Compiled by Princess Aysha Muhammad [10/7, 17:10] ‪+234 706 738 2588‬: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 'YAR AIKI. 0⃣1⃣ NA ALAWIYYA ADO 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷. Khalid ne jingine jikin kofar da zata sadashi da falon mahaifinsa, Alhaji Abbas, yakai kusan mintuna biyar yana buga kofar falon cikin nutsuwa, ganin ba à bude kofar ba yasa shi jingina da jikin kofar. Aunty salma ce ta fito ta bude kofar falon, ganin khalid à tsaye jikin kofa shine yasata sakin fuska, cikin fara à ta bude masa kofar sosai yasa kai ya shiga. "yarona sannu da zuwa yau kaine da wuri Haka ? Ina kabar min surukata ? Cikin fara à take masa wadan nan tambayoyin. " ko zama banyi ba Aunty kike tsareni da tambayar ina surukarki, surukarki na gida, KO tashi batayi ba ma na fito ". Tab ! Kace ko sallama ba kayi mata ba ka fito ? Inafatan dai lfy ? " lafiya lau Aunty sammako nayo muku Alhaji nakesan gani kafin ya fita shiyasa nayo sammako dan ko gun Hajiya ban Shiga ba " Ai kuwa ka daki gurbi dan wallahi Alaji yayi sammako sunje gidan Alhaji Bukar, jiya cikin dare akayo masa waya yana gida ciwan ciki ya murdeshi cikin dare, toh Sun kaishi asibiti cikin daren Amma basu kwana ba suka koma gida, shine yayi sammako yaje yaga jikin nasa ". Ya Salam ! Aikuwa bari intashi inbisu inga jikin nasa. bari in leka mu gaisa da Hajiya sai in wuce daga nan. Aunty Natafi, cikin sauri ya tashi ya fice daga falon . kai tsaye bangaren mahaifiyarsa y dosa Hajiya jiddah, à gurguje suka gaisa ya fito ya doshi gidan Aminin mahaifinsa Alhaji Bukar dake unguwar farawa. Karfe goma Sha daya na safe agogon dake manne à babban dakin ya buga, bugawarsa yayi daidai da farkawar SUHAIMA daga baccin da ta kwanta tun jiya, idanuwanta ta daga takai dubanta kan agogo ganin da tayi lokaci ya ja, shine ta tashi cikin sauri ta fada bandakin dake makale à cikin dakin barcin maigidan ta. Wanka tayi, sannan ta sanya doguwar riga ta gabatar da sallar asubahi ,bata tsaya yin doguwar addua ba tafada dakin girki dan samun Abinda zata Sanyawa cikinta, sabida azababbiyar yunwar da takeji. Ruwan shayi ta tafasa ta sanya cikin fulas, ta soya wainar kwai ta debo kayan shayi ta nufi falonta dan ta karya kumallo. Kusan karfe d'aya na rana taji ana kwankwasa kofar falonta, Dan kwalli tayafa akanta, ta je domin ta bude kofar, tana budewa idanuwanta suka sauka kan aminiyarta, wata wawar runguma tayi mata suka shigo falon suna dariya. "kai kawata baki da kirki kiri kiri kinki zuwa gidana sai da à waya ko muyi chart " ? cikin dariya Nabila tace "Amma dai kya barni in zauna kafin ki fara yin mitar" yauma sa a kikaci nazo miki kema Ai ba kirkin gareki ba daga ke har khalid din. Wallahi kawata KO jiya mun dade muna hirarki. Hmm ! Ku kuka sani dai. Tashi ki samo min abinci yunwa nakeji. yunwa ? Aikuwa sai dai kisha shayi nima daxu shi na gama sha ,ko kuma ki shiga madafin ki dafa Ai kema nan gidanki ne kawata. Nabila kuwa kasake tayi tana kallanta, cikin mamaki, toh yanzu daga zuwa na gidan mutane ina bakuwa sai à tura ni kichin yin girki, wato Suhaima kiwar nan taki har yanzu baki daina ba duk fadan da akai miki bakiji ba ko !! "yanzu mijin nakima ruwan shayin kika bashi yasha da zai fita ? kinji ki ko da wani zance, idan baisha ruwan tea ba me zan bashi ? ni yauma ina bacci ya fita, Ban saniba ko ya karya ko bai karya ba ya fita. wani wawan kallo Nabila ta jefa mata, Amma kedai kin zama shashasha wallahi ace mijinka shine zai fita kana kwance kana baccin asara, ki tunafa ke amarya ce ko wata guda baku rufe ba,, baxaki tsaya ki kula da rayuwar mijinki ba, sai ki zama shasha cikin gidan Aurenki. nikam kin bani mamaki wallahi karatunki ya zama na banza da wofi ma. ke ke ke dakata ! Suhaima ta daga mata hannu cikin bacin rai take magana ai gara muyi dama mun dade bamu kwafsa ba, dan nayi Aure kuma shikenan baxan huta ba menene amfanin auren Ai Nayi Aure ne dan muji dadi mu huta amma Sam bazan iya yin aikin gida ba kin san ko mumy ba sani takeyi ba. Nabila dai, takaici ya cikata ko magana taki yi, mayafinta ta cire ta shiga kichin din, tana shiga tafara cin karo da kayan wanke wanke jibgi guda, kichin din yayi gaja gaja, omo ta dauka tayi wanke wanken ta gyara ko ina à kichin din yayi fes. sannan ta dora musu abincin da zasuci. Bayan tagama girkin ta zubo musu suka zauna sukaci suna hirarsu ta sun dade basu hadu ba, sai kusan karfe biyar na yamma sannan Nabila ta tafi gida. wannan kenan [10/7, 17:11] ‪+234 706 738 2588‬: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷 'YAR AIKI 0⃣2⃣ Na ALAWIYYA ADO 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 Bayan tafiyar Nabila, suhaima komawa tayi tayi kwanciyarta, bayan wani lokaci bacci yayi gaba da ita. Khalid kuwa yana fita ya dauki hanyar farawa gidan Aminin mahaifinsa, Alhaji Bukar, da yake ya saba da masu gadin gidan yana zuwa suka bude masa tangamemen gate din shiga gidan ya sanya hancin motarsa ciki, kai tsaye cikin gidan ya shiga dan dan gidan ba bakunsa ba Ne bayan yaje Sun gaisa da mumy, bangaren Alhajin ya nufa ,à zaune ya samesu shida mahaifin nasa, Bayan ya shiga ya sami guri ya zauna har kasa yaje ya gaida mahaifinsa sannan aminin mahaifin nasa yayi masa sannu da jiki. "sannu yaran kirki wanene ya sanar maka bani da lfy ne ? Alhaji Bukar ya tambaya. Abba naje gida ne gun Alhaji shine Aunty take fadamin baka da lfy, Alhajin ma yana nan gidan" Shine na taho dan inga jikin naka. Ka kyauta kuwa, Nagode maka ai naji sauki aussi, jiya ban zaci zan kwana a duniya ba sabida azabar ciwo. Ayya sannu Abba, Ai jiki yayi kyau. Allah ya kara afuwa. Amen y Allah yarona. Shikam Alhaji yana zaune yana jinsu, sai da suka gama sannan yakai dubansa ga Khalid yace . "ince ko lafiya na ganka da wuri haka ? lafiya lau, Alhaji dama gaisheka naxoyi. À à babban mutum ban sanka da karya ba lallai akwai magana à bakinka, cewar mahaifin khalid. shikam dariya yayi yace Alhaji ,da gaske babu komai, tafiya ma zanyi tunda naga jikin Abban yy sauki. Ai jiki yayi sauki sosai nima tafiya nake sanyi, tunda ya warware. Karfe Bakwai na dare, khalid ya dawo gidansa, gimbiyar tasa tana kwance kan doguwar kujerar dake kewaye da falon,, Jin bude gate din gidan shine yasata tashi da sauri dan tasan maigidan Ne ya dawo, kafin ya shigo taje dakinta ta kara gyara fuskarta da powder, ta feshe jiki da turare. sallamarsa ce tasa ta fitowa da sauri daga cikin dakin, da dan gudunta tazo ta rungumeshi, tanai masa sannu da zuwa, shi kam kamshin turarenta da yabugeshi shine ya cenza masa komai. Baby na yau fa nayi fushi da kai, ta dan tureshi daga jikinta tana turo masa baki na shagwaba. Haba matata laifin me kuma nayi miki akai fushi dani ? Bacin kaine tunda ka fita tun safe baka dawo ba sai yanxu kuma ko ka kirani a waya kaji yaya ma nake. tasake turo baki tana shagwaba. Yi Hakuri matata, yau aiki ne yayi min yawa amma bazan karaba, ya kama kunnensa Alamar yanaja kamar wani yaro, Hakan da yayi kuwa abin dariya ya Bata. toh, Baby na hakura. Yauwa matata, ya fada cikin dariya. wanka yaje yayi a bandakinsa, daga baya ya dawo ya sameta zaune à kan kujera tana ta chart, kusa da ita yazo ya zauna ya karbe wayar dake hannunta ya ajiyeta gefe, wato ke dai bakya gajiya da chart kullum ? tashi tayi ta zauna daf da shi har takan jiyo bugun ziciyarshi, toh Baby na yaya zanyi, kullum ina zaune ni kadai daga kallo saï chart sune abokan hirar tawa. kada kansa yayi to shikenan, me kika dafa min yunwa nakeji. ta ware idanuwanta dara dara, wai gashi banyi girki ba, dazu ma Nabila ce tazo shine ta dafa mana Amman akwai ragowa ko in debo maka zakaci ? gyada kansa yayi kawai, yace to jeki ki kawo min. mekewa tayi taje kichin din ta dakko filet taje ta bude tukunya ta zubo masa, ganin taliyar bata da yawa kamar bazata ishe shiba har kanzo kanzon ta kwasu masa. yana zaune yana kallo ta shigo ta ajiye masa akan dan karamin teburin dake gabansa. Gefen sa ta dawo ta zauna, lomar farko yakai bakinsa yaji kanzo à bakinsa da sauri y furzar da ragowar dake cikin bakinsa. lafiya baby na ? kai kawai ya daga mata alamar ehhh lafiya nake. kawo min ruwa shine abin da yace mata. na urar sanyaya ruwa ta bude ta dakko masa ruwa roba daya, ko kufi Bata dora akai ba haka ya balle murfin ya kwankwadi ruwan, saï da ya kusa shanye ruwan sannan ya ajiye sauran. SUHAIMA, ya kira sunan ta, ita kanta ji tayi banbara kwai sabida bai saba fadar sunanta kai tsaye ba. cikin sanyin jiki ta dago da kanta takai dubanta gareshi. kina jina ko ? ya kuma magana a karo na biyu. "ehhh, ina jinka. ta fada jikinta a sanyaye. [10/7, 17:12] ‪+234 706 738 2588‬: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 'YAR AIKI 🙆 Page 0⃣3⃣ NA ALAWIYYA ADO SUHAIMA, kina ganin haka ya dace ace muna gudanar da rayuwar Auren mû ? Ki sanar dani menene matsalarki à gun girki da gyaran gidan nan ? Baki iya ba ne ? Inje in kirawa maryam kanwata ta koya miki. Suhaima tunda mukayi Aure yau kusan sati uku kenan, bakya girkan abinci, sai dai muje gidan cin abinci na siyo mana, ko inje gida inci acen, kina ganin haka kowanne magidanci yakeyi à gidansa ? Idan akwai matsala kiyi kokarin sanar dani matata, ya fada muryarsa cikin rauni. Tunda ya fara maganar nan, ita kam hawaye ne yake sassarfa zuba akan kumatunta, bata da Katar Da shi ba sai da ya gama maganarsa. Cikin kuka ta fara da cewa. "Haba Baby na, kasan inayin aikin gidan nan dai dai kokarina, kasan kuma abubuwan sai a hankali tunda ba sabawa nayi da yi ba bayan haka kuma ga wasu hidin dimun sun kara hawa kaina wadan da ban saba da su ba. Kaga dazu ma da kyar na iya tashi nayi sallar asubah sabida gajiyar da nayi duk jikina ciwo yake, ta karashe maganar cikin shagwaba, hmm toh yaya kakiso inyi ? Shiru yayi, yana jinjina magan ganunta, ya kuma gasgata abun data fada masa, musamman ganin hawaye akan kyakykyar fuskar tata. kamo hannunta yayi Ya sanya cikin nasa, ya tallafota yana rarrashinta, nan da nan ta sake ranta suka fada cikin nishadi. Karfe goma, na safe, khalid Ne rike da bakar jakarsa, wadda yake tafiya kasuwa da ita, gefansa kuwa suhaima ce ta rakoshi bakin motarsa. Baby na, cikin wata sigar Jan hankali ta kirashi, cikin kasalalliyar murya ya amsa mata. yaya akayi ne madam ? "Dama cewa nayi ko inzo mutafi tare ka sauke ni agun mumy na, kaga tunda makayi Aure bata zo gidan nan ba, nima kuma banje ba " Tabb ! Ai ke da ki fara fita sai bayan wata shida. Ya fada yana dariya. itama dariyar takeyi. Haba dai dan Allah ka barni inje. toh ki bari idan Allah ya kaimu gobé idan zan fita saï mutafi taré in saukeki agidan naku. Murna tayi sossi har da rungumarsa, motarsa ya bude ya shiga,mai gadi ya bude masa gate din ya fita. Suhaima kuwa ciki ta koma da tsananin murnarta, wayarta ta dauka tayiwa mumy Albishir din zuwanta à gobe, itama mumy taji dadin ziyarar ta 'yar tata zata kawo mata. Tunda Ta kwanta à kan doguwar kujerar falon, data ta bude ta fara sana ar tata ta chart, sallah ce kawai take tashinta ita ma ba akan lokaci ake yinta ba. washe gari tun da sassafe suhaima ta tashi ta shirya sabida murnar zuwa gida, karfe goma da rabi, ya sauketa a kofar gidan su, tare da bata sakon ta isar masa da gaisuwarsa à gun mumy, kafin yazo da daddre. da gudu ta tusa kanta cikin dakin mumy din ta tana kwance taji suhaima a kanta tana ihun murna. tashi tayi ta zauna tana fadin ohhh, suhaima ko yaushe zakiyi hankali ? Ki dubi yadda kika fadomin aka ko sallama babu, Dan Allah ki dinga nutsuwa. yi hakuri mumy murnar ganinki ce ta mantar dani komai. Gefen kujerar da take taje ta zauna ,mumy dady kuwa yana nan ? Sabida inganshi nayi sammakon nan. " Aikuwa kinyi sa a yana kusa bai fita ba" Da gudu ta tashi zata tafi gun dady, ke dakata cewar mumy ai baya gidan dan gidan mlm mude ne ya rasu sunje gun jana iza amma zai dawo dan ko karyawa baiyi ba" Jiki à sanyaye suhaima ta dawo ta zauna, mumy wanne daga cikin yaran gidan ? Wannan mara lafiyar kwakwslwar ne ya rasu. Allah sarki Allah ya jikansa ai ya hutama wallahi. Ke yaya maigidan naki, ince ko kuna zaune lafiya babu wata matsala ko ? Mumy bubu wata matsala,, sai dai gidan ne yayimin girma bana juré shareshi gaba daya, mumy ga wanke wanke ga girki, sune kawai suke bani wahala mumy. Shine matsalata kawai. Ai shiyasa nake fada miki ki koyi aikin Gida sabida duk macen data iya komai kafin tayi aure ta huta komai zaizo mata da sauki. Ni wallahi mumy bazan iya ba. kawai ki bani mu ifa in tafi da ita ta dinga tayani aikin. kema kin san wasane wannan, ta yaya zan dauki 'yar data ragemin in baki ita, Ai ko dadynku bazai yarda ba, shi khalid din ba yanada kanne ba abaki guda daya mana a cikinsu, sai ta dinga taimaka miki. Ni wallahi mumy bana san kannensa suzo gidan nan koda da yini ne bare su dawo gidan da zama. " ke SUHAIMa kada fa kizama irin matan nan da basa son dangin mijinsu su rabesu, kiyi kokari ki dinga jan 'yan uwansa à jikinki hakan zai kara bashi dama akan ya kara kyautata miki " Zumburo baki tayi Tom mumy zanyi tunda kince ayi din. ranar dai yini sukayi suna hira da mumy da kannenta, har dady shima ya jima ana hirar da shi daga bisani kuma ya shirya ya fice kasuwa. Kusan karfe takwas, saura Khalid ya shigo gidan, dukkansu à falo ya samesu, har da dady din. Bayan ya tsuguna ya gaida surukan nasa, ya jiyo kan kannen matar tasa, Suhail da Na ifa, manyan gari sannunku. Suhail ne ya fara gaida Shi sannan Na ifa, gaisuwa sosai sukayi da wasa da dariya. mukullin motarsa khalil, ya mikawa Suhail. "jeka cikin mota ka dakko muku alawa à bayan mota " Cikin girmamawa ya karba ya tafi aiken da mijin yayar tasa yayi masa. Suhaima na kwance jikin mumynta koda khalili ya shigo hakan baisata ta Mike ba daga kwancen tayi masa sannu da zuwa. Suhail ne ya shigo da mayan ledoji guda biyu kowacce shake da kayan kwalama yaje gaban mumy ya dire mata . cikin murna mumy tayiwa surukin nata godiya, da fatan samun zaman lafiya cikin Auren nasu. shikam dady fada yayi akan kashe kudin da khalil yayi gun siye siyen da Yayo. sannan yakara da yimusu nasiha, akan wasu nauyin da Allah ya dora musu akan junan su. sai kusan karfe goma na dare sannan suka koma gida cikin farin ciki bama kamar Suhaila dataje taga mumy da kannenta. wannan kenan [10/7, 17:12] ‪+234 706 738 2588‬: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 'YAR AIKI. Page 0⃣4⃣ NA ALAWIYYA ADO. 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🌐HAJOW📝🌐 👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧👩‍👧‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏾 Rayuwa tana ta tafiya a tsakanin, Khalil da Suhaima a yanzu haka suna cikin watanni hudu da Auren su sai dai babu abinda ya cenza, sai ma karuwa da wasu abubuwan sukai. Suhaima ta samu yadda takeso a gun khalil, kudi bata da matsalarsu, kuma da yake ta kasance bamai rowa ba ce, takan yawan yin baki daga bangaren 'yan uwanta da kawayenta, 'yan uwan khalili kuwa basa zuwa sabida basu samu fuska agun matar gidan ba. WACECE SUHAIMA ? Alhaji Salisu sharif, shine cikakken sunan mahaifinta, Wanda yake zaune à unguwar NA ibawa, Alhaji salisu, dan kasuwa ne cikin kasuwar kwari, Yana sai da atamfofi cikin shagonsa, rufin asiri dai dai gwargwado Allah yayi masa, Asalinsa dan garin katsina ne cikin wani gari da ake kira da KAYAWA, kasuwanci ne ya kawoshi garin kano har Allah yasa, zamansa à kanon yake. Bayan ya dawo kano da zama Allah ya hadashi da safiyya, kanwar Abokinsa ce Rabiu, tun ana soyayya à boye har da kowa yaji manya suka shiga maganar har Allah yasa safiyya rabansa ce akayi Aure akasha biki. gida madaidaici ya kama musu haya à unguwar tarauni, zaman lafiya suke sosai à tsakanin su. tunda sukayi Aure Allah ya budawa salisu harkokinsa, kasuwa ta bude masa, cikin ikon Allah yasiyi fili a unguwar Na ibawa sannu a hankakali yake ginin filin har Allah yasa ya gama. À wannan lokacin kusan shekarsu uku da Aure Amma ko bari safiyya bata taba yiba. ita kam Abin yana damunta, anma kullum mijinnata rarrashinta yake akan tayi hakuri, in Allah yaso zata samu rabonta itama. Kwanci tashi babu wuya a gun Allah ,safiyya ta samu ciki, bayan dogon laulayi da tasha, watan cikin tara wata ranar lahadi nakuda ta kamata, hankallin Alhaji salisu ya tashi sosai, cikin hanzari yaje gidansu ya fada . Tare suka taho da inna Rabi kishiyar mahaifiyarta, Asibiti suka tafi Cikin ikon Allah basu jima da zuwa ba ta sallubo jaririyarta, cikin koshin lafiya. Kar kaso kaga murna agun Alhaji salisu da danginta, ita kam safiya ji take tamkar ta hadiye jaririyar sabida murna. Ganin lafiyarta kalau, ita da jaririyar aka basu sallama. Kai tsaye gidan mijinta aka wuce da maijego. Dangi fa kowa sai murna, musamman idan anzo angajaririya kyakykyar gaske. Dan gin Alhaji salisu duk sunzo daga garin KAYAWA. Ranar suna jaririya ta amsa sunan AiSHA sunan mahaifiyar Alhaji salisu, Amma ana kiranta Da ( SUHAIMA) haka dai suka cigaba da rainan jaririyarsu, cikin hakan kuma Alhaji Salisu ya karasa ginin gidansa dake NA IBAWA. Bayan sun koma sabon gida, suka cigaba da gudanar da Al amuran su na yau da kullum. Shekarun SUHAIMA, bakwai à duniya sannan Safiyya ta sake haihuwa. Wannan karon namiji ta samu kar kaso kaga murna a wannan gidan. ranar suna yaci sunan mahaifin safiyya Umar ,shima suke kiransa da (SUHAIL) Shekarunsa hudu shima aka haifi NA IFA. haka dai rayuwar gidan ta kasance cikin mutunci da farin ciki. Soyayya mai karfi mumy takewa SUHAIMA, har zuwa lokacin da tafara girma, makaranta mai kyau mai tsada mahaifinta ta ya sanya ta. yarin yace mai kwazo da kokari, ko cikin makaranta takan dauki sakamako mai kyau na jarrabawa. wannan damar da t'a samu shine yasanya SUHAIMA sangarcewa kiwa ce da ita sosai. hakan kuwa ya farune da laifin mahaifiyarta, domin har shekarun ta sun fara ja Amma mumy wanki take mata koda pant din ta ne, shara kuwa batayi bare wanke wanke. wannan muguwar sangartar da mahaifiyarta tayi mata va karamin batawa dady rai yake ba. Hakan dai yake mata fada akan lallai ta gyara tarbiyar yarinyar ta sabida diya macece wata Rana gidan wani za à kaita. duk lokacin da dady yake wannan fadan mumy banza takeyi da shi. SUHAIMA ta zama cikakiyar budurwa, à wannan shekarar zata gama makaranta. Cikin wannan rugun tsumin ne samari suka fara fitowa neman Aurenta, nan fa mumy tayi mata huduba akan sai mai kudi ko dangidan masu kudi ta yadda zata samu jin dadi cikin gidan Aurenta . wannan karatun na mahaifiyarya ta dauka, Dan haka indai baka da wani abu ko kazo bata fita, idan kuna anyi sallama da ita dady na gida hakan zai tilas ta mata akan sai ta fita din. cikin hakan Allah ya hadata da KHALiL, tabbas Khalil shine irin mijin da take jira dan akwai kudi à kwai kyau. Hakan ne ya bashi damar samun soyayyarta cikin ruwan sanyi tare data mahaifiyarta, tunda ya gano su ai kuwa yake musu barin kudin kamar ba yaso. Cikin kankanin lokaci maganar Aure tayi karfi, aka tsaida maganar Aure bayan tayi candy da wata guda za a sha biki. Komai yayiwa mumy yadda takeso, lefe na gani na fada Aka kawo daga gidansu khalili. kar kiga murna da zakwadi agun uwar da 'yar. Ansha biki na kece raini, indai raina tayi kuka ta kowanne bangare. ranar lahadi akaje aka mika amarya gidan Angonta khalili, gida na kece raini da burgewa nan aka saka Suhaima. Ku biyoni muje zuwa. [10/7, 17:13] ‪+234 706 738 2588‬: ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 'YAR AIKI. Page 0⃣5⃣ NA ALAWIYYA ADO (Teeyma phaty) 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🔰 HAJOW ✏🔰 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👦👩‍👩‍👦 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS✍🏼 Cikin kwanakin amarcin su ba karamar kulawa suke da junan su ba, shi kam Khalil ganin yadda rayuwa tayi masa dadi da amaryarsa da take tararairayarsa, bashi da wata matsala. Kusan sati guda ya kwashe a gida ko kasuwa baya fita, suna dirzar Amarci, da gimbiyar tasa. Wani lokaci suna zaune da Suhaima suna hira ga dukkan alamu hirar tana kayatar da su, dan Suhaima ce kwance akan doguwar kujerar falon, kanta gaba daya yana jikin Khalil. ""Baby na " Ta kirashi cikin murya mai taushi da daukar hankali. " yaya akayi ne madam "? "kaga yau sati guda dayin bikin mu, Amma Hajiya batazo gidan nan ba sai su Aunty Salam ne sukazo, me zai hana yau ka kaini inje in gaisheta" "madam kenan, ke bakisan kunyar Hajiya bane "? "Ai bazata iya zuwa gidan nan yanzu ba, sai dai Muje mugaisheta, ko anjima da daddare ne" Hmmmm ! "Hajiya kenan " Cikin, dariya Suhaima, take magana. " mudai babu ruwan mu da wani Jin kunyar dan fari idan mun haihu ko " ? kunnenta ya kamo yanaja da karfi, Jin zafin da tayi ne ya sa ta tashi da gudu tabar masa falon. Bayan an idar da sallar isha i, suka dauki hanyar zuwa gidan su Khalid, kwalliya sosai Suhaima ta caba, abinka da kyakykyawar mace haka ta fito fes da ita. shi kansa Khalil ya yaba mata wannan kwalliyar da ta yi, less ne blue mai adon Pink, mai manyan flawers à jikinsa, kayan Adon da ta sanya komai Pink ne, dangin kayan kwalliyar mata, Sarka da awarwaro da tarkacen kayan kawa. Suna tafe suna hirar masoya irin masoyan da suka shagaltu gurin kaunar ju nan su. Bayan yayi parking din motarsa à harabar gate din gidan nasu, da kansa ya zagayo ya budewa Suhaima kofar motar, santala santalan kafufuwanta ta zuro, ta fara takawa cikin tafiyar yanga da jan hankali. À babban falon gidan suka yada zanzo, domin duk yaran gidan suna cikin falon suna hira. matan gidan ne babu su a cikin falon. Zulaikha ce ta fara tasuwa da murnar ta ta tari Auntyn nata. "Oyoyo ga Aunty mu " Abin da take ta maimaitawa kenan tun lokacin da ta hangi shigowar Khalid da Amaryar tasa. saurin kanin nasa ma tasowa sukayi gaba dayansu suka rungumeta. "Aunty Suhaima sannu da zuwa " "yaya Khalid meyasa baka fada mana zakuzo ba ? " "kai Ku kyaleta haka mana kada kuji mata ciwo mana, sai kace wasu yara kanana, Ku bata guri ta zauna tukuna ina su Hajiyar ne ? " Faiza ce ta dago ta bashi amsa da cewa. "tana daki sallah takeyi " "0k, bari inje inga ko ta idar. kallansa ya kai inda Jalila take zaune, wata muguwar harara ya zabga mata. "Ke bakiga baki bane ? " "yi hakuri yaya ina chart ne banji shigowarku ba " Gyada kai kawai yayi, ya fice yabar falon. Cikin sallama ya tusa kai ya shiga dakin mahaifiyar tasa, shigarsa tayi daidai da shafa adduoin da takeyi. "Amen wa alaikassalam, Khalid kaine tafe da daddaren nan ? "Hajiya bani kadai bane tare muke da Suhaima tazo ta gaisheki ne " Ohhhh Ikon Allah ! "sati guda dayin Auren shine har aka fara fita yawo ? " Allah dai ya shiryeku ! "toh ina ka barta kuma"? tana falo gun su Zulaikha. jeka shigo da ita mana. amma kafin nan Ku fara shiga gun Aunty yara ta gaisheta. "Tom Hajiya bari muje mu dawo din" Bangaren Aunty Salma sukaje suka gaida ta. "Amarya sannu da zuwa, yau kece bakuwar mu, zuwa bako waya bare mu taryeki "? "Khalil baka kyauta min ba ai ko ni kasanarwa zuwan naku. "Aunty kiyi hakuri, yanzu muka shirya zuwan shiyasa ban sanar miki ba, kuma naga zuwan namu na dare ne ba rana ba" "Ai ko dare ne ka fada" "kaina bisa wuyana baza a kuma ba Aunty na" Firinjin dake dakin ta taje ta bude, ta dakko ruwa da lemo ta kawo musu. kememe Suhaima taki sakin jiki tayi hira da Aunty Salma ganin haka ne yasa suka taho bangaren Hajiya. sanda suka shigo bangaren Hajiyar ta fito daga cikin dakin ta a falo suka sameta ita da yaran suna hira. tunda Suhaima ta shigo, ta nemi guri daya ta zauna,shi kam Khalil bayan Sun gaisa da Hajiyar ficewa yayi ya tafi gun Alhajinsa. duk yadda suka so yin hira da ita taki magana saï dai ta danyi murmushi idan anyi abin dariyar. Basu bar gidan ba saï da sukaje bangaren Alhaji, Aunty Salma ce tayi mata jagorar zuwa gun Alhajin, yayi musu nasiha sosai akan su zauna lafiya da kiyaye hakkokin da suka hau kan ko wannensu. kyautar kudi masu yawa Alhaji yayi mata à lokacin da sukai masa sallamar komawa gida. itama Hajiya tayi mata tata kyautar ta turare masu kamshi. Aunty Amarya ma haka, kannen Khalili kuwa har bakin mota saï da suka rakata amma banda Jalila, shi kansa Khalili yaji dadin yadda aka karrama amaryar tasa à gidan su. saï dai abin da ya daurewa Khalili kai bai wuce yadda yaga Suhaima taki sakin jikinta à gidan na su. KO bata saké tayi hira da su Hajiya ba ai ta saki jiki da kannen nasa suyi hira. tun à mota yake ta tunanin dalilin da yasa suhaima yin hakan. sai kusan karfe sha daya suka koma gida, bayan Sun koma gida, nan suka baje à falo suna hira tana yabawa da halin kirki irin na Hajiyarsa. Har cikin ransa yaji dadin yabon da tayiwa iyalan gidan su. ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷 'YAR AIKI Page 6⃣ to 1⃣0⃣ Na ALAWIYYA ADO (Teeyma phaty) 🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🔰HAJOW 🔰 👩‍👩‍👦👩‍👩‍👦👩‍👩‍👦JURIYA DA HAKURI ONLINE WRITERS✍🏼 Godiya mara adadi ga masoyan wannan labarin nawa, Allah yasa sakon dake cikin sa yaje ga al ummar mu masu hali irin na Suhaima. WANENE KHALIL ? KHAlili Bukar Hashim shine cikakken sunan Sa. Mahaifin Khalil hamshakin mai kudi ne cikin kewayen unguwarsu, asalinsa haifaffan cikin garin kano ne Wanda yake à unguwar yakasai cikin karamar hukumar birni da kewaye. mahaifinsa shine mai unguwar yakasai, Alh sani, yana da matan Aure guda biyu Zainab ita ce uwar gida tana da yara shida, Hafiz shine babba, saï mu azzam,San nan Sadiya da Aisha sai karimatu, sai kuma dan karamin su shine Abubakar Wanda suke kira da( Bukar) kasan cewar sunan ka kansa yaci Wanda ya haifi mahaifiyar sa Zainab . A bangaren Harira kuwa, amaryar Alh sani tana da yara guda Biyu mata, Sakina da zulaiha. zaman lafiya da kaunar juna shine abin da yake wanzuwa cikin gidan Alh sani mai unguwa. Alh Sani mutum ne adali cikin iyalan sa domin baya tauye wa kawa hakkinsa tsakanin zaman matan nasa, wannan ce tasa yaran gidan suka taso kansu à hade tamkar duk ciki daya suka fito. Hakan ma ya samo asali ne gurin hakuri da kawaici irin na inna Zainab, haka dai yaran suka taso cikin girmama iyayensu da junan su. Bayan Sun girma, kowanne Allah ya rufa masa asiri duk Sun fara kasuwanci, kuma cikin ikon Allah suna da Nasibi. manyan maxan gidan duk sunyi Aure, matan ma duk an aurar da su, Bukar ne kawai Baiyi Aure ba a cikinsu sabida yana karatun digiri din sa a jami ar bayaro ta kano. Bayan kammala karatunsa ya hadu da uwargidan sa, Hajja Maryam, 'yar unguwarsu ce gidan su babu nisa da gidan mai unguwa, cikin kan-kanin lokaci maganar Aure ta taso, biki anyishi cikin farin ciki da kwanciyar hankali. Gida ne mai kyau flat suka taré ango da amaryarsa, Haka dai rayuwarsu ta cigaba da tafiya cikin nuna kauna da kulawa da juna. kwanci tashi babu wuya à gun Allah Hajja maryam ta samu cikin dan ta na fari, murna kamar Sa goya cikin haka suka dinga yi ita da mai gidanta Bukar. Kasuwancin sa kullum habaka ya keyi yana sai da kayan abinci cikin babbar kasuwar singa ta cikin garin kanon dabo. À kwana à tashi babu wuya agun Allah ciki ya shiga watannin haihuwa, duk wani tanadi Babu Wanda Bukar baiyiwa maijego da jaririnta ba. Ranar wata litinin, cikin dare nakuda ta kamata, ya sanyata à mota sai asibiti, bayan doguwar nakuda ta sallubo jaririnta santalele kyakykyawan gaske, murna sosai kowa ya nuna da godiya à gun Allah da ya basu wannan kyautar. Dangin kam sunyi rawar gani dan yaro ya zama dan lele gun dangin uwa da uba, Ranar suna yaro yaci suna Ibrahim sunan wan mahaifinsa da yake duk sauran Yayye Sun rigaya Sun sanya sunan Alh Sani. dan haka tun ranar suna dangi suka fara kiransa da Khalil. tunda Khalil yazo duniya Al amura suka kara war warewa Bukar, kudi ya nunku komai ya yalwata, gashi ta ko ina yana yawan taimakawa 'yan uwa da abokan arziki. Bayan shekara uku, Hajja maryam ta sake haihuwa, wannan karan santaleliyar budurwa ta sullubo, nan fa murna da farin ciki suka kara yalwatuwa. Ranar suna aka sanya mata suna Zulaikha, dg nan fa haihuwa ta ballewa Hajja maryam yanzu haka tana da yara Bakwai, Shamsiya, Rukaiyya, Nasir da Jalila, saï karamin su shine Mus Ab... Bayan shekaru da Auren Hajja maryam, Alh Bukar ya tanfatsa gidansa na gani na fada a unguwar N'ai bawa 'yan lemo, gida ne na kece raini na nunawa sa à. iyalan sa Sun koma gidan cikin farin ciki da murna. Bayan tatewarsu da Shekara daya ya nemo Auren Aunty Salma A matsayin Amaryarsa. Zaman lfy sosai ake cikin gidan Alh Bukar, duk da yake Hajja maryam macace mai kishi amma tana guje duk wani abu da zai kawo musu sabani da abokiyar zamanta. À bangaren Amarya Salma itama tana mutun ta Hajja maryam dan haka zaman gidan yake gwanin dadi. Aunty Salma tana da yara guda biyu na farko Habib mai shekaru shida sai kuma muhsina mai shekaru uku. wannan kenan. Khalil ya samu karatun addini dana boko inda ya sauke Alqur ani tun yana shekarun sa na kuruciya . Haka ma a bangaren boko, ya hada digiri din sa a bangaren Business administration, sauran kanin sa ma duk suna karatun su, zulaikha tana jami à tana karantar low, Jalila tagama skul tana jiran fitar result din ta. dukka dai yaran gidan suna samun ilimin addini dana zamani. Tun lokacin da Khalil yazo musu da zancen ya samu yarinyar da yakeso ya Aura, kar kuso kuga murna agun iyalan gidan. shi kansa Alh yayi murna sosai ko ba komai yana San yaga gudan jinin nasa ya zama magidanci. Itama Hajja tayi murna sosai dan tana San ganin surukarta, lokaci kankani Alh ya siyi filoti babba a unguwar Sharada, ya fara ginawa dan nasa muhallin zama, gini na gani na fada ake kankarawa.. Bawani lokaci mai tsawo aka dauka ba aka kammala ginin katafaren gidan Khalil din, Nan fa 'yan uwa suka hau farin ciki da murna duk wanda yaje yaga gida San barka yakeyi da adduar Allah ya rika masa. Alh da kansa shida Aminin sa suka shirya duk wasu abubuwan da akeyi gun hudimar biki. tsoho mai dogon zamani Mai unguwa shima sai da yaxo yaga gidan da aka dan dasawa jikan nasa, yaron Kirki. CIKIN GIDAN KHALIL. Suhaima tana zaune, tana kallo à babban falonta ta Wanda ya kayatu da kayan kawa na daki, hannuta rike da remot, tana, cenza tasha Arewa 24 zuwa mbc 2 Kwakwaso kofar falon akeyi da karfi, da sauri ta tashi ta nufi gun dan ganin wanene yake mata wannan bugun kofar. cikin fushi ta ke tambayar. "waye ne " Jin muryar mumy din ta à bakin kofar ta amsa mata da cewa. "Suhaima mune" da murnar ta ta bude ki . "mumy sannu da zuwa " cikin falon suka shigo dukkanin su, saï dai yadda taga falon kaca - kaca Shine ya tsorata. "Suhaima me yasame ki haka ne"? "mumy me kika gani "? "Au ke bakiga yadda dakin naki yake ba ko ina kace _kace, sai kace kuturwa"? "Bakya yin shara ne Suhaima "? Girgiza kai tayi, mumy nifa wallahi gidan nan yayi min girma bazan iya aikin gidan ba. mumy dai gurin zama ta samu ta zauna, cikin bacin rai take magana a yanzu. Haba SUhaima !! yanzu wannan abin da kike ai bai kamata ba da ranki da lafiyar ki ace gari ya waye kafin mijinki ya fita, bazaki gyara jikin kiba ki gyara gidanki, shi kansa ya fita cikin murna da farin ciki ? Kiduba yadda kike fa" ace yarin yar mace kamar ki, karfe kusan uku na rana, Amma ko wankan safe bakiyi ba " Nikam banji dadin yadda naxo na ganki ba, gaskiya. "Na ifa" "Na am mumy " tashi kije ki dau tsintsiya ki gyara mata gidan " À gyara KO ina da ina. cikin awowi uku suka hadu suka gyara gidan tsaf gwanin sha awa. komai ya dawo kal. sai bayan sallar magariba mumy suka tafi gida, kafin tafiyarsu gidan mumy ta sanarwa Suhaima cewar za a samo mata. *'YAR AIKI* wannan kenan. ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 1⃣0⃣ to 1⃣5⃣ NA *ALAWIYYA* ADO (Teeyma Phaty) 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🔰HAJOW🔰 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼 Bayan mumy ta koma gida, waya ta dauka ta kira, Kawarta Hajiya Asma à, bayan Sun gaisa kamar yadda suka saba à duk lokacin da sukayi waya ko suka hadu à matsayin su na Aminan juna. "Hajiya yaya akayi ne naji Kiran wayarki da daddaren nan "? Hmm !!! "kedai bari kawai kawata, daga gidan 'yarki nake, kinganni duk raina a bace yake ". Hajiya lafiya dai KO !? Toh lafiyar kenan, Zuwa nayi gidan na tarar da ita duk tayi kaca -kace da gida, hatta jikinta babu gyara " Ace yarinya daga yin Aure ko wata shida Bata kwashe à gidan miji ba amma komai yayi daidai à gidan " Ai kam dolé ranki ya baci, cewar Hajiya Asma à. Duk irin dukiyar da muka labta à cikin gidan nan ace baza a gyara guri ba, lallai da saké. "toh shine dalilin da yasa na kiraki, tunda dama Delu tana kawo masu *AIKI* daga garin su, shine na keson asamo mata kinga ta dinga gyara mata gidan"? "wannan shine mafita Hajiya bari in kirata in fada mata, in yaso ko jibi ne saï ta tafi ta samo mata a cen garin nasu" "toh Hajiya Asma à Nagode sosai " haka dai sukayi sallama kowa ya ajiye waya. *KHALIL*tunda ya shigo falon gidan nasa ya tabbatar da cewar yau Suhaimà baki tayi, dan tun daga shigowarsa yaji kamshin turaren wuta mai dadin shaka, Wanda idan zai tuna raban da yaji hakan a gidan sa tun satin farko na Amarcin Suhaima. Da sallamarsa ya shiga cikin falon, yau dai babu laifi, tayi kwalliya ba kamar kullum ba, Cikin sauri ta tashi ta taryeshi ledar hannunsa ta karba taje ta ajiyeta kan dan karamin teburin dake tsakiyar falon, sannan ta dawo inda ta barshi à tsaye, shi kam gaba daya hankalinsa yana gun falon ganin yadda gurin yy fes ga kamshi yana tashi. rumgumar da tayi masa ita ce ta dawo dashi duniyar mu. "lafiya kuwa naga ka tafi tunani "? jawo shi tayi ta zaunar da shi kan daya daga ciki kujerun dake kewaye à babban falon nata. "Sannu da zuwa Baby na " Ta fada cikin sigar shagwaba. "yauwa madam " "ya gida yaya kika yini ina fatan komai lafiya ko " "lafiya lau " ta fada cikin dariya. zakayi wanka ne ko kuwa ? "A à yaufa na debo yunwa da yawa tashi ki dakko flet ki juye mana abincin à ciki. " Yadda ya umarce ta hakan tayi, flet ta dakko à kichin ta juye musu, farfeson naman kaxa ne à leda guda, daya ledar kuma yoghourt ne à ciki manya guda biyu. zama sukayi suna ci suna hirar su irin ta masoya, cikin hirar tasu ne take sanar masa da zuwan mumy din ta. Anan ya tabbatar da zargin da yake na cewar Suhaima baki tayi, shiyasa yau gidan ya dawo hayyacin sa. Bayan Sun gama cin abincin bangaren sa ya tafi dan ya watsa ruwa à jikinsa ko yaji dadi. tunda ya bude kofar falon nasa yaga komai ya sauya an gyara ko ina. Suhaima ce ta taimaka masa yayi wanka, doguwar riga jallabiya ta dakko masa ya saka, bayan ya gama wankan ita da kanta ta shirya shi suka dawo falonsa suka zauna suna hira. Bayan Sun gama wayar Hajiya Asma à ta, kira mai aikin ta Delu, bata Wani jima da Kiran nata ba Delu ta shigo cikin falon na Hajiya, cikin girma mawa ta durkusa À gabanta. "Hajiya gani, Hydar yace inzo kina kira na " "Ehhhh ,nice na ce ya kira min ke " "Toh Allah yasa dai lafiya uwar dakina"? "À à lafiya lau Delu, dama Hajiya ce tayo waya dazu tana san yarin ya mai *AIKI*, za a kawowa Suhaima. " "Ikon Allah Hajiya, à yanzu dai babu yara à kasa, sai dai ko ajira zuwa nan da dan lokaci idan ansamu sai à samo mata " 'À à Delu duk yadda za ayi dai à samo mata yarinyar nan sabida ana bukatar ta cikin gaggawa" Toh fa ! "inaga Abin da za ayi Hajiya zanje gidan da Ra shida take aiki in dakkota, sai ince da uwar dakin nata agida ne ake nemanta. Tunda dama basu San jikata ba ce, in ba haka ba kuwa Alqur an baza à samu da wuri ba " Cikin farin ciki Hajiya ta washe baki tana yiwa Delu godiya. "Haba Hajiya Ai kunfi karfin haka à guna ". Yauwa Delu, to idan Allah ya kaimu goben sai ki shirya da wuri kije ki taho da ita. À bangaren mumy, kuwa bayan ta bugawa Aminiyaarta waya kan tana son asamawa shalelen tata mai *AIKI* Bayan Sun gama maganar ta kashe wayar. Number Suhaima ta kira, ringin din farko, ta daga sabida wayar tana hannunta, bayan sallama ta gaida mumy cikin fara à duk da bata ganin ta amma daga jin muryar 'yar tata tasan tana cikin nishadi. "mumy yaya kukaje gida"? "munje gida lafiya lau, Suhaima ". "Dama na kiraki ki ne dan in sanar miki, nasa Hajiya Asma à ta samo miki yarinyar da zata dinga taimaka miki da Aikin gida, dan haka ki sanarwa da Khalili, kada akawo yarinya ba tare da an sanar da shi ba." "yauwa mumy wallahi nagode miki naji dadi sosai, muna tarema da shi ma yanzu zan sanar masa ai nasan bazai ki ba dama" toh shi kenan, idan ansamu zaki ganta an kawo miki ita. nan sukayi sallama da Mumy ta kashe wayar, nan ta sanar da Khalil sakon mumy na cewa tasa a samo mata mai aiki. Suhaima wacce irin mai *AIKI* kuma !!!? "yanzu ke bazaki iya gyara gida da yin girki ba "? "wai menene amfanin Auren ne"? Ace ke bazaki iya yin komai ba sabida Allah. Ni dai gaskiya bana so gara ki tashi ki dinga yin komai da kanki, idan ban fita ba, saï in dinga taimaka miki. Cikin kuka ta fara yi masa magana "Haba Khalil wai yaya ka keso inyi ne ? " ni dai gaskiya tinda mumy ta samo min mai aikin kawai kayi hakuri tazo kaima kaga ka huta siyo abinci kullum, saï ta dinga girkawa tana gyara gidan " Ke kuma ki zauna kina chart na banza da wufi KO !!? Nidai kayi hakuri kawai chart kuma ai shine yake debemin kewar zama shiru. sabida ta kaici baice mata komai ba ya cigaba da kallansa à babbar tv din dake jingina jikin bangon falon nasa. ranar dai haka kowanne ya kwanta zuciyarsa babu dadi. *WASHE GARi* À bangaren Delu kuwa ,tun wuri ta gama Duk wani aikin da tasan akanta ya ke , bayan ta gama ta shiga tayiwa uwar dakinta sallama dan zuwa dakko mai Aikin. wannan somin tabi ne. ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 1⃣5⃣ to 2⃣0⃣ NA ALAWIYYA ADO ALHASAN 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS ✍🏼 Karfe goma na safe, Inna Delu ta sauka daga cikin adai daitar da tahau dan ta kaita inda zata dakko tilon jikar tata. Bayan mai adai daitar ya sauke ta, ta kwance daurin kullin kudin data kullesu à jikin zanin ta, ta mika masa naira darin sa, tare da yimasa adduar wanyewa lafiya, sabida mutuncin da yayi mata. Cikin girma mawa yake amsa mata da Amin. Bayan yaja ya tafi, Inna Delu tasa kai ta shiga gidan da yake har kofar gidan ya sauketa. Rashida tana kichin tana hada Abincin karin safe, ta jiyo muryar Inna Delu a tsakar gida tana kwada sallama, da sauri ta fito daga kichin din ta amsa mata. da murnarta ta taho gurin Katar ta ta, rungume ta tayi à jikinta. "Inna sannu da zuwa, kece haka da sassafen nan ince ko lafiya Inna "? "ke sakeni kada Ki yadda ni, daga shigowata kin rukun kumeni kin hanani magana kuma kin tsare ni da tambayoyi". "kai Inna, toh bari in sakeki shigo daga ciki" Bangaren dakin ta taja inna suka shiga, Bryan ta kaita ta zauna, "INNA bari inje in karasa aikin da nake saï inzo mu gaisa sosai". À à dawo ki zauna, dama ba gunki nazo ba gun Hajiya naxo Allah dai yasa tana nan Bata fitaba, shiyasa nayo sammako ". Tunda inna ta fara magana jikin Rashida yayi sanyi, cikin matsanan ciyar damuwa, ta dawo kusa da innan tata ta zauna. "inna lafiya kikace gun Hajiya kikaxo "? Ehh to lafiyar kenan, naxo tafiya da ke ne " cikin raxana ta dafe kirji. Inna tafiya kuma ina zamuje !!!! "Ke 'yar nan wannan kaduwa haka sai kace kinga abin tsoro ki kwantar da hankalinki, idan munje zan miki bayanin komai cikin nutsuwa." kai kawai ta daga mata, saï dai duk yadda inna ta gano rashin san barinta gidan, bata hango yadda Rashida takeji à ciki zuciyarta ba. "maxa tashi muje ki kaini gun Hajiyar " kichin din tafara zuwa ta kashe gas din data dora girkin, sannan ta tafi dan isar da sakon innan. À falo ta sami Hajiya tana zaune tana duba sakonnin à wayar ta, cikin sanyin murya ta shiga tayi sallama, yadda taji muryar Rashida shine yasa ta dago kai ta kai dubanta gareta, bayan ta amsa mata sallamar da tayi. "Rashida lafiya, me yasa meki ne, naji muryarki kamar kinyi kuka "? À à mama ba kuka nayi ba, dama Inna Delu ce taxo take San ganinki shine tace in sanar dake taxo tana dakina " OK jeki kice mata ta karaso nan falon, sannan kuma kije ki kawo min break din tun daxu ke nake jirafa" Cikin ladabi da biyayya irin na uwar daki da uwar giyarta ta amsa ta tafi aiwatar da umarnin da aka bata. dakin ta takoma taje ta sanarwa da inna abin da Hajiya tace, sannan ta koma kichin din dan karasa aikin da take, sai dai acen kasan zuciyarta jitake Sam bazata iya barin gidan Hajiya ba, sai dai kuma kash tasan bata Isa tayiwa inna musu ko jayayya ba tunda tasan matsayin inna gareta. Bayan Sun gaisa da Inna Delu, Hajiya tace Delu ince ko lafiya dai, naji Rashida tace kina san magana da ni KO ? "Ehhhh, Hajiya dama gurinki naxo, jiya mahaifin Rahida yaxo har gida na, kan maganar Rahida, kan cewa yana san ta koma gida, tun jiyan ya rigime min saï na Takeshi gidan nan ya zo ya dauketa to da kyar na lallabashi nace ya bari inzo gobe in tafi da ita, in yaso saï yaje gidan danake aiki ya dauketa anjima" Kinji abin da yasa kikaga nayo sammako haka". Hajiya dai shiru tayi, har ga Allah bata San rabuwa da Rahida, musamman yadda take Jin dadin aikinta, komai ta iya bata da kiwa. ga iya girki da iya kulawa da yara. "Toh Delu wani abun nake mata à gidan nan mara kyau ko kuwa kudin albashinta yakeso à kara mata, indai shine babu matsala zan iya karawa "? ko kadan Hajiya ba wannan bace ,matsalar inaga dai wata matsalarce ta daban sai dai kiyi hakuri zuwa lokacin da zai dawo da ita, sai ta dawo mik. Nan dai inna ta kalallame Hajiya da dadaden kalamanta har Hajiyar ta yarda zata bada Rahida din. cikin lokaci kankani ta hada shirgin kayanta, inna ta samo musu adai daita har kofar gidan, suka zuba kayan à ciki, kudi mai yawa Hajiya ta bata taré da jaddada mata lallaifa ta dawo. har kofar gida tayo musu rakiya suka shiga adai daita suka tafi. Rahida kuwa ta cika fam, ko magana taki tayiwa Inna saï matsar hawaye takeyi, har sukazo inda zasu sauka. inna da kanta ta sauke kayan ta biya mai adai daita kudin sa, suka shiga cikin gidan. suna shiga cikin gidan, kayan Rahida ta ajiye à tsakar gida suka shiga cikin falon Hajiyar, cikin murna Inna take magana ke kisaki jikinki kici arziki inda yake kin San Hajiya ba karamar hudima take dani ba dan haka ki saki ranki kada mu shiga kinai mata wannan zobare _zubaren kinji na fada miki, ta karashe maganar tana dan jan kunnenta à hankali. Hajiya ce ta fito, ganin Delu da yarin yar da take sa ran gani shine ya sanyata farin ciki.cikin fara a Sannunku da zuwa, har kin dawo ? duk à jere take jerowa Inna Delu wadan nan tambayoyin. "Ehhhh, mun dawo Hajiya ga Rahida nan na kawo miki ita " Aifa kin cika aikin ki, bari in kira Hajiyar in fada mata ". wayar dake hannunta ta dauka ta fari bin sunayen dake kan war tana zuwa kan na aminiyar tata, tayi dealing sakanni kadan number ta fara ringin, bata jima da farawa ba aka daga wayar, bayan Sun gaisa nan take sanar mata cewar an samo yarinyar dan haka ki turo azo à dauketa. tayi murna sosai da godiya ga aminiyar tata. tana ajiye wayar ta aika akira mata Suhail à dakinsa, bayan yaxo ta dakko naira dubu guda ta mika masa. "maza ka tashi kaje gidan Hajiya Asma à, zata baka yarinya, kaje ka kaiwa Suhaima ita, kada ka dade ko batan lokaci dan Allah kayi sauri ". Tom mumy ya mike da sauri ya tafi gun aiken da akayi masa. Inna tayiwa rahida fada sosai akan ta kula da aikinta sosai, tayi komai na kirki Wanda za a yaba mata, ta gargadeta akan kada tayi abin da zata bata kunya. Kusan karfe daya da rabi na rana, Suhail ya shigo, cikin gidan dan tafiya da Rahida. taré da Inna suka tafi dan ta rakata gidan Suhaima din. *SUHAIMA* washe gari kowa sabgarsa yayi dan Khalili ko magana baiyi mata ba, ya shirya ya tafi kasuwa, itama Bata bi ta kansa ba ta shiga sabgar gabanta. Tunda ta tashi tun safe tana kwance ko kayan jikinta bata cireba haka ta kwana da su à jikinta gashi suna neman kara yini à jikinta, yunwar da ta fara damunta ce tasa ta ajiye wayar ta shiga kichin dan samawa kanta abin da zata sanyawa cikin ta, indomie ta dakko ta dafa guda biyu, sai ruwan lipton, data tafasa. bayan ta gama dafawa ta dakko ta dawo falonta tana ci, karar wayar ta ce ta dameta da hanzari ta dauki wayar ganin sunan mumy à jikin fuskar wayar shine yasata dannawa da sauri. "mumy barka da safiya " Yauwa Suhaima ya gida, dama kiranki nayi in sanar dake an samo miki mai *AIKIN* gasu nan zasu taho, Suhail yaje ya dakko ta dan Allah ki riketa da kyau ". Tom mumy in Allah yaso ". nan sukayi sallama suka kashe wayar. wannan kenan ✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 2⃣0⃣ to 2⃣5⃣ NA ALAWIYYA ADO ALHASAN. 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼✍🏼 *wannan shafin na kune masoya wannan labarin, dan haka inai muku fatan akhairi à duk inda kuke*. *sadaukarwa ne ga dukkan marubuta maxa da mata musaman marubutan kungiyar mace mutum*. *Suhaima*tana kashe wayar da suke da mumy, tayi tsalle tayi murna ganin ta samu mai taimaka mata da aikin gida. Kusan karfe uku da kwata,Suhail yayi sallama ya shigo cikin gidan, sallamar da taji à bakin gate, shine ya sata saurin bude kofar falon nata ,Suhail ko shigo mana, ta fada tana dauke da murmushi akan fuskarta. inna kuwa tunda maigadi ya bude musu gate suka shigo ta saki baki tana ganin irin yadda aka kawata gidan ,duk shige shigenta gidajen da take kai yara aikatau bata taba cin karo da gida mai kyau kamar wannan ba. Itama Rahida ta jinjinawa tsaruwar gidan, duk yadda take ganin kyan gidan Hajiya, sai taga wannan ya fi na Hajiya kwai sosai. Bayan sun shiga falon sun zauna, suhaima ta gaida inna cikin sakin fuska tunda dama tasan innar dalilin zuwan ta gidan Aminiyar mumy dinta. Bayan sun gama gaisawa, nan ta gabatar mata da Rahida à matsayin *Yar Aikin* da aka kawo mata, cikin sassanyar murya ta rusuna tana gaida uwar dakin nata. "Aunty ina wuni" "lafiya lau, kunzo lafiya ko, toh abin da zan sanar dake shine, na dakko ki ne sabida ki dinga yimin ayyukan gidan nan ,shara da wanke wanke da girki sai kuma sauran hidimomin cikin gida, ina fatan zaki bani hadin kai gun gudanar da ayyukan duk dana lissafa miki ". "In Allah yaso zanyi miki komai Aunty ". Suhaima ce ta dawo da dubanta ga Inna. "toh kinji abubuwan da na lissafa Mata sune ayyukan da zata dinga yimin, kudin aikin ta nawa za a dinga biyanta duk karshen wata "? aibubu wata matsala, duk wata a dinga biyanta dubu biyar " toh shikenan, Allah ya bamu sa a. Inna ta ama da amin. Nan inna tayi musu sallama suka tafi ita da Suhail, naira dubu biyu ta bawa inna, kar kuso kuga murna gun inna, haka dai inna tayiwa Rahida sallama suka tafi. Bayan tafiyarsu inna, suhaima da kanta taje ta nunawa Rahida dakin kwananta, kayan ta taje ta debo ta shiga cikin dakin. Dakin babu laifi komai à kwai cikinsa, gado ne dan madaidaici, sai katifa dake kan gadon, sai 'yar karamar sif, a jingine jikin bangon dakin, daga gefe kuwa mudubi ne ma daidaice ga dukkan alamu dai kayan gadon set guda ne dan komai iri daya ne, wata kofa ce daga gefen cikin dakin, banaki ne dan madaidaci, Rahida tayi murna da samun wannan masauki dan masaukin yayi mata yadda takeso, saï dai dakin yayi datti sosai, ga dukkan alamu ma ba a taba share dakin nan ba. sef din ta bude ta zuba kayanta à ciki, bayan ta ajiye komawa tayi falon, nan ta tarar da matar gidan zaune akan kujera, amma ga dukkan alamu waya take amsawa, tsugunawa tayi daga gefenta, saï da tagama wayar sannan ta juye gareta yaya akayi ne ? "Aunty tsintsiya zaki bani inaso zan sharo dakin " wata kofa ta nuna mata tashiga cikin dakin zata samu duk abubuwan da take da bukatarsu, cikin nutsuwa ta mike ta doshi cikin dakin, bayan ta murda kofar ai kuwa kofar ta bude tasa kai ta shiga dakin, komai na amfanin gyaran gida akwai shi cikin dakin, tsintsiya ta dauka ta dakko moper, bayan ta fito daga dakin, dakin da aka nuna mata à matsayin nata cen ta nufa, ta share dakin tas ta goge ko ina tasa omo ta wanke ban dakin tas, cikin mintoci kadan ta gama gyara gun gaba daya. bayan ta gama, ta dawo ta tambaye uwar dakin tata. "Aunty ko akwai abin da zan miki ne yanzu "? "ehhh akwai zomuje in nuna miki " Binta tayi abaya har suka shiga bangaren maigidan bude kofar dakin tayi ta umarce ta da tahigo ta gyara dakin, à lokacin da Rahida taga dakin Khalili ba karamin tsorata tayi ba sabida tsaruwar da dakin yayi, komai mai kyaune à cikin dakin abin da take fada kenan cikin zuciyarta. Suhaima falon khalili ta dawo ta zauna tace Rahida ta gyara dakin sosai, wayar ta ta bude tana danne danne. Rahida kuwa dakin nan ta koma ta debo kayan da zata gyara gun à cikinsa, sai da tafara share dakin fes, sannan ta goge komai na dakin, bayan t gama ta fada bandakin dake cikin dakin shima ta wanke shi tas, bayan ta gama dauwar dakin ta dawo falon dan ta gyara shi shima, Suhaima tashi tayi ta shiga cikin dakin nan taga abin mamaki cikin kankanin lokaci, yarinyar nan ta gyara daki haka, babban abinda tafi birgeta shine yadda taga angyara gado an dameshi yayi kyau sosai abun gwanin ban sha awa. cikin ranta taji dadi sosai har bandaki sai da ta leka taga yayi fes sai kamshi ne yake tashi. haka ma ta gyara falon yayi tas, Suhaima ta jinjinawa Rahida sabida ta fuskanci yarinyar bata da kiwa kuma ta huru da yin aikin gida sosai, sai dai ga dukkan alama ba anan ta fara yin aiki ba sabida yadda ta iya komai. sai kusan karfe biyar da rabi ta gama gyaran bangaren khalili din. dakin ta takoma taje tayo alwala ta yi sallar la asar. kiran da ake mata ne yasata fitowa da sauri gani Aunty. Bakya jin yunwa ne ? ta tambayeta tana duban fuskarta,.. "Ehhh, inaji Aunty ". Toh kin iya girki ne ? daga mata kai tayi alamar ehhh, na iya. Kichin ta nuna mata ta shiga ta fada mata abin da zata girka. sai dai tunda ta shiga kichin din komai à barbaje yake tukwane gasu nan birjiki duk ba a wanke ba, gaba daya dai kichin din à hargitse yake, ganin yamma tayi bazata iya tun karar gyaran kichin din ba ta dan rage wanke wanken, ta dora musu abin da zasuci ita da uwar dakin nata. jalof din taliya ta dora musu mai kyau, kamshin da suhaima take jiyowa daga kichin din shine ya sanyata shiga kichin din, Rashida haka kika iya girki dama " ta fada à lokacin da ta bude morfin tukuntar dake ta tafasowa. wani kamshi mai dadi ya daki hancinta. Rashida dai murmushi tayi... 'ehhh na iya Aunty a Gidan mama Ni nake mata girki ". Kai haba shiyasa kika iya komai, dama kin dade à garin nan ne ? ehhh, na danjima gidan mama har makaranta ma nake zuwa à gidanta ". Tab !!! Ashe shiyasa kika iya komai, babu wani ragowar kauyenci à kanki. À haka dai har Rashida ta gama gurkinta flet ta dakko, ta bugawa Auntynta sannan itama ta zuba nata. à falo ta sameta ta ajiye mata à gabanta, ta koma ta dakko mata ruwan gora cikin naurar sanyaya abubuwa ta zamani, ta koma kichin ta dakko mata kofi, bayan ta gama da yi mata komai itama ta dauki nata abincin ta tafi dakinta ta zauna tanaci. lomar farko Suhaima takai bakinta, tsabar dadi ne yasata lumshe idanuwanta, dan tajima bataji girki irin wannan ba. tas ta cinye abincin ta daga ruwan ta sha, tayi hamdala ga Allah, bayan tagama ci bandakin cikin dakinta ta shiga dan tayi wanka. karfe takwas da 'yan mintuna Khalili ya shigo cikin gidan, ganin sama sama suke da madam din shine yasa shi tafiya bangarensa ko zama baiyi à gunta ba, bayan ya tura kofar falon ya shiga makunnin dakin ya danna haske ya wadata cikin falon ,nan yaga komai ya sauya falon yasha gyara KO ina fes da shi, wani farin ciki ne ya shiga cikin zuciyarsa, ganin yadda tayi masa abin da yakeso. jakar hannunsa ya ajiye ya shiga cikin dakin baccin sa nan ma ya tarar komai ya cenza, ciré kayan jikinsa yayi ya daura tawol ya shiga bandakin dan ya watsa ruwa à jikinsa. tunda taji karar motarsa, tayi buris da shi bataje inda yake ba, sabida har yanzu fishi take da shi. bayan ya gama wankan jallabiya ya sanya a jikinsa, ya taho bangaren madam din tasa Suhaima. daga Alkamkin Teeyma phaty ✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 2⃣5⃣ to 3⃣0⃣ Na ALAWIYYA ADO ALHASAN 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼 *wannan shafin nakune masoya wannan labarin* *Aunty Hasana* *Mumy RUKY* *Zee Ado Alhasan* *Aina u gyaranya* *Maman Akram* *Aunty Nafisa* *Husunah isah Alhasan* Sakon gaisuwa gareku 'yankungiyar 3 sisters Nobel work. Godiya mara adadi gareku bisa kaunar da kuke nuna min, nagode sosai. Kai tsaye khalil bangaren Suhaima ya dosa, shigarsa falon nata shine ya sanya shi Jin dadi ganin komai yayi tas. Ganin da yayi bata falon, shine ya sa ya tafi cikin dakin kwanan ta ,hakimar tana kwance kan gadonta, ta kashe duk hasken da ke cikin dakin, kunna hasken dakin yayi, haske ya wadata cikin dakin hangota yayi tana kwance cen karshen gado ta takure jikin gadon, da sallamarsa ya karaso gareta. "madam ince ko lafiya kike "? Na shigo tun dazu amma banji motsinki ba . Shiru tayi masa, har ya gama maganarsa, ya yi shiru. ganin da yayi bata da niyyar yi masa magana shine ya sashi tashi ya koma falon ya barta a Dakin nata. falonta ya Koma ya zauna, tv ya kunna yana kallon labarai à tashar aljazera, kusan muntuna goma sha biyar yana kallo sannan, Suhaima ta fito daga cikin dakin nata , kusa da shi tazo ta zauna ta dora kanta ,hankade ta yayi daga jikinsa, ya matsa daga kusa da ita, ganin yayi mata haka, shine yasa ta kara fusata cikin muryar Kuka ta fara magana. "wai menayi maka ne kake min haka "? tunjiya kake wulakanta rayuwata ,sabida nayi maka magana kan zan dakko *mai Aiki* ,kaki kulani sai wulakanta ni kakeyi !! wani kakkarfan kuka ta kara saki mai tsuma zuciyar Wanda ake yiwa, tunda ta fara magana shi kam khalii yana zaune yana kallanta, har ta tsaya da magana dan kanta ta fara kuka. ganin kukan nata yana damunsa, tashi yayi ya sanya silifas din sa ya bar mata falon ,ai kuwa ganin yaki kulata ya fice à dakin hakan ba karamin tada hankalinta yayi ba, da karfi ya buga kofar falon yayi ficewarsa bangarensa. Suhaima, ganin bazai kulata ba, tashi tayi da gudu ta fada dakin barcinta, kuka sosai takeyi ganin yau Khalil ne yayi mata haka, abin da tasan ada khalil ko bacin ranta bayaso, amma abin mamaki yau ita Khalil yayiwa haka, toh ko ya daina so na ne ? wannan tambayar take ta nanatawa cikin zuciyarta. haka dai ta dauki lokaci mai tsawo tana laluben mafita cikin lamarin nan, tayi tunanin kiran mahaifiyarsa ta sanar da ita halin da suke ciki, sai kuma taga lallai da kunya ta kirata dan kawo mata karar danta, Dan tunda akayi Aurenta da Khalil Baifi sau biyu ta taba kiranta ta gaisheta ba, tuni zuciyarta ta watsar da wannan tunanin. cen tunanin ta ya hango mata gara ta kira mumynta ta sanar mata duk abinda yake Faruwa tsakaninta da khalil, wala Allah ko ta bata shawara. shi kam khalil tunda ya koma bangarensa ,zama yayi yana tunanin irin wannan halayyar ta Suhaima, shikam indai haka Aure yake gaskiya bai mure ba dan yadda yaji abokansa suna fada masa yadda matansu suke kulawa da su, ton shi kam sam baiga wannan kulawarba ,cikin zamantakewar Aurensa da Suhaima ba, tsaki yayi cikin bacin rai, ruwan dake kusa dashi ya dauka yasha, bai shanye duka ba ya ajiye sauran sabida bacin rai ,ko yunwar da yadebo à yanzu bacin rai yasa ko jinta baya yi. Wayar ta ta dakko tayi dealing din kiran ta kira mumynta, wayar na kusa da ita ta danna ta daga. "yaya akayi ne Suhaima"? kukan da tajiyo ne yasata jin faduwar gaba, Suhaima kuka kikeyi ? menene ya faru ne ? cikin muryar kuka suhaima ta fara kwararowa mumynta abin da ya faru tsakaninta da Khalil. cikin bacin rai Mumy take magana. Au shima har yafara iya shegen irin na mazan yanzu !!? toh ki kyaleni da shi wallahi ko yaso ko baiso ba, saï kin sami mai taimaka miki da ayyukan gida, soyake duk kibi ki galabaita gun aikin gidansa. ki rabu da shi, ni zan kirashi da kaina in sanar masa nice na kawo miki mai *AIKIN* dan kisamu ta dinga taimaka miki. goge hawayen dake kanfuskar ta tayi dan Jin kalaman da mumynta takeyi. Mumy ko kulani fa baiyi ba, ko dana yimasa magana ma banza yayi min ya bar gurin da nake ma. "ke ki daina kuka kiyi min shiru, ki tashi kiyi wanka ki gyara jikinki fes, kije ku shirya kada ki yarda Ku kuma samun sabani irin haka nima yanzu zan kirahi inyi masa magana, bazan nuna masa munyi waya dake ba". karar kiran wayarsa ce ta dawo dashi daga dogun tunanin da yayi nisa a cikin sa ganin sunan da ya sanyawa surukartasa ya fitakan fuskar wayar ,cikin sauri ya daga kiran wayar taré da yin sallama. Acen bangaren ma cikin muryar mai taushi ta amsa masa. Khalil dama kiranka nayi, inason muyi magana . kasan Suhaima yarinya ce Karama gashi kuma à yanzu nauyi da yawa ya hau kanta Wanda bata saba da suba, toh shine nakeso asamo mata yarinyar da zata dinga taimaka mata ayyukan gidan, kaga itama ta dan rage yawan aikace aikacen ta huta". ton Mumy ai babu komai, akawota din Allah yasa hakan shine alkhairi. cikin sauri ta amasa da Amin Amin dana na kaina., Ai tun daxu da rana na turo Suhail ya kawo yarinyar, Suhaiman bata fada maka ba ne ? ehhh Bata fadamin ba Mumy, ko da yake banjima da dawowa ba ma sai min zauna zata sanar dani abinda ake ciki. toh shikenan ai zatayi maka bayani idan kun zauna, sai dai ayi ta hakuri da junafa khalil. In Allah yaso babu komai Mumy nagode sosai," cikin dabara tace masa bani suhaimar mu gaisa mana tun dazu na kira wayar tata bana samunta. Ai bata kusa taje kichin amma idan ta dawo zan kiraki in hadaku kuy magana Mumy. bayan ta ajiye wayar khalil wani dogon tunanin ya tafi magan ganun da mumyn suhaima tayi masa sune suketa kai kawo cikin kwakwalwarsa. Har kusan karfe tara da rabi na daren baiga suhaima tazo dakinsa ba ganin kada à maimaita ta jiya haka ya tashi ya rufe dakinsa ya tafi bangaren Suhaima. Hakimar tana zaune akan kujera, tana kallon shirin H H pop à tashar arewa 24 ,karar bude kofar falon nata ne yasata dago kai taga Wanda yake shirin shigowa gurin nata. ganin khalil ne ya shigo, ta maida kanta ga kallon da takeyi, shima cikin dakiya da nuna KO ajikina ya kai dubansa gareta, dama Mumy ce takesan yin magana dake ya miko mata wayar da daurarriyar fusarsa, da sauri ta sanya hannu ta karbi wayar tasa, nan ta kira Mumy suka gaisa tamkar wannan ce wsyarsu ta farko Colin wannan yinin. guri ya samu ya zauna cen nesa da ita, bayan tagama wayar, ta taso da kanta ta miko m'as masa wayar hadawa yayi da hannunta ya matse, wata kara ta saka wadda tasa Rahida lekowa dan Jin KO wani abonne ya faru da Auntyn nata Suhaima. lekowarta yayi daidai da lokacin da Khalil ya jawota jikinsa ya manneta da kirjinsa, wani dadi ne ya sauka à ranta Jin da tayi masa à jikinta shine yasa ta kara rukun kumeshi kamar wadda za a kwace mata shi, shikam Khalil rungumar data kara yimasa ji yayi kamar ya hadeye ta dan so, bayan sun gama Shafa shaffensu nan suka fara maida numfashi nutsuwa ta dawo musu. khalil ne ya lakuce mata hanci da cewa mara kunya dama nasan bazaki iya yin fushi da ni ba , itama dariya tayi hmm !! kaima ai bazaka iya ba din gashi kwana daya ma duk ka rikice ka fita hayyacinka, balle kuma........... karasa maganarki mana mlm. Rahida kuwa tunda ta leko dan Jin ihun Aunty din ta cak ta tsaya guri guda àlokacin data hango uwar dakinta, rungume da wani mutum suna ta shafa junansu, hkn Data gani ba Karami kunyace ta kamata ba, ganin Sun shagala sunata Shafa junan, cikin sanda ta koma cikin dakinta ba taré da sunganta ba,godiya tayi ga Allah da basu ganta ba Sukam suna cen falo anata shan hira kamar basune dazu ake rigima ba, hmm tsakinin mace da miji sfa, cikin wannan daren Sun nunawa junansu sunyi miss din juna na kwana daya Bari in barku nan. *mrs Bilu ce* ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 3⃣0⃣ to 3⃣5⃣ NA ALAWIYYA ADO ALHSSAN 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼 Sakon gaisuwata gareku masoya na Ummu Ammar MAMAN akaram AUNTY ZUBY Rabi à yobe Wannan shafin naki ne Aunty na ta kaina Fauziya d sulaiman (maman Haydar) *washe gari* Tun da asubah, Rahida ta tashi tayi Alwala tazo ta gabatar da sallar Asubah, tayi addu ointa kamar yadda ta saba bayan ta gama ta nade shinfidar da tayi sallar akanta ta rataye ta jikin kofar dakin nata, tsintsiya taje ta dakko ta gyara falon, da yake kusa da dakin nata, saï da ta leka ta tabbatar babu kowa à falon dan gudun kada ta kuma gano Abunda idanuwan ta suka gano mata jiyan. ganin babu kowa à falon shine ta samu damar fitowa ta gyara ko ina cikin falon, bayan ta gama da nan, kichin t koma ta fito da komai na kichin din ta wanke su tas, wadan da ba wankesu za ayi ba, ta dakko tsumma ta gogesu tas, nan da nan kuchin din ya dawo hayyacin sa yayi kyau sosai, kafin karfe bakwai ta kwas ta gama komai, ta koma dakinta ta zauna. ganin shiru shiru Aunty bata leko ta sanar da ita abinda zata dora ba, da kanta ta mike ta koma kichin din, bude firij din kichin din tayi komai à kwai à ciki hatta kayan miya, saï dai gaba dayansu Sun zagwanye sabida ba amarkade suke ba gashi sanyi yayi musu yawa, hakan dai ta tsinci wadan da suke da dan dama dama ta gyara ta markada à blander, bayan ta gama markadan ruwan shayi ta dora, akan gas din, bayan ya tafasa ta juye cikin fulas din shayin, daga nan ta fereyi dankali ta soya, hanta ta ciro daga cikin firij din ta wanketa fes ta dora akan wuta. ta debo citta da sauran kayan kamshi ta zuba à ciki, ta yanka albasa mai dan yawa akai, nan da nan kichin din ya karade da kamshie, cikin awa biyu dai Rahida ta kammala musu komai na karyawa, kan teburin ajiye kayan abincin da aka tanada à falon nan taje ta jera musu komai, ita kuma ta dibi nata ta shiga cikin dakinta . karfe tara da kwata, khalil ya farka daga baccin da ya daukeshi bayan idar da sallar asubar da yayi. ganin lokaci ya ja masa da sauri ya tashi, kai duban sa yayi ga Suhaima sai dai ga yadda ya ganta hkn ya tabbatar masa bata tashi tayi sallar asuba ba, duk tashin da yayi mata, wannan dabia ta suhaima ba karamin kona masa rai take ba, cikin zafin nama ya dan bubbugata akan ta tashi tayi wanka tayi sallah, amma kememe taki tashi haka ya gaji har ya kyaleta, yaje yayi wanka ya shirya cikin Wata shadda Ash calour, hular da yasanya tayi machine da kayan dake jikinsa, har yasa kafa zai fita, komai ya tuna kuma oho, ya dawo ya xauna gefen gadon. à wannan karan ta karfi ya d'ala mata duka, ai kuwa zafin dukanne yasata tashi da sauri tana sosa gurin, "kai khalil menayi maka ka ci zalina haka"? shikam haushi ne ya kara kamashi ganin duk yawun bacci ne a bakinta. kauda kansa yayi ga barin kallanta. "toh ni na shirya zanfita, sabida ina san zan biya gun muhsin akwai magan ganun da zamuyi da shi, kada inje ban sameshi ba". Tabe baki tayi, toh ai da ka tsaya nayi wanka na shirya, sai ka karya ma kafin ka fita ". Bari inje Insa Rashida ta dora maka koda ruwan tea ne. shi kam tsabar haushi ma yasa ko maganar ma ya kasa yi, girgiza kai yayi à à ki barshi kawai idan naje gidan Muhsin din za n karya acen kawai, jakar sa ya dakko ya rataya yayo waje ,da sauri tazo tasha gabansa, hb khalil ka tsaya mana, kada mu kuma maimaita ta jiya fa. Cikin raunanniyar murya take masa magana. dawowa yayi ya zauna yace tayi sauri taje tayi wanka yana jiranta Bryan ta shiga bandakin dake cikin dakin nasa shi kam falo ya dawo ya zauna ya shiga nazarin rayuwar Aurensa da Suhaima, idan yayi yinkurin sanar da Aminin sa Muhsin, matsalar cikin gidan sa, sai kuma wata zuciyar ta gargade shi da yin hakan, amma fa matsalolin Suhaima Sun fara damunsa, muamman ma lura da yayi Sam addinin ta ma bai dame taba sai dai idan yana gida ya dinga matsa mata dayin Sallar farilla ma, idan zai tunawa tun da sukai aure da suhaima bai taba ganin ta bude alqur ani ba ta karanta koda aya biyu ne cikinsa. da wannan tunane tunanen ne har ta fito daga wankan da bata dauki lokaci gurin yin sa ba. Bangarenta ta jashi suka koma, saï dai suna Shiga suka fara jiyo kamshi cikin falon, kai dubansa yayi ga suhaima. "dama kin shigo ne ina bacci " gyada kai tayi ala mar à à me kagani kace na shigo kana bacci ? bakiga kan table din cen ba, ya nuna mata gun da Hannunsa. murmushi tayi khalil kenan inaga Rashida ce ta yi wannan aikin ". wacece Rashida kuma ? ya kara jeho mata da wannan tanbayar haba yarin yar da aka kawo min ta dinga yimin aiki mana. ta karashe maganar tana kallan kwayar idansa, zo muje kaci abincin kafin ka fita kaga basai Kaji gidan muhsin kaci ba, kaima kaci à gidanka, da kanta taja hannunsa suka tafi kan deaning din shi kam khalil ta kaici ne duk ya cika masa zuciya, Ace ga matarka, wai mai aiki ce zatayi maka girki, gasu yaran duk na kauye ne ko ta yaya ma zasu iya yin girkin mu na birni tsaki ya yi Wanda sautin sa ya fito fili, cikin sauri ta dago kai ta dube shi, À à lafiya dai ko ? à à ba komai, zuba min inci kada in makara goma ta kusa tayi. ruwan tea ta fara zuba masa ta sanya masa sugar kasan cewar baya San shan madara à tea, kamshin citta mai dadi yana tashi, bayan ta gama ta bude fulas din data gani à ajiye à gun tana budewa wani kamshi mai sanyi ya taso daga ciki shi kansa khalil jin kamshin ne ya sanya yakai duban sa ga abin d yake kamshin, farfesun Hanta ne da yaji kayan kamshi da albasa, ji kaki makwat khalil ya hadiyi yawu, nan suhaima ta zuba masa yaci ya koshi, saï dai mamakinsà ya karu lokacin da yake cin abin cin nan, domin baiyi tsammanin akwai 'yan Aiki da suka iya girki haka ? raban da yaji dadin abinci haka tun yana gidan su, kafin yayi Aure, haka yaci ya koshi yayi wa suhaima sallama akan ya tafi kasuwa, dg cikin daki tayi masa adawo lafiya ya fita. bayan ta gama shiryawa itama fitowa tayi tazo ,taci abincin ita kanta yau taji dadin yadda ta karya, dan tajima bata karya irin haka ba Rashida tana kwance cikin dakinta, ta jiyo uwar dakinsa tana kwala mata kira, da sauri ta fito har kasa ta tsuguna ta gaisheta Aunty gani. tana zaune ta bata umarnin taje ta gyara mata dakin Mai gidan kamar yadda tayi jiya, saï dai yau tana san ta cenza mata zanin shinfidar gadon. shigarta ta dakin ta fara gudanar da ayyukan da aka sanyata, saï dai à yaune ta gama kalle dakin cikin tsanaki, gado ne makeke à cikin dakin mai launin Pink sai sif din sa itama makekiya, mai kofa hudu, gefe kuwa mirrow ne madaidaici, à gefe gadon bed site ne na gadon Wanda aka dora wata Karama futula akansa, saï d'ya gefen dan Karamin hoto ne à ajiye agun, hannu takai ta dauki hotan ta duba shi, wani matashi ne fari kyakykyawa mai faffadar fuska, da dan sajensa da ya kara fito masa da kyau da kwarjinin sa, bayan ta gama karewa hotan kallo, ta gogeshi ta maida shi inda ta ganshi. haka dai ta yini tana aikin gyaran gidan ba taré da ta huta ba. cikin kwanaki uku komai ya gyaru à cikin gidan, ko ina zaka ganshi yayi tes, hatta mai gadin gidan yaga sauyi cikin gidan dan kullum gurkin sa akan kari ake miko masa. shi kansa khalil yaji dadin zuwan yarin yar nan gidan dan tunda tazo gidan shima ya daina yawan zuwa gidan sayar da abinci à yanzu baya Jin nauyin kawo bakin abokansa gidan, rayuwa ta cenza à gidan wata sabuwar soyyya akesha tsakanin khalil da suhaima, saï dai duk kwanakin nan da tayi à gidan ko da wasa basu taba cin karo da maigidan ba, hakan kuwa ba Karamin Jin dadi tayi ba. Wata rana suna zaune suna hira da uwar dakinta suhaima ,take tsmbayar ta. "Rashida wai in tambayeki mana "? toh Aunty ina jinki Wai à aina kika koyi girki kala kala haka ? ni abin fa yana bani mamaki kinga Maigidan nan bai cika cin girki idan ba Nawa ba amma abin mamaki cin naki yake sosai. "Aunty nima agun mama na koya dan ita macece mai san cin girkin zamani kala kala,toh kuma duk girkin da zatayi nice nake taimaka mata muyi tare. wacce mama kuma Rashida, suhaima ta jeho mata da wannan tambayar ? "Aunty Mama ita ce wadda na zauna à gidanta kusan shekarar mu hudu muna tare da ita, ita ta sakani à makarantar boko, kuma tana yimin duk wani abu ni abu da nake so". mun shaku sosai da yaran gidan, yanzu haka nasan suna cen suna rigimar rashin ganina musamman ma Abdul nasir ,mun shaku da shi sosai. suhaima ta tayi dariya, "ga dukkan alamu ma naga kema kina cikin kewarsu shiyasa kike komawa cikin daki kina takura "? À à ba haka bane ina dai tuna su Abdul nasir ne da kuma kawayena na makarantar mu ta boko ". À nan din ma zan maidake makaranatar tunda kina so. murna ce ta cika xuciyar Rashida Jin cewar za a maidata makarantar boko. *mrs Bilu ce* ✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 3⃣5⃣ to 4⃣0⃣ NA ALAWIYYA ADO ALHASSAN 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷. 👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧👩‍👩‍👧 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼 *sakon gaisuwa ta gareku bazan taba mantawa da karamcin Ku gareni ba, saï dai in muku fatan alkhairi Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira*. Aunty Hadiza gudaji Aunty Maimuna Beli Hamza dawaki Sanah s matazo AYSHA Ali Garkuwa Kawata ina cigiyar, duk inda kike ina mika sakon gaisuwata gareki. *Bilkisu H muhd*( maman yusura) cikin tsantsar farin ciki Rashida ta tashi ta koma cikin dakin da aka sauketa, tsalle tayi ta fada kan madaidaicin gadon dake cikin dakin, wannan ranar dai tayi yini cikin dadin rai. *Suhaima* kuwa iya jin dadi tana Jin dadin yadda Rashida take gudanar mata da Aiyyukan gidanta, dan haka kara mike kafa tayi bata gudanar da duk wani aiki na cikin gidan ta, ta sakarwa Rashida yinsa, hatta dakin kwanan Khalil ta barwa Rashida ragamar gyaransa. yau kusan sati guda kenan da zuwan ta sabon gidan aikin nata, komai yana tafiya yadda ya kamata, abin da yake daurewa Rashida kai bai wuce tun zuwan ta gidan bata taba ganin mai gidan ba, tun lokacin data hange su rungume da Aunty nata, saurin kawar da wannan tunanin tayi daga zuciyarta, ta shiga wata sabgar dake gabanta. Yau dai tun da wuri Rashida ta kammala duk wani ayyukan ta wanda tasan zatayi ,hatta girkin rana ta kammala, bayan ta gama taje ta feso wanka à banakin cikin dakinta, bayan ta fito à wankan mai ta dakko ta goga à jikinta, cikin kayan ta ta duba ta dakko karshen adaka ta sa, ta dauki takalmanta tasa ta fito falo ,da muryar ta sassanya tayi sallama, ta shigo falon, Suhaima tana zaune akan kafet à kasan falon, dago kai tayi ta kai duban ta ga Rashida,bayan amsa sallamar da tayi. Tambaya ta jeho mata. "Ina zuwa kuma "? Naga kinyi wanka da wuri haka, kin gama aikin komai ? "Aunty dama tambayarki naxo inyi, ina san zanje gurin inna ne in gaisheta kinga tunda ta kawo ne Bata dawo ba ". Ehh, Tom babu matsala kije din amma fa kada ki jima sabida zakiyi girkin dare, shiga cikin dakina ki dakko min jakata akan mudubin dakin" cikin nutsuwa taje ta dakko jakar, ta dawo ta kawo mata gabanta, naira dari biyar ta zaro ta mika mata ungo ki hau mota kije, Dan Allah kada ki jima fa, sannan kice ina gaishesu. bayan ta karbi kudin tayi godiya dakinta ta koma ta dakko wani ya gwalgwalallen mayafi ta rataya ta fito. tunda Manu mai gadi ya hangota yake ya'ke baki yana bude jajayen hakoransa, bayan ta karaso gunsa ta gaisheshi, cikin doki yake amsa mata yau kuma ina za aje ne ? ya Tambaya yana kare kaikaicewa yana kallanta. Zanje unguwa ne ba jimawa zanyi ba zan dawo " Toh Adawo lfy " ya kara maimaitawa. ganin zancen nasa ba karewa zanyi ba haka taja kofa ta fice tana sauri. gefen kan layin ta tsaya tana jiran mota, bata jima da tsaiwaba, wani mai adaidaita ya zo bayan ta sanar da shi inda zai kaita, sukayi ciniki akan dari da hamsin zata bashi, ba musu ta shiga suka dauki hanyar zuwa gidan inna. bayan sunje unguwar har kan layin gidan ya shigar da ita, kudinsa ta dakko ta bashi ya bata cenjinta ta shiga cikin gidan, inna tana zaune à tsakar gida tana tsince bushashshiyar shinkafar da take shanyawa idan tayi wanke wanke, muryar Rashida dataji shine yasa ta dago da sauri takai dubanta inda taji sallamar. ta washe baki cikin nuna farin ciki, kai kai kai !!! wa nake gani haka ? inna Nice " kai sannu da zuwa, zama tayi à gefen tabarmar da innan take kai, Ta gaisheta, dafa kafafarta tayi, lafiya lau Rahida, kinga inda kikayi kyau kika murje !! kai gaskiya naji dadin ganinki hankalina ya dad'a kwanciya, dama kuma nasan gidan da na kaiki wanda za a kula da ke ne ". tashi kije ki gaida Hajiya tana ciki ". dakin Hajiya ta shiga taje ta gaisheta, itama Hajiyar taji dadin ganin Rashidan. sunsha hira sosai da innan nan take sanar mata da maganar makarantar da Aunty tace zata saka ta, itama inna taji dadin hakan sosai. sai kusan karfe biyar na yamma tayi shirin tahowa gida, nan inna ta sake yimata nasiha kan ta kula da aikinta sosai naira dari biyu Hajiya ta Bata tace ta hau mota. tunda Rashida ta baro gidan, Suhaima take kwance tana chart din ta da bige bigen waya, har kusan karfe biyu na rana, yunwar data fara damunta, tasa ta tashi ta shiga kichin din ta bude fulas din abincin, shinkafa ce fara, sai daya fulas din kuma miyace mai kyau tana budeta kamshi ya doketa à hancinta, miyar tasha kashi mai hade da nama, flet ta dakko ta zuba wadda Zata iya cinyewa ta zuba miyar, tasa cokali ta dawo falon, bayan ta gamaci ta dakko ruwa mai sanyi ta sha, ta ture flet din gefanta ta zauna, bata jima da zama ba bacci ya fara fuzgarta, ganin yaci karfinta kwanciya tayi bacci mai karfi yayi gaba da ita. sama sama cikin bacci taji ana kwankwasa kofar falon nata, cikin magagin bacci ta tashi ta bude kofar, Naifa ce kanwarta ,ita da zuwaira, 'yar Kanwar Mumy din su ce , shigowa sukai cikin falon, suka zauna, duk suka gaida Auntyn tasu . bayan sun dan huta Naifa taje ta zubo musu abinci sukaci, saunyi santin girkin sosai, ai fa nan suhaima ta fara basu labarin Rashida da irin kokarin da take mata. nan suka yini suna hirar su, suhaima sai bayan sallar la à sar sannan ta tashi tayi sallar azahar da ta maida la asar ma. bugun kofar da ake ne yasa Naifa katse hirar da suke ta tashi taje ta bude kofar falon, ganin wadda take tsaye abakin kofar falon shine ya sata matsawa gefe ita kuma ta shigo cikin falon, Wata matsanan ciyar dariya ce ta zomata à lokacin da tayi tozali da fuskar Rashida, wata kwalliya ce dankare akan fuskarta. ta lura da dariyar da take mata dan haka ko kallanta batayi ba, kai tsaye inda Auntyn nata take ta dosa. Aunty gani na dawo " ta fada fuskarta babu wal wala, dan ganin rashin mutuncin da ake san ayi mata. ' toh sannu da zuwa kiyi maza kije kichin kiyi wanke wanke idan kin gama ki dora mana tuwan shinkafa miyar agushi yau ita za ayi. Tom Aunty Abin da tace kenan, ta ta tashi ta nufi dakinsa, mayafinta ta Kawai ta cire ta ,nufi kichin din. sai da ta gyara kichin din, duk da bawani datti dama yayi da yawa ba, sannan ta fara hada kayan da zatayi amfani da shi gun yin tuwan da miyar. *khalili*Shine zaune à falon maman sa gefensa kuwa kannensa ne duk sun kewayeshi, kai da ganinsu kowanne cikin nishadi yake, Jalila ce kawai take cen gefe tana yin game à kan wayar ta, duk hirar nan da akeyi ana dariya ko da sau daya bata sanya bakinta a ciki ba, wanan halin nata ba Karamin batawa yaran gidan rai yake ba. Aunty salma ce ta shigo falon, nan fa murna ta kara kama kananun yaran dake cikin falon, Xulaikha ce ta fara magana da karfi yauwa Aunty gara da kika shigo, kizo ki raba mana wannan garda mar. "Aunty dani da Rukaiyya wa yafi kokari à skul sanda muna framary, dan Allah ba na fita ba Aunty "? yaya khalil ne yace wai ta fini kokari, wai ya tuno lokacin da nake zuwa ta karshen aji ". yanayin da tayi maganar sai da kowa ya kuma darawa à falon. "À à yayan yara kaima kadai fadi San ranka ne ai duk gidan nan har yanzu ba ayo yarin ya mai kokarin Xulaikha ba ". yauwa Aunryna fada musu dai, nan dai suka kara rikicewa kowa na fadar albarkar bakin sa, ganin kusan goma saura shine yasa khalil mikewa dan tafiya gidan sa. dakin mama yaje yayi mata sallama, sannan ya kama hanyar shiga motarsa wadda yayi parking din ta a farfajiyar gidan nasu, Aikuwa mus ab ne ya kwaso da gudu ya biyo yayan nasa, ko takalmi babu à kafarsa, yaya yaya, haka yake ta fada har yazo gun motar tasa. YAYA ka tafi dani mana gidanka ya fada cikin gurbatacceyar hausa irin ta yaran da basu kware ba. da gaske zaka bini din "? ehh zan bika YAYA " toh jeka dakko takalmin ka kace da Aunty kuma ta baka kayanka, kemai mai yaki tafiya dan kada ya tafi ya barshi. da kansa ya dawo cikin gidan ya karbi kayan mus ab din, da kyar mama ta amunce akan ya tafi da shi sabida taga take taken Matar tasa batason kowa ya rabeta daga ita sai mijinta. *Bari in barku anan*. *mrs Bilu ce*✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 4⃣0⃣ to 4⃣5⃣ NA ALAWIYYA ADO ALHASAN 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS🌐✍🏼 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *Duk*yadda suka so, su shawo kan mus ab akan yaki zuwa gidan yayan nasa, shi kam yaki hakura, badan ran mama ya so ba haka tasa Rukaiyya ta debo masa kayansa kala biyu. Ya shiga motar yayan nasa suka tafi. Karfe takwas, Rashida ta gama aikin komai à gidan, hatta komai ta jera akan teburin da aka tanada dan ajiye abincin, cikin tsari ta shirya komai, ta gama, bayan ta hattama ta koma bangaren dakinta dan yin sallar isha 'i, bayan ta idar da sallah ki shingida tayi akan daddumar ta tayi sallah ai kuwa bacci ya dauketa à gun. Sai kusan takwas saura sannan su Naifa suka fara shirin tafiya gida, babu yadda batayi da su akan su kwana ba amma kememe sunki kwanan sunce DADY idan yaji fada zai musu, kaya niki niki suhaima ta basu su kaiwa Mumy. karfe goma da 'yan mintuna, khalil yayi parking din motarsa à farfajiyar gidan nasa, bayan ya bude kofar ya fito, komawa yayi bangaren zaman banza na kusa da maituki, ya budewa Mus ab kofa, ya riko hannusa suka shigo cikin gidan, à falon suhaima suka yada zango ganin bata falon hala ya xaunar da mus ab, akan kujera shi kuma ya doshi dakin kwananta dan yasan tana cen din. tana zaune akan dan karamin stole din madubinta, tana shafa hoda, hakan ne ya tabbatarwa da khalil cewa daga wanka ta fito, "madam kwaliya ake yi ne"? Ya Tambaya yana matsowa kusa da ita. Cikin yauki take magana. " sannu da zuwa baby na, yanzu ka shigo ne ? "yauwa madam yanzu na shigo tun daga falo nake kwala miki kira banjiki ba sai d na shigo nan kamshin turarenki ya fara yimin albishir din lallai kina nan din ". Ya karashi maganar yana rungumeta à faffadan kirjinsa, mai kwarjini, lafewa tayi à kirjinsa tana jin wani nishadi yana ratsa ko ina cikin jikinta. da kyar suka banbare juna daga jikinsu ga dukkan alamu ko wanne yana cikin bukatar dan uwansa, à gurguje ta bude sif din ta, ta debo kayan da zata saka, wata jar atamfa ta dakko mai ratsin yellow ajikinta, tana da manyan flowers à jikinta, shikam yana dawowa cikin nutsuwarsa daga rungumar da yayi mata, falo ya dawo ya zauna gun mus ab, yaron har ya fara bacci, da sauri khalil ya tashe shi suka nufi gun da aka ajiye kayan Abinci. "mus ab zakaci abincin ne in zuba maka "? Kai ya daga masa alamar zaici din, flet ya dauko ya zuba masa shima ya zuba suka fara ci, suna ci suna hira, kadan kadan. jin magan ganun da tayi ne yasa tayi sauri ta fito dan mamaki ne fal à zuciyarta na cewa dawa khalil yake magana, kuma ga dukkan alamu ba kallo yake à tv ba. tana fitowa gun da khalil din yake ta dosa, ganin wani yaro à kusa da shi shine abin da ya bata ranta sosai. cikin hanzari ta karaso kusa dasu ta tsaya, 'khalil yau kuma bako ka taho mana da shi "? Ta fada tana hade fuska. dago da kansa khalil yayi, ya kai dubansa gareta, dan ya tabbatar da abin da zuciyarsa ta sanar masa. shima cikin daurarriyar fuska ya bata amsa da "Ehhhh bako muka samu " Tabe baki tayi tabar musu gurin, tv ta kunna tana kallo, iya takaici yau kam khalil ya kunsa mata haka kawai ko haihuwa banyi ba afara yimin jajibe _jajiben yara suna lalata min dakina wlh kuwa da sake dan sam wannan ba zai yuyu ba, ita da zuciyar ta take magana. shi kam khalil, ganin yadda suhaima ta wulakanta masa mus ab, abin ba karamin kona masa zuciya yayi ba, dan haka yana gama cin abincin yace da mus ab su tashi su tafi bangarensa, ko kallanta baiyi ba yaja hannun kanin nasa suka tafi bangarensa, aifa hakan da yayi ba karamin kara tunxura zuciyarta yayi ba. yana shiga falon nasa, ya kunna fitular dakin haske ya kawo ko ina na dakin nan suka zauna suna hira kadan kadan daga kan har bacci ya dauke mus ab, wanka ya tashi yayi alwala yayi nafifulinsa, nan ya kwanta bacci ya fara fuzgarsa. da kansa ya tashi ya j'ai mus ab cikin dakin sa ya shinfide shi a kan gado, shima gadon yahau ya kwanta, saï dai Sam ya kasa yin barcin à wannan karon, domin tunano irin abubuwan da suhaima take masa da shi da danginsa. wannan al amari yana mutukar damun sa domin, ko kadan baya Jin dadin zama da suhaima kuma babbar matsalarsa à yanzu bai wuce yadda ya gano suhaima bata San 'yan uwansa su zo gareta, wannan wacce irin rayuwa ce haka ? haka dai ya kwanta yana sake -sake cikin zuciyarsa, saï dai à wannan karan ya dauki alwashin saï yayi maganin suhaima akan wannan iskancin da takeyi à cikin gidan nasa. sama sama yajiyo bugun kofar da ake masa, babu ko shakka yasan ita ce take bugun kofar kuma dama sabida ita din yasa mukulli ya rufe falon, bugu take sosai Amma ko kadan bashi da niyyar bude mata kofar. ganin ta dauki lokaci tana bugun baizo ya bude mata ba ,hakan yasa dole ta hakuri ta koma bangarenta, saï dai suhaima tayi alwashin zata rama wanan wulakancin da Khalil yayi mata. dakin ta ta koma ta kwanta kuka sosai takeyi tamkar ranta zai fita, ranar dai duk cikin su babu Wanda yayi baccin kirki. *washe gari* tun safe Rashida ta gama aikin komai, ta shirya musu abin karyawa ta kai gun ajiyewa, wanka taje tayi ta shirya itama ta kwanta ta huta. shi kam khalil tun kusan karfe tara mus ab ya farka, sai dai ya lafta fitsari akan gadon, dan haka tashi yayi ya ciré masa kayan jikinsa, da kansa ya tako yazo bangaren suhaima, sai dai yana murda kofar falon ya jita gam à kulle,yasan sabida shi ta yi hakan, nan ya rasa yadda zaiyi da ransa gashi ya bar mus ab à dakinsa ko kaya babu à jikinsa, nan dabara ta fado masa, tunanin sa yakai gun mai aikin gidan, babbar matsalar ko fanin yarinyar bai taba yi ba balle yasan sunan ta, haka dai ya yin kura yayi bangaren da dakin nata yake ciki, à kofar dakin ya tsaya ya bubbuga kofar , Rashida tana kwance bacci take sosai karar bugun kofar da ake ne ya farkar da ita da sauri ta mike ko dankwali bata daura ba ta fito, dan duk atunanin ta Aunty ta ce, saï dai kash, abin da tayi zato ba hakan bane, ganin sa tayi à tsaye à jikin kofar kallan da tayi masa ba Karamin Jin faduwar gaba tayi ba, dubur burcewa tayi ta tsuguna agaban sa gani. Abin da bakin ta ya iya furtawa kenan. shima ganin yadda ta fito duk surarta ta bayyana musamman ma dogon gashinta da yake kwance à bayanta duk da bawani gyarashi ake ba amma hkn baisa ya lalace ba, da zafin nama yayi kokarin dauke ganin sa daga gareta. cikin wata sarkakkiyar murya yayi magana. "jeki dakina akwai yaro aciki kije ki daukeshi ki gyara masa jikinsa, sannan ki gyara dakin ". gyada kai tayi kawai ta koma dakinta ta dakko hijab ta saka ta nufi bangaren maigidan. shi kam khalil falon suhaima ya koma ya zauna, yana nazarin halin da ya shiga lokaci guda. gaba daya tunanin sa ya tafi gun yarin yar nan cikin zuciyarsa sa dai tunaninsa yafi tafiya akan tausayin ta yaji ganin yarjnyar karama ce ba Wata babba ba. Rashida tana shiga dakin ta jiyo kukan mus ab à cen cikin dakin, kai tsaye dakin ta nufa yana ganinta yaron ya taso yazo gurinta, cek ta dauke shi ta kaishi bandakin dake makale à cikin dakin tayi masa wanka, bayan ta shirya shi ta dauke shi ta kaishi gun khalil dake zaune à falon suhaima. bayan ta kaishi dawowa tayi ta gyara dakin ta cire kayan da yayi fitsarin à kansu hatta zanin gadon sai da ta cenza ta fita da masu dattin taje bayan gida ta wanke su tas. khalil yaji dadin ganin yadda rashida ta gyara masa mus ab din, da kansa ya je ya hada masa shayi, ya zuba masa farfesun kayan cikin da Rashida tayi sai da ya tabbatar da ya cika masa ciki ya koshi, sannan ya tashi ya tafi bangarensa dan yayi wanka ya shirya. bayan ta gama aikin wankin kayan falon ta dawo ta zauna ganin mus ab a zaune à falon shi kadai shine yasa itama ta zauna suna hira da shi. lokacin da khalil ya shigo ya gansu ba karamun dadi yaji ba, bayan ya gama karyawa yace mus ab ya tashi su tafi gida, amma kemai mai yace ya barshi gun rashida zai zauna, da yake yaron yana da saurin sabo da mutane. nan ya yiwa Mus ab sallama ya tafi kasuwa. duk bain da yake wakana à falon tsakanin mus ab da yayen nasa suhaima tà kasa kunne tana jinsu, Jin yaron yace bazai tafi gida ba shine ya kara tsananta bakin cikin ta........................ *mrs Bilu ce*✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKi* Page 4⃣5⃣to 5⃣0⃣ NA Alawiyya Ado Alhasan 🌐 HAJOS🌐 🌐 HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS 🌐✍🏼 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *sakon gaisuwa gareku masoya n'a, da wadanda suke cigiyar gaban 'yar Aiki wannan tsaikon ya samu ne à sakamkon rashin lafiyar data sameni cikin kwana kinnan, amma naji sauki cikin yar dar Allah, masu yimun Addua ina mika godiya ta gareku, marasa lafiyar mu na gida da asibiti Allah ya wadace mu da lafiya baki dayan mu Amen*. *CIkin* hanzari ta yunkura ta fito cikin falon, ba wanda ta kalla à gun tayi bakin gâté din gidan sai dai kash duk surin nan da takeyi hkn baisa ta aiwatar da abinda ta kudira à ranta ba domin karasawarta gun yayi daidai da bude masa gate din gidan ya fice, haka ta dawo falon ta zauna tana daddaure fuska. Rashida ta sakko daga kan kujerar da take kai, ta rusuna har kasa ta gaida Aunty nata, yadda ta amsa mata gaisuwar abin ya bata mamaki sabida tasan Aunty nata macace mai yawan fara à, ganin babu fuska shine ya sa ta tashi ta koma dakinta, tashin da tayi ne ya yi dai dai da lokacin da suhaima ta yunkura ta nufi kan teburin da ta tabbatar rashida ta shirya mata komai, à hankali ta bude kula din abinci farfesu ta gani na kayan ciki, daya kular kuwa ,dankali ne da kwai, ruban shayi ta diba à dan Karami kofi ta zuba kayan shayin, sai da taci ta koshi sannan ta mike daga gun. Rashida kuwa, tunda ta Mike zata tafi dakinta shima Mus ab ya riko hannunta, ganin ya rike ta itama daukar sa tayi ta shiga dakinta da shi, har cikin ranta ita dai tana Jin kaunar yaron nan duk da ganin su daya à duniya, kiran da suhaima take mata shine ya dawo da ita duniyar tunanin da ta lula, wata harara ta doka mata bayan taje ta amsa kiran nata "ke wai raino na dakko ki kiyi ne à gidan nan"? Ta karashe maganar tana harararta. ita kam rashida tayi tsuru da ita tana wasa da dan karamin dan yatsanta. "Malama baki ji nane "? "Aunty dan Allah kiyi hakuri , wallahi ina cikin dakina, naji anbuga kofar dana bude shine naga maigidan ne da kansa, shine yace inje in gyara wa mus ab jikinsa ". amma kiyi hakuri Aunty idan na bata miki rai, abin da yasa na kula da shi din sabida ina cikin gidan nan a matsayina na *'yar aikin gidan* duk wata dawainiyar gidan ta dawo kaina, amma kiyi hakuri dan Allah ". gyada mata kai kawai tayi, "shi kenan ya wuce yanzu kizo ki gyara gun da naci abinci, sannan ki hada kwanukan guri daya Kije ki wanke su, sai kizo ki tsefe min kaina ya dameni da kaikayi ". "Tom Aunty " cikin nutsuwa ta tashi dan fara ciki umarnin uwar dakin nata . aitana tashi, mus ab ya biyo bayan ta ya riko hijabin dake jikinta, wata tsawa da suhaima ta doka masa sai da yaran ya girgiza, ita kanta rashida ta tsorata da jin karar balle kuma Wanda akayi wa, jikinsa ne ya ke ta bari. "maza nemi guri ka zauna dan uwarka, Kanwar uwarka ce ko ta ubanka ka ce da zaka dinga binbininta duk inda ta saka kafa kana biye da ita, " sum sum ya dawo kan kujera ya zauna, sai dai har ga Allah itama rashida Sam bataji dadin abinda akaiwa mus ab din ba . ai kuwa tana fita ya kece da kuka,mai karfi. kukansa ya dagawa rashida hankali sosai dan hk cikin azama ta gama aikin gyara kichin din tayi wanke wanken ta taho gurinsa, tsabar kukan da yasha har ya fara yin bacci ,da sauri ta taho inda yake ta daukeshi suka koma dakinta. kusan yinin ranar sai tare sukayi da rashida, duk inda zata suna tare da shi, har dare yayi bacci ya daukeshi à dakin rashida. *KHALIL* tun bayan da ya fita à gidan sa, kai tsaye gidan amininsa ya dosa dake unguwar Janbulo, duk da gidan yana da tazara da nasa gidan amma ko kadan baya Jin nisan tafiyar à yau, zuciyarsa gaba daya à jagule take sabida abinda suhaima takewa danginsa, shi kam yana mamakin hali irin na matar tasa mussaman idan ya dubi yadda take ikirarin tana kaunarsa à koda yaushe, amma sam bata kaunar 'yan uwansa suzo gareta KO kuma ita taje gun danginsa, wai wannan wane irin SO ne take cewa tanayi masa ne ? haka dai yayi ta zancen zuci har yazo bakin gate din gidan, bayan yayi parking da kansa ya zo suka gaisa da mai gadin gidan ,nan yake tambayarsa ko maigidan yana nan. "Allah ya taimakeka Alhjin Allah yana nan, ka shiga mana ". mlm Auwalu maigadi sai faman washe baki yakeyi dan ko babu komai yau yasan zai samu nacefane mai kyau. da kansa ya bude masa 'yar karamar kofar da zata shigar da kai cikin gidan. kai tsayi ya nufi babban falon gidan, à hankali yake kwankwasa kofar, baijima yana bugun ba akazo aka bude kofar , saratu ce mai aikin gidan tazo ta bude masa har kasa ta tsuguna ta gaidashi, nan yake tambayar ta ina masu gidan fitowar Naufa ce ta katse masa maganar "À à madam " gaku da bakin safe ina fatan mutumin yana nan dai ,dan ko à waya ban sanar masa da zanzo ba ". "lalai ka taki sa a, yanzu yake shirin fita kuwa, bari inje in kira Maka shi. daya daga cikin kujerun falon ya zauna, Bata jima da fita ba, saï gasu nan taré. "kai mutumina zuwa babu sanarwa, mika masa hannu sukayi suka gaisa, itama Naufa ta gaida shi taré da tambayar suhaima, cikin dabara ta zame jikinta ta bar musu falon dan basu dama gun tattauna abin da ya kawo shi. Abikina yaya naganka haka ne " Kai dai bari kawai, abubuwa ne sukai min tasa munir kaina duk ya kulle na rasa yadda zanyi da raina, nan ya zayyano masa duk abubuwan da suke faruwa à tsakanin zamansa da suhaima . shi kansa munir ya girgiza da Jin halayyya irin ta suhaima, lallai al amuran suna bukatar atsaya à duba su don akawo gyara cikin su. munir ne ya fara magana da cewa,"ina ganin abinda za ayi anjima bayan sallah magarib, zamuje gidan, in yaso sai muje aji inda matsalar take dan akawo gyara cikin al amuran, amma idan aka dinga tafiya à haka abubuwan bazasuyi dadi ba nan gaba. khalil ya yarda da wannan shawarar, Dan hk cikin kwarin gwiwa ya fice daga gidan aminin nasa ya tafi kasuwa. ranar dai haka rashida ta wuni tana dawainiya da mus ab ga kuma aikin gida, Dan kafin magariba ta hattama girki da gyaran gidan, ko ina yayi fes da shi, dakinta taja mus ab suka tafi suka kwanta. karfe takwas da rabi na dare khalil ya shigo gidansa, bayan ya shigo falon baiga kowa ba bangaren suhaima ya shiga , tana zaune kan gadonta tana game da wayar hannunta, cikin sallama ya shigo dakin à wannan karon akwai sauran mutunci à fuskar Tata danta amsa masa sallamar da yayi mata saï sai fuskar tata babu walwa à cikinta. "kina ciki kenan" shima abinda yace mata kenan " Ehhhh " shine amsar da ta bashi, ganin shirun yayi yawa à tsakaninsu, fitowa yayi ya tafi bangarensa, ruwa ya watsa à jikinsa bayan ya gama ya dakko jallabiya asalin 'yar maroco mai saukin nauyi ya sanya à jikinsa, bayan ya gama kintsawa,silifas ya zira à kafarsa ya dawo bangaren suhaima, gun teburin cin abincin ya nufa dan ya cika cikinsa, Dan tun zuwan rashida gidan ya manta da wani cin abincin waje ko nasiyarwa. jaluf din shinkafa ce wadda taji kifi da alayyahu yana budewa kamshin ta ya doki hancinsa, shi kansa tsintar kansa yayi da lumshe idanuwansa. sai da yaci ya koshi sannan ya tsayiyi Léman kwakar da yake cikin jug din yasha, nan yayi hamdala ga Allah ya dawo kan kujera ya zauna. cen mus ab ya fado masa arai cikin hanzari ya tashi ya nufi bangaren mai *Aikin* har ya murda kofar dakin zai shiga sai kuma zuciyarsa ta tunatar da shi rashin dacewar yin hakan, da sauri ya dawo da baya ya koma gurin da ya baro ya zauna. suhaima ce ta fito daga dakin bacinta Jin karar tv à falon ta hkn ne ya tabbatar mata cewar khalil ne yake kallo. bayan ta shigo cen nesa da shi ta nemi guri ta zauna, ko sallama batayi ba. shima baibi ta kanta ba, ya cigaba da kallon abin da ya tabbatar wa da kansa ba fahimta yake yiba gaba daya hankalinsa yana kan munir Wanda sukai alqawarin zaizo bayan sallar magarib amma gashi yanzu har tara da kusan minti goma, kuma ya kira wayarsa tafi sau goma amma à kashe take, wani tsaki yaja Wanda baisan ya fito fili ba, Jin fitowar tsakin nasa shine ya batawa suhaima rai duk à tunaninta da ita yake. kwan kwasa kofar falon da akeyi shine yasa ta tashi da sauri ta bude kofar ,ganin munir à bakin kofar shine yasata sakin fuska. "À à wata sabon gani yau kaine à gidan namu "? shima cikin faraa ya maida mata da martani " kun san ku amare bai kamata à dinga takurawa amarcin Ku ba" "hmmm !! " kai kasani dai bisimmilah " ta rakube shi kuma ya shigo cikin falon . shi kam khalil Jin muryar munir shine yasa ya daure fuskar sa, cikin raha ya zauna kusa da Abokin nasa "haba mutumina kuma yau fushin naka nima har dani à cikinsa ? " "kaima kasan ka saba min alqawari ka duba agogonka karfe nawa yanzu"? "toh Kaji hakuri wani azuri ne ya tasomin shiyasa ban samu zuwa à kan lokaci ba. suhaima ce ta dakko masa ragowar lemon kwakwar da rashida tayi ta kawo masa hade da kofi guda daya, bayan ya tsiyaya ya sha har cikin ransa yaji dadin lemon,cikin wasa yace "kai madam wannan lemo haka gaskiya zan turo Ummu bilal ki koya mata irin sa.............. kuyi hakuri da wannan.. *mrs Bilu ce*✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 5⃣0⃣to5⃣5⃣ NA Alawiyya Ado Alhasan. 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS 🌐 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *wannan shafin naki ne Aunty na ta kaina ma abociyar Alkhairi da sanin ya kamata, Aunty Allah ya taimakeke duk inda kike Allah ya baki lafiya ya kareki daga sharrin makiya Hajiya umma sulaiman Sha'aibu yan awaki*( Aunty Baby) *suhaima* ce ta dakko masa ragowar lemon kwakwar da rashida tayo, kofi guda daya ta dora akan farantin, bayan ya tsiyaya ya sha har cikin ransa yaji dadin lemon nan, cikin wasa yace mata " kai madam wannan lemo yayi dadi sosai, gaskiya zan turo Ummu bilal ki koya mata irinsa, ras taji gabanta ya fadi cikin zuciyarsa ta kuwa gani take khalil ne ya sanar da shi bata komai cikin gidan sai mai *Aiki* ce takeyi hatta girkin abincin ma, rausayar da kai tayi ta basar "ay babu komai Baban bilal duk sanda ka shirya ka kawota saï in koya mata din ". shi kam dariya yayi ya ajiye kofin à kasan kafet din dake shinfide à tsakiyar falon, tsam suhaima ta Mike dan tabasu guri su tattsuna à matsayinsa na aminin sa, har takai bakin kofar falon zata fita, taji yo, munir yana kwala mata kira "madam ina kuma zaki tafi ki barni, bayan gurinki na zo ba gurinsa ba ki dawo magana nazo muyi da ke ai". cikin sanyin jiki ta dawo ta zauna. fatanta dai Allah yasa ba asirinta ya tona agun abokinsa ba. munir ne ya fara magana da cewa. " suhaima nazo gareki ne bisa wadan su maganganu da nakeso muyi su tsakanina da ke ga kuma mijinki nan dan shine ya sanar dani duk abubuwan da yake faruwa à tsakaninku ke da shi. "farko dai ina san zan tuna tar dake abinda nasan kin sanshi saï dai kin manta da shi dan haka ya zama dole à tunatar dake su. da farko dai, kafin miji da mata sukai matakin zaman aure, anà bin wadansu matakai ne daya bayan daya, mataki na farko dai suhaima shine daga lokacin da saurayi yaga budurwa yana SO, ton daga wannan lokacin zai fara shirya yadda rayuwar Aurensu zata tafi tare da wannan masoyiyar tasa abu na biyu dg lokacin data amince tana sansa itama à sannan duk wani buri nata yana kansa dan haka duk wani tunanin kasancewarta cikin gidan Aure tare da shi zatayi, muje abu na gaba suhaima amfanin yin xance ga masoya shine su fahimci junan su ,à wannan lokacin, su shirya rayuwarsu ta Aure da yadda zasu gudanar da rayuwar aurensu, à tsakaninsu ko wannnesu yasan abunda abokin zamansa yake SO da Wanda baya SO, ton idan an fahimci hakan sai kiga KO anyi auren an zauna lafiya". toh amma kuma abin mamaki, suhaima Ace kunyi Aure Kuna san junan Ku amma bazaki dinga yiwa mijinki abinda yake SO ba haba suhaima ? ki sani idan kin kyautatawa mijinki umarnin Allah kikabi sakayyarki kuma tana gareshi, idan kuma kinci gaba da munana masa toh kisani Allah yana kallanki, kuma suhaima gaskiya nayi mamakin yadda kuke irin wannan zaman da khalil, sabida ni nasan wanene Abokina bawai dan yana aminina ba ni nasan halinsa, baxai zalunce ki ba suhaima " Amma abin da nake so dake idan akwai abubuwan da yake miki wanda bakyaso ki sanar dani yanzu dan à daidaita komai " tun lokacin da munir ya fara magana suhaima ta sunkuyar da kanta kasa tana zubda hawayen takaici da bacin rai. suhaima magana nake miki kinyi shiru fa, ya sake magana à karo na biyu " munir bawai nayi shiru bane domin bana jinka duk abinda kaki fada ina jinka, saï dai akwai abubuwan da yasanar maka Wanda Sam ba haka bane, munir tunda naje gidan su khalil ban samu karbuwa à gun 'yan gidansu ba, ton yaya zan musu, bayan hk kuma kullum bashi da gun zuwa saï dai ya tafi gidansü yin hira ni gaba daya bai daukeni da mahimmanci ba, shikenan hk zan kare rayuwata cikin bakin cikinsa, sannan jiya sai gashi da yaro Karami wai ya taho da shi kwana, dan Allah munir hakan ya dace "? Hmmmm !!! Haba suhaima taya ya zakice basu karbe ki ba me suke miki idan kinje gidan "? ""Basa yimin komai munir". abin da suhaima tace kenan ta tashi ta bar musu falon, ganin ta tashi fouuuu cikin fushi shine yasa khalil kara fusata da hanzari ya bita yana kiranta amma bata jiyo ta dubeshi ba hakan ya kara jagula masa lissafi, cikin zafin nama ya tafi zai danko ta, munir ne ya lura da abinda aminin nasa yake shirin aikatawa, cikin azama ya biyoshi ya jawoshi ya dawo kan kujera ya zaunar da shi. "haba Abokin me kake shirin yi ne "? "so kake ka biye mata kuzo kuna samun matsala, su mata ba haka ake musu ba, idan kaga suna irin wannan rabuwa ake da Al amuransu ayi kamar ba a sansu toh da kansu zasu dawo suna baka hakuri , Dan Allah kada ka saurareta, ka kyaleni da ita". dafe kansa yayi cikin zafin rai yake magana " haba munir me kakeso inyiwa suhaima ne taki kwantar min da hankalina taki ta bani kulawar da kowacce mace take bawa mijinta, taki yadda ta zauna da 'yan uwana lafiya, ka duba kaga yawan dangin da nake da su amma ko kadan bata shiga duk wata hidimar da ta shafi dangina, ace ina cikin Jin dadin aure kuwa abokina, "? hawaye ne mai zafi yake sauka akan fuskarsa, ganin hawayen ba Karamin tada hankalin munir yayi ba dan yasan ba karamin abu ne yakeso khalil zubda hawaye. haka nan ya zauna yayi ta bashi hakuri har zuciyarsa tayi sauki, saï dan à cen kasan zuciyarsa yayi alqawarin sai ya rama wulakanci nan da suhaima take masa, har farfajiyar gidan ya rako munir sukayi sallama ya tafi, shi kam bangaren rashida ya nufa dan yaje yaga halin da mus ab yake ciki. tura kofar dakin yayi ya shiga, suna kwance akan gadon gaba dayansu, mus ab ya rukunkume ta, haka tasa masa mayafinta ta lulluba masa à jikinsa, bacci suke sosai sai dai ga dukkan alamu suna Jin sanyi, gudun fankar ya ragé musu yaja kofar ya kulle, yayi musu fatan alkhairi. tunda sassafe suka tashi, rashida ta gyara komai kamar kullum, mus ab ma ta shirya shi tsab à dakinta suka karya ita da mus ab din. sai kusan karfe goma sannan khalil ya fito daga bangarensa, kai tsaye dakin rashida ya shiga aifa yaji dadin ganin nasu dan sanyi wanka gaba d'ayansu, da sallama ya shigo cikin dakin, aifa da gudu mus ab yaje ya daneshi yana dariya, YAYA abin da yace masa kenan, ita kuwa har kasa ta tsuguna ta gaishe shi da da wata siririyar murya mai daukar hankali da saukar da kasala, Jin muryar yayi har cikin ransa, cikin karfin hali ya amsa mata da lafiya lau, yaya gajiyar mus ab kinsha hudima, ton sannu nagode miki. abunda yace mata kenan yaja hannun mus ab suka koma falo, abincin yaje yaci ya rike hannun mus ab suka tafi, hannu ya dinga dagawa rashida yanai mata by by har suka ja motar suka tafi. Auntynta ta gani jingine jikin kofar falon tana leken motar khalil sai dai yadda idanun ta suka tasa shine zai tabbatar maka da cewa kuka tasha ba dan Karami ba, cikin sanyin jiki ta dawo palo ta zauna. rashida kam, tunda ta lura, da yanayin da Aunty ta shiga ciki tun bayan zuwan mus ab itama saï ta fara dari dari da ita, yanzu ma cikin sanyin jiki ta tsuguna ta gaisheta, da kyar ta amsa mata gaisuwar sabida kukan da tasha ya rike mata muryà. murya kasa kasa tace mata ta tashi ta hado mata abin karinta, ta kawomata nan inda take zaune, cikin sanyin jiki rashida taje ta hado mata komai ta kawo mata sai dai duk yadda taso tace abincin sam ta kasa cinsa dan ko dandanonsa bataji à cikin bakin nata, sabida zuciyarsa à jagule take, inda abin da ta tsana à duniya bai wuce taga suna fada ita da khalil ba. tana zaune kan kujerar sai faman saka da warwara take, cen wata dabara ta fadomata, nan take ta amince da shawarar da zuciyarta ta bata wayar ta ta dakko, tayi dealing din number khalil, ringin take amma bai daga ba, ta kira kusan sau shida amma bashi da niyyar dagawar, ganin hakan bazai yuyu ba yasa ta hakura da kiran wayar ta fara rubuta masa sako à cikin wayarsa. *Haba my khalil duk girman laifina ai baxai hana ka daga wayata ba dama kiranka nayi in baka hakuri shine kuma kaki daga kirana, kayi hakuri dan Allah, hakan bazata kuma faruwa ba* . dg suhaimarka. nan take ta tura masa da sakon, bai jima da tafiya ba, taji alamar sakon ya tafi, zaman jiran amsa tayi amma kusan mintuna talatin bai dawo mata da amsa ba hakan ta gaji da jira har ta hakura ta koma cikin d'akinta ta kwanta. itama rashida dakin nata ta koma tayi kwanciyarta, tunda duk wasu aiyukan ta ta gama da su sai dai Jin kewar mus ab da takeyi dan kwana biyun nan da yayi ba karamin shakuwa sukai ba. 🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃🍃 *khalil* bayan fitarsa daga gida, kai tsaye gidan su ya tafi, bayan shigarsa suka gaggaisa da sauran yaran gidan kassncewar ranar lahadi ce duk yaran gidan suna nan, mus ab kuwa sai tsalle yake da murnar ganin 'yan uwansa, yaran Sunata yi masa oyo yo, khalil kuwa bangaren mahaifiyarsa ya tafi, à kichin ya hangota tana hidimar hadawa Alhaji abin karyawarsa, har kichin din ya bita ya gaisheta Bayan Sun gaisa ta tambayeshi yaya suhaima take. ""tana nan lfy lau Hajiya tace duk na gaisheku " "Allah sarki muna amsawa, ina ka barmin autan nawa ne "? "kai Hajiya kinaji da wannan autan dai yana cen gun su Rukaiyya suna kwalamar kayan da yazo da su " cikin dariya ya karashe maganar. ""kaya kuma !! "wane irin kaya kuma khalil "? " suhaima ce ta bashi alawa da tarkacen kayan wasa shine ya tsaya à cen suna duddubawa ". "Allah sarki itama harda wata dawainiyya, to angode mata ". haka dai suka danyi hira kadan kadan, har yayi mata sallama ya fito zaije gun Alhajinsu ya gaishe shi. à palonsu, yaci karo da muhsina tana ganinsa ta fara tsalle ta dane shi, cikin farin ciki, YAYA shine ka dauke mus ab ka tafi da shi ni kuma ka barni ko ? " A à muhsina ba haka bane ke bacci kikayi da wuri shiyasa ban tafi da ke ba, amma idan na tashi tafiya dake zan tafi mubar mus ab, mima "? tsalle take da murna itama ance za aje da ita. hannunta ya rike suka tafi bangaren alhajin nasu, da sallama ya shiga ya duka har kas ya gaida Alhajin, shima ya shirya ga dukkan alamu shima shirin fitar yakeyi, à gurguje yaje ya gaida Aunty salma, sannan ya tafi kasuwa. Bayan ya shiga cikin motarsa sannan ne ya samu sukunin bude sakon da yaga ya shigo cikin wayarsa, sakon sahaima ya fara budewa ya karantae, bayan ya gama karantawa tsaki yayi ya ajiye wayar, nan fa ya shiga tariyo irin abubuwan da take masa, mussaman abunda tayi masa jiya à gaban aminin sa, wani tsaki yaja, ya kara bawa mota wutà yana jin tsanarta cikin ransa, sai dai kudirin da ya dauka à cikin ransa yana ganin shine mafita. *karfe tara saura kwata* khalil ya shigo cikin gidan, yau tana zaune à palo, ga dukkan alamu zaman jiransa takeyi ko kallanta baiyi bayan yayi sallama bangarensa ya tafi, binsa tayi abaya har zuwa bangaren sa, shi kam ko kallan inda take baiyi ba, kayan jikinsa ya ciré ya shiga bandakin ya watsa ruwa, suhaima tana zaune gefan gadon khalil, duk inda ya gifta binsa take da ido, sai dai ya tamke fuskarsa babu annuri acikinta tamkar bai taba yin dariya ba . haka ta gaji da zama ,ta hakura tabar masa dakinsa. Bari in barku nan . *mrs Bilu ce*✍🏼✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 5⃣5⃣ to 6⃣0⃣ NA Alawiyya Ado Alhasan 🌐HAJOW 🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS🌐 *cikin* dakin ta da dawo ta kwanta, sai dai ko kadan baccin ya gagari idanuwanta sabida tsananin bakin cikin da yake cikin zuciyar ta, shima à 'bangaren khalil din hakan ne domin kwana yayi yana mutsu mutsun rashin suhaima à kusa da shi, sai dai ya zama dole ya nuna mata bacin ransa akan abubuwan da take masa. Gari na wayewa wanka yayi, yae fucewarsa ko karyawa baiyi ba, jin bude gate kawai suhaima taji dan ko ta bangaren dakinta yau bai kalla ba, hakan kuwa ba karamin k'ona zuciyarta yayi ba. Rashida tana palo tana goge kayan kallo da kujerun palon, ta hango khalil zai fita ta kofar baya da sauri ta ajiye tsumman dake hannunta, ta bi bayanshi, jin ana binsa abaya shine yasa shi waiwayo wa, rashida ya gani à bayansa, har kasa ta durkusa ta gaida shi, har cikin ransa yaji dadin ganin nata. "À à lafiya dai ko, khalil ya tambayeta "? Cikin sassanyar muryarta ta ce da shi "lafiya lau Alhaji, dama zuwa nayi in tambayeka mus ab ". Dariya ce ta kwabce masa ba tare da ya shirya zuwanta à wannan lokacin ba, "dama shi kika zo ki Tambaya "? Ya sake jefu mata da Tambayar kai ta daga masa alamar Ehhhh. Shima cikin nishadi ya bata amsa. 'mus ab yana gidansu,tun jiya na maida shi sabida makaranta ". "Ayya dan Allah idan kaje ka gaida min da shi ". Cikin sakin fuska ya amsa mata da cewa "zaiji in Allah yaso amma inji wa zance masa ne "? Itama dariya tayi ta rufe fuskarta "kace masa inji Rahida ". jijjiga kai yayi, sannan yasa kai ya tafi gun motarsa. Suhaima kuwa ta gama shirinta tsaf, dan yau kam gidansu zata tafi dan ta gaji da irin wannan zaman da suke da khalil din, akwati ta dakko karama ta dibi kayan ta kala uku ta zuba à ciki ta dakko mayafi ta yafa, à palo taci karo da rashida tana goge kujerun palon," ke ajiye aikin nan, kizo mutafi " "Aunty ga abincin karin ki nan fa nayi miki, tun dazu". ya tsine fuska tayi, rashida kyale abincin nan banjin zan iya cinsa à yanzu, kije ki dakko mayafinki kizo mutafi". cikin hanzari ta tashi ta shiga cikin dakin nata ta dakko gyalenta, ta yafa suka rufe gidan suka sami adai daita sai gidan su suhaima. Mumy tana zaune tana gyaran sif din ta tana jera kayan da aka kawo mata daga wanki, sallamar suhaima ce ta dakatar da ita, " wa nake gani ne kamar suhaima "? Mumy nice, à à lallai munada manyan baki". sannunku da zuwa, yauwa Mumy yadda taga idanuwan suhaima sun cenza launi shine ya tabbatar mata da cewa ba lafiya ba, kafin ta kai karshen zancen nata kuma ta hango rashida na kokarin shigo da akwati, jikin Mumy yayi sanyi sosai, kallonta takai ga suhaima cikin rikita take tambayar ta ko lafiya. rashida ce ta mika mata cenjin kudin da ta tsaya karba gun dan adai daitar da yakawo su, cikin ladabi ta gaishe da mumy sannan ta fito ta dawo palo ta zauna. cikin kid'ima Mumy take tambayar suhaima dalilin zuwan ta, cikin kuka suhaima ta sanar da mumy duk abubuwan da suke faruwa tsakaninta da khalil, sam mumy bataji dadin abinda khalil yayi ba, sai dai ta bawa suhaima rashin gaskiya akan abinda tayiwa kaninsa, fada sosai Mumy ta yiwa suhaima, sannan ta kudirta aranta zata yiwa khalil waya ta bashi hakuri akan abubuwan da suhaima tayi masa , ashe har yanzu baki da hankali, ace ki samu miji kamar khalil amma baxaki dinga lallaba shi ba, kina kwantar masa da hankali, ta yadda zai dinga sakar miki duk wani Jin dadin rayuwa, ya sakar miki komai à hannunki, ke baki san siyasa ba ne ? Ai yanzu lamarin duniyar nan sai ana siyasa, dan haka abin da nake so dake, zankira khalil din in bashi hakuri da kaina ke kuma ki gyara duk sanda wani dan uwansa yazo cikin gidan nan ki dinga mutunta su ta hakane zamu samu duk abin da muke nema à gunsa ". share hawayenki in Allah yaso komai zai daidaita, dan ko babanku bazan bari yasan kinzo gidan nan ba ". waya ta dauka ta kira khalil, cikin, mutuntawa ya gaida surukar tasa, bayan Sun gaisa ta sanar masa da zuwan suhaima gida da kuma san ganinsa da takeyi, nan yayi mata alqawarin zuwa bayan sallar isha 'i, bayan gama wayarsu da Hajiyar yaji takaicin zuwan suhaima gidansu ba tare da izinin sa ba. karfe bakwai na dare khalil yayi sallama gidan su, suhaima dakin saukar bakin gidan aka saukeshi, Na ifa ce taje tai masa jagora har cikin palon, duk da palon ba bakonsa bane lokacin da yake zuwa xance gun suhaima nan ne gurin zaman su. haka ya shiga ya zaune, cikin daya daga cikin kujerun palon, bai jima da zama ba, mumy tayi sallama ta shigo, bayan Sun gaisa tasà aka kira mata suhaima, nan tayi musu fada gaba dayansu sannan ta bawa khalil hakuri akan abubuwan da suhaimar tayi masa, har ga Allah khalil yaji dadin sulhunnan da akai musu da suhaima, haka suka tashi suka fito gaba dayansu kowannen su ya saki ransa tamkar babu wata Matsala à tsakaninsu, mayafinta taje ta dakko rashida kuma ta dakko mata akwatun kayanta, aka saka cikin but din motar, da kansa ya bude mata gaban motar ta shiga, sannan ya kewaya shima ya shiga, itama rashida ta bude motar ta shiga, suna tafe suna hira kamar ba sune masu fadan nan ba, mata da miji sai Allah. kai tsaye, unguwarsu ya nufa, suhaima takai dubanta gareshi, "à à ina kuma muka nufa ne "? gun Hajiya xamuje ki gaisheta, toh shine kawai abinda tace masa, haka dai suka cigaba da hirarsu, Sun manta da wata rashida ma a cikin motar, hirar su suke cikin nishadi. À harabar gidan ya ajiye motarsa, sannan suka shiga cikin gidan, shigarsu yayi dai dai da fitowar Aunty salma daga bangaren mama da murnarta ta rungumo suhaima, tanai mata sannu da zuwa, bangaren maman taja suhaima suka koma, itama rashida da take ta rakobe rakobe à tsakar gidan binsu tayi cikin palon, duk yawancin yaran gidan suna ciki, mazan su da matansu, dama wannan al adar gidance zaman hira bayan an idar da sallar isha 'i, 'yan matan gidan duk Sun zo Sun gaisheta sai dai yadda suke mata ba haka ta samu à yau ba, har kas ta tsuguna ta gaida mama sannan ta gaida Aunty salma, itama rashida cikin ladabi ta gaida kawa hatta su Rukaiyya sai da taje ta gaishe su, Mus ab kuwa tunda yaga rashida ya hau tsalle da murna, ita ma da gudu taje ta rungumeshi, à jikinta, taji dadin ganin sa sosai. nan aka zaune anata hira har kusan karfe goma da rabi, ba laifi yau suhaima ta saki jiki anyi hira da ita agun,dan har su rukaiyya sun mata alqawarin kawo mata ziyara cikin satin nan mai kamawa. khalil ba Karamin jin dadi yayi ba fanin suhaima ta saki jikinta, mus ab kuwa yaki bacci har suka zo tafya da kyar aka banbareshi daga jikin rashida yana kukan sai ya bita, badan ranta ya so ba haka ta barshi ta shiga mota suka taho gida. kai tsaye gidan su suka nufa ,suna tafe suna hirar su tamkar sabbin amaren da sukai aure cikin satin nan rashida kuwa tun a cikin motar bacci ya fara fizgarta. jin an tsaida mota ta bude kofar ta fito ta nufi gun kwanata, khalil kuwa tare suka jero da madam din sa har cikin palon, bayan sun dan huta, dakin suhaima suka shiga nan suka shiga sukayi wanka, bayan sun fito suhaima da kanta ta tsane masa jiki, tashafa masa mai, nan fa labari yasha ban-ban dan cikin wannan daren kowannensu ya nunawa dan wansa sunyi kewar junan su. bayan komai ya lafa, suhaima tana rungume jikin khalil, ta cusa kanta cikin kirjinsa, shikam sannu à hankali yake shafa bayanta yana lumshe ido à haka bacci mai dadi yayi gaba da su. rashida tunda suka dawo, ta shiga dakinta ko mayafin jikinta bata ciré ba ta kwanta bacci yayi gaba da ita. *washe gari* tunda wuri ta tashi ta hattama komai da tasan zatayi à gidan, hatta wanka tayi, dakinta ta koma ta zaunà rashin zuwanta makaranta shine abinda ya dameta à yanzu, amma dai yau zatayiwa Aunty nata tuni akan sanyata à makarantar kamar yadda tayi mata alqawarin hakan. basu suka tashi ba sai kusan karfe tara saura à gurguje khalil ya tashi, ya Shiga bandaki yayi wanka, sannan ya tashi suhaima, amma kemai mai taki tashi wai ita tagaji, haka ya gaji ya koma bangarensa, ranar dai fai fitaba sai kusan shadaya da rabi, suna zauna suna hira da suhaima, cikin hirar tasu ne take sanar masa da san à maida rashida makaranta tunda dama ta fara, kiran rashidar yasa akayi har kasa ta durkusa ta gaida su. "dama kin taba halartar makarantar boko ne "? shine abin da khalil ya fara tambayarta, "Ehhh ,ina zuwa à wancen gidan da nake aiki ". Tom ba Matsala zan nemo miki wata anan kusa dan ki dinga zuwa. godiya tayi sosai ta tashi ta koma dakinta. murna agun rashida abin ba a cewa komai, kan gadonta ta koma tayi tsalle ta fada akai,. cikin kwanaki uku ,khalil yanemo mata makaranta à Kusa da gidansa, ta kudi ce amma bawata mai tsada bace sosai, da kafa ma zata iya zuwa, ai kuwa ranar wata litinin da kansa yaje ya kaita bayan sun gwadata aji biyu na j s suka kaita. rashida ta dage da karatun ta sosai, haka bangaren aikinta tana kokari ta gama shi, akan lokaci , cikin kankanin lokaci ta zama 'yar makaranta. rashida najin dad'in yadda suhaima take mata, ta fara gogewa, domin yanzu har daurin zani ta iya yinsa. tana matukar kokari, ta kwanne bangaren, kwanci tashi ba wuya agun Allah su rashida ne ake shurye shiryen zana jarrabawar zangon karatu na farko, kullum karatu baji ba gani kuma wani lokacin suhaima tana dan taimaka mata, à haka suka gama zana jarrabawar, hutu suka samu dan haka yanzu bata da aikin da ya wuce na cikin gida. ranan suna zaune a palo ita da suhaima, rashida tana aikin gogar vest din khalil ita kuma suhaima tana kwance kan doguwar kujerar palon, hira suke jefi jefi. cikin hirar tasu ne rashida ta sanarwa da Aunty ta cewa tana san taje gida gun mahaifinta, dumm ! taji faduwar gaba dan idan rashida bata nan yaya zatayi da aikin gidan nan, badan ranta ya so ba tayi mata alqawarin zata barta taje tayi kwanaki uku. har cikin ranta taji dadin abin da Aunty nata tayi mata. mu wai waya baya. *wacece Rashida*? Rashida haifaffiyar garin kano cikin Wani dan Karamin kauye da ake kira da Hayi, cikin karamar hukumar tofa, kauye ne da ya amsa sunan sa kauye domin tafiya ce mai nisan gaske daga inda mota ta ajiyeka koda akan mashin ka tafi ba karamar tafiya zaka sha ba, sabida babu hanyar ababen hawa cikin garin, kauye ne futuk dan ko wutar lantarki babu à cikin garin, belle ruwan famfo, amma duk da haka, mutanen kauyen ba karamin jin dadin zamansu cikin garin suke ba sabida zaman lafiya da kwanciyar hankalin da ake da shi cikin garin. mutane ne, iri iri cikin kauyen domin akwai hausawa akwai fulani à cikinsa,kan mutanen garin à hade yake babu nuna wariya ko bambamci. malam jibo shine mai garin hayi, yana da mata guda uku saude ita ce uwar gidansa, sai kuma nafisa suna kiranta da inna, sannan kuma Amarya sunan ta Laure. Mai gari yana da yara guda goma, maxa da mata, babban dansa shine shamsu wanda shine mahaifinsa yafi ji da shi cikin yaran gidan, wannan soyayyar da maigari yakewa shamsu ita ce ta haddasa masa tsana da tsangwama agun sauran 'yan uwansa..... Bari in barku à nan, mu hadu à gaba. *mrs Bilu ce*✍🏼 ✏🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page6⃣0⃣ to 6⃣5⃣ NA Alawiyya Ado Alhasan. 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS🌐 *Assalamu Alaikum* *Masoya na, inai muku fatan alkhairi duk inda kuke, da wadan da suke aiko min da sakon gaisuwa da wadanda suke kiran waya ina godiya sosai da nuna kulawar ku gareni, Allah ya bar zumunci*. *sha*msu yaro ne mai farin jini KO a gun ja ma ar garin sabida yana da nutsuwa ga girmama ja ma a wannan halayyar tasa ce ta kara jawo masa farin jini Sabanin sauran 'yan uwansa. Malam Audi shima haifaffen garin hayi ne, dan mahaifinsa ma cikin garin aka haife shi acen kuma yayi aure har Allah yasa y'a hayayyafa shima. Mlm Audi yana da matarsa guda daya, mai suna dija, tun farkon Aurensu suna zaman rufin asiri ne mlm audi ba mai wadata bane domin sana ar gyaran fasassun robobi yakeyi a bakin hanya, yaran su guda biyu Allah ya basu a duniya, rabi u wanda suke kira da rabe, sai kuma saudatu wadda suke kira da Sa ade. Rayuwar rufin asiri sukeyi a gidan mlm Audi tare da matarsa delu, inna delu, itama garinsu babu nisa da Hayi Aurene ya kawota hayin ai nihin kauyensu shine bugai, inna delu macece mai saukin kai da tausayi sai dai matsalarta macece mai san abin duniya, sabanin mijinta da yake mutum ne mafadaci dan kusan yara yaran kauyen ba karamin shakkarsa suke ba, wannan halayyar tasa bata tsaya a waje ba hatta a gidansa inna delu tsoransa take ji, bare kuma aje ga yaransa. Saade yarin ya ce mai hankali da nutsuwa cikin kauyen nasu duk wani shashanci irin na yara bazakaga Sa ade aciki ba. wannan halayyar tata ce tasa kowa yake san yin kawance da ita, cikin garin nasu. cikin hakan soyayya mai karfi ta shiga tsakanin sa 'ade da shamsu dan gidan mai gari, wannan soyayya ta su ba karamin jin dadin ta inna delu takeyi ba, dan ko babu komai, 'yar autarta zata auri dan maigari, shima mlm Audi yayi murna da jin soyayyar sa'ade da shamsu, lokaci kankani maganar Aure ta taso, sai dai a bangaren mahaifiyar shamsu laure ko kadan bata kaunar Auren nan da ake shirin kullawa, sai dai maigari ya dage akan lallaifa sai ya aurawa shamsu wadda ya ke so, ita kam laure asan ranta tafi kaunar shamsu ya auri sailuba 'yar kanwarta ko babu komai mahaifin sailuba mai arziki ne cikin garin hayi din . cikin ikon Allah, Aka daura auren sa'ade da angonta shamsu, cikin gidan maigari nan aka gyarawa shamsu, bangare guda maigari ya ware yayi masa gini dai dai da zamanin Auren nasu, ranar wata asabar akayi budar kai aka kai Amarya cikin gidanta, bangaren iyayen mijin aka fara kaita aka danka musu amanarta, sannan aka wuce da ita bangarenta sai dai yadda laure ta karbi surukar tata hakan ba karamun bata ran dangin amaryar yayi ba. haka aka kaita bangarenta, bayan doguwar nasihar da akai mata, haka 'yan kai amarya suka koma gida bayan sun bar amarya a dakinta. zaman amarci cikin farin ciki shamsu yakeyi da amaryarsa, sa 'ade, sai dai fa a bangaren laure ko kadan batajin kaunar surukar ta ta, hakan yasa duk wani aikin cikin gidan nan ita take bawa tanayi, duk wannan wahalar da sa 'ade take sha agun uwar mijinta bata ta'ba sanar da kowa ba, hatta shi kansa shamsu bai san abinda yake faruwa a cikin gidan ba. kwanci tashi babu wuya agun Allah, shamsu sun shiga wata na biyar da yin Auren su, sai dai cikin wannan watannin duk wanda yazo yaga sa'ade yasan ta rame sosai, dan ko cikar amarcin nan da amare suke ita kam batayi ba, sai ma kara zugewa da takeyi, wannan abu ba karamin tada hankalin shamsu yake ba duk lokacin da ya tambayeta ko akwai abin da yake damunta, amsa daya take bashi cewa babu komai, sai dai har ga Allah baya yarda da amsar da take bashi, wannan dalili ne yasa ya fara sanya ido akan duk wani motsinta a cikin gidan, idan kuwa baya nan yakansa kanwarsa zainabu ta kular masa da motsinta, cikin hakanne rannan suna zaune a babban tsakar gidan, matan gidan suna gefe a zazzaune daya gefen kuwa yaran gidan ne wadanda ba a aurar ba suke zaune suna hirar su suna tsinke ganyen rama wanda aka tsinko a gona sa 'ade ma tana cikin yaran gidan ana tsinkar ganyen da ita, fitowar inna laure ce daga dakin ta yasa sa'ade mikewa tabar gun sai dai tana tashi taji inna ta daka mata tsawa da cewa " ke malama ina kuma zakije ne kika tashi zokai zokai da ke kamar wata mutuniyar arziki " "dawo ki zauna" ta nuna mata guri da yatsan hannunta . kowa dake gurin binta yayi da kallo. "maza tashi kije ki surfa min wannan geron, kuma yanzu yanzu nake son ki gama ki kawo min shi kunu zumuyi na gidan mutuwar gidan Mlm tsalha, ". cikin hanzari ta tashi ta nufi gurin da taga an ajiye geron cikin kwarya, gurin turmi ta nufa taje ta fara surfin, duk ta gaji sabida yawan geron dan ya kai kusan kwano uku, haka ann, ta surfeshi duk da ta gaji ,taje ta kaimata. ire iren wadan nan ayyukan sune suke damun sa 'ade saboda rashin sabo da yinsu. haka dai rayuwa taci gaba da tafiya, katsam, ciki ya bayyana jikin sa 'ade murna agun shamsu kamar ya zuba ruwa akasa ya sha, haka suka cigaba da rainon cikin su . inna laure kuwa bataji dadin ganin bullar ciki jikin sa 'ade ba, duk yadda tayi yunkurin zubar da cikin hakan ya gagara Alkawarin Allah baya tashi, cikin yar dar Allah ciki ya fara girma har ya kai lokacin haihuwa, duk wani abun bukata na haihuwa shamsu ya tanadarwa sa'ade haka a bangaren inna ta komai ta siya mata dangin kayan wankan jego robobin wanka, da sabulun salo da kujerar jego har da yajin daddawa sai da inna ta tanadarwa Autar ta. cikin wani dare nakuda ta kamata, tun tana iya daurewa har ta kasa daurewa, haka badan taso ba ta tashi ta taso shamsu wanda yake ta tikar baccinsa, haka ya tashi yaje ya kira mata inna karama, wato amaryar maigari, cikin ikon Allah ta haifo santaleliyar jaririyarta kyakykyawar gaske, mai kama da mahaifinta sak, cikin daren nan kowa yaji haihuwar sa 'ade dan shamsu da kansa yaje ya sanar da innanta cikin daren nan. iya bakin ciki inna laure tayi da haihuwar jaririyar nan, haka dai ta dake ta shiga hudimar kula da maijego da jaririyarta, dan gudun kada jama ar gidan su zageta, haka dai akayi ta hudimar haihuwa har zuwa ranar suna, duk yadda inna taso abata sa 'ade ta tafi da ita, fafur megari ya hana yace abarta a gidan mijinta za a kula da ita yadda ya kamata, badan ran inna yaso ba haka ta hakura da daukar sa 'aden sai dai kullum tana zaryar zuwa gurin maijego dan kara kulawa da ita. ranar suna jaririya taci sunan Rahida, haka maigari yasa asaka mata gida ya cika ya tunbatsa sai dora sanwa ake ana saukewa, jama ar kauyen yawa yawansu duk sunje sunan gidan maigari kowa ya dawo cikin murna da farin ciki. bayan sati daya da yin suna, ranar wata talata ciwan ciki mai karfi ya kama rashida bata jima da farawa ba, rai yayi halinsa, Allah ya karbi baiwarsa, kuka shamsu yake tamkar ransa zai fita a lokacin da yasamu labarin mutuwar sa'ade, shima maigari mutuwar nan ta girgiza shi sosai, inna kuwa suma ta dingayi ana yayyafa mata ruwa sabida tsabar rudewa. cikin kan kanin lokaci aka yiwa sa 'ade wanka aka hadata aka kaita gidanta na gaskiya. kuyi min hakuri da wannan dan Allah ina cikin wani uzuri ne 🙏🏻 *mrs Bilu ce*✍🏼 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page 6⃣5⃣ to 7⃣0⃣ Na Alawiyya Ado Alhasan. 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS🌐 *Duk* yadda ake jin tashin hankali da rashin kwanciyar hankali shamsu ya dandana a wannan lokacin, musamman idan ya kalli jaririyar da abar kaunarsa ta tafi ta bar masa.sai yaji tausayin ta ya kara kamshi ga wata soyayyar jaririyar na shigarsa har cikin ransa. Bayan anyi sadakar uku inna delu ta fara haramar komawa gidan ta dan taci gaba da kar'bar gaisuwar autar ta ta a gidanta, bayan dare yayi yawan yawan mutane masu zaman makokin duk sun watse, yaro ta aika kofar gida tace ya kira mata maigari, yaran baijima da zuwa ya sanar da maigari sakon inna delun ba ya dawo yace mata yace gashi nan zuwa, har bangaren sa 'ade maigari ya shiga domin jin kiran da inna delu take masa, wannan shine shigarsa ta farko tun tarewar surukar tasa. Da sallama ya shiga ya samu guri ya zauna ,inna cikin jin kunya irin ta surukai suka gaisa, tare da kara jajanta wannan rashi da sukayi na sa ade.hawaye ne yake zuba akan fuskar inna delu, sannan ta fara da cewa "ranka ya dade dama wata magana nakeso muyi shine yasa na tura kazo dan yau nakesan zan koma gida ". Shi kam maigari ya kasa kunne yana jiran yaji bayaninta. "shine nake neman alfarma agunka dan nasan kai kadaine zaka iya yimun wannan alfarmar dan Allah ranka ya dade ina san ku barmin jaririyar nan a hannuna in riketa nayi maka alqawarin zan kula da ita tamkar yadda zan kula da kaina " ta karashe maganar tana zubar hawaye akan fuskarta. Tun da tafara magana maigari yayi shiru yana saurarenta . "To Alhamdulillahi shine abin da zan cemiki delu, domin kema kina da haqqi akan yarin yar nan, nima zanfi so ace kin dauketa kin tafi da ita gurinki zatafi samun kulawa fiye da nan din, ba wai dan bamu da abin kulawar da ita ba ,A a sai dan wadansu dalilai, Allah ya rayata, ya sanya mata albarka cikin rayuwarta, amma kafin yanke shawarar baki ita ya zama dole in sanar da mahaifinta dan shima inji ta Bakinsa sannan zan sanar da matan gidan suma, bawai dan idan na yanke hukunci zasuyi jayayya da hukunci na ba ne zandai bawa kowa haqqinsa ne ". godiya sosai inna tayi masa, sannan ya tashi ya koma cikin gidan bangaren iyalansa, duk matan gidan yasa aka kira masa su, sannan ya kira shamsu shima, nan ya zayyano musu bukatar inna delu, har cikin ransa shamsu yafi amincewa da inna ta tafi da jaririyar gurinta, sai dai inna laure ko kadan bata so hakan ba dan dai ba yadda ta iya ne. wannan shine asalin dawowar rashida hannun inna delu. Cikin ikon Allah inna da dauke ta, kulawa sosai ta dinga bata, madara maigari yake siyowa Abarni ake bata, har Allah ya rayata, ta fara cin Abinci sosai. bayan shekaru uku, shamsu yayi aure, da sailuba ya rinyar da inna laure take san ya aura tun da farko,. bayan yy Auren ya nemi da inna ta dawo masa da rashida hannunsa kemai mai inna take barmasa ita, haka dai ya hakura ya koma, sai dai duk sati yana zuwa ya duba rashida. Bayan shekaru biyar rashida ta samo girma, dan haka inna ta kara bata kulawa ta mussaman, har makarantar isilamiya aka sakata haka nan dai rayuwa taci gaba da tafiya, har zuwa lokacin da Allah yayiwa malam Audi rasuwa, inna taji d'acin rashin mijin nata haka nan tayi dangana ta dauki hakuri, bayan raduwarsa da wata shida shima rabe ya hada kayansa yace da inna ya tafi birni, neman sana a, cikin yar dar Allah ya samu sana 'ar siyar da lemo da ayaba abakin Hanya,da ikon Allah ya samu rufin asiri cikin sana ar da yake har ya fara neman Aure, yarinyace karama a kusa da shagon da yakama haya gidansu yake, yarinya ce mai hankali, da nutsuwa, itama iyayenta ba masu karfi bane awara take soyawa a kofar gidansu, bayan Aurensu da wata shida, ya shirya ya tafi kauyen su, murna inna tayi kamar zata hadiyeshi, kwanan sa biyu a garin ya fara shirye shiryen komawa birni, sai dai yaxowa da inna bukatar yana san ta bashi rashida ya koma da ita birnin ko dan sabida ya sanya ta a makarantar boko, inna jin cewa makarantar boko za a sata bata yi musun hanashi tafiya da ita ba, sai dai tasa yaje ya sanar da maigari bukatar tasa, shima mai gari baiyi gardama ba ya amunce da asanyata a makarantar bokon tunda a wannan lokacin ko kadan ba a karatun boko a kauyen, shima mahaifinta yaji dadin hk, lokacin da inna take sanar da rashida maganar tafiya burni tayi murna sosai ko babu komai zataje taga burni da 'yan birni balle da inna ta sanar da ita har makaranta kawun nata yace zai sakata, murna take sosai, nan ta shiga gidan su tsahare tayi mata sallama, ita kam tsahare ko kadan bataso tafiyar aminiyar tata ba ko dan shakuwar dake tsakanin su. har kwalla tayi lokacin data rakota hanya tare da inna da sauran abokan arziki, har bakin hanya suka rakosu sannan suka koma, kawunta ya rike hannunta suka nufi hanyar da zata kaimu inda zasu hau mashin din da zai kaisu tasha wannan shine sumuwar dawowar rashida birni, bayan sun shigo cikin gari, kai tsaye mota ya tsayar musu suka hau ta kaisu unguwar da yakama haya suke zaune da matarsa maryam, saukar mutunci tayi musu, bata nuna damuwarta akan ganinsa tare da rashida ba, nan yayi mata bayanin komai ta amince tare da adduar samun zaman lafiya a tsakanin su, rabiu yayi murna yaji dadin karamcin da maryam tayi masa, watan rashida shida a birni inna tazo kawo musu ziyara, kwarai taji dadin ganin yadda rashida ta samu kulawa agun surukarta, tayi murna kuma tayi mata godiya sosai, tun daga wannan ziyara da inna tayi musu aikuwa rabe ya hanata komawa kauyen su, ganin zaman bazai yuyu haka ba shine tasa aka cigita mata samun aiki gidan masu kudi, bata jima tana nemaba aka momata wani gidan Alhaji bata jima da farawa ba ta daina sai kuma ta samu gidan Hajiya Asma u wadda itace har yanzu suke tare da ita cikin aminci. ganin tana samun komai agun aikin da take shine yasata fara jigilar kwaso yaran kauyen tana rarrabasu wadan da itayensu suke da sha awar yaransu suyi aikin. ganin aiki babu wata matsala hakanne yasa ta samawa rashida aikin ba tare da kowa yasan jikarta bace, wannan shine mafarin zuwan rashida aikatau. *cigaban labarin* shiri sosai rashida takeyi domin tana dokin zuwa taga mahaifinta da kuma kakanta, bayan tagama shirya kayanta na tafiya kauyen, zuwa tayi ta sanar da Aunrynta kan cewa tana san taje gun inna delu, suhaima bata hanata ba kudin mota ta dakko ta bata sai dai ta bata umarnin kan da tawo da wuri kafin lokacin girki ya kusanto, da hanzari ta koma cikin dakinta ta dakko mayafinta ta yafa tayi mata sallama ta tafi gurin inna delu . bayan taje sun gaisa nan take sanar mata tana san zuwa kauye taje ta gaida mahaifinta, ko kadan inna batayi yunkurin hanata zuwa gun mahaifin nata ba. sun tsaida magana gobe zataje gidan kawunta rabe shi zai kaita kauyen nan su, nan sukayi sallama da inna, kan cewa sai ta dawo, har kofar gida innan ta rakota tare da yi mata fatan zuwa lafiya tare da dawowa. washe gari. tunda asuba rashida tagama gyara komai, hatta abin karyawa ta gama ta sanya akan teburin ajiye abincin, kusan karfe tara ta shirya tsaf kawai uwar dakin nata take jira , suhaima bata fito ba sai kusan karfe goma saura, tare suka fito da ita da maigidan, cikin mamaki suhaima take kallan rashida. "0hh sarkin zumudi!!! wai har kin shirya ne? sunkuyar da kai tayi tana dariya . "ehh, na shirya tun dazu Aunty " wata jaka ta nuno mata a gefen kujerar dake falon, ga tsaraba nan sai ki tafi musu da ita, har kasa rashida ta tsuguna tana godiya, sai da yayi magana sannan hankalinta ya dawo gareshi har kasa ta durkusa ta gaida shi, cikin sakin fuska yake amsa gaisuwar tata, kudi ya dakko masu yawa ya mika mata "ungo wannan kyayi kudin mota, Allah ya tsare ". Abinda yace kenan ya wuce ya koma cikin dakin suhaima. godiya tayi sosai da wannan dawainiyar da sukayi mata, suhaima ta dada jaddada mata akan kada ta wuce kwanaki uku, haka dai taja kayan tsarabarta tayi waje malam sabo yana ganinta da kaya, ya taso da sauri ya karbi jakar hannunta yana washe baki, "A a rashida ina zuwa haka na ganki da kaya haka " itama cikin fara'a ta maida masa da amsar tambayarsa, "zanje kauye ne amma ba jimawa zanyi ba zan dawo ". Amma babu labari to Allah ya tsare hanya, bari in rakaki da kayan ki sami mota, har bakin layin ya rakota da kayan sai da tasamu mai adaidaita sannan sukayi ciniki ta dura kayan cikin motar suka tafi tare da yiwa baba sabo godiya. kusan shadaya saura ta isa gidan kawunta rabe, shima yana zaune yana tsumayen jjiranta,. a tsaitsaye suka gaisa da Aunty maryam, sannan suka dauki hanyar zuwa tasha domin shiga motar garin nasu. iya tafiya sun shata dan sai kusan karfe biyar na yamma sannan suka karasa cikin garin, kai tsaye gidan maigari suka wuce, tarba mai kyau suka samu daga jama 'ar gidan kowa murna yake da ganin rashida shima mai gari yaji dadin ganin jikar tasa dan tafara zama budurwa kyaunta ya kara fitowa, kowa mamakin yadda rashida koma yakeyi, haka nan dai akaxo aka baibayeta yaran gidan da manyansu duk sun kewayeta kowa kallanta yakeyi............ nima garin kallan nata wayar hannuna ta subuce min😀 *mrs Bilu ce*✍🏼 [10/31, 10:36] ‪+234 706 738 2588‬: 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *'YAR AIKI* Page7⃣0⃣ to 7⃣5⃣ NA Alawiyya Ado Alhasan. 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITTERS✍🏼 *Assalamu Alaikum* *Barkan ku da war haka masoya labarin nan, inai muku fatan alkhairi a duk inda kuke musamman members din cikin gruop din MATAN KWARAI*. *inai muku fatan alkhairi, Allah ya saka muku da mafificin Alkhairi*. *inna* delu ce takai duban ta ga kofar dake kallosu, ganin rashida a zube a bakin kofar shine yasa suka zabura gaba d'ayansu suka yo kanta. innalillahi wa inna ilaihirrajiun, shine abin da suke ta fada, inna laure ce tayi namijin kokari, gurin janyo ta, suka shigar da ita cikin d'akin na inna. ruwa, inna taje ta debo ,cikin randar dake cikin dakin nata, ta zo ta yayyafawa rashida akan fuskarta, bayan ta yayyafa mata ruwan, sai ta dinga girgizata, a hankali ta bude idanuwan ta, kallansu take daya bayan daya, cak ta tsaida kallanta ga inna delu, hawaye ne ya fara sauka akan fuskarta , da kyar bakinta ya bude ta iya kiran sunan inna delu. " inna da gaske ne abunda kunnuwa na sukaji cewar baba na nan gidan Aure zaimin ba zan koma burni ba in ci gaba da karatuna ba "? itama innan hawaye ne yake zuba a kan fuskarta sabida tana tausayawa rayuwar rashida a wnnan yanayin da tasamu kanta a cikinsa. gefan zanin ta tasa tana goge hawayen kan fuskar tata. "kiyi hakuri rashida abinda kikaji haka ne amma kiyi hakuri yin biyayya dole ce ga mai gari sabida babu wanda ya isa yayi jayayya da shi a garin nan , balle shine yake da iko ga duk wani yaro ko yarinya dake cikin gidan nan, kiyi hakuri, ki dauka dama haka Allah ya kaddara miki kenan cikin rayuwarki ". tashi tayi ta zauna wani hawaye mai dumi yana sauka akan fuskarta, inna laure ce ta dafa kafadarta cikin rarrashi take mata magana, "kiyi hakuri rashida babu abinda za ayi miki dan a cutar da rayuwarki, yin hakan ma wata hanya ce ta samar miki da farin ciki da jin dadi, kiyi hakuri ki gode Allah ma da kika samu wannan karatun ma, yanzu duk cikin kauyen nan akwai wanda ya sami ilimi kamar naki ne? Ai ko wannan kya daga hannuwa ki godewa Allah ". ita kam inna lallashi ta bige da shi, tare da kwantarwa rashida hankali, har kusan magariba, inna delu tana gidan maigari bata tafi ba, sai da aka idar da sallar magariba sannan ta kama hanyar komawa gidanta, dan dare yayi bazata iya komawa cikin birni yanzu ba. da kyar sukayi sallama da rashida sabida kukan da take ta shekawa ita kam inna laure tun tana lallashinta, har ta hakura ta zuba mata idanuwa. kusan karfe tara saura na dare, baba shamsu ne yake zaune a gaban mahaifin sa, yana kwararo masa bayanin da yayiwa inna delu, daxu, ji yayi wani gumi yana sauka a jikinsa duk da ba wani zafi ake a wannan lokacin ba, hularsa ya cire ya dinga fifita fuskar sa, ko kadan baiso jin wannan maganar abakin mahaifin nasa ba, sai dai koda wasa bai isa ya musawa tsohon nasa ba dan haka fatan alkairi yayi da jin hukuncin da mahaifin nasa yayi, cikin sanyin jiki ya tashi yayiwa maigari sallama ya shiga cikin gida. kai tsaye 6angaren innan sa ya dosa dan yasan rahida Tana cen din, ai kuwa ya sameta cikin yanayi mara dadi, dan taki yiwa kowa magana, banda kuka babu abin da take yi, ganin halin da take ciki kasa shigowa dakin yayi ya koma 6abgaren matarsa, cikin wannan daren cikin su hudun nan babu wanda yayi kwanan farin ciki, musamman ma ita rashida din. inna delu kuwa gari na wayewa ta shiga kintsa jikinta dan komawa nini, karfe bakwai ta tafi gun hawa mota ta tafi, babu 6ata lokaci da yake safiya ce akwai masu tafiya da yawa, motar ta cika suka dauki hanyar cikin burni, sai dai ko kadan zuciyar ta inna babu sukuni a cikin ta, kusan karfe tara da wasu mintunan motar ta sauke so, kai tsaye adai daita inna ta tare ta hau suka ja suka tafi, kai tsaye gidan khalil suka dosa, bayan ya sauketa ta dakko kudin sa ta bashi ita kuma tasa kai ta shiga cikin gidan , a bakin gate din gidan suka gaisa da baba maigadi, bayan sun gaisa ta shiga cikin gidan, palon rashida taje ta kwankwasa, sai dai tajima tana bugun kofar kafin azo bude mata, suhaima ce ta bude kofar ga dukkan alamu bacci take yi bugun kofar ne ya tasheta, ganin inna a bakin kofar shine yasata sakin fuska, " A a inna kece sannu da zuwa" ta fada tana kara ware ido dan ganin ko zata hango rashida a bayan inna, A a inna na ganki ke daya ina rashida din? Hmmmmm!! kedai barni in shiga ciki kyaji bayanin da zanyi miki 'yar nan. Cewar inna, kai tsaye ta shiga cikin palon a kasan kafet din dakin ta zauna, suhaima tayi tayi ta hau kan kujerar amma inna taki hawa, a falo suhaima ta bar inna ita kuma ta koma dakin barcin ta dan cenza kayan dake jikinta, ita kam inna tana zaune tana zaman jiran ta fito, shi, kam khalil yana cen 6angarensa ya gama shurinsa na fita kasuwa, wata shadda ce dankareriya a jikinsa, mai launin ruwan bula, amma tana da haske ba mai duhu bace, dinkin rigar ita gwaiwarsa ya tsaya daga hannun rigar an matse shi bai bude sosai ba, wata hula ya dora akans wadda kalar ta tayi daidai da kalar shaddar tasa , agogo ya daura a hannunsa sannan ya feshe jikinsa da turaren da yasaba sanyawa ako da yaushe wayoyinsa ya debo guda biyu ya rike a hannunsa ya nufo 6angaren suhaima, yana shiga palon yaci karo da inna zaune, sallama yayi mata bayan sun gaisa nan ya fara tambayar ta rashida? bai tsaya jin abin da zata ce ba, ya nufi cikin dakin suhaima, yana tura kofar dakin nata, ya hangota tana yin sallah, ko babu tantama ya san sallar asuba takeyi agogon hannunsa ya kai duba gareshi karfe goma saura kwata, tsaki yayi ya ja kofar ya fita cikin zuciyarsa yana jin tsanar wannan halayyar ta suhaima, palon ya dawo ya sami inna a zaune, daya daga cikin kujerun ya sami guri ya zauna. bayan sun kara gaisawa, nan ya sake jihowa inna tambayar ina rashida,? nan inna ta fara yi masa bayani dallah dallah, har zuwa kokacin da ta taho ta bar rashida a cen din, wani irin tashin hankali yaji wanda bai ta6a jin irin sa ba a cikin rayuwar sa kasa zama yayi ya mike tsaye yana nuna inna da hannu, haba " inna baku da tausayi ne taya ya zaku 6ata rayuwar yarin ya karama kamar rashida? Sam wannan abun bama zai yuyu ba, zanje kasuwa anjima kadan zan dawo, zamuje ki rakani garin da kaina zanje in fahimtar da maigarin yiwa rashida aure a yanzu babbar matsala ce ba kadan ba. ko sallama baiwa suhaima ba ya fita yaja motarsa ya fita, ita kam inna tsabar mamaki ne ya hanata yin magana, sai da suhaima ta fito sannan ta sanar mata abin da yake faruwa, itama ko kadan bataji dadin wannan hukuncin da suke so su zar tar akan rashida din, ganin kowa yayi shiru babu mai cewa kala tsakanin inna da suhaima din, inna ce tayi karfin halin cewa da suhaima Hajiya me zan yi miki yanzu kafin Alhaji yazo mutafi? suhaima tace inna taimaka ki dora mana abin karyawa, kema ga dukkan alamu baki karya ba kika taho, wlh kuwa 'yar nan gaba daya 6acin rai ne ya cika min zuciyata, haka dai suke taba hira jefi jefi, inna da kanta ta shiga kichin din ta gyarashi fes sabuda dattin da yayi, abinci mai dadi ta shirya musu, kafin azahar ta gama komai ta gyarawa suhaima gidan, wajen karfe biyu da wani abun, khalil ya dawo dan ko motarsa bai shigo da ita ba a waje ya barta da kafarsa ya tako ya shigo cikin gidan, cikin sauri ya sanarwa da suhaima sakon ta kira inna taxo su tafi kada yamma tayi musu a hanya, nan taje dakin rashida ta kira inan, mayafinta ta dauko ta yafa ta fito cen kofar gidan taje ta tsaya. suhaima kuwa ta dage akan lallai itafa sai antafi da ita, duk yadda khalil yaso ya rarrasheta akan ta zauna ita kam ta dage tana san zuwa kauyen ko babu komai taje taga yadda kauye yake dan bata ta6a zuwa ba, ganin zata 6ata musu lokaci shine yasa khalil yace taje ta dakko mayafinta su tafi, da sauri taje dakinta, ta dakko mayafi ta kulle gidan suka fito tare, a bakin kofa baba maigadi yayi musu adduar dawowa lafiya, cikin sakin fuska suka amsa masa suka shiga cikin motar, suhaim ce a gaba, ita kuwa inna bayan motar khalil ya bude mata ta shiga, suka dauki hanya suka tafi. sai dai muyi musu adduar Allah ya saukesu lafiya. *KAUYEN HAYI* tafiya sukai sosai, sannan suka isa garin damma motar gida ce babu wani tsaye tsaye da sukayi, turyan turyan inna take nunawa khalil hanyar shiga garin, sai gasu a kofar gidan maigari, nan fa yara yaran garin suka fara dandazon ganin motar da ta tsaya a kofar gidan maigari, duk da ba wannan ne karo na farko da suka fara ganin motoci a kofar gidan maigarin ba, sai dai wannan motar tasha ban ban da wacce suka saba gani, khalil ne ya fara fitowa sannan suhaima ta fito itama inna ce ta rage a motar sai da khalil yazo ya bude mata sannnan ta fito, kai tsaye cikin gidan suka shiga, ita da suhaima, shi kuma khalil ya tsaya agun maigari, kar6ar mutunci da karamci ya samu agun mai garin tamkar dama ya sanshi koda yake dama wannan itace dabi ar wannan dattijon. Khalil kuwa bai zauna ba, sai da yasa aka kawo masa ruwan alwala yayi alwala dan yin sallar la asar da ta samesu akan hanya. suma su inna, da shigarsu 6angaren inna laure suka tafi, kowa kallan inna take ganin ta dauke da bakuwar da basu ta6a ganinta ba , karbar karamci sukai mata, sannan suka kewayesu da abubuwan motsa baki, suhaima kuwa bayan sun gaisa da inna laure nan ta fara tamvayar ina rashida take, inna da kanta ta shi ta tafi 6abgaren inna karama dan ta kira mata rashida din, ita kuwa inna delu alwala tayi tazo tayi sallar la asar, ita kam suhaima tana zaune ko ruwan da aka kawo mata bata kallaba balle tasanyashi cikin bakinta, sallamar da akayi ne cikin dakin shine yasa suhaima ta dago takai dubanta ga maiyin sallamar yarinya ce karama dan bazata gaza shekarun rashida ba, bayan ta tsuguna ta gaishesu nan ta sanarwa da inna sakon maigari na cewa yana nemanta ,nan inna tasa kai ta tafi gun kiran da ake mata. rashida tana kwance kan gadon inna karama zazzabi ne ya rufeta dan haka ta dauki zanin inna karama ta lullu6e jikinta da shi, shigowar inna laure shine yasa ta kara rintse idanuwan ta tamkar maiyin bacci, da kanta ta shigo dakin take tambayar inna karama ko rashida tana gurin ta ne, cikin gurmamawa ta amsa mata da cewar ehh tana ciki inaga bata jin dadi ne shine ta kwanta, inna da kanta ta shigo cikin dakin gadon da ta hangi rashida nan ta nufa, a hankali take mata magana "maza kitashi ga inna delu nan tazo ita da uwar dakinki maza kije tana nemanki ". da sauri ta yaye zanin dake jikinta wanda ta rufa da shi ta mike zaune tana kara kallan fuskar innan, ganin fuskar tata babu wasa shine yasa rashida ta gasgata maganar inan, da sauri ta mike ta nufi 6angaren inna laure, ai kuwa da gaske idanuwanta Auntyn ta suka hangomata a zaune, akan tabarma a dakin innan, da sauri ta fada cikin jikin Auntyn nata tana sakin kuka mai ban tausayi., itama rungumeta tayi tana rarrashinta haka inna nna ta dawo ta samesu nan tashiga sanar da suhaima hukuncin da maigari ya zar tar akan rashida. A cen kofar gida kuwa bayan khalil ya idar da sallah , komawa yayi suka gaisa da maigari nan yake sanar masa shine wanda rashida take hannunsa a birni, sai dai dazu inna taje masa da wani bayani na cewa rashidar aure za ayi mata ,kwarai maigari yaji dadin wannan bayanin na khalil sai dai kafin yace komai, sai da ya aika aka kira masa inna delu a cikin gidansa. bayan inna delu tazo sun gaisa da maigari nan ta gabatar masa da khalil, da irin dawainiyar da yake da rashida, maigari yayi masa godiya sossannan ya juyo ga kallansa gun khalil da cewa "" duk naji byanan da kukayi yanzu makasudin zuwanku shine nakeson ku sanar dani ?...... Bar in barku nan sai m kara dowara✍🏼 *mrs Bilu ce*✍🏼 [10/31, 10:36] ‪+234 706 738 2588‬: 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 *YAR AIKI* Page 7⃣5⃣ to8⃣0⃣ NA Alawiyya Ado Alhasan. 🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷🌷 🌐HAJOW🌐 🌐HAKURI DA JURIYA 0NLINE WRITTERS🌐 *Khalil* ne ya gyara zama cikin nutsuwa ya fara kwararowa maigari jawabinsa kamar haka "ranka ya dade dama rashida a hannuna take da zama kamar yadda inna ta sanar da kai, toh ranka ya dade yarin yar nan ba karamar baiwa Allah yayi mata ba, musamman ta 6angaren ilimi, domin tana da san yin karatu kuma Allah ya bata basira da hazaka, toh irin wadan nan yaran kulawa akafi san abasu, wala Allah nan gaba kaga ta zama wata abar so ga kowa a Duniya, ko kuma, ta zama silar kawo muku cigaba cikin al ummar mu, ko ta taimaka muku nan gaba cikin kauyen nan da irin su basu da yawa a duniya, da wannan nake neman alfar mar amincewarka akan kabarta ta cigaba da karatun ta, nan gaba idan tayi Karatun ta kara girma sai a aurar da ita, ni na daukar maka alqawarin da zarar ta gama makarantar da take yi a yanzu zan dawo maka da ita, ka aurar da ita, in yaso ko daga baya ne idan tasamu miji mai ra ayin karatun sai ya barta ta cigaba, ina fatan zaka fahimce sosai akan wannan jawavin da nayi maka ranka ya dade"? tunda khalil ya fara jawabinsa gaba daya hankalin maigari yana gareshi har zuwa inda yakai aya, nan maigari ya numfasa ya fara bawa khalil bayanan da suka taru cikin bakin sa. "yaro duk naji bayanin da kayi, na kuma ji dadin yadda kake kokarin kulawa da yarinyar nan, toh amma nima inada dalili na akan dagewa da nayi akan auren nan da zan mata, magana ta farko da zan sanar maka ita ce kaga kaf kauyen nan mazan su da matan su a dai cikin yara masu shekarunta babu wanda ya samu ilimi kamar nata duk cikin kar karar nan, wannan baisa ta gode Allah ba, sai abu na biyu babu Wata yarinyar cikin gidan nan da take wuce iya wadan nan shekarun ba tare da na Aurar da ita ba wannan tana daya daga cikin dokokin gidan nan, dan haka kayi hakuri bazan sauke wannan qudirin nawa ba, naji dadin abubuwan da kayi mana Allah ya saka maka da Alkhairi ya biyaka da Aljanna ". tunda maigari ya fara magana gaba daya hankalin khalil ya rashi, baya jikinsa, gumi kawai yake sharcewa, ganin lallai wannan tsohon yana da kafewa akan batun da ya zar tar, cikin tashin hankali ya kara jehowa maigari wannan tambayar. "yalla6ai, ka sanarwa da mijin nata na dauki alqawarin zan kula da shi, ya biyota bayan anyi Auren mutafi binni tare da shi, zan sama masa aiki ita kuma zata cigaba da Karatu ". shikam maigari, tsabar mamakin kalaman da suke fitowa a bakin khalil ne yasa shi gyara zama yana kara nazarin sa dan yanxu gani yake anya kuwa yaran nan kansa kalau yake? cikin zuciyarsa yake wannan maganar. a fili kuwa, cewa yayi kayi hakuri kawai babu inda rashida zata koma, kuma mu a tsarin garin nan bamu ta6a ganin macen Aure tana fita makaranta ba, dan idan nayi wannan abun ma, mutanen garin nan gani zasuyi kamar sai da jikar tawa nayi tare da mijin Auren nata " itakam inna tunda aka fara magan ganun nan kala bata ce musu ba sai dai duk wanda yayi magana ta bishi da kallo tsakanin maigari da khalil. "toh, yalla6ai ko zaka bani dama ta karshe aka ina so inga mijin dan mu tattauna da shi" Maigari fa ya fara sukewa da wannan abubuwan da khalil yake masa, cikin rashin walwala ya fara sanar da khalil, kai yaro wai kureni kazo kayi ne? duk maganar da nayi sai ka musamin, nifa din nan da kaganni idan nafadi magana koda wasa ba a yimin musu, toh tun wuri ka tashi ka bani guri, kuma ka bude kunnuwanka kaji da yau mijin aure har yanzu bangama tantance wanda zan aura mata ba, kaga kuwa babu hujjar kace sai kaganshi, wannan ita ce maganata da kai ta karshe akan rashida, cikin zafin rai maigari ya tashi zai bar gurin, charaf, khalil ya riko rigar maigari, " dan Allah baba ka tsaya kada ka tafi , tsayawa yayi bai taka karfarsa ba, sai dai har yanzu bai dawo ya zauna din ba, yana tsaye yace masa ina jinka duk abin da zaka fada ka fada ba sai na zauna ba " . khalil ya taso yazo gabansa ya tsuguna hawaye ne fal cikin fuskarsa, " Baba ka amince ka bani auren Rashida". cikin kidima inna ta mike tana nunoshi da hannunta sai dai bakinta ya gaza furta komai. shi kansa maigari sai da ya girgiza da jin abin da khalil din ya fada. dawowa yayi ya zauna, kan kujerar da ya tashi. "kai yaro mai kunnuwa na suke jiye min ne ,da gaske kake ko kuwa wata dabarar ka 6ullo min da ita dan in saurareka"? khalil ne ya fara magana " wallahi baba da gaske nake wannan abun da na furta maka, na dauki Alqawarin zan zan Aure rashida tsakanina da Allah kuma zan kula da ita yadda ya kamata wannan alqawari na daukarwa kaina, kuma zan cigaba da adduar Allah ya bani ikon cika wannnsn alqawrin da na dauka ". ita kam inna kunnuwanta gizo suka fara ji mata, dan haka bata tsaya karasa jin abin da suke tattaunawa ba ta sulale ta koma cikin gidan maigari. shi kuwa maigari kamo hannun khalil yayi ya jawoshi kusa da shi, lallai yayi murna da farin cikin jin wannan maganar nan ya shiga sanya masa albarka, farin ciki ne ya cika zuciyoyinsu gaba daya, nan suka tsaida maganar kan zai dawo sati mai zuwa dan tsayar da lokacin da za ayi biki. ita kuwa inna tana shiga cikin gidan 6ngaren data bari nan ta koma sai dai gava daya jikinta yayi sanyi, musamman lokacin da ta shiga cikin dakin ta hango rashida suna hira da suhaima, batace musu komai ba ta nemi guri ta zauna, rashida ce ta taso da gudu ta rungume innan. ita kam suhaima binsu tayi da kallo tana tunanin menene tsakanin inna da rashida ne domin ta hango shakuwa mai karfi a tsakanin ta da ita. a kofar gida kuwa, sun gama tsara duk wasu al a mura da yadda komai zai kasance, sai dai khalil ya nemi alfarma gun mai gari akan baya san kowa yaji maganar nan sai bayana an daura aure. sai dai khalil ya nemi alfarma gun maigari kan cewa ya basu rahida su tafi da ita cen birni, bai Musa masaba, da kansa ya tashi ya shiga cikin gidan, dakin laure ya nufa dan yasan suna cen, har cikin dakin ya shiga, suka gaisa da suhaima sannan ya umarci rashida akan ta shirya su tafi da ita, aifa nan ta hau murna, tana tsalle ta shiga hada kayanta, ita kuwa inna gaba daya hankalinta baya jikinta, haka nan dai take daurewa dan kada su ganota. basu suka bar kkauyen ba sai kusan magariba, tsaraba mai yawa maigari ya basu suka taho. tafiyar tasu tayi sauri dan kafin karfe tara na dare har sun shigo cikin garin, gidan da inna take nan suka fara zuwa suka sauketa, sannan su kuma suka wuce gida, bayan sunje gida gaba dayan su a gajiye suke, dan haka wanka, khalil ya shiga 6angaren sa yayi, itama suhaima dakinta ta shiga ta watsa ruwa sannan ta dauro Alwala tazo ta jero sallolin da bata samu tayi ba. bayan ta idar da sallah, 6abangaren khalil ta tafi, dan ta sanar da shi abin da ke cikin bakinta, shigar ta dakin shine yasa ta ja ta tsaya turus a bakin kofar dakin, ganin halin da ta samu khalil din a ciki, yana zaune akan kujerar falon, sai dai duk wanda ya ganshi cikin wannan yanayin dole, ya tambaye shi damuwarsa, tausayin mijin nata ne ya kama ta duk da batasan ainihin abin da ya kawo masa wannan damuwar ba har ya shiga cikin wannan rudanin da yake ciki har ya haifar masa da wannan damuwar. sannu a hankali ta tako ta shigo cikin palon, ko kadan baima san ta shigo din ba, sabida gaba daya hankalinsa baya jikinsa, matsowa tayi kusa da shi ta dafa kafadarsa, " khalil manene yake faruwa ne? ta6ashin da tayi ne yasa ya dawo da hankakinsa daga duniyar da ya lula. suhaima me kika gani! naga tun da muka taho daga kauyen nan na lura baka cikin sukuni, ko wani abu ne ya faru ne? girgiza mata kai yayi alamar ,babu komai tare da dafe kansa. "suhaima ciwan kaine yake damuna mai zafi, ga kuma zazzabi da yake san rufani sannan ga gajiya". cikin kulawa tasa hannu ta ta6a goshinsa dan jin yanayin jikin nasa, bataji wani zafin zazzabi a tare da shi ba, haka nan ta sashi yayi wanka ya shirya cikin doguwar riga, da gajeran wando, ruwan shayi yasa ta dafa masa, sannan ta bashi paracetamol yasha, a wannan lokacin yafi bukatar ke6abcewa shi kadai dan haka suhaima da taga ya kwanta Aman gado ya dauki bargo ya lullu6e jikinsa hakan ne yasa ta dole ta hakura da furta abin da yake cikin bakinta ta nemi guri ta kwana a bayansa ba dan ranta ya so ba. bayan ya tabbatar da suhaima tayi bacci, tashi yayi ya zauna, ya jima azaune yana nazari kan yadda zai 6ullowa mahaifansa kan maganar Auren nan da ya kinkimo shi a yanzu, nan wata zuciyar ta kara tunatar da shi rigimar da zasu kwasa da suhaima tunda ko babu komai yasan irin masifaffan kishinta, musamman a yanzu da ya ke ganin ya tarki rigima babbaba ta auren mai Aikin gidan ta, wata zuciyar ta na nuna masa illar abin da yake shirin yi, wata kuma zuciyar kara bashi goyan baya take akan wannan muradin nasa, ganin tunani yayi masa yawa yana neman tarwatsa masa kansa, tashi yayi ya dauro alwala ya shinfida sallaya ya tada sallah, raka a hudu yayi, bayan ya idar da sallar ne ya daga hannunsa yana kwararo addu oin zabin alkhairi, cikin wannan al amarun da yake tunkaroshi. ya jima yana adduar, sosai bayan ya gama ya cika da salatin Annabi muhammad (S A W) nan ya shafa ya koma gado ya kwanta, bacci mai nauyi ne ya dauke shi. rashida kuwa, tunda suka dawo tsabar gajiyar da ta debo, ko kayan jikinta bata cire ba, ta hau kan gadonta, bacci mai dadi yayi gaba da ita, sai dai acen 6angaren inna bayan sun sauke ta a gidan, da kyar take iya daga kafarta hakan nan dai ta shiga cikin gidan, bata samu ganin matar gidan ba, sabida da wuri take kwanciya, 6angaren da dakinta yake cen ta tafi duk jikinta yayi mata nauyi, haka dai ta kokarta, ta cire mayafin dake jikinta, ta shiga bandaki ta dauro Alwala dan ramuwar sallolin da batayi ba, sai dai cikin wannan daren ko kadan ta kasa runtsawa, sabida abinda yake damun zuciyarta, tunani kalakala shine yake bujero mata cikin ranta, sai kuma yawan tunanin kalaman khalil dayake mata kuwa a cikin kunnuwanta. *washe gari* Tun da sanyin safiya, rashida ta tashi ta gyara dakinta da yayi kura, ta shareshi fes ta gyarashi, bayan ta gama, ta shiga gyaran ko ina na cikin gidan, kafin karfe tara na safe ta gama duk wani aikin gyaran gi dan, kafin ta je ta dora abin karyawa, taji karar bude gate din gidan alamar maigidan ne yayi sammakon fita yau. Addua ta yi masa ta dawowa lafiya tare da yi masa fatan Alkhairi. khalil kuwa yana fita bai tsaya ko ina ba sai a kofar gidan su, bayan sun gaisa da maigadin gidan, yasa kai ya shiga cikin gidan, 6angaren mama ya fara zuwa ya gaisheta, sannan yaje ya gaida Auntynsa, yau gidan shiru babu kowa duk yaran gidan sun tafi makaranta, bayan y fito daga gun Aunty Salma, kai tsaye 6angaren mahaifinsa Alhaji bukar ya dosa, yaji dadin samun sa a gida, dan sabida yana son ganin Alhaji kuma dama sabida shi yayi sammakon man. cikin girmamawa ya durkusa har kasa ya gaida mahaifin nasa, bayan sun gama gaisawa, miko masa, kofi yayi, " ungo ibrahim kar6i ka zuba shayi kasha, babu musu yasanya hannu ya kar6i kofin da mahaifinsa ya miko masa, a kofin da Alhaji ya sha shayin shima a ciki ya zuba ya sha, bayan ya gama sha, ya samu nutsuwa a tare da shi ,ya gyara zamansa sosai ya dubi mahaifin nasa, cikin nutsuwa ya fara yiwa Alhajin nasa bayanin abin da yake tafe da shi. "Abba dama nazo maka da wata muhimmiyar magana ne, wadda nakesan ka bani goyan baya a cikin abin da zan zo maka da shi, sannan kuma ina san ka fahimci dukkan damuwa ta, Abbana Aure nakesan karawa " da sauri Abba ya dago da kansa ya kai dubansa ga khalil abin da yagani cikin kwayar idan khalil shine ya tabbatar masa da cewa abin da yake sanar da shi babu wasa cikin maganar. "Abba inada matsala tsakanina da matata, wannan dalilin ne yasa nake san kara auren dadan samawa kaina mafitaAbba dan kada in fada cikin sa6on ubangijina, dan haka nasan kaine wanda zaka fahimce ne a mtsayinka na namiji ,wanda ya san irin matsalolin zamanin nan, dan girman Allah Abba ka amince min da wannan maganar da nazo maka da ita dan fiddani halin da nake ciki " Wani hawaye ne mai dumi ta ya fara sauka akan kuncinsa. Abba ne da kansa ya, taso daga kan kujerar da yake zaune dafa kafadar khalil yayi, ya da dago da shi daga durkusan da yayi, "ibrahim share hawayenka indai nine mahaifinka toh na amince maka kaje ka nemo Auren da kake san karawa ni kuma zan tsaya maka Cikin al amuran auren ka " har kasa khalil ya dur kusa yana yiwa Abba godiya........ Bari in barku nan. *mrs Bilu ce*✍🏼