🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐 🪐🐦‍🔥 *MASARAUTA*🐦‍🔥🪐 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 BISMILLAHIRAHAMANIRAHIM. Book 1 Page 1 & 2 ........A babbar masarautar garin MAHAR,,,,wata matace ke gurfane tana naƙuda cikin mayuwacin hali, murƙususu takeyi sosai jini na fita abakinta da hancinta yayinda duka ilahirin jikinta ke karkarwa sabida azaba,,cikin ƙarfin hali Takoma rabka salati akarona ba'adadi tana faɗar "innalillahi wa'innailaihi raji'un Allah kabani cikawa da imani Allah kazama gatan kominene zan haifa aduniyarnan da batada tabbas gaya zeshigo cikin wani irin bahagon ahali me wuyar zama, ya Allah idan ba haihuwar kominene zanyiba Allah ka karɓi baƙoncinmu, ya Allah, tafaɗa cikin ɗan ɗaga murya mehaɗeda nishi lokaci ɗaya, sekuwa ga kan baby yafito tare da faɗowa gaba ɗaya. Baby na tsandara ihu jarinta nashigowa wannan doniyar mecikeda abubuwan al'ajabi da ruɗani,,,Itako wannan baiwar Allah na ɗaukar kallimar shahada ko ganin abinda tahaifa batayiba Allah ya karɓi abarsa😥 Murmushi matarda ke zaune agefenta tayi tana tauna bakinta cikin rashin imani tasaka hannu taɗauke babyn dake kwance cikin jini kana ta yanke mabiyuyarsa tare da saka ƙafa ta hankaɗe gawar uwar, kana tafito daga bedroom ɗin ɗauke da baby da aka haifa, wani tangamemen perlor tanufa inda tasamu wasu matasan maza zaune a perlor su biyu kowanne yana danna wayarsa, suna ganin fitowarta duk suka taso suna faɗar "yaya dai tahaihune? Suka tambaya ransu duk adagule.....wani kayataccen murmushi wannan dattijuwar tasaki kafin ta ɗago musu babyn data shigo dashi kana tabuɗe baki cikin farin ciki tace "tahaihu ga abinda ta haifa amma itakam ta gangara. Wani irin murmushi suka saki Lokaci ɗaya me ɗauke da tsantsan farin ciki kana suka ce anwuce da wannan babin...itama dattijuwar murmushin taƙara sakar musu kana tashiga faɗar "suwaiba suwaiba suwaiba kina inane wai? a'a.... dasauri subaiwa tashigo perlor tareda zubewa aƙasa tana faɗar "tuba nakeyi ranki yadaɗe ina bayine Amin aikin gafara, tafaɗa jikinta na rawa....tsaki wannan dattijuwar taja kana tace "gimbiya halima tahaihu yanzunan asanarwa jakadiya tagayawa memartaba abinda ta haifa yana cikin ƙoshin lafiya, sedai ita ɗin Allah ya karɓi abarsa....wani irin ɗagowa suwaiba tayi tana faɗar "innalillahi wa'innailaihi raji'un amma bata kalli fuskar wannan dattijuwar ba....cikin kuka tamiƙe domin isarda aiken da akamata, tana tafe tana kukan cikin baƙin cikin rasuwar wannan baiwar Allah, ɗaƙin jakadiya tanufa tare da isar mata da wannan mummunan saƙon,,,cikin tashin hankali jekadiya tanufi fada anan tasanarwa memartaba abinda ke faruwa a masarautar. Innalillahi wa'innailaihi raji'un shine kawai Kalimar dake tashi acikin fada, kafin kace me labarin mutuwar gimbiya halima dakuma haihuwarta ya gauraye ila ihirin wannan masa rautar dama garin MAHAR baki ɗaya. Cikin ƙanƙanin lokaci aka shirya kyakkyawan baby da aka haifa daganan aka shiga yiwa wannan gawa sutura akayi mata zana'iza tareda sadata da gidanta na gaskiya, batareda mijinta yasaniba. Bayan kwana uku da haihuwar wannan baby...atsakiyar dare naga wannan dattijuwar tsaye cikin ƙungurumin jeji daga ita se wani walki ɗaure a ƙugunta, cikin hargagi me masifar tsoron saurara wata mummunar halitta kemata magana kamar hakan. "Ba mutuwarta ce abin dubawaba rayuwar abinda ta haifa Shine tashin hankalinku domin kuwa idan abinda ta haifa yarayu tabbas zekawo ƙarshen duk wani azzalumi dake cikin masarautar ku idan kuwa ya mutu shine kwanciyar hankalinku mu itace muradinmu munsamu kukuwa abinda tahaifane abin harinku, dabara yana wurinku rayuwarshi kokuma mutuwarshi, daga hakan wannan mummunar halittar taɓace ɓat kamar bata wanzu awurinba....wani irin huci wannan dattijuwar keyi kafin tayi wata irin girgiza kawai seta ɓace itama. Kyakkyawar kulawa wannan baby kesamu agun duka mutanen masarautar masu son ubanshi dakuma margayiya gimbiya halima wato mahaifiyar tashi wannan babyn...hakama agun memartaba kullum seya saka aikai masa wannan baby yana kallonshi yana murmushi domin har cikin ranshi yakejin son babyn kamar yadda yakeson iyayenshi, dagashi har sauran yaranshi suna haba,haba da wannan haihuwar da waƴanda keyi har zuciyarsu dakuma waƴanda keyi iya fuska kawai.....wannan dattijuwar kuwa bayan tadawo cikin masarautar hankalinta yayi mummunan tashi tarasa yaya zatayi tunda ba itace ke kulada wannan babyn ba yana hannun suwaiba Amin tacciyar hadimar gimbiya halima to yaya zatayi takasheshi batareda suwaiba tasaniba? Dama ace tun ranarda akayi haihuwar ne dazata ahaɗa harshi takashe bawanda zeyi tunanin komai, amma ko yanzu bata ɓaceba zata bari se ranar suna takasheshi ta hanyar anfani da sarkin aska, da wannan shawarar tafita daga turakarta tanufi turakar memartaba. Daren suna dadare suwaiba tayiwa baby wanka tareda shirin bacci harzata kwantar dashi se wata hadimar tazo tace jekadiya tace takawowa memartaba babyn...subaiwa tace to taɗauko babyn takaiwa jekadiya ita kuwa takaiwa memartaba shi domin wani lokacin yakan ɓata dare agun sarkin, to yauma hakan abin yakasance domin har kusan ƙarfe 2 nadare baby na gum memartaba har bacci yaɗauke memartaba anan tare da baby....da asuba koda memartaba ya falka babu baby a inda yabarshi kwance, bekawo komai aranshiba sedai yayi mamakin Waze shigo har turakarshi yaduƙi babyn, sedai ƙila ɗaya daga cikin matanshine...da wannan tunanin yayi wanka tare da alwala yafito masallaci inda ya haɗu da Sarkin fada da galadima tare da zugar zaratan samarin ƴaƴan shi su biyar hadda mijin gimbiya halima daya dawo daga US acikin daren jiya shine yanzu aka fito masallaci dashi, dukkansu gaida mahaifin nasu sukayi, cikin Dattako yake ansa musu ɗaya bayan ɗaya yake kiran sunansu, "mubarak, Mansur Muneer, Abdullah dakuma jabeer, seda duk yakira sunansu kana yace "Abdullah yoshe kadawo? Jiya memartaba acikin darene shiyasa banje gunkaba, Abdullahi ɗin yafaɗa cikin ladabi...jinjina kai kawai yayi adede lokacinda suka ƙaraso cikin masallacin...suna shigowa aka tada sallar bayan an kammala suka fito ananne memartaba yaja Abdullah zuwa turakarshi domin ya fiso yasanardashi mutuwar matarshi da kanshi yadda ze kwantar mishi da hankali tun bekaiga tambayaba akagaya mishi kaitsaye,,,,, memartaba yajima yana jinjina zancen kafin yayi ƙarfin halin labartawa Abdullah abinda yafaru agidan na rasuwar gimbiya halima dakuma haihuwarta..."innalillahi wa'innailaihi raji'un faɗin tashin hankalin da Abdullah yashiga aciki ɓata lokacine, yajima yana jimami da kukan mutuwar matarshi da kyar memartaba ya lallaɓashi yayi shiru ananne ya ɓukaci ganin abinda aka haifa mishi.......acan cikin gida kuwa sosai hayaniya taɓarke taneman baby domin jekadiya taje ɗaukoshi a turakar memartaba bata ganshiba kuma tasan baze tafi dashi masallaci ba,,,gaya amduba ko ina agidan ba'aga baby ba, kuma kowanne pert adunba agidan bayanan kowa an tambaya be ganshiba....da labarin ɓatan wannan babyn yariski wannan dattijuwar ƙaramar hauka tayi tana faɗar sam bazeyiba sedai idan wani ya muna fumcesu yaɓoyeshi amma bazeyu a ajiye jinjirar baby ace ya ɓataba,,,wannan borin da dattijuwar keyi shine yaƙara ɗaga hankalin mutanen gidan...........acan turakar memartaba kuwa yana neman Akira jekadiya takawowa Abdullah babyn segaya mubarak yashigo turakar arikice yana sanarwa da memartaba ɓatan wannan baby daya cika kwanaki bakwai yau aduniya....tashin hankali kenan wanda ba'asaka mishi rana, wata irin zabura sukayi atare daga memartaba Sarki habibullah har ɗanshi Abdullah sabida jin mugun shuck ɗin wannan mummunan labari,,,atake Abdullah yazube awurin somamme, innalillahi wa'innailaihi raji'un doline Abdullah yasuma samun labarin mutuwar mata dakuma ɓatan baby ɗan kwana bakwai aduniya duka Lokaci ɗaya 😥 rigi rigin yowa kanshi sukayi daga memartaba har mubarak suka dagoshi atare suna kiran sunanshi cikin mugun tashin hankali dakuma fargaba. Tofa 🤔 waye yasace wannan jinjirin domin idan na fahimta Dede ba wannan dattijuwar bace data kashe mahaifiyarshi kuma take neman rayuwarshi Ayanzu wanine daban ya ɗauke shi, tirƙishi lallai wannan abun akwai ruɗani acikinshi... Bayan wasu shekaru. Adamawa state acikin wata rugar Fulani dake cikin garin mayebalwa...wata kyakkyawar yarinya ce ketafiya da ƴar tsumagiyarta ahannu tafiya takeyi cikin nutsuwa kallo ɗaya zaka mata kaga tsintsar nutsuwa da kamala irinta yarinta atareda ita duka shekarun yarinyar baze wuce 15 ba aduniya sedai tanada cikar halittar irinta manyan mata kuma nagano hakanne sana diyyar kayan fulanine ajikinta faffaɗan ƙugunta me tudu da faɗi yabaje ɗass acikin zannen datake daure dashi, gashin kanta kuwa yazubo har gadon bayanta sabida irin kitson bararone akanta.. ahankali nadubi fuskarta, wayyoo Allah seda nakusan zaujewa sabida tsananin kyawunta me ɗaukar hankali haƙaƙa wannan yarinya kyakkyawa ce takarshe tanada manyan lulu eyes kamar bana mutaneba masu ɗaukeda eyeball lite blue masu haske da sheƙi, ga siririn dogon hanci kamar na turawa, gawani gashin gira daya ƙara ƙawata fuskarta kamar zehaɗe wuri ɗaya, eyelashes ɗinta kuwa zara zara kamar taɗora wasu akan nata, gata da ɗan ƙaramin baki kamar bakin asusu, lips ɗinta jajir dasu sekace janbaki tashafa, duk inda ake neman kyakkyawa idan akazo gum wannan yarinyar tofa ankai ƙarshe, domin kyawunta zefi kace mata aljana domin bazaka kirata mutunba kaitsaye sedai idan kasanta.....tafiyarta takeyi ahankali hartazo bakin wata ƙatuwar bishiyar lemu tatsaya tana waige waige jin ana kiran sunanta ahankali,,,wani sassanyan murmushi tasaki wanda yaƙara fitoda asalin kyawunta cikin shagwaɓa tabuɗe baki ahankali dawani irin sihirtaccen voice tace "pappi, tana turo ɗan ƙaramin bakinta gaba....wanda takira da pappi na kallah Senaga ashe wani kyakkyawan matashin saurayi ne me matuƙar kyau da ɗaukar hankali wanda bazaka iya banbance tsakanin shi da wannan mubudurwar wayafi wani kyau ba, shima Murmushi yayi kafin yace.....! Autar alheri ✍️ 🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐 🪐🐦‍🔥 *MASAURATA*🐦‍🔥🪐 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 3 & 4 "Yace na'am ƙanwar pappi kuma ƴar lelen pappi y akayine? Yafaɗa yana murmushi. Baki taɗan tura gaba kana tace "shine jiya kaƙi zuwa ko? Bayan nashirya inata jiranka. "Ayya sorry ƙanwata yanzu ai gani ko? "Eh ta'ama fuskarta ɗauke da far'a kana tace "pappi kasan me wai jiya da hamma Ishaq yazo gidanmu shine wai inna kecewamishi yadena kulani Ni jahilace karna shafa mishi jahilci, shikuwa bece mata Komaiba tunda yasan tahana baffa yasakani a makarantar da zenu keyi ina zaune kawai agida..daze tafine yakirani waje wai nayi haƙuri ko inna tace Dani jahila zezo daga ɓoye yakaini makarantar,,,to kawai nace mishi inata kallonshi har yatafi senayi dariya araina nace ai itadake cemun jahila itace jahila tunda pappi na yakoyamin kowanne karatu nayi sauka kuma na iya boko sabida hakan tayita faɗa ko pappi? Taƙarasa bashi labarin dasigar tambaya... ɗan gajeren murmushi yayi wanda bayayinshi sedai idan yana tare da ita kana ya ɗage mata gira ɗaya kafin yace "of course my little sister she's very talented. "Yeah my lovely pappi, tafaɗa cikeda murna yana saka yatsarta Dede inda ya Lotsa agefen kumatunshi (demple) shima murmushi kawai yake yi amma na gefen baki. Pappi zansha sweet irinna ranar daka bani wanda kani last time beyi daɗin shi ba, ta faɗa cikin shagwaɓa..."okay muje musiyo kawai yace mata yanayi gaba abinshi...da sauri tabi bayanshi sukaci gaba da tafiya sunyi tafiya me ɗan tsayi lafin se tsallake wani ɗan rami dake gefen hanya, segasu awani haɗaɗɗen wuri me kyau da kayatarwa ga fararen fata nayawo tako ina kamar ba'a Nigeria sukeba kumawai duk acikin rugar Fulani,,,wani ƙaton moll suka shiga inda naɗaga kaina ina kallon rubutun dake kan Sible ɗin dake saman wurin ido nazaro cikin mugun mamaki ganin anrubuta *S S AMERICA* damanyan haruffa, kenan ina nufin nan AMERICA ne ko mihakan kenufi? Bangama tunani nashiga bin mutanen dake harabar tangamemen wurin da kallo, dukkansu farar fatane babu baƙar fata ko ɗaya gakuma gininsu me tsayi sosai da tsari wanda sam babu irinshi Aduk faɗin Nigeria balle acikin rugar Fulani 🤔to kenan wannan budurwar da saurayin nan datake kirada pappi suwaye anya mutanene kuwa?😱 Inacan duniyar tunani naga sunfito hannunta riƙeda leda babba me kyaun gaske suna shirin barin wurin aicin sauri na mara musu baya domin idan sukabarni anan nakaɗe🙆 tafiya suƙarayi ba sosaiba daganan kuma suka ƙara tsallaka wannan ɗan ramin nagefen hanya segasu acikin wannan rugar kamar dai yadda suka fita a ɗazu,,,,inda suka fara fira anan suka tsaya kana pappi yayi mata sallama yace taje gida anjima zezo,,,,,hakan wannan budurwar tabi hanya hankali kwance cikin tafiyarta me jan hankalin duk wani me kallonta cikin nutsuwa da kamala, tunda taɗaga daga gun pappi tahaɗe rai tamau kamar batasan minene dariyaba kana tanufi gidansu. Tun asoron gidan takejin bala'in innawuro cikin tijara take surfa masifa kamar zata ari abakin aku, ƙara haɗe fuska takarayi kana takutsa kai cikin gidan tareda yin sallama ciki ciki..wani irin zaburowa innawuro tayi tareda farmata da duka kamar tasamu jaka masifa takeyi tana faɗar "daga gidan ubanwa kike Allah yau sena kasheki agidannan *DANEJO* Nizaki shanya ina jiranki kiyi surfe amma kika saka ƙafa kikabar gidannan dan bakida mutunci shegiya aljanar banza aljanar wofi, yau senaga wanda yatsaya miki a rugarnan, sosai take kirɓar DANEJO kamar Allah ya aikota. Dagudu hamma Ishaq yaƙaraso cikin gidan jin DANEJO na ihun neman ceto domin yadda innawuro ke dukanta tabbas zaka ɗauka dagaske kashe tan takesonyi, cikin tashin hankali yake ƙoƙarin karɓarta daga hannun innawuro yana faɗar "haba inna dan Allah kidena karki jimata jiyo bazata iya ɗaukar wannan dukanba mitamiki hakan? Yatambaya adede lokacinda yafincike DANEJO daga hannun innawuro wadda ke haki kamar tayi dambe da sa'arta, cikin baƙar zuciya irinta Fulani tayo kan hamma Ishaq domin shima tafarmasa da dukan sabida yana tausayin danejo cikin tsawa baffa dake shigowa yace "dakata wuro karki kuskura kitaɓamin yaro miyayi miki zaki dakeshi? Arazane tajiyo domin tana mugun tsoron baffa cikin makirci ta ƙaƙaro kukan kissa tana faɗar"wlh barni na dakeshi mlm yo inba rashin imaniba mi wannan yarinyar tayi mishi daze kamata yana mata dukan ƙarti difa kaga yadda yayi mata sekace yasamu jaka, taƙarasa zancen tana share ƙwallah da haɓar zanenta. Sororo hamma Ishaq da danejo sukayi suna kallonta dudda cewar ba yau ne nafarko dasuke ganin makircin innawuro ba amma na yau kan yabasu mamaki matuƙa....kafeta baffa yayi da ido naɗan lokaci kafin yariƙo hannun danejo kawai suka nufi ɗan ƙaramin dakinsu itada zenu, shikuwa hamma Ishaq kayanda tashigo dasu hannunta ne yashiga tattara mata domin daga ganin wannan tarkacen kayan zaƙin yasan natane, yana gama tattarawa innawuro tayi zarab tawarcesu tana bankamai harara tashige ɗakibta. Masauratar MAHAR Atsiyace motocin ke darzar kwalta kamar zasu tashi sama, kafin sukaiga shiga masauratar tasu....wasu samari ne dake tsaye gefen hanya sukabi motocin da kallo kafin ɗaya daga cikinsu yace "kai jama'a ji yadda suke gudu akan kwalta kamar sukaɗaine masu ita wannan irin abu har ina? Da mamaki ɗayan yace "kai ai wannan ƙaramin aikinshine muddin yashigo gari domin daganin wannan gudun shine sabida baya tafiyar hankali akan atiti. "Waye wannan? Ɗayan yasake tambaya. "Au baka saniba? Humm *YARIMA SAMEER* kenan bakaga ga sunanshi nan ajikin nomber motarba *PRINCE S 1* da 2,3 har ƙarshen motocinshi. Dagacan gefen sukaji wani nafaɗar "babban gwaro kenan yashigo gari fari me farar aniya bangon sukari ba'ajigineka atashi abanzaba, yafaɗa cikin so da ƙaunar yariman kamar yana gaban idonshi hakan yake doka mishi kirari,,, murmushi sukayi atare kana sukaci gaba da abinda ke gabansu. Dagudun gaske motocin ketafe akan doguwar kwaltar dazata sadasu da pert ɗin kakanni nasu, wato matan takawa, suna ƙarasawa bakin ƙofar sashe suka tsaya kamar waƴanda ake bawa umurni, kusan minti 30 da tsayuwarsu kana wani dogari yafito cikin sauri yabuɗe ƙofar ɗaya motar wadda tafi kowacce kyau da ɗaukar hankali...cikin izza da mulki wanda ke nuni da jinin sarauta na yawo ajikin kowaye zefito daga cikin motar yaziro kafarshi ɗaya aƙasa....! Autar alheri ✍️ 🪐🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥🪐 🪐🐦‍🔥 *MASARAUTA*🐦‍🔥🪐 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 5 & 6 "Kusan minti 5 baya kafin yasake zuro ɗayar kana yafito gabaki ɗayanshi, wow watafarakallah bi'ahasanilhaliqeen, tabbas tsarki ya tabbata agun uban gijin talikai wanda ya ƙagi kyau yakuma ƙagi muni, haƙiƙa wannan bawa kyakkyawan mutunne mafi kyawo acikin masu kyau cikakken namiji ƙaƙƙarfa mecikar zati dakamala, wannan guy ɗin yanada kyau wanda bazan iya misilta muku shiba, farine tass afatarshi sedai lallausar suma tayiwa Fatar tashi ƙawa yadda tabi ilahirin jikinshi takwanta lubb baƙa wulik da ita, yanada dogon hanci sosai gakuma manyan idanuwa alumshe kamar na yan maye masu launin ruwan madara, eyes Ball ɗinshi kaɗai abin kallo ne, yanada wani irin baki wanda ko acikin farar fata wato turawa bakowane keda irinshiba domin bakin ƙarami ne sosai sedai lips ɗin nashine abin kallah domin kuwa daga ƙasan zagayen kowanne lips nasama dana ƙasa red ne sosai sedai daga cikin lips ɗin wato tsakiyarsu pink calor ne irin me walwali ɗinnan, bakin nashi yabada wata kalar daban, yanada kyakkyawan saje wanda ya ajiye iya kunnenshi bezagaye fuskarshi dukaba, kana ya ajiye zagayayyen gemu irinna gayu me kyau da tsari yasha gyara iya gyara abin se wanda yagani. Wannan matashin saurayin yawuce duk yadda zakuyi tunaninshi, sa'annan kallo ɗaya zaka mishi kaga yadda zallar mulki da sarauta keyawo ajinin jikinshi bugu daƙari Miskilanci ya haɗe da jinin mulki se yaya kenan 🤔 YARIMA SAMEER M HABIBULLAH MAHAR ƊAN FARI AGUN ALHAJI MUNEER HABIBULLAH MAHAR, JIKA AGUN SARKI MUHAMMAD HABIBULLAH MAHAR, MATASHIN SAURAYI MEJIDA IZZA DA KUƊI GAKUMA JININ MULKI DAKE YAWO AJININ JIKINSHI. Ahankali yashiga tako ɗaya bayan ɗaya cikin izza da mulki dogarai natake mai baya har yaƙarasa cikin babban parlor daze sadashi da kowanne sashen na matan sarki habibullah, ɓangaren dama yanufa inda ze sadashi da pert ɗin mebabban daki wato uwar gidan memartaba kenan dattijuwar tsohuwa me dattako da jijidai gakuma tujara domin bata ɗaukar reni, yana isa bakin ƙofar parlor ta dogaran suka tsaya abakin ƙofar shikuwa yaƙarasa ciki,,,,,zaune yasameta akan kilisa kuyangi kusan huɗu sun zagayeta suna mata tausa wasu na yanka mata kayan marmari Dasauri hadima uwani tarussuna tana faɗar "lale marhabin da yariman mahar ɗan zakin zakuna jikan sarki giwa me tafiyar ƙasaita ko acikin dawa se,anraɓe, bangon sugari kowa yaraɓe seya lasa, sannun dai da sarkin gobe. "Hannu yaɗaga mata alokacinda yake zama ƙasan kafafunta mebabban ɗaki domin Allah yasani shi bayason wannan ihun dasukeyi idan sun ganshi acewarshi, humm aiko doli ka haƙura yallaɓai tunda kafito a jinin sarauta 🤷 Ahankali mebabban ɗaki tamiƙe zaune kana tadafa kanshi, "sannu dazuwa yarima sameer sannunka da dawowa cikin mahaifarka ina Fatar wannan lokacin zaka ɗan jima muna anan kafin kakoma domin yadace kaɗan fahimci wani abun acikin sha'anin mulkin garinnan. Taƙarasa zancen fuskarta ɗauke da murmushi.....shirune yabiyo baya dudda yaji abinda tace kusan minti 15 kafin yabuɗe baki daƙyar kamar bayaso yace "ina fatar nasamu uwar gidan Muhammad habibullah lafiya, mebabban dakin masauratar mahar. Ɗan shiru yaƙarayi kana yace "banajin zan jima mebabban daki domin wani aikin kawai zanyi nakoma, yafaɗa kamar bayaso..tunda yafara magana nakebinshi da kallo domin kuwa yadda yake juya bakinshi yana fidda haruffa ɗaya bayan ɗaya abin gwanin sha'awa gawani irin sihirtaccen daɗi dake fita a sassanyar muryashi kamar ana busa sarewa. Murmushi me babban ɗaki tayi kana tace "dudda hakan inason ganin yarima sameer acikin yan uwanshi kamar yadda nasan suma suna buƙatarka atare dasu, gakuma abbanka kullun zancenshi kaine Indai mutum naso yaga far'a a fuskarshi to yazo masa da labari me daɗi akan ɗan lelenshi, shin kodan Abdullah bazaka zauna nawani ɗan lokaci ba. Taƙarasa zancen tana kallon jikan nata. Shikuwa shiru yayi bece komaiba se lumshe kyawawan idanuwanshi dayayi yanajin yadda zuciyarshi ke dokawa tabbas yasan abbanshi nasonshi fiyeda komai aduniya kuma shima yana sonshi amma bayajin ze iya zaman masarautar tasu mecikeda abubuwan bantsoro da ruɗani. Kusan minti 30 yakwashe a pert ɗin me babba ɗaki batareda yace mata komaiba...itama bata ƙarayimai maganaba domin tasan iya wannan dasukayi idan zasu kwana ahakan baze ƙara cewa komaiba, wannan halin nashi kuwa baƙaramin ƙonawa wasu daga cikin family nasu rai yakeyiba domin idan kana taredashi ze iya mako ɗaya bakinka danashi be haɗu ba koda kai kemishi maganar balle kace jirakakeyi yayima. Bayan yafito daga part ɗin me babba ɗaki yasake shiga motocinshi suka nufi ɓangaren yamma ɓangaren gidan ƴaƴan sarki habibullah wato iyayenshi. Wani tangameme parlor yashiga inda yasamu wata mata hakince akan ɗaya daga cikin manyan kujerin parlor hadimai kusan Shida nagefenta kowacce da abinda takeyi....suna ganinshi suka Miƙe dasauri suna kwasar gaisuwa sukabar pert ɗin...cikin tafiyarshi me ɗauke da ƙasaita yaƙarasa gun matar kyakkyawar mace masha allah, yana zuwa ya russuna agabanta tareda kawo fuskarshi dedetata ya manna mata kiss agoshi da gefen kumatunta kana ya rungumeta ajikinshi yana sauke ajiyar zuciya...wani ƙaya taccen murmushi taƙara saki tana shafa bayanshi ahankali kana tace "sannu dazuwa Muhammad sameer ka zo lpy? Tunda tafara magana yake lumshe ido yana sakin ajiyar zuciya kafin yasamu zarafin buɗe bakinshi daƙyar yace "lpy qalau mammi, ina Fatar nasameki lafiya. "Lpy qalau Muhammad kowa yana lafiya ƴan uwanka nacikin kaɗaicin rashinka ko ɗazu ameer da anwar dasukazo yin lunch se da sukayi zancen dawowarka nasan baka gaya musu zuwanka ba ko? Tatanbaya tana shafa kanshi...bece komaiba kusan minti 5 kafin yamiƙe kawai yanufi matakalar benen dake parlor cikin tafiyarshi me ɗauke da izzar mulkinshi...da kallon sha'awa mammi tabishi harya ɓacewa ganinta kafin tasauke ajiyar zuciya tanajin son ɗan nata harcikin ɓargon jikinta.....! Autar alheri ✍️ 🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥 🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 7 & 8 "Ajiyar zuciya taƙara saukewa akaro na biyu tareda ɗauke idonta daga wurinda ya wuce kana tamiƙe zuwa wani bedroom dake nan ƙasa.....shikuwa yana hawa saman tun a parlor yafara cire tsadadden agogon hannunshi, yana shiga bedroom ɗin yaƙarasa cire kayan jikinshi gaba ɗaya kana yafaɗa bathroom wanka yayi tareda brush sa'annan ya ɗauro alwala yafito sanyeda rigar wanka, mirro yanufa tareda janyo kujera yazauna, hakan yariƙa ɗibar mayuka kala,kala yana shafawa ajikinshi kowanne pert danashi kamar wata mace, yaɓata kusan minti 15 awurin kafin yamiƙe yasaka kayanshi inda yasaka farar riga da farin wando 3kwata, kana yafeshe jikinshi dawani mayen turare me masifar daɗin shaƙa, seda yagama duk abinda yakeda buƙata kana yaɗauki wayoyinshi yanufi parlor cikin tafiyarshi me ɗauke da ƙasaita...yana fitowa parlor yayi arba da ameer zaune akan ɗaya daga cikin kujerun parlor yana danna wayarshi, yanajin motsin fitowar yarima Sameer yamiƙe dasauri yazo yarungumeshi yana faɗar "I miss you so much my bro saukar yoshe bako sanarwa? Se yanzu mammi takirani tana sanarmin zuwanka, yaƙarasa zancen yana ɗan sakinshi daga rungumar dayayi mishi...kallon Ameer yayi da shanyanyin idanuwanshi kana yaɗan shafa sajenshi batareda yace komaiba yariƙo hannun shi suka zauna, kusan minti 5 bece komaiba, ganin hakan yasa ameer cigaba dayi masa fira domin yasan tabbas bazeyi maganaba tunda har yazauna beyiba, sunjima ahakan ameer ne keta famar surutunshi, sedai idan yafaɗi wani abin yaɗago kawai ya kalleshi wani kuma yalumshe idonshi shine kawai amsar, suna nan zaune aka kira sallar la'asar hakan yasa duk suka Miƙe domin zuwa masallaci bayan ameer yayi alwala anan cikin bathroom ɗin dake parlor kana suka nufi masallacin. Maye balwa Tunda baffa yakai danejo dakinsu take kwance tana rawar ɗari domin lokaci ɗaya zazzaɓi mezafi yarufeta, wasu irin zafafan hawayene kezuba a idonta tana tunanin se yoshene zataji daɗin zaman gidansu kamar kowanne yaro? Mitayiwa innawuro datake tsagwamarta hakan? Miyasa bata yiwa yarta zainab Hakan se ita? Tabbas badan da tana yimata kallon mahaifiyaba data nuna mata ko ita wacece,,,Da wannan tunanin datakeyi bacci yayi awun gaba da ita. ba ita tafarka ba se kusan magarib koda tatashi tasamu leda ajiye agefenta dawasu kayan aciki, ɗauka tayi tabuɗe domin tayi tunanin kayantane da pappi yasiya mata sedai tana dubawa taga wasu daban irin wanda ake sedawa ako ina kamar irin alawar da ake rabo gun biki, ƙwallar idonta tashare tanajin son hamma Ishaq har cikin ranta domin kobata tambayaba tasan shine kawai ze yi mata wannan aiki,,,,miƙewa tayi taje tayi alwala tayi sallar magarib bayan ta idarne taji innawuro nadoka mata kira kamar zata tada gidan... miƙewa tayi ahankali tafito sabida jikinta dake mata mugun ciwo sakamakon dukan datasha agun innawuro. Tana fitowa taga innawuro na Banka mata harara kafin ta jeho mata wata koɗiɗɗiyar hamsin tace maza taje tasiyo mata ashana da maganin sauro. Faɗuwa gaban danejo yayi sabida aduniya ta tsani a turata wurin bala siyen wani abun gaya wurin danisa sosai kuma dare yayi, tanacan duniyar tunani taji saukar ruwan randa ajikinta hakan yasa numfashinta ɗaukewa naɗan lokaci kafin kuma tajashi da ƙarfi yadawo sabida mugun sanyin ruwan gaya kuma lokacin hunturu abinka ga rugar Fulani, hawayene suka cika idon danejo kafin taɗauki kuɗin jikinta na karkarwa tafice daga gidan kamar zata kifa, ga sanyin gari gana ruwan da innawuro ta watsa mata gakuma zazzafan zazzaɓin dake tareda ita duk se abin yataru ya haɗe mata wuri ɗaya. Tafiya kaɗan tayi tawuce gidansu tazo gunda babu mutane sosai taji sassanyar muryashi yana faɗar "HUSNAH ina zakije hakan? Dasauri tajiyo tayi ido huɗu da kyakkyawar fuskarshi yana kallonta da shanyanyin idanuwanshi, wani irin kukane taji yazo mata wanda yasakata nufarshi dasauri tarungumeshi tana rushewada matsanancin kukan...shiru yayi yana saurarenta hartayi me isarta batareda yadakatarda itaba, seda yaji ta tsagaita ne yaɗagota tareda share mata hawayenta kana yace "muje asiyo abinda aka aikeki, yafaɗa tareda riƙe hannunta...batace komaiba tabi bayanshi domin tasan koda maganar tayi baze tanka mataba, tafiya sukayi kaɗan segasu awani tangamemen shago me ɗaukeda tambarin Englan seety, shiga ciki sukayi kana yasiya mata wasu kayan maƙulashe waƴanda sukafi naɗazu kana yaɗauko mata wani kalar maganin sauro me kyau da faɗi shima kunnashi akeyi da ashana kamar namu, sedai ba irinshi bane amma azagaye yake kamar wancan sedai yafishi girma kuma shi kalarshi daban. Riƙo hannunta yayi suka dawo adede inda suka tsaya ɗazu yabata maganin sauron sauran kayan kuma yace taje zekai mata. Baki taɓare zatayi mishi taɓara yaɗaga mata hannu yana murmushi, hakan yasa dole tawuce tana waiwayenshi harta ɓacewa ganinshi....shikuwa be ɗaga ba seda yaga tashiga gida kana yajuya afusace yabar wurin kamar zetashi sama. Da sallama danejo tashigo gidan a tsorace sedai tasauke ajiyar zuciya yafi goma ganin baffa zaune tareda hamma Ishaq suna fira...cikin sauri taƙaraso tana miƙawa innawuro aikenta tareda takewa Zenu ƙafa ganin tana harararta,,,aiko tabuga ihu tana miƙewa tsaye...duk kallonta su baffa sukayi ana tambayar lafiya? Amma takasa cewa komai dudda cewar tanason faɗar abinda danejo tayi mata amma harshenta yaƙi ko motsawa. Ganin taƙi Magana ne yasa hamma Ishaq daka mata tsawa hakan yasa dole takoma tazauna tana fatan gari yawaye tahaɗa danejo da innarta domin tasan itadai bata isa ta tunkari danejo dasunsn rigimaba. Sunjima awajen zaune suna fira amma Banda danejo data shige dakinsu tunɗazu takuwa samu kayanta da pappi yasiya mata sunma rigata zuwa, murmushi tayi wanda yaƙara fotoda asalin kyawunta kana tabuɗe abinta tasomaci harta ƙoshi kana ta lunke sauran ta ajiye, tayi kwanciyar ta bayan tayi sallar isha...tana anan kwance takejin faɗan innawuro akan maganin sauron data siyo mata wai bata taɓa ganin irinshiba, setazo tamaida, seda baffa ya tsawatar mata tukkunna tayi shiru, shikuwa hamma Ishaq yayi ficewarshi daga gidan yana addu'ar Allah ya shirya innar tasu.....hakan suka ɓata lokaci suna fira kala tanajin maganarsu har bacci ya ɗauketa,,,can cikin dare bayan kowa yayi bacci dare yaraba sosai, tafara jiyo ihun mutun sama,sama cikin azaba ana neman ɗauki,,,azabure tamiƙe zaune ta kalli Zenu dake kwance tana baccinta hankali kwance, kana tasake kallon ƙofa jin wannan ihun na ƙaruwa, seda takasa kunne sosai kana nagano innawuro ce ke ihun mamaki tayi sosai amma bata fitaba tayi kwanciyata sedai aranta tana mamakin abinda innawuro take yiwa ihu cikin dare.....ita kuwa innawuro ihu takeyi tana neman ɗauki amma babu ko wanda yamotsa balle atemaketa har baffa dake kwance cikin ɗakin nata, gaya se dukanta akeyi tako ina duk an farfasa mata jiki kamar dukan ƙato goma bataga me dukan nataba kawai saukar bulolin takeji kamar za'a tsaga mata fata, amma sam bawanda yasan anayi domin duk ihun datakeyi bamejinta balle ba'asin temakonta......! Autar alheri ✍️ 🐦‍🔥🪐 *AL' AJABIN*🪐🐦‍🔥 🐦‍🔥🪐 *MASARAUTA*🪐🐦‍🔥 🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Daga💪Alƙalamin👇🪸🪸🪸🪸🪸🪸 Dr Yasmeen Ahmad😚 Autar alheri ✍️ Al'ajabi, hummm Book ɗin al'ajabi wani sabon kabcene me matuƙar al'ajabi da ban mamaki, kabcene wanda ya banbanta da sauran books na masu ban al'ajabi kamar irinsu ( MEJO NAJEEB,,, SOLDIERS FAMILY,,,,IZZAR MULKI,,, JEJI GIRL,) inaga sune Books masu ɗauke da abin al'ajabi to wannan kabcen dabanne sam ba irinsu bane, idan kuna so kukashe ƙwarƙwatar karatu to kigarzayo domin samun damar karanta book ɗin AL'AJABI. ROMANTIC LOVE STORY 💋 KAMAR YADDA AKA SABA HUMMM MY LOVELY SISTERS ABUNFA BA'A MAGANA KAWAI MUTSUNDUMA ACIKIN WANNAN LABARI ME TAKEN AL'AJABI 💃 Book 1 Page 9 & 10 "Seda tadaku iya dakuwa domin seda aka farfasa mata jiki tukkunna akabarta batareda tasan me duka nataba, hakan innawuro takwana awahalece daƙyar taga wayewar gari dudda sallar asuba yau kam bata samuba, dagari yawayene baffa yadawo daga masallaci yanufi ɗakinta da mamakin rashin ganinta yau a harabar gidan tunda sassafe. Sedai ayadda yaganta kwance magashiyan ya tabbatar mishi dacewar batada lpy ne. "wuro miyake damunki? Yatanbaya yana ɗan taɓa jikinta, sedai beji komaiba. Itako cikin ƙarfin hali tamiƙe zaune tana cije baki sedai duk yadda taso tagayawa baffa abinda yafaru da ita cikin dare kasawa tayi domin bakinta yayi mata nauyi, kuma duk inda yafashe ajikinta har yana fidda jini yanzu babushi yaɓace ɓat kamar befashe ba, sedai tsamin kawai dajikinta kemata. Daƙyar ta iya cewa baffa "bakomai jikinane kawai keciwo. "Ash'shakuwa tashi kiyi salla to bara nasamo maki magani cikin fadama, yana gama faɗar hakan yafice daga ɗakin...hakan ta yunƙura daƙyar taje tayi alwala tadawo zuciyarta fal fargabar abinda yafaru da ita a daren jiya. Yau dai hakan innawuro tawuni kamar wadda kawai yafashewa aciki hakan yasa danejo samun kanta agidan domin me takurata batada wata damar yin hakan yanzu sabida fargaba tagama nuƙurƙusar zuciyarta MASARAUTAR MAHAR tafiya sukeyi ahankali cikin izza da isa irinta ƴaƴan sarauta bayi nazubewa suna kwasar gaisuwa, Hakan suka nufi wani pert megirma da tsaruwa wanda yafi kowanne pert dake cikin masarautar girma da tsaruwa. Sarkin ƙofa dake tsaye suna fira dawani dogarine yahangosu tafe cikin sauri yace "ina zuwa lawwali barana sanarda zuwan yarima sameer agun memartaba kafin ya iso, yana gama faɗar hakan yajuya zuwa cikin gidan kamar zekifa domin yasan tabbas yarima sameer baze jira yayimasa isoba sabida bayason jira hasalima baya jiran kowashi sedai ajirashi, idan kuma ya shiga batareda yasanarda zuwanshiba yasan Fulani huraira baƙyaleshi zatayiba hakama Fulani abu, garama me babban ɗaki idan itace aciki bata damuwa. Yana zuwa yazube yana faɗar"Allah yaƙarama nasara da nisan kwana su yarima sameer ne keneman iso shigowa gun adilin sarki. Murmushi memartaba yasaki wanda yafito tun daga zuciyarshi, amma beyi maganaba se Fulani huraira ce tace "kace suna neman iso shida waye? "Yallaɓai ameer ne da anwar, yabata amsa cikin ladabi da ƙasƙantarda kai. Yatsina fuska tayi zatayi magana kenan suka shigo cikin parlor na memartaba, kowan'nensu da sallama ɗauke abakinshi. Amma tasu anwar kawai akeji dominshi gogan acikin ranshi yayi. Cikin ɓacin rai Fulani huraira tace "wannan wanne irin rashin ɗa'a ne? kunnemi iso bazaku jira abaku izinin shigowa ba zaku faɗowa mutane kamar wasu dawaki....Ɗaga kai kawai anwar yayi yakalleta amma bece komaiba,, yayinda Ameer yace "haba matar waike abin faɗa baya miki kaɗan? Yanzu miye laifinmu dazaki alaƙantamu da dawaki? Koda yake kekanki kinsan ingarman mazaje ne agabanki dole idonki surufe kice mana dawaki tunda munfi wannan tsohon mijin naki ƙarfi, yaƙarasa zancen nashi cikin tsokana, domin ameer duk afisu barkwanci. Baki tamere tana faɗar "wacece matar taka? Humm wlh gama tallabe dai kakeyi kayi ɗana aikin banza yara se shegen tsaurin idon masifa. Shidai memartaba bece musu komaiba domin ko lokacinda sarkin ƙofa yazo neman ison ya tabbatar ba Muhammad sameer ne yabuƙaci hakanba domin yasan halin kayanshi. Adan gajiye yamiƙe daga zaunen dayake yana sauraren shirmen Fulani huraira acewarshi, yaƙarasa gun kakan nashi tareda ranƙwafawa yarungumeshi yana sakin ajiyar zuciya domin aduk faɗin duniya agun mutun ukku kawai yake samun wannan nutsuwar idan yaraɓesu, abbanshi mammi sekuma memartaba.... murmushi memartaba yaƙara saki yana shafa bayanshi cikin kalama da dattako yake faɗar "lale da mutun ƙasar jajayen mutane laleda sarkin MAHAR nagobe lale da sanyin idaniyar Abdullah, ina farin cikin dawowarka mahaifarka adede wannan lokacin danake shirinyin murabus domin inaso nabawa duk wanda zuciyarka ta aminta dashi acikin iyayenka riƙon mulkin MAHAR kafin lokacinda shekarunka zasukai yabaka sarautarka domin kuwa tabbas mulkin garin MAHAR nakane YARIMA SAMEER M HABIBULLAH. Yaƙarasa zancen nashi da ɗan kirari wa jikan nashi. Murmushi duka su ameer sukayi amma Banda Fulani huraira dataji kalaman memartaba tamkar saukar ruwan darma azuciyarta. Shikuwa daƙyar iya buɗe bakinshi cikin wani irin cool voice yace "I miss you meran ƙarfe ina fatar nasami haske MAHAR cikin ƙoshin lafiya, yafaɗa abisa dole danson kaucewa wancan zancen da SARKI HABIBULLAH kemishi wanda sam baya buƙatar jinshi....sarai memartaba yaganoshi amma bece mishi komaiba domin yasan dama ba lallai ne yatanka mishiba sabida ba yau ne karo na farko daya fara yimishi irin wannan zancenba sedai betaɓa bashi amsa ko ɗaya ba akan kala manshi, dama koyanzu yayine domin yana kwaɗayin jin sassanyar muryar jikan nashi wanda yakeda tabbacin badan yayi wannan zancenba to har subar wurin baze taɓa buɗe bakinshi ba balle wata kalima tafito daga cikinshi. Sunjima awajen memartaba kafin suka bar pert ɗin suka nufi na sauran iyayen nasu, ko inna sunje daga ƙarshe suka yada zango agun umman ameer wato Hajiya Hafsah wadda suke kira da umma, mace me mutunci dasanin darajar ɗan Adam anan sukaci abici kuma basubar pert ɗinta ba seda zasuje masallaci bayan sun fito daga masallaci ne suka koma pert ɗin mammi mahaifiyar yarima sameer, suna shiga suka sameta zaune itada abbey suna fira, zubewa sukeyi aƙasa suna gaisarda iyayen nasu cikin girmamawa bayan sun amsa abbey ya kalli anwar yace "yaran abbey yanzu kam ganinku bazeyi wahalaba tunda ɗan uwanka yazo ko, yaƙarasa zancen yana kallon ameer. Murmushi duka sukayi kansu aƙasa domin abbey nada tsokana amma baya ɗaukar wargi kuma hukunci ɗaya yakeyi,, hakama magana ɗaya yakeyi akan komai, kuma bayason musu ko jayya, wannan shine tsarinshi..cikin girmamawa Ameer yace "habadai abbey ai mune zamu faɗi Hakan domin fa kullun Anan muke breakfast hakama lunch, da dinner amma Bama ganinka ko mammi? Yaƙarasa yaƙarsa zancen nashi yana tambayar mammi.. murmushi tayi mesauti kana tace "rabudashi yarona dankarku tuhumeshine shiyasa yarigaku.."eyee shigar musuma zakiyi? Humm yayi Miki kyau, Cewar abbey yana sakin murmushi..kafin ya Gyara zama kana yace "Muhammad tunda Allah yayi kazo to gobe idan Allah yakaimu seku shirya zuwa taraba domin kudubo aikin da abbanka keyi acan kafin kawuceko. Kanshi aƙasa ya amsa da "okey abbey, kamar bayaso kana yamiƙe zuwa pert ɗinshi, suma duk miƙewa sukayi sunabin bayanshi domin sunsan sameer bayason tafiyar mota amma kuma wannan dolice dubada umurnin abbey ne kuma aikin abbanshi ne, sedai sunsan zasusha tsaki kam kafin suje sudawo damma baya magana ne da sesun gajida mita😂.....! Autar alheri ✍️