An dauko wannan littafi daga shafin https://gistrog.com.ng ku ziyarci shafin na https://gistrog.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348141702912 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://gistrog.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348141702912 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://gistrog.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.gistrog.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/SuleimanUsmanKurya Twitter : https://twitter.com/Kuryaloaded_Ng Telegram : https://t.me/+Um7CIRmWSIU2NTg8 FITAR TSIRO Rufaida Umar Paid book: 500 Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB Phone number: 09034973645 Free page 1 Bismillahir Rahmaanir Raheem. Ina roƙon Allah yanda muka fara ya bani ikon kammala maku lafiya. Allah ya baku ikon riƙe amanar labarina, ku bar shi a inda ku ka gani ku karanta. Nagode da kauna, Allah ya bar zumunci. Ameen. *** Ta ɗaga idanunta tarr ta sauke saman mahaifinta wanda ke tsaye riƙe da belt yana huci, zuciyarta ta zo iya wuya ta soma magana a kausashe. "Wallahi sai dai ka kashe mu, amma har abada ba zan taɓa yarda da auren nan ba. Idan kuwa ka takuramin sai na tona asirin ƙazamin sana'arka wajen hukuma idan ya so ka tsire ni da raina!" Bai san lokacin da ya saki belt din ba, a razane wannan karon yake dubanta kafin ya maida duba ga Mahaifiyarta wacce ke kuka ga jikinta duk a fashe tsabar dukan da ta ci a hannunsa. Ya ƙara duban ɗiyarsa karo na biyu, babu ko digon tsoro ko fargaba a kwayar idanunta sai ma wani ƙarfin gwuiwa da jarumta. Da rawar murya ya soma magana bayan ya maida duba ga Mahaifiyarta. "Na'ima...ni kika tonawa asiri wajen ɗiyarki?" Yana maganar yana matsowa kusa da ita, ji ta yi numfashinta ya kusan ɗaukewa tsabar tsoro da tashin hankali. Tana kuka tana ja baya tana girgiza kai. "Wallahi wallahi ban sanar da ita komai ba. Ban san a inda ta ji ba. Haulatu, a ina kika ji?" Yarinyar da aka kira da Haulatu ta dubi Mahaifiyarta hawaye kace-kace saman fuskarta ga wani malolon abu da ya tokare mata wuya tsabar takaicin irin wannan shakkar da Ummanta ke yiwa Baban, mutumin da bai dauke su a komai ba face wani nauyin wahala da yake buƙatar yakicewa ta kowane hali. Sai ta ji gaba ɗaya ma ta kasa magana, tamkar wacce aka naɗewa harshe. Ta miƙe kawai ta shige ɗaki a fusace. Ta yi zaton zai ƙara kai hannu jikin Ummanta da zummar duka sai kuma ta ji shiru. Karshe ta ji an buga ƙyauren gidan da ƙarfi shaidar ya fice kawai sai ta haɗa kai da gwuiwa ta shiga rusa kuka. A wannan yanayin Umman ta shigo dakin, cike da tashin hankali ta hau jijjigata idanu waje. "Haulatu, faɗamin a inda kika san wannan baƙar sana'ar ta mahaifinki? Wa ya fadamaki?"  Ta ɗago tana sheshsheka ta ce. "Umma don Allah ki rage tsoron wannan mutumin. Ki yarda mu gudu mu bar masa gidansa. Wallahi idan ya dage zai aurar da ni ga Nazifi za ki neme ni ki rasa, ni zan tseratar da rayuwata tunda kin ji kin gani za ki iya rayuwa da shi." Ta yi shiru kawai tana duban ɗiyarta, ta kasa ce mata komai sai ruwan hawayenta dake fita gami da numfashin da take saukewa lokaci zuwa lokaci ga uban radadi da jikinta ke yi wanda ba domin ba a sabo da wahala ba sai ace ya ci ace ta saba. Haulatu ta ƙara duban Umma da rinannun kwayar idanuwanta yayinda take wani ɗan murmushin takaici. "Na sani, dama wannan shirun da kika saba yi a duk sadda na nemi mu gudu, shi za ki yi. Shikenan, Umma ki cigaba da shirun idan har kina ganin wannan ne mafitar da kika zaɓamana. Kin fi kaunar yanda nake rayuwa a makaranta ana tsangwamata saboda halayyar mahaifina, toh shikenan, zan cigaba da rayuwa da ke a unguwar da ko makwafta ba sa shiga harkar mu su na mana kallon mutunen banza duk adalilin mijinki, babu wanda ke ganinmu da mutunci sai ƴan daba dake dandazo a kowace rana a ƙofar gidan nan suna taya ɓera ɓari, su na ƙara yiwa mijinki kirari da Oga kansa yana fasuwa.  Zan cigaba da zama watarana nima na bi sahunsa na zama mai siye da siyarwar ƙwayo..." "Yimin shiru Haulatu! Rufemin baki tun ban zubarmaki da haƙora ba!" Tsawar Umman ta katse zantukan da take yi kusan ba'a hayyacinta ba, sai kuma jikin Umman ya yi sanyi, tana kukan ta rungume Haulatu a jikinta. Ita kaɗai tilo ɗiyar da ta haifa ban da cikin da mijinta ya dinga zubar mata har sau shida, samun Haulatu da ta yi Allah ne ya ƙaddara sai ta fito duniya. Itama Haulatun tana kuka ta rungume Umman, a duniya babu wacce ta fi ta a wurinta. Tana mata so da kaunar da har abada ba ta ji za ta iya nunawa ga wanda yake amsa sunan mahaifinta, mutumin da har abada ba ta jin za ta ba shi wannan ragamar. Tana da burin ace watarana ta kwatarwa Umman ƴancinta ta kuma ga ƙarshen wannan zaluncin da ya ke yi musu. Tauye haƙƙoki ba iyaka, sun shallake tunanin dukkan mai tunani, ana zama ne don ba wata inuwar da za'a raɓa a ji sanyi, wannan inuwar ta zama ta dole amma hakikanin gaskiya abin ya soma kai ta maƙura. "Umma don Allah kar ki bari ya aurar da ni ga Alhaji Nazifi. Wallahi mutuwa zan yi." Ta ɗago fuskar ɗiyarta tana share mata hawaye lokaci guda tana mai girgiza kai. "Ba za ki mutu ki bar ni ba Haulatu, in sha Allahu za ki yi rayuwa mai tsawo, za ki samu farin cikin da nake yawan mafarkinki da shi. Aurennan kuma ba zai yiwu ba, ina ji a jikina daga yau an bar maganarsa. Mahaifinki ba zai ƙara tayarwa ba." Haulatu ta runtse idanu, zafi take ji na gaske a kirjinta, duk sadda aka alaƙanta sunanta da shi takan ji tamkar ta tsire kanta, ita fa ba ta kaunar a kirashi da mahaifinta. Ta dai ji abin da Umman ta furta amma fa ba don ta gamsu ba sai ma ta shiga al'ajabin ta yanda Umman ta aminta ɗari bisa ɗari cewar an bar zancen gaba ɗaya.   Kiraye-kirayen sallar la'asar ne ya katse musu shirun, Umma ta miƙe ta fita don ɗora alwala yayinda Haulatu ta ja jiki ta jingina jikin bangon ɗakin.    Har Umma ta shigo ta shimfida abin sallah a gefenta ba ta sani ba, ta dube ta sosai, jinkirta lokacin sallah ba wani abu ne sabo a rayuwar ɗiyarta ba, wannan yana daga cikin abin da yake ci mata tuwo a ƙwarya, ta sani kamar yanda kakarta ta wajen uwa ta faɗi mata kafin mutuwa ta raba, sallah babu musibar da ba ta magancewa hakan yasa duk runtsi take matukar kokarin yi akan lokaci ta kuma dage wurin gani Haulatun itama tana yi, sai dai tana mamaki yanda koyaushe sai an sha fama kafin ta miƙe ta yi. Tana tsoron ace ta dauki wannan mummunan ɗabi'ar na mahaifinta wanda sallar ma ba ta dame shi ba. Hakan yana daga cikin dalilin da ta tsaya ka'in da na'in take kokarin ganin Haulatun ba ta yi wasa da zuwa Islamiyya ba. Wasu lokutan ta je, wasu lokutan kuma ta fake da cutar ƙarya ta lafe a gida.    "Haulatu." Kiran sunanta da ta yi ya sanya ta firgigit ta dube ta. Wani abu ya tsirgawa Umma a zuciya, ta danne ta hanyar haɗiye miyau. Da muryarta mai nuni da rauninta ƙarara ta ce. "Maza tashi ki ɗauro alwala ki yi sallah, wannan tunanin da koke-koken babu amfanin da zasu yi maki. Kinji ko?" Ta yamutsa fuska sannan ta miƙe gami da jan ƙaramin tsaki, ba ta ce uffan ba ta fice daga ɗakin. Idan da sabo da wannan halayyar ta komai aka ce ta yi tsaki, Umman ta saba, ita dai tana kokarin ganin yarinyar ba ta sauka a kan turba ba, daidai gwargwado tana yi mata gyara a wasu guraren na kalolin rashin kunya ko ace tarbiyya, amma ta sani ƙarfe ɗaya ba ya amo. Addu'a ita ke maganin komai. Da wannan ta share zantukan zucin, ta tayar da sallar. Kafin ta idar itama Haulatun ta iso ta zura hijabinta ta tayar. Umman ta riga ta miƙewa ta fice tsakar gidan don kama aikace-aikace. Ita kuwa Haulatu koda ta fito sai ta nemi wuri ta zauna gami da zubawa uwar idanu yayinda take kiciniyar kaɗa omo don fara wanke-wanke.   Doguwar mace mai hasken fata da kyawun dirin halitta don idan suka jera ba za ka ce ita ta haife ta ba sai dai ko a kirata da yayarta ko kuma ƙanwar uwa saboda irin matan nan ne masu baiwar jiki mai kyau. Ta tabbatar da ace su na gudanar da rayuwa ne ta daula ko kuma rufin asiri ko yaya, da Allah ne kadai ya san irin gogewa da tsantsar kyawun halittar da za'a ga mahaifiyarta da shi. Sai ta ji murmushi ya suɓuce mata wanda nan take ya mantar da ita matsalolin da suke ciki, ta tafi hasko kawunansu cikin rayuwar da take da buri da mafarki a koyaushe. Wai ace ga su nan a gida mai kyau da tsari, Ummanta na daga zaune ga ma'aikata sai hidima suke yi. Duk abin da Umman ke buƙata na jin dadin rayuwa babu wanda babu a gidan, ita kuma a lokacin ta zama ƙwararriyar lauya mai kwatarwa jama'a haƙƙoƙinsu, ta hasko kanta a kotu tana mai ba Ummanta kariya akan shari'arta da Mijinta, gashinan har an yanke masa hukunci su kuma sun samu ƴanci. Haka ta dinga saƙe-saƙe a cikin ranta har hankalin Umman ya kai gareta. Ganin yanda ta zubamata idanu tana murmushi sosai ya ba ta mamaki, kar fa damuwa ta taɓamata kwakwalwar ƴa. "Ke, tunanin me kike yi? Kallon na mene ne haka?" Wannan magana ta Umma ya maido ta cikin hayyacinta. Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya gami da ɗan lumshe idanu kadan. "Ba komai Umma. Ki taya ni addu'a, Allah ya cikamin burina." Umman ta murmusa. "Haulatu kenan, kin fi kowa sanin cewa kina sahun farko a cikin addu'o'ina na kowacce sallah da ma sauran ibadu. Sai kuwa iyayena da mijina." Ta ƙarashe murya a raunane. Haulat ba ta ce mata uffan ba jin sunan da ta ambata a ƙarshe, ba yau farau ba, ta ce mata itama ta dinga sanya shi a nata addu'o'in, Allah yana karɓar adduar mace ga mijinta kamar yanda yake karɓar na ƴaƴa ga iyayensu, sanadin hakan sai ta ga Ubangiji ya nufe shi da tuba kafin mutuwa. "Tashi ki duba ko sauran manjan nan zai ishe mu sai ki siyo mana gawayi a dafa sauran taliyar can a ci ko?" Haulat ta amsa, ta tuna dazun Baban ya yi tamola da kaskon da manjan ke ciki kafin ya soma sababin wai Alhaji Nazifi ya zo zance amma ta ƙi fita wajensa. Ita ya soma kai wa mari kafin shigowar Umman tsakiya ya sanya ya maida dukan kanta ta hanyar zaro belt ya hau jibgarta, acewarsa ita ta hana ta fitar. Allah ya taimaka ta iske akwai saura kadan, idan har za su gauraye taliyar a kaskon tasan zai wadatar tunda dama babu Maigidan a tukunyarsu, koyaushe da ƙulli yake shigowa gidan. Ko na indomie, ko nama da gurasa kodai naman kai, wasu lokutan kuwa kaza. Ya ci iyakar cinsa babu wanda zai yiwa tayi acikinsu. Ta ɗan ja tsaki, sannan ta shaida wa Umman akwai.  Naira ɗari ta miƙa mata, Haulat ta ɗora hijabi saman doguwar rigar dake jikinta na wata koɗaɗɗiyar atamfa ta fice daga gidan lokaci guda tana share ƙwallar da ta cicciko mata. Koda ta dawo da kanta ta hura ta ɗora ruwan taliyar, kafin nan tuni Umman ta kammala wanke kwanuka tana hada-hadar share tsakar gidan, ita ta karɓi sharar hakan ya ba Umman damar komawa ɗaki. Koda ta kammala sharar madadin ta  bi ta sai kawai ta maida tabarma ta zauna a tsakar gidan don ba ta son takurawa Umman, a wannan lokaci na tsakanin La'asar da Magriba, baiwar Allahn na iyaka kokarin wurin gudanar da ibada a wannan sa'in, azkar da karatun Alkur'ani da salati. Tana son ta dinga koyi da ita wajen ibada amma ita kam ta sani a yanzun son jiki ba zai bar ta ba wanda ta biyewa zuciyarta ta kasa yaƙarsa. A ranar dai har ta yi bacci Baban bai shigo ba, ita kuwa Umma koda ta soma gyangyaɗawa sai ta yi firgigit ta farka cike da fargabar da yadda Mijinnata zai shigo. Aikuwa sai gashinan wuraren sha biya da mintoci ana bugun gidan kamar za'a ɓalla. A razane ta miƙe jiki na rawa ta bude ƙofar dakin ta fito tsakar gidan, ƙarasawa ta yi ta buɗe mishi ƙofar ya shigo yana tangaɗi, toshe baki ta yi tana jin wani zafi a kirjinta. Ashariya ya watsamata gami da fadin. "Don ubanki shi ne ina bugun ƙofar ba za ki buɗe da wuri ba? Ko tare da ubanki Saleh mai kalangu muka haɗa kuɗin muka sayi gidan?" Ita dai Umma ba ta ce uffan ba bayan kaucewar da ta yi ya faɗa gidan har yana buge kai da bango. Ta ƙarasa da sauri ta rufe ƙofar da sakata. Tana kallo ya shige dakinsa, idanunta ta ɗaga tana duban farin watan Rajab na daren goma sha hudu da ya haske tsakar gidan, lumshe idanu ta yi hawayenta suka zubo tana mai ambaton Allah a ƙasan ranta. Daga ɗaki kuwa, Haulatu babu abin da ba ta tsinkaya ba, ta ƙara tura kanta cikin zanin rufarta ba tare da ta iya ko hawaye ba, ya ci ace ta saba da wannan baƙaƙen halayyar na mijin Ummanta kamar yanda take laƙaba masa. Wai ace mahaifin da ya cancanta da ba ka tarbiyya, shima babu tarbiyyar tattare da shi? Aikuwa bai cancanci ta kirashi Uba ba. Wannan abu na mata ciwo, ta tuna da tsiraru daga cikin ƙawayenta na makaranta idan ta je gidajensu, har ba ta kaunar ta fito saboda ganin irin kyakkyawar mu'amalar iyayensu da ma yanda mahaifansu ke takatsantsan da duk abinda zai ruguza tarbiyyarsu. Har sha'awa take yi idan ta ga budurwa na shakkar wai mahaifinta ya ji ta aikata abu marar kyau koda kuwa a misali ne irin na hirar ƴan makaranta, amma ita kuwa, ta sani babu wannan ranar cikin babin rayuwarta. Sanadin nata Uban ta rasa ƙawaye da dama daga kan boko har islamiyya, mafi kuma yawansu iyayensu ke musu iyaka da ita. Abin ya kai itama an soma yi mata ƙazafin tana shaye-shaye. Ga kuma maza yan iska da suke mata kallon kamar itama fanko ce don wasu ma sun sha nemanta da hujjar ai iyayenta bariki suka haɗu kawai itama ta basu hadin kai tarihi ya maimaita kansa. Abin ya kai ko neman taimakon abinda za su sa a baki ita da Ummanta ta je, sai an nemi ta bayar da budurcinta sannan a taimaka musu, wannan dalilin yasa ta gwammace ta yi suyar awara a gefen titi. Nan din ma dai ba ta tsira ba don ƴanniskan samari ke taruwa, idan ta yi magana a yaɓa mata baƙa, hakan yasa ta tattara ta daina. Sana'o'i dai na cikin gida in zasu shekara su na yi babu mai kallonsu, daga an fara siya kamar abin arziki sai a ɗauke ƙafa gaba daya wannan ne dalilin da yasa suka hakura da sana'a a unguwar, Ummanta ke zuwa can kasuwar kantin kwari tana waina da miya da rana, tana da almajirai masu kai mata kaya da kuma taimaka mata da wasu abubuwan a kasuwa, ita kuwa ta fice makaranta sai an tashi ne take zuwa wajen uwar nan ma bisa umarnin Umma sai ta sanya niƙaf ta rufe fuskarta, ba don tana son niƙaf din ba sai don hakan ta sani zai fi mata kwanciyar hankali ita kanta kuma ya zame mata katanga wurin ɓata gari yasa ba musu ta bi umarnin. Itama kuma Umman ba ta bada fuskar da za'a kawo mata zantuka marasa ɗa'a ba wannan dalilin yasa mafi yawa ke girmama ta, tsakaninsu sai gaisuwar mutunci da kuma hira ba na kaucewa hanya ba. Anan za ta taimakawa Umman su wanke abin da ya kamata a wanke, su shirya kayayyakin cikin ɗan sahu su koma gida. Kusan kudin sai tace Baban ake nemowa, don duk sadda aka dawo toh fa sai Umma ta ba shi nasa kason, wataran ma sai ya ce dole ta ba shi duka kudin zai biyata ana binsa bashi. Sun sha yin kwanaki ba su yi sana'a ba saboda Umman ta yarda da romon baka wani sa'in kuma tursasawar Baban ta ba shi kudaden. Haulat kan ji haushi ƙwarai har kuka take yi da daukar alwashin ba za ta ƙara bin Umman kasuwa ba tunda kudaden Baba take damƙawa. A ƙarshe kuma ta huce. Idan zaman babun ya ishe su Baban ya ƙi ba su kudin da zasu ci su sha, takan faki idanun Umma ta shiga dakin Baba wanda koyaushe yake garƙamewa (bai san ta zare mukulli daya cikin muƙullayensa ba) ta lalubo musu kuɗi a ma'ajiyarsa. A ranar ba ta ba Umma ba sai a washegari ta ce ai ta ranto mata ne a hannun Mamar ƙawarta don su koma sana'arsu idan an tara riba za ta mayar mata da kuɗin. Duk ranar da ta yi haka kuwa Baban zai zo ya yi ta ɗura ashariya yana tambayar wa ya taɓa kudadensa sai dai ba ya wani faɗan kirkin a zo a gani yake bari tunda ya sani shi kaɗai keda muƙullin ɗakin babu wanda ke shiga yana dai mamakin lamarin, tun Umma ba ta gane abin da take yi har ta fahimci idan sun rasa jari ga yanda Haulat din ke samo musu. Anan fa za ta dinga fada da nunamata illar sata, Haulat ko a jikinta don kuwa a ganinta raba arne da makami ma ai ibada ne tunda akwai haƙƙoƙinsu da yawa da bai damu da saukewa ba. Ranar da ya gano Haulatu ke ɗaukar masa kudi ta ci duka tamkar zai kashe ta. Daga wannan lokacin ne ya ci alwashin aurar da ita ga wani ubangidansa da yake yiwa bangan siyasa a baya, Ciyaman Nazifi. Ta runtse idanu sakamakon sarawar da kanta ya soma, tabbas idan ta ce za ta zurfafa cikin tunane-tunanen abin da ya faru da su a rayuwa sanadin mahaifinta toh lallai za ta kwana cikin azabar ciwon zuciya da na gangar jiki wannan ne dalilin da ya sa ta fidda komai a ranta ta yi addu'ar kwanciya bacci, tana jin Umma ta miƙe ta fita ta dora alwala ta dawo dakin ta rufe, a haka bacci ya dauketa. ***  FITAR TSIRO Rufaida Umar Paid book: 500 Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB Phone number: 09034973645 Free page 2 Cikin sauri ta shirya cikin kayan makarantarta na sakandire mallakin gwamnati dake a unguwarsu, ta kusan makara wannan dalilin yasa ko tsayawa shan ruwan shayi da ƙosan da Umman ta ajiyemata ba ta yi ba. A gaggauce ta kammala ta fice bayan ta shaidawa Umman ta ɗauki muƙullin gidan don ba za ta bi ta kasuwa ba yau, Umman na kwalamata kira akan ta zo ko a leda ne ta ƙullamata abin karin amma ko waigowa ba ta yi ba face sakin guntun tsaki. Babban burinta ta ganta a ajinsu tare da Hindatu kawai don ta labarta mata yanda suka yi da Mijin Umman. Ba ta ko damu da gwajin ajin da zasu yi ba a ranar don ko nutsuwar karatu ba ta samu damar yi ba, koda ta isa abin takaicin ba ta ƙaraso ba. Hakanan ta shige ciki ta fiddo ƙaramar dardumarta a jaka ta shimfida ta zauna don kusan rabin ajin a ƙasa suke. Har Malaminsu na koyon turanci ya shigo, babu alamar Hindatu, sai can ta shigo kamar an wurgo ta. Kayan jikinta duk sun yi ƙura saboda aikin shara da aka sanya ta matsayin hukuncin makara. Hasken fatarta kusan ya zarce na Haulatu don ita tana haɗawa da mayuka hakan yasa har wani ja take yi, sai dai daga ta buɗe ƙafafunta za ka fahimci hasken ba na halittar ba ce, ƙafar baƙiƙirin. Ba ta da tsayi kamar yanda ba ta kasance cikin jerin gajeru ba, tana da jiki da girman halittar mama wanda hakan ya ƙara mata girma, ta zama kamar wata uwar mata a cikin abokan karatun nata. Wannan ya sanya ƴan ajin suka fi yi mata laƙabi da BigMama. Ba ta daukar raini, ba ta da munafunci balle gulma, faɗa ko ba da ita ake yi ba, za ta shigarwa mai gaskiya ta buga rashin mutunci son ranta. An sha ba ta hukuncin zaman gida (suspension), hakanan an sha kiran mahaifiyarta. Da yawa na mata kallon ƴar mace don a hannun mahaifiyarta ta rayu ba don wai Babanta ba ya raye ko wani abun ba, ko kusa, ana cewa ma ko Uban bai ji dadin zama da mahaifiyarta ba, dakyar da karfin addu'a ya samu ya fitar da ita daga rayuwarsa. Ko gidan Uban ba ta zuwa balle ta saba da wani a can, ita kuwa Uwa ƴar kasuwa ce, ba ta can ba ta nan, sai ta fice daga garin har ma wasu lokutan ta tsallaka boda zuwa Nijar da zummar kasuwanci ta bar Hindatun a gida daga ita sai sauran masu zaman haya sai abin da ta ga dama take yi da taƙamar gidan mallakin uwarta ce, a haka dai uwar ke samarmusu abin rufawa kai asiri su ci su sha, su sanya sutura mai kyau daidai gwargwado don kuwa suturunta ya take na Haulatu. Burin duniya kuwa ta ɗora akan Hindatu, tana mata kallon wata kadara da nan gaba za ta ci riba a kanta. Ta sanya a ranta da zarar Hindatun ta kammala sakandire za ta yi cuku-cukun kai ta jami'a don ta ƙara wayewa da gogewa. Wannan yasa tarbiyyar Hindatun ya zama sai a hankali, babu wani ko wata da ya isa ya juya tanƙwarata hakan yasa ta ke cin karenta ba babbaka. "Ke! Tsayuwar me kike?" Malamin ya yi mata magana a tsawance, ta ɗan bishi da kallo tana ƙunƙuni, a duniya idan da wanda ta tsana cikinsu har da Malam Bukari, yana cikin wadanda ba su fiye ba ta ƙofar kawomusu wargi ba. Ta kauda kai ta yi ciki, sai da ta gama kallon mazauna saman bencinan da ba su fi biyar ba a ajin, ta watsa musu harara kafin ta yi ƙwafa ta zauna gefen Haulatu saman darduma. Malam Bukari na juya baya ciki bada umarnin a yi sauri a bada amsoshin tambayoyin da ya rubuta a allo a ƴar takarda, ta kalli Haulatu cike da ɓacin rai da murya ƙasa-ƙasa ta ce. "Wai ke meyasa idan kin zo ba kya tashi shegu daga benci ki kama mana wuri? Kinsan dai na tsani zama a ƙasa ko?" Haulatu ta wurga mata harara. "Toh sannu Uwani, tunda kin zo ai sai ki tashe su. Kinsan tun lokacin da nake jiranki ne?" Hindatu jin haka ta ɗan fiddo idanu kaɗan. "Haba? Ki ce da labari." "Akwai labari amma fa ba wani mai dadi ba. Bari dai wannan ya fice naga idanunsa a kan mu." Wannan bai sa Hindatu damuwa ba, kallonsa ta yi kadan sannan ta ja guntun tsaki bayan ta kauda kai tana mai karɓar takardar da Haulatu ta fillo mata a cikin littafi. "Ke dallah rabu da shi, ni faɗamin kawai, duk na matsu na ji me Mijin Umma ya aikata don nasan dai tatsuniyar gizo bai wuce na ƙoƙi." Ita dai Haulatu sai ta yi dariya kawai ganin idanun Malamin dai na kansu, a dole Hindatu ta bar zancen sai bayan ya fita ne ta tashi wasu akan tebur suka koma, ganin haka Haulatu ta basu aron dardumarta su zauna a ƙasa. Ba yadda suka iya face su karɓa sanin da suka yi idan ma sun ƙi wannan zaluncin da Hindatun da ta yi musu babu wanda zai iya taka mata burki. Koda kuwa an yi magana, toh fa abin da zai biyo baya bai wuce ta tare su a hanya ta ci zalinsu son rai ba. "Ina jinki." Cewar Hindatu. Hakan ya ba Haulatu damar fayyace mata batun Ciyaman Nazifi. Wani uban ashariya da Hindatu ta yi murya a ɗage, sai da ƴan ajin duka suka dube su. Ta banka musu harara. "Uban me ku ke kallo?" Sai kuwa suka kauda kai, wasu kuwa suka ja tsaki. "Amma mijin Umman nan ya cika azzalumin ƙarshe, wallahi kar ki sake ya tauyemaki haƙƙinnan. Ke me kike jira da ba za ki bi shawarata ku bar masa gidan ba?" Cikin rashin kulawa da kiran Baban da azzalumi da aka yi, Haulatu ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki. "Wannan matar ce za ta yarda mu bar gidan? Ai ko asiri ya yi mata sai haka. Amma wallahi kin ji dai na rantse, ko sama da ƙasa za ta haɗe ba zan bari ya cimma wannan halakakken burinnasa a kaina ba. Zan nuna masa nima na iya rashin kirkin." "Ato, idan ba haka ba ko mu zo mu sha biki." Faɗin Hindatu cike da tsokana tana dariyar shaƙiyanci, duka ta kai mata a baya, aikuwa ta gantsare. Haka suka cinye lokacin babu wani Malamin da ya shigo ajin da har aka fita hutun rabin lokaci. Dama sun saba, malamai ba su wadaci makarantar ba wannan ta sa ɗalibai da yawa suna zuwa ne kawai ba don suna samun wadataccen ilimi ko fahimtar abinda aka koyar ba yanda ya kamata. Zasu iya zuwa su wuni amma bai fi su sami darussa uku kacal ba. Wannan na ɗaya daga cikin illar da dalibai ke fuskanta a ire-iren makarantun na gwamnati. Hakan kan jawo nakasu da koma baya a harkar iliminsu. Sai ka ga ƴar sakandire babu turanci a bakin, hakanan shi kansa rubutun ba kowanne ya iya yanda ya kamata ba. Sassauƙar kalma sai ta gagari ɗalibi rubutawa. Haka suka cinye ranar a makaranta da darussan da basu wuce uku ba aka tashe su. A hanya su na tafe su na hira inda Hindatu ke ƙara rura wutar tsanar haɗin auren a zuciyar ƙawarta. Aikuwa haƙanta ya cimma ruwa don Haulatu sai da ta ji ƙarfin gwuiwa fiye da na baya akan shirin yin gudun fanfalaki don tseratar da kai daga wannan mugun nufi na Mijin Umman. Har suka zo hanyar da ta raba su hirar da suke yi kenan, ƙarshe dole suka bar sauran da zummar gobe Juma'a zasu hadu a gidan su Hindatun. Kai tsaye Haulatu gida ta nufa, tun daga nesa ta hango su zaune saman benci ƙasan bishiyar darbejiya dake ƙofar gidan nasu. Wani guntun tsaki ta ja, majalisarnan ta su Audu Maada ya tsaya mata a ƙahon zuci, babu wani a unguwar da bai san da zamansu ba. Duk wani hira na dabanci da ma bushe-bushen hayaƙi ya tattara ne a wurinsu. Rigima ba irin wacce ba'a yi ba a unguwar akan majalisar nan amma hakan bai sa ta rushe ba sakamakon ɗaurin gindin da suka samu daga shi Uban gayyar, wato Maigidan, inda ya ce ai ƙofar gidansa ce ba ta wani ba kuma babu wanda ya isa ya hana su zama tunda ba shirginsu suke shiga ba. Magana har wurin ƴan sanda sai dai kasancewar shi ɗin mutum ne mai idanu cikin gwamnati yasa babu inda ƙarar ta je aka yi watsi da ita. Wannan ce ta sa kowa ya zuba musu idanu kawai, iyaye na takatsantsan wurin ja wa yaransu kunne akan shiga sabgar su Audu Maada balle kuma su kai ga shiga gidan. Ta ƙara jan guntun tsaki gami da ƙara haɗe girar sama da ta ƙasa. Haka har ta ƙaraso ƙofar gidan, za ta gifta su ta ji sun soma maganar tasu ta rainin wayo inda ta tsinkayi muryar Ɗan Aljan ya yi wani busa da baki sannan ya ce. "Kai! Kai!! Ni fa wallahi Oga Maada ba don da manya a gabanmu ba, babu abin da zai hana ni farautar wannan babbar tsokar. Billahillazee tana..." "Kai dallah ware can! Kai daɗina da kai ka cika zalama. Ina kai ina shiga gonar Ciyaman? Ai babu mai ninkaya a wannan kogin idan ba shi ba!" Suka kwashe da dariyar zancen Duuna, Haulatu ta dube su ta watsamusu harara kamar idanunta za su faɗo sannan ta ƙarasa tura ƙofar bayan ta fidda kwaɗon ta shige, tana jinsu suka ƙara sakin wata dariyar ba ta ko saurare su ba don ya ci ace ta saba da haukansu da ba shi da magani. Maida ƙofar gidan ta yi ta rufe ruf sanin da ta yi ba su da kai, don su ce zasu shigo kai tsaye ba komai ne a wurinsu ba. Wanka ta soma yi ta sanya riga marar nauyi gami da ɗaura zani, ba ta tare da yunwa saboda Hindatu ta siyamusu wainar fulawa sun ci sun yi nak a makaranta, madadin ta yi sallah kawai sai ta shimfiɗe a tsakar gidan inda iska mai sanyi da daɗi ke bugowa, aikuwa nan da nan bacci ɓarawo ya yi awon gaba da ita. Ba ita ta motsa na sai da ta ji kamar ana faman dukan ƙyauran gidan, a dole ta tashi tana murza idanu gami da ƙarewa garin kallo, ga dukkan alamu dai yamma ta yi ganin yanda rana ta yi sanyi sosai. "Ina zuwa!" Ta furta cikin muryar bacci, tana jin sadda Garba ɗaya daga cikin almajiran Umma masu yi mata dakon kaya na fadin. "Tana ciki, yanzu tayi magana." Hakan ya fahimtar da ita Umman ce ta dawo. Koda ta buɗe, ta gan su tsaye ga uban manyan kuloli biyu da tarkacen kasko da sauran kayan girki. Ba wannan ba har da su Ɗan Aljan tsaye da yake bin ta da kallo kamar wani tsohon maye. Fadi yake "Ai Ranki ya daɗe dama na faɗamaki tana ciki, muna nan ɗazu ta shige. Sai dai ko ta ɗan harba duniyar Mass (Mars)." Ya ƙarashe da dariyar shaƙiyanci, ita kuwa daga yanda Umman ta haɗe rai tana kallonta yasa ta fahimci kuskuren da ta yi na fitowa kai babu ko kallabi sai zanin da ɗaura saman ƴar rigar, duk dai ga ta a birkice alamun mai bacci. Bayan ta shige ciki, yaran su uku suka bi bayanta da kayan suka sauke, sai da Umman ta sallame su ta ba su abinci da kudi sannan ta dawo kan Haulatu. Rai a ɓace ta ce "Kin yi sallar Azahar da La'asar?" Ta turo baki kaɗan. "Yanzu fa na tashi daga bacci, shi zan yi." Cike da takaici Umma ta girgiza kai. "Ki ji tsoron Allah Haulatu, wannan rayuwar da ki ke yi na rashin sauke haƙƙin Allah a lokacin da ya kamata babban kuskure ne. Kina tunanin matsalolinki za su warware alhalin kina yiwa Allah yanda ki ke so? Wato yau ma ba ki yi ko tunanin zuwa Islamiyyar ba ko? Kin kyauta, ki cigaba, nidai Allah na gani ina iyakar bakin ƙoƙar.." "Kai Umma, nifa ba cewa nayi ba zan yi ba. Haba don Allah, wannan masifar ma da kike ta yi ai sai ya ƙara cinye lokacin." Umma ta saki baki kawai tana kallonta har ta cika ruwa a buta ta shige banɗaki tana ƙunƙuni, yanke ta idan tana cikin magana wannan ba sabon abu ne a wurinta ba, amma kalmar tana masifa ya yi mata ciwo ƙwarai. Haulatu sau da dama idan ta yi magana kamar an buɗe masai tsabar rashin sanin abin da ya dace ta fadi. Sam, ba ta iya tauna harshe kafin ta furzar ba, komai ya zo mata hakanan ta ke jinsa daidai a wajenta. "Allah ya shirya." Abin da ta iya fadi kenan zuciyarta babu dadi sannan ta shiga tattara kayan, tun a kasuwa ta saka yaran sun wanke komai, maida su ta yi kawai kicin ta adana, abincin da ta rage musu da zasu ci, shi ta juye cikin madaidaitan kwanuka sannan ta shige daki don rage kaya ta watsa ruwa. Koda ta fito daga dakin, ta iske ta a tsakar gidan ta tayar da sallah bayan ta zura dogon hijabin Umman dake ajiye saman tabarmar. Ita kuwa bokiti ta ɗauka ta cika ta shige. Haka Haulatu ta yi sallolinta kafin ta miƙe ta dauko faranti, kai tsaye ta dibi shinkafa da waken ta sanya kabeji da mai a samansu. Tana cikin ci Umman ta fito, cikin sakin fuska Haulatu ta dube ta. "Lah Umma yau dai kin yi sa'ar mai, babu warin nan irin na rannan." Ganin yanda ko kallonta ba ta yi ba ta shige ɗaki sai ta sha jinin jikinta. "Ita kuma wannan ita da wa?" Ta yi tambayar a fili babu mai amsa mata, sai kuma ta ja guntun tsaki tunawa da ta yi mai yiwuwa rashin zuwa islamiyyarta ne ya yi wa Umman ciwo. Hakan yasa ta miƙe duk abincin ma ta ji ya fice a ranta don ita fa ba ta kaunar ta ga ko alamar ɓacin rai a fuskar mahaifiyarta. "Umma ni ce ko? Ban je makaranta ba, kiyi hakuri na dawo kaina na ciwo. Amma zan je ran Lahadi tunda gobe juma'a." Kasancewar makarantar hutun juma'a da asabar ake yi. Umman dai ba ta ce uffan ba ta zura doguwar rigarta ta shan iska, ganin dagaske dai ba za ta kulata ba yasa hankalinta tashi. Nan fa ta shiga ban hakuri har da su hawaye, Umma ta dube ta, dagaske ita laifinta ɗaya ta ke hangowa kanta, wato na ƙin zuwa makaranta, a ganinta shi ne dalilin fushinta. Ta ɗan yi shiru tana nazarin wannan wauta na ɗiyarta. Can kuma ta numfasa gami da soma magana. "Shikenan, amma ki sani kalmar da kika yi amfani da ita na ina masifa, ba daidai ba ne yiwa babba ita. Ba ma wannan kaɗai ba Haulatu, ko kaɗan bai kyautu ace babba na magana ka katse shi ba, wannan yana nuni da rashin ladabi gareshi. Sannan ba sau ɗaya ba, na sha nunamaki illar wannan tsakin da kike yawan yi ga babba balle kuma ni da nake mahaifiya gareki ba daidai ba ne, na lura ya riga ya zamar maki jikin da yanzu da kuma nan gaba zai iya haifar maki da tarin matsaloli, koda ace ba a wurina ba, za ki iya samun matsala da gidan da za ki je nan gaba." Cikin rashin fahimta Haulatu ta ce. "Gida kuma? Ni zan je? Wayyo Umma kin amince kenan mu bar masa gidansa?" Ta ƙarashe a ɗokance tana jin nesa ta matso kusa, burinta zai cika sai dai kuma girgiza kan da Umman ta yi ya sanya ta yi kamar ta ja tsaki sai kuma ta tuma ta saita leɓɓan da ta turo gaba da farko. Sosai ta lura da abin da ta yi niyyar yi, ta sani yarinyar sai a sannu za ta gyara. "Umma wane gidan zan je na bar ki?" Ta katse mata tunanin da ta tafi. Ta numfasa. "Ita mace ai ba ta zama ba ce, dole wataran ki tattara ki je gidan wanda Allah ya ƙaddara shi ne mijinki." Dariya sosai Haulatu ta sanya. "Kai Umma kina magana kamar a irin Indiyarnan mai fassarar Hausa. Aure manya. Ai fa, Iro dai zai ga wacce zai kai gidan wancan tsohon ƙwarton mai sa..." "Haulatu!" Tsawar Umman ya dakatar da ita. A zafafe ta cigaba da magana. "Meyasa kika da taurin kai da kunnen ƙashi ne? Mahaifinki kike kira da wannan banzan sunan wai Iro? Na fadamaki duk lalacewarsa shi din Uba yake a wurinki! Kar ki kuskura ki kai ni maƙura! Aure kuma ai dole wataran ki yi shi! Kin fi kaunar ki zauna kina rayuwa cikin waɗancan ƴan daban masu shirin farautarki a kowane lokaci? Idan ke har yanzu ba ki san meke maki ciwo ba, ni na sani!" Umman na kai wa nan ta fice daga ɗakin. Dagaske sosai Haulatun ta sha jinin jikinta, ko mene ne ta aikata, tana da tabbacin wannan faɗan ba iyaka nan ya tsaya ba, akwai wani abin da ke ran Umman da ta kasa fahimtarsa. Kusan ta mance rabon da ta ga bacin ranta irin wannan. Wannan yasa duk ta rasa sukuni. Daƙyar da suɗin goshi ta shawo kanta har ta sake bayan ta mata nasiha akan gyara kalamanta ko don gaba musamman ma na wannan sunan da ta sanyawa mahaifinta daga Ibrahim zuwa Iro. Haulatu dai ta amsa da toh za ta gyara don komai ya wuce amma har a zuciyarta ba ta jin yana da wani sunan bayan Iro, ko a makaranta ma da Muhammad take amfani matsayin sunan Uba. Umma ba ta hana ta ba tunda dai ana jika, ita ta san sunan mahaifin baban Haulatun ne sai kawai ta rabu da ita. *** Ya yi shiru yana juya cokali cikin kofin ruwan shayin dake ajiye saman teburinsa a ofis. Numfashi yake ja gami da furzarwa tamkar wanda ya ci gudu. Can kuma ya cire hannun ya ɗan bugi tebur har ruwan shayin na ɓata wasu takardun dake ajiye gefe. Hakan ya ɗan tsoratar da mutane biyun dake zaune a ofishin tare da shi. Babu wanda ya samu damar cewa uffan a cikinsu har sai da uban gayyar ya soma magana don kansa. "Kai Ɗan Mutuwa! Ba fa zan yarda da wannan soki burutsun naka ba! Ya kake ƙoƙarin haramtamin abincin da Allah bai yimin iyaka da shi ba?! Ka fito kawai a mutum, kai tsaye ka cemin ba za ka iya auramin ɗiyarka ba kawai!" Mutumin da aka ambata da Ɗan Mutuwa cikin maƙurar ladabi ya soma magana. "Haba Yallaɓai, na rantse ka fi ƙarfin dukkan wata alfarma. Ni ko Na'imar ka gani kake so ai zan iya sakarta ka aura ballantana kuma abin da yake ƙarƙashin ikona? Kawai dai akwai babbar matsala ne." Ya ƙarashe murya a ƙasa da tunanin ƙaryar da zai shirgawa Ciyaman ya samu su rabu lafiya. "Wace irin matsala ce kai kuwa Ɗan Mutuwa da har za ka kasa biyawa Yallaɓai buƙatar da ba ta fi ƙarfinka ba?" Cewar wani kakkauran mutumin dake zaune a kujera suna fuskantar juna. Ɗan Mutuwa ya sauke ajiyar zuciya, ya kula gaba ɗaya hankulansu na gareshi wannan ya sanya shi haɗiyar yawu daƙyar. "Mata maza ce." Abin da ya tsinci harshensa da furtawa kenan, babban burinsa wannan ta kawo ƙarshen zancen, ya kasa haɗa idanu da su duka. Kirjinsa na bugawa tamkar zai fito. Kalaman Haulatu ɗiyartasa ke amsa kuwwa a dodon kunnuwansa cewar da ta yi za ta fallasa dukkan sirrinsa. Toh kuwa da fashewar ruɓaɓɓen ƙwan nan baragurbi, wanda warinsa zai shafi mutane da dama, ai ya gwammace ya yi wa maganar auren kisan gilla ko ta wace hanya. *FITAR TSIRO* *©️Rufaida Umar* Paid book: 500 Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB Phone number: 09034973645 Free page 3 "Ɗan Mutuwa, ni za ka kawowa wasa?" Cikin dakiya ya girgiza kai gami da ƙara narkar da fuska kamar muminin da ya tuna kwanciyar kabari. "Wane ni na zo maka da wasa Yallaɓai? Wa ya ƙi ɗakinsa da ƙwan jimina? Ai bakin rijiya ba wurin wasan yaro ba ne. Tunku, ya san jibar da yake yiwa kashi, ba irinku ake zuwa gabanku da ƙaramar magana ba." Jin haka sai kuwa jikin Ciyaman ya yi sanyi, komawa ya yi ya jingina da kujerar gami da ɗan rufe idanu. Tabbas dole ya yiwa abin tufka kafin wankin hula ya kai shi dare. Bai so ace wai Haulatu, mace ta uku cikin wadanda ya so aure amma ba a dace ba. Ga dai tafarkin da bokansa ya ɗora shi a kai, ruwansa ne ya yi gaggawar aure nan da sati lafin guguwar siyasa ta motsa, ruwansa ne ya yi fatali da zancen ya ci karo da sakamako mafi muni a rayuwa. Sharuɗɗa biyu bokannasa ya ba shi, ɗaya shi ne ya nemi matashin namiji su aikata alfasha, ɗayan kuwa shi ne ya nemi budurwa marar kowace nakasa ta kowane ɓangare ya aura, wato sabuwa dal a leda wacce aka yi mata kyakkyawar shaida ta kamun kai. Muddin ya cika waɗannan sharuɗɗan bayan layu da ya sa aka binne a sabon gawa, to babu abin da zai hana shi cimma nasara da yin tamola da abokan hamayyar kujerar takararsa na ɗan majalisar dokoki na Jaha. Budurwar farko ya samu rahoton tana shaye-shaye, ta biyu kuwa tana biye-biyen maza. Idanunta sun bude da son abin duniya hakan yasa take iya komai don ta samu biyan buƙata. Sai ga Haulatu wacce ya samu shaidu sama da hudu a kanta ta bakin majalisar su Maada cewar ba ta tsayuwa da kowa ba ta kula kowa. Asalima haushin ubanta take ji da munanan ɗabi'unsa, itama ashe ya yi kura ce lulluɓe da fatar akuya duk da dai abin ba daga gareta ba ne.  "Ayi hakuri ranka ya daɗe." Faɗin Ɗan Mutuwa karo na biyu, Ciyaman ya sauke ajiyar zuciya bayan ya dawo daga kogin tunanin da ya afka. "Shikenan, kar ka damu. Kuturu da kuɗinsa ai alkaki sai na ƙasan kwano, zan samu daidai da zaɓina. Nasan inda zan nufa kuma." Suka dube shi su biyun duka, shi dai Ɗan Mutuwa bai fahimci abin a zo a gani ba, shi kuwa ɗayan mai suna Mahadi, kasancewarsa na hannun damar Ciyaman ya gane karatun don haka ya dubi Ɗan Mutuwa. "Kana iya tafiya." Ɗan Mutuwa cike da jin haushin irin wannan mulkin mallaka da Mahadi ke nunamasa a gaban Ciyaman ya miƙe yana ɗaure fuska ya kama hanyar fita, Ciyaman ya maido shi baya ta hanyar kiran sunansa hakanan ya dawo kirjinsa na ɗan bugu, duk a zatonsa ƙullinsa ne zai warware. Sai kuma ya ji saɓanin tunaninsa. "Ka je gobe war haka ka dawo ka karɓi saƙo hannun Mahadi." Ya dubi Mahadi karo na barkatai, shima Mahadin fuskarnan babu fara'a, shi fa bi yarda da zancen Ɗan Mutuwa game da ɗiyarsa kawai dai yana ji a jikinsa akwai wata a ƙasa. Dama can ba son tarayyar Maigidannasu da Ɗan Mutuwa yake ba. Babu yanda zai yi ne kawai saboda akwai hannun mutumin dumu-dumu acikin ɓoyayyiyar harƙallar da suke yi. Ga wata baiwa da yake da shi na saurin siyar da dukkan kayan da suka shiga hannunsa ya kuma ninka riba har fiye da yanda aka tsammaci zai kawo. Sai dai har gobe ba ya kaunarsa, kuma yana fatan ranar da zai kawo ƙarshen alaƙarsa da Maigidan duk kuwa da sanin cewa abu ne da sai ya zage damtse. Har ƊanMutuwa ya yi godiya ya fice bai bar watsamasa harara ba. "Yanzu mene ne abin yi Mahadi? Kai kasan komai dangane da sharudɗan Na Kan Tudu, wa kake ganin ya dace na nemi aurenta wacce aka yarda da salihancinta da kamun kai?" Ya gyara zama. "Toh Ranka ya daɗe nifa na gama dukkan lissafina, tunda dai duk inda aka bi ba ya ɓillewa, me zai hana mu koma can gida Rano mu samo daga cikin dangi." Ciyaman ya ɗan yi shiru kafin ya amsa. "Nayi wannan tunanin, amma kuma ba ka tunanin asirinmu ya tonu sanadin auren ta gidan?" "Ba zai tonu ba, ai da ace bamu da Boka Na Kan Tudu, shi ne zamu tsaya wala-wala. Ai ba banza ba, mallake yarinya za'a yi ya kasance sai yanda aka yi da ita. Ni dai a nawa ganin can ɗin ya fi rufin asiri kan ko'ina. Aka ƙulle bakin mutum me ya isa ya faɗi?" Dariya sosai Ciyaman ya yi, sai a lokacin ya samu nutsuwa sosai. Ya kuma ji daɗin samun mutum irin Mahadi, koyaushe idan ya kasa samun mafita na matsala, sai ya zo masa da mai kyau. Har ya soma hango kansa a ɗakin taro na majalisu na Jaha ana damawa da shi. A nan suka yanke ranar da ta dace su kama hanyar garin. *** Ɗan Mutuwa ya koma wurin aikinsa na kanikanci inda yake fakewa da guzuma yana harbin karsana. Zuciyarnan fari ƙal saboda ko ba komai ya kashe maganar da ta fi kowacce damunsa a ruhi. Ya iske yaransa na ta faman aiki, tun kan ya ƙarasa wurin ɗaya a cikinsu ya iso inda yake yana yi yana waigen sauran da ke faman harkar gabansu sannan ya juyo da muryar ƙasa -ƙasa ya ce. "Boss, tun ɗazu fa yaron Prince ke jiranka zai karɓi kaya." Jin haka ai sai wani sabon annashuwa ya ƙara lulluɓe Ɗan Mutuwa. Ba shiri suka ƙarasa, yaransa na gaida shi yana amsawa cike da kulawa, can kuma ya ƙarasa ga wata baƙar mota Honda Accord wacce ta sha baƙaƙen tinted. Ya kalli ɗan tsamurmurin saurayin dake tsaye gefen yaran wurin. "Afuwan Harɗo, na tsaida ka." Wanda aka kira Harɗo ya maida waya aljihu yana dan murmushi ganin hankalin kowa a kansu. "Ai fa, jira ya zama dole tunda Prince ba ya buƙatar kowa ya taɓa motarsa sai kai. Mu ƙarasa don Allah na soma gajiya dama." Daga haka suka yi dariya suka yi can gefe inda motar take. Suna isa Ɗan Mutuwa ya shiga mazaunin direba shi kuwa Harɗo ya zagaya ta ɗayan gefen, idan ka hango su daga nesa sai ka rantse babu wani abu da ke wanzuwa face makaniki da ya mayar da hankali ga duba mota da kuma mallakin motar. "Na fa jima anan, Prince sai kirana yake gaba ɗaya ya rasa control." Ɗan Mutuwa bai ko kalle shi ba ya amsa. "Na je ganin Maigidana ne. Yanzu dai wanne za ka karɓa?" "Tayoyi za ka ba shi da turaren wuta." Ya jinjina kai yana wani murmushi. "Ya ci sa'a kuwa akwai su." Daga nan ya zura hannu cikin takalminsa sawu ciki, ya fiddo wata ƙaramar leda mai ɗauke da Codein (ƙwaya) ya miƙa masa ba tare da hankalin wani ya kai kansu ba. Ya zura hannu cikin rigarsa ta ƙasa inda yake adana tabar wiwi cikin wata ƙaramar jaka da yake ɗaure ta a ƙugu, idan ba jikinsa ka goga ba, ba za ka taɓa sanin da zamanta ba, ya fiddo na adadin da suka nema ya damƙawa saurayin. Sosai Harɗo ya ji dadi. Nan take ya fiddo waya ya turamasa damin kuɗaɗe cikin asusunsa na banki da tuni ya jima da adana shi cikin wayarsa. Sai bayan sun fito daga motar ne, Hardo ya fiddo takardun kuɗi har dubu uku ya ba shi a hannu yanda idanun kowa zai gane mishi. Da haka suka yi sallama Ɗan Mutuwa ya koma gurin aikin nasu yana ta washe haƙora don ya sani yau kam akwai shagali. *** *FITAR TSIRO* *©️Rufaida Umar* Paid book: 500 Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB Phone number: 09034973645 Free page 4 Ta daki ƙyauren gidan sau uku da ƙarfi kafin ta shiga da sallama, mata biyu ne zaune a tsakar gidan jikin ƙofar ɗaki inda ɗaya ke yiwa ɗayar kitso sai kuwa yaro da ke shimfiɗe saman tabarmar, suka amsa mata fuska a sake. "Wai ke kam Haulatu nidai ban san dalilinki na son buga gidan nan kafin ki shigo ba." Faɗin matar da ke yin kitson. Tana dariya ta ɗan dubi kewayen su Hindatun ganin a buɗe ya ba ta tabbacin tana nan kafin ta ƙarasa ga matar tana mai ba ta amsa. "Ni haka na fi so ai Baraka, da wannan kaɗai ku ke gane ni ce na zo. Nasan dai duk duniya bayan ni babu mai muku wannan sallamar. Amaryar gidan taku har ta soma fita ne?" Ta ƙarashe tana duban ƙofar ɗakin da ke gefen na Baraka. "Inye, ka ga masu gida, wato har rabin jikin taki ta labarta maki." Daidai nan Hindatu ta ɗan leko daga jikin ƙyauren da ya yi musu katanga da sauran mutan gidan daga ita sai ɗaura ƙirji, kallo ɗaya za ka fahimci daga wanka ta fito. Caraf ta karɓe zancen. "Me za'a fasa to? Mutuwar ko kuwa hisabin? Ai ni kin tunamin ma ban labarta mata cewar tare da ni aka ci kazar Amarcin ba." Suka yi dariya. Ita dai wacce ake yiwa kitso kallonsu kawai take, tana dai jin labarin Haulatun a bakin su Baraka kasancewarta makwafciyarsu amma ba su taɓa haɗuwa ba sai a yau. Yarinyar da ba ta wuce sa'ar ƙanwarta  ba, kyakkyawa ta bugawa a jarida kuwa sai dai tana tuna ance iyayenta ƴan bariki ne sai ta ji ta ba ta tausayi ta shiga yi mata addu'ar neman tsari daga shiga halaka. Har Haulatun suka miƙe da zummar tafiya ɓangaren su Hindatu bayan sun gama caftarsu da Baraka, ba ta iya ta kauda kai daga kallonta ba har sai da ƙilu ta ja bau. Haulatu na ganin yanda ta ƙure ta da idanu ta yi dariyar mamaki ta ce. "Ke kam baiwar Allah wannan kallon fa? Ko dai na maki kama da budurwar mijinki ne?" Ta ƙarashe har lokacin fuskarta ba ta sauya daga yanayin baya ba, itama Hindatu na taya ta darawa ta ce. "Ke dallah, Lubabatu ce fa, na taɓa baki labarinta na ce ta haifi ƴan biyu har ma ɗaya ya koma? Wacce na ce maki ƙaninta ya na sona?" Hindatu ta ƙarasa maganar da murya mai kama da raɗa. Baraka ta saba da wannan gwaɓa magana irin ta Haulatu wanda har ka ɗauki zafi ita ko a kwalar rigarta don ba ta gane ta yi kuskure ba, Lubabatu kuwa sosai kalaman sun daki zuciyarta, ranta ya ɓaci. Kafin ta kai ga tankawa sun ɓace daga idanunta sun shige ciki. "Haulatu kenan, sarkin iya magana." Cewar Baraka. "Wannan yarinyar na yarda ba ta da mafaɗi, wai Baraka ba ki ji dakyau baƙar maganar da ta yaɓamin ba?" Ɗan murmushi Baraka ta yi tana mai sakar mata gashi ganin ta ƙi ba ta damar yin tufka mai kyau. "Kaɗan kenan in dai Haulatu ce, kwanaki can da ta zo daga na ce mata Haulatu wannan kwalliyar fa sai ina? Buɗar bakinta cemin ta yi ai gidanmu za ta je neman sadaka tunda Iro bai ba ta na karin kumallo ba ai gwara ta je wurin Idi. Hum, ke tun daga ranar na ɗauke mata wuta, kuma abin da zai ba ki mamaki fa wallahi wai ita wasa ne ta yimin, har da za ta tafi sai da ta shigo wurina mu yi sallama. Ni dai daga baya ta yi zuwa kusan biyu amma babu alamar ta san ina wani abu wai fushi, sai da ta tambaye ni don kanta ko ta yimin laifi ne, na nunamata kurenta, ke yarinyarnan har da su ƙwalla wai ita wallahi wasa ne ta yimin. Na nunamata iyaye ba abin wasa ba ne ta daina. Ta ce ai wai ganin Idin sunan kakana ne. Nace ko kakan kakana ne kuwa. Toh ban ce ba ta ƙara gwaɓamin ba amma dai na iyayen gaskiya ba ta kuma maimaitamin ba. Shi dai Baban nata Iro da ba ta ganinsa da gashi ko kaɗan kamar yanda na taɓa faɗamaki, shi dai ba ta fasa ba." Lubabatu ta girgiza kai gami da sakin huci. "Amma dai kam ta kiyaye harshenta idan kuwa ba haka ba nan gaba zai haifar mata da tarin nadama nan gaba. Ai tunda ta fito daga irin wancan gidan, fiye da hakan ma za ta iya aikatawa. Kai, Allah dai ya kyauta, ya shirye ta kuma. Ga dai kyau iyakar kyau masha Allah, amma ina gujemata faɗawa halaka nan gaba. Don idan har za ta cigaba da zama da wannan yarinya da uwarta, toh abin fa sai du'ai. Mutanen da idanunsa kw buɗe da son naira." Baraka cikin raɗa-rada ta ce. "Kinga matar nan ki rufamin asiri, dama ya lafiyar giwa balle an jefe shi da kashi? Allah dai ya mallaka wa mazajenmu gidajen kansu mu yar da ƙwallon mangwaro mu huta da ƙuda kamar ya yiwa su Habiba gyaɗar dogo suka tashi." Lubabatu ta amsa da amin suka yi dariya. Nan kuma aka dasa gulmar Hindatu da Mahaifiyarta da irin zaman haƙurin da ake yi a gidan dalilinsu. *** Hindatu kuwa, su na shiga ɗaki suka kwashe da dariya.    "Wallahi ke kam Haulatu ba ki da kirki, ni na tabbata Lubabatu ta ji zafin maganarki. Ke ko kadan ba kya saita bakinki ko?" "Au, daga wasa sai ta ji haushi? Toh ni kuwa ina nasan ma mijin nata da har abin zai mata ciwo?" Murmushi kawai Hindatu ta yi bayan ta shiga mulka a jikinta. Haulatu ta fisge robar. "Ni dallah ki faɗamin, me na fadi mai zafi da kike tunanin ban kyauta ba? Bari na je na ji daga bakinta." Da sauri Hindatu ta dakatar da ita ta hanyar riƙo gyalenta. "Ke wasa nake maki fa, ba komai. Ai ke da zuciya daya kika yi mata wasan. Yau fa baƙo zan yi." Haulatu ta koma ta zauna. "Waye zai zo? Tj ko Nazifi?" Tana wani murmushi da fari da idanu ta ce. "Ba ɗaya, wani sabon kamu na yi. Sati biyu kenan da Momi ta ba shi lambar wayata sadda ta je siyayya a shagonsa. Shi ne fa zai shigo yau." Cikin rashin fahimtar zancen ta ce "Ban gane ma Malama, yimin dalla-dalla. Shi ne duk jimawarnan ba ki labartamin ba komai ba?" Dariya Hindatu ta yi. "Toh ai jira nake na kama dahir. Ke Momy ce ta je kasuwar kwari sarin kaya shi ne fa hira ta yi hira har ake maganar mata yanzu ba su iya kula da gidajensu ba. Mutumin ya nuna ra'ayin shi fa yanzu aure ma yake son ƙarawa, aikuwa Momi ta ce masa tana da ɗiya sai dai ita karatu ta ke son na yi, ya nuna shi ba shi da matsala da karatuna, idan har nayi masa zai bar ni naga ko ƙarshen biro da takarda ne. Toh nidai wallahi daga waya naji ya burge ni don ba laifi ya iya tsara kalamai ga lallaɓa mace da tarairaya kamar kwai. Nikam muna zana SSCE zan shiga daga ciki." Baki galala Haulatu ke kallonta har sai da ta kai aya kafin ta magantu. "Kina cikin hayyacinki kuwa? Mutumin da ko ganinsa ido da ido ba ki yi ba? Ba ki san halayyarsa ba amma daga ganin sarkin fawa sai miya ta yi zaƙi? Wai ke ce dai me ikrarin sai mun shiga jami'a an dama da mu kuma mun ci karenmu ba babbaka?" Farr da idanu ta ƙara yi tana duban Haulatu sai kuma ta yi dariya. "Ke Haulatu, cemin ya yi fa gidana daban, kuma duk abin da nake so zan yi? Ke har mota ya yimin alƙawari. Kuma kike maganar bamu ga juna ba wa ya fadamaki, ya turomin hotunansa ta whatsapp nima kuma Momi ta bani kuɗi na je an min kwalliya na yi hotuna tun wancan satin fa na turamasa. Ba kin ga hotunan da nayi ba kwanaki a wayata har na ce maki biki aka yi a makwaftanmu? Toh ƙarya nake yi, adalilinsa na ɗauka." Haulatu jikinta ya ɗan yi sanyi, ba ta yi zaton a cikin amintarsu akwai wani abu da suke ɓoyonsa ga juna ba. "Yanzu har akwai wani abu daman da za ki iya ɓoyemin? To idan kin faɗamin mene nawa ciki?" Hindatu ta ɗan yi shiru, Momi ce ta zuga ta akan kul ta sake ta labartawa Haulatun. Tunda dama can ba son amintarsu take yi ba, ganinta Haulatu ta fi ta kyau ta ko'ina, ga fatarta luwai-luwai kamar mai cin kaza. Uwa uba ba ta shafe-shafe farinta daga Allah ne. Momi ta ce tsaf za ta iya yi mata ƙwacen saurayi, uwa uba kuma ta iya barikanci irin na gidan da ta fito. Ta kuma tuna akwai saurayinta da suka taɓa rabuwa akan Haulatun, tun ganin da ya yiwa Haulatun ya sauyamata, a karshe ya fito mata a mutum ya nuna Haulatu yake so. Aikuwa suka hadu su biyun suka ci mutuncinsa da ya jawo sanadiyyar daƙile alaƙar baki ɗaya. Ita ba ta san ma ƙaiƙayin bakin da ya kai ta yin zancen a yanzu ba. "Kiyi hakuri tawan, hirar ce ba ta zo kansa ba. Kin san idan mun haɗu zantukan namu ba sa ƙarewa." Murmushi mai ciwo Haulatun ta yi, tana ji a ranta akwai wani abun bayan wannan. To ko dai itama Hindatun tana mata kallon ƴar barikin ne irin wanda saura sa'anninta na makaranta suke kallonta? An sha kawo mata zancen wai ita ɗin usulin iyayenta bariki, don haka za ta iya ƙwacewa mutum saurayi ko miji wannan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa kowa na unguwar ƙara nisanta kansa da ita. Ba ta mance ba akwai wata Amarya da aka taɓa kawowa unguwarsu, har sun fara sabawa kawai sai gaba daya ta sauyamata, a ƙarshe ma ta fito mata a mutum ta nuna ita fa mijinta ya hana ta sjiga sabgarta. Kafin ta kai ga ficewa a gidan sai ga mijin ya dawo, daga yanda kuma ya tarbe ta cikin sakin fuska ta fahimci ƙarya ne. Sai daga baya ta ke jin wai Amaryar ce aka gargaɗe ta da shiga shirginta. Haulatu na kai wa nan a tunaninta ta ji kwalla sun ciko mata, ta yi gaggawar kauda su. Sai kuma ta miƙe tana gyara zaman mayafi sannan ta ɗauki ƴar jakarta. "Wai don Allah mene haka? Kina nufin ki ce ba za ki tsaya ku gaisa ba? Daga zuwanki har za ki tafi? Ke ko dai haushi kika ji?" Ƴar dariyar da ba ta kai zuci ba ta saki kafin tana mai janye yatsun hannunta cikin na Hindatun da ke ƙoƙarin dakatar da ita. "Haushi a na me? Ko ɗaya, kawai dai dama Umma ta ce kar na sake ta riga ni dawowa gida. Kuma kinga yamma ta yi, gwara na lallaɓa." Sakin ajiyar zuciya Hindatun ta yi, ita kam koda ba haka bane, za ta so tafiyar Haulatun gudun kar Momi ta dawo daga amsomata rubutun da ta tafi su yi kiciɓus, don a yau Momin ba za ta so ganinta ba musamman tunda babban baƙo zasu yi. "Shikenan, amma don Allah kiyi hakuri. Kinsan ba ma ɓoyewa juna komai ko? Na rantse to mancewa nayi." Ƙaramin dariya ta ƙara saki karo na biyu. Ta ya ya mutum zai mance da hirar wanda ya fi so da kauna? Kawai dai ta karɓi zancen yanda ya ta faɗi don a zauna lafiya. "Dallah can sai ka ce ni na haifeki kina wani faman damun kanki da rantsuwa. Kar fa ki damu na fahimceki. Bari na wuce nidai, sai Monday idan mun haɗu a makaranta. Ki gaida Momi." "Aa, bari na taka maki." Fadin Hindatun da sauri tana mai janyo hijabinta ta zura. Ita kuwa Haulatu tuni ta fito. A tsakar gidan su Baraka kuwa, tuni Lubabatu ta miƙe tsaye tana gyara goyon ɗanta da ta yi, sun kammala kitson. Ta yi musu sallama ba tare da ta biyewa Baraka da ke tambayar ko lafiya daga zuwa sai tafiya ba ta fice, Hindatu na biye da ita. A daidai ƙofar ta jawo mayafinta. Suka dubi juna, Haulatu cikin kokarin danne ɓacin ran ta ɗan harareta. "Wai ke Malama lafiya kike ta ja min gyale? Bana ce maki magana ta wuce ba?" Cikin karyar da murya Hindatu ta ce "Kin tabbata har a ranki Haulatu? Na fa san ba ki da riƙo." "To kin san ba ni da riƙon mene ne abin damuwa? Ni don Allah koma ciki ki shirya kar ki je ya yi maki zuwan bazata ya ganki hakanan ba kwalliya sai ɗaura ƙirji da hijabi. Big Mama, inji ƴan aji." Suka yi dariya. "Ƴan duniya ba. Shikenan to ki gaida Umman." Ta amsa da toh sannan ta yi gaba, Hindatu ta ɗan bi ta da kallo. Taɓ, wato da gaskiyar Mominta da ta ce Haulatu tsaf za ta sace zuƙatan maza fa dama, ga ta dai bilhaƙƙi ta ke tafiyarta amma sai mutum ya rantse da biyu take girgiza jikinta. Ta ji wani abu ya tsaya mata a rai mai kama da haushi da burin inama ita ce mai kyawun halittar. Sai kuma ta yi saurin kauda zancen gudun kar shaiɗan ya jefamata wani abun daban mai akma da hassada da kishi. Ta ji gwara ma da Haulatun ta bar gidan da wuri. *FITAR TSIRO* *©️Rufaida Umar* Paid book: 500 Account details: 7145096012 Ibrahim Rufaida Umar. FCMB Phone number: 09034973645 LAST FREE PAGE. Da daddare misalin ƙarfe tara tana kwance saman ƴar katifarta ta yi shiru gami da zubawa rufin kwano idanu. Dagaske Hindatu itama tsoronta take ji? Ashe ita ce kawai ke zaune da ita da zuciya guda? Kodai ta yarda da abin da mutane suke yi mata ƙazafi a kai ne? Ta juya tana fuskantar tagar ɗakin, idanunta fes akan  farin watan da ya hasko su. To idan ma hakan ne, ai bai kamata ta ga laifinta ba, komai da ke faruwa a rayuwarta silar tsatson da za ta fito ciki ne. Nan da nan hawaye suka wanke mata fuska. Ba zato ta ji hannun Ummanta a kan ƙafafunta.   "Haulatu, tashi zaune mu yi magana." Ta share hawayen gudun kar Umman ta gani sai dai tuni ta makara, zama ta yi jikinta duk a mace ta ƙurawa ledar ɗakin idanu wanda duk ya cinye ana ganin ƙasar dake a ƙasa. "Tun da yamma da na shigo gidan nan na fuskanci akwai abin da ke damunki amma ƙoƙarin nunamin kike babu komai. Kina da wacce ta fi ni ne?" Ta girgiza kai, kukan da ta ke dannewa a ƙirjinta kawai ta saki gami da faɗawa jikin Umma. Ba ta hana ta ba, sai da ta yi mai isarta ta yi shiru kafin Umma ta ɗago kanta. Cikin murya ta rauni irin na Uwa ta ce. "Faɗamin meke faruwa?" Ta labarta mata yanda Hindatu ta yi mata ɓoyon sabon saurayinta har tsawon sati biyu, da kuma nunawa Umma abu ne da ba su yiwa juna. Ita komai da ya dangance ta Hindatun ta sani. Ta ƙara da faɗin. "Umma na soma zargin ko dai itama tana guduna ne saboda ƙazafin da jama'ar unguwa ke yimin wai nima yar bariki ce zan musu ƙwacen miji ko saurayi idan naga fuska. Ko dai shi ne dalilin da Mominta ba ta taɓa nuna tana kaunar alaƙarmu da ita ba? Umma zuciyata na zafi idan na tuna wai iyayena ba ku da asali. Dagaske ne a bariki ku ka haɗu kamar yanda ake faɗa? Don Allah ki taimaka yau ki fidda ni a duhu." "Haulatu, kenan dama duk zaman da nayi da ke na baki tarihin aurenmu da mahaifinki bai gamsar da ke kin yarda cewa ni ɗin ba ni da wani aibu ba? Ban fadamaki ban san inda mahaifiyata take ba? Duk bayanan da nayi maki bai gamsar da ke ba?" Umman ta yi maganar cikin nuna dakiya a zahiri, amma can ƙasan ranta ita kaɗai ta san baƙin cikin dake dunƙule a ciki. Ta ƙara duban mahaifiyarta fuska cike da rauni ta ce. "Ai ban ce ƙarya kike yi ba Umma, kawai dai so nake na ƙara sanin wani labarin dangane da rayuwarki. Yanzu ace ko sunan dangin mahaifiyarki, babanki bai taɓa sanar da ke ba? Anya zan yarda da wannan?" Ran Umma ya ɓaci da irin kalaman Haulatun. Magana idan ta furta shi gareta kai ka ce da ƙawarta Hindatu ta ke yinsa. "Kalmar ƙarya da kika ambata a maganata da ke kuskure ne, kar ki sake ki ƙara gangancin furtawa ga wani ma ba ni ba. Ina jiyemaki yanda kike furta kalamai gatsal ga kowa, don Allah ki yi kokarin koyon magana, duk abin da na hane ki na kuma ci gyaranki a kansa, ki dinga matukar kokari wajen kaucewa maimaici a zancenki na gaba. Kin ji ko?" Ta gyaɗa kai kawai don ita fa ba ta ga abin zafi ko wani abu da ta furta ba daidai ba cikin maganarta. Ta fi tunanin kodai Umma ba ta son zancen ne ta wayance da cin gyaranta. Sai can kuma ta tsinci muryarta cikin sanyi ta soma magana. "A rayuwa sai kin kauda kai kin kima koyi toshe kunne. Ba komai ne mutum zai yi ya dameki ba, kar ki sake ki kasance cikin masu zargi, ki kyautatawa ƙawarki zato tunda ba ki taɓa kama ta da laifi makamancin wannan ba. Kuma mene ne ciki idan ta yi maki ɓoyon samarinta? Komai ne ya zama dole ki sani na rayuwarta? Ko kuwa dole ne ta san komai dangane da ke? To me za ki amfana da shi idan kin san labarin saurayinnata? Ki koyi kauda kai a duk abin da ba'a nemi ki sa baki ciki ba." Umma ta ɗan numfasa sannan ta ɗora zancen ba tare da ta ba Haulatun damar cewa kanzil ba. "So kike na yi ta maimaita maki baƙin tarihina? Mene ba ki sani ba a kaina yanzu? Kin san mahaifina Kalangu shi ne sana'arsa, mahaifiyata kuwa an ce tun ina ƙarama ta maido ni hannunsa ba ta ƙara waiwayata ba. Kauna tsantsa, babu irin wacce ban gani a hannunsa ba, ya yi iyaka kokarinsa na ganin ya tsaremin mutuncina bai bar ni na faɗa hannun ƴan barikin da ke farautana ba koyaushe. Haka na taso ya sanya ni makaranta boko da arabi, ban yi nisan kirki ba iyakata sakandire ya cire ni ya aurar da ni ga Mahaifinki. Abu uku na sani game da mahaifiyata, na farko sunanta Asma'u, na biyu kuwa, ya cemin daga babban gida ta fito, alokacin za'a yi mata auren dole. Ya kuma ce ƴar Katsina ce. Bayan wannan abu ukun, babu abin da zan iya faɗi game da ita. Shi kuma mahai..." "Ni bana son sanin komai a kansa. Iyaka wannan ya wadace ni." Ta katse mahaifiyarta cikin sauri da jin zafi a kirjinta, a duniya anya akwai wanda ta tsana sama da shi? Kai ba za ta ce ga shi ba. Umma murmushi ta yi mai ciwo, sai dai ta kasa cewa komai. Ta tabbatar muddin za ta nunawa Haulatun hoton da ta ke ɓoyo shekara da shekaru wanda Babanta Mai Kalangu ya ba ta sadda yake kwance cikin ciwon ajali, to fa a taurin kai irin nata, za ta iya bazama ta ce za ta Katsina nemo mata asalinta idan ya so komai zai faru ya faru. Tun a baya ta yi niyyar ta nunamata hoton wanda a bayansa hatta da cikakken sunan Asma'un akwai da na mahaifinta wanda ba ɓoyayye ba ne har a yanzun ma koda ace ba ya raye, sai dai yanda ta kula da zafin ƙiyayyar yarinyar akan Uban nata sai ta fasa. Ita kuma a ranta ta riga da ta ƙullaci mahaifiyarta Asma'u da har za ta iya yin watsi da lamarinta har haka, ta tafi ta bar ta a bariki saboda kawai son zuciya irin nata. Ba ta taɓa muradin zuwa inda take ba har a yanzu da take jin zai wahala ace tana nan a raye ciki duniyarnan. Wasu lokutan takan fiddo hoton ta zubamata idanu idan Haulatun ba ta gida, ta yi hawayen ta share sannan ta mayar ma'adani, har ma ta tsinci kanta da sanya ta cikin addu'a. Babu yanda ta iya tunda wannan na daga cikin haƙƙin iyaye akan yaransu. Ba ta fasa yi ba. Yanda uwar ta zurfafa cikin tunani, hakanan Haulatun ke fidda hawaye tana tunanin baƙaƙen ɗabi'un mutumin da ya kasance uba a gareta. Bugun gidan da ake yi ne kamar za'a ɓalle ƙyauren shi ya fargar da su. Eani guntun tsaki Haulatu ta ja gami da komai katifarta ta runtse idanu tana jin wani raɗaɗi a kirjinta, bugun da yake yiwa gidan ji take inama za ta iya zuwa ta ɗauki mataki a kai, sai dai inaa, ta san hakan ba mai yiwuwa bane. Tana jin fitar Umma daga ɗakin ta ƙara jan zani ta rufe fuskarta. *** Ya dube ta sama har ƙasa, ta kauce ya shigo ta rufe gidan. Shigewa ya yi bai ce mata komai ba ɗauke da ƙullin baƙar leda a hannunsa ko sannu da zuwan da ta yi bai amsa ba. Ba wannan ne farau ba. Ita dai duk sadda ya shigo ba a buge ba ta sani akwai dalili babba. Har za ta koma ɗaki ya dakatar da ita. "Ke, ki zo ina son ganinki." Umma ta ji zafin kalaman sosai, ta tabbatar ɗiyarta sai ta ji. Juyowa ta yi ta amsa. "Ina zuwa." "Kina zuwa? Har in ce maki ki zo ki cemin kina zuwa Na'ima? To ban baki iznin shiga ɗakin nan ba, ki zo ki shige yanzu." Ya faɗi cike da jin isa. Dama tun can Ibrahim Ɗan Mutuwa bai iya wani abu wai lallaɓa ta ba, ta ga dai yana yiwa ƴan barikinsa hakan don kafin ta haihu har gidan yake kawo su, idan ta yi magana ta sha jibga. Zuciyarta zafi take yi sosai, wai ace mutum ba ya tashi tunawa da kai sai idan ya ga dama? Ko kuma ya nemi ƴan barikinsa ya rasa? A cikin rayuwar aurensu babu abin da ta fi gujewa kamar haɗa shimfiɗa da shi. Ba za ta iya zama ya goga mata cutar da za ta nakasta mata rayuwa ba. Ta gwammace sai dai su yi wacce za su yi. Har ga Allah ta san babu kyau juyawa miji baya, amma fa ita kam miji irin na... Tunaninta bai kai aya ba ta ji an haɗe kanta da ƙyauren ɗakin ji ka ke kau! Ta bugu a goshi. Sam ba ta ji tahowarsa ba hakan yasa abin ya zo mata bagatatan. "Don ubanki mai kalangu ni nake maki magana kina ji kika mai da ni wani banza? Ai ko sadda na ci zamanina Ubanki ma bai isa na yi magana ya ji ya yimin kunnen uwar shegu ba ballantana kuma ke da kanki!" Idanunta a runtse cikin jin zafi da raɗaɗin maganganunsa. "Ka daina zagin ubana, na faɗamaka ba ya min dadi." Ta furta cikin dakiya, ya kuwa kai mata bugu a baya, hakan bai masa ba sai da ya zaro belt. "Ni kike gayawa na bar zagin Ubanki? To yau kuwa za ki ci uban naki Na'ima! Kuma ki kwana da shiri don aure zan ƙaro naga uwar uban da zai hana ni! Wato na taimaka Ubanki na rufamasa asiri na karɓi sadakar da ya bani shi ne yau ki ke nunamin ni Ibrahim ban isa na kiraki ɗakina ki zo ba ko?" Bai jira amsarta ba ya ɗaga belt ya shiga lafta mata, ihun ma ta kasa yi wannan karon yayinda idanun suka bushe ta kasa fidda ruwa hawayen. Haulatu dake kwance a ɗaki tana jin komai, zuciyarta na wani irin suya, jikinta ya ɗauki rawa saboda tsananin ɓacin rai. Wani irin kaɗawa idanunta suka yi. Tana ji ana laftawa Mahaifiyarta belt akan abin da ba ta ɗauke shi laifi ba, ba ta san lokacin da ta miƙe daga katifarta ba kamar yanda ba ta san ya aka yi sai tsintar kanta ta yi a waje, Umma har ta kai ƙasa tsabar duka, yana yi yana zubamata ruwan ashariya da gori har da kiranta shegiya marar asali. Caraf ya ji an riƙe belt ɗin, ya juya yana duban ɗiyartasa wacce hasken farin wata ya haske masa fuskarta. Ya rasa dalilin da yasa tun sadda ta yi mishi barazanar tona masa asiri yake ɗan jin shakkar yarinyar. Sai dai ai sunansa Ibrahim Ɗan Mutuwa, ba zai taɓa bari abin da ya haifa ya gagareshi ba a cewarsa don haka ya ƙara tamke fuska yana kallonta. Kafin ya samu abin fadi, Umma tuni ta mike ta riƙo ta. Cikin rawar murya take faɗin. "Ke, me ya fito dake? Me ya tashe ki? Sakar masa, na ce ki sakar masa mu je ciki!" Magana ta ke yi amma ina! Haulatu ko gezau, har lokacin jikinta babu inda baya rawa, hawayen kuwa zubowa suke yi kawai saman fuskarta. Kallon Uban take ido cikin ido, jira take ya ce tak! Ta maida masa mai zafi. Umma kuwa hankalinta ya yi masifar tashi, ba za ta so abin da Haulatun ke yawan faɗi ya tabbata ba a yau. Shakka babu za ta yi kaico na gazawa da ba ɗiyarta ingantacciyar tarbiyya, kawai sai ta shiga jerawa Allahu kirari a ƙasan ranta. Ta zuba idanu tana kallonsu duka har lokacin ba ta saki Haulatu ba. *** Nan na kawo ƙarshen na free, ga duk wacce ta shirya biya na a lahira, ta fitarmin da labarina. *** "Sakar min." Ɗan mutuwa ya furta bayan ya tattaro jarumtarsa. Sai a sannan ta samu zarafin magana, tana yi tana jijjiga hannunta haɗi da nasa dake riƙe da belt ɗin. "Idan na ƙi fa? Cigaba da dukan uwata za ka yi a kan idanuna? Daga inda ka tsaya nan za ka ɗora? Kai Iro! Bar ganin wai ina maka shiru ina kyaleka  ka na kai hannu jikin Mahaifiyata ka yi tsammanin ko tsoronka ne ya sa, ka yi kaɗan! Nace ka yi kaɗan na tsorace ka! Waye kai? Me ka taɓa yi mana a rayuwa? Shi babanta da ka raina har ka ke zagarmata shi, ka fi shi ne?! Ai gwara shi na tabbata bai kafa wannan mummunan tarihin da ka ke kafawa a yanzu ba kuma ko ba komai ta hanyar aure ya haifar maka ita. To ina maka rantsuwa! Daga yau, yanzu, duk sadda ka ƙara gigin kai hannu jikin Umma ka rubuta ka ajiye sai na yi shari'a da kai! Sai na fallasa dukkan sirrinka! Kai ni ba ka cika namiji ba idan a wannan daren ba ka tsinke igiyar aurenka da Umma ba! Har ka na mata barazana da za ka yi aure? Aurenka ɗin wofi! Ai ba ka daga cikin salihan mazan da aurensu zai girgiza zuƙatan mata! Da Umma ta cigaba da rayuwa da kai wallahi ni Haulatu na gwammace ta rayu da mahaukaci!" "Haulatu! Rufemin baki! Mahaifinki kike jifa da waɗannan baƙaƙen kalaman?" Ta runtse idanu ta ture hannun Umma daga kafaɗunta bayan ta saki belt ɗin, murya a ɗage yanda maƙwafta na kusa duk za su iya ji ta ce. "Ni ki daina kiransa mahaifina! Mai irin halinsa bai haife ni ba! Wallahi gwara na kira mahaukaci Ubana da dai na ba Ɗan Mutuwa wannan matsayin! A kansa kina ji kina gani ana kiranmu ƴan bariki, ana yi min kallon karuwa mai ƙwacen miji! Ana yi maki kallon marar asali mai fakewa da siyar da abinci tana aikata masha'a! A dalilin wannan (ta nuna shi da yatsa), na rasa dukkan wani gata! Ki faɗamin nauyina ɗaya da ya taɓa ɗauka tun faɗowa ta duniya?! Umma ki faɗamin ko Ibrahim ya taɓa taimaka ma ki da kuɗin siyan magani idan cuta ta kwantar da ni? Ba zan taɓa kiran wanda ya yi yunƙurin ya kashe ni tun ina cikin ciki da sunan Uba kuma mahaifina ba! Gwara min kare a..." Wani wawan mari Umma ta kai mata, maimakon hakan ya kashe bakinta sai ma ta riƙo hannayen Uwar ta ɗora saman wuyanta, da muryarta da ta dusashe tsabar kuka da ɗaga murya ta ce "Ki kashe ni! Don Allah Umma yau ki kashe ni. Na rantse na yafemaki har a gaban Mahaliccinmu. Amma don Allah ki kashe ni, na gaji da rayuwar nan Umma. Na gaji da kallon bariki da ake yimin. Wayyo Allahna!" Sai kawai ta durƙushe sakamakon wani abu da ta ji kamar ya tokare ƙirjinta, numfashinta na kai kawo, tun tana jin muryar Umma na faman kiran sunanta da ƙarfi har gani da jin nata suka yi ɗif. Umma ta tarairayo ta zuwa jikinta tana mai jijjiga ta gami da salati. Shi kuwa Gogan kamar wanda aka daskarar a wurin, shi dai Ibrahim Ɗan Mutuwa ake zazzagawa rashin mutunci ya kasa kataɓus? Dama akwai wannan ranar a tafe? Babban tashin hankalinsa dare ne, kuma yana da tabbacin makwaftansu sun ji komai. Ai kuwa bai kai ga gama tunaninsa ba ya ji ana bubbuga ƙofar gidan da ƙarfi. Ya san kururuwar da Na'ima ke faman yi na neman agaji ya yi sanadiyyar hakan. Da sauri ya shige ɗakinsa ya rufe, takaici da baƙin ciki suka lulluɓe shi. Wai har akwai ɗiyar da za ta kalli tsabar idanunsa ta zage shi tas ya kasa ɗaukar mataki? Ƴar ma ta cikinsa? Ya furzar da iska ta hanci da baka kafin ya yi kwafa na tunanin matakin da zai ɗauka kan Haulatun.  Ya kasa kunne jin da ya yi Na'ima ta buɗe ƙofar gidan. Makwaftansu maza su biyu sai kuwa matasan samari su ma duk ƴan unguwa sai ko mata da ba ta iya tantance ko su waye ba. Wannan ne karon farko a tsawon shekarun da ta yi a unguwar da ta ga fuskar wasu a gidanta masu suffar kamala. "Na'ima, lafiya kuwa? Meke faruwa da Haulatun?" Faɗin wata mata kakkaura tana ɗaga tocilar da ke hannunta da zummar hasko inda Haulatun ke kwance. Umma ta ji kuka ya ƙwace mata, cikin tashin hankali ta mata nuni da ɗiyarta. "Don Allah da soyayyarku da Ma'aiki (s.a.w) ku taimakamin kada na rasa ƴa ta." Ganin haka yasa suka danna kai ciki, nan da nan mata aka haɗa ƙarfi aka ɗaga Haulatu, wasu kuwa cikin tawagar da gulma ce ta kawo su, gidan suke haskawa su na ƙaremasa kallo. Hatta da belt ɗin Ɗan Mutuwa dake yashe a ƙas sai da suka gani. Nan da nan aka fice da Haulatu, Umma dakyar ta samu nutsuwar ɗauko hijabin wanda garin sauri ma na Haulatun ne ta zura sai takalmi ƙafa daban-daban ta mara musu baya. Ƙa'idar lokaci na masu ɗan sahun tuni ya wuce hakan ta sanya cikin gaggawa wani magidanci da gidansa ke kallon na su Haulatun ya fiddo motarsa aka hau. Daga Umman sai mata biyu sai ko mai motar da wani a gefensa. Nan fa wadanda suka yi saura a wurin suka hau maida zance, wasu na fadin ko dai cikin shege ta yi, wasu kuwa kira suke watakila ma shaye-shayenta ta yi har ta sha ya fi ƙarfin garkuwar jikinta. Maƙwaftan da suka fi kusa da su ne suka hau ba da labarin abubuwan da suka tsinci Haulatun tana faɗi. Wasu da yawa sun ji tausayi ya tsirga musu, hakan har ya zama sanadiyyar wanke Haulatu da Umman a zuƙatansu, yayinda ƙalilan ke ganin ai dama tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka kuma kowa ya siya rariya ya san za ta zubda ruwa, da ace mahaifiyarta ba ta biyewa kwaɗayi da burika ba tun farko har ya kai ta ga auren mutum irin Ibrahim Ɗan Mutuwa ba, da yanzun wani labarin ake ba wannan ba. Haka dai suka yi ta tufka da warwara kafin daga bisani kowa ya watse. *** Alhamdulillah, cikin ikon Allah bayan likitoci sun yi iyaka ƙoƙarinsu aka samu Haulatu ta farfaɗo. Bisa shawarar likitan, ya ce a daure a daina bari tana shiga damuwa mai ƙarfi irin wannan da ya janyo ta yi doguwar suma, irin wannan yanayin zai iya jawomata hawan jini da kuma ciwon ƙirji. Ƙarshe ya yi mata allurar samun bacci don ko da ta farka maganar ɗaya ce ta ke maimaita "Wayyo Umma, duniyar ta ishe ni. Ku bar ni na mutu." A dole don samun nutsuwarta ya yi mata, ya kuma roƙi duk a fita a ƙyale ta da mutum ɗaya mai jinyar. Duka aka fito har Umman da ta yo musu rakiya. Tana ta zubamusu godiya ga hawayenta ya ƙi tsayawa, duk su ne suka ɗauki nauyin asibitin, daga mai siyan magani sai mai biyan kuɗin gado. "Haba kar ki damu, kawai ayi fatan samun sauƙinta. A kuma kiyaye abin da likita ya ce. Allah ya sawaƙe ya ba ta lafiya." Cewar motar da ake kira Alhaji Shu'aibu Mijinyawa. Ɗayan kuwa Malam Bukar ake kiransa sai mai ɗan jikin Hasiya, ita ce matarsa da kuma bazawarar ƙanwarsa Murjanatu. Haka ta yi ta zuba musu godiya daga ƙarshe suka ce ta koma wurin Haulatu kar a bar ta ita daya. Da wannan ta juya su kuma suka tafi. A motar ma sai jimami da tausayi suke yi, nan mazan suka yi ta tattaunawa ta yanda aka yiwa gidan gaba ɗaya mummunan shaida. Sun kuma fahimci sosai Uwa da yarinyar na buƙatar taimako, ga dukkan alamu ba su jin dadin zama da uban. Haka dai har suka isa gida lokacin ma asubahi ta gabato. *** Umma har ta yi sallar asuba ba ta iya ta rintsa ba, idanunta a bushe sai ciwon kai, ciwon jiki kuwa dama ta saba da shi. Hannunta duk ya yi ja saboda duka. Ga shatin belt kwance. Yanzu tunaninta bai wuce makomar rayuwar ɗiyarta ba. Shakka babu ta tsorata da Haulatun da ta gani a jiya da daddare, tana kuma da tabbacin tarbiyyar yarinyar na dab da samun matsala muddin za ta cigaba da ganin waɗannan munanan ɗabi'u na mahaifinta. Ta san zai wahala ya fasa dukkan abin da ya yi niyya, wannan na daga dalilin da yasa tun a baya mutane ke kiransa da Ɗan Mutuwa. Shi fa ko za'a mutu baruwansa, inda ya sa gaba sai ya ga ƙarshensu abun kafin ya haƙura. Anya lokaci bai yi ba da za ta fice a rayuwarsa su gina tasu rayuwar a wuri na daban? 'Ba kya tsoron a cewa ɗiyarki ƴar mace? Kuma ina za ku je?' Wadannan tambayoyin a koyaushe idan za ta yi tunanin rabuwa da Ibrahim, su na cikin dalilin da dole take haƙura ta fasa. Ta zurfafa cikin tunani a gefe guda kuma bakinta na motsi tana tasbihi sai jin motsin Haulatu ta yi, cikin sauri ta miƙe ta nufi gadon. Haulatun ta dubi ɗakin da ta ke kafin ta maida duba ga Umma wacce ta riƙe mata hannu. Ɗan murmushin da bai kai zuci ba ta sakarmata, itama Umman ta maida mata martani. "Alhamdulillah, kin farka? Sannu, bari na kira likita." Da idanu kawai take bin Umma har ta fice daga ɗakin, can suka dawo tare har da wata Nos. Ya tambaye ta ko akwai inda ke mata ciwo, ta girgiza kai, ya gama gwaje-gwajensa kafin ya kalli Umma. "Masha Allah, komai na ta lafiya lau yake. Anjima zan sa a sallame ku. Yanzu tana buƙatar ta ɗan ƙara hutawa amma a samu ta sa wani abu a cikinta sai ta sha magani." Umma ta amsa da toh, ita duk sai yanzu ma ta tuna da wai ana cin abinci, yanzu haka za ta bar ta ita ɗaya ta koma gida ko ya ya? Cikin taimako na Allah, ba ta kai ga gama tantance abin yi ba, suka ji ana buga ƙofar ɗakin, bayan Likitan ya bada iznin a shigo, sai ga matar Alhaji Shu'aibu, Hajiya Mabruka tare da Mama Hasiya (kamar yanda yan unguwa ke kiranta), sai ko wata budurwa da ba ta fi sa'ar Haulatun ba riƙe da kwandon abinci. A bayansu kuwa wani ɗan matashi ne wanda zai girme wa Haulatun da kaɗan hannunsa riƙe da filas na shayi. Suka gaisa da Likita sannan ya fice tare da Nos. Cike da girmamawa Umma ta gaishe su fuskarnan a sake. Zuciyarta kuwa tamkar an mata albishir da gidan aljanna, wai yau ita ce tare da makwaftanta haka a lokacin da ta ke cikin tsananin buƙatar wani a kusa? Nan aka zauna, ita dai Haulatu kallonsu kawai take. Ta kai duba ga budurwar mai suna Bahijja wacce ba baƙuwa ce a wurinta ba don islamiyyarsu guda kuma ajinsu ma haka, sai dai kawai babu mai shiga shirginta, asalima ƴan cikin su Bahijja sun fi kowa tsanarta kai ka ce wata sabuwar tuba ce a cikinsu. A bakinsu ta soma jin ana mata ƙazafin ƙwacen saurayi ko miji. Ta kauda kai daga gareta zuciyarta na zafi, lumshe idanu ta yi yayinda take sauraron Umma na yi musu bayanin da likita ya yi. Babu wanda ta kula cikinsu sai amsa sannun da ake yi mata ta hanyar gyaɗa kai. Mama Hasiya ce ta taimaka mata ta miƙe bayan fitar saurayin siyo brush da toothpaste, ta shiga bandaki ta yi tsarki da alwala. Can ya dawo ya miƙawa Bahijja sannan ya fita, ita kuwa ta kwankwasa ƙofar bandakin, Haulatu ta leƙo ta karɓa fuskarnan babu ɗigon walwala asalima kallon fuskar Bahijjar ba ta ƙaunar yi. Ai har da ita cikin masu yi mata mugun ƙazafi. Bahijja kuwa duk jikinta ya yi sanyi musamman a hanya da Mama Hasiya ta ba su labarin duk abin da ya afku a daren har sadda suka ji kururuwar Umma. Wani irin tausayin Haulatun take ji yana tsirga mata. Sai da ta yi sallah, aka zuba mata ruwan shayi ta soma sha kafin su yi musu sallama su tafi domin duk yanda Mama Hasiya ta so Umma ta koma gida ta kimtsa ta dawo ta nuna ita sam ba za ta iya motsawa ba. Sun sha godiya sosai, Hajiya Mabruka har kudi ta ba su saƙo daga maigidanta. Wuraren biyar na yammacin ranar aka ba su sallama, ɗan sahu suka shiga zuwa gida. A hanya Haulatu sai tunani, Umma abin har ya soma ba ta tsoro don tun da ta farfaɗo ta ƙi yin wata maganar arziki ga kowa. Daga um sai um um sai kuwa murmushi mai kama da yaƙe sai gyaɗa kai. *** Ina labarin Ɗan Mutuwa? Tun bayan fitarsu ya ke ta muzurai shi ɗaya a ɗaki. Ya san dai ko mutuwa yarinyar tayi, Na'ima ba za ta ɗagamasa ƙafa ba. Koda dai ya kula itama ta samu bakin yi mishi musu yanzu idan ya yi magana. Fitowa ya yi a ɗakin bayan ya kwashi abin da zai buƙata don ya rantse idan ya bar gidan ba zai dawo ba sai bayan kwana biyu. Ƙunshin nama da gurasar ya shigo da shi a daren ko kallonsa bai ba, sai da ya ji unguwar ta yi shiru shaidar kowa ya shige gida ya fito ya miƙi hanya. Bai zarce ko'ina ba sai gida Hajiya Adama Loma.   Gida ne da ba ya rabo da mutane safe da dare, babu ma kamar da daddaren. Yana ɗaya daga cikin manyan gidaje a unguwar, babu ruwan wani da wani musamman da ya kasance wurin yawanci baƙi ne, wasu ƴan Lebanon ne, sai ko ƴan China da Hausawanmu waɗanda boko ya ratsa.  Kowa harkar gabansa yake yi babu takura. Itama Hajiya Adama ta mallaki gidan ne da maƙudan kuɗaɗen da ta ci gadonsu daga tsohon mijinta da ya kasancewa Balarabe ɗan Libya, bayan rasuwarsa ne ta ci gadon gidan, ta kuma zama Hajiyar kanta don jifa-jifa gidan ba ya rabo da gyare-gyare wadanda yawanci duka manyan Alhazawan da take cuɗanya da su ke yi mata kyautuka na bajinta. Ga uwa uba tana buga kasuwancinta na siyar da duk wani abin ado na jiki da ma na amfani na mata. Katafaren shago ta mallaka a wuraren Unguwar da ta ke wato Nassarawa GRA. Kadarorin da ta tara shi ya zama rufin asiri na asalin sana'ar da ta ke yi a ɓoye.   Ibrahim Ɗanmutuwa yana cikin mutanen da ba'a yi musu shamaki da shiga ko'ina a gidan na Hajiyar, sun yiwa junansu farin sani tun ma duniya na kwance. Kusan shekarunsu ɗaya a bariki, asalima shi ya kasance kamar wani abokin shawararta tun a baya. Uwa uba da shawararsa aka kashe mijinta ta sigar da ba kowa zai fahimta ba. Sosai ta ba shi nasa kason a baya sai dai kuma kuɗaɗe a hannun Ɗanmutuwa sam ba su zama. Haka ya dinga kashewa ƙadangarun bariki ba tare da ya amfanawa kansa ko matarsa da komai ba.    Haka ya nausa ciki har babban falon Hajiya Adama bayan Maigadi ya buɗe masa ƙofa. Ƴanmata ne da ba su fi shekaru sha biyar zuwa sama ashirin ba, su huɗu kwance ba su san ma inda kansu yake ba, kallon da ya yiwa kwalaben da ke wurin ya fahimci mankas suka yi. Kai tsaye ɗakin da yake yawan sauka idan ya zo nan kawai ya zarce sai dai ya ji a rufe gam! Koda ya ɗan kara kunne ya ji ana jan munshari ya ja guntun tsaki. Dole falon ya koma ya ajiye jakarsa gami da fiddo sigari ya kunna ya soma zuƙa, kansa gaba ɗaya tururi yake, shi fa har a sannan mamakin wannan ɗanyen aikin da ƴar cikinsa ta yi mishi yake. Wato don uwarta don ta samu ya bar ta tana shaƙar iskar duniya bai hallakata ba tun tana jaririya shi ne har ta ke da ƙarfin cin zarafinsa. Ya yi ƙwafa, haka ya tashi da kara uku na sigari kafin ya kora da ruwan codein ya sheme a saman three-seater na gidan babu ko damuwa akan sallah. (Wa'iyazubillah). *** Tana zaune a bakin ƙofar ɗakinsu ta yi shiru, daga ita sai vest da zani kan babu ko dankwali, gashinta baƙiƙirin marar tsawo sai cika tufke da ribbon, gefe guda ta ƙurawa idanu tana sauraron shirin da ake yi a gidan rediyo dake magana akan tarbiyya. Wanda Malamin ke nuni da muhimmancin tarbiyya da kuma haƙƙin yara akan iyayensu. Shirin ya sa ta shiga fidda ruwan hawaye, ƙarshe kuma ta ɓige da kuka sosai. Cikin wannan yanayin ta ji ana ɗan bugun ƙofar gidan. Ta sani Umma ba ta jima da fita zuwa sana'arta ba hakan ya ɗan ba ta mamaki. Ta kashe rediyon sannan ta goge fuskarta. Miƙewa ta yi har ta kama hanyar ƙofar sai kuma ta dawo da baya ta ja hijabin Umma dake saman igiya ta zura. "Ana zuwa." Ta furta cikin shaƙaƙƙiyar murya. Wacce ta gani kwarai ta yi mamaki, Bahijja. Za ta iya cewa tun soma wayonta ita kam ba ta taɓa ganin ƙeyar mutum ɗaya a  ƴan gidansu ya shigo ba. Tare suke da ƙanwarta Nasiba, ta yi fuskokinsu farin sani tunda islamiyya guda suke.   "Ko mu juya?" Faɗin Bahijja cikin zolaya tana ɗan murmushi. Itama sai ta tsinci kanta da maida mata martanin murmushin kafin ta shige ciki ta yi mata iznin ta shigo. Bahijja na gaba riƙe da kwando sai Nasiba biye da ita ɗauke da wata baƙar leda mai ɗan girma, tsayawa ta yi tana bin tsakar gidan da kallo. Ba wani babba ba ne, ɗakuna biyu ne sai kuwa wani gefe da ta ke zaton nan ne kicin sai ƙofar banɗaki daga ɗan lungu. Haka ta yi ta nazarinta har Haulatu ta shimfiɗa musu tabarma. "Wai dama tabarma ki ka shiga ɗaukowa? Wallahi sauri ma muke zamu je islamiyya ne, dama Mama ce ta aiko mu, tana maki sannu. Ga wannan kuma ta ce a kawo." "Lallai, wato kin fi ƙarfin ki zauna a tabarmar gidanmu ko? Ai shikenan. Ki ce mata da sauki, an gode." Riƙe baki Bahijja ta yi. "Kai Haulatu, ni ba haka nake nufi ba don Allah kar ki fassara ni. Ai ke kin sani na shiga ajin ƴan hadda. Kiyi hakuri, ai yanzu muka soma aminci, na tabbata sai kin gaji da gani na a gidanku." Haulatu ta ɗan taɓe baki. "Ni dai mai ƙwacen samari?" Maganar ba ta yiwa Bahijja dadi ba, cikin sanyi ta amsa. "Kiyi hakuri, ki yafe min duk abin da na furta mai muni gareki a baya. Rashin sani ne da kuma jita-jitar mutane. Amma ina tabbatar maki yanzu na fahimceki." Murmushi kawai Haulatun ta yi, ai ita ta sani babu wani mai fahimtar ta bayan uwar da ta haife ta. Kawai dai ta bi ta da to, haka suka rabu ta taka musu har bakin ƙofa tana ƙara jaddada saƙon godiya ga Mamarsu. Abinci ne lafiyayye, shinkafa dafaduka a wata cooler ɗin kuwa farfesun kaza ne. Sai leda mai ɗauke da sabulai na wanka da kuma wanki sai kuwa omo. Kai har da auduga na mata leda biyar da mayuka har kala biyu na shafawa. Shiru ta yi tana kallon kayan, karon farko da irin wannan abin arziƙin ya haɗa su da makwaftansu. Haka ta mayar da komai cikin ledar, ta ajiye su a gefe. Ba ta tare da yunwa don haka  ko sha'awar abincin ba ta yi ba. Ta gaji da zaman tunani ta ja guntun tsaki ta miƙe, gaba ɗaya zaman gidan ba dadi yake yi mata ba ta ji inama ta bi Umma zuwa kasuwa, ƙarshe kawai sai ta ƙara zura hijabin da ta cire ta fito ƙofar gidan ta ɗan tsaya. Yana ɗaya daga cikin abin da Umman ba ta sonta da shi sai dai tana ji hakan kaɗai ta fi buƙata a yanayin da zuciyarta ke ciki. Hankalinta ya kai ga su Maada waɗanda suka ɗan kalli inda take. Ta kauda kai gami da ƙara tamke fuska. Ta rantse wataran sai ta sa ƴan sanda sun kawomusu cafka muddin ba za su daina zama a ƙofar gidansu ba. Ta tsinkayi muryar wani cikinsu mai suna Kwarkwar ya buga wani ihu na ƙwararrun ƴan daba kafin ya ce. "Kai! Ni fa barewar can tana kashe ni billahillazi! Oga Maada! Ya kamata idan Ciyaman ba zai iya farautarta ba mu, ya bari mu shiga da ƙwarinmu." Maada ya ja tsaki yana fesar da hayaƙin sigarin da ya zuƙa. "Kai don tsohuwarka ina tambayarka inda Ɗan Aljan ya shiga kana yimin maganar banza da wofi. Ai inda amana ruwa ba zai dafa kifi ba, duk runtsi kar wanda ya ƙara kai idanunsa ga irin gidan Boss." Kwarkwar da sauran mutane ukun da ke zaune tare da shi, suka harɗe hannuwansu suna kirarin kowa ya bi. Can kuma Kwarkwar ya ce. "Nifa Oga ban dan inda Ɗan Aljan ya yi ba, na fi tunanin ya haɗu da Kashi (ƴan sanda) sun sa mishi lalle (sun kama shi).  Kasan fa shi Boss ya aika gidan Cuna ya kai tayoyi! To ka san halinsa, ya fiye Nakura (tsoro), ƙila ya yi saranda." Ya ƙarashe yana mai ƙamewa kamar wanda ke gaban soja. "Aikuwa da matsala. Amma ina zuwa bari na sallami waccan ƙaguwar." Faɗin Maada, Haulatu ta saci kallonsa ta gefen idanu, can kuma ta kai duba ga inda ya nufa, wata budurwa ta gani daga can kan kwana ta rufe fuskarta da niƙab. Waige-waige ya yi kafin ta ga ya sa hannu cikin aljihu ya fiddo wani abu da ba ta iya tantance ko mene ne ba, ita kuwa ta karɓa da sauri ta cusa a jaka ta fiddo kudi ta miƙamasa daga haka ta bar layin da sauri. Shi kuwa ya dawo ya zauna suka bi shi da sowa. Iya Haulatu mamaki ma abin ya ba ta, ba su ko tsoron ta tona asirinsu?     'Tsoron me za su ji tunda dai halinsu guda da mijin Ummanki?' Wani sashi na zuciyarta ya ba ta amsa.   Hirarsu ta ƙara ɗaukar hankalinta, magana suke yi akan budurwar. Maada ke labartamusu cewa ai yau taro ne da su na birthday hakan ya sa zasu gwangwaje. Ganin tun tana fahimtar kan hirar har ta bari ga wani jiri da ta ke ji sakamakon jimawar da ta yi a tsaye yasa dole ta juya ta shige gida gami da zura sakata. Yinin ranar sam bai yiwa Haulatu dadi ba, har Umma ta dawo ba ta da wani walwala. Sosai Umma ta yaba da karamcin Maman Bahijja. Sai da aka yi Magriba suka ci suka ƙoshi, tana da lura da Haulatun. Anan take sanar da ita kiran da Hindatu ta dinga yi a wayar Umman tana nemanta. Yamutsa fuska kawai Haulatu ta yi, ita fa mamakin Hindatu take har lokacin, ta kuma ci alwashin sai ta nunamata rashin jin dadinta a fili. Umma na so ta tambayi ɗiyar ko Mahaifinta ya shigo gidan, sai dai ba ta kaunar ta tayarmata da abin da ya wuce. Yau kwana biyu da faruwar al'amarin kuma tun sannan ba su ƙara ganinsa ba a gidan. Ga diyar, hakan ya fi nono fari har addu'a ta ke yi a ranta akan Allah ya sa mota ce ta kaɗa shi ya mutu. Ga Uwar kuwa, duk ta damu. Zuciyarta na mata ba dadi, ko ba komai uban ƴarta ne.   A ranar ma har suka kwanta bacci babu labarinsa, tun Haulatu na jin Umma na juyi da sintirin fita tsakar gida, har dai bacci ya yi awon gaba da ita. ***   Hajiya Adama, mace ce mai jiki sosai, tana zaune a ɗaya daga cikin luntsuma-luntsuman kujerun falonta. Ta ci ado har ta gaji kamar koyaushe don tana saka ran tarbar manyan Alhazai da za su zo zaɓar iri daga cikin sabbin ƴanmatan da ta tanada musamman domin su. Daga ita sai Danmutuwa a falon. Shi ne abokin mutuwarta kamar yanda ta ke faɗi "Ɗanmutuwa abokin mutuwata." Haka kirarinsa yake a wurinta. Duk wani sirri nata ya sani kamar yanda ta yi mishi farin sani. Ya labartamata duk abin da ya faru tsakaninsa da Haulatu da Na'ima.   Ta yi murmushi yayinda take cigaba da taunar inibin da aka sanyamata cikin wani ɗan bowl na tangaran. Dama ta lura tun zuwansa daga yanda yake ta faman yiwa kansa mankas wata damuwar ce sai dai ba ta ɗauke ta mitsitsiya hakanan ba.     "Ita Haulatun ba za ka iya kawomin ita mu gaisa ba?" Shi ne tambayar da ta jefamasa ba tare da nuna wata damuwa akan cin kashin da yarinyar ta masa ba a nasa tunanin. Ya yi shiru, sai lokacin ta dube shi dakyau har sannan murmushin bai bar saman fuskarta ba.     "Ina fatan ka gane inda na dosa?" Ɗanmutuwa ya gyara zama bayan kora ruwan lemun da ke ajiye saman tebur a cikinsa. Ya dubi Hajiya Adama. "Wannan tunanin shi ya yi silar da ki ka ga na zo gareki da zancen. Ai nikam idan har kwalliya ta biya kudin sabulu to ba ni da wata matsala face na cigaba da sheƙa ayata son rai. Sai dai kuma ba nan gizo ke saƙar ba." "Ban fahimceka ba." Ya ɗan dakatar da ita da hannu. "Yanzu zan fahimtar da ke. Na'ima mace ce mai haƙuri na sani koda dai haƙurin na dole ne don duk faɗin ƙasarnan ba ta da gatan da ya wuce ni Ɗanmutuwa. Duk ranar da na yi watsi da ita, ina mai tabbatar maki sai kare ya fi ta gata." Hajiya Adama ta ɗan yamutsa fuska. "Ni fa daɗina da kai kenan, inda aka dosa daban, inda ka ke nufa daban. Mene ne haɗin abin da na nema da wannan soki-burutsun?" Ya yi ɗan murmushi. "Ai da ba ki katse ni ba, kin fiye ƙawa zuci, dalilin yin maganar Na'ima don na nunamaki ƙarfin ikon da nake da shi a gidana. Duk taurin kai irin na wannan yarinyar ba za ta gagare mu juyawa ba. A shirye nake na kawo maki ita ko ta ƙarfi da yaji ne. Ya rage naki ki san dabarun da za ki yi ta bada kai bori ya hau. Kinga gaba ta kai mu gobarar titi." Suka yi dariya. "Ko kai fa, yanzu ka yi magana mai kyau. Sai dai fanakwai sauran rina a kaba, kana da tabbacin ta cika duk sharuɗɗan da nake nema a wurin ƴan shila kafin ɗora ta kan network?" Bai ji ko ɗar dangane da tambayar ba sai ma dariya da ya yi karo na biyu. "Kin manta wace ce uwarta Na'ima ne? Ɗawisu muke kiranta fa. To ai ko ni ba don na ga jiya da yau ba, ba za ki jera ni sahun..." "To sarkin yabon kai, kar ka sauka daga kan layin da muke kai. Ka kawo min yarinyar kawai." "An gama Hajjaju." Da wannan suka ajiye zancen inda suka shiga tattaunawa dangane da abinda ya shafi kasuwancinsu. "An sanar da ni an kama yarona ɗaya, Ɗan Aljan, ya kamata a san abin yi kafin lokaci ya ƙure." Faɗin Ɗanmutuwa kenan. Ta duba lokaci a wayarta sannan ta ja guntun tsaki. Sai da ta fara watsi da maganarsa ksfin daga bisani ta dawo kan turba. "Nifa mutanen nan ba su san bana son saɓa alƙawari ba, mun yi da su ƙarfe uku amma ka ga har huɗu ta gota. Batun Ɗan Aljan ai ba matsala ba ce tunda muna da Kwamishina, ka sani ai dole ya fito. Yanzu fa nima na ƙara samun wata babbar kwastoma ta kaya. Kar ka yi mamaki a cikin garin nan ta ke fa, ita matan aure su ne abokan cinikayyarta. Matar inda ta burgeni duk wata hanya da za ta bi ta shigewa mace ta sani, za ta nunamata wannan hanya ita kaɗai ce ta gusar da damuwa, ya kuma sanya bacci mai dadi da munshari. Nifa Ɗanmutuwa duk inda zan ga masu jarumta da rashin tsoron gudanar da aikin kasuwancinsu burge ni suke yi ba kaɗan ba. Kaga akwai matashiyar da na sanya ta ke kawomin matasa cikin tafiyar, codein sai ya ƙare a ƙasa da minti talatin. A hankali su na sabawa da shi mu kuwa mu dinga ƙara farashi son ranmu." Ɗanmutuwa ya dara. "Ai sosai lamarin na tafiya yadda ake so. Ni fa kinga akwai wani yaro ana ce mishi Prince, ɗa ne ga wani babban Soja, ai idan kina neman hatsabibi ki ka sami ɗan gidan Major Musa Ahmad Gwadabe kin gama. Yana min cinikin sama da dubu dari biyu a wata." "Amma ba'a gani a jikinka, daɗina da kai ba ka iya tattalin kuɗi ba Ɗanmutuwa. Ka ƙi gina gida balle ka siyawa kanka suturun arziƙi. Ba dole irinsu Mahadi su rainaka ba su na ganinka da Ciyaman? Dubi fa suturar jikinka yadi duk ya koɗe." Ya yi ƙwafa bayan ya bi jikinnasa da kallo. "Shege ba, idan akwai wanda na tsana to fa ya biyo bayan mutumin nan. Amma kin yi magana, zan yi ɗinkunan kece raini don kwanan nan ma zan yi aure. Ba zan iya zama da Na'ima kaɗai ba." Ƴar dariya Hajiya Adama ta yi, kafin ta tanka sai ga sakatariyarta ta gidan ta shigo da sauri. Nan ta ke sanar da ita isowar manyan Alhazawan, hakan yasa suka miƙe. "A tabbatar yaran can sun kimtsa kinsan ba na kaunar matsala." Ta amsa da toh sannan ta fice. Su kuwa suka nufi waje domin yi musu tarba ta musamman. *** Cikin kwanaki uku Haulatu ta wartsake kamar ba ita ba, ta shiga harkokinta na yau da kullum. Ta koma makaranta, koda suka haɗu da Hindatu ko kallonta ba ta yi ba. Maganar duniya Hindatu ta yi amma ta share ta, haka har aka tashi ba ta bada wata fuska ba. Ta kama hanyar tafiya don yau kasuwa za ta leƙa wurin Umma, har ta isa bakin titi tana tsaye ta ji muryar Hindatu a gefenta. "Wai Haulatun Umma ni kike yiwa wannan wulaƙancin? Magana ta ƙi ci ta ƙi cinyewa? Matar da har haƙuri na ba ki? Ni wallahi kinsan dai ban iya gaaba ba, don sonki da Allah da Ma'aiki s.a.w ki yi hakuri. Kin ji? Haba Aminiyar kirki." Sam ba ta ma zaci tana bin ta ba, ba tare da ta kalle ta ba ta amsa. "Ai komai ya wuce." "Me kike nufi da ya wuce? Tun a aji kike nanata wannan kalmar, kina nufin kin yanke zumuntarmu ko me?" Cikin ɗaure fuska Haulatu ta amsa. "Aa, ai ba duka na yanke ba, da kika shigo ajin ba mun gaisa ba?" Kai, Hindatu haka ta dinga naci, ƙarshe sai ga ta a cikin ɗan sahu sun kama hanyar kasuwa tare. Haulatu dariya ta taso mata amma ta danne a zuciya, ta fiddo niƙaf ɗinta ta ɗaura gudun kar ta aikata abin da Umma ba ta so. Tun tana share ƙawarta tana mata mitar ba ta sauka ba ta da kudin da za ta biyamata na mota ita kuwa Hindatu na rantsuwa sai ta bi ta sun shirya a gaban Umma har tana fadin. "Kuma ma ai kasuwar tawa ce tunda ina da miji a cikinsa, kudin mota kema na hutar da ke zan biyamaki." Duk shariyar da Haulatu ta dinga yi haka ta haƙura ta sauko, kafin su ƙarasa sai hira da dariya kamar ba su ba. Anan Haulatun ke labarta mata ciwon da ta yi ba ta kuma ɓoyemata dalili ba, hatta da ɗasawar da suke yi da Bahijja da ƙawayenta ba ta ɓoyemata ba tunda dama Hindatun ta san da batun Bahijjar. Itama nan ta hau ba ta labarin zuwan Alhajin da kuma yanda ya ruɗe dagaske aurenta zai yi da zarar sun fita daga ajin da suke. A lokacin su na dab da rubuta jarrabawa wanda idan sun ci sun haye gwamnati za ta biyamusu NECO. Sosai Haulatu ta taya ta murna, ta kuma bi ta da fatan alheri. Har hotonsa ta nunamata a waya, babba ne ba yaro ba, yana da mata ɗaya da yaransa biyar. A iyaka ra'ayi irin na Haulatu, ko da ace tana da ra'ayin aure ba ta tunanin auren irinsu balle kuma babu auren ma a zuciyarta kwata-kwata. Tsakaninta da samari, sai ɗaure fuska da kallon banza. Duk wanda ya nuna yana sonta to fa taka masa burki take yi. Cikin samarin unguwa dama ba wanda ya taɓa nuna yana sonta a yanda gidansu yake. Sai ko ƴan bana bakwai.   Har suka isa kasuwar kwari su na ta hirarrakinsu. Haka suka dinga kutsawa Hindatu na faman mitar ya kamata Umma ta bar zuwa kasuwa tunda tana da suruki ɗan kasuwar yanzu (saurayin Hindatun kenan), ya fi ta dinga sarin kaya itama tana siyarwa yanda Mominta ke yi. Ita dai Haulatu murmushi kawai ta yi. Ba su ƙarasa ga Umman ba sai da Hindatu ta siya facemask ta rufe hanci da bakinta wai kar saurayinta ya hango ta wurin siyar da abinci. Umma ta yi mamakin ganin Hindatu. "Ke kuwa me ya kawoki nan daga makaranta? Kin sanar a gida ne?" Ƴar dariya ta yi. "Aa Umma, kar ki damu Momi ba ta gari ta je Katsina kai wasu kaya. Ni kaɗai ce a gidan." Umma ta jinjina kai ba ta ce komai ba. Abincin ta zubamusu sai da suka ci suka ƙoshi ta ce su tashi su kama hanya har Haulatun ganin wajen ya soma cika da samari. Kuma ga Hindu duk wanda ya tankamusu sai ta ga ta cafe zancen har su na dariya. Ita dai Haulatu ba ta yi wannan karambanin ba don ta sani muddin ta aika to fa za ta ɗanɗana kudarta a wurin Umma, balle ma irin rayuwar ba burge ta take yi ba sam. Sun bar wurin Umma sun yi nisa ta dakatar da ita. "Lafiya?" Faɗin Haulatu. "Don Allah muje ki raka ni mu gaisa da Noor. Minti biyar kacal." Zaro idanu ta yi. "Lallai ma BigMama, so kike Umma ta yanka ni ashe. Kuma ke yanzu girmanki ne ki bi saurayi har shagonsa? Nikam ba inda zan je. Malama zo mu tafi ko na bar ki anan." "Kai Haulatu, amma dai kinsan ba ani abin zan yi marar kyau ba ko? Kawai dai mun yi waya da shi ɗazu ai kinga sadda na tashi, ya cemin idan ban shiga mun gaisa ba zamu yi rigima. Taimaka don Allah, ni wallahi ko a bakin shagon ki tsaya muna gaisawa sai mu wuce." A dole, babu yanda Haulatun ta iya haka suka nufi shagon bayan ta ƙara gyara zaman niƙaf ɗinta. Ta gan shi a zahiri, ita sam ba ta ga abin burgewa a wurin mutumin da Hindatu ta kira da Noor ba, ainahin sunansa Alhaji Badamasi, ta shiga shagon ta zauna suka gaisa. Ta maida hankali ga matan da suka shigo siyayya, tana ji su na hira yana cewa meyasa ƙawarta ta rufe fuskarta, ba ta ce musu uffan ba. Can da ta ga abin ba na ƙare ba ne ta miƙe. Ganin haka tuni Hindatu ta miƙe itama suka yi sallama, ya takomusu har waje ya miƙawa Hindatu kudi har dubu uku su yi kuɗin mota. *** Ya shigo gidan yana ɗaure fuska babu ko sallama. Haulatu na zaune tana wanke kayan makarantarta. Umma dake shara ta dube shi, zuciyarta ko ba komai ta yi sanyi. "Sannu da zuwa." Ta furta baki na rawa. Ita kuwa Haulatu tamke fuska ta yi ba ta ko ƙara kallonsa ba, ɗan waƙen nishadin da ta ke rerawa tuni ta daina. Ƙirjinta zafi ya shiga yi tsabar takaici. Tana kallo ya shige bai ko amsawa Umma ba. Ita kuwa har da sauke ajiyar zuciya fuskarta babu yabo ba fallasa ta cigaba da shara. "Ke." "Na'am." Umma ta amsa da sauri kafin ta shiga ɗakin. Tsabar bakin ciki ya sa Haulatu miƙewa ta bar wankin ta shige ɗaki.    Fitar tsiro Page 9 Watanni uku da suka biyo baya, a wajen Haulatu sam ba masu dadi ba ne a rayuwarta cikin gidan, a makaranta kuwa sun zana jarrabawar qualify har kuma cikin ikon Allah tana cikin waɗanda suka yi nasara gwamnati za ta biyamusu kudin NECO. Gaba daya rayuwar gidan ba dadi ta ke yi mata ba kuma ba dalilin kowa ba sai mijin Umman da ya zame mata tamkar ƙadangaren bakin tulu. Duk iyakar kokarin da ta ga yana yi a gidan don nuni da lallai ya shiga taitayinsa ya nutsu hakan ba burgeta ya ke ba, tana kuma ƙara ji a jikinta cewar duk wannan abu da yake yi na banza ne kuma akwai lauje cikin naɗi. Sosai take son samarwa Umma hujjar da yasa take kokwanto amma ya toshe dukkan wata ƙofa. Don ta jarraba shi har cewa Umma ta yi, ta nunamasa ba ta son zaman majalisar su Maada a ƙofar gidan. Ta sha mamaki da ya amsa da cewar daga lokacin zamansu ya zo ƙarshe, kuma abin mamaki hakan ce ta tabbata. Har shigowa suka yi gidan suka yi sallama da Umman wani salon bariki da Haulatu ta yiwa abin kallo har da neman gafara.     "Madadin ki tsaya ƙoƙarin binciko laifukansa, kamata ya yi ki ƙara godiya ga Allah da ya karɓi addu'armu ya shirya bawansa." Haka Umman ta taɓa ce mata, a take kuwa ta zabura. "Wallahi ba dai addu'ata ba. Ni ban taɓa saka mijinki cikin addu'o'ina ba. Toh na tsaya ma na maida hankali ga yiwa kaina addu'ar mana. Hum um!" Daga haka ta tashi a lokacin don ba ta kaunar a ja magana. Tun sadda kacokam ragamar abincin gidan ya koma hannun Ɗanmutuwa, daga lokacin Haulatu ta bar cin komai da Umman za ta girka. Ta gwammace shiga gidan su Bahijja ta ci ta yi nak, ko kuma ta ci sauran abincin siyarwar Umman. Yanzu sosai suke zumunci da su Bahijja, tare da su take zuwa islamiyya, a dole ma ta ke zuwa don babu yanda za ta yi ta zauna a gidan baƙin cikin mijin Umma ya kashe ta. Cikin wannan lokacin ne aka sanya ranar auren Hindatu da ya kama watanni biyar bayan kammala sakandire ɗinsu. Ta shirya daga ita har Umma don zuwa yi musu fatan alheri. Suna tafe su na hira gwanin sha'awa, Umma har ta ɗan murmure kaɗan saboda kwanciyar hankali da nutsuwar da ta samu. Babu abin da ya kai damuwa jefa zuƙata cikin damuwa da takura. Idan ka gan su sai ka rantse Yaya ce da ƙanwarta, sam ba za ka kawo a rai wai Uwa ce da ɗiya ba domin Allah ya halicci Umma da kyawun jiki. Suna tafe su na hira abinsu, Haulatu cikin nishaɗi ta ke jinta da walwala sakamakon albishir da Umma ta yi mata cewa zuwa litinin, tunda yau su na Asabar, za ta ba ta kuɗin WAEC ta je ta biya. Sosai take murna, don dama Hindatu duka biyun za ta zana. Ba ta ci Qualify ba ita, amma Mominta ta biyamata duka jarrabawar guda biyu, daga Waec har Neco din.   "Amma dai Umma kin tabbata kuɗin daga hannunki za su fito ko?" Umman ta ɗan yi shiru sai kuma ta haɗe fuska. "Kina tunanin zan aikata abin da nasan ba kya muradi? To shikenan, bari a hakura da biyan sai ki zana..." Da sauri ta katse Umman ta hanyar ruƙunƙumeta tana dariya ita ta mance ma a hanya suke. Har sai da Umman ta tsawatar kafin ta sake ta. "Na tuba Uwata ƴar aljanna. Kiyi hakuri don Allah." Umma ta yi murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba. Can ƙasan zuciyarta ta ji wani iri, tabbas kudin daga aljihun Ɗanmutuwa zasu fito, shi da kansa ya cewa Umman zai biyawa Haulatun kuɗin WAEC sadda ya ji tana maganar za ta haɗa ƴan kuɗaɗen ta biyamata, shi ne ya soma kwaɓarta akan kada ta sanar da ita don ya sani ko za'a yi me, kafiyar Haulatu ba zai sa ta amince ba. Ko an biya daga baya ta ji labari, to fa ƙarshenta a yi asarar kuɗi. Har suka shiga abin hawa Haulatu hira kawai take jan Umman tana ba ta labarin saurayin Hindatun da irin kudin da yake shirin kashemata a bikin. Sun iske mutanen gidan duk suna nan ba su fita ba, Amarya da kuma Baraka. Kamar kullum wannan karon ma buga ƙyauren gidan ta yi da ƙarfi wanda har sai da Umma ta ɗan razana.   "Ya Salam, kina da hankali kuwa? Dama ashe har yanzu ba ki bar yi musu wannan sakarcin ba?" "Ina fa za ta bari, ai mun riga mun saba da wannan idan dai Haulatu ce." Faɗin Baraka dake aikin tankaɗe garin tuwo. Ita kuwa Amarya dake zaune ƙofar ɗakinta tana gyaran salad ta yi dariya kawai. Suka gaida Umma, ta amsa fuska a sake. Itama Haulatun sai sannan ta gaida su. "Wai ni ya naji shiru ne? Ko waccan yar duniyar ba ta nan? Bayan na fadamata zamu shigo." "Hindatun ce ƴar duniya?" Fadin Umma. "Lah, ai Umma idan dai su biyun nan ne kya ji abin da yafi haka ma." Umma ta girgiza kai kawai tana murmushi. "Ba sa nan ne?" Ta tambaya. "Suna ciki. Hajiyar ce ba ta jima da shigowa gidan ba, suna ƙule a ɗaki." Fadin Amarya cikin tsegumi. Haulatu dai dariya ta yi ta yi gaba Umma na biye da ita. Sallamar Haulatu da shigarta ɗakin duka lokaci guda ne, nan da nan ta ga Momin na tura wata leda ƙasan gado, ta kai idanunta ga layar da ta fito a ƙoƙarinta na tura ledar, tana gani ta wayance ta tura shi gami da hawa faɗan borin kunya. "Ke dai an yi marar hankali. Yanzu ana girma ana cin ƙasa daga sallama kawai kik banko labulen ɗaki, ai sai ki jira a amsa maki ko?" Ita kuwa Hindatu dake zaune gefe duk ta sha jinin jikinta, ta ɗan washe baki ganin har da Umma. "Wa'alaikumussalam, lah Umma sannu da zuwa." Momi ta ɗan saki fuska suna gaisawa da Umma, ita kuwa Haulatu zama ta yi gwuiwa a sake, wai ita Momi mene matsalarta da ita? Nan suka yi musu fatan alheri, har dai aka gama zaman babu alamar za'a nuna musu kayan sanya rana. Haulatu da ba ta shiru tuni ta mance da wancan ɓacin ran ta dubi ƙawarta. "Wai ke ba za ki nunamin leshin d kika ce ɗan dubu tamanin ɗin ba?" Umma ta watsamata harara amma ko a kwalarta, Momi nan da nan ta daure fuska. "Kayan ai an kai su ajiya, ba zan bar su anan ba kaya masu tsada a biyo dare a yi mana ɗan hali. Kinsan ban yarda da ɓerayen da muke zaune da su ba a gidannan." Ita kuwa Hindatu ta rasa dalilin Momi na ƙin nunamusu kaya, a iyaka zatonta wannan na daga burin Momi, kowa ya zo ya ga kayan bajintar da aka kawowa ɗiyarta. "Allah ya kyauta toh." Faɗin Umma sannan ta miƙe. "Bari mu koma. Allah ya sanya alheri Hindatu. Ya nunamana lokacin." "Ameen Umma nagode." Umma dai ta ɗan cika da mamaki, toh kenan su ma dai yaran yanzun ba kunya ne da su ba, irin amsawar da yarinyar ke yi ita kunya ma ta ji, tabbas dole ta yi addu'ar Allah ya fitowa da Haulatu miji itama ta yi aure duk da ta san yanda Haulatun ke fatattakar duk wanda ya zo da sunan soyayya wajenta. Haulatu dai ta tsaya tana kalle-kalle har idanunta ya kai ga wata babbar akwati sabo fil, kamar ta yi magana sai dai ta fasa ta miƙe. "To Amarsu, sai mun haɗu a makaranta. Allah ya sanya alheri Momi." Momi ta harare ta bayan ta juya baya. A fili kuwa ta amsa cike da gadara. "Ameen." Hindatu ta miƙe da zummar yi musu rakiya, ta gefen idanu Umma ta ga sadda Momin ta danne mata hannu wanda dole ta sanya ta komawa ta zauna.  Sai da suka fice ne Momi ta dube ta tana harara. "Kina saka ran zan yi sake ne su ga kayan bayan kina sane da cewa duk duniya idan akwai waɗanda na tsani na buɗi idanu na gan ta tare da ke bai wuce wannan shegiyar yarinyar ba mai idanu kamar mujiya? Ke ki sani, muddin kika yi aure toh ƙawancenku ya zo ƙarshe. Ba zai yiwu ina can ina tufka ba kina gefe kina min warwara. Wannan da kike gani baƙar inuwa ce ita, gwamma rana da ita. Amma ya rage naki, idan kin ga dama ki sakarmata fuskar da za ta yi maki illah a rayuwa. Mutum da gishirinsa, in ya ga dama ya dafa ƙaho." Hindatu shiru kawai ta yi, koyaushe idan Momi tana nusar da ita akan raba hanya da aminiyarta. Ita a iyaka tunaninta ai abokin cin mushe ba a ba a ɓoye masa wuƙa. A yau dai sam ba ta goyon bayan Mominta hakan yasa koda Momin ta fita ta dawo ta jawo ledar rubutuka da layun da ta karɓo wurin bokanta ba ta mayar da hankali wurin sauraronta ba. Ƙarshe ma miƙewa ta yi ta fice daga ɗakin uwar na kwalamata kira amma ta yi burus. *** A hanya Umma ba ta ce uffan ba sai sauraron Haulatu take wacce ke faman mitar wulakancin da Hindatu ta yi mata ita da Babarta. Ta yi ƙwafa. "Wallahi Umma na ga akwatin, kuma na tabbatar shi ne na sanya rana saboda shi Hindatu ta nunamin an haɗa bidiyo da hotonta har da su buhun shinkafa da su tabarma. Amma dai Momi ta rainamana hankali wallahi, toh kenan su Baraka ne ɓarayin ko kuma mu da muka shiga gidan? Kut! Ai..." "Kin ishe ni haka, za ki kama bakinki kimin shiru ko sai mun raba hanya da ke yanzu? Ban da shashanci muna tafe kina ɗaga murya kina hayagaga kina jazamana kallo?" Umma ta katse ta a zafafe, sai lokacin ta ɗan waiga ta ga wasu yara gefe suna ta kallonta can gefe kuma wasu samari ne su ma masu zaman majalisa sai ko na tafe da ke waiwaye. Turo baki ta yi ba ta ƙara magana ba. A ranta sai ayyana kalar rashin mutuncin da za ta yiwa Hindatun take yi, ta kuma ci alwashin ba za ta yi ankon bikinta ba. Koda suka je gida Umma ba ta ce mata uffan ba. Sai ranar litinin ne ma bayan ta ba ta kudin WAEC da kuma na karamin hoton passport sannan ta gargaɗeta akan nunawa Hindatu wani abu koda kuwa a fuska ne. "Muddin kika yi magana za ki tabbatar da zargin Uwar na cewa kina hassada ga ƴarta ne. Ki nuna hakan da aka yi kamar bai dameki ba. Bana son kananan magana, kema dai Allah ya nunamin naki mijin na aurar da ke." Dariya maganar Umma na ƙarshe ya sanya ta. "Umma kenan." Iyaka abin da ta ce kenan kafin ta fice. *** Kwanci tashi ba wuya a wurin Allahu, har lokacin jarrabawar su Haulatu ya yi. Hakanan suke zuwa, ba ta ko damu da karatu yanda ya kamata ba tunda a ɓagas ake rubuce musu komai a allo su rubuce. Wannan tsarin na jarrabawar sam bai yiwa Umma ba. "To Umma ai komai yanzu sai da taimako. Ai iyaka nan ne, gaba ba zamu yi haka ba." "Um um Haulatu, juma'ar da za ta yi kyau tun daga laraba ake gane ta." Wannan amsar ta samu daga Umma. Ko a jikinta, ita dai ta san idan an yi abu a aji tana fahinta, matsalar bai wuce rashin Malaman kirki da ba su da shi ba a makaranta don akwai darussa kusan hudu da zasu yi jarrabawa a kansu, ba a taɓa koyamusu ba a makaranta. Sai a wurin Bahijja ne ta ɗan koyi wani abun a ciki. Ita sosai makarantar kudin da yaran gidan su Bahijjar suke zuwa ke burgeta. Sosai Bahijja ta iya turanci, aikuwa tun lokacin Haulatu ta ƙwallafa ran sai ta koyamata. Wannan yana daga abinda ya dauke mata hankali da wuni tare da Umma a gida tana shan takaicin yanda Umman ke rawar jikin yiwa Ɗanmutuwa girki da gyaran ɗaki. *** Dariya suka kwashe da shi a lokaci guda. Hajiya Adama ta nuna Ɗanmutuwa ya yatsa. "Kai, kai, wallahi kai kam ba ƙaramin ɗan bariki ba ne. Kuma gashinan har wani kyallin angonci ka ke yi." Ya yi dariyar mugunta. "Ai sai kin ga yanda Na'imatu ke faman rawar ƙafa a kaina. Komai take yi don ta burge ni ne." "Lallai kam, kai dai shegen kanka ne. Yanzu dai wace mafita ka samo? Lokaci ya ja, ya ci ace yanzu mun san matakin ɗauka. Lokaci ya zo da za ka kawo su gidan nan, na ga Haulatu da idanuna." Ya jinjina kai gami da sauke ajiyar zuciya. "Hakane, kar ki samu damuwa, na gama yanke duk abin da ya kamata nayi ba tare da an zarge ni ba. Za su zo koda sau daya ne, amma ba yana nufin a lokacin ne zan bar maki Haulatu ba tunda dai ciniki bai faɗa ba, har yanzu da saura. Na fi kaunar ya kasance koda za ki ɗauke ta, ya zamana ko daga makaranta ko wani abin na daban. Kinga zai fi toshe dukkan wata kafa da za'a zarge ni. Af, ai na tuna, kwanaki Na'ima na cemin za'a yi bikin wata ƴar makarantarsu. Me zai hana a lokacin bikin ki sa yaranki su ɗauko maki ita?" Ta yi shiru can ta ce. "Idan kuwa hakane, babu amfanin zuwansu gidana, hakan kamar ƙofa ce wanda zai jawo zargi idan bincike ya tashi." Ɗanmutuwa ya jinjina kai. Haka suka yi ta ƙulle-ƙullensu, yana ƙara koɗawa Hajiya Adama ɗiyartasa, yana mata rantsuwar sai ta ture fadar dukkan ƴan gaban goshinta saboda za ta kawomata ribar da wasu ba su taɓa kawo mata ba daga wurin Alhazawa. (Wa'iyazubillah). Fitar tsiro Page 10 Tafiya ta yi tafiya, har a yau aka wayi gari su Haulatu suna bikin kammala sakandire. Sabbin uniform din da ta sanya gaba ɗaya an mata kaca-kaca da shi da biro. Duk zare idanu irin nasu ita da Big Mama Hindatu, hakan bai yi tasiri ba a ranar. Su kansu ba su jin manyantan a wannan rana, sauran ɓurɓushi na fushi da Haulatu ta ɗauki lokaci tana yi duk a wannan ranar ta ji ya kau. Suka ɗinke tamkar ba su ba. Haka aka rabu cike da walwala da kuma jin kewa. Wasu har da hawayensu. *** Zumuncin da ya ƙullu tsakanin Haulatu da Bahijja shi ne babban abin da ya fi faranta ran Umma. Shigowar Bahijja rayuwar Haulatu ya sanya ta a dole take mayar fa hankali wajen zuwa Islamiyya duk da kasancewar a sannan Bahijja ta yiwa Haulatun zarra a karatu. Ita tana cikin masu hafizan da ake saka ran makarantar za ta yaye, yayinda Haulatu ta koma ajin baya. Zuwa lokacin Malaman ba su yunƙurin dukanta idan ta gwaɓa musu zance sai dai ko hukuncin shara ko wankin banɗakin makaranta. A hankali kuma suka ƙara fahimtar cewa hakanan ta ke sai dai ko yau da gobe idan a na nusar da ita ta hanyar yi mata gyaran kalami zai taimaka ƙwarai wurin shiryuwarta. Albarkacin zuwa makarantar da take ne ya jawo Ɗanmutuwa ke samun arziƙin gaisuwa, hakan ma a daƙile ta ke yi don har wani ɗaci take ji a maƙoshinta. Wannan albarkacin kaɗai ya soma ci a kwanakin, shi ɗin ma darajar Umma ya ci ganin sosai Umman na damuwa da yadda take nuna halin ko'in kula da duk wata kyautatawa da Uban ke yi mata. Har gobe dai ba ta taɓa yarda ta ci abin da ya fito daga hannunsa, wani tsire da kaza da yake kawowa Umma duka ba burge ta suke yi ba. Umma itama tun lokacin da ta gwada sau ɗaya ba ta ƙara ba don a gaban Ɗanmutuwa Haulatun ta rantse ba za ta ci kayan haram ba. Har a lokacin Umma ta so kai mata bugu sai dai Ɗanmutuwa ya tare. Wannan rana kusan kwana Haulatu ta yi tana kuka, wai yau ita Mahaifiyar za ta kai wa duka akan wanda bai taɓa daraja a idanunta ba. Washegari kuwa ta tashi da ciwon kai mai zafi, wannan ya tashi hankalin Umma, tsoronta kada ta jefa ta a ciwo irin na can baya. Ita kanta sai daga baya ta fahimci mugun kuskuren da ta yi na ɗaga hannu da zummar dukan ɗiyarta. Tun ana sauran sati uku a fara bikin Hindatu, aka kawo lefe. Wannan karon Haulatu ko leƙe don ta rantse ba za ta ƙara zuwa Momi ta wulaƙanta ta ba. A lokacin Haulatu ta mallaki wayarta ƙarama wacce Umma ta yi mata kyautarta na taya murnar kammala sakandire. Ba ta ji mamakin komai ba kawai ta saka a ranta kuɗaɗen da Umma ke adashi ne ta karɓa. A sannan wani abu wai Chatting bai ko damu Haulatu ba, ba ta taɓa ma kallonsa da sha'awa ba. Iyaka saninta ba ta da wani ko wata da za su yi hira da shi. Ta gwammace duk sadda za ta yi waya da Aminiyarta ko Bahijja idan ba su haɗu ba, ta kira su ta waya, idan kuwa babu kudi ta yi ta dokamusu beep call har sai sun gaji sun kira don ji me ta ke so. Ko kusa ba ta yi karambanin cusa kai a sha'anin bikin Hindatu ba gudun jin baƙar magana daga bakin Momi. Hindatu har abin ya ba ta haushi don sai da ta tako har gida ta kawo ƙararta wajen Umma akan ta ƙi yi mata rakiya gurin gyaran jiki da na gashi kafin ta amince su je. Ranar da aka fara gyaran jikin, ta sha mamakin irin haɗuwar wajen, koda dai unguwar ma kanta ta manya ce, can wuraren Lamiɗo Crescent ne. Wurin na wata Basudaniyar mata ce ana ce mata Ayyush. Haka Haulatu ta yi zaune tana kallon ikon Allah yanda ake ta mulkewa ƙawarta jiki. Zuwansu na farko amma sai ta ga har ta sauya. Matar ta dube ta. "Kema dai ya kamata a yi maki, za ki yi kyau sosai tunda na ganki ba baya ba Masha Allah." Ɗan murmushi kawai ta yi, ita kuwa wace hidimar ce za ta tasar mata ta yi gyara irin haka? Ita da babu ma aure a ƙoƙon ranta, mene haɗin biri da gada? "Ai wannan da kike gani babu ma aure a gabanta yanzu. Sai na kai ta an yi mata ruƙiyya sannan." Ta harari Hindatun, tana ji matar ta hau yi mata faɗa da ƴar nasiha akan muhimmancin aure da kuma kuskuren cin alwashin ba za ka yi shi ba tunda ba kai ke iko da kanka ba. Sai ta yi dariya. "Toh ni ina ruwana? Ku da kuka ga za ku iya ai ga fili ga mai doki." Tun daga nan fuskar Ayyush ta sauya, Hindatu sam ba ta ji dadin zancen na Haulatu ba. Tun da ta kalli fuskar matar ta tabbatar Haulatu ta musu kwaɓa. Haƙuri ta shiga ba ta kafin cikin murya ƙasa-ƙasa ta ce "Ita fa muddin za'a yi mata zancen aure iskokanta tashi suke yi." Kasancewar Ayyush da tsoron abin da duk ya shafi aljani, hakan ya sa ba ta ƙara zancen ba. Ta kuma aminta da batun Hindatun wannan dalili ya sa ta ɗan saki fuska gami da yi wa Haulatun uzuri. Haka suka jera sati tana yiwa Hindatu rakiya gurin gyaran jiki, sau biyu suka haɗu da Alhaji Badamasi shima ya zo ɗaukarsu ne ya maida gida, ta dai kula mutum ne mai shegen kallo da sa idanu don tun ganin da ya yi mata na farko ta ji ta tsane shi saboda yawan kallonta. Tana daga kujerar baya amma haka yake saita madubinsa ya na kallonta ta ciki. Sau biyu da aka yi ba ta ƙara yarda Hindatu ta fita da Hindatun ba tare da niƙaf ba. Koda aka soma biki sun fara ne da Bridal Shower kamar yadda zamani ya zo da shi. Wannan rana yana daga cikin ranakun da Hindatu ta jima tana mafarki, babban burinta a gudanar da Bridal Shower. Ta kuwa samu yanda ta ke so, gidan wata ƙawar Mominta ko ace Uwar ɗakin Momin, Hajiya Zulai, nan aka ba su aron babban falonta aka yiwa falon tsari mai kyau na ado. Ƙawaye ma sai da ta zaɓa domin duk ciki ban da Haulatu aminiyarta, mutum biyu kacal ta gayyata a ƴan makaranta sauran wasu ƴan duniyan ƙawaye ne da ta haɗu da su rayuwar soshal midiya. Haulatu Ta yi ƙunshi ta yi kitso, ba ƙaramin kyau ta yi ba ranar. Shigar fari da ruwan gwal ɗin da suka yi, sosai ya fiddo ta. Duk yanda ta gujewa yin kwalliya haka Hindatu a dole ta matsa sai da aka yi mata. Sun ci sun sha kayan maƙulashe, ga mai hoto na musamman da Alhaji Badamasi ya kawo, haka ya dinga ɗaukar su, sai wuraren takwas na dare suka watse. *** Washegari kamu haɗe da yini wanda za'a yi a wani ɗakin taro na musamman. Marar kati ba zai samu shiga ba. Tare zasu je da Umman amma yanda Hindatu ta dinga jera mata kira tana ɗuramata zagi kan ta taho inda ake mata kwalliya tare za su tafi yasa a dole Umma ta ce ta wuce kawai zuwa yamma ita sai ta tafi tunda akwai waya zasu yi magana kawai. Sadda ta kammala daukar duk abinda take da buƙata a leda, ta fito a gaggauce suka kusan cin karo da Ɗanmutuwa, guntun tsaki ta ja kafin ta yi baya. Ta san da ace Umma ta ji wannan tsakin ranta ne zai ɓaci, shi kuwa shigowa ciki ya yi wannan karon ko arziƙin gaisuwar da ya saba ci bai ci shi ba. Wayarsa ta yi ƙara ganin mai kiran ya sanya shi saurin shigewa ɗakinsa, daidai lokacin ita kuma Umma ta fito daga nata ɗakin, sam bai kula da ita ba, ta ƙarasa, kafin ta kai ga shiga ta yi saurin ja baya tana sauraron abin da yake faɗi. Tashin hankali! Gobarar gemu kenan. Fitar tsiro Page 11 "Yanzun nan ta fita, ku fara bin bayanta, duk inda ta sa ƙafa ku sanya. Ku tabbatar kun fesa mata hodar yadda ko kun kai ta ba za ta iya gane hanyar dawowa ba. A kuma faɗawa Hajiya Loma, ina nan tafe anjima." Jin alamun zai katse wayar, jiki na rawa Umma ta fice zuwa ɗakinta. Jin kamar motsin mutum ya sa Ɗanmutuwa saurin juyowa gami da ɗan zura kansa ta tagar ɗakin, kasancewar tagarsa saitin ta Umma ce, hangota ya yi tana ta kiciniyar shiryawa. Ya yi tunanin ba ta ji komai ba don haka ya yi musu sallama da zummar zai ƙara kira kafin ya shiga ma'ajiyarsa na miyagun ƙwayoyi ya hau lissafa adadin da wasu suka buƙatar ya kai. Ɓangaren Umma kuwa, shirin dole ta kama jikinta sai rawa yake. Babban burinta kar ta yi wani motsin da zai ankarar da shi ta ji. Hakan yasa ta shiga jan Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un a zuciyarta, sai da ta kammala saka kaya ta ji ya rufe ƙofar ɗakinsa ya fito. "Na'ima." Ji ta yi ya kira sunanta, sai da ƙirjinta ya buga. Tsanarsa take ji sosai ga kuma tsoron abin da ake shirin yiwa ɗiyarta. Sai da ya kira na biyu kafin ta fito tana murmushin dole. "Na'am, yi hakuri ina sauri zan shirya ne. Fita za ka yi?" Ya yi wani murmushin mugunta. "Eh Ɗawisuna. Ni zan fita. Ba sai an yi girki ba kar na wahalar da ke. " Ta gyaɗa kai tana ƙara murmusawa a dole. "Ina godiya. Sai ka dawo." "Kema sai kin dawo. Ki kularmin da ɗiyarmu." Daga haka ya fice, ta bishi da banzan kallo wanda take ji kamar ta shaƙo shi. Da sauri Umma ta koma ɗaki, hijabinta kawai ta zura, wayarta ta ciro ta shiga gwada kiran Haulatun sai dai ta ji a kashe. Hankali a tashe ta dannawa Hindatu kira, nan ma yana ta ƙara ba su ɗaga ba. Ƙirjinta ta dafe tana ambaton Allah da nufin ya samar mata mafita. Nan da nan Hajiya Mama ta faɗo ranta, da sauri ta fita ta rufe gidan ta faɗa gidanta. Hajiya Mama na zaune a falo tare da baƙuwa sai ganinta suka yi kamar an jefo ta. Nan da nan suka miƙe, sosai ta tsorata su. "Maman Haulatu, lafiya?" Cewar Hajiya Mama. Cikin kuka ta riƙe hannunta jikinta ko'ina na rawa. "Haulatu na cikin hatsari Hajiya, don Allah ku taimaka min. Naji Babanta na waya yana bada umarnin a bi ta a kama ta." "Tana ina yanzu?" Ta tambaya a gaggauce. Umma ta ɗan watsa yatsunta. "Nima ban san inda ta nufa ba, na san dai wajen da ake yiwa Hindatu kwalliya ta nufa. Ku taimakamin don Allah." Nan da nan Hajiya Mama ta fiddo waya ta kira mijinta ta sanar da shi, ya ba da umarnin su je gidan iyayen Hindatun a ji inda take. Shi kuma zai sa direbansa da Mujahid (Yayan Bahijja) su je wajen. Ya buƙaci a turo masa lambar Hindatun. Ba musu kuwa suka yi sallama, Hajiya Mama ta karɓi lambar wurin Umma ta aikamata. Haka suka ɗunguma har baƙuwar wacce ƴar uwa ce ga Hajiya Mama. Momi ba ta yi gardamar faɗamusu inda Hindatun ta tafi ba ganin babbar mace kamar Hajiya Mama wacce da gani ka san ba daga rigija-rigijan gida ta fito irin nasu ba. *** Haulatu kuwa tsabar takaicin kiran da Hindatu ke faman jeramata ne yasa ta kashe wayarta baki ɗaya, ko kusa ba ta kula da motar da ke biye da su ba. Mai adaidaitarsu kuwa tun yana ganin kamar ba binsu ake yi ba, har dai ya fahimci duk kwanar da suka yi nan motar da ta sha baƙaƙen gilasai ke yi. Dab da zasu ƙarasa wurin shagon Ayyush inda nan ne dai ake yiwa Hindatun kwalliya ta ji mai Napep din ya yi magana. "Anya wannan motar ta baya ba mu take bi ba?" Haulatu ta ɗan leƙa kanta kafin ta ja tsaki. "Kyale ɗan wahala. Wataƙila zancen wofi suke son yi mana. Don Allah ƙara gudu ina sauri ne." Shi kuwa jin haka ya ƙarawa napep ɗinsa gudu. Faɗi yake yi amma bai taɓa ganin maye irin wannan mai motar dake bin su ba. Da gani masu bin mace su ce su na sonta ne. Amma fa shi abin wai na ba shi mamaki yanda ko akwai sarari ba sa wani kokarin yin overtaking. A bayan dai suke bibiyarsu. Ita dai Haulatu ba ta ko tanka ba sai ma wayarta da ta kunna, daidai lokacin suka isa shagon, ta fito da sauri ta sallame shi. Ko motar ba ta kalla ba. Su kuwa su Maada suna tsaye can gefen hanya, Duuna ya dube shi. "Boss, wai idan ba anan area ba, ina kake tsammanin za mu cafke ta ba tare da an samu matsala ba? Tun ɗazu eh cewa nake ka yi overtaking amma eh ba ka yi ba." Maada bai ko dube shi ba har sai da Mai Napep dinnan ya yi ribas ya wuce su har da leƙensu ya dinga yi amma ya kasa ganin ko inuwa. Haka ya haƙura ya yi gaba. *** Hindatu ta yi kyau sosai kamar ba ita ba, duk wannan kwalliyar bai hana ta hararar Haulatun gami da ɗuramata ashar ba. Itama ta maida martani kafin kuma ta zauna a soma yi mata nata kwalliyar, Hindatu cike da masifa ta ke fadin. "Ban taɓa ganin Aminiya irinki ba. Wa ya taɓa raba hanya da Amininsa ranar bikinsa?" Ta harzuƙo za ta yi magana mai kwalliyar ta ba ta hakuri da fadin don Allah kar ta motsa ba a yiwa kwalliya haka. Dole ta yi shiru tana huci. Ita ji take kamar ma ta fasa kwalliyar. Wayar Hindatu ta yi ƙara sa'ilin da ake ƙoƙarin yi mata ɗauri. "Madam tun fa ɗazu ake ta kiranki ya kamata ki ɗaga wayar nan. Wayasani ko Angon ne." Fadin Ayyush dake zaune can gefe tana cin abinci a robar takeaway ga drinks ajiye gabanta. Masu yin kwalliya a shagon mutum biyu ne ƙwararru. Hindatu ta ɗauki wayar tana ɗan murmushi, ganin baƙuwar lamba ya sa ta ɗan yamutsa fuska da tunanin ko masu damunta da neman kwatance ne. Sai kuma kawai ta ɗaga, jin muryar babbar mutum ya sa ta amsa da sallama. Nan ya nemi kwatancen inda suke bayan ya sanar da ita shi din makwafcin su Haulatu ne kuma yanzu haka tana cikin hatsari. Nan da nan cikin Hindatu ya ɗuri ruwa, ta sanar da shi ya kashe wayar bayan ya ce kar ta sake ta sanar da Haulatun. Haka aka cigaba da shirin ita duk jikinta ya yi sanyi, Haulatu kuwa ana cikin yi mata kwalliyar ba'a kai ga kammalawa ba sai kawai suka ji tsayuwar mota. Hindatu ce ta dubi waje don gilashin ana iya ganin na waje amma shi ba zai ganka ba. Ganin wasu maza biyu kuma matasa sai ta yi zaton ko su ne masu neman Haulatun. Suka kwankwasa gilashin wurin. Ayyush ta mike tana mita. "Su waye kuma? Maza ba sa shigomin wuri fa." Ta leƙa, ita Haulatu ko a jikinta, Hindatu kuwa ana ɗauri tana gocewa tana kallonsu sai da mai ɗaurin ta yi magana kafin ta nutsu amma kunnuwanta su na waje. Ayyush kafin ta kai ga magana sai ga motar ƴan sanda ta faka. Daga waje kuwa su Maada su na ganin motar hukuma ba shiri suka yi wani wawan ribas da ya ɗauki hankalin jami'an tsaron suka yi gaba, ganin haka tuni su dinma suka bi bayansu a guje. Ayyush dai ta gama tsorata, kirjinta ya hau bugu da ƙarfi. Mujahid ne ya fara tambayarta inda Haulatu take. Jin an ambaci Haulatu ya sa Hindatu miƙewa har tana sa mai mata ɗauri soke hannunta. Haulatun ma miƙewar ta yi, gaba daya suka nufi ƙofa. Mujahid na ganin Haulatu ya sauke ajiyar zuciya. Ita kuwa ji ta yi gabanta ya fadi. Me zai kawo yayan Bahijja wurinta? Ta ya ya ma yasan cewa tana nan? "Yaya Mujahid? Lafiya?" Ya girgiza kai. "Lafiya kalau, kar ki damu. Ki.." Bai kai ga ƙarasawa ba motar su Hajiya Mama ta tsaya, su dinma duk a ruɗe suke. Haulatu ta yi saurin fitowa daga ita sai doguwar rigar ankon bikin na ƴanmata. Ta ƙarasa ga Umma jikinta na rawa, ta samu nutsuwa da ganin Umman don a farko ta yi zaton ko wani mummunan abun ne ya fari da ita. Umma ta rungumeta tana kuka, itama kawai ta ji kwalla sun cicciko mata tun kafin ta san dalilin kukan mahaifiyarta. "Ya isa hakanan don Allah Na'ima tunda ga ta nan kin same ta cikin kwanciyar hankali. Allah ya kiyaye gaba." Haulatu dai kallonsu take yi. "Umma meke faruwa ne?" Nan Umma ba ta labarin abin da ta ji Ɗanmutuwa na shirin aikatawa gareta. Haulatu ta yi wani dariya lokaci guda mai haɗe da hawaye. "Umma kukan me kike? Mamakinsa ki ke yi? Dama ban faɗamaki ba? Ban faɗamaki mugun mutumin nan ba zai taɓa sauya hali ba? Ban ce maki yaudararki ya ke yi ba? Yau ga shi nan, wataƙila cinikina ya je ya yi ba tare da kin sani ba." Ta karashe muryarta na dusashewa tsabar wani daci da maƙogwaronta ke yi. Hajiya Mama ce ta dakatar da zancen, ta nemi Hindatu ta shiga a ƙarasa yi mata shiri. Haulatu kuwa komai fita ya yi a ranta amma Hajiya Mama ta dage ta tsaya a yi komai da ita. Mujahid ke sanar da su an cafke mutum biyu cikinsu amma saura sun gudu. Wannan ne ya haifar da nutsuwa a zuciyar Umma sai dai kuma abin da ke binne a zuciyarta da kuma ƙudurin da ta yi na matakin da za ta ɗauka wanda zai fiye musu alheri ita da ɗiyarta. Ta yi alƙawarin tafiya Katsina neman dangin uwarta koda ace ita ba su shirya karɓar ta ba suna mata kallon shegiya, to za ta nemi alfarmar su riƙe mata ɗiyarta ko bayan ranta. Bikin dai na Hindatu bai yiwa Haulatu dadi ba sam duk da irin burin da ta ci wa bikin na za ta yi rawa har sai jikinta ya yi ciwo. Gidan Hajiya Mama suka koma da rayuwa don ƙeyar Ɗanmutuwa ba'a ƙara gani a unguwar ba. Umma ta dauke duk wasu muhimman abubuwanta da ta sani zai sadar da ita ga dangin Mahaifiyarta Salma. Bayan komai ya lafa da kwanaki biyar Umma ta soma shiri tun safe, ta kuma tashi Haulatu da ke bacci akan ta yi wanka ta shirya za su yi tafiya. Haulatu ta na mutsika idanu ta dubi Umman, tun faruwar lamarin ko digon fara'a ba ta ƙara gani a fuskarta ba. Ta sha farkawa ta gan ta saman darduma tana kuka cikin sujjada. Itama sai ta ɓoye kanta cikin zanin rufa ta sha nata kukan. "Umma ina zamu je?" "Katsina." Ta ba ta amsa kai tsaye, Haulatu ta yi shiru tana tunani, Katsina dai? Wa suke da shi a Katsina? Duk kokarinta ba ta iya cankar komai ba. Ganin Umman ta cigaba da aikin shirya jaka yasa dole ta miƙe ta faɗa wanka. Fitar tsiro Page 12 A ɓangaren Ɗanmutuwa kuwa, tun lokacin da suka yi waya da Maada yake ba shi lamarin ƴan sanda sun tarfa su, ya shiga mugun tashin hankali. A sannan yana kwance tare da abokiyar hutawarsa a ɗaki a gidan Hajiya Adama. A hargitse ya ja kayansa ya mayar ya fito ya nufi wurin Hajiya Adama ya sanar da ita komai. Hannu ta ɗagawa mai yi mata tausar ƙafa gami da ba ta umarnin ta bar falon. Rai a ɓace ta dube shi. "Garin ya ya ka yi sake har wani ya ji wannan shiri? Ni na tabbata akwai sila, ba hakanan kawai labari zai kai ga ƴan sanda ba. Ko akwai munafuki a cikin yaranmu ne?" Ɗanmutuwa wanda duk sanyin falon bai hana shi fitar da zufa ba, cikin tsananin ɓacin rai ya amsa. "Ke ai kin san ni, ba zan yi sakacin da har wani zai ji wani abu ba. Na yi waya a gidana, amma ko alama babu wanda ya ji, asalima sadda na yi daga ni sai Na'ima, ita kuwa tana ɗakinta tana ƙura adakar fita biki. Yaran nan kuwa ƴan a mutu ne ko a yi rai kin san da haka." Ran Hajiya Adama ya ɓaci. "Ji fa, ashe ga inda aka haihu a ragaya nan. Kana tunanin za ka yi waya a gida amma Na'ima ta kasa fahimtar komai?" Ɗanmutuwa ya girgiza kai. "Ban maki musu ba, amma dai ina tabbatar maki cewa ba ta ji ba. Matsoraciyar mace irin Na'ima ban hangi ta inda za ta shanye tashin hankali irin wannan ba ta yadda ko a fuska ba zan gane ba." Ɗan murmushin ba ka da wayo Hajiya Adama ta yi mishi. Sai kuma ta yi ƙwafa. "Shikenan, muje zuwa wai mahaukaci ya hau kura. Ai kare na yawo zabo na yawo wataran za'a haɗu, idan ka ji labari za ka ce na faɗamaka." Aikuwa yin maganar da kwana ɗaya, labari mai zafi ya zo daga bakin Gwaska cewa ai Umma da Haulatu a yanzun sun tare gidan makwafcinsu Alhaji Mijinyawa. Ya kuma samu labari cewa ana zargin Ɗanmutuwan da yin garkuwa da ɗiyarsa Haulatun. Wannan magana ta jefa Ɗanmutuwa cikin tashin hankali. "Ya akai wannan zance ya fito?" "Ba ga shi nan ba! Ai na faɗamaka! Yanzu sai dai mu sa manya a gaba a kashe zancen. Raina kama kenan ka ga gayya. Yanzu ga shi nan ta shayar da kai mamaki." Wannan amsar ya samu daga bakin Hajiya Adama. A ƙarshe suka yi duk wata ƙulla-ƙullarsu aka tura Ɗanmutuwa wai ƙebantaccen gidan gona na wani  babba a ma'aikatar Custom dake harƙallar miyagun ƙwayoyi da su. Kusan su na ji sosai da Hajiya Adama a fagen kasuwancinsu wannan dalili ya sa duk wata alfarma tana samuna wurinsu. Ɗanmutuwa kuwa ya zame musu wannan mutum mai sa'a, duk wani kaya da zasu damƙa a hannunsa to fa nan da nan zasu ƙare. Wannan yana daga dalilan da suka ɗauke shi da muhimmanci a tafiyarsu.   Haka Ɗanmutuwa ya koma can Gwarzo inda gidan ginar yake, sai dai zuciyarsa ta kasa sukuni, ba kuma tsoron za'a cafkeshi yake ko wani abun ba, sai don jin bakin ciki da haushin Na'ima wacce ta jawomasa asarar maƙudai. Ya kuma sha alwashin idan komai ya lafa sai ya ɗauki mataki a kanta. Wannan kenan. *** Hajiya Mama da Mijinta zaune a saman kujera a falo, yayinda Umma da Haulatu ke gefe saman kafet. Ganin irin halaccin da suka yi musu ya sa Umma warware musu zare da abawa na asalin dalilin da yasa ta auri Ɗanmutuwa da kuma zamanta a cikin ƴan  bariki wurin mahaifinta. A ƙarshe ta miƙawa Abban su Bahijja hoton mahaifiyarta wanda ke ɗauke da sunan gari da kuma zuri'ar da ta fito. Da mamaki tsantsa Abban Bahijja ya dubi sunan, ba don wai ya yi mai sunan keɓantaccen sani ba, a'a, sai don sunan ba ɓoyayye ba ne tun zamanin iyayensu har kuma zuwa yanzu da matasan jikokin gidan suke nasu tashe na kuɗi da ma ilimin boko da arabi. Ya maida duba ga Umma dake sharar hawaye na fargabar abin da za ta je ta tarar a cikin dangin mahaifiyarta. "Na'ima, kina son cewa mahaifiyarki ɗiya ce ga Tsohon Attajirin nan Alhaji Bello Shu'aibu Malumfashi?" Hajiya Mama jin sunan ya sa ta kalli Abban da mamaki kafin ta kai hannu ta karɓi hoton, matar kamar an tsaga kara tsakaninta da Umma sai ko ta juya ta ga rubutun. Asma'u Bello Shu'aibu Malumfashi. Katsina. Har da kwanan wata na sadda aka yi hoton. "Ikon Allah." Shi ne abin da Hajiya Mama ta furta. Umma bayan ta amsa da Abban Bahijja da eh, shima jinjina kai ya yi cike da tsantsar mamaki. Ya sani akwai sauran rina a kaba a ɓangare na rayuwar Umma, bai ce ko ba za su karɓe ta ba ko wani abun makamancinsa ba, sai dai babban zuri'a ne da ya tara yara da jikoki. Yana da tabbacin wannan rayuwar da ta shimfiɗa a waje daga baya ta zo musu, za ta fuskanci wasu abubuwan dole kafin ta samu karɓuwa. A hasashen Abban Bahijja kenan. Ita kuwa Haulatu ta ma kasa gane me take ji, ita ba farin ciki ba ita kuma ba akasinsa ba. Ta dai sani Umman ta bata mamaki yanda ta iya ɓoyemata wannan hoto tun tsawon waɗannan shekarun da take nacin sai ta nemo danginsu. Haka suka rabu bayan Abban ya sa direba ya miƙa su tasha, ya kuma ba Umma kudi masu ɗan kauri cewa su riƙe. Ba iya nan ya tsaya ba sai da ya bi ta da nasiha akan ta yi hakuri ta jure dukkan wani abu da za ta fuskanta a cikin zuri'ar. Umma ta yi godiya sosai. Haka suka kama hanya bayan sun shiga har gidan makwaciyarsu  Maman Hasiya itama sun mata sallama. Haulatu ko ta kan Hindatu ba ta bi ba don tun abinda ya faru Hindatun ba ta ko neme ta a waya ba bayan biki ta ji ya ake ciki wannan ya sa itama ta watsar da ita.    Ƙarfe sha ɗaya daidai motarsu ta ɗaga daga tasha suka kama hanyar Katsina.  Abban Bahijja ya tabbatar musu cikin Katsina iyalan ke da zama kaf dinsu, ba wai a Malumfashin ba. Ita kuwa Hajiya Mama lambar wayar wata yar uwarta ta ba su akan su fara sauka a can su huta, ta kuma kira ta yi mata bayani, babu musu ta ce za ta jira su. A hanya haka ta dinga kira ta ji ko sun shigo. Suna isa kuwa, ta ce su nemi adaidaita sahu, su ba shi waya ta yi mishi kwatance.   Suka kama hanyar unguwar Dutsin Safe Low cost, ita dai Haulatu tana kallon wurare. Ta sani nesa ba kusa ba za ta haɗa garuruwan biyu ba a fagen abubuwa da dama, sai dai kuma muddin kwanciyar hankalinsu a nan yake, ta shirya shimfiɗa sabuwar rayuwa a Katsina, za ta taya Ummanta zaman haƙurin da ta ji Abban Bahijja na magana akai, akan dai ta ƙara rayuwa da mutum irin Ɗanmutuwa.   Ta kalli Umman ya fi a ƙirga, ko kusa babu ɗigon fara'a a fuskarta, ta dai bar zubar hawayen sai ko kumburin da idanunta suka yi da kuma ja da fuskar ta yi. Ta yi ɗan kwafa, a ƙasan ranta ta ce.   'Umma kukanki ya zo ƙarshe in sha Allahu koda ba a karɓe ki a dangin Mamarki ba, babu mu babu ƙara komawa Kano.' Wannan shi ne alwashin  da Haulatu ta ci. Sai a sannan ne ma ta ji ranta ya yi fari ƙal, har wani murmushi ta yi. Sun samu tarba mai kyau daga wurin yar ƙanwar babar Hajiya Mama, wacce ake kira Hajiya Rabi'atu. Mace ce babba sai dai ba ta kai Hajiya Mama a shekaru ba, gidanta madaidaici mai kyau da tsari. A falonta akwai tafkeken hotonta ita da miji da yaranta su bakwai har da ƴan biyunta maza masu ƙananan shekaru. Ta ba su lafiyayyen abinci da abin sha suka ci suka ƙoshi sannan suka yi sallar Azahar. Duk yadda Umma ta so ta bar su su ƙarasa gidan da zasu je a ranar ƙi ta yi, ta rantse sai sun kwana. Mace ce mai fara'a da son mutane ga hira. Nan ta dinga ba su labari na irin tarin arziƙin gidan Bello S Malumfashi, fadi take. "Ai Maman Haulatu ba komai ba ne daga arziƙinsa idan an haɗa da na matasan jikokinsa. Sai dai fa naji ance akwai rikici iri-iri a wannan gidan da kuma shegen gasa, kowa burinsa ya fi ɗan uwansa. Amma dai kaf cikinsu naji ance akwai ɗaya da ya fi su a komai, ni ko jikan Hajiya Saratu ne ko wa? Na dai manta. Ke na san fa duka wannan labarin a bakin wata ƙawata da Hajiya Iklima, ita ɗiyarta na auren wani ɗan riƙo a gidan ne." Haka ta dinga zuba hira wanda Umma duk hankalinta ba ya kai, fargabarta na kan abin da zai je ya zo. Yayinda Haulatu ta baza kunnuwa tana sauraro sai faman washe haƙora ta ke, babu ma kamar Hajiya Rabi da ta dage sai ta yi musu rakiya a goben, acewarta za ta tsaya tsayin daka wajen ganin an karɓi Umman hannu bibbiyu. "Uhm." Shi ne kawai abin da ya fito a bakin Umman. ***   *LATE ALH BELLO S MALUMFASHI RESIDENCE.* Fitar tsiro Page 13 *Late Alh Bello S Malumfashi Residence* Haka aka rubuta a ƙaramin allo wanda ya sha adon baƙi da kuma ruwan zaiba da aka liƙe a daidai tafkeken gate na shiga gidan. Haulatu ta ɗauke kai daga saman allon ta mayar da idanunta kan gidan wanda kusan tun farkon layin har zuwa ƙarshe shi ne ya ci ɓangaren dama. Gida ne mai adon fari da ruwan toka. An ƙawata wajen da shukoki masu kyau inda aka gewaye wurin shukokin da wasu fararen ƙarafina sai kuwa fitilu dake jikin bangon wanda ko ba a faɗi ba idan dare ya yi su na taimakawa wurin daɗa ƙawata su.   "Madams, ina zuwa?" Hankalin Haulatu ya koma ga jibgegen ƙaton dake tsaye jikin ƙofar shiga gidan, idanunsa akan Umma, sosai yake ganin kamanninta da mutan gidan, sai dai shigar da ta yi ko ƴan aiki albarka. Hajiya Rabi cikin sauri ta amsa. "Mun zo wajen Hajiya Babba ne." Ya ƙara duban Umma kafin ya dubi Haulatu, kai shi abin mamaki yake ba shi, to ko ƴan uwansu ne daga Malumfashi? Ƙarshe dai ya ce su jira yana zuwa. Cikin ɗakinsa na gadi ya koma ya danna kira ɓangaren Hajiya Babba. Koda aka amsa ya yi bayanin an yi baƙi, babu ɓata lokaci aka ba da umarnin su shigo. Ya sani dama idan har ɓangaren Hajiya Babba ne, ba a fiye disga baƙo ba. Matuƙar aka zo ganinta, to fa koda ace jikin girma ya hana ta fitowa wurinka, ba za ka tafi hakanan ba. Dawowa ya yi ya yi musu iznin su shiga. Nan fa suka shigo farfajiyar gidan da ya kusan tafiyar da numfashin Hajiya Rabi da Haulatu. Ita dai Hajiya Rabi tun da take ba ta taɓa shigowa gidan S Malumfashi ba sai dai ta ji ana koɗa shi a wani wurin, ga Haulatu kuwa, ta sha jinin jikinta don ba ta hangi inda za su sami matsagini a gidannan ba ita da mahaifiyarta. Umma kuwa ƙirjinta ke bugu da sauri-sauri, hatta da jikinta rawa yake yi. Ta daure ta shiga ambaton sunan Mahaliccinta. "Kun san hanyar kuwa?" Suka ji sautin Maigadin na tambaya. Kamar wasu ƙadangaru haka Hajiya Rabi da Haulatu suka shiga girgiza masa kai. "Hey! Siii!" Suka dubi wanda yake kira don su gaba daya yanda suka shagala da kallon gidan bai sa sun kula da wanzuwar wata halittar bayan su huɗun ba. Wani ne sanye da irin uniform din dake jikinsa, ga dukkan alamu shi dinma abokin aikinsa ne sai dai shi saurayi ne bai kai shi shekaru ba.  "Kai su wajen Hajiya Babba." Ya dube su, baki ya ɗan buɗe ganin Haulatu, da idanunsa suka sauka kan Umma kuwa, sai da ya ɗan fiddo idanu. "Wai ba ka ji ba?" Cewar babban a ɗan fusace hakan ya sa shi soma tafiya su na binsa a baya. Haulatu ta ƙirga gidaje masu kala iri guda biyar curr sai kuwa wasu gidajen a gefe guda masu kala daban. Har suka ƙarasa ɓangaren matar da aka ambata da Hajiya Babba ba su ci karo da kowa ba kai ka ce babu kowa sai su ɗin. Saurayin ya ƙarasa ya ƙwanƙwasa ƙofar, can babu jimawa aka buɗe. Wata ƴar dattijuwa ce. "Baba Saude, ga baƙin Hajiya nan. Bismillah ku shiga." Ya faɗi yana mai ba su wuri, Dattijuwar da aka kira da Baba Saude ta dube su, ta ƙurawa Umma idanu tana mai cika da ɗumbin al'ajabi da mamaki. Hanya ta ba su suka shiga ciki, har sannan kallonta take yi. "Wannan fa?" Ba ta san tayi furucin ba sai da ta ji Saurayin nan ya amshe zancen. "Kema kin ga kamanninta da Hajjaju ko? Ba ƴar uwarku ce ba daga Malumfashi kuwa?" Ya yi tambayar cike da son jin ƙwaƙwaf, Baba Saude ta harareshi. "To shaida, kai dai Bilya ban san sadda za ka shiga taitayinka ba. Wuce ni ka ban wuri." Daga haka ta rufe ƙofar shi kuwa ya yi dariya ya bar wajen. Su Umma kuwa da Hajiya Rabi duka su na tsaye suna sauraronsu, ba su yi karambanin ƙarasawa cikin falon ba. Sai dai su na bin ko'ina da kallo, falon daidai gwargwado ya tsaru, har da wajen dinningtable a gefe, sai kuwa wani tafkeken talabijin a jikin bango dake faman aiki kai ka ce za ka yi magana na cikinsa ya amsa. Falon sai ƙamshin turaren wuta yake ga lafiyayyen kafet dake shimfiɗe. "Bismillah ku shigo ku zauna." Ba musu suka ƙarasa suka nemi wuri ƙasan kafet suka zauna. Baba Saude ta ƙaraso aka hau gaisuwa ita dai idanunta ya kasa kaucewa akan Umma da Haulatu masu tsantsar kama da Hajiya Babba. "Bari na yiwa Hajiyar magana." Daga nan ta miƙe ta nufi wani ɗan tsukakken wuri da aka yi bene. "Wai Allah, Allah ka yi mana arziki duniya da lahira. Hajiya Na'ima Allah yasa kun shigo a sa'a. Ni wallahi wannan fargabar da kike yi ne bana so, ki yi ta addu'a in sha Allahu komai zai tafi daidai. Naga gaba daya tun zuwanmu kin rasa sukuni." Umma dai ɗan murmushi ta yi wanda ya fi kuka ciwo jin maganganun da Hajiya Rabi ke yi, amma dagaske a tsorace ta ke. Ko wace ce Hajiya Babbar nan? Ita ce mahaifiyarta ko kuma mahaifiyarta ma ta jima da rasuwa ne? Waɗannan tunane-tunanen su ne suka yi ta ƙara jefa ta cikin faɗuwar gaba. *** Hajiya Babba, tsohuwa mai ran ƙarfe. Yanayi na hutun da take ciki ya taimaka ƙwarai wurin ɓoye tsufanta. Allah ya yiwa zuri'a baiwa ta kyawun jiki. Tana zaune saman darduma hannunta riƙe da carbi bayan ta idar da sallar walha. Sallamar Baba Saude ce ya sa ta dubanta gami da yin gyaran murya na yi mata iznin shigowa. Ta shigo ta nemi gefe ta zauna. Mintuna uku kafin Hajiya Babba ta shafa addu'a ta dube ta. "Saude, akwai abin da ake buƙata?" Cike da girmamawa Baba Saude ta amsa. "Ko ɗaya Hajiya, baƙi kika yi." Hajiya Babba dake kokarin cire gilashin karatun da ta maƙala a fuskarta, ba tare da ta dube ta ba ta janyo gidan gilashin ta ce. "Su waye haka da safe?" "To, nima dai ban gane fuskokin ba. Ba zai wuce wasu cikin yan uwanku na Malumfashi ba don na ga kamanni." Ta ɗan yi jim kafin ta amsa. "Ikon Allah, ba damuwa, shigo da su nan." Baba Saude ta mike bayan ta amsa mata da toh. Ita kanta za ta so sanin su waye a cikin dangin nasu don ba ta taɓa ganin fuskar ba sai a yau. Ta ƙarasa sauka gami da yi musu iznin su biyo ta. Suka mike suka soma taka matattakalar, Umma dai ƙirjinta dukan tara-tara yake. Yau ne karo na farko da za ta sadu da wani a cikin zuri'ar mahaifiyarta, ko wani irin tarba za ta samu? Allah masani. Sallamar Hajiya Rabi ce ta sa Hajiya Babba kallon hanya. "Wa'alaikumussal..." Sauran sallamar ya maƙale a bisa fatar bakinta sadda ta ci karo da photocopy ɗinta sadda take Hajiya Asma'unta. Umma ma kallonta take yi jikinta babu inda ba ya rawa, idan har wannan matar ba ta kasance Uwa a gareta ba, shakka babu jininta ce. "Asma'u Bello?" Umma ta samu bakinta da furucin cike da rawar murya. Hajiya Babba ta haɗiyi wani miyau maƙwat ya wuce jin sunanta ɓaro-ɓaro a bakin wannan baiwar Allah. Ga Haulatu kuwa ta dubi Ummanta ta dubi Tsohuwarnan, hakanan Hajiya Rabi da ta yi sandar tana ganin ikon Allah. Bambancin Na'ima da wannan tsohuwa sai fa shekaru. Umma kuwa, ambaton sunayen Allah da ta dinga jerawa a zuciyarta shi ya ba ta damar jin ƙarfin gwuiwar soma magana. "Hajiya Asma'u Bello, wajenta na zo." Hajiya Babba ta ji kirjinta ya buga, leɓɓanta suka yi nauyi. Kar dai ace allura ce za ta tono garma? Kada dai asirin da ta riga ta binne a bayanta, shi ne bai tashi tonuwa ba sai da shekaru suka miƙa har tafiya ta yi tafiya? Wani gumi ta ji ya tsirfo mata. Kafin ta kai ga ba da amsa ta tsinci muryar Baba Saude na fadin. "Ai da ita kike magana Baiwar Allah. Wannan ɗin ita ce Hajiya Asma'u ake kiranta da Hajiya Babba. In ce dai lafiya?" Jin haka yasa Umma ƙara kallon Hajiya Babba da gaba daya ta ruɗe. Ta rasa me za ta yi, murna ko baƙin ciki. Ɓangaren Haulatu kuwa, murmushi kawai take yi mai bayyana haƙora. Ita sosai ta ke jin wani dadi tana ƙara bin gidan da kallo sannan ta maida hankali ga tsohuwar da ta kasance kaka a wajenta. "Wace ce ke? A ina kika san ni?" Tambayar da Hajiya Babba ta watsamata kenan. "Ku zauna mana kuna tsaye." Cewar Baba Saude don ganin abin na yi ne. Bayan sun nemi wuri sun zauna ta baza kunnuwa don jin abin da zai fito daga bakin Umma. Sai dai madadin Umma ta yi magana, kawai sai ta sa hannu ta fiddo hoto ta miƙamata tare da wani abin hannu na azurfa mai kyau da ba ta taɓa karambanin fiddo shi ba ko a baya, ta yi mishi ajiya mai nisan da ko hoton ba ta adana haka ba domin shi din sunan Asma'un ne da Maikalangu a haɗe wuri guda. Hajiya Babba hannu na rawa ta karɓi hoton gami da abin hannun. "Saude ina gilashina?" Ta furta da rawar baki. Baba Saude ta cika da mamaki, da sauri ta dauki gilashin ta miƙamata, Hajiya Babba ta zura ta karanta rubutun dake jikin azurfar kafin ta kai duba ga hoton har da juya bayansa ta ga kwanan wata da kuma na gari da aka rubuta a jiki. Shikenan, ta faru ta ƙare wai an yiwa mai dami ɗaya sata! Yau ranar wanka ce da ba a ɓoyon cibi. 'Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un!' Hajiya Babba ta furta a zuciyarta. Ta ƙara ɗaga idanu ta dubi Umma wacce ta yi mata ƙuri da idanu ga hawaye kwance saman fuskarta. Fitar tsiro Page 14 "Kina so ki cemin ke ƴar gidan Saleh ce?" Hajiya Babba ta fisgo tambayar daƙyar daga kwakwalwa zuwa harshenta. Murmushi mai ciwo Umma ta yi. "Ni ɗiyar Saleh da Asma'u ce. Akwai abin da kike tantama ne? Ko ki na so ki cemin kin manta sadda ki ka yi watsi da ni a bariki ba ki ƙara waiwayata ba?" "Bariki?" Faɗin Hajiya Rabi da Baba Saude a lokaci guda cike da wani irin mugun kaɗuwa. Ita Hajiya Rabi ai ba komai Hajiya Mama ta baje mata a faifai ba. Ga Baba Saude kuwa, kallon Hajiya Babba kawai ta ke yi, burinta ta ji gaskiyar zance daga bakinta. Gumi kawai Hajiya Babba ke yi, ranta ya ɓaci. Wato Saleh sai da ya karya alƙawarin da ya ɗaukarmata? Sun yi da shi duk runtsi ba zai taɓa barin ɗiyarsu ta san asalinta ba balle ta kawo kanta wataran ko kuma ya kawo ta, sun ƙulla wannan yarjejeniya shekaru masu yawa a baya wanda sanadin hakan ne ta yi mishi kyauta da wasu kuɗaɗe masu yawa da daraja irin na zamaninsu. "Me kika zo nema a wurina yanzu? Wace buƙatar ce ta kawo ki?" Haushi da bakin ciki suka mamaye zuciyar Umma, ta ma rasa me za ta ce.  Ita kuwa Haulatu wani irin kallo na mamaki take yiws Hajiya Babba. Ga ta nan dai a kallo ɗaya ta amsa sunanta da dattijuwar mace mai cikar kamala. Kalamanta sun bambanta da suffarta. "Granny! Granny!!" Maganar ta yi daidai da ƙofar da aka buɗe na ɗaya daga cikin kofofi hudu dake a falon. Gaba daya suka dube ta,  yarinya ce da shekarunta za su kai biyar a duniya. Tawul fari ƙal ɗaure a ƙirjinta sai kuwa gashinta mai cika da baƙi wanda ya sha tufka da ribbon. Yanayin yadda ruwa ke zuba daga jikinta za ka fahimci wanka aka yi mata. Tana zuwa ta faɗa jikin Hajiya Babba tana fadin. "Granny, ki cewa Mami kar ta shafamin mai. Bana so." Ya yi daidai da fitowar wacce ta kira da Mamin daga ɗaki hannunta riƙe da  kaya da kuma man shafawa na yara. "Ke Baby ki..." Sauran zancen ya maƙale a fatar bakinta sakamakon mutanen da ta gani zaune a falon, su dinma kallonta suka yi. Za ta yi shekaru ashirin a duniya, doguwa ce kuma baƙa mai ɗan jiki. Ta gaishe su mamaki dauke saman fuskarta na ganin wata mai ɗiban kama da ƴan gidansu. Wuri ta samu ta zauna kuwa. Hajiya Babba ta ture yarinyar. "Maimuna, ja hannunta ku wuce ɗaki ina da baƙi." "Baƙi kika ce fa Hajjaju? Ai ce mata za ki yi ɗiyarki ce da kika bar wa duniya ita ta dawo." Muryar Haulatu ta zo musu a bazata, zuwa lokacin ta gama kai wa wuya dama, ta kula Hajiyar za ta kawo musu rainin hankali da wayo.  Hajiya Babba duban Haulatu ta yi amma ta kasa magana. Ita kuwa Maimuna sai ta yi turus cike da tsantsar kaɗuwa. "Assalamu alaikum." Aka faɗi da murya kakkaura. Hajiya Babba ba ta san sadda ta miƙe tsaye ba. Wannan shi ne abin da take jiyewa tsoro, babban burinta ta san yadda za ta yi da su Umma kafin wani ɗan uwan nata ya shigo. Baba Saude da Maimunatu suka gaishe shi. Dattijon mutum. Dogo mai cikar farin ƙasumba. Kallo ɗaya za ka fahimci girman da ya kama shi sosai. Dakta Suleiman B.S Malumfashi kenan. Ɗa na huɗu a wurin Marigayi Alhaji Bello. Su biyar ya haifa. Hajiya Asma'u ita ɗaya ce mace a cikinsu. Su uku kawai suka rage a yaransa. Shigowar da ya yi ta musamman ce, magana ya zo su yi da Hajiya Babba akan jikarta Maimuna da ta yo yaji kuma Hajiyar ta ɗauremata gindin zama. Umma ta dube shi, shi ma Dakta ita ya zubawa idanu yana amsa gaisuwar su Baba Saude. "Yaya, sannu da zuwa." Fadin Hajiya Babba da rawar baki. Idanunta nan da nan suka kawo ruwa tsabar tashin hankali. Yau dai abin da ta binne shekaru masu yawa zai tonu. "Yauwa. Asma'u, wace ce wannan din?" Ya yi tambayar yana ƙara gyara zaman gilashinsa. Tuni Haulatu ta yi caraf ta ce. "Ni jikarta ce, wannan kuma (ta dafa kafaɗar Umma) ɗiyarta ce ta cikinta da ta haifa ta bar ta a hannun mahaifinta Saleh Mai Kalangu ba tare da ta ƙara waiwayon rayuwarta ba." "Saleh Mai Kalangu?" Dakta ya maimaita sunan, shiru ya ɗan yi yana nazarin inda ya  taɓa sanin wannan suna kafin ya yi salati a fili yana duban Hajiya Babba wacce tun shigowarsa ta miƙe tsaye kawai sai ta fashe da kuka. "Asma'u, kodai ban ji da kyau ba. Ɗiyarku ke da Saleh Mai Kalangu? Wannan zancen gaske ne ko kuwa dai wasa ne aka zo a ynda hankulanmu?" Ta kasa magana sai kukan, ranta na suya da zafi tana ji kamar ta kama Haulatu ta jibga tsabar yanda ta yi mata tonon silili a idanun mutumin da take yiwa kallon Uba kuma ɗan uwa mafi kusa da ita. Mutumin da ba ta taɓa ɓoyemasa komai ba kasancewarsu saƙo da saƙo kuma jininsu ya haɗu sosai fiye da sauran yayyunta maza. Yau dai ga babban sirrin da ba ta taɓa gigin sanar da shi ba. Bayan ita da wasu bayin Allah biyu da ta rayu da su a can wani gari, sai ko uban gayyar Saleh Mai Kalangu, babu wanda ya san da batun cikin Na'ima balle a san da wanzuwarta a doron ƙasa a dai nan garinsu Katsina. Shiru ma magana ce inji Hausawa, tabbas shirun da Hajiya Babba ya tabbatarwa Dakta zarginsa. "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un." Ya maimaita a karo na biyu. Wayarsa ya fiddo ya danna kira, yayansu babba da ya rage ya kira ya ce masa ga su nan zuwa da baƙi, magana ce mai muhimmanci. Yana katsewa ya dubi Hajiya Babba, gaba daya idanunsa sun kaɗa. "Ku muje can ɓangaren Alhaji a yi magana. Wannan ba ni zan yi hukunci ba." Ya ƙarashe da jin ɗaci a maƙoshi. Daga haka ya sa kai ya fice daga falon bayan ya ba Maimuna umarnin ta yiwa su Umma jagora sashin Alhaji. *** Babban falo ne mai dauke da ababen mora rayuwa daidai gwargwado. Tsaruwarsa ya shafe na sashin Hajiya Babba. Wani tsoho ne zaune saman dardumarsa ta ibada. A gefensa wasu matasa ne biyu wadanda duka ba su wuce shekara ashirin da takwas ko tara ba. Hira suke yi kafin wayar da Dakta ya yiwa Alhajin ta katse su. Ko bayan kammala wayar shiru suka yi baki daya domin da yawan lokuta Alhajin yana amsa waya ne ta hanyar sanya ta a handsfree. Wannan ya ba samarin damar jin abin da ya ce. Ɗaya a cikinsu wanda ya fi ɗan uwannasa jiki da kuma hasken fata ya miƙe. "Bari na ƙarasa ofis kafin wancan Baturen ya kore ni." Jin haka ɗayan ya yi dariya gami da faɗin. "Kai Haidar, ka iya bakinka fa, ko ka mance a gaban amininsa ka ke? Wannan ɗan tsohon ko tusa aka yi sai ya fesa mishi." Alhaji ya kai mishi duka da sandarsa dake ajiye a gefe. Aka yi dariya baki daya. Ya amsa. "Ja'iri, kun fi kowa sanin ai Sadaukina daidai yake da ku. A hankali zai saita ku kowannenku ya shiga taitayinsa tunda na kula ku kam ba ku da aiki sai kashe-kashen kuɗi. Kai kuma mai kiransa da Bature kamar a kunnensa." Wanda aka kira da Haidar ya kama kunne. "Tuba nake tsoho mai ran ƙarfe, Ango kuma miji gurin Hajja Bilkisu mai gadon zinare. Allah ya ja da ranka, idan ka mutu kuma Allah ya haɗaka da ita a aljanna." "Amin, amma mutuwa kam ba yau ko gobe ba da yardar Allah. Ɓacemin kafin ka kashemin jiki." Matasan suka tuntsire da dariya karo na ba adadi. Kafin su kai ga tashi sai ga sallamar Dakta, wannan ya sa duka suka ɗan nutsu. Dakta da Hajiya Babba suna daga cikin kakannin da sam ba su sakin fuska yadda ya dace ga jika. Babu ma kamar Hajiya Babba wacce ake masifar shakka idan ta tubure ta hau faɗa da bala'i akan duk abin da aka yi bai yi daidai da ra'ayinta ba. Ita ce ƙaramarsu amma su na ji da ita sosai don suna yawan cewa ita ɗin amana ce ta iyayensu, kuma sun musu Allah ya isa idan har sanadinsu ta shiga wani yanayin. Wannan ya sa ba a komai suke tsawatar mata ba sai idan sun ga tura ta kai bango. Samarin suka gaida Dakta cike da girmamawa. Kafin su maida duba ga wadanda ke shigowa falon. Duban junansu suka yi da tsantsar mamaki. Bayan sun zauna sai ga Hajiya Babba itama ta shigo. Idanun Baba Dakta ya rufe bai ma nemi su Haidar su tashi ba ya korawa Alhaji komai da ya je ya tarar a sashin Hajiya Babba. Ya yi mishi nuni da Umma gami da ba ta umarnin ta tashi ta matso kusa. Umma ta miƙe ba musu har jiri take ji tsabar damuwar da ke cinta ga wani zafi da take ji daga ƙirjinta sai kuwa kai dake sara mata lokaci guda. Har Umma ta ƙaraso ta durƙusa gaban Alhaji ta ƙara gaida shi bakinsa bai bar furta sunayen Allah ba. Alhaji ya dubi Dakta kafin ya maida kai ga Hajiya Babba wacce ke faman kuka na takaicin wannan ranar. "Ya Allahu, Sule, ai wannan Asma'u ce zaune a gabana." Dakta ya yi ƴar dariyar baƙin ciki. "Ita ce Yaya, ɗiyarta ce ta cikinta. Ta ɓoye mana bamu da labarinta. Haka iyayenmu ba su san da wanzuwarta ba har ƙasa ta rufe idanunsu. Watakila ba don Allah ya yi zamu san gaskiya ba, da har ƙasa ta rufe namu idanun ba mu da masaniya a kanta." Haidar dai sun yi mugun kaduwa da jin wannan labari, wayarsa da ta yi ƙara ce ta sanya Dakta ankara da su. Nan ya ce maza su fice. Suka miƙe don su dai kam sun gama jin kan labarin. Suna fitowa Haidar ya dubi ɗan uwana Jabeer. "Kai! Don Allah ɗan mintsile ni na ji ko dai mafarki nake?" Jabeer da shima ya yi mutuwar tsaye don mamaki ya kuwa girgiza kai bakinsa a bude, can kuma ya yi wata ƴar ƙaramar ashariya ya ce. "Kai! Yau akwai labari a gidan nan. Wai Allah, wa ya kamata na fara kira?" Haidar ya yi wata dariya. "Amma ashe tsohuwarnan ma ta buga duniya har haka take neman shigar mana hanci da ƙudundune? Kalli fa kamanni kamar ta yi kaki. Ai wallahi wannan ta fi kama da ita akan Anti Maryam. Kai! Akwai fa labari a gidannan! Ai mu shiga group kawai." Suka yi dariya, dariya irin ta mamaki da kuma ganin bala'i da masifar da abu kaɗan Hajiya Babba ta jefa akan jikokinta da ma wasu a yaran ƴan uwannata, sai ga su nan sun bayyana a tattare da ita. Suna da yaƙinin cewa labarin nan zai girgiza wannan zuri'a ta su. *** Hajiya Babba ta dubi Alhaji bayan ta gyara zama. Alhaji ya jefamata tambaya har sau kusan uku akan dagaske ɗiyarta ce amma ta kasa amsawa, sai a yanzun da ya haɗa da tsawa cikin muryarsa ta tsufa kafin ta yi yunƙuri na ba shi amsa. Haulatu kawai harararta take yi don a farkon ganin tsohuwar ta ji ta burgeta, sai dai a yanzu kam ji take yi babu wacce ta tsana sama da ita tun daga yadda ta nunamusu da farko. "Eh, ɗiyata ce da na haifa tare da Saleh." Ta ba da amsa kai tsaye, Umma ta sunkuyar da kai gami da lumshe idanu, hawaye kawai ke fita daga idanunta. Alhaji ya yi salati. "Ɗiyarki ce dai kenan Asma'u. Garin ya ya haka ta faru? Kin ce mana guduwa kawai ki ka yi daga gida kuma kika dawo bayan zuciyarki ta yi sanyi. Kin nuna mana ke ba Saleh kika bi ba, Asma'u wannan maganar kuma daga ina ta ɓullo?" Girgiza kai Hajiya Babba ta yi, wannan masifa da me ta yi kama? Meyasa asirinta bai tashi tonuwa ba sai bayan da tsufa ya zo mata? Kai, ita ta ma yi zaton tunda har labari ya risƙeta na mutuwar Saleh tun a baya, to ɗiyar itama ta mutu. Ashe dai dama akwai sauran rina a kaba? Ta sauke ajiyar zuciya ta ƙara duban Umma karo na barkatai sannan ta maida duba ga yayyunta. "Ranar wanka haƙiƙa ba a ɓoyon cibi, saboda ita Na'ima, zan ba da labarin komai tun farko har zuwa lokacin da na dawo gida wajenku. Da kuma irin rufi na asiri da marigayi mijina Yusufa ya yimin sadda muka yi aure." Gaba daya hankali sai ya koma kan Hajiya Babba har Umma. *** An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels