An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels Bismillahir Rahmaanir Raheem.              *DUKAN RUWA...* FARKO. Ta yi zugum kanta jingine jikin kujera tana kallon halittun manyan  duwatsun da suke ratsawa a wannan dajin, tafiya suke yi tamkar ba za su kai ba. Wani lokacin idan sun gifta bukkokin jama'ar wani yankin, takan yi murmushi cike da al'ajabin ta yadda mutum ƊAN ADAM ke iya rayuwa a wannan wuri. Tun tana kallon har dai ta zame ta gyara zama gami da lumshe idanu, bacci ke ƙoƙarin ɗaukarta tana yakicewa. Babu abin da ta tsana sama da bacci a hanya, hanyar ma da ko a mafarki ba ta taɓa ganin za ta bi ba,  zuwa Nijeriya daga Nijar. Ajiyar zuciya ta saki tamkar wacce ta ci gudu, lokaci guda nannauyen tunanin da take ƙoƙarin kaucewa na ƙara yi mata saukar aradu a kwakwalwa. Idanunta ta sauke akan matar dake kusa da ita, baccinta take haiƙan har carbin da ke riƙe a hannunta tana ja, ya faɗi. Sai dai duk da baccin da ta lula, hakan bai sa ta saki yaronta ba, yana rungume a kirjinta ɗam! Kai ka ce wani ne zai ƙwace mata shi. Juya kai tayi ta koma kallon hanya da murmushi ɗauke saman fuskarta. Soyayya da shaƙuwar dake tsakanin ɗa da uwa na daban ne, a kowane yanayi, a kowace rana burin kowace uwa ganin gudan jininta cikin walwala da annashuwa, ba ta fatan wani mugun abu ya same shi. Shakka babu duk wanda ya rayu da uwa ya more.   Sai kuma kewa ya lulluɓe ta dalilin Dada da ta tuno, watanni biyar kenan da rasuwarta amma jin sa take a rai tamkar jiya-jiya. Kullum mutuwar kakarta kamar sabo ne fil a wurinta, mace mai hakuri da dattako, ta yi namijin kokari wurin ba ta kulawa daidai gwargwado da kuma tarbiyyar islama. Ba ta shaƙu da kowa ba sama da ita sai ko Kawunta ɗan uwan Mamanta, Kawu Umaru. Shi ma ba ta jin za ta manta da irin namijin ƙoƙarin da ya yi a kanta, koda dai dama barewa ba ta yi gudu ba ɗanta ya yi rarrafe, wannan kyawawan ɗabi'un Dada ne suka kwaso. A wannan irin namijin ƙoƙarin ne a yau Kawunta ya tashi haiƙan suka bi wannan doguwar hanyar kawai don ya sada ta da mahaifinta, mutumin da tun da ta buɗi ido ba ta taɓa ganinsa ba. Hatta a waya ba su taɓa koda gaisawa ba.  Duka wannan bai sa ta riƙe mahaifinta a zuciya ba domin kuwa ya samu kyakkyawar shaida a gurin Dada da Kawu. Ko sau ɗaya ba su taɓa kawomata kushensa ba, asalima sun ce yana sonta sosai, kuma acewarsu ya sha zuwa ganinta tana ƙarama, su ɗin ne suka ƙi amincewa ya tafi da ita bisa dalilan da su kaɗai suka bar wa kansu sani. A yau kuma da aka wayi gari babu Dada, Kawunta ya ɗauki ɗamarar cika wasiyyar da Dada ta bari na cewar ya sada ta da Mahaifinta idan har rai ya yi halinsa.   Ɗan girgizar da motar ta yi sakamakon taka wani ɗan tudu ne ya sa ts ji saukar ruwa a saman leɓɓanta, sai lokacin ta gane kuka take. Kukan kewa da damuwa ne, Dada ta tafi, tafiya ta har abada, ta tafi wajen da ba za ta sake ganinta ba sai ko idan nata ajalin ya iso, ta je ta tarar da ita.   _"Kar ki taɓa bakin ciki da zuwa wurin Mahaifinki Shatu, mutum ne nagari mai sanyin hali, za ki yi farin ciki da ganinsa. Yana sonki sosai Shatu."_ Kalaman Dada suka faɗomata a rai, ta sauke ajiyar zuciya na samun nutsuwa, lokaci guda ta ciza leɓɓanta na ƙasa tana ƙara murmusawa karo na barkatai. Ya mahaifinta yake? Da wane ido za ta ɗaga ta kalle shi ya kalle ta? Dagaske tana kama da shi ko kuwa dai Kawu ya faɗi ne don ta ji dadi? To an ce yana da wasu yaran, su ma tana kama da su ko aa? Duka waɗannan tambayoyi ne da ta hargitsa lissafin kwakwalwarta da su alhalin babu mai ba ta amsa. Haka dai ta yi ta saƙe-saƙenta har suka fita gaba ɗaya daga Nijar suka nufi bodar Nijeriya. Nan ɗin ma bayan kammala cike-cike da duba kayyakinsu, suka gangara cikin Nijeriya, ta baza ido tana kallon yanda cikin iko da hukuncin Allah, shuke-shukensu ya sha bamban da na ƙasar da ta fito. *** "KATSINA" Ta karanta sunan a hankali, sannan ta dinga bin garin da kallo tana ƙarewa bambance-bambancen garin da nasu. Tunaninta ya katse sa'ilin da direba ya  tsaya a gefen hanya domin ba su damar gabatar da sallar la'asar. Mazan duk suka riga su sauka, su ma suka sauko. Kawu ya dube ta. "Ki bi su ku yi sallah kar ki je ko'ina kin ji ko?" Ta gyada kai ta amsa da toh, tana rungume da ƴar ƙaramar jakarta ta hannu haka ta dinga bin matan su uku har zuwa wani ɗan wuri da aka katange, suka samu gefe guda da ba mutane, masu jin fitsari suka yi sannan suka ɗaura alwala. Bayan sun idar suka dawo motar, nan kuma kowa ya hau zuge jaka ya na siyan abin motsa baki. Tana nan zaune cikin motar Kawu ya kawo mata ruwa da lemu sai nama a leda, kaɗan ta ci bayan ta yiwa ƴan motar bismillah, sauran ta naɗe ya ajiye a gefe, lemun dai ta sha sosai. Daga nan suka ƙara miƙa hanya har dai cikin hukuncin Allah suka ƙaraso cikin garin KANO. Ta nanata sunan a kan harshenta jin wata Mata ta ambata, ta maimaita har sau uku, lallai idan ba ta mance ba shi ne sunan da Dada ke yawan ambata idan ta tambaye ta sunan garin Mahaifinta.  Nan da nan zuciyarta ta yi fari ƙal, ta kasa rufe bakinta, wannan karon murmushi take tun daga ƙasan zuciyarta har saman leɓɓanta don har siririn wushiryarta na bayyana. Sai da suka ƙarasa tasha suka sauka, daga nan ne kuma Kawunta ya ɗauki akwatin kayanta suka fito bakin titi. Suna hawa taji ya ce unguwar Gadon Ƙaya, daga nan direban ya hau tafiya ita kuwa tana ta kallon hanya har suka sauka. Sun yi ƴar tafiya a ƙafa sannan ta ga ya tsaya daidai bakin wani ɗan shago ya yiwa mai shagon sallama. Koda suka gaisa ya ce. "Don Allah gidan Alhaji Isuhu Maiagogo nake tambaya." Mai shagon ya gyada kai ya ɗan fito sarari ya hau yi musu kwatance da hannu. Ya yi godiya suka nufi inda ya ce. Koda suka karasa wajen wani ƙaton gini ta ga ya tsaya cak a gaban ginin, ta bi ginin da kallo ta ji gabanta ya yanke ya faɗi lokaci guda, ba kuma don tasan dalili ba. Ta kasa kwakkwaran motsi har Kawunta ya taka zuwa ga kofar gidan yana tambayar wani dattijo ko nan ne gidan, amma ita kam ba ta dauke kai daga kallon ginin ba, gwuiwoyinta suka yi wani irin saki, ganin yanayin da ta shiga har zufa na tsastsafomata a goshi yasa ta dinga maimaita kalmar innalillahi. "Shatu ke!" Kiran da Kawu ya kwalamata ne ya maido ta hayyacinta, a hankali ta soma takawa har ta ƙarasa gefensa, ba ta kuma san dalili ba ya ji ta sa hannu ta riƙo nashi yatsun gam! Hakan da tayi ya sanya shi dubanta, itama shi din take kallo, ya yi dariya. "Tsoro gidan ya ba ki ne? To ki shirya yaƙar tsoron nan don nan ne gidan zamanki daga yau in sha Allahu." Dattijon ya taya shi darawa kaɗan duk da bai fahimci komai ba. Amma ta lura da yadda yake ta kallonta har ya kasa hakuri ya tanka. "Amma dai wannan ƴar uwar Alhaji ce ko?" Kawuna ya yi dariya ya amsa da eh kawai. Ita dai ba ta ce musu uffan ba sai sadda kai ƙasa da ta yi, ta na ji Dattijon nan na kara zuzuta kamanninta da Alhajin wanda shi ya sanya shi tankawa.  Suna nan dai  tsaye sai ga wani ɗan matashin yaro ya fito, ashe wai Dattijon ne ya aika shi gidan don a shaida wa Maigidan zuwansu. "Ya ce maza ku shigo ciki. Muje na raka ku." Daga haka  suka shiga ciki. Madadin faɗuwar gabanta ya ragu, sai ma ƙara hauhawa da ya yi, ta ci gaba da maimaita innalillahi har ƙarshe, sai ta ji gaba daya ta bar rawar ƙafar son haɗuwa da Babanta Isuhu.    Koda suka ƙarasa cikin ƙaton falo, wani irin sanyi da ƙamshi mai dadi ne ya daki hancinta. Ta gefen ido take bin wurin da kallo tana so tayi ido huɗu da Babanta, sai dai kuma duk irin girma da daular da ke shimfiɗe a falon wanda ya ƙara ƙawatashi, babu rai ko ɗaya mai numfashi face su ukun da suka shiga. Wuri ya nuna masu saman kujera suka zauna, ita kuwa ƙasa ta zauna gefen Kawu don ba'a ba ta tarbiyyar zama saman kujera alhalin manya na zaune ba. Matashin ya kara juyowa fuskarsa a sake.   "Ku jira Yallaɓai nasan ba zai jima ba zai fito." Kawu ya amsa daga nan ya fice ya bar su a nan. Sun samu mintoci goma da sakanni, don gaba daya hankalinta yana kan ƙaton agogon da ta zauna saitinsa, kafin ta ƙarasa ƙirgenta suka tsinkayi sallama. Lokaci guda suka kai duba ga gefen da muryar ta ɓullo, baki da ido ta saki tana kallon mutumin yayinda shi kuma idanunsa ke kan Kawu, kallon mamaki da tsantsar farin ciki yake binsa da shi. A gefenta kuwa halittar fuskarsa take ƙarewa kallo. Eh, tabbas suna kama, fuskarsa doguwa kuma siririya irin nata, yana da dogon hanci masha Allah, sai kuwa bakinsa daidai. Idanunsa manya kamar naya hatta da cikar halittar girarsa da gashin kai, duk kuwa da cewa shi nasa gashin ya yi fari fat na manyanta amma kamanninsu da shi sun fito fes har tsawon. Ba ta ƙara gani ba sai da ya saki dariyar farin ciki, anan kuma baki hangame ta ce. "Kai!" Ta furta a fili ba tare da ta shirya ba. Gaba daya suka juyo su na dubanta. Ta kama bakinta da sauri gami da ƙara sunkuyar da kai, mutumin ya matso ya durƙusa a gabanta, zuciyarsa ta yi wani irin nauyi, abubuwa da dama suka shuɗe a tsawon shekarun baya suka dawo mishi sabo fil. Ita kuwa kunya ce ta kama ta, bata ma gaida shi ba, ta gaishe shi a hankali don a zaton ta ma bai ji ba, amma ga mamakinta ya amsa. "Barka da zuwa Mamana. Ki saki jikinki nan gidanku ne, gidan Abbanki, ba ki da inda ya fi nan kinji ko?" Da ya fadi haka wai sai ta kalli Kawu, hakan da tayi ya ba su dariya. Kawu ya gyaɗamata kai. "Idan eh kike so nace ko aa, toh eh Shatu, gidan mahaifinki kenan. Abin tunƙahonki." Ta yi murmushi tana kara duban wanda ya kira kansa da Abbanta, sai nan da nan kwalla ta cikamata idanu. Wannan fargabar ta kau, so da kaunar suka dawo daga hutun da suka je, ta rungume hannunsa ta saki kuka sosai. Abubuwa da dama take tunawa, tabbas ta yi kewarsa a rayuwa. Koda ace ba ta rasa ci, sha da sutura ba daidai da kwana ɗaya a rayuwa, to ta rasa wannan kusancin na ɗa da mahaifi, shi din na dabanne. Ko ma dai tace ta rasa soyayyar iyaye gaba ɗaya. "Kiyi hakuri Mamana, ba zan ƙara yin nesa da ke ba, wancan ma ƙaddara ne, amma wannan karon in sha Allahu ni da kaina zan miƙa ki ɗakin mijinki. Allah ya ji ƙan Mahaifiyarki da Hajiya Dada." Suka amsa da amin. Nan kuma ya shiga jan ta da hira kadan har ta sake, waya ya zaro a aljihu ya danna kira, sunan wata ya ambata, Ummita, ya ce ta zo yanzu. Daga haka ya  juya ga Kawu suka yi ta hira yana ba shi labarin rashin lafiyar Dada har zuwa rasuwarta. Suna nan zaune ita kam ta kasa ɗquke ido akan Abban, suka tsinkayi sallamar wata ƴar budurwa da ba ta wuce sa'arta ba. Baƙa ce, irin baƙin da hutu ya ratsa, riga da wando ne a jikinta sai dai ba su ɗame ta ba, ta saka hijabi iyaka kafaɗarta. Ta gaida Kawu sannan ta maida hankali ga Abba. "Yauwa Ummita, kama hannun ƴar uwarki ku je a ba ta abinci ta ci ta yi wanka. Ki kuma faɗawa Maminki ina da baƙo a shirya masa abinci kafin mu yi sallah. A kawo ruwan sha." Ummita ta amsa da toh tana kallonta fuskarta a sake ta ce.      "Lah Abba wallahi kuna kama sosai." Duk sai ta ba su dariya, Abba ya dubi Aisha Humaira kafin ya maida duba gareta.   "Itama ƴata ce, ita ce mai sunan Umma." "Abba ita ce wacce ka ce tana Nijar ko?" Wannan karon da wani irin zumuɗi ta yi tambayar. Ya amsa mata da eh. Ta kuwa karaso da sauri ba tare da nuna kyankyamin komai ba ta rungumeta tana fadin. "Welcome Sister." Ba ta gane me ta ce ba amma itama ta rungumeta tana mai jin kaunarta har can ƙasan ruhinta.   Ummita kenan, tana daga cikin mutane masu girma da matsayi sosai a rayuwar Humaira, har abada Humaira ba za ta cire ta a tarihin rayuwarta ba, ta karɓe ta a yadda take, ƴar kauyen Maine. Ƙamshi take a yayinda ita kuwa ba ta ma sani ba, ƙarnin kifin da ta ci a mota take yi ko kuma naman da ta ci ne. Kai ko ma mene ne, ta sani Ummita ba ta irin wannan ƙarnin, ƙamshi ne a jikinta, amma ba ta duba komai ba ta rungumeta. Ta tabbata tana daga cikin masoyanta na haƙiƙa. Ta kama hannunta ɗayan hannun kuma ta ɗauki akwatin kayanta wanda duk ya ci gidansu, akwati ne irin na da da aka yi yayinsa, Dada ta ce nata akwatin tun na auren Mamanta ne.   Suka nufi wata ƴar siririyar hanya suka fito wurin wani ƙaramin hanya nan ma gefensa duk shuke shuke. Wurin ya burge Aisha Humaira sosai, a daidai ƙofar shiga wajen ma, shukoki ne sun kewaye jikin ƙofar da bango sun ba da zane mai kyau. Ummita ta ci gaba da tafiya har suka nufi wani ɓangaren, baranda ne sai kuwa wata ƙofa, suka shiga Ummita ta shiga kwala ihun kira. "Mami! Mami!! Fito ki gani!" Ihun da take tana kira ya sa sauran mutanen dakin suka fito. Maza da mata wadanda sun ɗan girme ta sai ko yara. "Wai Ummita me ke damunki haka? Tun ɗazu bakinki ya ƙi..." Aisha Humaira ta lura haɗa idanun da suka yi ne ya sa sauran kalaman bakin matar suka maƙale. Kallonta take kamar a razane, ita kuwa kallonta take tana so ta ga ta inda suka yi kama da Ummita don ko kaɗan ba su yi kama ba. Ummita baƙa ce, wannan kuwa ta tsaye a gabanta da alama ma buzuwa ce. Gashinta a tufke a baya, ta kai duba ga wasu a cikin yaran, su ma farare ne ƙal, kyawawa da su. "Wace ce wannan?" Ɗaya daga cikin ƴanmatan ta tambaya tana bin Aisha Humaira da kallon tara saura. Ummita ta yi dariya ta jawota ta rungumo kafaɗarta. "Mami, mai sunan Umma ce ta zo daga Nijar, Aisha Humaira. Abba ya ce shikenan ta dawo nan da zama cikinmu." Wacce aka kira da Mami, ta tamke fuska babu ko ɗigon annuri, suka kalli juna a kar na biyu. Kallon da ya da ya sa Aisha Humaira ta ji hantar cikinta ta kaɗa, dariyar matasan ne ya sa ta maida idanu kansu.    "Wai! Ni da yagwalgwal, amma wannan ma a Nijar ɗin a can ƙauyen kike ko?" Ɗaya a cikin matasan ya furta yana dubanta, idanunta nan da nan suka cicciko da kwalla. "Kai Yassar, bana son haka. Sannu da zuwa Humaira, maza Ummita kai ta ɗakinku ta yi wanka lokacin sallah ya gabato." Da sauri na kalli matarnan, na sha mamaki ganin kamar ba ita ba, ta saki fuska sosai tana murmushi har haƙorin makkanta ana gani. Har Ummita ta faɗi saƙon Abba, Humaira ba ta iya tankawa ba hakanan ba ta iya ɗauke idanu daga kanta ba, itama jefi-jefi tana magana da Ummita tana kallonta ta kuma rasa dalili. Har Humaira ta bi bayan Ummita zuwa ɗaki ba ta daina waigenta ba, kuma itama Mami ta ƙi matsawa balle ta dauke ido a kanta.    Ita kam Humaira jikinta ya ba ta kamar akwai wani abu. ®️Rufaida Umar.    02 A hankali ta bi kowace kusurwa a ɗakin da ido, gado ne kananu har hudu kowanne a nashi wurin, a gefen kowane gado akwai sif na kaya kamar dai ɗakunan makarantun kwana, babban daki ne mai yalwa wanda har akwai gurbin da ire-iren gadon uku za su samu matsuguni. Daga can gefe jikin taga kuwa, ƙaton madubi ne a saman dirowar gaban cike da kayayyakin kyalkyali na adon fuska da mayuka. Dakin tsaf-tsaf babu ƙazanta, ɗakin ƴanmata kenan. Ummita ta ɗaga akwatin tana shirin ajiyewa saman ɗaya daga cikin gadajen nan, baki bude tana kallon Humaira da niyyar magana, aka daka mata wani uban tsawa daga baya. Muka juyo, wannan dai budurwar ce ta ɗazu mai ƙibar ciki. Ta zo da sauri ta janye akwatin ta yi wurgi da shi gefe. Idanu cike da masifa ta soma magana.   "Wallahi kar ki kara  gangancin ajiyemin jakar wannan korar yunwar a gadona, don gulma da kinibibi idan abin naki dagaske ne meyasa ba za ki ajiye a naki gadon ba. Aikin banza kawai, uwar shishshigi. Haka za ki ƙare." Tana kai wa nan ta  fice daga ɗakin tana mita,  Ummita ta kalli Humaira gami da jifanta da murmushin yaƙe. "Ki yi haƙuri." Ta gyaɗa mata kai tana maida mata martanin murmushin sai dai can ƙasan ranta, tana maimaita kalmar da ta ambata "Korar Yunwa". Ta fahimci manufarta tsaf, ta kuma gane ko wace ce ba ta samu karɓuwa a wajenta ba. Koda dai, ba ma ita kaɗai ba, ta lura da irin kallon da Mami ta watsamata. Ko ya zamantakewarta a wannan sabuwar duniyar za ya kasance? "Hey, tunanin me kike? Amm..nidai bari kawai na kiraki da Humaira, kinga babu damar ce maki Aisha kai tsaye saboda sunan Umman Abbanmu kika ci ko? Hakan ya yi?" Humaira ta gyaɗa kai karo na biyu tana mai sakin fuska, ta lura Ummita akwai kirki.  Bandaki ta nuna mata, ita kuwa ta yi  godiya, har za ta shige ta dakatar da ita. "Yauwa Humaira ga wannan zanin ki yi amfani da shi ki goge jiki." Ta sa hannu ta karɓa, zani ne a wanke a goge. Ummita har ta kama hanyar fita sai kuma ta dawo ta shiga bandakin gami da ba ta umarnin ta bi bayanta. Su na shiga ta kunna mata famfo gami da faɗin amfanin kowannensu. Ta fiddo mata sabon sabulun wanka daga cikin wata ƴar kwaba dake a gefe jikin bangon, sai kuma ta tambayeta ko ta taho da soso, Humaira ta amsa da eh. Hatta da ƙofar banɗakin sai da Ummita ta nuna mata yadda za ta ƙulle kuma ta buɗe, daga haka suka fito, nan ma sai da ta ajiye mata dardumar sallah saitin gabas sannan ta fice ita kuma ta ciro  sosonta a akwti ta koma banɗakin ta rufe. Wanka ta yi gaba ɗaya ta ɗauro alwalar Magriba, koda ta fito wannan budurwar ta ɗazu tana zaune gefen gadonta tana waya, suna haɗa ido ta bita da harara ba shiri Humaira ta kauda kai. Idanunta ya kai ga akwatin kayanta, ƙarasawa ta yi ta buɗe sai dai gaba ɗaya ba'a nutse take ba sakamakon idanun wannan budurwar a kanta suke duk kuwa da wayar da take amsawa. Turanci zallah take zubawa har wani shagwaɓa take yi tana dukan gadon, kalmar I Lobiyun da ta ce yasa Humaira ta fahimci koma dai wane ne toh masoyinta ne. Ba ta ko ƙara kallonta ba gudun ganin abin da zai sosa zuciya, ta fiddo doguwar rigarta ta yadi ta warware ta zura. A gurguje ta ciro hijabinta, ta linke kayan da na cire na ajiye daga saman akwatin. Ba ta jima da tada salla ba sauran ƴanmatan nan biyu suka shigo suka cika ɗakin da hayaniya, rabin hirar tasu da harshen turanci suke yi. Koda ta idar ba ta iya nutsuwar jan addu'a mai tsawo ba, ta yi istigfari da hailala da salati ta shafa. Zama ta cigaba da yi anan ba tare da ta miƙe ba gudun ma kar ta yi wani abin ya jazamata baƙar magana. Hankalinta yana ga Abbanta wanda take da tambayoyi birjik da za ta yi mishi a kwakwalwarta. Eh yana sonta yana ƙaunarta, amma meyasa bai ƙara waiwayarta ba, meyasa ba ta taɓa ganinsa ba? Meyasa kuma koda a waya bai kira domin su gaisa ba? Dukkan wannan rashin kulawar nasa da ba ta samu ba, ace yana kaunarta ya kuma damu da itq? Ita kam tana son sanin amsar da zai fito daga bakinsa. "Ke Indo." Ta ɗaga kai ta dube su kawa, suka kwashe da dariya. "Kai Raihana ba ki da kirki wallahi, au ba ma za ki kirata Humairar ba sai Indo ko?" Wacce aka kira da Raihana ta yamutse fuska. "Aa, ina ce sunan Umma gareta, tunda kaka ce ai ko Indon ma da na ce ta gode min. Ku ni ba wannan ba, wallahi mu tashi mu yi magana fa tun kan a ƙaƙaba mana ita a ɗakinnan. Ni wallahi  tsoro ma take ban. Mu faɗawa Granny ta yiwa Abba magana don Mami ba za ta goyi bayanmu ba." Humaira ta kalle ta dakyau, doguwa ce kamar dai Abba, don ta fi Maminsu tsawo, Mamin ba ta da tsawo sai jiki kuma  gajeriya ce. Fara ce tas itama kalar buzayen, gashinta da ya sha kalba ya sauka har gadon bayanta, riga doguwa ce ƴar kanti ta sa mai kama jiki. "Kallon me kike yimin kamar wata mayya? Kar ki ji ance wai wani ke ƴar Abbanmu ce ki yi ƙoƙarin haɗa kanmu da ke, wallahi kar ki kuskura don bakin rijiya ba wajen wasan yaro ba ne, atoh. Gwara ma Abban ya zo a yi meeting ɗin a bambance tsakanin aya da tsakuwa." Duka wannan bayanin daga bakin Raihana su ke fitowa, Humaira ta sauke idanunta a hankali zuciyarta na zafi, dagasken dai ba ta samu karɓuwar kenan ba, zuciyarta na da ƙarfin jure abu idan har wanda ya fi ta a shekaru ne ya aikata gareta, amma ba ta jin za ta iya ɗaukar wannan rainin wayon. "Futuha mene ne haka wai? Meyasa kullum burinku ku tozarta mutum?" Maganar Ummita ya sanya Humaira ɗago kai, ashe wai akwatinta wacce aka kira Futuha ta nufa ta buɗe. Ita dai wacce ke faman  waya tun ɗazun. Ai kuwa kamar an mintsile ta haka ta miƙe tsaye a zafafe, ta ƙarasa daidai sadda Futuha ta ɗaga akwatin da niyyar doka shi da ƙas, da wani irin zafin nama ta ture ta, daga ita har akwatin suka faɗi, akwatin ya faɗa saman  gado, ita kuwa ta yi rashe-rashe a ƙasan gadon bayan ƙugunta ya bugi katakon. Ai kuwa  ta kurma ihu, Raihana da ɗaya budurwar da  Ummita ta ambata da Tasleem suka yo kai Humaira gadan-gadan, Ummita ta tare su. Ita kuwa Humaira  ko a jikinta ta nufi akwatin ta shiga harhaɗa kayan da suka zube tana maidawa lokaci ɗaya hawayen da ta fi zaton na ɓacin rai ne, su na kwaranya. Ya yi daidai da faɗowar Maminsu ɗakin wanda hakan  bai wuce sanadiyyar ihun Futuha da ya mamaye ilahirin ɗakin ba. Jin muryarta da ta yi sai da gabanta ya faɗi, ta rasa dalilin da yasa take jin haka a kanta. Ta shiga ambaton sunan Allah a ƙasan ranta.   "Lafiya? Me nake gani haka kamar waɗanda aka ƙwato daga bakin kura? Ke Ummita sake ta, kyale su na ga gudun ruwansu. Au, don ku nuna mata rashin tarbiyyarku ba komai ba ne ba ko? Har kun soma yada halin?" Tana maganar ne fuskarta a murtuke tana bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya, ita dai Humaira sam ba ta tofa ba sai ci gaba da tsince kayanta da tayi tana harhaɗawa tana mayarwa ciki. Ba ta san ma'anar juya harshe zuwa wani can daban da ba ta sani ba, ta dai ji Mamin a cikin yare ta yi musu magana wanda ba ta fahimci koda harafi guda a ciki ba, sai gani kawai ta yi duka sun fice daga ɗakin idan ka cire Ummita da ta durkusa tana taya ta haɗi da ƙara ba ta haƙuri. Tana niyyar amsawa Ummita ta ji  an shafa kanta, ta runtse idanu ba tare da ta  ɗago kai ba don tasan Mami ce. "Ki yi hakuri kin ji Humaira, su Tasleem su na da irin wannan halayyar na son yiwa baƙo shaƙiyanci. Kinga yau ki ka zo kuma kafin su karɓe ki za'a ɗan kwana biyu, a hankali idan sun gane ke ɗin ɗaya ce a cikinsu komai zai wuce kin ji ko? Ki ɗauke ni madadin Uwa, don mahaifiyarki mun yi zaman mutunci da nutunta juna da ita. Kema kuma nasan muddin dai kyawawan ɗabi'unta kika kwaso, ba za mu samu kowace iriyar matsala ba. Ina fatan haka?" Jin bayanan Mamin sai ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, ta ji lokaci guda kaso saba'in na fargabarta akan Mami ya ragu, wannan furuci nata na madadin Uwa, ba ta jin za ta iya kwatanta daɗin da ya sanya ta. Kai ta gyaɗa alamar toh,  Mamin ta maida dubanta ga Ummita. "Sai ku hanzarta ku fito ta ci abinci daga nan zuwa bayan sallar isha'i, Abbanku na neman mu duka." "Toh Mami." Faɗin Ummita cike da girmamawa. Daga haka ta fice ta bar mu. Ummita ta kalli Humaira da murmushi saman fuskarta. "Sai fa kin yi hakuri sosai Humaira, da gaskiyar Mami, dama ya lafiyar giwa balle an jefe ta da kashi. Su Tasleem ba su da kirki, har gwara su Yassar a kansu, don su ba su kunyar ido, za su yi maka abin da suka so. Ki yi hakuri don Allah. Nima haka nake fama da su, don ma dai babu yadda suka iya da ni ne, Mamin na taka musu burki sosai a kaina." Jin haka ta ji ta sosamata inda yake mata ƙaiƙaiyi. Aikuwa ta kasa shiru sai da ta furzar. "Yauwa nikam Ummita, amma ba Mami ce ta haifeki ba ko?" Ummita ta yi dariya. "Kin gan ni ƴar baƙa ko?" Sai kuma ta gyaɗa kai ta ɗan sauya fuska alamar damuwa. "Ba Mami ce ta haife ni ba kuma ba Abba ne mahaifina ba. Mahaifina ƙanin Abba ne, mahaifiyata kuwa ƴar asalin garin Bichi ce, gaba ɗaya sun rasu ne a sanadiyyar gobara. Ni kaɗai ce rai da aka fitar a gidanmu ko kwarzane tun ina da shekaru biyar a duniya, amma daga su har ƙannena jarirai ƴan biyu duka sun rasu. Tun daga wannan lokacin ne, na soma rayuwa a hannun Kakarmu sai daga baya ne Abba ya maido ni gidansa ya damƙa amanata ga Mami. Matar da ta riƙe ni har zuwa yau ba tare da ta nuna bambanci tsakanina da nata yaran ba, kusan ince a zamanin dai samun irin Mami abu ne mai wahala. Ga kirki da son mutane, ke ba don dai kar nayi hauka ba zan iya ce maki Mami ta fi nunamin ƙauna da so fiye da nata yaran domin hatta da ragamar kula da ɗakinta da na Anna ni ta damƙawa. Ke daidai da shawara wani lokacin da ni take yi. Sai ta ture shawarar nata yaran ta ɗauki nawa." Jinjina kai Humaira ta yi, eh lallai kam Mami ta yi abin a yaba mata, a zamanin nan kafin a samu mai fifita ɗan wani akan nashi abu ne mai matuƙar wahala. "Wace ce Anna?" Humaira ta watsa mata tambayar.  Ta miƙe ta shiga rufe akwatin a lokaci guda tana ba ta amsa.      "Anna kakar su Tasleem, wacce ta haifi Mami. Ai anan gidan take rayuwa, a baya ma har da ƙanwar Mami da ba ta yi aure ba muka zauna. Amma yanzu Allah ya taimaka tayi aure tana zaune a can Misra da mijinta, ke kam ai Allah ya taimake ki ba za ki rayu inuwa ɗaya da ita ba. Don ta fi su Tasleem zafi da tsangwama, ke ta dai tsani duk wanda ba jininsu ba. Hatta da dangin Abba ba ta kaunar gani a gidannan, sai kuma Allah ya sa su ɗin ma ba su fiye zuwa ba." Humaira ta buɗe baki za ta yi magana kenan sai ga wani ƙaramin yaro cikin yara ƙananu uku da ta gani ɗazun ya shigo a guje. Masha Allah yaron kyakkyawa duk kuwa da cewar bai ɗau hasken Mamin sosai ba, ya fi yin kalar Abba, amma kuma hakan ma sai ya ƙara mishi wani kyan na daban. "Adda Ummi ku zo inji Mami." Ya kai ƙarshe yana nuna su duka biyum da yatsa, alamun dai mu biyun ake nema. Sai ma ya ba Humaira dariya. Suka miƙe a tare zuwa falon. Ko ɗaya ba abokan faɗan nata a ciki, bada ɗayansu ba sa nan sai Mami da yaran, sai kuwa ɗaya a cikin matasan nan na ɗazu kwance saman doguwar kujera ya toshe kunnuwa da earpiece. Suka ƙarasa ga Mamin, ta zauna a gefe a ƙasa. Duk yadda Mamin ta so ta hau kujerar ta ƙi, haka dole ta rabu da ita. Ummita ta kawomata abincin amma gaba ɗaya ta kasa sakewa balle ta ci, ƙarshe dole dai ɗakin suka yi da abincin bisa umarnin Mami. Nan din ma dai kaɗan ta ci ta ce ta ƙoshi. Hankalinta kuma ya koma ga Kawu da Abba, ba ta gaji da ganin Abba ba, ba ta kuma gaji da jin muryarsa ba. So take ta samu damar da za su yi doguwar hira da shi, tasan dai ba yau ba domin dare ya yi. Suna nan da Ummita tana ƙara ba ta labari akan zuri'arsu har lokacin sallar isha'i ya yi, koda suka idar kai tsaye falon Abba suka nufa sakamakon kiran da ya yi musu. Nan suka tarar shima Kawu har ya ci abinci ya yi wanka, hirarsu kawai suke yi da Abba wanda shima ya sha doguwar jallabiya ruwan madara. Har Humaira ta zauna kallonta yake da murmushi saman fuskarsa kafin ya maida duba ga Kawu ya girgiza kai. "Allahu Mai Halitta." Kawun shima murmusawar ya yi, ita kam sai ta yi kasa da kai. Zamansu ba jimawa sai ga Mami ta shigo ta lulluɓe jikinta da ƙaton mayafi. Sai da ta zauna ne ta dubi Kawu. "Umar, kwana da  yawa. Idan babu Fatima  a gidan shikenan kuma sai zumunci ya yanke? Dama kun raba ni da ɗiyata, toh dama ƙarshen alewa ƙasa, ka ga yau dai ungulu ta komo gidanta na tsamiya." Kawu ya yi ƴar dariya. "Hajiya Maryam kenan, idan dai kin yarda kin amince da komai lokaci ne, ba za ki ga laifinmu ba. Sai dai kamar yadda kika ce, na yi kuskure kuma na ji kunya da ban tashi zuwa ba sai bayan babu Adda Fatima, Allah ya gafartamusu. Ina kuma neman afuwa." Gaba daya suka amsa da amin.  Abba ya yi gyaran murya ya dubi Mami. "Ina yaran nan suka shiga ne wai?" "Su na can wurin Anna, na rasa me suke yi alhalin na sanar da su. Bar..." Ba ta ƙarasa ba sai ga su sun faɗo ɗakin kamar daga sama, babu ɗaya cikinsu da ya yi tunanin yin sallama. Yaron ɗazu ne da ya je kiranmu ya shigo a guje ya rungume kafaɗun Abba, wani da ya fi shi tasawa yana biye da shi a gujen. Sai kuwa su Tasleem da samarin nan uku. "Kai Muhsin, me ya yi maka ne?" Wanda aka kira Muhsin ya turo baki ya nunawa Abba bindigar ruwa da aka raba gida biyu. "Ba shi ne ya karyamin bindiga ba. Allah kuwa sai ya biya ni." Abba ya ja hannun karamin mai suna Waleed ya maido shi gabansa. "Haba Autan Mami, ya haka? Ba shi hakuri toh." Da dariya irin na yarinta ya furta kalmar sorry. Abba ya maida idanunsa ga su Tasleem waɗanda suka yi ɗare-ɗare saman kujera ba su ko gaisar da Kawu ba. Fuska ya ɗan ɗaure. "Ba ku iya gaisuwa ba ne?" Jin furucin Abban ya sa suja gaida Kawu ciki-ciki, ba tare da jin komai ba  ya amsa har da nema musu albarkar Allah. Babu wanda ya amsa da amin a cikinsu. Mami ta kalle su ta yi musu alamar su sauko ƙasa su zauna, ba a son ransu ba dole suka zaune a ƙasan kafet kamar dai yadda Humaira da Ummita suka yi. Sai dai Abba ya buɗe taron nasu da addu'a sannan ya gabatar da Humaira a wajensa. Ya kuma gargaɗe su da kar su kuskura ya ji wani zance na daban koda nuna bambanci ne. A karshe ya sa kowannensu ya gabatarwa da Humaira sunansa. Su tara ne cif, Mubarak ne babban ɗan Abban, shi kuwa yana ƙasar Ghana yana karatu, sai Dawud, Yassar, Ƙasim, Futuha, Tasleem, Raihana, Muhsin da autansu Usman da ya ci sunan baban Mami suke kiransa Waleed. "Humaira toh, yanzu dai ba wanda ba ki sani a ƴan uwanki ba ko? Sai babban yayanku shi kam sai ranar da ya samu hutu idan ya dawo sai ku gaisa. Ko kuma ma ina iya haɗa ku a waya wataran." Jin abinda ya fadi ya sa ta murmushi, ta gyaɗa kai tare da furta toh. Daga haka Abba ya sallame su baki ɗaya suka tashi. A wannan daren dai ba ta samu damar hira da Abbanta ba, ta koma ɗakin da ba ta kauna dalilin yadda suka kaya da masu ɗakin. Mami ta sa aka yi mata shimfiɗar katifa a ƙasa kafin nata gadon da sif ya iso, acewarta. Hakanan ta kwanta, mutanen ba su ƙara tanka mata ba musamman ma Futuha da ta sha ƙasa har lokacin ƙugunta na ciwo. Sun dai sha jinin jikinsu, sun kuma fahimci Humairar ba kanwar lasa ce ba itama. *** Washegari tun da asuba ta ga ƴanmatan ba su koma bacci ba, ita daman baccin safe ba ya daga cikin ɗabi'unta, a can ƙauyensu daga sun tashi to sannan za'a hau ɗora ruwan wanka da kuma abin kari, wannan dalilin yasa ta kwanta kawai tana kalle-kalle da saƙe-saƙen zuci. Tana kallo suka yi wanka har Ummita, kowannensu ya hau shiri. Ummita da Raihana cikin shigar uniform na makaranta, ita kuwa Tasleem shigar fararen kaya ta yi na ma'aikatan asibiti riga da wando da ɗan ƙaramin hijab. Sun mata kyau kwarai, gogar kuwa, wato Futuha, kayan gida ne jikinta, riga doguwa ta atamfa da ya ɗame ta ɗam ya fiddo da surarta. "Wai ke Futuha ni ban gane ba, ina mamakin yadda kike rawar ƙafa da jiki duk sadda aka ce kuna da English, ko uban me yasa oho." Faɗin Tasleem kenan sa'ilin da take ɗora agogo a tsintsiyar hannunta. Kafin Futuha ta yi magana, Raihana dake fesa turare a jikin uniform dinta wanda iri ɗaya ne da na Ummita, kalar fari da ruwan makuna dinkin riga da wando sai ɗan hijab da ya rufe kirji kaɗan, dariya ta yi ta amsa wa Tasleem. "Wai ke ba ki da labarin IBB Gusau? Tab, ai kusan kaf matan department dinsu sonsa suke ban ciremaki matan aure ba, toh itama har da ita a ciki, ba ki ganin kwalliyar ta daban ce." Futuha ta jefowa Raihana murfin man shafawa, Raihana ta kauce tana dariya. "Af, akwai ƙarya cikin maganata ne? Ke fa naji kuna hirar da wannan ƙawartaki me wuya kamar mariƙin lema, ni me ma sunanta? Yauwa Khalisat, kina wani koɗa shi kina cewa nan duniya shi kike so." A fusace Futuha ta nufo ta, Raihana ta sunkuci jakar makarantarta da waya a gefen gado ta fice daga dakin da sauri tana dariya. Itama Tasleem dariyar ta yi. Ummita kam dama ta fice daga dakin tun da ta zura uniform, dakin su Muhsin ta wuce don yi musu shirin makaranta. Humaira lumshe idanunta ta yi tana ji suna faman hira tsakanin Tasleem da Futuha inda Futuha ke kara jaddada dagasken dai tana son Ibb Gusau. "Ke malamin fa ƙarshe ne wallahi, ya haɗu ba zan nuna masa komai ba. Nidai fatana Allah yasa ya karɓi tayina ya aure ni. Wallahi zan jure dukkan wulakanci muddin zai yarda ya so ni. Yau in sha Allahu sai na nemo lambar wayarsa." "Lallai, kina ruwa kusa da breaker." Cewar Tasleem. Fuska dauke da damuwa Futuha ta amsa. "Ai na yi nisa ma cikin ruwan Tasleem, ki dai yi fatan kar Allah ya jarabceki irin yadda ya jarabtan." Tasleem cike da mamaki ta ce. "To tsaya, don iskanci kwanakin nan da wa kike waya kike kashe murya kina furta kalaman so?" Yamutsa fuska Futuha ta yi. "Mujahid ne, wallahi akan dole nake kula shi, shi ke fa taya ni da attendance da ma test. Kinga kuwa dole ce ta haifar da shiga lamarinsa. Ɗan taya ni na ci jarrabawa ne." Suka sheƙe da dariya. Ba jimawa suka fice zuwa falo. Ita Tasleem nursing take karanta duk ta fi su kwakwalwa da basira, tana da kokari sosai shiyasa wasu lokutan take samun alfarma daga Abba koda zai yi hukunci ba ya tsaurara mata, yayinda ita kuwa Futuha ke karantar Mass Com, ba laifi tana da kokari sai dai matsalar tun zuwan wani matashin malaminsu makarantar ta susuce ta zama shiritacciya. Wannan yasa lokaci guda ta kwaso C.O a zango na biyu a aji na biyu a makaranta, hakan ba ƙaramin ɓata ran Abba ya yi ba. Shi mutum ne da ya tsani asarar kwandalarsa a abinda ba zai kawo mishi ribar komai ba sai asara, hakanan mutum ne mai son abin hannunsa sosai, dakyar Mami ta shawo kansa ya aminta da tura Mubarak karatu, ya kuma ce daga kansa ya rufe, sauran kowanennsu sai dai ya yi a jami'o'in Kasarnan. Dawud na ajin karshe a jami'a inda yake karantar Accounting, Yassar wanda tare suke tafiya da Dawud din adalilin maimaicin aji da Dawud ya yi a sakandire, shi kam Bussiness ya ke karanta, su biyun tare suke da Futuha a jami'ar Bayero. Sai Ƙasim dake karantar fannin Kasuwancin shima dai inda yake aji na uku a jami'ar Maitama Sule Kano. Wannan kenan. Humaira jin ɗakin ya yi shiru ta buɗe idanunta, ajiyar zuciya ta saki tana mai jinjina wannan rayuwa ta Futuha, shakka babu ta ɗorawa kanta wahala, koda dai faɗan da ba ruwanka, daɗin kallo gareshi. Mikewa ta yi ta nufi banɗakin bayan ta ɗauki zanin wankanta da brush. Sai da ta wanke jikinta tsaf kafin ta fito ta soma shiri cikin doguwar rigarta ƴar kanti ruwan madara, tana daga cikin suturun da Kawunta ke siyamata. A dai fannin sutura daidai gwargwado itama tana da su, sai dai ace ba wasu masu tsada ba ne, ba kuma masu kyawun gaske ba ne idan an haɗa da na su Tasleem da ta gansu a jikinsu a kwana ɗayan nan. Tana cikin kwashe shimfiɗarta sai ga Ummita ta shigo da sauri, ganinta ta saki fuska sosai. "Au Humaira ashe kin tashi, kinga mu ma makaranta za mu wuce. Mami tace idan kin kammala ga abin kari can an rufemaki a kicin, idan ma ba ki gani ba ki tambayi Ladidi mai aikin Mami tana falon tana gyara." Duka wannan zancen tana yi ne lokaci guda da sauri tana bincike dirowarta, littafi ta zaro ta dauki jakar makarantarta sai safarta a hannu da takalmi ta kama hanyar fita. "Toh, sai kun dawo." Faɗin Humaira, Ummita ta amsa ba tare da ta tsaya ba sakamakon hon din mota da ake faman dannawa. Ganin haka yasa Humaira ƙarasawa jikin windon wanda ake iya hango farfajiyar gidan, ganinsu tayi gaba ɗaya a motar sai Tasleem dake tsaye a waje rike da ƙugu, Ummita na karasawa ta hau ta da masifar wai tana ɓata musu lokaci. "Allah ya baku hakuri." Ta ji Ummitan ta fadi sannan ta shige motar da sauri, tsaki Tasleem ta ja ta bita da harara sannan itama ta faɗa ciki, direban ya ja suka fice. Ajiyar Zuciya Humaira ta saki ta bar jikin windon, mamaki fal a ranta na ɗabi'un ƴan matan. Ta lura ba su san wani abu wai shi kara da mutunci ba, haka dai ta ture zancensu ta hau gyaran ɗakin. Abin ban haushi a saman gadon Futuha daidai da ɗan kamfenta da ta cire anan ta bar shi a ajiye, aikuwa haka ta tsallake gadon, ba ta yi karambanin gyara musu gadajensu ba, da ace dai Ummita ba ta gyara nata ba to tabbas wannan kam za ta gyara mata, ita din mutum ce mai mutunta DAN ADAM. Fita waje ta yi, falon babu kowa hakan yasa ta nufi hanyar kicin da ta nakalceshi tun jiya da Ummita ta tattara kwanukan abinci ta nufi ciki. Anan ta iske wata mata da ba za ta girmi Mami ba tsaye tana goge gas nan ta fahimci ita ce Ladidi. Ta gaisheta a ladabce, matar ta amsa fuska a sake. "Baƙuwarmu Humaira ko? Sannunki da zuwa, ga abin karinki can." Ta fadi tana nuna mata wani tireda aka ɗora filet da kofi sai kayan shayi da flask a kai. Humaira ta murmusa. "Nagode, amma zan sharo dakin sannan na ci." "Ai da kin bar shi, idan na kammala da nan sai na share." Girgiza kai Humaira ta yi. "Babu komai kar ki damu zan yi ai ba wani girma ne da dakin ba." Ladidi ta amsa da toh gami da yi mata sannu. Tsintsiyar ta nunamata da makwashin shara, ta dauka ta nufi dakin. Sai da ta kammala tas kafin ta koma ta wanke hannu ta dauki abin karin ta koma daki don ba ta jin za ta iya ci a falon. Bayan ta kammala ne ta fito da niyyar maida kayan kicin suka yi karo da Ladidi. "Yauwa, ki je inji Alhaji wai za ku yi sallama da Kawunki zai wuce." Ladidi ta karɓi kayan hannunta ita kuwa jin haka jikinta ya yi sanyi, ta koma dakin ta dauki karamin mayafinta ta yafa a kai. Falon Abban ta nufa, Kawun ne kadai a ciki ya yi shiri tsaf na tafiya, sallamarta ya sanya shi dubanta.      03 Ta durƙusa ta gaida shi, ya amsa sannan ya ce. "Toh Shatu, ni zan koma. Ina fatan zaman nan zai maki dadi fiye da rayuwar da kika yi a Maine. Ina kuma roƙonki da ki zauna da kowa lafiya, kamar yadda suka karɓeki da hannu bibbiyu, kema ina son ki rike su haka. Gidan mahaifinki ne, nan ɗin dai shi ne gatanki, ba ki da sama da nan. Sannan don Allah ki zama mai hakuri, na sanki sarai muddin aka taɓo ki ba  kya kai zuciyarki nesa. Abu na gaba, kar ki sake ki bada kofar da za'a ga wallenmu, a ga kamar mun gaza a wurin ba ki kyakkyawan tarbiyya a iyaka zaman da kika yi hannunmu. Sannan addu'a, ki yawaita addu'a da ibada in sha Allah sun ishe ki." Humaira wacce tuni fuskarta ta yi jage-jage da ruwan hawaye ta sa hannu ta share su. Gani take yi tamkar shikenan fa za ta yi nesa da asalin garin da aka haifeta, shi kenan ganin Kawu da Tanti Hafsatu matarsa  zai yi wuya a gareta. "Nagode Kawu, in sha Allahu zan kiyaye abin da ka ce. Amma ai Abba zai dinga bari na naje maku wataran ko?" "Me zai hana na bar ki Mamana?" Jin maganarsa gaba daya suka dub shi, sam ba su san ya shigo falon ba balle kuma tsayuwar da ya yi a bakin  ƙofar da za ta sada shi da sashinsa na ainahi.  Ya karaso da murmushi saman fuskarsa ya zauna, ta gaishe shi, ya amsa. "Ban maki alƙawarin nan kusa ba, amma da yardar Allah duk sadda na tashi aurar da ke, zan kai ki har Maine ki kwana biyu. Nidai fatana yanzu shi ne  ki saki jikinki ki zauna da mu bisa kauna. Kin ji ko?" Ta gyaɗa kai tana murmushi mai dauke da kunya jin wai Abbanta ya ambaci aure. Ita duka nawa ma take yanzun a shekarunta goma sha huɗu? Koda dai, akwai sa'anninta su Murja, Fatsima da ma sauransu wadanda duka an aurar da su a can. Tashi tsaye da Kawun ya yi ne ya maido ta hayyacinta. Ta mike itama, Kawu suka yi sallama da Abba. Daidai nan Mami ta shigo da sallama, tana sanye da dogon hijabi har ƙasa, gaida Kawu ta yi sannan ta yi mishi sallama. Sai a sannan Humaira ta gaishe ta. Humaira ta takawa Kawu har wurin motar Abba inda direban Abban zai kai shi tasha. Tana hawaye haka ta tsaya har Kawun ya shiga motar, hannu ya ɗago mata itama haka har suka fice daga gidan. Ji ta yi zuciyarta ta yi wani irin tsinkewa, haka kurum ta ji wani irin tausayin kanta ya kama ta. Kanta Abba ya dafa da muryar rarrashi ya ce. "Haba Mamana, kukan fa? Ya isa haka, ba fa rabuwa ku ka yi kenan ba, in sha Allahu zumuncin ba zai yanke a nan ba matukar akwai rai da lafiya,  ki kwantar da hankalinki nan ma gidanku ne." Ta gyada kai, daga haka suka shige gidan. Mami dake tsaye a windon falon tana kallonsa, itama juyawa ta yi ta koma ɗakin Abban hawaye a saman fuskarta wanda ita kaɗai ta bar wa kanta sanin ma'anarsu. A falon Abban suka zauna yana fadin. "Bari dai nayi hira da ɗiyata kafin na fita aiki ko?" Ta yi murmushi har sannan yatsunta na saman fuska tana goge ruwan hawaye. "Ba ni labari toh, meyasa ba ki shiga makarantar boko a can ba? Kawunki dai ya cemin kina zuwa islamiyya har kin yi sauka, na kuma ji dadin hakan." Ta gyara zama ta amsa a nutse. "Dada ce ta ce ba zan je ba saboda koda na fara ba lallai na ƙarasa ba. Ta ce kuma faransanci ne." Abba ya yi shiru, ya gane sarai manufar Dada, wato dai ta san cewa ko ba jima ko ba dade ranar nan za ta zo da Humairar za ta dawo hannunsa, sai dai ya so ace ko na faransancin ne ta yi, da irin haka biyu babu. Ya tuna shawarar da Mami ta ba shi a daren jiya da suke maganar karatun Humairan. _"Zai fi dai ka sanya ta a inda za ta koyi sana'a koda kuwa na girke-girke ne, kasan can idan ma ta yi karatun faransanci ne, nan kuwa turanci ake. Zai iya ba ta wahala."_ Toh shi ɗin ma dai ya ga hakan ya fi mishi sauƙi, yanzun ma dubunnan da yake fitarwa na karatun yaran kaɗai sai godiyar Allah kawai, ina kuma da ace ya sanya Humaira wacce ya tabbatar kafin ta fara sai an yi mata lesson a gida sosai, ɗaukar karatun ne ma abin tunani, bai san ya kaifin kwakwalwarta yake ba. "Abba." Ya tsinci muryarta wanda  hakan ya katsemishi tunani. "Na'am Mamana." "Abba meyasa ba ka taɓa zuwa ka gan ni ba? Meyasa ko a waya ba ka damu da kira mu gaisa ba idan ma aiki ne ya tsare ka?" Ya tsare ta da ido, yanzun ya gama raina kaifin kwakwalwar yarinyar, sai dai ya sha mamakin tambayoyinta duk kuwa da ya sani lallai ne dama watarana ta yi mishi su. Sai dai bai tsammace su nan kusa ba. Dogon numfashi ya ja ya furzar. "Kiyi hakuri Humaira, eh na yi maki laifi amma hakan ba wai yana nufin ban damu dake ba ne. Sai dai nayi hakan bisa alƙawarin da na ɗaukarwa mahaifiyarki wanda hatta da bayan mutuwarta ban karya shi ba." Cikin sauri ta ce. "Wane alƙawari?" Ya yi shiru sai kuma ya ɗago da niyyar magana, muryar Mami ta katse hanzarinsa. "Wai nikam dai yau Abban yara ba ka da niyyar fita ko? Gashinan har goma ta gota." Suka dubeta, a ɓangaren Humaira ji ta yi gaba ɗaya zuwan Mamin bai burgeta ba, sai da aski ya zo gaban goshi tana shirin ta san ta ya ya aka haihu a ragaya lokaci guda kuma Mami ta yi mata katsalandan. Mami kuwa ganin hankalin Humaira ba ya kanta sai ta girgizawa Abban kai cike da damuwa. Abba shi din ma jinjina kan ya yi, ya fahimci manufarta. Don haka ya dubi Humaira da murmushin yaƙe. "Af, kinga na sha'afa har lokaci ya ja, kar ki damu Mamana, muna tare ai yanzu, a kowane lokaci idan na samu dama da kaina zan yi kiranki mu yi hirar nan kin ji ko? Yauwa Maminki ma ta ba da shawarar a sanyaki a makarantar koyon girke-girkenku na zamani, ina fatan za ki so hakan?" Duk da yanayin rashin jin dadin da take ciki sai da ta yi farin ciki da hakan. Dama tana da son girki, ko a can gida ita ke yiwa Dada dahuwa daga lokacin da ta soma zama budurwa. Ta kuwa saki fuskarta har wushiryarta na fitowa muraran. "Eh Abba ina so." Abba ya dubi Mami suka yi murmushi, Mamin ta karaso ta dubi Humaira. "Yauwa ƴar Abbanta, kin ga da girki adon mace ce. Kuma na tabbatar za ki iya sosai idan kika mayar da hankali. Ana samun alheri sosai da girki. Kar ki wani damu idan ba ki yi boko ba, da yawa babu bokon amma sun samu ci gaba ta fanni da dama a rayuwarsu." Humaira ta jinjina kai, tabbas haka ne don ta ga mijin Mammati wata ƴar uwarsu a Maine, shi ma babu bokon amma yanzu kaf ƙauyen nasu babu mai kuɗinsa. Idan ya zo hutu da yaransa kowa sai ya san ya zo saboda alherin da yake yi musu. "Ki je ciki nasan zaman da kaɗaici ke kadai, ki sa Ladidi ta kunna maki kallo a wayarta sai ki yi." Ta fadi hakan saboda babu wuta, ƙa'idar Abba tun sha biyun dare ake kashe masa inji, sai ko idan aka ci sa'a Kedco sun hasko wuta.  Humaira ta fice a falon bisa bin umarni.  Bayan fitarta Mami ta ƙarasa ga Abba fuska dauke da damuwa. "Ya haka? Kana son ka karyawa yarinya zuciya daga zuwanta? Ko kuwa so ka ke ta riƙi mahaifiyarta da mugun zato a ranta alhalin ba ta ji ba ba ta gani ba? Don Allah kar ka fara, kar ka yi wannan kuskuren. Tabo ne da yaro kan yiwa gurguwar fahimta." Abba ya numfasa. "Hakane, sai dai ki sani ba karamin taimakona ki ka yi ba don ba ki da masaniyar abin da zan ce a sannan. Na gama iyakar nazari ban san ƙaryar da zan shirga don rufe zancen ba. Na gode maki mace ta gari." Ya karashe yana jifanta da murmushi, ta rausaya  kyawawan idanunta tana maida mishi martani. "Nima na gode da wannan yabon, muje ka shirya lokaci na ƙurewa. Idan ka dawo ni kuma kafin nan na bincika wurin wacce ya dace a kai Humaira ta fara daukar darasi." "Hakane, amma zan fi so ta gama shiga ta san ƴan uwana. Kafin a durfafi wannan." Mami ta ɗan yi jim sai kuma ta amsa da toh. Bayan shigar su ɗakin yana cikin shiri ta sanyo zancen kaya. "Ka ga ya kamata a ɗan ɗinka mata suturu ko ba yawa, mutumin da ya zo daga ƙauye na tabbata ba wasu kayan kirki ne da ita ba." "Ke dai wato burinki kawai na karya bakin aljihu, toh wannan na jikinta ba sutura ba ce? Kin fi kowa sanin ba na son kashe-kashen kuɗi ko?" Ta yi ƴar dariya, an zo wajen. Ai idan har batu na fitar da kuɗi ne toh nan suke kai ruwa rana, a karshe dai hakanan ta ke cin nasara a kanshi, kafin ya botsare akan jima. "Haba Abban yara, Humaira fa uwa guda ce, idan ba ka yi mata ba wa za ka yiwa?" Ta ƙarashe murya a narke kamar wata matashiyar budurwa, hakan ya tuna mishi zamanin tashen soyayyarsu. Ya yi dariya gami da girgiza kai. "Maryam kenan, ke kam ba a kayar da ke a magana. Shikenan idan na dawo zamu ga yadda za'a yi. Na fita ai ko?" "Eh ka fita kam, Allah ya kara buɗi." Ta ba shi amsa tana dariyar itama. Ya amsa da amin. ***   Washegari kuwa Mami da kanta ta bada aka siyowa Humaira atamfa da leshin sai kuwa kananun kaya dogayen riguna duka dai ba masu yawa ba, hatta da takalmin shiga taro ƙafa biyu da mayafai kala uku sai da Mami ta siya mata, ba kuma ta tsaya anan ba sai da aka haɗo da kayan shafe-shafen mata da na kwalliya da kuma undies. Abba ya kalli kayan sannan ya kalli Mami. "Yanzu dukkan kayan nan a dubu talatin?" Mami ta ɗan bishi da hararar wasa. "Au, ka yi zaton kowa irinka ne? Wannan dai ya fi ƙarfin abin da ka bayar, Mami ta cika ta siyawa ɗiyarta. Wanda ka bayar ma mun gode." Ya yi ƴar dariya. "Maryam mai halin girma, ai shikenan, wannan tsakaninku kun fi kusa. Allah ya saka da alheri." Ta amsa da amin.  Sannan ta umarci Ummita dake zaune wadda ita ce ta dauko kayan zuwa sashin Abban akan ta ɗauka ta ba Humaira na shafe-shafen, suturun kuwa ta sa a leda Humairar ga shirya su kai wurin telansu. Ummita ta amsa da toh, sannan ta kwashi kayan ta fice. A falon Mami kuwa, Tasleem ce zaune a gefe daga ita sai vest sai kuwa wandon makarantarta da ba ta cire ba, zaune take tana cin ɗan wake tana ba su Raihana labarin wata ƴar ajinsu Suhaima da kusan kullum ta Allah babu ranar da ba sa taɗinta. Sosai ta tsayawa Tasleem ɗin a ƙoƙon rai, a cewarta yarinyar ta fiye rawar kai, ga nunawa sauran ɗalibai kamar ta fi uban kowa ƙoƙari. Tasleem ta cusa loma a bakinta sannan ta dube su. "Kun san yau wallahi ta ci arzikin Babandi da ya shiga tsakaninmu amma da sai na gwabje bakinta. Ƴar iskar yarinya ta dubi tsabar idona ta ce wai ina mata katsalandan a harkokinta saboda kawai tana yin tutorial din sanya kai na ce ita kanta ba ta gane ba shikenan fa ta tasomin, su kuwa ƴan korenta su Teema Small saboda na taɓa Hajiyarsu me zuwa da mota nan suka goyi bayanta." "Ke dai Tasleem ina raba ki da nuna bakin cikinki a fili ga Suhaima, kin kasa ɓoyewa har sun harbo jirginki, ke ba ki iya kwantar da kai ba? Ai irinsu da sannu za ki shige mata har ta yarda dake ki zama aminiyarta, kika san wane Don ɗin za ki samu ta hanyarta? Ko kin mance cewa ubanta fa ya fi naki arziki, koda dai namun akwai sai maƙo." Faɗin Futuha tana ƙarashewa da murya a ƙasa gudun kar ta yi shuka a idon makarwa. Suka kwashe da dariya, shiru Tasleem ta ɗan yi sai kuma ta ce. "Ke kuma fa haka ne wallahi, don ba ki ga wani arnen gaye da ya taba zuwa wajenta a makarantar ba, wallahi ƙarshen dai haɗuwa ya haɗu, ba wai kyawun fuska ba aa, motarsa ma kanta abin a kalla ce." "Ahaf, to kin gani. Ai kinga kakarki ta yanke saƙa muddin ki ka samu irinsa. Bare ma yanzu da Abba ya yi sanyi da batun auren, da ace ban da Mami ta shawo kansa ya bari ai da yanzun mun haihu. Taɓ ni nasan da yarana biyu." Suka yi dariya, hankalinsu ya koma ga niƙi-niƙin kayan da Ummita ta shigo da su daga bangaren Abba. "Ke." Cewar Futuha. Ummita yarinya mai sanyi da hakuri, ta juyo ta kalle ta. Da yatsa ta nuna ledojin kafin ta ce. "Wannan fa? Daga ina zuwa ina?" Duk da tambayar ta rainin hankali ne, amma ta amsa. "Aiken Mami ne, ta ce a kai wa Humaira." Daga haka ta ci gaba da tafiya, dukkan su ukun ba wacce ta tanka sai faman furzar da hucin ɓacin rai da baƙin ciki. Can sai Tasleem ta ja tsaki tana ture kwanon da ta ci ɗanwake da ƙafa. "Mami! Mami!! Wallahi ban taba ganin uwa irin tamu ba wacce ba ta damu da lamarin yaranta ba. Kunsan Allah, ba don kamanni da kuma Ann dake ƙara ba mu tabbacin cewa ita din mahaifiyarmu ce dagasken ba da zai yi wuya na yarda." Cikin taɓe baki Futuha ta amshe zancen. "Uhum, kema dai kya fada. Ai shiyasa nake so mu samu mazan kece raini da za'a kalla a ƙara kalla. Ko ba komai za mu huta da baƙin cikin Abba da Mami." Tsaki Tasleem ta ja ranta na zafi, sai dai ta kasa magana karshe kawai ta mike ba ta ko kara kallon kwanon ba kuma babu niyyar ɗaukewa. Bayan wucewarta kallon Futuha ya koma kan Raihana wacce ta maida hankalinta ga waya tana  murmushi. "Ke kuma ke da wa? Mu gani." Raihana kamar wacce aka tsikara ta mike tana ja baya da dariya. "Toh sa ido, ina ruwanki da wayata?" Futuha ta taɓe baki. "Kya ji da gulmarki dai, kullum latse-latsen waya, wayarki ta munafukai babu wanda kika taɓa bari ya ga meke ciki. Ni ban san irinki ba, ko hoto za ki nunawa mutum sai dai ya kalla haka tana dunkule hannunki kamar wacce za'a sacewa." Raihana na dariya ta yi hanyar waje gami da fadin. "Eh ɗin dai, wasu ma ba a san me suke shukawa ba. Gwara ni ko failed ban taɓa samu ba sai ku masu C.O." Futuha ta yi kwafa kawai tana huci, zafi biyu ya haɗe mata. *** Murna sosai Humaira ta yi da wannan kyautar ban girman. Ta ɗaga wata riga ja mai adon fulawa ruwan madara tana mannawa a jikinta. Haƙora a buɗe ta dubi Ummita. "Kinga kamar Mami ta auna, daidai da ni." Ummita ta yi dariya. "Eh mana, sai ki sa hijabi su na falon Abba kiyi musu godiya. Kinsan Allah, Mami tana ban mamaki. Wai fa har cikawa ta yi da kudinta ta ƙarasa yi maki siyayya, nidai ban taɓa ganin mace mai kirkinta ba." Humaira ta jinjina kai tana murmushi cike da gamsuwa da zantukan Ummita. Tabbas itama a farko ta yiwa Mamin gurguwar fahimta, amma yanzu kam ta ga saɓanin tunaninta. Sai kuma da sauri ta dubi Ummita. "Wai anya ban yi wauta ba? Kin ga ban je na gaida Anna ba tun da na zo." Ummita ta ɗan yi shiru alamar damuwa, har dai Humaira ta ce. "Lafiya kika yi shiru?" Girgiza kai ta yi. "Anna fa ba ta wani murna da zuwanki, ta cewa Mami koda wasa kar ta sake ta turo ki ɓangarenta. Ki share kawai, ni nasan Mami za ta shawo kanta, kuma tunda kuna tare a gidan dole watarana ku haɗu ai. Zance ne kawai irin na Anna. Kinga jeki ki yiwa su Abban godiya mu wuce, yamma na yi." Humaira ta gyada kai kawai ta numfasa, dama ba dole ne kowa ya ƙaunaceka ba. Ba tare da damuwa ba ta zura hijabin ta fice a ɗakin. 04 Humaira ta ware idanu tana ƙarewa garin Kano kallo a hanyarsu ta komawa gida bayan sun kai wa telan Mami dinkunan an kuma auna ta, sosai akwai bambanci da inda ta fito koda dai dama ita din a ƙauye take. Sai dai kuma hatta da titunan garin burgeta suke yi. Ummita ta kalleta ganin yanda gaba ɗaya hankalinta ke a waje, murmushi ta yi. "Humaira kenan, idan dai garin nan ne har sai kin gaji da shi ina tabbatar maki." Jin haka sai ta yi dariya. "Anya kuwa? Nidai sosai ya burgeni wallahi. Ji nake tamkar kada mu koma gida." Dariya Ummita itama ta ɗan yi. "Shiyasa ai na ce a bi da mu ta wannan hanyar ba ta farko ba, kinga sai ki ƙara kalle garin sosai ko?" Jinjina kai Humaira ta yi tana murmushi sannan ta jefo mata tambaya. "Ni kuwa yar uwa su Abba su nawa ne a wajen Umma? Umman na raye?" "Umman su Abba tun ina firamare, yaranta uku kawai Allah ya ba ta daga nan ba ta ƙara haihuwa ba sai ko yaran ƴan uwa da ta riƙe ta aurar. Kinga Abba shi ne babba sannan Babana, sai autar ɗakinsu Baba Amina, ita a can gadon kaya take zaune da mijinta. Kuma Kakanmu wanda ya haifi Abba shi ya riga ma Umma rasuwa, ita kadai ce matarsa har ya bar duniya. Kar ki damu kedai, tun da kika zo garin nan babu gidan da ba zamu je ki ga ƴan uwanki ba in sha Allahu." Murmushi ya suɓucewa Humaira har ta ɗan lumshe idanu ta buɗe su, ranta ya yi fari sol, burinta ya cika. Yadda ta san kaf ƴan uwan Mamarta, yau Allah ya nufa za ta san na Abbanta. Haka suka karasa su na tafe Ummita na mata nuni da wuraren ƙayatarwa a garin. ***     Dattijuwar mace ce hakimce saman kujera ta haɗe girar sama da ta ƙasa. Banda tsufanta da ya fito muraran, kallo ɗaya idan ka yi mata za ka ga tsantsar kamannin da ta yi da Mami har ta so ta fi Mami hasken fata. Ta gyara zama gilashinta gami da amsa sallamar da Mami ta yi mata ciki-ciki. Anna sam ba ta iya ɓoye abin da ke ranta wannan ya sanya a kallo daya Mami ta gane fushi take da ita. Da harshen buzanci ta ce. "Anna yanzu zancen nan ba zai wuce ba? Ina ce na yi maki bayanin komai?" Anna da sai a sannan ta dubeta ta ba ta amsa cikin yare don ba kasafai take yin hausa ba, kaɗan-kaɗan take ji. "Ki ka ce bayani? Yanzu ke har kina tunanin zan gamsu da bayananki na wofi Maryam? Kina da masaniyar irin wahalar da aka ci a baya? Wato ke dadi miji ko?" Mami gaba ɗaya ta dube ta fuskarta duk a jagule. "Haba Anna, idan ban godewa bawan Allahn nan ba  bai kamata na watsa mishi ƙasa a ido ba. Mutumin da ya amince na zauna tare da ku, muke rayuwa. Duk da irin son abin hannunsa, hakan bai sanya shi watsi da lamarinki ba. Duk wata kulawar da mai shekarunki ya dace ta samu, babu ɗaya da ya taɓa nuna gajiyawarsa wajen yi. Toh mene ne aibu a ciki don ɗiyarsa guda ɗaya ta zauna a hannuna?" "Shashashar banza da wofi, dama nasan ba alheri ne zai fito a bakinki ba. Wato dai gori za ki yimin ko? Dama nasan akwai ranar ƙin dillanci ai, dadin abin da baza  ta kike rawa. Shikenan zan sa maki ido na ga inda wannan rashin hankalin naki zai kai ki. Kin fi kowa sanin wahalar da aka sha a baya ai." Mami dai ba ta ce komai ba, ta so a bar maganar a sanyo wata amma sam ba ta samu fuska wurin Anna ba dole haka ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin, daidai ƙofa ta ɗan dakata kafin ta juyo ta sakarwa Anna wani murmushi da ita kanta Anna ya ba ta ɗumbin mamaki da baƙin ciki, to wannan sabon raini ne ya gifta tsakaninta da Maryam din ko kuwa dai kishi ya taɓa kwakwalwarta tun a shekarun baya? Haka Anna ta cigaba da saƙe-saƙenta da babu mai warware mata. ***   A kwana a tashi babu wuya a wurin Allah, har a yau Humaira ke cika sati uku cif a garin Kano. Abubuwa da dama sun faru na alheri a rayuwarta da suka rinjayi sharrukan ciki. Ɗaya daga ciki har da ƙarin suturu da ta samu, sai kuwa gadonta da sif din kayanta da Abba ya sa aka yi mata. A gefe guda Abba ya mallaka mata wata ƙaramar waya ƙirar Vivo sai dai tana yin whatsapp, kuɗin wayar dai dakyar suka  fito daga aljihun Abban nan ma sai da Mami ta sha fama har ta nuna ɓacin rai ƙarara, a duniya kuwa babu abin da Abba ya tsana kamar ganin Mami ta sauya mishi, nan da nan take cin galaba a ka sa muddin buƙatarta bai shallake tunaninsa ba.   Ummita ta yi mata rakiya wurin dangin Abbansu na kusa, sun yi murna kwarai da ganinta. Sun kuma karɓe ta da hannu bibbiyu, babu abin da ya fi faranta ran Humaira irin shaidar kirki da suka yiwa mahaifiyarta. Ta kuma ji dadin hakan ba kaɗan ba. Rashin abin yi ne ya sa kusan koyaushe idan ba ta komai tana kan wayar tana danne-dannenta ganin ta riƙe abubuwan da Ummita ta koyamata tunda dai harshen turanci ne, ta kuma sani koda faransancin aka mayar ba za ta tsinci abin kirki ba. Abba ya sanya mata lambar Kawunta, sun gaisa sau ɗaya ta waya don ita kam ko whatsapp ma cewa Ummita tayi kada ta buɗe mata, ba ta ga wanda za ta yi hira da shi ba. Ta dai gwammace ta kunna rediyo ta yi ta saurare don hatta da waƙoƙi iri-iri na soyayya da Ummitan ta sanya mata ba ta damu da su ba.   A wannan yammacin kamar koyaushe tana zaune a ɗakinsu gefen gado ta buɗe labule iska mai daɗi na dukanta, garin wuni aka yi cikin zafi yanzu kuwa sai ya ɗan huce. Rabin hankalinta yana ga farfajiyar gidan inda take hango Yassar tsaye da abokinsa wanda ta ji ana kira da Affan su na hira, a gefe ɗaya Muhsin ne da ball yana wasansa tare da Waleed, daidai nan Futuha ta buɗe gidan ta shigo, dawowarta kenan daga makaranta, Humaira na lura Affan na mata magana ko kallonsa ba ta yi ba, daga yanayin tafiyarta za ka fahimci ba a nutse take ba, har ta gifta hankalin Humaira na kanta, ta san dai babu lafiya, tana kuma fatan ba gurguwar shawarar da ta ji jiyan wata aminiyarta Aina'u da ta zo tana ba ta ba shi ta gwada a yau ɗin, gabanta ya faɗi. Ba ta mance kalaman da suka fito daga bakin Aina'un bayan Futuha ta gama amayar mata da damuwarta akan mahaukacin soyayyar da take yiwa Ibb Gusau.    _"Ke ki na ban mamaki wallahi Futuha, ki na da kyawun da babu namijin da zai kalleki bai ƙara ba. Da ace ni ce ke, wallahi babu abin da zai hana na kai wa Ibb Gusau kaina. Kina da sura irin wadda da zarar kin tallata mishi kanki zai ji nan duniya babu wata sai ke. Ke idan ma wannan bai yi ba, ki zo na raka ki wurin Malam Aci Bulus, na rantse maki ko me kike so za ki samu. Ke wallahi sai kin mallaki malamin nan kin juya shi kamar waina a tanda."_ Gaban Humaira ya yi wata iriyar faduwa, ta ambaci Allah a ranta, ta yi nisa da saƙe-saƙen zuci ta ji an banko ƙofar ɗakin an shigo, ta juyo da sauri, Futuha ce. Ba ta ko lura da ita ba ta kife a saman gadon Tasleem tana kuka har da sheshsheƙa. Humaira ta yi shiru, kafin ta lalubo abin faɗi duk kuwa da cewar ba shiga sabgar juna suke yi ba, Tasleem ta shigo ɗakin da sauri a bayanta kuma Raihana. Za ta soma magana amma idanunta na sauka kan Humaira ta fasa, cikin haɗe rai ta ce.   "Malama ba mu waje za mu yi magana." Jin haka tsam, Humaira ta miƙe ta kama hanyar barin ɗakin, bayan fitarta Raihana ta karasa ta rufe ƙofar har da sanya muƙulli sannan ta dawo. Futuha suka ɗago su na magiyar ta sanar da su abin da ya faru. Dakyar ta iya tsaida hawayenta ta shiga ba su labari. "Ai na faɗamaku yadda muka yi da Aina ko?" Suka gyaɗa kai duk sun ƙagu su ji komai. "Shi ne..shi ne.." Sai kuma ta yi shiru ta rasa me ma za ta ce. Tasleem ta zaro ido. "Shi ne me Futuha? Kada dai ki cemin kin gwada aiwatarwa?" Futuha ta runtse idanu gami da shafa gefen fuskarta tana kuka sosai. Sai a sannan idanunsu ya kai ga gefen fuskar, ya yi ja ya yi ruɗu-ruɗu alamun dai mari ta sha. Koda alama ma ba guda ɗaya ba.  Ba ta bari sun nemi ba'asi ba ta cigaba da maganarta. "Na iske shi zaune a ofishinsa shi kaɗai yana aiki a system, koda na shiga bai ɗaga kai ya kalle ni ba, daga motsawar leɓɓansa na gane ya amsa sallamata. Duk da cewa gabana na faduwa hakan bai sa nayi ƙasa a gwuiwa ba na karasa ga teburinsa. Na sauke mayafina yanda rabin kirjina ya bayyana, na shagwabe murya ina mai batun ban gane abin da ya koyar a aji ba. Koda naga bai kalle ni ba, sai na yi gangancin kai hannu saman nasa, shi ne ya gaggauramin tagwayen maruka a kuncina. Ya kum rantse idan na ƙara shiga ofishinsa sai ya ɓalla ni kuma daga kaina masu tunani irin nawa za su dawo hayyacinsu." Tana kaiwa nan ta ci gaba da kukanta. Tasleem da Raihana kusan a tare suka sauke ajiyar zuciya. Raihana ta ja tsaki. 'Kema dai Futuha wataran kina abu kamar Waleed marar wayo wallahi. Ke kin manta tun farko itama Aina'un sonsa take yi wai? Ko don ta ɓata ki a wurinsa ku yi biyu babu kinga ai za ta ba ki gurguwar shawara. Ai mun faɗamaki amma ke idanunki ya rufe." Tasleem ta amshe. "Yanzu shikenan koda ace wannan mutumin na ganinki da mutunci kin ɓarar da shi, yadda za'a yi ki gyara ma nikam ban sani ba. Kada dai garin gyaran a ƙara jagula abubuwan shi nake tsoro. Ke!!! Wai don uwaki shi kaɗai ne namiji a duniya ma? Aikin banza kawai! Ga samari ƴan kasuwa da ƴan bokon su na matowa a kanki a instagram amma kin tsaya biyewa wani so, so, ke fa kike ban shawarar na shigewa Suhaima don na samu na yi mata koda snatching ne, amma ke nan kin tsaya ɓata lokaci akan wani kuturu gurgu." Jin haka ran Futuha ya ɓaci, ta harari Tasleem kafin ta ja tsaki. "Da ace kun san mene so da duk baku ɓata bakunanku ba. Sannan Ibb Gusau lafiyayyan mutum ne kar ki kara aibata shi. Tunda kuma ba ku da shawarar da za ku ban, ni nasan me zan yi." Tana kai wa nan ta miƙe ta yaye mayafin ta faɗa banɗaki ba tare da ta amsawa Raihana da ke jefomata tambaya akan abin da za ta aikata ba. ***   Mami ce tsaye a farfajiyar gidan ta haɗa cikin atamfa ruwan ƙasa mai adon fari, ta sha mayafi ruwan ƙasa hakanan takalminta. Ta dai yi kyau ƙarshe, idan ka kalle ta ba za ka ce ita ta haifi yaran ba saboda daidai gwargwado ta iya ɗaukar wanka. A gefenta Yassar ne su na magana yana ƙorafin shi dai mota yake so tasan yadda zata yi Abba ya siya mishi. Mami jinsa kawai ta ke yi tana yi kuma tana duban gate, da ta gaji ta ja guntun tsaki. "Wai ina Yakubu ya je ne? Daga jeka ka sha mai shikenan har yanzu bai dawo ba?" Yassar ya taɓe baki yana zura hannu a aljihun wandonsa. "Mami ina magana ba ki amsamin ba, koda dai nasan wannan halin na Abba zai wahala ma ya siyamin. Amma fisabilillah ina ɗan jami'a ina kallon abokaina har ma da matan da na raina su a makaranta su na da motocin kansu ni kuwa ko keke Abba ya kasa siyamin saboda mammaƙo." Ran Mami a ɓace ta dube shi. "Yassar ka shiga taitayinka, mahaifin naka kake yiwa waɗannan kalaman marasa daɗi? Toh ya yi maku mammaƙon, kai ai namiji ne, namiji kuma da nema aka san shi. Guminsa ne ya gina wannan gidan, ya kuma mallaka mishi motocinsa, kai ma ka yi zuciya ka mayar da hankali a karatunka watarana ba Abbanku ba, da kanka sai ka siyawa kanka motar, ba na son shirme. Ni kiramin Yakubu a waya ka ce ya yi sauri ya ƙaraso, ina Humairar take ne..." Ba ta ƙarasa zancen ba ta waiga, Humaira na tsaye a gefensu kasancewar su na magana ba su ko lura da ita ba. Itama ta yi shirinta tsaf cikin atamfarta koriya wacce tana ɗaya daga cikin ɗinkunan da aka yi mata. Ta yi kyau sosai, murmushi ta ɗan yiwa Mamin. "Mami na fito ai." Yassar ya ja tsaki ya bar wajen don takaicin Mamin da kuma na ganin Humairar da yake jin haushi da kishin tattalinta da iyayen nasu suke yi sai ka ce su ba ƴaƴa ba ne, Mami na kwala mishi kira amma bai ko waigo ba sai amsawar da ya yi da ƙarfi. "Zan je na ɗau wayar ne na kiramaki Yakubun." Daga haka ya ci gaba da tafiyarsa, Mami ta girgiza kai fuskarta ɗauke da matsanancin damuwa. Sai jikin Humaira ya yi sanyi, wannan kalar zamantakewar mutanen gidan na ba ta mamaki, ace ƴaƴa ba sa ganin iyayensu da gashi, kowace magana ta fito a bakinsu hakanan za su watsa musu ba tare da taunawa ba, toh wace riba ake samu a hakan? Ita tunda ta zo ma ban da Ummita da Raihana sai Muhsin masu ƙokarin zuwa islamiyya, ba ta ga wani cikin su Tasleem na zuwa ba. Bar su dai da yawon gidan ƙawaye a ɓoye Abban bai sani ba. Itama dai Raihanan ba zama take sosai ba amma takan tsaya har a biya karatu da ita,  wasu lokutan sai dai ta ji tana amsa wayar zasu haɗu da wani saurayin idan ta fita makaranta.     A yanzu kuwa daga maganganun Mamin ta fahimci watakila Yassar kuɗi ya nema ko wani abin da bai samu ba ya faɗi abu game da Abban shi ne take goranta mishi. "Muje Humaira, ya zo." Ta amsa da toh ta bi bayan Mamin cike da jin tausayinta, kowace uwa na son ta ga nata na bin ta sau da ƙafa, amma Mami ba ta samu wannan biyayyar ba na yara. Daga manyan har ƙananan, koda dai ta ji Ummita na cewa shi dai babban ɗan nasu ya bambanta da sauran, kuma su na masifar shakkarsa, akwai abubuwa da dama wanda idan yana nan ba sa aikatawa. Ta ce daidai da hantarar da suke yi mata idan har yana nan ba sa yi. Har dai suka soma tafiya a titi tunane-tunane take yi, hankalinta jiya bai kwanta ba sai da ta tsinkayi Tasleem na hira da Raihana su na tsokanar Futuha akan marin da ta sha har su na faɗin gobe ma ta ƙara. Daga baya dai ko don tana ɗakin ne sai suka juye harshe zuwa turanci, ta lura ba su fiye yin buzanci ba su kam, a yadda Ummita ta ce ma, ba komai suka iya faɗi a yaren ba, sun dai fi ganewa idan an musu magana ba su iya mayarwa yadda ya kamata ba. Wannan sai babban yayansu. Shi dai yana ji sosai. Daidai wani babban gida motar ta tsaya, suka fito suka nufi ciki. Kyau da tsaruwar gidan har ya so ya kere na su. Da murmushi Mami ta dubi Humaira lokacin da suka shiga farfajiyar gidan. "Gidan aminiyata kenan Hajiya Lubna, ita ce za ta kai ki wajen koyon girki. Ƙanwarta ke yi." Humaira ta gyaɗa kai ranta ya yi fari sol, ta san dai Mamin ta ce ta shirya zasu je unguwa amma ba ta kawo a rai fitar ta shafe ta ba. Daidai za su shiga babban falon suka yi karo da ɗan Hajiya Lubna shi kuma zai fito, matashin saurayi mai jini a jika, ya sha ƙananun kaya abinsa ya yi tsaf. A fuska ba za ka kira shi da kyakkyawa ba sai dai hutu da jin dadi ya sa fatarsa murmurewa. Gaisawa ya ke da Mamin amma hankalinsa kacokam na ga Humaira wacce daga kallo ɗaya da ta yi mishi ta kauda kanta don ita kam a duniya ta tsani kallo. Mami na lura da yanayin kallon da yake jifan Humairar da shi, ita kanta bai mata ba don haka don ta katse shirun ta ce.   "Hajiyar dai na ciki ko? Don na san ta yanzu sai ta iya ficewa ta bar ni zaman jira." Dariya ya ɗan yi yana shafo ƙeyarsa. "Tana ciki Hajjaju. Ku shiga kafin na shigo." Ta amsa mishi ta yi gaba Humaira ta bi bayanta da sauri har tana tuntuɓe saboda kallon da yake bin ta da shi. Mami ta kalleta kawai ta kauda kai ba ta ce uffan ba. A falon gidan suka iske ƴan mata da yara ana kallo ana hira, wuta tarr a gidan madadin gidansu wanda idan har ba wutar Nepa aka ci sa'a suka kawo da rana ba, zai yi wahala ka ga hasken fitila a gidan sai Magriba zuwa ƙarfe sha biyun dare. Gaba ɗayansu suka gaida Mami, ta amsa. Ta dubi Humaira. "Ki zauna ki jira ni bari na ƙarasa wajenta." Ta amsa da toh ta nemi wuri ta zauna. Ta lura gidan dai ƴan boko ne, ba su ko damu da ita ba sai mai aikin gidan da ta miƙe ta kawo mata ruwa da lemu ganin da ta yi tare suke da aminiyar uwar ɗakinta. Godiya ta yi mata amma ba ta sha ba, hankalinta kacokam na garesu, wani shiri suke kallo na india, sun maida hankalinsu kacokam. Itama sai nata hankalin ya tafi can. Ta shafe mintuna goma a nan tana jiran Mami, can sai ga wani ɗan yaro ya sauko daga benen da Mamin ta hau. "Ki je ana kiranki a sama." "Toh" Kawai ta ce ta miƙe ta nufi hanyar da yaron ya fito, kafin ta ƙarasa ta tsinkayi wata muryar babbar mace na faɗin. "Ke dai ki bi a hankali, kar ki yi garaje kamar yadda ki ka so yi a wancan lokacin." Sallamarta yasa suka kalli hanyar da sauri, ba ta lura da yanayinsu ba ta karasa ta durkusa gefe ta gaida matar wacce kamanninta sak da wannan matashin da suka gani ɗazun. Matar ta amsa mata fuska a sake. "Ah Maryam, ki ce ɗiyar tamu kyakkyawa ce masha Allah. Humaira ko?" Humaira ta gyaɗa kai tana sunkuyar da kai murmushi a saman leɓbanta. "Masha Allah, Allah ya yi albarka kin ji? Allah ya gafartawa Hajiya Fatima, idan kika biyo halinta kin more. Mace mai hakuri da kawaici. Allah ya gafarta mata." Ta ji wani sanyi a ranta, a duniya tana jin daɗin a yabi Mahaifiyarta. Ta amsa da amin ita da Mami. Mamin ta dube ta. "Toh Humaira, gobe idan Allah ya kaimu koda ba ni ba, sai ku zo da Ummita a kaiki gidan koyon girkin. Na faɗamaki ta gida ce, ƙanwar Hajiya Lubna ce. Sai ki mayar da hankali ga abin da ya kai ki. Nasan kina da fahimta da saurin ɗaukar abu, don Allah kar ki ba mu kunya kin ji ko?" Ta amsa da toh Mami. Kafin Mami ta ɗora daga inda ta tsaya wannan saurayin na ɗazu ya hayo. Suka maida duba gareshi. Wani irin ajiysr zuciya ya sauke yana duban Humaira sannan ya maida kallonsa ga Mami. "Ai na ɗauka har kun tafi." Mamin ta ɗan yi murmushi kaɗan ta girgiza kai. "Ina nan Kabeer, amma yanzun za mu tafi. Abban yara ya kusa komawa gida." Ya karasa ya zauna. Hajiya Lubna nan da nan fuskarta ta sauya ganin kallon da yake jifan Humaira da shi. Mami ta dubi Humaira ta bata umarnin ta koma ƙasa ta yi jiranta za ta sauko su tafi. Daga fitarta shi ma ya miƙe caraf ya bi bayanta. Hajiya Lubna za ta yi magana, Mami da sauri ta hana ta ta hanyar ɗan dafe kafaɗarta. Dole ta fasa. Amma ta kudurce a ranta lallai za ta yiwa abin tufka don ita kam ɗiyar ubangidan mijinta take so ya aura, ta kuma lura da yadda yake bin Humaira kamar jela to akwai wata a ƙasa. Ƙwafa kawai ta yi ta watsar suka ɗora hirarsu daga inda suka tsaya. A can kuwa Humaira duk ya takura mata, ita ba ta saba da wannan rayuwar ba. Kawai wani garjejan saurayi ya zauna yana jan ta da hira ba hadin uwa da uba, ita kam abin ya girmi kanta. Ta kula bai ko damu da jama'ar falon ba waɗanda su din ma kallonsu kawai suke jifa-jifa su na mayar da hankalinsu ga tv.  Tambayoyi yake mata iri-iri, amma ba ƴar Mami ce ke ba? Yaushe ki ka zo? Karatu  kike? Da dai sauransu ita dai eh ko aa kawai take ce mishi duk ta takura. Haka Mami da Hajiya Lubna suka sauko, ganinsu ya sa ya miƙe yana shafar ƙeya. "Wai Kabeer ina aiken da na maka ne? Idan ba za ka je ba, ka fadamin na aiki Bala direba." Hajiya Lubna ta faɗi rai bace tana watsa mishi harara, sarai ya gane manufarta, amma shi kam yana ji a ransa ko karatu Humaira take yi zai iya dakon jira ta kammala ya aure ta. Ya lura auren jari Hajiyartasa take so ya yi. "Sorry Hajjaju, bari na tafi. Mami ku gaida gida, sai na tako har falonki na ƙara gaida ki." Mamin ta yi dariya. "Ai babu laifi Kabeer, ko da wacce ka zo ka shiryawa amsar da za ka samu." Ganin ta ɗago shi ya fice yana ƴar dariya gami da faɗin. "Na shirya Maminmu, amma dai ba zan ja baya ba." Mamin ta ƙara darawa. Humaira ta miƙe suka kara yin sallama da Hajiya Lubna, har farfajiyar gidan ta rako su. Humaira dai har ta ɗan kwashe mintuna a mota ba su gama tsayuwarsu a bakin ƙofar falon su na tattaunawa ba, ba ta san me suke cewa ba dakyar dai Mamin ta taho ta shiga motar suka tafi. ***   05 Humaira ce zaune a falo da safe, yaran gidan duka sun fice makaranta kasancewar sun soma jarrabawar zango na uku (Raihana da Ummita kenan), a yadda Ummita ta ce mata, daga jarrabawar to aji na gaba za su je. Kallon tashar Arewa24 take inda ake hasko wani wasan kwaikwayo na marigayi Ibro. Ta shagala gaba daya tana tuntsira dariya ta ji ɗif, wuta ta ɗauke. Guntun tsaki ta ja, ita kam ba ta san matsalar wuta a nijar ba domin koyaushe akwai. Ba ruwanka da tayar da janareto. Ganin haka kawai sai ta miƙe da zummar komawa ɗaki. "Humaira." Muryar Ladidi ta katse ta, ta juyo ta amsa. Tire ne a hannun Ladidin ta karaso gareta. Fuskarta duk ta yi narai-narai alamun roƙo. "Ki taimakamin don Allah ki miƙa sashen Anna, kinga suyar agadar Mami nake kada ya ƙone. Kuma Annar za ta sha magungunanta ne lokaci na tafiya." Kirjinta ya ɗan buga dam, ta kasa magana. Toh akan me za ta cewa Ladidin ba ta taɓa shiga sashin Anna ba? A ganinta hakan su ta shafa. Ganin yadda Ladidin ke magiya yasa ta karɓa, godiya ta yi mata ta koma kicin. Ita kuwa ɗan hanyar da take ganin su Muhsin na yawan zirga-zirga zuwa wajen Annar ta zubawa ido sannan ta sauke ajiyar zuciya ta nufi wajen. Anna ɗin ai mutum ce ba aljana ba balle ta illata ta, za ta je ta ga me zai faru idan ta yi karo da ita. Koro ta za ta yi daga ɗakin ko kuwa dai duka za ta yi mata. Da haka ta tunkari hanyar. A hankali ta tura ƙofar ɗakin da sallama, jin shiru yasa ta maimaita. Wata murya ta amsa, ta tabbatar ba shakka muryar ta Anna ce. Shiga ta yi ta karasa ta ajiye saman ƙaramin tebur dake wurin. Anna dake zaune gefen gado ta soma magana tana laluben gilashinta. "Ladidi sai yanzu ake kawomin abin karin? Yau me ya tsaida ki haka? Ina gilashina na jefa?" Humaira ta hadiyi miyau, kenan dai Anna ba ta san ma wace tsugune a gabanta ba. Ta daure ta ce. "Ina kwana. Ya karfin jiki?" Jin  baƙuwar murya ya sa Anna saurin sanya medicated glass ɗinta wanda da shi ne ta ke gani sosai ba dishi-dishi ba. Yarinya budurwa ce durƙushe a gabanta, fara sol. Kanta duk da cewar akwai hula, sumarta ba ta ɓuya ba don hatta da goshi da bayan ƙeyarta sumar ce kwance. Ta ƙuramata idanu tana ƙokarin tuno inda ta san fuskar. Sai dai a ɗan lokacin ba ta ankare ba don ita shaf tuni ta mance da wata wai Humaira a gidan tunda ba su taɓa karo ba. Ba ta damu da shiga sashin ɗiyarta ba, ya fi rayuwa anan dai ɓangarenta. Daidai lokacin Mami ta shigo ɗakin kamar wacce aka jefo, ta samu labari daga Ladidi cewar Humaira ta tura kai wa Annar kari. Shigowarta ya sa Anna mayar da dubanta gareta. "Ina kika samu yarinya ha..." Sauran kalaman Anna suka maƙale a fatar bakinta, shakka babu ta tuno komai. Ta tuna ashe akwai wani ran bayan jikokinta a gidan da aka ce tsatson Fatima ce. Ta tuna Humaira kamar yadda ta ji sunanta a bakin su Yassar masu yawon kawo ƙorafi a kan fifikon da Mami ke yi mata sama da su. Nan da nan ta haɗe girar sama da ta ƙasa. Daidai lokacin Humaira ta ƙara gaidata wannan karon muryarta har ɗan rawa yake. Ta nuna Humairar da yatsa idanunta akan Mami. "Me wannan abar ta zo yi wurina? Me na faɗamaki? Ban ce maki ba na son ganin baragurbi  a wurina ba? Ke don uwaki wa ya ba ki iznin zuwa wurina, ko ni na haifi uwarki?!" Maganar sosai ta daki Humaira, nan da nan idanunta suka cicciko da kwalla, uwarta kuma? Uwar dake kwance a kushewarta? Mene dalilin sanyo ta ciki? Ba ta jira umarnin Mami ba ta miƙe a zuciye ta kama hanyar fita daga ɗakin, Mami ta riƙe hannunta wannan ya dakatar da ita sai dai ba ta ko juyo ba. Daidai nan kuma hawayen suka sauka saman kuncinta. Da harshen buzanci Mamin ta yiwa Anna magana, Annar kuwa cikin harshen da Humairar za ta ji ta amsa a fusace cikin ɗaga murya. "Au! Don na zage ta kike kirana marar adalci? Ni Maryama kike kallon idona ki ce ba na adalci? Toh anyi rashin adalcin. Idan maye ta manta ai uwar ɗa ba ta mance ba. Ke da kika ga za ki iya haɗiye duk baƙin cikin da kika risƙi kanki a baya, ki yi. Nikam ba da ni ba, kuma ke duk radda kika kuskure ki ka ƙara gangancin takowa ɗakin nan sai na sa jikokina sun nakastamin ke. Sauran yunwa kawai." Humaira tuni ta janye hannunta a na Mami ta bar ɗakin da sauri. Kai tsaye ɗakinsu ta nufa ta zube saman kafet ta shiga kuka kamar ranta zai fita. Ita fa duk abin da matar ta ce bai dame ta ba kamar sanya uwarta da ta yi a ciki. To me Mamarta ta yiwa Mamin da har Anna ke batun ba za ta mance ba? Wane irin zama suka yi a baya? Ita Mami da ma ƴan uwan Abba, sun yiwa Mahaifiyarta kyakkyawar shaida, amma me Anna ke nufi da kalamanta? Ko kuwa dai ita ke taya ɗiyarta kishin kamar yadda Ummita ta taɓa faɗi? Ba ta ji shigowar Mami ɗakin ba sai ji ta yi an kama hannunta an ɗaga ta. Ta miƙe tsaye, Mami ta yi mata murmushi. "Ki yi hakuri Humaira, kin san iyaye ne sai mun yi hakuri da su mu samu a rabu lafiya. Ki taya ni yi mata biyayya,  kar ki kara zuwa ɗakinta har sai don kanta ta nemi hakan wataran wanda in sha Allahu nake fatansa nan kusa. Kar ki sa komai a ranki, ki kuma shirya anjima da kaina zan kai ki gidan koyon girki. Ki cire komai a ranki ki mayar da hankali, ni kuma anan gida idan kin dawo zan dinga iyakar ƙokarina wurin ganin an samar maki dukkan kayan girkin da ki ka koyo a can ki yi a nan mu ci mu ɗanɗana, kin ga daga haka hannunki zai miƙa. Wataran sai a wayi gari kina odar biki da suna har ma da wuraren party ko? Kin zama Hajiya." Zancen Mamin ya sanya ta murmushin da har wushiryarta ta bayyana. Mamin ma murmushin ta ƙara yi. Daga haka ta fice a ɗakin. Humaira tuni ta share batun Anna ta tattara ta watsar. *** Sun je gidan Anti Laila ƙanwar Hajiya Lubna tare da Mami, ta ba da form bayan sun biya komai, Mami da kanta ta cikewa Humairar. Anan aka ajiye ranar litinin matsayin ranar da za ta fara zuwa koyon girkin. Daga nan suka yo gida ranta fari sol. Kai tsaye ɗaki ta nufa hannunta riƙe da na Waleed wanda zuwa yanzu daga shi har Muhsin sun sake da ita,  fuskarta a sake, zuciyarta wasai. Ummita ce kaɗai zaune tana karatun jarrabawa, ganin haka Humaira ta dubi Waleed. "Tafi wajen Muhsin ku yi wasa ka ga Adda Ummita karatu take yi. Anjima sai ka zo ka koyamin turanci ko?" "Okay! Bye." Itama ta amsa da bye din tana dariyarsa, ya dage a lallai zai koyamata turanci, haka za ta biye mishi tana ɗan tsintar wasu abubuwan da ya iya. Ummita ta kalle ta tana murmushi. "Yau dai fara'arki ta musamman ce. Kada dai ki cemin har kin soma shiga aji?" Dariya Humairar ta yi daidai sadda take zama a gefenta. "Aa fa, amma an gama komai an biya, litinin zan soma zuwa." "Kai naji dadi wallahi. Allah ya nuna mana." Ta amsa da amin, ta mike ta hau cire kaya da zummar shiga wanka. Ta dai kula kamar Ummitan ranta a jagule ya ke, ba ta ce mata komai ba har ta shiga wanka ta fito. Anan kuma ta ga ta amsa waya ta yi jifa da wayar saman gado tana ɗan goge fuska. Jiki a sanyaye ta ƙarasa gareta ta zauna. "Ummita, lafiya? Meyafaru?" Ummita tana kallon littafin amma ta kasa karatun sai kawai ta girgiza kai tana shirin cewa ba komai amma tuni hawayenta ya zuba saman littafin. Humaira ta janye littafin. "Don Allah meke faruwa? Anyi wani abu ne bayan fitar mu?" Nan ma girgiza kan ta yi. Ganin haka sai kawai Humaira ta mike ta nufi sif dinta, har ta sanya kaya jiki a sanyaye Ummitan ba ta da niyyar cewa wani abu. Ganin haka sai ta ƙarasa wajenta karo na biyu. "Na tambayeki mene ne kin kasa cewa komai, kuma kina kuka." Jin ta yi shiru ne yasa Humaira fadin. "Toh bari na kira Mami mai yiwuwa ita za ki faɗamata." Har ta miƙe da sauri Ummita ta riƙe hannunta. Suna haɗa idanu ta girgiza mata kai, itama Humaira tuni idanunta sun cicciko don a duniya ta tsani kukan mutum. Kuka ma irin na waɗanda  ta ke yiwa ƙauna domin Allah. Duk abin da ya shafi irin mutanen nan tana jin abin a ranta tamkar ita ya shafa. "Kar ki je, zauna na faɗamaki." Ta koma ta zauna tana mai zuba mata ido bayan ta share kwallarta. "Yayar Mamana ce ta kira ni daga Bichi, kwanakin nan duk sun takura akan lallai sai na fiddo miji na yi aure wai karatun ya isa hakanan. Su sam hankalinsu bai kwanta da zamana a gidannan ba. Ita Babbar yayar Mamana, Anti Maijidda cewa take yi wai har mafarke-mafarke take yi a kaina don haka za su yiwa Abba magana a dakatar da karatun nan, ida n ma aure ne dai a yimin. Ni kuwa na dage akan ba zan yi aure yanzu ba, na ce musu ko zance ba na yi, sun ce ai kuwa anan da Bichi ba zan rasa mijin aure cikin ƴan uwa ba, Anti Maijidda har cewa ta yi ga babban ɗanta Yusuf nan, wai ya kammala  gininsa za ta turo shi ya zo mu yi hira mu fahimci juna. Kin taɓa jin wannan irin abu don Allah Humaira? Duka-duka nawa nake da za su ce za su aurar da ni yanzu? Zangon karshe nake a Ss1 zan wuce Ss2, idan ma auren suke buri su ga na yi, ai sa bari dai shekaru biyun da suka ragemin a sakandire na kammala su. Haka kawai don wasu mafarke-mafarken da ba su da tabbas ku rushemin ginin rayuwata? Sun bi sun kafawa Mami karan tsana, ban san hawa ba ban san sauka ba, amma nima su na hantarata akan na mayar da ita tamkar uwar da ta haife ni, gani suke na fifita dangin Babana sama da su. Toh don Allah faɗamin, mutanen nan sai na je wurinsu duk shekara a can nake hutun dogon zango da ake ba mu na makaranta har ya ƙare, amma su ko sau ɗaya ba su taɓa zuwa garin nan da zummar ganina a gidan nan ba acewarsu su da Mami har abada don ba su yarda da zuciya ɗaya ta ke riƙe da ni ba. Akan Mami na sha duka a wajensu idan na je domin duk wanda ya aibata  ta zan buɗe baki nace sam ba haka take ba, to fa anan sai na ɗanɗana kudata. Yanzu wannan matsalar auren da ta taso ki faɗamin Humaira, ta ina zan kashe ta ba tare da na samu matsala da su ba, nikam wallahi gaba ɗaya kaina ya ƙulle." Humaira ta sauke ajiyar zuciya. "Wai Allah!" Shi ne abin da ta furta don ita komai ma ya tsaya mata cak, ta rasa me za ta cewa Ummita. Mamaki take yi na yadda suke yiwa Mami kallon baibai alhalin matarnan iyakar kokari tana yi a kansu, irin kokarin da ko mahaifansu na usuli sai haka. Can kuma ta dubi Ummita. "Toh kodai ki yiwa Abba bayanin komai? Na tabbata zai fahimceki kuma ba zai rasa matakin ɗauka ba yadda zumuncinku ba zai taɓu ba." Shiru ta ɗan yi, sai kuma ta ce. "Ko? Nima na yi wannan tunanin, wallahi maganganunsu ke hargitsa ni tun wancan satin su ke huran wuta, tun fa ina dannewa har suka soma sanya ni kuka. Amma hakan zan yi kawai, zan faɗawa Abba komai, ke nasan ma kai tsaye zai nemi Kakana wanda ya haifi Mama ya yi mishi magana. Shi kaɗai zai iya tsawatar musu, daman tsoro ne ya sa na kasa faɗa mishi, amma na tabbatar zai magancemin." Humaira ta jinjina kai. "Sai dai don Allah kar ki faɗawa Abba zargin da suke yiwa Mami." Ummita ta kama baki. "Rufamin asiri Humaira, dama me zai kai ni?" Murmushi Humaira ta yi. Suka ɗan taɓa hira sannan ta kyale ta don ta yi karatu.   Aikuwa a daren Ummita ta samu Abban ta zayyane mishi komai, ransa ya ɓaci. Ƙarshe dai ya ce ta tashi ta wuce zai san matakin da zai ɗauka. A ranar kashe wayarta ta yi ta kuma yi alƙawarin ba za ta kunna ba har sai komai ya wuce don ta tabbata zagi ne dai za ta sha a wurin su. *** BAYAN WATA BIYU... Gadan-gadan Humaira ta fara zuwa koyon girki, abin da ya burge su Abba da Mami bai wuce irin hazaƙarta ba na saurin ɗaukar abu. Ita kanta Anti Laila sosai take yabawa da Humairar. A farko-farko ne dai idan aka koyar da su ta zo gida ta yi sai ya kasance bai yi dadi ba ko gishiri ya yi yawa ko dai wani abin, har su Tasleem na ci don su yi mata dariya da kuma kushe. Har su na cewa Abba ya yi asarar kuɗinsa. Amma yanzu kam duk da su na kaucewa ba su son nunawa a fili yana musu dadi, to fa a ƙasan zuciyarsu su na son su ɗanɗana idan ta yi. Amma fa ana ci ana yamutse fuska ana nuna ba laifi ya ɗan yi dadi. Ita dai ba ta tanka musu tunda har Abba da Mami da Ummita su na yabon girkinta. A farko direba ke kai ta, daga baya kuwa Mami ta nemi ɗan sahun da zai dinga kai ta kuma ya ɗauko ta. Watarana kuwa da aka yiwa ɗan sahun rasuwa da kanta ta Mami ta sanya yaron gidan me musu wanki ya raka ta titi ya sanya ta a adaidaita, a dawowa da kanta ta dawo. Tun kuma daga nan ta soma zuwa da kanta ta dawo, a karshe kuma ya kasance koda ɗan sahun bai zo ba ita ke zuwa ta dawo. Ganin ta gane hanya ya sa Mami kawai ta sallami ɗan sahun ake ba ta kuɗin mota. Komai idan ta koya tana samun ɗan littafin da Ummita ta bata ta rubuce tsaf da hausar ajami. Rubutunta mai ɗan karen kyau da burgewa har ya kasance Ummita ta yi ta santin handwritting din. A bangaren Islamiyya kuwa, kusan tare suke tafiya da Ummita a aji duk kuwa da cewar a can karatunta ya zarta na su, akwai abubuwa da dama da ta sani na daga litattafan addini wanda na ajin ƴan gaba ne. Hakan ya sa idan ba sa komai ta ke zama malamar Ummita. Su yi ta karatunsu musamman yanzu da ake cikin hutun dogon zango na makarantun boko. Idan ka cire Tasleem da Futuha sai samarin, babu wanda ke zuwa makaranta. Gidan sai yake yiwa Humaira daɗi fiye da a baya. Ranar wata Asabar da yammaci su na zaune a ɗakinsu, Humaira ke taya Ummita gyaran sif ɗinta, gaba ɗaya sun sauke kayan Ummitan saman gado. Humaira sai tsokanarta take yi akan da tuni yanzu an sanya ranar aurenta da Yusuf, ita kuwa tana kai mata bugu da ninkakkiyar rigarta. Sai kuma ta ja guntun tsaki ta zauna gefe tana murmushi. "Ke nifa ina da mijin aure a hannu, kawai dai bai taɓa zuwa gidannan ba, ba na so kowa ya sani sai na kammala karatu." Humaira ta zaro ido da wani irin zumuɗi ta ce. "Don Allah dagaske? Waye wannan mai sa'ar?" Ummita ta ɗan harareta sai kuma ta miƙe ta ci gaba da ninkin da take yi. "Oho, idan ta yi wari kya ji." Duk irin magiyar Humaira dai ba ta samu Ummita ta furta komai ba, da ta ga hakan ba mai ɓulla bane sai ta sauya ta ce. "Toh abu ɗaya za ki faɗamin, Allah kuwan daga shi ba zan ƙara tambaya ba. Na san shi, na taɓa ganinsa? Eh ko aa?" Dariya Ummita ta yi. "Wai ni za ki yiwa wayo ko me?" Itama dariyar ta yi. "Allah ba wayo ba, kawai ina son sani." Ummita ta ɗan yi shiru, ta sani idan har ta ce mata ta san shi to za ta ƙara damuwa da son ji ita kuwa duk data yarda da Humaira ba ta shirya kowa ya ji yanzu ba. Sai ta girgiza kai. "A'a toh." Jin haka Humaira ta taɓe baki. "Toh shikenan, idan ta yi wari ma ji." Kafin Ummita ta tanka sai ga Muhsin ya shigo a guje. "Adda Humaira, ki zo inji Mami za ku gaisa da Yaya Kabeer." Humaira ta ji kanta ya yi wani dum, wani irin ɓacin rai da bakin ciki na taso mata da ba ta san silarsa ba. Nan da nan ta haɗe fuska tamau kamar ba ita ke dariya yanzu ba. "Ka ce gatanan zuwa." Ummita ta amsa jin ba ta da niyyar amsawar. Ta sani Humaira ta tsani Kabeer, tun ganin da ya yi mata a gidansu tare da Mami yake bibiyarta. Amma yadda fuskarta ta sauya ita kam ba ta taɓa ganinta cikin wannan yanayin ba. "Ke lafiya? Daga ance maki Kabeer ya zo?" Tsaki ta ja ta miƙe a fusace cike da wata iriyar tsiwar da ita kanta Ummita ba ta san ta da ita ba ta ce. "Aikin banza da wofi, na tsani naci da takura wallahi. Mutum sai shegen naci, itama Mami ta biyemishi har da wani aikowa a yi kirana." Ta kara jan tsaki. Maganarta na karshe kan kunnen Raihana da ta shigo ɗakin tana danna waya, baki buɗe take kallonta. "Ke, Mami za ki yiwa rashin kunya? Har da tsaki?" Ko kallonta ba ta yi ba ta juya ta ci gaba da ninkin kayan da alama ba ta da ko niyyar tashi balle ta je. Ummita ta kalli Raihana itama ta dube ta, a fusace Raihana ta karaso ta fisge rigar dake hannun Humaira ta yi jifa da shi. Humaira ta mike a zuciye ta ce. "Malama na fada! Nace na fada! Kabeer din banza da wofi! Ba zan je ba din akwai abin da za ki iya yi? Ko waye ya tilasta ni shiga lamarinsa sai na gasa mishi maganganun da zai yi dana sani!" Raihana gaba daya ta tsorata, kamar dai Humaira kamar ba ita ba. Kawai sai ta gifta ta fice daga ɗakin ba tare da ta tanka ba don dama Raihana akwai tsoro. Ummita ta mike ta kama hannun Humaira a sanyaye. "Humaira, lafiyarki kuwa? Me ya yi zafi?" Ba ta ce komai ba kawai ta zare hannunta a cikin na Ummita, zama ta yi ta yi shiru sai huci ga gumi na tsastsafo mata. A haka Mami ta shigo dakin, Raihana duk ta ba ta labarin abin da ya faru, kallon Humaira take yi a nutse, sai kuma ta karasa ta zauna gefenta. A hankali ta dafe hannunta. Humaira ta kalleta, kawai sai ga mamakinsu ta fashe da kuka. "Mami don Allah kiyi hakuri, wallahi na tsane shi, ki ganinsa bana son yi. Kiyi hakuri don Allah ki janye batun zuwa mu gaisa da shi." Wani irin kuka ne da sheshsheƙa tamkar wacce ake kokarin raba ta da numfashinta. Mami da Ummita wacce duk ta firgice suka dubi juna sai kuma ta rungumo Humaira. "Kar ki damu, ya tafi ya bar gidan ma. Kuma na yi maki alƙawari Kabeer ba zai ƙara takura maki ba. Kin ji ko?" Sai a sannan ta gyaɗa kai ta bar kukan, lokaci guda kuma ta fara dawowa hayyacinta. Ita dai Ummita ikon Allah ta zubawa ido tana kallo. Abin dai kamar a wasan kwaikwayo. 06 Dare ne misalin karfe ɗaya da mintoci, ɗakin ya yi shiru ban da munsharin Tasleem ba abin da kan addabesu kullum ba abin da ke motsi. Humaira wacce abu biyu suka hana ta sukunin bacci, ta zubawa tagar ɗakin ido tana kallon farin wata da ya hasko har cikin ɗakin nasu. Garin babu zafi sai iska dake kaɗawa kaɗan kaɗan hakan yasa rashin wutar bai hana mutanen gidan sukuni ba. Ta ja guntun tsaki ta miƙe zaune gami da runtse idanunta. _'Humaira ba ki kyautata kalamai ga Mami ba. An sani maganar Kabeer kika tsana, sai dai yanayin da kika yiwa Mami magana kamar wata Humairar aka chanja ba ke ba. Idan kin yiwa Raihana wannan dama abokiyar yinki ce, amma ga Mami, kin yi kuskure.'_ Ta tuno kalaman Ummita, wannan na daga cikin abin da ya damu zuciyarta, Mami fa, matar da ta ke ba ta kulawa da zuciya ɗaya. Ta maye mata gurbin Dada da Mamarta wacce ba ta buɗi ido ta gani ba. Ta kuma zame mata abokiyar hira a lokuta da dama idan tana zaune ita kaɗai a gidan. Hakan za ta dinga ba ta labarin Nijar itama ta ba ta na ainahin garin iyayenta wato Agadez su yi ta nishaɗi. Abu na biyu da ya tsaya mata a rai bai wuce na mamaki da tunanin abin da ta yi ɗin ba. Eh ta san ba ta son Kabeer, ta tsani ma ganinsa, amma tsanar har ta yi yawan da za ta kasa ɓoyewa har haka? Ita kam abin ya sha mata kai. Tana nan zaune dai ganin ɓatawa kanta lokaci da tunani take yi da b zai magance mata komai ba sai kawai ta maida kai filo a hankali bacci ya sure ra. Duka wannan zaman da ta yi har zuwa kwanciyarta akan idanun Raihana wacce munsharin Tasleem ya hana ta sukunin bacci. Tsoron yarinyar ya ƙaru a zuciyarta, ta kasa kwakkwarar motsi ga fitsari cike fal a mararta amma ina, ga ni take ai tana miƙewa Humaira za ta tashi ta shaƙe ta don ta gama ba zuciyarta cewar iskokai ne da Humairar. A wannan daren dai bacci ɓarawo ne ya sace Raihana. *** Ta kammala shirinta tsaf kamar koyaushe za ta wuce wurin koyon girki, ta fito falon. Ummita na zaune tare da su Muhsin a falon, Raihana kuwa na gefe ɗaya ta hakimce tana abin da ta saba, latse-latsen waya. Ganin Humaira yasa ta kalle ta sau ɗaya ba ta ƙara ba don ita ba ta so ma su haɗa ido, har ga Allah tun can tana tsoron mai aljanu. Tana kuma shakkar yi musu rashin kunya tun wataran tana jss 2 da wata abokiyar karatunta ta shaƙe ta akan ta zauna a kujerarta ta kuma yi magana amma ta ƙi tashi. Da ta fusata ta shaƙo wuyanta sai da malaminsu ya kwace ta. Abba har makarantar ya je, iyayen yarinyar suka ba da hakuri aka kuma sauya musu aji. Tun daga nan ta ke tsoron duk abin da zai danganta ta da mai iskokai. Ko kusa da su ba ta raɓa. "Har kin fito kenan?" Ummita ta tambaya tana kallonta fuska a sake. Itama murmushin ta yi. "Na fito, ina Mami?" "Tana sashinta." Daga nan ta nufi sashin Mamin, a falo ta iske ta tana waya tana dariya, ganinta yasa ta yi sallama da ɗaya ɓangaren ta ajiye waya. Cike da walwala ta ce. "Ƴar Mami har an fito?" Kunya ta kamata, ita kunyar Mamin take ji wallahi, ta karasa ta durkusanta gaida ta. "To, wata sabuwar gaisuwa ce nan ban da wacce muka yi ɗazu?" Mamin ta faɗi cikin wasa da dariya, Humaira dake sunne kai ta ɗan murmusa, ita ta manta ma sun gaisa ɗin. Mamin ta ƙara magana. "Au, ashe gidan Laila za ki ko? Bari ma na ba ki saƙonta ki tafi da shi." Mamin daga haka ta miƙe ta nufi ɗaki, can ta fito ɗauke da leda wacce Humairar ba ta san ma ko mene ba ta karɓa. Ta ba ta kuɗin mota tana fadin. "Abbanki ya riga ya fita na mance ban karɓar maki na motar ba, ki je kawai idan ya dawo sai na karɓa." Ta gyaɗa kai ta sa hannu ta karɓa da godiya, ganin ta ƙi motsawa balle ta tashi ya sa Mamin tattaro nutsuwarta gareta. "Lafiya Humaira? Akwai magana a bakinki ko?" Gyaɗa kai ta ƙara yi a karo na biyu, cikin nutsuwa kuma ta soma magana. "Mami dama akan abin da ya faru jiya ne, ina neman gafara." Murmushi Mamin ta yi ta girgiza mata kai. "Kar ki damu, ni nasan ba laifinki ba ne. Hakan ya sa na yi maki uzuri. Ki cire komai a ranki kedai ki tattara nutsuwarki ki cigaba da maida hankali ga darussanki. Laila na ta yabon kwazonki don haka ki ƙara dagewa, na maki alƙawarin Kabeer ba zai ƙara shiga sabgarki ba, kin ji ko?" Sai a sannan ta sauke ajiyar zuciya ta samun nutsuwa, ta amsa da toh daga nan suka yi sallama ta mike ta fita, Mamin ta bita da kallo tana murmushi. *** Tuƙi ɗan sahun ke yi cike da nutsuwa, sosai tuƙin ke mata daɗi yayin da iskar dake kaɗawa a garin ke ƙara jefa ta cikin walwala. Damuwar da ta kwana da shi a ƙarƙashin ranta, tas ya wanke ya koma annashuwa. Don haka murmushi take yi ma ba tare da sanin tana yinsa ba. Ba zato ta ji ta yi wani irin hantsilawa sai ga ta a bayan ɗan sahun nan hannayenta rungume a kan wuyansa kai kace wacce aka goyo. Shi kuwa ɗan sahun kansa ya ƙumu da jikin gilashin da karfi har sai da gilashin ya tsage, saura kaɗan adaidaitar ta wuntsila amma Allah ya taƙaita faruwar hakan, sai ya koma baya da ƙarfi har tayoyin na bugun ƙasa da ƙarfi, wannan ya sa ta koma mazauninta, lokaci guda ta saki ƴar guntuwar ƙara sakamakon cikinta da ya bugu da ƙarfen jikin mazaunin direban yake mata zafi dalilin buguwar da ta ƙara yi dalilin komawa baya. Ta runtse idanu daidai sadda ta ji salatin jama'a a kansu. Gaba ɗaya ma ta kasa buɗe idanunta tana dafe da cikinta, ta yi shiru kawai don hayaniyar ma ba burge ta take ba. "Sannu ƴanmata, sauko." Ta tsinkayi ɗaya daga cikin jama'ar wurin na fadi, wasu kuwa na hayaniya su na fadin ai laifin mai motar ne. Can kuma ta ji an ce. "Alhaji kai ne da laifi, kai ka bugi motarsu garin cin burki a kurarren lokaci." Ta buɗe idanunta a hankali jin wani daddaɗan kamshi a gefe, a hankali ta sa hannu ta ɗauki jakarta da ta tarwatse a ƙasa, duk tarkacenta sun zubo. Wani matashi ya shiga tattara mata ita kuwa tana son ta fito a adaidaitar kamar yanda ɗan sahun ya fita ya zauna gefen kwalta, amma ina tururuwar mazan dake wurin ya sa ko motsin kirki ta kasa. Da murya irin ta manyan mutane ya amsa. "Baba, ba abin zafi ba ne. Na sani ni keda laifi, ina mai ba da hakuri garesu. Zan kuma yi kokarin gyara ɓarnar da nayi. Ku yi hakuri don Allah." Humaira ta juya ta kai duba ga mai maganar, daidai lokacin da shima ya ɗan rankwafo don ya yi mata sannu da kuma neman alfarma akan ta sauko su je asibiti. Kalma ɗaya ta kasa fita a bakinsa da ya yi nauyi. Ƙafafunsa suka soma ƙoƙarin kayar da shi. Zai iya rantsuwa ba kaffara son budurwar yarinyarnan yake da idan da ace Uwargidansa ta yi haihuwar wuri to fa ya ci ya yi haihuwar fari da ita. A ɓangaren Humaira kallon da ta bishi da shi bai wuce na son ganin marar hankalin da bai iya tuƙi akan ƙa'ida ba har yake shirin kai ta barzahu. Babban mutum wanda ba gigin kuruciya tattare da shi, ya sha manyan kayansa har da babbar riga da hula. Kana ganinsa dai ka ga wanda ya ba arba'in baya. Ganin yadda ya ƙuramata idanu sai nan da nan ranta ya yi masifar ɓaci, ta ja tsaki wanda ya ba Alhajin nan mamaki, ba ta jira komai ba ta sauko daga adaidaita sahun ta ɗaya ɓangaren mutane na mata sannu. Matashin da ya tattara mata kayan ta yiwa godiya ta karɓi jakarta, ba ta so dubawa ba amma da yake ya matsa sai kawai ta duba, komai nata yana nan cif ba abin da ya ɓata. Dakyar take tafiya dalilin gefen cikin da har sannan ke mata ɗan zugi. "Sannu baiwar Allah, kiyi hakuri ba da gayya hakan ta faru ba. Direbana ne ya ɗauki waya bisa umarnina ba kuma mu ankara ba hakan ta kasance. Akwai inda ke maki ciwo sai a karasa asibiti." Ya karashe yana kai idanunsa kan gefen cikinta da take ta faman dafewa. Ganin haka sai ta saki cikin don ba ta kaunar taimakonsa saboda irin kallon da yake jifanta da shi, kwatankwacin irin kallon Kabeer. Fuskarta a daure tamau ta amsa. "Na ce maku babu abin da ke damuna, lafiyata kalau. Nagode da taimakon." Daga haka ta karasa tana cije lebba ta yiwa ɗan sahun sannu kafin ta kai hannunta dake rawa don har lokacin ba ta dawo daidai daga razanin da ta shiga na hatsarin ba ta fiddo kudi za ta ba ɗan sahun na hakkinsa dake wurinta amma ta kara tsintar muryar Alhajin nan wannan karon muryarsa har ƴar rawa take yi, kirjinsa kuwa bugu yake da karfi tsabar son da ya shiga zuciyarsa farat ɗaya na yarinyar. "Ki bar shi zan biya. A wane unguwa kike sai mu sauke ki?" Jama'ar duk idanunsu a kansu, wadanda suka lura da yanayin mutumin ba su ga laifinsa ba don Humaira ta haɗu iyakar haɗuwa, sai dai a ganin wasunsu, girma ne zai fadi muddin ya bari ta gasa mishi magana. Aikuwa masu wannan tunanin ba su kai ga furtawa ba suka tsinkayi muryarya cike da tsiwa tana magana tana kara zaro manyan idanunta masha Allah. "Baba ina mutunta furfurarka hakan yasa nake gargadinka akan ka fita a hanyata wallahi tun ban gasamaka wacce za ta hanaka bacci ba. Haba! Wannan ai shiga sharo ba shanu ne, ka kusan kaimu lahira na maka uzuri yanzu kuma me ya shafeka da kudin da zan bayar? Da kai ke biyamin kudin motar? Ina ruwanka da ni?" Daga haka ta ja dogon tsaki ta miƙawa ɗan sahun dubun gaba daya na motarta zuwa da komawa ba tare da ta jira chanji ba, daga haka ta juya daidai sadda wannan matashin ya kara miƙo mata ledar da shaf ta mance da batunsa, saƙon Mami zuwa ga Anti Laila. Sai lokacin ta ga ashe ma leshi ne sai atamfa. Godiya ta yiwa matashin a fusace ta bar wurin tana huci, ga cikinta inda ta ɗan bugu bai bar raɗaɗi ba. Kunya da tarin bakin ciki suka lulluɓe Alhajin, bai taɓa zaton yarinyar ba ta da kunya ba da tuni ya ɓoye zalamarsa a kanta. "Sai hakuri Alhaji, yaran yanzu ba su da kunya." Ya basar da zancen yana maida duba ga Ɗan sahun nan da ba da umarnin ya tashi su karasa asibiti ko kuwa dai ya sallame shi yanzun a nan, ɗan sahun ya aminta da hakan, nan take ya ba shi kuɗaɗe masu ɗan kauri gami da ƙara ba shi hakuri. Daga haka ya juya zuwa motarsa har lokacin bai daina jin kunya da ɓacin rai ba su sake shi ba. Ya kuma ƙudurta a ransa idan har haka yaran zamani su ke, to ya yi Allah wadai da ire irenta, ba kuma ya jin zai kara kallonta da sunan wata da ya taɓa gani har ya ji kaunarta cikin ransa. *** A ɓangaren Humaira dakyar ta karasa gidan Anti Laila, ita sai da suka yi nisa ma ta tuno ba ta da chanjin da za ta sallami mai adaidaitan don haka ta ce ya jira ta kawo mishi. Wajen Anti Laila ta karɓa bayan ta mata bayanin hatsarin da suka yi, nan kowa ya hau ta da sannu. Anti Laila da kanta ta kira Mami ta shaida mata, hankali tashe ko mintuna talatin ba a yi ba sai ga Mamin da direban Abba. Daukarta ta yi suka nufi asibiti, koda likita ya duba ta ya tabbatar kawai buguwa ce. Magunguna ya ba ta sannan suka wuce gida. Maganin ta sha bayan ta ci abinci ta kwanta. Abba har ɗakinsu ya shigo ya duba ta, ganin da sauki bacci ma take ya sanya shi fita. Sai da ta yi kwanaki uku ba ta leƙa ko farfajiyar gidan ba a rana ta hudu ta koma zuwa koyon girke-girke abin ta. *** Rayuwar ta ci gaba da tafiya yau dadi gobe babu, rashin dadin a wajen Humaira bai wuce na yadda su Tasleem ke kara nuna mata kiyayya a fili ba. Har ta kai da an wayi gari watarana sun yi mata sharrin sata, domin an tashi Mami tana neman kudin har dubi ashirin da ta ajiye ƙasan filo, gaba daya ran Mami a ɓace yake, sannan ma ita Humaira ba ta nan kuma ita ce ta gyara ɗakin kafin ta fice gidan Laila. Ganin an duba ko'ina sai Futuha da su Yassar suka ba da shawarar a duba ɗakunansu. Mami a farko ta ƙi, sai da Ladidi ta ce ya kamata a duba ko'ina tunda dai nema ake kuma abin da yasa Ladidin faɗin haka ganin su na neman ɗorawa yarinyar kirki Humaira ita kuwa tana da yaƙinin idan har Humaira ce ba za a sami ko sisi na wani a kayanta ba. Tasleem da ta dage tunda Humaira ce ta yi gyaran ɗakin a soma duba kayanta ya sa Ummita cike da kwarin gwuiwar sanin wace ce Humaira ta shiga fiddo kayan Humairar daga sif dinta. Sai dai tun kan ta yi nisa Futuha ta zura hannu ta jawo wata doguwar riga. "Kambu! Dama yarinyar nan ita ta ɗaukarmin wannan rigar? Tasleem ku dubi rigar da nake tunanin ta ɓata a wajen wanki?" Mami ta kalle su, ta yi shiru da mamaki. Can kuma sai ga ɗan kunne da sarƙa sun faɗo. Raihana ta zaro ido tana ɗauka. "Innalillahi, ku ga sarƙata da nake nema kwanaki? Ashe ita ta ɗauka?" Kai kamar wasa jikin Ummita na sanyi da wannan sharrin, ba ta yi aune ba ta kai hannu kan takardun kuɗi, tsabar razanar da ta yi ya sa ta fiddowa da sauri. Ladidi ce ta karɓa tana salati ta ƙirga, aikuwa dubu ashirin cif ne wanda Mami ke cigiya, Ummita kawai sai ta fashe da kuka tana faɗin. "Wallahi Mami wannan sharri ne, Humaira ba ɓarauniya ba ce. Ko kwandalar mutum ta gani idan tana aiki ajiyesu take a wurin da ta gan su." Mami dai ba ta iya magana ba domin kanta ya ƙulle, a sanyaye ta sa hannu ta karɓi kuɗin ta fice a ɗakin tana ji su Yassar na yiwa Ummita masifa wai sai ta faɗi wa ke mata sharrin amma ba ta ko iya tankawa ba. Ita kanta ta sani sata ba ya daga halayyar Humaira don ta sha ajiye kuɗin da suka fi waɗannan kauri ba ta taɓa su ba, amma ta sani mutum ka iya sauyawa. Bare ma a irin gidan nan na Alhaji Isuhu da ba a facaka da kuɗi. Humaira ba ta dawo gidan ba sai yammaci bayan la'asar, da murnarta ta tura kyauren gate ta shigo bayan ta gaida Baba dattijo dake zaune a benci yana siyan rogo a wurin ƴar tallah. Farin cikin bai wuce na yadda suka yi snacks har biyu a yau ba, samosa da springroll kuma cikin ikon Allah ta yi ya yi kyau a ido ya kuma yi daɗi a baki har a foilpaper ta nannaɗe ta kawo don Mami ta ci ta ji. Muryar Ƙasim ta tsinta a kanta. "Ɓarauniya ta dawo." Kallonsa ta yi gabanta ya faɗi, a duk irin wulakanci da jefa-jefan mugayen sunaye da suke mata, babu wani cinikinsu a ya taɓa kiranta da ɓarauniya wannan ya sa ta ji wani irin sanyi har ta kasa mayar masa da martani yadda ta saba idan ya jefe ta da marar dadi. Ya ɗan ɗaga gira. "Oh, bakin ta kanwa ya yi la'asar kenan saboda kin sani kin sata shiyasa. Dama ustazancin ashe na ƙarya ne, toh yau asirinki ya tonu. Ɗan adam butulu." Ta dafa kirji idanunta da suka cicciko da kwalla tun soma maganarsa ta kafa mishi. "Yaya Ƙasim sata fa ka ce? Ni na yi satar?" Ya harareta ya wuce kawai ba tare da ya ce komai ba. Ta bishi da kallo har ya shige gidan, itama a hankali ta soma taka ƙafafuwanta da suka yi mata nauyi saboda mutuwar da jikinta ya yi ta yi cikin gidan kirjinta na harbawa. *** Ma sha Allah, Alhamdulillah. Sai kuma bayan sallah in sha Allah. Allah ya karbi ibadunmu, a sanya ni a addu'a ina bararta don Allah. 🤲🤲 Fatan alheri. 07 Tasleem, Dawud, Yassar da Futuha ne zaune cikin falon sai dai ba ta sha mamakin ƙin amsa sallamarta da suka yi ba, dama ya lafiyar giwa ballantana kuma an jefe ta da kashi? Su na ganinta Tasleem ta miƙe ta yi kerere gabanta hannuwa a ƙugu ta ce. "Ɓarauniyar banza da wofi, kin dawo kina wani sum-sum kamar munafuka. Koda dai dama munafukar ce, Mamin da ta daukake ki tana maki kallon kamar wata waliyya ai gashinan kin watsa mata ƙasa a ido. Ke ni ba wannan ba ma, earpiece dina da na jima ina nema idan kinsan ke ce ɓarauniyarsa wallahi tun wuri ki fiddomin abina. Atoh, bari ma Abba ya shigo gidan, ko Mami ba ta faɗamasa ba sai mun faɗa." Humaira wacce ta kasa tsaida hawayenta, kallon Tasleem din kawai take har ta kai aya, lebbanta na rawa amma ko harafi guda ta kasa fitarwa tsabar baƙin ciki. Wannan wace irin baƙar rana ce a wajenta haka da za a wayi gari da yi mata ƙazafin sata? Ta kasa motsawa, haka Futuha ma ta taso da nata kalar rashin mutuncin, su Yassar na taya ta. Ba ta iya cewa uffan ba sai kukan da ta ke rusawa kamar ranta zai fice. Tsawar da ta ji an daka musu ya sa ta kallon hanya, ruwan hawaye ya sa ganinta komawa dishi-dishi, sai a hankali bayan ta ɗan runtse idanu sun ɗan zuba ne sannan ta lura ashe Mami ce. Ƙarasowa ta yi fuskarta a ɗaure, sai ta koma mata Mamin da ta fara cin karo da ita a ranar farko na zuwanta gidan. Kirjin Humaira ya hau dukan tara-tara, ta runtse idanu saboda ta gama hasaso abin da zai afku, wato mari za ta sha a wajen Mami, sai dai ga mamakinta ta ji akalar faɗan sam ba a kanta yake ba, su Tasleem ta shiga yiwa tamkar za ta ari baki. "Ashe rashin mutuncin naku ya kai har haka? Raini ne wannan ku ka yimin ko mene? Ban hana ɗayanku yiwa Humaira maganar abin da ya faru ba? Ina ce har ɗaki ke Futuha kin biyo ni akan sai an ɗauki mataki na ba ki saƙo ga ƴan uwanki cewar na kashe maganar kada wanda ya tayar? Oh saboda ku nunamin ni banza ce wurinku, hukuncina ma na banza ne shi ne dalilinku na yin watsi da zancena a kwandon shara ko?! Toh wallahi ku fita idona tun wuri, kuma daga rana irin ta yau ku ka ƙara tada wannan batu sai na saɓamaku kamanni." Tana kai wa nan ta ja hannun Humaira zuwa ɗakinta. Ta bar yarannata a tsaye tamkar su haɗiyi zuciya su mutu don haushi, Yassar ne ya soma jan wani dogon tsaki kafin ya sa kai ya bar falon, Dawud ya mara mishi baya. Tasleem kuwa ƙwafa ta yi. "Innalillahi, ke Futuha na soma tsoro, na yarda dagaske ne da ake cewa ƴan ƙasarsu na da asirai, anya wannan shu'umar yarinyar da Kawunta hakanan suka  bar mana uwa? Anya ba sai da suka shuka tsiyarsu sannan ta dawo wajenmu ba?" Futuha da ta kasa magana kawai sai ta ja tsakin itama ta ɗauki wayarta ta wuce sashen Anna idanunta cike da kwallar baƙin ciki. *** A gefen Mami kuwa, su na shiga ɗakinta ta rungume hannuwanta a kirji ta daure fuska tamau har sai da Humaira ta sha jinin jikinta. "Zauna." Ba musu ta zauna a saman kafet, ita kuwa ta hakimce a gefen gado. "Na tsawatarwa yarannan saboda na riga da nasan takun saƙar da ke tsakaninku, ba na son a samu fuskar da za su ƙara ɗora maki karan tsana a matsayinki na yar uwarsu ta jini. Wannan ɗin ma da suke gwada maki fatana su daina na kashe shi gaba ɗaya. Amma meyasa haka Humaira? Har yanzun ina kokwanto akan kin aikata wannan laifin na ɗaukar kudi a ɗakina, amma idan  na tuna ganin da na yiwa kuɗin a cikin kayanki sai zuciyata ta tsinke. Ki faɗamin iyakar gaskiyarki, kamar yanda idan na ci karo da ɗaya cikin su Tasleem sun aikatamin laifi zan hukunta su, kema matuƙar da zuciya ɗaya nake zaune da ke ya zama wajibi na dauki mataki idan kin yi ba daidai ba." Humaira ta ja majina tana kallon Mami. Girgiza kai ta soma cikin muryar kuka ta ke magana. "Wallahi Mami, Allah ɗaya, ba zan yi wasa da Ubangijina wurin yi maki ƙarya ba, ban taɓa ɗaukar ko abin sakacen haƙori a ɗakinki ba tare da izninki ba ballantana kuma kudin da ba nawa ba. Mene ne bakya kokarin yimin a gidannan da zan yi maki sakayya da hakan? Kina yimin kyautatawar da ko na rayu da mahaifiyata abin da za ta yimin kenan. Toh a wane dalili zan zama butulu har na ɗauka daga asusunki? Mami wallahi ban ɗauka ba, ba ni kuma da masaniyar yanda aka yi kudin suka je cikin kayana, nidai na san na maki gyaran ɗaki, na kuma adana su a inda na gansu, na fita zuwa gidan Anti Laila." Mami ta yi shiru tana nazarinta, duk kushen mai kushe ba zai taɓa zama da Humaira ya ji ta masa karya ko sau ɗaya ba. Toh wannan dabi'a ce ta mahaifiyarta, ta sani sarai mahaifiyar Humaira haka take da faɗar gaskiya. Ta san kuma ko a gaban Abban maganar ba za ta chanja zani ba. Sai ta yi nufin kasheta a yanzu ta hanyar numfasawa ta dafa kan Humairar cikin taushin murya ta ce. "Ya isa hakanan, bari kukan kar ya ja maki ciwon kai. Na yarda dake ai dama, sai dai kin san kudi ba zai kai kansa cikin kayanki ba ko? Koda ace ba ke kika kai ba akwai yadda aka haihu a ragaya, kin ga kuwa dole na bincika matsayina na matar gida ko?" Humaira ta gyaɗa kai har sannan tana sauke hardadden numfashi irin na wanda ya ci kuka ya ƙoshi. Mami ta dora da fadin. "Toh don haka kar ki fahimce ni baibai don na tuhumeki, ya zama dole na aikata hakan ne ko don sauke hakki, yanzu kuma da ya kasance ba ke ba ce, zan bincika a sannu gaskiya za ta yi halinta. Tashi ki je ki ci abinci ki huta." Humaira ta gyada kai kawai ta mike ta fita. Har sannan jikinta bai bar ɓari ba, sharri ya fi komai ɗaga mata hankali, ta tsani sharri, ta kuma ci alwashin ita kanta za ta dage da addu'a har sai gaskiya ta yi halinta don a yanzu kam ba ta da amsar ba su Tasleem sai lokacin da komai zai bayyana muraran. A can ɗaki ma Ummita ta tarar tana nata hawayen, sai ya zamana ita ce mamai rarrashin Ummitan da nuna mata ai Mami ta fahimce ta. Ummita ta labarta mata yadda komai ya faru. Ta kara da fadin. "Ba ni da tabbaci akan ko su Tasleem ne da aikata hakan, amma shakka babu ina zarginsu." Murmushi Humaira ta yi. "Kar ki damu yar uwa, idan ma su ne ina mai tabbatar maki wataran gaskiya za ta bayyana." Daga haka suka bar zancen, koda Abba ya zo, babu wanda ya tunkareshi da zancen don ba karamin gargadi da jan kunne Mami ta yi musu ba, koda Anna ta hau faɗa, sai Mami ta sanyayar mata da jiki da faɗin abin da ta fi tunanin akan sharrin da aka yiwa Humairar. Dole itama Anna ta lallaɓa su akan zanceya mutu. Daga ranar kuwa ba a kara tayarwa ba kuma basu fasa kiran Humaira da wannan sabon suna na ɓarauniya da suka laƙaba mata ba. Wanda hakan ya fi komai yi mata zafi, duk kuwa da Mami ta tsawatar amma a fakaice a bayan idon Mamin ba sa fasa faɗi. *** WATA BIYU BAYAN HAKA... Ranar ta kasance yammacin Asabar, gaba ɗaya ahalin gidan su na nan idan ka cire Abba wanda ya fita zuwa kasuwa tare da Dawud. Fuskar Mami a kallo daya za ka shaida tana cikin farin ciki. Su Tasleem dai murnarsu ba yabo ba fallasa. Humaira kuwa da Ummita aiki suke tare da Mami ba kama hannun yaro, Raihana na can ɓangaren yayannasu tana aikin gyara bisa dole don ba yadda za ta kaucewa umarnin Mami, sai dai rabin aikin tana yi ne amma hankalinta na ga chatting din da take yi da sabon saurayinta wanda ya kasance abokin yayan ƙawarta. Humaira ta zage damtse wurin yin kayan snacks yayinda Mami da Ladidi su ke aikin girka masa dambun shinkafa da kuma kunun aya, kamar dai yanda ya buƙata. Sun kammala da wuri suka jera komai a saman tebur, Humaira a gajiye ta nufi hanyar ɗakinsu da zummar watsawa jikinta ruwa adalilin zafin da ke tasomata, Mami ta dakatar da ita ta hanyar kiranta. Juyowa ta yi gami da amsawa. "Maza je dakin Yayanki ki dubamin waccan mashiriciyar ko ta kammala gyaran nan, idan ta kammala ki dawo ga charcoal ki kunna a sanya turaren wuta." Ta amsa da toh sannan ta juya cikin bin umarnin Mamin. Tana zuwa daidai kofar dakin Yaya Mubarak ta ji muryar namiji kamar ta waya ya na fadin. "Um um sweetheart, ban gaji da ganin su ba, ni da ace za ki ɗan buɗemin ko saman ne kaɗai na kalla zai taimakamin ya magancemin wani abin. Please taimakamin kin ji? Gaba ɗaya ta miƙe wallahi." Humaira ta zaro ido, sam ba ta fahimci komai ba, ta na shirin faɗawa ɗakin don ta ga meke gudana ta tsinkayi muryar Raihana na amsawa da wata murya tamkar ba nata ba tana wata iriyar shagwaɓa. "Um um Baby, ba zan iya buɗemaka ba ina jin kunya." "Toh naji, ki yimin hotonsu na miki alkawari ina kalla zan goge, nima zan aikomaki da hotona nikam ko ace ba ki goge ba ba zan damu ba saboda ina maki son da nake jin cewa komai na jikina mallakinki ne koda ba mu yi aure ba. Uhum?" Humaira ta dafe kirji, yanzu kam ta fahimta, ta gane komai. Nan da nan ta nemi gajiyar da ke ɗibanta tana tafiyar rangaji ta rasa, da wani irin azama ta daga labulen dakin ta fada ba ta ko tuna da sallama ba. Raihana da ke fuskantar madubin dakin rike da waya tana videocall da wanda ta kira Baby, ta hango Humaira ta cikin madubi, ba ta san lokacin da ta kashe kiran gaba daya ba gami da saurin ajiye wayar saman madubi. Cikin rawar baki da danne firgicin da ta shiga na irin kallon zargin da Humaira ke watsa mata ta ja guntun tsaki tana kama gefen bedsheet wanda tuni ta kammala gyaransa amma ta hau kara cusawa. "Ke kuma Malama kawai sai ki faɗomin haka babu sallama babu komai?" Humaira ta karasa, ita ban da haushin Raihana da ta ji, har da wani irin bakin ciki da tsanar saurayin da Raihanan ta yi waya da shi ta ji. Ta yarda ba su ga maciji da yan uwanta, amma fa tana kaunarsu kuma tana ji a jikinta sai inda karfinta ya kare matukar ta ga ɗayansu zai cutu. Don haka tana zuwa saitin Raihana ta fizgo hannunta suka kalli juna, Raihana har sai da ta yi taga-taga za ta fadi kafin ta warce hannunta a tsorace, da karfi ta ce. "Ke kuma Malama wai mene haka? Me na yi maki za ki nunamin hauka?" Ta fadi ne cike da karfin hali domin a tsorace take, tana gudun ace aljanun Humairar ce suka tashi. Humaira wacce idanunta har sun rine tsabar bacin rai ta kalleta sosai. "Raihana kina da hankali kuwa? Kin san me kike shirin aikatawa kanki? Ɓangare masu muhimmanci da girma a jikinki wani jakin banza ya ke so ki tura masa? Kina hauka ne? Wannan saurayi ne da za ki kula? Toh wallahi muddin kika yarda kika aikamasa kin gama cutar da kanki har abada, balle kuma akai ga ya nemi ku hadu da shi a waje. Ina iliminki ya tafi? So ba hauka ba ne ki bude idanuwanki ki fidda baragurbi cikin rayuwarki." Raihana da tun da ta fahimci dagasken Humaira ta ji dukkan hirarsu sai ta hau borin kunya ga zufa na yankowa saman goshinta har yana jiƙa sumar dake kwance a wurin. "Me kike nufi? Ni ba ni da hankali ne da zan tura masa? Ko kin dauka shashasha ce ni? Toh ni nasan yanda nake tafiyar da ire-irensu don haka ki rabu da ni. Wannan rayuwata ce. Zan gudanar da ita ne yanda na so. Bai shafeki ba." Humaira ta yi shiru, can ta nisa za ta kara magana wayar Raihanan ya hau kara, aikuwa da azama ta nufi wayar har tana ture Raihana. Ɗagawa ta yi ta sa a kunne, Raihana na son dakatar da ita amma tana tsoron kar ta sha duka a hannunta. "Sweetheart na ji shiru, muna waya..." "Ba ita ba ce, wannan yayarta ce. Zan kuma yi maka gargadi da babbar murya. Wallahi wallahi ka kara gangancin neman yar uwata da tura maka wani hoto na sassan jikinta sai na nunamaka ba kowace mace ake taɓawa ba a sha ba. Sai ka raina kanka. Banza dan akuya kawai! Tirr da matasa irinku wadanda ba su ajiye komai a cikinsu ba sai tsabar iskanci da baɗala. Mu zuba ni da kai mafashi ya fasa!" Ba ta saurari me zai ce ba ta datse kiran ta wurgawa Raihana wayar tana jifanta da muguwar harara, Raihana dai kasancewar ta yi amannar wannan jinnun Humairar ne ke magana ba ita ba, ta kasa kataɓus sai rawar jiki tana ji kamar ta saki fitsari a gefe guda tana jin bacin rai da tsanar shiga hanci da kudundunen da take mata amma ba dama ta yi magana, ta kuma sa a rai za ta yi duk yadda za ta iya ta ga ta ba shi hakuri kar ya kai zancen Humaira zuci. "Idan kin kammala wayar ashararancin sai ki yi sauri ki kammala aikin Mami na jira. Shashasha da ba ta san ciwon kanta ba." Daga haka Humaira ta ja tsaki ta fice cikin zafin rai. Wayar Raihana na ta ƙara amma ta kasa ɗagawa don gani take yi da zarar ta ɗaga aljanun Humaira za su isar mata da saƙo ta kuma dawowa, wannan karon kam ta sani lugudar ta za ta yi mata. Hawaye na zubomata tana ci gaba da gyaran dakin, hawayen na bakin cikin abin da Humaira ta yi mata ne, tun da take samari a duniya ba ta taɓa yin wanda har a zuciya ta ji tana mishi son aure ba irin Musaddam, yanzu ga shi nan ta ɓata mata shirinta. Tana mishi so da zuciya daya wanda take jin ko mene ne za ta iya yi a kansa. Don haka a gaggauce ta share dakin ta fice zuwa bangaren Anna domin ta samu damar ba shi hakuri sosai. Ai kuwa duk kalar hakuri da karyar taɓin hankalin da ta dorawa Humaira duk domin ya aminta da ita ya kasa, cewa ya yi shi din son da take mishi bai je ko'ina ba tunda har za ta bari wani ya ji sirrinsu. Raihana kamar ta mutu don bakin ciki, ta tsinewa Humaira ya fi a ƙirga. Ita kuwa Humaira umarnin Mami ta cika ta sanya turaren wuta a dakin ta fice nasu dakin. Koda Ummita ta nemi sanin abin da ya jefa ta cikin ƙunci, cewa ta yi babu komai. Har ta yi wanka ta shirya ba ta cikin walwala. Misalin karfe takwas da mintoci Mubarak ya iso gidan. Su Muhsin suka cika gidan da Oyoyo, Tasleem su ma duk yanda su ke ganin yayannasu da shige musu hanci da kudundune sun yi murna da ganinsa. Humaira na gefe tana murmushi ba ta karasa ba tana karemishi kallo. Shi kam kammaninsa da Abba har ta ɓaci, shima dai ba ya kama da Mami, sai ko baƙi da laushin gashi irin na yan uwansa da ya dauko. Kansa cike taf da suma ya tara. Bayan ya zauna ganin Ummita ta karasa ta gaida shi ya amsa cikin sakin fuska ne ya sa itama karasawa su gaisa. Ya nunata da yatsa ya yi shiru alamar dai so yake ya tuno wani abin. Can kuwa ya ce. "Humaira, right?" Ta dai fahimci so yake ya tabbatar ko haka sunan ya ke sai ta gyada kai. Su Tasleem suka kwashe da dariya, ya tambayi dalili suka amsa da ba komai. Mami ta fito fuskarta cike da fara'a, ganin mahaifiyarsa ya mike tsam ya karasa ya dan rungumo kafaɗarta, ta dan tureshi tana murmushi. "Ba ka girma ko?" Ya kuwa kara marairaicewa. "Girma fa kika ce Mami, yaushe rabonki da ni don Allah?" Har lokacin murmushin take yi ta amsa. "Amma ai ana waya da videocall ko?" Da wasa ya sake ta ya juya. "Shikenan bari na koma inda na fito tunda kin ƙoshi da ganina." Da sauri ta riƙo rigarsa har duka falon aka dara. Ya ja hannunta suka nufi bangaren Abba su na hira. Abba ya yi murna da ganin ɗan nasa, ya kasa rufe baki. Nan suka hau taɓa hira karshe kuma Abban ya ce ya je ya kimtsa ya ci abinci tukunna. Da wannan ya mike ya fita, daga uwa har uban suka zuba mishi ido cike da kauna kowannensu kuma da abin da yake ayyanawa a ƙasan rai. *** Zaune yake a babban falon dake cikin Airport din Abuja, ya kalli agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa mai cike da gargasa ya fi a ƙirga, ya maida duba saman wayarsa yana latsawa. Cikin sa'a kuwa ya ji muryar ma'aikaciyar ya karaɗe wurin inda take umartar fasinjojin da za su je Kano akan su nufi ciki. Ya mike kuwa don dama abin da ya zaunar da shi kenan. Hannunsa ɗaya riƙe da trolley ɗinsa yana ja, tafiya yake da sassarfa. Bayan komai ya kammalu jirginsu ya ɗaga. Isar su keda wuya, ya yiwa abokinnasa IBB GUSAU waya. Kafin ya kai ga magana ya ji saukar muryarsa daga gefe. "Barka da zuwa." Juyawa ya yi yana dubanshi da idanunsa dake ɓoye cikin wani arnen baƙin gilashi, sai kuma ya ja guntun tsaki yana ɗan murmushi, lokaci guda ya ba shi hannu suka yi musabaha kafin su rungume juna suna cike da farin ciki. Bayan sun saki juna da mamaki ya ga idanun Ibb sun kaɗa, nan da nan ya daure fuska. "Ok, hakan na nufin ba ka yi murnar ganina ba kenan na koma inda na fito ko?" Girgiza kai Ibb ya yi ya sa hannu yana karɓar trolley dinsa yana fadin. "Hakan ba zai taɓa faruwa ba, in sha Allahu ka dawo kenan. Tafiyar kuma daga ni har Alhaji ba za mu ƙara bari ka yi irinta ba. Shekarun da ka yi sun isa hakanan." Ya shafi sumar kansa bai ce komai ba ban da baki da ya ɗan taɓe ya yi gaba kai kace ya san inda mazaunin motar amininnasa ya ke. Ibb da murmushi ya mara mishi baya. Suka jera su na gifta filin wurin, Ibb ba gajere ba ne, amma fa duk tsawonsa bai kama ƙafar abokinnasa ba, kusan su biyun duka sai ka rantse ba su ne suka gama yiwa juna murmushi da runguma ba, tafe suke su na kallon hanya kai ka ce ba su san juna ba, duk inda suka gifta sai an bi su da kallo, ƴan matan dake wurin kuwa ji suke inama inama, inama za su yi nasarar samun sa'a a cikinsu ɗaya ya yaba, da sun tabbata masu sa'a. Shi yana sanye da ƙananun kaya yayin da Ibb ke sanye cikin manyan kaya dinkin babbar riga har da hula kai kace wani Ango. "Ina ka nufa?" Ya yi tambayar fuska a haɗe a sadda Ibb ya murza sitiyari ya nufi gate din Airport din, shi ma ba tare da ya kalle shi ba ya amsa. "Ka fi kowa sanin inda ya dace mu soma manufa. Tushiya masomin dawa." Girgiza kai ya yi. "No Ibb, i am not ready for it, muje ka kai ni hotel. Hakan na fi buƙata. Please." Ba musu Ibb Gusau ya amsa da Alright, ba ya so fadi tashin da ya jima su na yi da Alhaji ya tashi a tutar wofi, ai an yi mai wuyar da suka samu ya dawo garin. Don haka kai tsaye Bristol Hotel ya kai shi ya kama mishi masauki, da wani irin walwala da annuri dauke saman fuskarsa ya fito ya rabu da shi ya kama hanya don ya je ya ba Alhaji kyakkyawan albishir. Lallai ya san da zuwan ɗan nasa, amma bai taɓa kawo wa a rana irin ta yau ba da ake shagalin bikin ƙaninsa mafi soyuwa ba a rai. 08 Kasancewar gidan cike yake da jama'a ƴan uwa, makwafta har ma da abokan arziki ne ya sanya Ibb zagayawa ta ɓangaren Alhajin ya shiga ainahin falonsa na karɓar baƙi. Kamar yanda ya yi tsammanin hakan ya tarar, wato dai Alhajin ba shi ɗaya ba ne a falon, yana tare da babban yayansa Baffa Gidado sai ɗan gidan Baffa Gidadon, Harɗo. Sai ko ƙannensa guda biyu dake zaune  su ma a gefe ana ɗan taɓa hira, kallo ɗaya za ka yiwa fuskokinsu ka fahimci su na cikin annashuwa. Sallamarsa ce ta katse hirar tasu wadda ke gudana da harshen fulatanci, suka dube shi gaba daya, ya karaso yana ƙara miƙa gaisuwa a karo na biyu domin dazun daga gidan ya fita. Alhaji ya amsa gaisuwar yana bin fuskar Ibb da kallo ganin yadda yake wata irin fara'a na musamman wadda rabonsa da ganin kwatankwacinta tun a baya kafin afkuwar wasu lamura marasa daɗi. Ganin bakin Ibb na ta motsi amma ya kasa magana ya sanya Alhaji miƙewa tsaye wannan karon kirjinsa bugu yake da sauri-sauri. "Muje." Shi ne kawai abin da Alhajin yace, aikuwa kamar jira yake har da tuntuɓe a kokarinsa na bin bayan shi. Wata ƙofa suka bi wacce kai tsaye main parlour din Alhajin na cikin gidan suka faɗa. Ko zama Alhaji ya kasa hakurin yi su na karasawa tsakiya ya juyo gaba ɗayansa. "Ibrahim, ya ake ciki? Meke faruwa?" Madadin ya amsa sai kawai ya rungume Alhajin kafin ya sake shi yana dariya. "Mafarkinka ya tabbata zahiri Alhaji." Alhaji hannunsa har rawa yake ya kama kafaɗun Ibb har idanunsa sun cicciko da kwalla. "Ya..ya..ya..da..wo?" Ya yi maganar da rawar murya, jinjina kai Ibb kafin ya amsa. "Eh, FADEEL ya dawo." Alhaji ya sauke nannauyan ajiyar zuciya. "Alhamdulillah, Alhamdulillah. Yana ina yanzu? Muje ka kai ni na gansa." Ibb zai musa amma babu dama domin dagasken dai ba abin da Alhaji zai saurara. Don haka sai kawai ya juya, Alhaji biye da shi suka fito. A farfajiyar gidan suka yi kiciɓus da Ango Fu'ad wanda shigowarsa gidan kenan daga Hotel din da abokan karatunsa suka sauka. Ya karasa ganin irin rawar jikin da Alhajinsu ke yi, ga Ibb na kokarin buɗe mota. "Alhaji, fita za ku yi ne?" Alhaji ya dafa kafaɗarsa fuska a sake ya ce. "Maza shiga mota." Ba musu ya zagaya ya shiga har sannan fuskarsa dauke da mamaki, ya kuma kasa tambaya. Ibb bai ko hana Alhaji wannan yunƙuri ba don ya sani Fadeel zai yi farin ciki kwarai da ganin ƙaninnasa. ***   Ya yi wanka ya shirya tsaf cikin riga body hug fara ƙal sai blue jeans. Yana zaune yana kurɓar ruwan shayin da aka kawo mishi, hankalinsa kaf yana wajen Mahaifinnasa, wata zuciyar na ce mishi ya je ya gan shi, wata kuma na kwaɓarsa. A hankali ya ajiye mug din dake hannunsa ya jingina kai jikin kujerar yana mai lumshe idanunsa. Dogayen gashin idanun suka kwanta luf saman fatar wurin. Ji ya yi ana buga ƙofar, ya buɗe su kafin ya miƙe. Yana da tabbacin Ibb ne. Hakan yasa koda ya bude bai tsaya kallonsa ba ya juya ya koma cikin ɗakin gami da faɗin. "Wato gadina ka koma kenan?" "Muhammadu." Ya tsaya cak a tsakar ɗakin, kaf duniya mahaifinsa kaɗai ke kiransa da ainahin sunansa, da hanzari ya juyo, tuni lumsassun idanunsa sun kaɗa. Alhajin ya taho da sauri ya rungumeshi, shi kuwa ya tsaya kamar wanda aka dasa a wajen ya kasa motsi. Fu'ad da bai san wainar da ake toyawa ba sai yanzun, kawai kuka ya sanya tsabar murnar ganin yayannasa da ya nisanta da su saboda wasu dalilai. Ya karaso da sauri ya haɗa daga Alhajin har Fadeel ya rungume yana kuka. Duk jarumta irin ta Fadeel sai kawai ya ji hawayensa sun zubo. Suka saki juna Alhaji da kansa ya sa hannu yana share masa hawayen. "Ashe da raina da lafiyata ban mutu ba zan ga wannan rana? Alhamdulillah." Abin da Alhajin ya furta kenan. Fadeel ya yi murmushi da gefen kumatu yana dafa kafaɗar Fu'ad. "Ango, har ka girma za ka yi aure." Suka yi dariya har Ibb, Fu'ad kuwa yan sunkuyar da kansa gami da shafar ƙeya. Nan fa Alhaji ya matsa akan lallai sai ya tattara sun tafi gida da shi. Anan ne kuma ya tamke fuska kwarai, ya koma Fadeel ɗinsa na ainahi. "Muddin tana gidan nan ba zan iya shiga ba. I am sorry Alhaji." Jin haka Fu'ad da Alhaji suka kalli juna suka yi murmushi. Shi sai a lokacin ma ya ji nauyin Fu'ad din, wai uwarsa yake ikrarin ba zai shiga gidan idan tana ciki ba. "Yaya Fadeel, Mama ba sa tare da Alhaji, tayi wani auren a garin Kogi. Sai dai ko Anti Amarya our new Mum." Sai Fadeel ya kasa cewa komai, ya maida dubansa ga Alhajin, ya gyaɗa masa kai don ya ƙara tabbatar da abin da Fu'ad ya faɗi. "Yanzun ka shirya bin mu?" Ya jinjina kai yana murmushi. Ibb tuni ya soma haɗa mishi shirginsa. Fu'ad ya karɓi akwatin suka fito baki ɗaya, suka yi mota yayinda shi kuma Ibb ya tsaya a reception. Isar su gidan kai tsaye suka nufi sittingroom wajen su Kawu Gidado, sai dai tuni sun fice masallaci gabatar da sallar La'asar. Koda dawowarsu ganin Fadeel gaba ɗaya dakin ya kaure da murna. Magana dai ta bazu a gidan Fadeel ya dawo, babban ɗa namiji a wurin maigidan. Nan fa mata gwaggonninsa ƴan uwan mahaifinsa kowa ya fito zuwa falon. Murna kam ba a magana. Yayyunsa mata waɗanda kaf dinsu su na da aure sai guda ɗaya bazawara da aurenta ya mutu take zaune a gidan da yaranta, su din ma kowaccensu ta halarci falon. Kallonsu kawai yake yi yadda kowacce ke haba-haba da shi, murmushi kawai ya ke yi don ba shi da tabbacin ko abin nasu ya kai zuci ko aa. Sanin da ya yi musu daban a baya, ba shi da masaniya akan yanzu. ***   Raihana ce zaune a can lungun gadon Tasleem ta maƙure a gefe tana zuba kuka ga waya saman kunnenta. Musaddam take ta ba hakuri adalilin ya ƙi ya huce tun sadda Humaira ta gasa mishi zafafan maganganu. Ya kuma ci alwashin ko don ya nuna wa Humaira ba ta isa ta tsaida shi daga abin da ya yi niyya ba, sai ya kusanci Raihana ko ta ƙarfi kuma ya yi hotuna don ya shayar da ita mamaki. Yana sane da gangan ya ƙi ya huce saboda kawai ya ƙara fahimtar irin matowar da Raihanan ta yi a kansa. Sati ɗaya kenan da dawowar Yayannasu amma ko kaɗan walwalwarta ba ta dawo daidai ba ga wani irin tsanar Humairar da take ji a ƙoƙon rai amma shakkar kada ta tona mata asiri da ma tsoron ita kanta Humairar ya hana ta labartawa koda Tasleem ce balle Futuha. Sai ƙawarta da ta ba labarin, ita kuwa ƙara hure mata kunne ta yi akan kar ta yarda wata can bare ta raba ta da abin sonta. Da wannan huɗubar da kuma mahaukacin son da take yiwa Musaddam idanunta suka rufe ruf. A wannan yanayin walwalarta ba ta dawo ba sai da ta tabbatar ya haƙura bisa alƙawarin za ta zo gidan su Munirat su gaisa. Humaira ta shigo ɗakin daidai sadda Raihanan ke fadin. "Shikenan zan zo goben idan har ganina zai samar maka da nutsuwa." Wannan kalmar ta daki zuciyarta, sai dai ta dake ba ta ko kalle ta ba ta ƙarasa ciki, dama mayafin abayarta za ta ɗauka zasu je Shoprite ita da Ummita, Mami ta aike su. Raihana kuwa ganin Humaira ya sa ta shan jinin jikinta. Ta kasa magana kwakkwara sai um da humm ina jinka. Guntun tsaki Humairar ta ja ta fice, ta sha alwashin ko ina ne a goben sai ta bi bayanta ta kuma kama ɗan iskan dumu-dumu ta ci uwashi.   A falon ta haɗu da Ummita, har suka soma tafiya ta ga dai hira suke amma ita ke kiɗa da rawarta hakan yasa ta dube ta. "Wai ke lafiyarki kin wani haɗe rai kamar wacce aka aikowa saƙon mutuwa? Koda dai ɓata bakina nake dama ai halinki ne. Amma naga ai yanzun ba kiciɓus kika yi da maƙiyinki naki ba ko?" Tana nufin saurayi, Humaira ta ja tsaki ta girgiza kai. "Ba komai fa." Taɓe baki Ummita ta yi ba ta ƙara magana ba sanin hali. Sai kuma can don kanta ta saki fuska suka hau hira. Kayan maƙulashe irin su Jam, Ketchup, Mayonnaise da sauransu, shi Mami ta bada su siyo na Yaya Mubarak. Sun kammala suna dab da ficewa suka tsinkayi sallama a gefensu. Lokaci guda suka juya ga mai shi, wani matashin saurayi ne gajere mai ƙiba. Irin ƙibar da ba ta da muni. Daga yanayin yadda ya saki fuska za ka fahimci mutum ne mai fara'a. Humaira wacce kallo ɗaya ta mishi ta dauke kai gami da ci gaba da tafiya, ganin haka itama Ummita ta mara mata baya, ya kuma bin bayansu da sauri ya sha gaban Humaira. "Ranki ya dade, kiyi hakuri na tsayar da ke. Nima kuma na san darajarki da ƙima ta zarce a tsayar da ke a hanya a..." "Kai Malam saurara don Allah! Ni nan da ka ke gani da mijina a hannu don haka kama kanka. Muje." Ta fisgi hannun Ummita ta bi gefe suka fice a nan. Hakan da ta yi ba karamin ɓatawa Ummita rai ya yi ba, ba yau farau ba, idan da sabo ya ci ace ta saba da ganin irin cin kashin da yar uwarta ke yiwa samari. Ita har mamaki take yadda gaba daya Humairar ke sauyawa kamar ba ta taɓa zama haɗa hanya  da wani abu wai shi mutunci ba. Ta fara gasƙata zancen Raihana da ta ce jinnu ne da ita. Kamar kuma ba ita ba, sai ga shi a hanya ta saki rai sun ci gaba da hirarsu lafiya lau. ***   Washegari tun safe take dakon Raihana tana jira ta ga sadda za ta fita ta mara mata baya. Aikuwa wuraren karfe biyu tana zaune a falon da littafi a hannunta na koyon rubutun hausa tana ɗan duba inda muhsin ya biyamata, Mami kuwa na gefe tana yankewa Muhsin farce sai ga Raihanar,  ta tambayi Mamin zuwa gidan ƙawarta Munirat. Farko Mamin ta hana sai can kuma da ta dage da naci ta samu Mamin ta aminta. Humaira ba ta ko ɗaga kai ba balle ta yi yunkurin miƙewa, har sai da Mami ta soma barin falon, tana nan zaune ba ta ko motsa ba har Raihana ta fito cikin shigar fita, ta ci wani arnen kwalliya ta sanya riga da siket da ya yi matuƙar kama ta sai ta dora afterdress a sama wanda da shi da babu duk ɗaya. Tana fita Humaira ta yi wuf ta miƙe ta zari hijabinta dake hannun kujera. Tuni ta yi shirinta dama ta sa kuɗi a bayan gidan wayarta. Bayan Raihana ta bi, sai da ta kai ƙarshen layin ta nemi can jikin wata  bishiya ta ɓoye fuskarta cikin facemask. Haka ta shiga ɗan sahu ta bi bayanta har gidan su Munirat. Kamar yanda ta zata kuwa hakan ne, wani saurayi matashi ne tsaye jikin wata mota suna hira da wata budurwa. Raihana na karasawa ta cafke da budurwar da bayan ta matso ta gane Munirat ce saboda ta taɓa zuwa can gidannasu ba sau ɗaya ba ba biyu ba.     Can kuma sai Munirat ta shige gida ita kuwa  saurayin ya buɗe mata gidan gaba ta shiga ya maida ƙofa ya rufe. Baƙar mercedez ce mai baƙin tinted wanda duk iyaka hangen mutum bai isa ya ga na ciki ba. Humaira ta ji ƙirjinta na dukan tara-tara da wani irin sauri ta soma takawa ta nufi wajen kai ka ce kafin ta karasa abin da take tsoron afkuwarsa ya afku. Da tsayuwarsu a wajen, da shigar budurwar motar, duka ya faru ne akan idanun Ibb da Fadeel wadanda ke tsaye a ƙofar gidan su Fadeel ɗin su na taɓa hira. Ya rako Ibb ne zai wuce gida suka tsaya. Ganin shigar budurwar ya sa Ibb jan tsaki. "Wallahi ina mamakin rayuwar ƴan matan yanzu da ba su da kunya kuma ba su san mutuncin kansu ba. Yau da ƙanwata ce daga ita har shi sai sun raina kansu." Ya faɗi ransa na wani irin ƙuna, Fadeel kuwa da zuciya ta kai mai wuya bai san sadda ya soma takawa ba da sassarfa hakan da ya yi ya sa Ibb bin bayansa da sauri ya dakatar da shi sanin hali. "Aa Fadeel, please don't, ba ka san waye ba a.." "Sai nasan waye? Idan ƙanwartaka ce za ka zuba ido kana kallo rayuwarta ta ɓaci!" Yana kai wa nan ya fisge hannunsa, sai dai kafin ya kai ga tafiya suka hangi Humaira wacce gadan gadan ta nufo motar a fusace.        09 Zuciyar Humaira har wani tafarfasa ta ke yi, tana isa ta sa hannu ta ja murfin motar cikin sa'a kuwa ƙofar ta buɗe. Raihana wacce yatsunta ke sarƙe da na Musaddam gaba ɗaya ta kasa sukuni amma ƙarfin soyayyarsa a ruhinta ya sa ta daurewa ranta, daidai sadda ya kai bakinsa ne da nufin sumbatar hannun aka wangale ƙofar hakan ya sa a firgice gaba ɗaya suka juya. Humaira ta fisgo Raihana, ba shiri ta fito har tana tuntsirawa. Ba ta yi wata wata ba ta ɗauke ta da mari hagu da dama ga wasu zafafan hawaye da suka zubo saman fuskarta lokaci guda. Musaddam tuni ya fito ya zagayo wurinta, hannu ya ɗaga shi ga marar kunya zai ramawa Raihana marin, amma tuni Humaira ta riƙe hannunsa ta ba shi nasa rabon. Hannunta har rawa yake ta sa hannu ta fisge facemask din da ke rufe a hanci da bakinta. Fadeel ya yi mata ƙuri da idanu babu ko kyaftawa yana jin tamkar gangar jikinsa ne kawai tsaye a wurin, hannu ya sarƙe a kirji yana so ya ga matakin da za ta ɗauka. Humaira da ba ta san wainar da ake toyawa ba, gaba ɗaya ba ta tattare da nutsuwa hankalinta kacokam a tashe yake, yana kan Musaddam da take jin kamar ta shaƙe shi. Ɗan firit da shi sai sirantaka, fari ne yayinda lebbansa suke baƙake wuluk shaidar yana shan sigari. Hannunsa dafe da ƙunci yake duban Humaira rai ɓace ya ce. "Ke! Ni kika mara?" Bai yi aune ba ta kara wanke shi da mari. "Yanzun ka daina tantama? Eh marinka nayi! Da kuma ace ni wata mai ikon ce, abin da ya fi mari shi zan maka. Ɗan iska marar tarbiyya! Ka yi amfani da son da ka ga yarinya na maka za ka cutar da ita saboda a gidanku ba a baka isassan tarbiyyar islama ba sai na bokon da bai amfaneka da komai ba. Idan har ba ka raba kanka da kanwata ba ina maka rantsuwa da Allah sai na yi maganinka ta yadda rayuwarka za ta ƙare a kurkuku. Ke kuma..." Ta juya gaba ɗaya ga Raihana wacce ke kuka ga dukkan ilahirin jikinta na rawa. Ba ta jin an taɓa tozarta ta irin yau, a gaban saurayin da take yiwa son duniya? Lallai Humaira ba ta da kirki ko kaɗan. Aljanun nata ma ƴan iska ne na ƙarshe da alama. "Kin ɗauka ba shi jikinki shi ne zai sa ya ga mutuncinki ya gane irin son da kike mishi har ta aureki? Toh kin yi kuskure, wallahi wallahi duk sadda kila bari wannan ɗan akuyan ya kusanceki kin cuci rayuwarki har abada Raihana, za kuma ki yi kukan nadamar da babu mai share maki hawaye. A haka kuke kirana da ƴar kauye, wannan ita ce wayewar? Toh wannan birnin naku na jahilai ku ke ciki, idan za ki farka tun wuri ki farka idan kuwa ba haka ba wallahi muddin irin haka ta ƙara faruwa a kunnen Abba. Wuce kuma mu tafi tun ban kakkaryaki ba." Raihana ta dubi Musaddam da ya haɗe girar sama da ta kasa yana kallonta, ta maida duba ga Humaira wacce ke cika da batsewa kiris take jira ta fashe ga hawaye kace-kace a fuskarta. Ta lura ma jikin Humairar har rawa yake. "Muddin kika bi umarninta ki sani daga yau babu ni babu ke Raihana, alaƙarmu ya zo karshe. Sannan ke kuma ba ki san waye ubana a ƙasar nan ba ko? Zan nunamaki daga kaina ba za ki ƙara gangancin marin wani namijin ba." "Musaddam ɗan gidan Alhaji Jafar Nababa, right?" Gaba daya har Humaira suka juya a inda suka tsinci muryar, Raihana ta yi mutuwar tsaye ganin Ibb Gusau mutumin da yar uwarta Futuha ke mahaukacin so tare da wani haɗaɗɗen guy wanda ko fuskarsa da take a haɗe ka kalla, sai ya burgeka. Kunyar da ta ji ne ya sa ta saurin amfani da gefen mayafinta ta rufe baki da hancinta gudun kar su gane ta. Humaira kuwa kallo ɗaya ta musu ta maida duba ga Musaddam ɗin fuskarta har lokacin a mugun ɗaure tana jiran ta ji amsar da zai ba da. Musaddam ya kai duba ga me maganar, nan da nan ya ji gumi ya karyo masa, Malaminsa ne a jami'a da ya taɓa yiwa gadara da matsayin Ubansa, shi kuwa ya nuna masa nashi Uban da matsayi sun kere na babansa. A sanadin wani rikicinsu sai da Musaddam din ya yi kwanaki uku a ofishin ƴan sanda kafin a fiddo shi. Ya kasa cewa komai sai shafar ƙeya, Ibb Gusau ya nuna shi da yatsa. "Kai ba za ka taɓa nutsuwa ba kenan a rayuwa ko? Ina mai gargadinka, wannan ya zama na ƙarshe, ke kuma zan ba ki lambata duk sadda kika ƙara ganinsa da ƙanwarki ki kirani kai tsaye nasan maganinsa. Ke kuma ki yiwa kanki faɗa ƴanmata, kar ki bari shaiɗan ya kaɗa maki ganga, irin su Musaddam ba su dace da ke ba. Daga ganin yanayin ƴar uwarki an san daga gidan mutunci ki ka fito saboda haka please be careful." Raihana da ta yi mutuwar tsaye da mamakin mutumin da Futuha ta ce ba ya magana mai tsawo yana zuba zance ta gyada kai. Ga kuma wani iri da ta ji cewa wai zai ba Humaira lambarsa. Aikuwa Humaira ta miƙa mishi wayarta ya sanya mata lambar ya danna kira ta fito kan wayarsa sannan ya miƙa mata. Musaddam dai na tsaye kamar an kafe shi a wurin ya kasa motsi sai wani ɗaci da ya ke ji a maƙoshi ganin an dake shi an kuma hana shi kuka. Ya yi biyu babu kenan. "Ko za su bi ka ka sauke su a gida?" Ya yi furucin da sassanyar murya. Sai a sannan ma hankalin Humairar ya kai gareshi karo na biyu don ta mance ma  da wanzuwarsa, ranta ya yi fari sol da taimakon da Ibb ya yi mata, ko ba komai ta ga tsoro fal a saman fuskar Musaddam wanda hakan ya fi komai faranta mata. Ganin irin kallon da Fadeel ke jifanta da shi ya sa ta kauda kai. "Aa mun gode, zamu hau ɗan sahu." Fadeel kamar ya tanka sai kuma kawai ya basar bai ce uffan ba. Humaira ta kalle su, kalmar godiya ce kadai ta fito a bakinta kafin ta juya ta dubi Raihana. "Muje." Ba musu kuwa Raihana ta bi umarninta, zuwa yanzu jikinta a mugun sanyaye yake. Ta dai tabbata Humaira ta fi ƙarfinta. Ba kuma ta son tada wani borin su Ibb su ƙara ganin rashin kunyarta ƙarara. Bayan tafiyarsu, Ibb ya shiga yiwa Musaddam faɗa mai haɗeda nasiha, a karshe  ya ba shi damar tafiya. Sai da ya bar wurin sannan ya dafa kafaɗar Fadeel yana murmushi. "Toh ya aka yi?" Fadeel ya zura hannuwansa cikin aljihu ya fiddo hannunsa na dama riƙe da waya ya miƙawa Ibb gami da ɗan ɗara  gira kaɗan. Dariya Ibb ya yi ya girgiza kai. "No, haba Malam, da wuri haka?" Ya narkar da wuya. "Please, ina rantsuwa da Allah ban taɓa jin abin da na ji a kan wata ba sai ita." Murmushi Ibb ya faɗaɗa. "Alhaji da sannu dai Allah zai cika masa burikansa." Guntun murmushi Fadeel ya yi. "Ko? Kai kuma kana neman ka dakile faruwar hakan." "Ah wane ni? Ba ni na sanya maka." Ya karɓi wayar Fadeel da tuni ya buɗe, lambar Humaira ya sa a ciki sai kuma anan ya dafe goshi. "Oh no, ka ga ko sunanta ba mu sani ba. Da me zan maka saving?" Jin haka ya lumshe idanunsa yana hasko kyakkyawar fuskar Humaira wacce kumatunta har wani sheƙi suke saboda fushi, ya kuma lura ko ya ya ta buɗe bakinta sai wushiyarta ta bayyana. A hankali ya ce. "Mrs Fadeel." "What?" Ibb da kunnuwansa kamar ba su ji ba ya tambaya. Buɗe idanunsa ya yi ya dube shi dakyau. "Yes, haka za ka yi saving lambar." "Aa, riƙe ka yi da hannunka. Ka gani koda wani abun ya je ya zo, ba za ka kalle ni da shi ba." "Babu abin da zai je ya zo face alheri. Da yardar Allah ba ta da miji sai Fadeel." Ya ba wa Ibb amsa sa'ilin da ya sa hannu ya karɓi wayar. Aikuwa da hakan ya yi saving sunan. Ibb dai mamaki ma yake, to kodai ɗan lokacin da ya kwashe ba ya tattare da su ya sauya ne daga yadda ya san shi? Mutum da zancen aure ma ba ya so a yi mishi, daidai da hira idan ta budurwa ce aka ɗauko cikin abokai yanzun gayyar za ta watse a wurinsa don tsam yake tashi ya bar musu wurin yana mitar ba shi da lokacin shirme. "Sai goben?" Maganar Fadeel ta katse mishi tunanin, ya sauke ajiyar zuciya. "Allah ya kaimu. Amma ina mai ba ka shawarar kada ka zurfafa, duk abin da aka zurfafa ana shan wuya a cikinsa. Balle kuma irin wannan faɗawar da ka yi lokaci guda." Madadin ya amsa sai ya yi murmushi ya soma tafiya kawai, sanin da Ibb ya yi shikenan sallamar tasu ya sa shima ya nufi motarsa cike da fatan shi din ma Allah ya kawo mishi mace ta gari ya huta da gorin ƙannensa sun yi aure sun bar shi da Mahaifiyarsa ke yawon mishi. ***   A can gida kuwa, Mami tun da ta ji wai Humaira ta fita ba da saninta ba gaba daya ta ji ta kasa sukuni. Har ta kasa ɓoye ɓacin ranta ta hau faɗa a falon. "Wannan wani sabon salo ne da har Humaira za ta sa ƙafa ta fice a gidannan ba tare da neman iznina ba? Me take so na faɗawa Abbanku idan ya tambaye ta?" Tasleem da Futuha suka kalli juna suka taɓe baki, yayinda Ummita da aka kira tuhumar ko ta san inda take, ta ke gefen kujera a zaune. "Toh wai Mami, ba Humairar na da waya ba? A kira mana." Faɗin Mubarak wanda ke shigowa falon daga masallaci, tun kafin fitarsa Mamin ke faɗan fitar har dai ya dawo ba ta chanja zani ba. Ganinsa ne ya sanya su Tasleem nutsuwa. Mamin kuwa dubansa ta yi kafin ta kauda kai ta ja guntun tsaki na takaici. "Kira na nawa kuma? Wayarta idan ba a kashe take ba to na fi tunanin babu network." Ya kai duba ga Ummita. "Ke ba ta faɗamaki komai ba?" Kafin Ummita ta amsa, Futuha ta yi caraf. "Nima dai ita nake zargi don babu ta yadda za ta fita ace ba ta sanar mata ba. Bakinsu daya wallahi Yaya." Kallon da ya watsa mata ya sa ba ta ƙara cewa uffan ba, Mami ta ja tsaki karo na ba adadi ta nufi ɗakinta. Ganin haka Ummita ta miƙe ta yi nasu dakin da zummar gabatar da sallar La'asar, ita kanta tunanin da take yi bai wuce na inda Humaira ta je ba tare da neman iznin Mamin ba kamar koyaushe. Tsoronta kar Abba ya dawo ya tambaye ta ace ta fita alhalin ba ta da makaranta yau. Aikuwa dai sai wuraren biyar da mintoci suka shigo gidan, ko ci kanki ba wanda ya cewa wani a cikinsu. Su Yassar dake zaune cikin abokansu a kofar gidan su ka bi su da kallo. "Ga uwar girman kan gidannan ta dawo." Faɗin wani abokin Yassar yana nuni da Humaira. Tun ranar da ya yi gangancin kulata da sunan so ta ci mishi mutunci yake jin tsanarta. Yassar tsaki ya ja. "Kai ka so ai dama ka ga kalar nata girman kan, amma ga mata a gari kamar ƙasa ka rasa ta kulawa sai wannan ƴar ƙauyen nijar din?" Sauran suka yi dariya. Shi kuwa Yassar miƙewa ya yi ya bi bayansu ganin kamar Raihana na sharce hawaye, jikinsa har mazari yake don muddin ya kasance Humaira ce sila to ya rantse sai ya rama mata koda kuwa gaban Abba ne ba Mubarak ba. *** A falon gidan suka iske su Futuha zaune, sallamar Humaira ta dakatar da Ummita daga shiga kicin, ta dawo cikin falon da sauri don ta ganewa idonta ko ita ɗin ce. Futuha da Yasmeen kuwa ido suka bi Raihama da shi ganin yadda fuskarta ta yi ja ga shatin yatsu kwance saman fuskarta. "Ke, Raihat, me nake gani haka? Uban waye ya mareki?!" Tasleem ta faɗi da buɗaɗɗiyar murya tana kallon Humaira. Humaira da ita dinma kiris take jira ta dube ta dakyau. "Ni ce nan, ko za ki rama mata ne?" Aikuwa jin haka gaba daya Tasleem da Futuha suka yo kanta, ta kuwa shiga tarewa, duk wacce ta bugeta sai ta sa hannu ta rama da iyakar ƙarfinta, duk da cewar su biyu ne a kanta, ta yi iyakar kokarinta amma itama ta ji jiki. Ummita ta hau kwala ihun kiran Mami, ga Yassar a gefe da ya ƙi ya tsawatar don dama ya jima da haushin Humaira a ƙoƙon ransa. Raihana na ihun su kyaleta akan ba ita ce ta mare ta ba amma inaa dama sun jima su na dakon rana mai kamar ta yau din hakan ya sa da gayya suka yi biris da ita. Yayinda a ɓangarenta shakkar tonuwar asirinta take musamman da ya kasance Yaya Mubarak na gari, ta sani koda ace Abba bai taɓa lafiyarta ba, shi kam ban da lafiya ma, hatta da wayar da take tunƙaho da ita sai ya raba ta da shi. Kusan a tare Abba da Mami suka shigo falon. Wata tsawa Abba ya daka da ta sa gaba daya suka saki juna, Humaira gefen kumatunta na fidda jini sakamakon yakushi da ta sha da dogayen faratan Futuha. Su kuwa daga mai riƙe baya, sai mai riƙe gefen fuska da naushin Humaira ya kumbura har ya tasa. Mami zuciyarta ta yi wani iri, ta kasa magana ta yi shiru tana kokarin hadiye abin da ke cinta. Abba ya karaso falon ya dube su gaba daya. Humaira tuni ta durkusa, ganin haka su ma suka durƙusa. "Mene ne hakan? Wane sabon shashanci ne haka? Ke Humaira wadannan ba su girmeki ba? Ku kuma manyan wofi ba kanwarku ce ba? Duk me ya kawo rigimar ne?" Humaira ba ta ce uffan ba, Yassar ya yi saurin sa baki. "Abba ba fa wani abu ba ne, Humaira ce ta mari Raihana har fuskarta ya yi shatin yatsu, shi ne don Tasleem ta yi magana kawai sai ta taso mata da faɗa wai ta mara ko akwai shegen da zai rama mata. Kalmar shege ya fusata su suka yi kanta da duka." Murmushi mai ciwo Humaira ta yi lokaci guda hawayen da take dannewa suka zubo samam fuskarta, zubar hawayen a inda Futuha ta mata rauni ya sa ta jin zafi amma ba ta ko damu da sharewa ba don wata azabar ta fi wata, ita daya ta san me take ji a zuciyarta. Ummita ma hawayen take na ganin yadda gaba daya Yassar ya juya magana. Ita kuwa Mami, karasowa ta yi ta ɗaga fuskar Raihana tana kallo. Tabbas mari ne, fuskar ta yi ja, ga yatsu kwance ta ko'ina a gefen fuskar. "Mari?! Mamana dagaske ne kin mari ƴar uwarki? Me ta yi maki da zafi har haka da kika ɗau hukunci da kanki?" Raihana nan fa ta shiga zare-zaren ido, Humaira ta kalleta na ɗan dakiku, har abada ba za ta tona mata asiri gaban iyayensu ba. Mami ta kai matsayin da ko laifin ɗiyarta ta gani za ta iya rufa mata asiri don haka dakyar ta haɗo abin fadi. "Ka yi hakuri Abba. In sha Allah ba zan kara ba." Nan kuma Abba ya kara fusata. "Oh, dagasken kenan kin mare ta ko?! Wannan ai hauka ne! Kamar babu manya a gidan? Ke waye ya mare ki?" Nan ya shiga bude mata wuta, sai da ya gama sannan ya maida hankali ga su Futuha wadanda duniyarsu ta yi dadi, ko babu komai wacce suke yiwa kallon ta fi su a wurin Abban yau ya rufe ido ya wanketa tas kamar zai kai duka. Hakan yasa ba su ji zafin nasu faɗan sosai ba. Sai da Mami ta sa baki sannan ya bar wurin. Humaira na ta kallon fuskar Mamin don ta hasaso yanayinta amma ba ta fahimci komai ba sai dai jikinta ya yi sanyi ganin ko kallonta Mamin ba ta yi ba. Hakan na nufin ba ta ji dadin hukuncin da ta yiwa Raihanan ba? *** "Ban da abinki Humaira, duk son da Mami za ta nuna mana ai ba zai kai son ƴaƴan da ta haifa da kanta ba. Ni ba abin sa ya fi ban haushi irin yadda ba a damu da tambayar inda ku ka je ba. A jikina nake ji ba hakanan kawai za ki mari Raihana ba, akwai abin da kike ɓoyewa. Amma wace rana zai maki? Zai siya maki daraja ne a gun Raihana da yan uwanta kike zato? Babu ɗaya fa, halinsu ne ba na jin za su taɓa sauyawa." Ummita ke zubo mata zance sa'ilin da suke kicin su na gudanar da girkin dare, awanni kusan biyu bayan afkuwar komai, Humaira wacce tuni ta yi wanka ta sauya shiga cikin riga da siket ƴan kanti ta yi murmushi daidai sadda ta motsa tukunyar miya ta rufe gami da rage wuta. Juyowa ta yi tana kallon Ummita da ta mayar da hankali tana juye farar shinkafar da ta dafa a cikin ƙaton warmer. "Ban damu da abin da kowannensu zai ce ba, ban kuma damu ko Raihana ta sauya ba ko aa, abin da na sani shi ne, ko a gaban waye, kuma a ko'ina ne, su din ko naƙi ko na so, ƴan uwana ne na jini, ba zan taɓa ganin abin da zai cutar da su na yi shiru na zuba ido ba, sai inda karfina ya kare. Kar mu ja zancen Ummita, ni yanzu damuwata Mami, ta ina zan soma wanke kaina a wajenta? Na mari diyarta har shatin yatsuna sun bayyana ƙarara a saman fuskarta, anya kuwa za ta karɓi dukkan hanzarina? Ni dai na san soyayyar uwa akan nata, dagaske ne Mami na yi mana so na hakika, amma wace uwa ce za ta kara kallonka da ƙima alhalin ka sa hannu ka daki nata?" "Sai ni nan, Maryam." Gaba daya suka kalli bakin ƙofar shigowa kicin din, Mami ce wacce ta tsinkayi zantukan Humaira na karshe. Humaira ta zuba mata idanu tana so ta ga ko za ta fahimci yanayinta, ba ta gane komai ba sai murmushin da ta gani kwance saman fuskarta. Kicin din ta karasa shigowa sosai ta ce. "Sai ni nan Maryam, haba Humaira, kina zaton ba ni da hankali ne? Na sani duk yadda aka yi akwai wani abu da Raihana ta yi kika yi mata wannan hukuncin. Kar ki manta tazarr fitarku ba nisa, da nayi nazari sai na ga kodai wani wurin za ta je da bai kyautu ba kika bi bayanta? Kar ki sa komai a ranki, koda ba ki faɗi komai ba ni na fahimceki kinji ko?" Humaira ta sauke nannauyan ajiyar zuciya na samun nutsuwa. Wai mami wace iri ce acikin matan uba? Komai nata daban ne, kirkinta da kawaicinta akwai mugun yawa. Sai kunya ta lulluɓe ta, ta sunkuyar da kai. "Kiyi hakuri Mami. Ban yi..." "Bana buƙatar ji ko sanin komai kinji ko? Komai ya wuce. Ku hanzarta shirya kayan abinci, Abbanku na jin yunwa." Suka amsa da toh a gaggauce suka ci gaba da aiki, Mami ta fice daga kicin din fuskarta ba yabo ba fallasa. *** Kwance take saman gadonta tana buga game a waya, hankalinta kacokam ya tafi a game din sai ga kira ya shigo. Ta yi tsam tana duban wayar, lamba ce da ba ta da masaniya a kanta. Ganin haka sai ta katse kiran ta ci gaba da game dinta, aka kara kira, ta katse, a na uku ta ɗaga a fusace amma sai ta danne ta yi sallama. Jin muryar namiji ya amsa sallamar ya sa ta jin wani abu tun daga tsakiyar kanta har zuwa yatsun ƙafa, ba ta san ma'anr hakan ba. "Ina mai ba da hakurin yi maki katsalandan a rayuwa. Hope ba za ki damu ba idan na ce jiya na karɓi numbernki wurin Ibb Gusau." Shiru ya biyo baya, ita ba ta fahimci komai ba don har ga Allah ta mance da su. Jin shiru ya sa Fadeel ƙara magana a tausashe. "Ok, ba ki gane ba ko? Jiya ni da abokina da ya ba ki numbernsa akan wannan saurayin ƙanwartaki, Musaddam nake tunanin sunansa ko?" Nan da nan ta tuna komai, wannan me kama da aljanun ne mai shegen kallo. Ta ja guntun tsaki kaɗan. "Uhm, na gane. Ina fatan lafiya?" Ya yi shiru yana jin amsarta a wata kala na daban, madadin ta ba shi haushi sai kuma ya ji bai ji haushin nata ba. "Lafiyar ce ta sa na kiraki. Suna na Fadeel, magana nake son mu yi amma ta fi ƙarfin waya, idan kin ba ni dama ko zan iya sanin kwatancen gidanku?" Ranta ya soma ɓaci, ta ji wani abu na taso mata. "Idan maganar ba za ka iya yinta a waya ba don Allah kada ka ƙara gangancin kirana. Hakan zai fi maka alheri, sannan ina bukatar ka goge lamba ta a wayarka, tunda ba wani muhimmin abu ne ya sa ka kira ba." Tana kai wa nan ta katse kiran, ta yi wurgi da wayar saman gado, game din ma ya fice a kanta. Ita kaɗai ce a ɗakin, sai ga Raihana ta shigo. Ko kallonta ba ta yi ba ta mike ta faɗa banɗaki, koda ta fito ganin Raihanan zaune saman gadonnata yasa ta mamaki. Fuska a ɗaure ta ƙarasa. "Malama lafiya?" Jiki a sanyaye Raihana ta soma magana. "Kiyi hakuri Humaira, na ja an maki faɗa an kuma zalunceki. Don Allah ki yi hakuri. Ina neman gafararki bisa dukkan abin da na taɓa yi maki a gidannan. Ban kara gasƙata kaunarki gareni ba sai a jiya da kika shanye faɗan Abba ba ki faɗi ainahin abin da ya faru ba. Wallahi na ji kunyarki sosai, kiyi hakuri ki yafemin." Taɓe baki Humaira ta yi tana fadin. "Ya wuce. Kar ki damu." "Dagaske kike?" Ta tambaya da sauri kamar za ta yi kuka don muryarta ta karye, Humaira ta zauna a gefe. "Ni ban taɓa binku da kallon maƙiyana ba, kallon da nake maku na ƴan uwana ya bambanta da irin wanda ku ke yimin. Sai dai dukkan wannan ba zai sa na ga abin da zai cutar da ku na kasa magana ba. Idan na yi hakan na ci amanar kaunar da Mami ke nunamin. Raihana mutunci da darajar mace ya fi gaban ta tsaya ta siyarwa wani ƙaton banza a waje. Musaddam da kike gani wallahi ba zai taɓa aurenki ba matuƙar kika yarda kika ba shi kanki a waje, ke koda ba ki bayar ba, yaron ba aure ne a ransa ba face iskanci. Idan kuma dagasken auren yake sonki da shi, meyasa bai taɓa zuwa nan ƙofar gidanku da sunan zance ba, kema kin san karya ne kawai. Tun wuri ki yiwa kanki faɗa ki rabu da shi zai fiye maki alheri." Raihana da tuni ta soma hawaye ta kamo hannun Humaira. "Toh naji Humaira, amma wallahi ina sonsa, wani irin so ne da ban san yanda zan fara yakice shi ba a rai. So ne da ya rufemin ido naji ko me Musaddam zai nema a wurina zan iya yi mishi." Sai kuma tausayinta ya lulluɓe ta, tana kuma godewa Allah da bai ɗora mata son kowane ɗa namiji ba balle har ya wahalar da ita. "Wannan son za ki yaƙa, domin halaka ne a wajenki. Musaddam ba sonki yake yi ba muna nan da ke watarana za ki ban labari. Ki kai kukanki wurin Allah sannan ki shagaltar da kanki wajen duk abin da kika san zai dauke maki hankali daga tunaninsa. Nima kuma zan tayaki addu'a har sai Allah ya amsa, ya rabaki da wannan makahon son. Ke ina kika hango dacewarki da shi wai? Wallahi ta ko'ina ke din ba ajinsa ba ce, ban da ma dai shi son da kike ikrari bai san inda zai je ba, ai sawun giwa ya shafe na raƙumi." Murmushi Raihana ta yi cikin jin salama, sai kuma hira ta buɗe tsakaninsu, tana ba ta labarin ainahin yanda aka yi ta hadu da Musaddam din. Humaira ta gefen ido na kallon wayarta da ke silent tana ta haske alamar shigowar waya amma ta yi biris da ita. Su na a haka Futuha ta dawo daga makaranta ta iske su, mamaki ya dabaibayeta, ta cire facemask din da ta sa don ɓoye kumburin gefen bakinta da Humaira ta daka, ba ta cewa Raihanan komai ba sai zama da ta yi gefen nata gadon tana ci gaba da kallon ikon Allah. Ita kuwa Humaira ko ta nuna ta san da wanzuwar wata a dakin bayan su. Can kuma Raihana na juyawa tana yiwa Futuha magana ta ga hasken wayar Humaira ta jawo. "Lah, kinga fa kiranki ake ta yi. Lamba ce. Kodai Ibb ne?" Jin sunan da ya fito bakin Raihana ya sa Futuha zaro ido waje a razane. Ita kuwa Humaira fuska ta yamutse. "Waya sani, tun dazu ya kira wai wani kwatancen gidanmu." "Wane Ibb din kika nufi Raihana?" Suka dube ta, sam Raihana ta mance, yanzu me za ta ce idan Futuha ta dage akan son sanin komai? Kada dai allura ta tono garma. Ita kuwa Humaira sai a sannan ta tuno ashe fa a hirarsu tana jin Futuha na yawan maganar son da take yiwa Ibb Gusau da haduwarsa. Kodai shi ne Ibb din da take magana? "Ibb Gusau wanda kika sani." Humaira ta furta da murmushi saman fuskarta, ta karbi wayarta a hannun Raihana ta katse kiran amma sai ta sa a kunnenta kamar gaske ta hau fadin. "Assalamu Alaikum, ina neman afuwa ka kira bana kusa. Fatan ka karasa gida lafiya?" Tana kaiwa nan ta sa kai ta fice daga dakin, sai da ta isa falo sannan ta kwashe da dariyar ganin yanda Futuha ta cika tayi tam har gefen bakinta da ya kumbura sumtum yana kyalli. Ta dai san ta harba mata bomb a zuciya. 10 Dariya take yi har ta shiga kicin ɗin, Ummita dake amsa waya tana lumshe idanu ta yi azamar katsewa tana dubanta. Humaira kuwa ganin haka ta karasa fuska dauke da walwala tana bin ta da kallon tsokana. "Waya kike amsawa ko? Shi ne ina shigowa kika yi saurin katsewa. Nidai ya kamata zuwa yanzu na san waye wannan majnun ɗin naki." Ummita dai ba ta tanka mata ba sai maida hankalin da ta yi wajen ɓarar tafarnuwa tana murmushi, sai kuma ta share zancen da hanyar fadin. "Wai dariyar me kike yi ne?" Sai a sannan ta tuna abin da ta yiwa Futuha, dariyar ta kuma taso mata. Ta fayyacewa Ummita labarin, baki buɗe take kallonta. "Ke kuma ina kika samu lambar shi?" Ita shaf ta mance Ummita ba ta da labarin komai, ta yi ajiyar zuciya. Labarin da ba ta so bayarwa ba amma ya zama dole ta sanarwa Ummita don ba ta da yar uwa kuma aminiya sama da ita. Ta labarta mata duk abin da ya faru da sanadiyyar marin Raihana ta kara da jan tsaki da fadin. "Shi ne wannan mayen ya takuramin da kira fa, toh ita Raihana ta yi zaton ma Ibb din ne. Ni kuma don na shaƙawa ƴar banza shi ne na sa wayar a kunne ina wayar gangan na soyayya." Ummita da iyakar burgewa yar  uwar ta burgeta sai ta shiga murmushi kawai da mamakin kaifin hankali da tunaninta, ta sani ko ita ba lallai ta iya shiru a irin wannan gaɓar ba. Amma ta gwammace kowa ya yi mata kallon rashin kyautatawa akan dai ta bayyana gaskiyar abin da Raihana ta aikata. Sai kuma karar wayar Ummitan ya katse tunaninta. Da sauri har su na rige-rigen ɗauka ita da Humairar, sai dai a karshe wayar ta faɗa hannun Humaira tana dariya, ga nata wayar ta na ta haske shaidar faɗowar saƙo amma ko a jikinta. "Ki yiwa girman Allah kada ki ɗaga." Gwalo ta yi mata suka hau zagaye a kicin din. "Sai kin rantse cewar za ki fadamin ko wane ne mai kiran." Da sauri ta amsa. "Eh wallahi zan fadamaki, yanzu dai ban wayar." Ba musu ta ba ta tana dariya, ta ja kujera ƴar tsugunno ta zauna tana duba nata wayar da saƙon ya faɗo tun ɗazun. _*Kar ki yi tunanin akwai abin da zai sa Fadeel ja baya ko tsoro. Ki tambayi wadanda suka san waye shi, yana da naci akan abun da zuciya da gangar jikinsa suka yi na'am da shi. Ba shi da saurin karaya, ba kuma ya jin zai soma daga kan ɗiya mace. Ina kuma farin ciki shaida maki ke ce halittar farko a mata da na ji zuciyata ta yi na'am da kasancewarta rabin jiki kuma abokiyar rayuwata. Nasara tana tare da wanda ya miƙa lamarinsa ga Allah. Have a nice day.*_ Ta karanta har da karkata kai kusan sau uku, sai ta ji ma abin kamar irin a fina-finan da ake haskowa a tashar Hausa da su Tasleem ke kunnawa. Ranta na wani irin huci da zafi, a gefe guda kuma duk da wannan radadin wai sai ta ji tana so ta san ma'anar kalmomin karshen da ya rubuta mai kama da farasanci da turanci. "Lafiya ki ka ba waya hankalinki?" Muryar Ummita ya katse mata tunani, ta isa wajenta ta miƙa mata waya. Har a sannan hausarta ba ta dawo daidai irin ta Kanawa ba. "Ɗan fassaramin ƙarashen saƙon nan, me yake nufi?" Ummita ta karanta tun daga farko, tun kuma somawarta take zabga murmushi don ba ƙaramin burgeta ya yi ba. "Fatan alheri ya yi maki a wannan rana. Kai Humaira wannan mutumin akwai iya tsara kalami, ina ji a jikina kin samu mijin aure." Guntun tsaki Humaira ta ja gami da warce wayarta tana ƴar harararta. "Ai ke ce mijin, ni raba ni da wannan shirmen soyayyar kin ji ko. Ba ni da lokacinsu." "Anya Humaira kalau kike kuwa? Ko dai sai an haɗa da addu'a?" Yamutse fuska ta yi kawai ta kwashi tafarnuwar ta dauraye ta watsa a turmi ta hau daka. Ganin haka itama Ummita ta share batun. A gefen Futuha kuwa, gaba daya ta yo kan Raihana. "Ke! Wane Ibb din ki ke nufi ne?" Raihana ta yi jim, ba ta son ta ce Ibb Malaminta allura ta tono garma don haka sai ta kife ta da fadin. "Ba fa wanda kike zato ba ne, wannan wani Ibb ne Ibrahim sunansa suka hadu da ita a hanyar islamiyya." Nannauyan ajiyar zuciya Futuha ta yi kafin ta juya ta koma gadonta tana jan tsaki. "Toh barkanta, amma da ace Ibb da nake mutuwar so da kauna ne wallahi sai na koyamata hankali. Ke kuma wani sabon salon gulma da munafunci tun da ta wanke maki fuska da mari kike wani shakkarta har da taya ta hira. Ke kika sani." Raihana dai ba ta tanka ba ta mime ta bar mata ɗakin. Amma ta sa a ranta babu wani abu da zai sa ta kara biye musu wurin nunawa baiwar Allah da ba ta ji ba kuma ba ta gani ba ƙiyayya kawai saboda don zuciya irin nasu. *** Gidansu cike taf da jama'a sakamakon daurin auren Fu'ad da aka yi a ranar, haka ya dinga kutsawa ransa duk a ɓace har ya shige bangarensu, kai tsaye dakinsa ya nufa, tun daga falo ya cire hularsa ya yi jifa da ita, hakanan babbar rigarsa blue itama ya ajiye saman kujera kafin ya zauna ya shiga kokarin cire covershoe din da ke a ƙafarsa da kuma safa. A duniya Fadeel ya tsani hayaniyar jama'a, wannan ta sa kansa har wani sarawa yake yi. Ya ja guntun tsaki gami da kwantar da kai jikin kujerar ya lumshe idanu. Zafi biyu ya haɗe mishi, ga na rashin samun haɗin kan yarinyar da yake jin ta a ƙoƙon rai, ga kuma wata irin yunwa da yake ji domin ko karin kumallo bai yi ba suka fice masallaci wurin daurin aure. Kowa kuma a dangin sai ya yo kansa da tsokana a wajen, su na fadin saura kai babban yaya. Wadanda ba su da labarin dawowarsa kuwa, sai a ranar suka gan shi. A hankali ya bude lumsassun idanunsa ya murza yatsunsa suka yi ƙara, har wani zogi suke yi mishi saboda gaisuwar da ya dinga yi da jama'a. Lokaci guda kuma ya miƙe ya nufi bandaki, hannun ya wanke tas da hand sanitizer sannan ya fito rike da karamin tawul yana gogewa. Ya yi daidai da shigowar Ibb tare da wani dan uwansu Imran. Sallamarsu ya amsa ya koma mazauninsa har da kwanciya wannan karon. Kafin Ibb ya yi magana ya riga shi. "Wai so ku ke na mutu? Yunwa fa nake ji." Harararsa ya yi. "Kai dai an yi ɗan iska, muna can Alhaji ya sa mu nemoka ku gaisa da abokansa ashe kai nan ka yo? To sai ka tashi ka shirya muje idan ya so kafin mu dawo na yiwa Anti Amarya magana a kawo mana abinci." Fadeel ya lumshe idanu. "Kasan Allah ba zan iya fita ko'ina ba, ni fa ji nake idan ma na kara sa ƙafa na fita cikin wannan ranar hanjin cikina za su fito waje." Imran ya kwashe da dariya, shi kuwa Ibb kamar ya shaƙo amininnasa haka yake ji. Yana niyyar magana kuma sai ga kiran Alhaji karo na uku. Ya ɗaga ya mishi bayani, dama bai tsammaci faɗan Alhajin ba, cewa ya yi babu komai maza ya yi waya a kawomusu abinci. Da wannan suka yi sallama shi kuma a nan take ya yi kiran Anti Amarya ya sanar da ita. A bangaren Anti Amarya wacce ta ci ado cikin arnen leshi ruwan toka da ya sha adon stones, ga ƙunshi ta yi sai baza ƙamshi take, jin wayar Ibb ya sa  da rawar jiki ta amsa ta ba ɗaya daga cikin hadiman gidan Larai umarnin haɗawa Fadeel da abokansa abinci za ta turo a kai musu. Ta shiga falonta inda yan uwanta hudu ke zaune su na shan hira. Uku a cikinsu matan aure ne, ɗaya yayarta sai sauran gaba daya ƙannenta. Ƙanwarta Murja dake kwance tana danna waya ta kai wa duka a ƙafa.  Ba shiri ta mike zaune. "Ke tashi maza ga dama ta samu, jeki wurin Larai na sa ta haɗa abincin su Fadeel ki kai musu, kika sani ko Allah zai sa a dace ko cikin abokansa wani ma ya ce yana so?" Jin haka babbar yayarta Saddika ta amshe. "Ke wallahi hakane kam, tashi Murja, Allah ya ɗora ki akan su." Murja ta haɗe girar sama da ƙasa. "Nikam wallahi Fadeel nake so. Shi dai za ku taya ni addu'a ya ce yana sona." "Kin ji wawiya, ke kanki kinsan kaf abokansa ma babu na yar wa musamman Ibb. Ai dai kinga irin jama'arsa da suka kawo masa ziyara muna nan dake a gidannan tun zuwansa ko?" Murja wacce ta zo hutun makaranta gidan ƴar uwarta ta, ta mike tana gyara zaman ɗaurin dankwalinta. "Nidai kam shi nake so, ai duk kyawunsu ba su kai shi ba. Malam ga aji na musamman. Kiga fa ko sadda su Sholy suka zo gidannan ko kallo basu ishe shi balle su ga haƙoransa. Nima din ba.." "Ki yi zaman hira har sai ya gaji ya turo wani ya karɓar musu abincin. Shashasha marar wayo kawai. Ana kai ki kina ƙin zuwa. Ke kika sani. Zauna har ki yi biyu babu." Jin haka da sauri ta fice daga falon tana dariyar maganar Zuwaira, mai bi wa Anti Amarya. A kwando ta ga Larai ta haɗa komai har da cokula da farantai, ta kinkima ta yi gaba inda ta tsallake yan uwan Alhaji da suka zo daga ƙauye ko kallo ba su ishe ta ba ballantana ta yi tunanin gaishe su. Su kam suna hau gulmarta da harshen fulatanci. A ƙasan ranta ta ja Allah ya isa. Tana zuwa ƙofar ta kwankwasa, Ibb ya ba da umarnin a shigo. Lokacin dukkansu har Imran sun cire babbar riga ana shan iskar fanka ana hira, sun zama su biyar a ɗakin sakamakon shigowar abokan Ibb biyu, Saifullahi da Idris. Da sallama a bakinta ta shiga, kasancewar Fadeel ne a saitin ƙofa ya bi ta da kallo ɗaya ya kauda kai ya maida saman kwandon dake hannunta. Dama abin da yake jira kenan, ita kuwa kusan zaucewa ta kusa yi sakamakon kwayar idanun Fadeel da suka haɗu da nata, gaba daya ta ji ta ƙara narkewa a tekun sonsa. A ranta tana ayyana ba gudu ba ja baya shi din dai ranta ke so. Babu wani abokinsa da ta ga ya burge ta, gwara ma Ibb don a baya tana mishi kallon hadadden saurayi duk sadda suka hadu ya zo gaida Alhaji, ita kuma ta zo gidan, yanzu kuwa ta fahimci Fadeel ya kere shi. "Ba sai kin zuba ba, bar shi za mu yi serving da juna." Fadin Ibb fuska a sake ganin ta sauke kwandon ta hau fito da kayayyakin tana shirin buɗe warmer. Ta kalle shi kadan tana dan murmushi. "Lah ba komai, bari na zubamaku, wannan ai aikinmu ne mata." Bai kara magana ba sai mayar da hankali ya yi ga Imran dake nuna mishi wani hoto a waya. Shi kansa Ibb ba mai yawan zance ba ne sai ta kama, don haka bai hanata ba. Shi kuwa gogan kallonta bai kara ba, sai Idris da ya zuba mata ido kamar ya haɗiye ta. Shi dai kam lokaci guda ya ji ta kwanta masa a ƙoƙon rai. Don haka bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya dubi Fadeel. "Wannan ƙanwarmu ce?" Tsaf Fadeel ya karance shi, don haka ya gyada kai kawai fuska ɗaure. Ita kuwa da rawar jiki ta miƙa kwanon abinci ga Fadeel. Madadin ya karɓa sai ya dube ta. Ta ji kallon tun daga tsakar kanta har tafukan sawayenta. "No, ki fara ba su tukunna." "Kai Malam, idan za ka karɓa ka soma ci ka karɓa. Tun ɗazu ka ke mana raki da kukan yunwa kamar wanda ya shekara bai ci ba. Wannan ta ya ya kake azumtar watan Ramadan?" Jin haka ya ja filo ya jefawa Imran a fuska, gaba daya aka sa dariya shi kuwa ya shafi sumar kansa yana mai lumshe idanu lokaci daya ya bude su akan Murja, wannan karon sai da ta ji miyan bakinta ya sarƙe ta sai ga shi ta soma tari ba ƙakƙautawa. Idris da sauri ya miƙa mata ruwan roba dake gefensa saman kafet. Ta karba ta sha tana satar kallon Fadeel da bai ƙara dubanta ba sai waya da ya ke faman dannawa. A haka da rawar jiki ta zuba kowa ta miƙa mishi. Friedrice ne da hadin coslow sai chicken pepper. Ta bude firij ta ciro musu lemuka ta ajiye. Daga haka ta sa kai ta fita. Tana fita Idris ya gyara zama ya shiga rantse musu akan ya ga matar aure shi dai yana sonta idan za'a ba shi. Fadeel ba ya fahimtar komai ban da ta cikinsa da ya ke yi, ganin duk da fankar da ke busawa yana gumi kawai sai ya mike ya cire rigarsa daga shi sai dogon wandon shadda da vest ya koma ya zauna. Sai da ya tashi da abincin tas kafin ya ɗauki ruwa ya kora ya dubesu. Kowannensu bai kai ga kammala ci ba, suka kwashe masa da dariya, shi kansa murmushi da tsaki ya yi lokaci guda kuma yana sa hankicif ya goge fuska. "Ku na da matsala wallahi, ba za ku gane illar da yunwa ke min ba. Yanzu sai ta tayarmin da ulcer." "Ai mun gane komai ranka ya daɗe. Ko za ka ƙara?" Saifullah ya faɗi da zolaya. Fadeel ya ɗan harareshi. "Saboda na zama rumbu ko?" Haka suka yi ta zolayarsa shi kuwa tuni ya maida kai kan wayarsa yana kiran abu na biyu da ya tsaya mishi a ƙoƙon rai amma har ta kammala ringing ba a ɗaga ba. Haka ya kira har sau uku, sai a na huɗun, aka ɗaga. Kafin ya kai ga cewa komai ta soma faɗa. "Wai Malam kai din maye ne?! Na ce ka bar kirana ka ƙi! Dole ne zuwanka gidan namu? Haba, wannan jaraba da naci har ina wai? Mtsw." Daga haka kit, aka kashe kiran, nan da nan kansa ya yi wata irin sarawa, dama ga ciwon kan da tun ɗazun yake ji. Gumi ya karyo masa saboda tsananin ɓacin rai, idanunsa tuni suka kaɗa. Sauyawar yanayinsa ya sa Ibb ƙuramasa idanu. Sai dai bai ce komai ba ganin ba su kaɗai ne a falon ba. Sai bayan da gaba daya suka fice don gaisawa da Alhaji sannan Ibb ya dube shi, lokacin ya mayar da kai jikin kujera ya lumshe idanu don har su Imran suka fita sun yi zaton bacci ne ya kwashe shi su na mishi tsiya. Shi kuwa duk yana jin su ba shi dai da karfin biyewa shirmensu. "Fadeel, wai meke faruwa haka?" Jin muryar Ibb yasa shi bude idanun, ya mike zaune sosai. "Yarinyarnan nema take ta kashe ni, daga ranar da na gan ta har zuwa yau ban huta ba." Cikin rashin fahimta Ibb ya dan wurga hannu. "Wace yarinya ce haka? A rayuwarka har ta hanaka sakat? Wace ce?" Tsakaninsa da Allah ya yi furucin don shi gaba ɗaya ma ya manta da wata Humaira. "Wacce muka haɗu da su tare da wannan ɗan iskan yaron." Shiru Ibb ya yi cikin nazari sannan ya dube shi a hanzarce. "Are you serious? Kana nufin ka kira ta?" Cikin ido Fadeel ya dube shi. "Yes, mun yi waya, amma duka ba masu dadi ba ne." Ya kora mishi bayanin duk abin da ya faru, Ibb ransa ya ɓaci. "Unbelievable! Yanzu akan mace ne ka shiga wannan yanayin? Fadeel kai ne dagaske dai wanda na sani? Mutumin da gaisuwar kirki abu ne mai wuya a ganka kana yi da wacce ba muharramarka ba, kai ne yau da bakinka ka ke faɗin cin kashin da wata shashasha can take maka? Kuma har ka ke tolerating in the name of love? Is this love or madness?" A fusace Fadeel ya soma magana, tun da Ibb ya jefi Humaira da kalmar shashasha ya ji ransa ya yi masifar zafi. "Oho! Idan ma haukan ne naji ni na jefa kaina ai ba da sa hannunka ba ko? Ban damu da duk wani tunani da za ka yi ba. Ina sonta, ka zo gabana kana kiranta da shashasha ba zan iya jura ba Ibb! Ina haɗa ka da Allah, idan har ba goyamin baya za ka yi ba toh kada ka kara kuskuren zaginta a gabana. Kawai dai ina ji a jikina wataran za ta gane ni din masoyinta ne na gaskiya." Yana kaiwa nan ya mike ya nufi hanyar ɗaki, Ibb kuwa baki a wangale yake binsa da kallo har ya ɓace masa. Meke damun Fadeel? Ya jefawa zuciyarsa tambaya, a take kuwa amsar ta zo masa, Soyayya ce. A fili ya ce. "Idan kuwa har wannan ita ake kira da soyayya, ina nemawa kaina tsari da ita. Kai kuma Fadeel ina roƙon Allah ya yayemaka wannan haukan son." Daga haka ya mike ya fita a dakin domin shi har ga Allah ba ya fatan wannan rashin hankalin da mace za ta zage shi ya kasa daukar mataki a kanta. Ko ƴar uban wace ce ba zai ƙara yi mata kallon wata abar so ba, ballantana har ta ci galabar yi mishi son ranta. *** Humaira na  kwance a yammacin ranar juma'a ta ji ihun ƴan matan gidan ya karaɗe falo, ta mike zaune tana mutsistsiƙa idanu. Hayaniyar ta mene ne? Kafin bacci ya gama wartsake mata sai ga Ummita ta shiga fuska ba yabo ba fallasa. "Wai hayaniyar me ake yi?" Fadin Humaira. Tsaki Ummita ta ja haɗi da taɓe baki. "Aunty Jannat ce ta zo, kanwar Mami." Humaira ta zaro ido, ba ta taba zama da ita ba amma ta sha jin labarinta a bakin Ummita na irin uƙubar da ta sha a wajenta sadda tana rayuwa a gidan. "Dagaske? Ki ce mun shiga uku." Ganin ruɗewae Humairar har ya so ya fi nata ne yasa ta dariyar dole wanda ba ta shirya masa ba. "Ke da ba ki taɓa zama wuri guda da ita ba? Ba lallai ki fuskanci matsalar da na fuskanta ba ai." Ita dai Humaira ta ji ne kawai ba don ya zauna a kwakwalwarta ba. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* Suna nan zaune Humaira na cewa  ita kam za ta so ganin ya wannan Jannat din take mai shegen son mulki sai ga Muhsin da Waleed sun faɗo ɗakin a  guje. Kira ne daga Mami akan su fito a gaisa da Jannat. Ummita ta dafe kirji, yayinda Humaira mikewa ta dube ta. "Wai ya haka, kinsan fa yarannan akwai daukar zance yanzun sai su fasalta musu yanayinki." Ummita sai ta maze ta mike. Suka kama hanyar falon, tun kafin ma su kai ga ƙarasa shiga ta hange ta. Kamanninta sak da Mahaifiyarsu wato Anna. Kusan har ta so ta fi Mamin hasken fata, siririya ce ba ta da tsawo duk kuwa da cewar tana daga zaune ne. Yaranta ƴan biyu tamkar an tsaga kara an karya, ba su wuce sa'o'in Muhsin ba. Wato shekaru goma a duniya. Riga da wando ne a jikinta sai abaya dake ajiye a hannun kujera wanda ga dukkan alamu cire ta ta yi. Gashinta ya sha kananun kalba an tufke a tsakiyar kan ya yi kamar ta sa ribos din acuci. Gaba daya iyalan Mami na falon ciki kuwa har da Anna wacce ba kasafai ta fiye fitowa ba. Humaira ita kanta sai da ta sha jinin jikinta ganin Anna a falon, sai da itama ta ji kamar ta ja hannun Ummitan su juya. Aikuwa su na ganinsu Anna ta tamke fuska gami da juya harshe zuwa buzanci. Ko me ta fadi oho, gaba daya suka kalli su Humaira, matasan suka gimtse dariyarsu sakamakon Mubarak dake zaune, sun tabbata muddin suka ce fiddo shi waje to fa kashinsu ya bushe wurinsa.  Hatta da Raihana ba ta ji dadin zancen Anna ba domin har ga Allah yanzu ba ta da matsala da su, ta riƙe su ƴan uwan na gaske kuwa. Ita kuwa Jannat kallon Humaira ta ke yi kamar wacce ta ga kashi. A yatsine ta amsa gaisuwarta, Ummita kuwa gaisuwar ma ba ta samu ba sai harara da ta watsa mata ta ja tsaki. "Wai Anti Jannat har yanzu wato kina nan yadda na sanki." Mubarak ya fadi ransa duk ba dadi, tun daga kalmar agolar da Anna ta kira Humaira da shi har zuwa yanda Jannat ta karɓi gaisuwarsu.  Rai a ɓace ta amsa. "Toh ko za ka sa hannu ka buge ni ne? Dama ai kai na faɗa can dai dangin uba ka biyo ba mu ba." Zai yi magana da sauri Mami ta ɗaga mishi hannu, aikuwa abin da take gudu shi ya afku domin Anna faɗa ta hau yi kamar ta ari baki wai laifin na uwarsa ce da ta fifita bare a kan nata. Ganin dai abu ya ƙi ƙarewa Humaira ta miƙe tana mai jan hannun Ummita, itama ba shiri ta miƙe sun kama hanya tana ji Jannat ta kwalawa Ummita kira tana ba ta umarnin ta ja Hassan da Hussein ɗakin su Muhsin ta musu wanka. Ita dai Humaira a fusace ma ta karasa ɗakin don ta matsu ta daina jin muryar tsohuwarnan da ma Jannat din wacce ta ji tsanarta lokaci guda ya rufe ta. Me ake da wanda bai san daraja ta DAN ADAM ba? Ita kadai a dakin ta yi ta mita tana tsaki. Ji take kamar ta je ta shaƙe wuyansu baki ɗaya. Sai kuma ta yi kwafa tana cije lebbanta, ita kadai ta san damuwar da take dannewa a ranta, amma a kwanakin nan abin yana neman fin karfin zuciyarta. Damuwar bai wuce Abba ba, mutumin da ya kasance bango majinginarta a gidan, wanda shi take yiwa kallon uwa kuma da uba. Wannan kauna da soyayyar da ya nuna mata a farkon zuwanta gidan yanzu ta rasa laifin da ta yi mishi ya sauya. Hira ma ya ƙi ba da fuskar ta ja shi da shi, idan har ita ɗaya ce a falonsa, nan da nan zai hau wasu ƴan aikace-aikacensa kamar gyara takardu ko kuma kiran abokan cinikayya, shaida dai ta cewar ba ya son ta ja wani dogon zancen. Ba dai za ta ce ba ya mata fara'a ba ne, sam a'a, sai dai babu ja a jiki balle har su shaƙu tamkar yanda ya nuna a farkon zuwanta. Toh wanda ma ka ke taƙama da shi bai wani damu da sha'aninka sosai ba ina kuma ga wasu can da har gobe sun ƙi karɓarta matsayin ƴar uwa ta jini? Kewa, kewar Dada da Kawunta duka suka mamaye ta, ba ta san cewar ta soma zubar da hawaye ba sai bayan ta sa hannu saman fuskar ta ji danshin lema. A hankali ta share su, ya kuma yi daidai da shigowar Raihana ɗakin. Ganin hawaye a fuskarta gaba daya sai ta ji ba dadi, ko ita ce ake yaren da ba ta ji tsarguwa yake sanya ta ballantana kuma wannan da dama din sun san ba da kowa ake ba sai su. "Humaira kuka? Don Allah ki yi hakuri." Ta fadi a sanyaye gami da zama a gefenta. Jin haka ta yi murmushin da ya fi kuka ciwo lokaci guda tana gwale idanun da hannu tana share su. "Ke ba fa komai, ba kuka nake ba. To me aka yi da zan yi kukan?" Raihana itama murmusawar ta yi ba don ta yarda ba, ta sani Humaira akwai juriya da nuna jarumta, sai dai kuma itama ai ƴar adam ce, tana da zuciya ta kuma san meke ma ta zafi. Kafaɗarta ta dafa. "Na sani su Anna ba su ..." "Raihana mu bar zancen, ya wuce wallahi. Ai komai mai ƙarewa ne. Lokaci ne." Cewar Humaira da sauri tana katse Raihana don a duniya yanzun idan da abin da ta tsana bai wuce a ambaci sunan Anna ba. Ta tsani mutum da ba ya ganin kowa da gashi. Tsohuwar sam ba ta riƙe girmanta. "Kinga kuwa mutuminki koda wasa bai ƙara gangancin kirana ba?" Maganar Raihana ya katse tunaninta. Cikin rashin fahimta ta ce. "Wa fa?" Ta yi tambayar don har ga Allah ta mance, sai kuma bayan ta yi ta tuno da Musaddam din. Ta ɗan ɗaga gira. "Au, ɗan iska za ki cemin." Suka ɗan yi dariya. A haka su Tasleem suka shigo ɗakin suka iske su.  Zuwa yanzu Raihana ba ƙaramin haushi take ba su ba don haka daga kallo daya ba su kara bi ta kansu ba. Tasleem ta nufi sif din kayanta ta buɗe  ta sa hannu a ƙugu tana kallo. "Oh God! Ni wane kaya ma zan saka? Wallahi gaba daya na diririce." Futuha da ta faɗa saman gadonta ta yi dariya. "Atoh, sai ki ƙure a daka ko ba komai dai wannan ne first meeting ɗinku." Raihana na jin haka ta mike da sauri ta karasa ga Futuha. "Wai Hamza D ne zai zo?" Harararta suka yi a tare, Tasleem ta ja tsaki. "Ina ruwanki? Ai ke yanzu munafuka kika zama. Ba a sirri da ke." Humaira ta yi tsam ta mike ta fice a dakin ba ta ko kalle su ba. Cin fuska ne ta san za a yi mata. *** Rayuwar ta ci gaba da gudana, Humaira tun tana ganin ire-iren bautar da Jannat ke sanya su na ƙare ne abin dai ya ci tura. Daidai da wankin pant da rigar mama su take ba, Mami ke tsawatarwa a wasu lokutan shiyasa kawai su ke hakuri. Idan kuwa ta kai Humaira abin ya ishe ta rantsuwa take yi da ƙari cewar ita ba za ta wanke ba, sai Ummita ke tausarta ta karɓa ta wanke gudun samun matsala. A wannan gaɓar kuma ba irin takurawar da Fadeel ba ya yiwa Humaira, iyakar ƙularwa ya yi mata, ta yi bakaken maganganun amma ko gezau, kusan kullum sai ya aiko mata da saƙonninsa da ke yiwa Raihana dadi. Ita ke karɓa ta yi ta karantawa har a wasu lokutan ta yi yunkurin ba shi amsa, Humaira ta nuna ba ta so. Jannat ba ta bar gidan ba sai da ta yi wata ɗaya cif. A sannan tuni Mubarak ya tattara ya koma, shima daf yake da kammala Masters. Yayinda  Yassar da Dawud suka soma jarrabawar ƙarshe na kammala degree dinsu a jami'a. Su Ummita ma tuni an koma karatu, Humaira kam ta yi nisa a fannin girke-girke don yanzu girki ɗaiɗaiku ne ba ta iya ba, kama daga cimar fulawa har dai sarrafa shinkafa da sauran kayayyakin abinci. Girkin gidan zuwa lokacin ya koma kan ta rankatakaf don kowa burinsa ta girka ya ci. Ita kam ko a jikinta, za ta yi girkin ba son jiki amma fa ba ta yarda da wulakancin su Yassar da Tasleem masu cewa su na son cin wani abu daban.  Yassar su na dab da kammala jarrabawarsu ne suka tada hankalin Mami lallai sai ta tambayar musu Abba kuɗin da za su haɗa party da abokan karatunsu sai dai duk inda  suka ɓullo Mamin ta ƙi asalima cewa ta yi su tuntuɓi Abban da kansu. Yassar ya mike tsaye yana huci. "Shikenan, idan Abban ya zo zamu yi mishi maganar. Mu dai gaskiya wannan karon ya sakar mana mu fita kunyar abokai. Wannan rayuwa har ina." "Ni ban san irin Abba ba wallahi, Mami ke ma ba kya mishi magana, tun farko ai Anna ta fadi, ke kika ba da damar ba ya hidimta mana sosai. Nifa Allah kuwa har kunyar nace Babana mai kudi ne nake, saboda ba a gani a jikina." Dawud ya fadi yana daga tsaye dafe da kujera. Mami ta yi mishi daƙuwa. "Karɓi nan Dawud, shi uban naku sa'anku ne da ku ka tsaya ku na wannan ɓarin zancen a kansa? Kuna maganar kamar yau idan kun je gabanshi za ku iya maimaitawa? Kunsan Allah ku kiyaye ni, gaba daya zan tattaraku na kai kararku wajensa tun da dai shi kuna shakkarsa." Suka ƙara tunzura, Humaira na gefe tana gogewa Mami mayafi bayan ta kammala goge nata kayan dalilin wutar nepa da aka kawo, biki ne Mamin za su je har da ita na ɗiyar mijin Anti Laila malamar girkinta. Katin gayyatar har ita aka ba da ta kuma tabbata saboda mutuncin da suke yi da Shema'un ne, sannan Anti Lailar ma ba ta da matsala ko kaɗan.  Gaba ɗaya hirarsu babu wanda ba ya shiga kunnuwanta, tana mamakin irin wannan rashin tarbiyya na su Yassar da ba sa tauna zance kafin su furzar kan kowa ma. Haka suka yi ta mita a karshe dai kiran sallar la'asar ya sanya su tattarawa su bar falon. "Allah ya shiryamin ku." Humaira jin furucin da Mami tayi kafin ta wuce dakinta yasa ta amsa da amin, zuciyarta sai ta cika da tausayin Mamin. Matar dai na iyakar kokarinta a kansu. Ba zato ta ji an watso mata kaya saman kafafunta da ke miƙe a harɗe. Ta ɗaga kai ta dubi mai wannan aiki. Futuha ce tsaye daga ita sai vest da leggings. Gashinta a barbaje a gadon bayanta take duban Humairar fuska a yamutse. "Ɗan dannemin kayan nan kafin su dauke wuta." Kallonta ba ta kara yi ba ta hadiye zafin da ta ji na wannan kalar rashin mutuncin na Futuha. Itama daga haka ta juya zuwa daki, ƙwafa ta yi ta kuma rantse ba za ta yi ba. Hakan yasa tana kammala na Mamin, ta hada da nata kayan da ta goge ta miƙe bayan ta ɗauke dutsen gugar a wajen gudun kar su Waleed su taɓa.    Dakin Mamin ta soma shiga, sallah ta iske ta tana yi don haka ta ajiye mata a saman gadon kusa da wani haɗaɗɗen leshinta peach colour da ya sha adon duwatsu, ya hau sosai da mayafin. Humaira har sai da ta murmusa don tuni ta hango Mamin a ciki, karshen kyau ko ba a faɗa ba ta sani kalar da kuma kayan za su karɓe ta. Abar ka da farar mace. Koda ta shiga ɗakinsu Tasleem na tsaye tana fente fuskarta da hoda. Ita kuwa Raihana tuni ta shirya tsaf cikin wata maroon atamfa mai haske an yi adon yellow colour jikinta sai dai bai yi dau ba. Tana tsaye ta karkace sai hotuna ta ke yi a gaban window. Futuha da alama tana bandaki. Suka dubi juna da Raihana, da wani irin zumudi ta karkace hadi da ɗan ɗaga gira. "Ya? Na yi kyau?" Humaira ta yi mata murmushinnan nata mai fiddo da zahirin kyawunta. "Kin fito tsab. Masha Allah." Raihana ta yi dariya, ita kuwa Tasleem dogon tsaki ta ja. Ba wanda ya ce mata ci kanki a cikinsu. Kasancewar ta yi wanka kafin zaman guga kuma ba ta da sallah hakan yasa ta kawai ta shiga sauya kaya. Itama atamfar ce amma nata dark brown ce mai haɗe da milk colour. Tana cikin shafa hoda Futuha ta fito daga wanka tana baza ƙamshin sabon showergel da suka ci arzikinsa a zuwan Antinsu Jannat gidan. Kallon Humaira ta yi kafin ta kalli gadonta ta gani wai ko ta ajiye mata kayan amma wayam. Don haka a fusace ta dube ta. "Ina kayan da na ba ki guga?" Humaira ta kalle ta da irin kallon wulakancin da suka saba yi mata itama. "Ai gugan Mami kika iske ina yi ko?" "Shekara kika yi kina gogewa Mamin mayafi? Don tsabar is..." Ba ta kai ga ƙarashewa ba ɗif aka ɗauke wutar, aikuwa Raihana ta tuntsire da dariya itama Humaira sai da murmusa a ranta tana fadin Allah ya ƙara. Nan fa Futuha ta hau zuba fada wai Humaira na sane iskanci ne ta fara sabo, tunda har ba a isa a sanya ta aiki ta yi ba. Ta tattara ta ba banza ajiyarta duk da cewa ranta wani irin tafarfasa ya ke yi na irin zagin da Futuha ke yi mata. Korar yunwa dai ya ƙi fita a bakinsu, ta kasa jurewa ta juyo, kamar ta maida martani da cewa su dinma asalin uwar Maminsu Nijar din ne, daga can suka fito can kauyen Agadas sai dai ta haɗiye tuna albarkacin Mami. Ummita ta shigo dakin, ita tuni dama ta shirya cikin atamfarta mai kyau ruwan sararin samaniya. Fitar da ta yi aiken Mamin ne zuwa siyan kati. "Mami ta ce ku yi sauri." Wannan ne ya katse zancen, kayan da Futuha ba ta sanya ba kenan sai kuwa wani ta sauya. Ba wata kwalliyar hayaniya Humairar ta yi ba amma iyakar kyau ta fito tsaf. Ba su suka yi haramar tafiya ba sai biyar da kusan rabi. Koda suka fito baki daya, Ladidi kawai aka bari tana musu a dawo lafiya sai kuwa su Muhsin dake can ɓangaren Anna, Ummita ta dube ta da murmushi. "Kin yi kyau sosai." Ta riƙe haɓa. "Idan babu wadannan buzayen a kusa ko?" Suka yi dariya. Anan farfajiyar gidan suka sha hotuna a wayar Raihana dake faman jan su, su Tasleem na gefe su na kallonsu ita da Futuha, ko me suke tattaunawa? Mami na fitowa suka shiga mota, kai tsaye ƙawataccen hall ɗin Marhaba suka nufa inda anan ne taron bikin. "Ba ku mance katinanku ba dai ko? Ba na so a je wurin taro mutum ya yi tsaye kamar wanda ya zo gayyar soɗi." Tasleem ta haɗiye dariyar muguntar da ya so kwace mata har sai da Futuha ta ɗan zungureta akan ta nutsu. Katin Humaira tun fitarta kiran Mami, ta ɗauke shi ta raba gida biyu ta wurga shi bayan gadonta. Ummita da Raihana suka amsawa Mamin bayan sun duba sun ga katinansu, ita kuwa Humaira ko jakar ba ta buɗe ba tunda dai ta riga ta sani duk wani abun buƙatarta ta jefa a ciki. "Humaira, Tasleem da Futuha fa?" Suka amsa da eh su ma yana nan. Su na isa bakin ƙofar kowaccensu ta fito, motoci ne na alfarma fake a wurin. Yanmata har ma da manyan mata ƴan gayu kawai kake gani a wurin, kasancewar Angon Shema'u ɗa ne ga kwamishinan ƴan sanda hakan yasa motar ƴan sandan har biyu a wurin su na lura da shige da fice. Mami ce ta soma gaba suna gaisawa da wata ƴar uwar aminiyarta ta miƙa kati ta shige. Hakan ba karamin dadi ya yiwa Tasleem da Futuha ba sanin muguntar da suka shiryawa Humaira. Suka shige abinsu zuciyarsu fari kal bayan sun miƙa katinansu, Raihana ma tuni ta yi gaba. Ummita kuwa ganin yanda Humaira ta rikice da bincike jaka ya sa ta tsayawa gami da ja baya ta ba wasu hanya. "Lafiya? Ya kika tsaya?" Humaira ta ja guntun tsaki. "Wallahi ban ga katina ba. Kinga ba ya cikin jakar." Ta dafe kirji. "Ba dai a gida kika bar shi ba?" Ta girgiza kai cike da takaici, ta kasa cewa uffan ma. Ganin su na tsaye kawai ya sanya ta duban Ummita. "Shiga ciki kawai, ni sai na koma gida." Girgiza kai Ummita ta yi. "Aa wallahi, sai dai ni na koma. Keda Shema'u da kanta ta damƙa maki kati?" Nan fa suka yi ta ja in ja a ƙarshe dai Humaira ta ce. "Toh naji, shiga ciki sai ki sanarwa Mami mu ji me za ta ce. Allah kuwa ba inda zan je ina nan zan jiraki." Ummita duk sai ta ji ba dadi, sosai Humaira a daren jiya ta ci burin bikin ba don komai ba sai cewa da ta yi tana so ta ga ya ake gudanar da biki a ƙasarnan. Ba ta taɓa halarta ba. Ganin ta tsaya yasa Humaira dafa kafaɗarta. "Rantsuwa fa nayi, kinsan ina nan din babu inda zan je." Jin haka yasa ta gyada kai ta juya ta shige ciki ita kuwa ta ja baya ta koma can gefen titi jikin wata baƙar mota me tinted ta tsaya. FADEEL.... ©️RUFAIDA UMAR *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Fitowarsu kenan daga Bristol Palace dake kam titin farmcenter, Ibb ke jan motar yayinda shi kuwa ya kwantar da kai jikin kujera idanunsa lumshe. Babu abin da ya kai su face gaishe da abokin baban Ibb da ya zo daga Kaduna zai tashi zuwa Egypt sakamakon rashin lafiya. "Hall dinnan ba ya rabo da biki." Jin haka ya sa a hankali Fadeel ya buɗe idanunsa. Cikin iko da hukuncin Ubangiji, dubannasa ya sauka kan Humaira dake tsaye ta harɗe hannuwa a kirji fuskar nan a ɗaure kamar koyaushe. "Wait please." Yanda ya yi maganar da sauri ya sa Ibb shima soma tafiya a hankali gami da neman wurin parking. Sai da ya daidaita motar a gefe kafin ya dube shi da alamar tambaya. "Lafiya?" Fadeel ya soma kokarin cire seat belt. "Ita ce. Ba na so na ƙara rasa damar da za ta kubcemin." Ganin yana kokarin bude ƙofar yasa Ibb saurin dafe hannunsa. Fadeel ya dube shi. "What? Kana nufin kar na je?" Girgiza kai Ibb ya yi. "No, ba haka nake nufi ba. Sai dai ina so ka ba ni damar muje tare, idan kuma da hali kar ka ce komai. Ma'ana kada ka yi mata zancen soyayya da ma sauransu. Ni zan san ta yadda zan ɓullo mata, ok?" Fadeel ya sauke ajiyar zuciya yana hangenta ta jikin side mirrow. Ba tare da ya dauke idanunsa ba ya amsa. "Ok." Daga haka Ibb ya kashe motar, suka fito kusan lokaci guda. Gaba ɗayansu ƙananun kaya ne jikinsu. Fadeel baƙar tshirt ne a jikinsa mai ƙaramin hannu sai blue jeans.  A tsintsiyar hannunsa kuwa, agogo ne ɗaure na fata baƙi, sumar kansa baƙa wuluk sai sheƙi take yi. Ya fiddo gilashinsa baƙi a aljihu ya rufe ƙwayoyin idanunsa, a yanda ya karanci Humaira a farkon haɗuwarsu hatta da kallo ta tsana. Ba ya jin kuma abu ne da zai iya jure bari ne, wato kallonta, musamman ma da ya kasance sun fi watanni biyu ba su sake haɗuwa ba. A ɓangaren Ibb kuwa, blue tshirt ya sa da baƙin wandon jeans. Kallo ɗaya idan ka yi musu sai ka kara. Fadeel fari ne tas kuma dogo, har ya so ya fi Ibb tsawo. Shi kuwa yana da ɗan duhun fuska balle idan ya jera da Fadeel, kai tsaye za a kirashi baƙi. Tana nan tsaye ba ta motsa ba har suka ƙarasa wajenta. Wani irin bugu kirjin Fadeel ke yi, kallonta yake tun daga sama har ƙasa, ba ya jin ta haura shekaru sha takwas, idan ma ta cika hakan kenan, amma ƙirarta ko a yanzun abin a kalla ne ina kuma ga nan gaba? Ya ja numfashi daidai sadda suka ci burki a gabanta. Sallama Ibb ya yi gareta, ta bar duban wayar da take yi a kokarinta na kiran Mami ta ce mata ita kam gida za ta koma. Zaratan samarin suka sanya wani irin kwarjini ya mamayeta da har ta kasa tantance su ɗin ko su wane ne, ta mance ma a inda ta san su. Daƙyar ta amsa sakamakon nauyi da harshenta ya yi, daga haka kuma ta  dauke kai ta raba jikinta da motar da nufin barin wajen.     "Kamar ba ki gane ni ba ko?" Cike da ƙosawar ta tafi ta dube shi. Kallo na ƙurilla don ta fahimci ko dagaske yake ta san shi ɗin, duk da cewa ba wannan ne karon farko da samari suke mata irin rainin hankalin nan ba idan sun ga ba ta kula su ba, amma hakanan a ranta ta ji wannan dai ya yi kama da kamilallan mutum, ba ta jin zai yi mata ƙarya. Bayan gama kallonsa ta maida kwayar idanunta kan Fadeel, ba ta ci nasarar ganin halittar kwayoyin idanunsa ba, shi kuwa wani yarr ya ji tun daga tafin ƙafarsa har tsakar kansa. Dakyar ya iya jarumtar juya fuskarsa gefe kafin ita ɗin ta kai ga ɗauke nata kwayar idanun a kansa. Ta tsuke baki ta ce. "Ban gane ku ba." Ibb ya yi mata bayani a taƙaice, nan da nan kuma ta ɗan sakar mishi fuska. Ko babu komai ta ji dadin mutunta da ya yi a wancan ranar wanda tun daga shi, Musaddam bai ƙara gigin shiga hurumin Raihana ba. Ba ta da masaniyar ko Fadeel mai yawan kiranta shi ne tsaye a nan ko kuwa dai wani abokin na Ibb ne daban kusa da ita hakan yasa ta gaishe su a jam'u. Suka amsa, Fadeel kam lebbansa ne suka motsa amma tuni ya yi nisa a kallonta, bai san lokacin da ya ƙara mayar da hankalinsa kacokam kan kyakkyawar fuskarta ba. 'Wallahi ina sonta.' Ya yi furucin a can ƙasan ransa kafin ya sa haƙori ya cije lebbansa ya sauke numfashi nannauya. A cikin ɗakin taron kuwa, Tasleem da Futuha suka hana Ummita zuwa ga Mami, karshe suka ce ta zauna su za su je su shigo da Humairar wurin taron. Suka fito suka kara amsar katinsu suna dariyar mugunta, kawai burinsu su ga fuskar Humaira a karshe su ce Mami ta ce ta wuce gida ba za ta sanya ta roƙon kati a nan ba. Haka suka fito su na ta rarraba idanu, Futuha idanunta ya kai kan Ibb dake tsaye yana zuba wannan murmushin nasa mai tsada, a gefensa kuwa wani haɗaɗɗen matashi ne da ya zarce shi a haɗuwar. Ta dan murza idanu tana kara dubawa, tabbas Ibb ne. "Ke, zo ki raka ni. Wayyo zuciyata, me Ibb ke yi a wajen bikin nan? Ko abokin Ango ne?" Tasleem ta juyo, tuni Futuha ta soma tafiya ganin haka kawai ta mara mata biya. Shi kuwa Ibb babu abin da ya sanya shi murmushi illa gani da ya yi Humaira ta ɗan saki jiki da shi tana sanar mishi cewa ai kam daga ranar Musaddam bai ƙara shiga rayuwar ƴar uwarta ba. "Alhamdulillah. Hakan na da kyau. Sai ki ci gaba da yi mata nasiha. Allah ya ƙara nesanta ta da ire-irensu." Murmushi Humaira ta yi lokacin da ta ke amsawa da amin. Kallon Fadeel ba ta ƙara ba balle ta fahimci hankalinsa kacokam a kanta yake. Har za ta tafi sai kuma ta kara duban Ibb. "Yauwa, nikam ranar da abin ya faru, akwai wanda ka ba lambata?" Fadeel ya yi saurin dubansa, girgiza masa kai ya yi don haka ya dube ta kamar bai fahimce ta ba. "No, meyasa zan ba wa wani lambarki alhalin ko ni ban taɓa kira ba?" Ta ɗan yi shiru, haka kawai ta ji abin kamar rainin hankali amma ta rasa tsakaninsa da wancan Fadeel din me kiranta a waya wane ya raina mata? Don haka ta ce. "Ba ka da aboki mai suna Fadeel?" Fadeel dake tsaye ya ji tamkar ta ci gaba da ambaton sunansa sanadiyyar hakan ba ƙaramin daɗi ya yi mishi ba. Ibb ya ɗan yi gyaran murya domin ankarar da Fadeel ganin yanda ya harɗe hannuwa a ƙirji yana faman zabga murmushi. Sai kuma ya ce. "Yau na fara jin sunan gaskiya, wani abun ya faru ne?" Ta girgiza kai. "Aa ba komai." "Humaira." Gaba daya suka juya ga inda kiran ya fito, Tasleem ce. Futuha kuwa idanunta sun cicciko da kwalla, ji take kirjinta na wani zafi. Mutumin da take kwana da tashi da tunani, shi dai wanda ya gagari kowace budurwa da ma zawarawa a jami'arsu, shi ne tsaye a gaban Humaira kucakar da ba ta kamo sawunta a kyau da hasken fata ba yana mata murmushinsa mai tsada da take ji a ranta za ta iya kashe ko nawa ne ganin ita ta sami wannan damar. Amma a banza gashinan ya na jifan Humaira da shi. Tasleem kuwa ta yi mutuwar tsaye wajen kallon Fadeel, sai yanzu take jin ba son Hamza D take yi ba, son ƙarya ne. Wannan abin da take ji game da Fadeel a yanzun shi ne so, soyayya kuwa ta haƙiƙa. Fadeel ya nanata sunan da ya ji Futuha ta ambata. Humaira, shakka babu ta dace da masu sunan. Ibb kuwa ganin Futuha ya sanya shi tamke fuska kamar ba shi ke yiwa Humaira murmushin ba. Sai gaba daya matasan suka yi musu kwarjini, ita Futuha da ta yi niyyar wulaƙanta Humairar a gabansu sai ta yi laushi, yayinda Tasleem dama tuni miyan bakinta ya kafe, tunani take irin wadannan tsadaddun ai sai irin su masu zubin larabawa. Dakyar Futuha ta yi magana. "Mami ta ce ki wuce ki tafi gida tun da dai kin manta katinki." Jin haka sai ta ji babu dadi kadan, ta kwallafa ranta a bikinnan ba don komai ba sai na son ta ga yanda tsarin biki yake a nan. Hatta da fuskarta ta nuna rashin jin dadinta. Tasleem kuwa da sauri ta gaida Ibb da Fadeel har da ɗan ladabin ƙarya. Suka amsa. "Sorry to ask, ba ta samu shiga wurin event din ba ne?" Fadeel ya tambaya a sanyaye, tun zuwansu wurin sai a sannan ya yi magana. Humaira ta dube shi, kamar muryar mutuminta na waya, ya kauda kai ya kara shan mur kar ta samu fuskar tambaya. Tasleem da ta kusa shiɗewa jin ya yi mata magana duk kuwa da cewa akan Humaira ne ya sa ta saurin tankawa da wata murya cike da yanga. "Eh ta bar katin nata a gida ne, so shi ne Maminmu kawai ta ce ta koma tunda ba za ta samu shiga ba." Humaira ta tsaya kallon ikon Allah kawai, mamaki da haushin irin wannan karairayar murya na Tasleem ya cika ta. Har sai da ta ja guntun tsakin da sautinsa bai fito sosai ba. "Muje." Yana  fadin haka ya yi gaba, Ibb ya kalli Humaira. "Ku je za ki shiga yanzu in sha Allah." Ta amsa da toh, ta bi bayansa ita da Tasleem, ita kuwa Futuha ta ja burki gefen Ibb. Ya kauda kai tamkar bai san da ruwanta ba. "Amm, Malam ba ka gane ni ba ko? Ni ɗalibarka ce a.." "Ban sanki ba." Ya tari hanzarinta da sauri, daga nan ya taka ya nufi wurin motarsa ya tsaya. Futuha ido ya raina fata, ta dubi wasu maza a gefe tsaye da wasu ƴanmata da ma matan auren da ba su kai ga shiga ciki ba suna mata dariya, tana kallonsu suka ɗauke kai. Gwuiwa a sake ta kama hanya ta bi bayan su Tasleem, ranta ya yi tsananin ɓaci.  Ita kam ta soma gajiya da wulakancin Ibb, amma za ta yi hakuri tunda Anti Jannat ta haɗa ta da wata ƙawarta dake garin za ta yi mata rakiya gurin wani Malami a yi musu aiki a kansa. Amma zuciyarta na kokwanton aikin don ta ji wadanda sun buga sun kasa a kanshi. Humaira kuwa na tsaye gefe Tasleem na tambayarta inda ta san su Ibb ta yi banza da ita kamar ba ta ji ba. Hankalinta na ga Fadeel dake magana da ɗaya cikin masu tsaron wurin. Ba ta san ya aka yi ba sai juyowa ya yi wannan karon gilashin da ya rufe ƙwayar idanunsa ya cire, lumsassun kyawawan idanun suka bayyana, suka kusan susuta Tasleem har ba ta san ta ce "Masha Allah." a fili ba sai da Humaira ta ɗan dube ta. Shi kuwa cikin ido ya kalli Humaira ya mata alama da ta zo. Sai da ta karasa dab da  shi kafin ya samu damar magana. "A sha biki lafiya. A gaida Mami." Ta ji dadi sosai ganin da ta yi an ba ta damar shiga. Ta kuwa buɗe masa haƙoranta har wushiryarta na bayyana a fili. "Nagode sosai." Ga Fadeel shima murmushin ya bita da shi, ji yake kamar ya jawo ta jikinsa ya rungume. Da ace shari'a ta halarta masa ita ma, sai ya sumbaci kuncinta wadanda har gani ya yi kamar su na sheƙi idan ta murmusa. Bai taɓa ganin murmushinta ba sai a yau, sai ya ji inama za su dauwama ta na jifansa da shi. "Always welcome." Ita dai ta yi gaba don bai san ba ta jin turanci bane, ta dai tsinci welcome din. Zuwan Mubarak ta ji yanda su Tasleem ke faman welcome welcome har ta nemi fassararsa a wajen Ummita. Babu wani iyaka kuwa aka bari ta shige, tana ɓacewa ganinsa ya maida gilashinsa. Ganin Tasleem tsaye tana kallonsa ya dauke kai, har zai wuce sai kuma dabara ta faɗo masa. Ya dubeta. "Gidanku ɗaya?" Ta yi wani farr da idanunta. "Eh, babanmu ɗaya da ita." Ya ɗan jinjina kai. "Idan ba damuwa, ko zan iya samun full address na gidan naku?" Ba musu jiki na rawa ta hau yi mishi kwatance, ta kara da fadin. "Ko na ba ka phone number dina kaga ko da ace ba ka gane ba sai na yi maka bayani ta waya idan ka tashi zuwa." Kamar ya ce aa, sai ya tuna ba lallai ya samu cikakken bayani daga Humaira ba dalilin haka kawai ya amince. Wayarsa ya ciro ya miƙa mata. Tasleem ji ta yi kamar ta daka tsalle ta yi rawa da juyi, hannunta har rawa yake yi. Ya dubi yanda take danna wayar cikin rawar jiki ya ɗan taɓe baki. Ya fahimci inda ta dosa kwarai amma ya basar. Babu gurbin wata ɗiya mace a rayuwarsa, madallah da Humaira da ta ciri tuta har ta yi nasarar sace zuciyarsa. Ya karɓi wayar kafin ma ya tambayi sunan da zai yi saving da shi ta riga shi. "Sunana Tasleem. Kar ka manta ka yi flashing ɗina kaga koda ka kira zan gane kai ne saboda ban fiye ɗaga unknown number ba." Bai sake kallonta ba kuma bai tanka ba ya fice yana zura wayarsa cikin aljihu. Ta bishi da kallo kamar ta haɗiye shi. Futuha ita kuwa tuni ta shige ciki saboda kunyar yanda Ibb ya yi watsi da ita. Ta kuma rantse koda ace son Humaira yake, sai ta yi yanda ta yi ta raba su har abada. Tana ji a jikinta ba lallai ta sami Ibb ba, toh kuwa Humaira ta yi kaɗan ta samu abinda ita din ta rasa shi. A ɓangaren Tasleem kuwa gani take yi kawai ta tsinci dami a akala, ta samu mijin aurenta. A farko har ta amincewa Hamza D da zuwa gaishe da Abba, amma yanzu kam za ta dakatar da shi tunda ga Fadeel nan. Wannan kenan. *** Tun daga wannan ranar Futuha ke tsananin sanya idanu akan Humaira. Daidai da wayarta idan ta yi ƙara sai ta yi saurin kallonta ta ga wane ne. Rannan ta titse Raihana sai da ta titse wai wato Ibb ke kiran Humaira amma ta nuna mata sam ba shi ba ne, tsabar ta koyi munafunci. Raihana rai a ɓace ta amsa. "Wai ke meyasa kin fiye son kanki ne? Toh koda ace soyayyar ce tsakaninsu ai ke kin fi sauran masu haukar sonsa cin riba tunda ko ba komai ƙanwarki yake aure." Wannan magana ta fusata zuciyarta nan kuwa ta hau kilar Raihana kamar an aiko ta. Lokacin Humaira na can gidan koyon girkinta. Ita kuwa Tasleem ba ta dawo daga asibiti ba don yanzu su na asibiti an tura su daga makaranta. A falon daga su Muhsin sai Ummita. Hankali tashe Ummita ta ruga kicin ta kira Mami. Ganin abin da ke faruwa yasa Mami dakawa Futuha tsawa. Sai a sannan ta miƙe daga ruwan cikin Raihana, gaba daya fuskarta ta yi tabo. Kuka kawai take da ihun fadin Allah ya isa, raini kam ta daɗe da raina su. "Wane irin hauka ne wannan? Kashe ta kike son yi?!" Cewar Mami tana duban Futuha dake faman huci. Sai kawai ta fashe da kuka. "Wallahi Mami ba don kamannin yarinyar nan da mu ba sai ince ba ƙanwata ba ce! Wai saurayina ne Humaira ke so har da karɓar lambar wayarsa suna waya. Raihana ta san komai tsakaninmu, kema Mami kin san shi, wai shi  ne take fatan da ace ya auri Humaira. A gaban idanuna." Mami ta saki baki galala tana duban irin kukan da Futuha take yi, lallai abin da zai sa ta kuka har haka ba ƙaramin abu ba ne. Tana da taurin zuciya a wasu lokutan, ita kanta zancen ya shige ta don ba ta mance yanda ta sha ba ta labarin wani Ibrahim ko kunyarta ba ta ji. Daidai da Anna ta san da zaman soyayyar da Futuha ke yiwa Ibb, sun kuma ji daga bakin Tasleem da ma su Yassar cewa mutumin bai damu da ita ba. Ta sauke ajiyar zuciya. "Allah ya kyauta, shi ne akan wanda bai damu da ke ba za ki kashe yar uwarki? Kar ku kuskura na ƙara ganin wannan rashin hankalin." Haka kawai ta fadi ta juya, madadin kicin ta wuce dakinta. Futuha ranta ya yi baƙi, wato ma abin da Mamin za ta ce kenan? Ita dai ta tsani halin rashin kulawar da Mamin ke nuna musu. A fusace ta yi sashin Anna har tana bangazar Raihanar. Ita dai Ummita ba ta ce uffan ba, toh ban da abin Futuhar ma, koda ace son Humaira yake, ta tabbatar ba zai samu fuska ba. Ita ta lura kowa ma Humairar ta tsana muddin zai furta mata kalmar yana sonta. *** Anti Amarya ta ƙurawa Murja dake zaune tana faman jijjiga ƙafafu ido waya ta ke amsawa amma gaba daya fuska a jagule sai bayan ta kammala ta ajiye wayar, sannan Anti Amarya ta soma magana. "Yanzu ke wannan Idris din kinsan matsayin babansa kuwa? Meyasa Murja ba ki da wayo da tunani? Kin maƙale akan yaron da idan ya shigo gidan nan kallo ba ki ishe shi ba? Komai kika yi ba ki iya ba, amma Idris tun haɗuwarku a bikin Fu'ad ya manne maki kuma dagaske aurenki ya ke son yi. Kinga ina raba ki, wannan fa shi ne saki reshe kama ganye. Kin gani sarai da idanunki yanda Ubansa ke ji da shi kamar ba shi da wasu yaran bayan sa, ko a haka ya dace ki fahimci babu wanda zai yi mishi auren dole. Ko da ace kuwa ba namiji ba ne, tun da ya sa ƙafa ya dawo ƙasar nan, Alhaji ke gudun abin da zai ƙara sanya wa ya yi nesa da shi. Toh kuwa ki kama kanki tun wuri ina shawartarki, soyayyar Fadeel ba za ta kai ki ko'ina ba. Ina kara faɗamaki wallahi ba ya sonki ba ya kaunarki." Ta sani gaskiya ne tsagwaronta yayarta ke faɗi, amma ina, ta riga ta yi nisa da son Fadeel. Ta gama tsara yanda za su yi rayuwar aurensu wannan ya sa maganganun ke shigarta su na fita ta kunnen hagu. Ta furzar da huci. "Shikenan, na yanke shawarar abin da zan yi." A zaton Anti Amarya, ta dauki shawararta don haka ta murmusa. "Ko kefa." Ita kuwa murmushi ta ɗan yi, ta kuma ƙudurta a ranta za ta tari Fadeel kawai ta ce mishi tana sonsa. A yanda ta ga yana ganin mutuncin Antinnasa, ba zai watsa mata ƙasa a idanu ba. *** BAYAN SATI ƊAYA... A wani yammacin ranar Juma'a ne, Humaira na tsaye tana ninkin kayanta tana jerawa a sif. Futuha kuwa ta ƙure volume ɗin waƙar Kalmar So na breaker tana bi tana daukar bidiyo na kanta a tiktok. Riga gown ne a jikinta lemon green fuskar ta sha make up. Gashinta a waje ko ɗankwali babu, sai raye-raye take. Raihana da Ummita na zaune su na aikin lissafi na makaranta da aka ba su, su na ɗan taɓa hira jifa-jifa da Humaira. Su na yi suna kallon ikon Allah wajen Futuha da ta saita Camera ta waya sai raye-raye ta ke yi. Wannan karon ta sauya waƙar zuwa Warr na Ado Gwanja. Kusan yanzun aikinta kenan, ta yi rawa ta ɗora a Tiktok da Instagram, babu laifi kuma ta samu mabiya sosai, wannan ya kara fasa mata kai, a farko hotunanta kawai take ɗorawa iri-iri a instagram, amma ba ta jima da soma Tiktok ba ta ga ta samu karɓuwa wannan ba karamin ɗauke hankalinta ya ke ba a yanzu. Su na a haka sai ga Tasleem ta faɗo ɗakin da gudu. Jiki na rawa ta karasa sif din kayanta ta bude. Futuha wacce ta kammala tana editing kafin ta dora ta dakata tana dubanta. "Ke kuma lafiya?" Ta juyo da wani irin zumudi. "Kalau, babban baƙo zan yi fa. Kin tuna guy dinnan da na hadu da shi ranar bikin Shema'u? Abokin Ibb?" Futuha ta gyada kai. Tasleem ta daka tsallen murna. "Shi ne ya yimin waya ya kara neman kwatance, yau zai zo." Ita kanta Futuha ta jiye mata dadi, amma haka nan ta ji ɗan kishin yar uwar a ranta. Me Tasleem ta fi ta da har za ta yi kamu me zafi haka lokaci ɗaya amma ita kuma ta kasa samun Ibb? Tun su na yara an sha cewa ta fi Tasleem kyau, balle kuma yanzun da suka girma. Kowa ita ya fi kira kyakkyawa a kan dai Tasleem. Wannan ma na daya daga cikin abin da ya fasawa Tasleem kai a yanzun, itama tana jin takaicin kusheta da yan uwan Mami har ma da na Abba ke yi a lokuta da dama su ce wai Futuha ta fi ta kyau. Sai Futuha ta kasa ce mata komai bayan "Inyee, na maki murna." Daga nan ta ci gaba da latse-latsen wayarta tana murmushin da bai kai zuci ba. Tasleem ta maida hankali ga duban sif dinta, ta san Futuha mace ce mai kishi, ta fi kaunar komai ta fi kowa, kuma sai gashinan nasarar a kanta take. Tashi guda ta yi kamun babban kifin da ya fi wanda Futuhar ke hari. Raihana kuwa duban Ummita ta yi. Cikin sanyin muryar da ba lallai su Tasleem su ji ba ta ce. "Kada dai ace Fadeel me son Humaira ne zai zo?" Ita ma Ummita hakan ta ke zargi, Humaira na jin su ta yi kamar ba ta ji ba. Ta sani tabbas shi ne, sai bayan sun rabu ta kara tabbatarwa shi ne mai kiranta adalilin saƙon da ya turo mata bayan shigarta wurin bikin Shema'un, inda ya ce mata ta yi kyau kuma ya yaba da murmushin da ta yi mishi a lokacin. Sannan bayan sallar juma'a a yau din, ya bar mata saƙo inda yake shaida mata batun zuwansa gidansu a yau. Ya kuma roƙe ta kar ta ƙi fitowa. Ita kuwa a take ci kanka ba ta aika mishi ba balle ta kira ta dakatar da shi daga zuwan, ta fi kaunar ya zo ta jaddada masa ido cikin ido cewa ita ba ta soyayya, kuma ba ta sonsa ya rabu da ita. Tunano hakan sai ta ji dariya ya kama ta, dakyar ta danne ta hanyar murmusawa. Wato dai yau din akwai kallo kenan. Ta kara duban Tasleem da ta sauya kaya zuwa wani leshinta ja mai ɗigon baƙi a jikinsa mai ɗan karen kyau, murmushin ta kara saki wannan karon har da sautin dariyar da ya sa su Raihana dubanta, suka kuma dubi junansu, sun tabbatar Fadeel ɗin Humaira ne a hanyar zuwa. Akwai dai matsala kenan. ©️Rufaida Umar. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Wayar Tasleem da ta ɗau ƙara ne ya sa ta saurin jifa da kwalbar turaren dake hannunta a saman gado, ta zari mayafinta da ya hau da leshin ɗan firit wanda ko kirjinta bai gama rufewa ba, ficewa a dakin ta yi bayan ta kara wayar a kunne tana fadin ga ta nan fitowa waje. Futuha ta mike ta bi bayanta wai za ta gani ko dagaske Tasleem din ta ke. Suna fita Humaira ta tuntsire da dariya har da faɗawa saman gado. Raihana da Ummita su ma dariyar suka shiga yi. "Ni dama ya ce yana son nata dagaske ai da naji dadi, ko ba komai na huta da alaƙaƙai. Haba, ina dalili mutum ana korarsa yana mannewa sai ka ce mayen ƙarfe." Ta ja guntun tsaki ta mike ta ci gaba da ninkin. "Kai Humaira anya a duniya za ki yi aure kuwa? Wannan abu har ina wai? Duk kyau da kwalisa na saurayi ba kya sonsa? Meke damunki?" Ummita ta ce tana duban ta, ji take kamar ta kai hannu ta buge ta tsabar haushi. Itama Raihana ta cafe "Rabu da ita Ummita, ai kanta akwai alamar kuncewar notina. Da ace ma ni ce ke, ko don na nunawa Tasleem ita ɗin ba komai ba ce a wurin Fadeel ai wallahi da hannu bibbiyu zan tarbe shi, shima dai Fadeel din da ba shi da zuciya ya kyaleki ya ƙi, ya bari kina ta wulaƙanta shi son rai. Da ni ce shi ko?" Ta yi ƙwafa amma ba ta ce komai ba, Humaira wacce tun soma maganarsu take kwaɗa musu harara, ta ja tsaki. "Matsalarsa, ni dai ai ban yaudareshi ba, tun farko kuma na faɗamasa ya rabu da ni, ya ficemin a rayuwa amma ya ƙi. Aikuwa babu abin da zan ce mishi, ya je can ya ƙarata da Tasleem." Ba su ce uffan ba sai kallon mamaki da suke mata, dagaske dai take ko a jikinta don ba su ga wani ɗigon kishi a saman fuskarta ba. A ɓangaren Tasleem kuwa, tana ƙarasawa falon ta ci karo da Mami a zaune tana amsa waya. Ganin ta da shirin fita ya sanya ta yi sallama da abokiyar wayar ta dube ta dakyau. "Ke kuma sai ina haka?" "Mami baƙo fa nayi, bari na shigo da shi falon saukar baƙi sai na zo." Ba ta ma kara jin abin da zai fito a bakin Mamin ba ta yi wuf ta fice, Mami ta yi kasake tana duban hanya, fitowar Futuha ya sanya ta maida akalar tambayar a kanta. "Wannan wane baƙon ta ƙara yi a yanzu ne? Duka-duka yaushe shi Hamzan ya zo da har zai ƙara zuwa?" Taɓe baki Futuha ta yi cike da jin kishin ƴar uwarta ta amsa. "Uhum, wai fa abokin Ibb ne yake sonta shi ne take wannan rawar jikin." Wani ɗan murmushi Mami ta yi. "Wato dai ruwan ido ne abin nata kenan? Ya za ta yi da shi wanda ta yiwa iznin zuwa su gaisa da Abbanta?" "Mami, wannan fa ya fi Hamza kudi da haɗuwa, na tabbata abin da ya ruɗe ta kenan." Mamin ba ta ce komai ba face Allah ya kyauta. *** Yana zaune a cikin motar hankalinsa rankatakaf akan ƙaton ƙyauren gidan da Tasleem ta yi mishi kwatance, ji yake tamkar ya yi tsuntsuwa ya shiga ya yi ido huɗu da abar ƙaunarsa, ganin ya kwashi mintuna babu alamar Tasleem sai ya ji gaba ɗaya ya karaya. Kodai ba gidan ba ne? Waya ya fiddo da niyyar ƙara kiranta sai ya hange ta ta fito daga gidan. Da farko sam bai gane ta ganin tamkar wannan ɗin shirin fita unguwa ta yi, ga dukkan alamu ma ba gidan ba ne. Amma a hankali tana matsowa ya gane ita ce don haka ya sauke tinted glass din motar wanda ya katange ta daga ganinsa sai waige ta ke. Tasleem kuwa yana saukewa ta ji numfashinta na barazanae ɗaukewa ba don tsoro ba sai domin tsananin burgeta da ya yi, ga kuma wani irin kyau da ya yi mata. Shadda ce a jikinsa coffee colour, ya ɗora hula a kansa, wannan karon babu gilashi a idanunsa don haka kyawun fuskar ya ƙara bayyana muraran. Ta kasa furta koda harafi har sai da don kansa ya fito daga motar ya rufe. Murmushi mai tsada ya sakar mata. "Ashe kin iya kwatance." Ta yi farr da idanu haɗi da sakarmasa nata kalar murmushin itama. Cike da yanga da kwarkwasa ta ce. "Kai kuma kana da basira tunda har ka iya ganewa. Barka da zuwa, bismillah mu shiga daga ciki." Ba musu ya karɓi tayinta, bayan sun gaisa da maigadi dake zaune a benci, tana gaba yana biye da ita yana ƙarewa gidan kallo. Hatta da gidan sai da ya ji kaunarsa a zuciya, ya kuma rantse albarkacin masoyiyar tasa ce.  Falon suka shiga ya zauna bayan ta mishi bismillah, sai ƙamshi kuwa ke tashi a ciki don dama tunda ya yi mata kiran farko ta ba mai wankin Abba dari biyu akan ya taimaka ya kara share mata a sa turaren wuta. "Ina zuwa." Ganin ta furta haka tana niyyar ficewa sai bai ce mata uffan ba, ba ya son ya yi garaje da tambayarta Humairar, tunda har ta ce tana zuwa to ya sani ba zai wuce ita za ta rako ba. Ya lumshe idanunsa kafin ya buɗe ya sauke saman hoton Abban dake maƙale jikin bangon. Ko wani bai faɗamasa ba, wannan mahaifin Humaira ne, kamannin ya ɓaci kwarai. Sai ya ji kaunar Abban ya lulluɓeshi, ƙauna dai kwatankwacin irin kaunarsa da Alhajinsa. Sallamar Tasleem din karo na biyu ya katse dukkan tunaninsa. Ganinta ɗauke da tray na kayan sanyi nan da nan ya ɗan ɗaure fuska, shi fa duk ba wannan ne a gabansa ba. Tana ajiyewa ya ga tana kokarin zama ya karya bille ya ce.   "Where is she?" Ta dube shi cikin rashin fahimta, ta yi ƙarfin hali ta ce. "Who?" Ya dauke kai daga kallonta, ya soma hasaso wani abun, ya gane ita ɗin manufarta daban, tunaninta ya tafi wani wajen. Mafarkinta daban. "Wacce na zo domin ta, Humaira." Kirjin Tasleem ya hau bugu, har ji ta yi ganinta ya ɗan dusashe. Miyan bakinta haka ta neme shi ta rasa, dakyar ta tattaro jarumta ta ce. "Humaira kuma? Dama wajenta ka zo." Sai a sannan ya dube ta tsakar ido. "Yes, wurinta na zo. Ko sadda muka haɗu dama haka nace wujenki zan zo?" Tasleem da har ta soma hawaye ta kasa magana, eh bai furta cewa wajenta zai zo ba, amma wane rainin hankali ne ya sa bai nemi kwatance daga Humaira ba sai a wurinta? Ta kuwa daure fuska tamau, ta rantse daga ita har Humairar sai dai su yi biyu babu. Kowa ya rasa don hana ta ce. "Toh Humaira ban santa ba, asalima a wurin biki muka haɗu. Na yi zaton gidanmu kake nufin na kwatanta mana. Don haka babu Humaira a gidannan." "Ko?" Ya furta idanunsa a saman hoton Abba, itama ta kalli hoton. Ranta ya ɓaci ainun, ta san kamannin Humaira muraran da ya gani a fuskar Abba ya sanya shi furta hakan. Ta mike tsaye ta  koma gefen Fadeel  ta zauna. Zuwa yanzu ransa ya kai maƙura wajen ɓaci amma yana tausar zuciyarsa da tunanin bai dace ba, ta ci alfarmar abin sonsa. Ko babu komai tace masa  mahaifinsu guda. Ita kuwa da muryar kuka ta soma magana. "Wallahi ina sonka. Tun ganin farko da nayi maka zuciyata ta kamu da begenka. Me za ka yi da Humaira? Da me ta fi ni? Na rantse babu abin da za ta nunamin." Ya runtse idanu, ransa ɓaci yake ya na kokarin danneshi, amma jin ana kushe abar sonsa ya bude idanunsa da suka yi jawur tarr a cikin nata. Sai da ta ji rishin kukan ya tsaya na ɗan lokaci tsabar fargabar kar ya shaƙo ta. "Ki san kalaman da za ki faɗi a kanta. Idan kuma kina son kanki da mutunci, ki yakice ni a ranki. Ki sani kuma ki kara, Humaira ta fiyemin ire-irenki dubu. Kyau da sura ba su ne a gabana ba. Da ace su ne, na bar da yawansu a inda na fito, ba na sonki, ba kuma na son kowa sai ita ɗin. Idan za ki iya ki shiga ki yimin sallama da ita, idan ba ki iyawa ni zan sa a kira ta." Da gudu Tasleem ta mike ta yi hanyar fita tana kuka sosai. Fadeel ya mike tsam ya fito farfajiyar gidan inda ya ci karo da Muhsin na wasa da keke. Ƙarasawa ya yi wurinsa ya ɗan durkusa daidai tsawon yaron yana murmushi kamar ba yanzun aka ɓata ransa ba. "Boy, ya sunanka?" "Muhsin." Ya jinjina kai, da alama duka sunayen yan gidan su Humaira masu dadi ne, shi kam dadi yake mishi, ya ji ance Futuha, Tasleem yanzu kuma ga Muhsin. Ganin yaron na shirin janye keken ya sanya shi saurin riƙe keken. "Ɗan shiga ciki ka ce Humaira ta zo, Fadeel ya iso." Jin haka Muhsin ya amsa da toh, ya juya kan kekensa bayan Fadeel ya saki ya wuce ciki. *** A can kuwa, Mami da Futuha na zaune sai gani suka yi  Tasleem ta fado falon a guje, tana  zuwa ta zube cinyar Mamin tana kuka. "Ke lafiya? Meyafaru?" Cewar Mami cikin ɗaga murya gaba daya ta ruɗe. Wannan ya yi sanadin fitowar su Humaira daga ɗaki sai a sannan Tasleem ta ɗago ta dubi Mami. "Wai ba ki yake so ba, wajen Humaira ya zo." Jin haka Futuha ta ji zuciyarta dan yi sanyi, ko ba komai Tasleem ba za ta ƙara hura mata hancin ta yi wanda ya fi Ibb ba kuma ta gane ba Ibb ne masoyin Humairar ba. Amma a gefe kuma kishi da tsanar Humaira ne ya kara mamaye ta, mene ne da ita wanda har namiji irin Fadeel zai gani ya maƙale mata, su da suke buzaye ma ta kasa shawo kan Ibb ya kaunace ta sai wata can bafulatanar ruga? Mami kuwa gaba daya fuskarta ta sauya, kafin ta yi magana dai ga Muhsin a guje da kekensa ya shigo falon, yana cin karo da Humaira ya ce. "Adda Humaira, ki je inji wani a waje." "Ka je ka ce ba za ta fito ba! Kada ya kara gigin zuwa gidannan!" Gaba daya suka dubi fuskar  kowannensu dauke da mamaki idan ka cire Humaira da kalaman ya yi mata dadi ainun, haba ta gaji da naci irin na Fadeel, shi bai san ba ta son komai da ya danganci saurayi ba. Meyasa ya ƙi fahimta? Ai gwara Mamin ta kora mata shi. A bangaren Raihana da Ummita kuwa tunaninsu daban da nata. Akan me Mami za ta ce Fadeel ya tafi? Wato don ba ya sin Tasleem shikenan kowa ma ya rasa? Tasleem da Futuha kuwa dadi ne ya mamaye su, wato dai uwa uwa ce, ta damu da yaranta. A farko sun yi zaton kwata-kwata Mamin ba ta kaunarsu ta fi kaunar ƴan riƙonta musamman ma Humaira. Amma a hukuncin da ta yi abin ya musu dadi, Tasleem ta ji gwara ma kowa ya rasa. Muhsin kuwa tuni ya fice don cika umarnin Maminsa. Humaira dai ta juya zuwa daki don ci gaba da abin da ya rage na ninkin da take yi, ganin haka Ummita ta bi bayanta, Raihana kuwa da sauri ta bi bayan Muhsin. Futuha na kwala mata kira ta yi mata banza. *** A can farfajiyar gidan kuwa, Muhsin ne ya karaso har kusa da Fadeel, yana shirin faɗin saƙon Mami da sauri Raihana ta kwala mishi kira. "Kai Muhsin." Suka juya har Fadeel suka dube ta, ta karaso da sauri ta ce. "Jeka zan faɗamasa." Ya kuwa tura kekensa ya ci gaba da zagaye a gidan yana waƙe-waƙensa da ake musu a boko. Ta gaida shi ya amsa, zuwa yanzu ya karaya da ganin Humaira. "Suna na Raihana ƙanwa ce ga Humaira, don Allah ka yi hakuri ba za ka samu ganinta ba a yau sai dai ko watarana idan an ɗan kwana biyu." Murmushin da bai kai zuci ba ya yi, ta tabbata shi kadai ke kiɗa da rawar sa, wacce ya ke yaƙin don ita ba ta san yana yi ba, ko kuma ya ce ta sani amma ra'ayinsu ya sha bamban. "Kar ki damu, ba komai. Idan kin shiga ki ce ina gaishe ta, na kuma cika alƙawarin da na daukarwa kaina na zuwa gidansu. Amma hakan ba ya nufin ko a mafarki zan iya fita a rayuwarta. Ina sonta." Daga nan ya juya ya fice. Raihana ta zuba masa idanu har ya fita daga gate din gidan, tausayi sosai ya ba ta, Humaira dai tana neman cutar da kanta. Samun masoyin gaske irin Fadeel abu ne mai matuƙar wahala. Ta ji haushin Humaira a zuciyarta kamar ta je ta rufe ta da duka. Gwuiwa a sake haka ta juya ta koma ciki. *** Tun faruwar wannan lamarin Fadeel ya shiga damuwa ainun, yana da tabbacin shi yake so ba a sonsa, ya kuma shirya rungumar wannan jarrabawar ya yaƙe shi. A gefe ga mahaifansu da suka soma matsawa akan su fito da matan aure shi da Ibb. Satinsa guda bai kira ta ba balle ya aika mata saƙo, jarrabawa ya yi domin ya ga ko zai iya yakice ta a rai bisa shawarar Ibb amma sai ya ji kamar yanzun ne ma ya soma kaunarta. Ba kuma ya jin zai iya haƙura da ita. Ya miƙe daga saman gadon da yake kwance wanda tashinsa kenan daga bacci mai cike da mafarkan Humaira, kamar daga sama ya ji ana kwankwasa ƙofar falon, agogon dake maƙale a bangon ɗakin ya kalla, ƙarfe goma har ta gota. Ya ɗan ja ƙaramin tsaki, ya tuna yau suka yi da Alhaji zai soma zuwa kamfaninsa ya kama aiki, jin ƙarar kwankwasar yake har cikin kansa dake radadin ciwo, iya sati ɗaya zuciyarsa ta jigatu da rashin ji ko ganin Humaira, ta ina zai soma fidda ta daga rayuwarsa? Wannan abu ne da ba zai yiwu ba sam. A hankali ya miƙe daga shi sai vest da dogon wando ya fito falon. "Waye?" "Ni ce Yaya Fadeel, abin kari na kawomaka." Guntun tsaki ya ja jin muryar Murja. Ƙofar kawai ya bude ya juya ba tare da ya ko kalle ta ba ya ce. "Ki ajiye ki fice. Na gode." Ta ji ciwon hakan amma da ta tuno da batun Malam na cewa idan har ya ci abinda ta girka da laƙanin da ya ba ta to fa ba makawa hankalinsa zai karkato gare ta. Ya yi mata gargadi akan lallai ta tabbata ya ci, idan kuwa bai ci ba to fa haka za ta kara narka uban kudade a yi mata wani sabon aikin. Don haka sai ta zauna a falon ta ƙi bin umarninsa, shi kuwa wanka ya shiga bayan sun yi waya da Alhaji ya buɗe mishi wuta akan rashin zuwansa ofis da wuri, hakuri ya dinga  a shi ya ce yana tafe. Suka yi sallama. Koda ya fito wankan a gaggauce ya shirya cikin kananun kaya, dark green din tshirt sai wandon jeans. Ya ɗaura agogo a tsintsiyar hannunsa, ya gyara sumar kansa. Fitowarsa falon ya ga mutum zaune, nan da nan ya tamke fuska, ita kuwa Murja da rawar jiki ta ce. "Barka da safiya, bari na haɗa maka shayin." Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "No ki bar shi nayi latti, Alhaji na jirana. Ki je da su kawai." Murja cikinta ya bada sautin kululu, ita dai ta shiga uku, wannan rashin sa'a har ina? Yanzu shikenan ta yi asarar dubu tamanin? Ita kuwa wa za ta je ya ba ta wasu kudaden a ƙara maimaicin aiki? "Ba kya ji ne?" Wannan karon ya yi maganar yana ji kamar ya ɗauke ta da mari hagu da dama, abu ɗaya da ya sa yake raga mata bai wuce na tunanin shi ɗin ma fa haka yake fama da soyayyar wata ba ta sonsa. Ganin yanayinsa sai ta maida kayan kwandon ta dauka ta fice har da kwallarta. Fadeel yana so ya kashe ta, yanzun ma ji take kamar ta faɗa wannan faɗaɗɗan kirjin nasa ya yi mata rumfa da hannuwansa, sai dai kash! Wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa. Amma kuma komai nisan jifa ƙasa zai faɗo kuma sannu sannu ba ta hana zuwa, ta na ji a jikinta watarana haƙanta zai cimma ruwa. *** Abba ne zaune fuskarsa cike da walwala, babu jimawa iyayen Hamza suka tafi bayan sun nemawa ɗansu auren Tasleem kuma ba musu ya amince ya ba su. Tasleem da kanta ta kira Hamza ta ce ya turo saboda bakin cikin abinda Fadeel ya yi mata, ga faɗan da suka yi da Futuha me  yi mata dariyar ta rasa shi, ita kuma don ta nunawa Futuha tana da mai sonta dagaske ba irin ita me bin Ibb ba ya sonta ba yasa ta kiran Hamza ta ce matukar dagaske yake toh ya turo a nema mishi aurenta a kwana uku, idan kuwa ya wuce haka to kaunar da yake mata a baki ne. Dama kuma shi abin da yake jira kenan, don haka sai kawai ya ba da kai bori ya hau. Mami ta shigo itama fuskarta dauke da walwala ta zauna gefen Abba. Kafin ma ta ce wani abu ya riga ta. "Maryama yau ina cike da farin ciki, ba ni da burin da ya wuce naga na aurar da yarannan mata lafiya kowaccensu ta tare a ɗakinta. Ina tsoron sharrin wannan zamani. Ita ma Futuha zan mata magana, ta fito da miji na haɗa aurensu baki ɗaya zai fi min. Karatun can su je su ƙarasa a ɗakin mazajensu, naji da kannensu masu tasowa." Mami ta jinjina kai, "Hakane Abban yara, in sha Allahu itama zamu yi magana da ita naji ko tana da tsayayye. Na san dai wani yaro da ta kwallafa rai a kansa amma shi bai san tana yi ba." Abba ya ɗan yamutse fuska. "Ai kinji irin shirmen yaran yanzu masu biyewa soyayya, ban da shiririta ke ba manema kika rasa ba, mutane nawa ne suka tare ni akan suna sonki amma ki nacewa wanda ba ya so? Allah ya kyauta, lallai ki ce mata nace ta nutsu ta fiddo miji a haɗa aurensu da ƴar uwarta. Kina ji dai iyayen shi Hamza sun ce nan da wata shida suke so a yi komai a ƙare." "Shikenan, zan mata magana." Mami ta amsa a sanyaye, fatanta Allah yasa Futuha ta cire ran da ta kwallafa akan Ibb ta kama wani. ***   Futuha na zaune tana danne-dannenta a waya kamar koyaushe, bidiyo mai zafi ta ɗora tana bin waƙa, ta ci ado a bidiyon har ta gaji, ta yi ɗaurin ture ka ga tsiya da dankwalinta na leshi, karanta comments kawai take tana jin dadi tana zabga murmushi, wasu kuwa zagi ne da addu'ar nema ma ta shiriya. Irin wannan sai dai ta ja tsaki ta wuce. Ta ci gaba da kallon bidiyoyin jama'a nan ta ci karo da wani bidiyo da ya ɗaga hankalinta wacce wata Sa'a Ƴar snow ta yi a kanta, zagi ne na cin mutunci da sharri, wai Baby Futuha ta tiktok karuwa ce kuma tana da hotunanta da shaidu akan hakan. Tashin hankalin har da hotonta daga ƙasa gefen bidiyon. Ba ta san sadda ta kwalla ƙara ba a ɗakin bar ya farkar da Humaira me baccin sha biyu. Su biyu ne dama kaɗai a ɗakin, ita Humaira ma ba ta san Futuhar ta shigo ba domin gaba daya sun fita makaranta, kenan ta dawo ita. Kuka sosai Futuha ke yi hannunta har yana kakkarwa. Humaira ta ji hankalinta ya tashi, duk kuwa da cewar ba sa shiri ta miƙe ta ƙarasa gareta.   "Anti Futuha lafiya?" Ba ta ko kalleta ba ta wuce da sauri ta yi hanyar fita. Humaira dai na kallon ikon Allah. Toh me ya yi zafi haka? Ta watsar da batunta gami da buga hamma. Futuha kai tsaye falo ta nufa, babu kowa, cikinta ya ɗuri ruwa, yanzu wa za ta faɗawa wannan abu? Muddin Mami ta ji ranta zai ɓaci don dama ba da son ranta Futuhar ke ɗora bidiyo a Tiktok ba. Anna kuwa, ba lallai shawararta ya yi wani tasiri ba. Don haka kawai sai ta yi ɗakin samarin yayyunta. Kwankwasawa take iya karfinta, babu kowa sai Dawud dake baccin rana. Ya taso a firgice, har zai soma masifa amman ganin yanayinta sai ya fasa. "Meyafaru?" Ya tambaya a ruɗe. Ta bude wayar da tuni ta shige lock, miƙamasa ta yi. Ya kalla tun farko har karshe, ya dafe kai yana mai runtse idanu. "Kinga irinta ko! Kin ga abinda nake faɗamaki. Na faɗamaki matan nan na Tiktok muddin suka ga kina musu shiga hanci da kudundune zasu sanyoki a gaba. Ballantana ma ganin kin kama hanyar shahara. Sa'a ƴar snow! Yarinyar ba ta da mutunci ko kadan, matar da ke ikrari a fili ita karuwa ce kuma ba ta ga ranar da za ta rabu da karuwanci ba sannan ta shirya tone-tonen yan barikin tiktok." Futuha ta jinjina kai har sannan tana sheshsheka, ta san da wannan, haka ɗin ne ma ya sanya ta shiga ruɗu da tashin hankali, waɗanda za su yarda da zancen sun fi waɗanda ba za su ɗauka ba yawa. Ko ba komai jita-jita ya fi saurin yaɗuwa koda kuwa akan ƙarya ne. "Ya zan yi Dawud? Na shiga ruɗani, me zan ce jama'a su yarda sharri ne aka yimin?" Dawud ya yi shiru, shima dai kansa ya yi masifar ƙullewa. Ya rasa me zai ce, daga  kuma irin yanda ake zuba ruwan comment na zagi da ma  masu rubuta ai za ta aikata lamarin ya samu karɓuwa kenan. Kafin su ce komai sai ga wayar Aina'u ya shigo, Dawud ya ɗaga. "Ke Futuha! Kinga wani  ɗan iskan bidiyo da Snow ta yi a kanki? Wallahi na shiga rudani, mene gaskiyar abin da ta ce game da ke?" Hankalinta ya kara tashi. "Aina'u ke ce mafi kusa da ni a ƙawayena, yanzu kin yarda da abin da aka ce a kaina? Idan kika yarda waye ba zai ƙi yarda ba? Wallahi Allah karya take yimin, ni Futuha ban taɓa zina ba a rayuwata. Ke kanki kin sani." "To ai kuwa wallahi kinji na rantse sai kin yi dagaske za ki wanke kanki a idanun duniya musamman ƴan Tiktok, yanzu na faɗamaki a whatsapp na ci karo da bidiyon an turo group dinmu na makaranta." Zaro ido Futuha ta yi, ji take komai tamkar a mafarki, ta kasa amsawa. Ga Aina'u a layi tana faman hello hello, ga kuma sunan Babban Yaya (Wato Mubarak) yana yawo a saman screen din, shaidar kiransa ya shigo. Dawud zai katse na Aina'u ya ɗaga  cikin sauri Futuha ta warce wayar ta kasheta gaba ɗaya. Cikinta ya murɗa ba ta tsaya ba shi amsa ba ta ruga ɗakinsu. Ta tsallake Mami wacce fitowarta kenan daga bangaren Anna su na tattaunawa akan auren Tasleem da wadanda ya dace su gayyata cikin yan uwansu na Agadez. Mami ta bi ta da kallon mamaki da tunanin ko lafiya, wayarta ta yi ƙara, ganin Mubarak yasa ta ɗaga. "Mami, kina sane da abin da yarinyar can ta aikata ko?" Cikin rashin fahimta da tsananin ruɗewa ta ce. "Wa kake nufi? Meyafaru wai?" Nan ya ba ta labarin ire-iren raye-raye da Futuha ke ɗorawa a Tiktok, ya kuma cewa Mamin ta duba whatsapp zai aikomata da wani bidiyo ta gani. Hannayen Mami har rawa suke yi, ta hau online bayan ta kunna data, saƙonni suka shiga faɗowa har na Hajiya Lubna wacce itama bidiyo ta aikomata. Sam hankalinta ya yi gaba akan saƙon Mubarak, ta buɗe ta soma kallon irin ruwan rashin mutuncin da wata wai Sa'a ƴar Snow ta saukewa Futuha, ga hoton Futuhar nan daga ƙasa. Mami tuni hawaye sun wanke fuskarta, ban da innalillahi ba abinda take furtawa, ya yi daidai da shigowar Dawud falon, ganin yanayin Mamin sai ya tabbatar abin da yake gudu ya afku, wato dai Mubarak ya sanar da Mamin komai. Ya kuma san halinsa, maganar ba iyakar Mami za ta tsaya ba, sai ya dangana da Abbansu. Ganin tsayuwa na neman gagarar Mamin sai ta zauna a hannun kujera mafi kusa da inda take tsaye. Dawud ya karasa da sauri. "Mami, yi a hankali." Ta girgiza kai, ina batun hankali anan bayan ɗiyarta ta jawomusu abin kunya abin kuma magana. Kamar kuma wacce aka tsikara ta mike da sauri ta nufi hanyar dakin su Futuha sam hankalinta ba ya tare da ita. Ganin haka Dawud ya mara mata baya, fadi yake "Mami wallahi sharrin ƴan Tiktok ta hadu da shi, ke kin sani diyarki ba za ta aikata maki abin kunya ba. Don Allah Mami ki saurare ni, nasan wace wannan Sa'ar, ba ta da mutunci na ƙarshe." Inaa! Ba ta san ma yana yi ba, shigarta ɗakin ya yi daidai da fitowar Futuha daga banɗaki, har a lokacin sheshsheƙa kawai ta ke yi. Humaira tuni ta tashi tana zaune gefen gado ta yi shiru, ita dai ta san babu lafiya. Ba ta taɓa ganin Futuha na irin wannan kukan ba kamar na wacce aka yiwa mutuwa. Shigowar Mamin ya sa ta maida hankali gareta, ba ta yi wata-wata ba ta hau dukan Futuha tana kuka tana fadin. "Shegiya marar tarbiyya! Wato ke ga yar iska ashe raye-rayen da na nunamaki bana so shi ne kika cigaba da yi har ya jawomaki kalmar karuwa?!" Mami bugu take ita kuwa Futuha tana ihun kuka. Humaira da Dawud hakuri kawai suke ba Mami, su kansu hankalinsu ba a nutse ba. Babu kamar ita Humairar da ba ta san hawa da sauka ba. Mami don kanta ta ture Futuha ta juya, har za ta fice ta dawo ta nuna ta da yatsa. "Na ba ki mintuna uku ki gaggauta goge account dinki kaf na social media da kike raye-rayen banza, wallahi kika bar ko guda daya ban yafemaki ba. Shashasha kawai!" Tana kai wa nan ta fice daga dakin har tana bangazar Dawud. Jikin Humaira a sanyaye ta kalli Dawud, kamar jira yake kuwa ya watsa mata banzan kallo. "Algunguma, ficemin daga daki za mu yi magana da yar uwata." Kamar ta ce mishi ai Abba ya hana su shigowa dakin sai dai ta hadiye ta fice sum-sum zuwa falon da babu kowa ta zauna jugum. Yau ba ta je gidan Anti Laila ba sakamakon rasuwar da aka yiwa Anti Lailar a can dangin mijinta. Tana nan zaune ta ji muryar Abba a bangarensa yana tashi har zuwa cikin falon, faɗa yake kamar zai ari baki. Mamaki ya kama ta, Abban bai fita kasuwa ba ko kuwa dawowa ya yi? Yanzun tare suke tafiya da su Yassar har Dawud wanda shi yau din bai jw ba sanadin ciwon kai da ya addabe shi Abban ya ce ya zauna, ya ce musu sam ba ya son zaman banza. Humaira ta mike tsaye kirjinta na bugawa da sauri. Ta dai tsinkayi Abban na cewa "Cire ta zan yi daga makarantar! Itama ta fiddo miji na aura mata ko kuma na aurar da ita ga koma wane ne don wallahi ni dai Isuhu ba za ta yi sanadin zubewar mutuncina ba a garinnan!' Gaba daya jikin Humaira ya hau rawa, ko ba a faɗa ba ta sani akan Futuha ake tashin hankalin nan. To me ta aikata mai muni har haka da maganar ta yi zafi? Tana nan tsaye Yassar ya shigo falon bai ko kalle ta ba ya yi hanyar dakinsu, shi ma Dawud na ciki. Ba ta motsa ba kuma sai ga yan makaranta sun dawo. Hankalinta ya dan kwanta ganin Raihana da Ummita. Ta karasa da sauri. "Ku gidannan fa ba lafiya. Kin sani ne?" Ta jefawa Raihana tambaya ganin yanda hawaye suka wanke fuskarta. Jikinta ya kara yin la'asar. Raihanar ce ta ba ta labarin abin da aka yiwa Futuhar, dafe kai Humaira ta yi gami da ambaton sunan Allah. "Tirƙashi!" Abin da kawai ta ce a baki kenan. Dama tun sadda Futuha ta soma yayin ɗora bidiyo Tiktok ta so ace ta mata magana amma ta sani ba za ta ji komai ba. Watakila ma ta kira ta da mai hassada kamar yanda ta kira Tasleem sadda ta yi yunƙurin hana ta ɗorawa. To na kusa ma an mishi wannan ikrarin ina kuma ga ita da suke mata kallon bare a cikinsu? Yinin ranar dai gidan ya kasance babu dadi, Abba ya yiwa Futuha kaca-kaca ya kuma rantse ya dakatar da karatunta har sai idan ta samu miji ta yi aure. Ya ba ta lokaci kankani akan ta fitar da daya cikin masoyanta a haɗa bikin da na yar uwarta. Idan kuwa ta ƙi shi da kansa zai nema mata abokin rayuwa. Tasleem haka ita ma ta dawo daga asibiti ta iske wannan abin wanda tuni tana da labarin komai. Futuha ranar kamar an aikomata saƙon mutuwa haka ta wuni babu ci babu sha, Mami ta ce a kyale ta. Ganin ba ta da mafita ya sanya ta komawa ɓangaren Anna inda anan ne ta samu sassauci domin Anna goyamata baya ta yi, ta ce Mamin su yi mata uzurin kuruciya. Ta dai lallaɓa ta kwantar mata da hankali. *** A sati biyun da Abba ya ɗibarwa Futuha don ta fiddo mijin aure, a wannan satin kafin su cika gaba daya ta rame ta zama mai wani irin sanyi, yan uwan Abba babu wanda ya goyi bayanta balle ya lallaɓa mata shi. Ganin haka Mami ta tashi takanas ta je ga aminiyarta Hajiya Lubna ko za ta amince Khalil ɗanta ya auri Futuha su rufawa junansu asiri. Amma ina, Hajiya Lubna ta nunamata ita gogaggiyar yar boko ce ta biyo mata ta kissa ta nunamata ta amince, amma bayan kwana biyu ta kira ta tace Baban Khalil ya ce shi kam ya riga ya gama magana da abokinsa akan ƴarsa da yake son Khalil din ya aura. Ta kwantar da Mamin hankali akan Futuha fa kyakkyawa ce son kowa ƙin wanda ya rasa, ta kwantar da hankalinta komai zai tafi daidai. Aikuwa cikin ikon Allah dai ga wani matashin ɗan chanji Alhaji Yakubu ya zo takanas ya samu Abba akan yana son aurenta. Mutumin ya jima yana ganin fuskar Futuha a Tiktok, kasancewarsa ɗan duniya, yana son mace mai irin wayewarta ya kuma jima yana bibiyarta akan ta amince ya aure ta, tana wulaƙatanshi. Tashi guda da ya ga abin da Sa'a ta yi mata ya ga dama ta samu da zai yi wuf da ita. Yana da mata ɗaya da yara uku, ya kuma tabbatarwa Abba koda Futuha ba ta son zama da matansa shi ɗin zai nema mata wani muhallin daban cikin waɗanda ya mallaka. Abba ya yaba da salon nutsuwa da ladabin da ya zo mishi da ita don haka ya ce ya je nan da kwanaki uku ya turo iyayensa. Wannan lamarin ya yiwa Yakubu daɗi sosai. Ya yi ta godiya. Bayan tafiyarsa Abba ya yiwa Mami zancen, ta yi murna da hakan a fili musamman ganin yana da rufin asiri. Abba ya san shi don Alhaji Yakubu ba ɓoyayye ba ne, yaro ne abokin tafiyar manya. Yana da kuɗi sosai sannan akwai shi da kyauta. Ko kusa abin hannunsa bai rufe mishi idanu ba. Ya samu kyakkyawar shaida wajen jama'a da suka san shi a waje, a halayyarsa kuwa na baɗini wannan daga shi sai Mahaliccinsa sai kuwa wadanda ya buɗamusu suka sani. Futuha fashewa ta yi da kuka sadda Abba ya yi mata zancen. "Wallahi Abba bana sonsa, mutumin yana da son mata kuma..." Wurgin da Abba ya kai mata da carbin dake gefensa ya sanya ta saurin yin gum da bakinta. "Rufemin baki nace! Ke har kina da fuskar da za'a gani a aureki da ita, ban da ma shi so ba ruwansa, mutum mai mutunci da ƙima irin Yakubu mai zai yi da ƴar rawa? Macen da ba ta killace jikinta ba ta sake shi ko'ina yana yawo ana kallonta? Toh bari ki ji, muddin ni dai mahaifinki ina raye, ba ki da miji sai Yakubu. Na kuma ba shi damar turo magabatansa nan da kwanaki uku, karatu idan ya amince maki ki cigaba wannan shi ya ga zai iya, nidai ubanki ba da yawuna ba saboda ni yanzu tsoro kike ba ni, nema kike ki fi karfinmu. Wannan wayewar ta banza kuma da kika ɗaukarwa kanki, ki je can ki ƙarata da ita, Allah ya shiryeki idan ke mai ganewa ce. Tashi ki fice ki ban wuri, saura ki je ki kai ƙarata tun da ban isa da ke ba." Yana nufin kai ƙara wurin surukarsa Anna kamar yanda ta yi a farko da ya yi batun auren har sai da Annar ta tako sashinsa da zummar lallaɓashi ya janye. Cike kuma da ba ta girma ya ce ta yi hakuri amma ba zai zuba idanu tarbiyyar yaransa su lalace ba. Ganin ba ta taɓa neman alfarma a wurinsa bai yi ba sai wannan ne ya sanya ta kama mutuncinta ta yi shiru da baki. *** Su Humaira na ɗaki sai ganinta suka yi ta shigo tana aikin da ta saba kullum, wato aikin kuka. Humaira kukan yanzu kam ko a jikinta, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan doka, ta lura hatta Tasleem itama abin ya bar sosa ranta, kowa ya fice a harkarta ya gaji da rarrashi. Tasleem dai waya take amsawa da Hamza, ganin ihun kukan Futuha ya cika dakin kawai sai ta ja guntun tsaki ta fice. Su din ma hirarsu ta tsaya, kowa ya shiga danna waya, su kansu Abba ya ja musu kunne sosai ya kuma rantse duk wacce a cikinsu ta yi irin gangancin Futuha ba zai duba komai ba zai aurar da su. Wannan ya sa bakinsu ya mutu murus. Humaira ta bude saƙon da ya faɗo wayarta a lokacin. Ta sani, shi kadai ne zai yi mata saƙo don haka ta buɗe. _"Ko kinsan mai hakuri ba ya taɓa karo da rashin nasara a rayuwarsa? Ki sani ni ɗin masoyi ne a gareki, ba kuma hakan zai sauya komai ba. Ma'ana, koda ace zamu shekara kina wahalar da zuciyata, Humaira ki sani, Fadeel bai fara sonki domin ya daina ba. Muddin rai ba zan fasa neman soyayyarki ba."_ Ta karanta kusan sau uku, ta rasa dalilin da yasa ba zai taɓa turo kata saƙo ta karanta sau ɗaya ba, kuma ko kadan ba ta iya goge saƙonninsa. Abin da yake ba ta mamaki shi ne, ta ga yana hawa whatapp amma ko sau daya bai taɓa yunkurin yi mata magana ta can ba. Kira ma da ya ga ba ta ɗagawa ya bari. Sai dai akwai lambar da take zargin ko shi ke kiranta da shi. Za a kira ta ɗaga amma ba za a ce komai ba sai dai ta yi ta sallama tana sababin anƙi magana ƙarshe kuma ta ji ɗif an katse kiran. Wannan abu na ba ta mamaki, tana kuma zargin Fadeel ne. Ta yi shiru tana so ta hasaso dalilin wannan ƙiyayya da ta ke yiwa Fadeel amma duk iyakar tunaninta ta kasa, karshe ta ja guntun tsaki. Ta bar shi akan kawai ita ba ta kaunar soyayya, ba ta kaunar kowace mu'amala da za ta haɗata da namiji. Da wannan ta watsar da tunaninta. *** BAYAN SATI UKU... Garin aka tashi da shirye-shiryen shiga wata mai alfarma wato Ramadan, wanda ake kyautata zaton ganin wata a ranar ko washegari hakan yasa Mami suka yi dogon list na cefane ita da Humaira. Mamin ta dube ta bayan sun kammala tana murmushi. "Wannan azumin a daɗinmu, girkinki zamu ci. Kin ga kina yi idan kin shirya komai sai ki yi hoto, Raihana ta buɗemaki account a instagram kina ɗorawa da sunan tallah, idan Allah ya taimaka zuwa sallah sai mu samu odar girkin sallah ko su samosa da sauransu. Da kaɗan-kaɗan kuma ki ji an soma neman ki yi na biki. Ina mai tabbatar maki da wannan iya girkin naki za ki samu alheri mai yawa da zai yi maki amfani har na kusa da ke." Humaira cike da jin dadi ta hau murmushinta mai bayyana wushiryarta ya kara fiddo da usulin kyanta. Ta ma kasa magana don murna. Mami ta yi dariya. "Allah ya kyauta, wannan dariyar duk ta murna ce? Tashi dai maza ki je kar yamma ta kawo kai. Kinga siyayyar da yawa." "Toh Mami." Ta mike ta gyara zaman mayafin doguwar abayar dake jikinta ruwan madara mai dark brown din mayafi. Ƙafarta sanye da safe ba ka ganin komai sai tafin hannunta sai kuwa fuskarta da ta shafa hoda ta zizira kwalli. Ta yi kyau tsaf duk kuwa da cewa ba kwalliya ta yi ba. Irin matan nan ne wadanda ko ba kwalliya su na kyau. Har ta fice a ɗakin Mamin na bin ta da kallo tana murmushin da ta ba kanta sanin ma'anarsa. Ta yi tafiya daga gidan zuwa titi na ɗan mintuna sannan ta fito babban titi. Garin akwai rana sosai duk kuwa da cewar an yi sallar azahar amma hakan bai sa ya ɗan yi sanyi ba. Dakyar ta samu abin hawa ta shiga. Sun yi tafiya mai ɗan tazara sun tsaya a daidai junction din sabon titi wayarta ta ɗau ƙara. Ta ji gabanta ya fadi don tsoro, Ummita ta ce mata ana satar waya a ɗan sahu wannan yasa kodayaushe idan za ta fita ta ke sanya ta a vibration amma yau sauri ya mantar da ita. Ta ɗan kalli mata biyun da ke gefenta sai ta ga ba su yi mata kama da ɓarayi ba don haka ta ciro ta da sauri, ganin sabuwar lamba ya sa ta ɗagawa da sallama. Madadin ta ji shiru an yi kamar yanda aka saba yi mata, sai ta ji wannan karon an amsa. Duk da ta ɗau muryar hakan bai sa ta tambayar "Wa ke magana." ba. "Wallahi ina sonki." Ya furta cike da kasala, abinda bai taɓa faruwa ne ba gareta ta afku a sannan. Ji ta yi tsikar jikinta ya tashi, ta ji lebbanta sun mata nauyi ta kasa buɗe baki balle ta rufe shi da faɗan da ta saba. Sai kawai ta zame wayar daga kunnenta ta katse kiran. Daidai lokacin da aka ba su hannu, juyawar da za ta yi suka yi ido hudu da shi, kallonta ya ke bilhakki har sai da na bayansa suka cikamasa kunne da hon, ta yi saurin kauda kanta. Kallon ya dawo mata da sabuwar tsanarsa, ta ji ranta ya ɓaci, ta kuma rasa dalili. Ba ta kara juyawa ba har suka yi mishi nisa, ba ta kuma san inda shi ya yi ba. Ƙarar shigowar saƙo wayarta ya sanya ta buɗewa. _"Kin min kyau. Ina roƙon Allah ya nunamin ranar da Fadeel zai mulki zuciyarki gaba ɗaya. Ya zame maki haske maganin kowane duhu. Ameen."_ Ta yi saurin maimaitawa sau ɗaya ta jefa cikin jakarta. Ana zuwa kasuwar rimi ta sauka bayan ta fidda facemask dinta a jaka ta rufe hanci da baki. Haka ta dinga kutsawa ta kammala siyayyar Mami, ba ita ta bar kasuwarnan ba sai yamma lis duk ta jiga ta. Washegari ma haka ta kara tashi ta fita zuwa haɗo kayan kwalam na yin Snacks iri-iri. Hatta da kayayyakin haɗin salad sai da ta siyo. Wannan karon dai Abba ya saki bakin aljihu domin shi dai idan har watan azumi ne yakan yi bakin kokarinsa wajen wadata gidansa, hakanan da sallah. Ya kuma ce lallai lallai su Tasleem da Futuha su dinga shiga kicin su koyi girki wajen Humaira. Rana ɗaya idan suka yi fashi, za su yi karo da fushinsa. *** Murja ce durkushe gaban Alhaji, ya kalleta dakyau jin ta kasa magana. Da murmushi dauke a saman fuskarsa ya ce. "Kin yi shiru Murjanatu, kiyi magana." Ta ga dai shirunta zai sa ta cuci kanta don haka ta muskuta ta soma cewa. "Dama Yaya Fadeel nake so a auramin." Jin haka kan Alhaji ya ɗaure, ya yi sakato yana kallonta. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 "Shi Fadeel din ya sani?" Ta girgiza kai tana kara sunne wa kamar mai jin kunya. Alhaji ya yi shiru sai kuma ya ce. "Shikenan, ni dai b na yiwa yarana dole balle kuma namiji. Zamu yi maganar da Fadeel duk amsar da ya bayar za ki ji daga Antinki." Ji ta yi kamar Alhajin ya harba mata mashi a ƙahon zuciya, da irin wannan amsar ai gwara kawai ya ce mata aa kansa tsaye. Abu ne da ya sani kamar yanda ta sani, zai wahala Fadeel ya amince da shi, ta yi zaton yanda Alhajin ke yabawa da nutsuwarta zai ce ya amince ya zaɓawa Fadeel din ita matsayin matarsa. Haka ta mike ta fice gwuiwa a sake. Bayan fitarta Alhaji ya yi shiru, ta ina zai soma ɓata ran ɗannasa wanda a baya ya sha baƙar wuya a dalilinsa da mahaifiyar Fu'ad? Ya musguna mishi, bai duba maraicinsa ba na rashin uwa ya yi watsi da shi. Karshe don kansa da ya gaji bayan ya yi hankali ya fice ya koma dangin mahaifiyarsa a can ƙasar Kamaru. Sai kuma bayan da ya kwashe dogon shekaru har kusan biyar ya dawo yanzun kuma ya hargitsa shi komai ya ƙara hargitse mai? Yaransa biyar kacal a duniya, Fadeel ne babba sai Fu'ad sai kuwa ƙanwar Fadeel uwa ɗaya uba ɗaya Hannatu dake aure a can Adamawa, sai yaran Anti Amarya biyu, Khadija da Abdulmaleek. Shi hakanan Allah ya yi shi ba mai yawan haihuwa ba, matansa babu me yin tsarin iyali.   A ƙarshe dai ya yanke zai mishi maganar auren don shi kansa yana damuwa kwarai akan zaman yaran haka(wato Ibb da Fadeel) ba tare da iyali ba. Har ga ƙaninsu Fu'ad ya yi auren ya bar su. ***   Fadeel ya nutsu a gaban mahaifinsa, bai katse shi ba har ya kai aya. Sai a lokacin ya yi magana.   "Na ji bayananka Alhaji, ina neman addu'arka musamman a wannan wata mai alfarma da za mu shiga akan neman zaɓin Allah. Sai dai kuma ba na kaunar Murja, ba na sonta matsayin matar aure. Don Allah abar zancenta." Jinjina kai Alhaji ya yi, ya ɗan murmusa kaɗan. "Shikenan, Allah ya sa hakan ya fi alheri. In sha Allahu zan tayaku kai da ɗan uwanka. Ya kamata ku maida hankali." Fadeel ya amsa a ladabce. Daga nan suka rufe wannan babin suka cigaba da tattaunawa akan abubuwan alheri na sadaka da neman lada da Alhaji ke yi duk shekara idan watan azumi ya kama. Kamar yin kunu da abincin sadaka, kyautar butoci, ruwa, dabino da ma sauransu a masallatai., daukar nauyin tafsir, sai kuwa idan sallah ta matso ya yiwa ƴan uwansa marasa ƙarfi da marayu da dama sutura. Da wannan suka rufe babin Murja da ma batun aure. Anti Amarya dake laɓe a bayan labulen ɗakin Alhaji, ta ji ciwon cewa da Fadeel ya yi ba ya son ƙanwarta. Ta yi ƙwafa, ai idan ya san wata bai san wata ba. *** A daren ranar Lahadi gaba ɗaya garin aka dau murnar ganin watan Ramadan. Lokacin Sahur gaba ɗaya gidan suka tashi aka yi idan ka cire Tasleem wacce ba ta da sallah.   Lokacin shan ruwa na kawo kai, Humaira da Ummita har Raihana ana kicin ana faman kai da kawowa, Tasleem ba ta shiga ba don langaɓewa ta yi wai mararta na ciwo. Ita kuwa Futuha tana tsaye kawai tana yatsine-yatsine da gwatsale wani abun idan Humaira ta yi wai ba haka ake yi ba. Ita dai ba ta tanka mata ba albarkacin watan da suke ciki na ibada. Sai da suka kammala komai sannan suka jera a tsakar falon bayan shimfiɗa ƙatuwar ledar cin abinci. Na Abba kuwa can ɓangarensa suka kai aka shirya komai. Itama Anna, Raihana ta kai mata komai ta bar ta tare da su Muhsin don a duniya Anna ba ta fiye son zuwa falon Mamin ba sai da kwakkwarar dalili.   Sai a sannan Tasleem ta shiga kicin din ta ɗibi abinci ta dawo falon tana ci ta a yatsine fuska wai gishiri ya yi yawa. Ba ta ko jin nauyin yan uwanta maza dake zaune a falon su na taɓa hira. Haka aka sha ruwa aka yi zaman cin abinci bayan kowa ya yi sallah. Mazan suka dinga santin girkin amma da zarar sun yi ido da Humaira su watsa mata harara idan ka cire Ƙasim wanda tun wata rana da ya shiga ɗakin Mami zai ɗau kuɗi ta gan shi kuma ta rufamasa asiri ba ta faɗawa kowa ba, tun a ranar ya soma ganin ta da ƙima a idanunsa. Ya ke kuma jin kunyarta. Yassar kuwa faɗi yake ai ba basirarta ba ce, koyamata aka yi. Futuha  ta ja tsaki.   "Wai kai kana wani zance, ina abin yake? Ni ba abin da ya kara ɓatan rai wai sai da Abba ya ce wani mu shiga kicin mu koyi girki wajenta. Don Allah ku ji wani abu." Dariya suka yi idan ka cire Ƙasim dake faman cin sandwich da ya ji kaza da su cheese yana santi. "So ya ke ki je ki yiwa Alhaji Yakubu kar a ji kunya mana." Jin an ambaci Alhaji Yakubu nan da nan ta ɗaure fuska. A duniya yanzu babu wanda ta tsana irinsa, mutum dai kamar maye. Abu daya da ta sani shi ne, daga maganar zuwa kamawar watan da suke ciki na azumi ya yi mata ɓarin kuɗi sama da dubu ɗari, wannan kaɗai shi ne ya burgeta musamman ganin cewa Tasleem ba  ta samu hakan ba. Rabu dai da Hamza akwai kulawa a baki amma babu ko asi da ya taɓa kawomata. Wannan abu na yiwa Tasleem ciwo kuma yana fasawa Futuha kai, tana son ta ga ba ta son mutum yana bibiyarta kamar jela. "Kar ka sa na tashi, har wani tsami na ji abincin ya soma yimin a baki." Yassar da Dawud suka kwashe da dariya. Tasleem ta yamutse fuska ta ce. "Gulma, a bakya so kike kwace ƴan chanjinsa. Fuska biyu." Futuha ta dire fork din hannunta da ta ke cin haɗin salad da shi, tun ba ta kai ga haɗiyar wanda ta ke tauna ba ta soma balbaleta da masifa. "An kwata ɗin, ina ce albarkacin kaza dai ƙadangare ke shan ruwan kasko? Ko kin manta abin da Mami ta ce akan amfanin kudin?" Tasleem ta hadiye zancenta, ta tuna Mamin cewa ta yi Futuhar ta saki jiki da Alhajin ta dinga nuna masa kulawar koda iyaka baki ne, muddin dai zai bayar da kuɗin ba za a ji kunya a auren ba tunda ba su da tabbacin samun yanda ake so daga wajen Abba. Wato na siyayyar kayan ɗaki da sauransu. Maganar Futuha ta katse ta. "Kuma ko banza gwara Yakubu tun daga nan an san zai iya riƙe mata biyu, wani kuwa da ko ɗayar ma ya kasa nunawa zai iya sai afkin waya da ƙalƙalar  turanci kamar tsatson sarauniyar Ingila." Suka kwashe da dariya. Ran Tasleem ta kai kololuwa a ɓaci, su Humaira na zaune su dai su na shan ruwa abin su daga gefe suna kallon ikon Allah. Raihana ce ta tofa. "Kai Adda Futuha, ramuwar gayya fa akwai zafi kar ki kai Adda Tasleem bango." Aikuwa tana cewa haka kamar ta kara zuga Tasleem sai kuwa ta yi caraf ta ba ta amsa. "Kyale ta Raihana, ai mugun abu ya ƙare a gindinta tunda ko ba komai nidai auren soyayya zan yi, Hamza gani ya yi yana so a mutunce. Wata kuwa sai bayan an jefe ta da kalmar karuwanci, ƴar rawar Tiktok sannan ta yi na'am da Alhaji mai zubin moɗa." Lallai, baki idan ya san me zai faɗi bai san me za a mayar masa ba. Aikuwa Futuha ta yi kukan kura har ta na cilli da bowl din salad dake saman cinyarta zuwa ƙasa, ta yi kan Tasleem da kokawa. Itama Tasleem kasancewar a wuya ta ke kawai sai ta biye mata suka hau jibgar juna. Dakyar Yassar ya shiga tsakaninsu gudun kar Abba ya ji. Tasleem na  huci ta ce. "Ni kuɗi bai dameni ba tunda zan auri wanda yake sona nake sonsa. Arzikin dai ai na Allah ne, kuma ko makaho ya shafa ya san Hamza ba talaka ba ne. Alhamdulillah ba a taɓa yimin wannan mugun ƙazafin na karuwanci  ba." "Shegiya! Ni kike kira karuwa, ai gwara ni sharri ne, ke kuwa sau nawa kina yiwa Mami sata? Ko ranar da aka yi na Humaira, ina ce ke ce kika kawo shawarar a yi mata wannan sharrin don ki wanke kanki. Ke ce kika ɗauki kuɗaɗen, ganin Yassar ya kama ki sai aka shiryawa Humaira tuggu don kar Mami ta zarge mu." Humaira da ke shirin kai kofin kunu bakinta ta yi saurin ajiyewa, ashe ma ɓarayin biyu ne? Ba ma wannan kadai ba sai ganin yau dai Allah ya karɓi addu'arta gaskiya ta yi halinta. Tasleem gaba ɗaya ta yi wuri-wuri da idanu, ko kaɗan ba ta zaci Futuhar za ta yi mata wannan tonon sililin ba. Yassar ya dakamusu tsawa amma kasancewar girma ya faɗi ko a jikinsu, sai dai tsawar farko daga Abba ya sanya gaba daya suka yi tsit. Ashe yana tsaye a bakin ƙofar falon tun sadda suka soma kokawa, Mami na biye da shi a baya. Gaba ɗaya hankalinta a tashe, wato dai ya allura ta tono garma? Ba wannan ba ma, babu uwar da za ta so ganin yaranta kansu a rabe. Gaba daya falon ya yi tsit su Tasleem sai rarraba idanu ake. Ya shigo tsakiyar falon ya wanke su ganin ba su duba girman watan da ake ciki ba na ibada su na yi mishi faɗa a falo. Daga nan ya nemi sanin abin da ya faru da Humaira a baya, nan fa Raihana kamar wacce ake tsikara ta ba shi labari. Humaira kanta a ƙasa tana hawayen farin ciki, wato da Allah ya tashi wanke ta sai ya sa Abba da kansa ya ji zancen ba iyaka Mami ba. A ranar su Yassar da Futuha sun ga tashin hankalin Abba, ya kuma ci alwashin saɓawa duk wanda ya ƙara jarraba musgunawa Humaira. Hatta da Mami mai kokari akan Humaira a ranar har da ita ya haɗa ya ce ai laifinta ne da ba ta tsawatar musu shiyasa suka samu sake. Haka Abba ya yi faɗan da ba su zata ba har Humairar daga nan ya fice daga falon. Mami ta bi yaran da kallo sai kawai ta juya ta bi bayan mijinta. Humaira ta mike ta kalle su fuskarta dauke da murmushi ta juya zuwa ɗaki.  Ranar jin ta take ranta babu ko ɗigon bakin ciki sai dai ba ta ji dadin dorawa Mami laifin su Yassar da Abba ya yi ba. Amma ta yi mamakin Abban, a baya tana tunanin ko sonta ne ya daina, ko ya manta ma da ita a lissafin ƴan gidan sai kuma abin da ya yi yau ɗin ta fahimci tana nan daram a zuciyarsa kawai dai ba shi da lokacin kansa balle na hira saboda yanayin kasuwa.  Banɗaki ta shige ta ɗora alwala ta dawo ta zura hijabinta ta shiga lazimi. Ta na nan zaune ta yi shiru, wani lokaci can take tunowa ita da Dada musamman a wata irin na azumi yanda suke zama bayan shan ruwa a yi hira kafin lokacin sallar isha'i.   Ƙarar wayarta ya katse mata tunani, ta sa hannu ta ɗauka. Fadeel, shi ne  sunan da ya bayyana saman screen din, haka Raihana ta adana mata lambar ba da son rai ba. Albarkacin watan da suke ciki ya ci ta ɗaga da sallama. Ya amsa daga can ransa fari sol.    "Ina fatan kin sha ruwa lafiya?" "Lafiya kalau." Ta amsa a taƙaice. Shiru ya ɗan biyo baya, ya rasa me zai ce yana gudun ya yi furucin da zai sa ta katse wayar gaba ɗaya. Ya kasa hakuri balle ya danne don haka ya ce. "Sai yaushe Humaira? Sai yaushe za ki samarwa wannan ɗan marayan gurbi a zuciyarki? Ba zan gaji da roƙo ba, ki ba ni dama Humaira. Wai kin san so kuwa?" Nan da nan ta ji ya har ta soma harzuƙa a sanadin kalmar so da ya ambata, cike da gatse ta ce. "Sai nan da shekara." "Kin yi alƙawari nan da shekarar za ki amince ki yarjemin da batun aure?" Ta dauki maganar a zancen banza, ta sani babu wahalallen da zai yi dakon shekara ya auri budurwar da ba ta ko son zancen auren balle auren. Don haka babu dogon tunani ta amsa. "Eh, na yi muddin za ka rabu da kirana ka bar takuramin." Shiru na wasu lokutan sai kuma ya sauke nannauyan ajiyar zuciya. "Za ki same ni da bin umarninki, amma kiyi hakuri koda saƙo na dinga aikomaki ta waya. Ke kuma ki daure ko da sallama ki amsamin domin na san kina sane da ni." "Naji." Ta amsa gabanta na faɗuwa ba tare da ta san dalili ba, ta ji zufa ta keto mata. Tsanarsa ta ke ji yayinda a wani gefe can a ƙasan ranta ta ke jin wani abu da ba ta tantance ba. "Na bar ki lafiya, ki yi hakuri na adana dukkan wayoyinmu, abin nufi nayi recording tun daga farkon wayarmu har na yau. Hakan kan ɗebemin kewa wasu lokutan idan son jin muryarki ya ci ƙarfin kwakwalwata. Ki dage da addu'a a wannan wata mai alfarma. Ina roƙon Allah ya yi maki zaɓin abokin rayuwa nagari, koda ba Fadeel ba." Yana kaiwa nan bai jira cewarta ba ya katse kiran. Ta yi ƙuri tana duban wayar, hakan na nufin wayar ƙarshe ce tsakaninsu sai nan da shekara? Ta taɓe baki, ta sani cewa ta ba shi aiki mai wahala. Kuma ba zai ma iya shekara yana wahala a kanta ba. Watakila ma kafin sannan ya yi aurensa. Ta watsar da tunani ta yi jifa da wayar ta mike jin an soma kiraye-kirayen sallar isha'i. *** Anna ce ke yiwa Mami faɗa kamar ta ari baki. "Kin bari miji ya rainaki ya raina uwarki, dama tun akan batun auren Futuha na san cewa Isuhu ya sauya daga yanda na san shi. Wato yanzun ya ci moriyar ganga ya yar da koren, ke yanzu ban da ke sakara ce wawiya, kina tunanin har wani karfin iko kike da shi a wajensa? Mutumin da ya dubi tsabar idon mahaifiyarki ya ce ba zai janye kudurinsa na aurar da Futuha ba? Toh wallahi Maryama ki shiga taitayinki tun kafin dare ya yi maki, mazan nan dai babu amana bar ganin wai girma ya soma kama shi, don ya dankaro maki kishiya ƴar zamani ba komai ba ne. Tun wuri ki ƙwatarwa yaranki ƴanci a wajen mahaifinsu, ki murje idanunki dakyau ki daina bari yana wulaƙanta min jikokina akan wasu bare can. Ban da ma mutum mai shegen mantuwa, Isuhu ko kare ne ya fito daga gidan su Fatima zai kalla da daraja? Matar da ta nunawa duniya cewa ta tsane shi har kwanciya ciwo take akan sai ya sauwaƙe mata ta koma garinsu? Mts, Allah ya wadaran naka ya lalace." Har Anna ta kai aya ita dai Mami ba ta ce komai ba banda huci da take furzarwa, daga ita sai zuciyarta ta bar wa sanin abin da take tunani. Dakyar ta taushi zuciyar ta soma magana bayan sakin ajiyar zuciya mai nauyi. "Anna ki yi hakuri, babu amfanin mayar da hannun agogo baya tunda mai afkuwa ya riga da ya afku. Na ba ki wuƙa da nama akan ƙwatarwa jikokinki ƴanci, ki yi abin da kika ga ya dace. Sai dai ki sani, ni Maryam ba da yawuna ba saboda daidai gwargwado yarannan su na kyautatamin, ba ni na haife su ba amma su na bi na sau da ƙafa fiye da ma yaran da na haifa a cikina. Kiyi hakuri idan maganata ta maki zafi." Anna ta wurga mata harara. "Au haka kika ce ko? Toh shikenan, ni zan san abin yi a kai kamar yanda kika ce. Koda kuwa zan rasa kwabo a asusuna, zan kwatarwa jikokina ƴancinsu, sai ya zama Isuhu ba ya ganin kowame ɗa a gabansa idan ba su ba. Mu zuba ni da ku." Mami ganin yanda ta ɗauki zafi kawai sai ta miƙe itama ranta a jagule ta bar mata ɗakin. Da ace Anna ta san damuwar da ke cin ranta da ba ta soma ƙara mata fetur a kan wutar da ta riga ta soma babbaka a zuciya da kwakwalwarta ba. Ta ja tsaki ya fi a ƙirga a hanya har ta ƙarasa ɗakinta. *** Azumi yana ta tafiya har a yau sun kai goma sha shida, lamarin su Tasleem da Abba ya ƙara tsauri musamman da ya fahimci ba su bi zancensa ba na shiga kicin. Futuhar da ta soma shiga, tun bayan faɗan da Abban ya yi ya goyi bayan Humaira sai ba ta ƙara leƙawa ba. Cikin ikon Allah wataran kwatsam sai ga shi a kicin din abin da Humaira za ta ce tun zuwanta gidan banda ranar da ya ji fitar gas ya cika gidan ya shigo, ba ta taɓa ganinsa a ciki ba. Ganin daga ita sai Ladidi da Ummita a kicin din ya shiga bambamin faɗa, a sannan Raihana na fama da Malaria mai zafi har allurai ta sha. Aikuwa har ɗakin ya shiga ya titsa ƙeyar Tasleem da Futuha zuwa kicin din yana gargadin Humaira akan lallai duk sadda ba su shiga ba ta sanar mishi. Tun daga wannan ranar ba su ƙara fashin shiga ba. Sai dai shigar da rashinsa ba amfani don kusan zama suke yi kawai ba sa komai. Abba ya yi siyayyar kayan sallah, kamar kowace shekara wannan ma da kansa ya yiwa kowa zaɓi idan ka cire samarin da ya ba kowannensu kudi su siya shadda. Yanmatan kuwa atamfa ce iri ɗaya sai dai bambancin kala, sai dubu uku da ya ba kowace budurwa a siya takalmin sallah. Shikenan bai ƙara daga haka ba, su Futuha aka dinga kauɗi ganin Alhajinta ya kawo mata shadda da atamfa har da leshi masu tsada sai kuwa dubu ashirin na mayafi da jaka da kuma ɗan kunne. Tasleem kuwa dayake ta soma shaƙa sai ta budewa Hamza wuta akan ko kyautar biyar bai taɓa ratsawa tsakaninsu ba. Ranar shi kansa ya yi mamaki da ta iya karya bille ta tambaye shi kuɗi, aikuwa ya ce ta turo acc no, take ya yi mata transfer dubu goma sha biyar. Tsabar rainin da ta yiwa kyautar ko faɗawa su Mami ba ta yi ba sai dai sun mata amfani ta siya abin da take so. Su Humaira kuwa Mami da kanta ta kara musu dinki, leshi mai kyau na ɗankwarai ta siya musu su uku kala ɗaya. Ana saura kwana biyar sallah sai ga Anti Jannat a gidan. Zuwanta ya yiwa su Futuha daɗi ko ba komai mace ce mai sakin bakin aljihu ga fankama. Burinta ta buɗa ko don ta nunawa Mami ita fa mijinta mai bayarwa ne, yana da kyauta sosai. Daidai da Anna ta fi ji da ita, abinda ya hana ta zama wajen Jannat din bai wuce na ganin surukanta sun nuna ba su kaunar hakan ba. A farko ta gwada amma aka so samun matsala, dole ta tattara ta dawo gidan da ta raina, gidan Abba. Suna zaune a ɗaki bayan sun kammala gwada dinkunansu na sallah, ya yi musu cif da cif, washegari kuma sai tafiya kitso da ƙunshi. Sai faman tsokanar Ummita suke yi ganin saurayinta ya kira tana kashe murya a waya, koda ta ajiye Raihana ta dube ta. "Wai ni yaushe za ki ba Ya Sayyadi damar zuwa gidannan?" Kasancewar zuwa lokacin sun sani ba kowa Ummitan ke soyayya da shi ba face Ya Sayyadinsu na makaranta hakan yasa suka samu abin tsokanarta. Ashe wai dama yawan tashinta da yake yi ta biya musu karatu mai dalili ne. Ummita ta ɗan harareta. "Ke me ya hana ki ba Jafar daman zuwa gida? Ni ai mun kashe magana da shi, na ce ya bari sai nan da shekaru biyu ko ma ince ɗaya da rabi idan mun yi candy, tunda yanzu muna SS2." "Kai Ummita, shekara ɗaya da rabi fa? Gaskiya sun yi yawa ina laifin ma shekara ɗaya?" Faɗin Humaira dake tsaye tana maida kayanta sif. Raihana ta tari numfashinta da sauri ta ce. "Wai ke ce mai yiwa wata faɗan shekaru sun yi yawa? Allah ya ba Fadeel hakuri. Wallahi idan na tuna abinda kika yi masa sai na ji kamar na yi maki dukan tsiya." Ummita ma kwafa ta yi cikin kunar rai ta ce. "Bar ta kawai Raihana, nima ba ki ji raina ba. Kuma babu kunya ba tsoron Allah har faɗamana take yi ya hakura sai nan da shekara. Shi marar zuciyar ina ne da zai biyemaki ya yi zaman jiranki? Ai tana sane, kora da hali ne kawai ta yi mishi. Ba fata nake maki ba, amma wallahi kafin ki samu kamar Fadeel a maza sai dai tsananin rabo." Humaira ta taɓe baki gami da jan guntun tsaki. "Kanku ake ji, ni na faɗamaku ina so nayi auren ne? Auren ku yake burgewa ba ni ba. Sai me? Idan ba auren zan fasa rayuwata yanda ya kamata ne? Ya yi ma gangancin zaman jirana ya gani idan haƙansa zai cimma ruwa. Ya ƙare rayuwarsa a tuzuru." "Allah ya kiyaye wallahi, bakinki ya sari ɗanyen kashi. Fadeel ya wuce nan, kuma ina masa fatan alheri, ya samu haɗaɗɗiyar da ta fi ki komai ƴar kwalisa in sha Allahu." Cewar Raihana. Haka kawai sai ta ji zafi a ranta, ta ji tana son yin kukan da ta rasa dalili, kawai sai ta fashe da kukan ba tare da ta yi shawara da zuciyarta ba. Raihana ta dubi Ummita kafin su dube ta jiki a sanyaye. Tun tana kukan su na ganin kamar wasa su na rarrashinta, har dai suka ga kamar kukan ba na lafiya ba ne suka fita da sauri suka yiwa Mami magana. Kai abin tsoro Humaira duk iyakar rarrashin Mami ba ta yi shiru ba, hakanan harafi ɗaya ya kasa fita a bakinta. Mami ta juya garesu. "Meyafaru ta soma kukan?" Nan suka ba ta labarin komai, ta ja hannun Humaira kawai suka fice a ɗakin. Su Raihana za su biyo bayansu ta dakatar da su, can falo suka tsaya yayinda Mamin ta shige ɗaki da ita. Sun yi jugum kuma sai ga Mamin ta fito ta dube su ranta a ɓace. "Don me za ku dinga yi mata batun saurayin da ba ta so?! Ina gargadinku daga rana irin ta yau koda wasa kada wanda ya kara kuskuren ko ambaton sunansa balle ya yi mata zancensa. Fadeel ko? Daga yau sunan nan ya fice a bakinku." Suka ce toh, su ma abin ya tsorata su, sun kuma kara gaskata zancensu, Humaira na da aljanu musamman da suka ji Mami ta mike tana fadin wai ta samu bacci idan ta tashi komai zai wuce a ranta. Tabbas zarginsu ya tabbata gaskiya, aikuwa ga mamaki Humaira sumul ta tashi tamkar babu abin da ya faru. Yanda ba ta yi zancen ba hakanan su ma ba su kara tada shi ba. Ba ma kamar Raihana mai shegen tsoron aljanu, Ummita sai dariya take mata ciki-ciki ganin ko zama kusa da Humairar ta ɗan rage yi a ranar. A gefe guda kuma ta yi alƙawarin muddin ta je Bichi za ta yiwa mijin yar uwar mahaifiyarta magana akan lamarin Humaira, yana ba da hayaki da maganin jinnu, in sha Allahu za ta karɓo mata. ***        *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Assalamu alaikum, ina mika saqon taaziyyar rashin member makaranciyar Dukan Ruwa kuma masoyiyata ta don Allah, Aysha Salisu. Allah ya gafarta zunubanta. Ya sa aljanna makoma, ameen. **** Malamin ya jinjina kai. "Aa Murjanatu, kar ki zo gaba kiyi kuka da ni, jimawar da muka yi da da yar uwarki da irin alherin da nake samu a wajenta, ba zan yi abin da zai cutar da ke ba. Ki je nan da kwanaki uku ki kara nazari, idan kin shirya fuskantar kowane ƙalubale da zai biyo bayan aikin, sai ki dawo." Murja ta yi jim, a yanda ta ke jin Fadeel gani take babu wani abu da ba za ta iya jurewa ba. Can ta nisa ta ce. "Malam, idan har dai ba hauka ba ne ko wata nakasa naji na gani zan jure." Ya yi wani murmushi. "Kina da gaggawa Murjanatu, eh ba nakasa ba ne, amma rushe maganar wannan yarinya a zuciyar Fadeel ba zai amfaneki da komai ba sai halaka. Abin nufi, har abada kema ba lallai ki aureshi ba, idan kuwa aurenku ya tabbata toh fa har ki mutu ba zai kusanceki ba. Ke za ki kasance kare ma ya fiki daraja a rayuwarsa. Ki yi hakuri, ita gaskiya ɗaci gareta kuma kin fi kowa sanin ni Malam Tanimu ba na ɓoyewa mutum koda kuwa idan ya aikata abun zai haɗu da mummunan bala'i sai na sanarmaka idan ka ji ka gani a tafi a haka, sai a tafi. Kin yarda kin amince?" Ta ji zufa na karyomata, ita da take burin rayuwa mai kyau da inganci da shi? Take burin ta mallake shi su ji dadin tarayyar aure? Kai sam ba ta yi imani da faɗar Malamin nan ba duk kuwa da sanin da ta yi mishi ba na yau ba don haka kawai sai ta ce ya ba ta lokacin shawara, daga haka ta miƙe ta bar wajensa da nufin sauya sheƙa. Wannan Malamin ba abokin tafiya ba ne, ba zai mata yanda take so ba. *** Sun yi yawo sosai gidan ƴan uwan Abba, wannan kam ita da Ummita ne sai ko Raihana da ta jera da su. Si Futuha kuwa daga gidajen ƙawaye sai ko ƴan makarantarsu na sakandire da suka haɗa reunion aka ci aka sha. Sun je hawan sallah Humaira ta sha kallo, abin ya yi matukar burgeta. Ta dauki hotuna sosai a wayanta, ita kuwa Raihana babu kwalliyar Humairar da ba ta ɗaukarwa Fadeel ba, daidai da bidiyonta a wurin kallon hawa sadda take murmushi da haska bidiyon sarki ta ɗauka ta tura wa Fadeel. Sosai sallar ta yi mata dadi, ta kuma yaba da kalar wasannin da aka yi. *** Zaune take a falo tana ta kallon yanda a hankali ta soma samun mabiya a shafin Instagram, hakanan hatta a facebook da Raihana ta budemata ta sanya ta a shafukan tallace-tallace na sana'o'i nan ma ta samu abokantaka da mutane da dama, sai dai babu wanda suka taɓa hira a akwatin sirri (inbox). Ita kaɗai tana ta murmushi ganin yanda hotunan girke-girken da ta yi yake samun likes da kuma comment. Jannat ta shigo falon da rawar jikinta, dawowarta kenan daga gyaran gashi. Su Futuha sun fice shoprite sun kai yara, Ummita ta je albarkacin yaran Jannat da suka sa rigimar su sai an tafi da ita don ba karamin shaƙuwa suka yi ba. Humaira ta ɗago tana dubanta don har ta tsorata ta, sam ba ta tunanin ta yi sallama. Su na cikin sati na uku ga sallah, a yanda ta ji daga Ummita, bai fi kwanaki uku ya rage Jannat ta bar gidan ba wannan yasa take ta shirye-shirye. Kallo ɗaya Jannat din ta yi mata ba ta ko amsa sannu da zuwan da take mata ba ta yi gaba, har ta ɗan yi nisa ta dawo baya tana yatsine fuska. "Ke, ki dafamin abu marar nauyi yanzu." Humaira ta amsa da toh, daga haka ta watsa mata harara ta shige. Taɓe baki Humaira ta yi, ko kaɗan ta daina jin ciwon ƙiyayyar da suke mata, ta lura ba ƙasa suka kwasa ba. Jinin Anna ne dole su kwatanta halinta. Ban da ma rashin ta ido, ina uwar mace da zuwa gidan surukai ta tare ko tuna asalinta ba ta yi? Mami ce dai ta sha bamban da su. Tana wannan saƙe-saƙen zucin wayarta ta ɗauki ƙara. Ganin baƙuwar lamba ya sanya ta yin jim tana tunani, tana da tabbacin ba shi ba ne. Mutumin da gaba ɗaya ya sauya bai ko ƙara kiranta ba, ganin wayar na shirin katsewa ya sa ta ɗauka. Muryar mace ce, ta amsa sallamarta suka gaisa. "Ina magana da Humaira? Humaira Yusuf mai yin snacks?" Ai sai ta miƙe tsaye ta hau washe haƙora. Ta amsa cikin zaƙuwa. "Eh, ita ce." "Masha Allahu, ina bibiyarki a shafinki na instagram, na ga tallace-tallacenki. Ina son snacks ne, za'a iya samu nan da kwanaki hudu haka zuwa biyar?" Humaira ta ɗan yi tsallen murna sai ta ɗan toshe baki gudun kar dariyar farin ciki ya suɓuce mata, wannan kusan shi ne order din farko tun da suka soma talla. Nan ta tambayeta kalolin snacks din da take so, ta yi mata bayani, a karshe suka yi sallama da zummar Humaira ta lissafa adadin kuɗinta sannan ta turo acc number. Ai don murna tuni ta mance da batun wata Jannat, gudu-gudu ta nufi falon Mami tana kwala mata kira. Amma ina! Ba ta nan tana bangaren Anna, tsabar rufewar idanu kawai sai ta sa kai har cikin dakin Anna tana kwala kiran Mami. Su na zaune su na hira sai ganinta suka yi. Mamin ta nemi ba'asi nan ta hau sanar da ita yanda suka yi da mai order. Itama sai murna da hamdala. "Kai Alhamdulillah. Dole kiyi murna, maza muje ayi lissafin sai a turamata." Da murmushinta mai bayyana kyawunta da tsantsar kamanninta da Abba ta amsa da toh. Har ta juya za ta fice ta ji tsawar Anna. "Ke!" A firgice ta juyo kuwa, har ga Allah sai a sannan idanunta suka buɗe. Ta tuna inda ta faɗo da kuma kuskuren da ta yi na rashin sallama ballantana gaisuwa. Kawai sai ta durkushe ta gaida Annar, Jannat ta karasa ta ja kunnenta har sai da ta saki ƙara. "Don ubanki dayake kin raina mutane uwarmu sa'arki ce da har ki faɗo ɗakinta kamar na uwarki?! Ba aiki na sanyaki a kicin ba? Kema kuma Mami laifinki ne." Daga nan ta juya harshe zuwa buzanci ta cigaba da sababin faɗa, Anna itama tana taya ta. Daga yanda Mami ta yi shiru ta haɗe girar sama da ta ƙasa Humaira ta fahimci magana suke gasamata. Nan da nan jikinta ya yi sanyi, a gefe guda ga na gorin ɗakin uwa da aka yi mata, ba don darajar Mami dake a idanunta ba sai ta faɗamusu mai zafin da ba zasu ƙara mararin daɗa kwana ko ɗaya a gidan ba idan har su na da sauran kunya. "Humaira, tashi ki je, ki yi aikin da ta sanyaki kafin na zo." Muryar Mamin ta katse ta. Ta mike tana mai amsawa da toh gami da share kwallar da ta cika idanunta. Bayan fitarta Anna ta ce. "Maryama ban san irinki ba, ban san wa kike son ki burge ba. Wato har wani girki za ta fara na harkar kuɗi? Wannan naki salon uƙubar ce ko kuwa dai son yarinyar ne fiye da naki yaran ya rufemaki idanu kike son ta kere su a komai ta yi musu zarra? Idan bacci kike ki farka, kin nemawa yarinya har ya zama mai arziki, a kuma yanda naji zaƙin miyarta ina mai tabbatar maki watarana sai ta fi ki kuɗi. Tukunna ma, kuɗaɗen kina nufin ita za ki dinga damƙawa?" Mami ta yi shiru na ƴan sakanni har Anna ta ƙara tankawa yayinda Jannat kuwa ta ja tsaki don tana jin haushin yayarta sosai, tana abu tamkar a duniya su Humaira ta haifa ba su Futuha ba. Can dai Mamin ta yi magana. "Ta asusuna kuɗin za su shigo." Murmushi Anna ta yi mai tarin ma'ana kafin ta ce. "Na sanki Maryama, ni na haifeki. Kar ki zo mini da rainin hankali da wayo kinji ko? Wato ni ga sakara shi ne za ki rufe ni ruf, to ai koda ta asusunki kuɗaɗen suka shigo a yanda kike nunawa yarinyarnan kamar ki lashe ta, ke me iya yin hidimar ta ce ba naki ko yaranki ba. Kaiconki Maryama, lallai idan ba bi a hankali ba yarinyar nan watarana sai ta watsa maki borkono a idanu. Kina wasa da wuta." Janant ta kalli Mami, sai kuma ta girgiza kai. "Anna, zai fi kyau ki bar wahalar da bakinki a kan wannan saboda ɗiyarki ta yi nisan da ba ta jin kira. Ita mai miji, burinta ta nunawa duniya ta fi kaunar ɗa wani sama da nata yaran. Idan kin ji yanda yarannan ke ƙorafin nuna halin ko in kula da take yi musu sai ki rantse ba ita ce ta yi naƙudar su ba a bola ta tsinto su. Babu ma kamar su Yassar wadanda su ubansu bai sakarmusu sun ji dadin rayuwa irin na matasa sa'anninsu ba, su ba su sami wata kyakkyawar kulawa a wurin uwar ba. Ni na rasa irin wannan gidan da rayuwar cikinsa. Ba haka nake rayuwa a gidan nawa mijin ba, shi koyaushe burinsa ya wadata mu da abinda za mu huta ni da yaransa, amma tun da na rayu a gidannan har na yi aure, mijinta bana jin ya kashemin sama da dubu ɗari biyar a rayuwa." Mami ta miƙe tsaye tana duban Jannat, zuwa yanzu ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci. "Ya isheki hakanan! Ke tsabar rashin kunya har kya kalli kwayar idanuna ki faɗan magana? A gidan dai da kika raina nan kika rayu sannan ko Yusuf bai kashe maki sama da kuɗaɗen ƙaryar da kika buga lissafinsu ba, ai kin ci kin sha daga jikinsa. Ke yanzu idan da kina can wannan dajin kina rayuwa, har kin isa ki ga shi mijin da kike tutiya da shi ki aura? Ni na isheki! Nan da kike ganina kar nake, na fi ku sanin inda ke mini ciwo. Ba damuwarki ba ce kuma balle ki sani, idan har ba za ki dauke idanu daga lamuran gidana ba, ki tattara ki..." "Maryama!" Tsawar da Annan ta bugamata ne yasa ta yin shiru tana fesar da huci mai zafi, ta kalli Anna sai kuma ta juya ta fice daga ɗakin. Jannat nan ta haukacewa Anna wai Mami ta yi musu gorin zama a gidan don haka su tattara su bar mata gidanta. Anna dai ta dinga lallaɓa Jannat, ta sani muddin ta bi cewarta ta bar gidan to fa komawa can wani ƙauyensu dake garin Agadez ya kamata, yanda ta fito ta ɗanɗani rayuwar daula koda ace bai kai yanda ta ke so ba, ta gwammace ta cigaba da rayuwa a nan. Ta sani babu ta yanda za'a yi shegiyar surukar zamani irin ta Jannat ta amince da zamanta a gidan ɗanta. Dakyar dai ta samu Jannat ta janye ƙudurinta, tsana da haushin Humaira ya ƙara ninkuwa a ƙasan ranta. *** Humaira kuwa sai ta nemi murnar da take yi na Oda ta rasa, jiki a saluɓe ta yi mata dahuwar dafadukan macaroni mai busasshen kifi. Ƙamshinsa ya karaɗe kicin ɗin da falo. Koda ta kammala ta haɗa komai a ƙaton faranti ta kai mata babu godiya ba kallon arziki, itama ba ta sa a ka ba kawai ta jya da zummar tafiya. "Ke zo nan!" Muryar Anna ta ji, ta runtse idanu kirjinta na dukan tara-tara cike da tunanin da wanne kuma Annar ta zo yanzu ta juya ta koma ta durkusa ba tare da ta kalleta ba. Ta soma magana a kausashe. "Ɗago ki kalleni nan, ni da kike gani dai na fi ƙarfinki. Mun ci dubu sai ceto, zuri'ar Mamman Ɗan Jika daidai nake da kowane bafillace mai taƙama da asiri. Har mu za a gayawa asiri? Tun wuri ina gargaɗinki ki fice a rayuwar ɗiyata, idan ma wani mugun ƙullin aka kawoki da shi don ki shiga tsakaninta da yaranta toh ahir ɗinku, ni dai na fi ƙarfinku balle kuma tsatsona. Ki kama kanki tun kafin na ɗau mummunan mataki a kanki. Ɗan girkin da kike taƙama kin iya ni mai iya juya lamarinki da shi ne, idan kuma kina da ja ki cigaba kar ki fasa. Asir dai ba za ki nunamana ba, mun saka Allah a gaba ne kawai shiyasa muka watsar. Amma muddin kika ce za ki cigaba da juya ɗiyata kamar waina da shiga tsakaninta da yaranta da ta haifa da cikinta ni nan zan nunamaki iyakarki." Tana kaiwanan ta juyar da kai tana girgiza ƙafa na bala'i. Humaira ta dubi Anna dakyau, an zo gaɓar da ba za ta jure ba sai ta ba ta amsa ko yaya ne. Ƙazafin sihiri ba za ta jure shi ba don haka ta soma magana da wani irin ƙunar rai. "Kiyi hakuri Anna, amma kalamanki laifi ne ko a wurin Ubangiji, kin yimin mummunan zato kin kuma yimin ƙazafi. Lallai Ubangiji zai yi mana hisabi a gobe ƙiyama. Na samu kyakkyawan tarbiyya a wurin Dada da Kawuna irin wanda nake da yaƙinin ko uwar da ta haife ni sai haka. Ban san boka ba balle mugun malamin da zan je ya yi min wani mugun aiki ba, asalima ban da a fina-finai da kuma labari ban taɓa karo da su ba. Wanda ya riƙi Allah, ai ba zai aikata abin da kuke yi ba. Kullum cikin zagi da aibata musulmi ɗan uwanku, ni Humaira babu wani mahaluƙi a duniyarnan da zan kai ya yimin aiki a kan wasu, kenan idan nayi hakan ma ban riƙi gaskiya ɗaya ba, ban yi imanin Allah zai iya amsamin addu'ata ba komai muninta komai kyawunta ba kenan. Ai Ubangiji ya wuce duk zatonku. Balle ma ban taɓa roƙo mai muni kan kowane ɗan uwana musulmi ba, kuma ba zan fara akan Mami ko yaranta ba. Tsakanina da Mami sai addu'a, ta yimin riƙon da ya sa nake jure dukkan wani abu da za ki yimin ke da jikokinki. Har abada kuma bisa darajar Mami ba zan taɓa daina ganin mutuncinki ba. Kiyi hakuri idan da abin da na faɗi mai zafi." Tana kaiwa nan tuni ruwan hawaye sun wamke fuskarta, a bisa tilas ta kalli idanun babbar da ba ta riƙe girma da tsufanta ba ta gasamata maganganu. Ita ta fi Anna jin ciwon haka, sai dai haka take, ba ta iya hakuri idan aka kai ta bango musamman idan abin ya kasance ya haɗu da baƙin ƙazafi. Juyawarta ya yi daidai da saukar igiyar chaja a gadon bayanta, Jannat ce wacce a farko ta yi ɗif don gani tayi tamkar a mafarki wai wata ƙaramar yarinya na gasawa uwarta maganganu, sai da ta motsa da zummar barin ɗakin sannan ta zabura ta janyo igiyar chazarta. Nan fa ta hau jibgar Humaira amma kamar ba mutum ake duka ba, ta ƙi tafiya ta kuma ƙi ƙwatar kanta. Zuciyarta tafarfasa take yi. Kallon Jannat take kawai tsakar idanu yayinda idanunta suka kaɗa sosai sai ruwan hawaye. Ganin da ta yi Humairar babu ko gezau sai kawai ta hau wanke ta da mari tana zaginta. Ta yi biyu, za ta ƙara ta riƙe hannunta gam, ba ta san ya aka yi ba, ba ta kuma jin za ta iya tunanin mai kyau da marar kyau a lokacin, kawai ta ji yatsun hannunta sun sauka saman fuskar Jannat da mugun ƙarfi ji kake tas!!! Ya yi daidai da faɗowar su Futuha ɗakin waɗanda dawowarsu kenan daga shoprite cike da nishadi. Ganin abinda ya faru ne ya sa Tasleem sakin ihu mai ƙara da ya ja hankalin Abba da Mami dake a sashin Abban, suka nufo da sauri Abba ya ɗan tsaya daga ƙofa yayinda Mami ta kutsa kai ɗakin. Alokacin rufewar idanun Humaira har ya kainta shaƙi wuyan Jannat ta dangana ta da bango, babu sautin kuka sai ruwan hawaye, Jannat ta raina kanta, ta ji ashe ba ta da ƙarfi don ji tayi kamar ba iyaka Humairar ba ce ta shaƙe ta ba. "Wayyo Allahna! Ku taimaka za ta kashemin yarinya!" Jin wannan furucin na Anna ya sa Abba danno kai cikin ɗakin. Tsawa ya dakawa Humaira ba ta ko kalleshi ba. Ya kuwa ƙarasa ya ɗauketa da wani marin sannan ya fincike hannunta. Mami kuwa mutuwar tsaye ta yi, ita kadai ta san me take ji a zuciyarta, wannan shi ne lokacin da take gudu, ta juya da sauri ta bar ɗakin. Su Futuha kuwa suka yi kan Antinsu suka rirriƙe suna kuka yayinda Anna ma kukan take har da biyu saboda ganin Abban. Shi kuwa rufe Humaira ya yi da duka sai da ya ga har ba ta motsi kafin ya karasa ga Jannat yana ba ta hakuri, Jannat kamar jira take kawai sai ta fashe da kuka sosai da fadin. "Wannan wane irin cin mutunci da zarafi ne? Da aurena da darajata da shekaru sa'ar ƙanwar ƙanwata ta shaƙi wuyana? Wannan rayuwar da me ya yi kama? Kiyi hakuri Humaira, watakila laifina ne da na zo gidannan. Na saba ganin girmamawa daga mahaifinki, hatta da marigayiya Anti Fati ba ta taɓa yimin koda kallon banza ba, amma yau ga ɗiyarta nan ta shaƙeni tana ƙoƙarin kai ni lahira. Aikuwa a yau zan bar maki gidanku." Ta ƙara fashewa da kuka, Abba ya ji kamar ya ƙara rufe Humaira da duka, wannan banzan halin a ina ta ɗaukoshi? Tabbas ba halin mahaifiyarta ba ce. "Nima yau zan bar gidanka Isuhu, tun zuwan yarinyarnan naga rashin kunya iri-iri da ban taɓa gani a wajen yan uwanta ba. Na yi kokarin janta a jiki da nunamata kauna, sai dai ban sani ba ko tana ji a ranta ni ban kai ta girmamani ba saboda ina zaune ina cin arzikin gidan mahaifinta ba, tunda abin ya kai ga haka in sha Allahu zan tattara na koma can Agadez, kiyi hakuri Humaira, wallahi ni ba muguwa ba ce. Tsakanina da duk abin da ya fito daga jikin Isuhu babu komai sai girmamawa." Dakyar Abba yake magana saboda ɓacin rai ga nauyin Anna da ya dinga ji, wai yau diyar cikinsa ce ke ci wa tsohuwar mutunci ta hanyar dukan ɗiyarta a gabanta. "Ki yi hakuri don Allah Anna, wannan gidana ne ba na Humaira ba. Mallakina ne, kamar yanda uwata mahaifiya da ace tana raye take da iko kai karfi a kaina da gidannan, haka nake ganinki don haka ina roƙonki kiyi hakuri ki janye ƙudurinki. In sha Allahu daga yau irin haka ko da wasa ba zai ƙara afkuwa ba. Ni zan ɗau mataki kwakkwara a kanta." Ya ƙarashe yana duban Humaira da sai lokacin take sheshsheƙar kuka, itama shi take kallo, ta sunkuyar da kai. "Don ubanki ba za ki buɗi baki ki ba su hakuri ba?!" Ya faɗi a tsawace, hakan ya yiwa ran su Tasleem dadi, yau dai ga wacce suke ganin ta fi su a wurin Abba tana ɗanɗanar kudarta. Abin ya zo musu a daidai. Ita kuwa mikewa ta yi dakyar ta durkusa sosai, hakuri ta shiga ba su har Jannat din. Dakyar suka ce ya wuce saboda ganin idanun Abba. "Muje." Ba musu ta mike jikinta duk ya yi tsami ta bi bayan Abban zuwa falonsa yanda ya buƙata. *** Fadeel da murmushi ya ɗagawa yayartasu hannu alamar jinjina. Yayar Ibb, Anti Ruƙayya wacce ke aure a Kano, sun saba sosai da Fadeel din tun kafin ma ta yi aure. Ibb ya dube shi. "Wai ni ban gane ba, toh idan odar ta sauka wa zai karɓa?" Fadeel ya yi murmushi karo na biyu. "Nan gidan Antinmu za'a kawo mana, ni kuma sai na zo na karɓi rabona." Hajiya Ruƙayya ta yi dariya. "Amma dai wannan ina zaton ita ce zaɓin ƙanin nawa ko?" Ya kasa magana sai shafar sumar kai, Ibb ya taɓe baki. "Ita ce dai yake yiwa son mutuwa ba ta san da zamansa ba." Fadeel ya harareshi shi kam dauke kai ya yi ya cigaba da ba Ruƙayya labarin komai. Sosai ta ji ya ba ta tausayi. "Allah Sarki, yanzu kai zaman jiranta za ka yi kuma?" "Um." Shi ne kawai abin da yace yana hararar Ibb da ya kasa rufamasa asiri. Ibb shima ya rama sannan ya ce. "Ai wai haka yake nufi, nidai ban san irin wannan abu ba, ace mutum ya kasa hakura da son wanda ba ka gabansa? Kinsan Allah, mutumin nan akwai mata da yawa da suke kawo mishi hari, na ce ya runtse ido ya zaɓa ya darje amma ina. Wai ya hakura da auren har sai Humaira ta yi koda ba shi ta aura ba sannan zai yi nashi." Rukayya ta yi salati. "Fadeel kana cikin hayyacinka kuwa? Wannan wane irin so ne?" Nan da nan fuskarsa ta sauya. "Nawa son da haka ya zo. A sanya ni a addu'a kawai Anti." Ta ɗan yi jim tana kallonsa. Sai kuma ta numfasa. "Shikenan, Allah ya zaɓa abinda ya fi alheri. Zan so naga wannan yarinyar da ta sace zuciyarka har haka." Ba musu ya fiddo waya ya buɗe hotunan Humaira wanda hatta a saman screen dinsa ita ce ya miƙa mata. Ta kalla sosai ta ce. "Babu ƙarya Humaira kam ta haɗu. Daga kuma yanayin fuskarta ka san za ta yi haƙuri." Yabon da ta yi sai ya karawa Fadeel farin ciki, a duniya ya tsani wanda zai kushe abar sonsa. Ganin har Ruƙayya ta yaba sai hankalinsa ya kwanta. Sun jima suna hirar lamarin Humaira kafin a karshe su yi sallama bayan Fadeel ya ce mata zai dawo idan an kawo odar snacks ya karɓa. *** Jannat ce tsaye tana kallon hanyar waje, har lokacin zafafan hawaye take fitarwa na baƙin cikin abinda Humaira ta aikata gareta. Fuskarta ya yi jazur, ta juyo ta kalli Anna wacce ta yi shiru tana kallonta, a duniya Anna ba ta son damuwar yaranta. "Anna, na yi alƙawari sai na ga bayan Humaira da duk abin da take taƙama da shi. Ta yimin cin fuskar da ban taɓa tsammata ba, ni zan nunamata iyakarta koda kuwa zan yi yawo tsirara." A firgice Anna ke duban ɗiyarta, ta san halin kayanta, muddin ta furta abu, komai nisan lokacin da za a ɗauka sai ta aiwatar. Wani lokacin ma, sai ta tabbatar da shafewar abin a kwakwalwarka kwatsam sai dai ka ga sakamako a aikace. Don haka ta sani ko mene Jannat za ta aikata ba ƙarami ba ne duba da yanda ta saki fuska lokaci guda har da dariya. A karshe ma hatta da abincin da Humairar ta kawo sai da ta ɗiba ta yi zaman ci tana santi. Ita dai Annar ba ta ce mata komai ba, ta fi kowa sanin baƙar zuciya irin na ɗiyarta. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA. KAR KI MANTA BAYAN NAN AKWAI CAN, ALLAH YA SA MU DACE AMEEN.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Gidan Alhaji Yusuf wanda aka fi sani da Maiagogo sun wayi gari ranar alhamis da shirye-shiryen bikin yaransa biyu, Futuhatul-Khair Yusuf da kuma Tasleem Yusuf wanda kwanaki uku kawai ya rage a fara. An samu sauye-sauye da dama, na farin cikin ya fi kowanne yawa ga Humaira da duk ma wanda ke tare da ita. A wannan watannin ta samu alheri mai yawa daga sana'arta. Babbar customer dinta ita ce Hajiya Rukayya wacce ta hanyarta kaɗai ma ta samu oda na biki da party har ya zamana tana gwada na abinci bayan snacks sai dai gaba ɗaya sau biyu ta gwada abincin taro ba laifi kuma masu shi sun yaba hakanan Hajiya Rukayya ta ji dadi da ba ta ba su kunya ba. Duk abin nan ba su taɓa ganin juna da ita ba sai dai waya. Mami ta sa an buga leda da stickers mai tambarin DEELSHA'S DELICACIES. Suna na musamman da Raihana da Ummita suka ba Humaira a sadda Mamin ta ce ta yi tunanin sunan da za'a sanya a ledar. Sunan ya yiwa Humaira daɗi ko kadan kuma ba ta tambayesu ma'anarsa ba. Mamin ma ta ji dadin sunan, ganin kalmar turancin ya sa ta tambayar wacce ta sa, nan Humaira ta sanar da ita su Ummita ne. Daga haka ba ta kara cewa komai a kai ba.   A yau da ya rage kwanaki uku bikin yan matan Mamin, gidan nasu ya soma karɓar baƙi ƴan uwan Mami daga Agadez sai ko ƙawayen Futuha waɗanda suka zo daga nesa kasancewarta mai jama'a fiye da Tasleem. Yan uwan Abba kuwa ba wanda ya zo gidan da zummar kwana. Mubarak shima ya zo gari, sai kuwa Anti Jannat. Ya kasance a wannan lokacin gidan ba ya rabo da jama'a, Mami ta sa Ladidi kawo mataimaka a aiki har su uku saboda yanayin cikar gidan da zummar bayan biki za ta sallame su.   Anko har kala biyar aka fitar, na ƙawaye daban wanda zasu sanya ranar kamu da na daurin aure da yini sai ko na ranar dinnerparty. Na manya su ma kala biyu, na fita kamu sai na ranar daurin aure. Humaira, Raihana da Ummita daban aka fitar musu da na sisters wanda zasu saka na yini sai kuma na dinnerparty da Mami ta yiwa su Futuha jan ido ta karɓar musu katinsu ta riƙe a wajenta don a farko sun nuna su ko kusa ba su kaunar su halarci dinner din.    Amare sun sha gyara ba na wasa ba daga mai gyaran jiki na musamman da Mami ta samar musu suke sintirin zuwa. Hajiya Lubna ita da kanta ta ɗauki nauyin gyara su, gyara irin na mata. Ta kashe kuɗaɗe masu kauri kuwa wanda hakan ya burge aminiyarta kwarai ta yaba.  Ba ma ita ɗaya ba, ƙawayen Mami da dama manyan mata masu kudi sun ba da gudunmuwa mai yawa na kudi, kanta ya fasu sosai ta kuna ga fa'idar mu'amala da masu hannu da shuni. Su Raihana sun karɓi dinkunansu a hannu, sun yo ƙunshi da kitso abinsu sun fito fes.    A na washegari kamu ne su na zaune suna hira a daki tare da wasu yan uwan su Raihana sa'anninsu da suka zo daga Nijar, Tasleem ta shigo. Fatarta har wani ɗaukar ido yake, ba ta da ƙiba irin na Futuha ita nata jikin daidai misali ne, duban Humaira ta yi fuska ba fara'a. "Ke Humaira, ke da Ummita ku zo na aike ku." Humaira ta ji ciwon ke din da tayi kiranta da shi, ita kuwa Ummita ko a jikinta ta miƙe tana murmushi. Hakanan halittarta yake, tana da yawan murmushi, abinda zai sanya hawayenta zuba kuwa, toh fa ba ƙaramin abu ba ne kamar dai akan Humaira ko kuwa wani abun daban. Kamar ba za ta miƙe ba sai kuma ta yi tunanin ba komai ta yi tunda dai aure ma za su yi su bar gidan sai ziyara don haka ta taushi zuciyarta ta miƙe itama. Saƙo ta ba su a leda na ankon Dinner su je su kai can asibitin Malam wajen ƙawayenta kuma abokan karatunta da suka samu dakyar don har ta ƙare. Ta miƙawa Ummita dubu su yi kuɗin mota sai kuma lambar wayar ɗaya daga ciki, Sadiya, sun gane ta, takan rako Tasleem din gida wasu lokutan don ta dauki wani abun ko kuma ta zo takanas ziyara.    Bayan sun fito waje Humaira ta dubi sararin samaniya yanda garin ya haɗu da hadari ana cida, lokacin uku da mintoci, ta ja guntun tsakin takaici.   "Kinsan Allah, sa'ar da ta ci kawai na ganin wannan shi ne aike kusan na karshe da za ta yi mana kafin ta bar gidannan shiyasa kawai zan je, amma ban da haka wannan ke ɗin da ta ce wallahi da babu inda zan je matukar ba Mami ce ta sa baki ba." Ummita dake kokarin cusa ƙaramar lema a jaka ta ɗago tana murmushi. "Humaira ko rigima, rabu da ita lokaci ne ai wataran sai labari fa. Yanzu kalli, ina Anti Jannat? Ba ta yi aure ba sai dai ta zo kawai ziyara ta tafi? Toh su din ma hakan ce za ta kasance, mu ma watarana sai ki ga mun yi namu auren mun tafi mun bar gidan. Sai a dade ma kafin a ganmu." Tsaki Humaira ta ƙara ja. "Ke dai Ummita kina son aure na lura, magana kaɗan za a yi da ke sai kin yi zancensa." Da mamaki Ummitan ta kalleta kafin ta amsa. "Aure ai abin so ne saboda sunnar ma'aiki (s.a.w) ne. Ke din ma ba sunnar kika tsana ba, mazan ne. Ban kuma san laifi kwakkwara da suka yi gareki ba." Taɓe baki Humaira ta yi daidai lokacin da suka fito babban titi. "Mu bar wannan magana, nikam ba kya ganin lamarin Anti Jannat da ɗaure kai?" Ummita ta yi shiru cikin nazari, tabbas da daure kai, tun bayan sadda ta zo hutun sallah lamarin nan ya afkuwa tsakaninta da ita, ba ta kara dawowa gidan ba sai yanzu. Wannan dawowar kuwa, daidai da kallon Humaira ba ta yi balle har ta jefe ta da kallon banza. Ta lura ko tana wuri Humaira ta shiga, mikewa take ta bar wurin. Haka dai tana ta kaucewa abinda zai haɗa su a inuwa guda.Har Humaira ta tarar musu abin hawa suka shiga ba ta amsa mata tambayarta ba sai da ta ƙara nanatawa kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ɗan yi murmushi.       "Na lura sosai, amma ni abin da tunanina ya ban ko dai ta sauya ne tana gudun wani abu ya ƙara haɗaku ki maimaita abin da kika yi. Kin san fa ba zai yiwu ace ta mance ba." Dariya  ta yi. "Ikon Allah, toh ni ai na mance. Kawai dai sauyin ne ya ɗan bani mamaki. Babu kyara babu hantara, babu kirana da bare da ta saba yi ba komai. Sai na ke ganin kamar da walakin goro a miya." "Ki yi mata kyakkyawan zato, Allah yasa sanadin abin da ya kasance ta yiwa kanta faɗa. Ni kaina idan kin lura ai ta rage ɗoramin aiki tunda wannan zuwan ta sa an nemo mata yarinya mai kula da yara. Kawai dai mun saba da yaranta ba yanda za a yi ta iya raba wannan kaunar." Humaira ta kalle ta, zuciyar Ummita mai kyau ne, da Allah ya tashi, sai ya yi haɗa ta da mutumin kirki irinta wato Malam Sahabi. Mutum mai hakuri da kunya kamar wani mace. Amma abin mamaki duk kunyarsa idan suka ga saƙonnin soyayyar da yake turowa Ummita sai mamaki ya kusan kashe su ita da Raihana. Har rantsuwa suke kusan yi su ce ba shi ba ne waninsa ne. Ummita ta harareta. "Kallon fa?" Murmushi Humaira ta yi mai kyau da ya fiddo wushiryarta. "Kawai kina bani mamaki da kike kokarin kare wadannan mutanen da ba su taɓa kaunarmu ba koyaushe." "Uzurin kenan Humaira. Aure fa zasu yi su bar mu yanzu. Mu ma kuma..." "Toh naji ya ishe ni hakanan Malama matar Sahabi." Ummita ta sa dariyar jin abinda ya fito bakinta, ita din ma taya ta ta yi. Har suka isa ƙofar asibitin su na hira abinsu ana iska kaɗan kaɗan mai daɗi.       Ibb ne tsaye tare da masoyiyarsa Dr Salma, yayinda Fadeel ke zaune cikin mota yana jira su yi sallama. Mahaifiyarta ce kwamce a asibitin inda anan take aiki, suka zo dubiya ta yo musu rakiya har gaban mota. Bayan sallama da Fadeel ya koma mota yayinda suke hirarsu da Ibb tamkar kada su rabu, shi kuwa Fadeel kansa ya kwantar jikin kujera yana ɗan kallonsu yana murmushi. Shakka babu sun dace dari bisa dari. Dogaye ne su duka biyun don zasu kusan yin kai ɗaya, Dakta Salma baƙa ce, kwayoyin idanunta da haƙora ne kawai idan ta bude masu haske a fuskarta. Tana da kyau, ba ta da jiki sosai amma ba za ka kirata da siririya ba. Tana da diri masha Allah, sanya take da doguwar riga sai coat na likitoci da ta sanya saman kayan, sai kuwa mayafi ƙarami da ta yi rolling kanta da shi. Hannunta cikin aljihun rigar, gaba daya hankalinsu ba ya kan Fadeel da ya lula duniyar tunani da jin inama ace shi da Humaira ke wannan hirar ta nishaɗi. Allah kaɗai yasan yanda zai ji a lokacin. Ya soma gajiya, hakurinsa ya soma kai wa karshe amma yana dannewa gudun ɓacin ranta. Ya horu da rashin ganinta ido da ido ba hoto ba, ya sha zuwa ya tsaya a nesa kaɗan da gidansu ko zai ga wulkawarta sai dai ko mai kama da ita Allah bai taɓa ba shi ikon gani ba. Tabbas Raihana na kokari gurin aikamasa hotunanta wasu lokutan ma ba ta san ana ɗaukarta ba. Hatta da karamin video sadda take aikin snacks sai da ta ɗauka ta aikamasa. Yakan ji inama yana da iko da ita, inama matarsa ce yana kusa ya riƙo ƙugunta ya sanya ta a jikinsa ya bayyana mata irin yanda soyayyarta ke cin zuciyarsa sai dai kuma babu hali. Azabar da bidiyon ke sanya shi ciki ne ya sanya shi dakatar da Raihana daga turo bidiyo face hotuna.   Ya ja dogon numfashi ya furzar gami da kallon gefe guda yana mai kauda kai daga kan lovebirds. Hango wata ya yi kamar Humaira, ya ɗan yi tsai da idanu don so ya tantance abinda yake gani, sai kuma ya kauda kai. Ya fi tunanin gizo Humaira ta soma yi mishi, sai kuma ya kara kallo. Wannan karon ita ce tabbas, tana sanye da doguwar riga na material mai mayafi Jajaye. Yanayin kalar da garin ya yi, sai ya ba wa hasken fuskarta damar sheƙi musamman da ya kasance tana cikin annashuwa da kwanciyar hankali da alama babu wani abu dake damunta. Sai hira suke da abokiyar tafiyarta wadda ya gane ta, Ummita ce. Ya ganta a hoto don ba hoton Humaira kaɗai ba, hatta da ƴan gidan sai da Raihana ta turamishi hotunansu da kuma bayanin alaƙarsu. Har ya kama murfin mota zai fito ya tuna alƙawarin shekara da ya ɗaukar mata kawai ya fasa ya cigaba da kallonta. Dab da motar suka tsaya suna kalle-kalle kasancewar gilasanta tinted ya sa basu ganshi ba, shi kuwa Ibb shalelan Juliet, bai ma gansu ba ya lula wata duniyar sai buɗe haƙora yake yi kamar gonar auduga. Humaira ta ɗan yamutse fuska tana gyara gyalenta da iska ke kaɗawa. "Nikam asibitin nan juyar da kai gareshi, don Allah ƙara kiranta ki ce bamu gane wajen da ta ce ba kinga garin yana kara haɗewa." Itama Ummita duk ta damu ganin hadari ta fiddo waya ta dannawa Sadiya. Nan ta ce su tsaya inda suke ta gansu. Suka ja kuwa suka tsaya, Humaira ta zubawa mutanen dake ta shawagi a wurin idanu tana godiya ga Allah a ranta idan ta ga an wuce da marasa lafiya dayake suna daidai Emergency. Ba su wani jima ba sai ga Sadiyar ta iso, bayan sun gaisa ta karɓa ta yi musu godiya suka juya suka kama hanyar fita. Fadeel kamar wanda aka tsikarawa allura haka ya zabura ya fito daga motar ya dubi Ibb. "Malam ka zo mu tafi ba ka ganin yanda garin ke haɗewa wai?" Suka dubeshi, Dakta Salma ta yi murmushi. "We are sorry Amininmu. Bari na kyale shi haka. Nagode sosai ku gaida gida." Bai ko kalleta ba ya amsa da toh don shi gaba daya hankalinsa na ga su Humaira yana fatan Allah ya sa su amince su sauke su a gida. Ibb ganin an soma yayyafi ya yi mata sallama ya shiga motar ya tayar. "Please and please ka yi sauri kada su hau abin hawa, so nake ko yaya ka yimin kokari ta amince mu kai su gida." Ya tayar da motar ya soma tafiya sannan ya dubi Fadeel cikin rashin fahimta ya ce. "Wa kenan kake magana a kai?" Fadeel da idanunsa ke kan su Humaira wadanda suka kara ɗaga ƙafa ganin ruwa ya soma sauka bai ce komai ba face nuni da ya yi mishi da hannu. Sam bai ga fuskokinsu ba sai baya, kafin ya yi magana Fadeel ya sake tarar numfashinsa. "Humaira ce." "Ohh." Abin da kawai Ibb ya ce kenan. Yana zuwa daidai saitin inda suke ya tsaya har yana tare musu hanya, Humaira dake saitin wurin ta kalli motar ranta a ɓace don a ganinta ko waye yana sane ya sha gabansu. Ta bude baki da zummar magana Ibb ya sauke gilashi suka kalli juna. A gaggauce ta gaishe shi, itama Ummita haka, ta gane shi saboda tana ganin hotunansa a wayar Raihana, shi ne dai wanda y taimaki Raihanar. "Gida ku ka nufa ne? Ku shiga na sauke ku don yanzu idan ku ka shiga napep jiƙewa zaku yi." Ruwan sosai ya ƙara ƙarfi, Humaira ta buɗe baki za ta ja musu Ummita ta dafe hannun da sauri ta amsa. "Toh mungode." Ta kalli Humaira, a hankali kuma a gaggauce ta ce. "Muje Humaira, yanzu ba lokacin jan musu ba ne, wallahi nidai ina mura kin sani, ruwannan ya dake ni kuma lafkewa zan yi da bikin nan." Jin haka Humaira ta amince suka shiga, ita ta soma shigewa sai Ummita. Motar sanyi sakamakon Ac dake aiki. Sai a lokacin ta lura da wanda ke zaune a gefen Ibb din, ji ta yi kirjinta ya buga dam, ta rasa dalilin bugawar kamar yanda ta kasa dauke idanu a kansa. Shi ɗinma ita yake kallo babu ƙakƙautawa har bai iya ya amsa gaisuwar Ummita ba. A bangaren Humaira ji ta yi idan ta cigaba da kallonsa ranta zai iya fita saboda wani irin zafi da take ji a kirjinta ga kanta dake faman sarawa don haka da sauri ta kauda kai ta matsa ta maƙure a kujerar bayansa tana jingina da kofar motar. A hankali Ibb ya dan bubbuga kafaɗar Fadeel, firgigit ya dawo hayyacinsa ya gyara zama, gilashinsa ya zaro a aljihu ya rufe kwayoyin idanun da so da tsananin kauna ga kewa suka haɗu suka galabaitar. Dakyar Humaira ta iya gaida Ibb sannan ta gaida Fadeel din ba tare da ambaton suna ba. Shi ma amsawa ya yi can ƙasa. Ibb ke tambayar Ummita abin da ya kawo su asibiti. "Kuna da marar lafiya ne?" "Aa, aiko mu dai Anti Tasleem ta yi. Ita ɗin ɗaliba ce a nan. Nursing take karantawa ne." Dan jinjina kai Ibb ya yi. "Ok, na fahimta." Jin motar ta ɗauki shiru sai rediyo dake aiki sai ko ruwa da ke jiƙa gilasan motar yana sauka a guje saboda karfin da ya yi. Ummita ta dubi Humaira. "Wai, da tuni yanzu fa mun jiƙe." "Uhm." Shi ne amsar da ta ba ta. Fadeel kuwa lumshe idanun ya yi ya ji sautin Uhm din har tsakar kansa, gaba ɗaya sai da ya ji tsikar jikinsa ya tashi. Kamar kuma haɗin baki sai ga gidan rediyon sun saki waƙar Breaker mai taken Kalmar So. Humaira sam hankalinta ba ya jikinta, ji take kamar ta buɗe motar ta dira a cikinta. Gaba daya koina a jikin rawa yake, Ac ke kaɗawa a motar amma ita zufa take. Ta tuna da ambaton Allah ba shiri ta shiga ambata a ƙasan ranta a hankali ta soma dawowa cikin nutsuwarta. A bangaren Ummita da Ibb, hira suke ɗam taɓawa kaɗan, shi kuwa Gogan da Humaira ba ka jin komai daga bakinsu, babu kamar Fadeel da yake jin waƙar ta zo daidai da yanayin da yake ciki. So yake ya tambayi ya take? Ya lamuran rayuwa? Ba ta hakura ba har yanzu? Ba ta amince ya turo iyayensa ba? Sai yaushe? Amma ina! Babu ko kalma ɗaya da yake jin zai iya furtawa, ba ya fatan rabin shekarar da ya kusan cinyewa ya tashi a banza balle ya ga shekarar ida  da rai da lafiya, wannan ya sa yake takatsantsan ya kuma jure bai ƙara kallonta ba tunda ko ya kalli side mirror ba ya ganin komai face danshin ruwan dake kwarara sai ko hasken fitilun motocin dake saman titi. Har suka iso gidan ba ka jin uffan daga Fadeel, shi kansa Ibb sanin halin mutumin ya sanya bai takale shi da hira ba ko sau ɗaya. Ya dai san yau Humaira ta fama mishi inda yake mai ƙaiƙaiyi. "Ko mu karasa da ku har cikin farfajiyar?" Wannan kalmar ya sa Fadeel cire gilashin idonsa, ya dubi gidan su Humaira, wato har an iso kenan. "Aa, mungode sosai. Bari mu karasa ciki." Cewar Ummita. Humaira kuwa har ta kama ƙofar ta bude, amma ina, iska mai karfi da ruwan da ya fesomata ya sa dole ta koma ta rufe. Fadeel ganin haka ya juya bayan, sai a sannan ya kara kallonta ido cikin ido, da sauri ya dauke idanunsa ya dan kai hannu baya ya dauko lemar dake ajiye a wurin. Fitowa ya yi ya buɗe lemar, babba ce don ta fi ta Ummita girma, Ummita kam tuni ta fita itama ta bude nata lemar da ba zai ishe su ba su biyu koda a dazun ne. Kofar Humaira ya bude gami da miƙamata lemar. A sanyaye take dubansa. "Karɓa mana Humaira." Ibb ya furta, ta kalleshi. "Mungode sosai, Allah ya kiyaye hanya." Daga nan ta fita, sai ya kasance su biyun a ƙasan lemar. Kan Fadeel a ƙasa ba ya son kallonta gudun ɓarowa kansa aiki, ta sa hannu ta karɓa sannan ta dan ja baya kaɗan. "Idan na shiga zan aiko a kawo." Murmushi ya yi mai kyau har a sannan bai kalleta ba ya amsa da toh. Daga haka ya fice ya koma cikin motar ya rufe. Ita ma ta nufi kofar da gudu-gudu. "Muje." Ba musu Ibb ya yi reverse ya juya kan motar suka bar layin. Ƴar dariya ya yi. "Fadeel kana son Humaira." Fadeel bai iya kallonsa ba ballantana ya samu amsa. Ya kara cewa. "And you know what? Kun dace sosai." Nan ma bai kalleshi ba sai dai ya yi murmushi. Ganin ba ya son magana ne ya sa Ibb rabuwa da shi. *** A can kuwa Humaira na shiga ta bada lemar a miƙa musu, ɗan aike ya dawo ya ce babu kowa a wajen, ta karɓa a sanyaye ta shige ɗakinsu da shi. Madadin ta karasa ciki sai ta ajiyeshi a ɗan gefen don ya sha iska. Suka sauya kayan jikinsu saboda jiƙewar da suka ɗan yi. Ummita ta ɗauro alwala sannan itama ta ɗauro, koda ta idar da sallah kwanciya ta yi saman dardumar don kanta har lokacin sarawa yake yi kamar jijiyoyin kan nata za su tsinke. Tuna Fadeel kaɗai yana haifar mata da rawar jiki da ciwon kai, daga haka kuma sai ta ji kamar ana mata ihu a kunne. Kafin ka ce wannan sai ga Humaira ta soma kuka sosai. Ummita da ke kwashe jiƙaƙƙun kayansu ta juya da sauri ta juyo. Allah ya taimaka su kaɗai ne a ɗakin ta roƙi yanmatan akan su fita ta gyara don sun yi kaca-kaca da shi. Tuni ta fahimci matsalar jinnunta ne, ta sha mamaki ma da bai tashi a mota ta yiwa su Fadeel rashin mutunci ba. Da sauri ta fice zuwa kicin, can baya ta zagaya inda ake dora babban tukunya a icce saboda yawan da aka yi. Garwashi ta zuba cikin kasko ta dauka da sauri gudu-gudu ta nufi dakinsu. Mami dake kokarin shiga kicin don ganin kwandunan kayan miyan da Abba ya ce an kawo na girki ta tsaya cak hankalinta ya yi kan Ummita wacce ke tafiya kamar wani abu ya faru. Da sauri ta bi bayanta. Ita kuwa Ummita, tun cikin babbar sallah da ta je Bichi ta karɓowa Humaira hayaƙi a wurin ɗan uwan mahaifiyarta hakan yasa Humaira na fara kuka ta yi niyyar turara mata. Abin mamaki har ta isa yanayin kukan Humairar bai sauya ba. Ta ciro maganin ta barbaɗa cikin kaskon ta ajiyeshi kusa da Humaira. Nan da nan kanta ya soma juyawa. Daidai lokacin Mami ta faɗo ɗakin. Abin da ta gani ne ya sanya ta kallon Ummita, "Lafiya? Meke faruwa da Humairar? Wannan wane irin hayaki ne kuma?" Ummita ta sha jinin jikinta don gaba daya ba ta sanar da Mami ta karɓowa Humaira hayaƙi ba. "Ba komai Mami, kukan nan ta soma wanda take yi idan aljanunta suka tashi shi ne.." Mami ta daka mata tsawa. "Shi ne me?! Shi ne kike yi mata hayaƙi ba tare da kin sanar da ni ba? Haba Ummita, yanzu idan Abbanta ya ji wa zai yiwa faɗa? Maza ɗauke hayaƙin nan." Ummita ta dauka ta fitar zuwa bandaki ta kashe, ta sani ta yi kuskure amma kuma cikin ikon Allah Humaira ta yi shiru sai gumi take haɗawa da alama kuma bacci ya ɗauketa. Ummita ta kai duba ga Mami, zuwa lokacin tana zaune gefen gado. "Ki yi hakuri Mami." Girgiza kai Mami ta yi. "Ba laifi kika aikata ba Ummita, na sani kulawa ce da yar uwarki, amma ko mene ne ya dace na sani saboda nima ina nawa kokarin a kanta don har na yiwa Abbanku maganar wani mai bada magani zan kai ta wurinsa bayan biki ya ga mece ce matsalarta." Gyaɗa kai Ummita ta yi tana murmushin farin ciki. Ba ta da fatan da ya wuce ta ga Humaira ta samu lafiya ta amince da auren mai kaunarta irin Fadeel. "Toh Mami. Allah ya sa a dace." Mamin da murmushi ta amsa da amin. Har ta mike ta kai ƙofa ta juyo. "Ɗaukomin maganin da kike turara mata, idan ya so sai na yi mishi bayani." Ba musu Ummita ta ɗauko ta ba ta, murmushi ta yi ta juya ta fita a dakin. *** BIKI BUDURI.... ®️Rufaida Umar. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Da taimakon Allah ta kammala aikin odar da aka bata. Kamar yanda ta saba, wannan karon ma waya ta yi akan a zo a karɓa. Aka ba ta lokacin zuwa karfe sha biyun rana. Bayan sun yi sallama ta sauke ajiyar zuciya tana mai jin wani irin nishaɗi. Hamdala ta yi kamar koyaushe kafin ta fiddo manyan ledojin mai tambarin Deelsha's Delicacies ta sanya. ***   Murja ta kammala shiri tsaf sai rawar jiki take yi ta je ta ga Humaira me snacks. Kausar na zaune a falo tana taya Khadija da Hanifa (Ɗiyar Saddika yaya ga Anti Amarya) hura  balan-balan su na tarawa. Murjar ta fito. Kallo ba ta ishe ta ba, ta gefen ido Murja ta watsamata harara. Daidai lokacin da Anti Amarya ta shigo bayan ta dawo daga farfajiyar gidan inda mai decoration ke ƙawatawa don anan za a gudanar da birthday din Abdulmaleek na cika shekaru uku a duniya.   "Ni na shirya zan wuce." "Toh tsaya na baki cikon kuɗinta. Don Allah ki yi sauri kina karɓa ki wuce ki karɓo Cake din." Ta amsa da toh. Anti Amarya na shiga ciki sai ga Fadeel ya shigo falon riƙe da Abdul yana mishi wasa. Nan da nan Murja ta ji ranta ya yi wani irin sanyi. Ta kuramasa idanu tamkar ta lashe shi musamman ganin yanda shigar jan t-shirt da baƙin jeans ya haskaka shi abinka da fari. Ta sauke ajiyar zuciya tana ji inama kawai ta tsinci kanta a faffaɗan ƙirjinsa. Sai da ta ji suna gaisawa da Kausar sannan ta dawo hayyacinta. Ajiyar zuciya ta sauke, ta ƙarasa ta zauna ita mai shirin fita. Murya cike da yanga ta ce. "Yaya Fadeel barka da rana." Kallo ɗaya ya yi mata ya kauda kai, shi a yanzu sam ba ta burgeshi tun sadda Alhaji ya faɗamasa saƙonta. "Yauwa." Daga haka ya maida hankalinsa ga Kausar suna hirar aikin Fu'ad da babu hutu. Ita kuwa Kausar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ta gama lura da irin matowar da Murja ta yi a kan Fadeel, ta kuma sani zai wahala ta same shi tunda sam ba ta gabansa. Murja ta shaƙa, saukowar Anti Amarya daga saman bene ya sa ta mikewa. Fadeel ya gaisa da ita. Ta miƙawa Murja kudin tana fadin. "Ina daɗa roƙonki, na san halinki kar ki je ki zauna don Allah Murja. Kina karɓar snacks din ki biya ki dauko cake." Ta amsa da toh, ji take inama direban gidan ba ya nan sai ta ce Fadeel ya kai ta. Amma tun dazun yana waje ita yake jira. Fadeel kuwa yana jinsu amma bai sa baki ba. Ba ya son ya zaƙe akan lamarin Humairar har su shinshino wani abu babu ma kamar Murjar da bai gama yarda da ita ba. *** Ta tsaya daga ƙofar gate din gidan tana ƙarewa gidan kallo, yamutse fuska ta yi. Eh ba laifi su na da rufin asiri amma ko daga waje bai kama ƙafar gidan su Fadeel ba. Ta karasa ta yiwa Maigadi sallama ta kuma faɗi abin da ya kawo ta, iznin shiga ya yi mata kai tsaye don dama yana da masaniyar sana'ar Humairar. A sadda ta karasa ciki Humaira na zaune tare da su Raihana a falo bayan gama yi mata kwatance a waya, ta sani ba za a ɗau lokaci ba za ta karaso tunda a sanda suka yi wayar tana kusa da su. Sallamarta ya sa gaba daya suka dube ta. Ba laifi tana da nata tsarin daidai gwargwadod. Abaya doguwa ce a jikinta sai mayafinsa, sai ko wani ƙaton gilashi da ta rufe kwayoyin idanunta da shi. Tunda ta shigo falon ya karaɗe da ƙamshin turarenta mai ƙarfi irin wanda ya zama haramun mace ta fesa ta fita da shi. Suka tarbe ta da hannu bibbiyu aka gaisa. Humaira har da kawomata ruwa da ragowar snacks din ta ci. Kasancewarta wayayyiya ta sake da su aka ɗan taɓa hira har Mami ta fito suka gaisa da ita. Murja ta yaba kwarai da tarbar da aka yi mata, ta kuma ji a jikinta Fadeel ba zai so Humaira ba, ba ita ce wacce yake so ɗin ba don dai wannan din ba wata babba ba ce ba za ta wuce shekaru goma sha biyar ba. "Kina da page a instagram ne?" Humaira ta gyaɗa kai da murmushinta har wushiryarta na bayyana. "Eh akwai." "Mene sunan?" Nan fa daya, ta sani furtawar ne aiki ba ta iya ba sosai. Raihana ta karɓe zancen ta fadi. Murja har sai da ta ɗan kalli Humaira sannan ta kalli Raihanar da murmushi. "Ok zan yi following dinki. Na ji dadin ganinki na kuma ji dadin ɗandanon snacks dinki duk da daman na san ɗandanon. Akwai ɗan uwana Yaya Fadeel yana kawomana sosai. Ta wajensa muka sanki." Murjar ta fadi tana mai ƙurawa Humairar idanu don ta ga yanayinta, so take dai ta samu tabbacin babu komai tsakaninsu. Raihana kuwa ɗan jim ta yi a ranta tana tunanin wane Fadeel din? Kodai Fadeel wanda ta sani ne, tabbas ya faɗamata yana odar snacks din Humaira ta hannun wata Antinsa. Ko shi din wannan ke nufi? Idan kuma hakane ita wace ce a wajensa? Ta maida dubanta ga Humaira don ta ga yanayinta, sai ta lura ko kadan ba ta sauya daga murmushin da take yi ba, sai dai jin sunan kamar jikinta ya dan yi sanyi. "Allah Sarki, na kuwa gode sosai." Abin da ta ce kenan, wannan ya sa Murja kuma sakin jikinta sosai. Lallai wannan ba ita ce Humairar da Fadeel ke mutuwar so ba, wannan da alama ba ta ma san da zamansa ba. Dama ya ce ba shi ke yin odar da kansa ba. Yanzu kam ta yarda. Murja ba ita ta bar gidan ba tsabar shagala da ta yi suna ta kwasar hira da su musamman Raihana wacce ta fi su sanin mutane, kusan ma akwai ƙawayen Raihana na makaranta wadanda duk Murjar ta san su hakan yasa hira ta musu dadi sai da Anti Amarya ta kira wayarta tana faɗan jimawarta ba shiri ta mike, su Humaira kuwa har mota suka raka ta da ledojin. Murja ta karɓi lambar Raihana da zummar a dinga gaisawa duk da ta girme musu don za ta yi sa'ar Tasleem. *** Sadda ta isa gidan har yara sun fara zuwa ƴan party. Ta karasa Anti Amarya na mata faɗan dalilin jimawarta. Hakuri ta ba ta, ganin Fadeel a wurin wanda ke cin abinci a nutse saman dinning ta ce. "Wallahi hira muka sha da su Humaira, mutanen gidan akwai kirki kar ki so kiga kamar kada a rabu." Fadeel ya ji maganar har ransa, ya kuma ji dadi sosai. Bai dai ko ɗago ya kalle ta ba. Yana ji dai tana ta ba Anti Amarya labari ita dai ledojin ta hau buɗewa tana kallon snacks din. Koda ta dandana sun mata dadi kwarai. Nan aka shiga sanya wa a takeaway ana rufewa, Kausar na nan ana aikin da ita. An gudanar da party cikin armashi, yaran Daddy da Mommy ne suka cika gidan don Anti Amarya sam ba ta barin mara shi ya raɓe ta. Yawanci duk abokan makarantar Abdul din ne sai ko makwaftansu. Hatta a yaran yan uwanta ba kowa ta gayyata ba. *** Ɓangaren Amare kuwa, Amarya Futuha an ci amarcin sati daya cif ko ƙofar gida ba ta leƙa ba. Hotunansu ita da mijinta kala-kala babu wanda ba ta ɗorawa a Instagram, shi kansa Angon hakan na mishi dadi kwarai bai taɓa hanata ba. Tunda ta zo ba ta taɓa sanya Uwargida a idanunta ba, karshe ma sai Ango Yakubu ke sanar da ita ta yi tafiya Saudia ita da yaranta. Futuha tun da ta ji haka duk sai ta matsa mishi akan ita ma ya dace su tafi hutun honeymoon Dubai. Hakan ya yi mishi dari bisa dari, a lokacin ji yake ko nawa ne zai iya kashewa Futuha saboda dadin angoncin da yake kwasa. Ba ɓata lokaci aka soma shirin yi mata passport da sauran abubuwan da ya kamata ma tafiya. Sai bayan kammaluwar komai sannan washegari ta yi nufin zuwa gidansu ziyara da kuma sallama. A ɓangaren Tasleem ma, babu laifi Hamza na iyakar kokarin faranta mata, sun ci soyayyarsu yanda ya kamata, ba ta dora koda ruwan zafi daga gidan iyayensa ake kawomusu abincin safe zuwa dare. Sai da ta yi sati cif sannan suka kara shiga ta gaida Mahaifiyarsa da abokan zamanta su uku. Gidan dai babban gida ne mai tarin yara da jikoki. A ranar har gidajen facalolinta sai da ta shiga, wasu sun kata tarbar kirki yayinda wasu kallon tara saura suka dinga yi mata. Haka tattara ta dawo gida. A ranar da suka yi waya da Futuha take ba ta labarin tafiyarsu Dubai hankalinta ya yi mugun tashi, ji tayi inama ita ce ta samu wannan damar. Ciki-ciki ta yi mata murna, dama tana jin haushin hotunan da take karo da su a media na Futuhar da mijinta yanda kowa ke santin kyawun da suka yi. Futuha ta ce ta shirya za su zo har gida su yi mata sallama. Ba ta ma iya amsawa da toh ba ta katse kiran gami da jan tsaki. Ya yi daidai da shigowar Hamza falon, hannunsa rike da ledoji ya yi mata siyayyar kayan sanyi da kaza. Har ya karaso kusa da ita ba ta san ya yi ba tsabar ta lula duniyar tunani. Sai da ya ajiye ne ya dan zunguri kafaɗarta kadan. Ta dubeshi, murmushi tattausa ya sakar mata, itama ta bishi da na yaƙe. Rungumo kafaɗarta ya yi. "Tunanin me kike yi ne haka? Har na shigo da favourites dinki amma ba ki lura ba?" Ta kai duba ga ledojin dake ajiye, har gumin sanyi ɗaya yake, sai ta ji ta kasa farin ciki da abin da ya ajiye din duk da cewa a baya har so take ya kawo su ta dinga tsalle kenan tana rungumeshi. A yanzun kuwa ko ɗigon annashuwa ba ta yi ba. Sai jikinsa ya yi sanyi, ya kamo yatsun hannunta. "Wai me ya sauyamin ke haka? Ko bayan fita na kin yi baƙi ne?" Dama kiris take jira ai sai ta tunzura ta yakice hannunta. "Me kake nufi?! Na yi baƙi sun zugani ko sun ɓatan rai? Yan gidanmu kake nufin sun zo ko ƙawayena?! Au zargina kake yi akan wani zai iya zuga ni akanka? Ai ba sai an zuga ni b, ni mai zuga kaina ce!" Gaba daya ya razana, ya yi jim yana kallonta, a iya saninsa babu inda maganarsa ta kai nan. Me ya kawo batun zuga kuma ana zaune kalau? A ina ya ce hakan? "My Noor, me ya kawo zancen zuga? Ban gane inda kalamanki suka dosa ba?" Sai a sannan ta ɗan dawo hayyacinta. Ta ja guntun tsaki ta zauna. Nan da nan kuma Hamza ya ɗan sauya fuska. "No please, zan dauki komai amma ban da raini, ina maki warning na farko da karshe, bana son tsaki. Kar ki kuma." Ba ta ce komai ba face turo bakin da ta yi, sai ya ji ma gaba daya ta ɓata masa rai kawai ya mike ya yi daki. Ta bishi da harara, ita ta sani ko wannan motar tasa zai siyar ba zai ishe su su je Dubai har su kashe kudade irin wanda Futuha zasu kashe ba. Ta san muddn Futuha ta yi wannan tafiyar to fa kanta zai fasu, za ta ƙara jin wani girman kai har ma ta dinga yi mata fi'ili iri-iri. Don haka hankalinta ya tashi, ga babu yadda ta iya, nata mijin ba ta tunanin ma ya taɓa taka farfajiyar Airport balle ya shiga jirgi. Ta ja tsaki karo na biyu. Madadin ta kwashe ledojin da ya kawo ta adana komai koda ba lokacin za ta sha ba, kawai sai itama ta bar su anan ta shige nata dakin ba ta ko bi ta kansa ba don har sannan zuciyarta zafi take yi, hassada mugun ciwo ne. *** Tun karfe goma Humaira ta je kasuwa yin cefane bisa umarnin Mami wacce ke ta shirin tarbar Futuha da za ta zo. Tana dawowa kicin kawai ta shiga ta soma shirin girki, tuwon semovita miyar kuɓewa danya wanda ya ji nama da busassan kifi, shi Futuhar ta ce tana muradi sai ko lemun kwakwa. Wuraren karfe ɗaya ta kammala komainta jera a saman tire ta kai falon ta ajiye. Daga nan ta koma dakinsu. Ita ko kusa ba ta wani zumuɗin ganin Futuhar kamar yanda su Ummita ke yi. Tun dawowarsu daga makaranta jin ance tana hanyar zuwa suke faman rawar ƙafa. Ai kuwa ko awa ɗaya cikakka ba su yi da dawowa ba sai ga mota direba ya kawo ta har farfajiyar gidan. Da gudu Raihana ta fice tarbar yar uwarta, itama Ummita ta mara mata baya a nutse take tafiya. Humaira sai ta ja guntun tsaki ta cigaba da danna wayarta tana ganin sabbin likes da comment da sabon hotunan da ta dora na girke-girke suke samu. Ta shagala sosai sai ji ta yi an warce wayar, ta juya da sauri. Raihana ce. Dariya ta yi mata. "Ki taso inji Mami ku gaisa da Futuha. Ashe Dubai za su wuce da mijinta sati na sama." Ta ɗan yi murmushi, ba ta fiye son kushe su a gaban Raihana ba don haka ta taya murna a fili. "Kai amma na mata murna, Allah ya kai su lafiya. Muje toh. Bani wayata kuma." Raihana ta mika mata suka yi dariya. A falon ta iske Futuha zaune, masha Allah ta ƙara ƙiba da kyau, kumatunnan har wani kyalli suke yi. Wani arnen leshi ne a jikinta fari da ruwan toka ya sha aikin stones sai faman baza ƙamshi take yi, hira sosai take yi da Mami. Ƙassim ma na zaune banda Yassar da Dawud wadanda sula tafi Camp a can garin Jigawa. Humaira ta karaso ta gaida ta, ta amsa mata tana yamutse fuska kaɗan daga nan ta maida hankali ga uwarta su na cigaba da hira. Humaira wacce dama ta san a rina kawai sai ta mike ta saci jiki ta koma daki, Ummita ta mara mata baya. "Ke kuwa daga gaisuwar sai ki taho?" Harara ta dan watsa mata. "Idan na zauna me zan mata? Goyata zan yi? Ai dai kinga yanayin amsar gaisuwar da ta yimin ko? Toh ni kuwa marar zuciyar ina ce da zan tsaya?" Ajiyar zuciya Ummita ta yi. "Allah ya kyauta, kinsan Allah na yi zaton aure zai sauya su, amma naga har yanzu da sauransu." Taɓe baki Humaira ta yi ta ce. "Toh yaushe ma aka yi daren? Ke ta dai samu duniya ne kawai shiyasa abinta ya ƙara gaba. Nifa kinsan ba abin da ke ban mamaki face irin yadda matarnan ba ta yiwa kanta faɗan ta nutsu ba take faman ɗora hotunanta a media. Shi ma mijinnata soloɓiyo da ya biyemata." Ummita ta kama baki har da ɗan waigawa ta ga ko babu wani a kusa da ya ji kalamin Humaira. "Kinga ki rufamana asiri. Mutum ba shi ya ga zai iya ba? Kar ki manta har da shi din Ogan nata ake wannan taɓargazar kinga kuwa abu nasu maganin a kwaɓe su. Wayewar yanzu ce ta shirme ta zo da haka." Dariya Humaira ta yi. "Kenan kema haka za ki yi da Sahabinki ko?" Duka ta kai mata a cinya. "Allah ya sauwaƙe, mu aurenmu ko party ba zamu yi ba, walima kawai a cikin gida ta isa. Albarkar auren muke nema. Hum, nifa yanzu duk ya dameni akan zai turo a sanya rana kafin nan da shekara idan mun kammala nayi Candy a yi auren. Wallahi kwanakin nan duk akan hakan muke ta rikici. Na rasa yanda zan ɓullo masa." Humaira ta mike zaune sosai. A duniya ta tsani ta ga Ummita cikin damuwa ko na sakan, don haka ta ce. "To me kike jira? Me zai hana ki ba shi wannan damar? Kina sonsa yana sonki fa. Kuma sa rana ba shi ne auren ba, don Allah ki yi shawara da Mami tunda kinga ta san da zamansa, na tabbata za ta goyi da bayan ya turo." Ummita ta zubamata idanu ta yi shiru cike da damuwa, ga mamakin Humaira kuma sai kawai ta ga hawaye sun soma zuba daga kwayar idanunta. "Lafiya? A maganata akwai wacce ta maki zafi? Kiyi hakuri don Allah kinji?" Girgiza kai Ummita ta yi, "Ko ɗaya Humaira, ke ce dalilin da yasa na kasa ba Sahabi damar turo iyayensa. Wallahi bana jin dadin mafarkaina a kanki kwanakin nan. Humaira na damu da rashin bada ƙofa ga kowane saurayi ya nemi aurenki da kike yi. Ba na so na yi aure na bar ki a wannan halin. Gaba daya na damu." Shiru Humaira ta yi, toh ita da kamar abin yana damunta kamar kuma ba ta damu ba. Ta ma kasa fahimtar komai sai kawai ta dubi Ummita a sanyaye. "Kin manta ke ce me nusar da ni idan na ɓata? Ke ce me ƙarfafamin gwuiwa akan imani da Allah a irin wadannan lokutan? Toh ki sani, har ga Allah ba na jin son kowane namijin ba balle na ji son auren a raina. Hakan ba yana nufin wata matsalar ba, ki kaddara lokaci ne, duk sadda na ji son wani a raina, watakila..." Sai kuma ta ma rasa me za ta ce, kawai sai ta sunkuyar da kai ta riƙe hannun Ummita cikin nata. Karon farko da ta ji tana hawaye, hawaye mai dalili ba wanda ta saba yi a irin gaɓar nan babu dalilin ba. Ummita sai ta ji tausayinta ya lulluɓe ta, Humaira ai itama da zuciya a kirjinta. Dole akwai abin da ke damunta amma ba ta faɗa, ba ta magana sai dai ta yi shiru idan sun taso da zance ta maida su wasu cali cali. "Ki tayani addu'a Ummita, ina da damuwa amma ban gama gane kan damuwar ba. Ina da abin faɗi, amma zuciyata na kwaɓa ta a koyaushe akan bai kai abin magana ba nayi shiru kawai. Na rasa meke damuna, idan na ce zan zurfafa tunani sai jikina ya hau rawa, kaina ya hau sarawa. Watakila iyakar abin da zan iya faɗa kenan. Nidai ki dinga sanya ni a addu'a." Ummita ta ɗan rungumeta suna kuka. Kowannensu da kalar tunaninsa, dakyar suka rarrashi junansu suka share hawayen. Sai kuma Humaira ta cigaba da karfafa mata gwuiwa akan ta bari Sahabi ya fito a yi magana. Ta kara da fadin. "Kinga itama Raihana zan ce ta amince ta bar Imran ya turo. Shikenan sai ku bar min gida na huta." Ummita ta harareta, ita kuma ta yi dariya tana kokarin danne radadin ciwon kan da take ji gudun kar ta kefa Ummita a wata sabuwar damuwar. Koda Ummita ta fita don amsa kiran Mami wacce ta turo Muhsin, sai ta zame ta kwanta ta runtse idanu tana tauna maganganun da suka yi da Ummitar, hannuwanta riƙe da kan da ke faman sara mata. Tana nan kwance har bacci ya sure ta, Raihana ta zo ta tashe ta akan ta je Mami na kira. Ta ci sa'a zuwa lokacin ya rage ciwon, don haka dankwalinta da ya zame ta maida ya rufe kan ta fita. Anan fa Mamin ta mata umarnin ta shirya za ta bi Futuha don ta taimaka mata da girki abokan mijinta za su je gidan nan zuwa jibi. Kamar ta cewa Mamin a bari mana sai jibin ta je ta dawo, amma ba ta son jan musu da ita kawai sai ta ce toh. Ranta na zafi haka ta shirya ta bi Futuha suka tafi. Tana ji Futuhar na yiwa Tasleem waya wai gatanan a hanyar gidanta, ita dai ba ta ce mata uffan ba sai kallon window da take yi zuciyarta na zafi, wani sashi na zuciyar na kokarin ce mata Mami ba ta kyauta mata ba yayinda wani gefen ke kwaɓarta yana nusar da ita irin kirki da mutuncin Mamin. Bai kyautu ta munana mata zato ba. Da haka suka karasa gidan Tasleem. *** A yau Murja ta yi niyyar zuwa sashin Fadeel don ta rantse ko ta yaya sai ya saurareta ya ba ta damar amayar da abin da ke ranta ido da ido. Kwanakinnan ko bacci kwakkwara ba ta iya yi tsabar so da tunaninsa da ke neman zautar da ita, wannan ya sa ta zuri takalmanta kawai ganin an yi Magrib tana kuma da tabbacin yana nan ta nufi sashinsa. Yana zaune ya kafe manyan frames guda biyu da aka yi mishi na hoton Humaira da idanu yana kallo. Ta yi kyau matuka, daya tana tsaye ne a farfajiyar Manal Event Centre ranar bikin su Futuha, dayan kuwa wanda ta dauka da sallah ne ba ta san ma an yi hoton ba ta rike kafaɗar Ummita tana dariya mai bayyana wushiryarta. Ta yi kyau ainun, masifar son da yake yiwa hotunan ne ya sanya aka wanko da zummar zai adana duk radda suka yi aure ya kafe su a ɗakin baccinsa. Uzurin bandaki ya kama shi, ya mike ya shige ƙuryar dakin don kama ruwa. Daidai lokacin Murja ta hau kwankwasa ƙofar dakin, tana ji kamar ta tura kanta ciki ko ba izninsa. A yau ta kai maƙura a so da kauna da begen ganinsa. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 A can kuwa, Wizzy yana kammala magana da Abba ya fidda layin a wayarsa ya kakkarya ya zubar, lokaci guda kuma ya mayar da layinsa. Suka dubi juna suka kwashe da muguwar dariya. Humaira da Ummita aka titsa ƙeyarsu zuwa cikin ɗakin. Babu laifi wajen da suka sauya ya fi wancan kyau, komai tsaf sai ƙura kuma ga dukkan alamu sabon gida ne da ba a kammala aikinsa ba. Banɗakin akwai ruwa har da butar alwala. Wajen dai ya fiye musu ɗayan amma kuma hankulansu ba a kwance suke ba. Ai babu wani gata da za a yi musu alhalin su na hannun azzalumai abin ya yi musu daɗi su samu kwanciyar hankali. Daga Ummita har Humaira tun sadda aka garƙame su a ɗakin ba sa aikin komai sai kuka hakan na da nasaba da jin muryar Abba da suka yi wanda gaba ɗaya sun fitar da ran ƙara ji ko ganin wani cikin fuskokin da suka sani. Wizzy kuwa bayan dawowar Badboy daga rufe ƙofar ya dube su ya ce. "Aski fa idan ya zo gaban goshi ya fi zafi, wannan lokaci ne da zamu ƙara zage damtse kuma mu yi takatsantsan don cik umarninta, a ƙarshe mu ma mu kwashi rabonmu, ta sallame mu." Babba wanda ke faman hura hanci yana fitar da huci ya soma magana a kausashe. "Wai ni fa bana son rainin hankalin da take yi mana! Matar nan tun da ta bamu aiki ba ta yarda ayi waya da uta sai rubutun saƙo. Ita ba ta san hatsarin da ke tattare da hakan ba? Idan fa ta yi sakaci har wani ya yi ya gani to fa akwai matsala. Sannan ta ƙi ta bayyana kanta sai ɗan aiken da ta ke turowa, ita kenan ko kama mu za a yi ta tsira kenan? Ba mu san wace ce ba, kuma ba mu san komai a kai ba, namu kawai aiwatarwa idan an cafke mu ta ci bulus kenan?!" Wizzy ya ɗaure fuska bai ce komai ba, ganin haka Badboy ya cafe. "Kai Babba ka iya kalamanka, ka sani koda wasa idan har ba mu ne muka so ba, toh fa ba za mu taɓa kamuwa ba. Mun fi ta iya shege ai kai ka sani. Ni fa duk ba wannan ne damuwata ba, yarannan su na hargitsa lissafina amma kai Oga ka ƙi bani damar gwangwajewa. Kenan haka muna ji muna kallo za mu bar su shikenan sun sha?" Sai a sannan Wizzy ya kalle shi. "Ba wannan aka umarcemu  da yi ba, asalima don horo ne ya sanya muka kai su tsohon gidan gonar can don kawai su shiha taitayinsu amma tun farko ba ya daga cikin bajat dinmu. Kai ne ka fiye garaje, ai na ce maka akwai lokacin da hakan za ta kasance, mu bari mana har mu samu tabbacin kuɗaɗen nan za su faɗo hannunmu tukunna mana, sai mu yi duk abin da muka ga zamu iya. Mu dai tabbatar ba mu kashe su ba don ba shi aka sanya mu ba." Suka yi shiru babu wanda ya tanka masa musamman Badboy da ke jin haƙurinsa na dab da ƙarewa akan ƴanmatan musamman Humaira da surarta ke fisgarta. ***   Hankalin Anti Maijidda (babbar yayar mahaifiyar Ummita ta Bichi) a tashe ta shigo babban falon na Mami da jama'a ke zaune ana jajanta wannan lamari na su Humaira. Ba ta ƙasar gaba daya ta je Umarah sai a jiya ta diro Kanon, ko gida ba ta je ba kai tsaye ta ce a sauke ta a gidan. Tana shiga ta zube jikin ƙanwar Abba, Baba Amina  da suka saba tun a baya tana kuka sosai ana ba ta haƙuri. A lokacin ne kuma Mami ta shigo daga ɓangaren Abba cikin dogon hijabinta, ta gama jin yadda aka yi da Abba da kidnappers din akan kuɗin fansa. Jin muryarta su na gaisawa da makwaftan da ba su jima da leƙowa gidan ba ya sa Anti Maijidda miƙewa kamar wacce aka tsiƙara ta hau tafi raf raf har sau uku, wannan ya ja hankulan kowa kanta yayinda wasu suka shiga tunanin kodai ɓatan Ummita ya girgiza kwakwalwarta har haka? Mami kuwa cak ta tsaya kawai tana mai zubamata idanu. Maijidda kenan, macen da ba su taɓa raɓar juna da alheri ba, babu wata jituwa da ta ƙara haɗa su tun bayan rasuwar Fatima mahaifiyar Humaira. Maijidda ta soma magana murya a ɗage kuma a kausashe. "Ki zuba ruwa a ƙasa ki sha Maryam! Ki tara jama'arki ku yi kiɗa ku yi rawa har da juyi! Yau burinki ya cika! Abin da kika jima kina ƙullawa akan yarannan yau kin cika shi!" Jin haka Baba Amina ta miƙe a firgice cikin kaɗuwa ta fisgo hannun Maijidda. "Maijidda ki shiga hankalinki mana! Ki yarda da ƙaddara ki yi imani da ita. Wannan wane irin zantukan banza ki ke yi akan baiwar Allahn da ta riƙi amanar ɗiyar ƴar uwarki da amana da kulawa tsawon shekarunnan koda wasa Ummita ba ta taɓa kokawa da ita ba? Wane irin baƙin ƙazafi kike shirin yiwa baiwar Allahn nan?!" Anti Maijidda ta fashe da kuka sosai tana nuna Mami da yatsa. "Har abada ni Maijidda ba zan taɓa kaunarta ba, kuma ba na jin zan yarda da ita koda ace gaba ɗaya mutanen duniyar nan za su taru su yi mata kyakkyawar shaida! Baƙar azzaluma ce! Amina ni nasan wacece Maryam, ni zan ba da labarinta! Don haka idan har bincike ake son yi na gaske daga cikin gida, a soma daga kanta da kuma azzalumar uwarta!" Wannan ƙazamin furucin ya sa Mami ta fusata sosai.  Hannunta na rawa kamar yadda dukkan gaɓɓan jikinta suke yi ta nuna ta da yatsa, daƙyar maganarta ke fita saboda zuciyar da ta taso mata da kuma ruwan hawayen da suka wanke mata fuska lokaci guda. "Na shanye dukkan baƙaƙen maganganunki na tsawon shekarunnan ba don komai ba sai domin albarkacin ƴar uwarki marigayiya Maimuna da muka yi zaman mutunci da ita! Na kuma cigaba da jure duk wani cin kashinki a dalilin Ummita jinin Maimuna ce da Naziru. Ban da haka ba ki da wata ƙima ko daraja a idanuna!" Baba Amina da mutanen ɗakin dakyar suka tsawatar aka kashe zancen inda Mami ta fice daga falon cikin ƙunar rai zuwa ɗakinta inda Anna ke zaune kuma tsaf ta ji dukkan abin da ya faru. Allah ya taƙaita lamarin Jannat ba ta gidan, ta fita dubiyar wata ƙawarta da aka yiwa aiki a asibiti, da abin zai fi haka ɓaci. Anna ta dube ta sai kuma ta yi dariya. "Maryama kenan, wannan shi ne sakamakon bautar da ki ka yi na riƙon Ummita ko? Wannan ranar nake jira dama, ban kuma zaci zan gani nan kusa ba. Shashashar yarinya! Ga shi nan tun ba a je ko'ina ba kin kwashi kashinki a hannu. Da ace tun a farko kin ji maganata hakan da bai faru ba. Yanzu sai kiyi kuka da kanki akan duk abin da ya faru." Mami ba ta ce da Anna komai ba, sai ta fidda hijabin da ta zumɓula ta ɗauki wayarta kawai ta zauna ta yi shiru tana aikin dannawa, Anna ta cigaba da zabga ruwan bala'i, da Mami ta ga abin ba na ƙare ba ne, kawai sai ta fice zuwa ɗakin su Raihana ta bar mata ɗakin. *** Fadeel ya farka gami da ƙurawa silin idanu, shiru ya yi yana ƙoƙarin tunano dalilin kwanciyarsa ciwo, a hankali kuma ya juya kansa ya dubi ɗakin. Ibb ne kaɗai a zaune yana danna waya bai ma lura da farkawarsa ba. Ya lumshe idanunsa lokaci guda komai ya dawo kwanyar kansa, a firgice ya miƙe zaune. "Ya Salam!" Ya faɗi da ƙarfi yana mai fisge drip din da aka sa mishi. Furucinsa ya sa Ibb mikewa da sauri ya nufo shi gami da riƙe kafaɗunsa. "Fadeel yi a hankali mana." Jin haka ya dube shi da rashin kwarin jiki. "No Ibb, kwana nawa nayi a nan? Humaira na hannun kidnappers, za su kashemin ita. Ka bar ni na je nemanta." Daidai nan Alhaji da Daddy suka shigo. Fadeel ya miƙe jiri na kwasarsa yayinda Ibb ke ɗan riƙe shi, Daddy da sauri ya tarbe shi ganin kamar zai faɗi ya ce. "Fadeel kwantar da hankalinka, in sha Allahu za'a ga Humaira." Kawai sai ya ji hawaye sun zubomasa, wato za ma a gan ta ba wai an ganta ba? Ya girgiza kai yana kallon Daddy amma sai ya kasa magana. Suka taimaka suka mayar da shi mazauninsa. Daddy a nutse ya karanta masa duk yadda suka yi da Abba ya kuma ƙara da faɗin. "Yanzu haka ba mu jima da waya da shi ba, ya tabbatar mana da cewar sun samu kira daga mutanen, sun kuma buƙaci kuɗi. Wannan damuwar ba zai magance maka kowacce matsalar ba, addu'a da kuma sadaka ita zamu duƙufa yi. Yanzu idan ka ce za ka fita nemanta, ta ina za ka fara? Ka san a inda suke ne? Daji, cikin gari, kasuwa, ƙauye, kai ko ma ba a garin suke ba gaba ɗaya wannan sanin Allah ne kaɗai don haka ka samarwa kanka ƙarfin zuciya ka dage da kai wa Allah kukanka. Babu abin da ba ya magancewa." Daddy ya cigaba da kwantar masa da hankali har da cewa koda ace kudaden da Abban za su haɗa ba za su kai ba, shi ya ji ya gani zai san yadda za'a yi a cika a bayar don su kuɓuta, balle kuma shi Fadeel din wanda yake jin zai iya sadaukar da dukkan abin da ya mallaka a doron ƙasa don kuɓutar rabin jikinsa daga hannun azzaluman nan. Sosai ya ji dadin zantukan Daddy, da wannan ya lallaɓa ya yi wanka, brush, da alwala, Ibb ya ba shi kaya ya sauya. Daga nan ya hau ramuwar sallolin dake kansa. Bai kai ga idarwa ba sai ga Anti Amarya tare da Murja sai ko Fu'ad da ya kawo su, hannun Murja riƙe da kwandon abinci. Ta gaida su Abban sannan ta karasa ta ajiye gefen gadon. Gefe ta koma tana satar kallon Fadeel ɗin da a kwana ɗaya kawai ya zabge. Zuciyarta na wata iriyar tafarfasa.   'Ka yi ka gama Fadeel, na rantse maka koda ace Humaira ta fito ni Murja sai na kashe ta da hannuna. Ballantana ma ba za ka ƙara ganinta ba.' Ta yi maganar a zuci, su Alhaji suka tafi saboda yamma ta kawo kai yayinda Ibb suka fita don yi musu rakiya. Fadeel na idarwa ya dubi Anti Amarya ya gaishe ta, ta amsa tana mishi sannu. Ido ta ɗan yiwa Murja hakan ya sa ta saurin gaida Fadeel, ya amsa ba tare da ya kalleta ba.   Nan suka zauna har sai da Fadeel ya ɗan sha ruwan shayi dakyar amma sam ya ƙi yarda da cin abinci, tunaninsa ko a wane yanayin Humaira take? Watakila ma ko abincin ita ba a ba su sun ci ba. Wannan ya daƙilar da shi daga ci. ***   Sahabi saurayin Ummita kullum sai ya zo gidan ya gaida Abba da Mami, gaba daya ya komaɗe ya rame tsabar tunanin Ummita. Iyaye da ƴan uwansa babu wanda bai shigo jajantawa ba. Hakanan ƴan makarantar islamiyyar su sun zo sun kuma yi saukar Alkur'ani akan Allah ya bayyana su. Hatta da yan makarantar su Ummita na boko sun zo har da malaman makarantar an jajanta. Aka yi addu'a suka tafi.   Labarin dai yana ta yaɗuwa don har waɗanda su Abban ba su ma sani ba sun zo sun taya su jaje, da yawansu a social media suka ci karo da shi. Mubarak dake Ghana yana jarrabawar ƙarshe hankalinsa gaba daya yana Kanon, ba don Abba ya ce kar ya zo ba ya zauna har ya kammala da tuni ya dawo. Hakanan su Yassar ba su zo ba. Amma sosai abin ya taɓa su duk da ƙiyayyar da suke yi musu.         Ɓangaren Futuha kuwa ƴar Dubai, kasancewarta mai mu'amala sosai da yanar gizo sai ga abin nema kuma ya samu. Bidiyo sosai ta yi tana kuka ga hotunan Ummita da Humaira daga ƙasa ta ɗora a shafinta tana addu'ar Allah ya bayyana su a ƙarshe ma har da sanya muryar shahararren Malamin nan wato Sudais yana addu'a. Koda ta ɗora hankalinta kwance ta shiga duba yadda ba a ɗauki dogon lokaci ba bidiyon ya yaɗu, nan fa jama'arta suka fara jajanta mata su na tambayar dama Humaira mai shafin Deelsha's Delicacies yar uwarta ce? Da yawa ma wadanda ba su san Humairar ba ko shafinta sai lokacin suka dinga followinh dinta, lokaci guda shafinta ya yi jama'a fiye da dubu talatin. Hakanan shafin Ummita ma ya yi jama'a. Raihana tana kallon duk abin da ke wakana amma ba ta magana, karshe ma sai ta kashe wayarta gaba daya ta ajiye.  Tun da Abba ya shaida musu da kuɗaɗen da aka ce a bayar na fansar Humaira da Ummita ta ke jin ƴar nutsuwa, ko ba komai kenan su na lafiya kuma Abban ma ya tabbatar musu ya ji muryoyinsu amma bai ce musu ga a yanayin da ya ji ba gudun tayar musu da hankula. ***   Fadeel da Ibb suka shirya tsaf a washegari zuwa gidan su Humaira kamar yanda Fadeel din ya nema. Hankalinsa ya kasa kwanciya da zamansa a asibiti alhalin ba a ga Humaira ba, kuma bai je ga iyayenta ba. Wannan ne ya sanya su Alhaji goyamishi baya don haka ana ba shi takardar sallama ya kama hanyar gidan. Sun samu tarba na mutunci daga Abba, Tasleem tun ganin da ta yiwa Fadeel matsayin saurayin Humaira ya zo jajantawa ta ji hankalinta ya yi mummunan tashi. Kishin nan daɗaɗɗe na Humaira ya taso ya soma  cin zuciyarta. Har gobe akwai son Fadeel a ƙirjinta, ta kuma tabbata da ace shi ta aura da yanzu wani labarin ake ba wannan ba. Kusan lokaci guda suka shigo gidan da Fadeel anan ta gan shi, shi kuwa bangaren Abba suka nufa inda Ƙasim da ya yi musu iso ya raka su ciki. Fauziyya ce ta yi mata rakiya gidan, tana kuma lura da sauyin da ya zo mata lokaci guda sadda Ƙasim ya dawo yana shaida mata ai manemin auren Humaira ne. Ta yi shiru ba ta ce mata komai ba tana ƙara nazarinta.   A falon ta bar Fauziyya ta faɗa ɓangaren Anna tana huci. Nan ta tarar da ita zaune da Jannat wacce ke zaune tana taunar gasasshiyar kazar da ta siyo suna hira da Anna kai ka ce babu wani tashin hankalin da ake yi a gidan. Ganin yanayinta ya sanya su dubanta.   "Toh mai ciki, yau kuma wa ya taɓo ki?" Ta zauna idanunta suka cicciko da kwalla yayinda zuciyarta ke faman tafarfasa. Kwafa ta yi kana ta amsa. "Wai Fadeel na gani ya zo jajantawa Abba fa? Har yanzu dama yana tare da Humaira? Shi ne don munafunci Humaira ta ci amanar Mami ta ɓoye zancen?" Murmushi Jannat ta yi. "Ke ban da abinki ina Humairar take a yanzu? Kina tunanin shirin na wasa ne za ta dawo, ai daga can inda take sai wata duniyar kuma ba wannan da muke ciki ba. Duk fa wanda ya samu dama ya dama.  Kuma da kike wannan maganar ba yanzu gashinan kin auri Hamza ba? Ba kya sonsa kika bari ciki ya shige ki?" Tasleem ranta ya ɗan yi sanyi jin yadda Anti Jannat ke fadin kaddarar Humaira kai ka ce ita ta rubuta hakan. Batun cikinta ya ƙara jefata damuwa, dama ba da son ranta ta samu ba kuma Hamza ya rantse sai ya yi mugun saɓa mata idan ta zubar. "Wallahi Anti idan har zan samu na auri Fadeel zan iya kashe ko nawa ne a yimin aiki a kan Hamza ya sake ni. Anti wai kin taɓa ganin Fadeel kuwa da irin yadda ya haɗu? Wallahi ba zan iya zuba idanu wata ta kwacemin shi ba." Anna tsohuwar banza ta kwashe da dariya madadin ta yi kwaɓa akan wannan haramcin da ake aikatawa sai ma ta ce. "Kina da Jannat Firdausi ai babu ke babu fargaba. Yadda aka yi wancan haka wannan ma zai kasance labari." Suka yi dariya. Can kuma Jannat ta ɗan jinjina kai. "Ko wane ne wanda ya aikata wannan kidnapping din ya yi matuƙar burgeni, da ace ina da damar ganinsa sai na mishi babbar kyauta. Sai hakan ya zo mana da nasara kuma akan gaɓa, Boka ya tabbatarmin da cewa Humaira a can za ta haɗu da ajalinta. Itama Ummita babu tunanin za ta rayu balle har su samu damar kuɓuta su dawo. Kawai dai zan so dawowar ita Ummita, yarinyar ta iya bauta." Tasleem ta yi murmushi. "Nima dai Ummita ba ta yimin komai ba, ba ni da wani ƙulli da ita kamar Humaira. Wallahi Anti na tsane ta na kuma tsani duk wani mai sonta." "Har da ni kenan!" Suka juya don ganin mai furucin a razane. ®️Rufaida Umar *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 *TALLAH!* *TALLAH!!* *Ina ma'abota ƙamshi, su yi ƙamshi suna birge kansu suna birge wanda ya shaƙa* *Ku danna wa.me/2347010137848 ku ce ta yi saving lambar ku watarana zaku ga garabasan ƙamshin da ba za ku iya Bari ba* Tasleem ce ta soma  kauda kanta gami da jan guntun tsaki ciki-ciki ba tare da ta ce uffan ba. Raihana wacce ta gama jin dukkan munanan maganganunsu  ta tako tsakiyar dakin sosai ta cigaba da magana. "Har da ni kenan! Wannan ba Ummita ko Humaira kaɗai ku ka tsana ba Anna, har mu jinin Abba. Na yi mamaki dama da Anti ba ki ɗau mataki akan abin da Humaira ta yi maki a kwanakin baya ba, ashe dama ke tarkon da kika ɗana babba ne? Ashe wannan damar kike jira? Kai duniya! Mutum ya ƙi mutum har ta kai yana mishi fatan mutuwa? Me suka tare maku? Ku ji tsoron ranar da haƙƙin su Humaira zai kama ku!" "Me kika ji ance da za ki rufe mutane da faɗa tamkar kina magana da Muhsin ko Waleed?" Jannat ta furta a ƙoƙarinta na shanye firgicin da ta ɗan shiga, toh koda ace ba su da hannu a satar Humaira da Ummita, ai wannan ɓarin zancen da suke yi zai iya jawomusu matsala tunda ana kan bincike ko yau ɗin da safe sai da D.P.O ya zo wurin Abba. Raihana ta yi murmushin takaici. "Kar ku yi tsammanin ban ji mugun ƙullin da ku ke yiwa bayin Allahn nan ba. Amma ku sani, Allah na tare da bayinSa a duk inda suke kuma cikin kowane hali. Na rantse muku, duk iya yinku, duk iya ƙoƙarinku, ba za ku iya kawo sanadin koda karta a fatarsu ba balle a kai ga rasa rayukansu ba face sai da iznin Allahn da ya halicce su. Ku yi dukkan kokarinku, akwai ranar ƙin dillaci." Tana kaiwa nan ba ta ko ƙara kallonsu ba balle ta ji me zasu ce ta sa kai ta fice daga dakin a guje zuwa nasu ɗakin wanda suka mallaka da su Humaira a baya. Haka kawai sai ta buɗe sif din kayan Humairar da Ummita ta fiddo abin da ta san sun fi so cikin kayansu ta yi ta kuka. Lamarin da ya sanya Mami hana ta kwanan ɗakin sai dai nata ɗakin. Ba za ta iya misalta baƙin cikin da ta ke ciki ba sanadiyyar ɓatan ƴan uwannata. A gefe guda ga baƙin cikin kasancewar Jannat yar uwa ga Maminta ballantana a kai kan Tasleem da take ji kamar ta shaƙe ta. Sai ko Anna da har ba ta kaunar ganin fuskarta a kwanakin nan tun da ta nuna ba ta wani bakin ciki da ɓatan yan uwanta. *** Abba ya yiwa su Fadeel tarba na mutunci da dattako, gaba ɗaya idan ka ga Abba sai ya mugun ba ka tausayi sakamakon yadda ya koɗe ga kuma rama.   "Ka yi hakuri Fadeel, in sha Allah ƙiris ya rage na kammala haɗa kuɗaɗen fansar su, lafiya kalau za su dawo hannunmu. Kai dai ka ci gaba da addu'a." Fadeel ya ƙara yin ƙasa da kai, Abban da ya ke da burin ya wayi gari ya gan shi a gabansa da zummar neman auren Humaira, su yi hira da dariya tsakaninsu sai gashinan ganin da suka yiwa juna na farko ba mai daɗi ba ne ko kaɗan.  Zuciyarsa ta yi rauni nan da nan kuma ya ji idanunsa sun kawo ruwa daƙyar ya iya daurewa ya amsa. "Toh Abba, Allah ya kuɓutar da su." Abban ya amsa da amin, yana son ya ce idan da yadda zai tallafa, a ba shi dama amma ba ya so Abban ya ga kamar ya mishi katsalandan wannan ne dalilin da ya sa shi jan bakinsa ya yi shiru. Sun ɗan jima anan har Abban ke faɗamusu cewa Kawun Humaira suna hanya daga Maine, Ƙasar Nijar. Suka yi musu fatan isowa lafiya a karshe dai Ibb ya soma yiwa Abban sallama kan zasu wuce ganin Fadeel kamar ma ba shi da niyyar motsawa. Bayan fitarsu Abba ya yi tagumi cike da tunani, a yanzu duka-duka dai abin da ya haɗa bai fi miliyan shida ba, ya kuma sani muddin ba gidansa da suke ciki zai siyar ba bayan motocin da ya sa kasuwa ya siyar, to fa babu ta inda zai samu cikon miliyan goma na fansar yaransa. Yana wannan halin ne Mami ta yi sallama ya amsa gami da ba ta damar shigowa. Ta shigo sanye da hijabinta ta zauna gefensa fuskarta dauke da damuwa ta ce. "Baƙi ka yi ne?" Ya numfasa. "Eh, yaron nan Fadeel ne ya zo da abokinsa, ba su jima da tafiya ba." Ta ɗan yi jim sai kuma ta numfasa ta ce.   "Allah Sarki." Daga haka ba ta ɗora komai ba, shiru ya biyo baya kafin Abba ya girgiza kai ya ce. "Maryam, an zo gaɓar da dole sai na siyar da gidannan na cika kuɗin fansar yarannan. Idan ya so sai mu koma wanda bai fi shi ba, lokaci na ƙurewa sosai, kaina ya ƙulle gaba ɗaya, dole na tashi na nemi mai siya ko kaɗan a kuɗin ne aka ba ni zai isa na cika na kaiwa wadannan mutanen." Murmushi Mami ta yi. "Kamar ka san shawarar da na zo na ba ka kenan Abban yara, sai kuma naji dadi da ka kasance mai yarda da ƙaddara. Siyar da gidan zai fiye mana alheri matuƙar dai za su bar yaranmu su dawo garemu." Abba ya jinjina kai. "Hakane Maryam, dama na riga da na yi magana da lauyana, na kuma bada damar an sa gidannan a kasuwa, ina ta tunanin ta yadda zan sanar maki kada ki ji abin daga sama shi..." "Haba Abban yara, wace irin magana kake yi ne? Mene ne ciki don ka sadaukar da abin da yake mallakinka don fansar yarana? Idan da ace yau nima na mallaki wata dukiya kana tunanin ba zan iya sadaukar da ita domin ceto ransu ba? Don Allah kada ka sa naji kamar kana bambanta Humaira da Ummita da yan uwansu." Tun faruwar al'amarin na su Humaira, Abba bai yi koda murmushi ba sai a yanzun, ya kamo hannun Mami ya riƙe gam cikin nashi. "Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka. Nagode da kika fahimce ni." Itama murmushinta ta faɗaɗa gami da shafar gefen fuskarsa. "Nima ina kaunarka. Yanzu ajiye godiyarnan, ka daure ka sa abu a cikinka sai a je a san ya za'a yi. Ina fatan dai ba ka faɗawa  D.P.O yadda ku ka yi ba ko?" Abba har ya buɗe baki zai magana sai ya tuna yadda suka yi da D.P.O da safe. Sun tattauna ya sanar da shi komai bai rufe ba akan batun kuɗaɗen fansa da aka nema. *_Koda wasa Yallaɓai kar ka nunawa kowa ka faɗamin yadda ake ciki. Komai kusancinka da mutum, ka ɓoye wannan tattaunawarmu saboda mutane su na da ban tsoro, koda ace ka faɗawa wanda ka yarda da shi yadda muka yi, to fa zai iya sanar da wani maƙiyin. Kaf duniya tun da dai daga ni sai Alhaji Bashir (Daddy) muka san da hakan, to ya tsaya iyakar nan, koda ace sun ƙara kiranka a waya kar ka bari wani cikin iyalinka ko ma waje ya sani.  Mu kuma zamu yi iyakar yin mu, mu yi kokari mu cafke su duk sadda ka tashi kai musu kuɗin._* "Ya naji ka yi shiru?" Mami ta nemi sani tana mai ƙuramasa idanu. Ya numfasa. "Babu komai Maryam. Ina tsoron na furta masa su ji labari tunda sun gargaɗe ni. Bana fatan a samu matsalar da yarannan za su rasa rayukansu." Ta jinjina kai. "Ina ji a jikina za su dawo gida cikin aminci." Daga haka ta jawo kayan abinci ta shiga zubamasa tana mai lallaɓa shi don ya ci. Dakyar ya tsakuri kaɗan ya miƙe ya yi shiri ya fita don ganin ya kammala kafin ya kai. Cikin rashin nasara, aka rasa mai siyan gidan Abba, a karshe dai tayin da ya ƙi karɓa a farko na iyayen Fadeel hakanan ya karɓi cikon miliyan huɗu ya haɗa aka tashi kuɗin fansa, babu abin da ya rage sai jiran waya daga kidnappers don a ji lokaci da kuma wurin da za a miƙa kuɗin. Mami ba ta san ya aka yi da batun gida ba, Abba dai ya ce mata an samu an haɗa kudade. Daga nan bai ƙara ko harafin A ba. *** Humaira da Ummita na rakuɓe a lungu guda na ɗakin sun yi shiru don zuwa lokacin kukan ma ya ƙi fita, aka banko ƙofar ɗakin aka shigo. Su ukun dai da suka zame musu tamkar baƙaƙen kumurci su ne suka shigo. Suka ƙura musu idanu tamkar za su lashe su, Wizzy kamar koyaushe sigari ne a hannunsa, ya fesar da hayaƙin ya dubi Babba da Badboy cikin murmushi ya ce.   "Ni zan fara, ku kuma sai ku biyo baya." Ba su ji dadin wannan hukuncin ba amma babu yadda suka iya, hakanan suka lashi lebbansu suka ja gefe. Shi kuwa kai tsaye ya ƙarasa ya finciko Ummita wacce ta ƙanƙame jiki guri guda ga jikinta dake masifar rawa. "Ina za ku kai ta? Ku yiwa girman Allah ku yi hakuri." Humaira ke zancen cikin ruɗu da tashin hankali. Suka kwashe da dariya. "Haba Baby, kema ai zan zo kanki. Duk inda zan kai ƴar uwarki kema za ki je. Kuɗin fansarku aka kawo, za a tafi da ku gida." Humaira sam zancen bai shige ta ba balle Ummita da ba ta san lokacin da ta shiga kuka sosai ba, su na jan ta tana tirjewa, Humaira na zabga uban ihu suka dauke ta da mari suka fidda kyalle suka rufemata baki da idanu. Wizzy haka ya ja Ummita har sai da ya dangana ta da wani ɗakin. Humaira da suka fita suka rufe kamar ta yi hauka haka ta dinga bugun ƙofar tana gurnani tamkar wacce ake  zarewa rai. Babban fatanta bai wuce su ceto Ummita da ko ihunta ba a ji ba sakamakon rufemata baki da aka yi da kyalle. Ummita na ji tana gani Wizzy ya keta alfarmarta. Tsananin azaba ya sanya ta sumewa ba tare da sanin inda kanta yake ba. Shi kuwa ya fito yana sharɓar gumi, ya dubi su Badboy cikin annashuwa ya ce. "Ku bari shegiyar ta farfaɗo sai ku ƙara farr mata, suman dadi ta yi." Suka kwashe da muguwar dariya. Yana kai wa nan ya shige wurin Humaira. Tana ji an bude ƙofar ta yi saurin karasawa gami da shaƙe wuyan rigar Wizzy tana um um saboda bakinta da ke ƙulle ta ma kasa magana. Ya yi dariya gami da tura ƙofar da ƙafarsa ta baya ya damƙe hannunta. "Haba my love? Kokawarnan da kike wani sanyamin ƙarfi ai sai ki jigatar da kanki tun ma ba a je ko'ina ba." Daga nan ya soma kiciniyar raba ta da kayanta yana taɓa wasu ɓangare na jikinta, nan da nan ta ji kanta ya soma wani irin sarawa, wani irin baƙin ciki da ba ta za ta iya kimantawa ba ya tsaya mata cak a ƙahon zuci. A sadda Wizzy ya yi nasarar keta rigar dake jikinta, a lokacin ne gaba ɗaya tsikokin jikinta suka mimmiƙe. Idanunta suka ƙara turuwa suka yi ja, ba ta san lokacin da ta shaƙo wuyansa ba har ya shiga kakarin mutuwa. Duk iya ƙarfin da ya sa da zummar ƙwatar kansa ya kasa, ga shi ba damar ihu saboda koda ya yi abokan aikinnasa za su yi zaton na lafiya ne. Haka suka ƙarasa har jikin ƙofar da ba ta rufe gaba ɗaya ba. Anan ne Badboy da ke zaune saitin ƙofar ya hangi hannun Wizzy na lilo, da wani irin gudu-gudu ya tunkari ƙofar, shima Babba ya mara mishi baya. Daƙyar suka tura ƙofar ta buɗe. Abin da suka gani ya yi mugun rikita su, Humaira dai ta zame musu tamkar wata ƙaƙƙarfar damisa, daƙyar da suɗin goshi suka ƙwace Wizzy a hannunta, Babba ya fice da shi daga dakin yayinda Badboy ya tunkareta da niyyar kifamata mari sai dai yanayin da ya ga ta taso ta yi kansa ne ya sa shi ficewa babu shiri. Nan ta kife zaune tana rirriƙe kanta dake azabar sarawa tana huci ga uban gumi kuma ga baki a ƙulle. Kukan nan da ta saba yi ta shiga rerawa mai mugun tsuma zuciya, ta fi rabin awa a haka har ba ta san an shigo da Ummita an watsa ta a kusa da ita ba.   Abin da Humaira ta aikata ne ya sanya Wizzy dakatar da su daga ketawa Ummita haddi, ya ce su kyale su kafin su kashe su labari ya sauya tunda gobe za su cafki kuɗadensu. Da wannan suka rufe su gam suka bar gidan su Babba da Badboy na ɗacin ran ganin samu da kuma rashi lokaci guda. Ganin haka Wizzy ya yi musu alƙawarin zai ba su sabuwar yarinyarsa da ya yi a wurin mashayarsu kowannensu ya more da ita, sun ɗan ji dadin hakan tunda ko ba komai ita bariki ke yayi a lokacin. Kowa kuma mararinta yake. Ummita da har lokacin ba ta da kuzari, kusan ma yanzun suman zaune ta yi. Ga uban azaba da ta ke ji a ƙasanta, gaba ɗaya hawayenta ya kafe ta ma kasa koda kukan, tun shigo da ita abu ɗaya ne a bakinta take furtawa sanadiyyar ƙyallen da aka ciremata, Innalillahi kawai take ambato daga farko har ƙarshe, wannan daren babu wanda ya runtsa sai Humaira da bayan gama koke-koken wani bacci marar dalili ya ɗauketa kamar yadda ta saba. *** A firgice Raihana ta farka daga mummunan mafarkin da ta yi wai an soka wuƙa a wuyan Ummita, Humaira kuma tana kwance cikin jini. Wani ƙara ta saki mai firgitarwa ta zabura ta miƙe daga gadon Mami ta nufi hanyar fita daga ɗakin. A hanyar ƙofa ta ci karo da Mami kasncewae asuba ta kawo kai, Abba ya fita masallaci. Cikin tsananin ruɗani Mami ta riƙe ta. "Meyafaru Raihana?" Ta ruƙunƙume Mamin sai kawai ta fashe da kuka mai tsanani. Mami ba ta ce mata komai ba ta shiga shafar kanta. Don kanta Raihanar ta sassauta kukan sannan ta ɗago kai ta ce. "Mami nayi mafarki marar daɗi akan su Humaira. Har yanzu ba su kira Abba a waya ba? Mami a kai kuɗaɗennan a dawomin da ƴan uwana yanzu kafin lokaci ya ƙure. Kar su kashemin su." Mami ta riƙe hannuwanta. "Kar ki damu da mafarkin da ba lallai ya kasance gaskiya ba. Ki yi addu'a da fatan alheri. Ina mai tabbatar maki babu abin da zai faru da su, lafiya kalau za su dawo gidannan ki gan su." Raihana ta ɗauki maganganun Mami kawai don ta kwantar mata da hankali ta faɗi, amma ina da ta ke da tabbacin ganin ƴan uwannata cikin kwanciyar hankali? Haka dai ta dinga lallaɓa ta ƙarshe ta samu nutsuwa ta fice ta ɗora alwala ta tayar da sallah amma har sannan kirjinta na dukan tara tara. Wannan dalilin ne ya sanya ta tsaya ta yi addu'a sosai har ta jawo Alƙur'ani ta karanta ta roƙarwa yan uwanta tsari daga sharrin dukkan masu sharri. *** Ƙarfe shida na safe daidai sai ga kiran Wizzy ya shigo wayar Abba.  Abba ya ɗaga jiki na rawa. Nan yake tambayar ko kuɗaden sun samu, ya amsa da eh. Daga nan ya yi mishi kwatancen inda za su haɗu, ya ƙara da faɗin. "Ina ƙara gargaɗinka, kar ka sake ka yi kuskuren zuwa da jami'an tsaro idan ba haka ba a gabanka zan yanka wuyan ƴaƴanka." Abba ya hau girgiza kai tamkar Wizzy na gabansa. "Aa aa, ni kadai zan zo. Ba zan saɓa alƙawarinku ba." Daga nan kit aka kashe wayar, ya ɗaga kai ya dubi lokaci, yanzun shida da mintuna, an kuma ce mishi bakwai daidai ya isa wannan dalilin ne ya sanya shi miƙewa ba shiri ya janyo jakar kuɗaɗen. Tunanin ya kira D.P.O ya sanar masa yake amma kuma yana jin tsoron kar su cutar da su Humaira sai dai ya ɗan yi shahada ya dannawa D.P.O kira, suna cikin magana Mami ta iso, Abba bai ko lura da ita ba don hankalinsa ya yi gaba. D.P.O ya ce za su fito su ma cikin kayan gida da kuma motar da ba ta aiki ba, ya kwantarwa da Abban hankali ya nunamasa kar ya damu su Humaira za su kuɓuta a hannun ko ma su waye. Mami ta dubi Abban a rikice bayan ya gama wayarsa. "Abban yara sun kiraka ne naji kana sanar da D.P.O?" Bai kalle ta ba ya ja akwatin jiki na tsuma ya ce. "Eh Maryama mun yi waya da su. Bari naje kar lokacin ya ƙure mintuna kawai suka ba ni." Mami ta sha gabansa. "Meyasa za ka yi ganganci da rayuwar yarana? Mene dalilin sanar da D.P.O? Ba ka tsoron su cutarmin da su?" Sai ta fashe da kuka jikinta babu inda ba ya rawa. Abba bai da lokacin rarrashinta sai kawai ya ce. "Kiyi hakuri, babu abin da zai faru da su lafiya kalau zan maidomaki su in sha Allahu. Ku sanya ni addu'a har na dawo dai." Yana kaiwa nan ya fice riƙe da muƙullin motar Jannat da Mamin ta aro masa tun jiya an kuma zuba mai dama jiran su kira kawai ake. Tasleem dake laɓe ta yi baya da sauri zuwa dakin Anna jikinta har tsuma yake. Abba yana hanya ma sai ga kiran Fadeel, Abban ya kwantar masa da hankali ya ce sun yi waya yanzun yana hanyar fita amsar su. Ya tambayi Abban inda suka ce, kamar ba zai faɗi ba sai dai ya faɗamasa. Fadeel ya ce zai biyo bayansa. Dakyar Abban ya hana shi gudun samun matsala. ***   Bakwai da mintuna uku Abba ya iso dab da kogin da suka yi masa umarni. Yana tsayuwa ya ji wayarsa na ringing. Jiki na rawa ya fiddo ya ɗaga. "Mun ganka, ka fito da jakar ka ajiye gefen wannan kogin, mu kuma za mu turomaka yaranka. Ba ruwanka da kalle-kalle, ka saukar da kanka ƙasa har ka ajiye ka bar wurin." "Toh." Yana faɗin haka a gaggauce ya ja jakar ya fita.  Bisa bin umarnin nasu kansa yana ƙasa amma fa ta ƴan maza kawai yake sai dai zuciyarsa na ta harbawa da ƙarfi. Sunayen Allah ya shiga ambato da fatan samun matsaya. Wizzy kuwa da suke can gefe ƙasan wata ƙatuwar bishiya, su na ganin fitar Abban ya sanya Badboy da Babba cicciɓar su Humaira da suka ba su kwayoyi suke ba a cikin hayyacinsu ba suka nufi motar Abban da nufin sanya su ciki. Kiran da Wizzy ya samj ne game da batun zuwan ƴan sanda wurin ya sanya shi fitowa gami da dakawa su Badboy tsawa. "Ku dawo da su mu bar nan! Shegen ya kira ƴan sanda!" Jin haka sai kuwa aka soma harbi, dayake Allah ba azzalumin bayinSa ba, sai kawai suka yashe su a wurin sakamakon harbin da aka yiwa Badboy a kafaɗa ya saki ƙara,  da gudu suka koma cikin motar kiii suka tayar suka soma yunkurin barin wajen. Abba da sai kawai maganganu ya ji da ƙarar harbi bai san sadda ya juya ba a ruɗe hantar cikinsa na kaɗawa don ya gama saddaƙarwa su Ummita aka harba. Sai dai ganinsu a yashe a tsakar filin ya sa shi sakin jakar kuɗin ya nufe su da gudun da a shekarunsa bai san ma zai iya ba. Su Wizzy tuni sun bar nan su na cizon yatsar wannan babbar asarar da suka yi. Yayinda D.P.O da mutanensa suka ƙaraso cikin jin zafin kubcewar da suka yi musu. "Yallaɓai ba kuka ya kamata ka yi, kamata ya yi mu miƙa su asibiti." Jin haka sai Abban ya ji kamar an masa tuni, ya ɗaga Humaira, macen ƴar sandar da ta biyo su ta ɗaga Ummita suka sanya su a mota sai asibiti. Jakar kuɗaɗen kuma yana cikin motar ƴan sandan suka mara musu baya. Fadeel da ya kasa haƙuri ya biyo bayan Abban, kafin ya kai ga ƙarasawa ya hango Abba a mota kawai sai ya yi reverse ya bi bayansu jikinsa babu inda ba ya kaɗawa. Yana son ya kira Abban don jin ko an same su amma yana tsoron jin akasin haka daga gareshi wannan ne ya hana shi kiran gaba ɗaya. Murja ta jima tsaye jikin tagar falo tana hangen fitar Fadeel a gigice. Ranta idan ya yi dubu toh ya ɓaci. Hankalinta kuwa idan akwai abin da ya fi gaban tashi toh ta ya yi wannan dalilin ne ya sanya ta komawa cikin daki da sauri-sauri ta ɗauko gyalenta sai ko waya da jaka ta fice daga gidan a birkice har Anti Amarya wacce ta fito daga nata ɗakin tana tambayar ko lafiya kuma ina za ta je amma babu amsa. *** Kasancewar tare suka isa asibitin da ƴan sanda wannan ya sa a gaggauce aka karɓi Humaira da Ummita zuwa emergency. Abba ya kasa zaune balle tsaye, ban da hawaye babu abin da ke fita daga idanunsa, ga jiri na kwasarsa yana ta ambaton sunan Allah kamar zai ciri baki. Daidai lokacin Fadeel ya shigo a birkice ya ƙarasa ga Abba. "Abba sun fito? Su na ina? Me ya same su?" Dukkan waɗannan tambayoyin ba a hayyaci yake yin su ba. Abban ma da ba a wani nutse yake ba sai ya kasa tanka mishi kawai sai ajiyar zuciya da kallo ga lebban na motsi amman ko harafi guda ya kasa fitarwa sai D.P.O ne ya karɓi zancen ya yiwa Fadeel bayani. "Ka kwantar da hankalinka, in sha Allahu babu abin da zai faru garesu. Likitan ya tabbatar mana ga dukkan alamu kwayoyi aka ɗura musu amman in sha Allah za su yi iyakar ƙoƙari a kansu." Fadeel ya dafe kansa ya yi juyin, ya yi safar ya dawo ya kai marwar amma wannan kalmar ta ya kwantar da hankalinsa ya kasa samun matsaguni a zuciyarsa. Kwayoyi? Ya ma rasa inda zai jefa zancen a kwakwalwarsa ballanta ya samu ya yi aiki da shawarar D.P.O Salahuddeen.  *** A can gida kuwa, Tasleem tun sadda ta kai labarin tafiyar Abba fanso su Humaira, Jannat ta dauki waya hankali tashe ta kira Bokanta. Kaca-kaca suka yi sosai tana zaginsa akan ita fa ba su yi haka ba. Wannan ya sa  Boka tun a wayar ya ci alwashin sai ta girbi wannan tozarcin da ta yi masa. Kasancewar idanunta sun rufe ruf sai kawai ta ja mugun tsaki ta katse kiran. Awa bai fi ɗaya tsakani ba, sai ga wayar Abba zuwa ga Mami, a gaggauce ya sanar da ita kuɓutar su Ummita ya kara shaida mata cewar su na asibiti. Hankali a mugun tashe suka fice tare da Ƙasim da Raihana wacce lokaci guda wani mugun zazzaɓi ya rufe ta musamman jin cewar su na asibiti. Suka yi kiciɓus da Kawun Humaira da matarsa Hajjo wadanda isowarsu kenan garin. Ba su tsaya yi musu dogon bayani ba, Kawu ya bi su yayinda ya ce Hajjo ta tsaya ta jira dawowarsu a gida. ***   BAYAN AWANNI... Mummunan labarin da ya iske su Abba na keta alfarmar da aka yi ga Ummita ya sanya shi sumewa bai ko iya jin ƙarshen ba balle ya san ko har Humairar ma an taɓa. Nan aka kwashe shi shima don ba shi taimakon gaggawa. Raihana kuka kamar ranta zai fita yayinda Mami ke taya ta. Kawu da Fadeel kuwa tashin hankalin da suke ciki ba zai misaltu ba. A gabansu aka fiddo su bayan an yiwa Ummita ɗinki na mugun raunin da aka ji mata aka sauya musu ɗakunan zuwa na hutu, daki mai gado biyu. Fadeel ya ƙurawa Humaira idanu kamar kirjinsa zai fashe haka yake ji, nan take idanunsa suka kaɗa jawur. Gaba ɗaya ta lalace ta yi rama tamkar wata halittar ce ba ita ba sai ko hancinta da ya ƙara fitowa. Har aka shige da su bai iya kauda kansa ba. Shi ya yi ƙarfin halin biyan dukkan abin da aka kashe har da na kama ɗaki.   Cikin ƙanƙanin lokaci labarin kuftowar su Humaira ya cika gari, mutane da waɗanda suke dangi da ma yan uwa na gari suka dinga tururuwar zuwa yi wa su Abba barka, babu wanda aka bari shiga wajensu, hakanan labarin abin da ya afku gare su bai fita ba. Yan jarida kuwa suka dinga yaɗa rahoto, hakanan social media ta dauka.  Futuha mutanen Dubai ta ƙara yin bidiyo mai nuni da damuwa da kuma farin ciki tana shaida wa jama'a cewa an ga ƙannenta. Nan aka hau taya ta murna sosai. Mutanen Bichi da labari ya iske su su ma baa bar su a baya ba. Anti Maijidda ta yi kuka kamar ranta zai fita jin labarin keta haddin da aka yi ga Ummita, matsayinta na babbar yaya ga uwarta ya sa Abba sanar da ita a sirrance.   Sahabi kuwa baki har kunne, sun zo shi da abokansa yayinda mahaifinsa takanas ya zo ya taya Abba murna da addu'ar Allah ya kiyaye gaba.   Kwanakin su Humaira biyu suka dawo hayyacinsu. Ummita ce ta soma farfaɗowa, ranar Allah ya taƙaita Anti Maijidda na zaune tare da Baba Amina sun yi jugum su na dan hira jefi-jefi hannuwansu riƙe da casbaha. Wani gigitaccen ƙara Ummita ta saki da ya yi masifar tayar da hankulansu. "Wayyo Allahna! Kar ka kashe ni! Ka rabu da ni! Na haɗa ka da Allah ka rabu da ni!! Wayyo Allahna!!!" Cikin kuka da tashin hankali suka yi kanta su na riƙewa, aka bankaɗo ƙofar aka shigo, su Abba ne da  ihun Ummita ya iske su. Raihana a guje ta nufi wurin Nurses dake tahowa, kafin ta kai ga magana suka ce sun ji. An tafi kiran likitan. Su na shiga sai ga Likita, aka fitar da kowa a ɗakin. Gaba ɗaya matan kuka sosai babu kamar Raihana da take jin kamar ta shiɗe. A yadda take jin zuciyarta za ta iya fille kan wanda ya aikata wa yan uwarta wannan tozarcin. Koda likitan ya ƙarasa gareta flask din ruwan zafin dake ajiye a gefenta kawai ta ɗauka ta jefa masa. Ba don Allah ya sa shi kaucewa ba da babu abin da zai hana a same shi. Tana cikin wannan gigitar Humaira ta farka a matukar firgice, ta kira sunan Ummita da karfi sannan a guje ta diro ta zo ta rungumeta tana kallon jama'ar ɗakin kamar wasu sabbin halittun da ba ta taɓa gani ba. "Su waye ku? Me za ku yi mana?! Ku fice ku bar nan! Wallahi ku ka yi ƙoƙarin zuwa kusa da mu zan ji maku ciwo." Sai kuma ta juya a mugun firgice tana tattaɓa jikin Ummita dake kuka kamar ranta zai fita. "Ummita! Yi shiru, Abba zai zo. Naji suna cewa yana hanya. Yi shiru, sai mun kashe su." "Kin.." Likitan ya ƙaraso zai soma magana Humaira ta juya da azama tana nunashi da yatsa. A sannan su Abba gaba daya sun shigo sun kasa daurewa. "Kar ka taɓamin ƴar uwa! Zan kashe ka!!" "Humaira, Ummita." Humaira na ganin Abba ba ta ko damu da sauran jama'ar Abba ta karasa a guje ta rungume Abba tana kuka mai tsuma zuciya. "Abba za su kashe mu! Abba ka cece mu! Ka ɗauke mu mu bar nan!" Irin riƙon da ta yiwa Abban ba na wasa ba ne har maɓallan wuyar rigarsa sai da suka fita. Cikin hawaye ya ce. "Mamana babu abinda za su yi maku, likitoci ne. Kun kuɓuta daga hannun azzalumai. Ki kalla dakyau, ga Maminki ga yar uwarki Raihana. Kin gane Kawunki?" Ta tsaya cak kamar wata sokuwa tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya, Ummita kuwa da nos ta lallaɓa ta yi mata allura tuni bacci ya kwasheta. Kawai sai ta soma ruwan wasu sabbin hawayen ta ma kasa cewa uffan. Zuciyarta ta gasƙata eh sun kuɓuta daga hannun azzaluman, amma kuma ta ji tana tantama tana gani ko mafarki ne. Wannan ya sa Raihana tahowa da sauri ta rungumeta ta kara sautin kukanta. A hankali ta ɗaga hannunta ta ɗaga fuskar Raihana ta na kallo kamar wata baƙuwar halitta ce gabanta, sai kuma da rawar murya ta ce. "Raihana ce?" Raihana saboda ƙarfin kukan ma ta kasa magana sai kawai ta ɗagamata kai. Humaira ta rungumeta sosai suna kukan tare. "Amm, don Allah a ragu a ɗakinnan. Alhaji ina son magana da kai." Fadin Likita, ganin haka duk aka fice banda Raihana wacce Humaira ta riƙe hannunta gam tamkar ita kaɗai ta gani. *** Likita ya dubi Abba cikin nutsuwa ya soma magana. "Lamarin ita Ummita na buƙatar rarrashi da ja a jiki. Kaso casa'in na ire-irenta da hakan ke afkuwa a kansu sukan samu matsala ta rudani, firgici da kuma rashin yarda ga kowa. Wasu kuma yakan taɓa musu kwakwalwa. Zamu yi mata gwajin kwakwalwa don a tabbatar da komai na ta lafiya kalau yake." Abba ya share fuskarsa. "Toh Likita, nidai babban burina lafiyarsu. Allah ya sa komai lafiya." "Ameen." Ya amsa cikin tausayawa yana mai lallaɓar Abba. *** Cikin iko na Ubangiji an yiwa Ummita gwajin kwakwalwa kuma an tabbatar da komai lafiya. Wannan ya kwantar da hankulansu. Humaira dai ba ta dogon magana tun farkawarta, kowa ta gani sai dai ta ambaci sunansa, idan an rungumeta an sa kuka itama ta soma. Da daddare ba bacci sai razana, ga Ummita haka. Wannan yasa aka raba musu ɗaki. Fadeel na zuwa, kuma abin mamaki Humaira na ganinsa ta kira sunansa, abin sosai ya ji dadinsa ya kuma tsaya a ransa. Sai da suka kwashe sati biyu a asibiti kafin su tattara su dawo gida. Babu laifi sosai zuwa lokacin sun samu nutsuwa ba kamar farko ba. Sai dai daga Ummitan har Humaira duk sadda tunanin cin zarafin da aka yi musu da kuma keta haddin da aka yiwa Ummitan sai su yi ta kuka. Har zuwa lokacin babu wanda ya san da mummunan labarin sai ko Anti Maijidda da Mami wadanda Abban ya faɗawa. Anti Maijidda nan fa ta dage akan lallai sai a ba ta Ummita su tafi Bichi, Abba ya ƙi amincewa. A dole ta haƙura ta tafi tana ƙunar rai da jin tsanar Mami har cikin ƙoƙon ranta. Jannat ko a fuska sai ka rantse nan jimamin duniya take yi akan lamarin don ba ta nuna komai wanda zai sa wanda bai sani ba ya fahimci takun saƙarta da su. Hakanan Anna wacce ta daurewa zuciyarta ta taka har ɗakinsu ta duba lafiyarsu bayan ta je asibitin a baya har sau uku. Wannan ya wanke ta daga zargin mutane da rashin nuna kauna ga su Humaira a baya. *** *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Sai da su Humaira suka samu sati hudu cif kafin su ɗan maido da jikinsu, da kuma walwala kaɗan. Sukan zauna cikin jama'a, a taɓa hira da su idan ka cire Ummita da har lokacin ta tuno aika-aikar da aka yi mata sai kawai ta fashe da kuka wanda hakan ke tayarwa Humaira hankali itama ta sa nata kukan sai su haɗu su yi ta yi. Kawun Humaira ya so su koma can Nijar da ita amma nan ma Abba ya nuna sam bai amince ba dole haka ya tattara matarsa suka koma gida.   Su na zaune a ɗaki, Ummita riƙe da Alƙur'ani tana karantawa zuciyarta na yin sanyi yayinda Humaira ke kwance saman katifa ta yi shiru gami da zubamata idanu kusan ma hankalinta ba a kanta yake ba, ta lula wata duniya ta daban na tunani. Raihana ta shigo ta iske su haka, dawowarta kenan daga makarantar boko wanda har lokacin Ummita ta ƙi amincewa ta koma ganin haka babu wanda ya takura mata shi ma mai makarantarsu da ya zo har gida ya jajanta ya ce a kyale ta zuwa wani lokacin. "Wash! Wallahi na gaji! Ke kuma kina da baƙo a falon Abba." Ta faɗi da murmushi tana duban Humaira duk a ƙokarinta na son ta ga komai ya dawo daidai a mu'amalarsu. Humaira ta ɗan dube ta gami da ɗan haɗe gira kaɗan. "Wa kenan?" "Fadeel." Ta yi shiru, ita ba ta ce uffan ba balle ta yi wani yunƙurin kawai sai ta maida kai ta kwanta ta yi shiru. A karan kanta ba za ta ce ga abin da take ji game da Fadeel din ba, lamarin dai ba yabo balle kuma fallasa. Ummita na ji ba ta iya cewa komai ba, Raihanar ma ba ta sake magana ba sai ta miƙe ta rage kayan jikinta ta shiga wanka, ba ta son duk abin da zai takurawa rayuwar ƴan uwannata da ta ƙara sanin girman ƙauna da shaƙuwar da ke tsakaninta da su bayan sun yi mata nisan da ta zaci har abada ba za ta ƙara sanya su cikin kwayar idanunta ba.   Ummita tana kai wa ƙarshen surar da take karantawa ta juya ta dubi Humaira.    "Ki je ku gaisa mana." Humaira ta yi mamakin jin wannan furucin naga bakin Ummita, tun bayan dawowarsu ba ta wani magana kwakkwara, ko hirar Raihana ke jansu da shi, sai dai ta basar ta yi shiru. Wannan murmushin da ba ya barin fuskar Ummita, babu shi babu labarinsa tun dawowarsu. Ita ɗinma ƙarfin hali take yi don faranta ran Mami da su Raihana ga kuma Ƙasim waɗanda gaba ɗaya suke nuna musu kulawa da ƙoƙarin ganin sun saki jikinsu. "Kin ji?" Maganar Ummitan ya ƙara katse mata  tunani. Tana so ta ja musu amma a yanzun duk duniya babu abin da ta ke so irin ta ga ƴar uwarta ta dawo tamkar yadda ta ke rayuwa a baya. Abu na  biyu kuma ta sani ba ta jin za ta iya ɗaukar waya ta kira shi da zummar godiya bisa hidimar da ya yi akan fitowarsu, don ko cikon da suka bayar na kuɓutar da su a hannun ƴan fansa ƙin karɓa suka yi da Abban ya maida musu, ta sani wannan ita ce damar ta amma hakanan ba ta son Fadeel din ya cigaba da shigemata shiyasa. Abban har gidansu ya je ya ƙara godiya sosai shi da Mami wacce a sannan ne ta ga gidan da ya kere na Aminiyarta Hajiya Lubna. Ganin Ummitan ta zubamata idanu ya sanya ta miƙewa. "Toh, na ji Ummita." Ta faɗi kamar ta fashe da kuka sai ta miƙe ta ɗora hijabi akan doguwar rigar atamfar da ke jikinta. Suka ci karo da Mami a falon wannan ya sanya ta tsayawa. Gidan yanzu duk an watse sai su kadai, Jannat ta tattara ta koma bayan dogon kiran da mijin ya dinga danno mata har abin ya kusan zame musu rikici sannan ta tafi ba don ta so ba. Tasleem kuwa tun fitowarsu da kwana biyu Hamza ya zo suka koma gida.     Cikin sakin fuska Mami ta dubi Humaira. "Ina zuwa haka?" Ta sunkuyar da kai sannan ta ce. "Wai Fadeel ne ya zo za mu gaisa." Nan da nan fara'ar dake saman fuskar Mamin ya ragu. "Zuwan me yake ta yi haka ne alhalin jinyar ta ƙare? Ina ce na muku iyaka da shi tun a baya?" Humaira ta jinjina kai. "Hakane Mami, kiyi hakuri. Ai gaisawa kawai zamu yi. Ya yi abin da ko maƙiyina ne ya cancanci na ƙara yi mishi godiya." Mami ba ƙaramin mamakin furucin Humairar ta yi ba wanda daidai da fuskarta ta nuna. Sai kuma ta jinjina kai. "Shikenan, ki je amma kar ki ɗau lokaci." Murmushi kaɗan Humaira ta yi sannan ta amsa da toh ta cigaba da tafiya. Ban da abin Mami, ita ba ta tunanin ma za ta yi auren, wane namijin ne zai aure ta bayan ta gama wulaƙanta duk masu kaunarta domin Allahn? Ta rasa dalilin da a ƴan kwanakin nan take jin sauyi a jiki da kuma kwakwalwarta. Wannan ne ya sa Fadeel samun rangwame daga wurinta. Ɓangaren Mami kuwa ji ta yi kirjinta ya yi wani irin bugu. Meke shirin faruwa haka? A duniya ba ta kaunar Fadeel ya raɓi Humaira kamar yanda bai raɓi Tasleem ba. Kai ba ma shi ba... Sai kuma tunaninta ya katse, ta haɗiyi miyau da ta ji yana mata zafi. Sai kawai ta nufi ɗakinta a gaggauce. Tabbas ta yi sake a kwanakin da suka shuɗe ba ta bayar an ɗoramata sabon aiki ba.  Wayarta ta fiddo ta shiga zarya a tsakar ɗakin tana jira a ɗauka daga ɗaya ɓangaren. Doguwar magana suka yi sai kuma ta hau murmushi hankali a kwance ta katse kiran ta shiga danna wayar karo na biyu inda ta tura kuɗi ga wani akawun lamba. Daga nan kuma ta ji wata irin nutsuwa ya saukar mata. ***   Ya kwashi mintoci  masu yawa a zaune anan, shigowar su Waleed ne ma ya ɗauki hankalinsa suke hirar makaranta yana biyemusu. Ya gama fidda rai daga ganinta, gefe guda ga tsoron kada a koma ƴar gidan jiya, tunanin da ya sanya gumi tsastsafo masa a goshi duk kuwa da iskar dake kaɗawa a falon har tana kaɗa labule. Sai dai kuma ba zato ya tsinci sallamarta, cikin sauri ya kalli hanyar yana mai amsawa da rawar murya.    'Please Fadeel, Control.' Zuciyarsa ta ba shi shawara, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya. Ya zubamata idanu, ta  fara dawowa ainahin Humairarsa, fuskar ta ɗan ciko ba kamar farkon dawowarsu ba. Hakanan ta yi haske fayau dama can a bayan har da rashin samun wanka ga uban cizon sauron da tabonsa ya yi ja a jiki da fuskarta.   Ita kuwa kanta a ƙasa ta ƙarasa ta zauna ɗan nesa da shi, tana ji ya kaɗa su Waleed ciki akan su je su cire uniform dinsu. "Barka da rana." Ya yi furucin yana dubanta tamkar ya haɗiye ta. Sai a sannn ta ɗan ɗaga kai ta dube shi. Ganin yanda ya zubamata idanunsa ya sanya ta maida kanta ƙasa ta na jin wani yaam a jikin da ba ta saba ba a baya. "Ina wuni, ya wajen su Baba?" Fadeel da ke jin kamar an tsoma shi a aljanna ya faɗaɗa murmushin fuskarsa yana hamdala a ƙasan ransa. Dama komai ɗan hakuri ne, idan ka yi to fa zai wuce. Ya shanye wulakancin da zagin, yanzu ga shi nan ya soma cin galaba. "Kowa lafiya kalau Alhamdulillah, Sisterna ma ta zo daga Adamawa. In sha Allah zuwa gobe za ta zo ku gaisa." Sai ba ta watsa masa ƙasa a ido ba ta amsa da toh. Shiru ya biyo baya, a ɓangaren Fadeel ba ya so ya faɗi abin da bai yi daidai da ra'ayinta ba ta sauya fuska ta miƙe ta bar shi anan, ita kuwa godiya take son yi mishi don su yi sallama ta koma ciki amma ta rasa ma ta inda za ta fara sai can da ta ga ba shi da niyyar ce mata uffan sai aikin kallon da ba za ta ce yana ba ta haushi ko kuma faranta mata ba a lokacin, ta daure ta soma magana. "Mun gode bisa dukkan ɗawainiyar da ku ka yi mana, Allah ya ƙara arziki." "Ban yi abin da za ki godemin ba. Ke kika yi wanda zan godemaki. Nagode sosai and I..." Sai kuma ya yi saurin haɗiye zancensa, ya san komai na tarihin Humaira a sannan daga bakin Raihana, ya san ba ta jin turanci amma kuma dai kalmar I Love You ko yaro ƙarami da bai je makaranta ba ya sani. Shirun da ya yi ganin zai yi taɓargaza ne, gaba ɗaya ji yake da ace Humaira za ta ba shi dama, zancen aurensu kawai za a yi. Ya sani hatta da Abbanta ya buƙaci a ba shi lokaci kaɗan yaransa su dawo cikin nutsuwa sai a haɗa auren Ummita da na su, shi ne a karon kansa ya roƙi alfarma a kyale Humaira ta amince da batun aurensa da kanta. Yana kuma ji a jikinsa hakan ce za ta kasance daga yanayin sauyin da ya gani tattare da ita. "Shikenan?" Ta katse mishi tunani, ya ɗan lumshe idanu sannan ya buɗe su a cikin nata, ta kauda fuska ta yi shiru. "Toh, zan koma bakin aiki, dama zuwa nayi na duba lafiyarku. Ki gaishemin da Ummita da mutan gidan. Allah ya ƙara lafiya." Ta amsa da amin, cikin sanyin muryar ta ce. "Zan fadamusu. Nima ka gaidamin ƴar uwarmu, sai ta zo goben in sha Allahu." Ambaton ƙanwarsa Hannatu da ƴar uwarmu da ta yi ya sanya shi jin tamkar yana tafiya a iska tsabar mamaki da farin ciki. Ya ji dadin wannan lamarin sosai. "Nagode." Hakan ya furta kawai sannan suka miƙe kusan lokaci guda, sai da ya ga shigewarta sannan shima ya juya yana murmushin da har haƙoransa suka bayyana, ga duk wanda ya ga fuskarsa ya san yana cikin farin ciki da annashuwa. *** Washegari Mami ta tashi da aikin girki na tarbar Futuha wacce ta yi waya ta sanarmata dawowarsu a ranar. Daga Dubai sai da suka je Saudia suka yi Umarah kafin su juyo. Humaira ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wajen shiga kicin ɗin din taimaka mata da aiki, zaman kaɗaicin babu abin da yake jefa ta ciki sai kogin tunani. Ummita ma ta fito falo kasancewar akwai wuta ta kunna tashar Saudia tana kallo. Gaba ɗaya samarin gidan sun dawo, Mubarak da ya kammala shima yana gida hakanan Yassar da Dawud wadanda sun fi sati da dawowa daga Camp suna nan tare da su. Anan Kano aka yi posting ɗinsu inda zasu yi service. Daga Humairar har Ummita ba su ƙara samun matsala da su Yassar ba, musamman Humaira wacce a baya suke ƙi sosai, ita hakan ma har mamaki yake ba ta. Tsakaninsu gaisuwar mutunci, wasu lokutan har su ɗan tsoma ta a ciki idan suna ƴar hira. Har a lokacin ba ta saki jikinta da su ba don ba ta saba da hakan ba. Suna girkin Ladidi na taya ta murnar yanda ta soma sakin jikinta tamkar a baya. Raihana ta shigo kicin din kamar an jefo ta har Mami na mata faɗa. "Ku yi hakuri. Humaira, Yaya Fadeel ya kira Sister dinsa Hannatu tana hanyar zuwa." Gaba ɗaya ta manta da wani batun zuwansu, Mami kuwa haɗe rai ta yi ba ta ce uffan ba har sai da Raihana ta ƙara magana. "Ki je ki ɗan sauya kaya don Allah. Kar ta ganki da Tshirt." Ladidi ta yi dariya Humaira kuwa ta maka mata harara ta rasa dalilin kuma da aka yi ta ɗan dawo da jin haushi-haushin Fadeel, sai lokacin kuma Mami ta yi magana. "Toh uwarta, ke kuma Humaira meyasa ba ki faɗamin kina da baƙuwa yau ba?" Cikin sanyin murya da kuma rashin jin dadin ɓatawa Mamin rai da ta yi ta ce. "Kiyi hakuri Mami, gaba daya na manta ma ya faɗamin." Mami ta sauke ajiyar zuciya, ta sauya yanayinta na farko sannan a sanyaye ta ce. "Ai shikenan, ba don girkin da ake na Futuha ba da sai dai ta zo ba a yi nata tanadin komai ba kenan. Ladidi ƙaro shinkafar nan kafin ki wanke." Ladidi dake shirin wanke ɗanyar shinkafa ta zuba a ruwa ta amsa da toh, sai da ta ƙara ruwan tukunyar sannan ta ƙara awon shinkafar da ajiye. Raihana dai ta tsaya jiran Humaira ta dage lallai sai ta sauya shigar jikinta. Mami ba ta sa musu baki ko kadan ba, Humaira har haushin Raihanar ta dinga ji saboda irin wannan nacin ba ta ko fuskantar yanayin fuskar Mamin. "Ki rabu da ni don Allah." Faɗin Humaira cikin haɗe gira. Sai lokacin Mami ta sa baki ta hanyar bin Humaira da murmushi. "Aa Humaira, da gaskiyarta. Maza je ki sauya suturar jikinki. Bai kyautu baƙuwarki ta ganki a hakan ba. Jeki." Ganin yanayin Mamin har a sannan ba ta gamsu ba, amma ta bi umarninta suka fice da Raihana zuwa nasu ɗakin. Ta iske Raihanar ta fiddo mata wata atamfarta purple mai ratsin fara da baƙi, ta kalle ta. Raihana ta murmusa. "Ya aka yi? Da magana ne? Ko na sauyamaki kayan?" Guntun tsaki Humaira ta ja. "Ke dai yadda kika damu da wannan Fadeel din da ma ke kika aure shi." Raihana ta ji ba dadi jikinta kuma ya yi sanyi, tana tunanin Humaira ta fara sauyawa daga lamarin nata da na Fadeel sai ta ga abin ba haka ba. "Allah ya huci zuciyarki tawan." Ta fadi tana riƙo hannun Humaira, sai itama ta ji ba dadi. "Shikenan. Bari na watsa ruwa na sauya ko don ke." Sosai Raihana ta ji dadin kalamanta. Ta yi dariya. "Toh." Daga haka ta fice ta bar Humairar da shiga bandaki. *** Murja tana zaune gaban motar ta hakimce yayinda Hannatu da yarinyarta mai shekaru uku da ta ci suna Husna suke a baya zaune. Tun da Murjar ta ji inda Hannatun ta nufa ta kafe akan sai ta bi ta, a farko Hannatu ba ta so ba don tana da labarin irin son da Murjar ke yiwa Fadeel daga bakin Kausar. Shi Fadeel dayake bai ɗauki maganar da muhimmanci ba ya sa bai ce mata komai a kai ba. A karshe dai ganin yadda Anti Amarya ta nuna ta yi na'am Murja ta raka su ya sa itama ɓoye nata rashin yardar suka tafi tare ba da sanin Fadeel ba. Karfe biyar na yamma suka shiga gidan. Raihana ta tare su da fara'arta zuwa ciki. Murja sai raba idanu ta ke ta ga inda Humaira za ta ɓullo kuma ta ga yanda ta sauya. Ummita itama ta fito suka gaisa da su, nan suka jajanta musu da addu'ar Allah ya kiyaye gaba. Ba ta amsa ba sai ta mike sakamakon idanunta da suka cicciko da kwalla ta nufi daki. A duniyarta yanzu babu abin da ta tsani ta tuna kamar abin da ta faru gareta a hannun Kidnappers. Gani take duk ranar da aka ɗaura mata aure da Sahabi babu abin da zai hana shi gano komai, Abba ya yi niyyar sanar da shi amma Mami ta nuna kar ya yi hakan. Ita kuma a karan kanta ta rasa ta ina za ta fara gayamishi. Ga wata sabuwar kauna da yake nunamata tun bayan fitowarsu duk domin ya kwantar mata da hankali. Ganin da ta yi Humaira na ɗakin, ta yi saurin share fuskarta ta dubeta fuskar a ɗan sake duk da ba kamar can baya da take Ummitarta ba. "Sun ƙaraso su na falo. Ki je ku gaisa, mace mai kirki da ita." Taɓe baki Humaira ta yi. "Toh." Shi ne abin da ta iya cewa, daga haka ta sa kai ta fice. Bayan fitarta Ummita ta tura kai a filo ta yi kuka mai isarta tana mai tausayawa kanta. Wannan baƙin ciki na keta alfarmarta da aka yi ta kasa gogeshi daga kirjinta, ta dai san an gogamata baƙin fentin da har abada ba za ta iya gogewa ba. Amsar da ta kasa ba wa kanta har yau shi ne, wane ne wanda ya sa a yi kidnapping dinsu. *_Ba don kar asirinmu da na Boss ɗinmu ya tonu ba, da sai na nemi aurenki na killaceki saboda kin haɗu ƙarshe._* Ta tuna wannan ƙazamin zancen da ya fito daga bakin Wizzy a sadda yake kam ganiyar raba ta da mutuncinta. Kenan dai akwai wanda ya sanya su wannan aika-aikar. Waye shi? Kuma a ina yake? Allah ne kaɗai masani. A karshe dai ta yakice wannan tunanin ta mike ta shiga bandaki. *** Hannatu ta dubi Humaira har ta ƙaraso ta zauna tana mata ɗan murmushi. Murja kuwa kallon Humaira kawai take yi cikin tafarfasar zuciya tana mai kuma cin alwashin ganin bayanta. Babu wani abu da ya sauya daga kyawunta wannan ne ya ƙara wa Murja baƙinciki a ƙasan rai. Ta kauda fuska tana amsa gaisuwar da Humaira ke yi mata a yatsine. Ita kuwa Humaira mamaki take na dama Murjar ta san Fadeel amma sai ta bar wa cikinta ba ta tambaya ba. Hannatu ta saki jikinta ta yi ta jan Humaira da hira, kasancewar da Raihana a falon ta samu ƴar tayi, tun dai Humaira ba ta saki jiki ba har sai gatanan ta soma murmusawa haƙoranta na bayyana. Raihana ta kawomusu abin motsa baki da kuma abinci. Husna ta maƙalewa Humaira tana mata hira iri iri na yara. Itama ta dinga biyemata. Can dai Murja ta kasa jurewa ko Mami ba ta tsaya sun gaisa ba ta amsa wayar ƙarya sannan ta dubi Hannatu. "Ni zan wuce sai kun taho. Ƙawata ce ta zo." Suka dube ta har Raihana da ta fahimci sauyin fuskar Murjar da irin harare-hararen da take wurgawa Humaira jifa-jifa. "Shikenan, sai mun taho." Ranta ya ƙara ɓaci, wato dama so take ta tafi ɗin don haka ta dauki jakarta ko sallama ba ta tsaya yi da su ba ta fice a fusace. Ba jimawa kuwa da fitarta Mami ta fito cikin shirin fita. Daga ganin yanayinta sauri take kuma fuskarta ya nuna rashin nutsuwa. Hannatu ta gaida ta, ta amsa da ɗan sauri. Ganin haka Raihana da Humaira suka tarbi Mamin da neman ba'asi. Guntun tsaki ta ja fuskarta dauke da tsantsar damuwa. "Wajen Tasleem zan je, sun yi dambe da wannan Fauziyar shi ne fa jini ya ɓalle mata amma sun wuce asibiti." Hankalinsu su din ma ya tashi. Suka nuna za su bi ta amma fir ta ce aa su zauna da baƙuwarsu sannan ga Futuha dake hanyar zuwa kada a bar gidan babu ƴan tarbarta. Dole suka jajanta suka dawo ga Hannatu aka cigaba da hira. Ba ita ta bar gidan ba sai bayan Magriba. Ta kuwa ajiyewa Humaira leda babba ta kayan kwalam sai ko turarukan da ta yo mata tsarabarsu. Firr Humaira ta ƙi karɓa sai daƙyar sannan ta yi godiya. Lokacin itama Ummita ta fito falon, tare suka yi mata rakiya har gaban motar da suka zo cikinta. *** Karfe takwas da mintoci sai ga Futuha a gidan, tun yamma ta sauka a garin tana gidanta, Ƙasim ne ya kai musu girke-girken da aka yi musu. Ta shigo gidan gaba ɗaya jikinta a mugun sanyaye. Matasan samarin duka suna falo aka tarbe ta da murna, su Humaira su din ma duka ana zaune ana kallon film din Krissh da ake haskawa a mbcbollywood. Ganin yanayin yadda take amsa musu hirar ya sanya Yassar dibanta dakyau. "Are you okay?" Ta yi murmushin yaƙe kai ka ce ba Futuhar nan ba ce mai ɗora hotuna iri-iri da murnar zuwa Dubai a tiktok. "Yes. Mamin ba ta dawo ba?" "Ta dawo tana ɗaki." Faɗin Raihana. Ta kuwa nufi ɗakin, ban da gaisuwar su Humaira babu wani jimamin da ta yi musu na abin da ya faru. Ƙamshin turarenta da ya cika falon ne ya sanya Ummita jin kanta na juyawa, ta ji tamkar hanjin cikinta ke kaɗawa. Da sauri ta mike ta yi dakinsu, kafin ta ƙarasa shigewa banɗakin wani amai ya tahomata wanda sai da ta amayar da duk abincin da ta ci a ranar. Humaira da Raihana wadanda suka biyo bayanta ganin irin miƙewar da ta yi ta bar falon suka tsaya cak cike da fargaba mai tsanani su ke bin ta da kallo. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Raihana ta karasa cikin sauri bayan fitowar Ummita daga banɗakin ta riƙe ta.    "Lafiya? Meke damunki?" Ummita ta yamutsa fuska kaɗan. "Ban sani ba, kawai dai na ji zuciyata tana tashi." "Allah ya sauwaƙe, ki ɗan kwanta ko za ki ji dadin jikin." Fadin Humaira cikin dauriya da ƙaryata zuciyarta har da jan istigfari bisa saƙe-saƙen da ta jefa mata. Ummita kuwa ɗan murmushi ta yi. "Kar ku damu, kalau nake. Naga duk kun yi wani sukuku da ku." Cikin kokarin basarwa Raihana ta zauna gami da jan guntun tsaki. "Ai dole, ga Tasleem can kwance asibiti dakyar aka tsaida jinin. Wai kawai saboda ta kama Fauziyya na waya da tsohuwar budurwar Yaya Hamza kuma ƴar uwarta tana ba ta labarin rayuwar ita Tasleem din da Yaya Hamza shikenan fa daga cacar baki sai cibi ya zama ƙari. Nima Mami naji tana ba Anna labari. Yanzu dai Maman Hamza ta ƙi zuwa ko duba Tasleem ta ce wai kashe mata ɗiya ta so yi." Humaira ba ta ce uffan ba, domin tun dawowarsu ta ƙara jin Tasleem ta fice a ranta, ta kuma ƙudurta ban da dai gaisuwa ta musulunci to fa babu abin da zai sa ta cigaba da tura kai ba kwarjini wurin waɗanda ba za su taɓa kaunarsu ba. Ko kaɗan Tasleem ba ta wani nuna farin cikin dawowarsu ba, ita kuwa me zai sa ta cigaba da shiga sabgar wacce ba ta yin ta? "Allah Sarki, Allah ya kawomata da sauki." Cewar Ummita sannan itama ta ja bakinta ta yi shiru. *** Yanayin da Futuha ta shigar wa Mami ne ya sanya ta ɗago kai daga wayar da take amsawa har da hawayenta. Cikin wani sauri ta sallame wayar ta miƙe, Futuha ba ta kawo komai ba ta ƙarasa da sauri ta rungumeta ta fashe da wani irin kuka mai tsuma zuciya. Mami wacce ta ji kirjinta ya yi wani irin bugu da ƙarfi ta ɗago kai da azama ta kalle ta har hannuwanta a rawa. "Ke mene ne ya faru ne? Ina Yakubun?" Gaba ɗaya ta ruɗar da cikin Mami wanda ta ji har wata ƴar ƙara ma yake yi. "Mami ƙarya yake yimin, ashe matarsa tana gidansa cikin wata irin ƙasƙantacciyar rayuwa?" "Toh ina ruwanki da ita! Ke ba kanki kika sani ba?!" Yadda Mamin ta yi furucin a zafafe ya sa Futuha shiru tana kallonta da ɗan mamaki saman fuskarta, kamar dai ba Mamin da ta saba karo da ita ba. Sai kuma ta tuno labarin ƴanmatancin Mamin da Anna ta ba su, mace ce da a tarihin soyayyarta ba ta taɓa kallon mai mata balle ta ji zuciyarta za ta iya ɗaukar zaman kishi da ita ba, har tana jinjina mamakin zaman da ta amince suka yi da Fatima ta kuma ƙaunace ta. A baya dai Mami ba ta san kowa da komai ba sai kanta da kuma nata. Wannan tunanin da Futuha ta yi ne na tsohon tarihin Mamin ya sanya ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda kuma mamakinta na farko ya gogu tas daga kwanyarta. "Nifa ba wannan ƙaryar ce ta tada hankalina ba, tun kafin mu dawo likita ya bayyanamin ina da ciki bayan ƴar rashin lafiya. Na bar abin na ɓoye ban sanar mishi ba akan zan ba shi labari mai dadi, sai yau da muka dawo ne nake sanar da shi toh kawai sai ya sauya fuska. Ya kuma rantsemin shi bai aure ni don na haifarmasa, daga uwargidansa kawai yake da kwaɗayin samun yara. To fa shi ne da faɗa ya kaure tsakaninmu, ya ce na zubar ni kuma na ce ba zan zubar ba tunda ba shege ba ne, kawai Mami sai ya ja hannuna ya kai ni ɓangaren Uwargidansa. Nayi mamakin ganin ashe yaransa takwas har da budurwar da za ta yi sa'ar Raihana. Komai nata ya ci uwarsa a falon. Goyon ɗa take yi ma, a gabanta da na yaran ya nunamin yaranta sun ishe shi ba ya kaunar haihuwa daga kowace mace. Ya kuma aure ni don ya ci duniyarsa ganin da ya yi ni ƴar rawa ce wai a Tiktok na kuma san ta kan rayuwa sai ya ɗauka zan san dabarun family planning kafin aure." Kawai sai ta fashe da kuka. Mami zuciyarta har wani tafarfasa yake yi. Ta ji kukan Futuhar tamkar yana ƙara tafarfasa ƙwaƙwalwarta don haka ta dakamata tsawa. "Ya isa! Nace maki ya ishe ni haka! Haba! Da wanne ku ke son na ji? Da mummunan albishir din da Babandi ya faɗamin ko kuwa da hargitsinku?! Ke ba za ki iya cin uban shege ba?! Ba za ki iya yadda za ki yi ki ga kin fitar da yar iska daga gidanki ba?! Shashasha kai marar wayo!" Tana kaiwa nan ta nemi bakin gado ta zauna kirjinta na dukan tara-tara tana maida numfashin gajiya. Futuha kuwa ai sai ta ƙara yin mutuwar tsaye don mamaki. Toh Mamin nan dai ta tabbata ita ce ainahin Mamin can baya lokutan yanmatancinta, ita ce Mamin da Anna ta yi mugun kewarta. Faɗa, zagi kuma duk akan kishi? Yau Mami dai da bakinta ta mata iznin daukar kowane mugun mataki ne akan kishiyarta da mijinta. Futuha ta juya cikin sassarfa tana kukan har lokacin ta fice zuwa ɗakin Anna. Mamin kuwa sai bayan da kwanyarta ta ɗan samu nutsuwa, tashin hankalin dake ƙasan ranta ya ɗan lafa sai ta soma tunano irin maganganun da ta faɗawa Futuha. Ta lumshe idanu ta ja guntun tsaki. Ta san yarinyar dole mamaki ya kashe ta, amma ita ta san azabtuwar da take yi ko kuma ta yi a shekarun baya da suka gushe. Ta tsani kishiya tsana mafi munin gaske. 'Ciki har da Fatima?' Wani ɓangare na zuciyarta ta watso mata wannan tuni. A fili ta ɗaure fuska tamau, idanunta nan da nan suka kaɗa tsabar masifa da kuma abin da ta tuna na daga rayuwar Fatima da Yusuf a baya. "Har da Fatima." Ta furta a zahiri, can kuma ta miƙe ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta. Sai bayan ta dawo daidai ne sannan ta fito zuwa ɓangaren Abba. Ta iske shi zaune yana kallon labarai, itama wuri ta nema ta zauna da wani irin sanyin jiki. Abba ya maido hankali gareta. "Maryama, na ganki wani iri, Futuhar ba su dawo ba ne?" Mami ta girgiza kai. "Sun dawo, tana wajen Anna ma suna gaisawa." "To ko jikin Tasleem din ne? Ni me ma ya faru ne da ita ta yi rauni?" Ko kusa ba ta sanar da Abban gaskiyar abin da ya yi sanadin kwanciyar Tasleem din a asibiti ba. Ta sani muddin ya ji to faɗa zai yi wannan ya sa ta gyara batun. "Zamewa ta yi ta faɗi a banɗaki. Amma ai da sauki tunda jinin ya tsaya." Jinjina kai Abban ya yi. "Allah ya raba su lafiya. Sai ta ƙara kula." Ta yi shiru tana kallon gefe guda ta kasa amsa mishi, ya riƙo hannunta cike da kulawa murya a tausashe ya ce. "Faɗamin, meke damunki?" Ƙasa ta yi da idanunta sai hawaye, suka zubo saman hannun Abba da ya ɗora bisa nata. Nan da nan ya ƙara shiga tashin hankali. "Kinsan bana son kuka ko? Taimaka ki faɗamin damuwarki Maryam. Zuciyata ba za ta ɗauki wani sabon tashin hankalin ba bayan wanda na fuskanta kwanakin nan." Ta jinjina kai ta dube shi. "Abban yara tunanin yarannan ya kasa barin zuciyata ta huta. Tun dawowarsu zan iya ce maka Ummita har yau ta ƙi dawowa cikin nutsuwarta. Yarinya mai fara'a da son jama'a marar hayaniya, ta koma wata iriya. Babu doguwar magana balle hira, koyaushe zaman tunani da shiru. Wannan abu yana damuna matuƙa." Shima Abban hakan da ta faɗi sai ya ƙara taso mishi da nasa damuwar. "Hakane Maryama. Toh a shawarce me kike tunanin za'a yi? Mece ce mafita?" Mami ta numfasa. "Mafita a samar mata abin da zai dawo da walwalarta. Abin nufi, madadin lokacin da aka sa na aurenta da Sahabi, me zai hana a yi mishi magana idan sun shirya kawai ya kawo lefe a sanya bikin nan da kamar sati biyu?" Ɗan jim Abba ya yi cikin hali na tunani. Sai kuma ya ce. "Kina tunanin idan an yi hakan ba a tauye ta ba kuma. Bana jin yarinyar nan ta samu nutsuwar da za ta karɓi aure a yanzu. Kada ki manta fa, keta haddinta aka yi ta ƙarfi. Aa Maryama, mu dai yi hakuri tun da abinda ya rage cikin shekarar bai wuce watanni biyar ba, ki jira mu ga abin da Allah zai yi a gaba." Ba haka ta so ba sam, ba kuma ta taɓa tunanin Abban zai watsamata ƙasa a ido ba. Kai ta mance rabon ma da ta bada shawara irin haka dangane da abin da ya shafi yaran ya musanta. Ganin sauyin dake saman fuskarta ne ya sa Abban ƙara riƙo hannunta ya ɗan matsa. "Kiyi hakuri Maryama, ba fa watsa maki ƙasa a idanu nayi akan al'amarin yaranki ba. Aa, ki dai daure na sani da zafi ka dinga ganin ɗanka cikin yanayi mai firgitarwa. Amma a shawarce, me zai hana ta je Bichi ko sati biyu ta yi kinga za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali." Daure fuska Mami ta yi. "Shikenan, ɗauke ta a yau ka kai ta sai Maijidda ta zuba ruwa a ƙasa ta sha tunda ta ga gazawata a kula da Ummita. Nagode." Tana kaiwa nan ta zame hannunta cikin na Abban ta soma kokarin miƙewa tsaye. Ya yi saurin dakatar da ita. "Haba Maryama, to kiyi hakuri naji na yi laifi a kalamaina. Ba zan kai Ummita ba face da izninki. Kiyi hakuri, shikenan? Yanzu me kike tunanin za'a yi don sama mata nutsuwa?" Ta sauke ajiyar zuciya. "Tunda har shawarar da na bayar bai yi ba, toh na fi tunanin ka bayar da kudi muje da su ukun nayi musu ƴar siyayya sai kuma ita Humaira da ka riga ka san matsalarta akan maza. Ganin wannan abu da ya afku ga Ummitan ya ƙara sanyawa ta tsani al'amarinsu. Daidai da Fadeel din da muke murnar ta soma sakin jiki da shi suna ƴar hira yanzun ko muryarsa ba ta wani son ji. Tun wuri gwara a yi mata maganinsa. Na kuma fadamaka labarin wani mai magani, idan har ka amince sai na kai ta a karɓo a gani ko za'a dace." Abba ya kurawa Mami idanu, a duniya bai taɓa ganin matar da ba ta damu da nata ba sai na wasu. Ba ruwanta da damuwar yaranta sai abin ya ci tura. Matar da ɗiyarta ke kwance a gadon asibiti amma ba ta ko zancenta, burinta ta samar da farin ciki ga yaran wasu. Kaunarta ya ƙara mamaye zuciyarsa, ya riƙo hannuwanta ya sumbata sannan ya sakarmata murmushinsa da ya san yana daga cikin abin da yake ƙara dulmiyar da ita cikin kogin sonsa. Ita kuwa sai ta ɗan kauda kai tana murmushi. "Ina kaunarki Maryam, Allah ya yi maki albarka ya bar mu tare. Kin cikemin gurbin mace hudu a duniya. Babu abin da zan ce maki sai fatan alheri. Yanda kika ce haka za'a yi, gobe ki shirya zan baku kudi, ku fara da siyayyar, koda zuwa jibi ne kuma sai ki kai ɗiyartaki wurin mai maganin. Ina fatan hakan ya yi maki?" Har lokacin tana murmushi ta gyaɗa mishi kai. "Ya yi ranka ya daɗe. Fatanmu Allah ya maidowa yaranmu farin cikinsu." Cikin jin dadi Abba ya amsa da amin amin. *** Washegari kuwa hakan aka yi, tamkar ba Mamin da Tasleem ɗiyarta ke kwance gadon asibiti ba, tamkar kuma ba wacce ɗiyarta mace ta farko ba (Futuha) ta kawo mata ƙorafin tashin hankalin da take ciki. Daga fuskarta za ka fahimci kamar a duniya ba ta da wata aba wai ita matsala ko kuma damuwa. Ta saki ranta suka zagaye shoprite da su Humaira da Raihana. Ummita sosai kuwa ta sake ɗin kamar yanda Mamin take buƙata, su kansu sun ji dadin yadda yanayinta ya sauya. A ɓangaren Ummitan kuwa, ta tabbatar domin ta saki jiki ne aka yi duk wannan shiri hakan ya sa ba ta watsawa Mamin ƙasa a ido ba, ta daure ta yakice damuwarta ta saki jiki. A ɓangare guda shima Sahabi na nashi iyakar kokarin ganin ya faranta ran abar kaunartasa. Wannan ma ya yi tasiri kwarai a zuciyarta amma har lokacin wannan baƙar ranar ta ƙi ɓacewa a tunaninta da mafarkanta. Su ne har gidan Hajiya Lubna, sun ɗan jima tare da yaranta a ƙasa inda Mami ta haye saman kafin daga bisani ta sauko su wuce. "Mami ba zamu leƙa Anti Tasleem ba?" Cewar Raihana. Mamin ta yi shiru. Ganin haka sai Ummita ta sa baki. "Mami don Allah muje a duba ta." Humaira kuwa uffan ba ta ce ba, asalima kallon shuke-shuken dake farfajiyar gidan Hajiya Lubna kawai take. "Shikenan, muje. Yarinyar ce ta ban takaici, kina da ciki don sakarci ki tsaya wani faɗa akan kishin banza da wofi." Su dai babu abin da suka ce. Humaira ta buɗe bayan mota ƙarama ƙirar KIA da Abba ya tsiya ta shiga. Mami ta ɗan bita da kallo sai kuma ta murmusa ba ta ce uffan ba. Ta dubi Hajiya Lubna. "Shikenan Hajjaju, sai mun yi waya." Ƴar dariya Hajiya Lubna ta yi. "Toh Hajiya Mamin yara. A gaida Tasleem din ki ce mata ta sha kuruminta zan zo." "Ai shikenan. Za ta ji." Daga haka suka yi sallama. *** Malamin ya yi shiru yana duban ƙasa, can kuma ya ɗago ya kalli Murja ya girgiza kai. "Abin da kike so ba zai taɓa kasancewa ba." Wani malolon baƙin ciki ya turnuƙe zuciyarta. Daƙyar ta haɗiyi miyau mai ɗaci ta ce. "A yanzu kake nufi ko har a gaba? Kenan Humaira ba za ta kasu ba?" Malamin ya yi ƴar dariya. "Wane mutum! Inji mutuwar. Ai Hajiya Murja babu wanda ba zai mutu ba. Kuma ni da na isa na duba mutuwar wani ai da nawa zan fara dubawa. Abin nufi kina son ta mutu kada ta auri Fadeel din ko? Toh hakan ba zai taɓa yiwuwa ba." Ji tayi wani abu mai nauyi ya tsaya a ƙahon zuciyarta. Malamin ya zubamata idanu, ya lura ba ta saduda ba don haka ya sauya zancen. "Amma fa idan kina so za'a iya nakasata rayuwarta. Zamu iya nakasta ta gaba ɗayanta. Amma da sharaɗi, matukar aikin bai ci ba, zai dawo kanki. Kin amince?" Ba tare da dogon tunani ba ta amsa. "Eh na amince." "Murja, ko za ki yi shawara?" Ranta ya ɓaci sosai. "Wancan karon haka ka ce min, wannan karon ma kana nema ka tauye ni da faɗin haka ko? Toh yanzu ba shawarar da zan yi, ga kudi nan ka yi duk abin da ya kamata." Ta bude jaka ta ciro bandir na dubu ta dire mishi. Ya yi murmushi. "Shikenan, ni nawa aiki. Sauran ke za ki yi da kanki. Dole kina bukatar zuwa inda ita yarinyar take. Ki je ki dawo nan da kwanaki uku." Murja ta ji kwanakin tamkar watanni a wurinta. Tana jin zuciyarta za ta iya bugawa na yanda Fadeel ke rawar ƙafa akan Humaira, kullum ya zauna da Hannatu a falon Anti to fa hirarta ne kawai. "Babu wani aiki da za ka yimin akan Fadeel?" "Aiki kai, ga wannan layar ki tabbatar kin saka a ƙarƙashin katifarsa, muddin ya kwana ya tashi ki ɗauke ki binne. Wannan kwallin kuma ki zizira ki tabbatar kun yi ido hudu." Ta yi murmushi, duk da cewa ta yi abubuwa da dama ba ta yi nasara a kan Fadeel ba amma hakan ba zai sa ta karaya ba. Ta karɓa ta sa a jaka ta mishi sallama ta tafi zuciyarta sol. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Misalin bakwai da mintoci ne, Fadeel ne zaune a falon Alhaji tare da Hannatu da Alhajin. Wannan damar Murja ta yi amfani da shi wajen kokarin ganin ta ƙaddamar da shirinta, sai da ta fakaici idanun su Khadija da Abdulmaleek wadanda suke kallo ta nufi ɓangaren Fadeel. Sai dai ta yi mugun mamakin jinsa a garƙame da muƙulli. Ta ciji leɓɓa don takaici kamar ta haɗiyi zuciya ta mutu haka ta ke ji, sai kuma ta tuno duk abinsa da safe yana barin mukullin ɗakin ya fice don a yi mishi gyara. Wannan ya sa ta yi murmushin mugunta ta juya tana mai kara cin alwashi. *** Futuha na zaune tana faman cika da batsewa kamar ta fashe, Alhaji Yakubu ya shigo fuskarnan a murtuke ya zauna yana dubanta gami da jefamata ledar dake hannunsa. "Idan har kina son mu cigaba da rayuwar farin ciki da ke, to ki gaggauta shan magungunan nan, an tabbatarmin zasu yi sanadin zubewar cikin dake jikinki. Idan kuwa har ki ka ƙi, kika dage sai kin haihu da ni, toh shakka babu baƙar rayuwar da za ki fuskanta sai kin sha mamakinsa. Sannan rashin bin umarnina zai yi sanadin da zan yi aure." "Wallahi ba zan sha ba! Idan kuma aure ne ka yi idan ka isa! Kuma wallahi ka ji na rantse maka matukar ka ce za ka wulakantani ba zan zauna ba sai dai ka sakeni!" Ya yi wata muguwar kyakyacewa da dariya. Ya nunata da yatsa. "Ke Futuha, ba ki da hankali ashe? An fadamaki ni Yakubu zan saki mace? Ai babu wannan ranar a duniyata. Zaman aure da ni ya zamar maki dole. Koda bakya so kuwa sai kin zauna da ni. Na dai fadamaki, muddin rayuwarnan mai dadi da na ɗanɗana maki kina so ya ɗore, to sai kin bi umarnina. Idan kuwa kin ƙi zan auro..." Sai kuma ya yi shiru yana jinjina kai duk a kokarinsa na shanye sirrin dake ransa. Tun su na Dubai ya yi wani irin sabo da ɗinkewa da Sa'a Ƴar Snow, kullum yana shafinta yana jifanta da likes da kuma chatting da suke yi a ɓoye. Tsantsar kalaman iskanci da ma hotunan tsiraicin da take turomasa ya yi mugun hargitsa shi, ba ya fatan ya kusanci zina amma ya sha alwashin aurenta. Ta kuma amince sannan ta ba shi lokaci ya gama cin angoncinsa kamar yanda ta buƙata. Ya fi kowa sanin ƴar tsamar dake tsakaninta da Futuha, ya tabbatar idan zancen ya fasu to fa ba za su kwashe da dadi ba hakan ya sanya shi zaɓar yin shiru. "Ka auro wa?! Ka faɗamata ko ma wacece don ubanta ta yi kaɗan ta shigo gidannan!" Ya mike ya watsamata harara. "Saboda ke kika haife ni kenan? Titse ni za ki yi na faɗamaki ko? Toh sai ki yi da wani." Yana kaiwa nan ya kama hanyar fita, aikuwa ta yi tsalle ta dire gabansa idanunta har sun kaɗa tsabar kishi da ɓacin rai, cakumar wuyan rigarsa ta yi tun ma ba ta kai ga furta ƙala ba ya cire hannu sai ji kake tas a saman fuskarta. "Ke! Ashe iskancin naki ya kai haka? Ni kike cakumarwa wuya?! Wannan ya zama na ƙarshe idan kika ƙara mugun gangancin nan sai na nunamaki ba ki da wayo! Banza marar tarbiyya ƴar rawar Tiktok kawai! Mtsw." Yana kai wa nan ya fice yana gyara zaman babbar rigarsa, dama dawowarsa kenan daga wurin Ƴar Snow, don dai kalamai da rungume rungume wadannan ya sha su kamar ba gobe, ita ta yi mishi rakiyar siyan magani kafin ya maida ta gida da siyayya mai yawa sannan ya dawo gidan. Futuha ta yi kuka mai isarta tamkar ranta zai fita sai dai ta ƙudurta a zuciyarta Alhaji Yakubu bai isa ya wulakanta ta ba. Sai ta ɗauki mummunan mataki a kansa kamar yanda Mami ta ba ta shawarar ta kwaci kanta da gidanta, to kuwa za ta ƙwata ta ƙarfin tsiya. Gama tunaninta kawai ta ciri waya ta kira wata tsohuwar aminiyarta Aneesa Jafar. Matar aure ce amma tantiriyar ƴar duniya ce domin ko a rayuwarsu ta makaranta tana cikin masu neman soyayyar Sir Ibb duk kuwa da auren dake kanta. Ita din shaida ce a yanda take juya mijinta a gida hakan yasa ta yanke shawarar tuntuɓarta. Tun sadda ta yi aure ba ta ƙara nemanta ba saboda a ganinta ajinta ya fi nata, sai a yanzun da buƙatarta ta taso. Kasancewae Aneesa ta iya barikanci, ko kusa ba ta nunamata komai ba suka gaisa hannu bibbiyu. Sai kuma Futuha ta warware mata damuwarta. Dariya Aneesa ta yi kafin ta amsa. "Ai wannan ba matsala ba ce yar uwa, amma ki yi yanda yace. Ke banda abinki mene ciki don kin zubar da cikin wanda ya nuna ba ya son haɗa zuri'ar da ke? Kuma wallahi kika yarda kika haihu da shi to ina mai tabbatar maki nan da nan za ki lalace ki zama wata daban. Ki daurewa ranki ki zubar da cikin idan ya so ki kawo kudi mu san hanyar da zamu bi ki mallake shi, yanda ko tsinke bai isa ya tsallake ba matukar ba ki yi mishi izini ba." Cikin sanyin jiki da kuma ɗan nutsuwar da Futuha ta samu ta ce. "Toh Aneesa. Ni dama tsoron mutuwa nake, kada na sha na mutu naji ance masu zubar da ciki mutuwa suke yi." "Mutuwa ai sai lokaci ya yi, nidai ina ba ki shawarar ki zubar kuma ki je ki yi planning abinki hankali kwance. Matukar dai kina so mu cimma burinmu." Ta sauke ajiyar zuciya ta jawo ledar magungunan sannan ta ba Aneesa amsa. "Shikenan, yanzun nan zan sha. Nagode Aneesa, zuwa gobe duk yanda ake ciki zan kiraki mu ji abinda ya dace a yi." "Shikenan, sai na ji ki." Daga nan suka yi sallama. Ta ƙurawa magungunan idanu, a wata farar takarda suke, ta yi shiru can kuma kamar wacce aka tsikara ta mike ta dauko gorar ruwa ta bude, ta zazzaga magungunan a hannunta ta shanye su tas sai jiran sakamako. *** Tana kwance tana juyi yayinda yan uwanta duka ke bacci abinsu. Ta mike zaune ta yi shiru, tashin zuciya take ji sai dai ta rasa yanda za ta yi ba ta kaunar ta yi amai motsin yunƙurin ya tashe su. Zuwa lokacin ta soma shan jinin jikinta, tsoro da firgici ya soma shigarta. Bai fi kwanaki uku watan da suke ciki ya mutu ba amma har yau babu labarin ganin al'adarta. Tsoro iyaka Ummita na cikinsa. Ta kasa jurewa tashin zuciyar da take ji sai ta bude dakin ta fita da sauri zuwa falon bandaki, nan fa ta shiga kelaye amai kamar hanjin cikinta za su zubo. Duk wani kayan kwalam da ta ci a ranar sai da ta dawo da shi. Ta kammala ta wanke fuska ta gyara wurin, ta kuma ɗauro alwala ta dawo falon ta zauna. Sai kawai ta fashe da kuka mai tsuma zuciya ga wani irin mugun sanyi da ya lulluɓe ta lokaci ɗaya. Ba ta son koda tuna kalmar da take tunanin shi ya zama damuwarta balle har ta furta. 'Idan ya tabbata haka din ne ya za ki yi da Sahabi?' Zuciyarta ta watso mata tambayar, ta rike kai sai kawai ta fashe da kuka sosai. Ba ma Sahabin kawai ba, ta ina za ta soma karɓar wannan ƙaddara na rainon cikin da ta same shi ta hanyar fyaɗe? Fyaɗen ma daga ɗan ta'adda? Tana wannan kukan mai tsuma zuciya ba tare da sanin irin ƙarfin buɗe muryar da ta ke yi ba har sai da ta ga hasken fitila a falon an kunna saboda akwai wuta. Mami ce, kafin Mamin ta ce wani abu sai ga Humaira a gigice ta fito itama. Kusan lokaci guda suka ƙaraso gareta. "Mene ne ya faru Ummita?" Humaira ta tambaya jikinta har yana rawa nan da nan itama ta soma hawaye ba tare da sanin ainahin dalilin kukan yar uwarta ba. Ummita ta rungumeta tana kuka sosai. "Ciki Humaira, Humaira zan haifi shege." Da karfi kuma cikin daga murya Humaira ke girgizata kamar zararriya tana fadin. "Wa ya fadamaki kina da ciki? Karya ne! Karya ne ba ki da ciki!!" Mami ta dago Ummita. "Wa ya fadamaki wannan mummunan labarin? Kin ga wasu alamomi ne?" Mamin ta fadi nata hankalin itama a mugun tashe, nan da nan cikinta ya duri ruwa. Cikin sheshsheka Ummita ta ce. "Ma..ma.mi, amai nake ta yi." Ajiyar zuciya Mamin ta sauke. "Haba Ummita, amai kuma sai aka ce maki yana nuni da cewa kina da ciki kenan? Amai ai alamun cutuka ne da dama, ba lallai sai ciki ba. Lokacin al'adarki ya yi ne?" "Eh Mami, har ya wuce." Gaban Mami ya buga da ƙarfi, Humaira sunan Allah ta shiga ambato sakamakon ji da ta yi tamkar an zare mata wani laka na jiki. A durkushe take amma kuma jiri ne ke kwasarta. Tana ji tamkar a mafarki ake wannan diramar ba a farke ba. "Maryama, meke faruwa ne?" Suka juya gaba daya, Abba ne sanye fa jallabiya a tsaye a ɗan rikice, ya tako ya ƙaraso ganin Ummita na kuka ya sanya shi ƙara jin rashin nutsuwa sosai. "Ummita, meyafaru kike kuka?" Mami ta yi saurin share hawayen da suka zubomata, ta miƙe tsaye. "Babu komai, ba ta jin dadi ne. Humaira ku shiga ciki. Ki kwantar da hankalinki gobe idan Allah ya kaimu zamu yi test a gani." Bayan wucewarsu Abba wanda ya daskare a tsaye cikin wani mugun faduwar gaba ya ce. "Maryama, meye hakan kuma? Na kasa gano bakin zaren wannan tattaunawar da tsakar dare?! Me kike son ki ce?" Gaba daya ma Abban ya diririce ko kadan ba ya cikin nutsuwarsa. Mami ta dafe hannunsa. "Babu komai Abban yara, muje zan maka bayani." Zai ƙara magana ta hana shi ta hanyar roƙonsa akan su tafi dare ne kar a ji sai kuma ya hadiye maganar ba musu ya yi gaba zuwa ɗaki ta bishi a baya bayan ta kashe fitilun falon. Ya ji zancen tamkar saukar aradu, nan da nan ya dafe kansa. "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Maryama wannan mummunan labarin da me ya yi kama? Tashi tashi muje asibiti yanzu a dubamin ita." Mami cikin hawaye ta yi saurin dakatar da shi ta hanyar dafe kafarsa gami da girgiza kai. "Aa Abban yara, kar muyi haka. Yin hakan tamkar tonuwar asirinmu ne. Duniya sai ta san halin da muke ciki. Ka kwantar da hankali tunda ana siyar da Pt-strip na awon ciki, gobe da safe mu bayar a siyo a auna fitsarinta don mu ga halin da take ciki. Mu yi fatan alheri da fatan kar zatonmu ya tabbata. Ajiyar zuciya mai karfi Abba ya saki. "Innalillahi...Ya Ilahi! Wannan ranar dame zan kirata ni Isuhu? Inama tun farkon fari ban hana Hajiya Maijidda riƙon Ummita ba tun tana ƙarama, da watakila ba zan ga wannan ranar ba." Wani irin zuciya ya tasowa Mami, ta ji tamkar ta haɗiyi zuciya ta mutu. Ranta ya yi mugun ɓaci, wato duk hakuri da dauriyar shanye damuwa da bakin cikin RIƘON BARE da ta yi, da wannan sakayyar Abban zai bi ta? Ta so ta furzar da abinda ke ranta sai kuma ta daure kamar koyaushe ta shanye rabi da kwatan ɓacin ranta ta ce. "Wane irin rashin tawakkali ne haka Abban yara? Ka isa ka hana Allah ikonsa ne akan al'amarin Ummita? Ummita ko bangon duniya ta je idan hakan ya ƙadartu a kanta sai ya afku. Ban da haka ma, kenan kana kaicon rayuwar da ta yi a hannuna? Kana kaico da irin abin da ya fada mata? Ko a tunaninka a sanadina ne aka sace su har kaddarar fyaɗe ya faɗa kan Ummita?" Ta karasa zancen da wani irin kausasshen murya, ganin ya kalleta da sauri da alama zancen bai mishi dadi ba kuma bai san fassarar da za ta ba shi kenan ba ya sanya ta fashewa da kuka mai tsuma zuciya. "Dama na sani Yusuf, watarana sai ka ga gazawata akan yarannan duk kuwa da..." "Haba Maryama, don Allah don Annabi s.a.w ki yi hakuri. Wallahi zafin bacin rai da damuwa da tashin hankali ne ya sanya ni wannan maganganun marasa kyawun ji. Ko daidai da kiftawar ido ban taɓa kawowa za ki cutar da wani a cikin yaran da kika haifa a cikinki ba ma balle a kai ga Ummita. Yarinyar da kika daukaka ta kika kuma riƙe ta hannu bibbiyu tamkar ke kika haife ta a cikinki. Wane irin butulu ne ni da zan yi maki haka? Ki yafemin domin Allah. Na tuba kiyi min uzurin halin rudani da tashin hankalin da na tsinci kaina ciki." Mami ta mike ta ja guntun tsaki ya yi saurin tarar gabanta. "Haba Maryama, da wanne kike so na ji ne? Da tashin hankalin nan na Ummita ko kuwa da ɓacin ranki? Faɗamin, me kike so nayi ki huce?" Jin haka sai kuma ta yi shiru tana goge fuska. "Kar ka ƙara irin wadannan kalaman naka na rashin tawakkali." Ya yi murmushin karfin hali ya rungumeta. "Idan har wannan ne ba zan kara ba. Na ma yi istigfari tun sadda kika ankarar da ni kurena. Mu ji da damuwa daya yanzu." Ta gyada kai, bandaki ta shiga ta ɗora alwala ta sanya hijabi ta hau saman darduma. Sosai yake jin so da kaunarta a zuciyarsa. Shima sai ya fasa neman wuri ya kwanta kamar yanda ya so duk kuwa da irin sakensa a ibada lokuta da dama. Kusan wannan shi ne kadan daga inda ya kuskuro, rashin tsayawa kai da fata wurin ibada sosai sai idan ya fada matsala babba. *** Washegari tashin hankalin da suka riski kansu ciki sai ya mantar da su wani batun zuwa kai Humaira asibiti. Gidan ya zama tamkar gidan makoki. Suna zaune jigum suna jira Mami da Ummita su fita daga bandaki don sanin matsayar Ummita, akwai cikin ko babu. Abba ya kasa fita kasuwa si safa da marwa yake a falon balle kuma Raihana wacce tun jin abinda ke faruwa ta kasa motsawa ballantana ta wuce makaranta. Sai Humaira da ta dau carbi tana jin tamkar an yi mata mutuwa. Mubarak kuwa wanda shi ya fita ya siyo abin awon cikin, sai ya jingina jikin bangon falon ya yi shiru cikin bugun zuciya. A wannan yanayin Mami ta fito a gigice kuma a guje, gaba daya suka yi kanta har suna rige-rige. "Meke faruwa?" Faɗin Abba yana jin kamar ya kife tsabar jiri. Mami ta fashe da kuka. "Mun shiga uku! Shikenan Abban yara asirinmu zai tonu. Ciki ne da Ummita." Abba ya ja baya da sauri ya zauna saman kujera mafi kusa da inda yake, yayinda Humaira ta yi mutuwar tsaye. Ita kuwa Raihana kwasa ta yi a guje zuwa bandakin don ganin halin da Ummitan ke ciki. Aikuwa ta iske ta a kife tamkar babu numfashi. Ta kuwa ƙwalla ihun kiran sunan Abba. Kusan da rige-rige suka shiga banɗakin. Mubarak ne ya yi ta maza ya cicciɓe ta bayan ya tabbatar da bugun zuciyarta ya fiddo ta falon ya shimfiɗe saman kujera sai dai duk wani kokari na watsa ruwa da ma sauransu anyi amma babu alamun Ummita ta san ana yi. Ana shirin fita asibiti Mami ta dakatar ta ce gwara a kira makwafciyarsu wata likita gudun fashewar zancen a duniya. Abba ya yi na'am, Mubarak ne ya fita da rawar jiki har gidan Dakta Inteesar an ci saa kuwa ta fito cikin shirin tafiya asibiti. Ganin Mubarak aboki ga babban ɗan ta Najeeb ya sanya ta dakatawa. Roƙon da ya hau yi mata ya sa ba ta iya yi mishi musu ba sai ta shiga motarta suka kama hanyar gidan don akwai ƴar tazara kaɗan ita daga bayansu take. Cikin ikon Allah ta ba Ummita taimakon gaggawa ta farfado sai kuma ta dube su. "Ya dace a yi mata gwaji sosai din tabbatar da abin da ke damunta." Ta furta hakan ta yi shiru don jin me za su ce, a matsayinta na likita ta gama tabbatarwa Ummita na da juna biyu. Shiru ta yi musu don ta fi son ji daga bakinsu sun amince da gwajin. Tana sane da labarin abinda ya afku ga Ummita. Su kansu mutanen gida ba su da masaniyar cewa duk yadda suka so da ɓoye labarin fyaɗen Ummitan sai da ya fita ba. A duniyar yanzun ai mutum ake kiwo ba dabba ba, kana abu kana ganin tamkar duniya ba ta sani ba amma zirr ake kallonka. Abba ya yi yaƙe. "Babu damuwa Dakta, zamu kai ta asibiti." Ta lura ba su son zancen ya fasu, ita kanta ta tausaya musu babu kamar Ummita wacce tunda ta farfado uffan ba ta ce ba, kukan ma ta ƙi yinsa sai sauke ajiyar zuciya akai-akai. Haka Dakta Inteesar ta yi musu sallama bayan ta rubuta magungunan da ya dace wanda take da tabbacin zai taimaki Ummita bisa yanayinta na mai juna biyu. Mubarak wanda ke tsaye ya ƙurawa Ummita idanu yana jin abu mai nauyi na taso mishi wanda ya fi kama da tsabar tausayinta da kuma kauna ta ƴan uwantaka.  Kamar dai yanda yake tunani. Shi ne ya karɓi takardar magungunan ya fice. *** Kwance yake idanunsa a lumshe, babu komai a ransa sai Humaira. Yana ji a jikinsa an soma zuwa gaɓar da yake da tsananin buƙatar kasancewarsu tare a inuwar aure. Shi din fa ba dutse ba ne, namiji ne kuma lafiyye da yake buƙatar aure. Soyayya mai ƙarfin da yake yiwa Humaira shi ne silar da ya danne wannan buƙatuwar ya ɗora shi kacokam a kanta yana jiran lokacin da mafarkinsa zai tabbata. Sai dai kuma yaushe ne? Wannan damuwar ce ta hana shi fita ko'ina, hatta da mai gyara mishi dakuna bai san yana nan ba, shi dai Nura yana falo yana aiki kafin ya shiga ɗakin. Hatta shi bai dan cewa Fadeel na gidan ba sakamakon motarsa da ba ta nan tun daren jiya. Ɓaci ta yi a hanya ya bar ta can  makanikinsa ya je ya ɗauka. Daidai lokacin Murja ta faɗo ɗakin da ƙunshin kayan gugan Fadeel din a hannunta wanda ta karɓa a hannun Sadi mai gugansu, dama  ta jima a yar barandar da zau sada ta da ɗakin Fadeel tana tunanin dabarar da za ta yi wa Lawal ta shiga. Sai ko ga Sadi ya zo wucewa nan da nan ta karɓa ta ce za ta karasa da shi. Suka gaisa da Lawal a falo, ta nuna zai karɓa ya shigar da su ta ce masa ya bar shi za ta karasa ladanta. Bai ce komai ba, dama a farko gargadin da Fadeel din ya yi mishi ne ya sanya shi dakatar da ita, ya hana kowa ya shigo masa sashinsa idan ba ya nan matukar dai ba Fu'ad ko Alhaji da Ibb bane. Amma ganin kayan wankin ne kawai za ta ajiye ta fito ya sanya shi ba ta wuri shi kuma ya ci gaba da kakkaɓe kakkaben kujeru da kayan kallo. A lokacin da ta shiga dakin, Fadeel ya zagaya bandaki, yana dab da fitowa ya ji motsin mutum a dakinnasa, bai kawo kowa ba sai Lawal. Ya san ba shi da masaniyar yana gida bai fita ba. Don haka ya fito daga shi sai singilet da dogon wandon sport. Daidai lokacin da ta ajiye kayan a gefe ta yi wurgi da filo ta ɗaga katifar gaba ɗaya da zummar sanya layar. Kasancewar idanunta ya rufe ko kadan ba ta ga wayoyin Fadeel din dake gefe ba a ajiye. Tana zuci-zucin ta yi ta ƙare kafin shigowar Lawal ya isketa. Fadeel ya bude kofar ya fito, hakan ba  karamin razanata ya yi ba ta saki layun dake a hannunta suka zube a ƙasan darduma. Mamaki mai tsanani ya kama shi har ya bude baki ya kasa magana. Ya karasa sosai ya kara kallo, tabbas layu ne. Nan da nan ya tamke fuska tamkar bai taɓa wani abu wai shi dariya ba. "Zamanki a gidannan ya ƙare. Wallahi kin ji na rantse maki ko yau Anti Amarya ce ta haifeki dole ki bar gidannan. Ni Fadeel na fi ƙarfinki, na kuma fi karfin duk wani da zai sanyaki aikata mugun abu don ki ci galaba a kaina." Jin haka sai kawai ta hau tsuma da borin kunya. "Ni..nifa ba.." "Shut up!" Tsawar da ya yi ya sanya Lawal faɗowa ɗakin. Nan da nan hankalinsa ya tashi, shima idanunsa suka sauka kan layar dake ajiye a tsakar dakin. Fadeel ya hau shi da faɗan don me ya bari ta shigo masa daki alhalin ya gargaɗeshi. "Ka yi hakuri Yallaɓai, wallahi na yi nayi da ita ta bani kayan gugar na kawo ta nunan ita za ta kai. Shi ne.." "Shi ne me?!" Fadeel a zafafe ya tari numfashinsa jikinsa har ɓari yake yi ga tsikar jikinsa da ya tashi gaba daya. Abin da ya faru shekarun baya kawai ya fadomasa a rai, sadda ya kama  Mamar Fu'ad tsamo tsamo a ɗakin Mahaifiyarsa tana barbaɗa magani. Daga ranar ya tsane ta, rashin wayo da wauta kuma ya sanya bai yi tunanin sharewa ba. Tun daga kuma sadda mahaifiyarsa ta taka wannan magani ba ta ƙara zaman lafiya ba da Alhajinsu, har dai a karshe Alhaji ya yi mata sakin wulakanci. Shi kuma ya sha baƙar wahala a hannun Mamar Fu'ad. Ya ji ya ƙara tsanar Murja ninkin ba ninkin. Kuma yanda ya rantse ba zai yi kaffara ba sai Murja ta bar masa gida ubansa idan ko Alhaji ya ƙi to fa shi zai bar gidan gaba ɗaya. Murja cike da kunyar kamen da aka yi mata ga uwa uba Lawal dake tsaye ya ƙi fita yana kallon ikon Allah, ta durkusa ta kwashi layun ta fice tana dakawa Lawal wata uwar harara kamar idanunta zasu zazzago. Fadeel ya dafe kai yana mai runtse idanu zuciyarsa na tafarfasa tamkar an kunna ruwan heater.  "Ka yi hakuri in sha Allahu zan kara kiyayewa." Gyada masa kai kawai ya yi gami da yi mishi alama da hannu akan ya fita, Lawal ya juya ya fice mamakin wannan hali na Murja da bai taɓa zato ba. Lallai mutum ba abin yarda bane. Shi kuwa Fadeel sai da ya samu nutsuwa sannan ya fada wanka, ba shi da niyyar fita daga gidan amman daga faruwar al'amarin ya ji gaba daya gidan ya fita a kansa. Kai tsaye wurin Ibb ya tafi, dama tun jiyan yake faman kiransa akan zancen bikinsa da ya taso yana ƙin zuwa yana ba shi uzurirrika saboda damuwar Humaira da batun auren Ibb ke taso masa da shi. Murja kuwa tana zuwa ta shiga haɗa kayanta, ta gwammace ta bar gidan da ace Fadeel ya fasa zancen nan har Alhaji ya tsane ta ya kuma ƙi jinin haɗa zuri'ar ɗansa da ita. Anti Amarya kadai ta fadawa, nan da nan hankalinta ya yi mugun tashi, ta hau ta da faɗa tamkar ta ari baki. Babban baƙin cikinta ma ba ta yi shawara da ita ba ta yi raɗin kanta. "Ba ki da wayo ko kaɗan Murja! Wa ya fadamaki samun Fadeel a hannu abu ne mai sauki? Ke kinsan irin karfin ibadar wannan yaron? Toh wallahi ko wani Malamin ba zai nuna masa tashin dare da nafilfilu ba ko an fadamaki baƙin tabon sallar dake goshinsa da goge dutse a goshin ta same shi? Kai Murja! Toh kuwa  ya zama dole ki bar gidannan! Ni zan samu shi Fadeel din nasan siyasar da zan mishi don kar magana ta je kunnen Babansa." Murja ta kara jin wani malolon abu ya tsaya a ƙahon zuciyarta. Dama ta sani Anti Amarya ba za ta taɓa goyamata baya ba. Ta kuma soma  yarda da yayarsu Rabi da ta ce Anti Amaryar kanta kawai ta sani, ba wani so take yi ta tallafe ta ba shiyasa ta ce  ta sauya dabi'u ta nuna ita wata salihar ce. Ban da haka ai ta san wannan ba abu ne mai sauki ba da kuma zai yiwu kawai a yi duka ɗaya lokaci daya a wuce wajen. Ta shareta ta cigaba da hada akwatin kayanta. Kafin wani lokaci ta kammala ta fice abinta, Anti Amarya ba ta kara cewa uffan ba, ba karamin ɓata ranta ta yi ba, ita yanzu babban tashin hankalinta yanda za ta rufe maganar kar ta je kunnuwan Alhaji. Ta tsinewa Murja ya fi a ƙirga. Wannan ya sa ko kallonta ba ta yi ba da ta fice. Allah ya taƙaita Hannatu ba ta gidan ta je wurin dangin Alhajinsu. *** Gidan su Humaira tamkar gidan makoki, babu walwala a fuskar kowanne, Abba kasuwar ma kasa fita ya yi. Mami kuwa ta ƙulle a ɗaka ba wanda ya san me take yi. Ummita kuwa tana kwance shiru kawai har baccin dole ya dauketa sanadin magunguna da ta sha kuma a daren jiya ko kadan fargaba da damuwa sun hana ta runtsa. Karatun alkur'ani Humaira ta kunna a waya ya karaɗe ɗakin don su samu nutsuwar zuciya. Tana sauraro tana bi a hankali ta hanyar motsa lebɓanta duk cikinsu sun kasa yiwa Ummita kwakkwarar magana don ba su san ta inda za su fara ba. Raihana kuwa kanta ta cusa karkashin pillow tana kuka a hankali tana kuma bin karatun. Ji take yi inama komai dake faruwa a mafarki ne. Amma ina, wannan zahiri ne, shi ne kuma gaskiya mai mugun ɗacin da ke addabarsu. Hatta da Mubarak ya shiga wani irin hali, komai yake yi Ummita ce a ransa, bisa umarnin Abban ya bi su Yassar shago amma yana zaune cikin mugun ɓacin rai. Ya rasa dalilin da ya sa ta tsaya mishi a ƙahon zuci watakila kuma tsananin tausayi ne da duba da irin kirkin Ummitan yarinya mai kirki da sanin ya kamata. Bai taɓa ganinta ba face da murmushi saman fuskarta, tana da hakuri sosai da sanyi. Dabi'unta abin so ne ga kowane namiji. *** Mami a hargitse take ta faman danna kiran layin wayar amma abu ɗaya kwamfutar ke nanata mata, a kashe wayar take. Koda ta gaji ta yi wurgi da ita tana mai jan tsaki. Goshi ta dafe cikin tsananin ruɗu. Can kuma ta ji wayarta ta ɗauki ƙara. Ta yi azamar karasawa saman gadon ta ɗauka. Lambar dai da take ta kiciniyar kira ita ce aka kirata da ita. Ta ɗaga cikin sauri. "Kai Bala! Ina ka shiga ne?" "Kiyi hakuri Hajiya, chaji na bayar sadda kika kira ba'a ɗaga ba sai mai chajin kawai ya kasheta gudun a yi ta kira. Ina fatan lafiya?" Ta girgiza kai idanu a runtse tamkar yana ganinta. "Ba lafiya ba Bala, aiki ya ɓaci! Duk inda mutanen nan suke ina buƙatar ganinsu. Wannan karon ni da su zamu tattauna. Sun min ba daidai ba, na fadamusu dama idan har sakamako bai yi kyau ba to sai sun maidomin hatta rabin kudin da na ba su. Ba za su ci komai daga dukiyata ba tunda har kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba." "Hajiya ban fahimci me kike son cewa ba? Ke ce fa kika ba su umarnin barin wajen koda kuwa kudaden ba su shiga hannunsu ba? Ta ya ya kuma za ki ɗora musu laifi kacokam?" "Bala sun yiwa yarinya fyaɗe, yarinyar da ban so hakan ta kasance da ita ba. Da ace waccan mayyar aka yiwa ba zai dameni ba. Yanzu dai mugun abun da suka yi ya bayar da mummunan sakamako, ciki ya shiga." Bala ya doka salati mai karfi. Can kuma cikin rage murya ya ce. "Ciki kuma Hajiya? Toh me ake jira da ba za'a zubar ba?" Mami ta sauke huci. "Zubarwa ai wajibi ne. Dole na zubarmata da shi ko don gudun tonuwar asirina. Amma yanzu ni ka nemo min su mutanen ko kuma ka aikon lambar shi Babban nasu sai muyi magana." "An gama Hajiya, zan kira na sanar da shi sai na hadaku a waya don dama ina shirin ce maki ba ya garin ya dan yi bulaguro zuwa Kaduna." "Shikenan, sai ka turo." Tana kaiwa nan ta katse wayar tana ji kamar ta zabga ihu, babu abin da idan ta tuna take takaici kamar rashin cin nasarar mallakar dukiyar Abba da ta kwallafa a rai. Ga kuma shirin tonuwar asirinta da ke son afkuwa, matukar cikin Ummita bai fita ba lallai babu shakka watarana abin ɓoye zai fito fili. *** Mami ta tabbatarwa Abba lalali sai dai a zubar da cikin Ummita gudun zubewar mutuncinsu a idanun duniya. Tun Abba ya na nuna bai amince ba har dai ta ci nasara a kansa ya yarda. Ranar da zasu je a daren Mami ta shiga wurin Anna don amsa kiranta. Anna ta dube ta a yamutse. "Sai wani rawar ƙafa kike yi a cire cikin yarinyar nan, idan an cire wa kike tunanin zai aure ta? Shi Sahabin ko kuwa dai shi mijin naki ya ba babban ɗansa aurenta? Ba kya wannan hangen?" Mami ta ji kirjinta ya buga da ƙarfi. Wannan zance na Anna ko kusa bai mata dadi ba amma sai ta zaɓi ta ɓoye saboda dalilin da ita kadai ta bar wa kanta sani. "Idan har asirinmu zai rufu mene ne ciki Anna?" Daƙuwa Anna ta wurga mata. "Ungo nan nace! Ni dai da ace a asibiti nayi naƙudarki zan iya rantsewa sauyamin ke aka yi ba ke ce jinina ba. Yanzu ke koda wasa idan mijinki ya ce zai hada auren wannan gantalalliyar da ɗansa abin yarda ne a wurinki? Babban ɗanki wanda bai taɓa kusantar zina ba a duniya shi ne za ki yarda a hada shi da ita?" Kafin Mami ta kai ga cewa komai Anna ta ji an bata amsa. "Anna, kar ki kara danganta yan uwana da zina, kowa shaida ne ba zina suka aikata ba, kaddara ce da za ta iya faɗawa kan kowa. Sannan idan auren ne ma sai me? Ni ina sonta kuma na rantsemaki a yau Sahabi ya janye da batun aurensa da Ummita to fa ki rubuta ki ajiye ba ta da miji sai ni nan Mubarak!" Ba Anna kadai ba, hatta da Mami wanda ganin inuwar mutum a farko yasa ta ɓoye abinda ke ranta sai da maganar ta yi mata wani irin duka a kirji. Ta dago tana kallon Mubarak din, sanin da ta yi mishi ba ya taɓa sauya magana. Mutum ne mai magana daya wannan ya yi matukar ɗaga mata hankali har ta kasa siyasar data saba na danne abin a zuciyarta. Fuskarta ta nuna tsantsar ɓacin rai na gaske, idanunta har wani kaɗawa suka yi tsabar bala'i. "Mubarak! Kar ka kuskura na kara jin makamancin wannan maganar daga bakinka. Wacce kake faɗawa ka dinga tunawa ita ta haifar maku ni. Ka kiyayi harshenka!" Mubarak ya yi shiru kawai yana jin zafin maganganun Anna har lokacin suna tarfafasa zuciyarsa. Anna kuwa ta hau zagin Mami tana fadin ta yi mata shiru ai da sa hannunta a rainin da yaran suka yi mata. Shi dai ya dubi Mamin ya isar da sakon Abba akan ta fito su wuce asibiti sannan ya kaɗa kai ya bar musu dakin. Mami ta mike ba ta ko biyewa maganganun Anna ba ta bar dakin. Wannan kalma ta so da Mubarak ya furta yana yiwa Ummita ya tsayamata a ƙahon zuci, abu ne da har abada ba za ta bari ya afku ba muddin rai. *** A kokarin zubar da cikin Ummita aka kusa jaza mata matsala, zubar jini sosai ta shiga yi dakyar aka samu ya tsaya. Sai dai cikin hukuncin Allah mai kaddarawa cikin yana nan daram bai fita ba. Haka aka shafe watanni hr biyu ana fama da abu daya amma cikin bai ko girgiza ba wannan dalili ya sanya Abba cewa a hakura kawai amma gudun masu shiga da fita na gidan Ummitan ta rage fitowa falon idan ya so duk abinda take so a kai mata daki. Ga biki ya matso amma sun kara neman alfarma an ɗaga bisa hujjar kayan dakin da ba a kammala haɗawa ba na Ummitan. Wannan abu mai yiwa iyayen Sahabi da shi kansa dadi ba, ga raɗe-raɗin da aka kawowa uwar Sahabi wai Ummita na da juna biyu, ko kadan ba ta ji ta amince da zancen ba, da hakan ne ai ta san iyayen Ummitan masu dattako ne ba za su ɓoye musu ba. Wannan yasa inda ta ji zancen anan wurin ta bar shi kuma a cewarta ai ciki ba ya ɓuya, idan har akwai to fa zai fito. Mami ta yi nasarar samun wayar WIZZY. Wayarsu ta farko ya nuna bai ma san zancen da take yi ba don gaba daya hankalinsa ba a nutse yake ba gani yake kamar an hada baki ne don a kai musu cafka. Sai da aka kwashi lokaci mai tsawo sannan ta kara nemansa a waya ganin dai cikin dake tattare da Ummita ya ƙi fita uwa uba ga wani irin kulawa da Mubarak ke yiwa Ummita wacce har gobe ba ta da walwala. Wannan abu ya tashi hankalinta ya kuma jefa ta cikin rudani da tsoro. Ya tabbata kenan idan ciki bai fita a cikin Ummita ba za ta iya zama rabon ɗanta nan gaba. Ta kuwa gwammace gwara ta sanar da Wizzy cewa Ummitan na dauke da cikinsa har na watanni hudu don su ga matakin da za a dauka a kai. Cikin sa'a ya ɗaga wayar. "Wai Malama ba mun gama aikin da kika sanya mu ba? Kiran da kike yimin na mene ne bayan kin jaza mana asarar maƙudai?" "Kaga Wizzy, kar ka yimin rashin kunyar banza da wofi! Ni na jazamaku asara ko kuwa ku ne kuka jazamin? Da na ba ku aiki na ce ku ketawa yarinya haddi ne? Shegen halin akuyancinku ya sanya kun afkamata yanzu yarinya tana dauke da ciki har tsayin watanni hudu." Wizzy ya kantamo wata ashariya ya saki. "Ciki kuma?!! Don uwarta ita din akuya ce daga yi sau daya sai ciki!" Mami itama ji tayi tamkar ta sakar masa ashar, da kusa da ita yake a yadda take ji za ta iya shaƙar wuyansa har lahira. "Ko mece ce ni ba wannan ne ya sa nayi kiranka ba. Mafita nake so, idan kuma babu to lallai kuɗina ya dawo. Sadik shi ne sunanka na gaskiya, kai din haifaffen Katsina ne. Ina da kaf tarihinka na kuma san inda zan sameka, wallahi muddin ka bani matsala sai na yi maganinka." Shiru ya ɗan biyo baya tamkar ba zai ce komai ba don ba karamin dauremasa baki ta yi ba, ita kuwa Mami ta san komai bisa shawarar Hajiya Lubna, tun ma basu kai ga ba da aiki ba sai da suka sanya aka nemi dukkan bayanan sirri na wadanda suka ba aikin sannan suka amince. "Hajiya bai kai ga nan ba. Ni dai yanzu kudi mun ci ubansu. Kawai dai abin da ya kamata a bar ta ta haihu, ni kuma zan zo na dauke gudan jinina na kai garinmu." "Me kake so ka ce?" "Eh ina so nace maki ni Sadik Wizzy ina son abina. A bar min ciki ta haihu na karɓi abina." Mami ta yi shiru tana nazari. Idan har Ummita ta haihu ya karɓi abin da ta haifa watarana asiri zai tonu, ita kuma ta rantse ta gwammace gwara abin da za ta haifa din ya mutu da dai wannn gurguwar shawarar ta Wizzy. "Ya ne wai kika yi shiru Hajiya? Ba ki ji nace maki ina son abina ba? Toh ina son abina, duk wanda kuma ya yi yunkurin aika shi lahira nima zan sanya shi dogon bacci. Ina fatan kin fahimta? Idan na karɓe abina ba sai ta je ko uwar ina za ta je ba mu raba gari?" Zufa sosai ya rufe Mami, gaba daya kanta ta ƙulle ta kuma rasa mafita. Dole haka ta amsa da toh suka yi sallama. *** *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Ganin lamuran bana ƙare ba ne, ya sanya a dole suka rungumi ƙaddarar cikin Ummita. Babu yanda suka iya don a gaban idanunsu an yi dukkan wani kokari don a zubar amma hakan bai yiwu ba. Hankalin su Abba da ma kansu su Humaira ya ɗan kwanta ganin yadda Ummitan ta samu nutsuwa don sosai take kokarin ɓoye nata damuwar saboda samarwa ƴan uwannata nutsuwa musamman Mubarak wanda kullum kokarinsa ya kyautata mata. Shi ne siyo banza siyo wofi, kunna mata fina-finai a wayarsa da ma bidiyon sanya nishadi da dariya, tun ba ta dariyar har ta zo ta ɗan soma murmushi. Ranar da abin ya ishi Mami sai da ta tunkari Abba a siyasance tana ba shi shawarar ya dace Mubarak ya dinga fita kasuwa kafin lokacin da zai tafi bautar ƙasa. Abban ya nuna hakan daidai ne sai dai ya kara da fadin.   "Amma na so ace ya hakura da kasuwarnan ya cigaba da daukewa yar uwarsa hankali ta hanyar hirar da yake taya ta. Naji dadi kwarai da na ga murmushin fuskarta jiya, na kuma sani hakan yana da alaƙa da shi. A duniya yanzu bani da burin da ya wuce na ganin farin cikin yarinyarnan. Ina kuma cike da fargabar yanda yan uwan Mahaifiyarta za su karɓi batun cikinta." Wannan magana ta Abba ko a fuska ba ta yiwa Mami ba. Ta fakaici idanunsa ta watsa mishi harara sai kuma da ta ga ya kalleta ta gyara fuskar sosai kai ka ce gaba daya damuwar duniyarnan ita aka ɗorawa. "Ni kaina hakan yana yimin dari bisa dari, sai dai kuma hakan fa ba mai ɗorewa ba ne tunda wataran din dole ne ya wuce bautar ƙasa. A yi hakan dai yanzu, na maka alkawarin in sha Allahu zan tsaya tsayin daka wajen ganin ba ta faɗa cikin ƙuncin baya ba. Ga yar uwarta Humaira ma kullum tana nan tare da ita." Sai da ta ambaci Humaira sannan Abba ya ce. "Af, kinga zan manta, mun yi magana da iyayen Fadeel, mun kuma yanke nan da watanni shida zuwa sadda shi Fadeel din ya kammala gini za a tsaida zancen aurensu." Wani irin jiri ya nemi kwasar Mami daga zaune, ta hadiyi miyau sannan cikin yaƙe ta ce. "Wannan abin farin ciki ne sosai Abban yara, amma kuma ba ka ganin kamar zai zama mun zalunci yarinyarnan? Har wannan lokacin fa Humaira ba ta kula shi, ba ta kaunarsa." Abba ya dan daure fuska. "Bar ja'irar yarinya marar wayo. Ai ba ita ta haife mu ba. Ni na gaji da wadannan mugayen dabi'unnata na korar samari da wulakantasu. An kawomin ƙararta ya fi a ƙirga, a yan watannin nan da fitowarsu dalilin da yasa ban tayar da maganar manemanta ba saboda halin da yar uwarta ke ciki ne, amma ko sati ba a yi ba akwai wanda ya same ni bayan na fito daga masallaci cewa ɗansa ya gani kuma yana so. Hakuri dai na bayar. Ni ba zan biye mata ba. Aure ne dai sai ta yi, idan ba ta son shi Fadeel din ta zo ta kawo wani." Tsaki Mami ta ja a ƙasan ranta, kamar ta shaƙo wuyan Abba haka ta ji. Kamar yanda ta saba kuma sai ta shanye bacin ran, fuskarta a ɗan daure ta ce. "Aa fa Abban yara, nikam ba wanda zan yarda ya yiwa ɗiyata dole. A dai bi abin a sannu. Yanzu dai ya muka kwana batun kai ta wurin mai magani." Girgiza kai Abban ya yi, wato dai Mami ba ta taɓa ganin laifin ƴaƴanta. "Duk sadda ku ka shirya zuwa Mamin Humaira, ni mene nawa a ciki zan mata dole ta je ne?" Ya fadi cikin gatse da kuma zolaya hakan sai ya ba Mamin dariyar da bai kai ciki ba, ta ɗan dara ɗin tana mai farr da idanunta. "Naji din, ko ma me za ka ce hakan ne kawai. Yau dai muna da baƙi, yaran Abba zasu kawo mishi ziyara. Zuwa gobe sai muje." Abba murmushin shima ya yi, ya gane Tasleem da Futuha take nufi. "Toh Allah ya kawo su lafiya." Ta amsa da amin. Humaira ce ta yi girkin gidan a ranar, ta dawo da aikinta tuƙuru na shiga kicin ganin hakan yana ɗebemata dukkan damuwa sai dai kuma har gobe masu neman ta karɓi odar su ta kasa, ko Mami ba ta sanarwa ana neman odar abinci ba saboda a ganinta ba ta da nutsuwar da za ta yi abin da ya dace. Bayan ta kammala komai ta zuba a kuloli, ta bar Ladidi da gyaran kicin din ta koma nasu dakin. Kamar dama jira yake, sai ga waya ta shigo. Koda ta duba Fadeel ne, wani irin ɓacin rai ta ji ya danne wani sashi da ke kokarin sanyayamata rai, ta kasa fahimtar yanayin da take ji akan Fadeel tamkar dai guda biyu ne. Farin ciki da bakin cikin da ya danne wannan farin cikin. Babu walwala ta amsa da sallama. Shima ya amsa sallamarta. "Ina fatan ban takuraki ba? Fatan kuna lafiya?" Ta tsuke baki, tsiwa take son ace ta yi amma sai ta ji tamkar wani ɓangare na zuciyarta na kwaɓarta. Ta kai duba ga Ummita da ke kwance idanunta a kan Humairar. Sai ta ji dagaske ta kasa tsiwar a gabanta don haka murya ciki-ciki ta amsa. "Lafiya muke. Fatan kaima haka?" Daga ma muryarsa za ka fahimci ya ji dadin yanda ta amsa ba kwanaki da take balbale shi da faɗa da bakaken maganganu ba, shi kuwa bai ma san zafi biyu ne suka hade mata a baya ba, ga na halin da cikin jikin Ummita ya jefata, ga kuma na wani ciwon kai da bacin rai da muryarsa ke haifar mata marar dalili. "Lafiya kalau nake. Ina neman ɗan wata alfarma wajenki Boddo." Sarai ta san me yake nufi da wannan sabon sunan da ya raɗa mata, wato kyakkyawa. Sai ta zaɓi ta basar ta hanyar fadin. "Ina jinka." "Zan iya shigowa mu gaisa?" Ta ɗan yi jim, ba komai take tunawa ba sai zuwansa na karshe a watannin baya da har Mami ta ji babu dadi. Yanzu idan ta ce ya zo kuma fa? Ta ji wani abu na tafasa zuciyarta, bakin cikk na saukar mata da ba ta san na mene ne ba. Wani bangare na jan ta da kokarin ta furta ya zo din, amma wani bangaren na kwaɓarta da nuna ta tsane shi, ta tsani ganinsa to me zai zo ya yi mata? "Toh." Ta ji lebbanta kawai sun ba da wannan amsar. Shi kansa sai a ya ji wani shock don bai zaci wannan amsar zai ji ba. Ya yi makamancin tambayar ya fi a ƙirga amma kullum amsar aa, karshe ma ta kashe wayar da hujjar ya dame ta.  Ya yarda addu'a tabbas na tasiri akan Humaira, don duk sadda ya dage iya dagewa a kan lamarinsu sai ya ga sauyi tattare da ita, ya kuma soma yarda da hasashen Hannatu kanwarsa da kafin ta koma Yola da ta ji irin yanda Humairar ke yi da komai ta ce ba yin kanta ba ne a nema mata magani. "Nagode Boddo, sai na shigo." Yana fadin haka ya katse kiran, itama Humaira ba ta ce komai ba ta sauke wayar daga kunnenta. Ta dubi Ummita da ke kallonta cikin murmushin da ba ta san dalili ba. "Mene ne?" Ta tambaya. Ummita ta girgiza kai. "Ba komai, ina dai ganin wani abin mamaki ne a saman fuskarki. Idan ban yi karya ba kina mutuwar son Fadeel amma na rasa meke danne wannan son." Humaira ta dan harareta da wasa. "Ni ba sonsa nake ba. Mu bar zancen don Allah kafin raina ya ɓaci." Murmushin dai Ummita ta ƙara yi, ba ta ce komai ba ta lumshe idanu tana ci gaba da jan carbin dake hannunta. Ita kadai ta san tunanin da take yi, Humaira ta dube ta. Tausayinta sosai ta ji, Sahabi har ya gaji da zuwa hira don ba fita take ba, hakanan ta daina daukar wayarsa. Kullum zancenta guda daya ne, ba za ta yaudari Sahabi ba, ta fi kaunar ya san ita din ta haramta aurensu koda kuwa bayan ta sauke nauyin cikin dake jikinta ne. Ba za ta aure shi ba sam. Ba ma za ta yi auren a duniya ba kamar yanda ta ke faɗamusu a yanzu. Shigowar Raihana ɗakin ne  da sallama ya sa Ummita bude idanun, itama Humaira ta kauda dubanta daga gareta zuwa ga Raihanar. Wannan ne ya katse tunanin dukkansu. "Mami ta ce ku fito ku gaisa su Tasleem sun zo." "To." Shi ne amsar da Humaira ta bayar ba don tana kaunar ganinsu ba domin ta gama sanyawa a ranta su din ba masoyansu ba ne. Ba kuma zasu kaunace su ba har gaban abada. Sai da Raihana ta kara maimaitawa sannan Humaira ta mike, Ummita daman tuni ta yi gaba. Cikinta bai da girma bai fito ba. Tasleem wacce daga makaranta ta shigo gidan sanye take cikin uniform dinta ga tirtsetsan cikinta dan watanni takwas sai faman taunar aya take yi suna hirar makarantar da Mami, watanni shida kawai ya rage ta kammala karatun gaba daya. Ba ta yi ko mintuna uku ba sai ga Hajiya Futuha ta shigo tana ta faman shan ƙamshi. Tasleem ta harareta ta gefen idanu ta kauda kai tana ɗan huci, fatar Futuha ta kara kyau kamar ka taɓa jini ya fito, kamshin turarenta kuwa ya buɗaɗe falon gaba daya. Ƙasim na rike da jakarta yana take mata baya, babban burinsa shi dai ta ba shi na kashewa. Yassar ya dube ta. "Ka ga manya matar Alhaji naku daban da nasu. Irin wannan ƙamshi haka? Gaskiya zan zo a sammin turaren." Ta karaso ta zauna jikin Mami tana dariya. "Har ka bani kunya ɗan uwa. Idan dai turare ne, ko direba zan aiko ya kawomaka na siyo su kala-kala a Dubai." Aka sa dariya Dawud na fadin. "Inyeee! Ka ga Hajjaju mutan Dubai." Mami dake murmushin jin alfahari ta ce. "Ya ishe ku hakanan toh." Tasleem dai ba ta tanka ba sai dariyar yaƙe kamar bakinta zai rabe biyu amma ƙasan ranta ji take tamkar ta kurma ihu. Shigowar Ummita da su Humaira ya sanya hirar ta tsagaita, suka gaishe su, Futuha ta amsawa Humaira faram-faram don tsakani da Allah so take ta wuce da ita gidanta ko don girki. Tana da mai aiki amma ko kusa ba ta iya abincin da Alhaji Yakubu ke so ba kullum sai ya yi mita wannan dalilin ne ya sanya take son tafiya da Humaira gidan koda na kwanaki ne ta nunawa yar aikinta yanda take sarrafa tukunya. "Humaira sannu, bayin Allah har kun dawo hayyacinku wallahi." Fadin Futuha, sai kuma Raihana ta sanyo wani zancen gudun kar a tada abin da zai sosa musu inda ke ƙaiƙayi. Yassar da sun riga sun samu labarin komai kuma har a zuci ba su yi farin cikin ƙaddarar cikin Ummita ba sai ya sanyo hirar abinci yana kiran a kawo a ci ya kwaso yunwa daga kasuwa. Tasleem kuwa ƙuri ta yi da idanunta akan Ummita ba ta ko ƙiftawa musamman ma da Ummitan ta mike tsaye ta sauya wurin zama. Da ta kammala tabbatar da zarginta sai ta ga ta nan a tsaye ta miƙe har ayar da take ci na zubewa a saman kafet. "Kut! Me nake shirin gani Mami?" Ta yi furucin har a sannan idanunta na kan Ummitan. Gaba daya suka dube ta, Ummita kuwa ganin idanun Tasleem a kanta ya sanya ta ɗago me take son fadi, wato dai itama ta gane tana da ciki don haka sai ta mike da sauri-sauri ta shige daki saboda kukan da ya tahomata na tsantsar damuwa. "Me aka yi kike mana ihu? Ita kuma wannan me aka yi mata ta miƙe?" Futuha ta jero tambayoyinta lokaci guda.  Tasleem ta cafe zancen tana kara hura hancinta da ya buɗe saboda ciki. "Ciki na gani jikin yarinyar nan." A razane Futuha ta buɗe idanunta ta dubi Humaira da kuma Raihana sannan ta maido hankali ga Tasleem. "Wa kenan?" "Ummita mana. Mun shiga uku, shikenan yarinyarnan za ta ɓata sunan gidanmu, image din gidanmu zai lalace a idanun duniya. Meyasa ba a zubar da cikin ba Mami?" Humaira wani tururi zuciyarta ke yi na ɓacin rai, wato ita Tasleem ba ta ko tausayawa halin da Ummitan ke ciki ba balle tayata jimami. Kamar ta tofa sa kuma albarkacin Mamin dake zaune a wurin ta ja baki ta kuma zuba idanu ga Mamin don ganin me za ta ce. Mami kuwa ta gefen idanu ta ga irin duban da Humaira ke mata don haka nan da nan ta daure fuska. "Idan ita ba ta ɓata mana suna ba, ke gashinan ai kina ihun da makwafta za su ji su fahimci halin da muke ciki! Wannan wane irin rashin tunani kike aikata mana? Kina haukar tonawa yar uwarki asiri?" Jin haka sai Tasleem ta koma ta zauna, ta ja guntun tsaki ba ta ce uffan ba. Ita wannan duk bai dameta ba kamar yanda kawayenta da dangin miji da ma abokan hulda da ake kunya za su samu labarin cikin Ummita ya zamar musu abin habaici da zagi. Futuha kuwa, babu abin da take hangowa sai irin yanda labarin zai karaɗe social media alhalin ta gama karaɗe ko'ina da nuna hotunan su Ummita tana shaidawa duniya su din kannenta ne. Yanzu idan zancen nan ya fita ai ta shiga uku. Yassar ne ya basu labarin duk fadi tashin da aka yi don ganin an zubar amma abu ya faskara. Tasleem ta ja tsaki karo na biyu. "Ba dai abi hanyar da ta dace ba. Ni wallahi da tun farko an faɗamin da kaina zan zo na yi mata alluran da na tabbatar sai cikin ya zube. Amma yanzun ma ai ba ta ɓaci ba, me zai hana a markaɗe shi?" "Wai Sis Tasleem meyasa ba ki da imani ko ƙanƙani? Kina magana babu ruwanki idan an yi ko Ummita ta mutu ta rayu." Tasleem ta harzuƙa da zancen Raihana. "Da wannan abin kunyar ba gwara ace ma mutuwar ta yi ba! Ai gwara mu lulluɓe ta cikin sutura a kai ta kabarinta da dai ta haifa mana shege." "Sai dai ke ki mutu! Ai dama wanda bai sonka ba zai taɓa sonka ba. Na kuma gama gasƙatawa ke din azzaluma ce da ba kya kaunar naki. Ciki kuma ƙaddarar Ummita ce da bai wuce faɗawa kan kowa ba koda kuwa matar auren ce. Nawa aka yi? Yanda ba kya kaunarmu har abada ba zamu taɓa kaunarki ba, yanzun ma albarkacin masu albarkar kika ci da ban ɗaga yatsuna na watsa a saman fuskarki ba." Humaira ce ke wannan zantukan cikin tsananin rufewar idanu jikinta har tsuma yake yi. Tasleem ta yi laƙwas, ina za ta mance shaƙar da ta yiwa Anti Jannat, me ya yi mata zafi da za ta yarda ta yi katoɓarar da itama za a shaƙe ta ga tsohon ciki. Falon gaba daya aka rasa mai tankawa Humaira, su Yassar wadanda sun soma hankali sun ragewa zuƙatansu ƙiyayyar Humairar ba wanda ya goyi bayan zantukan Tasleem din. Mami kuwa kamar yanda ta saba danne bakin cikinta da soyayyar yarannata a lokuta barkatai don siye zuƙatan yaran wannan karon ma haka ta yi. "Koda wasa kar na ƙara jin makamanciyar wannan magana daga bakinki. Kina kiran mutuwa ga yar uwar da ke ganin girmanki. Ban san me yarannan suka tare maki ba. Kina dai kan gaɓar haihuwa ki ji tsoron Allah." Mami na kai wa nan ta mike tana ɓata rai ta kama hannun Humaira suka yi daki wurin Ummita. Itama Raihana ta mara musu baya. Tasleem ta ja tsaki. "Ni ban ga amfanin abin da Mami take yi ba. Duk lalacewar naka, naka ne. Ta guji ranar da wadannan mutanen za su yi mata butulci." "Uwar biyu kenan, sai kin zauna da su sosai za ki fahimci ba su da kowace matsala. Ni kaina a farko rashin ba Humaira dama ya sanya ni tsanarta amma yanzu da na dan zauna na saki jiki da su na fahimci kirkinta. Wallahi sosai na tausaya musu sadda suka yi nesa da mu, na kuma gane ina kaunarsu a jinina, ba zan iya fasalta yanda labarin cikin nan ya jefa ni ba. Duk da ban kai Yaya Mubarak shiga damuwa ba." Fitowar wannan zancen daga bakin Dawud ya ba Futuha da Tasleem mamaki, dama akwai ranar da Dawud zai fadi mai kyau akan su Humaira? Yassar wanda shima bai jin ƙinsu ko kuma kaunarsu a zuciyarsa, dariya ya yi. "Kai babban yaya ai ya faɗa, rannan Anna ke fesamin wai son Ummitan yake yi. Tana ta masifa da tsinewa zancen ta ce ko bayan ranta ba da yawunta ba." "Wallahi ba za ta saɓu ba. Tab! Me Yaya Mubarak zai yi da sauran ƴan ta'adda?" Futuha ta yi furucin a zafafe. Tasleem kuwa ta ma kasa cewa komai ji take kamar abin da ke cikinta zai fito idan ta ƙara magana saboda tsabar takaici da ya yi mata lulluɓi a ƙirji. "To sai me? Ni wallahi don ya riga ni furtawa ne amma na ƙudurta ni zan aure ta matukar wancan Sahabi ya guje ta." Cewar Dawud. Kiran sallar azahar ne ya tashi mazan, Tasleem ta dubi Futuha. "Me kike tunani akan maganar cikin nan?" Futuha ta yamutse fuska. "To me zamu iya yi tunda an binne zancen ba a sanar da mu ba sai da ya fito?" Tasleem ta yi ƙwafa. Ta ciro wayarta ta kira Jannat ta fesamata abin da ke afkuwa. Jannat ta feshe da muguwar dariya. "Dakyau! Ki ce abu ya yi dadi? Toh ai wannan maganar ba abin a ɓoye ba ne. Ke ban da abinki tunda har ya afku ai zai fito. Kawai mu juya zancen mu yaɗa cewar dama karuwancinsu suka tafi, itama Humaira an keta mata haddi. Idan har duniya ta yarda ta amince kinga ai shikenan? Ban da Abbanku da DPO akwai wani da ya san an gan su kafin a kama su sun gudu?" "Aa." Tasleem ta furta da sauri. "Toh kinga idan ma an bada wannan hujjar zamu ce a kawo shaida, wacce kuma babu ita ba za a same ta ba." Shiru dai Tasleem ta yi, Futuha ta zubawa Tasleem idanu, so take ta kammala wayar don ta labarta mata abin da Antin ta ce. "Anti toh dan jira zan kiraki." Daga nan suka ajiye waya, ta labartawa Futuha yanda suka yi. Tun ma kan akai aya Futuha ta hau girgiza kai. "A'a, a'a, Tasleem kar ku yi haka. Nidai Futuha babu hannuna ciki. Ba fa sunansu kadai za a ɓata ba kenan har da na gidanmu. Nikam ba za'a yi haka da ni ba gaskiya, count me out!" Tasleem ta harareta kawai sai ta yi shiru ba ta ce uffan ba. Futuha ta zubamata idanu, ta san halin muguntar Tasleem, shirunta na nufin abubuwa da dama. "Ina fatan dai ba kina son cemin za ki haɗa kai da Anti Jannat ku aikata wannan babban kuskuren ba?" "Sai aka ce maki bani da hankali ko? Mtsw." Ta ja mata tsaki ta mike ta nufi dakin Anna amma ta gama ƙudurtawa a ranta babu fashi. Idan har ƙimar ita kanta ƴar tiktok Futuha zai taɓu a zage ta a idanun duniya toh wannan daidai ne. Gwara ma su yi hakan kawai. *** Mami ta taushi Ummita dakyar ta samu ta yi shiru, ta yi musu ƴar nasiha sannan ta fito. Kai tsaye dakinta na nufa ta dauki waya ta kira Hajiya Lubna. Komai dake afkuwa ta zayyane mata. Ta kara da faɗin. "Yarannan sun tada hankali lallai sai dai a zubar da cikin Ummita, kinsan dai yadda muka yi da Sadik Wizzy. Ina tsoron su kwatanta wani mugun abun." "Haba Maryam, sai ka ce ba ke kika haife su ba. Ba za ki yi musu jan ido ba? Wai ni Maryam duk ba wannan ba, ina aka kwana batun kai Humaira wajen Babandi?" Mami ta sauke ajiyar zuciya gami da ƙara gyara zaman wayar. "An kashe wannan zancen, gobe zan kai ta. Na fi so a yi a ƙare, na gaji ba zan iya ci gaba da wannan pretending din ba. Idan an hana ta auruwa a tura ta bariki kawai mana ba shikenan ba? Na tsani wannan Fadeel mai baƙin nacin tsiya, Babandi ya tabbatarmin muddin dai bai fice a rayuwarta ba to lallai shi zai rusa komai. Mun kasa jefa mata ƙiyayyarta a zuciyarsa kamar yanda ita muka jefamata, ba na nasa kaɗai ba har na dukkanin wani namijin da zai furta mata kalmar so. Kamar kuma yadda muka yi wa FATIMA har ya zamo silar rabuwarta da Yusuf. A ƙarshe kuma muka zama ajalinta ta hanyar yi mata turen aljani ya kashe ta." Wannan zancen ne ya yi dirar mikiya a kunnuwan Futuha wacce ta nufo Mami don sanar da ita yanda suka yi da Tasleem, ta tsaya cak a ƙofar ɗakin cikin wani irin kakkarwar jiki da zufa. Juyowar da  Mami za ta yi ta ga mutum tsaye cak a bakin ƙofa, ba ƙarama razana ta yi ba wannan ya sanya ta ajiye wayar cikin rawar murya ta ce. "Ke kuma me ya kawoki nan?" Futuha ta karasa shigowa dakin sosai har lokacin bakinta a hangame saboda tsananin mamakin da ya gama baibayeta. "Mami, duk ke kika aikata waɗannan abubuwan?" Cikin sauri Mamin ta ƙarasa ta rufe ƙofar ɗakin, ita dai Futuha bin ta take yi da kallo har lokacin kamar a ranar ta soma ganinta a duniya. Cikin kausasshiyar murya ta amsa. "Eh ni ce, na aikata kuma ina kan aikatawar, ina kuma gargadinki da babbar murya! Bar ganin kin fito daga tsatsona na rantse maki matukar kika yi gangancin tonan asiri koda a wurin yan uwanki ne sai na manta da ni na haifeki, zan iya daukar kowane irin mataki muddin dai buƙatana za ta biya." Futuha ta jinjina kai ta kasa ma cewa uffan don gani ta yi tamkar wata Mamin ce daban a gabanta. Sai kuma ta daure ta hadiye fargabanta ta ce. "Mami, kenan duk wannan kauna da muke gani kamar kin fi yiwa su Humaira a kanmu duk ba gaske ba ne? Har fa kidnapping din da aka yi naji kin ce ke ce." Ta juya tana wani mugun murmushi ta karasa ga madubi tana kallon kanta. "Wawaye, ina ku ka taɓa gani ko ji uwar da ta so ɗan wani sama da nata? Babu ita kaf faɗin duniyarnan. Idan ma akwai toh ni Maryam ba na cikinsu." Sai ta ƙara sakin murmushi mai haɗe da ƴar dariya. "Tun auren Yusuf da Fatima, nake ƙunshe da baƙin ciki a zuciyata, kakkarfan shaidar da aka yimin a garinmu da ma makwaftan da muka zauna da su a garin nan kafin rasuwar mahaifina na cewa ina da baƙin kishi kuma har akan kishin ne na taɓa marin (wani ɗan uwana da mahaifina ya so na aura) a bainar jama'a, na zazzagi uwa da ubansa kawai don ya ambatamin sunan tsohuwar budurwarsa kuma yar uwata da aurensu bai yiwu ba yana mai yabonta a kan idanuna. Tun daga wannan ranar ne na fasa aurensa. Ba shi kadai ba, na rabu da mutane da dama saboda kishi, saboda tsanar da na yiwa kishiya, mahaifina ya taɓa neman aure na wanki ƙafa har gidan da ya je nema na ɓata sunansa kuma aka fasa auren. Baƙin shaidar da na samu sanadiyyar zazzafar kishi ya sanya da Yusuf ya shigo rayuwata matsayin saurayin da bai taɓa aure ba, ya shiga zuciyata sosai. Na sa a raina ba zan taɓa nunamasa zazzafar kishina ba saboda a lokacin labarin komai da na aikata a baya ya je kunnensa ta wurin munafukai, wannan ta sanya ya yimin gwaji kala-kala kamar ya yimin wasan yana da mata auren haɗi, yana da budurwa da dai sauransu. Ni kuma na danne bana nuna masa ɓacin raina har sai da ta kai ya ƙaryata zantukan mutane a kaina. Amma fa duk radda ya yimin irin wannan idan na koma gida ranar ko tsinke ba zan ɗauke da sunan aiki ba, kuka kuma zan yi shi. Babu wanda ya isa ya taɓa ni a ranar ya sha. Mahaifina ya rasu dab da aurena da Yusuf. Bayan aurenmu babu irin faɗi tashin da ba mu sha ba saboda rashin kuɗi. Soyayyar da nake yiwa Yusuf ta sanya ban taɓa gujemasa ba daidai da kwayar zarra. Kasuwanci iri iri babu wanda bai yi ba har siyar da kayan miya, gwanjo, da dabino. Kowanne sai an fara rimi-rimi sai lamarin ya ɓaci." Mami ta haɗe girar sama da ta ƙasa ta juyo tana duban Futuha dake tsaye tana sauraronta ta cigaba da magana. "Mahaifin Ummita ya fi mijina rufin asiri sosai, shi mutum ne mai arziƙi, matarsa duk sabgar dangin miji ta fi kowa gayu da kuma kyauta saboda mijinta yana da kuɗi. Ba ta da taƙama balle wani abu wai shi girman kai, wannan kyawawan ɗabi'unta da na tsana, da su ne ta siye zuƙatan uwar mijina kafin ta rasu, ta yi bake-bake a wurin yan uwan Yusuf, ba a ganina da mutunci sai ita. Duk yawan kirkina saboda mijina ba shi da kudi sai na zama tamkar mujiya. Eh uwar mijina tana sona amma soyayyar da take yiwa Jamila ya wuce gejin nawa. Saboda tsabar yanda tsanar Jamika ya rufemin idanu har gani nake yi ba a nunawa yarana kauna a lokacin alhalin ita ko haihuwar ba ta samu ba daga ta samu cikin sai ya ɓare. Haka na jero yara biyar Mubarak,Yassar, Dawud, Ƙassim da kuma Ke. Wannan  lokacin ne kuma Yusuf ya zo min da labarin ƙara aure bayan mutuwar mahaifiyarsa, a sannan kuma ba laifi asirinmu a ɗan rufe yake. Yusuf har shago yake da shi a kasuwa yana siyar da kayayyakin agogo wanda ƙaninsa Muntari ya buɗe mishi. Wannan ma ya ƙara tsananta tsanar Jamila da Muntari a zuciyata ganin wato dai arzikinsu muke ci, da azumi haka Muntari ke sauke mana kayan abinci, da sallah, Jamila ke zuwa ta kawomana kayan fitar sallah wannan abu ya tsayamin a ƙahon zuci. Maijidda ita ce macen da ta soma lura da tarin ƙiyayyar da nake yiwa yar uwarta, akwai sadda ta taɓa ganina muraran ina yiwa Jamila barbaɗen magani a abinci wanda daga shi ne ta tsane ni ta kuma ce Jamila ta yi hankali da ni.   Toh zuwan da Yusuf ya yi da batun ƙara aure ya yi mugun ɗagan hankali amma damuwa ko ta ɗigo ban gwada masa ba, a farko da na ɓata rai, sai ya rude da rarrashina, sai kawai na fashe da dariyar baƙin ciki na nunamasa tsokana ce kawai amma nikam bani da matsala da aurensa. Da wannan ya auro Fatima wacce ya haɗu da ita a kasuwa ta rako Dadarsu siyayyar kayan auren dan uwanta Umar. Shikenan soyayyar ta kai su ga aure. Anna ba ta tare da ni a sannan saboda mijina ba shi da kudi babu wurin da zamu ajiye ta, ita kanta a sannan zagina take yi wai don me zan maƙale nace sai Yusuf da ba shi da ko keken hawa. Nidai son da nake yi masa ya hana ni karɓar ƙorafe ƙorafenta. Ba ta damu da zuwa gidana ba a lokacin. Aka yi auren Fatima da Yusuf, jininta ya hadu da Jamila. Madadin ni da muke dan shiri da Jamilar a baya, sai suka dinke da Fatima suka zama tamkar wasu ƙawaye, a sannan ina da cikin Tasleem, na kai zuciyata nesa na danne da taimakon shawarar sabuwar ƙawata Lubna da muka hadu a wurin wani bikin tsohon ubangidan Yusuf na kasuwa, mijinta mai arziki ne lokacin yana rike da matsayin Chairman. Da taimakonta na san Boka Babandi, muka niƙi ƙafa daga nan har Katsina wajensa ba tare da sanin Yusuf ba. Na samo magungunan hana Fatima daukar ciki muka dawo. Cikinta na farko kuwa ya bi rariya, ni ce mai jinyarta da nuna mata ƙololuwar kulawa. Dadarta koda ta zo ta dinga sanyamin albarka da yabona. Yusuf kuwa tamkar ya haɗiyeni ganin a lokacin ko arba'in din Tasleem ban yi ba na haihuwa amma ina fama da kula da Fatima, wannan dalili ya siyomin sabuwar kauna a zuƙatan yan uwan Yusuf.   Kamar kuma a mafarki ina dauke da karamin cikin Raihana sai ga Fatima da ciki har watanni biyar ya soma fitowa a jikinta, ba karamin firgita nayi ba da na gani saboda ko kadan ban ga wasu alamomi ba. Kuma na rasa yanda aka yi ko a hira ba ta sanar da ni ba. Hankalina ya yi mugun tashi, sai da na kai zuciyata nesa sosai kafin na iya danne damuwata. Ga wani irin soyayya da Yusuf ke nunawa Fatima har a gabana wanda nake ji kamar na shaƙe su duk biyun na huta. Ganin haka ni da Lubna muka ƙara miƙar hanya wurin Babandi, anan ne na je masa da buƙatar jefa tsanar Yusuf a zuciyar Fatima yanda ko sunansa aka ambata sai ta ji haushi. Babandi ya ban tabbacin ba ma Yusuf ba, kowane namiji sai ta tsane shi a rayuwarta muddin ya haɗa ta da wani arnen aljani. Da wannan na tattaro duka chanjina na ajiyemasa. Muka rabu da zummar zan ga aiki da cikawa, ya kuma ban wani hayaƙi yace duk sadda ta shiga halin ƙunci da kuka marar iyaka na yi mata hayaƙin. Wannan zai ƙara tasirin tsanar a zuciyarta. Da wannan muka rayu, Yusuf ya shiga tashin hankalin sauyin Fatima. Akwai radda ta taɓa shaƙe masa wuya dakyar aka ɓamɓare ta sai da na nemi taimako a waje, daga wannan ne kuma ya aikawa Dada saƙo ta zo takanas daga Nijar aka tafi da Fatima saboda ta rantse muddin aka bar ta ta cigaba da rayuwa a gidan za ta kashe shi ko kuma ta kashe kanta. Na yi kuka sosai kamar raina zai fita a gabansu, na ce su kyale ta ayi mata magani a nan idan har larura ce, Dada ta dinga rarrashina ta ce gwara ta tafi da ita. Daga wannan ranar ne na rabu da Fatima, rabuwar da har gobe ba ta ƙara tako Nijeriya ba. Wannan abu ya yimin masifar dadi, cikina nada watanni shida, Jamila ta haifi ɗiyarta mace mai sunan mahaifiyar Jamila, Rahina suke kiranta da Ummita. Sun yi gagarumin sunan kashe kudin da naji tamkar na dora hannu a ka nayi ihu da kuka  ina ji inama Yusuf keda kudin Muntari. Da wannan na soma tunanin duk runtsi sai dukiyar Muntari ta zama rabon Yusuf watarana." Mami ta numfasa ta karasa ta zauna gefen gado, ganin haka Futuha itama ta nemi wuri ta zauna, wasu abubuwan za ta iya tunawa wasu kuwa ba ta da wayo. Ta dai san Mubarak na yawan yabon mahaifiyar Humaira da kaunar da ta nunamasa, yayinda su Yassar suka tsaneta saboda tsanar da ta yiwa Abbansu. Maganar Mami ya katse tunaninta. "Haka rayuwar ta cigaba har na kusa haihuwa, Yusuf gaba daya ya rame ya tashi hankalinsa saboa Fatima, ya kai mata ziyara har sau biyu daga nan ne hankalina ya yi mugun tashi, wato soyayyar da Yusuf ke yiwa Fatima ya ninka nawa kenan? Ban yi ƙasa a gwuiwa ba, ban kuma damu da cewar tsohon ciki gareni ba, na bi shawarar Lubna na niƙi ƙafa na koma wurin Babandi. Nan na nemi a yimin aikin da zai sa a raba Fatima da abinda ke cikinta da duniyar ma baki daya. Ya nunamin yanzu haka da muke magana Fatima naƙuda take yi, ya tabbatarmin zaa turamata baƙaƙen aljanun da za su yi sanadin rayuwarta. Na yi murna kwarai, amma abin baƙin ciki ya cemin abin da za ta haifa dole zai rayu a doron ƙasa, nidai ban wani damu sosai ba. Koda ya gama dubansa ya ce aikin zai yiwu haka na tattara na tafi da farin cikin Fatima za ta bar duniyar baki ɗaya. Za ta bar mijina. Sati uku da haihuwar Fatima, labari ya zo mana na rasuwarta. Zo ki ga kuka a wurina kamar zan shiɗe. Na nuna zan je gaisuwa, amma Yusuf ya hana ni saboda cikina ya shiga watan haihuwa, da wannan hujjar ya tafi har ina ce masa ƙafarsa ƙafar jaririyar Fatima ya kawomin ita zan riƙe. Wannan ya sa Yusuf ya ji dadi sosai ya dinga yimin godiya bisa kaunarsa da nake. Har a zuciyata addua nake kada a ba shi Humaira ya kawomin. Aikuwa haka ya dawo babu ita ya cemin wai Dadar ta daukarwa Fatima alƙawarin kula da Humaira, ya yi hakuri. Daga nan fa rayuwa ta dawomin sabuwa fil a gidan mijina. Daga ni sai yarana, na haifi Raihana bayan Jamila ta haihu da kusan watanni shida, Humaira na da watanni hudu itama lokacin. Shekaru suka tafi har aka shekara biyar, zuwa lokacin rayuwar kunci da talaucin ya ishe ni, samun Yusuf ya ja baya sosai. Gaba daya ya zamana hatta kudin makarantar yara daga aljihun Muntari yake fita, wannan ya kara sanyamin ƙiyayya mai tsanani na Muntari da Jamila. Ban samu sukuni ba har sai da na biya wasu yara suka haɗa gobarar da ba a fitar da komai a gidan Muntari ba sai Ummita." Idanu waje Futuha take duban Maminta wannan karon. "Ma..ma.." Ta ma kasa magana taabar firgicin da ta shiga da tsananin ruɗani. Tana kara tabbatar da nisan da mahaifiyarta ta yi a fannin da suke ganin sun fi ta. Mamin ta yi yar dariyar mugunta. "Yes, ni na sanya aka ƙona iyayenta, aka kashe jaririyar da Jamila ta haifa da Jamilar ma. Ban san ya aka yi shegiyar yarinyar ta tsira ba. Haka labarin gobarar ta zo mana, hankalin kowa ya tashi ciki har da ni da na nuna ban san komai ba. Shegiya Maijidda tun a sannan ta nuna ita wallahi ba ta amince gobarar gaske ce ta kashe Jamila ba. Ta ce a bincika amma kowa ya yi burus da ita ga tunaninsu kawai zafin mutuwar Jamila ne saboda irin shaƙuwar da suka yi da juna. Da nayi wani tunani akan dukiyar Muntari sai na shawarci  Yusuf akan ya ɗau riƙon Ummita kar a raba ta da dangin mahaifinta. Nan fa ya amince, ya kuwa dage akan lallai shi sai an ba shi Ummita. Sun so yin fada da Maijidda wacce ta dage lallai ita za ta dauketa, a karshe dai da Kawunnansu suka sanya baki dole ta hakura ta kuma kalleni ta bini da Allah ya isa. Na fashe da kuka ina nunawa jama'a Maijidda ta tsane ni, nan aka hau rarrashina har yan uwan Jamila ana ganin baƙin Maijidda. Yusuf har kusan faɗa ya yi da Maijidda a kaina dakyar dai komai ya lafa. Wannan shi ne silar dawowar Ummita hannuna, daga baya kuma Humaira ta zo wannan kin sani." Futuha ta ja dogon numfashi. "Tab! Mami kina da abubuwan mamaki sosai. Wallahi ba don ke da bakinki kike fadamin ba, da ace a wani wurin na ji dukkan wadannan zan ƙaryata ko waye ya faɗi." Murmushi Mami ta yi. "Ku ne ba ku san rayuwa ba, yanzu da ace wani mugun halin na nuna a zahiri, kuna zaton Abbanku zamu kai yanzu da shi ba tare da mun rabu ba? Ko kuwa kuna tsammanin a baya ida  kishi ya kwashe ni na kashe Fatima da hannuna yanzun zan cigaba da rayuwa a duniya? Ai hakan ba zai taɓa afkuwa ba, komai ɗan hakuri ne da bi sannu-sannu. Ka yi siyasa a komai, ka shanye komai ka danne sai ka ci riba. Ina dab da cin ribar kwace dukiyar Yusuf saboda na faranta maku, na ba yarana maza jari su huta daga maƙon da Yusuf ke yi musu, na kuma nunawa Anna ba Firdausi Jannat ce kaɗai ɗiya ba, nima na san yanda zan iya kwatar kaina a wurin miji, wannan ne dalilin daya sa na sanya aka sace yarannan, sai dai kuma kuɗaɗen su na dab da samuwa, komai ya rushe saboda zuwan ƴan sanda. Amma ban saduda ba, ban kuma karaya ba, har gobe ba zan fasa yunƙurin ƙwatarwa yarana haƙƙi ba tunda ubansa marowaci ne mai shegen maƙo." Fuska a sake Futuha ta rungume Mami kafin ta saketa ta ce. "Wai Mami ashe daman kina kaunarmu?" Harararta ta yi. "Wa ye ba ya kaunar nasa? Na fadamaki ai duk duniya wanda za ki ga ya nuna ba ya son nasa ya fi kaunar wasu toh ƙarya yake yi, munafuki ne." Jinjina kai Futuha ta yi tana washe baki. "Hakane, Mami na kara sonki wallahi. Kin wanke tunanin dake zuciyata na ganin bakya kaunarmu. Ni fa lallaɓa Humaira nake yi so nake ta zo gidana ta koyawa yar aikina girke-girke. Shiyasa kika ga ina ta janta a jiki da kissa." Mamin ma dariya ta ce. "Sai ki bada himma." Sai kuma ta daure fuska sosai. "Ina kara jaddada maki, koda wasa kika yi yunkurin sanar da wani ko wata labarinnan wallahi zan iya kashe ki." Sosai furucin ya tsoratar da Futuha, ta yi saurin rike hannunta. "Aa Mami, wallahi na rantsemaki babu wanda zai ji. Ai ina sonki, ba zan so hukuncin shari'a ko yaya ya hau kanki ba." Sai anan ta saki fuska ta shafa kan Futuha. Daga haka suka bar zancen suka koma falo inda Tasleem suke zaune da su Mubarak ana cin abinci. Ko kallon Futuha ba ta yi ba, tsanarta take ji a zuciya, wato saboda tana da kudi shiyasa har wani shiga daki suke su rufe su na kwasar hira ita da Mami. A duniyarta ko a mafarki aka ce Futuha za ta samu miji wanda ya fi nata za ta ƙaryata. Ga Hamza yanzu ya sauya mata, zamansu gaba daya babu dadi hatta a bangarenta da uwar mijinta da ma yan uwansa. Albarkacin cikin jikinta kawai take ci ta san da wannan. Don ma dai Anti Jannat ta ce ta kwantar da hankalinta har ta haihu sannan su san yanda za su ɓullowa lamuran. Wannan ne kadai ya sa ake ganinta cikin nutsuwa, kuma ita dinma ba ta ragawa Hamzan. ***   Da yammacin ranar daidai lokacin da su Futuha suka fito da zummar tafiya gida har da Tasleem wacce za ta sauke nata gidan sanadiyyar Hamza da ba  zai samu zuwa daukarta ba, sai ko Humaira wacce a dole ba don ranta ya so ba bisa umarnin Mami za ta bi Futuha gidanta ta yi zaman sati biyu kawai don ta koyawa yar aikinta girke-girke, su Raihana sun yo musu rakiya farfajiyar gidan. Humaira tana tuno Fadeel wanda ya ce yana hanya, tana son ta dakata ta jira shi amma wata zuciyar na kwaɓarta da nuna mata babu amfanin sauraronsa tunda ba aurensa za ta yi ba. Suna nan tsaye, tana sanye da yadi mai taushi maroon colour wanda ya fiddo tsantsar kyawunta da hasken fatarta, ta ɗora karamin mayafi a kanta golden colour. Babu kwalliya ko na ɗigo a fuskarta amma kuma sosai kalar ta karɓe ta, zama wuri ɗaya babu fita ya sanya har wani sheƙi fatarta ke yi. Daidai sadda Futuha ta bude ƙofa tana shirin shiga, daidai lokacin maigadi ya wangalewa Fadeel ƙofa ya turo da hancin motarsa ciki. Bisa umarnin Abba, Fadeel ya zama ɗan gida, duk sadda ya zo yana da damar da zai yi parking a farfajiyar gidan. Ya kuma shiga idan an mishi izni su gaisa da mutane. Shi din ne dai ya zaɓi rashin zuwan akai-akai saboda gudun kada ya baƙantawa Humaira ta ga kamar yana neman shigarmata hanci da ƙudundune alhalin gidansu ne. "Wannan motar kuma fa?" Fadin Futuha tana karewa motar kallo, lexus Ls blue black sai sheƙi take yi, daga gani ba a moreta sosai ba don ba ta nuna alamun tsufa ba. "Wannan motar Fadeel ne. Na gane, ya taɓa zuwa da ita sau ɗaya wurin Abba." "Fadeel?" Tasleem da Futuha suka nanata sunan a zahiri. Aikuwa kafin su rufe bakunansu haɗaɗɗen matashin nan mai sa numfashin yan mata tsayuwa na wucin gadi ya fito daga cikinsa. Sanye yake cikin maroon tshirt da baƙin wandon jeans kamar da hadin baki shi da masoyiyartasa. Ya rufe idanunsa da baƙin gilashi yana wani murmushi mai ruɗar da zuƙata. Duhun kayan da ma motar da yake jingine a jikinta sai suka kara fiddo da tsantsar farinsa na usulin bafalutani ɗan asalin garin Yola.  Gaba daya Tasleem ta yi wani shock, suka yi mutuwar tsaye. Idanunta har wani ruwa-ruwa yake yi saboda tsabar kallonsa da ta shagala yi ga wani irin so da kauna dake fisgarta har ta mance da wasu igiyoyi masu ƙarfi da suke nannaɗe da ita suka yi mata shamaki da dukkan wani ɗa namiji da ba muharraminta ba. Shi kuwa Fadeel idanunsa a saman na Humaira har dai su Yassar suka karaso aka yi musabaha. Humaira kuwa ta yi wani irin dauke kai daga kallo daya ba ta ƙara ba. "Wajenki ya zo ne?" Futuha ta wurga mata tambayar tana ɗan murmushin yaƙe, a ranta kuwa jinjinawa Mami ta yi, tabbas ba karamin kokari tayi wurin danne abin da ke ƙasan ranta ba, akwai masifar wahala. Sosai itama ta ji kishin ace Humaira ce ta samu wannan kyakkyawan matashin kuma mai rufin asiri. "Ban sani ba." Amsar da Humaira ta bayar kenan tana ƙara tamke fuska. Tasleem kamar ta shaƙe ta, yarinyar ta samu dama amma tana nuna girman kai. Ita da ace itace da wannan damar ai sai inda ƙarfinta ya ƙare. "Assalamu alaikum." Sallamarsa ta katse musu tunani, Raihana ta jingina jikin Humaira dab da kunnenta ta ce. "Ki riƙe wannan bawan Allahn sosai idan kuwa ba haka ba ni zan maye gurbinki." Ba ta san ya aka yi ba sai tsintar idanwanta ta yi da wurgawa Raihana wata muguwar harara mai nuni da tsantsar kishi, Raihana ta sa dariya tana riƙe kunnuwa gami da ɗan jujjuya kai alamun ta tuba. Tana kuma kara gasƙatawa Humaira na son Fadeel, ba kuma ta san abin da ya danne wannan soyayyar ba. Tasleem ta amsa sallamarsa ciki ciki yayinda Futuha ta saki fuska sosai aka gaisa sannan ya dubi Humaira da shanyayyun idanunsa bayan ya cire gilashin. "Boddo, barka da yamma." Ya fadi yana mai ɗan dunƙule hannu da ɗan ranƙwafar da kai kaɗan tamkar wani basarake. Nan fa gaba ɗaya idanun ya koma kansu ana ganin ikon Allah. *LITTAFIN NAN NA KUƊI NE. SIYA AKAN NAIRA ₦400 KI KARANTA BA TARE DA SHIGA HAKKI BA.* *5407827015* *FCMB* *Farida Abdullahi* 09034973645 Ba ta ce uffan ba sai idanuwanta da ta sauke a cikin nasa. Ya ji kallon har a ƙasan ransa. "Sauri fa muke yi." Tasleem ta furta cikin ɗaure fuska, gaba ɗaya wani irin mugun kishi ke cin zuciyarta. Fadeel bai ko kalle ta ba ya dubi Futuha. "My sis, ko za ki ban aron ƙanwartaki for just 5mins?" Murmushin da bai kai zuci ba Futuha ta yi. "Ba ka da damuwa. Humaira jeki." Humaira da ke jin kamar ta shaƙo wuyan Fadeel amma sai ta kasa yi mishi musu ta bi bayansa sadda ya yi gaba zuwa inda ya ajiye motarsa. A jikin motar suka tsaya su na hangen su Futuha da ke hira sai ko Tasleem da ta zubamusu idanu tamkar makauniyar da ta samu ido. "Ka kirani kuma sauri muke za mu tafi." Ya ji babu dadi daga yanayin muryar da ta yi mishi magana, ya dai daure ya haɗiye kamar koyaushe. "Humaira kina addu'a sosai kuwa? Kina nafilfiloli da sallar dare? Kina mayar da hankali wajen yawan karatun Alkur'ani?" Ta yi shiru kamar ruwa ya cinye ta, ta sani tana sallolinta biyar akan lokaci, tana kuma addu'a daidai gwargwadon yinta, amma yawan karatun Alkur'ani da kuma sallolin dare da ma nafila ba za ta iya buɗe baki ta ce mishi aa a kansu ba, kawai sai ta ji hakan ya yi mata nauyi a saman harshenta. Ya tsinci amsoshin tambayarsa daga shirunta, don haka ya cigaba da magana a nutse ba tare da ya dauke idanu daga saman fuskarta ba. "Salollin farillah wajibi ne Humaira, amma su Nafiloli neman ƙarin lada ne da kusanci ga Ubangiji. Za su buɗemaki ƙofofin rahma wadanda ba ki taɓa zato ba. Hakanan shi kansa karatun Alkur'ani, yawan tilawarsa da yin azkar safe da yamma zai ba ki kariya daga shaiɗanu da ma jinnu. Babu wani ko wata ko kuma wani abun da zai cutar da ke. Ina roƙonki ki yawaita addu'a, ina kuma ba ki shawarar yawan hailala, istigfari da salatin Annabinmu s.a.w. Ki ɗauka tamkar wani ɗan uwa ne gareki na jini yake ba ki wannan shawarar. Kin yarda kin amince za ki amfani da ita?" Ba ta taɓa jin wani irin sanyi da nutsuwa tattare da kasancewarta da Fadeel ba sai a yau kuma a yanzun da yake kwararo mata waɗannan shawarwarin. Sai gaba daya ya tuno mata da Kawunta da ma Dada, ta tuna da kalar rayuwarta a Nijar, koda wasa idan ta idar da sallah, Dada ba ta barinta ta bar saman darduma sai ta yi nafila ta kuma tsaya ta ga ba ta yi wasa da addu'a ba, hakanan tilawar Alkur'ani, duk juma'a Kawunsu na tattara su har yaransa su yi tilawa, kowacce ta biya inda ta iya. Shaiɗan kwarai ya yi tasiri a zuciyarta da har ya sanya ta yi watsi da dukkan wannan, ta zama daga ta idar da sallar asuba sai bacci ba kamar a farkon zuwanta Kano ba da ma rayuwarta a Nijar inda koda wasa ba ta isa ta koma shimfaɗarta ba har sai rana ta fito bisa koyarwar Dada. A farko tana yi daga baya duk ta watsar. Ummita duk ta fi wannan kokarin. Ita kuwa kasala ya mata yawa. "Kinji? Please." Ya kara nanatawa. Ta dube shi sai ta yi murmushin da rabon da ya gan shi saman fuskarta har ya mance. Ta gyada mishi kai. "Naji, nagode sosai da tunatarwa kuma zan kiyaye in sha Allah." Ai sai ya ji tamkar an jefa shi wata duniyar ta nishadi da farin ciki, sai kawai ya rasa me zai ce ban da leɓe da ya ɗan lasa yana maida mata martanin murmushin. Ƙarar hon da aka danna da ƙarfi ya sanya suka dubi wajen, har ga Allah shi Fadeel ya ma mance adadin mintocin da aka yi mishi alfarmarsa, balle kuma Humaira da ta lula tunanin sakancin da take yi da addu'a tun zuwanta garin. Tasleem ce da wannan aikin ranta a mugun ɓace. "Nagode, kije suna jiranki. Sai mun yi waya ko?" Ta ji tamkar ta ce eh, sai kuma ta fasa ta juya kawai ta kama tafiya, ya bita da kallo sai kuma ya buɗe motarsa ya shiga, ya sani Abba ba ya nan balle ya shiga su gaisa. Don haka ya yi ribas aka buɗe gate ya fice. Itama tana shiga gaban motar kusa da direba, direban ya ja suna ɗagawa juna hannu ita da Raihana. Tasleem da Futuha a bayan motar zaune sai yare suke yi. Ita kuwa duk ta tsargu amma ta haɗiye ɓacin ranta. Tasleem ke mitar dole ne ma Humaira ta rabu da Fadeel tunda har ita ba ta same shi ba to kowa ma ya rasa. Yayinda Futuha ta ce ta kwantar da hankalinta soyayyar babu inda za ta kai. Haka suka yi ta gulmar Humaira ba tare da ta tsinci ko harafi ba. Ba ta da haɗi da buzaye balle ta fahimci akan abin da suke tattaunawarsu. Har aka sauke Tasleem, ba ta da walwala, ganin haka itama Humaira ta ja jikinta ko ki gaida gida ba ta ce mata ba. A gidan Futuha, ɗakin dai da ta taɓa sauka wannan karon ma shi ne ya kasance masaukinta. Ta ajiye jakar kayanta ta faɗa ta ɗauro alwala ganin ana dab da kiran sallar magriba, sai a lokacin ta jawo waya ta kira yar uwarta Ummita. Suka ɗan taɓa hira don ta ƙara kwantar mata da hankali, cikin ikon Allah ma sai ta ga ko a muryarta babu wata damuwa. Koda ta ajiye ta kara tsunduma da tunanin Fadeel, wai me ya yi mata ne ma da har ta tsaneshi hakan? Oho, ta ba kanta amsa, sai kuma ta ja tsaki cikin jin zafin rai, to meye nata ma na tsayawa tunaninsa? Don haka sai ta miƙe ta shimfiɗa darduma jin an soma kiraye-kirayen sallah. Koda ta idar sai da ta yi nafila sannan ta yi salati da istigfari. A karshe ta yi addu'a sosai. Sai kuma ta tsinci zuciyarta da yin wani sanyi tamkar an yayemata wata damuwar. Sabuwar wayarta ƙirar Huawei da Abba ya damƙa musu bayan fitowarsu daga hannun ƴan ta'adda ta yi ƙara sauti mai dadi shaidar shigowar saƙo. Ta ɗauka ta duba. *_Babu wata damuwa ko baƙin ciki da Allah ba zai iya magancewa ɗan adam ita ba. Ki miƙa dukkan lamuranki gareshi, ki kusanceshi, zai kusanceki. Allah yana son masu ambatonsa safe, rana da kuma dare. Ina miki fatan alheri koyaushe._* Ta karanta fiye da sau uku, ya yi mata dadi sosai, ta kuma kasa barin murmushi. Fadeel ne, koda babu suna a lambar tana da haddarta saboda kira na yau da gobe da yake yi kuma duk da ita ne. Ta sauke ajiyar zuciya, kwankwasa ƙofar da Futuha ta yi da shigowarta da sallama ya sanya ta ajiye wayar ta dube ta. Murmushi Futuha ta yi mata. "Yauwa Humaira idan kin huta ki fito ki ɗebi abinci a kicin. Daga gobe za ki soma gwadawa Hafsatu yanda kike tsara abinci da komai, yau kinga sai ki huta ko? Ni zan shiga ciki ba lallai kuma mu haɗu ba sai da safe." Ita dai ta amsa da toh kawai, bayan fitar Futuhar ta girgiza kai. Mamakin wannan rayuwa ta yaran Mami take, tabbas albasa ba ta yi halin ruwa ba, da ace sun biyo Mami hatta da girkin ba su da matsalarsa. Ta rasa menene ribar ɗiya mace idan ta zauna har ta yi aure ba ta iya girki ba. Banda shiriritar Futuha, ta gwammace a koyawa Hafsatu girki ta cigaba da yi mata bauta ita kuwa ta zauna ta miƙe ƙafa. A ƙarshe dai ta watsar da tunane-tunanen da ta tabbatar ba za su yi mata wani amfani ba ta cigaba da ambaton sunayen Allah har aka kira sallar isha'i ta gabatar ta kuma haɗa da nafila ta yi addu'a anan ma sannan ta ninke dardumar ta fita, abincin sam bai yi mata ba. Shinkafa ce dafaduka ta dai ji kaji wadanda daga ka kai saman hancinka sai ƙarni ya bugeka, da sauri ta mayar ta ajiye. Sanin da ta yi idan ta zauna sai ta kwana da yunwa ne ya sanya ta daukar indomie kanana biyu ta dafa ta ci ta sha ruwa. Saita alarm ta yi ya tashe ta karfe uku, dakyar ta tashi saboda ba ta saba ba ga bacci dake neman fin ƙarfinta, sai da har uku da rabi ta buga sannan ta iya miƙewa firgigit tana ambaton sunan Allah. Hakan ya ba ta wani ƙarfi ta kuwa ɗauro alwala ta dawo ta yi nafiloli ta karanta alƙur'ani bacci na ɗaukarta, dakyar ta daure ta yi sallar asuba sannan ta kwanta anan bacci mai karfi ya kwashe ta. Sai wuraren takwas na safe ta tashi ta yi wanka ta shirya tsaf ta dora hijabinta ta nufi kicin. Ta sani mutanen gidan ba sa tashi da wuri, maigidan kansa sai ya kai goma bai fita ba. A kicin ta tarar da Hafsatu na zaman jiranta har ta yi gyara ta wanke kwanuka. Suka gaisa fuska a sake, nan suka shiga haɗa kayan kari, kasancewarta babbar mace kuma mai basira tana hankalta kwarai da yanda Humaira ke sarrafa girkinta. Suyar dankali da agada suka yi sai ko sauce da ta haɗa, sai ruwan shayi da ya ji citta da kanumfari. Sai ko farfesun nama da ta yi da ya ji kayan lambu. Kicin din ban da ƙamshi ba abinda ke tashi, komai ta yi daidai gwargwado yanda ta tabbatar ba za'a yi almubazzarancinsa ba. Hafsatu ta fita da shi zuwa dinningtable na Futuha, ita kuwa Humaira bayan ta zuba wa Hafsatu ta ɗebi nata ta yi ɗaki don ba za ta iya jurar har sai su Futuha sun tashi ta karya ba saboda yunwar da ya addabe ta, a ranar kuma ta tashi da wani irin karfin jiki da walwala. Ta ƙara gasƙata cewar Fadeel, babu abin da ibada ba ta ɗaukewa na daga damuwa da ma ƙuncin zuciya. Hamdala kawai ta ke yi bisa yanayin da ta tsinci kanta a ciki. *** A ɓangaren Fadeel kuwa, sosai suke shirin bikin Ibb da Dakta Salma wanda bai fi sati ya rage a yi ba. Abokansu duk wanda ya ji zancen auren Ibb sai ya tambaya ko an yi na Fadeel? Amsar dai bai wuce nan kusa shima zai yi ba. Kamar koyaushe a kwanakin nan, yau ma su na tare bayan ya raka Ibb wurin Dakta Salma jin tsarin events din da za ta gudanar, Ibb sai faman mita yake yi mishi akan kawai ya kai kudi a sanya aurensu lokaci guda shi kuwa murmushi kawai ya ke yi. Girgiza kai Ibb ya yi. "Fadeel na sanka, kana da ƙoƙari sosai gun ɓoye damuwa, ba ka fiye son ɗorawa mutane nauyin damuwarka ba, amma ba yanda ka iya, mun taso tare kuma kai ɗin aminina ne dan uwana na maka sanin da wani mafi kusa da kai ɗin bai yi ba. Yanzu a ture zancen wasa, please and please ka yi abin da muke da tabbacin yiwuwarsa, idan yin a yi, idan barin a bari." Tuƙi yake yi amma sai da ya ɗan juyo ya dube shi. "Ban fahimceka ba. Me za a bari?" Ibb ya kauda fuska yana ɗan shan ƙamshi. "Auren mana, ko dole ne sai ita? Lamarinta ya fara kai ni bango, ita ba ƴar kowa ba a ƙasarnan sai ji da kai da taƙama. Matan da suka fi ta sun nuna su na yi da kai sun kuma nuna sun ji sun gani kowane yanayi ma a tafi da su amma ka nace mata, ka maƙale sai ita. Haba Fadeel, yaushe duk wannan zai wuce? Har yanzu kana da hope din cewa za ta amince da aurenka da bakinta?" Fadeel bai ce komai ba, amma zuciyarsa zafi take. A duniya bai taɓa yin so ba sai akan Humaira, kuma da son ya tashi kama shi, sai ya yi mishi wani irin kamun dabaibayi wanda ko ya ƙi ko ya so, hakanan zai rayu da shi. Bai dai san abin da gaba za ta haifar ba. "Ban iya ƙiyayya ba, kamar yanda ban iya soyayya ba ka san da haka ko? Meyasa ka ke tunanin akwai ranar da zan iya haƙura da Humaira alhalin ba ta yimin laifin da zan ƙi ta ba har yau? Ko ka yi zaton ta taɓa wulaƙantani ko zagina? Toh Humaira ba ni ta wulaƙanta ba, soyayyar da na furta ina yi mata ta wulaƙanta, amma na yi mata uzurin kasancewarta daga jinsin Dan Adam wanda muka riga muka san ajizancinsa. Ka yi hakuri, na sani kana jin babu dadi yadda ake maka ƙorafi akan aurena har da masu nemana da sharri. Please ina son ka toshe kunnuwanka daga garesu. Duk radda ni Fadeel na furta maka cewa na bar Humaira, toh ka sani ina nufin rabuwa ta har abada, amma yanzu bana jin ko ɓurɓushin hakan a zuciyata. Ba na jin kuma wannan mafarki naka mai tabbatuwa ne saboda ba ta yimin kamun wasa ba. Ka bi wannan ɗan uwannaka da addu'a Ya Sheikh, komai zai zamo tarihi fa in sha Allahu." Harara Ibb ya wurga masa jin ya ambace shi da sunan zolaya, Fadeel kuwa murmushi ya yi mishi yana ƙara yi mishi kirari da Angon Salma. Nan kuma ya saki fuska aka bar maganar gaba ɗaya. *** Cikin hukuncin Allah, a kwana a tashi har tsawon lokacin da su Abba suka ƙara roƙar alfarma a yi bikin Ummita da Sahabi ya kusa cika, a sannan Humaira ta tattara ta bar gidan Futuha adalilin mijin Futuhar da ko kallo suke sai ya dinga kiran Humaira wai ta fito su yi kar ta ƙumshe a ɗaka. Ko kuma ya yi ta santin girki yana fadin ai kaf gidan su Futuha ta fi su iya girki, Futuha tun tana yaƙe har ta zo ta kasa jure ɓacin ranta ganin tashi guda ya siyo wani rantsetsen leshi dan dubu arba'in ya kawo wa Humaira matsayin ladan girki da take yi musu. Anan ne gaba daya ta sauya fuskarta ta ce Humaira ta tattara ta koma gida, ta sa direba ya kai ta bayan ta karɓe leshin. Ba tare da sanin cewa ita Humaira hakan ya fiye mata komai dadi ba don dama ta gaji da zaman gidan, dadinta daya bai wuce na ibadar da take yawan yi yanzu ba sosai, kuma abin mamaki koda Fadeel ya kira ta ta rage jin wannan tsanar da ɓacin ran sai dai ba yabo ba fallasa. Tashin hankalin daake gudu dai shi ne ya afku, Abba ya zaunar da Sahabi da wani Kawunsa a dakin baƙi ya sanar da su abin da ke faruwa. Sahabi da yake jin wai wai a gari bai yarda ba ji ya yi har wani jiri na neman kwashe shi daga zaune. Kawunsa kuwa ya jinjina lamarin, ya kuma yi addu'ar Allah ya sauki Ummitan lafiya a karshe ya ce idan ta haihu ta yi aure ban da Sahabi don tuni dama sun yi mishi mata ganin ana ta yawo da hankalinsu akan Ummita. Sahabi ya kasa cewa uffan, idanunsa sun kaɗa. Tsakani da Allah yake son Ummita, ya kuma so aurenta, amma bisa gargadi iyayensa ga Kawu, matukar idan sun je ta tabbata ciki ne a jikin Ummita toh lallai su faɗi hakan. Sun kuma yi barazanar saɓawa Sahabi muddin ya musa zancen. Da wannan aka ƙulle mishi baki ya kasa cewa komai. Sai ma da zai tafi ne ya roƙi arziƙin ganin Ummita, nan Abba ya ba shi hakuri gami da nunamasa ba za ta iya jure ganinsa ba. Ya yi hakuri dai ya bi umarnin iyayensa. Daga wannan Sahabi ya ja jikinsa suka bar gidan bayan Abba ya damƙa musu dukkan wani abu da suka kawo da sunan aure. Ummita na ɗaki ban da kuka babu abin da take yi, Humaira wannan karon ta ma kasa rarrashinta, ga ciki ya fito ras ana gani kasancewar bai fi watanni biyu ya yi mata saura ta haihu ba. Ta shiga watanni bakwai cif. Ita kanta Humairar hawayen take yi tana gogewa. Ta dai tabbata shikenan Sahabi ya rabu da Ummita duk kuwa da irin dogon wayar da suke yi da soyayyar da suke nunawa juna. "Kaddararki ce Ummita, kiyi hakuri mu rungumeta da hannu bibbiyu. Watarana komai zai zama tarihi." Ta girgiza kai. "Humaira na sani ƙaddarata ce, amma wallahi Humaira na tsani cikin jikina da abin da ke cikin. Ba zan taɓa sonsa ba. Humaira duk sadda cikina ya yi motsi ji nake kamar na ɗauki wuƙa na caka a cikin abin da ke cikin ya mutu gaba daya koda ace nima nawa ajalin kenan. Allah ya isa, Humaira ba zan taɓa yafewa azzaluman nan ba. Har gobe mummunan fuskokinsu na nan a kwakwalwata, wallahi yau idan Allah zai nunamin su, sai na raba su da numfashinsu." Hawaye sosai itama Humaira take yi, balle kuma Raihana wacce shigowarta kenan dakin sanye da Uniform ta dawo daga makaranta ta tsinci labarin fasa auren Sahabi da Ummita kwata kwata a bakin Mami, kuka sosai take yi sanin irin kaunar da suke yiwa juna. Ta karaso ta rungume kafadar Ummita tana kuka tamkar ranta zai fita ta ma kasa magana. Sai Humaira ke aikin rarrashinsu cikin ƙarfin hali duk da itama hawayen ne ke zubomata. "Humaira! Raihana!! Kuna ina?!" Jin muryar Mubarak yana kiran sunansu murya a sama ya sanya su duban juna kafin su fito zuwa falon gaba daya ban da Ummita da ko motsi ta kasa. Kirjinta ne kawai ke dukan tara-tara, zai wahala ta yi mafarki bai afku ba, tana tsoron kuma yanzun ace mafarkin nata ne ya tabbata. Sai ta hau ambaton Innalillahi a ƙasan ranta. Ba Mubarak ne kaɗai a falon ba, har da Mami da Abba wanda bai je kasuwa ba saboda lamarin fasa auren Ummita sosai ya taɓa ransa, dama kuma ya san da zuwan ranar, amma babu yanda iya. "Kai Mubarak, mene ne haka kake ihu a gida?" Mubarak da idanunsa suka kaɗa gaba daya ba cikin nutsuwarsa yake ba, daga shi sai singilet da wando three quarter, fuskarsa ta yi jazur abinka da farin mutum. Waya kawai ya miƙawa Abba, Mami da su Humaira har su na rige rigen zuwa leƙa saman wayar. Rubutu ne a ka yi dogo, headline din rubutun mai jan hankali sai ko rubutun. _*GASKIYA TA YI HALINTA..._* _*Rahina Sani da Humaira Yusuf wadanda kwanakin baya ake tunanin sace su aka yi, a yanzu gaskiya ta yi halinta._* _*Yan matan sun bi samarinsu ne yawon sharholiya inda a karshe har ɗaya ta zubar da cikin da ta yi yayinda ɗayar kuwa Allah ya tona asirinta cikin ya ƙi zubewa tana nan yanzu haihuwa yau ko gobe. Bincikenmu ya tabbatar da cewa ba sace su aka yi ba, dama ƴan hannu ne suka bi abokan watsewarsu ganin asirinsu zai tonu ne ya yi sanadin da suka haɗa baki suka yi ƙaryar an sace su._* *_Tabbas inda ranka za ka sha kallo da mamaki._* Sakin wayar Abba ya yi har yana taga-taga zai fadi, da taimakon su Mami dake kusa da shi ya samu ya zauna a kujera mafi kusa saboda rawar jiki. Humaira kuwa zuciyarta ke wani irin tafarfasa ranta idan ya yi dubu ya ɓaci, waye wannan ke kokarin ɓata musu suna a idon duniya? Mene ne ribarsa? "Wannan wace irin rayuwa ce? Daga wannan sai wannan? Waye da wannan aikin? Kai Mubarak a ina ka samo mummunan labari haka?" Duka wannan zantukan Abba ke yinsu lokaci guda cikin rawar murya mai nuni da zallar ɓacin rai. Mubarak da ya dauki wayarsa ya amsa. "Abba ina zaune naga an turo group din da nake har da masu bibiyata ta inbox su na tambayar ko dagaske ne. Da na duba naga an yi forwarding sama da sau hamsin. Wannan ya sa na fahimci koda ace ba a jima da baza labarin ba, toh ya samu karɓuwa ainun." "Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! A duniya ba ka sanin cewa kana da maƙiya sai irin hakan ta kasance. Ina so maganar nan ta tsaya iya mu da wadanda suka sani a gidan, koda wasa kar a faɗawa yarinyarnan ko don yanayin da take ciki. Mu rufe duk wata ƙofa da za ta tsinci labarin. A karɓe wayarta, ku kuma ku kiyayi tayar da zancen a gabanta. Ni kuma in sha Allahu sai inda ƙarfina ya ƙare wajen ganin an bi maku hakkinku, koda ace abin da na mallaka zai ƙare sai na sanya an bincikomin me wannan aika-aikar an hukuntashi ya kuma faɗi dalilinsa na aikata wannan abu." Kowa a wurin ya gamsu da batun Abban, Mami kuwa tunani kawai take yi na waye wannan da ya fi ta nuna ƙiyayya ga yaran? Fatanta kar ya kasance wacce take zargi. Ta sani tunda har Abba ya ci akwashin ɗaukar mataki akan al'amarin to fa babu fashi. Da wannan aka kashe zancen amma fa ran kowa a ɓace, koda su Humaira suka koma ɗaki, sun tarar Ummita ta shiga bandaki wannan ya sanya da sauri ta ɗauke wayarta ta kashe ta jefa a sif, da Ummitan ta fito ma babu wani a cikinsu da ya nuna mata komai. Ita ɗin ma ba ta lura da yanayinsu ba balle ta mayar da hankali, damuwar rashin Sahabi ya rinjayi komai. Tana buƙatar ganin ta samu nutsuwa ko ya ya ne, tana tsoron ciwon da damuwa za ta haifar mata. Wannan dalilin ne ya sanya ta jin tsoron tambayarsu dalilin kiran da Mubarak din ya yi musu, sai ta zaɓi yin shiru gami da kwanciya ta hau jan carbi. *** Wasa-wasa sai ga zance ya yaɗu a duniya. Abinka da soshal midiya masu jran ƙiris sai ga labari salo-salo ana juyawa har da masu fitowa su na ƙara nasu gishirin su na ƙara yaɗawa. Abin mamaki da tsoron shi ne har asalin su Humaira da Ummita na kasancewarsu yaran riƙo a gidan da suke haka aka dinga yaɗawa ana faɗin watakila musguna musu ake yi ya yi sanadin shigarsu karuwanci yayinda a wani gefen wasu ke cewa mai yiwuwa son duniya ne ya kai su ga faɗawa halin da suka tsinci kansu. Har da kuma wadanda suka ce koda ace ba karuwancin suka fita da zummar yi ba, zai iya yiwuwa sun yi ne domin su samu maƙudan kuɗaɗe amm a ƙarshe abokan ta'addar nasu suka cutar da su ta hanyar yi musu fyaɗe. Labaru dai iri-iri akan bayin Allahn nan biyu Humaira da Ummita babu irin wanda bai yaɗu ba. Mafi rinjaye sun fi aminta da cewar da haɗin bakinsu aka sace su hakan ta kasance. Ƙalilan ne masu tsoron Allah wadanda ba su yarda da wannan labaran ƙanzon kurege da ake ta fafutukar yaɗawa ba.   Tsintar wannan labari a wurin dangin Ummita da ma Humaira sam bai zo musu ta daɗi ba. Hankali tashe Anti Maijidda ta diro Kano, ko kaɗan ba su da labarin wai Ummita na da ciki, a hakan ma ba ta amince ba sai da ta zo don kanta ta ga Ummita da tulelan ciki, wannan baƙin ciki yasa har suma ta yi ta kuma tiƙe lallai sai dai Abba ya ba ta Ummita su tafi. Mami kuwa tashin hankalinta bai wuce na wayar da Wizzy ya ƙara yi mata bayan bayyanar labarun da ake ta yayatawa ba akan lallai Ummita na haihuwa ta ba shi ɗansa yana so zai kai wa gyatumarsa idan kuwa ta saɓa zai iya tona asirinta. Wannan dalilin ne yasa itama ta kafe akan Ummita ba za ta tafi ba. Anti Maijidda ta fusata ainun ta dubi Mami da hawaye jage-jage saman fuskarta tana kai nunata da yatsa. "Ke Maryam! Ni ba sakara ba ce ki dube ni dakyau! Idan idanun kowa ya rufe ba a ganin aibunki ni kuwa Maijidda ko ruwan teku za ki shiga ki wanke jikinki ki fito ba za ki taɓa sauyawa daga yanda nake kallonki ba. Don haka tun wuri ki fita idanuna na runtse, idan kuma ke kika yi naƙudar Ummita a yau sai ki hana ni tafiya da ita mu gani!" Jin haka sai kawai Mami ta sa kuka sosai, Abba ransa ya ɓaci yayinda Ummita ta kwantar da kai a kafaɗar Humaira tana nata kukan. "Hajiya Maijidda ina ganin ƙimarki kuma albarkacin Jamila da abin da ta haifa ya sa ban taɓa ɗaga idanu na faɗamaki maganganu ba. Ko ba komai kina ganina da wannan girman, amma fa ba zai yiwu ace koyaushe ki zauna kina kushe Maryama ba. Haba, duk ƙoƙarin da take yi akan Ummita bakya gani? Meyasa kike nema ki yanke zumuncin da ke tsakanina da ɗiyar ɗan uwana? Ke a ganinki idan ace yau Maryama na cutar da ita zan zuba idanu ne nayi shiru? Ni ga sakarai?" Mami ta ɗan dube shi ta gefen idanu kawai, yayinda Maijidda ta ji zafin maganganunsa. "Alhaji Yusuf, na ji Maryam ba ta cutar da Ummita, amma yau idan har ni na isa da Ummita matsayin yaya ga mahaifiyarta ina neman alfarma a wurinka ka bar ni na tafi da ita Bichi. Ka ga dai yadda abubuwa suka rincaɓe, sunanmu gaba daya ya gama ɓaci, ba naku ba, ba kuma ga namu ba ƴan uwan mahaifiyarta. Don haka ina  roƙon arziki ka bar ni na wuce da ita." Ummita ko kusa ba ta gane ɓacin sunan da Antinta ke magana a kai ba, sai ta yi tunanin ko don cikin dake jikinta ne kuma ga shi nan an soma sani a gari. Abba kuwa, ya yi shiru yana nazarin maganganunta, da alama sun yi tasiri a zuciyarsa. Ganin haka da sauri Mami ta dube shi. "Yau kenan kana ƙoƙari ka nuna ba ni na haifi Ummita ba? Kokari ka ke yi ka sallamawa Maijidda Ummita ta wuce da ita ko? Kana son nunamin ba ni na haifeta ba, ashe Raihana idan ace ita hakan ya faru a kanta ba zamu yi hakurin duk abin da zai je ya zo ba mu bar ta karkashin kulawarmu ba? Lallai ka sani Yusuf, a yau idan ka amince da dauke Ummita daga hannuna toh ka sani cewa ta tafi kenan har abada ba za ta dawo wurina ba. Na kuma gode da nunamin iyakata da ku ka yi." Tana kai wanan ta juya ta soma tafiya cikin zubar hawaye, wannan ya tashi hankalin Abba da ma su Ummitan.  Abban na kiran sunanta ta yi banza da shi, ita dai Anti Maijidda na tsaye riƙe da hannuwa a kirji tana kallon irin salon makirci na Mami mai ban mamaki. Ummita cikin sauri ta miƙe ta riƙo hannun Mami tana kuka  kamar ranta zai fita lokaci guda tana girgiza kai amma kalma ɗaya ta kasa fita daga bakinta. Mami ta dube ta cikin hawayen sai kuma ta shafi gefen fuskarta ta yi murmushin yaudara. Cikin karyar da murya ta ce. "Kar ki damu Ummita. Da nan din da can duk ɗaya ne." Sai a sannan Ummitan ta magantu. "Aa Mami, kiyi hakuri. Wallahi babu inda zan je, ke din tamkar uwa kike a gareni. Idan har a duniya za iya barin mahaifiyata toh kuwa zan iya rabuwa da ke. Kin rungumeni a sadda na buɗi idanuna babu iyaye, kin maida ni tamkar ɗiyar cikinki, kin kaunace ni ta kowace fuska. Ni kuwa me zai sa na zama mai butulci a gareki? Kiyi hakuri da kalaman Anti Maijidda, ta yi su ne saboda tsantsar tausayi da kuma ganin kamar zan fi samun kwanciyar hankali a can, amma na tabbata ita kanta ta sani kina nunamin kaunar da ba don kar nayi wauta ba, zan ce ta fi na Raihana da su Anti Tasleem." Anti Maijidda ta kasa cewa komai tayi gum sai kallo, Abba kuwa sai kalaman Ummita suka kashe mishi jiki, shakka babu gaskiya ta fadi kuma ba zai so a yiwa Mami butulcin nan ba. Ya dai so a farko ya amince da batun Anti Maijidda idan har sauya wurin zai dawo da walwala da farin cikin Ummita. Humaira sosai ta ji dadin kalaman da Ummita ta yi ga Mami, ta tabbata hakan ne kawai zai sanyaya zuciyar Mamin, sai kawai ta ji Anti Maijidda ta sire a ranta. Ita a duniya yanzu ba ta da maƙiyi irin mutumin da zai kushe Mami da ƙoƙarinta a kansu, abin da dai ta fahimta shi ne, ba a iyawa DAN ADAM, wannan sai mahaliccinsa. Ba ta san mene ne ribarta na aibata Mami ba. Murmushi Mami ta yi tana dubanta kafin ta dubi Anti Maijidda da ta yi mutuwar tsaye. Sai a lokacin Anti Maijidda zuciya ta tunzurota ta soma magana tana duban Ummita. "Yau kin watsamin ƙasa a ido ko Ummita? Ni kika nuna bani da wani matsayi ko ƙarfin iko a wajenki? Wa.." "Anti please. Ki duba yanayin da take ciki mana ki rabu da zancen nan haka. Ina haɗa ki da Allah ki bar komai har ta rabu da abin da ke jikinta lafiya idan har dagaske farin cikin kike nema mata." Mubarak ke wannan tun soma zancen ya shigo yana kuma sauraronsu. Ransa ya ɓaci ba kaɗan ba da yanda Anti Maijidda ke kushe masa uwa kuma mahaifiya amma ya fi jin zafin yadda take neman haifarwa da Ummita wai sabon ɓacin ran na daban. Jinjina kai Anti Maijidda ta yi, ta hadiye ɓacin ran nata kamar yanda ya nema. Dagaske ta fi kaunar samun lafiyar Ummita a yanzun da kuma kwanciyar hankalinta wannan yasa ta taka zuwa ga Ummita ta janyota ta rungume. Yadda Ummitan ke kuka hakanan itama take yi. "Kiyi hakuri ya isa hakanan, shikenan magana ta wuce. Kiyi zamanki anan zamu dinga waya kin ji?" Ummita ta gyada mata kai, daga haka kuma aka kashe zancen. Abba da Mubarak suka fita don haɗuwa da D.P.O don tsaurara bincike akan wanda ya yi wannan aika-aikar da ma neman alfarma gurin D.P.O akan ya fito gidajen yaɗa labarai ya faɗi abin da ya sani kan satar su Ummitan zuwa yanda aka kaya sadda aka je kwato su. Mami kuwa ta ƙara jifan Anti Maijidda da murmushin cin nasara sannan ta juya ta bar falon zuciyarta fari ƙal yayinda ta bar Anti Maijidda da ɗumbin takaici da cizon yatsa. Ta sani addu'a babu abin da ba ya magani, za kuma ta dage da kai kukanta ga Allah, watarana halin Mami zai bayyana ƙarara a idon duniya. *** Anti Amarya ta dubi Alhaji bayan gama nuna masa jita-jitar da ake yaɗawa akan su Humaira ta ce. "Yanzu Alhaji wannan magana ko ƙarya ne a yanda sunan gidannan ya ɓaci fisabilillahi sai ka aminta da auren Fadeel da Humaira?" Nan da nan Alhaji ya ɗaure fuska ya ajiye wayar. "Me kike son ki cemin? Sai na tauyewa ɗana farin cikinsa akan ƙaryar da maƙaryata suke yamuɗiɗi da shi?" Ta tari numfashinsa. "Saboda farin cikin ɗanka mu kuma za ka zubar da namu ƙimar gidan a idon duniya? Ka san wannan ɓacin sunan kuwa ba iyaka Nijeriya ya zagaye ba? Allah kaɗai ya san inda lamarin ya tsaya. Alhaji ya kamata ka buɗe idanunka sarai ka dubi lamarin da idanun basira, ni ban taɓa ƙin Humaira ba saboda ban ga abin ƙi tattare da ita ba kamar yanda babu wani aibu da ta taɓa yi gareni ba. Amma ana magana ne na haɗa zuri'a, idan ya kasance sai bayan mai afkuwa ya afku maganar duniya ta tabbata gaskiya sai ka sa hannu a kumatu ka ce za ka yi tagumi da nadama?" Shiru Alhaji ya yi, maganganun Anti Amarya suka shiga tasiri a zuciyarsa. Dagaske yanzu idan har zancen duniya ya tabbata shikenan ya haɗa iri da ɓata gari? Anti Amarya ganin ya yi shiru sai ta yi ɗan murmushin mugunta, ko babu komai dai alamu sun nuna kwalliya za ta biya kuɗin sabulu, alƙawari ne ta ɗaukarwa kanta yanda Fadeel bai auri Murja ba ya yi sanadin barinta gidan, toh shima har abada sai ta raba shi da Humaira. Sai ta ga iya gudun ruwansa. "Shikenan Antin yara, zan dai duba zancen. Mu yi addu'a mu kuma jira mu ga ta inda gaskiya za ta yi halinta." Ta sauke ajiyar zuciya ganin ta yi nasara. "Hakane, Allah ya bayyana gaskiyar." Ya amsa da amin. Ɓangaren Fadeel kuwa har tsawon kwanaki uku da al'amarin ya fasu yake cikin wani irin tashin hankali da baƙin ciki. Soyayyar da yake yiwa Humaira ta yi ƙarfin da ko daidai da ƙiftawar idanu ba ya zarginta da fasiƙanci balle kuma ya aminta da jita-jitar da ake yaɗawa. Wannan ya sanya a ɓangarensa shima ya sanya aka soma bincike akan al'amarin don a gano bakin zarensa. Ga bikin babban amininsa nan da kwanaki uku amma hakanan damuwar yanayinnan ya gusar da murnar bikin a zuciyarsa. Ta yaya mutanen da aka ceto su cikin wani hali na maye da kuma muguwar rama da baƙi ace yawon duniya suka shiga? Har abada ba zai yarda da wannan ba. Da taimakon wani abokinsu na makaranta wanda yake babban ma'aikacin sirri na SS, bincikensu ya dinga zurfi. Ibb dai ya zuba idanu kawai yana ƙara mamakin wannan irin zazzafar kaunar ta Fadeel akan Humaira. Har shakka yake yi kada bayan aure ya zame mata mijin tace saboda shi kam abin ma ya shallake tunaninsa. *** Tasleem tsaye tana safa da marwa a ƙuryar ɗakinta daga ita sai vest wacce ta ɗage mata saboda girman da cikinta ya yi sai ko ƙaramin short, waya ne a kunnenta, burinta kawai Antinta ta ɗaga domin ta ƙagu ta ji labari. Har sai da ta kusan katsewa sannan Jannat ta ɗaga muryarta a sake. Ko gaisawa ba su yi ba ta gangara inda yake ci mata tuwo a ƙwarya. "Anti, ina ta neman wayarki a kashe na ƙagu naji daga bakinki. Kin ji labarin da ke yawo a media akan su Humaira ko? Anti hala aikinki ne?" Wata dariya Jannat ta yi daga ɓangarenta tun ma kafin ta ce komai Tasleem ta samu amsar tambayarta, sai kuma ta magantu. "Ni ce nan my daughter, ai ban fanshi marin da munafukar ƙanwarki ta yimin ba. Idan sunansu ya ɓaci a idanun duniya wa kike tunanin zai aminta da auren ɗaya a cikinsu? Ko a zatonki wancan sakaran Fadeel ɗin zai ƙara kallonta? Tasleem ki kwantar da hankalinki, yanzu na san na gama ɗaukar fansa akan Humaira don uwarta. Ita kuwa Ummita kinga cikin dake jikinta ya taimaka wurin da jama'a za su yi saurin aminta. Ke tun sadda al'amarin ya faru nake bibiyar kalaman jama'a ina dariya. Huumm muje zuwa." Tasleem ta yi murmushi sosai. "Na ji dadin rabuwar Fadeel da Humaira, na sani ko ya nace akan sonta zai wahala iyayen da suka san mutuncin kansu su yarda ɗansu ya aure ta. Amma Anti naji fa wai Abba zai sa ayi binciken wanda ya fara yaɗawa don a gano gaskiyar magana. Bakya tunanin idan aka kama shi asiri ba zai tonu ba?" Tsaki Jannat ta ja. "Nawa aka yi irin haka Tasleem, kin taɓa ganin waɗanda aka yi nasarar cafkewa?" "A'a." "Toh ki sa ranki a inuwa tawan, babu abin da za su iya. Yanzu ai na kira Abbannaku na jajanta masa har da kukan shegantaka, shi kuwa sai faman godiya da ban hakuri yake." Suka yi dariya Tasleem har tana riƙe cikinta da ya ɗan motsa saboda dariya. "Ina yinki sosai Antina." "Nima haka yar uwa. Maminki ce dai ta matsamin da tambayoyi tun ranar farko shiyasa nake ta kashe waya, wai ita ga mai wayo, bugar cikina take yi don ta gane ko ni ce na sanya a yi amma na nunamata ban san komai ba sai ma da ta faɗamin. Kema ina jan kunnenki koda wasa kar ki kuskura kiyi maganar da kowa." Tasleem ta amsa cikin jin dadi da walwala. "Kar ki samu damuwa Anti. Ba ki da matsala da ni." Daga haka suka yi sallama zuƙatansu cike fal da annashuwar ƙuntatawa bayin Allah. *** An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels