An dauko wannan littafi daga shafin https://gistrog.com.ng ku ziyarci shafin na https://gistrog.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348141702912 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://gistrog.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348141702912 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://gistrog.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.gistrog.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/SuleimanUsmanKurya Twitter : https://twitter.com/Kuryaloaded_Ng Telegram : https://t.me/+Um7CIRmWSIU2NTg8 ο»Ώ[9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* PAGE 1 Wata matashiyar buduruwa na hango a zaune akan tabarma,tana ta guga,dagani kayan mijinta take gogewa Muhibba kenan,wacce bata fi wata Biyar da aure ba,gidanta madaidaicin gida ne,dan wanda take aure ba mai k'arfi bane,Palo d'aya ne da d'akuna biyu,sai kitchen da toilet,Mijinta Abdulmajeed Mallamin Makarantar primary school ne,dai dai gwargwado suna cikin rufin asirin Allah,auren soyayya suka yi,Muhibba tana da kirki sosai ga kyauta,tsafta awajenta ba a magana,Dan inka shiga gidanta kamar karka fito sabida kamshi da tsafta da gidanta ke dashi,kayan mijinta data wanke take gogewa taji ana kwankwasa gidan,d'aga murya tayi tace "Waye"? Ji tayi an k'ara kwankwasa wa batare da anyi magana ba,mik'ewa tayi ta nufi k'ofar Dan taga wa ke kwankwasawa,doguwar Riga ce a jikinta tayi parking ba dankwalli akanta,daga bayan k'ofar ta Dan tsaya ta bud'e k'ofar tana leko da kai Dan taga waye, wani irin fad'uwa gabanta yayi jikinta ya d'au rawa sakamakon tozali da tayi da wata farar mata mai tsayi,idonta manya manya girmansu ya wuce misali,tsayinta ma yayi yawa, farinta wani irin d'aukar ido ya ringayi,gashin girar ta jajaye,haka ma leb'enta,murmushi wanan matar tayi mata tace"kiyi hakuri na zo na takuraki da kwankwasa k'ofa Dan Allah fitsari ne ya matseni shine nakeso ki taimaka min inyi dan bansan kowa anan ba," Muhibba tunda tafara magana gabanta ya tsananta fad'uwa ta kuma kasa addu'a dan matar yanayinta abar tsoro,Dan zata iya cewa tunda take ba ta tab'a ganin mai irin tsayinta ba,d'aurewa tayi tace cikin rawar baki " lah bakomai shigo kiyi" da sauri matar ta shiga ciki,ta tsaya atsakar gida,Muhibba kuwa kamar tabar gidan da gudu Dan wani irin tsoro ne ya rufeta,gashi tana so tayi addua ta kasa,d'aurewa tayi ta shiga tayi hanyar da band'akin yake tace mata "bismillah ga band'akin akwai ruwa aciki" gani tayi matar ta nufo ta kamar ba tafiya take ba turota ake, ware ido tayi tana kallonta cikin tsananin tsoro da tashin hankali,dasauri tabi k'afarta da kallo taga babu alamar k'afa illa ma doguwar Riga dake jikinta kawai dake Jan kasa,jikinta ne ya d'au rawa kafin tayi yunkurin yin wani Abu wuf matar ta shige band'aki ta rufo k'ofar,"innalillahi wa inna ilaihi rajiun" muhibba tace cikin tsananin tsoro da fad'uwar gaba hanyar waje tayi da sauri taje ta tsaya daga bakin k'ofar tana kallon band'akin shiru shiru matan nan bata fito ba,tsoro ne ya k'ara rufe Muhibba ta d'aga murya tace " Baiwar Allah har yanzu baki gama ba" shiru taji,ba ayi magana ba,hakan ne yasa tayi waje da gudu ta nufi gidan dake kallon gidanta,gidan surayya makociyarta ce suna mutunci sosai da ita,bubuga gidan taringayi da sauri tana kallon gidanta,Surayya kin bud'e k'ofar tayi sai data ce "Muhibba kin tabbata kece"? " nice mana yi sauri ki bud'e min"bud'ewa Surayya tayi ahankali ta leko da kanta itama kana ganinta kasan a firgice take,da sauri Muhibba ta shige kafin tayi magana surayya tace " kema kinganta ko" ? Cikin tsananin tsoro Muhibba tace wacece"? Cikin sauri tace " bakiga wata farar mata mai kama da aljana ba,gidan nan tazo wai na taimaka mata fitsari takeji tuni na rufo k'ofata dan wlh baki ganta ba kamar ba mutum ba" tunda surayya tafara magana jikin Muhibba yafara rawa gabanta in banda fad'uwa babu abinda yakeyi d'aurewa tayi tace " Innalillahi wa inna ilahi rajiun Surayya na shiga uku na lalace,wlh tazo gidana tunda ta shiga band'aki taki fitowa har yanzu, nashiga ukuna DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO zan janyo wa kaina balai Dan Allah zoki rakani inga mai take yi a band'aki tunda zu,Wani irin tsalle surayya ta buga tayi gefe tace " wa tab bazan iya rakaki ba,wane tsautsayine ya kai ki kika barta ta shigar miki gida,wlh wanan da gani ba mutum bace Aljana ce," ai tun kafin Surayya ta rufe bakinta,Muhibba ta d'ora hannu aka taringa kuka tana ta shiga uku ta lalace " Yanzu surayya ya zanyi wlh tana cikin band'aki har yanzu bata fito ba," sallati Surayya tayi tasa hijabinta tace "muje in rakaki Allah yasa ba aljana bace. [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* PAGE 2 Rik'e hanun juna sukayi suka nufi gidan gabansu in banda fad'uwa babu abinda yake,Dan Muhibba har wani gumi take,suna zuwa k'ofar gidan,Surayya tayi sauri ta koma bayan muhibba,muhibba ita kuma taja da baya da sauri ta juyo tana kallon surayya "Haba Dan Allah surayya mai yasa kike min haka ne ko bazaki rakani bane"? Muhibba tace cikin rawar baki dan kiris take jira ta zuba aguje sabida tsananin tsoro,Surayya cewa tayi " kijiki da wani zance in bazan rakaki ba zan biyoki ne,kawai dai tsoro nakeji dan wlh Matan nan dak'yar in ba aljana bace kinga tsayinta kuwa",katseta Muhibba tayi da sauri tana k'ara ja da baya tace "haba Surayya ya kike kuma tsoratamu Dan Allah muje ki rakani insha Allahu ba aljana bace,muyi addua kafin mushiga ciki," na yarda zamu shiga ciki amma ke zakiyi gaba in biki abaya, Surayya tace tana k'ara lab'ewa abayan Muhibba,hanunta Muhibba ta rik'e gam, suka fara adduoi sai sun je zasu shiga sai su dawo aguje,sai da sukayi haka sau uku ana hud'u Muhibba ta d'aure suka shiga gidan,a bakin k'ofa suka tsaya suna kallon band'akin,yana nan arufe kamar yanda yake,cikin tsananin tsoro Muhibba tace " baiwar Allah Dan Allah ki fito har yanzu baki gama bane karki cuceni DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KA miki" motsi suka jiyo daga band'akin sukayi waje dagudu, Surayya kuwa cikin kiftawar ido ta shige gidanta tana k'ok'arin rufo k'ofa Muhibba ce tayi saurin shigewa tace " Surayya wai mai haka ne mai yasa Kika gudu kika barni ai da kin tsaya munga fitowarta inkece kinsan bazan miki haka ba ko" d'aga wuya Surayya tayi tana kallo k'ofar gidan Muhibba tace "kiyi hak'uri Muhibba wlh tunda naga wanan matar na rasa nutsuwata,wlh wani irin tsoro nakeji kinga bari mu samu namiji ya shiga ya dubo mana ita" kuka Muhibba ta fashe dashi tana " innalillahi wa inna ilahi rajiun nashiga uku ni Ummi( sunan da iyayenta suke kiranta dashi) DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO na janyowa kaina masifa," tsayuwar lifan a k'ofar gidan Surayyan ne ya katse mata maganar da takeyi,Ayuba mijin Surayya ne ya dawo,da sauri Surayya tayi waje ta gayawa Mijinta abinda ya faru sallati yayi ya kalli Muhibba dake tsaye abakin k'ofa tana ta kuka,tambayarta yayi yanda akayi,ta kuma bashi labarin abinda ya faru, addu'a yayi aransa yace su biyoshi abaya,tsoron da sukeji ya d'an ragu sakamakon sun samu mai taimaka musu,Muhibba tana daga bayansa Surayya kuma tana daga bayanta ahaka suka shiga gidan,Band'akin ta nuna mishi ya nufi band'akin yana addu'a su kuma suka tsaya daga bakin k'ofa suna kallon band'akin,in banda fad'uwa babu abinda gaban muhibba keyi,"Auzibikalimati tamaaaβ€’β€’β€’β€’β€’β€’ Ayuba ya karanta har karshe ya tura k'ofar ahankali tura k'ofar yayi gabad'aya yaga ba kowa,juyowa yayi ya kalli su Muhibba dake Neman sakin Fitsari a wando sabida tsananin tsoro,durk'ushewa tayi a lokacin data ga ba kowa a band'akin kuka ta fashe dashi tana nuna band'akin " Wlh Aljana ce ta shiga band'akin nan,ta ina ta fita,oooo ni Ummi DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO na Janyo wa kaina" Mijin Surayya rufo k'ofar band'akin yayi,yayi hanyar waje, suka bishi dasauri,Dan Surayya har tayi gaba,Ayuba tsayawa yayi yacewa Muhibba "ki kwantar da hankalinki babu kowa a gidanki watak'ila ma idonki ne yake gane miki kinga wata ta shiga band'akinki" dasauri Surayya ta katse shi tana "Wlh Ayuba Aljanace Nima naganta da idona Dan gidana tafara zuwa,Ina ganinta na rufe k'ofata Dan wlh Baka ganta ba kana ganinta kasan ba mutum bace,bansan tsautsayin daya sa Muhibba ta barta ta shigar mata gida ba"jikin Ayuban ne yayi sanyi daya ji abinda Surayya tace, Muhibba kuwa ta k'ara rushewa da kuka tana " Allah yasani TπŸ…°IMπŸ…°KONTπŸ…° nayi bansan Aljana bace ni yanzu mai zancewa Abdul,gashi ya kusa dawowa ko girki ban d'ora ba" Ayuba kwantar mata da hankali yafa yi yana "karki damu muhibba ai Allah yaga zuciyarki TπŸ…°IMπŸ…°KO kika yi niyyar yi,Insha Allahu Allah bazai bata ikon cutar dake ba",juyawa yayi ya kalli Surayya dake zare ido yace mata "jeki rakata ta d'ora abincin lokaci na tafiya,", da sauri Surayya taja da baya "Ayuba wlh ni tsoro nakeji Dan baka ga matar bane" wani kallo ya watsa mata taja bakinta tayi shiru,"wuce ki rakata bana San shashanci ke kin isa ki ga aljana da idonki" "Nima fa ban d'ora girki ba" "eee wuce kije zan d'ora mana ai Nima na iya girkin" Ayuba yace yana janyo hanunta,Muhibba ita dai tana tsaye,tana kallonsu,a zuciyarya kuma tana tunanin yanda zata kwashe da Abdulmajeed Dan yana da tsatsauran raayi Dan yasha yi mata warning akan kwashe kwashe,Dan lokacin da take amarya yaran makota haka suke cika mata gida,ita kuwa dayake ba ruwanta murna takeyi ta Shiga tsakiyarsu suyi ta hira sai da Abdulmajeed ya taka mata birki tukuna,dan ko kawayenta daina zuwa gidanta sukayi Dan sunce Mijinta baya San mutane,Yanzu idan ya dawo ta bashi labarin abinda yafaru batasan wane irin mataki zai d'auka akanta ba,"ki wuce mu tafi ki d'ora girkin" Surayya tace a lokacin da ta tsaya a gefen Muhibba,gaba Muhibba tayi Surayya ta bita abaya,sai da tafara lek'a band'akin taga a rufe yake tayi sauri ta shiga gidan,tana addu'a k ayan data goge tafara kwashewa ta kai d'aki ta nad'e tabarmar data shimfid'a tasa abayan k'ofa,ta rufo d'akin,Kitchen ta shiga da sauri ta kunna risho ta d'ora ruwa,duk abinda ta keyi idonta na kan band'akin Surayya dake tsaye abakin k'ofa itama band'akin take kallo Dan jira take taji motsi ta d'iba aguje,Muhibba ruwan da ta d'ora ko zafi bai yi ba ta wanke shinkafa ta zuba,Dan gabad'aya a tsorace take,Allahn daya taimaketa tun safe tayi miyarta,Salad da tumatir ta d'auko Dan ta yanka,Surayya motsi taji asaman kwanun gidan tayi waje da gudu,Muhibba wurgi tayi da wuk'a da salad d'in Hanunta itama tayi waje da gudu,atsakar gida ta Tarar da Surayya tana maida numfashi Ayuba dake k'ok'arin d'ora musu jellof d'in taliya na tambayarta mai ya faru,ce mishi tayi motsi taji asaman kwanu,tsaki yayi yace ta wuce su koma Muhibba ta gama girkin,k'in tafiya tayi atakaice sai da Ayuba ya rakasu ya tsaya abakin k'ofa,Muhibba tasamu ta gama abincin,aranar Dan turaren data ke yiwa gidan bata samu tayi ba,ballantana azo ga wankan da takeyi tayi kwalliya ta jira dawowar Abdulmajeed kamar yanda ta saba,gidan ta kulle bayan ta gama abincin ta tafi gidan Surayya Dan ta jira dawowar Abdulmajeed Dan bazata iya zama a gidan it a kad'ai ba, Dan taga alamar Surayya a takure take. Ana kiraye kirayen Sallahr Magriba Abdulmajeed ya dawo,Muhibba fitowa tayi daga gidan Surayya Dan tagane k'arar Lifan d'inshi,binta yayi da kallo a lokacin daya ke sauk'owa daga lifan d'in,had'e rai yayi yace " ke kuma mai kike jeyi a gidan mutane da magriban nan,share tambayar daya yi mata tayi tace " Sannu da zuwa" "tambayarki nake mai kika je yi agidan mutane da magriban nan kinsan na hanaki shige shigen nan banaso," itama had'e rai tayi tace " yanzun nan fa na shiga gidan abinci na kai mata dan batajin dadi" tsaki yayi yace "uwar San gwaninta ni bud'e min k'ofa na Shiga da machine d'ina,nufar k'ofar tayi gabanta na fad'uwa sai addu'oi takeyi a zuciyarta,Shigar da lifan d'in yayi ta bishi abaya,sai da yayi parking a tsakar gida,ya nufi inda generator yake ya tayar,Muhibba tunda suka shigo ta tsaya daga bakin k'ofa tana kallon Band'akin Dan gani take kamar matar tana ciki,Abdulmajeed ganin ta kame awaje d'aya ne yasa ya zuba mata ido, " keeeee" wani irin tsalle tayi ta nufeshi a firgice,"kallon mamaki ya bita dashi yace ", ke lafiyarki kuwa mai yake damunki?dasauri ta daidaita nutsuwarta dan bataso Yagane halin da take ciki,tace "bakomai mai kagani," binta ya k'arayi da kallo tunda daga sama har kasa,yace " Kin ganki fa da kayan dana fita nabarki sune ajikinki har yanzu,gidan ma wani iri ba kamshin daya saba well ke kika sani tunda kince ba komai,zuba min ruwa inyi wanka zafi nakeji" Abdulmajeed yace yana shiga d'akinsa,da Sauri tabi bayansa Dan wani irin tsoro ne ya rufeta dayace asa mishi ruwa a band'aki,Abdulmajeed juyawa yayi yana kallonta a lokacin da yake k'ok'arin cire rigar jikinsa, "wai bakiji mai nace bane ki zuba min ruwan zanyi wanka,wai yau Muhibba mai ke damunki ne?", juyawa tayi, tayi hanyar waje gabanta na mugun fad'uwa,adduoi taringa yi ta nufi band'akin Dan ta d'auko bokitin wanka, tura k'ofar tayi bakinta d'auke da addu'ar Shiga band'aki, wani irin razananan k'ara ta saki tayi baya da gudu sakamakon ganin rigar da matan nan ta sa atsaye,babu alamar mutum acikin rigar. [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* *TRUE LIFE STORY* PAGE 3 K'aro suka yi da Abdulmajeed daya taho band'akin a guje,kankameshi tayi sosai tana nuna band'akin in banda rawa babu abinda jikinta ke yi,"ke Wai mai yake damunki ne menene acikin band'akin? Abdulmajeed yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,k'ara kankameshi tayi tana nuna band'akin,gaba d'aya ta firgice,tsaki yayi yace " wlh wani sain idan kika yi Abu kamar a rufeki da duka,ni cikani inga abinda yake cikin band'akin,yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,ina ai k'ara rungumeshi tayi gam tana kuka sai gumi take,haushi ne ya rufe Abdulmajeed daya ga taki magana sai nuna mishi band'aki take,yakice ta yayi da k'arfi daga jikinsa ya nufi band'akin Muhibba ta saki wani k'ara ta bishi aguje ta k'ara rungumeshi,adai dai lokacin daya bud'e band'akin yana k'arewa koina kallo,babu abinda yagani daya wuce butocin data dura Ruwa aciki,sai mudubin dake jikin bango,tsaki yayi ya d'auki bokitin wankan,Muhibba kuwa tana mak'ale abayansa,janyota yayi ta dawo gabansa yace " Muhibba Wai yau mai yake damunki ne ko dai gamo kika yi?Yanzu menene a cikin band'akin nan daya baki tsoro,banasan irin wanan wasan Sam ya kamata ki sani,idan ina cikin mode din wasa kin sani, idan bana cikin mode d'in wasa ma kinsani,dan haka in wasa ma kike min ki daina banaso"magana take sanyi amma inta tuna murd'adden Halin Abdulmajeed sai ta fasa dan ita kanta wani sain tsoronshi take ji dan har mamakin yanda akayi ta aureshi take,duk da yana da wuyan sha'ani wani sa'in dan akwai shi da tsare gida,wuceta yayi yaje ya debo ruwan wankan yakai band'akin,ganin yana k'ok'arin rufo k'ofar ne yasa tayi sauri ta k'arasa band'akin dan wani irin tsoro ne ya rufeta,had'e rai yayi yace " menene?" Hawaye ne ya hau zubo mata tace "dan Allah bari na jiraka a band'akin kayi wankan tsoro nakeji wlh" ayanayin da tayi maganar ne yasa yaji tausayinta yace to "k'aro mana ruwan wankan sai muyi wankan tare dan dama bakiyi wanka ba,ni yau bansan mai yake damunki ba" da Sauri ta kinkinmo bokitin ruwan ta shiga band'akin dashi,jikinta sai rawa yake Kalle kalle tafara yi dan gani take zata iya ganin wanan matar,Abdulmajeed brush ya farayi,hakan data gani ne yasa itama ta matsa jikin mad'ubin dake rataye aband'akin ta zura hannu a d'an kwandon dake mak'ale ajikin mudubin dan ta d'auko brush d'inta da MacLean itama tayi brush,kamar cewa akayi ta kalli madubin,matar nan ta hango a mudubi tana tsaya ajikin bango tana mata murmushi hakoranta amadadin farare jajaye ne,wani irin gigitacen k'ara ta saki ta zube a band'akin a sume,sallati Abdulmajeed yayi ya kinkimeta yayi waje da ita, a d'aki ya kwantar da ita, ya debo ruwa yazo yana yayyafa mata,ajiyar zuciyar tayi ta bud'e idonta ahankali,kuka ta fashe dashi ta rungume Abdulmajeed tana "Abdul na shiga uku na lalace DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO na janyo wa kaina masifa laifine dan na taimaketa,meyesa take San cutar dani" duk maganar da take kuka take jikinta na rawa,Abdulmajeed d'agota yayi yana share mata hawaye yace " Muhibba mai ya faru wa kika taimakawa? Ki fad'amin gaskiyar abinda ya faru dan ni ina dawowa nasan ba dai dai kike ba,dan gabad'aya a firgice kike" tunanin Muhibba ta fara yi na ta fad'a mishi gaskiyar abinda ya faru,wani tunani tayi kwanakin baya wasu 'yan mata sun zo lokacin Abdulmajeed yana nan, 'yan matan suka ce ta taimaka musu da ruwan sha,shigowa tace suyi tayi musu jagora har palo,ta debo musu ruwan suka sha daga nan kuma hira ta b'arke musu kasancewar mata akwai saurin sabo,suna cikin hirar Abdulmajeed ya shigo yace su fita su bar mishi gida,jiki na rawa suka bar gidan,aranar Abdulmajeed kwana yayi yana mata fad'a kamar ya daketa,Ya kuma ce mata duk lokacin da ta k'ara barin bakon mutum ya shigo masa gida,sai ya d'auki mumunan mataki akanta,da wanan tunanin tak'i gayawa Abdulmajeed gaskiyar abinda ya faru,Abdulmajeed ganin tayi shiru tak'i magana ne yasa yaji ransa na b'aci wani irin tsawa ya daka mata yana " ina tambayarki kin yi shiru wa kika taimakawa yake Neman cutar dake" jikinta ne ya hau rawa tsoron Abdulmajeed ya rufeta magana tafara yi tana kuka "wata tsohuwa ce dazu tazo bara tace na taimaka mata da sadakar abinci,shine na bata,ta tafi,tunda ta tafi take tsoratani duk Inda nayi sai na ganta"wani mugun tsaki yayi ya mik'e "Dana San abinda kika yi kenan wlh ko saurarenki ba zanyi ba badai bakya jin magana ba ki cigaba watak'ila ma aljana kika taimakawa,ke gaki uban yan San taimako,hanyar waje yayi ta bishi da gudu,tana tsaye a band'akin yayi wankansa ko kallonta bai yi ba,itama cire kayanta tayi dasauri ta watsa ruwan duk abinda take yi idonta a rufe dan gani take inta bud'e idonta zata iya ganinta,a tsakar gida ta k'arasa sa towel dan Abdulmajeed fitowa yayi ya barta a band'akin,alwala tayi tabi bayan Abdulmajeed daya shige d'akinsa yana shimfid'a sallaya,doguwar Riga tasa ta zura hijabinta ta tsaya daga bayansa,sai da suka yi sallar magriba kafin suka yi isha,Muhibba addua ta ringayi a sujadar karshe tana addua'r Allah ya rabata da sharrin matar da ta taimaka wa,Abdulmajeed Palo ya nufa bayan sun shafa,biyo shi tayi da sauri ko hijabin jikinta bata cire ba, a tsakiyar palon ya zauna inda ta jera abincinsa,zama tayi ta ta d'auki plate tafara zuba abincin jikinta sai rawa yake dan har yanzu tana ganin fuskar matar a idonta,ajiye plate d'in tayi a gabansa bayan ta zuba mai abincin,bismllah yayi,yafara cin abincinsa Muhibba kuma ta zauna tayi tagumi tana hawaye,"ke bazaki ci abincin ba kenan"? Abdulmajeed yace batare da ya d'ago ya kalleta ba,Share hawayen daya zubo mata tayi tace " a koshe nake bana jin yunwa" Abdulmajeed d'agowa yayi ya kalleta ya ajiye cokalin Hanunsa,yace," Wai Muhibba kukan mai kike yine,wani ne ya aike ki bawa tsohuwa abinci,ke kika fi kowa San kiyi taimako,haka kika ga sauran makotanki nayi,ban hanaki taimako ba amma na fad'a miki kinsan irin wayanda zaki na taimakawa dan tun daga lokacin da Aunty Ainau (yayarsa) ta bawa Almajiri sadaka ta kamu da rashin lafiya mai tsanani sai da akayi dagaske aka gano Ashe almajirin nan ba mutum bane Aljani ne,Ashe kud'in nan da ta bashi sadaqa dashi ya ringa cutarta sai da aka runga adduoi ana sauk'ar qurani kafin ta samu lafiya,wlh tunda ga lokacin nake tsoron in taimakawa Wanda bansani ba,dan kai da zuciya d'aya za kayi taimakon amma akarshe Wanda ka taimakawa ne yake cutarka shiyasa nake hanaki kwashe kwashe," tunda ya fara magana taji wani tsoro ya kuma rufeta,matsawa tayi kusa dashi da sauri tana " Abdul yanzu ya zanyi wlh bansan ba mutum bace"tace tana fashe da kuka,"ki kwantar da hankalinki kiyi Addu'a insha Allahu,Allah bazai bata ikon cutar dake ba,this would serve you a lesson next time zaki San irin wayanda zaki ringa taimaka wa,yanzu dai ki zuba abincin nan kici sai na raka ki kiyi alwala kizo ki kwanta,"Abdulmajeed yace yana bud'e kular abincin,dak'yar taci cokali uku ta ce mishi ta koshi,kwashe kwanukan yayi da kansa ya kai kitchen, yace mata tazo tayi alwalar,alwala tayi a tsakar gidan kanta a sunkuye dan gani take inta d'ago zata iya ganin Matan nan,d'akinsa ta nufa dasauri ta rufo k'ofar,dan Abdulmajeed har ya kwanta,shiryawa tayi cikin kayan barci,ta fesa turare ta kwanta agefensa kamar zata shige jikinsa sabida har yanzun a tsorace take,tashi yayi zai kashe fitilar d'akin tayi sauri ta rik'o shi "dan Allah Abdul karka kashe wutan d'akin wlh tsoro nake ji" wani kallo ya watsa mata yace " kin tab'a ganin nayi barci fitila a kune,kashewa zanyi dan bazan iya barci ba ina barshi a kune,ke kika sa tsoro aranki amma ina gefenki mai zai tsorata ki,"sauk'a yayi ya kashe fitilar d'akin tayi sauri ta runtse idonta da k'arfi dan tuni duhu ya mamaye d'akin,yana kwanciya ta rungumeshi gam,shi kuwa ya lalubo bakinta ya fara kissing d'inta,duk abinda yake idonta a rufe yake gam,ko kwakwaran motsi bata yi,shi kadai yayi kidansa yayi rawansa,sai wajen k'arfe biyu ya k'yalleta aikuwa nan da nan barci yayi awon gaba da ita, wajen k'arfe hud'u ta juya da zumar ta gyara kwanciyarta,ji tayi hanunta ya sauk'a akan Abu kamar gashi,shafawa tayi dan ta gaskata gashin ne,ji tayi gashi ne mai tsayin gaske,bud'e idonta tayi a hankali tayi tozali da wanan matar a kwance a gefenta ta kura mata ido bakinta a bud'e jajjayen hakoranta kuwa awaje, wani mugun ihu ta saki ta rufe idonta gam.b [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 4 A firgice Abdulmajeed ya tashi yana sallati lalubota yayi ta rungumeshi gam jikinta na rawa sai cusa fuskarta take a k'irjinsa girgiza ta ya fara yi yana "Muhibba menene mai yake damunki" ahankali ta fara magana tana k'ara rungumeshi "ka kuna wutan d'akin matan nan tana gefena"tace cikin rawar murya,atare suka mik'e da ita dan kankameshi tayi sosai kamar zata koma jikinsa,kunna wutan d'akin yayi bai ga komai ba dafe kansa yayi yace " cikani ki duba kan gadon ba kowa,kankameshi ta k'ara yi tana cusa fuskarta a k'irjinsa " wlh a gefena ta kwanta tana kallona Abdul na shiga uku ka taimaka min matar nan tana Neman ta zautar dani" d'ago da fuskarta yayi ta rufe idonta sosai dan gani take idan ta bud'e idonta zata ganta,"Muhibba tsorata kawai kika yi babu kowa a d'akin nan,kina barci taya akayi kika ganta wlh tun jiya kin hanani sakat sai d'aga min Hankali kike, gashi wlh barci ne a idona dan Allah ki cikani muje mu kwanta" Abdulmajeed yace yana k'ok'arin raba jikinsa da nata,kankameshi ta k'ara yi sosai tace "Abdul ankusa Kiran sallah asuba dan Allah muje muyi wanka muzo muyi sallah,agogon bangon d'akin ya kalla yaga hud'u da minti goma,"yanzu k'arfe hud'u lokacin sallah bai yi ba,barci nakeji idan wankan kike so kiyi, jeki yi wankan ni sai na tashi zanyi,",Abdulmajeed yace yana nufar kan gadon,k'ok'arin magana take ya daka mata tsawa " dalla ki rabu dani kin dameni tun jiya in bazaki koma barcin ba ki koma d'akinki ki barni nayi barcina" yace yana kwanciya,da sauri ta hau kan gadon jikinta na rawa sai hawaye take,juya mata baya yayi,tayi sauri ta rungumeshi ta baya ta cusa fuskarta a bayanshi,Abdulmajeed barcinsa yake hankalinsa kwance,ita kuma idonta biyu in banda tsoro babu abinda take ji,tana jiyo kiraye kirayen Sallah amma babu dama ta tashi sabida tsoro,wajen Biyar da rabi tafara jin motsi a gefenta,kasan gadon ma motsi take jiyowa,k'ara kankame Abdulmajeed tayi cikin tsananin tsoro da firgita jikinta sabida tsabar rawa gadon ma har dan motsi yake,rufe idonta ta k'ara yi hawaye kuwa sai ambaliya yake a fuskarta,a zuciyarta kuwa duk addu'ar daya zo bakinta karanta wa take,acikin wanan yanayin take har k'arfe shiddan safe in taji motsi sai ta k'ara rungume Abdulmajeed, Tashin Abdulmajeed tafara yi tana bubuga bayansa dan taga gari yafara haske,zai je makaranta,motsawa yayi yana bud'e idonsa yaga haske ya d'an shigo d'akin,mik'ewa yayi da sauri itama ta mik'e,tabi bayansa,atare suka yi wankan tsarki ,suka yi alwala suka fito,shi ya jasu sallar asuba suna idarwa yace tayi sauri ta d'ora mishi breakfast kar yayi lati,mik'ewa tayi gabanta na fad'uwa dan gani take in taje Kitchen d'in ma zata iya ganinta,kwai kawai ta soya mishi sai ruwan tea da ta dafa dan ba zata iya soya dankali ba dan duk abinda take yi waige waige kawai take,k'arfe bakwai dai dai ya shiryaa zai tafi makaranta,Hawayene ya hau zubo mata dan gani take yana fita zata ga matar,Abdulmajeed kuwa ko kallonta bai yi ba yafara k'ok'arin fita da machine d'insa dan aganinsa abin nata har da iskanci,Muhibba d'aurewa tayi ta share hawayen fuskarta tace " Abdul ni kadai zaka bari a gidanan wlh tsoro nake ji,dan Allah kabani izini naje gida Idan ka dawo daga makaranta sai ka biya ka d'aukoni" d'agowa yayi yana kallonta,Sunkuyar da kanta tayi hawaye na k'ara zubo mata dan tasan ma'anar kallon da yake mata ,Abdulmajeed bai ce mata komai ba ya hau kan lifan d'inshi sai da ya tayar,yace "Muhibba bazan yi tolerating wanan iskancin da kika tsiromin dashi ba,babu ko mai a gidana ke kika sa tsoro aranki,kike Jin tsoron dan haka ban yarda ko nan da k'ofar gida ba ma ki leka," yana gama magana yaja lifan d'insa ya tafi,durk'ushewa tayi awajen ta fashe da kuka,tana " wayyo Allahna na shiga uku na lalace DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°Ko na janyo wa kaina Baiwar Allah laifine dan na taimake ki mai yasa kike san cutar dani"?Muhibba sai da ta samu minti 30 a zaune tana surutu ita kadai,sai da ta gaji dan kanta ta mik'e ta Shiga ciki,d'akin Abdulmajeed ta shiga dan ta gyara dan ta sa aranta ko da taga matar bazata gudu ba,zata tsaya ta tambayeta akan mai yasa take San ta cuce ta alhalin ita Taimakonta tayi, gyara d'akin ta fara yi amma duk a tsorace take,cikin ikon Allah ta gama gyara d'aki,hakan da ta gani ne yasa hankalinta ya d'an kwanta,Palo ta nufa ta gyara,ta gyara d'akinta,daga nan kitchen ta nufa tayi wanke wanke ta goge ko'ina,tsakar gidan ma wanke shi tayi tas ta moper,ganin babu ruwa a gidan ne yasa,tayi deciding ta ja ruwa a rijiya ta wanke band'aki,bud'e murfin rijiyar tayi ta zura gugan ta fara Jan ruwan,saura guga d'aya bokitin ya cika,tana jefa gugan dan ta debo ruwan,taji an rik'e gugan, gabanta ne ya yanke ya fad'i ta lek'a rijiyar,Fuskar Matan nan ta hango akwance a saman ruwan ta wangale baki jajjayen hak'oranta sun k'ara tsawo,ruwan rijiyar yana yowa sama, wani irin ihu tasa,ta saki igiyar ta nufi d'akinta a guje ta rufe k'ofar ta fad'a kan gadonta ta ja bargo ta rufe kanta,adduoi ta ringa yi jinkinta na rawa,tsayawa tayi cak da addu'ar da take sakamakon jin da tayi an bud'e k'ofar d'akin,tsayar da numfashinta tayi ta yaye bargon daga fuskarta,babu abinda ta gani a bak'in k'ofar hakan ne yasa wani mugun tsoro ya rufeta dan ta ciki ta kulle d'akin waige waige ta fara yi ganin bata ga kowa ba yasa ta fashe da kuka tana " mai nayi miki kike San cutar dani? Laifine dan na taimaka miki, kiyi hak'uri dan Allah bansan ke ba mutum bace"ji tayi an dafata ta baya,fitsarin da ya matseta ta saki awando,ta juya ahankali,numfashinta ne ya d'auke na wucin gadi sakamakon tozali da tayi da matar a zaune a bayanta,ji tayi matar tace da muryar yara " _ba cutar dake zanyi ba sanki nake_ " wani irin hantsila wa muhibba tayi daga kan gadon ta d'iba aguje,bata tsaya a ko ina ba sai gidan Surayya,Surayya da itama mijinta bai Dade da fita ba, fitowa ta yi dan tafara 'yan aikace aikacen ta Dan jiya kwana tayi tana mafarkin wanan matar,da tuni ta gama aikinta,ganin da tayi Muhibba ta shigo aguje ne yasa ta wurgar da tsintsiyar hanunta,ta shige d'akinta da gudu tana k'ok'arin rufe k'ofa. [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 5 Wuf Muhibba ta shige itama,Surayya kuwa ta kulle k'ofar sabida tsananin tsorata da tayi wardrobe d'inta ta nufa da gudu ta bud'e tana k'ok'arin shigewa dan ta d'auka Aljanar ce ta biyo muhibba,,Mubibba da a gigice take,binta tayi itama a gujen ta rik'eta tana "bani Hijabi gidanmu zan tafi bazan iya ba"Surayya zare ido kawai take tana kallonta tace" Aljanar ce ta biyoki?" "Nidai kawai ki bani Hijabi inkina da d'ari biyar ki bani aro in yi kud'in mota" Muhibba tace tana share hawayen da suka zubo mata,Surayya dafata tayi tace "haba Muhibba ki fad'a min abinda ya faru mana kike so ki tafi gida" muhibba kuka ta fashe dashi tana "Surayya gida zan tafi tun jiya banida kwanciyar hankali matan nan dana taimakawa in banda tsorata ni babu abinda take yi,jiya ban runtsa ba,nayi wa Abdul bayani bai yarda dani ba,dan haka gidanmu zan tafi bazan iya zama a gidanan ba" tunda Muhibba ta fara magana jikin Surayya ya hau rawa,cikin tsanin tsoro tace " yanzu Muhibba idan kika tafi ta shigo min fa,dan Allah karki tafi ko ina ki zauna anan inya so idan Ayuba ya dawo zan sa ya kira Abdulmajeed ya mishi bayani in bai yarda. ba ma da kaina zan mishi bayani kinga bai kamata ace kin tafi gidanku ba da izininsa ba kin kuma San halin mijinki" Muhibba kallonta tayi tana girgiza kai tace " Surayya bazan iya ba ni nasan mai nake gani DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO na janyo wa kaina masifa,gidanmu zan tafi,idan Abdulmajeed ya dawo ki fad'a masa na tafi gidanmu,Surayya babu yanda bata yi ba akan Muhibba ta zauna a gidanta kar ta tafi,amma Muhibba tak'i Hijabi ta bata,ta d'auko dubu d'aya ta bata da sauri Muhibba ta saka hijabin dan burinta kawai ta ganta a gida padlock ta k'arba awajen Surayya ta kulle gidan,Surayya ma kulle gidanta tayi dan cewa tayi bazata iya zama ba ita ma gidan d'aya makociyar ta su ta tafi,Muhibba kuwa ta dau hanyar bak'in titi,dan gidan nasu a dan lungu ya ke,tana isa bakin titi ta tari adaidaita sahu ta hau,tafiyar minti 20 ne ya kai ta karkasara,tana sauka ta shige gidansu dan gidansu a bakin titi yake, atsakar gida ta tarar da Nafeesa kanwata dake binta tana wanki,da alama uniform d'in islamiyya take wanke wa,Sallamar da tayi Nafeesa ta amsa cikin murna ta tafi ta rungumeta tana "oyoyo" murmushi Muhibba ta yi tana kallo k'ofar palonsu tana "ina Umma"? "Tana d'akinta" Nafeesa tace a dai dai lokacin da ta cika Muhibba ta na kallonta dan taga Muhibban a firgice ba kamar yanda ta saba ganinta ba. ita kuwa Muhibba d'akin Maryam mahaifiyarta tayi da saurinta,da sallamarta ta shiga d'akin Maryam dake linke kayanta ta juyo da sauri tana amsawa,Muhibba dan dukawa tayi tana gaisheta,Maryam ta amsa tana leka fuskar Muhibba," Muhibba lafiya dai na ganki awani firgice" Maryam tace a lokacin da take ajiye kayan hanunta,shiru Muhibba tayi nan da nan hawaye ya hau zubo mata," Subhanallahi Muhibba mai ya faru? ina Abdul d'in? Fad'a kuka yi?" Duk ajere Mahaifiyarta tayi mata tambayar,shiru muhibba tayi bata yi magana ba,"ina tambayarki kin min shiru mai ya faru" muhibba d'agowa tayi ta fara magana cikin sheshek'ar kuka "Umma Aljana ce take bibiyata DπŸ…° GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KA mata wlh na d'auka mutum ce bansan aljana bace" Ware ido Maryam tayi tana "bangane mai kike nufi ba,taya ya kika taimakawa Aljana"? Muhibba share hawayen fuskarta tayi tafara bata labarin abinda ya faru,sallati maryam ta ringayi bayan ta gama jin labarin abinda ya faru,"muhibba mai ya kai ki bud'ewa aljana k'ofa har ta Shiga band'akinki? Mai yasa kika b'oyewa mijinki gaskiyar abinda ya faru ai dole yak'i yarda dake ya d'auka karya kike" oooo ni maryam daga taimako kin janyo wa kanki,Allah ya kareki daga sharrinta,bari babanku ya dawo ya kira mijin naki awaya ya fad'a masa abinda ya faru Idan addua za adage da yi kafin ki koma gidan dan hatsarine komawarki gidan yanzu, wuce kije d'akinku ki kwanta tunda kince jiya bakiyi barci ba" mik'ewa Muhibba tayi ta nufi d'akinsu dan barcine a idonta sosai,tana kwanciya barci yayi awon gaba da ita. K'arfe biyar da rabi Abdulmajeed ya dawo gida,mamaki ne ya rufeshi daya ga k'ofar gidansa a kulle,parking d'in lifan d'insa yayi ya nufi k'ofar gidan Surayya dan yana kyautata zaton Muhibba a gidan take,aransa kuma yana ayyana irin rashin da zai yiwa Muhibba wato shi zai ce ko k'ofar gida kar ta fita,amma sabida bata jin magana shine zata tafi gidan makota har da kulle gida,buga k'ofar yyi da k'arfi,Surayya da bata dade da koma wa gida ba sabida tsabar tsoron da take ji,ganin biyar tayi ne yasa ta nufi gida dan ta d'ora girki,tana cikin jajjage taji an buga k'ofa wurgar da tabaryar hanunta tayi ta shige d'akinta da gudu ta rufe k'ofa jikinta sai rawa yake,jin da tayi an k'ara buga k'ofar ne yasa ta fara" wa innahu sulaimanu wa innahu bismillahi ku kuke ganin Mu, ba mu muke ganinku ba"duk adduar daya zo bakinta karantawa kawai take in banda gumi babu abinda ta keyi,Abdulmajeed jin shiru ba amsa bane yasa yayi tunanin ko basa gidan,suna gidan Hadiza d'aya makociyar tasu da wanan tunanin ya nufi gidan Hadizan yana shirin kwankwansa,ta bud'e k'ofar ta fito da alama wani wajen zata,da sauri ta gaishe shi,ya amsa yana tambayarta ko su Muhibba na nan,ce mishi tayi,Muhibba bata nan amma Surayya bata Dade da barin gidanta ba,ta tafi ta d'ora girki,godiya ya mata ya nufi gidan Surayya yana mamakin inda Muhibba taje,k'ara kwankwasa gidan yayi,Surayya da tun lokacin tana jikin labule sai addua take,jin an k'ara buga k'ofar ne yasa ta saki fitsarin daya matseta,dan duk a tunaninta aljanar ce take buga gidan tunda taga Muhibba bata nan,Abdulmajeed gajiya yayi da buga k'ofar ya koma kan lifan d'insa ya zauna ,zuciyarsa sai tafarfasa take, Yana zama da minti biyar,Ayuba shima ya k'aryo kwana parking yayi a k'ofar a gidansa ya sauk'o daga machine d'insa ya nufi wajen Abdulmajeed dake karkada k'afa hannu ya mik'a mishi suka yi musabiha yana kallon k'ofar gidansu Abdulmajeed,tambayarsa yayi Muhibba bata nan,cikin tsananin Bacin rai Abdulmajeed yace masa bata nan shima bai San Inda ta tafi ba ya ma d'auka tana gidansa Ashe itama surayyar bata nan,Ayuba juyawa yayi ya kalli k'ofar gidansa,ganin babu padlock daga waje ne yasa yace mishi Surayya ta nan k'ofar gidan ya nufa shima ya fara kwankwasa k'ofar,ganin ya kwankwasa sau hud'u ba a bud'e bane yasa yayi yayi amfani da mukullin gurinsa ya bud'e k'ofar,Surayya kuwa tana jin an bud'e k'ofar ta saki ihu tana " wayyo Allahna kiyimin rai Ku kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Allahu la illah ha illa huwa Al hayul al qayyum,inna anzalnahu fi lailatul kadir,wa shamsu wa duhaha,kowane sura kamowa kawai take jikinta na rawa,Mamakine ya rufe Ayuba yace " Surayya kina da hankali kuwa mai yake damunki,"?shiru Surayya tayi da taji muryar Ayuba lek'a wa tayi ta windown d'akin sai da ta tabbata shine tafito daga bayan labulen ta bud'e k'ofa ta fito,Ayuba jikakken skirt d'inta yafara bi da kallo,ya dawo da kallonsa kan fuskarta da ta had'a gumi,sai muzurai take,"Surayya lafiyarki kuwa? Ayuba yace yana k'ara binta da kallo,"ina fa lafiya ayuba aljana ta sako Mu agaba tun dazu take buga min gida,Muhibba ma ta tafi gida tace bazata iya ba ta tafi gidansu,Ayuba mamaki ne ya rufe shi yace "bangane mai kike nufi ta da tafi gidansu ba"? Surayya kwashe komai tayi ta fad'awa Ayuba,girgiza kai yayi yace mata Abdulmajeed na waje bari ya fad'a masa Muhibba ta tafi gidansu,Surayya Hijabinta ta zura ta bishi suka yi waje dan tace tsoro take ji,Ayuba bayani yayi wa Abdulmajeed,Surayya itama ta bashi labarin yanda aljanar ta ringa tsorata su tana ita bata San tsautsayin da ya kai Muhibba ta bari aljana ta shigar mata band'aki ba,Ayuba Shawara ya hau bawa Abdulmajeed akan yasa ayi mishi sauk'ar Qurani,tunda suka fara mishi magana ya saki Baki yana kallonsu dan ba haka Muhibba ta ce mishi ba,kenan karya muhibba take mishi data ce Almajira ce tayi bara,aljana ta bud'ewa gida ta shigar musu band'aki,wani irin tafasa yaji zuciyarsa nayi yana ganin Muhibba ta gama rainashi duk gargadin da ya mata Ashe bata ji ba, godiya yayi wa Ayuba ya k'arbi mukullin padlock d'in daga hanun surayya ya bud'e gidan ya shigar da lifan d'in sa [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 6 Abdulmajeed ransa a mutuk'ar bace ya zauna a Palo sai karkad'a k'afa yake yana tunanin matakin da zai d'auka akan Muhibba,ga yunwan da ya koro shi,gashi bai iya girki ba,tsaki yayi a fili yace "zaki gane kurenki bazan je gidan naku ba,in kin gaji zaki dawo da kanki" kwanciya yayi akan dogon kujeran yana jin yanda cikinsa ke k'ugin yunwa. B'angaren Muhibba kuwa sai wajen k'arfe 2:30 ta tashi daga barci wanka ta farayi,tayi sallah abincin da Nafeesa ta zubo mata ta jawo taci ta koshi,ta nufi d'akin Mahaifiyarta,ganin bata d'akin ne yasa ta koma d'akinsu ta zauna ta rafka tagumi tana kallon Nafeesa dake shirin tafiya islamiyya,tunanin Abdulmajeed ta fara yi tana tunanin ko ya zai ji idan ya dawo ya tarar ba ta nan,tunani tayi na ta kirashi a waya, ta fad'a mishi da kanta,wayar Nafeesa ta k'arba tayi dailing Number Abdulmajeed,taji switchoff,mik'awa Nafeesa wayarta tayi ta cigaba da tunaninta,ta rasa mai yasa aljanar data taimaka wa take bibiyarta,Muhibba ahaka ta wuni tana tunanin sai wajen k'arfe shidda Mallam Hashimu Mahaifinta ya dawo daga kasuwa,sai da yayi sallar isha yaci abinci Maryam take bashi labarin abinda ya faru da Muhibba,sallati yayi yasa aka kira mishi Muhibba,ya k'ara tambayar ta abinda ya faru ta k'ara bashi labarin abinda ya faru,ba k'aramin firgita Mallam Hashimu yayi ba daya ji abinda Muhibba tace dak'ewa yayi bai nuna mata ba ya rufe ta da fad'a yana mai ya kai ta ta bud'e k'ofa ai gashi nan DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO ta janyo wa kanta fad'a ya ringa mata sosai yana kar ta sake irin wanan gangancin,gobe zai bata adduoi ta koma gidanta insha Allahu,Allah zai kareta daga sharrin aljanar,jin abinda yace ne yasa Maryam tayi magana tana "bai kamata Muhibba ta koma gidanan ba tare da anyi saukar Qurani ba ita ganinta a kira Abdulmajeed awaya ace masa yazo inyaso sai su bashi shawaran yasa ayi saukan,da wanan shawarar suka yanke zasu nemi Abdulmajeed,Muhibba ta tashi ta nufi d'akinsu tana tunanin Abdulmajeed. Abdulmajeed kuwa da k'yar yayi sallar magriba dan jikinsa har rawa yake sabida yunwar da yake ji,mik'ewa yayi daga kan sallayar ya d'auki mukullin lifan d'insa dan bakin titi yake so yaje ya siyo tsire yazo yaci,ji yayi ana kwankwansa gidan,hanyar waje yayi yana bud'ewa yaga Ayuba a tsaye da flask a hannu,Ayuba mik'a mishi flask d'in yayi yana cewa "ga abinci nan yaci tunda madam bata nan,da sauri ya k'arb'a yana mishi godiya,kulle k'ofar gidan yayi,ya ajiye flask d'in hanunsa sai da ya fara tada engine tukuna,ya nufi Palo, a tsakiyar Palon ya zauna ya bud'e flask d'in lafiyayyen jollof d'in shinkafa da yaji kayan had'in kayan lambu yayi tozali dashi,aikuwa da gudu ya nufi kitchen ya d'auko plate da spoon, yazo ya zauna ya zuba ya fara ci, sai da yaci ya koshi sosai yayi hamdala,dak'yar yayi sallah isha sabida koshin da yayi,plasma dake mak'ale a jikin bango ya kunna bayan ya idar da sallah ya fara kallo Dan ya rage dare,Dan ji yayi gidan ya mishi fad'i ya kuma rasa mai yake mai dadi,tsaki yayi a lokacin da ya dau remote Dan ya chanza tasha yana " gida idan babu mace tamkar kango ne" kallo yake amma tunanin Muhibba yake ahaka ya ringa zuba tsaki shi kadai,wani irin tsoro ne ya rufeshi a lokacin da yaga horror film akeyi dan Inda aka nuno yanzu ba k'aramin tsorata yayi ba da sauri ya kashe kayan kallon,yayi waje band'aki ya nufa Dan ya d'auko bokiti ya zuba ruwa ya watsa Dan kwanciya ya keso yayi duk da bashi da tabbacin in zai iya baccin,ganin babu ruwa abokitan gidan ne yasa ya ja ruwa a rijiya,ya kai ruwan band'aki ya koma d'akinsa ya cire kayansa ya d'auro towel ya nufi band'akin brush ya farayi kafin yayi wankan Dan ya Riga ya saba,takun takalmi ya fara jiyowa daga tsakar gida,takalmin ma irin mai tsinin nan,"kwas kwas kwas " kawai yake jiyowa,gabansa wani irin fad'uwa yayi Dan yasan ya kulle k'ofar,towel d'insa ya janyo da sauri yayi waje yana "waye" waige waige ya fara yi yayi hanyar k'ofar gida yaga k'ofar na nan a kulle,ciki ya koma ya duba ko ina bai ga kowa ba,rufe ko ina yayi ya koma band'akin yana tunanin kunensa ne ya jiyo masa takun takalmi towel d'insa ya cire ya fara wanka,yana wanka yana kallon mudubi,duk'awa yayi Dan ya debo ruwa ya watsa yana d'agowa idansa ya sauka akan mudubin band'akin Matan nan ya hango abayansa ta zuba mishi ido tana kallonsa idonta jajaye kamar jini, dogwayen hak'oranta awaje,gashinta kuwa har kasa,wani mugun ihu Abdulmajeed yayi,yafita waje dagudu,cal cal cal ya shige d'akinsa ya kulle jikinsa na rawa, Numfashin sa kamar zai d'auke sabida tsabar tsoro,ahankali ya zauna akan gado yana mai da numfashi ya ma manta babu komai a jikinsa" adduoi yafara yi yana dafe da k'irjinsa ahankali ya fara samun nutsuwa,sai da kai Minti talatin azaune,ya mik'e ya d'auko gajeran wandonsa yasa,yana shirin sa vest yaji an bud'e k'ofar kitchen aguje ya hau kan gado ya janyo bargo ya rufe kansa jikinsa kuwa sai rawa yake,hawaye ya hau zubo mishi yana " Ashe Muhibba dagaske take da aljana a gidanan shi kenan tawa ta kare" ahaka ya cigaba da rawar d'ari yana adduoi ganin bai k'ara jin motsi ba yasa ya yaye bargon da ya rufe Kansa ya zauna akan gadon sai da yafara lek'a ko ina ya duro daga kan gadon,Touch light ya d'auko ya kuna,yasa agafen gadon,duk da engine a kunne yake fitilar d'akin a kunne yake,wayarsa ya d'auko ya kuna torchlight d'in Dan ba k'aramin tsoro yake jiba Dan in ya rufe idonsa aljanar nan yake hangowa,gadon ya hau ya kwanta yana kalle kalle,bakinsa d'auke da addua Dan babu yanda zai yi ne in ya fita zai iya ganin aljanar da ba abinda zai sa ya kwana a gidan,ahaka ya kwanta a tsorace said wajen k'arfe d'aya da rabi barci ya d'aukeshi,wajen k'arfe uku na dare yaji motsi a gefensa ahankali ya bud'e idonsa cikinsa wani irin murd'awa yayi gudawa mai k'arfi ya taho masa sakamakon tozali da yayi da aljanar nan azaune a gefensa tana murmushi idonta ya k'ara girma razanan ihu ya saki ya mik'e aguje ya bud'e k'ofa yafita waje,ganin zai iya kashi awando ne yasa ya nufi band'aki da gudu ya rufe k'ofa ya hau kan Masai ya hau sakin gudawa jikinsa na rawa rufe idonsa yayi gam,kirjinsa sai dukan goma goma yake,babu abinda kake ji sai sauk'ar gudawansaπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚(readers Ashe dai Abdulmajeed matsoraci ne) ji yayi kamar an bud'e k'ofar band'akin,cikin tsananin tsoro da firgita ya fara ihu yana " kiyi min rai karki cutar dani kiyi hak'uri Dan Allah" ihu yake sosai jikinsa na rawa shirun da yaji ne yasa ya bud'e idonsa ahankali ganin bai ganta a band'akin bane yasa ya d'iba a guje ko tsarki bai tsaya yi ba,ballantana akai ga yasa wandonsa,k'ofar gida ya bud'e ya fita waje,kasancewar babu wuta garin duhu,wandonsa yasa da sauri ya nufi gidan Ayuba ya fara kwankwansa da sauri yana waige waige ,Surayyan dake rungume ajikin Ayuba tana barci,jin da yayi ana kwankwasa gidan ne yasa ta tashi a firgice ta hau kan Ayuba tana nuna mishi k'ofa. Abdulmajeed buga gidan yake da sauri yaji an dafa bayansa fitsari mai zafi ya saki awando a juya ahankali aljanar nan ce ta da fashi tace da muryar yara "Abdulmajeed ina zaka ni Dana zo na ta yaka hira"Abdulmajeed zubewa yayi akasa sumame. [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 7 πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ *Readers bari dai na rufe bakina kar ya yage garin dariya Ashe haka page 5 da 6 yake da abin dariya sai da na karanta nima Dana yi posting naci dariya na gode Allah bare wajen matuniyata Surayya mai karatu kala kala gaskiya naji dadi babu laifi duk inda na lek'a jiya dariya kawai ake,masoyana.burina a kullum na saku nishadi*πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ *Note*- *yar uwa maman mamy sorry for scaring you,i don't mean to scare you please,like serious wanan novel d'in ya faru agaske amma ba exactly yanda nake rubutawa ba na k'ara abubuwa sosai sabida kawai na nishadantar,zan iya cewa adaidaita Sahu na hau kunsan mata da hira naji wasu suna labarin wacce abun ya faru da ita Dan da dukan alamu 'yar uwarsu ce, labarin ya mutuk'ar tsumani Dan sabida naji karshen labarin har an wuce inda zan sauk'a kunsan marubuci da San kwasan rahoto tuni jikina ya fara rawa nafara tunanin yanda zan juya labarin ya zama novel,aikuwa ina zuwa gida na sungumi wayata na fara typing, Dan haka sis ban yi novel dinan Dan in in tsorata kowa ba,nayi ne Dan na nishad'antar kuma Alhamdulillah ba laifi Sadnaf sunsa mutane dariya in kika kwantar Da hankalinki gajeran novel ne ba mai tsayi ba stay blessed everyone love you oll* πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Ayuba tashi yayi ya zauna ya duba agogon wayansa yaga k'arfe hud'u saura shima jikinsa ne ya fara rawa tsoro ya rufeshi yana tunanin Wanda ke kwankwasa k'ofa uwar haka,Kallon Surayya yayi da ta jike da gumi sabida tsananin tsoro yace ta d'aga shi yaje ya duba Wanda ke kwankwasa k'ofar,kankameshi tayi tace kar yaje ko ina yasani ko aljanar ce take kwankwasa musu k'ofa,ce mata yayi ba bud'ewa zai yi ba zai lek'a ta ramin k'ofar ne yaga waye, Surayya kin cika shi tayi,suka mik'e tare Ayuba ya bud'e k'ofa ahankali suka fito suna dab da isa k'ofar suka jiyo guje gujen maguna asaman kwanu, taku biyu Surayya tayi ta shige d'aki,Ayuba ya rufa mata baya,karkashin gado Surayya tafara shirin shigewa,Ayuba ya rufe k'ofar har da Dan tusar sa. Abdulmajeed dake kwance a kasa a sume,ji yayi an yayyafa mishi ruwa ahankali ya bud'e idonsa,ganin bai ga kowa bane yasa ya mik'e aguje yana bubbuga gidan Ayuba,Surayya da Ayuba da jikinsu tun a lokacin bai bar rawa ba,suna dunkulle awaje d'aya,jin da suka yi an k'ara bubbuga gidan ne yasa suka wage baki suna adduoi Ayuba na karanta Laqadjaakum,Surayya na karanta Fatiha Dan ba k'aramin tsorata suka yi ba Dan har a lokacin suna jin guje guje asaman kwanu,Abdulmajeed da shima a mugun firgice yake ganin babu alamar za a bud'e k'ofar ne yasa ya hau k'wallawa Ayuba kira yana yazo ya bud'e masa shine Abdulmajeed,cak Ayuba ya tsaya da karatun da yake,ya kasa kunne Dan kamar sunansa yaji ana kira,muryar Abdulmajeed ya jiyo yana Kiran sunansa,da sauri ya raba jikinsa Dana Surayya ya mik'e yayi waje Surayya sai kiranshi take ya dawo,Abdulmajeed kuwa waige waige kawai yake yana kiran sunan Ayuba ga tsanin tsoro ga wani gudawar da yake ji,Ayuba na bud'e gidan ya shige da gudu,Ayuba kuwa yayi sauri ya rufe gidan,a tsakar gida ya sameshi yana kai da kawowa, " Abdulmajeed Lafiya kuwa daddaren nan waye ya koro ka"? Ayuba yace yana kallon gajeran wandansa dake Neman sub'alewa daga jikinsa "Ayuba bani touchlight na Shiga band'aki tukuna kashi nake ji" Ayuba d'akinsa ya shige ya tarar da Surayya a zaune akan gado duk ta had'a zufa sai ajiyar zuciya take Dan sai da ta jiyo muryar Abdulmajeed hankalinta ya kwanta,Touch light d'in dake gaban mudubi ya d'auka yayi waje da sauri Abdulmajeed ya k'arbi touch light d'in daga hanun Ayuba ya shige band'akin Dan ginin Gidansu iri d'aya ne kasancewar haya duk saka kama,yana hawa kan Masan yafara sukurkuta gudawan,Ayuba ciki ya koma ya zauna a gefen Surayya aikuwa suka jiyo karar sauk'ar gudawan Abdulmajeed ji kake "buut bubut" Surayya mai zata yi in ba dariya ba har da rik'e ciki,Ayuba shima duk yanda yaso ya gintse dariyar da ta taho masa kasawa yayi sai da ya saki dariyan,Surayya kasa tayi da murya tafara maganar " Ayuba duk yanda akayi Aljanar nan ce ta tsorata Abdulmajeed shi yasa kaganshi daddaren nan gashi sabida tsorata da yayi bar da su gudawa Ashe Muhibba ma ta fishi jarumtaka"Surayya tace tana k'ara kyalkyalewa da dariya,Ayuba shima kasa yayi da murya yace " aikuwa inaga aljanar ce ta koro shi Dan babu Riga a jikinsa da gashi sai gajeran wando" Abdulmajeed Sai da yayi minti goma sha Biyar a band'akin kafin ya fito,yana sauke ajiyar zuciya,Ayuba mik'ewa yayi, ya yi hanyar waje,palo ya bud'e yace wa Abdulmajeed bismillah,tare suka shiga palon, Abdulmajeed ya ajiye touch light d'in hanunsa yacewa ya Ayuba taimaka masa da Riga ya sa,Ayuba d'akinsa ya koma ya d'auko masa doguwar Riga Surayya kuwa ta biyoshi Dan tace bazata iya zama ita kadai ba,zura rigar yayi ya zauna,Ayuba yace "Abdulmajeed ina jinka mai ya faru," " Ayuba Allah ne yayi ina da sauran numfashi agaba da tuni kaji labarin na mutu tun k'arfe 11 Aljana ta sako ni agaba ina zaman zama na Muhibba ta janyo min" ba irin gargadin da ban mata ba akan tasan irin wayanda Zata na taimakawa tana Sanin irin wayanda zasu na na shigar min gida Sai gashi ta janyo min masifa DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO,"Subhanallahi kace abinda ya faru kenan,Allah ya tsare mu da tsarewarsa ya kare mu daga sharrinta" " Ameen kai dai ai naga masifa wlh har k'ofar gidanan ta biyoni Allah Ayuba ba Dan ina da dauriya ba da tuni na mutu," "innalillahi wa inna ilaihi rajiun Allah ya tsare mu kace ba k'aramin tashin hankali Muhibba tagani ba" Ayuba yace yana girgiza kai,"yanzu ya zaka yi Abdulmajeed? "Ai Ayuba barin gidanan ya kamani ana iddar da sallahr asuba zanje gidanmu in fad'awa Mahafina bazan iya zama agidanan ba gaskiya"Katse shi Ayuba yayi yace " aa ba haka zaayi ba dudu watanku biyar a gidanan Sauk'ar Qur'ani za'ayi a gidan insha Allahu aljanar zata bar gidan," "hmm Ayuba kenan Dan ba Kai ne kaga aljanar ba da wallahi kai ma barin gidan zaka yi. Ana idar da sallar asuba Abdumajeed ya k'arbi kud'i awajen Ayuba Dan yace babu abinda zai sa ya k'ara shiga gidansa babu yanda Ayuba bai yi ba akan ya Shiga gidan zai raka shi ya d'auko machine d'insa ya hau bai kamata ace yana da machine yaje ya hau adaidata sahu ba,fir Abdulmajeed yak'i da gashi sai doguwar rigar da Ayuba ya bashi da Dari biyar d'in da ya k'arba awajen Ayuba ya dau hanyar bakin titi,sai da ya samu awa d'aya abakin titi bai samu abun hawa ba,Dan gari bai gama waye ba,wani adaidaita Sahu ya hango daga nesa ya taho ta inda yake,hannu biyu ya d'aga yana "wait wait ",adaidaita sahun sai da ya d'an wuce shi Kafin ya tsaya ,da sauri ya k'arasa inda adaidaita sahun yake yahau yacewa mai adaidaita Sahun " kofar nassarawa zaka kaini,"mai adaidata sahun bai ce komai ba ya ja suka tafi,juyawa yayi ahankali ya kalli gefensa,wata matashiyar buduruwa ce a zaune agafensa faraa ce tas Dan farinta har d'aukan ido yake,bak'ak'en kaya ne ajikinta,babu abinda kake gani sai hannyenta Dan kanta ma anad'e yake, ta kau da kanta tana kallon gefe, ,Abdulmajeed gabansa ne yayi wani irin fad'uwa tsoro ya rufeshi yana tunani ko aljanar ce ta biyoshi,matsawa yayi nesa sosai da ita gabansa na fad'uwa ahankali ya lek'a k'afarta yaga shima arufe,har a lokacin tana kallon gefe bata juyo ba,Abdulmajeed madubin adaidaita sahun ya kalla dake , saitin ta, Aljanar nan ya hango ta mudubi ta sakar mishi murmushi hakoranta amadadin jajjaye bak'ak'e ne ma su tsini Kamar allura,"wait wait anan zan sauk'a," Abdulmajeed yace agigice adaidaita sahun bai gama tsayawa ba ya duro daga adaidaita sahun ya sa gudu,mai adaidata sahun aguje shima ya bishi ya rik'e mishi Riga yana "ya zaka gudu kabani iya kud'in Dana kawo ka nan"Abdulmajeed doke hanunsa yayi yace " cikani Dan ubanka aljana ce acikin adaidaita sahun ka""Al me"? "Aljana" Abdulmajeed yace yana k'ara dibawa aguje,abin mamaki Mai adaidaita sahu ne gaban Abdulmajeed yana ta zuba gudu,duk Wanda ya tambayesu akan mai suke gudu,suna cewa aljana ce shima zai diba aguje.πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* Aunty Fannah kisa *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 8 *wanan shafin naki ne ke kadai Auntyna (Aunty sis* πŸ’ž) tnx for your love and support *Jinjinar ban girma gareku*, *Zauren* *Adda Bena* *MieMiebee* πŸ‘„ *Novels 2* *Musha karatu na Ybk inasan yanda kuke comment Kuna yi ina jin dadi dafatan babu wacce ta saki fitsari awando garin dariya* πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Wani dake zaune a can gefe da duk abinda yake faruwa yana gani adai daita sahun ya fara lek'awa Dan yaga ko wani abun ne aciki shi yasa suke gudu, babu abinda ya gani acikin adaidaita sahun ,da gudu ya bi su Abdulmajeed,ya kamo Mai daidaita sahun da tsabar gudu kamar ya tuntsira,Mai adaidaita sahun juyowa yayi afirgice, mutumin ya tambayeshi mai ya faru suke gudu,da sauri mai adaidaita sahun ya gaya mishi yana Neman kwace rigarsa daga hanun mutumin Dan tunda ga lokacin da ya tab'a mak'ala earpiece a kunensa ya shiga band'aki yana jin waka,yaji an sharara masa mari,yake tsoron aljanu ko sunansu yaji sai ya tsorata,mutumin kwantar masa da hankali yayi yace ya kwantar da hankalinsa ya lek'a adaidaita sahu babu komai,mai adaidaita sahun mukulin adaidaita sahun ya bashi yace masa Dan Allah ya taimaka masa ya d'auko mishi adaidaita sahun shi dai tsoro yake ji. Abdulmajeed sai da yayi nisa sosai ya tsaya gabad'aya ya gama tsorata,bus ya Tara ya hau Dan bazai iya kuma hawa adaidaita sahu ba,hankalinsa ne ya kwanta da yaga bus d'in acike,ajiyar zuciya ya ringa saukewa yana bin mutanen cikin bus d'in da kallo in banda zare ido babu abinda yake yi. Muhibba kuwa aranar barci bai ga idonta ba dan kasa barci tayi,tunda tayi aure bata tab'a raba shimfid'a da Abdulmajeed ba,gashi yau sabida tashin hankalin da masifa da Aljanar da ta taimakawa ta sata yasa ta zo cikin kanenta ta kwanta,kewar Abdulmajeed ne yabi ya dameta tana tunanin yau ko mai yaci,tasan tunda bai zo ba,bai kuma kira awaya ba tasan bak'aramin fushi yake da ita ba,dan ya d'auka karya take yi babu wata aljanar da take tsorata ta, agogo ta duba taga k'arfe biyun dare,wayar Nafeesa ta d'auko ta kuna, tayi dailing number Abdulmajeed,ji tayi yanata ringing bai d'auka ba,ahaka ta cigaba da kiransa,sai da ta gaji Dan kan ta ta ajiye wayar,kuka ta fashe dashi tana tunanin yana ganin kiran kin d'auka yayi,sabida Fushin da yake yi da ita,Dan tasan halin Abdulmajeed ya tsani yaga ya bata umarni ta tsallake,to ya zata yi, zuwa gidan shine mafita agareta Dan in ta cigaba da zama agidan aljanar Zata iya zautar da ita, ga Abdulmajeed yaki yarda da ita, dana sani ta ringa yi na Taimaka aljanar da tayi,yanzu Surayya da ta rufe k'ofarta bata bari aljanar ta shigar mata gida ba tana can hankalinta kwance babu abinda ya raba ta da mijinta,ahaka Muhibba ta zauna tana kuka tana tunani,sai da aka fara kiraye kirayen sallah ta mik'e ta nufi band'aki Dan tayi alwala. Abdulmajeed kuwa ana sauke shi ko canji bai tsaya k'arba ba ya nufi gidansu da sauri,a tsakar gida ya tarar da mahaifinsa mallam Isah yana shan koko da kosai,mahaifiyarsa kuma tana kitchen,Mallam Isah mik'ewa yayi da sauri da ya ga yanda Abdulmajeed ya shigo yace "Subhanallahi Abdul lafiya daga ina"? Abdulmajeed zubewa yayi a kasa yana sauke numfashi kamar Wanda yayi gudu,Hafsat Mahaifiyarsa itama lek'owa tayi tana kallonsa,Abdulmajeed bai ce komai ba ya cigaba da sauk'e ajiyar zuciya,Hafsa fitowa tayi daga kitchen d'in tace "Abdul ba tambayarka ake ba daga ina kake da sassafe nan?,ina Muhibbar? Mallam anya lafiya kuwa ka ganshi fa duk a firgice kamar Wanda aka koro" Hafsat tace tana k'ara kallan Abdulmajeed,"kai bana San Shashanci ana tambayarka lafiya kazo mana gida da sasafe ina ka baro iyalin naka?" Mallam isah yace atsawace. " Abba aljana ce ta sako in agaba ta hanani sakat,wlh jiya ban runtsa ba,yanzu ma Dana taho sai da ta biyoni,watak'ila ma yanzu ta biyoni gidanan" Mallam Isah da hafsa had'a baki suka yi wajen rafka sallati Mallam isah yace, "Aljana kuma bangane ba kayi min bayani sosai mai ya had'a ka da Aljana ina Muhibbar?share zufa yayi,ya fara basu labari,tundaga lokacin da Muhibba ta taimakawa Aljana ta shigar musu band'aki,zuwa lokacin da Muhibba ta tafi gidansu sabida tsorata ta da aljanar take yi,da yanda shima aljanar ta ringa tsorata shi har a adaidaita sahu,ya k'ara da "gaskiya Abba bazan iya cigaba da zaman gidanan ba Dan aljanar tana gidan,tashi zanyi daga gidan,wlh badan na ga aljanar da idona ba,na d'auka karya Muhibba take yi,Umma wlh baki ga aljanar ba, sallati Hafsa tayi tana tafa hannu tace "Ikon Allah DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO kun janyowa kanku masifa,ni Muhibbar ma nafi tausayawa abinda zai firgita namiji kamar Abdulmajeed sabida tsanin firgita da yayi rigar ma abaibai ya sako ta,lailai tashin hankalin da Muhibba tagani ba kadan bane," Mallam Isah cewa yayi "Hafsa ba dole Aljanu su ringa bibiyarsu ba,kin San irin sakacin Abdulmajeed tun Kafin yayi aure, babu irin fad'an da bana mishi,shine wasa da sallah,baya azkar yanda yaga kanensa nayi,kai tsaye zai shiga band'aki batare da yayi add'ua ba,ballantana azo gasu karatun Qurani ,yanzu da zaki tambayeshi yaushe Rabin da ya d'auko Qurani ya karanta wlh bazai iya gaya miki ba, Abdulmajeed ne zai ga abinda ya tsorata shi amadadin yayi addua sai dai ya kurma ihu, nan massallaci yaje bazai je ba,sai dai yayi sallar agida,ki gayamin ya aljanu baza su sako shi agaba ,duk wani Abu dazai kareshi daga sharrin aljanu ba yi yake ba,ko karya ne"? Mallam Isah yace yana kallon Abdulmajeed da ya sunkuyar da kai,Dan yasan tabbas duk maganar da mahaifinsa ya fad'a gaskiya ne,Dan Muhibba ma bata fiye sa dankwalli ba kullum gashinta a bud'e yake, tunani ya hau yi, yanzu akan wanan d'an k'aramin dalilin sai Aljana ta sako su agaba,maganar mahaifinsa ne ya katse masa tunanin da yake,Dan haka in zaka gyara halinka ka gyara,matarka ma naji ance zama take babu dankwalli Nura da yaje gidan kwanaki naji yana fad'awa mamanku,duk wata k'ofa abud'e take da aljanu zasa dame ku,da kake cewa zaka tashi kabar gidan kana da kud'in kama wani gidan ne, Dan in kana tunanin ni zan kama maka Nima nan bani da kud'i,gwara ma ka hak'ura da zancen tashi,zan sa mallamai suje suyi sauk'a agidan,kuma sai Ku daina sakaci da addua,insha Allahu zata daina tsorata Ku,gidan ya daina rabo da karatun Qurani,in bazaku iya karantawa ba kuringa kunawa, awaya,"nasiha Mallam Isah yayi mishi sosai ya bashi addu'oi,godiya yayi wa Mahaifinsa ya mik'e ya nufi d'akinsu da samarin gidan ke kwana Dan barcine a idonsa yana kwanciya ya hau tunanin babu yanda zaayi ya cigaba da zama agidan zai nemi kud'i ya kama wani gidan,da wanan tunanin barci yayi awon gaba dashi. K'arfe hud'u na yamma ya shirya ya nufi gidansu Muhibba a machine d'in kaninsa,yana isa gidan ya samu Mallam Hashimu a k'ofar gida yana zaune shi da wani makocinsu,parking yayi ya tsuguna har kasa ya gaishe su,suka amsa,Mallam Hashimu tambayarsa ya hau yi lafiya suke ta gwada wayarsa yana ringing bai d'auka ba,sai a lokacin ya tuna wayar na gida,karya ya mishi da wayarsa fad'uwa tayi shima yana kira ba a d'aga ba,Malam Hashimu ce masa yayi jiya Muhibba tazo ta fad'a musu abinda ke faruwa dama shi yasa yake neman shi ,anan yake fad'a masa yasa ayi musu sauk'ar Qur'ani a gidan,insha Allahu aljanu zasu daina damunsu,godiya Abdulmajeed yayi mishi,Mallam Hashimu yace ya shiga ciki bari yah kira masa Muhibba,d'akin da suke zance da Muhibba kafin suyi aure ya shiga ya zauna,Muhibba da bata Dade da fitowa daga wanka ba tana zaune agaban mudubi tana so ta shafa mai Abdulmajeed ne ya fado mata arai ta kasa shafa man,tana cikin Tunanin Abdulmajeed Mallam Hashimu ya d'aga labulen d'akin yace mata taje Abdulmajeed na kiranta yana d'akin yayanta,wani irin farinciki ne ya rufe ta,ta mik'e da sauri ta zura doguwar Riga ta fesa turaren Nafeesa tayi waje,tana zuwa k'ofar d'akin gabanta ya hau fad'uwa Dan bata san ya zasu kwashe da Abdulmajeed,sallama tayi ta shiga ahankali,Abdulmajeed kuwa Dama yana Shiga ya had'e rai,Muhibba sunkuyar da kanta tayi sakamakon kallon da yake jifanta dashi,"sannu da zuwa " Muhibba race tana k'ara sunkuyar dakai,Abdulmajeed wani mugun kallo ya mata yace " Muhibba Ashe baki da hankali ni zaki yiwa karya kice min tsohuwa ce tayi bara kika bata abinci Ashe aljana kika bud'ewa k'ofa ta shigar min band'aki,"Muhibba jikinta ne yafara rawa Dan bata tab'a ganin b'acin ran Abdulmajeed haka ba,cikin rawar murya tafara magana " Dan Allah kayi hakuri nayi kuskure wlh bansan aljana na bud'ewa k'ofa ba," Dalla rufemin baki wane irin gargadi ne ban miki ba akan kwashe kwashe ai gashi nan kin janyo wa kanki DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO,Dan babu abinda ya shafeni,haka zamu koma gidan ayau duk abinda tayi miki ke kika janyowa kanki,Dan da baki bud'e mata k'ofa ba babu yanda zata shigo gidan,Surayya da ta ganta ta kulle k'ofarta kinga tana can hankalinta kwance,tunda ya fara magana hawaye ke zubo mata,"Abdul wlh bazan iya kwana agidanan ba ni nasan mai nake gani," Abdulmajeed d'aga mata hannu yayi yace " wa ya janyo?babu abinda ya dameni jiya barcina nasha lafiya lau babu komai a gidana ke da kike bud'e mata k'ofa ke kike ganinta dan haka" shiru yayi sakamakon ganin aljanar nan daya yi abayan Muhibba ayanayi na ban tsoro ta gwalalo idonta gabad'aya tana kallonsa,jikinsa ne ya hau rawa ,cikinsa yayi wani irin murd'awa ya saki tusa mai shegen d'oyi ihu ya saki yana " kiyi min rai wlh karya nake jiya ban runtsa ba wayyo Allahna" Muhibba ido ta gwalo tana kallonsa cikin tsananin mamaki Dan ta waiga bata ga komai ba,Abdulmajeed ganin Ajanar ta nufoshi yasa yayi waje dagudu,sabida gigicewar da yayi d'akinsu Muhibba ya shige ya kullo k'ofar. [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 9 Muhibba itama waje tayo da gudu duk tabi ta rude,kicibis suka yi da Mahaifiyarta Dan itama agigice tafito daga palon data ga shigewar Abdulmajeed abakin k'ofar palon "Muhibba lafiya kuwa mai ya faru naga Abdulmajeed ya Shiga d'akinku da gudu," "wlh umma Nima bansani mai yagani ba muna cikin magana ya fito aguje," Muhibba tace a dai dai lokacin da take kwankwansa k'ofar d'akinsu tana ",Abdul lafiya mai ya faru ne,"? Abdulmajeed da sabida tsabar tsorata da yayi dan ayau Aljanar tafi masifar bashi tsoro,Dan fitsari ya saki ajikinsa,ya had'a gumi in banda rawa babu abinda jikinsa yake,sai da Muhibba ta k'ara kwankwasa k'ofar ya tuna Ashe a gidansu muhibba yake, wani irin kunya da tsoro ne ya k'ara rufeshi,ya kalli jikinsa da ya jike da fitsari,muryar Mallam Hashimu ne ya dawo shi daga tunanin da yake Dan Maryam k'ofar gida ta tafi ta gaya mishi abinda ke faruwa,"Abdulmajeed kunya ce ta k'ara rufeshi ya kasa bud'e k'ofar Dan fararen kaya ne ajikinsa,suna ganinsa zasu San yayi fitsari"Abdulmajeed ka bud'e k'ofar mana mai ya faru ne"? Mallam Hashimu yace yana k'ara buga k'ofar,bud'e k'ofar yayi ahankali yayi waje da gudu,Mallam Hashim ya rufa mishi baya, Muhibba sallati ta saki tana " Umma na shiga uku ko dai Abdul gamo yayi"? Maryam itama bayansu tabi tana sallati Dan itama Abdulmajeed ya tsorata ta Dan ta rasa mai yasa shi gudu, Abdulmajeed na k'ok'arin hawa machine d'insa Mallam Hashimu ya rik'eshi yace" Abdulmajeed lafiyarka kuwa mai yake damunka mai ka gani daya tsorata ka haka" da sauri yace " Wlh wanan aljanar ce ta sako ni agaba duk in da nayi sai na ganta,narasa mai yasa take bibiyata,tun jiya ta hargitsani, ta hanani zaman lafiya duk da ba ni na bud'e mata k'ofa bar,na rasa yanda zanyi,"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Aljanar kagani ka gudu kenan" Mallam Hashimu yace atsorace,"eeee wlh yanzu haka ma tana gidanku,yace yana k'ok'arin Tayar da machine d'insa, Muhibba a gigice itama ta fito waje Dan gabad'aya Abdulmajeed ya rudata,hangosu da tayi da Mallam Hashimu ne yasa ta fasa k'arasawa wajensu,Abdulmajeed kuwa hango Muhibbar da yayi a k'ofar gida ne yasa ya ja machine d'insa da gudu yatafi Dan yana jin kunyar karyar da ya mata,binshi su kayi da kallo, Muhibba ta k'arasa gurin Mallam Hashimu da ya daskare a tsaye,"Baba wai mai yace ma ya tsorata shi ne"? Muhibba tace cikin tashin hankali, ajiyar zuciya Mallam Hashimu yayi yace "Muhibba kuna cikin tashin hankali ke da mijinki kuna bukatar taimako," "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun Baba wai mai yace ma ko shima aljanar ce take tsorata shi" Muhibba tace hawaye na zubo mata "Zo mu shiga ciki Muhibba maganar bata tsayuwa bace" Mallam Hashimu yace yana shiga ciki bayansa Muhibba tabi da saurinta Dan ta matsu taji abinda ya tsorata Abdulmajeed tsorata haka,atsakar gida suka zauna Maryam itama ta matsu taji abunda ya tsorata Abdulmajeed,Dan har d'akin da suka zauna ta lek'a bata ga komai ba,magana Mallam Hashimu ya farayi bayan ya goge gumin fuskarsa,"Maryam Abdulmajeed da Muhibba na bukatar addua Dan sun had'u da sharrin aljanu,ba iya Muhibba aljanar ke tsoratawa ba,har da Abdulmajeed,yanzu ma haka ita ta tsorata shi shi yasa kika ga ya gudu" "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Muhibba da Maryam suka ce atare, "Baba yanzu har Abdulmajeed aljanar ke tsoratawa cemin fa yayi Jiya lafiya lau yayi barci babu abinda ya gani" "To haka dai yace jiya bai runtsa ba duk inda yayi sai yaga aljanar" Mallam Hashimu yace yana kallon d'akin da suka zauna Dan gani yake kamar aljanar tana ciki, "Yanzu mallam mai abin yi Dan bamu ga ta zama ba" "Ai yanzu nan zanje insamu Mallam Isah muyi magana Dan dole sai ansamu mallamai sun taya mu da addua,Allah ya rabasu da sharrin aljanar idan baha ka ba,haka zata cigaba da bibiyarsu Dan Allah dubi yanda Abdulmajeed ya firgice,dole Muhibba ta dawo gida,Dan abinda zai firgita irin Abdulmajeed ba k'aramin abu bane, Mallam Hashimu Sunan Muhibba ya kira dake ta risgar kuka yace "Muhibba duk yanda akayi har yanzu kina nan da jin wanan wake waken Dana hanaki,kina zama babu dankwalli akanki,kina shiga band'aki babu addua abakinki,Dan matsawar kina nan da wanan halin Dana sanki dashi dole aljanu su dameki" Muhibba d'agowa tayi da Sauri tana kallon Mallam Hashimu Dan duk abinda ya fad'a gaskiya ne Dan hasali ma in zata Shiga band'aki da wak'a take shiga,wayarta kuwa kullum cikin rashin chajin chaji yake sabida jin kid'a,ita da dankwalli kuwa dama sai dai in zata je unguwa,itama tunani ta hau yi yanzu akan wayanan 'yan dalilan sai aljana ta sako ta agaba,bata ga arna dake yawo ba dankwalli ga Karin gashi da suke da chineke suke Shiga band'aki su fito da chineke sai ita aljanar zata takurawa,ita bata yarda akan haka Aljana ke takura mata ba,To Abdulmajeed da ta takura wa fa shi kidan yake ji ko dankwalli shima zai sa ya d'aura kansa,sam bata yarda wanan dalilin ne yasa aljanar take bibiyarsu ba,mugunta ce kawai,Nasiha shima Mallam Hashimu yayi mata na inta San duk abinda ya zayyano tana yi to ta daina Dan duk hanyo yi ne da aljanu zasu iya takura mutum. B'angaren Abdulmajeed kuwa yana zuwa gida ba zarce ko Ina ba sai band'aki Dan Allah Allah yake ya k'araso gida,sai da ya samu Minti goma aband'aki kafin ya fito,wajen Mahaifiyarsa ya nufa dake Palo a zaune tana kallo,,sallamar da ya yayi ta amsa ta zuba mishi ido har ya zauna,ganin shi tayi awani hargitse, jiran tace " Abdulmajeed lafiya kuwa naganka haka yasu Muhibbar,"? "Umma ina fa lafiya Aljana ta sako ni agaba na rasa mai nayi mata,yanzu ma da naje gidansu Muhibba sai da ta biyoni,bansan mai nayi mata ba,ni bani na bud'e mata k'ofa ba amma ni ta sako agaba, yanzu a haka zan na fita tana tsorata ni sai dai kawai aga ina gudu,sai kace mahaukaci Dan babu Wanda yake ganinta sai ni kadai"',Abdulmajeed yace cikin tsanin damuwa da tashin hankali,Hafsa shiru tayi ta kasa Magana Dan abun yanzu ya wuce tunaninta,to wai mai yasa aljanar ta daina bibiyar Muhibba ta koma tana Bibiyar Abdulmajeed,kwantar masa da hankali tayi tace ya bari Abbansa ya dawo zasu nemi mallami suyi mishi bayanin abinda ke faruwa. Abu kamar wasa ya zama gaske,Dan babu dama Abdulmajeed yafita sai anga ya dawo da gudu,Dan Duk inda yayi sai yaga aljanar,dai dai da makaranta da ya shiga Dan ya koyar da dalibai sai da ta bi yo shi,yana tsaka da koyar da Maths ya hangota acikin dalibai wanan Karin a sifar yara ta bayyana,Abdulmajeed bai San lokacin da ya wurgar da chalk d'in hanunsa yasa gudu ba,daliban kuwa ganin Mallaminsu ya diba aguje yasa suma suka rufa mishi baya, makaranta tuni ta hautsine dalibai suka ringa tik'ar gudu a bakin titi,Jamaar gari hankalinsu ya tashi da su ka ga yanda dalibai da mallamai ke zuba gudu a bakin titi,Abdulmajeed da k'yar ya k'arasa gida, yana shiga gidan yaga aljanar abakin k'ofa a tsaye,ja da baya ya fara yi yana " wai mai nayi miki kike bibiyata?,mai kikeso awajena? Mai yasa kike San ki cutar dani? Wani mahaukacin dariya ta kwashe dashi cikin yanayinta na ban tsoro ta fara nufar shi tana " Abdulmajeed Baka ga komai ba tukuna ba dai ka iya wulak'anta mutane ba,zan koya maka hankali,gobe Idan kaga wani bazaka k'ara marmarin wulak'an ta shi ba, ahaka zan ta bibiyarka har sai ka kusa zaucewa", Abdulmajeed fad'uwa yayi kasa sumamme sakamakon ganinta da yayi akusa dashi. Readers wai shin wane wulakanci Abdulmajeed yayiwa aljana take bibiyarsa Ku biyoni sadnaf kusha labari apage 10 kuma na karshe insha Allahu kunsan na gaya muku labarin bashi da tsayi. [9/22, 12:18] Sadnaf: πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* πŸ™†πŸ™† *DπŸ…°GπŸ…° TπŸ…°IMπŸ…°KO*😭😭 *Written by* πŸ’…πŸ’… *SADNAF*πŸ’ž PURE MOMENT OF LIFE WRITERS _We don't just entertain and educate we touch the heart of the readers_p.m.l *TRUE LIFE STORY* Aunty Fannah kisa *#WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM* *#IG PML WRITERS* *#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035* *#http://maryamsbello.blogspot.com* PAGE 10 πŸ”š *Wanan shafin na sadaukarwa dumbin masoyana masu K'aunar novel d'in daga taimako hakika naji dadin irin k'aunar da kuka nuna min Allah ya barmu tare,kamar yanda na fad'a muku labarin daga taimako ba labari bane mai tsayi,gajeran labarine Wanda yake k'unshe da fadakarwa da kuma Nishadi,ba tsayin novel ke nuna had'uwarsa ba abinda yake kunshe dashi shi ke nuna novel ya had'u,Alhamdulillahi anan nazo Karshen novel d'in daga taimako kuskuren da nayi a ciki Allah ubangiji ya dubeni da idon rahama ya yafemin,darasin dake ciki Allah yasa Al umma su amfana*❀❀❀❀❀❀ *Whuuuuuuh Pure moment of life writers,takun ku daban yake Dana kowa ina mugun ji daku,domin da bazarku nake rawa Allah ya d'auka ka wanan Kungiya tamu ya k'ara had'a kawanunmu,kai kubani kid'an 'yan pure Asama,because they don't just entertain they touch,educate and melt the heart of the readers love you oll* ❀❀❀❀❀❀❀❀ _up up up pure moment may the sky be your limit_πŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒπŸ’ƒ *Aunty sis* πŸ’žKai kai kai kai kaiπŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚πŸ˜‚ Ni *Auntysis*πŸ’žnayi daria harda ciwon ciki Masha Allahu *Sadnaf* writer daya tamkar da dubu Ya salam Gaskia na dade banyi ma novel daria irin haka ba tin daga zamanin iffatu har zuwa yanzu.. *Sadnaf* mai salo kala kala Kinzo mana da sabon salo ma wannan karan. Farko munji tsoro sosai da sosai sbd yadda kike firgitamu har cewa nayi na dena karantawa sai daga baya kuma abun ya zama na daria ba kadan ba..gaskia kin samu daria kin sakamu nishadi mara misaltuwa..jz bil jannah All hakika yawan page na novel ba shi bane dadin littafi ko maanarsa ba, novel na maana da dadi akan abinda ya kunsa ne kuma ya koyar da al-umma wani muhimmin darasi na rayuwa. Komin kankantarshi kuwa. *Aljanu gaskia ne sbd Allah ne ya haliccesu harda surarsu cikin Al Qurani mai girma(suratul jinn)* *_sannan suna shiga jikin dan Adam musamman jikin da babu kariyar al-qurani da ambaton Allah._* _Ya kamata mu kiyaye duk wata hanya da jinnu zasu iya shiga jikinmu har su firgita mana rayuwa_ Duk da lbrn nan true life story ne amma nayi imani *Sadnaf* ta baje basirarta wajen tsara shi don yayi dadi kuma sakon da take son Isar ma jamaa ya iskesu ta hanyar da zasu ji dadin fahimta. Tabbas dunia makaranta ce, Abdul Majeed ya hadu da babban karatu mai kyakkyawan darasi na sharrin *wulakanci* dama haka rayuwa take,ka zauna kana wulakanci babu ji babu gani,insha Allahu wata rana sai Allah ya hadaka da gamonka tun a dunia. Allah ubangiji ya karrama dan Adam a cikin dukkan halittun da yayi na dunia. *Kai waye da zaka wulakanta shi kuma kayi tunanin Allah zai barka a haka* ?????????? Ya kamata mu saka hattara a rayuwarmu musamman haduwar nan da muke ta social media wadda ba sanin juna mukayi ba,bamu san dawa muke zaune ba, wata rana wani zai maka yanzu ko nan gaba,ina Allah zai hadaka da mutun nan gaba,wace irin alfarma zaka nema ko a nema a wajenka. Wadan nan duka abun dubawa ne idan mukayi laakari da cewa duniar kanta is a small place. Ya kamata mu rage wulakanta juna, mu fahimci juna mu zauna lfy kodon rashin sanin dawa muke zaune, *idan ba haka ba mutum yayi irin na Abdul Majeed* Sakaci da addua shine babban matsalarmu a yanzu tsabar yadda muka sa dunia a gaba. Ya kamata mu dage da Azkar na safe da marece don neman tsarin Allah akan dukkan wata azzalumar halitta. Zama ba kallabi,shiga bayi anyhow, yawan kide kide a cikin gd daga safe har marece duk hanya ce ta gayyatar aljanu,maraba da su da basu kyakkyawan wajen zama a gdnka da jikinka. Fatan alkhairi nake maki da zuriarki baki daya Allah yasa kifi haka Allah ya kara baseerah da kaifin ido. *Much luv daga Auntynki*πŸ’ž K'arar fad'uwar Abdulmajeed dasu Mallam isah suka ji ne yasa suka yo hanyar waje dagudu,abakin k'ofa suka ga Abdulmajeed akwance,sallati suka yi Mallam Isah yayi Sauri ya d'agoshi yana k'iran sunansa,Hafsa da sabida gigicewar da tayi bokitin ruwa ta kinkimo,ta fara watsa mishi,dogon ajiyan zuciya Abdulmajeed yaja ya bud'e idonsa ahankali,kuka ya fashe dashi yana " na shiga uku na lalace Abba aljanar nan tana so ta zautar dani,ni da mai tab'in hankali babu maraba,tace na mata wulak'anci haka zata yi ta bibiyata Abba Dan Allah Ku taimaka min Ku rabani da ita " Abdulmajeed yace yana k'ara fashewa da kuka,Hafsa da tunda Abdulmajeed ya fara magana itama take kukan Dan Tausayin d'anta take ji jarumi irin Abdulmajeed yabi ya rame ya susuce kamar bashi ba, Magana ta fara yi tana " Mallam Dan Allah mu kai Abdulmajeed gun wani Mallamin ba sai mun jira dawowar Mallam Saminu mai Rukiyya ba, idan muka ce zamu yi ta jiransa bamu San ranar dawowarsa ba gashi aljanar nan kullum sai ta tsorata shi,ba dama ya fita sai ya dawo da gudu,in bai suma ba zai tafi band'aki,wanan Masifar da mai tayi kama," Hafsa tace tana k'ara fashewa da kuka, "Hafsa bazaki gane ba,Mallam Saminu mai Rukiyya shi kadai ne zai iya raba Abdulmajeed da Aljanar dake bibiyansa Dan yana aiki da aljanu,amma duk inda zamu je sai dai aci kud'inmu yanzu kinga Mallam Jamilu da ya zo cemin yayi na kawo dubu ashirin ya rabashi da aljanar Dan ta aureshi,kiji fa,amma idan wajen Mallam Saminu mai Rukiyya muka kai shi kud'in sadaka kawai zamu bashi,ya kuma rabashi da aljanar,tunda kinsan shi yayi wa Ainau addu'a ta samu sauki" Mallam Isah yace cikin tsanin damuwa " Hafsa share hawayen da ya zubo mata tayi tace " to shikenan Mallam yanzu yaushe zaka koma Gidan Mallam Saminu mai rukiyyar,ka duba kaga ko ya dawo"? "Ai basai naje gidansa ba inada Numbers zan kirashi naji yaushe zai dawo,Abdul tashi mu Shiga ciki kaji Insha Allahu,zamu rabaka da aljanar",Mallam Isah yace yana mik'awa Abdulmajeed Hannu daya yi Shame shame akasa yana zubar hawaye,Abdulmajeed Mik'ewa yayi,suka shiga ciki,jin ana kiraye kirayen sallah ne yasa yaje yayi alwala ya nufi massallaci Dan tun daga lokacin da aljana ta sako shi agaba ya daina wasa da sallah Muhibba kuwa tundaga lokacin da Abdulmajeed yazo gidansu ya tafi take ta kuka gabad'aya ta rasa mai ke mata dadi,ta rasa mai yasa aljana take bibiyar ita da Abdulmajeed,laifin ne Dan ta taimaka mata,ahaka Muhibba ta wuni tana kuka,sai da ta ga ba kukan shine Mafita agare ta ba,addua ya kamata ta dage ta ringa yi Na Allah ya rabasu da aljanar ya karesu daga sharrinta,Da wanan tunanin Muhibba ta dage da addua ba dare ba rana akan Allah ya rabasu da Aljana dake bibiyarsu,ayau kwana hud'u kenan rabonta da Abdulmajeed ko awaya bata samunsa,hakan kuwa ba k'aramin damunta yake ba,shawara ta yanke zata je gidansu taji ko Lafiya. K'arfe uku na rana ta nufi band'aki tayi wanka ta d'aura alwala,tafito tazo gaban mudubi ta fara shiryawa Dan so take tana idar da sallar la'asar ta tafi gidansu Abdulmajeed,tana cikin shafa hoda ta hango wanan aljanar abayanta ta zuba mata ido tana kallonta,Muhibba duk da ta tsorata adduoi ta ringa yi azuciyarta ta d'aure ta fara magana Dan ta sha alwashin indai aljanar ta k'ara bayyana bazata gudu ba,zata tsaya ta tambayeta mai takeso awajensu take bibbiyarsu,cikin jarumta da rashin tsoro Muhibba bakinta d'auke da ayatul kursiyyu ta juya abun mamaki bata ga aljanar ba amma da ta juya ta kalli Mudubin aljanar na nan a tsaye,bata tsorata ba ,tace "mai yasa kike bibiyar ni da mijina? Mai muka miki ? Laifine Dan na taimakeki? murmushi aljanar tayi da ya k'ara sa ta zama abun tsoro hak'oranta mai kama da na allura ya bayyana cikin Muryar da tafi kama da sauk'ar aradu ta fara magana " baki min komai ba Muhibba,laifin mijinki ne ya shafeki,banida niyyar in cutar dake,hasali ma sanki nake yi,Dan gashinki na burgeni,wak'ok'in da kike sawa awaya yana sani nishadi,Dan abinda ke kawoni gidanki kenan,ba abinda yafi burgeni dake kamar in kika shigo band'aki naga kina d'an wak'a gashinki a bud'e ,ni sanki nake yi ,Mijinki ne dai ya min laifin domin ya wulak'antani,ya mareni akan nace ina sansa ,ya koreni Dan naje bara,ya zageni Dan naje gidansu neman taimako ,Dan haka sai na rama abinda yamin," Muhibba da jikinta ke rawa sabida muryarta ba k'aramn tsoro ya bata ba,tambayarta ta ke so tayi mai Abdulmajeed ya mata ta b'ace,addua tayi,ta cigaba da kwalliyarta,k'arfe hud'u saura ta fito daga gida ta nufi gidansu Abdulmajeed. Atsakar gida ta samesu a zaune Abdulmajeed na kwance akan tabarma,yana jin karatun Qurani,Mallam Isah da Hafsa na daga gefensa,sallamar da tayi suka amsa,Abdulmajeed ya d'ago yana kallonta,Dan ayanzu haka ita yake tunani Dan yayi missing d'inta sosai amma ba dama yaje gidansu Dan yana fita aljanar zata kunya ta shi ta sa shi gudu abakin titi ko ta sa shi sakin fitsari a wando,Muhibba durk'usawa tayi tana gaishe da su Mallam Isah idonta akan Abdulmajeed da ya tsura mata ido,gani tayi yabi ya rame kamar ba shi ba ,take taji hawaye na Neman zubo mata sabida tausayinsa da ya rufeta,Wai Abdulmajeed d'inta da baya tsoro ba yasan wargi,shine ya zama haka abun tausayi,amsa gaisuwarta su Mallam Isah sukayi suna tambayarta ya mutanen gidan,ce musu tayi lafiyarsu kalau,dama taji Abdulmajeed shiru ne kwana biyu shine tace bari tazo taga ko Lafiya,ashe ma bashi da Lafiya,Dan duk a tunaninta Abdulmajeed bashi da Lafiya,Hafsa cewa tayi ina fa lafiya Aljana ta sako Abdulmajeed agaba tana Neman zautar dashi,bashi da aikin da wuce gudu, da zuwa band'aki,tausayin Abdulmajeed ne ya k'ara rufe Muhibba tace musu ba abanza Aljanar ke bibiyar Abdulmajeed ba,laifi yayi mata,zaro ido suka yi suna kallonta, Abdulmajeed yayi sauri ya zauna yana tambayarta wane laifi yayiwa Aljanar da zata sako shi agaba,ajiyar zuciya ta sauke ta fara basu labarin abinda Aljanar ta gaya mata,ak'arshe tace " Abdulmajeed zaka iya tuna wacce ka mara Dan tace tana sanka,zaka iya tuna wacce tazo bara gidanku ka koreta?zaka iya tuna wacce tazo Neman taimako ka zageta"? Shiru Abdul majeed yayi,yana tunanin wa ya tab'a Mara dan tace tana San shi,sai da yayi tunani mai zurfi kafin ya tuna,ya tab'a zabgawa wata mari da ta dage tana sanshi, *WAIWAYE* Lokacin da Abdulmajeed ke zuwa high institution ,Dan gayu ne na k'arshe yana mugun ji da kansa gani yake yafi k'arfin ,yan matan makarantar,Dan aganinsa babu ajinsa a cikinsu,Dan ba laifi 'yan mata suna sanshi, hakan ne yasa ya d'orawa kansa Girman kai yake wulak'anta 'yanmata,abokanansa suyi ta mishi wa'azi,watarana suna zaune ak'arkashin bishiya suna hira da abokanansa,d'aya daga cikinsu yake basu labarin yarinya da yakeso a ajinsu,Abdulmajeed dogon tsaki yaja yace wa abokin na shi, yayi asara ya rasa wacce zaiso sai wanan bak'ar hallitar mumuna, Aljana da tafito shawaginta tana saman bishiya tana jinsu,jin abinda Abdulmajeed yace ne yasa ta rikid'e ta koma mutum, a mumuna siffa,Wanda sabida muninta bazaka so ka k'ara ganinta ba,gata bak'a wuluk,taho wa tayi daga nesa ta nufi inda suke,abokanan sa kuwa dama suna da kallon mata,hangota da suka yi daga nesa ne yasa suka fara gulmarta suna cewa basu tab'a ganin mai muninta ba,duk abinan da suke Abdulmajeed bai d'ago ba yana dai jinsu,ganin da suka yi wajensu ta nufa yasa suka ja bakinsu su kayi shiru suna mamakin wajen wa zata zo,tana isa wajensu ta saki murmushi tana gaishe su kasa amsawa sukayi sakamakon tozali da suka yi da hakoranta jajjaye da ya k'arawa fuskarta muni,Sagir ne yayi k'arfin hali ya amsa gaisuwarta yana tambayarta mai take nema awajensu,murmushi ta k'ara yi tace wajen Abdulmajeed tazo,Abdulmajeed d'agowa yayi da sauri Dan duk abinda ake kansa a sunkuye yake,tozali da yayi da fuskarta ne yasa yaji wani zafi a zuciyarsa,Dan arayuwarsa ya tsani munana,gani yayi ma ta raina mishi hankali yama zaayi tace wajensa ta zo,cikin had'e rai yace mata lafiya tak e nemanshi,batare da wani b'ata lokaci ba tace mishi sanshi take yi,abokanan Abdulmajeed k'yalk'yale wa suka yi da dariya da suka ji abinda tace,Dan sun San Abdulmajeed ya tsani mumunar mace,dariyar da suka yi ne ya tunzura Abdulmajeed ya zabga mata lafiyayyun mari guda biyu,yace shi sa'arta ne da zata ce tana sanshi,in taga level d'inta bata sani ba,zagi ya rufeta dashi,Aljana ta durk'ushe akasa tana kuka,zaginta ya cigaba da yi kamar zai daketa Dan ma abokanansa na rikeshi,mik'ewa tayi ta goge hawayenta ta ce Dan ta ce tana sanshi shine zai mareta,d'aga hannu zai k'ara marinta su sagir suka yi sauri suka rik'e mishi hannu,girgiza kai tayi tace yaje zai gani,da zagi ya bita har tabar gurin,tun daga lokacin Aljanar nan ta ringa zuwar wa Abdulmajeed a siffar mutane,yana wulak'anta ta,a almajira taje gidansu,yana tsakar gida yana cin abinci,Almijira ta ringa zabga bara tana a taimaketa Dana abinci yunwa take ji,sai da ta kai minti talatin tana bara,Abdulmajeed ko d'agowa bai yi ya kalleta ba,ganin da yayi ta cika mishi kunne da bara ne yasa ya mik'e afusace ya koreta yana ce mata mayya sai kace dole,Aljana kuwa ta k'ara zuwa gidansu daddare yana zaune a k'ofar gida wata tazo Neman taimako wai bata da kaya ataimaka mata,ganin Abdulmajeed bai kulata bane yasa ta fara k'ok'arin shiga gidan,tsawa ya daka mata yace mata ajiya ta bawa mutanen gidan zagi ya rufeta dashi na uwa na uba ya koreta,Aljana kuwa tana tafiya ta sha alwashin sai ta rama abinda Abdulmajeed ya mata itama ta zautar dashi,wanan kenan. Da sauri Abdulmajeed yace ya tuna wacce ya tab'a zabgawa mari,girgiza kai Muhibba tayi tace mishi "To ba mutum bace Aljana ce,sallati su Mallam Isah suka yi suna sun shiga uku Abdulmajeed kuwa jikinsa ya fara rawa Dan ya tuna tace yaje zai gani, Muhibba k'ara tambayarshi tayi ko ya tuna almajirar da tazo bara da kuma wacce tazo Neman taimako,?Abdulmajeed sai da yayi tunani mai zurfi yace ya tuna,nan ma Muhibba tace mishi Aljanar ce,, Abdulmajeed hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba,ya ringa kuka yana Dana sani,Mallam Isah kuwa jin fad'a ne tsakanin mutum da aljan ne yasa ya suri wayarsa ya k'ira Mallam Saminu mai Rukiyya,Mallam Saminu mai Rukiyya yace mishi dawowarsa kenan daga kauye,ai da sauri Mallam Isah ya ajiye wayarsa yace musu su zo su tafi wajen Mallam Saminu mai Rukiyya basu ga ta zama ba,ahaka suka dunguma suka nufi gidan Mallam Saminu mai Rukiyya ,basu samu ganinsa ba sai wajen Magriba,suna zama,yace suje suyi alwala su dawo,dukansu Alwala suka yi Muhibba kuwa sai addua take Allah yasa ya iya masu tsakani da Aljanar,bayan sun zauna yabi Abdulmajeed da kallo,gyaran murya yayi yace yasan mai ke tafe dasu, Dan Aljanar tariga su isowa wajensa ta gaya mishi duk abinda yafaru,Dan haka tace ya cire hanunsa a lamarin,Dan sai ta d'au fansar wulak'ancin daya yi mata,Sallati Suka yi gabad'aya Abdulmajeed kuwa ya saki tusa,kuka yasa yana ya taimaka ya bata hakuri ya daina ya tuba bazai sake ba,Mallam Isah da Muhibba ma rokon Mallam Saminu mai Rukiyya suka ringayi suna ya taimaka musu,ya bata hakuri,Mallam Saminu bai ce komai ba ya tashi ya shige d'akin sai da ya samu minti arbain kafin ya fito,ce musu yayi ya samu ta hakura dak'yar amma tace bata hakura gaba d'aya ba,zata rama nan gaba yanda masu hali irin nashi zasu daina,amma tace insha Allahu bazata k'ara bibiyarsu ba,Abdulmajeed hankalinsa ba k'aramin tashi yayi ba daya ji abinda Mallam Saminu yace,magana yake so yayi,Mallam Saminu ya dakatar dashi yace ya yi iya yinsa Dan haka yaje su dage da addua wanan kuma ya zame masa darasi,adduoi ya basu da shawarwari na hanyar da zasu bi su nisan ci kansu da aljanu,Godiya Mallam Isah ya mishi ya bashi sadaka suka fito. A takaice washegari Abdulmajeed yaje gidansu Muhibba ya d'auketa bayan dogon nasihan da iyayen Muhibba suka musu,Dan Muhibba ta gaya musu komai suka nufi gidansu,suna isa Muhibba ta duro daga kan machine ta nufi gidan Surayya Dan tayi missing d'inta sosai,Surayya dake band'aki tana wanka ta bar k'ofar band'akin a bud'e dan tunda daga lokacin da su Muhibba suka tafi gidansu take cikin matsancin tsoro ko an kwankwasa k'ofa bata bud'ewa sai kayi magana tasan wanda ke kwankwasa k'ofa da yake Muhibba ta kagu taga Surayya buga gidan ta ringa yi da k'arfi, tuni Surayya ta wurgar da soson hanunta ta diba aguje,tayi d'aki ta ma manta tsirara take ta fara wa innahu Sulaimanu,sai da taji muryar Muhibba tana ta bud'e mata sanan ta d'aura zani taje ta bud'e k'ofar,rungume juna suka yi,suna murnar ganin juna atsaitsaye Surayya ta ringa bata labarin abubuwan da suka faru da bata nan,da irin gudawan da Abdulmajeed yazo yayi a gidansu, Muhibba in banda dariya babu abinda ta ringa yi tana rik'e ciki,anan itama ta bata labarin abinda yasa Aljanar take bibiyarsu,Surayya tsoro ne ya kamata tana Allah ya karesu daga sharrinsu. A Daren Abdulmajeed a ango yake sak, Dan ya dirje Muhibba kamar kayan wanki to an kwana biyu ba ahadu ba, tun daga lokacin Abdulmajeed baya wasa da sallah da tashin dare,Muhibba kuwa kullum kanta a d'aure tana jin karatun Qurani. Bayan shekara biyu Muhibba na asibiti tana nakuda,Abdulmajeed hankalinsa yabi ya tashi,sai kai da kawowa yake Dan tun cikin Muhibba na karami Allah ya jarrabce shi da San cikin,bayan awa d'aya da rabi da aka shigar da Muhibba nurse ta lek'o tace Abdulmajeed yazo yaga jaririya matarsa ta sauka lafiya,da saurinsa ya nufi d'akin,har yana Neman yayi tuntub'e Surayya na biye dashi abaya,Gani yayi Muhibba ta kau da kanta, bata kallon inda jaririyar ke kwance,bai kawo komai aransa ba,ya nufi inda aka kwantar da jaririyar,abinda yagani ne yasa yaja da baya,jaririyar bak'a ce irin k'irin d'inan,gata katon kai ne da ita, muni iya muni wanan jaririyar ta had'a,cikin tashin hankali,ya d'ago zai yi magana,Muhibba tayi sauri ta ce yayi shiru,anan ta tuna mishi abinda Aljanar tace na zata rama,shiru yayi bai ce komai ba. A takaice duk Wanda yaga jaririyar da Muhibba ta Haifa sai ya girgiza,ahaka aka lallaba akayi suna Muhibba ta cigaba da kula da jaririyarta Dan ita bata k'i jaririyar ba,Abdulmajeed kuwa shima haka ya ringa ririta jaririyar Dan yasan abinda ya shuka shi ya girba. Ahaka Muhibba ta k'ara haihuwar yara hud'u amma kyawawa Zainab ce dai ta banbanta acikinsu wato ta farin, Dan muni kamar ayanka a b'oye,Abdulmajeed kuwa tunda ga lokacin ya daina wulak'anta mutane,duk wanan zafin kan babu. Anan na kawo karshen daga taimako kuskuren Dana yi aciki Allah ya yafemin. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels