu dabarun yaki masu yawan gaske musamman a irin karawa ta aljanu daga wurin Sarki Ifritu, shi kuma Sarki Ifritu ya Karu da wasu dabarun masu yawa wadanda a da bai sani ba a wurin jarumi Idrisu dan Hamidu. Bayan sun gama nasu gwajin kuma sukan kewaya filayen da aljanu ke samun horo suna Kara nuna musu wasu dabarun da kuma gyara a wuraren da ke da kuskure. WATANNI shida da aka diba sun cika. Kowa ya shirya, an tanadi duk abin da ake bukata don wannan karawa, jama’‘ar Sarki Ifritu wannan karon gaba daya suka fito, ba a bar kowa ba sai Kananan yara, mata da tsofaffi, aka tunkari babbar daular Jarirul Waki-waki ta Sarki Sham’‘una. ‘Ta waccan hanya da Idrisu ya kubuto da Sarki Ifritu dai suka sake komawa, wato kan dutse, don ita Www.bankinhausanovels.com.ng kadai ce hanyar da za a iya bi in za a shiga yankin Sarki Sham’una. Haka suka yi ta tafiya kwana da kwanaki har suka iso Karshensa. Sarki Itritu ya ba da shawara a kan cewa lallai ya kamata a tsaya a huta kwana biyu tukuna, a shawarta abin yi kafin a ci gaba da tafiya. Babu ko gardama aka yi hakan. Bayan cikar kwanaki biyun sai aka yi addu’o’i masu dumbin yawa don neman dacewa da nasara, kowa ya sake dubawa da tabbatar da ingancin makaminsa. Shi Sarki Ifritu wani irin gwalmi gare shi na wani irin katafaren bakin Karfe, kai da ganin sa ka san daga shi sai aljanin da ya isa don irin girmansa. Shi wannan makami yana da wasu irin kusassari masu tsawo da tsini. Ga dukkan alama kuma Sarki Ifritu ya yarda da gwalmin kuma yana matukar alfahari da shi. Har ma ya ke ba jarumi Idrisu labarin cewa, “Wato Idrisu shi wannan gwalmi nawa da kake gani, gadonsa na yi wurin mahaifina Sarkin aljanu Nagujungu, shi kuma ya gada a wurin nasa mahaifin, wato Sarkin aljanu Wourkilili. Sannan kuma ka san wani abu? Babu mai iya daga shi sai wanda ya gaje shi, wato kakana, mahaifina da kuma ni, kuma mu a wurinmu nauyinsa kamar na kowane makami ne kawai. In Www.bankinhausanovels.com.ng kuwa har ba mu ba, kuma ana son daga shi, to akalla sai an samo Karatan aljanu majiya Karfi guda ashirin sannan za su iya dauka, shi ma cikin tsananin wahalar nauyi.” Idrisu ya ce masa, “Ka ga kuwa in na sa mashina zan iya daga shi.” Jin haka sai Sarki Ifritu ya yi murmushi sannan ya ce masa, “To kai banda abinka Idrisu ai ba a gardama in abin da ake gardama a kansa yana kusa, bismillah, jarraba mu gani.” Idrisu ya ciro mashinsa ya sa a Karkashin wannan gwalmi na Sarki Ifritu, tsakanin wasu kusassari, cak ya daga shi babu ko nishi. Mamaki ya rufe Sarki Ifritu don bai taba zaton yiwuwar haka ba, ya bude baki kawai yana kallo. Daga karshe dai zancen da ya fito bakinsa shi ne, “Babu shakka akwai abin mamaki cikin lamarinka. Ya zama dole a rubuta labarinka ko don nan gaba masu sha’awar labarai su rika karantawa don hira, kuma abin da ya sa na ce don hira shi ne in zamani ya tsawaita wani sai ya yi zaton labarinka almara ce kawai don abubuwan da kake yi mamakinsu ya isa.” Caraf Sarki Ifritu ya kai wa mashin Idrisu cafka don daga shi da kuma jinjinawa ya ji irin nauyinsa, amma ina, sai ya ji kamar ya shafa tsauni don Www.bankinhausanovels.com.ng tsananin nauyi Sarki Ifritu ya ce, “Kai, Idrisu lallai al’amarinka sai dai a bar ka.” Jarumi dan Hamidu ya ce, “Ranka ya dade yanzu ba lokacin a yabe ni ba ne, ka tuna fa cewa muna da babban aikia gabanmu.” Sai Sarki Ifritu ya amsa masa da cewa, “Ai ina ganin kamar duk mun gama nazarin dabarun yaki. Karin bayani kawai shi ne yanzu a Kokarin tafiyar da muke yi zuwa daular Sham’una, za mu tashi sama dukkanmu kamar tsuntsaye. Wannan tafiya ta kai misalin kwanaki arba’in kafin mu shiga cikin Kasar Sarki Sham’una, amma ina fata ka fahimta a nan, da nace maka shiga cikin kasarsa ba wai ina nufin za mu je ainihin garin da ya ke zaune ba ne, a’a, ina nufin za mu tarar da gari na farko ne da ke karkashin mulkinsa, a takaice za mu yaki garuruwa akalla goma sha wani abu kafin mu riske shi. Sai dai kuma babbar matsalar da nake zaton za ta kawo mana cikas in mun isa wurin nasa ita ce wata gunkinsu, wato wata kakar Sham’una din wadda ita ce shugabar tsafinsu. Tsawon shekaru dubbai babu wanda ya taba ko iya yi mata rauni ballantana maganar samun nasaraa kanta da yaki.” Da Idrisu ya ji maganar Sarki Ifritu sai ya ce, “Ya Www.bankinhausanovels.com.ng kai wannan Sarki mai daraja, in dai don wannan tsohuwar mushrika ce, to ka bar ni da ita, ni ne zan kashe Bakayalu in Allah Ya yarda.” Sarki Ifritu jin Idrisu ya ambaci har sunan wadda ya ke nufi ma sai ya dada tsinkewa da lamarinsa. Ya ce, “Ya kai Idrisu, yanzu zan sa aljanu biyar su dauke ka kai da Jagora mu tafi.” Suna wannan magana sai Jagora ya yi wata ‘yar haniniya, ya kwanta a Kasa ya mike Kafafuwa. Idrisu ya fahimci cewa ishara ce wadda ke da dangantaka da ainihin abin da ke faruwa ko kuma maganar da ake yi a lokacin, saboda haka sai ya ce wa Sarki Ifritu, “Ran Sarki ya dade, ni da dokina ba mu bukatar a dauke mu, shi zan hau mu tafi.” Sarki Ifritu ya ce, “Wannan daidai ne.” Nan da nan jarumi Idrisu ya dora wa Jagora sirdi, shi kuma Sarki Ifritu ya umurci jarumansa, su misalin dubu dari biyar a kan cewa kowa ya yi haramar tashi sama. Idrisu da Sarki a gaba, sauran aljanu suna biye, aka tashi sama, Jagora yana taka iska kamar yana taka tsandaurin kasa, har ya fi sauran aljanu sauri, shi kansa Idrisu sai ya fara tunanin shin ko wannan doki nasa dokin aljanu ne? Haka shi ma Sarki Ifritu ya ke tunani. Tafiyar wannan gagarumar runduna ta su Sarkin Www.bankinhausanovels.com.ng aljanu Ifritu da jarumi Idrisu a sararin samaniya, da a ce mutum zai ji rurinsu, to babu shakka zai hakikance cewa duniya ce za ta tashi. Wannan runduna ba ta bata wani lokaci ko kuma wani hutawa ba saukarsu gari na farko sai suka yi fata-fata da shi. A irin wannan karon ma ko damuwa da kama aljanu ba su yi ba, kisa kawai suka yi ta aiwatarwa, kuma ba su kyale duk wani kakkarfan aljani ba. “Yan kadan da suka tsira suka ruga zuwa gari na biyu suka sanar da su irin bala’in da ke tafe. Aljanun gari na biyu suka shirya cikin gaggawa suka fito don tunkarar abokan gaba. Kwana biyu kawai ana gwabzawa aka ragargaji wannan gari, masu tserewa suka tsere. Abin da kawai wannan runduna ta Idrisu da Sarki Ifritu ba sa tabawa shi ne basa kashe Kananan yara da tsofaffin aljanu, wato sabanin Sarki Sham’una wanda in yana yakar wata kasa, shi har jarirai ya ke halakawa. Kai kafin dai wasu kwanaki an lankwame garuruwan Sarki Sham’una har guda tara, wanda hakan ya sa babu makawa Sarki Sham’una ya sami labari, don a Ka’ida, masu kwatankwacin mukamin hakimai da dagatan da Sham’una ya nada don jagoranci a wadannan garuruwa dole ne sai sun yi HMMM ASHA RUWA A KOMA AIKI LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 22 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Tafiyar wannan gagarumar runduna ta su Sarkin Www.bankinhausanovels.com.ng aljanu Ifritu da jarumi Idrisu a sararin samaniya, da a ce mutum zai ji rurinsu, to babu shakka zai hakikance cewa duniya ce za ta tashi. Wannan runduna ba ta bata wani lokaci ko kuma wani hutawa ba saukarsu gari na farko sai suka yi fata-fata da shi. A irin wannan karon ma ko damuwa da kama aljanu ba su yi ba, kisa kawai suka yi ta aiwatarwa, kuma ba su kyale duk wani kakkarfan aljani ba. “Yan kadan da suka tsira suka ruga zuwa gari na biyu suka sanar da su irin bala’in da ke tafe. Aljanun gari na biyu suka shirya cikin gaggawa suka fito don tunkarar abokan gaba. Kwana biyu kawai ana gwabzawa aka ragargaji wannan gari, masu tserewa suka tsere. Abin da kawai wannan runduna ta Idrisu da Sarki Ifritu ba sa tabawa shi ne basa kashe Kananan yara da tsofaffin aljanu, wato sabanin Sarki Sham’una wanda in yana yakar wata kasa, shi har jarirai ya ke halakawa. Kai kafin dai wasu kwanaki an lankwame garuruwan Sarki Sham’una har guda tara, wanda hakan ya sa babu makawa Sarki Sham’una ya sami labari, don a Ka’ida, masu kwatankwacin mukamin hakimai da dagatan da Sham’una ya nada don jagoranci a wadannan garuruwa dole ne sai sun yi ZAMU TASHI iyaka iyawarsu wurin murkushe kowane irin yaki da ya tunkaro su kafin har labari ya kai zuwa wurin Sarki, in kuwa ba haka ba, to su sun san sauran. Shi yasa ma har abin ya kai haka kafin ya sani. Kuma ma a tarihi ai baa taba taka irin wannan mataki ba sai yanzu. Mamaki ya rufe Sarkin aljanu Sham’una jin cewa wai an nufo shi da yaki har gida, kuma ma wai maganar da ake yi har an lashe birni na tara, alhali shi yana birni na goma sha biyu ne shi da kakarsa Bakayalu. Sham’una ya yi tunani da kyau cewa, to ai duk cikin aljanun da ke raye babu wanda zai taba yin irin wannan mafarkin ma sai dai Sarki Ifritu, shi kuma ai yana can sarkafe a inda babu mahalukin da zai iya ceto shi. YANZU kam Sham’una ya hakikance cewa Sarki Ifritu ne tare da wani jarumi dan Adam suka kawo masa yaki. Wannan labari ya yi tsananin bakanta masa rai, hankalinsa ya tashi, ta yadda aljanin da ya kawo labarin ma bai tsira ba, don kuwa an yi rashin sa‘a, irin dundun da Sham’una ya dunkula hannu ya yi masa a baya shi ne sanadiyyar rugurgujewar bayan aljanin, bai dade ba ya mutu. Sarki Sham’una ya shiga tunanin yadda aka yi har Sarki Ifritu ya sami kubuta, da kuma yadda aka yi har mutum dan Adam ya iso nan da ransa. Lallai babban al’amari na tunkaro shi Ya sa aka tsaurara matakan tsaro a birni na goma, aka kai gudummawar jarumai da dakarun aljanu don kara karfafa tsaro da shirin tunkarar yakin da za a yi gobe, Ya ba da.umurnin cewa a kashe duk abokan hamayya, ba ya ma bukatar ganin su. Washegari, wato ranar da za a gwabza da aljanun birni na goma sai wani babban abin Bacin rai ya faru ga Idrisu, wato tun da safe sai ya, lura cewa dokinsa Jagora na fama da matsanancin. rashin lafiya, saboda hhaka sai ya ja shi zuwa KarKashin wata yar inuwa ya sa shi ciki yana mai rarrashin sa cewa, Jagora ka yi hakuri, kuma Allah. Ya ba ka lafiya, in Allah ‘Ya so munkusahutawa.” sa – Idrisu ya koma gefe ya yi zugum yana tunanin . yadda zai bullo wa lamarin wannan yaki, kwatsam sai ya tuna.dardumar tashinsa, sai ya yi sauri ya kwanto ta, sannan ya kwance wa Jagora sirdi ya ce,,,”Jagora kanta huta.” Ya kama shi ya kwantar da shi kamar zaiyikuka saboda.irin tausayin halin da ya ganshi aciki. Ya sake shafa kan ;~gora yana mai cewa, “Allah Ya ba ka lafiya, ka ji?” Www.bankinhausanovels.com.ng Daga jin irin rugugin da ke tashi daga nesa Idrisu ya hakikance cewa yanzun nan za a fara karawa. Ya warware darduma, ya dora sirdin dokinsa a kai sannan ya rike mashinsa ya rataya takobi ya ce, “Sama da ikon Allah.” Darduma ta tashi da shi kamar tsuntsu, ya nufi fagen fama. Sarki Ifritu ya yi matukar mamakin ganin jarumi Idrisu a cikin wannan yanayi. Suka raba runduna biyu, kowanne ya ja nasa gefe. Bakaken aljanu suka yiwo musu dauki, nan take yaki ya kaure, sai wuta kawai kake gani tana tashi, ba ka jin komai sai hargowar jarumai. Irin kisan da Idrisu ya yi wa wadannan bakaken aljanu a ranar abin sai wanda ya gani, duk inda ya juya sai dai kawai a dare. Kai ya zubar da kawuna baa san iyaka ba. A daya gefen kuma Sarki Ifritu ne ya ke tasa budawar, da ya buga kokarar nan tasa, bugawa daya sai ya zubar da aljanu sama da goma nan take su mutu, wani lokaci ma saboda kosawa hannu ya kan sa don cafko bakin aljani ya karairaya shi ya watsar, su kuma jama’a mayakan Sarki Ifritu kamar wadanda hankalinsu ya rabu da su saboda irin yadda suka sami gangara suna ta wulakanta jama’ar Sarkin aljanu Sham’una. Wani abu wanda ya ba jarumi Idrisu da Sarki Ifritu Www.bankinhausanovels.com.ng da jama’arsu mamaki shi ne irin yadda a can gefe wani kyakkyawan saurayin aljani ya ke ta nuna irin tasa bajinta da jaruntar wurin yakar jama’ar Sarki Sham’una. Shi wancan saurayi duk wurin babu mai irin kyansa, fuskarsa sai wani irin kyalli take yi, sannan kuma ga shi da wani irin gashi mai kyau layalaya a kansa, ga shi kakkarfa, ya yi shigar kayan yaki irin nasu na jaruman aljanu, ba ya komai sai kisa, duk inda ya waiga sai fili, babu shakka bakaken aljanu sun yi matukar firgita da shi. Ba a kuma san kowane ne shi ba. In ya yiwo kora, sai Idrisu ya taro, shi kuma Sarki Ifritu ya tarba. A wurin yakin aljanu babu maganar dare ko rana, duk daya ne, kuma babu maganar hutawa. A haka sai da aka kwana uku ana hudu kafin a sami nasara a kan jama’ar wannan birni na goma na Sarki Sham’una. Aka kacaccala su aka karkashe, wadanda suka gudu cikin gari aka bi su aka kakkama aka zuba cikin ankwa. Aka shiga cikin gari, aka gabatar da abin da baa taba yi ba; Sallah, har ma da dubban aljanu bisa dubbai cikin jam’i! Bayan hankali ya dawo jiki duk sai aka koma ana ta yi wa juna barka da arziki. Aka duba ko ina don ganin jarumin saurayin aljanin nan mai tsananin yaki Www.bankinhausanovels.com.ng amma babu ko alamarsa. Mamaki ya kama jarumi Idrisu har ya tambayi Sarki Ifritu cewa, “Shi kuwa wannan wane irin jarumi ne? Ana son a san ko shi wane ne amma yayi tafiyarsa?” “Af, don wannan? Ai ko kadan kada ka damu kanka, mu aljanu haka muke, yana taimakonmu ne saboda wani dalili, ko dai shi Musulmi ne, ko kuma Sham’una ya taba zaluntarsa ko wani nasa, ka san mu aljanu sai mu yi hamayya tun ta kakanni.” Suna gama tattaunawa sai jarumi Idrisu ya mike ya nufi bayan gari, wurin dokinsa Jagora, ya tarar dai har yanzu babu wani alamar karsashi a tattare da shi, ya shafa jikinsa yana mai yi masa addu’o’in samun lafiya. Ya dai san wannan yaki dai da wahala a yi shi da Jagora, aKalla dai a bar shi na wasu ‘yan kwanaki ya sami sauki. Ya janyo shi zuwa cikin gari don’ samar masa da inda ya dace da doki mai daraja irinsa, tun da dai yanzu gari ya Zama nasu. Tun a hanya ya tattaro masa game-gamen sauyoyi da sassaken itatuwa wadanda zai jika masa a cikin ruwan shansa. A daidai lokacin shigowarsu gari sai ya tarar da Sarki Ifritu yana ta koKarin shirya dakaru kamar dai yadda suka shirya da jarumi Idrisu din. TSOHUWAR aljana Bakayalu! Gara a ji labarinki da a gan ki! In dai ba wata irin kariya daga Ubangiji Allah ba, to ko a mafarki ta ziyarci aljani ko mutum da mugun nufi babu ko shakka ba zai kwana da rai ba, saboda irin mugun alkaba’inta. ‘Tsohuwa ce wadda babu mahaluKkin da zai ce maka ga ainihin shekarunta, sai dai a lalace ta bai wa shekara dubu hudu baya. Gata ta tamuke, ta yankwane, ga wani irin farfarin gashi a duk jikinta. Tana da miyagun jajayen idanu da wasu irin hakora zako-zako, sannan kuma gashin girarta a tsaitsaye suke. Tana da tsananin tsawo sannan kuma ga Kusumbia baya da keyarta. Wani abin mamaki kuma ma shine _ irin yadda silin gashin kanta kowanne ke da wasu irin hakora-hakora a jikinsa. Kai duk wanda zai ba da labarinta sai dai ya takaita kawai saboda ba a taba iya KARE mata kallo. A matsayinta na shugabar tsafin aljanu gaba daya, sai ta zamanto wani gunki da ake bauta wa. Kai, da Bakayalu da sharri duk ma’anarsu daya! Kisa ba wani abu ba ne a wurinta, musamman ga duk wanda ya nuna jayayya ko kuma rashin biyayya ga sabon matsayin allantaka da ta daukar wa kanta, to tabbas kuwa za ta halaka shi, ko wane ne. Misali shi ne irin yadda ta kashe danta na cikinta, wato Kailanu, mahaifin aljana Dailanu Kawar su yarinya Nur. Dalilin kisansa a wancan lokaci shi ne rashin biyayyar da aljana Bakayalu ke ganin cewa yana nuna mata a duk lokacin da ta ba da umurnin kashe aljanu, shi kuma sai ya rika nuna mata cewa hakan bai dace ba. A irin haka wata rana ta sa shi yin azaba tare da kashe wasu aljanu da ba su yi mata sujuda ba a lokacin da ta zo wucewa, ko da yake sun yi rantsuwa da wuta da rana cewa ba su gan ta ba ne, amma duk da haka ta ce a kashe su don zama darasi ga sauran aljanun Kasar, cewa a duk inda aljani ya ke ya rika zama cikin taka-tsantsan don tana iya wucewa ko yaushe ta ga dama. Aljani Kailanu da aka sa yin wancan kisa sai ya nuna wa Bakayalu cewa hakan bai dace ba tun da dai WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG sun ce ba su gan ta ba, to sai aka yi rashin sa’a tana cikin tsananin fushi a lokacin da ya riske ta da maganar, ai nan take ta aikata wani tsafi irin na ajin farko, Kailanu danta da aljanun da aka sa ya halaka din suka kone Kurmus, tokarsu ma tashi sama ta yi. Watakila irin abin nan da akan ce, ‘A tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro.’ Daga cikin aljanun da suka fi KoKari wurin bauta mata akwai wani na hannun damanta mai suna Zirimuzi wanda wata rana ya amshi addinin Islama, kuma a dalilin sanin halinta sai ya yi gudun hijira don tsira da ransa da addininsa kamar yadda wasu suka taba yi. duk wannan ba shi ne ya fi tayarwa Bakayalu hankali game da shi ba sai lokacin da tsafinta ya nuna mata cewa a dalilin yarda da shidata yi har awancan lokacin yake da damar shiga har cikin dakin bautar da sauran aljanu ba su da ikon shiga, ya taba ganin littafin nan wanda asirin ransu ke ciki ita da jikanta Sham’‘una, kuma har ya taba littafin da hannunsa, sannan kuma ga shi yanzu ya gudu, yana kuma tare da abokan gaba! Saboda haka sai ta sa Sham‘una ya bi shi har Kasar da ya Musulunta din ya kashe shi har da Sarkin garin da sauran jama’‘a masu dumbin yawa, ba don komai ba sai don kawai Bakayalu tana kyautata zaton Zirimuzi ya taba bude Www.bankinhausanovels.com.ng littafin, to a wurinta ko ma dai bai bude baa kashe shi kawai tunda dai hannunsa ya taba tabawa, kuma tun daga wancan lokaci ta sake wa littafin ma’ajiyar da in banda Dailanu babu mai shiga, kuma ta san ita Dailanu ba ta damu da komai ba sai harkar gabanta kawai. ‘Tabbas irin wadannan kashe-kashe da azabtarwa da Bakayalu kan yi har ga wadanda suka fi kusanci da ita kuma ba tare da bayyana wa jama’a wani dalili ba ya sa aljanu suka kara shiga taitayinsu a game da lamarinta. Saboda tsananin sharrin wannan ‘ aljana, musamman a wancan lokaci da take ganiyar abin, babban danta ma fa ita ta halaka shi, duk da cewa shi kadai ya rage mata, wato Sarkin aljanu Damsalu, mahaifin shi kansa Sarkin aljanu‘ Sham’‘una, a lokacin Sham’unan yana Karami ita*kuma Dailanu tana ciki ba a haife ta ba. Shi kuma dalilin halakarsa shi ne wata rana ya sami aljana Bakayalu tana cikin tukukin bakin cikinta ya ce shi yana sha’awar irin halin da Musulmin aljanu ke ciki da irin dabi’unsu da sauransu. Aiba ta san lokacin data sa Kafarta ta haure shi ba, kuma a Ka’ida duk abu mai rai da tsohuwar aljanar nan ta haure da Kafarta, to kuwa nan take zai halaka, kai ko babban dutse ne, to zai fashe. Nan dai Www.bankinhausanovels.com.ng Sarkin aljanu Damsalu ya bakunci lahira. Ko da yake ba ta taba da-na-sani baa rayuwarta sai wannan. WataKila shi ya sa duk soyayyarta ta koma kan Sarki Sham’‘una, musamman kasancewar ko kadan bai bar mugun halinta ba, kuma take matukar takatsantsan ba ta yin fushi da shi, ko me ya aikata kuwa. “Tana da wani daki na tsafi wanda takan shiga ta sake girka kanta a cikin duk shekara dari, kuma in ta shiga takan dauki tsawon kwanakin shekara ne cur _kafin ta fito, babu abin da ya isa ya kusanci dakin _tsafin matukar ta shiga cikin sa, ana ma zaton in ta shige cikin wannan daki wata duniyar can take Bulla don aiwatar da girkar. Duk lokacin da ta fito daga irin wannan tsafi, to takan fito da wata sabuwar mugunta mai tsananin gaske, shi ya sa a duk lokacin _da aka ji labarin fitowarta kowane aljani kan shiga taitayinsa don kada fushinta ya rutsa da shi. Ga shi. kuma yanzu an cinye birni na goma, _tsohuwa Bakayalu tana can wurin girka. Hankalin Sarki Sham!‘una ya yi matukar tashi don shi ma duk da kasancewarsa jikanta ba zai iya kusantar dakin ba ko da kuwa wani irin bala’i ne ke faruwa da shi, , ballantana har ya sami damar da zai kai mata kukansa. – Ana cikin haka sai Sarki Sham’una ya rika jin Www.bankinhausanovels.com.ng Karkashin fadarsa na wani irin girgiza. Ai sai ya mike cike da farin ciki da murna don kuwa hakan alama ce da ke nuna cewa nan da wasu ‘yan sa’o’i kadan kakarsa Bakayalu za ta bayyana ta cikin dakin da takan shiga. Haka ko aka yi. Sham’una ya zube a gabanta yana yi mata wani irin kirari, nasu na manyan bakaken aljanu. Aljana Bakayalu ta yi kekkewa sannan ta Kyakyace da dariya. Ta ce, “T’safi da wuta da rana su kare ka ya kai jikana dan dana Damsalu. Yaya na gan ka a haka? Wani ya saba maka ne? Wa kake so a toya shi da ransa ya kai abin da na fiso a rayuwata?” Sham’una ya mike sannan ya sake rusunawa, ya ce mata, “Ya ke kakata wadda babu irinta a ciki da wajen duniya, ina son in sanar miki ne cewa lamari mai Karfi ya tunkaro mu, maganar da ake ciki yanzu biranena guda goma suna hannun abokan gaba, yanzu sun tunkaro birni na sha daya. Yanzu na zo neman yardarki ne in je in tarbe su a can in karairaya su gaba daya.” Bakayalu ta ce, “Ya kai jikana, tun da ake babu wanda ya taba cin wannan Kasa da yaki, saboda haka duk wasan Kananan yara suke yi. Wane aljani wane mutum? Irin wannan rashin kunya ai kananan aljanu Www.bankinhausanovels.com.ng ake yi wa a kwana lafiya. Mu da ke neman tashin hankali da fitina da bala‘i ruwa a jallo balle kuma sun biyo mu har gida. Kai Sham’‘una, shin ba ka san cewa kai ke da nasara a kan duk abin da ka tunkara ba? Nice nan fa na raine ka da kaina, kuma ina jin dadi cewa irin bakar muguntata da mugun nufina da rashin tausayi da kuma sharrina duk ka koye su ka iya. Babu shakka ka yi nisa a fagen sharri, shi ya sa ma ka ga ban cika shiri da ‘yar’uwarka Dailanu ba, don ita ina ganin alamun tausayi tattare da ita, kuma shi ya sa kakan ji ina gwaba tare da goranta mata cewa ta musulunta mana kowa ya huta don na ga kamar tana da wasu halaye irin na Musulmin aljanu.” Bakayalu tana da wani irin madubin tsafi na Karau, duk abin da ke wakana in tana buKatar ganin sa sai dai kawai ta duba madubin. In ma ta ga dama ta cikin madubin kawai sai ta halaka abin. Ta ce, “Bari in ga su wane ne suka kawo kansu ga halaka.” A wannan karon abin ya yi matukar ba ta mamaki, don tana dubawa sai dai ta rika ganin wani irin haske yana walkawa kawai, amma bata ganin kowa. Hakan ya faru ne a dalilin mashin da jarumi Idrisu ke dauke da shi, shi ne ke dasashe madubin nata ba taiya ganin su. Asalin burin aljana Bakayalu a lokacin shi ne a Www.bankinhausanovels.com.ng gaban Sham’una ‘ta halaka shugabannin yakin ta ‘cikin madubi don shi maya koyi yadda ake yi. Ta yi iyaka iyawarta amma ina. Tun lokacin da aka samar da wannan madubi’ ta hariyar wani irin gagarumin gamayyar tsafi na taron matsafa, shekaru dubu biyu da dari biyu da ashirin da biyu ke nan, bai taba kasawa irin na yau ba! Ta ce, “Tashi ka tafi’na amince maka! Je ka tunkare ka cinye-makiya danyayyu da ransu! Kada ‘ka’ kuskura ka bar ko “kwaro!” F Sham‘una ya duka ya yi’ban-kwana: Ya debi ~ zaratan jarumai dubu talatin ya nufi birni na goma ‘ sha daya. Isar sa fagen fama ke da wuya sdi ya tarar ashe tuni -abokan gaba sun dade da tayar da hankalin bakaken aljanunsa na birnin. Jarumi Idrisu dan Hamidu ya takura gefen Yamma, Sarki ifritu ya kange Bangaren Gabas, shi kuma daya saurayin jarumin nan da ba a san shi ba ya toshe sashen Arewa; kakkaba: kawai sukeyi,° Ta fuskar Kudu ne Sham‘una ya shigo. Jama’arsa na ganin sa sai suka ga ai shi ke nan yaki ya kare, an ” cinye abokan gaba an gama, don ga uban gayya nan da kan sa ba sako ba. Suka labarta masa cewa tun da suke yaki ba su taba ganin yaki mai wahala da ake Www.bankinhausanovels.com.ng samun galaba a kansu irin wannan ba. Sham’‘una ya tambaya, “Su wane ne shugabannin yakin.” Wani aljani da sarautarsa ke matsayin Magayakin birni na sha dayan ne ya amsa masa cewa, “Wuta da rana su kare ka, wani jarumi ne dan Adam ke shugabantarsu, yana kuma yi mana muguwar Barna, ya kashe:-mana dakaru da jarumai babu iyaka, yana kakkarya wuyaye kamar da sihiri, wannan babu shakka karawa da shi sai kai. Kuma ran sarkin aljanu ya dade, a can gefen Gabas Sarki Ifritu ne rike da wani gwalmi, duk bugawa daya , aljanu kusan ashirin ke zubewa. Daga gefen Arewa akwai wani jarumi da suka zo da shi wanda babu ko alamar cewa ya yi niyyar barinmu da rai, don kuwa yanka ya ke yi kamar yana wasa.” Zuciyar Sarki Sham’‘una ta yi kunci, fuskarsa ta sauya, gashin girarsa ya mike tsaitsaye, idanunsa suka yi jawur kamar garwashin wuta, bakinsa kuma sai wani irin tururi ke ta fita don tsananin fushi. – Sharri da’ sake-sake suka cika zuciyarsa don tunanin irin kisan da.zai yi wa wadannan abokan gaba nasa. Sham’‘una ya ce, “Da mutumin zan fara, in cinye shi danye da ransa.” Ya debi aljanu dubu goma daga cikin dubu talatin HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 23 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Sham’‘una ya tambaya, “Su wane ne shugabannin yakin.” Wani aljani da sarautarsa ke matsayin Magayakin birni na sha dayan ne ya amsa masa cewa, “Wuta da rana su kare ka, wani jarumi ne dan Adam ke shugabantarsu, yana kuma yi mana muguwar Barna, ya kashe:-mana dakaru da jarumai babu iyaka, yana kakkarya wuyaye kamar da sihiri, wannan babu shakka karawa da shi sai kai. Kuma ran sarkin aljanu ya dade, a can gefen Gabas Sarki Ifritu ne rike da wani gwalmi, duk bugawa daya , aljanu kusan ashirin ke zubewa. Daga gefen Arewa akwai wani jarumi da suka zo da shi wanda babu ko alamar cewa ya yi niyyar barinmu da rai, don kuwa yanka ya ke yi kamar yana wasa.” Zuciyar Sarki Sham’‘una ta yi kunci, fuskarsa ta sauya, gashin girarsa ya mike tsaitsaye, idanunsa suka yi jawur kamar garwashin wuta, bakinsa kuma sai wani irin tururi ke ta fita don tsananin fushi. – Sharri da’ sake-sake suka cika zuciyarsa don tunanin irin kisan da.zai yi wa wadannan abokan gaba nasa. Sham’‘una ya ce, “Da mutumin zan fara, in cinye shi danye da ransa.” Ya debi aljanu dubu goma daga cikin dubu talatin ZAMU TASHI din da ya zo da su, sauran dubu ashirin din ya ce su auka fagen fama su kai dauki. Ya tarar da mazaje suna ta karen-batta da jarumi Idrisu, shi kuma ga mutumin naka nan a kan dardumarsa, ya kai gwauro ya kai mari yana ta tsinke wa aljanu kawuna. Shi kansa Sarki Sham’una ya yi mamaki. Sham’una ya daka wa wadanda ke karawa da Idrisu tsawa a kan cewa su janye, ai suna lura cewa shi ne sai murna ta lullube su don sun tabbatar cewa yanzu salon yaki zai sauya, yanzu za a yi ta ta Kare. Ya ba da umurni ga dubu goman da ke tare da shi a kan cewa su kamo masa Idrisu, amma fa kada su kuskura su kashe shi, don yana buKatar cinye shi danyensa ne da ransa, yana ji yana gani. Nan take askarawan aljanu suka yi wa Idrisu dauki, kamar za su yaki jama’a dubu dari. Da suka kusa sai suka dauki wata dabara irin ta yaki, suka fara yin wani irin jerin gwano suna zagaye shi a hankali, shi kuwa da ya farga sai ya girgiza takobinsa, sai ga takobin ya kara tsawo. Askarawan nan ko suka rufar masa, sai dai kuma ba don su jarumi Idrisu ya fito ba. Trin jerin da suka yi a kan kuskure sai ya bai wa jarumin wata irin dama a kansu, musamman a farkofarkon karawar, don kuwa duk lokacin da ya sara ya tafi da kaifin takobin nasa a shimfide sai kawai ka ga Www.bankinhausanovels.com.ng akalla kawunan aljanu dari a Kasa, kai a taKaice dai kafin ka gama tunani da ta’ajjubin yadda wannan lamari ke faruwa tuni cikin jama’‘ar nan ta Sarki Sham’‘una su dubu goma da ya zo da su saura ba su wuce dari shida ba wadanda suka rika ja da baya har suka koma wurin Sarkinsu. Sarki Sham’‘una ya mari fuskarsa, ya yi wuf ya bangaje wasu daga cikin wadanda ke KoKarin rugawa din ya kutsa ta tsakanin su a fusace ya nufi wurin jarumi Idrisu, yana zuwa sai ya tsaya cak, ya ce, “Kai mutum! Daga ina? Mene ne labarinka? Kuma ma me ya sa kake yakar mu kake ta kashe mana jarumai tun _ daga birni na farko har zuwa nan na sha daya? Me kake so, dukiya ko me?” Sai Idrisu ya ce masa, “Ai sai na san ko kai wane ne kafin in mayar maka da amsoshin tambayoyinka.” Sham’una ya ce, “Ai ba sai an gaya maka ba, da ganin Sarkin aljanu yaro ba sai an nuna maka ba.” Sai jarumi Idrisu. dan Hamidu ya ce, “Alhamdulillahi! Yau mun gamu ke nan. dan nema! Kai ake cewa Sham’‘una ko? Mugu jinin muguwa. Da ma musamman don kai na zo, kai da muguwar kakarka Bakayalu. Kuma ina tafe muku da albishir ne cewa ni ne nan zan salwantar da ku!” Nan take mamaki da bakin ciki a lokaci daya suka Www.bankinhausanovels.com.ng lullube Sarkin aljanu Sham’una. Dalilin mamakin shi ne irin yadda tun farko wannan dan Adam din ya san sunansa, har ma da na kakarsa, lallai babu shakka wannan saurayi yana tattare da labarai. Sai Sham’una ya yi tunanin cewa, “Bari sai ya zo hannu tukuna, in yi masa tambaya kafin in halaka shi.” Dalilin bakin cikin Sarki Sham’una kuma shi ne tun da aka haife shi ba a taba zagin sa a gabansa ba, sai ga shi yau wani saurayi, dan Adam ma, yana surfa masa, ba kunya ba tsoro. Ya tuna irin ikonsa da jaruntarsa da irin yadda dukkan aljanu ke tsoro har wasunsu ke bauta masa, sai ga shi yau mutum ne har babban birninsa da yaki, har ma da zagin sa shi da uwar matsafa Bakayalu. A fusace Sarkin aljanu ya daga hannayensa sama kamar zai karbi wani abu, kawai sai ga wani irin takobi ma‘abocin tsawo, girma da fadi a hannunsa, wanda za a iya siffantawa da gaya-wa-jini-na-wuce, amma irin nasu na aljanu, a daya hannun kumasai ga wata irin garkuwa wanda akalla sai an sami Karfafan aljanu guda dari za su iya daga ta, ya nufi Idrisu yana tafiya yana wani irin Karaji mai ban tsoro, yana ihu da hargowa irin na jarumin da ke ji da kansa. Jama’ar Sham’una da suka ga haka sai suka sakankance cewa yanzu kam yaki ya Kare don ko zai kamo Idrisu ne Www.bankinhausanovels.com.ng kamar agwagwa. Ganin Sarki Sham’‘una ya tunkaro shi sai ya zama jirace da shi. Ya girgiza takobinsa a daidai lokacin da shi kansa ya yi wata irin budawa, shi kansa a lokacin sai da ya ji takobinsa ya dan Kara nauyi, wanda hakan ya sake tabbatar masa cewa lallai wannan karo na musamman ne. ° In dai ba a manta ba, daga cikin horon da jarumi Idrisu ya samu a wurin Shaihi Ibrahim a zaman da suka yi akwai yin’yaki ba-tare da garkuwa ba, wato wata baiwa:wadda Shaihin ne: kawai ya fi kowa dacewa da ita a ciki da wajen duniya, sai kuma yanzu shi Idrisu Karar haduwar takubban Sarkin aljanu Sham’una da jarumi Idrisu ta sanya duk wanda ke fagen sai da hankalinsa’ ya -dawo wurin’ kafin a ci gaba da gwabzawa. A dalilin haduwar takubban ne fa sai da wata irin wuta ta yi tartsatsi ta tashi sama ta yadda su ma kansu jaruman wato Idrisu da Sham’una sai da suka yi baya kafin kowannensu ya sake gyarawa don sake bugawa. Www.bankinhausanovels.com.ng Baudiya da kariya wasu abubuwa ne da saurinsu ya kama hanyar na walkiya a-wurin mai kallon wannan karawa ta Sarki Sham’‘una da jarumi Idrisu; don irin tsananin kwarewar jaruman. Kai abin.dai kamar’a Www.bankinhausanovels.com.ng labari. Yawan bugawar da ake yi ta sa har takobin da ke hannun Sarki Sham’una ya fara lauyewa. Hakan ya yi matukar ba shi mamaki, da tafiya ta yi tafiya sai ya tabbatar wa kansa cewa yanzu takobin ba shi da sauran Karfin da za a ci gaba da gwabzawa da shi, saboda haka sai ya wurgar da shi, ya daga hannu sai ga wani mulmulallen bakin Karfe mai wasu irin hakora, ya riKa kai wa Idrisu bugu da shi jarumin yana gocewa, can da Idrisu ya sami sa’a sai kawai ya sa kaifin takobinsa ya sare tsakiyar mulmulallen Karfen, ai nan take ya watse. A irin haka Sarki Sham’una yana kawo miyagun makamai Idrisu yana lalatawa har sai da ya kawo guda tamanin. Abin da kawai bai lalace a hannun Sham’una ba tun fara gwabzawarsu da jarumi Idrisu ita ce garkuwa. Akwai wata babbar bishiya a kusa da inda gumurzun nasu ya kai su, kuma a takaicen takaitawa itaciyar ta kai shekara dari biyar a wurin, ai kawai sai Sarkin aljanu ya sa hannu ya fisgo ta don yin bulala da ita, a daidai lokacin da jarumi Idrisu ya bi shi ya daga takobi ya kai masa sara, babu shakka Sham’una ya isa jarumi, don irin gocewar da ya yi akwai matukar mamaki, sai kawai ya kare saran da wannan Www.bankinhausanovels.com.ng itaciya da kuma garkuwarsa. Irin dirar mikiyar da jarumi Idrisu ya yi masa da sara shi ne karshen labarin wannan itaciya da kuma garkuwa ta Sarki Sham’una, don ita wannan shahararriyar garkuwa rabewa biyu ta yi. Jikin Sarki Sham’una ya yi matukar sanyi, kuma wannan abin mamaki ya sa ya mike ya dafe keya a guje. Jama’arsa da ke gefe suna kallon yadda fafatawar ke kasancewa ba su bari ya Karaso inda suke ba, su ma sai suka juya a guje, suka fuskanci babban birninsu na goma sha biyu. Sauran aljanun da ke cikin fagen fama kuwa da ma azabar Sarki Ifritu da na wancan matashin jarumi ta gallabe su, saboda haka ganin shi kansa uban tafiyar ya ranta a na kare sai su ma suka ce Kafa me na ci ban ba ki ba, suka juya karce suka rufawa jagoransu baya. Wato dai suka bar fagen faman da kuma birninsu na sha daya a hannun abokan gaba. Suka shige birninsu na goma sha biyu suka rufe shi bam yadda ko allura ba za ta iya shiga ba. Ko bin sawunsu ba a yi ba, an ci wannan birni ke nan, ya shiga hannu. Aka yanke shawarar kada a tsaya wani Bata lokaci kawai, a nufi birni na sha biyu cikin natsuwa ana tafiya ana sake kintsawa da hutawa, wato birnin Sham’una shi da kakarsa Bakayalu, birni Www.bankinhausanovels.com.ng na Karshe, don ayi ta ta kare. SARKIN aljanu Sham’una dan Damsalu ya isa wurin kakarsa Bakayalu cikin wani irin tashin hankali da bai taba mafarkin tsintar kansa a ciki ba. Ya fadi a gabanta ya yi mata sujuda. Duba daya kawai ta yi masa ta fahimcei irin halin da ya ke ciki.. Ya ce, “Ya ke kakata ke ce kika raine ni, kika koya mini tsafi da muguntar da nake cikin sa, hasali ma ke ce kika kai hi ga wannan daukaka ta sarautar aljanu da duk duniya da wajenta kowa ke shakka ta, to yau tabbas ga abin da ke neman fin Karfina, dole in ba ki sa hannu ba, to za mu tozarta.”. -‘ Ya kara da ce mata, “Makiya suna nan kan hanyarsu ta zuwa babban birninmu. Mun buga ni da wancan jarumi dan Adam din kuma ba yadda ban bullo masa ba amma abin ya gagara. Duk tsawon lokacin da muka dauka muna gumurzu da shi babu wani labari, sai shi ne ma ke neman kunyata ni, ko kuma ma in-ce ya kunyata ni din, don ban taba juyawa a fagen fama ba sai wannan karon! Wani irin takobi ya ke da shi mai tsananin ban mamaki. A gaskiya na hadu da jarumai ban san iyaka ba wadanda na karairaya tare da turmusa hancinsu, Www.bankinhausanovels.com.ng na shayar da su dacin mutuwa, amma ban taba haduwa da jarumin da na ji cewa wai ina fada ne ba, jin banda Sarki Ifritu wanda muka taba daukar lokacin da gaba daya bai wuce sa‘o’i uku da rabi muna karawa kafin akarshe insami galabarsaba. = Wani abin mamaki ma game da wannan jarumi dan Adam shi ne irin yadda har ya san sunanki da sunana. Wai ma har yana cewa musamman don mu yazo.” . ‘Da tsohuwa Bakayalu ta ji wannan bayani daga ‘bakin jikanta sai ta-yi shiru tare da tsunduma cikin tunani, san-nan ta ce, “Duk yadda: aka yi wani ya ‘ munafunce mu ke nan, an fita da bakin littafi zuwa ga hannun makiya. ‘ Sham’una-ya tambaya, “Kaka, -me. ya. hada matsalarmu da wani bakin littafi can?” Bakayalu ta ce, “Dangantaka ta kut-da-kut kuwa. In‘ba ka manta ba na taba sanar da kai shekaru masu “yawa da suka wuce cewa asirin rayuwarka na wurina ‘ kuma babu wanda zaitaba iyakashekako? Sham’una ya amsa, “E na tuna kwarai, ai ba zan ’ taba manta irin wancan albishir ba, shi ne ma dalilin “da ya sa na fara tunkatar wadanda nake jin tsoro ada, har ya zo ya kasance babu wanda nake tsoro a cikin tarayyar aljanu da mutane sai dai ni ake jin tsoro.” Www.bankinhausanovels.com.ng Sai Bakayalu ta ce, “To asirin gagarar taka da rayuwarmu ni da kai gaba daya suna cikin littafin ne. A kansa ne na taba sa ka je ka nemi aljani Ziri-muzi ka kashe shi, lokacin da na yi zaton ya taba bude littafin, a wancan lokacin ba ka san dalilin ba amma na baka umurnin cewa in ka je ka zagaye garin da ya shiga ka kashe shi taredawadanda suka ba shi masauki.” Bakayalu ta ci gaba da cewa, “Abin da ban fada maka baa wancan lokaci shi ne, wurin koKarin mayar da kai gagararre, da kuma kare rayuwarka yadda babu wanda zai iya samun nasara a kanka ballantana wai har ya kashe ka. Mun yi amfani da wani irin tsafi ne ajin farko daga cikin tsafuffukan farkon zamani, irin tsafin da yanzu babu irinsa ya bace sai dai tarihi. Shi ne na sami labari daga cikin kakannina cewa matsafi guda daya tak da ya rage da irin wancan tsafi a wancan zamani wato aljani Jamboro kasancewar ba shi da magaji sai ya dauke bayanan tsafin ya kai wata duniya can mai wahalar zuwa ya Boye, wanda kuma zuwa waccan duniya sai matsafin aljanin da ya isa tukuna. Ni ma nan da ka gan ni sa’ar gaske na samu har na sami shiga waccan duniyar a cikin irin tafiyetafiyen da na rika yi. Ya kai jikana, ka sani cewa shekara daya da wata -_ – Www.bankinhausanovels.com.ng takwas na yi ina lalube-lalube har na yi nasarar tono wanda ya Boye, ko da yake a karkashin haka saura kadan ni ma in halaka, kai hasali ma ban taba cin bakar wahala kamar ta samo wancan tsafi ba. Ya kai Sham’‘una, lokacin da na gamsu da biyayyarka shi ne na hada maka tsafin, har ka zo ka gagara. Saboda kuma tsananin Kaunar da nake yi maka na sadaukantar da raina a matsayin fansa ga tsafin. Sai Sham’‘una ya ce mata, “Ke ma kaka akwai naki kuskuren! Ta yaya za a aikata irin wannan ganganci haka? Yanzu ya kamata ace Sarkin aljanu mai yawan makiya a rubuta wani sirri nasa a ajiye haka kawai ballantana kuma har asirin rayuwata? Sai Bakayalu ta ce, “Abin da ka sani ne wanda kuma ba sai na sake maimaita maka ba cewa duk, kuma kowane irin tsafi yana dauke da wata illa ko cutarwa Boyayyiya ko bayyananniya ko kuma duk biyun ga wanda ya aikata shi kansa. To ai bayyanar bakin littafin ne abin da ke nuna cewa tsafin ya hadu, kuma salwantar da shi babban hadari ne, duk da cewa yana Kunshe da bayanin abin da zai kawo karshen tsafin. A cikin littafin ne aka yi bayanin wasu miyagun makamai da suka gagari kowane irin tsafi, har ma aka Www.bankinhausanovels.com.ng siffanta rijiyar da suke a cikin duniyar ‘yan Adam, kuma sai dan Adam din ne kawai zai iya fitar da su ya mallakesu to.kuma duk wanda ya mallakesu to shi ma ya zama gagararre ke nan, shi ya sa da ka ce mini daya daga cikin shugabannin yakin dan Adam ne ka gaina tunani. . A wadancan shekaru na farkon hada tsafin, ni da Kaina na rika zuwa dajin da makaman suke ina tsaron rijiyar, amma da na ga alamar babu komai sai na , daina zuwa, don akwai wahala ko da a mafarki wani mahaluki ya taba sanin irin sarkakiyar matakin da za – a taka wurin.halaka mu, shi,ya sa na ce babu shakka ; wani ya munafunce mu ya fita da wancan bakin littafi.A gaggauce tsohuwa Bakayalu ta nufi dakinta cikin taskar da take ajiye kayayyakinta mafi muhimmanci ta. bankada .inda-:ta ajiye littafin sai kuwa ta gan shi ‘kamar ba,a;taba.motsa shi daga, wurin ba, saboda – haka sai ta dauko shi.ta fito ta sami Sarkin aljanu Sham ‘una a inda ta bar,shi tun dazu a durKushe. Ta . Nuna tare da ce masa, “Ashe.muna neman tayar da hankalinmu, bakin littafi dai yana nan a inda na bar shi, kuma ina zaton babu wanda ya taba shi. Sai ta gabatar da waniirin sihiri, ai nan take sai ga taswirar fuskar Dailanu a jikin littafi,,, . . Bakayalu ta ce, “Babu shakkayari yarnan Dailanu ce ta taba littafin nan.” Saboda haka sai ta fita ta sa aka kamo Dailanu aka fara azabtar da ita da wata irin ukuba mai tsananin gaske. Bakayalu ta zo tana tuhumar Dailanu a game da fita da littafi, ta ce, “Ke ce ki ka fita da wannan littafi, don ga taswirar fuskarki nan a jikinsa.” Aljana Dailanu ta yi wani irin marairaicewa ta ce, “Ya ke kakata, kin sa ana ta azabtar da ni alhali ban san maganar fita da littafi daga cikin dakinki ba. Kuma maganar ganin fuskata kada ki manta ni kadai ce ke shiga ko’ina a dakinki. Kuma fa ba a dade ba da ki ka umurce ni a kan cewa in share tare da goge ko ina a dakin, to yaya za a yi in share ko kuma goge wani abu ba tare da na taba shi ba?” Aljana Dailanu ta ci gaba da bayani ga kakarta Bakayalu cewa, “Littafi dai yana nan, duk da cewa ba a fada min abin da aka Boye a cikinsa wanda ya Bace ba. To ko ma dai mene ne kada fa mu manta cewa masifar yaki ne ta tunkaro mu gaba daya, kuma a matsayina na jinin gidan nan ina ganin wannan ba lokacin da za a tsaya zargi ba ne, don wannan masifa in aka yi sakaci za ta yi wa gidan sarautar nan muguwar Barna gaba daya.” Jin wannan zance fa sai tsohuwa Bakayalu ta sa aka HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 24 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA . A wadancan shekaru na farkon hada tsafin, ni da Kaina na rika zuwa dajin da makaman suke ina tsaron rijiyar, amma da na ga alamar babu komai sai na , daina zuwa, don akwai wahala ko da a mafarki wani mahaluki ya taba sanin irin sarkakiyar matakin da za – a taka wurin.halaka mu, shi,ya sa na ce babu shakka ; wani ya munafunce mu ya fita da wancan bakin littafi.A gaggauce tsohuwa Bakayalu ta nufi dakinta cikin taskar da take ajiye kayayyakinta mafi muhimmanci ta. bankada .inda-:ta ajiye littafin sai kuwa ta gan shi ‘kamar ba,a;taba.motsa shi daga, wurin ba, saboda – haka sai ta dauko shi.ta fito ta sami Sarkin aljanu Sham ‘una a inda ta bar,shi tun dazu a durKushe. Ta . Nuna tare da ce masa, “Ashe.muna neman tayar da hankalinmu, bakin littafi dai yana nan a inda na bar shi, kuma ina zaton babu wanda ya taba shi. Sai ta gabatar da waniirin sihiri, ai nan take sai ga taswirar fuskar Dailanu a jikin littafi,,, . . Bakayalu ta ce, “Babu shakkayari yarnan Dailanu ce ta taba littafin nan.” Saboda haka sai ta fita ta sa aka kamo Dailanu aka fara azabtar da ita da wata irin ukuba mai tsananin gaske. Bakayalu ta zo tana tuhumar Dailanu a game da fita da littafi, ta ce, “Ke ce ki ka fita da wannan littafi, don ga taswirar fuskarki nan a jikinsa.” Aljana Dailanu ta yi wani irin marairaicewa ta ce, “Ya ke kakata, kin sa ana ta azabtar da ni alhali ban san maganar fita da littafi daga cikin dakinki ba. Kuma maganar ganin fuskata kada ki manta ni kadai ce ke shiga ko’ina a dakinki. Kuma fa ba a dade ba da ki ka umurce ni a kan cewa in share tare da goge ko ina a dakin, to yaya za a yi in share ko kuma goge wani abu ba tare da na taba shi ba?” Aljana Dailanu ta ci gaba da bayani ga kakarta Bakayalu cewa, “Littafi dai yana nan, duk da cewa ba a fada min abin da aka Boye a cikinsa wanda ya Bace ba. To ko ma dai mene ne kada fa mu manta cewa masifar yaki ne ta tunkaro mu gaba daya, kuma a matsayina na jinin gidan nan ina ganin wannan ba lokacin da za a tsaya zargi ba ne, don wannan masifa in aka yi sakaci za ta yi wa gidan sarautar nan muguwar Barna gaba daya.” Jin wannan zance fa sai tsohuwa Bakayalu ta sa aka ZAMU TASHI kwance ta duk da cewa jikinta bai ba ta da bayanan ba, har ma take ce mata, “Akwai sharadi guda, yanzu ba lokacin bincike ba ne, lokacin yaki ne, amma babu shakka bayan an kammala zan yi cikakken bincike, kuma duk wanda muka samu cewa ya taba fita da wannan littafi, to babu shakka za mu Kona shi da ransa. Ko wane ne.” Aljana Dailanu ta doddogara ta nufi bangarenta don fara jiyyar raunukan da ta samu a lokacin azaba. ‘Tsohuwa Bakayalu ta juya ta fuskanci jikanta Sham’‘una tana mai tambayar sa, “Ka ce mene ne sunayen jagororin yakin?” Sham‘una ya ce, “Sunan dan Adam din Idrisu dan Hamidu, sannan sai Sarki Ifritu wanda muka taba yaki da shi har na sa shi a cikin battar Karfe, sannan na sa shi a tsakanin dutse. Na yi mamakin yadda aka yi ya kubuta shi da jama’‘arsa da ke daure a cikin sarKka.” Bakayalu ta ce, “Sarki Ifritu dai da na sani kake magana?” Sham‘una ya amsa, “EF, shi kaka.” Sai Bakayalu ta nisa sannan ta ce, “Sarki Ifritu kuwa ka san in ba mu ba babu wanda ke ja da shi ya kwana lafiya a duk cikin aljanu, amma wannan karon zan bayyana masa sharrina baki daya. Abin da nake — Www.bankinhausanovels.com.ng so da kai yanzu shi ne ka je ka shirya dukkan mayakanka, ni kuma zan fara girka nawa.” To yadda lamarin ya ke shi ne, ita wannan makirar tsohuwar aljana Bakayalu har rundunonin mayaka take da su na musamman, kuma wadannan zaratan mayaKan aljany ba sa aikin kowa babe sai nata, ta tsaface su da wani irin tsafi mai ban al’ajabi. Ga su nan launi daban-daban, akwai wasu mayu daga _ cikinsu wadanda ba su da abinci sai dai shan jinin aljanu, wasu kuma ga su nan bakake, wasu koraye, algashi, jajaye da sauran launuka gwargwadon abin da ita Bakayalun ta san dalilin da ya sa ta juyar da su haka. Miyagu ne, wanda daya daga cikinsu kawai in rana ta Baci zai iya karawa da jaruman aljanu dari biyar. Shirin yaki ya kankama a bangaren Sarkin aljanu Sham’una, jarumai da dakaru dubban daruruwa kowanne sai Karaji ya ke yi don za a kara da abokan gaba, sannan kuma duk da haka sai da Sham’una ya sa masu yekuwa cewa su kewaya cikin duniya da wajenta, duk inda wani bakin aljani dan asalin yankin ya ke, to ya koma don kare gida. Aljana Bakayalu kuma tuni ta shiga don fara girka wadancan mayun aljanu nata. Amma lamarin aljana Dailanu kuwa bayan an kwance ta don yin jinya, kuma kasancewar ranar Www.bankinhausanovels.com.ng Juma’a ce, washegari Asabar sai ta zame jikinta ta sulale ta nufi wurin kawayenta su Nur. Ta yi musu sallama suka amsa, suka rungume ta suna tambayar lafiya yau mako biyu ba su gan ta ba? Shi kuma Sarki Sham’una yau kwana takwas ke nan ba su gan shi ba? Sai aljana Dailanu ta ce musu, “Ina fa lafiya, Idrisu dan Hamidu ya tunkaro, ya tayar wa da matsafa hankali, ai nesa ta zo kusa don kuwa a halin yanzu ya cinye birni na sha daya, yanzu saura birni na sha biyu wanda azzalumin karen aljanu Sham’una da muguwar kakarmu Bakayalu ke ciki.” Ta Kara da ce musu, “Ai ni ma Allah ne Ya sa kwanana yana gaba, ba don haka ba da tuni shaidaniyar kakata ta babbaka ni.” Saitakware musu jikinta suka ga irin yadda aka tsattsaga shi a lokacin azaba. Tace, “A kan littafin nan ne dana taba kawo muku, in ba ku manta ba har a wancan lokacin na ce kar ku kuskura ku taba shi da hannunku, har na rika bude muku shafukan da hannuna lokacin da kuke juyewa. To na yi haka ne don tsoron kada bincike ya tashi su ga fuskokinku, to binciken kuma ya taso, an ga tawa fuskar, ko da yake taimakon Allah Mai girma zuwa yanzu ba ta gama tantancewa ba tukuna, lallai da ba ku sake gani na ba, don da a ce ta gane da kuwa Www.bankinhausanovels.com.ng ni za ta yi kamar yadda ta halaka mahaifina. Ba ni kadai ba, ku ma kanku da tuni muna can lahira tare. Amma in Allah Ya so kafin Bakayalu ta mutu sai na mayar mata da jawabi, muguwar kafira!” Ai fa nan ‘yan matan nan suka jajanta mata da kuma Kara karfafa mata guiwa, kafin su Balle da labaransu yadda suka saba, sai dai yau babu wasanni don ba ta jin dadin jikin. Cikin labaran da suke yi ne har take sanar da su cewa an yi karen batta a karon farko tsakanin jarumi Idrisu da Sarki Sham’una, har shi Sarkin aljanun ya dafe keya ya ranta~a-na-kare. Jin wannan labari sai murna da farin ciki suka cika , zukatan ‘yan matan nan, suka fara tuna dangi da masoyansu tare da addu’o’in Allah Ya bai wa jarumi | Idrisu cikakkiya kuma tabbatacciyar nasara a kan Sarki Sham’una da kakarsa Bakayalu. Aljana Dailanu yau ba ta bari yamma ta yi ba sai ta mike don sallama da Kawayenta. : Nur ta tambaya, “Yau da wuri za ki tafi haka?” Dailanu ta ce, “Kawata na san za ki fahimta, kin san Kasa babu lafiya, kuma kin san akwai dan zargi a kaina, saboda haka ma dai ni ba za ku sake gani na ba sai abubuwa sun lafa tukuna, in Allah Ya so.” ZUWA yanzu babu abin da ya fi damun jarumi Idrisu fiye da rashin lafiyar dokinsa Jagora. Kuma a dalilin halin da dokin ke ciki ne tafiyarsu zuwa birni na sha biyu ba ta yi saurin gaske ba. Tun da suka dunfaro wannan birni, shi kansa Idrisu da kuma wasu da yawa daga cikin aljanun da ke tawagarsu suka tabbatar da cewa ba su taba ganin birnin da ya fina Sham‘una kyau ba. Tun daga nesa cikin sararin samaniya za ka hango taswirar Sarki Sham‘una shi da kakarsa, wato masu gidan mulki. Kana kallon fuskar Bakayalu da ke cikin taswirar ka san sharri ya zauna daram da gindinsa a wurin. Dole ne ma gabanka ya fadi. Akalla akwai aljanu dubu dari sau dari a cikin wannan birni na goma sha biyu na Sham‘una. Kafin su jarumi Idrisu su kammala karasowa tuni labari ya isa, ashe da ma jirace ake da su, kuma da ma tsarin da aka shirya ke nan, ai sai kawai aka bude Www.bankinhausanovels.com.ng Kofar birnin jarumai suka shiga fitowa kamar ba za su taba Karewa ba, tun daga nesa Sarki Ifritu ya lura da haka amma babu abin da ya ke shelantawa a cikin rundunarsa sai, “Kada gabanku ya fadi, Karfi da nasara suna wurin Allah ne ba yawa da Karfin jiki ba, kowaya natsar da hankalinsa.” A haka har suka Karaso inda suka yi sansani don fuskantar Sham’una da jama’arsa wanda akalla wadanda suka fito zuwa yanzu ‘sun nunnunka yawansu kuma ci gaba da fitowa suke. ‘ anan Jarumi Idrisu ya ba Sarki Ifritu shawara a kan cewa kada a jira sai sun gama fitowa don ba a ‘san irin shirinsu ba, ya ce, ‘Mu afka musu kawai, tun kafin jikin mayakanmu yayi ganyi.” Haka kuwa aka yi, aka rufar wa mayakan Sarki Sham’una da sara da suka. Masu harbi na yi karfafa kuwa ba abin da suke yi sai karya wuyaye. – Jarumi Idrisu, Sarkin aljanu ‘Tfritu da wancan saurayin jarumin kowanne ‘nasa gefe ya ja yana ta Ta yankan aljanu kamar kubewa. Sarkin aljanu Sham’una sai ya ga abin kamar a . mafarki a lokacin da ya fito fagen fama, zuciyarsa ta hasala matuka. A kan wata irin katuwar giwar aljanu ya ke, ya juya ya kealli irin yadda Idrisu mai takobi ke masa Barna, sannan sai ya waiwaya wancan bangaren Www.bankinhausanovels.com.ng ai sai suka yi ido da ido shi da Sarki Ifritu yana ta kwankwatsa masa kan aljanu da gwalminsa, ai nan take ya nufi wurin Sarki Ifritu din da nufin bari ya fara da shi su yi ta ta Kare. Suka fa fuskanci juna, Sarki Sham’una a kan giwa shi kuma Sarki Ifritu a kan doki. Abin da Sarki Ifritu ya fara yi kafin ma giwar Sarki Sham’una ta gama tsayawa sai ya dubi Kwaurinta ya buge da gwalmi, ai sai ta durkushe, kafin ta kai Kasa sai ya sake daga gwalmin ya dankara mata a kanta, nan ta fadi a mace, amma abinka da aljani kafin giwar ta kai Kasa . Sham’una ya tashisama abinsa kamar tsuntsu. Shi ma Sarki Ifritu sai ya tashi fir ya bi shi suka hade can sama. Ko kadan fadan nasu babu kyan gani, sai Kara kake ji kamar aradu ce ke faduwa, wannan shi ake cewa turnuku fadan iblisai, yaro bai gani ba balle ya raba. Can kuma sai suka dawo kasa aka ci gaba da fafatawa. Da ma Sarki Ifritu ya san karonsu da Sham‘una, shi ma kuma Sham’una ya san shi. Wani irin mummunan bugu da Sarki Ifritu ya kai wa Sarki Sham’una da gwalminsa wannan karon an sami tangarda bai iya kaucewa ba, ai sai ga shia Kasa, amma abin mamaki ko a jikinsa, hasali ma sai ga shi ya mike yana dariya tare da kakkabe Kura. Da Sarki Ifritu ya ga haka sai ya sake kai masa hari, amma ina, ai da ma kowa ya san cewa Sarki Sham’una ba Karamin jarumi ba ne, ai nan take ya zame tare da yin wata irin tsawa mai tsananin firgitarwa, sai ga wata irin sarka mai tsananin tsawo da kauri caf kamar kiftawa da bismillah ta nannade Sarki Ifritu ta yi sama da shi. Tsawar da Sham’una ya yi ne ta janyo hankalin Idrisu da ke can yana zabge kan abokan gaba, Dubawar da zai yi sai ya ga Sarki Ifritu a daure ana yin sama da shi, kafin ka ce yaya aka yi haka jarumi Idrisu ya nufi Sham’una da sara, amma kasancewar tuni Sarkin aljanun ya rigaya ya tsorata da wannan takobi na Idrisu sai ya janye cikin dabara ya koma cikin mayaka yana mai ci gaba da fada. Sham’una ya kamo wani farin aljani da hannunsa, ya dunkula hannunsa ya yi masa dundu, tafiyar wancan aljanin ke nan zuwa barzahu. Ya finciko wasu biyu ya gwara musu kai, ai sai ga kwakwalensua waje! Ashe haka kwakwalwar aljanu take? Cikin wata dabarar kuma Sham’una ya zame daga wurin yakin ya nufi cikin gari ba tare da mayakansa sun fahimci ba ya fagen ba. Shi kuwa jarumi Idrisu abin da ya yi shi ne sai ya daga takobinsa ya sari gefen sarkar da ta daure Sarki Ifritu, nan take ta warware, Ifritu ya tashi rike da —_ Www.bankinhausanovels.com.ng gwalminsa ya yi wa Idrisu wata irin jinjina irin tasu ta manyan mayaka, daga nan ko kallon juna ba su sake yi ba kowannensu ya juya ya rufar wa abokan gaba, abin dai babu kyan gani. Shigar Sarki Sham’una cikin gari bai zame ko ina ba sai wurin kakarsa Bakayalu, yana zuwa sai ya zube a gabanta yana mai cewa, “Ni fa jarumin dan Adam din nan ina jin tsoron takobinsa, ina ganin kamar in aka yi rashin sa’a ya sauka a jikina zai iya yi mini Jahani.” Jin wannan jawabi ya sa idanun Bakayalu suka yi jajawur kamar garwashin wuta, tana mayar da nunfashi da sauri-sauri, kuma da ta mayar da nunfashin sai ka ga ga wani irin hayaki mai dan karen doyi ya fito daga cikin hancinta. Ta ce, “Ya kai dana, ina zaton mugun takobin nan ne da shi kadai zai iya yi mana illa. Amma in tambaye ka, shin shi wannan jarumi yana rike da wani mashi?” Sham’una ya ce, “A’a babu mashi a hannunsa. Ni dai ban gani ba.” Bakayalu ta yi shiru ta tsunduma cikin kogin tunanin irin yadda wannan lamari ke nema ya shige mata duhu. Dalilin da ya sa dai Sham’una bai ga mashin Idrisu ba shi ne, shi wannan mashi yana da wani abin al’ajabi tattare da shi, wato jarumin kan iya Www.bankinhausanovels.com.ng nade shi kamar damara ya daure a Kugunsa. In ba ka san yana da shi ba, to ba za ka taba cewa akwai ba. Da aljana Bakayalu ta kammala tunaninta sai ta ce, “Wannan lamari bai kamata mu dauke shi da wasa ba, ya zama dole mu gaggauta halaka su don kada dan hakin da ka raina ya zo ya tsone maka idanu. Tashi ka koma filin yaki, ni kuma zan shiryo maka babban dauki nan da wasu kwanaki in na kammala girka dakaruna.” Ta fara shirya sahu-sahu na mayaka. A jerin korayen aljanu akwai dubu dari biyu, Haka nan na bakake suduf, su ma akwai jarumai dubu dari biyu, Haka nan algashi da shudaye, kowanne dubu dari biyu ne, sai jerin karshe mai dauke da aljanu dari biyu, jajaye kamar jini. , Su wadannan aljanu jajaye mayu ne, duk aljaninda ka sani ba ya son ko haduwa da su. Miyagu ne masu tsananin Keta da ketare iyaka da kuma kasancewar babu wani makami da aka taba samun cewa ya taba kama su. Kai ita ma kanta Bakayalu ba don ita kanta shaidaniyar ba ce, to da wadannan jajayen aljanu sun gagare ta. A fagen fama kuma ana can ana ta karawa, can sai aka nemi saurayin jarumin nan da ke cikin tawagar su Idrisu aka rasa, amma kasancewar yaki ake yi babu Www.bankinhausanovels.com.ng damar dubawa ko bincikawa sai dai kawai Kakkarfan tunanin cewa watakila shi tasa ta Kare. Yaki ya yi yaki, can sai aka ji wani irin diri wanda dole sai da aka dan tsahirta da yaki don ganin ko mene ne haka, ai sai aka ga saurayin jarumin nan da ba a san kowane ne ba tare da dubban daruruwa na aljanu tare da shi sun dira a fagen faman, suna zuwa sai jarumin nan ya yi wa jarumi Idrisu da Sarki Ifritu jinjina, su ma suka mayar masa, ai kafin a ankara sun auka wa abokan gaba da sara da suka, sai girbe musu kawuna kawai suke yi, abin sai wanda ya gani. Labari ya riski Sarki Sham’una a daidai lokacin da ya dawo fagen fama, cewa abokan gaba fa sun sami tallafin mayaka masu yawa, ai sai hankalinsa ya sake tashi tare da ba da umurni ga jama’’arsa cewa a auka tare da yin yaki gaba daya. Yanzu al’amari fa ya sake Kazancewa, Sarkin aljanu Sham’una a nasa bangaren sai murmushe aljanu ya ke yi kamar yana murmusar soyayyar gyada, babu ko Shakka ya isa Kasaitaccen jarumi, saboda sadaukantakarsa duk inda ya fuskanta sai a dare a ba shi wuri. Shi ne da kansa ya ke bi da gudu yana kamowa yana kashewa, amma ba dai a tarbe shi ba. A’a, Sarkin aljanu Sham’una ya wuce haka a wurin gama-garin aljanu. Www.bankinhausanovels.com.ng Ran nan sai Karajin mazaje kake ji da hargowa, da ma ko fadan mutane ne yaya, ballantana kuma na aljanu har ma da manyan jaruman sarakuna irin Sham’una da Ifritu? A takaice dai kwanaki ashirin da daya da aka yi ana ta gwabzawa kafin a rabu don hutawa da kuma sake shiri, kumaa cikin kwanakin nan daidai da rana daya Bangaren Sarkin aljanu Sham’una bai taba samun nasara baa kan daya bangaren. Tsananin yawansu ne kawai ya sa ba a saurin gane irin nasarar da ake samu a kansu, sai dai ko in an kwatanta yawan gawarwakin kowane bangare tukuna. Bayan an dan natsa ana hutawa sai shi jarumin aljanin nan wanda har yanzu ba a san kowane ne ba ya zo wa Idrisu da wata irin riga da wando da takalmi ya ce masa, “Ya kai Idrisu amshi wadannan kaya ka saka a jikinka kafin a ci gaba da yaki.” Jarumi Idrisu ya karba tare da tambaya, “To su kuma wadannan kaya mene ne labarinsu da kuma hikimar sanya su? Kai hasali ma kai kanka mene ne labarinka?” Jarumin saurayi ya ce, “Ya kai Idrisu, labarina dai ka bar shi sai in Allah Ya taimake mu mun kammala yaki, amma labarin sutura da na ba ka shi ne, kaya ne na kare tartsatsi da kuma zafin wuta, don mu aljanu HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 25 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Yanzu al’amari fa ya sake Kazancewa, Sarkin aljanu Sham’una a nasa bangaren sai murmushe aljanu ya ke yi kamar yana murmusar soyayyar gyada, babu ko Shakka ya isa Kasaitaccen jarumi, saboda sadaukantakarsa duk inda ya fuskanta sai a dare a ba shi wuri. Shi ne da kansa ya ke bi da gudu yana kamowa yana kashewa, amma ba dai a tarbe shi ba. A’a, Sarkin aljanu Sham’una ya wuce haka a wurin gama-garin aljanu. Www.bankinhausanovels.com.ng Ran nan sai Karajin mazaje kake ji da hargowa, da ma ko fadan mutane ne yaya, ballantana kuma na aljanu har ma da manyan jaruman sarakuna irin Sham’una da Ifritu? A takaice dai kwanaki ashirin da daya da aka yi ana ta gwabzawa kafin a rabu don hutawa da kuma sake shiri, kumaa cikin kwanakin nan daidai da rana daya Bangaren Sarkin aljanu Sham’una bai taba samun nasara baa kan daya bangaren. Tsananin yawansu ne kawai ya sa ba a saurin gane irin nasarar da ake samu a kansu, sai dai ko in an kwatanta yawan gawarwakin kowane bangare tukuna. Bayan an dan natsa ana hutawa sai shi jarumin aljanin nan wanda har yanzu ba a san kowane ne ba ya zo wa Idrisu da wata irin riga da wando da takalmi ya ce masa, “Ya kai Idrisu amshi wadannan kaya ka saka a jikinka kafin a ci gaba da yaki.” Jarumi Idrisu ya karba tare da tambaya, “To su kuma wadannan kaya mene ne labarinsu da kuma hikimar sanya su? Kai hasali ma kai kanka mene ne labarinka?” Jarumin saurayi ya ce, “Ya kai Idrisu, labarina dai ka bar shi sai in Allah Ya taimake mu mun kammala yaki, amma labarin sutura da na ba ka shi ne, kaya ne na kare tartsatsi da kuma zafin wuta, don mu aljanu ZAMU TASHI in yaki ya yi yaki, to mukan juya yin amfani da wuta, kuma babu shakka ka san cewa jama’ar Sham’una sun ji jiki sun wahala, Karshe nan gaba kadan ka ga sun fara yin amfani da wuta.” Idrisu ya yi godiya, kuma zuciyarsa ta natsu a kan amfani da wadannan tufafi. Wannan saurayin aljani ya ci gaba da sanar da Idrisu cewa, “Akwai fa babbar gwagwarmaya a gabanmu, don har yanzu muguwar tsohuwar aljanar nan shaidanunta ba su fara yaki ba tukuna, ko da yake ba wai muna jin tsoron mayaKanta ba ne, a’a, duk da cewa mun san akwai tsananin wahalarwa saboda irin Kwarewa da siddabarunsu, amma duk da sauki in an kwatanta su da wasu mayu su dari biyu da take da su, wasu jajayen iblisai ne wadanda gaba daya mun hakikance cewa babu abin da zai iya kama su sai dai takobinka kadai.” Jarumi Idrisu dan Hamidu ya ce masa, “To tun da haka ne wadannan ku bar ni da su kawai, in Allah Ya yarda za mu sami rinjaye a kansu.” Ya dauki suturun wuta da aka ba shi ya saa jikinsa. Babu dadewa da faruwar wannan lamari sai ga jama’‘ar Sarki Sham’‘una sun sake kawo hari, aka ci gaba da gwabzawa, kawunan mazaje sai zuba suke yi kamar ana kakkabar yalwatacciyar itaciyar Www.bankinhausanovels.com.ng mangwaro. Sham‘una yana can gefe sai kayar da mazaje ya ke yi babu KakKautawa, ya yanke shawarar Kokarin rage yawan mayakan Bangaren abokan gaba ne tukuna don su ma jama’‘arsa su ga cewa ba su kadai aka fi kashewa ba, wato maimakon ya.bata lokacinsa wurin fuskantar manyan jaruman yaKkin, a’a wadannan yace sai daga baya tukuna. Ko kuma in Bakayalu ta fito ta gama masa da su. Wannan hari da jama’ar Sham’una suka sake kawowa sai da aka yi kwanaki hudu ana karawa, a rana ta biyar sai aka rika jin dirin takawar mayaka na fitowa daga cikin gari. Aljana Bakayalu ce da tawagarta. Ga aljanunta nan jejjere, kowane launi Kungiyarsu daban, bakake da koraye da sauransu. Jeri na shidasu ne jajayen mayun iblisan nan su dari biyu, kumasu ne ke dauke da kujerar aljana Bakayalun wadda take kai a zaune rike da wata Katuwar bakar tukunya ta tsafi. ‘Tsohuwar aljana fa ta duba da kyau ta lura da yadda aka tsara yaKin, sai ta umurci rundunar farko ta aljanu dubu dari biyu da aukawa. Abinka da Kwararru sai nan na nan salon yaKin ya sauya, Bangaren su Idrisu suka fara shan bakar wahala, amma haka Sarki Ifritu da wancan saurayin jarumin Www.bankinhausanovels.com.ng ke kewayawa filin daga suna ihu suna Kara karfafa wa mayaKansu guiwa a kan cewa ajure, nasara tana kusa. Aiki ya Karu a kan maza, Idrisu da Sarki Ifritu da wancan jarumin dole suka Kara Kaimi wurin rufar wa musamman wadannan aljanu na Bakayalu wadanda ke murtsuke aljanu kamar suna wasan yara. Cikin wasu ‘yan sa’o’i wadanda ba su wuce bakwai ba sai ga shi wancan runduna ta farko ta Bakayalu sai dai tarihi, don kuwa an gama dasu. Wannan al’amari ba Kankanin Kara karfafa guiwar jama’ar Bangaren su jarumi Idrisu ya yi ba, suka ji wani sabon Karfi ya shigar musu, saboda haka ko lokacin da aljana Bakayalu ta sako daya rundunar ba su tsorata ba, sai aka ci gaba da gwabzawa kawai, kuma irin yankar Kaunar da aka yi musu a baya ba su yarda an sake yi musu irinta ba. Lokacin da runduna ta uku na bangaren Bakayalu ta tunkaro cike da wani irin fushi sai jarumi Idrisu ya ja wata babbar tawaga ta aljanu da gaggawa suka nufi bangaren dama, shi kuma Sarki Ifritu da ya fahimcei abin da ake nufi sai ya janye wata tawagar da gaggawa suka nufi hagu, kuma kafin a hade da abokan gaba tuni wadanda suka yi dama da wadanda suka yi hagu din suka yi wa wancan runduna ta jama’ar Bakayalu zobe suka sa su a tsakiya suka hau su da kisa babu Www.bankinhausanovels.com.ng kakkautawa, shi kuma wancan matashin aljani abokin su Idrisu ya dirar musu ta tsakiya. Yaki fa ya kankama yadda ya kamata, a haka dai cikin kwanaki tara da fara artabu da mayakan aljana Bakayalu sai ga shi an cinye mata rundunoni hudu, kuma ba tare da Bata lokaci ba runduna ta biyar ta shigo, wadanda daga su fa sai jajayen mayun nan wadanda har yanzu aljanar ke kan girkawa, sunajiran lokacin shigarsu ya yi. Shigar runduna ta biyar fa sai yaki ya koma na feshin wuta, da kuma jefa mulmulen wuta, bayan sun kammala sai kuma aka shiga gwabzawa gaba da gaba, yaki ya yi Kamari, sai da aka yi kwana_ hudu ana gwabzawa da wannan runduna. A rana ta biyar Bangaren su Idrisu suka sami nasara, abin kamar a labari. Kaka-tsara-kaka, yanzu fa abin da ya rage wa aljana Bakayalu na jarumai sai dai mayun aljanunta kawai, kuma babu shakka lokacin shigarsu fagen daga ya yi, saboda haka sai bangaren Sham’una ya ba da umurni ga mayakansa da ke cikin filicewa gaba dayansu, har shi kansa Sham’una din su janye, don jajaye za su shigo. Dalili kuwa shi ne, ita Bakayalu a irin girka da tsafin da ta yi wa wadannan shaidanu, da zarar suka Www.bankinhausanovels.com.ng shiga fagen fama, to duk abin da ke cikin filin halaka shi kawai za su yi, ko mene ne kuma kowane ne, to da zarar sun kammala sai ta sake yin amfani da tsafin don sake mallake su, fitinarsu ta koma karkashin ikonta. Ganin mayakan Sham’una suna janyewa daga fagen fama suna komawa baya har da shi kansa uban gayyar, da kuma lura da cewa wadancan jajayen iblisan sun fara tunkarowa zuwa cikin fagen fama, sai Idrisu ya tuna da bayanin da wancan matashin jarumi ya yi masa game da wadannan mayun aljanu, sai ya fahimci cewa lallai akwai makircin da aka shirya, saboda haka sai Idrisu ya rika yekuwa cikin wata murya mai Karfi yana umurtar Sarki Ifritu da wancan jarumin su janye gaba dayansu su da jama’arsu, har ma ya ke cewa, “Ku juya… na ce ku tsere.” Abin dai kamar tatsuniya, cikin dan Kankanin lokaci sai ga filin babu kowa sai jarumi Idrisu kadai, su kuma jajayen aljanun nan, mayu sun yiwo tsinke gare shi. Haka Idrisu ya yi ta fafatawa da su, kuma duk irin maitarsu sun yi amma ina, Allah Bai yarda sun cutar da shi ba, da suka kammala siddabarunsu irin na mayu sai suka nufo shi don ayi ta ta kare. Tuntuni abin dada maya ke ta jira ke nan. Ya sa takobi ya yi ta datsa jikkunansu bibbiyu, ta Www.bankinhausanovels.com.ng yadda sai da abin ya ba kowa mamaki, har ita kanta Bakayalu, wato irin yadda takobin wannan jarumi dan Adam ke yi musu muguwar Barna. Da zarar ya sari jan aljani sai kawai ka ga wata irin wuta ta kama shi ta cinye kurmus. Kai a takaice dai babu ko daya da ya rage. Bayan ya kammala da su bai yi wata-wata ba sai ya dum fari inda manyan aljanun nan suke su da kakarsu Bakayalu ya yi wata irin dirar mikiya da sara baki daya a tsakiyarsu, abinka da wanda ya tunzura. Rashin sa’ar da aka samu shi ne, duk da Kokarin kaucewa da jaruman aljanun nan suka yi sai da takobin jarumin ya ratsa tsakanin hannayen wani jarumin aljani da ke dauke da wani gefe na kujerar da Bakayalu ke kai, sarar ta datse hannayen har ta sami wani sashe na kujerar. Haka dole wancan jarumin yana ji yana gani ya rabu da hannayensa kamar yadda gefen kujerar da ya ke rike da shi shi ma ya gutsure. Bakayalu ta sulmuyo, amma kafin ta fadi Kasa sai ga shi ta dire riKe da tukunyar tsafinta a hannu. Ta dunKula hannu ta kai wa jarumi Idrisu wani bugu, shi kuwa sai ya sa fadin takobinsa ya kare, ji kake yi tatsatsatsa… wuta ta tashi ta yi sama, amma abin mamaki a wurin aljana Bakayalu maimakon wannan takobi ya narke a dalilin haduwarsa da tsafataccen Www.bankinhausanovels.com.ng hannunta, sai ga shi ko lanKwashewa bai yi ba, kafin ka ce haka jarumanta sun rufar wa Idrisu aka ci gaba da gwabzawa ita kuma ta samu ta janye zuwa bayan fage. Yanzu kam Bakayalu ta hakikance cewa akwai magana game da wannan takobi na jarumi Idrisu dan Hamidu, saboda haka sai ta ruga zuwa gidanta cikin sauri kuma a fusace, tun kafin ta shiga sai ta fara kwalla wa jikanyarta aljana Dailanu kira. Nufinta shi ne ta fada mata gaskiya game da al’amarin fita da bakin littafi wanda asirin rayuwarsu ke ciki, don yanzu ta gama hakikance cewa Dailanun ce ta fita da littafin, to lallai ne ta zo yanzu ta fada mata gaskiya sannan ta kashe ta, in ma dai ba ta fada mata gaskiyar ba dai ta yanke shawarar halaka ta. Shigarta dakin Dailanu sai ta tarar ba ta nan, amma kuma ga rubutacciyar takarda a kan shimfida. Kuma tabbas rubutun Dailanu ne, *Zuwa ga shugabar matsafa Bakayalu. Babu sauran bukatar ci gaba da wahalar neman wanda ya dauka tare da fita da bakin littafin . da sirrin rayuwarku ke ciki, ni ce jikarki Dailanu na fita da shi zuwa ga mutanen kirki wadanda suka yi amfani da shi suka assasa yadda za a Www.bankinhausanovels.com.ng kwato wa al’umma ‘yancinsu. daga mulkin kama-karya da zaluncin da ke Bakayalu tare da jikanki la’ananne Sham‘una ku ka dulmuya su ciki, ba aljanu ba ba mutane ba, ku biyu kadai! Haba Shigata cikin addinin Islama ne ya sa na kara fahimtar irin dulmuyar da al‘umma da ki ka dauki dumbin shekaru kina yi, dubi irin yadda zaluncinki bai bar hatta ‘ya’yan da kika haifa ba, musamman mahaifina da kika kashe ba kan wani kwakkwaran dalili ba Shawarata a gare ki ita ce har zuwa yanzu da ki ke karanta wannan takarda kina da sauran dama guda daya ta samun tsira ke da azzalumin jikanki barawon ‘yan mata ‘ya‘yan mutane, damar kuwa ita ce ku bar bautar tsafi da wuta da rana, ku gaggauta musulunta, in kuwa ba haka ba, to ina yi muku albishir din cewa ku taku ta kare, kuma ko lahira ba na fata Allah Ya hada fuskata da ‘yan wuta Ni ce dai jikarki, Dailanu ‘yar Kailanu-” Tsananin mamaki na irin wannan ba zata ya sa nan take aljana Bakayalu a karo na farko a tarihin rayuwarta ta yanke jiki ta sume har na wasu ‘yan Www.bankinhausanovels.com.ng dakikoki. Tana farfadowa sai ta yi wata irin Kara wadda duk aljanin da ke makwabtaka da wurin sai da ya tsorata, sannan ta sa barorinta suka kira mata Sham’‘una daga fagen fama, yana zuwa sai ta mika masa takarda ya karanta. Yau Bakayalu ce take tambayar sa, “To yanzu kana ganin mene ne abin yi?” Sai Sham’una ya ce mata, “Ya shugabata, yanzu dai lokacin yaki ne, kusan babu abin da za mu iya yi game da wannan yarinya, amma ina ba ki hakuri da kuma alkawarin cewa duk inda ta shiga a cikin duniya ko wajenta bayan yaki zan kamo ta in taune ta da bakina da ranta kina kallo.” Bakayalu ta nisa sannan ta ce, “Yanzu abin da zaa yi bari in shiga cikin kayan tsafina mu je mu ga yadda zaayida wannan yaro dan Adam mai tsaurin kai.” Wasu irin jajayen kaya ne, kai daga gani a lokacin da ta sa su ka san an yi shirin sharri. Yanzu dai yaki ya dan sassauta, aljanun Sarki Sham’una sun fahimci cewa shugabanninsu ba sa cikin fagen, wanda hakan ya taimaka kwarai wurin sa mayakansu su dan janye jiki. Ko kadan bangaren su jarumi Idrisu,ba su matsa ba, don tuni suke jiran irin wannan dama don sararawa. Kowa kuma yanzu yana ji a jikinsa cewa in Www.bankinhausanovels.com.ng Bakayalu ta tashi fitowa, to abin ba zai yi kyau ba, don tabbas za ta zo ne da gaurayen makirci da mugunta gaba daya, sai dai kawai Allah Ya kiyaye. Can kuwa sai aka hango su. Ga Bakayalu nan a gaba tana jagorantar tafiyar, jikanta Sham’una yana biye a baya da sauran wasu dakaru masu yawan gaske, Sarki Ifritu ya yi wuf ya sungumi gwalminsa zai nufi inda suke, sai Idrisu ya sa hannu ya dafa kafadarsa yana mai cewa, “Allah Ya dade da ran Sarki wannan fada ba naka ba ne, ka bar ni da muguwar tsohuwar nan, don _ tsatsubetsatsubenta suna da yawa, kuma ka san cewa Sarki Sham’‘una ba ya mutuwa in ba an kashe ta gaba daya ba a gangar jiki da kuma ruhi.” Sarki Ifritu dai bai kammala fahimtar abin da jarumi Idrisu ke nufi da cewa sai an kasheta a gangar jiki da ruhi ba, amma kasancewar babu lokaci bai tambaya ba sai kawai ya amince ya koma baya din ya bar Idrisu don ya kammala kintsawa. ~ Kafin dan Hamidu ya kammala addu’o’in da ya ke yi don fuskantar wannan tsohuwar iblishiya, abin mamaki sai kawai ga dokinsa Jagora a guje ya nufo shi, yana gudu yana haniniya tare da harbin iska kamar bai taba jin Karfi da lafiya ba a rayuwarsa irin ma ranar. Www.bankinhausanovels.com.ng Wani irin farin ciki da murna suka lullube jarumi Idrisu, ganin cewa dokinsa da ya dade babu lafiya ga shi yau ya ji sauki kuma ma kamar ya fi shi zakuwar haduwa da abokan gaba, ai nan take Idrisu ya dauke sirdin dokin da ke kan dardumar da ya ke ta yaki a kanta ya dora wa doki abinsa, ya nade dardumar tashin ya saKala a kurciyar sirdi. Doki yana jin an hau “shi sai ya yi wani irin rimi ya dire, ya daga kafafuwan baya ya harbi iska sannan ya zabura ya nufi inda su Bakayalu suke. Aka hade a tsakiya, su biyu kadai, jarumi Idrisu dan > Hamidu da tsohuwar aljana Bakayalu. ALJANA Bakayalu ta ce masa, “Kai dan Adam! Me kake bukata ne haka kake ta kashe mana jama’a babu dalili?” Jarumi Idrisu ya amsa mata cewa, “Ranki kawai nake son dauka, ke da azzalumin jikanki Sham’‘una saboda irin mugun zalunci da kuka dade kuna yi.” Cikin fushi sai ta ce masa, “Kai Karamin alhaki! Ka san da wadda kake magana kuwa? Nice kakar aljanu, nice sharri, ni ce mugunta gaba daya, na kashe aljanu da mutanen da babu wanda ya san adadinsu, wadanda suka fi ka jarunta da tsageranci. Ba a taba nasara a kaina ba kuma ba zaa taba yi ba…” Idrisu ya katseta, “Ke dakata! Yi gaggawar janye wadannan kalmomin cewa ba za a taba ba, don ina yi miki albishir din cewa lokacin ne ma ya zo yanzu. La’ananniyar tsohuwa kawai wadda rayuwarta ba ta da wani amfani sai cutarwa.” Da Bakayalu ta ji irin wannan magana da mutum HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 26 BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Wani irin farin ciki da murna suka lullube jarumi Idrisu, ganin cewa dokinsa da ya dade babu lafiya ga shi yau ya ji sauki kuma ma kamar ya fi shi zakuwar haduwa da abokan gaba, ai nan take Idrisu ya dauke sirdin dokin da ke kan dardumar da ya ke ta yaki a kanta ya dora wa doki abinsa, ya nade dardumar tashin ya saKala a kurciyar sirdi. Doki yana jin an hau “shi sai ya yi wani irin rimi ya dire, ya daga kafafuwan baya ya harbi iska sannan ya zabura ya nufi inda su Bakayalu suke. Aka hade a tsakiya, su biyu kadai, jarumi Idrisu dan > Hamidu da tsohuwar aljana Bakayalu. ALJANA Bakayalu ta ce masa, “Kai dan Adam! Me kake bukata ne haka kake ta kashe mana jama’a babu dalili?” Jarumi Idrisu ya amsa mata cewa, “Ranki kawai nake son dauka, ke da azzalumin jikanki Sham’‘una saboda irin mugun zalunci da kuka dade kuna yi.” Cikin fushi sai ta ce masa, “Kai Karamin alhaki! Ka san da wadda kake magana kuwa? Nice kakar aljanu, nice sharri, ni ce mugunta gaba daya, na kashe aljanu da mutanen da babu wanda ya san adadinsu, wadanda suka fi ka jarunta da tsageranci. Ba a taba nasara a kaina ba kuma ba zaa taba yi ba…” Idrisu ya katseta, “Ke dakata! Yi gaggawar janye wadannan kalmomin cewa ba za a taba ba, don ina yi miki albishir din cewa lokacin ne ma ya zo yanzu. La’ananniyar tsohuwa kawai wadda rayuwarta ba ta da wani amfani sai cutarwa.” Da Bakayalu ta ji irin wannan magana da mutum ZAMU TASHI dan Adam ya danKara mata, a cikin Kasarta, sai ta yi fushi ta dunkule, ta yi wata irin tsawa sannan tazama wata irin Katuwa mai kiba, daga nan kuma sai ta zama yarinya, can kuma sai ta tuna cewa an ce wai jarumin yana da karfi, saboda haka sai ta sake rikidewa zuwa wanijarumin namijin aljani. Kawai sai ga wani irin doki jajawur da shi a wurin wanda ba a san daga inda ya zo ba, kuma sai kawai aka gan ta a kansa ba tare da ganin lokacin da ta hau ba, ta daga hannuwanta sama sai ga makamai, ta dumfari Idrisu, fada ya kaure tsakanin su abin sai wanda ya gani. Idan ta bullo masa ta nan sai dokinsa Jagora ya baude da shi, ta yi ta yi amma ya gagare ta, suka buga matukar bugawa, abin dai ya zama turnuku. Babu ko tantama wannan tsohuwa ta isa jarumar gaske, don tun fitowar Idrisu har zuwa yanzu bai taba cin karo da jarumin da ya sha wahalar gaske wurin neman nasara da kariyar kai kamar yadda a yanzu suke gwagwatawa da aljana Bakayalu ba. Da fada ya yi fada sai aljanar ta fahimci cewa dole ne ta sake salo, saboda haka sai ta shiga dabaru irin nasu na aljanu, sai ta shiga fesa wa jarumi Idrisu wani irin dafi a jikinsa don ya zagwanye gaba daya, amma saboda makarin dafin da ke jikinsa sai ya rika jin kamar ruwa take fesa masa. Da ta ga wannan bai yi masa komai ba sai ta shiga jifan sa da mulmulen garwashin wuta, shi ma dai hakan babu nasara. Kafin Kiftawar idanu sai ga hannayen aljanar sun koma guda ashirin, kowane hannu rike da mugun makami yana kai wa Idrisu sara, bugu ko suka, amma ko taba shi ba ta sami damar yi ba. Shi kuma duk Kokarin kai sara da dan Hamidu ke yi ko ya sari hannayen nata sai ya ga babu abin da ya faru kasancewar tsafaffun ne ba na hakika ba. Irin wannan yawo da hankali da jarumar tsohuwar ke ta yi masa da wadannan hannaye nata da kuma neman rikita shi da take neman yi ya sa Idrisu tunzura, ya girgiza takobinsa, sai ga takobin ya kara tsawo, girma da nauyi, ya tattakura ya auna tsakiyar jikinta ya kai sara. Aljana Bakayalu ta kauce, takobin Idrisu ya sari Kasa ta yadda saboda nauyi da kuma irin kaifin sarar sai da wurin ya zama wani dan madaidaicin rami da sai Kato ya tattakura sannan zai iya tsallakawa. Ita kuwa aljana sai ta rikide zuwa wata irin dabba mai tsananin ban tsoro, baka kuma Katuwa, kai ko a mafarki gama-garin mutum ya ga irin wannan dabba, to babu shakka zai zautu in ma bai bakunci lahira ba. Ta zaro harshenta wanda girmansa ya kai na wata Www.bankinhausanovels.com.ng babbar bishiya ta rika fyadawa tana kai wa Idrisu duka da shi, amma dokinsa Jagora ya rikKa zamewa da shi. Da a ce harshen nan ya taba shi, to babu ko tantama zai yi mugun jin jiki, in bai mutu ba ke nan. Da ta fahimci cewa Jagora yana ba da gagarumar gudummawa wurin ceton uban gidansa, sai ta nufe *“ shi, ta yarfo harshenta daidai Kafafuwansa da nufin sarKafesu, amma saboda kwarewarsa da kuma gane nufinta sai Jagora ya yi sama shi kuma harshen nata ya sauka a Rasa, kafin ta janye har ya dira Kasa, shi kuma Idrisu ya sa takobi ya datse harshen. Aljjana Bakayalu ta yi wata irin Kara, alamar cewata ~ ji zafi a jikinta, ai nan da nan ta rikide ta koma aljana sosai sai ga jini irin nasu na aljanu yana ta zuba daga bakinta, da Sarki Sham’una ya ga haka sai zuciyarsa ta harzuka ya yi kukan kura don fada wa Idrisu, amma kafin ya Karasa tuni Sarki Ifritu ya zabura ya tare shi, da suka hadu suka bangaji juna sai da kowannensu ya zube a Kasa saboda tsananin Karfinsu, sauran jarumai kuwa sai yaKi ya sake Barkewa. Karajin mazaje kake ji kamar aradu na fada wa manyan itatuwa da duwatsu, hayaki da wuta kuwa ba a magana, da ma yaKin aljanu sai su. Aljana Bakayalu wankin hula na nema ya kai ta dare game da al’amarin karonta da jarumi Idrisu dan Www.bankinhausanovels.com.ng hamidu. Yanzu kam ta fara tsorata da shi, saboda haka sai ta sake dabara, ta koma wata irin iskar goguwa mai tsananin Karfi ta yi ta zagaye shi, shi kuma Idrisu sai ya yi ta kai wa iskar sara ta duk inda ya ke zaton za ta ji a jikinta. Da dai ta ga wannan shawara ma ba za ta fitar da ita ba sai ta koma kamanninta na asali suka ci gaba da karawa. Da dai ta ji cewa lallai ta wahala sai ta tattakure da nufin yin wata irin rikida ta ko dai a mutu ko kuma a yi rai, wato rikidar da a zuciyarta ta tabbatar cewa ta karshe ke nan wadda kuma tana jin cewa ko birni ta yi wa wannan rikida tana iya halaka shi ballantana mutum daya. Wurin wannan rikida irin Karar da ta yi sai da kowa ya razana. Hankalin kowa ya koma kanta, wurin ya gauraye da wani irin hayaki mai kauri kuma jajawur, bayan hayakin ya wanye sai ga wani abu gangaram kamar tsauni, ga shi baki Kirin gwanin ban tsoro, sannan kuma ga shi yana ta motsawa, kai a wannan lokaci hatta Jagora sai da ya fara ja da baya saboda razana; abin da bai taba yi ba. Wadannan tsauni mai kama da dutse gadan-gadan ya daga sama ya nufo Idrisu da nufin murKushe shi. Jagora dai yana ta ja da baya shi kuma Idrisu yana zungurinsa da nufin Karfafa guiwa. Shi dai jarumin Www.bankinhausanovels.com.ng tun da wannan abu mai kamar dutse ya nufo shi babu abin da ya ke lura da shi sai wani abu dan madaidaici mai launin ja dake ta dan harbawa yana motsi a jikin tsaunin, saboda haka sai Idrisu ya yi zaton ko idon Bakayalun ke nan, saboda haka sai nan take ya warware mashinsa ya girgiza, ya auna shi ya saki. Ashe ba idonta ba ne, shi ya sa ma ba ta lura ta baude ba, zuciyarta ce! Mashi sai dada shiga ya ke yi yana Kara tsawo da fadi, ita kuwa sai mirginawa take tana ihu da kururuwa ta yadda har Idrisu sai da ya tsorata a lokacin, shi dai murnarsa yanzu kam ya tabbatar da cewa ya same ta a makasa. A Bangaren Sarki Sham’una kuwa a daidai wannan lokaci ga alama an sami gangara a kansa, don kuwa ga shi can yana ta kurmususu Sarki Ifritu ya kayar da shi kasa yana ta tiKkarsa da gwalmi. – ‘Tuni Bakayalu ta koma ainihin siffarta, ta faditana Karaji, sai ta yi yunKuri ta tashi da mashi a jikinta ta nufo Idrisu gadan-gadan tana kawo masa raruma da nufin a yi mutuwar kasko, shi kuma Idrisu ya fahimci nufinta, saboda haka sai ya kauce ya ba ta wuri, sannan ya sa takobinsa ya sare mata kafada, nan take ta durKushe, kuma kafin ta kai Kasa ya yi sauri ya sa hannu ya zare mashinsa daga jikinta. Zare mashin nan kawai irin Karar da ta yi kada ma Www.bankinhausanovels.com.ng mutum ya taba fatan jin makamancinsa, don ana iya kurumcewa. Tana fadowa Kasa sai ta kama da wuta, tana karaji da kururuwa har dai ta kammala Konewa. Sai ga tarin toka him. Wasu da yawa fa sai yaki ya dakata aka koma ana kallo, musamman wadanda suka fi kusa da wurin da abin ke faruwa. Wannan toka ta aljana Bakayalu sai ta shiga rikidewa tana musanya launi zuwa wata Katuwar macijiya baka, ga tsawo ga kauri, kanta jajawur, girmansa kamar kan jaki. Kunnuwan macijiyar har da wasu ‘yan kunne, jelarta kuma fari : fat. Wannan macijiya sai ta yi wani irin kuka kamar na dan jariri, sannan ta tashi sama ta fuskanci hanyar wasu manyan duwatsu guda uku da ke nan bayan duniya, ai nan take sai jarumi Idrisu dan Hamidu ya tuna jawabin da malaminsa Shaihi Ibrahim dan Yahaya ya taba yi masa a lokacin da ya ke bayani game da abin da da aka samu a cikin baKin littafin da ke dauke da sirrin rayuwar Sham’‘una da kakarsa, wato inda Shaihin ke cewa, “Ya kai Idrisu, ina so in jawo hankalinka game da wasu muhimman kalmomi wadanda ko ni yanzu ban san hakiKanin abin da suke nufi ba, sai dai in Allah Ya yi maka tsawon kwana ka kai lokaci da kuma Www.bankinhausanovels.com.ng yanayin, to za ka fi kowa fahimtar abin da ake nufi, wato wannan wurin da ke cewa, “Muddin ana so a kashe Sham’‘una, to sai an kashe kakarsa mai rayuka biyu, wato sai an kashe ta a gangar jiki sannan’a kashe ta a ruhi. Ruhin nata kuma ‘wata tirin hatsabibiyar macijiya ce mai mazauni a wani kogon dutsen da ke cikin manyan duwatsun bayan duniya. Kuskure ne babba a kashe ta ba acikin kogon dutsen ba. Da Idrisu ya kammala wannan tunanisai ya yi sauri ya sauka daga kan Jagora,. ya shimfida darduma ya haye ya tashi sama abinsa ya nufi wurin:da macijiyar nan ta fuskanta, ya ba ta ‘yar tazara yadda ma ba ta san yana biye da ita ba, suka’yi ta tafiya’a haka: “Tana isa wurin babban dutsen sai ta:shige cikin’ kogonsa abinta, shi ma bai yi wata-wata ba wurin aukawa, Shigarsa sai ya fahimci:cewa ashe cikin: wannan kogon dutse a nan wurin hutawar Bakayalu ya ke, nan ne kuma turken tsafinta ya ke, abin da‘ke cikin.sa na alatu::sai wanda ya gani,:‘kuma banda ita babu wanda ya taba shiga cikin sa, har shi Kansa Sham!’‘una din. Yana shiga sai ya ga wani-Katon gado ‘na zinare wanda aka yi wa ado da lu’ulu‘u;: babu: shakka. in banda aljani irinta babu wanda ya isa ya.mallaki irin wannan gado. A kan -wannan gado kuma ga Www.bankinhausanovels.com.ng macijiyar nan ta yi gammo ta fito da kanta sama tana kallon sa. Irin dadewar da Idrisu ya yi zaton za su yi suna marKabu da ita abin bai kai haka ba, watakila ko don ta rigaya ta gaji ne oho, don kuwa yana shiga zare da takobinsa a hannu daya, mashinsa kuma a daya hannun sai ya riKka nufar gadon a hankali. Macijiya ta yi masa dirar mikiya bakinta bude da nufin halaka shi, shi kuwa sai ya yi sauri ya cilla mashinsa cikin bakinta, a daidai lokacin da ya baude gefe guda, kuma kamar walKiya ya sa takobi ya raba tsakiyarta gida biyu. Nan take ta fadi ta yi wani irin ihu tana mai cewa, “Shi ke nan ka kashe ni.” Tana zubewa Kasa sai ga shi ta koma cikin cikakkiyar siffarta ta tsohuwar aljana Bakayalu. Ga ta nan an rabata biyu. Idrisu ya yi wa Allah godiya. Ya tattara gawarta ya zuba a kan dardumarsa ya yunkura ya koma can fagen fama inda ya bar mazaje suna fafatawa. Ya kuwa je a kan lokaci, wataKila ba don Allah Ya kawo shi a daidai lokacin ba, to da labari ya sha bamban. Abin nufi kuwa shi ne irin markabun da ya bar Sarki Sham’una da Ifritu suna yi, to yanzu sa’ar ta koma wurin Sham’una, yanzu har ya buga Sarki Ifritu da Kasa ya daga tasa kokarar zai kwankwatse masa kai. Www.bankinhausanovels.com.ng Shi dai Sham’‘una ya ji an buge shi ne kawai ya fadi gefe. Jarumi Idrisu ne ya yi amfani da gindin mashi ya bazar da shi, kuma kafin ya kammala mikewa sai ga gawar kakarsa an watsa masa a jiki, Idrisu ya ce masa, “Ga mushen kakarka nan, Allah Ya Kara mata azabar lahira, saura kai.” Rayuwa ta yi wa Sarkin aljanu Sham’‘una Kunci, zuciyarsa ta kumbura kamar za ta fashe, idanunsa suka firfito suka yi jajawur fiye da garwashin wuta, ya sake kallon gawar kakarsa, shugabar tsafinsu, sannan ya kalli talakawansa, ya tabbatar gara ya fafata ko da kuwa zai mutu ne da ya zauna cikin KasKanci, ya bude baki da Kakkarfar murya ya bai wa jarumansa umurni cewa, “Me kuke jira ne? ayi ta ta Kare, ko dai rai ko kuma mutuwa.” Yaki ya sake rincabewa, shi kuma Sham’una a tunzure ya nufo Idrisu kamar zai cinye shi danye. Ji kake tim, tititim. Fada tsakanin su ya kai wani yanayi da babu kyan gani. Bayan kamar kwana uku suna gwabzawa sai bege ya taso wa Idrisu, ya tuna da masoyiyarsa, ya kuma tuna cewa wannan aljani da suke bugawa yanzu shi ne babbar katangar da ke tsakaninsa da ganin ta ai sai wani irin Karfi ya sake shigar sa, ya sa gindin mashi ya banke Sham’‘una har Kasa, ya yi sauri ya sa takobi ya Www.bankinhausanovels.com.ng sare masa Kafa daya sannan ya ba da umurni ga Sarki Ifrita da wancan jarumin da a ba san shi ba a kan cewa su ma su ZO su more. Habawa, haka suka rufa suka yi ta jibga tare da tumurmusa Sham’una har sai da ya yi lilis, kai karshe dai ya some. Sarki Ifritu ya sa aka daure shi tamau da sarka suka sa shi cikin battar Karfen nan da ya taba kulle Ifritu a ciki. Ashe da ma suna tafiye da ita don tunanin yiwuwar samun irin wannan damar. Sauran mayakan Sham’una ganin yadda aka yi da shugabansu sai jikinsu ya yi sanyi, kuma ashe da ma su a al’adarsu in an kama shugaba, to fa babu sauran yaki, saboda haka duk sai suka watsar da makamansu danufin mikawuya. Abin da ya ba su mamaki sai suka ga bangaren su jarumi Idrisu ba Kokarin tozarta su suke yi ba, don kuwa ba a bi su an ci gaba da kisa ba irin yadda su suke yi, a’a sai suka ji an ce kowa ya dauki makaminsa atattaru wuri daya jarumi Idrisu zai yi jawabi. Dan Hamidu ya fara gode wa Allah da yin salati ga Manzon tsira, sannan sai ya yi wani dan takaitaccen jawabi yana mai cewa, “Ya ku taron jama’ar aljanu, yanzu dai yaki ya Kare, Sarki Sham’una yana hannu, kuma tsohuwar azzaluma Bakayalu tuni ta bakunci lahira, duk wannan ba don komai ba sai don tsananin Www.bankinhausanovels.com.ng zaluncinsu. . ‘Su ne suka jawo muku wahala. Suka gayyato muku yaki, suka jefa ku cikin hadari da kisa duk ba don wani abu da ya shafi kiyaye mutuncinku ba, a‘a sai dai don tsananin son zuciyarsu kawai Mun sani cewa biyayya ce da‘kuma cewa babu ‘yadda za ku yi don an fi Karfinku suka’sa kuka sallama musu rayukanku duk da cewa’ba wai sun Kyale ku ba ne da zalunci’da cutarwarsu.’Saboda‘haka ya ku *jama’ar wannan kasa ina bukatar‘ku sani cewa ba “ zalunci ya kawo mu ba, a’a adalci ne da kuma Kwatar ‘yancin wadanda aka dade ana zalunta,; wato a”yantar ‘da mutane da aljanu’’daga~ mulkin ‘kama-Karyar wadannan ‘yan tsiraru guda biyu. ‘ Sarkinku shi da”yan kanzaginsa sun‘dade’suna yi “wa matanku“da ‘matan ‘mutane«fyade; ‘‘suna’ ‘cin ” karensu babu’ babbaka.‘ Sham’una’ ya kamo ‘yaran + mutane mata-ya kai-su ‘can ‘Saman ‘tsibiti ‘ya kange. Saboda‘ me? : Ina’ sake’ ‘tambaya, ‘wai ‘shin da‘ wane dalili? Idrisu‘yana cikin wannan jawabi sai suka ji muryar ‘wata mace ‘tana ‘cewa, “Tabbas Wannan’ gaskiya‘ne, kuma babi karya cikin jawabin wannan saurayi dan -‘A’dam.” Sai ga’aljana Dailariu ta bayyana. Ganin ta sai jama’ar garinta gaba daya suka gaishe ta don da Www.bankinhausanovels.com.ng ma ita suna matukar kaunar ta, har zuci. Dailanu ta ce, “Ni ma shaida ce game da bayanan da wannan jarumi ke yi.” Ko gaisawa ba ta tsaya an yi ba ta umurci jaruman aljanu guda dari cewa su bi ta. Ba ta zame ko ina da su ba sai can tsibirin da su yarinya Nur suke, ta ce su jira ta za ta shiga ta fito, gidan take so za a dauka a kai can fagen da aka kammala yaki. Tun kafin ta shiga cikin gidan take ta rafka sallama, Kawayenta suka amsa mata cike da farin cikin sake ganin ta bayan tsawon lokacin da ta dauka rabuwarta dasu., Nur tace, “Ke kuwa baiwar Allah ai alkawari bai ce haka ba, yaya za’a yi tun da kika bar nan sai yanzu muke sake ganin fuskarki? Don Allah yau kwana nawa? Ko kuma dai’yi hakuri in tambaye ki, shin lafiya dai ko? Meke faruwa?”..dailanu ta’cé, “Ke rufa mini‘asiri, gudu na yi can “wani’wuri ina Boye wa‘kakata Bakayalu, don ta hakifance cewa tana gani na sai’kisa. Yanzu dai ba wannan labarin ba, maganar da ake ciki akwai aljanu dari a waje suna jiranmu, saboda haka sai ku shirya da Sauri zan-sa su dauke wannan gida mu gudu abinmu.” Jin wannan zance sai hankalin Nur ya tashi matuka, ta yi sauri ta tambaya, “Don Allah Dailanu babu Boye-Boye tsakanina da ke, fada mini me ya faru da masoyina Idrisu?” Dailanu ta ce, “Ke kwantar da hankalinki, zolayar ku nake yi, kuma babu wani abu mai muni da ya faru da shi sai alheri. A taKaice dai sai in ce albishirinku.” Gaba daya suka ce, “Goro, fari sal kuwa.” Sai Dailanu ta ce, “To a yau dai Allah Ya ba jarumin jarumai Idrisu dan Hamidu nasara a kan muguwar tsohuwa Bakayalu, yanzu ma maganar da ake yi tuni ta zama ‘yar gida a lahira, shi kuma wancan karen saurayin naku Sham’una yana can a hannu daure cikin sarKa.” Ai fa ‘yan mata sai rungume juna saboda irin wannan labari mai faranta zuciya, suka ciccibi Dailanu suka daga ta sama suna rera wata irin waka mai tausasa zuciya. Da suka sauke ta sai ta ce, “to yanzu ai sai mu yi harama, ni zan tafi, kuma aljanun da na ce muku yanzu za su dauki wannan gida don mu isa wurinsu Idrisu din.” Dailanu tana fita sai ta yi wa jama’arta nuni, ai nan da nan suka sungumi gida, tana gaba suna biye har tsakiyar dumbin aljanun nan da ke fagen fama sannan aka sauke shi. Aljana Dailanu ta shiga ciki, Www.bankinhausanovels.com.ng can bayan wani dan lokaci sai ga ‘yan matan nan gaba daya suna biye da ita. Wannan al’amari ya yi matukar bai wa jama’ar aljanu mamaki, suka Kara tantance cewa wato a banza ke nan Sham’una ke daukarsu tun da har ba zai iya soyayya da ‘ya’yansu mata ba sai dai na mutane. Ai nan fa suka yi ta tsine masa, kuma zaluncinsa ya Kara bayyana a gare su. Wasu daga cikin jama’ar da ke wurin sai suka yi ta cewa, “A fito mana da azzalumi, a fito mana da mugu.” Aka kuwa fito da shi daga cikin battar Karfe, daure cikin sarka. Wasu daga cikin ‘yan matan nan suna kuka haka suka rika tashi suna bayyana irin yadda Sham’una ya rabo su da gidajensu da masoyansu ya mayar da su Karkashinsa don fin Karfi. Bayan sun kammala, sai aljana Dailanu ta mike ta yi bayanin irin yadda ta hadu da wadannan ‘yan mata mutane, yadda ta taimaka musu da kuma sanar da taron nan cewa ita ce ta dauki bakin littafin da asirin rayuwar Sham’una da kakarsa Bakayalu ke ciki har zuwa dai irin wannan gagarumar nasara da aka samu. Sham’una da ke daure duk yana jin abubuwan da ke faruwa kuma yana kallo da idanunsa. Zuciyarsa ta Kuntata matuka, hankalinsa ya tashi musamman HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NGYARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA CHAPTER 27 KARSHE END BY HARUNA USMAN Www.bankinhausanovels.com.ng MUN TSAYA Dailanu tana fita sai ta yi wa jama’arta nuni, ai nan da nan suka sungumi gida, tana gaba suna biye har tsakiyar dumbin aljanun nan da ke fagen fama sannan aka sauke shi. Aljana Dailanu ta shiga ciki, Www.bankinhausanovels.com.ng can bayan wani dan lokaci sai ga ‘yan matan nan gaba daya suna biye da ita. Wannan al’amari ya yi matukar bai wa jama’ar aljanu mamaki, suka Kara tantance cewa wato a banza ke nan Sham’una ke daukarsu tun da har ba zai iya soyayya da ‘ya’yansu mata ba sai dai na mutane. Ai nan fa suka yi ta tsine masa, kuma zaluncinsa ya Kara bayyana a gare su. Wasu daga cikin jama’ar da ke wurin sai suka yi ta cewa, “A fito mana da azzalumi, a fito mana da mugu.” Aka kuwa fito da shi daga cikin battar Karfe, daure cikin sarka. Wasu daga cikin ‘yan matan nan suna kuka haka suka rika tashi suna bayyana irin yadda Sham’una ya rabo su da gidajensu da masoyansu ya mayar da su Karkashinsa don fin Karfi. Bayan sun kammala, sai aljana Dailanu ta mike ta yi bayanin irin yadda ta hadu da wadannan ‘yan mata mutane, yadda ta taimaka musu da kuma sanar da taron nan cewa ita ce ta dauki bakin littafin da asirin rayuwar Sham’una da kakarsa Bakayalu ke ciki har zuwa dai irin wannan gagarumar nasara da aka samu. Sham’una da ke daure duk yana jin abubuwan da ke faruwa kuma yana kallo da idanunsa. Zuciyarsa ta Kuntata matuka, hankalinsa ya tashi musamman ZAMU TASHI lokacin da suka hada ido da Dailanu, ya tuna irin, karfinsa da yadda ya karya mazaje da kumajnin yadda ake tsoron sa, sai ga shi wai shi ne yau kaskance ake tozartawa a gaban talakawansa da kuma yarinyar da ya fi so a rayuwarsa gaba daya, wato Nur, kuma sai ya tuna cewa wai duk wannan ‘yar’uwar tasa ce Dailanu sanadin wannan tozarci, ai sai ya yi wani irin kukan kura ya yunkura ya tsinka sarkar da aka,daure shi din ya nufo aljana Dailanu gadan-gadan da nufin daga yanzu ko bai sake samun nasarar komai ba, a rayuwarsa, to aKalla dai ya sami damar salwantar da ita. Ya kuwa yi nasarar kawowa har inda take, amma ya hadu da rashin sa’a, jarumi Idrisu ne ya girgiza mashi ya sakar masa a baya, wanda ya sa shi yin wata irin Kara mai ban tsoro, ya yi sama, kuma kafin ya fado. Idrisu ya sa takobi ya datse shi, shi kuma Sarki Ifritu yasa gwalminsa yabaramasakai, Irin wannan mummunan kisa da Sham’una ya samu ya sa jikin kowa a wurin ya sake yin sanyi. Aka yayyanka gawarsa gunduwa-gunduwa don samun saukin Konawa, aka kwashe tokar aka yi ta watsawa. a cikin teku ruwa na tafiya da ita. Aka dunguma gaba daya aka shiga cikin gari, jama’ar birnin cike da murna don duk da cewa an Www.bankinhausanovels.com.ng zo da yaqi an kuma shigo cikin garinsu, to amma kuma kamar ba a yi ba, don babu wanda zai hadu da wani kaskanci da a al,adance aka saba in irin hakan ta faru. Ko ba komai dai sun ci albarkacin ‘yar’uwarsu aljana Dailanu * Bayan komai ya natsa sai jarumi Idrisu ya ba jama’ar wannan birni shawara a kan cewa, ba zai yiwu su zauna haka babu shugaba ba, saboda haka wajib? ne su zabi wanda zdi jagorance su, amma wannan karon lallai ne su’zabi wanda suke jin zayyi musu adalci,ai sai duk taron ‘da ke wurin kamar sun hada baki suka ce su ba su da wanda ya wuce Dailanu, don kowa ya santa da adalci da mutunci da tausayi da kyauta da son jama‘a ko da wancan mulkin, saboda haka ita’ suka zaba’ a‘ matsayin Sarauniyarsu-, wannan abu yayi marukar faranta wa duk masoyan Dailanye rai, don Kawayenra mutane ma Barkewa da ‘wake-wake da rafka Bayan waurin yayi shiru sai Dailanu ta miqe don yin jawabi,-ta farada bismillah da kuma salati; abin da mutanenta basu. sani ba, sannan sai taci gaba da cewa“Yaku *yan‘uwana, na yi farin ciki da godiya da kuka nuna irin wannan Kauna da soyayya gare ni, ta yadda har kuke ganin cewa na cancanci in Www.bankinhausanovels.com.ng shugabance ku, sai dai kuma dole ne in ba ku hakuri don a zahirin gaskiya ba zan iya ba…” Ai ba ta kammala fadin abin da take nufi ba sai wurin ya yamutse da hayaniya kamar ana fada, suka harzuka a kan cewa sai dai in za ta tozarta su ne, amma abin da suka zartar ke nan. Dailanu ta ce, “To ku saurara.” Wuri kuwa yayi tsit. Sai ta ci gaba da cewa, “Ya ku jama’ata, ina da dalilai guda biyu masu Karfi da suka sa ni cewa ba zan karbi sarautarku ba. Na farko dai shi ne addinina da naku ba daya ba ne, yanzu ni Musulma ce, ku kuma kuna bauta wa rana da wuta, to yaya za a yi in mulke ku kuji dadi nima in ji dadi?” Sai wani aljani mai matsakaicin shekaru ya yi wuf ya mike, ya ce, “Ya ke Dailanu, ke din nan kin fi mu sanin wasu Ka’idoji na bautar rana da wuta, amma kuma kika yi watsi da addinin, kuma ke kanki kin san cewa ina daya daga cikin shugabannin bautar tamu, amma a zahirin gaskiya yanzu ni kaina na fahimci cewa bautar da muke ta banza ce mara tushe, saboda haka ni dai na yi amanna da addinin da kike kai.” Ai nan take dumbin jama’ar aljanun da ke wurin suka yi ta cewa sun yi imani da Musulunci kamar yadda Dailanu ta yi. Dailanu fa cike da murna da walwala ta ci gaba da Www.bankinhausanovels.com.ng jawabinta na murnar fitarsu daga kafirci, ta ce, “Sai dai kuma ba shiga cikin Musuluncin ba ne kawai, a’a akwai sauran aiki a gabanmu. Aikin kuwa shi ne, shi addinin Musulunci ba a yin sa da jahilci, kuma a Ka’idarsa ba a yin sa da cewa wai haka na ga wane yana yi, ko kuma haka ya dace da al’adarmu, ko kuma haka ya fi dacewa ayi, a’a. A Ka‘ida mutum ba shi da wata kirKira tasa sai dai abin da Allah da Ma’‘aikinSa suka koyar a yi ne kawai addini. Wato ba kamar tsohon addininmu ba da a kan Kirkiro sababbin dokoki ko kuma a yi musu gyaran fuska daga lokaci zuwa lokaci. Abin da nake nufi shi ne dole ne kowannenmu ya tashi ya nemi ilmi don da shi ne ake tauna gardin addinin tare da fahimtar inda aka sa gaba, kuma babu wanda zai taba zuwa ya iya sa ku musanya addininku, don za ku sami hujjojin da suka gagari dukkan wani abin halitta wanda kuma hakan ke nuna cewa ku ne ke kan hanya ta Kwarai, wato hanyar da Allah Mahaliccin komai Yake so. Amma fa matukKar kuka zauna babu ilmi, to shi ne zaayi ta muku yawo da hankali, ko a cikin addinin Musuluncin ma wancan ya ce muku kaza yau, gobe wancan ya ce ba haka ba.” Nan take wani dattijon aljani ya mike ya ce, “To Www.bankinhausanovels.com.ng Dailanu duk mun yarda, yaya za mu yi mu sami shi wannan ilmi?” Nan take Sarki Ifritu ya mike tsaye ya fuskanci wannan dattijo, sannan ya juya ya fuskanci sauran jama’a ya ce, “Ni, a maimakon jama’‘ata na ba ku gudummawar malamai dubu goma don su fara imantar da ku.” Aljana Dailanu kamar za ta daka tsalle don murna, ta kalli Sarki Ifritu ta ce, “Na gode, na gode, mun gode.” Kasancewar wancan dattijon aljani bai riga ya zauna ba sai shi ma ya ce, “A gaskiya mun gode Kwarai ya kai mai alfarma Sarki Ifritu. Sai dai kuma akwai wani abu da tun tuni ya dan dame mu game da ke ya ke shugabarmu Dailanu. A zahirin gaskiya muna ganin ba zai yiwu a ce Sarauniyarmu ba ta da miji ba.” Idrisu kuwa sai murmushi ya ke yi, Dailanu ta dukar da kai Kasa sannan ta dago ta ci gaba da bayani, “To da ma dalilai biyu ne na ce za su hana ni shugabantarku, na kawo na farko sai lamarin farin cikin Musuluntarku ya dauke mana hankali. Dalili na biyu shi ne, a dai dan karatun da na yi na addinin Islama ina fahimtar cewa Shari’a ta fi son shugabancin da namiji a kan jama’ar kasa fiye da shugabancin mace. Saboda haka abu daya zan iya yi, kamar yadda kuke so ni kuma yanzun nan zan fitar da miji, in har ya amince ya aure ni, to ni na yarda in zama Sarauniyarsa mai ba shi shawara, shi kuma ya zama Sarkinmu, amma fa in kun amince.” Jama’‘a suka ce sun amince don sun san ba Za ta cuce su ba. Dailanu ta waiwaya ta kalli Idrisu ta ce masa, “Ya kai jarumin jarumai, in ba ka manta ba lokacin da ka shigo cikin koriyar ciyawar nan, wato lokacin da ka shigo ‘yankin aljanu har kuka hadu da masoyiyarka Nur, na roke ka cewa ina son in Allah Ya ba mu nasafa akwai abin da nake so daga wurinka.” idrisu ya ce, “E Kwarai kuwa an yi haka.” Ya dubi yarinya Nur ya ce mata, “Ai ke ma kin tuna ko?” Nur ta amsa musu cewa, “Tabbas an yi haka. Amma dan dakata Kawata, kin san fa ba irin haka tsakaninmu, kada kuma ki ce shi kike so! Ko a ranar ma ina ce wasa kike yi.” Dailanu ta yi murmushi sannan ta ci gaba, “Ya kai Idrisu ba wani abu ne nake bukata ba face wannan doki naka ya zama mijina.” Mamaki ya rufe Idrisu, ya ce, “Dailanu ko ban ji abin da kika ce da kyau ba ne?” ‘Tace, “Kwarai kuwa ka ji da kyau, dokinka Jagora Www.bankinhausanovels.com.ng ne nake so ya zama mijin aurena, sai dai in ba ya so na.” Jama’a fa suka yi haja-haja ana neman karin bayani daga wurinta, ta yadda a matsayinta na Sarauniya take bukatar doki ya zama mijinta. Hatta kawayenta su Nur abin ya yi matukar kulle tunaninsu. Dailanu ta nuna Jagora dokin Idrisu da dan yatsanta ta ce, “Don Allah Jagora koma siffarka ta asali, yau ba ranar boye-boye ba ce, in ma kowa bai sani ba, to ninasani.” Abin mamaki sai ga Jagora ya rikide ya koma asalin siffarsa. Kuma ma babban abin mamaki sai kowa ya ga ashe kyakkyawan saurayin jarumin nan ne wanda ke ta taimakon su jarumi Idrisu da Sarki Ifritu tun daga birni na goma lokacin da Jagora ya fara rashin lafiya. Ashe dai shi ne Jagora, kuma duk lokacin da ba ya kusa da Idrisun rikidewa ya ke ya koma siffarsa ta asali. Kuma shi ne wanda ya zo da gudummawar dumbin jama’arsa lokacin da yaki ya yi Kamari sosai, kuma aka yi ta dauki-ba-dadi da shi har zuwa yanzu da aka yi nasara. Mutane da aljanun da ke wurin kowa ya yi shiru ana ta mamaki, shi kuwa Idrisu bude baki ya yi ya kasa cewa komai yana tunanin yadda hakan ta Www.bankinhausanovels.com.ng kasance. Jagora ya bude baki ya yi magana, ya ce, “Ya shugabana ina roKon kafin in shaida muku labarina, Dailanu ta fada mini yadda aka yi ta san sirrina yadda har ta gane cewa ni ba doki ba ne.” Kowa fa ya juya ya kalli Dailanu, ita kuwa sai ta ce masa, “Ka tuna ranar da na kai Kawata suka hadu da jarumi Idrisu a cikin gonakin Ifritu? To in ba ka manta ba kai kana can waje kana kiwo ni kuma da muka gama gaisawa sai na fito waje don in bar su su dan zanta, to ina cikin wasu ciyayi ina shakar Kanshinsu alhalin kai ba ka gani na, sai ka koma cikin siffarka ka je ka yi Sallar Azahar da La’’asar sannan ka sake komawa doki. Ni kuma tun daga ranar na ji babu namijin da nake so a duniya kamar ka.” Sai Idrisu ya kalli Jagora cikin murmushi ya ce, “To yallabai, kai muke saurara, ba mu labarin dalilin komawarka doki, domin dai ‘yar budurwar nan ta farke maka laya, ta bayyana maka yadda aka yi ta san ka.” Jagora ya gyara murya sannan ya ce, “Ya shugabana ka gafarce ni kafin in fara bayani, dole ne in yi wa Allah godiya da Ya sa na sami amsuwa a wurin wannan yarinya kyakkyawa mai hankali da tausayi da kulawa da addini. Wato tun lokacin da muke cikin Www.bankinhausanovels.com.ng dajin nan wurin malam mahaifin Nur kana daukar karatu, to ita ce kan zo ta kawo wa malam abinci, kuma takan zo daukar karatu duk ina ganin ta, kuma a duniyar nan na ji babu wadda nake bukatar aure kamarta. Ashe ita ma za ta kamu da so na.” Jarumi Idrisu ya katse shi, “Malam tun da dai ka sami karbuwa kar ka yi ta jan mu da nisa, mu dai ba mu labarin dalilin kasancewarka doki.” Jagora ya ce, “To, ya shugabana. Ni dai asalin sunana shi ne Ramalanu dan Rayalanu. Ni dan Sarkin aljanu ne na can Kasar Yamma, mu Musulmi ne, kuma dalilin zamana doki shi ne don in taimaka wa Idrisu ya sami saukin tafiyarsa zuwa nan ya yaki azzalumi Sham’una. Dalili kuwa shi ne, Sarkin aljanu Sham’una da ‘yan kanzaginsa sun daden gaske suna zaluntar mu kuma babu yadda za mu yi da su kasancewar sun fi mu Karfi nesa ba kusa ba. Haka kawai yakan shiga cikin Kasarmu ya kakkamo matasanmu ya tura su fagen fama su yi masa yaki, ko kuma a wasu lokuta su shiga shi da jama’arsa su sami ‘yan matanmu, kai wani lokaci ma har da matan aure su aikata mummunan aikin fyade da su. Irin wadannan ayyuka na zalunci da makamantansu sun dade suna aukuwa a cikinmu ta bangaren Sham’una. Www.bankinhausanovels.com.ng Maimakon abubuwa su yi sauki sai wani lamari ya faru wanda a wancan lokaci ya zama mummuna a garemu. Duk aljanin da ke bautar tsafin su Sham‘una a wancan lokaci ya san akwai wani aljani na hannun daman tsohuwa Bakayalu wanda ta amince wa Kwarai mai suna Ziri-muzi. To shi Allah Ya kaddara masa shiriya, saboda haka sai ya gudo kasarmu a matsayin hijira. To duk ba wannan ya fi dugunzuma wa aljana Bakayalu rai game da shi ba face lokacin da tsafinta ya nuna mata a wancan lokaci ta ga surar fuskarsa a jikin bakin littafin nan da sirrin rayuwarsu ke ciki, ta tabbarar cewa ya yi mata leKen asiri. Ta bugo tsafinta sai ta fahimci yana wurinmu, saboda haka ta umurci jikanta Sham’una ba tare da wani Kwakkwaran dalili ba ya je ya halaka shi kawai. Mahaifina shi ne Sarki, a lokacin da Sham’una ya shigo bai zame ko ina ba sai fadar garinmu, ya yi ta kisan aljanu, wanda hakan ya sa dole mahaifina ya ba da umurnin kariyar kai, shi ma ya fito aka gwabza wanda kuma ba a dauki wani lokaci mai tsawon gaske ba, musamman irin yadda suka duro mana babu shiri, suka sami galaba a kanmu. Sham’una ya sa hannu ya kashe mini mahaifi, sannan ya kashe duk wanda ke gidanmu. Ni kadai ne Karami Kwarai, watakila kuma bai lura da ni ba ne, amma a yanzu ma ina kallon lokacin, sannan sai lauma wani Kanin mahaifiyata da ba ya gari a lokacin da abin ya faru. A karshe dai suka ga wanda suka zo nema, a nan wurin Sham‘una ya tsire shi tare da fada masa cewa duk da cewa yana son sa, to amma babu makawa zai kashe shi don haka kakarsa Bakayalu ta ce a aikata. Sham‘una ya yanke kan ya je ya kai mata. Shi wancan aljani Ziri-muzi wanda Sham‘una ya kashe, a lokacin zaman da ya yi a garinmu ba shi da wani amini da malamin da ya wuce wancan kawu nawa da ba ya gari lokacin da Sham’una ya shigo ya yi kisan gillarsa. Lokacin da ya dawo sai ya dauke ni na girma a wurinsa yana koyar da ni ilmi da dabarun yeki. A kallum cikin zuciyata in na tuna lokacin da Sham‘una ya kashe mini mahaifi da *yan‘uwa da jama’‘a sai in ji babu abin da nake bukata ko da zan rasa raina ne face daukar fansa. Lokacin da na girma sai kawuna ya ce mini, “Yaro tun da yanzu ka kawo Karfi to abin da kake jira na daukar fansa ina ganin kamar ya kusa, don kuwa zaman da muka yi da Ziri-muzi ya taba bayyana mini sirrin kashe wannan mugun maKiyi namu Sham’una, wato abin da ya karanta a bakin littafin, kuma tun daga wancan lokaci na wajabta wa kaina gano inda ke da Korama da rijiya kusa da ita a cikin duniyar mutane. Na kuma dace, ko da yake wurin yana can cikin wani kungurmin daji ne mai wuyar shiga ga mutane, kuma wani abin mamaki shi ne ina kyautata zaton akwai wanda ke da irin wannan buri namu, don kuwa jiya da na kewaya na tarar da wasu dakuna guda biyu an kafa su a wurin, kuma na ga wani dattijo dan Adam, malami, wanda kuma ina kyautata zaton zai yi Kokarin tafiya ne shi kansa, saboda haka nake son ka zama doki mu san yadda za a yi tafiyar nan da kai, kasancewar irin wannan tafiya ba za ta yiwu ba sai a kan dokin aljanu. Ni kuma zan ta yi maka addu’a yadda zai yi wuyar gaske aljanu ma su iya tantance cewa kai ba doki ba ne.” Jagora ya ci gaba da ba da labarinsa cewa, “Sai nida kawuna muka mayar da wancan daji wurin zamanmu, muna lura da malamin nan mahaifin Nur, wani lokaci in zama doki din in rika zuwa kusa da shi ko zai yi kokarin mallakata amma shi sam sai na lura babu ruwansa da ni, saboda haka sai muka sake lura cewa ai ba ya zuba ruwa a cikin rijyar wanda hakan ya tabbatar mana cewa ba shi ne Zai yi tafiyar ba. Www.bankinhausanovels.com.ng Shaihi Ibrahim ya sha kallon irin artabun da nakan yi da manyan jaruman da wani lokaci hanya kan ratso da su ta dajin. Musamman in suka zo gadan-gadan suna son kama ni. Wata rana muna kan wata bishiya zaune sai muka hango maigidana Idrisu yana tafe shi kadai, sai kawuna ya ce min, “Ka kuwa san wani ikon Allah? Wancan saurayin ne nake ta gani a cikin mafarki cewa zai kashe Sham’‘una, kuma kai ne dokinsa, saboda haka yanzu sai ka yi sauri ka zama doki ka tare shi.” Shi ne na sauko na je na sa Kafata cikin wata sarkakiya har ma na ji rauni, shi kuma Idrisu ya zo ya taimaka mini ya yi jiyyata, ya sa mini sunan da na yi matukar Kauna, wato Jagora. Babu shakka Idrisu saurayi ne mai mutunci da tausayi, don tun daga wancan lokaci har zuwa yau din nan bai taba daga bulala ya buge niba. Wannan shi ne takaitaccen labarina.” AKA fara hada-hadar daurin aure tsakanin Jagora dokin Idrisu, wato Ramalanu dan Rayalanu da kuma Dailanu ‘yar Kailanu. Idrisu ne waliyin ango, shi kama Sarki Ifritu waliyin amarya, bisa amincewar Www.bankinhausanovels.com.ng sauran dangin ango da amarya da ke wurin. Jarumi Idrisu ya ce, “A matsayina na aboki kuma uban ango ina son don Allah a dan saurare ni don yanzu zan je in taho da sadakin wannan tsaleliyar budurwa da abokina ya samu.” Ya debi aljanu ya ce su biyo shi, shi kuma ya haye dardumarsa, bai zame ko ina ba sai cikin kogon nan da ya kashe Bakayalu, ya ce su ciccibo masa Katon gadon nan nata na alfarma, sannan duk wani abu mai daraja da ke wurin shi ma su dauko shi. Haka ko aka yi. Jama’‘a a filin daura aure kawai sai aka ga abu gingiringin haka tun daga cikin sama yana ta Kyalkyali. Idrisu ya ce, “Ga sadaki nan.” Murna wurin amarya da Kawayenta in aka ce zaa misalta sai abin ya zama Kauyanci. Aka dai daura aure, sannan aka tabbatar wa Jagora da sarautar wannan babban birni. Jama’‘ar garinsa suka ce su ma suna bukatar don Allah a je garinsu don tabbatar masa da sarautar mahaifinsa, wato a takaice dai Ramalanu Jagora ya zama Sarki a manyan Kasashe biyu na aljanu. Gaskiya an ragargaji buki da shagali yadda ya kamata. Www.bankinhausanovels.com.ng BAYAN an natsu sosai sai hankalin kowa ya koma zuwa garinsu. Aka yi shiri mai kyau na mayar da kowa gidansa tare da ya da zango a wasu muhimman wurare. An fara ne da garin Sarki Ifritu, sannan sai birnin Idris inda Sarki Abdurrahman ke mulki, wato tsohon garin Sarauniya Zinkadaziyya mai macizai, wanda a lokacin da aka je suka ji irin rugugin da ke sauka daga sama na jama‘ar aljanu da mutane da ke cikin tawagar sai suka rufe birninsu suka je masallaci suna ta neman kariyar Allah. Daya ke a bayan gari aka sauka sai Idrisu ya sa wani aljani ya dauke shi ya sauke shi cikin gari, ya same su a masallaci ya yi musu sallama, suna ganin sa farin ciki ya lulluBe su, ya tambaye su lafiya, suka ba shi labari, sai ya yi dariya ya ce wa Sarki Abdurrahman, “Ai baa san jarumi da tsoro ba.” ; Suka mika masa budurwarsa suka tashi suka Kara gaba, haka nan suka yi ta sauke ‘yan matan nan daya bayan daya a garuruwansu bayan an shiga an yi wa jama’‘arta bayanin yadda abubuwa suka faru. Duk tafiyar nan da ake yi ‘yan matan nan suna cikin wancan gida ne da Sham’‘una ya gina musu, a ciki ake ta karakaina da su. Duk yarinyar da aka sauke a garinsu sai a kawo dumbin dukiya ta zinare da lu’u’lu’u da yakutu da zabarjadi da sauransu a bata. Daga Karshe aka je aka sauke wa jarumi Idrisu wannan Kankararren gida a garinsu bayan daurin aurensa shi da masoyiyarsa Nur ‘yar babban Shehi Ibrahim. Murna wurin duk wadanda abin ya shafa ba ya misaltawa musamman ma iyayensu da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki. Babban abin sha’awa game da wadannan ‘yan’uwa da abokai da Kawaye shi ne yau wannan na garin wancan gobe wancan na wurin wannan. Babu yadda za a yi Dailanu da mijinta Ramalanu su yi wata uku ba su kai wa Idrisu da Nur ziyara ba, ko kuma wani gari inda Kawayensu suke. Ita kama Nur da mijintaa kai-a kai ba su yanke ziyara zuwa garin Bashari, Yahaya, Habu ko Abdurrahman ba. Haka suka kasance cikin jin dadi da farin ciki da Kauna har mai raba jin dadi kuma mai raba masoya ta zakke musu. MASHA ALLAH TO JAMA,A NAN MUKA KARKARE WANNAN KAYATACCEN LITTAFIN NA YAKI MAI SUNA YARINYA NUR DA SARKIN ALJANU SHAM’UNA PLEASE IDAN HAR KA KARANTA KIN KARANTA WANNAN LITTAFI KUMA KUNJI DADINSA KUYI COMMENTS A KASA HAKANNE ZAI BANI KARFIN GWIWAR SAKE NEMO MUKU WANI LITTAFIN NA YAKI MAI DAN KAREN DADI INAMA KOWA FATAN ALKHAIRI An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels